[18/07 8:51 PM] MIM✍🏻: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com ********************** ? ************************** ********** Ai Hausa Novels **************** *************************? ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ? ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ? ************************** loadιng...........✍🏻 🌐 _*FAHIMTA FUSKA*_ Written by UMMU MUFEED (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- BILKISU INA DANGINA IZZAR MULKI JININA AMANATA MAIMUNATU YAƘI A SOYAYYA And now FATIMTA FUSKA _Ina kuke Masoyan Hikima, kuma Masoyan Maimuna Isah Musa (Mrs Aliyu) masu son ci gaban ta, gata ta yunƙuro ta farfaɗo muku da wani Sabon shahararren littafinta me suna *Fahimta fuska*_ _Tab ay ko daga jin sunan ma kasan labarin zaiyi Sugar, sannan tazo muku da salon rubutu salon labari wanda baku saba gani, domin labarin yasha bam-bam da sauran labarai, ga duk me buƙata zaibi wannan tsarin👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻_ *FAHIMTA FUSKA Na kuɗine Naira 300 kacal👌🏻Zaka/ki biya ta wannan account* *0019138715* *Maimuna Isah* *StanbicIBTC* *Sai ka/ki tura min shaidan biya ta wannan number 09034313679* *Ko katin MTN na 300 ta wannan number* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page 1&2 Fitowa tayi daga cikin ɗaki tasa riga da wando sannan ta matse cikinta da belt tasa takalmi me tudu wanda da kyar take tafiya tasa abaya akan riga da wandon ta yafa ɗan kwalin abayan ta fito a kicin ta shiga ta samu Mamanta tana faman hura wuta ta ce "Mama na tafi " Mama ta ce "Ina zaki je kuma Rahma?" Ta ce "Birthday ɗin ɗan ajin mu mana ba na faɗa miki ba" Mama ta ce "To da kika faɗa min kuma sai na amince ko?" Ta ce "Haba Mama dan Allah ki kyale ni naje mana" Ta ce "Rahma bawai ina hana ki bane baki san kallon da ake miki a unguwar nan ba, saboda yawon zuwa biki da kike yi, har cewa fa ake ciki gare ki saboda yanzu idan zaki fita ɗaura belt kike a cikin ki, kuma nima na fara zargin hakan duba da yadda fatan ki ta dawo kiga yadda kika canja Salma fatan ki sai sheƙi take " Tuni Rahma ta durƙusa ƙasa ta ce "Wallahi tallahi Mama ban ta'ba sanin ɗa namiji ba, balle nayi ciki, Mama ki min kyakykyawan zato ba haka nake ba, Allah ne shaidata, nidai nasan ina da son zuwa biki da fita birthday amma wallahi Mama bana bin maza" Mama ta ce "Na yadda da ke Rahma, saboda nafi kowa sanin halinki, abin da nake so da ke kibar maganan zuwa biki da kike Idan kika yi hakan wannan zaisa mutane su fara zargin ki sannan kuma maganan ɗan ajin ku kuma ki barshi tunda yanzu fita zakiyi daga makarantar tunda kin zana jinior waec ay yanzu ma ana shirye-shiryen tafiyanki boading school ne, ki karasa babban secondary acan tunda kince kinfi son makarantar kwana , dan Allah Rahma kada ki bamu kunya kinga ku biyu ne kawai muka haifa a duniya keda yayanki shima fatan mu Allah ya bashi nasara akan aikin da yake nema " Ta ce "Amin" Komawa tayi ɗaki tana zubda hawaye ta fara cire kayan tana duba jikin ta, tabbas ta canja kuma ba komai bane illa shafe-shafen kurkur da lalle da ta fara yi saboda Allah yayi ta baƙa, baza tayi bleaching ba amma tana son ta gyara fatar ta to gashi fatar tata tayi sheƙi kalanta ya fito da kyau, Mama ce ta shigo ta ce "Kije amma ki dawo kafin magrib" Ta ce "A'a Mama bazan je ba, kuma daga yau biki idan ba na dangina bane na barshi" Asalinsu... Garin Kaduna gari ne wanda ya haɗa yarika da dama wanda duk cikin yarikan Nigeria ɗaiɗaiku ne babu haka kuma suke auran junan su, mafi yawanci zuwa suka yi ɗaiɗaiku ne wada zaka ji suna cewa su ƴan garin Kaduna ne. Malam Auwalu kuwa Maraya ne a gidan Marayu ya girma a cikin gidan ya haɗu da matarsa Lariya ya aureta, shekaran su ɗaya da aure ta haifi ɗa Namiji aka sakabmasa suna Lukman. Saida Lukman ya shekara shida kafin Lariya sake samun wani cikin ta haifi ƴarta mace sunan ta Rahma, Lukman fari tas kyakykyawa, sa'banin Rahma da take baƙa sannan ita ɗin ma ba baya ba wajen kyau. Rahma akwaita da rawan ga galli shiko Lukman yakan tsokaneta ya ce Ƴar baƙa, haka zata yi ta kuka har sai Mama tayi magana. Baban Su Auwalu kuwa sana'an gwanjo yake yi dan haka baza ka kira su masu arxiki ba sai dai ace suna da rufin asiri. Rahma ta tashi idan dai ta ji kiɗa ko ana biki a wani gurin haka zata tafi, duk wani biki idan dai a unguwar ne sai ka ganta a gurin, ta taso da son sa ƙananan kaya, duk gwamjon da Baba ya ɗauko sai ta fara za'bewa kafin yakai kasuwa koda ta gama primary rawan kai ya ƙaru, ita da kanta take shiryawa ta ce "ta tafi biki" ƴan unguwa suka fara kawo wa Auwalu tsegumin wai idan baiyi da gaske ba ƴarsa zata lalace, ya ce "Shidai yana bin ƴaƴansa da Addu'a kuma Allah zai