*************************⬇********************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************* *YAREEMA ASAD🌸* {Saɓan taƙu} a historical fiction *HASKE WRITERS ASSOCIATION* Home of expert perfect writers💡 *Story written by* Khadeejat Dahiru *SAKO* _Assalama alaikum masoyana masoyan littafai na da fatan kuna ciki lafiya kamar yadda kuka sani baya da shekara biyu na yi littafina mai suna yarima Asad to yanzu kuma ga shi yasake dawowa tare da wani saban salo mai dauke da birge fa kuma zaku karantashi a kyauta domin nuna maku irin kaunar da nake maku masoyana fatan zaku bani haɗin kai wajen rantamanin comment🤓_ GARGAƊI wannan littafin ƙirƙiraran labari ne kuma ɗan girman Allah idan kina da ra'ayi ki fara karantawa yanzu kada sai nayi nisa ace min daga farƙo sannan ban yarda wani ya daukar min littafi ya sayar min ba ko kuma ya dora min shi a wani manhajar ba na yarda da tura group group Amman ban yarda koda facebook a saka min shiba saboda wasu pages na dauke da lambobin waya bana san lambata ta kareɗe duniya fatan zaku dauka😊 Gaba daya wannan page ɗin na mallaka ma yan Daura shi rankata kaf ɗin ke kinsan yar daura ce to kema na mallaka maƙi badan saboda da kauna da soyyayyar daƙe tsakanina daƙu😘 Babi na farko 1 Motoci ne ƙirar marcenɗi baƙake guda shidda sun hayo layi ko wannen dauke da lambar yarima 1 har zuwa yarima 6 motocin yan sanda ne gaba da baya sun yo rakiya ba abinda ke tashi sai jinyaryar yan'sanda duk ida suka gitta sai an kallesu wata kofa ce aka shigo dauke da rubutun *welcome to Daura*{ta Abdu tushen Hausa} tafiya suka cigaba da yi a nitse har suka kai ga baƙin gidan sarƙi yan sanda suka fito dan tseda mutane sai da kaf mototocin yarima suka gama shiga kafin su ka cigaba da wucewa bayan sunyi parking aka buɗe wa yarima ya fito kafar sa ya sako Mai dauke da wai takalmin wanda tunda nake ban taɓa ganin irinsa ba sanye yaƙe da white suit agogonsa fara takalminsa fari komai na jikinsa fari ne ban ƙara gigicewa sai da na matsa na kalli fuskar sa kyawunsa bai misaltawa hadaɗɗen ajin farko wanda kalo ɗaya,zaka masa kasan yana jikin hutu tafiya yake escort na take masa baya,tun da suka shiga fadawa,dogarai,bayi ke zuɓewa dan kwasar gaisuwa Amman shi wayarsa kawai yake ɗan nawa koda suka isa ga fada. Sarki ne ne zaune kan kuragar mulƙi da fadawa a gabansa shigar sa ke da wuya fada kowa ya mike suna kwasar gaisuwa "Barka da zuwa yarima yarima mai jiran gado"wani bafaɗe yace"yarima ya amsa"ya na zama kowa ya gaisa sarki ya miƙa masa hannu cikin jin daɗi yace"Barka da zuwa ɗan na"sai anan yayi murmushi yace"yawwa mai martaba" sarki yace"haƙika naji daɗin dawowarka dan haka ka shiga ciki kaci abinci ka huta anjima karfe huɗu mu haɗu a dakina"tashi yayi suka fita escort na binshi alamu ya masu dasu koma. Direct bangarensa ya nufa bayi nata aiki duk inda ya wuce sai gaidashi Amman hannu kawai yake daga masu yana zuwa yafi daƙin da kallo irin yadda ya chanza ya tasha kayan alatu da more rayuwa a cikinsa babu abinda babu a ciki lumfashi yaja yace"can't love you less my father"{banza iya kwantata yadda nake kaunarka ba mahaifina}.ida shiga uwar daka yayi ya zauna kan gado ya fara rage kayan dake jikinsa. Kilishi zaune kan kilisarta Bayi nayi mata fifita wasu kuma suna bata kaya marmari a baki wata baiwa ce ta rogo da gudu ta zube a gabatan tana haƙi tace"ranki shi daɗe yarima ya dawo"kilishi ta furzar da tuffar dake bakin ta ta miƙe tace"mairo kin tabbatar da abinda kike gayamin yarima ya dawo" mairo tace"wallahi yanzu daga faɗa nake tabbas naga yarima"kilishi ta yarfar da hannuta tace"ba shakka baya ta haihu ta buji iska tayi gaba bayi suka mara mata baya. Bayan yarima ya cire kayansa ya shiga ya watsa ruwa ya fito saye da tuwul mai ya shiga shafawa yana gamawa ya dauki farar jallabi ya saka ya kabbara sallah koda ya daga hannu ya daga yayi addu'a kusan minute 30 kafin ya shafa ya tashi ta baya ya fita zuwa daƙin Fulani already ta san da zuwanshi da ko iso ba aminci falo ya zauna kan kujera Fulani ce ta fito da fara'ar ta bayi na bayanta ta sallame su tace"oyoyo my son"miƙewa yayi yace"thank you mum nayi rashin ki sossai" dariya tayi tace yanzu ba gashi ka dawo ba Hanifah ce ta shigo da gudu itama ta baiwar ta ta rugo ta kadandamesa tace"You Are highly welcome my darling brother nayi kewarka matuka" tsawansa ya rage yace"to Kuma bagani ba darling" Hanifah tace"ina tsaraba"Fulani "daga dawowarsa sai tambayar tsaraba bama ki bari ya huta"Asad yace"tana daki"Fulani tace kaga tashi muje muci abin cin nan kafin ya huce"dariya yayi yace"kuma idan yayi sanyi bana ciba"dariya tayi tace"kai mai hali baya chanzawa" Asad yace"kema sai randa diyarki ta girma"Dukansu dariya sukayi suka ɗun guma zuwa dining ɗin" Kilishi zaune a falo ita da Abdulra'uf shi sai kai da kawo wa yake da ga ita sai shi sai jakadiyar ta Abdulra'uf ya kalleta tace"Hakika uwata kinzama munafuka marar cika alkawari da kanki kika fadamin cewar ba yarima ba dawo cikin gidan nan sai gashi rana tsaka ya fado"kilishi ta mike ta dafa shi tace"kayi haƙuri ka kara bani wata damar" Abdulra'uf cikin zafi yace"wata dama kike so na na baƙi dama nawa na baki a baya" Kilishi"ka kara hakuri yanzu aka kara wasan akafta" To ya kukaji Share Comment 09121692033 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FwndtmiicpLFSArXOxQouk Dan Allah wanda ke cikin group 1 kar ya shiga wannan dan Allah dan Allah *YAREEMA ASAD🌸* {Saɓan taƙu} a historical fiction HASKE WRITERS ASSOCIATION *home of expert and perfect Writers* story&writting by *khadeejart official💃* wannan shafin na mallaka ka shi ga mutane ne na biyu yan amana Khadija&Hajara ina sanku irin sosai ɗin nan Allah ya kare min ku mutanena na amana👌 page 3&4 Amatullahi Amatullahi,wata dattijuwar mata ce dake zaune a kan tabarma wanda a shekaru baza ta wuce shekara 30,zaune a tsakar ta saka faratin koko da a gaba tana kalo,"amatullahi"umma dan Allah gani nan handout ɗita nake nema"umma tace"waike kullin baƙi tashi neman handout sai zaki tafi makaranta safinatu ce ma da bata gajiya kullin sai kin makarar da ita". "Assalama Alaikum" "Amin alaikis salam safina an fito yanzu nake ta faman kiran ta kinganta ko karin safe ma batayi ba. safina ta sami waje ta zaune tace"umma ai kinsan mai hali baya fasa wa Ina kwana". "lafiya qlau safina ya umman ku". "lafiyan ta qlau tama ce na gaidake". Amatullahi ce ta fito sanye da material mai flowers baƙi ta pink sai ratsin fari ta saka abaya pink da ta sha guga hijabin taji jiki Amman kasancewar gyaran da ake mata bai bari ta nuna ba,yarince ce karama wanda kallo ɗaya zakayi ka gane hakan sai dai tana da garin jiki Amman ba sossai ba,baka ce Amman Black beauty idanun ta tamkar na mace dan idan da dare fitila ta haska ta takan ma iya baka tsoro Amman sam batayi kama da mahaifiyarta ba da mahaifiyar tamkar bafullatana ita kam kamar baturiya dan dai bakake. safina tace"Amatullahi kiyi sauri kin dai ji abinda malan zailani ya ce game da saban malamin da zai dauke general English yau kuma kinsan gaba daya yan deparment ɗin mu kada muje bamu sami waje ba". tsaki Amatullahi tayi tace"wai maganar da Malan zailani ya miki shine kika dauka aini wallahi jinsa nake kefa kiji wasu