*HIKIMA WRITERS ASSOCIATION* ********************** ? ************************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************? ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ? ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ? ************************** *GIDAN NAGOGGO* 🏨 This is my first novel. *A true life story* *Written by fateeyzah 🥰🥰* Bismillahir rahmanir rahim. Page0⃣1⃣ Tsawar da naji shi ya dakatar dani da bude dakin Ammy na. "wallahi Bahijja in kika shiga dakin nan sai na bata miki rai,Uban mai kika zo yi mini a gida,ki tashi ki koma inda kika fito,tunda baki daukeni a bakina komai ba "cewar Alhaji kenan. Take naji wata wata fargaba ta ziyarceni,wai yaushe zan fara samun kwanciyar hankali da maslaha tsakanina da Mahaifina,maganar Ammy tace ta tsinke min dan gajeran tunanin da na shiga wacce take tambaya abunda ke faruwa. Alhaji ne ya fara magana cikin fushi "Amina ki juya ki koma ciki, in ba so kike fushin wannan mara kunyar ya shafeki ba,in kuma ba haka ba wallahi zanyi mummunar saba miki". Da sauri na juya domin fita daga gidan don ganin Ammy na ta juya tana hawaye,ji nayi na tsani kaina,don tun ina Yarinya har girmana ta dalilina Ammyna ke zubar da hawaye. Daga gefen gidan na tsaya ina kokarin tsaida hawayena da tunanin mafita. Yanke hukunci nayi kawai akan na tunkari gidan Yaya Baffa wanda shine Babba a mazan gidan,don ina tunanin duk da 'Yan Uba nake dashi zai iya taimakona ya rokan mun Alhaji duk da wannan karan bansan laifin da nayiba. Achaba na tare na hau tare da fada mai Anguwan dazai kaini,cikin 10minutes muka isa gidan saboda bamu da nisa,kasancewa Alhaji yana Banzazzau shikuma Yaya Baffa yana filin Mallawa,sallamar dan Achaba nayi na karasa nayI knocking din gidan,after some seconds Gateman yazo ya budemin tare da mun sannu da zuwa na kutsa kai harabar gidan. Gida ne wanda ya amsa sunansa wanda kallo daya kayi ma gidan kasan mai gidan ya jiku da naira,hanyar da zata sa dani da main door din gidan na nufa,zuciyata na bugawa kamar zata tsago ta fito saboda shima bansan irin karban da zaya min ba. More comment,more typing. Yaya zata kaya tsakanin Bahijja da Yaya Baffa. *HIKIMA WRITERS ASSOCIATION* *GIDAN NAGOGGO* 🏨 *A true life story* *Written by* *fateeyzah** 🥰🥰 Bismillahir rahmanir rahim . Page0⃣2⃣ ....Knocking din main door din nayi ,sai da nayi some seconds tukunna aka bude min kofar,Murmushi tamin tare da cewa "Bahijjah ce,sannu da zuwa,yaushe a Garin" dukka ta min wannan tambayar a lokaci daya. Nima na maida mata da martanin murmushi tare da cewa"Nice Aunty Hanna,yau nazo". "Karaso ciki mana"cewar Aunty Hanna. Shiga cikin parlour nayi tare da kulle kofar,nan danan ta cika mini gaba da Snack da Drinks,tukunna ta zauna muka kuma gaisawa tare da tambayarta ina Yara. Tace "Sun tafi school. sannan tace "kici Snacks din mana" Nace "Aunty Hanna bazan iya cin komai ba,don Allah Yaya nanan"? Ta amsa min da"Yana nan bari inyi masa magana amma don Allah Bahijjah ki daure ki danci Snack din ko kadan ne". Na amsa da "to Aunty" Tashi tayi ta nufi ciki,ni kuma nasa Hannu na dauki Samosa daya na fara ci,ji nayi kamar ina cin magani. Sun dau lokaci Basu fito ba,don har na fara gundura da zaman,sai gashi Sun fito dukkansu fuska ba yabo ba fallasa,nan da nan nasha jinin jikina,na zamo daga one sitter da nake zaune na gaisheshi,Ya amsa fuska a hade kamar hadari,sannan na koma na zauna,suma suka zauna a 2sitter dake facing din inda nake zaune. Gyaran murya Yayi tare da tambaya ta"me ke tafe dake"? Muryata a sanyaye nace "Yaya nazo ne don Allah ka taimake ka rokan min afuwa a gurin Alhaji Don naje ya koreni,kuma ni bansan mai nayi mai ba wannan lokacin "na kara she tare da kokarin maida kwallar dake barazanar saukomin. Ya tambayeni "Bahijjah kikace baki son mai kikayi ma Alhaji ba"? Na amsa da gyada kana sama. Yace" alhaji Yace tunda kika koma Sokoto baki taba kiranshi kin gaishe shiba har maganar auren nan naki da ya taso,baki kira kin sanar dashi ba sai da Yaya Arsala ya kira shi ya fada mai,kuma Tace yana ji kuna waya da Ammy,amma shi kin maida shi Makiyinki,yanxu watan ki nawa da komawar ki Sokoto amma ko so daya baki taba kiranshi ba,yanxu tsakaninki da Allah Bahijjah kin kyauta?,yanda fa Ammy keda hakki a kanki haka Alhaji shima yana da hakki a kanki". Kaina a duke nace"Yaya nasan nayi laifi amma wallahi Yaya ko na kirashi baya dauka,so uku ina kiranshi bai daukaba,shi yasa ni kuma ban kuma kiransa ba,saboda na dauka bai bukatar gaisuwar tawa". Kara gyaran murya yayi tare da cewa"look Bahijja ni kwata kwata ban ganin laifinku,na Ammy nake gani,amma zan sami Alhaji muyi magana,yanxu dai mai ya kawo ki garinnan,ina zaton yau saura 3weeks bikinki?"ya karashe da tambayata. Nace"Kaduna zan wuce,in gyara kayan bed dina" Yace"to da kike maganar gyaran kayan bed kina da kudi ne?" "eh,angon ya ban 10k saboda in gyaran kayan" Anan Aunty Hanna ta saka baki tare da cewa«Honey,ni a ganina da Bahijja tabar maganar gyaran gadonnan kawai ka canza mata sababbin gado,tunda wancan auren nata shekara 10,kaga sun tsufa da yawa" Yace"A,ah Sweety kibarta taje ta gyara kayanta,tunda tazo da niyyar gyarawa"sannan ya juyo gareni tare da cewa"Bahijja kije ki gyara kayanki,zan sami sauran 'yan uwa muyi maganar gudunmawar da za a hada miki ".ya karashe tare da mikewa yana kallon Aunty Hanna sannan yace Sweety ni na dita,in zata tafi ki duba drawerta ki bata 2k tayi transport" Bai jira cewarmu ba yasa kai ya fita,sai da mukaji fitar motor dinshi sannan Aunty Hanna ta juyo tare da cewa"Bahijjah kiyi hakuri da rayuwa wata rana sai labari". Fateeyzah *HIKIMA WRITERS ASSOCIATION* *GIDAN NAGOGGO* 🏨 *A true life story* *Written by fateeyzah* 🥰🥰 Bismillahir rahmanir rahim Page0⃣3⃣ Nace "to Aunty nagode,kuma muna nan muna kai kukanmu wurin Allah,Allah ya kawo mana dauki a wannan rayuwar ta gidanmu,wallahi Aunty Hanna ban damuwa da kaina akan yanda nake damuwa da mutum biyu wato Ammyna da Aunty Zubaida,kina gani yanxu Aunty Zubaida abin nata kamar hauka amma duk da haka Alhaji yaki dena fushi da ita,kuma yace idan Baban Fadila ya maida ita gidanshi,wai bashi ba Baban Fadila". "aini Bahijja ban ganin laifin Alhaji sai na Ummeey da yaranta Mata,wallahi wadannan ba Allah a ransu,shi yasa nake fadin ma Honey ya bar yadda da kananan maganganunsu amma yaki,kiri_kiri sun tsare ko inna acikin gidan suna gidan aurensu amma kunnansu na gidan Alhaji,duk su suke hada fitina,shiyasa ranar da muka yi da Mamy na wanke ta tsab wai naje gidan Alhaji ta fara min hayagaga wai in fita daga gidan tunda ba gidan Ubana bane,ni kuwa nace mata ai tasan nawa gidan Uban yafi nasu,don baza ma a hada gidanmu da nasu ba,wai fa duk abinda ya kawo fitinar sunce wai Alhaji ya karbi dukiyarshi a wurin Honey saboda wai da kudin yake Almubazaranci wai yana kashemun". Nace"ai mu Aunty 'Yan dakinmu duk abinda yake faruwa a gidannan bama sani,kina ganin Asma'u da take kusa da gidan ma Alhaji ya hana ta zuwa wai sai bayan 3month saboda wai 'yan dakinmu muke hada fitina a gidan,tsakani da Allah ga Mamy nan da kullin tana gidan da ita da Mijinta da 'Yarta amma su ba a hanasu zuwaba sai mu". Aunty tayi gyaran murya tare da fadin"kedai Bahijja mubar maganar nan Allah ya shiryesu,don ni ina fada ma Honey abun kunya ne a wurinsu ace kamar gidan Alhaji Nagoggo,ana Samun wannan matsalar.yanxu wai a ina za ayi bikin tunda Alhaji yace badai gidanshi ba kuma kinga Dokoto tayi nisa". Nace"Mun yanke shawara zamuyi biki ne a Kano gidan Aunty Aisha tunda kin ga nan zan zauna". "Ok,yanxu abunda za ayi in kinje Kaduna kin dawo ki biyo tanan ki karbi bedsheets a matsayin gudunmawa ta don nasan ba bari za a yi inje bikin ba". "shi kenan Aunty na gode,Allah ya kara budi". Tace "amin,ina zuwa". Tashi tayi ta Shiga daki,sai da tayi like 3minute tukunna ta fito ta mika min kudi tare da cewa "Ga 12k nan,2k kudin da Honey yace in baki na transport,10k kuma ki kara a kudin gyaran bed". Take naji kuka ya tawo min na mike tsaye tare da rungumeta ina kuka tare da mata godiya. Itama kukan ne yazo mata tare da cewa"Allah ya tona asirin wanda ya raba Bahijja da Alhaji,yanxu Bahijja akan 12k kike kuka,sai kace wadda aka bata millions". Nace"Aunty ba komai ya sani kuka ba,sai alamarin Ubangiji dana tuna,wai yau nice na ke murna akan 12k,abunda lokacin da nake auren Tasi'u nafi karfinsa,sai dai ni in bada,lallai na yadda duniya juyi juyi wanda ya dauketa da fadi yana tattare da wahala,Allah dai yasa mu dace". Tace Amin Bahijjah. Mikewa nayi tare da saba jakata Nace Aunty ni xan wuce dai na dawo a gaishemin dasu Baby,ta amsa da za su ji,Rakiya ta yimini har main door tukunna muka kuma sallama ta juya,ni kuma na fice gidan,Achaba na hau wanda zaikaini Agoro Motor Park don in shiga Motar Kaduna. Wacece bahijja? Pls manage 🖊fateeyzah *HIKIMA WRITERS ASSOCIATION* *GIDAN NAGOGGO* 🏨 *A true life story* *Written by* *fateeyzah* 🥰🥰 Bismillahir rahmanir rahim Page0⃣4⃣ Tafiyar one hour ta kaini garin Kaduna,inda Driver ya saukemu a Kawo,nan na samu Napep din da zata kaini gidan Kakata dake Unguwar dan Bushira,tafiyar 30minutes mukayi,inda Mai Bapep ya saukeni a kofar Gidan,na biyashi kudinshi na karasa cikin gida. Babban gida ne,wanda kallo daya zakamai kasan masu gidan suna fama da rashi,gidan cike yake da 'Yan uwan Ammyna daga Yayyinta zuwa Kannita kuma kowanne da Iyalanshi,akalla Mutanen gidan zasu kai dari(100),bayan gaishe gaishe tare da taya ni muryar auren da zanyi,direct dakin Kakata na wuce wacce muke kiranta da Granny,shiga nayi ina mata wasa irin ta Kaka da Jika,bayan mun gaisa,nayi wanka hade da salla sannan na zauna cin Abincin da aka kawo min daga dakin Matar Kawu Muhammadu. Hira muka dasa ni da Granny wadda yawancinta hiran gidanmu ne da halin da Ammyna take ciki,anan na bata labarin abinda ya faru dana je gida da gidan Yaya Baffa da naje. Aikuwa nan ta bude baki tayi ta surfa balla'i,saboda Granny irin mutanen nan ne da basu daukar wargi,sai da ya koma ni nake bata hakuri sannan tayi shiru saboda zaka dauka dani take fadan. Can kuma kamar an tsikare ta tace"ni wallahi badon Amina ta wuce zaman gida ba da sai na raba Aurensu da NAGOGGO,tunda kwata kwata naga alamar wannan Matar tashi mai hanci kamar bututu👃(lol😃irin hancin Sophie ta)ta gama Mallake shi,in banda kaddarar Allah da rabon Haihuwarki data Kanninki da munsani sanda ya taba sakinta bamu bari ta koma ba (kaji Granny da tonon asiri,irin haka har yanda aka nemi auren Mahaifiyarka sai an fadin maka)amma kana naka ne Allah na nashi gashinan har tsufa abu yaki daidaita". Nace"don Allah Granny kibar maimaita maganar nan,wallahi in hadda ce ya isa na haddace wannan karatun dakike fadamun tun zaman da nayi a gidan nan".na karashe maganar tare da tashi na shige bedroom dinta,inajinta Taci gaba da sababi. Gado mai runfa na samu na haye tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya,'Ya'yana ne suka fado min arai ko yanxu ya suke,oho,don nadau Alkawarin bazan kuma zuwa ganinsu ba tunda last zuwan danayi sai da Tasi'u ya bini da sharri(anya ko Bahijja zaki iya yanke alakarki da ta Yaranki). Nan danan naji kwakwalwata ta fara tariyo min abubuwan da suka wuce har ..... Manage Insha Allah next page zamu ji wacece Bahijja? *Fateeyzah🖊* *HIKIMA WRITERS ASSOCIATION* *GIDAN NAGOGGO* 🏨 *A true life story* . *Written by fateeyzah* 😍😍 Bismillahir rahmanir rahim. Page0⃣5⃣ *FLASH BACK* Mahaifina da ne ga Alhaji Akilu kudan,wato sarkin kudan na wancen lokacin,mahaifiyarsa Hajiya Atika wacce suke kira da Goggo ita ce mata ta farko a wurin mai martaba sarkin kudan. Hajiya Atika 'ya'yanta biyu a gidan wato mahaifyana Alh Ahmad NAGOGGO da yayarsa Hajiya Hajara wadda nake wurinta a sokoto, a lokacin Mahaifina na da shekara daya Allah ya kaddara rabuwarsu wanda har yau da basu a duniya babu wanda yasan dalilin rabuwar aurensu,sannan Alhaji Akilu ya auri matansa biyu wato Dayyiba(Umma,wacce ita kadai ce take da dai a yanxu), da Amaryarsa Zulai(Mama) wanda suka haifammai 'ya'ya kusan sha shidda, ba lallai bane in iya lissafo su tunda ba wani zumunci mukeyi dasu ba duk da sun kasance 'yan uba suke da Babana,duba da irin yadda zumunci ya kasance a yanxu. Bayan rabuwar kakata Hajiya Atika da Kakana,sai ta dauki Babana wanda suke cema NAGOGGO (sunan NAGOGGO ya samo asaline da yanda a unguwarsu masu suna Ahmad suna da yawa, shine ake kiransa da Ahmad din Goggo wanda daga baya suka maida sunan Nagoggo,Wanda har sunansa Ahmad ya bace Mutane suka koma kiransa Nagoggo),ta daukeshi ta dawo garin zaria dashi wurin iyayenta tabar Hajiya Hajara a kudan. Tabama ma Babana tarbiya dai dai gwargwado saboda Hajiya Atika irin mutanan nanne masu fadin gaskiya,wanda komin girmanka sai ta fadin maka,Mace ce mai tsauri wanda ko cikin Dangi kowa yana shakkarta,Babana nada shekara biyar a duniya tayi aure anan zaria ta tafi da Babana gidan Mijinta, kasancewa shi baya haihuwa sai ya zamana ya rike Babana kamar danshi.anan zaria yayi primary school daga nan bai ci gaba ba,duba da yadda mutanen da suka dauki karatun boko,daganan ya fara bin kanin Mai Martaba legos,wanda wannan ne musabbabin arzikinsa. Matar Mahaifina ta farko ita ce Hajiya Maryam,wadda ya auro daga k Kano,daka ganta kaga bafulatana, fara ce tas,ita keda manyan yara a gidan,yaranta sha daya,mata hudu maza shidda,Amina,Hauwa,Akilu(Baffa),Faruq,Atika (Mamy),Ibrahim,Aminu,Jafar,Auwal,Salma,Ahmad(Abba).Hajiya Maryam Mace ce mai son kanta,kwata kwata batason wani ya rabesu,bayan ita Alhaji ya auri kusan Mata biyar amma basu dadewa suke fita saboda ta kasan kasa take azabtar dasu,wadanda suka dade a gidan sune wadanda suka haifi 'ya'ya biyu2,Amina wacce ta haifi yara biyu, Fatima da Zubaida,sai Huwaila da ta haifi Halima da Bello. Mahaifiyata itace Matar Babana ta shida a jerin Matan da ya aura,ita a Bazawara ya Aureta,tanada yara biyu a gidan da ta bari,Zainab da Mustapha, Haifaffiyar garin zaria ce,don daga baya su Granny suka koma cikin garin kaduna. Mu biyar ne yaranta a wurin Babana,Asma'u itace Babba,wanda bayan haihuwar Asma'u sai da suka rabu da Babana,ta koma gidan b'Babansu Aunty Zainab,chan ma auren yaki tunkunna ta dawo gidan Babana,bayan dawowarta ne ta haifeni(ni Bahijja,Aliyu,Abdullahi,Taheer. Mahaifiya Allah yayota mai hakuri don yanda ake takurata a gidan Babana abun ba a magana,duk wani cigabanta Alhaji ya dakusheshi,tun muna kanana bama fahimta har muka girma muka fahimci Mahaifiyar mu itace bora agidan mukuma 'Ya'yan bora. Pls ur comment is needed. Fateeyzah 🖊*HIKIMA WRITERS ASSOCIATION* *GIDAN NAGOGGO* 🏨 *A true life story* *Written by fateeyzah*😍😍 Wannan page din nakine *MUM IRFAAN*Allah ya baki abunda kike nema DUNIYA da LAHIRA,Amin. Bismillahir rahmanir rahim Page0⃣6⃣ Duk wani hakki namu an take shi a gidannan,don ko Almajirin gidan an fi daukarshi da daraja fiye damu,a hakan ma ana raga mana ne saboda hajiya kaka(Hajiya Atika ),saboda tana kokarin nuna ma Alhaji abunda yake yi bai daceba,kasancewa bayan rasuwar mijinta Alhaji ya gina mata gida nan kusa da gidanmu ta dawo,ya saka mata 'yan haya duk da akwai jikoki('ya'yan 'yarta hajiyan sokoto). Su kuwa sauran yaran da iyayensu basu gidan,suma Alhaji ya rarrabasu,Aunty fatima da Bello ya bama Hajiya kaka,Aunty khadija kuma ya bama Hajiyan sokoto sai Halima da take wurin mamarta. Bayan ammy ta haifi aliyu ne ta samu teaching a wata private school,amma daga baya sai da Alhaji yasan hanyar da yabi ya hana ta teaching din,abunda ya faru shine, ummy ta kawo kararta wurin Alhaji akan wai tana barin mata yara da yunwa,hakan ya kawo musu rashin jituwa,har sai da hajiya kaka ta sasantasu tace kowa ta ringa girkinta daban,daga baya kuma yace wai sai dai ta zaba ko teaching ko aurenta,saboda kullin tana fita ana kalle mai mata,haka ammy ta hakura tabar teaching ya koma sai dai abinda ya kawo ya bata,don ko