*************************⬇********************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** [1/4, 12:21 am] Takori: Shin wace ce Fa'izah? Me take takama da shi da take neman haukatar mana da Fa'iz haka? I dare you (Ina baka karfin gwiwa) kafin Fa'izah ta haukata ka, ko ta maida kai Fa'izah ta koma Fa'izun". Su da basu san dawar garin ba sai abin ya basu dariya da yake da Turanci yake maganar. Fa'iz ya kufula, a fusace ya ce. "Uban waye ya ce da kai tsoron Fa'izah ne ya hana ni tahowa da ita?" Maajid ya ce, "Yo in ba tsoro bane mene ne wannan? Yarinya tana matarka, karkashin ikonka amma ka tsaya kana shayinta? Anya kuwa zaka iya lankwasa Fa'izah Fa'iz? Ni wannan so ya yi yawa, ka bata (power) sosai ko da ace laifin naka ne kamar yadda kake ikirari. Muna da sati biyu kwarara na kintsawa kafin mu fara aiki da British Airlines, kayi amfani da su kaje ka dauko Fa'izah ta zauna a damanka zuwa duk inda ka cilla kafa cikin duniya ko ma samu nutsuwar ka, ko da ace haukan gaske zata yi ba na karya ba, a Turai akwai (psychiatrics) da (Asylums) iri-iri (gidan mahaukata). Fa'iz kam tsiyar Maajid ta ishe shi, yana neman tona masa asiri gaban abokan su bayan ya kasance mutum mai son sirri a rayuwarsa, musamman idan abin ya hada ne da (personal-life) dinshi ba harkar karatu ko aiki ba. Sai ya mike ya dauko robar ruwa ya kuskure bakinshi ya furzar. Amma bai daina mishi azabar yajin da yake mishi ba,. Maajid ya ciro karan sigarin dake bakinshi ya mika mishi. "Sha wannan, zai kashe 'shatter' (yaji)". Ya dalla mishi harara, sai Javed Saddyqy ya tsiyaya sanyayyen lemun 'shany' cikin tanbulan ya mika mishi. Ya karba ya kwankwade ya dire kofin Javed ya kara bincire hancin 'Rany' ya cika tambulan again ya sake mika mishi. Wannan karon ma ba musu ya amsa ya kwankwade ya dire kofin. Sunyi haka har sau hudu, sannan Fa'iz yaji dai dai, ya ce. "Shukran Yaa Siddiqy" wato (thank you Saddyqy). Ya wuce su ya nufi (lifter) da zata kaishi dakinsa dake hawa na goma sha uku. Ya bude dakin ya shiga ya maida ya rufe. Kai tsaye na'ura mai kwakwalwa ya nufa, yana duba tsarin tashin jiragen su cikin satin inda ya samu akwai jirgin British da zai tashi zuwa Abujar Nijeriya a safiyar gobe. Kuma a goben ne hutun kintsawarsa zai fara. Kafin ya dawo ya kama aikin da aka dauke shi cikin nasarar da dukkaninsu basu zata ba. Ya tabbatar aurensa da Fa'izah alheri ne a gareshi, domin daga ranar da ya furtawa Hajjah yana son Fa'izah a aura masa ita don ya gyara zumuncinsu da ya bata yake ta ganin fatahi wato budi ta kowanne bangare cikin hanyar samun abincinsa, kai har ma da wata irin nutsuwa cikin zuciyarsa. Zama yayi a bakin kayataccen gadon dakin yayi shiru, ya rasa abinda ke masa dadi, haka ya rasa abinda ke cunkushe masa zuciya. Baya farin ciki da komai kamar yadda ya rasa walwalar sa dungurungum. Kada dai zancen Maajid ya kasance gaskiya ya zama FA'IZAH maimakon FA'EEZ. Tabbas yana tsoron haduwarsa da Fa'izah a karo na biyu, amma haduwar (is something inevitable) wato wani abu da ba makawa sai ya faru, don haka ya zama dole ya aro jarumtar dake neman kufce masa ya koma ya kawo karshen kalubalen da suke ciki shi da Fa'izar da gidansu baki daya da kowa cikin zuri'arsu da suka zame musu wake daya mai shegen doyi. Don haka cike da karsashi ya shigar da kanshi cikin jerin fasinjojin da jirgin British zai kwasa a safiyar gobe zuwa kasar haihuwarshi Najeriya. Da ya kammala ya janyo jakar tafiye-tafiyen shi ya soma shirya kayansa, cikin tarin nutsuwa da Ubangiji Ya halicce shi da ita. A karo na farko yayi tunanin gwada daya cikin (theories) din Maajid na lallashi ga Fa'izah duk da ya san ba wani tasiri zata yi ga Fa'izah ba. Rufe jakar yayi ya mike ya sauya kayan jikinsa, ya dauki wayoyinsa da (mastercard) dinsa ya fito daga dakin ya rufe. Mota ya dauka a harabar adana motocin dake cikin hotel din wadda ta kasance ta haya ce kirar 'camry' ya hau bisa kwalta a hankali. Bai tsaya ba sai a bakin wani (Jewellery shop) a tsakiyar birnin Wales ya fito cikin wandon jeans ruwan kasa-kasa da riga ARMANI itama ruwan kasar ce amma mai haske, yayin da wandon ya ciza sosai, saye a idanunshi gilashi ne 'prada' baki mai duhu wanda bai faya amfani dashi ba in ba a lokacin aiki ba. Ya tabbatar ajiyar da yake da ita cikin (mastercard) dinsa sun isa da ya shiga wannan kantin domin ba kantin (fashion jewellery) bane, kanti ne na duwatsu masu madaukakiyar daraja (diamond, sapphire, gold, emirald) kadai. Kamin ya isa ga kofar shagon wadda ta kasance ta gilashi tuni ta bude kanta. Ya tsaya yana nazarin siraran sarkokin farin 'diamond' a wani bangare dake cikin shagon, ya zabi wadda yake ganin zata yi dai-dai da siririn wuyan Fa'izarsa, haka zoben dake hade da ita yayi bala'in dacewa da zara-zaran yatsunta daya gani ranar da suka kantara masa kwalba... Ya yi murmushi shi kadai, ya kai hannu ya shafo lallausar sumar kansa daidai inda kwalbar ta huda, ya kame yazama tabo, ya dauka ya biya. Aka sanya su cikin gidansu mai martaba aka bashi tare da risidi (reciept) bayan an ciri kudin daga (credit-card) dinnasa. Akan hanyarsa ta komawa hotel din da suke, ya shiga shagon "NEXT” ya yiwa Fa'izah sayayyar sutturun NEXT samfuri daban-daban, riga ne, siket ne, wando ne, jacket ne, sweater ne duka 'yan gidan 'NEXT' masu daraja ko daga kallon su a ido ba sai an tambaya ba. Daga nan shagon turaruka ya tsaya ya daukar mata gigitattun turarukan ESCADA (sentiment and magnetism) sannan ya dawo hotel ya hada cikin kayansa. A daren ya hada komai nasa cikin jakunkuna manya har uku, daya sayayyar Fa'izah ne taf, daya na Mama da kannensa, sai ta kayansa. Washegari ya biyo jirgin British mai zuwa Abuja. **** Da ya sauka a Abuja waya ya yiwa Yaya Sa'id yaje (airport) ya dauko shi, kasancewar Yaya Sa'idu Na'ibi kani ga Yaya Aliyu aiki yake a Abuja da (Federal Ministry of Agriculture) zuwa gidansa. Ya kwana ya huta suka sha hirarsu ta zumunci duka akan 'yan uwa washegari ta kama asabar dama Sa'idun zashi gida Giwa, sai suka taho tare. Ya sauke shi Kaduna (Jabi Road) shi kuma ya wuce Giwa. Ba zato Mama ta ga Fa'iz yana sallama a kofar falonta. Wani dogo kuma katon saurayi (giant and gentle) ma'abocin kwarjini, cikar zati da kamala da ya gama zama mutum, wanda in ka kalle shi dole ka sake, mace ne kai ko namiji saboda wasu ilhamomi da Allah Ya yi masa da ba duk maza Allah Ya mallakawa ba. Abubakar Mukhtar Abubakar (Fa’iz), kamar yadda cikakken sunansa yake, mutum ne (extraordinary) tun yana kankaninsa har girmansa, komai nasa daban yake da na sauran maza tsararrakinsa cikin A.B Bamalli House. Mutum ne mai matukar kyau da kwarjinin da idan ya shigo wuri sai kowa dake wurin ya ji shi (inferior) wato kasa dashi, ko da ya girme shi da shekaru, sai an san ya shigo saboda haibarsa, sai an san yana wuri saboda zatinsa. Sai an san namiji ne saboda kamalarsa. Duk da ya kasance mai kin ji da kiriniya a lokacin kuruciyarsa, shi ne da mafi soyuwa a zuciyarta cikin ‘ya’yanta guda tara, wanda kuma tafi shan wahala akansa kafin ya tsaya ya ginawa kanshi (future), wanda sai da ya shekara goma bai iya rubutu ba, ya kuma yi karatu ba tare da rubutu ba. Idan ta hada rayuwar Fa'iz gaba daya, daga yarinta zuwa girma, akwai baiwarwaki masu yawa a ciki. Ya kuma ci ace tun yana yaro sun gane yana da karama a fannin sarrafa abin hawa da (passion) akan duk wani al'amari da ya shafi injin hawa. Kai dai barshi da kabilanci da wariyar launin fata ga wanda ba ahalinsa ba ko ba jinin sa ba. Ta sauke idonta cikin nasa a hankali tana murmushi, shi kuma sai ya zarce da dariya yana fadin. "Ga bakon Mama babu sanarwa". Ta amsa, "Ina maraba da wannan bako nawa duk da nasan wannan zuwan ba nawa bane". Sai ya yi dariya cikin bagararwa ya zauna kasan kafafunta suka shiga gaisawa. Mama ta kasa zaune ta kasa tsaye da hidimar saukar (unexpected) bakonta, Abubakar-Fa'iz. Fitinannen danta (a da) amma dan lele a yanzu tunda ya auri abin sonta Fa'izah, ya kuma tsaya ya fuskanci rayuwa ya gina kansa irin yadda, ko ma fiye da yadda suke so ya fuskanta. Kalolin abinci har biyar da ta jere a gabansa sai da suka bashi dariya cikin jin dadin kulawar mahaifiyarsa gareshi yake fadin. "Duk ni kadai, ni Abubakar dan gatan Mama!". Ta harare shi idanunta cike da kauna. "Ko kunya baka ji ba da abinda kake fada wai dan gata na, ina ruwana da kai, (after all) nasan ba wajena kazo ba. Amfani nayi da Hadisin Manzo da ya ce, "Bakonka-Annabinka..." da kuma kasancewar mai yin bata kusa da ina ruwana da hidimar ka?" Dariya yake yi wadda ya manta rabonshi da yin irinta, watakila tun kafin Fa'izah ta shigo tayi sallama cikin sabuwar rayuwarsa ta baya. Ya ce, "ya yi min yawa ne Mama". Ta yarfar da kai, "Ko da baka cinye duka ba dai ka daure ka dan tsakura, don wadda kake rawar jiki da dokin ganin ba baka zata yi ba". Murmushi ya yi, ya dauki (spring roll) mai taushi ya sanya a bakinsa ya gutsira yana ci. 'Yan kannenshi su Junior duk sun zagaye shi suna tambayar shi yadda sama take. Ya ce, "Kuje ku tambayi malamin 'Geography' dinku (I'am not an astronomist)". Shu'aib ya ce, "Yaya Fa'iz nine planet suna yi muku magana a sama?" Shi kuwa Yahya cewa yayi, "Wai Yaya ta saman su kuke bi ko ta kasansu?" Junior ya ce, "Yaya bakwa take su?" Ya zuba lemu 'Don-simon' cikin tambulan ya ce. "Kai don Allah ku saurara mini, na ce (I'm not a geographer, neither an astronomist) amma ku bari na muku alkawari ranar dana shiga duniyar wata (journey to the moon) na dawo zan amsa muku wadannan tambayoyin naku". Sai Yahya ya ce, "Amman da Fa'izan gidan Baban ABU ce ta tambaye ka da ka gaya mata ko Yaya?" Fa'iz ya dauke wuta, cikin mamakin kalaman yaron, dariya ta kama Mama amma bata yin ba sai a zuci. Ya tsurawa yaron ido yana kallo cikin hada amsar da ya kamata ya bashi, kafin ya samu ya harhada sai Shu'aib ya ce. "Kasan ko tun ranar da Fa'izah suka zo da Aunty Ummi daga Kano muna gyaran dakinka ta zo ta leka dakin ta tambaye ni na ce mata ku za ku dawo, bata kara zuwa gidan nan ba". Yahya ya ce, "Ai bata son sa, kaga wannan tabon na goshinsa ma ance ita ta ji masa". Junior ya ce, "Kai ya akayi ka sani?" Ya ce, "Rannan ina dakin Aunty Zainab (Maman su Yaya Aliyu) naji Ummi na gaya mata har tana cewa tayi asara...". Da sauri Mama ta cira ido ta dubi goshin Fa'iz a hanzarce, Fa'iz bai san sanda yasa kafa ya kaiwa Yahya wani mugun hauri ba, Mama tayi sauri ta rike kafar gam, ta ce. "Kada ka karya min yaro, ba shi ya kar zomon ba balle ka rataya masa, ba a bakinsa na fara ji ba. Waye bai san Fa'izah ta kwada maka kwalba ba? Ni dai rokona akan ka duk rintsi kada ka biye mata domin ka cancanci hakan daga gareta ko ma fiye. Ka ringa yi kana TUNA BAYA... domin TAKORI ta ce "TUNA BAYA SHI NE ROKO" sai dai ina da yakinin yadda komai a rayuwa ke zuwa ya wuce (with time) kiyayyar Fa'izah mai wucewa ce tunda kaima sanda kake kinta baka kayyade lokacin daina kin nata ba. Zuwa ya yi da kansa, don ma anfi karfinta ne amma da ko kusa baka cancanci auren Fa'izah ba, Aliyu shi ne mutum mafi dacewa da auren Fa'izah ba kai ba Fa'iz!". Banda Mama ce, UWA! Wa ya isa ya dubi tsabar idonsa ya gaya mishi haka Ya yi kwafa kamar zai hadiyi zuciya ya mutu don takaicin kalaman Mama, ya yi shiru yana gwama numfashi kamin ya dubi Mama cikin sanyin jiki. "Wa yafi karfin nata? Gaba daya cikin ku wa yafi karfin nata a yanzu Mama? Cikin ku duka an rasa mai sanya baki a bani matata kamar yadda aka baiwa kowa tasa, saboda ita ishasshiya ce kowa yana tsoronta. To ni kam na zo daukar aurena ne (dead or alive)!" Mama tayi dariyar da ta kara kular dashi, ta ce. "Kofar hanyar Zaria a bude take ai kullum Fa'iz, kai da baka tsoronta sai ka je ka dauki abarka, munji mu tsoron ta muke ji kada muje ta fasa mana kai kamar yadda ta fasawa jarumi Fa'izu Abubakar". Haushin maganganun Mama koko ya ce shagube ko gugar zana yasa shi mikewa ya nufi dakinsa ba tare da ya kara tofawa ba. Yayi wanka, ya zuba shaddah 'getzner' koriya sharr. Ya bi jikinshi da turaren (212). Bai dauki sanya hula da muhimmanci ba kasancewar sa mai tara sumar kai da bata (extra) kulawa, don haka yau din ma bai sa ba. Ya zura lafiyayyun takalma budaddu bakake sidik kirar Thailand. Ya jawo kayanshi da ya zo dasu ya ware tsarabar da yayowa Fa'izah wadda dama ya wareta cikin (troller) guda. Ya daga ido ya dubi jerin akwatunan dake girke a gefe masu suna lefen Fa'izah wanda har yau babu wanda yace ya kawo a kai mata duk da an kai na Yaya Bash da alama ma da baya nan anzo an bude an zari wasu. Ya kwalawa su Shu'aib kira, ya ce su fidda akwatunan su zuba mashi a 'Roll-Royce' din Baba da ita zai fita. Suka kwashe har ta tsarabar, ya fito ya nufo dakin ya isa sashin Mama ya shiga ya zauna cikin lumtsuma-luntsuman (leathers) dinta. Tana jera kayanta a sif ta amsa mishi sallamar kafin ta juyo. Tayi murmushi ganin yadda ya hade kamar wani angon so, nan kuwa angon ki ne, shi kuma sai ya fara sakin tsaki. Ta ce, "Ya akayi? Sai ina kuma ango sha kamshi? Ko sai Zariyan?" Ya ce, "No Mama, ina son zuwa gidan yaya Bashir ne, bana nan suka tare". Ya sha mur sosai ya ja fasali ya ce. "Yanzu Mama da ita mutuniyar kirki ce da bamu je tare ba?" Tayi dariya ciki-ciki kamar bata gane wa yake nufi ba, ta ce. "Ita wa?" "Fa'izah mana!". Tayi 'yar dariya, "Mutuniyar kirki ce mana". Ya yi tsaki, "Ban ga alama ba. Yanzu don Allah Mama da gaske kike ba zaki sa baki Fa'izah ta sakko mu tafi tare ba? Na gaya miki British Airlines sun dauke ni aiki, zan fara sati biyu masu zuwa don haka (most of my stay now will be in Wales, London and Scotland) ba zan iya zaryar zuwa gida akai-akai ba sai bayan watanni uku-uku. Zai fi sauki idan muna tare a duk inda nake don samun cikakkiyar nutsuwa da kwanciyar hankalin gudanar da aikina yadda ya kamata. Ki taimaka min Mama, ni kadai ba zan iya ba, kunyi min aure amma kun barni ni kadai da yakin kwatar sa, baku cika ladar ku ba". Mama ta ce, "Kaga babu ruwana cikin rigimar ku, can muku. Wanda ya jawo ruwa shi kadai zai doka. Yadda Fa'izah ke ganin bakin kowa kan maganar auren nan banda ni, sannan kazo ka tsoma ni ciki, salon ta ce na bi bayanka don ba ita na haifa ba? Bayan sanda kake tsula mata tsiyar ka baka nemi taimakona ba idan kuma na hana ka ba ka ji. Kowa ya debo da zafi, bakinsa". Kamar zai fashe da kuka, "Amma Mama haka za'a zuba mata ido tana yin abinda taga dama, ni me na yi mata da zafi haka? Don kawai ina cewa ta dinga tsafta kamar su Zanirah? Ni ba dukanta nake ba, ba zaginta nake ba...". Ta tare shi, "... in ita baka zageta ba, ai ka zagi uwarta, kana tsammanin 'ya'ya mata suna yafe wa in an taba musu uwa?" "To ba na ce ayi hakuri ba? Waye kuruciya bata sa shi yin kuskure? Babba ma yana aikata kuskure balle yaro karami kamar Hafizin Hajjah!". Sai ya bata dariya a yanayin yadda ya yi maganar, ya kuma bata tausayi duka a lokaci daya. Ta dan dube shi tayi murmushi, da gaske cikin damuwa yake, duk jarumtakarsa damuwar ta kasa buya. Lallai ta yarda SOYAYYAH halitta ce mai zaman kanta, kuma (reality of man's existance)... sannan bata shawara da kai idan ta shirya yin awon gaba da kai, da ta tabbata bai barta tayi wannan tasirin mai yawa a kansa ba, kasancewarsa namiji daya da daya mai ra'ayi da akidu da 'principles’ masu zafi. A yanayin yadda tayi magana yanzu ya fahimci ta fara jin tausayinsa ta kuma fara fahimtarsa amma bata so ya gane hakan. Cewa tayi. "Kai da baka tsorontan me ya hana ka yin maganar? Ba matarka bace? Ko ko zaman dadiro ka nema ba hakkin ka ba?" Ya yi wani irin murmushi, yanzun kam ya fuskanto inda Maman ta sa gaba, wato itama zaman Fa'izar a gidansu ya dameta illa alkunya da kara irin ta mallawan usli don haka ba zata bari aji daga gareta ba sai dai shi din. Ya mike zai fita, wannan karon cike da kuzari, sai ta ce. "Akwai kudi a aljihunka ne? Motar babu mai, naji Hadi yana fade dazu". Ya shafa aljihunshi akwai kudi, amma 'pounds sterling'. Ya ce, "Ban je canji ba sai zuwa gobe insha Allah". Ta bude jakarta ta fiddo bandirin 'yar Sardauna dauri uku ta mika masa, bai yi musu ba ya sanya hannu biyu ya amsa yayi godiya. Ita kuma tayi hakan ne don sanin halin sa, ya gwammace ya zauna baya da ko sisi da ya tambaye su ko kwandala. Ummi da angonta Yaya Bashir suna cikin (kitchen) suna hadin (burger) da suke so su ci. Da ya fito sashen Mama a bakin kofa suka yi karo da Shu'aib ya tambaye shi kwatancen gidan Yaya Bashir. Ya ce, "Yaya Fa'iz muje mana in raka ka, nan ne Kabala Custain ba nisa". Ya ce, "Amma da kanka za ka dawo? Don ni daga can ba gida zan dawo ba". Shu'aib ya daga mishi kai suka jera suka fito suka shiga motar Baba, Fa'iz ya ja motar a hankali suka fita daga gate din gidan nasu. Ummi ce ta fara hango shi ta tagar (kitchen) din wadda ke santar harabar adana motar su. Tayi ihu harda dan tsalle ta ce. "Ya Fa'iz in town". Suka fito da sauri ita da Bashir suka game dashi a main falonsu. Daga matar har mijin bakin su yaki rufo sai jera masa sannu da zuwa da yaya hanya suke yi yana amsawa da ka, yana dan yatsine fuska. Ya bi daya daga cikin lafiyayyun kujerun falon ya nitse. Takaici ko kishin yadda yaga Ummi da Bashir ne suna rayuwarsu babu abinda ya dame su duk sunyi haske sunyi kiba, koko tunanin tashi 'yar bala'in amaryar ne yasa shi yatsine fuska oho! Da irin tarbar da shi zata masa? Allah kadai Yasan ZUCIYAR MUTUM (sunan wani littafin TAKORI). Suka zauna kusa da shi suna manne da juna. Ya dube su sai ya saki fuska. "Mr. and Mrs.". Suka hada baki wurin cewa, "Allah Ya taimaki angon Fa'izah!". Ummi har da jinjina da hannunta. Bashir dariyar shegantaka yake mishi ganin yadda ya zabge amma ba zai fasa halinsa na rainawa mutane wayau ba da ginshirar babu gaira babu dalili ya ce. "Shin Pilot Giwa yayi ciwo ne?" Ya ce, "Lafiyata kalau, me ka gani?" Tare da cin laya kada su kawo mishi shegantakar da ba zai dauka ba, amma sai da Ummi ta ce. "Kaima dai dear! Fa'izah's calamity mana! 'Yar banza Bakin Bunu Bata Baibaya...". Ji yayi kamar shi ta zaga, kuma dai shi baya son a dinga shigar masa rigimarsa da Fa'izah ko ace tayi ba dai-dai ba, zai fi son ka zauna a gaban sa kayi ta yabonta kana bashi labarin rayuwarta fiye da nuna kana taya shi takaicin abinda take yi akansa. Ya share zancen da cewa. "Shin kuna lafiya? Na same ku lafiya?" Bashir ya ce, "Gani ya kori ji". A yayin da yake tuttula mishi (fresh milk) din Peak cikin tambulan din dake hannun Ummi, ta mika mishi ya daga mata hannu. "Barshi, bana tare da yunwa, Mama ta bani abinci na ci". Ummi cikin rashin jin dadi ta ce, "Amma ta yaya zaka shigo gidanmu ka fita ko ruwa baka kurba ba?" Kamar zata fashe da kuka, sai ya mika hannu ya karba ya shanye ya dire kofin bisa (center table). "Na yaba da tsarin gidanku, Allah Ya ba da zaman lafiya. Ni zan wuce". Ya mike. Dan uwa rabin jiki, Yaya Bashir sai yaji tausayin Fa'iz ya kama shi duk da basu cika shiri ba ya gano damuwar dake tare dashi da halin da ya shiga ganin irin rayuwar da suke yi shi da Ummi suka mike suka fito tare da shi. Bashir ya ce, "Wai ina Fa'izar ne?" Ba tare da ya juyo ba, kamar yadda bai fasa tafiya ba ya ce. "Tana nan". Ummi da Bashir suka hada ido suka yi murmuishi, shi kuma ya sake hade rai da fuska har da tsuke baki kada su kara tambayarsa game da Fa'izah, kowa yayi (minding business) dinsa. Ita kuma Ummi bata fahimci hakan ba, sai ta ce. "Don Allah ka kawo min ita mu wuni yaya Fa'iz, na matsu in ganta, nayi-nayi tayi hakuri ta ki saurarona...". Sai kawai ya samu bakinsa da furta, "Me kika yi mata?" Alhali bai yi niyyar yin furucin ba. Ummi ta ce, "Matsalar mu ce, amma ka tambaye ta mana, ai kunfi kusa". Sai yaji kamar shaguben da yake gudu suka yi masa. Ita kuwa Ummi tsakaninta da Allah ta fada, ta kara da cewa. "Sai yaushe za ku tare mu zo rakiya?" Ji yayi kamar Ummi ta zage shi, ya ce. "Ummi, ina wasa dake? To babu rana babu wata!". Dai-dai sanda suka kawo inda ya yi (parking), Shu'aib na zaune bencin megadi suna hira yana jiransa. Ya bude boot din motar yasa Shu'aib ya fitar musu da tsarabar da ya kawo musu. Electronics ne na amfanin (kitchen) cikin kwalayen su guda biyar samfurin 'Binatone' microwave, juicer, mixer da 'rice boiler' sai 'blander masu karshen (quality). Shu'aib ya shigar musu da su gida ya dawo suka shiga motar suka tafi, Ummi da Bashir na godiya suna daga musu hannu har suka fice daga harabar gidansu suka hau titi. Yana tukin ya dan juyo ya dubi Shu'aib ya ce. "Yo kai in haka ne ai zaka yi min amfani wajen sauke kaya, shige muje Zaria kawai". [1/4, 12:22 am] Takori: *** Ban tashi kaduwa da al'amarin Fa'iz ba sai da na ganni cikin jihar Niger (Minna). Ya samu gefen wani titi yayi (parking) ya doshi wasu masu kirar wukake da ludaya na garin Minna ya yi cinikin wata sharbebiyar wuka gayawa jini na wuce, irin ta yankan shanu, suka yi 'yar magana da makerin, sai naga an fara rubutu a jikin wukar. Ya kunso wukarshi cikin takarda ya biya kudi ya shigo ya ajeta a gefenshi ya kunna mota. A raina na ce. "Eh, gara kayi min yankan rago ya fiye mini da hada rayuwa da kai. Mugu, azzalumi, munafiki, mara imani. Ko kuma kayi min yankan kifi gunduwa-gunduwa zai fiye min kwanciyar hankali fiye da in karashe rayuwata matsayin matar Fa'iz Bamalli Giwa. Uhh! Daga wurin masu wuka kun san ina Fa'iz ya dosa? Fa'iz shahararren kogin Nigeria da nake ji cikin tarihi da 'Geography' sanda nake sakandire, wato 'RIVER NIGER' ya nufa damu wanda an tabbatar yanki ne daga kogin Nilu (Nile). Can ya dosa damu gadan-gadan ya zagaye masu kamun kifi zuwa can inda babu mutane ko daya. Ya danna wani madanni jikin motar glassai bakake suka maye gurbin farare (tinc) suka rufemu ruf. Ya kwantar da kujerarshi baya sosai ya bita ya kwanta yayi matashi da hannayensa ya yi 'facing' dina (fuskantata) sai kuma ya yunkuro ya taso ya dauko wukar nan ya cireta daga cikin takardarta tana walwali da walkiya. Duk da abinda na ce a baya na gara min ya kashe nin, yayi min yankan rago ko na kifi gunduwa-gunduwa amma a wannan lokacin da matuwar ta iso muraran sai na samu kaina da matsawa gefe na soma marmasa kalmar shahada tare da duk irin addu'ar da tazo bakina. Walwali take da walkiya inba za'a ce idona bane yake min gizo da sai ince har huci wukar take yi. Sunan Allah nake kira a halshena da zuciyata, idanuna sun kankance sunyi wuri-wuri, amma babu hawaye a cikinsu sai firgita da razana. Na tabbata yanzu Fa'iz ya fini hauka, na dubi rubutun da aka yiwa wukar a sace, "FA'EEZAH". Na fiddo ido kuru-kuru na sake makurewa jikin kofa. Fa'iz ya cillo mini wuka akan cinyata ya tube riga baki daya, har singiletin jikinsa itama ya cire yayi kira da kakkausar murya. "Fa'izah!". Subhanallahi-subhanallahi, Hasbunallahu wani'imal wakeel kawai na shiga furtawa, na runtse idanuna. Ban taba ganin namiji a tube ba balle kato mai girma irin Fa'iz, yayinda haiba da kwarjini na Fa'iz Giwa yayi min lullubi, ya kara fuskantata ya ce. "Dauki wukar nan ki caka mini ko ki yanka ni karewar kiyayya kenan, ko kya huce bakin cikin zamowa na miji a gareki, ko kya yafe laifin da kike ikirarin na miki, wanda kika kasa yafewa! Kika kuma ki saurarona inyi miki bayaninsa. Idan kika yi hakan na tabbata zaki huce ba karya...". Nayi salati na dire ba tare da na kai karshen sa ba na dauko sabo. Na ture wukar daga cinyata ta fadi kasan kujera, na soma murda murfin motar ko na samu ya bude in san inda dare yayi min amma ko gezau kofa bata yi ba, yasa (lock) ya kulle ta gaba daya. Cikin dakiya da tsare gida ya ce. "Haba Fa'izah, (be brave) mana! Babu wanda zai sani, babu wanda zai ganki. Na tabbata in kin yankani zaki huce kiyi rayuwa mai dadi da nagarta. Ki samu rangwamen kullaci na dake zuciyarki na zagin Momi, mugunta da azabar dana kwashe shekaru ina yi miki, takardar saki dana hanaki, tare da huta auren direban tasha tunda ni dai hannuna ba zai iya rubuta saki ga Fa'izah ba ko da ace na iya rubutu!!!". Idona rufe na ce, "Fa'iz ka bude min kofa in fita, naga alama ka haukace. Wallahi ba don komai na yarda na sanyo kafata a motar ka ba sai don furucin Babana, na yafeni da ya ce zai yi". Na fashe da kuka. Ya sake matsowa ya dauki wukar dana yasar, ya ce cikin taushin murya. "Fa'izah, ki kwantar da hankalinki ki yanka ni, kinga in ba hakan kika yi ba baki huce haushi na ba, baki kuma ci nasarar kiyayyarki ba. Kamar yadda bakin cikina ba zai kyale zuciyarki ta samu sassauci ba don kuwa ni ba sakinki zanyi ba...". A yayin da ya zura min kotar wukar cikin hannuna, nayi maza na yi baya da hannuna na kwalla kara tun karfina. Ihun da ake kira kunu a makota babu wanda yasan ina yi. Ihu nake ina karawa ko Allah Zai kawo wani giftawa yaji ya kawo min dauki. Sai dai ga dukkan alamu ihu na ya tsaya ne cikin motar kadai ko ta taga baya fita. Ya ce (in subdued) wato cikin raunin murya. "Ki yiwa Allah ki aikata abinda na umarce ki, sai ki jani ki tura cikin kogin nan. Babu wanda zai ganki, wukar ma ki jefata cikin ruwan. In yaso ki samu wani ki roke shi ga kudi zan bar miki ya tuka ki zuwa Kaduna ko Giwa tunda baban ABU yasan tare muka fita...". Na girgiza kai da sauri, "Ko da nake kinka babu yadda za'ayi in kashe ka da hannuna tunda ba ni nayi maka ran ba. Sai dai na kasance cikin addu'ar Allah Ya kashe ka in huta wannan bala'i". Wannan karon murmushi ya yi, sannan ya cira ido a hankali ya dube ni. "Kin kasa gane abinda nake ankarar dake har yanzu, wato babu wanda zai ganki, ki kashe ki tura RIVER NIGER shi ne maganin kiyayyarki ga Fa'iz. To tunda kina tsoron kama wukar taki...". "Ka daina cewa wukata, ba tawa bace, kai ka san inda ka samo abarka...". "Ai don ke aka yi ta. Ko baki ga sunanki ne a jiki ba? Wai ma shin, ina haukanki da rashin imaninki yaje ne da kike yin baya-baya dani yanzu ba kamar dazu da wannan bakin ke gartsa min cizo ba?" "Na rantse da Allah ka isheni, ka maida ni inda ka dauko ni, ko kuma ka bude min na fita". Ya sha mur sosai, "Ki fita kije ina? Wajen 'yan daudu da 'yan ashana? Fa'izah babu wannan damar in har kin barni da rai. Baya ga wannan kyakkyawar dama da na baki, (remember that opportunity comes only once in life!) Muddin kika bar wannan damar ta subuce miki, to kiyayyarki ta karya ce... Kina son FA'IZ BAMALLI. Ba kuma zaki iya kaiwa 'yan bariki, 'yan daudu da 'yan ashana jikin da ya zam mallakin Fa'iz ba! Za ki bar mishi abinsa ne ya yi yadda yaga dama da shi daga yanzu har gaban abada! Muddin baki aikata abinda na umarce ki ba kina son rayuwar Fa'iz Bamalli Giwa ta ci gaba da wanzuwa a doron kasa...!". Ai jin hakan da ya fada, ya sani daukar wukar na riketa gam-gam cikin yatsuna amma na kasa motsa hannuna ko kadan. Sai Fa'iz ya matso gaba gareni sosai har hucin numfashinsa na dukan fuskata tare da sassanyan kamshin 212 dake tashi sannu a hankali daga jikinsa. Ya daga gira, tare da dan ware ido, ya kuma buda hannuwansa. "Uhm? Ina jiranki, (I'am ready)". Na runtse ido tamau, yayin da hawaye suka shigo kwaranya babu kakkautawa, a kundukukina, fadar Ubangiji (S.W.T) ke zuwa mini cikin kunnuwa na ta "WANDA YA KASHE A KASHE SHI" haka wanda ya kashe kansa ya mutu kafiri da sai in kashe nawa kan kowa ya huta, shi ya huta ni in huta, iyayenmu su huta. Sannan muddin na kashe Fa'iz dukkan dunguma-dunguman zunuban da na tabbatar ya wanzu yana dauka a rayuwarsa rubdugowa za suyi kaina. Baya ga haka in Baba ya nemi bayanin inda Fa'iz ya shiga bani da hujjar kare kaina. Ga wuka an rubuta sunana a jiki, idan ma na cilla ta cikin ruwan wani ya tsintota fa, ko masu kamun kifin nan? A hankali na saki wukar kasa, na sanya kaina cikin cinyoyina na shiga shakar kuka. Fa'iz murmushi yayi. "I achieve what I want to achieve, ... all of a sudden... it's obvious that you LOVE ME! (A fili ya ke kina so na, na cimma abinda nake son cimmawa)". Ya dauki wukar ya sauke (glass) ya cillata waje, ya mayar dashi yadda yake. Ya dauki farar (singletinsa ya maida, ya kuma maida shaddarsa. Ya tsallako ya dawo kusa dani ya zauna kafadunmu na gugar juna, ya shiga wakar 'YAN ASHANA' wadda marigayi Dr. Mamman Shata ya rera. Iyakar zuwa wuya na zo, ga yunwa dake cina kamar me. Babu abinda na iya baya ga rufe ido da yin shiru. Na kuma saddakar na saduda duk iskancina Fa'iz ya dameni ya shanye. Da Aunty Rabi na nan da ta kada mishi tutar da tayi alkawarin kadawa WINNER, ya tabba ni ce na fadi 'game' din, (I'am the LOSER!!!) Wasu hawaye masu zafi suka shiga biyo kuncina. A lokacin ne naji ni cikin danshi sosai a inda nake zaune, alamu ne na isowar (period) dina wanda ban zata a wannan lokacin ba. Na tabbata tashin hankali ne ya kawo shi ba wani abu ba, don lokacina bai karasa ba. Na jike sharkaf kamar wadda tayi fitsarin zaune. Don haka ko wani kwakkwaran motsi na kasa, nayi fiki-fiki dani idanuna sunyi ciki sun zurma don bala'i da kaduwa. Na kai idona ga agogon motar ya nuna karfe shidda na yamma. Shin yaushe zamu kai gida in mun fita jihar Neja yanzu? Gani da shegen tsoron 'yan fashi, bansan sanda na sake tsandarewa da kuka ba. Duk dai ni na jawowa kaina, da na kama Fa'iz na kulle a dakin Walida. Da na barshi ya wuce abinsa tun shigowarsa da ya nemi tafiya da duk hakan bata faru ba. Akuyar cikina ta sake yin kukan yunwa da karfi, ji kake