kaidojji da yake zaiyanawa tamkar wani dan minister ko shugaban kasa to Kinga idan tafiya zakiyi kiyi dan Ni sai na karya" umma tace"kedai ko Amatullahi baza ki chanza ba to nima bazan gaji da miki addu'a ba Allah shiryeki" "Amin" ta janyo kwanukan tace"safina kizo muci" badan komai ta saka hannu suka fara ci ba sai ɗan ta san wannan abincin sai tayi awa tana cin abinci. bayan sun gama umma ta zaro dari biyu ta bata safina tace"a'a umma Abba ya bamu" Amatullahi ta maza ta amsa tace"muje mun ƙara" tace"ki dai rago idan ba haka ba gobe ki tafi a ƙasa" suka fita kofar makarantar DR YUSUF BALA USMAN haka na gani nanne a baƙin makarantar dalibai ne keta tururuwa wajen shiga wasu a ƙasa wasu a mota wasu a keke. su Amatullahi ne suka sallami a dai daita suka shiga sauri safina ke tayi tamkar zata tashi sama Amatullahi kam ,kamar wanda kwai ya fashe wa cikin ciki a haka har suka shiga safinatu tayi Hamdala ganin malan bai shigaba waje suka samu suka zauna Hall ɗin duk hayaniyar maza da mata a ciki. wata bakar motace ƙirar marcendi tazo ta faka a gaban autorium sai da yayi kusan minite 5 kafin a fito,sanye yake da bakar suit da baƙin takalmin komai na jikinsa baƙi ne yayi matukar amsar sa kayan wayoyinsa ya dauka ya shiga cikin Hall duk kan matan dake ciki tsayawa sukayi kallan sa Amatullahi kuma da hankalinta na kan charting da take. Asad ta matse fuska sakon hayaniyar da ta cika masa dodon kune,hannu yake dagawa alamun a saurara Amman aji ya sai da yayi kamar zai fita sannan akayi shiru. glass ɗin fuskarsa ya aje yace"gaskiya You Are out of you senses Taya zan shigo cikin aji kamar na shiga kasuwa" yan ajin suka kwashi "sorry sir" Amatullahi kam haushi tamfar a ran ta ganin yadda yake magana. Asad ya fara magana yace"i hope Sauran lectures ɗin ku sun muku bayani na kafin na bayyana a nan" yan aji "Yes sir" hancinsa ya done yace"Amman gaskiya jikin ku kam akwai wanda basu wanka suka fito dan jin yadda ajin ke wani irin wari" ajin yayi shiru Amatullahi tace"bamayi uwarka tazo tayi mana" kowa jiyowa yayi dan ganin wanda tayi maganar,ita kanta Amatullahi batasan maganar ta fito ba. Asad yace"waye yayi maganar nan" akayi shiru cikin tsawa yace"nace wanene yayi maganar nan" bilkisu ta miƙe tace"sir Amatullahi ce" okay why is shi tuni jikinta ya dau kyarma. Asad yace"get out from my class and uwata zatazo ta maƙi wanka" jikinta na tsuma harda qwallarta ta fita kalan bilkisu yayi yace"follow her kema tunda gidan ku ba rifin asiri daga yau kada na kara ganin ki cikin class ɗina. cikin jin zafi ya kwashi kayan sa ya fita yace"mu haɗu next week Kuma ku tabbatar ajin baya wannan warin" office ta nufa ya rasa abinda ke masa daɗi. safinatu ta fito da sauri ta tarrada Amatullahi gaban bishiya tana zaune"haba Amatullahi wai ke miyasa bakya jin magana da zuwansa har kin Hauda sa" Amatullahi tace"wallahi bansan na fada ba nima" safina tace"yanzu ke ko wani mataki zai dauka a kanki naga ya kori bilkisu yace kada ta kara shigo mashi aji,Amman ke yadda za a yi tashi muje wajen malan zailani ya taya mu bashi hakuri" cikin jin zafi tace"Allah ya kiyayi gagarina da sarar shuka Amman wallahi bazan bashi hakuri ba" kuyi manage share like comment *YAREEMA ASAD🌸* {Saban taku} a historical fiction HASKE WRITERS ASSOCIATION *home of expert and perfect writers* *Rubutawa&tsarawa* khadeejart official👌 wannan page ɗin mallakar mutane biyu ne masu daraja a wajena *Khadija name sake* *hajara Haruna mai nasara* Alherin Allah ya kaimaku a duk inda kuke🙏 ina gaida mutane biyu kamar yadda nayi alkawari *mmn husna* & *zainab* _zuwa ga dukkan groups ɗin dake karantawa basa comment ina mai farin cikin sanar daku cewa na daina wahalar banzan sake turo wa zuwa group ɗin ba dan idan ma na gan shi a group ɗin zan maida abuna na kuɗi💁‍♀️tunda bakwai iya karantawa kuyi magana yawwa idan kuma mutun na san shiga group ɗina yamin magana ta lambata kamar haka 09121692033 dan Allah banda kira saboda kilan ina wani uzurin mutun zai kirani kuma idan ban daga ba yaga na mashi wulankanci duk wanda yamin magana ta whatapps zan karanta kuma na sakashi😊_ page 5&6 _____safina tace"wallahi Ni dai wanan baƙin halin naki ya isheni ke sai bakar zuciya yanzu fa ji abinda kika ja wa kanki a aji ke da yake kece mai bakin magana babu wanda yayi magana sai ke wallahi idan har baki chanza halin ki ba zai kaiki ya baro ki". tsaki Amatullahi taja ta dauki jakar ta tace"Ni na tafi kuma abinda zan gaya maki kada ki kara biyo NI gidan mu" safina tayi murmushi tace"idan da sabo ai na saba kuma haka zan ringa maki addu'a Allah ya shiryeki Amatullahi" yarima na zuwa office ya zauna yake ta huci tun da yake ba wanda ya taba zagin mahaifiyar sa daga Fulani tashi yayi yace"i will take a serious action on this dirty girl"{zan dauki mummunan mataki akan wannan kazamiyar yarinyar} fita yayi zuwa office din school appears ya ce yana san list ɗin daliban neutroco student kaf ɗin su. malan zailani yace"Dr Asad ko lafiya" cikin tsawa Asad yace"I'm in need of it ko dole sai ka tambayeni ne abinda zanyi dashi ne" jikin malam zailani na rawa ya maza typer masa list ɗin ya bashi ya figa ya fita". yana zuwa office ya aiki Massinger sa da ya kira masa daya daga cikin daliban neutroco ba jimawa sai gashi da wani. Dr Asad ya tambayesa yace"ya sunan wannan yarinyar da na kora dazu" dalhatu yace"ta farko ko kuma ta biyu" Asad yace"ta farko " yana mashi kallan da wayazo dawa ya koma. dalhatu ya fara tunani yace"sir ban san sunanta ba" Asad ya mike ya buga teburin yace"I'm possible zaka fada ko kuma sai na tsayar maka da karatu. cikin inda inada dalhatu yace"sunanta A'isha Kabir dikwa" mai mai mata sunan yayi yace"Aisha Kabir dikwa" dubu biyu ya zaro ya watsa masa yace"ka je ka sayi sabuli kayi wanka ka daina shiga cikin mutane kana tashi". maza yayi ya washe kudin shi ko haushin maganar bai yi ba yace"nagode sir" dubawa yayi yace"ashe ma itace 001 zanyi maganin ki" wallahi idan banga comment ba zan maida shi na kudi fakat *YARIMA ASAD* {saban taku} a historical fiction👌 HASKE WRITTERS ASSOCIATION *home of expert and perfect writters💡* tsarawa da rubutawa *khadeejart_official💃* *ina gaidaku mutane na amana* _zainab_ _khadija admin khadeejar conservation_ _hajara mai nasara_ _hafsat muhammad_ _momyn abdallah_ _shamsiya muhamad_ _zainab zakari_ kai wallahi kuna da yawa idan na fara Zai ya naku wallahi sai na kwana hakika ina bala'in kaunar comment ɗinku 💃💃💃 keep it up💗 page 7&8 ...................yarima ya zaro waya ya kira school appears yace"yana san a kawo masa file na A'isha Kabir dikwa Amman tabbas ya kasa gaskata shi Alhaji Kabir dikwa dan kwangilar da ya sani ko kuma wani ne,Amman miya kawo diyar sa local school haka?,tsaki yayi ya share ganin idan ma diyarsa ce bazai hana aiwatar da abinda yayi niya akan wannan yarinyar ba duk duniya babu mahalukin da ya fi kauna fiye da mahaifiyarsa wanda ta rasu Amman yau har a samu fitsarar yarinyar da zata zageta yana wannan tunanin yaji an turo kofa. "Assalama alaikum" Masinja ne ya shigo dake da file a hannuna hannu biyu biyu ta miƙa masa yace"gashi sir" Amman yayi ya kwashi wayoyinsa yace"ka rufe office ɗin na tashi". bakin mota ya shiga yayi tafiyar sa. Amatullahi