sana'a a cikin gida ya hanata. A wannan lokacin kuma an aurar da mata uku a gidan mu duk daga dakin ummy,wato Amina(ta auri babban dan Hajiyan sokoto), Hauwah da mamy, dukkansu duk sun hayayyafa. A lokacin da nake da shekara sha biyu yayi dai dai da ina j.s.s one a kayi bikin yaya Baffa da Aunty hanna wacce ta kasance diyar aminin Alhaji,a lokacin ne kuma komai na gidan mu ya kara tabarbarewa dalilin Alhaji ya dauki dukiyarsa gaba daya ya damka ma yaya Baffa don yaci gaba da juyawa,a dai dai lokacin kuma Tasi'u ya shigo rayuwar gidanmu,wanda dalilinsa na tsinci kaina a wanna rayuwar da nake ciki. *Comment* *Share* *Vote* *Fateeyzah* *HIKIMA WRITERS ASSOCIATION* *GIDAN NAGOGGO*🏨 *A true life story* *Written by fateeyzah*😍😍 Bismillahir rahmanir rahim Page0⃣7⃣&0⃣8⃣ A wannan shekaran na taso da wani irin hatsabibanci,duk nabi na addabi kowa a gidan, don duk wanda yayi ma Ammyna rashin mutunci ni ma sai na yi masa, don har Alhaji ban raga mawa, hakan ya jawo mun tsana a wurin 'yan gidan especially Yayyina maza da yayyina mata da sukayi aure,Don duk wacce tazo tayi ma Ammyna rashin kunya, nima kafin ta tafi sai na yi mata wanda yafi nata,hakan ba karamin duka yake jawo mun ba musamman wurin Alhaji da Yaya Farooq wanda shine ya kasance babba a gidan bayan auren Yaya Baffa.Duk sanda ko ake dukana Ammyna da Asma'u zasu shiga daki suyi ta kuka, saboda yanda suke zage karfi su dakeni zaka dauka wani Gardi suke duka,haka zasu min likis, amma haka bashi zai hana in ka ma Ammyna ko Asma'u da kannina wani abun ni ma in karta maka nawa Rashin Mutunci. Aikuwa wata rana fada ya hada Ammyna da Ummy, sai Yaya Farooq ya shiga ma Ummy yayi ta zagin Ammyna,a lokacin da abun ya faru ina school,ina dawowa na kira Almajirinmu na tambaye shi mai ya faru da bana nan,don naga idon Ammy yayi jawur alamun taci kuka,aiko ya kwashe ya fadamun(dama indai na dawo naga Ammyna a wani yanayi, Almajirinmu nake tambaya don nasan ita ko Asma'u baza su sanar dani ba, saboda sanin bana yafiya). A Hankali na shiga part din Mazan gidan,nan na hango Yaya Farooq yana wanki,ga Radion shi a gefe yana shan disco,wata bishiya na samu na make ina kallonsa,lura da nayi Manyan kaya yake Wankewa ya tunasar dani washegari zasu je Nadin Sarauta Kudan(kakana yayi murabus ya bama Kanninsa saboda rashin lafiyar da yake fama da shi da kuma maida Aurensa da Za ayi da Hajiya Kaka),Aiko nan farin ciki ya rufeni don na samu hanyar da zan Rama ma Ammyna zagin da yayi mata,Shigowar Yaya Ibrahim ne ta katse mun tunani,inaji ya na cema Yaya Farooq wai sabon kaya ne yake wankewa,shi kuma ya bashi amsa da Kyamar kayan yake yi Saboda ya dade a wurin Tailor,dariya Kawai Yaya Ibrahim yayi ya ajiye Bucket ya fita,Ina nan make har Yaya Farooq ya gama wankinshi ya shanya ya fita, sai dana kara kamar 5minutes sannan na fito daga maboyata,kitchen na nufa direct naje na dauko Almakashi,Wurin kayansa na nufa na ciro su a Igiya na samu kayan nan na yankasu kuci2 da Almakashi na zubar mai a wurin na kama gabana,dakinmu na nufa nayi kwanciyata a Gadon Ammy nayi baccina. Cikin bacci naji an kwada min mari wanda zafinshi ya sani sakin fitsarin da ban shiryaba,haka ya jani ya fita dani harabar gidan ya jefar dani gaban kayan dana yanka,daka mun tsawa yayi tare da tambayata wa ya yanka kayannan ya karashe tambayar yana nuna min kayan dake gabana,bakina na rawa na amsa mai da ni ce,saboda wani tsoronshi da ya dirar mu a zuciya ban shiryaba,zare belt yayi ya shiga jibgata,ni Kuma ina ihu,ihuna ne yayi raising din Alarm din da kowa sai da fito har da Ammyna dake Kitchen,duk taron yawan gidanmu an rasa mai kwata ta a wurin Yaya Farooq,haka ya ringa jibgata sai da yaga na dena motsi tukunna ya yarda belt din,da gudu Ammy da Asma'u sukayo kaina suna girgizani,amma ina ba labari,Ammy ce ta kwala ihu tare da Fadin "shikenan Farooq ka kashe min ita,wallahi bazan yarda ba,ke Asma'u miko min Hijab dina in kaita wurin Hajiya".da gudu Asma'u ta shiga daki ta dauko mata Hijabi ta saka,haka ta ciccibeni ta goya ni a bayanta tayi hanyar gate din gidan,tana fita suka ci karo da Alhaji ya dawo daga masallaci,ko kallonsa batayi ba ta rabashi ta wuce,shi kuma ganina goye a bayanta ga Asma'u na binmu yasa shi rufa mana baya. A kusan tare muka shiga gidan Hajiya tawa,kukan da ammy take yine yasa Hajiya fitowa da sauri zani a hannu tana tambayar lafiya,shimfideni tayi tare da fadin "shike nan Farooq ya kashemun ita",salati Hajiya ta dauka tare da fadin"garin yaya?", babu wanda ya bata amsa tsakanin Alhaji,ammy da Asma'u,ganin baza ta samu amsa bane yasa ta maida hankalinta kaina,ganin alamun suma nayi yasa ta shiga daki da hanzari ta debo ruwa a fridge ta zo ta watsamin,sauke ajiyar zuciya nayi hade da fashewa da kuka,rungume ni Ammy tayi a jikinta itama tana kuka,ba wanda yace hanamu,sai da muka yi shiru don kanmu,sannan Hajiya ta nemi sanin dalili,nan Asma'u ta fada mata abunda ta sani,juyo wa tayi ta tambayen mai nayi masa nan na kwashe na fada mata,aiko nan ta hau sirfamin zagi sai da tayi mai isarta sannan ta koma kan Alhaji,shima ta zageshi tas,sannan tace mu tashi muje Gida gatanan zuwa itama,da taimakon Ammy na mike don duk jikina a fashe yake,don na daku. Isarmu gida mu ka tarar da duk ' yan gidan a harabar gida,kallonsu kawai zakayi kasan suna cikin tashin hankali,ganin shigowarmu yasa duk sukayo kanmu har da uban gayyar(Yaya Farooq),duk jikinsu a sanyaye,suna mana magana amma ba wanda muka tanka,ana cikin haka Hajiya ta karaso ko zama batayi ba ta fara surfa bala'i,sai da ta zage kowa tas,sannan tace duk ranar da wani ya kuma dukana koda Ammy ce bata yafe ba, tace ma yaya Farooq ya biyota gida, ta fice daga gidan. Haka Ammy ta dafa ruwan zafi ruwan zafi ta Gasa mun jiki,sannan nasha ruwan Lipton da paracetamol na kwanta.basan ya aka kare ba tsakanin Hajiya da yaya Farooq,na ga dai da safe Ummy ta hada kaya ta tafi kano da sunan yaji(abun kunya tsofai2 da ita). *Fateeyzah* 🖊🖊 *HIKIMA WRITERS ASSOCIATION* *( _Burunmu mu fad'akar, mu nishad'antar, mu wa'azantar da al'umma)_* *GIDAN NAGOGGO*🏨 *_A true life story_* *_Written by fateeyzah_*😍😍 *_Wannan page din Nakune_ HIKIMA WRITERS _Allah ya kara basira da daukaka_* *Bismillahir rahmanir rahim* _Page_ 0⃣9⃣&1⃣0⃣ Haka su Alhaji suka tafi suka bar Yaya Farooq,saboda bashi da manyan kayan da zai saka, kasancewa duk kayansa Jeans ne da T_shirt ne. Kwana biyu na dauka ina jinyar jikina saboda ba karamar illa Yaya Farooq yamin ba,godiyar Allah ma weekends ne babu school. Sai da Ummy tayi sati daya tukunna Mahaifinta ya dawo da ita,don ba yanda Ammy batayi da Alhaji ba akan yayo bikonta,shikuma ya dage bazai jeba tunda bashi yace ta tafi ba, ita ta tafi da kanta,gaskiya a cikin satin da Ummy tayi bata gidan ba karamin wata yawa mukayi ba,su kuma 'ya'yanta ina lura duk a takure suke. Bayan Wata biyu,Yaya Farooq ya samu soja ya tafi,a lokacin ba karamin dadi naji ba don na lura duk cikin yaran Ummy yafi kowa tsanata,A dai dai lokacine kuma Tasi'u ya samu admission a A.B.U zaria(Tasi'u kani yake wurin Alhaji don da Babanshi da kakanmu Alh Akilu 'Ya'yan mata suke),anan Gidan Hajiya Kaka aka Bashi daki,kasancewa duk 'yan uwan da yazo karatu daga Kudan Gidan Hajiya Kaka suke zama har su gama,daki guda ake ware musu kusa da dakin Aunty Amina(inba ku mantaba itace babbar 'ya wurin Alhaji kuma ita ke auren Babban d'an Hajiyar Sokoto,Yaya Kabeer,kasance wa auren Zumunci ne sai Alhaji ya basu daki anan gidan Hajiya),shima nan Tasi'u ya zauna, wanda ni nake kaimai abinci Don Alhaji yace kwanonshi yana dakin Ammy ne. A wannan shekarar abubuwa sun faru da yawa,ciki harda aurar dasu Aunty Asma'u,Aunty Fatima da Aunty Khadija,wanda Aunty Asma'u ta auri Suleiman(Yaron Alhaji ne da yake jamai Trailer Zuwa Lagos),aka kaita dan gaba da Gidanmi don nan Mijinta ya gina gida,Aunty Fatima kuwa ta auri Salihu,shikuma yana aiki ne a Embassy na Egypt,Ita kuma Anguwan k'aya aka kaita kafin su wuce can Egypt din,Aunty Khadija kuma auren zumunci aka mata da Yaya Al'amin ('yan Hajiyar Sokoto)can Sokoto aka ajiyeta Gidan Hajiya. Bayan Bikinsu ne kuma da Wata Biyu,Allah yayi wa Hajiya Kaka rasuwa(Allah ya jikanta),Rasuwarta ta girgiza mu especially 'yan dakinmu da'ya'yan Hajiyar Sokoto(duk ita ta rikesu,su biyar,har aurensu),aka raba gado,kowa ya watse. Bayan wasu watanni aka yi passing out don Yaya Farooq,wanda ya fito da mikamin second Lieutenant,Anyi POP da sati biyu aka daura mishi aure da Aunty Zeenatu,shi ma dai auren zumunci ne don da Babanta da Alhaji cousin ne,wannan bikin ne akayi biki da ba a taba yi a *GIDAN NAGOGGO* ba,don sai da akayi event kusan hudu da kuma crossing of sword,tukunna aka dauko Amarya daga Kaduna aka kawo ta nan Gidan Hajiya Kaka(ta gaban gidan Alhaji ya fitar mai da part dinsa kuma yace ya mallakamai wurin). Haka rayuwa taci gaba da tafiya watarana Farin ciki ko bakin ciki,wanda bakin cikin yafi yawa.Acikin Shekarun nan an hayayyafa sannan anyi Rashi,wanda har da Alhaji Kaka da Allah ya mai rasuwa. Acikin shekarar da na gama School,Abubuwa marasa kyau sun faru,daga ciki akwai Rikicin da ya faru tsakanin mijin Aunty Asma'u da Alhaji,inda Alhaji yace yana cutarshi bai kawo mai balance da yawa,shi kuma yace motor na bashi matsala,kudin na Tafiya a gyaran motor,Haka Alhaji ya rufe idoshi ya karta mai rashin mutunci kamar ba Sirikinshi ba,kuma daga baya ya karbe motarsa,Dalilin haka har auren Aunty Asma'u ya kusa mutuwa,Allah dai ya taimaka suka samu masalah. Yaya Al'amin Mijin Aunty Khadija kuma ya kara aure,inda suka yi ta samun matsala tsakaninsu,har dai ya saketa,ita kuma ta aje mai Jariri dan wata biyu ta tawo Gida,ba tare da Alhaji ya tsaya yabi ba'asi ba yace ta fitar mai gida Bashii bata,kuma yace in Yaya Al'amin ya maida ita gidanshi,shima sun raba Hanya kuma sai ya tsine mata, ya kuma hana a bata d'anta haka Alhaji ya raba Jariri d'an wata biyu,haka tattara ta koma Dagin Mahaifiyarta. A shekarar ne kuma Tasi'u ya gama degree ya tafi services,ni kuma na ci gaba da zaman gida,saboda Alhaji baya bari mu shiga university sai munyi aure,shima sai mijinki ya barki.Haka na kara wata shekara a gida ba tare da na samu miji ba,don Alhaji ba bari yake in fita ba. Bayan Tasi'u ya gama service ne ya samu aiki a wani filling station a Lagos,wanda aka bashi matsayin manager,a lokacine Sarki (sarkin kudan) yace yazo gidan mu ya zabi mata,yana zuwa aka tura mu wurinshi ni da Halima muka gaisheshi,bayan ya tafi ne yaje ya sanar da sarki ya zabeni,shikuma ya Sanar da Alhaji,nan ko Halima tayi ta murna don dama ita da wanda take so,nan muka fara soyayya da Tasi'u ba a dauki dogon lokaci ba aka daura mani aure dashi,Halima kuma da Salis saurayinta. Nan Alhaji yace tunda ba dani zai tafi Lagos ba, ba sai ya kama hayaba,nan muma ya bamu daki a gidan Hajiya Kaka. Ya zaman zai kasance tsakaninmu: Aunty Amina Yaya Farooq(abokin fadana) Ga kuma ni Bahijjah. Karku manta dukkanmu 'ya'yan Alhaji NAGOGGO ne,sai mun hadu a next page. *Comment* *Vote* *Like* *Share* *Fateeyzah* 🖊 *HIKIMA WRITERS ASSOCIATION* *_(Burinmu mu fad'akar,mu nishad'antar,mu wa'azantar da al'umma)_* *GIDAN NAGOGGO*🏨 *_( A true life story)_* *_Written by fateeyzah*😍_ _Bismillahir rahmanir rahim_ *_Page_* 1⃣1⃣ Tunda aka daura aurena na tsinci kaina a cikin farin cikin samu FREEDOM,ta wani 'bangaren ina bakin cikin rabuwa da Ammy da Kannina. Ammy ko tana can bedroom tana Kukan tausayina,don a ganinta ba a rabu da bukar bane an samu habu,domin an aurar da nine,amma har yanxu ban bar *GIDAN* *NAGOGGO* ba. Karfe hudu nayi Alhaji ya umurci su Yaya Amina a fara shirya Amare domin karfe biyar yake so kowacce ya danka ma mijinta(yana daga cikin Al'adar *GIDAN* *NAGOGGO*,duk yarinyar da aka ma aure Alhaji dakanshi zai kai ki dakin miji,zai hadaki da kanniki maza sune 'yan rakiya). Bayan an gama shiryamu ne aka fara kaimu wurin Ummy don yi mana fada,daga nan kuma aka wuce damu dakin Ammy,nan ma dai fadan ta mana,sannan aka wuce damu palourn Alhaji,gyaran murya Alhaji yayi tare da kiran sunanmu"Halima,Bahijja"bai jira amsawarmu ba yaci gaba"Allah ya kawo mu yau na sauke nauyinku da ya rataya akaina,ba wata doguwar magana zanyi ba,don nasan duk abunda zan fadi,iyayenku mata da 'yan uwa sun fada muku,abinda zan tunatar daku kusan Gidan nan ba a yaji(barkono🤪),duk abunda ya hada ku da mazagenku Ku ringa hakuri ba wai ku kwaso 'kafa ku tawo gida,don bazan dauka ba,sannan ke Bahijja(ya nuno ni da yatsa)ki kiyayeni wallahi in naji ance kiyi ma Amina ko Zeenatu wata rashin kunya wallahi zanyi mummunar sa'ba miki,kibar ganin wai yanxu da aurenki,zan iya zuwa har dakinki in zane ki,don Amina ya isa ta haifeki,kina da shekara biyu a duniya aka mata aure,don haka ki kiyaye,ku tashi muje Allah ya muku Albarka,yasa ku shiga dakin miji a sa'a. Halima muka fara kaiwa gidan ta dake Tudun wada kasancewa ita ce karama,muna zuwa Alhaji ya kira mijinta a waya,ya damka mai matarshi,sannan muka juyo muka dawo,Alhaji da kanshi ya rike mun hannu ya kaini har cikin dakina,sannan ya tafi ya barni,bude idona nayi na kare ma dakin kallo,ba laifi,Dakin ya tsaru.Gab da Sallar magariba sai ga su Aunty mamy, Aunty Amina,Aunty Zeena da Aunty Asma'u sunzo,suka kara gyara dakin,sannan suka sani inyi wanka, in dauro Alwala,anan ne nace musu banda tsarki sai zuwa gobe zanyi wanka,Nan Aunty Mamy ta kwashe da tariya tare da fadin "lallai bahijjah kina ruwa".haka dai suka karasa gyaran daki tare da mun 'yan nasihohi,suka mana bankwana ni da su Aunty Amina suka tafi. Bayan sallar Isha'i Aunty Amina da Aunty Zeena suka mun sallama kawacce tayi dakinta. Sai wurin karfe tara tukunna Tasi'u ya shigo,sai ya umurceni da in tashi muyi nafila,ina dan nokewa na Sanar dashi ban da tsarki,muka dan yi ciye ciyen mu muka kwanta. Washe gari na wuni ina ta karban baki 'yan ganin amarya,wurin la'asar na yi tsarki,a daren ranar Tasi'u ya maidani cikakkiyar mace,wayewar garin ranar kuma yayi mini kyautar gold half set(half set shine dankunne,da sarka) kirar Dubai. Zamana da Tasi'u sai dai san barka saboda bai rageni da komai ba yana kokarin kyautatamin dai dai gwargwado,yana gudun bacin raina. Haka kuma zamana da Aunty Amina shima banda matsala haka 'ya'yanta na girmamani,don wani zubin har tunani nake yanda Aunty Amina take jana a jiki,amma ni duk da haka na kasa sakin jiki da ita saboda tun can dama ba wani sabo a tsakaninmu,saboda duk da muna Anguwa daya bata cika zuwa gida ba,kasancewarta nurse ce yawanci a Asibiti take wuni. Ta bangaren Aunty Zeena ma banda matsala,saboda ita mutumce mai hakuri da kawaici,ni dama tunanina ko da zan samu matsalah,wai wuce ta Yaya Farooq ba,amma sai naci sa'a a week din da akayi bikinmu akayi masa transfer ya koma Ilorin da aiki. A ranar da muka cika sati biyar da aurenmu,Tasi'u ya fara shirin komawa bakin aiki,Don washe gari da daddare yake so ya wuce,karfe takwas ya umurceni da in shirya muje mu gaida Alhaji,aiko nayi ta murna don nayi kewar Ammyna don ma muna waya,cikin shigarmu ta alfarma muka kama hanyar zuwa gidan,direct parlourn Alhaji muka wuce,nan muka tarar da shi da Ummy,bayan mun gaisa,Tasi'u yake sanar da shi yazo mushi sallamane ,nan Alhaji ya sa mana albarka,daganan dakin Ammyna muka wuce,muna shiga na rungumeta ina murnar ganinta,sannan suka gaisa da Tasi'u,nan ma dai albarkar aka samana tare da mai fatan sauka Lafiya, tukunna muka taso muka tawo,bayan dawowarmu gidane ya shirya ya tafi Kudan. Wajen karfe biyu sai ga Aunty Mamy da Aunty hauwa sunzo nan muka hadu dakin Aunty Amina (kasancewa night duty gare ta ranar)mukayi ta hira,cikin hirar ne Aunty Mamy ke tambayata wai anya ba ciki gareni ba,nayi saurin ce mata ni banda komai,sai ta kuma tambayata yaushe rabona da menstruation nace mata tun lokacin bikina,anan Aunty Amina tasa mana baki tare da fadin ai ita tun last week ta lura cikine dani,nan dai suka