[12/31, 6:20 AM] Abbu Saleh AlQuyraemey: *_Typing📲_* . *************************⬇********************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** *_🔮TAKUN SAAƘA!!🔮_* *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* _ZAFAFA BIYAR 2K22_ *_Da sunan ALLAH mai rahama mai jinƙai. Ya rabbi ka bani ikon rubuta abinda zai amfani al'umma. Ka haneni rubuta abinda zai cutar da wanina da ni kaina. ALLAH ka gafartama mahaifina masoyina da dukkan bayin ALLAH da suka bar duniya😭🙏🏻_*. _Masoya abokan tafiya ga ZAFAFANKU BIYAR sun sake dawowa a karo na biyar insha ALLAH☺️🤗_ *_______________________________* *Chapter one* ............Sosai motocin ƴan sandan guda uku na farin kaya ke zuga uban gudu a titi tamkar suna a jerin gasar tsere, bakajin komai sai jiniya mai tsanani da zata iya tada hankalin duk wani mai tsoro. Da yawan sauran motocin dake a kan titin sauka suke gefen hanya domin basu fili, dan duk mai hankalin da yaga wannan gudun yasan bana lafiya bane ba. Sai dai kowa mamakinsa da tambayarsa shine (Mike faruwa haka?).        Basu da mai basu amsa, kamar yanda nima bani da amsar. Sai dai mu cigaba da binsu domin sanin mike faruwar? Baki ɗaya. ★★       A lokacin da waɗancan motocin ke tsere-tseren gudu mai kama dana kai agaji ko ceton rayuwaka anan headquarters na ƴan sandan jihar a kusan hargitse take a wani yanki na cikinta, hargitsin nata kuma yanada tabbacin alaƙa da waɗan can motocin.       Kusan gaba ɗayan ma'aikatan department ɗin tsaye suke cirko-cirko a ɗakin na'urorin bincike cikin matuƙar taraddadi da ƙaulanin fargabar abinda ke faruwa. Yayinda kusan ma'aikata bakwai ke zaune sun duƙufa wajen sarrafa Computers ɗin cike da ƙwarewa da nuna matuƙar ƙwazo. Bakajin sautin komai sai na keyboards da ajiyar zuciyoyi.       “Sir mutumin nan yana da matuƙar wayo, bana tunanin zamu iya dakatar da shi da ga zuƙar kuɗaɗen nan fa a wannan karon ma”.        Ɗaya daga cikin masu sarrafa computers ɗin ya faɗa yana yarce uwar zufar daketa faman tsatstsafo masa a goshi, duk da ac dake aiki a ɗakin. Dafe kai wanda yake ma maganar yayi cikin matuƙar dagulewar tunani. Sai kuma ya ɗago a fusace yana kallonsa. Cikin tsawa ya daki desk ɗin gabansa yana kallonsu da idanunsa da ke jajur na ɓacin rai.        “Idan har kuka bari ya cimma burinsa a wannan karon kuma bazan yafe muku ba. Har sai yaushe ne zamu iya daƙile wannan tsageran ɗan ta'addan yaron dake ganin a kullum yafi ƙarfin hukuma?!!”.      Yanda yay maganar da bugar desk ɗin a tsawace ya saka da yawansu zabura. Wanda yay maganar yay saurin maida hankalinsa ga computer ɗin gabansa jikinsa na ɓari ya cigaba da sarrafata da sauri-sauri. Shima ɗayan dake gefensa tsawar ta rikitashi matuƙa, dan haka ya ƙara ƙaimi wajen sarrafa na'urar gabansa.         Ogan nasu ya cigaba da masifar data sake hargitsa sauran harma suka rasa nutsuwarsu wajen sarrafa na'urorin. Ɗif komai dake wajen ya tsaya, hakan ya jawo yin tsitt ɗin ɗakin lokaci guda. Gaba ɗayansu suka zubawa Computers ɗin ido a hargitse, dan sun san aikin gama ya gama kawai. kamar yanda ya saba cin nasara a kansu yauma ya sake ci........ ★                           A ɓangaren motoci masu rera gudu bisa titi kuwa sun isa banki ne, inda suka iske mutane da duk ma'aikatan bank ɗin hankalinsu a tashe. Musamman ma shugaban bankin da yafi kowa birkicewa. Dan kuɗin da guy ɗin ya ɗiba ya tatsesune cikin asusun matar gwamna. Duk da dakatar da shi da aka samu nasarar yi ya zuƙi biliyoyin kuɗin da su kansu tsoron bayyanama duniya sukeyi saboda gudun abinda zaije ya dawo kuma.       Cikin ƙanƙanin lokaci jami'an nan na hukumar farin kaya da ƴan sanda sun gama zagaye bankin dan ana ƙyautata zaton wanda ya aikata laifin ko wani nashi yana cikin bankin har yanzun basuyi nisa ba. An garƙame ko'ina da ina, duk wanda ke a ciki baida damar fita sai an bincikesa ciki da bai ɗinsa, musamman ma wayoyin hannu da bags.       Al'amarin tamkar rufa ido har aka gama bincike mutane aka koma kan ma'aikatan banki babu mai ko alamar aikata laifin. Zuwa yanzu kuma babban ɗa ga gwamna ya iso wajen tare da mahaifiyarsa matar gwamna ɗin da securitys ɗinta. Hakanne yasa wajen ƙarayin tsamari dan ta nuna tsananin ɓacin ranta na ƙarancin tsaro da bankunan ƙasarmu ke fama da shi. Inda kake tunanin ka ajiye kuɗinka ka koma kai barci mai daɗi a gidanka shine kuma ya zama gidauniyar wawaso na salon ɓarayi masu aiki da ilimi, ta tabbatar musu bazata yardaba, kodai kuɗinta su dawo cikin asusunta kokuma ta ɗauki tsatstsauran mataki akan bankin da ma'aikatan cikinsa. Wannan shine ya ƙara ɗaga hankalin duk wani ma'aikaci dake a reshen wannan banki.       Abu ya ƙara tsamari dan har C.P da kansa ya iso wajen tare da mataimakin gwamna da wasu manya-manyan ƙusoshin gwamnatin dan ɓarnace ta ɗunbin kuɗi wannan ɓarawo ya aikata wadda a ƙiyasi bama ya taɓa aikata kwatankwacin irinta ba a duk hatsabibancin da ya aikata, dan babu hukumar tsaron da babu sunansa a ƙasar matsayin mai-laifi saboda tsagerancinsa.           Takaici da baƙin cikin halin da ake ciki ne ya saka wani ɗan sanda yima mabaratan dake zaune a ɗan gefen bankin korar kare, dan yanda suka zauna zuru-zuru suna kallon duk wainar da ake toyawa ne yasa takaicinsu kamashi. Ya fatattakesu tare da bada umarnin idan sunƙi barin wajen a saka musu barkonon tsohuwa maisa hawaye.         