12/01/19 à 22:18 - Mme Sami😘: 💔 BASO BANE 💔 Na📚 Samira Harouna ( Meerah) 💝💝💝💝💝💝💝💝 Bismillahi Rahaman Rahim 💝💝💝💝💝💝💝💝 1-5 📗 ********************** ? ************************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************? ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ? ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ? ************************** Zaune take cikin Kananan kaya riga da Siket iya Gwiwa ta saki Gashin ta iya wuyan ta Kwalliya ce sosai a fuskar ta ga wasu dogayan takalmin d'à tasaka Kyakyawar Gaske ce gata Fara tas ga Manyan Idan nu da Allah ya wadata ta dasu, remonte ce a hannun ta tana canza tasha Buda kofar da tabi yasa ta taso tsaye tayi kofar dakin tana Kallan mijin nata dake shigowa da babur kinshi har saida ya shigo da shi a dan karamin filin kewayen nasu ya ajeshi a inda ya Saba sannan ta karaso rumgumeshi tayi cikin farin ciki tare da fadin" El moc sannu da zuwa ya aiki? jin bai amsa ba yasa ta dago daga Jikin nashi tana Kallan shi kokadan babu Annuri a fuskar shi yana kare mata kallo fara'ar tace ta koma ciki cike da Kulawa tace" El moc lafiya Miyake damunka naga gaba daya Baka farin ciki kodai namaka wani Abu ne?" wucewa yayi cikin dakin batare da yace kala ba dafe Kai tayi cikin damuwa tace" Oh Allah yaou kuma kome nayi?" bin bayan shi tayi tana shiga tsaye ta sameshi da wayar ta a hannunshi yana dubawa Murmushi tayi dan tasan Abinda ya ke Fara dubawa kenan duk lokacin da ya shigo gidan karasawa tayi kusa dashi cikin nuna rashin damuwa tace" Yaya har zuwa yaoushe zakakai kana binciken waya ta?" wata Muguwar harara ya wurga mata sannan yace" har saï Lokacin da naji zuciya ta tadaina sakamin cewa kinacin Amana ta idan bananan" kauda kai tayi lokaci guda ta Kalleshi tace" Walahi Baka kyaoutawa bantaba ganin irin haka ba kana zargina akan Abinda ko Tinanin shi bantaba yiba koda a Mafarki, miyasa kake Tinanin zanci Amanar ka?" Mtsssss ! Dan Allah gafara can ta yaya zanyarda dake bayan kina dauke da wannan Babbar Waya wacce babu Abinda bazaki'iya yi da Ita, Watakila ma wannan Kwalliyar da kikayi tini wasu sun rigani ganin ta" kai tadan Girgiza sannan tace" su wa kake Tinanin zasu gani kenan, karfa Kamanta MUKHTAR akwai Abubuwa da dama Wadanda na hakura da su badan Komai ba saidan farin Cikin ka, daga cikin Abubuwan danasa kafa nashuru farin ciki su harda Mahaifiya ta da sawran yan Uwa badan Komai ba Sabida San da nake maka amma a karshe ace cikin zargin ka zankare a gaskiya wannan ba Adalci bane kuma BASO BANE kake nunamin Kishi ne kawai na Banza da bashida tushe" wata dariyar kan labba yayi ya Zauna akan Kujera sannan ya kalleta yace" ai Wanda ake So ake kishi kenan Kinga tsabar Sanki ne yasa nake kishin ki,ke kuma Abinda kikace kinyi Sabida farin ciki na KO kuma So na to ba gaskiya bane kawai kinyi ne sabida wata manufa taki da ke kadai kike boyema kanki sani,amma Walahi BASO BANE ". Hawayen da suka makale mata ne suka zubo cike ta takaicin halin mijin nata tace" El moc kadaina abinda kake Walahi baidace Bakada dalilin zargina, har yanzu kakasa samun hujjar da ka jima Kane nema akaina , ka hanani Wast up bare kace tanan nake samun damar yin abinda naga dama ya zamar maka kamar Ibada duba waya ta dan kaga wana kira waya kirani wayamin message wana ma message kuma duk da haka bakasamu abinda kakeso mizaihana kahutar da kanka kasama Zuciyar ka Salama kasa kani daya daga cikin Amintantun ka ka Yarda dani yardar da zaka'iya Dogon zango ba tare da Kaji dar a Zuciyar kaba" wata irin Dariya yayi kafin ya kalleta yace" Yarda dai ke din haba ai bari kiji infada maki Walahi ko kujerar Makka aka biyamin to cikin Biyu za'ayi daya,kodai azubamin natafi tare da ke,ko kuma dai nafasa tafiya ta yaya zantafi inbarki kisamu damar da zaki Fara kawomin irin Mutanen da kike mu'amula da su kuci amanata har cikin gida na ko" Kuka ta fashe dashi Jiyake kamar ta kuma Ihu cikin Kuka tace"Mukhtar miyasa kake zagina da aikata Abinda ko a baya ina budurwa baiyi ba miyasa" saida ya tsaya gab da ita yace" sabida kawai banyarda da ke ba" kuryar daki ya shiga ya cire kayan shi ya fito douche ya shiga wacce ke cikin dan karamin kewayan su dan yayi Wanka" Kuka ZEINAB tadinga yi kamar ranta zaifita ta rasa wannan hali na Mukhtar ta rasa irin Wannan kishi nashi da bayada tushe, a haka ya fito ya sameta zaune yayi kusa da Ita rumgumota yayi Jikin shi cikin Rarrashi yace" Kiyi hakuri Zeinab ina sanki Walahi bana Kaunar naga wani ko wata a kusa da ke shiyasa take miki duk wannan Abubuwa amma ba inayi bane dagangan, kiyi Hakuri kinji kidaina Kuka kitashi ki dauko min Abinci taci Yinwa nakeji" tashi tayi dan ta dauko mashi inda ya bita da kallo wani irin kucci ya sakeji da ya Tina idan fa wani ya ga wannan shirin da tayi idan fa ta dauki photo ta tura ma wani, wata zuciya ce tace mashi ina haka baya Faru ba ma tinda bata shiga social media,wata Zuciyar ce tace kaidai kaga mace kawai zata'iya yin Komai zata'iya maka rufa rufa sannan Sharrin mace ai yanada yawa zata'iya yin Komai domin ka Yarda da ita. 12/01/19 à 22:18 - Mme Sami😘: 💔BASO BANE💔 *Gajeran Labari* Na📚 Samira Harouna (Meerah) 5-10📗 Koda ya kammala cin Abinci sudan taba kallo kafin ya bukaci da sutafi su kwanta dan yanada 1er heur a ajin yan 3e B, bayan sun saka kayan baccin su sun kwanta ne suka Fara kokarin raya Daren nasu sati daya kenan Mukhtar baya samun damar Sawke Wannan Hakkin sabida karatu daya tsananta hakan yasa Zeinab tayi kewar mijin nata sosai cire kunya tayi ta dinga nuna mashi zalamar ta akan hakan wannane yasa ran Mukhtar ya baci tsayawa yayi da Abinda yake yana kare mata kallo kafin ya ja dogon Tsaki yace mata" Zeinab wannan ba halin ki bane ba Zeinab kita bace Zeinab kinda nasani tanada kunya bata'iya nuna hadamar ta a fili sannan bata Yarda muhada ido da ita har zuwa lokacin da Komai zai kammala amma Kiduba kigani ke da kanki kike kokarin shigar dani,walahi wannan ba dabi'ar ki bace koyanta kikayi ko kuma ankoya maki" ficewa yayi daga dakin bayan ya saka Doguwar rigar shi Bandaki ya shiga ya tsarkake Kanshi koda komi bai Faru ba amma dukkan Jikin shi ya amsa cewa yana tare da Zeinab,yana dawowa baya ya bata ya kwanta tana ganin haka ta tashi itama ta garo Jikin ta ta dawo ta kwanta tana Kallan keyar shi tana Hawaye har bacci ya dauketa bata sani ba. *Waiwaye* MUKHTAR ABDOU: haifanfan garin Maradi kuma ma Zauna unguwar dan Tudu Mahaifin shi ba wani Babban Mutum bane Ladani ne a Massalaci dake Unguwar tasu yana Mace daya Wato Mahaifiyar su mai suna Hajara suna Kiran ta da Inna su Bakwai ne suka Haïfa Mukhtar ne na Biyu bayan mace daya kebima, Mukhtar ya kammala karatun shine duk a makarantar Gwamnati sabida yanayin Rayuwar babu halin da Zai'iya yin karatu a Makaranta Kudi burin shi shine ya zama malami mai koyar wa kuma ALLAH ya cika masa burin sa inda ya Fara koyar da English a Makarantar Kudi CSP Wangari kafin ya kara samun wata damar ta koyarwa a CSP Moufida amma anan iya en Lycée yake koyarwa. Mukhtar Sawrayi ne dan kimanin Shekara Talatin da Biyar a Duniya ba Kyakyawa bane sannan baki ne saidai ba baki can ba dogo ne kuma daka ganshi kaga kakkarfa Wanda Jinin shi ke tafasa Mutum ne mai sha'awar barin saje wanne ne yake dan kara masa kyaou. ZEINAB NAFI'OU MAI KUDI: ita ma Yar garin Maradi ce wacce suke zaune Unguwar Cité Casse kafin su tashi daganan su koma ADS da zama Mahaifin ta shahararran mai Kudi ne na ganina fada, yana da Mata Biyu Mahaifiyar Zeinab itace uwar gida Wato RAMATOU tanada Yaya Shida kuma Zeinab itace autar ta, Abokiyar zaman ta kuma NADIA wacce Takeda yaya hudu. Alhaji Nafi'ou cikakken dan Boko ne hakan yasa yakeda ka'ida a gidan shi ko wajen Haihuwa bai Yarda mata sudinga mashi ita ba barkatai, Zeinab sunan Mahaifiyar shi ce ya saka mata sakamon itace mace ta Farko da aka Fara Haïfa a gidan tindaga kan Mahaifiyar ta har Tantin su Nadia, hakan yasa taci wannan sunan Wanda yasa aka fifita Santa akan Kowa dake gidan daga uwayen mata har Uban ba'a taba Zeinab a Kwashe lafiya saidai Babbar Sa'ar da akayi shine Zeinab yarinya ce mai matukar hakuri gata batada fada ko hayaniya wannan yasa Mahaifin ta ya kara Santa yake kuma taussaya mata dan tin Yarintar su ita da yan uwan ta zakaga suna Cutar ta amma idan aka tambayeta saita rufamasu Asiri bazata fadi laifin suba, hakan yasa ta kara shiga ran Kowa. Kamar Yanda Zeinab ta kasance mace ta Farko a gidan su haka ta kasance Kyakyawan Farko a gidan su dama a mujalla Fara ce Allah ya hada mata Komai tanada kabrin jiki gata kuma Doguwa. Zeinab da Mukhtar sun hadu a École wangari inda yake Matsayin Malami ita kuma daliba anan Soyayyar su ta kullu shiya Fara firta lata Kalmar so dan natsuwar yarinyar tana Birgeshi duk da kudin Mahaifin ta amma batada girman kai sabida halayar Monsieur Mukhtar yasa Zeinab ta amince da shi suka Fara tada Soyayya a cikin École har Basu san rabuwa ko bayada koyawar a makaranta yakan zo Kodan yaga Zeinab Soyayya lai karfi ta shiga tsakanin su ya na Fara mata Maganar Aure Zeinab ta amince da bukatar shi dan Yanda yake kasheta da irin Salan tashi Soyayyar burin ta kawai taga ta zama matar shi, duk da tasan lokacin baizama lalle Mahaifin ta ya mata Aure ba sabida gaba daya a lokacin ne ta shiga 4e kuma shekarar ta sha Bakwai amma haka ta rufe Ido ta tura Mukhtar gidan su dan yasamu Mahaifin ta d'à Maganar. Sai a lokacin ne Mahaifiyar ta ta bijiro da Magana dan Magajiyar ta Tanti MARI Wanda yace a kama mashi Zeinab tin tana karama yana massifar san Zeinab yana so ta zama matar shi a lokacin da Mahaifiyar ta tazo da Maganar shi baya garin Yana Canada inda ya zama Babban Docteur acan, baya ga Shi akwai Yayan Abokan Mahaifin ta saidai Zeinab soyayya ta rufe mata Ido hakan yasa duk ta watsa ma Iyayen ta kasa a ido tace saï Mukhtar. Hakan ba karamin tashin hankali ya jawo bâ anyi ta kai komo ankai ruwa rana sosai saida Alhaji Nafi'ou yaga mai Sunan mama tana neman saka Kanta a hadari dan tayi ikrarin indai akace Za'a Aura mata SAIFULLAHI ne dan Uwan ta to cikin Biyu daya zaifaru kodai ta shiga Duniya ko kuma ta kashe Kanta,bayada wani zabi daya wuce ya bata abinda takeso ya amince Mukhtar ya turo Iyayen shi sun tsaida magana akan a bari tagama 3e inyaso ta Karasa gidan mijin nata saidai ina Mukhtar ya nuna ma Zeinab halin da yake ciki bazai'iya bari harna da wata Shekara ba dan lokacin girma yazo mashi sosai yana da matukar bukatar Mace a wannan lokacin, akaro na Biyu Zeinab ta saké biga kai ga kasa akan ita kawai a mata Auren ta yanzu sawrayin yace idan aka kai wannan lokacin to zaiyi Aure ya kyaleta. Hakan ne yasa Mamar ta ta kara Tsanar Mukhtar sosai dan gani ta yi dagangan ne yake hure kunnuwan Zeinab dan ya ganta karama kuma marar Wayo, Dole aka saka Yanda Zeinab takeso badan Kowa ya soba hatta yan uwan ta babu bai Goyon bayan ta gaba daya dangi sun juyama Zeinab baya idan kacire Mahaifin ta amma Mahaifiyar ta da Tanti Nadiya ma duk sun fita harkar ta Musammam da sukaga Mukhtar cewar Mama sunan shine kadai abin birgewa, shi mummuna ga yawan shekaru ga bayada Kudi kuma Shi ba dan wani ba., haka dai Zeinab Takesa ruwa tana hadiye komi da aka fada mata har Lokacin kawo kaya yayi aka kawo da goro. Akwati Bakwai aka kawo saidai Vide ne saï Kudi da aka azo Jikka Dari Biyar da Goro kasancewar Conjen PAC ya kusa hakan yasa aka saka wata daya da rabi, ba tare da bata lokaci ba ALLAH ya kawoni ranar duk da akwai Wadanda suka fito kiri Kiri suka nuna bakin cikin su da Auran Tanti Mari bata saka Hannun ta bâ a cikin Komai d'à yashafi bikin Zeinab Yayan tane dai tace babu ruwan ta idan sunga dama suje idan basuyi niya ba bazata takura Kowa ba, Saifullahi yashiga damuwa sosai yaji façon rashin Zeinab Komai na Yarinyar yana Birgeshi amma yanzu Tinda tazama ta wani Dole ya Fara cire ta a ranshi. Tin kafin a daura auren su aka turo masu gyaran daki, gidan haya ne ya kama masu su hudu ne a gidan duka suma duk sababbin aure ne Kowa da kewayen sa a cikin Kowane lungu da douche kinshi saï daki ciki da falo , kayan da akama Zeinab basu shiga dakin ba Dole tasa baban ta yasa aka hurhura su aka dauko daidai da sakin su, shagalin biki kawai akayi lura da Mukhtar yayi kamar akwai cin Mutunci a tare da dangin Zeinab yasa yace damu ma abarshi tinda ba al'ada bane saidai duk da haka Mahaifin ta Saïda yayo masu wata Babban Mota cike da kayan Abinci Hatta Lipton da Sucre saida aka saka a ciki haka ma Attarugu da Gishiri babu Abinda aka rage su da shi. Daren ranar da aka kawo Zeinab kokadan Mukhtar bai sawrara mata ba Haushin shi ne ya huce a Kanta kamar Wanda yayi kwana Goma ne baici Komai ba ya kuma samu Abincin mai Ray da lafiya kaga Dole ya masa cin Wulakanci da keta,to haka yama Zeinab sakamakon haka yasa taji ta tsaneshi tsawon kwana Biyu haushin shi ta dinga ji kwana Biyu tayi bata iya zama daidai da tafiya gashi babu Wanda aka turo daga gida haka shima bai turo Kowa ba Sai shi ya taya ta jinyar Kanta, saida aka dauki tsawon sati Zeinab tana gudun Mukhtar dan ba karamar wahala tasha ba Daya shiga ciki ita zata fito idan ya kwanta ita zata tashi saï a kwana na tara ne kadai ya samu y'a shawo Kanta daya ce mata tana cikin tsinuwar Mala'iku da ALLAH sannan ta bashi Hakuri tare da gindaya masa Sharadi akan karya saké mata keta irin ta wacan ranar. Tinda Mukhtar ya Saba da Lasar zumar Zeinab a lokacin ne ya Fara jin wani Azabanben kishin ta yana ratsa gaba daya Illahirin Jikin shi, Kasancewar shi Wanda yake shiga cikin mata da yan mata da Samari yana ganin yanda Rayuwar take tafiya babu Amana wasu Matan auren kamar ba Matan aure ba Yanda suke sheke ayar su hakan ne yasa ya Fara Tinanin Zeinab zata'iya anfani da wayar ta wajen yin sabo wajen aika ta badaidai ba tinda Babbar waya ce K9. Ya karbe puce kinta ya canza mata wani ya kuma hanata bude Wats up da Instagram kin da take acan ta kuma babu sabida ta faran ta mashi,saidai abin na Mukhtar baya yin baya Kullum saidai gaba, gaba daya yanzu Watan su Uku ne da Aure amma Zeinab Kullum cikin Takurar Mukhtar take. 12/01/19 à 22:18 - Mme Sami😘: 💔BASO BANE💔 *Gajeran Labari* Na📚 Samira Harouna (Meerah) 10-15📗 Mukhtar ya hana Zeinab shiga cikin Jama'a duk wani taro na biki ko rassuwa da za'a fada mata baya bari taje saidai idan ya dawo wani lokacin ya kaita da Kanshi Hatta gidan su idan zataje saidai ya kaita y'a dauko ta shima idan zataje nasu gidan shi yake kaita koda bayada dama to zaisab Yanda zaiyi dan ya kaita kuma baitaba bari ta Wuni a canba ko wadanda Suke gida guda yanzu ya Hana ta shiga sashin kowace ace warshi mazan su zasu'iya shigowa a Kowane lokaci su tarada ita dan haka bayaso kamar Yanda ya Hana ta shiga sashin kowace Haka ya Hana ta fitowa tsakar gidan sabida maza zasu'iya Shigowar bazata, ya zama Dole idan Zeinab zata fita ta saka hijaban daya shine yasa aka dinka mata su Wanda suka sawkar mata kasa har suke sharar kasa ga nikab da safar kafa sannan ko nikab tasa bai Yarda ta fito da idan ta waje ba dan yace duk Wanda ya Santa idan ya kalli Idan ta zaigane ta, da wannan tsananin yasa Zeinab duk batajin dadin zaman gidan idan bayanan kadaici ya isheta idan ya dawo gidan saiya kakaro Abinda zaicewa tayi sannan ya mata fada. *Cigaban Labari* tinda tayi Sallah bata kwanta ba yan gyare gyare ta shigayi koda gari ya ida Wayewa abinda yafisan Karyawa dashi shi ta hada mashi Tea babu Madara saï Indomie da Fritte tana idawa ta shiga Wanka har tagama shiryawa baitashi ba, a hankali ta Karasa Kusan gadon saida ta Durkusa cikin Tautausan murya ta Fara shafar kumatun shi tare da fadin" Yallabai Yallabai Safiya tayi Karka Makara" cikin rada take dumin a hankali ya Fara bude Ido yana ganin ta ya saki wani Murmushi tare da mutsutsuka idan shi mikewa yayi zaune a Sawke nunfashi tsaye ta Mike tace" na gama hada ruwan Wanka Abinci ma is ready" Kallanta yayi yana dariya yace" to yaou kuma hada turanceni" gira ta daga masa tana Murmushi tace" to ba Dole naba au zama da ma daukin kanwa shike kawo farin kai" kai ya jinjina mata Alamar eh tare da sawkowa daga kan gadon ya nufi bandaki. Gaban tane kawai keta Faduwa Allah Allah