********************** ⬇ ************************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** [3/18, 22:22] Hafsat Rano: *SAUYIN K'ADDARA* SHAFI NA DAYA (1) ©HAFSAT RANO HASKE WRITERS ASSOCIATION 💡 ✨✨✨💫💫 Zaune suke a karkashin bishiyar dake tsakiyar harabar makarantar, zaman jiran siwes supervisor suke tun kimanin awannin biyu da suka wuce, yau ce rana ta uku da suke irin wannan zaman jiran ba tare da sun sami ganin sa ba. Hira suke ɗan taba wa sama-sama har zuwa lokacin da matasan samarin guda biyu suka nufo su, daga nesa Asmy ta hango su tayi saurin tabo Maryam "Gafa mutanen nan su tawo." "Suwa?" Tace tana gyara zaman glasses din idon ta, kafin Asmy tayi magana har sun ƙaraso, a tsakiya suka sasu Khamil ya zauna a bangaren Asmy shi kuma Saddi ya zauna ta bangaren Maryam "Babes kuna nan ashe?" "Muna nan Khamil, mun zo ganin Malam Bahahuddin ne, kaga tun dazu muke zaman jiran sa." "Ai wannan malamin bashi da mutunci wallahi, haka fa ranar mukayi ta zaman jiran sa muma sai daga baya yazo." "Haka fa yake yi." "Saddi manyan ƙasa." Asmy ta zuba mishi ido tana murmushi, a dakile yace "An gaishe ki." Cikin kallon kasa-kasa ya furta "Yah... Maryam me glass ba magana ne wai?" Yadda yayi maganar yana kashe ido daya irin na yan duniya, yasa ta kara hade fuskar ta sosai, ta sunkuyar da kanta ƙasa tana jin haushin sasu a tsakiyar da sukayi ga wata shigar banza kamar wasu y'ay'an arna, askin Saddi kamar zakayi amai, banza tayi kamar bata ji ba sai da Asmy ta dan jungureta, daidai lokacin Malam Buhahuddin ya ƙaraso a wata yar kurkurar motar sa golf ja, da sauri ta mike "Gashi ma ya zo taso kar ya yi wani wajen kuma dan Allah." Da sauri Asmy ta miƙe ta kalli su Saddi, "Guys bari mu wuce sai next time." "Owk take care." Shafa dan siririn gemun sa ya shiga yi me kama da na dan zakara, kallon bayan su yake har suka haura saman barandar da zata sadaka da ofishin malamai. A hankali ya mai da kallon sa wajen Khamil yana wani shu'umin murmushi, "Yah ne?" Ya tambaya yana mik'ewa. "Guy yarinyar nan fa yar rainin wayo ce, ji yadda ta yarfa ka." Dage kafad'a yayi yana taɓe baki yace; "Zata shigo hannu ne soon, muje wajen Zuhra tana can albarka tana jiran mu." "At toh mu fasa kawai, Allah sa tare suke da Soffy kaga nima sai na rage time." "Shegen sama, haske ne dai tarwai balle kace zaka lalubi yar mutane." Tafawa sukayi suka bar wajen, duk in da sukayi sai kaji ana musu kirari irin na manyan yara,  wasu su amsa wasu su wuce kawai. *** A kofar office ɗin suka tsaya suna jiran ya basu izinin shiga, Asmy ce ta bata rai tana kallon Maryam kafin ta daure tace "Gaskiya abinda kike bak'ya kyautawa, ji fa yadda Saddi ke binki kina wulakanta shi, bayan kinsan irin su ba ababen wulakanta wa bane wallahi, ji yadda matan school ɗin nan ke binsa amman ke kina wani sha masa kamshi." "Na faɗa miki be yi min ba, beside ba ma tsara na bane yanayi na da nasa bazai taba zama daya ba kin gane?" "Amma.. " "Naji, a bar maganar dan Allah " "Shikenan, ke kika sani." Buɗe kofar yayi suka shiga da sauri, daga gefe suka tsaya sai da ya gama yauƙi da yanga sannan ya ciro form guda biyu ya mika musu, "Gashi nan ku dawo dashi bayan kwana biyu." Ya dora "Sai dai bana son private waje ba wani koyan aiki ake ba." Shiru Maryam tayi don ita burin ta ta kai nan wajen dake gaba kaɗan da gidan su saboda matsalar yau da kullum, "Malam..." "Ina jinki." "Dan Allah Malam ka barni na kai Arkel Poultry Farm." "A ah gaskiya, ban yarda ba." "Malam dan Allah." Ta cigaba da magiya saboda nan ne kaɗai tasan zai fi mata sauki ko saboda kudin mota ma, a kafa zata taka kamar yadda take takowa zuwa makaranta, idan yace sai waje me nisa zai iya zama karshen karatun nata, ba zata so hakan ba saboda ta zo gangara level 3 suke, faɗi tashin da aka sha kafin azo in da ake yanzu ba kaɗan bane. Ganin yadda ta nace ne yasa shi cewa "Kije ki kai musu mu gani, ba lallai ma su yarda ba nasan." "Nagode, Nagode malam." "Karku manta ƙwana biyu na baku." "Mun gode malam." Suka haɗa baki suka faɗa sannan suka masa sallama suka tafi. Daga nan gate suka nufo tun da dama abinda ya kawo su kenan, Asmy ta hau napep ta wuce ita kuma ta shiga takawa a kafa, kallon gaban ta take har ta gangara gefen titin ta shiga lungun da take bi kullum da zai kai ta unguwar su, tana tafiya cikin nutsuwa zuciyar ta gaba daya ta tafi wajen da take son kai form d'in kar su ƙi karba su jaza mata. Yadda ta lula da tunani yasa har bata ji sautin takun tafiyar su ba har sai da suka cimmata, da sauri ta waigo jin kamar an taba bayan ta, Saddi ne shi da su Khamil sai Sameer da Adnan su hudu fuskar nan tasu dauke da murmushi cike da wani irin kallo. Ras gaban ta ya fad'i jikin ta ya soma rawa ganin layin babu kowa, waige-waige ta shiga yi tana neman hanyar gudawa, dariya suka kwashe a tare Saddi ya damko hijab din ta yana ƙoƙarin manna ta a jikin sa, kici-kicin kwacewa ta hau yi ta saka kuka tana magiya, fisge hijabin jikin nata yayi doguwar rigar atamfa leda ta bayyana a jikin ta, dam ta kamata tayi mata d'as a jikin ta, "Wow..." Suka haɗa baki suka furta a tare. Hannu Saddi ya kai zai taba ta yaji an bigi hannun nasa, ihu ya saka cikin jin zafi, tsaye yake fuskar sa a daure tamau yana faman huci, ido suka zuba masa cike da mamakin kokarin sa "Waye kai?" Khamil ya tambaya yana kallon yadda Saddi yake yarfe hannu, wani banzan kallo ya watsa masa yana mika hannun sa wajen Saddi "Bata hijab d'in ta." "Ba zan bayar ba, uban waye kai da zaka dake ni? Kasan waye ni?" Be tanka mishi ba ya matso kawai yasa hannu ya fizge hijab din ya wurga mata yana d'auke kai, da sauri ta chafe tayi saurin sawa har lokacin kukan take, hanya ya nuna mata alamar ta wuce ta tafi, tsayawa tayi zatayi masa godiya ya daka mata tsawa "Dalla leave.!" Da sauri sauri ta bar wajen tana jiyo hayaniyar su Saddi suna zagin sa da maganganu mara dadi, juyawa yayi ya bar wajen bayan yayi making duk fuskokin su. A wajen wani me kayan miya ya tsaya ya ciro Naira dari sai da ya miƙar da ita saboda duk taji jiki sannan ya mik'a masa "Baba ga kudin kayan jiya da Inna ta karba, mun gode Allah saka da Alkhairi." "Nima nagode Hafizu, ga gaida mutanen gidan." "Zasuji." *** A zauren gidan su ta tsaya ta share hawayen ta kafin ta shiga, umma tayi wa sannu da gida tayi saurin wucewa daki, ciro komai tayi ta ajiye ta daura zani ta fito waje bayan ta ɗora hijab a saman zanin, bokiti ta dauka ta buɗe in da suke zuba ruwa, dan kuntun ruwa ne a ciki gashi yau ba ƙaramin rana ta kwaso ba so take ta dan watsa ko taji dadin jikin ta "Umma ba ruwa fa a gidan." Fitowar ta kenan daga bayi rike da buta, gefen dan dandamalin dake wajen wanke-wanken su ta zauna sannan tace "Sai dai ki maida kayan ki ki zagaya gidan Hajiya Mama ki samo ruwan nan, yau miftahu be zo ya debo ruwan ba." "Gidan Hajiya Mama?" "Eh." "Na hakura gaskia, in sun dawo daga islamiyya sun samo me ruwa." "Ba wankan kike so ba." "Allah ina so Umma, Hajiyar ce sai a hankali." Umma bata sake magana ba ta cigaba da abinda takeyi. Daki ta wuce ta jawo kwanon abincin ta ta zauna ta fara ci, tana ci tana tunanin abinda ya faru a hanya, bata san iskancin su Saddi ya kai haka ba, lallai dole ta sa Asma'u ta fito harkar su wallahi, in bazata iya ba toh gwara ta fita harkar ta kuwa. Tana nan tana tunani har kannenta suka dawo. *** Wajen karfe goma ta isa, a harabar ta tsaya tana shaƙar iska wajen, a rayuwar ta tana son duk wani abu daya danganci kiwo, ilimi ne sosai a cikin sa, tana kuma son shuke-shuke suna sata nishadi sosai. Sai data gama kallon wajen sannan ta tambayi wani da yazo wucewa office din da zata, nuna mata yayi da hannu ya wuce ita kuma ta nufi office d'in, a bud'e yake mutane biyu maza suna zaune a ciki, shiga tayi Salim na ganin ta ya fadada fara'ar sa kamar ya santa "Sannu da zuwa Hajiya." "Ina wuni?" Ta gaishe shi tana dan rissinawa, hakan ya kayatar dashi ya tattare aikin da yake ya bata hankalin sa "Siwes student ce Sir daga Buk." "Siwes... Siwes...?" "Eh sir Siwes." "Ko dai IT?" Anas ya tambaya "Yes shi." "Ohh... IT zaki ce ai, irin yan attachment ne daga makaranta, kuna karbar yan IT anan kuwa?" Ya tambaya yana kallon Salim da baki daya hankalin sa na kanta, wurga masa biro Anas yayi yana hararar sa, dariya yayi yana sosa keya yace; "Sai a karba mana, kawo takardar muga." Mika masa tayi daga gefe ya duba, "Tirkashi, gashi dole sai oga ya sa hannu anan, shine matsalar." "Toh, baya nan ogan?" Ta tambaya cikin zulumi. "Gaskia baya nan, bansan kuma yaushe zai zo ba." "Ah tsaya..." Ya jawo wayar sa yana dubawa "Alhamdulillah, zai shigo gobe na tuna yayi min text jiya, kin ga ki dawo gobe kawai da wuri kamar takwas tayi miki anan, sai kawai yasa hannu a gaban ki ma ki tafi da a barki" "Ok tam, Nagode, sai anjima. "Sai goben dai." Murmushi tayi ta wuce suka cigaba da hirar su. ** Tun wajen karfe shida umma ke tashin ta taki tashi, da k'yar ta samu ta mike lokacin bakwai ma ta kusa, a gurguje ta tube kayan ta ta nufi bayi, nauyin dad'ewar ta a bandaki ne yasa Umma tashin ta tun dazu amman duk da haka sai data bata lokaci. Fitowar ta kenan daga wanka umma ta shigo d'akin rik'e da dan madaidaicin flask, ajiye shi tayi a gefe tana kallon ta baki bud'e ganin sai yanzu take fitowa daga wanka, kwafa tayi ta juya ta fice ba tare da tayi magana ba. A gaggauce ta shirya ta zuba kunun ta nufi kitchen in da take jiyo kamshin kosai da umma ke soyawa, zama tayi akan turmin dake jikin kofar kitchen d'in tana kurbar kunun tana jefa kosai a bakin ta tana bawa Umma labarin makaranta. "Kina ganin lokaci kuwa? Ko kin tsaya zance." "Wayyo ashe takwas ta kusa,na tsaya ina ta zuba, bari na tafi Umma." "Yafi dai, Allah ya bada sa'a." "Amin ya Allah." Dogon hijab me hannu ta saka har kasa light brown ta rataya jakar ta ta fice da sauri tana duba lokaci. Karfe takwas da minti hudu ta isa wajen, gaisawa sukayi da me gadin in da ta shiga ciki. A rufe office din yake alamun be zo ba kenan duk sammakon da yace tayi, kallon hadaddiyar motar dake harabar wajen ta tsaya yi baki bud'e dan ba k'aramin burgeta motar tayi ba, matsawa tayi jikin motar ta dan shafa ta tana niyyar ciro wayar ta ta dauka ta nunawa Asma'u don ita ce mayyar mota taji an turo kofar bangaren da take tsaye, da sauri ta matsa gefe, kafafuwan sa ne suka fara saukowa cikin wani hadadden takalmi irin na motsa jiki, kananan kayane a jikin sa na sport Ash da layi layin Green an rubuta ARKEL da manyan baƙi a bayan rigar, cikin tafiyar sa ta kasaita wadda ta zama na nature d'in sa ne ya nufi kofar yasa key ya bud'e ya shiga gami da bugo kofar da karfi. Sai data bari kamar da mintina goma ta yanke shawarar shiga, knocking tayi a hankali ta murd'a kofar ta shiga kanta a kasa, a masife ya d'ago jin bud'e kofar duk a tunanin sa Salim ne, ganin har takwas da rabi babu wanda yazo a cikinsu, ido ya zuba mata yana kallonta har ta k'araso gaban desk d'in cikin inda-inda tace; "Malam Ina kwana?" "What did u want?" Yayi magana cikin bacin rai ganin yadda take simi-simi da kai "Am... Am.. Dama..." "Get out !!!" Tsayawa tayi tana zare ido a matukar tsorace kuma taki fita, nuna mata kofa yayi be sake magana ba, saurin tsugunawa tayi kasa tace "Dan girman Allah kayi hakuri." "Wai baki da kunne ne? Ko brain dinki bata aiki, get out please." "I Hate to see girl acting decent, Allah a fili, a zuciya babu." Yayi maganar kasa, a kunnen ta taji komai, kallon sa tayi ta juya cikin tsananin tashin hankali, a daidai kofar shiga sukayi kichibis da Salim zai shigo, kana ganin shi kasan shima hankalin sa a tashe yake ganin mota a waje, be yi mata magana ba ya wuce ciki da sauri, gefe ta samu ta rakube tana jin zuciyar ta kaman zata bullo ta fito, sama sama take jiyo muryar sa, faɗa yake sosai, sai da ya gama ciwa Salim mutunci tas sannan ya fito, motar sa ya nufa yaja ya bar wajen ba tare da yayi abinda ya kawo shi ba. Office din ta koma da sauri lokacin Salim na tattare takardun da ya watsar a kasa, "Ina kwana?" Ta gaishe shi tana kokarin fito da wata takarda daga jakar ta datayi photocopy "Lafiya lou, sorry kinzo ashe tun d'azu." "Eh nazo tun 8 d'in da kace." "Opss, wallahi uzuri ne ya makarar dani." "Ba komai." "Sai dai kinyi rashin sa'a..." "Na'am?" Ta zaro ido tana kallon shi. "Kinzo kin tarar da oga, gashi form din naki ma dana bashi da wasu takardun ya haɗa ya watsar dasu kin gansu ina kwashewa." "Innalillah wa inna ilaihi raji'un." "Kiyi hakuri, dole yanzu sai dai ki jira, yanyin oga ne in kika ci sa'a in ya dawo next time ya duba ya gani, amma dai karki damu in sha Allah zanyi kokari na." "Toh... Nagode Allah saka da alkhairi, amma dan Allah ka taimaka min, gobe yace wallahi na mayar." "Zanyi kokari, amma gaskiya sai dai ko jibi ki sake shigowa, goben nan bana jin zai shigo gaskiya." "Toh... toh.. shikenan nagode." "Ba komai." A sanyaye ta ja kafarta ta fita daga office d'in, gefen wani dutse taja ta zauna zuciyar ta tayi rauni, kuka take so tayi sai dai babu hawaye saboda tsabar yadda zuciyarta ta k'ek'ashe, wajen mintuna goma sha biyar ta dauka a zaune a wajen kafin ta bar wajen. Yanayin da ta shiga gidan ne yasa Umma tasan babu nasara, gefen tabarmar da umman ta shinfid'a taje ta zauna bayan ta cire hijab d'inta ta rataye shi a saman igiyar shanyar dake tsakar gidan "Umma sannu da gida." "Sannu Maryam, ya na ganki haka sukuku?" "Ba labari ne umma, ogan wajen na tarar baki ga yadda ya sauken kwadon bala'i a kaina ba, harda cemin kwakwalwata bata aiki, wallahi umma tun da nake ba'a taba wulakanta ni irin yau ba." "Sai hakuri, haka rayuwar nan take, kasar nan tamu dai sai addu'a kawai." "Wallahi fa,shikenan kai talaka sai dai ka mutu in baka dashi." "Allah ya kyauta kawai." "Amin Umma." "Su Habubu an tafi makaranta gidan shiru sai ku kad'ai." "Sarkin rigima ba, ana chan." Tashi tayi ta shige ciki, ganin rana ta fara zuwa in da umman take zaune yasa itama ta koma cikin falon, hira suke d'an tabawa sama-sama har lokacin dora abincin rana yayi, shinkafa da wake ta dora akan charcoal. Matsala charcoal d'in ya bata ashe ba bushashe bane, har su Habubu suka dawo daga makaranta ba'a gama girkin ba, kukan yunwa ya fara Allah yaso akwai ragowar kunun safe Umma ta bashi sannan aka samu yayi shiru, yana shan kunun Maryam tazo ta dangware masa kai tana tabe baki "Mutum sai rigimar banza an girma ba'a san an girma ba." Umma na jin haka tayi saurin amshewa "Shi kuma mutum ya dinga jan girman sa mana." "Allah Umma yaron ne tabarar tsiya." "Yayi d'in." Walid ne ya karb'e "Allah nima haushi yake ban abinda yake." "Yayi d'in wai ina ruwan ku ne, a'ah? Kun fa samun auta a gaba." Gwalo Habubu yayi wa Walid ta gefen kofin yadda babu wanda zai gani, "Zan kamaka ne." Walid ya fad'a yana kwafa. Haka dai sukayi ta hira suna tsokanar juna har lokacin islamiyya yayi suka shirya suka tafi. *** Kai tsaye gida ya wuce, parking yayi ya fito yana kallon harabar gidan, motar Alhaji da ya gani a fake a wajen yake kallo, fitar da yayi dazu be lura da ita bane ko kuwa bayan fitar tasa ya dawo? Tab'e baki yayi ya wuce ciki. Tana zaune a cikin ɗaya daga cikin jerin luntsuma-luntsuman kujerun da suka zagaye falon, da sauri ta ajiye wayar hannun ta cikin kulawa tace, "My boy ina kaje da sassafen nan a mota?" "Naje duba wani aiki ne, goodmorning." "Morning dear, ka tashi lafiya." "Normal fa." Yace kawai ya juya ya nufi d'akin, da kallo ta bishi har ya kai kofar d'akin zai bud'e tace "Alhaji ya dawo fa." "Ok." Ya sa kai ya shige ciki. Hararar kofar tayi taja d'an k'aramin tsaki ta koma ta zauna. Kwance take kafafuwan ta zuwa cikin ta lullube da bargo, idonta a rufe alamun barci, a bakin gadon ya tsugunna ya kamo hannun ta cikin nashi, kuka ne ya taso masa ya shiga yi a hankali, sama-sama take jin kukan nasa, a hankali ta bud'e idonta ta dora shi akan sa. Tausayin sa ne ya kamata ganin yadda yake kuka kamar mace, shafa kansa take son yi tana kokarin maida hawayen da taji yana neman zubo mata. "Ummi..." Kallo ta bishi dashi, murmushi yayi mata yana sake rik'e hannunta "Duk wanda ya mai dake haka wallahi tallahi sai na ga bayansa, sai na dau miki fansa bazan taba yafe mishi ba, kowaye shi Ummi wannan Alk'awari na ne." So take tayi magana amma babu dama, ganin haka yasa shi saurin cewa "Karki yi kokarin magana Ummi, karki jawo wata matsalar kuma dan Allah." Hawaye ne ya gangaro daga idon ta ya sauka a fuskar ta, hannu yasa ya goge mata. Turo kofar akayi aka shigo nurse din da take kula da Ummin ta shigo rik'e da ruwan allura da ake mata duk kwanan duniya, murtuke fuska yayi kamar be taba dariya ba ya kalle ta a wulakance, in da sabo ta sab'a da halin sa dan haka ko a kwalar rigar ta tayi abinda ya kawo ta ta fice, tun shigowarta ummin ta kafe ta da kallo har zuwa lokacin da tayi mata allurar ta tafi, a hankali idonta ya koma ya rufe alamun tayi bacci. Gyara mata blanket d'inta yayi ya fita yana jin sa wani iri. Kai tsaye yayi hanyar part d'insa dake saman gidan, matattakalar dake shinfide a tsakiyar falon ya kama yana kokarin hawa muryar Alhaji ta tsaida shi "ARKEL..." Chak ya tsaya da hawan ya juyo fuskar sa babu yabo ba fallasa, kallon sa daddy yayi na yan sakanni kafin yace "Ya jikin nata?" Cire kansa yayi kad'an kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru, ganin hakan yasa Alhaji dorawa "Ya aiki? Hope komai yana tafiya yadda ya kamata." "Alhamdulillah, ya hanya?" Ba tare da jiran amsar sa ba ya juya zai haye saman ya katse shi "Ka bawa Hajiya kuɗi zatayi amfani dashi." "Nawa zai ishe ki Hajjaju na?" Hajiya Mero dake zaune kusa da Alhaji tayi murmushi tana kanne masa ido cikin kissa tace "Dari ma ai ina ganin zata isa, kar abun yayi masa yawa." "Kin tabbata?" Daga masa kai tayi tana murmushi. "Toh kaji." "In na fita anjima zan sa Salim ya tura mata." Ya k'arasa hawa saman ba tare da ya sake juyowa ba. Kallon ta Alhaji yayi cikin jin dadi yace; "Nagode k'warai da irin yadda kike kula da Yaron nan da mahaifiyar sa, bani da bakin gode miki sai dai nace Allah yayi miki albarka." Dadi ne ya kama Hajiya Mero ta wani karya kai tana sake kashe murya tace; "Soyayyar da nake maka ce ta jawo komai, karka wani gode min ai yiwa kaina, bayan haka ma ai Arkel ni kallon sa nake a matsayin wanda na haifa ba wai d'an miji ba." "Nagode miki, Allah yayi miki albarka." "Amin Alhaji na." *** Tsaye yake gaban mirror yana fashe jikinsa da wasu shegun turaruka masu matukar kamshi da tsada na companing Rexona, agogo ya d'aura a tsintsiyar hannunsa yana kokarin taje sumar kansa Zee ta bud'o kofar, kallo daya yayi mata ta cikin mirror ya cigaba da abinda yake, kasa karasowa tayi ta tsaya jikin kofar tana admirring irin kyaun da taga yayi, a gaskiya guy din yana kashe ta da wanka, har ya gaama tana tsaye tana imagining yadda zata bullo masa. Takalmin sa sau ciki samfurin John Lobb Dark Blue ya ciro a jikin shoe rack ya zura bayan ya sa Dark blue din half socks, dark blue yadi ne a jikin sa hakan ya sake fito da wankan sosai, a hannu ya riko hular ya dauki abinda zai dauka "Please." Ya nuna mata hanya alamun ta matsa zai wuce "Wajen ka nazo fa Ya Arkel." Kallon hannu sa yayi kadan sannan yace "Sai dai Next time." Tsaye tayi tana kallon sa ya wuce barta kaman statue, yadda yake tafiya cikin takunsa na cikakken namijin duniya me ji da kansa ta fanni da dama yasa ta sakin ajiyar zuciya a hankali ta furta "Take your time, I ll wait." Kallon kanta tayi daga sama har kasa cikin shigar red gown, babu karya tayi kyau ko ta ina amma me yasa ko kallo bata isheshi ba, a sanyaye ta d'aga kafarta ta bi bayansa. Lokacin har ya isa dining yana had'a tea, kujerar kusa dashi taja ta zauna tana kafe shi da ido, haushi ne ya turnik'e shi ganin yadda ta zuba masa ido kamar sabuwar mayya, kasa ci gaba da cin abincin yayi ya ture ya tashi. "Ya Arkel." Ta biyo shi da sauri ganin yana neman fita, tsayawa yayi kamar zai rufe ta da duka, tun da yake be taba ganin mayya irin Zee ba, duk yadda yake wulakanta ta ta kasa ganewa, daraja daya take ci ta mahaifiyarta da wallahi sai yayi mata abinda zata yi zuciya ta daina damun sa. "Ya Arkel." "What!!!" Ya fad'a a dan tsawace Tsoro tsawar ta bata tayi saurin ja da baya, juya kansa yayi yana saita kanshi kafin yace "Am sorry." Dadi ne ya kamata tayi murmushi, "Dama so nake naji when zaka dawo yau? it's my birthday and  I want..." "I can't gaskiya, kinsan bana son irin shiriritar nan, I have no time to waste a irin stuffs like birthday." "Help me pls na fad'a ma friends dina." "And so? Zee please, Am running late see yha." "But you are the CEO, you don't need to be in such a hurry, i know u are just avoiding me." "Sai kuma kiyi." Motar sa ya shige ba tare da ya sake magana ba yayi ficewar sa ya barta a wajen, Hajiya Mero dake kallon komai ta tab'e baki ganin Zee din ta dawo ciki jikin ta a sanyaye, ganin Hajiya Mero yasa ta k'arasawa wajen ta kamar zatayi kuka tace "Mummy..." "Wuce muje." Rano [3/18, 22:22] Hafsat Rano: *SAUYIN K'ADDARA* *©HAFSAT RANO* *®Haske Writers Association 💡* (Home of expect and perfect writers) *PAGE 2* Hannun ta taja har cikin bedroom d'in ta kafin ta sake ta tana fuskantar ta "Shine kawai matsalar ki?" 'Daga kai tayi tana jin kamar tayi kuka, murmushi Hajiya Mero tayi ta jawo ta jikinta, bubbuga bayan ta tayi cikin isa da kasaita tace. "Karki wani damu kanki, uban ma yayi saurin bi balle shi, shi 'din banza! Zanyi maganin abun." "Yawwa Mom, please kisa shi ya aure ni da wuri please and please kinji my love." "Aure kuma zainab?" Ta fad'a tana kallon ta "Eh Mom." "Shikenan zan san yadda zan." Da sauri ta rungume ta tana murna, fita tayi da gudu tayi d'akin su. Zagaye Hajiya Mero ta shigayi hannun ta sakale ta bayan ta, tunanin yadda zata bullo wa Zee kawai take don babu yadda zatayi ma ta yarda ta had'a su aure kafin cikar burin ta, ta sani sarai Zee na bala'in son sa, ba zata taba yarda da duk bukatar da zata zo mata da ta akan sa ba. Kayan jikin ta ta sauya zuwa wani tsadadden lace purple ta zuba sar'ka da d'ankunne na zallan gold, yafa mayafin tayi a kafada ta gyara zaman hudar hancin ta daurin nan ya zauna daram irin na ture kaga tsiya. A tsakiyar falon ta tsaya tana kwalawa Sadiya me aikinta kira, da sauri ta fito ta zub'e a 'kasa jikin ta na rawa, a yatsine ta shiga yi mata bayanin komai kafin ta juya ta fice hannun ta rik'e da mukullin mota. Buzu na hango ta ya taso da gudu ta cilla masa mukullin tana shiga owner's corner. Sai da suka daidai ta akan babban titi kafin ya tambayi ina zasu je, cikin tsoro yayi tambayar saboda ya san kad'an da aikin ta ta ki amsa masa, aikuwa sai data ja fasali sosai kafin tace ya kaita gidan Hajiya Mama. Remote na a hannun ta tana neman tashar arewa 24 ta rasa, gefenta Sultan ne yana shan kunu me zafi had'e da kosai daya karbo a wajen Umma, ta gefen ido yake kallon ta yadda ta dage sai ta nemo ta kasa ta kuma ki cewa ya taymaka mata, mik'ewa yayi dauke da kofin bayan ya gama sha ta tsaidashi cikin borin kunya tace "Sa min arewa 24 malam." "Da kika kasa?" "Oho." Yana sa mata ya bar falon, hararar bayan sa tayi ta sake gyara zama tana murmushi, jin an budo kofar ne yasa ta maida hankalin ta wajen. Fad'ad'a farar ta tayi ganin Hajiya Mero ta shiga yi mata sannu da zuwa, amsawa tayi ta samu gefe ta zauna, daidai lokacin Rauda ta fito tana hamma, hankalin su baki daya ya koma kanta. "Hajiya Mama yunwa." Ta fad'a tana matsowa wajen da suke, sai a lokacin da lura da Hajiya Mero dake kallon ta, da sauri ta matsa wajen ta tana dariya "Mummy yaushe kika zo?" "Zuwan kenan Rauda, sai yanzu aka tashi kenan." "Wallahi Mom baccin ne akwai sugar, yunwa ce ta tashe ni ma wallahi. "Yayi, maza jeki ki nemi wani abun kici." Tashi tayi tana kwala kiran me aikin su Ummu, ajiyar zuciya Hajiya Mero ta sauke kafin ta maida kallon ta wajen Hajiya Mama "Magana zamuyi Mama." "Toh muje ciki kenan, kafin waccan ya shigo yaji muna magana kinsan shi yanzu sai ya hau kunci." "Yaya Alhaji ba zai taba chanja wa ba, sai yayi tayi ai ya tare baki daya a wajen matsiyatan chan, muje kafin Alhaji ya fara kira kuma." A gefen gadon suka zauna Hajiya Mama ta tattare hankalin ta gaba daya ta bata, "Me ya faru?" "Aure nake so muyi wa Rauda Mama." "Aure kuma!?" "Aure, kinsan yaron chan ya dau wata rayuwa ya d'orawa kansa, gaba d'aya ma ya daina walwala tun abin da ya faru da uwar sa, toh dazu Alhaji ya fara min zancen Aure ya kamata ya ajiye iyali, toh kinsan fa shegen kudi ne da yaron, so nake na had'a auren shi da Rauda in yaso sai ta taimaka mana muyi aiki a kansa." "Uhum..." Hajiya Mama ta sauke ajiyar zuciya "Kina ganin zai yadda ya auri Rauda? Kin fa san shi da shegen taurin kai." "Idan na biyo ta hannun uban, be isa ya ketare ba, cewa zaiyi muyi duk abinda muka ga zamuyi nasan. Matsalar d'aya ce, Zainab ta nuna min tana son shi, sai dai kinsan banbancin halin Zainab da Rauda, Zainab bata min plan xatayi wallahi na sani." "Gaskia kar ma mu fara hada shi da Zainab, yanzu ki bar komai na bangaren Rauda a hannu na, zan sanar da ita komai nasan ba zata k'i ba, sai kiji da shi mijin naki da ita zainabun, idan komai ya tabbata ai mun warke har ita." "Sosai wallahi." Sallama yake tayi a tsakiyar Falon, suna jinsa suka ki amsa masa, Alhaji Farouk wanda suke kira da Yaya Alhaji ne ya shigo falon a daidai lokacin "Yaya..." Juyowa yayi fuskar sa d'auke da murmushi cikin tsantsar farin ciki ya ƙaraso shima "Umaru, ashe kana ciki baka fita aiki ba " "Ina kwana yaya?" "Lafiya lou, kaga nazo gaida Hajiya ne kafin na wuce kasuwa ko bacci take ina ga." Kallon kofar dakin yayi yasan ba wani bacci suna ji tun da ai ya ga shigar Mero gidan yana part din sa, ransa ne ya ɓaci yayi kokarin danne wa ya kalalo murmushi yace "Ko dai tana bayan gida ina ga, ka zauna Yaya bari na kira ta." "Okh toh ba matsala." Buda kofar yayi suka kalle shi a tare, d'an sakin fuskar sa kad'an yayi ya rissina har k'asa "Ina kwana Hajiya?" Amsawa tayi Hajiya Mero ta gaishe shi, ba yabo ba fallasa ya amsa ya maida kallon sa wajen Hajiya Mama yace "Yaya Garba yana ta sallama baku ji ba, gashi chan a falo yazo gaishe ki ne zai wuce kasuwa." "Bamu ji ba, kasan shi baya bud'e murya in yana magana." A cewar Hajiya Mama Ko kuma kuna ji kuki amsawa ba, ya fad'a a ransa, a zahiri kuma sai ya girgiza kai kawai ya juya, tashi Hajiyan tayi tabi bayan shi tana wa Mero nuni da hannu akan ta taso ita ma. Yana zaune ya bawa Tv hankalin sa baki daya suka fito, yana jin fitowar su ya zamo har kasa ya gaida Hajiyan, a sake ta amsa masa ganin yadda Alhaji Faruku ya tsare gida, gaishe shi Mero tayi ya tambaye ta mutanen gida da yaran, amsawa tayi a yatsine ya girgiza kai kawai yayi musu sallama ya tafi. Tare suka fita da Alhaji Faruku ya sauke shi a kasuwa shagon da yake sai da kayan d'inki da yadin hijabai sannan ya wuce office. *** A nutse take tafiya tana kallon gaban ta har ta isa wajen, addu'a dauke a bakin ta ta shiga tana sa ran samun abinda taje nema, a farfajiyar wajen ta hangi Salim yana magana da masu kula da customers d'in dake zuwa wajen, yana hango ta ya sallame su fuskar sa d'auke da fara'a ya nufo ta, "Zuwan kenan?" Ya tambaya yana karasowa, dan rissinawa tayi kad'an ta gaishe shi kafin ta amsa masa, yar dariya yayi ganin  bata cikin nutsuwar ta kafin yace "Ki shiga yana ciki, kinci sa'a yau dana bashi ya karba har ma yace in kinzo na tura ki ciki." "Ba zai mun masifa ba?"  Ta tambaya cike da fargaba "Kila..." Ya dora "Ke dai ki nutsu kawai karki wani ji tsoro, duk tambayar da yayi miki ki amsa kai tsaye ba in-da-in-da, bari naje na sauya wa fingerlings ruwa kafin naji kira." "Please ina so na gani, ka jira na shiga na fito dan Allah." "Owk best of luck." "Thanks." Juya tayi yanayin bugun zuciyar ta ya sauya lokacin data isa kofar, sai data karanto addu'a kafin ta saka kanta ciki bakin ta dauke da sallama, a tsaye yake ya bawa kofar baya yana duba wata locker, ciki-ciki ya amsa sallamar ya cigaba da abinda yake yi, sai daya gama tsaf kafin ya juyo hannun sa rik'e da wani k'aton littafi na Fisheries and Aquaculture, d'an kallon ta yayi kad'an kafin ya zauna yana fuskantar ta. Dakewa tayi ta isa gaban table d'in taja kujera ta zauna tana gyara zaman yar karamar jakar dake makale a hannun ta. Share wa yayi ya shiga duba littafin yana nazari, "Good morning sir." "Morning..Ya akai?" Ya dago kan sa idanun su suka sark'e da juna, wani irin abu yaji ya bige shi, tuno da maganar Salim yasa ta daidai ta kanta tace "Siwes Student ce daga Buk, na kawo request form ina so ayi min signing ne." "Wanne course kikeyi?" "Applied Biology." "Bana son un-serious student, are you hard-working da zaki iya aikin wajen nan?" "In sha Allah." Ta fad'a confidently Be sake magana ba ya ciro request form din ya sa hannu had'e da stamp ya mik'a mata, kanta a kasa tana wasa da hannun ta zuciyar ta cike da tsoron kar yak'i sa hannun, saboda haka bata san ya yana mikowar ba, hannun nata ya zuba wa ido yana kallan yadda yan yatsun ta suka sha jan lalle, be taba gani a hannun wani ba sai ummin shi, ita ma rabon da ya gani a wajen nata an jima, tun kafin ta shiga halin data ke ciki a yanzu, d'an siririn tsaki yaja ya d'an daki table d'in, d'agowa tayi da sauri ta kalle shi, daure fuska yayi ya nuna mata gaban table d'in, hannu tasa ta d'auka cikin tsananin farin ciki ta hau yi masa godiya, cigaba yayi da duba littafin yana amsawa a zuciyar sa. Fita tayi ta tarar da Salim a chan wajen wasu manyan tankuna, wajen ta nufa ta tarar zasu fara chanja ruwan cikin wajen, tsaye tayi tana kallon komai cikin tsananin farin ciki, sai da suka sauya wa kananun kifayen ruwa suka gyara wajen kafin tayi musu sallama ta tafi, direct Buk ta tsallaka tana addu'ar samun Malam Bahahuddin a office, a kofar gate tayi kichibis da Saddi da yan clique d'in sa, dauke kai tayi kamar bata gansu ba tayi shigewar ta, maimakon su fita sai suka fasa suka koma ciki, tana jin hayaniyar su a bayan ta, basu dai yi mata magana ba har suka k'arasa ciki. A bud'e ta tarar da office d'in, babu kowa ciki sai shi kad'ai yana aiki a na'ura me k'wak'walwa, sai daya k'arasa sannan ya karba ya duba komai, murmushi yayi kawai yace mata shikenan. Zuciyar ta fes ta fito tayi gida tana Allah,Allah ta isa gida ta bawa Umma labari, ko ta kan su Saddi bata bi ba ta dai hange su chan tare da su Zahra da Sophie suna hayaniya, sauri tayi kafin ma su lura da ita ta fice daga makarantar. *** Tsaye yake gaban layin kad'an yana amsa waya, tun daga nesa ta gane shi, gaba d'aya tun ranar da tunanin taimakon da yayi mata take bacci, ganin ya cigaba da tafiya still yana wayar yasa ta daga kafa ta cimmasa, sallama tayi masa ya amsa yana juyowa, d'an sakin fuskar sa yayi kafin yace "Bari zan kira ka dai." "Sannu... ina wuni?" " Lafiya lou Maryama yan jami'a." "Ka san sunana kenan?" "Ga zahiri." Mamaki ne ya kamata ta yi dariya kad'an kafin tace "Tun ranar nake son yi maka godiya wallahi, nagode sosai fa." "Uhum, sun sake matsa miki ne?." "A ah, kawai dai naga dacewar nayi ma godiyar ne." "Ba damuwa." "Nagode fa, sai anjima." "Ki gaida gida." Dan sosa kai yayi kad'an yana kallon ta, kansa ya kalla da shigar sa ya sake kallon ta, dawowar sa kenan daga aikin leburan ci zai wuce gida ya tsaya yana amsa wayar abokin sa, har ta kule be bar kallon ta ba, sauke ajiyar zuciya yayi ya juya ya nufi gida zuciyar sa na saka masa abubuwa da yawa. *** Tun daga zauren gidan ta fara jiyo kamshin alala, murnar ta ce ta karu don ba karamin son alala take ba, da Habubu ta fara cin karo da kwanon sa yana ci, hannu tasa ta dauki guda yayi saurin saka ihu, Umma na jin ihun sa ta san an taba masa abinci ne, bata ce komai ba har Maryam ta karasa Kitchen din "Nasan dama ke ko Ahmad ne wallahi, a dinga jan girma gaskiya." Dariya tayi ta zauna kawai tana cire hijab kamar yadda ta saba ta rataye shi a igiya kafin ta shiga ciki, labarin yadda sukayi da mutumin da kuma malam Bahahuddin ta shiga bawa Umma, sai data kai aya ta dire kafin umman tace a takaice "Allah ya bada sa'a." Kwanon alalar Baba ta dauka tayi cikin dakin sa, sai data ajiye masa sannan ta dauko sabon flask ta zubawa Hajiya Mama. "Maryam." "Na'am." "Zo ki mika wa Hajiya Mama alalan nan, daga nan ki gaishe ta, kwana nawa rabon ki da ki shiga gidan ne ma ni." "Ranar nan fa naje gidan." "Karya ne, dauki maza ki kai mata." "Tom." Kamar ta fasa ihu taji, babu yadda ta iya taja Habubu suka shiga tare. Hajiya na ganin su ta sake hade rai kamar ta ga kashi, Sultan ne yayi saurin karb'e flask d'in yana murmushi, a cunkushe ta gaida ta itama don ita sam matar bata cikin sabgar ta, sai data sha kamshi sannan ta amsa. "Muje Abbakar." "Sai kace ana korar ku?" Sultan ya fad'a yana juye alalar a plate da ya dauko, murmushi tayi kawai ba tare da tayi magana ba tayi hanyar fita, da k'yar Hajiya Mama ta daga baki tace su ce ta gode. Bata amsa ba tayi ficewar ta tana ji Rauda na fadar wani abu akan ta sai dai bata ji ko menene ba. ©Rano [3/18, 22:22] Hafsat Rano: *HAFSAT RANO* 3 ***Gaba d'aya ya gama barbaza takardu a tsakiyar gadon, mouse ne rike a hannun sa yana duba wani Pdf na Forex a cikin computer, tun da ya dawo yau ya shiga ya duba Ummi be sake sakkowa kasan ba, so yake ya gama had'a komai kafin ya sauka gaba d'aya don yana son zuwa suyi magana da Alhajin su akan Ummin, bashi da wata bukata a yanzu a duniya sama da ya ga Ummin sa ta dawo daidai, shiyasa bashi da wani lokacin kansa sai na aiki saboda ba kananun kudi rashin lafiyar tata ke ja ba, tun daga kan tests da magunguna hada da nurse d'in da aka dauko me kula da ita duk kuwa da ya kori nurses a k'alla goma kafin ta yanzu wadda ita ma yana gab da korar ta. Tun bayan abin da ya faru, sai ya zama baya iya yadda da kowa sai shi kansa, shiyasa da yaga suna yin wani abu da be gamsu dashi ba yake saurin korar su, dama Hajiya Mero ce ta d'age akan sai ta kawo din kuma ita ce ma take kawo sun shi nasa biya ne kawai. Hannu yasa ya wargaza sumar kanshi ya saka biro yaana sosa wa a hankali, tunanin Poultry farm d'in sa ne ya fad'o masa a take ya jawo wayar sa ya shiga kiran number Salim, bugu daya ya daga ya sake gyara zaman Bluetooth din dake kunnen sa yace "Kun tashi ne?" "A ah muna shirin tashi dai." "Owk good, Please ka duba wajen nan da nake so a zuba kajin nan , na riga nayi komai zasu iya zuwa gobe ko jibi ma, a tabbatar komai daidai " "Owk sir, an gama in sha ALLAH." "Thank you." Rufe komai yayi ya tattara takardun da yayi jotting important abubuwa ya isa gaban mirror ya gyara kansa ya sake fesa turare sannan ya fito, shiru saman babu kowa dama shi kadai ne duk sauran a kasa suke. Da fuskar Ya Nabila ya fara tozali yana sauko wa yarinyar ta Amna ta taho da gudu yayi saurin karasa sauka ya daga ta sama. "Ashe kana ciki." Yaya Nabila ta fad'a tana murmushi, murmushi yayi shima ya karasa gefen ta ya zauna fuskar sa dauke da farin cikin ganin ta yace "Ina nan wallahi, aiki ne ya rik'e ne, yanzu kuka zo?" "Sannu agogo, wajen minti talatin fa da zuwan namu." "Wai... Sannun ku, ina wuni yasu Afnan?" "Lafiya lou Arkel, ya aiki ya jikin Ummi." "Alhamdulillah." Ya fada yana kallon dakin jiki a sanyaye, "Allah ya kara sauki, na shiga naga tana bacci ai." "Amin... Baccin ai ko da yaushe ne." Zuciyar sa ce tayi rauni ya mike sa'be da Amna ya nufi dakin, daga jikin kofar ya tsaya yana kallon ciki, girgiza kai yayi ya fito bayan ya ja mata kofar. "Abinci fa?" Zee ta tambaya tana kallon sa dauke da murmushi, tun dazu take zaman jiran sa dama, yatsine fuska yayi ya girgiza mata kai alamar a'ah "Abincin ma?" Ya Nabila tayi magana tana rike ha'ba "Allah bana son cin komai, bari zan sha wani abun kawai anjima." "Da ka daure amma..." "Owk tam, anjima." "Kawo masa kawai kinji Zee." Ta fad'a tana hararar sa, zama yayi ta kawo mishi a plate sai ruwa da cup ta ajiye ta dauki Amna ta wuce ciki, fara ci yayi a kasalance kamar dole haka yake turawa, kallon sa take cike da tausaya, "Kanina... Ta "Na'am." "Wani tunani nayi, me zai hana ka auri..." "Zainab?" Ya karasa yana kallon ta, daga masa kai tayi alamar eh, girgiza kai yayi ya ajiye spoon d'in ya fuskance ta sosai "Please sis, I can't wallahi, kinsan dai komai." "Amma baka ganin hakan shine daidai? Atleast tafi nurses din da ake kawo wa, in ka aureta zata cigaba da kula da Ummi kai ma kaga hankalin ka zai kwanta nawa ya kwanta nima." "Amma why Zainab?". "Saboda ita muka sani, a rashin yardar kan nan ita kadai zata iya da kai da wannan murdadden  hali naka." "Shikenan dai, zanyi tunani akai." "Owk think hard, zaka gane me nake so ka gane." "I hope so." Amsa wa kawai yayi saboda baya so a ja maganar, babu yadda za'a yi ma ya aure ta. *** Tsalle tayi ta dire a saman gado ta fara daga Amna tana dariya, idan har ya yarda da shawarar Ya Nabila shikenan ta samu cikar burin ta, chocolate ta dauko a jakar ta ta shiga bare musu ita da Amna suna ci tana yam wake waken ta cikin tsantsar farin ciki. Duk maganganun da sukayi taji komai *** A tare suka fito tana rike ta hular sa a hannu, a tsakiyar falon ya ja ya tsaya yana kallon dakin da take ci, kallon sa tayi taga in da yake kallo ta taɓe baki ta dawo gaban sa, rike kai tayi alamun tunani kafin tace "Kash... Allah dai ya yaye min mantuwar nan tawa wallahi." "Me ya faru?" Ya tambaya yana kallon ta "Maganar Muhammadu fa zanyi maka tun jiya, kaga na manta wai me yasa in dai ina tare da kai nake manta komai ne?" Yarfe hannu tayi, hakan ya sashi yin dariya cikin jin dadi yayi kasa da murya yace "Hajiya tah kenan, me ya faru da Arkel din" Dan marairaice murya tayi kafin tace "Bana son naga yaron nan cikin rashin walwala kullum, hankali na baya taba nutsuwa idan na ganshi yana kunci, na zauna nayi tunani babu abinda zai saukaka zuciyar sa fiye da aure Alhaji." Tagumi tayi da dukkan hannun ta cikin wani irin yanayi ta karashe maganar tana kallon yadda maganar tayi tasiri a zuciyar sa. Gauron numfashi ya sauke cikin gamsuwa da bayanin ta yace "Kinyi tunani me kyau wallahi Hajiya, kinsan ban kawo hakan ba." "Nima jiya ne na kasa bacci duk juyi sai ya fado min, sai kawai nayi tunani me zai sa ba zamu hada shi da Rauda ba, kaga tuwo na maina kenan kuma soyayyar mu zata sake karfi tun da zamu hada ya'yan mu aure." "Gaskiya samun mace ta gari ma wani abu ne, kinsan tunani wa zai aura nake a zuciya ta sai kawai kika kawo Rauda, Nagode Nagode Nagode sosai da karamcin ki a gareni." "Ba komai ai yiwa kaine." "Masha Aallah, idan ya dawo kice ya sameni a head office dan ba zan iya jiran sai na dawo da yamma ba." "A dawo lafiya, zan sanar dashi sakon ka." Cikin kissa ta dora "Baka shiga ka duba ta ba fa zaka fita kuma." "Ba yanzu ba, sauri nake bari in na dawo." "Amma... Shikenan toh, Allah ya kiyaye." "Amin." Komawa tayi ta zauna tana murmushi, number Hajiya Mama ta kira don tayi mata albishiri, sai dai bata daga ba. Lokacin Yaya Alhaji yana zaune a falon tana yi mishi maganar Rauda, ransa babu dadi yake sauraron ta yana ayyana abubuwa da yawa a ransa, ya riga ya san halin Hajiyar tasu shiyasa kawai yake biya mata a haka, yanzu ma data zo da maganar Rauda yasan komai amma babu yadda ya iya amsa mata da toh kawai yake don shima yafi so Rauda tayi aure ta bar gaban Hajiyar ko hankalin sa ya kwanta, abu daya ya sani shine abun da ya tsara ba zai taba yadda a samu matsala ba. *** Zaune yake yana kallon komai na cikin dakin, maganar da Ya Nabila tayi masa ce take masa yawo akan sa, kallon Ummin ya sake yi, tabbas tana buk'atar makusanci, auren shi ne kadai mafita a halin yanzu, runtse ido yayi yana tuna wa zai aura da zai iya damka amanar kula masa da ita, babu kowa zuciyar sa ta amsa masa, idan kuma yace ya nema wa ya sani da har zai iya neman ta? Gaba daya kansa ya kulle ya rasa mafita, mafita daya yake hangowa ita ce Zainab, ba son ta yake ba sai dai kawai zai aure ta ne don mahaifiyar sa, babu bata lokaci ya amince da abinda zuciyar sa ta hasaso masan. Tashi yayi tsam ya chanja shigar shi zuwa manyan kaya don da beyi niyyar fita ba saboda ranar Ummi ce, ya kan ware mata rana daya a cikin sati ya kula da ita yayi mata komai, sai dai dole yaje ya ga Alhajin su ya sanar dashi abinda ya tsara game da maganar Zee. Durkusawa yayi a gabanta cikin sanyin murya yace "Kiyi min addu'a Ummi, Allah yasa abinda nake shirin yi ya zame mana maslaha, kar naje na jawo mana matsala." Murmushi ya gani a saman fuskar ta, hawaye ne ya biyo fuskar sa yasa hankici ya goge, runtse ido yayi yana hango abin da ya faru a baya, take jijiyoyin kansa suka fito sosai, wani irin bacin rai yake ji idan ya tuna dalilin sa ne komai ya faru. Tashi yayi ya soma bin bango dafe da kansa kamar wanda yasha ya bugu, tsabar bacin rai da k'yar ya daidai ta kansa ya fita yana ja mata kofar. Direct head office din ya nufa in da yasan zai same shi, zaune suke da wani abokin sa suna maganar kasuwanci sakatariyar sa ta sanar dashi zuwan Arkel din, izinin shigowa. Gefe ya samu bayan ya gaida mutumin ya tsaya yana jiran su gama, hada komai yayi ya fita ya barsu su biyu, kofa yaja musu hakan yasa Alhaji kallon Ahmad sannan ya nuna masa kujera yace "Zauna magana zamuyi." Zama yayi ya sauke kansa k'asa yana sauraron sa Da sauri ya d'ago kansa jin abinda yace "Rauda kuma?" Ya tambaya ido waje, "Ita fa, mun riga mun gama yanke magana da Hajiya, bana son kuma kace a'ah don hakan kamar cin fuska zai zama wajen ta." "Nagode." "Yawwa, Allah yayi ma albarka." "Amin." Ya amsa a hankali "Ya wajen naka? Ina fatan babu wata matsala." "Babu komai." "Madallah, shikenan zaka iya wucewa, akwai tarin aiki a gaba na." Jiki a sanyaye ya tashi ya fita yana son tuno wacece ma Rauda? Har ga Allah ya kasa tuno me sunan, yana tuki wayar Alhaji ta shigo, d'agawa yayi kafin yayi magana yace "Zaka iya zuwa ka fara ganin ta, ba bata lokaci za'ayi ba." Jin zai katse yasa shi bud'e baki da k'yar yace "Ina ne gidan?" "Gidan su Hajiya mana, ko baka gane wa nake nufi bane?" "Na gane." Ya amsa da sauri ya katse kiran, sai a lokacin ya tuno yarinyar ai, tana zuwa sosai gidan su ya gane ya sarai, duk rawar kan Zee da yake gani ta dame ta ta shanye. Saurin taka burki yayi ransa ya gama baci, da ya san ita ce tun farko bazai taba yadda ya amsa ba duk da dama rashin son aja maganar ne yasa shi saurin amsawa kawai. Da k'yar ya saita kansa kamar zaiyi kuka ya kira Yaya Nabila ya fad'a mata yadda akai. *** Gaba d'aya satin cikin farin ciki tayi sa a wajen, tun ranar farkon data fara zuwa wajen bata sake ganin shi ba, shi din ma yayi busy sosai da harkar Forex shiyasa bashi da lokacin duba wajen sai Salim ne yake kula da komai, a hankali a hankali suka fara sabawa da Hafiz har sukayi exchanging number sukan yi waya da chatting ma, tuni zuciyar ta ta fara nutsuwa da Hafiz ya sanar da ita komai da sanar da yake saboda ya rufawa mahaifiyar sa da kanwar sa asiri. Ranar juma'a yanayin garin ya sake rikicewa da sanyi sosai, da wuri ta shirya don sunyi waya da Hafiz yace zai rakata, atamfar ta me kyau ta sallah ta saka coffee and milk colour ta dora katuwar rigar sanyi ta yafa mayafi kalar milk a maimakon hijabin da ya zame mata dole, har ta fito ta koma ta dauko glasses d'in ta ta saka, Umma tayi wa sallama ko ta kan abinci bata bi ba tana sauri ta tafi. Jin ta take sakayau saboda rashin hijabin, a daidai in da suka saba haduwa ta hango shi ya saka wata doguwar rigar sanyi da hula, dariya tayi ta k'arasa wajen, gaishe shi tayi ya amsa yana kallon ta daga sama har k'asa, shigar tayi mata kyau sosai, jerawa sukayi suna tafe suka hira har suka isa, ciki suka shiga ta dauko musu kujerar roba suka zauna suna cigaba da hirar. Suna zaune wajen ya fara cika a hankali don ma kowa ya makara saboda sanyin da aka tashi dashi. Duk wanda ya wuce sai yayi mamakin ganinsu a wajen, salim ma da ya zo ya gansu sai ya dauke kansa yaki bari ma ya kalli wajen balle har yayi mata magana, ganin haka yasa ta d'an sha jinin jikinta, kallon shi tayi ta karyar da kai "Zaki gudu ko? Nima bari na wuce kinsan juma'a karamar rana ce yanzu zai kiji kira." A tare suka mik'e, shigowar sa kenan wajen ya hango su tsaye, ransa ne ya ɓaci ganin yadda take ta dariya, babu abinda ya tsanan irin rashin jan aji mace ta wage baki a waje tana dariya. Parking yayi ya fito bayan ya had'e girar sama data k'asa. "Oga yazo." Ta fada muryar ta a hargitse, tashin hankalin da ba'a sa mashi rana, kallon wanda ta kira da Oga Hafiz yayi sannan ya kalli Maryam yaga yadda ta rud'e, haushi ne ya kamashi yace "Sai kije kar ya kashe ki." "Kisa kuma?" Ta fad'a tana kallon shi "Baki ga yadda kika rikice bane." Ya amsa a dakile, zatayi magana ta hango salim ya nufo su, yana karasowa yace "Oga na kira." Be jira amsar ta ba ya juya cike da jin haushi. "Muyi magana a waya kawai." Da sauri ta bar wajen ta nufi office d'in. Kamar munafuka haka ta tura kofar ta shiga tana sand'a Ajiye Inhaler hannun sa yayi ya kalle ta tayi saurin sauke kanta kasa. #Sauyin Kaddara _ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU😁._ *ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma *SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano) *KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo) *BURI ƊAYA!* (Mamu gee) *WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull) 👇🏻karku bari ayi babuku *ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu* *za'a tura kudin ta wannan accnt number din* Hafsat kabir umar 0225878823 GT bank Saika tura shaidar biya ga wannan number ta WhatsApp 08030811300 Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din 07067124863 Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya. *Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon wani*🤝🏽🤝🏽🤝🏽 [3/18, 22:22] Hafsat Rano: ©*HAFSAT RANO* # *SK*                4 Ido ya zuba mata yana kallon ta, haushi ne ya sake turnik'e shi ganin ko gaishe shi bata yi ba, tsaki yaja da karfi ya bigi table d'in, "Baki iya gaisuwa bane?" Ya  tambaya rai a bace Da sauri tace "Ina kwana?" "Ban ganshi ba, aikin da kika zo yi kenan?" "Na'am..." Rainin wayo, ya fad'a a ransa, a ƙufule yace "Fita." Raba ido ta fara yi kafin ta juya ta nufi hanya "Baki iya bada hakuri ba?" Ya katse ta ganin da gaske fitar zatayi Juyo wa tayi da sauri tace "Kayi..." "Jeki kawai." Tsayawa tayi taki fita, komawa yayi ya zauna zuciyar sa ba dad'i, tari ne ya taso masa da karfi, tun daya tashi yake jin alamun Asthma, mantawa yayi be fito da inhaler ba sai da yazo ya tuna, duddubawa yayi babu duk sai emty container. Matsawa tayi gaban table d'in tana kallon sa, sannu ta shiga jera masa ganin yadda yake tari sosai, a hankali tarin ya tsaya yaja baya da kujerar ya daga kansa sama, idon sa a rufe ya daga mata hannu jin sannun taki karewa, cikin tausayawa ta juya ta fita tana waiwaye. Ranar gaba d'aya kasa yin komai tayi, tunani biyu ne ya haɗe mata , ta kira Hafiz wajen sau uku yana k'in d'agawa, ta san fushi yayi ita kuma sam bata ga abin fushi ba. Sha d'aya nayi tayi musu sallama don bata so ta hadu da masallaci,  in da suka saba haduwa da Hafiz tafi sai dai baya wajen, bata yi tunanin fushin nasa har ya kai hakan ba, duk sai taji ba dadi har ta k'arasa gida tana tunanin yadda zatayi. A kofar gida ta tarar da Baba da Alhaji Faruku zasu tafi masallaci, k'asa ta tsuguna ta gaishe su ta shige ciki. Tana shiga ta gane Umma bata nan, kamar zatayi kuka ta shiga ciki tana hararar Habubu dake wasan ruwa, da gudu Walid ya fito ya fito yana fad'a mata Anty Maryam ta haihu ta haifi twins, murna ta hau yi ta shiga kiran wayar Umman, a gurguje ta shirya su Habubun ta basu abinci suka tafi gidan Anty Maryam d'in,  saboda zumud'i ko ta kan abinci bata bi ba, zuwan su gidan yasa ta manta da fushin da Hafiz yake da ita ta shiga cikin yan'uwa ana ta hira da farin ciki, wajajen magriba Umma ta sa suka tafi gida don ita achan zata kwana, a hanya ne kiran sa ya shigo mata, bata fuska tayi kadan kafin ta d'aga, shiru yayi be ce komai ba, sallama tayi ya amsa a cunkushe "Fushin ne?" Ta tambaya jin yadda ya amsa matan, katse kiran yayi kawai cikin tsananin mamaki tabi wayar da kallo, mene abun haushi kuma? Ta tambayi kanta, shiru tayi tana tunani, bin bayan kiran tayi har ta katse be d'aga ba, ajiyar zuciya ta sauke ta maida wayar jaka daidai lokacin da me napep ya ƙaraso kofar gidan su. *** Tsaki yaja yayi cilli da wayar yana mik'ewa akan yar katifar sa, globe din dakin ya kurawa ido yana tuna yadda Maryam ta rud'e daga ganin wani kato, tun dazu zuciyar shi bata kwanta ba yana ta tunanin abubuwa da yawa game da ita, mik'ewa yayi kawai ya fita waje. Dakin Inna ya shiga ya tarar da ita zaune da suwaiba suna hira, rake suke sha suna hira gwanin sha'awa. Gefe ya samu ya zauna ya dauki nasa raken ya hau sha don kawai ya manta da haushin da yake ji. *** Weekend d'in gaba daya a gida yayi shi saboda yadda tarin ya matsa masa, so yake ya fita yaji yadda abubuwan suke tafiya shi yasa ya shirya da yamma lik'is ya fito, Alhaji ne a falon tare da wani bako da be san waye ba, gaishe su yayi zai wuce ya dakatar dashi "Ya tarin?" "Ya tsaya ma, zan d'an fita ne." "Allah ya kara sauki." Bakon ya fad'a "Amin." Ya amsa a ciki ya juya zai fita, "Am... Muhammadu, nace kaje kaga yarinyar nan fa, dama nayi shiru ne saboda tarin naka, tun da zaka fita yanzu sai ka biya ko?" Da toh ya amsa yayi gaba, har ya juya ya sake tsaidashi "Koma ka sanar da Hajiya zaka je in yaso sai ta kira ta sanar musu chan d'in." A ba yadda zai yi ya amsa da toh,  yana jin kamar ya fasa ihu. Sai da ya gama uzurin da ya fitar da shi sannan ya shiga contact d'in sa ya lalubo number Zee, tana kwance taga kiran sa ta mike da sauri, tana d'agawa taji yace "Wacce unguwa ce ma gidan su Hajiya?" "Salanta?." "Tambaya kike?" "A..." Kit ya kashe wayar sa yana tsaki, juya motar yayi ya koma baya don ya baro hanyar, ya manta ne ma yana wani tunani chan daban, duhun magriba ne yasa ya d'an saki ransa saboda yasan kafa ta dauke, a masallaci kan layin ya tsaya yayi Sallah, sosai yaji dadin karatun limamin dan k'in fita yayi har sai da ya jira aka watse sannan ya k'arasa wajen sa ya gaishe shi. A wajen masallacin ya ajiye motar sa ya taka a kafa hannayen zube a cikin wandon sa. Kofar gate d'in ya zubawa ido yana kallo, juya kansa yake yana tunanin ta ina zai fara shiga gidan, Sultan ne ya fito da sauri yana gyara hannun rigar sa alamun alwala yayi yana sauri kar ya rasa sallah, yana ganin sa yayi saurin tsaidashi "Sannu." Ya mik'a masa hannu yana kallon gidan, "Wajen ta nazo ko zaka yi magana." "Wa fa?" Sultan Ya tambaya dan be gane kan zancen ba. Susa kansa yayi yana son tuno sunan, kallon sa Sultan ya sake yi sosai "Ikon Allah, wallahi ban gane ku ba, ashe Arkel ne." "Ni ne." Ya fad'a yana yak'i "Shiga toh mana, ka tsaya anan, rabon ka da gidan nan fa ka dade, ashe zaka gane." "Uhum." Kawai yace don be san wacce maganar zai amsa masa a ciki ba, bin bayan sa kawai yayi ciki yana jin kamar ya fasa ihu. Idar da sallar Hajiya Mama kenan taji maganar Sultan yana ce masa ya shigo, farin ciki ne ya lullube ta mik'e da dukkan saurin ta ta shiga dakin Rauda, tana zaune a gaban mirror tana shafe-shafe "Tashi tashi maza, gashi nan yazo." "Haba?" Ta fada da sauri tana mik'ewa "Me?" Hajiyan ta fad'a tana kallon ta "Naga kamar ya zo da wuri, ina laifin kamar 8." "Kin tashi ko sai na make ki?" Turo baki tayi ta sake gyara kanta ta, Hajiyan ce ta fara fita suka gaisa, sannan ta koma ta turo ta. Gefen kujerar da yake kai ta zauna tana murmushi, saurin dagowa yayi ya watsa mata kallo, far tayi da idon ta hakan ya sake kular dashi. Surutu ta hau yi masa cike da wayewa, jin ta kawai yake ya ma rasa me zai ce mata, batan ta gaji ba tayi shiru tana kallon sa "Are You done?" Ya tambaya yana kallon gefe, mamaki ne ya kamata, "Are You done?" Ya sake tambaya a karo na biyu, "Eh." Ta daga kai kawai dan ba karamin haushi maganar ta bata ba, mik'ewa yayi kawai yace "Kice mata na tafi." "Wa?" Ta tambaya ranta na sake ɓaci, da hannu ya nuna mata dakin Hajiyar, bin hannun sa tayi da kallo ta gane me yake nufi, kafin tayi magana har yayi gaba, komawa tayi kawai ta zauna a cikin kujerar tana cire dankwalin kanta. Tsaki yaja bayan ya fito daga gidan, be taba ma ganin mara class ba irin ta, wayar sa ce tayi k'ara ya tsaya cirowa yana sake sakin tsaki sau ba adadi, daidai lokacin Maryam ta fito daga gida zata shiga gidan Hajiyar Umma ta aiko ta ta gaya mata haihuwar Anty Maryam, tun ranar haihuwar bata dawo gida ba sai yau tayi tunanin ma sun fadawa Hajiyar, sai da ta tambaya sannan Habubu yace mata basu fada ba, fad'a ta hau maryam tace lallai sai ta je ta fad'a mata a lokacin kafin washegari ta shiga. Jin an fito ne yasa ya d'an haska da hasken dake kan wayar sa, a tunanin ta Sultan ne, dariya tayi ta ce "Ya Sultan ana nan ana yaudarar ne?" Jin beyi magana ba yasa ta matsowa sosai, cire wayar yayi daga kunnen sa ya haska ta. Da mamaki yake kallon ta, me take anan kuma? Ya ayyana a ransa, daidai lokacin wutar kofar gidan ta kawo, da sauri ta matsa baya tana xaro ido. _ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU😁._ *ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma *SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano) *KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo) *BURI ƊAYA!* (Mamu gee) *WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull) 👇🏻karku bari ayi babuku *ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu* *za'a tura kudin ta wannan accnt number din* Hafsat kabir umar 0225878823 GT bank Saika tura shaidar biya ga wannan number ta WhatsApp 08030811300 Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din 07067124863 Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya. *Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon wani*🤝🏽🤝🏽🤝🏽 [3/18, 22:22] Hafsat Rano: *SAUYIN K'ADDARA* *5* *©HAFSAT RANO* *®Haske Writers Association 💡* (Home of expect and perfect writers) **** "Laaa..." Kallon da yayi mata ne yasa tayi saurin cewa "Ina wuni." "Hello... Ina jinka..." Gaba yayi kawai tabi shi da harara tana tabe baki "Bakin ran tsiya." Gidan ta shiga, bangaren su Sultan ta wuce da shiga ta tarar da umman su tana cin tuwo, zama tayi ta gaishe ta kafin ta sanar mata da sakon umman su, murna tayi sosai tace zata shigo da safe in Sha Allah. Hajiya Mama na jin tafiyar sa ta fito da sauri taji kanun labari, yanayin data ga Raudan ne yasa ta sha jinin jikin ta, gefe ta zauna tana kallon ta "Ya kukayi?" "Gaskiya Hajiya da sake, bashi da mutunci wallahi Allah." "Toh... Me yace miki ni nake so naji, kar dai korar sa kikayi fa?" "Allah ni ba zan iya ba, me yake ji da kansa?" "Ba zaki fada min bane sai na makeki?" "Saboda wulakanci fa cewa yayi na gama?" "Sai me? "Babu fa abinda yace min, sai kace kanya ya barni ina ta zuba, kai da sake wallahi." "Ke fa ba'a abin arziki dake, shegiyar zuciyar ki ce zata kaiki ta baro ki, ba a hankali ake bin komai ba, a hankali zai saki jikin in kin iya yin ki." "Ayi masa magana gaskia, ba zan dauka ba ni dai." Kamar karta shiga wajen Hajiyar sai dai kuma tasan kadan da aikin Umma ta sake dawo da ita, bude kofar tayi suka juya gaba daya, saurin katse maganar ta tayi ta dan bata fuska, "Ba sallama sai ki fado haka." "Nayi baku ji bane, ina wuni.? "Lafiya." "Umma ce dama tace na fad'a miki Anty Maryam ta haihu, zata shigo gobe." "Yaushe ta haihun?" " Ranar juma'a." "Sai yau za'a fada min, saboda bani da muhimmanci?" "Ni tace na fad'a miki mantawa nayi ba laifin ta bane." "Saboda kin raina ni?" "Ayi hakuri." Da k'yar ta bud'e baki tace "Allah ya raya." *** Wanki ta tashi dashi ranar, bata yi niyyar zuwa aikin ba yau, mamakin yadda Hafiz ya dau fushi da ita take gashi har kwana  kusan uku kenan be sake neman ta ba, sosai abin ya dame ta saboda ba kad'an tayi kewar sa ba. Karatun suratul bakra da ta kunna a wayar ta ne ta tsaya alamun kira, da sauri ta goge hannun ta a jikin gefen zanin ta tana daukar wayar, ganin Hafiz ne ke kiran yasa tayi saurin d'agawa kar ta katse. "Zaki fita yau kuwa, naga shiru ina ta tsaye fa." "Kana wajen? Bari na fito toh." Ba maganar wanka tayi saurin daurayi wanda ta wanke ta shanya, a gurguje ta shirya tayi wa umma karyar supervisor d'in su ne ya kira ta fito, a chan ta hange shi ya jingina da jikin wani shago yana danna waya, ajiyar zuciya ta sauke ta k'arasa wajen sa, daga idon sa yayi yana kallon ta, murmushi yayi mata ta mayar masa. "Na zata ba zaki fito ba, wai fushi kike dani?" "Kai dai kake fushi dani." "Haka dai kika ce, sai ina? Naga kamar kinyi rana da zuqa." "Ban niyyar zuwa bane ma yau, kai ka fito dani, mu shiga school kawai ko?" "Muje toh, naga samarin ki na chan." "Kishi?" Ta fada tana dariya "Koma mene dai." *** *MUHAMMAD ARAB* Kida ne yake tashi sosai a wajen har baka jin maganar dan uwan ka, mata da maza ne cike da wajen kowa da abinda yake, yanayin wajen da shigar su kadai ta isa ta sanar da kai ina ne, babban club ne dake babban birnin na Cross river Yan mata biyu ne suka nufe shi suna taka rawa kadan kadan, tun da suka taho ya hango su sai dai bashi da niyyar motsawa daga in da yake, hannu daya daga ta mika masa ya kalli hannun ya kauda kansa, bangaren kan nasa ta sake komawa tana sake bashi hannun, a fusace ya tashi, tangal tangal yayi kamar zai fad'i dayar tayi saurin taro shi. Mustapha dake chan nesa dasu ya hango abinda yake faruwa, da sauri ya taso yazo wajen yana hararar su "Me haka?" Ya tambaya yana dank'ara musu harara, hararar suka maida masa a tare ta ja ta suka bar wajen, kama hannun sa yayi kawai ya riko shi jikin sa ganin yadda ya bugu sosai yana kokarin faduwa, matsa musu hanya sukayi ya fita dashi daga wajen gaba daya. A mota ya saka shi ya koma dayan bangaren yaja suka bar wajen. Gida ya ajiye shi ya wuce yana mamakin abokin nasa ***Bacci ya ke sosai har be san sanda gari ya waye ba, mik'a yayi ya mike ransa a jagule, toilet ya fara shiga ya watsa ruwa cike da k'yamar kansa, zuciyar sa babu dadi ya shirya ya tafi office. Aiki yake sosai baya ko gajiya, duk abinda zai yi don ya mantar dashi komai kawai yake ba tare da la'akari da halin zai shiga ba, a gajiya ya koma gida likis ya wurgar da komai a tsakiyar falon, sassauta zaman necktie din wuyan sa yayi ya fad'a saman kujera yana dafe da kansa, runtse idon sa yayi yana hango komai kamar alokacin yake faruwa. Saurin dauko wayar sa yayi ya saka #31 a farkon number da zai kira, Arkel na zaune gaban Ummi yana aiki da system d'in sa, duk motsi kad'an sai ya juya ya kalle ta, kiran da ya shigo wayar sa ya ne yasa shi kura wa wayar ido, private number da ya gani yake sake kallo, ya rasa wanda yake kiran sa da number tsawon wannan lokacin, duk lokacin da ya d'aga baya jin komai sai shashek'ar kuka k'asa-k'asa, ba karamin daure kai abin yake masa ba, yau ma hakan ce ta kasance ya d'aga kawai ya barta a handfree ya cigaba da aikin sa, sai bayan lokaci me tsawo sannan yaji an kashe. Kasa cigaba da abinda yake yayi kawai ya sauke komai ya kashe computer ya kwantar da kanshi a jikin gadon. Jin kiran sallah yasa ya fad'a toilet d'in dake manne dakin ya dauro alwala, fitowa yayi yana nad'e hannun rigar sa suka yi kicibis da Zee "Kana ciki dama?" "Kinje chan ne?" "Naje ai baka nan." "Owk. Sallah." "Owk." *** Zuciyar ta fes ta dawo gida dan ba k'aramin hira suka sha da Hafiz ba, kallon da umma ta aika mata ne yasa ta sha jinin jikin ta, bin bango ta fara yi dan tasan akwai magana, umman bata ce mata komai ba ta cigaba da aikin gyaran zogalen da take, sai data ajiye komai ta fito tana so tayi wa umman hira ta kasa samun fuska, har dare umman bata sakar mata fuska ba balle tasan laifin da tayi, gaba daya ta sha jinin jikin ta ta kasa sakewa, sai da umman ta bari su Habubu sun yi bacci sannan ta kira ta dakin ta, zama tayi tana leken fuskar umman, cikin in da in da tace "Umma ina wuni?" Dariya umma ta kunshe  ta sake tsare gida sosai kafin tace "Waye yake bin ki a unguwa kuna yawo.?" Zaro ido tayi ta dafe kirji "Umma waya gaya miki?" "Karya akayi miki? Amsa nake so kin dai san halin mahaifin ku sarai wallahi, bashi da zafi amma akan wannan ranki zai mugun ɓaci." "Hafiz ne." Ta fad'a tana sunkuyar da kai Fad'a sosai umma ta hau ta dashi a karshe tace sai ta fad'a wa Baban,tashin hankali sosai ta shiga dan tasan zafin umman ba daga mata zai ba, hakuri sosai ta hau bata da k'yar ta yarda akan ta fad'a masa lallai in har da gaske yake ya turo bata son hauka. Tana komawa d'aki taga misscals d'in Hafiz d'in, bin kiran tayi ya kashe ya kirata, hira yake mata amma ita sam hankalin ta baya wajen sa, daure wa tayi ta cije da k'yar tace "Am... Amm.. an ce wai ka turo." "Na'am." Ya fad'a cikin tashin hankali dan beyi tunanin hakan kusa ba. Sake maimaita wa tayi yayi shiru yana tunanin rayuwar, yanzu ma shi da mahaifiyar sa da Kanwar sa wani lokacin sai an sha wuya suke ci sau uku a rana, gashi buga bugar da yake ba wani samu ake sosai ba da har zai iya daukar nauyin mace, jin shirun yayi yawa ne yasa tace "Kayi hakuri kaga hakan shine ya dace." Da k'yar ya tattara nutsuwar sa waje daya yace "Shikenan zanyi magana da Inna gobe." "Karka damu please, kasan tambaya ba wai aure bane, kuzo d'in Baba ya san da kai shine." "Shikenan Allah ya taymaka mana." "Amin ." Kasa k'arasa hirar yayi ya mata sallama. Shiru tayi tana tunanin mafita, tasan dai Hafiz basu dashi, gashi ba wani zurfin ilimi yayi ba saboda halin yau da kullum, kamar tayi kuka haka take ji saboda halin da taji muryar sa kawai tasan akwai matsala, daren ranar haka ta raba shi tana tunanin makomar su. ** Mustapha ne ya kura masa ido yana kallon sa, kamar k'aramin yaro haka yake kuka sosai, sai da yayi me isar sa sannan ya tashi, cilla masa mukullin mota yayi yace "Lets go clubbing." "Amma Man baka ganin rashin dacewar hakan?" "Kai kaga haka, rayuwa ta bata da amfani kwata-kwata, barni kawai." "Amma..." "Bana son ji please, muje kawai am bored." "Shikenan lets go." *** Dan Dan, waye wannan kuma? Menene asalin labarin ne wai? Ga Ummi kuma a gefe, wace Hajiya Mama? Wace Hajiya Mero? Me yake Shirin faruwa da zai zama wata kaddara a rayuwar su? Sauyin ƙaddara!!! Akwai sarkakiya sosai ko? Muje zuwa komai zai warware. 🚴🚴🚴🚴🚴🚴🚴 #Muhammad Arkel #Hafiz #Muhammad Arab #Maryam #Rauda #zainab. _ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU😁._ *ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma *SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano) *KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo) *BURI ƊAYA!