Tuni suka fara haɗa kayansu suna barin wajen da sauri-sauri. Wani gurgu dake a tsohon kekensa (Wheelchair) ya murzata da ƙyar yana barin wajen, keken sai wani irin mugun ƙara yake saboda tsabar tsufan da yayi.        Cikin layi na uku dake akan titin da bankin yake ya shiga, sai da ya iso saitin wani kango makahon dake biye da shi a baya yana raira ƴar waƙarsa da laluben hanya da sanda yace, “Boss mun iso point”.       Wani irin ƙuuu! Yaja birki da keken, ya waiga bayansa ya kalli makahon da ya buɗe idanunsa ras yanzu, ɗauke kansa yay ya maida idanunsa ga ko'ina na layin babu kowa sai jefi-jefin yara dake wasa. Cak ya miƙe daka saman keke yana jan wani uban tsuki dasa hannu ya yaga daddauɗar rigir malun-malun ɗin shaddar jikinsa data fita hayyacinta saboda tsufa. Ya fincike rawanin daya aza akai da hular suma duk ya jefa saman keken.          Ba ƙaramin ɗunbin al'ajab da mamaki bane suka lulluɓe ni saboda ganin lafiyayyen mutum ƙyaƙyƙyawa tsaye akan ƙafafunsa, a yanayin jiki dai daka gansa kaga matashin mai tashen ƙuruciya da cikakkiyar lafiya, amma abin mamaki fuskarsa ta tsoffi ce, hasalima harda tarin furfura a saman kansa da sajensa zuwa gemu. Sosai raina ke cike da ɗunbin mamakin hakan, dan nidai ban taɓa gani ba tunda nake. Ace matashin saurayi da fuskar tsoffi............✍🏻 *TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *ALSHIRINKU MASU KARATU!!!* *_NAJI DADI SHINE GARI......_* *KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA* _ILIMI_ _NISHADI_ _TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_ *MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR* *NA SABUWAR SHEKARAR 2022* *WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!* *SABBIN LABARAI* *SABUWAR SHEKARA* *SABON NISHADI* *_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_* *MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN* *ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa* 6019473875 MUSAA ABDULLAHI SAFIYA keystone bank Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 08184017082 *IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA* 09134848107 Littafi daya 1____300 2____400 3____500 4____700 Duka gamayyar biyar din(1k) 1,000 *INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽 #team ZAFAFA BIYAR *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*         [12/31, 6:20 AM] Abbu Saleh AlQuyraemey: *_Typing📲_* *_🔮TAKUN SAAƘA!!🔮_* *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* _ZAFAFA BIYAR 2K22_ *________________________________* *Chapter two* .........Idanu sosai na ware domin ƙare masa kallo, sai dai isowar mashinan power bike guda biyar cikin layin ya rabamin hankali biyu, tuni makaho shima ya yaye kayan dattin jikinsa ya fito a lafiyayyensa. Cikin girmamawa ɗaya daga cikin wanda suke a saman mashinan ya faka nasa gabansa, ya sakko tare da sauke jakkar bayansa dake goye ya ciro takalma masu azabar ƙyau da sauran kayan bada kariya daga haɗari na mashin ɗin. Cikin sauri wani ma ya sakko a nasa mashin ɗin ya warware kujera ya ajiye masa sai kace wani sarki. cikin wani salo na isa da ƙasaita yakai zaune tamkar wanda ya samu kujerar falonsa, yanda yake abu cikin izza da isa ya sani yin zuru ina kallonsu.        Wanda yake riƙe da takalmin ya kai tsuggunne gabansa ya fara zare masa takalman robar dake ƙafar tasa irin na masu kiwo ɗin nan duk sun fashe saboda wahala. Takalman ya shiga saka masa, shi kuma ya amshi hular kwanon ya ɗaura a kansa tare da sauran kayan. Miƙe yay cike da ƙwarewar ƙasaita ya ɗare bisa mashin ɗin. Makaho da wanda ya kawo masa mashin ɗin suma duk suka haye sauran mashinan da ƴan uwansu suke..        Kasancewar nashi mashin ɗinne a gaba ya sake daidaitashi. Cikin sallon ƙasaitarsa ya ɗaga hannunsa sama, ƙaramin yatsansa ya fara miƙarwa alamar (ɗaya), ya ɗaga na kusa da shi (biyu), yana ɗaga na ƙarshe alamar (uku) suka saki wata irin sautin ƙara data gigita kusan mafi yawan jama'ar layin. Tuni mata suka shiga gudun afkawa cikin ɗakuna, masu ƙarfin hali naɗan leƙowa suga mike faruwa?.         Kasancewar layin da suke yana gab da bankin tuni saƙonsu ya isa kunnuwan jami'an tsaron dake zagaye da wajen. Har rige-rige jami'an tsaron keyi wajen hawa ababen hawansu, dan sunsan wannan singing ne na tabbatar da shiɗin na kusa da bankin.         Daga ɓangarensu kuwa a wani irin mugun gudu suka harbo mashinan suka fito daga cikin layin, hakan yayi dai-dai da gabatowar motocin jami'an tsaron kwanar layin suma. Isowar jami'an tsaron ya sakasu danna wani abu a jikin mashinan nasu tuni hayaƙi ya gauraye titin baki ɗaya suka harba mashinansu tamkar walƙiya.        ALLAH yaso a ƙaramin titi suke, da tabbas babu abinda zai hana haddasuwar gagarumin haɗari saboda yanda gaba ɗaya titin ya lulluɓe da hayaƙi, mai tahowa baya ganin mai tafiya. Sai dai duk da wannan hayaƙi hakan bai hana mota ɗaya cikin motocin jami'an tsaron bin bayansu ba a guje suma. Kusan mintuna uku cikakku hayaƙin ya ɗauka kafin ya baje, zuwa lokacin tuni mashinan nan sun ɓace ɓat daga yankin ma baki ɗaya tamkar na aljanu.        