*************************⬇********************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** [2/29, 6:28 AM] Matr Mamman: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸 HAJIYA DUDUWA ME KAN BARI 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story & Written by Rahmat Matar Mammam Dasunan Allah mai Rahma mai jinkai Ina rokon Allah yadda ya bani ikon fara littafin nan ya bani ikon ga mashi lafiya. Sadaukarwa ga mutanen boye🙊🤣 ❌not editing❌ 🅿👉🏻1⃣&2⃣ ''''''Dandaline cike da "yan mata da samari kidan kalangu na tashi masu rawa nayi masu kallo nayi,sai "babbaka dariya suke. Gefe guda na hango wata "yar matashiya tana zaune akan wani gungumen itace,sai shan rake take tana susar kai. Kara matsowa nayi kusa da ita, dariya ce ta kubce mun, ganin irin kwalliyar dake fuskar ta, fuskar tasha panti da wata jar hoda.tayi wasu irin digo_digo a kumatu har zuwa goshinta. Sannan taja kwalli a kan girarta har kusada kunne ga wani irin jan Jan baki da tasa a saman leben ta kamar zai zube a kasa tsabar yawa. Tana shan rake abunda hankali kwance tana susar kanta. Jitayi ana kwala mata kira,HAJIYA DUDUWA ME KAN BARI hade rai tayi,bata motsa ba tashigaba da shan rakenta ruwan raken duk ya bata mata jiki. Karasowa budurwar tayi ta tsaya akan ta tace Hajiya duduwa me kan bari, tun daga nesa nake kwala maki kira.kikayi banza dani. Tashi tayi shikeda masifa tace kinga Asabe mai kunu ban son iya hege kina kwala min kira kamar wata uwata ko kin ban ajiya ne? Asabe mai kunu tace aa ban baki ajiya ba inna ce take nemanki wai kizo ga yaya talle yazo. A zabure ta tashi tana mai dafe kirji na higa uku ni Duduwa dan Allah dagaske kike? Dafe hanci Asabe mai kunu tayi kai Duduwa har yanzu baki bar halinki nasake wannan hegen tusan mai tsananin wari ba. Batako saurari Asabe mai kunu ba ta suri sauran raken da saurayinta idi yasaya mata ta ruga a guje. Asabe mai kunu tace yanzu Duduwa bazaki tsammin raken ba.juyowa tayi ta galla mata harara tace yaseen bazan baki ba. Nima idi ne yasaya min in kina so kema kice Audu ya saya miki.ta cigaba da gudu abunta Bin ta yi da kallo har takule dafa kafadar ta akayi ta juyo Ladi mai awara kece murmushi ladi mai awara tayi tace banda ke da abunki Asabe mai kunu inake ina rokon Duduwa me kan bari kinsanta da hegen rowa,kekuma gaki da hegen kwadayi kamar mai ciki. Harara Asabe mai kunu ta dalla wa Ladi mai awara tace to zageni,dariya ladi me awara ta sheke da ita Allah yabaki hakuri mai kunu na isa in zageki, aminiyata Audu ne yakaraso yana washe jajayen hakoransa. Aa wayata bamin Asabebe na ya fada yana mai buga gorar dake hannunsa a kasa ladi me awara tace itada mutuniyar tace Duduwa me kan bari kasan Duduwa da hegen rowa ita kuma mutuniyar taka Asabe mai kunu ta dalla mata harara tace nikuma me iyehh? Audu yace ladi me awara fadamun me Duduwa ta ma Asabebe na dariya tasake shekewa da ita tace rake tahanamu tace idan tana son sha tafada ma itama idi ne yasaya mata. Yace rake kawai ladi me awara tace eh yace Asabebe na saki ranki yanzu zakisha rake har sai kinji ya isheki. ✨✨✨✨✨✨✨ Hajiya Duduwa me kan bari guduwa take kamar zata tashi sama tana ta surutai, Yaw idan yaya talle ya kamani sai yayi perpesu na na higa uku ni Duduwa dan zan fita saida inna ta hanani naki gashi yau zan sha suburbuda a hannun yaya talle Ya Allah kasa kar yaya ya dakeni. Hakatacigab da gudu tana sambatu jitayi an riketa cak ta tsaya ta juyo kawarta jummai me panke tagani cikin kwalliya. Kamar kamar ta ta taci damara da wata gyale tana rike da kara a hannunta. Tace Duduwa me kan bari me yake faruwa ne naganki a wani hargitse,tace humm!kedai bari ina cikin tashin hankali yaya talle ya dawo daga legas. Zaro ido jummai me panke tayi yauce yaya tallen yadawo cikeda kosawa tace jummai me panke ina zan sani kinsan tun safiya na fice daga gidan. Jummai me panke tace kinsan me wannan adu'ar da muka taba yiwa mallam me tozo shi zakiyi yanzu yaya talle bazai jibgeki ba. Rike haba tayi tace qur'anin ubangiji namanta da adu'ar jummai me panke tace to zan tuna miki amma sai kin tsammin raken ki. Harara ta galla mata tace yasiin bani bada raken nan idi ne yasaya min kema idan kinaso sai ki fada ma mudi ya saya miki jummai me panke tace to hikenan kije kisha duka agun yaya talle kinga tafiya ta. Jawota Duduwa tayi tace haba jummai kawata kinsan dai bazan hanaki rake na bako kiyi hakuri gaci. Tamika mata wanda takesha yamutsa fuska me panke tayi tace banason wannan wanda baki fara sha ba nakeso. Duduwa kamar ta makure jummai me panke takeji saboda haushi ba abunda ta tsana kamar tayi kyauta. Mikamata wanda bata fara sha dinba tace fadamun kar in kara bata lokaci. Jummai me panke tace to ga adu'ar "zanagurugu lakumu ya ayyuhassakalimi" Rugawa tayi a guje tana maimaita adu'ar. Banke kofar gidansu tayi da karfi ta ciga inna dake tuka tuwo tajuyo tace Allah ya shiryeki ace mutum kullum ana masa magana akan Abu daya. Kicigoma mutane gida kamar an koroki wai ke Duduwa yaushe zaki girma kiyi hankali ne.tana tsaye tana susar kai sai rarraba ido takeyi. Jitayi anyi mata wata mahaukaciyar damka ta kurma ihu wayyo innata na mutu na lalace............✍🏻 Kubiyoni a next pg dan jin waya damke Hajiya Duduwa me kan bari Shin wannan adu'ar tata zata karbu kuwa kudai ku biyoni. Comments dinku shi zai tabbatar min da littafin ya muku in shigaba Comments and share Matar Mammam ce👐🏻 [2/29, 6:28 AM] Matr Mamman: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 HAJIYA DUDUWA ME KAN BARI 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story & Written by Rahmat Matar Mammam Bismillahirrahmanirrahim Labarin Hajiya Duduwa me kan bari kagaggen labari ne Sadaukarwa ga mutanen sarari🤣🤣 🅿👉🏻3⃣&4⃣ """"""Wayyo Allah yaya talle kayi hakuri kar ka sheqene,karatun allo naje bayan muntaci kuma sai Asabe mai kunu tace in raka dandali. Falla ma bakinta mari yaya talle yayi ki rufe mun baki yanzu tasake saka wani ihu wayyo Allah jama'a a zo aceceni yaya talle zai kaheni. Ran yaya talle yakara baci ya daka mata tsawa ke zan zubar miki da hakwara idan baki rufe bakinki ba, Sake kurma ihu tayi wayyo baffana yaya talle zai zai cire mun hakwara,haushin yaya talle ne yacika inna ganin yakasa dukan Duduwa me kan bari. Cikin bacin rai tace yaro me katsaya kallo ne ko yaw ma biyema shirmen ta zakayi bazaka hukuntata ba. Ya furzar da iska cikin bacin rai yace kina ganin tun ban mata komai ba tana kokarin tara mun jama'a inna tace bani ita anan idan bazaka iyaba. Yace aa inna barni da ita Jan hannunta yayi har bakin itace mangwaro dake tsakiyar gidan yaja igiyar da suke daure dabbobi da shi ya daure ta tana ihu da kuruwa amma saida ya daureta. Yaje ya daura alwala ya wuce masallaci,Duduwa me kan bari a daure amma bakinta bai mutu ba sai ihu take tanata sambatu. bata ishi inna kallo ba alwala ma ta daura ta shige cikin kurya sai bayan sallar isha'i yaya talle ya cigo gidan,Duduwa na jin muryar baffa ta bude murya tana ihu da kururuwa wayyo ni Duduwa ba'asona an daure kamar akuya. Nashiga uku na lalace ni Duduwa inna bata sona yaya talle ma baya sona ya pasa mun baki ya cire mun hakori. Baffa na gab da cigowa gidan yaji yadda Duduwa me kan bari ta ke ihu da maganganu,Sauri yake kamar zai kife a kasa ya cigo gidan. Cikin sauri ya nufi inda aka daure Duduwa ya kwanceta, yana kwance ta ta kwanta a kasa flat kamar matatta tana wani irin nunfarfashi hankalin baffa ya tashi matuka. Ya kwala ma yaya talle kira yaro!!!yaya talle ya taho ransa a bace yace baffa sannu da dawowa wani kallo baffa ya masa yace ............