* (Mamu gee) *WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull) 👇🏻karku bari ayi babuku *ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu* *za'a tura kudin ta wannan accnt number din* Hafsat kabir umar 0225878823 GT bank Saika tura shaidar biya ga wannan number ta WhatsApp 08030811300 Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din 07067124863 Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya. *Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon Rano🚴🚴🚴 [3/18, 22:23] Hafsat Rano: *S K*     *6* *Littafin nan na kudi ne me so ya karanta ya nemi wannan number 08030811300* *** Tun bayan ajiyar wayar sai ya rasa in da xai saka ransa, wannan shi ake kira ga koshi ga kwanan yunwa, a tsarin sa beyi niyyar aure ba nan kusa,saboda bukatu na yau da kullum haka ya kusan kwana be runtsa ba yana tunanin mafita, da safe ya makara sosai dan har sai da Inna ta leko shi data ji shiru, sai a lokacin ya mike da k'yar idanuwan sa sun kad'a sunyi jajawur kamar gauta, kallo Inna ta bishi tana son gasgata abinda idon ta ya gani, basarwa yayi ya zari buta ya zagaya bayi, yana idar da sallar suwaiba ta shigo kiran sa, ya san sauran maganar, aljihun sa ya laluba ya ciro Naira dari biyu ya mik'a mita, hijab din ta ta zura ta tafi gidan koko, kokon hamsin sigan hamsin ta siyo musu ta hado da kosan d'ari, yana dauraye fuska da hannun sa ta shigo, kallon ta yayi cike da tausaya wa ya cigaba da abinda ya keyi, kayan jikin sa ya bari ya shafa mai ya fito, Inna tana lura dashi bashi da walwala kwata-kwata, gaishe ta yayi yana daga kofa kansa ya kasa yace '"Bari na fita Inna, naga ma ba ruwa a gidan, in na dawo sai a siya." "Abinci fa?" Kallon kwanon shan yayi ya kalli kosan, bashi da yawa su kansu ma ba dole ya ishe su ba "Kuci kawai Inna, zanci wani abu." "Kana da kudin ne?" "Za'a samu in Sha Allah." D'an jim tayi kafin tace "Allah ya kiyaye Allah ya tsare." "Amin." Ya amsa yana mik'ewa, a dawo lafiya Suwaiba tayi masa yayi mata murmushi kawai ya sa kai ya fice yana tunanin in da zai kama. Kofar famfo gidan kawun su ya sa'be ba tare da ya shirya ba, yaci sa'a kawun na gida yau be fita kasuwa ba yana hutawa, gaisawa sukayi da matar gidan kafin ta sanar ma kawun da zuwan sa. Da fara'a ya karbe shi suka gaisa da tambayar su Inna. Kadan kadan suke d'an taba hira yana ta ayyana ta ina zai fara masa maganar? Ya motsa bakin sa yafi sau hudu yana kasawa har sai da kawun yace "Akwai magana ne Hafizu?" Sosa kansa yayi cikin kunya yace "Dama... dama yarinyar da muke tare ne iyayen ta suka ce na tura magabata na." "Toh." "Eh wai daama a san dani ne dai kawai ba auren za'a yi ba." "Yar ina ce yarinyar?" "Anan unguwar tamu ne ba nisa." "Toh..., Shikenan dai, zan zo gida muyi maganar da mahaifiyar taka zuwa gobe in Sha Allah." "Nagode Allah ya k'ara girma." "Amin." "A huta lafiya." Karka cewa yayi ya ciro gudar dubu a aljihun sa yace "Ungo a sai wani abun, a gaishe su kafin na shigo." Hannu biyu yasa ya karba yayi masa godiya ya tafi. Kayan miya ya tsaya ya siya a gaban layin su da indomie ya kira me ruwa suka tafi gidan tare. Indomien ya bawa Suwaiba ta dafa mishi ya shige daki dan ranar baya jin sake fita, kwanciyar sa yayi yana tunanin yadda inna zata dauki maganar gobe idan Allah ya kaimu. Washe gari da wuri Kawu ya duro gidan, tabarma aka baje masa Hafiz naji kamar ya shige kasan gado, haka dai ya daure ya fito ya gaishe shi, har ya mik'e ya dawo da shi yana nuna masa wajen zama "Zauna ayi a gaban ka." A gefe ya zauna yana jin wani iri, kora wa Inna bayani yadda sukayi Kawu yayi karshe ya k'ark'are da "Shine dai maganar dama, ya kike ganin za ayi tun da dai nasan kun riga kunyi maganar tun ba yau ba." Kallon shi Inna tayi ya sunne kai k'asa, rasa abinda zatace tayi dan bata san kan zancen ba, numfasawa tayi tace "Duk yadda kukayi ai yayi, sai aje a tambayar masan." "Shikenan, zuwa karshen satin nan in sha Allah xamu zo dasu Bashari sai shi yayi mana jagora zuwa gidan." "Kana zuwa zance wajen yarinyar ai ko?" Ya fad'a yana kallon sa Girgiza kai yayi yana sake kasa da kai dan ba k'aramin nauyi ne da maganar aure ba, tafa hannu Inna tayi yayi saurin cewa "Ai yanzu ne idan aka tambaya min idan mahaifin nata ya san dani zai barni naje gidan nasu, haka tsarin gidan su yake sai an fara tambaya kafin a fara zuwa." "Hakan ma yayi ai, zamu zo zuwa karshen sati sai a sanar da iyayen yarinya." "Allah ya nuna mana, Allah ya saka da Alkhairi." Inna ta amsa Mik'ewa yayi ya musu sallama ya tafi, yana fita inna ta rike habarta tana tafa hannu "Yanzu Hafizu aure zaka jajibo wa kanka muna fama da wannan kauma- kaumar?" "Ai ba auren zasuyi mata yanzu ba fa, tace kawai a san dani ne dama." "Lallai, aka ce ma jiran ka zasu zauna yi kenan? Lallai baka da hankali." "Inna...ki sa albarka kawai dan Allah." "Shikenan, Allah ya tabbatar da alkhairi." "Amin Inna, ko ke fa." Har ya mik'e ta tsaidashi "Nace Allah sa baka yi mata saurin fushin nan naka da zafin rai? Kasan dai ina ce maka ka rage ko." "Ah haba banayi mata." "Allah yasa." Fita yayi shagon unguwar su ya karbi bashin katin dari biyu ya saka, gefe ya koma ya kira Maryam ya fesa mata abinda ya faru, ranar wuni sukayi suna farin ciki kamar an musu albishir da zama ma'aurata. **** Ranar jumma'a ta kama ranar sunan Anty Maryam, da wuri suka tashi ta shirya su Habubu da Walid ranar ba zasu makaranta ba, Umma da asubah ta tafi saboda aiki su kuma sai su tawo daga baya, tana gama shiryawa kiran Salim ya shigo wayar ta, ta san kwanan zancen, tana d'agawa taji yace "Baki zo ba har yanzu, zaki shigo kuwa?" Ahaap zancen kenan, dariya tayi tace "Afwan Oga, yau sunan Aunty na ne wallahi, na manta shaf jiya nace ba zan zo ba, ka bawa oga hakuri." "Toh... Amma kinga baki zo Monday ba fa, zaki hadu da fushin babban oga ba ruwana." "Ni dai ka taymaka min, ko kace ma bani da lafiya." Shigowar sa kenan office din yaji maganar ta a cikin waya saboda a handfree salim ya sakata yana cike wasu takardu, be taba tunanin ogan zai shigo a wannan lokacin ba, zama yayi ya harɗe kafa ya sa hannu ya dauki wayar ya matso da ita wajensa "Dan Aallah kace ban da lafiya, ko kuma kace dai wani abun idan yazo d'in, ogan ne baya d'aga kafa wallahi gashi kullum fuskar sa a turbune ba ya ko yar dariya." Jin yayi shiru ne yasa ta cewa "Ka dai taimaka, nasan kaima tsoron sa kake ko? Shi din ne da abin tsoro wallahi ba fara'a, sai dai anjiman yadda kukayi naji." "Kin gama." Ya fad'a cikin husky voice d'in sa Wani irin das taji tun daga saman kanta har kafarta, kiris ya rage ta subutar da wayar hannun ta, "Kin gama zagin nawa? Kizo yanzu kar ki wuce minti goma ." Kafin tayi magana ya kashe, kallon Salim yayi da yayi cilli -cilli yace "Wacce irin magana kuke haka da yarinyar nan har take irin wannan zantukan?" Share zufa salim yayi yace "Yau ne farko oga, ka yarda bamu taba magana makamanciyar wannan ba, ita ɗin ma tsautsayi ne kayi mata afuwa dan Allah dani baki d'aya." Daga masa hannu yayi kawai ya bar office d'in Tashin hankalin da ba'a sa masa rana, gidan Hajiya Mama ta tura su Habubu tace suje bangaren su Sultan su jira taje wajen aikin su ta dawo, sun saka rai da fita haka ta raka su gate d'in gidan ta dau hanya, ko gaban ta bata gani wulla kafar ta take ko ina, tsoron ta daya kar yayi rubutu a kanta ya aika dept, shikenan ta kad'e har ganyen ta, kad'an kad'an take saka gefen hijabin ta tana share hawaye har ta isa cikin kankanin lokaci, yanayin tafiyar ta kawai zaka kalla ka gane yanayin tashin hankalin da take ciki, ko ta kan me gadin wajen dake ta gaishe ta bata bi ba tayi ciki kawai,wajen salim ta wuce yana ganin ta ya saka hannun sa kasan bakin sa "Ya zanyi?" Ta fada a marairaice "Kije yana office d'in sama." "Na shiga uku, kar yayi reporting d'ina a makaranta." "Kai anya, jeki dai kiji." Kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki haka ta ja ƙafafuwan ta da k'yar ta hau saman tana wasi-wasin abinda zata tarar, knocking tayi yace ta shigo, wayyo Allah ,kunya kamar ta nutse haka taji, bude mata idon sa yayi baki daya ya zuba su akanta, kallon ta yake babu dauke ido yana danne dariyar da take son taso masa dan raban da yaji abinda ya bashi mamaki da dariya ya dade, tun da ya baro wajen salim yake dariya yana tuno yadda ta dage yana munafurcin sa, muryar ta tar babu alamun tsoro, amma ji ta yanzu kamar tsohuwar munafuka sai sunne kai take, sai daya gama kallon ta tsaf kafin yace "Me ya hanaki zuwa Monday?" "Kayi hakuri dan Allah." "Haka kawai?" "A ah wanki nayi.". "Wanki?" Ya fad'a yana kallon ta Daga kai tayi, "Yau ma wankin kike?" "A ah." "Mene?" "Haihuwa akayi mana yau suna." "Wa kika gaya wa?" "Ba kowa." "Me sa? "Ba komai." "Hmm." "Kayi hakuri." "Ni masifaffe ne? Tsoro na kike ji?" "A ah." Ta girgiza kai da sauri. "Hmm, shikenan." "Toh kayi hakuri dan Aallah." "Kinyi min laifi ne?" "Eh..." "Laifin me?" Ya sake gyara zama "Dama... Dama maganar ka nayi da bata...." "Magana ko gulma?" Ya katse ta yana yin murmushi kad'an "Gulma?" Ta fad'a da sigar tambaya "Are u asking me, ba gulman bane?" "Shine,amma kayi hakuri." "Jeki kawai, nayi magana da yawa kaina har ya fara ciwo." A ranta tayi tsaki kad'an ta juya da sauri zata fita taji yace "Kin san haramcin mace ta saka turare ta fita waje?" Tsayawa tayi chak dan bata yi tunanin maganar ba "Kin sani?" Ya sake tambaya "A ah." Ta fad'a a sanyaye "Ba kyau toh, ki daina." "Tom... Nagode." Rufe idon sa yayi be kara magana ba, tunani ya fara yi, a hankali ya furta _"Where are you? I need u please come back soon"_ *** Maryam na fita tayi waje kawai tana saurin tafiya gidan suna, ashe yana da kirki haka ta dinga raya wa a zuciyarta, bata tab'a tunanin iya kar abinda zai ce mata kenan ba, gaskiya ya iya rud'a mutum. *** Shafa kowa a jikin hoton yake daya bayan daya, su biyar ne cif hadda shi, sanye suke da kaya iri daya shadda dark ash, mazan sun sha babbar riga matan kuma doguwar riga, a tsakiya suka saka Ummi da Alhaji su biyu yaya Nabila ta sunkuyo ta bayan Ummi. Dariya suke gaba daya akayi hoton da wata karamar Sallah, kana ganin hoton kasan anyi shi ne cikin so da kaunar juna. Girgiza kansa yayi ya share kwallar data zubo masa, ba zai taba manta wa da komai ba, tsawon lokacin da ya dauka ba tare da su ba yanayin rayuwar ne a cikin mawuyacin hali, bashi da wani walwala ko farin ciki shi dai gashi nan ne, a duk san da ya tuna gida da abinda ya faru ya kan ji kamar rayuwar sa zata kare, kamar bashi da wani sauran amfani a duniyar ma baki daya, amfanin me zai yi da rayuwar sa bayan abinda ya aikata? Gaba daya ya cire tsammani da wata rayuwar jin dadi shi yasa yake abubuwan sa kawai da yake ganin sune daidai, hakkin mutanen biyu ba zai taba barin sa ya cigaba da rayuwa me dadi ba. Ƙatuwar kwalbar giyar da ke gaban sa ya sake kafa wa a bakin sa, sai daya tabbatar yayi mata tatas sannan ya ajiye yana lumshe idon sa, wannan shine kadai abinda yake ganin shine daidai da rayuwar sa. *Waye wannan? Mene asalin labarin sa?*😳🤔 *** Kiran ta Hajiya Mama tayi tana son ganin ta,sam Rauda ya kafe akan ita fa ba zata aure shi ba, bata a wulakanci, Babu bata lokaci ta taho gidan. A gaba suka saka ta suna ta yi mata huduba, ta in da suke fita ba tanan suke shiga ba, sai da suka tabbatar da amincewar ta suka kwadaita mata abinda suke so ta samu, dama ita a tsarin ta tana son huta, ba wuya suka hilace ta suka sa ta amince da abinda suke so. Duk abin nan a kunne Alhaji Faruku, fasa shiga yayi ya koma yana jin zuciyar sa na tafasa,be taba tunanin abin nasu ya kai haka ba, gaba daya Rauda halin Hajiya mahaifiyar su ta dauka shiyasa kullum tana wajen ta, ba halin su daya da Sultan ba shiyasa sam baya shiri da ita, da yana murnar auren nata ne kawai zai sa ta dawo hankalin ta dan har ga Allah babu wanda baya son dansa ya zama nagartacce sai dai babu yadda zaiyi da ita dan ance uwa uwa ce kuma tafi gaban wasa. Bangaren sa ya koma kawai yana jin ba dadi,be sake fita ba har sai da Baban su Maryam ya turo yana son ganin shi *********** _ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU😁._ *ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma *SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano) *KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo) *BURI ƊAYA!* (Mamu gee) *WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull) 👇🏻karku bari ayi babuku *ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu* *za'a tura kudin ta wannan accnt number din* Hafsat kabir umar 0225878823 GT bank Saika tura shaidar biya ga wannan number ta WhatsApp 08030811300 Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din 07067124863 Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya. *Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon Rano🚴🚴🚴 [3/18, 22:23] Hafsat Rano: *Sauyin Kaddara* *7* *Littafin nan na kudi ne me so ya karanta ya nemi wannan number 08030811300* * *** Dogon Hijab purple ta saka har k'asa ta nufi gidan Hajiya Mama, Alhaji Faruku na falon sa yana ganin ta ya sake fuskar sa, a kasa ta zauna duk kunya ya ishe ta, waya yake sai da ya gama sannan ya ajiye yana duban Sultan dake kallo "Bamu waje malam." Sosa kai yayi ya juya ya fita yana hararar ta kasa kasa ba tare da ya bari ya gani ba "Maryama." Ya kira sunan ta A hankali ta amsa, "Ajin ki nawa yanzu?. "Level 3 muke last semester." "Masha Allah, iyayen yaron nan sun zo sun same ni akan maganar, toh alhamdulillah na yaba da su, har ma na saka an gudanar min da bincike akan shi yaron, abun farin ciki shine ban same shi da wani abu naki ko na batanci ba, abu daya na ji a game dashi da yasa ni dan shakku akai duk da shima ɗin ina ganin ba wani babban abu bane dama mutunci ake so, kina ganin zaki iya zama dashi a hakan kinga dai ke kinyi karatu daidai gwargwado amma shi ance min iya kar sa NCE ita ɗin ba ance be karbi result ɗin ba har yau, kina ganin hakan ba zai jawo muku matsala ba? Shiru tayi tana tuno wata rana da suke waya daga tayi magana akan karatu shikenan ya hau fushi yace ta fada masa magana dan taga be je jami'ah ba, haka dai da k'yar ta samu suka shirya gashi ta kwallafa rai akan sa sosai, Alhaji Faruku na ta kallon ta yana lura da yanayin ta, sai data gama tunani kafin ta sauke kanta kasa ba tare da tace komai ba "Na fadawa iyayen sa zai iya zuwa wajen ki tun da kin aminta dashi" Wani irin farin ciki ne ya taso mata har ta kasa boyewa, ganin haka yasa shi cewa "Bana son dogon zance sannan bana son zuwan dare, in Sha Allah da kun gama fuskantar juna za'a saka komai ayi a gama, ita ma yar uwarki Rauda na faɗa mata kamar haka." "Nagode Abba Allah ya kara girma." "Amin." Jiki a sanyaye ta taso ta fito, tunanin maganar take idan Hafiz yaji, zancen gaskia idan aka ce maganar aure nan kusa tasan ba lallai Hafiz din ya iya ba, gida ta koma ta zabga tagumi tana tunanin mafita. Umma na kallon ta ta share ta, tun daga lokacin ta daina walwala kwata-kwata. Lokacin da Hafiz ya fara zuwa ranar kasa fada masa komai tayi game da maganar, sai da yayi zuwa na uku sannan ta daure ta sanar masa, maimakon taga ya shiga tashin hankalin sai taga al'adun haka, wakewa yayi suka cigaba da hirar su har lokacin tafiyar sa tayi ya tafi. Ko da yaje gida ya sanar wa Inna komai dama tasan za'a rina, shawarwari kawai ta bashi tun da dai ya riga ya kai kansa kuma dole ayi, haka dai ya koma daki yana tunanin mafita. Tun daga ranar ya shiga fafutukar yadda zai yi, bashi da lokacin kansa sai bige-bige, sosai take tausaya masa dan ba karamin wahala yake sha ba, yar wayar ma ba sosai suke samu suyi ba. Watan ta uku ta daina zuwa Siwes sai dai taje sau daya a sati, rabon da ta hadu da shi ba zata iya tunawa ba, Allah Allah take ma tayi tayi ta gama gashi da sauran wajen wata uku. *** Fito da komai yayi ya ajiye shi a saman centre table, d'aya bayan d'aya yake bin su da ido kafin ya tsaya akan farar takardar dake ninke, kura mata ido yayi yana nazari, chan k'asa ya mai da ita ya rufe komai, daukar abinda zai dauka yayi ya fice kawai yana ayyana abubuwa da yawa. Dakin da Ummi take ya kalla, har zai wuce sai kuma ya dawo da baya ya bude kofar, Hajiya Mero na zaune a gefen gadon nurse tana goge wa Ummi jikinta, magana suke k'asa-k'asa tana ganin shi tayi firgigit, cikin salon waye wa ta fadada fara'ar fuskar ta "Son, Ashe kana ciki, sai ina kuma?" Dan kallon ta yayi yace "cafe" ya maida hankali akan nurse din dake matse towel daka cikin ruwa, saurin kauda tunanin sa tayi ta hanyar sakin ajiyar zuciya cike da jimami tace "Akwai improvement sosai a tare da ita, shi yasa nake so kayi aure saboda kai kanki sai kafi samun kwanciyar hankali da matar ka wajen ta akan nurses din, su sai suzo su dinga dubata ko duk sati ne." "Hmmm. Dan bamu waje mana" ya fada yana kallon nurse din, tsam ta mik'e ta raba ta gefe ta fice, takowa yayi har wajen gaban gadon ya zura wa ummin ido, ya rasa dalilin da yasa hankalin sa yaki yarda da barin ta da nurses din, maida kallon sa yayi kanta ta sake gyara zaman ta "Hajiya... Me ya sami Ummi ne wai ni? Tsawon wannan lokacin babu abinda aka ce sila, me hakan ke nufi ne?" Sosai gaban ta ya fadi ta kalle shi da sauri dan bata yi tunanin tambayar ba, kamar daga sama ta kuma jin tambayar sa data sake dagula lissafin ta "Shi fa? Ina yake? Me ya faru a ranar ne? ke kadai kike gidan nan, ya kamata ace kinsan komai." "Zanyi maka karya ne? Bansan komai ba, ranar na fita unguwa, kuma wallahi tallahi bansan komai akai ba, ka yadda dani." Runtse idon sa yayi kawai ba tare da ya tanka ba, jijiyoyin kansa ne suka sake fitowa sosai cike da bacin rai, kaf duniyar nan ya rasa wanda zai warware masa komai, me ya faru? Me ya faru? Ya shiga tambayar zuciyar sa. "Arkel..." "Shikenan." Juyawa yayi da sauri ya fita daga dakin, fasa fita yayi ya koma saman zuciyar sa a cunkushe, kansa wani irin sarawa yake kamar zai rabe biyu, saman gadon sa ya fada kawai ya kudundune a bargo yana jin wani irin yanayi yana huda ko ina na jikin sa. Kiran sa Ya Nabila take tayi yana jin ta ya kasa d'agawa, yau duk tsawon ranar a daki yayi kamar mara lafiya, Forex din da yakeyi ma yau be samu ya duba ba, komai ya taso masa kamar farko, tunanin sa ya kasa wuce masa in da ya tsaya, menene dalili ko sababin da yasa komai ya tarwatse? Ya akai haka? Kiran sallar magriba da ake tayi a masallatai yasa ya yunkura ya tashi da k'yar yana cije lebe, alwala yayi ya cire kayan jikin sa ya mayar da jallabiya ya dora hula ya nufi masallaci, ya dade yana addua akan komai kafin ya fito daga masallacin, ji yayi ba zai koma gida ba kawai ya tafi titi ya tari me napep ya tafi gidan yaya Nabila, a waje ya tarar da mijinta da wani abokin sa suka gaisa ya shiga ciki, mamaki sosai tayi ganin shi dan tasan ba karamin abu ne yake kawo shi ba, yaran ma haka su ka hau murna ga uncle ga uncle, daya bayan daya ya bisu da chocolate da ya siyo musu a hanya sannan ya samu suka barshi. Kallon sa tayi bayan ta kora yaran dakin su, "Suprise visit inji Bature." Ya riga ta yin korafin da take shirin yi, dariya tayi kawai tasan baya son korafin nata ne, gaisawa sukayi ta mike ta shiga Kitchen, tuwo da miya ta hado masa akan tray sai zobo me sanyi, yana ganin fitowar ta daga kitchen yayi saurin sauka kasa ya gyara zama tana nad'e hannu riga "Wai har ka gane?" Tayi dariya tana ajiye wa "Tun da na ga yallabai a waje ai nasan kwanan zancen." "Wato har kasan idan yana nan tuwo nake kenan." Dariya yayi kawai ya wanke hannun sa a d'an bowl d'in data kawo masa ya shiga cin tuwon, kurbar zobo yayi ya kalle ta yana dan bata fuska "Dama zan dinga samun irin tuwon nan naki kullum, da ai ni na huta." "Aure fa?" Ta yi dariya Nan danan ya bata rai da ya tuno da Rauda, tsaki yaja kawai ya ce "Har kin tuna min wallahi." "Toh sai me? Ni ai hankali na ya kusa kwanciya wallahi, ka rage wannan masifar taka." "Masifa kuma? Haka nake?" Ya tambaya yana bata attension din shi gaba daya "Yes masifa mana, abu kadan sai ka hau kayi fam." Murmushi yayi kadan yana tuno wayar ta, wai shine masifaffe? Wallahi yarinyar nan ma taci abinci. "Wa fa?" Ta tambaya tana kallon sa ganin yana magana har da murmushi Saurin girgiza kansa yayi dan be san ma a fili yayi maganar ba, wanke hannun sa yayi ya mike ya hau kwashe kayan, saurin dakatar dashi tayi ta karba taje ta ajiye ta dawo. Saman kujerar ya zauna yana maida hankalin sa kan tv, remote ya dauka ya chanja tashar zuwa channels, hoton da ya bayyana a akan screen din ne yasa daga shi har ita suka yi wata irin zabura, labarai yake karantawa cike da kwarewa, fuskar sa ta cika sosai da sai dai yasha gyara saboda aikin sa, babu abu daya daya banbanta da shi a da sai cikar fuskar sa da gashi, daidai lokacin yake kokarin tattare shirin, duk sunyi tsaye a gaban talabijin din suna jira suga karshe, cikin harshen nasara ya yi godiya a karshe ya fadi sunan sa. MUHAMMAD ARAB ALMUSTAPHA. Screen din na dauke wa ya Nabila ta shiga lalubar wayar ta da sauri, Arkel kamar gunki haka ya kame a wajen ya rasa yadda zai fassara al'amarin, dan uwan sa rabin jikin sa da suka jima suna nema shine ya cigaba da rayuwa a wani waje daban ba tare da su ba? Duk shakuwar su da kaunar junan su ya tashi kenan? Wanne irin babban laifi ne haka da har zai bar gida? Ya bar dangin sa da kowa nasa? Wa zai amsa masa tambayoyin nan? Manage dan Allah ciwon ido ya sani gaba. 😭 Bana so kuyi ta jira ne shiyasa nayi wannan [3/18, 22:23] Hafsat Rano: *SAUYIN K'ADDARA* *8* *HAFSAT RANO* *ZAFAFA BIYAR MASU ZAFI*😅😂 *Littafin nan na kudi ne me so ya karanta ya nemi wannan number 08030811300 *** A hannu ya riko wayar ya shigo gidan ba tare da ya daga ba, "Ya akayi? Naga kin kira." Ya fada yana shiga falon, kallon yanayin da Arkel yake ciki ya yi kafin ya maida kallon sa kanta "akwai matsala ne?" Ya sake tambaya "Please wa ka sani a channel tv?" "Mutane da yawa, me ya faru ne wai?" Ido jajir Arkel ya dawo tsakiyar falon ya zauna, yaya Nabila a tsaye ta tsaya ta kasa zaman, cikin dashewar murya yace "Yanzu muka ga an nuna shi, ashe yana raye?" Yayi maganar yana jinjina da jikin kujerar yana jin wani irin yanayi "Are you serious? Arab yana nan da rai kake nufi??" "Yes... Yanzu ma aka gama program din sa a channel Tv, he's still alive." "Toh how comes? Bari kiga dai,bari nayi mana confirming." Daukar wayar sa yayi ya kira wani abokin aikin sa da ya san sun yi aiki tare a gidan Tv na NTA daga baya ya koma channel Tv, har ta k'araci ringing d'in ta be dauka ba, haka yayi ta fama kiran mutane baya samun su. A yadda yake jin kirjin sa yayi nauyi yasa kawai yayi musu sallama ya fito, ko ta ina gefe kafar sa yake har ya isa titi ga dare ya soma yi dama, yana tsayewa ya samu abun hawa ya nufi gida zuciyar sa kamar zata tarwatse ta fito, kansa cike yake da tunanin abinda ya faru, Hajiya Mero na zaune a falon ita da Alhajin su ya shigo bakin sa dauke da sallama duk kuwa da ba wai da karfi yayi ba amma dai sun ji shi, niyyar sa ya wuce daki amma ganin idon su akansa yasa ya dawo da baya ya zauna daga dan gefe ya yi irin zaman rakumi kansa a kasa yana kokarin danne komai. Maganar Rauda sukeyi ya shigo hakan ya k'ara yi wa Hajiya Mero dadi "Ya ake ciki kai da Rauda?" Muryar Alhaji ta daki dodon kunnen sa. "Mun gama ai." Ya amsa dan har ga Allah baya son ko sunan ta yaji balle wani abu da ya dangance ta, idan sun ga dama su dauko ta su auro masa ita a gobe ma ba sai jibi ba shi bashi da wata damuwa balle yanzu da wannan abin ya kunno kai, "Magana fa nake ma" Dagowa yayi da sauri dan be ji me aka ce masa ba ya tafi tunani "Cewa nayi kun game me? Ko kana nufin kun sasanta kanku?" "Eh." Ya amsa kai tsaye. "Masha Allah, wannan labari yayi min dad'i, kinji yaran naki Hajiya ashe sun hade kansu har muna tunanin kar suki." "Wallahi fa, dama ita Rauda tuni na gama gano ta, ta riga ta amince dari bisa dari kunya ce kawai irin ta ta." "Kunya?" Ya fad'a a zuciyar sa, gaskia an cuci kunya wallahi. Dariyar farin ciki Alhaji yayi ya sake kishingid'a yana mike ƙafafuwan sa, matsa masa kafar ta shiga yi cike da kissa, "Zan iya tafiya?" Arkel da ya kagu ya bar wajen yayi maganar. "Sarkin daki, ina Sarkin falo kuma?" Da Sauri ya kalli Alhaji, shi din ma kallon sa yayi dan be yi tunanin maganar zata fito mishi ba, hankali tashe Hajiya Mero ta dago ita ma jin abinda Alhajin yace, "Kana tuna shi dama?" Idon sa ya cicciko yayi maganar, kauda kai Alhaji yayi kawai ba tare da ya ce komai ba, ya zai ya manta da shi? Akwai mutumin da zai ce ya manta da d'an sa kuwa duk duniya? Kawai dai ya rasa dalilin da ko zancen sa baya so ayi masa. Girgiza kai Arkel yayi ya mik'e kawai, har zai tafi sai ya dawo a hankali yace "Na gano in da yake." Wata irin zabura Hajiya Mero tayi kofin da Alhaji ya gama shan Lipton ta bige da hannun ta ragowar ya zube akan carpet, kallon ta sukayi dukkan su suna mamakin abinda ya sata wannan firgicin, saurin waskewa tayi tace "Me kace? Kaga kasa na kasa zama sosai saboda zumud'i." Kin magana yayi ya bar wajen kawai, kallon Alhaji tayi taga yana kallon wani wajen daban, cikin tararradin amsar da zata tarar tace "Kaji kuwa me yace? Ko kunne na ke min gizo?" "Bana son maganar nan dan Allah." Ajiyar zuciya ta sauke da karfi har sai da ya sake dubanta, mikewa tayi tana kwala kiran Sadiya ta shiga daki a zuwan abu zata dauko. Tana shigewa ya tashi ya fara zagaye a tsakiyar falon, duk yadda yaso yayi tunanin maganar sai yaji ya kasa, sai yaji kamar ana hanashi tunanin su, dakin ya kura wa ido yana tuno dad'ewar da yayi be shiga ba, kamar ana fizgoshi baya ya dau hanyar dakin yana wasi-wasi, murd'a handle din yayi yaji kamar an turo shi baya, daidai lokacin Hajiya Mero ta fito hannun ta dauke da kwalbar turaren wuta, ganin shi a kofar dakin ba karamin kadawa cikin ta yayi ba, da wani irin sauri da bata san tana dashi ba ta isa kofar tasa hannu sai ji yayi an riko rigar sa, kallon ta yayi kawai ya saki handle din, "Kana so ka ganta ne?" Tayi masa tambayar tana kallon cikin idon sa, girgiza mata kai yayi ya juya kawai ba tare da ya shiga ba.. Wata wawuyar ajiyar zuciya ta sake sauke wa a karo na uku, dire kwalbar tayi a jikin wajen ta juya da sauri tabi bayan sa, kafin taje har ya rufe kofar dakin, hannu biyu tasa ta rik'e kanta, idan komai ya bayyana fa?" Ta shiga tambayar kanta, babu abinda zai faru, dayar zuciyar ta ta ta sanar da ita *** Wajen karfe biyu ya rasa abinda yake damun sa, wayar sa dake gefen sa tana ta haske alamun akwai sako a kan wayar, bashi da zarafin dubawa dan baki daya kuzarin sa ya tafi wajen matsanancin tunanin da ya sawa kansa, duk yadda yaso ya gano dalilin da yasa ya tafi ya barsu ya kasa samun ko da kwakkwara guda daya, tunanin rayuwar su ta baya da yadda suka gina komai yasa yake jin lallai akwai wani babban al'amari da yasa shi yin haka. Da safe a makare ya tashi saboda ya raba dare yana tunanin mafita, babu wani abu da yasan ya cimma na nasara a tunanin nasa shi yasa ma ya hakuri ya kwanta dan ya ga alamun zai iya kai asubah be samo bakin zaren ba, abu daya ya sani shine dole zai yi bincike ya gano garin da yake zaune, idan ya samu wannan komai me sauki ne, hakan kuma ba zai yi wuya ba tun da har ya iya bayyana fuskar sa a gidan Tv. Sharce kansa yake a gaban mudubi ya kurawa fuskar sa ido, gani yayi yayi zuru zuri da shi kamar wanda ya kwanta jinya, dan sakin ransa yayi yana cigaba da kallon kan nasa, so yake ya hango abin tsoron da yar rainin hankalin chan tace, shi yasan daidai yake abubuwan sa amma ya rasa dalilin da yasa yake yawan tunawa da maganar ta mafi akasarin lokuta, share wa yayi ya bude wardrobe d'in sa ya ciro shud'iyar riga long sleeve da baƙin jeans, yana balle botir ɗin karshe wayar sa ta hau vibration, da sauri ya dauka ganin number Kamal mijin Ya Nabila, "Owk gani nan."Abinda yace kenan ya zura takalmin sa ya fito, Zee na zaune a falon ta sauko tayi saurin sakin murmushi, mai da mata yayi da murmushin duk da ba wai yana da walwala bane sai dan tausayin data ke bashi, har waje ta rakashi ba maganar breakfast ya fice da sauri. A office din sa suka hadu nan branch na NTA dake kano, yana zuwa suka shiga mota suka nufi unguwar danladi na sidi, a hanya yake fada masa jiya ya kira abokin nasa da sukayi aiki tare ya koma channel kuma ya bashi tabbacin cewa shine kuma yana Cross river yanzu ma address din sa zasu je su karba a wajen wani abokin aikin sa zai kuma iya barin Kano a yau shi yasa ma suke sauri. Rufe gidan yayi kenan yana mai da dan mukullin cikin yar karamar jakar sa ta matafiya suka riske shi. Ido ya zura wa Arkel cike da mamakin ganin sa nan bayan ya baro shi a Chan, duk da dama ya taba fada mishi dan asalin Kano ne shi amma beyi tunanin ganin sa ba, be bar mamaki ba sai da suka ƙaraso wajen sa. Rike ha'ba yayi yace: "Man yaushe kazo Kano bayan na baro ka CR? Dariyar yak'e Arkel yayi dan ya gane in da zancen ya dosa, kamal ne ya fara miƙa masa hannu suka yi musabah sannan Arkel ma ya bashi. Jikin motar su suka matsa Kamal yace "Kar dai tafiya zakayi muka tsaidaka?" "No ba komai, zamu iya magana ai akwai sauran lokaci." "Owk mun gode, Please alfarma muke so wajen ka, wannan da ka gani twin brother d'in wanda ka sani ne, be shi d'in bane." "Are You Serious?" Ya fad'a yana xaro ido dan idan ba yaga girman Kamal ba zai iya cewa karya yake. Dariya Kamal yayi yace "Gaskiyar kenan, twins ne wannan Muhammad Arkel sunan sa, wanda ka sani kuma Muhammad Arab." "Ikon Allah." "Abun da ya kawo mu shine number Arab, ka taimaka ka bamu number sa muna so mu kai masa ziyara gashi mun yi loosing contact din sa, tsohuwar number sa kuma ta daina shiga, kaga tafiya ba zata yiwu babu number ba, gashi irin suprise visit muke so muyi masa, ba ma so ya sani sai yafi murna." "Haka ne, tare muke dashi ai a wajen aiki, yana da kirki sosai gaskia, dan idan ba dan nasan ba zaku min karya ba ma sai nace shine wannan, bari muga." Number ya lalubo a wayar ya karanto musu, godia sukayi masa suka tafi, a hanya Arkel ya kasa nutsuwa sai da yayi dialing number, tana ta ringing ba'a daga ba, cigaba da kira yayi ba kakkautawa, Kamal ne ya rik'e wayar yana kokarin sake kira, "Ka sani ko yana da number ka? He won't answer idan yasan kai ne." "Me nayi masa?" Ya faɗa cikin Muryar rauni "Baka yi masa komai ba, mu bi komai a sannu, kar kayi stressing kanka da yawa zamu samu komai a hankali." Ajiye wayar yayi ya cigaba da tukin sa kawai, a wajen aikin ya ajiye kamal ya wuce. **** Shara take kunnen ta sakale da waya, magana suke da Hafiz kasa kasa take dariya, shigowar Baba gidan bayan ya tafi yasa ta yi shiru da wayar da take, kiran umma yake ta fito da sauri, daga tsayen ba tare da ya shiga dakin ba yace "Umaru ne ya tsaidani akan maganar yaran nan, yace min ya riga ya gama shirya komai rana ma zai saka, tare yake so ayi dana Raudatu, toh ni dai nace masa duk yanda ya yanke, sai ki fito da tsohuwar ajiyar ki dan nan kusa za'ayi komai." Ya kasashe cikin zolaya, shiru umma tayi bata ce komai ba, ya riga ya san ba zata ce d'in ba kuma, juyawa yayi ya fice daga gidan. Gaba daya sai sharar ta fita akan ta, kasa k'arasa wa tayi ta ajiye tsintsiyar ta shige daki da sauri, umma bata kulata ba ita ma tana bukatar tunani, dama tasan haka za'ayi kuma ita shine kwanciyar hankalin ta, karatun daidai gwargwado ai an same shi, auren shine mutuncin mace. Daki ta koma ta kira Anty Maryam ta sanar da ita abinda yake faruwa. *** Kallon shi Hajiya Mama take har ya kai aya, wata uwar harara take watsa masa tana girgiza kafa "Ka gama?" Tace tana kallon sa "Na gama Hajiya." Ya fada cike da ladabi "A wanne dalili zaka hada mana biki da wadanchan mutanen?". "Yaya Garba ne fa Hajiya." "Yaya Garban! Kanin uban ka ne ko na uwar ka?" "Allah ya baki hakuri Hajiya,Allah ya huci zuciyar ki, nayi ne dan karfafa zumunci kawai, bansan zai bata miki rai ba." "Toh naji." "Allah ya huci zuciyar ki." "Amin." Ta amsa tana kauda kai gefe Tashi yayi ya gyara babbar rigar sa, Rauda ya kwala wa kira ta fito da sauri, daga gefe ta tsugunna tace "Gani Abba." "Na riga nayi magana da mahaifin yaron, sati hudu na saka tun da kun riga kun gama daidai ta kanku, sai dai babu lefe, babu laifi idan yayi miki ya ajiye idan kika je gidan sa ya baki, amma ban yarda a kawo min nan ba." Baki sake Hajiya Mama take kallon sa, wani salon wulakanci ne wannan ko me? Dan wadanchan matsiyatan zasu auri matsiyaci kamar su sai a hana jikar ta wataya wa, ta san halin shi sarai yayi hakan ne saboda su, kar a kawo lefen aga nata kamar na kaza, dan a yadda taji labari yaron bashi da komai sai garari kawai yake a gari da sunan bige bige. "Hajiya mun fita ayi mana addu'a." "Allah ya bada sa'a." Yana jin yadda ta amsa ɗin yasan bata ji dadin abinda yace ba, sai dai dole ba zai yadda su wulakanta ba, da Rauda da Maryam duk daya suke a wajen sa babu bambanci, kuma yasan abinda yake yi akan daidai yake. Yana fita tace wa Rauda "Kira min H Mero da gaggawa." *** Hafiz abin dunya ya ishe shi tun bayan da Kawu ya kira ya sanar masa sakon Alhaji Faruku yasa biki wata daya kachal, duk da ya dauke masa babban aikin wato lefe amma ko muhallin da zasu zauna babu, gidan nasu daki daya ne felle sai nasa dake zauren gidan, ga Inna ga Suwaiba da babu alamar tashin ta nan kusa. Yana kwance inna ta budo labulen dakin nasa, cire kansa yayi da k'yar ya kalle ta cikin mugun ciwon kai da yake ji kamar zai rabe biyu, "Maganar da Kawun ku ya fada ce ta kwantar da kai wai?" "Ita ce inna, bansan ya zanyi ba wallahi, gashi ina son ta, wata daya yayi min kadan Inna, son samu asa kamar shekara daya, zuwa lokacin na nemi kudi na karbo result d'ina a Sa'adatu Rimi, kinga ko teaching sai na nema." "Toh sannu, da yake jiran ka zasu tsaya yi ko?" "Amma inna ai yayi wuri, shi in ya shirya ni ai ban shirya ba, sai a duba ni fisabilillah" "Kasan baka shirya ba ka tura kawun ku? Ko shawara bakayi dani ba sai ganin sa nayi, shiyasa babu ruwana in kana son Yar su toh, ga dakin nan naka ai zaku iya zama a ciki." "Nan dakin kuma Inna?" "Toh ba aure kake so ba?" Shiru yayi dan ya gano Inna so take ta nuna masa kuskuren sa nakin shawara da ita, shi dai yanzu ba wannan yake bukata ba, yadda zai gama komai cikin wata daya kachal shine kawai. Sakin labulen tayi ta shige ciki ta barshi da karantun wasikar jaki, rashin mafita yasa ya tashi ya fice daga gidan *** Allah sarki Malam Hafizu, rashin kuɗi be ba wallahi, Allah ya bamu me albarka, talauci ba dadi😔. Duk wanda ya karanta page din Nan Allah ya sa yana daga filon barcin sa yaga kudi dumus😂😂🤣 Akwai runguntsumi a gaba, har yanzu bamu shiga ainihin labarin ba, masu magana sun ce slow and steady win da race, a hankali zamu zo in da muke son zuwa. **** _ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU😁._ *ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma *SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano) *KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo) *BURI ƊAYA!* (Mamu gee) *WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull) 👇🏻karku bari ayi babuku *ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu* *za'a tura kudin ta wannan accnt number din* Hafsat kabir umar 0225878823 GT bank Saika tura shaidar biya ga wannan number ta WhatsApp 08030811300 Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din 07067124863 Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya. *Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon Rano🚴🚴🚴 *SAUYIN K'ADDARA*          *9-10* ©*Hafsat Rano* *_ZAFAFA  BIYAR na kudi ne idan kana son kowanne daga ciki ka nemi Wannan numbers din_* *08030811300* *07067124863* *_Daurin boye_* _safiyya huguma_ *_Buri daya_* _mamuhgee_ *_Wutsiyar rakumi_* _billyn Abdul_ *_Kai min halacci_* _Miss xoxo_ *_Sauyin kaddara_* _hafsat rano_ *** A in da suka saba haduwa da Hafiz suka hadu, kallon sa take duk yayi baki ya rame kamar ba shi ba, yanayin fuskar sa kadai zaka kalla ka gane yana cikin matsala gagaruma, cike da tausaya wa take kallon sa, kallon ta yake shima sai yaga ta kara fresh hadda yar kiba, be sake cewa komai ba bayan gaisuwa suka shiga takawa a hankali, yau ce rana ta karshe da za tayi sallama da Arkel Poultry farm, a kofar wajen ya tsaya ganin motar sa a fake a wajen, gefen bencin me gadi ya zauna yana kallon ta "Ya ka tsaya kuma?" Ta tambaya da mamaki "Shiga ki fito kawai ina jira." "Haka mukayi?" "A ah, hakan dai naga ya dace." "Shikenan." Shigewa tayi da sauri cikin nuna jin haushin ta, a tunanin ta zai biyo ta sai taga yayi zaman sa ya ciro karamar wayar sa yana dannawa. Sama ta fara hawa ta dudduba ba kowa ta sako, bin kowa na wajen tayi daya bayan daya sukayi sallama kafin ta nufi office din Salim in da ta san zata same shi, yau ma kamar kullum ya zaune gaban computer yana dube dube, jin takun tafiyar ta yasa ya d'ago da sauri, dogon hill shoe ta saka sai dogon Hijab me hannu, fuskar ta fayau babu ko powder sai d'an wetlips data matsa a lips din nata, tun daga sama ya kalle ta har k'asa, kallon glasses din idon ta yayi kafin ya sauke kansa kasa, simple and cheap shiga tayi sai dai tayi kyau ainun, fatar jikinta chocolate colour ta dace da tsarin ta "Ina kwana?" Ta katse mishi tunanin daya tafi "How are you?" Ya d'ago yana kallon ta a karo na biyu "Alhamdulillah, sir dama yau ne last day d'ina anan, log book d'ina kuma ba'a yi signing kowanne page ba, gashi na duba oga salim be zo ba." "Sai ki jira shi." Ya faɗa kai tsaye yana mai da kanshi kasa Sake dagowa yayi yaga ta a tsaye, mika mata hannu yayi alamar ta bashi log book din, dan tsaki yayi yana bude pages d'in ganin babu wajen da aka yi signing d'in, gashi kowanne page sai anyi signing hade da stamp. Gefe ya tura computer tasa ya ciro pen ya matso da abun stamp din, kallon handwriting din yayi yaga kamar computer ce tayi shi saboda tsaruwa, kasa hakura yayi har sai da ya tambaya "Waye yayi miki rubutun nan?" Kai tsaye tace "Ni nayi sir." "Hmm... Are you sure? Kece zakiyi rubutu haka me kyau." Ya furta ba tare da ya sani ba, kallon sa tayi da sauri dan tasan shi komai akayi ba'a iya ba. "Yayi kyau?" Ta fada tana murmushi, da sauri yace "Ni nace kyau?" hararar littafin yayi ya cigaba da bubbud'e pages d'in, shiru tayi bata kara cewa komai ba, chan kamar ba zai sake magana ba sai kuma yace "So nake nace wannan jagwalgalon,rubutu kamar tafiyar tsutsa, nema yake ya kashen ido ma, mtsw." "I'm sorry sir." Ta fada yana kunshe dariya, kallon ta yayi tayi saurin hadiye dariyar ta, kwafa yayi ya cigaba da sa hannu, chan ya ture kawai ya maida kansa baya, a hankali taji yace "Sai na huta gaskiya, ki jira." Kallon agogon office din tayi ta kalli kofa, Hafiz na chan na jiran ta, mik'ewa tayi yayi saurin bude ido "Ina zaki?" Ya tsare ta da idon sa Da hannu ta nuna masa kofa, kada kai yayi ya maida idon sa ya rufe "Cewa nayi ki jira ba ki fita gulma wajen maza ba." Kallon sa tayi taga idon sa a rufe kamar bashi yayi maganar ba,sosai maganar sa tayi mata ciwo, dan ma ya raina mata wayo wai gulma, cikin bacin rai ta koma ta zauna tana hararar sa ta gefe. "Harara ta kike?" Taji ya fada,da sauri ta kalle shi, idon sa akanta fes yana kallon ta, dan motsa baki tayi kadan ta yi kasa da kanta. Rufe log book ɗin yayi ya kalli sunan, a hankali ya furta "Maryaaam." "Na'am." Ta kalle shi "Meye cgpa dinki?" "Sir?" "Barshi ma,daga gani ba wani kokari ne dake ba." "Allah ina da kokari..." "Ban ga alama ba." *Jin shirun yayi yawa yasa shi baro kofar ya shigo ciki, tun dazu ya hango ta shiga office din Amma shiru bata fito ba, a daidai window ya tsaya yana dan lek'awa ciki, ransa ne ya baci ganin su zaune su biyu a ciki, Arkel yana facing din ta, lokaci lokaci yana dagowa yana kallon ta, haushi ne ya turnik'e shi wani azababben kishi ya taso masa, da sauri ya juya ya bar wajen ba tare da ya shirya ba. Arkel ya ganshi, take ya tuno fuskar, shine wanda yazo ranar, hade fuska yayi ya cigaba da abinda yake yi. Gaba daya ajiye komai yayi ya tashi ya fita daga office din, bin sa tayi da kallo,me yake nufi? Ta zauna tayi ta jiran sa kenan? Buga kafar ta tayi kamar ta saka ihu. Dialing number Hafiz tayi har ta k'araci ringing be dauka ba, lekowa tayi ta hango shi ya sakale hannayen sa ta bayan sa suna magana da wani, daidai kofar shiga office din suke babu ta yadda za'a yi ta fita, komawa tayi ta zauna tana jan tsaki. Sai da ya dade kafin ya dawo, rufe log book din yayi ya mika mata, ashe dama tuni ya gama signing din yana sa ne yak'i bata kenan? Juyar da kanta tayi gefe kwalla na taruwa a idon ta, karba tayi ta juya kawai ta fita da sauri ba tare data ce komai ba, jikin sa ne yayi sanyi ya bita da kallo, haushi taji? Ya tambaya a ransa, komawa yayi ya zauna yai shiru yana so ya tuna abinda yayi mata da zataji haushi har haka. *** Ganin babu Hafiz tasan za'a rina, tun data kira taji be daga ba tasan yayi fushi kenan, samun kanta tayi da jin haushin Arkel, a haka ta karasa gida duk bata da kuzari saboda tasan fushin Hafiz sai yayi kwana uku be kulata ba. Ko data koma gida zaman ta tayi a daki tayi kwanciyar ta, abincin ma bata da muradin ci a halin yanzu, tana nan kwance ta jiyo muryar Anty Maryam a tsakar gida, da sauri ta fito ta tare ta, saurin karb'e Areef tayi daga hannun me aikin ta tana dariya "My baby." Ta daga shi sama "Ba'a son daga yaro sama fa." Umma tayi magana tana fitowa, karbar Abid tayi suka shiga falon. Zuwan Anty Maryam yayi mata dadi sosai, daki suka shige bayan sun gama hira da umma kamar wasu kawaye suka dora sabuwar hira,a cikin hirar ne take bata labarin yadda sukayi da Hafiz, idan abu ya haɗa su shikenan sai ya dau gaba da ita, gashi da saurin fushi abu kadan sai ya hasala ya hau zargi, tun abun baya damun ta har yaxo ya fara damunta, auren irin masu halin nan akwai wahala, gashi komai kayi baka birge ba abubuwa dai da yawa sai dai kawai ayi kurum. Shawarwari Anty Maryam ta bata masu kyau, taji dadi sosai dan ba karamin haske ta kara mata ba, dole ta koyi hakurin xama da shi da halin sa kuwa tun da dai shi ta zaba. Sai wajejen Isha'i sannan mijin anty Maryam ɗin yazo daukar ta, har waje suka rakota umma dai ta tsaya a zaure Maryam ce ta rakata har gaban motar ta bude mata, sai data shiga sannan ta mika mata Areef, Abid dama yana wajen me aikin ta a baya Sai da suka fita daga layin sannan ta juya zata shiga gida, sosai taji tsoro ganin mutum a tsaye kikam a jikin kofar gidan su, ja tayi da baya da sauri, "Matsoraciya." Ya fada yana matsawa jikin gate din, kallon sa tayi shine kuwa, tunanin abinda yake yi ne yasa ta tsaya, kallon ta yayi ganin ta a tsaye yasa yace "Gidan ku?" Ya nuna gidan da hannun sa, kafin tayi magana an turo gate din, kamshi ne ya fara yi musu sallama kamar anyi barin turare, Rauda ce ta fito tana taku daidai kamar wata sarauniya, a gaban sa taja ta tsaya tana taunar cingum, haushi ne ya turnik'e shi yaji kamar ya shaketa, mamaki ne sosai ya kama Maryam, kallon da take yi masa na mutum ne me tsaurin ra'ayi da akida, idan kuwa har hakan ne toh me yakeyi a wajen Rauda? Duk da alaka ce me karfi a tsakanin su da Raudan amma bata tunanin shi a irin mazan da zasu zo wajen Raudan ko dan saboda yanayin rayuwar ta daban da tashi, duk da ba wai tayi masa sanin sosai bane ba, a dan zaman da tayi ne ta fuskanci hakan, jikin ta a mace ta juya ta shige gida jin maganar Umma tana bawa Walid sakon yazo ya dubo yaga me ta tsaya yi bayan ta ji tafiyar tasu tuni, tana shiga umman ta rufe ta da fadan abinda ta tsaya yi. "Me kika tsaya jira duk kowa ya dawo ke kin ki shigowa?" "Gidan Hajiya Mama na shiga ne." "Karki yi min karya, kece zaki shiga gidan? Da ban san halin ki bane dai." Shiru tayi ta wuce daki kawai. *** Bin ta yayi da kallo har ta shige ciki, kallon sa Rauda take babu ko kiftawa, "Wacece ita?" Ya jefo mata tambayar, cikin halin ko in kula tace "Yar brother Abba ce, step brother fa amma." "Owk, cousin dinki ce kenan." "Cousin? Ah no ba cousin d'ina bace." "Kamar ya?" "Please ka share kawai, muyi maganar da Mummy tace zaka zo muyi akan biki, kaga zamuyi dinner, moctail, barbaque tea party,...." "Aina? Bana son shirme, babu ko daya da zamuyi, in ma zakiyi dai ni count me out, ba zan iya wannan haukar ba, send me ur account details sai na tura miki kudi kiyi abinda kika ga zakiyi." Buɗe baki da hanci tayi tana kallon yadda ya dage yake xubo mata rashin mutunci, gaskiya ba zata dauka ba, daddagewa tayi ta tsaidashi "Malam gaskia ba zai yiwu ba, komai daka ji na lissafa sai anyi kazo ko kar ka zo wannan ruwan ka, zaka tsaya kana gaya wa mutane magana,ba fa rasa masoya nayi da zan aure ka ba ehe,ka sani ka daina jin kanka a sama." Dafe kansa yayi kawai ya juya da sauri, ba zai iya daukar maganganun nan nata haka ba, tsaki ta ja ta juya tana mita, _"Idan banda kudin ka da takurawar su Hajiya ka isa ma, ni ba wai na shirya aure ne ma yanzu ba, mutum na tsaka da life din sa ace za'a takura shi, aikin banza matsoraci kawai."_ Ji tayi ta bige da abu, da sauri ta juyo, Abba (Alhaji Faruku) ne a tsaye ya harde hannayen sa a kirjin sa ransa a matukar b'ace, tsoro ne ya kamata ta hau karkarwa "Biyo ni." Yace kawai yana wucewa part din sa. *** Tun da ya koma gida ya shiga tunani, tunanin maganganun yake, tun da yake ba'a taba ma gaya masa magana me zafi irin hakan ba, sosai yaji zafin maganar har yaji gaba daya komai ya sake fice masa akai, tashi yayi ya hau hada yar karamar trolley d'insa da zai tafi da ita Cross river, rashin me kula da Ummi ne yasa ya jinkirta ta tafiyar har zuwa weekend saboda su samu su tafi tare da Kamal in yaso sai Yaya Nabila tazo gida ta zauna, kaya kala biyu ya dauka sai single da boxers, perfumes da brush sai chargers din sa na pad din sa,waya da computer. Fitowa yayi kasa ya tarar da Hajiya Mero da Zainab a zaune suna kallon Mbc, kamar ya wuce sai ya fasa ya dawo zauna, kallon gefen Zainab yayi yace "Hajiya kiyi mata magana, ba zan dau rashin kunya ba gaskiya." Da sauri Zainab ta kalle shi,sannan ta kalli Hajiya Mero, "Mummy!..?" "Bake ba." Ya fad'a yana mikewa "Kayi hakuri zanyi mata magana." Hannayen sa ya zuba a cikin aljihun wandon sa ya sa kai yayi ficewar sa, wajen su buzu me gadi ya nufa yana tafiya yana tunani, shi fa ko yaushe cikin tunani yake ya rasa yadda za'a yi ya bar tunani gashi hakan ba karamin chusgunawa ransa yakeyi ba. Gefen Hajiya Mero Zainab ta koma tana kallon fuskar ta bakin ta dauke da tambaya "Wa yake nufi wai?" "Wai Rauda, kinsan ita zai aura har ansa bikin saura three weeks ma." "What!!!" Ta ja baya da sauri "Zanyi miki bayani, muje daki." Fusge hannun ta tayi ta saka kuka, sake riko hannun ta Hajiya Mero tayi ta kwace ta shige daki da gudu ta saka key. Dafe kai tayi a hankali tace "Yaran nan zasu haukatani." *** Bangaren Hafiz ya rasa ina zai tsoma kansa, duk in da ya buga babu, gashi dama fushi yake da ita sai abin ya sake yi masa yawa, duk yadda yaso ya saukaka wa zuciyar sa idan ya tuno sai yaji komai ya kara dagulewa, inna tayi tafiya ta tafi chan garin su Gumel ta sanar wa yan uwa da abokan arziki tun da kowa nasu suna Gumel din su ka dai ce sai Kawun su Hafiz din. Yana zaune a kofar wani shago yana kokarin kiran wani wan Innan da yake aiki a Jigawa FUD ko zai taimaka masa da wani abun kiran ta ya shigo, rejecting yayi ya ja dogon tsaki yana kashe wayar gaba daya, haushin ta sosai yake ji duk da kasan ransa yana son ta baya so kuma ya rasa ta, sai dai zafin rai irin nashi ya hanashi sam ya gane irin son da take masa ita ma duk da talaucin sa, duk da su ɗin ma ba wani shine dasu ba amma ba za'a hada su da su Hafiz din ba. *** Jirgin karfe 10 zasu shiga zuwa Abuja daga nan sai su hau wani, a tsanake ya shirya ya dauko wani yadi fari kal me masifar kyau, tsayawa yayi rike da yadin yana tunani, ajiyar zuciya ya sauke ya maida yadin ya ciro wasu daban ya saka, taje sumar kansa yayi ya fesa turare ya saka hula, kwantancen sajen sa da ya sha mai ya sake kwantar wa sannan ya makala Bluetooth a kunne sa ya riko jakar ya fito, dayan hannun nasa rike da wayar sa yana kokarin neman layin Kamal. Dan Dan....... Ko Arab zai yarda su hadu a CR ɗin? Ko zai yarda da abinda zasu j masa? Ko zai sanar dasu dalilin sa na tafiya ba sallama? Ko asirin da yake binne zai fito? Ko za'ayi auren Maryam da Hafiz? Arkel da Rauda? Wacce irin kaddara ce zata zo musu? Me zai faru? Me zai kasance? Ku biyo ni, akwai soyayya me zafi da tsayawa a rai a gaba, za kuma kuji asalin labarin kowanne family, mu bi komai a sannu Nagode sosai da kauna😍😍🚴🚴 Kuyi hakuri wlhi ciwon ido ne ya sani gaba, kallon screen yayi yawa shiyasa kuke ji na haka, kar naje garin neman gira.....🚴🚴🚴 *** _ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU😁._ *ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma *SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano) *KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo) *BURI ƊAYA!* (Mamu gee) *WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull) 👇🏻karku bari ayi babuku *ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu* *za'a tura kudin ta wannan accnt number din* Hafsat kabir umar 0225878823 GT bank Saika tura shaidar biya ga wannan number ta WhatsApp 08030811300 Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din 07067124863 Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya. *Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon Rano🚴🚴🚴 *SAUYIN K'ADDARA* *11-12* ©*Hafsat Rano* *_ZAFAFA BIYAR na kudi ne idan kana son kowanne daga ciki ka nemi Wannan numbers din_* *08030811300* *07067124863* *_Daurin boye_* _safiyya huguma_ *_Buri daya_* _mamuhgee_ *_Wutsiyar rakumi_* _billyn Abdul_ *_Kai min halacci_* _Miss xoxo_ *_Sauyin kaddara_* _hafsat rano_ *** Saurin bude kofa tayi ta fito jin kamshin turaren shi daya gauraye tsakiyar falon, a gaban sa ta ja ta tsaya tana kallon sa, idon ta da yayi jajawur yake kallo, dauke kansa yayi ya daga wayar kamal, "Ok gani nan." "Lafiya?" Ya tambaye ta yana watsa hannun sa gefe "Aure wai zakayi?" "Yes. Akwai matsala ne?" Ya fada cikin halin ko in kula "Anty Rauda zaka aura kuma?" "Are you asking me?" Daga kai tayi alamar eh "Jeki tambayi Hajiya nima ban sani ba." Rabawa yayi ta gefen ta zai wuce ta saka kuka, tsaki ya ja ya dauki jakar hannun sa zai fita Hajiya Mero ta fito da sauri, kallon Zainab tayi dake kuka ta kalle shi, idon ta ne ya kai kan hannun sa tayi saurin cewa "Kai kuma ina zaka? Na ganka da jaka." "Ni wai?" Ya juyo yana kallon ta "Da wa?" Ta fada a ƙufule jin yazo da rainin wayo, "Ohh okh... zan je wani waje ne." Fita yayi ta saki tsaki tana hararar Zainab, "Shegiya me k'aton baki, ubanki ne da zaki saki baki kina masa kuka? Kin wuce ko sai na kakkaryaki?" Buga kafa ta hau yi cikin kuka tace "Dama nasan kin tsaneni, kuma wlhi yau zan koma gidan Hajiya Mama, ba zan sake zama a wajen ki ba." "Kifi ruwa gudu, in Zaki birgeni ki koma wajen dangin ubanki mana kiga idan zasu tsinana miki komai." Juyawa ta ta shiga daki ta shiga hada kayan ta. Da baya ta zauna tana dafe kai,rigimar zainab ta soma isarta, tun jiya suke abu daya, ga wannan ɗan rainin hankalin ya soma daga mata hankali, tsoron ta daya kar ya lalata mata aiki, shiyasa ma take so ayi ayi ayi auren ko ta dinga jin komai akan sa wajen matar. Tana nan zaune Zainab ta fito da jakar kayan ta da tarkacen abinda zata bukata tayi ficewar ta, ci kanki bata ce mata ba sai ma dauke kanta da tayi ta cigaba da aikin tunani. *** Yana harabar gidan suka shigo, gefe kamal ya samu yayi parking ya karkace yana kallon matar sa "Dear ba zakiyi missing dina ba ne naga kina zumudin sauka?" "Kasan zanyi sosai,kawai an eager naga Ummi ne, kuma kaga Malam Sammani yana jiran mu." Ta fada tana kallon windon motar, kallon Arkel yayi da ya zuba wa motar ido yana jiran fitowar su, "Wai shine Sammani?" Ya fada yana dariya, dariyar tayi ita ma tace "Ba ruwana wlhi, yanzu sai ya hau kamar bread din da aka sawa yeast." "Zaki bayani ne, ai sai na faɗa masa." "Ba yadda zai ba ai." Ta fada tana kokarin danna central lock din motar. knocking yazo yayi a jikin glass d'in, dan sauke glass din Kamal yayi yana kallon sa "1 mint muyi sallama da Madam kaji malam Sammani." Zaro ido yayi, da sauri kamal ya daga glass din motar ya jawo ta jikin sa, peck yayi mata a both cheeks din ta sannan ita ma tayi masa, sakin ta yayi ta balle murfin motar ta fito, kallon su Arkel yayi ya taɓe baki a ransa ya ce "Iyayi kawai." "Morning babbar Yaya." Ya fad'a yana murmushi "Morning small kani." Ta amsa tana daukar Amna a bayan motar "We are running late fa, nasan kece kika rike shi." Dariya kawai Nabila tayi ta daga wa kamal hannu, "Safe Dear." "I ll miss u." Ya fad'a yana marairaice murya Saurin fadawa motar Arkel yayi ganin zasu sake bata lokaci kuma, dariya kawai sukayi masa ta shige ciki. ***A airport suka ajiye motar sannan suka daga zuwa birnin tarayya, daga nan suka dauki hanyar CR. Runtse idon sa yayi lokacin da suka shigo garin, ajiyar zuciya ya sauke ya bude idon sa yana kallon ko ina, Uber suka kira ya kai su babban hotel din garin na Calabar, a gajiye suke saboda haka basu iya yin komai ba a ranar, kwanciya sukayi suka huta sukayi ordering abinci daga reception din hotel din. Da safe Arkel ya riga Kamal tashi saboda zumud'i, sai daya shirya tsaf sannan yaje yayi masa knocking, lokacin tashin sa kenan suna waya da Nabila yana kokarin shiga toilet, jallabiyar sa ya zura ya bude masa, kallon sa yayi daga kasa har sama ganin har takalmi da socks ya riga ya saka, Daga mishi hannu yayi sannan yace "Bari na shirya baby naga kanin namu har ya shirya a kular min da kids." "Owk bye." Ya zare wayar, kallon Arkel yayi ya nuna hannun sa "Bari na shirya Malam S... Auw..." Yayi dariya yana juyawa, dariyar shima yayi kawai ya koma dakin sa. Address d'in dake kan wayar sa ya kurawa ido yana kallo,  searching location din yayi ya ga komai, Uber ya sake kira musu sukayi amfani da Navigation system suka isa unguwar, kallon kofar gidan Arkel yake jikin sa a sanyaye, dan dukan kafad'ar sa Kamal yayi "Be brave to face him." Ajiyar zuciya ya sauke Kamal ya danna Door bell, daidai lokacin yana zaune yana shiryawa, gefen sa wayar sa ce ke fitar da karatun Alkur'ani me girma cikin kira'ar ghamid'i, lokaci zuwa lokaci yana dan duba agogon wayar saboda kar ya makara sosai. Yana jin karar Door bell ya mike yana saka links a hannun rigar sa, a tunanin sa Mustapha ne ya zo dan babu wanda yake zuwa din sai shi, kai tsaye ya isa kofar ya bude da dukkan karfin sa, idon sa ne ya sauka akan shi, yayi saurin ja da baya yana kallon su dukka, kallon shi suke suma musamman Arkel da a take idon sa ya ciko da ruwa. Da baya da baya ya dinga ja har ya isa tsakiyar falon yana juya bayan sa, kallon Arkel Kamal yayi yayi masa alamar da su shiga, jiki babu k'wari ya saka kafarsa cikin gidan yana jin zuciyar sa na wani irin bugawa da sauri da sauri. Arab da yayi suman wucin gadi ne ya dawo hayyacin sa, maganganun da kamal keyi ne suka fara shiga kansa a hankali a hankali ya soma fuskantar su, kenan da gaske ne ba wai gizo idon sa keyi masa ba, dan uwan sa, rabin jikin sa ne yau a gaban sa? Wanda kullum da tunanin sa yake kwana yake tashi. Da sauri ya jiyo da niyyar yi masa magana, wani abu me karfi kamar iska ya bigi fuskar sa, a take ya ji ba zai taba iya yi masa magana ba, Juyawa yayi da sauri ya shige daki, cikin zafin nama Arkel ya bishi Amma kafin ya isa har ya rufe ya murza mukulli. Dunkule hannu Arkel yayi ya daki bangon dakin, me yake faruwa? Wanne irin abu yayi wa dan uwan sa haka da har zai guje shi, yazo kuma yaki sauraren shi, ji yayi gaba daya duniyar ta tsaya masa chak, "Me nayi maka ne!!!"ya fada da karfi, shiru Arab yayi yana jin komai amma yaki magana "Ka manta komai? Shakuwar mu? Komai tare mukeyi, bacci cin abinci sallah karatu? Duk ka ma ta? Kayan mu daya,maganar mu daya,kama daya komai daya,hali ne kawai ya banbanta,duk ka manta?" "Ban manta ko daya ba." Ya amsa a raunane. "Then why? Laifin me nayi maka har haka da zaka tsaneni, ka guje mu ni da Ummi, kasan halin da take ciki? Kasan yadda muke rayuwa? Ka tafi ba sallama, bamu ji daga gareka ba, yanzu na zo baka son kayi magana dani, tell me wanne irin laifi ne wannan?" Shiru babu amsa, dan ja baya yayi daga jikin kofar yace "Baka da abinda zaka ce ko, na san baka da shi dama, U r so selfish and cruel, kanka kawai ka sani, shikenan, tun da hakan ka zaba, yayi kyau am leaving, karka yi tunanin i ll come back for you, kowa yayi rayuwar sa yadda yake so, ka sani da kai ko babu kai zamu rayu har zuwa lokacin da Allah ya diba mana." Danne bakin sa Arab yayi kar kukan da yake taso masa ya fito, girgiza kai kawai yake yana sauraron sa, bashi da baki ko fuskar da zai iya fuskantar sa ya fada masa abinda yake son ji, duk abinda yake so ya fad'a ya fada amma ba zai taba yadda su sake haduwa ba balle har ya tuhume shi akan boyayyen al'amari. Juyawa Arkel yayi idon sa yayi ja sosai be ko kalli kamal ba yace "Muje kawai." Kin binsa kamal yayi ya isa kofar yana kiran sunan sa ko zai bude, biris yayi masa sai chan yace "Idan kun fita ku ja min kofa." Jiki a sanyaye suka koma masauki, babu wanda yake da karfin gwuiwar yiwa dan uwan sa maganar, haka suka kwana dukkannin su zuciyoyin su babu dad'i, da sassafe Arkel ya shirya yayi wa kamal knocking, janye yake da trolley din sa alamar tafiya zaiyi, da k'yar kamal ya shawo kansa suka kara kwana biyu, a kwana biyun nan kamal yaje gidan Arab yafi sau nawa amma baya samun sa kwata kwata. Haka suka gama zaman su na tsawon kwana uku babu wani abu da ya sauya suka tattaro suka dawo gida. *** Zama yayi cikin bacin rai, gefe ta samu ta rakube cike da fargaba, a zafafe ya d'ago bayan ya gama kallon ta "Ashe baki da hankali?!" "Dan Allah Abba kayi hakuri." Ta fada tana sauke kai kasa, shiru yayi yama rasa me zai ce mata, ya sani sarai ba wai laifin nata ne baki daya ba, Hajiyar su ce babbar me laifi wajen bata ta, ya rasa yadda zaiyi da ita kuma dan an bar kari tun ran zane. "Tashi ki bani waje mutuniyar banza." Da sauri ta mike, gyara zaman sa yayi sannan yace "Kuma Ki tabbata kin tattaro kayan ki kin dawo nan kafin anjima." Tun da ta fita ya shiga tunani, ya rasa ta ina zai ɓullo wa Hajiyar su akan maganar auren Rauda da yaron, ya riga ya san babu wani abu da Raudan zata aikata sai abinda Hajiya Mero ta ɗora ta akai, a matsayin sa na uba na gari ba zai taba so ayi amfani da yar sa wajen cutar wani ba, tun ranar da yaji maganganun su ya zama bashi da wani sukuni, gani yake idan har ya yarda akayi auren a haka ya cutar da bayin Allah, gashi kuma Hajiya Mama mahaifiyar sa ce, ba zai so su bata ba akan yar da ya Haifa, da shi da yar tashi dukkannin su ikon ta ne, tana da damar da zata saka su ko ta hanasu, tashi yayi yana zagaye a tsakiyar falon ya rasa mafita. *** Hafiz na kwance a saman yagalgalalliyar katifar sa Inna ta dawo daga Gumel, daga labulen dakin tayi ta tsaya tana kallon sa, sai data dade a tsaye sannan ya san da zuwan ta, mik'ewa yayi da k'yar yace "Inna... Ashe kin dawo." "Uhum... Ka sameni a ciki." Gaba tayi ya mike da k'yar ya kuskure bakin sa, vest ce a jikin sa da gajeren wando ya shiga gidan yana bin bango saboda yadda yunwa ke nukurkusar sa, kujerar tsuguno ya jawo ya zauna yana kallon Innar tana kwance kayan data zo dasu, sai data gama gyara komai waje daya sannan ta saka Suwaiba ta kwashe ta kai ciki, daurin gyara me gishiri ta mika masa yayi saurin karba yana washe baki. "Gyada muka samu Inna." "Wai ka manta yadda ake sannu da zuwa ne Hafizu?" Dafe kansa yayi "Wallahi shaf na manta, Ya hanya?" "Lafiya lou, duk suna gaishe ka." "Ina amsawa kuwa." "Toh dai Hafizu Allah ya yanke ma wahala, na samo maka aiki a gidan mai, aikin matsa mai." Gyadar da yake kokarin zubawa a bakin sa ya saki yana kallon Innar cikin tsantsar farin ciki "Da gaske Inna!!?" "Ina maka wasa ne?" Ta fada tana bata fuska "Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Allah na gode maka mafita tazo min." A kaikaice inna ta kalle shi, girgiza kai tayi a ranta tace "Yaro man kaza." "Aina ne aikin inna? Yanzu zan tafi ko sai gobe? Na rasa in da zan saka raina ne ma wlhi." "A Gumel ne." "Gumel inna?" "Eh Gumel dai, gobe da safe zaka tafi idan Allah ya kaimu, chan Gumel din ne wani sabon gidan mai da Hajiya Khadija Rano🤪 ta bud'e, kasan yanzu gidajen man ta sun fi na kowa yawa a Kano, toh yanzu ta sake yin sababbi shine har da Gumel din, gidan Hajiya talatu na shiga muke hirar rashin aiki, shine ta hadani da mai gidan ta ashe shine me daukar ma'aikatan a take kuwa ya saka sunan ka, kaji yadda akayi" "Toh yanzu Inna... Idan na tafi Gumel sai yaushe zan dawo, gashi fa bikin nan ya sake matsowa." "Kana tunanin zasu baka yar su ne baka da ko sadaki? Toh bikin nan dai ba zai yiwu a yadda suka saka ba, nayi magana ma da kawun ku badamasi zai zo yaje har gida ya sami iyayen nata, a daga bikin idan yaso sai kaje la dan tara wani abu, idan ka dawo sai ayi cikin karfin gwuiwa." "Zasu yadda kuwa Inna?" Ya fad'a jiki a sanyaye, "Me zai hana? Yarinyar ma naga karatu kace tanayi ai ko? Toh ba sai ta karasa ba itama cikin kwanciyar hankali." "Haka ne kuma." "A'ah... Hakan dole zamuyi, in Kuma ba haka ba da me za'a yi auren? Shekaru da naka zamu hada ko me?" "Aikuwa." "Ka je yanzu ka watsa ruwa ga rogo nan na taho dashi, Suwaiba zata dafa sai kaci kaje wajen yarinyar, idan kaje amma karka fada mata komai kai dai kace mata ka samu aiki zaka tafi gobe, idan yaso shi Badamasi yayi musu bayani dan sai sun fi gane wa akan ace ita ta sanar musu." Ciki da gamsuwa ya aiwatar da abinda Inna ta dora shi, a tsaitsaye ya ci rogon ya nufi gidan su Maryama. Tana zaune tana tsefe kanta Walid ya shigo gidan da gudu "Uncle Hafiz yazo." Da sauri ta dago dan batayi zato ba,kallon Walid tayi da alamun tambaya "Allah da gaske nake yana waje." Gefen da umma take tana gyara zogale ta kalla, jiki a sanyaye ta mike ta shiga daki, Hijab ta zura bayan ta tufke gashin nata waje daya ta fito "Umma zanje wajen Hafiz." "A dawo lafiya." Kawai tace ta cigaba da aikin ta A zauren gidan ta same shi ya jingina da bango yana kallon kofar fitowar ta, fuskar sa a sake take dan ya ma manta fushin da yake yi, ajiyar zuciya ta sauke ta k'arasa, yadda yake kallon ta ne yasa ta ɗan ji kunya ta tsaya da nesa dashi tana wasa da gefen hijabin ta "Ina wuni?" "Lafiya lou, ya kika tsaya nan wai? Ki ƙaraso mana ko ba'a maraba dani ne?" Dan matsowa tayi kadan ta tsaya ba tare da tace komai ba, ya gane sarai fushi take dashi "Na samu aiki." Ya faɗa kai tsaye dan yasan shine kadai abinda zai wanke shi a wajen ta. Da sauri tace "Dan Allah!?" "Da gaske." "Kai masha Allah, Alhamdulillah amma wlhi nayi maka murna sosai, alhamdulillah." "Kamar ya kinyi mun murna?auw ban da ke?" Yayi saurin fassara ta, da sauri tace "Wallahi ba wani abu nake nufi ba, toh nayi mana murna Alhamdulillah." Dariya yasa kawai ta kalle shi tana mamakin hali irin nasa, daga abu kadan sai ya fassara mutum bayan ba haka take nufi ba. Hira suka cigaba da yi hakan ya mantar da su fushin da suke yi, ko da magriba tayi ma sallah kawai yaje yayi ya sake dawowa suka cigaba da wata hirar sai wajen takwas sannan ya tafi shima saboda Alhaji Faruku baya gida ranar amma da in ya gansu sai yayi fad'a. washe gari Hafiz ya shirya ya nufi Gumel cike da daukin sabon aikin sa, yana tafiya Kawu Badamasi ya duro gidan, inna ce ta kimtsa masa abinda zai je ya sanar, abokin sa guda daya ya kirawo yayi masa rakiya har wajen Alhaji Faruku. Da mutunci ya karbe su musamman lokacin da suka zo tambayar auren Hafiz ya gane Badamasin, ruwa da lemo yasa aka kawo musu suka sha kafin yaji abinda yake tafe dasu. **** Bayan sati daya Abun duniya ya taro yayi wa Maryam yawa, gaba daya Hafiz ya rufe ta, idan ta kirashi baya dagawa, duk sanda taso tayi wa Umma maganar sai ta kasa, ranar dai data gaji ta shirya ta tafi gidan anty Maryam saboda dai dole ta sanar ko dan asan halin da suke ciki, ga biki ya matso ana ta shirye shirye, Hankalin Anty Maryam ya tashi ta sako ta a gaba suka dawo gidan, Umma suka sanar wa abinda yake faruwa, sosai hankalin ta ya tashi ita ma ta shige neman layin Baba, abinda yake faruwa ta fada masa yace suyi hakuri ya dawo gidan. Da wuri kuwa ranar ya baro shago ya dawo gida, yan tambayoyi yayi wa Maryam ɗin kafin ya kira Alhaji Faruku ya sanar dashi komai, be ce komai ba shima yace zai ƙaraso gidan yana hanya. Ko da ya dawo sai yaki shigowa kamar yadda yace, zama yayi yasa matar sa ta kira masa Rauda, kallon ta yayi kawai yana tunanin abinda yake shirin aikatawa "Rauda!" Ya kira sunan ta "Na'am Abba." "Ki fada min tsakanin ki da Allah, kina son yaron nan ko ba kya son shi, tsakanin ki da Allah." "Bana son shi Abba, kuma ban tsane shi ba." Ta amsa masa kai tsaye "Me yasa zaki aure shi?" "Hajiya Mama ce da Mummy suka ce na aure shi, idan na aure shi wai dukkan mu mun huta,shine kawai ya yarda." Ajiyar zuciya ya sauke yace "Kinsan aure Rauda?" Girgiza ai tayi "A'ah." "Zaki aure shi ki cutar dashi da mahaifiyar sa ko? Haka ne ko ba haka bane?" "Mahaifiyar sa kuma Abba?" "Eh abinda suke so kiyi kenan, aikin da Mero take so kiyi mata kenan da har taki saka yar cikin ta sai ke da ake ganin ki shashasha." Shiru tayi bata ce komai ba tana tunanin maganar sa "Kiyi hakuri Rauda, kiyi min biyayya wannan karon,batun yaron nan a barshi." Da sauri tace "Nayi Abba." "Allah yayi miki albarka." "Amin." Ta amsa, "Kina da babbar kyauta, bani number sa zanyi magana dashi." Number Arkel ta karanto masa ya saka a wayar sa Tashi tayi ta shige daki hakan yayi wa mahaifiyar ta dadi ta tashi tabi bayan ta da sauri. Arkel na kwance be dade da farfaɗo wa daga zazzabin da ya kwanta ba bayan dawowar su daga CR yaji wayar sa na ringing, Kamar ba zai daga ba sai kuma ya daga ɗin, jin Muryar babban mutum ne yasa ya mike da sauri yana sake kara wayar "Ok Tam in sha Allah zanzo yanzu." Shine abinda kawai yace ya ajiye wayar Tsam ya mike ya hau shirya wa,samun kansa yayi da ciro wata sabuwar shaddar sa fara kal anyi mata aiki da bakin zare tayi masifar kyau, bakar hula ya dora mata ya fito sosai sai yar ramar da yayi. Yana driving yana tunanin kiran da Alhaji Faruku yake masa har ya karasa, kallon kofar gidan su Maryam yayi kamar me nazarin abu kafin ya fito ya nufi cikin gidan Hajiya Maman, a harabar wajen ya tarar da Alhaji Faruku yana ganin sa ya fadada fuskar sa, har kasa ya tsuguna ya gaishe shi sannan suka nufi falon sa da yake ajiye bakin sa masu muhimmanci. A d'arare ya zauna yana karewa falon ido, kafin ya maida hankalin da wajen Alhaji Faruku da yake ta tattauna maganar da yake son fad'a masa. Da k'yar ya aro jarumta cikin dakiya yace "Zaka iya auren 'yata (yar wana) Maryam??????? Da sauri Arkel ya d'ago yana kallon shi, wani irin kwarijini yaji yayi masa cikin rawar murya yace....... " _ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU😁._ *ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma *SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano) *KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo) *BURI ƊAYA!* (Mamu gee) *WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull) 👇🏻karku bari ayi babuku *ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu* *za'a tura kudin ta wannan accnt number din* Hafsat kabir umar 0225878823 GT bank Saika tura shaidar biya ga wannan number ta WhatsApp 08030811300 Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din 07067124863 Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya. *Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon Rano🚴🚴🚴 [3/18, 22:24] Hafsat Rano: *SAUYIN K'ADDARA* *13-14* ©*Hafsat Rano* *_ZAFAFA BIYAR na kudi ne idan kana son kowanne daga ciki ka nemi Wannan numbers din_* *08030811300* *07067124863* *_Daurin boye_* _safiyya huguma_ *_Buri daya_* _mamuhgee_ *_Wutsiyar rakumi_* _billyn Abdul_ *_Kai min halacci_* _Miss xoxo_ *_Sauyin kaddara_* _hafsat rano_ *** Da sauri Arkel ya d'ago yana kallon shi, wani irin kwarijini yaji yayi masa cikin rawar murya yace....... "Abba..." "Karka zurfafa tunani, Maryam da Rauda duk daya ne a wajena, Rauda yar ciki na ce Maryam kuwa yar dan uwana ce, nasan maganar Rauda ce a wajen ka, sai dai ina so ka dau hakan a matsayin wata qaddara me karfin gaske, ka san dai duk bawa na kwarai ba ya iya gujewa qaddarar sa, in Sha Allah zakayi alfahari da ita." "Haka ne." "Kaje kayi shawara, kayi tunani me tsawo akai, duk da ni ubane kuma kowanne uba yana so ya aurar da yar sa, sai dai ba zan zama daga cikin mutane masu son kansu ba, hakan da nayi sai ka ga Allah ya fito min da wata hanyar da banyi zato ba." "Bana bukatar shawara ko tunani akan hakan Abba, na yarda na amince da duk abinda ka yanke." "A'ah, ba za'ai haka ba, kana da na gaba da kai, dole ka sanar musu su baka shawara." "A musulunci namiji yana da ikon ya karbar wa kansa aure, bayan haka Abba kai ma a matsayin uba kake a wajena, idan babu damuwa ka bani mintuna goma ina zuwa." Tashi yayi ya fita yana jin wani karfi da kwarin quiwar aikata abinda zuciyar sa ta tsara masa. Waya ya ciro a aljihun sa ya kira Kamal, sun dade suna magana sannan ya kashe, Salim ya kira ya sanar dashi abinda yake so yayi masa kafin ya kashe kuma ya kira kanin Alhajin su, shima sun jima suna magana dashi kafin ya ajiye wayar yana sauke ajiyar zuciya, agogon hannun sa ya kalla ya daga kansa sama yana kallon sararin samaniya. "Ya Allah." Ya furta a hankali sannan ya koma cikin falon, zama yayi yana fuskantar Alhaji Faruku da tun dazu yake jiran shigowar shi. "Abba... Idan babu damuwa xan auri Maryama a yanzu." Da sauri Alhaji Faruku ya d'ago ya kalle shi, dan gyara zama yayi yana sake kasa da kanshi dan ba karamin nauyi da kwarijini Alhaji Faruku yake masa ba, "Ayi min wannan alfarmar Abba,kuma dan Allah karka ce a'ah. Ina ganin hakan shine kadai zai sa na biya maka da karamcin daka nuna min." "Kana ganin babu matsala?" Alhaji Faruku ya tambaya yana jin wani irin farin ciki na ratsa shi Daga masa kai kawai Arkel yayi dan yadda yake jin zuciyar sa na bugawa da sauri da sauri be taba fuskantar irin hakan ba, tashi Alhaji Faruku yayi ya shiga cikin gidan, dakin sa ya wuce da sauri ya chanja kayan jikin sa, waya ya ciro ya kira wasu numbobi, cike da farin ciki ya fito ya dawo falon, lokacin Arkel na magana da Salim a waya, yana ganin Alhaji Faruku ya shigo ya kashe yana gyara zama. "Dama nayi waya ne da yan uwana suna kan hanya yanzu zasu ƙaraso." Ya fada yana sauke kansa kasa "Madallah, kira su toh kace su same mu a masallacin cikin buk nayi magana da limamin masallacin yana kusa, in Sha Allah muna zuwa zai daura auren." "Owk tam." Direct masallacin cikin buk suka nufa kowa a motar shi, suna zuwa dukka suma suna karasowa, da sauri ya isa wajen Kamal yana jin shi kamar ya fita da gudu saboda tsabar zulumi, dariya Kamal ya hau yi masa yana leka fuskar sa, kasa kulashi yayi ko ya maida mishi komai har salim ya iso da uban alawa da goro na daurin aure, dariyar sa kawai yake kunshe wa ganin yadda oga yayi kicin kicin da fuska kamar zai saki kuka. Sallah suka fara gabatarwa kafin ayi sanarwar daurin auren, mutanen masallacin suka zauna aka fara gabatar da daurin auren bisa sharad'i na addinin Islama. Tun daga sama har kasa yaji wani abu ya tsirga masa lokacin da yaji limamin masallacin na cewa "Alhamdulillah, an daura auren Malam MUHAMMADU ALMUSTAPHA DA AMARYAR SA MALAMA MARYAMA ABUBUKAR HAMZA akan sadaki naira dubu d'ari lak'adan ba ajalan ba... Allah......" Iya nan ya iya ji gaba daya sai yaji jin sa ya dauke, wani irin yanayi me wuyar fassarawa ya samu kansa a ciki, yana jin lokacin da Kamal yake dora masa babbar riga a saman kayan jikin sa, bashi da kuzari ko ƙarfin jikin sa zai iya buɗe baki yayi magana. Farin cikin da Alhaji Faruku ya shiga ba zai misaltu ba, ya rasa in da zai kansa, a daddafe ya amsa gaisuwar mutanen wajen yayi sauri ya yakice ya fita daga cikin masallacin, kamal da Salim na hango shi ya fito sukayi saurin isa wajen sa, hakan yasa Arkel ya bi su suka karasa gaba daya suka zube, gaishe su suka yi sannan suka yi godiya. "Ka sameni a gida da daddare Muhammadu." Kamal ne ya amsa suka tashi, sauran kayan alawa da goron suka zuba masa a booth ya ja ya bar masallacin. "Wai kai baka da abokai ne?" Kamal ya faɗa yana hararar sa "Kaga nan." Ya maida mishi yana kokarin cire babbar rigar, rike hannun sa kamal yayi yace "Aiko karya kake ni wan ka ne wallahi, kar ka cire rigar kuma ka bari muje my wife ta ga kanin ta ango tasan ta girma ta daina abun yara." "Uhum.." "Wai ya akayi hakan ta faru ne duk dazu baka min wani bayani ba." "Allah ne ya tsara, kana ganin zan iya gujewa faruwar hakan?" "Gaskia dai a'ah.". "Toh mu barshi kawai a matsayin wata babbar ƙaddara, Allah ne kaɗai yasan dalilin juyawar al'amarin." "Allah ya sanya alkhairi kanina, ho ango ho ango." "Allah bana so." "Dole kaso angon Maryama, muje muyi wa Baba Karami godia muji ko ya samu Alhaji a waya ya sanar masa, ni fa ban masan Alhajin baya gari ba sai da kake fada min wlhi, Allah ma ya taimaka Baba Karami yana nan ya karbi auren da kuwa ni zan maka aure yaro." 