na zuwa gida ta taradda mahaifiyar ta tana shara Amman tayi ta gama ta shiga daki ta ta hau kan katifa tayi tagumi. yarima na zuwa gida ya nufi bangarensa wanka yayi yayi Sallar azahar yayi addu'o'insa ya fice bangaren Fulani kamar kullin yadda ya saba abinci yaci ya wuce inda ake kiwata masa dokunan su,bayi sai kaida kawo suke. kilishi ce falo ita da Abdulra'uf yace"umma wallahi matukar baki cika min Alkwarina ba zan fita tsakiyar fada in tona maki asiri cewar ke" bai ida fadaba ta maza ta rufe mai baki tace"haba Abdulra'uf kamar yadda nayi maka alkwari wallahi wallahi sai na kauda yarima,kuma nazo na kawar da sarki babu wanda zai kara mulkar garin Daura idan ba kai ba" Dariyar mugun yayi yace"muɗin kika cikamin alkawarina kema zaki ga tukwuicikin ki" yana kaiwa dai dai nan ya fita kilishi ta duke tace"Abdulra'uf ya zame min hadari a rayuwa ta" jakadiyar dake tsaye tace"ranki shi dade mizai hana ki saka boka laritu ya mantar dashi akan wannan abin da kullin yake maki barazana dashi" kilishi tace"zan duba yi yuwar hakan ta baza riga ta tashi. yarima na zaune ya sa wani fadade da ya kira wo masa Sarki cikin gida ba bata lokaci sai gashi. "Allah ya taimaki yarima mai jiran gado gani" yarima yace"kamar kasan Alhaji Kabir dikwa ko?" Sarkin gida yace"mutumin da yayi kwangilar sabuwar court dake kan Giwa ko" yarima yace"shifa Amman yanzu yana ina kuwa" Sarkin gida yace"Allah sarki kwanakin baya kana America a ka dira har gidan sa aka mashi yankan ragon da ba a san wanene ya mishiba" yarima yace"zaka iya tafiya" tashi yayi ya shiga cikin gida wayarsa ya dauko ya latsa wata lamba ya kira yace"itace na baka nan da kwana biyu dukan wani information ina so game da ita" *wacece Amatullahi* sunanta na gaskiya A'isha Kabir dikwa diyace ga Alhaji Kabir mahaifinta haifaffen garin Daura ne a wata unguwa ana ce mata kofar baru mahaifinsa su ukku kadai ya haifa mato shine babba sai Alhaji Kabir sai kuma autarsu zakiyya,Alhaji Kabir shi kadai yayi karatun boko mato tun yana karami ya tsiri shaye_shaye wanda ba karamin bakanta ran mahaifinsu yake ba shiyasa iyayenshi suka zuba masa idanu,wata rana aka wayi gari mahaifinsu ya rasu ba a yi arba'in ba innar itama tace ga garin kunan. duk yadda Alhaji Kabir yaso da mato su hada kansu ya ƙiya haka ya cigaba da kula da zakiya har Allah ya kawo mata miji wani dan kasuwa tayi aure a wani gari dake jahar Jigawa ana ce masa roni. ganin Alhaji Kabir shi ɗaya ya rage ya fita zuwa Adamawa dan neman aiki a chan ya gami da Amina mahaifiyar Amatullahi ya aureta bayan shekara guda ta haifi ɗan ta namiji yaci sunan mahaifin Kabir Ibrahim. bayan shekara daya ya rasu sai da tayi haihuwa kusan ukku a haka basa wuce shekara suke mutuwa. ba karamin damuwa sukayi da hakan ba sai da zakiya ta haifi mace ta bayan ta yaye ta mallakawa Alhaji Kabir ita dai dai da rana daya basu taba nuna mata ba ita ta haife ta mijin zakiyya Usman ma haka saboda yanzu su yaransu ma 4 maza ukku mace ɗaya sai dai A'isha kanje yin hutu. Alhaji Kabir cikin kankanin lokaci yayi wasu irin kudi har akan bashi kwangilar gina ginen kwannati. mato ma yayi aure shima cikin garin Daurar ne ya kama hayar wani gida shida matarsa. A'isha tana da kokari fiye da tunaninku duka boko da isilamiya sai dai ita zafi ke gareta abu kadan ke bata mata rai bata da hakuri ko kadan ta gama candy kenan aka zo har gida aka kashe Alhaji Kabir mato yazo ya kwashe dukiyar tsab ya bar garin hatta gida da suke ciki sai sallama aka masu cewar an sayar da gidan da suke ciki. sai makwabacinsu mahaifin su Safinatu ya kama masu hayar wani gida dan karami wanda ake biyan dubu ashirin duk wata. duk irin arzikin da mato ya tara suka gudu da matarsa itama ta kwashe kudi ta barshi a tsiyace ba arziki ya dawo. Amina bata tada hankalin ta ba dan ya kwashi kudin saboda ko bar kwashe ba shi za a ba da zakiyya Amman ita zakiya mijin ta mai kudi ne duk garin roni ba wanda ya kashi arziki mahaifin sa kuma shine babban malami har daga wasu garuruwan akan zo wajensa neman magungunan asiri da kuma hauka. Alhaji Ahmed maihaifin safina ya sanya su makaranta tare duk abinda zai wa safina namakaranta sai ya hada da Amatullahi. wannan kenan share comment like *YARIMA ASAD* {saban taku} a historical fiction👌 HASKE WRITTERS ASSOCIATION *home of expert and perfect writters💡* tsarawa da rubutawa *khadeejart_official💃* _thank You so much for you comment I really appreaciate may Allah swt blessed you life💃💗_ *page 9&10* *cigaba labarin* bayan kwana ɗaya. amatullahi kwance a kan katifa ta zubawa sillin idanuwa gaban tane keta mummunar faduwa wanda hakan ya haifar mata da figirci da kuma tsoro. Ammi kuma kuma na makwabta wajen rasuwar da akayi,Amatullahi na cikin wannan tunanin taji sallama "Assalama alaikum" jin Muryar kamar ta aunty zakiya yasa ta maza ta firgita ta ɗira daga kan katifa ta fita da gudu taje ta rungume aunty zakiyya. ramlat ce mai biyawa Amatullahi tace"waike aunty aisha miya sa ne baki girma idan fa kika karya mana ummar tamu". amatullahi taja baya ta tafe fuska tace"to sannu mai mama nima yau da bani da ita da nayi kuka" zakiyya tace"Kinga Amatullahi mu kara sa ciki" amatullahi ta kama hannun Abul mai kimanin shekara 3 wanda shine yayo kama da Amatullahi tamkar an zaga kara haske kawai zai nuna mata daman duk cikin ya'yan zakiya Amatullahi tafi kyau daga ita sa abillahi. bayan sun karasa ta dauko masu tabarma ta shifiɗa masu tace"bari naje na kirawo ummar na nan wajen rasuwar Inna gaje". aunty zakiya tace"to ga Abban mommy Nan ku gaisa a waje" mommy ce mai kimanin shekara 10 tace"aunty Amatullah zan biki". amatullahi tace"tashi mu tafi my sister". a kofar gida suka gamu da Abban mommy har kasa ta duka gaidashi ba yabo ba fallasa ya amsa,suka wuce. tare suka taho da Ammi,bayan sun dawo akayi gaishe gaishe ne Ammi tace"aje a taho da babban mommy suna shigowa aka gaisa. aunty zakiya tace"Amatullahi ta tashi ta fita Suda su mommy suje gidan su safna" amatullahi ta tashi ta hada kansu su ukku ita ta hudu suka tafi. aunty zakiya tace"Aunty Amina daman ba wani abu bane ya kawo mu munzo mu tafi da Amatullahi. gaban Ammi ya yanke yayi wata muguwar faduwa ta fashe da kuka tace"kullin wannan ranar nake jira dan na tabbatar ko min nisan dare wannan ranar na zuwa" baban mommy yace"Ammi ba haka bane Kinga nauyi muka dora maki shine muka yanke shawarar zamu tafi da Amatullahi kema sai ki kuma Yola chan cikin danginki tunda wanda yayi sanadiyar zuwanki ya bar duniya,zamu maidata gaban mu mu cigaba da kula da ita. taɓa ka lashe kenan to fah idan aka dauke Amatullahi kuɗurin yarima akan tafa😜 sai mun haɗu next page *YARIMA ASAD* {saban taku} a historical fiction👌 HASKE WRITTERS ASSOCIATION *home of expert and perfect writters💡* tsarawa da rubutawa *khadeejart_official💃* _wannan paging saudakarwane zuwa ga Khadija Nagode da kokari Bani da abinda zan biya ki Amman ina rokon Allah ya biya ki ya raba ki da iyayenki lafiya ya biya mana bukatun mu na alkhairi😊_ *page 11&12* Ammi tace"badamuwa tun da har kuka bukaci hakan nasan ko nan gaba zaku iya amshe Amatullahi tana faɗi kuka yaci karfin ta tashi tayi ta daga dorowa ta fara fito da kayan Amatullahi sai kuka take. tuni zuciyar Zakiya ta