✍🏻 Comments and share Matar Mammam ce👐🏻 [2/29, 6:29 AM] Matr Mamman: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 HAJIYA DUDUWA ME KAN BARI 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story & Written by Rahmat A Abba Jada Matar Mammam Bismillahirrahmanirrahim Sadaukarwa ga mutanen boye🙊🤣 da mutanen Sarari🤣😁 ❌Not Edition❌ 🅿👉🏻5⃣&6⃣ "”""dauketa ka kaita daki burinku ya cika kun kashe mun "ya yajuya cikin azama yafita cikin gidan Duduwa me kan bari ta bude idonta gudaya tana kallon inna da yaya talle dake tsaye cirko_cirko kasa_kasa Yaya talle yace inna kinga iya shegen Duduwa me kan bari ko? Muzata nunawa iya shege nida nake zaune a legas,zata nunawa hauka. Inna tace yaro kayi abunda baffanku yace kafin yadawo in bahaka ba kasanci ba kyalemu zai ba yace inna barni da fitsararriya ina zuwa Duduwa me kan bari najin abunda yaya talle yafada ta zabura ta kurna ihu taruga a guje tanufi hanyar fita. Yaya talle yabi bayanta inna tace nashiga uku saude wannan wace iriyar yarinaya ce Allah ya shiryamun ke. Taku daya biyu yaya talle ya shafkota.ihu tasa da kargin gaske saida gabadaya unguwar ta amsa baffa da ke kofar shigowa gidan shida malam me tozo. Ya ruga cikin gidan har yana tuntube yakarasa shigowa yaga Duduwa me kan bari a hannun yaya talle yamata damka mai kyau sai mutsu_mutsu take. Malam mai tozo ya shiga yace subhanallahi saketa talle yaya talle yasaketa. Malam mai tozo ya karaso kusada Duduwa me kan bari yace zauna Nutsuwa tayi ta zauna,kamar gaske. Yajuya ya kalli baffa yace wato malam sule abunda nagani ajikin yarinyar nan yabani mamaki,aljani guda dari ba daya ne suka ciga jikinta. Waro ido Duduwa me kan bari tayi kamar zata fashe da dariya ta daure ta maze baffa yace subhanallahi yanzu ya za'ayi,malam mai tozo yace eh to zamuyi mata rukiya da hayaki yanzu zasu fita. Malam mai tozo yace yaya talle yazo ya rike mai Duduwa me kan bari, zabura tayi zata tashi yayi saurin riketa gam takasa yin koda kwakwaran motsi. Malam mai tozo yafara karatun rukiya kamar haka. Kulli shashinnn ya tattaro "yawun bakinsa ya tofe ma Duduwa me kan bari a fuska tuuuph.wanafsin shashin.tuuuuuph! Washashin kulli wanafshin kulli washashiii tuuuuph Haushin malam mai tozo da kyamar "yawunsa yasa Duduwa me kan bari kurma ihu. Malam me tozo yace yawwa goma sun fita, tayi kokarin fisgewa ta gudu amma takasa yaya talle yayi mata rikon maza haka malam me tozo yayi ta tofe Duduwa me kan bari da "yawunsa haushin su yasa Duduwa yin luf ta daina motse_motsen da take. Malam me tozo yace da inna debo gaushi mu mata hayaki Azabure Duduwa me kan bari ta mike wallahi ba abunda ke damuna ni ku kyaleni wayyo baffana zasu kasheni ihu take hade da kururuwa kan kace kwabo gidan yacika taf da mutane. Kamata yaya talle malam me tozo yace kawo ta nan abamu zani ina takawo babbab zani aka rufawa Duduwa me kan bari tana ihu tana kuruwa amma ba wanda yasaurareta. Danne kan ta yaya talle yayi akan kaskon gaushin malam me tozo ya zazzaga garin maganin hayaki ya tashi ihu takeyi tana kuka tana tsinewa yaya talle da jummai me panke. Wallahi jummai me panke sai kin biyani rake na tsinanniya kawai ni zakiyiwa karya gashi nayi asarar rake na Allah ido na idonki sai kin bani rake na. Adu'a bata karbu ba nasha mari ga dauri ga hayaki Allah ya isana Saida tari ne ya saketa tayi ta tari Malam me tozo yace a bude ta ana budeta idon ta ya kada yayi jazur. Sai jawa yaya talle da jummai mai panke Allah ya isa take tashi tayi na nufi daki tana jin malam nayi ma baffa bayanin yadda zatayi anfani da magungunanda ya hada mata. Taba makaryaci kawai wai sun dauka dagaske aljanu ne suka shigeni, hhhhhhh!!kai amma malam ya kware wajen iya karya wai aljanu dari ba daya tasake fashewa da dariya inna da ke tsaye akanta tana kallonta tace Allah ya shirya mun ke. Tace Ameen inna ta Tace aranta dayanzu nasha suburbuda a wurin yaya talle nasan baffa ma bazai goyan baya ba Allah yakaimu gobe wata zataci banten...... (🙊tab kar inji mazgah ban na fece🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀) Washegari tun da sanyin safiya sa'daf_sa'daf Duduwa me kan bari ta lallaba ta nufi kofar fita baffa dake fitowa daga daki yace ina kuma zaki yanzun da sauri ta juya aa baffa akuyar gidan su larai ce tashigo tana cin masarar da inna ta shanya shine nake korar ta tafada tana kifkifta ido hade da susar kai baffa ya kada kai yace to tunda akuyar ta tafi dawo ki zauna. Cikin sanyin jiki ta dawo ta zauna tana Allah Allah baffa yafita ita ma tasamu ta fita burin ta kawai tahadu da jummai me panke ta biyata raken ta....................✍🏻 Idan naga comments anjima inyi typing 😁 Comments and share Matar Mammam ce 👐🏻 [2/29, 6:30 AM] Matr Mamman: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 HAJIYA DUDUWA ME KAN BARI 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story & Written by Rahmat A Abba Jada Matar Mammam Bismillahirrahamanirrahim Sadaukarwa ga mutanen boye🙊🤣 Kagaggen labarine kuma gajeren labari 🅿👉🏻7⃣ """"Tana zaune tana susar kai sai kifkif da ido take baki a zumbure,inna tafito daga cikin bayi ta kura mata ido na tsawon mintuna ta kadai. Allah ubangiji ya shirya mun ke tanufi daki tsayawa tayi kamar wacce ta tuno wani Abu tajuyo ga duduwa me kan bari tace,ke duduwa me kan bari ban hanaki zama akan turmi bane. Susa kai tayi takara zumbura baki tamike tana kunkuni ta nufi dakinta inna tace Allah ya shirya mun ke baffa,dake kokarin fita ya amsa da amin. Duduwa me kan bari najin inna nayi ma baffa adawo lafiya ta daka tsalle tafada kan "yar karamar gadon karfen dake dakin tace Allah ya tsaremun baffana. Yanzu kuma jummai me panke zata ga bala'in hajiya duduwa me kan bari ta kyalkyale da dariya inna dake waje tana jinta tace oh ni saude ace diya ba nutsuwa kokadan tananan kamar ruwa a cikin daro,wuf duduwa me kan bari tafice daga cikin dakin. Ta leka dakin yaya talle taga akulle tace yawware mugun bayanan a guje tanufi kofar fita bata ko saurari inna da ke kwala mata kiraba. Tunda ta fita bata tsaya a koina ba sai kofar gidan su jummai me panke tana zuwa taga kannen jummai me panke suna tsalle_tsalle a kofar gidan tace kai habu zonan habu na zuwa kusada ita yace gani yaya duduwa. Jeka kiramun yayarka yace ay batadawo tallar panke ba batadawo ba yace tace dakyau hakan ma daidai ne tajuyo da gudun bala'i ta nufi dandalin tallar su. Yadda take guduwa haka take sake tusa jikake "bararararaaaaaa" kamar tsohuwar machine YAMAHA (🙊🙈) Tun daga nesa jummai me panke ta hango duduwa me kan bari tana tahowa a guje tasan tsiya ne yakawota,taraya aranta za'a kwaci "yan kallo yaw. Jitayi anyi kwallo da bokitin pankenta gabadaya panken ya watse a kasa almajirai suka fara wasoso. Tace kan batasi wace "yar (🙊momy tahanani karasawa🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀) Tazubar mun da panke duduwa me kan bari tace nice nan hajiya duduwa me kan bari 'diyar baffa da inna kuma kanwa ga yaya talle, kina da maganane tace tab aiko yaw za'ayi yakin duniya na uku. Duduwa me kan bari tace hehehehehh!! Sannu Hitiler yake kowa, nidai ba wannan ba rakena zaki bani jummai me panke tace eyehh kaji karfin hali,to wallahi bazan bayarba saidai kiyi abunda zakiyi. Tace haka kikace eh hakana nace Duduwa me kan bari ta zare dankwalinta taci damara aiko itama jummai me panke ta cire nata dankwalin tayi damara itama wani dattijo dake zaune yana shan kunu a gefe baiyi magana ba sai yanzu yace kar wacce ta kuskura tace zata yi fada tika_tikan "yammata daku kuma kawaye kuce zakuyi fada. Asabe mai kunu da ke dariya tun da suka fara shashar bakin tace aa baba kyalesu su daku ay kowa da gaskiyarsa ita jummai me panke an barar mata da pankenta itako duduwa me kan bari an cimata rake kaga ko dagaskiyar su ladi me awara ta amsa kwarai kuwa ay sun fi kusa mu jiya da muka roketa raken ba hanamu tayi ba tace idi ne yasaya mata