'Dan cije bakin sa yayi ba tare da yace komai ba yayi gaba dan ya gano kamal so yake ya kaishi kasa da tsokana, sun sami Baba Karami a cikin masallacin suka gaisa da sauran wanda suka rage kafin su jashi gefe, godiya kamal yayi masa sannan ya tambaye shi ko ya sami Alhajin a waya, "Na same shi, har ma munyi magana, sauran bayanin nace zakayi masa." "Owk nagode Baba, Allah ya kara girma." "Amin, Allah ya sanya alkhairi." "Amin."  suka haɗa baki.' Tun da suka fito kamal yake ta tsokanar sa yaki tankawa wa, kansa ne ma yake neman damun sa gashi yau ko Forex din be duba ba, haka suka jera har wajen mota Kamal be daina tsokane tsokanen nashi ba, dariya kawai salim yake bashi da bakin magana, kamal ɗin ne kawai zai iya yi masa ya zauna lafiya amma shi kuwa yanzu sai ya faɗa masa bakake. Dan yatsine fuska yayi ya shiga motar kamal, jefa wa salim mukullin motar yayi yace. "Ka barta a nan wajen naka, anjima da daddare zan dawo unguwar sai na dauka." "Zaka dawo wajen amarya kenan, wai kanina an shigo layin manya." "Amma dai kanaji yace na dawo na same shi da daddare ko? Ni ina ruwana da ita da zan dawo wajen ta?" "Kai ka sani dai, ango ango, a daina kwana kwana kar a zo ana yar murya dan wallahi na saurarar ka zan ba." Be sake cewa komai ba suka dauki hanyar gidan. Jingina yayi da saman kujerar motar ya lumshe idon sa yana tariyo komai kamar a lokacin yake faruwa, har suka isa be d'ago ba sai da kamal ya bude motar sannan ya cire kansa da k'yar yana kallon harabar gidan. Yaya Nabila ce ta fito tana guda  yaja dan karamin tsaki kafin ya ɓalle murfin motar ya fito. **** Alhaji Faruku na komawa gidan be ko shiga gidan sa ba ya kutsa kai gidan bakin sa dauke da sallama, Hijabi Walid ya miko wa umma ta saka Anty Maryam ta gyara ita ma sannan ya shigo, Baba na d'aki ya dan kishingid'a yana jiran sa ashe har bacci ya dan dauke shi, jin sallamar sa ce yasa ya mike da sauri yana gyarawa, gaisawa sukayi da Umma kafin yayi sallama a kofar dakin baban yana cire takalmin sa, "Shigo mana Umaru, kaima kamar wani bako." "Sannu da hutawa yaya, kana ta jirana ko?" "Toh ya za'ai, nasan ai wani uzurin ne ya rike ka." "Tabbas kuwa, uzuri ne babba ya rike ni, sai dai komai ya zama yadda nake so Alhamdulillah." "Ah toh Masha Allah, kaji abinda yaron nan yake so yayi mana ko? Nace idan ma fasawa Yayi ai ya turo magabatan sa asan kan maganar ko? Amma hakan shiru ga abu yana matsowa ai babu dadi kuma dai kasan mata da saka damuwa." "Haka ne, sai dai fa sun zo sun same ni, kayi hakuri yaya na rashin sanar maka da ban yi ba, yaro dai ya turo wakilan sa akan shi fa gaskiya aure ba yanzu ba, saboda haka idan yar mu ta samu miji muyi mata auren ta, idan kuma zata iya jiran sa har ya gama shiri a tsanake toh sai ta jira.". "Ashhssha. Ashe haka akayi, shi yasa ya daina kira kenan." Baba ya fad'a yana kokarin danne zuciyar sa "Tabbas haka akayi, rai na ya ɓaci sosai dan ba karamin cin mutunci bane sukayi mana, tun daga ranar nake neman mafitar yadda zai sanar maka da wannan labarin hade da wani na farin ciki da zai maye gurbin sa, toh alhamdulillah, yadda suka so tozartamu, Allah be basu dama." "Basu kyauta ba gaskiya." "Kansu sukayi wa yaya, yaro dai bashi kadai bane namiji a duniyar ba." "Haka ne, kansu sukayi wa, babu komai Allah yasa haka ne mafi Alkhairi." "Yama zama alkhairin yaya." Karkace wa yayi kadan ya ciro kudin sadakin daga aljihun sa, ya ajiye a gaban sa "Yau ma a karo na barkatai na sake yi masa shishigi a al'amuran ka yaya, sadakin Maryam kenan, na daura mata aure da wanda nake ganin shine daidai da ita, na yarda na aminta da tarbiyyar sa, haka ita ma Maryam na gamsu da ita nasan ba zata watsan k'asa a ido ba, dan haka nake baka hakuri a bisa wannan, ka yafe min dan Allah yaya." "Me zan ce maka? Da wanne irin ido xan kalle ka na gode maka? Me zan ce maka a rayuwa ta? Yau a karo na biyu ka sake yi min abun da ba zan taba mantawa dashi ba a rayuwa ta, na rantse da Allah da ace akwai yan uwa irin ka masu zumunci da kaunar juna da kowa ya zauna lafiya a duniya, Allah Ubangiji ya faranta maka kamar yadda ka faranta min, Allah ya raba ka da sharrin duk wani abun ki ya raya maka gaban ka da bayan ka." "Amin yaya, hakan shine zumunci, kai ne ya koya min yadda ake son dan uwa, kaine ka dora ni akan turbar daidai lokacin da ban samu ingantacciyar tarbiya daga wajen mahaifiya ta ba, kaine ka sadaukar min da komai naka har na kai matakin da na kai a yanzu, ni kuwa wanne irin butulu ne da har zan manta wannan? Allah karya nuna min ranar da zanyi maka butulci a rayuwata." "Naji dadi sosai, hakan shine zumunci, Allah ya saka maka da Alkhairi ya raba ka da mahaifiyar ka lafiya, ya jikan iyayen mu da suka rasu." "Amin ya Allah." "Yaya... Ka sanar da su dan Allah, nasan nayi musu laifi na aikata abu ba tare da izini ba, abu me girma irin aure, suyi hakuri in Sha Allah alkhairi ne zai biyo baya." "Kana nufin Maryama da mahaifiyar ta wai?" "Su fa yaya... Kasan babu dadi abu daga sama haka." "Babu matsala in Sha Allah, na san wacece me daki na, babu wani abu da zan zo mata dashi ta bijiremin, kar ka damu da wannan." "Itama Maryam din..." "Wai Umaru baka da iko akan ta ne? Baka isa ka yanke hukunci akanta tabi bane da har kake shakku?" Ya katse shi a hasale "Allah ya huci zuciyar ka yaya,bari naje na sanar wa Hajiya." "Yawwa, ita zaka bawa hakuri dan ita akayi wa laifi ma, tana matsayin uwa ya kamata a sanar da ita, karka sake irin haka ba tare da ka sanar mata ba." "Tuba nake yaya, bari na saka Fahad ya shigo da kayan daurin auren." "Toh uban Amarya, duk yadda kayi yayi." Ya fada yana dariya, Fita yayi tsakar gidan umma na ganin ya fito tace "Yau mutumin ka akayi dambu, bari na sa Walid ya biyo ka dashi." "Amma naji dadi,dama na kwana biyu banci dambu ba, a ajiye min bayan sallar magriba Maryama ta kawo min." "Toh shikenan." "Ayi hakuri nayi laifi, yaya zai sanar dake komai." Ya fada yana ficewa, kofar da yabi umma ta kalla sannan ta kalli kofar dakin Baba, jin yana kiran ta yasa ta tashi tsam ta nufi dakin tana ji a kasan ranta akwai wani abu a kasa. Tana shiga ya nuna mata wajen zama, sannan ya kira Maryam, a d'arare ta shigo ta samu gefe chan ta rakube tana sauraron shi. Sai da ya fara da tuna musu karfin zumuncin da yake tsakanin sa da dan uwan sa Alhaji Faruku kafin ya sako maganar auren, daga Umman har Maryam ba karamin kada su maganar tayi ba, kuka Maryam ta saka tana tuno Hafiz, lokacin da taji Baba yana mika mata sadakin ta ne yasa ta k'ara tabbatar wa kanta ta rasa Hafiz har a bada, toh wa aka aura mata? Kila ma sadaka aka bashi saboda Hafiz din ya fasa auren ta, nasiha sosai Baba ya shiga yi mata, har ya gama bata samu kukan da take ya tsaya ba, a haka ta fito ta shige daki Anty Maryam na ganin haka ta bita da sauri, kuka take tayi ta kasa fada mata komai har umma ta shigo dakin ta same su. Zama tayi a gefen gadon ta shiga bawa Anty Maryam labarin abinda ya faru, dukkan su shiru sukayi kowa da abinda yake sakawa a ransa. *** Hafiz na zaune ya saka shinkafa da wake a gaba yana kallon, yau saura kwana biyu ya koma gida, tunanin Maryam yake da halin da ake ciki, gashi babu waya a hannun sa balle ya kira tun da wayar ya siyar ya bawa su Inna kudn da zasu d'an rike kansu kafin ya dawo, Allah Allah yake kwana biyun su cika ya zo gida yaji in da labarin su da Maryam ya kwana, Allah yasa iyayen nata sun yadda zasu jira shi din. Da haka ya saka chokalin ya fara ci yana yi yana duba lokaci saboda manajan gidan man ba mutunci ne dashi ba. Allah sarki Hafizu 😭 laifin inna ne. *** Yana kwance a falon gidan Yaya Nabila har akayi magriba, sai datayi mishi magana sannan ya mike da k'yar yayi alwala, a falon yayi Sallah saboda masallaci sun idar, shiru yayi yana kallon Tv yana tuno dan uwan sa, a haka ta fito tarar dashi, zama tayi a kusa dashi ya d'ago yana kallon ta "Tunani ko?" Ta fad'a tana kallon shi "Mamaki nake ne,wai nine nayi aure, unexpected aure.". "Haka Allah ya tsara." "Haka ne kam, kana taka Allah ne  nashi, ban taba imagining rayuwar haka ba, na kasa iya figuring abinda nayi wa Arab." "Mu cigaba da addu'a kawai, Allah zai kawo mana mafita." "Haka ne." Ya koma yana jingina a jikin kujerar dakin. Ba zaka je gidan su bane naga kana kwanciya?" "Zanje, am just too weak, ga tunanin Ummi yau duk na barta ita kadai." "Daurewa zakayi, ka sani ko a bamu amaryar mu a yau ma." "Wa? Ba dani ba wallahi, su barta chn ma ni naje da abinda yake damuna." "Tashi Ni dai toh." Ta fada tana dariya. Da kyar ya tashi ya shiga karamin dakin da yake falon, watsa ruwa yayi yana yi yana tunanin Maryam, dan murmushi yayi lokacin da ya tuno wayar da yaji tana yi wa salim, zaki bayani dalla-dalla. Ya furta yana cije kasan lips din sa. Sabon kaya ya tarar a saman kujerar dakin ya dauka yana dagawa, yasan aikin kamal ne dan haka babu bata lokaci ya saka ya fito fes dashi. Yana fitowa falon Kamal ya shiga tafi, banza yayi masa yace "Mukullin motar ka Please." "Wai kai zaka kai kanka kake nufi? Toh baka isa ba sai naje naga kalar amaryar tamu." "Dear kafa samun k'ani a gaba gaskiya, ka barshi yaci lokacin sa kai naka ya wuce.". "Haka kika ce?" Ya daga mata gira "Bari na dawo zakiyi bayani ne." "A Dawo lafiya." Ta fad'a tana dariya. Anty Maryam ce ta ciro mata kaya a cikin jerin sababbin kayn da Alhaji Faruku yayi musu na cin biki saboda ba lefe, sawa tayi duk idonta ya kumbura saboda kuka, hadaddun turarurruka ta shiga fesa mata ta shirya ta tsaf ta fito sosai kamar ka sace ta ka gudu. Flask d'in dambun Walid ya daukar mata suka shiga gidan Hajiya Mama. Suna shigewa su arkel na karasowa, gefe Kamal yayi parking yce "Zan d'an samu waje na makale idan ka gama sa ka kiran ko ango?" Bude motar yayi ya fito sannan yace "Ka je kawai in na gama zan dau mota ta a wajen salim." "Owk shikenan, a gaida amarya." Dariya kawai yayi bece komai ba ya saka kanshi a cikin gate din, bangaren Hajiya Mama ya kalla yaga an saki labule da sauri, wucewa yayi ya tsaya a bakin kofar part din Alhaji Faruku yana tunanin yadda zai sanar masa da zuwan sa. Walid ne ya bude kofar ya fito yayi saurin riko shi, "Ina wuni?" Be amsa ba yace "Abba na ciki?" "Eh shi da yaya Maryam ne." "Owk shiga kace nazo." Juyawa yayi ya sanar wa Alhaji Faruku, izinin shiga aka bashi ya shigo kansa a kasa, kamshin turaren sa ne ya daki hancin ta tana durkushe a kasa, da fara'a Alhaji Faruku ya karbe shi suka gaisa sannan ya mike "Ina zuwa." Yace yana fita hadda jawo musu kofa. Dan Dan.... Ga Arkel ga Maryam. Babu ruwana Yasin🚴🚴🚴🚴🚴🤣😌🤣🚴🤣🚴🤣🚴 _ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU😁._ *ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma *SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano) *KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo) *BURI ƊAYA!* (Mamu gee) *WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull) 👇🏻karku bari ayi babuku *ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu* *za'a tura kudin ta wannan accnt number din* Hafsat kabir umar 0225878823 GT bank Saika tura shaidar biya ga wannan number ta WhatsApp 08030811300 Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din 07067124863 Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya. *Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon Rano🚴🚴🚴 [3/18, 22:24] Hafsat Rano: *SAUYIN K'ADDARA* *15* ©*Hafsat Rano* *_ZAFAFA BIYAR na kudi ne idan kana son kowanne daga ciki ka nemi Wannan numbers din_* *08030811300*ii *07067124863* *_Daurin boye_* _safiyya huguma_ *_Buri daya_* _mamuhgee_ *_Wutsiyar rakumi_* _billyn Abdul_ *_Kai min halacci_* _Miss xoxo_ *_Sauyin kaddara_* _hafsat rano_ *Bangaren Hajiya Mama ya shiga bakin sa dauke da sallama, tana kan abin sallah tana lazimi, kasa ya samu daga gefen ta ya zauna sannan yace "Barka da gida Hajiya." Bata amsa ba sai data gama addu'o in ta sannan ta amsa, shiru yayi kamar ba zai magana ba dan be san ta ina zai fara ba, kallon sa tayi tasan akwai abinda zai faɗa mata, tunowa tayi da alawa da goron da Sultan ya shigo mata dasu dazu tayi tace "Kayan daurin auren da naga an shigo dashi daga ina ne? Ajiyar zuciya ya sauke jin ya samu hanyar da zai yi maganar yace "Kayan auren Maryama ne Hajiya." "Maryam kuma? Ban gane ba." "Eh Hajiya, dazu aka daura auren  nata da..." Katse shi tayi "Auw ka ji magana ta kenan ka fasa hada auren, ya yi kyau hakan ai." "Ba haka bane Hajiya, yaron da zai aure ta ne..." "Ya nemi alfarmar a daura da wuri ko? Baya so a haɗa dana masu arziki yaji kunya kenan, toh ai ya kyauta wa kansa." Kallon ta kawai yake ya rasa ta ina zai fara sanar mata ma, dafe kansa yayi da dukkan hannun sa yana kallon saman dakin. Nannad'e sallayar tayi ta mike da k'yar tana barin dakin, jiki a sanyaye ya biyo bayanta, zama tayi tana kallon kayan kafin tace "Ka turo Sultan idan ya dawo yazo ya tattare kayan nan ya mayar musu, gayyar tsiya." "Haba Hajiya, wai yaushe zaki daina irin haka ne? Yaya fa kamar d'an ki ne duk wata biyayya ta d'a ta mahaifi yanayi miki kuma naga..." "Kul ka fadan magana wallahi, kuma ni ba d'ana bane bana gayyar cin amana, wai duk ka manta abinda uwar sa tayi min, ta auren miji ta riga ni haihuwa dashi sannan a karshe ta shi ya sake ni, ni ko uban me zan yi da ahalinta?" "Amma Hajiya..." "Dan Allah barni na sarara,  zancen ya ishe ni haka,alawa da goro dai akansu kake neman fada min magana ko? Toh a ajiye ko almajirai na raba wa, tashi ka koma Allah ya bamu Alkhairi." Kauda kanta tayi gefe tana yatsine, jiki a sanyaye yace "Allah ya huci zuciyar ki Hajiya, sai da safe." "Amin." Fitowa yayi ya jawo mata kofa, part din sa ya nufa yana ayyana kalar rikicin da Hajiya zatayi idan taji yadda al'amarin ya juye. *** Tun da ya fita babu wanda yayi magana a cikin su, maganar sa da yayi ce lokacin da suke gaisawa da Alhaji Faruku ke mata yawo akai, idan ba har kuskuren ji tayi ba toh tabbas shine, maganar sa ce toh amma shi kuma? Me hakan ke nufi? Ta cikin mayafin ta ta d'an kalle shi kadan, kansa na k'asa yana danne danne a wayar sa, yawun bakin ta ta hadiye da k'yar ta zaro ido, dukkan hannu tasa ta rik'e saitin zuciyar ta da ke wani irin bugawa da sauri da sauri. Gyara zaman sa yayi ya kashe wayar ya d'an kalli gefen ta, a takure take ta sadda kanta ƙasa kamar tsohuwar munafuka, samun kansa yayi da sakin murmushi kad'an kafin yace "Baki iya gaisuwa bane wai?" Hadiye yawon bakin ta ta sake yi da karfi ta saka hannun ta ta damƙe saman mayafin ta, "Haka ake karbar ango ne a kauyanku?" Da sauri ta d'ago idanun su suka sark'e da juna, a saman labbanta ta furta "ango?" Ciki ciki tayi maganar, kallon bakin ta yayi ya gane me take nufi, daga kansa yayi sama yana kallo kafin ya maida kallon sa gareta, d'an bata fuskar sa yayi yace "Ba zaki gaishe nin ba dai a takaice ko?" "Ina wuni.?'" ta fada murya a cunkushe, ya k'yale ta ma da abinda yake damun ta zai zo ya k'ara mata da wani, a tunanin ta ma tare aka daura auren da nasu dana Rauda, amma menene dalilin da yasa aka hada su waje daya? Kila Abban yaje kirawo Rauda ne, zuciyar ta ta bata amsa. Kurawa Tv ido kawai yayi yana ayyana yadda zasu kwashe, suna nan zaune shiru Abba be dawo ba, kallon ta yayi zai yi magana yaga kyankyaso d'an karami ya hau kan mayafin ta, tsam ya mike ya isa wajen ta, kallon shi tayi shima ita yake kallo, ganin kyankyason na neman shigewa jikin ta yasa shi saurin saka hannun sa ya fisge mayafin. Yarfe shi ya hau yi zatayi magana kyankyason ya fado, da sauri tayi tsalle ta haye saman kujera saboda bala'in tsoron kyankyaso take, dariya ta bashi yadda tayi tsallen kamar wata mage, "Look at u,matsoratsiya kawai." Kasa tayi da kanta duk kunya ta kamata, kamshin turaren dake jikin mayafi ya shak'a a hankali ya lumshe idon sa, damƙe mayafin ya sake yi yaki bata ganin yadda ta takure kanta, komawa yayi ya harɗe kafa a saman kujerar sannan ya mika mata "Zo ki karba Malama." "Ka kawo min toh, ba zan iya tashi ba." Ta fad'a tana mika hannun ta daga nesa itama, banza yayi mata ya cigaba da kallon tv mayafin na rik'e a hannun sa, so yake ta taso ta karba da kanta. Gyaran murya Alhaji Faruku yayi hade da sallama, da sauri ya jefa mata mayafin yana sauka k'asa, tana kici-kicin yafawa ya shigo, dauke kai yayi kamar be ga komai ba ya zauna sannan yace su matso, kusa dashi, matsowa sukayi suka sashi a tsakiya, jikin maryam ne ya k'ara sanyi sosai, nasiha ya shiga yi musu me ratsa jiki da zukata, har ya gama babu wanda yayi ko da kwakkwara motsi a cikin su, kuka maryam kawai keyi k'asa-k'asa saboda ta gama fuskantar komai. Kallon Arkel yayi kafin yace "Kayi mana alfarma ayi biki zuwa karshen sati sai ta tare, kafin nan kai ma ka gama shirin ka." "Babu damuwa Abba, duk yadda akayi yayi." "Toh madallah, Allah yayi muku albarka." "Amin ya Allah, Allah ya k'ara girma." Juyawa yayi ya dora hannun sa a saman kanta yace "Maryama... "Na' .. am.." Tayi maganar Muryar ta na rawa "Raka shi wajen yaya." "Toh Abba." "Kuje Muhammad." "Ok tam, nagode Allah ya k'ara girma." Tashi tayi jikin ta yayi sanyi, tana gaba yana bin ta a baya har suka fita daga gidan, zasu shiga zauren gidan yayi saurin rikota ganin zata shige, kallon ta yayi ya bata fuska "Muje mana." Tace "Ki shiga ki ce zan shigo tukunna sai kizo ki tafi dani, ba kai tsaye zan shiga ba ai ko?" Bata ce komai ba ta shige ciki, wayar sa ya ciro zai kira salim saboda yana so ya kawo masa mota, yana danna wayar ta fito "Ka shiga wai..." Ta fad'a a ciki ciki. Juyawa tayi yabi bayanta bakin sa dauke da sallama, Umm da Anty Maryam ne a tsakar gidan, hasken nepa ya haske ko ina na tsakar gidan, Walid da Habubu na gefe sai Ahmad dake tsaye a jikin kofar Kitchen. Kallo ɗaya Anty Maryam tayi masa taji wani irin farin ciki, Allah Allah take su gama gaisawa ya fita, ya dan jima a wajen Baba kafin ya fito yayi musu sallama, hannun Walid ya riko suka fito zauren, walet ɗin sa ya zaro ya ciro dubu biyar ya damka masa. "Ku sai sweet kaji?" "An gode." Ya karba yayi ciki. Yana fita Anty Maryam ta fad'a daki ta sauri, taso ta tayi tace taje ta rakashi, yana tsaye a zauren yana magana da Salim yaji tafiyar ta, dan juyowa yayi ya kalle ta ya cigaba da waya. Tana tsaye tana ta cika tana batsewa har ya gama ya maida wayar aljihun sa. "Are you not happy?" Ya tanbaya ganin yadda take bata rai, shiru tayi tana jin duk babu dadi, tunanin abinda Hafiz yayi mata take da yadda auren ya kasance, samun kanta tayi da sakin kuka a hankali. "Gosh... Me nayi miki? Daga tambaya?" Shiru tayi yace "Am sorry, kije ciki zan wuce yanzu nima, ina jiran salim ne." Juyawa tayi ya bita da kallo har ta shige, dan fitowa yayi ganin hasken mota. Mika masa key salim yayi bayan sun gaisa, shiga yayi shima salim ɗin ya shiga ya rage masa hanya, suna zuwa titi yace "Dan cire min password ɗin wayar ka." Ba musu Salim ya cire ya mika masa, contact ya shiga yayi searching Maryam, Maryam Siwes yaga yayi saving number, kallon ta yayi ya haddace sannan ya danna delete ya mika masa. Godiya yayi masa ya bude motar ya fita. *** Hajiya Mero na zaune a daki tana gyara zaman sarkokin ta, so take ta sake musu ma'ajiya me kyau, jin wayar ta na k'ara yasa ta d'an sa hannu ta dauko, ganin sunan Alhaji ne yasa ta daga cike da zumud'i "Please ki turo Buzu Airport nan da 1hour zan sauka." "An gama ranka ya dade." Da sauri ta maida sarkokin waje daya ta fita dan sanar wa buzu, bata zata yau zai dawo ba a tunanin ta ma sai irin jibin nan. Cije bakin ta tayi tana tuno sharadi nan, yanzu da ace kwatsam ya dawo da ya kenan? Ta mutu ta gama yawo Daki ta koma ta shiga wanka da sauri bayan ta zuba garin maganin, doguwar riga ta zura kawai ta nufi kitchen tana kwalawa Sadiya kira, daga dakin Ummi ta fito ta kalle ta da mamaki "Uban me kike a ciki?" Ta tsare ta da tambaya dan ta hanasu shiga dakin, "Kiyi hakuri Hajiya, naga yau duk babu kowa shiyasa na duba na gani." "Zaki ci ubanki kuwa wallahi zaki bar gidan nan in dai zan sa doka kina karya min." "Kiyi hakuri wallahi ba zan k'ara ba." "Wuce muje Kitchen munafuka, yanzu ina da abin yi zan dawo kanki." Kitchen suka shiga ta saka ta ɗora abinci, tana tsaye har ta gama ta kwashe a food flask, karba tayi ta fita daga kitchen din, a saman dinning ta ɗora masa ta fito da wani kullin ta sake barbadawa, tana rufewa Arkel ya turo kofar ya shigo, da sauri ta maida hannun ta baya, ko kallon in da take be ba ya shige ciki kawai, dakin Ummi ya bude ya shiga yana kallon gadon cike da tausaya wa. Yana zaune yaji tsayuwar mota a harabar gidan, bude labulen dakin yayi ya hango Alhaji yana fitowa, tashi yayi ya fito falon yayi daidai da shigowar Alhaji, Hajiya Mero ya kalla sannan ya maida kallon sa wajen Alhaji yace "Sannu da zuwa." "Yawwa, kaga ka taso ni ban gama abinda nake ba ko?" Sosa kansa yayi yayi murmushi kad'an, Hajiya Mero data shak'a kadan ta danne zuciyar ta ta karasa wajen sa tana yi masa sannu da zuwa, amsawa yayi ba yabo ba fallasa sannan yace "Fushi fa nake dake da d'an naki." "Da mukayi me kuma ya Haj." "Had'a baki mana, sai ji nayi za'a daura, ko nace an daura, na rasa saurin me akeyi kuma." "An daura me kuma Alhaji?" "Karki ce min baki sani ba mana, gashi nan da kike ganin sa ai ango ne, dazu Alhaji karami ya kirani yake fada min, Alhaji Faruku ne ma ya jagoranci daurin auren, shine fa dalilin dawowa ta ba shiri." Kamar zaurance haka taji maganar, bata fuskanci komai ba hakan yasa tace "Allah ni fa Alhaji ban fuskanci komai ba fa." Dariyar kasa kasa Arkel yayi ya harɗe hannun sa kawai yana jin su "Toh aure dai an daura shi, in ma dai su chan basu sanar miki ba ko kuma dai ya akayi ni ban sani ba wallahi, amma tabbas an daura aure dan ga alawa nan da goro ma Karami ya zuba mana a booth da yake ta wajen sa na fara biyawa kafin na zo gida." Wucewa yayi ciki tayi saurin kallon Arkel, "Me Alhaji ke cewa ne wai? An daura auren ku da Rauda kenan ko me?" "An daura Hajiya..." Da sauri tace "Kai Alhamdulillah... " "Amma fa ba da Rauda ba, da Maryam ne." Da sauri ta kalle shi, daga kansa yayi cikin son sake gamsar da ita yace "Sati daya ma yace za'a yi biki sai ta tare, kafin nan zan fara gyaran gida." Tashi yayi ya haye saman be jira amsar ta ba, Daurin dankwalin kanta ta cire tayi jifa dashi ta shiga neman wayar ta a cikin kujeru tana ji kamar zata yi hauka. Nace Kadan kika gani Madam🤪🤣 sai ma mun shigo gidan *** Daga shi sai singlet da boxer ya kwanta rigingine yana busa sigari, Mustapha dake gefen sa yana rike da remote yana kallon wasan sport, lokaci zuwa lokaci yana juyawa ya kalli shi, hankalin sa sam baya wajen kallon wasan, tunanin gida yake da yan uwan sa, tun ranar da suka zo abubuwan suka sake tabarbare masa, da ya ja baya sosai da shan sigari amma yanzu ya dawo dashi fiye ma da dah din, duk yadda yaso yaji sauki a ran sa abin ya faskara, bashi da sukuni ko kwanciyar hankali sam, rayuwar baki dayan ta yin ta kawai yake babu wani alamun farin ciki a ciki. Tashi yayi ya wuce toilet, amai ya shiga yi sosai kamar zai fidda komai na cikin sa, cike da tausaya wa Mustapha ke kallon kofar yana mamakin irin matsalar sa, tsawon lokacin da suka dauka tare a garin na Calabar be taba ganin wani abu na jin dadi a tattare dashi ba, a yadda yake abubuwan sa ma baki daya zaka san ya fitar da rai da rayuwar da komai da yake ciki, gani yake bashi da wani sauran amfani a duniyar. Shi kuwa wane irin abu ya aikata haka? *** Yar karamar jakar sa ta makaranta ya zuba kayan sa kala biyu, sai zumud'i yake zai zo gida, yan kuɗaɗen sa ya kalla daya tara, wajen matsa mai suke samu suyi rara ko wasu su bar musu chanji, tattare kansu yayi ya tura a cikin jakar sannan ya saba ta ya fito. Yana sauka daga mota ya wuce farm center, yar karamar waya ya siyo sannan ya nufo gida yana Allah Allah ya isa ya saka sim ya kira Maryam. _ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU😁._ *ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma *SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano) *KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo) *BURI ƊAYA!* (Mamu gee) *WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull) 👇🏻karku bari ayi babuku *ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu* *za'a tura kudin ta wannan accnt number din* Hafsat kabir umar 0225878823 GT bank Saika tura shaidar biya ga wannan number ta WhatsApp 08030811300 Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din 07067124863 Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya. *Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon Rano🚴🚴🚴 [3/18, 22:24] Hafsat Rano: *SAUYIN K'ADDARA* *16* ©*Hafsat Rano* *_ZAFAFA BIYAR na kudi ne idan kana son kowanne daga ciki ka nemi Wannan numbers din_* *08030811300* *07067124863* *_Daurin boye_* _safiyya huguma_ *_Buri daya_* _mamuhgee_ *_Wutsiyar rakumi_* _billyn Abdul_ *_Kai min halacci_* _Miss xoxo_ *_Sauyin kaddara_* _hafsat rano_ ** *** A gigice ta d'ago wayar data kusa shigewa cikin kujera, number Hajiya Mama ta kira tana ta Allah Allah a daga, har ta k'araci ringing d'in ta bata d'aga ba, cigaba da kira tayi tana zagaye a tsakiyar falon kamar wata zararriya, sai datayi wajen kira sau goma babu alamun xa'a daga, Rauda ta kira da Sultan dukkan su kamar hadin baki basu daga ba basu kuma biyo kiran ba, "Wayyo na shiga uku." Da sauri ta tuno da Zainab, "Yawwa..." Tace tana danna mata kira, ringing d'aya kuwa ta dauka, da sauri tace "Ina Hajiya Mama?" "Suna falo." "Maza jeki kai mata wayar." "Mummy ina dan abu ne ki kirata a wayar ta mana." "Dan ubanki kinje kin kai ko sai na zo na kakkaryaki?" Ta fad'a a harzuk'e, da sauri ta mike tana kunkuni "Kullum sai masifa haba dan Allah." Lank'anji ta tsaya yi tana neman hular ta, sai data gama jan aji da shan kanshi sannan ta fito falon ta mikawa Hajiya Mama wayar "Mummy ce." "A daren nan, toh Allah sa lafiya." "Mero ya akayi?" Ta kara wayar a kunnen ta tana nuna wa Sultan hannu alamar ya rage volume d'in TV "Na shiga uku Hajiya, abinda na ji gaskia ne ko kuwa?" "Me kika ji? Me yake faruwa?" "An daura auren Maryam ne ko kuwa?" Ta tambaya cike da tashin hankali "An daura mana..." "Innalillah wa inna ilaihi raji'un., Hajiya garin yaya haka ta faru?" "Me ya faru? Wai dan sun mata aure ko me? Aini dadi naji an raba auren, baki ji farin cikin da nai ba." "Amma gaskia yaya Alhaji ya cuce ni, ko nace ya cuce mu Hajiya, kinsan da Arkel aka daura auren? Muna can mun saki baki ashe ya san shirin mu?" Zumbur Hajiya Mama ta mike ta manta da wani ciwon kafar da ta wuni tanayi, "Ban fahimce ki ba dai, me kike so kice!?" "Hajiya yanzu dare yayi, zan shigo gidan da sassafe, zakiji komai, zanzo na sami yaya Alhajin sai ya faɗa min dalilin da yasa yake son yaga bayana, kwata kwata baya kauna ta Hajiya, yafi son wadanchan mutanen akai na, me nayi masa??." "Kwantar da hankalin ki, Allah ya kaimu goben, idan har da gaske ya kulla auren nan toh kuwa dole ya warware shi, ba zan masa da sauki ba sam sakarcin nasa ya fara isata." Kallon ta Sultan yayi da sauri, "Dena kallo na malam." Dariya yayi kawai a ransa yace "Hajiya masifa, gobe Abba zai sha ta." Huci kawai take ta rasa me yake mata dadi, sai data zagaye falon yafi sau nawa, shirun da Alhaji yaji yayi yawa ne yasa ya leko, tana ganin shi tayi saurin daidai ta kanta ta nufi dining da sauri ta kwaso kayan abincin sa ta shirya masa a tsakiyar falon. *** Daren ranar baccin mutane da yawa ƙalilan ne, Hajiya Mero kuwa bata ko runtsa ba tana Allah Allah gari ya waye. Bangaren Maryam da Arkel ma hakan ce ta kasance, kowanne a cikin su da tunanin yadda al'amarin ya kasance ya kwana. Shida da yan mintuna ta dira a gidan, a zaune ta samu Hajiya Mama tun da tayi sallar asuba bata tashi daga wajen ba, tana ganin ta ta saki ajiyar zuciya, alawa da goron da ke zube a falon Hajiya Mero ta kalla, hakan ya sake tabbata mata da komai. Ka'ida sa ce duk asubah duniyar idan yaje sallah ya dawo yana fara zuwa ya gaida mahaifiyar sa, yau ma kamar kullum hakan ce ta kasance, tura kofar yayi a nutse hade da sallama, da mamaki yake kallon Hajiya Mero, babu wanda ya amsa masa sallamar a cikin su, murmushi yayi kawai ya zauna yana gaida Hajiya "Da wa ka daura auren Maryam?" Maimakon ta amsa gaiswar sai ta jeho masa tambayar Kai tsaye yace "Da Muhammad Hajiya." "Wanne Muhammad?" "Yaron dai da zai auri Rauda dah, Ashe Maryam ce rabon sa,kinji al'amarin Allah." "Dakata... Me kake so kace min??" "Dan Allah Hajiya wannan ba abun tashin hankali bane, da Maryam da Rauda duk daya suke a wajena, ni nayi masa sha'awar Maryaman da yake kuma Allah ya ƙaddara sai kawai hakan ta kasance, mu dauki hakan a matsayin tsarin Allah." "Hmm..." Kawai tace ta rasa me zatace, cikin bacin rai Hajiya Mero tace "Amma Yaya ai baka kyauta ba sam, ga wadda ya gani yace yana so sai kuma..." Daga mata hannu yayi yace "Ke kika haifi Rauda?" Hadiye yawon bakin ta tayi ta zaro ido dan bata zata ba, dauke kansa yayi ya bar kallon ta yace "Karki kara shiga hurumin da ba naki ba, ki tsaya matsayin ki." "Hajiya nayi laifi kuma na roki alfarma da ki yafe min tun jiya, ki bar komai ki daina sawa kanki damuwa, kin ga dai yanayin da kike ciki, ki daina bari wata chan tana zuwa tana dora miki matsalar ta kina hawa kai." Da sauri ta kalle shi, idon ta ne ya cicciko tace "Nice wata chan Yaya? Uwa daya kuwa ai tafi gaban wasa, dama nasan ka tsane ni, saboda ba mahaifin mu daya ba ko? Gani kake ni bare ce." Kuka ta saka sosai, danne zuciyar sa yayi yace "Ni ban tsane ki ba, halin ki nake gyamata, ki daina zuwa kina assasa matsala tsakani na ni da mahaifiya ta, shine kawai zamu shirya ni dake." "Ya Isa..." Hajiya Mama ta katse shi, "Tun da har kayi abin da kake ganin shine daidai, kaji kawai Allah ya bada sa'a." Sosai jikin sa yayi sanyi, a haka ya mike kawai ya fita. Ba ya son yadda Mero take zuwa tana juyawa Hajiyar tunani, ko tsofan da Hajiyar tayi bata gani kullum sai ta bullo da abinda zai zama fitina. "Kika barshi ya tafi Hajiya? Yanzu shikenan aure ya dauro,maimakon ki tilasta masa ya warware." "Ya zanyi toh ni? Kina jin yadda yake magana, sai mu zuba musu ido kawai." "Ba zai sabu ba, dole na cimma buri na, dama na sani tun farko Zainab ɗin na bashi, tun da ita ce tawa, da babu wanda zai nemi ya gaya min magana, amma babu komai, zan dau mataki da kaina." "Da dai kin bar sun kawai, sai kiyi tunanin yadda zaki ɓullo musu ta bayan gida, tada hankali ba shine zai warware komai ba." "Haka ne kuma, nasan me zanyi kawai." "Shikenan,kibi komai a sannu." Mik'ewa tayi ta goge fuskar ta, "Toh Hajiya, bari na koma na kwantar da kai naji komai wajen Alhaji, in sun san wata basu san wata ba." Hmmm...🙄🙄🤔 *** Tatar koko Suwaiba keyi sana'ar da Inna ta fara tun bayan dawowar ta daga Gumel, sallamar da taji ne yasa ta d'ago da sauri, sakin abin tatar tayi ta hau dariya "Yaya sannu da zuwa." "Sannu suwai suwai, tata ake yi ne?" "Eh, Inna! Inna!! Ga yaya ya dawo." Ta hau kwala wa inna kira, kamar a mafarki inna taji kiran, da sauri ta bantari goron dake hannun ta ta fito tana gyara zani, kallon mamaki ta bishi dashi dan bata tsammaci zuwan sa nan kusa ba, gefen tabarmar dake shinfide a tsakar gidan ya yi wa kansa masauki yana sakin yar k'ara "Wash... Inna barka da gida." "Barka, wai har kayi me kenan? Na ganka haka katsaham." "Wallahi inna hankali na ne ya kasa kwanciya sam, gashi kwata kwata ba yar waya ma balle na rage shiyasa kawai na taho naji yadda ake ciki sai na koma lahadi in Sha Allah." "Toh sannun ka ya ka baro su chan?" "Duk lafiya inna, kai duk wanda ya bar gida..." "Gida ya barshi inji malam bahaushe." Ta karashe masa tana mik'ewa "Sai kaje huta ka zo muyi magana." Da sauri yace "Ai bar hutun nan inna, gwara naji halin da ake ciki kafin komai." Kallon Suwaiba inna tayi tace "Kawo masa ragowar farau-farau ɗin nan bari na zagaya." "Toh Inna." Buta ta zara tayi bayan gida tana tunanin yadda zata fara sanar mishi. Kallon kwanon da Suwai ta dire masa yayi kawai ya mike ya nufi dakin sa, duk yayi kura haka ya cire kayan sa ya d'an tattare abinda zai iya tattarewa ya dan haye saman katifar sa yana kokarin bude wayar da ya siyo, sim din sa ya dauko ya saka ya kura wa wayar ido yana jira ta gama kunnu wa, a zahiri kallon wayar yake sai dai baki daya hankalin sa yana chan wajen maganar da Inna tace zatayi masa, a yadda yaga tana dojewa maganar ya riga gama shan jinin jikin sa. Account balance ɗin sa ya duba yaga Mtn na binshi bashin dari uku, tsaki yayi ya ajiye wayar ya rufe idon sa kawai yana hasaso yadda yake so komai ya kasance idan har Allah yasa iyayen Maryam sun ƙara masa lokacin. Suwaiba ce tayi sallama a kofar dakin, yana daga kwance ya tashi ya fito, "Ya akai suwai? "Inna ce take kiran ka." "Ok muje." Cikin gidan suka shiga inna na zaune, zama yayi ya tattara hankalin sa kachokam a kanta, sai data ja fasali kafin tace "Maganar yarinyar nan..." Sake nutsuwa yayi, tausayi taji ya bata har taji maganar tayi mata nauyi a harshen ta, Kallon ta yayi ta marairaice yace "Inna dan Allah..." "Iyayen ta dai basu amince da jiran ka ba, a takaice dai ma sun ce ka rabu da yar su Allah ya haɗa kowa da rabon sa." Yana zaune ya mike da sauri, kauda kai inna tayi tana jin kamar bata kyauta ba, be yi magana ba kawai ya bar tsakar gidan da sauri,kiran sa inna ta hau yi be ko juyo ba ya shige dakin sa, rigar sa dake rataye ya saka ya fito ya bar gidan. Kai tsaye gidan su maryam ya nufa yana tafe yana hada hanya. Maryam na zaune tayi shiru tana tunani, haka kullum take bata da aiki sai tunani, jin kamar ana buga zauren gidan ne yasa ta kalli Umma, "Kamar bugu nake ji umma." "Gashi su Walid basa nan, ko yan Nepa ne?" "Anya? Nepa da yamma haka?" "Shi na gani kuma." Bugawar aka cigaba, umma tace "Sa hijabin ki ki duba waye." Hijabin ta ta saka ta fito, yana tsaye ya zubawa kofar gidan ido, da sauri ya shigo zauren yana ganin ta "Hafiz..." Ta furta a hankali tana kallon cikin gidan "Maryam dan Allah kuyi hakuri, wallahi wallahi bansan cewa idan aka nemi alfarmar a kara mini lokaci su baba zasuyi fushi ba, na rantse da Allah Maryam ba zan iya rayuwa babu ke ba, kuyi hakuri dan Allah a yi bikin yadda aka tsara." Sakin baki tayi tana kallon sa, surutai kawai yake data kasa gane kansu, yanayi yana sake matsowa cikin zauren sosai, hawaye ne suka taru a idon ta, kenan Hafiz yana nufin ba da sanin sa komai daya faru ya faru ba kome? Amma ai kuma daina kiranta yayi gaba daya, shine yanzu zaizo ya raina mata hankali kenan, tunani yayi zata jirashi ko me? Daure wa tayi ganin kamar baya cikin hayyacin sa tace "Ni sam ban gane in da maganar ka ta dosa ba, me kake nufi ne wai? Bayan kace ba zaka aure ni ba ka daina kirana yanzu shine zaka lallabo ka dawo?" "Ni, ni nace bazan aure ki ba Maryam? Ni ko me yasa zanyi haka? Billahillazi ban ce ba zam aure ki ba, cewa kawai nayi a kara min lokaci wallahi Allah." Dariya tayi wadda tafi kuka ciwo, ta riga ta gano rainin wayo ne kawai zai yi mata, juyawa tayi zata shige ciki yayi saurin riko hannun ta, da sauri ta jiyo tana kallon shi cike da mamaki, "Cika ni malam." "Ba zan cika ki ba, idan har ba zaki tsaya ki saurareni ba, toh wallahi sai dai mu kwana anan." Kici-kicin kwace hannun ta take ya rike kam, cikin takun sa na kasaita ya zuro kafar sa cikin zauren, kamshin turaren sa ne ya fara yi musu sallama hakan yasa Maryam kallon kofa, zaro ido tayi gaban ta yayi mugun faduwa, hade rai Hafiz yayi yana tuno fuskar mutumin da ya tsana. Kallon hannun nata tayi ta kalli Hafiz "Ka cika ni dan Aallah." Banza yayi mata ya sake rike hannun nata sosai, gashi yayi mata riko na sosai wanda ba zata iya kwace wa ba Idanun sa rufe suke ruf cikin bakin glass baka ko ganin fuskar sa, cikin dakakkiyar muryar sa yace "Sake ta malam." "In naki fa? Uban waye kai da zaka sani nayi ko kar nayi? Ko shine sabon saurayin da kikayi bayan kin yaudare ni?" Ya fada cikin kishi, dariya Arkel yayi kadan ya tako har gaban su, kallon cikin ido yake mata hakan yasa baki daya ta duburburce, hannu yasa ya fisge ta ta hade ta da jikin shi, wani irin rawa jikin ta ya dauka kamar mazari, a hankali ya furta "Da izinin wa kika fito wajen wannan wawan?" D'ago kanta tayi ta kalle shi, ya kafe ta da ido tana hango haske ƙwayar idon sa a cikin glass din, "Wai me kake haka? Kai muharramin ta ne da zaka hada kazamin jikin ka da ita? Wato abin da kike yi kenan tun da Maryam da kuke kebewa a office din sa ko?" Wani mugun kallo Arkel yayi masa, "Kana so kaga kalar abinda mukeyi a office din?" Ya d'aga masa gira "Lemme show u." Jikin sa ya sakata sosai ya saka hannun sa ya zagaye ta. Cikin bacin rai Hafiz ya bud'e baki zaiyi magana kawai sai gani yayi Arkel ya hade bakin su waje daya. Gaba d'aya daina gani yayi, tashin hankali da ba'a sa maka rana kenan🤣🤣 Kansu yayi kamar zai yi hauka, ganin kamar ma basu san dashi a wajen ba yasa ya juya daga sauri ya fita, dutse ya dauka kato zai koma ciki, hango Baba yayi ya taho yayi saurin ajiye dutsen ya tsaya yana jira ya karaso. Ko uban wa zai buga wa dutsen oho😂😂 kai gaskia Hafizu ya shak'a. Arkel fa ba sauki 😳🤔🤣😅 Hafiz na fita ya janye jikin sa yana hade rai, kamar kazar da aka tsamo daga ruwa haka Maryam ta ji ta, gaba daya wata irin muguwar kunya ce ta rufe ta. "Malama bude idon ki, ki bude kunnen ki kiji, na rantse da Allah na sake ganin ki da wawan chan a tsaye kuna magana har ya yi gigin taba ki sai na kusa sumar dashi." "Sannan kema sai nayi miki hukunci me zafi, kuma zan sanar wa su Abba." Da sauri ta kalle shi, harara ya dalla mata ya kauda kansa "Zuwa nayi muyi magana amma kin batan rai, ki shige gida zan dawo da daddare." "Kayi hakuri." Ta samu kanta ta furtawa, daga kafadar sa yayi ya nuna mata hanya "Koma gida." Juyawa tayi ta shige, murmushi yayi kawai ya fito, lokacin Baba ya karaso, Hafiz ne ya karbi kayan hannun sa yana gaishe shi, karasawa Arkel yayi shima ya tsuguna a kasa. Harara kawai Hafiz ke aika masa, yana kallo ya shiga motar sa ya tafi, kallon Baba yayi yana sosa kai yace "Baba dama maganar Maryam ne..." "Kaga mijin ta nan yanzu ya tafi, muyi hakuri da abinda Allah ya tsara kawai." Yana kaiwa nan ya karbi kayan sa ya shige gida. Allah sarki Hafizu 😭 *** Masu kwamplain na short page kuyi HAKURI, am trying my best wlhi Allah, answering messages kawai aka barka dashi an barka da aiki ga masu kira, masu siyan littafi, masu so a turo musu page kaza, ga typing banda al'amuran gida da iyali. A kullum nakan amsa messages ta private fiye da 200 Ina kokari sosai ku kara hakuri Please. Abubuwan sun min yawa ga ido ya sako ni a gaba. Sannu sannu bata hana zuwa sai dai a dade...... _ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU😁._ *ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma *SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano) *KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo) *BURI ƊAYA!* (Mamu gee) *WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull) 👇🏻karku bari ayi babuku *ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu* *za'a tura kudin ta wannan accnt number din* Hafsat kabir umar 0225878823 GT bank Saika tura shaidar biya ga wannan number ta WhatsApp 08030811300 Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din 07067124863 Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya. *Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon Rano🚴🚴🚴 [3/18, 22:25] Hafsat Rano: *SAUYIN K'ADDARA* *17-18* ©*Hafsat Rano* *_ZAFAFA BIYAR na kudi ne idan kana son kowanne daga ciki ka nemi Wannan numbers din_* *08030811300* *07067124863* *_Daurin boye_* _safiyya huguma_ *_Buri daya_* _mamuhgee_ *_Wutsiyar rakumi_* _billyn Abdul_ *_Kai min halacci_* _Miss xoxo_ *_Sauyin kaddara_* _hafsat rano_ *** Da k'yar yaja kafafunsa ya bar kofar gidan zuciyar sa na matuƙar suya, be taba tunanin Maryam zata yaudare shi haka ba, duk yadda yake ta fafutukar ganin ya samo abinda zai taimaka musu amma tayi masa haka? Ba zai taba yafe mata ba kuwa, dole ya dau fansar abinda ta aikatawa zuciyar sa. Ko da ya shifeega gida be nemi kowa ba ya bude dakin sa kawai ya shige, kwanciya yayi lamo baya jin zai iya runtsawa a daren yau ga wata uwar yunwa dake nukurkusar sa, duk sanda ya rufe ido abinda ya faru yake hangowa, hakan ya saka masa zazzafan zazzaɓi da ciwon kai me tsanani. *** Gidan Ya Nabila ya zarce kai tsaye yana tafe yana tsaki har ya isa, knocking yayi yaji shiru hakan yasa ya kira wayar ta, bata gida ta dan fita ashe amma ba nisa tayi ba, komawa mota yayi ya jira ta. Kujerar ya kwantar sosai ya jingina kansa a jiki, lumshe idon sa yayi ya fada kogin tunani, wayar sa ce tayi kara ya dan bude idon sa kadan, private number da ya gani ne yasa shi saurin tashi, d'agawa yayi ya kara a kunne sa, shiru babu wanda yayi magana, cire wayar yayi daga kunnen sa ya saka ta a handfree yace "Stop calling me idan baka shirya magana ba, Ina da abubuwa da yawa da zan yi so stop wasting my time. Am hanging...." "Wait..." Yayi saurin tsayar da shi "Da gaske kayi aure bro? kayi aure ka barni? Dnt You care about me anymore?" Wata bazawarar dariya Arkel yayi ya bigi sitiyarin motar "Look who's talking! Yanzu har kana da bakin tambaya ta wanann? after all abinda muka shiga akan ka?" "Baka tunanin komai nayi akwai dalili me karfi?" Shima ya katse shi Share zancen yayi yace "Me ka kira kace min? Na zata mun gama da wannan maganar ai." "Arkel har yanzu kana nan da zafin ranka, baka chanja ba, man u need to grow up." "Zan kashe please, bana son jin komai." "Arkel ka..." Kafin ya k'arasa magana ya kashe wayar,ransa ne ya ɓaci sosai, fasa jiran Ya Nabilan yayi ya tafi kawai. A harabar gidan ya tarar da Hajiya Mero tana tsaye ita da wani mutum, kallon su yake har ya dangana da ma'adanar ajiye motoci, ganin ya bude kofar ne yasa tayi saurin cewa "Gashi nan ya dawo, kaje kawai zamuyi waya." Dan kallon shi mutumin yayi ya daga kai "An gama hajjaju." Da sauri ta juya zata koma ciki ta tsaida ita ta hanyar cewa "Hajiya." Dagata wa tayi har ya karaso, "Ya akayi Arkel? Tun dazu nake jiran dawowar ka ina so muyi magana akan shirye shiryen bikin nan, kai ma naga ka zama busy." "Maganar da zanyi kenan." Ya amsa mata "Muje ciki toh." Gaba tayi ya bita a baya yana kallon harabar gida. Kallon falon yake yana ayyana yadda komai zai kasance "Anjima masu kawo furnitures zasu kawo, falon saman chan za'a zuba su zuwa gobe zasu dawo su gyara, na bedroom d'ina ma za'a fito dasu..." "Baka bukatar su ne kuma? Naga basu wani jima ba." "Eh gaskia, da nace musu su hada su tafi dasu amma idan kina so sai ki dauka." Yayi maganar yana basarwa dan ya gano in da maganar ta ta nufa. Da sauri tace "Nagode kuwa, amarya ai dama komai yar sabo ce, gwara a ake mata sabo, amma Arkel sai naga kamar be kamata ace baka hada dana Yaya ba." "Sama zata koma." Yayi maganar yana hade rai. Da sauri ta kalle shi "Sama kuma? A wannan yanayin nata?" "Eh!" Ranta ne ya baci har ta kasa boyewa "Amma mesa ba zaka barta a kasan ba? Baka yadda da ni bane ko me? Ko ita maryam zata iya d'awainiya da ita ne ita kadai?" Kallon ta yayi cike da mamaki, yadda taga yana kallon ta ne yasa ta tuna abinda take neman yi, da sauri tace "Naga ace daga zuwan ta kaga aikin zai mata yawa, gwara ka barta a kasan kawai a hankali idan ta saba da gidan sai a mai da ita saman." Shiru yayi be ce komai ba, "Shikenan dama shawara ce, kayi yadda kaga yafi maka kwanciya hankali, ni dama ita yayan na duba saboda kasan zai fi mata." "Shikenan, hakan yayi." Murmushi tayi cikin jin dadi tace "Ko kaifa, Allah dai ya bata lafiya." Mik'ewa yayi ya wuce saman ta bishi da harara sannan tace "Shegen taurin kai." Number ta kira ta kara a kunnen ta, dariya tayi sosai kafin tace "A nemo min shi." Ajiye wayar tayi cike da farin ciki *** Toilet ya d'aura a kugun sa ya tsaya a gaban mirror yana kallon kansa, hannu yasa ya shafi bakin sa sannan yayi murmushi "So soft." Ya furta a hankali wanka ya fad'a ya jima yana gurzar jikin sa kafin ya sakar wa kansa ruwa saboda zafin da ake yi yau ba sauki. Karamar riga ya saka da wando wanda ya tsaya masa iya guiwar sa ya sauko kasan don duba Ummi, tana nan kamar kullum a kwance babu wani abu da ya sauya, a kasan gadon ya dire guiwowin sa ya riko hannun ta "Sannu Ummi, kwana biyu nayi laifi na barki ke kadai ko?" "Ayi min afuwa Ummi, na aikata wani babban al'amari a rayuwata ba tare da sanin ki ba, nayi aure Ummi." Shiru ya dan yi yana jin kamar zai yi kuka, gyara zaman sa yayi, "Ummi yau ya kirani, ya kira har munyi magana Ummi, bansan me zanyi ba Ummi, yace komai ya aikata yana da dalili, na rasa me zanyi? Na yadda dashi Ummi ko na share shi? Dan uwana ne Ummi, idan yana cikin matsala ni ya kamata ya fara sanar wa amma me? Ya zanyi ne Ummi?" Hannu yasa ya share kwallar da ta gangaro masa, ya mike "Kiyi min addu'a Ummi, ki kuma yafe min idan abin da nake shirin aikatawa ba daidai bane." Juyawa yayi ya rufo mata kofa, kuka ta saka cike da tausayin rayuwar ya'yan nata. Ta dogara da Allah tasan akwai ranar da gaskiya zatayi halin ta, duk ni san jifa... Turus yayi yana kallon uban akwatu nan dake zube a tsakiyar falon, ya Nabila ce ta shigo kunne ta rike da waya alamar magana ta keyi, harɗe hannun sa yayi ya zuba wa kayan ido yana kallon ikon Allah, bata kula shi ba ta wuce dakin Ummi tana cigaba da wayar da take, sai data fito sannan ta harare shi "Wannan uban kayan fa?" "Ban sani ba, ka saka nayi ta sauri ban gama abin da nake ba nazo naga ka tafi." Shafa kansa yayi yace "laaa... Sorry mantawa nayi." "Mantawa?" Ta harare shi "Eh wallahi, wani abu ne ne ya taso na tafi ba shiri." "Kaji dashi." "Toh wannan kayan fa?" Ya tambaya yana nuna mata da hannu "Karka damen malam, tana ciki ne?" Ta nuna dakin Hajiya Mero Dage kafada yayi "Nima ban sani ba." Dariya kawai tayi ta murd'a kofar, da sauri Hajiya Mero ta boye ledar tana kallon kofar "Mummy... Ashe kina ciki, sannu da gida." "Ina ciki Nabila, zuwan kenan?" "Eh wlhi, wanchan yaron ne ya taso ni, ga kayan chan a falo nasa an shigo dasu." "Auw wai har kin gama haɗawa, lallai kinyi kokari, muje na gani." "Toh ai naga lissafin ya chanja ne shiyasa kawai na gama komai." "Kin kyauta kuwa." Kallon kayan Hajiya Mero tayi, haushi ne ya turnik'e ta ganin uban kayan, take ranta yayi mugun ɓaci, kokari tayi ta danne ta hau bud'e kayan, da tasan abin zai juya daga kan Rauda da bata sa ta hado wannan uban kayan ba, ranta be gama baci ba sai data bude kit din da aka zuba sarkoki, d'ago wata dank'areriyar sarkar gold tayi, kadan ya rage ta suɓuce a hannun ta tayi saurin taro ta, kallon Nabila tayi tace "Amma wannan sarkar batayi girma ba kuwa?" "Ah haba batayi ba, komai yadda kikayi list haka aka zuba, sauran jewelries din ma duk Dazz ne duba ki gani." Yawun bakin ciki ta hadeyi da k'yar tana zare ido kamar akuya a dakin gari, rufe kit din tayi kawai dan in ta ci-gaba da kalla zuciyar ta zata iya bugawa. Akwatin night wear ta bud'e Arkel ya sake gyara tsaiwar sa sosai yadda zai hango komai, daya bayan daya ta dinga daga su hakan ya saka shi xare ido, sai a lokacin ya Nabila ta tuna dashi "'Laaa wai dama kana nan." da sauri ya juya zai bar falon aiko ta kwashe da dariya "Daka tsaya ka gama gani ai." Ta fada tana sake tuntsurewa da dariya, be kulata ba yayi ficewar sa yana danne tashi dariyar dan ba karamin kunya kayan suka bashi ba. Shaf ya manta da shigar jikin sa kawai ya fada mota ya bar gidan, sai da ya hau titi sosai sannan ya tuna, babu damar komawa haka ya dau hanyar gidan yana addu'ar Allah yasa kar suyi kicibis da Abba ko Baba. Ba dan ma ya sanar mata zai dawo ba da bari zai yi ya je gobe, toh ya ga lokaci na tafiya gwara yaje suyi magana idan akwai abinda zata bukata. *** Zaman sa yayi a cikin mota lokacin da ya isa kofar gidan dan be san ta inda zai fara fitowa ba a shigar jikin sa, tunowa yayi da sauri ya ciro wayar sa daga jikin chargy ya lalubo number ta daya dauka a wayar Salim. Kira yayi lokacin tana zaune gaban anty Maryam ta tsare ta da wasu magunguna a gaba, da kyar take sha tana yatsine dalilin da yasa ka ma ta taho gidan anty Maryam ɗin kenan dan ita xata saka ta dole ta sha, kallon wayar ta da take ringing tayi ta ajiye kofin da sauri ta daga dan dama neman abinda zai sa ta ajiye ɗin take "Hello." Tace cikin muryar ta very cool kamar ta miss Xoxo 🙄🤪 "Ina waje." Kawai taji yace,da sauri ta kalli Anty Maryam wadda tayi kamar bata san me take ba. Wayar tabi da kallo har ya kashe, tsaki tayi a hankali kar Anty Maryam taji "Mijinki kika wa tsaki Maryam?" "Bafa tsaki nayi ba." "Kinsan bani da kunne ai." "shine Allah sai yayi ta abu wani iri, wai kawai cewa yayi yana waje fa, toh ni ya zan masa?" "Yayi ɗin, kina da shiri ta wlhi Allah, kamar ba yar jami'a ba, kira shi maza ki bashi address din nan din." Turo baki tayi irin an takura matan nan tayi dialing number tasa, "Ban ganki ba?" Shine abinda yace yana daga wa, harara tayi kamar yana ganin ta kafin tace "Ina gidan Anty Maryam." "Da izinin wa?" "Na'am?" "Nace kin tambaye ni ne? Ko bakiji dazu nace karki sake fita ba." Shiru tayi kawai tana jin ikon Allah, sai da ya gama sababin sa tana jin sa sannan yace "Bani address din." Zatayi magana yayi saurin cewa "Yimin sharing live gps din kawai." "Me fa?" "Yar kauye, shiga whatspp kiyi min sharing location din da kike, zanyi navigating nazo." "Ohhh." "Baki sani ba ko?" "Na sani mana, kawai dai." "Malama don't' lie, just do it na fara gajiya da jira." Turo baki tayi tace "Toh." sannan ta kashe, shiga tayi ta tura masa tana ta mamakin dama amfanin abin kenan, suna nan zaune suna hira da Anty Maryam kawai ya kirata yace gashi a waje, dama ta sauya kayan jikin ta shima saboda Anty Maryam ta matsa ne, mayafi ta dauko mata a cikin kayan ta ganin zata junbula hijabi ta mika mata "Kai Anty Maryam kamar zanje wani biki?" "Baki da hankali wlhi,dalla wuce kin bar mutum a mota." "Ni yanzu kin daina sona." "Na daina ɗin, kije in yaso sai ki shigo dashi falon chan, saura kiki jin magana ta." Kumbure kumbure ta hau yi da haka ta fita, hasken motar sa ne ya haske ta tayi saurin sa hannu ya kare, sai da ya gama kallon ta sannan ya kashe, ja tayi ta tsaya a wajen taki karasa wa ganin shima yaki fitowa, gyara zaman sa yayi kawai yana so yaga iya gudun ruwan ta. Ganin bata da niyyar karasowa yasa shi balle murfin motar ya fito, gaban ta ne ya hau faduwa ganin ya tunkaro ta har ya iso sannan a hankali ta sauke ajiyar zuciya. "Wuce muje." "Ina?" Ta d'ago da sauri ta kalle shi "Sai da ke zanyi." "Mu shiga ciki inji anty Maryam." Kallon kansa yayi, "Kalli shiga ta fa, a haka zan shiga?" Kallon sa tayi daga sama har kasa, tayi saurin dauke kanta a ranta ta furta "Ji wani iskanci." Jin tayi shiru ne yasa shi riko hannun ta, "Kina batan lokaci." Bangaren me zaman banza ya bude mata ta shiga sannan ya koma side din sa ya shigo, sanyi Ac hade da daddadan turaren jikin su ya hadu ya bada wani irin scent me masifar kamshi da dadi, lumshe ido tayi a hankali taji wani irin yanayi na shigar ta, shi din ma hakan ce ta kasance masa yayi ta maza ya daure yace "Me kuke bukata na biki, amma kamu kawai ya isa,bana son wani tarkacen biki." Kasa buɗe baki tayi kawai tayi shiru, dan bata san me zatace ba "Ba zakiyi magana ba?" "Duk abinda Allah ya hore maka yayi, ni in tani ne ma a kyale komai." Kallon ta yayi lokaci na farko data fara birgeshi kenan, ajiyar zuciya ya sauke cikin jin dadin amsar ta ya matso sosai sai jin maganar sa tayi a cikin kunnen sa "A kyale komai kawai a kaiki ko? Are dat desperate to be with me?" "Haka nace maka?" "Toh menene? Nayi karya ne? I can see it a idon ki ai." Da Saurii tasa hannu ta rufe idon nata, sake matsowa yayi sosai, shi kanshi be san me yake damun sa ba kwana biyun nan. Hannu tasa ta dan ture shi yayi baya, gyara zaman sa yayi yana basarwa yace "Zan san me zanyi akai, amma bana son wannan make up din da kuke komawa kamar wasu aljanu, kayan da zaki sa kuma su zama ba transparent ba, su zama masu kauri so samu ki hada da babban mayafi, please karki yi abinda zai hurting dina, Ina da kishi akan duk abinda ya zama mallakina, and komai nawa ina maida shi so important, akwai abubuwa da yawa da zan sanar dake nan gaba, for now wannan ne kawai." "Owk tam." Ta amsa a sanyaye *** Ranar Friday aka yi kamu me kyau a amneef, komai shi ya shirya ya dau nauyi, sosai amarya tayi kyau ta gayyato kawayen ta na buk su Asma'u su Sadiya zango da sauran su, babu wani hauka ko bidia komai anyi shi cikin tsarin addini Islama, ango ne halatta ba sai su Hajiya Mero (da ta zama uwar biki karfi da yaji) da Ya Nabila sai yan uwan Alhajin su. Su Ma'u an so aga ango har gulmar sa tayi wa Sadiya zango ko ta sanshi ta kwatanta mata shi, bata samu ba haka ta hakura da niyyar idan an kai amarya gobe zata tsaya ayi sayan baki dasu.🤪 *** Hafiz na xaune ya hada kai da gwuiwa yana tunanin yadda abubuwan suka zama, babu irin rarrashin da ban baki da inna batayi masa ba sam yaki sauraran ta, har ta fara danasanin aikata abinda ta aikata. Tun dazu ake ta faman kiran sa da wani layi yaki d'agawa, text d'in da ya shigo ya bude "Kazo wajen Sabuwar Kofa zamuyi magana, magana ce akan maryam, ko ka fasa daukar fansar???." Zumbur ya mike ya zura rigar sa, takalmi ya zura ya fice da sauri yana kiran layin _ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU😁._ *ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma *SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano) *KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo) *BURI ƊAYA!* (Mamu gee) *WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull) 👇🏻karku bari ayi babuku *ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu* *za'a tura kudin ta wannan accnt number din* Hafsat kabir umar 0225878823 GT bank Saika tura shaidar biya ga wannan number ta WhatsApp 08030811300 Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din 07067124863 Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya. *Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon Rano🚴🚴🚴 [3/18, 22:25] Hafsat Rano: *SAUYIN K'ADDARA* *19-20* ©*Hafsat Rano* *_ZAFAFA BIYAR na kudi ne idan kana son kowanne daga ciki ka nemi Wannan numbers din_* *08030811300* *07067124863* *_Daurin boye_* _safiyya huguma_ *_Buri daya_* _mamuhgee_ *_Wutsiyar rakumi_* _billyn Abdul_ *_Kai min halacci_* _Miss xoxo_ *_Sauyin kaddara_* _hafsat rano_ *** Daga chan nesa ya hango shi a tsaye ya rufe fuskar sa ruf da glass, k'arasawa yayi wajen, kallon sa asase yayi daga sama har k'asa, sai a lokacin ya lura da ashe rigar ma a baibai ya sakata, "Kaga garin sauri shaf na manta a juye na saka rigar." Ya fad'a cikin borin kunya "Ba case ai, shiga mota muje ko?" Kallon motar Hafiz yayi ya dan yi jim kafin yace "Na zata anan zamuyi maganar ai." "Ba anan bane, Hajiya ce take son ganin ka." "Toh..." "Muje ko?" "muje toh!" Ya fad'a a sanyaye dan sai yaji jikin sa yayi sanyi kuma. Motar suka shiga wadda take rufe ruf baka hango ko na ciki irin dark tint ɗin nan, sanyin ac ne ya bige shi ya lumshe ido yana budewa kafin ya gyara zama sosai yana ayyana wa a ransa dama shine me wannan jibgegiyar mota haka.? Be sake shiga rudani ba sai da aka wangale musu babban gate din gidan a jerin sababbin gidajen dake jere a hadaddiyar unguwar ta jan bulu 3rd gate, sai da Asi ya daidai ta kan motar a harabar gidan dake cike da motoci da mutane kungu-kungu yan biki, kallon Hafiz yayi yace "Ka jirani a nan zan kira Hajiya." "Toh." Fita yayi bayan ya cire kwalbar fuskar sa ya koma gefe yana danna mata kira, tana zaune cikin jama'ar ta yan biki ana shirye shiryen tarbar Amarya duk da ba wani taro akayi ba saboda lafiyar Ummi amma ba laifi gidan ya dan cika saboda dangi musamman yan uwan Alhaji da ke cikin birnin na Kano da kewaye. Kallon wayar tayi ba tare da ta daga ba ta mike tsam sannan ta kalli aziza tace "Duk wanda yazo nema na ina zuwa." Fita tayi cikin shigar alfarma tana tafe tana kallon ko ina na gidan, dakin dake chan gefe ta sake kallo kafin ta karasa wajen motar, kallon Asi tayi tayi masa alama daya bude mata motar, baya ta shiga ya rufo hakan yasa Hafiz saurin juyowa. "Kai ne Hafiz?" Ta fada tana kallon yanayin sa, kunya ce ta kamashi ganin yadda ta tsurawa rigar sa ido, dauke kanta tayi ta amsa gaiswar da yake mata "Basu kyauta maka ba gaskia, naji labarin komai da ya faru da kai, sannan na tausaya maka matuka, dalilin haka ne yasa nake so muyi aiki tare, dan dukkannin mu a bigire daya muke." "Aikin menene?" "Biyan ka zanyi ai, abu na farko zaka fara dawowa gidan nan da zama." "Nan gidan kuma, amma me yasa?" Dan dafa kanta tayi, daga ganin sa talaka ne me uban girman kai, in ba haka ba menene na tsare ta da tambayoyi haka, tunani tayi kafin tace "Aiki zamuyi tare, dole sai kana kusa dani, idan har kana so ka rama abinda Maryam da Arkel sukayi maka, dole sai mun hada karfi." "Idan nace na yafe mata kuma fa?" Da sauri ta kalle shi "Yes... idan nace bana son daukar fansar ba "Zan dinga baka albashi duk wata, zan sa a chanja wa mahaifiyar ka gida.". Kallon ta yayi da sauri, cikin gamsarwa tace "Zaman ka a nan din na dan lokaci ne, idan komai ya kammala zaka koma chan." "Wacece ke?" "Wannan ba matsalar ka bace, anan gidan Maryam zata zauna, anjima za'a kawo ta, idan ka amince da bukata ta ka kira wayar Asi, ina da baki sai na jika." Balle murfin motar tayi ta fita tana hararar motar "Shegen taurin kai, mtsw." "Ka maidashi zai kiraka." Har ya juya tace "Ka kira me gidan da suke haya kace kwana uku ya basu su fitar masa daga gidan sa, ni zan siya in yaso sai ka maida mahaifiyar ka ciki." "Godiya nake Hajjaju." Motar ya shiga ya tada ya bar gidan, tun da suka dau hanya Hafiz yake cikin tunani, har kofar gida ya mai dashi ya ciro dubu biyar ya mika masa, kin karba yayi ya shige gidan yana mamakin yadda akayi ma yasan har gidan nasu. Dariya Asi yayi ya maida kudin sa yaja motar ya bar unguwar yana hasaso abinda yake shirin aikatawa. *** Gaba daya jikin ta ya gama sanyi musamman nasihar da Baba yayi mata sosai akan muhimmanci zaman aure, komai yin sa kawai take ba tare da tana gane wa ba, duk yadda Anty Maryam ke mata nacin ta tashi ta fara shirya wa ganin har anyi magriba tana zaune gashi takwas yayi mata text zai zo ya dauke ta. Da kyar ta tashi ta shiga wanka zuciyar ta na tsananin harbawa kamar zata fado saboda tashi hankalin rabuwa da gida, ko da ta fito daga wankan sai da Anty Maryam ta sata ta sake komawa ta daureye jikin ta da wasu hadin turaren ruwa da ta siya a wajen wata kanwar mijin ta da yake barebari ne su, sosai ruwan yayi mata kamshi da dadi hakan yasa ta ɗan jima a ciki har sai da aka buga mata kofa, tana fitowa ta hau shiryawa a cikin haddadden lace ɗin ta dark Ash da touches na gold dinkin riga da zani, lafiyayyiyar laffaya Anty Maryam ta nada mata tayi kyau kamar ka sace ta ka runtuma da gudu😝 Hannun ta ta riko har dakin umma dake zaune cikin yan uwan ta suna ta shan shafta, ana ganin amarya a ka hau guda hakan ya sake saka zuciyar ta tayi rauni, kuka ta saka wiwi jin wata tsohuwa tana ta tsokanar ta tana Allah sarki zata bar gida. Kowa kuma sai ya hau magana akayi mata cha masu fada nayi masu surutu dai ana tayi, tuni kanta ya fara daukar zafi babu abinda take fuskanta a maganganun nasu, ganin haka ne yasa Anty Maryam ta saka kawarta Asma'u ta fita da ita suka koma chan d'akin suka zauna ana jira ango duk da yace da shi kadai zai zo sai data saka masa kuka sannan ne yace zai duba, ko da aka fadawa Baba yace shi zai zo murna ya hau yi dan dama shi ba wani son bidi'ar yake ba, suna nan zaune Walid ya shigo da gudu yana ihun ga motoci nan sun fara zuwa, wani irin tashin hankali taji ta shiga wanda bata taba tunanin akwai irin sa ba, lamo ta sake yi a saman katifar tana jin kamar zata fita a dari saboda wani irin yanayi na tsoro tsoro daya ziyarce ta a take. Sama sama take jiyo gaishe gaishe a tsakar gidan nasu, tana nan zaune tana jiran tsmammani text ya shigo wayarta "Are You ready?" Kallon sakon tayi, bata san me zata ce masa kuma ba, jin batayi reply bane yasa ya ajiye wayar ya fito harabar gidan yana kallon ko'ina. A hankali ya daga kansa sama yana duba taurarin da suka yi wa saman ado, zuciyar sa ce ta lula chan wasu lokuta shudaddu, runtse idon sa yayi yana hango lokacin da suke wata hira shi da Arab, shekara kwana, yau gashi har sun cika shekara talatin da doriya a duniya, shekaru biyar kenan cif da barin sa gida, be taba tunanin rayuwa tana gudu haka ba, sauke kansa kasa yayi yana jin rauni sosai a kasan ransa, so yake ya tabbatar wa kansa auren da yayi hakan ba zai zama abin magana ba duba da yanayin da mahaifiyar sa ke ciki, yasan za'a yi magana tun da dai mutane ba'a raba su da magana, amma yana ji a ransa hakan shine daidai, shine cikar mutum da darajar sa. Dafa shi yaji anyi ya jiyo da sauri, sakin hannun sa yayi ya koma baya yana jingina da mota "Sun tafi ne?" Ya tambaya yana ciro wayar sa daga wandon rigar sa, "Munyi waya da Anty Nabila tace sun je, amma suna bukatar a karo motocin saboda mutanen da yawa." "Amma nace fa bana son gayya,na fada mata ita ma shine kuma za'a ce a karo mota, i cnt gaskia." "Kayi hakuri dai, kasan sha'anin mata, ayi a gama lafiya shine." Hararar sa yayi "Ka taimaka dai kaga ta sake kira." "Sai ku hada data Alhaji, biyu kawai sun isa ai, kai ka dau wannan sai shi ismo ya dau ta alhajin." "Yauwa babban yaya, sai kayi Arkel Poultry farm." Duka ya kai masa ya goce yana dariya. "Zan kamaki ne." *** Kuka sosai take kamar ranta zai FITA, tana ji tana gani aka fito da ita daga gidan iyayen ta, gidan data taso ta saba yau ta barshi, sabuwar rayuwa da bata saba ba bata san da ita ba zata fara ta da mutane da bata taba sanin su ba iya kar rayuwar ta. Tausayi sosai ta bawa kowa masu raunin zuciyar ciki sai da suka tayata koka wa, a haka aka ɗauki hanyar Arkel Mansion da ita kowa yana kulafucin so zuwa su bawa idon su abinci. Sadiya da Asma'u kowacce ta kame a gaban mota, abinda Zaid da Ismo ke so dama kenan shiyasa suka dage aka karo motar. Lokacin da suka isa tangamemen gidan sai da yawun bakin kowa ya kusa daukewa dan babu wanda ya taba zaton abin ya kai haka tun da ko jere ba'a zo anyi ba dan yace musu ba'a bukatar komai, duk da haka sai da Alhaji Faruku ya bata kayan da yayi mata a take tace ta bar wa umma aka zuba mata ita ma dakin ta ya fito fes kamar na sabuwar amaya. Hakan kuwa ba karamin bata wa Hajiya Mama rai yayi ba, Rauda kuwa ko a jikin ta sun sake hadewa da saurayin ta Aseem dan dama fada sukayi a lokacin da maganar Arkel ta fito. Duk suna zazzaune a falon aka shigo da amarya, da kafar dama ta shigo bakin ta dauke da addu'a haka aka hau gaishe gaishe tsakanin ahlin biyu. Bayan doguwar gaisuwa da yan al'adu na malam bahaushe suka damka musu amarya, kukan ta ne ya karu har tana kokarin shidewa, damƙe hannun Anty Maryam tayi da suka mimmike, kallon su Hajiya Mero tayi cikin kasaita tace "Ku rakata saman kawai naga kamar akwai masu son ganin dakin Amarya." Shiru sukayi dukkan su dan sun gano magana ta gasa musu,babu wanda ya bi ta kanta suka haura saman suka dangana ta da hadadden shiryeyyen dakin ta daya sha lafiyayyen zanen gado fari kal da wasu jajayen fulawowi masu masifar kyau da kawa. Tsayawa Bayyana haduwa ko tsaurwar da dakin yayi ma bata baki ne, a gefen gadon ta zauna tana jin su suna ta santi da yabawa, Asma'u dai ta rasa bakin magana dan gaba daya gidan ya tafi da zuciyar ta, sai da Sadiya zango ta dungure ta sannan tayi saurin rufe bakin ta dan har wani kuda yana neman fadawa. (Amma fa babu kuda a wannan hadadden gidan sai dai in ta abinta tazo a mayafi)😂😂 Sorry kawar zango😝 Assalamu alaikum dearies Yan uwa masu kamshin apple Nasan dai kuna ta jira kunce wannan ina ta makale Kamar yadda wasu suka sani dai wlhi ido ne ya saka ni gaba, babu yadda na iya dan a halin yanzu ma gobe asubanci zanyi naje naga likitan ido, kar kuyi tunanin ko wai da chan Ina da matsalar idon, haka nan wlhi dalilin ZAFAFA biyar ido ya samu matsala. Nasan zakuyi mun uzuri saboda dai ido babbar kadara ce kuma ba abin wasa bane Nagode muke da kauna in Sha Aallah zaku samu Sauyin Kaddara fiye da yadda kuka yi zato _ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU😁._ *ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma *SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano) *KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo) *BURI ƊAYA!