karye Amman mahaifinta bazai iya jure ganin ta cikin wahala ba tunda Allah ya rufa masa asiri ya zama dole ya amshe diyarsa. Ammi ta tashi tace"Bara na leka kofar gida na sami wani ya kira mana su. bayan sunzo amatullahi ta dubi akwatin da aka cika mata da kaya kalan Ammi tayi tace"umma ya naga kaya na a haka kuma" Ammi kasa magana tayi dan data kuskura ta buɗe baki hawaye dake makale ne zai kwaranyo. zakiya tayi karfin hali tace"ya zama dole mu tafi dake tunda anan nauyi ne aka barwa aunty Amina tunda Kinga yaya mato yadda ya zama Kinga dole dai mune zamu dauke ki A'isha. Amatullahi tace"wallahi babu inda zanje gwara mu zauna ko tuwan kasa munyi muci idan na tafi na barta aunty zakiya wa gareta dan Allah ku barni kada ku amshe Ni a daga wajen Ammi na roke ki na rasa Abbana bana so na marasa Ammi na". Abban mommy na kwalla ya fita zakiya ya kira ta bishi yace"bakomai kije kicewa Ammi na mallaka mata Amatullahi duniya da lahira na bar mata ita kuma bazan sake waiwayen amsar taba da yar Dar Allah daman ba asan raina zan amshe ta mahaifiyata ce ta takura min Amman zan koma dan yi mata bayani nasan zata fahimta. zakiya ta share hawayen ta shiga dakin Amatullahi ta hada kai da gwiwa sai shabar kuka take aunty zakiya ta duka ta dafata tace"bakomai Amatullahi ki zauna wajen ummarki Allah ya jikan yaya Kabir". ana nefa kowa ya warware aka cigaba da hira sai kusan bayan la'asar suka tafi har safina ma tazo sun gaisa. babban momy ya zaro dubu ashirin ya ba Ammi da kayan abincin da ya kawo masu ba karamin dadi suka ji ba" yarima zaune akan kujerar falansa ya daura kafa daya kan daya yana danna system wayarsa ta dauki ringtone duba yayi yaga Salim baija wani lokaci mai tsayi ba ya daga Amin yace a wayar shine"shigo" ya datse wayar. shigo yayi ya mikawa yarima hannu suka gaisa yarima ya kallesa yace"ina fatan kazo min da kyakkyawan saka mako" salim yayi murmushi yace"kaima da kasan zan kawo maka shirita ai da baka bani aiki nan ba" yarima yace"kaga fadi min abinda ya kawo ka ina matsu na ji" salim yace"kamar yadda ka bukata yarinyar nan de marainiya ce hasali ma gidan haya suke zaune da mahaifiyar ta kuma gidan yanki gidajen mai unguwa rabi'u ne kuma mahaifinta yayi shekara kusan 3 da rasu" yarima tashi yayi yayi wata dariyar mugun ta da shi kansa bai san raban shi da yayi irin taba yace"kaga zan je na nuna mata cikar iko irin na yarima". salim yace"kai yarima dan Allah kadai tausaya mata kaga dai marainiyace" yarima yace"to ni ma ba Marayan bane" *waye yarima* Abdulrahaman Ali Ibrahim shine cikkaken sunansa ɗa'ne ga mai martaba sarkin daura Alhaji Ibrahim shine sunan sarkin Daura wanda ya gaji saurata a wajen mahaifinsa marigayi Ali mahaifinsa shi kadai ya haifa ganin haka ne bayan rasuwarsa aka hadasu aure da dan diyar kishiyar mahaifiyarsa wanda Alhaji Ali ya rike tun tana yarinya, Alhaji Ibrahim baiso auran ba Amman ganin saurautar na neman barinsa ya sashi yarda da auran aka naɗa shi sarki *Garin Daura* Bayan auransa da shekara daya Hajiya maryam wato kilishi ta haifi diyarta mace wanda taci sunan Hajara kilishi tayi bakin ciki sossai dan ita burinta kullin ta haifi na miji. bayan shekera 3 ta kara haihuwar wata macen wanda taji sunan Khadija ,kilishi ta rasa mike yi mata daɗi a duniya. wata rana sarkin Adamawa ya gayyaci sarkin Daura Bayan yaje ya ce "badan komai ya gayyace sa ba yana san bashi auran yarsa rauda idan har ya amince da hakan" Alhaji Ibrahim yaji dadi matuka anan take aka daura auran a fadar Adamawa aka taho da amarya. kilishi tamkar zata mutu dan haushi da baƙin ciki Amman ba yadda ta iya. bayan shekara biyu rauda ta haifo danta namiji da ya ci sunan Abdulrahaman ana kirasan da yarima Asad,sakamakon sunan mahaifin rauda ne Sarkin Adamawa. Tun yana jinjiri kilishi ke san sace shi ko ta kashe shi ganin haka yasa rauda kiyayewa da kuma kula dashi. saida yarima ya shekara 7 a duniya kilishi haifi Abdulra'uf ,rauda bata kara haihuwa ba. sarki ya dauki san duniya ya ɗorawa yarima inda duk inda zaije shi ne ke masa Rakiya. hajara cikin bakin hali na maihaifiyar ba abinda ta bari dan harma ta dame ta ta shanye kullin suka hadu da yarima sai ta dankwasheshi duk da bayin dake tare dashi baya hana Hajara Bugunsa. Tun yarima na karami sarki ya maidashi Adamawa wajen kakansa anan ya hadasu ya sakasu wata makaranta bayan sun gama ya kaisu b.u.k inda anan yarima yayi first degree ɗinsa sarkin Adamawa na mugun san yarima,daman ko cikin ya'yansa yafi san rauda kuma gashi ɗan ta yaci sunan ta,rauda mutun ce mai hakuri wanda ta tashi hannun kishiyar uwa wanda ta takura mata ta hana ta sukine ganin haka tana gama secodry ya aurar da ita. bayan yarima ya dawo gida mahaifin sa ya sama mashi lecture a Dr Yusuf Bala Usman. yarima nada shekara 22 a duniya ne wata rana aka wayi gari an sakawa rauda guba a abinci kuma baiwar da ta saka ta tattara kayanta ta bar gidan. sai da yarima yayi sati 2 a asibiti bayaci baya sha da kyar sarki ke lallabasa yana cin abincin. bayan mutuwar ta da shekara daya sarki ya auri zainab wanda ita kadai ke kula da yarima bayan rasuwar mahaifiyarsa. kilishi kuma cikucukun amshe saurautar take tabawa Abdulra'uf zainab wato kilishi diyar ta daya Hanifah wanda sai kace uwarsu daya ubansu daya da yarima ganin yadda sukayi wata muguwar shakuwa. Hajara tayi aure a Abuja,ita kuma Khadija tana cikin garin Daurar ina ta auri dan magajin garin. jakadiyar rauda itace mace ta farko da fara daukar dawainiyar yarima tun randa mahaifiyarsa ta rasu dan ko jinyar asibiti ma ita tayi shiyasa koda magana jakadiya ta mashi yana ji. ko cikin bayi ita ya yarda da ita ko gyaran daki saboda yasan za a iya hada baki da wata baiwa a cuce sa ko a abinci daga wajen zainab jakadiya ke amso masa ko kuma yaje yaci. itama da kanta take girka masa dan har ga Allah tana kaunar yarima har cikin zuciyar ta wannan kenan. idan har kuna comment yadda ya dace kilan kuringa samun page 2 a rana safe da dare insha Allahu😜👌 *************************⬇********************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************* 🪀09121692033 dan Allah karku kirani charting kadai *YARIMA ASAD* {saban taku} a historical fiction👌 HASKE WRITTERS ASSOCIATION *home of expert and perfect writters* *©khadeejat official🥰* wannan shafin yayi tsutsuwa ya dira ga Khadija my name sake bazan taɓa gajiya da mallaka maki page ba ina godiya marar adaɗi💗😊🙏 masu naima daga farko zaku iya yiwa wannan lambar da zan rubuta maku magana insha Allah zaku samu,dan Allah banda maza matar aure kuma banda kira kumata magana kawai ta whatapps ~07032620576~ ta whatapps only banda maza _wasikar godiya zuwa ga masoyana_ _Hakikka ba karamin daɗi nake jiba tayar da kuke nunawa mun kauna tare da littafi masu sani a group Nagode masu bani admin nagode a baya ma na sami irin wannan kaunar a littafina yarima Asad na daya Yanzu gashinan yazo return amman still kum an shesa hakika addu'o'inku ba karamin tasiri suke a waje na ba 🙏🙏ina godiya matuka da gaske wanda nake maidawa comment da ma wanda bana samun damar maidawa ina karantawa kuma yana min daɗi a zuciyata Allah ya jibanci dukkan lamiranku👌🥰_ *wasan fa ya soma chanzawa✍️😜* page 13&14 __________"Assalama alaikum" Salama