Rai a ɓace sauran jami'an tsaron ke yarfar da hannaye, kowa yanajin takaici da ƙunar rai cikin zuciyarsa. Masu ƙarfin hali ne ke ƙoƙarin tsintar ƙananun takardun dake yashe a ƙasa alamar masu power bike ne suka sakesu tare da hayaƙin. Abinda ke a jiki ya ƙara harzuƙasu, dan kamar yanda ya saba barin sunansa idan ya aikata laifi a wannan karonma hakane. Sunan nasa ne a jikin takardar tare da zanen fuskarsa ta tsoffi raɗam.       A zabure ɗaya daga cikin jami'an yace, “Kai! Wannan ai yana cikin al'amajiran dake a ƙofar bankin suna bara”.      “What!!?” C.P ya faɗa a matuƙar zabure.        Manager da shima ɗaya daga cikin takardar ke hannunsa muryarsa a hargitse ya ce, “Tabbas wannan al'amajirin sati biyu da suka wuce na fara ganinsa a wajen nan. Amma dai wannan ya cika matsiyaci”.          Zafi da ƙunar da zukatansu suke musu ya hana kowa ƙara magana. A kuma dai-dai lokacin matar gwamna da yaronta suka iso wajen suma. Dan sun gaji da jiran tsammani a cikin banki. Jin cewar basu kamashiba yasa ɗanta ya fara masifa tamkar zai haɗiye harshensa. Hakama mataimakin gwamna ya tabbatar musu karsu wuce awanni ashirin da huɗu basu kamo hegen ba.     Daga haka kowa yabar wajen rai ɓace. Jami'an tsaron ma kowa ya koma inda ya fito domin ƙulla mai yuwuwa. ★ Jami'an farin kaya harsun kama hanyar barin wajen suma suka dawo, sakamakon kiran wayar oga kwata-kwata na hukumar tasu da ɗaya daga ciki yayi domin sanar masa halin da ake ciki. Shine ya basu umarnin komawa su duba inda wannan gagarumin ɓarawo ya fito bayan barinsa banki.       Sun shigo layin, inda suka iske mata da yara cike suna kallon kujera da kayayyakin da gurgu da makaho suka cire. Cikin mamaki suma suke duban kayayyakin, tare da ɗanyin tambayoyi ga mutanen wajen kowa na faɗin albarkacin bakinsa.        Ɗaya daga cikin jami'an yakai duƙe yana ɗaga kayan dake bisa keken guragun. A mamakinsu sai ga facemask exactly da wadda ke jikin fuskar guy ɗin, kuma itace zane a jikin takardar da ya bar musu a titi.        Komai basuce ba, saboda basusan da mutanen da suke tare a wajenba dan ya zama shu'umi kuma. Suka tattare kayan kaf har sandar makaho suka bar wajen..       A lokacin da mashinan power bike ɗin can ke reren gudun tserewa wasu daga cikin ɗaliban babbar jami'ar jihar ke tururuwar fitowa domin neman ababen hawa da zasu maidasu gidajansu dan sun ƙare darasin karatu na wannan rana.        Matasan ƴammata uku dake ƙoƙarin tsalla titi cikin matuƙar gajiya da yunwa suka daka uban tsale domin komawa baya sakamakon gabatowar waɗanan mashina dake gudu tamkar su kaɗai ne a titin.        Ɗaya a cikinsu takai ƙasa sakamakon tuzguɗewa da takalmin ƙafarta yayi, ƙarar data ƙwalla ne ya maido mafi yawan hankalin mutane da idanunsu ke akan power bikes ɗin kansu. Ɗayar budurwar tai saurin kamo wadda ta faɗin tana ambaton kalmar “Subahanallahi Hafsat!”.      Ɗayar kuwa a wani irin harzuƙe ta wurga musu wani abu dake hannunta, cikin sa'a kuwa sai gashi ya manne saman jikkar ɗaya daga cikin masu power bike ɗin. Cikin zafin rai da tsiwa tai alamar harba bindiga da yatsunta biyu tana faɗin, “Ku tafi duk iya inda kuke buƙata a tafin hannuna kuke, ko ƴaƴan ubanwaye ku a ƙasar nan zakusha mamaki, dan sai nayi sanadin da hawa power bike zai gagareku insha ALLAH”.         Karaf wannan furuci na ƙyaƙyƙyawar matashiyar budurwa da shekarunta bazasu gaza sha takwas ba a kunnen ɗaya daga cikin jami'an ƴan sanda nan da suka biyo bayansu, sai dai dandazon ɗaliban daya rufe kusan rabin titin ya rage musu ƙaimin gudun da sukeyi suma domin son cimmasu. Sassauta gudun nasu ya basu damar jin furucin wannan matashiyar budurwa da tuni ta maida hankalinta ga ƴar uwarta data faɗi suna ƙoƙarin ɗagata tsaye dan da alama taji ciwo a ƙafarta ne.       Cikin sauri jami'in nan da yaji furicin budurwar ya dirgo a motarsu ya nufi wani mai taxi, magana sukai da babu mai jinsu, mai taxi ɗin ya miƙa masa key ɗin motar. Sauran ɗalibai na ƙoƙarin tsaidama ƴammatan nan napep da basu shawarar su kai wadda ta faɗin asibiti dan da alama taji ciwo babba jami'in nan yazo gabansu ya faka taxi ɗin nan, batare da yin wani tunani ba suka taimakawa ƴar uwarsu ta shiga suma suka shiga.          Sai da suka fara tafiya ɗayar budurwar tace, “Kai gaskiya kosu waye akan mashinan nan sun cika tantirai, dole ne a dinga cewa ƴaƴan manyan ƙasarnan sai sun sha kayan haukansu suke hawa power bike sunama mutane hauka da shi a tituna kamar nasune su kaɗai. Yanzu dan ALLAH bayan ALLAH ya taƙaita wahala ai za'a iya rasa rai ta dalilinsu ko?”.          Wani banzan tsaki budurwar nan data jefa musu abu taja tana cije lip. A tsiwace tace, “Aiko a wannan karon ko duniya suka sha sun sako kansu a tarkon da iyayen nasu da suka saya musu mashinan sai sunyi dana sani insha ALLAHU. Dan wlhy har gidan ubanninsu sai nayi sanadin da za'a bisu ɗai-ɗai a kamo koda iyayensu zasu ɗauki mataki ne sai sunayensu ya ɓacin da bazasu sake gigin hawa power bike a cikin jama'a ba”...........✍🏻 *TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *ALSHIRINKU MASU KARATU!!!* *_NAJI DADI SHINE GARI......