muma mu fada ma samarin mu su sai mana. Larai me waina tace kunsan fadan duduwa me kan bari yadda yake kuce abarsu gwara dai arabasu ni anawa ganin Baba yatashi yace ke duduwa maza ki bar nan. Ta zumbura baki tace baba kace tabiyani rakena baba yace bake kika zubar mata da panke ba ay shikenan madadin rakenki kenan duduwa me kan bari ta dora hannu aka ta zunduma wani ihu tace wayyo. Baba yace ke bakida hankali ne,nace ki barnan ko yanzu in bata miki rai cikin kunkuni tace wallahi sai ta biyani rakena kuma saina rama marin da yaya talle yamun eheh ta murguda baki. Baba yace ni kikewa kunkuni yabita taruga a guje taje ta boye a bayan wani itace tana hangosu jummai me panke ta dauki bokitin pankenta takama hanyar gida duduwa me kan bari tace yawwa ay dole ki biyani tabi bayanta. Jummai me panke natafiya kawai saiga duduwa me kan bari a gabanta, tace bani rakena jummai me panke tace bani badawa. Dake itama a cike take da duduwa me kan bari nan take kokowa ta barke a tsakaninsu dukansu sun daku sai haki sukeyi tsawa sukaji a bayansu cikin duduwa me kan bari ne yayi wata irin kadawa ya duri ruwa jin muryar yaya talle abayansu tasan yaw mai kwatar ta ahannun yaya talle sai Allah gashi baffa yatafi kasuwa inna kuma ko kasheta zaiyi bazata ce uffan ba saima takara zugashi. Sake jummai me panke ta yi tafara rantse_rantse tace yaya talle wallahi ita tafara tsokanata,inna ce ta aikeni sai muka hadu da ita takamani da fada. Jummai me panke ta ce karya take yaya talle har wajen sana'ata tabiyoni tabarar mun da panke na. Yaya talle yace Ashshahh nawane kudin panken jummai me panke ta ce yaya talle talatin ne sa hannu yayi a aljihu ya lalabo talatin ya mikamata. Yace jeki gida kiyi hakuri karba tayi tace yaya nagode duduwa me kan bari ta ce kutt sai kin biyani rakena wallahi babu inda zaki. Yaya talle yadaka mata tsawa keeee!wuce mutafi gida duduwa me kan tace wallahi yaya talle...kan ta karasa taji saukar mari a fuskarta saida taga wasu taurari biyu.tace wayyo Allah baffa namutu jan hannunta yaya talle yayi suka nufi gida...............✍🏻 Comments and shared Matar Mammam ce👐🏻 [2/29, 6:30 AM] Matr Mamman: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 HAJIYA DUDUWA ME KAN BARI 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story & Written by Rahmat A Abba Jada Matar Mammam Bismillahirrahamanirrahim Sadaukarwa ga mutanen sarari🙊🤣 Kagaggen labarine kuma gajeren labarin 🅿👉🏻8⃣ """"""Tafiya suke duduwa me kan bari na kurma ihu wayyo Allah baffa na namutu na lalace yaw yaya talle yasamu nama sai yayi perpesuna. Wayyo Allah jama'a ataimaka abaiwa yaya talle hakuri kar yadakeni tsawa yaya talle yadaka mata tayi tsit tana kifkif da ido,suna zuwa kwanar gidansu duduwa taja tunga ta tsaya. Yaya talle yace wuce muje,ta fara rantse_rantse wallahi tallahi yaya talle cikina na ciwo bazan iya zuwa gidaba,ta sulale ta kwanta a kasa ta kama birgima wayyo ni duduwa me kan bari cikina. Zan mutu yaya talle kayafe mun duk abunda namaka nasan ni tawa ta kare kataimaka ka kira mun inna zan bata wasiya ne birgima take tana sambatu. Wayyo yaya talle kaga wasu mutane da fararen kaya sun zo wai inbi su mutafi ko wallahi bazan,bikuba ni zan zauna da yaya na da innata masu sona ku tafi ku kyaleni. Sororo yaya talle ya tsaya yana kallon ikon Allah yace lallai Duduwa me kan bari abun naki ya wuce sanin tunanina ni zaki gwada fitsara ko to bari ina zuwa. Yafara nade hannun kodaddiyar rigarsa,cak ya dauke ta yadorata a kafadarsa kamar ya dauki buhu, Yanufi hanyar gida duduwa me kan bari fah baki ya mutu sai zuzzura ido takeyi kamar na mujiya. Duk inda suka wuce mutane sai sun tambayi me yake faruwa haka amma ko kallo basu ishi yaya talle ba duduwa dai tana asankame a kafadar yaya talle kamar mutum mutumi. Suna shiga cikin gidan yaya talle yasauketa,yaji wani iri wari da abu mai zafi akafadarsa yana gangarawa ta bayansa . Inna tasaki salati tace yanzu duduwa me kan bari saboda tsabar iya shege da fitsara zawo kika yi yaya talle yajuyo afusace ya shake duduwa me kan bari yafara zuba mata mari a fuska,ni zakiyiwa zawo a jiki qur'anin ubangiji yaw sai kin yabawa aya zakinta. Yashigabada sambada mata tafi a fuska tana ihu tana wallahi yaya bansan nayi zawo ba tsautsayine Allah wasu masu fararen kayane suka tsorata ni Allah wallahi. Saida ya suburbudi duduwa me kan bari da kyaw kafin yaje ya cire kayan yazo ya watsa mata su maza,maza dauki kayannan ki wanke yanzu in bai fitaba zakisha duka. Duduwa me kan bari ta dora hannu akai wayyo Allah na mutu na lalace yaya talle kasan ban iya wanki ba gubbbb ya buge mata baki ya daka mata tsawa dauki nace daukar kayan tayi tana kuka tana wankewa,yana tsaye akanta datayi wani kuskure ya labta mata duka da dorina kai yaw dai duduwa me kan bari tasha suburbuda a hannun yaya talle. Duk aiyukan gidan ita tayisu tanayi tana kuka,ta qagu baffa yadawo tasan yaw mai raba baffa da yaya talle sai Allah. Bayan tagama duk ayyukan da ke taje ta zauna a hanyar kofar gida taji tahowar baffa tasa kuka tana dafe ciki wayyo Allah na baffa na yunwa zai kashe maka 'diyar ka rabona da abinci tun karin safe yunwa zata sheqeni ni duduwa me kan bari gashi baffa na baya kusa dani wayyo Allah cikina tafara birgima akasa inna. Najinta ta kada kai Allah ya shirya mun ke duduwa me kan bari, da sassarfa baffa ya shigo gidan daga ta yayi yana share mata guntun hawayen da ta kakalo yi shuru daina kuka ki fada mun me ya faru. Kasa tsayuwa tayi wayyo baffa kafafuna sun karye wallahi bazan iya tsaiwa ba an karyamun kafa wayyo Allah. Ran baffa ya baci matuka ya kwala wa inna kira saudeh!!! Inna tafito cikin dakin tace malam sannu da dawowa,me akayiwa duduwa gashi takasa tsaiyuwa inna tace mekuma za'a mata ka tambayeta man. Ran baffa yaqara baci musamman ma da yaji duduwa me kan bari tana kiran "yunwa zai kasheta ina yaro ya tambayi tace yafita be dawoba. To tayain mu kaita daki inna tace wa bafa abunda yasameta iya shegene kawai irin nata wani kallo baffa yamata yasa dole suka riketa suka kaita dakin yace kawo abinci yanzunnan inna tace taci abincinta fa. Baffa yace saude wai kina nufin ban isa insakiyimin abuba,tace aa malam Allah yabaka hakuri. Tawuce ta kawo abincin baffa yafara bata abincin abaki tsaf duduwa me kan bari ta shinye abincin. Sai sannu baffa yaketa jera mata yajuyo yafara yiwa inna fada ta inda yashiga batanan yake fita shikuma yaron zai dawo yasameni............✍🏻 Comments and share Matar Mammam ce👐🏻 [2/29, 6:31 AM] Matr Mamman: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 HAJIYA DUDUWA ME KAN BARI 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story & Written by Rahmat A Abba Jada Matar Mammam Bismillahirrahamanirrahim Sadaukarwa ga mutanen boye🙊dana sarari🤣🤣 Kagaggen labari ne kuma gajeren labari 🅿👉🏻9⃣ """"Sallamar yaya talle ne ya katsewa baffa bunbunin dayake tayi,yawwa gara da Allah ya dawoda kai kazo kamun bayanin dalilin dukar da kayiwa wannan yarinya. Duduwa me kan bari najin baffa yace yaya talle yayi masa bayanin dalilin dukar ta sa ihu wayyo baffa hannu na yayi targade. Arikice baffa ya cigo dakin inna takada kai makarcin Hajiya duduwa me kan bari na bata tsoro tasan idan yaya talle yafada masa abunda tayi baffa bazai goya mata bayaba shiyasa ta kurma ihun. Baffa na shigowa dakin yakama hannun ya rike sannu uwata Allah yasawwake,ya kwalawa yaya talle kira kai yaro!!. Yaya talle yashigo dakin maza jekakira malam me tozo yazo yaduba mata hannun duduwa me kan bari najin za'a kira malam me tozo ta kara rikicewa wallahi baffa bana son akira shi ni abarni hannuna zai warke,ko bai zoba kuka take wiwiwi. Bata son akira malam me tozo ganin kukan yayi yawa ne yasa baffa yace to yaro maza zo ka