ce ake dokawa daga bakin kofar gida Amatullahi dake zaune kan abun tsalla a tsakar gida tace "Ammi kamar sallama Abban safina fa" Ammi tace"to ki tashi ki leka kingan nima naji kamar shi". Amatullahi ta zuri takalman ta ta fita har kasa ta duka ta gaidashi yace"Innar taki tana ciki kuwa" Amatullahi tace"ey tana ciki" yaje to kije kice ina sallama". Bayan ta shigaAmmi tace"daukomin hijabi ta kan dokin kofar kice ya shigo". tabarma aka shifiɗamasa ya zauna yace"Barka dai Amina da fatan kuna lafiya". Ammi tace"lafiya qlau" Abban safina yace"daman ba wani abu bane ya kawo Ni nazo ne akan na shaidamaku dazu bayan an gama sallar azuhur mai gidan nan da kuke ciki ya sheda min cewar ya sayar da gidan dan haka nazo na baku notice ɗin yau kadai dan wanda ya shiga ma gobe zai murje ya fara aiki hatta nima nawa ya siya duka har gidan su jummai to Daman Kinga Ni dan Kano ne aiki ne ya kawo Ni kuma na nemi transfer zan koma mahaifata da zama ɗan mu zuwa anjima ma zamu tafi. "innalillahi wa'inna illahir raji'un" Ammi ta furta tace"Abban safina yanzu ina zamu dosa kai talaka na shan kalo a duniya" baban safina ya sa hannu a aljihu ya zaro dubu goma yace"Ammi ga wannan kunyi kudin mota dan sauri nake kafin magariba mu isa insha Allahu,yanzu idan na koma yan gidan zasu zo su muku sallama". Ammi kasa ma mashi godiya tayi haka ya fita Ammi nata kuka Amatullahi tace"wai Ammi ke ina dangin ki suke ne basai mu koma wajen su ba". Ammi tace"Amatullahi a sannu zaki san dalilina na ƙin koma wa ta Adamawa" su safina da yan gidansu ranka kaf suka zo akayi sallama Amatullahi da safina suka kadan dame junansu sai kuka suke yi da kyar a ka rabasu dan basu taba rabuwar koda kwana ɗaya ba sai dai idan Amatullahi zata roni wani lokacin ma tare suke tafiya. suna kallo motar su taja ta tafi. bayan sun koma gida amatullahi tace"yanzu umma miye abinyi" Ammi tace"bari muga zuwa goben idan munga mai gidan mu rokesa ya bamu koda sati ma". washe gari Ammi ta kasa ci ta kasa sha tunani ne tunkushe cikin kwakwalwar ta Amatullahi na ta faman kada kaya. sallama suka ji kadam an shigo gidan gardawa ne majiya karfi su biyu. Ammi tace"malan lafiya zaku shigo mana gida babu ko iso" daya daga cikin su lado yace"lafiyar ce ta kawo haka zanje an fada maku cewar ku tashi kafin Yau,dan haka yanzu zamu fitar maku da kayan ku. basu jira mizasu ce ba suka fara fitar da yan abubuwan da suka rage masu dan amfani,suka aje masu a kofar gida. bayan sun fita Ammi tace"yazama dole na koma garin mu ko da kuwa manira zata kashe ki Amman ke dole kizo ki tafi roni " Amatullahi tace"Umma zan biki duk abinda zai sameki ya sameni nima" haya suka dauka suna tafe suna kuka wata bakar mota ce har ta gitta ta dawo garesu mai tuka motar ne ya fito da sauri. yace"a'a miya sameku naga kuna tafe kuna kuka" Amatullahi tayi karfin halin cewar"muma bamu san inda zamuje ba inda muke haya ne aka koremu" karka dai yayi yace"ina danginku " Amatullahi tace"duk sun mutu bamu da kowa kuma bamu san inda zamu je ba" Salim yace"umma idan ba damuwa kuzo na kaiku wajen mahaifiya kafin Ku sami inda zaku je mana" sai a sannan Ammi tace" haba yaro kawai kayi tafiyar ka haka kawai baka sanmu ba bamu sanka ba kane mi ka taimaka mana" Salim yayi murmushi ya zaro ID card dinsa yace"mama Ni jami'in tsaro dan haka ki saki jikin ki dani taimakon ku ne zanyi" dakyar ya lallaba Ammi ta yarda suka tafi. gidan su ya kaisu ba laifi gidan mai kyau ne dan harda gate din sa ma horn yayi mai gadi ya bude suka shiga. falo ya tarar da mahaifiyarsa da bayan sun gaisa ya mata bayani. dattijuwar tace"ba komai kaga na sami mai aiki daman laure mijin ta ya rasu tana gida" Salim yace"Kinga Ni kuma na dauki yarinyar daman mubaraka kullin cikin complain ɗin aike take" Hajiya tace"gashi bansan sunan baƙin ba" Amina ta dukar dakai tace"sunana Amina ita kuma wannan A'isha " Hajiya tace"Allah sarki Ni kuma Hajiya rabi" wannan da nane Salim shi kadai na haifa. *bayan sati guda* su Amatullahi tamkar yan gida Hajiya rabi na mugun kyautata masu tamkar yan uwanta tun basu saki jiki da suba har suka saba. amatullahi ke shiri dan salim yace"yau zai maidata gidan sa dan taya matarsa aiki" Ammi tace"nifa Amatullahi tsoro nake ji kada ya cutar dake" Amatullahi ta aje mudubin dake tace"umma da ace mutanen nan da na niyar wani abu a kan mu di tuni sunyi ki barni na kyautata masa kamar yadda suka fitar damu daga rana Ammi" Ammi tace"to Amatullahi ki zama mai kiyaye wa akan dukan abinda zakisa ransu ya bacci" "to Ammi insha Allahu" salim ne ya turo kofa yace"Amatullahi fito mu tafi". Ammi ta rungume tace"to Ammi sai na zagayo". bayan sun tafi ya dauki hanya bai tsaya ko ina ba sai cikin fada security suka bude mashi kofa ya shiga. mamaki ne ya kama amatullahi tace"ya salim dama gidan ka a cikin gidan sarki yake ne. Salim da tuni kirjinsa ke bugawa yace"a'a zan amshi sako ne wajen wani abokina" parking yayi yace"muje ki rakani" karkada kai tayi tace"a'a kaidai ka shiga ka fito" Salim yace"yanzu fa zamu fito" ganin ya takura ta yasa ta fito badan taso ba" yarima ne a gardern ya juya yana wa dokin sa hoto. Salim da sallama ya isa Amatullahi na biye da shi a baya kamar yadda suka shirya kenan yana kawo ta nan Salim kuma zai juya ya tafi. Salim ya dubi amatullahi yace"Bara nayi mantuwa a mota" nan ta tsaya yarima na jiyowa suka yi ido hudu da Amatullahi. gaban tane yayi mummunan faduwa ganin yarima a tsaye. gunta ya isa ya waka mata mari guda 3 kwarara yace"a tunaninki Salim a banza ya taimake Ni to nine Nan na sashi aiki" dariya yayi yace"kin dauka zaki silla ne to kin shigo cikin azaba da ukuba cikin gidan nan zaki kasance kassantaciyar baiwa mai mun bauta" kuka amatullahi ta fashe dashi tace"dan Allah kayi hakuri kada ka cutar min da mahaifiyata" kafa ya sa ya take mata kafar ta wani irin kara tayi sakamon azabar da taji" yace"Ni an gaya maki bana kaunar mahaifiyar ta wane" Tofa!!!! 🪀09121692033 idan banga comment ba ya zama na kuɗi😊🙄 *YARIMA ASAD* {saban taku} a historical fiction👌 HASKE WRITTERS ASSOCIATION *home of expert and perfect writters* *©khadeejat official🥰* _dedicated to my love khady_ *advertising* Ina masoyana masu san faranta min rai a ko daushe😜ina masoya dan wanke masu dan samun garin danwake tare da haddaden yaji dakan hannu🙆‍♀️to ku kwantar da hawayen *deeys treat and more* ta shirya tsaba da kan ko maku ingantaccen garin danwake mai suna ready to make me baida bukatar ƙarin komai ruwa kawai zaki sakaki kwaba sannan kuma ga curry wanda yaji kayan hadin gyaran fata dakuma jiki gaba daya kai karde na cikaku da Surrutu ance waka a baƙin mai ita tafi daɗi zaku iya nemanta ts wannan lambar kamar haka +234 913 715 9321 kada kuma dai a manta da Khadija wanda ya siya. *page 14&15* ___________Amatullahi cikin kuka ta hade hannuta tace"na roke ka duk azabar da zakamin kamin amman bana so ta shafi mahaifiya ta" yarima yace"yayi kyau zaki fansheta da bulala dari kullin da safe akwai dogarin da zai Maki bulala hamsin" Amatullahi tace"na yarda na amince" hawaye na cigaba da wake mata fuska" yarima ya kalli mai kula da dokunansa yace"je ka kira min jakadiya". babu bata lokaci sai gasu har kasa ta duka tace"ranka shi dade gani" yarima na zaune