_* *KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA* _ILIMI_ _NISHADI_ _TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_ *MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR* *NA SABUWAR SHEKARAR 2022* *WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!* *SABBIN LABARAI* *SABUWAR SHEKARA* *SABON NISHADI* *_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_* *MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN* *_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_. *_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_ *_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_ *_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_ *_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_ *ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa* 6019473875 MUSAA ABDULLAHI SAFIYA keystone bank Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 08184017082 *IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA* 09134848107 Littafi daya 1____300 2____400 3____500 4____700 Duka gamayyar biyar din(1k) 1,000 *INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽 #team ZAFAFA BIYAR *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻._*        [12/31, 6:20 AM] Abbu Saleh AlQuyraemey: *_Typing📲_* *_🔮TAKUN SAAƘA!!🔮_* *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* _ZAFAFA BIYAR 2K22_ _________________________ Chapter Three ...........Hafsat tai azamar ɗago kanta tana dubanta, duk da hawayen da ke sharara a kumatunta na azabar da take ji a ƙafarta, cikin ƙarfin halin ta ce, *_“Muhibbat!_*  dan ALLAH karki sakamu a wahala da hatsabibancinki. Kwana huɗu kenan kacal da gama kashe wata wutar da kika kunno, indai dan nice karki damu, dama ALLAH ya ƙaddara sai naji ciwon nan koda bata sanadinsu ba, ina roƙonki kibarsu Ya Abubakar su huta da shegen tsokanarnan taki”.        Harara Muhibbat ta zubama Hafsat da murguɗa baki tana juya idanu, harta buɗe baki zatayi magana sai kuma tayi shiru saboda isowarsu cikin harabar asibitin.        Ko kaɗan jami'in nan baiso Muhibbat tayi shiru ba, amma kasancewar yasan aikinsa sai bai nuna hakanba, sai ma ƙoƙarin taimaka musu da yayi domin ganin an shiga da Hafsat taga likita akan lokaci.       Da taimakon jami'in aka duba ƙafar Hafsat da ta samu tsagewar ƙashi, Zahidah sai godiya take masa saboda ƙoƙarin da yaketa musu, dan sunso su kira gida ya hanasu. Hanawar tasa kuma ta bama Muhibbat haushi, dan a ganinta ya cika shishshigin tsiyane kawai, musamman daya kasance duk wani motsinta sai ta ritsa idanunsa akanta.       Tun tana hararsa a ƙasan ido da masa ƙunƙuni har takai ta fito fili tana dalla masa harara. Ganin dai ba daina kallon nata zaiyi ba a tsiwace ta ce, “Wai malam kallon fa? Dan ALLAH karka cinyeni a tsaye mana”.         Sosai yanda tai maganar ya bashi dariya, dan tsaf ya gama fahimtar itaɗin matsiwaciyace ta gaske. Sannan babu tsoro sam a cikin idanunta kona sisin kwabo. Komai baice mata ba, sai ma ɗauke kansa da yayi kawai gefe tamkar bai jita ba. Taja tsoki tana murguɗa baki da miƙewa tabar wajen.        Can gefe ta koma tana ƙoƙarin sarrafa wayarta cike da ƙwarewa. Cikin ƙanƙanin lokaci kiran da tayi ya shiga, sai da aka ɗaga sannan takai kunne tana faɗin, “Assalamu alaika Yaya”.     Amsa mata akai da ga can, kafinma ya gama rufe baki cikin shagwaɓa taci gaba da magana. “Yah Uthman muna hospital ne”.          A tsananin tsorace muryarsa ta bayyana, “Hospital Auta?! Waye bai da lafiya?”.          “Oh Yaya calm dawn, Hafsat ce taji ciwo a ƙafa amma da sauƙi, dan yanzu haka ma an gama mata gyaran sunce tsagewan ƙashine”.         “Ya ALLAH! Auta wai sai yaushe ne zakuyi hankali ku kam? Yanzu haka a wajen shegen rawan kan nan naku hakan ta faru?”.         “Na rantse Yaya bafa da gangan bane, wasu marasa kirki ne suka kusan turemu a power bike”.        “What?!. Power bike fa? Ku miya kaiku kan titin da masu power bike kebi!!?”.        Yanda yay maganar a tsawace ne ya sata zabura, duk cikin yayun nata yafi kowa sauƙin hali bayan Yah Abubakar. Sai dai kuma idan ya rikice tafi tsoronsa fiye da kowa a cikinsu..... Cikin katse mata tunani yace, “Zan turo muku Ammar yanzun nan danni naje katsina ne..”          Yana gama faɗan hakan ya yanke wayar. Kasaƙe Muhibbat tayi tana kallon wayar, yayinda gefen zuciyarta ke ayyana mata neman mafita. A fili tace, “Tab Yah Ammar! Wlhy bazan bari ya samemu a asibitin nan ba wannan ɗan matsalar”. Da sauri tabar wajen zuwa inda jami'in nan mai amsa sunan driver-n taxi yake da Zahidah.        “Zahidah tunda sunce zasu iya sallamarmu gara mu wuce gida, dan na haɗa gurmi wlhy”.      Zahidah dake mata kallon mamaki tace, “Gurmi kuma! Nami to?”.        “Humm daga kiran Yah Uthman fa na faɗa masa shine wai zai turo mana Yah Ammar shi yana katsina. Ni kuma wlhy banason Yah Ammar yazo asibitin nan ya samemu saboda yafi gidan haya matsala kema kin sani”.        Kafin Zahidah dake dariya tace wani abu jami'in nan yay saurin cewa, “Ai sunma sallemu daman, inaga ku shiga ku fito da ita kawai mana”.         Harararsa Muhibbat tayi tana ɗaure fuska. “Ikon ALLAH sai kallo, wai ni kam bawan ALLAH ca'akai ka kula damu ne kokuwa? Taxi ɗinka muka hau ka kawomu inda muke buƙata, to sai mi kuma ya rage?”