********************** ⬇ ************************** ********** Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** [12/6, 10:15 AM] First Lady🌹: 🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻 🙆🏻🙆🏻 🙆🏻 *ILAR YAR AIKI* *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *Following us as* -------- *like us page* Fb.me/Zamaniwritersassociation ----- *check us blogger* Zamaniwriters.blogspot.com ----- *email us your comment and reports* Zamaniwritersassociation@Gmail.com ----- *da sunan Allah mai rahma mai jin kai, kudkan yabo ya tabbata, ga fiyayyen halitta, daya bani ikon rubuta wannan NOVEL din* *page 1* Falone yasha kaya, naira tayi kuka, wata matashiyar matace, azaune daga cikin kujerun alfarma, rumot ne ahannun ta, tana canza tasha, magana tafara cikin, isah. " uwani!!!." Wata gajeriyar budur wace tafuto daga kicin tazo kusa da ita ta tsugunna.wani kallo take binta dashi, ahankali tafara magana. " kin gama girki." Ee nagama komai har dakin oga nagama gyarawa." Yar aikin ce take fada cikin rawar murya. " to Kaza kije ki karasa aikin ki saura, in affan yadawo ki 'kizuwa kiyi masa abinda, aka saba yimasa, sai naita 'ba'batu, tashi kibani waje." Uwani da sauri tabar gun, kicin taje tagama abunda zatayi cikin sauri. Har yanzu mata shiyar nan bata motsaba daga inda take, saidai yanzu chati take, karar mota tajiyo alamun anshigo gidan, murmushi tayi tasan affan ne yadawo. Matashin saurayine yashigo cikin fara. " hello byba yakike." Dago kai tayi tamasa mur mushi. " sannu da zuwa, daer ya office." Zama yayi akan kujera yace. " sumul wallahi nagaji yau dayawa." Hankalinta yana kan chat gaba daya ahaka take magana." Ai naga alama bara waccan yarinyar tazo." Rufe bakinta keda huya, sai ga uwani ta futo daga kicin dauke da cup da ruwan roba mai sanyi, tsugunnawa tayi agabansa. " sannu da zuwa oga." Wani kallo yake mata, yana murmushi. Zuba masa ruwan tayi, tabashi takalmi sau ciki tafara cire masa, sannan ta dau jakar sa da ta kalmin ta nufi dakinsa. " ke uwani inkin ajiye kayan, kihada masa ruwan wanka, kifuto masa da kayan daze saka, saura kiyi shiririta." Ciki ta Karasa ta fara futo masa da kayan sannan tamai da jakar inda take, tahuce bandaki domin hada masa ruwan wanka. ************* "Byba bara inje in fara wankan." Affan ne me wannan maganar. Ko 'kala bata ceba, shidai yahuce cikin dakinsa, yana shiga yahuce ban dakin, uwani tajuya baya tana zuba masa, abun 'kamshin wanka, hannu yasa ya ruko 'kugunta ya ringume ta tabaya, magana yake mata a kunne." Tawan ya aiki danna san kina Sha aiki, amma tare zamuyi wankan ko." " sokake sai anty ta gane." Uwanice mai wannan maganar. Cikin shauki affan yace. " bazata ganeba, kinsanta bawani kula take daniba." Tare sukayi wankan suna wasanni, da juna futowa sukayi suna murmushi, rungumo ta yayi suka fada kan gado, hannu yasa yacire tahul din, wasanni sukeyi da juna, ahaka aka tafi babban aji dan daukar darasi. [12/6, 10:15 AM] First Lady🌹: 🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻 🙆🏻🙆🏻 🙆🏻 *ILLAR YAR AIKI* *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *following us as* ---------- *Like us page* Fb.me/Zamaniwritersassociation ----- *check us blogger* Zamaniwriters.blogspot.com ------ *email us you comment and reports* Zamaniwritersassociotion@email.com *✍🏻by:shaxee* *Page 2* Sai da suka gama sukayi wanka, shiyafara, futowa yazo fallo, tanan inda yabar ta, amma yanzu waya take, zama yayi akusa da ita. " byba tunda nasa uwani aiki, muje kizuban abinci naci wallahi hunwa, nakeji( badole aji hunwa ba ansha aiki🤓) '" kabari tagama yin aikin, tazo tazuba mana, wallahi duk Gajiye nake." Najwa ce mai wannan maganar cikin, shagwa'ba. 'kala bai kuma cemata ba, uwanice ta futo daga dakinsa, tayi tsuru tsuru, Abunka da mara gaskiya. " kihuce kije kizuba mana abinci, kin wani tsaya kina sinne kai." Najwace mai wannan maganar cikin isa. Tebirin cin abunci taje ta zuzzuba musu tazuba musu lemo, affan sai satar kallonta, yake gata ba tsarin sa bace ita saboda baya son gajerar mace, amma yarasa yadda akayi yake biye mata." Katashi muje muci abincin kace hunwa kakeji, kuma la tsaya tunani." Najwace takatse mata dan guntun tunanin sa. Tasowa yayi sukaje suka zauna, abinci suka baci, ita kuma uwani tayi dakin ta, waya ta dakko takira wata nomber, hello hafsa aikin mai 'kwaran gwal fa yanaci, allah kuwa, kedai bari gobe ma zanzo muje, yayimin na yadda za ayi, ya aureni dan bazan zauna cikin bauta, ba wallahi, nima saina shiga arzikin naji yadda suke ji." Banji mai akace adaya ban garenba." To kijirani karfe 2:00 nasan duk sun futa, sai nazo muje, to sai nazo." Wayar ta kashe ta kwanta, tana saka mugun abu aranta. Dare yana yi misalin karfe 9:00 uwani kwance, tana barci. Najwa ce ta tashigo dakin, uwani, kallonta tayi, sai munshari take, d'aka mata duka tayi." Kedan ubanki baki gama aikin kiba zaki kwanta barci, kin hadawa, affan ruwan wanka ne, maza tashi ki'bacemib daga gani." Najwa mai wannan maganar, cikin fad'a da har gagi. Uwani tashi tayi cikin 'bacin rai." Zaki gane bakida da wayo, wallahi saina gasa miki aya a tafin hannu." Azuciyar ta take wannan zancan, dakin affan ta shiga, bakowa aciki bandaki tahuce dan ta hada masa ruwan wanka. Adakin najwa kuma, affan ne a gefan gado najwa kuma akan gadon, affan ne yake magana, cikin lalla'bawa." Haba najwa yazakice haka, kinsan keka d'ai ce matata inbakeba, gun wazanje da bukatata." " nifa affan wallahi banaso, ace aita abu daya kamar wasu yan iska." Najwa ce mai wannan maganar, cikin alamun 'kosawa. Cigaba dacewa tai." Kaje kicin zaka sami lemon tsami da kanwa, ka jika kasha zakaji daidai." Cikin fusata affan ya tashi ya fuce daga d'akin, dakinsa tahuce, yana shiga ita kuma,uwani tazo futa run gumeta yayi." haba tawan sokike kitafi kibarni, ni kadai bazaki tayani kwana ba." " ina anty ba ita zata zo kukwana tareba." Uwanice mai wannan maga nar. Ya tsina fuska affan yayi." Rabu da ita race bazata zoba, shiyasa nakeso kimaye gurbinta." "aikwa zan maye gurbinta nan bada dadewa ba." Azuciyar ta take wannan maga nar. Tundaga bakin kofa suka fara aikawa da juna sa kwanni, kan gado suka koma, uwani ta rikitashi sosai, jiyake dama najwa ce daya more.... [12/6, 10:15 AM] First Lady🌹: 🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻 🙆🏻🙆🏻 🙆🏻 *YAR AIKIN GIDANA* *nacanza sunan novel din daga ilar yar aiki zuwa yar aikin gidana* *ZAMANI WEITERS ASSOCIATION* *following us as:* ------- *Like us page* Fb.me/ Zamaniwritersassociation ----- *Check us Blogger* Zamaniwriters.blogspot.com ------- *Email us your comment and Reports* Zamaniwritersassociation@gmail.com *✍🏻by:shaxeee..* *page 3* Asuba tanayi uwani tabar dakin, takoma nata. Misalin karfe bakwai da rabi, uwani ta tashi tafara gyara gidan, sannan ta dafa musu shayi ta soya kwai, sai cake data debo musu, tajera akan tebur, kasan cewar basa cin abinci da yawa wai karsuyi kiba. Tana gamawa ta koma dakinta, affan yana tashi yayi wanka ya shirya ya futo, kai tsaye tebur ya nufa, zubawa yayi yanaci najwa ce ta futo daga d'akinta cikin shirin futa aiki." Dear har ka tashi, good morng" "Mornig" kawai yacemata yacigaba da cin abincinasa. "Yauwa dear in natashi daga aiki zan biya gidan samira kawata na dade ban jeba." " ok badamuwa kice ina gaisheta." Atare suka gama suka futa kowa ya hau motar sa yayi hanyar sa. Suna futa uwani ta gyara dakunan su, tayi wanka ta futo sai gidan hafsa kawar ta. ********** "Shegiya uwani wallahi kina sha a ninki, jibi yadda kikayi bul 'bul dake, konima dena barikin nan zanyi, infasa aiki gidan wani hamsha 'kin mai kudi, in aureshi" hafsa ce mai wannan maga nar. Yatsina fuska uwani tayi tace." Amma aizaki sha huyar aiki, inkin ga na huta to wannan shegiyar matar ta futa, son jikinta yayi mata yawa, kin tashi ni muje, kinsan da nisa gun kuma inaso in koma da huri." Tashi hafsa tayi tadau wani yalolon mayafi." Muje ai nagama shiryawa dama kenake jira." Motar hafsa suka shiga suka dau hanyar wani 'kauye. *********** Wani gidan kasa suka shiga, daki dayane agidan, sai ban d'aki, d'akin suka shiga, wani 'kwaran gwal ne arataye, shiyasa ake cemasa mai 'kwaran gwal. Wani bakin mutun ne azaune, akan buzu, sai hura hanci yake, magana yake murya ba dad'in ji." Nasan abinda yake tafe daku, bu'katar ki zata biya, indai zakiyi yadda akeso, ungo wannan wani 'karamin kwaran gwal ya bata, ki ajiyeshi a kwabarki kindai ya fad'i ya fashe to komai zai ruguje, domin shine ruhin affan, sai yadda kikeso zakiyi dashi." Wani irin surutai yake tare da bade shi da wani ruwa mai yauki, yana gamawa yabata." Kudin aiki ki fanshi kanki." Murmushi uwani tayi domin tasan me yake nufi, hafsa ce ta futa ta basu guri. Suna gamawa ta futo tasami hafsa acikin mota. " sannu naga kinji jiki sai d'in gisawa kike." Hafsace mai magana cikin dariya. " kedai bari yadda kikasan yasami tunkuzar 'kuli 'kuli ko tausayi na beba, nidai muje duk nagaji." Motar ta kunna duka dau hanya. ******** Najwa na tashi daga aiki gidan samira ta huce, a falo ta ganta tayi ta gumi alamun tana cikin matsala." Lafiya samira naga kin canza gaba daya, mai yake damunki." Najwa ce mai fad'a cikin damuwa. Cikin nuna damuwa datake damunta, samira tafara magana. " kedai bari ina cikin tashin han kali, najwa kokinsan cewa *yar aikin gidana* cikine da ita, kuma cikin na mijinane." A zabure najwa ta tashi magana take cikin rawar murya." Tayaya hakan ta faru, kekuma kina inah." " ina gidannan yadda akayi shine wata rana..... *😉fans naga kun gaji bara in barku gobe na fada muku yadda akayi.