jamata hannun badon yaya talle yaso ba ya zo ya jamata hannun. Duk da zafin da duduwa me kan bari takeji haka tadaure tacije tace a ranta kaima kaji wahalar danaji saura inna kuma. Bayan yaya talle yagama jan hannun tace baffa zan sha kunun tsamiya cikin sauri baffa ya juyo yace saude yi sauri ki damamata kunun inna sake baki tayi tana kallon baffa Yanzu malam biyewa shirmen duduwa me kan bari zakayi bafa abunda ke damunta iya shegene kawai. Baffa ya kulu iya kuluwa bai cemata uffan ba yamike yanufi kofar fita tunda Allah yasa tanada uba ay Alhamdulillah zan damamata, dakaina inna tayi saurin bin bayansa malam yi hakuri abun bai kai ga hakaba bara in damamata. Duduwa me kan bari tasaki murmushin jin dadi hooh baffa na Allah yabar mini kai rankwashi taji akanta tsabar zafin rankwashin batasan sanda tasaki tusa mai sauti ba jikake phiiiiiiiiit!!!kamar horn din mota(🙊🤣🤣🤣) Tabude baki zatayi ihu yaya talle yayi sauri ya rufe mata baki yace karki yi ihu idan bakiyi ihu ba zan baki goma kisai rake kada kai tayi alamar bazatayi ihun ba ya shire hannunsa akan bakinta ya zauna a gefen ta duk haushi yabi ya cikasa ga abun duka ba damar dukan yaraya aransa zamu hadu dake gobe ay baffan ba sabarki zaiyi a kafada ya tafi kasuwa dake ba. Baffa ne ya shigo da kunun a wata babbar Kofi saida ya fifita kunun tukun kafin yabata,ta zunbura baki tace babu sukari baffa bazan iya sha ba tafada tana mai kakalo hawayen karya. Baffa yace yaro yi maza kaje shagon Dan tani ka karbo mata sukarin bayadda yaya talle ya iya ya karbi kudin ya fita. Washe gari bayan baffa ya fita kasuwa da doguwar gargadi da yayiwa yaya talle da inna akan duduwa me kan bari tsabar takaici ma ya hana yaya talle yazama cikin gidan. Duduwa me kan bari na ganin yaya talle yafita tamike tanufi kofar fita inna tace karki sake kibar gidannan tajuyo da sauri inna rakena zanje in karbo a wajen jummai me panke tace koma menene kika kuskura kika fita gidannan sai ranki ya baci. Tace inna bafa zataci bulus ba eheeh ba baffa yace duk abunda nakeso a barni inyiba inna tace bazaki fitaba muddin kika sa kafa kika bar gidannan kuma duk abunda yasameki ki kuka da kanki,tace ba abunda sai alheri. Tajuya tafice aguje kamar wacce aka koro gudu take kamar wata sabuwar kamu cak ta tsaya sakamakon hango malam mai rawani yana tahowa duk iya shegen duduwa me kan bari tana shakkar malam me rawani. Sumkuyar da kai tayi kamar mara gaskiya,har saida ya wuce ta dago kai tace Allah yasoni bai ganeniba da yanzu yafaramun wannan shirmen nasihar tasa. Kaitsaye ta wuce dandali amma tana isowa akace jummai me panke tatafi yo icce tace ay ko sai na bita. Wucewa tayi abunta masifa na cinta tafiya take tana "yan wake_wake da tsalle_tsalle har ta iso wani rafi tsayawa tayi cak taga yadda ruwa ke gudu tace Allah yaw saina ga kaeshen rafin nan yadda ruwan yake gudu bari in gwada bin ruwan nima cire takalminta tayi tasakalasu a hannayenta tayi damara tafara bin gefen rafin tana gudu tana kallon ruwan Allah yaw saina riga ku zuwa inda kuke zuwa ta kyalkyale da dariya ta Ruga aguje...........✍🏻 Hhhhhh🤣🤣🤣🤣 Hajiya duduwa me kan bari ayi gudu lfy Comments and share Matar Mammam ce👐 🏻[2/29, 6:28 AM] Matr Mamman: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸 HAJIYA DUDUWA ME KAN BARI 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story & Written by Rahmat Matar Mammam Dasunan Allah mai Rahma mai jinkai Ina rokon Allah yadda ya bani ikon fara littafin nan ya bani ikon ga mashi lafiya. Sadaukarwa ga mutanen boye🙊🤣 ❌not editing❌ 🅿👉🏻1⃣&2⃣ ''''''Dandaline cike da "yan mata da samari kidan kalangu na tashi masu rawa nayi masu kallo nayi,sai "babbaka dariya suke. Gefe guda na hango wata "yar matashiya tana zaune akan wani gungumen itace,sai shan rake take tana susar kai. Kara matsowa nayi kusa da ita, dariya ce ta kubce mun, ganin irin kwalliyar dake fuskar ta, fuskar tasha panti da wata jar hoda.tayi wasu irin digo_digo a kumatu har zuwa goshinta. Sannan taja kwalli a kan girarta har kusada kunne ga wani irin jan Jan baki da tasa a saman leben ta kamar zai zube a kasa tsabar yawa. Tana shan rake abunda hankali kwance tana susar kanta. Jitayi ana kwala mata kira,HAJIYA DUDUWA ME KAN BARI hade rai tayi,bata motsa ba tashigaba da shan rakenta ruwan raken duk ya bata mata jiki. Karasowa budurwar tayi ta tsaya akan ta tace Hajiya duduwa me kan bari, tun daga nesa nake kwala maki kira.kikayi banza dani. Tashi tayi shikeda masifa tace kinga Asabe mai kunu ban son iya hege kina kwala min kira kamar wata uwata ko kin ban ajiya ne? Asabe mai kunu tace aa ban baki ajiya ba inna ce take nemanki wai kizo ga yaya talle yazo. A zabure ta tashi tana mai dafe kirji na higa uku ni Duduwa dan Allah dagaske kike? Dafe hanci Asabe mai kunu tayi kai Duduwa har yanzu baki bar halinki nasake wannan hegen tusan mai tsananin wari ba. Batako saurari Asabe mai kunu ba ta suri sauran raken da saurayinta idi yasaya mata ta ruga a guje. Asabe mai kunu tace yanzu Duduwa bazaki tsammin raken ba.juyowa tayi ta galla mata harara tace yaseen bazan baki ba. Nima idi ne yasaya min in kina so kema kice Audu ya saya miki.ta cigaba da gudu abunta Bin ta yi da kallo har takule dafa kafadar ta akayi ta juyo Ladi mai awara kece murmushi ladi mai awara tayi tace banda ke da abunki Asabe mai kunu inake ina rokon Duduwa me kan bari kinsanta da hegen rowa,kekuma gaki da hegen kwadayi kamar mai ciki. Harara Asabe mai kunu ta dalla wa Ladi mai awara tace to zageni,dariya ladi me awara ta sheke da ita Allah yabaki hakuri mai kunu na isa in zageki, aminiyata Audu ne yakaraso yana washe jajayen hakoransa. Aa wayata bamin Asabebe na ya fada yana mai buga gorar dake hannunsa a kasa ladi me awara tace itada mutuniyar tace Duduwa me kan bari kasan Duduwa da hegen rowa ita kuma mutuniyar taka Asabe mai kunu ta dalla mata harara tace nikuma me iyehh? Audu yace ladi me awara fadamun me Duduwa ta ma Asabebe na dariya tasake shekewa da ita tace rake tahanamu tace idan tana son sha tafada ma itama idi ne yasaya mata. Yace rake kawai ladi me awara tace eh yace Asabebe na saki ranki yanzu zakisha rake har sai kinji ya isheki. ✨✨✨✨✨✨✨ Hajiya Duduwa me kan bari guduwa take kamar zata tashi sama tana ta surutai, Yaw idan yaya talle ya kamani sai yayi perpesu na na higa uku ni Duduwa dan zan fita saida inna ta hanani naki gashi yau zan sha suburbuda a hannun yaya talle Ya Allah kasa kar yaya ya dakeni. Hakatacigab da gudu tana sambatu jitayi an riketa cak ta tsaya ta juyo kawarta jummai me panke tagani cikin kwalliya. Kamar kamar ta ta taci damara da wata gyale tana rike da kara a hannunta. Tace Duduwa me kan bari me yake faruwa ne naganki a wani hargitse,tace humm!kedai bari ina cikin tashin hankali yaya talle ya dawo daga legas. Zaro ido jummai me panke tayi yauce yaya tallen yadawo cikeda kosawa tace jummai me panke ina zan sani kinsan tun safiya na fice daga gidan. Jummai me panke tace kinsan me wannan adu'ar da muka taba yiwa mallam me tozo shi zakiyi yanzu yaya talle bazai jibgeki ba. Rike haba tayi tace qur'anin ubangiji namanta da adu'ar jummai me panke tace to zan tuna miki amma sai kin tsammin raken ki. Harara ta galla mata tace yasiin bani bada raken nan idi ne yasaya min kema idan kinaso sai ki fada ma mudi ya saya miki jummai me panke tace to hikenan kije kisha duka agun yaya talle kinga tafiya ta. Jawota Duduwa tayi tace haba jummai kawata kinsan dai bazan hanaki rake na bako kiyi hakuri gaci. Tamika mata wanda takesha yamutsa fuska me panke tayi tace banason wannan wanda baki fara sha ba nakeso. Duduwa kamar ta makure jummai me panke takeji saboda haushi ba abunda ta tsana kamar tayi kyauta. Mikamata wanda bata fara sha dinba tace fadamun kar in kara bata lokaci. Jummai me panke tace to ga adu'ar "zanagurugu lakumu ya ayyuhassakalimi" Rugawa tayi a guje tana maimaita adu'ar. Banke kofar gidansu tayi da karfi ta ciga inna dake tuka tuwo tajuyo tace Allah ya shiryeki ace mutum kullum ana masa magana akan Abu daya. Kicigoma mutane gida kamar an koroki wai ke Duduwa yaushe zaki girma kiyi hankali ne.tana tsaye tana susar kai sai rarraba ido takeyi. Jitayi anyi mata wata mahaukaciyar damka ta kurma ihu wayyo innata na mutu na lalace............