.         Murmushi yayi idanunsa a kanta, “Sai ku bani kuɗina ya rage ƙanwata”.        “Ya salam! Dan ALLAH kayi haƙuri bawan ALLAH. Wlhy gaba ɗaya mun shafa'a ne”. Zahidah ta faɗa tana laluben bag ɗinta.       “Karki damu ƴammata babu damuwa. Nasan kuna a rikicene ai. Amma ƙawar nan taki ya kamata ta rage tsiwa”.       Zahidah dake miƙa masa ɗari biyar tai dariya, “Kaga fita batunta ga kuɗinka mun gode sosai”.      “Ai karki damu riƙe kawai sai na kaiku inda zaku yanzu sai na amsa”.        “Malam gara dai ka amshi kudinka kai gaba, dan bazamu sake shiga motarkaba ɗan sarkin shiga sharo ba shanu”. Muhibbat ta faɗa tana hararsa.        Saurin toshe bakinta Zahidah tayi itama tana hararta, “Wai nikam Hibbat kodai wadda tai miki wankan jego bata gasa bakin nan bane da baya barin kowa. Ina laifin bawan ALLAHn nan, kigafa ƙoƙarin da yay mana akan Hafsat”.       Hibbat ta buge hannun Zahidah da haushi, “To dan kuma ya taimakemu sai ya ishemu da shishshigin jaraba. ALLAH ni banason shishshigi da ƙwala kai a faranti irin na wasu mazan”.     Tana gama faɗa tai shigewarta ɗakin da Hafsat take. Duk binta sukai da kallo, kafin Zahidah ta maido kallonta ga jami'in. “Ayya dan ALLAH kai haƙuri. Ita haka take sam ba'a gane kanta tamkar mai aljanu”.           Ƙaramar dariya yayi yana sosa tsakkiyar kansa da key ɗin taxi ɗin. Yace, “Kinga karki damu ni salon natama birgeni yakeyi, irin waɗanan sam ba'a cutarsu a duk inda suka shiga. Je kawai ki fito dasu na kaiku kafin a sake kirana ɗan shishshigi”.        A yanda ya ƙare maganar cikin langaɓe kai kalar tausayi yasa Zahidah ƙyalƙyalewa da dariya tana shiga ɗakin domin su fiddo da Hafsat.. Da ƙyar Muhibbat ta amince jami'in nan mai taxi ya ɗaukesu zai maida gida. Dan ko sai kumbura take a motar tana ƙananun ƙunƙuni alamar bataso hakan ba. Shi dai yakanyi murmushi lokaci-lokaci idan ya ɗago ya dubeta ta mirror yaga yanda take cika baki da iska tana harare-harare........ ★.★.★.★.★.★        Kamar yanda aka saba yau ɗinma tuni media ta ɗauka. Gidajen redio dana televisions harma da yanar gizo mutane sai tofa albarkacin bakinsu suke. Dan lamarin wannan gagarumin ɓarawo ya daina bama mutane tsoro sai al'ajabi da mamaki.  Kullum ji suke jami'an tsaro na farautarsa, mai makon ya tsorata ya ɓuya sai ƙarama gawurta yake a al'amuransa. Gashi babban abinda zai baka mamaki manya-manyan ƙusoshin ƙasar masu lasisin iya ɗaukar mataki yake bi yana yashewa da saka rayuwansu cikin tarkuna. Dan da wahala ya kafa maka ƙahon zuƙa daga ƙarshe baka koma ƙarƙashin binciken hukumar *EFCC🐦* ba, ko ka ƙare rayuwarka da ciwon paralysis saboda barazanarsa idan yay dirar mikiya aka kaddarorinka da kuɗaɗenka. Yanzu dai yanda ya yashe asusun matar gwamna bawai ya barta bane kenan. Duk da neman da ake masa ruwa a jallo cikin kwanaki ƙanƙani zai sake silalowa ya danƙara mata wani harbin mai zafi har sai ya kai rayuwarta ƙasa kwance zai barta.            Duk yanda ƴan jarida sukaso jin ta bakin jami'an tsaro da gidan gwamnati akan wannan al'amari abin ya gagara. Sun haƙura dole suna bada labarin iya abinda idanunsu suka gani da ɓarnar da wannan mutumi ya tafka a baya kafin wannan ɗin.     Yayinda a gefe kuma jama'ar gari suketa tofa nasu. Wasu najin daɗin abinda yakeyi ɗin dan bawai a satar kuɗin manyan ƙasar kawai ya tsaya ba, har ƴan fashi da suka addabi mutane da ƴan ta'adda yakan kama waɗanda har yanzu babu wanda zai iya cewa ga inda yake kaisu ya ɓoye. duk da kuwa shima ɗin mai laifi ne a bayyane, wasu ko na jifansa da ALLAH wadai saboda suna ganin bashi da maraba da ƴan ta'addar da yake kamawa ai. Yayinda ƴan kanzagi ke zaman rubuta shaci faɗi su yaɗa a kafafen yanar gizo game da shi da ayyukansa..............✍ . *************************⬇********************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** *TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *ALSHIRINKU MASU KARATU!!!* *_NAJI DADI SHINE GARI......_* *KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA* _ILIMI_ _NISHADI_ _TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_ *MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR* *NA SABUWAR SHEKARAR 2022* *WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!* *SABBIN LABARAI* *SABUWAR SHEKARA* *SABON NISHADI* *_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_* *MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN* *_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_. *_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_ *_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_ *_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_ *_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_ *ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa* 6019473875 MUSAA ABDULLAHI SAFIYA keystone bank Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 08184017082 *IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA* 09134848107 Littafi daya 1____300 2____400 3____500 4____700 5____1,000 (1k) *INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽 #team ZAFAFA BIYAR *_ALLAH ka gafartama iyayen mu😭🙏🏻_*     [12/31, 6:21 AM] Abbu Saleh AlQuyraemey: *_Typing📲_* *_🔮TAKUN SAAƘA!!