* [12/6, 10:15 AM] First Lady🌹: 🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻 🙆🏻🙆🏻 🙆🏻 *YAR AIKIN GIDANA* *ZAMANI WRITERS ASSOCIATOIN* *folowing us as:* ------ Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION ------ *check us blogger* Zamaniwriters.blogspot.com ------ *email us your comment and reports* Zamaniwritersassociation@Gmail.com *shaxeee..✍🏻* *page 4* "wata rana salman yazo yace anturasu wani aiki 'kasar waje, zaiyi sati biyu, inshirya muje nikuma saboda aikina nace bazaniba, daya nunamin yana 'bukatar mai temaka masa, sainace yatafi da *yar aikin gidana* asabe domin yarinyar akwai hankali ga addini, ransa ya'baci kawai yaje yagaya wa mahai fiyarsa, dama basa sona saboda rashin mutuncin danake musu, itama taji haushi kawai iyayan sa suka tsaya masa ahar aka je garinsu asabe aka nema masa aurenta, iyayen suka bashi ita, a cikin kwana hudu akayi komai harda d'aurin aure, ni ina nan gaho, suka tafi da ita inata murna ya amshi shawara ta, tunda suka tafi bana samun wayar sa, shima kuma bekira niba saida sukayi wata hudu tukun suka dawo, dawowar data gir gizani, naga asabe ta goge tazama wata babbar mace, sai kuma naga ciki yad'an futo zan matso kusa da ita in tambayeta,salman ya tsaida ni yake cemin. "kar ki matso kusa da ita, domin ahalin yanzu matsayinku daya aguna ke harma tafiki matsayi wallahi." Na gir giza sosai daskare wa nayi agun, sai kan warsa tamatso kusa dani tana tana murmushi take bani labarin duk yadda akayi, tundaga ranar yan uwansa suke layi zuwa dubata, har mahai fiyarsa shima sai rawar kai yake, tun sannan nayi na damar shan maganin hana daukar ciki, gashi har yamin illah, yazu inta 'kai cemiki bama sa garin tunda cikin yayi wata shida, aka tafi da ita saudiya, wai acan zata karasa rainon cikin kuma ta haihu, kinji halin danake ciki." Iska najwa ta furzar daga bakinta, magana tafa cikin jimami." Tabbas kin ga tashin hankali, kuma kina cikinsa, amma gani ga wane ya ishi wane tsoron allah, nima ayau dinnan zanwa tufkar hanci, korar uwani zanyi in kawo tsohuwa, hankalina kwance. ( 😁kunjita bata san uwani tarigata yiwa tufkar hanciba harda baki) bara inyi sauri in koma gida wallahi." " gaskiya kam kema kar amiki irin nawa, koma fiye sa hakan." Samira ke wannan maganar cikin zubda kwalla. Tuni najwa ta futo tashiga mota ta nata huta, gudu kawai take tana tunani a ranta. *********** Uwani har ankoma gida an gasa jiki, tayi girki ta gama, dakin affan ta huce wani garin magani ta dakko tuna wa tayi sanda boka yagama gurzarta, yabata shi yace ta zuba inda affan zai taka, kuma ta kula dawannan 'kwaran gwal din, indai yafadi yafashe to komai zai war gaje. Barbada tayi akofar bandaki, tafuce ta koma d'akinta. Affan yariga najwa dawowa domin jinsa yake wani iri yarasa mai yake damunsa, yana shigowa falon ya huce dakinsa shirin wanka yayi koyaji dadin jikinsa, yana taka kofar ban d'akin yaji wani abu kamar huta ta jashi, uwani ce kawai take masa gizo, daga shi sai tahul ya futo, ita kuma ta futo taduba shi domin taji shigowar shi, yana ganin ta yaje kusa da ita, dan allah uwani zaki aureni, wallahi ina sonki. Najwa ce tashigo falon mezata gani, affan daga shi sai tahul uwani kuma kananun kaya. " kan uban can yau Za ayita agidannan, wallahi sai kinci ubanki... *koya zata kaya*🤔 [12/6, 10:15 AM] First Lady🌹: 🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻 🙆🏻🙆🏻 🙆🏻 *YAR AIKIN GIDANA* *ZAMANI WRITERS ASSOCIATOIN* *following us as:* -------- Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION -------- *check us bloggt* zamaniwriters.blogspot.com ------- *email us your comment and reports* Zamaniwritersassociation@email.com *shaxeee...✍🏻* *page 5* " kuma wallahi yau zaki bar gidannan, shegiya algunguma dama abinda kukemin kenan in bana gidan." Najwace mai wannan nasifar. Cikin hargagi affan yake cewa." Saidai kekibar gidan, dan uwani aurenta zanyi, kuma wallahi kika ta'bata saina illataki." Das karewa najwa tayi, mai yake shirin faruwa da ita kodai itana irin ta samira za ayi mata, " nashiga uku ni najwa yau ni affan yake cewa zai sakeni akan *yar aikin gidana* wayyo allah na." Uwa ni kuwa dakinta ta koma tadinga rawa tana waka, bu'katar ta tabiya, "yanzu gobe zan koma garinmu in gayawa su inna, dama ita inna indai da kudi to angama, baba kuwa dama inna ta shanyeshi yazama mijin tace, shikenan bani da ma tsala." Uwani ta kwashe da dariya, "wallahi sai na tsula tsiyata agidannan." Najwa fashewa dakuka tayi, affan kuwa ya huce dakinsa yabarta anan tana kuka, ganin bashine mafutaba yasa ta tashi ta koma daki, sai zagaya dakin take, yazu mai mafuta yazanyi wajan ganin affan yajanye 'ku dirinsa na auren uwani, anya kuwa lafiyarsa kalau. Affan yana komawa daki wanka yayi ya shirya yafuto, motarsa ya hau ya tafi gidan su dole ne a aura masa uwani, indai anason Zaman lafiyar kowa. Najwa tana jin affan yafuce ta futo, dakin uwani ta huce tasameta akan gado tana danna waya. Cikin fad'a najwa tace." To yar matsiyata dangin mayu mai kika bawa affan, nasan dai lafiyar sa kalau bazai ce zai aurekiba, wallahi kiyi gaggawar futa daga harkarsa in ba haka ba kuma, saikin yi nadama." Ko tsayawa ta saurari uwani bata yiba, ta futo ta dauki motarta, kai tsaye gidan kawarta maryam ta huce dama su ukune suke amintarau. Tana zuwa gidan mai gadi yabude mata kofa ta shiga, falon gidan ta shiga bakowa, shiyasa ta huce dakin ta, maryam tana zaune abakin gado tana share hawaye. Zama najwa tayi kusa da ita, "kardai kema *yar aikin gidanki* ta 'kun ta ta miki, nima haka tayimin munshiga uku, yanzu yazamuyi." Cikin tashin hankali maryam tace." Metayi miki kema kaddai kema tasaki a tashin hankali, nima tamin abinda har na mutu bazan mantaba, najwa gayamun mai ta miki, samira ta gayan nata awaya d'azu." Najwa ta bata labarin duk abunda yafaru da ita, har i 'kirarin auren uwani da affan yace zaiyi. Murmushin ba'kin ciki maryam tayi." Wallahi wallahi duk naku sharar fagene ni nafiku shiga ba'kin ciki da tashin hankali, domin ni har ciwon zuciya ne ya kamani lokaci guda, kokin sa cewa *yar aikin gidana* yau sati daya da d'aura mata aure da baba na..... *fans naga kuna jin 'kishirwa, kuje kusha kudawo muji ita kuma taya yar aikin gidanta ta auri babanta* *😅😅ammafa kuyi sauri kudawo konan da gobene muji labarinta* [12/6, 10:15 AM] First Lady🌹: 🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻. 🙆🏻🙆🏻 🙆🏻 *YAR AIKIN GIDANA* *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *following us as:* ---------- Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION ------- *check us blogger* Zamaniwriters.blogspot.com -------- *email us your comment and reports* Zamaniwritersassociation *whatsapp me 09020334118* *✍🏻shaxeee..* *page 6* "Tayaya haka tafaru ." Najwa tafada cikin furgici. Cigaba da magana maryam tayi." Tana yimin aiki, wata rana kuma in yar aikin umman mu bata nan ko bata da lafiya, sai tamin waya intura ta, ashe sun 'kulla muguwar harka da baba na, harta kaisu ga ya aureta, sai bayan and'aura muka sani, umma na data sameshi tace masa ita bataji komai ba akan ya 'kara aure tafi jin damuwar rashin gaya mata da baiyiba, nanfa yahau bambamin fada, ya zageta tas bayan ta tare kuma, suke mata hula'kanci kala - kala, tana jurewa rannan tana kan sallaya tana lazimi kawai yashigo yabata takaddar saki, ana gayan zuciyata ta buga, nayanke jiki nafad'i aka kaini asibiti, sati na biyu sannan aka sallameni, yanzu addu a kawai muke masa, domin munsan ba 'kalau yakeba akwai abinda tayimasa." Tashi najwa tayi tace. " duk mu muka jawa kanmu, baza muyi aikiba wai saidai *yar aikin gidana* tayi maka, kuma mun sakar musu komai na mijinmu, bara inkoma gida nasan nima ba'kin cikine zaiyi ajalina." Futa kawai tayi tana hawaye, mota tashiga ta fuce gidan ta ta koma, d'akin uwani ta duba taga ba ta nan, kuma ta kwashe komai nata, murna take shikenan komai ya 'kare tunda ta tafi, dakinta ta huce kawai. Affan yana zuwa gidansu yasami iyayen nasa a falo azaune, affan dan gidan alhj kabiru umman sa kuma hjy ramatu, yayan su biyu, affan sai aesha, sun basu tarbiya daidai gwar gwado. Tsugunnawa yayi yagaishesu. Abba ne yafara magana cikin kulawa." Affan naga kamar da maga na abakinka." Sun kuyar dakai affan yayi yafara magana." Abba dama aure nakeso in kara, kuma iyayen yarin yar sunce inturo iyaye na, shine nazo in gaya muku." Tunani abba yatafi." To mai yasa affan zai kara aure, aiya saninsa yasan suna zaune lafiya da matarsa najwa yar amininsa, kuma ba auren dole aka yimusu ba, amma bazai hana shiba tayu yana bu'katar hakan." Duk azuciya abba yake wannan maga nar. " bada muwa affan gobe zan gaya wa su nasiru sai suje sutam bayo maka." Yana 'karashe maganar yana kallon affan d'in ganinsa yayi a furgice ba kamar daba. Umma kuma bata ce komai ba, sai fatan alheri da ta yi masa, tunda batasan dalilin sa na 'kara aureba, dan tasan ra ayinsa na mata d'aya. Tashi affan yayi yamusu sallama ya fuce, ko aesha bai tambataba, kuma sunsan indai yazo bai gantaba sai ya tambayeta, saboda sha 'kuwar dake tsaka ninsu. " anya alhj affan kuwa ba yadda nasaba ganin sa bane, duk ya furgice ya ma canza gaba d'aya ko dan wasan nan dayake mana, kamar kakanninsa, yau beba." Ummace take wannan maganar cikin damuwa. " nima na kula, kuma naga 'kwayar idonsa ta canza kala, duk yadda akayi akwai matsala, amma muci gaba da addu a kawai." Abbane yayi wannan maga nar. ************* Affan ne yake tafiya amota zai koma gida, wayar sace tayi 'kara yana dubawa yaga sunan uwani. " hello