✍🏻 Kubiyoni a next pg dan jin waya damke Hajiya Duduwa me kan bari Shin wannan adu'ar tata zata karbu kuwa kudai ku biyoni. Comments dinku shi zai tabbatar min da littafin ya muku in shigaba Comments and share Matar Mammam ce👐🏻 *************************⬇********************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** [2/29, 6:28 AM] Matr Mamman: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 HAJIYA DUDUWA ME KAN BARI 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story & Written by Rahmat Matar Mammam Bismillahirrahmanirrahim Labarin Hajiya Duduwa me kan bari kagaggen labari ne Sadaukarwa ga mutanen sarari🤣🤣 🅿👉🏻3⃣&4⃣ """"""Wayyo Allah yaya talle kayi hakuri kar ka sheqene,karatun allo naje bayan muntaci kuma sai Asabe mai kunu tace in raka dandali. Falla ma bakinta mari yaya talle yayi ki rufe mun baki yanzu tasake saka wani ihu wayyo Allah jama'a a zo aceceni yaya talle zai kaheni. Ran yaya talle yakara baci ya daka mata tsawa ke zan zubar miki da hakwara idan baki rufe bakinki ba, Sake kurma ihu tayi wayyo baffana yaya talle zai zai cire mun hakwara,haushin yaya talle ne yacika inna ganin yakasa dukan Duduwa me kan bari. Cikin bacin rai tace yaro me katsaya kallo ne ko yaw ma biyema shirmen ta zakayi bazaka hukuntata ba. Ya furzar da iska cikin bacin rai yace kina ganin tun ban mata komai ba tana kokarin tara mun jama'a inna tace bani ita anan idan bazaka iyaba. Yace aa inna barni da ita Jan hannunta yayi har bakin itace mangwaro dake tsakiyar gidan yaja igiyar da suke daure dabbobi da shi ya daure ta tana ihu da kuruwa amma saida ya daureta. Yaje ya daura alwala ya wuce masallaci,Duduwa me kan bari a daure amma bakinta bai mutu ba sai ihu take tanata sambatu. bata ishi inna kallo ba alwala ma ta daura ta shige cikin kurya sai bayan sallar isha'i yaya talle ya cigo gidan,Duduwa na jin muryar baffa ta bude murya tana ihu da kururuwa wayyo ni Duduwa ba'asona an daure kamar akuya. Nashiga uku na lalace ni Duduwa inna bata sona yaya talle ma baya sona ya pasa mun baki ya cire mun hakori. Baffa na gab da cigowa gidan yaji yadda Duduwa me kan bari ta ke ihu da maganganu,Sauri yake kamar zai kife a kasa ya cigo gidan. Cikin sauri ya nufi inda aka daure Duduwa ya kwanceta, yana kwance ta ta kwanta a kasa flat kamar matatta tana wani irin nunfarfashi hankalin baffa ya tashi matuka. Ya kwala ma yaya talle kira yaro!!!yaya talle ya taho ransa a bace yace baffa sannu da dawowa wani kallo baffa ya masa yace ............✍🏻 Comments and share Matar Mammam ce👐🏻 [2/29, 6:29 AM] Matr Mamman: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 HAJIYA DUDUWA ME KAN BARI 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story & Written by Rahmat A Abba Jada Matar Mammam Bismillahirrahmanirrahim Sadaukarwa ga mutanen boye🙊🤣 da mutanen Sarari🤣😁 ❌Not Edition❌ 🅿👉🏻5⃣&6⃣ "”""dauketa ka kaita daki burinku ya cika kun kashe mun "ya yajuya cikin azama yafita cikin gidan Duduwa me kan bari ta bude idonta gudaya tana kallon inna da yaya talle dake tsaye cirko_cirko kasa_kasa Yaya talle yace inna kinga iya shegen Duduwa me kan bari ko? Muzata nunawa iya shege nida nake zaune a legas,zata nunawa hauka. Inna tace yaro kayi abunda baffanku yace kafin yadawo in bahaka ba kasanci ba kyalemu zai ba yace inna barni da fitsararriya ina zuwa Duduwa me kan bari najin abunda yaya talle yafada ta zabura ta kurna ihu taruga a guje tanufi hanyar fita. Yaya talle yabi bayanta inna tace nashiga uku saude wannan wace iriyar yarinaya ce Allah ya shiryamun ke. Taku daya biyu yaya talle ya shafkota.ihu tasa da kargin gaske saida gabadaya unguwar ta amsa baffa da ke kofar shigowa gidan shida malam me tozo. Ya ruga cikin gidan har yana tuntube yakarasa shigowa yaga Duduwa me kan bari a hannun yaya talle yamata damka mai kyau sai mutsu_mutsu take. Malam mai tozo ya shiga yace subhanallahi saketa talle yaya talle yasaketa. Malam mai tozo ya karaso kusada Duduwa me kan bari yace zauna Nutsuwa tayi ta zauna,kamar gaske. Yajuya ya kalli baffa yace wato malam sule abunda nagani ajikin yarinyar nan yabani mamaki,aljani guda dari ba daya ne suka ciga jikinta. Waro ido Duduwa me kan bari tayi kamar zata fashe da dariya ta daure ta maze baffa yace subhanallahi yanzu ya za'ayi,malam mai tozo yace eh to zamuyi mata rukiya da hayaki yanzu zasu fita. Malam mai tozo yace yaya talle yazo ya rike mai Duduwa me kan bari, zabura tayi zata tashi yayi saurin riketa gam takasa yin koda kwakwaran motsi. Malam mai tozo yafara karatun rukiya kamar haka. Kulli shashinnn ya tattaro "yawun bakinsa ya tofe ma Duduwa me kan bari a fuska tuuuph.wanafsin shashin.tuuuuuph! Washashin kulli wanafshin kulli washashiii tuuuuph Haushin malam mai tozo da kyamar "yawunsa yasa Duduwa me kan bari kurma ihu. Malam me tozo yace yawwa goma sun fita, tayi kokarin fisgewa ta gudu amma takasa yaya talle yayi mata rikon maza haka malam me tozo yayi ta tofe Duduwa me kan bari da "yawunsa haushin su yasa Duduwa yin luf ta daina motse_motsen da take. Malam me tozo yace da inna debo gaushi mu mata hayaki Azabure Duduwa me kan bari ta mike wallahi ba abunda ke damuna ni ku kyaleni wayyo baffana zasu kasheni ihu take hade da kururuwa kan kace kwabo gidan yacika taf da mutane. Kamata yaya talle malam me tozo yace kawo ta nan abamu zani ina takawo babbab zani aka rufawa Duduwa me kan bari tana ihu tana kuruwa amma ba wanda yasaurareta. Danne kan ta yaya talle yayi akan kaskon gaushin malam me tozo ya zazzaga garin maganin hayaki ya tashi ihu takeyi tana kuka tana tsinewa yaya talle da jummai me panke. Wallahi jummai me panke sai kin biyani rake na tsinanniya kawai ni zakiyiwa karya gashi nayi asarar rake na Allah ido na idonki sai kin bani rake na. Adu'a bata karbu ba nasha mari ga dauri ga hayaki Allah ya isana Saida tari ne ya saketa tayi ta tari Malam me tozo yace a bude ta ana budeta idon ta ya kada yayi jazur. Sai jawa yaya talle da jummai mai panke Allah ya isa take tashi tayi na nufi daki tana jin malam nayi ma baffa bayanin yadda zatayi anfani da magungunanda ya hada mata. Taba makaryaci kawai wai sun dauka dagaske aljanu ne suka shigeni, hhhhhhh!!kai amma malam ya kware wajen iya karya wai aljanu dari ba daya tasake fashewa da dariya inna da ke tsaye akanta tana kallonta tace Allah ya shirya mun ke. Tace Ameen inna ta Tace aranta dayanzu nasha suburbuda a wurin yaya talle nasan baffa ma bazai goyan baya ba Allah yakaimu gobe wata zataci banten...... (🙊tab kar inji mazgah ban na fece🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀) Washegari tun da sanyin safiya sa'daf_sa'daf Duduwa me kan bari ta lallaba ta nufi kofar fita baffa dake fitowa daga daki yace ina kuma zaki yanzun da sauri ta juya aa baffa akuyar gidan su larai ce tashigo tana cin masarar da inna ta shanya shine nake korar ta tafada tana kifkifta ido hade da susar kai baffa ya kada kai yace to tunda akuyar ta tafi dawo ki zauna. Cikin sanyin jiki ta dawo ta zauna tana Allah Allah baffa yafita ita ma tasamu ta fita burin ta kawai tahadu da jummai me panke ta biyata raken ta....................