🔮_* *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* _ZAFAFA BIYAR 2K22_ _________________________ *_Chapter Four_* ...........Suna baro cikin asibitin Muhibbat ta kashe wayarta dan ma kar Yah Ammar ya sameta.         Tun farkon shigowa anguwar tace a saukesu. Amma sai Zahidah tace sam basu yarda ba a kaisu har ƙofar gida. Zata fara masifa Hafsat ta ce, “Kiyi haƙuri ya kaimu saboda bazan iya taka ƙafarnan ba Hibbah”.        Shiru tayi bata sake tankawa ba har suka iso ƙofar gidan su Hafsat daya kasance a farko, sai nasu Zahidah, Muhibbat ce ƙarshe. Saboda ciwon dake tare da Hafsat ɗin ya sakasu cewa a tsaya ƙofar gidansu. Zahidah ta bama mai taxi kuɗinsa tana godiya. Amma sai yaƙi amsa. Mamaki ƙarara a fuskar Zahidah da Hafsat. Sun buɗe baki zasu magana yay musu alamar suyi shiru.        “Basai kunce komai ba, inhar da wannan mai bakin tsiwar tare da ku anta kaiku waje ƙyauta kenan babu ko sisin ku”. Yay maganar idanunsa akan Muhibbat yana wani sassanyan murmushi.           Hararar da yay tsammani ta watsa masa, cikin takaici tabar wajen batare da tace komai ba. Kira Zahidah da Hafsat suka shiga ƙwala mata suna dariya, amma ko waiwayensu batai ba harta ƙarasa gaban wani gida mai baƙin gate. Sai da ta kama murfin zata shiga ta waigo, ganin har yanzu mai taxi ɗin na tare da su yasata jan tsaki akan laɓɓanta ta ce, “Maye kawai”. Daga haka ta shige ciki.          Gida ne da zamu iya kiransa babba a girma da ginuwa. Dan a ƙalla akwai ɓangarori biyu zuwa uku a cikinsa. Ɓangarori biyu na farkon shiga gidan sunfi haɗuwa da tsaruwa, zakaga hakan tun daga wajema kafin ka kai ga shiga ciki, sai dai kuma ɗayan dake daga ciki ya fisu girma, amma bai kai su ƙyawu ba.         Harara ta zubama sashen guda biyu tana taɓe baki, tana gab da wucesu taja tsaki a zuciyarta wanda batai zaton ya fito har waje ba.      “K!! Dan ubanki wa kikema tsoki!!”. Wata buɗaɗɗiyar murya mai cike da hargowa ta faɗa. Cak ta tsaya ƙirjinta na bugawar tsoro, tabbas da ace tasan mugun nan ya dawo gidan da bazata shigo ba sai magriba. Jin takun tafiya a bayanta alamar ya taso ya sakata juyowa. Ƙiris ya rage ya iso gareta, babu shiri ta kwasa da gudu zuwa sashen can ciki tana ƙwala kiran sunan Ummi!.        “Ya ilahi! Tanee lafiyarki kuwa? Wai sai yaushe ne hankali zai game jikinki kisan girma ya fara zuwa miki!”.       Ummi dake ƙoƙarin fitowa a kitchen riƙe da ludayin miya a hannu ta faɗa. Dai-dai isowar Hibbah cikin falon itama a guje. Bayan Ummi taje ta maƙale.       “K da wa kuma?”. Ummi ta faɗa tana juyowa gareta fuska a ɗaure.       “Wannan mugunne fa Junaid Ummi. daga na shigo ina tsaki ya hau zagina kamar nasan da zamansa ma a gidan”.           Baki Ummi ta buge mata, tai saurin ja da baya daga jikinta tana dafewa.         “Wannan bakin naki da kanwa bata jiƙa a cikinsa shi zaisa kiyita shan wahala a wajen mutanen gidan nan Tanee. Mara kunyar banza matsamin a hanya”.        Gefe Hibbah ta matsa gudun kar Ummi ta sake kai mata wani dukan hawaye cike da idanunta. Sai da taga ta koma kitchen ɗin sannan ta nufi ɗakinta zuciyarta na ƙara jin tsanar mutanen gidan nasu. Da ace zata samu wata dama a hannunta koda ta yini guda ce sai ta bisu da bulala hansin-hansin, musamman ma Hajiya Mama da Abba da wannan azzalumin Junaid ɗin. Mukulli ta murza a ƙofar tata dan batason sake magana da kowa.           Tunda Ummi ta jiyo ƙarar rufe ƙofar Hibbah sai tai murmushi, tasan hakan na nufin tayi fushi, ba kuma zata buɗe ba sai Yah Abubakar yazo ya lallasheta ko jarabar danna Computer ɗin tata ta motsa. Watsar da ita tai ta cigaba da aikinta saboda bataso magriba ta sameta. Cikin ranta tana tunanin yaushe Junaid ɗin ya dawo ƙasar? Dan bataji alamun murna da ga yaran gidan ba sam. Rashin mai amsa mata zancen ya sata watsarwa ta cigaba da aikin gabanta.       Harta kammala ta shige babu wanda ya shigo a cikin samarin ƴaƴan nata, fatan dawowa lafiya tai musu sannan ta shiga wanka.        A ɓangaren Hibbah ma wankan tayi, kasancewar tana fashin salla tana kammala kintsawa ta fito, dan ta tabbatar Ummi ta shige. bakuma zata sake leƙo falon ba sai bayan sallar isha'i. Yayunta kuwa bata tsammanin yau zasu kwana a gidan ma. Musamman Yah Abubakar da Yah Usman da yace yana katsina.           Study table ɗinta ta haye dake can gefen falon a wani ɗan lungun. An shirya mata wajen tsaf da kayan karatu na musamman saboda kasancewarta ƴar gata, sannan haziƙa wajen sanin sirrin sarrafa Computer.         Tun ana ɗaukar lamarin nata shashanci har takai yanzu Yayansu Abubakar naci da ga tagomashin ƙwazon nata ta hanyar aikinsa na tsaro. Dan yasha sakata ayyuka masu muhimmancin gaske ana kuma samun nasara tunma bata kai haka shekaru ba. Wannan dalilin ne ya sakashi tsaya mata wajen ganin ta cika burinta akan zurfin nazari game da na'ura mai ƙwaƙwalwa.          Cike da ƙwarewa ta kunna Computer ɗinta saboda aikin data tarkatarma kanta na bibiyar masu power bike. Dan ta ɗauka alwashin kosu ɗin ƴaƴan uban waye sai ta gano su insha ALLAH.          