take ya gama cin Abinci su rabu lafiya kafin yace ga Abinda ya Faru, tana ganin ya Mike ya dauki Jakar shi data aje mashi akan Kujera wata ajiyar zuciya ta sawke kafin ta Mike ta rakashi daga iya inda ya mata iyaka daga kofar daki yana ficewa tadawo ta tattare kwanukan ta fita ruwa ta hada ta wanke su sannan ta shiga bandaki ta wanke kamar Yanda ta sabayi Kullum sannan ta komo daki ta Zauna ta Fara kallo, gajiya da tayi yasa ta kwanta daganan bacci ya dauketa. koda ta tashi Sallah Azahar ta farayi kafin ta soya Kwaï da Indomie taci ta koma ta Zauna a haka har Yamma tayi saida taji Matan gidan sun fito tsakar gida suna hira tare da yan aikace aikacen su lekowa kawai tayi suka gaissa ta koma ciki saï Khadija Diya Aisha da bata fi Shekara Biyu va ta shigo tanata wasar ta. Bayan ta kammala aikin ta Wanka tayi kamar Yanda bata Yarda yafa kazanta a Jikin ta har Kanta ta wanke dan tanaso ta kira mai Kitso gobe tazo tamata sabo tinda bata samun damar tafiya koda salon Tsap ta gama shirin ta tana Jiran Shigowar shi, saï bayan Isha'i ya shigo gidan batasan dalilin jimawar ba kuma bata isa ta tambaya ba ko ta tambaya ma zauce shifa namiji ne, Tarbar shi tayi Yanda ya dace bayan duk ya gama abinda ya sabayi ya ci Abinci zaune sukayi akan Kujera 3 siter kallanta yayi sosai kafin yace" waini yanaga saï wani Fari kike kina kara kyaou kodai ammana ajiya ne bansani ba" yayi Maganar ne cikin sakin fuska tare da shafar cikin ta,kunya ce tasa ta rufe Ido tana dariya tare da fadawa kan kafafun shi shafar Kanta ya farayi saidai yanajin lema ya daga Kanta yana mata wani tuhumamman kallo Kallan shi take itama har saida yace"Zeinab ruwa ne a kanki?" kai ta daga masa tana nufin eh fuska daure yace"garin yaya kenan haka ta Faru?" duk da batasan Miyake nufi da tambayo yin nashi ba ce masa tayi" ina so zanyi Kitso gobe kuma ma har nakira mai kitson tace zata zo"kin tabbata?" cikin mamaki tace" eh na Tabbata" OK kawai yace ya maida hankalin sa a TV Zeinab data kasa Fahimtar komi ce masa tayi" El moc Maganar karatu na Har yanzu kaki kace komi fa kaga anbar ni baya sosai?" kare Hade fuska yayi baida niyar amsa mata dan haka ta saké cewa"Dan Allah El moc kataimaka min kabar ni naci gaba da zuwa kar karatu na ya lalace kaga dama ina tsaka da yine" saida ya mata wani Banzan kallo kafin ya Mike tsaye tare da aje remonte kin hannunshi yace" Zeinab ni ba Mahaukaci ne ba zantaba Yarda ki koma Makaranta a haka ma ya muka kare bare kinkoma Makaranta" daki ya shige inda ta bishi tana fadin" amma miyasa Bazan komaba Karka manta fa Alkawari kamin ba zanci gaba da karatu na" juyowa yayi cikin bacin Ray yace" Zeinba kinada damar yin karatu idan kinaso amma fa ba a gida na ba" cike da mamakin Maganar shi tace" kana nufin bazaka cika Alkawari daka Dauka ba, kana nufin Bazan koma Makaranta ba kenan, kana nufin indai zanyi karatu saidai nabar maka gida, kana nufin zaka'iya rabuwa dani akan wannan har Matsalar?" saida ya kalli kwayar Idan ta yace" kwarai kuwa haka nake nufi" Kallan cikin idan shi tayi kafin tace mashi" aiko zanbar gidan ka dan bazan'iya datse karatu naba, haba wannan ma ai abin kunya ne ace kana daya daga cikin Wadanda suke cin anfani Ilimi amma ace ina matar ka bazanyi karatu ba bayan kafi Kowa sanin yanke karatu na ne nayi sabida na aure ka bazaiyiyu ba gaskiya" Kafada ya daga tare da fadin" Tempie pour toi" tare da hayewa kan gadon ya barta nan. Tajima kafin tayi bacci Har saida Zuciyar ta ta bata hakuri akan ta Zauna gidan mijinta Watakila hakan Shine mafi Alkairi a gareta shiyasa ma ALLAH ya Kaddara auren ta da Wuri kuma ma ai ance darajar mace gidan mijin ta,sannan ta Tina da furucin Mahaifiyar ta da tace duk ranar da tazo gida da sunan yaji to ina kuma zatabar gidan Mahaifin su nabar Abada, uwa Uba kuma ace sakin ta yayi dan haka zata hakura ta Zauna duk da tasan akwai kalubale sosai dan tasan Dole Mahaifin ta zaifara mata magana dama kuma magajinta NAZIR ya fada mata cewa Baban yasa mata Ido ne kawai yaga iya gudun ruwan ta,da wannan Tinani bacci ya dauketa. kamar Yanda ta Saba bata koma bacci ba bayan sunyi Sallah hankali kwance ta kammala Soyayyar doya da Kwaï da Miyar sardine da lemon Orange, haka tayi Wanka gaba daya batajin dadin Jikin ta kasala duk ta rufeta gashi idan ta yi tsaye saitaji kamar jiri zaidebeta ya kayar da ita haka ta ida ta fito,tana gaban madubi tana shiryawa ta tsinkaye shi ta madubi ya duba wayar sa ya gyara kwanciyar shi hakan na nufin bayada fita da Wuri tana gamawa falo ta koma ta Zauna tana Kallan TV bata jima ba taji ana kwankwasa kofar su tinnin ta Khadija ce dan haka ta dauki Hijabin ta iya Gwiwa ta dora akan Doguwar rigar Atanfar budewa tayi tare da leko kai saidai va Khadija bace Jamilou ne Baban ta cikin Sawri tace" ina kwana?" lafiya kalaw madame, ko mai gidan yana ciki?" kai ta daga Alamar eh sannan yace mata" OK dan Allah ko zaki mishi magana zanje biyan kudin wuta ne dama" kai ta saké daga masa dan hajinta ya mutsawa Sukeyi tana Tsoron kar Mukhtar ya ganta komowa tayi koda taga har yanzu yana bacci saida taji Wani sanhi a hankali kamar Yanda ta Saba ta shinshi daga baccin saida ya tashi zaune yace" tinda kikaga banta shia kinsan kenan banfita da Wuri miyasa zaki tasheni" dama Jamil ne yace namaka magana" mamaki ne ya bayyana a fuskar shi sannan yace" Bangane ba wane Jamil kin?" Jamil baban Khadija " What! Ya fada iya Karfin shi yana sawkowa daga kan gadon" Zeinab kunnuwa nane basuji daidai ba Komai kina nufin ke kika bude kofar kuma a haka kikaje fuskar ki a bude?" saï lokacin Zeinab ta gane baram baramar da tayi shiru tayi tana Jiran hukuncin ta jikinta duk ya dauki bari"dake nake magana kinajina kinyi shiru" Tsawar daya mata ce tasa ta ja da baya tana fadin" Dan Allah Kayi Hakuri El moc walahi bansan shibane shiyasss''' gigitancen marin daya sawka akan fuskar ta ne yasa bata Karasa ba dafe Kunci tayi duk maganganun daya fada mata bataji ko Daya bâ sabida ganinta da jinta duk sun dauke. fita yayi inda ta fada kan gado Zuciyar ta na mata kuna, yana shigo y'a saké dora fadan daga inda ya tsaya bata kula shiba har yayi ya gajiya ya shirya ko takan Abincin datayi baibi ba ya fita. Zazzabi ne ya rufe ta hakan yasa koda mai kitso tazo saï manya tace ta mata dan dai karta taxi hakan nan, haka ta wuni da Zazzabi gashi batayi ajiyar koda Paracétamol ba kuma babu yaro da zaisawo mata tayi Kiran wayar Mukhtar amma bai Dauka ba dan Tinanin shi hakuri ne zata bashi da haka ta galabaita da Zazzabi nan sosai,baidawo gidan ba saï misalin 21:40 ba tare da ya kula taba ya shiga yayi wanka saida yagama kimtsawa sannan ya zaune kusa da Ita fuska daure yace"ko zaki'iya kawomin Abinci na?" faruwar gaban tane taji ya kara tsananta cikin Sarkewar murya tace" Kayi Hakuri banda gaba nayi ta Kiran ka dan infada maka banda lafiya amma Baka Dauka ba" wani kallo ya watsa mata yace" to yanzu ya kikeso ayi kenan a wannan Daren yanzu ina zan samu Abinda zanci?" cikin Sanhin murya tace" Kayi Hakuri dan Allah bari na soja maka koda kwaine da Indomie tinda Jikin ma yayi Sawki" batajira abinda zaice ba ta wuce gaz kinta Fara fiddawa kafin ta Fara aikin gadandan. 12/01/19 à 22:18 - Mme Sami😘: 💔BASO BANE💔 *Gajeran Labari* Na📚 Samira Harouna 15-20📗 Indomie da Kwaï ta hada mashi gaban shi ta dire tiren ta dauko Ruwa da exotic a yar karamar frige kin su ta aje mashi kasa ya sawko ya mike kafa daya ya fara ci zaune tayi itama kasa tana Kallan shi, kallanta yayi yace" kefa bazaki ci ba ne?" kai ta Girgiza gira ya daga Alamar mamaki yace" mikika ci to?" murya kasa kasa tace" Komai kawai dai bana san ci ne?" ajiye Cokalin Hannun shi yayi yace" kawai ba Magana bace kifadamin dalilin da yasa bazakici ba" wuyanta tanan shafa kafin ta Kalleshi da Manyan idanun ta wanda suka cika da Kwalla tace" banajin dadin jikina" matsawa yayi kusa da ita ya jawota tare da dora hannunshi akan wuyanta Zafi sosai yaji kwalo ido yayi cikin razani yace" Zeinab haka abin yayi tsanani dama amma kikayi shiru kikaki fadamin kinaso ki illatar min da kanki, kinga tashi mutafi Asibiti ya duba minke ko Allura ce a miki" tsaye ya mike yana kokarin daga ta kara Narkewa tayi da taji maganar Allura cikin shagwaba tace" a'a kabar shi ni basai munje Asibiti ba ma kawai dai kasamomin magani idan nasha zan warke" girgiza kai yayi yace" a'a ban yarda ba tashi mutafi kawai idan kika sha Magani zata iya dawowa ai dan haka kitashi kawai matsoraciya allurar ce bakiso Shiyasa" hawaye ne suka fara taho mata ganin haka yasa yace" to Shikenan naji zantafi na Siyo maki amma kisani idan har ta dawo to saidai mutafi Asibiti dan Bazan Yarda da wannan Shaye Shaye Maganin ba barkatai" kai ta daga Alamar ta Yarda haka ya fita dan nemo mata Maganin, ganin ya fita ta rufe mashi Abincin shi tana mai fadada murmushin fuskar ta har yanzu tana tsananin san Mukhtar kuma shima yana Santa Kishi ne kawai gareshi wanda yake san kaishi ya baro shi. bayan ya dawo ya kawo mata maganin tasha taci Sanduite kin daya taho mata da shi dan karta kwanta da yinwa shikuma ya kammala Cin Abincin shi kafin nan suka kwanta. kida sukayi Sallah bai bari tayi Wani aiki ba yace ta kwanta ta huta hakika taji dadi sosai akan kulawar da ya nuna mata daren jiya zuwa yanzu, bacci tayi sosai shikuma da gari ya waye Falo ya Zauna yana kallo dan bai cika baccin safe ba kuma yaou bashi Cour ganin Goma na shirin yi yasa ya tada Zeinab tare suka shiga Wanka suka fito Suka shirya bakin Zeinab Yaki rufuwa dan Rabon da haka ta faru harta manta suna fitowa Mukhtar da kanshi ya buga Kwaï ya soya masu tare dankalin turawa ya hada masu Tea sannan sukayi break. Kallanta yayi yace" tashi ki shirya zan kaiki gida daganan na wuce dan innabar ki nan zakiyita bawa kanki wahala ne ki dauko waccen aiki ki dauko waccen" farin Ciki ne ya bayyana a fuskar ta saidai tinawa da tayi ya tsani idan zata fita yaga tana zumudi hakan yasa ta hadiye farin cikin ta cike da san basarwa tace" amma da ka barni ai idan kace karnayi aikin ai bazan yiba" Wani irin murmuchi yayi Wanda shikadai yasab fassara shi yace" kinga kiyi abinda nace kawai" to " tafada ta shiga kuryar daki saida ta daka Wani Tsalle tare da jujjuyawa tana fadin" wai bayan wata uku yaou zanje gidan mu na wuni" kayanta ta dauko hijab safar kafa da nikab wacce ko ido ba'a gani ta saka Tsap ta fito ta sameshi mikewa yayi yazo kusa da ita saida ya duko da kanshi ga Hijabin ta ya shinshina yaji babu kamshin turare saidai kamshin da yazama kamar dashi Aka haifeta alama yamata da kai sutafi, bin bayan shi tayi tana fada a ranta*El moc kenan taya kake Tinanin zan saka turare ai saidai in banasan tafiya* da haka suka kama hanyar gidan su Zeinab Tinanin ta duk ya koma ga Mahaifiyar ta ko Wace irin tarba zata mata wacce ko tare da Mukhtar suka tafi kai tsaye sudawo sai Ray ya bace bare kuma yaou zata wuni, da haka suka kai gidan Mukhtar ya tabbatar yanzu Mahaifin Zeinab baya gida Mahaifiyar ta kuma bazaiji dadin abinda zai fito Daga bakin taba dan haka ma bai shiga ba yace ta gaishe su idan ya dawo daukar ta zaishiga su gaissa, bata damuba itama dan tasan ranshi zaibace idan yashiga, har ta juya zata shiga ya kira sunanta " Zeinab " juyowa tayi tare da tahowa Hannu ya tara mata yace" wayar ki zakiban" cike da mamaki tace" yaya waya ta kuma?" eh ita nake nufi ko dan bani nasaya ba banda yancin da zan amsa?" cikin inda inda tace" a'a Walahi na daiyi mamaki ne da kace inbaka" tayar da Bâbur kinshi yayi Hannu tasa sacs kinta ta fiddo ta Mika mashi, karbar wayar yayi yasa Aljihu ya saké karbar sacs kin tata dubawa yayi dan yaga abinda ke ciki daga makullin dakin su sai yan canjin ta sai karamin littafin Husnul Muslim, Wani banzan kallo ya bita da shi ya burka Bâbur kin shi ya barta nan kai ta girgiza cikin rashin jin dadi ta shiga cikin Gidan. Zaune suke a Babban Falon da yasha kayan more rayuwa kala kala da gudu Fadila ta tarbe ta tana Murnar ganin ta Dauke ta tayi sama sunata murna kafin ta karaso da ita da karfi ta fada saman Kujera cikn Massifa Mahaifiyar tata tace" wannan wane Iskancin ne kuma idan da haka ake zaunawa da karfi da ke zaki samu Kujerun a haka, koda yake ma na manta Ashe Bakuda irin su Dole idan kikazo kiyi haka Kodan kiji laushi" ta karashe maganar tare da tashi ta shige dakin ta tabar sunan, binta tayi da kallo kafin ta kalli tantin tata tace" Tanti ina kwana" lafiya kalaw hajia ya kike ya gida da mai Gidan?" lafiya kalaw Tanti ina su Yusra duk sun tafi École ki?" duk suntafi saidai idan sun dawo" Tanti Abba fa ko ya fita?" ah ai neman kinsan bazaki samu Abban kiba yanzu ana wajen kujuba kujuba" dariya tayi tace" ai yaou ina nan har sai Abba ya dawo" da gaske kike kinga ko ai da kin kyaouta dan kullum maganar ki yake yana san ganin ki shima" nasani dama Tanti zanjira har sai ya dawo" to kinga kafinan tashi kije ki gaida Mahaifiyar ki kinji ko" tashi tayi rike da hannun Fadila suka shiga zaune ta samu Mahaifiyar ta ta a bakin gado tana danna wayar ta tin kafin ta karaso ta Mike tsaye cikin fada ta fara nuna ta da Hannu tana fadin" wuce karki shigomin daki , ko ban fada maki bani ba ke ba ki ficemin daga daki kodai ki koma Gidan tsinannan mijin naki ko kuma kije ki Zauna can amma ni va Wuri na kika zoba Shashasha kawai yar dadi miji wacce ta zabi namiji akan farin cikin Iyayen ta kije zaki gani walahi tinda kikace Iyayen ki Bazasu rintsa ba sabida bakin cikin ki to walahi kema bazaki rintsava kuma bazaki samu kwanciyar hankali Gidan auren kiba har sai kin gudo da da kafar ki ki amshi zabin mu lokacin kuma tu est déjà trop tard" rufe kofar Dakin ta tayi da karfi Dole Zeinab ta dado Falo ta zauna Kuka ta fariyi sai Tanti ta ta fara rarrashin ta cikin Kuka tace" haba Tanti kijifa abinda mama take fadamin a Matsayin ta na wacce ta Haifi bakin ta ba karamar Massifa a gareni bakin ta daya tak daya yake da bakin baba so goma amma duk da haka har yanzu bansamu sa albarkar ta ba kullum sai mummunan fatan da baki takemin har tana fatan kar nasamu kwanciyar hankali a Gidan da Kowa mace anan ne take takama dashi take kuma fatan samsamu ingantaciyar soyayya da farin cikin mai dorewa" ( ALLAH Sarki ). da kyar ta shawo Kanta ta kwantar mata da hankali haka ta wuni a dakin tantin ta kwance Tanti ta lura da Zeinab kamar tanada ciki saidai bata fada mata ba gani da tayi ita kokadan babu wannan a ranta, har bayan Sallah Magriba sannan Abba ya dawo lokacin ne Zeinab taji dadi dan tinda ta shiga dakin Abban bata fito ba Hira sosai Sukeyi suna nishadi na da da Uba Abba ya tambaye ta zaman Gidan nata tace babu Komai tare da Abba sukaci Abinci har saida Mukhtar yazo lokacin ne fadila tace da ita Za'aje saida Zeinab tayi ta Rarrashi sannan Tanti tabari suka tafi tare da sa bakin Abba, ta shiga dan tama mama ban kwana saidai dakin nata a rufe bata bari ta ganta ba har suka tafi... 12/01/19 à 22:21 - Mme Sami😘: 💔BA SO BANE💔 *Gajeran Labari* 👉 Yan Uwa ku gafarce ni a bisa kuskuren da nayi👏👏👏 Akasi ne👈 Na📚 Samira Harouna 20-25📗 Kayan shi ya shiga cirewa yanaso yayi Wanka cike da Ladabi Zeinab tace masa" Grand Frère mikake so Kaci na dafa maka dan ni naci Abinci tare da Abba,banajin yinwa" Murmushi yayi yace" ahan kenan wayo kikamin kikaci Abinci tare da Abba kika manta da mijin ki, ni kuma lokacin da zanci nawa abincin tare da Inna saida na tinaki a Rayna nace ko kinci abinci yanzu sabida ina Tsoron Allah ya kamani da Hakkin ki" dariya ce ta kwace ma Zeinab tace" oho kenan bani kadai ba za'a hukunta ba harda kaima" umm! to shikenan nayafe maki kema nasan kinyafe ko?" kai ta daga masa alamar eh sannan ta saké cewa" to fadamin mizakaci?" a'a kibarshi nima naci abinci kije ki huta kawai, ya jikin naki da sawki dai ko?" umm da Sawki Sosai ma" to yayi kyaou" ya fada lokacin da yake kokarin fita daga dakin. bayan ya fito ita ma ta shiga wankan taayi sannan sukayi zaune suna kallo har zuwa karfe 23:30 kafin suka kwanta ita da fadila a kuryar daki shi kuma a Falo akan karamar katifar da Zeinab ta shinfida mashi, har gari ya waye. Zeinab nata hada hadar abin Karin kummalo Mukhtar na shiri shima sai fadila dake tare