Mutum Da Aljan Littafi Na Biyar (5) Part A. Ku ziyarci Shafin www.rumbunlabarai.com domin samun littattafai masu daɗi da debe kewa JARUMAR TA MIKE TSAYE DAGA KAN KARAGAR MULKIN, ta tako kafafunta tazo har daf da alkasim ta tsugunna fuskarrta na kallon tasa yadda har suna iya jin numfashin juna sannan ta dubeshi fuskarta a daure ta dubeshi fuskarta a daure tace wnene kai kuma me kake takama dashi har da zakayi kokarin zaluntata ka rabani da abinda na farauto a daji alhalin hannuna ya riga naka kaiwa kan dabbar? Sa adda yarima alkasim yaji wannan tambaya sai yayi murmushi yace bazan baki amsar wannan tambaya ba sai kin fara gabatar da kanki tukunna nasan ko ke wacece. Koda jin haka sai jarumar ta fusata ta mike tsaye zumbur ta koma da sauri zuwa kan karagarta ta zauna zamanta keda wuya sai ta yi nuni da hannunta zuwa kan alkasim take wannan murtukekiyar macijiya data kanannadeshi ta sauka daga jikinsa amma sai wadansu sarkokin karfe suka fito daka cikin bango kimanin guda dubu suka kanannadeshi har kansa suka janyeshi zuwa jikin bangon suka shiga matseshi yarima alkasim bai san sa adda ya fara kurma ihu da kururuwa ba sakamakon tsananin zafi da zugin da yake ji koda ganin haka sai jarumar ta fara kyalkyala dariyar mugunta tana cikin yin dariyar ne kwatsam taji alkasim ya daina yin ihu da kururuwan kuma nan take sarkokin suka karkatse suka zube kasa gutsungutsun sai gani tayi Alkasim ya baro jikin bangon ya durfafota yana tafiya da karfinsa tamkar wani abu bai taba samunsa ba Manya gatan wasa kenan sarki Alkasim. Cikin tsananin kaduwa da mamaki jarumar ta mike tsaye tana kallonsa kawai alkasim ya iso har daf da ita yadda suna iya jin numfashin juna kamar yadda tayi masa dazu ya dubeta cikin murmushi yace duk abinda kike takama dashi nima ina da irinsa ko ma wanda ya fishi akan wane dalili zaki dauki girman kai a gareni alhalin nine yakamata na zamo mai girman kai a gareki tun da na kasance da ga sarkin dake mulkin wannan kasa da kike cikinta. Koda jin wannan batu sai jarumar tayi murmushi sannan tace dama saboda kai nazo wannan kasa abinda yasa banje fada kai tsaye ba shine ina son na gabatar da abinda nazo yi a sirrance ya kasance a tsakaninmu ne kawai mu biyu sunana LUSLAIYA YA GA SARKIN MAFARAUTA NA BIRNIN TEHERAN tun ban fi shekara takwas ba a duniya mahaifina ya bani horon yaki wanda ina iya fuskantar zaratan mayaka guda dubu sannan ya bani horon gumurzu da manyan dabbobin daji baya ga hakan ya bani horon rayuwa a cikin daji gami da yin gudu na tsawon kwanaki tara ba tare da tsayawa ba sama da dakika arba in ba bugu da kari mahaifina ya tsumani a cikin tsumin tsafi irin wanda samun mai irinsa sai an tona lokacinda na samu shekaru goma sha takwas ina samun wannan horo ya zamana cewa na zama budurwa cikakkiya sai na kawai da dukkan yan fashin dake cikin dazuzzukan kasarmu ni kadai hakanne yasa yan fashin suka fusata suka nemo taimakon yan uwansu dake cikin kasashen ketare amma duk da hakan sai na zame musu alakakai na zamo tamkar shaidaniya a cikin bil adama akwai wata ranar da wadannnan yan fashi suka ritsani a daji adadinsu yakai miliyan shida amma ni kadai na kashe mutum miliyan uku da rabi daga cikinsu sauran suka tsere daga wannan rana ne na dinga jin kamar babu wani mayaki ko sadaukin da yafi ni jarumtaka amma sai mahaifina ya dubeni yace yake yata kada ki kuskura ki dorawa kanki girman kai bisa wannan jarumtaka da kika ga kin samu a halin yanzu ina mai tabbatar miki da cewa akwai wani dan sarki wanda karfinsa da jarumtakarsa har da karfin sihirinsa zasu iya zuwa dai dai da naki koma yafiki koda jin wannan batu saina kamu da tsananin mamaki na tuna irin karfiin da nake dashi amma ace wai har akwai wanda ya kaini koma ya fini bisa wannan daliline na yanke hukuncin nazo na hadu dakai domin muyi gasa guda mu banbance tsakanin aya da tsakuwa gasa ta farko itace gudun tseren da zamuyi tsawon kwana tara ba tare da tsayawa ba ta sama da dakika arba in ba gasa ta biyu itace akwai wani babban gari na arnan daji dake can kudancinmu na taheran ina son mu je mu sato gunkin da suke bautawa domin mu tsokano yaki dasu wadannan arnan daji suna da mugun yawanda ba asan iyakar adadinsuba ni dakai dai zamu yakesu domin mu tantance iyakar jarumtakarmu gasa ta uku wacce itace ta karshe zamu shiga daji kowannanmu yayi farautar dabbar da babu kamarta ya kasheta yazo da gawarta idan har dabbar da na kashe tafi taka hadari ka tabbata cewa nafika karfi da jarumtaka kenan Al amin Ahmed Misau Guyson sunana kenan daga zauran labarai page nake typing nan take zamu rabu na koma kasata cikin farin cikin cewa nafi ka komai yayinda jaruma luslaiiya tazo nan a zancenta sai hankalin alkasizancenta sai hankalin alkasim ya dugunzuma ainun saboda zuciyarsa ta karaya akan wannan abu guda uku amma daya tuna cewa shifa mutum ne mai sa a da nasara bisa duk abinda yasa a gabansa sai yaji dukkan tsoro