kare ta, wannan abin ma da yaga ay yarinta ne. Haka aka gyale shi sai kuma aka fara gulmace-gulmacensu. Koda ta fara secondary tayi ƙawaye to duk bikin da za'ayi a gidan ƙawa ko aboki ɗan ajin su sai taji, musamman ma kuma ace an gayyace ta, tana JS 3 suna shirin zana jinior waec ne take jin labarin wai idan kana shafa Kur-Kur da lalle hasken fatan ta zai yi kyau, kasancewan ta baƙa kuma tana son tayi kyau yasa ta tambaya ko zai sata bleaching aka tabbatar mata bazai sata wani bleaching ba, saidai zata yi kyau da sheƙi. Haka kuwa da take yi tayi kyau baƙar fatan ta ta sake fitowa da kyau, a lokacin kuma take da shekara sha uku lokacin kuma duk alamomin budurcin ta suka ƙara ha'baka hip ɗinta yayi babba ƙirjinta ma ya ciko, ga hasken da tayi ta ƙara kyau, lokacin kuma ta tsiro da wani kwalliya na ɗaura belt a ciki, idan ta ɗaura ta fita abin ta, ganin magulmata sunyi yawa yasa bata gaida kowa a unguwar wannan yasa suka fara raɗeraɗin cewa hala ciki gare ta, ay dama wannan yawon bin maza da take dole tayi ciki, abu har yaje kunnen Auwalu ay kuwa ya nuna musu 'bacin ransa. Koda ta jana jinor waec ya cire ta a makarantar ya ce "Zai kaita ta kwana saboda saboda ya huta da tsegumin mutane itama zata fi nutsuwa dan ya lura itama tana da rawan kai. Ci gaba... Tun lokacin bata ƙara fita ba haka tana jin ana biki amma bata zuwa ita komai ma ya fita mata a rai so take ma ta tafi makarantar ta ko ta huta a can. Ganin ta a takure kamar bata da lafiya yasa Mama ta fara yarda da Maganganun mutane gashi sai ƙara yin sheƙi da haske take kuma hips ɗinta sai ƙara ciƙo wa take, kuma wannan ya faru ne saka maka kurkur da take shafawa sannan tayi wanka da lalle. Kiba kuwa saboda a lokacin ne alamimin budurcin suke fitowa gaba ɗaya, a hakan aka mata aka shirya mata komai aka kaita Makarantar kwana da ke cikin garin kano, Baba da Lukman ne suka rakata saida tabbatar sun gama mata komai sannan Baba ya bata babbab waya da labtop ya ce " Na siya miki waɗannan ne saboda karatun ki ko kuma idan an baki assingment kiyi anan" Lukman yayi Dariya ya ce "Kai Baba sai kace jami'a me a karatun secondary" Baba ya ce "Kai zaka ce haka tunda ka riga ka wuce ita yanzu zata fara" Idon ta ne ya ciƙo da kwalla ta ce "Na gode Baba, Kuma ku ya yafe min ka faɗa wa Mama ma dan Allah ta ya fe min" Lukman ya ce "Me haka, dalla shiga ciki, kije ki samo mana likita, ohhh na manta ashe ma lowyer ce" Juyawa tayi tana kuka zata shige cikin sauri ya kamota, sai da suka tabbatar sun lallasheta harda sata dariya sannan ta shiga ciki. Har ta ɗan yi nisa sai ta juyo da sauri ta ce "Lah Yaya na manta da Lallena da Kurku dan Allah kace Mama ta ajiye min kada ya 'bace idan zaka zo sai kazo min da shi". lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻 [18/07 8:51 PM] MIM✍🏻: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐 _*FAHIMTA FUSKA*_ Written by UMMU MUFEED (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- BILKISU INA DANGINA IZZAR MULKI JININA AMANATA MAIMUNATU YAƘI A SOYAYYA And now FATIMTA FUSKA *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page 3&4 Murmushi yayi ya ɗago mata hannu alamun bamsuwa, saida taga fitansu a get sannam ta juya tana share kallan dake zubo mata. Ss 1 ta shiga, tunda ta shiga makarantar ba ruwanta da kowa karatunta kawai tasa a gaba, bata da ƙawa, ƙawarta kenan biro da takarda, yawancin ɗalibai suna mata ganin mai girman kai dan bata fiya magana ba sai akan karatu, hakan kuwa da take ba ƙaramin birge ɗalibai yake ba domin suna son yara irin haka. Rayuwan makaranta yasa ta rame wannan hasken da ta fara babu shi don yanzu ba shafe-shafen take ba karatunta tasa a gaba, takura kanta da tayi ne yasa ta ƙara min bakin akan asalin baƙin ta. Koda ranan Visting yazo ba wanda yazo mata, haka wani watan ma ba wanda yazo, da wani watan yazo kuwa wanda shine ƙarshe sai kuma hutu Ya Lukman yazo saidai kuma kuma yazo a ƙurarren lokaci bai samu ganin ta ba, ita kuma dama ta ce baza ta fito ba dan tasan ba wanda zaizo mata, dalilin hakan yasa ta zauna a hostel. Randa akayi hutu kuwa ta haɗa kayanta bayan an bada hutu ta ɗauka ta fito get sannan taje banki ta ciro kuɗi dan Yaya Lukman ya turo mata kuɗin motan komawa garin su Kaduna, tana cire kuɗin tayi tasha tahau mota saida ta jira motar ta cika sannan suka tashi. Saidai kuma sha'anin ƙarfe saida suka shiga daji motar ta lalace a hanya, haka suka tsaya dan a gyara ta, amma bata gyaru ba, ƙarshe dai aka kira bakanike sannan me motar ya fara neman motar da zaisa fasinjojinsa, a hakan yake share motoci duk a cike wanda ba a cikin bane kuma sai a samu asa mutun ɗaya. Mata masu yara ake sawa kasancewan Magrib ta kusa. A hakan dai har isha