byba na ganina nakusa 'kara sowa gida, inganki dama gun su abba naje nagaya musu, sutura gidan ku gobe, kuma sun amince." Saida uwani tagama sauraran sa tukun tafara magana. " kai amma naji dad'i wallahi, ai yanzu bana gidanka ina gidana, nafiso inzo amatsayin mayarka kwanannan, dama kasan gidanmu ko." " ok kar ki damu hakan ma yayi, yanzu sonake suje subada harda sadaki nan da sati d'aya ad'aura auren." Affan ne yake maganar cikin kulawa. " to shikenan bara inbarka haka sai kazo." Kashe wayar uwani tayi ga bikin zuwa amma zanin d'aurawa yana nema ya gagareta. " uwani ga abincin kici tunda kikazo bakici komai ba, sai buge bugen waya kike, natura asiyo miki lemon kwalba." Inna ce mai wannan zubar. Ya tsina fuska uwani tayi tace. " barshi inna yanzu nakira hafsa zatazo mutattauna wata magana, intazo maci tare, kisama a 'karo lemon." " to uwani ta mace tamkar da dubu, kinga inkika auri alhj nan kaka ta ta yanke sa'ka, gidan ki zankoma inci dadi wallahi mushana abinmu, muma muyi gayu mushiga mota mu je babban wajen nan me uwa garinaka muma muyi siyayya, harda abinnan maisanyi mai kalar gaji mare wanda za asaka cokali mai kyau dad'i ( tana nufin ice cream😁) kinga nima na zama hajiya, dama ance haihuwa maidad'i, Kum....." " haba innah sai zuba kike kidinga had'iyar yahu mana, saikace wadda ta 'kone Akaka." Uwanice take wannan maganar. Sallamar hafsa uwani taji. " yauwa inna jeki dan Allah kuma kar kizo gunnan harsai nakiraki, dannasanki da ro'ko yanzu zaki bani kunya agun 'kawata." Uwanice maifad'a tanayi tana tura innar waje. Hafsa ce ta 'karasa shigowa d'akin, wata tsohuwar kujera tasamu tazauna akai duk sun yayyage sun kode. Magana hafsa take cikin 'karewa fata kakken dakin kallo. " uwani wannan kiran gaggawa haka, duk kinsani wani tunani kodai affan din yafasa ne." " kedai bari hafsa ina cikin wani tashin hankali ne, kokinsan inada ciki wata d'aya da sati d'aya."uwanice mai wannan maganar " wane irin ciki uwani kaddai kice min wai cikine yanzu ajikinki kuma na haihuwa." Hafsace mai wannan maga nar. Uwani ce ta fara magana. " kedai bari kuma kin san cikin na waye." Wani kallo hafsat tayi mata. " taya Zan sani uwani kamar wata allan musuru, nidai kigayan nawaye kuma mune mo mafuta, yanzu dan kinsan bazaki je gidan affan da cikiba, ko gwara ma kisani, kodai cikin affan ne. " a a bana sabane shida sau biyar muka kasan ce tare dashi, kuma duk acikin satinnan ne fa, nidai kimin alkawarin cewa inkin ji cikin konawaye bazakiji haushi naba." " namiki alkawari uwani, ai ni dake bata 'baci." Inji hafsa kenan. " cikin *anas* ne ( anas saurayin hafsa ne tana matu'kar sonsa) kuma wallahi sanda nazo gida ba'kya nan shikuma yana cikin wani hali, shine natemake ki nabashi kaina, to duk sanda ba'kyanan sai ya kirani in temaka masa, amma kiyi hakuri balefi na bane." Murmushin ya'ke hafsat tayi, acikin zuciyar ta take magana. " uwani kin d'auka bansan cin amanar dakikaminba, nasani kuma wallahi saina d'auki fansa akanki saina 'kuntata miki na 'bata miki farin ki, na ga auren affan shine farin cikinki ko, to kwa zaki gane baki da wayo, bari zanyi sai kin yi sati d'aya agidan sa sai in....... *I love u ol my fans*💋 *ina godiya da yadda kuke min fatan alheri Allah yabar mu tare* *quee kema ina jinjina miki da yadda kike kokarin nisha d'antar damu da NOVEL dinki na ILLAR BASHI. Allah ya 'kara basira.* [12/6, 10:15 AM] First Lady🌹: 🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻 🙆🏻🙆🏻 🙆🏻 *YAR AIKIN GIDANA* *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *following us as:* ------- Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION --------- *check us blogger* Zamaniwriters.blogspot.com ------- *email us your comment and reports* Zamaniwritersassociation *whatsapp me 09020334118* *✍🏻shaxeee..* *page 7* Uwanice ta katse mata tunaninta. " hafsat yanaga kinyi shiru kodai kinji haushi ne, ai na gaya miki ba lefi na bane, shine ya takuramin har na amince." Wani malalacin murmushi hafsa tayi. " karki kidamu, ai ni dake bata 'baci, nayafe miki komai yanzu abinda za ayi tashi muje azubar dashi, kowa yahuta." Inji hafsat kenan. " yauwa 'kawata ai nasan ki da mutunci, shiyasa banji shakkar gaya mikiba." Shiryawa uwani tayi suka tafi,wani karamin asibiti sukaje dama hafsa tasan likitan nan danan aka zubar da cikin, uwani tasha huya, suna dawowa gidan su uwani, inna ta kalli uwani, anan ta gane mai yake faruwa. " sannu uwani dama wannan ce matsalar, amma kika 'ki gayamin, da tare zamuje ayi komai agabana, bara inje indafa miki ruwan wanka ki gaggasa jikinki." Inji inna kenan sarkin surutu. Ruwan zafi tadora, yana dahuwa ta juyeshi a 'katuwar roba, takai band'akin temaka wa uwani tayi ta gasa jikinta, aikwa taji dad'in jikinta, hafsat tamusu sallama ta tafi tana saka mugun abu aranta. Uwani subiyu iyayansu suka haifa musa sai ita, inna itace ta haifesu, inna ta kasance yar duniya ita indai da kud'i to kome kakeso zata yimaka, kuma ta shanye baban su uwani wato malam hadi, sai abinda tace yakeyi, shiyasa ta tura uwani aikatau dan tasamomata kud'i, wannan kenan. ************** Washe gari iyayen affan sunzo sunkawo komai da komai, na harkar aure, sunkoma sun gayawa abban affan antsaida ranar biki sati daya, kamar yadda affan ya bu'kata, haka kawai abban affan yaji bai yadda da aurenba amma zai bincika. Zaman doya da manja affan suke da najwa, ko inda take baya kalla, tayi duk iya 'ko'karinta amma abin yaci tura. Najwa tana zaune afalo tana tunani, affan yashigo yawatsa mata katina na biki, ya fuce warsa. Bud'e wa tayi ta karanta, wayyo zokuga tadda najwa takusa haukacewa, tarasa inda zata saka tunaninta. Shirye shirye biki kawai ake, ango ya kacame, amarya sai gyara akeyi. Yau aka daura auren uwani da affan, yayin dawani maroki king boy😉yaketa zuba kiri, ana masa likin kud'i. Dayamma akaje aka d'akko amarya ita da 'kawayenta. Najwa duk ta rame ta bushe tana d'aki tana jiyo haya niyarsu. An rako ango d'akin amaryarsa sai washe baki yake.asuba ta gari. ************* Safiya nayi najwa tahau gyara gidan dama yanzu ita take abinta. Kicin ta shiga ta dafa shayi ta soya kwai. D'akinta ta huce tana karyawa. Basu futoba sai karfe 11:00 na safe, jerowa sukayi atare suka futo, karewa falon kallo uwani tayi. " jeka kiramin najwa." Uwanice mai fada cikin ta 'kama. Zuwa yayi d'akinta yakirata, biyoshi tayi suka tawo tare. " wato najwa sai angaya miki abu zakiyi, ke da 'ki'kiyar inace dabazaki dafa mana abin kariba, ko da kaina kikeso indafa, tobara kiji daga yau kezaki dinga yin komai agidannan, girki safe da rana da dare, kuma kiyi maza ki huce kicin kid'ora abin kari, in ba hakaba yanzu insa ayan kar miki tiket." Cikin masifa uwani ke wannan maganar. 'dago kai najwa tayi ta kalli affan, gaba d'aya hanka linsa yana kan tibi. Tashi tAyi tahuce kicin din tadora musu abu mai saiki. Cikin zuciyar ta uwani take magana. " zaku gane bakuda wayo daga ke harshi affan din, saina cuz guna muku, yanzu ma ban fara komaiba, saikun yi nadamar sanina a rayuwarku, shashashai kawai...... [12/6, 10:15 AM] First Lady🌹: 🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻 🙆🏻🙆🏻 🙆🏻 *'YAR AIKIN GIDANA* *wannan shafin nakune ya kungiyar zamani kuna huta ina binku da gas Allah ya kara zakin hannu* *following us as:* ------- fb.me/ZAMANIWRITESASSOCIATION ---------- *check us blongger* Zamaniwriters.com ------- *email us your comments and repots* Zamaniwritesassociaton@email.com *whatsapp me 09020334118* *✍🏻shaxeee* *page 9* " dan rashin mutunci shine ina kiranka, kamin bansa saboda hula 'kanci." Cikin ban ha'kuri affan yace. " wallahi banjiba saboda tv a kunne take, amma dan Allah kiyi ha'kuri." Cikin isa uwani tace. " maza cire kayanka kamin tausa har inyi barci, kuma saura in kaga nayi barci ka fice yawon banzar ka." Cikin sauri affan yacire kayansa daga shi sai singileti, da gajeran wando, kallonsa uwani tayi ta kwashe da dariya. " haba affan kamar kai kanada kudi amma ace gajeran wandonka, robar tasaki jibi sai wani jansa sama kake, Allah ya shiryeka inka futa aganka fes da kai nankwa basu saniba cikin, ba magana, nizo kamin tausa ta." Cikin dariya uwani ke wannan maganar. Tausa yake yimata hartayi barci, baidenaba saida yaga tayi nisa tukun yakoma falo, alwala yayi domin anfara kiran sallar magariba. Saida akayi sallar isha tukun uwani ta tashi, ba magariba balle isha, falo tafuto inda ta tarar da najwa na jere abinci. " kinyiwa kanki 'kiyamillaili da wallahi sai kin gane baki dawayo." Uwanice mai wannan maganar cikin nuna isah. Itadai najwa bata ce mata cikankiba, tana gamawa tayi d'akinta. Teburin uwani taje ta zauna,tacika filat, da dambun shinkafa yaji albasa sa zogale gefe kuma ga farfesun kaza, sai lemon kwakwa yaji madara sa ayaba.