* (Mamu gee) *WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull) 👇🏻karku bari ayi babuku *ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu* *za'a tura kudin ta wannan accnt number din* Hafsat kabir umar 0225878823 GT bank Saika tura shaidar biya ga wannan number ta WhatsApp 08030811300 Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din 07067124863 Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya. *Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon Rano🚴🚴🚴 [3/18, 22:25] Hafsat Rano: *SAUYIN K'ADDARA* *21* ©*Hafsat Rano* *_ZAFAFA BIYAR na kudi ne idan kana son kowanne daga ciki ka nemi Wannan numbers din_* *08030811300* *07067124863* *_Daurin boye_* _safiyya huguma_ *_Buri daya_* _mamuhgee_ *_Wutsiyar rakumi_* _billyn Abdul_ *_Kai min halacci_* _Miss xoxo_ *_Sauyin kaddara_* _Hafsat rano_ *** A hankali ta dinga rage kukan da take bayan tafiyar kowa, shiru saman kamar babu wata halitta a ciki, dan bude fuskar ta tayi ta kalli dakin, da ido take bin komai   kafin ta dire kallon ta akan jerin sabbin akwatunan dake zube a chan wani d'an karamin corridor, ba kad'an ba suka yi mata kyau, shiru tayi tana nazarin yadda abubuwan suka sauya baki daya. Kwance yake a kan resting chair a dan karamin dakin da ya mayar study room din sa, yana jin hayaniyar jama'ar kadan kadan har ya daina ji baki daya, tashi yayi ya fito idon sa akan dakin nata ya sauka kasa. Hajiya Mero da jama'ar ta wanda sukayi saura na zaune a falon, dauke kai yayi ya wuce bangaren Alhajin yana tunanin samun sa ko akasin haka. Da kallo dukka suka bishi kafin Aziza ta kalli Hajiya Mero tace "Yaron nan fa akwai girman kai, ji yadda ya ɗebe mu yi watsar ko yar gaisuwa babu." "Haka yake ai,barni dashi." "Gwara dai kiyi maganin sa tun wuri, in ba haka ba duk ranar da komai ya fito a yadda yake jin kansan nan ba zai miki da dadi ba." Dan shiru tayi kadan sannan tace "Ba ma za'a kai nan ba." *** Da kallo Alhaji ya bishi har ya karaso cikin dakin, a kasa ya zauna ya tankwashe ƙafafuwan sa kamar me shirin daukar karatu, yau ce rana ta farko shekara biyar baya da har hakan ta shiga tsakanin su da mahaifin sa, tun bayan abinda ya faru ya dauke shi ya ajiye shi a gefe a tunanin sa baya son ummi ne kuma tun da ta hadu da lalunar nan, tun daga lokacin ya cire idon shi akan duk wani abu na Alhajin ya dage ya gina kansa domin mahaifiyar sa . Tsawon wannan lokacin be san halin da take ciki ba, babu ruwan sa da maganin ta, hakan ne ya sake tunzura Arkel ya fita daga sabgar shi. "Ango ne da kansa." Alhajin ya fada cikin son tabbatar da hakan, dariyar yak'e kawai yayi ya dubi mahaifin nasa yace "Alfarma nazo nema a wajen ka, ba dan na isa ba, sai dan matsayin ka na mahaifi a wajena, zuciya ta kasa nutsuwa da komai da yake faruwa, ba ina neman alfarmar ka dawo da ita kamar da ba, sai dai ina neman alfarmar ka taso muji ka ganta." "Arkel..." Ya kira sunan sa cikin faduwar gaba "Ka daure dan girman Allah, yau ne rana ta farko dana nemi hakan, ka sani ba zan iya aiwatar da komai da nake so nayi ba face sai da sa albarkar ku ku biyu, xan so ace kune gaba da zaku sani a kan hanya daidai duba da irin rayuwar da zan shiga a yanzu." "Hakan shine kawai bukatar ka?" Daga masa kai yayi kawai, "Je ka ka kira matar taka, mu hadu a dakin." Da sauri ya kalle shi dan beyi tunanin hakan ba, fita yayi kamar zai tashi sama saboda sauri ya haura saman, sa'a daya yaci duk yan falon sun tashi babu kowa. Murd'a kofar yayi tayi saurin d'age mayafin ta sama zuciyar ta ta hau dukan uku uku, tsaye yayi a bakin kofar ya kasa shiga, kallon ta yake yana jin wani abu me kama da tsoro yana kokarin dakusar dashi, cikin takun sa na kasaita ya taka har gaban gadon, batayi aune ba sai ji tayi ya riko hannun ta, da sauri ta zame hannun jin wani irin abu me kama da mayan karfe ya bigi hannun nata. Hannu yasa ya kama kafad'ar ta ya miƙar da ita tsaye, mayafin ya gyara mata sosai yadda fuskar ta zata rufe ruf sannan ya matsa daf da kunnen cikin wata irin murya yace "Calm down, ba abinda zan miki, matsoraciya." Kasa tayi da kanta, hannun nata ya saka cikin nasa suka shiga takawa a hankali har suka bar dakin, ita dai tana cikin mayafi tana kallon ikon Allah. Sai da suka zo step ɗin karshe sannan ya dan sa hannu ya janye mata mayafin ya saki hannun ta yana matsawa dan nesa da ita A tsakiyar falon suka tarar da shi ya makale hannun sa ta bayan sa yana Safa da marwa, yana jin motsi ya juyo da sauri, tun dazu ya fito sai dai ya kasa karasawa dakin, da yayi yunkuri sai yaji ya kasa, hakan yasa ya tsaya a falon yana ta zagaye chan kasan zuciyar sa na son ganin ta sai dai wani abu ya danne hakan har ya kan ji kamar zai bar numfashi daga lokacin da ya shiga cikin dakin. "Ga Alhaji ki gaishe shi." Ya rada mata a kunne Da sauri tayi kasa cike da wata masifaffiyar kunya tace "Ina wuni Abba?" "An wuni lafiya? Ya bakunta?" Bata iya amsawa ba, bude kofar Arkel yayi ya nuna mata ciki da hannu. Shiga tayi ya mai da kallon sa wajen Alhaji, da kyar ya d'ago ƙafafuwan sa ya isa kofar, a bude kofar take babu wani makari hakan ya bashi damar hango ta a kwance sambal kamar gawa, da sauri ya kalli Arkel da shima shi yake kallo, kafar sa daya ya saka a cikin dakin yayi saurin ja baya "Ba zan iya ba Muhammad." Ya fada yana juyawa da sauri. "Ba zan iya ba?!" Ya maimaita a ransa, da kallo ya bishi har ya shige dakin sa ya rufo har da saka key. Duk abinda ke faruwa tana kallon su, da sauri ta juya ganin ya kalle ta, a take idanun sa suka kada sukayi ja sosai, shiga dakin yayi ya maida kofar ya rufe. A gaban gadon ya tsaya yana, idon ta a bude tana kallon sa, fuskar ta a sake alamar tana cikin farin ciki. Samun kansa yayi da sakin fuskar sa "Matso nan." Ya kalli Maryam, taso wa tayi ta dawo gaban gadon, da hannu ya nuna mata wajen zama. "Umma?" Ta tambaya tana kallon shi, daga kansa yayi sama alamar eh, da saurin ta sake kallon ta, tausayi ne ya kamata ta kalle shi idon ta na cicciko wa. "Please don't." Ya fada yana zama a daf da ita, duk abin nan ummin na kallon su, so take tayi magana babu halin yi, kamo hannun ta yayi ya saka cikin nasa sannan ya kamo na ummin ya rike a dayan "Wannan ita ce mahaifiya ta." "Shekara biyar kenan tana a wannan yanayin, babu in da bamu buga ba dan neman mata magani, amma Allah be sa mun dace ba, ni namiji ne sannan akwai abubuwa da yawa a kaina,  dole tana bukata ta a ko da yaushe, ina neman alfarmar da ki tayani kula da ita dan girman Allah, wannan shine babban dalili na na yin auren nan..." Dan dakatawa yayi sannan yace "Ina da son kai ko? Daga zuwan ki na dora miki babban nauyi akan ki ko?" Girgiza kai tayi da sauri cikin raunin murya tace "Nima mahaifiya tace ai." "Nagode sosai, in Sha Allah zaki same ni me sauke dukkan nauyin da Allah ya dora min." Shiru tayi tana tunanin matsalar, shima sai yayi shiru kawai be sake cewa komai ba tunani yake kamar yayi wuri da ya sanar da ita, kar ta ga kuma kamar dama amfanin ta kenan, amma ya xai yi? Bashi da zabi da ya fi hakan, tun da dama ai ko su Ya Nabila da suke maganar yayi aure yayi aure ai dama dan ummin ne. *** Babu wanda yayi wa dan uwan sa magana har suka dangana da dakin su, shine a gaba tana bin sa a baya, saman gadon ya haye da dukkan jikin sa ya saka fillo a kasan kansa ya kwanta rigingine yana kallon sama, ja tayi ta tsaya tana tunanin in da zata zauna, dan cire kansa yayi ya kalle ta,hannu yasa yayi mata alamar tazo, ba musu ta karasa tana dan hada hanya saboda yadda idanun sa ke yawo a kanta yasa taji tafiyar na harhade mata, tana zama ya mike da sauri yana dafe kai yace "Ina zuwa!" Fita yayi tabi bayan sa da kallo,jim kadan sai gashi ya dawo dauke da ledeji manya guda uku, zube su yayi a kasan gadon ya kalleta "Ga kayan ki nan in ji kamal." A kunyace ta jawo ta bubbuda, roasted chicken da wani haddin veggies a gefe leda daya,dayar ledar kuwa soft drinks ne da fresh milk sai dangin su fruits a dayar ledar, rufe wa tayi ta kurawa kasa ido dan bata san ya zatayi da shi ba. Yana nan kwance yaji shiru bata fara ci ba, tashi taga yayi ya fita, plate da cups ya shigo dashi ya buɗe ledojin ya zuba mata ya tura gaban ta, "Sako malama." Marairaice fuska yayi tace "Na koshi." "Kika isa ma, sauko nace." Kallon sa tayi "Stop looking at me, sauko nace " Saukowa tayi ta zauna ya nuna mata hannun ta, kadan kadan ta shiga ci yana kallon ta, gashi ya tsare wajen gaba daya duk sai taji ta kasa sakewa musamman idan ta daga kanta taga yana kallon ta, da sauri take saukewa saboda yadda idon sa ke mata. Tun tana ci har taji ta fara koshi amma duk da haka ya ki barin ta ta tashi da tayi yunkurin zare hannun ta zai sake hade rai ya kuma kafe ta da ido, sai data ji kamar zai dawo mata ne yasa ta hade hannun ta waje daya tace "Please ka barni haka wallahi na koshi." "Sai kin kara." Zaro ido tayi "Zan dawo dashi Allah idan na kara ci." "Idan kika dawo dashi sai ki kara samun space ɗin xuba wani." "Na shiga uku." Ta fad'a ba tare da ta sani ba ma. Murmushi yayi kawai ya tashi, "Jeki wanke hannun kiyi alwala daga nan." "Eh....?" Tayi kamar bata ji karshen ba "Yes, yadda kika ji. Ina zuwa." Ya juya ya fita Tattare komai tayi tasa a gefe ta bude handbag din ta dake gefen gadon ta ciro pad da sabon pant ta shiga toilet, sai data fara gyara jikin ta sauƙin ta ma ta samu ruwa a heater hakan yayi mata dadi ta shirya tsaf ta fito, be dawo ba har lokacin, hakan yasa tayi saurin buɗe wardrobe d'in ta zura handbag din tata a ciki ta rufe. Da sauri sauri ta haye gadon bayan ta kashe wutar dakin ta kwanta ta rufe idon ta, bata san ya dawo ya sake yi mata maganar alwala bata san yadda zata ce masa tana period ba. Ta na nan kwance taji ya shigo, tsaye yayi a kanta yana nazarin ta, hawa gadon yayi ta sake runtse idon ta, wayar sa ya ciro ya haske ta, idon ta ya gani yana ta rawa alamar barcin karya take, "Kinyi alwalar?" Ya tambaya yana kashe hasken wayar. Kin magana tayi wai ita bata yadda ba irin me baccin nan, be sake magana ba ya sauka, toilet ya shiga ya jima a ciki dan da alama wanka yayi dan taji karar ruwa, fitowa yayi ya kunna hasken dakin, da sauri ta sake runtse idon ta, yana ganin ta murmushi kawai yayi ya hau shirya wa. Light kaya ya saka marasa nauyi saboda garin akwai dan zafi, sallaya ya shimfida yayi shafa'i da wutri yayi yan addu oinsa sannan ya kashe wutar dakin ya kwanta. Babu wanda yayi bacci a cikin su, kowa da abinda yake tunani. Tunanin maganar dazu ne ke mata yawo akai, idan har da gaske abinda ya fada saboda mahaifiyar sa yayi aure, kenan yana nufin baya son ta kenan, ya aure ta ne saboda mahaifiyar sa, tausayin kanta ta fara ji hakan ya saka wa zuciyar ta rauni, ta rasa dalilin da yasa maganar tasa ta yi mata zafi duk kuwa da iya kar gaskiyar sa tasan ya fada amma ta kasa jin hakan a zuciyar ta. Matsowa taji yayi sosai ya dora kansa a saman pillon da take kai, hannu yasa ya matso da ita jikin sa yayi mata rumfa da dukkan hannayen sa. Cikin maganar rada rada yace "Kwana nawa kike yi?" "Na'am??" Ta zaro ido waje, sake matse ta yayi yace "Eh... Naga pack din a dustin din toilet so don't pretend." "Na shiga uku." "Just tell me." Ya fad'a yana saka hannun sa a cikin gashin kanta "Please ka bari." "Naki, fada min or else?" "Dan Allah...." "Kawai ki faɗa min ina jin ki." Gaba daya ta rasa yadda zatayi gashi ya bi ya kanainaye ta da dukkan jikin sa, hannun ta ya kamo ya matsa da d'an karfi tayi kara kadan "Fada min toh." Da sauri tace "10." Dariya yayi sosai bayan ya dan matsa, shiru tayi tana kallon sa a cikin duhun dakin, sai da yayi dariya sosai sannan ya matsowa ya sake nanike mata, mutsu mutsu ta hau yi ya sake rike ta gam, a kunne ya rada mata "Please..." Bata sake motsawa ba tayi lamo tana mamakin shi. 🚴🚴🚴🚴🚴😂 Ba ruwana Yasin Gudnight Malama Maryama.🤭🤫 *** Haji Hafiz abun duniya yayi masa yawa, tun da ta shige daki yake tunanin maganganun da Matar tayi masa, ya rasa yadda zai yi gashi ga dukkan alamu babu abinda ba zata iya aikata wa ba. Bugun kofar gidan ne yasa shi tashi ya fito, malam rabe ne a tsaye ya dafe saman kofar yana kada kafar sa, gaban Hafiz ne ya fad'i. "Malam Rabe..." "Ba wannan ne ya kawo ni ba, kasan dai alƙawarin da kayi akan zaka biya kudin nan, na kara maka wajen wata uku gashi har an doshi wata shida babu labari." "Kayi hakuri dan Allah, wallahi abubuwan ne.." "Ai hakuri ya zama dole, dan zancen da nazo yi maka ma akan cewa ku bar duk kudin da ake bin ku na zaman da kukayi." "Alhamdulillah... Amma." "Dana katse min hanzari mana malam Hafizu, gida dai na riga na sai dashi tuni, a takaice dai wanda suka siya sun ce na sanar daku kwana uku suka baku ku tattara naku ya naku ku bar musu gidan zasu yi gyara." "Innalillah wa inna ilaihi raji'un,haba malam rabe, ya zakayi mana haka? Yanzu dan bamu biya ba shine zaka saida gidan? Naga fa nayi maka alkawarin zan biya, zan biya wallahi." "Ai kuwa bakin alkalami ya riga ya bushe, ni yanzu gida ya bar hannu na, kunci Sa'a ma sun biya ni har kudin da nake bin ku na wata biyar da kwanaki, yanzu sai ku fara shiri." Yana kai wa nan ya juya ya bar kofar gidan. Kamar zai yi ihu haka yaji, zafi goma da ashirin. Gefe ya samu ya zauna kawai hankalin sa a matukar tashe. Asi dake gefe yana kallon komai yayi murmushi, text messages ya tura masa ya juya ya bar unguwar. ****** Wayyo Hafiz kana tsaka me wuya😭😭😭 Nagode da adduoin ku. Ido Alhamdulillah toh😔😔 _ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU😁._ *ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma *SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano) *KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo) *BURI ƊAYA!* (Mamu gee) *WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull) 👇🏻karku bari ayi babuku *ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu* *za'a tura kudin ta wannan accnt number din* Hafsat kabir umar 0225878823 GT bank Saika tura shaidar biya ga wannan number ta WhatsApp 08030811300 Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din 07067124863 Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya. *Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon Rano🚴🚴🚴 [3/18, 22:25] Hafsat Rano: 22*_ZAFAFA BIYAR na kudi ne idan kana son kowanne daga ciki ka nemi Wannan numbers din_* *08030811300* *07067124863* *_Daurin boye_* _safiyya huguma_ *_Buri daya_* _mamuhgee_ *_Wutsiyar rakumi_* _billyn Abdul_ *_Kai min halacci_* _Miss xoxo_ *_Sauyin kaddara_* _hafsat rano_ *** Farkawa yayi jin ana ta kiraye kirayen farko a wasu masallatan, zare jikin sa yayi bayan ya gyara mata kwanciya ya fada toilet, wanka ya fara yi sannan yayi alwala ya fito, ko motsi batayi ba daga in da ya barta, murmushi yayi ya janye mata mayafin da ke jikin ta ya dan kara gudun Ac dakin doguwar rigar sa ya saka ya tada raka'atanul fajr. Bayan ya idar ya dauko Alkur'ani me girma ya shiga karantawa a hankali har aka kira sallah sannan ya tashi ya fita masallaci. Bayan an idar ya hango Alhaji yana fita daga masallacin, ya ganshi amma sai ya ki bari su hadu, girgiza kansa kansa kawai yayi yayi zaman sa a cikin masallacin. Sai da gari ya dan fara haske sannan ya fito ya koma gida, yana shiga gidan aka dauke wuta gashi wani bacci ya ji yana dan fusgarshi, ko dan basu yi bacci da wuri jiya bane oho. Har yayi hanyar sama yaji ba zai iya ba ya koma ya saka aka tada gen. Mamaki ne ya kamashi ganin har lokacin baccin ta take hankali kwance, fita yayi ya rufe mata kofar ya koma dayan dakin ya kwanta. Be dade da fita ba ta farka, ganin baya dakin ne yasa ta tashi da sauri tana duba jikin ta, da sauri ta dauko pad ta shiga toilet. Har ta gama shiryawa bata ji ya dawo dakin ba, zama tayi kawai ta ciro wayar ta kunna, karfe bakwai lokacin da yan mintuna, rasa me zatayi ma tayi kawai sai ta shiga gallery ta hau kallon hotunan bikin, tana cikin kallon ne tazo kan hoton Hafiz, da sauri ta kalli kofar dakin, runtse idon ta tayi tana jin kamar zatayi kuka, hannu kawai tasa ta danna delete bayan ta rufe idon ta. Ji tayi kallon ya fita daga kanta, ajiye wayar tayi ta kwanta rigingine tana tunani. Tunawa tayi da Ummi da halin da take ciki, abun ya tsaya mata sosai, juyi ta hau yi tana tunanin hanyar da ya kamata ta taimaka mata Tana nan kwance har karfe goma babu motsin kowa, zaman ne ya kundure ta gashi datar ta ta kare balle ta hau whatspp ta duba. Tashi tayi ta kwashe kayan jiya da daddare ta fito falon, tsaf tsaf ko ina ga wani sanyayyen kamshi dake tashi, kallon ko'ina tayi tana tunanin kofar Kitchen, a saman Centre table ta ajiye kayan ta bude kofar dake kallon ta, tayi sa'a kuwa nan ne kitchen, kayan ta dauko ta kai Kitchen din, kallon tsaruwa da haduwar Kitchen din ta tsaya yi, kafin ta zuba kayan a cikin sink ta fara wankewa. Sai data gama tas sannan ta zuba ragowar kayan a fridge ta jawo kitchen din ta fito. Kofa taji ana bugawa ta bude, Sadiya ce tsaye da kaya a hannun ta, da fara'ar ta tace. "Ƙaraso mana." Kin karasowa tayi ta ajiye kayan kawai tace "Ina kwana Anty?" "Lafiya lou ya gida.". "Gashi nan inji Hajiya tace na kawo muku." "Toh mun gode." Jera su tayi a saman Centre table din ta bude dayan dakin, yana kwance daga shi sai gajeren wando babu ko yar singlet, da sauri ta ja kofar tana zaro ido. Karar kofar ce ta tashe shi ya bude idon sa, wayar sa ya jawo ya duba time, dan yatsine fuska yayi ya sake mai da kansa, kasa komawa yayi kawai ya tashi, har zai fito a haka ya tuno, komawa yayi ya maida doguwar rigar ya fito. Kallon kayan dake kan table ɗin yayi ya wuce dakin, yana bude kofa ta juyo da sauri, kallon ta yayi da shanyayyun idon sa da sukayi kalar bacci, dauke kanta tayi da sauri, "In shigo?" Yace tana takowa ciki, a gaban ta ya tsaya ya harɗe hannun sa, "Ina kwana?" Ta fada duk ta duburburce, sai daya ja fasali kafin yace "Shine kika tashe ni ko? Are you dat desperate to see me da kika kasa hakuri na tashi?" Marairaice wa tayi "Ba haka bane? Na fa ganki kina leke na." "Allah ba leken ka nake ba, zuwa nayi fa naga..." "Ki ganni ko? Toh gani, what did u have in store for me ?" Ya fad'a yana matsowa. Da sauri taja baya, ya sake matsowa ta sake ja baya taku biyu yayi ya rikota, hannun ta ya mayar baya ya rike su yana mata shu'umin murmushi. In a low voice yace "Lemme just..." Hugging din ta kawai taji yayi from no where, mamaki ta hau yi, shi kuma wannan haka yake ko wani abun ne ya hau kansa? Sai daya dade sannan yayi breaking hug din ya dan matsar da ita baya, "Muje muyi breakfast." Kamar mutum mutumi ya juya ya bar ta a wajen yana murmushi kasa kasa da shi kadai ya san manufar sa. He just don't know me yasa duk sanda yake tare da ita sai yaji wani nishadi na ratsa shi. Haka sukayi breakfast din duk da ta kasa sakewa, shi din ma ba wani ci yayi sosai ba ya matsa kawai yana kallon ta, duk sai taji ta takura da yadda yake kallon nata, wayance wa tayi ta hau kwashe kayan ta shige kitchen ta hau wankewa. Jin shiru bata fito ba yasa ya bita Kitchen din, da sauri ta waigo jin mutum a bayan ta, hannun sa zube a cikin aljihun rigar sa ya babbake kofar ba hanyar da zata bi ta fita gashi sai wani irin kallon kasa kasa yake mata. Ganin ta gama abinda take gashi tana son fita yasa kawai tayi ta maza ta nufo shi yana dan yarfe hannun ta, kin matsawa yayi ta kalle shi ta kalli kofar, bata yi aune ba sai ji tayi kawai ya saka hannu ya jawo ta, babu wani dogon tunani ya hade bakin su waje daya🤭🤫🚴🚴 Ba ruwana ba hannu na bane oo🤣 hannun Teema Gabas ne. Gaba daya Maryam ta rasa in da Arkel ya saka gaba, abubuwan da yake mata gaba daya sun girmi tunanin ta, bata taɓa zaton sa haka ba sai taga ashe ya wuce hakan. Sai wajen sha biyu na rana sannan ya riko hannun ta suka sauko kasan, Hajiya Mero kamar ta shako su har suka ƙaraso falon be saki hannun nata ba. *** Gaba daya abin duniya ya hadu yayi masa yawa, duk yadda yaso ya boye wa inna kasawa yayi, gashi manager ya ishe shi da waya akan lallai ya dawo kan aikin sa dan basa son daga farawa yazo musu da kailula. Sosai ya fira hayyacin sa a yan awannin da basu gaza goma ba, sakonnin da yake karbar duk bayan wani lokaci daga wajen Asi shi ya sake saka shi cikin halin da yake ciki, baya so ya amsa musu tayin su sai dai ya lura ba zasu taba hakura ba idan ba ya amsa ɗin ba. Shigar da yayi gida ya tarar da inna a kwance zazzaɓi ya rufe ta ko abinci ta gagara ci ne yasa ya juya kawai ya fita ba dan yasan in da ya nufa ba. Tafiya kawai yake yi ba tare da ya san in da zai nufa ba, a karshe ya yada zango a kofar wani shago bayan doguwar tafiyar da yasha a kafa ba tare da sanin adadin nisan da yayi ba. Zama kawai yayi daga gefe yana sauraron hirar da suke yi sama sama, hankalin sa ya sake tattara wa jin wani a cikin su yana bada labari me shige da kalar nasa, zumbur ya mike ya bar wajen bayan ya gama jin komai. Tafiyar da yayi ne sosai da zai koma gidan ne yasa ya gane ba karamar tafiya ya sha ba dazu dan dai baya hayyacin sa ne. Sai daya fara tsayawa a shagon layin su ya saka katin hamsin sannan ya kira lambar Asi, bugu daya kuwa ya dauka dan dama jiran kiran nasa yake yi. "Ka gaya wa Hajiya na amince da tayin ta." Wata irin mahaukaciyar dariya Asi yayi cikin jin dadi yace "Ka ceci kanka dan samari, ka shirya anjima zan zo na dauke ka." Be yi magana ba ya kashe kawai yana jin karfin guiwar aikata abinda ya yanke. Da farin ciki ya shiga gidan sabanin yadda ya fita, wanka yayi a gurguje ya shirya ya fito waje yana jiran shi, yana nan zaune ya hango shi yayi parking a dan gaba kadan, tashi yayi ya karasa babu wata magana ya bude mishi motar ya shiga ya ja suka bar unguwar. Yau be shiga cikin gidan ba a waje ya tsaya ya kira wayar ta, ok kawai tace ta ajiye wayar tana murmushi me cike da ma'anoni. Tun da ta fito ya ke kallon ta da yanayin ta, har ta shigo motar ta zauna kafin tace "Muje gidan ko?." "Owk Hajjaju." Wata unguwa me yanayin gidajen masu rangwamen karfi suka nufa babu wanda ya kula shi shima kuma beyi magana ba har suka isa, bude masa kofa Asi yayi bayan ya bude mata ta fita, mukulli yasa ya bude gidan sannan suka shiga gaba daya, karamin gida ne sosai zaman mutum daya da karamin tsakar gida sai rijiya daga chan gefe, toilet da Kitchen sai dakuna guda biyu falle daya daya sai dan karamin falo daga gefe. Daga mukullin tayi ta mika masa, "Gashi nan daga nan zuwa kowanne lokaci zaku iya tattaro kayan ku ku dawo, komai zai fara ne daga ranar da kuka dawo gidan, amma zan so ku dawo a gobe ma saboda yadda nake so komai ya tafi yadda na tsara." Kamar ba zai karba ba sai kuma ya danne zuciyar shi ya karbi mukullayen ya zuba musu ido kamar me son gano wani abu, bubbud'e kofofin duka Asi yana shafa kansa "Duba ka gani, gaskiya kana da sa'a sosai gida haka sukutum, Allah ya taimaki Hajiya." "Wannan kadan daga cikin tanadin dana yi masa kenan idan har ya bani hadin kai, shi yasa zan ajiye takardun gidan a wajena har sai lokacin da ya cika sharuddana daga nan zan damka masa a hannun sa halak malak. "Zan yi kokari na cika duk sharadin da kika saka, sai dai kema ki cika alkawari kuma karki yaudare ni." Kafe shi tayi da kallo tana mamakin kalaman sa, ko dai ya san abinda take shirya wa ne? Amma ta yaya? Bata jin ya sani kawai dai yanayin nasa ne haka. "Karka damu, zan yi maka yadda nace." "Shinkenan, zan koma wajen aiki na gobe zan sanar musu na ajiye aikin, zan dawo washegari daga nan sai komai ya fara, duk abinda za'a yi ayi shi a cikin wata daya nayi gaba." "Hakan yayi, sai su dawo goben tun da dama gobe aka ce ku tashi ko?" Kallon ta yayi tayi saurin waskewa "Dazu naji kamar kace gobe masu gidan da kuke sun ce ku tashi ko? Ko dai kunne na ne?" Ta kalli Asi, da sauri yace "Haka ne Hajjaju." "Shikenan kawai." Yace yana kokarin fita daga gidan, yana fita ta kalli Asi da sauri tana rufe baki "Na kusa nayi banbarma fa." Dariya ya saka "Wallahi Hajiya, Allah dai ya kiyaye kamar be fuskanci komai ma" "Toh Allah yasa dai." Fita sukayi aka jawo gidan, yana tsaye daga gefe sai da suka shiga motar sannan ya shiga, a hanya ya ce su sauke shi ya wuce gida, dubu biyar Hajiya Mero ta mika masa, da zai ki karba sai kuma ya tuno ko kudin kwaso kayan nasu basu dashi shiyasa kawai ya karba beyi ko godiya ba ya wuce kawai. A daren ranar suka gama tattare komai da sassafe kafin gari ya waye suka tattara suka bar gida tun kafin azo ayi musu tijara. Inna na son tambayar sa yadda akayi ya samu gida sai dai ganin yadda yake ta tsare gida yaki bari sam suyi doguwar magana yasa ta share kawai ta bari idan ya zauna sai suyi maganar. Ana gama saka komai a gidan ya dau hanyar Gumel. *** Kuyi hakuri da wannan pls Ko editing banyi ba wlhi. _ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU😁._ *ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma *SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano) *KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo) *BURI ƊAYA!* (Mamu gee) *WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull) 👇🏻karku bari ayi babuku *ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu* *za'a tura kudin ta wannan accnt number din* Hafsat kabir umar 0225878823 GT bank Saika tura shaidar biya ga wannan number ta WhatsApp 08030811300 Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din 07067124863 Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya. *Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon Rano🚴🚴🚴 [3/18, 22:25] Hafsat Rano: *23* S K ©*Hafsat Rano* *_ZAFAFA BIYAR na kudi ne idan kana son kowanne daga ciki ka nemi Wannan numbers din_* *08030811300* *07067124863* *_Daurin boye_* _safiyya huguma_ *_Buri daya_* _mamuhgee_ *_Wutsiyar rakumi_* _billyn Abdul_ *_Kai min halacci_* _Miss xoxo_ *_Sauyin kaddara_* _Hafsat rano_ *** A hankali ta zame hannun ta tana karasawa gaban Hajiya Mero, duk kunyar yadda take kallon ta ya rufe ta. Da sauri ta taro ta tana kokarin zama a kasa "Karki soma zama a kasa sanyin tiles." A kunya ce tace "Ina kwana Hajiya?" "Lafiya lou amarya, ya bakunta?" Kallon Arkel tayi da ya dauke kai yana kallon dakin Ummi "My son an fito kenan, an tashi lafiya?" "Ina kwana?" Yace yana dan zama a kujerar falon, "Lafiya lou ango, babu wata matsala dai ko?" Dan kallon ta yayi kamar zai yi magana sai kuma ya fasa, murmushi tayi kawai tana kallon Maryam "Ki sake fa nan gida ne, ko da yake kwana nawa ne ma?" Ita dai Maryam bata ce komai ba, tasan dai tun asali ba wani alaka ce da ita dasu ɗin ba, kuma tasan harda ita a kara tunzura wutar kiyayyar su ga Hajiya Mama, shiyasa ita sam matar bata sabgar ta amma sai tayi mamakin yadda take ta nan nan da ita yanzu. Toh koma dai meye ita ta sani. Tashi yayi kawai ya fita yana danna kira a wayar sa. Chan suna nan zaune babu me magana a cikin su sai gashi ya dawo. "Taso." Kawai yace yana nufar dakin Ummi, da sauri ta mike dan dama zaman ya ishe ta, hankalin ta kuma na kan dakin tana so ta kara ganin matar, da kallo Hajiya Mero ta bisu baki sake dan bata kawo hakan ba, har suka shige dakin tana kallon su cikin wani yanayi. Zama yayi a gefen gadon nurse din dake ciki tayi sauri gaishe su sannan ta fice. Tana fita hajiya Mero ta Kira ta cikin daki "Ya ake ciki? Akwai wani cigaba?" Dan kallon gefe tayi kafin tace "Hajiya babu komai, allurar nan dai ita nake mata ko yaushe, duk jikin ta fa yayi saba sai ma kinga bayanta." "Yawwa haka nake so, kije kawai yau tun da uban iyayin yana gida gaba daya yau ga dukkan alama." "Shikenan Hajiya, Nagode bari na tafi." "Owk bari kiga." Kudi ta ciro ta mika mata sannan ta tafi, kallon kanta tayi a cikin mudubi tana tuno wani abu da take shirya wa, dariya tayi kawai ta juya ta bar d'akin. *** Wunin ranar Maryam a dakin tayi, taki motsawa ko nan da can tana lura da komai, mamakin abinda zai kwantar da mutum haka take sannan kuma ace duk anyi magani babu? Tana nan zaune duk farkawar da Ummi zatayi akan idon ta take yi, mamaki ne ya kamata ganin hannun ta daya yana motsi a hankali wanda idan har ba ka kula sosai ba ba zaka ga komai ba, da sauri ta mike tana sake kallo da son tabbatar wa, hakan kuwa ne da gaske motsi yayi, kokarin nuna abu take daka chan saman drawer sai dai bata san menene ba, wajen ta kalla sannan ta sake kallon Ummi, idon ta fes akanta ko kiftawa batayi, a hankali ta taka har gaban wajen tana sake kallon komai na kai,magunguna ne birjk akai da allurai kala kala, bata gane me take nufi ba ta cigaba da kallon magungunan daya bayan daya tana karanta jikin kwalin, rubutun da ta gani ne a jikin allurar data dauka a karshe ne ya ta sake tsorata ta ainun, sake karanta wa tayi a karo na biyu, kanta ne ya kulle baki daya, da sauri ta hau bubbud'e drawers din dakin tana binciko wa, katin asibiti ne ya fado ta dauko shi da sauri tana dubawa, duk magungunan da suke jikin katin ba sune a wajen ba, hasalima wadandan magungunan da ta gani basu chanchanci mutum ya sha ko yayi amfani dasu ba, wani irin jiri-jiri taji ya fara daukar ta, kwalla me zafi ta biyo gefen idon ta, a yanzu ta fuskanci komai, ana amfani da shi ana cutar mahaifiyar sa, toh amma ta yaya? Kamar be shiga makaranta ba ko me? Dama ita tun data ga halin da Ummi take ciki sannan ta tuno da Hajiya Mero a matsayin kishiiyar ta sai taji sam hankalin ta ya kasa kwanciya, daren jiya gaba daya da abin ta kwana ta tashi. Tattare komai tayi ta cire dankwalin ta ta zuba su a ciki ta kulle tana goge fuskar ta, fara lekowa tayi taga babu kowa a tayi saurin hayewa saman ta bude dakin ta ta zuba su a cikin wardrobe d'in ta ta rufe sannan ta koma kasan da sauri, murmushi taga ummin tayi hakan ya sake karyar mata da zuciya ta gane lallai akwai wani babban al'amari, abinda ta fuskanta ma shi be masan da wani abu ba, yawancin maza basa fuskantar irin wannan sai ayi ta maganin asibiti a banza. Tana nan zaune tana tunanin mafita kiran sa ya shigo wayar, bin wayar tayi da kallo ta kasa d'agawa har ta katse. Tsaki yaja a hankali ya ajiye wayar ya cigaba da trading(Forex) din da yake, chan ya gaji ya ajiye komai ya kashe computer ya fito, bata san ma yana gidan ba sai ganin shi tayi ya shigo dakin, kallon ta yayi ya kalli wayar dake hannun ta.. "Baki ga kira na ba." Ya tambaya yana kallon ta "Na gani, kafin na daga ne ta zama misscals." "Uhum... Dont lie malama. Ki jirani a saman ina zuwa." Bata ce komai ba ta tashi ta fita,ita wallahi kunya ma yake bata yadda ko kunyar magana da ita bayaji a gaban ummi, ko dan yaga bata da lafiya ne oho." Tana tsaye ya shigo yana nannad'e hannun rigar sa zuwa sama, hannun ta ya kama suka shiga dakin da yake aikin Forex din sa, sauke computer yayi daga kan kujerar ya karasa tattare ragowar kayan ya ajiye su a gefe sannan ya nuna mata wajen zama. Babban album ya d'auko ya dora mata a saman cinyar ta, kallon shi tayi sannan ta kalli album din, Ummi ce rike da yara biyu maza akan kafarta suna dariya da babban cake a gabanta, twins? Ta fad'a a ranta, bude na gaba tayi, yara yan shekara biyar identical twins babu abinda ya raba su a tsaye, haka ta cigaba da kalla cikin tsananin mamaki, sai data kusa kai wa karshe sannan yace "Ba zaki tambaya ba?" Rufe wa tayi ta kalle shi "Twins?" Daga mata kai yayi yace "Yes." Baki bude take kallon shi, bata taɓa tunani ba, kenan irin sa guda biyu ne to ina dayan "Kina mamaki ko? Am the youngest, shine babba." "Yana ina?" Ta fada tana sake bude hoton tana kallo Dage kafad'ar sa yayi kafin yace "I don't know ko yana ina." Shiru tayi da tunanin ko ya rasu ne? Amma kuma ai da sai yace mata ya rasu, bata ce komai ba ta cigaba da kallon hotunan tana admiring nasu. Ji tayi yace "You can ask me kome kike so ki sani, i dnt know why kawai naji ina so nayi sharing abubuwa da ke, feel free to ask komai, banda maganar shi amma." Ajiyar zuciya ta sauke tace "Ummi?" Idon sa ne ya dan kada kadan, be ce komai ba tsawon wani lokaci har ta fara dana sanin tambayar sai kuma taji yace "Komai ya faru ne bayan na tafi anambra saro kaya. Kamar yadda kika gani a pictures din nan mu uku ne a wajen iyayen mu, ni da shi sai Yaya Nabila, it was a nice family saboda yadda muke komai a tare, bani da hayaniya kamar shi and he's more friendly, shine komai na gidan nan, duk wani abu shine akai, banbanci na dashi kenan, he's my only friend Amma shi yana da abokai da yawa, haka muka taso kowa yayi choosing part din sa a University, bayan mun gama karatu dama ni bussiness nake so and anything kiwo, daga nan ne na fara tunanin yadda zan fara, a lokacin shi kuma yana zaune a gida yana jiran aiki tun da shi dama bangaren mass communication yayi." "Bakar rana ita ce ranar da na tafi anambra, tare muka tafi da Kamal wanda yake auren ta jikin hoton nan (yaya Nabila) har tasha ya rako mu sannan ya dawo gida. Sati biyu mukayi a garin muka dawo gida in da nazo na tarar da Ummi a wani irin hali, babu kowa a gidan, abun da ya kara tayar min da hankali shine ban san in da ya nufa ba, bansan ina zan ganshi ba, ko na kirashi bana samun sa, gashi kwata-kwata Ummi ko magana bata iya yi, daga nan muka hau yawon asibitoci bama nan bama chan, lokaci me tsawo muka dauka ana abu daya babu wani sauki, abubuwan suka taru sukayi min yawa gashi Alhaji ya janye hannun sa baya komai, tun daga nan komai nawa ya chanja, na sake jajircewa a komai, bansan komai ba sai nema, tun lokacin zuwa yanzu take a haka, ban kuma sami amsar da nake nema ba har tsawon wannan lokacin." Da wayo tasa hannu ta goge hawayen da taji yana neman zubo mata, wani irin tausayi ne ya kamata, lallai idan ban da shi namiji ne da mace ne da ba zai kawo haka ba ma, sake goge kwallar tayi, gani tayi ya taso ya dawo kusa ta ita, hannu yasa ya jawo ta jikin sa ya rungume ta. Wajen minti biyar babu wanda yayi magana sai ajiyar zuciya da yake saukewa Lokaci zuwa lokaci, kamar me rada tace cikin tararradin amsa da zai bata "Hajiya fa? Tana ina abin ya faru?" Dora kansa yayi a saman bayanta yana kallon kofa yace "A sati biyun da bana nan Alhaji ya aure ta, amma bata tare ba sai bayan wata daya da auren." Shiru tayi bata kuma magana ba, sakin ta yayi ya kwantar da kanshi a jikin kujerar ya jawo ta kusa dashi "Me yasa nake sanar dake komai? Ban taba maganar nan da wani stranger ba." Kallon sa tayi bayan ta janye jikinta daga nashi tace "Nima stranger ce?" Daga mata kai yayi alamar eh, tashi tayi ta koma dayar kujerar ta kauda kanta gefe, bude ido yayi yana kallon ta da mamaki, haushi taji kome? Jin yaki magana tasa ta mike zata bar dakin yayi saurin tashi ya tsai da ita ta hanyar rikota "Ina zaki?" "Zanje daki ne." Ta amsa kai tsaye "Nan fa? Shima ai daki ne." "Uhum." Tace kawai ta sake juya da kanta. "Please ki zauna har a kira sallah, i just need a company." Shiru tayi kawai tana mamaki be masan me yayi mata ba, wai ita ce stranger hadda ce mata eh, aikuwa wallahi sai ta saka shi maimaita kalmar nan wataran. Share wa tayi ta dawo ta zauna tun da be ma lura da fushin da tayi ba kenan, kansa taji ya dora a saman ƙafafuwan ta ya rufe idon sa. Murmushi kawai tayi dan har yanzu mamaki yake bata, tunawa tayi tace "Zan iya samun zam-zam Please.?" "Owk muje mu siyo in anyi sallah." Wayar ta ce tayi kara, Anty Maryam ta gani da sauri ta daga, a shagwabe tace "Anty Maryam...." Daga dayan bangaren Anty Maryam ta saka dariya "Ke fa kina da shiririta, kuka zaki kome?" Dariya tayi kawai "Anty Maryam ina wuni yasu Areef." "Lafiya lou amarya, ya bakun ta?" Da sauri ta kalle shi, ya bude idon sa ya zuba su akanta, turo baki tayi ta kauda kanta gefe. "Shine Babu wanda yazo Anty Maryam." "Shiririta, sai kuma mu debo kafa muzo ko? To sannun ki, kira nayi naji ba matsala dai ko? Kinsan yanayin dai." "Na'am?" "Babu wata matsala dai ko? Kiyi amfani da ruwan dumi dai kinji?" Kasa magana tayi ta hau in-i nah har Anty Maryam ɗin ta d'ago ta, da sauri tace "Ki gaishe shi toh, zamuyi waya dai." Kafin ma ta kashe ita ta kashe da sauri, dariya yayi sosai dan ya kusa gano in da maganar ta nufa tun da yana jiyo maganar Anty Maryam ɗin sama sama. Yunkurawa tayi zata tashi ya sake matseta yana dariya. Haka suka zauna har aka kira sallar magriba sannan ya tafi masallaci ita kuma ta koma dakin ta dan shirya wa tun da yace zasu je siyo zam-zam idan anyi sallah. Yana dawowa bayan an kunna gen ya shigo ya chanja kayansa, kofa ya bude mata ta baya suka fita dan bata ma san da kofar ba sai lokacin. *** Satin ta daya a gidan tuni ta fara bawa Ummi ruwan zam-zam da take karanta fatiha kafa bakwai a ciki, (zaku iya gwadawa domin ita suratul fatiha waraka ce ga dukkanin wata cuta, a karanta kafa Bakwai a cikin ruwa amma ba wai tofi za'a yi a ciki ba,abinda ake so karatun ya shiga cikin ruwan) Ba karamin kona ran Hajiya Mero haka ke yi ba, bata so dai tayi saurin fito da komai shi yasa take bin komai a sannu. Tun ranar data kwashe maganin nan da alluran ta kafa ta tsare duk sanda nurse din tazo bata barin ta ita kadai a dakin, bata sanar wa da Arkel komai ba dan ta lura kamar ma be san komai ba shiyasa kawai take komai kai tsaye tana dagewa sosai wajen azkar din safiya da maraice dan shine babban makari ga duk wani abin ki. Tana zaune a dakin ta kunna karatun Alkur'ani a wayarta yanayi a hankali, nurse ɗin ta shigo, gaisawa sukayi sama-sama ta tsaya kawai ba tare da tayi komai ba, saboda dama a ka'ida goge wa ummin jiki take sai da bata magunguna da allurai shine aikinta, yanzu kuwa kafin tazo ma Maryam tayi komai shi yasa idan tazo sai taga babu abinda zatayi. Ta dade a tsaye Maryam na kallon ta ta gefe, sannan ta juya ta fita, da sauri ta rufe alkur-anin ta bi bayan ta, dakin Hajiya Mero ta shiga tayi saurin zuwa ta tsaya a kofar. "Yau ma wai?" Taji ta tambaya "Eh wallahi, tana dakin karatu ma take, duk ta kankane komai." "Gaskiya zanci uban yarinyar nan wallahi Allah, shegiya zata bata min aiki." "Ni wallahi tsoro ma take bani, kamar tasan komai da mukeyi, kinga fa ita ta tattare duk alluran nan babu ko daya yanzu.". "Kan bala'in chan,alluaran da na sa kudi masu yawa na siyo su, tun yaushe ba'a yi mata ba kenan?" Ta fada a rude "Wajen sati kenan walalhi, na kasa fada miki ni kiyi hakuri " Da sauri ta mike "Har sati?" Amma wallahi kin cuce ni, baki gaya min ba amma, kai amma wallahi ban taba ganin tsinanniya irin ki ba, Allah ya isa ban yafe ba wallahi, kuma sai kin bar gidan nan." Magiya ta hau yi ta hambare ta tayo waje, turus tayi ganin Maryam a tsaye, kallon kallo sukayi wa juna tayi saurin daidai ta kanta "Ke kuma fa?" Ta fada a fusace Kin magana tayi ta juya zata bar wajen tayi saurin riko ta "Uban me kike a nan? Kinji wani abu ne?" Girgiza kanta tayi tace "Banji komai ba, dama so nake na tambaya me za'a dafa da daddare?" Tsaki taja ta juya ta koma dakin. Da kyar ta daga kafarta ta bar wajen saboda yadda ta sake tsorata da lamarin hajiya Meron. Kasa barin dakin Ummin tayi har zuwa lokacin da Arkel ya dawo, rike hannun sa tayi a karo na farko ta jashi har dakin "Ka zauna zanje na dawo dan Allah." Zama yayi cikin mamakin dalilin hakan, sharewa yayi ya dauki alkur-anin dake gefen gadon ya fara karantawa. Sama ta koma bayan ta kawo masa abincin sa dakin,wanka ta shiga a gurguje kafin a kira sallah saboda ta sami tsarki, bata wani tsaya k'alk'ale k'alk'ale ba ta saka gown kawai ta shinfida sallaya tayi sallar la'asar, tana idarwa ta sauko. Da kallo ya bita har ta dauko ruwan zam-zam din ta dan karkata ta zuba mata a baki. Be yi magana ba yana ta kallon ta har ta gama komai ta tofa mata addu'o i. Tashi yayi ya shiga toilel ɗin dakin yayi alwala, yana fitowa yaga zata bar dakin yayi saurin cewa "Ina zaki?" "Sallah zanyi." Ta bashi amsa kai tsaye ba tare da tunanin komai ba. Wata irin shu'umar dariya yayi irin ta gfen bakin nan ya shafi saman kansa. Woow ango Arqe😂 *** Yau duk bamu ji ina Malam Hafizu ya shiga ba, gobe gobe zai duro wasan ya fara in Sha Allah. Nagode sosai da jimirin jira,ido Alhamdulillah ina samun sauki Nagode da adduoin ku. Allah ya saka da Alkhairi. _ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU😁._ *ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma *SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano) *KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo) *BURI ƊAYA!* (Mamu gee) *WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull) 👇🏻karku bari ayi babuku *ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu* *za'a tura kudin ta wannan accnt number din* Hafsat kabir umar 0225878823 GT bank Saika tura shaidar biya ga wannan number ta WhatsApp 08030811300 Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din 07067124863 Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya. *Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon Rano🚴🚴🚴 *24* S K ©*Hafsat Rano* *_ZAFAFA BIYAR na kudi ne idan kana son kowanne daga ciki ka nemi Wannan numbers din_* *08030811300* *07067124863* *_Daurin boye_* _safiyya huguma_ *_Buri daya_* _mamuhgee_ *_Wutsiyar rakumi_* _billyn Abdul_ *_Kai min halacci_* _Miss xoxo_ *_Sauyin kaddara_* _Hafsat rano_ *** Kasa zama tayi saboda yadda abin ya dake ta, bata taɓa tunanin Maryam ɗin ta kai haka ba, kenan magungunan data ɗebe ta san komai akan su shiyasa ma ta dauke din, lallai ta debo ruwan dafa kanta, haukan datayi daya ne ga dukkan alama bata sanar wa uban gayyar ba, hakan ya saka mata nutsuwa har ta fara ƙoƙarin lalubo wayar ta. Ta riga ta shirya komai sanin cewa babu wani abu daya shiga tsakanin su, tana lura da duk wani takunsu shiyasa ma hankalin ta ya kwanta. Kira tayi ana d'agawa tace "Ka shirya komai yadda ya dace? Shigar sauri zamuyi mata kafin ta shige mu." Daga chan dayan bangaren yace "Na hada komai jira nake gobe tayi, babu yadda za'ai ya ƙaryata report ɗin dan na gasken ne." "Yawwa hakan nake so, sai dai fa a daren nan nake so a aiwatar da komai, ka sami mutumin ka bashi dubu ashirin sai yazo kawai, ba zan iya jira har gobe ba kar tayi min illah." "Shikenan Hajjaju. An gama sai kinji bayani." Ajiye wayar tayi ta cije Lebanta kafin ta bushe da dariya "Yanzu wasan zai fara, 1,2,3 bom." Kofar aka buga ta kalla a fusace kafin tace "Waye." Zainab ce ta shigo hannun ta rataye da handbag "Ke kuma? Kin dawo kenan." Dauke kanta tayi, "Mummy baki so na dawo bane?" "Da ni na aike ki?" Girgiza kai tayi "Atoh, kinga ba ci ai kin dawo ko? Sai ki wuce dakin ki." Tashi tayi ta fita tana kallon saman zuciyar ta duk babu dadi. *** Har wajen goma suna zaune a dakin dan har sallar Isha'i a dakin sukayi ta, jefi jefi suke hada ido duk da aikin da yake a cikin na'ura me k'wak'walwa, a hankali yaga ta soma gyangyadi har tana dan yin baya kamar zata fadi, murmushi yayi ya kalli gefen sa, dan karamin fillo ya dauka ya wurga mata, firgigit tayi tana zaro ido "Bacci?" Ya tambaya yana lankwasa hannun sa suka bada sauti me dan karfi "Ba bacci nake ba." A yadda ta amsa muryar ta kadai ta nuna baccin take amma saboda musu na me bacci sai tace ba bacci take ba, dariya yayi ya hau tattare kayan nasa, gyara Ummi ta hau yi sannan ta tofa mata addu'a yana tsaye ya makala computer a tsakankanin hannun sa yana kallon ta. Sai da ta gama ta gyara mata komai sannan ta dauki wayar ta. A jere suka fito ya zura mata ido kawai yana aikin kallon ta, dauke kai tayi da suka zo zasu hau step sai ya ja ya tsaya yana kallon ta, tsaya wa tayi ita ma dan bata son tayi gaba yana bayan ta duk sai taji ta kasa tafiyar har wani harhaddewa kafarta keyi. "Muje ko?" Yace yana gyara tsaiwar sa, "Dan Allah ka fara tafiya." Make kafardar sa yayi yana kunce dariyar sa, kamar ta fasa ihu haka ta hau takawa a hankali kamar me koyon tafiya, a baya yake binta yana kallon duk wani takunta har suka dangana da dakin kwanan su, maimakon ya shiga sai ya zarce dayan dakin ya ajiye kayan. Tsaye yayi rike da kugu yana kallon kayan sa da ya ware yake sawa a irin wannan lokacin na zafi, be fiya zama da kaya ba ma yafi zama daga shi sai boxer saboda yadda yake da jin zafi kamar maciji, sai daya dade yana kallon kayan kafin ya zaro wasu fararen riga da wando rigar armless wando kuwa babba ne ya bude sosai ta wajen kafar, kaya ne masu matukar kyau gasu unique dan shi a rayuwar sa yana son komai nasa ya zama ya fita daban shi yasa a komai sai ya tsaya ya dubo abinda yasan zai yi masa. Wanka ya fara yi yana yi yana ayyana komai a ransa, ya sani ba wai auren soyayya sukayi ba sai dai akwai wani al'amari game da ita da yake fusgarshi zuwa gare ta,har ya watsa ruwan ya fito tana cigaba da tunanin, a kasalance ya shirya tsaf ya saka haɗaɗɗun turarukan sa masu sanyin kamshi sannan ya rufo dakin ya fito. Tana tsaye bayan ta gama karanta text d'in Anty Maryam taji ya shigo, da sauri ta kashe wayar ta juyo tana kallon sa, kallon ta yake shima har ya tako ya iso gaban ta. Zagaye ta yayi ya wuce toilet ba tare da yayi magana ba, da kallo ta bishi har ya shige yana mamakin kayan jikin sa, wandon ne ya bata dariya har taso yi sai kuma taga ya fito. "Kinyi sallah?" Taji ya wurgo mata tambayar, daga masa kai tayi ya dan yi murmushi sannan yace "Owk yi alwala sai muyi nafila." "Owk tam." Har ta juya sai kuma yace "Madam..." Dan juyo wa tayi, "In zai yiwu ki fara watsa ruwa akwai dan zafi a garin." Fita yayi ya rufo mata kofar dan dauko wayar sa, yana zuwa yaga an masa misscals da wata bakuwa number, sharewa yayi zai kashe wayar kenan kiran ya sake shigowa, kallon lokaci yayi ya sake kallon kiran, d'agawa yayi ya makala a kunnen sa. Doguwar riga ya saka a saman kayan nasa ya fito harabar gidan, daga chan kofar gate ya hango su tsaye su uku, buzu ne sai me gadi da mutumin dake tsaye, har ya karasa wajen su be daina mamakin dalilin kiran nasa ba. Ganin shi yasa buzu saurin cewa "Gashi nan oga, tun dazu muke yi dashi ya nace lallai sai ya ganka, nace ma ya bari zuwa safiya yaki sam, gashi nan bamu san meke tafe dashi ba." 'Dan kallon mutumin yayi kafin ya juya yana cewa "Dan ƙaraso ciki." Daga nesa suka tsaya ya harɗe hannun sa yana kallon shi, "Malam lafiya kuwa? A wannan daren haka." Dan kallon gefe yayi zuciyar sa na dukan uku uku yace "Abu ne muhimmi ya kawo ni, ba zan iya bari a kwana ba dan bani ne rike da raina ba." "Ina jinka." Ya fada yana kallon sa "Game da matar ka ne, uhum Maryama, toh dama-dama..." "Dama me?" Ya katse shi yana tattara dukkan hankalin sa. Ajiya zuciya mutumin yayi kamar zaiyi kuka yace "Dana likita ne, a halin yanzu Allah yayi masa rasuwa jiya, kafin ya mutu ya sanar dani wani babban al'amari da yake ganin ba zai iya mutuwa ba tare da ya sanar maka ba, yayi kokarin ya neme ka sai kuma ciwo daya kwantar dashi yayi masa kwaf daya toh..." "Malam!" Ya fada à zafafe "Ka faɗa min abinda ya kawo ka karka batan lokaci." Share kwallar data taru a idon sa mutumin yayi ya ciro takarda a aljihun sa ya mika masa "Ka karanta wannan duk bayanin komai yana ciki, amma dan Allah kayi hakuri da abinda zaka gani." Da sauri ya warce takardar ya hau budewa, "Dakata! Dan girman Allah karka bude anan ka shiga ciki saboda abinda zaka gani ba abu ne me sauki ba." Banza Arkel yayi masa ya bude, ganin haka yasa mutumin juyawa zai bar gidan da sauri ya riko shi "Tsaye nace!" Ya fada yana karanta abinda yake rubuce a jikin takadar, hannun sa ne ya fara karkarwa idon sa suka fito waje, a take yaji jiri na neman diban sa, kokarin sake karanta saman yake yana son tabbatarwa kansa ba gaskiya bane. Tuni idon sa ya rine zuwa tsananin ja, hankalin mutumin ne yayi mugun tashi ganin yadda lokaci daya ya koma, a matukar bacin rai ya hau kwalawa su buzu kira. Da gudu suka ƙaraso ya nuna musu mutumin da hannun sa "Ku saka shi a dakin chan zuwa gobe zan dawo kansa." Nan fa ake yin ta, kamar zai tashi sama ya shige ciki ko ishasshen ganin hanya baya yi, Hajiya mero dake makale ta kalli shi lokacin da yake hayewa sama, murmushi tayi ta shige dakin ta tana tafa hannu, magana ta hau yi tana dariya. "Yarinya in kin san wata baki san wata ba wallahi, ba dai ki zauna a gidan nan ba, tsawon shekarun dana dauka ina gina komai baki isa ki rushe ba. Shegiya dangin Mayu, Allah yasa ma ya lakada mata duka ya karya shegiya." ** A yadda ya budo kofar ne yasa ta tsorata, tsaye take a gaban mirror tana taje kanta, dogon hijabi ne a jikin ta ta sauke shi a gafadar ta, towel ne kawai a ciki dan bata jima da fitowa daga wankan ba. Kallon rinannun idon sa take da yayi dishi-dishi ga shi yayi wani irin ja ya taru da jini a ciki, tsoro ne ya kamata ta fara ja da baya da baya har ya karaso daf da ita, takardar ya kalla sannan ya nufi wardrobe d'in ta, daya bayan daya ya hau watsi da kayan ciki zuciyar sa na matuƙar harbawa yana tunanin abinda zai gani. A hankali idon sa ya sauka akan takardar dake ninke a kasan jakar ta, da kyar ya mike hannun sa ya dauko yana jin tashin hankalin sa na daduwa da tunanin abinda zai gani. A hankali ya warware ta yana runtse idon sa, babu abinda ya raba ta da takardar dake rike a hannun sa ta saman, da sauri ya rike kofar wardrobe d'in Jin Kamar zai fad'i *Pregnancy test report. Shine a saman takardar farko sai sunan ta dake rubuce baro baro a saman da babban baki, Sai kuma takardar sa hannu ta *abortion* a kasan ta. "Innalillah wa inna ilaihi raji'un." Kawai yake maimaita wa dan ya rasa abinda zai ce,da sauri ta matso kusa dashi tana kokarin riko shi ganin kamar zai fad'i, hannu yasa ya bige hannun ta ya juya da sauri ya bar dakin. Kanta ne ya daure, da sauri ta hau tattare kayan daya zubar, ajiyar zuciya ta sauke ganin be riga ya xubo dana alluran ba, tana gama kwashe wa sai ta tsaya kuma ta kasa komai tana tunanin bin shi zatayi taji menene ko yaya? Har ta zauna sai kuma ta kasa nutsuwa, gashi ko kaya ta kasa sawa saboda tunanin abinda yake faruwa. Tashi tayi kawai ya yanke shawarar bin shi taji damuwar sa kar yaje ya aikata wani abin. Kama handle din kofar tayi ta jita a rufe ta ciki, komawa tayi ta zauna a falon tana kallon dakin zuciyar ta duk babu dadi. Tun tana zaune tana tunanin zai bude har ta fara bacci a wajen. Sai chan cikin dare ya fito, yadda ya ganta tana bacci a zaune ne yasa ya tsaya akanta yana kallon ta,zafi ya saka ta finceke hijab din daga ita sai towel Wanda ta tattare gaba daya ya fito da ilahirin jikin ta. Zuciyar sa ce ta hau bugawa da sauri da sauri cikin wani yanayi yake kallon ta, idon sa ya daga sama yana jin wani irin tashin hankali idan har ya tuna abinda ya gani "Allah karka sa abinda na gani ya zama gaskiya, Allah ka kawo min mafita ya Allah." A hankali yasa hannu ya dauke ta cak yana kallon fuskar ta a bacci so innocent, tun dazu ya rasa in da zai saka kansa idan ya tuno gashi ya kasa daidai ta abin ya dora shi a mizani guda, ba wani sani na azo a gani yayi mata ba balle yace ya san abinda zata iya da wanda ba zatayi ba, babban tashin hankalin sa daya ga takardar a cikin kayan ta wanda ita kadai take da ikon ajiya a wajen. ***Rugumtsumi*** wayyo Mero😭😭😭😭 *** Sai daya bari yayi aikin sati ya dan samu wani abu sannan ya sanar musu da ya ajiye aikin, babu wanda beyi mamakin hakan ba haka ya tattaro ya dawo gida. Abin mamaki yana dawowa Asi na kiran sa akan su hadu, be fito ba sai daya huta sosai sannan ya kira shi, a chan wani waje suka hadu sukayi magana sannan ya dawo gida. Daddare Inna ta kirashi akan maganar gidan da kuma dalilin dawowar sa,be sanar da ita ainihin maganar ba kawai ya barta ne a zuwan wani aikin ya samu anan sannan uban gidan nasa da ya dauke shi aiki shi ya taymaka ya basu gidan su zauna na dan wani lokaci, murna sosai Inna ta hau yi tana shi masa albarka, zuciyar sa ce tayi nauyi be kuma cewa komai ba ya bar dakin yana wasi-wasin abinda yake so ya aikata. Wajen takwas na dare Asi yazo kofar gidan ya tsaya bayan ya kirashi a waya, be wani bata lokaci ba ya fito suka wuce bayan ya rufo gidan saboda be san lokacin dawowar sa ba. Tafiya sukayi me nisa da har ya wani abu ya darsu a ransa sai dai kuma ya zuba ido ya ga yadda komai zai tafi. Sanda suka karasa wajen Asi ne kawai ya fita ya bar shi a motar shi kadai bayan yace ya jirashi zai karbo sako ne. Be wani jima ba ya fito rike da leda babba sannan yaja suka bar wajen. Sai da suka daidai ta a titi kafin Asi ya mika masa takardar "Ka duba bayanin komai yana ciki, ba wani aiki ne me wuya ba, dashi zaka fara kafin kuma kuyi magana da hajiya, zan dawo na dauke ka da safe." Kallon sa Hafiz yayi ya kalli ledar, a kasan kafar sa ya ajiye ta yayi shiru kawai ba tare da yace komai ba. Not edited... Manage dearies🚴🚴🚴😔😔😔 Kunsan Idon nawa sai a slow wlhi *25* S K ©*Hafsat Rano* *_ZAFAFA BIYAR na kudi ne idan kana son kowanne daga ciki ka nemi Wannan numbers din_* *08030811300* *07067124863* *_Daurin boye_* _safiyya huguma_ *_Buri daya_* _mamuhgee_ *_Wutsiyar rakumi_* _billyn Abdul_ *_Kai min halacci_* _Miss xoxo_ *_Sauyin kaddara_* _Hafsat rano_ *** Kayan ya shiga fiddawa daya bayan daya yana kallon su, sai daya gama gaba daya sannan ya tattare su gefe daya, tsiren daya tsaya ya siya a hanya ya jawo ya hau ci yana korawa da fanta me sanyi. Har ya gama gaba daya ransa a jagule yake, ya rasa yadda zai bullowa al'amarin gashi babu wani kwakwaran dalilin ta na son ya aikata abinda take so ya aikata. Gefe ya ture komai ya kwanta bayan ya kuskure bakin sa. Bashi da wani zabi illa kawai yayi yadda take so ɗin in yaso sai ya aiwatar da abinda shi ma yake ganin shine daidai. °°°° Yana ajiye ta tana buɗe idon ta, da sauri ta kalle shi tana kokarin tashi,hannu yasa ya mai da ita ta koma baya, bin ta yayi ya rufa akanta,da sauri ta runtse idon ta zuciyar ta ta shiga harbawa da sauri da sauri. Be yi magana ba haka nan be daga ta ba yayi shiru ne yana tunanin yadda zai yi, ilahirin jiki da zuciyarsa sun gama aminta da abinda yake ganin shine sai dai yana tararradin yadda zaiyi idan har zaton sa ya zama gaskiya. Sosai ta fara gajiya ta hau kokarin janye jikin ta, rinannun idanun sa ya zuba mata yana tamke fuskar sa kamar be taba dariya ba "Idan kika kuskura kika kara motsi sai kinyi mamaki." Ya fada yana sake sakar mata dukkan nauyin sa. A take tayi tsit dan ba karamin tsorata tayi da yanayin sa ba, daga sama taji yace "Takardar dake cikin kayan ki." Dan kallon sa tayi ya sake hade rai sosai, shiru tayi hakan ya sake tunzura shi, cikin daga murya yace "Am asking u,takardar cikin kayan ki, can U depend it?" "Wace takarda?" Ta tambaya adan tsoro ce "Are You asking me?" Da sauri ta girgiza kai. Buga hannun sa yayi a kusa da fuskar ta, da sauri ta rufe ido, "Ya Allah, ya zanyi?? Menene matsalar, waye yake son ganin baya na ne wai, I have face alot yanzu kuma dis? No I cnt take it." Zame wa yayi ya sauka kasan gadon ya dora kansa a saman ƙafafuwan sa, so yake ya fitar da abinda yake ji a ransa saboda yadda ya tokare masa makoshi ji yake kamar ransa zai fita. Ita dai Maryam gaba daya kanta ya daure ta rasa gane kan abinda yake faruwa, bata kawo tunanin komai akan ta ba har sai da yayi maganar takarda, iya sanin ta bata ajiye wata takarda a dakin ta ba, sai dai kuma ai ta ga lokacin daya dauki takardar a cikin kayan ta, toh takardar mece ce? Ita ta saka shi a halin da yake ciki ko kuma me? Ta rasa ganewa. Jin kamar yana jan numfashi sama-sama yasa tayi saurin saukowa ta manta da yadda take, da sauri ta rike hannun sa ganin yana kokawa da numfashi, kuka ta saka ta tashi da gudu ta shiga neman inhaler sa, babu a dakin haka ta sake fita tayi dayan dakin, a saman drawer ta hange ta tayi saurin daukowa ta fito, da sauri ta koma dakin jikin ta sai rawa yake dan bata taba ganin wani mutum a makamancin halin da yake ciki ba,wani irin zama tayi a gaban sa irin na yan bori ta mik'a masa inhaler, da kyar yasa hannu ya karba ya fara shak'a, zura masa ido tayi cike da tausaya wa, sai daya fara dawowa daidai sannan ta matso kusa dashi sosai tana kokarin rike hannun sa, kasa hanata yayi ya dai sauke kansa kasa yana sauki ajiyar zuciya da sauri da sauri kamar wanda yayi gudun tsere. Sau uku tana yunkurin yin magana sai dai ta rasa yadda zata yi, da kyar tace "Dan Allah kayi hakuri, idan ma wani abu ne ya faru, ka sani duk tsanani yana tare da sauki, mu cigaba da addu'a komai zai zama norma'." Gyara zaman sa taga yayi, ya d'ago yana fuskantar ta "Zaki fada min gaskia duk abinda na tambaye ki?" Da sauri ta daga kanta "In Sha Allah." "Owk taso." Yace yana mik'ewa, da sauri ta kalli kanta, kasa tashi tayi, be ce komai ba yayi hanyar fita,sai daya kai kofa sannan yace "Ina jiran ki." Tashi tayi ta zura doguwar riga a gurguje ta fito, baya falon, kai tsaye dakin ta wuce tana wasi-wasin abinda zata tarar. Yana zaune yana tattara takardun waje daya ta turo kofar hade da sallama, kai tsaye ta karasa wajen kafarsa ta zauna a kasa tana kallon shi, mika mata yayi yana tashi tsaye "Ki fada min gaskiyar abinda ke cikin takardun nan guda biyu, bana son ki boye min." Cikin rawar hannu ta karba tana kallo, da farko bata gane abinda takardar ta kunsa ba sai da idon ta ya sauka akan sunan ta dake rubuce baro-baro a dukkannin su. Wata irin zabura tayi tayi jifa da takardun ta mike cikin tsananin tashin hankali, "Innalillah wa inna ilaihi raji'un." "Tell me the truth." "Wallahi wallahi Allah ne sheda ta, bansan komai akai ba, wallahi Allah sharri..." "Sharri?" Ya katse ta, "Wallahi sharri akayi min, na shiga uku, innalillah wa inna ilaihi raji'un. Yake yayi wanda yafi kuka ciwo "Amma ya akayi na ga same report a kayanki?" Wani irin matsanancin bari jikin ta ya hau yi, gaba daya ta rude ta rikice, ihu zatayi yayi saurin sa hannu ya rufe mata baki, wani irin kuka ta saki, bata da wata dabara da zata iya kare kanta, duk wanda yayi mata sharrin nan ba karamin mara imani bane. Yadda take kuka sosai ne ya bashi tausayi, gaba daya ta rikice ta rasa in da zata saka kanta, dana sanin sanar da ita yayi dan beyi tunanin kalar tashin hankalin da zata shiga ba kenan. Juyawa yayi da nufin barin dakin tayi saurin rike masa kafa "Dan girman Allah ka yarda dani, wallahi tallahi ban aikata abinda aka ce na aikata ba, wayyo Allah na wayyo Umma na shiga uku." Runtse idon sa yayi bayan ya tsaya chak, gaban sa ta dawo ta sake zubewa yana fama magiya da roƙo. Kafad'arta ya kama ya miƙar da ita tsaye yana girgiza mata kai "Ya isa, don't hurt ur self, I believe u." Ya samu kansa da fada mata ba tare ya shirya ba. Da sauri ta rungume shi tana rage karfin kukan da take yi, shiru yayi yana jin yadda zuciyar ta ke bugawa da karfi da karfi. Kallon agogon dake saman dakin yayi yaga biyu har ya ta gota, ajiyar zuciya ya zare ta daga jikin sa "Zaki iya Sallah?." Kasa magana tayi sai jan hancin ta kawai take, riko hannun ta yayi "Muje kiyi alwala muyi sallah, ki daina kuka and please forgive me owk?" Alwalar tayi kafin ta fito ya dauko mata hijabin ta, kasa kallon shi tayi yana mika mata hijabin, karba kawai tayi ta saka tana jin idon ta kamar zai fado saboda radadi. Raka'a biyu sukayi kowa yayi addu'o in sa sannan yace su je su kwanta, tashi tayi ta ninke carpet din da sukayi sallah zata koma dakin ta ya hanata yace su kwana anan. Ba musu ta koma ta hau gadon ta kwanta dan bata so suyi wata doguwar magana ma dashi a yadda take ji, ta san kawai ya kyale maganar ne ba wai dan ya yarda ba sai dan ya tausaya mata, shi yasa ma tun data kwanta sai faamn juyi take ta kasa baccin a hankali take sa hannu ta goge hawayen dake faman zarya a kan fuskar ta. "Kinyi bacci.?" Taji maganar sa dan bata yi zaton ma idon sa biyu ba "Um um." Ta amsa mishi, daga gefen sa ya sa hannu ya bubbuga wajen yace "Matso nan." Ba musu ta matso, matsowa yayi sosai ta dan matsa kadan bayan ta juya masa baya, hannun sa taji ya sa a saman fuskar ta ya shafo hawaye "Ohh Allah, kukan dai?" Ya tambaya yana mirgino ta ita tana fuskantar shi Ji tayi wani sabon kukan ya sake taso mata me karfi ba kamar da data ke yin sa a zuci ba. Dafe goshin sa yayi jin yadda take shasheka, irin kukan nan da kana ji kasan mutum na jin ciwo a kasan ransa. Share mata ya hau yi yana share wa wani na bin wani, sosai kukan nata ke taba shi ya hanashi sukuni, ganin da gaske ba zata daina ba yasa shi yanke shawarar sata tayi shirun ko da kuwa batayi niyya ba. Cikin wani irin salo me cike da karsashi taji ya had'e bakin su waje daya. Tuni taji kukan ya dauke dip, a hankali a hankali komai ya shiga sauya wa, sabon shafin rayuwar su ya bude a lokacin, abubuwa da yawa sun faru, masu tsawa wa bawa a kahon zuciya, masu wanzuwa a tsakanin kowanne ma'aurata, wani irin kundi ne me wuyar fassarawa, a ranar Maryam ta shiga jerin mata masu daraja, fagen manya kamar yanda hausawa ke cewa, komai da ya faru kamar wasan kwaikwayo haka Arkel yaji shi, abinda yake zato sam babu makamancin sa, hakan yasa ya rasa in da zai dauki tunanin sa ya kai, menene alakar sakon da aka aiko masa da zamantakewar sa da ita? Waye ne baya son ganin su tare. Da sauri zuciyar sa ta rayo masa Hafiz. Sai dai bashi da wata gamsasshiyar hujja akansa, toh amma idan ba shi bane toh waye? Ganin zai matsawa kansa da tunani yasa ya bar komai zuwa wayewar gari, sauƙin ta daya yayi dabarar rike mutumin, dole ya sanar dashi wanda ya aiko shi idan ba haka ba kuwa sai ya kulle kaf ahalinsa. Gefen sa ya kalla, tana kwance tana kuka kadan-kadan, kukan da ya zama dole ga duk wata macen kwarai a irin wannan ranar, cikin tsananin tausayi ya matsa daf da ita sannan ya jawo ta jikin sa. Shafa bayan ta yake yana jin tsananin haushin kansa akan tuhumar da yayi mata, sai dai fa hakan ya kara mata wani babban girma da matsuguni me girma a ransa, yana jin ta tana goge hawaye da majina a jikin rigar sa, dariya yayi ya janye ta yana kallon fuskar ta, da sauri ta rukumkume shi ta cusa kanta a kirjin sa cikin tsananin kunya. Shafa kanta yayi ya gyara mata kwanciyar. Kafin safiya tayi jikin ta yayi mugun rikicewa da zazzafan zazzaɓi saboda uban kukan data sha ga wahalar ba kadan bace, daa k'yar ya tayamaka mata tayi alwala bayan ta gasa jikin ta, a zaune tayi sallah saboda jirin dake kokarin kayar da ita, sai a sannan ta tuno babu wanda yaci abincin dare a cikin su. Hijabin ya cire mata ya taymaka mata ta koma ta kwanta, duddubawa yayi babu ko paracetamol dole ya hakura zuwa gari ya kara wayewa. **** Babu irin zagayen da batayi ba tana jiran taga Maryam ta sakko da kayanta zata koma gidan uban ta, shiru har ta hakura ta kwanta ba dan taso ba. Shi yasa da safe tayi sammakon tashi sai dai abin mamaki babu ko alamun sun tashi ma a lokacin, haka ta hakura ta zauna a falon tana jiran ta ga ya abin zai kasance. Karar text message ce ta shigo wayar ta tayi saurin dubawa, da sauri ta ajiye wayar bayan ta gama karantawa jiki na rawa ta fito harabar gidan, buzu na hango ta yayi saurin tahowa "Waye jiya yazo da daddare Arkel yace ko ajiye masa shi?" Da sauri yace "Wani bako ne, bayan sun gama magana yace kar mu barshi ya tafi." "Yana ina? Me yasa yace a rufe shi?" Duk ta rude "Gaskia bansan dalili ba , sai dai naga hankalin oga ya tashi sosai." "Owk muje na gani." Be kawo komai ba ya rakata har kofar dakin, zai bude kofar tayi saurin cewa "Kyale shi ma, in yazo da kansa zai fi." Juya wa tayi tana dan kallon gefe, sai kuma ta juyo "Ka gyara mota kazo na aikeka." Da sauri ya juya, tunanin in da zata aike shi da uwar safiyar nan take, chan tunanin yazo mata tayi murmushi. Kudi ta shiga ta dauko ta mika masa "A chan kofar famfo akwai wata me sai da masa, kaje ka siyo min." Babu bata lokaci ya karba ya tada mota ya bar gidan, me gadi dake chan kofa be san abinda yake faruwa ba, dakin ta nufa ta bud'e, yana takure yana ganin ta ya tashi "Hajiya na shiga uku." "Shish." Ta dora hannun ta a saman bakin ta "Ka shirya, idan kaga mun shige ciki kayi gaggawar barin gidan." "Nagode Nagode Hajiya." Juyawa tayi tana kwalawa me gadin kira, da gudu ya karaso, "Muje ciki ka duba min kafar kujera, kamar rawa take." Yana ganin sun shige ya bude kofar ya fice daga gidan a dari. **** Yanayin fuskar sa take kallo har ya sauko kasan, a tunanin ta zata ji ko ta ga ya tattara Maryam ya watso ta watakila ma a kakkarye sai kuma daga akasin haka, yadda ya saba ya gaishe ta ya sa kai ya fice, saman ta kalla shiru bata ji ko motsi ba a ka'ida Maryam tana fitowa da wuri sai gashi yau har 10 ta gota bata fito ba alamun kenan babu matakin da ya dauka, kamar zata zare haka ta koma duk tabi ta shiga matsananciyar damuwa. Tana nan zaune ya dawo dauke da leda me dauke da tambarin wani drug store dake kusa dasu, da sauri ta tare shi cikin son nuna kulawa tace "Waye ba lafiya?" Kai tsaye yace "Ita ce." Hannu ta ɗora aka tace "Subhanallah, me ya same ta? Bari naje na gani idan abin babba ne gwara a tafi asibiti gaskiya." Da sauri ya dakatar da ita " Ba wani abu bane Serious,am...amm dama bige wa tayi ne tazo fita." Dadi ne ya kamata har ta kusa yin murmushi, saurin saita kanta tayi cikin tausaya wa tace "Ayyo...Allah sarki, na zata abun Serious ne, ta dinga kula dan Allah, Allah ya sauwake." "Amin." Ya amsa yana haye wa Dariya ta yi ta shige daki tana fatan Allah yasa targade tayi ko ta karye ma baki daya. A makure ya hange ta a chan karshen gado, gaba ɗaya idon ta ya koma ciki saboda azabar kuka, gadon ya hau ya jawo ta yana girgiza mata kai "I'm sorry please,kukan ya isa haka nan kinji jikin ki har yayi zafi." "Kin daina ko?" Yace yana mata murmushi Ciki-ciki tayi magana be jiba sai daya sake matso wa sosai, "Me kika ce?" "Ummi, kaje ka duba ta Please." Sakin ta yayi ya dora mata ledar akan kafarta yace "Bari naje, Please ki sha maganin sai ki sha tea din kar yayi sanyi, paracetamol ne sai wani pain reliever shikenan." Ya mutsa fuska tayi, murmushi yayi yana ayyano kalar rashin mutuncin da zai yiwa mutumin nan na jiya, sai a lokacin ya tuno dashi dan shaf ya manta. Dakin ummin ya shiga, tana kwance idon ta biyu, kallon gadon yayi ya tuno da maganar da Maryam tayi masa, salim ya tuno yayi saurin kiran sa "Sai oga." "Kana ji, wheel chair nake so kaje ka siyo anjima kadan, sai ka kawo min gida." "Owk an gama, yau ba zaka shigo bane?" Har zai ce zai shigo sai ya tuno "Ba zan shigo ba, Madam bata jin dadi." "Madam...?" Salim ya maimaita, kafin yayi magana ya kashe kiran. Dariya kawai yayi yana mamaki. Wai Madam. Ah lallai. *** A firgice ya tashi saboda mummunan mafarkin da yayi, gaba daya ya jike da zufa da kyar ya ja ƙafafuwan sa ya fada bayi,haka ya fito jikin sa duk a mace, yanke shawarar fasa zuwa aiki yayi ya kwanta kawai bayan ya dan sha tea kad'an Har wajen azahaar yana kwance sai ga mustapha ya shigo, daga wajen aiki yake ya zarto saboda ya kirkira shi a waya be daga ba. Ganin shi a kwance ne yasa ya tabbatar babu lafiya. "Baka da lafiya ne?" Ya tambaya yana ajiye jalar hannun sa "Bana jin dadi ne musty, yau mafarkin gida nayi." "Shine yasa ka kwanta? Naga ba yau ka fara ba ai." "Amma na yau is totally different, Arkel yana cikin matsala, i can feel it, ya zanyi?" "Kaje kawai?" "Kai! Ina? I can't face him, kasan kuwa laifi na? Ko kai kaji abinda na aikata sai ka guje ni, sai dai nasan ba yin kaina bane, bansan me ya hau kaina ba, bansan ya akayi ba. Duk da haka amma laifi nane, shiyasa ba zan iya yafe wa kaina ba, ba zan iya taba zuwa in da suke ba, na cuci kaina na cuci dan uwa na." Mike wa Mustapha yayi ba tare da yayi magana ba ya dauki kayan sa "Ka dade kana fada min hakan, ba tare da ka sanar dani ainihin matsalar ka ba, na sani baka daukeni yadda na dauke ka ba shiyasa har ka kasa sanar min, babu komai bari na wuce kawai, ina ganin ba sai na sake dawowa nan ba, ba amfani zuwan nawa." Hanyar waje yayi da sauri Arab yace "Dawo na faɗa maka, amma ka shirya rabuwa dani dan nasan kana ji zaka gujeni." Abinda dama yake so kenan, dawowa yayi ya zauna yana bashi dukkan attension din sa. *** *Assalamu alaikum jama'a Ni dai bansan da bakin da zan kuma yin bayani ba, na sanar muku wlhi ciwon ido nake, abu har ya kai da glass, Amma wasu sun kasa yi min uzuri, suna ganin bana musu typing ko ina jan rai, abubuwan ne sun min yawa dole ba zan iya typing me yawa kamar yadda wasu a cikin mu sukeyi ba.