✍🏻 Idan naga comments anjima inyi typing 😁 Comments and share Matar Mammam ce 👐🏻 [2/29, 6:30 AM] Matr Mamman: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 HAJIYA DUDUWA ME KAN BARI 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story & Written by Rahmat A Abba Jada Matar Mammam Bismillahirrahamanirrahim Sadaukarwa ga mutanen boye🙊🤣 Kagaggen labarine kuma gajeren labari 🅿👉🏻7⃣ """"Tana zaune tana susar kai sai kifkif da ido take baki a zumbure,inna tafito daga cikin bayi ta kura mata ido na tsawon mintuna ta kadai. Allah ubangiji ya shirya mun ke tanufi daki tsayawa tayi kamar wacce ta tuno wani Abu tajuyo ga duduwa me kan bari tace,ke duduwa me kan bari ban hanaki zama akan turmi bane. Susa kai tayi takara zumbura baki tamike tana kunkuni ta nufi dakinta inna tace Allah ya shirya mun ke baffa,dake kokarin fita ya amsa da amin. Duduwa me kan bari najin inna nayi ma baffa adawo lafiya ta daka tsalle tafada kan "yar karamar gadon karfen dake dakin tace Allah ya tsaremun baffana. Yanzu kuma jummai me panke zata ga bala'in hajiya duduwa me kan bari ta kyalkyale da dariya inna dake waje tana jinta tace oh ni saude ace diya ba nutsuwa kokadan tananan kamar ruwa a cikin daro,wuf duduwa me kan bari tafice daga cikin dakin. Ta leka dakin yaya talle taga akulle tace yawware mugun bayanan a guje tanufi kofar fita bata ko saurari inna da ke kwala mata kiraba. Tunda ta fita bata tsaya a koina ba sai kofar gidan su jummai me panke tana zuwa taga kannen jummai me panke suna tsalle_tsalle a kofar gidan tace kai habu zonan habu na zuwa kusada ita yace gani yaya duduwa. Jeka kiramun yayarka yace ay batadawo tallar panke ba batadawo ba yace tace dakyau hakan ma daidai ne tajuyo da gudun bala'i ta nufi dandalin tallar su. Yadda take guduwa haka take sake tusa jikake "bararararaaaaaa" kamar tsohuwar machine YAMAHA (🙊🙈) Tun daga nesa jummai me panke ta hango duduwa me kan bari tana tahowa a guje tasan tsiya ne yakawota,taraya aranta za'a kwaci "yan kallo yaw. Jitayi anyi kwallo da bokitin pankenta gabadaya panken ya watse a kasa almajirai suka fara wasoso. Tace kan batasi wace "yar (🙊momy tahanani karasawa🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀) Tazubar mun da panke duduwa me kan bari tace nice nan hajiya duduwa me kan bari 'diyar baffa da inna kuma kanwa ga yaya talle, kina da maganane tace tab aiko yaw za'ayi yakin duniya na uku. Duduwa me kan bari tace hehehehehh!! Sannu Hitiler yake kowa, nidai ba wannan ba rakena zaki bani jummai me panke tace eyehh kaji karfin hali,to wallahi bazan bayarba saidai kiyi abunda zakiyi. Tace haka kikace eh hakana nace Duduwa me kan bari ta zare dankwalinta taci damara aiko itama jummai me panke ta cire nata dankwalin tayi damara itama wani dattijo dake zaune yana shan kunu a gefe baiyi magana ba sai yanzu yace kar wacce ta kuskura tace zata yi fada tika_tikan "yammata daku kuma kawaye kuce zakuyi fada. Asabe mai kunu da ke dariya tun da suka fara shashar bakin tace aa baba kyalesu su daku ay kowa da gaskiyarsa ita jummai me panke an barar mata da pankenta itako duduwa me kan bari an cimata rake kaga ko dagaskiyar su ladi me awara ta amsa kwarai kuwa ay sun fi kusa mu jiya da muka roketa raken ba hanamu tayi ba tace idi ne yasaya mata muma mu fada ma samarin mu su sai mana. Larai me waina tace kunsan fadan duduwa me kan bari yadda yake kuce abarsu gwara dai arabasu ni anawa ganin Baba yatashi yace ke duduwa maza ki bar nan. Ta zumbura baki tace baba kace tabiyani rakena baba yace bake kika zubar mata da panke ba ay shikenan madadin rakenki kenan duduwa me kan bari ta dora hannu aka ta zunduma wani ihu tace wayyo. Baba yace ke bakida hankali ne,nace ki barnan ko yanzu in bata miki rai cikin kunkuni tace wallahi sai ta biyani rakena kuma saina rama marin da yaya talle yamun eheh ta murguda baki. Baba yace ni kikewa kunkuni yabita taruga a guje taje ta boye a bayan wani itace tana hangosu jummai me panke ta dauki bokitin pankenta takama hanyar gida duduwa me kan bari tace yawwa ay dole ki biyani tabi bayanta. Jummai me panke natafiya kawai saiga duduwa me kan bari a gabanta, tace bani rakena jummai me panke tace bani badawa. Dake itama a cike take da duduwa me kan bari nan take kokowa ta barke a tsakaninsu dukansu sun daku sai haki sukeyi tsawa sukaji a bayansu cikin duduwa me kan bari ne yayi wata irin kadawa ya duri ruwa jin muryar yaya talle abayansu tasan yaw mai kwatar ta ahannun yaya talle sai Allah gashi baffa yatafi kasuwa inna kuma ko kasheta zaiyi bazata ce uffan ba saima takara zugashi. Sake jummai me panke ta yi tafara rantse_rantse tace yaya talle wallahi ita tafara tsokanata,inna ce ta aikeni sai muka hadu da ita takamani da fada. Jummai me panke ta ce karya take yaya talle har wajen sana'ata tabiyoni tabarar mun da panke na. Yaya talle yace Ashshahh nawane kudin panken jummai me panke ta ce yaya talle talatin ne sa hannu yayi a aljihu ya lalabo talatin ya mikamata. Yace jeki gida kiyi hakuri karba tayi tace yaya nagode duduwa me kan bari ta ce kutt sai kin biyani rakena wallahi babu inda zaki. Yaya talle yadaka mata tsawa keeee!wuce mutafi gida duduwa me kan tace wallahi yaya talle...kan ta karasa taji saukar mari a fuskarta saida taga wasu taurari biyu.tace wayyo Allah baffa namutu jan hannunta yaya talle yayi suka nufi gida...............✍🏻 Comments and shared Matar Mammam ce👐🏻 [2/29, 6:30 AM] Matr Mamman: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 HAJIYA DUDUWA ME KAN BARI 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story & Written by Rahmat A Abba Jada Matar Mammam Bismillahirrahamanirrahim Sadaukarwa ga mutanen sarari🙊🤣 Kagaggen labarine kuma gajeren labarin 🅿👉🏻8⃣ """"""Tafiya suke duduwa me kan bari na kurma ihu wayyo Allah baffa na namutu na lalace yaw yaya talle yasamu nama sai yayi perpesuna. Wayyo Allah jama'a ataimaka abaiwa yaya talle hakuri kar yadakeni tsawa yaya talle yadaka mata tayi tsit tana kifkif da ido,suna zuwa kwanar gidansu duduwa taja tunga ta tsaya. Yaya talle yace wuce muje,ta fara rantse_rantse wallahi tallahi yaya talle cikina na ciwo bazan iya zuwa gidaba,ta sulale ta kwanta a kasa ta kama birgima wayyo ni duduwa me kan bari cikina. Zan mutu yaya talle kayafe mun duk abunda namaka nasan ni tawa ta kare kataimaka ka kira mun inna zan bata wasiya ne birgima take tana sambatu. Wayyo yaya talle kaga wasu mutane da fararen kaya sun zo wai inbi su mutafi ko wallahi bazan,bikuba ni zan zauna da yaya na da innata masu sona ku tafi ku kyaleni. Sororo yaya talle ya tsaya yana kallon ikon Allah yace lallai Duduwa me kan bari abun naki ya wuce sanin tunanina ni zaki gwada fitsara ko to bari ina zuwa. Yafara nade hannun kodaddiyar rigarsa,cak ya dauke ta yadorata a kafadarsa kamar ya dauki buhu, Yanufi hanyar gida duduwa me kan bari fah baki ya mutu sai zuzzura ido takeyi kamar na mujiya. Duk inda suka wuce mutane sai sun tambayi me yake faruwa haka amma ko kallo basu ishi yaya talle ba duduwa dai tana asankame a kafadar yaya talle kamar mutum mutumi. Suna shiga cikin gidan yaya talle yasauketa,yaji wani iri wari da abu mai zafi akafadarsa yana gangarawa ta bayansa . Inna tasaki salati tace yanzu duduwa me kan bari saboda tsabar iya shege da fitsara zawo kika yi yaya talle yajuyo afusace ya shake duduwa me kan bari yafara zuba mata mari a fuska,ni zakiyiwa zawo a jiki qur'anin ubangiji yaw sai kin yabawa aya zakinta. Yashigabada sambada mata tafi a fuska tana ihu tana wallahi yaya bansan nayi zawo ba tsautsayine Allah wasu masu fararen kayane suka tsorata ni Allah wallahi. Saida ya suburbudi duduwa me kan bari da kyaw kafin yaje ya cire kayan yazo ya watsa mata su maza,maza dauki kayannan ki wanke yanzu in bai fitaba zakisha duka. Duduwa me kan bari ta dora hannu akai wayyo Allah na mutu na