farrr! Fa'iz ya dan saurara kana ya yi dariya, ya ja kujerarsa ta koma dai-dai ya yi tsalle ya haure ya koma mazauninsa ya tashi motar. Bai tsaya ko'ina ba sai tsakiyar birnin Minna. Ya karya kan motar ya shiga wani katafaren gidan saukar baki, a samansa an rubuta (MINNA GUEST INN). Ya yi (parking) a wuri na musamman da aka tanada don adana motoci cikin wata rumfa kamar tanti Hankalina ya kara tashi, me Faiz yake nufi? Hotel ya kawoni? Ni karuwa ce? Tunanina ya kasa boyuwa cikin raina sai da ya bayyana a kunnensa. "Ni karuwa ce da zaka kawo ni hotel?" Wani irin kallon biyu ahu yayi mini bai ce komai ba. Ya kashe motar ya soma tattara 'yan shirginsa dake cikin motar ya ce. "In zaki fito, ki fito. Gara da na kawo ki hotel ki zama babbar karuwa mai (class) ban kaiki matattarar 'yan daudu da 'yan asahana ba, ki zama (low level or classless prostitute)". Na kara tsananta kuka na, baki shi ke yanka wuya, da na sani banyi furucin nan ba da Fa'iz ya mayar garkuwarsa a komai. A wannan lokacin (I'm speechless) kalma ta kare a bakina. Alal hakika ina tsoron kwana cikin motar ni kadai saboda ina da labarin garin Minna cike yake da mayu tare da tunanin koda na kulle motar ba za'a rasa masu (master key) ba. Ya ce, "Ke kina bata min lokaci fa, abinda kike tunani ba shi bane, dube ki don Allah, me zan dauka anan kayan najasa? Dubi yadda ki ka batawa Baba motarsa, ni taimakon ki zanyi, a kuma wankewa Baba motarsa...". Idan na ce banji kunya ba kema kin san nayi karya. Eh, Fa'iz na da damar fada min duk abinda yaga dama. Nayi Allah Ya isa tafi cikin carbi, amma a zuciyata. Na mike da kyar, duk kafafuna sun kumbura suntum saboda zama, ya zaro ido sanda na idasa fita a motar, ya ce. "Kai-kai-kai! Ke tsaya nan, koma ki zauna kada ki bata masu (tiles) ki jawo min idon mutane, sai nayi (booking) daki tukunna zan dawo". Ban yi musu ba na koma na zauna, ko ni naso hakan sai dai babu wani alamun sassauci a fuskata. Na koma inda na tashi na zauna nayi tagumi, na gama saki da al'amarin Fa'iz ni yanzu tsoron shi nake ji ma. Tunanina na ya gangaro yadda zai yiwu in kwana daki daya da Fa'iz? Na kama kaina da hannuwa na biyu na rike, saboda barazanar tsage min da yake yi. kaina sarawa yake ta ko ina, ga kugin da cikina ke yi min babu sassautawa. Kuka ya kafe daga kwayar idona, nayi amanna babu yadda zanyi da Fa'iz yafi karfina a wannan lokacin duk ma wani yunkurin hauka ko tashin hankali da zanyi akaina zai kare don haka na alkawartawa kaina kunshe bakina don mu wanye lafiya. Nayi zama na kamar awa daya, in saka wannan in kwance kamin ya dawo ya bani zani na bakin yadi da ake kira kofilin ko (plain yard) ya dora bisa cinyata ya ce. "In kinga dama kina iya fitowa". Ban yi musu ba na fito na daura, na kwanto dankwalina na daura daga wuya. Sai a wannan lokacin ne Fa'iz ya lura ko takalmi babu a kafata balle mayafi. Ina kallon sanda ya kada kai, ya saci kallona ta gefen ido. Haka nake tafe tamkar mai tafiya bisa fasassun kwalabe saboda hardewar da kafata ke yi, duk da babu mutane sosai ko ince sunyi nesa damu a harabar (guest inn) din ji nake tamkar idanun kowa akaina yake. A lokacin duhu ya shigo, hasken fitilu ya wadata ko ina, haske ne kamar rana. Dadi daya naji da na lura babu wanda ya damu da harkar wani a wajen. Ganin irin tafiyar da nake, sai ya rage taku duk da bai tsaya mun jera tare ba. Wata sabuwa inji 'yan caca! Ganin mu nayi a bakin matattakala wanda ke nufin bene zamu hau. Nayi tsaye jimm! Rike da kafar benen ina tunanin ta yaadda zan hau shi. Ban yi aune ba naji Fa'iz ya sunkuce ni ni da kazantata ya soma taka matattakalar dani dauke a hannayensa cikin sassarfa, bai tsaya ba sai a hawa na biyu, daki mai lamba (82) yasa mukulli ya bude sannan ya dire ni, ya ce. "Ga daki nan, ki kintsa ki huta. Duk yadda naso mu koma gida a yau ba zai yiwu ba sai sanda Allah Yayi. Duk wanda ya buga in ba muryata kika ji ba kada ki bude, ko da yake 'yan ashana ne ba damuwa". Ban tsaya sauraron kalolin rashin mutuncinsa ba na nufi (toilet), shi kuma ya ja kofar ya fita yana murmushi. Kai Fa'iz sai a barshi, duk abinda zan iya nema dama wanda banyi zato ba na gani a (toilet) din, sinkin (always pad) (pantis) har shidda, dogayen riguna guda hudu, body lotion, brush da macleans har da mouth-wash, da saitin kayan wanka na 'suddenly' har da abin tazar kai, ga towels kala-kala a (toilet) din. Nan da nan ban bata lokaci ba na hada ruwan wanka cikin kwami na wanke ko'ina na jikina da ya yi tsami ya warware. Na gasa kumburarrun kafafuna da suka suntume saboda zaman mota. Sannan ne na fito daga kwamin na bude ruwan ya tafi na zura daya daga cikin dogayen rigunan da ya aje mani kalar kofi. Na wanke wadanda na tube na shanya. Na dauki brush da maclean ina goge hakorana kenan naji bugun kofa. Tare da cewa. "Zo ki bude ni ne". Ban san abinda ya ruda ni ba na kasa tsayawa in wanke kumfar baki na ko duk sabon tsoron Fa'iz daya shigeni ne oho! Da burushin a bakina da kumfar duka nazo na bude kofar. Fa'iz ya shigo rike da manyan ledoji, ban yarda mun hada ido ba na juya na koma na kuskure bakina. Na dubi kaina a madubin bandakin inda na tabbatarwa kaiwa na karamin ramewa nayi ba rana daya kacal da Fa'iz ya sanyani a duniyarsa. Duniyar bala'i da masifa. Haka na fito ina ciccin magani, inda kamshin wani hadadden gashasshen nama ya bugi hanci na. Miyau na yayi bala'in tsinkewa, na hango shi bisa (three seater) ya ja (centre table) ya dora ledar (foil-paper) mai cike da gasasshen naman mai ruwa-ruwa da yaji tumatiri da albasa yana ci yana korawa da lemon (7Alive). Na hadiyi miyau, ji kake mukut! Na samu daya kujerar na zauna ina kau da kai. Ya yi murmushi ya dauko wata ledar ya ja (table) irin nasa ya dora mini, ya mike ya shige (toilet) ya barni ina kintsa hanjin cikina wanda baya yarda aja masa aji. Bayan gashasshen naman akwai (fried sphagetti) da hadin salad. Na kusa tashi da duk abinda ke cikin ledar nan sannan na mike na isa ga dan firjin dake dakin na bude. Ya cika shi da nau'in lemuka kala-kala (squash juice) da (fruit cocktails), na dauki kwali daya na kwankwadi iya yadda zan iya nayi wata katuwar gyatsa, sannan nayi hamdala ga Allah. Sai naji bude kofarsa daga (toilet) da alama wanka yayi ya sanya ruwan madarar jallabiyya yayi sharr yayi (fresh) (very handsome) da shi. Nayi maza na dauke kaina bayan da muka hada ido. Shima cin magani yayi kada in kawo masa wargi, bai san nayi rantsuwa cikin zuciyata har ya maida ni inda ya dauko ni ba zai ji wani furuci ko wata kalma daga baki na ba. Ban zauna a kujera ba bisa carpet na zauna na mike kafafuna na dauki (remote) ina canza tasoshi har saida nazo (Bollywood) na tsaya ina kallon shirin da suke yi a lokacin mai suna (Baabul). Shi kuma sai ya dasa sallah bisa dardumar da ya sayo. A raina na ce, "Lallai direban tasha ya canza, da can mutum ne wanda baya wasa da sallah, amma yau sai da ya zauna ya take ciki yayi wanka sannan zai yi sallolin dake kansa. Ya jima yana sallar da ban san la'asar ce ko magariba ko isha ba, kamin ya yi sallama ya kunna sautin Abdurrahman Sudaith cikin wayarsa yana saurare cikin Suratul An'ami. Ya kuma shiga gyaran akaifarshi da ‘nail cutter’ yana bin karatun da wani irin sauti mai dadi da na kasa tantance Fa'iz ko Sudaith wane ne hafizin gaskiya? Dole na rage sautin talbijin tunda dai ni ba shaidan bace. A hakan wani irin barci yan soma fisgata, barci mai dadin gaske wanda na tabbata gajiya da samun nutsuwa ne suka saukar dashi. Ni dai sai juyi nayi na jini bisa tsakiyar ni'imtaccen gado, lalluve da lallausar bargo. Ban farka ba sai washegari misalin karfe goma na safe. Nayi mika, nayi salati, nayi tasbihi ga Ubangijina na nufi (toilet) na cika baho nayi wanka. Na tarar kayana da na tube na wanke jiya sun bushe don haka maimakon daya daga cikin dogayen rigunan su na mayar. Atampha ce (exclusive Sheraton) riga, zane da kallabin su. A (toilet) din na shafa (lotion) din E45 cream da ya sayo nayi daurin kallabina tsaf, sannan na fita ina cin magani ina harbin iska. Zaune yake cikin kujerar zaman mutum daya, ya daura kafa daya kan daya, yayi kyau har ya gaji cikin (light blue) din jeans, na tabbata suma siyo su yayi jiya tare da nawa kayan. Don dogayen rigunan daya sayo min ma kalar makuba maroon, milk da black daga gani sayen (boutique) ne. Rike da 'yar karamar radio yana sauraren harshen Hausa na Rediyo Najeriya Kaduna. Na samu wuri can nesa dashi na zauna na zuba tagumi. Da alama Fa'iz bai da niyyar tafiya ma kwata-kwata, na dai ja bakina na kara tsukewa cikina ya soma kiran ciroman garinmu Giwa. Ya rage sautin rediyon cikin sassaucin kallo. "Madam, babu gaisuwa?" Kokari yake mu hada idanu amma na ki. Ya yi murmushi . "Kiyi hakuri, na canza miki wurin kwanciya ne jiya saboda kada wuyanki ya kage". Ya sake yin shiru. Ya tabbata ba zai samu amsa ba. Hakan bai hana shi karawa ba. "Me kike son kiyi (break-fast) da shi?" Ya dan canza fuska, wato ya dan sha mur. "Fa'izah ba zaki magana ba?" Na sunkuyar da kaina hawaye suka soma mirginowa a hankali ta kasan idanuna. Ya aje rediyon ya taso ya iso har inda nake, ya kama hannuna na dama ya rike cikin nasa, nayi kokarin janye hannuna amma ya rike tamau, gam-gam. "Me zaki ci eye Fa'izah na?" Da wani irin karyayyen sauti, mai kassara gabban jiki da sanyaya zuciya. Da hanzari na mike na nufi (toilet), duk da nasan bani da abinda zanyi a ciki. Gaba daya jikina rawa yake yi, haduwar fatar jikimmu wani 'chemistry' ne da bazan iya fassarawa ba, mai dauke da wani irin (shock) tamkar (electrical shock). Na maida kofar bayin na rufe, na jingina da ita, na lumshe ido a hankali cikin kokarin (regaining consciousness) wanda ya yi min wahalar dawowa. Sai da na samu nutsuwa sannan na fito. Wannan karon bashi a falon. Na dauki takarda da biro nayi rubutu layi biyu kacal, ina kokarin ajeta a inda ya tashi ya bude kofar ya shigo da sallama ciki-ciki. Nima ciki-cikin na amsa, ko kadan bai ji ta ba, don dai amsawar ta zama farillah ne. Ina kokarin dagowa ya dafa ni, "Me ki ke rubutawa?" Kamshin '212' dinshi da kamshin bakinsa na (mouthfreshner) mai karfi da yayi amfani dashi ya cika hanci na. Ban son irin wannan kusantar da yake son assasawa a tsakaninmu ko kadan kuma ba zan lamunta ba. Nayi saurin aje takardar na ja da baya da zafin nama. Ya yi murmushi ya dauki takardar ya bude ya soma karantawa a fili. "Don Allah don Annabi Yaya Fa'iz ka kaini Kaduna wajen Mama. In kuma ba yanzu zaka tafi ba, to don Allah bani kudin mota in tafi, ina da abinda zanyi da yawa". Ya aje takardar ya dube ni da shanyayyun idanunsa. "Kina da wani abin yi ne dama wanda yafi mijin ki muhimmanci? Na duaka miji shi ne (foremost) a rayuwar kowacce diya mace indai tagari ce. Nima ina da abin yin na tattara na watsar saboda matata Fa'izah, ko bance ita tafi komai muhimmanci cikin rayuwata ba tana da hakki cikin lokuta na, wani neman duniya ko sabgogin duniya wadanda ba sa karewa basu isa su sa nayi watsi da wannan hakkin ba. Ko da yake nasan ke baki dauke ni a matsayin mijin ba, balle ki bani wannan muhimmancin. Zamu tafi, amma sai kinyi min magana cikin dadin rai, irin wadda macen da ke son mijinta take masa. Son samu kice I LOVE YOU YAYA FA'EEZ!!! Har sau uku. In ba haka ba, mu karashe sati biyun hutuna anan, daga nan mu wuce Birtaniya, ke da gida sai kinzo haihuwa. Kin san dai ba mai nemanki don an san muna tare. Don haka zabi na gareki". Ya juya ya soma fiddo abinciccikan daya sayo a ledar su, yana dorawa a (centre-table). Ya ci abinshi cikin kwanciyar hankali ya dora da Gahwah mai zafi (Coffee). Ya shige uwar dakin ya bi lafiyar gado da yake dakin ciki da falo ne. Amma ya sauke kafafunshi a kasa. Ni fa na kammala, ke nake jira. Na zauna na ci son raina na koshi, har da kara tea bayan na shanye kofi guda. Naji ni dai-dai, nayi hamdala ga Allah. Na kwance daurin da nayi na dankwalin atamfata na yafa da yake dankwalin babba ne sai ya rufeni ruf. Na nufi kofa na tsaya. Ya mike ya fito falon ya jingina da kofar da ta raba uwar dakin da falon, ya ce. "Au, baki ji abinda na ce ba ko? Tunda kunya kike ji dauki biro da takarda ki rubuta min kinji sabuwar kurma?" [1/4, 12:22 am] Takori: Ban musa ba, sai dai a raina na ce, "Inji kunyar ka? Amma da nayi asara. Kunyar maras kunya ai asara ce!". Na dawo na dau takarda da biro na jingina da bango na soma rubutu. Da na kammala na aje nan, na sake komawa bakin kofa na lafe. Ya dauki takardar ba tare da ya bude ba ya sanya a aljihu ya taho yana fadin. "Kin manta da guzurinki". (Yana nufin sanitary pard). Ban bashi amsa ba ya shiga (toilet) din ya kullo duka kayan a ledar da ya shigo dasu ya fito ina ta manna masa harara kamar kwayan idanuna sa fado. Ya yi murmushin sa (broad smile) ya ce cikin rada. "Wannan hararar, wata rana kallon so zai koma, wannan hararan, wata rana in wata tayi min Fa'izah dukan tsiya zata yi mata, sai inda karfinta ya kare akan duk wanda yayi min ita. Wannan hararan, ni a ganina 'I love you ne, I can't do without you ne'. Ba abinda lokaci baya magani". Ni dai bance komai ba, kulawa ma yabawa ce koko Hausawa sunce sai an kula kashi yake doyi. "Saura ki sake batawa Baba mota, wannan karon Shu'aib zansa ya wanke. In yaso in ya tambayi na mene ne? Sai in turo miki shi kiyi masa bayani". Kokari yake mu hada ido, na ki. Na koma na sanyo (slippers) din bandakin don bai sayo da takalmi ba. Muka sauka kasa ya basu mukullin su muka wuce, 'parking lot'. Nayi-nayi in bude kofar gidan baya, na kasa ban sani ba ko kulleta yayi, dole na hakura na shiga gaba, shima ya shiga mazauninsa ganin naki rufe kofar daga inda yake ya sunkuyo har muna gugar juna ya rufo kofar ruf. Maimakon ya ja motar, sai ya bude takarda ta ya soma karantawa a fili. "I hate you. And I would never love you forever... In mafarki kake, ka farka...!!!" Ya zuba min shanyayyun idanunshi masu cike da wata irin fitina, maimakon kalamaina suyi tasiri mara dadi a kansa. Sai naga kamar dadi sukai masa. Na juyar da kai domin ba zan iya jure kalon abubuwan da ke cikin idanunshi ba masu kama da (magnet) mai jan zuciya tamkar jan wutar lantarki, wadanda a fakaice wasu irin sakonni ne suke bayyanawamasu nuna matukar bukatar miji zuwa ga matarsa ta sunnah. Sai naji wasu bangarori na jikina suna kokarin karbar wannan sako, idan har banyi da gaske na zama jajirtacciyata ba kamar yadda nake wannan mutumin zaiyi saurin cin galabata dole in kara jajircewa. Wanda ba komi bane illa kokarin ganin ban yarda mun sake kadaicewa ba. Domin nima din 'adolscent' ce mai bukatar mahadin rayuwa, don dai auren ya zo ba a yadda na so ya kasance bane. Ya kasance ya zo min tareda wani mutum da ba abinda zai yi ya burgeni a rayuwata, ko ya wanke dattinsa dake raina. Ya yi murmushin da yafi kama da takaici ya tada motar. Bai sake magana ba har muka fita garin Minna. Yayin da ni kuma na tsayar da idanuna gefen da bishiyoyi suke zuciyata cike da farin cikin ko yaya ne dai kalamaina sunyi tasiri. *** Wajejen karfe uku sai gamu cikin garin Kaduna. Ya karya kan motar ya dauki hanyar anguwar Kabala Custain. Ni sam bam ma san nan gidan Ummi yake ba. Yayi (parking) bayan maigadin gidan ya bude get din gaba daya. Su Yahya ne suka fito ashe duk suna gidan sunzo musu wuni, abin mamaki har da su Walida, Abdallah, Kausar da Walid autanmu. Nan gidan ya rude da sowar kannen mu kamar zasu hadiye mu. A sannan ne na gane gidan Ummi da Yaya Bashir ne ganin tangamemen hoton su (window size) ranar (cocktail) din (Indoor sport hall) kafe a kayataccen falon. Sai na wuce kai tsaye zuwa uwar dakin matar gidan babu wanda na kula a cikinsu sai cika nake ina batsewa. Na zauna a gefen gadonta ina kallon dakin kallon kurilla, na jiyo alamar tana (toilet) ne wanda ke makale da dakin nata tana wanka. Ummi tunda taji ana oyoyo Yaya Fa'izah, oyoyo Yaya Fa'iz tayiwa wankan baja-baja ta fito a guje duk rabin jikinta kumfa ta fado mini. Na ture ta na ce, "Ke baki da hankali ne za ki jikani? Don kawai nazo gidanki? Ba tambayar mutum ya yake? Ko wane hali yake ciki?" Ta daga ni tana dariya, ta rasa inda zata sa kanta don farin ciki. Na bita da kallo har cikin ta ya tasa. Na kama baki cikin tsananin mamaki domin na dauka da da wasa take kamar a bakin kofa ake tuntube da cikin? Ta sunkuya ta zauna a gefena hannuwanta duka biyu tallabe da fuskarta tana murmushi, ta ce. "Fa'izah matar Yaya Fa'iz! Sai kyallin amarci kuke don na hango shi ta taga, daga ina kuke haka? Naji labarin Baba ya kore ku, tsammanin mu kun bar kasar babu sallama ga kowa". Na hade girar sama da na kasa, na ce. "Kin san Allah ki fita daga harkata, wane irin an kore ni kamar wata shegiya? Maras kunya fitsararriya, kyallin amarcin uban wa? Amarcin yaci ta kaza-kazan sa". Na mirgino ashariya. Ummi ta dafe baki, sai kuma ta fashe da dariya. "Oho dai! Mun gane kiyayya taci uwatar, Pilot yayi fari yayi kiba, Fa'izah ta rame saboda wuyar amarci amma ta zama kyakkyawa. Shin wai a ina aka yada zango ne?" Ganin tana neman maishe ni mahaukaciya na mike nayi (toilet) don inyi wanka in sauya kunzugu na ko naji dadin jikina. Na fito daure da tawul tana make-up a (dressing mirrow) fuska kamar jikakken kwaki don turbunewa na ce. "Bani kaya in sauya, ko ba hali?" Tayi dariya kawai, ta dauko min atamfa Vlisko mai ruwan ganye mai karamin dinki na karba na saka nayi kwalliyata sosai nayi sharr, tuni kuma tausayin 'yar uwata ya kamani ganin yadda take ta rawar jiki dani cike da kauna. Sai na ware nima muka shiga hirar arziki. Duk sanda ta sako zancen Fa'iz cikin hirarmu bana yarda ince mata komai, dolenta ta kyale, muka koma hirar makaranta da dakace iri-iri na cewa yanzu an shiga zangon karatu na farko na sabuwar shekara babu mu, Haulatu na can tana ta (missing). Ko da wasa Ummi bata yi zancen marigayi N.S ba, nima banyi ba. Na ce. "Wai ina Yaya Bashir ne?" Ta ce, "Ya koma Russia zai harhado kan takardunshi don na ce ni ban yarda yayi aiki a can ba, sai dai ya je, ni in zauna anan duk sanda ya samu dama ya neme ni, dalilin komawar shi amso takardun kenan ya dawo nan ya nemi aiki". Nayi dariya na ce, "Kin hadu, wai kema mai tsarawa miji rayuwa ko?" Ta ce, "Ba wani tsarin rayuwa ko dai gaskiya. Na rantse miki shashanci yake a can ba aikin da yake yi. Ya jima da gama karatu babu yadda Mama bata yi ba ya dawo yaki, wai jiran Yaya Fa'iz yake ya kammala da yake karatun Fa'iz yafi nashi nisa. Gara Fa'iz idan ya ce zai yi aiki a waje yana da hujja a Nigeria bamu da wasu Airlines na arziki, kuma ba zaki hada albashinsu da nagartarsu da 'Internationals’ ba. Shi kuwa Yaya Bashir su Nigeria ke bukata suzo su amfanar da al'ummar su yafi, (Global; security) ya karanta. Na samu da dabara da taimakon Allah da na addu'a na tsayar da hankalin Yaya Bashir a kaina, anan bai fita ko'ina sai tare da ni, don kar in zarge shi. Firinji kuwa (fridge) duk gidan daya ne na (kitchen) don kar ince yana boye (gulder) wani wuri. Don haka ko ya dawo ya samu aiki zan ci gaba da sa masa ido sosai duk da cewa na tabbata a yanzu yaya Bashir ya bar shashanci 90%". Na jinjinawa Ummi a fili da zuci, kaga mace duk gabuntarta a fannin mu'amala da miji kada ka rainata. Ban taba zaton Ummi na da hankalin da yau na sameta da shi ba. Na ce, "Bani abinci Ummi, yunwa nake ji, tun karin kumallon safe rabona da abinci, kin san kuma ba iya jure yunwa nake ba". Ummi ta dafe kirji, kai Fa'izah, amma kin iya rashin mutunci, kin shagaltar dani ko ki tuna mani da dan uwa na dake waje cikin yara ko ruwa ban bashi ba, kanki kawai kika sani, (selfish!)". Ummi ta fita falo da fara'arta sai taga wayam! "Ku! Ina Yaya Fa'iz?" Ta tambayi Walida. "Ai tun dazu ya debi Shu'aib, Junior da Yahya suka wuce wai Zaria za su raka shi. Haushi ya kashe Ummi ta harari Walida. "Shi ne baku gaya min ba? Ban bashi ruwa ba, ban bashi abinci ba". Ta fada kamar ta fashe da kuka. Abdallah ya ce, "Shi ne ya ce mu kyale ki hira ku ke, kun jima baku hadu ba. In ya dawo daukan Yaya Fa'izah gobe ko jibi kun gaisa". Ba haka ta so ba, sai dai tayi farin cikin jin cewa ya bar mata 'yar uwarta barin rayuwarta su kwana su hantse tare, wani abu da suka rabu da samu tun barowar su Kano gidan Yaya Rabi. Da kuzarinta ta fada (kitchen) don dora sanwar dare. Ta dawo ta ci gaba da yi min sababi, ta gaji ta koma wa'azi na hakkin miji akan matarsa da girmama shi da kula da cin shi da shansa da shimfidarsa. Amma ga mamakina na kasa tanka mata duk da nasan gaskiya take fada ban dai furta komai ba mai nuni da na amshi wa'azinta ko a'ah? Ba zata gane ba, ba zan iya bane, da zata gane ta adana yawun bakinta a gaba zai yi mata amfani, ta barni yadda ta ganni, rayuwata da tata ba zata taba zama daya ba. [1/4, 12:22 am] Takori: ZUMUNTAR KENAN?-4 Washegari da safe, mun karya kumallo cikin farin ciki, ni Ummi da ragowar kannen mu. Daga nan muka tare a falon Ummi muna hira muna shan dariya. Na mike na barsu nayi (toilet) din Ummi nayi wanka na sha kwalliya da daya daga cikin lesukan Ummi da ta ci biki dasu. Na dawo falon na cimma su kafin in zauna kararrawar kofar shigowa tayi kara. Sai na fasa zama a raina na ce bari in hutar da kowa. Na karasa a natse na bude kofar. Fa’iz ne cikin shadda wagambari babbar, ruwan makuba tare da abokinsa Surajo na Central Bank, shi kuwa cikin kananan kaya. Da ganinsu kaga matasan da rayuwa ke garawa tare dasu, suna cikin lokacinsu, kuma ana damawa dasu a fannonin da suke. Muka hada ido da Fa’iz na yi maza na kawar da nawa na wuce ciki na zauna kusa da Ummi ban kara kallon su ba. Na kuma bi na maida fuskata kamar hadari sai ka rantse ba dani ake hira da dariya yanzun nan ba. Su Ummi suka shiga gayar dasu daya bayan daya, a sannu kuma su Walida duk suka bar falon. Na maida idona kan t.v (Indian movie) ne ake yi mai suna 'Welcome-Back' na John Abraham. Dai-dai lokacin da aka nuno jarumin shirin, wato John Abraham yana magana. Abin mamaki dana juyo sai naga shi da Fa'iz suna matukar diban kama, illa ace yafi Fa'iz haske sosai da tarin suma. Nayi maza na kawar da wannan tunanin na mike ina kokarin barin falon. Kallo Fa'iz ya bini dashi shi da Surajo, Suraj ya ce. "Madam Fa'izah ba gaisuwa?" Bai san cewa haushinsa nake ji ba tun ranar (Cocktail) ko kallon sa banyi ba na ci gaba da tafiya. Ya ce, "Ba don ni ba, don Allah don Annabi ki koma ki zauna, wajenki muka zo". Duk wanda aka hada da Allah da Annabi, indai cikakken Musulmi ne da yayi amanna dasu dole ya aikata abinda aka umarceshin. To hakan ce ta faru dani. Na koma na zauna don ba yadda zanyi, amma ban kalle su ba. Ummi ta girgiza kai da alama na bata haushi ta harareni ta mike tayi ciki. Suraj ya ce, "Na dauki Fa'izah a sahun yara nutsatstsu, masu hankali da sanin yakamata. Kowanne irin laifi Fa'iz yayi mata ya kamata ace lokaci da isowar hankali sun shafe shi hakannan. Riko, ba ta'adar dan Musulmin kwarai bane. Allah Ubangijin mu mai afuwa ne, kuma yana son masu afuwa. Fa'iz dan Adam ne kamar kowa, ajizi kamar kowanne bil'Adama. Babu wanda yake sama da aikata kuskure, sai fiyayyen Halitta. Sai ake son kullum mu kasance cikin Istigfari, domin Allah Ya yafe mana kura-kuranmu, mu fita daga cikin rafkanannu. Laifi kuma na tsakanin dan-Adam da dan uwansa, sai aka ce mu nema daga junanmu. Mun nema anki yi mana, mun ce a saurare mu, anki sauraron mu. Anyi mana mummunar fahimta, sabanin ta hankali da tunani. Ya kamata a sanya al'amarin mu a mizanin hankali, laifin da muka aikata bisa sani, ko bisa kuskure a bamu dama mu kare kanmu, kafin a cigaba da hukuntamu akanshi, kada ya zamo da daukar hakki". Idan na ce jikina baiyi sanyi da kalaman Surajo ba, kema kin san karya nake. Amma ba zan iya ba da kai ba, ba duka na yarda dasu ba, (it's not the hightime). Don haka ban basu amsa ba, kamar yadda ban dube su ba. In iskar da ta debo su ta isheni kallo, to suma hakan. Sai ma na dauki (remote) na karo sautin t.v kamar banji me yake fadi ba. Fa'iz ya mike a fusace yayi waje, Suraj ya mara masa baya cikin tsananin mutuwar jiki da sarewa da al'amari na. Ni da kaina nasan ban kyauta ba, duk abinda zanyiwa Fa'iz a dalilin kiyayyarsa, bai dace inyi a gaban abokinsa irin Surajo ba, da suke matukar martaba juna da girmama juna. Yadda Fa'iz yayi fushi, na tabbata akwai abinda zai biyo baya na daukar mataki na karshe don kawo karshen rashin da'a ta. Don na lura bai iya daukar mataki ba idan ranshi ya baci, idan na tuna karon mu a 'river-niger'. Don haka wunin ranar zungur nayi shi ne sululu! Cikin rashin kuzari, Ummi dai bata ce min komai ba don itama haushina take ji, tana kuma tsoron ta shiga maganar ince zan bar mata gidanta. Don haka sai ta bini da ido tun safe har dare bata shiga shirgina ba. Nima kuma sai banji dadin hakan da tayi min ba. *** Karfe takwas na dare muna cin abincin daren da Ummi ta girka mana muka ji kararrawa (door-bell). Kasancewar na riga kowa gamawa ni na doshi kofar na bude, ina kwance ne da fari cikin kujera duk abin duniya ya isheni na rasa abinda ke min dadi. Duk da rashin wadataccen haske a wurin hakan bai hana ni gane fuskarsa ba, ma'abociyar zati da kamala. Hannunshi duka biyu zube cikin aljihun bakin wandon 'ARMANI' dake jikinsa. A jikin sa t-shirt ce ruwan bula mai haske (Tommy Hilfiger) ya saya idanunshi cikin bakin 'prada' mai duhu ainun ta yadda ba zaka iya tantance halin da kwayar idanunshi ke ciki ba. "Ki dauko mayafi ki wuce muje, Baba ke kiranki". Cikina ya hautsina ya ba da wani irin sauti kulululu! Idona ya yi rau-rau gab da rushewa da kuka. Na saki kofar na fito har gabanshi na durkusa na soma kuka. Idan ubana ya tsine min albarka wacce irin rayuwa nake tsammatarwa kaina? Wace irin rayuwa zan ci gaba da yi? Mene ne makomar rayuwata? Ya daga kai sama, kamar mai irga taurari, Allah kadai yasan me yake tunani. Sautin kukana na karuwa, yana tafiya da bacin ransa. Na tabbata na kawo shi bango ne bashi da sauran dabara akaina shi yasa ya sake maida al'amarin ga mahaifina. Amma ganin irin kukan da nake sai ya ce. "Is o.k, ba Baban ABU ne ke kiranki ba, Baban Kaduna ne". Anan ne naji dan sanyi, na mike na dauko mayafi da takalmin Ummi ko sallama ban musu ba don hankalina ya dugunzuma ya tashi, bana so ko kankani wata magana akan Fa'iz ta sake hadani da iyayena, nafi son mu ci gaba da ci muna sidewa a tsakanin mu. Har aga wanda zai shanye miyar. Tunda Baba ya fara ikirarin zai tsine min, na fara shiga taitayina. Na bude kofar gaban motar na shiga, Ummi ta biyo bayana da shirgina a leda, abin mamaki kayayyakina dake gidanmu da akwatinan da ya kawo min da sunan lefe da tsaraba su na gani a bayan motar-baki dayansu wasu ko a leda ba'a zuba su ba. Ga takalmana da jakunkuna na Giwa da na Zaria da takarduna na makaranta. Hakan ya tabbatar mini tafiyar dani ta tabbata. Hawaye suka cicciko idona. Ya je Giwa kenan ya kwaso kayana duka, haka wadanda suke Zaria. Ummi na daga min hannu muka bar harabar gidanta, sai na samu kaina da daga mata nima, don watakila rabuwar kenan. Tunda muka hau titi babu wanda ya ce uffan, babu kuma wanda ya kalli dan uwansa. Ga mamakina ba Jabi Road muka nufa ba, haka ba filin jirgin sama ba, Fa'iz ya karya kan motar ne zuwa anguwar Malali G.R.A anguwa mai kyawun tsari. Na ciro kaina daga kallon gefen hanya na zube su a kanshi ban san yaushe furucin ya subuto daga bakina ba. "Ina zamu je?" Fa'iz bai kula ni ba. Ya mika hannu ne ya karo karfin na'urar sanyaya mota. A hankali kuma ya rage gudun motar yana tafiya (slow-slow) kamar baya son mu kai inda zamu. Cikin sanyi ya soma magana. "Fa'izah, bana so in rika hadaki da iyayenmu, a bisa dalilai da dama. Na farko za'a dake ki ne, duka kuma ba zai taba sawa ki so ni ba. Na biyu za'a tsaneki, kasancewar kowa na son ki tare dani. Amma ke har yanzu kin ki saduda ki zubar da makaman yakin da kika diba, ki fahimci aurenmu na har abada ne. Tunda baki tashi kinga an taba yin saki a cikin gidanmu da kewayenmu ba. Na san kiyayya halitta ce, kamar yadda soyayya take halitta mai zaman kanta. To amma komai na duniya mai canzawa ne ke naki al'amarin yaki ya canza, yinsa kike tamkar cin kwan makauniya babu azanci babu tunani balle tsoron Ubangiji. Nasan zafin kiyayya to amma kada ki manta ni dan uwanki ne na jini wanda jininku ke gauraye da na juna. Idan babu so na soyayya akwai so na 'yan uwantaka. Me zai hana ki ture wancan matsayin da ba zaki iya bani ba ki bani wanda Allah Ya umarceki ki bani? (Na 'yan uwantaka da na darajar aure). Kina amfani da abinda ya wuce a sabuwar rayuwar ki wanda ba zai amfane ki da komai ba, da zaki saurare ni ma da kin gane (you are totally mistaken!). (For how long) kiyayyar taki gareni zata kare? Tunda ni tawa ta kare? Kina kwasarwa kanki zunubai iri-iri wurin Ubangiji akan sanin ki, don ba zan ce cikin rashin sani ba tunda akan idona kika sauke Alqur'ani da sauran littattafan addini. Bana jin zafin duk abinda kike mini ko kadan, illah tausaya miki azabar Allah. A dalilin bacin ran da kika sanyani dazu, naji dole in kawo karshen tatsuniyarmu ta zama kurunkus! Daga yau yawon gidajen 'yan uwa da iyaye ya kare mana baki dayanmu. Za muyi rayuwa ne (on our own) kowa yayi irin wadda yake ganin zata fisshe shi. Ba zan kuma hanaki ba, ki ci gaba da abinda kike yi