ya kau daga cikin ransa don haka bai san sa adda ya dubi jaruma luslaiya ba yace na yarda da duk wannan sharadi na gasar da kika shirya mana kuma saina tabbatar miki da cewa nafiki karfi da jarum taka wow nima Guyson saina tabbatar muku da cewa jarumi ne ni. Yanzu idan na lashe wannan gasa menene sakammenene sakamakona? Koda jin wannan tambaya sai mamaki ya kama luslaiya tace inda dai ace kai ba dan sarki bane toda saina baka dukiyar da har ka mutu kai da danginka ba zaka yi talauci ba amma ai mahaifinka yafi mahaifina dukiya yanzu ban san dame zan iya biyanka ba koda jin wannan batu sai alkasim yayi murmushi yace ai kuwa kece kike da abin da zaki iya biyana yake jarumar jarumai kuma tauraruwar taurari ba komai nake so a wajanki ba face soyayyarki da aurenki idan har na lashe wannan gasa akanki to na siyi soyayyata kenan kuma babu abinda zai hana aurenmu koda jin wannan batu sai jaruma luslaiya taji zuciyarta tayi baki kirin kuma nan take taji ta tsani yarima alkasim fiye da komai a duniya saboda tunanin cewa ya na so yayi mata dole ta soshi kuma ta aureshi cikin tsananin fushi ta dubeshi tace nayi maka alkawari zaka sha bakar wahala da baka taba sha ba a rayuwarka a cikin wannan gasa wacce zata kaika ga rasa lafiyarka ko rayuwarka gaba daya kuma ina tabbatar maka da cewa baka da jarumtakar da zata iya burgeni har zuciyata ta kamu da sonka don haka duk yadda zanyi naga ka fadi wannan gasa sai nayi ya kasance ne ne na lashe gasar ka sani cewa babu hada kai a cikin wannan gasa ni dakai sai dai kowa tasa ta fishsheshi kuma kowannanmu zai iya shiryawa dan uwansa tarkon mugunta domin ya hallaka iana son mu zamo tamkar abokan gaba masu farautar rayukagaba masu farautar rayukan juna lokacin da sarki alkasim yazo dai dai nan a labarin da yake baiwa yarima kamsus sai yaga idanun yarima sun ciko da kwalla kuma hankalinsa ya dugunzuma ainun ya tari numfashinsa yaana mai cewa daka ta yakai abbana yanzu kana bani labarin wata jaruma a matsayin itace mahaifiyata to ita kuma junaina wadda na taso nake ganinta a matsayin uwata wacece ita?? Koda jin wannan tambaya sai hawaye ya zubowa sarki Alkasim yayi shiru kamar ba zaice komai ba daga can ya dago kai ya dubeshi cikin rawar murya yace yakai dana kayi hakuri zakaji amsawar wannan tambaya da kayi min a karshen wannan labari da nake baka kafin mu isa birnin masarul anjana Tabbas zaka tantance a tsakanin mahaifiyarka junaina da kuma mahaifiyarka jaruma luslaiya zaka san matsayin kowacce a wajenka koda sarki alkasim yazo nan a zancensa sai zuciyarsa ta karaya ya fashe da matsanancin kuka al amarin da ya dugunzuma hankalin yarima kamsus kenan ya shiga rarrashin sarki a lokacin da yaji ya kamu da tsananin tausayin mahaifin nasa sarki Alkasim da kyar ya shawo kansa ya daina kukan sannan yarima kamsus ya dubeshi cikin zakuwa yace na rokeka dakaci gaba da bani wannan labari domin naji yadda karshen gasarkdomin naji yadda karshen gasarku da jaruma luslaiya zata kasance sannan kuna na gane banbancin dake tsakanin luslaiya da mahaifiyata junaina Al amin Ahmed Dan misau Guyson sunana kenan daga zauran labarai nake magana tayaya zan karbi luslaiya a matsayin uwa ta alhalin ban san wata uwa ba face junaina gama fadin haka keda wuya sai hawaye ya kwararo bisa kumatun yarima kamsus take shima sarki alkasim yaji ya kamu da matukar tausayinsa don haka sai ya rungumeshi akan kirjinsa sannan yaci gaba da bashi labari yana mai cewa..... . LOKACIN DA NAJI ABINDA LUSLAIYA ta fadi cewar a cikin wannan gasa zamu zamo tamkar abokan gaba kuma zamu rinka shiryawa juna tarkon muguntar da zan iya hallaka sai hankalina ya tashi saboda dalilai guda biyu. Dalili na farko shine na kamu da tsananin sonta dalilina biyu kuwa bazan iya shirya mata mugunta da zata hallaka ba nan take zuciyata ta gamsu cewar lallai zan sha bakar wahala a cikin wannan gasa musamman da na tuna cewa inda zamu je mu gabatar da wannan gasa acanne nahiyar su jaruma luslaiya don haka ban san sirrikan dazuzzukan dake can ba. Yayin da luslaiya taga na sunkuyar da kaina kasa ina tunani da nazari saita kyalkyale da dariyar mugunta sannan ta hade fuska tace yaro bai san wuta ba saiya taka ta yanzu saika tashi ka koma gida ka sanar da iyayenka duk abinda ya faru a tsakaninmu domin kayi musu sallama ka dawo mu tafi ka sani cewa tun daga nan gasar mu zata fara don haka kayi amfani da damarka ta kowa a gidansa sarkine duk yadda zakayi ka tabbatar kaga bayana kafin mu bar nahiyarku dajin wannan batu sai yarima Alkasim yayi murmushi ya mike tsaye ya juya mata baya har yayi taku uku gaba zai yi tafiyarsa sai ta kira sunansa ya waigo ya dubeta cikin mamaki ita kuma sai tace da sassafe zaka fito gobe ka sameni anan wurin idan ka baata min lokacin zanyi tafiyata sai kayi da gaske zaka riskeni alkasim yayi murmushi yace babu matsala zanzo akan lokaci yana gama fadin hakan sai ya juya yayi tafiyarsa har