lalace yaya talle kasan ban iya wanki ba gubbbb ya buge mata baki ya daka mata tsawa dauki nace daukar kayan tayi tana kuka tana wankewa,yana tsaye akanta datayi wani kuskure ya labta mata duka da dorina kai yaw dai duduwa me kan bari tasha suburbuda a hannun yaya talle. Duk aiyukan gidan ita tayisu tanayi tana kuka,ta qagu baffa yadawo tasan yaw mai raba baffa da yaya talle sai Allah. Bayan tagama duk ayyukan da ke taje ta zauna a hanyar kofar gida taji tahowar baffa tasa kuka tana dafe ciki wayyo Allah na baffa na yunwa zai kashe maka 'diyar ka rabona da abinci tun karin safe yunwa zata sheqeni ni duduwa me kan bari gashi baffa na baya kusa dani wayyo Allah cikina tafara birgima akasa inna. Najinta ta kada kai Allah ya shirya mun ke duduwa me kan bari, da sassarfa baffa ya shigo gidan daga ta yayi yana share mata guntun hawayen da ta kakalo yi shuru daina kuka ki fada mun me ya faru. Kasa tsayuwa tayi wayyo baffa kafafuna sun karye wallahi bazan iya tsaiwa ba an karyamun kafa wayyo Allah. Ran baffa ya baci matuka ya kwala wa inna kira saudeh!!! Inna tafito cikin dakin tace malam sannu da dawowa,me akayiwa duduwa gashi takasa tsaiyuwa inna tace mekuma za'a mata ka tambayeta man. Ran baffa yaqara baci musamman ma da yaji duduwa me kan bari tana kiran "yunwa zai kasheta ina yaro ya tambayi tace yafita be dawoba. To tayain mu kaita daki inna tace wa bafa abunda yasameta iya shegene kawai irin nata wani kallo baffa yamata yasa dole suka riketa suka kaita dakin yace kawo abinci yanzunnan inna tace taci abincinta fa. Baffa yace saude wai kina nufin ban isa insakiyimin abuba,tace aa malam Allah yabaka hakuri. Tawuce ta kawo abincin baffa yafara bata abincin abaki tsaf duduwa me kan bari ta shinye abincin. Sai sannu baffa yaketa jera mata yajuyo yafara yiwa inna fada ta inda yashiga batanan yake fita shikuma yaron zai dawo yasameni............✍🏻 Comments and share Matar Mammam ce👐🏻 [2/29, 6:31 AM] Matr Mamman: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 HAJIYA DUDUWA ME KAN BARI 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story & Written by Rahmat A Abba Jada Matar Mammam Bismillahirrahamanirrahim Sadaukarwa ga mutanen boye🙊dana sarari🤣🤣 Kagaggen labari ne kuma gajeren labari 🅿👉🏻9⃣ """"Sallamar yaya talle ne ya katsewa baffa bunbunin dayake tayi,yawwa gara da Allah ya dawoda kai kazo kamun bayanin dalilin dukar da kayiwa wannan yarinya. Duduwa me kan bari najin baffa yace yaya talle yayi masa bayanin dalilin dukar ta sa ihu wayyo baffa hannu na yayi targade. Arikice baffa ya cigo dakin inna takada kai makarcin Hajiya duduwa me kan bari na bata tsoro tasan idan yaya talle yafada masa abunda tayi baffa bazai goya mata bayaba shiyasa ta kurma ihun. Baffa na shigowa dakin yakama hannun ya rike sannu uwata Allah yasawwake,ya kwalawa yaya talle kira kai yaro!!. Yaya talle yashigo dakin maza jekakira malam me tozo yazo yaduba mata hannun duduwa me kan bari najin za'a kira malam me tozo ta kara rikicewa wallahi baffa bana son akira shi ni abarni hannuna zai warke,ko bai zoba kuka take wiwiwi. Bata son akira malam me tozo ganin kukan yayi yawa ne yasa baffa yace to yaro maza zo ka jamata hannun badon yaya talle yaso ba ya zo ya jamata hannun. Duk da zafin da duduwa me kan bari takeji haka tadaure tacije tace a ranta kaima kaji wahalar danaji saura inna kuma. Bayan yaya talle yagama jan hannun tace baffa zan sha kunun tsamiya cikin sauri baffa ya juyo yace saude yi sauri ki damamata kunun inna sake baki tayi tana kallon baffa Yanzu malam biyewa shirmen duduwa me kan bari zakayi bafa abunda ke damunta iya shegene kawai. Baffa ya kulu iya kuluwa bai cemata uffan ba yamike yanufi kofar fita tunda Allah yasa tanada uba ay Alhamdulillah zan damamata, dakaina inna tayi saurin bin bayansa malam yi hakuri abun bai kai ga hakaba bara in damamata. Duduwa me kan bari tasaki murmushin jin dadi hooh baffa na Allah yabar mini kai rankwashi taji akanta tsabar zafin rankwashin batasan sanda tasaki tusa mai sauti ba jikake phiiiiiiiiit!!!kamar horn din mota(🙊🤣🤣🤣) Tabude baki zatayi ihu yaya talle yayi sauri ya rufe mata baki yace karki yi ihu idan bakiyi ihu ba zan baki goma kisai rake kada kai tayi alamar bazatayi ihun ba ya shire hannunsa akan bakinta ya zauna a gefen ta duk haushi yabi ya cikasa ga abun duka ba damar dukan yaraya aransa zamu hadu dake gobe ay baffan ba sabarki zaiyi a kafada ya tafi kasuwa dake ba. Baffa ne ya shigo da kunun a wata babbar Kofi saida ya fifita kunun tukun kafin yabata,ta zunbura baki tace babu sukari baffa bazan iya sha ba tafada tana mai kakalo hawayen karya. Baffa yace yaro yi maza kaje shagon Dan tani ka karbo mata sukarin bayadda yaya talle ya iya ya karbi kudin ya fita. Washe gari bayan baffa ya fita kasuwa da doguwar gargadi da yayiwa yaya talle da inna akan duduwa me kan bari tsabar takaici ma ya hana yaya talle yazama cikin gidan. Duduwa me kan bari na ganin yaya talle yafita tamike tanufi kofar fita inna tace karki sake kibar gidannan tajuyo da sauri inna rakena zanje in karbo a wajen jummai me panke tace koma menene kika kuskura kika fita gidannan sai ranki ya baci. Tace inna bafa zataci bulus ba eheeh ba baffa yace duk abunda nakeso a barni inyiba inna tace bazaki fitaba muddin kika sa kafa kika bar gidannan kuma duk abunda yasameki ki kuka da kanki,tace ba abunda sai alheri. Tajuya tafice aguje kamar wacce aka koro gudu take kamar wata sabuwar kamu cak ta tsaya sakamakon hango malam mai rawani yana tahowa duk iya shegen duduwa me kan bari tana shakkar malam me rawani. Sumkuyar da kai tayi kamar mara gaskiya,har saida ya wuce ta dago kai tace Allah yasoni bai ganeniba da yanzu yafaramun wannan shirmen nasihar tasa. Kaitsaye ta wuce dandali amma tana isowa akace jummai me panke tatafi yo icce tace ay ko sai na bita. Wucewa tayi abunta masifa na cinta tafiya take tana "yan wake_wake da tsalle_tsalle har ta iso wani rafi tsayawa tayi cak taga yadda ruwa ke gudu tace Allah yaw saina ga kaeshen rafin nan yadda ruwan yake gudu bari in gwada bin ruwan nima cire takalminta tayi tasakalasu a hannayenta tayi damara tafara bin gefen rafin tana gudu tana kallon ruwan Allah yaw saina riga ku zuwa inda kuke zuwa ta kyalkyale da dariya ta Ruga aguje...........✍🏻 Hhhhhh🤣🤣🤣🤣 Hajiya duduwa me kan bari ayi gudu lfy Comments and share Matar Mammam ce👐🏻 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 HAJIYA DUDUWA ME KAN BARI 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story & Written by Rahmat A Abba Jada Matar Mammam Bismillahirrahanairrahim Sadaukarwa ga mutanen boye dana sarari🙊🤣 Kagaggen labari ne kuma gajeren labari Shigiya!Shigiya!!shigiya!!! Ina shigiyar Momy na official Khady Marubuciyar Mummunar kaddara Dan Allah duk wanda yaji duriyarta ko yakeda number ta ta taimakamun pls😭 🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚 🅿👉🏻🔟 """"Hajiya duduwa me kan bari tunda tafara gudu bata tsaya ba tun tana gudu da karfin ta har tafara tafiya a hankali tsabar kafiya da naci kuma taki ta hakura. Saida tayi tafiyar minti arba'in kafin tatsaya tana fidda nunfarfashi tace tab qur'anin ubangiji bazan iyaba yo ina ni ina irin wannan gudun dubi yadda ruwan ke gudu Kamar baya gajiya. Kaga bara inkoma nasan zan hadu dasu jummai me panke a hanya kawai ayi wacce za'ayi tabiyani rakena. Juyawa tayi tana tafiya tana surutai kamar sabuwar kamu,tayi tafi kusan minti ishirin tace kai ace nayi nisafah, bara kawai in tsallaka ruwannnan inyi yanke kawai in isa dandali da wuri tarike haba kai to ay kuma matsala ta ban iya ruwaba yadda ruwan nan yake uban gudu idan nashiga ay sai ta Allah. Cigaba tayi da tafiya hankalinta kwance tayi tafiya sosai kan ta iso wata "yar mararrabar