tunda kinga shi zai fisshe ki. Na daina rokon SO sai rashinsa, na daina rokon zaman lafiya sai akasinsa, na daina rokon kwanciyar hankali sai tashinsa, na daina rokon yafiya sai rashinta, na daina rokon a daina ki na sai a cigaba da kina. Wannan shi ne hukunci na karshe, kuma rayuwa mafi kyau da na zaba mana, don ba zan kwashe ki in kaiki inda ake ganin mutuncina ki ci gaba da zubar min dashi ba". A dai dai lokacin da ya tsaya gaban wani karamin (flat) mai jan get, yayi (horn) wani buzu yazo da sauri ya bude. Gidan karami ne, amma fa wanda akayi amfani da hikima da fasaha wajen gininsa da tsarinsa tamkar (European-building). Rufinsa ja ne, fentinsa ciki da bai fari da ruwan madara. Ainihin ginin gidan a tsakiyar gidan aka yishi fili fetal ya zagaye shi ya sanya shi a tsakiya. Gini ne na hawa daya (flat). Korran shuke-shuke sunyi kyakkyawan layi a gefe sun bi katangar gidan har wajenta, haka akwai wayar lantarki ta (security) akan katangar gidan. Grass carpet ne lullube da harabar gidan korra sharr sunyi lub-lub alamun suna samun matukar kulawa. Wannan shi ne ainahin gidan da Pilot Fa'iz Mukhtar ya kwashe shekaru biyu kacal yana ginawa cikin garin Kaduna, ba da sanin kowa ba sai mahaifinsa Baba Muntari wanda shi yake turowa da komai ake masa ginin daga Ukraine, hatta zanen gidan shi ya turo masa ko kwabon Baban Kaduna babu a cikin ginin Fa'iz, cikin tsararriyar unguwar Malali GRA. Ya bude motar zai fita, sai kuma ya juyo ya dube ni. Bani da alamar fitowa illa kuka da nake yi a hankali wanda yafi kama da kukan amarya mara gata, wadda iyaye da 'yan uwa basu rako gidan miji ba. Me na yiwa A.B haka da zafi? Wane irin rashin so ake min cikin zuri'armu? Me Fa'iz yake musu wanda ni bana musu? Daga can kololuwar zuciyata naji wata murya tayi (whisphering) rada cikin kunnuwana, "BIYAYYAH". Wannan ya tabbatar min na dai tabbata matar FA'EEZ MUKHTAR ABUBAKAR tunda har yau gani cikin gidanshi matsayin matar gidan. Na karbi kaddarar Ubangiji wanda Shi Ya nufi Fa'iz da zama miji a gareni. Bani da inda zani, bani da yadda zanyi, mu zauna a hakan, zaman dolen da ya zaba mana. Sai dai bana jin har illah masha-Allahu zan so shi, soyayya guda daya ce kuma na tabbata na yita na gama. Na karbi Fa'iz a matsayin mijin kaddara, na kuma ci alwashin ba zan kuma yi masa musu ko rashin kunya ba tunda ina kwadayin rahamar Ubangiji kamar yadda na yarda da tunasarwarsa gaskiya ce tsagwaro. Sai dai SO daga gareni bana jin har abada Fa'iz zai samu haka har in koma ga Ubangiji na Fa'iz ba zai samu dariya ta ba balle walwalata. Biyayya ita ce wajibina nayi alkawarin yinta da dukkan iyawata. Na bude murfin mota na fita ba tare da na dauki komai ba, na doshi kofar da na tabbatar ita ce ta shiga falon gidan. Ya karaso yasa (key) yana budewa. Wani saurayi ya bullo daga bayan gidan ya fadi yana gaishe shi yana amsawa, sannan ya juyo yana min sannu da zuwa. Ban amsa ba sai daga kai nayi. Fa'iz ya ce da shi, "Yaya suke yau? Ince ko an basu abinci sosai?" Ya ce, "Ranka ya dade an basu sunci sun koshi sun sha ruwa tun yamma yau suka kwanta". Ya yi murmushi ya ce, "Sai da safe to Malam Ya'u. Ka zo da wuri don Allah don zan aike ka kayowa Madam cefane". Ya ce, "An gama Yallabai. Mu kwana lafiya". Na rasa suwa ake magana akan su. Bai sake dubana ba ya bude kofar ya wuce ciki ya janye (curtains) ya sarkafe su a masarkafinsu. Na tube takalmana na shiga, duhu dindim, naji kafafuna bisa wani sassanyan (marbles) mai sulbi kamar bayan tarwada. Yasa hannu ya kunna fitila daga bayan labule haske ya gauraye falon, kamar rana, sai dana runtse ido, sai ya rage fitilun ta hanyar kashe wadda tafi kowacce haske ta tsakiyar falon, hasken ya koma dai-dai. Ya yi murmushi ya ce, "Ga dakinki Fa'izah, ga dakinki, bayan shi a ko'ina na gidan nan baki da shamaki. Wannan falon saukar baki ne, naki yana hade da dakin barcin ki, nima haka. A falonki (kitchen) yake, ba abinda su Yaya Rabi basu zuba miki ba irin na 'yan uwanki, amma sunce in gaya miki ba zasu rakoki ba, saboda halin ki ba irin na 'yan uwanki bane. Haka ba zasu ziyarce ki ba sai ranar da suka ganki da ciki irin na Ummi. Suna yi miki fatan ALHERI". Wata harara na zabga masa, shima ya mayar min da wadda ta fita zafi, ya ce. "Daga fadar sako? Allah Ya huci zuciyar ki; O.K?" Na samu daya daga cikin tausasan kujerun (leather) da suka yiwa falon kawanya na luntsume. Ina kallon yadda aka shirya dakin abin sha'awa, na tabbatar aikin Aunty Rabi ne da Aunty Hauwa, sai na lalace ina kallo kamar a talbijin. Komai (orange) da (lemon green) kamar ka lashe, sannan babu tarkace amma kaya ne masu daraja baki daya tun daga kan (dining table) na tsurar bakin gilashi a can gefen falon ga na'urar sanyaya daki ta girke, doguwa (split) tana ta buso sanyi mai dadi, kayan lantarkin 'Samsung' kaloli ne kawai suka bambanta da na Ummi, ita nata komi (milk and brown) ne. Ya dauko wayarsa yayi magana, ashe buzu mai gadi ya kira. Ya zo bakin kofa da sauri yana sallama. Ya ce, "Kaga na manta Ya'u ya wuce, ungu mukullin mota ka kwaso duk kayan dake bayan motar da wadanda ke cikin (boot) ka kawo mata. Ka shigar dasu dakin can". Ya karba yana fadin, "An gama Yallabai". Da buzuwar Hausarsa. Ya dubeni kasa-kasa kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya ce. "Ki tashi ki shiga nawa dakin har ya gama, ko zama za kiyi sai ya gama kalle ki cikin falon nan?" Nayi mamakin dalilin fusatar shi haka bayan banyi wani abu da zai fusata shin ba. Na zambura baki, sannan na mike, kada inje ya faska min marin da ya saba faska mini. Don na lura yana matukar son tada hankalin fuskata da tafukansa. Dakin daya kira nashi nan na shiga ina shan kallo. (INa ruwan 'yar kauyen Giwa). Ina jin Baba Buzu yana ta shiga da su, sai da ya gama tas ya rufo motar ya kawo masa mukullin. Suka yi sallama shi kuma ya rufo kofar falon da (keys) ya ce. "Malama fito min daga daki kada ki shafa min najasa a gado". Kamar wata rakumi da akala sai na fito nayi wanda aka bani, babu musu, ba busa ba daga hannu. Ni kaina har mamakin (silence) dina nake yi. Ko da yake shaidan ne kadai za'a ce masa ga allah Ya kautar da ido. Ganin bana jin barci, na ce bari kawai in shirya kayana a (wardrove). Ina jinshi ya kunna t.v a (main) falo yana sauraron labaran ALJAZEERAH na soma ninke kayana ina tsara su ina adanawa. Na cikin akwatunan da dinki suke bukata na barsu a ciki na jera akawatunan haka cikin (wardrove). Ina tsaka da aikin nawa ya shigo, ya tsaya daga bakin kofa, ya canza zuwa pyjamas farare sol, hannunshi daya cikin aljihun 'pjs' din daya rike da kofar. "Yunwa nake ji, ya za'ayi?" A raina na ce, "Wannan wace irin tambaya ce? Ban biyo shi don in yi sana'ar kuku ba ko zaman aure irin na mata da miji, sai don amsa kiran Baban da yace min, ashe wayo yayi mani duka na hakura na fauwalawa Allah na mika wuya ga hukincinsa, yanzu kuma yazo yana son dora mini abinda ba dole na ba. Wanda ko kusa ba zan karba ba. Ai ita wannan din (girki) ba fadar Allah bace, al'ada ce, don haka ba zan karbeta ba. Allah cewa yayi su kawo a dafe su ciyar damu, babu ayar da ta ce a sayo mu girka, ni kuma da fadar Allah kawai nake amfani. Don haka nayi masa shiru, ya gaji da jiran jin ta bakina, ya tabbatar ba zan tanka ba, sai ya ce. "To a gasa min kaza da (chips) (favourite food) dina kenan. Don naga alamar ke a koshe kike. Akwai kajin a (freezer) din (kitchen), dankalin ma akwai a (kitchen). Duka Ya'u ya sayo, kayan gwari (su tattasai da tumatir) ne kawai babu gobe zai sayo miki, dazu da yaje sun tashi". Ya juya ya fice. Ban amsa ba, amma a zuciyata na yanke shawarar zanyi, tunda sawa da hanawar duk a cikin umarnin Ubangiji suke. Sai na saki aikin da nake yi na fito zuwa (kitchen) din. Ashe kallo na sama, babu irin na'urar girkin da iyayenmu basu jera min ba, komi na cikin (kitchen) din (orange) ne (freezer) da (cooker) sune (lemon-green). Na ba da ajiyar kallon zuwa gobe da safe na fara abinda ya shigo dani. Cikin minti goma sha biyar na gama da yake dankalin ma a (fryer) na soye shi bai dauki lokaci ba. Na jera a (tray) yana zaune na dora a (dinning). Naga mamaki a fuskarsa da na juyo zan koma daki sai na tuna ban ajiye ruwa da lemu ba, kada inci gaba da aikina ya kara taso ni. Na koma firjin dake dab da (dining) na ciro masa (Pepsi) da ruwan Faro. Har na kai bakin kofar daki na, ya ce. "Aunty Fa'izah saura ruwa da lemo". Na cuno baki na harari tebirin sai shima ya kalle shi. Dariya yayi. "Aunty Fa'izah ta soma zama (full-house wife): It's a job weldone!". Da sauri na shige daki bana son zuciyata taji yabon da yayi mata. Wani gashin kaza yake ci yau da bai taba cin mai dadi da taushinsa ba, koko santin hannun daya sarrafa shi ne, bai sani ba. Kunnensa har motsi yake musamman da abin ya hada da yunwar wuni guda. Tun barowar mu Minna bai ci wani kwakkwaran abinci ba, sai ruwa da lemo yake daddaka. Tunda ya fara bai yi motsin kirki ko magana ba, sai da ya zuge kasusuwan katuwar kazar nan gaba daya. Da ya kammala kasa jurewa yayi sai da ya dangana da kofar dakina. Ya rausayar da kai yana rike da kofar. "Aunty Fa'izah, daga yau, a duk inda muke, zaki gasa min kaza da (chips) da wadannan yatsun naki, a kowanne dare matsayin (dinner) dina. Zan samu Fa'izah na?" Ban amsa ba, sannan ban kalle shi ba, na ci gaba da jera kaya cikin (wardrove) kamar bada ni yake magana ba. Ya gaji da sauraron amsata, ya aro (extra) hakuri ya kara akan wanda yake da shi, murmushi ya karawa zuciyarsa. Wani bangare na zuciyarsa na cewa, "There's alot of improvement. Is a matter of time!". Washegari ban tashi da wuri ba sai misalin karfe tara na safe. Badon komai ba sai don sanin babu nauyin sallah akaina. Nayi wanka ba tare da wata kwalliya ta kuzo ku gani ba. Babbar rigar shadda mai aikin surfani na sanya, nayi daurin kai sassauka da kallabinta, na fesa turare 'Escada sentiment' na nufi (kitchen). Ruwan tea na fara dorawa a (water heater) sannan na debi dankali dai-dai cikin mutum biyu na soma ferewa. A haka ya cimmani cikin madafin. Ya hade cikin bakar shaddar rini mai ratsin ruwan makuba, yayi sharr yayi (fresh) kamar sabon ango sai fesa kamshin '212' yake. Ya saki murmushi mai kayatarwa cikin fadin, "Good morning Aunty Fa'izah". Na ci gaba da firar da nake yi, ban kalleshi ba sai ta gefen ido, haka bai samu amsar gaisuwarsa ba. Bana son wannan kulanin da yake yi, na fi son tunda zama tare ya zama dole, to kowa ya ci gashin kansa kamar yadda ya ce a farko kamin in shigo gidan kowa yayi wadda zata fisshe shi, koko rayuwar da yayi amanna da ita. Ya dauki wata wukar cikin fadin, "Bari in tayaki ba don halinki ba". Ya fara ferewa da gani bai iya ba, sai zaftare tsokar dankalin yake. A haka aka yi firar aka zo wajen daddatsawa, nan ma ba iyawa yayi ba sai yanka su yake ba fasali, wani kudi wani bashi. Bai ankara ba ya sharce dan alinsa da wukar. Nan da nan jini yayo ambaliya. Ya yi saurin ya da wukar ya tara danyatsan a famfo jinin na bin ruwa. Sai naji tsigar jikina na tashi ganin yawan jinin dake fita. Kamar yadda ya ce din ne idan babu soyayya akwai kauna ta 'yan uwantaka. Ban san sanda na wuce daki na dauko turaren dana fesa ba na dawo na kashe famfon (sink) din da ya kunna na soma fesa turaren akan yankar. Ban fasa ba sai da gudun jinin ya tsaya. Na gutsiro (tissue) na danne yatsar, duk kokarin da zan iya nayi wurin ganin bamu hada ido ba. Shima bai takura da sai mun hada din ba, kawai cewa yayi. "Thank you!". Na bi na tattare fuska na hade wuri guda cikin raina cewa nake, " Ni bana son wani tayin aiki, a barni da likitancin da ban karanta ba". Amma a fili aikina na ci gaba da yi bance komai ba. Sai ya jingina da kabinet din (kitchen) din yana kallon yadda nake ayyukana cikin nutsuwa da hada hankali guri guda. Na bude firji na debo kwai ina fasawa sai ya baro jikin (cabinet) din ya iso gareni. Cikin murmushi ya ce. "Let me help you". Na ce ciki-ciki, "Barshi nagode". Bai karbi godewar da nayi ba ya dauki daya, maimakon ya hada shi da uwansa ya fasa ko ya fasashi da wuka, sai ya hada shi da goshina ya juye a fadi ka mutun da nake juyewa. Ya sake daukar daya, ya hada shi da tsinin karan hancina shima ya juye ya yar da bawon a (dusbin). Nan da nan ya fashe su duka guda takwas din a goshi da hanci na, ko a ina ya koyo wannan fashin kwan oho! Nan take na soye shi tas na gama duk abinda nake yi yana tayani. Amma cikin raina bana godewa, a kyaleni yafi mun. Karar kararrawar shigowa tasa na samu yadda nake so, wato ya fita ya barni. Can na jiyo tashin sautin su shi da Surajo ne. "Na dauka tuni ka kama hanya?" Cewar Fa'iz. "Ni na isa in tafi, ban zo naga dakin Madam rikici na sayi baki ba?" Tare suka zauna kujerun falon rike da hannun juna. Kai sai yaushe zaka wuce? Ko kazo kenan". Ya ce, "Two weeks off gareni, yau kuma kwana na hudu, saura kwana goma inaga". "Tare zaku wuce amma?" Surajo ya tambaya. "Don Allah ka rufa min asiri kada ka ballo min liki irin wanda ka saba ballowa, na samu an daina yi min hayagaga ko ba'a bini ba na gode". [1/4, 12:23 am] Takori: Abin ya baiwa Surajo dariya, in wani ne ya bashi labarin Abubakar Mukhtar (sunan da suke kiranshi) zai koma haka akan mace karyatawa zai yi. Soyayya ba karya bace, a yau ya kara yarda da hakan. Ya shiga girgida kai kamar kadangare. "Tana ina ne? Ban ji motsinta ba. Ga hotunan (cocktail) din ku fa na wanko". Ya amsa ya aje gefe ba tare da ya bude ba yayi mai nuni da (kitchen) da girar shi. Dariya Surajo yayi, "Kace har girki ake mana!". Shima dariyar yayi, "Mai dadi kuwa". Suka yi ta dariya kamar wasu shashashan madina, sai da suka yi mai isarsu tukunna. Surajo ya ce, "To yanzu yaya za'ayi batun tafiya UK?" "Sai yanda ta yiwu Surajo, bani da sauran dabara, duk abinda zan iya nayi, na bada hakuri, nayi fada, nayi wa'azi, nayi nasiha. Zan iya cewa (there are lots of improvements) sai dai bata yi min magana, sannan in nayi bata amsa min da baki, sai dai tayi a aikace. Kuma ba musu, ba rashin kunya, duk abinda nasa ta daga jiya zuwa yau tana yi". Surajo ya ce, "To Alhamdulillahi, hakuri (still) ba abinda baya bayarwa. Kuma ina ganin inta bar kasar zuwa inda bata da kowa komai zai tafi (normal)". Ya ce, "Nima tunanin da nake kenan, amma Surajo (how easy is that)?" Dai-dai lokacin da na fito daga (kitchen) dauke da fadi ka mutu ina jerawa akan (dining). Duk suka yi shiru kamar ruwa ya cinye su. Jikina ya bani zancena suke yi. Zan koma (kitchen) Suraj yayi gyaran murya. "Madam ba gaisuwa yau ma?" Ina tafiya ban tsaya ba na ce, "Ina kwana?" Ya ce, "Lafiya lau, sannu da aiki". Na ce, "Yauwa". Na shigo don dauko filas din ruwan zafi. Suka dubi juna suka yi murmushi. Tare suka karya kumallon shi da Surajo yana tambayarsa abinda yaji masa ciwo. Ga ammakin Fa'iz sai ya kasa gaya masa kada yayi masa dariya don a hakan ma bai daina mamakin canzawarsa da rauninsa ba, gani yake yayi min sako-sako da yawa. To abin ne shima yazo amsa 'beyond comment' (sunan wani ganyen shayi), idan yana gaban Fa'izah manta kansa yake da (identity) dinsa. Cewa yayi yankewa yayi da reza ya ce. "Kai me ya hadaka da reza kamar wani wanzami?" Ya ce, "Don Allah ka kyaleni haka Surajo, kwakkwafin ka ya isheni". Wata irin dariya Surajo yayi wadda ke nuna ko dai bai gano ba to ya kusa ganowar. Ni kyale su nayi na koma daki na kwanta don rama bacci. *** Ban jima da kwanciya ba bacci ya dauke ni, ba ni na farka ba sai azahar. Nayi wanka nayi (brush) ba don banyi na safe ba sai don inji dadin cin wani abu. Domin da mahaukaciyar yunwa na tashi. Na fito falo na duba (dining) na tarar da (plate) daya da basu taba ba, na hada 'tea' mai kauri na fara warware hanji na dashi sannan na zauna na soma ci. Na kammala na kwashe komi na hada da wadanda nayi amfani dasu a (kitchen) na wanke. Na adana komi wurinsa. Dana kammala sai kadaicin ya isheni, na kasa zama wuri daya. Tunanina ya bani in zagaye gidan cikinsa da wajensa in gani, sai na sanya mayafi da (slippers) na fito harabar gidan na zagaya baya. Dawisu ne guda biyar (peacock) mata da maza, wasu a kasa, wasu akan katanga sun bude kyawawan jelunansu abin gwanin ban sha'awa. Sai na gane sune ake maganar su jiya sun kwanta da wuri. Na debi dawar da na gani cikin buhu a kofi ina cilla musu da dai-daya. Sai ga wani saurayi ya bullo yayi min sallama, na amsa muka gaisa. Jiya ban kalle shi ba balle in san kamanninsa, da yayi magana ne na gane shi. "Kai ne Ya'u?" "Eh, ni ne Madam. Wannan aikina ne, don Allah ki bari zanyi, basu dade da cin abinci ba". Nayi murmushi na ce, "Ka dinga share kashinsu daga yau kawai Ya'u. Ina so na karbi ragamar ciyar dasu da hannuna, ina son Dawisu Ya'u". Sai yayi dariya ya ce, "Hakan ba zai zama matsala gareni ba wurin Yallabai?" Nayi murmushi nima, "Ba zai ji ba insha Allahu". Ya ce, "To Allah Ya ba da lada Aunty". Na amsa, "Amin Ya'u". Ya wuce ya barmu, na ci gaba da jefa musu dawa duk suka yo gabana suna dauka da bakunansu masu kyau suna kara baza bindi. *** Cikin wannan yanayin kwanaki suka ci gaba da mirgina mana har muka kwana goma, ranar Juma'a da yamma naji kugin mota, sai dai ba irin na motar Fa'iz bane. Na mike na daga labulen falo, sai na hangosu Walida, Shu'aib, Yahya, Junior, Abdallah, Kausar da sauransu suna fitowa daga mota, direban Mama Malam Sani ya kawo su, kowanne da 'yar karamar 'troller' din dana tabbata kayan sanyawarsu ne a ciki, yadda dai na gansu a gidan Ummi. Wani irin farin ciki naji ya rufeni don dama ina fama da kadaici da kewar su. Har da hadawa da gudu wurin bude musu kofa, kowanne yabi lafiyar kujera yana wash-wash, 'ya'yan hutu malam. Manyan su Shu'aib ne kawai basa cewa wash din, sai gaisheni cikin girmamawa. Na nunawa Junior dakin dake kusa dana Fa'iz shima (bedroom) ne (single) ba falo, ba abinda babu na ce su mazan su kai kayansu can, matan suzo mu hadu a nawa dakin sai ina-naka-saka nake dasu. Kausar ta kwantar da kanta a cinyata kasancewarta shiru-shiru ba kasafai ta fiya magana ba. Na ce, "Wai daga ina kuke ne?" Walida ta ce, "Gidan Aunty Ummi". Na ce, "Tun (last week) dana baro ku kuna can?" Suka ce, "Eh". Kausar ta dago kanta daga cinyata ta ce, "Koro mu fa suka yi ita da Yaya Bashir, yau ya dawo bayan hutun mu bai kare ba". Abdallah ya ce, "Kora da hali dai ba kora ta ku tashi ku tafi ba". Nayi musu kallon son jin karin bayani, dariya na son kama ni. Walida ta dora bayani. "Saboda Yaya Bashir ya dawo ta barmu a falo tun safe, sannan bata dora mana (break) da wuri ba, suka kyalemu yunwa na cinmu. Da ta fito bata hada mana ruwan wanka ba, ta ce kowa yayi da ruwan sanyi wai hitar (toilet) din gidan duka ta lalace. Ki dubi sanyin nan da ake. Shi kuwa Yaya Bashir din kai tsaye daya fito ya ce mu hada kayanmu mu koma gida, wai mun cika mishi kunne". Dariya nake kamar cikina zai fashe, Walid ya karasa. "Tunda dama hutun sati biyu muka je sai yaya Junior ya ce muzo nan kawai mu karasa kwana biyun mu sai mu koma gida, don dama Monday duk zamu koma (school) ke kam mun san ba za kiyi mana abinda Aunty Ummi tayi mana yau ba". Na janyo autan Momi jikina ina dariya, "Ina kuwa zanyi muku Walid? Ni farin ciki nake da zuwan ku, inma kun dawo gidan kwata-kwata ne (you are most welcome) dakunan gidan zasu ishemu". Duk suka hau murna sosai. Na ce, "Yanzu me zaku ci?" Abdallah ya ce, "Chicken burger?". Yahya da Junior suka ce, "Shinkafa da salad". Shu'aib ya ce, "Quaker oat kawai zansha da 'peak' ta ruwa". Kausar da Walid suka ce, "Wake da shinkafa da mai da yajin tafarnuwa". Taashin hankali gobarar gemu, (inji hawwa lawan meturare) tawa ta sameni ni Fa'izah. Na fada cikin raina, naja numfashi. "Uhm! Gaskiya abin naku (is too much). Dankari! Sunan wata jarida, dole Ummi tayi muku kora da hali har da sandan ma in tana dashi, in haka kuke kullum to tayi bala'in kokarin rike ku har kwana goma. 70% na abubuwan da ku ka lissafo bani da kayan hadinsu, kuma ko inada su jikina akwai jini da bargo ba zan iya ba. Chicken burger da Indomie kawai zan yi muku dukkan ku. Shi kenan?" Gaba daya suka ce, "Eh, ya isa". Banda Yaya babba (Shu'aib) shi harar su ma yake, ya ce. "Ai basu da hankali ne". Na ce, "Naga alama Yaya Shu'aib". Gaba dayanmu muka shiga (kitchen) banda Shu'aib, aka zage ana aikin hada burger, mai yanka tumatir da salad daban, mai baking da blending tsokar kazar da za'ayi amfani da ita shima daban. Haka mai tsaga biredin da shafa masa mayonnaise da salad cream shima daban. Nan da nan aiki ya kammalu kowa da (plate) dinsa ina ta rabo Fa'iz yayi sallama ya shigo. Sai kuma ya tsaya turus! A bakin kofa yana kallonmu, hannunsa dafe da habarsa. Yake fadi cikin kidayawa da dan alinsa. "1,2,3,4,5,6,7... duk a dan gidana? Ina zamu kaiku? Gaskiya ba zai yiwu ba, ba kuma zata sabu ba wai bindiga a ruwa. Banda dukkan ku taron mahaukata ne ana zuwa gidan mutane ba (notice in this century?) Kuma wai kwana? Ba daya ba har biyu? (Look at you all with your noses like hippopotamus's". (Dube ku duka hancinanku kamar na bauna). Suka aje lomar burger hankali tashe, rai bace. Ya samu kujera ya rage tsawo, ya dora kafa daya kan daya yana karkada 'yan mukullayen motarshi, ya sake fadin. "Wai da ba gidan Ummi na ganku ba?" Walida tayi rau-rau da ido, "Ai sun koromu...". "Au, shi ne ni aka zo aka tare min? Ga gidan dan iska ko? Abokin wasan ku?" Suka yi shiru tsuru-tsuru dasu abin tausayi, da alama wani abu ya bato masa rai a waje yazo ya huce a kansu. "To kuje kuci abincin duk kuzo in kaiku Jabi Road, ba mai kwanar min a gida". Kausar ta sha mur, Abdallah ya turbune, Junior ne mai karfin halin musantawa. "Haba don Allah Ya Fa'iz! Ka barmu mana? Don kwana biyu kawai?" Yahya ya yi kicin-kicin da fuska, "Kaima in kaje gidanmu ai Mama bata korar ka, daki ma take baka". Fa'iz ya fiddo ido waje saura kadan dariya kufce mana ni da Shu'aib, ya ce. "Kuji min marasa kunyan yara, ina fade kuna fade? To wallahi ba zaku kwana ba, ko ana dole? Bana son bakuntar, aje na gode. In ba wuni ba kada wanda ya kara zuwar min gida kwana, OK?" Tsit suka yi, sannan suka karasa cinye abinda suke ci. Duka suka mike cikin sanyin jiki suka dauko jakunkunansu suna ja a hankali duk suka bani tausayi. Wato mai hali baya fasa halinsa. In ka jima baka hadu da mutum ba, tambaye shi wani abin amma banda halinsa. Shi kuma irin tasa ZUMUNTAR KENAN! Idanuna suka cicciko da kwalla amma na rantse ba zanyi magana ba tunda nasan don inyi maganar ne kawai da bashi da alfarmar samunta haka kawai shi ne yake neman dalili. Suka yi waje, ya tashi ya bisu yana, "Oya! Kuyi sauri ku shige muje". Kamar ya samu wasu tumaki, haushi da takaici ya sake kamani. Na kudurta a raina duk yadda za'ayi yau ba zan gasa kazar da (chips) ba ladan korar min kanne. Sai dai nima ya kore ni. Anan kan kujerar da nake zaune ina sakawa da kwancewa barci ya kwasheni, har ya dawo ya rufe ko'ina ya kashe kayan wuta ban sani ba. Sai ji nayi yana tashina ta hanyar kiran sunana da jan babban yatsan kafata. "Yaya banga (chicken) akan (dining) ba?" Na mike na kalle shi cikin matukar fushi amma na kasa magana, na mike tsam kawai na shige dakina na rufo kofa, garam! Da safe ma kin fitowa nayi in dora karin kumallo duk da jiya ya ce in dora da wuri zai je Abuja da sassafe kan visar sa. Har bakwai da rabi ban bar gadona ba, duk da ba barci nake yi ba. Ya tabbatar bazan fito din ba balle in bashi ko ruwan zafi, sai ya iso kofar dakina yana balle 'links' din hannun rigar shaddar 'hilton' dake jikinsa fara sol. A bakin kofar ya tsaya yana fafin. "Ran Aunty Fa'izah ya dade, an tashi lafiya?" Shiru babu amsa, don haka ya dora gundarin bayaninsa. "Jiya nasan ban kyauta ba dana kori su Junior. Ina da dalilai na nayin hakan (which are all for our own goodness: Na farko kin sani Allah bai halicce ni da son hayaniyar yara ba. Na biyu ke ba kirki ne dake ba abubuwan da kike aikatawa ba lissafi a cikinsu, yaran nan kuma suna da fahimta sannan basu da mantuwa, gasu da daukar zance komi aka yi akan idanunsu sai ya koma kunnen Mama da Baba. Hatta rotsen da kika yi min a (Area One) Yahya ya gayawa Mama Junior ya gayawa Baba na kuma rasa ta inda suka jiyo. Haka kike so suje suce kina hararata, ba kya kulani wani zubin har tsaki kike mini komai da ya kamata ace mata na yiwa mijinta ni sai na roka sannan a hagunce ake yi min...". Tsakin da baya so na sake saki na juya masa keya na ba banza a ajiyarsa. Kai ni surutan da yake yi ma sun isheni nasa hannu na toshe kunnuwana. "Ina (breakfast) dina? Na gaya miki Abuja zan tafi". "Banga damar girkawa ba". Ya ce, "To Allah Ya bamu rai da lafiya". Na ce, "Amin Ya Rabbi". Ya juya ya fita ya janyo min kofar a fili, na ce. "Umma ta gaida Assha". Bai jima da fita ba na mike nayi bayan gida wurin Dawisu don basu abincin safe. Ina watsa musu hatsi daga nesa suna kara matsowa gareni cikin alamun nuna sabo, wato sun fara ganeni. Ya'u ya iso ya gaida ni ya ce. "Aunty na kawo cefane yana can kofar falo". Na ce, "Ina godiya Ya'u, anjima a sake musu ruwa, wannan ka gani duk yayi kura". Dariya abin ya baiwa Ya'u, amma sai ya ce. "Aunty kina son 'yan gidan nan naki, zan kara himma wurin kulawa dasu". Na ce, "In kayi hakan kaima Allah zai kula da kai". Na koma na kwashe cefanen da ya aje dokin kofa na shiga (kitchen) na adana kowanne a muhallinsa. Fa'iz bai dawo ba sai dare, sanda ya shigo gidanma bacci nake, ban san ya shigo ba. Na fito ne da daren don samawa cikina abinda zai ci naji yana kwalamin kira kamar tashin duniya. Duk da na firgita da irin kiran amma na share na shige kicin sai gashi ya biyo ni (kitchen) din a sukwane hannayensa rike da tulin hotuna. Fusatar dake fuskarsa ba zan iya bayyanata ba. Ta gefen ido nake kallonsa ina ci gaba da abinda nake yi, sai ji nayi ya finciko ni ta baya, saura kadan in fadi Allah Ya taimakeni na dafa (cabinet) na mike a lokacin na lura hotunan da Surajo ya kawo ne rike a hannunsa, fuskarsa a murtuke, idanunsa sun kada sunyi jajir yake magana harshensa na sarkewa. "Meye na daukar hoto da Suraj haka (very so close) har jikinku na gugar juna? Meye na tsayawa kusa da shi haka kusa da kusa a bainar jama'a? Da na ce yazo ya tsaya min cewa nayi kuyi hoto? Shi kuma Ya'u da kullum kike bare baki kina hira dashi da izinin uban waye? Ina ruwanki da duk namijin da na kawo na aje cikin gidan nan da har kike dafa musu abinci? Cewa nayi dake bana basu kudin da zasu ci abinci ko me?" Wani matsanancin haushi da takaici suka taru suka rufe ni, naji in ba rushewa nayi da kuka ba bazan huce wannan cin mutuncin da rainin hankalin na Fa'iz ba. Na kasa cewa komai sai ido dana zuba masa cikin matsanancin haushi. "Ina magana kin zuba min wadannan kwala-kwalan idanun naki, ba zaki amsa ba? Na ce shi kuma Ya'u ina ruwanki da shi har yake gaya min kince masa kaza da kaza? Na kirashi na aje domin baiwa tsintsaye abinci hirar da kike yi da shi ta mece ce? In hirar kike so kiyi dani mana? (Am I not applicable to meaningful talks than him?) Ni baki yi hirar dani ba sai da wani gardin kauye can daban. Ba zai yiwu ba to! Daga yau Ya'u ya bar gidan nan. Shima buzun in kika sake kula shi wallahi tafiya zai yi, ki zauna ke kadai ba zaki kasheni da raina ba... Akwai masu bukatar rayuwata ba don ke kadai aka halicceni ba!!!". Bayan takaici da haushi da buyaginshi ya bani, sai ya dawo bani dariya saboda da iyakacin gaskiyarshi yake wannan hargagin, akwai (gesture) a tare dashi mai nuna abinda yake fadin, haka yake har zuciyarsa. Dariya ta cika min ciki ban san sanda nayi murmushi ba irin murmushin nan na tura haushi da maida kai shashasha domin na rantse da fari na firgita, matukar firgita kuwa. Ko da kwartaye biyar aka kamani yanayin da ya zo min dashi sai haka! Ko ni nace a daukemu hoto da wani Surajo oho! Balle kuma bawan Allah Ya'u. Naga idan na kula shi ma (is a waste of time) don haka da sauri nabi ta gefensa zan fice daga (kitchen) din, sai jin hannuna nayi rike cikin nasa, cikin wani irin riko mai tsauri dana kasa fincikewa kamar ba mutum ne ya rike ni ba. "Ina magana kin maidani dan iska?" Yanayin da yayi maganar muryar kamar ba tasa ba kuma cikin wani irin 'tune' da ban taba jin wani mahaluki yayi magana dashi ba. Abubuwa biyu sautin da yayi amfani dashi din ya haifar a gareni. Faduwar gaba da wani irin bugun zuciya, hannun nasa da jikinsa duka rawa suke yi yana wani irin tsuma. Wani matsanancin tsoro ya shigeni. Na daga kai a hankali na dube shi don tantance ko dai wani ne ya rikide yazo min da suffarsa don ya cutar dani. Daga idon dana zo ina dakacensa, domin kamar jira yake na dago idon yayi hanzarin ya sanya bakinsa cikin nawa ya soma 'kissing' ba ji ba gani kamar wani mahaukacin zaki. "Na tuba Fa'izah, na bi Allah na biki. Kiyi min duk abinda kike ganin in kinyi shi zaki huce bacin-ranki, amma ki barni in rayu dake muddin rayuwata...". Kalaman da yake maimaitawa kenan ba adadi, babu 'comma' ba 'full-stop'. Saura al'amuran da yake kokarin bijiro dasu masu nauyin fada ko misaltawa ne, kuma ban shirya karbarsu ba daga nan har gaban abada. Don haka na tattara karfina da Allah Ya hore min a wannan lokacin wanda ya kasance fiye da nashi na angaje shi na taka da gudu nayi dakina na shige na rufe da 'key' ban kuma yarda na zare key din daga jikin