😋 Saida tayi nak tukun. " shegiya ashe ta iya girki haka, amma takesani inyiwa mijinta nad'auka bata iyaba wallahi." Uwanice mai fad'in haka. Affan ma dayadawo daga masallaci, yabaje tunbi yaci ya koshi. Falo yadawo yakunna labarai, a tv yana gani uwani kuma ana d'aka ana waya da hafsat ana bata labari, saida karfe 10:00 tayi tukun yakashe kayan kallon ya shige d'aki. " tsaya mezakayi, naga kana 'ko'karin hawa gado, to wallahi saidai kaje falo ka kwanta, haka kawai yau kaci dammu kadameni da tusa, ka kumburamin ciki, baze yuhuba ungo fulo katafi kan kujera ka kwanta." Uwani ce maiwannan gadarar. Cikin sanyin jiki affan ya amshi fulon yafuta falo, doguwar kujera ya samu ya kwanta, yana tunanin wannan wane irin bala inee... *kuyi hakuri da wannan banji dadi wallahi yanzuma daga asibiti nake* [12/6, 10:15 AM] First Lady🌹: 🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻 🙆🏻🙆🏻 🙆🏻 *'YAR AIKIN GIDANA* *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *wannan shafin nakine 'yar mutan arkilla Allah yakara basira* *following us as:* ------ Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION ------ *Check us blogger* Zamaniwriters.blogspot.com -------- *Email us your comment and reports* Zamaniwritersassociaton@email.com *✍🏻shaxeee* *page 8* Najwa tana gamawa ta jere atebir din cin abinci, takoma d'akinta,tashi sukayi sukaje sukaci suka 'koshi. Uwanice tafara magana. " affan inaso kaje gidan hafsa,zaka amso min sa'ko." Tuni affan yami'ke yayi hanyar waje. " to bara naje saina dawo." Motarsa yashiga yatafi gidan hafsa, akofar gida yaganta zata futa ita dawani dan duniya. " uwanice tace inzo zaki bani sa'konta in kai mata." Affan ne mai wannan maganar. Cikin duniyanci hafsat take magana. " ok bara ina dakko maka, dama yanzu nake cewa bara in kai mata, in bata turoba." Gidan takoma, ta dakko 'karamar akwati, ta futo ta bashi amsa yayi, yashige mota ya yo gida. Uwani ana kan kujera ana cin apple,( abinka da farin shiga saiwani murmushi take kamar king yaga queen d'in sa😉)sallama affan yayi yashigo falon, ko amsawa batayiba. Cikin kulawa affan yace. " gashi tace agaisheki kuma tace zatazo,( to yaushe akayi haka🤔)." Wani ta bud'e akwatin, kananun kayane aciki, gaba d'aya ba na kirki duk afige suke, wani dan karamin siket ta dakko ko cinya bai rufeba, kuma rigarsa bireziyyace kawai mai mad'aurin a huya, sun had'u (dan koni sun ban sha awa kamar in kwace😎) " ungo affan jeka sako muga yadda zasuyi yimaka kyau." Inji uwani. " haba uwani taya zan saka wad'annan kayan, kuma na mata." Cikin nuna damuwa affan yake wannan maganar. Cikin masifa uwani take magana. " in bazaka sakaba saika gayamin, zaka wani tsaya yimin musu, kasaka kagani mana, base ka saka tsumma ba a bireziyyar, maza jeka saka kazo inga ni." Mi'kamasa tayi ya amsa, yaje yasa kamar yadda tace,kwalla yake yana gogewa abin kunyar har ina, haka yafuto falon. " woww kaga yadda kayi kyau kuwa, dakai macene daka more, yauwa tsaya in kunna maka wa'ka kad'an taka, dan na dad'e banga ana rawaba." Uwanice mai wannan maganar. Wakar kujerar tsakar gida tasaka, ta 'kure vol din tibin, rawa yafara badan ya iyaba. " yabaka girgiza maza kadinga mur gud'a duwawu mana, bakaji taken wa'kar bane." Cikin dariya uwani take wannan maganar. Haka yadage yanata girgiza( 😂😂wayaga maza da girgiza) juyi jawai yake, yana jijjuyawa, in yafaki idonta kuma ya share hawaye. Najwa duk tana jinsu dan tana le'kensu ta kofarta, kuka kawai take duk itace sular shigarsu wannan halin, dabata takura masa ba saiya nemomusu yar aiki, datuni suna zamansu lafiya. Saida yagaji tukun tace ya tsaya haka. " jeka cire kayan tukun, kawanke min ban d'aki, sannan zakaga kayan barcin dana cire acikin band'akin, kawanke su sufuta." Cikin izza uwani ke wannan maganar. Tashi yayi ya shiga d'akin,saida ya canza kaya tukun yafara aikin data sakashi. **************** "Nifa alhj hankalina ya kasa kwanciya, dawannan auren affan din, ga mugayen mafarke - mafarken danake akansa masu muni." Inji umman affan kenan. Cikin damuwa abban affan yace. " nima haka wallahi shiyasa naketa yimasa addu'a sosai domin abin ba dad'in ji, nayi binkice sosai shiyasa nagayamiki kema." *asalinsu* Alhji kabir d'an kasuwane mai tashe, yana zaman lafiya da iyalinsa yabasu tarbiya dai-dai gwar gwado, 'ya'yansa biyu affan sai aisha affan dakansa yace yanason najwa domin yar aminin babansa ce wato alhj abubakar, saita yi wata biyu agidansu, iyayensu sunji dad'i dasuka had'a kansu, anyi bikinsu nagani na fad'a, bayan sun tare da wata bitu najwa ta takurawa affan saiya kawo musu yar aiki saboda zuwa office, dakyar ya yarda, yakawo mata wata tafara aiki, da kwanaki tace bata yimataba,aka canza wata tace itama bata yimataba, saida aka kawo mata yan aiki guda shida tana canzawa, sai akan uwani ta ce tayi mata, iyayenta dana sa basusan abinda yake faruwaba, tunda aisha agidan su najwa take tana karatu saboda gidan yafi kusa da makarantarsu, shiyasa ta koma can, da zama. *wannan kenan* ************* Uwani ana zaune a gefan gado affan kuma yana falo. " affan!! Affan!!! " uwanice take wannan har gagin. Yana rawar jiki ya shigo. " kai dan..... 😳😳😳😳😳😳😳😳 *to komai uwani zatayiwa affan Allah yasa karta mareshi*😭 [12/6, 10:15 AM] First Lady🌹: 🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻 🙆🏻🙆🏻 🙆🏻 *'YAR AIKIN GIDANA* *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *nasadaukar da page dinnan wa ALJANAR FATIMA aikinki yana kyau* *following us as:* Fb.me/ZAMANIWRITERASSOCIATION --------- *check us blongger* Zamaniwriters.com ---------- *email us your comment and reports* Zamaniwritersassociation *✍🏻shazeee..* *page 10* "Ace kaida gidanka amma yafi karfinka,dazan iya ai dana tattakata amma ko dogon kallo bana iya yimata." Duk azuciya affan yake wannan maganar. Itakwa uwani barci harda minshari. Najwa kuma adaidai lokacin takira ummanta tamata bayanin komai. " najwa duk laifinki ne nabaki tar biya daidai gwargwado,amma kikaje kawayenki suka zigaki,yanzu wa gari yawa duk kanku kunga tashin hankali, abinda nakeso dake kidinga sallar dare kina addu a sosai, sannan kidinga yawan karanta alkur,ani banda wasa da salla,kiri'ke tsafta da girki dannasan kin iya girki saidai 'kiwa ta hanakiyi, kidinga kula da mijinki koda baze kulakiba, wataran da kansa zai dinga kulaki, inkikayi haka zakiga cigaba." Duk wannan bayanan umman najwa ce kemata awaya. " to umma insha allah zan yi yadda kikace." Najwace mai wannan maganar. Sallama sukayi ta kashe wayar, tashi tayi tayo alwala ta gabatar da sallah, tadad'e tana kai kukanta gun allah( wai mutane sai anji huya aketunawa da allah sanda kake shanawa mantawa kake dashi.). Tafi awa biyu, tana addu,oi sannan tashafa takwanta, tuni 'barawon dayafi kowa iya sata aduniya yasaceta, wato barci. Da asiba kowa yatashi yayi sallah amma banda uwani. Misalin karfe 7:00 najwa tafuto, zata d'ora girki affan tagani akan kujera yana kallon labarai, zuwa tayi kusa da shi ta tsugunna, sunkwiy da kai tayi,cikin rawar murya tace. " ina kwana antashi lafiya." Cikin jargagi yace. " waimeyasa zakizo kidameni ne nafuto falo dan in kalli labaran nan,saboda shifa natashi dahuri, nabaro matata tana barci,amma zaki hanani sakat,dan allah 'bace min daga gani." 'Dago kai najwa tayi, ganin fulo tayi akusa dashi ga wayarsa ma ga agogo da zobe duk azube,alamun anan yakwana,murmushi kawai tayi ta shige kichin. Shayi ta dora doya ta feraye, tawanke ta tas tasami abin goga ku'bewa ta gogata tajuyeta aroba, tazuba su maggi da kayan kamshi, ta jajjaga attaruhu tazuba tafasa kwai wanda ze isheta tasaka ludayi ta juyashi sannan ta dinga bugashi kamar 'kullin kosai saida yabugu tukun ta sami leda ta 'ku'k'kullashi tazuba ruwa atukunya tazubashi ta rufe, saida ta tabbatar yadahu sannan ta sauke ta kunce shi a filet, tabasa kwai aroba ta yayyaka doyarnan kamar yankan awara ta dora mai ahuta tadinga tsomashi a ruwan kwai tana soyawa saida tagama tukun ta juye a kula takai falo tajere shi, shayinma ta kaishi tadawo tafara gyara cikin din,tana gamawa tadawo falo yanzu affan baya nan. Gyarashi ta fara yi sallama taji anayi, juyawa tayi wata mata tagani yar 'kauye da ita ga 'kullin kaya akanta duk tayi kura da ita, sai washe jajayen hakora take. Saiga uwani ta futo ita da affan sunyi wanka da kwalliya. " inna kece da sanyin safiyar nan haka " uwanice mai wannan maganar. Tuni inna ta 'karasa shigowa falon tazauna akan kujera, tafara magana cikin farin ciki. " wallahi nice 'yannan cewa nayi bara inzo inga yakike, kuma in dan kwan biyu." Cikin jin kunya uwani tace. " to shi abban fa da yaya yusha,u waze dinga yimusu abinci." Muskutawa inna tayi tace. " rabu da wad'annan basu damu daniba, kekad'aice kike sona, shi yusha,u yatafi yawon sace sacen sa,kuma inya sami kudi sai yatafi ya kashewa karuwansa, ko ficika baya bani, shikuma babanku kinsan ba..." " to duk naji mekike so adafa miki." Uwanice tayi saurin katseta haka domin tasan zata iya 'balle mata ruwa, yanzuma duk kunya ta isheta, agaban najwa da affan taketa zuba. Najwa duk rana jinsu tana aikinta, ko 'kala bata ceba. Inna ce tafara magana. " adafamin shayi mai kauri sai aban biredi d'an dari biyu sai Asoyan kwai guda shida yaji albasa sai akawomin wannan abunda isa mai shayin garinmu yake shafawa a tsakiyar biredi, shikenan sun isheni, kinsan bawani cin abinci nakeba danaci 'kadan saikiga na koshi, ko ran..." " ina kwana inna." Affan ne ya katseta dan yaga bayaninta baya 'karewa saidai atsaida ita. " lafiya kalau yaro, ya hada hada, danna sanka da aiki, da bikinnan naku naga kata hada hada, kayinan kayican ka d'au wannan ka kai wannan, dama haka akeson mutun mai kuzari, kuma kasan wani abu wallahi ingaya ma w..." " inna ya isa haka kiyi shiru, akawo miki abin karin mana." Uwanice ta taka mata birki. Uwani ta kalli najwa. " kinji abinda inna takeso ko, base na maimai ta mikiba, maza a kawo mata da sauri. Najwa batace komaiba domin umman ta tace kome akamata tayi shiru, kicin taje dama ta dafa shayi kwai kawai tasoya tanayi tana dariyar hirar inna. " kai zamusha dirama agidannan kan wannan matar ta tafi." Tana gamawa ta dakko biredi ta kawo musu falon, harsun fara karyawa ajiye musu tayi ta 'karasa aikinta ta huce dakinta domin takai nata can dan ra karya. Suna gamawa affan yafuce, uwani bata hanashi ba sanin cewa