yarima alkasim ya isa gida jikinsa a sanyaye yake kuma hankalinsa a tashe yake domin guiwarsa tayi sanyi ainun bisa wannan gagarumar gasa dake gabansa da isar yarima Alkasim a lokacin da magariba ta gabato sai ya nufi kai Tsaye bisa mamaki sai ya hango kofar dakinsa a bude al amarin da yayi matukar bashi mamaki kenan domin babu wanda yake da ikon shiga dakinsa ba tare da izininsa ba face mutum biyu daga sarki sai mahaifiyarsa a fusace yarima Alkasim ya kunna kai da sauri cikin turakar tasa da nufin yaci mutuncin wanda ya bude ya shiga koda yayi arba da wanda ke zaune a cikin dakin sai zuciyarsa ta buga da karfi ba wani bane ba face mahaifiyarsa tana zaune bisa shimfidarsa kanta a sunkuye hawaye na diga daga idanunta cikin firgici ya karasa gareta da sauri ya durkusa a gabanta ya rike hannayanta biyu yana dubanta cikin tsananin damuwa yace yake ummina ina dalilin zubar wannan hawaye daga cikin idanunki sa adda taji wannan tambaya sai tasa hannunta na dama ta share hawayan nata sannan ta janyo yarima izuwa jikinta ta rungumeshi akan kirjinta tace ya kai dana yau shekara talatin da kadan kenan ina tare dakai bamu taba rabuwa ba amma yau sarki ya tabbatar min da cewa a wannan karon zaka nisanta dani kuma zaka yi wata tafiya mai hadari wacce zama ka iya rasa rayuwarka koda jin haka sai yarima alkasim yayi murmushi cikin nutsuwa yace haba yake ummina akan wane dalili zaki damu kanki alhalin kin san duk ahalin gidan nan yana da sa a da nasara bisa duk abinda yasa a gabansa ke da bakinki kin sha bani labarin irin gwagwarmayar da sarki yayi a rayuwarsa tamkar ba zai tsira da rayuwarsa ba wai shin ma me yasa kika shigo cikin turakata kika zauna kina ta kuka? Shin yanzu kina nufin ki ce dake za ayi wannan muguwar tafiya ne? Nayi murna da ganinki a yanzu domin dama akwai wani abu daya shige min duhu ina son kiyi min cikakken bayani kada ki boye min komai taji zuciyarta ta buga da karfi tsoro ya shigeta ta fara zargin anya kuwa sarki bai sanar dani sirrin da suka boye ba tsawon shekaru cikin karfin hali na budi baki nace yake umma ina sonki sanar dani matsayina kafin yarima alkasim ya karasa fadin abin dake bakinsa sai yaji motsi a bayansa don haka sai ya waigo da sauri sarkine tsaye a bayansa fuskarsa a murtuke yana mai kada kansa wato yana yi masa nuni da kada ya fada mata abindake bakinsa... Zidane kd Mutum Da Aljan Littafi Na Biyar (5) Part B. . Marubucin littafin Abdul aziz sani madakin gini typing by Al amin Ahmed Misau Guyson Call;- 08064594218 Doka;- Ban laminta ba ayi edit na post dina ba tare da sanina ba. . Labari ya isowa guyson cewa...... KAWAI SAI SARKI YA DUBI MAHAIFIYATA yace ina son nayi magana da dana shin zaki iya bamu dama? Ba tare da tace uffan ba sai ta mike tsaye ta fice daga cikin tantin a sannan ne sarki ya dubi alkasim a fusace yace shin baka da hankaline har da kake shirin tambayarta matsayinka a wajenta kana yin garaje a cikin al amarinka kuma ita gaggawa bata haifar da komai sai nadama kayi hakuri kaji karshen labarin da nake baka tukunna a sannan ne zaka san matsayinka a wajenta ba wai sai kaji daga bakin taba ni yanzu abinda ya kawoni wajenka ba komai bane face na sanar dakai cewa kada ka kuskura ka bar zuciyarka ta karaya bisa gasar da zakuyi kai da luslaiya yar sarkin mafarauta na birnin taheren duk irin masifar da zaka gani a cikin tafiyar taku duk irin tsananin wahalar da zaka sha kada ka karaya domin ba a samun komai a banza a cikin wannan duniya dolene sai an sha wuya sannan akansha dadi duk abinda ya faru a daji tsakaninka da luslaiya na gani a cikin madubin tsafina don haka kayi sammakon riskarta a dajin gobe da safe kamar yadda ta umarceka taimakon da zan baka a matsayin babban guzuri a cikin wannan gasa da zakayi shine ka rike abu uku wannan abubuwa uku ba komai bane ba face gaskiya hakuri da amana sune kadai abubuwan da zasu kubutar dakai daga sharrin luslaiya amma ba karfin damtsenka ba ko karfin sihirin tsafinka ba saboda duk a bin da kake takama dashi itama tana dashi ka sani cewa nima na taka irin wannan matsayin da kake kai yanzu kafin na mallaki mahaifiyarka wannan al adar gidannance babu wani sarki da ya taba auren matar da bata kasance basadaukiya ba Al amin Ahmed Misau Guyson sunana kenan kuma jaruma abar kwatance a duniya an tsara hakanne domin dukkan zuri armu su rinka shan jarumtaka a nono da wannan furuci nake yi maka sallama kuma nasa maka albarka ka tafi abinka nasara na tare dakai koda gama fadin hakan sai sarki ya dora hannunsa na hagu akan tsakiyar kaina faruwar hakan keda wuya sai naji wani irin gagarumin karfi ya shiga jikina kuma naji dukkan tsoro da fargaba sun kau daga cikin raina har ina jin kamar cewa ni kadai zan iya yakar duniya. Saboda farin ciki bansan sa adda na duka har kasa ba zan yiwa mahaifina sujjada amma saiya kamo kafaduna ya tasheni tsaye yace kwanta ka huta dana gobe akwai gagarumin aiki gabanka