* *Karku manta yawancin ku ta wajena kuka siya books din mu, bafaa karamin aiki bane, na tura maka details, idan ka biya sai na je na duba account name ɗin ka, sannan nazo nayi saving dinka , nayi adding a kowanne group, kuma a haka bana mantawa ina kokarin saka kowa a in da ya dace tun da wasu ba dukka biyar din suka siya ba, sannan dana yi adding sai maganar turawa daga farko, plus am married, Ina da iyali ga typing banda aikin gida,ga lalular ido da ta sakani a gaba. Ya kuke tunanin xan iya zama nayi typing me readmore biyar shida ko bakwai bayan a kullum nakan amsa mutane sama da 200 a rana. So ni dai ina kara baku hakuri, sannu sannu bata hana zuwa, akwai yiyuwar ku dan jini shiru ma kwana biyu saboda lafiyar ido na kar na kashe ido na garin neman gira*😅 Nagode *26-27* S K ©*Hafsat Rano* *_ZAFAFA BIYAR na kudi ne idan kana son kowanne daga ciki ka nemi Wannan numbers din_* *08030811300* *07067124863* *_Daurin boye_* _safiyya huguma_ *_Buri daya_* _mamuhgee_ *_Wutsiyar rakumi_* _billyn Abdul_ *_Kai min halacci_* _Miss xoxo_ *_Sauyin kaddara_* _Hafsat rano_ °°° "Da wani yammaci ina zaune a daki ni kad'ai bayan tafiyar Arkel ina kallon wani film sai Ummi ta kirawo ni ta aike ni wani store, a kafa na fita na tari abun hawa. bamu yi nisa ba wani holdup ya rik'e mu, ganin haka yasa na ciro wayata na shiga chatting saboda na rage wa kaina zaman. Ina cikin duba wayar ne naji wata mata na tambayar in da zamuyi, ina ji ta shigo napep ɗin da alama hanya daya mukayi kenan, daga sama naji muryar ta saboda haka ban iya tantance yanayin ta a lokacin ba, ban ko d'ago ba na cigaba da danna wayata. Tsawon mintuna biyar aka fara ja, ganin haka yasa na kashe wayata na maida aljihu saboda yanayi na tsaro. Kallon gabana kawai nake kamar wasa sai naji alamun ana taka mun kafa, kallon kasa nayi sai naga ta janye kafarta da sauri, sai a lokacin na kalle ta, mace ce babba a ƙalla zatayi shekara 40 da sauri ta sakar min murmushi tace nayi hakuri bata sani ba, ban ce komai ba na gyara zama na kawai. Lokacin da muka isa in da zan sauka sai naga ita ma ta fito, muka sallami me napep na juya zan shiga store din , da sauri ta tsayar dani tana gyara mayafin dake makale a kafardar ta, kallon kurillah nayi mata fara ce tas daga gani ta sha bleaching sai uban jambaki data saka ja wanda ya kara sakata tayi bau kamar ba mutum ba. "Sannu dai." Nace mata ina kallon ta, "Sannu handsome, ya gida ya komai.?" "Lafiya." Na amsa mata kai tsaye sannan na juya na shige ciki, ba wani abu na siyo da yawa ba shi ya sa nayi saurin fitowa, abun mamaki tana nan a tsaye tana dube-dube, dauke kai nayi na tare wani me napep din, tare muka shiga da ita kuma dai har aka zo unguwar mu, ina sauka naga ta sauko ita ma, daga nan sai naji zuciya ta bata yarda da ita ba sam, ja nayi na tsaya cikin hade rai nace "Malama lafiya kike bina?" Murmushi naga tayi kafin tace "Kawai naji kayi min ne wallahi, so handsome Masha Allah, so nake muyi magana shiyasa ma nayi ta maka alamar da zaka ankara ka gane sai kuma naga kamar baka gane ba, yanzu dai idan zai yiwu muyi exchanging number a Kaduna nake zama nazo ganin gida ne so ba dadewa zan ba." Kallon banza na watsa mata saboda yadda ta kular dani, sake kallon ta nayi sosai rai na ya kara baci, tsohuwa ce sosai amma banda iskanci tace nayi mata, yawo na zubar a gefe ta fito da ido waje tana kallo na "Allah ya sauwake dai, wallahi kinyi asarar zuwa duniya, bari kiji ni ba sa"an ki bane mata a haife kin haife ni shine zaki kawon maganar banza." "Ni ce na haife ka? haba dan samari, Kalle ni sosai mana, ni ba wani abu nake nufi ba kawai ina so mu zama friends ne." "Chab, Allah ya kiyaye ni wallahi, kije ki nemi tsoho daidai dake ki aura kin tsaya bata wa kanki lokaci." "Ni fa ba mijin aure nake nema ba, kawai dai na ganka na k'yasa ne idan zai yiwu, ka duba dan Allah." "Allah ya kiyaye, ke kuma Allah ya shirye ki, dama ance akwai irin mata haka tsofaffi amma basa jin kunyar rashin mutunci, toh dai kinyi asara wallahi." "Dakata dallah, dan kaga ina binka shine zaka nemi ka zage ni, ka kula da maganar ka karka jawa kanka da ahlin ka abinda zai zame muku masifa." "A lokacin kaina ya dau zafi dan ba karamin bata min rai tayi ba,haka na zage na zage ta tas na juya na shige link din mu, ashe bansani ba hakan danayi ba shine daidai ba, ban sani ba na daba wa kaina wuka a ciki na. Ashe bata bar ni ba, sai data bibiye ni tsawon kwana uku tasan komai akai na da gidan mu, a kwana uku ta kama mahaifina, ta saka mishi soyayyar ta me zafi, duk ban san wainar da ake toyawa ba." Sati daya da faruwar al'amarin sai na dinga jin hayaniya daga ɓangaren su Ummi, abun yayi matukar dauren kai nayi saurin fitowa, cikin tsananin mamakin abinda ban taba gani ba naga Ummi da Alhaji suna hayaniya sosai cikin tsananin bacin rai, ina zuwa ya juya ya fita ita kuma Ummi ta saka kuka, zama tayi na hau tambayar ta abin da yake faruwa, bata boye min komai ba ta sanar dani wai Alhaji aure zai yi, saura sati daya ayi bikin ma, sannan binciken da tayi ta gano matar muguwar hatsabibiya ce babu Allah ya zuciyar ta, kwantar mata da hankali nayi tayi na yi mata alkawarin binciken abinda yake faruwa dan musan yadda zamuyi." "Abin mamaki washegari sai na tashi a wani irin yanayi me wuyar fassarawa, naji bana sha'awar komai face kayan maye, wani irin tashin hankali na shiga na kasa sukuni a daren ranar sai dana nemo sigari na fara zuka, kamar wasa a cikin kwana uku sai gani na zama tataccen dan maye sai na fara neman in da zan samu giya, duk abin nan da nake babu wanda ya sani saboda ina daki kullum a rufe gashi Ummi da Alhaji kullum cikin tashin hankali zaman yaki dadi, a haka na cike kwana biyar cif ina wannan halin na maye, ana i gobe daurin auren Alhaji Ummi ta shigo daki na katsaham, abin da ta gani ne ya saka ta rawar jiki saboda tsabar k'aduwa, lokacin ina cikin yanayin maye saboda haka ban ji komai ba, duka ta rufe ni dashi ko ta ina ina jin sautin fitar kukan ta a saman kaina sai dai babu abinda zan iya yi, har da gaji da dukan ta juya da sauri ta fita daga dakin." Hawayen daya zubo masa yasa hannu ya share ya juya wa Mustapha baya saboda abinda zai fada yana da matukar nauyi "Na cuci kai na na cuci yan uwa na da dangi na." Ya fada yana jan Muryar sa cikin wani yanayi da kana ji zaka san ba karamin nauyi yake ji a zuciyar sa ba "Kayi hakuri man, komai yayi zafi maganin sa Allah, ka daure ka karasa min labarin nan, in Sha Allah komai ya zo karshe." Da kyar Muryar sa na rawa yace "Washegarin ranar da Ummi ta kamani bansan me ya hau kaina ba, bansan wani irin mummunar ƙaddara ce take bi na ba, na sha giya sosai na bugu har bana jin komai saboda tsabar yadda na bugu, babu kowa a gidan me aikin ta ta tafi Ummi ce kawai tana zaune a dakin ta tayi tagumi tana tunanin abinda ta gani, damuwar ganin da tayi min ce ta danne damuwar auren shiyasa duk abin duniya yayi mata yawa,babu wanda ta sanar wa da auren tun da dama ba wasu mutane take harka dasu sosai ba, a yadda na shigo mata daki ne yasa ta tsorata, maganganu kawai nake bansan ko me nake cewa ba Mustapha, wallahi tallahi bansan me ya hau kai na ba, kawai sai naga ta rikid'e ta koma min kamar wata budurwa yar shekara sha takwas, wallahi Allah ba Ummi na gani ba Mustapha, wallahi ban san komai ba, bani da wani iko da kaina ko zuciya ta, komai ji nake ana ingizani, bansani ba? Na aikata abinda zuciya ta ta ingizani ko ban aikata ba? Shine abin da na kasa sani har yau iya kaci dai naji Muryar matar a kaina tana salati, wannan shine silar shiga halin da Ummi take ciki, wannan shine silar barin gida na, da wanne ido zan iya zama na kalli mahaifi na? Dan uwa na? Da sauran mutanen gari? Wanne irin mutum ne ni?  Bani da wani sauran amfani a duniya shiyasa nake yin komai da rayuwa ta saboda nasan ni tawa ta kare, tsawon wannan shekarun ina dauke da wannan masifar, gashi har na kawo yanzu ban mutu ba, bayan tun a lokacin na roki mutuwa ta akan rayuwa ta." Da sauri Mustapha ya taso ya rike shi ganin yana neman sakin layi, kuka dukkan su suke dan yadda abin ya girgiza Mustapha be taba shiga tashin hankali irin wannan ba, lallai dole ne ya aikata abinda yake aikata wa yanzu ko ma fiye da haka, wannan wacce irin kaddara ce haka? Wacce irin rayuwa ce haka? Innalillah wa inna ilaihi raji'un." Kawai dukkan su suke nanatawa,wani irin tsoron Allah ne ya shigi Mustapha a lokaci daya yaji komai ya dauke masa. yake sakawa a ransa, abu daya Mustapha ya sani ya kuma ɗaukar wa kansa alk'awari shine sai yayi kokarin yadda ya kawo wa abokin nasa sauyi a rayuwar sa. *** A tare suka fito da safe zuwa wajen aiki, kallo ɗaya zakayi masa ka tabbatar da tsantsar damuwar da yake ciki. Sanda suka isa office Mustapha be zauna ba, signing kawai yayi ya fita bayan ya dauki excuse. Direct wajen siyan ticket din mota ya nufa ya yanki ticket biyu na zuwa Sokoto sannan ya dawo office. Da daddare suna cin abinci duk da ba wani dadin abincin yake ji ba Mustapha ya zaro ticket din ya mika masa "Gobe idan Allah ya kaimu zaka rakani sokoto, alfarma nake nema a wajen ka saboda haka karka ce min a'ah, idan har ina ko da muhimmanci a rayuwar ka." Be jira amsar sa ba ya kwashi shirgin sa yayi gaba, hannun sa kawai yake kallo ya rasa yadda zai yi, ga dai ticket ya karba sannan yasan zuwan ba karamin aiki bane a wajen sa,sai dai ba zai iya musa masa ba bayan bashi da kowa sai shi, shi yayi masa dukkan gata tun da ya baro gida har kawo yanzu bai taba nuna gajiya wa da al'amuran sa ba, bashi da wata hujja ko dalilin kin amsa gayyatar tasa. Haka ya kwana sukuku  washegari suka dauki hanyar sokoto. *** Wajen azahar tadan ji ƙarfin jikin ta, wanka ta sake ta shirya cikin atamfa riga da zani ta ɗora hijabi a saman ta sauko tana jin ta kamar iska zata kwashe ta ta watsar gefe, babu kowa kai tsaye ta buda dakin Ummi ta shiga, da sauri ta karasa wajen gadon ganin ta a gefe saura kadan ta fado, da k'yar ta gyara ta tana mamakin yadda akayi hakan ta faru. Cike da tausaya wa yake kallon ta kafin ta tashi ta duba magungunan dake zube a gefen gadon, ajiyar zuciya ta sauke ganin na gaskiyar ne, gefe ta zauna tana tunanin makaranta da zasu koma dan har an fara registration. Tana nan zaune ya shigo dauke da wheel chair din, da sauri ta tashi ya sakar mata murmushi dan beyi tunanin ganin ta ba, sunne kanta kasa tayi cikin kunya ta kama masa ya ajiye, gumi ya goge yana sauke ajiyar zuciya. "Sannu." Ta fada kasa-kasa. "Tun yaushe tayi bacci?" Ya fada yana kallon ta. "Tun da nazo." "Ok ya jikin?" Ya fada kasa-kasa yana daga kashe mata gira, shiru tayi taki magana yayi dariya kawai. Kallon wheelchair din yayi yace "na kira wani Dr ya fada min yadda zamuyi mata, yanzu anjima sai mu taimaka mu sakata akai a zagaya da ita, a hankali a hankali sai a maidashi twice a day." "Owk." Tace tana kallon ummin, "baki fada min magungunan sun kare ba." Da sauri ta kalle shi, kallon ta shima yayi, "I'm sorry." Kawai ta samu kanta da cewa dan bata san me zata ce ba, murmushi yayi mata ya matso kusa da ita yace "karki damu, Hajiya ma ta fada min dazu, gashi nan har na siyo." Bata san me zata ce ba sai kawai tayi shiru, shafa cikin sa yayi ya kalli kofa "yunwa muje ki bani abinci pls." Ba musu ta tashi suka fito, Hajiya na ganin su gaban ta ya fadi, fita tayi dawowar ta kenan bata yi tunanin hakan ba, ganin sun hada ido ne yasa Maryam ɗin gaishe ta, kamar babu komai ta amsa tana kallo Arkel ɗin "an siyo maganin kuwa?" "An siyo." Ya fada kai tsaye. Kallon Maryam tayi, "Ki dinga kula dan Allah,kinga ke kika kori me zuwa tana kokarin ta gashi kuma an fara samun sakaci, ki kula sosai gaskia, bama wasa da komai nata." Mamaki sosai tayi har ta kasa magana sai da tace "Baki amsa ba, kar dai ko haushi kika ji Dan na fad'a miki gaskiya?" Da sauri tace "zan kiyaye in Sha Allah." Harara ta sakar mata ganin Arkel ya yi gaba sannan ta shige ciki, jiki a sanyaye ta ja kafarta tayi gaba tana mamakin matar, duk in da take tunani ta wuce nan, toh ta Allah ba tata ba wallahi,zata dage da addu'a kawai. Yana cin abinci yana tunanin maganar Hajiya Mero, baya so ya ga laifin Maryam amma dai ba zai yadda da sakaci ba kuma, a haka dai ya gama ya dan mike yana duba kasuwar tasu ta Forex. Kiran da ya shigo wayar sa yabi da kallo, salim ne, yana dagawa yace "ka samu in da mutumin yake?" Daga dayan bangaren salim yace "Na saka dai a kara bincika mana, in Sha Allah xaa samo shi." "Shikenan, thank you so much." Dariya salim yayi kawai ya kashe wayar. Shiru yayi yana tunanin abin, dole ne ya sake tuntubar su buzu yaji garin ya hakan ta faru har suka bari ya gudu. Da daddare suna zaune a falo bayan ta baro dakin UMMI, sallah ta shiga dakin tayi ta sake wanka bayan ta karanta text d'in Anty Maryam akan lallai bayan kula da mahaifiyar sa ta dage wajen kula da kanta da gayu da wanka kar ta zama kamar wata yar kauye, haka ta haɗa ruwan tayi wanka ta fito ta shirya tsaf cikin shigar ta me kyau da sauki, kamshi ne kawai ke tashi daga jikin ta kamar anyi barin turare, tana gama daurin dankwali taji ya turo kofar, sai da wata masifaffiyar kunya ta taso mata amma sai ta dake har ya karaso yana kallon ta irin kallon up and down din Nan, ba kadan ba tayi masa kyau dan tayi shar da ita so cute Masha Allah. Nan fa mutumin ku ya kara shiga ciki ya dora kansa saman bayan ta suka kurawa juna ido ta cikin tafkeken mudubi da ya kusa cinye jikin su taf, ita ta fara dauke kanta saboda yadda ta ga yana wani lumshe ido tana budewa kadan kadan. "U look gorgeous." Ya rad'a mata a kunne ta, wani irin yar taji tayi da saurin damƙe idon ta, hannu yasa ya juyo da ita tana fuskantar sa, gefe yaja yana screening din ta tayi kanta da kasa, dariya yayi kawai ya riko hannun ta, "muje nima a hada min ruwan." Make kafardar ta tayi tana dariya, dariyar yayi shima ya hau cire kayan sa. Da sauri ta fita daga dakin tana sauri kamar zata tashi sama. Shi kadai yake ta murmushi har yayi wankan ya shirya ya fito, tana zaune bata ji fitowar sa ba sai ji tayi yayi hugging din ta ta baya, da sauri ta juya suka yi gware, hannu tasa a wajen shima ya saka kamar tayi kuka saboda zafi. Yadda ta yi da fuskar ta ne ya bashi dariya ya dungure mata kai "raguwa kawai." "Allah baka ji zafi ba." Ta fada tana taba wajen, "Kawo na danna miki toh." Matsowa tayi ya zauna yana dan danna mata wajen a hankali yana kallon fuskar ta. "Bakya so ki ga umma?". Taji yace, da sauri tace "Ina so wallahi." Shiru yayi yana tunani kafin yace "ki shirya gobe muje kiyi registration sai ki je ki gansu." Manage pls *28* S K ©*Hafsat Rano* *_ZAFAFA BIYAR na kudi ne idan kana son kowanne daga ciki ka nemi Wannan numbers din_* *08030811300* *07067124863* *_Daurin boye_* _safiyya huguma_ *_Buri daya_* _mamuhgee_ *_Wutsiyar rakumi_* _billyn Abdul_ *_Kai min halacci_* _Miss xoxo_ *_Sauyin kaddara_* _Hafsat rano_ *Assalamu alaikum, jiya nayi mistake ɗin sa Number instead of 26 nasa 27 afwan. A tafi a hakan kawai kar mu zama confuse. So yanzu Number 27 shine 26. Nagode* °°° Da sassafe ta tashi ta shirya tsaf saboda zumud'i, bata kira umman ba so take kawai sai dai ta ganta, dan in taji zata zo zata iya hanata shiyasa tayi shiru, har gidan anty Maryam take son zuwa zata tambaye shi idan sun je ya taymaka ya barta. Tana gyaran gado ya shigo tun fitar sa sallar asubah be shigo ba, yana can suna magana da Alhaji da yake yana gari, maganar ritayar sa yake masa dan gaf yake da yin ritayar, kallon mamaki ya ke mata ganin ta a shirye daga gani shirin fita tayi. Be ce komai ba dai ya amsa gaiswar da take mishi ya haye gadon dan wani bacci bacci yake ji, dan fitar ma da yake da wuri wani lokacin yanzu ya daina sai dai yayi ta bacci, tsaye tayi tana kallon sa ita a tunanin ta wanka ma zai shiga dan har ta gama hada masa ruwa da komai, yana kallon ta ta kasan idon sa tayi kicin-kicin da fuska kamar zatayi kuka, ganin da gaske bashi da niyyar tashi yasa ta fita daga dakin, dariya yayi kawai ya maida kansa yana mamakin zumudin ta. *** Hajiya Mero na ganin fitowar Arkel daga dakin tayi saurin fadawa tana addu'ar samun abinda taje nema,Ummi na kwance idon ta biyu taji an budo kofar, da sauri ta rufe idon ta ta dan bar shi kadan yadda zata ga komai, Hajiya Mero ce ta shigo tana kalle kalle, a gaban gadon ta tsaya tana yatsine fuska, kanta ta rankwafa wajen saitin kanta tace "Kin ga karshen abinda kika jawo ko? Yanzu rayuwar da kike kina ganin dadi ce? Ke kika jawa kanki amma dai, ban yi niyyar akai haka ba, kika tursasa ni, ki sani rayuwar dayan dan naki ma gab take ta tarwatsewa, da shi da tsinanniyar yarinyar da kike ganin kamar itace jigon ku, yadda na juya tunanin kowa naki daga kanki, har yar cikin ki, haka zan juya tasu yanzu, zaki kare rayuwar ki ne a haka in dai ina numfashi." Numfashin Maryam ne ya dauke saboda tsabar tsoro, ta kama kofar kenan zata shiga taji wannan maganar, da sauri ta ja da baya da baya ta haye saman da mugun gudu, a falon ta tsaya tana matukar haki, ta rasa me zatayi, kawai sai ta fara zagaye tana kai wa da komowa, dakin da yake ta shiga tana neman bugewa da kofa, bude idon sa yayi ganin ta a kansa tana haki, kallon da taga yana yi mata ne yasa tayi saurin saita kanta. "Menene.?" Ya tambaya yana nazarin ta "Um.. um dama so nake ka taymaka min na daga Ummi, so nake na sata a wheelC din na zagaya da ita kafin ka tashi." Be musa ba ya sauko, hannun ta ya riko ganin kamar rawa yake, da sauri ta kalle shi, hannun ya kalla tayi saurin kallo itama. "Are You ok?" Ya tambaya yana matse hannun nata, bata iya magana ba sai kawai ta daga masa kai, be kuma magana ba har suka sauko kasan, tsoron ta ne ya karu tana tunanin abin da zasu tarar. Tana tsaye a kanta suka shigo, yadda tayi firgigit da ta gansu ya kamata ace gogan ya dauki wani haske, amma sai kawai Maryam taga ya matsa jikin gadon yana kokarin d'ago Ummin "Ina kwana?" Yace yana yin abinda ya kawo shi Cikin in ina ta amsa tana ficewa daga dakin bayan ta aika wa Maryam da wani irin kallo me cike da ma'anoni da yawa. Ajiyar zuciya Maryam ta sauke ta rasa ta ina zata fara sanar masa, haka dai ta taymaka masa suka dora ta a kujerar, shi kadai ya fita da ita ya zazza gaya sannan ya maida ita. Wanka ya fara sannan yayi breakfast suka fito, manyan kaya ne a jikin sa ta zarce masu ruwan bula, a hannu ya riƙe hular hakan ya zama kamar wata dabi'a tashi, ita kuwa Maryam hadadden lace na cikin kayan lefan ta ta saka pink and ash ɗinkin bubu, tayi kyau sosai kana ganin ta ka ga amarya tayi fresh da ita abun ta. Zainab na fitowa suna fita, sosai suka birge ta ba karya ta san ko ta ina sun yi matching, kallon kanta ta sakeyi ta zauna tana jin haushin kanta. School suka fara zuwa tayi abinda zatayi yana zaune yana jiran ta a mota, kawayen ta su Asma'u sai tsokanarta suke yi ita dai kawai murmushi take yi, sun jero zasu rakata wajen mota sai ga Saddi da jama'ar sa, wani kallon kasa kasa ya ke mata tayi saurin had'e ranta dan ma kar yayi mata magana, da sauri ta karasa wajen ta bude motar ta shiga tana daga musu hannu. Duk abinda ya faru ashe yana gani har sanda Saddi yake kallon ta, gani tayi yayi kicin kicin da fuska ya figi motar da gudu, shiru tayi tana tunanin abinda ya chanja masa mood, gashi ya tsare gida babu halin tambaya. Yana ajiye ta a kofar gidan ya dauke kansa gefe, kin fita tayi tana kallon sa, jikin ta ne yayi sanyi "Ki gaida umma idan na dawo zan shigo." Taji yace Kin fita tayi, juyowa yayi da nufin magana idon su suka sark'e da juna, marairaice fuska tayi kamar zata yi kuka, kauda kansa ya kuma yi kawai ta saka hannu ta riko shi "Kayi hakuri." Tace muryarta na dan rawa, Bata san me tayi masa ba amma tasan tabbas fushi yake da ita tun da yaki kallonta "Kaji dan Allah,." Ta sake maimaita jin yaki cewa komai. Hannu sa ya zare ya danna lock din motar, dama tint ce ba'a ganin na ciki ta waje, ta zata cire hannun nasa da yayi fushin ne sai ji tayi kawai ya jawo ta jikin sa "Baki yi min komai ba fa, kawai ji nayi ina jin fushi." "Haka kawai?" Ta tambaya Daga mata kai yayi "Ka faɗa min pls." "Kinsan me? I'm just jealous dana ga kazamin yaron nan yana kallonki, saurayin ki ne ko?" Ya dan danne mata hannu da karfi yana bata fuska, da sauri tace "Allah ba saurayi na bane, ni bama magana nake dashi ba." "Fadi gaskia dai, nasan halin samarin jami'a, in sun ga me kyau." Dariya ta saka ta boye kanta a jikin sa. "Allah ba haka bane." "Toh shikenan na yarda, Amma one condition sai dai aka fara lectures kina saka nikab gaskia." "Mika?" Ta zaro ido "Yes of course, ko ba Zaki saka ba?" "Hmm, bari na shiga sai ka dawo." Tace tana zare jikin ta dan bata ma san maganar taja da yawa Allah ya gani bata son nikab. Hana ta fita yayi yace "Kin fasa shiga ma gidan komawa zamuyi kawai tun da ba zaki sa nikab ba." Da sauri tace "Zan saka wallahi." Dariya yayi, kiss yayi mata a saman hannun ta sannan ya bude mata kofar. "Da wuri zan dawo mu tafi." Kallon sa tayi yayi saurin cewa "Kin ga saboda Ummi ko?" "Haka ne, sai ka dawo tom." Tana fita ya shafi kansa yana murmushi, a hankali ya furta "Saboda Ummi da kaina zan dawo da wuri, i just want u close." Hannu ta daga masa ta shige ya k Ja motar ya bar kofar gidan. Da gudu gudu ta karasa shiga gidan, Habubu ne ya fara ganin yana wajen kajin sa da ya zuba yana chanja musu ruwa, ihu ya hau yi ga yaya Maryam su Walid suka fito da sauri. Murnar ganin ta suka hau yi kowa so yake ta kula shi. Umma na daki taji ana ga yaya Maryam, da sauri ta fito fuskar ta dauke da tsantsar farin ciki ta hau yi mata lale marhabin. Kamar wata bakuwa haka aka mai da ita, komai aka debo aka zube mata a gaba, farin ciki bakin ta yaki rufuwa gata ga yan uwan ta. Zuwan ba karamin dadi yayi mata ba, bayan yaran sun gama murna suka kulle a daki da umma ta fara bata labarin abinda yake faruwa, sosai al'amarn ya bawa Umma tsoro sai dai bata nuna mata ta karaya ba, shawarwari sosai ta bata ta kuma jaddada kar tayi sakaci da addu'a dan ita ce makamin mumini. Be tashi dawo wa ba sai bayan magriba hakan kuwa yayi mata dadi kamar kar ta tafi gida dadi, shigowa yayi suka gaisa da Umma lokacin Baba ya dawo shima suka gaisa, da zasu tafi umma ta saka suka shiga gidan Hajiya Mama suka gaishe ta sannan suka je suka gaida Alhaji Faruku yaji dadin ganin su kuwa sosai dan har kudi ya bawa Maryam ɗin ko zata bukata. Da haka suka yi musu sallama suka tafi. *** Arab da Mustapha Basu isa Sokoto ba sai wajen magriba, hakan ya saka babu wani abu da suka iya aiwatarwa, washegari tun kafin ya tashi Mustapha ya fita, bashi ya dawo gidan ba sai bayan azahar, lokacin Arab ya gaji da kiran shi a waya ya hakura, da harara ya bishi ganin ya shigo yana wani wash Allah alamun ya gashi, a hotel dama suka sauka abincin da yayi musu order ya nuna masa da hannu, kai ya hau ci ba kakkautawa saboda ba karamar yunwa ya dauko ba, gidan wani babban malami abokin babanshi yaje wajen sa ya sanar masa da matsalar abokin nasa, be rufa ba kaf labarin ya kwashe ya fada masa, ya jinjina lamarin kuma ya gane sihiri ne akayi masa aka raba shi da yan uwan sa, sai dai dole sai ya dage da addu'a dan ba karamin kulli akayi musu ba. Magunguna ya bashi na su ganyen magarya, habbatussaudah sai ayatusshifa sai wani rubutu sannan yace lallai suzo tare gobe akwai tambayoyin da zai yi masa. Babban matsalar shine ta yadda zai fara sanar masa da abinda yake shirin yi, ya san kafiya irin ta shi ba lallai ya yadda ya sha maganin ba. Har suka tashi da safe suka shirya ya kasa sanar masa, sai da suka dau hanya ne idea ta fado masa, da sauri yace "Man, kasan wani abu?" "Sai ka fada." "Wani babban malami ne abokin me gidan mu, tun wani zuwa na kebbi aka sa nazo na karbi wani dan rubutu haka dai kasan Rayuwar yanzu sai kana tsare kanka da yan addu'o i gamu mu da muke cikin kabilu mabanbanta ina ganin why not mu k'arasa kawai mu karba sai ka rakani family house din mu kaga dangi na." "Owk hakan yayi, kace main family ɗin ku anan suke kenan?" "Eh gaskia kusan haka ne, aiki ne kawai ya kai me gidan namu Kebbi." "Owk." Da haka ya samu ya hada mishi duk magungunan Malam yayi mishi bayanin yadda zai yi amfani dasu, daga nan suka je chan arkilla main house din su Mustapha, anan ne jikin Arab yayi sanyi yaji dama shine sai dai hakan ba me yiwuwa bace. Kwanan su uku suka koma Mustapha ya tattaro ya dawo gidan Arab saboda dai magungunan dan idan babu me sashi yasha toh ba zai sha ba. *** Ran Hajiya Mero ya baci sosai, gidan Hajiya Mama taje ta wuni a hanya ta kira Asi suka hadu, maganar Hafiz tayi mishi taki shiru babu wani abu da yace gashi lokaci yana ta tafiya, kiran Hafiz din yayi kawai yazo ya same su. Sai da ya dan bata lokaci sannan yazo, yadda Hajiya Mero ta hau shi da masifa da bala'i ransa yayi mugun baci, shi fa dama baya daukar raini kuma ba'a nuna masa yatsa, a ransa ya ayyana abinda zaiyi ko dan ya fanshe cin mutuncin da tayi masa. A take ya karbi aikin su ya tabbatar mata a daren yau komai zai wakana, ta zama cikin shiri ita ma sannan ta tanadi kudi. Da haka sukayi sallama ya koma gida yana tunanin babban dalilin da yasa Hajiya Mero ta nace sai lallai shi zai yi mata aiki, bayan gashi tana da yara irin su Asi amma me yasa sai dai shi? Bashi da amsar haka ya hakura ya jira zuwa dare kamar yadda suka tsara. *** Girki tayi ta gama wajen magriba, wanka ta shiga tayi sannan tayi alwala, sai data fara sallah sannan ta hau shirya wa, gidan Yaya Nabila zasu je tun rana ya fada mata, tasan yana kusa tun da ce mata yayi ta zama cikin shiri da anyi magriba zai dawo. Aikuwa ana idar da Sallah taji shigowar sa, be shigo dakin ta ba nasa ya wuce baya jin zai iya cin komai haka ya ajiye kayan da ya shigo dasu ya fito, tun dazu yaya Nabila ke kira shiyasa kawai ya haqura da abincin idan yaje chan yaci. Lokacin da suka fito zasu tafi Hajiya Mero na falo, farin ciki sosai tayi ganin sun fito da alama fitar zasuyi, hakan yayi mata dadi sosai komai zai tafi yadda ta shirya, suna fita ya kira Asi ta sanar masa sun fito,Hafiz ya kira yace su hadu a in da sukayi zasu hadu. Yau ma manage😝 Affan ya hanani typing kememe wlhi, hannu na yake rikewa yana ihu😔 Mun dai kusa zuwa in da muke so. Zuwa in Sha Allah. Thanks for ur soyayya 😍😍😍😍 SAUYIN KADDARA 29-30 *** Ciki ya shiga wajen Inna, suna zaune da suwaiba tana waya k'asa-k'asa, tana ganin shi tayi saurin shigewa daki, dariya inna tayi ganin ya bita da kallo tace "Dama ina jira shigowar ka, yaron da yake neman Suwaiba ne yace mata wai zai turo, shine nace bari na sanar maka dan kai yanzu ba zama kake ba." "Aure ya zo kenan, Allah ya sanya alkhairi." Yace yana daukar kwanon abincin sa, budewa yayi a wajen ya fara ci sama sama inna ke yi masa hira sai ta ga kamar bashi da walwala da nutsuwa ba baki daya, tunanin abinda ta aikata masa ne ya fado mata, tun jiya take fama da abin tun bayan saurayin Suwaiba yace zai turo, sai a lokacin tayi tunanin irin bacin ran da iyayen Maryam suka ji lokacin da ta aika aka ce musu sun fasa, bata taɓa auno abin a ranta ba sai yanzu da maganar Suwaiba ta tashi sai taji idan ita akayi wa haka dole abin da ciwo, shiyasa gaba daya ta rasa sukuni jiya sai yau ne ma da yake ta dan fita taji dama-dama. Tana ta tunanin taji ya ajiye kwanon ya na kokarin fita tayi saurin dakatar dashi "Zo ka zauna, magana zamuyi." Sai da ya fara kallon agogon wayar sa kafin ya dawo ya zauna ɗin yana fuskantar ta "Kayi hakuri da abinda zan fada maka, a matsayi na na mahaifiyar ka dole ne idan naga abinda zai saka a matsala nayi iya kar iyawa ta naga na tsare ka da abun, bansan ashe ba haka ya kamata nayi ba, ban kyauta maka ba Hafizu, kuma ban kyautawa yarinyar da iyayen ta ba, na manta Allah shine yake azurta bawa a duk sanda ya so, ni a ganina hakan shine maslaha ga dukkanin mu, ashe ba haka bane." "Wai me ya faru ne inna? Irin wannan wa'azi haka?" Murmushi tayi tace "A lokacin da naje Gumel sai nake bawa Baba Ladingo labarin halin da muke ciki, toh a gaskia ita ta bani shawarar cewa na tura ka chan Gumel din idan yaso sai na tura gidan iyayen yarinyar nace musu ka janye suyi wa yarinyar su aure..." Wata irin zabura yayi da jin abinda tace ba zato, "Na san halin ka sarai idan nace ka hakura ba zaka hakura ta sauki ba, shiyasa nayi hakan ni a tunani na shine daidai." "Innalillah wa inna ilaihi raji'un, yanzu inna dama aikawa kikayi kika ce na fasa? Haba Inna, haba Inna ya zakiyi hska? Idan suwai akayi wa haka inna ya zakiji? Wallahi inna ban taba ko da da rana daya tunanin matsalar daga mu ne ba, hakan tasa na kullece su kulla ta me ksrfi,kinsan halin da nake shirin sa kai na kuwa Inna? Innalillah wa inna ilaihi raji'un." "Tabbas nayi maka laifi, amma na riga ya wuce yanzu, kuma tabbas ban kyauta ba ko kadan, na biye wa  shedan tun da shine dama baya so ayi sunnar ma'aiki, in Sha Allah zan je kafa da kafa har gida na bawa iyayen ta hakuri na wanke ka kuma,ayi hakuri." Bashi da abinda zai ce kuma, uwa tafi gaban wasa, dan haka sai kawai ya tashi ya bar dakin yana jin kamar ya dora hannu aka yayi ta kurma ihu. Uban kiran da Asi ke tayi masa ne ya dawo dashi daga hayyacin sa, wannan shi ake kira tsaka me wuya, sai yanzu ya tabbatar da Hajiya Mero ba mutuniyar arziki bace, niyyar ta tayi amfani dashi ta cimma wata manufa tata kenan. Ransa ne ya kara baci ganin kira yaki karewa ya daga ya makala ta a kunnen sa "Kana ina ne wai? Kar fa ka raina mana hankali malam." A cunkushe yace "Gani nan zuwa ai ko? Kar ka damen mana." A tunanin Asi ya zata ya l Kashe wayar sai kawai ya jefa ta aljihu, Sambo ya kalla ya kwashe da dariya yace "Shegen yaron nan ba dai izza ba, shiyasa naji dadi zai yi daidai da aikin da muke so, gashi be san rufta shi muke so muyi ba, da zarar ya aikata zamu maida laifin kansa, kai baka san wani rainin wayo ma da mukayi masa ba fa, gidan da suke haya Hajiya ta siye shi sannan ta barmin nasa tsohuwa ta a ciki, shi kuma ta kaishi wani tsohon gidan ta in da take kai mutanen ta da." "Shegen kai, ashe kana nan kana dukan kan hajjaju,wato har gida ta baka mutumina, yanzu ka maida tsohuwa ciki kenan." Dariya ya shek'e da ita suka tafa "Wacce tsohuwa kuma ana zaune kalaou, gyara shi nake so nayi na samu na shek'e aya ta wallahi." "Shegen sama, ina yin ka wallahi, muje daga can mu jira shi." Kamar wanda aka dasa haka Hafiz ya tsaya kawai yana jin su, Allah ya taymaka yayi saurin danna recording tun fara maganar tasu, gumi ya sharce yana jin wani zafi na taso masa, wato Allah ne ya soshi dan ba karamin tarko sukayi niyyar dana masa ba kenan. Tashi yayi a gurguje ya shirya ya fito bayan ya kulle gidan ya dau hanyar in da zasu hadu yana ayyana yadda komai zai kasance. *** A tare suka kalli juna bayan sun zauna a motar, shigar da yayi ba karamin kyau tayi masa ba haka take ayyana wa a ranta, ashe shima hakan ce dan sosai yaga ta sake yi masa kyau ainun gashi a yadda ya lura da ita mace ce me son classy abubuwa tun daga shigar ta idan tayi zaka ga komai yayi matching tun ba yanzu ba ya lura da hakan tun tana gida balle yanzu da ta samu uban kaya masu kyau da tsari, wani irin farin ciki ne yake bin kowacce kofa ta jikin sa ga sanyin Ac da ya hadu da sanyayyen freshner da hadaddun turaren jiki dana kaya da ta hade jikin ta dashi sai ya chakude ya bada wani kalar kamshi na daban da be taba shaƙar irin sa ba, ita ma mutuniyar taku hakan ce ta faru da ita shiyasa ta koma tayi luf a jikin kujerar motar tana sake bude kofofin hancin ta tana shaƙar ni'imattaccen kamshin da zai iya saka ka bacci ba tare da ka sani ba. * (Jama'a turare Rahma ne, yana cikin main main Abu da yake saka annashuwa da farin ciki by the way ma ai kamshi is part of sunna in ban manta ba, tsafta Rahman ce, tsafta wajibi ce, kamshi yayi, try as much as possible a dinga turara kaya da gida dan ba karamin weapon bane to bring ur man close to u ba tare da ya shirya ba🚴🚴🚴🚴😂 Ghen ghen......na fece, Ohh wait na tuna ma, me son haddadden turare dan ubansu ya nemi *Miss Xoxo* *CEO YERWA* kenan gidan kamshi🤓 amma bata taba ban alakoro ba😂😂🤫🤭🤪)* A hankali yake driving d'in kamar baya son zuwa saboda yadda yake jin wata iri yar kasala be ki ba su kwana a haka, ganin da gaske abun na neman tabashi yasa ya lalubo hannun ta ya damke a cikin nasa, kashe mata ido ɗaya yayi ganin ya kalle shi. Har suka isa gidan be sakin hannun nata ba yana murzawa a hankali. Jin tsayuwar mota yasa Yaya Nabila fitowa da sauri, kamal dauke da Amna ya riko hannun Afnan, suna turo gate din suka gansu a tsaye, da sauri Ya Nabila ta karasa tayi hugging din  Maryam tana mata sannu da zuwa, duk kunya ta kama ta ta rasa ina zata saka kanta, haka dai ta daure tana ta yake baki suka shiga ciki. Kamal ne ya bigi kafad'ar Arkel ya kwashe da dariya. "Ango ango." Yace yana mika mishi Amna dake ta miko hannu ya dauke ta, Maimakon ya gimtse fuska kamar yadda ya saba sai kawai yayi dariya dan sunan angon ba karamin dadi yake masa ba yanzu, ya rasa dalili kuma amma yana jin dadi idan aka kira shi da sunan. Ohh su malam Arqe 😂🤭 "Ashe kana gida." Yace bayan ya zauna "Ina nan ango,ina zan motsa bayan kace zaka kawo maana amaryar, Madam ma tun dazu take kallon hanya saboda zumud'i." "Ah lallai, toh gamu dai, me aka shirya mana?" "Ba zaka ji a baki na ba,amarya ya gida ya komai da komai." Kanta a kasa ta amsa "Alhamdulillah." "Masha Allah, ya hakuri da kanin nawa kuma? Kinsan auta nasan yana nan yana taba miki halin nasa." Da sauri Arkel ya tabo shi "Auw wai so kake nayi shiru, kinga wai nayi shiru, Allah idan bakayi wasa ba sai na bata labarin nan." Jin haka yasa Arkel yayi saurin cewa "Allah ya baka hakuri Uncle, na tuba wlhi." Gaba daya suka kwashe da dariya har ya Nabila dake jera musu uban kayan kwalam da makulashe, "Allah Dear ka takura kanina." "Auw yar haka ce? Toh nima ai ga kanwata nan Maryam sai mu hade kai." "Ita ma tawa ce ai." Dariya aka sa gaba daya, sosai gidan ya birgeta dan kamal mutum ne me barkwanci ga fara-faran. Haka suka sha hira a gidan har wajen goma suna nan kamar ma basu da niyyar tafiya, tun Maryam na kunya har ta sake da yaya Nabila sosai dan daki suka shiga, da suka tashi tafiya ta haɗa mata kaya masu yawa har da yan kayayyakin gyara tayi ta jin kunya da tana mata bayanin yadda ake amfani dasu, haka suka fito sukayi musu sallama suka tafi, hankalin su dukka a kwance yake shiyasa suka shantake saboda Iya talatu yar uwar Alhaji tazo gidan zata kwana biyu kuma a dakin Ummi ta sauka dama chan ita din mutuniyar ta ce sun saba sosai. Tun zuwan Hajiya Mero gidan ne duk kowa ya ja baya da zuwa saboda bata son kowa ya rabi gidan da suka gano haka sai duk suka dauke kafa saboda gudun wulakanci. *** A yan kwana biyun da yayi yana shan magungunan sa ba karamin sauki yake samu ba, a hankali nauyi da yake ji a zuciyar sa yake raguwa kadan kadan tunanin gida ya fara zuwa masa kadan kadan shima dan ya kasa tasiri ne amma ga dukkan alamu koma menene yana gab da barin kansa,  Mustapha dai yana lura da duk wani chanji kuma yana sanarwa malam shiyasa komai yake tafiya a daidai cikin tsari da ka'ida, ko da yayi shaunin shan maganin da Mustapha ya tuna masa zai dauka yasha dan baya son yayi masa musu ko ya bata masa shiyasa yake bin komai yace. *** Daga nesa Hafiz ya hango motar, sauka yayi ya taka a kafa fuskar sa cikin wani irin yanayi da ba zaka iya tantance wane iri bane, hannu ya mika musu suka bashi a d'arare ganin yadda ya gimtse fuska kamar be taba dariya ba gashi dama irin giant din nan ne kallo ɗaya zakayi masa kaji ya maka kwarjini musamman idan ransa ya baci. "Kun tabbata dai sun fito ko?" Ya tambaya yana fadawa bayan motar "Hajiya da kanta ta tabbatar mana, kawai zaman jiran dawowar su zamuyi tun da baka zo ba har suka wuce." Bece komai ba ya kunna yar wayar sa ya makala earpiece yayi kamar baya jin me suke cewa. Gani dare ya soma yi yasa duk suka karaya suka fara tunanin ko ba zasu dawo bane, kiran Hajiya Mero Asi yayi ta sake tabbatar musu da su kara jira sunanan dawowa komai dare dan tasan ba zasu kwana a waje ba. Haka kuwa akayi suna nan a labe sai ga su nan sun shigo layin, face mask Sambo ya ciro ya wurgawa Hafiz, sai da ya fara bin ta da kallo sannan yayi ajiyar zuciya ya dauka ya saka. Duk a tare suka fito kowa rike da yar karamar bindiga mara harsashi a ciki, wani irin birki Arkel ya taka da ya sa Maryam dagowa da sauri "Innalillah wa inna ilaihi raji'un." Suka hau furtawa a tare, tsantsar tashin hankali ya rasa ya zai yi, kallon gefe da gefe yayi babu hanyar juyawa gashi baya sun tare, layin tsit baka jin komai sai karar injina dake wasu gidajen dake chan nesa dasu, knocking din glass din sambo yayi Asi kuma ya zagaya ta bangaren Maryam. "Buɗe malam." Sambo ya fada yana saita bindigar, da sauri ya sauke glass din kasa ya bude motar, "Fito." Yace masa a dan tsawace, kallon Maryam yayi da ta kankame hannun shi dan har ta fara kuka, ji yayi ya kasa fita, "Ba zaka fito ba sai na yi maganin ka ne?" Asi ya murde murya yayi maganar yana saita wa sosai akan maryam "Idan kana so ka ceceta ka fito daga motar nan, idan kuma kayi taurin kai zan saki kunamar bindigar na fasa mata kai." Da sauri Arkel yace "Me kuke so? Su waye ku waya turo ko?" "Tambayar mu kake kenan? Toh uban ka ne ya turo mu, ka fito ko ka tsaya bata mana rai?" Zai sake magana Sambo yasa hannu ya finciko shi da karfi, ihu maryam ta saka Hafiz yayi saurin sa hannu ya rufe mata baki, jan ya yayi har wajen motar sannan ya buɗe ya sakata ciki, hannun Asi na saman bakin sa dan karma yayi ihu, wajen zaman sa Hafiz ya shiga, ya tada motar bayan ya rufo kofar yadda Maryam ba zata iya budewa ba, ihu take tana bige bige tana rokan sa, wani irin karfi ne ya wa Arkel ya fincike, kan mtar yayi da gudu kafin ya k'arasa Hafiz ya juya da mugun gudu ya fita daga layin, motar dake tsare a bayan ta Arkel ɗin da suka tare kar yayi reverse sambo da Asi suka shiga suka taka ta da gudu suka bi bayan Hafiz saboda ba haka suka tsara ba sam.. Gudu yake baya ko jin kuka da nacin da take yi masa, shi kansa be san in da zai je ba, hanyar ya dauke musu ganin suna bin bayan sa, sai da ya ga ya bace musu sosai kafin ya zare abinda ke fuskar sa. A razane ta ce "HAFIZ!!!!" **** NOT EDITED, IGNORE ALL ERRORS. *29-30* S K ©*Hafsat Rano* *_ZAFAFA BIYAR na kudi ne idan kana son kowanne daga ciki ka nemi Wannan numbers din_* *08030811300* *07067124863* *_Daurin boye_* _safiyya huguma_ *_Buri daya_* _mamuhgee_ *_Wutsiyar rakumi_* _billyn Abdul_ *_Kai min halacci_* _Miss xoxo_ *_Sauyin kaddara_* _Hafsat rano_ 31 *ARADDAK NIYUAS* ©ONAR TASFAH ®RAYIB AFAFAZ 🤫🤭😂 *** Gudu yake sosai babu alamun zai tsaya, shi kansa be san in da yake kokarin zuwa ba sai dai abu daya ya sani dole ne ya taimake ta, dole ya nuna wa Hajiya Mero kuskuren da tayi na shiga gonar sa, kukan da take yi ne yake kara taba shi gashi Asi kiran sa yake ba kakkautawa ya rasa yadda zai yi. Ganin bata da niyyar daina kukan ne yasa shi daka mata tsawa da ta saka ta yin shiru da sauri "Kar na sake jin bakin ki, dame zanji? Mtsw." Yaja dogon tsaki yana gangara wa gefen hanya, karfe 12 ta gota garin yayi shiru sosai babu kowa sai yan tsirarin mutane da suka baro a baya, a saman sitiyarin motar ya dora kansa da yake ji kamar zai rabe masa biyu saboda tunanin mafita, kiran dake jerin gwanon shigowa wayar sa ya kalla ya yanke shawarar d'agawa kawai, a handsfree ya saka ta bayan ya daga, "Karamin kwaro, me kake tunanin ka aikata? Kana nufin ka lalata komai da muka shirya ko me?" "Abinda kake zato shine, na riga na gano komai da kuke shirya wa, ya kake tunanin zan goyi bayan ku bayan ni kaina amfani kuka so kuyi dani ku cimma manufar ku." Dariya sosai Asi yayi har sai da ya dau lokaci me tsawo kafin yace "Lallai kayi dabara, ashe kasan duk plan din amma ka biye mana, babban kuskure kenan na farko daka aikata, lallai ka taro match ɗin da babu ranar karewar sa, ko ka manta da tsohuwar ka da kanwarka suna karkashin ikon mu ne? Wai har ka manta fa ko? Dadi SOYAYYA hahahaha." Da sauri HAFIZ ta matso da wayar kunnen sa "Karka saka kowa nawa a cikin wannan abin, be shafe su ba ya tsaya iya ni da ku, kar ka kuskura kayi musu wani abu wallahi tallahi." A yadda yayi maganar Asi ya gane a rikice yake sosai, kuma ya tsorata, dariya ya sake kecewa da ita ya kalli Sambo dake gefe yace "Mu fasa kawai na tuna akwai yar chamas ɗin kanwar sa zatayi daidai da kai mutumi na." Dariyar shakiyanci suka kwashe da, roko da magiya Hafiz ya hau yi musu amma suka ki sauraran sa karshe ma suka kashe wayar baki daya. Cikin tsananin tashin hankali ya juya kan motar ya hau titin da zai mai dashi cikin gari, gudu yake yana innalillah wa inna ilaihi raji'un, Maryam kam gaba daya kanta ne ya kulle ta kasa gane in da suka sa gaba, me Hafiz yake nufi? Me kuma suna suke nufi? Idan har abinda taji daidai ne kenan Hafiz taymakan ta yayi kenan, toh amma ya akayi suka fara aiki tare? Bata da amsar, kadan kadan take goge hawayen dake faman sintiri a saman fuskar ta da gaba daya ta sauya saboda tsabar kuka, tausayin kanta da yadda in dan su Umma suka ji labari yadda za su ji kawai takeyi, bata san me yasa ba amma a kasan ranta tana jin kamar da sa hannu Hajiya mero, idan haka ne kuwa to tabbas Hajiya Mero bata cikin jerin mutanen duniya basu hankali, bata ki ba, zata iya sakata a jerin mugayen mutanen bara gurbi masu fuska biyu. Sake takure jikin ta tayi ganin yadda yake gudu da su ko tsoron rayuwar su baya yi, babu wanda yake yi sai kiran layin Suwaiba dake nuna alamun waya take gashi ba bata yi activating call waiting ba balle idan ta gama ta ga misscals ɗin, haka ya cigaba da gwadawa har suka shigo cikin gari sosai still amsar daya ce, ya rasa yadda zai yi, yana son taimakon Maryam sai dai kuma wani sashi na zuciyar sa na tuna masa su waye inna da suwaiba a wajen sa, kallon ta yayi tausayin ta na sake shigar sa, abu daya yake ganin shine kawai mafita shine ya kira mijin ta ya ajiye a wani wajen yazo ya dauke ta shi kuma ya wuce wajen su Inna, baya so sanadiyar sa wani mummunan abin da zai tarwatsa farin cikin Kanwar sa ya faru, ya san ba zasu taba yafe masa ba kuwa idan har gaskiya tayi halin ta. "Bani number Mijin ki." Daga sama taji maganar sai bata gane ba, sake kallon ta yayi ganin bata da alamar bashi yace "Number mijin ki nake so, ya kamata a dan zaman nan ki fuskanci ba cutar dake zan ba, mafita zan neman miki." "Babu waya a hannu na ai." "Baki haddace ba?" Daga mishi kai tayi tana janye kukan dake taso mata, dukan sitiyarin motar yayi da dan karfi ya danna kiran Asi, ringing d'aya ya daga yana kara wayar a kunnen inna "Tsohuwa yi magana da mara kunyar danki." "Hafizu, Hafizu, dan girman Allah kayi sauri kazo, kar suyi wa Suwaiba illa dan Allah Hafizu, innalillah wa inna ilaihi raji'un...." "Inna... " Warche wayar Asi yayi yasa dariya "Ka tsaya wajen mace ka bar su anan, toh ai shikenan tun da haka ka zaba, Sambo muje da ita in yaso sai mu bar masa tsohuwar." "Zan ƙaraso yanzu, ku jirani dan girman Allah." "Minti nawa?" "Goma, ko sha biyar." "Na baka ishirin, Ina jiran ka." Ya kashe wayar yana kallon inna da suwaiba dake takure a gefe. "Kiyi hakuri bani da ishashen lokacin da zan iya kai ki gida na kuma taimaki mahaifiya ta da kanwata, na miki alkawarin taymaka miki amma kiyi min wannan alfarmar." Toshe bakin ta tayi jin wani kuka ya taso mata, tayi saurin yin kasa da kanta dan kar ya gani. Cikin mintunan da basu ga za goma sha shida ba ya karasa unguwar tasu, motar su ya hango  a gefen gidan yayi saurin yin parking, "Ki zauna a ciki ina zuwa." Kwantar mata da kujerar yayi baya ya fita bayan ya rage mata glass din yadda iska zata shiga. *** Kamar zai yi hauka haka yaji, gudu yake yana bin su har suka tsare masa saboda mota da kafa ba abu daya bane, haki yake sosai numfashin sa na neman dauke wa, yanzu ta ina zai fara neman ta? Ya zai yi? Yana kallo aka tafi da ita ya kasa aikata komai. Wanne irin miji zai kira kanshi kenan? Haka ya juyo ya dawo in da ya bar motar sa, wayar ta ya gani a yashe a kasa yayi saurin dauka yana kankamewa, wa zai kira ma? Ya shiga tunani, da sauri ya danna kiran Kamal dan shine kawai mafitar sa, yana zaune yana duba wayar sa yana ganin kiran Arkel yayi saurin d'agawa "Lafiya?" Yana d'agawa abinda yace kenan, dan duk wanda ya ga kira a irin wannan lokacin ya san babu lafiya, muryar sa a shake chan ciki kamar alamar kuka-kuka yace "Sun tafi da ita." Da sauri kamal ya mike, "Ban gane ba, su waye? Kuma wa?" Kasa magana yayi saboda yadda numfashin sa ke hawa da sauka, sosai Kamal ya rude ya shiga tambayar sa yana ina, da kyar ya iya bashi amsa ya koma jikin motar yana jingina da kansa. Kuka yake so yayi amma ya kasa, yana nan tsaye ya hango hasken motar kamal, da sauri ya karaso wajen ko kashe motar beyi ba ya fito da sauri yana riko shi "Ya akayi Arkel? Ina Maryam ɗin me ya faru?" Tun daga farko ya fada mishi abinda ya faru, kafin ya riko hannun kamal ɗin hawayen da yake makale wa a idon sa ya samu damar fitowa. "Yanzu ya zamuyi? Ta ina zamu fara neman ta? Abu har cikin unguwa, kuma kace basu taba lafiyar ka ko tata ba?" "Basu yi mana komai ba, ita ɗin kawai suka dauka, idan kudi suke so ko motar da sai su dauka ai amma why ita? Me yasa?" "Innalillah wa inna ilaihi raji'un, na rasa me xance ga dare ya soma yi ina zamu fara?" Mota suka shiga suka bi hanya ba wai dan suna tunanin zasu gaan su ba, gaba daya Arkel ya rikice masa har wasu maganganu yake da be san yana yi ba saboda tsabar yadda abin ya taba shi. Duk iya tafiyar da sukayi babu ko alamun su, maimakon su koma sai kawai Arkel yace su tafi gidan su maryam ɗin, "Baka ganin tada musu hankali zamuyi a daren nan? Me zamu ce musu? Yar su an sace ta? No be kamata ba ai, mu jira gobe dai mu gani idan Allah ya kaimu." "Yanzu ita kadai zata kwana a wajen su? Ita kadai? innalillah." "Addu'a zamuyi kawai, in Sha Allah babu abinda zai faru." Hannu kawai ya dora aka yana juya shi cikin tsananin tashin hankali. Juyawa sukayi suka koma gidan Kamal ɗin, yaya Nabila bata san me ake ciki ba sai da kamal ya taso ta bayan sun shiga gidan, aikuwa sai da yayi danasanin tashin ta dan kuka ta saka musu wiwi abun ka da mace. Arkel kuwa juya kansa kawai yake shi kadai ya san me yake ji, duk sanda ya tuno tana waje tare da wasu maza sai yaji hankalin sa ya kara tashi fiye da yadda yake a da. Ganin bashi da mafita yasa ya shiga toilet ya dauro alwala ya tada sallah. *** Bayan an gama taskar labarai Baba ya kashe radio, bacci ne yake daukar sa daga zaune yana neman kwantar dashi, Umma kuwa da yake yau ta fita kasuwa da wuri tayi bacci saboda gajiya saboda haka gidan yayi tsit babu motsin kowa in ka cire radion Baba data zama kamar wajibi a gareshi duk daren duniya sai yaji shirin siyasa da labarai har zuwa lokacin da za'a gama taskar labarai sannan fa yake kashe wa ya kwanta. Kwanciyar sa kenan Umma ta farka a dan firgice, kallon ta yake har ta nutsu tana ta faman sharce gumi, muhucin dake gefe ya jawo ya mika mata kafin yace "Da alama dai yau bakiyi addu'a ba ko?" "Nayi wallahi, wani mafarki nayi mara dadi wallahi akan Maryam." "Mtsw." Ya ja dan gajeren tsaki yace "Shedan ne, Maryam da tana gidan ta, me zai same ta? Ki sake addu'a ki juya ki chanja bangaren da kike kwance, babu abinda zai faru mafarki ai ba gaske bane." "Haka ne, abin ne da ban al'ajabi." "Allah ya rufa asiri." Kawai yace ya juya ya kwanta yana addu'a. Shiru umma tayi tana tunanin mafarkin, sosai abin ya tsaya mata a rai, ganin ko ta kwanta ba baccin zatayi ba yasa ta tashi ta fito tayi alwala kawai gwara tayi nafila ko ta samu saukin abin da ya tsaya mata a rai. *** A zaune ya tarar dasu kowanne ya dora ƙafarsa akan kujera, Inna da suwaiba na durkushe a kasa sun hana su kwakkkwaran motsi,  suna ganin shi suka kwashe da mahaukaciyar dariya "Aka ce baka ji?" Sambo ya fada yana dariyar shakiyanci. "Ina take?" Asi ya fada bayan ya mike yana tarar shi Runtse idon sa yayi kawai yace "Tana mota." "Ka tabbata?" "Kuje ku duba mana." "Owk muje." Da sauri inna tace "Ina zaki kaishi?" "Old woman, danki fa yanzu ya zama nama, ya shiga fadan da ba nashi ba, kiyi ta addu'a kawai ya fi karfin mu." Kuka inna ta saka, da sauri ta rufe bakin ta ganin ya nuno mata bindiga. "Karki tara mana jama'a mana tsohuwa." Kan Suwaiba Sambo yayi ya riko hannun ta yana murmushi "Allah oga babe din nan ta min fa , a lamunce min." Kaga Hafiz yasa ya bige hannun sa "Karka kuskura ka sake taba ta wallahi, muje kuyi abinda zakuyi ku wuce kawai." Kallon Asi Sambo yayi, daga masa kai yayi alamun ya share kawai, "Shikenan." Kawai yace yana gid'a kai kamar kadangare. Fita sukayi Hafiz ya jawo kofar gidan ya rufe ta waje, dariya suka kwashe da ita Sambo ya nuna masa key din hannun sa "Muna da spare ai." Motar suka nufa kirjin Hafiz na bugawa sosai, wayam babu kowa a motar, da sauri Asi ya kalle shi, boyayyiyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya sake leka motar don san tabbatar wa, babu ita babu alamar ta, kenan ta gudu? Amma ina ta tafi a wannan daren? Beyi niyyar barin ta dasu ba, tare yayi niyyar su tafi duk in da zasu da ita, amma kuma dama ba kowa ne zai zauna ba, ka zauna zaman me kenan? Dole ka nemi hanyar da zaka kubutar da kanka. "Ina take.? Kai karamin kwaro har ni zaka raina wa wayo." "Me yasa zan yi maka karya bayan ba tsoron ka nake ji ba? Na kawo ta har nan, bansan kuma me ya faru ba bayan shiga ta." Hade rai yayi dan kar su ga alamun wasa ma, shiru sukayi suna tunanin gaskiyar maganar tasa, "Mu bi hanya kawai." gani yayi kawai sun shiga mota sun bar layin. Kalle-kalle ya farayi yana tunanin in da zatayi a wannan daren. 😭😭Maryam. *** Tsawan daren babu wanda ya runtsa, Hajiya Mero tayi ta kira Asi amma ya kashe wayar sa gashi babu Arkel babu Maryam ɗin da alama dai sun cika aikin su, Allah Allah take gari ya waye taji ba'asi, in Sha Allah ta gama da Maryam kenan,sai daji da abinda yanzu yake gabanta na hada auren Arkel ɗin da Zainab dan cimma babbar manufarta. Arkel kuwa tun asubah bata karasa ba yayi alwala yana zaman jiran a kira, anan kira kuwa ya gabatar da sallar sa ya fito, be jira fitowar Kamal ba ya kama hanyar gida, yana zuwa ya shige daki ya hautsuno komai, takardar da mutumin nan ya kawo mishi ya fito da ita ya sake dubawa sosai, ko zai gano wani abu, be gani ba haka ya fito ya koma wajen su Buzu, basu ko tashi ba ya buga musu, buzu ne ya fito da sauri dan be san sanda bacci ya dauke shi haka ba,yana ganin Arkel a tsaye gaban sa ya fadi yasan babu lafiya, cikin in da in da yace "Ranka... ya.. dade." "Ina habu driver?" "Yana ciki yallabai." "Mutumin ranar nan, ya akayi ma ya gudu ne?" "Am amm ni dai lokacin na shiga wajen Hajiya ne zan duba abu toh kafin na dawo sai na tarar ya gudu." "Aikin ka a bakin kofa ne ko a cikin gida." Zaro idon sa yayi "Ai Hajiya ce tace na zo na duba mata." "Habu fa?" "Am am shi kuma kamar shima ɗin Hajiya ce ta aike shi ranar, na dai manta." "Ka manta kace!??" "Eh...eh, a ah na tuna ma, tabbas ita ta aike shi ya siyo mata masa,saboda bayan ya dawo ma mu ta barwa masar tace muci." Be yi magana ba kawai ya juya ya koma ciki, computer din sa ya dauko ya jona da wata yar karamar na'ura, kasan kayan takardun sa ya daga ya dauko takardar da yake ta ajiyar ta tsawon wannan lokacin, zama yayi a gaban ta yana bada dukkan hankalin sa akanta. Komai ya fara ne daga ranar, ranar da ta zama ainihin ranar da ke cike da babban kalubele, babban al'amarin da yayi sanadiyyar ruguza komai na wannan family, sanadiyyar shigowar ta rayuwar su, da dalilin ta na ganin bayan wani me numfashi a cikin ahalin nasu. Are You guys ready for this? Hmmm rugumtsumi ya fara. Me arkel yake shirin aikawata? Kar dai?????? Ba ruwana🚴🚴🚴 *** Mustapha na zaune ya zuba mishi ido ganin yadda duk birkice dakin, babbar jakar sa data fi kowacce girma yake kwashe kayan sa yana zubawa a ciki, har ya gama be ce komai ba ya tattara komai ya ajiye a gefe yana rike kugunsa, dubawa yake ko akwai abinda be dauka ba. Ganin ba shi da niyyar magana yasa mustapha cewa "Man me kake shiryawa ne wai?" Hannun sa ya saki ya juya falon, chan sai gashi ya dawo dauke da wani k'aton kwali, dire shi yayi kansa na sake daukar zafi, lek'awa Mustapha yayi yaga menene a ciki, duk wasu tarkacen kayan shaye-shayen sa ne a ciki. Da ido ya nuna masa su kafin yace "Wannan fa? Duk na menene.?" "Ko kana so ne? Wannan uwar tambaya haka?" Dariya Mustapha yayi kafin yace "Ah sun fi karfi na, kune manya ai." "Dah kenan, Please anjima kadan zaka yi dropping dina a airport." "What did you mean, Ina zaka haka unexpectedly?" "Kano!." Ya amsa masa boldly yana shigewa toilet. Mustapha be san sanda yayi tsalle ya dire ba saboda murna. Ghen ghen. Hajiya mero we are coming for u🚴🚴🚴🚴🚴💃💃💃💃💃💃 Three against 1 Masha Allah Ku fito wasan zai fara. This is just a halfway #Arkel #Arab #Hafiz Masu tambaya Novels dina zaku iya shiga link din nan na wattpad zaku samu in sha Allah. ttps://my.w.tt/ALaIc4HB43 Dont forget to follow please. Thanks [3/18, 22:26] Hafsat Rano: *SAUYIN KADDARA* *32-33* ©*Hafsat Rano* *_ZAFAFA BIYAR na kudi ne idan kana son kowanne daga ciki ka nemi Wannan numbers din_* *08030811300* *07067124863* *_Daurin boye_* _safiyya huguma_ *_Buri daya_* _mamuhgee_ *_Wutsiyar rakumi_* _billyn Abdul_ *_Kai min halacci_* _Miss xoxo_ *_Sauyin kaddara_* _Hafsat rano_ *** Sai data tabbatar da shigar sa ciki sannan ta fito da sauri, gudu ta saka iya kar karfin ta, sai data yi gudu sosai sannan ta fita bakin titi, wani me adaidaita sahu daya dauko passenger daga airport ya juyo zai gida yana ta sauri, tana hango haske ta shiga daga masa hannu,  kamar ba zai tsaya ba sai kuma ya ga mace ce, gashi daf yake da shiga gida, tausayin ta yaji ya tsaya, sai dai unguwar da tace ne yayi masa nisa, ganin ya tsaya yana tantama yasa tace ya kaita gidan anty Maryam bayan ta tambayi sunan unguwar da suke dan ba ma gane ina take tayi ba. Da sauki yafi kusa akan gidan su data ce masa da farko shiyasa ya amince ya dauke ta. Har suka isa tana ta addu'a ga mugun tsoro daya cika ta, tunanin ta daya halin da yake ciki, kadan kadan take share kukan da yake sauko mata har suka isa, knocking tayi bayan ta rok'i ya tsaya a bude mata saboda tsoro, daidai lokacin Mijin Anty Maryam na shirin kwanciya yaji ana bugu, kallon lokacin yayi cike da mamakin me bugawa, har ya share yaji bugun yayi yawa kawai yayi shahada ya tafi budewa "Waye?" Ya fada yana dan tsaya wa kafin ya k'arasa kofar, jin Muryar Maryam yasa yayi saurin budewa yana kallon ta ta dan hasken daya leko, "Subhanahi, Maryama? Kece? Shigo ciki." Shiga tayi ya kalli me dan sahun "Sannu malam, an gode sosai, bata sallame ka ba ko? Bari nazo." Ciki ya koma ya dauko kudin ya bashi ya sake masa godia sannan ya rufe gidan ya koma ciki da sauri, tana rakube a gefe Anty Maryam ya shiga ya taso yau tun wuri ta kwanta saboda rigimar da twins sukayi ta mata, daga zuwa ta lallaba su ta bige da bacci, a gigice ta taso ta fito tana salati. A gaba suka sakata da tambaya duk sun dauka ma ko matsala suka samu, labarin abinda ya faru ta basu cikin tashin hankali Anty Maryam take salati, bata san abin ya kai har haka ba, sun jima suna maida zancen kafin su kwanta a zuwan a bar wa gobe komai. Kasa barci tayi tana tunanin halin da yake ciki, ita tsoron ta daya kar suyi masa wani abu, ga Hafiz ma da take tuno ko ya zasu kwashe da su, har asubah tayi tana abu daya, tashi tayi ta yi sallah sannan ta zauna tana jira su tashi. *** A hankali yake kallon ko ina yana sake shaƙar iskar dake busawa kadan kadan, iska ce me cike da ni'ima irin yanayin zafi-zafi hade da iska, kwallar da ta taru a idon sa yasa hanky ya goge yana tuna lokacin da ya bar gari, lallai gaskiyar bahaushe da yace kowa ya bar gida, gida ya barshi. Wayar sa ya jawo yana kokorin duba Bolt, sai dai sam ntwrk din yaki bashi hadin kai, tsaki yaja ya kalli uban kayan dake gaban sa, hannu ya yarfe ya shiga waige-waige kamar me neman wani abu. Daga nesa ta hango shi tayi saurin taka birki, kallon ta Hidaya tayi da sauri. "Ya dai Lubna?" "Babe kin ga wani handsome? Ohh my G... He's so handsome." "Handsome kuma? Aina?" "Bari kiga kawai." Balle murfin motar tayi ta fito tana gyara nadin veil din ta, har ta karaso gaban sa be ma lura ba, duba wayar sa kawai yake yana jan tsaki saboda sam babu ko alamar network ɗin ma zai dawo. "Hi handsome!" Dan kallon ta yayi ya kauda kai "May i help?" Tace tana kallon kayan dake gabansa "Be my guest." Ya amsa mata yana sake duba wayar sa Kayan ta hau ja ganin tana kici-kici yasa ya rik'e da sauri, idon su ne ya hadu da juna yayi saurin basarwa "Karki damu zan samu taxi." Marairaice fuska tayi tace "Please allow me to help handsome." Dakata tawa yayi yana sake kallon ta "Please." Ta hade hannayen ta Dauke kai yayi ya ja kayan ya nufi motar ta, a booth suka zuba kayan ta bude wa Hidaya kofar. "Please koma baya kinji." Kamar zatayi magana sai kuma ta fasa ta bude ta fito, shiga yayi ya zauna sannan ta ja motar suka fita daga airport din. "Ina mukayi?" Ta tambaya tana saita mirror sosai "Are You Serious? Dama wai baki Sanni ba amma kika dauko ni a motar ki?" Dariya tayi kawai bata ce komai ba "Owk ki aje ni anan sai na samu cab." "No Dan Allah bari na ajiye ka, ka dawo daga tafiya ka kaya Please Please." "Owk janbulo." Runtse ido yayi daya ambaci sunan unguwar. Be sake magana ba ya hau tunanin yadda zata kasance *** Tun da ya fara kalla har ya gama yana share gumi saboda tsabar yadda ya rikice, da kyar ya daure ya karasa kalla, tsawon wannan lokacin yana ajiyar shi be taba ko da tunanin duba wa ba sai yau, be taba tunani ko kawo hakan a ransa ba, ya san dai tun daga dawowar sa daga crossriver ya saka ido akan komai, duk wani abu da yake faruwa ya sani tun daga kan magungunan da komai ma, hatta ranar da suka tarar da Hajiya mero a dakin Ummi ya ga komai yadda ya wakana, tun daga lokacin ya sake bata wani babban matsayi a ransa, akwai babban dalilin sa na boye komai bayan komai ya bayyana, gashi yanzu ya gama hada komai, yayi mata kofar rago ya kamata da hujja, a yau ba gobe ba zai damka su a hannun da ya dace, ya daura damarar yakar duk wani me hannu a ciki. Yana gama duba komai ya rufe yana mik'ewa, toilet ya shiga ya dauraye fuskar sa kawai ya yi fito,kayan jikin sa ya sauya ya rufo kofar, kallon dakin ta yayi, duk babu dadi, girgiza kai yayi ya wuce kasan, dakin Ummi ya buda Baba na zaune tana goga goro a mogogin karfe irin na iyaye da kakanni, Ummin kuma na kwance kamar ko yaushe sai dai yau tayi wani iri da ya kasa gane dalilin hakan, gaishe ta yayi ya duba ummin sannan ya juya ya fito duk da yana tunanin abinda yake shirin yi shine daidai sai dai yana jin tausayin Ummin matuka , tsawon wannan lokacin tana a wannan halin da yake dashi da marabar sa da mutuwa banbancin babu yawa. Hajiya Mero na jin sa tayi saurin fitowa daga in da take labe, dan ta sake tabbatar da komai, shirin yi masa magana take kawai ya fice be ko kalle ta ba, murmushi tayi ta sake danna wa Asi kira, a kashe dai har yanzu gashi babu wani bayani gamshasshe da taji daga gare su, hakan yasa hankalin ta yaki kwanciya sam tana tunanin ko an dace ko akasin haka. Hakan ya saka ta a tunani. Yana fita ya kira wayar, yana kashewa ya maida ita aljihu, a kafa ya taka har titi ya tari abin hawa. Daidai Arkel Poultry farm ya ajiye shi ya sallame shi ya taka ciki yana jin kansa na dan masa dum, Salim na tsaye daga waje yana jiran sa. "Ka same shi?" Abinda yace masa kenan yana kallon ciki alamun ba shiga zai ba "Eh yana jiran mu ma." "Owk." Gaba kawai yayi salim ya bi bayan shi, sai da suka dade a titi sannan suka samu abin hawa, suna tafe shiru kamar kurame babu me cewa wani kala har suka isa. Yana tsaye a kofar gida yana jiran su dama, da fara'a ya sauke su, suka gaisa sannan ya shigar dasu gidan, tabarma ce a shinfide a tsakar gidan da alama su ake jira ga rana nan ta fara fitowo sai dai bata tadda in da suke ba, sai daya fara cire takalmin ƙafarsa sau ciki sannan ya ajiye a gefe yana zama hade da tankwashe ƙafafuwan sa. Daki ya shige chan ya fito da komai ya zube gabansa, salim ne ya mike yana dan rissinawa "Oga bari na jira ka a waje." Daga kansa yayi bece komai ba har ya fita sannan ya mai da kallon sa wajen mutumin yana sake gyara zama. "Malam Nagode kwarai da duk taymakon ka, komai ya tafi yadda muka tsara, sai dai matsalar data faru jiya bata cikin shirin mu, shiyasa na kasa hakuri ina ganin lokaci yayi da komai zai bayyana." "Gaskia ne, an dade ana ruwa ƙasa na shanye wa, kuma tabbas kayi hakuri ka bi komai a sannu har Allah ya nuna maka komai, tabbas kai jajirtacce ne me nagarta, a yau ni kaina ina goyon bayan komai da zaka aikata, sai dai ina baka shawarar kabi komai a sannu, har mu kai in da muke san xuwa, kaga idan ta warware daga nan zamu ji ainihin yadda komai yake.." "Haka ne." "Amma sai dai wani hanzari ba gudu ba... Kira ne ya shigo wayar sa, kurawa number ido yayi yana tuna in da ya san number, ganin ya kasa ganewa yasa shi daga wa. Da sauri ya mik'e annurin fuskar sa ya sauya zuwa tsantsar farin ciki, yana ajiye wayar ya kalli malam yana kunshe murmushin sa. "Zan je na dawo anjima in Sha Allah, duk yadda mukayi da shi zan sanar maka." "Hakan yayi, Allah ya taymaka ya bada sa'a." "Amin." Da sauri-sauri ya fita, salim na ganin sa ya taso. "Mu wuce ko? Na kira yace yana jiran mu tun dazu ya zo." "Kira shi kace yayi hakuri zan kira shi, an samu change of plan abinda zamuyi magana akai zan je naji, pleasd ka bashi hakuri it's urgent ne " "Owk ba damuwa, bari na sameshi kawai achan din, in ka gama sai muyi waya." "Owk... Ga kamal na kira na ma, sai mun yi magana." Kara wayar yayi a kunnen sa "Wai kana ina ne? Mun tashi babu kai gashi ya kamata muyi reporting case din as soon as possible." "Haba, sai nayi ta zama sai kun tashi, my wife gone missing ai banga ta bacci ba." "Haushi kaji? Please kayi hakuri wlhi makara mukayi kasan bamuyi bacci ba sai wajen asubah ya sace mu dukka, ka gan mu ko breakfast mun kasa yi wallahi, ina ta kiran ka Kuma not reachable." "Ba damuwa, zan kira ka anjima, kace mata ta kwantar da hankalin ta, yanzu ina sauri ne akwai in da zani." "Arkel!?" "Just pray for me, sannan dan Allah kar kowa yaji maganar, she's fine and healthy tana gidan aunt din ta ma, zanje chan ne, sannan maganar Barr. Nasir Kayi mishi magana Please." "Ahh Alhamdulillah, shi yasa naji kanin nawa strong, jiya kuwa baki ya mutu murus." Dariya yayi "Sai anjima." Be wani bata lokaci ba ya isa kofar gidan, yana zuwa ya kira Number Mijin Anty Maryam, yana ciki sai gashi ya fito, da sauri ya rissina ya gaishe shi, hannun sa ya kamo ya riko cikin nasa suka shiga gidan, duk da safiya ce amma komai an gama gyara shi neat har turaren wuta an saka sai kanshi gidan yake, a gefen kujerar ya dan saka jikin sa hankalin sa gaba daya ya koma kan kofar dake cikin falon wanda ta nuna alamun nan ne ainihin cikin gidan, kayan breakfast aka hau jere masa sai dai shi sam hankalin sa baya kansu, so yake ya ga ta in da meron sa zata bullo, ganin ta ne kawai zai tabbatar masa da tana gidan da kuma kwanciyar hankalin sa, da hira ya ja shi ya dai daure yana amsawa duk da tarin abubuwan da suke kansa a yau gashi babu ishashen lokaci hakan ya hakura da yana sake duba hanya, be ko kalli abincin ba, ganin haka yasa ya kira Anty Maryam, tana fitowa yace "Kuzo tare da Maryamu." Boyayyiyar ajiyar zuciya ya sauke ya kuwa kafe hanya da ido, Anty Maryam ce a gaba tana bin ta a baya fuskar nan ta kode saboda kukan data sha jiya tayi fayau da ita babu komai a kan fuskar ko arzikin powder balle lipgloss, babu yadda Anty Maryam batayi da ita ba akan ta dan shafa ko kadan ne kemaimai taki haka ta fito duk idanun kuwa sun kumbura. Akan shi ta fara dora idon ta, shi din ma hakan take, tsadadden murmushi ya sakar mata me narkar da zuciya, da sauri tayi kasa da kanta dan yadda taji sakon nasa har tsakar kanta, ya gane sarai yadda hakan yayi tasiri a tattare da ita sai kawai ya basar ya cigaba da jujjuya hannun sa har suka zauna. Alhaji Muhammad Rabi'u ne (Mijin Anty Maryam) ya fara bayanin abinda ya faru daren jiya, zuwa lokacin da Maryam ta sanar musu abin da ya faru, daga karshe ya dora "Gata nan sai ta sake sanar damu dukka abin da ya faru bayan barin ku." Tsuru tayi kunya duk ta kamata, tana lura da dukkan motsin sa yana kanta, ga wani irin kallo me wuyar fassarawa da yake aike mata dashi, sai da Alhaji Rabi'u ya sake magana sannan ta shiga bayani bayan guduwar Hafiz da ita. Har ta gama idon sa na kanta ko kiftawa bayayi, wani abu me kama da mayan karfe yaji yana fusgar sa zuwa gare ta. Anty Maryam ce ta yi magana sannan ta bada shawarar lallai a tsaurara bincike sannan Maryam ta zauna anan har zuwa lokacin da komai zai daidai ta, in yaso ita kuma sai ta je ta sanar wa gida abinda yake faruwa. Duk abinda akace be musu ba saboda hakan ma duk wani tsari ne nasa, hakan kuma shine zai kara wa komai sauki. Tashi Alhaji Rabi'u da Anty Maryam sukayi suka basu guri, shi gaba daya ma Alhajin ficewa yayi daga gidan dan dama ya riga ya shirya daga nan zai wuce kasuwa ya samu Baban su Maryam ɗin ya sanar dashi komai. Thanks da uzurin ku, jiki alhamdulillah naji sauki Nagode kwarai. _ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU😁._ *ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma *SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano) *KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo) *BURI ƊAYA!