in ya zauna, inna saita sakata taji kunya, kokuma yafara rainata. " innah ga d'akina can nada sanda nake musu aiki kije can akwai 'ban d'aki kiyi wanka ki kwanta kiyi barci, kima ajiye kayan ki ad'akin." Inji uwani kenan. Dakin ta rakata tanuna mata komai, tafuce saida inna tayi wanka sanna ta kwanta sai barci. Misalin karfe 12:30 uwani tana falo azaune ita da inna, inna sai zuba take uwa kanya. Najwa ce tafuto tazo gun uwani. " zan d'ora girki maiza a dafa." " innah mekikeso kici." Inji uwani kenan. ********************** ⬇ ************************** ********** Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** Gyara zama inna tayi tafara lisafi. " adafan shinkafa yar gwamnati domin yar hausa tacika tsakuwa, sai ayimin miyar dage dage tasha kaza, tasoyu sai lemon roba mai sanyi." Tuni najwa tashige kicin tana bude firig ta dakko miyarta dama yanzu dayawa takeyi ta ajiye, tana amfani da ita ahan kali, shinkafa ta dora, tana dahuwa ta tace ta juye a kula, ta dora taliya, itama tana dahuwa tajuye ta ta dumama miyar tazuba a kula tamaida ragowar, ta dakko salak da kabeji ta yanka tawanke ta dafa kwai ta yayyanka akan salak tasaka kokwamba bayan ta yayyankata kanana, tazuba waken gwangwani da bama tajuyasu, ta saka afirij domin yadanyi sanyi, ta dakko abarba ta markada ta ta zuba zuma kadan aciki, tasaka abin kwamshin lemo, tasaka 'kan'kara, taje tajere komai takai nata d'aki, duk tanayin wannan abunne saboda affan tasan da beciba yanzu takeso yaci, yasan ta iya itama, shiyasa ko ajikinta. Su inna harda kunce zani saboda ci, lodi kawai take, tana kora lemo. " dama haka 'yan bunni suke cin dad'i haka amma mu muna 'kauye abushe wallahi bazan komaba ainazo jenan, harnima insami Miji mai kudi, inje malan yasakeni inzo in aureshi." Azuciyar ta take wannan maganar. *naga sakwanninku sosai nagode allah yabar zumunci, nagode nagode nagode.* [12/6, 10:15 AM] First Lady🌹: 🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻 🙆🏻🙆🏻 🙆🏻 *'YAR AIKIN GIDANA* *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *wannan page din nakine quee tawa allah yabar zumunci, allah ya kata zakin hannu, acigana da suburbudo mana ILLAR BASHI* *follawing us as:* Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION ________ *Check us blongger* Zamaniwriters.com ---------- *Email us your comment anda Reports* Zamaniwritersassociation@Email.com *✍🏻shaxeee..* *page 11* " innah Wai tunanin mwkike ne haka." Uwanice ta katse mata tunaninta. Cikin inda inda inna tace. " a a wallahi bakomai kawaidai ina tunanin jin dad'in dakike cikine abin sha awa, jibi yadda kika mirje abinki, kuma ki.." " innah ya isa haka kici abincinki kar ki kware." Uwanice ta katseta. *********** " dazu abban najwa yamin waya, yake gayamin halinda gidan affan yake ciki, yace najwa ce tayiwa umman su waya ta gayamata komai." Abban affan ne yake wannan maganar. " nima tabugon waya tagayan saidai muyi tamusu addu,a allah ya dawo da al amarin daidai." Inji umma affan. " zanje gun malan nuhu yadinga yimusu addu a da sadaka,in sha allah komai zezo da sauki." Abban affan ne yake wannan maganar. ************ Dare yanayi affan yakasa shiga dakin, yana tunanin kar uwani taci mutun cinsa. Inna ce tafulo daga dakinta, ganin affan tayi akwance akan kujera, matsawa tayi kusa dashi tace. " d'annan mekake akwance anan yanzufa karfe 11:31 kai aiyanzi ba a yayin gudun amarya, ko a kwauye ma anddena, kuma da d'inma ai mata ne suke guduwa ba maza ba, tashi muje in rakaka." Ko 'kala baice mataba, yatashi yabita itace agaba, suna shiga d'akin, sukaga uwani a kwance tasaka kayan barci, innah ce tafara magana. " yar albarka ga mijin naki a falo naganshi akwance, shine nace masa ai yanzu andena yayin gudun amarya ko a kwauye ma bar birni, shine narakoshi nidai na tafi saida safenku." Fucewa tayi Tarufo musu 'kofa, shidai affan yana tsaye beyi gaba ba beyi bayaba. Dago Kai uwani tayi ta kalle shi, tace masa." Kaje kayi wanka kashirya kazo mukwanta." Dasau ri yashige banda ki wanka yayi yafuto yashirya, yazo ya kwanta.asiba ta gari. Gari yana wayewa bayan sun karya affan ya futa najwa tana d'akinta, uwani kuma tana shirin futa unguwa. " kar kije ko ina kizauna agida inkika futa zaki iya bata,ko 'yan yankan kai sukamaki." Uwanice mai wannan maganar. " karki damu ba inda zanje ina gida, kuma ai kince ba dadewa zajiyiba, sai kindawo kitawomin da abarba da lemo." Inji innah kenan. Futa uwani tayi tashiga mota direba yajata suka tafi. Innah tanata kallo harta gaji tarasa mai zatayi. " bara inshiga d'akin 'yannan ingani koda kayan dad'i kuma insami kud'i." Innah ce mai wannan zancan. Tashi tayi tashiga d'akin uwani tanata bunkice, tabude kwabar affan taga kudi, aikwa saida ta 'kirga taga dubu saba inne. " bara indau ki dubu talatin, na yi siyayya dama su masu kud'innan basa ganewa in an d'auka." Azanin ta taboye su, kwabar uwani ta bude babu ko fucika, sai wani kwaran gwal data gani, an soke zuciyarsa dawani 'karamin karfe. " uwani da kwashe kwashe,komai zatayi dawan d'an aljanin." Juyashi takuma yi ahannunta, kawai jitayi tana sha war karya masa kafa, kafar dama takarya ta sai kuma ta karya ta hagu, har ta ajiye saita kuma dauka. " bara inkarya hannayan ma aljani dakai harda wata kafa akayima, ko ina ruwan aljani da kafafu shida tashi yake sama." Hannayen ta karya duka ta mayar ta ajiye, futowa tayi takoma d'akinta, zuwa tayi ta 'boye kudin, sannan ta kwanta akan kago. " gobe sai kasuwa insiyo kayan kwalliya na yan birni indinga irin shigar su, konima nasamu miji mai kudi." Afili innah take wannan maganar. ********** Affan yana office yaji gaba daya jikinsa yana ciwo, waje yasamu ya kwanta, yafi minti goma a kwance tukun yadawo daidai jin sa yake sakayau amma zuciyar sa kamar ansa dutse andanneta, kayan sa ya had'a ya futo dan komawa gida. ************* " haba hafsa yaza kice in kula wani bayan kinsan yanzu inada aure." Uwani ce mai wannan maganar. Cikin lallashi hafsa tace. " kinga wannan irinku yakeso kuma kud'i zai saki, shiyasa ma nakiraki amma tunda ba kya so shikenan." Cikin hazari uwani tace. " to shikenan tunda zai saki kudi, nayarda." Dakin hafsat uwani ta shige, domin yana ciki yana jiranta. Murmushin mugunta, hafsat tayi. " da ga yau zaki gane ramin kura bagun wasan akuya bane, nizaki ciwa amana... [12/6, 10:15 AM] First Lady🌹: 🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻 🙆🏻🙆🏻 🙆🏻 *'YAR AIKIN GIDANA* *ZAMANI WRITERS ASSOCIATOIN* *wannan shafin nakine zuwaira madara allah yakara basira* *following us as:* Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCAITOIN --------- *check us blongger* Zamaniwriters.com --------- *email us your comment and report* Zamaniwritersassociation@email.com *✍🏻shaxeee..* *page 12* Hafsat tana zaune afalo tana kallo yayin dasukuma su uwani ana d'aki. " kinga uwani indai zakiyi harka dani, to yazama dole kidena kula mijinki, inba hakaba to saidai inne mo wata." Wani tunani uwani tayi, dama dan kudi ta auri affan, kuma gawani shima zai sakar mata kudi, to maizaisa ka ta 'ki amincewa. " kaga ciko na amince kawai, mushana nima bason mijin nawa nakeba, kawaidai ina zaunene." Daga nan suka shiga aika aikarsu( allah ka tsaremu da tsarewar ka ameen kasa mufi karfin zuciyarmu.) ************** Najwa ta gama kimai har girki tagama, jerawa kawai take a tebur affan yashigo. Tsugunnawa najwa tace. " sannu da zuwa ya hanya." " lafiya kalau ya gidan." Yabata amsa. Ba 'karamin mamaki tayiba, dan bata d'auka zai amsaba. 'kara sawa gunsa tayi ta amshi jakarsa tayi hanyar d'akinta, binta yayi abaya. Tana jin takunsa yana binta, murna kamar tayi rawa ta juya. Suna shiga d'akin ya zauna abakin gado, tacire masa takalmi, ta rage masa kayan jikinsa, ruwa ta dakko mai sanyi a 'karamin firij dinta,irin na gefen gado. Zuba masa tayi yasha tashiga ban d'aki saida tayi rawa ta juya, sannan ta had'a masa ruwan wanka ta futo. " dear na had'amaka ruwan wanka, kaje kayi." " ok baza ki taya niba ne yau." Ta girgiza sosai kodai affan yadawo daidai ne, inkwa hakane saita fi kowa murna. " mai zai hana muje bama taya ka zan yiba yimaka zanyi." Tare suka shige 'ban d'akin suna dariya abin sha awa. ************* Innah saida ta sha barcinta tukun, sannan ta tashi ruwa ta watsa ajinta, sannan ta canza kaya cikin kwana biyunnan harta fara haske, tayi shar da ita. Futowa tayi falo, ta haye kan kujera ta 'kurawa tv ido, bata gane komai amma ita alallai dole saita kalla. Su affan suna gama wanka suka futo cikin farin ciki, suka shirya junan su. " byba kawomin abincina nan, bansan mai yasaba bana son futa." Affan ne mai wannan maganar. " yadda kace haka za ayi ranka ya dade." Murmushi sukayi gaba d'ayansu, wayarta najwa ta d'auka ta futo. Zuwa tayi ta huce inna tana kallo, kicin ta shiga takira umman ta a waya. " hello umma kitayani godewa allah affan ya dawo hankalinsa." Gaya mata tayi yadda affan yanzu yadawo. A 'ban garan umman najwa kuma cemata tayi. " dama inaso inbugo miki waya, d'azu naje gun malam hassan 'kanin abban ki yayi istahara, yace duk wani asiri najikin affan ya karye, amma banda guda d'aya, d'ayan kuwa shine baze iya sakin uwaniba, amma komai zai iya yimata banda saki, dan haka yanzu fagen naduk wadda ta iya kwace mijine." Nan umma tabawa najwa shawar wari, da yadda zata kwace affan cikin sauki, da kissa kala kala( haka akeson iyaye mata mukasance mucire kunya mubasu shawara mai kyau.). Najwa ta nutsu ta ji komai, kuma ta d'auke su. Umma ce tacigaba da cewa." Ina fatan kinsha magun gunannan, domin basu da illah dan agun *maman khalifa* na siyesu, kayanta sunada kyau, kuma zata cemaka idai bemaka aikiba kadawo ta baka 'kudunka, shiyasa banaso kiyi wasa dasu." " e umma duk nasha har kazar ma nacinye, tsiminne kinsan dayawan sa shine ban shanye ba." "To yimaza ki koma gunsa, kikula da duk abinda nace miki, sai anjima." Wayar suka kashe. 