yana gama fadin haka sai ya juya ya fice daga cikin dakin ya barni ni kadai nan dai naje na kwanta a shimfidata na lumshe idanuna domin nayi barci amma saina kasa domin fuskar luslaiya naci gaba da gani ba sassauci har gari ya waye barcina rabi da rabine wato rabi tunani rabi barci kashe gari kuwa tun kafin alfijir ya keto na gama shiri kuma nayi sallama ga mahaifiyata duk mu biyun muna kwalla muka rabu cikin gaggawa nayi gagarumar shigar yaki mai matukar kwarjini da ban tsoro na hau dokina na sukwaneshi da guda na fice daga cikin gari na naushi daji hakika masu iya magana sun yi gaskiya da sukace komai sammakonka wani a tafe ya kwana a iya tunanina sai dai naje wannan wuri inda mukayi alkawarin haduwa da luslaiya na jirata amma ina isa wajan na isketa a tsaye gaban wannan katuwar bishiya wacce ta zukeni waccen karon luslaiya ta ruke kugunta tana kai kawo alamar cewa har ta gaji da jiran isowarta koda ta hangoni na durfafota sai tayi dan guntun murmushi da isowata daf da ita sai ta dubeni tace in dai baso kake ka zalunci wannan doki naka ba zai fi kyau ka sake shi ya kama gabansa domin zaka ja shine izuwa hallaka kuma kada ka manta cewar daga nan ne zamu fara yin gasar gudu ta kwana tara kuma tabbas wannan doki ba zai jure hakan ba ba tare da wata gardama ba saina sauka daga kan dokin na bugeshi ai kuwa sai dokin ya juya da baya da gudu yana mai bin hanyar da muka fito nan da nan kuwa ya kule muka daina ganinshi a sannan ne na juyo na dubi jaruma luslaiya da kyau ai kuwa sai na rude kuma na kidime naji na kara kamuwa da tsananin sonta fiye da koyaushe a wannan lokaci luslaiya na sanye da riga da wando ne na fatar damisa wadanda suka kasance matsatstsu don haka gaba dayan surorin jikinta sun fito karara ni kam in dai tambayata za ayi to zance duk duniya babu wata ya mace mai kyan sura da kyan fuskar mahaifiyarka luslaiya luslaiya ta daure wadansu gajerun adduna guda biyu akan cinyoyinta dama da hagu a gadon bayanta kuwa tana rataye da wata sharbebiyar takobi dogon gashin kanta kuwa ta tattareshi a bayanta ta daureshi ya zuba har kan kasan kwankwasonta sai sheki da walwali yake duk da cewa nayi gagarumar shigar yaki sai da na raina kaina domin tata shigar tafi tawa kyau da kwarjini luslaiya ta sake dubana cikin wani irin murmushi mai kama da mugunta ko yaudara tace idan ka shirya yanzu zamu fara gasarmu ta farko ta gudun kwana tara babu tsayawa ta tsawon sama da dakika goma Al amin Ahmed Misau Guyson, Dajin haka sainayi murmushi nace ai tunda har na dawo gareki na gama shiri kafin na gama rufe bakina sai kawai naga luslaiya ta zabura ta falfala da azababben gudu izuwa cikin daji koda ganin haka sai nima na falfala nan da nan kuwa na risketa muka jera muna gudun tare da zarar naga ta rage karfin gudun nata sai nima na rage nawa ya dawo dai dai da nata koda ganin haka sai tayi murmushi na mugunta nima sai na maida mata da martanin murmushin muguntar saboda nasan cewa na fita sanin sirrin wannan daji da muke ciki kuma na tabbatar da cewa bata san irin hadarin dake gabanmu ba akan wannan hanya da muka biyo Abinda luslaiya bata sani ba shine anan gabanmu kadan akwai wani kogi na tabo wanda indai mutum ya fada cikinsa babu yadda zai iya kubuta sai dai ya nutse a cikinsa face wani ya taimakeshi koda ya rage saura baifi dakika dari ba mu iso inda wannan kogin tabo yake saina fara rage guduna ta hanyar nuna alamun cewa na fara gajiya koda ganin haka sai luslaiya ta fara murna kuma ta karawa kanta karfin gudu hakika rashin sani yafi dare duhu tabbas inda luslaiya tasan masifar dake gabanta da batayi wannan ganganci ba na kara karfin gudun nata shi dai wannan kogin tabo gaba da bayansa a lullube yake da tsirrai babu yadda mutum zai iya ganewa cewa kasan tsiran tabone sannan kuma tabon yana da zurfin gaske Al amin Ahmed Misau Guyson nake magana daga zauran labarai page. Da isowarmu daf da wannan kogin tabo luslaiya na kan gaba ina bayanta koda ta waigo taga na karo guduna ina son na risketa saita daka tsalle sama domin ta bani tazara mai yawa kawai saiji tayi ta fado cikin tabo ta makale da kasa gaba da baya nan fa ta fara amfani da karfin sihirinta na tsafi domin ta fito daga cikin tabon amma saita kasa kuma sai taji tana kara nutsewa kasa a hankali Al amarin da yayi matukar dugunzuma hankalinta kenan ta juyo bayanta da sauri ta dubeni kawai sai gani na tayi a tsaye nayi turjiya na zuba mata idanu ina mata murmushin mugunta luslaiya ta daka min tsawa tace meka tsaya kana jira ka ci gaba da gudunka ka barni a anan tawa ta fishsheni idan ma na mutu anan shi kenan ka lashe gasar koda jin wannan batu saina sake yin murmushi a karo na biyu nace tayaya zan iya tafiya na bar masoyiyata a inda zata hallaka ai dole ne na ceto rayuwarki luslaiya tace ai kuwa inka ceci rayuwata kayi babban kuskuren da saikayi nadamarsa da jin haka saina gyada kai nace har abada masoyi baya nadama akan