kofar ba har safiyar washegari. Kwana nayi jinyar tsallake rijiya da bayan da nayi jiya wanda ko a mafarki ban kawo shi cikin rayuwar dolen da nake yi da Fa'iz ba. Wanda ya hankaltar dani ga cewa in sauya taku. Hanyar dana dauka ta yin sako-sako ga rayuwar da muke yin bisa tilas ba zata bille dani ba, ba kuma mai billewa bace ba. Idan kuma na ci gaba da binta, la-shakka ina cikin hatsarin da bazan iya maganinsa ba idan ya sameni. Nayi kuka har na gode Allah. Daga baya bacci mai nauyi ya dauke ni. Can cikin barci na naji yana buga kofar ba da karfi ba. Na bude ido na ga hasken rana ya ratso ta labulen taga nayi mamaki matuka, sallar asuba ta kufce min cikin shagala! Ina rokon Allah Ya yafe mini. Na fada (toilet) da sauri nayi alwala, saida nayi sallah sannan na koma nayi wanka. Sannan na shiga (kitchen) don kwana nayi da bakar yunwa. Har kicin din ya biyoni ya tsaya daga kofa yana sanye da kayan wanka na 'versace' da alama fitowarshi kenan daga wanka. Daga inda nake ina iya jiyo kamshin 'bathrobb' din da yayi amfani dashi na 'desire dunhill’. "In kin kammala ki shirya muje Jabi, Area One (Zaria) da Giwa kiyi musu sallama don jibi zamu tafi". Na wani irin juyo nayi masa kallon kayi hauka ka warke, na juya na ci gaba da aikina. Ya girgiza kai ya juya ya kyaleni. Duk yunwar da nake ji sai naji ba zan iya cin abincin ba ma saboda tashin hankali. Amma sai wata zuciyar ta ce bishi kawai kuje wajen Maman, wannan ce kawai mafitarki sai kiyi amfani da damar ta inda bai zata ba. Sai kawai na aje komi na fito na sauya kaya, kwalliya sosai nayi da 'pitch swiss-lace’ mai ratsin baki, na yafa bakin gyale na rufo dakina. A falo na cimmasa yayi nasa shirin cikin riga da wandon shadda getzner dark-green dinkin tazarce kanshi ba hula. Sai 212 ke tashi a falon. Ya hadu ya cakude da 'escada sentiment' da nayi amfani dashi wani sanyin ni'ima ya baibaye dukkanin mu, da ganinmu kasan ango da amarya ne ba karya. Ko kallona baiyi ba yayi waje, na bishi a baya naki rufo falon na shige mota. Ina kallon yadda yayi kwafa, ya fito ya rufe ya dawo, sannan ya tada motar muka fita harabar gidan buzu na daga mana hannu muka nufi gidan Baban Kaduna. Su Yahya dake ball a harabar gidan babu wanda ya taremu da murna ko tsalle kamar yadda suke yi da, tabbacin haushin yayan nasu da abinda yayi musu bai sake su ba. Sun dai yi mana sannu da zuwa suka ci gaba da 'ball' dinsu. Ya kalle su ya gyada kai yayi murmushi bai ce dasu komai ba, muka wuce kai tsaye falon Mama. Mama waya take sanda muka shiga kafarta daya kan daya a hamshakin falonta. Ta daga ido ta dube mu muna shigowa, fara'arta ta karu, ta ce. "Kinga 'yan halak, gasu nan sun zo". Ta miko min wayar tana fadin, "Rabi ce daga Kano". Na karba sannan na zauna a kusa da ita daga gefe na kara a kunena na ce. "Hello Ya Rabi". Kafin in karasa ta fasa min guda aka mai barazanar tarwatsa min dodon kunne. Da sauri na dubi Mama da danta don tsammani nake suma sun jiyo mahaukaciyar gudarta Ya Rabi, sai naga hankalinsu baya kaina sam, gaisawa suke. Yaya Rabi ta ce, "Diyata 'yar albarka, ya aka kare da BOXING? WHO IS THE WINNER?" Nayi tsaki, "Tsiyarki kenan Ya Rabi, ba a maganar arziki dake". [1/4, 12:23 am] Takori: Tayi dariya sosai, "Ni kuwa ake maganar arziki dani, ‘yar Abubakar uwar Abubakar da Fa'izah, uwa ga Zanira uwa ga Ummi, sha lelen Muftahu autar Hajjah. Kirarina kenan, na zama duwawu dole a zauna dani. Tafiya ta tashi ko? Birtaniya ko Murtaniya? Na so ace nazo rakiya Allah bai yi ba, naji tafiyar taku ne ba shiri, a tabbatar in za a dawo da baby aka taho min sai inzo in zauna zaman dabaro mai dalili...". Nayi tsaki na katse wayar don nasan in ta Ya Rabi ne sai mu kwana muna yi bata gaji ba. Ga haushin da take kara kuma mini ta barni inji da wanda nake fama dashi. Mama ta dubemu duka tana murmushi bayan ta karbi wayarta. "Komai lafiya ko?" Tana duban Fa'iz. Ya hade gira ya ce, "Tambayeta mana Mama!". Mama ta ce, "Fa'izah ta ina Fa'iz ya kuskuro ki ko ince yake bata miki?" Na girgiza kai kaina a sunkuye. "Babu Mama". Ta dube shi, "Fa'iz Giwa fa?" Ya ce, "Mama ba sharri ba, tunda dai gatanan a zaune a gabanta zan fada. Da abinda take yi min na kisan mummuke gara min ta bude baki tayi ta zagina kamar da, ko ta ware hannu tayi ta dukana kamar yadda ta faro. Bata yi min magana, bata shiga sabgata, ba ruwanta dani ko rayuwar da nake yi cikin gidan. Bata yi min biyayya sam, ta maida kanta kurma domina". Na dago idanuna da suka yi jawur na ce. "Wallahi Mama ina iyaka yina, ina masa girki duk abinda ya ce dani bana musawa nake masa, to ban san kuma wace irin biyayya yake nufi ba...". Ya katse ni tare fidda ido, "Girkin banza! Mama baya ga girki me take yi min na hakkin maza akan matansu? Fa'izah bata kula ni, bata taba zuwa shimfidata ba, bata gaida ni, ga tsaki da harara kamar wani sa'an wasanta". Maganar ta dan girme mu ni da Mama, amma dukkanin mu sai muka yi kamar bamu ji ta ba. Na kawo wata daban. "Saboda Allah Mama ya yake so nayi? Ya zo ya sani gaba da bala'in wai don me zanke kula Ya'u leburanshi? Bayan a karkashinmu yake, dole ne ko gaisuwa ta hada mu, wai kuma don me zan ke basu abinci bayan ciyarda barori wani abu ne da muka taso muka tarar a gidanmu a matsayin kyakkyawan koyi koda ana basu albashi. Ban kula shi ba sai ya koma wai don me nayi hoto da Surajo ranar Cocktail? Bayan bani na gayyato shi ba, ban kuma je fatin nan don kowa ba sai don kaina ko ku baku san zan je ba. Ban san ma sanda aka dauki hoton ba da abinshi ya zo. Sannan kannena suka zo min zumunci ya kore su, yanzu duk haushina suke ji kamar yadda suka kullaci Ummi. Sannan ya kawo wata magana wai wani tafiya, ko ina oho! Ni kam kiyi masa magana ya fita harkata, babu inda zani gaskiya in har ba so yake ya kuntata rayuwata ba (by all means from every angle). Na yarda na amince zan zauna a can Malali ko ni kadai ce yaje duk ranar daya samu dama ya kawo min ziyara babu damuwa". Ya fiddo ido cikin kidima, "Baki isa ba, Allah kinyi dan kadan, duk abinda kike ji dashi ina shirye da dauka amma banda wannan". Fada yake yi sosai har jijiyar kansa na mikewa kamar ma ya manta da Mama a wurin. Mama tasa masa ido tana kallo sai da yayi mai isarsa tukunna, daga ni har ita babu wanda ya tanka, sai dai jikina naji ya soma rawa, kuka na son kece mini. Ya yi shiru ganin na soma sharar hawaye da mayafi na. Sannan ne Mama ta nisa cikin bacin rai ta soma magana. "To tunda zuwa kayi ka kare mana tanadi ni da ita, to tattara iyalinka ku tafi ka fini iko dasu. Ni dama ban kirawo ku ba balle kuzo ku daga min hankali". Ya soma bata hakuri tana kaucewa, daga karshe ta ce. "Laifi duk naka ne Fa'iz. Meye don Fa'izah tayi magana da yaron gidanta tunda kana da tabbacin ba zata yi maganar banza dashi ba? Don ta girka abinci ta basu domin kyautatawa bai kamata ka nuna jin zafin ka ba, sai ma kayi alfahari da ta zamo mai kyautar abinci ga na kasa da kai ba kace ta daina ba. Hoto kuwa duk muna tsaye aka yi shi, kasan baka so ayi hoto dashi don me ka turo shi? Suraj ya rufa maka asiri babu wanda yayi zaton ba kaine a wurin ba, meye laifi anan? Magana da kace bata yi maka ina ce komai sai ta dauro za'ayi? Ka sani Fa'izah ba mai son yawan magana bace tun tuni. Tunda har da bakin ka ka furta bata yi maka musu, sannan tana girka maka abinci, sai me ya saura? Dan Adam da ba'a iya maka har kana fadin gara maka zagi da duka da wannan. Yau da Fa'izah zagin naka take da duka da rashin kunya, ko kuma bata baka abinci dole ne in tsawatar mata. Don Allah ka koyi hakuri Fa'izu, zafin zuciyar nan baya da amfani ko kadan, kabi komai a sannu, a baya ka zaci wannan din da kake rainawa cikin kankanin lokaci haka? Har kullum addu'armu na tare da ku, komi zai yi dai-dai a gaba insha Allahu". Da alama jikinsa yayi sanyi, amma ba duka ba. Ya ce, "To amma Mama tsaki da harara fa? Gaskiya ba zan jure ba, don ban taso naga kuna yi ba ga su Baba ko wani cikin A.B baki daya. Wannan ai raini ne. Ko don Fa'izah ana sonta kowa na tsoron masifarta?" Abin ya bawa Mama dariya, amma ta gimtse. "In ma hakan ne bamu yi laifi ba tunda ai amarya ce, amarya kuwa kowa yasan bata laifi. Kuma ka dinga tausaya mata tunda dai auren nan kasan ba da saninta akayi shi ba, zuwar mata yayi kamar saukar aradu. Don haka ni yadda ta dawo yanzun naji dadi, ta fara nuna mana ta haifu, bata fi karfinmu ba kamar yadda muke zato, huce bacin ranta take yi kuma ta fara hucewar to ka bimu a sannu in kana son mu ci gaba da hucewa". Yayi kwafa ya ce, "Me nayi mata? In zaki yankata ta fadi laifin da take ikirarin nayi mata bashi da yawan hukuncin da nake karba. Banda ni din nine Fa'izun Hajjah Abubakar-Saddiqu, na Baban Kaduna da ABU wa zai yi hakurin dana yi? Ko anan aka tsaya an san ni jarumi ne wanda mace bata isa ta girgiza ba ko ta sani abinda ban yi niyya ba. Don haka nayi niyyar mu tafi tare wajen neman abincina, kinyi kadan ki canza min ra'ayi. Wallahi Mama yarinyar nan ba abar tausayi bace, ki daina jin tausayinta kina ganinta haka kamar wata mumina. Musa ce a baki Fir'auna a zuci, rashin mutuncin dake cikin bakinta da zuciyarta yafi bakinta girma". Mama tayi dariya tana mamakin yaushe bakin Fa'iz ya bude yake zaro Hausa haka? Abar da ada sai dai kaji yana yi mata baragada in ya jima yana magana, lallai Fa'iza bata kama kurwarsa da wasa ba. Ta gyada kai ta ce, "To ke Fa'izah kinji wannan?" Na ce, "To Mama tunda ya ce tsaki nake masa to yayi tafiyar sa shi kadai mana ya huta da jin tsakin? Maimakon inje ina yi mai ranshi na baci? Tunda cikin hutu su Junior suke sai muyi zaman mu tare a gidan har su Walida a karo, amma ni ba inda zan iya matsawa inbar iyayena da 'yan uwana zuwa inda ban san kowa ba tunda duk abinda nake yi masa baya gode ko daya, haka idan na bishi rai zai yi ta baci gara inyi zamana". Mama ta ce, "Kwarai kuwa, ba inda Fa'izah zata, zata zauna har ka samu hutu. Ni dama bana son yawon jirgin nan, tukunna ma kai da baka zama wuri guda, a tafe kake kwana a tafe kake wuni, meye amfanin bin naka da kake so tayi?" Kamar zai yi kuka ya ce, "Amma ba kullum nake kwana a tafe ba ko Mama? Abin cikin tsari ne, (we have breaks!)". Mama ta ce, "Oho maka! Na gama magana, ku tashi ku tafi don Allah. Allah Ya yi muku maganin abinda ke damun ku, Ya yaye muku shaidanun dake yawo akanku. Duk 'yan uwanku kowanne na zaune lafiya da abokin zamansa ba mai jin kanshi da dan uwansa sai ku. Ku taka a sannu, duniya ba'a yi mata gaggawa". Mun mike kenan Baba ya shigo, zuciyata kamar farar takarda nake gaishe shi. Fa'iz bai bari na dire gaisuwar dana debo ba tun kamin Baba ya zauna ya soma karanto masa yadda akayi, da hukuncin rashin adalcin Mama. Shi dai Baba da dadin ganinmu tare har ana zancen tafiya Birtaniya sai ya hau hamdala ga Allah a zuci, a fili kuma ya ce. "Tunda bata so a kyaleta man Fa'iz? Ba a son tilastawa cikin zamantakewar aure, watarana da kanta zata ce zata bika ne". Tun daga ranar da aka yi mana aure Fa'iz bai ji na bashi bakin ciki da takaici irin yau ba. Ya mike cikin fushi ya zari mukullin motarshi ya yi hanyar waje. Baba da karin tura haushi ya ce. "UHm! Na ce ba?" Fa'iz ya dakata amma bai juyo ba. "Ka nemo motar hawa a kyale min tawa ta huta. Haba, ya za'a ce in hau abu, kaima ka hau, wannan sam ba tsarina bane. Duk kabi ka zage min gari da motar ma bana so, ka je ka rike ka kirgo kudinta ka biya ni, fakat". Ya ce, "Zan kawo abinda ya samu, shi kenan?" Baba ya ce, "Wane irin abinda ya samu? Naira miliyan biyar cur na sayi mota ta, haka za'a bani ko Naira biyar ban yarda tayi ciwon kai a ciki ba. Mota ta 'R-Class' ce kaje ko'ina ka tambaya haka kudinta yake". Takaici a wurin Fa'iz baya faduwa, ya ce. "Haba Baba, ai babu ciniki tsakaninmu. Yaushe ma na fara aikin da har zan tara abinda kake fadi? Duk ajiyar da nake yi ta kananan ayyukan da nayi kai na turowa aka yi aikin gidan nan da muke ciki". Baba ya ce, "Kai ka sani. Albarkacin shekara biyu da tayi a hannuna, na shigeta sau bakwai, a kawo min naira miliyan uku, cash ba ta 'credit card' ko 'cheque' ko 'internet banking' ba. Ni nasan bankin da nake mu'amala da abina". Mama dariya take har da kyakyatawa. Fa'iz bai kara tankawa ba ya fice. Na bi bayanshi nima dariya ta cika min ciki amma na kame kaina tunda ni ke da nasara. Ina shiga motar kafin na kai ga rufewa ya fisgeta kofar ta rufe kanta da kanta, saura kadan ta guntile min 'yan yatsu. Tunda muka hau titin da zai kaimu Zaria bai ce min komai ba, kazalika bai kalleni ba. Ya maida hankali sosai a tukin da yake yi (at a speedy level). Momi kurum muka samu a gida muka gaisheta, bai iya yayi hira da ita ba duk kokarin da yake na boye bacin ransa. Daga bisani ya tashi ya barmu ya ce zai je cikin (city) ya dawo sai mu tafi. Bayan fitarsa Momi ta zuba min ido tana kallo. "Wato mai hali dai baya fasa halinsa. Ana murna kwana biyu an jiki shiru ashe wata sabuwar tsiyar kike shukawa a inda babu mai ganinki balle ya tsawatar. To in kowa baya ganinki ko Fa'izu bai kawowa kowa kararki ba, Allah da Ya halicci kowa da komai Shi Yana ganinki da duk abinda ki ke aikatawa na zahiri da badini. Daga ganin yadda Abubakar yake kumburi wanda ba halinsa ba, kinyi rashin mutuncin naki ne". Na ce, "Wallahi Momi banyi masa komai ba, lafiya muke zaune tunda muka bar gidan nan. Tsakanin shi da Mama ne, don kawai ta ce sai ya sake dawowa na bishi inda yake, shi kenan yake fushi". Momi ta harzuka, ban kai ga direwa ba ta ce. "Ubanki za ki zauna kiyi eye? Na ce ubanki za ki zauna kiyi, ke ba zakiyi zaman aure irin na kowacce mace ba? Shashasha maras mutunci. In don ni kike yin wannan dabbancin wallahi kin dauki alhakina don ni babu abinda Abubakar yayi min wanda ban dauka a yarinta da kuruciya ba tunda dai ni dai gaba da gaba bai taba fuskantata ya zagenin ba sai dai inji a bakinki, wanda tun lokacin ba sauraron ki nake ba, bani kuma da tabbacin ko karya kike don bacin ke ban taba jin wani ya ce Fa'iz ya zageni ko baya sona ba. Akwai abinda baki sani ba wanda in kin sauke iskokin dake kanki kinbi a hankali watakila nan gaba za ki sani. Baka taba jin ZUCIYAR MUTUM... baka kwantar da hankalinka a kanshi ba. Don masu iya magana sunce ZUCIYAR MUTUM.... BIRNINSA!. Kin san Allah ki ka sake sako kafarki gidan nan sai nasa Babanku ya kakkaryata, ba dakin Abdallah ba ko cikin kuratandu kika shiga indai a gidan nan ne sai dai ki bi yawon duniyar daga yau babu mai hana ki". Idanunta suka cicciko da kwalla amma bata bari sun zubo ba don sanin hatsarin da zubar tasu ke tattare dashi a tare dani. Nayi murmushin da na tabbatar zai kwantar da hankalinta, gaba daya jikina yayi sanyi kalau. "Ba gidan nan zan dawo ba. Tunda muka tafi ma ai ba a gidan Baban Kaduna muke ba, Walida bata gaya muku ba? Muna gidanshi ne a Malali GRA". Ta dan zuba min ido kamar bata yarda da abinda na ce ba. Na ce, "Wallahi Momi da gaske nake, kuma ki tambayi Mama. Ko ya tafi a can zanyi zamana nayi miki alkawari, in kin ganni gidan nan ko gidan Baban Kaduna ko Giwa ko Kano wajen Ya Rabi gaishe ku nazo yi". Anan ne ta saki fuska ta ce, "Shi kenan. Su Walidar basu dawo bane, daga can suka wuce Lagos wajen su Zanirah". Dai dai lokacin da muka ji sallamar shi a dakin, abin mamaki ya saki ba kamar yadda muka zo ba. Ya ce, "Momi zamu wuce, ni kuma gobe zan wuce Wales din kasar England, na samu aiki da 'British-Airline' zan jima ban zo ba sai na samu (break) mai dan tsaho". Momi ta sanya albarka tayi addu'a da Allah Yasa matakin arziki ne, Ya kara rufa asiri, Ya kiyaye sharrin karfe da na iska, Ya cire haramun daga cikin abinda za'a samu alfarmar Manzo (S.A.W). Ya fadada murmushinsa cikin jin dadin addu'arta yana fadin. "Amin Ya Rabbi Maman Walida". Na mike, ta dubeni ba yabo ba fallasa. "Akwai garin semo da bushasshiyar kubewa da bushasshen kifi in kuna bukata". Na ce, "A'ah Momi, ba yanzu ba dai, zan aiko in ina bukata". Ta ce, "Ke kika sani". Da muka shigo Kaduna ya tsaya wani babban 'Shopping Mall' bai yi min ko tayin shiga ba shi kadai ya shiga abinsa. Ya jima sosai kafin naga yaran kantin sun biyo shi da manyan ledoji, suka zuba a bayan motar, sai katon-katon na abin sha (ruwa da lemo) kala daban-daban. Akan hanyarmu ta shigowa Malali ya tsaya ya tsayi gashasshen nama muka karaso gida duk jikina a sanyaye yake. Muna shiga Ya'u ya taremu, sai na samu kaina da kara jan lullubina na rufe har rabin fuskata ban san dalili ba ko don ya nuna baya so din ne da gaske? Bazan so ya zamo nayi sanadin hanyar abincin wannan bawan Allah ba, wanda ga dukkan alamu ita ce madogararsa kadai. Ya kwashe komai daga bayan motar ya shigar (kitchen). Yayi mana sallama ya fita. Ya maida kofar falon ya rufe da (key) ya dawo ya zauna bisa (carpet) ya kunna t.v tashar CNN yana rike da (remote) ya dawo ya zauna, ya janyo ledar namansa yasa a gaba yana ci yana sauraron labaran, bai kara kallo na ba kamar yadda bai nemi 'chips & chicken' ba. Na mike ba don an sani ba na shiga (kitchen) na soma sarrafa su kamar yadda na saba, amma na yau (with additional aroma and taste) saboda kamar ina neman hanyar shiri ne ko yaya ne dai na kasa gane kaina. Wata zuciyar ta ce tunda ni nayi nasara nawa ra'ayin aka yi masa fin karfi aka bi, bari in dan kyautata. Dana kammala na aje a (dining) kamar yadda na saba, na ce. "Ga (dinner) din". Kamar ba da shi nake ba kallon t.v kawai yake duk da na tabbatar ya ji ni saboda ba wai yasa muryar t.v din da yawa bane, a'a dai-dai jinsa, raina ya dan baci na wuce na shige daki na sayo kofa amma ban sa mukulli ba. Can naji motsin kwanuka a (kitchen_, na daga labule ta taga ta wadda kana hango duk abinda ke faruwa a (kitchen) sai na hango shi ya dora 'yar tukunya akan (cooker) ya saka indomie guda biyu bai ko cire ledar maggi da chili din dake ciki ba ya kawo ruwan zafi wajen kofi uku wanda ya sha kan indomin har baka hango ta ya zuba, ya rufe. Ya fita daga kicin din ya koma ya ci gaba da sauraron labaransa. Kamar inje in duba wannan lamari wata zuciyar ta kwabeni abinda ba ruwan ka ance dadin kallo gare shi, na koma nayi kwanciyata. Anfi minti talatin kafin inji shi ya koma (kitchen) din, ban san abinda ya faru kuma ba bayan nan. Bayan kamar minti biyar naji fitarsa a mota, tsegumi har tsunkuli na yake nayi (kitchen). Na bude tukunyar daya dora a wuta. Indomin ta hadu ta dame ta zama kunu zance ko koko ko tuwo, gatan nan dai ba suna ba fasali. Na tabbata ba zai iya ko tabawa ba balle ya sanya a bakinsa shi ne ya fita yaje ya sayo. A raina na ce, "Ashe dai girkin banza na da amfani tunda sai da shi ake rayuwa". Na kara duban dabgen da yayi nayi dariya na mayar na rufe na koma daki. Nayi zaton zan kuma jin duriyarshi kafin nayi barci, amma har garin Allah ya waye banji ba. Haka dana tashi yin sallar asubahi na fita falon ko zan ganshi sai abincina na daren jiya (chips and chicken) kadai na tarar akan (dining table) inda na ajiye shi ko matsar da shi ba'ayi ba. Daga nan nayi brush na koma daki, ban tashi ba sai karfe tara na safe. Da hanzari na nufi (kitchen) na soma aikin hada masa karin kumallo, amma na yau 'is special' kamar na daren jiya duk da raina ya sosu da rashin cin da bai yi ba. Cikin dan lokaci na kammala 'scottish egg, plantain with syrup, bread with jubnah' da ruwan na'a-na'a. Cikin dan lokaci kalilan na kwashe na jiya na shirya su a inda ya saba karyawa a kwanaki goma sha ukun da muka yi tare. Na koma daki nayi wanka nayi shiri cikin atamfa sufa ja mai ratsin kore da baki wanda dinkin ya zauna a jikina sosai, zanin ya bude daga kasa. Na fesa turare 'escada sentiment' na kalmasa dauri sassauka, na dubi kaina a mudubin dogon yaro na yi wani irin 'fresh' (looking takeaway) ko ni kaina na baiwa kaina sha'awa. Sai na samu kaina da tambayar kaina kwalliyar ta mece ce? Mene ne dalilinta? [1/4, 12:23 am] Takori: Dana gaza samarwa kaina wadannan amsoshin guda biyu, sai kawai na fita, ina juyowa muka hada ido yana kokarin fitowa daga nashi dakin janye da (travelling bag) mai matsakaicin girma 'troller' ruwan zuma. Dammm! Naji kirjina ya buga, bugawar da ba'a kirjin kadai ta tsaya ba ta hudo ne har cikin zuciyata. Sanye yake da riga fara anyi rubutu da shudin zare 'TOMMY HILFIGER' da shudin wandon (jeans) turrare, sumar nan ta kwanta tayi luf a saman kansa sai sheki take, inda duk ya motsa sassanyan kamshin '212' ke tashi.. Ya saya kwayar idanunshi cikin gilashi 'porsche' mai duhu ainun, don haka kai tsaye ba zan iya cewa ga halin da kwayar idanunshi ke ciki ba. Ya ajiye jakar a kusa dashi ya zauna a kujera sosai ya zage zip dinta, ya ciro katin ATM ya dago ido ya dubeni ina tsaye a inda nake ban ko motsa ba. "Ko zaki iya zama?" Abinda ya ce dani kenan. Tamkar wata rakuma da akala na bi umarnin furucin nasa, na zauna a kujerar dake fuskantarsa. ATM card din ya aje mani gabana, ya yagi takarda yayi rubutu itama ya turo mini. "Ga PIN dinsa nan na rubuta a jikin takardar na bankin UBA ne, in kina da bukatarsu sai ki kira Shu'aib a waya ki turashi ya debo miki adadin da kike bukata. Anjima Surajo zai kawo miki waya ni na tafi ban san kuma ranar da zan dawo ba. In kina da matsala ki kira Mama ki gaya mata, Ya'u zai ke kawo miki (recharge-card) duk sati, ban yarda da fita ko bakin (gate) ba in ba lalura ta rashin lafiya ba tunda rayuwar da kika zaba kenan". Ya mike yana zuge jakarsa. Idona ya cicciko da kwallah. Ba zan ce bai yi min dai-dai ba, kuma bazance yayi min dai-dai ba. Na san akwai hakkokin shi da yawa akaina, wadanda na sanya kafa na shure na take akan sanina, wadanda hujjojina babu ruwan Allah dasu. Auren Fa'iz dake kaina kadai ya sani dole in bude baki yau inyi magana saboda halin rai, yau yake da tabbatas gobe babu shi. Sannan sha'ani na tafiya wanda bana fatan hakan. Muryata na rawa na ce, "Ga abincinka fa ka karya mana sai ka tafi". Ya dubemu duka ni da abincin ya hararemu duk da ance aikin banza wai harara cikin duhu don kuwa bakin gilashi ne a idonsa, ya ce. "Ki rike kayanki, na gode. Akanshi dai kike yi min tsaki in na saki, to insha-Allahu ba zan sake cewa ki dafa min wani abu ba, sai kin ganni ma balle ince ki bani abincin. Zan tafi inda ba sai nace a bani za'a bani ba, balle aje ga goranta min ko yi min tsaki". "Kayi hakuri don Allah...". Na fadi cikin kuka. Ya dubeni cikin mamaki, nasan bai zata ba. Ni kuma harga Allah banyi hakan ko fadi hakan don wata manufa ba, sai don kar ya tafi da fushina in kasance cikin fushin Ubangiji da tsinuwar Mala'iku har yaje ya dawo, wanda ban san ranar dawowar tasa ba. Ya koma ya zauna, sannu a hankali yake zare gilashin idonshi, ni kuma ina ta sharbe. Ya kirani da wata irin kankanuwar murya. "Fa'izah!". Na cira jajayen idanuna na dube shi, ban amsa ba amma idanuna sun nuna ina sauraron sa ne. "Komi ya wuce?" Ya tambaya. Na sunkuyar da kai ina jan zaren carpet bance komai ba, amma na daina kukan sai ajiyar zuciya. Ya baro kujerar shi ya iso gabana yayi zaman dirshan, ya kamo hannuna na dama ya sarke cikin nashi. Na dago kai na dubeshi kana nayi sauri na maryar na sunkuyar. Ko da can bama iya hada ido da wadannan 'sexy' idanun balle yanzu? Da aka samu karin ilhamomi masu yawa a cikinsu? Ya sumbaci goshina, idanuna, karan hanci da bakin da yakan ce rashin mutuncin dake cikinshi ya fishi girma, mun dade cikin wannan halin, da dukkannin mu bamu taba tsintar kanmu cikinsa ba, zuciyoyi da ruhinmu sun hade sun cure wuri guda, muka samu kanmu cikin mantawa da duk abubuwan da suka faru cikin rayuwarmu. Dai dai lokacin da kararrawar shigowa falon ta soma kara. Mikewa nayi cikin sanyin jiki, don dama neman hanyar mikewar nake yi na rasa, saboda gangar jikina da zuciyata sun gaza karbar sababbin al’amura masu girma irin wadannan da Fa'iz ke bijirowa dasu a wannan lokacin, wadanda bazan ce ban sani ba ko ban san sune suke wanzuwa a cikin aure ba. Sai dai ban taba yi ba ko kusantar yi ba a kulliyar rayuwata, daga yarinta har zuwa girma, sai ko yanzu da Fa'iz ke son tabbatar min da cewa, lokacin yin nasu ya zo. Goyon bayana da hadin kaina kadai yake jira, domin tabbatuwarsu, 'and I lack such a courage!' (Na rasa wannan kwarin gwiwar). A ganina ‘it’s not the hightime. ..... (lokaci bai yi ba). Don haka wanda ya danna kararrawar nan in banyi masa addu'ar alheri ba hakika ya cancanci inyi masa fatan ALHERI. Na bude kofar ba tare da tambayar ko waye ba haka ba tare da waiwayar halin da Fa'iz ke ciki ba, Surajo ne. Nayi murmushi na bashi hanya ya wuce amma kallo daya zai yi min ya tabbatar a rikice nake, kuma hankalina a tashe yake domin na tabbata ya zo ne domin ya dauki Fa'iz ya kaishi filin jirgi. "Madam rikici, ke kika rike Pilot ko? Kina sane da cewa karfe goma sha daya zai tashi? Don Allah a ringa lura da lokacin aiki cikin lokutan ayyukan soyayyar kada a koro ko ku koma direban tashar da kuka saba". Fa'iz ya harare shi yana gyara zaman gilashin sa a kyawawan idanunsa, bisa doron karan hancin sa. Ya kwalawa Ya'u kira, ya shigo da sauri, ya dauki jakar suka fita. Surajo ya aje min kwalin waya (Samsung-tablet) ya janyo kofar falon. Na bisu da kallo cikin shatatowar hawaye dana kasa maida su ko rage gudun zubarsu akan kundukukina. Ko hawayen menene? Bazan iya cewa ba. ***** BAYAN TAFIYAR FA'IZ Wani ikon Allah ko abin mamaki tun tafiyar Fa'iz sai naji sam bana jin dadin gidan. Kewa da kadaici suka yi min sallama. Da yana nan, ko banyi masa magana ba shi zai mani, zanji motsin dan Adam cikin gidan ta hanyar karakainarsa, a falo da (kitchen) da nasa dakin. Amma yanzu gidan ya zame min kamar makabarta ko motsin kyankyaso babu. Kusan kullum ina baya wajen Dawisu ina jefa musu abinci, har kujera nake kafawa in zauna. Yanzu har sun saba dani har kofar falo suke biyoni in na haura lokacin da nake fitowa basu abinci. Sai suzo kofar falo su tsaya su bude bindinansu abin ban sha'awa suna juya su gabas da yamma, kudu da arewa cikin nuna baiwar kyan da Ubangiji Ya yi musu da bai yiwa wani tsuntsu a duniya ba. Yaran gidanmu duka an hana su zuwar mana dagani har Ummi. Haka 'yan uwa ba mai zuwa don kamar yadda na fada a baya sunce sai ranar da suka ganni da ciki irin na Ummi ko 'ya'ya irin na Zaneerah. (In fact) ina kewar Fa'iz duk da bana so na yardarwa zuciyata cewa kewar tasa nake yi. Duk da bamu dade tare ba, sati biyu kacal muka yi tare, abubuwan dake cikin sati biyun masu yawa ne (it seems like a journey of two year full of blissful adventures) da suka kasa goguwa a zuciya da kwakwalwata. Fadansa na bani dariya, haka kishinsa na babu gaira babu dalili. In ka debe wadannan na fahimci wasu abubuwa wadanda ada ban sani ba, wato Fa'izu Abubakar, mutum ne mai saukin kai, barkwanci, dadin mu'amala da dadin zama amma fa ga wanda yake so kadai, shi yasa iyaye da dangi duka kowa ke sonsa. Idan baya yi da kai ko ya tsaneka zaka dauka ne cewa babu wanda ya kaishi rashin kirki da rashin dadin mu'amala a duniya. Hakazalika yawan kiran sunana da yake yi cikin gidan Fa'izah-Fa'izah-Fa'izah kai kace shi ya rada min suna Fa'izah ko Aunty Fa'izah. (I also missed his regular sayings) "O.K?" Wannan ban san me take nufi ba har ya zamanto nima ta zauna min a baki ko magana na yiwa Ya'u na gama sai na ce "o.k?" A da kam nasan ba haka Fa'iz yake ba sam, magana ma wuya take masa balle mu'amala da mutane, ban san sanda bakinshi ya bude ba domin ada sai ya wuni baiyi magana ba. Ina kewar Fa'iz ne a bisa dalilai da yawa dani kaina ban san adadinsu ba, ko ba komai ina jin motsinsa cikin gidan da maganganunshi ko a waya ne nasan dai ba ni kadai bace cikin gidan. To amma ya tafi, ya bar min kangon gidan da abin da ke cikinsa, gidan yayi shiru, yayi tsit sam babu dadi kamar babu mahalukin dake rayuwa a cikinsa. Ina kwance tsakiyar kafet din falona na tada kai da filon kujera kwanaki uku da tafiyar Fa'iz, aka danna kararrawar son shigowa fallon. Daga nan inda nake kwance nake tambaya, "Waye?" "Ni ne Shu'aib". Na bude ina dariya, "Yaya Shu'aib kaida wa?" Shima dariyar yake yi, ya shigo na bashi hanya ya wuce ya zauna a kujera muka soma gaisawa. Sannan ya ce. "Yaya Fa'iz ya turo ni inzo in karbi ATM dinki in amso miki kudi a bankin UBA ko kina da bukatarsu, in kuma hada miki (tablet) dinki in sanya miki 'Interner data' in dora ki akan 'social networks' akwai 'group' na A.B family a (whatsapp) kowa yana ciki ki dinga hira da 'yan uwa madadin kiyi ta zama shiru". Ban yi musu ba na mike na dauko masa 'Samsung tablet' din na kawo mishi ko ni zanso hakan. Amma jaganar karbo kudin a UBA na ce. "Shu'aib bar kudin nan a muhallinsu, me zanyi dasu? Bana bukatar komi sai abinci gashi nan dankare nau'i-nau'i a 'store' da 'freezers, ga Ya'u na kawo katin waya. (I need nothing)". Ya gyada kai cikin gamsuwa, hannunshi da idanunshi akan tablet din yana ta shiga 'applications' muna ci gaba da hirar mutanen gida da na Giwa. Na mike na kawo masa lafiyayyen 'yoghurt' din 'L&Z Dairies' dake cike da (fridge) dina da sabon cup-cake din da nayi jiya. Na ce, "Shu'aib, ina Hajjaty?" Sai bayan da na fada ne kunyar kaina da nadama suka zo suka rufe ni, muryata ma a lokacin tayi kasa sosai. Dariya yayi, "Hajjah tana nan lafiya ko jiya na je Giwa sun tafi Umrah ita da Baba Na'ibi". Ya cigaba da shan L&Z Dairy yana lumshe ido saboda