hadu su uku sukayi ta zugani kar in yarda in haihu da wuri,su bana ganin su basu da yara da yawa(Aunty Amina nada yara hudu,Aunty Hauwah uku,sai Aunty Mamy nada daya),nan da har na hau kai na zauna,nan Aunty Amina tace tana da Maganin da zata bani cikin ya zube tunda tasan bai wuce 4 weeks ba,a lokacin duk na manta kiyayyar da suke nuna mana mu da mahaifiyarmu,don gani nake banda masoya irin su(kar ku ga laifina,alokacin shekarata 18),nan Aunty Amina ta tambayeni yaushe Tasi'u zai dawo nace mata sai dare,tace ai ya isa cikin ya zube lokacin,haka tabani kwayar nan guda biyu tace in Hadiya da ruwa,take ko na sha magani. Har kusan 2hours ba labari,nan dai su Aunty Mamy suka tafi suka barmu cikin jiran tsammani,in takaice muku har bayan isha babu bayani. Wurin karfe tara sai ga Tasi'u ya dawo,nan dai nayi ma Aunty Amina sallama na nufi daki,gabana na dukan uku uku don ko girki banyiba,Allah ya taimakeni karin in kirkiri karyar da zanyi yace in dafo mai Lipton don bazai iya cin abinciba. Around 10pm muna kwance sai naji wani azababban ciwon mara ya taso mun tun ina dauriya dai har na fara ihu,nan Tasi'u ya rikice yana tambayata mai ya sameni,kafin in bashi amsa sai ga jini na bin kafafuna. Don jin ya zata kaya,sai mun hadu a next page. *Comment* *Vote* *Like* *Share* *Fateeyzah* ✍ *HIKIMA WRITERS ASSOCIATION* *GIDAN NAGOGGO*🏨 *_(A true life story)_* *_Written by fateeyzah*😍_ _Wannan page din nakune masoyen *GIDAN* *NAGOGGO* a duk inda kuke,nagode da kaunar da kuke nuna ma novel dinnan._ _Bismillahir rahmanir rahim_ *_Page_* 1⃣2⃣ Ganin jinin na bin kafata yasa Tasi'u ya kara rikicewa,ihun dana kuma saki ne ya dawo dashi hayyacinsa,daukan key din motar yayi tare da sunkuta ta yayi waje dani,sa key yayi ya bude motar ya kwantar dani a back seat ,shiga driver seat yayi ya figi motar a guje,Da taimakon Allah muka isa ABUTH dake Tudun wada saboda reckless driving da yayi,yana parking ya kuma sunkuta ta da gudu ya shiga cikin Asibitin dani,da gudu nurses sukakarbeni a hannushi,daganan kuma ban san abunda ya faru ba sai farkawa nayi naganni daure da drip a hannuna,ga cikina ya na min wani matsiyacin ciwo,gefen damana kuma Tasi'u ne a zaune,wanda kallonshi da nayi sai da na shiga cikin firgice,don fuskarshi da idon shi yayi wani irin da alamun yasha kuka,juyin da cikina yayi shiyasani fasa ihu,da sauri ya juyo gareni,irin kallon daya watsa min shiyasa na manta da ciwon dana ke ciki,don in idona bai min karya tsanata na gani a idon Tasi'u. Har gari ya waye,yana zaune a inda yake bai kuma kallon bangaren da nake ba ballantana insa ran zai mun magana,ni kuma na kasa mai magana saboda wani tsoronsa da ya shigeni. Sai around 7,tukunna naga ya tashi yana jan kafa ya fada toilet din dakin, sai da yayi kusan minti biyar tukunna ya fito da alamar alwala yayi,fita yayi daga dakin. Zafin dana ji a hannuna ya dawo dani daga gajeran tunanin da na shiga,drip din dake hannuna ne ya kare har ya fara dawowa da jini,yunkirin tashi nayi amma na kasa. Turo kofa akayi aka shigo,Tasi'u ne da doctor,da sauri suka karaso wurina ganin yanda jinine ke dawo cikin cedar,cire min drip din yayi tare da"sorry madam,bamu zo da wuriba".kada kai kawai nayi. Wurin karfe takwas sai ga Aunty Asma'u tazo,lokacinne kuma naji Tasi'u yake mata sallama zai je ya dadi. Tunda na kwanta Asibiti ba wanda yazo agidan sai Aunty Zeena,shima bata dadeba ta tafi,naso tambayar Aunty Asma'u datake jinyata Amma itama ba fuska,Tasi'u ko a Asibitin yake Wuni amma ko magana bata shi ya tsakaninmu don ko na masa bai amsawa. Sai da na kwana biyar A Asibiti sannan akayi discharging dina,direct GIDAN Alhaji aka wuce dani,dakin Ammyna Auto Asma'u ta kaini nayi wanka,sannan muka je parlourn Alhaji wanda duk yaran gidan,masu aure,da marasa shi duk suna parlourn,ina hada ido da Ammy ta sakar mun harara,saurin dauke kaina nayi tare dajin wani takaici ya rufeni,har na samu wuri na zauna ba wanda yamun magana sai ido da kowa ya zuba min,Aunty Amina na hango zaune a gefe tayi tsiru tsiru,duk alamun rashin kwanciyar hankali ya bayyana a fuskarta. Mun kusa minti goma da zama sai ga Alhaji da Tasi'u sun shigo,samun wuri sukayi suka zauna,sannan Alhaji ya dago Fuska a hade ya yaficeni da hannu,take cikina ya kada haka na tashi jikina a sanyaye,ina zuwa na tsugunna a gabanshi,baiyi wani jinkiri ba ya tsinkeni da mari ........ More comment,more typing *Comment* *Vote* *Like* *Share* *Fateeyzah* ✍ *HIKIMA WRITERS ASSOCIATION* *GIDAN NAGOGGO*🏨 *_(A true life story_)* *_Written by fateeyzah_*😍😍 Wannan page din naki ne,Aminiyar kwarai,sahibata,is easiest to cut my hand than to loose u as a friend, *SOPHIE* *MUHAMMAD* *BUBA*👩‍❤‍👩👩‍❤‍👩 (The potential banker and the financial analyst),Allah ya barmu tare har *CBN*(insha Allah),Allah kuma ya nuna min auranki da *ABDULJABBAR*❤ *Fateeyzah* *novel* *group* inaji dadin addu'ar ku ako da yaushe,ina godiya🙏. _Bismillahir rahmanir rahim_ *_Page_*1⃣3⃣. Marin da yamun sai da yayi sanadiyar dauke war jina👂 na wasu dakika alokacin da jina ya dawone,na tsinci Alhaji na magana cikin matsinancin fushi"wai bahijja yaushe zakiyi hankaline,wace irin dakikiya ce ke,duka duka shekarunki goma sha takwas a duniya amma har kin iya shan magani don ki zubar ciki(duka ' yan parlourn suka dau salati don yawancinsu basu sasan dalilin da Alhaji ya kira wannan meeting din gaggawar ba)sai da parlourn yayi shiru tukunna,sai nan Alhaji ya cigaba da bambami wanda ayanxu bazan iya tuna wa duka ba,ranar na sha zagi don Allah komawa yayi kamai wani bamaguje,sai da ya gaji don kansa sannan ya umurci Tasi'u yabani key din dakina in tashi in tafi don yana son magana dasu,haka na karfi key na tashi na fita hawaye na bin idona,haka na kama hanyar gida ba tare dana damu da kallon da mutane ke bina dashi ba. Ina shiga gida na hadu da Aunty Zeena ta fito part dinta,ganin yanayin da nake ciki yasata karasowa da sauri tana tambaya ta mai ya faru,amma nakasa bude baki in bata amsa haka ta jani har part dinmu ta karfi key din hannuna ta budemin dakin muka shiga ta zaunar da ni akan two seater,direct fridge dina Ta nufa ta dauko min maltina mai sanyi ta bude min ta kafa min abaki,batare da bata lokaci ba na shanye tas,sai databari na dan wuta,sannan ta kuma tambaya ta mai ya faru,kwashe duk abinda ya faru nayi na fada mata tun daga maganin da Aunty Amina ta bani har abunda ya faru a gidan Alhaji,nan ta hau salati tare da fadin lallai biri yayi kama da mutum,saurin kallonta nayi tare da tambayar mai ya faru?. Gyara murya tare da fadin"ana sauran kwana biyu ki kwanta a Asibiti naji Aunty Amina na waya tanan bayan window bedroom dina tana cewa kamar ma ciki gare ki,bansan dai da wanda take wayaba amma nadai ji ta ambato sunanki ina kyautata zato indai bada Aunty Hauwah take waya ba to da mamy ne takeyi,to tunda naga su Mamy sunzo nidai jikina bai bani ba banzo dakin bane saboda Aunty Hauwah kinsan na samu matsala da ita saboda salma lokacin bikinki"? Nace "ai ban sani ba" Tace"abunda ya faru shine yaya Farooq ne ya dinko mana dogayen riguna na shadda ni da salma,sai ya kasance dankwali daya ne shine sai na dauki dan kwalin sai ya kasance na salma ba dan kwali,kinsan namiji da yakai mata kayan sai Ummy ta tambayeshi ina dankwalin,sai ya ce mata wai guda daya ne kuma na dauka,to bansan yanda akayi ba sai ga salma tazo wai in bata dankwali,ni kuma na ce bazan bada ba,shine fa ta fara fadamin bakaken maganganu,ni kuma naga bazan jura ba na mareta,to bayan ta tafi ne sai ga Aunty Hauwah tazo wai rama mata mari,nan fa muka fara cacar baki sai ga daddyn Abdul(Yaya Farooq) ya shigo shine fa da yaji abunda ya faru ya bata rashin gaskiya". Na numfasa tare da fadin"Allah ya kyauta,ni yanxu matsalata Yaya Tasi'u,bansan yanda zan bullo mai ba don fushi yake dani sosai,saboda tunda na farfado a Asibiti bai mun magana ba"na karashe magana tare da goge hawayen da ya sulalo daga idona. "Daurewa zakiyi ki kaskantar da kanki ki basa hakuri amma kar ki yarda yasan da sa hannun Aunty Amina a wannan lamarin saboda in ya sani abun zai fi kamari"cewar Aunty Zeena. Nace"zanyi kokari Allah ya daurani kanshi" Tace" amin,amma Bahijjah ina mamakin Aunty Amina,ban taba tunanin zata aikata haka ba,shiyasa Aunty Hanna tace min inyi taka tsantsan da ita don green snake ce under the green grass,duk ita take kitsa musu duk iskancin da sukeyi" Nace "Allah ya kyauta nima dai nayi saurin sakin jiki dasu" Tace"gaskiya kam,bari in kawo miki,Abinci don nasan baki ciba"fita yayi daga dakin. Sai da tayi minti biyar sanna ta kawo mun abinci tare da fadin"kici kisha magani,bari inje inshirya su Abdul zasu tafi islamiyya hudu tayi". Sai da naci Abincin, nasha magani,sannan na wuce Kitchen don in dafa ruwan wanka,ina tsugunne sai ga Aunty Amina tayi shigo,motsin ta danaji ne yasa ni dago kai,muna hada ido ta watsa mun harara sannan ta bude dakinta ta shiga. Anan na zauna har ruwan yayi zafi na juye nashiga nayi wanka. Bayan na fito wanka ne ina zaune ina shafa mai sai ga kiran Ammy ya shigo ta phone dina,cikin sanyi jiki receiving tare da sallama,na gaisheta ta amsa tare damun ya jiki,sannan tayi gyaran murya tare da cewa"Bahijjah na kira ne ki fadamin gaskiyar abunda ya faru don zuciyata taki amincewa ke kika zubar da cikin sunna,saboda nasan baki da wayewar da har zaki aikata haka". Nan na kwashe duk abunda ya faru na fada mata,salati tayi tare da fadin"Amma Amina bata kyautaba,girman ta baida amfani,ita da ya kamata ta tsawata miki,Amma ita ta aikata haka,Allah shi kyauta kuma banaso Tasi'u yaji maganar nan saboda duk lalacewa dai 'yar uwarkice". Nace"insha Allahu Ammy bazai jiba".nan dai tamin sallama tare da jamun kunne akan Aunty Amina. Juyowar da zanyi kawai muka hada ido da Tasi'u,yanda naga idonshi ya kada yayi jane ya tabbbatar mun da ya gama jin maganarmu da Ammy,take naji gabana ya fadi,juyawa naga yayi cikin tsananin fushi ya fice daga dakin,hankalina naji ya tashi don bansan hukunci da zai yanke ba. Ji nayi yana ta kwada ma Aunty Amina kira tare da bugun kofar dakinta. Don jin yanda zata kaya a *GIDAN* *NAGOGGO* sai ku jira next page. More comment,more typing *Comment* *Like* *Share* *Vote* *_Fateeyzah_*✍ *HIKIMA WRITERS ASSOCIATION* *GIDAN NAGOGGO*🏨 *_(A true life story)_* *_Written_ _by_ _fateeyzah_* 😍😍 *_Jinjina gareki 'yar GIDAN DC,Hauwah A Abba(mrs Mur)Allah ya bar kauna_*❤. _Bismillahir rahmanir rahim_ *_Page_* 1⃣4⃣ *_to_* 1⃣5⃣ Jin kiran da yake mata ne yasa gabana ya fadi, ban tsaya dogon tunaniba na yi hanyar fita dakin, fitowa ta yayi dai² da bude kofarta, tsaye tayi tare da watsa mai hararara hade da cewa"wai kai Tasi'u me ke damunka ne kake ta kwala mini kira sai kace wani mahaukaci, kaje kaji da abinda mahaukaciyar matarka ta yimaka, ba kazo ka sauke fushinka akaina ba,ai bani na kashe zoman ba,rataya aka ban"ta karashe maganar tana yamutsa Fuska. Gyara tsayuwarsa yayi tare da yamutsa fuska yace"ba wannan ya kawo niba,nazo ne in miki gargadi hade da kashedi ki fita daga harkar matata, don naji abunda kikayi na bata magani ta zubar min da ciki,to wallahi ki shiga taitayinki,in ba haka ba zan nuna miki true color dina, don naga Alamar baki da mutunci,(ya tsaigaita da magana for 3seconds,sannan yaci gaba)kuma daga yau na yanke alakar da ke tsakaninku". Yana gama fadin haka yazo ya wuce ta gefena ya shige daki,niko ina tsaye kamar mutum mutumi,don na kasa ko motsi,ita ko Aunty Amina jikinta a tsanyaye taja tsaki ta shige dakinta hade da turo kofa,haka naja kafata hade da dafa bango na shige daki. Direct Bedroom na nufa don ina kyautata zaton acan zan sameshi,ina shiga na ganshi zaune a gaban mirror dafe da kanshi,wurin shi na nufa gwiwata a tsanyaye na zube a gabanshi tare da kai hannuna kafarshi,ban zata ba naji saukar mari a kumatuna, saurin sakin kafarshi nayi don ji nayi duniyar na juya min don tun da nake ba a taba min marin daya shigeni ba irin wannan,saboda masifar shigata da yayi na kasa kuka sai sauke ajiyar zuciya nake,ganin yana kokarin mikewa yasa naja baya da sauri,ji nayi ya damkoni,da sauki kulle idona ina jiran saukar wani marin,sai jinayi yayi hugging dina hade da fashewa da kuka,nima kukan na saka tare da kankameshi,haka mukayi tayi babu mai lallashi.(Allah sarki Bahijja yanxu kika fara kuka😭😭😭). Sai da mukayi kukan mu muka gaji tukunna muka kwanta kowa na sakin ajiyar zuciya,anan bacci ya daukemu wanda sai kiran sallar magariba ne ya tashemu(kasancewa jikin gidanmu akwai masallaci),tashi yayi ya fita ba tare da ya tanka munba. Sai wurin karfe Tara ya dawo hannunshi dauke da takeaway wanda ledan ke dauke da tambarin chicken republic,yana ajiyewa ya kuma fita sai gashi da plate da fork,fridge ya bude ya dauko maltina guda biyu yazo ya ajiye akan center Table,takeaway ya bude hade da juyewa a plate gasasshiyar kaza ce wadda taji hadi,haka ya ringa yaga ya na samun a baki hade da maltina sai da nace mai na koshi, tukunna ya fara cin nashi. Sai da ya gama ya tattara kayan yakai kitchen hade da daura ruwan wanka aka gas,tukunna ya dawo daki ya kunna TV hade da kamo tashar Mbc Action yana kallo,zuwa nayi na durkusa a gabanshi tare da kamo kannunshi na rike ina zubar da hawaye hade da fadin"Yaya Tasi'u bansan da wata irin kalma zanyi amfani wurin baka hakuri ba,amma don Allah ina rokon ka ka yafe mini ko na samu sassauci acikin Zuciyata ba,domin wallah fushinka a gareni zai iya sa in shiga halin da yafi wanda na tsinci kaina kaina yanxu a ciki,wallahi nayi nadama ji nake na tsani kaina tunda har zan iya saba ma mahaliccina,sannan kuma na yaudari mijina wurin zubar mai da jininshi"na karashe magana hade da fashewa da kuka. Hannu yasa ya sharemin hawaye tare da sauke numfashi yana fadin"komai ya wuce Bahijjah amma ki sani abinda kikayi ya fara sani shakku akan kina sona kuwa,don da kina sona da baki yadda an baki maganin da kika zubar min da jinina ba,amma innayi la'akari da auren hadi aka mana,sai inga kamar an miki dolene wurin aurena,saboda tun kafin auremu ban taba ji kin bude baki kin fada min kalmar I LOVE YOU a bakiba koda bata kai ZUCIYA ba" Nayi saurin cewa"Wallahi yaya ina sonka,sharrin shedan ne kawai hade da zugin su Aunty". Yace.shikenan ya wuce sai ki kiyaye gaba sannan ki dukufa wurin rokon Allah yafiyar abinda kika aikata,sanna daga yau bake ba Aunty Amina ban yadda ki ringa shiga dakinta ba ko wata magana ta hadaku mai tsawo,abunda na yarje miki shine yimata sallama ko gaisuwa". Nace.insha Allah zaka sameni da bin umurninka". Kamoni yayi yai hugging dina tare da fadin"shikenan Allah ya miki Albarka,amma ya kamata a canza mun suna daga Yaya ya koma Sweetheart ko baby,tunda yau dai an tabbatar mun da ana sona". Sunne kai nayi ina dariya,a wannan daren yaya Tasi'u (aw😷sweetheart) ya nuna mini soyayya don hatta wanka sai da yamin kafin mu kwanta. Sai da ya kara kwana biyu tukunna ya koma Lagos ya barni da kewa. Tunda ga abunda ya faru,sai ya zamana ko na gaida Aunty Amina bata amsawa ,yaranta ma basa shiga harkata,sai ya kasance ina zaman kadaici a gidan don itama Aunty Zeena ta samu admission a A.B.U,yaran Aunty Amina kuma in suka tafi school tun safe sai yamma. Da naga zaman ya fara isata sai na fara zuwa gidan Alhaji in a rage wuni,nan ma a rana ta hudu Alhaji ya koroni yace na cika yawo,bayan nan Kuma su Aliyu suka fara zuwa suna tayani hira in sun dawo makaranta,nan kuma Aunty Amina tace in sunzo wai suna mata rashin kunya basu gaisheta,daga nan Alhaji ya hanasu zuwa. Bayan shekara biyar,A lokacin inada 'ya'ya biyu duka mata, Amina(Iman) da maryam(Ilham) da kuma cikin na uku. A lokacin da cikina ya kai wata takwas ne mai afkuwa ta afku, abinda ya faru shine ana sauran kwana biyu sallah Daddyn su Iman ya dawo daga Lagos, sai na dafamai ruwan wanka na kai bathroom,nashiga daki in dauko sabulu, kawai ina fitowa sai naga Aunty Amina ta zubar da ruwan ta jefo min bucket dina waje, ni kuma naga bazan iya daurewa ba sai na tambayeta dalilinta nayin haka, budar bakinta kawai sai ta cemun gani tayi wanda aka kai ruwan dominshi ba gidan ubanshi bane, ni kuma kawai da abun ya bata mun rai sai nace mata shima naga wannan mai jan GOLF(Mijinta) din ba gidan ubansa bane, ina fadin haka na shige kitchen domin in kara dafa wani ruwan, kawai sai jinayi an rufeni da duka da wata zabgegiyar bulala, ihun dana kwala shi ya fito da Daddyn su Iman, yana fitowa yaga abunda yake faruwa bai yi wata² ba ya tsinketa da mari, shikuma dai² Yaya Farooq ya fito shi da Aunty Zeena, yana karasowa baiyi wata² ba ya tsinke Daddyn sun Iman, nan suka kaure da dambe, kasancewa training din soja daban yake haka, haka Yaya Farooq yaringa kwala Daddyn su Iman da kasa,ganin yana niyyar yin kisa yasa na fita GIDAN da gudu ina neman taimako,ina fita nayi kicibus da Alhaji zai shiga masallaci,ganin yanayin yanda na futo ne yasashi tambayata lafiya, kasa bashi amsa nayi,sai dai nuna mai cikin gida nayi da hannu,a dai² lokacin ne mukaji an saki wani ihu, da gudu muka karasa cikin gida,muna zuwa na tarar da Daddyn su Iman a kwance baya motsi da gudu na karasa wurinshi ina jijjigashi ina kuka,amma kwata² bai motsa ba nan na kwala ihu tare da faduwa kasa tim........ Alqur'an na gaji da typing🤪 *Comment* *Like* *Vote* *Share* *_Fateeyzah_*✍ *HIKIMA WRITERS ASSOCIATION* *GIDAN NAGOGGO*🏨 *_(A true life story)_* *Written by fateeyzah*😍😍 *_Jinjina gareki sharifat niamey,Allah yabar kauna❤_* *_Allah ina rokonka ka*_ *_kara daukaka*_ *HIKIMA WRITERS* *ASSOCIATION* , *_ka_* *_karemu daga sharrin mahassada_*. *_Bismillahir rahmanir rahim_* *_Page_* *_1⃣6⃣to2⃣0⃣_* Tunda na fadi bana cikin hayyacina sai washe garin ranar na farka na ganni a Asibiti, shafa cikina danayi ne naji ba komai yasa hankalina tashi, nayita kokarin mikewa amma na kasa. Nakai kusan minti goma da farkawa amma ba wanda ya shigo dakin, hakan yasa ni cikin tunani, don zuciyata cike take da tambayoyi, wanda na rasa wanda zai amsamin. Turo Kofan da akayine yasa ni maida hankalina wurin don ganin mai shigowa,ganinsu Aunty Asma'u da Daddynsu Iman ne yasa wani farin ciki ya lullubeni, don ganinshi danayine ya tabbatar mun yana raye, karasowa wurina sukayi tare da tambayata ya jiki, a hankali na amsa idona akanshi Saboda ganin fuskarshi da bandeji, ganin haka yasa Aunty Asma'u ta juya tafita, ganin fitar tane yasa shi karasowa bakin gadon ya zauna. Kallonshi nayi hade da tambayarshi me ya samu cikin jikina,anan yake fadamin kasancewa wurin faduwa cikina Yaya bugu,shine aka min C.S aka ciremin babyn,amma sun sata a Incubator (kwalba) saboda watanta bakwai ne da sati biyu. *_A gurguje_* Satina hudu a Asibiti tukunna aka sallamoni da ni da Jaririyata wadda taci sunan mamar Daddynsu wato rukayya(ruhaima), duk cikar dakin Ummy ba wanda yazo dubani, haka ma dana dawo,Su Aunty Hanna ne kawai da Aunty Fatima suka zo dubani,amma Aunty Amina ko lekowa batayi ba domin ta min barka sabanin haihuwar su Ilham da duk da bama magana tana min barka,Ammyna ma bata zo ba sai dai ta sanar dani Alhaji ne ya hanata Zuwa. Kwananmu biyu da dawo wa Alhaji yazo gidan,a lokacin Daddyn Iman na nan, dukkanmu ya tara mu a dakin Yaya Farooq,anan ya yanke hukuncin akan Daddynsu Iman ya dena shigo mai gida,Amma ni bazai iya cewa in bar gida ba,sai dai in zai ganni,ya ringa zuwa bakin GIDAN ya kirani,in kuma ya na ganin ba haka ba ya tattara ni yaje ya kama min haya,sannan ya min kashedu in zan je Gidanshi kar in yadda in shigo mai da Jinin Tasi'u,hakanan Alh ya kakkabe Rigarshi ya kara gaba,ba tare da ya saurari ban hakurin da muke yiba. Aunty Amina ko kamar ta zuba ruwa a kasa tasha na wannan hukuncin da Alh ya yanke,sabanin Yaya Farooq da jikinsa yayi sanyi. Haka Daddynsu Iman ya shirya kayansa tare da diremin ATM card dinsa ya wuce Kudan tare da min Alkawarin zaije yayi shawara da Iyayensa don samun mana mafita. Bayan tafiyarshi da kwana biyu ya kirani ya sanar dani zai wuce lagos,don sunyi shawara da iyayenshi akan ya barni anan kafin ya karasa gininshi (kasancewa yana gini a kaduna). A wannan zaman da nayi ba karamin bakin ciki nake kunsa ba,don Aunty Amina bata da aiki sai na yada min da habaici, saukin tama Iman ta girma,don da ita nake hira in bata je school ba. Ruhaima nada wata hudu akayi bikin Yaya Ibrahim da ya auro matarshi daga Abuja,bikin ba karamin kashe kudi akayi ba,inda har mutanen unguwa suka fara tambayar aikin da Yaya Ibrahim din yakeyi,anan naji Aunty Hanna na cewa wai Yaya Aminu ne ya daukeshi suna hakar Gold,nan ma sai da suka yita sakin habaici na sunyi mana fintinkau bamu da yanda zamuyi,shima dai Alhaji ya bashi Gida anan unguwar. Bayan bikin ne da sati uku, Daddynsu Iman ya kirani akan in shirya kayan mu don zai zo ya tafi damu kasancewa ya samu scholarship na yin M.sc a Dubai kuma damu zai tafi don harda Gida aka bashi acan. A ranar ne kuma *GIDAN* *NAGOGGO* suka tashi da wani tashin hankali inda aka kama Yaya Ibrahim dalilin satar motar da yayi ta wasu 'yan India da suke yi ma Yaya Aminu Aiki, wanda kafin wani lokaci maganar ta zagaye unguwa,ranar dai su Ummy sun shiga tashin hankali ni kuwa ko a kwalar rigata,don a ganina Alhakinmu ne ya fara kamasu,don ko Jaje ban ma kowa cikinsu ba,anan dai su Alhaji,Yaya Baffa da Yaya Farooq sukayita ciku² har sai da suka fito dashi, sannan Alhaji ba wani mataki da ya dauka akan hakan,sai ma fushi dayayi akan abunda Yaya Aminu yayi na kama Yaya Ibrahim din da yasa akayi. Wani satin na zagayowa, Daddynsu Iman yazo ya kwashe mu kuka tafi Kudan,kwanan mu biyu anan muka wuce lagos inda zamu yi sati biyu kafin mu wuce Dubai. Satin mu daya sai ga kiran Yaya Farooq,ina dauka ya fara duramin zagi akan tunda na zabi mijina akan su in zo in kwashe kayana daga Gidan,bai jira cewa naba ya kashe wayar, hankalina ba karamin tashi yayi ba da jin zancensa,dialing din Number Yaya Farooq nayi amma yayi rejecting,nan na fashe da kuka,sai da naci kukana na gaji sannan na yanke Hukuncin kiran Aunty Asma'u. Bayan na kira Aunty Asma'u ne take sanar dani yanxu suka gama meeting a kaina anan Gidan Alhaji,ana take fadinmin wai sarki ne da Mahaifin Tasi'u suka zo bama Alhaji Hakuri akan matsalar dasuka samu da Tasi'u,shine bayan sun gama tattaunawa ya dauki waya ya kira Tasi'u yace mai ya samu lokaci kafin mu tafi Dubai yazo a musu sulhi da Alhaji,shine shi kuma baisan wayar a speaker take ba yace wai ai a share Alhaji da 'ya'yansa duk munafikai ne(wannan shine ruguntsimi), anan Alhaji yace to ya sakanmai 'yarsa,shine yace ai tun da abin ya faru yaso sakina,amma na roke shi ya rufamin asiri kar ya sakeni saboda bazan iya zaman Gidan Alhaji ba. Tana gama min wanna bayanin naji zufa tana keto min,na rasa a inda zan sa kaina,don Alhaji shima sai da ya kirani yace kar in kuma zuwa mai Gida in dai akwai Auren Tasi'u a kaina. Ruguntsimi kenan🤔, Shin Bahijjah zata bi maganar ko kuma zata bi Tasi'u domin tafiya Dubai?. Amshoshin tambayar nan zata zo a page na gaba,wanda anan ne zamu ci gaba da Asalin labarin. Ayi hakuri da Errors saboda banyi Editing ba. Kar ku manta comment dinking,shine karfin gwiwa ta. *Comment* *Like* *Vote* *Share* *Fateeyzah* ✍ *HIKIMA WRITERS ASSOCIATION* *GIDAN NAGOGGO*🏨 *_(A true life story)_* *_Written by fateeyzah_*😍😍 *GIDAN NAGOGGO FANS* *Mmn Abdoulaziz* *Queen candy* *Hassinat Muhammad* *Fadiey* *Rabi'atu Y* *Sharifat niamey* *Saudah* *Fa'iza Auwal* ' *yar Asalee* *Zainab zee* *Fatima imilan* *Maman farhiyya* *Munlex* *Hafsat s bello(maman fadila)* *Meerah* *Adizatou zanna* *Ummu farha* *Amina Sufi usman* *Maman safwan* *Nazma* *Maryam* *Zabba'u Abdulrahman* *Mrs Annur* *Mrs Yarima* *Maman Deeja* *Aisha jibril(Aj)* *Innah sharrif* , *da sauran wadanda baku ji sunanku(sorry sai next page) dukkanku barka da jumma'a,ina jin dadin comment dinku,ina godiya.* *jinjina gareku 'ya'yana fadila,khaleefa,Affan Allah ya raya minnku* *_Bismillahir rahmanir rahim_* *_Page2⃣1⃣to2⃣5⃣_* A ranar haka na wuni cikin tashin hankali,don ko girkin dare na kasa daurawa, sai dai cornflakes na hada ma su Iman suka sha sannan sukayi bacci, niko ko ruwa na kasa sawa a bakina , haka nayi ta zaman jiran Tasi'u ya dawo saboda nata kiran phone dinshi amma baya dauka daga baya ma sai ya kashe wayar. Sai wurin karfe sha biyu tukunna ya shigo gida alokacin har na fara gyangyadi don karar rufe kofar shi ne ya tasheni, kallon da na watsa mai ya sa jikinshi sanyi da jan kafa ya karaso wurina hade da fadin"bahijjah mai ya faru, tunda nake da ke ban taba ganin kin min mafificin wannan kallon ba". Na kalleshi fuskata cike tab da hawaye nace"dole kace haka mana, tunda kasan abun da kayi,haba Daddynsu Iman koda Alhaji sa wuka yake yana yankan naman jikinka ai bai kamaci zagi a wurinka, ko ba ka aurena ai akwai dangantaka ta jini, amma wai har kai zaka iya bude baki ka kira Alhaji munafiki, aiko kaga ka cancanki wannan kallon daga gare ni " na karashe magana ina goge hawayen dake fuskata. Riko hannuna yayi tare da fadin"wallahi Bahijjah ba abunda ya faru kenan ba, nasan dai Alhajinmu ya kirani yace mun shi da sarki sunzo sun samu Alhaji sun bashi hakuri akan abunda ya faru, shine Alhaji yace yana bukatar inzo saboda akwai maganar da yake so yayi a gabana shine fa nacemai bazan samu zuwa ba saboda ina shirye shiryen tafiyar mune, to kinji yanda muka yi dasu,kawai kuma sai ga Yaya Baffa ya kirani yanata zagina wai na zagi Alhaji, tunda bansan mutunci ba in sakeki, ni kuma nace mai ina sonki ne shi yasa ban sakeki ba, amma da bana sanki da ba mu kai wannan lokacin a tare ba". Ajiyar zuciya na saki tare da fadin"kar kaga laifina hatta Aunty Asma'u abunda ta fada min kenan, amma me yasa da na kira wayarka ba ka dauka ba daga baya kuma ka kashe wayar gabaki daya"na karashe da tambayarsa. Sakin hannuna yayi sannan yace"wallahi sanda kika kirani ina meeting ne kasancewa yau nayi handing din komai ga sabon manager da aka kawo". Hausawa nace wa tsakanin miji da mata sai Allah,a wannan dare muka shirya da ni da Tasi'u don ni aganina abunda ya fada min shine gaskiya sabanin abunda Alhaji da sauran ' yan uwana suka ce. Sati na zagayowa,jirgin mu ya tashi zuwa Babban birnin Dubai wato Abu Dabi city, zaman mu a Dubai zama ne mai cike da FREEDOM hade da jin dadi,banda wani tashin hankali ko fargaba, don duk na manta da wani tashin hankali a Nigeria,don daga Ammy sai Aunty Asma'u kawai nake waya don nasan ko na kira Alhaji dauka zaiyi ba. Kasance wa in Daddynsu Iman ya tafi school sai yamma yake dawowa,sai ya neman ma Iman da Ilham school acan,inda akasa Iman a nursery two,Ilham kuma a pre nursery,ni kuma sai ya neman mu wani school na fashion designers, wanda anan na koyi yanda ake dinka jallabiya da veil. Shekara mu daya da wata biyu acan muka tattaro muka dawo Nigeria inda muka sauka a Lagos,kwanan mu biyu muka yo Arewa inda Daddynsu ya ijiyemu a zaria shi ya wuce kudan. Wurin karfe biyar keke napep ya sauke mu a bakin gate din Gidan Alhaji,nan na nemu Almajirai suka daukar mun trolleys dina suka shigan mun dasu gidan,ni kuma na biyar mai keke napep kudinsa na kama hannun yarana muka shiga ciki. Muna kusa kai Gidan,naga Almajiran da na bama kayana na tsaye a farfajiyar Gidan,gefe daya kuma ga Alhaji,Ummy,Ammy da wasu daga cikin yaran Gidan a tsaye,ganin irin kallon da Alhaji yake watsamin ne yasa na kasa ci gaba da tawo wa,nuna ni yayi da dan yatsa tare da fadin "kar ki kuskura ki karaso wurinnan in baso kike na bata miki rai ba,ai dama an fadamun kin dawo,shiyasa na kasa na tsare don nasan dole zakizo, toh ki bude kunnan ki kiji wallahi bazaki shigo mun gida da auren Tasi'u akanki ba, inkin ga na kuma bari kin shigo gidannan to kinzo min da takardar sakine,don haka na baki minti buyu ki tattara kayanki da yaranki ku bar min Gida kuma kar ki sake inji kinje wani gidan dan uwa, sannan kayan dakinki na baki nan da sati daya kizo ki kwashe in ba haka zan zubar dasu a waje,kinji dai na fada miki" San ya juya ga 'yan gidan tare da fadin" ku kuma ku wuce muje",haka ya tasa su a gaba suka shige cikin falonsa,ina gani Ammy idon ta cike da hawaye tana waiwayoni har suka shige. Haka ina kuka muka fito Gidan inda nasamu keke napep na muka shiga, sannan na sallami almajiran na umurci Driver da ya kani motor park. Muna hanya Ammy ta kirani tana kuka tana ban hakuri sannan ta ja mun kunne akan kar in sake in ce zan kashe aurena,don ko na dawo Gida bazan iya jin dadin zaman Gidan ba,don ita ma saboda Kannena take zaune, haka tayi ta bani shawarwari da nasiha, sannan muka ajiye waya. Muna karasowa motor park na sallami mai keke napep na kama yarana muka hau motar Kudan,minkai minti goma sannan motar ta cika muka tashi,a hanya ma Aunty Asma'u ta kirani ta ringa bani hakuri tare damun kashedin kar in sake in kashe aurena. Sai bayan magriba muka iya kudan,muna sauka na samu Almajirai suka daumin kayana muka kama hanyar Gidansu Tasi'u kasancewa babu nisa daga inda aka saukemu. Muna isa, mukaci karo da Tasi'u a kofar Gida, da mamaki ya tare mu, ya amshi kayanmu kayanmu sannan na sallami Almajirai muka wuce cikin Gida,yana ijiye kayanmu ya fita domin yin sallar magariba,mu kuma muka shige dakin mahaifiyarsa(umma). Bayan munyi sallah hade da cin abinci sannan Alhajinsu ya kirani zuwa falonshi,nan na tarar da Tasi'u da umma da Alhaji, bayan na gaisheda Alhaji sannan ya tambayeni abunda ya faru na tawo kudan bacin Tasi'u yace ya barni a zaria, nan na kwashe duk abunda ya faru na fadamai,nan ko ya fara fada ya dauki waya ya kira Alhaji, yana dauka ya fara surfa mai masifa kamar haka"wai kai *NAGOGGO* wani irin zuciya gare kane,an bak hakuri amma kaki hakura, ko Allah ana mai laifi kuma atuba, ballantana kai, to wallahi ka guje randa Allah zai kama ka saboda hakkin yarinyar nan kaji na fada maka,kuma insha Allahu auren Bahijjah da Tasi'u har mutuwa" yana kaiwa nan ya kashe wayar bai jira amsarshi ba. Nan Alhaji ya shiga yi mini nasiha tare da kwantar min da hankali,sannan yace min zasuyi shawara da Tasi'u suji inda zamu zauna,ranar dai sai kusan asuba nayi bacci. Kwanan mu biyu a Kudan,Tasi'u yazo ya sameni da murna yake cemin ya samu aiki a NNPC nanan Kaduna,nan mukai ta murna nan yace mun gobe zai je don sun kirashi,washegari ko yayi sammako ya tafi kaduna. Sai bayan magariba ya dawo,bayan ya yi sallah yaci abinci yake cemin sunce ranar monday zai fara aiki saboda haka yayi shawara da Alhajinsu akan sai kama mana haya a kaduna kafin ya gama nashi ginin,nanko naji farinciki ya rufeni, don ko ba komai kafi sakata ka wala anaka dakin. Acikin sati naje na kwashe kayana a Gidan Alhaji, tukunna muka wuce kaduna inda ya kama mana haya a Kinkinau, gida ne mai dauke da Flat biyu kowanne flat yanada 2bedrooms, kitchen, toilet da store. A farkon zaman mu, muna zaune ba tare da wata matsala ba,haka ma makociyata wacce take dayan flat din itama bata da matsala. Matsalar dana fara facing daga Tasi'u shined dana samu ciki, sai ya nemi in zubar da cikin wai saboda shi yara uku sun isheshi, ni kuma naki yadda,nan fa yafara min rashin mutunci hade da gori, sai ya kunle store ya tafi da mukullinshi sai dai makociyata ta bani,su Iman dama ya sasu a makaranta insuka tafi tun safe sai la'asar sai ya zamana in yaje daukosu sai ya biya dasu ta restaurant suci abinci,da daddare kuma sai ya dafa musu indome ko ya siyo musu snack su ci nikuwa bai damuba, haka ya raba daki dani ya zamana yana kwana da 'ya'yansa. Ranar da bazan manta da itaba,itace ranar wata babbar salla alokacin cikina wata shidda, sai na sami Tasi'u don in tunatar dashi hakkina daya danne,aiko na ya balbaleni da masifa har da cemun dama halin 'yan gidan mune rashin kunya ni kuma da abun ya ban haushi sai nace mai ai munfi 'yan gidansu da suke maneman mata,aiko nan ya tsinke ni da mari yaci gaba da zagina nima ina ramawa,aiko da ya gaji sai naga ya shiga daki sai gashi ya fito da farar takarda ya mikomin........ 