taimakon masoyinsa koda na gama fadin haka saina kwance jakar guzurina dake rataye a kafadata na fiddo wata doguwar igiya na cillawa luslaiya ta cafe sannan na rinka janyota daga cikin tabon a wannan lokaci tabon ya shanye dukkan wuyanta don haka gaba daya jikinta ya baci da tabon da kyar na samu na fito da ita tana gama fitowa sai ta nufi cikin wata korama ta kama yin wanka ni dai ina tsaye a gefe daya ina kallonta kawai saita daka min tsawa tace shin tarbiyarka daka samu kenan ta kallon mata? Koda jin haka sai nayi sauri na juya mata baya ina mai cewa ki gafarceni nayi kuskure bayan luslaiya ta gama wanka gaba dayan tabon jikinta saita fito daga cikin kogin tazo kusa dani ta dubeni tace yanzu ta yaya zamu iya haye wannan kogin tabo muci gaba da yin tafiyarmu duk inda kika ga nasa kafata kema ki saka naki ina gama fadin hakan saina nufi kan karshen gefen kogin tabon naci gaba da tafiya akan kogin hankali kwance tamkar ba akan kogin tabo nake ba ita kanta luslaiya sai abin ya daure mata kai ta kamu da tsananin mamaki sai da na fara taka inda nake takawa sannan na gane cewa ashe bushashshen tabone a wajan ba danye ba duk da haka luslaiya bata yadda taci gaba da yin gudu ba akan busashshen tabon a hankali ta rinka tafiya har muka tsallake kogin tabon gaba daya muna fita saita sake falfalawa da gudun gaske nima saina rufa mata baya sai da muka yini muna gudu ba tare da mun tsaya ba ko mun hadu da wata matsala ba ko kishirwa ta kama daya daga cikinmu sai dai ya daga battar ruwansa yana cikin gudun ya dan sha kadan yaci gaba da gudu a binsa A wannan lokacine nayi tunani na gane cewa zamu gane kuskurenmu anan gaba tunda bamuyi guzurin abinci ba sai guzurin ruwan sha shi kansa ruwan shan ba zai ishemu ba a cikin tsawon kwanaki taran da zamu yi muna wannan gudu to wai shin idan yunwa da barci suka kamamu a cikin wannan gudu ya zamuyi? Amsar da na kasa baiwa kaina kenan haka muka ci gaba da gudu har gari ya soma duhu koda luslaiya taga gari ya soma duhu bata ganin gabanta sosai saita daga hannunta na hagu sama nan take fitilar ice ta bayyana a hannunta nima sai nayi irin tsafin da tayi na samu fitilar Wohoho ! Ba a sanin maci tuwo sai miya ta kare kuma ba a sanin jimrau sai idan ba a san karshen wuya ba haka dai muka ci gaba da gudu a cikin dajin ba sassauci tamkar jikinmu bana jini da tsoka bane domin babu alamar cewa zamu sare ba wai gajiyar bace babu a jikinmu tsabar juriyace kawai da sabo, sai dare ya soma yi sannan yunwa da barci suka fara damunmu amma saboda naci muki yarda mu sare ko mu tsaya hutawa ko yada zango Al amin Ahmed Misau Guyson Lokacin da luslaiya taji cikinta ya fara murdewa saboda yunwa saita fara tunanin mafita nima a wannan lokaci na fara shiga irin wannan hali da ta shiga don haka burina kawai shine naga ta sare na fadi kasa nima sai kawai na zube kasan don haka dolenemu yada zango a wajan ba zato ba tsammani sai kawai naga luslaiya ta daka tsalle sama izuwa kan wata bishiya ta cafko wani tsuntsu tana dirowa kasa taci gaba dagudunta tana cikin gudun ta kafawa tsuntsun hakoranta akan makoshinsa ta cisge masa wuya kawai sai ta kama shan jininsa bayan ta gama tsotse jinin saita kama fige gashin tsuntsun tana gama figeshi ta kama cinsa danye a haka ta gama cinyeshi Koda ganin abinda luslaiya tayi sa nayi koyi da ita amma fa sai dana ji kamar zanyi kumallo domin ban taba cin danyen nama ba a rayuwata sai a sannan. Zidane Mutum Da Aljan Littafi na biyar (5) Part C. . Marubucin littafin: Abdul aziz sani madakin gini Typing by' Al amin Ahmed Misau Guyson Contack: 08064594218 for more Doka' ban yarda a sarrafa wannan post ba inbada izinina ba. ! Labari ya isowa guyson cewa... Hakika dole kanwar naki ce domin inda banci wannan danyen tsuntsun ba da tabbas yunwa zata iya min lahani hakika a cikin wadannan kwanaki tara naga abubuwan al ajabi a tare da jaruma luslaiya babban abin da yafi burgeni da ita shine yadda take iya yin barci a lokacinda take cikin yin gudu ba tare da tayi karo da bishiya ba ko dutse da zarar ta tunkari bishiya ko dutse saitazo daf da su saikaga ta goce musu ta wuce lafiya lau ni kuwa sai da na rinka yin karo da bishiyoyi da duwatsu ina jin ciwo da faduwa tsabar naci da juriya ce tasa ban sare ba naci gaba da gudu a hakan a wannan lokacine na tabbatar da cewa luslaiya ta samu horo da ni bani dashi hakika munsha bakar wahala a cikin wadannan kwanaki tara tamkar zamu rasa rayukanmu amma har lokacin ya cika ban sare ba a ranar kwana na taran ma a jere muka iso farkon wani daji wanda ke cikin nahiyar kasar teheren da yammaci ne muka iso farkon dajin kawai sai naga luslaiya ta zube kasa bisa guiwoyinta tana haki nima sainazo na zube kasa daf da ita kawai saita dubeni tace tabbas na yarda kai jarumine na gaske domin kaine mutum na farko daya jure irin wannan wahala tare dani tsawon kwana tara ba tare da ya rasa rayuwarsa ba yanzu ka tsallake