ta cin musu a gurin da kyar aka sama wa Rahma mota ita ma ta shiga, duk hankalinta a tashe Allah-Allah take ta ganta a gida ga kuma garin ya haɗu da hadari hakan yasa garin yayi duhu sosai. Suna cikin tafiya barci ya kwashe ta kar a mafarki sai ji tayi ana cewa "Innalillahi wa Inna'ilaihir raju'un" Buɗe ido tayi taga hanken fitila me haske akan titi ji tayi suna cewa "Ku fito duka" Rahma ta ɗauki kayan ta dama wayarta ta mutu ba chaji yasa ta tura ta cikin jakan kayan ta labtop ɗin ma tana ciki dan haka ta ɗauki jakan suka fito, suka basu umurnin su kwanta, itama ta kwanta tana yin hawaye, cikin ranta kuwa Addu'a take Allah ya ku'butar dasu daga hannun waɗannan azzaluman. Shiga motar suka yi sukayi ta binciken su can kuma suka fito, suna kallon su ɗaya bayan ɗaya idon ogan yakai kan Rahma ya dalle mata ido da fitila ganin jikin ta da Uniform ya ce "Ke ƴar makaranta me kike har dare yayi baki shiga mota kin koma garin ku ba?" Kasa magana tayi sai kuka da ta fashe da shi. Isowa gareta yayi da bindiga a hannunsa ya riƙo maya hijabi ya ɗagota ya ce "na miki wani abu ne" Tuni ta haɗiyi wani miyau me kauri cikin rawan murya ta ce "Kayi haƙuri dan Allah" Ya ce "Dawo ta nan" Ta kinkimi jamar kayanta ta koma gefen sa tana kuka, ya ce "Kina son na?" Shiru tayi ta kasa magana ɗaya daga cikin yaransa suka ce "kyale Aunty kawai oga nasan cewa tana no" Ya ce "Yo Idan ma taƙi basai in farfarke cikin ta ba" Ya kalleta yadda take kuka ya ce "Ƴar Baƙa faɗa min mana ko bakya sona" Da sauri ta ce "Ina son ka" Dariya suka kece dashi ya kalli sauran ya ce "Albarkacin Masoyiya ta na kyale ku ku tafi" Suka tashi suka shiga mota wani tsoho ya kasa shiga ya matso gaban ogan ya durƙusa ya ce "Dan Allah yallabai ka kyale yarinyar nan, kaga ƴar makaranta ce, kuma yanzu haka zata tafi gun iyayen ta ne in yaso daga baya kaje gun iyayen ta" Bai ce komai ba yasa bingiga a kirjin sa ya harbeshi tuni ya faɗi ya mutu. Kuka tasa kai ƙara, wata mata bayan ta shiga motar tana kallon ta tana yin kuka koda Oga ya kalle ta ya ce "Ku fito min da matar nan ta faɗa min kukan me take yi ?" Da Sauri Rahma ta miƙe ta tare motar tana cewa "Dan Allah ka kyale su su tafi " Ya ce "Driver ja akwalar motar ka" Driver kuwa yaja motar suka tafi. Durƙushewa tayi a gurin tana kuka, oga ne ya ɗauke mata kayan ta ya ce "Muje gida ko" Ta tashi suka tafi, suna tafiya tana kuka, ya ce " Nikan ma yadda za'a fara ruwan nan Fashi zaifi daɗi ku tsaya ku sama mana masarufi ni kan zan je naji amarci" Duka suka haɗa baki suka ce " To Oga" Su suka tsaya yayin da su kuma suka tafi, ɗakin bukka suka shiga ta zauna ya ce "Kina jin yunwa?" Ta ce "A'a Ya ce "Ok ni to barin fara ɗanɗanaki daga yanzu ko Matata" Wani Wari ne ya dosheta daya buɗe baki yana magana domin ɗakin matsatstsene shi kuma yayi kurkusa da ita. Ganin ya fara cire kayanta yasa ta fasa kuka. lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻 [18/07 8:51 PM] MIM✍🏻: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐 _*FAHIMTA FUSKA*_ Written by UMMU MUFEED (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- BILKISU INA DANGINA IZZAR MULKI JININA AMANATA MAIMUNATU YAƘI A SOYAYYA And now FATIMTA FUSKA *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page 5&6 Torch light ɗin hannun sa ya faɗi haka ya haska Sama ta hango ƴar ƙaramar wuƙa a damtsen sa, yana ƙoƙarin cire wandon tayi tsalle ta zare wannan wuƙar batayi wata-wata ba ta luma masa a cikin sa tabar wuƙar a jiki faɗuwa ya kama gurin tuni ya fara malala a gurin ta tsallaka shi zata wuce ya ja ƙafarta ta faɗi a kan cikin sa wuƙar ta kuma shige ciki ya kuma tsala ihu ita kuwa tayi azama ta fito daga ciki kwashi kayanta ta fita tayi cikin daji da gudunta saida tayi nisa sannan ta tsaya tana haki saida ta ɗan huta sannan taci gaba da tafiya, hanyan da zatayi titi ma ta 'bace mata ita dai tafiya take gaba daji baya daji, buɗe jakan ta tafi ta ɗauko wayarta ta kunna sai taga 5% ne haka ta ringa haskawa daga bisani kuma ruwa me ƙarfi da ƙankara ya zuge ta juya ba inda zata ra'be dan haka tasa wayar cikin aljihunta taci gaba da tafiya, jin kukan jarirai ta riga yi wanda ba guda ɗaya ba, tsoro ya kamata cikin ranta ta ce "Shikenan na haɗu da Aljanu" Ta ɗaga kai ta ce "Ya Allah kai ka ce kana amsar Addu'a lokacin da ake ruwan sama ya Allah ka fidda ni daga cikin wannan daji, Allah ka ka kare ni daga mungwayen Aljanu" Ji tayi ba sauran tsoro kuma a ranta kuma tana ci gaba da jin kukan, ba tare da tsoro ba tayi inda taji kukan tana zuwa gurin akayi walƙiya haɗe da tsawa ya haska mata wata mata da jarirai a kan kirjin ta ta rungume. Addu'a ta fara yi sannan ta ce "Mutum ce ke ko Aljana?" Sai taji shiru ɗauko wayar ta