da Zeinab tana wasa Kiran wayar ta akayi sai lokacin Mukhtar ya Tina baimaida ma Zeinab wayar taba dan haka yafito daga dakin ya Mika mata dan yaga Sunan kawar tane Haulatou, cike da mamakin kiran da Haulat kin ta mata a Safiyar nan ta dauka da Sallamar ta sannan suka gaissa, a daya bangaren ne akace, Haulat" dama banace maki idan nazo zan kiraki nabaki su Muhssina ba to gasu sai kifada masu Abinda ya hanaki dawowa école tinda ni nace masu dadi aure ne amma sunki yarda" Zeinab " ni dai narasa wannan jaraba da Kuka takuramin sai kunji abinda ya hanani dawowa, nace maku Zandawo nanbada dadewa ba Insha Allah" Haulat" banga alama ba aiba yaou kikayi aure ba yanzu ma haka nasan anfara amaye amaye kinga monsieur zaice sai kin haihu idan kika haihu yace sai kin yaye kafin nan kinsamu Wani cikin da haka zaiyita miki yawo da hankali walahi" Zeinab " to inma hakane saime Mijina nefa kuma ina san shi ina san haihuwa da shi kinga ai ba Wani Abu bane, kinga ni kibani sawran mugaissa kawai aiki nake" Muhssina Aka ba suka gaissa sosai suna cikin magana wani dan ajinsu Okasha ya shigo Haulat ce ta fada mashi suna magana da Mutumniyar shi Zeinab cikin zumudi ya roki Alfarma abashi su gaissa, sun gaissa da Zeinab jikin ta duk a darare tanayi tana juyawa cikin alamun rashin gaskiya tace" Okasha dan Allah kabawa Haulat Waya" cikin Zolaya yace" Zeinab kin manta da karatu ko, Zanzo Gidan ki da kaina nama Monsieur kin magana akan ya barki kidawo Makaranta Cin amarcin ya isa Haka nan" cikin sawri Zeinab harda alama da Hannu kamar tana gaban shi tace" a'a Dan Allah ka rufamin Asiri karkazo kaidai kabari nadawo nace, kawai kabata wayar" tin kafin ya Mika mata Zeinab na juyowa ta Sawke idan ta akan Mukhtar daya Hade Ray kamar Bani shedan sakin wayar tayi ta fadi daga Hannun ta jikin tane ya fara Rawa ganin haka yasa Mukhtar ya tako har inda take kafin tace wani Abu ya Dauke ta da Wawan mari kuncinta kawai ta dafe batare da tayi kara ba, Fadila dake zaune tana wasa Tsoro ne ya kamata da karfi ta fashe da Kuka ta Rungume Zeinab iya Karfin ta wucewa yayi ya barta tsaye va tare da yace kala ba. Tinda ya fita bai saké dawowa Gidan ba, da kyar Zeinab ta Rarrashi Fadila Kuka ta dingayi ita sai anmaida ta gida har saida ta goyata sannan tayi Bacci, da Rana sai gida Mukhtar yaje yaci abinci Inna ta lura yana cikin damuwa dan haka saida ya gama ya nutsu cikin kwanciyar hankali tace" Mukhtar lafiya Miyake damunka naga gaba daya ranka a bace yake?" saida ya wani cilla Ido kafin yace" babu Komai Inna kawai dai wani dan karamin soucis ne" Mukhtar nifa banasan ganin ka cikin irin Wannan yanayin, banaso fa kullum ina gaya maka Sawrin Fushi babu Abinda yake haifarwa sai aikin da nasani,haka ma Sawrin Hannu wata rana Zai'iya jefaka cikin matsala Dan Allah karage wannan zafin Zuciyar kaji ko mai Babban suna" to kawai ya fada ya tashi ya Tafiyar shi. Bayan Sallah Isha'i ya dawo gidan shima dan yasan zai maida Fadila gida ne koda yazo suka tafi dagacan baidawo ba sai 00:30 Zeinab harta gaji da Zuba ido bacci ya Dauke ta Akan Kujera bai ko bi ta Kanta ba ya shiga ya fito yayi wanka ya kimtsa yayi Kwanciyar shi a daki, koda Zeinab ta Farka Karfe 06: 10 dan haka ta farayin Sallah bayan ta ida ta shiga kuryar daki inda ta sameshi zaune yana lazimi Zaune tayi a bakin gado tana kallo har ya gama, gabanta Faduwa kawai yakeyi ga Zuciyar ta daketa Rawa tana bugawa kamar zata fasa Kirjinta ta ta fito waje kasa ta durkushe cikin Sarkewar murya tace" El moc Dan Allah kayi,,,,,,mtssss! Dogon Tsaki yaja tare da tashi ya koma falo, bin bayan shi tayi jiki a sanyaye ta saké durkusawa zatayi magana cikin bacin Ray da tijara yace" da zaki Adana hakuri watakila tamiki anfani nan gaba amma ba yanzu ba karki soma cewa zaki bani hakuri dan hakan sai yafi konamin ray, Zeinab walahi kinbani mamaki kinci Amana ta bantaba tinatib haka daga gareki ba" wucewa yayi kurya ya bartanan durkushe Kuka ta fashe da shi dan shine kadai mafita data rage mata. 12/01/19 à 22:21 - Mme Sami😘: 💔BA SO BANE💔 *Gajeran Labari* Na📚 Samira Harouna 25-30📗 Tana cikin hada abin Karya'wa ya fito cikin shirin shi ya fita bâ'tare da'ya kulata ba,tsayar da aikin tayi ta koma d'aki ta'aza wani sabon Kuka, har'saida rana ta fito sosai kafin ta tashi ta samu abin Karya'wa taci. Haka ta'wuni jikin'ta d'uk babu k'wari sai kasala da tsargin yawu take har'dare Mukhtar bai'dawo ba,koda ya shigo kamar kullum wanka yayi ya kwanta a'binshi, wasu Hadan'dun kayan bacci Zeinab tasa'ka inda yake k'wance ta fuskan'ta ta saké durkusawa dan'taba shi hakuri,Yana ganin haka ya sawko daga kan Gadon dan'yabar mata d'akin, da sawri ta Mike tsaye ta'sha ga'banshi tare da rike hannuwan shi duka biyu'n, k'asa magana tayi sai ido data zuba'mashi cikin daka'kkiyar murya yace, "Sake'ni " kai'ta girgiza masa cikin Kuka tace" dan Allah Grand Frère kayi Hakuri ka sawra'reni nafada maka abinda ya faru" kallan'ta yayi sosai kafin yace" ki'fadamin me Zeinab, kinga,,,,, bai'karasa ba Zeinab ta fada jikin'shi tana Kuka, cikin zafin nama ya dago da kan'ta daga jikin'shi bakin'shi ya saka a'nata ya fara tsutsa da iya karfin'shi , ta'ke suka fita hayyacin'su da haka Mukhtar ya manta da Komai sabida Zumar Zeinab da'yake lassawa. Yaou Zeinab da'kanta ta'ke saka'ma mijin'ta kaya har'takai ga Balla masa botle 'kin rigar'shi ba'tare da ya kalleta'ba, ta lura da hakan saidai ta rasa dalili, ko kunya ya'keji? Ko'ko hushin'ne har'yanzu? Oho! Ba'tare da ta kalleshi'ba ita'ma cikin Tautausan murya tace" Grand Frère, i am very Sorry for Evrything's, is not my Faulte, but I promise i can't repeat' again by God Grâce" tinda tafa'ra maganar yake kallan'ta cikin tsananin mamaki, dan baiyi Tinanin zata'iya turanci haka'ba, Baisan Sanda dariya ta kubuce masa ba kallan'ta yayi yace" Zeinab dama kin'iya turanci haka?", "Ashe'dai Zamuje da'ke" bata kalli kwayar idan'shi ba tace" to ai ya'zama Dole na na'iya ina matar theather" kai ya girgiza yace" haka'ne kam, gaskiya kinyi kokari sosai" Thank you" Murmushi yayi yace" da'alama an'kusa daina haussa a gidan'an ko?" tare sukayi dariya har'suka Karasa Falo suka gama Karyawa har'ya tashi zai'fita sannan ya kalli Zeinab da k'yaou yace" Zeinab ina sanki Dan Allah ki'kiyaye duk wani abu da zai'dinga sani Sawrin Hushi akan'ki,kinji" Insha Allah El Moc,bazan'sake ba" Good" ya fada tare da sumbatar'ta a baki, ta rakashi har'ya fita sannan ta dawo d'aki, farin ciki karmar zai'kashe ta Soyayyar Mukhtar na'kara ratsa duk ilahirin jikin'ta, a cikin farin ciki ta wuni ranar, Mukhtar ya dawo da rana ya'ci abinci ya saké fita, haka'ma dare sunyi'shi cikin farin ciki. Washe Gari, Zeinab ce k'wance akan Kujera tana kallo bacci yana'san d'aukar ta, NAZIRU Yaya ne a wajen'ta wanda take bima. k'wank'wasa mata k'ofa, cikin kasala ta tashi ta b'ude, da farin ciki ta tarbe'shi suka gaissa ya shigo ciki, bayan sun'gaissa ya fada mata Haihuwar Kanwar ta'ta Diya ta Biyu ga Tanti Nadiya wato AIDA. Tayi farin ciki sosai ta'kuma ce mashi zata'je ta'gano Bébé, a nan'ne taga yar karamar wayar'shi TECNO tace ya bata, bai tsaya lissafi'ba ya karbi tata ta amshi tashi, a ganin'ta tarage matsalar da'ke shiga tsakanin ta da Mukhtar Musammam a'kan Waya. Saida ta'bari yayi d'uk abinda ya dace ta'tabbatar ya samu Nutsuwa sannan ta'fada masa Haihuwar Aïda, ya taya'ta murna sosai ya kuma'ce ta'shirya gobe tinda baya fita da Wuri idan zai'fita sai su fita tare, murna sosai Zeinab tayi dan batayi Tinanin haka'ba, sai lokacin ne ta nuna ma shi sabuwar wayar'ta, budar bakin shi cewa ya'yi.... "Sabida Abban'ki ya saya maki ita shiyasa bazaki'iya shawar'ta taba,ko kijira umani'na?" cikin sauka'kar muryar'ta tace" kayi Hakuri Dan Allah, ko'kadan ba haka'ba bane" ba'tare da'ya kalle'ta ba yace" to miyasa kika canza'ta?" cikin Fara'a tace" naga muna samun matsala ne da waccen shiyasa na sauya'ta" wani Shu'umin Murmushi yayi yace" Zeinab a'she har'yanzu baki'da Wayo kur'ciya na damun'ki, in'banda abinki Waya ai waya'ce, zaki kira da wannan za'a kira'ki, zakiyi message da'ita za'ayi miki, to miye banban'ci a ciki, kinga Zeinab ni matsala'ta bawai da waya bane a'a da'ke ne ke kanki gaba daya" maida kallan'shi yayi ga TV yana kallo, Zeinab kam ta ma rasa mi'zata ce dan haka ta yi shiru har Lokacin k'wanciyar su yayi basu kara wata magana'ba ba. K'oda suka tashi da safe kamar ba suba cikin farin ciki sukayi w'anka tare s'uka shirya tare sannan sukayi break, bayan nan suka kama hanyar gidan Aïda, har kofar gida Mukhtar ya'aje ta bayan ta sawka yace mata" Zeinab ki'kula da k'anki ki'rike min Amanar k'anki, sannan ban'yarda ba kije ki'cire hijab kiyi'ta yawo haka'nan a cikin gida,bare kuma ki'fito waje, kinji'ko?" kai'ta girgiza tace" amma Grand Frère ai'naga d'uk mata'ne a ciki ko?" Eh! Mata'ne amma yanzu mata nawa ki'ka sani masu kamar maza, suna biyan bukata da yan'uwan su mata, kedai kiyi abinda nace kawai" cike da Gamsuwa tace" Insha Allah zan'kula maka da kaina" OK prend bien soin de toi,compris?" Murmushi ta'sakar masa duk'da ba ganin fuskar'ta yake'ba,sannan tace" J'ai Compris " har'saida ta shiga ciki sannan ya tayar da Bâbur kin'shi ya tafi. Koda ta'shiga ta samu sawran yan uwan'ta duka suna'ta hira, suna ganin'ta suka sheke da dariya, haushi'ne ya kamata dan'tasan da ita suke saidai abin takaicin d'uk kannan'tane babu sa'an ta a cikin su dan haka ta ki kula'su, saida suka gaissa da Aida ta'karbi Jaririyar tana mata wasa, FAUZIYA cike da Raini tace" haba Zeinab wai'ke dan Allah a'cikin gidan'ma bazaki hidda kayan'an kisha Iska ba duk kinbi kin'rufe jikin'ki ana Rumtuma wannan zafin" kafar Zeinab ta'jawo ta cire mata safar kafar'ta tana shirin cire mata hijab Zeinab tace" ke Dan Allah ki'rabu dani ina ruwan'ki ne?" baki saké Fauziya tace" ah! Kema ya koya'maki wannan mur'tukewar ko,to Allah ya shirya'ku" Zeinab ce tace" Ameen idan da gaske ki'ke" Aïda dake'ta masu dariya tace" shi'kenan Hade Ray yake Fauziya?" cike da kara kambama maganar tace" kam,walahi sai kingan'shi a école baya dariya sai yaga'dama, ko Murmushi bai'cika yiba walahi, tinda Zeinab tabar école ya sauya'mamu" wani irin dadi'ne ya kume Zeinab hakan ya tabbatar mata mijin'ta Yana kula mata kan'shi ko bata tare da'shi, Aïda ce tace" yo'ai taji dadin'ta walahi, yaou ace kasa'mu wanda zai'bada shedar mijin'ka baya kula mata a waje ai'ba Karamin abu bane, da'nice ita da'naji dadi walahi" Zeinab ce tace" Voilà Yer Uwa fada'mata dai, ita dan bata'san mi'ake cema miji'ba" Tsaki Fauziya tayi tace" kudai kuka'sani kishin tsiya ne da'ku shiyasa, to mima zamu'yi da mazajen na'ku, daga mai tsoho sai'me Katon kai kamar dan gwara'wa" duk'da magana'ce ta fada'masu amma bai'hana suka dara'ba haka sukaci'gaba da hirar'su har yamma. 12/01/19 à 22:21 - Mme Sami😘: 💔BA SO BANE💔 *Gajeran Labari* Na📚 Samira Harouna 30-35📗 Sai'da suka kammala ma Aida d'uk aikin gidan sannan Zeinab ta shirya ta Zauna ta'na Jiran zuwan Mukhtar, lokacin da yazo ya shiga ciki ya'ga Jariri sannan suka fito, a kofar Gidan suka'ci karo da Maman Zeinab tare da Tanti sun'zo ganin bébé su'ma, saida Mukhtar ya Durkusa dan girma'mawa ya gaishe'su amma Mama tayi banza da'shi,Zeinab ma gaishe da ita ta yi amma budar bakin ta cewa tayi" ke! bance ki'fita harka'ta ba idan ban wuni ba da zaki ganni?" kafin Zeinab tayi magana Mama tace" Dan Allah gafara'cen Sakariya k'awai" wuce'wa tayi tabar'su nan sai Tanti tace" Dan Allah kuyi hakuri kunji kar'ranku ya'bace, wata rana sai labari" godiya suka'yi suka wuce, Zeinab kamar ta yi Kuka takeji, ace sabida ka auri Wanda ranka ke'so shike'nan sai ka zama Abokin gabar Mahaifiyar ka, da haka har suka'kai gida babu wanda yayi magana a cikin'su... saida tadan hada mashi Abinci mai s'awkin sarrafawa sannan sukayi kallo suka kwanta. Washe gari, Zeinab ita kadai'ce zaune a d'aki ta'gaji da zama sosai, hakan yasa ta sanyo hijabin'ta ta fito tsakar gida, su AISHATOU da ABIDA ta samu suna'ta hirar'su saida suka gaissa sannan ta Zauna akan Tabarma suka fara taba hira cikin nishadi...., Karar Bâbur kin da Zeinab taji'ne yasa ta tashi da gudu ko ta'kalama bata tsaya d'auka ba ta rumtuma a guje da k'aton hijabin'ta kamar zata ta'shi sama, d'aki ta'shiga ta cire Hijabin da s'awri tayi zaune kamar ba ita'ba, shiru shiru babu Mukhtar babu labarin sa fito'wa tayi filin'ta anan taji muryar SANI hakan ya tabbatar mata da Mijin Abida ne ya shigo, ajiyar zuciya ta s'awke ta koma d'aki ta zauna, dan k'unyar saké fita ta'keji, su Aishatou Kallan mamaki su'kabi Zeinab da'shi ,sauda su kaga Sani ya shigo suka fahimci abinda Zeinab ta'guje ma, ta d'auka mijin ta'ne, sun jinjina Al'amarin sosai hakan yasa suka jima suna hira a'kan zaman Zeinab da Mukhtar cikin murya kasa kasa. Ta kammala shirin'ta Shigo'war shi k'awai ta'ke jira, ta najin Bâbur kin'shi ta tafi'to ta tarbe sa d'aki suka shiga ya Zauna ta kawo masa Ruwa, zaune tayi tana kallan'sa kafin ya kalle'ta yace" wayar ki?" mike'wa tayi ta d'auko wayar ta Mika mashi ba'tare da taji Wani Abu a ranta ba dan hakan ya zamar mata jiki, saida ya duba Kap kafin ya kalle'ta yace" Zeinab kina goge abu a wayar nan ko?" cikin ladabi tace" a'a wallahi ban'taba ba,tinda na'san kana dubawa" kin Tabbata?" eh!" ka'fada ya daga yace" Allah ya'sa da gaske ne" Murmushi kawai ta'yi, Abinci ta k'awo masa ya'ci sannan ya yi d'uk abinda ya saba'yi. Abinda Zeinab bata'taba tinani ba'ne ya Faru, batayi zatan Mukhtar zai'sake barin ta taje gidan Aida ba idan bâ ranar suna ba,amma k'o'da ya shirya zai'fita yace ta tashi su'tafi tare, farin ciki baya misaltuwa wajen Zeinab har suka'kai gidan bakin'ta bude yake. Ta samu su WASILA da ANISSA a gidan kannan Saif, gaishe'su tayi amma su'kayi banza da ita, ita'ma bata saké kula suba dan suma suna cikin makiyan'su, ta d'auka abin zai'tsaya iya haka amma ina sai suka fara mata habaici iri iri, duk tayi banza da'su Wasila ce tace" humm! ai wallahi d'uk wanda yace baya k'aunar mu, to banga dalilin da zai'sa muci gaba da zama da'shi ba" Anissa ce tace" ah to ai'ke ki'ka k'ula ma da tsiyar ta wallahi, dan'ni idan na raina Kassuwa ko sabtun ta bana'ci, ita bata zabi Namiji a'kan yan uwa ba?" to wallahi muje zuwa in'dai mutan'mune zasu mata halin na'su" Wasila ce ta harari Zeinab sannan tace" ta'ina zan'iya kwana Mahaifiya ta na hushi da'ni, ai bazan'iya ba, amma ita dadi miji babu ruwan'ta Mahaifiya na kwana da bakin cikin ta amma ita ko a jikin'ta dan H'auka" Tsaki su'kayi a tare, hakan ba karamin Sosa ran Zeinab yayi'ba, cikin tattausan murya tace" babu Mahaifiyar da'take kwana da bakin cikin yayan'ta Musammam ma ni da na zama Auta a wajen'ta, ku yan uwa na'ne Dan Allah ku rike girman'ku" Anissa da'ma jira ta'ke dan haka ta Mike cikin Massifa tace" ke Zeinab wa'kike fadma wannan maganar,?" autar banza autar wofi tinda ki'kasa sharewa Mahaifiyar ki hawayen'ta ki nuna baki k'aunar ta ita da yan uwan'ta" Zeinab bata kula su'ba har Allah ya k'awo Maman ta gidan tazo ta k'awo ma Aïda Maganin nono, tambayar su tayi miha'ke faruwa, anan suka fada mata, maimakon ta k'ashe Wutar sai tace" Auta fa ki'ka ce, ai ni tini nayi Wuri na aje'ki da zaki cire kanki a sahu'n yaya'na da yafi miki Alkairi, ai Tinda kina nuna kinfi'san wannan banzan mijin naki akai'na, nima na'daina sanki dan haka kiji ki kara'ji ni Ramatou wallahi babau'ni babbu'ke", kuka Zeinab ta'fara sosai hakan yasa Mama ta saké cewa" na'fada maki ki dai'na shiga har'kata da na yaya'na dayafi'miki" cikin bacin Ray Zeinab ta tashi dama bata'aje Komai ba tinda tazo ficewa tayi tabar gidan tana kuka, saida ta fita ta Tina Mukhtar ya kawo'ta, Adaidaita ta tare ta shiga kai tsaye gida ta tafi, tinda ta shiga d'aki suka ta saké a'zawa sabo tsawon lokaci. 