* (Mamu gee) *WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull) 👇🏻karku bari ayi babuku *ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu* *za'a tura kudin ta wannan accnt number din* Hafsat kabir umar 0225878823 GT bank Saika tura shaidar biya ga wannan number ta WhatsApp 08030811300 Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din 07067124863 Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya. *Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon Rano🚴🚴🚴 *** [3/18, 22:26] Hafsat Rano: *SAUYIN KADDARA* *34* ©*Hafsat Rano* *_ZAFAFA BIYAR na kudi ne idan kana son kowanne daga ciki ka nemi Wannan numbers din_* *08030811300* *07067124863* *_Daurin boye_* _safiyya huguma_ *_Buri daya_* _mamuhgee_ *_Wutsiyar rakumi_* _billyn Abdul_ *_Kai min halacci_* _Miss xoxo_ *_Sauyin kaddara_* _Hafsat rano_ *** Suna fita yayi saurin dawowa kasa in da take zaune, sosai ya matsa daf da ita, ƙafarsa na gogar ta ta. Murmushi tayi ya sa hannu ya riko fuskar ta "Sannu." Yace yana murmushi "Uhum." Ta amsa ta a sake kasa da kanta "Babu wani abu da yayi miki? Babu in da ke miki ciwo?" "Umm babu." "Are you sure? No bari na duba na gani." Hannu yasa zai daga dan mayafin da ta yafa a saman kanta tayi saurin rike masa hannu tana marairaice murya "Allah ba komai fa." "Toh bari na duba da kaina mana, me kike tsoro.?" "Ni ba komai, kawai dai." Dungure mata kai yayi yasa dariya "Bafa abinda kike tunani bane, so nake naji wani flavour be da turaren da kika sa." Ido waje ta kalle shi, wai flavour, har wani flavour ne da turare kenan? "Baki sani ba kenan? Yar kauye." Dariya suka saka a tare "Me kika sani game da matsalar ummi?" Daga sama taji tambayar, gaba daya sai ta duburburce dan bata zata ba, ganin yadda tayi ne ya sake fahimtar lallai ta san wani abu akai, be zai matsa mata ba amma zai nemi taimakon ta nan gaba, tunanin yadda zata sanar masa take a zuciyar ta, tsoron abinda zai je yazo takeyi ga shi bata san yadda al'amarin zai juye mata ba, wasa take yi da hannun ta tana kisisima yadda zatayi sai kawai taji yace "Ki adana duk abin da kika sani zuwa wani lokaci kadan, i ll need ur help kinji?" Kallon sa tayi ya daga mata kai "In Sha Allah." Tace a hankali "Thanks dear." "Bari na tafi, zan dawo da daddare, ayi min tuwo kinji?" "In kuma ba tuwo za'a yi ba?" "Dama ai ba ina nufin ayi dukka ba, ke zaki yi min nasan dai Anty Maryam ba zata hana ba, zan shiga busy ne ba lallai na samu naci ba, and kinsan ni da abinci dai musamman tuwo." "Allah ni ba wani son shi nake ba." "Whatever, ni dai ina so." "Owk tam." "Good girl, yi wa Anty magana zan wuce." Tashi tayi ta shiga ciki ta sanar wa Anty Maryam zai tafi, fitowa tayi sukayi sallama sannan ta koma ciki, kudi ya dauko ya mika mata ya juya hannayen sa zube a cikin aljihun sa, har ya kai kofa ya juyo ganin ta a zaune bata taso ba, bata fuska yayi tayi saurin tashi dan ta san nufin sa, a harabar gidan suka tsaya jim sannan ya mika mata hannu alamun ta bashi nata, a kunyace ta mika masa ya rike cikin nasa yana dan murzawa a hankali a hankali. "Ki kula da kanki, just three days zakiyi anan, i ll come and take you home." "Owk Tam." Murmushi yayi mata ya saki hannun ta ya juya ya fice gaba daya, sai da taji gaba daya komai ya tsaya mata, wani irin abu me kama da iska na kada ta, gaba daya sai taji dama kar ya tafi suyi ta zama a haka, he's so cool and nice, dama an ce ba zaka taba sanin ainihin halin mutum ba sai kun zauna, ita da ganin mutum me tsauri take masa, sai yanzu ta gane baya son wasa da aikin sa kuma da gaskiyar sa shi kadai yasan wahalar da ya sha kafin ya tara, ajiyar zuciya ta sauke ta koma ciki jiki a sanyaye duk sai taji ta nemi walwalar ta rasa, sai da Anty Maryam tayi ta jan ta da hira sannan ta saki jikin ta. Da yamma likis sai ga umma ta zo gidan bayan sunyi waya an sanar mata da abinda ke faruwa. *** Ya kasa zama sai zagaye yake yana tunanin mafita, ya san tun da hakan ta faru Asi ba kyale shi zasuyi ba, damuwar sa daya su Inna gashi duk sun tsorata sosai, tunanin yadda zai yi dasu yake idan yaso shi sai ya nemi Arkel ya sanar dashi komai idan ma abu ya baci dai zai taimaka. Shawarar ya yanke kawai ya shiga gidan, Inna na jin sa ta taso da sauri dama zaman jiran sa take shiyasa yaki shigowa gidan ya tsaya a waje, "Hafizu, me yake faruwa? Me ka aikata musu kuma menene hadin ka dasu?" "Inna?" "Ka fada min kawai, wanne irin bala'i ka jajibo mana? Na shiga uku ni." "Ba wani abu bane babba, ku shirya kuje Gumel zan zo." "Ai ko baka ce mu tafi ba dole tafiya zamuyi, sai dai kafata ƙafarka ba zan barka su kashe min kai ba, wacce yarinyar suke nema ka hana su? Wannan wacce irin rayuwa ce haka?" Dafe kansa yayi kamar zai rabe biyu saboda zulumi, iyakar kokarin sa na son ya fahimtar da inna ya kasa, haka dai ya bita da to suka tattara kayan su suka nufi Gumel, har suka isa inna bata daina mita ba, shi dai nasa ido ya gama tsara yadda zai baro Gumel din da zarar sunje. *** Tsoron sa ne ya dadu ganin sun shigo layin, duk sai yaji kamar ya koma bashi da idon da zai iya duban su, abubuwan da suka faru ne suka shiga dawo masa daya bayan daya, haka dai ya daure ya hau addu'a har ya samu ya ɗan ji daidai, nuna mata hanya ya cigaba da yi har suka karasa kofar gidan, kallon gidan yake ganin yadda ya sauya sosai, tun daga kan gini da tsarin gidan  da komai ya zama sabo, ajiyar zuciya ya sauke ya kalle ta, itama shi take kallo. "Thanks alot, can I have ur number pls? Saboda watarana." "Yeah of course." Da farin ciki ta karanto masa ya saka yana murmushi, bude kofar yayi ya fito tayi saurin fitowa ta tayashi kwashe kayan, hannu ta sa ta rike kofar tana kallon shi, "Suna da?" Dafa kansa yayi alamun mantuwa yace "Kinga na manta ma, I'm Muhammad , U? "Barr. Lubna Abbas." "Ok Masha Allah, nagode sosai sosai, Allah kawo ranar da zan saka miki, sai anjima." Juyawa yayi ya fara takawa har gaban sa na dukan uku uku, sai da ya tura gate din ya shige sannan tayi ajiyar zuciya ta shiga , ita dai Hidaya ta kasa magana saboda tsabar mamaki dan bata taɓa ganin kawar ta a irin wannan yanayin ba. **** Buzu na zaune yaga ya shigo, da sauri ya mike yana kokarin karbar kayan hannun sa a tunanin sa Arkel ne, kallon harabar gidan yake baki bude ganin irin girman da aka kara wa gidan ba kamar yadda ya tafi ya barshi ba, shekara biyar ba kwana biyar bace komai ya sauya, da sallama ya bude falon ya shiga, babu kowa a ciki sai karar na'urar sanyaya daki dake dan kara kadan, a cikin sakan da be wuce biyar ba ya gama kallon ko ina na cikin falon da duk wasu kofofi dake manne da falon, idon sa ne ya tsaya a kan dakin da ba zai taba mantawa dashi ba, duk da gyare gyaren da akayi wa gidan dakin na nan a yadda yake, Sadiya ce ta fito daga kitchen, tana ganin shi ta rissina har kasa ta gaishe shi, amsawa yayi ba tare da ya maida hankali a kanta ba, ganin zata wuce ne yasa ya dakatar da ita. "Ina Ummi?" Dakin da take ta nuna masa, da sauri ya nufi dakin sai mamaki ya kamata, ya zai yi yace ina Ummi bayan yasan babu in da take zuwa balle har ta iya fita?ita kadai take ta tunanin hade da mamakin sa bayan shine mutum mafi muhimmanci da zai san komai. Duk a tunanin ta oga kwata-kwata ne tun da duk cikin su babu wanda yasan shi balle yayi tunanin ko shi ne yazo. Cikin dakiya ya murd'a kofar, tana kwance kamar ko wanne lokaci idonta a rufe, sakin kofar yayi jin ƙafarsa na neman gagarar sa tsaiwa da abinda ya gani, tuni hawaye ya cika fuskar sa, har a lokacin wani sashi na zuciyar shi na kalubalantar zuwan da yayi sai dai Shashi mafi karfi ya fi bashi kwarin guiwa. Hakan ya daure ya karasa gaban gadon yana sauke guiwowin sa dukka a kasa, a daidai lokacin Ummi ta bude idon ta, a kansa ta sauke su tayi wata irin zabura tare da kwalla masifaffiyar karar data saka gaba daya gidan amsa kuwwa, Hajiya Mero na zaune a daki tana shirya wa fita wajen su Asi taji karar, wata irin faduwar gaba taji take wani abu me kama da ruwa ya biyo kafarta, cikin tsananin tsoro tayo waje, ƙarar na fitowa daga dakin Ummi hakan ya sake hautsinata ta nufi dakin da mugun gudu. Kokarin tashi take Muryar ta na fita chan kasan makoshin ta, rike ta yake ganin da gaske yunkurin tashi take bayan babu yadda zatayi ta iya tashi bayan dogon zangon data dauka tana jinya a kwance, kuka suke dukka su biyun sai dai nasa yayi karfi sosai na Ummi kuwa kadan kadan yake fita, kusan shidewa Hajiya mero tayi ganin wanda ke durkushe a dakin. "Muhammad!" Ta kwala masa kira tana ja da baya da baya, tashi yayi ransa na suya ya fuskance ta yana daure fuskar sa, babu alamun sassauci ko afuwa a tattare dashi hakan ya sakata kokarin juyawa, ji tayi ta bige da abu, da sauri ta d'ago, Arkel ne ya harɗe hannun sa a kirjin sa ya zuba mata ido yana kallon ta, "Me ye HakA wai, me kuke nufi dani?" Babu wanda yayi magana a cikin su, cigaba da takowa yayi yana saka idon sa cikin idon dan uwansa rabin jikin sa. Lallai ba karamin cutar dasu akayi ba, iya kar rudewa Hajiya mero ta rude dan bata taɓa kawo ranar ba, bata taɓa hasashen ta ba. _ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU😁._ *ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma *SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano) *KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo) *BURI ƊAYA!* (Mamu gee) *WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull) 👇🏻karku bari ayi babuku *ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu* *za'a tura kudin ta wannan accnt number din* Hafsat kabir umar 0225878823 GT bank Saika tura shaidar biya ga wannan number ta WhatsApp 08030811300 Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din 07067124863 Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya. *Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon Rano🚴🚴🚴 *SAUYIN KADDARA* *35-36* ©*Hafsat Rano* *_ZAFAFA BIYAR na kudi ne idan kana son kowanne daga ciki ka nemi Wannan numbers din_* *08030811300* *07067124863* *_Daurin boye_* _safiyya huguma_ *_Buri daya_* _mamuhgee_ *_Wutsiyar rakumi_* _billyn Abdul_ *_Kai min halacci_* _Miss xoxo_ *_Sauyin kaddara_* _Hafsat rano_ *** "Kinyi mamakin gani na ko, kinyi tunanin ba zan dawo ba ko, kin tuna maganar da muka yi ta karshe?" "Idan kin manta bari na tuna miki, na raba ka da kowa naka, dangi yan'uwa da duk wani jin dadi na rayuwa, kaje chan kayi rayuwa irin ta mutum mara inganci, rayuwar kunci da wahala.." "Wacce amsa na baki a lokacin?" Ya dora "Na fada miki zan dawo,ko mai daren dadewa zaki girbi abinda kika shuka, a yau gani a gabanki, bayan tsawon lokaci na dawo, ba zan taba barin ki ba, ko zanyi spending last kobo dina akanki, wannan Alk'awari na ne." A yadda taga yana magana ta san tabbas karshen ta yazo, amma ya akayi haka? Bayan madugu ya bata tabbacin babu abinda zai iya karya shi, abinda yayi a tsakani babu wanda ya isa ya karya shi, Arkel na tsaye ya rungume hannun sa yana kallon ta, juye juye take tana neman in da zatayi, daidai lokacin Ummi tayi wani irin nishi, nishi me matukar firgitarwa, da gudu sukayi kanta hakan ya bawa Hajiya Mero damar guduwa, kofa tayi ta jita a rufe kam alamar an shirya kenan, da gudu tayi d'akin ta zata shiga, nan ma a rufe, wuri wuri ta tsaya yi yana neman hanyar guduwa, babu wata hanya sai kawai ta tsaya a falon ta ɗora hannu a ka. Magana take tayi amma basa jin me take cewa saboda rashin murya, duk sun rikice musamman Arab da ya ke ganin kamar ganin shi ne ya haddasa hakan, har lokacin kallon juna suke babu wanda ya yi wa wani magana har suka samu numfashin ta ya daidai ta, ajiyar zuciya suka sauke a tare, hakan yasa suka kalli juna, Arkel ne ya yayi saurin basarwa ya dauke kai kamar be gani ba, gefe ya samu ya zauna yana kura mata ido. Arab kuwa sai ya tsaya a tsaye yana karewa ko ina kallo tare da share kwallar dake faman bin fuskar sa babu kakkautawa, ya rasa ta ina zai fara magana gashi ko fuska Arkel yaki bashi yana harɗe yana juya kai. Chan sai wayar sa tayi kara yayi saurin dauka. "Ina gida, ku shigo kawai." Abinda yace kenan ya datse kiran  yana lankwasa hannayen sa, jin ana knocking yaasa shi mik'ewa a nutse kamar babu abinda ke faruwa, yayi hanyar fita, da sauri Arab ya bi bayan shi, Hajiya mero na ganin sun nufota su biyu ta sake rikicewa, Arab da ko ganin ta baya san yi, da gudu yayi kanta, hannu yasa ya shako mata wuya, take idon ta ya firfito waje ta shiga kakari, hannu kawai take yarfewa cikin tsananin zafi, daidai lokacin Zainab ta fito, ihu tayi ganin abinda yake faruwa, da gudu tayi kansa, hannun sa take kokarin rikewa tana ihu, be ko ji ta ba, Arkel daya fasa bude kofar ya tsaya yana kallo ganin zai mata illa yasashi karasawa ya rike shi, da sauri Zainab ta riko ta tana kallon ta, gaba daya bata hayyacin ta, dakin ta ta ja ta tana kuka, sakin sa yayi ya juya ya bude kofar, police ne su uku suka shigo, biyu cikin kakhi daya babu dayar mace ce, hannu ya mika musu suka gaisa. "Tana ina?" "Muje sir." Har dakin Zainab ya kaisu ya sa hannu ya kwankwasa kofa, gaban Hajiya mero ne ya fadi da sauri ta rike Zainab "Karki bude dan Allah." "Amma mummy me yasa? Me wai yake faruwa ne? Waye dayan that look exactly like him." "Dalla karki isheni da tsinannan tambaya, mafita kawai nake nema ba zancen banza ba." Sake buga kofar akayi, tashi Zainab tayi kawai ta bude aikuwa sai ga yan sandan nan sun dira a cikin dakin, wani irin zawo ne ya tasowa Hajiya mero tayi toilet da gudu, riko ta macen tayi tana cewa "Ita ce sir?" Daga mata kai Arkel yayi yace "Yes." "Za muje dake Station muna so Zaki amsa mana wasu tambayoyi." "Na shiga uku? Me nayi wai? Menene haka arkel? Ya zakayi min haka? Ka manta wacece ni?" Kin magana yayi, magiya ta hau yi tana turje-turje. Tsaye yayi kawai yana kallon ta, ihu da haukan ta ya cika gidan gefe daya zainab na tayata da kuka dan bata san mene ke faruwa ba, "Dan Allah kayi magana, karka bari su tafi dani, shirin nan naka yana kashe ni kayi magana dan Allah, wayyo Alhaji menayj musu zasu kashe ni?" "Dan sake ta Madam." Ya fada A hankali ya furta "Where is my wife?" "Ban gane ba, matar ka kuma? Aina?" Dan murmushi yayi yace "Sambo da Asase, Malam lado, nurse Latifat, Hajiya Turai?" Zamam yan bori tayi jin waɗanda ta ambato, be sake magana ba ya juya ya bar dakin yana kokarin kin kallon Zainab, haka suka fito da Hajiya Mero suka tisa k'yeyarta, tana ihu tana kunji suka tura ta amota suka tafi da ita. *So sad🤪* *** D'akin Ummi ya koma, a gefen ta ya zauna ya sadda kansa kasa, tana kallon sa, hawaye ne kawai ke bin fuskar ta, komai na jikin ta na aiki, hannu, kafa, ido har ma maganar ta ta dawo sai dai ba zata iya wani kwakkkwaran yunkuri ba saboda shekarun da yawa, Arkel ne ya budo kofar ya tsaya yana duba abu daga nesa, ganin bashi da niyyar yi masa magana yasa ya taso "Bro." Da Sauri yace "What?" "Baka ganni bane? Are you not happy to see me or what?" "Eh toh kusan hakan ne, amma right now ba zan iya baka amsa eh ko a'ah ba, I'm very busy as u can see." Kallon sa yayi, da confidence yake masa maganar alamar da gaske dai be yi wani mamakin ganin sa ba, juya masa baya yayi ya gama abinda zai yi a dakin ya fice. Wayar sa ya dauko ya kira Mustapha, yana dauka yace "Man ka sauka? Ina ta kiran ka baka daga ba, ya gida ya kowa." "Alhamdulillah wallahi, Komai lafiya, Number malamin nan zaka turo min, ina so muyi magana naji yadda za'ai." "Karka damu, na sanar dashi komai, ya gama shirya wa ma jiran lokaci kawai yake, yanzu in sha Allah zan bari weekend zan je sai mu taho kanon tare dashi, duk da dai ya girma ga shekaru, amma a hakan zamu zo in Sha Allah." "Alhamdulillah, U r indeed a true friend, bansan me zan ce maka ba, all I know shine in Sha Allah I ll repay this kindness." "Haba haba, karka wani damu, ka nutsu kawai in Sha Allah komai yazo daidai, dnt stress ur self." Jinjina kansa yayi, "Shikenan, Thanks." "Welcome." Ajiye wayar yayi ya duba Ummi, kasa ya sauka ya durkusa "Ummi...." Dan jim yayi kansa a kasa yace "Bansan da wane baki zan fara magana ba, bansan me zance ba, dan girman Allah kiyi hakuri, ki yafe min, hakika ban chanchanci yafiyar ki ba, ban cancanci ki kalle ni ba ma, dan Allah Ummi nah, ki yafe min." Kuka ne yaci karfin sa ya shiga yin sa wiwi, daga hannun ta take tana magana a hankali, be ji ba saboda yadda yake kuka sannan Muryar tata bata fita sam, haka yayi tayi tsawon lokaci kafin ya tashi yana jin kansa na juya masa. Ya dade a zaune yana duban ko ina na dakin, haushi kansa yake ji gashi sam ya kasa sukuni, so yake suyi magana da Arkel ko yaji saukin abinda yake ji. Turo kofar akayi, da gudu ta karasa shigowa ciki, tsayawa tayi tana kallon sa, shi din ma ita yake kallo, babu wani dalili ko abu da zai sa ta kasa banbance su, tare suka taso komai nasu daya ne, mik'ewa yayi da dukkanin karfin sa, sai kuma ya tsaya yana kallon ta, a dah babu wani shamaki zai rungume ta sai yau yaji kamar bashi da karsashin ta zai iya fuskantar su, ba shi da fuskar da zai iya kallon ta, baki sake take sake kallon sa "Ya bilaaaa.." Ya ja sunan yadda ya saba faɗa mata, sai data ji abin akanta, wani irin yanayi ya zo mata abubuwan da suka faru a baya suka fara gudu a zuciyar ta, ta rasa a wanne irin yanayi zata ajiye abinda take ji, farin ciki ne ko me? Yadda ta tsaya still tana kallon sa yasa shi karasa wa, rungume shi tayi ta saki kuka me cin rai. Har cikin ransa yake jin kukan, babu abinda ke masa yawo akansa sai tunanin halin daya jefa kowa akai, sakin sa tayi tana ja da baya "Moha..." "Kaine? Ashe zan sake ganin ka? Why? Why?" "Am so sorry, am sorry." "Alhamdulillah ya Allah, Alhamdulillah." "Ya Bilaaaa... Ya bayan rabuwa, kin ga yadda abubuwan suka zama ko? Haka na tarwatsa komai? Haka nayi da rayuwar mu?" Da sauri tace; "Baka yi komai ba, haka Allah ya tsara nice dai me laifi, ban kula da Ummi yadda ya kamata ba, Arkel shi kadai ne yake komai, babu wanda ya damu da halin da yake ciki, me yake yi? Ina yaje? Me Ummi take bukata? Wacce irin rayuwa mukayi haka!" "Allah ya gani bansan in da zan yi da rayuwata ba, bansan menene ya hau kaina ba, bana jin komai a raina, Ya Allah... Me muka aikata ne wai?" Girgiza kai kawai yake Ummi dake jin su babu abinda take sai tsiyayyar hawaye, duk abinda ya faru itace sila, ita ce musambabin komai, gashi abun da hakan ya jawo mata. *** Zainab na fita tayi gidan Hajiya Mama, tana tafe tana kuka har ta karasa, Hajiya na ganin ta ta mike da sauri. "Menene ya faru.?" Kuka take taki magana, hakan yayi mugun kular da Hajiya ta buga tsaki tace "Ke dan ubanki kinzo kin sani a gaba kina kuka, uwar me akayi miki?" Kwafa tayi ta juya fuska ganin taki magana, sake jan tsaki tayi yadda kukan ke hawa mata kai ta kai mata bugu tana cewa "Kin tashi kin bani waje ko sai na kakkarya miki kafa, kinzo kin sani a gaba da shegen kuka ke murya ba dadi ba, Haba!" Cikin muryar kuka tace "Mummy ce aka tafi da ita Station." "Ina ne kuma Station, dalla kiyi min bayani." "Police station fa, yan sanda ne suka tafi da ita." A zabure ta mike har tana kusan yadda zani "Yan me? Yan sanda kuma? Na shiga uku ne indo." "Me ya faru haka? Na shiga uku." "Nima ban sani ba." Sultan ya hau kwala wa kira, daga nan ta koma Rauda, sai Maman su, a tare Rauda da Maman tasu suka shigo a tunanin su wani abu ne ya sake ta. "Ina Abban su, ayi maza a kira shi ba lafiya." Basu tsaya tambayar me ya faru ba Rauda ta ruga ta dauko wayar ta a daki ta kirashi, a gaggauce ya ajiye abinda yake ya taho gida yana fatan kome ne ya zama da sauki. *** Hafiz ganin inna sun nutsu sai ya sudade ya dawo, yana zuwa Number Arkel ya nema, be wani sha wahala ba ya samu, kiran sa yayi yace yana so su hadu. Wajen magriba suka yi zasu hadu, ranar duk abu daya kawai arkel ke tayi har wajen magribar be nutsu ba yana so ya tabbatar da abinda ya saka a gaba komai ya tafi daidai, haɗuwar su da Barr.Nasir ce ta sake rike shi sosai gashi Asase da Sambo na tsare har ma da shi kansa Malam Lado wanda shine ya taimaka aka samu su Sambon, kansa ya dau zafi sosai sai dai hankalin sa na kwance saboda yasan Ya Nabila da Arab suna tare da Ummi, duk wani abu da ya kamata suyi mata ya san zasuyi, mutum daya yake jira yaga yadda zai yi shine Alhaji da ake saka ran dawowar sa gobe. A in da sukayi zasu hadu suka hadun sai dai zaman jiran da Hafiz din yasha kafin yazo, bayan sun gaisa ya zayyano masa komai daga farko har karshe, jin sa kawai Arkel yake har ya gama sannan ya sauke ajiyar zuciya, hannun sa ya lankwasa ya dan jingina yana murmushi da shi kadai yasan manufar sa, Hafiz na kallon sa har ya gama sannan yayi masa godiya sosai, sannan yace zai neme shi lokaci kadan, maganar su Asase kuma ya barta a hannun sa, idan zai iya ya dawo da Innar sa daga Gumel babu abinda zai faru. Akan haka suka rabu a daren ya juya ya koma kafin inna ta tada hankalin ta idan ta lura baya nan. A yadda ya gaji gida ya kamata ya wuce, sai dai a yadda yake ji ba zai iya ba sai yaje ya ganta. Gidan ya nufa ya kunna kira'ar Ghamid'i lokaci lokaci yana bi a hankali. A hadaddun flask na Alhaji Rabi'u aka zuba masa tuwon semo miyar zogale, gefe kuma coconut milk shake ne yana ta kamshin flavours masu dadi ga kankara da akayi crushing aka watsa, a babban tray aka jera komai aka jiya. Wanka Anty Maryam ta sata ta fara yi kafin ya zo ya shirya tsaf, doguwar rigar abaya ta saka me masifar kyau anyi mata ado da wasu duwatsu farare kal masu matukar kyau da kyalli, kanshi kuwa da yake tashi ba'a cewa komai. Kamar anyi barin turare haka ko ina ya dau kanshi, Anty Maryam sai farin ciki take ganin yadda ta zage ta gyara kanta gashi nan ta fito kamar ka sace ta ka gudu, tana nan zaune suna dan hira da Anty Maryam duk rabin hankalin ta na chan ganin shiru be zo ba, wayar ta datayi kara ne yasa tayi saurin jawowa a tunanin ta shine, ganin kawar ta Asma'u ce ke kiran ta yasa ta ɗan bata fuska kadan sannan ta daga, maganar school da zasuyi resuming tayi mata suna cikin wayar kiran sa ya shigo, bata san sanda ta jefa Asma'u a hold ba ta d'aga da sauri. Tana daga wa yana kashewa, saboda yaji busy, samun kanta tayi da katse kiran asma'un ta sake kiran shi, yana d'agawa yace "I'm out." "Owk ka shigo tom." "Um um... Ki zo dai ki shigo dani." "Please ka shigo falon dazu." "Nima please ki Zo ki shigo dani ko na koma." "A'ah wait... I'm coming." Da sauri ta tashi, takalmin ta flat ta zura ta rik'e wayar a hannu ta fito, a cikin motar ta hange shi, tsayawa tayi tana maamki, nufin sa kenan ta karasa, sai ta tuno ranar da yazo ya sata dole taje, tasan yau din ma hakan ce sai kawai ta karasa ta bude motar ta bangaren sa. Yana hakimce ya manna kansa da jikin kujerar alamun gajiya, idon sa a rufe yake daya ƙaraso sannan ya bude ya dora su akanta, kallon tsaf yayi mata kamshin nan ya bigi hancin sa, take yaji ya nemi kaso tamanin cikin dari na gajiyar daya kwaso ta ragu, hannu ya mika mata ta kama ta taimaka masa ya fito, gefe ya matsa ta rufe kofar sannan tace "Ina wuni?" "Gaisuwar ki kenan, ina wuni?" "Toh me zance?" "Hmm." Kawai yace yana girgiza kai "Me zance dan Allah." "Baki sani ba?" Daga kanta tayi "Owk bari kiga what i prefer." Kafin tayi aune sai ji tayi yayi hugging nata tight, lamo tayi zuciyoyin su na karbar sakon kowacce zuciya, sai daya dade sannan ya sake ta "Nafi son irin wannan gaisuwar, ina wuni kamar wata yar kauye." Dariya ta saka kawai "I'm serious fa, na soke ina wuni." "Toh." Kawai tace tayi gaba dan taga alamar jan magana yake son yi, bin ta yayi suka shiga ciki, suna zama Anty Maryam tasa me aikinta Rabi ta kawo kayan abincin, tana ajiye wa ya zamo ya zauna yana tankwashe kafa, babu ko kara ya hau bubbud'e kwanukan, murmushin jin dadi yayi ya nuna mata gefen sa "Sauko kiyi saving dina, ga yunwa ga gajiya, idan naci sai kiyi min massage kin ga idan dadin yayi min yawa sai kawai na karasa lada na na kwana nan." "Anan!?" Ta zaro ido "Kina mamaki ne?" "Uhum." "Ke dai bani abincin tukunna, sauran bayanin zaizo daga baya." Da mamakin sa ta zuba abincin dan bata taba tunanin shi haka ba, ya sake sosai da ita a dan wanakin nan freely yake watso maganar sa babu wani kunya ko nauyi. Tana daga gefe tana kallon sa yake cin abincin yana lumshe ido, ba karamin dadi tuwon yayi masa ba, dadin dadawa kamshin dake tashi ta kowanne lungu da sako na gidan, gata ita kanta uwar gayyar tana ta feso masa nata, dukkan wata damuwar sa ajiye ta yake a gefe a duk sanda yake tare da ita, a hankali a hankali take shiga jikin sa, gashi har tana so tayi masa shigar bazata, wani abu me kama da mayen karfe ne yake fusgar shi zuwa gareta, babu tantama ko shakku, ya san ta samu tarbiyya wadda tayi wuya da karanci a wannan zamani. Sosai yaci yasha milk shake din ya masa dadi ainun, cikin sa ya cika kamar zai fashe, tsalle ya tashi ya hau yi aikuwa Maryam ta samu abin dariya, dariya sosai ya bata ganin yadda ta daddage yana tsalle, ganin da gaske dariyar take sosai sai ya kara kaimi wajen tsallen dan ba karamin birgeshi dariyar ta ta take ba. *** Hi dearies, I'm very very very sorry for the inconveniences. Ido ne sai godiyar Allah. I'm just managing saboda am not seeing clearly wallahi. But alhamdulillah sha. A kara hakuri dai dan Allah.,🤝🤲 Ba editing just manage a haka _ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU😁._ *ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma *SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano) *KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo) *BURI ƊAYA!* (Mamu gee) *WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull) 👇🏻karku bari ayi babuku *ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu* *za'a tura kudin ta wannan accnt number din* Hafsat kabir umar 0225878823 GT bank Saika tura shaidar biya ga wannan number ta WhatsApp 08030811300 Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din 07067124863 Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya. *Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon Rano🚴🚴🚴 *** *SAUYIN KADDARA* *37-38* ©*Hafsat Rano* *_ZAFAFA BIYAR na kudi ne idan kana son kowanne daga ciki ka nemi Wannan numbers din_* *08030811300* *07067124863* *_Daurin boye_* _safiyya huguma_ *_Buri daya_* _mamuhgee_ *_Wutsiyar rakumi_* _billyn Abdul_ *_Kai min halacci_* _Miss xoxo_ *_Sauyin kaddara_* _Hafsat rano_ *** Zama yayi yana fuskantar ta, sai ta katse dariyar ganin ya zama serious alamun magana yake so suyi, hankalin ta dukka ta tattaro ta ajiye waje daya tana dan gyara zama, a kan kafarta ya jingina tasa ya sa hannu ya dora kafad'arta a saman tasa, shiru sukayi na wani lokaci kowa da abinda yake tunani, shine ya fara karya shirun ta hanyar riko hannun ta yasa a nashi, kadan kadan yake murzawa yana kallon hanya kamar wani ne zai shigo, ajiyar zuciya ya sauke ya dan ja baya kadan. "Kinsan me?" Girgiza kai tayi jin yana yawo da hannun sa cikin kanta dake tufke waje daya cikin ribbon "I'm so happy yau, and it's because of you." Dan cire kanta tayi ta kalle shi "Yes, kece silar komai, ko kin dauka bansan me yake faruwa ba.?". "Ka sani dama? Kasan komai?" "Na sani, da taimakon ki na sani, kece fitila me haske data saka na gane komai, i owe you alot." "Ummm... Alhamdulillah." "Maryam..." Sai taji wani yarr saboda shine farko a irin wannan yanayin daya kira ta da wannan sunan, yadda sound din ya fita sai taji kamar ba'a taba yi mata magana me sanyi da dadi irin ta ba, samun kanta tayi da sake narke masa har bata jin shi sosai saboda tunanin data tafi, tabo ta yayi ganin yayi magana sai murmushi take, da sauri ta yawance tana sunne kanta a jikin sa, sai ta bashi dariya yayi murmushi sannan ya d'ago ta yana mana duban tsanaki "Yau na cika wani bangare na buri na, bangare mafi girma a rayuwata, a yau na tabbatar da cewa mace ta gari itace silar komai, alhamdulillah ya ALLAH, na gode miki." "Me ya faru ne? Dan Allah ka fada min." "Sai kin kawo cin hanci." "Na me?" "Umm bari na ga." "Me?" "Tashi kiga." Tashi tayi yace "Koma chan jikin kofar." Komawa tayi tana facing d'insa, kallon ta yayi daga sama har k'asa yana danne dariyar sa, sai daya dan bata rai sannan yace "Toh taho da gudu mu gani ko kin iya gudu." "Gudu kuma?" "Eh ni ba tsalle nayi miki ba, toh in ba zakiyi gudu ba yimin rawa toh." "Na shiga uku, wallahi ba zan iya ba." "Aiko kin fasa jin albishir ɗin da zanyi miki dah." "Dan Allah,Dan Allah... kajiiiiii." "Na'am?" "Dan Allah, I'm eager fa." "Toh shikenan, Ummi tayi magana yau...." "Wayyo Allah..." Ai bata san sanda tazo gabansa sai kawai gani yayi ta fada kansa tana dariya, dadi ne ya kamashi ganin yadda take farin ciki, be san wai har haka ta dauke su ba, sai kawai ya tsaya yana kallon ta cike da sha'awa, ita kuwa sai murnar ta take ta rasa in da zata saka kanta, sai daya bari ta nutsu sannan ya sanar mata da abinda ya faru a takaice, sosai tayi farin cikin dawowar Arab ɗan ji tayi ma kamar tace ita binshi zatayi kawai dan hankalin ta gaba daya ya koma chan, shi din ma haka ne sai dai dole zata zauna anan din kafin abinda suka shirya ya tabbata, daga nan sai komai ya daidaita, school ma da sukayi resuming sai dai ta yi hakuri zuwa lokacin da komai zai tabbata, ya riga ya tsara ya shirya musu daddadar rayuwa me cike da soyayya da shiga rai, babu wata tantama ko shakku ya riga ya san ya gama fadawa kogin son ta, lokaci kawai yake jira da zai tabbatar mata da hakan, anan ne zai sanar da ita abinda bata taba sani ba, da duk wani abu da ya shafi zaman ta tun daga ranar farko a gidan su, ko ma ace tun ranar daya fara dora idon sa akanta. Da kyar ya yakice ya tafi yana ji kamar su dawwama a hakan, sai dai dole ne ya karasa abinda ya faro, abinda ya katse shi ya dakile shi tsawon wasu shekaru ya hana masa jin dadi da kwanciyar hankali, komai yazo karshe da izinin Allah sai kuma shirin ginin kyakkyawar rayuwa dashi da yan'uwansa baki daya. Ko da ya isa gida dukkan su suna zaune a falon, Baba Ladingo ma data tafi cikin gari ta dawo ta tarar da abinda ya faru murna tayi tayi harda kwallar ta, Ummi kuwa an samu ta koma bacci bayan Nabila ta goge mata jiki ta gyara ta tsaf, kamal da ya san komai be yi yunkurin zuwa ma daukar ta ba saboda yasan tana bukatar lokaci da yan uwanta, sai kawai ya gyara su Amna ya shirya su ya saka su bacci sannan ya samu sukunin sawa cikin sa wani abu. Bayan ya duba Ummi ya tabbatar komai kalou dan dama yasan hakan shi yasa ma ya bar su da ita su samu lokaci, saman ya haura agajiye yake tikis dan ma wajen Maryam daya tsaya ya dan huta kadan, yana shiga ya jefar da kayan hannun sa, ya cire komai na jikin sa yayi saura daga shi sai singlet sai karamin boxer ya fad'a toilet, kasalar yin wankan ma yake ji dan dai kawai ya saba ne yasan in be yi ba, ba zai ji dadin barcin bane shiyasa, aikuwa ya dade a ciki yana zubawa kansa ruwa sai daya ji bashi da wani sauran gajiya sannan ya fito.' Kayan sa marasa nauyi ya zura ya fito falon, da mamaki yake kallon sa a zaune yana duban hanyar, sai da ya kalle shi sannan ya dauke kai zai wuce Kitchen. "Arkel..." Yaji muryar Ya Nabila, juyowa yayi ya ganta a tsaye ga dukkan alamu shigowar ta kenan, da baya da baya ya dawo ya tsaye daidai gaban ta "Kanina magana zamuyi dan Allah." "Maganar me? Ko mu bari da safe?" Dan kallon bangaren da Arab yake zaune tayi ganin su yake kallo yasa tace "Yanzu zamuyi tun dazu muke jiran ka." Daga kafadarsa yayi ya samu waje ya zauna. Zama tayi a gefen sa ta nuna Arab kusa da ita "Dawo nan.". Tashi yayi ya dawo kusa da ita shima, hannun su ta kama ta saka a nata sannan ta shiga magana a hankali. Kusan raba dare sukayi suna hira da labarin bayan rabuwa, tun Arkel na basarwa Arab har ya sake dashi bayan yayi masa bayanin komai, shi dai yayi shiru da komai da yake shiryawa har zuwa ranar daya tsara , ranar ne zasuji komai da ya faru. **** *** Bangaren Hajiya Mama kuwa ganin Alhaji Faruku shiru yasa ta zari mayafin ta ta shiga gidan su maryam, tsawon lokaci kenan rabon data shiga ko da zauren gidan ne yau sai gata a ciki, da sauri umma ta tarbe ta ta shinfida mata tabarma, bata zauna ba daga tsaye take tambayar baba, lokacin yana ciki yana Sallah ya dan makara be samu jam'i ba, tsaya wa tayi ya idar ya fito, yana ganin ta ya rude yana tambayar ta ko lafiya, ita kanta a rud'e take ta sanar masa abinda yake faruwa, takalmin sa kawai ya saka suka fita yana bata baki, suna fita sai ga Alhaji Faruku, gida suka sata ta koma suka fita tare, tun a hanya suke tunanin in da aka kaita, gashi Arkel ɗin duk wayoyinsa a kashe suke, haka suka k'araci yawon su Baba yace suje gidan Alhaji Faruku yace sam ba za'a yi haka ba, shi da yake ya san komai ya san halin ta shiyasa ya kafe akan su koma gida kawai idan gari ya waye sai su tuntubi Alhajin su Arkel ɗin suji. Haka suka hakura suka dawo gida,Hajiya Mama sai kuka take tana tsine-tsine, Zainab da Rauda ma kukan suke sai dai zainab naji a ranta tabbas wani gagarumin abun tayi dan tasan halin uwarta, ta dade tana abinda take so. *** Tashin hankalin da ba'a sa maka rana shi ake kiran wannan, cikin tsananin mamaki Hajiya mero ke kallon Sambo da Asase a cikin wajen, duk sun yi wujiga wujiga alamun sun sha wahala, babban dalilin da ya saka kenan ta kasa samun daya daga cikin su, bata sake tsorata ba sai lokacin da ta ga mutumin da ta saka kawo takarda, anan ne ta sake tabbatar wa kanta tata ta kare, ihu da kuka ta hau yi a wajen sai da suka tsawatar mata da barazana sannan aka samu tayi shiru duk ta tuje daurin kanta sai kanta ya bayyana kamar hammatar dan iska, irin gashin nan ne da ita kamar na yara marasa gashi ga taurin masifa ya sha wani abun kitso babu kyan gani, tana nan tana kallon hanya a tunanin ta zasu zazzo har dare ya fara yi shiru babu kowa haka aka tattara ta aka zuba a bayan cell, k'aramin daki ne me yar karamar window daga chan sama ga banɗaki irin pit din nan a ciki da yake buso uban wari da doyi, kamar zatayi amai haka ta dinga ji haka ta takure kanta tana kallon mata biyun dake ta fada a ciki an kawo su sun cinye wa wata mata kudi. Yadda taga rana haka taga dare ga uban sauro kamar ruwan su ake, bata taɓa ganin masifa irin wannan ba, gaba daya jikin ta yayi tsami ga wani irin hamami da yake tashi abin ba'a cewa komai. Sanda gari ya waye ne aka fito dasu ana jiran dpo yazo, Asase da Sambo sunki yarda ma su hada ido da ita gashi babu abin tayi musu magana tana tsoro, duk da haka tana nan akan bakanta dole ta dau fansa ba zata taba kyale Arkel ba dan ba karamin shammatar ta yayi ba har ya iya bata mata aiki, bayan ta samu tabbacin babu abinda zai iya karya abinda ta kulla, haka dai take ta sake saken ta har aka zo aka kwashe su sukayi ciki. *** Dukkan su babu wanda yayi ishashen bacci gashi basu kwanta da wuri ba suka tashi saboda yadda Ummi take wani irin abu kamar zata mutu, nishi ne me cike da firgitarwa, magungunan ta tasha sannan aka kira nurse Latifat tazo tayi mata allurar bacci, ko data tashi jikin da sauki tana kallon kowa tana jin su, asibitin suka shirya maida ita kafin zuwan malam saboda jin ta in da zasu fara dan kuwa har tafiya sai an fara koya mata daga farko dan babu abinda zata iya yi duk da komai nata ya dawo yana aiki yadda ya kamata amma shekara biyar ba kwana biyar bane. Arkel be bisu ba ya zauna a gida bayan ya amsa kiran Alhaji Faruku da suka ce zasu zo gida su same shi, ya riga ya san kwanan zancen sai ya zauna yana jiran su, fatan sa daya kar azo da baban Maryam ya nemi wata alfarmar ba zai iya ki ba. Tare kuwa suka zo, da sauri ya fita ya shigo dasu suna zama sai ga motar Baba ta shigo, curtains din falon ya buda ya hango shi sanda driver din sa ke gyara parking din motar, ajiyar zuciya ya sauke ya ajiye musu ruwa da leme. Alhaji na ganin su ya karbe su hannu bibbiyu aka gaisa a mutunce dan dama ba haduwa suka taba yi ba sai ranar, Arkel dai na gefe kansa a kasa yana jiran yaji ta in da za'a fara, Baba ne ya sako maganar da sauri Alhaji ya kalli Arkel dan be san komai akai ba, fada ya hau shi dashi ta in da yake shiga ba tanan yake fita ba, sai da Alhaji Faruku yasa baki sannan yayi shiru yana kokarin danne abinda yake taso masa tun yana chan, daurewa kawai yake amma bashi da wani kuzari kamar zai yi zazzaɓi haka yake ji sai dauriya kawai irin ta maza dan ita mace ce take jin abinda yake ji dole ta kwanta. Tashi sukayi gaba daya suka nufi station din har lokacin Baba na jin sa kamar ba a duniyar ma yake ba baki daya. Lokacin da suka je an gama shigar da case ɗin komai an dau report ɗin su Hajiya meron dasu Asase da suka ƙaryata duk abinda ake bin su, ganin haka ya saka DPO ya tattara case din gaba daya ya aika su kotu sannan ya bada belin Hajiya meron a zuwan sai ranar da za'a zauna amma da sharadin idan suka barta ta gudu toh fa dole a cikin su ukun nan dole daya za'a kama a cikin su, su Asase kuwa cigaba akayi da tsare su har zuwan ranar. Godiya su Baba sukayi sannan suka tafi, Hajiya mero saboda tsabar bacin rai ta kasa ko magana dan bata taɓa ganin wulakanci irin wannan ba, har suka zo gida babu wanda yace komai shi kansa Alhaji ya kasa mata magana gashi abinda yake ji a jikin sa na kara tasiri sosai haka dai ya daure ya shige dakin sa ya kwanta, kafin wani lokaci zazzaɓi me karfi ya rufe shi, karkarwa kawai yake ya rasa in da zai tsoma ransa yaji dadi, Ya Nabila ce ta shigo dakin jin ance ya dawo ta tarar dashi a haka, da gudu ta fita ta kirawo su aka yi saurin kiran Dr dake dubasa sai gashi yazo, duk abin nan Hajiya mero ta kulle kanta a daki bata san me yake faruwa ba, Arkel kuwa yana sauke su ya juya dan ba zai iya zama a gidan a lokacin ba, tsaro sosai ya saka dan ba zai taba yarda Hajiya mero ta kubuce musu ba sai ta fuskanci hukunci ne tsanani sannan ne ya san ya cika dan halak ne kishin iyayen sa. Magunguna da allurai aka bashi hadda allurar bacci da haka aka samu yayi bacci, Arab dake kansa tsaye yana kallon sa cike da tausaya wa, hannun sa ya Nabila ta kama suka fita tana kokarin kwantar masa da hankali. *** Shirya shiryen dauke Ummi suke daga gidan su mai da ita gidan ya Nabila saboda zuwan malamin dan ya samu damar aiwatar da abinda zai aiwatar, duk da yace gidan ma dole ne ayi aiki akansa amma yafi so su dauke ta daga gidan baki daya hakan zai saukaka musu aikin, hakan kuwa akayi a daren ranar suka dauke ta ba tare da sanin kowa ba suka tafi da ita. Bayan tafiyar su Alhaji ya farka a firgice yana kwala kiran Ummi, Hajiya mero da take tunanin yana bayan ta tana jin abinda yake ta sake tsurewa gashi lambar malamin ta sam bata tafiya not reachable gashi arkel ya saka tsaro wasu manyan maza ne masu siffar samudawa ke gadin gidan gaba daya.😂😂😂 *** Dakakkiyar shadda light brown ya saka ya kafa hula damanga sai sheki da kyalli take, agogon hannun sa na kamfanin apple yayi kyau ainun, so yake yaje ya dauko Maryam dan ya ji fa ba zai iya hakura ba har zuwa yadda aka ce gwara kawai ta dawo daga kusa dashi kafin ranar da za'a zauna, duk wasu shedu da hujjoji ya gama hada su waje daya ya damka wa Barr. Nasir yana jiran ranar, a jikin motar sa ya tarar da Arab yana jiran sa, yana bude motar shima ya bude ya shiga. "Yau dai dole na ga matar mu, nasan dai wallahi can zaka." "Haka nace maka? Wajen aboki na zani." "Aboki? Haba malam nafa sanka, wanne abokin kake dashi?" "Toh zama zan tayi a yadda ka sanni kenan." "Eh toh kusan haka ne ai." "Toh ba haka bane, na chanja sosai fiye da yadda kake zato." "Tabbas na gani kuwa, ga babban chanji nan na gani, shiyasa nake so naga wadda ta sace ma kanina ciyazu, har tasa ya zama haka." Da Sauri Arkel ya kalle shi "Nifa ba kanin ka bane, girman mintinan awa ga bani ne wai? Haba mr man gyara maganar ka." "Ko sakan nawa ne dai na girme ka yaro kake waje na." "Sai kayi ai." Dariya Arab ya saka har da buga kujera, da haka suka karasa kofar gidan anty Maryam, da sauri Arab ya ɓalle murfin motar ya fito yana gyara jikin sa "Bari na ga ko zata gane ka, ko zata rungume ni a matsayin kai lover biyu." Dariya ya saka Arkel yayi saurin fitowa yana hararar sa "Wallahi karma ka fara kaji na rantse, mata ta mata ta ce." "Matar mu dai point of correction." "Kaji da..." Bude gare ɗin akayi hakan ya saka Arkel yin shiru yana kallon ta, kokarin daidai ta kanta take ganin su su biyu babu abu daya da ya banbanta su, sai ta kasa karasawa ta tsaya tana kallon su, ta kalli wannan ta kalli wannan ta rasa me zatayi kuma. "Taho mana matar..." Arab yace yana cin Serious Kamar gaske Harara Arkel ya sakar masa hakan yayi saurin bata satar amsa dan tasan babu yadda za'a yi Arkel yace mata matar. Bude mata hannu yayi alamun ta taho gare shi, da sauri Arab ma ya bude yana sake kanne idon sa. Ganin haka yasa Arkel karasawa ya rungume kayar sa tsam a jikinsa. Baki bude Arab ya saki yana kallon ikon Allah, lallai ma gayen nan ya bala'in raina masa hankali, wato dan yaji haushi ya aikata hakan kenan, aikuwa ya shak'a su kuwa suka hau nasa dariya Maryam harda kwallar ta ganin yadda Arab ɗin keta yarfe hannun daya bude alamun kamar abu yake nema. Karasowa yayi suka gaisa yana dariyar kansa shima, farin ciki ne yake shigar sa ganin yadda rayuwar dan uwansa ta ji gaba, harɗe hannu kawai yayi yana imagining kansa a condition din, lalli dole yayi aure da komai ya lafa dan ba zai juri kallon su suna soyewa yana gefe ba😅 ** Niko nace yazo ya zaba ga su nan ko hudu yake so zan bashi #teema gabas #meema #pinky #Sai wama dayar? Ba ruwana Anty Farida ki fara shirin biki kawai 😂🤾 #Not edited 🙈 _ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU😁._ *ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma *SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano) *KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo) *BURI ƊAYA!* (Mamu gee) *WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull) 👇🏻karku bari ayi babuku *ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu* *za'a tura kudin ta wannan accnt number din* Hafsat kabir umar 0225878823 GT bank Saika tura shaidar biya ga wannan number ta WhatsApp 08030811300 Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din 07067124863 Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya. *Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon Rano🚴🚴🚴 *** *39-40* ©*Hafsat Rano* *_ZAFAFA BIYAR na kudi ne idan kana son kowanne daga ciki ka nemi Wannan numbers din_* *08030811300* *07067124863* *** A hankali ya rada mata "Tafiya zamuyi fa." Da sauri ta d'ago, daga kansa yayi sai tayi dariya "Malama don't pretend kema so kike ki tafi na gane ai." "Ni nace haka?" "Ko baki fada ba, na sani." "Allah ni bance haka ba." "Kin fada mana, ta zuciyar ki, U know I can read tru ur mind.". Dariya tayi kawai, "Toh ku shiga kuyi ma Anty Maryam sallama, dan bata san ma tafiya zan ba." "Toh shikenan, fara shiga sai ki faɗa mata, sai mu shigo." "Owk." Komawa yayi wajen Arab daya harɗe yana waya da Mutsapha, taɓe baki yayi ganin ya nufo shi yayi wa Mustapha sallama sannan ya kalle shi. "Ka gama soyayyar ne? Mr Lover Boy?" "Ina ai ba'a gama wa, saboda tuxurai irin ka, dole mu rike wuta ko zakuyi zuciya dai kuma." "Kan bala'ee, amma wallahi ka cini wasa." "Sai ka tsaya ai, saura kiris ka ganni da baby ma, kaji ana dada, dada daga nan zaka gane ai." Duka ya kai masa ya goge yana dariya, a haka Maryam ta fito ta tarar dasu suna tsokanar juna, sai suka bata sha'awa. Shiga ciki sukayi suka gaida Anty Maryam, a sace take kallon su, ba karamin birgeta sukayi ba, sai ta dinga hango Areef ɗin da sun girma suma haka zasuyi, dama suma gasu identical, har sun fara rarrafe ma kamar ka sace su very cute Masha Allah. Fita sukayi kowanne su dauke da yaran dan suma sun shiga ransu yan kubul-kubul dasu kamar yayan turawa, daki Anty Maryam ta jata ta kwaso shirge shirgen kayan gyara ta cika mata wata babba leda bayan ta gama mata bayanin kowanne su, aikuwa ta hau kunya tana wani murmushi dan wasu bayanan sun fi karfin kai na nima🤭. Kayan ta ta kai mota sannan ta karbo yaran ta dawo dasu ciki, suka tafi. Gidan Ya Nabila suka nufa Arab dai sai tsokanar su yake Maryam nata aikin dariya Arkel kuwa ji yake kamar ya mazge shi ya huta, haka dai ya daure suka karasa. Maryam bata san Ummi na gidan ba sai da suka shiga ciki ta ganta, idon ta biyu a zaune akan wheelchair din, da gudu gudu ta karasa ta zube a gaban ta farin ciki kwance a fuskar ta, kuka ne ya taso mata cike da tausayin baiwar Allah, sai ta durkusa a wajen ta saki kuka a hankali. Kukan Ummi ta saka itama ta mika mata hannu alamun tazo gareta, hannun ta ta kama ta rike a hankali ta furta "Daina kuka yar albarka, alhamdulillah na samu sauki ai.". "Ummi..." "Alhamdulillah." Kallon kowa tayi na falon idon ta ya sauka akan Arkel, ido ɗaya ya kanne ya girgiza mata kai, alamun tayi shiru, sai tayi kasa da kanta tana murmushi. Ya Nabila ce ta daga ta sannan suka shige ciki, dakin ta kaita sannan ta dawo ta tura Ummi ta kaita, fitowa tayi ta kwashi sauran kayan da sauri Arkel ya tsaida ta "Tafiya zamuyi fa." "Toh ku tafi man, wana rike? "My wife mana, naga kin shige da ita." "Anan ai zata kwana, kuje kawai sai da safe." "Inaaa." "Toh muje ko?" Arab yace yana kunshe dariyar sa. Key ya wurga masa yana kallon ya Nabila "Kaje kai ni gaskia ba tafiya zan ba." "Toh shikenan, ga BQ nan sai kaje ka kwana, Kanina ka gaida gida." "Gida ya ji, sai da safe." Marairaice fuska Arkel yayi, duk suka saka dariya, haushi ne ya kamashi yayi kicin kicin da fuska "Please kice mata ta fito mu tafi dare." "Allah ka zama mara kunya, saboda tsabar rashin kunya ni ba cewa nayi zan rike ta ba, magana kawai na shiga zamuyi sai ka zauna ka jira mu gama." Sosa kansa yayi kunya duk ta kamashi amma sai ya basar yana zama, gaban Arab ta taka tana kallon sa "Har yanzu ka kasa fuskantar ta? Ya kamata kayi magana da ita." Take annurin fuskar sa ya dauke "Tsoro nake walalhi, karki manta laifi na me girma ne.". "Ka yarda abinda kake tunani ba haka bane in Sha ALLAH." "Hmmm." "Karka damu, kazo gobe da safe nasan me zanyi." "Shikenan, Allah yasa muji alkhairi." "In Sha Allah." "Amin." *** Wani irin kallo yake bin ta dashi kamar yaga wata sabuwar halitta, duk ta gama tsorata da yanayin sa, kasa k'arasa wa kusa dashi tayi ya tashi yana kallon ko ina "Alhaji nah." Ta fada a dan tsorace da son tabbatarwa kanta abinda take tunani "Ina A'isha?" "Na'am." Ta zaro ido "Nace ina A'isha? Me kike anan? Waya baki izinin shigowa daki na? Ban miki katanga da ahlina ba? "Alhaji..." Daka mata tsawa yayi, ja da baya da baya ta hau yi yayi kanta da sauri ya rik'e ta "Muguwa bakar azzaluma, yau sai naga bayanki wallahi." Rikon da yayi mata ba karami bane, gaba daya idon ta ya firfito waje ta kasa magana, babu wanda yasan me yake faruwa, gaba daya ya haukace mata, babu yadda zai ya kyale ta ta tafi, wani irin naushi ya kai mata a fuska tuni bakin ta ya fara jini, gefe ya wurgar da ita cikin jina ya fito daga dakin yana kwala kiran Ummi, Baba ce ta fito da sauri yayi wajen ta "Ina A'isha? Me ya same ta? Tana ina?" "Alhamdulillahi, Allah shine abin godia, Maddapha ka dawo hayyacin kenan." "Baba Ina take.? Ina sauran yaran? Naji gidan shiru me yake faruwa.?" Budo kofar da akayi ne ya saka su dukka kallon kofar, Arab ne a gaba sai Arkel na binsa Maryam a kusa dashi, da sauri Alhaji yayi kansu yana tambayar inda Ummi take, kallon juna sukayi a tare cikin tsananin mamaki aka rasa wanda zai yi magana, "Baku ji bane wai?" Ina take? Me ya ke faruwa ne da ba zaku sanar min ba?" "Tana gidan Ya Nabila." Arkel ya bashi amsa, da sauri yayi hanyar waje, bin sa sukayi maryam dai sai ta sulale ta haye saman ta tana mamakin al'amarin, yana fita yayi wa driver magana ya fito da mota, ko ta kan su be bi ba da suke ta magana yace da driver su tafi kuma yayi sauri. Basu yi yunkurin binshi ba, dan dukkan su wannan shine abinda suka dade suna neman, ranar da suka dade suna jira kenan, ciki suka koma Arkel yayi sama ya bar malam Arabu yana cizar yatsa.😅 *** Gaba daya fuskarta ta haye tayi suntum da ita kamar wadda akayi mata shegen duka, da k'yar take fitar da numfashin wahala, a hankali ta rarrafa bayan gidan yayi tsit ta koma dakin ta ta murza masa mukulli, ba karamin wuya tasha ba ita kadai ta dinga juyi saboda azabar da take ji a bakinta, iya kar tunanin ta bata taɓa kawo wa rayuwa zata juya mata baya a dan taki kadan haka ba. Nace Kadan kika gani ma. *** Jirgin sassafe suka hau, saboda haka da wuri suka fice dan Maryam ko tashi bata yi ba sanda suka fitan, ko data tashi babu alamar su, gyare gyaren tayi da taimakon Sadiya me aiki suka hada breakfast sannan ta koma sama dan yin wanka. Direct suna dauko su gidan ya Nabila suka koma, Alhaji na nan, tun asubah ya sake komawa dan a daren Nabila ta sanar dashi komai da yake faruwa, kamar yayi kuka haka ya dinga la'antar mero saboda ba karamin zaluntar shi tayi ba dashi da iyalansa, shiyasa ya kudira a ransa tilas ne yaga shima ya saka ta a kwatankwacin rayuwar data jefa su. Addu'io da magungunan hade sai turaren hayaki haka duk yazo da su, a ranar aka fara yi mata komai aikuwa ta ga sauyi sosai dan maganar ta ma ta sake fitowa kuma ba laifi taji dadin jikin ta sosai har tana kokarin tashi da taymakon masu daga ta sai dai tafiyar ce sai a hankali. Zuwan malam ya sake warware abubuwa da yawa, ana i sauran kwana biyu za'a koma kotu asirin da Hajiya mero tayi ya gama warwarwa tsaf, babu wani abu daya yi saura, suna ta murna da farin ciki duk sun taru ana maida magana Arkel yafi kowa murna ya rasa in da zai saka kansa dan tsantsar farin cikin da yake ciki, gida ya koma ya dauko Maryama dan ita ma ayi da ita, yana shiga gidan yaji kamar ihu a dakin Hajiya mero, babu wanda ya san takunkumin daya sa mata har na fitowa ne illa kawai a tura mata abincin ta, Hajiya Mama ma da tazo hanata shiga gidan akayi haka ta k'araci zage zagen ta da tsine tsinen ta ta hakura ta tafi, shiyasa babu wanda ya damu da halin da take ciki, Maryam kam dama ba wani saukowa take ba idan ba kowa sai tayi zaman ta a saman hakan ya saka ba'a san halin data ke ciki ba. Yana bude kofar yayi saurin ja da baya ganin ta jefo babban glass Allah ya taymaka Bata same shi ba, dakin yake bi da kallo ganin komai ya hargitse duk wani abun fashewa ta fasa shi tas kayayyakin ta duk ta yayyagasu, gefe kwanunan da ake kawo mata abinci ne birjik wasu taci wasu kuma ba'a taba ba, maganganun da yaji tanayi ne ya sake tsorata shi, babu abinda take sai maganganun hauka tana yi tana jan gashin kanta kamar zata tsinke shi, kofar ya maida ya rufe tana jingina a jiki wani irin tashin hankali na ratsa shi, da sauri ya haura saman Maryam na kwance rigingine tana duba wayar ta ya shigo, hannun ta ya kama ba tare da yace komai ba, kayan jikin ta ta kalla doguwar riga ce sai dai babu dankwali a kanta hakan ya saka gashin kanta bayyana, "Bari na rufe kai na." Tace ganin da gaske be ma lura ba, sakin ta yayi ta saka hula sannan suka fito, dakin ya bude yana nuna mata ciki "Kalli kiga...." Da sauri ta ja baya taana zare idon ta, "Is she ok?" Girgiza kanta tayi kwalla na kokarin zubo mata, hannun sa taji a saman fuskar ta ya sa ya goge mata "Karki kuskura ki zubar mata da hawaye, bata chanchanci tausayin mu ba, Allah ne ya nuna ikon sa Maryam, wannan matar ta dade tana cutar damu, sau daya bata taba tunanin wannan ranar ba, nagode Allah daya kawo komai cikin sauki, duk abinda ya shuka dama shi zaka girba." "Amma..." "Shissh..., Dont say a word, muje kawai I'm hungry ma me Kika shirya min?" "Uhumm..." "Comman... Dont tell me kinji tausayin ta?" "Allah naji." "Wasa kike." Hannun ta ya kama suka haura saman, sai daya fara rage kayan jikin sa sannan ya dauki waya ya jira Zainab, ce mata yayi kawai tazo ya kashe ya kira su Ya Nabila ya sanar musu. Abincin da take jera masa ya kalla, shifa yau yadda yake jin sa so happy abinci ma ba zai shiga ba, kallon kasa-kasa yake mata, tana gama jera wa ya damko hannun ta "Bismillah." Tace tana nuna masa kayan "Yunwa ta tafi wallahi." Shagwabe fuska tayi "Kai fa kace yunwa kake ji?" "Na koshi toh ai, kinga... Zo kiji." Make kafada tayi tana dariya dan sarai ta gano wayon sa, hannu biyu ya hade alamar roko "Um um.." Wata kujerar ta koma ta zauna tana hard"e hannun ta, tsam ya taso ya dawo, zata tashi yayi saurin rikota yana dariya, kamar zatayi ihu haka ya maida ita ta zauna ya dora kansa a saman cinyarta. "Muyi hira toh, na fasa abinda nayi niyya." "Innalillah..." "Me? Ko kar na fasa ne?" Da Sauri ta rufe bakin ta "Ni wallahi bance ba." "Toh ni nace." Tashi yayi zaune yana duba wayar sa, kiran Zainab ne, be daga ba kawai ya kama hannun ta suka wuce other room.🙈🤭🤾🚴 *** Sai daya gyara jikinsa ya chanja kaya sannan ya fito, Zainab na zaune tana ta kuka bayan ta leka taga halin da Hajiya Mero take ciki, bata iya zama ba ta dawo falon dan saura kadan tayi mata illa sai jefe-jefe take tana maganganu mara sa dadin ji, yana kallon ta yaji tausayin ta ya kamashii, Bata da wata illa sai ta rashin samun uwa ta gari, da wucewa zai yi amma sai ya fasa ya samu waje ya zauna "Kin duba ta?" Daga kanta tayi "Me kike ganin za"a yi? Ko zaki kira chan gidan ne?" Ya fada kamar be damu ba. "Wai Hajiya Mama?" Ta fada cikin Muryar kuka "Su." "Na fada musu a waya, suna waje an hana su shigowa ne." "Oh okh." Tashi yayi hannun sa zube a cikin aljihu, kamshin turaren sa daya bar mata ta cigaba da shaka tana kallon saman tana ayyana irin sa'ar da Maryam tayi da irin rashin sa'ar da tayi ita kuma. Yana fita hajiya Mama tayi saurin saukowa daga mota, kuka take sosai Alhaji Faruku na gefen ta ya harɗe hannu, nauyi da kunyar yaron yake ji dan yasan ba karamin dauriya yake ba, ba dan da alaka ba ma babu yadda za'ai yi haka, toh ya san alakar Maryam suke ci, bude musu akayi suka shiga shi kuma suka tsaya waje tare da Alhaji Faruku da yace ba zai shigo ba, shi kanshi Arkel ɗin kunyar Alhaji Faruku ke hana shi aikata wasu abubuwan tun da duk tsiya dai shine ya shige masa gaba a lokacin auren sa. Da k'yar suka fito da ita aka saka ta a mota bayan an daure mata hannu da kafa da k'yar, suna kuka suka tafi da ita, ajiyar zuciya Arkel ya sauke yana juyawa sukayi ido biyu da Arab, be san yana wajen ba sai daya ganshi, yanayin fuskar sa kadai zaka kalla kasan akwai wani abu daya ke ji, shi din ma hakan ce, danne wa kawai yake yana nuna babu komai, ciki suka koma daga nan kuma suka sake fita dan zuwa wajen Barr. Nasir. Sai da suka gama dashi sannan ya samu ya bi kiran Hafiz, bayan sun gama magana ne ya kashe sannan suka koma gidan ya Nabila. Washegari Hafiz ya tattaro ya dawo amma sam inna tace ita da Kano sai ko gawarta, yana zuwa suka hadu da salim ya nuna masa aikin da zai yi a Arkel Poultry farm, cike da farin ciki ya fara aikin cikin kwanciyar hankali. *** Gaba daya sun hallara a babban falon gidan, Ummi ta warware sosai, har tana takawa abinta, babban taro aka shirya saboda kowa ya fadi ainihin abinda ya faru, Maryam da Ya Nabila ankon lace sukayi dan ubansu, shi kuwa Arkel da Arab Getzner suka sa me masifar kyau, suna zaune ana hira kafin fitowar Ummi da Alhaji,, lokaci zuwa lokaci Arab duba sakon Lubna yana murmushi, haka Ummi ta fito cikin shiga ta alfarma kayan su kala da ya da Alhaji, Babban me hoton da aka ɗauko Ahid Sufi ne ya fara aikinsa cikin kwarewa da iyawa, sai da aka fara bude taro da addu'a sannan aka fara komai cikin ilimi da wayewa. Yadda CIkin ta ke hautsinawa ne ya hanata sukuni, wani irin tashin zuciya irin me tukukin nan ne ke taso mata, Arkel dake gefe yana lura da ita, ganin ta tashi da sauri ta bar wajen yasa ya bita da sauri. Da ido suka bishi dukkan su, Ya Nabila da dama tun tuni take hasashen wani abu game da yadda taga sauye-sauye a tattare da Maryam ɗin yasa ta sake sakawa ranta abinda take tunani. *** THE BEGINNING OF SOMETHING NEW, SAUYIN ƘADDARA DAI SHINE TITLE DIN LITTAFIN, SO DONT EXPECT A HAPPY ENDING😂🧚 *** Pressure din mutane yasa nayi rushing din page din Nan walalhi, please allow me nayi shi a nutse saboda ido na kar nazo na yanke labarin kuma azo ana abu ba dadi. In Kuma kun fiso nayi rushing din toh ba damuwa na iya rushing Yasin 😂😂😂😂😅🤣 *41-42* ©*Hafsat Rano* *_ZAFAFA BIYAR na kudi ne idan kana son kowanne daga ciki ka nemi Wannan numbers din_* *08030811300* *07067124863* *** Da gudu ta shige toilet, cikin tane ya baci shiyasa ta tashi da sauri, kafin ya k'arasa ta rufe, buga kofar yayi, a tunanin sa ko wanne abu ne, kamar zata yi ihu take matse jikin ta bata so yayi kara, gashi a matse take gashi ya tsaya a kofar yana tambayar ko lafiya? Da sauri tace "Dan ALLAH ka tafi, ciki na ne ya ɓaci wallahi." Wata irin dariya ce tazo masa sai ya sake rike kofar yana kyakyatawa, ashe gayu ma ana fafatawa, ganin yaki tafiya gashi iya kar yadda zata iya matsewa ta matse saboda bata so yaji karar, magiya ta cigaba da yi masa, gaba daya ta rude zufa kawai take fitarwa ta ko ina, sai daya gama tsonarta sannan ya juya ya tafi, sai data tabbatar ya tafi sannan ta saki jikin ta, ta zuba harkar ta a nutse, kunya take ji sosai bayan ta gama kawai ta watsa ruwa ta fito, riga kawai ta zura ta fesa turare ta sauko, duk suka zuba mata ido, ji tayi kamar zata harɗe, ido ɗaya Arkel ya kanne mata da suka hada ido tayi saurin dauke kanta, sannu duk suka hau jera mata, kanta a kasa take amshewa kunya kamar ta nutse dan bata san sannu me ake mata ba, Ummi dake ta faman fara'a tace ta dawo kusa da ita ta zauna, a kunyace ta koma ta zauna har lokacin taki yarda su hada ido dashi, dan ta lura ma har wani farin ciki ya kara akan dazu, shiyasa sam taki bari ma suyi magana balle ya fallasa ta. Dukkan su sun bawa Ummi hankalin su waje daya, Alhaji daya dan tashi amsa waya ne kawai baya wajen, a hankali ta soma da asalin labarin. "Abu daya na sani a rayuwata shine na taso a gidan mu muna da matukar yawa, gida ne babba irin gidajen hayar nan masu dakuna a ƙalla 20, Ni kadai ce a wajen Baba yelwa, da ita ba taso na buda ido duk da tace min ba ita ce ainihin mahaifiyata ba, a haka nayi rayuwa ta me cike da kalubale da gwagwarmaya, duk wanda yasan gidan haya irin wannan yasan ba zai rasa kalubale da tashin hankali ba, hakan kuwa akayi wata rana Baba Yelwa sukayi wata rigima da wata mata dake kusa da dakin mu, rigimar har ta kaisu da police station, aka bawa Baba Yelwa rashin gaskiya dan dama itace me fitina kaf gidan, dalilin haka yasa aka tattara mu aka kore mu daga gidan, ni dai ba zan ce Baba bata yi min komai na rayuwa ba, sai dai dani da almajira banbancin mu kadan ne, kullum ina cikin mummunar shiga, abinci kuwa sai taci ta koshi take bani, haka dai muka harhada muka koma Kaduna da zama, daga Niger Minna, komawar mu Kaduna ne muka hadu da mutane kala-kala, wanda suka fi Baba Yelwa wayewa da komai, a lokacin ne kuma suka zuga Baba Yelwa akan ta kaini aikatau kawai ta huta da wahala dani,a take ta amince ta bukatar su, a daren naga ta koma gefe tayi waya, ta dade tana wayar kafin ta ajiye tana me matukar farin ciki dana kasa gane dalilin sa, washegari muna tashi da sassafe muka shiryo mukayi Kano, gidan da ake kai yan aiki aka kaini, ina kallo Baba Yelwa ta tafi ta barni, nayi kuka sosai haka na hakura, sati na daya wata mata babba tazo ta dauke ni. ”Tun daga lokacin rayuwa ta ta saka sauya wa, aiki ne babu dare babu rana, haka na jure wa duk wata wahala, ana nan kuma sai Allah ya taimake ni maigidan ya saka ni a islamiyya asabar da lahadi, tun daga lokacin rayuwa ta samu haske, na san addini, wanda da duk bansan komai akai ba. Sosai na sake a gidan, ayyukan da nake sun riga sun zama jiki na, bana jin komai, gashi na fara jin dadin karatun nawa shiyasa na sake jajircewa dan bana son abinda zai jawo min na rasa karatun. "Akwai wata rana na shigo daga islamiyya kenan sai ga Hajiyar da  ta badani aiki, gaba na ne ya yanke ya fadi ganin ta danayi nasan ba alkhairi bane, bayan na gaishe ta naje na cire kayan jiki na sai kawai na zauna a dakin na kasa fitowa ina jiran tsammani. Ina nan zaune Hajiya ta leko, gaba na ne ya yanke ya fadi, sai data gama kallon dakin sannan tace "Shirya Indo, tafiya zakuyi marikiyarki ce ba lafiya, kiyi sauri kar kuyi dare." "Jiki na na rawa na tashi, ba hada yan kayana na fito, muka kama hanya, sai dare muka isa dan mun tsaya a gidan matar, halin dana ga Baba Yelwa ne ya firgita ni sosai, ciwon kafa take kafar ta rube gaba daya ga wani mugunyar wari da kafar ke fiddawa, haka na cigaba da jinyar ta dan kudin da muke dashi har yazo ya kare, daga nan ne kuma na shiga gararin rayuwa, na rasa yadda zan yi da ita gashi ko abincin da zamu ci da kyar muke samu. "Ranar da ciwo ya ishe ta ne ta saka na kira mata wannan matar, a handfree na saka mata wayar sai da tayi ta ringing sannan ta d'aga. Gaishe ta Mama Yelwa tayi cikin tsananin ciwo,  dakile take amsa gaisuwar kamar zata kashe kiran, "Lafiya Yalwa? Akwai matsala ne?" "Akwai Hajiya, jiki na yaki dadi, komai na iya faruwa dani, shiyasa na kira ki kizo ki dauke ta, bana so Allah ya kamani da laifi." "Toh... Kin kusa tafiya kenan? Toh a gaskiya Ni dai ba zan iya zuwa daukar ta ba, kina gani da kyar na samu na koma daki na, ki san yadda zakiyi dai da ita ta riga ta bar hannu na yanzu ba zan iya wani abu akai ba." "Dan Allah ki taymaka Hajiya, yarinyar nan abar a tausaya mata ce, ni dai nayi nadamar abinda na aikata wallahi Allah, ki taymaka kizo ki dauke ta ki mayar da ita wajen iyayen ta." "Zancen kike so, na gama magana ta sai anjima." "Shikenan, tun da haka kika zaba, zan kawo ta har in da kike, sauran bayanin sai ki nemi yadda zakiyi ai." Tana kaiwa nan tayi min alamar na kashe, kashe kiran nayi na kura mata ido ina neman karin bayani. Bata ce komai ba ta nuna min wata babbar akwati "Miko ta kinji?" Tashi nayi na dauko ta, kallon akwatin tayi nima n kalla,. "Wannan ita ce komai naki, ita ta ƙunshi duk wani abu daya shafe ki, na cutar dake sosai,na taymaka wajen kashe miki rayuwa, amma zan Allah ki yafe min." A yadda take maganar da kyar ne yasa nace tayi shiru kawai, fita waje nayi na samu wani waje na zauna nayi kuka na, kukan rashin mafita, kukan rashin gata, bani da kowa sai Allah, haka nayi me isata na share hawaye na nayi shiru, ciki ka koma na tarar har tayi bacci, ashe baccin tafiya ne,baccin da ya tafi da duk wani sauran farin ciki na, a ranar nayi kuka kamar ido na zai makance, na riga nasan tabbas rayuwa ta ta gama yawo, bani da kowa bansan kowa ba, bansan in da na kama ba. Bayan rasuwar ta sai na fara tunanin yadda zan rike kaina,duk in da naji labarin masu kawo yan aiki sai naje ko Allah zai sa na samu, sai dana sha bakar wuya sannan na samu aiki a wani gida. Zuwa na gidan nan shine asali ko nace tushen da ya saka duk abinda ya faru yanzu ya faru, tun bayan zuwa na gidan komai ya chanja, bayan fuskantar kalubale da nayi ta fannin yaran gidan,Mero ita tafi kowa bani matsala, kyara da wulakantawa babu wanda bata yi min, duk da cewa na girme ta,amma hakan be saka ta daga min ba, haka nayi ta hakuri saboda idan ma nayi fushi bani da in da zan kama. Gida ne babban gida family house, Yaran da yawa iyayen su basa gidan sai dai matan uban, shiyasa babu wata gamshashiyar tarbiyya a tattare da gidan. Ni dai na kama mutunci na bana shiga sabgar kowa aiki na kawai nakeyi. Akwai watarana da saurayin Mero yazo, bayan taje wajen sa sai ta bukaci na kawo masa abin sha, ba asan raina ba na dauka na kai masa, tun daga ranar shikenan sai reshe ya juye,, wannan shine asalin abinda ya haɗa mu da ita har taci alwashin daukar fansa tana ganin munci amanar ta, duk da da farko ni kaina ban amince ba, ganin yadda kowa na gidan ya juya mun baya har ana shirin kora ta ya sa na amince, haka akayi auren ba tare, na bar Kaduna na dawo Kano, ashe ban sani ba har lokacin abin be bar zuciyar ta ba, wannan shine babban dalilin daya saka ta shigo rayuwar mu, ta tarwatsa mu ta tarwatsa dukkan farin cikin mu." Dukka falon babu wanda jikinsa be yi sanyi ba da labarin Ummi, Alhaji ne kawai be ji komai ba saboda ya san komai, sai kuma Arkel da ya nuna kamar be san me yake wakana ba, dukkan su sunyi shiru kowa na tunanin wannan al'amarin. Kan Arab a kasa cikin dararradin abinda zai tarar yace "Ummi..." Murmushi tayi "Karka damu, babu abu daya daya faru da kake tunani, Allah ya duba zuciyar mu, ban cuci kowa ba, Allah ba zai bari irin wannan abun ya faru da mu ba, dukkan shi shirin ta ne, ita ta shirya komai, ita ta tsara komai dan ta dauke hankalin kowa daga kaina." Wata iri yar ajiyar zuciya ya sauke, farin ciki ne yake ratsa dukkanin kofofin jikin sa,abinda ya dade kenan yana dako a ransa, abinda ya hanashi walwala da jin dadin rayuwar ma baki daya. Daki Ummi ta shiga ta fito da akwatun, duk wasu abubuwa masu mahimmanci na ciki ne banda takarda guda daya, sama ko kasa ta duba takardar nan babu ita, kayan aka sauke komai amma babu, Kallon su kawai Arkel yake har aka gama be tofa komai ba, tuno da in da ya ajiye takardar yayi, lokaci yayi da amfanin ta zai tashi, sai ya sake gyara zaman sa kawai yana ji ana neman da ya riga yasan babu yadda za'a yi a ganta. Hotuna ne guda biyu a cikin kayan, wasu maza ne masu kama daya a cikin shigar Fulani daya ya rataya sanda a kafad'ar sa, hoton irin Black and White din nan ne gashi yayi mugun dade wa, motsawa Ummi tasa sukayi sannan tace "Wannan shine Arkel, wannan kuma Arabu, gashi nan kowanne an rubuta sunan sa a kasan hoton sa, wannan hoton shi kadai nake dashi daya rage min, shi din ma bansan ya akayi na same shi ba, a cikin kayan da Baba Yelwa ta bani ne na gansu, na san dai yana tattare da wani abu game dani, hakan yasa dana haife ku na sa muku sunan, Muhammad shine sunan ku, Arkel kuwa da Arabu inkiya ce, nayi hakan ne dan ko watarana Allah zai sa ta hanyar sunan na samu wani nawa, suna ne da ba kowa ya san shi ba, hasalima sunan Fulani ne, wannan tunanin ne ya saka ni kiran ku da sunan, ko da aka zo za'a saku a makaranta ni na saka lallai a saka muku sunan, ina fatan wannan dalilin ya hadani da ahalina, dangi na kamar kowa." Duk sai suka kalle ta cike da tausaya wa, Maryam Sarkin kuka sai share hawaye take dan ba karamin tausayi Ummi ta basu ba. Kowa sai da yayi magana a wajen amma banda Arkel, ko da aka ce yayi sai ya nuna ba yanzu ba, akwai abinda yake so ya karasa. Sai kawai aka kyale shi aka tafi cin abinci da Sallah ganin lokacin ya ja. *** *Bayan Kwana Biyu.