tayi ta haska taga da sauran chaji saidai da yake ruwa ya ta'ba wayar screen ɗin yana rawa, ta haska matar cikin ranta ta ce "Ƴar Adam a wannan dajin kuma" Sa kunne tayi a ƙirjin ta taji zuciyar bata bugawa ta saka a wuyanta nan ma shiru ta kalli yaran su uku taga yadda suke tsala kuka gasu ƙanana ne sosai kuma ba kaya a jikin su daga su sai pampas ta ɗauke su ta rugume cikin hijabin ta ta kama jijjiga matar tana cewa baiwar Allah ki tashi ki basu Nono, ɗaga kai tayi ta hango hanken torch light sai ji tayi nuna cewa "Bata Mutu ba, ga can hasken waya ina kalli" Sai kuma taji wani daga cikin su ya ce "Ku kasheta sannan ku kashe ƴaƴan, na faɗa mata Bana son ganin gudan jinin AL'AMIN a duniya, amma tabar taurin kai shine zata haifa masa har uku" Duba wayan tayi tana ƙoƙarin kashewa sai kuma ta mutu gaba ɗaya, tashi tayi da yaran ta sake nausawa cikin daji dasu, 'boyewa tayi a cikin wani shinge tana kallo suka zo gurin taji suna cewa "Ta mutu, Amma Ina yaran suke" Taji wani ya ce "Dalla kyale su kasan Bakwaini ne, basa son sanyi musamman ma yadda ake ruwan nan mutuwa zasuyi" Ya ce cikin ɗaga Murya "Al'amin bana son ganin ka haihu, yau ga Masoyiyar ka nan ta mutu, yaran ka sun mutu sai inga yadda za'ayi ka sake haihuwa" Ɗaya ya ce "Ni duk randa na ga yayi aure sai na masa dandaƙar ɗan taure na fasa ƙoyayen haihuwar" Dariya suka fashe dashi sannan suka bar gurin, ta kalli yaran cikin duhu duk da ba kallonsu take ba sabo da duhu dan ma yanzu an ɗauke ruwan. Ganin sun tafi yasa ta isa gurin tana zuwa ta kuma jijjigata sai kuma ta tuna ta mutu, ta kwantar da yaran a jikin gawar sai itama ta kwanta lokacin duk sunyi barci, Can kuma ta tuna ay zasu iya dawowa da sauri ta tashi ta buɗe jakan kayanta ta ɗauko bargonta ta sanya su a ciki ta ɗauke sy ta tafi dasu sai da tayi nisa da gurin sannan ta shimfiɗe su, Tunawa tayi batayi Sallah ba yasa tayi taimama ta rama sallolin da ake bin ta wato Magrib da isha" *** Mama kuwa tasan yau ƴarta zata dawo har da yi mata girki Ya Lukman kuwa Kaji ya siyo aka soye mata, duk suna farin cikin zata dawo, Saidai tunda La'asar tayi Mama ta fara sarewa dan tasan tsakan Kano da Kaduna yayi ace ta iso amma shiru har yanzu. Dan ta kirasu ta ce tana hanya, ga wayanta a kashe. Koda Magrib tayi kowa ya shiga damuwa Musamman Ya Lukman. Da dare kuwa sunyi cirko cirko dukan su a tsaye, karshe dai ba wanda yayi barci a cikin su. *** Batayi barci ba har asuba tayi taimama tayi Sallah, Saida gari yayi hanke ta miƙe ta ɗauki yaran dan yunwa suke ji tun daren sukayi ta kuka, data je tasa musu Nonon gawar Uwarsu a baki koda zasu samu ruwa, duk da tasan ba abin da za'a samu a jikin mamaci. Tana zuwa gurin taga wayam, dube dube ta fara yi ko ba gurin bane amma kuma sai taga wayar ta a gurin da jakarta, tabbas gurin ne amma gashi ba gawar matar. Wata zuciyar ta ce "Kodai sun dawo sun ɗauketa ne " Durƙusawa tayi tare da sa wani kuka me ban tausayi ta kalli yaran da suke yin kuka, ta cire musu Pampas taga duka Mata ne, tausayin su ne ya kamata, kawai ta gyara zama ta ɗaga rigarta ta bawa wacce tafi yin kukan Nonon ta ay kuwa ta fara ja duk da Bakwaini ne, Zabura tayi dan wani irin zafi taji, ta cire bra ɗin dake jikin ta ta ɗauko ɗaya ma ta ɗosana mata Nonon Itama ta fara ja, Duk zafin da take ji ba hanabta cire musu ba, A haka sukayi barci ta sasu a kan bargon ta ɗauki ɗayar ma ta fara bata, itama tayi barci duk da ba Wai sun sha wani Abu bane Illa tsotsan fatar ta da sukayi tayi. Canja taya tare da Tattara sauran kayanta tayi, buɗe jakarta tayi ta ciro zaninta tayi ƙokari tasa biyu a bayan ta ta goye su kamar yadda taga ana goyon ƴan biyu sannan haɗa kyar ta tukuikuye ɗaya a cikin bargo ta riƙeta da hannu ɗaya, hannu ɗaya kuma ta ɗauki jakarta, tana miƙewa ta fara hango motoci Alamun titi ne a gurin da sauri tayi Titi tana zuwa ta tare mota dama tana da ƴan Sauran kuɗinta, duk cikin motar kallonta ake aganin jarirai ƙanana a hannun ta saidai ba wanda yayi magana. Suna Isa kaduna Ta hau Napep tayi gida, ana sauƙeta ta shiga gida taga Mama, Baba da Ya Lukman. Ganin ta da Jarirai yasa suka waro ido cikin Mamaki... lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻 [18/07 8:51 PM] MIM✍🏻: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐 _*FAHIMTA FUSKA*_ Written by UMMU MUFEED (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- BILKISU INA DANGINA IZZAR MULKI JININA AMANATA MAIMUNATU YAƘI A SOYAYYA And now FATIMTA FUSKA *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* ********************** ? ************************** ********** Ai Hausa Novels **************** *************************? ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ? ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ? ************************** Page 7&8 Mama ta ce "Me nake gani ne haka ni lariya, dama abin da mutane suke faɗa akan ki gaskiya ne, waɗannan yaran su suka hanaki dawowa tun jiya, dama haihuwa kika tsaya yi" Baba ya ce "Rahma waye uban yaran nan" Ta ce "Ban sani ba Baba nima..." Ji tayi Mama ta bata mari har saida yariyar hannunta zata faɗi ta saki jakan hannunta ta tallafeta tare da rungumeta tana kuka ita ko Yarinyar ta saki ƙara ta calla kuka. Cikin kuka Rahma ta ce "Mama Yaran nan yunwa suke ji ki taimaka ko ruwan ɗumi ne ki basu " Wani Marin ta kuma ji tana ɗaga kai taga Baba ne, kuka tasa yayin da yaran duka sukayi ta calla kuka Ya Lukman ya ce "Rahma waye Uban su, ki faɗa min mun ɗauki ƙaddara kuma muna farin cikin zuwan su duk da cewa ba ta hanya me kyau aka same su, amma zamu rungume su" Zatayi Magana sai gani tayi An watso mata kaya Ya Lukman ya miƙe ya ce "Mama me haka kuma" Ta ce "Baza ta zauna min da shegu ba, dan haka ta koma gun Uban su" Ya Lukman Ya ce "Yanzu Ina zata je ga yara suna kukan yunwa " Baba ya ce "Rahma kin cuce ni kin cuci kanki kije na sallama ki a duniya" Ya Lukman ya ce "Baba harda kai" Rahma ta ce "Bani na ha..." Mari Mama ta kuma mata a baki tare da ɗauko muciya zata buga mata Ya Lukman ya Amshe yarinyar hannunta da take ta tsala kuka yana kuka ya ce "Indai Rahma zata bar gidan nan nima bazan zauna ba, Me yasa baza ku bita a hankali ba, ga yara suna jin yunwa, ko ruwa kun kasa basu, ita kanta nasan tunda ta haihu bata ci komai ba, ya kamata abi komai a sannu amma kunƙi kun yanke mata hukunci cikin fushi " Amsan Yarinyar Mama tayi ta tunanin ta ta huce ne, sai gani yayi ta miƙa wa Rahma, shi kuma Baba ya hankaɗa shi ɗaki ya kulle tare da sa kwaɗo. Mama ta kalli Rahma ta ce "Ki tattara kayan ki ki bar min gidan nan Idan ba so kike na rotsawa yaran nan kai ba" Ta ce "Wallahi Mama bani na haife su ba, idan ƙarya ne muje ki duba ni" Ba ke kika haife su ba uban wa zai baki yara har uku ko zaki ce tsintansu kika yi, daga ganin su yara ma Basu cika tara ba, bakwaini ne waɗannan yara, to ma waye zai zubda yara Uku kuma Bakwaini dama can kin tafi da ciki makaranta gashi kin haife su sai ki koma gun uban su" Zatayi Magana Mama ta ɗaga Muciyar "Idan baki tafi ba zan rotsa muku kai dada ke har su" Tashi tayi tana kuka ta ɗauki jakan da tazo dashi ta rataya a wuyanta sannan ta gyara biyun da suke bayanta ta tallafi ɗaya kirjinta ta riƙe da hannun hagu sannan ta ɗauki jakan kayan ta, taji ya mata nawi kawai sai ta ajiye ta ta fita daga gidan tana kuka. Tana fitowa anguwa kuwa aka ringa kallonta yayin da wasu suke mata dariya, koda tazo wata majalisa sai ji tayi wani ya ce "Ƴar gidan Auwalu Me gwanjo ne cikin shege tayi gashi har yara uku hala koranta yayi" Wani kuwa ya ce "Ba ana faɗa masa irin shigar da take ba yana ƙin yadda ba yaƙi tsawatar mata" Wani ko ya ce "To ay shi yake bata kayan idan yayi Dilan gwanzo" "To ba gashi ta ja masa abin tsiya ba" Suka kwashe da dariya harda tafawa Da saurin ta ta wuce gurin kasuwa tayi ta siyar da Labtop ɗinta 35k, wanda zata kai 50k da wayar ta, wayar ne ma ta siyar da ita araha banza saboda ruwa ya ta'bata, su kuma zasu shanya idan ta bushe sai su siyar ma wani. Shagon kayan jarirai tayi kayan sanyi ta siya musu sai kuma ƴan ƙanana masu Arha sannan ta siya Madaran yara Nan da abubuwan da zasu buƙata haka ta fito kasuwa ta shiga Napep kawo tayi tana zuwa taga ya kamata ta sa musu kaya, wani gida ta shiga cikin ta yi Sallama bayan sun gaisa da matar ta ce "Dan Allah zan ɗan bawa yara Abinci ne, na sa musu kaya" Ta ce "To shigo mana ki basu" Ta shiga har ɗakin matar ta roƙi ɗan ruwan zafi aka haɗa musu madaran ta fara basu sai da ta basu duka suka sha, saidai atishawa suke tayi Matar me Suna Salma ta ce "Yaran kin nan suna Mura gashi ba kaya a jikin su ko za'a musu wanka ne" Ta ce "eh" Salma ce ta musu wanka duka aka buɗe su da powder sannan aka sa musu kayan sanyi tuni suka fara barci, Sannan Matar ta ce "To ko kema zakiyi wankan kafin su tashi" Ta ce "To" Ruwa me zafi ta sirka mata sannan ta kai mata soso da Sabulu bayi tayi wanka ta fito tasa kayanta riga da zani tana kallon su, Sai yanzu ta ƙare musu kallo ta gane Guda biyu suna ka da juna saidai ɗayar kamanninta daban. Barci suke amma kuma suna fitar da wani irin numfashi ga atishawa da suke akai akai. Salma ce ta shigo ta ce "Keko baiwar Allah Ina zaki nufa da jariran nan haka gashi ko cibi bata faɗi ba ?" Ta yi shiru tana tunanin abin cewa can ta tuno wata ƙaryan ta fashe da kuka ta ce "Yaya ta ce ta haife su sai ta rasu, shine Mijinta ya ce mu tafi garin mu da su shi bazai iya ciyar da su ba" Ta ce "Yanzu