12/01/19 à 22:21 - Mme Sami😘: 💔BA SO BANE💔 *Gajeran Labari* Na📚 Samira Harouna 35-40📗 Haka ta wuni jikin ta d'uk babu k'wari sai kasala haka har takammala ai'kinta, tana gama shirya'wa k'wance tayi a'kan gado daga bacci ya d'auke ta bata Ankara ba, Mukhtar da ya shigo a kufule kai t'saye d'akin ya shigo cikin bacin Ray, Zeinab d'ake bacci cikin jin'dadi taji an'jawo kafar ta da karfi har saida ta fado daga kan gadon cikin Firgici da t'soro ta saki wata kara da s'awri ya rufe mata baki dan kar makotan su suji, zaune yayi bakin gadon ya saka kafafun shi ya sata t'sakiya ya t'aushe kafafun ta da kafar sa Kallan da yake mata ko'kadan babu wasa da karfi yace mata" ina kika'je, miyasa kika'ki d'aukar waya ta?" diririce'wa Zeinab tayi dan har'ga Allah ta'manta da Wayar ta tinda tazo gidan bata Buda Jakar ta ba, tana cikin piki piki da ido ne taji Wani G'oron mari a fuskar ta dafe Kunci tayi cikin kidimewa ta zabura tana kokarin gusawa daga wajen cikin Hushi ya finciko'ta ya saké k'wada mata Wani marin yana fadin" bazaki fadamin ba, ni zaki Mayar dan Iska Zeinab ? " cikin kuka ta fara magana" a'a wallahi babu in'da naje gida nazo tin'da rana kuma ni ni wallahi", ta rasa abinda zatace k'awai ta saké fashewa da kuka, shako rigar ta yayi da karfi yace" karya kike sai kin fadamin gidan Uban da kika'je, naje gidan Aïda amma akace da zuwan'ki da Tafiyar ki bakifi Minti goma sha'biyar ba, dan haka wallahi kifadamin in'da kika'je ko kuma jikinki ya fada maki" kai ta dinga Girgiza'wa tana fadin" a'a Dan Allah kayi hakuri El moc wallahi wayar tana cikin jaka'ta dan Allah kayi hakuri kar'ka dakeni Wallahi...., Wani s'awkar marin ne ta'ji a fuska, da iya karfin'ta ta fashe da kuka ganin zata tara mashi Jama'a yasa ya Mike yana nunata da Hannu yace" ki'shirya fadamin in'da kika'je dan Bazan Yarda ba da wannan iskancin'ba" wucewa yayi yabar'tanan kuka ta dinga'yi kamar ranta zai'fita ta jima nan t'sawon dare har bacci ya d'auke ta..., Tin'da safe Mukhtar ya saké tit'siye Zeinab a'kan ta fada mashi in'da ta'je, cikin rawar murya da kunburan'ran fuska tace" wallahi Grand frère baije ko'ina ba tin'da naje gidan mun'samu mat'sala ne da su Wasila kuma Mama ta goyi bayan su shiyasa na baro masu gidan, kuma tin'da nazo gidan ina k'wance banajin'dadi Shiyasa ban duba waya ta'ba, Dan Allah kayi hakuri wallahi ba dagangan nayi ba" Zeinab ban'yarda ba dan Na-san bak'ya barin wayar ki ne sa da ke, saidai idan k'awai..." shirun da yayi ne yasa ta dago ta k'yaleshi idan ta Tap da Hawaye tace" saidai in'mi?" kafadu ya daga tare da tabe baki yace" watakila kina tare da Wani ne" zaro ido tayi cikin mamaki ta Mike daga durkushin da tayi tace" kamar ya Wani, Mukhtar kana nufin kana zargina da cin amanar'ka, kana nufin Baka Yarda da ni ba"? Tsaki yayi ya Mike zai'fita daga d'akin, s'awrin rike hannun shi tayi tace" ka'fadamin mika'ke nufi dani, Mukhtar wai zargina kake Wani fa kace?" Fizge Hannun shi yayi ya fita ba'tare da yace mata kala ba...., Zaune tayi tana Tinanin Rayuwa, wai Mukhtar Zargin ta yake to miyasa wai kodai ba Mukhtar kin da ta sani ba'ne, wanda ya shagala adah wajen fada mata kalamai masu dadi, yaou shine ya'ke fada da bakin shi wai tana tare da Wani Namiji ba shiba sabida Kishi, indai irin Wannan kishin za'ace sabida So ne to wallahi BA SO BANE,. har dare bai'dawo gidan ba Kusan 22:30 ya shigo, lokacin Zeinab ta'gama galabaita da matsanan'cin Ciwon ciki da ya addabeta tin rana, taki fita kuma bare ta fada ma Wani dan gudun saké Wani laifin kuma ba'tada Kudi a waya haka tayi'ta fama har'sai yanzu da ya shigo ganin abin k'warai ne yasa ya d'auke ta suka tafi Likita, bayan dubata da akayi ne ma'aikaciyar lafiyar ta fito a t'sait'saye take fadama Mukhtar cewa" am! Malam gaskiya Yarinyar nan tana cikin hadarin,cikin tane ya fita daga mahaifar ta Kasancewar shi Karami ya dawo a mara Dole yanzu tana bukatar a mata aiki" cikin mamakin jin Zeinab tanada ciki yace" aiki kuma, wane irin aiki kenan?" saida ta nisa tace" Dole a zubar da cikin sabida lafiyar ta, dan bazai'yiyu a barshi a jikin ta'ba, yanzu dai muna bukatar ka saka mana Hannu dan aikin" ba tare da bata lokaci ba yasa Hannu aka fada aikin, kafin nan ya kira Inna suka'zo tare da Mahaifin shi har lokacin Zeinab na ciki Inna ce ta tambayi Mukhtar " Muntari ya nagan'ka kai kadai a wajen ta, ko yan gidan na su basu sani ba?" saida yadan Sosa kai sannan yace" Inna ban kira suba," to miyasa , Yarinya na cikin Wani hali ace kuma gidan su basu sani ba, kaga bana san haka ka kira ka'fada masu halin da take ciki, dan a yanzu tana bukatar Mahaifiyar ta a kusa da ita" ya kira Mahaifin Zeinab ya fada mashi, ya shiga tashin hankali sosai jin'yar autar shi bata lafiya cikin Gaggawa ya'zo Asibitin tare da Tanti Nadiya dan Mama ta tace sam wallahi ko mutuwa Zeinab tayi ko Allah ya jikanta ba'zata ceba, haka ya taho ranshi a bace ya'zo Asibitin dai ya fara gajiya da halin na Ramatou tana nuna ma Zeinab kiyayya kamar ba ita ta haife taba, sabida k'awai ta ki amince'wa da zabin'ta dan yana Dan yar uwar ta..., 12/01/19 à 22:21 - Mme Sami😘: 💔BA SO BANE💔 *Gajeran Labari* Na📚 Samira Harouna 40-45📗 An d'auki lokaci Kafin aka fito da Zeinab aka kaita d'akin hutu, dungumu sukayi suma cikin d'akin dan ganin halin da Zeinab kin take ciki, nurse kinn'da ta kawota ce ta fada masu cewa" Dan Allah a'kula da ita sosai sannan a daina barin'ta tana zama ita kadai hakan yana haifar da kadaici Musammam ga mai ciki, sannan ta rage yawan damuwa da tinani dan da muka auna tension kinta bai kamata ace kamar wannan jinin'ta yana hawa haka ba, sannan abu na karshe kunga yanzu an'mata aiki dan haka akw'ai bukatar ta samu hutu ya kamata a d'auke mata d'uk Wani aikin gida irin wanda mata Sukeyi na'yaou da kullum a'kalla na t'sawon sati Biyu." Kallansu tayi daya Bayan daya Kafin ta nuna Mukhtar da Hannu tace" ai kaine mijin ta ko?" cikin Sanhin jiki ya amsa mata da" Eh! nine" dorawa tayi akan" yawwa to ka'biyoni dan ak'wai magungunan da za'a Siyo mata ta fara aiki da su yanzu" kai kawai ya Girgiza ya'bi Bayan ta, yana fita Inna ma da Malam binshi sukayi dan abu daya ne a ransu, suji ko yanada kudin Siyan Maganin, hakan yaba Baban Zeinab damar Tambayar yar'ta shi da ke k'wance d'uk a galabaice ya gyara Zama yace, " Mamana, kifadamin idan ak'wai Wani abu dake damunki ni Mahaifin kine bakida wanda zaki fada ma damuwar ki sama dani, kifadamin ko na'iya taimaka maki tin'kafin kijama kanki Wani ciwo dan da kunnan ki kinaji abinda likatar ta fada" cikin kasala da Siririyar murya tace" Abba babu Komai wallahi, babu abinda ya ke damuna idan ma ak'wai bazai wuce zaman kadaicin ba, kuma shima ba sosai ba tin'da inada makota kuma muna wuni tare da su" cikin rashin gasgatawa Abba yace" haba Zeinab ai d'uk wanda ya ganki ya san kina cikin damuwa in'kika duba aiba haka kike ba a baya, kifadamin abinda ke faruwa kinji Auta ta" cikin sigar Rarrashi yayi Maganar, Tanti Nadiya tace" gaskiya ne Zeinab ba haka kike ba kin rame in'banda haske da kikayi shima kuma Na-san na ciki ne kuma yanzu babu shi Kinga Komai zai'fito kenan a fili har'sai kowa ya gane halin da kike ciki, ki fadama Mahaifin ki abinda ya ke damunki kinji ko Hajia" kuka ne ya k'wace ma Zeinab badan ta soba da k'yar ta fara magana cikin muryar kuka tace" Abba yaushe Mama zata daina Hushi da ni, miyasa Mama na ta kasa Yarda da Kaddara ta Yarda cewa aure na da Mukhtar Allah ne ya Kaddara faruwar shi sabida Wani dalili, miyasa Mama ta kasa gane Mukhtar shine wanda nake'so nake'san zama da shi a Matsayin Miji na ba Yaya Saif ba, miyasa Mama ta ke Hushi da ni har yanzu, shin idan aure na da Mukhtar aure ne na mutu ka Raba hakan na nufin zata cigaba da hushi da ni kenan har Abada?" tsagaita kukan ta tayi ta kalli Tanti Nadiya tace" kamata yayi ace Mahaifiya ta ce anan amma sabida tana Hushi da ni bata zoba hakan na Tabbatar min cewa ko mutuwa nayi bazata zo kan Gawa taba bare na samu Addu'ar Rahama daga wajen ta" Hannun Tanti Nadiya cikin Kuka tace" Tanti Nadiya ke kadai kika tsaya tare da ni, ke kadai kika zamar min Uwa da sawran yan uwa na, Tanti kinmin abinda Mahaifiya ta ta kasa yimin Nagode Sosai" fadawa tayi jikin ta tana kuka daddaba ta ta dinga tana bata hakuri haka'ma Abba hakurin yake bata bai'kuma jidadin abin ba Hakan yasa ya daura damarar gyara t'sakanin Uwa da Diyar. Inna dake kofar d'akin Tsaye d'uk taji abinda ya faru, ba karamin taussaya ma Zeinab ta yi ba kuma Babban Abin dubawa ma ace d'uk wannan ta yi ne Sabida San'da take ma Dan'su, Abin Alfahari ne a wajen Mukhtar samun macen da ta ke san'ka kamar haka, wannan yasa ta dauki Niyar tirsasama Mukhtar rike Zeinab da Hannu Biyu tare da burin fada mashi ko da bata ma Zeinab yayi to bata yafe mashi ba, badan Komai ba saidan wannan itace sakayyar da zasu'iya yima Zeinab akan Soyayyar da ta nuna masu dan d'uk wanda ya'so naka to Tabbas kai ya'so, shigowar da tayi yasa Zeinab ta yi shiru sai Ajiyar zuciya ta ke sawkewa a hankali babu wanda ya yi magana har Mukhtar ya dawo da magungunan daya sawo. Saida tasha Maganin ta kwanta, Abba ya kalli Mukhtar cikin Tautausan murya yace" Mukhtar dama kai muke jira ka dawo ina so ne zan nemi wata Alfarma a wajen ka?" gaban Mukhtar ne ya fadi dan Tinanin shi kar ace Zeinab ta fada masu Wani abu a game da shi, cikin i'ina yace" Abba Alfarma kuma, a waje na?" kai Abba ya daga tare da fadin" k'warai a wajen ka kuma ina fata zan'samu" Murmushin yake yayi yace" Abba ai kun'wuce neman Alfarma a waje na saidai ku bada Umarni kawai, ku fada Insha Allah za'ayi maku" cike da jin'dadi Abba yace" dama wai ina Tinanin ko zaka amince mutafi da Zeinab gida, tin'da Likitocin sunce babu d'uk wani aiki da zatayi shiyasa ne ke'so mutafi da ita sai ta samu tadan huta nan'da sati Biyu saita koma d'akin ta,koya kuka gani?" ya karashe maganar yana Kallan d'uk mutanen dake d'akin, Mukhtar kam jiyayi kamar za'a tabashi da Zeinab ne ta hanyar dabara da wayo dan haka ya yi shiru ya kasa cewa Komai, Malam daya fahimci Mukhtar yasan zaiyi Wuya ya amince dan haka yace" ai wannan ba Abin damuwa bane Alhaji, Zeinab yar'ku ce muma kuma yar'mu ce bazaku Cutar da ita ba dan haka Zaku'iya tafiya da ita, kuma hakan bayana nufin zamu cire Hannu Daga Al'amarin ta ba a'a zamu dinga kula da ita kamar tana tare da mu" Abba yaji dadi sosai Godiya ya fara masu Malam yace" haba Alhaji miye na Godiya, Zeinab fa yar'ka ce ai mune da Godiya muda aka ba" Murmushi Abba yayi yace" ai ya mace daga lokacin da aka d'aura mata aure to ta fita daga Hannun iyaye ta koma Hannun mijin ta Dana Iyayen shi, Iyayen ta suna nan ne a Matsayin su na Wanda Suka haifeta amma ba masu jibanta Al'amuran taba, Zeinab yanzu ai tana Karkashin kulawar Mukhtar ne shi zaisa tayi zai kuma hanata ta hanu ba niba, idan yace bai amince ba wallahi bazanji Komai a Rayna ba zan hakura da tafiya da Zeinab sai ta Zauna d'akin mijin ta dama shi yafi Alkairi a gare ta ya kuma fi da cewa tayi jinya a ciki, ina da dalilin da yasa nake'son mutafi da ita ne"cike da jindadin Kalaman girma da Abba yayi ne yasa Mukhtar ya saki fuskar shi yace" wallahi Abba babu Komai ni dai a waje na na amince kutafi da ita, fatan mu dai Allah ya bata lafiya" saida Abba ya dafa kan Mukhtar yace" Ameen Nagode Allah ya yi maku Albarka, Allah kuma ya maida maku da mafi Alkairin wanda ya lalace" keya Mukhtar ya Sosa dan jin kunya sai a Zuciyar shi amsa da Ameen. Tanti Nadiya har race zata k'wana anan kuma Abba ya amince dan yanajin dadin yanda ta ke nuna kulawa ga Mamar tashi, amma sam Inna taki Yarda tace taje gida ita zata kula da yar'ta, haka kowa yabar Asibitin kamar kar ya tafi, Mukhtar ma saida Inna ta matsa mashi ya tafi dan har ya ce anan zai k'wana shima, haka akabar Inna da Zeinab wacce take ta bacci cikin nishadi. Koda su Abba Suka shiga gida Mama ta kasa zaune ta kasa t'saya Tinanin abinda yake faruwa take, tana Ganin su tayo kansu da sawri tana fadin " Alhaji lafiya Miyake Faruwa ne naga kun'dade?" wata harara ya bita da ita yace" bansani ba, ko kin aike mune?" baki ta saki tace" Alhaji lafiya miyayi Zafi shi ba wuta ba?" cikin bacin Ray yace" ai wallahi ya mafi Wutar , ina ruwan ki da dadewar mu, kefa nace kizo mutafi kikace bazaki ba, karshe ma kikace ko mutuwa ce ta yi to bazaki ce Allah ya jikanta ba to miye na tambayar mu a inda ke faruwa" har ya juya zai wuce ya tsaya tare da juyowa yace mata" kuma kiji Gobe Mama na zata dawo gidan nan da zama zatayi jinya har na tsawon sati Biyu, bama bukatar sa hannunki a kula da ita haka bama bukatar Addu'ar ki gareta mu muna tare da ita, kuma wallahi so daya idan kika daga mata hankali to zaki tafi gidan ku tin'da ai kince kinada gidan Uba ko to itama nan gidan Uban tane Dole tayi yanda ta keso, sabida ita Mama nace" wucewa yayi ya bar tanan ita da Tanti Nadiya Suka bishi da kallo..., Tanti Nadiya ce ta kalle'ta tace" Hajia Dan Allah kiyi Hakuri kidaina Hushi da hajia, wallahi tana cikin damuwa da rashin ki a kusa da ita Abin yana damunta sosai kuma wannan damuwar tana daya daga cikin abinda yayi sanadiyar lalace'war cikin ta har saida aka zubar da shi, kiyi Hakuri kiyafe mata ki d'auka auren ta da Mukhtar tsananin Rabo ne" wata Harara ta galla wa Tanti Nadiya cikin Massifa tace" to uwar kicihi da kinibibi ina ruwan ki da rayuwar mû, ke zakisa inyafe mata to ko wanda ya ajeki gidan bai isava wallahi bare ke Karan kada miya" Tsaki tayi ta wuce ta barta nan, Tanti Nadiya kuma binta tayi da kallo tana Murmushi tace" toh yaou kuma kishin ya motsa, hum kina so ki na kai Kassuwa, Da'da Mahaifiya ai sai dai Allah kina damuwa da halin da ta ke ciki amma saiki dinga shafama fuskar ki toka kia muzurai" wucewa ta yi ita ma nata dakin dan ta k'wanta. 12/01/19 à 22:21 - Mme Sami😘: 💔BA SO BANE💔 *Gajeran Labari* Na📚 Samira Harouna 45-50📗 Sammako Abba yayi ba tare da Matan shi sun sani ba yaje dan ya d'auko Zeinab idan aka Sallameta daga Asibitin, yana zuwa ya tarada Mukhtar hakan yasa Bayan sun gaissa yace mashi" Mukhtar halan nan ka k'wana kai'ma?" dariya yayi yace" a'a Abba nima yanzu nazo" saida ya jinjina kai yace" ah! Lalle kazo da Wuri, ai na d'auka babu wanda zai'riga ni ganin nayi Sammako Ashe kai asuban'ci kayi" dariya sukayi har'da Inna ma da Zeinab, hira Suka dinga'yi har ma'aikatan Suka fara zuwa sannan aka sallami Zeinab Suka tafi tare da Abba da kayan ta da Mukhtar ya taho mata da su, Mukhtar kuma école ya wuce dan har ya Makara sosai, Inna ma gida ta wuce Kafin ta saké zuwa ganin jikin Zeinab kin..., Duk Yaran sun'tafi école dan haka gidan yayi shiru, Mama ce kadai a Falo zaune tana gyangyadi Shigowar motar Alhaji ta farkar da ita Tanti Nadiya ma fitowa tayi dan taji ko lafiya ya fita basu sani'ba, ganin Shi tare da Zeinab yasa tasan inda yaje cikin murna ta tarbi Zeinab tana mata ya jiki sabanin Mahaifiyar ta data Mike Tsaye tace" Alhaji kenan da gaske kake, yarinyar nan zata dawo gidan nan?" saida Abba yadan Harare'ta K'afin yace" k'in d'auka da wasa Nake?" Girgiza kai tayi cike da Gamsuwa tace" to yayi k'yaou, ka nuna'min nan gidan Mahaifin ta'ne amma kasani nima fa a gidan Mahaifi'na ka d'auko'ni ba akan titi ba dan haka zan'bar maka gidan in'yaso sai'ka Zauna da ita" juyawa tayi ta nufi d'akin ta cikin daga murya Abba yace" Dan Allah Ramatou idan kin'tafi gidan ku kar'ki dawo kinji, Mama'na kuma zama daram da ita a gidan nan har'sai ta samu sawki sannan zata koma gidan ta, naga wanda ya' isa ya takura mata" wucewa Mama tayi ba'tare da tace Komai ba, Zeinab Kallan Mahaifin nata tayi cikin muryar kuka ta fara Rarrashin shi, "Abba Dan Allah kayi Hakuri Karka bari Mama ta bar gidan nan, idan ta tafi wallahi Douniya ma sai'ta zagemu Abba inaso na Zauna gidan nan tare da Mahaifiya ta idan har ta tafi to nima saidai na koma can nayi jinya'ta, Dan Allah Abba ka'bata hakuri bai'kamata ace kuna samun irin Wannan sabanin a t'sakanin kuba Musammam ma ace a'kaina ne, Abba Dan Allah kuyafemin indai nice silar wannan takon sakar naku" fashewa tayi da kuka ta Durkusa taci gaba da rokon Mahaifin nata har'saida Mama ta'fito da katuwar jaka wai ita zata tafi gida, saida ta t'saya gaban shi tace" na'tafi ka aiko'min da takarda ta gidan mu" rike jakar'ta Zeinab tayi zata bata hakuri cikin Hushi ta fizge jakar'ta tayi gaba, Zeinab ta saké Kallan Mahaifin nata a raunane tace" Dan Allah Abba ka'bata hakuri karta tafi, yanzu mi'kakeso taje gida ta fada da girman'ta ace taje gida a wannan halin Dan Allah Abba ka'bita" baya jurar ganin hawayen Zeinab dan Haka yabi bayan Ramatou wacce take'ta Addu'a a Zuciyar ta Allah yasa su'bata hakuri Kafin ta'fita dan wannan ba'karamin Abin kunya ba'ne gare'ta, tanajin muryar Alhaji ya kira sunan'ta ta t'saya cak ba'tare da ta juyo ba, saida ya fuskance'ta sannan yace" kibiyo'ni d'aki na muyi magana" wucewa yayi yabar'tanan cikin sanhin jiki tabi bayan'shi izuwa Bangaren shi... Zaune sukayi dukan su dan su'fahimci junan su da k'yaou, Abba ne ya kalli ta cikin nut'suwa yace" Ramatou yanzu abinda ki'kayi kina ganin kinyi dai'dai kenan, sabida Allah ace a gaban yar'ki da kishiyar'ki amma kina'cin Mutunci na yanda kika'ga dama, ace tin'da Hajia tayi aure ni'da'ke bamu saké samun k'wanciyar hankali ba d'uk kin'canza halin'ki kina gani'na da laifin na bawa Hajia wanda take'so ba dan yar uwar ki'ba", ********************** ? ************************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************? ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ? ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ? ************************** " karfa ki'manta ni'kaina nama Hajia tayin Yayan abokanai'na amma taki tace bata'so, kinga ni'kuma banta'ma yara'na auren Dole ba Kinga ko ai bazan fara da Mama'na ba, Ramatou Dan Allah ki'nut'su kisan Annabi ya faku ki'gane cewa auren Hajia da Mukhtar Allah k'awai ya hada'shi wanda shi'kadai yabar'ma kansa sani, sannan badan abinda ya'ke cikin taba yanzu ya lalace kinga sai'muce hada t'sananin Rabi wanda Wallahi da Wani zaiyi yin'kurin hana wannan auren to'fa Zai'iya zama Ajalin'sa dan anriga da an'rubuta a Lauhil Mahfuz" cike da Gadara Mama tace" Wallahi Alhaji babu wata Kaddara Zeinab bata dace da wannan Yaron ba, wai'ke Baka gani ne, a haife fa ya haifi Zeinab amma ka'd'auki yar'ka ka bashi Haka k'awai bayan ga dan yar uwa'ta nan yana massifar san'ta da yanzu tana kasar Waje tana hutawar ta amma tazo ta d'auko mana wannan wanda ya aje'ta a gidan haya,ko gidan kan'shi ba shida'shi haba wannan ka'daina saka Kaddara a ciki", cikin Tautausan murya yace" yaou sunan hajiar ma ake kira gat'sau ba sakaya'wa Ko'dan Albarka'cina?" kara Hade Ray ta yi tace" ai'ko Hajia ma Hushi ta'ke da ita sabida abinda da tayi" kai ya Girgiza yace" a'a Hajia bata Hushi da tak'warar ta, sannan da kike cewa wai Mukhtar ya haifi Zeinab a haihuwa, in'kikace Haka kenan fa Mukhtar ya'kai sa'a na, wanda ni'kuma a gani'na Mukhtar baifi warin dan'ki ba SAMINOU" cikin sawri ta kalle'shi tace" ahan, ana nan'dai ace kamar Zeinab ta auri warin Saminou ai'takare mata, Saminou shine Babban dan'ka fa Kasan shekarar shi nawa, haba Alhaji wallahi basu dace ba" ganin har'yanzu basu fara magana akan sulhu'ba yace" kinga ni'yanzu ba wannan ne yasa nace kizo ba, Ramatou " ya kira sunan'ta cikin ka'kkausan murya yace" Mama'na ita'ce ta bani hakuri ta'kuma ce na dakatar da'ke amma Wallahi badan haka'ba, ke Kinsan ni Kinsan mi'zan iya yi da wanda bazan'iya yiba, dan Haka nake'so ki'bini a'hankali murabu lafiya, idan ki'kayi lissafi ma ni'da'ke Awa nawa ya rage mana a'douniyar da'har zamuyi kokarin rabuwa yanzu bayan shekarun da muka d'auka muna tare, tin Sawrayi da Budurwa, idan muka rabu yanzu wallahi sai'anzage mu sai'kuma an'mamu dariya dan za'aga kamar mun'haukace ne daga'ni har'ke din, dan Haka nake'so in gargade'ki da ki'kiyaye mu'zauna lafiya sannan mu'ida Karasa yar gutun Rayuwar da'tayi mana sawra a'mats'ayin miji da mata, dan Wallahi idan danyan kan'ki yasa kika fita daga gidan nan to nidai kiji ki'kuma sani baza'je ko'ina ba da sunan b'iko da girma'na Haka k'awai ki sani zarya, saidai idan kin'gaji da zama to k'yamaido kan'ki" tabbas ta'san wannan ka'dan daga cikin aikin shi'ne babu abinda bazai aika'ta ba wanda ya fada dan Haka tama kan'ta kiyamar Laili tace" Lalle Alhaji ka'nunamin Banida Wani Mat'sayin a wurin'ka,yar'ka ma ita ta Baka hakuri ka t'sayar da'ni kenan da saidai na'tafi kai'kuma Kaci gaba da k'wasar amarcin'ka da Amaryar ka ko?" Murmushi yayi yace" ke Kinsan ba'gaskiya kika fadaba dan mace ta Biyu da na'fara samu a Rayuwa ta bayan Mahaifiya'ta to ke'ce, Mahimmancin ki a waje na baki ba'zai iya anbatan'shi ba, kuma da bana'san zaman'ki a tare da'ni aida ban'hakura ba ko" Wani parii aka mashi da ido daya aka bude mashi hauran makka'nan guda Biyu sai walkiya suke tare da fadin" Allah KO Alhaji na?" shi'ma dariyar ya yi yace" sosai ma ai'ke ta daban'ce babu kamar'ki ba'ayita ba kuma baza'a yi taba" wai dadi kashe'ni kamar ta d'auki Alhaji ta Goya dan tasan Gaskiya ce da ga Zuciyar shiyake yaje fadama'ta, shima Alhaji dadi'ne ya kama shi dan ganin ya shawo kan mat'salar dan shi'kanshi da Kuru ce zaiyi ya k'yaketa idan ta tafi gidan su dan Ramatou mace ce da bazai'iya manta'wa da ita ba har'karshen Rayuwar shi, k'awai dai rashin auren Hajia da Mukhtar ne ya canza kalar zaman su, amma ba'dan Haka ba itadin ta daban'ce kamar yanda ya fada. 12/01/19 à 22:21 - Mme Sami😘: 💔BA SO BANE💔 *Gajeran Labari* Na📚 Samira Harouna 50-55📗 Wanka Zeinab tayi tana fitowa Tanti Nadiya ta kawo'mata Abin Karyawa tana'ci ta k'wanta dan ta saké hutawa, cikin kankanan lokaci bacci ya d'auke ta cikin nut'suwa da nishadi...., Missalin 12:30 na rana yan makaranta Suka dawo, Fadila da gudu ta shigo d'akin da Tanti Nadiya ta fada mata Zeinab na'ciki, t'salle tayi ta haye saman Zeinab tana fadin" eyeeee! hajia ki'tashi na ganki,yaoushe kikazo gidan mu?" da k'yar Zeinab ta tashi zaune tana fadin" haba Fadila so kike ki'yarni ne ko baki'san Banida lafiya ba" cikin shag'waba tace" kiyi Hakuri Hajia dama ganin'ki nazo nayi" Murmushi tayi tare da kama bakin ta tace" yaou kuma hajia na'samu ba Abba yace ku'dinga kirana da suna naba" dariya Fadila tayi tace" ai Abba ne Rannan da nace inaso naje gidan Zeinab sai'yace wai Maman shi nake kira haka" shiyasa ni'kuma yanzu nace hajia" to naji yanzu dai tashi mu'tafi farfajiyar gida sai muyi hira" tare Suka fito kowa na zaune farfajiyar gidan ana ta hira ana aiki,Zaune tayi ta dora Fadila akan kafafun'ta, Tanti Nadiya ce dake yankan Albassa tace" a'a Zeinab Sawke ta Dan Allah, keda bakida lafiya kina fama da kanki" Murmushi tayi tace" ki barta Tanti ba Komai Fadila nawa take" Fauziya ce tace" Zeinab ke kuma yaoushe ki'kazo, k'wana ma kikayi ko?" tabe baki tayi tace" kenan baki'san ina ciki ba?" a'a bansani ba daga École muka dawo fa, to miyasa meki naji ana cewa baki lafiya?" ki'tambayi Tanti kiji zata fada maki" sai lokacin Mama tayi wani t'saki ta Mike cikin bacin Ray ta shige ciki, bin bayan'ta Zeinab tayi da kallo kafin ta maida kallan'ta ga Tanti Nadiya dake fadama Fauziya abinda ya Faru da Zeinab kin, cikin nuna rashin damuwa Fauziya tace" lalle, kwara ma da Cikin ya zube kinga yanzu saiki koma École ai indai kema kina'san karatun" shiru Zeinab tayi tana Kallan Fauziya tana mamakin Kalaman'ta Tanti Nadiya ce da ranta ya bace Matuka cikin daga murya tace" ke Fauziya Ashe bakida Hankali Miyake damunki, wannan ba Yayar'ki bace ba da zaki fada mata haka, wannan ai fatan t'siya ne kike mata" shiru tayi itama ta kasa cewa komi sai lat'se lat'sen waya da takeyi, Zeinab ce tayi murmushin yake tace" Tanti ki rabu da ita ai ba Komai Na-san ta naso'ne na koma École dan ta samu samu Yer uwa itama" cikin fada Tanti tace" to ina ruwan ta kuma KO kin koma ai ba'tare zaku dinga tafiya ba tin'da yanzu ke kina gidan Mijin kine ba gidan ku ba" fada Tanti ta dinga'yi hakan yasa Fauziya ta tashi ta shige d'akin ta dan surutun ya fara hawar mata kai...., Kamar yanda Suka Saba a Al'adar gidan anan zaune waje daya a ciki a'ci abinci lokaci guda, yanzu ma kiran Zeinab akayi daga d'aki dan Taci abinci, zaune tayi kusa da Maman'ta tare da fadin" Mama sannu da hutawa?" ba'tare da ta kalle'ta ba tace" miye mat'salar ki da'ni, bance kar'ki saké shiga harka taba?" cikin tausassan murya tace" Allah huci Zuciyar ki Mama,kiyi hakuri" cikin hassala tace" idan ya bani hakurin kibi dare ki k'wace" shiru tayi ba'ta saké magana ba, sai AFDAL ne Dan Tanti Nadiya maibi'ma Fauziya yace" Tanti wai miyasa har'yanzu kike Hushi da Zeinab kiyi Hakuri mana, kinga fa ta dawo gidan mu yanzu" cikin bacin Ray tace" kai ina ruwan'ka da maganar mu, wayace ka sama'na bakin ki a ciki idan na sake'ji sai jikin'ka ya gaya maka" a ka'idar gidan kowa yana iya ladabtar da d'uk Wanda yake kasa dashi haka'ma koda ba daga cikin ka Dan ya fito ba, Tanti Nadiya taso tama Afdal magana kan ya k'yale amma gudun wata massifar yasa ta k'yaleshi dan Tantin tashi ta hukunta shi da kan'ta, tashi Zeinab tayi ta wanke hannun'ta ta nufi hanyar d'akin ta muryar Mama tasa tayi t'saye tare da juyowa tana sauraran ta danjin tana fadin" ke ba'wai kinzo bane dan ki dinga zama a d'aki idan lokacin cin abinci yayi kifito kisa Hannu kici, ya zama Dole ki dinga kama aiki kamar yanda kike adah tin'da ke ba bakuwa bace Kinsan d'uk abinda akeyi a gidan, kuma zaki fara ne daga anjima kinji na fada maki" wucewa tayi ba'tayi magana, sai Tanti Nadiya ce tace" amma Maman hajia kina ganin hakan ya dace, hajia fa jinya ce tazo tayi ba zaman jin'dadi ba rashin lafiya ce kina ganin ya dace ace zatayi d'uk wannan aikin da kika lissafa mata" cikin Gadara tace" Nadiya ince dai Zeinab ni na haife'ta?" kai ta Girgiza tare da fadin" eh diyar'ki ce amma nima Diya tace ai" cike da t'siwa tace, " a'a ni na'haifi Zeinab dan haka tin'da bata'min abinda nake'so ba to itama bazata samu abinda takeso soba indai a gidan nan ne,saidai in'tana gidan mijin tane" shiru tayi kafin tace" gaskiya dai baidace a sata aiki ba tin'da dai ak'wai masu aiki kuma gamu muma ga yara d'uk muna kamawa a nayi kenan aikin mi ya rage da zatayi?" karamin t'saki tayi face" ke kika sani kuma Zeinab Diya ta ce sai'kuma tayi abinda nace" shiru akayi ba aka kara maganar ba... Bayan idar da Sallah La'asar Zeinab na zaune akan Sallaya Mukhtar ya shigo d'akin da Sallama, juyawa tayi dan taga ko wanene tana ganin Mukhtar ta sakar masa wani Murmushi tare da mikewa cikin sawri ta Rungume shi sosai shima Rungume ta yayi yana shafa bayan'ta yana fadin" Zeinab nayi kewar'ki, Na-san kema kinyi kewa'ta ko?" kamar zatayi kuka tace" eh nayi kewar'ka sosai... daga Kanta tayi ta Kalleshi tace" ina so ka zauna tare ni" hannun'ta ya kama ya zaunar da ita akan gado yace"Zeinab kenan, a cikin k'wana daya har'kin fara damuwa da'ni haka, keda zakiyi sati Biyu anan" cikin shagwaba tace" eh wallahi ni jinake ma kamar na bika mutafi gida dan Na-san kaima zaka kula dani kamar yanda suma zasuyi" jinjina kai yayi yace" sosai zan'kula dake, amma Kinsan ni ai bana zama gida ba kamar yanda zasu kuka dake ba, kuma kinga yanzu muna kusa da jarabawa dan haka anata devoir akai'akai kinga bazaki samu lokaci na ba yanda ya kamata" a haka suna d'auki lokaci suna hira kafin Mukhtar ya tashi tafiya ta rakoshi, farfajiyar gida Suka tarada Mama da Tanti suna hira jefi jefi fitowar su ce tasa Mama ta maida kallan'ta garesu sannan tayi t'saki tana kunkuni sallama yama su cikin Girmamawa sai Tanti Nadiya kadai ta iya amsa mashi, ficewa yayi ba tare da ya damu da rashin amsawar ta dan inda sabo ya saba da wannan halin nata, Zeinzab ma komawa tayi ciki inda ta fara gyara Falo. 12/01/19 à 22:21 - Mme Sami😘: 💔BA SO BANE💔 *Gajeran Labari* Na📚 Samira Harouna 55-60📗 D'uk da Ciwon mara da takeji sama sama da jiri haka ta d'aure ta kammala tana idawa d'akin ta ta shiga k'wance tayi d'uk da anfara Kiran Sallah Magriba, ta jima kafin ta tashi tayi Sallah sannan tayi Wanka ta shirya cikin doguwar Riga ta Atanfa, fitowar ta falo yayi daidai da Shigowar Abba cikin Sanhin jiki ta zauna akan Kujera tana fadin, " Abba sannu da dawowa?" cike da walwala yace" yawwa sannu Mama'na, ya jikin naki ina fata dai da sawki?" kai ta fara dagawa kafin tace" da s'awki sosai Abba" Bayan ya karbi gaissuwar s'awran Yaran d'à Matan nashi sannan ya kama Hannun Zeinab yana fadin" taso muje Mama'na na Siyo maki wani abu mai dadi" binshi tayi Afdal ne yace" Abba to mufa mi'aka Siyo mana?" to kai miza'a Siyo maku, ku da kullum muna tare da Ku ku bari taji dadin ta nadan wani lokaci" wucewa sukayi sai Fadila da tabi Bayan su..., Ledar hannun'shi ya Mika mata ta bude ta fara fito da kayan ciki Fadila nata tabe tabe ta rasa wanne zata d'auka daga ciki, Zeinab kam samu tayi taci sosai daga gasassar Kaza da cake din da su chocolat ga kuma t'sire wanda yasha birji, taci ta koshi sosai ita da Fadila daga'nan Suka shiga hira ita da Abba kamar yanda Suka saba lokacin da take gida har Abba yaci abinci sun d'auki t'sawon lokaci kafin ta kamo Fadila Suka komo Bangaren su, Mama kadai'ce a falon tana kallo cikin ladabi tace" Mama ni zanje na k'wanta saida safe" mtssss! To ina ruwa'na miya'min Zafi da'ke, ke Idan ma zaki shiga taitayin'ki tin'wuri gw'ara ki shiga hankalin'ki kin'ji na fada maki" ba'ta saké magana ta wuce d'aki ta k'wanta..., Kiran Mukhtar ne ya tada'ta daga bacci, cikin magagin bacci ta fara da sallama ya amsa'mata kafin ya tambayeta, " Mata'ta ya jikin naki?" " jiki da s'awki Yaya el moc, ka'tashi lafiya?" "to da dama zance, amma Kinsan tin'da baki kusa da'ni ai bazanji dadi ba" Murmushi tayi kamar ta'na gaban'sa sannan tace" nasani dama el moc nima haka nakeji" cikin sigar Zolaya yace"Anya ko kin'kaini ke fa kina gida tare da su Abba suna kula da'ke yanda ya kamata, ni'kuma kin'ganni nan ni na kai ruwan Wanka da kai'na ni nasa kaya da kai'na na shafa mai da kai'na sannan yanzu sai'na fita sannan na'siyi Abinci naci, kinga kenan na'fiki shiga wani hali" ( Allah sarki Zeinab uwar taussayi) take ta fara mat'so k'walla sabida taussayin mijin ta, jin'tana kuka yasa yace" kinga Dan Allah ni rufamin Asiri daga yar wannan maganar sai kuka Salan kisa ace wani abu na'miki ko kiyi Hakuri kinji karki damu da'ni zan'kula da kai'na yanda ya kamata" saida ta share Hawayen'ta sannan tace" amma haka zaka z'auna har t'sawon sati Biyu kana Siyan Abinci a waje, gaskiya ina ganin ka dinga zuwa nan kana karya'wa" dariya ce ta kubuce mashi kafin yace" haba Zeinab ta'yaya zan'dinga zuwa gidan'ku da sanhin Safiya dan naci Abinci, kema Kinsan hakan ai bazai Faru ba" to naji yanzu kana'ina harka fita ne?" a'a banfita ba yanzu dai zan'fita, daina dawo"to Grand Frère sai'ka dawo Allah ya t'sare ya ki'yaye hanya" Ameen Nagode sai mun'yi waya" sallama sukayi sannan ta shiga tayi Wanka ta fito falo su Fauziya nata hada hadar tafiya école, gaishe da Iyayen nasu tayi sai Tanti Nadiya ta amsa mata zaune tayi tana Kallan su har'suka fita taji a ranta kamar ta bisu, Abba ne ya shigo cikin Shirin fita Kusan tare Suka gaishe'shi har'da Zeinab, cikin kulawa ya amsa kafin ya maida hankalin shi ga Zeinab yace" Mama'na kin'tashi lafiya ya jikin naki da s'awki dai ko?" Murmushi tayi tace" da s'awki sosai Abba" to yayi k'yaou Allah ya kara s'awki" Ameen Suka amsa tare da Tanti Nadiya juyawa yayi zaifi'ta Mama tace" Alhaji Shikenan kaman'ta da Al'amuran mu tin'da yarinyar nan tazo gidan nan ko?" dariya yayi yace" Hajia Ramatou kenan kinshin kuma akan diyar'ki ya koma yanzu?" murguda baki tayi tace" ba wani Kishi gaskiya ce na fada maka, jiya abinda kasawo mata ko kannan'ta basu gani ba bare kuma mu uwa'ye" kai ya'dan girgiza dan in'ya Biye mata to sai an'samu mat'sala dan haka yace" indai akan wannan ne ki'bari kema zan'siyo maki in zan'dawo" d'auke Kanta tayi daga kallan'shi tace" hum in'madai Baka Siyo ba ai'kasan inada kudin da zan'iya Siyan koma minene" wucewa yayi baice komi ba, Abin Karin kumallo Tanti Nadiya ta kawo'ma Zeinab taci Bayan ta gama anan Suka dinga hira ita da Tanti Nadiya Mama kuma tana d'aki..., Tare da Zeinab aka'yi Girkin rana d'uk da Tanti Nadiya tayi kokarin Hana ta amma sabida tana'so ta shirya t'sakinin ta da Mahaifiyar ta hakan yasa ta kama aka'yi da ita, Bayan sun ida taci abinci tayi Sallah ta k'wanta dan tadan huta, sai Kusan La'asar ta tashi Bayan tayi Sallah Mukhtar ya kira'ta suka'sha hirar su sun'jima kafin sukayi Sallama..., Bayan Sallah Magriba Inna da Malam sun'zo ganin jikin Zeinab, saidai karbar da Maman ta ta'masu bata masu dadi ba ita kadai Suka samu zaune a falon duka