'ka'ka'kara 'kara, sai mun hadu a next page. Kuyi hakuri na gaji banyi Editing ba. *Comment* *Like* *Vote* *Share* *_Fateeyzah_*✍ ********************** ? ************************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************? ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ? ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ? ************************** *©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION* *( _Home of peace,joint of entertainment,to educate and enlighten our readers)_* *GIDAN NAGOGGO*🏨 *_(A true life story)_* *_Written by fateeyzah_*😍😍 *_Bismillahir rahmanir rahim_* *_Page2⃣6⃣to3⃣0⃣_* Mika min takardar yayi tare da fadin "gashinan sai a kara gaba,ki tafi gidan masu tarbiya wadanda basa neman mata"yana gama fadin haka ya dauki key din motar shi ya fita. Take kukan da nakeyi na nemeshi na rasa, jinayi kamar in hadiye zuciya in mutum, aranar na tabbatar da namiji badan goyo bane duk wanda ta maidashi uba zata mutu marainiya, a ranar na kuma tabbatar da namiji ko service din MTN ya fishi guarantee, sannan alokacin nadama ta kamani na yanda na fifita mijina akan ubana, na zabi in zauna da mijina akan mahaifina,a wannan lokacin nayi danasani da naki bin maganar Alhaji,aganina duk wulakancin da yamini da hana ni abinci bai isheni ba har sai daya hada ni da saki a lokacin danafi bukatarsa,sannan nayi danasani na rashin sanar da Ammy da Aunty Asma'u halin da na ke ciki, don ko Granny da muke gari daya karya na mata nace cikin yazo mun da matsala shi yasa bana zuwa gaisheta wanda kuma saboda rashin kudin mota ne dalilin, ita kuma ba kafa ba ballantana tazo. Nakai kusan awa biyu a inda ya tafi yabarni,ba komai nake tunani ba sai rashin sanin abin yi,da rashin sani wanda zan fada ma maganar nan,ganin shigowar Humaira (makociyata) ne ya bani kwarin gwiwar tashi na nufeta nayi hugging dinta sannan na fashe da kuka, cikin rikicewa take tambayata mai ya faru ,kasa bata amsa nayi sai zame jikina danayi daga jikinta na nufi inda na tashi na dauko takardar na mika mata, karba tayi cikin mutuwar jiki ta warware takaddar,cikin sanyin jiki tace "inalillahi wa'inaillahir raji'un maman Iman saki har biyu", cikin azama na karfi takardar daga hannunta na kai duba cikin takardar ba komai na fahimta acikin takardar ba sai layi biyu da na iya kai duba na kai wati inda ya rubuta _Ni Tasi'u Ibrahim Kudan na saki matata Bahijjah Ahmad Nagoggo saki biyu_...........nan naji wani irin jiri ya debe ni da sauri na dafe hannu kujera ana Humaira ta karaso wurina ta taimaka min na zauna. Mun kai minti talatin ba tare da mun furta komai ba don kowannan mu yayi nisa cikin tunani, humaira ta fara janne shirun tare da fadin"Maman Ihsan ya kamata ace kin sanar da gida halin da ake ciki" Sai da na dau dan lokaci tukunna nace "haka ne humaira amma kinfi kowa sanin halin dana ke ciki,ni wayata babu ko sisi". "Bari in dauko wayata akwai credit"ta karashe maganar tana ficewa. Cikin minti biyar sai gashi ta dawo ta mikamin wayar tare da juyawa ta fita, jikina na rawa haka na fara dialing din Number Ammy sai da tayi ringing so uku tukunna ta dauka tare da yin sallama, cikin Muryar kuka na fara magana"Ammy ya sakeni ba tare da nayi mai komai ba". Salati tayi tare da fadin"Bahijjah kikace ya sakeki?, mai kika masa?, dama baku zaman lafiya ne kika boyemu?,oh ni Amina wani irin abune wannan ka saki matar ka ranar sallah". Jin wadannan tambayoyi daga bakin Ammy yasa hankalina yakuma tashi, nan na zayyane mata abunda ya faru tun daga daukar cikina har zuwa sakin daya mini, nan Ammy ta kuma zabga salati tare da fadin"Bahijjah kina da hankali kuwa,duk wadannan abun na faruwa amma kika kasa sanar da kowa". Nace"Ammy don Allah kiyi hakuri wallahi banson ya zamana ko yaushe ni nake daga miki hankali,kuma kinga kema kina ji da kanki, ga matsalar nan gidan, shiyasa naga bai kamata in kara miki wata damuwar ba" "To yanxu ina su Iman din" Ammy ta tambaya Nace"inaga ya kaisu Kudan ne,saboda naga ya hada musu kaya". "Bari yanxu xan kira Asma'u muji yanda za a yi, don gaskiya bansan yanda zan tunkari Alhaji da wannan maganar" haka mukai sallama da Ammy na kashe wayar. Can wurin karfe biyar na ranar sai ga sallamar Yaya Baffa,Yaya Farooq da Aunty Asma'u, suna shigowa Yaya Baffa ya umurceni da intashi in hada kayana inzo mu wuce, cikin rawar jiki na shiga daki dan hado kayana, ina cikin hadawa Aunty Asma'u ta shigo tace inje Yaya Baffa na kirana, cikin sanyin jiki na bita zuwa parlour, ina zuwa na samu wuri na zauna sannan Yaya Baffa ya fara magana cikin bacin rai "Bahijjah ganin mu da kikayi munzo, Alhaji ne yayi umurni akan muzo mu tafi dake Saboda Asma'u tazo mana da maganar Tasi'u ya sake ki,Hakika dukkanmu ranmu ya baci akan abunda ya faru,duk da a baya mu muka nemi daya sake ki,amma ya nuna mana yana son matarsa,ko yanxu abinda ya bata mana ran baiwuce yadda Ammy ta fada mana irin wulakancin da ya miki hade da hanaki abinci da yayi,Amma kuma yanxu Alhaji ya kuma kiranmu akan mubarki anan ki haihu, inyaso inkin yi arba'in sai ki ijiyemai 'yarshi ko 'yanshi ki koma gida". Nan naji gabana ya fadi in ijiye dana kuma, ai abunda bazai taba yiwuwa ba kenan in bar dana ko'yata mai kwana arba'in a duniya, ina kokarin magana ne Aunty Asma'u ta girgiza min kai, ma'ana kar ince koma.Anna Yaya baffa ya tambayeni in bashi Account number na, ina bashi yayi mini tranfern dubu dari yace inje in sayi abinda nake bukata in kuma akwai wata matsalar in kirashi a waya, ina ji ina gani suka tafi suka ganni. Haka naci gaba da rainon cikina cikin kulawar 'yan uwana da Humaira, tsakanina da Tasi'u kuwa sai dai ido ban shiga harkarshi nima bai shiga tawa, su Ihsan kuma bai dawo dasu ba. Bayan wata uku na haifo dana da taimakon unguwar zoman da Humaira ta kira mun a bayan layinmu, duk wanda yaga yaron sai ya yabashi,a ranar ne kuma Allah ya dauki ran Alhajin Tasi'u. Haka 'yan uwa sukayi ta kirana suna min barka hade da gaisuwa, sati na zagayowa aka rada ma yaro suna ibrahim khaleel,ba wani taro akayiba ,amma duk 'yan gidanmu da surukan gidan sunzo illa 'yan dakin Ummy, ba laifi an tara mana kaya ni da khaleel, Tasi'u ko khaleel kadai yai ma kaya niko ko kyale bai min ba. Nayi arba'in da kwana daya sai ga Yaya Baffa yazo wai Alhaji yace in ajiye ma Tasi'u danshi in bishi mu tafi gida. Please manage. Shin Bahijjah zata ijiye danta ta tafi ko zata zabi danta akan Alhaji? Sai mun hadu a next page. *_Fateeyzah_*✍ *©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION* _*(home of peace,joint of entertainment,to educate and enlighten our readers)*_ *GIDAN NAGOGGO*🏨 *_( A true life story)_* _*Written by fateeyzah*_😍😍 *Godiya gare ku real Fateeyzah novel group,ina jin dadin comment dinku ako da yaushe especially maman Abdulaziz,Aisha jibril(Aj),yar Asalee da sauran members ina yinku.* *Da masu kirana,da masu text ina yinku,naga tsakonninku na gode da nunamin kulawa da kukayi.* *Hafsat .s.bello(maman fadila) thanks for the visit,gskiya na ga alama ke babbar fan ce ta GIDAN NAGOGGO, ina godiya* *Aisha jibril(Aj)thanks for the call,Allah kara zumunci.* *Sis Zuby Allah ya kara sauki,yasa kaffarane* *_Bismillahir rahmanir rahim_* *_Page3⃣1⃣to3⃣5⃣_* Take naji hankalina na tashi,don kwata² na manta da maganar Alhaji na in na haihu zan barmai yaron, tsawar da Yaya baffa ya daka munne ya dawo dani daga gajeran tunanin dana tafi tare da fadin "don Allah Yaya Baffa kayi hakuri, bazan iya barin khaleel ba in tafi,don Allah ka taimakeni ka rokon min Alhaji ya barni da dana"na karashe maganar ina zubar da wasu zaffaffun hawaye. Wata harara ya banka min tare da fadin "wai ke Bahijjah wata irin kafaffiyar yarinya ce,duk wulakancin da Tasi'u ya miki ba ki gani ba,amma har yanxu kina nan nanike da dansa,mufa gata muke so mu miki amma kinki ganewa, kinsan ko daya sake ki sai da muka sha artabu da Alhaji kafin ya bari muka zo wurinki,amma kike nema ki watsa mana kasa a ido". Dago kaina nayi a karan farko na kalleshi tare da fadin"wani irin gata ne wannan nasan rabani da d'ana mai kwana arba'in da biyu a duniya, wanda ta dalilinsa na samu kaina a cikin halin dana ke ciki,ta dalilinsa na rasa ubansa da yayyinsa, a yanxu in ka cire Ammy ba wanda nakema son da nake ma khaleel a duniya, don haka in baza ka iya yimin taimakon dazan kasance da d'anaba ka tafi ka barni kawai"na karashe magana cikin daga murya. Yanayin yanda nayi magana da hargagi da kuka yasa jikinsa yayi sanyi tare da fadin "Bahijjah kinsan halin Alhaji, inya zartar da hukunci ba wanda ya isa ya saba, Bahijjah duk irin rashin jituwar dake tsakanin 'yan dakinmu da naku baki ji bakin cikin damuka tsinci kanmu ba da mukaji sakin da Tasi'u ya miki, wannan ne dalilin dayasa mukayi confronting din Alhaji lokacin da abun ya faru, dakar muka shawo kanshi akan muje mu dauko ki amma da sharadi inkin haihu da zaran kinyi arba'in zaki maida mishi danshi, wanda daga baya kuma ya canza shawara akan abarki anan, in kinyi arba'in din kya ijiye yaron ki dawo gida, a yanxu basan yanda zan tunkari Alhaji akan ya barki ki koma gida da..... "Ringing din wayar shine ta katse mai magana, cikin sauri yayi receiving din wayar tare da sata a speaker, muryar Alhaji ne ta doki kunnena wanda dalilin haka yasa 'yan hanjin cikina kadawa, Yaya Baffa ne yayi mai sallama tare da fadin" an wuni lafiya Alhaji" Daga can bangaren Alhaji ya amsa tare da fadin " lafiya lau Baffa, kun tawo ne Saboda kunake jira, don inason zuwa ta'aziya". Saida Yaya Baffa ya kalleni, tunkunne ya kwashe duk yadda mukayi ya sanar da Alhaji, nan fa Alhaji ya fara bambami, nan dai ya ringa bala'i, sannan daga karshe yace ma Yaya Baffa ya taho ya kyaleni sannan ya shaidamin kar in sake in tako gidanshi batare dana maida dannan ba. Inaji ina gani Yaya Baffa ya tafi tare da cemun in mai kwatancen Gidan granny zaije ya sanar da ita in yaso sai in koma wurinta da zama kafin su samo mafita. Bayan fitarshi da awa biyu sai ga kiran Ammy inda take fadin mu Yaya Baffa ya kirata ya fada mata komai,sun yanke hukunci zan koma Gidan Granny da zama, don haka gobe Aunty Asma'u zatazo ta rakani Gidan, nan dai tayi mini nasiha tare da fadin wannan karan zata kai karar Alhaji wurin Hajiyar Sokoto don ta gaji da irin abinda ya kemun. Bayan na gama waya d Ammy ne kuma sai ga kiran Yaya Baffa inda yace min in turo account number na, take ko na tura wanda anan yamin transfer dubu dari, kiranshi nayi don in mai godiya anan yake cemin ya turamin ne don in samu sana'ar yi, nan dai shima yamin nasiha sannan muka yi sallama. Nan na zauna inata mamakin Yaya Baffa,don dai nasan da ba haka yakeba, don shima nuna mana tsana yake kiri kiri, ina cikin wannan tunanin sai ga Humaira ta shigo nan dai na fada mata yanda mukayi da su Yaya t Baffa,nan da muka fara kukan rabuwar. Wurin karfe takwas na dare,sai ga Tasi'u ya shigo ya hada kayanshi dana yara da duk abinda yasan mallakinsane yayi ta futa dasu,sai daya gama sannan ya miko min key tare da fadin in na kwashe kayana na kulle ma masu gida dakinsu,bai jira cewata ba yasa kai ya fita ya barni da tunani. Ina zaune a inda yabar ni,ina ta juya maganarsa acikin kwakwalwata, don na kasa fahimtar inda ya dosa, sai ga Humaira ta shigo cikin sauri tana kwala min kira, ganina zaune a parlour yasata karasowa wurina cikin hanzari tare da cewa" Maman Iman kinji abunda na jiyo kuwa(na girgiza mata kai)wai sauran sati uku bikin Daddynsu Iman". Bakina na rawa nace mata"da gaske Humaira ko dai jita² kikaji kan cewa zai yi aure" "Wallahi da gaskene don mai gidana ya fada mawa, na ma manta, yaufa ya tare a sabon gidanshi tare dasu Iman da ummanshi", take naji cikina ya fara juyawa,nan danan naji wani zazzabi yana son rufeni,ban san har yanxu akwai son Tasi'u a raina ba sai da naji maganar aurensa, sannan gidan dana zabi plan da kaina shine wata zata shiga bani ba,nan dai naji wani irin kishi ya rufeni, ganin halin da nake ciki yasa Humaira tafara lallashina tare da min nasihohi,sannan ta tashi ta fita. Daukar waya nayi nakira Ammy tana dauka na sa mata kuka tare da fada mata abinda naji daga bakin humaira. Gyaran murya tayi tare da cemin"Bahijjah mun riga mun sami wannan labarin, Alhaji ne yace kar a fadamiki, don tunda Tasi'u ya sakeki da sati biyu aka samasa rana da wata yarinya anan kaduna,don ko su Iman ba kudan ya kaisu ba suna nan gidansu amaryarsa" Cikin rawar murya nace" Ammy duk kunsani kuka kasa sanar dani?, a ganina Ammy koda Alhaji yace kar a fadamin ai ke bai dace ki'ki sanar daniba" Cikin sanyin jiki Ammy tace"Bahijjah kiyi hakuri don sanar da ke baida amfani, mutuwar auranki bakaramin rikici yaja a dangiba wanda yaja rarrabuwar kawunansu, a ranar da kika sanar dani Tasi'u ya sakeki, saina kasa sanar da Alhaji don nasan duk abunda zai biyo baya ba mai dadiba ne, sai na yanke shawarar kiran Baffa na fadamai wanda cikin tashin hankali ya hado kannisa suka samu Alhaji suka fada mai, cikin bacin rai yace shi ba ruwansa, dakyar suka shawo kan Alhaji inda ya yadda su Baffa su daukoki, bayan tawowarsu wurinki ne sai Alhaji ya dauki waya ya kira Babban Tasi'u ya sanar dashi abunda ya faru, amma budar bakin shi sai yace ya sani, don shi farin ciki ma yake Tasi'u ya rabu dake saboda wai Tasi'u yace rikemai riga kikayi kikace in ya cika cikin uwarshi da ubanshi ya sakeki, shine shi kuma ya sakeki, haka dai yaci mutuncin Alhaji a waya, wannan dalilin ne Alhaji yace a bari ki haihu anan,don bazaki kawo mai jinin Tasi'u gida ba, wallahi bahijja ko da mahaifin Tasi'u ya rasu muka je gaisuwa bakiga irin wulakancin da 'yan gidan suka mana ciki kuwa har da ummanshi, wannan dalilin ne yasa Alhaji cewa ki ijiye khaleel ki dawo gida, don dacan ya sake shawara akan in kinyi arba'in ki dawo gida da khaleel inyaso inkin yayeshi kya maida shi". Cikin kuwa nace"Ammy tabbasa biri yayi kama da mutum don tunda Tasi'u ya sakeni wani dag gidansu bai taba kirana ba, don ko lokacin da Alhajinsu ya rasu da na kirasu nayi musu gaisuwa yanda suka amsa mini kamar akwai wani abu, ni kuma sai na dauka mutuwarce ta taba su,Ammy ayau na tabbatar da Alhaji abunda yayi shine daidai, don haka zan ijiyemai danshi in dawo gida tunda dai abun rashin mutunci ne". Ya kuke gani,shin Ammy zata yadda Bahijjah ta ajiye danta mai kwana arba'in da biyu a duniya ta koma gidan Alhaji? _Sorry fans insha Allah daga next page zamu dawo cikin labari don jin yadda auren Bahijjah na biyu zai kasance._ *Comment* *Like* *Vote* *Share* *Fateeyzah*✍ *©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION* *_(home of peace, joint of entertainment and to educate and enlighten our readers)_* *GIDAN NAGOGGO*🏨 *_(A true life story)_* *_Written by fateeyzah_* *Ta'aziya* *Inalillahi wa inna illayyir raji'un.