Ina ne garin ku" Ta ce "Kano" Ta ce "To Amma kafin ki hau mota ki fara kai su asibiti dan yaran basu da lafiya, dan kinga yadda suke numfashi ba a daidai ba" Ta ce "To" Tashi tayi Salma ta saka mata biyu a baya ta goyesu ɗaya kuma a hannu sannan tasa jakarta a wuya jakan Babies ɗin kuma a ɗayan hannun, Asibitin Barau dikko tayi tana zuwa aka nuna mata shashin yara, tana zuwa da akaga jarirai ne sai akayi da ita Matanity anan kuma aka kaita gunda ake kula da jarirai, Tana zuwa gun likitan da sauri ya amshi na hannunta yayi sauri ya cire mata kaya ya bar mata Pampas ya sata a cikin Kwalban da ake sa jarirai sannan ya sa mata naƙuran ƙarin numfashi. Ta sauƙe sauran ya amshe su cire musu kaya ya bar musu Pampas suma ya musu yadda yayi wa ɗayar saidai kuma bai sa musu naƙuran numfashi ba ya rufe du duka sannan ya dawo ya zauna ya ce "Madam kinyi kusa ki kashe yaranki, yakamata a ce suna fitowa duniya a sasu a nan, dan haka yanzu ma Addu'a zaki musu dan suna gab da su mutu" Durƙusawa tayi ta Fara hawaye tana ce wa "Dan Allah Doctor ka taimaka mana" Ya ce " Ki kwantar da hankalinki ki roƙi Allah ya ɗaga miki yaran ki" Ta dawo ta zauna ta ce "To Dan Allah akwai maganin da zaka bani don in samu ruwan Nono?" Ya ce "Ruwan Nono be zo bane" Ta ce "Yaran Yayata ce kuma ta rasu shine nake son in shayar da su " Ya ce "to kin ta'ba aure ne" Ta ce "A'a". Ya ce "Akwai Maganin da zan baki saida da kyar ruwan Nono yazo saboda kina budurwa, kuma me ƙarancin shekaru nasan baki wuce 14 ba, amma idan munyi Sa'a zai iya zuwa, saidai kuma idan sun ɗan sake girma sai a haɗa musu da Madara, amma yanzu barin baki yankan musu kati sannan in rubuta miki magungunan da zaki siyo musu, ya Sunan su da Sunan Mahaifin su? Shiru ta tana tunanin me zata ce, tasan dai sunan Mahaifinsu Al'amin dan taji a bakin Maƙiyansu, Su ɗin ne dai bata san sunan su ba, hala ma ba'a sa musu sunan ba. Sake cewa yayi "Madam Ina Sauraron ki". lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻 [18/07 8:51 PM] MIM✍🏻: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐 _*FAHIMTA FUSKA*_ Written by UMMU MUFEED (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- BILKISU INA DANGINA IZZAR MULKI JININA AMANATA MAIMUNATU YAƘI A SOYAYYA And now FATIMTA FUSKA _Ina kuke Masoyan Hikima, kuma Masoyan Maimuna Isah Musa (Mrs Aliyu) masu son ci gaban ta, gata ta yunƙuro ta farfaɗo muku da wani Sabon shahararren littafinta me suna *Fahimta fuska*_ _Tab ay ko daga jin sunan ma kasan labarin zaiyi Sugar, sannan tazo muku da salon rubutu salon labari wanda baku saba gani, domin labarin yasha bam-bam da sauran labarai, ga duk me buƙata zaibi wannan tsarin👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻_ *FAHIMTA FUSKA Na kuɗine Naira 300 kacal👌🏻Zaka/ki biya ta wannan account* *0019138715* *Maimuna Isah* *StanbicIBTC* *Sai ka/ki tura min shaidan biya ta wannan number 09034313679* *Ko katin MTN na 300 ta wannan number* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page 9&10 Shirun ta ƙara yi tana tunani kamar baza tayi magana ba can kuma sai ta ce "Babbar Sunanta ISLAM AL'AMIN" Ya sake tambaya Sunan Mahaifiyarsu fa, ta ce "Rahma" Ya tambaya ya ce "Ta biyun fa" Ta ce "IMAN AL'AMIN" Ya mata tambayoyi ta bashi amsa Sannan ya ce "Ƙaramar fa?" Ta ce "IHSAN AL'AMIN" Nan ma ya rubuta tare da yib tambayoyi bayan ya gama fitar musu da kati ya kalleta ya ce "Islam kenan na fara amsa dan naga ita ce Babba" Ta ce "Eh" Suka je tare suna ganin su yaga Temprature ɗin ƙaramar wato Ihsan yayi High da sauri ya buɗe kwalban sannan yaɗan rage zafin kwalbar ya kalleta ya ce "Me kika basu ne haka" Ta ce "Madaran jariraine" Ya ce "Kash waɗannan fa ba jariran da kika saba gani ana haifa bane, waɗannan lokacin haihuwansu baiyi ba aka haife su, dan haka ba komai za'a na musu ba, Ba wanka, ba bada ruwa sai ruwan Nono Zalla Idan bamu samu bane ba yadda muka iya dole mu basu madara, ba kowa zai na ɗauka ba, zaki barsu anan zansa Metro ta kaiki wani ɗaki duk bayan awa daya zaki na zuwa duba su kina basu Abincin su" Ta ce "To" Ya rubuta mata magani ya ce "Ga waɗannan kije ki siyo yanzu ki kawo" Ta fita da sauri taje Pharmacy ta haɗo magungunan ta dawo, Drip ya saka musu ya samu, ko wannen su a bayan hannunsu na hagu aka samu jijiya, sannan kuma ya buɗe magungunan ya ciro wani ya ce bata tablet ƙwaya uku ya ce "Kisha wannan zuwa yamma mu gani ko ruwan Nonon zai zo nan da yamma" Ta amsa ta shanye sannan ya ce ta zauna ya gwada mata yadda zata na goge musu cibi da sprit da Auduga Iman ta fara ɗauka tana gogewa sannan ta ɗauki Ihsan, lokacin da ta gama wa Ihsan kuwa Ya cirewa Islam Naƙuran ƙarin Numfashi har numfashin ta yayi daidai sannan tayi barci, itama