Yaran suna d'akin Tanti Nadiya tana masu leson, d'uk gaissuwar da Suka dinga mata bata amsa ba t'saye sukayi suna Kallan Ikon Allah kafin ta masu wani Kallan banza tace" lafiya dai'ko, ku wani t'sayamin a'ka?" cikin mamaki Inna tace" a'a dama Munzo duba jikin Zeinab, ko dai baki gane'mu ba Hajia?" hhhhhhh! ta sheke da wata dariya kafin tace" ni'ko na'gane ku, ko ba Iyayen wannan Sakaran Mukhtar din'bane?" toh! Mukhtar dinne Sakarai Hajia, amma ai naga..., Malam ne ya kat'se Innar ta hanyar daga mata hannu, Mama ce tace" ai'da ka barta Dan'naki wani kayan kishi'ne da baza'a ce mashi Sakarai ba, ko wata t'siya yaje t'sinana ma yarinyar?" Malam ne yace" Hajia Dan Allah in Zeinab tana ciki ki'mana magana da ita mu gaishe'ta da Jiki, in kuma bata'nan sai mu tafi idan tazo a gaishe mana da ita" muryar da Zeinab kiji kamar ta mutanen da ta sani yasa ta fito ganin su Inna yasa ta saki fuskar ta tana Fara'a ta karaso cike da Girmamawa ta Durkusa tana gaishe'su har'saida Inna ta dago da ita tana fadin, " haba diya'ta keda bakida lafiya ai'da kin zauna ma da mun'shigo da kan'mu" Murmushi k'awai tayi sai tambayar ta da sukayi jiki, kafin ta basu amsa Mama ta ta kat'se su da fadin" Wallahi Zeinab kinyi asara ace kina yar gidan Alhaji Nafi'ou mai Kudi amma wai ki durkusa gaban wadannan mat'siya tan kina gaishesu a mat'sayin surukai tirrr da ke wallahi" cikin zafin nama ta tashi ta shige d'akin ta dan bazata iya ganin wannan kayan takaicin ba, Hakuri Zeinab ta soma basu har'da Hawaye suna cewa babu Komai kafin ta nemi Alfarma a wajen'su, Inna ce tace" Wace Alfarma kuma Ya'ta?" cikin jin'nauhi tace" Dan Allah Inna karku fadama Yaya abinda ya Faru,kin'san shi da zuciya bazaiji dadi'ba" Murmushi sukayi dukansu kafin Malam yace" haba Zeinab kamar wasu Yara, karki damu bazai'sani ba Insha Allah kinji ki k'wantar da hankalin ki" kai ta girgiza cikin ladabi rakasu tayi d'uk da tayi tayi su shiga ciki ko ruwa su'sha amma suka'ki dan yanda Suka fahimci Mamar'ta batada k'irki zata iya masu wani cin mutin'ci.... 12/01/19 à 22:21 - Mme Sami😘: 💔BA SO BANE💔 *Gajeran Labari* Na📚 Samira Harouna 60-65📗 Tana tashi daga bacci data koma bayan tayi Sallah Asuba, sawti ta'keji ana hayaniya dan haka ta taso da nufin ta'leko taga ko su waye dan rigar bacci ce a'jikin ta iya g'wiwa babu ko kallabi a kan'ta, yaya Saif ta gani wanda Mama ta tit'siye'shi tana fadin" haba Saif kai'de k'afadamin gaskiya k'awai ni'dai nasan bazaka'zo gidan nan'ba daga zuwan'ka jiya cikin dare ba'tare da wani dalili'ba?" Sosa k'eya yayi yace" da gaske Mama na'ke fadamaki babu komai, k'awai nazo na'ganku ne" k'afin tace wani abu Zeinab ta d'anno da gudu sai'ko a kirjin Saif ta fada cike da farin ciki tana fadin" yaya Saif y'aoushe kadawo?" shiru yayi sabida sanhin da jikin'shi yayi cikin ran'shi yana fadin, ko'dai Zeinab ta manta yanzu ita matar aure'ce bah'da bane da'shi ya'ke tinanin samun'ta ta'zama mallakin'shi, cikin murya kasa kasa yace" kanwa'ta ashe har'yanzu baki girma'ba?" dago da kan'ta tayi cikin sigar shag'waba tace" kai yaya na'girma fa ai'kai kadai nakewa haka kai'ma dan nayi missing din'ka ne" daga'ta yayi daga jikin'shi yana fadin" nima haka kanwa'ta, to ya ki'ke?" k'afin tayi magana Mama ta k'arbe da cewa" ke! wani irin iskanci'ne wannan kamar wata karamar yarinya zaki'zo ki'fada kan'mutum haka k'awai, in'kinsan kina'san jikin'shi miyasa kika'ki auren'shi Mutumniyar Banza k'awai?" tin'da ta fara magana hawaye suka cika idan Zeinab dan haka ba'tace komai ba ta juya ta koma d'akin ta, Saif ma da bai'jidadi ba yace" kiyi hakuri Mama har'yanzu ai yarinya ce" hararan'shi tayi tace" a g'unka ba kai'da ke Namiji ai haka zaka'ce dama tin'da Zeinab ce wacce bata laifi a wajen'ka" k'eya ya saké sosa'wa ya mike t'saye yace" Mama kin'bata ran gimbiya bari naje nayi rarrashi" bai'jira abinda zatace ya wuce d'akin Zeinab, Mama k'am bin'shi tayi da k'allo ta rasa Wace irin soyayya Saif ya'kema Zeinab haka shi'ko kishi'ma bayaji a zuciyar shi, yanda yaga tayi ta'gumi yasa yayi dariya lokacin da yake zauna'wa kusa da ita saida ya gama mata k'allo sannan yace" kanwa'ta miye na'kuka kuma?" ba'tare da ta goge hawayen'ta ba cikin kuka tace" yaya Saif har'yanzu fa Hushi suke da'ni Mama ma ta'ki ta'yafemin" cike da tausayawa yace" kin'ga kar'ki damu Insha Allah komai zai'zo k'arshe, tin'da na'zo bazan'tafi ba har'sai nasa sin'yafe maki kin'ji ko" Murmushi tayi ta goge hawayen tace" to yaya Saif, dama nasan kai ba'zakayi Hushi da'ni ba" s'awya a'kalar zancen yayi ta hanyar Tambayar ta" wai'ke mi'kikeyi gida ne?" cikin jin'kunya ta rufe ido tace" yaya b'ari nayi" dammm! yaji gaban'shi ya fada zuciyar shi yaji ta'fara bugawa kamar zata fito Waje, baisan sanda yace"Mi! b'ari Zeinab?" d'uk da ta t'sora'ta ganin yanayin'shi amma haka ta basar tace" eh yaya Saif Avortement nayi" b'ugun zuciyar shi'ne ya k'aru amma sai'ya d'aure yace" halan har'yanzu baki dai'na t'salle t'salle ba'ko, ba'kisan karamin ciki baya'san k'waramniya ba?" rufe Ido ta sake'yi cikin kunya tace" a'a yaya ni'fa ba laifi'na bane, k'awai dai Allah ne yasa ba'zai fito duniya ba" maganganun Zeinab sosai suke k'ona masa Ray dan bazaijuri jin' Zeinab ta samu ciki da wani ba shi'ba, dan haka ya mata sallama ya tafi tare da alk'awarin zai'sake d'awowa...., K'oda ya shiga gida ganin babu kowa a t'sakar gida da'ma falo k'ait'saye d'akin shi ya shiga ya fada kan'gado yana k'allan sama idan'shi rufe kamar mai bacci yana tinanin abin k'aunar'shi Zeinab wacce ya raine'ta yaci burin mallakar'ta amma y'aou gâta a Karka'shin milkin wani ikon wani mallakin wani ba'shiba, NASREEN ce kanwar'shi ta shigo dan ta'ji kamar an'buda d'akin ganin'shi k'wance yana aikin tinanin dan ta tabbatar ba k'wana ya'keba, saida ta kare ma d'akin k'allo taga yanda d'uk ya barbaza k'aya daga shigowar dare zuwa sanyin safiyar'nan ga photo nun Zeinab da d'uk ya c'ike bangon ko'ina da'su, wasu ma sai in'anfada maka ita'ce sannan ka'sani sabida wasu tin'batafi shekara uku zuxa hudu ne a duniya har'girman'ta i'yanzu zaka'iya cewa kamar kowace Rana'ce yake d'aukar photo na'ta sabida yawan'su wani irin'ma ko kayan kirki babu a jikin'ta wani tana kuka wani tana dariya wani bata'masan an'd'auka ba wani tana'cin Abinci wani tana bacci ga'sunan bar'katai, cikin bacin Ray ta fita daga d'akin ba'tare da ya sani'ba, tana'ta g'unguni har'ta zauna kusa da Mamar tasu Hajia KARIMA k'allan'ta tayi tace" ke kuma miye?" cikin bala'i tace" Mama Dan Allah yanzu haka yaya Saif zai'mayar da kan'sa wani mahaukaci akan yarinyar'nan ?" t'saki Mama tayi tace" to sai'me miye naki a ciki dan'ya h'aukace ai'shi yakama kan'shi ina ruwa'na ni?" cike da damuwa Nasreen tace" haba Mama idan'fa haka ta faru sai'kinfi kowa shiga damuwa ai,ita'kuma tanacan tana Soyayyar ta ki'duba yanzu kiga d'akin dana'sha Wahalar g'yara jiya amma shi'ne d'uk ya yamut'sa shi lokaci daya da t'summokaran yarinyar can da wasu banzayen photo nun'ta" da k'arfi Mama ta k'alli k'ofar d'akin shi sannan ta k'alli Nasreen tace" wallahi ki'rufama k'anki asiri ki'daina zagin wannan k'ayan dan yanzu'ne zai'huce a kan'ki kinsan kuma ni'dai ba'iya masa nake'ba idan ran'sa ya bace sai'ya k'wana yana dukan'ki ba abinda zan'yi kin'ji na'fadamaki" t'abe baki tayi tace" haba Mama ai'bazaki yarda ba,amma Dan Allah ki'masa magana ya fitar da kayan'nan haka k'awai ya tarawa kan'sa t'summa" dariya Mama tayi tace" wannan k'ayan bazasu fita daga gidan nan ba in'ko aka'ce su'fita to saidai ya fita tare da su, Shekara Goma sha'bak'wai kenan Daya fara ajiyar'su har'kayan da Zeinab tasa'ka tana shekara biyu idan ki'ka duba a bolar'shi zaki samu kin'ga kenan ki'fita harkar'shi da k'ayan'shi" Murmushi tayi tace" wai'ni Mama ta'yaya y'a samu k'ayan ne wai?" cike da Zolaya Mama tace" Satar su ya'ke mana wasu kuma bayan ta'gama anfani da'su yake d'aukowa" cike da Girmama lamarin tace" lalle, nasan yana ajewa'ne dan yasama diyar'su k'ayan wasa kuma yaba diyan'su suyi wasa yace, kayan da Maman sune tayi aiki dasu tana kamar su" dariya Mama tayi sosai tace" shi'dai y'a sani Sarkin soyayya". Please kuyi manage da wannan👏👏👏.. 12/01/19 à 22:21 - Mme Sami😘: 💔BA SO BANE💔 *Gajeran Labari* Na📚 Samira Harouna 65-70📗 Makara da Mukhtar yayi wajen k'wantawa sabida wayar da sukayi da Zeinab ne yasa ya Makara wajen tashi, a gaggauce ya shirya ya fita yana zuwa makarantar ya nufi hanyar ajin'shi cikin s'awri ya zuwa daidai k'ofar shiga yayi k'aro da MARYAM wacce ta taho a guje bata an'kara ba, faduwa taje tayi saidai d'uk da Mukhtar baisan ko'wacece ba yayi hanzarin riko kugun'ta, sallatin da yan ajin sukayi'ne yasa yayi s'awrin sakin'ta sunata raba ido irin na marassa gaskiya, cikin i'ina Maryam tace, "ka'kayi Hakuri ban'lura bane" wucewa yayi ba'tare da ya amsa mata ba, take ya fara abinda ya k'awo shi... Bayan yazo gidan'su Inna yaci abinci ya kira Zeinab bayan sun'gaissa take tambayar shi" el moc ya kake?" saida ya s'awke wani goran nunfashi sannan yace" ba'dadi" cikin kulawa tace" miya'faru kuma?" cikin tausassan murya yace" Zeinab za'fada maki amma kimin alk'warin bazakiji h'aushi na'ba?" cike da k'warin g'wiwa tace" yaya'na indai nice to ka k'wantar da hankalin'ka bazan'taba yin'hushi da'kai ba har'abada" yaji dadin maganar ta dan haka ya fada mata d'uk abinda ya faru t'sakanin shi da Maryam dan yana ganin bazai'iya boye'mata ba dan ba'hallayar sa bace, d'uk da Zeinab taji harbawar k'irjin'ta amma bai'hana ta yafe'masa ba suka'kula ci'gaba da hirar'su irin'ta Massoya..., Maryam ce ta t'ari Fauziya K'anwar Zeinab bayan sun'gaissa tace" Fauziya wai miyasa mu wayar Zeinab ne ana kiran'ta ba'a samun'ta?" cike da rashin damuwa Fauziya tace" ai'ko wayar ta lafiyar ta k'alaw,watakila mat'salar network ne" eh kuma hakane, to Dan Allah ko'zaki k'watantamin gidan'ta kinsan banta'ba zuwa ba?" cike da Mamaki dan Fauziya a iya sanin'ta babu wani abu t'sakanin Zeinab da Maryam ko gaissawa bata taba ganin sun'yiba hasali'ma ak'wai ranar da Zeinab kin'take cewa Maryam tana bata h'aushi dan batada halin k'warai fit'sararriya'ce ta gaske, cikin shakku da mamaki tace" amma ai'yanzu bata gidan'ta tana gida tana jinya" wani irin sanhi Maryam taji a'ran'ta dan faduxa ce tazo dai'dai da zama, cike da kissa tace" ayya, Dan Allah to kifadamin gidan naku da gidan'ta koda bansamu damar tafiya gidan'naku ba sai'naje gidan'ta idan ta koma" ba'tare da tinanin wani abu ba Fauziya ta fada'mata duka adresse kin gidan..., Mukhtar na zaune da littatafai a gaban'shi ya kasa duba ko daya sabida k'ewar Zeinab d'uk ta'ishe shi ita k'adai yake tinani yake gani, hirar'su suke cikin farin ciki da annashuwa suna'ji kamar ace Suna tare ne, Buda k'ofar da yaji'ne yasa yayi s'awrin kashe wayar ya mike t'saye cike da mamaki dan baiyi tinanin k'ofar bude take'ba, mamakin'shi ne ya saké ninkuwa lokacin da sukayi tozali da Maryam cikin wata irin shiga da bai'taba tinani ba, cikin mamaki yace" ke mi'kike anan, mi'yakawo ki'nan, wanne wace irin shiga'ce kuma?" cike da Izza da jin'kai ta zauna saman Kujera tana t'aunan shewin'gum kafin tace" na'zo ne na'tayaka hira" cikin rashin Fahimtar yace" hira kuma, Wace irin hira yanzu, ke ko'bakida hankali?" wani irin murmshi tayi iya labbanta tace" nasan matar'ka bata'nan Namiji kamar'ka kuma dole kana bukatar kulawa, shiyasa nazo na'debe maka k'ewar'ta" cikin bacin Ray ya fizgo hannun'ta yana fadin" ke zo'ki fita daga gidan'nan tin'kafin ran'ki ya'bace" ganin zai'fitar da ita ta karfi yasa ta'mashi rada" wallahi ka'bini sannu ko'na tona maka asiri,babu wanda zai'karya tani idan nace kai'kakawoni gidan nan kuma muna soyayya da'kai" s'akin'ta yayi yana huci ya nuna'ta da hannu yace" to maza ki'bar gidan'nan kafin na kakkarya'ki" Banza tayi da'shi ta komo cikin d'akin ta zauna kafa daya bisa daya, yana shigo'wa cikin zafin nama ya d'auko wata doguwar waya ya'yo kan'ta ganin babu alamun wasa yasa ta tashi da gudu ta shige uwar dakin bin'ta yayi yana fadin" wallahi zoki fita ko naci uwar'ki gidan'nan ni zaki nuna'ma ke yar iskace,wane budadden ido'ne bamu gani'ba ki'tsaya mana mara kunya k'awai" yana dosa kai cikin d'akin yayi turus ya t'saya sabida ganin tana cire kayan jikin'ta da s'awri ya juya mata baya yana cewa" ke wai miye Haka kin'san abinda ki'keyi kuwa?" bata ce'mashi komai'ba sai'jinta da yayi a bayan'shi ta rumgume'shi cikin wata irin kissa da salon Iskanci d'uk da yayi yin'kurin k'aucema Sharrin Maryam amma hakan ya'ci tira har'saida tasa'shi ya aika'ta Babban zunubi ya aikata sabo ya aika'ta zunubin da bai'taba aika'tawa ba t'sawon rayuwar'shi, cikin dare Maryam ta'bar gidan ba'tare da wani ya san tazo ba, Mukhtar bai rint'sa ba ko kadan yanda yaga rana haka yaga dare yana'ta kuka da Nadamar abinda ya faru yana kara kambama girman laifin da yayi idan ya tina yaci Amanar Zeinab kin'shi, takaicin nashi ya kara karuwa ganin babu wani abu da'yaji dan'gane da tarayyar'shi da Maryam babu dadi babu nut'suwa babu kimt'si babu'ma tayi yawa gashi babu wani abu da tama'shi wanda Zeinab kin'shi bata mashi saidai banbancin'su shine Zeinab tana nuna k'unya ita kuma babu k'unya a Al'amarin'ta ko kadan,da haka har'ya Wayo gari ba'tare da ya rint'sa ba..., y'aou gida babu kowa d'uk sun'tafi harakokin gaban'su, Fauziya da Fadila sun'tafi kit'so da kunshi dan k'wana biyu ya rage bikin Aida Mama ta fito Siyo wasu s'awran kayan da zasu bukata a wajen Tuya, sai Zeinab da Tanti Nadiya da yan aikin'su guda biyu, yaya Saif ne Yazo bayan sun'gaissa fitowa sukayi farfajiyar gida shi'da ita Suna hira, saida ya kare mata Kallo na t'sanake yaga ta kara k'yaou da gari saidai ta'dan rame kadan dan haka cike da Zolaya yace" kanwa'ta kin'ga yanda kika'kara k'yaou ki'kayi fari, ko'dai cikin nan bai'zube ba duka?" dariya tayi ta turo baki tace" wallahi yaya bana'san haka, babu'shi fa yanzu ya fita" dariya yayi yace" to naji, yanzu baki jin Komai a jikin'ki?" kai ta girgiza tace" a'a yaya bana'jin Komai saidai wani lokaci mara'ta takan dan'yi min ciwo" bata fuska yayi yace" amma kula kinajin haka an'baki fadaba ko jiya na'tambaye'ki ba'kijin Komai?" cike da shag'waba tace" kayi Hakuri bazan sake'ba" daya daga cikin hallayar da suke birge'shi kenan danga'ne da Zeinab gane kuskuren'ta bayar da Hakuri lokacin da ta gane kuskuren'nata, Murmushi da take'yine yasa ya manta da abinda suke magana akai, wani irin mayan k'allo ne yake mata hakan yasa ta t'sargu kasa tayi da k'anta sabida kunya a hankali ya dago da kan'ta yana Kallan ida'nunta d'uk da taki Hada ido da'shi kamar s'awkar Aradu taji muryar'shi yace" Zeinab dan Allah kice kina sona ko sau'daya ne" da s'awri ta daga ida'nunta saidai ina Hawayen dake makale suka zubo dan haka ta ruga a guje ta koma cikin d'akin ta tana kuka, tabbas tasan wani bangare na zuciyar ta yana san yaya Saif haka kuma tana k'aunar shi da dukkanin ilahirin zuciyar shi amma ya'zatayi Soyayyar Mukhtar ita ta mata pin'tink'au..., 12/01/19 à 22:21 - Mme Sami😘: 💔BA SO BANE💔 *Gajeran Labari* Na📚 Samira Harouna 70-75📗 Tin'da Saif ya'dawo gida ya shiga d'aki ya rufe kan'sa a ciki ya d'inga sheka kuka kamar dai yaro Karami, hankalin Mama ne ya fara tashi jin'yanda yake'ta kuka bata'so ta kula'shi ba amma haka ta d'aure ta fara bubbuga d'akin da k'yar ya bude, tausayin'shi ne ya kamata da'taga d'uk ya fita hayyacin'sa, zaune tayi kusa da'shi tin'kafin tace wani abu ya d'ora kan'shi a saman kafafun'ta ya kara fashewa da kuka yana fadin, " Mama Zeinab bata'sona ba'kuma zata taba so'na ba, Mama adah Zeinab tana K'allan cikin k'wayar ido'na tace'min tana so'na amma y'aou ta kasa k'allo'na ta fada'min haka, Mama yanzu Zeinab ta t'sane'ni ban'san mina mata'ba, Mama Zeinab ta'ci amana'ta ta y'audare'ni, miyasa tamin haka miyasa ta ki'ni, miyasa lokacin da ta'ke yarinya kullum ta'ke cemin yaya Saif ina san'ka tin harufan bakin'ta basu fita har'na fara gane mi'take nufi, saida ta'bari na'kamu da san'ta sai'ta juyamin baya ta guje'ni tace bata'sona miyasa Mama miyasa tamin haka, idan wani laifi na'mata miyasa taki hukunta'ni dai'dai da abinda na'mata miyasa taki min