* _Ina mika ta'aziyata zuwa ga ummu salma daya daga cikin member na_ *HIKIMA* *WRITERS* *ASSOCIATION* , _na_ _rashin danta(naeem),wanda ya rasu ranar kamar haka 11/04/2020,muna rokon Allah ya jikanshi,ya gafarta masa yasa masu ceton mune,ameen._ *_Bismillahir rahmanir rahim_* *_Page3⃣6⃣to4⃣0⃣_* "Kul Bahijjah, ki dena fadin zaki ijiye mai dansa, kina ganin abinda ya faru da zubaida sakamakon rabata da danta da Alhaji yayi dan wata biyu,ranar kakarta t kawota gurin Alhaji take fadamai, yanxu haka Asibitin mahaukata ake karbat mata magani, don doctors sunce tunanin 'yayanta yasa kwakwalwarta ta tabu, don haka ki barshi da Allah duk abunda yayi, yai ma kansa, sannan na san ki da kulafacin 'ya'ya don Allah kicire 'ya'yan nan aranki, sannan karkiga garinku daya kiyi ta daukar kafa kina zuwa gidan, don bansan abunda za ayi ta kananan magannanu akai, sannan kinsan irin gidan dazaki koma zama, don haka ki kama bakinki, ba ruwanki da gulma da tsegumi irin na family house"haka dai Ammy tayi tamin nasiha sannan mukayi sallama. Washegarin ranar, wurin karfe goma na safe sai ga Aunty Asma'u tazo, nan muka samo Almajirai suka tayamu kwashe kaya sannan muka rankaya har da Humaira sai dan bushiya Gidan Granny. Daki guda aka waremun a shiyar Granny,inda anan akasa mun kayana,suka gyara min daki kamat wata amarya,sannan bayan la'asar suka tafi suka barni,wanda munci kuka da kyar Granny ta rabamu(lol 🤪su Bahijjah masu idon kuka) . Kudin da Yaya Baffa ya bani,shine na dauka na siya keken dinki hade da materials,na fara dinka gowns mai kamar jallabiya inasa stones,sannan ina dinka kimono,kasancewa dan bushiya akwai gidan masu kudi, Sai ya zamana ina ciniki sosai don da kaina nake shiga gida² ina masu talla. A bangaren zamana a gidan,banda wata matsala da kowa,ban shiga shirgin kowa ,in mun hadu a tsakar gida kuwa gaisuwa ke shiga tsakanin mu,in ko ban fito ba sai mu dade basu sani a ido ba. Su Iman kuwa, so biyu ina zuwa dubasu, nan na tarar yara sunyi kyau sunyi bul² kamar 'ya'yan turawa don Amayar Daddynsu na kula dasu kuma Tasi'u yanxu kudi ya zauna mai sosai don dakaga irin dukiyar da aka sama gidan kasan mai gidan ya jiku da naira, ko da naje nasamu tarban mutunci a wurinshi da kuma Amaryarshi mai suna Sumayya don har mukai exchanging din number sukace zasu ringa kawo mun su,aiko so biyu suna zuwa sumin yini ranar da ba makaranta. Gidan Alhaji ko so uku ina zuwa,wanda so biyu ya barni na shiga shima sai da nakai khaleel Gidan Aunty Asma'u,ana ukun ne yace indai bazan maida khaleel ba kar in kuma shigo min gida, haka nayita kuka tukunna nabar Gidan na koma Gidan Aunty Asma'u na kwana, washe gari kuma na koma kaduna, wanda ina zuwa kuma na tarar da abin tashin hankali, barayi sun shiga dakina sun dauke min keken dinki da naira dubu ashirin,take hankalina ya tashi haka akayita min jaje, faruwar haka na shiga cikin wani hali, wanda ya zamana komai sai an taimaka min dashi saboda rashin sana'a, yau da gobe sai Allah, ganin suma masu taimakona sun fara gajiy yasa na fara sa'kar hannu,ba laifi ina ciniki, da haka rayuwa taci gaba, yau da dadi gobe akasin haka. A lokacin dana cika shekara daya a Gidan granny,sai autan su Ammy yazo zaiyi aure, kuma dakin danake da dakinshi yakeso ya hadama Amaryarsa, hakan yasa na koma dakin Granny, kayan dakina kuma aka kai ajiya makota. Gani haka yasa na kira Ammy a kan maganarmu ta baya da tace zata yima Hajiyar Sokoto magana, shine tace in bari in hajiyar tazo bikin Yaya sadeeq da za ayi zata mata magana. Haka dai na cigaba da zama a gidan Granny cikin hakuri don ji na nakeyi a takure, don abinci ma sai an kawo ma Granny daga wurin 'ya'yanta sannan nake sami inci sabanin da kafin a sace mun keke girkina nakeyi daban. Anyi bikin Yaya sadeeq lfy,inda sai danayi danasanin zuwa don duk inda nabi su Aunty Mamy nuna ni suke suna ga bazawarar gidansu, washe garin bikin da sassafe nabar gidan don banason Alhaji ya ganni saboda baison nazoba. Biki da sati daya Yaya Arsala(dan Hajiyar Sokoto) ya kirani awaya yace in shirya in tafi sokoto, nan ko nayi ta murna don nasan ko ba komai zanci in koshi. *SOKOTO* kamar yanda na fadi Hajiyar sokoto yaya take wurin Alhaji su biyu kadai ne awurin Hajiya Kaka, farkon auranta tayine a Kudan inda ta haifi Yaya Kabeer(mijin Aunty Amina) daganan sai suka rabu da mijin tayi aure a sokoto ,mijinta shahararren mai kudi ne kuma mai sarauta,wanda a farkon auransu lagos a ka kaita saboda acan yake kasuwanci tana da yara takwas dashi, Aunty Atika,Yaya Arsala, Aunty huzaima, Aunty zainab, Aunty Aisha, Yaya Alamin(wanda Aunty zubaida ta aura kafin su rabu), Aunty shafa'atu da Aunty zuhura dukkansu sunyi aure sun hayayyafa don akalla hajiya nada jikoki hamsin da hudu, ban taba ganin family masu zumunci irinsuba dasu da 'ya'yansu kansu a hade yake, family ne da kowannensu yakeji da naira don duk cikinsu ba mai auran talaka, kuma kowanne business sukeyi sosai ba matan ba,ba mazan ba, hakan yasa kowa yake ji da kanshi a cikinsu. Mijin hajiya Alhaji sammani kafin ya mutu yabar dukiya da yawa bacin gidaje,da gonaki har kuma tsabar kudi, hajiya na zaune ne a Gidan Alhaji Arsala, don tunda ta gama aurarwa ya zamana ita kadai ce a gida,sai ya sai wani karamin fili dake gefen gidanshi ya gina mata 3bedroom flat,sai ya zamana in kinshigo gate din gidan part dinta na hannun dama na Yaya Arsala na hannun hagu dashi da matarshi da 'ya'yanshi shida biyu mata, hudu maza. Tunda nake ba a taba karramani irin yanda akamin a sokoto, ina zuwa na tarar da an waremin daki daya a part din hajiya an zuba min set din italian bed,ga plasma tv, Ac, center carpet da sauran kayan bedroom. Zamana a Sokoto,zama ne mai cike da FREEDOM inci,insha abunda nakeso duk wani jin dadin rayuwa na sameshi a sokoto nan danan ni da khaleel hasken mu ya fito muk kara wani kyau don duk wanda yasan mu shekara daya baya zuwa yanxu yasan mun canza, anan ma na cigaba da sakata ina samun kudin kashewa, banda wata damuw don ko duk Gidan mu daga Ammy sai 'yan dakinmu suka san ina Sokoto,don Yaya Arsala ne yace kar a fadama Alhaji don yasan zai iya hanani Zuwa. Watana you a Sokoto akayi karamar sallah,mun samu kaya dani da khaleel sosai, don ni ina da kala goma, khaleel na da shabiyu, don duk cikin 'ya'yan hajiya kowa sai da yamini kayan sallah,anyi sallah da kwana biyu sai ga Yaya Farooq yazo gaida Hajiya aiko nan yayita mamakin ganina, ni kuwa tsurewa nayi don nasan dole zai fada ma Alhaji. Anyi sallah da sati biyu na yaye khaleel,sannan na daukeshi na kaishi kaduna na mika ma ubansa daga nan na wuce zaria, ina zuwa Alhaji yace in wuce in bashi wuri in koma inda na fito tunda sanda yace in bar yaron banji maganarsa ba, sannan wai don na rainashi da munafunci irin na Ammy dani na dauki kafa na koma sokoto ba tare da mun sanar maiba haka ina kuka nabar gidan,don bakinciki ko Gidan Aunty Asma'u banjeba na wuce park na hau motar Sokoto. Tunda na dawo daga sokoto ko hajiya ta shiga gyarani don kullun addu'arta insamu miji anan inyi aure ko na samu kwanciyar hankali. Satina biyu da dawowa daga zaria sai ga Aunty zubaida tazo wadda kallo daya zaka mata kasan kwakwalwar tata da matsala,nan dai hajiya tayi ta neman mata magani don abin nata kamar asiri saboda wani zubin lafiya wani zubin cuta. Ana cikin hakane kuma kawu Muhammadu ya kirani yake sanar dani dakin da akasa kayana ya fadi,sundai kwashe kayan amma duk wasu sun fashe, dana sanar da Yaya Arsala sai yace in shirya in tafi in duba kayana, dazan wuce sai ya hadani da Aunty zubaida in kaita wurin mai magani da ya samu nan kaduna. Bayan naje na duba kayana wanda duk wani kayan kitchen dina da kujera sun lalace,kayan gado kawai na tsira dashi, daganan nan kuma muka nufi gurin mai magani da Aunty Zubaida. Bayan mai magani yayi mata tambayoyi yace mun aljanu aka turo mata,kuma ba shiganta sukayiba,shafenta sukeyi,sannan wani dan uwa na jikine yasa a tura mata, sannan makaryinsa sai dai a maida ma wanda ya turota........kakakarakara,asirin wasu ya kusa tonuwa. *Comment* *Like* *Vote* *Share* *Fateeyzah*✍ *© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION* *_(home of peace,joint of entertainment,to educate and enlighten our readers)_* *GIDAN NAGOGGO*🏨 *_(A true life story)_* *_Written by fateeyzah_*😍😍 *_Bismillahir rahmanir rahim_* *_Page4⃣1⃣to4⃣5⃣_* Daukar waya nayi na kira Yaya Arsala na sanar dashi abunda mai magani ya fadi, sai yace adai yimata magani amma kar ace za a maida ma wani tunda yace cikin 'yan uwane, anan dai malam yace maganin na sati biyu, hakan yasa Yaya Arsala yace in zauna harsai angama maganin sai mu dawo tare. Kwana na biyar a kaduna na shirya na tafi ganinsu Iman, tarba akamin ta mutunci kamar yanda aka saba, kuma naji dadin yanda sumayya take kula dasu especially khaleel dana ga ya zamo wani kato kuma ya dada wayo(rainan madara🤪), suma su Iman da ka gansu kasan suna jin dadin zaman gidan,nayi mamakin yanda yaron bai manta dani ba don yana ganina ya taho da gwarancinsa yana cewa yummy(mummy), wannan karan harta umma ta sakarmun fuska don haka tayi ta jana da hira, nan dai na basu chocolate din dana saimusu na dawo Gidan Granny cike da kewarsu. Washe garin ranar da naje wurinsu Iman sai ga kiran Tasi'u, ina dauka muka gaisa yake tambayara ashe nazo kaduna, nace mai kwanana shida kenan, nan dai yayi ta jana da surutu, tun ina biye mai har na gaji nayi mashi sallama. Bayan kwana uku,ranar na tashi da kewar yarana , hakan yasa na daidaici lokacin tashinsu break na shirya na tafi school dinsu, nan dai na gansu mukayita hira tare da daukar hoto, harsai da aka kada bell na komawa class tunkunna nabarsu suna daga min hannu,nima ina daga musu. _(😭😭 rabuwar aure wallahi bata da dadi,especially in akwai yara a tsakani,sai yara su taso kamar marayu gasu dai suna da iyaye duka,amma rashin iyayen a wuri daya matsala ne duk yanda wata zata kula miki da 'ya'ya ba kamar yanda ke zaki kula dasu ki basu tarbiyya ba,inma aka hadu da mai rikon mara kirki sai tayi ta azabtar da yaran, amma kuma wani auren rabuwarshi shinr maslaha kamar wannan na Bahijjah mai cika da matsaloli wanda har takai babu ganin girma da mutunci tsakaninsu, Allah ya tsare ya kara dangana, hakuri da soyayyya tsakanin ma'aurata ya shiya mana 'ya'yanmu,shiriya ta tafarkin addinin musulunci,Ameen)_ Ina tafiya ina kokarin maida kwallar dake shirin futowa,kiran sunana da akayine yasa ni saurin juyowa,Yaya Mahmood na gani(yaya Mahmood cousins yake wurina, amma dangantakarsu tafi kusa da Tasi'u), nan dai na karasa muka gaisa sannan ya tambayeni hala su Iman nazo gani na amsamai da eh,nan dai yayi tamin fada na zubar da zumunci tunda na rabu da Tasi'u ko kira banayi a gaisa nan dai nayi ta kawo excuses, sannan muka yi sallama muka rabu. _(Haka mutane suke,su suke zubar da zumunci amma insun ganka suyita borin kunya wai bakason zumunci🤔)_ Bayan kwana biyu, ina zaune ina shafa ma Aunty Zubaida magani, kawai sai ga kiran Alhaji ya shigo wayata, take gabana ya yanke ya fadi, don nidai a wurina kiran Alhaji ba Alkhairi bane a wurina, sai da wayar ta kusa katsewa tukunna na dauka cikin rawar na dauka tare da karawa a kunne hade da sallama, ya amsa sallamar tawa tare da fadin "uban mai ya kaiki kaduna?" yayi mini tambayar hade da hargagi. Cikin rawar baki nace"naje kai Aunty Zubaida wurin mai magani ne daga nan kuma na duba kayana da akace ginin dakin ya fadi" Cikin daga murya yace"Bahijjah yaushe kika fara karya?, kuma karyar ma kirasa wa zakiyi mawa sai ni" Cikin sanyin jiki nace" wallahi Alhaji ba karya namaka ba,kafi kowa sanin ko yankani za'ayi indai na........"bai bari na karasa maganaba ya yanke kiran. Haka ranar na wuni suku²,don duk iya tunani na na kasa tuna laifin dana yi ma Alhaji. An gama yima Aunty Zubaida magani,inda abin nata yadanyi sauki, kwana biyu muka kara muka kama hanyar Sokoto. Bayan mun huta tukunna Hajiya da Yaya Arsala suka kirani palour,jin kiran sai da gabana ya fadi don nasan ba lafiya ba, ina zuwa yay Arsala ya fara magana cikin bacin rai"Bahijjah kinsan maganganu da tijara da kika jama na cikin dangi kuwa?". Jikina na karkarwa nace "A'ah". Yace"maganganu nata yawo cikin dangi akan kinje kin samu Tasi'u kina kuka akan ya maida ke dakinki, hakan yasa yace muki bazai maida kiba don Allah yace inkin koma bashi bake, Amma wai sai kikayi hugging dinshi kika ce wai ya maida ke zaki zauna dashi yabar maganar Alhaji,shine yanxu muka kiraki muji gaskiyar magana don na kasa gasgata haka". Cikin matukar razana na zayyane musu abunda ya faru, ina fadi ina kuka,don tunda nake ba'a taba mun irin wannan sharrinba. Take Yaya Arsala ya kira Alhaji ya zayyane mai abunda ya faru, nan Alhaji yace abar maganar zai zo da babbar sallah. Anyi sallah da kwana biyu su Alhaji suka zo Sokoto, bayan sun ci abinci sun huta aka fara meeting wanda duk akaina akayisa,nan dai aka maida magana akamana sulhu da Alhaji(dani da Aunty Zubaida)nan dai Alhaji yace ya hakura sannan yace kowa ya zama shaida ko bayan ransa na koma Gidan Tasi'u bai yafemun ba. Kwanan su biyu tukunna yace mu shirya yatafi damu don canma zaria meeting din zamuje muyi. A ranar da muka dawo ba karamin farinciki na tsinci kaina ba saboda ko ba komai ranar na shiga gidan Alhaji batare daya koreni ba, kwana mukayi muna hira da Ammy don rabon da mu zauna muyi hira batare da wata fargaba ba shekara goma kenan. Washe gari,Alhaji ya hada meeting wanda duk wani dan gidan sai daya halatta, nan dai Alhaji yayi mana nasiha tare da nuna mana muhimmancin zumunci, da alama dai mazan jikunansu sunyi sanyi don har gafarar Ammy suka roka sabanin matan da sai wani cika suke yi suna batsewa. Satina daya a zaria na fara shirin komawa Sokoto,ba yadda Ammy bata yi daniba akan in bari akwai buki a gidan Aunty jummai dake katsina(kanwar Alhaji dasuke uba daya ita zata aurar da danta)amma naki,don gaba daya dan zaman gidan da nayi naji zaria ta fitarmun a rai,haka na shirya kayana na koma Sokoto. Daga nan Sokoto ma Aunty shafa ce kadai taje bikin, itama kwananta biyu ta dawo. Ina kwance da dadddare sai ga kira ya shigo wayata,ganin number ba suna yasa naki daga wayar, sai da aka kira so uku tukunna nayi picking, muryar babban magidancine ya bugu kunnena, jin hakan yasa na gaisheshi cikin girmamawa, bayan mun gaisa tukunna yayi gyaren muya tare da fadin"Bahijjah nasan baki gane mai magana ba,sunana Alhaji Suleiman,ina zaune ne a garin kano,inada mata biyu da yara hudu, ban taba ganinkiba amma na karfi number ki a wurin kawunki ne Alqasim da yake kano, abunda ya faru shina naje biki katsina ne kasancewa Mamar Aunty Jummai kanwa take a wurin babana,to anan naga 'ya'yanki kakarsu taje da su bikin,to gaskiya yaron sun bani sha'awa anan na tambayi Aunty umma(kanwar Aunty Jummai) yaron waye,anan dai ta bani labarin ki da abunda ya faru dake ba,gaskiya anan naji na kamu da sonki, ban yi nauyin bakiba na fada mata ina sonki, anan dai ta fada ma Alqasim da mijinta sabitu kasancewa sabitun yaya nane uban mu daya, shine sai Alqasim ya bani numberki"ya karashe magana cikin sanyi murya. Nan na rasa bakin magana don jin maganarshi nayi kamar saukar aradu,sai da yayi gyaran murya sannan na dawo daga guntun tunanin da na tafi tare da cewa"ya za ayi baka ganniba amma kace kan sona?, don kaga 'ya'yana bai zama hujjar daza ka amince dani ba. Ajiyar zuciya yayi tare da fadin"ina nan zuwa Sokoto sati mai zuwa saboda akwai wani abokina senator dazai kara aure, in nazo zan karaso wurinki". Hmm ya kuke ganin,don da alama Bahijjah ta samo babban fish,abokin senator fa🤔. Sorry for the errors ban yi editing ba. *Comment* *Like* *Vote* *Share* *_Fateeyzah_* ✍ [4/17, 12:47 AM] ~Fateeyzah✍✍: *© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION* *_(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)_* *GIDAN NAGOGGO*🏨 *_(A true life story)_* *_Written by fateeyzah_*😍😍 *_Bismillahir rahmanir rahim_* *_Page4⃣6⃣to5⃣0⃣_* Haka dai mukayi sallama dashi, yabarni inata sake² don ban dauki maganarshi da wani muhimmanci ba,don a ganina daga gani 'ya'yana kawai batare da ya ganniba sai yace yana sona. Washe gari kuma sai ga Aunty Umma ta kirani,bayan mun gaisa again dai maganar Suleiman tayi mini,tare da gargadina kar in basu kunya don suna son nuna ma Tasi'u da magoya bayanshi nafi karfinshi da har zai min sharri wai naje ina kuka ya maidani, bayan mun gama magana da ita ta umurceni da in kaima Hajiya wayar, nan dai nakai ma Hajiya wayar, bansan yanda suka Kare ba ,don ina bata wayar na juyo dakina ita kuma Hajiyar bata cemin komai ba. Tunda ga ranar Suleiman kullun sai ya kirani so hudu, tun ban saki jiki da shiba,har nazo na yi,Suleiman namijine da ya iya tattali don yadda yake nuna min so bazakiyi tunanin ya ajiye mata biyu ba har da yara hudu. A cikin satin nan nayi wani irin sabo dashi, wanda nake ji kamar mun yi shekaru tare, don wani irin zafaffan so nake masa wanda nima bansan