ta ɗauketa a hankali tana goge mata tana gamawa aka fara kiran Sallah Azahar, ya kira Metro ta nuna mata ɗakin da zata zauna sannan, Mata ce a ciki su biyar sai gadaje uku Metro ɗin tayi Sallama ta ce "Maman A.J ga Abokiyar kwana na kawo miki" Wacce aka kira Maman A.J ta ce "A sannu da zuwa su Maman Najeeb nima nayi wata, ba Maman Salma ta tafi kuna min iya shege ba to ga wata tazo, wannan kan ma ƙanwata ce" Tayi gun Maman A.J ɗin ta zauna a bakin gadon da suke ta gaida su suka amsa, Suna haka Maman Sayyid ta shigo ta ce "Kece me ƴan uku ko"? Maman Najeeb ta waro Ido ta ce "Ƴan uku ta haifa" Maman Sayyid ta ce "Sa wasa" Maman Najib ta jinjina mata ita ko sai murmushi take. Sallah duk kan su suka je suka yi sannan suka dawo saura suka je suka dubo nasu jaririn. Kafin kace me Nonuwan Rahma sun ciko da ruwa saidai kuma zafi yake mata, bata damu da zafin da yake ba sai murna ma da take tayi, zuwa tayi ta samu likitan ta ce "Doctor mun samu nasara" Ya ce "Masha Allah to ki shiga ki basu zan turo nurse ta gwada miki yadda zaki basu" Ta shiga, Islam ta fara ɗauka ta bata Nonon tana ji ta fara tsotsa ta zabura saboda zafi saidai kuma bata fizge mata ba ta daure taci gaba da bata, Nurse ɗin ne ta shigo ta gwada mata yadda zata yi, ta yadda zata sa yaron ta ba tare da ya zuƙi iska ba. ( Wajen shayarwa mata suna yin sakaci da yawa, da yawan mu idan zamu bada Nono bamu san yadda zamuyi ba, sai yaro yayi ta tsotsan Iska idan yana tsotsan Nonon yana ɗan zuƙa yana yin ƴar ƙaran zuƙa kamar Babba yana zuƙan pure water sai kaji ana cewa ahhh yaron nan da tsotso yake, alhalin kuma iska yake ja ya shiga masa ciki, sai kaji cikin yaro ya kumbura ka sara me yasa, Wannan Iskan nan ne da yasha yake damun su, sai kaga yaro yayi ta yawan tusa, sannan idan an gaba bada Nono kawai sai a kwantar dashi tanan kuma yaro sai ya dawo da Nonon da yasha. Yadda zakiyi ki bada Nono kuwa abu me sauƙi ne, Zaki ɗauke shi, ki sashi a cinyar ki, kisa kansa a gwiwar hannun ki, tafin hannun ki kuma ya tallafo ɗuwawunsa ta yadda zaki manna cikin ki da nashi, sai ki ciro Nononki da ɗaya hannun zaki sa Babbar yatsarki a Saman Nonon sannan sauran yatsunki huɗu suna ƙasan Nonon kin riƙe masa, kiyi bismillah ki sa masa a baki, ki tabbatar wannan baƙin ya shige bakin sa duka, wallahi zakiji yana sha sosai, sanna idan yasha sosai sai ki juya shi ki bashi ɗayan kiyi yadda kika yi a wancan, Idan ya gama kuma ki sa shi a kirjin ki kina shafa masa baya har sai yayi gyatsa, da yawan mu kuma ba haka muke ba, sai a ɗauki yaro kawai a sashi a cinya a sake masa Nono yana sha wanda ta riƙe ne ma zata sa yatsan ta manuniya da ta kusa da ita ayi kamar almashi, to taya yaronki bazaiyi ciwon ciki ba. Ƴar uwa idan kina da yaro ki gwada wannan shawara ki gani.) Bayan Islam ta ƙoshi ta bawa Iman sannan Ihsan. lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻 [18/07 8:51 PM] MIM✍🏻: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_ 🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com loadιng...........✍🏻 🌐 _*FAHIMTA FUSKA*_ Written by UMMU MUFEED (Mrs Aliyu) Marubuciyar:- BILKISU INA DANGINA IZZAR MULKI JININA AMANATA MAIMUNATU YAƘI A SOYAYYA And now FATIMTA FUSKA _Ina kuke Masoyan Hikima, kuma Masoyan Maimuna Isah Musa (Mrs Aliyu) masu son ci gaban ta, gata ta yunƙuro ta farfaɗo muku da wani Sabon shahararren littafinta me suna *Fahimta fuska*_ _Tab ay ko daga jin sunan ma kasan labarin zaiyi Sugar, sannan tazo muku da salon rubutu salon labari wanda baku saba gani, domin labarin yasha bam-bam da sauran labarai, ga duk me buƙata zaibi wannan tsarin👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻_ *FAHIMTA FUSKA Na kuɗine Naira 300 kacal👌🏻Zaka/ki biya ta wannan account* *0019138715* *Maimuna Isah* *StanbicIBTC* *Sai ka/ki tura min shaidan biya ta wannan number 09034313679* *Ko katin MTN na 300 ta wannan number* Last free page Daga yanzu free page ya ƙare duk me buƙata sai ya biya 300 yasha labari. *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Page 11&12 Duka saida ta sasu ka kafaɗa suka yi gyatsa sannan ajiye su. *** Saida suka tabbatar tayi nisa sannan Mama ta buɗe shi ganin sa suka yi yasha kuka, wanda rabon da yayi tun yana yaro, bai musu magana ba ya fita Mama ta kalli Baba ta ce "Wai mu yarinyar nan zata yi wa haka? harda haihuwa, ka duba kallon da mutanen unguwar nan suke mana mun sangarta ta ashe da gaske ne" Ya ce "Yanzu ay sai taje ta nemi uban yaran" Lukman ne ya dawo ya ce "Da ba a gabana aka haifi Rahma ba wallahi da nace ba ku kuka haife ta ba, dan tayi cikina waje Allah ya azirta ta da ƴaƴa har uku sai mu kore ta don me, meta muku yarinyar nan ko Abinci bata ci ba ga jego, to me yasa ma