gardin madarar ya aje gorar, ya ce. "Wai kuwa don Allah Aunty Fa'iza yaya kike yi Yaya Fa'iz yayi miki magana?" Shu'aib kusan sa'a na ne domin bai fi shekaru biyu ya bani ba, tsakaninsa da Fa'iz kuwa shekaru bakwai ne , mukan tattauna matsalolinmu da junanmu tun sanda muka fara hankali. Nayi murmushi na ce, "Kamar Yaya Shu'aib?" Ya ce, "Yo mutum ba fara'a kullum fuska kamar bindinga, babu alamar rahama sai muzurai. Duk inda yara suke ya tashe su. Shi ne nake mamakin yadda zai zauna da iyali yayi mu'amala ta dadin rai dasu. Don na tabbata in ba mace mai tsantsar hakuri ba, babu wadda zata iya daukar ginshirar Yaya Fa'iz ...". Dariya nayi, "Baka da dama Shu'aib! Ni dai toh!! Ba zan ce baya magana ba, amma yafi yi a waya da abokansa!!!:. Na jawo wata hirar don hirar Fa'iz da yake sani ya na sanyani cikin wani hali, da ni kaina ban san shi ba. Ban san irin shi ba, mai wuyar fassarawa ne. Har la'asar muna tare da Shu'aib bayan ya hada min 'Whatsapp, wattpad, Facebook, Twitter da Instagram. Sannan ya zuba min duka numbobin 'yan uwa, muka yi sallama na juye duka 'cup cake' dinnan nace ya kaiwa Mama. A ranar na soma (chatting) dasu Ummi nima da (family group) dinmu ta watsapp. Sati biyu bayan nan Mama ta sake aiko Yahya ya kawo min wasu jarkoki cike da magani mai zaki wai Mama ta ce in sanya a (fridge) in maida su ruwa sha na (tsumi). Da zuma iri-iri 'yan asali da abubuwa dai daban-daban wani ta ce asha da nono,. wani da peak-milk. Zuciyata tayi ta raya min meye nufin Mama na bani wadannan magunguna? Amma da nayi tunani mai zurfi Mama dai uwata ce wadda ba aurena da Fa'iz ne ya hadamu ba. Mama uwata ce ta tun fil'azal ba zata bani abinda zai cutar dani ba, sai na dukufa shansu dare da rana yadda tayi 'prescribing' kowanne a rubuce a 'yar takarda har suka kare. Satin ya kare ta sake aiko da wasu, haka muka yi tayi har watanni biyu. Rannan a (chatting) nake tambayar Ummi ko tasan magungunan mene ne mama ke dirka min? Ta ce in fasalta mata su. Na fasalta har 'prescription' dinsu. Tayi alamar dariya ta hanyar turo 'emotions' na dariya ta ce. "Mama nayi mana gatan da Hajjah, Aunty Hawwa da MOmin ABU suke kunyar yi amna. Ke dai kiyi ta sha Fa'izah ba zai cuce ki ba. Nima nan haka take aiko min dasu jarka-jarka kulli-kulli. Kiyi godiya kawai ga Allah da yayi mana baiwar uwar mazaje tagari mai kaunarmu tsakani da Allah. Daga nan Mama ta koma aiko turaruku iri-iri 'yan Borno. Ni kam karba kawai nake ina faman turara daki. Amma sai Mama tayo waya ta ce. "Fa'izah! Turarukan dana aiko miki fa ba na turara daki bane, jikinki zaki ke turarawa, kullum da yamma bayan kin fito wanka. Akwai abin turaren wuta na lantarki (burner) cikin lokas din (kitchen) dinki ki dauka kiyi amfani da ita, nasan hankalin ki bai kai wurin ba". Na ce, "Akwai wata dana samu ne a falo da ita nake amfani, insha-Allah zanyi yadda kika ce. Mama Allah Ya kara girma". Murmushi tayi ta aje wayar. Tunda nayi nisa a sha da amfani da magungunan da Mama ke aikowa, sai na soma samun wani irin sauyi a jiki da zuciyata. Na nemi kiyayyar da nake yiwa Fa'iz na rasa tana (decreasing gradually) a kullum. Sai wani irin bege da son ganinsa. Da tsananin son kebewa dashi da son jin koda muryarsa ne amma babu. Tunda ya tafi ko sau daya bai kira ni ba har na soma zargin anya ba asiri Mama ke yi min ba, inso danta in kaunace shi? Nayi saurin kawar da wannan tunanin tare da yin istigfari a zuciyata. [1/4, 12:23 am] Takori: *** Na wayi gari ne yau cikin matsanancin nishadi, irin wanda ban taba tsintar kaina a ciki ba. Don haka na share ko'ina na goge lungu-lungu da sako-sako na gidan ya zama tas, sai sheki yake kamar lomarka zata fadi ka sanya baki ka side, duk da gidan ba wani datti yayi ba, don akai-akai nake kula da tsaftarsa. Na samu kaina da son shiga dakin Fa'iz, ko na rage kewar sa data addabe ni. A hankali na murda kofar na shiga dakin ga mamakina a bude ya barshi, sallama dauke a baki na. Fa'eez ya kawata dakin baccinshi da duk wani nau'in kayan jin dadin rayuwa. Duk da A/c a kashe yake, amma dakin da sanyinsa, wanda ya hadu ya cakude da sassanyan kamshin '212'n da Fa'eez ke amfani dashi (on a regular basis). Babu komi dake cikin dakin da aka saye shi cikin Kadunan, bayan gidan Fa'iz kadai abin kallo ne, wanda bai cika girma ba. Banda katifar ruwa data mamaye gadon shi, karamin 'frame' din dake aje dai-dai santar inda yake sanya kanshi guda biyu kanana su suka dauki hankali na. Sannu a hankali nake takawa zuwa garesu, yayin da kafata ke nitsewa cikin (center-carpet) mai tsananin taushi dake gaban gadonsa. Wanda ya sha bamban da sauran carpet din dake cikin gidan baki daya. A hankali na russuna na dauki 'frame' din. Wani dadadden hoto na ne mai rungume da (teddy bear) wanda da alama ya kaiwa gwanaye ne sun wanke shi sun adana a cikin 'frame' din ya zama kamar daukar jiya-jiya. A kusa dashi wani hoton nawa ne cikin (swiss-lace) da goggoro, wato ranar partyn 'Indoor-sport hall' na nan Kaduna. Na tsuke giran sama da ta kasa wanda hakan ba karamin kyau ya kara min ba tamkar anyi shi ne 'in-style' ba bacin rai ba. Na tambayi kaina wannan shi ne 'SO' kenan? Wanda ni bana jin shi? Don ko cikin wayata ba zan iya ajiye hoton Fa'iz ba balle a dakin barci na, inda nake ta da kai da mayarwa, a yayin kwanciya da tashi daga barci. To me ya hana inso Fa'eez? Babu! Illa shi SO din abu ne wanda ke yin kansa, ko ince yin Allah ne, ko kuma wani hali na mutum ko wasu (personal-attributes) kan zamo sila na samuwarsa, and Fa'iz 'lack any loving attribute to be loved upon'. Wato bashi da wani hali da za'a so shi don su, sai wani sashe na zuciyata ya ce dani. "A bisa rashin saninki kenan a da, banda yanzu, da kika fara lakantar ainihin waye FA'EEZ BAMALLI?" (And I came to the conclusion that) ba wani abu ne ya hana ni son Fa'iz ba illa tunanin baya... Inada RIKO, bani da mantuwa, sannan inada gudun wulakanci. Ina son momi na, Ina ganin muddin na sake da Fa'iz nan gaba zai koma min Fa'izun Hajja, wato Fa'izunsa na baya, zai sake sanya ni cikin 'problem' sannan zai sake tsanata... Na cigaba da kallon dakin tare da komi dake cikinsa ba tare da na bude kowacce ma'adanar kaya ba (locker). Ba don komi ba sai don nasha jin Hajjah na fadin, "Yiwa miji bincike ba ta'ada ce mai kyau ba, duk mai yiwa mijinta bincike wata rana sai ta binciko abinda zai daga mata hankali, ya hana ta bacci, ya sanyata bakin ciki wanda bata da maganinsa. Watarana sai ta binciko abinda ba alkhairi ba!". Duk da baya dakin amma kamshinsa 'permanent' ne. Turaren '212' tamkar shi kadai aka yiwa. Komi na Fa'iz kamshinsa ne a jiki hatta takardunsa, bedsheet da labulayen dakin nasa. Na kasa fita a dakin Fa'iz, sakamakon wani shauki (emotion) dake dibana, zan so ace a lokacin yana cikin dakin ne ko yana falo yana kwala min kira in kawo masa kaza da 'chips' dinsa. Shaukin dake dibana ne ya debe ni ya kwantar a gadon Fa'iz, ya janyo tattausan bargonsa ya lullube ni dashi. Da filon shi na tada kai na lumshe ido ina cigaba da shakar daddadan kamshin na '212' (men). Na soma zargin kaina da son Fa'iz a karo na farko. Wadannan (emotions) din (are for real!) YAA SATTAR!!! Ya Sattaru, idan mafarki nake ina rokon ka da ka farkar dani. Na bude dukkan idanuna dake lumshe, da karfi nayi wurgi da filon na zauna dabas a tsakiyar gadon ina wurga ido kamar mara gaskiya. Eh, mara gaskiya ce (in fact!) Domin son karyata 'emotions' din nawa nake da gangan suna fin karfina. Na sakko daga gadon cikin barin-jiki, amma ga mamakina na kasa fita a dakin Fa'iz! Ina son dakin!! Ina son nayi bacci a dakin ko na samu nutsuwa. Na koma na kwanta cikin mutuwar jiki da zuciya, naja bargo na rufe har kaina. Bacci mai karfi ya fisgeni. Tafiya nake cikin wani kungurmin daji, ba gida gaba ba gida baya, na bullo ta gabas aguje nake a dalilin wutar dake bina, wuta bala-bala wadda ke tafe ta hanyar cin busassun kirare na jejin. Ina gudu ina kiran sunan Allah amma wutar nan bata bar bina ba. Gudu nake kamar raina zai fita har na sare, karfina ya kare. Ina gab da faduwa a yayin da muka iso gab da wani tafkeken kogi, na daga kafata da niyyar in fada ruwan kawai ya cinyeni in huta, ya fiye min cinyewar wutar. Sai ji nayi wani sassanyan hannu ya rungume ni. Wannan hannun ya ce. "QUL YAA NARU KUNI BARDHAN WA SALAMUN ALA IBRAHEEM... (Yaa ke wuta ki zamo mai sanyi da aminci ga Ibrahim)". "Na yafewa Fa'izah dukkan abinda tayi min wanda na sani da wanda ban sani ba, wanda tayi akan sani da wanda tayi bisa kuskure, daga ranar da aka daura mana aure... har zuwa ranar da zan daina numfashi...!". Kamin in dago inga wane ne? Wutar nan tabi ruwan. Bata ba dalilinta. Haske ya mamaye duhun dake mamaye dani. Na dago a hankali a lokacin zuciyata tayi fari kal! Babu sauran wani kunci ko wani kullaci a cikinta. Na dubi wanda nake rike a kirjin nasa, wani kirji ma'abocin tarin ni'ima da sanyi da sanya salama, ba wani bane FA'IZ ne, FA'IZ MUKHTAR ABUBAKAR BAMALLI GIWA. Idona ya bude 'vivid' na tabbatar mafarki ne nake yi. In banda gumi ba abinda nake shirbinawa. Illahirin jikina duka rawa yake, na rasa abinda ke min dadi. Na kifa fuskata cikin tafukana na soma kuka. Wannan mafarki shi ake kira kukan kurciyaa...! Wani irin sarawa kaina ya shiga yi saboda kuka. A hankali na mike na nufi kofa don fita daga dakin ko na samu sa'ida cikin zuciyata. Sai nayi tuntube da wani abu kamar littafi gab da bakin kofar dakin. Na russuna na dauka, littafi ne na ajiye tarihi da mihimman bayanai (Diary) da alama garin fita ya yarda shi ba tare da ya sani ba. Anan bakin kofar nayi zaman dirshan ina buda shafukan littafin. Rubutu yayi na abinda ya kunshi tun daga ranakun kuruciyarsa, da tafiyarshi kasar Russia. 'Tittle' din rubutun shi ne; "ONLY ALLAH KNOWS WHAT FUTURE HAS IN STORE FOR US". A wani shafi Fa'iz yayi wani rubutu wanda da alama tun tali-talin kuruciyarsa yayi rubutun domin kwanan wata na kalanda wanda aka buga littafin cikinsa ya nuna hakan. Rubutun yayi matukar bani dariya. "MEYE DALILIN DA YASA NA TSANI FA'IZA? BAN SANI BA! ILLA SAI DON CEWA ITA DIN KYAKKYAWA CE, TA FINI KYAU, A LOKACIN DA NAFI DUK ZURI'AR A.B KYAU SAI TAZO TA DAMENI TA SHANYE, KOWA YA KARKATAR DA KAUNAR DA YAKE YI MIN GARETA; MAIMAKON FA'IZ KOWA SAI FA'IZAH!". Murmushi nayi na cigaba da buda shafukan. Wannan rubutun na shafi na gaba ga abinda ya rubuta. "A Giwa ne. Misalin karfe goma na safe. Ina zaune falon Hajjah ina kallon fadan Isra'el a CNN. Wayar falon Hajjah dake ruri a gefena ban dauka ba sakamakon tunanin da yayi min rubdugu a wannan dan tsukin. Wanda bai wuce SON FA'IZAH ba! Fitowarta da daukar wayarta cikin kumfa ya sanyani kai dubana gareta. Duk da kasancewarta yarinya karama a wannan lokacin, 'yar shekaru goma sha hudu amman ta mallaki suffa kyakkyawa irin suffar da nake so ga 'ya macen da nake burin mallaka matsayin matar aurena. Tun daga wannan lokacin son Fa'izah ya ci gaba da ruruwa a zuciyata kamar gobarar daji. Nayi kuka nayi nadamar da bata da amfani, musamman da na fahimci kakkarfar soyayyar dake tsakaninta da Yaya Aliyu. Tsananin kishin Aliyu da nake, ya sanya ni hantarar Fa'izah a kullum a duk lokacin da yake zaune. A wauta ta a wancan lokacin Aliyu yaga bakin Fa'izah ya janye daga gareta, ya daina sonta amma ya ki. Asali ma sai kareta yake, yana bin bayanta cikin kowanne hali. Akwai ranar da suka amso takardun jarrabawar firamare, don Aliyu yaji haushi kawai nace takardun Fa'izah basu yi kyau ba, komi 'fail' 'poor'! To Aliyu yaji haushin, amma ba irin wanda nake so ya ji ba. A ranar ne yaga "love colour" na matsananciyar soyayyar Fa'izah cikin kwayar idanuna. Hankalin Aliyu ya tashi kwarai domin yana gudun abinda duk zai kawo mishi matsala a soyayyar shi da Fa'izah. Musamman ni dana kasance dan gatan Hajjah, wanda dana furta sai aikatawa. Aliyu ya dubeni cike da masifa, cikin harshen Turanci ya ce. "Ina gargadinka Fa'iz! 'Don't dare say it'... wato kada ka taba furtawa sai kayi nadama anan gaba". *************************⬇********************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** Na yiwa Aliyu kallon ko ni ko kai har su Fa'izan suka zargi wani abu. A ranar munyi musayarta ba dadi nida Aliyu da muka fito waje, har saida maganar ta hada da manya. Inda naji dadi shi ne inda Baba Barau ya ce babu wanda zai kuma yin auren soyayya cikin A.B tun daga kan Baban ABU wanda shima yayi ne ba bisa sanin mahaifinshi marigayi Abubakar Giwa ba. Ya kara da cewa. "Fa'izah ta mai rabo ce. Don haka kada wanda ya sake ya furta mata yana sonta cikin mu duka". Akwai ranar da na sanya Fa'izah cikin bacin ran da ya rudata har ta rungume Yaya Aliyu. A ranar ni kadai nasan abinda naji. 'In fact' kishi ne matsananci . Abinda tayi min bai bani haushi ba illa haushin Aliyu. A ranar ne nasan na fara kuka 'for sake of Fa'izah's love' (saboda son Fa'izah). Fa'izah in tana kuka sha'awa take bani, in tana tsiwarta burgeni take, (I drive pleasure in making her cry). In tana kuka kyau take mini, sha’awa take bani. Shi yasa na kasance kullum cikin kirkirar abinda nasan zai sata kuka. Bakin cikin tafiya ta Russia? Ba na komai bane ba don komi ba illa tsoron kada Aliyu ya aure Fa'izah kafin na dawo. Na karyata kaina a wurin Hajjah da su Baban ABU, Baban Kaduna da Baba Na'ibi ranar da suka kawo min ziyara ta farko kasar Russia, na gaya musu cewa dukkan abinda nake cewa Fa'izah tayi, don inga hawayenta ne wadanda ke sanya ni nishadi, su kuma sanyani MURMUSHI. Komai na Fa'izah ina son shi, sannan 'is special' agareni. Duk abinda nayi mata nayi ne domin KAUNARTA da 'pretending' kaunar, 'as I have no option' banda yin hakan. Na farko ban isa in furta ba, na biyu kishin yadda Aliyu ya kankane komai nata, na uku ita kanta Fa'izar ta dauke ni makiyinta ne na a buga a jarida, ba abinda zanyi ya goge hakan daga zuciyarta. A zahiri, na soma son Fa'izah ne daga ranar data dawo Giwa. Ta cinye min naman miya. Babu abinda na tsana irin inga Baban ABU na dukan Fa'izah. A duk lokacin da naga hakan kukan zuci nake da azabta a zuci da gangar jiki. In shige daki inyi ta kuka. Akwai ranar da Aliyu ya kamani ina kukan ni kadai a daki bayan na yiwa Fa'izah sharrin da ya sanya Baban yi mata dukan kawo wuka, ya tuhume ni amma sai na ce masa bani da lafiya ne. Ranar da naji Hajjah ta ce mu tafi da su Ummi Kaduna (party) babu tunanin hanyar da zan bi in soke zuwanta da banyi ba amma na rasa. Cikin ikon Allah ta nemi da inzo rabon fada, anan ne na samu hanya ba don komai ba sai don KISHIN KADA WANI YA SO TA CIKIN A.B saboda yadda tayi kyau. Duk da kasancewar ta yarinya karama a wancan lokacin, tafi duk 'yan matan A.B iya tsara kwalliya, tafi su kyau mai daukar hankali. Sau da yawa nakan ji samarin cikinmu na fadin DAMA A BASU FA'IZAH! Na kan ji kishi kamar in kashe su, amma sai inga bari kawai in batata a wurinsu ta yadda zata yi bakin jini, koda an basun suce 'a’ah, inyaso ni sai ince a bani in karba da hakuri, don haka nayi furucin tana bin Yaya Aliyu B-Q, ko ince bata da kunya bata da kokari, kazama ce, kuma masifaffiya. Sai kuma tazo tana kazantar kowa ya gani hakan ya nuna ba kage nayi mata ba. Nayi wauta da tazo ta zame min bala'i, ko ince alhaki ya zame min dan kwikwiyo. Wautar da ta jawo Fa'izah ta tsane ni fiye da kowa a duniya har take addu'ar ALLAH YA KASHE FA'EEZ BAMALLI IN HUTA! Ni kuma Ya jarrabce ni da matsananin SO irin wanda ban ta ko gani ko cikin hikaya da labarun almara ba. A zahiri na nunawa Fa'izah kiyayya domin SONTA da yayi min katutu, bani kuma da yadda zanyi dashi. Duk kiyayyar da na nunawa Fa'izah KISHI NE da PRETENDING. Amma da hankali ya zo min, na gane na kuma fahimci wannan ba hanya ce da ake nuna KISHI ba, ga wanda aka yimawa KIYAYYA NE. Bayan ni a wauta ta nayi ne don samarin A.B su ki Fa'izah baki dayansu. Da sun kammala sakandire ni in aureta, tunda ta rasa mai so. Na manta da cewa ma babu batun nagani ina so a cikin A.B, a ganina koda an basun dai suce basa so. Tunda babu wanda zai so mace mai wadannan halaye da na kaga mata, har shi Aliyun, don dai yana da wata irin zuciya ne data sha bamban da ta sauran 'yan Adam. Ashe ni ban san wannan na nufin gina kiyayyata mara iyaka a zuciyar wadda na yiwa KIYAYYA DON SO. Ban tashi jin son Fa'izah na neman hallaka ni ba sai da nayi nisa da ita. Na kasa karatu na kasa ci, na kasa sha, barci ya kaurace min fau-fau. Da hoton ta na 'teddy bear' nake kwana nake tashi. Nayi kuka domin son Fa'izah, abinda ban taba yi akan mace ba: Nayi abinda ban taba yi ba a rayuwata domin SON FA'IZAH, wato "NADAMA". A shekarun karatuna, baki daya, kowanne sakan, kowanne minti, kowanne dakika da kowanne awa son Fa’izah da kaunarta ke kara habaka a tare dani. Ba komai ya hana ni yiwa Fa'izah aike tamkar su Ummi ba illa TUNA BAYA... Yadda Fa'izah ta tsane ni, yadda ta ki jinina, na tabbata ba zata amshi abin hannu na ba ko za'a kasheta. Tsammani ma zata yi wata cutar na kunso zanyi mata. To amma nayi mata aike da abu mai daraja a gareni, nake kwana nake stashi tare da shi. Nayi mata aike da HANKICI na, wanda ke nufin sakon kaunata zuwa gareta, domin na sanya anyi rubutu da harshen Larabci a jiki, an rubuta 'AHUBBIK' wato ina sonki da dukkan zuciyata! Daga ranar da aka daura aurenmu da Fa'izah na tabbatar Fa'izah alkhairi ce a gareni, kuma wani bangare ce ta cigaban rayuwata. Daga ranar na soma ganin budi takowanne bangare, aikina, nasara da cigaba cikin duk abinda na sanya hannu, mutunci da martabata a idanun iyayena suka karu. A dalilin aurena da Fa'izah ne mahaifiyata ta dawo da soyayyar ta gareni wadda ada ta haramta mini saboda na ki karatu kuma na takurawa Fa'izarta. Ta kuma fifitani a tsakanin sauran 'yan uwana. Kiyayyar da Fa'izah ke nuna mini tana kara min kaunarta ne a koda yaushe, tana nuna min ta san ciwon kanta, tasan mutuncin mahaifiyarta, tasan makiyinta, ta san masoyinta (in comparison to yaya Aliyu!). Tana hangen abinda ka je ya zo, tana hangowa kanta dacewa da rayuwa da wanda soyayya ce ta hadasu ba kamar ni data rika a matsayin makiyi ba, tunda (that's the way I proved myself to her). Kuma masu iya mmagana sunce "Makiyinka baya taba dawowa ya zama masoyinka". Wannan ne dalilin da yasa nake yi mata 'UZURI'. A hakikanin gaskiya ba kin Fa'izah nake ba, WAUTA ce ta KURUCIYA domin in samu ABINDA NAKE SO, wato ita FA'IZAH. Idan kowa yace baya so. Ni kaina nasan mutum ne miskili da akan rasa gane inda yasa gaba, mutane irina ba sa karantuwa (from every perspective). Ubangijin da Ya halicci zuciya Shi Ya sirrantata, Ya sanya ta zamo HIJABI a tsakanin 'yan Adam da abinda ke zuciyar su. Don su sirrinta al'amuran da Ya boye cikin zukatansu. Ina kaunar Fa'izah da dukkan ruhi, zuciya da bargon jikina 'but I cant express, neither explain. Bakin da ya furta sharri, zalunci da rashin kirki, ya dawo yana furta SO (will never be trusted) don haka Allah Yayi zamu cigaba da rayuwa ni da Fa'izah. Burina ya cika tunda ta zamo mata agareni kuma wani babban JIGO na rayuwata, kuma wani BANGARE na jin dadin rayuwata tunda mallaki na ce ko da har abada ba zata yarda da ni ba. Zaman mu tare a hakan ya fiye min zaman kuncin da na dandana a Ukrain ina azabtuwa daga soyayyarta. THE ISSUE OF MOMIN ABU Sha'ani na da Momin ABU kamar yadda Fa'izah bata fahimce shi ba ko ince bata sani ba. Babu kuma wanda ya taba tararta ya gaya mata, Momin ABU bata daga cikin Zuri'ar Abubakar Bamalli. Kamar yadda ya faru tun muna kanana, an tura Baban ABU bautar kasa Jihar Taraba, kamar yadda Baban Kaduna yake bamu labari, yana (service) din ne a gidan marayu na Jihar Taraba (Taraba State Orphanage Home). Maimunatu marainiya ce, da ta tashi ba uwa ba uba, ba dangi a gidan marayu. Kamar yadda Baban ABU ya baiwa su Baban Kaduna labari, ni kuma a lokacin bani da wayo da nayi wayo ne naji labarin a bakin Hajjah. An tura Ahmadu A.B bautar kasa Jihar Taraba, acan yaga Maimunatu, inda yake (serving) wato Taraba State Orphanage Home. Tana daga cikin 'yan mata goma a gidan marayun da suka kai minzalin aure, sannan mafi nutsuwa da kamalar cikinsu. Ya je ne a matsayin malamin (secondary school) dinsu, yana koyar dasu kimiyyar noma, wato (Agricultural Science). Maimunatu hazikar yarinya ce wadda Allah Ya yiwa baiwar kwakwalwar fahimtar karatu. Kamar yadda yake a cikin (psychological nature) na kowanne malamin makaranta. Wato kaunar hazikin dalibi da girmama shi hakan ce ta faru tsakanin Baban ABU da Momin ABU har kuma ya rikide zuwa soyayya mai tsafta da inganci. Wadda tausayi da kauna, shi ne tubali da ginshikinta. Kamar yadda Hajjah ke bamu labari, ta ko'ina Ahmadu A.B ya hanga ya tauna baiga ta inda marigayi mahaifinsa A.B zai amince masa auren Maimuna ba. Bar ta auren zumuncin gidansu da suka maida shi farillah, kuma shika-shikan rayuwarsu, rashin ASALI wani babban abu ne domin kashi tamanin cikin dari na yaran dake gidan marayu har abada ba'a sanin asalinsu ko ganin wani nasu. A haka suke zuwa duniya su koma, cikin kiyayewar Ubangiji. Wannan yasa Ahmadu A.B cikin tsaka mai wuya da tunanin abin yi. Na farko ba zai iya barin Maimunatu ba, maganar ma ace ya hakura da ita bata taso ba, domin ba karamin sonta yake ba, kuma shakuwar dake tsakanin su ta wuce tunanin kowa. Sai ya yi tunanin wadda yake ganin zata fisshe shi saboda KURUCIYA irin wadda ta faru dani akan Fa'izah! Ahmadu yaje kotun Musulunci an daura musu aure da Maimuna ta yin amfani da malaman shi na Jami'ar Ahmad Bello. Ya dauko Maimunatu ta kawowa Hajjah, a lokacin da cikin Fa'izah wata bakwai. Mafari kenan dana tashi cikin nunawa Momin Fa'izah wariya da kabilanci a tsakanin su Mama, Aunty Hauwa da tsararrakinta. Shi din ma na fatar baki ne, ko kallon banza ban taba yi mata ba, sannan a bayan idonta musamman idan Fa'izah ta bani haushi. Hali ne na zuri'armu baki daya (kabilanci) da 'ethnocentrism' duk wanda ba daga zuri'ar A.B ya fito ba, to fa ba cikakken mutum bane. Da Hajjah da marigayi suka ji kowacece Maimunatu hankalinsu ya tashi kwarai, sunyi fushi da Baban ABU fushi mai tsanani, sannan 'punishment' dinsa shi ne 'suspension' daga duk wani abu da ya shafi zuri'ar A.B zuwa wani lokaci da basu kayyade ba. Duk Ahmadu ya ce yaji ya gani, indai zasu barshi ya cigaba da rayuwa da ita. A lokacin hatta zuwa daurin auren cikin gida an dakatar dashi, haka itama, zuwa wani sha'ani na mata kamar biki ko suna duk ba’a bukatar su. Zance ko da Baban ABU ya damu to kadan ne tunda gogaggen dan boko ne wadanda (time matters a lot for them) wato lokaci abu ne mai matukar muhimmanci a garesu. Sai ya yi amfani da lokacin 'suspension' din nasu ya koma makaranta ya nemi (degree) na biyu. Ita kuma ya sanyaata a (school of Nursing and Midwifery). Ba da bata lokaci ba yana kammalawa A.B.U suka dauke shi 'lecturing' ya kuma samu gida a cikin makaranta, domin ada a gidan haya suke domin gidansa na A.B Quaters an hana shi mukullin an rufe. A lokacin tuni an haifi fa’izah har tayi wayo. Kafin A.B ya rasu ya yafewa dansa Ahmadu, ya kuma karbi Maimunatu a matsayin surukar kaddara, bayan haihuwar danta na biyu, wato Abdallah, saboda kyawawan halayenta da zuri'a da tazo musu da ita mai albarka mai kama da nasu 'ya'yan. Domin Abdallah sak mahaifinsa, Fa'izah kuma Aunty Rabi ta debo, sai dai ta dauko duhun Maimunatu. Dama kuma abinda basa so kenan na auren bare, domin zai haifar da sauyin kamanni a cikinsu. Amma tabbas da Maimunatu na da iyaye, da sun maida ta ga iyayenta ko Ahmadu zai mutu, sun karbeta ne saboda MARAICIN ta. Nayi nadama, nadama mai yawa akan duk abinda na yiwa Fa'izah! Nadamar da bani da tabbacin akwai ranar da Fa'izah zata karbeta, tunda ba zata taba tsayawa ta saurari kalaman bakina ba. Fatana Allah Ya bani iko da damar nunawa Fa'izah kuskurena da karbarsa kafin na kwanta dama... Ya yaye min wannan ginshiran, domin ni kaina yana wahalar dani...". Da na kawo nan kuka na rikice da shi sosai, na kasa ci gaba da karatun, na ya da littafin. A guje nayi daki na ina kuka wiwi, na fada tsakiyar gadona na ci gaba da rasgar kuka. Nayi kuka-nayi kuka har naji babu dadi. Wannan shaukin ke kara mamayar zuciyata yana kara habaka. Wanda da nayi tsai da zuciyata na fahimci abinda bana so in fahimta da gangan. Wato SON FA'IZ ne yake mamayata cikin kowanne dakika na bayan da ya barni. Wani irin so mai cin rai, da tafarfasa zuciya. *** [1/4, 12:24 am] Takori: *** Washegari haka na tashi sukukui! Babu kuzari ko yaya a cikin jikina. A wannan lokacin, babu abinda nake tunani illa hanyar da zan bi na gyara girgidadden aurena tun lokaci bai kure min ba. Kaunar Fa'iz da soyayyar sa ke lallasa ni ta duk hanyar da suka ga dama. A duk lokacin da na daga ido na dubi tangamemen hotonmu (window size) da aka manna a (main-palour) kamar za muyi magana, sannan tsananin kamar mu da juna ta fito sosai a hotunan. Kyau ne ke bugun kyau na mallawan usili, sai kwarjini da ya dara mini da wasu ilhamomi na daban da aka halicci Fa'izun dasu da ban taba ganinsu a tare da wani da namiji ba. Nakan tuno abubuwa da dama na irin cin kashi da rashin arzikin da na shekara yiwa iyayena da 'yan uwana akan auren mutumin da na tabbatar ban dace da kowa ba cikin duniyar nan face shi, sai inji na tsani kaina da mata masu irin halina na kafiya da taurin zuciya, riko da zuciyar rashin afuwa da yafiya, bayan dukkaninmu da Allah ba Ya hakuri damu, Yana afuwa a garemu albarkacin mai albarka, da bamu kawo yanzu ba. Hakika da Allah Baya afuwa ga al'ummar Annabi Muhammadu (S.A.W) da tuni an shafemu a doron kasa kamar yadda aka shafe al'ummar sauran Annabawa da suka gabacemu saboda kura-kuran da muke tafkawa Ubangijinmu da tsakanin mu kanmu 'yan Adam. Misalin karfe uku na yamma na dauki waya na bugawa Momi, jikina a matukar sanyaye, kamar yadda zuciyata ta mace, babu karsashi ko kankani a tare dani. Jin muryar Momi tana yi min sallama wani matsanancin tausayinta yazo ya lullubeni. Kenan ita bata da kowa a duniya da zata kalla ta ce nata ne, bayan mijinta. Baiwar Allah koda wasa bata taba gaya min ba don kar hankalina ya tashi. Ni Allah Ya bani dangin kamar ruwa masu kaunata da son yiwa rayuwata gata amma nake wulakanta su ina bata musu rai akan abinda sunyi ne amma sai nafi kowa cin ribar sa. Wato zaba min miji daya da daya a cikin 'ya'yansu wanda sun tabbata ko bayan ransu zai rikeni amana kamar rikon da uwa da ubana za suyi min. Momi taji nayi shiru, bayan ta jima da amsa wayar, ta ce. "Lafiya?" Na ce, "Lafiya". "Kin kirani kuma kinyi min shiru". Na sharce hawaye da suka yo wani irin ambaliya akan kuncina, sai naji ba zan iya tambayarta komi akan rayuwarta ba, kada in tado mata abinda ta riga ta manta dashi, tana cikin rayuwarta mai tsafta. 'And a total submission to ALLAH' da yadda Ya kaddara mata rayuwar. Na kasa 'controlling' kaina da tausayin Momi, kawai sai na fashe da kuka gaba daya. Kuka kawai nake ta rusa mata a wayar har na gaji don kaina bata katse ba, kamar yadda bata nemi taji dalilinsa ba, balle ta lallashe ni akansa. Sai da nayi mai isata sannan naji muryarta cikin sanyi tana magana. "Na rasa ke wace irin yarinya ce, na rasa a cikin mutane ke wacce iri ce, na rasa abinda yake damunki, ba mamaki gata ne yayi miki yawa. Menene aibun Fa'izu? Me kika fishi? Dame kike takama nayin butulci da irin wannan miji da Allah Ya baki? Har sai yaushe zaki shiga hankalin ki kisanAnnabi Ya faku? Duk sa'o'inki da tsararrakin ki kowanne na dakinshi cikin kwanciyar hankali, ga albarkar aure, sai ke don dai ki tabbatarwa da danginku da cewa uwarki bare ce abinda suke gudu a bare dai-dai ne. To ni dai wannan hali naki ba a wurina kika gado ba (kafiya da taurin kai na rashin tunani) ke kadai kika san inda kika kwaso abinki. Yanzu da kika ki kwantar da kai kibi Fa'izu ribar me kika ci? Meye ribar zaman da kike yi? Ke ba ga ladar aure ba, ke ba kwanciyar hankali ba, ke ba ga komawa karatun ba, ba wan ba kanin wai karatun dan kama... Saboda ke shashasha ce kuma dabba, wadda bata san ciwon kanta ba ko?" Hawaye ya ci gaba da wanke min fuska, ita bata san cewa tausayinta da nake ji ya rinjayi tasirin fadan da take yi min. Muryata cikin sanyi da shasshekar kuka mai yawa, na ce. "Don Allah Momi kiyi hakuri, ni yanzu babu abinda yake damuna. Hakuri zan baiwa Fa'iz din ma in ya dawo. Insha Allahu nayi alkawarin daga yau ba zaku sake jin wani abin assha daga gareni ba. Shima Baba zanzo in bashi hakuri. Walida nake so ki taimaka min tunda sauran sati biyu su koma wannan hutu, ba wanda ke zuwa min daga Giwa har Jabi Road, ni kadai cikin wannan katon gidan... Don Allah Momi...". Na rushe da kuka sosai wanda ya tayar da hankalin Momi, maimakon kalamaina su sanyaya mata domin kukan nawa mai zafi ne irin na kauna da tausayin DA ga MAHAIFIYARSA, yafi karfin ace akan fadan da tayi min nake yinsa. Wani irin kuka ne mai fitowa tun daga karkashin zuciya na wani abu mai nauyi da ya taba rayuwar mahaifanka. "Don Allah don Annabi Momi kiyi hakuri, ba zan kara ba... ba zan sake ba... Na tuba na bi Allah na bi ku... Zan bi Fa'iz sau da kafa kamar yadda kike bin Baba, ba zan sake tada muku hankali ba... Ni kaina na gaji, na gaji da wahalar da kaina, ina son mijina yanzu. INA SON SHI Momi...". Banga Momi ba, amma nasan murmushi tayi, (a very deep smile) kasancewarta mai yin murmushi mai fidda sauti. Ta jima bata yi magana ba, daga baya kuma ta yin. "Ki yiwa Abubakar waya, ki nuna nadamarki gareshi. Wannan zai sa shi watakila dawowa nan kurkusa. Amma in ba haka ba, mawuyaci ne yasan hakan, har ya yi marmarin dawowa gareki. Babu kunya tsakanin mace da mijinta, akwai inda ya dace aji kunyar, amma ba a irin nan ba, musamman idan baya ganin ki". Na ce, "Ba zan iya ba Momi, wallahi bazan iya ba, ina jin kunya, ina jin nauyinshi sosai domin sai a yanzu na fahimci abubuwa da yawa wadanda ada ban fahimta ba. Tsiyar dana tsula tana da yawa, tijarata gareshi mai yawa ce, da kyar in zai yarda ya kara hada rayuwa dani...". Na ci gaba da kuka mai tada tsigar jikin mai kaunar ka, musamman UWA! A sanyaye Momi ta ce, "Ai sai kiyi tayi, tunda kinga shi zai fisshe ki. Ki tsaya jin kunya ya dawo da matar dake son shi, ina ce shi kenan ko? 