matakin farko na gasarmu amma ina mai tabbatar maka da cewa babu yadda zaka iya tsallake mataki na biyu bare har ka kai kan mataki na uku yanzu ne zamu yada zango mu huta kuma mu kwana sai gobe da safe zamu ci gaba da tafiyarmu koda gama fadin hakan sai luslaiya ta zare addarta guda dake kan cinyarta ta hagu ta yunkura zata wuce ta gabana a zatona ni zata kawowa hari don haka nima saina yunkura na zare takobina amma sai naga kawai ta wuce ta nufi inda wata bishiya take mai dogayen rass ta fara saranta da yake masu iya magana sunce idan kaje gari kaga kowa da bindi kaima saika daurawa kanka sai kawai nima naje na taya luslaiya aikin da takeyi nan da nan muka saro rassan bishiyoyin da yawa muka tarasu a waje guda daga nan kuma sai naga taje ta kama yanko wadansu busassun jijiyoyi na bishiya masu kwari gami da wadansu irin manyan ganyaye na wata bishiya ta musamman masu fadi nidai sai naci gaba da yin koyi da ita bayan mun gama tara wadannan kyayyakin sai luslaiya ta shiga gina daki kawai saina tayata muka kammala ginin har da kofa da rufi kai kace kwararrun magina ne suka yi aikin abin gwanin ban sha awa saiga kyakkyawan karamin gida a tsakiyar dokar daji tunda muka fara wannan aiki da yammacin bamu kammala aikin ba sai da dare ya soma a sannan ne wata irin matsananciyar gajiya ta riskemu kuma kwasam sai hadari ya gangamo aka fara tsawa da walkiya nan take luslaiya ta shige cikin wannan daki da muka gina ta turo kofa zata rufe saina kare da hannuna nace ya ya zaki shige kuma ki rufe min kofa koda jin wannan tambaya sai luslaiya tayi min. Wani irin kallo mai nuna tsantsar kiyayya tace wane ne kai a gareni har da kake tunanin zamu kwanta tare a cikin daki guda hm Guyson sunana wannan abun ya ban mamaki.. Ni ba kowa bane a gareki kuma bazan taba kusantarki ba amma ina da ikon kwana a cikin wannan daki tunda dani aka ginashi luslaiya ta sake hade fuska tace gani kayi ina aikin ginin wannan daki ka tayani amma ban gayyaceka ba don haka daki nawane ba naka ba idan ka matsa saika shigo saidai muyi yaki mu baje dakin gaba daya tana gama fadin haka saita bangajeni nayi baya taga taga kuma ta banko kofar dakin ta kulle abinta faruwar hakan keda wuya aka fara yin wata irin iska mai karfin gaske sannan kuma aka kece da ruwan sama tamkar da bakin kwarya nan take na jike sharkaf, kawai sai naga luslaiya tana lekena ta cikin tagar dakin nata tana yi min murmushin mugunta haka dai ruwa yaci gaba da dukana inaji ina gani ga inda zan fake amma babu dama ba komai ne yasa naki matsawa akan saina shiga dakin ba face nasan cewa ruguza dakin zamuyi a banza alhalin mun sha wahalar gaske wajan ginashi baya ga haka ni har a cikin zuciyata bana son abinda zai sa luslaiya ta sha wuya ko zuciyarta ta sosu saboda soyayyata a gareta ta gaskiyace hm So kenan ' lokacin da ruwan saman yaci gaba da dukana ga iska mai dan karan sanyi na kadawa sai nan da nan zazzabi ya rufeni jikina ya kama karkarwa nan fa na fara tunanin neman mafaka kawai sai na ruga izuwa gabas da yamma kudu da arewacin dajin ina neman inda zanga wani kogon dutse na shige cikinsa amma ko alamunsa ban gani ba nan take na gane cewa luslaiya mugunta ta shirya min dama tasan cewa babu mafaka a ko ina cikin dajin kawai sai naji raina ya baci zuciyata ta fara ayyana min cewa kawai na koma wajan luslaiya na fasa kofar dakin na shiga da karfin tsiya in yaso kome zai faru ya faru har na yunkura zanje na aiwatar da hakan sai na tuno da nasihar mahaifina cewa na jure duk irin wahalar da zan sha a cikin wannan tafiya tawa tare da luslaiya don haka Haka saina fasa kawai na dawo kusa da dakin nata na haye kan wata bishiya na kwanta ina mai takure jikina a lokacin da ruwan saman yaci gaba da zaneni ina ta karkarwar jiki saida aka shafe kusan sa a hudu ana tafka wannan ruwan sama sannan aka dauke dif A sannan ne zazzabin jikin nawa ya kara zafi ainun gashi kayan jikina a jike suke sharkaf kuma gashi duk itatuwan dajin sun jike babu damar na kunna wuta naji dumi A wannan lokaci alfijir ya keto don haka har gari ya waye sosai ina cikin mugun yanayi na rashin lafiya sannan ga tsananin yunwar dake damuna domin rabonmu da abinci tun jiya da rana sa adda muke gasar tseren gudu na tsawon kwana tara sa adda kowannenmu yaci danyen naman tsuntsu kwatsam saiga luslaiya ta fito daga cikin wannan daki a shirye cikin nutsuwa da cikar lafiya a hannunta akwai cinyar wani katon tsuntsu gashashshiya tana ci Al amarin dayayi matukar daure min kai kenan na cika da tsananin mamaki na tambayi kaina a cikin zuciyata nace yaushe ne luslaiya ta farauto tsuntsu har ta gasashi ban sani ba koda nayi tunani mai dan zurfi saina gane cewa lallai yaudarata tayi dama can ta tanadi wannan nama a cikin jakar guzurinta ban sani ba kuma tana sane taci naman danyen tsuntsu don kada nasan tana da wani guzuri a boye kawai sai naji wani irin takaici ya rufeni na sake tambayar kaina nace