hukuncin da zan'iya d'auka amma saita zabi ta nisan'tani da kan'ta" ran' Mama na bace'wa sabida yanda taji d'uk ya rude akan wacce bata masan yanayi'ba, daga kan'shi tayi ta k'alli idan'shi tace" Saif miyasa kake haka, miyasa ba'zaka manta da wacce ta manta da kai'ba?" wani irin k'allo yama Mama yace" bazan'iya ba idan'da zan'iya da tini nayi hakan Mama" ki'karin boye bacin ran'ta tayi tace" to dama ta yaya zaka manta da ita bayan kana ta're da ita a kullum, ai kokartawa zakayi ka cire'ta a ran'ka k'awai" kai ya'keta giegiza'wa kafin yace" Mama kiyi hakuri, Allah ne yasa'min san Zeinab bazan'iya cirewa da kai'na ba k'awai ki'tayani da Addu'a" mai'da kan'shi yayi saman kafafun'ta cikin muryar kuka ya kara da cewa" ina san'ta Mama ita'ce a mafarki'na ita'ce a tinani'na ita'ce buri'na, na'so na same'ta ta zama Matata uwar yaya'na amma waccen banzan Mukhtar kin ya raba'ni da ita" tashi yayi zaune cikin gushewar hankali da baiyyana t'sant'sar abinda ke zuciya cikin bacin Ray yace" Mama mi'waccen ya'fini mi'yake da'shi da bana'da miye gare'shi da har Zeinab ta'juyamin baya ta zabe'shi ta bar'ni, miyasa zata d'auke'shi bayan gani ni'ne na'jima ina jiran'ta na raine'ta har'ta girma amma karshe abinda zata saka'min da'shi kenan?" Mama ganin abin zaifi karfin'ta yasa ta jawo kan'shi da karfi ta maida kan'ciyen'ta ta d'inga rarrashin'shi tana bashi hakuri tana daddaba'shi , haka ya'keta sambatu ba'a kojin abinda yake fada sabida shakewar da muryar shi tayi, bacci'ne ya d'auke shi daga haka badan yayi niyar yin'baccin ba..., d'uk abin Duniya ya'ishi Zeinab ga tinanin makomar yaya Saif ga tinanin halin'da Mukhtar ya'ke ciki tin'daren jiya har y'aou bai'kira ba bai'kuma zo'ba, gashi SALISOU da AMINA kannan'shi sun'zo sunce yana gida sun'baro shi k'wance yana zazzabi hakan yasa d'uk hankalin'ta ya kara tashi tin'da ya tashi jikin'shi babu k'wari a'haka har'akayi Sallah Magriba da Isha'i, bayan yaci abinci yace ma Mama" zan'dan fita na'dawo" ganin yanayin shi yasa Mama tace" amma Saif ina zakaje ai'da kayi zaman'ka ka huta'ma ran'ka?" kamar mai'jin bacci yace" a'a Mama zanje naga Zeinab ne nasan yanzu kan'ta yana ciwo kuma bata'sha magani ba, watakila ma har'yanzu kuka ta'ke" cikin bacin Ray Mama tace" Saif kanada hankali kuwa anya Baka h'aukace ba, maganar Zeinab fa ka'keyi har'yanzu har'ma kake tinanin tafiya gidan'su to kamata Wace uwar?" jiki asanyaye yace" Mama kuka fa nace maki na'baro tanayi, kuma kinsan da'ta fara kuka kan'ta ne ke fara ciwo"cike da massifa Mama tace" to sai a'kayi yaya dan tana kuka yar zinariya'ce data Wuce kuka, kai'ba kuka ka'gama da'zu ba" wani irin murmushi yayi yace" Mama ai'ni Namiji ba'gashi yanzu nayi shiru ba, ita'kuma yanzu babu wanda zai'yi rarrashin'ta kema kinsani Mama tin'da babu wanda ke shiri da ita idan kika cire Abban'ta" k'allan bakada hankali ta mashi tace" to shine mi basai ka'bari idan uban'nata yazo ko Mijin'nata wani ya lallaba'ta ba, sannan ma gidan uban'wa kasan tana kukan har'da kan'ta zaiyi ciwo?"Murmushi ya sake'yi yace" Mama a hannu'na fa Zeinab ta girma dole nasan Komai a game da ita, in'har bazan'iya sanin halin'da take ciki ba ai'ina ganin bai'kai mat'sayin a kira'ni masoyin'ta ba" cikin kossawa Mama tace" kaga Kaje kayi abinda ran'ka yake'so tin'da dai ban'isa na'fada maka kaji'ba" sunkuya'wa yayi cikin ladabi yace" kiyi hakuri Mama'na kitaya'ni da Addu'a k'awai" wucewa yayi ya fita bin k'wanan da'ke gaban'ta tayi da k'allo zuciyar ta na kara t'sanar Zeinab. yana gaissawa da su Mama ya'wuce d'akin Zeinab, zaune take idan'ta sun'kumbura sunyi jah, t'saye yayi yana k'allan'ta kamar mai wani tinani kafin yace" har'yanzu baki dai'na kukan'ba?" sai lokacin ka'dai ta daga ido ta k'alle'shi ta shafi Fuskar ta da hannu sannan tace" ba kuka na'keba k'awai dai kai'na ne ke ciwo" ajiyar zuciya ya s'awke yace" kin'sha magani?" kai ta girgiza cewa yayi" to abinci fa kin'ci?" nan'ma kai'ta girgiza, juyawa yayi zai'fita tasan in'da zaije da s'awri ta rike hannun'shi ta fashe da kuka, juyowa yayi ya k'alke'ta yace" lafiya miye na'kuka kuma?" ba tace komai'ba dan haka ya saké Tambayar ta" Zeinab lafiya miye na'kuka, ki'bari in'dawo zan'kawo maki magani ne da abinci" cikin kuka tace" yaya Saif ko ka kawomin bazan'iya ci'ba" cikin mamaki ya Tambaye'ya" miyasa?" kara fashewa tayi da kuka ta daga kai tana k'allan'shi hawayen'ta na s'awka akan hannun'shi kamar karar an'sa kuwa yaji muryar'ta tana cewa" dan Allah yaya Saif ka'taimaka min ka kai'ni gidan'su Inna naga el moc tin'jiya bai'kira ni'ba kuma bai'zoba sabida zazzabi" tin'da ta fara magana ya rint'se idan'shi dan zaifi mashi s'awki ta d'inga soka mashi wuka akan abinda take fada, cikin t'sananin bacin Ray baisan sanda ya d'auke'ta da wani gigitancen mari ba sabida ta'kaici,dafe Kunci tayi tana k'allan'shi yaci gaba da fada" Zeinab wai'ke ma'h'aukaciyar ina'ce miyasa bazaki gane mai'sanki, Zeinab ko kinsan cewa d'uk t'sawon rayuwa'ta na bata tane da tinanin'ki da burin ganin na mallake'ki kin'zama tawa ni kadai,miyasa ke baki taba tinani naba ko na second daya, Zeinab kinsan yanda nakeji cikin rai'na idan kika anbaci sunan wani da'namiji ba'niba, amma Zeinab har k'allo'na kinyi kin'fadamin kinyi barin cikin wani, shine bai'isheki ba yanzu kine cewa na'kaiki kinganshi d'uk kin'damu sabida k'awai kin'yini baki gan'shiba bai'kira kiba, Zeinab ki k'watanta abinda kikeji a Ranki na wuni daya da wanda kina hadu da'shi cikin yan watanni, da wanda ni'nakeji a game da'ke na t'sawon shekaru." zaune yayi ya d'inga s'awke wani irin huci mai karfi, Zeinab kam kamar ruwa sun'cinye ta ido k'awai ta sakar masa dan tasan abinda ke ran'shine zuciyar shi ta kasa boyewa ta fallasa d'uk da kokarin da yake na boyewa. ganin k'allan da take'mashi yasa ya'dan saisaita nut'suwar shi yace" kin'ga kiyi hakuri kar'ki damu da abinda ki'kaji yanzu k'awai dai rai'nane a bace shiyasa" k'allan mamaki ta mashi cikin murya kasa kasa tace" 12/01/19 à 22:21 - Mme Sami😘: 💔BA SO BANE💔 *Gajeran Labari* Na📚 Samira Harouna 75-80📗 "akan'mi yaya Saif kake bani hakuri, bayan zuciyar ka ta fallasa'min halin'da kake ciki a'game da'ni" share Hawayen'ta tayi tana fuskan'tar shi tace" yaya Saif miyasa kake'so sai'ka nuna babu abinda ke damun'ka?" kan'shi kasa yace" to ya kike'so nayi?" hawaye'ne suka cika idan'ta Karfin hali tayi tace" yaya Saif kayi hakuri hakika bancancanci Soyayyar'ka bai'kamata Kaci gaba da so'na ba sabida ban'maka hallaci'ba yaya Saif ban'zamar maka yar Halak ba..." shhhhhh! ya d'ora hannun'shi a labben'ta yace" miyasa zaki fassara kan'ki da irin wannan Mumunar fassara, Zeinab ina'so kigane wani abu da ace Allah ya kaddara aure'na da'ke to da babu mahalukin daya isa ya dakatar da'shi, nasani Allah ne bai'nufa ke Matata bace shiyasa ban'same ki ba" dora kan'ta tayi akan kafafun'shi taci gaba da rera kuka mai'ban tausayi, kan'ta ya d'inga shafawa har'bacci ya d'auke'ta a hankali ya g'yara mata k'wanciyar ta ya aza kan'ta saman pillow durkushe yayi yana k'allan fuskar'ta tayi wani haske kamar ya sumbace ta Haka wata zuciyar ke raya'mashi amma sai ya'tina auren da'ke kan'ta hannu yasa ya shafi fuskar'ta ya tofa mata Addu'ar bacci sannan ya fita, ko sallama bai'ma su Tanti yabar gidan ya rasa mike mashi dadi yayi Nadamar dawowar shi dan haka ya fara tinanin koma'wa a cikin satin nan... tin'da safe wanka tayi ta koma ta zauna kan gado tana tinanin halin'da Mukhtar yake ciki, tana tinanin halin'da yaya Saif yake'ciki, Mukhtar ne ya shigo dakin cikin sallama sabida ya yanke shawarar ya fada mata abinda ya faru dan ta'yafemasa, tana ganin'shi da gudu ta tarbe'shi rungume juna sukayi cikin sh'aukin juna a hankali Mukhtar ya dagata ya kamo hannun'ta suka zauna saman gado Suna k'allan juna cike da damuwa tace" Grand Frère lafiya miyasa meka k'wana biyu?" ya kasa Hada Ido da ita haka cikin kunya yace" kiyi hakuri aiki'ne yamin yawa kuma da zazzabi daya takura'ni" ajiyar zuciya tayi tace" ai'na d'auka bazaka fadamin kayi rashin lafiya ba dan dama su Amina sun'fadamin" mannewa tayi a jikin'shi tana fadin" nasan d'uk rashina'ne a kusa da'kai yaja maka haka, amma nima nayi missing din'ka" idan'shine suka cika da k'walla daga kan'ta yayi ya k'alli fuskar'ta yace" Zeinab i have someting to teld you but am scared" yanda ta k'alleshi ya tabbatar mata da ak'wai mat'sala cikin nuna t'sant'sanr kulawa tace" what happend,teld me what happend to you?" hannayen'ta ya kamo ya rike yana zubar da hawaye yace" promise me you c'ant leave me?" d'uk da faduxar da gaban'ta keyi haka ta d'aure tace" yaya Moc zan'rayu da'kai bazan'taba barin'ka ba har'abada" Suna Hada Ido yayi s'awrin s'awke nashi cikin i'ina da Sarkewar murya ya fara bayyana ma Zeinab abinda ya faru t'sakanin shi da Maryam a gidan su...., Tin'da Zeinab ta'kura mashi ido ta kasa s'awkewa hawaye'ne kebiyar fuskar'ta kamar panpo, Mukhtar na ganin haka ya durkeshe kasa ya fara magiya" Zeinab Dan Allah kiyafemin wallahi ba'asan rai'na na'aikata ba Sharrin shedan ne bansan garin yaya haka ta faru ba, Zeinab na'zabi in'fada maki ne dan bana'so na mutu da hakkin'ki Zeinab wallahi...." cikin Sanyanyan murya Zeinab tace" kafitar'min daga d'aki " k'allanta yayi a marairaice yace" Zeinab kimin alkawarin bazaki guje'ni bakar'kimin haka wallahi bazan'iya rayuwa babu ke'ba" k'allan'shi tayi cikin bacin Ray da kunar zuciya tace" nace ka'fitar min daga d'aki wallahi bana'san ganin'ka, kafita nace" tayi maganar cikin Daga murya a hankali jiki asanyaye ya mike ya fita yana k'allan'ta ba'tare da ta k'alle'shi ba harya fice daga d'akin, kuka mai t'sanani ta fashe da shi tana jin'nadamar auren Mukhtar karara Tanti Nadiya ce ta shigo ta fara rarrashin'ta da k'yar ta samu taci abinci tasha magani sabida Ciwon kai sannan ta'koma bacci. tana tashi tayi wanka tasa Doguwar rigar Atanfa tayi mata k'yaou Sallah Azahar tayi sannan ta fito falo Tanti Nadiya k'adai ce a gidan dan har masu aiki Suna gidan Aida ko'da abinda zasu kama, Mama kuma tana'can gida wajen tuya dan ita ta d'auki n'auhin'ta, koda taci Abinci ta tashi da nufin komawa falo Abba ne ya shigo cikin hanzari yana ganin'ta ya t'saya yana fadin" Mama'na har'kin tashi, ai'na shiga dubaki dazu kina bacci" cikin sanhin jiki tace" eh Abba na'tashi, ina wuni" mat'sowa yayi kusa da ita ya dafa kan'ta yace" Mama'na ak'wai abinda kedamun'ki ne?" kai ta girgiza tace" babu komi Abba" a'a ya zakicemin babu Komai d'uk wanda ya gan'ki yasan ak'wai wani abu da'ke damun'ki" Abba babu Komai k'awai dai ina'jin baccin da nayi'ne shiyasa d'uk jiki'na yayi sanhi" d'auke hannun'shi yayi daga kan'ta yace" to Shikenan tin'da haka kika'ce amma kisani barin kashi a'ciki baya maganin yinwa, yanzu kifadamin abinda kike'so in anjima in'siyo maki" Murmushi tayi tace" Abba gafarar'ka k'awai na'ke nema nasan ban'k'yaouta maku ba amma....." kat'seta Abba yayi da fadin" haba Mama'na yafiya kuma akan me, kinga nidai babu abinda kika'min kuma nayafe'maki Duniya da Lahira kin'ji ko" cike da jin'dadi ta rungume mahaifin'ta kafin ya wuce bangaren shi ya d'auko abinda ya mai'do shi gidan...., Bayan Sallah La'asar tana zaune kumshe akan gado tana kuka maganganun Mukhtar ne ke'dawo mata a'cikin k'wak'walwa, yaya Saif ya k'wak'wasa ya shigo cikin sallama bayan ta amsa Sallamar shi, zaune yayi yana k'allan fuskar'ta d'uk ta Kumbura sabida kuka yace" miya faru kuma miye haka?" cikin kuka kamar jira'take dama tace" yaya Saif ya'ci amana'ta ya cuce'ni wallahi bazan'yafe mashi ba" cikin rashin fahimta yaya Saif yace" wanene ya'ci amanar'ki Zeinab?" sabida ta bacin Ray yasa bata Boye komi ba d'uk abinda Mukhtar ya fada mata ta kara da cewa" sabida cin'amana da ke'ta haddi ya rasa in'da zai'ci amana'ta sai a cikin gidan'mu a d'akin mu a saman gado'na na sunna wallahi Allah sai'ya saka'min" fadawa tayi akan kafafun'shi taci gaba da rera kuka shiru yayi yana s'awraran ta kafin yace" Zeinab bana'so na'saje jin kina cewa wai mijin'ki ya'ci amanar'ki, dan d'uk Macen Arziki tana rufama Mijin'ta asiri bata fadan Sirrin shi, sannan kafin ki'yanke ma mijin'ki Hukunci kiyi tinanin mijin'ki wane irin mutum ne, ina nufin kiyi tinanin akan yanayin mijin'ki shin mai'karfin sha'awa ne ko kuma ya nada r'auni sannan miye yafi s'awrin daga mishi hankali a tare da mace, idan kikayi haka sai'kiyi abinda ya dace" ba'tare da ta dago da kan'ta ba tace" yaya Saif wannan ba hujjaba'ce da zatasa ya'ci amana'ta" a'a kanwa'ta na'sanki da fahimta da kuma hakuri, ina fada maki wannan ne daga zuciya ta zan'so ma mijin'ki abinda zan'soma kai'na idan da ni'ne haka ta faru zanji dadi ba ka'danba idan kika yafemin, kinga Dole na'mashi fatan ki'yafema shi". 12/01/19 à 22:21 - Mme Sami😘: 💔BA SO BANE💔 *Gajeran Labari* Na📚 Samira Harouna 80-85📗 K'allan'shi tayi tace" yaya Saif idan kai'ne kai'ma haka zaka'min?" shirun da yayi ne yasa ta d'ora kan'ta a kafadar'shi tana kuka, cikin ranshi cewa yayi( ta'yaya zan'iya haka Zeinab nayi hakuri tin'kina karama har'kika girma, bayan na'same'ki na sati biyu ne zan'kasa jiran'ki wallahi bazan'iya ba zan'iya kokari'na na kare kai'na da taimakon Ubungiji na) a hankali yace" Zeinab ki'nemi gafarar Mama idan ba'haka to irin Wannan zata dinga faruwa da'ke" daga kan'ta tayi tace" yaya Saif zaka rakkani to, watakila idan Mama ta'gan'ka ta hakura?" kai ya daga mata yace" zamu'je tare idan Mama ta'dawo zan'zo sai'na rakka'ki" a haka suka rabu. Bayan Sallah Magriba su Mama ta dawo bayan Isha'i kuma yaya Saif yazo dan'cika Alkawarin da'yama Zeinab, tare suka shiga d'akin Mama tana zaune bakin gado tana Hada kayan da zata fita da'su gobe dan bata'so ta manta wani abu, gaishe'ta sukayi bata amsa ba sai Saif ne yace" Mama dama Zeinab ce tazo ta baki hakuri akan d'uk abubuwan da suka faru a baya kuma ta gane kuskuren'ta Insha...." bai karasa ba Mama ta kat'se shi ta hanyar daga mashi hannu tace" kaga dakata, Saif ni'fa ina hushi'ne da ita Sabida bata aure'ka ba, kuma zan'daina Hushi da ita'ne k'awai idan ta aure'ka" ci'gaba tayi da abinda take cikin sanhin murya yace" Mama shifa aure nufi'ne na Allah idan ya kaddara shi babu abinda ke dakatar da'shi idan'da Allah ya kaddara aure'na da ita to'fa koda kune baku'so da sai'anyi shi kamar dai yanda da ya kaddara auren'ta da Mukhtar gashi d'uk da baku'so ba amma anyi" k'allan'shi Mama tayi tace" Saif wai'ke wane iri ne wane irin So ka'ke ma Zeinab anya'ko wannan So'ne?" Murmushi yayi yace" Mama d'uk San'da nake mata Dole na'hakura da hukuncin Ubangiji" cikin tausassan murya tace" hakane amma kasan abinda yafi ko'namin Ray a game da yarinyar nan?" kafin ya'bata amsa tace" Saif kai kasan Wahalar da'nasha tin'da nasamu cikin yarinyar nan nasha fama da Azabanben l'aulayi wanda ban'taba yin'shi kasancewar'ta mace ta farko da nasamu cikin'ta, Saif kasani ba'komi nake iya ci'ba ba komi yake birgeni'ba haka nabi d'uk na'lalace, nazo saida nayi sati biyu ina nakudar'ta kafin lokacin Haihuwar ta yayi mukaje Asibiti, sanin kan'kane saidai aka shiga d'akin tiyata da'ni ana shirin parka ciki'na a fiddo'ta Allah yayi Ikon'sa na'haife ta da kai'na, sannan nazo rainnan'ta aka muka dinga samun mat'sala da Mahaifin ta Sabida shi bai'yarda yaji kukan'ta ba koda da wasa take kukan kamar dai'kai, amma wai y'aou wannan Yarinyar ce dana rejeta t'sawon shekaru ita'ce takasa yi'min abinda zai'sani Farin ciki so'daya tak taki abinda nake'so" kuka ne ya k'wance ma Mama haka Zeinab ma kuka take kamar ran'ta zai'fita har'saida Mama ta ci'gaba da cewa" kin'gan shinan Zeinab wannan shi'ne na'so hada'ki da'shi amma kika'ki, ina'da Tabbacin Saif bazai'taba bari kiyi kuka ba, wannan da kike gani d'uk zama'na na Mahaifiyar'ki amma shine ya'ke kuka idan kina kuka, shine yake rashin lafiya idan baki'da lafiya shine yake shiga Farin ciki idan kina walwala, idan bakida lafiya baya bari a kai'ki ko'wace Asibiti da kan'shi yake duba'ki amma idan za'a maki Allura saidai wani ya'maki ita amma ba'shiba, Zeinab kin'gan shi'nan akan'ki saida ya koma kamar Sakarai akan'ki saida yasa hannu ya mari malamar Asibiti sabida ta maki Allura kin'fashe