'It's not too late for you to correct your misdeed' ba'a tsufa da tuba muddin ana raye. Mutuwa ce kadai shinge ga tuba da nadamar bawa. 'Atleast ya san kinyi, koda ba zai karba ba... Walida da Kausar duka na nan zuwa". Jikina duka ya saki a yayin da Momi ta kashe wayar. Na kifa kaina cikin kujera na rasa me yake min dadi. A yinin ranar baki daya, na kare shi ne cikin tunanin ceto kima ta a idon Fa'iz da sauran son, in akwai. Yamma lis misalin karfe shidda na yamma, direban Bababn ABU ya sauke Walida da Kausar a harabar gidan. Walida tayi sallama ta aje (trolly) dinsu, ta dube ni duk nayi firgai-firgai dani, tun safe banyi wanka ba ga yunwa, tun kofin ruwan lipton dana zuba ma cikina da safe. Da yake yarinya ce mai hankali bata yi magana ba, gaisheni kawai tayi ta aje mayafinta ta shige (kitchen) ita kuwa Kausar wai wanka zata yi. Uffan na kasa ce masu, ashe Walida girki take yi, sai bala'i kamshi mai tada tsohuwar yunwa naji yana bugun hanci na kafin ince wannan ta aje min (tray) a gabana, (fried-rice) da taji kayan lambu tayi sharr da farfesun koda na tiriri da tashin kamshi. Nayi ajiyar zuciya na dubeta cike da kauna a raina, na ce. "Dan uwa rabin jiki". Na sa cokali na soma ci hannu baka hannu kwarya. Rabona da su tun ranar da Fa'iz ya kore su. Kausar ta fito ta dau wanka ta dau gayu da tirare dai-dai sanda na kammala cin abincin. Ta samu kujera ta hakimce ta kunna t.v tashar 'Bollywood' na galla mata harara na ce. "Inda Walida ta fiki kenan, hankali da sanin ya kamata. Wawuya kawai, kashe talbijin din nan bana son hayaniya". Kausar ta zumburo baki, "Ni fa hutawa nazo yi ba aikatau ba. Tun ranar da maigidan ya koremu ban kara marmarin zuwa gidanku ba. Yanzun ma ba don Momi ce ta takura min ba da banzo ba". Na kama baki na ce, "To yi mana rashin kunya ke da aka turo ki taimakeni mu sada zumunci. Tashi maza-maza ki wanke (plates) din da aka yi amfani dasu da tukwanen, kiyi 'mopping' (kitchen) din ko mu raba gari yanzu-yanzun nan har bakin 'gate' a jiyo mu". Ta mike tana kumburi kamar zata fashe tayi (kitchen) din Walida na yi mata dariya. Na ce, "Lallai Momi tana fama da wannan yarinyar, Allah Yan shiryeta". Walida ta ce, "Ai in tana yi Momi cewa take gadon Fa'izah". Nayi murmushi sosai cikin raina na ce, "Fa'izar da". Da daddare muna kwance a gado daya, Walida Kausar nata barci abinsu cikin kwanciyar hankali amma ni sai juye-juye nake daga wannan gefen zuwa wancan. Na kasa barcin magan-ganun da muka yi da Momi ke cina ta ko’ina, suna babbaka ni. A karo na farko nayi tunanin jarraba shawarar Momi na. To amma in kira Fa'iz ince masa me? Ince Fa'izu Abubakar, yanzu ina son ka? Da wane baki? Da wane harshe? Da wacce siga? Na ciza na hura na kasa samo sigar. Ina cikin rukunin mutanen da basa iya fadin abinda ke zuciyarsu a fatar baki, sannan ni mutum ce mai tsananin kunya da kama kaina. Wata zuciyar ta ce, "Fa'izu ba matsayin miji kadai yake takawa a gareki ba. Dan uwa ne na jini. Ba lallai sai kince sonshi kike ba, 'actions show feelings atimes...". Da wannan shawarar da wannan tunanin na kira Ummi, cikin barci mai nauyi ta daga bayan wayar ta sha (ringing) ta gode Allah. Har bana jin abinda take fadi sosai sai da na harhada na gane cewa take. "Waye?" Ajiyar zuciya na saki mai nauyi, tattare da jin nauyi, na ce. "Ni ce, kiyi hakuri 'for' damun barcinki. Lambarshi nake so ki bani". "Shi wa?" Ta katseni cikin kaguwa. Sai na kasa bata amsa, don naga alamun rainin hankali cikin tambayartata. To lambar wa zance ta bani ba ta mijina ba? Ko zance ta bani lambar wani kato ne bayan mijin da Allah Ya halatta mini? Sai na kasa ce mata komai. A fusace ta ce, "Wai lambar wa zan baki? Yaya Bashir yana kirana". Na tattara sauran karfin halina da guntun kashi na a katara na ce. "Yaya Fa'iz". Sai cewa tayi, "Wanne?" Cikin iya shege. Kamar na fashe da kuka na dai daure na ce. "Na Hajjah". Dariya Ummi ta saki mai ban haushi da bakanta zuciyar wanda aka mawa. Sai da tayi ta harda hawaye duk da bana ganinta ina jinta tana share shi, sai da ta mula cikin ginshira irin ta su ta 'ya'yan A.B sannan ta ce. "Gashi kuma ya gargademu baki dayanmu kada mu sake mu baki lambarshi don gudun kada kisa mai (bomb) a kunnen wayar ya tashi da shi, kin san makiyinka har kullum nesa-nesa kake yi da shi musamman wanda ka sanshi farin sani cewa makiyinka ne dole ka sha masa lahaula". Cikin tsananin takaici na ce, "Umm!". Ta ce, "Na'am Fa'izatu!" "Bana cikin kayan 'yan wulakancin ki. In banda dole banga me zai sa in neme ki ba balle har ki wulakanta ni...". "To ni na ce ki neme ni?" Ta katse ni. "Sanda ki ke shuka rashin mutuncin ki wa kike nema? Wane irin zagi da wulakanci ne baki yi min ba a lokacin da kike tsula tsiyarki? Sai yanzu da taki ta kawo ki ne kika san ina da amfani?" Na ce, "Shi kenan Ummi, zan nemi Zaneerah, nasan ba zata yi min abinda kika yi min din nan ba. Na dauka abokin kuka shi ake gayawa mutuwa, dalilin da yasa na neme ki kenan". Ta ce, "A'ah ba shi ake gayawa ba, abin dariya ake gaya masa kuma ni abokiyar dariya ce ba ta kuka ba, Allah Ya raba mu da duk abinda zai sa mu kuka...". Ban tsaya jin karshen iskancin nata ba na kashe wayata. Na kudure a raina ba zan sake neman Ummi a duniya ba. Don haushi sai da hawaye suka zubo min. Ban yi kasa a gwiwa ba na kira Zaneerah dake Lagos, (with full confidence on her) don kowa yasan Zaneerah 'is nice' kuma yarinya ce mai sanyi da sanyin hali fiye da kowa cikin A.B baki daya. Bugun farko layin ya shiga, amma har ya katse bata daga ba. Ban hakura ba na sake kira a karo na biyu, ya jima yana ringing shima kafin naji sassanyar muryar Zaneerah ta ce. "Hello!". Da sauri na ce, "Kinyi barci ne Zaneerah?" Ta ce, "Ko nayi barci ko banyi ba ina ruwanki Fa'izah? Kiyayyar Yayana da ta shafe ni... Ba kya nemana balle YAYA ALIYU! In maye na cin kowa baya cin kansa, Yaya Aliyu bai cancanci burus din da kika yi dashi ba in ni na cancanta saboda Yayana Abubakar. Diyata mai sunanki wadda aka sawa sunan domin KAUNAR ki balle wadda na sake haifewa ita ko darajar Allah Ya raya ko da 'text message' ne bata samu ba. A lahira da kallo akan ZUMUNCI da kuke yin wasarere dashi a yanzu akan wasu hujjoji marasa madafa. Yanzu ma zancenki da irin butulcin ki muka gama ni da Yaya Aliyu. Umh! Ina sauraron ki yanzun da wacce kika zo?" Sai kalamai suka kare a yawun bakina domin na yarda na amince nayi amanna da gaske ni din mai laifi kan laifi ce ga Zaneerah wadanda bazance ban san nayi ba, sai dai a wancan lokacin basu dameni bane domin ina da damuwata ta kashin kaina da ta dame ta kowa, ta mantar dani kowa da komai har da YAYA ALIYUN. Gaskiyar Zaneerah a LAHIRA da kallo akan zumunci, zamani ya canza al'umma da dama muna wasa da zumunci da hakkokinsa ta yin amfani da uzrorin kanmu da suka sha gabanmu, wadanda in ka bibiya duk na neman duniya ne wadanda ba zasu karemu gaban mahalicinmu ba ranar da yake binciken wannan amana da hakki mai girma mai suna ZUMUNCI da Ya bamu a hannayenmu cikin Alqur'ani da Hadisi. Zumunci abu ne mai girma. Allah Ya kawo mu wani zamani da baka neman dan uwanka na jini don jin lafiyarsa ko ta iyalinsa da halin dayake ciki, sai kana bukatar amfanuwa dashi 'in any way or the other'. Ina rokon Allah Yasa al'umma MU GYARA mu dawo da zumunci a muhallinsa irin na iyaye da kakanninmu a inda baka bambance dan wa da dan kani ko da shi ne beran masallaci saboda talauci, ko da shi ne karuna saboda arziki ba zaka bambance dan wa da dan kani ba koda da fatar baki ne ba za'a bambance maka ba sai dai ace "DUKA DAYA!" Na nisa cikin mutuwar jiki da ta zuciya da tunanina yazo nan. Na rantse na manta waya muke ni da Zanira kuma kudin wayata na tafiya. Zanira bata aje ba haka nima sai dai kawai taji shasshekar kukana. Allah Sarki Zaneerah, Zanin Hajjah, Zanin Mama, Zanin Yaya Aliyu... Sai ta kama dariya, dariya sosai mai nuna maida komai wasa, kuma ta fada ne don ta huce fushinta ba don ta kullace ni ba 'And she's relieved by expressing it'. "Ni fa komai ya wuce kuma har ga Allah nayi miki UZRI dai-dai har saba'in Fa'izah Fa'iz Abubakar...". Murmushi nayi, wani irin dadi ya ratsani da wannan suna mai sanyi data kirayeni da shi. "Bani da bakin da zan wanke kaina, sai dai ince KIYI HAKURI, KIYI HAKURI, KIYIHAKURI ZANEERAH...!" "Kema kiyi hakuri 'for hurting your feeling with my words'. Na fada ne don in huce bacin raina kuma na huce". "Nayi miki alkawarin zuwa har Lagos in Yaya Fa'iz ya dawo inga 'yata da takwarata, in baiwa Yaya ALiyu hakuri. Yanzu ma ina bashi wani na bin wani, kamar yadda na baki. Bayan nan ki bani lambar Yaya Fa'iz ko ki tambayo min Yaya Aliyu in baki da". Sai bayan da na fada ne wata kunya ta rufeni, wai macece take neman lambar mijinta a wurin 'yan uwa da dangi wannan abin kunya har ina! Ai kiyayyah ba hauka bace, sai ko in ta hadu da tabin hankali. Abin kunyar ma kuma ga kanwar mijin uwa daya uba daya. Allah ka agajeni. Wata irin guda Zaneerah ta sakar min a kunne wadda har saida ta dode min dodon kunne, nayi saurin kauda wayar daga kunena. Sannan na jiyota tana cewa. "Mafarki nake ko ido na biyu?" Na amsa da karsashi, "Idonki biyu Zaneerah, don Allah ki bani. Kada kiyi min abinda Ummi tayi min, kada ki hukuntani da laifina bayan na riga na amshe shi, na kuma aikata shi ne bisa kuskure. Don Allah Zaneerah...". Na karasa cikin karkarwar murya da rishin kuka. "Saurare ni Fa'izah". Ta fada cikin jin kai da kauna irin ta dan uwa shakiki. Na rage sautin kukan ina sauraronta. "Wallahi kinji nayi rantsuwa ta 'yan Musulmi kenan Yaya Fa'iz ya hana kowa ya baki lambarsa. Ya hana ni, ya hana Yaya Aliyu, ya kuma yi rantsuwa duk wanda ya baki ya yanke zumunci dashi har abada! Ki karbi uzurina domin ina daga cikin mutanen da yake mutuntawa, ya kuma yarda da amanarsu". Sai na zamo 'standstill, wordless, speachless, motionless! Me Fa'iz yake nufi da hakan? Kuma me yake nufi da katse duk wata hanyar sadar dashi gareni? Bani da sani akan hakan, haka itama Zanirar. Don haka tambayar ta ma baya da amfani. Hawaye ya sake ciko idona. Muka yi sallama kowanne jiki ba kwari. Tana fadin sai sunzo ganin gidan Malali, ko da yake ta gani a hoto wai Mama ta tura mata ta watsapp. A wannan daren, mai cike da sauyin sabbin al'amura masu dama a gareni, dai-dai da minti daya ban runtsa ba. Kuka nake yi wanda ni kaina ban san dalilin sa ba. Nayi kuka nayi kuka har na ji babu dadi. Idanuna suka shiga radadi, da zugi dole na sassauta musu. Anya ba asiri Fa'iz yayi min ba? Domin ko ga marigayi Nazir S. da Yaya Aliyu dana so a baya, so mai azalzalar zuciya ta, yake azabtar da ruhina bai kama kafar na yanzun akan Fa'iz Bamalli ba. To ko Mama ce tayi min asirin? Nayi saurin kawo A'uziyyah da Istigfari a bisa wannan mummunan zato da yake darsuwa a zuciyata. Na tabbata Mama, ko wani cikin zuri'armu ta ABUBAKAR BAMALLI GIWA ba zai taba yi min asiri wai don in so Fa'iz ba. Domin bamu san shi ba, bamu san hanyar nemoshi ba, bamu san inda ake yinsa ba haka bamu san yadda ake yinsa ba. Abinda muka sani shi ne idan muna da bukata, mu tashi cikin dare mu tsarkake kanmu da tufafinmu mu daura alwala, mu fuskanci alkibla muyi sujjadah ga Ubangiji mu fada mishi bukatar mu. Wannan ce tarbiyyar da aka rainemu da ita yaranmu da manyanmu. Ko da zata yi yunkuri akan inso Fa'iz sai dai tayi addu'a na Allah Ya daidaita tsakaninmu in da ALHERI (sunan wani littafin Takori). Idan kuwa har ta yin to ta tabbata an amsa addu'arta, ina sozn Fa'iz a yau, wani irin so da bazan iya fassarawa ba!!! Abinda na yarda da shi a tsayin daren baki dayansa shi ne. NA SOMA SON FA'IZ A DAN ZAMAN DA MUKA YI TARE na gajeren lokaci wanda yayi tsayin dare dubu da goma sha hudu a idanu da zuciyata. Dabi'unsa, saukin kansa, barkwancinsa, rayuwarshi gaba daya, addininsa, nutsuwarsa, ‘his unique personal attributes’ da tsananin KISHINSA akaina a fili da boye su suka ja ni ga kaunarsa. [1/4, 12:24 am] Takori: *** Cikin wannan mawuyacin hali da sabuwar rayuwa mai wahalar da dan Adam a zuci da gangar JIKI da RUHI, duk da tarin jndadi da daular da ke zagaye dani, na cigaba da gurgurawa har tsayin wata guda. Ya zamanto ba abinda ke burgeni, ba abinda zan ci inji dandanonsa sai dai inci don in zauna da hanjin cikina lafiya, ba abinda nake son ji da gani sai FA'EEZ da MURYARSA... Wadanda ya haramta min haihata-haihata ya kuma toshe duk wata kafa da zan same su daga iyaye da 'yan uwa. Hutunsu Walida tuni ya kare amma nayi tsalle na dire na hana su komawa gida balle su koma makarantar, in sun bar gidan ban san makomar rayuwata cikin wannan fankacecen gida ba. Domin dai komai na gidan tun zuwansu su suke tafiyar dashi, girki da tsaftace shi. Abinda nasan ina iyawa kawai shi ne jefawa Dawisu kwayoyin dawa da sake musu ruwan sha idan yayi kura. Na daina ado, na daina wannan kwalisar. Hana rantsuwa nasan ina wanka, wannan kullum ne insha-Allahu. To sai dai bayan shi fa ko Vaseline baya ganin tattausar fatar jikina. Don ma Allah Ya so ni lokaci ne na zafi, da ban san yaya fatata zata koma ba, saboda rashin kula da hakkinta. Ina yin burushi sau biyu a rana, da safe kafin inci komai, da daddare in zan kwanta. Ina sauya kayan jikina bayan kowacce kwana uku, shima idan na gaji da mitar Walida ta cewa bana fesa deo-spray kayana suna tashi. Na zama wata irin Fa'izatu mara sanin inda rayuwarta ta dosa. Na zama mara lissafi ko tunanin wasu hanyoyi na inganta rayuwa. A ganina duk wani jin dadin, walwalar da ingancin rayuwar zai samu ne idan naji muryar Abubakar Mukhtar, na kuma ganshi da idanuna. Ko da bai sake cewa yana sona ba 'atleast' in nemi gafararsa, inyi zaman aure dashi irin na iyaye da kakanninmu. Wanda babu I LOVE YOU din sai tarin mutunta juna da darajja juna da sauke hakkin juna da Allah Ya dora a tsakani. Tunda na riga na bar damar ta kubuce min. Dama na sha jin ana cewa, tana zuwa ne sau daya a rayuwa. Hatta Yaya Rabi na tambaya lambar Fa'iz, na daure duk wani dizgi, shagube da izgilancin ta. Amma 'yar tahalikar nan bata bani ba. Ta rantse ta maya idan na sake tambayarta sai ta kwankwatsa wayarta in daina damunta. Mutum daya ya rage in tambaya ban tambaya ba, wato MAMA, don ita Hajjah bata rike waya, ko tana rikewa 'issue' dina da Hajjah a yanzu yafi karfin in nemeta a waya, ko in nemi lambar Fa'iz daga gareta. Ina jin bayan hauka da suka manna min a baya, idan nayi hakan zasu manna min fitowa daga turu. Kafin nan kafin in doshi Hajjaty a halin yanzu wani 'issue' ne na musamman mai zaman kansa, ban san da wane kalami, da wace fuska, da wane harshe zan doshi Hajjah in nemi gafararta ba, a bisa rashin kyautawar da nayi ta yi mata har da kauracewa. Anya Hajjar ta cancanci hakan? Da wannan dumbin tunani marar madafa ko zabi ta kowanne bangare na hada komai na tattara wuri guda na mikawa Subhana, Sarkin da babu abinda ya gagare shi. Ni na raunana, al'amarin ya gagareni iyawa da sarrafawa don haka na mika masa dukkan al'amarin yayi min iko da iyawarsa, bani da tsimi bani da dabara, duk suna ga Sarki ALLAH! Walida da Kausar suka kasa gane kaina, na farko bana zama dasu muyi hira, kamar yadda muka saba a baya. Bana sanya kaina cikin komai na al'amarin gidan, kullum ina daki nade cikin bargo kamar daddawa, bana umh bana uhm-uhm, sai gululun ido. Wadanda suka fada ciki suka zurma. Fa'iz kawai suka mace da son gani, ko son jin wani abu da ya dangance shi. Bazan iya kwatanta rayuwar da nake yi ba da halin da nake ciki, sai dai ince sunana FA'IZATU!!! Wadda son FA'IZU ke neman hallakarwa!!! *** Mun wayi gari yau da gingimemen hadari, mai dauke da sassanyar iska, wadda ke kadawa tare da yayyafin ruwa kadan-kadan yaf-yaf akan rufunan gidajen unguwar Malali GRA, wanda hakan ya tada kamshin kasa mai dadi da dadin shaka a hancin kowanne bil'adama. Dai dai lokacin da nayi wani juyi akan gadona domin gyara kwanciya don karin jin dadin kwanciyar tawa, naji ban zunguri Kausar ko Walida ba wadanda suke kwance gefe da gefe na. Hakan ya sanya ni bude ido sosai tare da tashi zaune. Can na hango su jikin gado suna shirya kayansu kaf a cikin (troller) din da suka zo da ita. Sosai na wartsake na dube su cikin mamaki, a lokacin da suka gama kintsa kayan suka ja zip suka zuge jakar. Na tashi zaune sosai na ture bargon na ce. "Ku, lafiya? Ina zaku je?" Walida ta mike tsaye tana gyara lullubin da tayi da mayafin Abaya baka. "Lafiyar kenan, tafiya zamuyi". Na ce, "AMma ba haka muka yi da Momi ba, munyi da ita zaku kara sati daya, na rantse daga shi ko kwana daya ba zan ce ku kara ba. Kuji tausayina Walida, kuyi hakuri mu zauna". Idona ya raina fata, ya kuma cicciko da kwallah. Kausar ta ce, "Allah ko minti daya ba zamu kara ba, balle yaya Fa'iz yazo ya taddamu a gidan nan ya sake korarmu. Tunda yau zai dawo zaman me zamu yi?" Da farko ban fahimci me Kausar take nufi ba, abinda na fahimta shi ne Kausar yarinya ce mai riko kamar ni, har yau haushin korar Yayan nata take ji. Don haka cikin lissafina ban lissafa da abinda ta ambata ba sai fahimta nayi kawai bata so ta ci gaba da zaman. Ina wannan harhaden ma'anar ne, Walida ta dora da bayanin da ya warware maganar Kausar. "Tun karfe bakwai ya kira wayarki, ni lokacin na tashi sai na dauka, Ya tambaye ni yaushe muka zo na ce da shi yau watanmu guda a gidan nan. Ya ce in sanar dake yana bisa hanyar dawowa karfe hudu na yammacin yau. A gayawa Yaya Bashir yaje filin jirgin saman Kano ya dauko shi ta can zai sauka. Ya ce ina kike? Na ce baki tashi ba, ko in tashe ki in baki? Ya ce in kyaleki kiyi baccinki, amma in gaya miki sakon". Jina nayi kamar ina yawo akan gajimare, cikin wata alkarya ta madara da zuma saboda dadi, farin ciki, godiyar Ubangiji, murna. Sauran abinda naji a cikin zuciyata a lokacin (unexpressable) ne. Ciki kuwa har da faduwar gaba da bugun zuciya. Wanda suka fito a tare da farin cikin, murna da godiyar Ubangijin suka saukar da wata irin nutsuwa da salama cikin zuciyata. Na lumshe ido a hankali. Ina rokon Allah a zuci idan mafarki nake kada Yasa na farka sai nayi tozali dashi din. Koda cikin mafarkin ne. Sai kuma na soma jin motsi cikin kaina, mai cewa in tashi in taka rawa, inyi juyi, in kuma rungume 'yar uwa shakikiya da ta kawo labarin, in bata tukuici da duk abinda na mallaka. Maimakon hakan, sai na mike na sanya hijabin sallah ta dake bisa darduma, wanda nayi sallar subhi dashi dama da alwalata, na sauko na dungura goshina gaban Subhana, na tsarkake shi, na tsarkake tsarkin mulki da iyawarsa! Duka walidar da Kausar suna kallona, sai suka kama yi min dariya suna tambaya. "Duka farin ciki ne Yaya Fa'izah?" Ban iya na tanka musu ba. Na lula a wata sabuwar duniyar ta daban, ta tunanin wacce irin tarba zan shiryawa Hafizin Hajjah? Fa'izun gidan Baban Kaduna? 'The one that is always hunting my dream?' Wanda tunanin ranar dawowar tasa ke zuwa min a farke, wato (ido biyu), cikin barci, ranaku da darare guda casa'in da nayi ba tare da na sanya shi cikin idanuna ba? A yau ga ranar tazo, 'so it will be a hectic and busy day; that needs planning and coordination'. Na daga ido a hankali na dube su ina murmushi wannan karon, wani irin murmushi da bana jin na taba yin ni'imtaccen sa a rayuwata. "To ai tafiya bata ganku ba, ajiye mayafin za kuyi ku tayani aiki ko? Mu gyara gidan, mu yiwa maishi girkin sannu da zuwa. Kuyi min kwalliya irin wannan da kuka caba, mai 'eye-shadow' da mascara, jambaki da lip gloss, ko 'yan matana?" Walida ta saki dariya, Kausar kuwa zumburo baki tayi da ya sha AVON lipstick yayi jajawur, Walida na fadin. "Kin burgeni Yayata, baki taba sa ni farin ciki irin na yau ba. Allah Yasa ki dore da hakan, Yasa ki cigaba da hakan har zuwa karshen rayuwar ku, ko mu ma 'yan baya ma yi koyi dake ko?" Murmushi nayi cikin matsanancin nishadi, "Sai kuyi ta addu'a ya yarda ya amshi tuban nawa, ba kwa ganin yadda yayi 'deleting' dina 'from the screen of his sight and mind?" Walida murmushin tayi itama, “Ni na gaya miki zai yafe miki, yana sonki yadda ba kya zato. Idan daso kuma ba aibi, sai dai 'FUSHI' wanda ba inda yake zuwa. DOn baki san me ya ce min dazu ba". Na kamo hannunta da sauri na zaunar a kusa dani. "Me ya ce miki Walida? Eye, gaya min? ". "Cewa yayi "Gyara mata bargon rufar garin da sanyi, tunda ruwa ake". Da na duba sai naga da gaske bargonki ya yaye daga kafafunki, na gyara miki. Ya ce, "Kin gyara?" Na ce, "Eh". Sannan muka yi sallama. Don haka zai fi kowa farin ciki da kika gane kuskurenki, ki ka amshi laifinki. Ki ka kuma yi dammarar gyarawa. Na lumshe ido a hankali ina mai gasgata kowace kalma dake fita daga bakinta. *** Muna (kitchen), abinda zamu karya kumallo dashi muka fara hadawa, sai dai nasan ko naman Dawisu na ne na gidan nan yau aka soya, aka farfesa min ba zan iya ci ba, farin cikin da nake ciki, doki da kuzarin da har yayi min yawa ba zasu barni in iya kai komai baki na ba, bayan ruwan lipton, shima don ya warware min hanji, ba don ina da 'appetite' akanshi ba. Kausar dake firar dankali ta ce, "UHm! Yaya Fa'izah in miki wani tsegumi mana?" Walida ta sanya bawon kwai da ta fasa cikin 'dustbin' ta ce. "Uwar tsegumi, yau kuma gulmar wa za'ayi?" Kausar tayi dariya, "Ba na kowa bane, naki ne. Don ni bana gulmar mutum sai dai in fadi akan idonshi don nasan illar yi da mutum". Cikin matsanancin nishadi nake wanda har baya kwatantuwa, don haka dariya suka bani. "Ina jinki Kausar, me ya faru?" Ta dubi Walida tana dariya alamar akanta zata yi maganar kuma Walidar bata sonta. Ta ce, "Kwanaki ko? Na ji Baban Kaduna yana gayawa Baban ABU a dakin Hajjah, an yiwa Yaya Walida miji". Duka Walida ta kai mata nayi hanzarin boyeta na riketa. "Wallahi ba zaki dake ta ba, ai ba ke take baiwa labarin ba ni take baiwa. In ba zaki iya ji ba ga hanya ki fita. Ina jinki Kausar, wane ne mijin?" Kausar dake tuntsira dariya ta ce, "Ki canka". "In canka Kausar?" "Eh, ki canka". "A cikin A.B ne?" "Eh mana". "Mus'ab?" "Gaba dai". "Abba?" "Can gaba dai". "Sani?" Ta ce, "Saura kiris". Na ce, "Shu'aib?" Tayi dariya, "Wannan ya mata nisa, yafi karfinta". Na harareta na ce, "Badar?" Tayi dariya, "Lallai kin manta magajin Ya Fa'iz wajen ginshira irin na 'ya'yan A.B". Ta fara kular dani, na ce, Ke na baki gari wane ne?" "A nawa zan fada miki?" "Au, sai mun tsadance?" "Eh Mana!". Na ce, "To #500 zan baki cash ba cheque ba". Ta mere baki, "Allah Wallahi yayi kdan". Da yake a zake nake da son jin abinda zata gaya min, na ce. "To #1,000". Murmushi tayi, "Shi kenan sai mun gama aiki". Walida dai na jinmu bata kara tofawa ba sai anan ne tayi tsaki, muka ci gaba da aiki duk na kosa a gama ta gaya min don Kausar miskilar yarinya ce, na san ko na ci gaba da na ci ba gaya min zata yi ba sai sanda ta ga dama". Muka kammala muka baje a kasa kan ledar cin abinci muka fara karyawa, ko ince suka fara don ni abinda na ci din ba wani na azo a gani bane. Ganin Kausar bata da niyyar gaya min har suka gama na kwada mata duka a baya, na ce. "Ke don Allah ki gaya min mana, ko so kike sai jini na ya hau?" Ta tintsire da dariya, ta kai kofi mug bakinta mai cike da kunun farar shinkafa ta kurba ta hadiye, ta ce. "Gaskiya sai naci na koshi Ya Fa'izah". Don haka nayi zuciya na kyaleta. Amma da suka gama ta shiga wata sabgar haushi ya kume ni, na ce (kamar zanyi kuka). "Uhm! Ke nake sauraro fa Kausar". Ta ce, "Kai don Allah Ya Fa'izah, kya bari abincin da naci ya tsirga mini mana". Ta sha toka abinta muna haka wayata tayi kabbara (call tune) din kenan. Na mika hannu zan dau wayar ina fadin. "Ke don Allah kada ki fada min in kina kaunar Annabi, ko ba dade-ko ba jima zanji ne ai". Kamin in dauka Walida dayake tafi kusa da wayar ta daga, ta ce. "Hello Yaya!.." "Eh ta tashi, abinci muke ci ma yanzun". "O.k toh". Ta kashe. Cikin zabura nake tambayarta, "Wane ne?" "Yaya Fa'iz ne. Ya ce in kin gama cin abincin ya sake kira". Kamar in maketa don takaici, muryata kamar ta wadda ta sha duka. "Amma ai kina ganin mun gama ko? Tun dazu muka gama ci fa!". Na karasa cikin karkarwar murya kukan takaicin Walida na neman kubce min ba da niyya ba. Ga idona ya ciko da kwalla. 'Yan banzan yaran nan sai suka kyalkyale da dariya. Karfe goma sha biyu da rabi na rana sai ga Shu'aib, Ya'u ya biyo bayansa niki-niki da kaya, jakunkuna saiti biyu samfurin (Argos). Na mike ina yiwa Shu'aib sannu da zuwa, Ya'u na shigo da jakunkunan falo. Ya zauna yana satar kallon Walida, ita kuma yana shigowa sai naga ta bar falon bata gaishe shi ba kamar yadda Kausar tayi, sai yasa murya yana kiranta amma bata dawo ba. "Ke 'yar kauyen ABU... Ina Yaya Sa'id Na'ibi A.B Giwa?" Cikin mamaki na ce, "Au, dama Yaya Sa'id ne mijin da Kausar ke fadi tun safe take ja min rai ta ki gaya min?" Yayi dariya, "Nima haka naji ana fada, ni na ce a bani an hana ni wai tunda ni na furta ba za'a bani ba. Yaya Sa'idu za'a baiwa, amma ai munga wanda ya furta aka bashi ba tare da an tuna cewa shi ne ya furta din ba, saboda mu ne ba'a so kawai sai Yaya Fa'iz". Murmushi nayi ya kuma matukar bani dariya da maganarsa. Ashe dai ba ni kadai nasan Hajjah tafi son Fa'iz akan kowa ba kowa ma ya ganeta ayi magana ta ce shima yafi kowa sonta, mu bama mata sai dai ta mana, Hafizinta fa? Komai nashi nata ne, komai ya samo ita yake fara tunowa kafin iyayen da suka haife shi. Ban kai karshen zancen-zucin nawa ba Shu'aib na tsinkaya yana fadin. "Ga kayan mijinki nan sun riga shi isowa, yanzu haka daga Airport din Malam Aminu nake, shi sai yamma zai iso wai sai biyar jirginsu zai sauka. Yaya Bashir zai je ya taho dashi ni yanzu haka Giwa zan wuce". "Allah Ya kiyaye hanya Yaya Shu'aibu". Na fada ina shiga (kitchen) don kawo mishi abinda zai ci a hanya ko da ba abinci bane ya samu na motsawa a baki. Ya'u ya shigo da kayyakin cefane har da buhunhunan kayan abinci ya shiga (store) dasu wanda hade yake da (kitchen), sai nama nau'i-nau'i, nasa Kausar ta adana kowanne daban a (freezer). Shu'aib ya mike zai tafi yana godiyar 'snacks' da dambun naman da na zuba masa a leda, ya ce. "Af! KInga ko na manta da sakon Mama a mota, bari inje in dauko". Ya koma ya dauko ya dawo ya miko min. "Ta ce kowanne akwai takarda a cikinsa, yana dauke da yadda za'ayi amfani da shi". Na amsa da hannu bibbiyu ina zabga godiya kamar shi ne Maman. Na ce, "Ka turo min Malam Isah (direban gidan Baban Kaduna) ko ta waya ne zai maida su Walida Zaria anjima". Murmushi Shu'aib yayi, "Ai yayarmu, haka za'a kora su 'so early' don maigidan ya dawo har an gama cin amfaninsu za'ayi (dumping) dinsu?" Na harare shi cikin wasa, "NI ban kore su ba, su suka kori kansu. Tun safe suka hada kaya za su tafi da kyar na samu suka kai yanzu". Shi dai ya fice yana min dariya, ya barni da guntuwar kunyata a katara. Cewa yake. "'Yau Mama zata sha labari idan na dawo daga Giwa, zata yi murna da farin ciki kwatan-kwacin na a zuba ruwa a kasa a sha. Fa'izah, ta sauke tata GINSHIRAR ta Bamalli, saura Pilot Fa'eez Giwa". Na ce, "Lala! Shu'aib ba ma haka da kai kada mu soma, kada kayi min sharri. Su Walida su suka nemi tafiya ni ban kore su ba". Ya ja motarshi kowannenmu cikin matsanancin nishadi marar misali. Ni da Walida muka share ko'ina na gidan nan kal-kal, muka goge, muka kade, musamman (side) din Fa'eez, da kaina na wanke (toilet) din shi na kawata da (toiletries) da turaren bandaki ko ina sai tashin kamshi da (atmosphere) mai dadi. Na canza (bedsheet) din dakin da wani (light-blue) mai hade da (duvet) da Baban Kaduna ya bamu tsarabar Umrah ni, Ummi da Zanirah. Na feshe (bedroom) din da (room-freshner) na 'HARAMAIN'. Na kunna na'urar sanyaya daki duk da sanyin da garin ke dashi, nasan daga 'Europe' zai fito, don haka zai bukaci sanyin. Sannan muka yi sallar azahar muka fada (kitchen). Da taimakon su Walida komai ya tafi dai-dai cikin dan lokaci, munyi faten acca da bushasshen kifi, baked moi-moi, tuwon shinkafa da miyar yakuwa da alayyahu da kabewa da tantakwashi zallah. Sai gashin 'Turkey' wato tolo-tolo. A fannin abin sha munyi coconut and milk shake, carrot drink, sai zobo mai abarba da pinaplple flavour. Dukkansu fresh da na sarrafa da kaina. Na ce a raina, "Yau babu 'chips', babu 'chicken', 'you need change HAFIZIN HAJJAH, as everything around us would completely change. Babu abinda LOKACI baya canzawa. 