akan wane dalili luslaiya ta tsaneni haka har take son ta cutar dani matuka ga ya Alhalin ni ban taba zama abokin gabarta ba amsar dana kasa baiwa kaina kenan luslaiya ta taho gareni a lokacin da nake bisa wannan bishiya cikin halin rashin lafiya jikina nata tsuma kawai saita dago kai ta dubeni cikin murmushin mugunta tace lokacin gabatar da gasarmu ta biyu yayi sai ka sauko domin mu kama hanyar zuwa birnin Arnan daji inda zamu sato gunkin da suke bautawa koda jin wannan batu sai hankalina ya dugunzuma ainun na dubeta cikin mamaki da fushi nace Shin bakya ganin halin da nake ciki ne na rashin lafiya da matsananciyar yunwa? Ta yaya zan iya ci gaba da yin wannan gasa a haka kodajin wannan batu sai luslaiya ta bushe da dariyar mugunta lokaci guda kuma ta hade fuska tace ashe kenan ka yarda na lashe wannan gasa tabbas baka cika jarumi ba wannan ya nuna cewa na fika karfi da jarumtaka kafin luslaiya ta gama rufe bakinta tuni na duro kasa daga kan bishiyar da nake kwance na duro bisa kfafuwana na tsaya cak a gabanta nace har abada namiji yana gaba da mace yunwa da rashin lafiya ba zasu saki lashe wannan gasaba mujezuwa mahaukaci ya hau kura zamuga inda zata kaishi. Koda jin wannan batu sai luslaiya tayi min murmushin mugunta ba tare da ta sake cewa dani uppan ba saita juya ta falfala da gudu izuwa cikin daji ai kuwa nima saina ware na bita a guje muka kasa tsere tamkar babu wata lalura a tare dani amma ni nasan abin da nakeji tabbas nasan cewa ba karamin ganganci nayi ba domin idan har yaki ya balle a tsakaninmu da Arnan dajin da zamujewa ina cikin wannan hali komai zai iya faruwa a gareni tun da babu cikakken karfi da kuzari a jikina. Kash! Tabbas rashin sani yafi dare duhu ashe wani babban tarkon mugunta luslaiya ta shirya min wanda ta tabbatar da cewa indai na fada cikinsa babu makawa saina hallaka ni kuwa gogan naka sai naci gaba da tsala gudu kokarina kawai na risketa mu jera tare in yaso duk masifar da zan shiga mu shiga tare sai da muka shafe sa a daya da rabi muna ta tsala azababben gudu a cikin dajin tamkar zamu tashi sama a wannan lokacine naji jiri ya fara dibata saboda muguwar yunwar da nakeji gami da rashin lafiyar dake addabata amma saboda bakin naci irin nawa gami da juriya irin ta manyan mazaje sai naki sarewa. Ita kanta luslaiya tayi tsananin mamaki bisa ganin yadda nake iya yin wannan gudu da dukkan karfina tamkar bani da wata lalura muna cikin yin wannan gudu ne ba zato ba tsammani naga wani wawakeken rami a gabanmu mai tsananin fadi da zurfi gashi babu damar muyi turjiya mu hana kanmu fadawa cikin ramin, kawai sai naga luslaiya tayi wuf ta zaro wata doguwar igiya daga cikin jakar guzurinta mai kugiya a karshenta tana sama ta cilla igiyar izuwa can karshen ramin ta sakalo dutse sai gani nayi ta tsallake ramin da dire can samansa ni kuwa saina fada can kasan ramin ina mai kwala uban ihu saboda na tabbatar da cewa mutuwace tazo da sauri luslaiya ta rugo izuwa bakin ramin ta leko lasansa amma saboda tsananin zurfin ramin ko hangoni batayi kawai saitayi murmushin farin ciki saboda ta tabbatar da cewa na halaka ita kuwa ta lashe wannan gasa cikin murna ta juya tayi gaba ta kule cikin daji Al amarina kuwa lokacin dana fada kasan wannan mugun rami mai tsananin zurfin gaske ina kwala ihu cikin karayar zuciyar saina fara kokarin ceton ratuwata ta hanyar amfani da karfin sihirin tsafi amma sai tsafin nawa yaki tasiri Al amarin daya kara tabbatar min da cewa lallai ajalina ne yazo ban isa karshen wannan rami ba sai bayan kimanin dakiku dubu daya da dari shida saboda mugun zurfinsa. Nidinne Dai Al amin Ahmed Misau Guyson sunana kenan First Admin na zauran labarai page 2017 Zidane Mutum Da Aljan Littafi na biyar (5) Part D. . Marubucin littafin Abdul aziz sani madakin gini typing by Al amin Ahmed Misau Guyson contack: 08064594218 for more Doka' banyarjeba a yi edit na post dina.... . Labari ya isowa guyson cewa.. Ashe acan karshen ramin kasusuwane na matattun dabbobi, tsuntsaye da mutane bisa rashin sa'a kuwa sai na fado akan kashin wata dabba mai tsini take kashin ya sokeni a gefen cikina ya faso ta gadon bayana nidai kawai naji ganina dajina sun dauke duf, ban sake tuno da komai ba sai bayan wadansu sa'o'i sannan na farfado daga dogon suman da nayi koda na bude idona naga katon kashin dabba a cikin cikina har ya bullo ta gadon bayana kuma ga jinina ya zuba da yawa a kasa sai na kamu da tsananin mamakin abinda ya hanani mutuwa cikin tsananin juriya da karfin hali na yunkura ina mikewa sama kashin na fita daga cikin cikina a sannanne na rinka kwarara uban ihu gami da kururuwa mai ban tsoro saka makon mugun zafi da radadin da nake ji a cikina aikuwa ina gama zare kashin daga cikin cikin nawa na sulale kasa mutuwa nayi ko suma ban sani ba lokacin da jaruma luslaiya ta barni a cikin wannan rami wanda ta tabbatar da cewa na gama halaka sai ta nufi wata hanyar daban