baza mu hamshi ƙaddaran da Allah ya aiko mana da ita ba, mu rungumeta, yanzu da kuka koreta kunfi son ta koma gun ɗan iskan kenan suci gaba da zaman zina, tayi kuskure abaya amma a yanzu duk abin da Rahma tayi bata da laifi, Wai Mama kun manta da asalinku ne, a gidan Marayu fa kuka rayu, bamu da dangi to dan me yasa mun fara haɗa family zamu guje su, Baba kai da kanka ka ce kana son mu haɗa zuri'a saboda kasancewar ku baku da ƴan uwa, to ga Allah ya fara Azirta mu kuma kunyi watse da mu, shin kuna zaton Allah zai barmu haka nan ne ba tare da yayi fushi da mu ba?" zai ci gaba da magana yaga Mama tana hawaye da sauri yaje ya kama hannun ta ya ce "Banso in saki hawaye ba Mama, amma kun aikata babbab kuskuren da baza mu ta'ba gyarawa ba, dan ba musan inda zamu samu Rahma ba" Ta girgiza kai ta ce "Ba kai ka sani kuka ba, Ina nadaman kuskuren da na aikata ne, lalle ni ba uwa ta gari bane, bai kamata in mata hukunci ta wannan hanya ba, ya kamata in rungumeta a jiki ita da abin da ta haifa" Baba ya ce "Gaskiya mun aikata kuskure amma yanzu kira mana number ta muji kota kunna" Lukman ya ce "A kashe ne, Baba da ka bari na bita da duk haka baza ta faru ba, nasan kuna cikin fushine yasa kuka aikata hakan a niyyata duk inda muka je idan kun huce sai mu dawo gare ku" Baba yace "Yanzu tashi muje ko zamu samu labarinta" Tashi suka yi suka fita suka bar Mama tana kuka. *** Tana dawowa daga Sallah la'asar Maman A.J ta ce "Wai Maman ƴan uku har jinin ya ɗauke miki ne, naga kina zuwa Sallah" Murmushi tayi ta ce "Ay washe garin da na haihu jinin ya ɗauke yanzu baya zuwa" Maman Sayyid ta ce "Ni kwana na uku da haihuwata jini ya ɗauke" Maman Najeeb ta ce "Mukan gamu muna ta fama " Zuwa tayi ta goge musu cibi sannan ta musu Addu'a zata wuce likita ya ce "Akwai Sallan gawa idan zakuyi wani bawan Allah ya kawo matarsa da ta rasu a haihuwa ba ɗan garin nan bane shine ya kawota nan don al'umman Musulmai su sallaceta" Ta ce "Allah ya jiƙanta barin je in fada wa ƴan ɗakin mu waɗanda zasu iya zuwa sai muje" Ya ce "Kice wa Maman Najeeb Najib na kuka tazo ta bashi Nono" Ta ce "To" Tana zuwa ta sanar dasu Maman Sayyid Maman Abdul ne kawai suka ce "Zasu je, Maman AJ.da sauran suka ce su ba daman zuwa dan basu da tsarki" Maman Sayyid ta ce "To ga Sayyid, Abdul da ƴan uku duk suna ƙarkashin kulawar ku" Suka je suka samu an kawo gawar mutane da yawa sun halarta maza da mata Saida maza suka yi Sahun su sannan mata ma suka yi nasu a baya. (Da yawan mu mata bamu san cewa Mata na Sallah gawa ba, Idan an mana mutuwa sai maza su fita suje suyi Sallah mu kuma a barmu a gida muna ta kuka bamu je mun samu lada ba, yakamata muma muna fita muna yin Sallah Idan an tafi da gawa sai mu dawo gida muna gurawa mamacin Addu'o'in mu" Koda suka dawo saida taje ta duba su Islam taga suna barci ji tayi ƙaunarsu ta mamaye mata zuciya wanda taji zata iya sadaukar da rayuwanta a kansu kuma koda yanzu ƴan uwan su sun zo baza ta iya bada su ba, koda kotu za'a shiga cewa zata ita ta haife su, sannan ta dawo ɗakin su. Ƙarfe biyar suna zaune Likita ya aiko kiranta, ta tashi ta je ta same shi tare da wani mutum Fari ne dogo yana da kyau sosai kuma idan ka ganshi zaka san Naira ta zauna. Likita ya ce "Wannan Sunan sa Al'amin, ɗan Mai duguri ne wanda Matarsa ta rasu muka mata Sallah, to ya dawo ne dan ya taimakawa maras sa ƙarfi da suke asibitin nan, shine na bashi labarin ki, sai ya ce a kira ki" Cikin sanyi Murya ya ce "Da Mamaki amma ke kika haifi ƴan ukun nan kuma har zaki iya shayar da su" Ta ce "Da ikon Ubangiji zan iya" Ya ce "Ko da yake ay Saniya bata gazawa da ƙahon ta zaki iya ɗin" Likita ya ce "Da yake ay bakwaini ne ƙanana ne baza suyi tsotso sosai, amma idan sun girma dole zata haɗa musu da Madara" Ya ce "Kina da Account? Ta ce "eh" Ya miƙa mata biro da takarda ya ce "Rubuta anan" Ta amsa ta rubuta ta miƙa masa nan take ya mata transfer na 2m sannan ya ce "ki duba zaki ga na tura miki kuɗi kya siya musu madara" Ta ce "Bani da waya" Ya ce "To na sa miki 2m " Zamewa tayi ƙasa ta ce "Mungode Allah ya biya maka buƙatar ka ta alheri" Ya ce "Amin, Ki sani a cikin Addu'anki, Ina buƙatar ƴaƴa, sau uku matana tana haihuwa suna mutuwa, wannan haihuwar ne aka mata C.S kaka ciro mata ƴan wata bakwai duka suka rasu daga ita har su" Ta ce "Ayya, Allah ya kawo masu Albarka" Ya ce "Amin, muje muga yaran naki?" ********************** ? ************************** ********** Ai Hausa Novels **************** *************************? ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ? ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ? ************************** lιĸe coммenт ѕнare 🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