'diban duk abinda zatayi amfani dashi, tayi tafuce takai d'aki ta dawo ta kwashe abincin kan tebur duka, takai d'aki tajere agaban affan. Futowa tayi ta dibi lemo a firij, inna ta gani tafara hamma, murmushi tayi. " nima yanzu likacina yafara, zaku gane bakuda wayo, wallahi sai kunyi nadama ada nayi saka ci amma ayanzu zan nuna muku nima yar ri'ka'k'kiyar karuwace amma ta gidan aure." Duk azuciya najwa ta take wannan maganar. Huce ta tayi yakoma gun affan, sukaci abinci cikin farin ciki da raha, suna gamawa najwa ta kwashe ragowar abincin ta kaiwa masu gadi, suka juye ta koma ta maida su kicin, tana sane ta 'ki wankewa. 'daki takoma ta keyiwa affan tausa.( mata kuna sakaci dayiwa maza jenku tausa, tanada mihimmanci so sai, misammamma in miji yadawo daga kasuwa.) Innah kuwa har yunwa tafara tumur musar ta, gashi taje kicin ba abinci, gashi bata iya kunna gas ba, bare ta dafa tarasa yadda zatayi, ragowar biredi tasamu taci da ruwa, tana zaune afalo sai ga uwani. " yauwa 'yata tun d'azu nake jiranki, baki dawoba ga hunwa ta addabeni." Innace mai wannan bayanin. Waje uwani ta samu ta zauna." Ina waccan sakaryar take, bata dafa bane, nima hunwar nakeji sosai, kuma naga motar affan koshi mai yasa baki gaya masa, yasaka ya ta dafa miki." " hmm inafa kallonta harta dora a wancan tebur d'in, saikuma ta kwashe ta kai d'akinta, data futo dashi tayi waje tabayar, ta dawo da kwanukan, kuma shi affan d'in bansan inda yakeba, kuma baya d'akinki." " taf ta tsokalo sama da kara ni zata hula 'kantawa uwa, kiyi ha'kuri inna bara in kira affan d'in awaya, yazo ya d'au hukunci akanta." Huci kawai uwani take, ita kanta bata san irin hukuncin dazata d'auka akan najwa ba, ga shi tanajin hunwa ga shi wancan ya gurjeta son ransa, kuma ta kira affan bed'agaba. Itakwa najwa duk ta jisu, neman abinda zata nuna musu yanzu fa va da bane, dabara ce ta fad'o mata. Cakulkulu tafara yiwa affan, yana dariya, shima yana yimata, mintsilinsa tayi acinya, aikwa yatashi ya biyota 'kofa ta bud'e ta futa falo sai zagaye kujeru suke. Baki innah da uwani suka bud'e, ko kula da su affan beyiba, bin najwa kawai yake, saida ya kamata suka fad'a kan kujera. " wana kama kingama gudunko." Cikin haki affan yake magana. Saiyanzu yaga su innah. " au sannun ku ashe kuna falon, wallahi ban kulaba, ashe kin dawo." Affan ne yake wannan maganar. Uwani rasa abin fad'a tayi mai yake shirin faruwa. Najwa kuwa tana kan cinyar sa. Bata sauka ba, inna sai raba ido take. Cikin kissa najwa tace, dear kacewa uwani tamin wanke wanke wallahi na gaji dayawa, shiyasa ban hiba.. *muje zuwa* [12/6, 10:15 AM] First Lady🌹: 🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻 🙆🏻🙆🏻 🙆🏻 *'YAR AIKIN GIDANA* *ZAMANI WRITERS ASSOCIATOIN* *bazan gaji da baki kyautar page ba ALJANAR FATIMA Allah ya ja zamaninki* *Masoyan yar aikin gidana ina ganin sakonninku Allah yasa da alheri* *following us as:* Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION ---------- *check us blongger* Zamaniwriters.com ------------- *email us your commernt and report* Zamaniwritersassociation@email.com *✍🏻shaxeee..* *page 13* Kallon najwa affan yayi, duk ta yi kalar tausayi, ta marairaice. Juyowa yayi ya kalli uwani, ta ziba masa ido tana harare harare. " mai zai hana tayi himiki, ai naga duk aikin gidan kekikayi, uwani maza jeki hi mata wanke wanke." Cikin masifa da uwani take magana." Bazan yiba kehar kin isa kija dani, kewacece to wallahi kome kika bawa affan ni zan dawo dashi yadda nakeso, kuma Bari kiji ba a ja da ni wallahi, dan ahaka kikiyayeni zan iya 'batar dake adoron duniya." Innah ce itama ta tashi tafara nata guntun bala in." Tabb wallahi baku isa kumayar min da 'ya *'yar aikin gida* ba Wallahi,kekuma kifita daga idona in...."tassss kakeji affan ya mari uwani, bashiri inna tayi shiru. " ke har kin isa kidinga zagin matata, agabana keda uwar ki wallahi kushiga hankalin ku inna ba hakaba zaku gane kurenku, kuma ki gaggauta zuwa kiyi wanke wanken, inkika 'ki hi wallahi saina zaneki shashasha kawai." Cikin fada affan yake wannan maganar. Abin hada d'a bawa uwani mamaki, kodai ba affan din data sani bane. Tuni tashige d'aki domin duba halin da kwaran gwal yake. Tana bude kwaba ta d'ad'd'aga kaya, ta d'akko shi, tashin hankali wanda ba a saka masa rana. Ganin kafafu da hannayen kwaran gwal akarye suna reto. " wayyo Allah na waya min wannan ta asar, nashiga uku, dolene inkira hafsat dan ta koma gun boka, sake sabon shiri ayau d'innan." Waya ta d'aukko takira hafsa, tana d'agawa tahimata bayanin komai. " karki damu 'kawata yanzu zanko ma gun boka, in amso miki magani." Cikin murmushin mugunta hafsat take wannan maganar. Kashe wayar uwani tayi, tafuce falo bakowa sai inna tayi ta gumi." Innah kije kiyi wanke wanken, kinzauna kinyi tagumi danni bayi zanyiba, gwara kije kiyi inba hakaba kuma inyafuto ya koreki kyauye." Jin za maida ita kyauye yasa ta tashi tashige kicin, tafara wanke wanken. Tana gamawa uwani tazo ta d'ora musu indomesukaci. **************** Hafsa agaban boka mai 'kwaran gwal. " sonake kayi wanda zai tsaneta ita da uwarta yadinga gana musu azaba, kuma ya saketa saki uku." Hafsa ce mai wannan jawabin. Hhhhhhhhhhh boka ya yi dariya." Za ayi wanda zai tsaneta tsana mai tsanani,harda uwarta amma baze iya sakinta ba har sai, an zare wannan kibiyar ta zuciyar kwaran gwal din ana cirewa kominti biyar baza ayiba, zai saketa." " hakanma yayi, gwara saita jigata tukun da kanta zata cire." Wata laya yabata yace " kijefa arijiya tana fadawa to zaiji yayi mugun tsanarta uwa ya kashe ta ita uwar." Amsa tayi tabiya shi ta futo. A hanya ta sami rijiya ta cilla ta tafi. **************** Affan yana zaune a kan gado yana danna loptop, najwa kuma tana kicin tana girkin dare. Jiyayi kansa ya sara, yaji duk duniya bawanda yatsana kamar innah da uwani. Tashi yayi yafuto falo bakowa, dakin uwani yashiga, tana kan gado akwance ana barci. Futa yayi bakin get gurin mai gadi. " baba dan Allah ban aron bulalar ka babbar mai baki biyu dinnan, ta korar awaki." " to shikenan mai gida." Dakinsa ya shiga yad'akko masa wata shar'bebiyar bulala yabashi. Gidan yadawo d'akin uwani, betsaya wata wataba yafara lafta mata, wani ihu tasaki tatashi afurgice, dukanta kawai yake ba 'ka'k'kautawa. Najwa tagama komai tana goge guri, taji ana ihu bashiri tafuto, innah ma taji ihu uwani bashiri tafuto, har zaninta yana nema ya fad'i. Yana ganin inna yajawota ya hada da ita yana lafta, duka bana wasaba itakanta najwa abin yabata tsoro gudin kar ahada da ita yasa ta ruga da gudu tashige dakinta. Saida yaga basa motsi tukun ya kyalesu, gun mai gadi yakoma. " baba daga yau inba niba sai najwa kar wanda ka bari yafuta ko yashigo, gidannan indai bani nace abar shi ya futa koya shiga, kuma wannan bulalar narike ta zan dinga amfani da ita." " angama ranka ya dade." Ciki yakoma yashige dakinsa, ganin najwa yayi tayi tsuru tsuro, aikwa abin yabashi dariya. Dariya yake harda rike ciki, kamota yayi yarungumeta." Haba byba na me na tsoron kinsan keta dabance, suma kawai jinayi na tsanesu wallahi barima in koma dan abinda nayimusu be isheniba." *kuyi hakuri da wannan nadan futane naje asibiti dubiya* [12/6, 10:15 AM] First Lady🌹: 🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻 🙆🏻🙆🏻 🙆🏻 *'YAR AIKIN GIDANA* *ZAMANI WRITERS ASSOCIATOIN* *yau zaga yowar ranar rasuwar mahaifina ta shekara 4 nasadaukar da wannan page din washi duk wanda yakaranta yayi masa Addu,a allah yajikansa* *following us AS:* Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCAITION --------- *check us blongger* ZAMANIWRITERSASSOCAITION.com ----------- *email us your commenrt and reports* Zamaniwritersassociation@email.com *✍🏻shaxeee..* *page 15* Saida innah tayi kuka harta gaji ga rana tana dukanta, bashiri ta tashi takoma ciki. " innah yanaga kin dawo mai ya faru kuma." Uwani ce mai wannan maganar. Cikin ta'kyaici inna tace." Badole indawo ba ja irin yaronnan ashe yace kar abar kowa yafuta, shikuma mai gadin kwata kwata bashi da mutuncu, gidanma yakulle yakoma d'aki yakwanta." Haka suka zauna suka jimami taya zasu futa, agidan suje gidan boka. ************* Falone anhadu sai hira ake abin sha awa, affan najwa da umma sai abba da eesha, dan tazo gida hutu. " to ni bara in huce Office, lokaci yayi inna dawo sai inbiyo mutafi." Affan ne yake wannan maganar. " to allah yabada sa a " inji abba da umma. Tashi najwa tayi taraka shi mota saida yatafi tadawo. Tabasu labarin yadda affan yadawo daidai. " Allah zamuyiwa godiya, kekuma aiki kiyaye gaba, kunga dai halin dakuka shiga." Abba ne yake wannan maganar. Fada sosai sukayiwa najwa, kuma ta sauraresu sosai, ta dauki abinda sukacemata, abba ma futa yayi kasuwa najwa kuma suka cigaba da hirarsu. ***************** Hunwa ta addabi su inna, sunrasa yazasuyi da rayuwar su kuka kawai inna take yi, tana zaman zamanta takwaso 'kananun 'kafafunta ta tawo inda za a kasheta da hunwa. Inna tunawa dakud'in data sata tayi, dubu ta dakko. " ungo jeki bawa mai gadi yasiyo mana abinci muci." Innah ce mai wannan maganar. " dama inna kinada kudi amma kika barmu cikin yunwa." Cikin tsiwa uwani take wannan maganar. Amsa tayi ta je gun mai gadi tabashi tace dan allah