lokacin daya shigeni ba, don a wannan lokacin na tabbatar da son dana yima Tasi'u kadan ne akan wanda nake yi ma Suleiman. Week na zagayowa kamar yanda yayi alkawari sai gashi yazo,kallo daya zaka masa kasan akwai 'yan gidan rana(naira),wanda yasha shaddar shi gezna sai kyalli takeyi,chocolate color ne gashi giant,duk inda ake neman namiji, Suleiman yakai har ya wuce, nan dai na sauke shi a falon hajiya sannan na fara kawo mai su snacks da abinci dana tanada donshi,sai daya cika cikinsa sannan ya shiga ya gaida hajiya da Aunty suwaiba(matar yaya Arsala)sannan muka dawo parlour muka dasa hira, duk da yawancin hirar shi yakeyi don ni daga eh sai a'ah. A dan zaman da mukayi na fahimci Suleiman mutum ne mai saukin kai, ga sanin ya kamata nan dai ya tabbatar mun shifa da gaske yake,don in so samune in aka tashi saka rana a saka wata daya, haka dai mukayi ta hira har Yaya Arsala ya dawo suka gaisa nan ya sanar da Yaya Arsala yanaso ya turo iyayensa amma kafin nan yanaso inje inyi HIV da Genotypes test nan dai nan dai Yaya Arsala ya amsa mai da zanyi kuma shima yanaso yayi bincik, inyaso in ya kammala ya turashi wurin Alhaji, anan dai sukayi sallama dashi. Dawo wa gurina yayi mukayi sallam, ya kirgo 30k ya bani tare da fadin ga kudin hira Kya sa kati, nan dai nayi godiya tukunna namai rakiya ya tafi don jirgin karfe hudu zai bi zuwa kano. Bayan sati daya naje nayo test inda result ya fito HIV Negative, Genotypes kuma AA, nan nayi snapping na tura masa shima ya turo min nashi wanda the same thing ne da nawa. Bayan sati biyu yaya Arsala ya gama bincike sannan ya kira Alhaji ya sanar dashi nan dai Alhaji yace ya waliyi na, amma aje Kudan a daura aure, nan dai ya tsayar da ranar sati biyar. Suleiman dubu dari uku ya bani in hada lefe, sannan danace mai zanje kaduna in gyara kayana ya bani dubu hamsin(wanda nayi karya nacema Yaya Baffa dubu goma ne)naki fada mai gaskiyane sabodah nasan sai ya fada ma su Aunty Amina. Bayan nanne ya zamana in nakira Alhaji bai daukar wayata,ni kuma danaga baya dauka sai na dena kiransa. Biki yana sauran sati uku shine na shiryo don in gyara kayana,wanda na biya gidan Alhaji yayi mini koron kare batare da nasan abunda nayi masa ba. *BACK TO STORY* Nauyayyar ajiyar zuciya na saki yare da goge hawayen dake idona, jin an tada kiran sallar magariba ne yasa na mike da sauki na fito,a kofar daki na taradda Granny na alwala kallona tayi tare da fadin "sannu hakima,sai yanxu kika tashi daga baccin asara, ai da niyata inna gama alwala inje in tashe ki da ruwan sanyi"ta karashe magana tana miko min butar hannunta. Karfa butar nayi yare da fadin"ni ba bacci nayiba,tunanin rayuwar gidanmu nayi". Tabe fuska granny tayi tare da fadin"rayuwar gidanku har abin tunawa ce, ai wannan mai hancin kamar biro itace matsalar gidanku,amma da *NAGOGGO* zai gane daya bincike rayuwar gidanshi"ta karashe magana tana shiga daki. Inayi sallah isha'i naci abinci nayi shirin bacci na haye gadon Granny na kwanta,kamar jira yake sai ga kiran Suleiman, nan dai muka gaisa sannan yake cewa "wai darling har yau baki tambaye ni inda zan ijiyeki". Lumshe ido nayi tare da fadin"indai zan zauna tare da kai, ko daji ka ajiyeni ba damu wata bane" Murmushi yayi tare da fadin"wannan dadadan kalaman naki,shi yasa nake karaa sonki, Bahijjah zan hadaku keda matata ta biyune kasancewa no wacce cikin matana gidanta daban, to ke kinga yanda aurenmu yazo a kurarran lokaci babu time din gina miki naki gidan amma insha Allah kema zan miki naki daban, sannan kinyinmu babban laifii,hakan kuma yaja na fara tunani baki damu da lamarinaba" Bakina na rawa kuma cikin sigar shagwaba nace"haba sweetheart me nayi maka,don Allah kayi hakuri". Cikin sanyin murya yace"duk lokacin da muka dauka tare baki taba tambayata sana'ata ba kuma nasan baki sani ba" A kunyace nace"sorry sweetheart, amma ni a tunanina tun ran farko da muka hadu kai ya kamata ka sanar dani". "Gaskiya ne abunda kika fada gimbiyaata,to nidai sana'ata itace siyar da GOLD". Cikin jin kunya nace"Allah sarki,Allah ya bada sa'a". Haka dai muka cigaba da hirar mu sai wurin goma muka yi sallama. Ina shirin kwanciya kuma sai ga text ya shigo,ina dubawa sai na ga number Tasi'u ne cikin sauri na bude sai gani nayi ya rubutu _wallahi_ _Bahijjah baki isa kiyi aure ba indai ina raye,ba wani dan akuya daya isa ya shigarmun gonata,dan haka mu zuba ni dake shege ka fasa._ Wallahi nayi nan kafin 'yan Bahijjah team su fasa ma Tasi'u kai,azo ace dani a ciki💪🏃‍♀️🏃‍♀️. *Comment* *Like* *Vote* *Share* *_Fateeyzah_*✍ [4/18, 8:00 PM] ~Fateeyzah✍✍: *© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION* *_(home of peace, joint of entertainment and to educate and enlighten our readers)_* *GIDAN NAGOGGO*🏨 *_(A true life story)_* *_Written by fateeyzah_*😍😍 *_Bismillahir rahmanir rahim_* *_Page5⃣1⃣to5⃣5⃣_* Ina gama karanta text din shi na tuntsire da dariya 🤣🤣don a tunani na sanda Tasi'u yayi typing din text din kamar kwakwalwarshi ta juya, ban tsaya wani tunani ba na kashe wayata na kwanta don na riga na fitar da Tasi'u da duk wata matsalarshi a raina, don a yanxu na riga nayi mai nisa,yarana kuma kullun bana fashin addu'a akansu, Allah ya rayasu, ya shiryasu a tafarkin addinin musulunci. Washe gari da safe, wurin karfe goma na bude inda aka ajiye kayana,duk kayan sun lalace duk gara ta cisu,kallonsu nake nama rasa ta inda zan fara,shawara kawai na yanke a zuciyata akan kudin da Suleiman ya bani na lefe inyi amfani dashi in canza gado,saboda yaya Arsala shi yace zai mun kujeru, ina tsaye inata tsake² sai ga kiran Aunty Aisha a wayata, bayan na dauka muka gaisa take cemun inbar gyaran gadon don sunyi magana da yaya Al'amin zai canza min gado,nan naji wani farin ciki ya lullubeni, tsakanina da 'ya'yan Hajiyar Sokoto sai dai addu'a don sunyi mini abunda ko wadanda muke uba daya sun kasa yiminshi, nan dai na koma na sanar da Granny, ita ma tayi murna tare da sa musu Albarka. Haka na kira Aunty Asma'u na sanar da ita, sannan nakira Ammy, bayan na sanar da ita itama ta tayani murna sannan tace "Bahijjah Baffa yazo ya bama Alhaji hakuri, ya amsa ya hakura, amma yau da safe yace min ince miki kafin ki wuce Sokoto ki biyo ta zaria yana nemanki". Cikin rikicewa nace "Ammy Mai kuma nayi?" Ta amsa da"nima bansani ba,abinda dai yace kenan" Cikin sanyin jiki na sanar da ita text din da Tasi'u yamin, nan dai Ammy ta kuma kwantarmun da hankali tare da nuna min in dogara da Allah ba abunda ya isa yamun. Kamar jiya,yauma bayan nagama waya da Suleiman sai ga text din Tasi'u, ina budewa sai naga ya rubuta: _(Bahijjah don ke aka yini,haka nima don ni aka yiki, don Allah Bahijjah karki aure wannan jakin mutumin, na miki alkawarin zan maida ke dakinki tare da Alkawarin rayuwa mai inganci, rayuwa ta jin dadi, ki taimaka ki dawo ki rungumi yaranki)._ Wannan karan text dinshi ya daga mun hankali tare da tambayar kaina wai mai Tasi'u yake nema a gurina, duk abinda yayi min bai isheshi ba sai ya kuma dasa mun wani bakin cikin, ganin bani da mai ban amsar tambayata yasa na kwanta, wanda sai wurin karfe biyun dare bacci ya daukeni. Sha biyu dai² na shiga Gidan Alhaji wanda direct palourn shi na wuce, nan na tarar da shi da Ummy a parlourn,bayan na zauna muka gaisa, duk suka amsamin fuska ba yabo ba fallasa, take jikina yayi sanyi, don dama zuciyata tun jiya take bani akwai wani abu da ya faru, daukar waya yayu ya kara a kunne, an sai da yayi kamar sakon biyar tukunna yace kisa meni a parlour. Bayan mintina kadan sai ga Ammy ta shigo da sallama, samun wuri tayi ta zauna tare da fadin"sannuku da hutawa". Umm Ummy ce kawai ta amsa sabanin Alhaji da daga kai kawai yayi tare da gyaran murya" Abinda yasa na taraku shine jiya da daddare ina zaune a parlour nan sai ga sarki da Tasi'u sunzo, bayan mun gaisa da sarki shine ya fadamin musassbabin zuwanshi wai Tasi'u ne yaje yana tamai kuka akan shi baisan sanda ya saki Bahijjah ba, a taimaka a dawo mai da matarsa yana sonta, jin abinda sarki ya fadine ya tunzurani nafara fad'a amma kuma sai ya dakatar dani akan mu tsaya mu saurareshi, nan dai Tasi'u yafara bamu labari wai yaje karatu da akeyi ne tsakanin magariba da isha'i sai malamun yafara karatu akan sihiri, daganan sai yafara karanto ayoyin da suke karya sihirin, wai daganan sai kanshi ya fara juyamai, daganan baisan inda kanshi yakeba, sai farkawa yayi ya ganshi a kwance a gaban malamin daga nanne kuma malamin ya fada mai abunda ya faru wai Aljanu aka turo mai amma sun samu su fitar dasu, sannan ya fadamai Aljannun sunce turo su akayi su shiga jikinsa don su raba aurenku, wanda ke ma akwai asirin a jikinki wanda zaisa Tasi'u ya tsane ki, daga karshe dai har kuka rabu, sannan zaman da sukayi a jikinsa sun taba masha kwayoyinsa na haihuwa" Alhaji ya karashe magana hade da goge zufar da ta tsattsafo mai. Dukkanmu damuke parlourn kasa magana mukayi, sai zufa datake ta tsattsafo mana, ni kuwa har da wani firgice daya shigeni. Alhaji ne ya ci gaba da cewa"malamin yace akai Bahijjah don yayi mata rukiyya,sannan ko za a samu na jikinta su fadi wanda yayi musu wannan aikin". Take Ummy ta zaro ido,zufa nata keto mata. Pls manage Not edited *Comment* *Like* *Vote* *Share* *Fateeyzah*✍ *© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION* *(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)* *GIDAN NAGOGGO*🏨 *_(A true life story)_* *_Written by fateeyzah_*😍😍 *_I dedicated this novel to my late father(Alh Babangida N.T.C)who die on 23rd August 2014, may his soul rest in peace._* *_Bismillahir rahmanir rahim_* *_Page5⃣6⃣to6⃣0⃣_* Cikin kidima Ummy tace "yanxu in aka yi rukiyyar zasu fadi wanda ya turo su". Cikin mamakin tambayar ta yasa gaba daya muka kalleta, lura da tayi hankalinmu ya koma kanta ne yasa tayi saurin cewa"Allah ya baki lafiya Bahijjah,Allah ya saka muki", gaba dayan mu muka amsa da "Ameen" Alhajine ne ya mike hade da fadin" Amina sai ki shirya kayan ki kema don gobe in Tasi'u yazo dake zamu tafi, daga nan sai ki dan kwana biyu wurin Goggo tunda kin dau lokaci bakije ba" Cike da murna Ammy ta amsa da "nagode Alhaji,Allah ya kara tsahon shekaru". Amsa wa yayi da "Amin"sannan ya shige bedroom dinshi. Nan muka tashi muka bar Ummy wanda tayi nisa cikin tunani don bata san sanda muka fita ba. Yini ranar hirar mukayi tayi da Ammy, wanda yawancinta ta bata gidanmu ce kawai ba har da ta matsalolin family dinmu gaba daya, duk yanda naso Ammy ta tsaya muyi magana akan aljanun da akace an turo min da asirin da aka yomin taki, don dana kawo maganar take Zamora wanda bansan dalili ba. Wayewar ranar bakwai tayi ma Tasi'u a gidanmu bayan gaishe² muka kama hanya wanda Tasi'u ne ke driving, sai Alhaji a gefenshi, sannan nida Ammy a baya,don Alhaji ya hana a sanar da sauran yaran Gidan, saboda yace a bari dai muje mu dawo, yana ta satar kallona ta mirror, damun hada ido sai ya dauke kai don na lura yanxu Tasi'u kamar kunya ta yake. Muna isa kaduna, direct gidan malamin dake Malali muka wuce, bayan mun isa, Tasi'u ya kira malamin a waya don neman iso, muna tsaye sai gashi ya fito, bayan mun gaisa yayi mana iso cikin gida inda ya sauke mu a wani Babban parlour da aka lailayeshi da brown carpet sai wata cabinet a wata kusurwa dake shake da manyan Qur'anai da sauran littafan Addini. Bayan mun zauna Tasi'u ya yi masa bayani kamar haka"Allah ya gafarta malam wannan ce tsohuwar matata da muka yi magana dakai kwana uku da suka wuce, wadannan kuma iyayentane" ya karasa magana yana nuna Alhaji da Ammy. Sai da malam ya kalleni for some minutes, sannan ya maida kallonsa kan Ammy daga bisani yayi gyaran murya tare da cewa" Alhaji da Tasi'u ina tunanin zaku dan bamu waje" yayi magana yana kallonsu. Nan dai Alhaji ya amsa mai da"toh,babu damuwa" Bayan fitarsu Alhaji, malam ya umurceni da inbashi tarihin aurena da Tasi'u, aiko nan na fara bashi wanda kafin in gama na wanke fuskata da hawaye wanda Ammy take tayani. Gyara zama yayi tare da fadin" gaskiya zan fada muku kuna da matsala dukkanku,don ke(ya nuna Ammy da yatsa) dadadden asiri ne a jikinki wanda karya shi lokaci daya zai yi wuya, sanna ke (ya nuno ni da yatsa)Aljana ne aka turo miki kamar yanda aka turo ma Tasi'u wanda shi harda Asiri aka hada mai wanda kuma asirin yafi tasiri a jikinshi, sakamakon rashin maida hankali akan ibada da azkar, bayan na karya asiri jikinshi ne na mai rukiyya inda Aljananin yake sanar dani dashi data jikinki tare aka turo su, kasancewa shi ya tsani aljanar jikinki ita kuma tana sonshi, wannan ne yasa aka turashi jikin Tasi'u don yasa mai kiyayyarki acikin zuciya, wannan ne yayi musabbabin rabuwar ku wanda kuma Allah yasa zaman aurenku ya kare". Kafin ya gama maganar nan gaba daya hawaye ya wanke mana fuska, Ammy ce tayi karfin halin cewa" Allah gafarta malam, ko sun fadi wanda ya turo su" "Tabbas shi Aljanin ya fadi uwar gidankine ta turo su, naki fadama Tasi'u ne saboda na fison in gama yi ma ita Bahijjah rukiya itama, don ko asirin da ke jikinki ita tayi shi"ya karashe magana yana nuno Ammy. Cikin kidima muka hada baki muna salati,sai da muka kwashi mintina sannan Ammy tabude baki tace"don Allah malam ina neman wata alfarma na karka fada ma Alhaji ko Tasi'u wanda yayi wannan abun don nasan wannan maganar ba karamin tashin alkali zata jaba, ni na barta da Allah, Allah ya saka mana, don insha Allahu da sannu zata girbe abinda ta shuka". Malam ya amsa"da insha Allahu baza suji wannan maganar ba,wannan dalilin ne yasa nace su bamu wuri, don na saba samun irin wannan case din naku, yanxu ke zan hada miki magunguna da ruwan magarya, indai kina amfani dashi da izinin Allah komai zai warware, sannan ke Bahijjah zamu miki rukiyya kema insha Allahu komai zai daidaita, yanxu bari in kirasu su shigo ayi a gabansu"ya karashe magana ya na kokarin tashi". Bayan su Alhaji sun shigo ya nuna musu toilet din dake parlourn a kan su shiga su dauro Alwala, da ya bayan daya mukayo Alwala,sannan malam ya ibi wani ruwa daga cikin wata jarka ya watsa min akai, sannan ya bama Ammy wani turare ta shaka mun, tunda ta shakamun bansan inda kaina yake ba. Wurin la'asar na tashi na ganni akan gadon Granny, kokarin tashi nayi amma na kasa don jinayi duk jikina kamar an mini duka, jin muryar Ammy da nayi daga falo yasa na fara kwala mata kira" Ammy, Ammy". Cikin hanzari ta shigo dakin Granny na biye da ita, kokarin tada ni tayi tare da fadin "sannu Bahijjah, Goggo dan Allah miko min maganin da malam yace inta tashi a shafa mata" Cikin sauri Grand ta fita sai gashi ta dawo da wata kwalba ta mikia ma Ammy, karfa tayi ta shafa mun tare da jero mun sannu, bayan ta shafamun da kusan minti biyar sai gashi inata zufa daganan kuma sai naji jikina ya canza take naji wani karfi yazo min, ganin haka yasa fara'ar fuskar Ammy ta karu. Kwana biyu na kara a kaduna sannan na shirya komawa saboda inaso in biya zaria in kwana daya kafin in wuce sokoto, kafin in tafi sai da Ammy ta kuma jamin kunne akan kar in sake ko Aunty Asma'u in fada mata abinda ya faru. Bayan na kuma warwarewa nasamu nayi wanka hade da rama sallolin da ake bina. Ina sauka a zaria direct gidan Alhaji na nufa,wanda bayan gaishe², Alhaji ya nemi ganina cikin sirri a bedroom nashi, bayan na shiga na samu wuri na zauna tukunna ya gyaran murya yace"abunda yasa nace ina son ganinki ba komai bane illa in nemi yafiyarki akan abubuwan dana yi muki, hakika Bahijjah ban miki adalci a matsayina na mahaifinki don nasan na cutar dake, so da yawa sai nayi miki abu amma daga baya kuma sai abin ya zo ya dameni, Amma daga yanxu insha Allahu kin dena zubar da hawaye saboda ni" ya karashe magana cikin sanyin murya. Cikin karayar zuciya wanda duk wanda yaji muryata yasan dauriya kawai nake nace" na yafe maka Alhaji,amma nima don Allah ina neman yafiyarka, don nima na saba maka na tsallake duk wata magana taka". Yace"Bahijjah ba komai Allah ya yafe