kan kujerar sa ya na latsa waya yace"ki dauke ta ki kaita dakin ki ki bata kaya ta saka da ga yanzu itace sabuwar baiwata mai min aikin cikin gida" jakadiya ta kalli Amatullahi tace"angama ranka shi daɗe tashi mu tafi" har takaita daki tana kuka ba komai tsakar dakin sai katifu guda biyu sai kayan jakadiya. jakadiya ta safketa bakin katifa tace"zauna nan ina zuwa" leda ta daga ta janyo wasu kaya ruwan kasa riga da siket ta bata tace"ta shiga ban daki ta saka" Amsa tayi ta shiga bandaki ta saka dai da ta dauki lokaci mai tsayi ta fito. jakadiya tace"diyata mi ya sameki kike kuka ko ba a san ranki kika zo bane" murmushi tayi tace"a'a ina kukan rabuwa da mahaifiya ne" jakadiya tace"Allah sarki Ni gashi diyar da zata kula dani ma bani da ita". amatullahi tace"baki taɓa haihuwa bane" jakadiya tace"Bamma taɓa yin auren ba shekarata 18 a cikin gidan nan bana san rabuwa da yarima dan a ganina idan na tafi ko sati bazai kara ba zai a sami damar kashe sa duk da raina ba a hannuta na yake ba" tunani Amatullahi ta tafi duk da bakin cikin dake tun kushe a ranta jakadiya tace"nasan baki gane abinda nake nufi a Amman makircin gidan nan a bayyane yake nan da lokaci kankani zaki fahimci abinda nake nufi". Abban safina ne a dankareren falan sa Ummun safina ta fito tace"Niko baban safina jiya wani irin mafarki nayi wai su Amatullahi suna cikin mawuyacin hali" Abban safina yace"Amman ai kinji abinda sukace taimakon su zasuyi baza ya cutar dasu ba yanzu sakamakon su ji irin daular da muka shiga kuma" *washe gari* Amatullahi ce ta fita kancewar yarima ya fada mata dukkan abinda zatayi kuma ya sa jakadiya ta nuna mata yadda ake komai. misalin ƙarfe 7am na safe Amattullahi ta tashi ta tafi dan amsar bulalar ta kafin a gama mata ba karamin galabaita tayi ba tana kuka ta tashi ta tafi. dakin sa ta nufa ta duke a ƙasa tana ta kuka tana tuna irin gatan da mahaifinta ya masu Amman yau an wayi gari itace tazo a matsayin baiwa,dakin a gyara yake tsab baida bukatar komai kitchen ta shiga taga cups an Sha tea sune ta dauka ta wanka tayi mooping,ta fara daura masa break fast kenan. Hanifah ce ta shigo falan da Assalama bakin ta Amattullahi ce tace"Amin alaikis salam" Hanifah tayi mamaki tace"Amman ke sabuwar baiwace ko" Amattullahi tayi murmushi tace"ey jiya nazo" Hanifah tace"Ko kece uncle yake fada ma mommy yayi sabuwar baiwa" Amattullahi tace"ey" ta gaji da Surrutu Hanifah Hanifah tace"kai Amman kina da kyau sossai ke kam miya kawoki a matsayin baiwa da ganinki baki kalar bayi ba". Amattullahi tace"Nagode" Hanifah tace"shekarun nawa" cikin kosawa tace"16" Hanifah tace"taf kice kune sweet sisteen" dariya taba Hanifah wai "sweet sixteen" Hanifah ce tayi cikin dakin sa knokking tayi tace"uncle na shigo" Asad da ya fito daga wanka yana shafa mai yace"Yes come in". tana shiga tace"good morning my uncle" Asad yace"morning sister har kin shirya kenan" Hanifah tace"ey na shirya uncle kai nake jira" yace"tam kije falo ki jirani ganin fito wa". tashi tayi ta fito falan kamshin pepper soup din da Amattullahi ke dafa ya daƙi hancin ta kitchen ta shiga tace"sannu ki ina na dawo nima in koyi girkin" Amattullahi tace"ke kam mizai gada ki d girki ai sai da kusa a yi maku" Hanifah tayi murmushi tace"a'a Ni kam da kaina zan rinka wa mijina abinci sai dai idan har baza ki koyamin ba" Amattullahi tace"yanzu Kinga kiyi shirin makaranta ki bari zuwa wani lokaci zan koya maki" Hanifah tace"to shikenan kullin idan ina gida zaki ringa ko ya mana nida baiwata ikram kinji,gashi baki faɗa min sunan ki ba. Amattullahi tayi dariyar yake dan ita harga Allah surutun Hanifah ya fara mata yawa a kana tace"sunana Amattullahi" Hanifah tace"wow nice name aunty Amattullahi" Amattullahi tace"a'a ki kirani da sunana Amattullahi ke bance maki aunty ba ai ke bazaki ki cemin ba" Hanifah tace"mu bamu d wannan alfaharin irin na sauran masarautin,kuma kema zaki fahimci hakan mu da bayin duka bayi ne na Allah,Allah ya mai da su hakane kawai dan ya jarrabece mu suma ta jabbacesu" kamshin turaren yarima ne ya daki hancin su da sauri Hanifah ta isa gareshi tace"uncle da Allah ka bari na karya sai mu tafi" yace'baga abinci nan cikin food plask ɗin ki ba" baki ta tafe tace"na aunty Amattullahi nake san naci" 🪀09121692033 *YARIMA ASAD* {saban taku} a historical fiction👌 HASKE WRITTERS ASSOCIATION *home of expert and perfect writters* *©khadeejat official🥰* wannan shafin yayi tsutsuwa ya dira ga Khadija my name sake bazan taɓa gajiya da mallaka maki page ba ina godiya marar adaɗi💗😊🙏 page 16&17 bayan sati biyu Amattullahi ba karamin sabo sukayi da Hanifah da kuma Fulani ba hatta sauran kuyangun da suke gidan yau takama Monday tun jiya da dare Amattullahi ke fama da ciwon ciki Amman ba wanda ta gaya wa. kwance take kan katifa ta kama cikin ta hawaye Masu zafi na wanke mata fuska sai mutsu mutsu tu take. jakadiya ta shigo dauke da abinci a hannuta a tunaninta ma Amattullahi ta tafi wajen aikin ta da sauri ta isa gareta ta aje shayin dake hannuta. dagota tayi tace"Amattullahi lafiya kuwa" kasa mata magana tayi sai nuni take mata da ciki". fita tayi ta dawo da kanwa a hannuta jikawa tayi ta bata tasha Amman tamkar an karo mata ciwon cikin dan har suma take,ganin karta mace a daki yasa sauri zuwa wajen yarima" tana shiga ta iske sa a falo a rude tace"ranka shi daɗe Amattullahi bata da lafiya gata chan har suka take yi" zumbur ya mike yace"tana ina" jakadiya tace"tana daki a kwance". yarima yace "tashi muje". tashi tayi yayi gaba ta bishi a baya wannan shine karon farko da yarima ya taba shiga dakin su jakadiya. lokacin da suke shiga Amattullahi tayi kwance tamkar bata da rai a rude yayo kanta Bai masan sanda ya sa hannunsa a kirjin taɓa dan jin idan tana numfashi"Amman baiji komai ba a rude ya zaro waya ya kira abokinsa Fahad cikin lokaci kankani sai gashi da kayan aikinsa. dubata yayi duk abinda ake yarima na tsaye yana kallo Fahad ya kallesa yace"bata mutu ba yanzu zan mata allura Amman nasan nan da awa biyu zata farfaɗo tayi muje waje akwai abinda zan fada maka". yarima fita sukayi jakaddiya ta zauna gefen ta tana kallon ta tanajin tamkar ita ta haife ta. bayan Fahad da yarima sun tafi hanya yake ce masa"ba wani abu bane ke damun yarinyar nan face ciwan cikin period saboda sex cell dinta suna ta increasing dan Allah sune wanda Allah ke halitta da mugun sha'awa kuma ta dinga irin wannan abun duk watan duniya" yarima yace"to yanzu Fahad su basu da wani magani da ake basu" fahad yace"kamar yadda ka gani na mata allura haka za a ringa mata sai kuma magunguna ina tunanin anjima zan kawo mata" yarima yace"No ka barshi kawai rubuta zan aika sai a sayo mata" daki suka isa ya rubuta masa ya bashi yace"Amman Asad bayan miyasa bazai ka bar yarinyar nan haka ba" Asad yace"lokaci baiyi ba" fahad yace"okay bari in tashi kaga Madan har ta fara kirana" Asad ya watsa masa wani mugun kalo yace"kaji masu Madan" fahad yace"to idan anji haushi mana ayi mugani" Asad ya jefa masa filon dake kan kujera ya kauce ya fita yana dariya" yana fita Hanifah ta shigo. "Assalama Alaikum" Hanifah ta shigo kuyangar ta na rike mata riga a baya Asad yace"Amin alaikis salam sister" ikaram ya zube a ƙasa tace"Allah yaja zaminka" hannu