*ne *** Sai data sauke komai na wardrobe dinta, kallon ta yake ta gefe yana so yayi dariya amma sai ya dake, ranta duk babu dadi haka ta sake maida kayan ta jera su ba tare da ta san dalilin da yasa ta sauke ɗin ba, tana zuba na karshe ya ajiye wayar hannun sa ya tako a hankali ya rungume ta ta baya, da sauri ta juyo, suna hada ido tayi kicin kicin da fuska kamar zatayi kuka, jan ta yayi a haka har gaban gadon sannan ya zauna ya jawo ta jikin sa "Bak'ya so na tafi ne?" Da Sauri ta daga kanta "Umm." "Toh me yasa? Ko zaki bini?" Kallon sa take kawai tasan ba zuwa zai yi da ita ba, ga makaranta ma karatun su ya fara zafi, sai ta girgiza kai kawai alamar a'ah. Zama ya gyara mata a jikin sa sosai ya dan zamota "Karki damu, na shirya komai just one week zanyi, Idan na dawo si ki rakani muyi weekend ko?" "Da gaske?" "Da gaske mana, ko bak'ya so.?" "Ina so wallahi." Nan danan ta saki fuskar ta, kayan sa ta tayashi ya karasa haɗawa, dambun naman da aka yi jiya ta zuba masa a wata roba me kyau, ta hada masa da doughnut tayi rapping d'insa ta hada masa dashi. Abinci suka ci a saman dan yace ba zasu sauka ba yau, so yake su soye abin su, dakin sa suka shiga ya dauko laptop dinsa da charger suka koma nata dakin, Frozen 2 ya kunna musu, dan a dan zaman da sukayi ya lura da ita tana son irin films din shiyasa yayi mata downloading dinsu da yawa. Pillow suka saka guda daya suka jingina dashi, kafadar sa na gogar tata a haka suka zauna suna kallon Film ɗin, gaba daya hankalin ta ya tafi wajen kallon, hakan ya bashi damar tunanin abinda ya kamata yayi kuma. Idon sa ya rufe ya sake mike ƙafarsa sosai, kallon sa tayi ta jima sosai kafin ta dauke idon ta tana sauke ajiyar zuciya, ranar kawai take jira da zai furta mata yadda yake ji game da ita, da haka bacci ya dauke ta, gyara mata kwanciyar yayi ya kashe komai ya ajiye a in da ya dace, sai daya sauka kasan ya tabbatar da komai daidai sannan ya dawo ya kwanta kusa da ita yana tofa mata addu'a. *** Yana tsaye gaban mirror yana sharce ruwan kansa da hannu daya, hannun sa daya ya dora shi a saman kugun sa yana kallon duk wani motsin ta ta cikin mudubi, gaba daya bata ta kuzari da walwala a kasalance take komai, duk sai yaji ba dadi, sai dai ya zama tilas yayi wannan tafiyar ko dan ya cika wa Ummi burin ta, kallon kananan kayan data ajiye masa a gefen gadon yayi ya dauka ya saka, yana daure belt ta sake shigowa dauke da kayan tea da flask, da sauri ya karbe ta ya ajiye a saman carpet din dake gaban wajen, idon ta yake nema ya saka cikin nasa amma sam taki yarda su hada ido, ta juya ya riko ta yana juyo da ita . "Menene?" Yace yana kallon cikin idon ta, hawayen da ya biyo fuskarta ya kalla da sauri yasa hannu ya tare "Kuka dai? Wai ko na fasa tafiyar nan ne?" "Um um." "Gosh, toh ki saki ranki please, kar kisa na kasa aikata komai, kinji? I ll come back for you in Sha Allah." Gid"a kanta tayi, ta saka hannun ta tana share hawayen fuskar ta. "Ki shirya mu fita tare, sai kije ki kwana biyu a gidan umma." "Da gaske?" Nan da nan ta saki fuskarta, dariya yayi kawai ya zauna don karyawa. Karamar trolly ta fito da ta zuba kayan ta kala biyu sai under wears da sauran kayan da zatayi amfani, sai murna take tana sauri yana zaune yana kallon ta yana murmushi. Wankan ma a gurguje tayi ta fito, ta saka wata atamfar ta super ta cikin lefenta Lemon Green and Orange me zanen ganyen bishiya, mayafi ta yafa orange ta saka flat shoe, fuskar ta babu komai daga powder sai dan wetlips data murza, sosai tayi kyau ta fito fes, har wani sheki da kyalli fuskar ta take yi, tana gaban mirron sai jin mutum tayi ya zuro fuskar sa a saman kafad'arta, tana dagowa ya dauke su hoto, ba karamin kyau sukayi ba, sunyi matukar dacewa da juna, bata wayar yayi ta kura wa hoton ido tana ta aikin kallo kamar me sunyi kyau. Ummi suka sauka sukayi wa sallama ya fada mata zata je gidan kwana biyu, komawa tayi daki ta dauko mata yan abubuwa tace ta kaiwa umma kafin tazo zuwa na musamman. Arab na ganin su ya hau tsokanar sa yana cewa ko dai tare zasu tafi zai wani waske da gida zata, shi dai be kula shi ba dan yasan sarai so yake ya sashi yaji kunya a gaban ummi, waje ya rako su aikuwa ya kai mishi duka yayi saurin gocewa yana dariya. Shine zai kaishi airport din, a baya suka zauna suka barshi shi kadai a gaba aikuwa ba karamin shaka yayi ba, babu yadda be yi akan Arkel ya dawo gaba ba fafur yaki haka ya hakura ya tada motar yana ayyana kalar rashin mutuncin da zai shuka masa idan suka ajiye Maryam. A kofar gidan suka tsaya, da sauri aka saki gate din gidan Hajiya Mama alamun akwai mutum da yake labe da a jiki, kalla sukayi sai kuma suka dauke kai basu ga kowa ba, tare suka fito ya sauke mata jakarta suka shiga zauren gidan, a kasa ya ajiye mata kayan ya jawo ta jikinsa. Ya dade a haka kamar kar su rabu sai da Arab ya ishe su da horn sannan ya sake ta yayi mata sallama ya tafi. Sai ta kasa daga kafa daga wajen tana jin babu dadi, sati dayan da zai yi jin sa take kamar shekara daya, bata taba tunanin ta shaku dashi har haka ba sai yau, yanzu da take ganin zai tafi ya barta, hawaye taji masu zafi sun fito, hannu tasa ta goge sannan taja jakar ta shiga gida. **** Hafiz Saukar sa kenan daga adaidaita sahu yaga wucewar motar Arkel, da kallo ya bita har suka wuce shi, juyawa yayi zai shiga yaji wata motar ta taho, tsayawa yayi yana kallon motar, da gudu take har suka kusa bin kansa yayi saurin ja baya, zaro ido yayi a daidai lokacin da glass din bayan motar ya sauka kasa, kallon sa tayi ta sakar masa murmushi sannan ta daga masa hannu, a hankali glass din ya koma ya rufe, kansa ne ya kulle ya rasa me zai yi, wayar sa ya ciro da sauri ya kira Number Arkel , har ta gama ringing ba'a d'aga ba, da sauri ya shiga cikin wajen, machine din baba me gadi ya ara ya bi bayan motar da mugun gudu, sai da yayi da gaske sannan ya kamo su, a hankali ya shiga bin su duk in da sukayi dan san tabbatar da abinda idon sa ya gani. [3/18, 22:27] Hafsat Rano: SK 43-44 Na kudi ne, kina so ki karanta ki nemi wannan Number. 08030811300 Greetings to u *Fatima Hussayn Isari* (Maman Walid). *** Suna daukar hanyar Arab yace masa "Wai tafiyar me zakayi ne." Dan jim Arkel yayi kafin yace "Akwai abinda zan saro ne, ba wani jimawa zan ba." "Kai kuma yaushe zaka koma?"  Ya ɗora Sai daya sha kwana sannan yace "Bana jin komawa wallahi, na fiso nayi ta zama a cikin family na." "Ya zakayi kenan, kazo kayi joining bussiness din nan, its very good." "Allah ko?" "Emana." "Owk tam, da yake ma suna ta shirye shiryen bude branch anan Kanon, zan koma na nemi transfer cikin wanda zasu kawo Kanon, in sun ki sai na ajiye musu aikin su na dawo gida, amma zaman crossriver kam na gama shi." "Owk hakan yayi sosai, Allah ya taymaka Mr Kanu." "Kut.. ni ne kanun?" "Toh ko Samuel ne?" "A ah okonkwo ne, dan air. Dariya sukayi gaba daya, haka suka karasa har airport ɗin suna hira dan ma sun hadu da holdup ne. Yana ajiye shi ya daga kiran Lubna, tun suna tare da Arkel take kira baya so ya daga ne yasan sai ya rama abinda yayi masa shi yasa yaƙi d'agawa "Hello." "Barr. Kina lafiya?" "Lafiya lou Moha, ina ta kira ina ka shiga ne?" "Ina nan na kawo kid bro dina airport zai yi tafiya, amma na juya gida ma." "Kai haba,kuma babu nisa fa da unguwar mu, please ka biyo mana, tun ranar bamu sake haduwa ba." Kallon agogon jikin motar yayi "Beyi safiya ba kuwa?" "Haba dai, sha biyu fa ta kusa." "Kinsan yan gayu basa tashi da wuri fa." "Su waye yan gayu?" "Manyan Barristers mana." Dariya tayi "Babu wani wayo da zakiyi min, I'm waiting for u, zan tura ma address ɗin, bye." Ta kashe kiran bata bari yayi magana ba, girgiza kai yayi yana dariya ya sake kallon kansa ta cikin mirror, text ne ya shigo wayar sa ya duba, address ɗin ne, location ɗin ya duba a wayar sa, juya wa yayi ya dau hanya yana jin sa wani iri kamar wanda zai je aikata wani abu, tsoro tsoro haka yake ji har ya karasa, Babban gida ne dan har sai daya dan tsoro ta da yanayin girman gidan, yana tsayawa ya kirata a waya, lokacin ta gama shiryawa ta hade cikin doguwar riga baka tayi rolling mayafin sai flat shoe data zura a kafarta, Babu makeup din komai tayi kyau kana gani kasan boko, hutu da tsantsar wayewa sun zauna a wajen. Lekowa tayi ta hangi motar sa a dan gefe, yana ganin ta ya kashe motar ya fito, kallon sa take ba dauke ido har ya karaso, dan kunya taji ta ja mayafin ta ta rufe gefen fuskar ta. "Sannu da zuwa." "Sannun ki, yau dai gani a gidan ku." "Da na takura ba,Allah Muhammad ka iya shariya." "Ayi min afuwa toh, ba zan kara ba ai." "Yawwa dai, mu shiga ciki toh.". Kallon kansa yayi "Ƙananan kaya ne fa jiki na, no gaskia." "Toh menene? Kamar wanda zai shiga gidan surukan sa?" Ta fada don son jin me zai ce "Kuma fa haka ne, na manta ba gidan surukan bane, sorry muje toh." Da sauri ta kalle shi, ya dauke kai kuwa kamar be san me yace ba, jikin ta yayi sanyi sosai har sai da ya sake magana sannan ta juya ciki ya bi bayanta yana danne dariyar da tazo masa, tuni ya gano ta sai dai har yanzu be san a wanne stage ya ajiye ta ba tukunna, zai cigaba dai da bin ta a hakan zuwa lokacin da zai gama tabbatar wa kansa komai, sai dai shi a tsarin sa yafi don yarinya karama yar secondary School ma so samu, amma dai zai bar komai a wajen Allah ya zaba masa mafi Alkhairi dan gani yake kamar Lubna tafi ƙarfin sa. *** Zuwan ta gida yayi mata dadi sosai, wunin ranar tare da yan uwan ta tayi shi. Har lokacin Arkel be kira ta ba, ta kira wayar sa kuma bata shiga, lokaci zuwa lokaci take dubawa har yamma tayi babu wani labari, ganin gidan shiru Umma ta je kasuwa yasa ta dau Hijabin ta ta zura ta tafi gidan Maman Walid (Fatima Hussayn Isari), a bayan gidan su take suna dan shiri da ita kafin tayi aure, da sallama ta shiga gidan, a share gidan yake tas babu ko tsinke, kamshin turaren wuta ne yake tashi irin na tsinken nan ta sakale shi daga jikin bangon tsakar gidan, da murna ta tarbi Maryam ta shinfida mata tabarma, sosai yanayi da tsarin gidan hade da tsaftar ya burge maryam, girki take yi shi yasa ta saka mata tabarmar a dan gefen dan madaidaicin Kitchen din ta. Tana zaune suna yar hira Abban Walid ya dawo, da sauri Maman Walid ta tashi ta tarbe shi, kayan hannun sa ta karba tana mishi sannu a jere, gefen jikin sa ya dan jawo ta ganin da bakuwa, dariya tayi babu kunya ta rike mijin ta sukayi ciki tana cewa Maryam tana zuwa, sosai hakan ya birgeta ta fara ayyano ta a irin yanayin, zata so ace gidan su su kadai ne daga ita sai shi, duk da har yanzu ba wai yace yana son ta bane amma dai ita kam ta riga ta gama fadawa kogin son sa, bata jin kuma akwai abinda ba zata iya aikata masa ba, jira tayi Maman Walid ta fito dan akwai abubuwan da kuma take son sake gani kafin ta tafi, sai ta gyara kafarta ta mike ta kawai tana murmushi ita kadai. Fitowa Maman Walid tayi ta mika mata Walid daya tashi daga bacci sannan ta koma ciki, karbar shi tayi tana masa wasa, chan sai maigidan ya fito, da sauri Maman Walid ta dauki buta ta zuba masa ruwa sannan ta saka masa yar karamar kujera yar tsuguna, zama yayi yayi alwala bayan ya gama ya fita, har zauren Maman Walid ta rakashi sannan ta dawo ciki. Sosai abin ya birge Maryama, tashi tayi ganin magriba na kawo kai tace zata tafi, daki Maman Walid ta shiga ta hado mata wasu abubuwa a cikin leda yar madaidaiciya, kallon ledar Maryam tayi tana neman karin bayani "Gashi nan ba yawa amarya, ki bani number ki in yaso sai nayi miki bayani ta waya, sauri nake na karasa girki kafin Mu'allim ya dawo daga masallaci, ga baban rigima Walid ya tashi nan da lokaci kadan zaki ji ya bude murya." "Toh shikenan, Nagode sosai, sai na jiki." Ta karanto mata Number sannan tayi mata sallama ta tafi. Umma ta dawo ta bude kayan data siyo tana dubawa maryam ta shigo, gefe Habubu ne akan sabon keken sa su Walid sai binshi suke yi, da kallo Umma tabi Maryam har ta zauna. "Ke kuma daga ina?" "Wallahi zaman ne ya ishen, sai na shiga gidan Maman Walid, Sannu da Dawowa." "Yawwa." Kallon su Habubu tayi tace "Habubu an siyo keken kenan, yaro me zuciyar nema,wai da gaske umma kajin nasa ya siyar ya sai keke?" "Gashi kuwa kin gani, amma fa ni nayi kiwon, shi dai ya tara yan kuɗaɗen sa da wanda mijin naki ya bashi ranar ya siya kajin, amma kam ai ni nasha wahalar kiwo." "Ai gaskia wallahi ya burge ni, haka fa ake son mutum me zuciyar nema, ji fa tun yana karami kenan." "Aikuwa dai." "Allah ya sanya alkhairi, Walid zo ka siyo min awara dan Allah." Da sauri Habubu yace,, "Ni zan siyo miki, sai naje a keke." Walid ne yace "Eh sai muje tare." Dariya Maryam tayi "Ai fa yanzu Habubu zai zama Sarki a unguwa, yara da keke yanzu za'a yi ta masa biyayya." Dariya kawai umma tayi ta tashi ta shige ciki ta barsu suna ta faman yi. Bayan sun gama hira ta sake gwada numbr sa shiru, sai kawai ta kwanta jikin ta a mace tana tunanin dalilin da ya hanashi kiran ta. Kasa baccin tayi lokaci zuwa lokaci sai taji kamar wayar ta na ringing, da sauri take dubawa sai ta ga babu komai, tashi tayi, ta dauro alwala tayi sallah tana fatan komai lafiya, ba tare da sanin ta ba bacci barawo ya sace ta a wajen sallar sai kiran farko ne ya farkar da ita. Da kyar tayi breakfast waina bandashe da kunu duk san da take musu amma sai taji ba dadi saboda tunanin halin da yake ciki, bata so ta sawa zuciyar ta wani tunani amma kuma ba zata iya sakin jikin ta ba ba tare da taji daga gare shi ba. Umma na lura da ita duk tayi sukuku da ita, wajen azahar zawon da take kwana biyu ya sake dawo mata, haka ta wuni sur tana abu daya, ga wani irin murdawa da cikin ta yake, dole umma ta kira Baba ta sanar masa, shiryawa tayi suka tafi asibiti duk jikin ta ya mutu bata da kuzari. *** Yana ajiye shi a airport ɗin daya tabbatar ya fita sai ya da dau wayar sa ya kira Salim, jim kadan sai gashi ya zo, daukar sa yayi suka je suka dauki mutumin nan sannan suka dau hanya. Tafiya ce me nisan gaske, sunyi ta ne cikin wahala da tashin hankali, babu wani titi me kyau sai rubud'i cike da tarin kasa babu ko bishiya a hanyar, hakan ne ya tabbatar masa daf yake ta in da yake shirin zuwa, sai ya sake zama yana kallon hanyar sosai. Dare ne ya riskesu har lokacin basu kai in da suke so ba, saboda yanayi na wajen yasa suka tsaya domin kwana a wajen saboda tsaro. Zaune suke a cikin motar baka jin karar komai sai tsuntsaye garin yayi shiru, tunanin Maryam ne ya fado masa ya kalli wayar sa, samun kansa yayi da shiga gallery ya bud'e hoton ta da yayi mata ba tare da ta sani ba lokacin tana kula da Ummi, tsaya wa yayi chak yana kura mata ido, komai nata simple and unique yadda yake son mace ta zama, babu baragada ko hayaniya a duk abinda take yi tana yin sa ne cikin sanyi. Murmushi yayi yana dan shafa wayar, sai ya kashe ya rufe idon sa yana jin komai ya taho karshe idan har abinda yake fata ya tabbata, kaddarori ne da yawa suke bibiyar rayuwar su, ya riga yayi imani da kaddara me kyau ko mara kyau kuma yana fata da sa ran tasu ta zame musu wani tsani da zai kaishi ga rahamar Allah. Lokaci zuwa lokaci yana duba wayar sa,babu wanda zai iya wani ishashen bacci a cikin su, duk da salim na ta gyangyadawa a zaune amma shi da malam babu ko alama ko digon baccin har zuwa lokacin da asubah ta riske su. Alwala sukayi suka yi salla a cikin motar, kayan Dan snacks din da Salim ya taho musu dashi duka dan ci suka sha ruwa sannan suka cigaba da daukar hanya suna fatan isa kafin lokacin sallar azahar. Sai da suka sake ninka wata doguwar tafiyar sannan suka hangi Gari. Gari ne da yake kasar ta Mali, ajiyar zuciya Malam yayi ya kalli Arkel "Mun kusa nan da awa biyu zamu shiga kauyen Mandar, duk da ni kaina rabona da garin shekaru ne masu yawa, sai dai ina fatan mu samu abinda muke je nema." "Allah yasa." Arkel da Salim suka haɗa baki. "Mu biyu ne muka fara fita daga kauyen namu, tun daga lokacin bamu sake waiwayar gida ba, shi me sunan naka da yake tare suka tafi da me dakin sa, Ni kuwa achan nayi aure." "Kun dade gaskiya." Salim yace yana jinjina kai "Dadewa ma bata wasa ba, karka manta bayan nan suka haifi Arabu wanda suna ne na dan uwan shi Arkel ɗin ya maida wa dansa ,shi kuma Arabun shine ya  haifi ita kakar taku, ita kuma ta haifi mahaifiyar taku da wan ta namiji, idan ka fahimce ni, Arkel shine asalin ku, bayan ya zo Nijeriya sai ya haifi Arabu, daga nan shi kuma arabu sai ya haifi kakar ku wadda ita ce ya haifi mahaifiyar ku, kafin kuma azo kanku." "Wai, ni wallahi kaina ya kulle gaba daya." Salim yce Yana sosa kansa dan be fuskanci komai a alakar ba." Murmushi Arkel yayi "Na gane ni kuwa, abu daya nake son tababtar wa shine rayuwar shi wan Ummin, shin yana raye? Idan yana raye zan fi kowa farin ciki, ina da yakinin zai san wani babban dalili da ya sa aka raba Ummi da iyayensu" "In Sha Allahu da ransa." Kallon sa Salim yayi, daga masa kai Arkel yayi yace "Kana da tambaya ko? Feel free kayi tambayar ka, trust ne yasa na saka ka akan komai nawa, Allah ne ya hada mu amma ina jin ka kamar wani nawa makusanci." "Ni ɗin ma hakan take oga, ni kawai wasu abubuwan ne idan kayi suke ban mamaki, ya akayi ka gano Malam ne wai?" Murmushi Arkel yayi irin na gefen bakin nan ya kalli malam "Allah ne ya duba zuciyata ya kawo min komai cikin sauki, watarana ina zaune abubuwa sun min yawa, na rasa yadda zanyi sai kawai na fita dan na wasa kafata saboda zaman waje daya, ina tafiya ne ba tare da sanin in da zani ba sai naji ana kiran sallah, tsayawa nayi nayi alwala a dan karamin masallacin dake kusa da wajen, bayan an idar ne na fito zan wuce sai nji ana kira na a waya, gefe na matsa na daga kiran, kaya ne da nayi order online ne suka zo saboda haka sai da suka fara tambayar suna na saboda su sake tabbatar wa ni ne me kayan, kai tsaye nace musu Muhammad Arkel , a lokacin Malam na gefe, jin sunan da na fada ne ya saka shi sai dani bayan na gama wayar. Kaji yadda muka hadu, sauran bayanin kuma sai nan gaba, ka daina mun kallon wani daban, ni ne dai Muhammad Mustapha daka sani." "Angon Maryama kuma ba." Salim ya fada yana dan matsawa, dadi ne ya kama Arkel ya sake sakin fuskar sa, a tunanin Salim zai ce ya bari amma sai ya ga akasin haka, sai ma wani lumshe ido yake yi yana murmushi kasa-kasa. *** Iska ake sosai a garin, da sauri Arkel ya lalubi hanky a aljihun sa ya rufe hancin sa saboda asthmar sa, gidaje ne tsilla-tsilla suke wucewa har suka zo tsakiyar garin, da kallo suke bin babbar masarautar dake girke a tsakiyar garin, gine ne irin na zamani wanda aka kawata shi da ado irin na sarautar Fulani, mutane ne kyawawa suna ta hada-hada a wajen kowa da abinda yake yi, kallon motar suke har suka samu gefe sukayi parking, Babu Wanda ya motsa a cikin su, shi kanshi Malam ji yayi bashi da kuzarin fuskantar mutanen gari da yake ganin tsantsar chanji tattare dasu, lallai duk wanda ya bar gida gida ya barshi, gefe Arkel ya kai idon shi inda ya ga wajen cike da dabbobi tun daga kan shanu har zuwa kan zabbi da kaji sun fi duba wane dari, basu da adadi, lallai shi yasa kenan yake masifar kaunar kiwo a rayuwar sa, gado ba karya ba, sai yaji wani sanyi na ratsa dukkanin kofofin jikin sa, take yaji shi kamar ya zo gida cikin dangin sa. Wani magidanci ne ya nufo su ya tsaya daga dan nesa dasu sannan yace "Barkan ku da zuwa, me kuke so? Shanu ko kaji, zabbi, agwagi, ko akuyoyi?" Cikin harshen sa na Fulani da baya fita da Hausar sosai, kenan ana shigowa sarar dabbobi wajen su kenan shiyasa sukayi tunanin ko su ne. Malam ne ya fito yana kallon sa. "Sarki muka zo nema." Da sauri ya kalle su, "Sarki ?" "Eh sarki." Juya harshe Malam yayi zuwa Fulatanci, da sauri mutumin ya washe fuska, "Bari ayi muku iso, sannun ku da zuwa." Da sauri ya juya, fitowa sukayi suka tsaya, Arkel dai sai kalle kalle yake ya rasa inda zai sa kansa, da sauri ya koma motar ya dauko hoton nan da sauran abubuwan da yake ganin zasu taymaka wa, mutumin ne ya dawo ya basu umarni su shigo ciki, bin sa sukayi suka kutsa kai cikin gidan da yafi kama da gari guda saboda girman sa. Manya manyan gine gine suke din ga wucewa, duk in da suka wuce sai an kalle su an gaishe su, yara ne kanana daga gefe gwanin sha'awa suna ta wasa, har suka dangana da babbar fadar basu ci karo da mace ko daya ba, salim da yake ta zare ido ko zai ga wata saboda yadda yaga tsananin kyau da mutane suke da su shiyasa ya kwallafa rai yana so ya ga ya matan su suke. Yana zaune akan karagar sarki irin tasu, gefe da gefe manyan yan fada ne ana ta fadanci cikin harshen Fulatanci, kansu a kasa suka shiga, da kallon Sarkin ya bisu yana kurawa Malam ido, tsantsar kamar da ya gani ne yasa ka shi kasa dauke idon sa, sai ya cigaba da rarraba idanun sa tsakanin kan Arkel da Malam. *** Ganin yana bin su ne ya saka suka kara gudu sosai, gudun shima ya kara don san tabbatar da zargin sa, idan har da gaske itan ya gani ya zama lallai Arkel ya sani, a yi gaggawar daukar mataki akanta, cigaba da binsu yayi ba tare da ya bari sun kubuce masa ba har suka sauka daga kan titin suka gangara wata hanya mara kyau, cigaba yayi da binsu, ganin yadda suke shiga layuka ya dan tsorata shi, amma kuma ba zai taba yarda su kubuce masa ba, gwara yayi risking life din sa ya tabbatar da ita akan ya koma saboda mutane ne da yawa zasu shiga a matsala a dalilin hakan. Gani yayi sun taka birki sun tsaya, daga gefe chan ya tsaya shima yana hangen su, yana kallo ta fito, mika tayi irin ta gajiya tayi magana da direban motar sannan tayi gaba, a kafa take tafiya shi kuma direban ya juya ya shiga wani layi, ganin haka ya saka Hafiz bin ta da sauri, layin da ya ga ta shiga ya shiga shima, ashe layin baya fita, juyowa tayi tana murmushi. Da sauri yace "HAJIYA MERO!!!" Wani abu yaji an buga masa a kansa, daga nan be sake sanin komai ba ya fadi a wajen sumamme. Hafsat Rano Sauyin ƙaddara 43-44 #Not edited, [3/18, 22:27] Hafsat Rano: *SK* 45 ©Hafsat Rano *** Jan sa sukayi suka shigar dashi gidan dake gefe hannun hagu, bin bayan su Hajiya Mero tayi ta shiga falon,dan karamin dakin dake gefen wajen suka chillashi suka datse kofar, daga waje suka tsaya suna gadin kofar. Zama tayi tana jan dan karamin tsaki, ba karamin haushi Hafiz ya bata ba, dan karamin kwaro dashi amma yace zai kara da ita, shi ma uban daya tsaya matsan Arkel sane take dashi, ba banza ta maida kanta mahaukaciyar karfi da yaji ba ai, ba zata kyale kowa a cikin su ba, cin amanar da Ummi tayi mata ba zata tafi a banza ba, sai ta cire dankwalin kanta ta mike kafarta tana lalubar number sa. *** Duk wajen kowa yayi shiru yana sauraron Malam, Arkel kansa a kasa be yadda ya sake dagowa ba saboda yadda ido yayi masa yawa, gaba daya manyan wajen wani irin kallo suke bin sa dashi kamar zasu cinye su, Sarkin kansa ya gaza dauke idon sa daga kansa har wani dan zamowa yayi daga kujerar sa yana sake fuskantar sa,tsufa da tarin haifa da suke tattare da Sarkin kadai zaka kalla kaji ya maka kwarjini, komai nasa yana nan be yi wani mummunan tsufa ba duk da akalla ba a kasaru ba ya bawa dari baya. Cikin rada rada Salim ya ce masa "Oga kaga yadda suke kallon ka kuwa? Ni fa abin ya fara bani tsoro, kar muje malam ya kawo mu ni a sayar damu fa." "Kayi shiru dan Allah." Yace cikin kuluwa, daidai lokacin Malam ya karasa bayanin sa, gani sukayi Sarkin da kansa ya sauko daga karagar sa ya nufo su, kafin suyi wani yunkuri sai gani sukayi ya saka dukkan hannun sa biyu ya rungumo Arkel, cikin Yaren da Salim da uban gayyar suka zama kamar wasu dolaye yayi wa sauran dake fadar magana, ai sai suka hau murna suna sambarka, shi dai Arkel sai yak'e yake yana kallon fuskar malam don neman garin bayani, daga masa kai kawai yayi alamn kar ya damu, sai kawai ya saki jikin sa ya biye musu suka cigaba da kawo  gaisuwa kamar yadda suka fara bayan Sarkin ya koma wajen zaman sa. Wasu maza ne su biyu suka rike hannun malam suka fita dashi daga fadar, dan zabura Arkel yayi zai tashi Sarkin yayi saurin dakatar dashi cikin kwararriyar Hausa yace "Karka damu dashi, ya riga yazo gida, su yanzu wannan sune iyayen garin nan, kai kuwa dan mune, jikan mu ne, tattabakunnen mu ne." Duk sai aka sa dariya, Arkel ma sai ya samu kansa da murmushi kad'an, ɗorawa Sarkin yayi "Tun shigowar ka nan duk muka tabbatar da kai din ahalinmu ne, jini ba karya ba, ya riga ya nuna akanka." Kallon juna sukayi a tare shi da Salim suka sakar wa juna murmushi. "Allah ya kara maka lafiya, kenan an yarda da abinda muka zo dashi?" "Tabbas mun yarda, saboda babu in da ka bar mu, komai naka namu ne, sannan zuwan ku da shi ardo ya sake tabbatar mana , ka sani babu ta yadda wani namu zai taba guje mana mu kasa shaida zuriyar sa, Arkel be taba barin ranmu daidai da rana daya ba, duk kuwa da nisan dayayi mana, muna tuna wa dashi a kullum kuma muna yi masa addu'ar amince, Allah yayi maka albarka yaro, lallai ka cika mutum nagartacce da har kayi kokarin sada zumuncin da ya dade da yankewa." "Alhamdulillah." Arkel yace yana kai goshin sa kasa, ji yake kamar ya zuba ruwa a kasa ya sha, haka aka cigaba da tattaunawa da dawo da tarihi da kuma wasu tambayoyi da Sarkin yake tayi masa, sai ya ciro hotunan nan ya mika wa sarki, hawaye ne ya biyo fuskar Sarkin, mika wa sauran yan fadar hoton yayi suka kalla, daya bayan daya duk suka gama gani sannan Sarkin ya karba yana sake dubawa "Allah sarki dan uwana, ashe ka tafi chan ka tara zuri'a, Allah yayi maka Rahma." Hada baki sukayi wajen cewa Amin, haka aka cigaba da tattaunawa har aka dawo da malam cikin shiga irin tasu sai gashi ya fito sosai, gefen sarki aka sashi, sannan sarki ya cigaba da bayanin rayuwar su ta baya, a cikin bayanin ne Arkel ya fuskanci shine Arabun kenan dake jikin hoton, hakan ba karamin dadi yayi masa ba, sai ya shiga ayyano kalar farin cikin da Ummi zata shiga, a rayuwa bashi da wani buri kamar na farin cikin Ummin, tun ranar daya karanta labarin ta, ya shiga kunci, babban abinda ya katse mishi hanzari tun da ma rashin lafiyar ta ce, a yau ya san ko babu ransa Ummi zata samu farin ciki, zata san dadin yan uwa, zata san dadin dangin ta. Cikin gidan Sarki Arabu ya sa aka rakasu, tun daga hanyr shiga suka fara cin karo da mutane masu yawan gaske, kalle kalle kawai suke cike da burgewa. Dakin wata tsohuwa aka kaisu, aka gabatar dasu, sai gashi har da yan koke koken ta na farin ciki, a nan suka zauna aka shiga jere musu kayan abinci kala-kala, wasu abubuwan ma basu taba sanin akwai su a duniyar nan tamu ba sai yau, da ido suke bin kowa kawai basa wani jin abinda suke cewa tun da masu jin Hausar cikin su kadan ne. Abinda zasu iya ci suka chacchakala sannan aka tafi kaisu masauki. Suna tafiya suka ji ana maganar ga Gimbiya Bongel nan ta dawo, duk sai sukayi jere suna jiran ta, tsayawa bawan da zai raka su yayi alamun shima jira yake tazo ta wuce, baki hanci Salim ya bud'e yana kallon halitta, cikin tsananin ado fuskar nan ta ta sam babu walwala, sanda tazo gaban su ne taja ta tsaya tana kare musu kallo, kallon ta Arkel yayi cikin ido, hakan ya saka ta saurin janye idon ta daga kansu ba tare da tayi magana ba ta wuce kawai masu bin ta suka take mata baya. Dan karamin tsaki Arkel yaja sannan sukayi gaba, haushi duk ya kamasa tsaida sun da tayi, dan dai be san wajen bane da babu abinda zai tsaidashi. Allah Allah yake ashe dama su isa masauki, da sauri ya hau rage kayan jikin sa saboda zafin da yake ji, dariya kawai salim yake masa har ya shiga toilet dan watso ruwa. Bayan ya fito ya ciro wayar sa dake a kashe tun jiya ya kunna, yayi tunanin zai ga ko da sakon Maryama ne, amma sai ya ga wayam, duk sai yaji ya damu, har ya ajiye wayar yaji ba zai iya ba kuma, Ummi ya fara kira suka gaisa, tayi masa korafin wayar sa a kashe, hakuri ya bata ya dora "Babu chargy ne Ummi, sai yanzu na samu sakawa, ayi min afuwa." "Babu komai, Allah ya bada sa'a." "Amin Ummi nah." Dariya tayi ta ajiye wayar, sai ya danna Number Maryam, tana ta ringing baa d'auka ba har ta katse, d'an jim ya sake yi sannan ya kuma kira a karo na biyu, Walid ne yaji ringing d'in a d'aki suna wasa da Habubu ya shiga da sauri, daukowa yayi ya daga. "Hello, Yaya Maryam ɗin bata nan sun je asibiti da Umma bata da lafiya." A kwance yake sai ya mike da sauri "Me ya sameta? Walid ne ko Abubakar?" "Walid ne, bata da lafiya ne shine suka je asibiti." Dafe goshin sa yayi, jiki a sanyaye yace "Shikenan , idan sun dawo zan kira." Kashewa yayi, duk sai yaji babu dadi, ya tuna tun a gida take dan shiga toilet, be kuma bada hankalin sa har ya kaita asibitin ba, gaba daya sai yaji yana jin haushin kansa, kasa zaman yayi ya mike ya fito yana dan zagaya wa hannun sa sakale ta bayan sa. Tsaye take a kofar bangarenta, tana hango shi ta kafe shi da ido daga nesa, kallon ta yayi, sai ya sauke kansa da sauri yana chanja direction din sa, da sauri ta juya ta shige ciki tana buga kofa. Yawo yayi sosai a cikin masarautar da tafi kama da gari guda, sosai abun ya bashi sha'awa yadda suke kiwo sosai, kiwo shine sana'ar da suke yi tun iyaye da kakanni, kowanne bangare ya nufa sai ya ga ana kiwo a wajen. Tafiya yayi sosai ba tare da ya sani, wani babban waje ya hanga cike da ya'yan itatuwa birjik babu kalar da babu iya ganin mutum, gefe wani dan karamin ruwa ne daya saka lambun a tsakiya, kai tsaye wajen ya nufa ya shiga yana tafiya a nutse, iska ce me matukar dadi ke kadawa, wani irin yanayi yake shaka yana ayyano wasu abubuwa a ransa, daga chan gefe ya hangi wasu kujeru masu matukar kyau da kyalli, sai ya nufi wajen ya zauna yana daga kansa sama. Sosai wajen yayi masa dadi, waje na da zai dace da yanayin ma'aurata wanda suke cikin shauki da begen juna, masoya masu son su tabbatar da soyayyar su ya kamata su kasance a irin wajen, sai ya shiga auno kansa da Maryam suna zaune suna hira, hira me cike da nishadi, so yake ya ji labarin ta, kuruciyarta, komai nata yake so ya sani, shiyasa yake son shirya musu wata yar tafiya da zasu kadaice ta juna, hakan zai kara kusanci a tsakanin su, a lokacin ne zai fallasa mata asirin zuciyar sa, lokacin da ya riga ya san babu wani nauyi ko tunani akansa. Tsawon lokaci ya dauka a wajen ba tare da ya sani ba, sai da wayar sa ta dawo dashi daga tafkin daya afka na tunanin ta, a dan zabure ya ciro wayar yana tunanin ita ce, jikin sa ya bashi itace, aikuwa ita ɗin ce, babu wani bata lokaci ya daga cikin tausayawa yace "Mero ta." Sai taji wani yar, yadda ya narke murya sosai da yadda ya fadi ta ɗin yasa ta a wani yanayi na soyayyarshi, bata iya amsawa ba har sai daya sake cewa "Baby kina jina? Ya jikin naki?" Cikin hado kalmomi ta cije tace. "Da sauki, drip ake samun." Muryar ta kasa tayi maganar, da sauri yace. "Subhanallah, abun har ya kai haka?" "Uhum..." kawai tace ganin umma ta shigo dakin, abu ta dauka ta fita, tana jin sa ya cigaba da jera mata sannu babu kakkautawa, uhum kawai take binshi dashi dan bata da wani kuzari gaba daya jikin ta babu kwari dalilin kenan da ya saka ake sa mata drip din amma a gida. "Me suka ce yake damun ki?" "Ciwon ciki nake, wai naci wani abu ne." "Ayya, basu kuma ce ga wani abun ba bayan nan?" "Me?" Tace da sauri "No I'm asking ai, bayan ciwon cikin, basu ce wani abu ba?" "Basu ce ba." Ta amsa a gajarce. "Shikenan, Allah ya Baki lafiya kinji, get well soon." "Amin." "I miss u." Yace yana chanja topic din dan son ya ga ta dan ware dan yaji muryar ta wani iri, sai kawai tayi murmushi ba tare da ta mayar masa ba. Hira ya cigaba da jan ta har yaji an fara kiran sallah a masallacin cikin Masarautar, sallama yayi mata da alkawarin zai kira anjima. Yana kashewa ya jefa wayar a aljihu yana barin wajen. Bayan sun gama wayar Maryam bata bar mamakin shi ba, duk yayi laushi kamar bashi ba, sai kawai ta bar abin a matsayin dan ya ga bata da lafiya ne yake lallabata, duk da haka taji dadin yadda yayi mata, ita kadai take murmushi tana kallon takardar serum test din da akayi mata and it's positive, sai ta kunshe fuskar ta kunyar Umma na sake kamata tunowa da tayi da ta san komai. *** Da k'yar hafiz ya bude idon sa guda daya, wani irin mugun sarawa kansa ke masa, juyi ya fara yi yana son tuno abun da ya faru, daya bayan daya komai ya dinga dawo masa a kwakwalwa, da sauri ya yunkura zai tashi, a daddaure yake ta ko ina, yar karamar kara yayi jin duk ko ina na jikin sa ya dauka saboda daurin daya sha, kalle kalle ya shiga yi a dakin, babu komai sai wasu tarkacen kaya a wani dan karamin buhu,jikin sa ya shiga jaa a hankali yaji an budo kofa. Da sauri ya daga kansa, tare suka shigo ita ce a gaba suna bin ta, ransa a matukar bace yake kallon ta, ji yake kamar yaje ta shako ta ya kashe ta kowa ya huta, ya rasa hatsabibancin ta, da rashin tsoro kamar namiji. Kama shi daya daga ciki yayi ya daure masa baki sannan ta nuna masa wani katako, "Kuyi masa laga-laga har sai ya bar numfashi sannan kuje ku wurgar dashi chan bayan gari, wannan shine sakamakon sa ma cin amana ta, iya kacin adalcin da zan iya yi masa kenan, wawa, be san setup bane daga ganin mota ka fara bin ta." Babu bata lokaci suka cika aikin su,tana tsaye suka kwashe su suka fita dashi a bayan mota sannan ta koma ciki tana jin tayi wani abu da ya saka ta farin ciki. *** Gidan babu kowa duk sun fita makaranta, Maryam ta dan ji karfi ta fito ta dau tsintsiya zatayi shara Baba ya fito zai tafi kasuwa, yana ganin ta yayi saurin cewa ta ajiye, a kunyace ta ajiye tsintsiyar ta koma ciki tana tunanin ko Baba ya san labarin ne? Rufe fuskarta tayi tana jin kamar tayi tsuntsuwa ta gudu daga gidan saboda yadda take jin kunya. Yana fita kai tsaye gidan Hajiya Mama ya shiga dan gaishe ta, kwana biyu kenan be shiga ba saboda abubuwan sun kara yawa, yana shiga Alhaji Faruku ya tsaya da yake kokarin shiga shashen Hajiyar, gaisawa sukayi a mutunce cikin girmamawa kafin su nufi bangaren zasu shiga a tare. Tana zaune ta bude wasu kayan ta,duk ta barbaza su, kayan jaririya ne a ajiye a gefe ta kura masu ido, duk da girma da tsufa sun kamata gashi dama kwana biyu abun nata kara gaba yake, ita kadai sai tayi ta soko zance marasa kan gado, asibiti aka kaita suka ce sai hakuri tsufa ne ya taba ta, haka aka dawo da ita gida ana dai bata magani amma abin babu wani sauki. Gaishe ta sukayi ta amsa acikin nutsuwa, dan jim baba yayi sai kuma ya mike zai fita, "Garba..." Ta kira shi a karo na farko bayan wasu lokuta masu tsawo, sai ya ja ya tsaya yana jin kamar bada shi take ba. "Zo ka zauna zamuyi magana." Be Musa ba ya dawo ya zauna a in da ya tashi. "Zaka iya tuna kanwarka A'isha? Da aka sace ta a ranar sunan ta? Duk da lokacin baka fi shekara goma ba." "Na tuna Hajiya, dalilin kenan da Gwaggo ta kamu da hawan jini me tsanani har yayi sanadiyyar mutuwar ta." Kallon sa ta ke tayi har yayi shiru yana sake sauke kansa kasa. Gaban Alhaji Faruku ne ya fadi yana tunanin abinda zata faɗa dan har ya gano in da ta dosa. Kar dai??? "Nice nasa aka sace ta, saboda sanadiyyar da mahaifiyar ku tayi min na bar gidan mijina, shiyasa ni kuma nayi mata abinda zai kashe ta a hankali, kai naso a lokacin na dauke sai dai matsalar duk san da aka zo sai a tarar da kai tare da Umar, dalilin kenan da ya saka na...." Wata irin zabura Alhaji Faruku yayi, shi kansa baba zaman yan bori yayi, "Hajiya... Ma..ma..." Alhaji Faruku yace yana mik'ewa, kamar zai zare saboda yadda zancen ya kada shi, kallon Baba yake yana so ya fuskanci yanayin da yake ciki, gani yayi ya mike tsaye, be ce komai ba ya juya yayi hanyar fita, sai daya je karshe sannan yace "Shari'ah ce zata raba mu dake wannan karon, bazan iya kyalewa ba, kayi hakuri Umaru." Zuciyar sa na tafasa ya juya ya koma gida Alhaji Faruku ya biyo shi yana kiran sa, banza yayi masa ya shige gidan har da rufo kofa kafin ya kai ga shiga. Gefe Alhaji Faruku ya samu ya zauna yana jin zuciyar sa kamar zata bullo kirjin sa ta fito. *** Assalamu alaikum dearies Ina gaisuwa Thanks for ur supports😍😍 Rano [3/18, 22:27] Hafsat Rano: *SAUYIN KADDARA* *46-47* ONAR TASFAH _ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU😁._ *ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma *SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano) *KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo) *BURI ƊAYA!* (Mamu gee) *WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull) 👇🏻karku bari ayi babuku *ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu* *za'a tura kudin ta wannan accnt number din* Hafsat kabir umar 0225878823 GT bank Saika tura shaidar biya ga wannan number ta WhatsApp 08030811300 Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din 07067124863 Sai kayi wa Number magana ta WhatsApp *** Yana shiga ya datse kofar, Maryam na tsaye a bakin rariya zuciyar ta na faman hautsinawa Baba ya shigo a matukar fusace, tun da take bata taɓa ganin bacin ran sa irin na ranar ba, da kallo ta bishi har ya shige dakin sa ya ja kofar ya rufe. Tashi tayi jiki a sanyaye ta nufi dakin Umma tana ayyana abinda ya faru da Baban, Umma na zaune tana gyara dakin Maryam ta shigo, da kallon umman ta bita har ta zauna a yar kujerar dake gaban keken dinki daya kusa shekara babu wanda ya haushi. "Lafiya dai?" Ummm ta tambaya tana ajiye zanin "Baba ne ya shigo a wani yanayi, ya shiga dakin sa ma ya rufe." "Toh!"  Umman tace tana ajiye kayan hannun ta, "Bari naje naji." Taso wa Maryam tayi ta dawo saman gadon ta kwanta zuciyar ta duk babu dadi ga wani zazzaɓi zazzaɓi dake son rufe ta. Tana nan kwance ta fara jiyo muryar baban a sama, da alama fada yake sosai, sai tayi lakwas tana sake gyara kwanciya tana hasaso abinda ya saka baban yake wannan fadan ba karami bane. Bugun kofar da ake ta faman yi ne ya dawo da Maryam daga baccin daya sace ta, tashi zaune tayi tana sake kasa kunne sosai, fitowar umma taji, chan sai taji Muryar Alhaji Faruku tsakar gidan suna magana da Umma, tasowa tayi ta fito, yanayin fuskar sa kawai ta kalla ta san akwai matsala, sai ta rakube a jikin bangon, gaishe shi tayi ya amsa a takaice, shiru yayi bayan umman ta gama masa bayani, jikin sa a sanyaye ya juya ya fita. Hada ido sukayi da Umma, sai ta girgiza kai kawai ta koma dakin baban, gaba daya sai kanta ya kulle, so take taji me yake faruwa, duk da alamu sun nuna yar matsala ce tsakanin Baban da  Alhaji Faruku tun da har yaki fitowa da yazo. Addu'a kawai tayi Allah ya gyara komai ta juya daki. *** Hayaniyar su Zainab da Rauda ne ya sake bata mishi rai, fada suke kamar zasu cinye kansu, Hajiya Mama na zaune a falon tana ta jera charbin data tsinka dazu, idan ta gama shiryawa sai ta sake tsinkasu, haka take tayi, kamar zai yi kuka ya shigo falon, ta zubo masa ido tana kallon sa, kamar zai yi magana sai ya fasa ya nufi dakin da suke ciki, suna ganin sa sukayi shiru, a fusace ya daka musu tsawa "Wanne irin hauka ne haka? Tun daga waje nake juyo hayaniyar ku." Kansu a kasa babu wacce tayi magana, kwafa yayi ya juya ya fita, harara Rauda ta sakar wa Zainab kafin ta tashi ta bar dakin gaba daya. *** A gaba Umma ta saka shi, babu irin nacin da bata yi masa ba akan ya sanar da ita me yake faruwa amma fafur yaki, kayan sa da yake ta ajiya tsawon wasu shekaru ya tattaro ya fito dasu kaf, dayan bayan daya yake binsu yana dubawa, sai daya gama duba komai sannan ya tattara ya ajiye yana kokarin fita ta sake tsaidashi "Haba, ya kamata ka sanar dani me yake faruwa, shirun nan naka be dace ba, na chanchanci nasan me yake faruwa karka manta ni matar ka ce." Kallon ta yayi, wajen sakan biyar yana nazari kafin yace "Zaluncin da aka dade ana yi mana ne yau Allah ya bayyana shi, labarin dana taba baki na batan A'isha, yau da kanta ta bayyana kanta, ashe Hajiya Mama ce ta shirya komai." Da sauri umma ta dafe kirjin ta dan tasan babu abin da Baban yake jin ciwo kamar wannan,tsawon zaman ta dashi tasan babu abinda ke dauke walwalar  sa idan ya tuna kamar batan yar uwar sa da mutuwar mahaifiyar su. "Wannan karon hukuma ce zata raba mu wallahi, ko zanyi yawo tsirara sai na bi hakkin wanda aka cuta." Kafin tayi magana ya fice, Maryam dake jin komai ta fito "Umma menene yake faruwa, wallahi na kasa sukuni.?" "Sirrin boye ne ya fito fili, bansan yadda zata kaya ba, amma tabbas ko ni ban yarda da kyale wa ba, wannan zaluncin yayi yawa." Ciki umman ta shige sai tabi bayan ta da sauri. Zama sukayi umman ta shiga bata labarin abinda ta sani har zuwa yanzu da abinda ya faru, sosai maganar ta kada maryam, shiyasa ashe baban nasu bashi da kowa da wasu dangi sai Abba (Alhaji Faruku da suke uba daya)jiimanin abin suka wuni sunayi yi, har sanda Baba ya dawo babu abinda ya sauya na daga fushin da yake, haka dole Alhaji Faruku ya hakura da jiran Baban ya kyale shi, dan ba karamin fushi yayi ba. Shi kanshi Baban baya so wata magana ta hadasu,,kar nauyi da kunyar da yake ji su hanashi aikata abinda yayi niyya tun farko, yasan yadda yake da Alhaji Faruku zai ji nauyin aikata wa mahaifiyar sa wani abu,amma idan ya fita harkar sa ya rufe idon sa shikenan, dan baya jin akwai abinda zai hanashi aiwatar da abinda yayi niyya. *** Hajiya Mama surutan nata kara gaba yake, ras da ita idan ka ganta amma kan da sauki, Alhaji Faruku kuwa abin duniya ya hadu yayi masa yawa, ya rasa in da zai saka rayuwar sa,gashi dai duk tsiya uwa uwa ce, duk muni da rashin kirkin uwar mutum son ta yake kuma ba zai so abinda zai same ta ba. Ganin bashi da wata mafita yasa kawai ya fawwala wa Allah al'amarin da. Ya zuba ido ya ga abinda zai faru. *** Kwanan sa biyu a gaban bular, gaba daya jikin sa jini ne, kasancewar hanyar babu masu wuce wa yasa har ya kai hakan, a kwana na biyun ne ya fara farfaɗo wa, da kyar ya bude idon sa daya yi masa mugun nauyi, a kumbure yake sosai ya ja jini, dishi- dishi ya soma gani kafin ya fara jin garin na juya masa, wani mutum ne yazo wucewa a mota ya ganshi, har ya wuce ya yi shahada ya dawo ya duba shi, ganin yana numfashi a galabaice yaayi saurin daukar sa ya sashi a mota da taymakon dan uwan sa da suke tare, asibiti suka wuce dashi, babban likita ne ashe saboda haka suna zuwa aka karbe shi babu wani bata lokaci aka shiga bashi taimakon gaggawa. *** Kusan raba dare sukayi ranar suna waya da Arkel, duk rabi da kwatar hirar tashi ce, ita dai daga umm sai a'ah, sai kuma wani abun idan ya kure ta ta bada amsa, da kyar ya kyale ta kwanta bayan ta marairaice masa dan ba karamin bacci take ji ba, gobe take son komawa dan taji sauki sosai, gashi Ummi ta kirata jiya akan taji shiru, gidan babu dadi, da tace mishi ma zata koma sai yace tayi zaman ta idan ya dawo sai su tafi, amma kiran Ummin yasa ta ga kawai gwara ta koma din. Da safe ta tashi da dan ciwon kai,  da kasala, tunanin labarin da Ummi ta basu akan rayuwar datayi da kuma labarin da Umma ta bata na Baba da kanwar sa da aka sace take ta hadawa waje daya tana tattaunawa da zuciyar ta, chan kasan zuciyar ta tana jin kamar akwai babbar alaka a tsakanin labaren biyu, sai dai ta rasa da wa zata tattauna,Anty Maryam ce abokiyar hirar ta gashi kuma sun yi tafiya sun ji garin su mijin ta biki, dole ta yanke shawarar sanar wa umma. Bayan tayi wanka ta saka riga da skirt na material ta daura dankwalin, sai ta fito tsakar gida wajen Umma, tana tsaye gaban kejin kajin da Habubu ya sake zubawa tana dubawa ko basu da ruwa, sai data tabbatar komai daidai sannan ta dawo ta zauna tana kallon ta "Yaushe zaki tafi?" "Zan jira broda din sa, Ummi tace zai zo ya dauke ni bayan magriba." "Ok, kinci abincin?" "Wallahi umma abincin ne yaki shiga, awara nake so." "Daurewa ake ai, sai kin kula da cikin ki, ki godewa Allah ma bakya laulayi me wahala." Kunya ce ta kamata. "Kin ga dazu kuwa kawar nan taki zango ta kiraki kina wanka na daga, wai an saka muku lecture ranar asabar." "Kash... Ni wallahi duk karatun nan ya ishen, ga project da zamu fara." "Allah dai ya taimaka, aski dama idan yazo gaban goshi yafi zafi." "Haka ne." "Umma magana zamuyi." "Ta me?" "Wani abu nake ta tunani." "Na me fa?" Gyara zama tayi ta sanar wa umman komai, shiru umman tayi itama tana auna maganar kamar akwai alamar tambaya a cikin ta, duk da basu da tabbas amma zasuyi iya kar kokarin su suga sun taymaka, tun da a halin da ake ciki ma Baba ya gama shirin sa na komai kara kawai zai shigar. *** Tana idar da Sallah sai ga kiran Arkel, lokacin ya fito kenan yana zagaye masarautar, da Bongel suka hadu yau ma kamar kullum ta kalle shi, ganin yana waya yasa ta fasa wuce tayi wajen sa, cigaba yayi da tafiya salim na gefen sa ita kuma ta cigaba da tunkarar su "Oga kai fa take kallo." Salim yace yana kunshe dariyar sa, sai gaban Maryam ya fadi jin abinda Salim yce, banza Arkel yayi masa ya cigaba da wayar sa har ta karaso, "Sannun ku." Tace "Bby, zan kiraki bari na karasa masauki." Kafin tayi magana ya kashe wayar, wani tukukin bakin ciki ne da kishi suka taso mata, radau taji maganar mace, kuma ga abinda salim yace, ai gaba daya sai taji komai yayi mata zafi, duk sai ta kasa cigaba da aiwatar da abinda take har Arab yazo suka tafi bata da wata walwala. *** Satin su daya sannan suka dauko hanya, wannan karon su biyu suka taho babu malam wanda yace ya zo gida, aikawa kawai iyalin sa da sauran jikokin sa suzo su ga dangin su. Arkel yana cikin tsananin farin ciki har Allah Allah yake ya isa gida, babu wanda ya fadawa zuwan sa, maigadi na zaune yana jin yar Radio sa yaji ana buga gata ɗin,, tashi yayi ya leka, da sauri ya zare sakatar ganin ashe oga ne da kansa, da sauri ya karbi kayan hannun sa suka wuce ciki. Lokacin Maryam na zaune a falon tare dasu ummi da Arab suna ta hira, magana ce a bakin Maryam ɗin amma ta kasa furta ta, sai sakawa da warware wa take ta rasa ta in da zata fara, ita kadai take ta hasashen ta har zuwa lokacin da ya turo kofar bakin sa dauke da sallama, ita ce a saitin kujerar da ke kallon kofa, saboda haka yana shigo wa da ita yaci karo, idon sa a kanta ya zuba mata su,  Ummi da ta saki baki tana mamakin ganin sa dan bata yi zata ba, murmushi ne kwance a fuskar sa ya karasa gaban Ummin yana sauke dukkannin jikin sa a kasa, "Ummi..." "Ikon Allah... tafiya ba shiri dawowa ma ba sanar wa." "Wallahi Ummi." "Sannu da hanya toh." Kallon Arab yayi yaga ya dauke kai yana danna waya, ya san haushi yaji da be sanar dashi ya sauka ba, sai ya maida kallon sa wajen Maryam data sauke kanta kasa tana wasa da gefen mayafin ta. "Wasu basu iya sannu da zuwa bane Ummi?" Sanar ta gane da ita yake, dariya kawai Ummi tayi, ta tashi tana cewa "Kaga ban san maka ba, bari na shiga ciki." Tashi tayi ta shige ciki a nutse tana dan taka kafar, bin ta sukayi da kallo cike da tausaya wa, tana shigewa Arkel yayi saurin dawowa gefen ta, kallon sa tayi ya bata fuska "Baki ganni bane wai madam." "Sannu da zuwa." Ta fada a kasa kasa kar Arab yaji, "Tashi tashi, muje ciki kawai akwai yan sa ido anan, muje sama." Sai a lokacin Arab ya kalle shi, dariya kawai yayi yace "Idan ka dawo normal munyi magana." Da sauri Arkel yace "Yanzu hauka kaga ina yi kenan?" "Kusan hakan ne." Yace yana dariya gami da mik'ewa yayi waje gaba daya. Sai ya maida kallon sa wajen Maryam dake dariya k'asa-k'asa, hannun ta ya kama ya murd'a, da sauri ta daina dariyar. "Tashi muje." Yace yana rike ta, har sunyi hanyar saman sai ya tsaya "Samo mana abinci a Kitchen din Ummi idan mun hau mun hau kenan sai da safe." Zame hannun ta tayi ta juya Kitchen din, hancin ta tasa hannu ta rufe hancin ta sannan ta shiga, kamshin da Kitchen din yake ne bata so, abincin ta hado akan tray da duk abin da zata bukata ta wuce saman. Tana ajiye kayan yayi saurin rungume ta jikin sa yana saka hancin sa a saman wuyan ta "Ya naga kin rame, rashin lafiyar da kikayi ne haka?" Daga mishi kai tayi, kashin wuyanta ya taba "Gobe dole mu koma asibiti, ba zai yiwu ba, ba zan yarda kashi yana cizo na ba." "K'ashi kuma? Ina k'ashin?" Ta fada tana hade fuska ka Gefen kugunta ya taba "Gashi nan kashin wajen ya fito ba meat, kin ga ai sai ki dinga buga min shi cikin dare." "Kai ko?" Ta fada tana dariya Dariyar shima yayi "Ko nayi karya ne?" "Uhum." "Bari na watsa ruwa nazo, ko zaki taymaka min ne?" Ya fada yana kanne mata ido ɗaya, girgiza kai tayi "A fito lafiya." Zama tayi tana dora hannun ta a saman cikin ta, mamakin abinda ya mai dashi so happy haka take, murmushi tayi ta cigaba da jiran shi har ya fito. *** Da daddare suna kwance ta rasa ta ina zata fara fada masa, kunya da nauyi take ji,gashi gogan naka sai budurin sa yake yi be san dawar garin ba. Hakura tayi kawai har zuwa gobe idan taji yadda Baban sukayi da Umma sai ta sanar dashi komai, tana fata da hasashen hakan ya zama gaskiya. Da safe kuwa kusan makara sukayi, a gurguje ta shirya tayi kicin saboda yadda cikin ta yake kiran ciroma, Allah ya taymake ta babu abinda bata ci sannan babu amai sai yar kasala kawai da kuma tsanar Kitchen, wari yake mata sosai shiyasa idan zata shiga sai ta toshe hancin ta dukka da abu, tea ta hado ta zo tasha da cake ta koma dakin, baccin safen nan kamar farilla ya zame mata, lokacin Arkel ya fita ma hakan yasa tayi kwanciyar ta bayan ta karo karfin Ac. A harabar gidan suka hadu da Arab, hannu ya bashi kafin yace "Baka yi min murna ba.". Dan kallon sa Arkel yAyi "Ka samo matar aure halan." Dariya Arab yayi "Wanne matar aure ana maka maganar na kusa zama DAD!." "Kai fa matsala ta da kai kenan, yaushe kayi auren har ka zama DAD?" "Wallahi da gaske nake, yaron ka ai nawa ne, idan Maryam ta haihu ai ni ta haifa ma." Dariya yayi "Auw auw. Toh sai ka jira ta samu cikin ai ko? Sarkin azarbabi." "Auw wai baka sani ba? Wallahi jiya Ya Nabila ke fadan ashe na kusa zama DAD, anan naji ai ashe Madam ce ke da juna biyu." Wani gingirin Arkel yaji maganar, da sauri ya kalle shi "Are You Serious?" "Allah kuwa, na zata ka sani ai." Da sauri Arkel ya juya "Mu hadu anjima a falo akwai babban al'amari, for now bari na ganta, Thanks bro for this beautiful news." Dariya Arab yayi "Sai ka fito, ina jiran gift d'ina." "Baka da matsala." Yace yana shigewa da sauri. Tana kwance taji an daga ta sama, a firgice ta bude ido saboda baccin ya fara hawa kanta, zagaye ya fara yi da ita a tsakiyar dakin kafin ya ajiye ta yana dariya. "Shine baki fada min ba? Kika barni na wahalar dake jiya." "Me?" "Ban sani ba, zauna." Yace yana nuna mata kan kafarsa, zama tayi ya zagayo da hannun sa ta bayan ta, rigar ta ya daga ya shafa cikin nata sannan yayi mata peck a gefen kunnen ta. "I so much love... Children Maryam, Allah na gode maka." Ta zata cewa sai he so much love her, har da dan rufe idon ta sai taji yace children, shiru tayi masa ya gama lalube laluben sa ya maida ta saman gadon yana gyara mata kwanciyar. "Kin daina komai daga yanzu, kiyi ta hutawa abinki kinji my lady." Haushi take ji shiyasa tayi masa kus ya gama maganganun sa ya fita. Tashi tayi ta dauke waya ta kira umma, tana d'agawa tace "Ya jikin naki?" "Da sauki, ina wuni? Yasu Habubu?" "Lafiya lou, ina ganin ki sanar wa me gidan baki abinda yake faruwa idan yaso sai kiga yadda zai dau al'amarin, kafin nan sai nasan me ya kamata muyi." "Shikenan, zan kira." *** Dakin Ummi suka shiga a tare , daki ne hade da falo bayan main falo a in da kowa ke zama, suna zaune da Alhaji yana shan kunu a dan madaidaicin kofi, gefen Alhaji Arab ya zauna shi kuma Arkel ya zauna a bangaren Ummi, kallon su Ummi tayi ta bata rai "Ban ga 'yata ba, ina kuka barta?" "Yanzu zata zo ummi." "Yawwa, ga Nabila shiru, ko wani ya sake kiranta." "Bama sai an kira ba Ummi, gani ma." Duk sai suka kalli kofar, da sauri Arkel ya bude wa Amna hannun sa, da gudu ta yi wajen sa tana dariya. Gaisawa sukayi a cikin farin ciki da son juna sannan Maryam ta shigo, kanta a kasa yake kamar ko yaushe, hakan ba karamin kara mata daraja da kima yake a wajen iyalan gidan ba, a rayuwa kunya abune me matukar amfani, karka zama ka fitsare kafa duk tsiya akwai nauyi tsakanin ka da surukan ka, ka mutunta su ka girmama su. "Malam Arkel, dukkan mu nan kai muke jira da sauraro, dalilin tara mu anan da kayi, me ya faru?" A cewar Alhaji yana ajiye kofin kunun da yasha, magani Ummi ta mika masa ya karasa sannan ya gyara zama. °°° "Ummi, Alhaji. Akwai wata rana da ina duba wasu takardu na zo kan akwatin Ummi, hotunan da na gani da bayanin dake jikin takardar dake nuna tarihin Ummi da asalin ta, duk da rubutu ne akayi shi da wani yare daban, sai na dauke takardar nayi ta bincike akanta, a karshe sai da nayi nasarar gano fassarar yaren. Tun daga lokacin na dauki aniyar gano wa Ummi dangin ta, na sha wahala matuka, an cuce ni sosai akan hakan, nasha yawo gari gari, kafin Allah ya haɗa ni da Malam, ladanin wani masallaci da ke nan kasa da unguwar gano, bansani ba, ashe sunana ne babban alamar da zata bayyana dangin Ummi, rashin lafiyar Ummi ita ta dakatar dani, ta tsayar dani da aikata komai, toh cikin ikon Allah sai gashi yanzu Allah ya taimake ni, ya cika buri na a sanda ban zata ba, a yau na tabbata ko na mutu, ba zan tafi da bakin cikin rashin cikar buri na ba, a yau ina me farin cikin sanar muku da cewa Na gano dangin Ummi, asali tushe me karfi, ingantaccen ahali wanda kowa ne mutum zai yi alfahari da kasancewar sa a ciki." A tare suka yi kabbara, hawayen tsantsar farin ciki ne ya shiga jeran gwano a fuskar Ummi, Nabila da Maryam, Arab da Alhaji kuwa rasa ta cewa sukayi, tsam Arab ya mike ya rungume Arkel "Ban taba ganin mutum kamar ka ba, U r the best broda." Satar kallon sa Maryam take ya shiga basu labarin komai da ya faru a Mali, gaba daya Ummi ta kama shiga tsananin mamakin dan nata, albarka kawai take shi masa ta kasa magana sai share hawaye take. Takardar ya fiddo musu, a kasan ta an fassara komai, karba kowa yayi ya kalla, kura wa sunayen dake jere ido Maryam tayi, ABUBUKAR HAMZA ne ya tsaya mata a rai, sunan Baba ne baro-baro, ajiyar zuciya tayi ta cigaba tayi da karantawa har tazo wajen sunan wadda tasa aka dauke ta, numfashin ta ne ya dauke chak ganin sunan Hajiya Mama baro baro, *Azeema Audu* sai ta cigaba da nanata sunan cikin tsantsar mamaki. Not edited Ignore typos [3/18, 22:28] Hafsat Rano: 48-49 *SK* *** Mika takardar tayi ta tashi tsam, duk suka bita da kallo, sama ta haye ta dauki wayar ta ta kira Umma, ta sanar da ita abin da yake faruwa, tsabar rudewa yasa Umma tayi dakin Baba da sauri, jin tafiyar sa a bayan ta yasa ta jiyo kunnen ta rike da wayar, kafin ya karaso tayi kansa da gudu, ganin haka yasa ya bude mata hannun gaba daya ta fada, sannan ya sa ya rufe. Wajen mintuna biyu suka dauka a haka kafin ta janye tana riko hannun sa. "Muyi magana." Sai ya bita kamar raƙumi da akala har gefen kujerar dake ajiye a wani bangare na dakin. Sai data ja fasali kafin ta soma magana cikin wani irin yanayi me nuna tsantsar farin ciki. Tun da ta fara maganar yake kallon ta, bakin sa a bude ya rasa me zai ce, baya so ya katse ta ya fiso yaji komai, sai ya sake gyara zama sosai a jikin ta yana sauraron duk wani abu dake fitowa daga bakin ta daki-daki. Sai data kai karshe sannan ne yayi magana cikin tsananin murna. "Maryam..." Ya ja sunan ta cikin wata iriyar murya da be san yana da ita ba, sai ta rausayar da kanta cikin wani irin yanayi ba tare da ta san tayi ba. "You Are the real example of mace ta gari, barakallahu fikh, muje wajen su Ummi, wannan maganar abar dubawa ce, idan hakan ya kasance gaskia bansan wanne irin tukwaici zan miki ba." "Amin ya ALLAH." "I..." Sai ta bude idon ta sosai tana sauraron sa. "Muje dai." Yak'e tayi kawai tabi bayan shi kasan Zuciyar ta na jin haushin rashin furtawar sa. *** Kowanne bangare ya rikice da farin ciki, duk da akwai sauran manya manyan dalilin da zasu sake tabbatar da komai, sai dai ko a hakan kawai zaka tabbatar da gaskiyar maganar. Tare suka shiga dakin Ummi yana rike da hannun ta, tana tsaya tana kokarin saka hijabin ta, fuskar ta kamar gonar auduga tayi saurin taro Maryam da ke shirin zubewa a kasa "Ina alfahari dake 'yata, tun ranar da na fara ganin ki naji ina kaunar ki, ashe ke din jini na ce." "Allah yayi muku albarka." Murmushi sukayi a tare suka hada baki "Amin Ummi." Wayar Maryam ce tayi kara, Baba ne ke kira da kansa, tana d'agawa yace "Kun taho ne ku muzo?" Kallon Arkel tayi sukayi dariya kfin tace "Gamu nan Baba, mun fito ma." "Ina MUHAMMAD?" Ta kallli Arkel, kallon waje yayi "Ai tuni yana mota shida Alhaji, Nabila ma ta karaso, tana waje." "Muje toh, na shirya ai." Jakar ta Maryam ta karba suka sata a tsakiya, a haka suka jera har waje kafin su shiga mota su dauki hanyar gidan na su Maryam. *** A gyara gidan yake tsaf, komai an ajiye shi a wajen daya dace, kejin Habubu ma an sake matsar dashi dan ya bada fili, babbar tabarma aka aro a gidan bayan su aka shinfida, ana jiran zuwan su, kiran Alhaji Faruku Baba yayi kafin su ƙaraso yace idan zai yiwu yana bukatar sa a gida yanzu yanzu. Be wani bata lokaci ba sai gashi har ya riga su Maryam ɗin ma zuwa, Baba be sanar masa da abinda yake faruwa ba yace dai akwai bakin da zasuyi shiyasa yake so yana wajen, sai ya shiga gidan sa a gurguje ya fito. Sun dan samu holdup a kabuga da kofar famfo shiyasa ka suka dan kara bata lokaci, Ummi duk ta kagu aje bata sauraran hirar da suke tayi, ana isa kofar gidan taji kwalla ta zo mata, kwallar tausayin kanta da dan uwan ta, jiki a mace ta fito daga motar tana kallon su Baba dake tunkaro su, sai ta tsaya tsak a maimakon ta karasa kamar kowa, ido ta zuba musu kwallar da take ta kokarin boye wa ta sake zubowa, Maryam da Ya Nabila ne suka taimaka mata suka shiga gidan, da fara'a Umma ta tarbe su tana musu lalle marhabin, suka zazzauna Ummi dai sai kalle kalle take, shi kanshi Baban kallon ta yake babu ko dauke wa, babu tantama balle shakku, tsantsar kama da mahaifiyar su, babu ko digo na babbanci kamanni, duk da shi be yo bangaren Mahaifiyar tasu ba, bangaren mahaifin su daya kasance bahaushen Kano sukayo,  a yan ganin da yayi wa Arkel na duk da ba wai kallon sa yayi sosai ba, ya raya wani abu a ransa, sanin babu abu makancin haka yasa ya watsar ya bar hakan a matsayin kamace kawai, dadin dadawa be taba sanin Arkel ne sunan nashi ba, da Muhammadu ya sanshi, shine sunan da Alhaji Faruku ya fada masa lokacin da ya haɗa auren, shine kuma sunan da Ummi take fada masa a duk sanda zata sanar dashi wani abu daya danganci ita Maryam ɗin, sau tari ma sai dai tace mijin wance a dabiaa da kara irin ta malam ba haushe. Duk shaidun da ya kamata dukka bangaren biyu su gabatar sun gabatar, tsananin mamaki Baba ya shiga in da sau daya be taba raya ya nemi dangin mahaifiyar tasu ba duk da ta sanar dashi wani bangare na labarin su, duk sai yaji kunya ta kamashi da jin ai Arkel yayi komai ya gama, Alhaji Faruku kuwa ya kusan fin kowa farin ciki, yana da yakinin Hajiya Mama zata samu saukin wani abu, duk ba be san kuma ya makomar maganar tatan take ba, sai dai yana fatan ta samu afuwa duk da baya goyon bayan abinda ta aikata ɗin, gashi yanzu komai nata ya lalace tun a duniyar, shiyasa a kullum ake so mutum yayi abu me kyau, hakan shine zai tabbatar da mutum akan tafarkin daidai har zuwa ranar sa zai koma ga mahaliccin sa.  Yinin ranar baki dayan ta cikin farin ciki aka yi ta, da labarin Rayuwar data wuce, Ummi ji take kamar sallah gashi sun dinki da umma kamar dama sun san juna, aikuwa da aka zo tafiya sai tace su tafi ita anan zata kwana, kallon Arkel Maryam tayi alamun ita ma zata zauna aikuwa yayi kicin kicin da fuska, tana ji tana gani ta bishi suka tafi, sai da suka fara sauke Ya Nabila a gidan ta sannan suka wuce nasu. Bayan magriba Umma ta raka Ummi gidan Hajiya Mama bisa umarnin Ummin da tace lallai sai taje, tana zaune kamar kullum dai babu wani ci-gaba ta bangaren yanayin nata, tana ganin su ta hau surutai da suka-suka. Babu ɗaya daga cikin bayanan da Ummin tayi mata da ta gane sai data ambaci sunan Ummin da sunan Baba Yelwa sannan ta ne ta zabura kamar zata fita da gudu, rirrike ta suka yi cike da tausaya wa, babu wani abu da mutum zai aikata na sharri face Allah ya nuna maka iyakar ka. Ummi sarkin tausayi tuni har ta fara sharar kwalla da kyar Umma ta janye ta suka koma gida. Da daddare Baba ya zauna suka sake sabuwar hira, hira tsakanin Ya da kanwa da basu taba sani ko hasashen irin wannan lokacin ba, basu farga ba saboda tsabar hira har sai da Umma ta ankarar dasu da dare sannan suka hakura akan gobe zasu dora. Duk wasu tambayoyi da Ummi take buƙatar sani ta sansu yau, hatta da yarintar Maryam sai da aka bata labari, ji take kamar bata da wani sauran bacin rai a duniya, abu daya yanzu ya rage musu shine tafiya zuwa Mali. A ranar duk suka shirya komai suka saka rana. *** Yana zaune a gaban system din sa bayan ya gama abinda zai yi, so yake ya shirya da wuri ya shiga office, kwana da yawa duk ya zama unserious dan ma akwai Salim ne. Wucewa tazo yi ya kalle ta, tashi yayi yabi bayan ta Matse ta yayi a jikin kofar yana hararar ta "Me kika ci yau?" Cikin in da in da tace "Naci fa abinci, Walid ya siyo min awara kuma naci." "Awara abinci ce? Kina so kiyi min wasa da baby ko?" Bata fuska tayi ta turo baki "Ni wacce baby Kuma?" "Ta nan." Yasa hannu a saman cikin ta, kwace jikin ta tayi ta bar shi a tsaye yana murmushi "Zan kamaki ne, dura zan miki Allah." Gwalo tayi masa ta wuce ta barshi a tsaye yana cije yatsa. Wayar sa dake saman kayan takardun sa ya dauka, karawa yayi a kunne "Ya akayi?" "Oga wallahi ina taso na fada maka Hafiz fa kwana biyu shiru be shigo site ba." Daga dayan bangaren akayi magana, "Subhanallah, tun yaushe amma be zo aikin ba?" "Almost a week kenan fa." "Shine amma baka sanar min ba? Wannan ai kuskure ne kana aiki da mutum kwana kusan biyar babu shi babu aike sannan ace baka neme shi ba, baka kyauta ba gaskiya." *** Sosai ya farfad'o, duk ciwukan jikin sa anyi masa dressing din su, hannun sa da kafar sa guda dai-dai ya samu karaya kuma suma an dora shi, sosai yake samun kulawa daga mutanen da be san su ba, wani masinja aka saka yake jinyar sa. A chan Gumel kuwa hankalin inna a tashe yake, babu irin kiran sa da batayi ba, amma amsar daya ce kullum a kashe, gashi babu wani da ta sani da zata kira shi akan Hafiz din, ta dai san wajen da yace mata yana aiki, ganin babu wata hanya yasa kawai ta shirya ta nufo Kanon ita da suwaiba. *** Duk da shirye shiryen da ake tayi na tafiya amma hankalin Arkel baya jikin sa, gaba daya tunanin sa yana wajen in da Hafiz yake, duk ya bincika in da zai bincika amma shiru babu labarin sa, da wuri ranar ya fita ko breakfast be samu yayi ba, da salim suke waya har ya karasa, yana zuwa shima yana zuwa, sai suka shiga office. Bayan sun gaisa yake tambayar sa "Baka san wani da suke harka anan ba?" "Gaskiya ban sani ba wallahi, amma bari a tambayi sauran ma'aikatan ko za'a samu wani ya san shi." Dafe kansa Arkel yayi ya juya baya yana jin a ran sa tabbas babu lafiya, shiru yayi yana ayyana komaai zai iya faruwa, kar dai ace sun kashe miciji ne amma basu sare... Shigowar Salim yasa ya kalle shi da sauri "An samu?" "Me gadi yace ranar ya karbi machine din sa a gurguje, sai dai be san in da ya tafi ba, rabon sa dashi kenan, daidai ranar da mukayi tafiyar nan kenan, da safe." "Kana nufin tun ranar be dawo ba, kenan babu shi babu machine din." "Babu, kasan Baba Megadi da dattako, baya so ya tada maganar shi yasa ya tsaya ya ga ko za'a yi magana, yana da yakinin dai ba zai gudar masa da abin hawa ba, ya yarda dashi dari-bisa -dari." "Akwai matsala." Arkel yace yana mik'ewa "I'm afraid to say that evil witch is still alive, ya Allah, tayi wasa da hankalin mu." "Ko dai yaje gida ne, kasan fa yace mahaifiyar sa ta koma Gumel, ko mu fara tuntubar su chan din." "Ba haka bane, babu yadda za'a yi yaje gida be sanar ba, idan lissafi na yayi daidai da ranar da Megadi yace zaka ga daidai ne da ranar da mukayi tafiyar nan, babu dalilin da zai sa ya tafi gida ya dau wannan tsawon lokacin, bayan haka ma ai yana da Number ta, zai kira ni ai, something is fishy gaskia,baka kyauta min ba kuma da baka sanar dani da wuri ba, getting to three weeks kenan fa, haba!" "Ayi hakuri Oga." Be yi magana ba ya fice daga office din Yana tunanin in da zai yi, yana zuwa gate su Inna suna sauka daga adaidaita sahu, kallon su yake har suka sallami me keken suka nufo shi, babu wani dogon tunani ko nazari ya gane su saboda tsantsar kamar da ya gani da Hafiz. "Sannu da Zuwa Hajiya." "Yawwa sannu dan nan, dan Allah nan ne wajen da Hafizu yake aiki?" Gaban sa ne ya fadi, sai yayi saurin dakewa yace eh "Dama kwana..." "Ku shigo ciki Hajiya." Ciki suka shiga ya basu kujera suka zauna sannan ya zauna yana sauraron ta "Dama kwana biyu Hafizu shiru babu wani labarin sa, babu waya be zo ba kuma, shine nace bari na zo naji menene yake faruwa, jiki na yana bani na lafiya ba." Abinda yake tunani ya tabbata, sai ya mike da sauri yana kallon su, tunanin yadda zai sanar mata yake, idan ya boye mata be mata adalci ba tun da uwa ce, ko ba komai zatayi masa addu'a a duk in da yake Allah ya tsare shi, sai daya ja numfashi kafin ya daure yace "Hajiya muma nan rabon mu dashi wajen sati biyu kenan da doriya, sai dai nayi tunanin ko nan gida ya taho, zancen da nake miki yanzu maganar muka gama da ma'aikata na." Inna na Jin haka ta ɗora hannu aka ta saki kuka. "Shikenan abin da nake tsoro ya faru, sai dana ce masa ya hakura da zaman Kanon nan, amma yaran yanzu ka haife su ne amma baka haifi halinsu ba, sai su nuna maka ma sun fika wayo da sanin abinda yafi, yanzu na shiga uku ina ya shiga?" "Kiyi hakuri Hajiya, in Sha Allah zamuyi iya kokarin mu, kiyi hakuri kiyi masa addu'a." Share hawayen ta tayi tana addu'a, sun dade suna tattaunawa kafin ya dauke su a motar sa ya kaisu gidan Ya Nabila bayan ya basu tabbacin zai nemo Hafiz a duk in da yake. *** Dariya sosai tayi bayan ta gama waya dashi, sai ta ajiye wayar ta mike ta shiga dakin ta, kayan jikin ta ta rage ta jawo karan sigari guda daya ta zuk'a ta kwanta dan so take ta dan rage baccin da take ji, tana kwanciya wayar ta dake falon ta hau karar neman agaji, sai data yi tsaki sau ba adadi ganin kiran yaki daina shigowa ta tashi ta fito falon, a fusace ta dau wayar sai dai sunan data gani a saman wayar yasa ta tsaya ba tare daga ba, duk da kasancewar ta jaruma mara tsoro amma tabbas ganin sunan ya saka taji wani yar har sai da wayar ta tsinke bata daga ba, tana kallon kiran ya sake shigowa sai dai bata da kuzari ko ƙarfin zuciyar d'agawa dan bata shirya wa hakan ba, bata shirya nuna kanta ba har sai ranar da zasuyi tafiyar da suka shirya, a ranar ne kowa zai san abinda da ta ke so a sani ɗin. Ganin bata da niyyar daga kiran sa gashi dai dama be yi tunanin zata daga ɗin ba amma jin wayar a kunne ya kara bashi tabbacin abinda yake tunani, abu daya zai yi shine kawai yake ganin mafita, sai ya juya akalar motar sa zuwa gidan su maryam. Yana zuwa ya tsaya daga chan nesa da gidan ya kira Zainab, yace tazo zasuyi magana, kamar mintuna biyu sai gata ta fito taana kalle kalle, horn yayi mata ta nufi wajen, kallon ta yake har ta karaso ya bude mata kofar ta shiga, kafin tayi magana ya ja motar. "Babu gaisuwa?" Yace yana hararar ta, da sauri tace "Ina wuni." Sai ya sassauta maganar sa tunowa yayi da sai ya lallabata idan har yana so ta taimaka masa "Haba dear, shikenan daga tafiya sai ki manta da kowa, ba waya ba komai? Ko baki dauke mu yadda muka dauke ki bane?" "A'ah, kawai ina jin kunya ne." "Kunyar me? Common abun da ya faru ai ya riga ya wuce, and am sorry for making u sad, a time din bansan me ya hau kai na ba, amma ni yanzu komai ya wuce a waje na." "Da gaske?" Daga mata kai yayi "Nagode bro." "Karki damu." Shiru sukayi sai chan yace "Ya jikin Mummym? Ranar naga wata kamar ita ai, jikin ya samu sauki da alama." "Uhum." Tace a gajarce tana tuna maganar da sukayi, warning ɗin da tayi mata akan karta faɗa wa kowa haukan karya tayi, yana lura da ita yadda ya tafi tunani gaba daya,murmushi yayi irin na gefen bakin nan yayi parking a daidai kofar store din. "Shiga ki dau duk abinda kike so, ga Atm d'ina nan sai kiyi payment din Ina jiran ki a mota." Da sauri ta kalle shi ya sakar mata lallausan murmushin dake narkar da ita, har gaban gobe tana nan da soyayyar sa a ranta, sanin yayi mata nisa ne yasa ta hakurr wa zuciyar ta, ta rungumi kaddarar ta, sai dai abinda ya faru yau gaba daya yasa ta sake dawo da tsohon tsumin dake boye a karkashin ranta. Tana gama daukar abinda zata dauka wanda mafi aka sari kayan kwalliya ne ta fito, yana waya yana ganin ta ya ajiye yana sakar mata murmushi "Are You Done?" Ya tambaya yana tada motar, daga mishi kai tayi ya ja motar suka bar wajen, duk ya gama tsara yadda zai ɓullo mata, sai da suka kusa zuwa gida sannan yace "Zaki aure ni?" Ras gaban ta ya fadi, yadda taji maganar, duk sai ta duburburce, murmushi yayi ganin ta kasa controlling kanta ya dan rage tafiyar da yake "Na shirya auren ki idan har kin yarda, amma da sharad'i." "Zaki fad'a min komai da kika sani game da Mummy, Ina take yanzu haka? Ita dawa suka harka?" Sai ya dora "Nayi miki alƙawarin babu abinda zan yi da zai cutar dake, Ina son dai nasan halin da family ne yake ciki, kinsan halin ta, kinsan me zata iya, idan kika yi shiru kika bari aka cutar da wani ta sanadiyyar ki, Allah ba zai barki ba, hakki ba zai barki ba, ki taymaka mu haɗa karfi da karfi mu ceto ta daga fadawa halaka, ina ji a raina akwai wanda yake sakata komai." Ga koshi ga kwanan yunwa, babban burin ta shine auren Arkel, ga kuma tsoron abin da zai faru da mahaifiyar ta idan ta tona mata asiri, shiru tayi tana aunawa da zuciyar ta, dole zabi daya zata dauka, abu guda biyu da ana ta tunanin take ganin sun fi komai muhimmanci a rayuwar ta. Jin tayi shiru a karo na biyu yasa ya gangara gefe yayi parking ya juya jikin sa sosai yana kallon ta "Ki taimake ni, ki dubi rayuwar da mukayi a baya, bana fatan sake shiga irin ta, karki tunani na kawo maganar aure ne saboda na yaudare ki ki faɗa min abinda baki yi niyya ba, ban yi hakan ba sai dan son kubutar dake da dukkan wani sharri." "Kayi alƙawarin babu abinda zai same ta idan na fada ma?" "In Sha Allah." "Ka rike amana." "Mummy ba ita kadai bace take aikin ta, sannan Mummy tayi rashin lafiyar karya ne saboda ta kubuta daga abinda kake shirin yi mata, bana son yadda yake tsara mata komai, sannan duk wani abu shine yake fada mata akan ka, duk wasu shirin ka ta sani, ba kowa bane face yaron daka yarda dashi fiye da kowa, wanda kake ganin yafi duk wani makusanci kusanci da kai, Salim shine abokin aikin Mummy, tare suke aikata komai." Tsabar rudewa kusan daskarewa Arkel yayi a wajen, a take jin sa ya nemi daukewa na wani tsawon lokaci, sunan salim dake karakaina tsakanin kunnuwan sa da ƙwaƙwalwar sa ne ya hadu ya cunkushe masa a waje daya ba tare da ya san takamaimai me yake shirin faruwa ba. Ba karamin kokari yayi ba wajen tattaro dukkan nutsuwar sa, cikin Muryar sa da ta gama dishewa saboda tsabar k'aduwa yace "Tana ina yanzu? Karki kuma ki faɗa min, taymakon ta zanyi." Sai data kalle shi ta kara kallan sa dan ba karamin tsoro ya bata ba yadda a lokaci daya yanayin sa ya koma, cikin in da in da tace "Badawa Lay-out." *** Nagode sosai Affan ya samu sauki, kuyi hakuri da rashin jina kwana biyu. #Not edited **** _ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU😁._ *ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma *SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano) *KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo) *BURI ƊAYA!