Babu wanda ya shigo gidan sai Ummi data fito bayan sallar isha'i tace ta tashi taje taci abinci tunda babu wanda ya dawo a yayun nata har yanzu. Da to ta amsawa Ummin, tana gani ta koma ciki ta cigaba da aikinta cike da zaƙuwa. Ummi dake jiyo motsin Hibbah ta shiga ƙwala mata kira ganin dare ya farayi. ta tabbatar kuma inba da gaske tayi mata ba, zata iya kaiwa biyun dare akan Computer ɗin batare da gajiyawa ba. *_Tanee! Tanee!!_* wai bazaki tashi a gaban Computer ɗin nan kije ki kwanta ba sai na ci ƙaniyarki ko?!”.        Hibbah dake zaune a cikin falon daga can gefen study table ta ƙwaɓe fuska tamkar zatai kuka. A kallo ɗaya zaka fahimci tarin ƙuruciyar dake tattare da ita, dan kwata-kwata bazata gaza shekaru goma sha tara a duniya ba. Jin tahowar mutum ta bayanta ta miƙe da sauri a gaban Computer ɗin tana faɗin, “Wayyo Ummi nafa kusan gamawa wlhy”.       “Ai ba Ummi ɗin bace, mai kunnen ƙashi nine”..   Ƙyaƙyƙyawan saurayi mai tsananin kama da ita da bazai wuce shekaru ashirin da takwas ba ya faɗa a bayanta tare da kai mata ranƙwashi bisa kai. Tsalle tai zuwa gefe tana fasa ƙara duk da kuwa bai sameta ba. Ya balla mata harara yana kai hannu kan mouse ɗin Computer ɗin ya kasheta baki ɗaya. Dai-dai lokacin da yake ɗagowa ya nuna mata hanyar ƙofar ɗakinta yana faɗin, “kama gabanki kafin jikinki yay tsami anan”.         Idanunta dake tara ruwan hawaye ta shiga ƙyaƙyƙyaftawa. Cikin narkewar fuska tace, “Yah Umar dan ALLAH ka barni wlhy zuwa 12 zan shige na kwanta. ALLAH akwai abinda nakeyi mai muhimmanci a ciki”.             Charger ɗinta dake jikin socket ya fizga da nufin kai mata duka. Da sauri ta dirga wani uban tsalle da ihu tare da kwasa a guje zuwa hanyar ɗakin nata.         “Wai wane irin salon iskanci ne haka za'a dinga damun mutane da ihu kamar ƴaƴan rashin ƙwaɓa!”.     Wata murya mai kauri da amo ta faɗa daga bayansu. Basai an sanar musu wanene ba, dan haka Tanee dake gab da shiga ɗakinta ta ida afkawa da sauri tana rufo ƙofar.  Umar yaɗan rumtse idanunsa yana cije lip ɗinsa na ƙasa da ƙarfi alamar son saisaita kansa dan jin zafin furucin mutumin da aƙalla zai iya kai shekaru Hamsin da huɗu zuwa da biyar        “Wai dan iskanci ba magana nakeba akaimin banza saboda rashin tarbiyya!. To dan uban mutum dai duk yanda yake kallona nine uban ubansa ma bama shi ba. Sannan kuma mijin uwarsa ne ni!!”.      Murmushi mai ɗaci Umar yayi yana haɗiye abinda ya tsaya masa a maƙoshi saboda kallon da Ummi dake fitowa tai masa. Yaja numfashi a sarƙe da faɗin, “Kayi haƙuri Abba ba wani abu bane ba. Nine da Tanee”.         “Eh lallai ai basai ka faɗaba na gani kai da taɓararriya ne, to ubanmi kale mata da har takema mutane ihu kamar wadda ake lalub....”      Cikin ɓacin rai Ummi ta katsesa da faɗin, “Kai Umar wuce ka tafi sai da safe”.           Zuwa yay ya wuce yana faman taunar lips ɗinsa dan shi kaɗai yasan tuƙuƙin baƙin cikin da yakeji a cikin ransa game da ƙanin mahaifin nasu da a yanzu suke kira da Abba saboda maye gurbin mahaifinsu da yayi dalilin ƙaddarar mutuwa, tabbas badan mahaifiyarsu ba da ko kallon hanyar da sukabi tuni kawun nasu bazai ringayi ba. Amma dasun yun ƙuro itace mai taka musu burki.                Umar na ficewa Abba ya saki wani shegen tsaki da nufar hanyar ɗakin Ummi. Itama bayansa tabi a fusace. Suna shiga cikin ɗakin a zafafe tace, “Halilu ina rabaka da jifarmin ƴaƴa da mugayen furuci amma baka kiyayewa. Ka sani idan ada ni dasu mun ɗauka wulaƙancinka da tozarci wlhy yanzu bazamu ɗauka ba. Dan badan ina takama yaran nan birki ba a kanka bisa dalilin mahaifinsu da tuni sun tabbatar maka da suma sunkai girma. Idan kuma bazaka bariba to lallai zan buɗe musu ƙofar dana rufe domin maka hijjabi akan hakan.....”         Wata wawuyar dariya ya saki yana faɗawa saman gadonta. Cikin salon iskanci da izgilanci yakai ƙafa ya taɗota sai gata ta faɗo kansa. Yunƙurawa tai zata tashi ya birkiceta zuwa ƙasa ya koma samanta. Dogon gashin da ALLAH ya azurtata da shi duk da tsufa yasa ya fara sirkawa da furfura ya damƙe cikin hannunsa tare da ɗan kwalin kanta ya fisga da ƙarfi, tare da sak ɗayan hannunsa ya danne mata baki............✍ *TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *ALSHIRINKU MASU KARATU!!!* *_NAJI DADI SHINE GARI......_* *KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA* _ILIMI_ _NISHADI_ _TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_ *MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR* *NA SABUWAR SHEKARAR 2022* *WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!* *SABBIN LABARAI* *SABUWAR SHEKARA* *SABON NISHADI* *_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_* *MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN* *_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_. *_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_ *_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_ *_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_ *_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_ *ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa* 6019473875 MUSAA ABDULLAHI SAFIYA keystone bank Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 08184017082 *IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA* 09134848107 Littafi daya 1____300 2____400 3____500 4____700 Duka gamayyar biyar din(1k) 1,000 *INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽 #team ZAFAFA BIYAR *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [12/31, 6:21 AM] Abbu Saleh AlQuyraemey: *_Typing📲_* *_🔮TAKUN SAAƘA!!