da kuka, nasan kin'san s'auran abubuwan daya maki sabida kinada Wayo wasu abubuwan suke faruwa, amma yaou wannan massoyin'naki shine kika'ki kika'ce baki san'shi, yanzu gashi'nan sabida bayada zuciya kula yana'ta zarya akan'ki" wani irin kukan Nadama da dana'sani ne Zeinab take'yi tashi tayi da gudu ta fita farfajiyar gida tanaji kamar ta ka'she kan'ta ko zata huta, ji'take wani gagarumin abu a game da yaya Saif haka'ma kuma tana jin'shi a game da Mukhtar to miye mafita, idan da Allah zai'd'auki ran'ta da taji dadi tasan Dole kowannen su zai'hakura. Saif ne ya same'ta nan Kafin yayi magana Abba ya shigo, dukawa Saif yayi ya Gaishe shi ya amsa cike da Kulawa yace" lafiya miya faru na'ganku anan?" Saif ne yace" babu komi Abba" k'allan su Abba yayi kafin yace" to Shikenan, amma Dan Allah ku'rage kebewa ku'kadai sabida gujewa fadawa halaka, na'yarda daku amma kunsan zuciya da Sharrin shedan yanzu ne sainya kai'ku ya baro'ku Musammam yanzu da ta'ke matar wani bai'kamata ku'dinga taba juna ba kamar yanda ku'ke adah, akwai Haramci akan hakan ku'kiyaye kin'ji ko" cike da Gamsuwa Saif yace" Mun'gode Abba Insha Allah zamu'kiyaye Allah kara girma" Ameen ya amsa ya dafa kan Zeinab yace" Mama'na jikin da s'awki ko?" kai k'awai ta g'yada juyawa Abba yayi zai'wuce ta rike hannun'shi cikin kuka tana fadin" Dan Allah Abba ka'yafemin laifin dana maku, Abba ka'rokamin Mama ta'yafemin laifi'na" kan'ta ya dafa yace" Mama'na na fada maki ba kimin komi'ba idan'ma kinmin to na'yafemaki kin'ji ko" wucewa yayi ya'barta dan harga Allah ya san ak'wai abinda ke damun'ta. Saif ne ya k'alle'ta yace" kiyi hakuri kin'ji kanwa'ta, Insha Allah Komai zai'yi daidai" hawayen'ta ta shahe tace" yaya Saif ina'ji kamar wani abu zai'faru da'ni Dan Allah ka'yafemin ka'kuma rokamin Mama ta yafemin, sannan ka'shaida na'yafema Mukhtar laifin da'yamin wala'alla nima ALLAH ya yafemin a dalilin yafemasa da'nayi" Murmushi yayi yace" haka ake'so kanwa'ta yafema wanda ya'maka ba'daidai ba Insha Allahu Allah zai'dubi wannan Jarumtar da kikayi ya yafe maki kurakuran'ki kema" kafin tayi magana mukhyya shigo gidan saidai ganin'su tare ba'karamin tinzira'shi yayi'ba, dan haka cikin hassala yayo kan'su da hanzari, yaci k'wallar rigar Saif yana fadin" kai miya hada'ka da matata mi'kake a wajen'ta?" cikin mamaki Saif ya k'alli Zeinab yace" a sani'na kamar an'ce mijin'ki malamin makaranta ne mai ilimi,amma naga aikin'shi baya nuna haka yafi kama da jahili?" kafin Zeinab tayi magana Mukhtar ya k'alle'ta yace" ni'dama nasani tin'da kika'zo gidan nan kika s'awya nasan ba banza'ba ashe kin'samu wannan kiba holewar'ki da'shi" maida k'allan'shi yayi ga Saif yace" wallahi idan na'sake ganin da matata to sai'nayi ajalin'ka" jin'haka ne yasa Zeinab ta mat'so cikin bacin Ray ta rike hannun'shi tana fadin" El moc kasan abinda ke keyi kuwa miye haka wannan fa yaya Saif ne dan Uwa'nnn..." ba'ta karasa ba ya'juya da karfi tare da g'alla mata wani Wawan mari ta bayan hannu, wanda akayi rashin sa'a ya sameta a wuya hakan kuma ya'zo daidai da Ajalin ZEINAB take ta fadi kasa babu rai'ajikin ta, ganin ta fadi ne yasa Saif fincike hannun Mukhtar daga rigar shi ya zube Kasa yana Kiran sunnan'ta hannun'shi ya kara Kusan hancin'ta taji babu sheda haka'ma ya dora dan yat'san shi a saman mashedar'ta a wuta nan'ma shiru, kara sunkuyawa yayi da nufin yajiyo bugun zuciyar'ta da karfi Mukhtar ya fizgo'shi yana fadin" Karka soma cewa zaka taba jikin matata" cikin zafin nama Saif ya'kaima Mukhtar wani Wawan n'aushi yana ya nuna shi da hannu yace" ba jikin matar'ka zan'taba ba ceto ran'ta nake'so nayi, idan kayi wasa to zata zama gawa'ne" juyawa ya yi da karfi ya dora kunnen'shi a kirjin'ta saidai ina babu ko alamun sheda, wata irin kara ya fashe da ita tare da ida faduwa zaune yana'ja da baya kamar gurgu yana Kiran" Shikenan ka kashe'ta ka kashe'ta ka kashe'ta Inna Lillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un, Inna Lillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un Inna Lillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un. 12/01/19 à 22:21 - Mme Sami😘: 💔BA SO BANE💔 *Gajeran Labari* Na📚 Samira Harouna 85-90📗 Sambatun da Saif keyi'ni yasa Nazir da'ke cikin d'akin shi tare da abokan'shi suka fito cikin s'awri dan ganin abinda ke faruwa, to basu fahimci wani abu ba gadai Zeinab k'wance a kafafun Mukhtar Saif kuma a gefe a kidime dan haka suka fara tambaya ganin babu wanda ya basu amsa yasa Nazir ya shiga cikin gida da gudu ya fada masu halin'da suka same'su, Abba da Tanti Nadiya ne suka fito da s'awran Yaran gidan Mama kuma tace babu inda zataje koma miye ya faru da ita ita tasani ita babu ruwan'ta, Abu dai kamar wasa haka aka d'auki Zeinab zuwa Asibiti inda aka tabbatar masu da rassuwar Zeinab kin, t'sananin tashin hankalin da naga'ni a wajan ba'zai misaltu'ba saidai nafi t'ausaya ma Saif sabida har'yanzu abu daya yake firtawa shine" ya kashe'ta ya kashe'ta shikenan ya raba'ni da ita" tinani nayi kodai k'wak'walwar shi ta samu mat'sala, Mukhtar kam hawaye ne k'awai ke'iya fita daga idan'shi haka Suna k'allo har'aka nufi da gawar Zeinab izuwa d'akin ajiye gawa ( Morgue) tin'lokacin akayi Karfin halin Kiran mutane ana sheda masu mutuwar ta'ta dare yayi sosai su Abba sukabar Asibitin amma banda Saif da Mukhtar wanda akayi'ta masu Magana kamar basuji suma'dai kamar gawawwakin..., a takaice dai anan suka k'wana basu masan cikin halin da suke ba, Abba ne ya shigo gida tare da s'awran magajiyan Zeinab kin dukan'su, Mama ce Zaune a falo ta kasa bacci sabida rashin dawowar'su amma tana ganin'su saita waye ta nuna bata cikin wata damuwa, zaune sukayi sai Abba daya wuce ya nufi d'akin Tanti Nadiya jin bata masu magana ba yasa ya t'saya ba'tare daya k'alle'ta ba yace" ki'shirya daga safiyar gobe zaki fara karbar ta'aziyar ta, ki'taimaka ki karbi gaissuwar'ta koda baki mata Addu'a" dammmm! gaban'ta yayi wata irin faduwa da s'awri ta k'alle'shi ta yunkura ta tashi amma sai'jiri ya debe'ta dan haka ta zauna da rarrafe ta karasa wajen'shi cikin kidimewa tace" Alhaji ina ya'ta miyasa'mu ya'ta ina ta'ke Dan Allah ka'fadamin?" wani irin Murmushi yayi mai'kama da kuka yace" yar'ki yar'kifa kikace, ko kin'manta kince kin'cireta daga yayan da'kika Haïfa sannan ba'ke ba'ita har'abada?"dafe kirji tayi ido waje cikin daga murya tace" a'a Alhaji kar'kemin ya'ta ta rassu dan Allah ka'fadamin gaskiya, nasan Zeinab bazata bar'niba ya'ta bazata mutu yanzu ba, ita kadai gare'ni mace mutuwa zanyi idan narasa'ta ka'taimakamin ka'kaini naga ya'ta" t'saki yayi ya wuce ya barta'nan k'allan yayan nata tayi gaba daya ta ma rasa kama sunan koda daya daga cikin'su dan haka k'awai sai'tace" kai" hakan yasa dukan'su su Shida suka juyo cikin kuka tace" ina ya'ta take miyasa'meta?" Nazir da'ke Karami a cikin'su ne yace" Mama kiyi hakuri Allah ya mata" bai karasa fada'ba AABOUBACAR ya wurga mashi harara, hakan yasa Mama ta fadi k'wance some da s'awri sukayi kan'ta na'dai ita'ma ta k'wana batasan inda take ba..., *Washe Gari* haka kowa ya samu labarin rassuwar Zeinab ba'karamin kidima da Damuwa kowa ya shiga'ba babu wanda bai'zubar da k'walla ba idan ya tina Zeinab matashiya amma Allah ya karbi abar'sa ( to Allah kenan baya barin wani dan wani yaji'dadi haka Mutuwa bata Duban Yaro'ne ko Babba, Tsoho ko Tsohuwa idan lokaci yayi to bamakawa zaka'tafi, Saidai muyi fatan Allah yasa mu'cika da Imani)👏 farin ciki ya koma bakin ciki shiyasa akace( wai ana bikin Duniya akan'yi na'kiyama) gashi'dai ana jiran Safiya tayi asha bikin Murnar karuwa da Aida ta'samu, amma yanzu ya koma bakin Cikin rasa uwa ga wasu kuma kamar Kaka take a wajen'su, abindai kam babu dadi Masha Allah gida ya cika da mutane kasancewar su masu hannu da shuni da kuma yawon familly gida yayi shiru ga Mama da'ke k'wance har'yanzu bata farfado'ba, haka aka d'auko gawar Zeinab daga Asibiti ake wuce da ita gidan'ta na gaskiya( To Allah yasa k'wanciya Hutawa ce). Shigowar Abba yayi daidai da fitowar Mama tana Kiran a kawo'mata yar'ta Abba ne cikin kunar Ray yace" Ramatou kenan wai'kece kike wannan h'aukan akan Zeinab ta rassu ai'kamata yayi kiyi farin ciki sabida ta rabu da wanda baku'so, haba Ramatou ace yar'da kika Haïfa ta cikin ki amma ki'ts'aneta sabida kaddara Ubangiji kina ganin da Allah bai'nufi auren ta da Mukhtar ba da zata aure'shine ai'kod muna'so to bazata taba Zala matar shiba, yanzu dai babu Mama'na dan haka sai'ki zauna kiyi farin ciki" Saif ne ya shigo a gigice rike da wuyan rigar Mukhtar yana dariya Yana fadin" kun'ganshinan wallahi shine ya kashe'ta shine ya bige'ta ta fadi ku'rike'shi kar'ya gudu" dakin rigar shi yayi ya nufi wajen Maman shi dake kokarin rike Mama ya rike hannun'ta yana fadin" Mama kin'gani ko ta'mutu shi kenan yanzu wazai kular mana da yayan'mu guda uku da muka Haïfa gashi kuma dan karamin yana'shan nono, kuma kinga Mama ni'dama na'fadamaki bana'san yarinyar nan k'awai dai ina san'ta ne amma ni ba k'aunar ta nake'ba k'awai tana birge'ni ne ko dariya yayi sai'takara k'yaou wallahi Mama sai'na bita, jiya mafa saida tace'min na'jirata a Aljanna amma gashi kuma ta tafi bamu hadu ba"kowa dake wajen ya fuskanci wani abu wanda nima na fuskan'ta wato Saif ya samu gushewar hankali, Mukhtar ya biyo Saif ne dan ya samu hukuncin shi dan rayuwa babu Zeinab batada wani anfani, Mama ce cikin tsananin fitar hayyaci ta shaki wuyan Mukhtar tana marin'shi iya Karfin ta har'saida hannun'ta yayi ciwo ta bari dan kan'ta sannan ta sake'shi tana kuka tace" miyasa miyasa Mukhtar miyasa zakayi haka mi ya'ta ta'maka, shin'kokasab Zeinab zallah soyayya ta nuna maka ta so'ka so'na hakika taki'bin umarni'na sabida san'da take maka,amma ka rasa hanyar da zaka saka mata saita hanyar rabata da ran'ta, wallahi wannan BA SO BANE ka nuna mata ko kadan BA SO BANE kuma wallahi sai Allah ya tada'ku ranar gobe kiyama ya Maku Hisabi mugu k'awai dama dan ka'rabani da ita ka'shigo Rayuwar ta ka raba'ta da dan uwan'ta" Kalaman Mama Suna kona mashi Ray Matuka ya Zaiyi yanzu saidai kafin ya farga Mama dake t'saye sukaga ta fadi, Wata irin kara naji mai karfi ana fadin Inna Lillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un.🤣🤣🤣 13/01/19 à 13:33 - Mme Sami😘: 💔BA SO BANE💔 *Gajeran Labari* Na📚 Samira Harouna 90-95📗 A firgice ta mike zaune tana'ta maimaita kalmar Inna Lillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un ta dafe kirjin'ta da hannu biyu, juye juye ta farayi bataga kowa a cikin d'akin ba da s'awri ta diro akan da gudu ta Buda kofar douche bataga kowa ba ko rufe kofar batayi ba ta fita da gudu tana k'walla kiran sunan" Honney, Honney, Honney" har'farfajiyar gida ta fito, kai t'saye wajen da aka kebe domin mot'sa jiki ta nufa tana'ci gaba da kiran sunan Honney, to nima dai ido na baza ina'so naga wannan Honney..., juyowa yayi tare da jefar da Ball kin dake hannun'shi ya na k'allan'ta cikin mamaki yanda take gudu kamar ta manta cikin da'ke jikin'ta, k'yak'yawa ne sosai gashi dogo sanye da kayan sports bude hannayen'shi duka biyu ta fada ciki ya mat'seta yana fadin" miye faru ne Mon Chouchou waya taba'min ke, keda nabari kina bacci?" dago da kan'ta tayi cikin kuka tace" yaya'na wallahi Mafarki nayi mara dadi" dariya yayi yace" haba Ma Belle yanzu mafarkin ne keda wannan hawayen?" cikin shag'waba tace" dan baka'san ko wane iri bane shiyasa kace haka, amma d'uk mafarkin da zai'sa naga bana tare da'kai ai ba'karamin mummunan Mafarki bane a gare'ni" shima cikin shag'waba kamar yanda ya rene'ta yace" Ohh My Gosh, sorry kin'ji Chouchou'ta hakan bazata saké faruwa ba" ita'ma cikin kuka mai kama da shag'waba tace" kuma fa Baka gani'ba wai na auri wani bâ kai'ba, kuma wanda na aura shiyayi sanadiyar mutuwa ta, sannan Mama ma ta fadi ina'jin t'soro kar'ace ta'mutu ita" hannun'ta ya kama suka koma falo ya zaunar da ita yace, "kin'ga kanwa'ta ta kai'na ki k'wantar da hankalin ki babu abinda zai'faru, ga'ki nan a raye babu abinda ya same'ki, sannan ga'ni tare da'ke kuma a mat'sayin mijin'ki sannan d'auke da cikin da'na na wata biyar" Murmushi tayi tace" hakane kuma fa, to amma ai a mafarki'na ma nasa'mu ciki amma dai shi zubewa yayi" ti kin'gani ko, amma ni naga nawa'nan a jikin'ki ba kuma jiya kinje awo an'tabbatar mamu da lafiyar shi" amma kasan abinda ya sani jin'dadi?" kai ya girgiza yace" sai'kin fada" cikin karsa'shi tace" naji dadin yanda naga ko a Mafarki irin Soyayyar da ka'ke nunamin a zahiri ita nagani a badini ma" jawota yayi ya Rungume ta yace" Zeinab ina san'ki sosai nasan ko a zahiri ko a Mafarki abinda zaki gani kenan" dago kan'ta tayi tasa bakin'ta a nashi ta t'sot'sa kafin ta k'alle'shi tace" ni'ma ina san'ka yaya Saif, wallahi naji nakara san'ka yaya'na tabbas bazaka iya Rayuwa Babu ni'ba kamar yanda bazan'iya rabuwa babu kai'ba" Murmushi yayi yace" to da kika mutu a Mafarki ni'kuma yanayi?" cikin kunya tace" haukacewa kayi" tabbas Zeinab ko ban'biki ba nasan abinda zai'faru da'ni kenan idan narasa'ki" tashi tayi tace, " ni Yinwa ma nake'ji bari na dafa'mana wani abu mu'ci" rike hannun'ta yayi yace" ai'kema kinsan tin'da kika samu cikin nan ba'kullum kike girki ba, yanzu ma Mama ta aiko maki da abinci kina bacci wai karki'sha wahala" zaune ta koma tana fadin" gaskiya su Mama suna'san su shag'waba'ni sosai karfa nazo na zama bukekiya" wani k'allo ya bita dashi yace" to zama bukekiya kuma ba y'aoushe ai saidai kiguji karawa" k'wabe fuska tayi tace" kaga fa bana'so ko wallahi zan'fa ma su Mama kana cemin bukekiya" dariya yayi ya jawota yace" yi hakuri kar'ki fada kinfa san yanzu yanda su Mama ke ji'dake basu'son wani abu ya tabaki ni narasa dalilin wannan shag'waba kin da suke" cikin ji'dakai tace" sabida ina d'auke da jikan'su ne kuma Mama ni'kadai gare'ta mace shiyasa sukemin haka". Abinci sukaci inda Zeinab ta takura sai sun'buga Ball kamar yanda suka saba, ba yanda ya iya Dole suka'yi kafin yace ya gaji gashi kuma La'asar ta'kusa t'saye tayi waise ya goya'ta ko taki shiga d'akin yana sunkuyawa tayi kalam ta Haye bayan'shi haka har'saida ya kai'ta douche wanka sukayi suka fito cikin shirin sannan ya nufi Massalaci ita ma tayi Sallah, ta jima tana Addu'a da Allah yasa Saif ya zama miji'ta ya kula nuna mata ai'nahin wane'ne Mukhtar sannan tayi farin ciki da taki karbar Soyayyar Monsieur Mukhtar Ashe ba Alkairi bane a gare'ta, da haka ta saké daga hannu sama tace" Allah Nagode maka da ka bani Yaya Saif a Mat'sayin Mijin aure'na Allah ka kara Bamu zaman lafiya mai dorewa Allah ka sa na'haihu lafiya, Allah ka kare'min Yaya Saif ka bani ikon K'yaoutata mashi da yi'mashi biyayya" Ameen. Yana dawowa daga Massalaci suka zauna akan Kujera Zeinab d'uk ta nar'ke a jikin'shi taki zaune da kugun'ta, cikin Zolaya yace" ke dan Allah ki'daga ni d'uk kibi kin haye'ni haba sai'san jikin t'siya" dariya tayi tace" to ai d'uk kai'ne ka sabamin kai'ka kaya'min koma minene" eh to dan nakoya maki sai'kuma akace bazaki z'auna da kugun'ki ba kamar wata marar lakka" bata Ray tayi kamar zata'yi kuka ta bashi baya wai ita antaba'ta, rarrashi ya fara kuma" haba yar Mama da Abba da Mama da yaya Saif kiyi hakuri wasa nake maki dama" cikin shag'waba tace" ni ban hakura ba wallahi sai'kaban wannan abun sannan" sanin ko miye yasa ya tashi ya shiga d'akin shi ya fito yana Mika mata Chocolat Babba yace" to ga Shi sai a hakura yanzu ko?" kara juya baya tayi tace" ni ba Daya nake'so ba sai guda biyu" ya sani dan haka ya fito da Daya hannun da yasa Aljihu ya Mika mata yace" to gâta shi kenan yanzu?" da karfi ta jayo'shi ya zaunar dabas ta Rungume' shi tace" Merci beaucoup Mon Ange" to nidai na peceee Alla bar Soyayya❤🙏?. *Yan Uwa anan nakawo karshen Wannan littafi mai sunan BA SO BANE ina fatan za'a anfana da shi* ********************** ? ************************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************? ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ? ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ? ************************** Idan Zeinab ta haihu zan'fada maku muje biki😁 *My Meelat bazan manta da'ke ba*😘 Alhamdu lillahi Kassiran👏