* (Mamu gee) *WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull) 👇🏻karku bari ayi babuku *ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu* *za'a tura kudin ta wannan accnt number din* Hafsat kabir umar 0225878823 GT bank Saika tura shaidar biya ga wannan number ta WhatsApp 08030811300 Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din 07067124863 Sai kayi wa Number magana ta WhatsApp [3/18, 22:28] Hafsat Rano: SK 51 HAFSAT RANO *** Tana shiga dakin ta ganshi a zaune akan drawer yana duba abu a wayar sa,ja tayi ta tsaya daga bakin kofa ta kasa shiga, sarai ya ganta sai ya nuna kamar be san tana wajen ba, ya tashi ya shige toilet d'in, zagaye idon ta tayi a dakin cikin sakan da bazasu wuce biyar ba, dakin yayi mata kyau ainun, duk sai taji tana sha'awar zaman gidan ba kamar chan ba da suke a hade. Fitowa yayi yana gyara link din rigar sa yazo zai wuce ta kusa da ita, riko shi tayi ta dawo dashi baya, idon su suka hadu waje daya, kasa tayi da kanta da sauri ganin yadda ya tsare ta da idanun sa yana neman lallai sai ya sata dole taji kunyar sa. "Mu tafi ko?" Yace yana basarwa, kallon hannun sa yayi ya kalle ta alamun ta sake shi, jiki a sanyaye ta cika shi ya juya ya bar dakin, da kyar ta ja kafufuwan ta ta fito falon jikin ta a matukar mace, sai dai bata karasa ba taji an rufe mata ido, a hankali yake janta har ya kai ta gaban wajen,  a hankali ya cikata ya na ja da baya da baya har ya fice daga falon, duhun daya mamaye ko ina na falon ne ya dauke haske ya bayyana, idon ta ne ya sauka akan babban allon dake manne a jikin falon yana fitar da wasu irin kaloli masu ban sha'awa da birgewa, a hankali rubutun dake jiki ya fara bayyana daya bayan daya wata irin waka me kama da busar sarewa na tashi a hankali. ``` _At first i never care who you are, but now I don't know who I'm without you, you walk lightly into my heart,captivating and lovely to my heart._ ``` ``` _My life has forever change, the first time we met, I could see that you and I were meant to be together, your eyes were so gentle, your smile so true._ ``` ```_For you are my heart, My Soul and my oneness, with you I know I will find my completeness, my eternal peace_ ``` ``` _You are the better half of me, you mean the world to me, both of our hearts will forever bond into happiness, falls, pains and sorrow. I promise you together we will meet tomorrow._ ``` ``` _These  little words I have written speaks some of my love for you._ *I LOVE YOU SO MUCH CARIAD* Wani irin yanayi ta shiga me kama da almara, sosai maganganun suka taba ta, cigaba da kallo tayi in admiration kamar zatayi me dan murna, yana tsaye a bayan ta yana kallon ta, hannun sa sark'e a kirjin sa ya kasa ko da kwakkwaran motsi yana jin wani irin yanayi, nauyin da yake ji a zuciyar sa ya kau a dan lokacin nan, babu wata fargaba ko shakku sai dumbin soyayyar ta, soyayya me karfin gaske da mutum ba zai iya kuje mata ko juya baya ba, amma ba irin wanda idon mutum zai rufe ya kasa gane daidai da akasin sa ba, ganin yadda take juya jikin ta da kanta cikin tsananin farin ciki yasa yaji kamar ana ingizashi, cikin sassarfa ya isa gareta sai ji tayi an zagaye hannu a tsakiyar cikin ta, ajiyar zuciya ta sauke da karfi tana daidai ta nutsuwar ta,maganganun yaa shiga rada mata a kunnen ta wanda ni kaina bazan ce ga su ba sai Echo din husky voice d'in sa sake yin fita kamar bugun ganga kawai zaka ji, ita kadai take jin me yake ce mata, duk ya gama sagar mata da jiki babu sauran shakku ko noke wa, ta gama aminta dashi da soyayyar sa wadda take ganin kamar a mafarki. Tsawon wasu lokuta suka dauka a wajen yana sake fallasa mata asirin zuciyar sa, da wayo da wayo yake mata har ya samu ta fallasa ta ta zuciyar cike da karsashi da son faranta wa wanda kake so, a duniya bashi da wani sauran damuwa, yadda ya bata shekaru masu yawa yana faman rayuwar kunci a yau ya ajiye komai, dole ne shima ya dandani ruwan soyayyar da yake gani a tattare da Kamal mijin ya Nabila, a rayuwa mutumin na yawan fado masa a rai saboda yadda yake nuna soyayyar sa ga matar sa a gaban kowa wanda muka rasa hakan a wannan society din namu, Kamal mutum ne daya san daraja da kimar iyalin sa, baya fatan bata musu ko wulakanta musu sai dai duk da hakan akwai lokutan da suke samun sabani tun da dama aure ya gaji haka, babu ya yadda zakayi kashe zaka dawwama a cikin farin ciki babu wani kalubale, dole ne akwai kalubalai masu yawa sai dai mutum ya san yadda zai yi handling komai ba tare da tsangwama ko wulakanta abin zaman ka ba. *** Duk da kowa ya gama aminta da rayuwa me dorewa a dan uwan sa, sai dai har lokacin Arkel na ji a ransa akwai sauran abubuwan da ya kamata ya sanar mata, tashi tayi daga jikin sa ganin dare yayi sosai tace "Ya kamata mu tafi gida." Noke kafada yayi yana sake miko mata hannu "Ba yanzu ba gaskiya, zo kiji." Dawo wa tayi ta sake kwanciya a jikin sa, hannu ya saka cikin gashin kanta yana yawo dashi a hankali. "Bani labari.." "Uhmm.. Abu daya na kasa mantawa, time da kayi min tsawa nazo office din ka, har kuka nayi." "Wayyo I'm sorry, ban kyauta ba, kinsan yadda naji ba dadi kuwa? Bayan kin tafi nayi ta damuwa." "Ba wani nan, Allah ni ba zan yarda ba." "Allah da gaske, nace me yasa nayi wa me kyau masifa, sai daga baya na gane kuskure na." Dariya ta saka "Wai me kyau, banda fasa kai." "Allah kuwa. My wife." "Uhum.. Wai dama kana magana haka sosai sosai." "Kinyi mamaki, anything for you, feel free with me,share all your problem with me I promise zan tsaya miki." "Nagode sosai." "Kice kina so na toh." Rufe fuska tayi da sauri tana dariya. Basu koma da wuri ba sai wajen goma Ummi har ta shiga daki ta kwanta. *** Tana kwance bata ko iya buɗe idon ta sosai saboda azaba, kwana tayi tana zawo saboda warin bandakin, wasu manyan kuraje ne suka fito mata a gadon bayan ta duk sun ja ruwa babu kyaun gani, tsananin azaba ga yunwa ta haɗar mata, iya kar galabaita ta galabaita bata taba tunanin hakan a tattare da ita ba, a kullum burin ta ta kuntata wa kowa ta raina kowa tana ganin babu me iya takata sai yau ta tabbatar da ita ɗin ba komai bace a wannan sahun. Tana ji aka zo aka bude ta, abinci ya turo mata cikin harshen sa da baya fita sosai yace "Ka tashi kaci abinci, dan iska kawai." "Magana nake maka fa? Ka tashi ko sai naci ubanka?" "Zan tashi wallahi, bani da lafiya ne." Tace cikin raunin murya "Ka taimaka min zan mutu." "Ka mutun, kai ka sani." A tunanin ta zai tausaya mata sai ta ga aka cin haka, sai ji tayi ya kai mata gula a ciki ba shiri ta mike ya tura mata kwanon abincin da kafa "Maza ka cinye shi." Tana kallon abincin zuciyar ta ta tashi ta hau amai, dariya ya saka ya juya ya fita ya rufe ta yana jin dadi a ransa. Satin ta guda tana cin uwar azaba, tayi kuka tayi magiya amma sam basa ko sauraran ta ma, babu alamar sassauci shiyasa ta hakura ta daina rokon su, ta riga ta saddakar ita shikenan ta kare mata, kila ma sai ta mutu zasu fitar da gawar ta. Da daddare suka shigo mata su uku, saboda tsabar rudewa sai data saki fitsari a wando, toshe hancin su sukayi dukka saboda masifaffen warin da dakin yake, mik'ewa tayi saboda taga yadda suka tunkaro ta, hannun ta daya ya kama ya ingiza ta waje, wani dan corridor ya kai ta ya nuna mata tsintsiya. Da sauri ta dauka jikin ta na bari "Je ki wanke toilet d'in chan kin cika mana gida da wari, har yanzu baki mutsu ba." "Wallahi tallahi na nutsu, ka dubi girman Allah ka barni na tafi, wallahi na zan sake shiga rayuwar kowa ba, barin garin ma zan yi wallahi Allah." "Kinsan da wannan kika yi ta iskanci kika cuci bayin Allah? Kin manta abin da kikayi ko?" "Na tuna Wallahi ban manta ba." Daka mata tsawa yayi "Kin wuce ko sai na kakkaryaki na zubar? Da girman ki da komai shegiya baki kama kanki ba, mu nan wallahi bama tausayin kowa sai mun tabbatar kin ci ubanki sosai da sosai sannan zaki tafi." "Wuce ki wanko bandakin nan kuma ke zaki dauko ruwa a waje kin cika mana duk kayan ruwan gidan nan." "Na shiga uku." Hannu ta ɗora aka zatayi ihu ya bige bakin ta. *** Zainab na kwance sai jiran Arkel take amma baya dauka, ta rasa yadda zata yi gashi wani irin mahaukacin son sa ya kara sakata a gaba, Rauda sai habaici take mata, sam bata jin dadin zama a gidan Hajiya Maman saboda Rauda, Sultan ne ma suke dan zama suyi hira amma idan baya nan shikenan zata shiga kunci, gashi uwar gayyar gaba daya ta sake birkicewa, surutai kawai takeyi babu magana daya ta kamawa, a haka zaka ganta a nutse a zaune amma idan ta fara sako maka zance sai kaji kamar kayi kuka, shi kuwa Alhaji Faruku ya tattara su dukka ya zubawa sarautar Allah ido, ya san tabbas abinda suka shuka ne zasu girba, shiyasa ya daina takurawa kansa ya cigaba da sabgogin sa kuma be bari hakan ya shafi alakar sa da Baba ba, yadda suka saba tun da haka suka cigaba da zumunci su, shiyasa yayi niyyar duk ranar da za'a tafi Mali toh lallai dashi za'a je. ***  Sosai sauki ya samu a gun Hafiz, karo na uku ya sake aran wayar me kula dashi ya saka Number Inna ya sake kiran, cikin sa'a ya samu ta shiga, suna zaune da suwaiba sun dawo Gumel abun duniya yayi mata yawa, duk sanda sukayi waya da Arkel sai yace mata ai ana kan nema in Sha Allah zaa ganshi, Kiran na shigowa tayi hanzarin dauka. "Assalamu alaikum." Yace yana kara wayar a kunne "Hafizu, Hafizu kai ne? Alhamdulillah ya Allah." "Inna... Ni ne Inna." "Kana ina? Ina ka shiga ka barmu da fargaba?" "Ina asibiti inna, asibitin murtala." "Na shiga uku, me ya faru? Hatsari kukayi?" "Sai dai kunzo inna, idan kunzo ku kira lambar nan, amma ku bari da safe sai ku taho yanzu yamma tayi." "Da yau zan tawo ai, hankali na ba zai kwanta ba." "A ah, kiyi hakuri zuwa goben, ina samun kulawa daidai gwargwado." A sanyaye tace "Shikenan Allah ya baka lafiya, Suwaiba na gaishe ka." "Amin Inna" "Na bata wayar?" "A ah Inna, Kinga Kar a cinye kudin ara nayi, tayi hakuri zuwa gobe, idan baku da kudi ki ranta zan biya." "Shikenan, sai munzo." Kashe wayar tayi duk sun rikice, "Kinga kira mun yaron nan Arqe yake ko wa?" "Kai inna Arkel." "Yawwa shi, kira na sanar masa an ganshi, ko zai taymaka tun da kin ga bamu da kudi asibiti kuwa dole a charji kudi." "Gaskiya ne, bari na kira shi." Kiran shi tayi be daga ba, shine ta tura masa text. Ya gama yadda zai ɓullo wa Salim dan sanin ainihin gaskiyar sa, jira suke su hadu kawai yayi masa yadda zai masa, gwara ya san a in da zai ajiye shi dan ba zai cigaba da zama dashi in dai ha'intar sa yake ba. Kiran sa yayi a waya yace su hadu bayan sallar magriba a gidan su. Yana ajiye wayar ya ga text ya shigo, har zai share sai ya duba dan ya tuno yayi wa Maryam text dazu batayi masa reply ba, yana budewa yaga Number Inna, karanta text din yayi sai kawai ya juya zuwa asibitin Murtalan maimakon gida da zai je. *** Manage pls yau dai sai a hankali Please i need ur du'a🤲 [3/18, 22:28] Hafsat Rano: 52 SK Yana isa asibitin be wani sha wahala ba ya gane bangaren, sosai Hafiz yaji dadin ganin sa ba zato, hira suka dan yi yayi masa maganar abinda ya faru, cike da tausaya wa Arkel din yake sauraron sa, be taba ganin mace kamar Hajiya Mero ba, zata iya komai akan abinda take nema, zuwa yayi ya karbi Bill din komai yaje ya biya ya chanja masa daki sannan ya tafi da nufin zai zo gobe. Inna ma asubanci sukayi suka zo,  dan bata iya baccin kirki ba, shiyasa ana idar da Sallah gari ya ɗan yi haske suka taho. *** Kafin ya isa gida har Salim ya riga shi zuwa, ya matsu yaji abinda yasa ka gaba daya Arkel ya sauya masa, babu fuska duk da yana kokarin nuna babu komai amma shi yasan akwai wata a kasa. Yana ganin ya shigo da mota yayi saurin tashi ya isa, shi ya bude masa kofar ya fito ya bashi hannu "Sannu da zuwa." "Yawwa, ka ƙaraso kenan." "Eh tun dazu, na shiga na gaida Ummi shine na fito nan ina shan iska." "Ok yayi, dan jirani ina zuwa." Ciki ya shiga, motsin da ya ji a toilet yasa ya murd'a, tana gaban sink ta gama amai kenan, duk ta galabaita, riko ta yayi suka fito yana mata sannu "Me ya faru kuma?" "Zuciya ta ce naji tana tashi." "Haka kawai? Me kika ci?" "Dan-malele." "Dan me?! Disgusting, aina kika samu?" "Sadiya ce tayi min na taho dashi daga school." "Kin ganki ko? Bana son kina cin irin abubuwan nan gaskiya." "Huta bari na ga Salim, idan na dawo sai muje asibiti." "Owk tam." Har ya juya ta tsai dashi "Please dear karka masa da zafi, don't be harsh kaji.?" "Zan kokarta, for you." "Thank you." Murmushi yayi ya juya ya jawo mata dakin, ruwa ya dauka yasha sannan ya fito, a in da ya barshi anan ya same shi, zama yayi a gefe ya ciro waya ya kira Arab, yana cikin gidan yace ya fito compound. Tashi yayi ya zura rigar sa ya fito, ganin su tare da Salim yasa ya gane dalilin kiran. Kujerar dake gefen shima ya ja ya zauna suka gaisa kafin Arkel ya kalle su duka yace "Salim, iya zaman da nayi da kai akwai wani abu dana taba maka da baka ji dadi ba.?" Kai tsaye yace "Idan nace akwai nayi karya, babu abun da ka taba yi min." "Nagode." "Menene matsalata? Wanne abu ne kake ganin ina yi be dace ba?" "Babu gaskiya, abu daya na san kanayi yawan fada sosai, shima da ne kuma amma tun da komai ya daidai ta ka daina, amma ko alokacin bana damuwa ko jin haushi, saboda na san wayr kai, nasan matsalar dake sa ka hakan." "Gaskiya ne wanna." Arab yace yana bawa Lubna amsa ta chat, ba wani fuskantar zancen nasu yake ba, hankalin sa na chan suna soyewa. "Akwai abin da na taba boye maka? Akwai abin daya dangance ni da baka san shi ba?" "Babu shi." "Amma me yasa na yarda da kai ka ha'ince ni?" Zubura yayi "Ha'inci Oga, Subhanallah, wannan wacce iriyar magana ce ?" "Yadda kaji." "Ban gane ba wallahi oga, ya za'a yi na ha'ince ka, ka taba duba kudin da ake samu kaga wani abu ya bata? Ko na taba kawo maka cikas a harkar? Wallahi tallahi tsakani na da Allah nake maka komai, duk da ba zance bana samu a karkashin ka ba, amma wallahi tallahi ban taba cutar ka ba, ban taba tunanin cutar ka ba, me yasa zaka ce haka? Ka manta waye ni? Ka manta hali na?" Kallon sa Arkel yake, ya gaza cewa komai, maganganun sai yawo suke a kunnen sa, ya rasa a wanne bigire zai dauke su ya ajiye su? Me yake shirin faruwa? Waye me gaskiya.? Maganar Arab ce ta dawo dashi daga tunanin daya tafi, "Karka damu salim, ina ganin dai wani dan tangarda aka samu da rashin fahimta, kasan dai maganar Hajiya Mero, toh a gaskiya mun samu leakage ne na cewa duk wani sirri kai kake sanar mata dashi, kai ne partner din ta, shiyasa hankalin sa ya tashi, amma ba wai zargin ka yake ba, so yake dai ka fada mana gaskiya." "Ya Salam. Abinda ya faru kenan? Ta nan ta bullo min? Hmm lallai ma." "Bari kuji, wallahi tallahi ban taba daukar maganar da mukayi na fada wa wani mutum ba, abu daya na sani ta zo ta same ni akan lallai sai na hada hannu da ita wajen lalata dukiyar ka, da fari ma wasu kudade ta nema na hanata, a lokacin babu irin barazanar da batayi min ba wallahi, ban bata ba na hana ta, shine daga baya tazo akan waccan maganar, Allah ne shaida ta, ban bata goyon baya ba, a lokacin tayi min ikirarin sai ta bata ni a wajen ka, sai ta jawo ka kore ni. Ban dau hakan a matsayin komai ba sai barazana, dan tasan da aikin na dogara, ni kuwa da na yarda da ita gwara na rasa aiki na, wannan shine abinda ya faru a takaice wallahil azim karya take min, so take ta bata ni." Shiru duk sukayi suna kallon sa "Ku yarda da ni, wallahi sharri tayi min." "Arkel, hanya daya ce kawai,bari na kira Abdul ka gani." Daga mishi kai yayi dan baya jin zai iya magana kuma. Dubawa yayi babu Number a wayar sai a karamar wayar sa dake daki "Bari na dauko wayata Please." Zagaye kawai Arkel yake a wajen ya kai nan ya kawo yana fatan Allah yasa ya zama sharrin, zuciyar sa ba zata iya daukar akasin haka ba, shi kanshi Salim ɗin a rud'e yake, ya rasa me ma yake masa dadi a duniya, addu'a yake tayi kawai har Arab ya dawo daga dauko wayar ya kira shi. Handfree ya saka duk suka yi shiru suna sauraran sa "Oga how far?" "Oga Arab, komai fine fine kwana biyu?" "Normal sir, ya ajiya ta? Tayi laushi dai ko?" "Ah sosai." "Good, haka nake so, tayi kamar two weeks nan gaba kafin ka sake ta, for now Ina so Kayi mata tambaya ne, amsa kuma muke so ta gaskiya, if she tried to hide the truth kaci ubanta sosai dan Allah." "An gama, bari na kira Samuel ya fito da ita nan dakin da take babu network." "Ok Ina jira." Tana tsugune ta saka kafarta a cikin guiwar ta taji ana bude kofar, abinda ta tsana kenan taji ana budewa saboda tasan ba sauki sai sun ci zalinta, mik'ewa tsaye tayi har ya shigo ya damke ta ya fito da ido, raba ido da dinga yi kamar tsohuwar munafuka har ya kaita. Tana hada ido da oga kwata-kwata ta tsure, ta hau rawar jiki "Ke...!!!" Da sauri ta durkusa kaasa "Kayi hakuri dan girman Allah." Wata irin dariya ya kece kafin ya bata rai kamar ba shine yayi dariya ba, tana ganin haka ta sake shiga tashin hankali, jiki ta ta ko ina rawa yake kamar mazari "Me yasa kika yi wa Salim sharri?" "Eh... Na'am?" "Eh? Me yayi miki?" "Umm.. umm dama bashi da kirki..." "Kee!!!" Da sauri ta ce "Wallahi sharrin shedan ne, na rantse da Allah babu ruwan sa." "Ohh.. sai kika sa yarki tayi mishi sharri kenan ko?" "Wallahi ba haka bane, ba ta gane kan maganar bane wallahi, ni bana ma sata a abubuwa na saboda bata tare dani, taji muna waya ne ina ga ranar ta zata da shi ne." "Gaskiya zaki gaya min in ba haka ba yanzu na sa a kawo yar taki nan itama na haɗa ku." "Toh.. Toh mmm mmm wallahi sharrin shaidan ne." "Kece ai shaidan ɗin da kanta, kin yi hakan me kinsan zata fada, gaskia baki da kirki wallahi, aikuwa har yanzu baki gama horuwa ba, maida ita ka chanja mata dakin da muke ajiye robbers, batayi hankali ba." "Wayyo na shiga uku, wallahi na tuba na daina, na shiga uku zan mutu wayyo Allah na." Jan ta yayi shi kuma ya maida wayar kunnensa "Kaji komai Oga, matar nan criminal ce ta gaske, ina ganin kuje ku dawo kafin nan ta sake hankali." "Yadda kayi yayi ai babban Oga, Allah ya baka General na Nigeria Baki daya." Dariya ya saka "Amin toh, sak anjima." Kallon Salim da Arkel yayi ya mike yana zura wayar sa a aljihu, "Sai ku karasa tattaunawar ni na gama,." Dariya suka saka a tare ya juya yana daga kafada, sai da yayi gaba sosai sannan ya waiwayo yace "Baban soyayya, karka manta da auren yar ta daka yi Alk'awari." Dariya suka saka gaba daya ya cire takalmin sa ya jefe shi dashi, gocewa yayi yana dariya ya shige, a hankali ya furta "Dan iska." "Oga zan wuce." Kallon sa yayi duk babu dadi yace "Zamuyi waya, I'm sorry." "Babu damuwa." *** *Bayan sati biyu* Kwana biyar visar su ta fito, tafiyar awa biyu da yan mintuna ne zai kaisu kasar ta Mali a jirgi, abinda ya sa ma aka jinkirta tafiyar saboda Maryam ne da aka jira ta gama first trimester din ta, tafiya a jirgi tafi ga me ciki idan ta shiga second trimester, duk shirye shiryen da ya kamata yayi yayi musu har ticket ya siya. A ranar ne kuma yaje asibitin tare da Maryam aka sallami Hafiz in da zai karasa jinya a gida, dan madaidaicin gida aka samu na haya da zasu zauna a ciki bayan da Arkel ya shawo kan inna da kyar ta amince dan ma tana tsananin jin nauyin sa saboda alkhairin sa gare su. *** Tafiya ce da zata hada bangarori da yawa, bangaren Maryam, Baba, Umma, Habubu, Walid sai Alhaji Faruku. Bangaren su Arkel kuwa Ummi, Arkel, Arab, Alhaji, Nabila, Kamal da yaran su biyu. Tun safe aka hau shiryawa kowa sai zumud'i yake, snacks akayi a gidan Ummi na tafiya a daren jiya saboda dai yanayi karsu nemi wani abu, kafin sha biyu kowa ya gama shiryawa tsaf, Maryam da Arkel anko sukayi na shadda kalar cheese me matukar kyau da kyalli, mota biyu suka Ummi, Umma, Ya Nabila, Maryam  sai Habubu da Walid suna mota daya Arkel ne yake jan motar, in da motar Arab kuwa shi yake jan Alhaji na gaba sai Baba da Alhaji Faruku da kamal a baya rike da su Amna, suka nufi airport abun sha'awa, suna zuwa basu wani jima ba jirgin su ya daga zuwa kasar ta Mali babban birnin Kasar Bamako a in da nan ne filin hawa da saukar jiragen kasar yake, tafiyar awa biyu da yan mintuna suka isa, Maryam hannun ta yana damke dana mijin ta duk a tsorace take, ko da za'a fito ma sai daya taimaka mata ya rike ta suka fito, Nabila da Kamal sai dariya suka musu su kuwa basu san ma anayi ba wai kunu a wani gida. *** Babban hotel din garin na Bamako suka sauka saboda su huta gobe su dau hanyar garin na Mande,da la'asar bayan kowa ya huta suka fita zaga gari suka bar manyan a hotel din, ba laifi garin yayi kyau sosai duk da suna da yawan sahara amma ba karamin kayatar dasu yayi ba, sai wajen isha suka dawo masauki. Da daddare bayan kowa ya kwanta Arkel ya kira Maryam a waya, kallon ya Nabila tayi ganin kamar bacci take yasa ta tashi a hankali ta fito, yana tsaye a wajen dakin yana ganin ta ya sauk ajiyar zuciya. Hannun ta ya rike suka sauka gaba daya daga saman, hawa na farko suka koma ya bude dakin suka shiga. Kallon tuhuma take masa ya kanne mata ido ɗaya yana dariya "Wayo ko?" "Emana, shikenan sai a wani hada ni da garada ace na kwana,haba ina ai ba zai yiwu ba wallahi." Dariya tayi tana buɗe baki "Su Ya Kamal ɗin ne garada, bari ya Nabila ta ji ka." "Taji mana, ina zan iya, zo ki ji wata magana." Make kafada tayi ta saka dariya "Ahaap ai na sani, sai da safe kafin Ummi su tashi da safe su ga bana nan." Hanyar waje tayi zata fita yayi saurin durowa ya riketa "Ai wallahi baki isa ba, na riga nayi budget dake, babu in da zaki wallahi, chab mutuwa ma kenan." Ita dai dariya kawai take masa ganin yadda ya hakikance, babu yadda ta iya da rigimar arkel,dole ta bada kai bayan jan aji da noke-noken da tayi ta gama. *Asubah ta gari Mr and Mrs M.Arkel😍 Ke kuma Maryam  Kin dai ji me Anty Farida ta fada ranar babu ruwana wallahi nima🤣🤣🚴🚴🚴 [3/18, 22:28] Hafsat Rano: 53 *SAUYIN ƘADDARA* *HAFSAT RANO* **** Sanda suka isa Mande dukkan su kowa dauki da murna yake, tuni dama an san da zuwan su, an shirya abubuwa kala kala dan tarbar su, Ummi da ke ta faman goge hawaye kadan kadan saboda yadda take ji a ranta abinda bata taɓa tunani ko kowa wa a ranta ba, sanda suka karasa masarautar ta kowa sai daya buɗe baki saboda mamaki da Al'ajabi, ba zaka taba tunanin akwai halittar dake rayuwa a wajen ba kafin ka karasa. Firfitowa sukayi aka hau bushe bushe da kad'e-kad'e, Sarkin da kansa ya fito ya tsaye a daidai kofar yana me tsananin farin ciki, karasawa sukayi cike da farin ciki aka hau gaisuwa duk da yaren da sukeyi ya banbanta amma da yawansu suna jin hausa, sai kuma france da ya zama shine official language na kasar sai kuma yaren Bambara da ya zama kamar Hausa a Nigeria bayan fulatanci da ya zama yaren garin nasu. Hannu Baba Sarki Àraàbú ya kama suka shiga ciki, a fada aka yadda zango aka shiga sabuwar gaisuwa sannan Arkel ya gabatar da Ummi da Baba,da kowa da kowa, daga nan kuma ne aka sa matan da yaran suka tafi cikin gida dan su huta su ci abinci suyi sallah, babban masaukin da aka tanada domin su aka kai su, ba karamin kawata wajen akayi ba duk saboda zuwan su, Ummi da take jin ta kamar an sata a aljanna don murna sai taji bata da wani sauran damuwa a rayuwar ta, duk da Allah be sa taga iyayen ta ba, amma tana tunanin hakan wani tsari daga Allah cikin hikimar Sa ya hukunta mata hakan, ta gode Allah ta kuma sawa ranta wannan shine jarabawar ta. *** Tana zaune ana gyara mata gashi ta cigaba da jin bushe bushen da akeyi tun safe, duk da ita mutum ce ba me son kwaramniya ba amma hakan ya saka ta son sanin abinda yake faruwa a masarautar tasu, ta san dai koma menene yana da matukar muhimmanci ga ahalin gidan. Janye kanta tayi ta tashi tana daukar rigar ta zata dora a sama, da sauri baiwar ta ta mike ta taimaka mata, takalmi ta zura  ta sake gyarawa sannan ta kalle ta "Me akeyi a gidan nan?" "Ranki ya dade, bakon nan ne na kwanaki ya dawo, sai dai wannnan zuwan da yawan su suka zo har da mata da yara." "Suna ina?" "Mazan na tare da maimartaba, matan na chan karshen babban gida anan aka sauke su." Bata yi magana ba ta juya ta fito, tsayawa tayi a kofar bangaren ta tana kallon fadar daga nesa, zuciyar ta na ingizata taje ta ganshi, ta rasa dalilin da yasa ya tsaya mata arai tun ranar data fara ganin shi, sai dai a yadda take jin kanta da mulki ba zai a iya ba, tsaki tayi ta juya wani shashen tana tafe tana kallon in da aka ce an sauki bakin a chan. *** Da daddare duk kowa ya hallara a fadar, har da Bongel da sarki ya aikata tazo ita da dan uwan ta yôùsòfà, sai sauran dangin da abin ya shafa, bayan dogon jawabi daga bakin sarki da abinda ya tara su sai ya bawa Baba dama yayi magana ya sake gabatar da kansa da yar uwar sa Ummi, sannan aka bawa sauran kowa dama shima ya fadi nasa bayanin, Bongel na daga ɓangaren dake fuskantar Arkel, shi kuwa hankalin sa na kan Maryam, duk motsin ta a idon sa yana lura da ita, ya san ta gaji so take ta huta shiyasa kawai ya ga gwara ya nema mata alfarma tun da tana da uzuri, fita sukayi duk kunya ta kamata bayan ya nemi alfarmar zai rakata ta kwanta, suna barin wajen mutane yayi saurin jawo ta jikin sa. "Sannu my wife." "Uhum sannu, kawai sai ka bani kunya a cikin mutane." "Kunyar me? Dan nace zaki huta kina da uzuri?." "Baka ga yadda kowa ke kallo na ba, wanda be gane ba da yanzu kasa duk sun gane, sai wani sannu ake jera min." "Haha, toh me kike so suyi, ni ai tausaya miki nayi ashe ban yi gwaninta ba." "Kayi... Kadan amma, kuma wallahi idan munje baccin zanyi karma kace..." Rike ta yayi ya tsaya yana mata kallon mamaki "Wai me kika mai dani ne yarinyar nan?" Zame wa tayi tana dariya tace "Bance komai ba ni." "Zakiyi bayani ne." "Daga fadan gaskiya." "Zaki sani ne, wanka zanyi kinji zafin garin nan kuwa? Ai sai ka dafe dan ma akwai wuta." "Kasan sahara, dole za'a yi zafi dama." "Aikuwa akwai, kwana uku zamuyi mu tattara mu koma gaskiya, sai dai in Ummi zata zauna da Baba bamu sani ba." "Suyi kamar sati ba, nima in zasu zauna zaman zan gaskia." "Sannu toh." "Please...." "Kafata kafarki Madam." Tura baki tayi gaba ta hau kunkuni, be bi ta kanta ba ya shige toilet d'in ya tara ruwa sannan ya fito, towel ya dauko a cikin kayan su ya daura sannan ya matso kusa da ita, rigar jikin ta ya kama zai cire ta rike hannun sa da sauri, hannun ya janye ya cigaba da abinda yake, sai daya gama ya mika mata dayan towel din yace "Manzon Allah (S.A.W) ma yana wanka tare da iyalin sa, sunna ce me kyau so don't ever deny me again ba zanji dadi ba." A sanyaye tace "In Sha Allah." *** Washe gari aka gabatar da wasanni a kofar fadar, mutanen gari duk sun zo har da wanda suke makwaftaka dasu, wasan ya kayatar sosai sun ga banbancin al'adah, bayan an gama kowa ya watse, gari aka zagaya dasu aka nuna musu ko ina sannan suka dawo da yamma likis. Kwanan su biyu Bongel ta gama fuskantar alakar Maryam da Arkel, duk da sau tari bata iya banbance su sai dai idan an kira sunan, sai kawai ta hakura ta watsar da komai ta cigaba da addu'ar Allah ya zaba mata mafi Alkhairi. Shi kuwa Arab ko lura da ita be ba, abu daya ya riga ya sawa zuciyar sa zai bawa Lubna dama, yana komawa zai sanya aje a tambaya masa auren ta. Washegari suka fara shirye shiryen tafiya in da za'a bar Ummi da Alhaji, sai Baba, Maryam da Ya Nabila sun so su kara zama amma sam ogannin nasu sun rufe idon su sun ce no, haka suka tattara suka bi su ba dan sun so ba, ita kanta Ummin taso a bar mata wata tun da sati biyu kamar yau ne, sai dai tun da ta lura da yanayin yaran nata ta share batayi zancen ba, musamman Arkel daya fi kowa rawar kafa babu yar kunyar nan duk mantawa yake da kowa na wajen idan aka ce abu ne daya danganci Maryam. *** Sati biyu aka sallami Hajiya Mero, saboda tsabar yadda ta koma da kyar zaka gane ta, har kofar gida suka kawo ta suka tafi, bata bari ta kwana a garin ba ta saka Zainab a gaba suka koma Kaduna, bata fatan ko da wasa ta sake dawowa Kano, Hajiya Mama kuwa bata gane komai gata nan dai hakkin mutane ke bibiyar ta. Shi kanshi Alhaji Farukun ya daina damuwa da lalular ta ta bikin Rauda ne a gaban sa yanzu, ya matsa so yake kawai yayi mata aure dan rashin jin nata kara yawa yake shiyasa kawai ya yanke shawarar aurar da ita ko ya huta. *** Bayan dawowar su abubuwan duk suka hade wa Maryam, ga project ga ciki yayi nauyi ga hidimar gida haka dai take daurewa tana kokartawa dan bata son samun matsala, shi kanshi uban gayyar ya sake zama busy saboda ginin da yake yi ga shagunan da yake shirin budewa, haka dai yake yakicewa yana kula da Madam din  tasa, har aka samu aka kammala karatun dai da kyar lokacin cikin ya tsufa haihuwa ko yau ko gobe. *** Shagon Baba na kasuwa aka sake buda masa aka zuba masa kaya, sabon gida Arkel ya haɗa mishi ya bashi a matsayin sa na wan mahaifiyar sa kuma uban matar sa, sosai Baba ya zama Babban mutum harka ta bude masa ba laifi yana samu a shagon nasa tun da yanzu ya zama saro kayan yake yana siyar wa ba pieces ba. *** Bayan kwana biyu Arab ya nemi aje a tambaya masa auren Lubna, Alhaji ne ya wakilta Baba da Alhaji Faruku suka je suka tambayar masa aka ce an bashi, murna ba'a magana tsakanin masoyan biyu, ba a wani ja da yawa ba aka kai kayan aka saka rana wata hudu. Tun daga lokacin aka shiga shiri bangarorin biyu kowa yana so ya burge danuwan sa. *** A gajiye ya dawo tun daya fita be zauna ba, shirye shirye kawai yake na shagunan da zai bude, Maryam na gaban akwati tana jera kayan da za'a tafi dasu asibiti ya shigo, tashi tayi da kyar ta yi masa sannu da zuwa, ruwa ta doro akan tray ta kawo masa ya sha sannan ya kalli kayan "Komai ya zama ready ko?" "Eh, Zaitun da Spirit ne kawai babu." "Owk hadda su ko? Mantawa nayi wallahi." "Ai dole, kana kokari ma Allah ya saka maka da Alkhairi." "Amin." "Allah ya raba lafiya." Kasa ta sauka ta jawo kayan abincin data ajiye mishi ta zuba masa, zama yayi kusa da ita ya karba yace "Thanks." Murmushi tayi ta sake mike ƙafarta da take jin tayi mata nauyi sosai. Da magriba suna sallah sun kai raka'ar karshe taji kamar an buga mata ciki, suna sallama ya juyo yana fuskantar ta, ganin da yayi tana ya mutse fuska yasa yace "Ya dai?" Cikin ta ta nuna masa tace "Ji nayi kamar an buga ni ta cikin." "Toh, sannu Bby ke exercise." "Uhum." Tun daga lokacin ta cigaba da jin babu dadi, wajen goman dare ciwo ya fara tsananta, tun tana dauriya har ta zama ta kasa, dole ya sauka ya kira Ummi, tana zuwa tace su fito a tafi asibiti haihuwa ce, kayan kawai ya dauka ya saka mata Hijab ya rikota suka sauko da kyar. A motar abun ya cigaba da karuwa, sosai take kokarin ganin tayi dauriya sai dai ciwon ma neman fin karfin ta, bata san lokacin data fara kuka ba tana kiran sunan Allah. Arkel duk ya rikice ya rasa me yake masa dadi, sauƙin ta ma Arab ke tukin da kuwa an samu matsala. [3/18, 22:28] Hafsat Rano: SAUYIN KADDARA 54 *** Zagaye kawai yake a wajen ya rasa abinda yake masa dadi, tsawon awa biyu babu wani labari, kana kallon fuskokin su zaka san suna cikin tashin hankali, jiran me haihu bashi da dadi akwai tashin hankali da zulumi, kallon Arab Ummi tayi tace ya kira mata Ya Nabila, gefe ya koma ya kirata ya kashe ya dawo yana kallon yadda Arkel yake zagaye baya ma gane komai, har Nabila ta karaso bata haihuwa ba, duk sun yi jigum jigum dasu babu me wa wani magana ana addu'a. A chan gida gaba daya sai Umma taji jikin ta babu dadi, tun daren ranar ta kasa sukuni, jikin ta ne ya bata Maryam ba lafiya, addu'a tayi ta yi mata tana fatan idan haihuwa ce Allah ya raba su lafiya. Gaf da asubah ta haifo yar ta bayan bakar wuyar data sha, da sauri nurse din ta fito ta sanar dasu, ta koma, Arkel na Masallaci yana addu'a be san anyi haihuwar ba har aka fito dasu daga labour room aka mai da su dakin hutu, kiran wayar sa Arab ke tayi be daga ba dan basuyi tunanin yana masallacin ba, duk sun shiga wajen ta sai sannu suke mata, da ido kawai take bin su,ta riga ta dandano bakar wuyar da kowacce uwa take sha yayin haihuwa, lallai ba karamin kokari iyayen mu suke sha ba da zaka ga sun haifi goma sha sannan suzo suyi tarbiyyar dukka. Allah ya kara wa iyayen mu daraja. Fitowa yayi daga Masallacin yana kallon sararin sama, jikin sa babu kuzari ko kadan, tsoron sa daya kar ya rasata, zuciyar sa ba zata iya dauka ba, wayar sa dake haske a aljihun sa ya lalubo ya duba, kiran Arab ne ya sake shigowa yayi saurin d'agawa "Kana ina ne? An fito dasu fa." Da sauri yace "Ta haihu?" "Emana, kayi sauri." Be jira komai ba yayi saurin komawa ciki, yana tafiya iska na kada shi saboda tsananin farin ciki, yana zuwa nurses din wajen suka hau yar rige-rigen tare shi, murmushi kawai yake yana kokarin yin gaba yana sauraron su "Bari na fito zan ganku." Cike da karsashi ya isa ya tura kofar, da sauri Maryam ta rufe idon ta ya Nabila ta hau gud'a, dariya kawai Ummi take tana kallon Arkel, sai ya tsaya chak ya kasa karasawa kunya na kamashi, dariya Arab ya saka yana kallon shi "Su kunya manya." "Ƙaraso mana angon karni." Kallon Ummi yayi yaga shi take kallo, sai ya sauke kansa yana dariya "So yake mu fita naga alama." Ajiye baby tayi a gefen Maryam ta kalli Arab da Nabila "Muje waje." "Gaskiya ni ban ga gama ganin my princess ba." Arab yace yana sake zama "Amma ai ka bashi waje ya ga lafiyar matar sa ko?" Nabila tace tana dariya, lokacin Ummi ta fita ganin haka yasa ya cije yatsa yace "Allah muma ya aurar damu a daina mana gori." "Da dai yafi,muje ni." Fita sukayi Arkel ya maida kofar ya rufe har da saka key, da sauri ya dawo gefen ta ya zauna yana kallon fuskar ta yadda tayi fayau, d'an yatsan yasa ya zagaye a saman girar ta, bude idon ta tayi kadan tana kallon sa, dariya yayi ya manna mata peck a kuncin ta yasa hannu ya dauko babyn sa ya zuba mata ido, babu in da ta barshi, hannun ta ya rike a cikin nashi yana kallon kankantar hannun, murmushi ne kwance a fuskar sa ya rasa ya zai fasalta ranar, "Sannu Wife." Yace yana shafa fuskar ta, "Haka ake shan wahala dama?" Tace tana girgiza kanta, fuskar tausayi yayi ya rike hannun ta da dayan hannun sa "Kinsha wahala ko? Sannu Allah yayi miki albarka." "Amin." "Kinga carbon copy d'ina ko? She looks exactly like me." "Uhumm.. Son kai ko?" "Kalle ta mana, ba wani son kai." "Uhum." "Ya kike ji?" "I'm weak." "Sannu Allah ya Kara lafiya." "Amin." Wasa ya cigaba da yi da babyn, idon ta ta soma budewa kadan-kadan har ta samu nasarar bude shi dukka, kallon ta kawai yake in admiration, Wai shine yau da baby, Allah kenan, kuka ta fara tana taɓe baki yayi sauran kallan Maryam "Ya zamuyi? Kuka." "Nima na sani." Baya ta juya ya kwantar da ita ya fita waje, be ga su Ummi a reception ba sai wajen nurses yaje yace musu tana kuka. Kallon juna sukayi suka sa dariya a tare "Baban baby, madam ta dan daure ta gwada mata maman." "Ok." Yace yana juyawa dan yaji haushin dariya da sukayi masa, komawa dakin yayi yace "Sun ce ki dan bata ta sha." "Wa! Hum um." "Haka suka ce ai." Kin tashi tayi babyn ta sake bude murya sosai, jijjigata ya hau yi daga kwancen da take yana kallon Maryam yana mata magana ta tashi, banza tayi taki tashi har sai da Ya Nabila ta shigo, daukar babyn tayi ta jijjigata. "Kanina dan bamu waje mana." "Ok toh." Yana fita ta kalli Maryam "Daure ki tashi kiga." Kamar ta fasa ihu ta tashi da k'yar saboda ɗinkin da akayi mata ya soma daddaure mata jiki shiyasa bata son ko motsawa "Sai fa kin daure, shi dinki dole sai kana motsawa, idan kaso jikin ka ya kwabe ma." "Akwai zafi ne Ya Nabila." "Sannu... Daurewa ake." *Uhum." Mika mata ita tayi ta taimaka mata da yadda zatayi, duk kunya ta mamaye ta haka ta daure tana ciccije baki kamar zatayi kuka, tsabar azaba da rashin sabo. Gari na fara haske Ummi ta kira umma da kanta da sanar mata, Barka sukayi wa juna Umma na ajiye waya ta shiga dakin Baba da murna, zama tayi a gefen gadon bakin ta yaki rufuwa, kallon ta baban yayi ya gane akwai magana "Ya akayi ne?" "An samu karuwa." "Ah Alhamdulillah, Masha Allah, lafiya dai ko? "Lafiya lou yanzu Ummi ta kira ni." "Toh Alhamdulillah, me aka samu?" "Kayi amarya." "Lallai, kice na fara hada lefe, Allah ya raya yayi mata albarka." "Amin ya ALLAH." "Sai ki aika a sanar da mutanen gidan chan ko, ko kiyi musu waya?" "Eh idan garin ya sake wayewa zan aika." "Ok Allah ya Raya, sai Hankali ya kwanta yar ki ta sauka lafiya." "Baban Maryam!" "Karya nayi? Kwata-kwata baki da sukuni tun da watan nan ya kama ina sane dake." Dariya ta saka kawai ta tashi ta fita, wayar ta ta dauka ta kira Anty Maryam ta fada mata, murna ta hau yi tace zata taho anjima kadan. *** Likita ne yazo ya duba ta ya tabbatar lafiya sannan ya sallame su, Alhaji na gida suka dawo, yar aka kai masa shashen sa ita kuma me jego Ummi ta sa aka gyara mata daki a kasa ta saka ta, Arkel be gane kan hakan ba, zuba ido yake yaga sun hawo sama tun da suka dawo amma yaji shiru, yana saukowa ya tarar da aika-aikar da Ummi tayi masa, kamar ya dora hannu a sama yayi taa zunduma ihu yaji, tuni gidan ya fara cika da yan uwa da abokan arziki na bangaren Alhaji da Umman su Maryam din, ganin haka yasa ya bar gidan ba dan yayi niyya ba. Da daddare bayan kafa ta dauke ya faki idon Ummi ya fada dakin, Ido ta zuba masa har ya karaso ya zauna a gefen ta yana kallon babyn, saman dakin ya kalla ya ga fan din a kashe, tashi yayi da sauri zai kunna tace "Ba'a kunna wa jarirai fan, it's to early." "A haka zamu kwana?" "Zaku kwana?" Ummi dake cikin toilet d'in d'akin ta fito tana hararar sa "Aina zaka kwanan?" "Umm... na'am um dama." "Minti biyu na baka kayi musu sai da safe ka kama gaban ka, bari naje wajen Alhaji." Marairaice wa yayi yace "Ummiiiiii!!!" Sa kanta tayi ta fita ya bata fuska yana kunkuni "Kina jin Ummi fa, ganin ku ma sai an bani time?" "Emana." "Tab lallai, ashe mun kusa parking daga gidan nan kenan." "Babu in da zamu" Dariya take masa ya dauki babyn ya kalle ta "Wanne suna zamu sa mata?" "Uhmm.. wanne kake so?" "Zabin ki ne, ke kika sha wahala so ki zaba kinji." "Sunan Ummi?" "Yayi miki?" "Sosai, sai muce mata Hudah." "An gama ranki ya dade." "Thanks dear, nagode Allah ya saka da Alkhairi." "Shishshi, karki wani yi godiya,next haihuwa sunan Umma zan sa idan baby girl ce." Zaro ido tayi "Zan kara haihuwa kenan?" Dariya ta bashi sosai, kwantar da Baby Aysha yayi ya kamota ya sakata a jikin shi yana dariya "Menene na tsorata haka daga maganar haihuwa." "Hmm ba zaka gane ba, a bar zancen kawai." "Na barshi toh, yanzu me zaki bani tukwaicin sa sunan Ummi da nayi." Ture shi tayi tana dariya tace "Babu wayon da zaka min wallahi, ka tafi kafin Ummi ta dawo ba ruwana Allah." "Kora ta kike? Ni, Ni Ko? Shikenan bari na tafi." "Sai da safe." "Haka ma zaki ce." Daga kanta tayi ya tashi ya fita yana cewa "Zaki neme ni ne yarinya, Ni da nasan ki." *** Shirye shiryen taron suna aka ake tayi, komai an tsara shi, ba karamin kudi Arkel ya kashe ba wajen ganin yayi komai cikin wadata, raguna hudu manya manya aka yanka aka rada sunan sannan aka aika dasu gidan su Maryam ɗin, in da za'a yi aikin su a chan. Tun azahar Yan uwa da abokan arziki suka fara zuwa na kusa dana nesa, har jama'ar Mali ma sun zo tawagar su guda ana gobe suna. Sallar la'asar akayi sannan aka fito harabar gidan in da aka saka kujeru akayi decorating wajen, ba a san ran Arkel ba amma Ummi da Ya Nabila suka ce sai anyi, abinda ba wani taro aka tabayi a gidan ba, haka ya hakura ya bar musu gidan ma gaba daya tun bayan da akayi yanka. Babban Photographer aka dauko yake ta aikin sa, gefe kuma mutane ana ta cin abinci baka jin komai sai tauna, Maryam na zaune a in da aka tanada ta hango kawayen ta na buk sun shigo, zuwa sukayi suka gaisa akayi hotuna sannan suka samu waje suka zauna aka kawo musu abinci. ( Yau dai kawar zango bata diba wa Ya Bello ba kamar yadda ta saba😂😂). Yana tsaye a waje yana kallon wayar sa, shigowar ta layiin ya hango motar , gyara tsaiwar sa yayi har suka ƙaraso. Hannun sa rataye a saman kirjin sa ya zuba mata ido yana kallon ta, Lace ne a jikin ta purple and Ash yayi masifar yi mata kyau, simple shiga tayi irin ta classy mata wanda suka jiku da wayewa, tare suke da Hidaya kawarta, bude mata kofar motar yayi yana murmushi "Sannun ku da zuwa." "Yawwa sannu ango." Hidaya tace tana dariya, dariyar yayi ya kalli Lubna data bata rai taki kallon sa yace "Ayi min afwa princess." "Wai me akayi ne, tun da muka taho take bata fuska." "Wai fa mantawa nayi ban fada mata haihuwar ba sai yau shine take fushi dani." "Gaskia baka kyauta ba." "Shiyasa ai nake ta bada hakuri, idan ma so ake na durkusa har kasa ne toh sai nayi." "Shikenan, karka sake." "Ba zan sake ba, i promise, ke da ma zaki shigo gidan kwanan nan." Dariya sukayi suka jera har gate din gidan, a kofa ya tsaya ya matsa baya "Sai kun fito." "Ok." Shiga sukayi kallo ya dawo kansu gaba daya, babu karya kaf wajen babu wanda ya kaisu haduwa da gayu, text yayi wa Ya Nabila saboda haka suna shigowa ta gane su, da fara'a ta karbe su ta samar musu waje suka zauna kafin ta je ta sanar wa Maryam ɗin. Abinci ta fara kawo musu sannan tace su taso, wajen su Ummi ta kaisu da suke cikin gida duk kunya ta kama Lubna musamman yadda aka ɗin ga nuna ta ana ga wadda Arab zai aura, wajen suka dawo suka je wajen Maryam anan ya Nabila ta barsu ta koma wajen mutane, a mutunce suka gaisa ta karbi Huda ta rike a hannun ta tana jin kaunar yarinyar, tsabar kamar da take da iyayen ta twins kana kallon ta zaka ga kamar, har sai da aka tashi taron bayan magriba sannan suka tafi bayan ta bada uban kayan Barka akwati guda. A kafa suka fito tawagar kawayen Maryam suna neman abun hawa, ran Teema Gabas a bace yake ko takeaway din da aka raba bata iya tsayawa ta karba ba, Sadiya zango ce ta dafa ta tace "Kawata me akayi miki ne?" Yatsine fuska tayi kafin tace "Ki bari kawai, na sa rai da twin brother d'in Mijin Maryam wallahi gayen yayi min ya tafi dani sai gashi naga wadda ta yaga min a haduwa da komai, tun daga nan naji komai baya min dadi." "Ayya... Gaskia babu dadi, amma fa ta hadu ba karya." "Shine matsalar ai, naji ance Barrister ce ai." "Auw haba, ah dole, mu muna nan muna fama da biology gwara ma ni nayi na gama ke kuwa har yanzu kin kasa wucewa." "Kawata ya da cin fuska ne, haba daga fada miki matsalata.?" Goyon Afaf Nabila Rano ta gyara tace "Kuyi sauri mu samu ko ma samu abun hawa ga magriba tayi baban Afaf nake tsoro kar naje ya koma." Sauri suka kara babu wadda ta sake magana da yar uwar ta. 🤣🤣🤲😂🤣🚴 *** Sauke kayan barkar Anty maryam tayi aka bude su, kaya ne hadaddu atamfofi da kayan jarirai masu masifar kyau,daga uwar har yar sun samu kaya masha Allah, waje daya aka saka su bayan an nuna wa Ummi. Tana zaune tana bawa Hudah mama ya shigo, bata yi tunanin ganin sa ba, tun safe take ta kiran  wayar sa bata shiga, da kallo ta bishi ganin ya tafi gaban warmers din dake ajiye a gefe ya hau bubbuda wa, "Karka ce min baka ci abinci ba yau gaba daya." "Toh kin bani ne?" "Ai ban ganka ba, nayi ta kiran ka kuma bataa shiga." "Ina chan na shiga busy." "Busy busy kullum dai Baban Hudah." Da sauri ya kalle ta, sai kuma ya kwashe da dariya har da rike ciki, sai da yayi me isar sa sannan ya dawo ya zauna yana miko mata hannu "Kawo ta ki samo min plate naci abinci please, Wai Baban Hudah ko dadi babu." Dariyar tayi ita ma ta mika masa ita tana gyara zip din rigar, wajen yake kallo bako dauke ido tayi saurin rufewa tana dariya "A gama boye boyen da za'a yi, ina nan ina jira bawan Allah." Ta sani sarai jan magana ne sai kawai tayi waje tana dariya a hankali. Bayan ya gama cin abincin ne ya ciro keys guda biyu ya mika mata, hannu tasa ta karba tana masa kallon tuhuma "Alk'awari na dauka da zuciya ta tun sanda kika shigo rayuwar mu, sai yau Allah ya cika min buri na, motocine guda biyu, taki daya dayar kuma ki bawa Baba." Wani irin yanayi ta shiga, bata taba kawowa ko a mafarki ba, bata san sanda ta rungume shi kam ta saki kukan farin ciki, abun ka dame jiran kiris da sauri ya maida hannun sa saman nata ya rike ta kam kam yana shaƙar kamshin jikin ta, gaba daya sun saki jiki tuni ya fara mantawa da duniyar da suke, kukan Hudah ne ya dawo da su tayi saurin janyewa yana sunne kanta, yaushe ta haihu da har zata saki jiki haka, taso tayi wauta Allah ya taimaka mata Hudah ta ceceta, juya bayan sa yayi jiki a sanyaye ya gyara kwalar rigar sa yana cije leben sa, babu niyyar komai a ransa be san ya akayi yaso zarmewa ba, yayi browsing yaga illolin dake tattare da hakan ba zai so ta samu matsala ba, zai bi komai a sannu har zuwa lokacin da zasu dawo daidai. Tashi yayi zai fita tayi saurin dakatar dashi ta hanyar cewa "Ummi fa? Har da ita ma ka bata?" Murmushin jin dadi yayi ganin Allah ya cika masa burin sa na samun wadda zata kula da Mahaifiyar sa kamar yadda zai yi, ya san ba kowacce mace bace dan mijin ta yayi mata kyauta zata tuna mahaifiyar sa fa, dawowa baya yayi ya mika mata hannu cikin son sake tabbatar wa yace "Kawo taki sai na kai mata, idan yaso sai nan gaba sai a sai miki wata idan Allah ya hore." Babu musu ta mika masa tana bata fuska "Dama ita ai ya kamata ka fara saiwa bani ba, baka kyauta ba." Murmushi yayi ya rankwfo daidai saitin fuskar ta yace a hankali "This is what makes me love u more and more everyday, u are so special with pure heart, Allah yasa Hudah tayi halin ki, I love U endlessly my wife." Lumshe Ido tayi a hankali tace "I love You more." *** *SAUYIN KADDARA*     55 © Hafsat Rano *** Yana fita ta kira Umma ta sanar mata, godia sosai ta din ga yi tace ba zata fadawa baban ba sai ta kawo masa da kanta ta fada masa, tana ji daga wayar su Habubu nata ihun murna, dariya kawai tayi ta kashe tana tunanin rayuwa. Babu yadda Allah baya maida bawa, idan yaso a rana daya zai sauya maka rayuwa daga mara shi ka koma me shi, ko daga me shi ka dawo mara shi, gashi dai irin sauyin da ya samu tasu rayuwar, sau da dama abu na faruwa da mutum yaji kamar shi kadai duniya ta juya wa baya, sai dai ashe alkhairi ne yake bibiyar mutum ba tare da ya sani ba, kowacce rayuwa tana da kalar jarabawar ta, walau ta dadi ko akasin haka, kowanne bawa da yadda kaddarar sa take zuwa, ƙaddara na sauya wa ne da yadda aka tsara wa mutum, bashi da zabin guje mata face ya karbe ta hannu bibbiyu, ya mutunta ta watakila shine alkhairin. ***Shirye shiryen Biki ya kankama, sati daya ya rage, dukkan su ukun sun shiga busy Ya Nabila nata korarin hada lefe gashi har lokaci ya kusa kurewa ba'a kai ba, ginin gidajen da sukeyi guda biyu a kusa da juna shi ya saka duk suka kara shiga busy sosai, Arkel ma so yake ya tashi daga cikin gidan su tun da yanzu ko da yaushe Alhaji yana gida sai dai da la'asar ya fita gate ya zauna abokan sa suzo ayi hira, ga Baba Ladi ma ta dawo gidan saboda haka Ummi tana da masu ɗebe mata kewa ga Sadiya me aikin ta, so yake shima ya haɗa family sa waje daya shiyasa yayi hakan amma ba wai dan baya son zaman gidan bane sai dan kowa zai zama comportable da iyalin sa. Baby Hudah ta yi yawo sosai a dan lokacin nan masha Allah, suna ta kokarin yin arba'in ga shirin biki, haka dai take daurewa tana yin gyare gyaren ta wanda yawanci Ummi ce tsaye akanta sai wasu abubuwan da Anty Maryam ke aiko mata. Sati ya zagayo aka shiga biki gadan gadan, events hudu amarya tayi amma daya ango yaje dinner sauran ita da kawayen ta ne sai kamu hade da mother's Eve da Maman ta tayi, ranar Lahadi aka kai amarya gidan ta in da sati daya bayan nan Arkel zai koma shima. Washegarin ranar ne Maryam tayi arba'in, murna a wajen Arkel baa magana, gida ya fara kaisu in da zatayi kwana biyu ta je duk in da ya kamata, yana ajiye su ya juya wajen aikin sa, a yadda yake sa rai sati me zuwa za'a bude shagunan, babu abinda ba'a zuba ba sai dan abinda ba za'a rasa ba. Gaba daya yadda rayuwar gidan su ta chanja kadai take kallo tana jin wani irin dadi, kauna da kimar Arkel ƙara nin kuwa take a zuciyar ta, da yamma ta leka gidan Maman Walid suka sha hira, wasu kayan ta sake bata sannan ta dawo gida. Washegari tayi gidan Anty Maryam, bata barta ta dawo ba tace sai ta kwana, kiran umma tayi ta fada mata kar ta ji shiru, daren ranar kusan raba shi sukayi suna hira da Anty Maryam, anan ta sake fahimtar wasu abubuwan yadda zata sake kai mi wajen kula da mijin ta da yan uwan sa baki daya. Daga nan kuma sukayi gidan sauran kannen Umman da yan uwanta na kusa, sai gidan Hajiya Mama bisa tursasawar Umma, anan ne taji labarin bikin Raudah sati biyu bayan na Arab, ta dan tausayawa Hajiya Mama ganin yadda take jin jiki komai sai dai ayi mata hatta da kashi wani lokacin a kwance take yin abinta, gashi yar ta ta data gatata bata nan balle ta tausaya mata, Maman su Raudan ce ke kula da ita da wata yar uwar su da Alhaji Faruku ya dauko daga kauye take kula da ita, kullum cikin zagin ta take da hantarar ta, sai tayi ta kuka idan Alhaji Faruku ya shigo duba ta tana so ta fada masa amma ba dama. Sai yamma likis ta koma gida da daddare sai gashi yazo, kamar kar ta tafi haka taji, haka ta tafi a ba yadda zatayi gashi Baba baya nan ko sallama batayi masa ba. Washegari ta tafi gidan Ya Nabila daga nan suka tafi gidajen yan uwan Alhaji, daga nan sukayi gidan ango Arab. Yana manne a gidan be je ko ina ba, gaba daya ya rasa yadda zai misalta aure, sai alokacin yake dana sanin shekarun daya dauka be yi aure ba, gashi ya hadu da Lubna wayayyiya, sai yake ganin kamar yafi kowa sa'a a duniya. A falo suka tarar dashi ya wani bararraje yana kallo a cikin tafkekiyar Tv dake girke a tsakiyar falon, da sauri ya mik'e yana dariya "Mun yi fushi." Dariya suka sa Ya Nabila ta kalli Jallabiyar jikin sa tace "Wai kowanne ango burin sa yasa jallabiya ya zauna a falo ne?" Share ta yayi yayi dariya kawai ya mika mata hannu "Bani princess dita, naga alama so kika ki kai ni kasa." "Ina wuni ango?" Maryam tace tana kunshe dariyar ta "Auw kema wai? Toh ai shikenan tun da yar haka ce." Zama sukayi aka gaisa Ya Nabila ta cigaba da tsokanar sa kafin tace "Ina amaryar ne?" Bude murya yayi yace "Baby!" Shiru bata amsa ba ya mik'e yana cewa "Ina ga tana toilet, bari na dubo." Hada ido Maryam sukayi da Ya Nabila suka yi dariya, wucewa yayi dauke da Hudah a kafad'ar sa Amna ta bishi ya shiga corridor da zai sadaka da master bedroom d'in, turawa yayi ya shiga, tana tsaye ta sake wanka tana fesa body spray a jikin ta, murmushi ya sakar mata ta mayar mishi, mika masa hannu tayi bayan ta yafa dan karamin mayafi ta karbi Hudah sannan suka jero a tare suka fito yana rik'e da hannun Amna " Sannun ku da zuwa." Gefen Maryam ta zauna tana murmushi suka gaisa, wasa take wa Hudah kafin ta mike tayi Kitchen bayan ta mik'a wa Arab ita, kayan snacks ta doro akan tray ta hado da lemo ta kawo musu, hira suka cigaba kamar dama sun saba bata wani jin nauyi ko kunyar su, duk abinda take yi Maryam na ta lura da ita, dole ne ta sake saban zama yadda ta ga ana kallame miji kowa na adana nata dole ita ma ta zage damtse ta kula da nata. *** Gaba daya satin sun yi shi ne cikin zaga dangi, na kusa da na nesa duk ta kai wa kowa ziyara, a na gobe zasu koma sabon gidan su ne jikin Hajiya Mama ya sake tsanani, bata san ma waye a kanta ba, kiranta Umma tayi tace lallai tazo ta duba ta idan zai yiwu a yau ma, kiran Arkel tayi bayan sun gama wayar ta fada masa, cewa yayi ta jirashi, chanjawa Hudah kaya tayi ita ma ta sake kaya ta sakko kasa ta sanar wa Ummi, suna zaune da Ummin ya shigo, tashi tayi ta bar Hudan a wajen ta bishi, sai daya fara watsa ruwa ta taimaka masa sannan yaci abinci, tun da dadewa ta gane Arkel baya wasa da harkar abinci, musamman na gargajiya, ta rasa a ina ma ya koyi cin ire iren abubuwan gargajiya duba da yanayin gidan nasu, haka take daurewa tana yi masa da taimakon Ummi da Baba Ladi. Sun fito Ummi tace su je idan ba dadewa zasuyi ba su bar Hudah tun da tayi bacci har ma ta goya ta, irin murmushin gefen bakin nan Arkel yayi da Maryam ce kadai ta san manufar sa, kamar tace a kawo ta haka dai ta bishi suka tafi, suna shiga mota ya kalle ta yana dariya "Ya akayi?" tace tana gimtse fuska "Da sai kice wa Ummi ta baki yarki ai ba zaki barta ba." "Ni nace maka haka?" "Gashi nan a fuskar ki." "Ni bance ba, kawai nasan halin Baban Hudah ne, nasan me kake shiryawa." Dariya ya saka har da buga sitiyari yace "Da yake ni kuma kullum sai aka ce miki abinda nake kenan." "Toh ai kai ne." "Zakiyi bayani dalla-dalla yarinya, wanne asibiti take?" "Bari na kira Umma, na manta ban tambaya ba wallahi." "Owk." Yace yana rage speed din motar, kiran Umma tayi tace mata suna AKTH, chan suka wuce suna tafe suna hira gwanin sha'awa. Suna shiga asibitin suka tarar da Alhaji Faruku zai fita hankalin sa a tashe, be gansu ba har sai da Arkel ya yi masa horn, tsayawa yayi suka samu waje sukayi parking suka fito, suka karasa wajen motar tasa. Gaishe shi sukayi ya fada musu dakin ya tafi su kuma suka shiga cikin asibitin. Su Umma zaune a waje suka karasa, saurin sauke kanta Umma tayi data hango su sun nufo wajen, har suka ƙaraso bata daga kanta ba saboda nauyi da kunya irin ta surukunta, ciki suka shiga suka duba Hajiyar suka dawo wajen abin tausayi dan ba karamin jiki take ji ba. Komawa mota yayi ya barta ta zauna a wajen su Umman kadan sannan ta tashi ta tafi. A hankali yake tukin yana so ya ga iya gudun ruwan ta, chanja hanya yayi a dawowar ma duk sai ya ga ta kagu aje gida, ya san tunanin Hudah take sai, murmushin yayi ya kai hannu saman rigar ta yana dariya "An ce idan yaro yana kuka uwa tana iya ganewa ko?" Kallon sa tayi ta kalli in da hannun nasa yake kai, tasan me yake nufi sai kawai ta dauke hannun nasa tayi dariya kawai batace komai ba, cikin son sai ya kure ta yace "Ko za'a taimaka min da kaso na ne? Kar baby Hudah ta ci da rabona fa." "La'hailah wai baka jin kunya ta anymore?" Tace tana dauke kanta gefe, dariya yayi kawai be sake magana ba har suka zo gida, sai data zo fita ya rage murya yace "Just get ready hakuri na ya kare, I need u back." Sauka tayi tayi cikin gida tana mamakin shi. *** Washegari aka tare a sabon gida, sosai gidan ya hadu babu karya, komai na ginin gidan irin na Arab ne sai dai kayan ciki su banbanta, a ranar Maryam ta jisu sukayau, bayan yan rakiya sun watse ta rufe gidan ta ta saka dan karamin bom short da half vest ta dinga yawo tsakanin falo zuwa kitchen da dinning area, yau kam ji take kamar ta samu wani freedom da da bata dashi duk da kuwa a sama suke a chan din Amma ba kamar kai kadai ba, sai dai zatayi kewar Ummi tasan ko dan yadda take rainon Hudah, sai ta dade bata yi kuka ba ta goye ta. La'asar likis ta shiga kitchen ta dauko tarkacen kayan da Maman Walid ta bata, ganyen idon zakara, mazarkwaila, ya'yan zogale, minannas, kanumfari, zogale an dake su waje daya ta hada madara a kofi da yawa ta zuba su kayan sannan tasa zuma me yawa ita ma ta juya ta hade su ta shanye, sosai abin yayi mata dadi, wanka tayi ta goya Hudah tayi sallah, kafin ta idar tayi bacci, kwantar da ita tayi ta ciro sababbin English wears din ta, ta saka bata wani bata lokaci a wajen kwalliya ba saboda ita na gwanar kwalliya bace, sanyayyen kamshin khumra da haaddadun turarukan jiki dana kaya ke tashi, burner ta kunna daga corridor din falon kamshi ya shiga tashi ta kowanne lungu da sako na gida. Sai da ya tsaya ya sai abin da zasu bukata da safe sannan ya nufo gidan yana jin wani karfi, yana bude gate din gidan kamshi ya daki kofofin hancin sa, ja yayi da baya ya lunshe idon sa yana jin wani sanyi na ratsa shi, bayan ya shigo da mota ya kwaso kayan ya turo kofar, bata falon sai karar Tv dake ta faman yi, ajiye kayan yayi a saman Centre table ya nufi dakin ta, tana zaune kan gado tana bawa Hudah abinci ya shigo, sam bata ji shigowar sa ba saboda kukan da hudan keyi, kafe ta yayi da ido yana noticing din ta, sannu da zuwa tayi masa sannan ta ajiye Hudan a hankali saboda ta samu ta koma barci, sake kallon sa tayi ganin Ranar wata Laraba aka gabatar da bude shagunan guda biyu dake manne da juna, babban shine na Ummi in da aka zuba mata kayan provision da su kayan abinci, da sauran abubuwan bukata, dayan kuma dake gefen shine na Maryam, babu ce kawai babu a shagon dangin su handbags kayan ado dai na mata sai saloon da wajen spa d'aga gefe, babu wanda be yi farin ciki ba a ranar *** Bangaren Hafiz kuwa ya warke sosai har ma ya dawo aikin sa,  shine ya zama me taimaka wa Salim sabida aikin sun fara masa yawa, tare suke komai, a haka ne suka hadu da wata yarinya Zaituna yar secondary ce a shekarar zatayi candy, be wani sha wahala ba iyayen ta suka amince aka saka rana da komai, Suwaiba ma lokacin wanda zai aure ta har ya kawo lefe, sai aka saka rana daya kawai ayi komai a lokaci daya, Inna ba k'aramin farin ciki tayi ba da Allah ya dube su ya kawo masu sauki a rayuwar su ba, gashi Hafiz din ya koma makaranta yana karatun sa yana kuma aikin sa babu laifi yana samu shima, Arkel  bashi da mugunta wa ma'aikatan sa, ya buda wa kowa a cikin su, tuni ya sake habaka arzikin sa har yfi na da. *** A kwance take gaba daya ta sauya kamanni tun bayan dawowar ta take ta fama da rashin lafiya, ciwon siga ne ashe da ita yayi mugun karfi, bata iya komai sai kwanciya ga kafarta har ta fara kumbura tana fitar da wani irin ruwa me wari, duk yan kudin da take dashi ta karar dashi wajen magani amma babu wani sauki abu sai gaba yake, so take ta koma asibiti babu kudi gashi tana jin jiki sosai, ko waya bata iya dauka, tana nan k'wance a falo da yake dauke da kujerar zama one seater sai ledar tsakar d'aki duk ta yayyage, babu komai duk ta tattara ta sai da saboda neman magani, Zainab ce ta fito daga dakin zata fita waje tana ta yatsine fuska, da kyar ta daga kanta ta kalle ta cikin ciwo tace "Yanzu Zainab kina gani na a halin nan kike ficewarki ki barni, baki da tausayi ko?" Dan tsaya wa tayi daga fitar tace "Haba Mummy ya kike so nayi? Zan zauna ne ba zanje makaranta ba? Me zanyi tun da ba auren ai gwara nayi karatu." "Amma Zainab da kudin makarantar ba gwara ki kawo na sai magani ba." "Kai karatun? A ah gaskia mummy, ki barni kawai kika ma san da ya na koma makarantar? A ah gaskia." "Ba zaki taimaka min ba Zainab? Eh? Me nayi miki haka kika tsaneni?" "Kai Mummy ki jiki da wani zance, sai kin min wani abu zan fadi gaskia? Ni babu abinda kikayi min kawai ina da bukatar kudin ne nima." "Ai shikenan, ki zo ki kira min Yaya Alhaji toh." "Kai innalillah, na fa makara walalhi, idan kika fara waya sai kin fi rabin awa kina masa koke koke, ki bari na dawo kawai ba yace ma zai aiko da kudin bane wai? Zai aiko ai." Tana kai wa nan ta sa kanta ta fice tana kunkuni, kuka ne ya taso mata ta hau yin sa babu kakkautawa, wato a duniya ana so ka zama na gari, kada ka cuci mutane, idan ba haka ba tun a duniya zaka ga sakamako, gashi dai yanzu rayuwa ta juya wa Hajiya Mero, a lokacin da take tunanin tana cikin jin dadin rayuwar. Haka ta cigaba da jinya kafar na sake rubube, da k'yar Alhaji Faruku ya zo data matsa masa da kira, sosai ya girgiza da yadda ya ganta, be yi tunanin abin nata ya kai haka ba, a take ya dauke ta ya kaita asibiti sai dai suna zuwa likita ya duba kafar ta yace lallai sai dai a yanke, dukka biyun sun lalace ba zata sake taka su ba har a bada, kuka ta dinga yi tana kiran sunan Ummi akan ta yafe mata, duk wanda yazo wucewa sai ta bashi tausayi yadda take kuka kamar ranta zai bar jikin ta. Rayuwa kenan *SAUYIN KADDARA* *56* ©Hafsat Rano **** *Bayan Wasu shekaru* Abubuwa dayawa sun faru ciki har da mutuwar Hajiya Mero bayan tasha jinya, a lokacin ne Ummi ta dauko Zainab tace zata rike ta ai d'a na kowa ne, Arab yaso ya hana amma sai ya kyale ganin shi ne kaɗai baya goyon baya. Wani zuwan Mustapha Kano abokin Arab bayan ya koma Sokoto da aiki suka hadu da Zainab ɗin a gidan taje kai wa Lubna sakon Ummi, tun daga lokacin yace ya ga mata, duk da Arab be so ba amma haka ya hakura, akayi auren Zainab da Mustapha, aka kai ta Sokoto. Rayuwa ta cigaba da tafiya yadda ya kamata, kowa ya samu abinda yake so. Salim ma yayi aure da dadewa suna nan yadda suke da Arkel babu abinda ya chanja na daga amintar su. A chan Mali ma Bongel ta hakura da komai ta samu mijin ta daidai da ita da tsarin rayuwar su, gaba daya suka je bikin aka sha shagali da irin al'adar yan garin. *** Tana zaune a falo tana duba kayan da sukayi order a shagon su Habubu ya turo kofa ya shigo dauke da Aman a kafadarshi, kallon su tayi ta cigaba da abin da takeyi, shi din ma be yi mata magana ba yasan idan tana aiki bata son hayaniya, yana zama  suka ta jiyo ihun su a compound din gidan, da sauri ta daga curtains din falon ta hango su suna sauke kayan su daga mota, kallon shi tayi yayi saurin kama kunnen sa yana dariya "Wallahi Umma ce tace a dawo dasu, sun ishe ta kuma, wai a kaiwa Ummi su." "Amma dan Allah ba kaga aiki nake ba, sai kawai ka kawo su ai da ka kai su gidan Ummin." "Ita ma tace bata so." Dafe kanta tayi ta cire glass din idon ta ta hau tattare kayan aikin mata tana cewa "Sai ka zauna dasu anan bari na hau sama, kace musu ina bacci kar wanda ya tashe ni wallahi." Dariyar sa ya kunshe har tayi gaba ta tsaya tace "Kajin naku nawa ne ma umma tace sun mutu?" "Guda hamsin ne saboda ruwan da akayi." "Owk sai a zuba wasu, a madadin su, so nake umma wannan karon ta fitar da kamar guda 500 haka.' "Allah yasa babbar yaya." A guje suka shigo su uku duk maza sai Inas da Iman dake take musu baya, dafe kanta tayi ta harari Habubu dake dariya ta fasa shiga dakin ta dawo tsakiyar falon "Maaamaa mun dawo." Suka hada baki a tare, "Na ganku, sannun ku, a wuce daki a cire kaya sannan bana son gagara kuje compound kuyi wasa." Ihu sukayi mazan suka shige dakin su matan ma, Hudah na zaune tana karatu suka fado dakin a guje, hararar su tayi ta tashi ta bar musu dakin dan tasan yanzu zasu hargitsa gidan, ita kuma a rayuwar ta bata son hayaniya ko kadan. Mazan biyu twins din Lubna da Arab ne amma kusan rabi da kwatar rayuwar su a gidan Arkel sukeyin ta, ko yaushe suna tare da Taufiq sai suka tashi kamar yan uku duk da sun dan girme shi da kadan. Bayan Taufiq Maryam ta haifi Iman da Inas sannan Aman, yanzu haka Lubna cike ne da ita tsoho haihuwa ko yau ko gobe, tun bayan twins bata sake ba sai yanzu da ake sa ran ta haifo musu Bby girl. *** Ruwan sama ake zugawa kamar da bakin kwarya, kwance take akan chest ɗin sa a hankali suke hira kasa kasa wadda duk yawanci akan rayuwar su ce, yanayin yayi musu dadi dukka su biyu, hakan ya haifar musu da wani yanayi na shaukin juna, iska ce take busawa kadan kadan hade da kamshin kasa, lumshe idon ta tayi ta sake bude so a hankali ta lalubo hannun sa ta saka a cikin nata ta damƙe shi kam tana sake shigewa jikinshi, be hanata ba sai ma kara matsowa da yayi, a kunne ya rada mata "You Are the best wife in the whole world." "And you are the best husband to." "Allah ya barmu tare." "Amin my wife, my everything." Bacci me cike da ni'ima wanda suka dade basu taba yin irin sa ba ne ya dauke su kowanne su da tsananin so da kaunar abokin rayuwar sa a ransa. Alhamdulillah ana na kawo karshen wannan littafin nawa, Nagode kwarai da kaunar da kuka nuna min, Allah ya saka wa kowa da Alkhairi ya haskaka wa kowa rayuwar sa, Allah ya sa mu gama da duniya lafiya. Wanda na bata wa da sani na ko bisa rashin sani yayi hakuri ya yafe min dan Allah. Nagode Nagode kwarai da gaske, domin dai ku ɗin masoya ne na kwarai. ZAFAFA BIYAR na godia bisa halaccin ku karemu. Anan ne kuma nake so nayi amfani da damar nan wajen tallata muku bussiness din mu na Longrich, bussiness ne da ya kamata ace duk wata mace ta yi, zama haka kawai bashi da amfani, yadda muke amfani da wayoyin hannun mu ko da yaushe ya kamata ace mun koyi sana'a da su muna samun wani abu ba wai karatun Novel kawai ko chatting da kallon status ba. Duk wadda ta san ta shirya tana son ta shigo a dama da ita tayi min magana da number ta 08030811300. Sauran bayanin mu hadu ta pc. Nagode Nagode Nagode Rano🚴🚴🚴🚴 *** _ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU😁._ *ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma *SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano) *KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo) *BURI ƊAYA!* (Mamu gee) *WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull) 👇🏻karku bari ayi babuku *ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu* *za'a tura kudin ta wannan accnt number din* Hafsat kabir umar 0225878823 GT bank Saika tura shaidar biya ga wannan number ta WhatsApp 08030811300 Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din 07067124863 Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya. *Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon Rano🚴🚴🚴 *** ********************** ⬇ ************************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ **************************