yasiyo musu abinda zasu ci, amsa yayi yaleka yabawa yaron makocinsu yasiyo musu. Mintuna kadan tsakani yakawo musu harda lemo, duniya sabuwa agun su inna sukaci suka koshi, suka 'boye ragowar a daki. Sai karfe goma na dare su affan suka dawo, kota kan su uwani basu biba suka shirya suka kwanta abinsu. ***************** Gari yana wayewa su innah suka tashi suka fara aikinsu. Najwa kuma tana kicin, affan yana falo yana waya. " karka damu kawai ina gida yanzu kayi sauri kazo ka kawomin, in baka kudin kawai." Banji mai akace adaya bangaranba. " ok muhadu a Office din, badamuwa." Wayar yakashe. Ya ajiyeta. Tashi yayi yabude dakin uwani na da, yana shiga yabude kwabarsa don d'aukar kudinsa dan har ya manta dasu, saiyanzu yatuna, yana dakko kudi yaga ankwashe kudi. " tab dijan dama ai yau ban disfula suba, dan in basuba babu wanda zai taba min kudi, wallahi saikunyi nadamar daukar min kudi. Cikin murmushin mugunta affan yake wannan maganar. Futowa yayi falo lokacin har najwa ta gama komai." Byba zomuje kitayani wani aiki." Tashi tayi tabishi. Farfajiyar gidan suka futo lokacin su inna ana zaune ana hutawa. Hade fuska affan yayi uwa *ALJANAR FATIMA* " ku kuzo nan nace." Tuni suka tawo domin bawasa afuskarsa. Mai gadi yakira, yana zuwa yace." Dakkomin farar kujerarcan guda biyu." Tuni mai gadi yaje ya d'akko yakawo, zama yayi shida najwa, sukwa su inna ana tsugunne agabansa. " kowane Cin mutunci kuma yau zai mana oho." Duk azuciya innah take wannan maganar. Cikin isa affan yace. " na ajiye kud'i adakinki nada, amma yau naje dauka naga andibi kudin, dan haka kufuto min da kudina ko kugane baku dawayo." Kallon kallo sukewa juna dan uwani tasan innah ce ta dauka dan tagaya mata. " wallahi bamu muka dauka ba." Harsuna hada baki. " wato dai bazaku futo dashiba ko." Rantsuwa suketa yi basu dauka ba. " tunda kundage shikenan amma ni zan amsa tadda bazaku ji dadiba, mai gadi dama kai kayi harkar daba ko to gayamin kalolin mugunta." Washe baki mai gadi yayi yace." Ai mai gida nasansu sunada yawa. Akwai wanda za a sami barkono addadakashi ahada da fasassun kwalabe aturawa mutun ta baya, akwai wanda za a sami ruwa adanna kan mutun aciki, akwai wanda za a sami 'katuwar roba wadda mutun zai iya shiga azuba ruwa aciki asaka mutun sai asa wayar shokin aciki. A kwai..." " wadannanma sun isa maza jeka samo kayan daza ayi amfani dasu." Jin wannan kalolin azaban daza ayi musu tuni innah tafara fitsari harda guntun kashi, tuni inna tace." Basai anyi hakaba wallahi ni nadauka, bara indakko maka kudinka." Tuni inna ta tafi tana rawar jiki, taje ta dakko tabashi, 'kirgawa yayi yaga ba dubu d'aya. " naga babu dubu d'aya ina taje." Cikin rawar baki uwani tace." Wallahi abinci muka siya jiya muka ci saboda ba abinci agidan." " ina ruwana yanzudai kun kashe min kudi ko to zanmuku hukunci daidai da kudin da kukaci." Komawa gida yayi yad'akko bulalarsa, yadawo gunsu duk abinda ake najwa tana kallo. Cikin fada affan yace. " maza tashi kufara tsallan kwado kuma duk wanda ya tsaya zan tsula masa bulalarnan." Tuni suka fara yi saisun kai 'karshen farfajiyar sai su dawo, inna kuwa tagaji, shiyasa ta dan tsaya ta huta, aikwa affan yasaita duwawunta ya tsulamata, wata kara tasaki tacigaba uwanima ya tsula mata, sunfi awa biyu sunayi, najwa ce taga abin yaki 'karewa shiyasa tace. " dear dan allah kabarsu haka ai sun daku kaji nawan." Cikin murmushi affan yace. " maza kutashi kuje ku tsugunna agabanta kuyi mata godiya kuma kuhuce daki saura inga kunfuto." Da rarrafe suka karasa gunta suka yi godiya, da rarrafe suka shiga gidan suka koma d'akinsu. Suma komawa gidan sukayi sukaci abinci, ruwan shayi da biredi yaje d'akin yakai musu, yafuto saida sukayi wajen awa awa hudu sannan suka tashi suka sha shayin duk da yayi sanyi. Wanka sukayi suka zauna suna tunanin wannan irin azaba. " innah gyara d'akin duk kin zubar da kaya bara ni inje inmata wanke wanke nasan tagama girki yanzu. Uwanice mai wannan maganar. Fucewa uwani tayi zuwa kicin. Innah ce tafara gyara musu kaya, tagama hada nata tazo hada na uwani aikwa tayi karo da wannan 'kwaran gwal din." Shegen aljaninnan komai uwani take dashi, ni wallahi nagaji da ganinsa a cikin kayanta." Cikin fada innah take wannan maganar. Bata tsaya wata wataba tazare kibiyar jikin zuciyar sa, ta kakkaryashi 'kanana 'kanana tazubar adakin, daidai lokacin uwani tashigo tana ganin abinda inna tayi ta daskare agun.... [12/6, 10:15 AM] First Lady🌹: 🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻 🙆🏻🙆🏻 🙆🏻 *'YAR AIKIN GIDANA* *ZAMANI WRITERS ASSOCIATOIN* *jinjina gareku masoyana Allah yabar zumunci ina matukar alfahari daku* *following us as:* Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION ----------- *check us blongger* Zamaniwriters.com --------- *email us your comment and report* Zamaniwritersassociation@email.com *✍🏻shaxeee..* *page 14* Yana futowa yagansu akwance inda yabar su, duk jikinsu afarfashe, murmushin mugunta yayi yahuce kicin. Ruwan dimi yasamu azuba uban gishiri, yajuya sosai yafuto. Bai tsaya wata wata ba yadinga yayyafa musu, ihu kawai suke suna neman temako, saida ruwan yakare yamayar da kwanon kicin, dakin uwani yashiga ya katse hutar dakin gaba d'aya. Bandaki ma yashiga ya yanke hanyar daruwa zezo bandakin yafuto yakoma daki gun najwa. Da'kyar suka tashi awalce suka koma daki, wahalce inna tace. " uwani maikika yiwa yaron nan haka kotausayi babu yamana wannan azabar, harda ni koganin cewa ni babar matarsa ce beyiba." Cikin 'kunar rai uwani tace. " nima bansaniba haka kawai ina barci yazo yana dukana, dole inkoma gun boka yanzu basai gobe ba wallahi, amma affan yayi babban kuskure daya dakeni har najwan saina musu abinda zasu yi nadama mai girma." " yauwa uwani maza hanzarta kije konima bayafewa zanyiba." Dakyar uwani ta sake shiryawa, tadau kudi da jaka tafuto, tana zuwa bakin get maigadi yahanata futa, yace. "mai gida yace karwan da yafuta saida izininsa." Haka ta hakura tadawo cikin bacin rai, waya ta dakko takira hafsat, amma tanata ringin amma ba a d'agaba, harta gaji ta hakura, tagumi tayi "maiyake kokarin faruwane wayamin wannan ta asar karyamin asiri." Abinci najwa takowo musu saki sukaci suka koshi ragowar affan yace takaywa mai gadi, haka kuwa tayi dakansa yazo ya kulle kicin din yakoma daki, sukayi shirin barci suka kwanta. Waje karfe 1:39 hunwa ta addabi su innah da uwani gashi kicin arufe, uwanice ta duba d'akinta ta samomusu ragowar cake, sukaci daruwa suka kwanta gazafi ga duhu dakin sun rasa yazasuyi ahakadai sukayi barci. *************** *DA A SIBA* Affan yana dawowa daga masallaci dakin su uwani yaje, sunata barci harda minshari. Komawa yayi yaje ya dakko bulalarsa yashigo dakin. Tsula musu yayi afur gice suka tashi. " kunyi sallane kuketa barci haryanzu sai kace kafurai." Cikin fada affan yake wannan maganar. Saida ya yimusu uku uku tukun yace sufuce waje suje farfajiyar gidan gun famfo suyi alwala. Suna futa yakarewa dakin kallo, dakinsa ne fa nada amma wadannan masu kama da a gwagin suke zama aciki. Bude kwabar yayi yasami jaka yazuba wa uwani duka kayanta aciki harda mayuka. Yafuto dasu falo komawa yayi yabude akwatinanta na lefe, ba abinda aka taba aciki, gani kayan yayi ko lokacin bikinsa da najwa, baimata kaya masu yawan haka da tsadaba. Duka ya kwashe yakai dakin najwa, yadawo ya kulle dakin. Zama yayi a falon kan kujera, yana kallo duk wannan diramar da ake najwa tana kicin bata saniba tana kokarin hada abin kari. Su uwani anyi sallar da ba asan ya akeyintaba, sun tawo domin komawa akwanta suna shigowa falon affan yakirasu. " ku kuzonan " bamusu suka zo. " kinga kayanki daga yau kin koma wancan d'akin naki nada kuhadu keda uwarki kukwanta aciki, sannan daga yau duk aikin gidannan kuzaku dinga yi harda bawa shika ruwa da share farfajiya, da wankin mota, harda wankin mu insun yi datti nadena asarar kudina tunda ga 'yan aiki agidana, kuma duk ranar dakuka 'ki yi ko kukayi ba dai daiba ko kuka yiwa najwa rashin mutunci, wallahi saikin ji badadi agidannan maza kuje kufara aiki." Kayan uwani tafara kaiwa dakin innah, ta ajiye ta futo shara suka fara hi har falon suka goge komai sukaje kicin sukayi wa najwa wanke wanke, suka futa farfajiyar gidan duk busassun ganyayyaki suncika wajen, haka suka share da kyar suka bawa shuka ruwa, sannan suka fara wanke motoci guda ukun. Sukwa su najwa ana ciki ana karyawa ana raha abinsha awa, Adaddafe suka karasa suka koma ciki lokacin su affan ana kallo najwa kuma tana kan cinyar sa ana shagwaba. Awahalce sukace. " mungama aikin duka komai da komai." Biredi da ruwan shayi ko siga baijiba yamika musu. " allah yasoku da rahma da bakuyiba wallahi saina azabar tar daku, banzaye masu kama da a gwagi, nibansanma jarabar data sani na kwasokuba, ku ungo kuje kusha kuma da ranama haka zakuyi kullun sau biyu." Najwa kuwa sai gwalo take musu suna gani bayadda zasuyi,amsa sukayi suka shiga dakinsu, ci sukafara kamar wanda suka ashekara basu ciba( dama hausawa sunce jiki magayi). " dear inshirya muje gaishe dasu umma daganan miyi siyayya mudawo gida." Najwa ce maiwannan maganar. " byba yaudai yawo kikeji, to muje mushirya sai in ajiyeki intafi Office inna dawo sai in biyo mutafi ko." Tsallan murna tayi, suka shiga ciki suka shirya suka fice, kan affan yafuta saida yajadda dawa mai gadi karwanda yafuta ko yashigo. Su uwani ansha huya suna kwance suna hutawa, innace ta tashi zaune." Wallahi bazai yuhuba ace nida natawo inhuta a Birni ko agidana ba a dukana, ga horon hunwa ga aiki kamar bayi, wallahi gida zan koma bazan mutu abanza ba in nakoma zan sami wani bokana yamiki aiki akansa, yadawo mijin tace kiyi yadda kike so agidannan, amma bazan iya zamaba wallahi." " yauwa innah kitemaka min in mallaki affan insami kudi sai inbar gidan, amma ko nabar gidan yanzu yazama ban amfana da komaiba." Innah kuwa tuni ta hada kayanta tayiwa uwani sallama ta futo tana zuwa bakin get. " mai gadi budemin zan koma garinmu, dama cewa nayi bara inmusu kwana biyu kuma nayi yau zan koma." Mai gadi kuwa yahade rai yace. " hajiya mai gidan yace kar kowa yafuta kuma karwanda yashiga dan haka kiyi hakuri, dan wallahi bazaki futaba." Kulle kofar yayi da kwado yakoma dakinsa yarufo kofa. Zaman da'baro inna tayi tadora hannu aka." Nashiga uku ina nakawo kaina, shegen kwadayina ne yajamin, gaji na 'bige da aikatau wayyo allah na.. [12/6, 10:15 AM] First Lady🌹: 🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻 🙆🏻🙆🏻 🙆🏻 *'YAR AIKIN GIDANA* *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *FOLLOWING US ON THIS DETAILS:* ------- *LIKE OUR FACEBOOK PAGE:* 👇🏻 *fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCAITON* --------- *CHECK OUR BLOG'S* 👇🏻 *zamaniwriters.blogspot.com* ------ *DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:* 👇🏻 *Zamaniwritersassociation@email.com* *✍🏻shaxeee..