wacce zata kaita can birninsu na taheren a maimakon ta nufi birnin Arnan daji inda zamu yi gasarmu ta biyu har tayi nisan zango Arba'in a cikin tafiyar tata sai wani tunani ya fado mata a rai ta tsaya cak a inda take ta tambayi kanta a cikin zuciyarta tace yanzu idan na isa gida da wacce hujja zan gamsar da mahaifina cewar nice na lashe wannan gasa wacce mukayi nida yarima Alkasim lallai idan ina son ya gamsu dolene na koma can bakin ramin nasan dabarar da zanyi na shiga cikinsa na dauko gawar Alkasim na tafi da ita gama ayyana hakan keda wuya sai luslaiya ta juya da baya da gudu ta nufi inda ta baroni bata iso ba sai bayan sa'o'i da isowarta bakin katon ramin sai tayi turjiya koda ta leko kasan ramin a karo na biyu taga baata iya hango karshensa ba saboda tsananin zurfinsa sai hankalinta ya dugunzuma kuma zuciyarta ta buga da karfi tace kai kada nima fa naje na hallaka a banza a kokarin shiga wannan rami tunda kowanne irin tsautsayi zai iya faruwa a gareni wata zuciyar kuma sai tace da ita to ai baki da wani zabi wanda yafi ki shiga cikin wannan rami ki dauko gawar sarki alkasim inba haka ba kuwa duk wannan wahalar da kika sha a baya ta zama ta banza domin baki da hujjar da zaki tabbatar da cewar kece kika lashe wannan gasa taku a wajen mahaifinki sarkin mafarauta na birnin taheren koda gama ayyana hakan sai ta fara tunanin irin dabarar daya kamata tayi don shiga kasan wannan mugun rami ai kuwa bata dade tana tunanin ba dabara ta zo mata wannan igiyar tata mai kugiya ta sake fiddowa ta sakalata a jikin wata bishiya mai kauri ta sulala izuwa kasan ramin sannan ta runtse idanunta ta fara yin wani irin sihirin tsafitake igiyar ta ringa karawa kanta tsawo tana sauka izuwa kasan ramin nan fa luslaiya ta rinka ganin zurfin ramin a cikin idanunta ai kuwa igiyar bata isa can karshen ramin ba sai bayan sa a uku al amarin daya yi matukar dugunzuma hankalin luslaiya kenan amma da yake bata da wani zabi dole ta kama igiyar ta fara sauka kasan ramin kafin luslaiya ta isa kasan ramin saida ta shafe tsawon sa a ukun ta sha bakar wahala kuma babu yadda bata yi ba ta isa kasan ramin da sauri bisa karfin tsafi amma abu ya gagara koda ta dira a karshen ramin sai tayi arba da gawata a kwance cikin rub da ciki ga ramin da kashin dabba yayi min a gadon bayana cikin farin ciki ta matso daf dani ta tsugunna tana haki sakamakon muguwar gajiyar da tayi don haka dolene ta huta tsawon lokaci sannan ta dauke gawata ta saba a kafadarta ta kama igiyar ta hau tayi sama wannan tunani da tayine hankalinta ya dugunzuma ta tuno da wahalar da tasha ita kadai bare kuma yanzu ga dakon gawa sai da luslaiya ta shafe sa aguda tana huce gajiya dake jikinta sannan ta mike tsaye ta kama gawata da nufin ta dorata akan kafadarta kwasam ba zato ba tsammani sai taji nasa hannuna na tunkudeta ta fadi can gefe daya cikin tsananin juriya da zafin nama na kama rigar jikina na yageta sannan na daure ramin raunin jikin nawa kuma na mike tsaye bisa kafafuna na dubeta tana daga zaune a kasa dirshan gaban kwarangwalolin dabbobi da mutane nace har yanzu ban mutu ba don haka gasa bata kare ba saimu ci gaba saboda tsananin kaduwa da mamaki luslaiya kasa yin magana tayi da motsi kawai saita bude bakinta tana kallona kawai daga can saita bushe baki tace kai mutun ne ko Aljan? Yaya akayi ka rayu baka mutu ba alhalin ga wannan mugun rauni a cikinka mazajen kwarai basa faduwa a banza domin ransu tamkar na karfe ne Ina gama fadin hakan sainayi wuf na finciko jakar guzurinta na budeta na fiddo ragowar wannan gasasshshen tsuntsu data boye na kama ci har saida na koshi ina gamawa na zura hannuna a cikin aljihuna na fiddo wani kullin garin magani na zazzagashi akan raunin cikin nawa take wajen ya kama turon da hayaki tamkar wuta aka zuba masa na rinka ihu da kururuwa saboda tsananin zafi da Radadin da naji har saida raunin yayi baki kirin kuma ramin ya toshe tamkar wajan bai taba hujewa ba sannan na daina ihu da kururuwa kawai saina dubi luslaiya nace tare zamu hau wannan igiya taki mu fice daga cikin wannan rami don bazan yarda ki rigani fita ba koda sarki Alkasim yazo nan a cikin labarin da yake baiwa yarima kamsus sai ya daga masa hannu yana mai dakatar dashi yace tsaya haka yakai Abbana nifa gaba daya kaina ya daure da jin abubuwan da suka faru a cikin wannan labari naka Wai shin kana son kace dani sai da kuka kammala wannan gasa kenan? Anya kuwa zaka gama bani wannan labari kafin mu isa birnin sarki Masarul Anjana? . SHIN ME ZAI FARU A CIKIN TAFIYAR YARIMA ALKASIM DA JARUMA LUSLAIYA? KAFIN SU KAMMALA GASARSU HAR TA KAMU DA SONSA SUYI AURE KUMA MENENE SANADIN AJALINTA? IDAN AKA ISA GARIN SARKI MASARUL ANJANA ME ZAI FARU TSAKANIN GIMBIYA ZULFULAIFA DA YARIMA KAMSUS KUMA MAI ZAI FARU A TSAKANIN SARKI ALKASIM DA SARKI MASARUL ANJANA? INA LABARIN JARUMI ZAIHADA DA YAR'UWARSA? SHIN ZASU SAMU NASARAR DAUKAR FANSA AKAN SARKI ALKASIM???