hanya tsayawa tayi tana nazari kwarankwasa na mance da hanyar ko nanne tanuna kudu tace kai aa ba nan bane baradai inyi gabas. Haka duduwa me kan bari tacigabada tafiya har saida tayi tafiya mai nisan gaske tsananin gajiya da kishin ruwa yasa ta tsaya to wai ina hanyar ne diyar baffa da inna kuma kanwa ga yaya talle. Zama tayi a karkashin wata bishiya tana hutawa iska mai dadi na kadata tsaki taja wanna iskar daidai shan rake wallahi kai Allah ya isar mini jummai mai panke rakena da kika sha kuma wuta balbal. Ta dan kishingida take bacci ya dauketa bacci take harda mishari. Tayi baccin awa uku kan ta farka tana bude ido tafara mika tace oh ace ina cikin daji na dauka ina kan gadon inna ta cikinta yaba da sauti kululuuuu!!ta dafe cikin haka zakayi hakuri har naje gida tafada tana zunbura baki tafara tafiya. Duduwa me kan bari fah ta rikice iya rikicewa dan ta mance da hanyar da ta biyo sai yawo take a cikin daji tana kiran jummai kande Asabe ladio larai ina kuke,haka tacigabada yawo har la'asar tayi rana tana shirin faduwa hankalinta yakai kololuwar tashi wayyo Alla inna ta nashiga uku na lalace wallahi ba'a son raina na zo nan ba jummai me panke ce tajamin wayyo baffa na yaw idan naje gidan yaya talle zai dafi ni ya cinye nasan baffa kuma bazai hanashi tunda ya hanani yawo wayyo ni duduwa me kan bari na mutu. ✨✨✨✨✨✨✨✨ A can gida kuwa tunda duduwa me kan bari tafita gida ran inna a bace yake matuka yaya talle ya shigo gidan tunda yaga yadda inna ta amsa masa sallamar yasan ranta a ab'ace yake yazo ya durkusa a gabanta yasunkuyar da kansa kasa cikin tsantsar ladabi yakasa furta koda kalma daya idonsa yakada yayi jazur. Inna tadan yi murmushi tace yaro ka kwantar da hankalinka ba abunda yake faruwa wallahi kanwarka kace tasani cikin wannan halin yaya talle yadago cikin tsantsar bacin rai yace ina ita duduwar take. Inna tace tafita kasan ba jin magana ta takeba da kana gida ne dai nasan bata isa ta fitaba taci yaya talle yayi bara in dubo ta inna tace to adawo lafiya. Tunda yaya talle yafita duk wanda yatambaya koyahaduda duduwa me kan bari ace ay tatafi jeji ransa yakara baci me Duduwa zatayi a daji kuma. Tsaki yajuya yanufi gida ransa a abace yayiwa inna bayani kada kai inna tayi tace Allah ya shiryeta taje zata gani yaya talle yayi zaro ido waje yace inna kiyi hakuri ki janye Kalmar nan wallahi bakinki zai yi gaggawar kamata inna na rokeki kiyi hakuri ki janye kalmar kada kai inna tayi batace komai ba tashigabada aikinta. Gajiya Yaya talle yayi da tsugonon yataci yanufi dakin sa. ⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡ Al'amarin Hajiya duduwa me kan bari kuwa tafiya take tana yawo a cikin dajin har gari ya soma duhu hankalinta ya matukar tashi wani irin matsanaiciyar tsoro na shigarta. Ajiyar zuciya tasauke sakamakon hango, wasu tsirarrun gidaje wanda bai wuce biyar ba ta hango wuta a kunne da sauri ta nufi bukkokin data hango. Hayaniya taji kamar ihu ne ko yaya ne haka tacigaba da tunkarar wurin gabanta ba tsananin bugawa,koda ta iso daf dasu. Saurin buya tayi a jikin baya katuwar bishiya ta hango su wuta ne a kunne yana shi bal_bal sun zagayeta suna rawa da waka mutane ne basu wuce gomaba a kugunsu daure da ganye maza da mata suna rawa suna zagaye wutar. Hmmm bara ingwada rera muku wakar dasuke yi kadan(🙈). "Suku sameh,sameh,suku,gajeh surubarareh suku,sameh. itadai hajjaju duduwa tana labe tana kallon ikon Allah ko a tatsuniya bata taba ganin mutane irin suba ihu sukasa cikin wani irin harshe mara dadin ji suke magana tanaganin lokacinda suka ciro kafar mutum a cikin wutar suka farashi. Dora hannu aka duduwa me kan bari tayi wayyo ni Duduwa me kan bari ina nashigo ne mutum suke shi nima yadda suka shi wannan mutumin haka zasu cinyeni nashiga uku nalalace wayyo inna ta danasani da na bi maganarki ban fita ko inaba da yanzu ina gida tareda baffana. Gabadaya ilahirin jikinta rawa yakeyi tayi pitsari yafi sau uku, Can ta tuno da wani adu'ar da malam me tozo yataba basu dazasuje daji itadasu Asabe mai kunu suka hadu dashi yabasu yace musu idan suka rike adu'ar zata tsaresu da duk abun cutarwa walau mutum ko aljan. Nan take tafara adu'ar kamar haka: Yakurawal yalum, balumshi jatidire arre bilhakki,tattara girigisi marhabi hibi haba,kuyum muyum mahalakum,mata lakum. (🙊wannan adu'ar malam me tozo ce duk wanda yadauka hmm 🤣🤣🤣🙊) Tanata maimaita adu'ar jitayi anyi sama da ita, ihu ta kurma wayyo Allah baffa diyar ka tasheka barzahu. Gani tayi an jefata cikin wani Abu kamar raga dago kanta tayi taga an tattaro mutanen da suke rawa da waka an jefasu cikin ragar tsabar tsoro da kaduwa batasan sanda tasaki zawoba. Wadannan mayun,naganin duduwa me kan bari suka fara lasar harshe suna tunkaro ta. Runtse ido tayi tana jiran su yagalgalata,tunowa da wani adu'ar da malam me rawani yake yawan yi in yaga abun tashin hankali. Innalillahi wainna ilaihi raji'un tafada da karfi jitayi anyi sama da ita jefata akayi cikin ruwa bata samu damar ganin waya jefataba taji ace ki ceci kanki. Duduwa me kan bari fah ido ya raina fata bata iya ruwaba ta nutse a cikin tun tana kokarin fita har takasa tayita kwankwadar ruwa daga lokacin bata kara sanin inda Kanta yakeba. ✨✨✨✨✨✨✨✨ Hankalin inna da yaya talle yatashi matuka ganin har anyi isha'i ba'aga duduwa me kan bariba lokacin dawowar baffa yayi amma ko alamarta ba'a ganiba anje gidajen su Asabe me kunu amma ba'a gantaba. Hankalinsu yakara tashi gabadaya gari yadauka duduwa me kan bari ta bata idi ya rikice sai kuka yakeyi. Yaya talle ya rikice yakasa zaune yakasa tsaye yawo yake a cikin daji kamar ba dareba zuwa yayi ya zauna a gefen kogi ya wanke fuskarsa ya kurawa ruwan ido can yatashi zai tafi ya hango tahowar idi zama yayi abakin ruwan yana jiran karasowarsa. Jiyayi abu ya bugesa a kafa haska touch yayi saiga duduwa me kan bari a saman ruwa alamar tasha ruwa sosai kamar bata nunfashi. Cikin Sauri yaya talle yajawota ya shinfideta a gefe yafara danna mata ciki ruwa nata fita baki da hanci murna suka farayi ganin tanan nunfashi. Yaya talle ya dauketa suka nufi gida, baffa da inna sun yi farin cikin dawowar su lafiya take aka fara mata magani. Bayan farfadowarta,bude ido tayi a hankali da baffa ta farayin arba tazabura ta rike hannun baffa baffa Kaine ace zan kara ganinka. Ta fashe da kuka inna da yaya talle suka shigo dakin taci tayi ta rugunmesu ta fashe da kuka inna wallahi bazan kara bijirema umurninki ba kiyafemun inna ta shafa kanta tace ishuru nayafe miki Allah ya Dada shiryamun ke. Tajuyo ta kalli yaya talle tace yaya talle kayi hakuri duk abunda namaka kayafemun wallahi bazan kara rashin ji ba. Kuma bazan karayin tsokana da rowa ba rakena da jummai taci nayafe mata. Baffa yace Alhamdulillahi da diyata ta gane gaskiya ta shiryu tace insha Allah baffa da ga gone zan koma makarantar malam me rawani. Inna tace Alhamdulillahi. Nima Matar Mammam nave Alhamdulillahi anan na kawo karshen wannan dan gajeren labari kuskuren dake ciki Allah ya yafemun Allah yasa hajjaju duduwa a sanja hali🤣 Wannan labarin kagaggen labari ne Dan nishadi. Wannan labarin dungurungum sadaukarwa ne a gareki Hajjaju duduwa me kan bari tawa 🤣 Hmm gara ori da weti tare hanya kawai sukeyi amma Babagana da shetima kama 🙊sai barugo himbe be wawi😜 Duk babarbarenda bai gane abunda nace ya tuntubi adireshi na na yanar gizo akan. Www.na mazgeh maloho.com😜 We are leaders oooooo leader ooooo Fulani leaders ooo kokunki kokunso mune dai leaders ooo😜 Sai mun hadu a Sabin littafina mai suna Babagana da shettima masu tare hanya😜🤪 Barebari how market😎 Matar Mammam ce👐🏻*************************⬇********************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ **************************