* *page 16* Cikin tashin hankali uwani tace." Inna kinkwa san mai kikayi, asirinefa akamin, yanzu kuwa affan zai sakeni nashiga uku, gashi ban tara komai ba zan futa abanza." " yo ni danasan ana cirewa zai sakeki ai da na dade da cirewa, wannan irin bala i haka, jibi yadda nayi ba'ki na rame ni ai farin ciki ma zanyi dan zan bar gidannan." " nama gama ganoki innah kekika fara karya min asiri, kika karya wa gwaran gwal dinnan hannu da kafa ko." Cikin bacin rai uwani take wannan maganar. Tsuru tsuru innah tayi dan tasan itace ta karya bawani ba. ********* Affan yana office yaji zuciyar sa kamar ana kunna mata huta, can kuma sai yaji tayi sanyi yaji uwa bashiba. Kamar an tsikareshi haka yaji, tuni yatashi ya futo, ko kulle office din bai tsaya yiba. Motar sa yashiga yakunna, hanyar gida yanufa, gudu kawai yake kamar wanda zai je maka. Yana zuwa gida ya yiwa mai gadi wani ham mai 'karfi, mai gadi shi kanshi yarikice tuni yabude get din, saura kadan ayi ciki da mai gadi Allah yasa yamatsa. Futowa yayi daga motar ya shiga gidan. " UWANI!! UWANI!!." Cikin d'aga murya yake kiranta. Saida cikin uwani ya kad'a shikenan yanzu zata koma kwauye, cikin hanzari ta futo ita da innah. Najwa ma saida ta futo cikin furgici tadauka wani abinne yafaru. Affan yana ganin ta yace." Kije nasakeki saki uku, kuma Allah ya isah tsakanina dake dan bazan taba yafe mikiba, kuma na baku minti uku kubar min gidana." Yana gama fada ya shige dakin najwa. Najwa ce ta yi buda tace." Sai akoma kyauye acigaba da cin bakin tuwo da koriyar miya, ansami miji anyi yadda akeso ko, dama ance in zaka gina ramin mugunta ka ginashi daidai dakai dan wata rana kai zaka fada ciki."tana gama fada tayi hucewarta Daki. A sanyaye suka shige daki suka hada kayansu gaba daya, suka futo suna zuwa bakin get mai gadi yahana su futa saida yakira affan yace yabarsu sufuta tukun yabarsu. Cikin jimami innah tace. " uwani yanzu a ina zamu sami kudin mota, mukoma kyauye." " karki damu inna akwai wayata kuma tanada tsada ita zan siyar, saimu koma amma saina fara biyawa ta gidan hafsat tukun, inga ko lafiya bata nemeniba kwata kwata." Haka kuwa akayi sukaje wani shagon waya, yabasu fubu hamsin dukda cewa wayar tafi haka, mai adaidai ta ta tsayar tace ya kaita gidan hafsa. Suna zuwa ita kuma zata shiga mota. " yauwa hafat dama nace lafiya naga baki neme ni ba ko awaya nakira baki d'auka ba." Uwani ce mai wannan maga nar. Wani irin kallo tayi mata sannan tace. " ke atunaninki zan nemeki to bari kiji cin amanar da kikamin ba yafewa nayiba, shiyasa nabiki asannu narama abinda kikamin, nafarko nasa boka ya yimiki asirin da affan ya tsaneki, na biyu kuma wannan ciko din dana kawoki gunsa, dama nina turoshi saboda yanada kanjamau, kuma nasan kema yanzu kin dauka, dan haka maza kibar min gidana konasa ayi muku hulakanci." " abinda zakiyim kenan hafsa am ma kin cuceni wallahi kuma bazan taba yafe mikiba, kuma gida yanzu zamubar miki." Cikin kuka uwani take wannan maganar. Kama hannun innah tayi suka tafi, adai daita suka kuma hawa zuwa tasha. Suna zuwa suka hau motar garinsu basu dadeba mota ta tashi inbanda kuka ba abinda uwani take, ga nadama data shigeta, data tabi duniya asannu da bahaka ba. Awa daya ce takai su garin su, dama banisane da shiba. Suna zuwa gidan su sukaga abban uwani awaje a zaune yana ganinsu yashige cikin gidan. Suma binsa sukayi ciki, suna shiga suka ganshi da wata tsohuwar akwatin karfe. " dama ke nake jira kidawo in gaya miki abinda zan gaya miki intafi gun yan uwana, dafarko dai kin cuceni kin rabani da kowa nawa, saida Allah yasa wani bako damukayi a garinnan malami yatemaka min asirin da kikamin ya karye ni nayafe miki, duniya da lahira kije nasakeki saki uku, kuma ki nemi baban su uwani kibashi 'ya 'yansa, ni narafi tunda dama gida nakine, Allah ya hada kowa da rabonsa." Fucewa yayi suna kallo yarafi, kuka kawai innah take. Cikin fur gici uwani tace. " inna dama mu ba 'ya 'yan sa bane ina baban mu yake... [12/6, 10:15 AM] First Lady🌹: 🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻 🙆🏻🙆🏻 🙆🏻 *"YAR AIKIN GIDANA* *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *FOLLOWING US AN THIS DETAILS* -------- *LIKE OUR FACEBOOK PAGE:* 👇🏻 *fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCAITION* ------------ *CHECK OUR BLOG'S* 👇🏻 *zamaniwriters.com* -------- *DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME* 👇🏻 *Zamaniwritersassociation@email.com* *✍🏻shaxeee..* 🔚🔚 *page 17* Cikin kuka inna take magana. " gaskiya ne bashi ya haifekuba, ubanku daban amma yanxu xan baki labarin komai." Zama sukayi sannan innah tafara bata labari. " iyayena duk sun mutu, ahannun kishiyar mama na natashi ita take turani gun wata *DIJE MAI TUWON YAN GAYU*( littafi na mai zuwa) ina hiwa matar aiki anan nafara bin maza, duk da innar tawa tasani amma bata hananiba saidai ma ta kara dorani akan hanya, ana haka ciki yabayya na ajikin, data fuskanta saita kaini aka zubar dashi, bayan wasu kwanaki tafara rashin lafiya har ta mutu, yan uwana sukace bazasu dauke niba saboda kowa yasan halina, suka siyar da gidanmu suka bani dubu biyar waishine rabona nikuma nabar garin nadawo garinnan, gun wata mai abinci atasha ina taya ta girki har nazama babba agunta komai ninake bada umarni, ana haka na hadu da babanku tasi,u yana kashemin kudi sosai, ahaka nasami cikin wanki, yace inzubar damukaje asibiti akace zan iya mutuwa nikuma naki yarda ahaka harna haifi wanki, bayan na yayeshi, sai tasi,u yakuma dawomin, nayarda dashi bayan wasu watanni nakuma samin ciki, yana ganin haka yagudu haryau ban kara ganinsaba, ahaka har na haifeki, inata rainonku harnima nazama wata atasha nasai gidannan, ana haka naga malam shikuma daga wani gari yake yana zuwa nan kasu wanci, tunda naganshi nace ina sonsa yaki amincewa tunda yasanni, saina kaishi gun boka ya asirceshi harya aureni namallakeshi, tundaga sannan bai kara zuwa garinsuba, to kinji yadda abin yakasance." Inbanda kuka ba abinda uwani take, tana nadama datasan asalin labarinta toda bata yadda ta 'bata rayuwar taba. ********* Rayuwa mai dadi su najwa ake abin sha awa har ta sami ciki suna tattalinsa kamar d'anyan kwai a kan dutse. ********** Haka su wani suke rayuwa cikin 'kunci yara har gidan suke lekowa ganin su. Ga ciki ya bayyana ajikin uwani, wanda tasan na osi ne kuma ance yanada hiv. Tarasa yadda zatayi darayuwar ta. Kuma yayan ta shima yadawo gida ashe fashi yake aka harfeshi a hannu. Yana gida yana jinya harya d'an sami sauki. Shawara sukayi susaida gidan su bar garin. Haka kuwa akayi suna tawo kano ta dabo. Suna zuwa garin barayi suka sace kudinsu, uwani kuma tayi tuntube ta fadi, jini ya balle mata haka suka sami wani dan kango suka zauna. Yusha,u yayan uwani shine yatemaka yasamo musu ruwa ta gyara jikinta . Haka suka cigaba darayuwa awannan kangon, yusha,u yafuta dako sukuma bara suke. Yauma sun tawo bara sukaga wata mota, dagudu sukazo gunta, suna lekawa danyin bara wazasu gani. Su affan ne da bybe su namiji, sun tsaya siyan lemo sa ayaba, zubewa uwani tayi agaban affan tana neman yafiyarsa. " tashi uwani ba komai nayafe miki tunda dadewa." Affanne mai wannan maganar. Yafiyar najwa tanema itama ta yafe mata. Gayamusu halin dasuke ciki sukayi, sun tausaya musu, inda affan yanemin kwatancan inda suke gobe zaizo. Gaya masa sukayi yabasu kudi sukayi masa godiya. ********* Washe gari affan yazo kangon dasuke, yadaukesu duka. Wani gidan mai daki biyu sai karamin tsakar gida yabasu kyauta, godiya suke mai harda kukansu kudi yabasu yace suyi sa na a. Yashe gari uwani taje asibiti akayi mata gwaji, allah yatemaketa bata da HIV murna harda kuka. Abincin siyarwa suka fara dalemo kuma suna ciniki shikuma yusha u akofar gida yayi tireda yana saida kayayyaki. Isilamiya suka samu dukansu suka koma har yusha u, din. ********************** ⬇ ************************** ********** Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** ALHAMDULILLA ANAN NAKAWO KARSHEN WANNAN GAJERAN LABARIN ALLAH YASA MU AMFANA DA AKON CIKI AMEEN. *INA MIKA GAISUWATA AGAREKU MASOYANA NIMA INA ALFAHARI DAKU* *JINJINA GAREKU YAN ZAMANI WRITERS ASSOCIATION ALLAH YABARMU TARE YAKA DAUKAKA AMEEN SOYAYYAR KU AJIKIN BARGONA TAKE 💋💋❤