'With TIME change is possible in everything we do". (Lokaci yana canza komai). Sannan na koma 'snacks', ba tun yau ba, ba tun jiya ba na sha jin Hajjah na ba da umarnin a yiwa Fa'iz (samosa) 'best snacks' dinshi kenan. Don haka shi kadai muka yi, muka adana komai inda ya dace. Walida da Kausar suka gyara min komai suka goge min (kitchen) tas suka wanke duk kayan da muka bata, sannan suka shiga wanka. Karfe hudu Isa direba yazo suka tafi muna cike da kewar juna, sai da Walida tayi hawaye. [1/4, 12:25 am] Takori: Wankan da nake ninkaya ina yi cikin kwami yau (unexpressable) ne. Wani irin wanka (slow-slow) da ban taba yin irinsa a rayuwata ba. Fatar jikina ta wanku har santsi take da silki tamkar mai canza launin fata... "Kazo ga jikin nan FA'EEZ, zan baka abinka, ba na yawon dandi bane naka ne, mallakinka ne, a yau sai yadda kayi dashi... Nayi kuskure Yaya Fa'iz, kuskuren da nayi farin cikin amsar shi tun a duniya na kuma yi dammarar gyara shi tun a duniya kafin Mahalicci ya tambaye ni shi". Karar wayata ne ya katse min sambatun da nake yi, na mika hannu na daga. Mama ce. "Yaya magungunan da na aiko miki dasu dazun Fa'izah? Kin shanye ko?" Cikin jin kunya irin wanda bai taba faruwa tsakaninmu ba, na ce. "A'ah!". "Dalili?" Ta tambaya. "Aiki nake tun safe Mama, su Walida sunce yau Yaya zai dawo". Wata matsananciyar kunya tazo ta lullube ni, na kuma kasa fadin wane yayan? Tunda yayun namu yawa gare su. Tayi murmushi na manyance, "Shi bai gaya miki da kansa ba sai su Walida?" Nasa hannu na kautar da zirin gashina dake disar da ruwa a jikina, na ce a hankali. "Ya yo waya ina bacci, ya sake yowa ina cin abinci, daga nan bai sake yowa ba. Kuma laifin Walida ne da bata bani wayar ba, sai ta ce wai ina bacci, ko ta ce abinci nake ci don shirme irin nata". Mama ta ce, "Ai shi kenan. DOn Allah kiyi amfani da kayan lefenki kinji Fa'izah! Ya gaya min baki taba amfani da duk abinda ya dauka ya baki ba. Sakon da Shu'aib ya kawo kuwa kada kiyi wasa da yadda na ce a cikin takarda kinji Fa'izah na?" Tausayin Mama da wani bala'in son danta ya kara kamani, na kara kwantar da kai a cinyoyina na kasa magana. SHin ita din wacce irin UWA ce mai maida nata ba nata bane? Ta ce, "Ba abinda kike bukata ta fannin kayan girki?" Na ce, "Ba abinda Shu'aib bai kawo min ba Mama, har da wanda bana bukata duka ya kawo". "Yayi kyau". Inji Mama. Muka yi sallama cikin girmama juna. Ni na fara aiwatar da umarninta. Wata irin kwalliya na soma da Voyal din Hilton pitch and maroun, kasancewata wankan tarwada sai kalar ta wani irin kwanta ta bi fatar jikina. Na dauki voyel din ne cikin kayan da Mama ta kira da lefe na a dinkensa na ganshi, dinki mai kayatarwa da daukar ido na doguwar riga budaddiya, sai dai daga sama ta kama jikin tsam. Na nada dankwalin a kaina ya kwanta lambam. (Make up) dina bai yi yawa ba, (very cool and sexy). Don karawa aya zaki na dauko takalmi cikin kayan, (flat) ne pitch dan Italy na zura siraran kafafuna. Turaruka kala-kala nayi amfani da su, duk dakin ya dumame da kanshi mai sanyi da sanyaya zuciya. Na karashe shanye romon kazar Mama, na shiga (toilet) nayi (brush) na fito na dawo falo na kishingide cikin (three seater) ina kallon tashar ALJEZEERAH. Dai dai lokacin da agogon bangon dake 'main palour' yua buga karfe hudu da minti talatin. A lokaci daya na murdo radio daga I-pad dina ina sauraron sashen Hausa na BBC, ni kaina ban san wanne nake sauraro ba tsakanin Radio da talbijin. Sai dai babu wanda hankalina ke kansa cikinsu, hankalina ya karkasu ne. Wani ya tafi ga tunanin wace irin tarba zan yiwa Fa'izun in ya shigo? Sannu da zuwa ko sannu da hanya? Sannu da hanya ko ina wuni? Ni kaina ban sani ba. Wata mutum ce ni din a yau dake ninkaya cikin maliyar SO, take neman a karbeta ko yaya ne a zuciyar da bata da tabbaci a kanta. Daya kashin kuma ya lula ne cikin tunanin tarbar da shi zai yi min. 'Will I be accepted? Appreciated? Trusted? Believed? Ignored or abandoned??? Karfe biyar ta buga na soma waiwaye ina duban kofa, haka duk motsin da masu karanta labaran Aljezeera da na BBC suka yi tsammani nake shigowar mota ne, ko kararrawar shigowa falo. Biyar da rabi... shida na yamma babu Fa'eez babu mai kama da shi. Bakwai na dare ta shude babu labarin Fa'eez Bamalli balle sallamarsa. Na soma karaya, kwalliyar ta soma gushewa da kanta, Gwiwata ta soma sagewa da kagara da zakuwa. Mutumin da akace zai zo biyar na yamma, shi ne har karfe takwas na dare, babu shi babu alamarsa. Da kyar na iya mikewa na bada faralin magariba da isha. Takwas da rabi na samu wayar Mama, ina dagawa ta dora da tamabayar da ta girgiza ni ko ince ta firgita ni. "Fa'eez Malali ya soma isowa kenan? Ni ina nan ina ta zuba ido shiru, to kice da shi in ya huta Babanku na son ganinsa da safe kafin yaje ko'ina...". Ban san sanda hawaye ya barke min ba, na soma shasshekkar kuka da ma kiris nake jira. Hankalin Mama ya tashi. "Ke lafiya? Babu lafiya yazo ko kuwa?" Cikin kuka na ce, "Bai fa dawo ba kwata-kwata, kuma babu wayarshi babu ta Yaya Bashir. Nayi (trying) ta Yaya Bashir din a rufe take. Shi kuma wadda ya kira da ita dazu da na duba sai naga ashe anyi (hidden No.) din". Mama tayi dan jim! Kafin ta ce, "Ya isa! Nan da karfe tara in bai iso ba zan turo Malam Isa ya dauke ki, Babanku sai ya bi sawun su Kanon shi da Shu'aib, idan yayi tafiya irin wannan ba inda yake fara sauka sai nan Jabi Road, daina kukan hakanan, watakila suna Kanon". Nayi shiru ina goge hawayena tana bani hakuri, da cewa kukana yana tayar mata da hankali. Jikina a matukar sanyaye na aje wayar gefe, lokaci guda hankalina ya kai ga abinda ake fade a tashar ALJEZEERAH, tare da wanda BBC ke fadi duk a lokaci daya, wato; "JIRGIN BRITISH DA YA TASO DAGA HAVERFORDWEST AIRPORT DA KARFE GOMA NA SAFE, YA FADI A SYCHELLS ISLAND TSAUNIN DAKE HADAKAR KASAR SINGAPORE DA...... Ihu da kururuwa na saka, wanda ya tafi tare da yin fatali da I-pad din da kafata ta kwankwatse a kasa, na mike tsaye ina ta kururuwa hade da INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'OUN. Na dora hannuna duka biyar a kaina, wani irin azababben kuka na saka dake ketowa tun daga cikin hanji da koda ta, cewa nake. "Noooooo!". Na yunkura na doshi kofa hannuwana aka, juwa ta kwasheni ta kayar. Ban daddara ba na sake yunkurawa, burina in bar gidan zuwa inda za'a ce min ba dai dai naji ba, ko kuskuren hanyoyin sadarwa ne. Juwar ma bata yi kasa a gwiwa ba wajen sake kayar dani. Sai na soma rarrafe akan gwiwoyina dai-dai lokacin da wayar da ta fashe a kasa ke nata kuwwar duk da tsagewarta. Da rarrafen na isa gareta na sata a 'handsfree' dukkan hannuwana da jikina baki daya rawa suke da karkarwa. Tun kamin inyi magana naji muryar Surajo cikin karaji da kuwwa yana tambayata. "Fa'izahhh! Fa'eez ya sauka karfe hudu na yamma?" Na kara rikicewa da kuka, cikin in'in'ina..., "Naji...naji...nima...nima Suraj...jir...jirginsu ya fadi ko?" Surajo ya ce, "Hasbunallahu wani'imal wakeel! Ni'imal maula wa ni'imal naseer!!! Gani nan zuwa yanzun, nima bisa hanya nake". Na durkushe anan na cigaba da kuka ba kakkautawa, hawaye na hade da majina. Dai dai lokacin da ALJAZEERAH suka shiga hasko jirgin a tsaunin daya fadi, ban san sanda na kwarara ihu da dukkan muryata ba. Abinki da unguwa irin GRA Malali, ba ruwan kowa da kowa balle wani yasan halin da nake ciki ya kawo min dauki, buzu yayi nisa domin na tabbata akwai tazara tsakanin bakin gate da cikin gidan wadda mota ma sai tayi tafiya zata iso. Ya'u kuwa tin dazun yayi min sallama da cewa ya tafi gida. Haka nan yanayin gininmu mawuyaci ne ko zubar ruwan sama aji balle a jiyoni, daga ni sai Ubangiji na muka san halin da nake ciki. A wannan halin Isa direba ya cimmani har cikin falon, ko yayi sallama ko bai yi ba ni ban sani ba, na dai ganshi tsaye a kaina, shi kanshi yayi wujiga-wujiga, idanunshi sun firfito sunyi jawur. "Mama ta ce inzo in tafi dake...". Ko tunanin rufe gidan banyi ba balle yafa mayafi na bi bayan Isa, sai shi ne ya dawo ya rufe kofofin. Tunda muka hau titi nake rasgar kuka, babu abinda nake tunawa illa musgunawa da kaskanci gami da rashin albarka, dana shekara yiwa mijina Abubakar Fa'iz tun ranar da aka daura mana aure. Muka kuma rabu, ba tare da na nemi cikakkiyar gafararsa ba, ashe Allah Ya rubuta iya tafiyar kenan, iyakacin sallamar kenan, iyakacin zaman kenan SAI A DARUS-SALAAM....! Na tuna yadda naci burin sauya akalar rayuwarmu, (from negative to positive). (So, kauna da mutunta juna. Ashe Allah Ya riga ya kaddara cikin kundin rayuwata BAZAN TABA CIN WANI BURI A RAYUWATA IN SAMU BA... BA ZAN TABA SON WANI ABU KO WANI MUTUM A DUNIYA IN SAMESHI BA!!! Inama ban zo duniya ba... YA LAITANI KUNTU TURABA...!!! Idan kuma zuwan duniyar kaddarata ce, inama ban kawo wannan lokacin ba, ina ma ban kawo wannan ranar ba, inama na rungumi KADDARA TA ta auren Abubakar ZABIN IYAYENA kowanne irin hali gareshi na yiwa iyayena biyayya kamar yadda Ummi ta ce! Kamar yadda Ummi tayi, kamar yadda Zaneerah tayi... gasu nan da manyan rabo tun a duniya kafin aje Lahira, da tabbataccen farin ciki da kwanciyar hankali wanda na tabbata ni har tawa mutuwar ta riskeni ba zan same su ba...!!! Inama mun rabu ne bayan na bashi jikin da yake rokon na bashi ya dauki budurcina da nake tattalawa shekaru ishirin da uku yana mai sa min ALBARKA??? Inama ban taba yin ramuwar gayya a rayuwata ba? Inama ban taba nunawa Fa'iz kiyayya ba... Inama mun rabu lafiya... da ko ba komai na tsira da wannan koda ban haifi kyakkyawan Da irin Fa'iz ba... inama...inama...inama... Inaman tana da yawa!!! A halin yanzu bani da abinda zan fuskanci Ubangijina dashi, ranar da tawa mutuwar ta riskeni. Banyi biyayya ga mahaifina da iyayensa ba tun farko, na sanya shi cikin bakin ciki da bacin rai maras misali. Na bashi kunya... na ba mahaifiyar shi da 'yan uwanshi... wadda ta sadaukar da kacokan rayuwarta da inganta rayuwarmu kuma komi tayi tayi ne 'for our own betterment' bata da ribar da zata tsinta a ciki, ta riga ta gama rayuwarta, ta gama cin ribarta ta Allah kawai take jira Hajjaty... bata cancanci abinda nayi mata ba ko sakayyar dana yi mata. Har kaurace mata nayi, don ta bani abinda tafi so a rayuwarta. Babu wanda ta yiwa zabi irin wanda tayi min, tabbacin ni din ma tana so na! Shin ni FA'IZAH cikin butulallun 'yan Adam wace iri ce??? Anya ba ni ce SHUGABAR su ba??? A yau FA'EEZ din ya bar min duniyar baki daya, in ci ta yadda nake sonta, da tsinke koda cokali, koma da cokalin kaya (fork). Banga amfanin sauran rayuwata ba, rayuwar da babu FA'EEZ a cikinta. Wanda suna ma daya aka sa mana, kamar yadda kamanninmu suke daya, duk da zuciyoyinmu basu samu daidaito ba tun muna kanana. Na tabbata na kuma yi amanna da cewa baki daya zuri'ar A.B ni zasu zarga da gushewar Fa'eez a doron kasa, tunda na sha faden ina addu'ar ALLAH YA KASHE FA'EEZ BAMALLI IN HUTA. Duk da cewa tsakanina da Ubangijinnawa ban taba yi ba sam. Kuma ban taba fadin hakan daga karkashin zuciyata ba, sai, dai a fatar baki. Banga amfanin sauran rayuwata ba! Idan nayi la'akari da manya-manyan kura-kuran da na tafka ban yi 'repenting' dinsu ba. Wadanda nake ikirarin LOKACI zai bani damar goge su, gaskiya ne babu wanda yake sama da KUSKURE sai dai lokacin da nake ikirarin zai canza komai... bai bani wannan damar ba...!!! Kuka da gunjin da nake gunzawa da shekawa a fili da zuci, yasa ban san tuni munzo gidan Baban Kaduna ba sai da naji Isa na kira. "Munzo fa Hajiya...". Na sunce kullin kaina na zagayo dashi wuyana don sai a lokacin na lura ko mayafi ban dauko ba. Na rarrafa na fito daga motar. Bana ko ganin abinda yake gabana. Banyi mamakin rashin haduwa da kowa a harabar gidan zuwa ciki ba, bana ganin hanya, illa kafata da tuni ta riga ta gane kowanne sako da kowanne lungu na gidan Baba Mukhtar A.B Giwa. Gaba dayansu suna tattare a babban falon gidan inda na sanya kafata, manyan gidan da yaransu, babu wanda baya kuka na fitar rai a falon cikin matukar kidima na doshi Mama Asma'u, wadda idanunta suka yi luhu-luhu don kukan da harshe ba zai iya bayyanawa ba... Nayi zaton ma zan tadda FA'EEZ a falon. In hadiye bakin cikina. Amma yanzu na tabbata FA'EEZ YA RASU A HADARIN JIRGIN SAMA!!! Na kama Mama cikin gigicewa ina wani irin kuka hawaye na min lugulgude da ambaliya a fuska... "Mama da gaske Fa'eez ya mutu??? Da gaske bazan ci ribar wannan SON ba ma a wannan karon???" Mama kuka kawai take, ko amsa daya cikin tarin tambayoyina ta kasa bani, Ta kankameni a kirjinta kawai amma ta kasa magana. Baban Kaduna ne ya shigo yana dafe fa kansa, yana fadin. "INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN... da gaske jirgin ya fadi, daga Kanon muke, Bashir din ma ya kamo hanya ne don ya gaya mana yayi (accident) yana asibitin koyarwa na Zaria babu yadda yake... Bamu san wa yaje ya gayawa Hajjah ba ta fadi! Barin jikinta ya jikkata. Allah daga gareka muke kuma gareka zamu koma... Ba Ka daurawa rai abinda ba zata iya ba, amma wannan jarrabawoyi da kayi a garemu masu tsauri ne... muna rokon sassaucinka da afuwarka idan mun kasance ne masu saba maka a kan sani ko bisa rashin sani. Hakika Kai Kaine Sarkin da bashi da mahadi, muna rokonka kudurah da iradarka akan wadannan jarrabawoyi namu zuciyoyinmu sun gaza dauka, kwakwalen mu sunyi rauni ga rungumarsu... Yaa ASSAMADU, KADIRAN ALAA MAN YA SHAA'U muna rokon sassaucin ka....!!!" Wani rugugi da hargagi naji a cikin kaina. Na tabbatar dai yanzu FA'EEZ YA RASU!!! Bayan wannan ban sake sanin me ke faruwa a duniyar ba... Ban sake sanin inda kaina yake ba...! *** Sanyin ruwan da ya ratsa kwanyar kaina, ya dangana da hakarkarina, ya zagayo zuwa wuyana da kirjina, shi ne ya maido ni hayyacina. A hankali nake bude idanuna ina lumshe su da son tantance halin da nake ciki? A ina nake? Me ya same ni? Cikin mafarki nake, ko kuwa idona biyu? Cikin 'yan sakanni na fahimci a gadon asibiti nake, akan cinyar mutum mai taushi, fanka na wulwulawa, A.C na burari. A hankali kwakwalwata ta soma tariyo abinda ya faru, da kuma musabbabin abinda ya kawoni gadon asibiti, wanda ba zan gushe cikin addu'a da fatan Allah Yasa mafarki nake ba! Nayi salati cikin wara idanuna sosai da jin muryoyi mabambanta na tashi cikin kunnuwana, daga mutanen dake zagaye dani. A lokacin memory dina (is back on network) duk abinda ya faru, ya kuma yi musabbabin zuwan nawa gadon asibitin ya dawo 'fresh' a kwakwalwata. Na yunkura zan mike zaune cikin fashewa da sabon kuka, sai naji an kamani an maidani kwancen. "Koma ki kwanta, 'relax Fa'iza, relax... 'Main Hoon Naa... (I'm here now)! And I will be here for ever, I'll not die and leave you... We are meant for each other!!!" Wata tattausar murya ke fadi, cikin turanci mai gardi da taushin amo. Sai kuma dariyar Mama akunnena da muryar Momina na fadin. "Ta gama suman, ta koma iya shegenta. Da dai ba ita din ce ba...". Muryar Walida, "Kai Momi! 'She's no longer the FA'EEZAH YOU KNOW... Na rantse tana son mijinta". Muryar Shu'aib, "Kaji Momi da wani zance mara dadi, ai mijinka-mijinka ne, kana son shi ko baka sonshi". Na daga kai a sukwane, na dubi wanda ke rike dani, kuma wanda nake kwance akan cinyoyinsa, wanda ke shafa min ruwan a fuska, wuya zuwa kirjina... FA'IZ (ABUBAKAR), FA'IZ BAMALLI NE, FA'IZU MUKHTAR ABUBAKAR BAMALLI GIWA...! Mijina abin sona, sanyin idaniyata, cikon farin cikina... 'The one that is always hunting my dream!!! Makiyina, abokin fadana ada can, masoyin da babu kamarsa a yanzu...Wanda zaton guhewar sa a doron kasa kadai ke neman aikawa dani nima. Mikewa tsaye nayi cikin wani irin zafin nama na rungume shi. Wata irin runguma kakkarfa, mai tafiya bisa umarnin zuciya da jagorancin gangar jiki, cikin kuka mai yawa wanda ya kasa tsayuwa daga idanu da zuciyata, amma wannan karon NA GODIYA GA UBANGIJI NE da ya kaddara zan sake ganin Fa'iz kafin Allah Ya dau raina. Zan rungume shi cikin jiki na kafin saduwata da Ubangiji na! Sosai yayi min masauki a katafaren kirjinsa, ya rufe ni ruf da gaba dayan gangar jikinsa ya zagayeni da hannayensa, ba tare da la'akari da iyayenmu da kannemu dake zagaye damu ba, su din dariya suke suna karawa, har da masu yin tafi, cikin nasu farin cikin, da godiyar Ubangiji. Na dago kaina na dube shi ina kuka, na shiga bugun kirjinsa da hannayena biyu. "Don me kayi mana haka yaya Fa'iz? Don me? Me yasa ka tsoratani ka tayar min da hankali irin wanda zai iya sawa zuciya ta buga! Kasan baka cikin jirgin kace kana ciki kawai don ka tayar da hankalinmu? Eye Yaya Fa'iz me yasa? Me yasa?? Me yasa???" Na koma na rukunkume shi da karfin gaske na cigaba da kuka kamar mai tsoron kada ya sake tafiya ya barni, ko wani al'amari makamancin wannan ya sake rabamu. Baice komai ba, idanunshi ya rufe bai bude ba, ina iya jiyo bugun zuciyarsa mai bugawa da sauri-da-sauri. Wannan wata rana ce mafi soyuwa cikin ranakun rayuwarsa da ba zai iya fassarata ba, ranar da yake tsammanin har ya koma ga mahaliccinsa ba zata taba zuwa ba! Ya rasa abinda zai yi ko zai ce da zai nuna dumbin farin cikin da yake ciki. Yau Fa'izah ce rungume da shi gaban BABA da MAMA, BABAN A.B.U da MOMIN A.B.U... Wata rana cikin ranakun rayuwarsa mai dumbin tarihi in ka cire ranar da ya karbi aninin zama cikakken matukin jirgin sama, da ranar daurin aurenshi da FA'IZAH A.A GIWA. Duk dakin asibitin ya dauki tsit, bayan shasshekar kukana dake tashi a hankali a dakin da bugun zuciyar Fa'iz Abubakar. Abinda ya iya cewa a wannan lokacin cikin sassaucin murya, inka cire ni Fa'izar dake rungume dashi, babu wanda ya iya yaji a dakin, ni din ma don na kasance cikin masu karfin ji ne. "FA'IZAH, ashe kina sona kike wahalar dani?" Ya fadi tare da kai hannu ya dago habata, ya dubeni cikin ido. A hankali Baba Muntari ya zame ya fice daga dakin, Baban A.B.U yabi bayansa, Momi da Mama suma ficewar suka yi, Shu'aib da Yahya suma suka fice. Amma Walida da su Junior suna tsaye kyarr idanunsu na kallon soyayya mai dumbin tarihi cikin zuri'arsu. Kallo daya Yayan yayi musu, suka fice cikin murmushi da susar keya (It's a show that they don’t want to miss). TAKORI. Muka yiwa juna kirr da ido, kamar kowanne so yake ya karanto adadin kaunarsa cikin idanun dan uwansa. Abubuwa da yawa sun faru cikin rayuwarmu wadanda duka marasa dadi ne, kowanne kuma yana 'blaming' dan uwansa da shi ne SANADI. Amma a yau mun yarda mun amince haka rayuwarmu ta zo a rubuce babu wanda shi ne SANADI. Mu din da rayuwarmu gaba daya kamar wani rubutaccen KUNDI ne wato LITTAFI mai dadin karantawa da koyarda darussa da dama. MUhimmi shi ne na 'YAN ADAM MU DAUKI RAYUWA DA SAUKI BAMU SAN INDA KADDARA ZATA KAIMU BA. ZA KA KI ABU, BAYAN WATA KILA ABIN NAN ALKHAIRI NE A GAREKA, ZAKA JARABTU DA SON ABU, ALHALIN SHARRI NE A GAREKA. DON HAKA NE IN ZAMU YI SO KO KI MU YI SU SAISA-SAISA. MAFI A'ALA SHI NE MU BAIWA UBANGIJINMU ZHABI A DUKKAN AL'AMURANMU NA DUNIYA BA WANDA MUKE SO KO MUKA JARABTU DA KIN SA BA!!! Ubangijin da ya halicce mu shi ya halicci SO ya kuma halicci ki ya sanya su a zukatan bayinsa. Kamar yadda ya halicci komai mace da namiji (feminine and masculine) ya kuma ya halicci komai da kishiyarsa (opposite) dukkansu kuma halittar Allah ne da babu dan Adam da ya isa yayi yadda yaga dama dasu face UBANGIJIN da ya halicce su. Mu karbi rayuwa a duk yadda ta zo, mu kasance cikin GODIYAR UBANGIJI. *** Mintuna masu dama suka shude kafin Fa'iz, yayi magana. 'It's not my fault' (Ba laifina bane). Akan me zanyi irin wannan mummunan 'joking' gareki har ma da IYAYENMU? 'I missed my flight', karfe goma na safe zan tashi nayi zaton na safe ne shi yasa na gayawa Walida da yaya Bashir zan taso goma na safe. A daren ranar kuma na kwana akan 'internet' ina gudanar da wasu muhimman ayyukana. Koko ince rai bata tafiya a lokacin da Ubangijinta bai kirata ba. Abu in aka ce miki da karar kwana to babu dabara. Idan kuwa rai bai zo wa'adinsa ba, ruwa da iska, mutum da aljan basu isa suyi ajalinsa ba balle abin hawa. Wani irin bacci ne mai tsananin nauyi ya kwasheni bayan nayi sallar Asuba da yake ma banyi bacci ba sai da na bada faralin Asubahi gudun kada in kwanta ya wuce ni, dana idar na ce bari in dan kishingida zuwa takwas na safe in shiga wanka in wuce Airport. Wallahi shi kenan, nayi ta baccin da ban tashi farkawa ba sai karfe goma sha daya na rana. Don haka da na tashi banji dadi ba, don na riga na fadawa Walida da Yaya Bashir na sake yin 'booking' na samu na goma na dare. Ina zuci-zucin in kira Shu’aib in gaya masa canjin da aka samu abokina Jeved yayi min waya matarshi Barya na labour in taimaka mishi inje in tsaya dasu a asibiti shi yana bisa aiki a Lusaka. Sai hakan ya janye min hankali na tafi garesu aka ce sai dai ayi mata 'CS’ ba zata iya haihuwa da kanta ba. Don haka ina wajensu har karfe takwas na dare. So ina komawa gida bayan an ciro mata yaron shi kuma Javed ya dawo, wanka kawai nayi na wuce 'Airport' karfe goma na dare muka taso zuwa Asuba muna Abuja, ban samu jirgi ba aka ce sai sha biyun rana kuma ban tsaya kiran Yaya Bashir ba kawai na biyo wani wanda muka sauka tare wanda shima Kaduna zai zo akazo daukarshi filin jirgin saman Abuja. Lokacin da na iso Maigadi ya ce duk gidan suna asibiti, lokacin ne na kira Shu'aib yazo ya sameni. Da ya ganni sai ya rungume ya fashe da kukan da ban san dalilinsa ba. Shima Malam Amadu (maigadi) kuka ya saka yana fadin. "Alhamdulillahi". A lokacin ne suke gaya min sunyi zaton ina cikin jirgin da ya fadi wanda dalilin hakan Yaya Bashir yayi hatsari, Hajjah ta samu paralysed, ke kuma kinyi dogon suma tun daren jiya har zuwa lokacin baki farfado ba, kina gadon asibiti. Muka garzayo muka taho. Na ganki cikin wani hali daya bani mamaki wai a dalilina kika shige shi. Ina tantama har yanzu... Ina shakkah... I still doubt! Fa'izah tabbatar mini, kin fadi ne don baki so na mutu......kin fadi ne don kina son mu rayu tare ko akasin haka? Am I not dreaming..?.". Hannu na kai na rufe mishi baki, 'before I start kissing him passionately'. Fatana ya yarda ni ce... ya yarda nayi nadama... Nadama irin wadda Ubangiji Yayi alkawarin karbarta. Na tuba nabi Allah na bishi... Na tuba na bi umarnin Allah! 'He is the one I love today and always... Burina Allah Ya barmu tare har zuwa karshen rayuwar mu. Mu rayu tare idan wa'adi yazo mu cika tare. Ina rokon Allah Ya cika min wannan buri... Yasa na rayu tare da FA'IZ rayuwa mai tsaho da nagarta... Sauran al'amuran da suka biyo baya (unexpressable) ne. Wata sabuwar duniya ce kuma wata rayuwa ta daban da biro ba zai iya bayyanawa ba. Wadda daga ni har shi bamu taba tsintar kanmu a ciki ba sai 'kintace' wato (Imaginations) tun lokacin da muka fara kamuwa da son junanmu. Muke kissimata cikin mafarki da ido biyu, muke kintacen ta da 'how deep it will be, how passionate, and how romantic! It's indeed the pleasurable one, EVER! Cikin wannan duniyar ne wadda bata kintatuwa 'no matter how efficient the description of a WRITER' wato duk kwarewar mai rubutu baki iya rubuta ta ba, muka kwashe awanni biyu, ban gaji ba, bai gaji ba, ZUCIYA da GANGAR JIKI kadai ke aiki a tare. Har sai da suka samu 'healing' na ciwon da ya kassara su, yayi 'overwhelming' Abubakar shekara da shekaru, ya kayar da Fa'izatu watanni uku. Ubangiji da Ya halicce mu, Shi kadai Yasan adadinsa a zuciyoyinmu. Dr. Alkasim Bello, kwararren likita a A&E na asibitin da muke, ya kwankwasa kofar Nurse na biye dashi. Bai shigo ba sai da Fa'iz ya yi mishi izinin shigowa. Amma hakan bai sa ya rabani da barin jikinsa ba. Murmushi Dr. Alkasim ya yi, "Darling didn't die, Fa'izah will not die...". Maganarshi ta bamu dariya dukkanmu. Yayi rubutu a (file) dina ya rufe ya dubi Fa'iz fuska fal fara'a. "Kana iya daukar amarya ku tafi Mr. Fa'iz, She's o.k, is a normal shock. Allah Ya kara dankon kauna". Babu kowa a (reception) din cikin 'yan gidanmu tabbacin duk sun tafi gida. Mukullin motar Baba yana hannunsa, don haka shi ke janmu zuwa Malali. Tafiya sosai mikakkiya, don asibitin yana unguwar Rimi ne. Ina gefensa yana tukin cikin sukuni da kwarewa. Na lalace a kallonsa tamkar wani furen fulawa don kyau. Ubangijin da ya halicce shi ya suranta shi, ya kyautata halittarsa da haiba da kamala. Idan na dube shi kallo daya kaga nitsatstsen mumini mai kiyaye iyakokin Ubangijinsa. Wanda kuma ya dama, ya kutsa cikin ilmin zamani mai tsada da daraja. A goshinsa tabon Sujjadah ne, ya taru yayi baki sidik cikin nuna babu ranar Allah da zata fito ta fadi bai russuna ga Ubangijinsa ba, Ma'abocin wata iri tsafta bayyananniya da ko cikin faratansa ya nuna. Komai nashi garai-garai kuma tsaf-tsaf kamar a lashe. Babu abinda nake yi cikin zuciyata sai tasbihi ga Ubangiji na da Ya mallaka min wannan ‘giant-handsome’ a matsayin miji a gareni mai so na da kaunata ba. Idan bance nafi sauran mata sa'a ba to hakika ina cikin sahun masu sa'ar ta kowanne bangare a rayuwa. Sautin Sheikh Mahmoud Khaleel Al-khusairi ke tashi a rediyon motar cikin Suratul-Ankabut. Watakila jikinsa ne ya bashi kallonsa nake yi kamar zan cinyeshi, ya juyo a gicciye ya saci kallona. Murmushi yayi, wanda ya fadada shi har fararen hakoransa suka fito. "Da yanzu wata na nan da lullubi aka, ta fara takaba". Na galla masa harara wadda ta fito ne hakikatan daga zuciyata, na dauke kai na mayar gefen titi. "Na matsu mu isa gida, (am running at a speedly level) amma motar bata sauri. Na matsu inji dalilin da yasa makiyinka yake kokomawa mutuwarka, har ya sume dominta". Juyowa nayi na kalleshi na 'yan sakanni, na sake maida kaina a titi cikin jin zafin maganganunsa. Na sadda kaina kasa, sai hawaye suka fito, suna diga akan tafukana. Sanyin na'urar motar yayi min yawa domin har raba ke naso daga kofofin A.Cn. Ga sanyin da jikina yayi da kalamansa, suka hadu suka haifar min da zazzabi-zazzabi, na soma jin kaina a sama, ban bari mun hada ido ba, don bana so yaga hawayena. Ya karya kan motar ya shiga layinmu, wannan karon yana tafiya ne cikin (slow-motion). Tamkar baya so mu karasa gidan. "I'm hungry, yaya za'ayi kenan? Gashi nayi alkawarin bazan sake cewa ki dafe min wani abu ba, 'above all' kema din baki da cikakkiyar lafiya, kin jigata kin wujijjiga da mutuwar maigida ba zaki iya girkin ba ko na janye alkawarin nawa. ‘I still wonder’ dalilinki na damuwa da mutuwata maimakon kiyi farin ciki na baki duniyar ki sha sharafinki...". Wannan karon ma shiru nayi, banyi magana ba, hawayen ne dai suka ninka na baya. "Insha sharafina, ko in shiga uku na?" Zancen zuci nake, ban san cewa ya subuto fili ya shiga kunnensa ba. Yi yayi kamar bai ji ni ba, ko da gasken ne bai ji ni ba bazan iya sani ba. Domin cewa yayi. "Kina jina? Na ce don mene kika damu da mutuwa ta?" Har tsakar kaina naji shock, cikin kwanyar kaina naji kunya, wata irin kunya da ban taba jin irinta a rayuwata ba. Wadda ta haifar min da dabarbarcewa. Ya sake maimaita tambayarsa. Wannan karon, tambayar tasa tana dauke da 'intonation' na ba da umarni kuma da gaske amsata yake bida, ko rai ya baci. CIkin karkarwar murya da in-ina na ce. "Uhm... uhm abincin yana... yana gida, na riga na dafa... ba sai ka sayo ba!". Dariya yayi mai hade da kallo daga can kasan ido. "Shi kluma cefanen fa?" Nima sai abin ya bani dariya, ganin ya saki daga daure fuskar da yayi. "Tambayar da nayi miki daban take da amsar da kika bani Fa'eezah!. 'Anyway' jikina ya bani kinyi kewana, idanuwanki sun nuna, kwayar idonki ta fada, kazalika kasusuwan da suka yiwa cikakken wuyanki ado, suka kuma maida dara-daran idanunki lungu. Don haka ne na zamo 'curious' wajen son jin dalili? Dalilin da ya sumar dake don NA MUTU! Alhalin sanin kowa ne mutum yana murna ne da mutuwar makiyinshi...". Na katse shi cikin kosawa, "Indai cefane ne ai Shu'aib ya kawo, Ya'u ya sanya su a (kitchen) da (store) da firinji, don Allah ka rabu dani haka!". Sai hawaye. Dai-dai sanda ya sanya hancin motar cikin gate din gidanmu. Buzu ya bude bakin shi yaki rufuwa don murnar isowar Ubangidan shi lafiya. Ya sanya motar a ma'adanarta, ya kashe fitilunta amma ita motar bai kasheta ba. Na murda mabudin motar don in fita, ko motsi ya ki yi. Na juyo a hankali na dube shi, da idanun bidar dalili. Har yanzun murmushi yake, ya ce. "Cefanen? Guda nawa ne?" Na ce cikin kauda kai, "To bude min kofar mana tukunna muje ciki kaga yawan cefanen da idanunka?" [1/4, 12:25 am] Takori: Rausayar da kai yayi, a cikin kallona, ya lumshe idanunsa ya bude. "Yaya akayi kika sauya haka? 'What a sudden and awkward change! I need an explanation if you want to go out". Idanuna suka wani irin lumshe da kansu, na debo karfin zuciya na bude su tangararau akanshi. "Allah Ya hana bincike, kaga Allah Yaya Fa'iz yunwa nake ji... ka bude min kofa". "Allah Ya hana bincike, amma ke kika yi?" Na fiddo ido na ce, "Binciken me nayi maka?" Murmushi yayi (again), "Za ki rantse da Allah baki shiga dakina ba?" "Na shiga mana, amma ban bincika komai ba wallahi, gyarawa kawai nayi". Ya miko min hannun shi na dama na alamar karbar abu. "Bani DIARY dina!'