ya daga yayi mata nuni data miƙe Hanifah ta zauna akan kujera tace"uncle ina Aunty Amatullah banji motsin taɓa" fuska ya taɓe yace"tana dakin su bata jin daɗi shi yasa bata fito ba" Hanifah tace"uncle miya sameta" Asad yace"kije mana idanunki su gane maki" Hanifah cikin kalar kuka tace"uncle bansan dalilinka na tsanar Amattullahi ba Amman ina rokonka ka ban ita zan yan tata da kudi masu yawa". miƙewa yayi ya barta anan ya shiga daƙi. Hanifah tace"ikram muje mu dubuta" tura kofar dakin sukayi suka shiga bayan sun gaisa da jakadiya dake yiwa Amattullahi firfirtu duk da iskan dake kadawa. Hanifah tace"jakadiya ashe aunty bata da lafiya Amman miyasa baki kaita wajen likitan gida ba" jakadiya tace"yarima ya turo likita yazo ya dubata" Hanifah tace"Amman fa kamar ma bata lumfashi fa" jakadiya tace"yarima yasa an duba ta nan da awa 2 ma yace zata farka" Hanifah tace"Allah ya sauwake Bara naje kafin ta farka". dakin Fulani ta nufa tana dakin ta kuyangun na dan na mata kafa. shigar ta duk suka kwafe a ƙasa suka ce"Allah ya taimaki gimbiya Hanifah" ikram tace"gimbiya ta amsa" Fulani tace"Hanifah naga fuskar ki da damuwa haka" Hanifah tace"mommy uncle Asad ne amatu fa bata da lafiya ta chan ranta hannun Allah nayi mashi magana ana zan fansheta na 'yan Tata amma ya ƙiya gashi ta dalilin ta na iya abubuwa da dama miyasa bazai ban fansar taba" Fulani tayi murmushi tace"kai Hanifah daman dan wannan ne kika tada hankalin ki " Hanifah tace"ey momy" Fulani tace"zan mashi magana akan hakan" Hanifah ta rungume ta tace"Nagode momy zanje daki na kwanta kaina ciwo yake" toofa a ganinku yarima zai bada fansar Amattullahi ko kuwan *YARIMA ASAD* {SABAN TAKU} a historical fiction *HASKE WRITTER'S ASSOCIATION* home of expert and perfect writters ©khadeejart_official dedicated to yarima Asad special group,ina jin dadin comment dinku💗💃 kina raina har gobe my besty Khadija Allah ne kaɗai zai biyaki da abinda kike min💗🥰 *page 18&19* Asad ne ya dauko kudi ya fita yaba wani dogari yace"yaje abashi wannan magunguna abun kasa kuma babbar ciki za'a bayar" dogari yace"angama ranka shi" bai wani wani jima ba ya dawo bashi yayi yace"ya kai dakin jakadiya yaba ta " yana zuwa ya kwankwasa kofa jakadiya ta fito yace"gashi nan inji yarima". jakadiya ta amsa ta koma tana shiga dai dai lokacin Amattullahi na farka wa mike tayi ta zauna akan katifar. jakadiya tace"sannu Amattullahi" ganin jikin tayi duk jini jakadiya tace"ki tashi ki yi wanka ki tsabtace jikin ki ga magungunan ki nan yarima ya bada a kawo maki Ni zan je madafa na amso abinci sai kici. Amattullahi ta amsa da "to" Alhamdulillahi jikin ta yayi sauki sakamakon Allurar da aka yi mata ta sami sauki yanzu. bayi ta shiga tayi wanka ta kwashe kayan da taɓa ta kaisu suma bayin ta ajje. fito tayi ta shafa mai ta daga cikin kayanta da tun da tazo bata saka ba under wears kawai take dauka. wata doguwar riga ta dauko ta material ruwan kasa da kuma fari ta saka ba karamin amsar jikin ta tayi ba ta zauna das a jikin ta. zama tayi tana tunani inda zata ma sami pad gashi bata da kudi bare ta siya tana wannan tunanin sai ga Hanifah,ta shigo. kusa da ita ta zauna ta zuba mata Ido tace"sannu Aunty Amatullah,ashe bakiji daɗi ba na shiga bangaren uncle yace baki da lafiya" Amattullahi tace"ey Amman ai naji sauki anjima ma zanje nayi dinner" Hanifah tace"kai dukka yaushe kika tashi har kike cewa zakiyi abinci ki bari ki kara jin sauki" jakadiya ta shigo dauke da kwanukan abinci jallof din shinkafa ce da kifi. da kyar taci abincin bayan tagama cin abincin hanifa tace"zanje wajen mai martaba" jakadiya tami kawa Amattullahi ledar da yarima ya kawo tace"ke kikayi makaranta ki duba kiga yadda zaki shasshasu" amsa tayi tana buɗe taga harda pad kunya ya kamata tace a ranta "shikenan wannan azalimin ya san mike damuwa na" fuska ta tabe ta balli maganin tasha shima saboda da taji jiki Amman Amattullahi bata kaunar magani ko kadan haka ta masa bi da ruwa. tana kwanciya wani wahala lan bacci ya dauke ta. jakadiya ta shiga ta wanke kayan da fata. kiran sallar la'asar ne ya fargar da ita daga baccin da take miƙewa tayi dauke da salati a baƙin ta banɗaki ta shiga tayi wanka ta fita zuwa part ɗin yarima. sa'a aka ci baya fallan dan har ga Allah ita ko ido bata ma san su haɗa dashi saboda kunya. tana mooping falo ya turo kofa da sauri zata shige kitchen ya daka mata tsawa dawo tayi ta rage tsayin yan kare kare taringa yi ganin kayan jikin ta sun kame ta. tsaki yace"me kike wani bobbeyewa mutane wani dare jemage bai gani kina wannan kwailar har kike wani kare wa mutane kirji" ji tayi kamar ta nitse ya kalleta yace"kinsan baki amshi punishment dinki na farko ba dan haka kije ki gabatar dashi". kalansa tayi cikin rashin imani baya ganin halinda take ciki Amman har yake mata maganar taje ayi mata bulala. daki ya shije ta cigaba da mooping din dakin tana gamawa ta fita sai da taje aka mata bulalar ta tafi. daki ta koma ta haɗa abincin dare ba abinda ke mata takaici yarima Bama yaji yadda take ajewa haka take zuwa tana daukar sa. bayan ta gama gab da magariba ta shirya abincin zata fita kenan ya fito zaije masallaci. kalla yayi yace"kina da tsarki ma bana cin abincin ci bare yanzu ku dauka kije kiba dokuna na suma da cikali zaki basu har ya kare. dauka tayi ta fita ranta a bace. bayan ta koma daki ne jakadiya tace"Amattullahi kije kilishi na san ganinki" gaban ne ya faɗi tace"to shikenan" tashi tayi ta tafi Bayan anyi mata iso wajen kilishi ta shiga har kasa zabude kan gwiwowin ta ta kwashi gaisuwa. kilishi ta Sallami kunyangun dake wajen ya rage daga ita sai jakadiyar a dakin Amattullahi sai raba ido take kilishi "tace a matsayin ki na yarinya mai cike da Kuruciya miya kawoki nan kina bauta zaki kashe rayuwar ki a banza wajen bautawa wanda ke wulakanta ki safe rana dare dan haka na kawo maki mafita ina san zan yi amfani dake wajen kawar yarima zan baki gwala gwalan da zinari Wanda za su fitar da danginki kaf daga talauci,kin amsar bukatata kuma kan iya janyo maki Barazana a rayuwarki dan haka zan baki guba ki zuba wa yarima a cikin abinci daga lokacin zaki fita daga masarauta nan bake ba kara ko waiwayar ta. Amatullahi tace "zanyi" kilishi tayi dariya tace"kin ceceki kanki" hannu ta mikawa jakaddiya ta amshi tasaka mata gubar ta saka mata gubar a hannu" kilishi tace"ki zuba ki dawo da sauran dan ta mai martaba ce daman ta mutun ukku ce" Amatullah ta amsa ta jimke ta a hannu. shin Amatullahi zata saka gubar ko kuwan *YARIMA ASAD* {SABAN TAKU} a historical fiction *HASKE WRITTER'S ASSOCIATION* home of expert and perfect writters ©khadeejart_official dedicated to yarima Asad special group,ina jin dadin comment dinku💗💃 *mussaman mutanene na amana* UIA mommyn Abdullah umman Aryan bariratu sani Khadija admin iyan Abba seema maman Yazid maryam sani isa sayyada Suwaiba samha momy zeey pretty Maryam yahayya sani comment ɗinku na sani nishaɗi matuka masu cewar yarima baida imani kuma wannan kudashi🤐amman duk sai shune kuma yazo ya tafi daku😆 page 20_21 koda amatullahi ta koma dakin su jakaddiya batanan kwance tayi akan kafita tana ta sake saken abinda kilishi ta fada mata tunanin ta wannan wata irin macece marar imani haka tofa yanzu