mana gaba daya, abu na gaba kuma shine Tasi'u yazo mini da wata magana akan yanaso a maida auranku, to amma sai na nuna masa yanxu haka da sa ranar wani akanki, to dayake a gaban sarki mukayi sai yace a bari aji ta bakinki ,in zaki koma gidan Tasi'u ne ki rike yaranki sai aba ma shi Suleiman hakuri, inkuma Suleiman din kika zaba shi kenan don dai wannan karan bazan miki doleba kamar wancan karan". To Bahijjah fans sai ku zabar mata miji a karo na biyu tunda Alhaji ya baku zabi😍. Ina Suleiman fans banda son kai,haka kuma Tasi'u fans. Insha Allah saura page daya na gama novel dinnan saboda azumi ya gabato. *Comment* *Like* *Vote* *Share* *_Fateeyzah_*✍ *© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION* *_(home of peace,joint of entertainment,to educate and enlighten our readers)_* *GIDAN NAGOGGO*🏨 *_(A true life story)_* *_Written by fateeyzah_*😍😍 *_Page 6⃣1⃣to7️⃣0⃣_* Cikin tsarkewar murya nace"don Allah Alhaji kayi hakuri da abinda zan fadi, na zabi auran Suleiman akan komawa Gidan Daddynsu Iman, don ko na koma zan ringa kallonshi da irin wulakancin da yamun duk da ba a hayyacinsa yayi ba, sannan su Iman sunyi dace da uwar riko, don nasan sumayya na kula dasu dai² gwargwado". (Lol🤪 duk kun bude kunne kuji zabin Bahijjah, to dai ta zabi naku nikuma ta ajiye nawa my Tasi'u😢😢). Cikin sanyin jiki Alhaji yace"Allah yasa haka shi yafi zama Alkhairi, su kuma yaran Allah ya shiryasu". Cikin jin kunya na amsa da"Amin". "Ina zuwa Bahijjah"Alhaji ya fada tare da mikewa ya nufi drawer da ke dakin, bayan 'yan mintoci kuma ya nufo ni da kudi a hannushi, mika min yayi tare da fadin" Bahijjah ga gudunmawata nan a matsayina na mahaifinki, kije ki sayi abinda baki da dashi, sannan zan kira 'yan sokoto in musu godiya don Ammynki ta fada mun sunyi miki kayan daki". Cike da murna na karfa tare da fadin "nagode Alhaji, Allah yasaka da alkhairi ya kara girma. Fuskarshi cike da fara'a yace "Amin Bahijjah,Allah yayi miki albarka, yaushe zaki wuce Sokoto?" Ina mirmushi nace" Amin Alhaji, gobe zan wuce". Ya mike tare da fadin" Allah shi kaimu,bari in tafi masallaci naji an fara kira" ya karashe magana yana fita. Bayan nabar dakin Alhaji, Gidan Aunty Asma'u na wuce don magana nacina na kosa inje in fada mata yanda mukayi da Alhaji, da sallama na shiga Gidan, da gudu Aunty Asma'u tazo ta hugging dina tare da fadin" wallahi yanxu nake zuci² kiranki" ta fadi fuskarta cike da fara'a. Nace" gani nan nazo ai, nima bakina cike yake da magana, wallahi Aunty Asma'u yau ji nake kamar an mini kyautar Aljanna, wai yau ni Alhaji ya nemi yafiyata har da samun Albarka, wanda tun dana taso nayi Wayau ban taba jin wata kalma mai dadi da Alhaji ya jefeni da ita ba" na karashe magana cikin zubar da wasu zafaffun hawaye. Idon Aunty Asma'u cike da kwalla tace" Bahijjah ba kuka zamuyi ba, godewa Allah zamuyi don nima jiya Alhaji har gidan nan yazo ya nemi yafiyarmu nida baban Amira, Ammy ma tace ya nemi yafiyarta, kinga wannan babban ni'ima ce daga Allah". Nan dai na nuna mata kudin da Alhaji ya bani, itama tayi ta murna tare da yima Alhaji addu'a sannan tace zata kirashi Tayi masa godiya koda muka irga kudin naira dubu hamsin muka gani. Nan dai na taya ta mukayi girki sannan na mata sallama na nufi Gidan Yaya Baffa. Bayan gaishe gaishe, yaya Baffa ya kawo dubu dari biyu ya bani yace ga gudummawar da suka hadamun nan, cikin farin ciki na masa godiya sannan yamana sallama nida Aunty Hanna ya fita. Bayan fitarsa kuma muka dasa hira da Aunty hanna inda take fadinmin wai su Aunty Amina sunce bazasu bada komai ba da sunan gudun mawa, tunda ai farko sunyi meeting akan bazasu bani komai ba, amma Yaya Baffa yaje matarshi ta zugo shi don haka bazasu bada komai ba. Cike da mamaki nace "yanzu to dubu dari biyun nan wa ya bada" Gyaran murya tayi tare da fadin"Farooq yabada dubu hamsin,sai honey yabada dari, sauran dubu hamsin din Kuma da Asma'u,fatima da halima suka bada, sai matar Ibrahim da ta Baki food flask, zeena ta baki tukunya, sannan fatima ta kara miki da bedsheets". Fuskata dauke da murmushi nace"Allah ya saka musu da Alkhairi ya kara budi, kinga can ma Yaya Arsala ya yimini gado, yaya Al'amin kuma kujeru". "Ai na ma mantane ban miki murna ba don honey ya fada mini, su Aunty Amina su kuma na lura bakin ciki ke damunsu" ta karashe magana fuskarta cike da damuwa. Nace"su suka sani, ni yanxu banda lokacinsu" Nan dai muka shigaba da hira,da natashi tafiya ta hado mun kayan dana samu gudun mawa, sannan ta bani zanin gadon data saimuni. Ina komawa, direct parlourn Alhaji na wuce na nuna masa kayan da kudin, nan yayi ta sa Albarka, sannan yace in nuna ma Ummy ta gani na ansa mai da toh, amma ban nuna mata don Aunty Hanna tayi mini kashedin kar in sake in nuna mata don zanja ma wadanda suka bani magana. Dakin Ammy na shiga na ajiye kayan sannan na nufi gidan Yaya Ibrahim don inma matarshi godiya, daga nan na shiga Gidan yaya sadeeq muka gaisa da matarshi , itama da zan fito ta bani wani jug hade da cups dinshi, daga nan nayi wurin Aunty zeena. Ina shiga nayi kicibus da Aunty Amina zata fita ko kallonta ban yiba na wuce ta, ita kuma ta bini da tsaki. Aunty Zeena da murna ta tare ni tare da fadin "maman Iman kece". Na amsa"da nice Aunty zeena" nan dai muka gaisa tare da mata godiyar tukunyar da tabani. "Bahijjah ba godiya tsakanin mu,ke dai Allah sanya Alkhairi ya bada zaman lafiya"cewar Aunty zeena. Nace"amin, dama inaso in karbi number Yaya Farooq in mai godiya kudin daya bada". Aunty Zeena ta gyara zama tare da fadin"Bahijjah kar kiji komai, kuma dama yace in neman mai yafiyarki akan abubuwan daya miki a can baya, don wai kunyarki yake ji, shi yasa bai kiraki ba". Nace "ba komai Aunty, zan kira shi" Nan dai muka dan taba hira, sannan na karfi number Yaya Farooq na kuma komawa Gidan Aunty Asma'u, wanda ban dawo gidan Alhaji ba sai dare, na leka dakin Alhaji na masa sai da safe, daganan kuma na leka wurinsu Aliyu sannan na wuce dakin Ammy ko kallon part din Ummy ban yiba don har ga Allah ba karamun tsanarta nake ji a raina ba. Ina gama waya da Suleiman bacci ya daukeni saboda ba karamin gajiya nayiba yau, da safe ma sai dana makara don banyi sallar asuba ba sai karfe shidda da rabi, wurin karfe takwas na gama shirya wa, sannan na dauki wayata na kira Ammy, tana dauka nace" Asslamu alaikum, Ammy ina kwana?" Daga can bangaren Ammy ta amsa da"wa'alaikumussalam, lfy lau bahijja badai har kin shirya ba". Na amsa da na shiya, amma sai karfe goma zan wuce, dama nakira ne in fada miki yaya Baffa ya bani dubu dari biyu gudunmawar da suka tara, Alhaji kuma ya bani dubu hamsin, Aunty Hanna bedsheet, Aunty zeena tukunya, Aunty Rukayya food flask sai matar yaya sadeek da ta bani jug, sannan Aunty Fatima ta bani bedsheets". Ammy cikin murna tace "Alhamdulillah Bahijjah kinga riban hakuri ko?, ubangiji Allah ya saka musu da Alkhairi ya kuma hada kanku, ya kareku daga sharrin makiya". Cikin jin dadi na amsa da "Amin Ammy", nan dai mukayi sallama na kashe wayana. Haka na kira Yaya Farooq,Aunty Fatima da Halima na yi musu godiya. Wurin karfe takwas sai ga breakfast Ummy ta aiko salma dashi(first in history), karfa nayi tare da godiya, ina ganin fitarta na samu leda baka na zuba nasa a jakata, don niyyata in na fita insa a kwata, don da inci abincin ummy gwara na kwana da yunwa. Wurin karfe tara da rabi na dauki kayana na kulle ma Ammy dakinta, sannan na shiga dakin Ummy na gaisheta tare da mata sallama, sannan na wuce part din Alhaji shima mukayi sallama tare da bashi keyn part din Ammy yana ta samun albarka, ina fitowa harabar gidan na ga Aliyu yana kokarin hawa lifan dinshi, tsaida shi nayi tare da umurtarshi ya a jiyeni Gidan Aunty Asma'u, bayan ya ajiyeni mukayi sallama na kawo dubu goma na bashi nace ya dauki dubu biyar yabama su Abdullah da Taheer su raba dubu biyar, godiya yamun tare damun addu'ar sauka lafiya. Ina shiga muka gaisa da Aunty Asma'u sannan nace" maman Amira ga dubu hamsin ki ijewa Ammy inta dawo ta siya abinda bata da shi" na karashe magana ina mika mata kudin. Bata fuska tayi tare da fadin"Bahijjah baza ayi haka ba ke da kike da hidima a gabanki, in bamu kara muki ba ai baza mu karba a wurinki ba". Bata fuska nayi tare da fadin"don Allah ki karfa, wallahi yanxu haka kusan dubu dari shida gareni, kuma kinga abinda zan siya ba wasu masu yawa bane, tunda duk an riga an gama siyansu, kinga ita kuma Ammy ko gas a saimata don naga da gawayi take girki". Gyara zama Aunty Asma'u tayi tare da cewa "shikenan bahijja tunda kince akwai kudi a hannunki,kuma dama nayi niyar saimata gas din ko karamar cylinder ne, ko itama ta huta, don tunda gas din gidannan ya lalace Alhaji yasa aka futa dashi nayi ta son in siyan mata, amma kuma sai Aunty Hanna tace Yaya Baffa yace zai siya, to sai dai daya tashi sai ya siyan ma Ummy, sai da muke magana da Aunty hanna tace wai Ummyn ce ta hana ya siya har da Ammy". Tabe baki nayi tare da cewa ita ta sani, kayi da kyau ma ya ka kare ballantana bakayi ba" na karashe magana ina kokarin tashi. Aunty Asma'u itama tashi tayi tare da fadin"Allah dai ya kyauta". Na amsa da"Amin, ni dai na wuce". "To Allah ya kiyaye hanya ki gaida su Hajiya, sai mun hadu a kano"cewar Aunty Asma'u. Na ams da"Amin zasuji". Ina fita na bude jakata na fito da bakar ledar dana zuba abincin wurin ummy na jefa a kwata na wuce abuna. *Sokoto* Tunda na koma Sokoto ban zauna ba don kullun muna hanyar kasuwa dasu Aunty Zuhura, duk wani abu da nasan ba'a siya ba especially kitchen equipment na siyesu, sannan na siya set din akwatina mai guda hudu, sannan na sayi kaya kala goma sha biyar na bada dinki. Bangaren hajiya kuma, ta dinka mun kaya kala goma wanda duk kayan bamai arha. 'ya'yan hajiya kuma mata su suka siyarmun blanket 2,TV, reciever, center carpet,gas cooker ,bedsheets 5, da tukwane biyar. Garaah ko wadda sukayi mini ko aurena na farko ba ayi min ba. Sosai Hajiya dasu Aunty shafa suka tsima ni da magungunan karin ni'ima. Biki na sauran sati daya Suleiman ya samu matsala da matarsa ta biyu, inda abun har ya kai da saki, har cikin raina banji dadin haka ba dukda an sanarmun masifaffiyace ta karshe, kuma da da ita zai hada mu. biki sauran kwana biyu, aka wuce da kayana kano, wanda washe gari kuma mukayi mota uku daga Sokoto mukayi kano, don hajiya kawai aka bari a gida. *KANO* Direct gidan Aunty Aisha muka wuce inda na tarad da su Aunty Asma'u,Aunty Hanna da Aunty zeena, sai manyan 'ya'yan hajiya su Aunty huwaila da Aunty Atika har sun iso, nan dai mukaci abinci, muka yi sallah sannan aka fara aikace², ni kuma aka kiramun mai lalle aka fara muni. Washe gari, karfe shadaya aka daura auran a Kudan, auren da Alhaji shi ya bada da kansa batare daya wakilta kowa ba. Ana daura aure ,fateeyzah tazo ta tsantsaramun kwalliya wadda ta dace da fuskata. _(Fateeyzah makeover for_ _u at affordable price)_ Ana gama min makeup sai ga kiran sumayya ya shigo, ina picking naji tana kuka tana fadin" maman Iman don Allah Daddynsu Iman yake son magana dake, satinmu daya kenan a asibiti sakamakon hawan jini dayayi masa mugun kamu". Nan naji hankalina ya tashi don nasan ciwon bazai rasa nasaba da kin komawa gidanshi da nayiba, don dana koma sokoto Ammy tace yazo yana ta kuka, cikin sanyin jiki nace "bashi wayar sumayya" Cikin murya irin ta marasa lafiya ya fara fadin" Bahijjah nasa sumayya ta kira kine in roke ki gafarar abunda nayi miki, wallahi Bahijjah ba a hayyacina na aikata miki haka ba, don Allah ki taimaka min ki yafemun" ya karashe magana cikin karayar zuciya. Cikin mutuwar jiki nace" yaya Tasi'u na yafe maka,don Allah nima in cikin zamanmu akwai abunda na maka ka yafemun " Cikin sanyin murya ya amsa da"na yafemiki Bahijjah, Allah kuma ya sanya Alkhairi ya bada zaman lafiya" Kasa amsa mai nayi saboda wani kuka da yazomini, kashe wayar nayi tare da kifa kaina a cinya ina kuka, don gani nayi ban kyauta ma Tasi'u ba. Karfe hudu su Aunty Ateeka suka tafi gyara mini gida. Bayan magriba kuma motocin daukata suka iso, haka aka futo dani ina kuka sai kace wata budurwa aka wuce dani gidana dake nassarawa g.r.a, gidanne na alfarma wanda ke dauke da flat biyu, kowanne flat akwai parlour daya, bedroom biyu,dinning sai kitchen da store. Su yaya Arsala ba kananan furnitures suka Samun ba, don da bed dina da kujeru duka Royal furniture aka samun, kitchen dina kuwa ko wata budurwar albarka. Karfe tara su Aunty Asma'u suka juya bayan sun gama min nasihohi. *A gurguje* Zamana da Suleiman, zama ne naso da mutumta juna, zamane na kwanciyar hankali, haka ita ma uwargidansa banda matsala da ita don macece mai sanyin hali. Satina biyu a gidan Suleiman ya siyan mini dinning table da fridge, sannan ya bani naira dubu dari inyi jali, wanda na hada da kudin hannuna na sari kaya na tura ma Aunty Asma'u ta ringa saida muni. Matsalar dana dan fuskanta a Gidan Suleiman, shine matsalar matarshi da suka rabu, wanda ta ringa turomin da bakaken maganganu tare da alwashin sai taga bayana tunda na rabata da mijinta, ba karamin tsorata nayi da maganganunta ba amma daga baya na dage da addu'a da tsayuwar dare, wanda ko da ta yimini wata muguntar kanta take komawa. Sannan ina yawan tunanin su Iman amma daga karshe sai na hakura ina binsu da addu'a. *Bayan shekara biyu* Abubuwa sun faru da yawa, ciki kuwa harda haihuwar 'yan biyu da nayi mace da namiji wanda aka sa masu suna Muhammad da Fatima. Asirin dake jikin Ammy kuwa duk ya karye wanda yazama kaikayi koma kan mashekiya, don Alhaji gaba daya yanxu ya fita hanyar Ummy wadda abu ya mata yawa yanxu don salma tayi aure biyu kenan cikin shekara daya, wanda yanxu haka zawarci takeyi. Aunty Amina kuwa yanxu duniya ta juya mata, don d'an aikin da take fafa dashi an koreta, sai dai abinda miji ya kawo ya bata, don shima mijin ba karfi gareshi. Aunty Mamy kuwa itama dai duk daya suke da Aunty Amina don shima mijinta an koreshi daga aiki sai dan buga². Aunty Hauwah kuwa ita mijinta kishiya yayi mata da sa'ar 'yarta ta uku, sannan sati daya kenan da mukaje bikin babbar 'yarta inda aure ya mutu washe garin bikin saboda ango yazo ya musu karyar kudi suka dauki yarinya suka bashi wanda daga karshe akazo ba dakin da za a saka amarya, shikuma uban amarya yace a sakar mai 'ya. Muko rayuwarmu yanxu sai dai muce Alhamdulillah don irin daukakar da muka samu, don yanxu Aliyu ya sa mu aiki a refinery, Abdullah kuwa yana aikine a ministry of finance, Taheer kuma sannan shekarar ya samu admission a A.B.U inda yake karanta medicine. Bangaren Aunty Asma'u kuwa yanxu mijinta trailer shi uku, sannan itama tana samu a business din da mukeyi ni da ita. Zuminci mai karfine tsakanina da yaya Tasi'u, don har gida yake kawomun su Iman hutu, sannan ya sami sauki don sumayya ta haifi 'yarta mace wanda taci sunana sai dai yarinyar Abnormal ce. *GIDAN NAGOGGO* kuwa yanxu sai son barka don in ka cire su Aunty Amina zumunci muke yi sosai har da surukan gidan. Alhaji kuwa a kunlin addu'ace da sai Albarka ke shiga tsakaninmu, Ammy kuwa yanxu itace 'yar gaban goshin Alhaji. *ALHAMDULILLAH !* *ALHAMDULILLAH* Anan na kawo karshen littafina mai sunan *GIDAN NAGOGGO* , ina rokon Allah ya yafemun kuskuren dake cikin wannan littafi. Jinjina garekuu *HIKIMA WRITERS ASSOCIATION* *REAL FATEEYZAH NOVEL* *REAL FA'EEZAH NOVEL* *MUM IRFAAN NOVEL* *OUM RAMADAN FANS CLUB* *WUTA DA AUDUGA FANS* *KUNDIN HIKIMA WRITERS* ina godiya daa irin kaunar da kuka nunamin, sai mun hadu bayan sallah a sabon littafina mai suna *DOCTOR* *ZAHRAH* 💉💊,Allah yasa ayi Azumi lafiya. ********************** ? ************************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************? ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ? ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ? ************************** *Comment* *Like* *Vote* *Share* *Fatima Zahra Muhammadu sani* *(Fateeyzah)* ✍