. Na kai tafukana na rufe fuskata cikin matsananciyar kunya. "Koda na gani, ba lallai ne ya zamo na karanta ba. Kuma ma ai duk rabi Larabci ne ba iyawa nayi ba". Ya girgiza kai, "Fa'eezah! Kin dauka ban san cewa tun kina 'yar ficikar ki kike yara Larabci ba? Kin zaci ban san cewa (B.A Arabic) kike karantawa a BUK ba???" Baki na saki galala! Ina kallonsa. "Rufe bakin kada kuda ya fada". Dariya nayi na juya masa keya. "Duk wani motsi na rayuwarki nasan dashi, haka duk wani abu da kike aiwatarwa a kan wadannan fitinannun idanun ne, ko ba haka kuke cewa ba keda 'yan uwanki Ummi da Zaneerah?" "To mai yasa kake sa min idon? Ko kasan sa min idon da kake yana daga cikin abubuwan da suka sa na ki jininka a lokacin? Ina ganin kana sa min ido ne domin ka kuntaci rayuwata". "Kina so ki ji dalili?" "Eh". "To amsa min tambayata, ta shin kin karanta min DIARY bada izinina ba ko?" "Eh, na karanta, shi kenan? Amma wallahi ba bincike nayi don na samo shi ba, tuntube nayi dashi a dokin kofa". Murmushi yayi, "...Fa'izah matar Fa'iz! Insha Allahu jirgi ba zai zamo ajalina ba sai SON FA'IZAH!". Na dago cikin (slow) na dube shi, kwayan idanunmu suka hadu, suka sarke da juna. Babu komai cikin kwayar idanunshi sai 'gesture' wato motsi mai nuna zahirin abinda ke zuciya. Tsigar jikina ya tashi yarrr! Jikina yayi bala'in sanyi, ban san yaushe kalaman ke fitowa a hankali daga baki na ba. "Balle ma in Allah Ya yarda tare zamu mutu, tare za'a binnemu, kuma ba ta hadarin jirgi ba. Tukin-jirgi, hanyar abincin mu kenan ba hanyar ajalinmu ba, yanzu muka fara tukashi muna saukewa daga kuruciya har tsufa, ranar da ba zamu iya ba 'ya'yanmu su karba, haka har jikoki". Ni kadai nasan abinda naji... da na tsammaci mutuwarka! Da ka mutu a wannan lokacin Yaya Fa'iz I'll no longer be in existence. Na tabbata in 'so' bai kasheni ba kewa da 'kauna' za su kasheni...' Wata irin runguma Fa'eez yayi min da saida kasusuwana suka amsa. Hawayen dake makale tun dazu suka balle mini suka shiga shan sharafinsu a kundukukina zuwa gadon bayan sa. Ya kai hannu ya shafo hawayen, "Daina zubar dasu haka nan Fa'izah. Na tabbata ba ni ne baki so ba HALINA NE. Wanda a zahiri ba halina bane KISHI NE. Ba ke nake sanyawa ido ba, SOYAYYAR DA KIKE YIWA YAYA ALIYU NE! Ina kishin Aliyu Fa'izah, yadda bakya zato, har gobe ba zan daina ba. Domin wani mutum ne shi da kika so da zuciya daya saboda HALINSA! Na yarda na amince halin mutum jarinsa ne daga yau nima na zama dan kirki, dama ke kadai nakewa rashin kirkin, kema kuma don kina son ALI NA'IBI ne! Tunda kin maido son gareni na miki alkawarin zama mai kirki fiye da Yayanki ALIYU HAIDAR NA'IB A.B GIWA!" Na dago kaina ido sharkaf da hawaye. "Ko baka canza ba INA SON KA HAKA! I go along with the people I love da halinsu...". Dariya yayi, "Da can dinma bakya ki na, bacin ranki kike expressing' na bakanta miki da nayi. Da kina ki na da kinbi shawarar dana baki a RIVER NIGER". Na dunkule hannu na bugi kirjinshi da shi. "Kai ne baka iya kishin ba ai, kishi na mugunta?" Na sake bugunshi, "Ba'a nuna KISHI da KIYAYYAH... Ga wanda aka yimawa KIYAYYAH NE. Ka daina kishi da Yaya Aliyu don Allah, dan uwanka ne, kuma surukinka. Na so yaya Aliyu, kasancewar shi wani mutum da ya wahalta mini, da gangar jikinsa, da zuciyarsa, da aljihunsa da lokacin shi a kaina. Ya shiga kunci a lokacin da ya rasa ni. Kai da ka samu bai yi kishinka ba ya bada kyakkyawar gudunmawa wurin ganin na hakura na rungumi aurenka Yaya Fa'iz. Aliyu ne ya sani yin zuciyar da na tsaya nayi karatu na shiga sahun dalibai nagartattu a lokacin da nake cikin shagaltattu. Don me ba zan so shi ba a wancan lokacin tunda an halicci zuciya ne da soyayyar mai kyautata mata? Ina son shi ne a lokacin, amma wani irin so irin wanda nake yiwa BABA NA ban taba kimsawa zuciyata sha'awar tarayya a tare dashi ba sai so na 'KAUNA' da mutuntawa hadi da ganin kimar juna. Amma wannan son da nake ji a yanzu akan Hafizin Hajjah? Wani iri ne da harshe ba zai iya bayyanawa ba, kwakwalwa ba zata iya fassarawa ba, da ya gagari fahimtar mutum sai dai zuciya ta jishi amma ba zata iya bayyanawa ba. Haka nan zuciya da kwakwalwa basa iya daukar shi ba tare da sun nuna gazawa ba saboda GIRMANSA! Daban yake dana YAYA ALIYU kazalika NAZIR SANI GALADANCI. A kansu duka, banji irin wannan lullubabben son da nake yiwa FA'EEZ MUKHTAR ABUBAKAR BAMALLI GIWA BA!!!". "Barni haka... kada ki kasheni da raina". "Ya fadi ne a galabaice, cikin tsananta rungumar da yayi min. "Allah Ya bani tsawon ran da zan ninka farantawar da Aliyu yayi miki, Allah Ya bani tsawon ran da zan nuna miki bakiyi asarar Yaya Aliyu ba! Nayi alkawari Fa'izah zan nuna miki so da kulawa fiye dana Yaya Aliyu. Ko da can din ban samu dama bane, babu kuma hanyar da zan samu damar. Sai dai kisa a ranki, na rantse ALIYU BAI FINI SONKI BA... DAMA YA FINI SAMU!" Ni kadai nasan halin rudun da na shiga a lokacin da kike neman hallaka kanki don kiyayyata, sai ko abokina Maajid. Kada ki kara sawa a ranki wai bana son ki. Kisa a ranki Fa'eez naki ne KE KADAI". Shudewar mintuna masu tsayi cikin wasu al'amura masu tsayawa a rai, da zuciyar wanda ake mawa. Na nemi ji na da ganina na wucin gadi na rasa. Fa'eez ya daukeni ya kai wata duniya ta daban irin ta Adamu da Hauwa'u da ma'aurata kadai ke zuwa kwatankwacinta. Ya manta da yunwar cikinsa na manta da tawa, da kyar muka rarrafa zuwa cikin gidanmu muka dangana ga dakin baccinmu. A can komai ya kwance, al'amuran suka sauya taku, baga Fa'iz ba, ba ga Fa'izar ba, kowanne so yake ya nunawa dan uwansa ya fishi so da kaunar kansa. Ina rokon Allah Ya tsawaita rayuwarmu, Ya kara soyayyar junanmu cikin zukatanmu, ya bamu 'ya'ya masu albarka da biyayya ga iyaye. Bana burin in haifi da mai irin halina na kafiya, riko da taurin zuciya. Addu'a nake, Allah Ya bani Da ko 'YA mai hali irin na Ubansa/ubanta, mai yakanah irin ta Ubana da Baban Kaduna, mai son zumunci da kyautatashi irin HAJJAH. Mai tsaftattar zuciya irin ta MOMI na ma'abociyar rungumar kaddarorin UBANGIJI. (Ku ce Ameen, makarantan TAKORI). * * * Kwanaki bakwai da suka biyo baya, babu abinda ke wanzuwa a gidan sai amarci zallah, na a buga a jarida. Babu inda Fa'iz ke zuwa daga gida sai masallacin wani gida makwabtanmu, sai gidansu a Jabi Road shima duk dadewarsa baya wuce rabin awa. Ranar da ya cika kwana goma sha hudu ya ce in shirya zamu je zaga dangi daga nan mu wuce Giwa wajen Hajjah, sun dawo daga Jeddah ita da Baba Na'ibi da Aunty Zainab inda aka kaita asibiti tsayin sati biyu. 'Yan uwa dake kewayen Kaduna muka fara zagewa, su Aunty Hauwa Maman Ummi, sai Jabi Road. Mama dai hadiyeni ne kawai bata yi kullum sai zuba mana albarka, haka Baban Kaduna albarka suke saka mana babu kakkautawa a duk lokacin da kafafun mu suka taka gidajensu. Da kara jan hankalinmu kan riko da ZUMUNCI. Su kan ce. "Ko babu aure mu 'yan uwan juna ne, don haka hakuri da junanmu ya zama dole don cigaba da (maintaining) burin Abubakar Bamalli, ya cigaba da ganin abinsa can inda yake, suna rokonmu ko bayan ransu...kada mu warware wadannan igiyoyi da suke kukkullawa a tsakaninmu kan kannenmu da 'ya'yayenmu, jikoki da tattaba-kunne. Mun dauko hanyar Zaria bayan mun baro Kaduna, bayan motarmu shake da tsarabar su Walida (trolly) guda da Fa'iz yayo musu. Amma cikin rashin sa'a bamu same su a gidan ba. Walida tana makarantar WTC Soba tana shirin zana jarrabawar fita (SSCE) yayin da Abdallah ke makarantar horas da sojoji a Jaji (National Defence Academy). Kausar na S.S I a Sarauniya Amina, inda Walid autan Momi ya shiga shekararsa ta farko a karamar sakandire. Babana Prof. Ahmadu A.B da Momina Maimunatu A.B, sun rasa ina suka-saka-ina-suka aje damu don farin ciki. A fili Baba ya daga hannu yana yiwa Allah godiya a cewarsa da Ya nuna masa wannan rana, wadda Hajjah har kullum ke ce da su tana zuwa! Yayi addu'a Allah Ya karawa Hajjah lafiya da tsawon kwana., Ya jikan ABUBAKAR BAMALLI. Gaba daya muka shafa da amsawa da "Ameen". Fa'eez ya tafi cikin city ya barni, ya ce zai je yaga Surajo ya dawo. Bayan fitarsa ne Baba ya dubeni yana murmushi yake fadin. "Yo ko ke fa Fa'izata?" Na dago kai na dube shi nina murmushin nake yi. Rabon da inga yana walwala irin haka tun muna kanana sanda yake kaimu (Nursery) 'staff school'. Yana tuki yana mana tatsuniya har muje makaranta. Idan ya debo mu akan hanya zai tsaya ne ya sai mana dafaffen kwai da gishiri ni da Walida da Abdallah. Kullum ne ranar Allah sai ya sai mana dafaffen kwai da zuma wai suna kara kwanyar karatu. Idona ya ciko da kwallah da na tuno wahalar da na bashi 'in return' "Na ce ko kefa? Dubi yadda kika yi kyau, kika ciko, da kika kwantar da hankalin ki. Amma watannin baya baki ga irin takaicin da kike sanya ni ba. Kullum idan na daga ido na dubeki a gidan nan wai na kasa lankwasa ki, wani abu ne ke tokareni a kahon zuci. Kullum tunanina wai 'yar da na haifa tafi karfina, tafi karfin UWATA da yayye na, a duk sanda nayi tunanin haka, na duba na hanga naga cewa babu wanda keda irin wannan dan cikin A.B ... sai inyi dakacen dama ba ni na haife ki ba!!!'. Da rarrafe na isa ga Babana, kuka sosai nake har da majina. "Ka yafe min Babana, ka dubi Allah kayi min afuwa, kuskure ne da aikin shaidan ina rokon Allah Ya kara nisantani da shi. Duk abinda nayi nayi ne a bisa kuskure da rashin fahimta. Na roki afuwar yaya Fa'iz tuni ya yafe mini... Ina rokon ku kuma ku dubi Allah da nadamata ku yafe mini ko na cigaba da ganin haske a rayuwata... Ku taya ni rokon Hajjaty ta yafe mini...". Baba yasa hannu ya dago ni, "Tuni na yafe miki Fa'izah, ina gaya miki halin da na shiga a baya ne ba don ban yafe miki ba. Allah Yayi muku albarka, Ya kyautata gabanku da bayanku, Ya baku zuri'a masu albarka!!!". Ya sanya hannu ya janyo 'brief-case' dinshi ya fiddo wasu takardu, ya duba sannan ya miko mini. "(Share) ne na banki na saya muku dukkanin ku, ke kuma na hada da bude miki 'account' da bankin JA'IZ don saukakawa mijinki wasu daga cikin lalurorinki. Na kuma bude shi ne da niyyar duk wata idan na dau albashi zan sanya miki wani abu a ciki, haka kason ku na wata-wata da ake baiwa duk wani da na A.B shi kuma na bude mishi 'account' daban da Bankin 'Fidelity' ga (details) dinnan ki adana a wurinki ko ki bawa mijinki ya adana miki". Hannu biyu nasa na karba ina godiya. Na kare da cewa. "Baba Allah Ya bar min kai!". Murmushi yayi, "Nima Allah Ya bar min ke". Momin tayi dariya tana jinmu bata ce komai ba, dana juya gareta sai naga ta sunkuyar da kai hawaye na diga daga idanunta. Wato wannan din wata irin soyayya ce ta da da mahaifi da ita bata samu ba! Kaico da iyayen dake haifar 'ya'yan su zubda su ko masu sacewa su raba su da iyayensu, saboda cimma wata manufa ta duniya. Ya Allah ka barmu da iyayenmu har karshen rayuwarmu, Ka kara musu lafiya da tsawon kwana, Ka basu ikon kula da hakkokinmu, muma Ka bamu iko da zuciyar yi musu BIYAYYAH don gamawa da duniya lafiya (Ameenm summa Ameen). Dai-dai lokacin da Fa'eez yayi sallama shi da Surajo, Surajo ya gaida Baba da Momi ya koma tsokanata. "Yau sati biyu kacal cikin takaba amma aka rangada kwalliya?" Na galla masa harara Baba kuwa dariya yayi suka shiga hira na abinda ya shafi aikin Surajon (Banking), tashin zabuwar 'Doller' da 'sterling pounds' abin babu dadin ji. Sun dade suna hirar, tare da yiwa kasar mu addu'a. Muka yi sallama dasu muka dauko hanyar Giwa, shi kuma Surajo suka yi hannu ya shige motarsa ya koma cikin city inda gidan iyayensa yake. Har zuwa yanzun bai yi auren fari ba, na dai ji jiya Fa'iz na fadin ya kai kudin aure. Muna tafe akan hanyar Giwa, sanyin na'urar sanyaya mota na ratsa kasusuwa zuwa bargon mu, sautin Abdurrahman Sudaith na tashi cikin Suratul Tagabun, Nake gayawa Fa'iz. "Ko kasan rabon da kalami mai dadi ya hadani da Momi da Baba irin na yau, tun ranar da tsinkayi labarin daurin aurenmu? Na rasa wane irin so kafatanin A.B ke maka, kana da wata ilhama ta musamman da duk cikin zuri'armu babu mai ita. 'I salute!" Na kai hannu na gefen goshi na daga. Gaisuwar girmamawa irinta bature. Dariya na bashi sosai yayi harda bugun sitiyari. "The salute best suits you! Yarinyar da ta gasawa kafatanin A.B gyada a hannu. Ta nuna musu JIYA BA YAU BA... GABA DA GABANTA WAI ALJANI YA TAKA WUTA... I salute too!!!". Ya daga hannu a goshi, ya kankantar da ido cikin kallona. Murmushi nayi cikin jin kaina yayi girma kamar fanteka. Na mika hannu na rike nasa, ya ce. "Kinga matsa, kar kisa in watsar damu tun ban ajiye mai ce min BABA ba". Dariya ta kamani sosai saboda yadda yayi maganar cikin zare ido da barazana launin idonsa na canzawa. "To Baba Abubakar, direban zuciyata, the pilot that drives me crazy...". Kuuu!!! Ya ja wani irin birki a tsakiyar titi, saura kadan ya yiwa wani mai babur diban albarka, motar tayi gaba tayi baya kamar zata hantsila. Kafin ayi haka kankame nake dashi ina shahada, idan mutuwarce ta zo ta daukemu tare ko yanzu ne na shirya mata. A hankali ya gangara muka sauka a gefen titi. Rikon da yayi min mai tsauri ne da saida kasusuwana suka amsa. Idan al'amuranshi suka birkita bana iya doje su a ko'ina ne. Ko nayi kokarin hakan bana cin nasara. Al’amuran soyayyarsa unimaginable, unabandonable' ne a gareni, and also, irresistible. "Yaa Allah ka barni da Fa'iz, ka makantar da duk 'yan matan duniya daga kan mijina Fa'izu Abubakar, ka munanta shi a idanunsu ya zamo ni kadai nake ganin kyansa. "You are my life Yaya Fa'iz... I'll always keep on loving you..." "To say I love you Fa'izah, is not a way to express the feelings. .....!!!". Muryarshi har bata fita, kuma kalaman, yana fadinsu ne tun daga karkashin zuciyarsa. Bamu isa Giwa ba, sai karfe shidda na yamma. *** MURFI Hajjah na kwance tsakiyar falonta, 'yan kananan jikokinta zagaye da ita lokacin da muka shiga tana ta faman bari-barinta data saba daga kwance. Hannuna cikin na Fa'iz muka yi mata sallama a falon. Allah Sarki Hajjah! Mikewa tayi zaune daga kishingiden da take akan tuntu tana kyafta 'yan makyabtanta amma bata iya ta gane ko su waye ba. Hakika tsufa ya zo, amma mai tafe tare da nutsuwa wadda riko da addini ke haifarwa a shekarun tsufa, hakoranta duka rabi sun zube, gilashin take lalube don ya kara ma ganinta karfi ta gane mu. Kasancewar bayan sallama da mukayi kasa-kasa, daga ni har Fa'izun babu wanda ya sake magana balle ta shaida muryarmu. A tare muka isa ni da Fa'iz zuwa ga akwatin gilashin nata wanda yayi gefe guda, hannuna ne ya riga na Fa'iz sauka akan akwatun gilashin. Don haka ni na dauka na sanya mata. Kallon-kallo ake tsakanin Hajjah Hadiza Giwa, da jikokinta Fa'izah da Fa'izu. A nasu fatar bakin, murmushi ne. A nata kuma cewa tayi cikin raunin murya. "Abin tamkar a mafarki, ranar dana dade ina jira. Ranar da Fa'izu zai zo min tare da Fa'izah a matsayin matarsa, suna masu farin ciki da juna... suna annuri a fuska da zuci...". Na zame hannuna daga na Fa'iz na runtuma na rungume Hajjaty.... "Yau ga ranar Hajjah... Ki yafe min Hajjah kuskure ne, ajizanci ne irin na dan Adam!" Ta rungume ni sosai a jikinta tana dariya ina kuka. "Daina kuka Fa'izan Hajjah, ni ai nasan wannan ranar na nan zuwa, ni ai nasan dama shirmenki kike da tarin kuruciya ke haifarwa. Fa'izu nawa! Mijina na kaina, Abubakar Saddiku... akwai gaular data isa tace bata son sa? Ai sai dai ta fada don kawai taji dadin bakinta". Murmushi Fa'iz yayi, ya zauna a gefen ta yana kada 'yan mukullayen shi. "Hajjah tawa! Hajjaty!". Duk sai suka bani dariya, su basu yadda ba mata da mijin ne. Ina dariya mai cakude da hawaye na ce, "Tsinkayenki dai dai ne. Hasashenki bai zama a banza ba. Ki yafe min Hajjah kuskure ne wanda babu dan Adam din da ya isa ya kauce masa. Na yarda na amince ko iyayenda suka haifeni basu fiki so na ba, sai dai su ce su suka haifeni. Ina kira ga 'yan mmatan zamani su nutsu, su dawo cikin hayyacin su daga tasirin ilmin zamani, wajen akida da al'ada. Su daina kallon zurfin iliminsu da wayewarsu wani mataki na fin karfin iyayensu, sanin ciwon kansu ko abinda yake dai-dai ga rayuwarsu. Muna jarabtuwa da son abu alhalin shi din ba alkhairi bane a garemu, haka mu kan ki abu karshen ki a yayinda shi ne alherinmu. Mafi a'ala shi ne mu baiwa Allah ZABI a dukkan lamuranmu musamman 'AURE' mu daina bin soye-soyen zuciya da baiwa soyayya muhimmanci idan aka zo magana ta aure. Mu yiwa iyayenmu biyayya shine mafita. Soyayya ta kwarai a hankali ake samunta ba farat daya take samuwa ba. Ba ina nufin babu 'Love at first sight' ba, 'a'ah, 'it is normally not a geniune one'. Kuma bata da karko. Na gaba har gobe na gaba ne, haka iyaye har gobe iyaye ne koda a kungurmin daji suke zaune karewar rashin wayewar kai. Ina rokon Allah Ya barni da ku Hajjaty! Ya kara muku lafiya da tsawon rai. Ya bani ikon yi muku biyayyah koda ta wuta kuka hura ganga-ganga kuka ce in shiga anan gaba. Hajjah Allah Ya bar mana ke!!!". Murmushi tayi, wanda ya fadada zuwa dariya, ya fiddo wawulon da ya kara fadi a bakinta a dalilin faduwar hakora uku a bayan rabuwa ta da ita. Amma bata ce komai ba. [1/4, 12:26 am] Takori: Fa'iz ya ce, "Hajjah me ya sami wayarki ne? In an bugo bata shigowa". Ta ce, "Kai don Allah rabani da wayar nan, kubi ku ishi mutum da kararraki, ko sallah yake ba zaku barshi yayi ta cikin nutsuwa ba. Ku dai ku kira mutum kiranma maras dalili. Na bude na cire batirin don ku kyaleni na huta ku da ubanninku da uwayenku". Yayi dariya ya ce, "Haba Hajjah, ai muna jin muryarki cikin koshin lafiya dadi muke ji musamman in muna nesa. Hankalin mu na kwanciya mu cigaba da fafutukar rayuwa cikin kwanciyar hankali Hajjah". Hajjah ta ce, "Idan ta zama dole ku kira Barau, sai ya kawo min muyi maganar a tashi amma ni ba zan iya ba. Tunda na cire batirin nan na jefa bayan gado kunnuwana suka huta na samu nutsuwar gabatar da ibadu na". Ya ce, "Talbijin fa? Don me ba'a kunnawa alhalin abar taya hira ce? Kina kallon mutane koyaushe suna gilmawa kina kuma jin muryoyin su yafi zama shiru". Ta ce, "Rediyo na ta isheni, in murdo tashar Kaduna in koma sashen Hausa na BBC, duk abinda ake fadi ina ji na kuma san 'yan uwana ne Hausawa Musulmi ba wadannan jajayen fatar da ba jin me suke fada nake ba". Da alama ta bashi dariya amma bai yi dariyar ba, ya ce. "Shi kenan Hajjah, yadda kike so haka za'ayi". Ta ce, "Yo dama mana? Ayi ba yadda nake so din ba a gani in zan yarda, ga jikoki ashirin, tattaba kunne goma sha biyar, kullum suna zagaye dani muna hirarmu, kuje ku ku kadai nake jira ku karo in roki Ubangiji na Ya dau raina haka. Duk wani burina da na marigayi na cika shi, da taimakon Allah da taimakon babanninku 'ya'yan albarka, wadanda har yawun bakina ya bushe ba zan daina sanya musu albarka ba. Bana jiran komai sai fatan cikawa da imani". Ta mike cikin dafa bango da taimakon Ya Fa'iz, ta nufi uwar dakinta tana fadin. "Yau tunda na tashi da safe jikina yake bani zaki zo gareni Fa'izah, don haka na sanya aka yi miki dambun naman kaza cikin katuwar samira, aka kuma yi miki gashin naman rago irin yadda kike so da ruwa-ruwanshi, yana nan cikin magashi (oven) bude ki dauko, dambun na kai daki na boye don in Na'ibi ya shigo ya gani sai ya kwashe rabi". Ina dariya cikin jin dadi na ce, "Allah ko Hajjaty? Sakallahu khairan". Ta dakata a kofar dakin nata tadan yi murmushi. "Irin wanda nayi miki ranar kamun ki, ranar da kika ja kafa kika gujeni baki kara waiwayata ba". Tausayin Hajjah ya kamani, na mike na bita na amso dambun cikin samira. Muka zauna a tare a gefen Ya Fa'iz mun sanyashi a tsakiya, na bude na diba na kai bakina ragowar nace. "To bude wawulon bakinki in zuba miki". Ta bude bakin tana dariya na sanya mata lomar dambun naman mai dadin da baya misaltuwa. "Nayi-na yi kimanta kin ki ko Hajjaty? Ni fa ban gudu na barki ba, naje inga Momi ne". Ta harareni ta ce, "Nono kika je sha ba ganin Momi ba". "Kenan baki yafe min ba Hajjah? Baki yarda kuskure ne ba? Idan baki yafe min ba Hajjah ina zani? In samo irin sanyin da nake samu a cinyoyin ki? Baki yarda ina son Hafizin ki ba kamar koma fiye da yadda nake son kaina? Yaya Fa'iz don Allah ka fada mata 'how much I love you'". Dauke kai yayi ya cigaba da danna wayarsa kamar bai san bikin da muke yi ba. Wani tunani yazo min, ya zanyi in goge wannan tabo a zuciyar Hajjah na cewa ina son Hafizin nata yanzun? Wata zuciyar ta ce. "Show her in another way". Sannu a hankali na tashi daga mazaunina na koma gaban Ya Fa'iz. Na zube gwiwoyina na sumbaci goshinsa zuwa labbansa, sumba mai tsayi da zurfi. Ya bude ido cikin barazana yana zazzare su. "Ke Fa'izah, meye haka? A gaban hajjahhh?" Hajjah ta fashe da kuka, wanda a cewarta, "Na farin ciki ne". "Na yafe miki Fa'izah, Allah Ya yafe mana baki daya". Muna takawa a hankali a harabar gidan zuwa bakin mota, Hajjah a tsakiyarmu ta yo mana rakiya muna 'yan hirarraki wadanda duk akan 'yan uwa ne, masu haihuwa, masu aure da masu karatu. Su Indo, Inna Kubra suka biyomu da tsarabar Hajjah (dambun nama) basu barni na rike ba. Don haka da muka fito kofar gida nayi musu ihsanin da zasu jima basu manta ba. Har mun kai jikin mota zamu bude Hajjah ta ce, "Au, Hafizi?" Fa'eez ya juyo ya dakata da bude motar. "Na'am Hajjah". Ta karaso garemu. Sai ta kama hannuna ta kamo nasa, ta hada ta dunkule. Da wani irin murmushin kauna a gefen bakinta, ta ce. "Sai ina kuma kuka yi yanzun?" Ya ce, "Gida zamu koma Hajjah. Gobe da safe kuma zamu bi jirgi zuwa Lagos wajen su Yaya Aliyu. Da mun dawo za muyi kaura zuwa (Wales) can inda nake aiki don jaurar tayi min sauki, in samu nutsuwar gabatar da ayyuka na Hajjah da Fa'izahta a gefe na, duk karshen shekara zamu zo mu ganku kuma ku ganmu. Ko in aikowa Baban Giwa tikiti ya kai min ke duk lokacin da naji son ganinki. Hakan yayi Hajjah?" Murmushi tayi, wani irin murmushi da ban taba ganin Hajjah tayi irinsa ba. "Nayi ta zama a duniyar kenan Hafizi kuna ganina kuna jin dadi? Ai mun iso gangara, me yayi saura Hafizi bayan fatan cikawa da imani? Ga amanar Fa'izah a hannunka, na roke ka ka kyautata mata muddin rayuwar ka. Baku sani ba, kuma ban taba fada ba koda ga iyayenku, yadda nake sonka haka nake sonta ko a cikin jikokina ku na daban ne. Ina rokon ku ku hada kanku, ku kaunaci juna saboda Allah!". Fa'iz ya sake damke hannuna cikin nasa, ya lumshe idonsa. "Na yi miki wannan alkawarin Hajjah". Har muka shiga motar ya tayar, Hajjah bata koma cikin gida ba. Ta sake matsowa jikin tagar da yake ta russuna dai-dai kunnensa, ta ce. "Kayi tukin a hankali". Sannan ta dago ta dubeni nima, "Fa'eezah ga amanar maigidana, Hafizina Abubakar Saddiku, ki bishi, ki yi masa biyayya kinji Fa'izah? Ki dawo min da mai sunansa in kin tashi dawowa ko mai sunana. Ina kulafucin ganin 'ya'yanku wanda nasan DA KYAR NE...". Jikina yayi wani irin sanyi da al'amarin Hajjaty a yau. Magana take kamar mai yin wasicci kuma kamar mai hango gobe. Ko dan yatsana na kasa motsawa haka shima Hafizin. Na kasa amsawa sai kallon Yaya Fa'iz, shi kuma sai ya sadda kai kasa bai ce komai ba. Da kyar na iya na ce, "Insha Allah Hajjah". Ya yi ribas da motar gate din A.B Houses Hajjah na daga mana hannu. Ni kam mai raguwar zuciya sai nasa kuka, kuka nayi ta yi ba dan kadan ba. Kalaman Yaya Fa'iz ya kara tunzura kukan nawa, cewa yayi. "Yau Hajjah duk ta kashe min jiki da kalamanta, ban san me yasa ba, gata dai lafiyarta kalau... Don Allah ki daina kukan nan Fa'izah, kina kara tayar min da hankali, kina sawa inji tamkar Hajjah mutuwa zata yi kafin mu kai Kaduna". Na tsagaita da kukan amma ban daina ajiyar zuciya da sauke numfashi ba har muka zo gida. A daren shima bai yi wani isasshen barci ba. Sau uku yana bugawa Aunty Maryam Maman Yaya Aliyu da Baba Na'ibi waya yana tambayar yadda Hajjah take har suka yi mamaki. Suka ce lafiyarta kalau, yanzu haka girki take yi wai zata yi sahur dashi, sannan ya samu ya rintsa sama-sama. *** Jirgin 'Aric' muka bi zuwa Lagos a washegari, 'already su Zanirah sun san da zuwan mu. Don haka muka same su a filin jirgin saman sunzo tarbar mu da yaransu Fa'izah da Amra mai sunan Hajjah. Yaya Aliyu yayi kiba har da tumbi tabbacin hutu ya zauna, kazalika itama Zanirar, Zannura inji Hajjah tayi kiba mul-mul da ita, tayi haske na tsabar hutu, daliba a jami'ar Lagos (UNILAG) tana karantar likitancin kashi. Suka tarbemu da farin cikin da baya misaltuwa. Ni da Zanirah muka rungume juna, haka Fa'iz da Yaya Aliyu. Tun daga (Airport) labari ke cin kowannenmu har cikin gida bakinmu bai yi shiru ba ni da Zanira. Na kasa shiru da irin daular da naga yaya Aliyu da iyalinsa ciki, na ce. "Shin wai Zanirah ba aikin kamfani Yaya Aliyu ke yi ba?" Zanirah tayi dariya ta ce, "Da kenan. Ai Yaya Aliyu likkafa ta mugun ci gaba. Yana daya daga cikin mamallaka kamfanin sarrafa gilashi tsura dake Japan. Sannan yana safarar tagogi da kofofi na gilashi daga kamfanin zuwa gida Nigeria". Na ce, "Na fahimta. Allah Ya kara arziki mai albarka takowanne fanni". Anyi zumunci wanda aka dade ba'ayi ba. Diyar Zanirah ta biyu mai sunan Hajjah da suke kira Amrah kamar Ya Fa'iz ya haifeta saboda kamanninsu. Kwananmu uku a Lagos muka juyo gida Kaduna, muka fara shirye-shiryen tafiya Wales. *** A CARDIFF (WALES) Gidan da Abubakar Mukhtar Giwa yake zaune yana Cardiff, wata irin rayuwa ce muka tsinci kanmu, wadda ba zan iya bayyanawa ba. Ubangijin da Ya halicce mu, Ya kuma yo mu jini daya, Ya sanya wata irin soyayya da shaquwa a tsakanin mu da biro ba zai iya rubutawa ba. Abinda zan iya cewa kawai shi ne aurenmu tattare yake da albarkar iyaye wadda ita ce komai. Ita ke haifar da komai, ita ke bude hanyar kowanne alheri cikin rayuwar dan Adam. Ko wata uku bamu rufa a Cardiff (Wales ) ba Yaya Fa’iz ya samar min ‘admission’ a jami’ar Cardiff University of Cardiff ). Ala dole na sauya layi kasancewar turai basa yin ‘course’ dina. Na soma karantar (Civil Law). Watanninmu Shidda a Wales muka ji kira daga gida Nigeria. Wani irin kiran waya mafi muni a rayuwarmu da dukkan zuri'ar Abubakar Bamalli. Wato mu zo gida Hajjah babu lafiya, jikinta ya rikice kuma mu kadai ne a bakinta. Haka Ya Fa'iz ya tattara hidimomin nemansa ya ajiye a gefe muka taho gida. A lokacin ina da cikin fari dan wata hudu. Ashe Hajjah sa'i yayi, kwananmu uku a Giwa Allah Ya yiwa Hajjah rasuwa tana mai sa mana albarka da mu da iyayenmu baki daya, da alfahari da haihuwar su. Tana addu'ar da rokon su ko bayan ranta, su cigaba da daura igiyoyin data bari na aurarraki a tsakanin jininta. Mutuwar Hajjah ta girgiza ta kuma dimauta baki dayan A.B, wata irin girgizawa da ba'ayi irinta ko lokacin mutuwar Abubakar Bamalli ba. Babu wanda bai gigice ya fita hayyacinsa ba, kada Abubakar Fa'iz ya ji labari. Wanda sai da aka yi da gaske kafin ya koma bakin aikinsa. Hatta abinci yasan Hafizi ya rasa Hajjah, tunda shima ya rasa Hafizin na lokaci mai tsawo. Watanni biyar da rasuwar Hajjah na haifi yaro namiji, Fa'iz ya cika burin Hajjah ya mayar mata da maigidanta kuma takwaransa muna kiransa Sadiq. Bayan haihuwar Sadiq da shekaru biyu na haifi Mukhtar, a lokacin karatuna yayi nisa sosai. Ahmad ya biyo baya muna kiranshi (Khazrajy), sai haihuwata ta hudu ne Ubangiji (S.W.T) Ya nufe ni da cika burin Hajjah na samu 'ya mace. Gaba daya daga mu har 'yan uwa HAJJATY muke kiranta. Allah ya dauki son Hajjaty ya sanya a zuciyar Yaya Fa’iz. Su Mukhtar sai suka zama ‘yan kallon sha’anin Daddy da Hajjaty. Gashi ta yo kamannin Hajjah sosai da dan banzan wayau. Haihuwar Hajjaty ta zo mana da sabon sauyi. Rana daya naga Yaya Fa'iz yana tattara 'belongies' dinsa daga kasar Birtaniya, ya aje aiki da 'British Airways' akan kashin kansa ba da son ransu ba, a cewarsa lokaci yayi da zai bada gudummuwarsa ga jiragenmu na gida Najeriya wanda rashin kishin kasa namu na ‘yan Nigeria yasa har gobe suke koma baya, British Airways suka yi mishi tukuici mai yawa wanda koda bai koma aiki ba nan da shekaru ashirin a gaba, a rayuwa dai ta dan Nigeria, Nigeriar ma Arewa, kuma dan asalin garin kauyen Giwa, ta ishe shi shida iyalansa su kasance cikin rufin asirin Ubangiji. Gidanmu na Malali aka sabunta aka fadada shi don walwalar yaranmu. Muka dawo Kaduna ina dauke da cikin kanin-ko-kanwar Hajjaty. Ya debi samarin dukkaninsu ya zuba a British International School dake Lagos, Yaya Aliyu ke kula dasu a can. Gidan daga ni sai Hajjaty, itama da cikina ya shiga watanni takwas Maman Kaduna ta dauketa. Ranar da na haifi MAIMUNATU ranar Yaya Fa'iz ya fara aiki da 'Aric’. Duk yadda dan Adam ke burin rayuwa zan iya cewa mun sameta. Ba zamu gushe ba face muna masu godewa Ubangijin Halitta. Mai azurta wanda Yaso, a kuma lokacin da Yaso. Ya talauta wanda yaso, ba don baya son shi ba sai don ya jarraba imaninsa. Rayuwa mai cike da so da kauna, irin wadanda basa 'fading' (kodewa) har muka fara furfura. A lokacin da nake da mukamin babbar Lauyar Gwamnatin Tarayya a Federal High court reshen jihar Kaduna, ina rokon Allah Ya kara soyayyar juna a zukatanmu, yarda, aminci da arziki mai albarka, ya raya mana yaranmu cikin tarbiyyar islama har zuwa ranar da muka daina numfashi. MASHA ALLAHU LA-QUWWATA ILLA-BILLAH!!!! Nan na kawo karshen littafin ZUMUNTAR KENAN! Da fatan za'a dauki darussan da littafin ke koyarwa muyi amfani dasu cikin rayuwar mu ta yau da kullum. Taku har abada Sumayyah AbdulQadir (Takori ). *************************⬇********************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ **************************