idan har bata sakawa gubar nan ba kilishi na iya sawa ita ma a kashe ta "innalillahi wa Inna illahir raji'un kawai take furtawa" yazama dole ta san abin yi a hakan Amman gsky bazan iya kashe wani ba balan tana yarima yanzu shikenan da asirinta ya toni nima kashe Ni za a yi kamar yadda na kashe sa,tana cikin wannan tunanin ne jakadiyya ta shigo "amatullahi har kin dawo daga kiran da kilishi ta miki" miƙewa tayi daga kwanciyar da take tace"ey na dawo" jakaddiya tace"ina dai fatan lafiya ko" Amatullah ta mikawa jakaddiya abinda kilishi ta bata. jakaddiya tace"minene kuma wannan" amatullahi tace"guba ce ta bani tace nasawa yarima cikin abinci" jakaddiya tace"innalillahi ita da kanta" amatullahi tace"dan Allah ki rufamin asiri wallahi na rasa yadda zanyi shiyasa na fada maki" jakaddiya tace"share hawayen Amatullahi bani gubar nan nasan yadda zanyi da lamarin Amman kija bakin ki kiyi shiru bana so ki bari wani yaji maganar nan" amatullahi ta share hawaye ki tace" Jakaddiya insha Allahu babu wanda zai ji" bayan kwana ukku koda Fulani ta cewa yarima zata yanta Amatullahi yakiya amman ya tabbatar mata dacewa akwai deal ɗin da yake da ita kuma bazai kara sawa a mata bugun safe ba. Amatullahi da wuri ta shiga bangaren yarima dan ya tabbatar mata da yau abinda zai ci dan haka da wuri ta shirya hada break fast Dan tun ranar da aka bata guba washe gari ya fara cin abincin da take dafawa ita kanta abin ya bata mamaki. bayan tagama gyara ko ina ta shirya abincin ne ya fito sanye da kwanun kaya wanda sukayi matukar amsar jikin sa. har kasa ta duka ta gaidashi karfin farko da ya taba amsa gaisuwar ta tun sanda ta shigo cikin gidan nan. bayan ya masa ya zauna akan dining tace"dan Allah idan ba damuwa ina san zuwa naga Ammina" kallan ta yayi yadda tayi maganar yaso bashi dariya Amman ya dake yace"ki badawa jakadiyya ta shirya ku tafi tare" godiya ta mashi baya ya daga kular abincin yaga bai sauya ba kamar yadda Fahad ya faɗa mashi ,dago yayi ya kalleta yace"miyasa kika kasa zubamin gubar da a ka baki" jikin ta ya dauki rawa ta kasa magana tunanin tayi tace"ko jakadiyya ta fada masa Amman kuma tayi mata alkawarin cewar bazata fada ba" cikin karfin hali tace"wa guba ku kuma" yarima yace"wanda aka baki ki saka min cikin abinci" Amatullahi cikin karfin hali tace"Ni ba wanda ya bani guba ba saka maka" yarima yace"ok You can go " tana fita ta haɗu da Abdul ra'uf ya fito daga bangarensa yana zugar sigari abin sa. amatullahi na fito ya kama ya kama hannuta ya taja suza coridor ɗin da ya rabasu da yarima dan ba kowa a wajen. kokarin rabata da kayan jikin ta yake dan har yayi sa'ar keta mata riga duk na shanun ta sun bayyana sai romantic yake da ita tana ta faman zabga ihu. bama jinta a wajen kasancewar ko wani bawa na bakin aikinsa. yarima ihu yake taji kuma ya tabbatar na Amatullahi ne tashi yayi a fusace ya fita yana bin inda yake jin ihun. chan ya hango Abdulra'uf ya kai Amatullahi kasa na biyar cire wanda sa kuka kura yayi yayi tsalle ya gama mashi kansa da bango nan da nan ya fadi a kansa kanshi na zubar da jini. Amatullahi ta tuni ta sadar ta tashi ta kanme jikin ta yarima ya kalleta yace"ai da kin bari ya maki maganin damuwar ki" da sauri ta tashi ta tafi dakin su kayan jikin ta duk a yage. nan ya tafi ya bar Abdulra'uf a yashe idan naga ruwan comment 9pm zaku ga wani undated din *YARIMA ASAD* {SABAN TAKU} a historical fiction *HASKE WRITTER'S ASSOCIATION* home of expert and perfect writters ©khadeejart_official kina raina har gobe my besty Khadija Allah ne kaɗai zai biyaki da abinda kike min💗🥰 page 22_23 Nan kan Abdulra'uf ya dunga zubar jini ba adadi sa da wani dogari ya shigo ta wajen nan ya kashi dan karamin asibitin dake cikin gidan akayi mashi dressing aka sa mashi bandage. Amatullahi a kiɗi mice ta koma daki duk yadds jakadiiya tayi dan ta fada mata abinda ys sameta Amman ta kiya haka ta hakura ta kyaleta. a ranar dai ba'a je gidan Ammi ba dan har wani zazzaɓi ne ya rufe ta mai martaba ne zaune da iyalansa dukan su da kilishi,Fulani,abdurauf,Hanifa da kuma yarima Asad. sarki ne ke ta faman faɗa "zancen banza zancen wofi a rasa inda za a ringa wannan iya shegen sai gida to wallahi ku sani dukkan abinda kuke ciki ina sane zuba maku ido kawai nake to wallahi muɗin baku hada kanku ba Ni kadai nasan hukuncin da zan yanke wanda na tabbata babu wanda zai wa dadi idan har baku hada kanku ba yaushe zaku hada ke kilishi kina babba Amman duk wata fitina ke kike hada ta. kilishi tace"daman ai nasan Ni zaka daura wa laifin daman nasan zaman nan dani aka yishi,yanzu duba fa kaga yadda Asad ya fasa wa Abdulra'uf kai ai baki magana ba. sarki ya kalli Asad yace" kai kuma mun yanke shawara da magajin gari zan baka auran yarsa yusra kuma nan da sati ɗaya ne za daura maku aure ku tashi ku ban guri" duk yadda yarima yaso yayi magana Sarki ya hanashi haka ya tashi yana ta sake sake ya nufi bangaren sa. kwanciya yayi akan gado ya kana kallan ceeling Amman miyasa sarki zai yanke masa wannan mummunar hukuncin kuma shi yasan dalilin da yasa magajin gari yake so ya auri yar sa,tashi yayi ya tafi part Fulani. ita kanta Fulanin tunani take yi bayan ya isa kasa magana yayi Fulani tace"bakin alkalami ya riga ya bushe kabi umarnin mahaifin ka ka zabi abinda ya zaba maka saboda bazan iya dakatar mai martaba ba" Asad idanunsa ya ciko da kwalla yace"yanzu kina ganin nabi hanyar da sarki ya zaba min" Fulani tace"to ya zamuyi zuwa gaba tun nasan bazai hana ba sai ka auri wanda kake so" tashi yayi ya tafi fada duk ta dauki yarima zaiyi aure masu farin ciki nayi masu baƙin ciki nayi. kilishi kuwa tun bayan da Amatullahi ta shaida mata ta yada gubar da ta bata ta dauki wani salan muguntar. bayan sallar magariba jakadiiya ta shigo daki tar yarda Amatullah nata bacci tada ta tayi tayi sallar bayan ta gama jakadiiya take fada mata auran da yarima zaiyi. amatallahi sai da ta dauki lokaci kafin tace"Allah ya sanya alkhairi" bayan kwana biyu yarima ya sallami Amatullahi ta koma gida Amman haka kawai ta tsinci kanta da kewar su Hanifah da jakadiiya. Ko kadan bata gaya Ammi dukkan abinda Salim yayi mata ba haka ta dawo gida kullin tana tunani duk yadda Ammi taso ta gaya mata tunanin da take Amman ta kiya. yau takama Litinin saura kwana hudu daurin auren yarima. sarki ya kira yarima yace"anjima ya shirya yaje gidan magajin gari dan ya gano yusra su satin ta junan su. haka ko akayi da yamma aka shirya motocci suka tafi yarima ko tamfar wanda aka aiko wa mutuwa suna isa akawa yarima iso. Tun safe yusra ke faman shiri harda zuwa wajen kwalliya sossai tayi kyau yusra doguwar marar jiki tana da doguwar fuska da katan baki😆a takaice dai farin fatar ta ne ya fiddo ta. magajin gari ba laifi ya kashe kudi sossai dan yar karamar walima ce haɗawa yarima. yana masafkin baki sai ga yusra ta fito tana ta yakunar fuska tana shigo taje kan kujerar da yarima ke zaune. tashi yayi yace"gaskiya mai martaba bai min adalci ba,yanzu wannan aljanar ce zai aura min to wallahi ki sani muɗin baki je kika fadawa mahaifin ki kin fasa aure na wallahi sai nayi ajalinki. toofa *************************⬇********************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************* kuyi manage