🔮_* *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* _ZAFAFA BIYAR 2K22_ 🔥🔥🔥🔥🔥 *_LAST BONANZA_* *KARO NA QARSHE!* *_farincinku shine namu,ZAFAFAN DAI,sun sake amsa kokenku,sun sake rage muku kaso 20 cikin 100_* *_Daga yau 29 ga wata,har zuwa 31 ga watan nan,xaku iya biyan 800 a amadadin 1000 na kudin litattafai biyar_* *_za'a fara posting in sha Allah 3st January da yardar Allah_* *HANZARTA KI BIYA NAKI KAFIN RANAKUN SU QARE* *XAKI BIYA TA WANNAN ACCOUNT NUMBER DIN* 6019473875 MUSAA ABDULLAHI SAFIYA SAIKU TURA SHAIDAR BIYA 08184017082 GA MASU TURA KATIN WAYA KO KUMA VTU,SAIKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYANKU 09134848107 _________________________ *_Chapter Five_* ............Wani irin rawa jikin Ummi ya fara saboda azaba. Ya ƙyalƙyale da dariya yana wani fici-fici da ƙananun idanunsa jajaye. “Asiya idan kin manta bara na tuna miki. Daga ke har ƴaƴanki da kikeji girmansu ya kai yanzu a tafin hannuna kuke wlhy. Zan kuma iya binku ɗaya bayan ɗaya na salwantar da rayuwarku batare da wani mahaluki ya iya gane hakan ba ko zargina. Kamar yanda na gagareki a baya da kikeji da ƙuruciya a yanzunma hakan take. Dan haka ki cigaba da buɗemin ido da tsagerancin nan naki kiga idan ban kai rayukanku ƙasa ba cikin ƙanƙanin lokaci”.     Ya ƙare mganar da hankaɗa kanta ta bigi fuskar gadon. Wata siririyar ƙara ta saki ta zaba. Cike da juriyar zaluncin data saba sha daga garesa ta dubesa da idanunta da suka kaɗa zuwa ja tana ƙoƙarin haɗiye ƙwallar dake taruwa a cikinsu. “Insha ALLAHU Haƙilu bazaka taɓa cin nasara akan zuri'ata ba bayan nasarar aure na da kayi a baya, bazan gaji da faɗa makaba ko yanzu kana samun nasarane a kaina saboda wasu dalilai na lizzamin zaren ƙaddara, amma ka jira lokaci, dan kaɗan ya rage azo dai-dai wajen da zakasha mamaki.......” Sake buga kanta yay a fusace kafin takai ƙarshen zancenta saboda sukar zuciyarsa da kalamanta sukeyi a duk sanda ta maimaita masa su, ya saka hannunsa ya danne mata baki yana ƙyalƙyalewa da dariya. “Iyakarki kauɗin banza da cika baki Asiya, amma ki sani ni Haƙilu nafi ƙarfinki, dan baki da maraba da wulaƙantacciyar dabba a gareni, amfaninki a wajena kawai samun abinda nai kwaɗayi a gareki tun farko kika hanani, yanda kika wulaƙantani a kansa a baya haka zan cigaba da samunsa a gareki cikin wulaƙantarwa da ƙasƙantar dake a ƙasan takalmana.” Da iya ƙarfinta tai yunƙurin turesa amma ta gaza hakan, sai ma ƙara jigata da wahaluwa da takeyi a hannunsa. Yayinda shikuma yake ƙyalƙyala dariyar shaƙiyanci a gareta da izgili, cikin tsantsar zalunci da wulaƙantarwa ya shiga ƙoƙarin yin tarayya da ita kamar wanda ke tare da ƙasƙantacciyar karuwarsa. Yanayi yana kai mata mari saboda ƙoƙarin ƙwatar kanta da takeyi a garesa.          Kamar kullum sai da ya galabaitar da Ummi son ransa sannan ya barta yana faman tuntsurar dariyar rashin imani. Yaja kayansa ya saka bayan ya goge ƙazantar jikinsa da gashin kanta tare da tofa mata yawu ya fice yana cigaba da ƙyalƙyala dariyar.          Wani irin siririn kuka Ummi ta saki mai cin rai a wajen. Takai kusan awa ɗaya tanayinsa kafin ta miƙe zuwa toilet da ƙyar saboda azaba. Dukkan dabarun data sabayi domin gyara jikinta a duk lokacin da hakan ta faru tsakaninsu su ta gudanar, koda ta fito doguwar riga ta saka tahau saman abin salla ta fara gayama ALLAH kukanta akan zaluncin Alhaji Haƙilu ƙanin mijinta ada, sannan kuma mijinta a yanzu.          Bayan tayi nafilfilinta tai zaman karatun AL-QUR'ANI. Sai da taji zuciyarta tayi mata sanyi, nutsuwarta ta dawo jikinta sannan tai addu'a ta ɗan kwanta, cikin lokaci ƙanƙani barci mai daɗi yay gaba da ita tamkar bata da wata damuwa. ★         Kamar yanda ta horar da yaranta tun suna ƙanana yau ma tun kiran sallar farko na asuba suka tashi. Sai da duk sukai alwala sanann suka firfito daga ɗakunansu su biyar abin sha'awa, dan a daren duk suka dawo ba kamar yanda ta tsammaci zasu kwana a wajen ba, a tunaninsu tayi barci ita da auta shiyyasa basu shigo ba. Ammar ne ya nufi ƙofar ɗakin Hibbah ya shiga mata knocking da kiran sunanta har sai da yaji ta amsa. “Tashi kiyi salla, saura kuma idan kin idar ki sake kwanciya tunda kinsan dai yau kinada text ɗin safe”.           Bai jira amsartaba yabar wajen dan yayunsa na jiransa. Basu damu da tada Ummi ba, dan sunsan ita bata makara saboda mace ce mai tsantseni da yawan kula da ibada, bata da wasa sam akan bautar ALLAH. Hakama koda suka fito daga sashen nasu basuyi gigin tada sauran jama'ar gidan ba suka fice abinsu zuwa massallacin anguwar.         Daƙyar Hibbah ta tashi zuwa toilet saboda barcin dake cikin idonta. Cikin layi da rangaji irin na wadda ta tashi a barci ta shige bayin. Kusan mintuna ashirin sai gata ta fito ɗaure da towel tana tsane gashinta da wani alamun ta samu tsarki. Zani ta ɗaura ta saka hijjab har ƙasa ta tada salla. *_7:34am_*            A gurguje take shiri tana yawan kallon agogon ɗakin nata saboda kiran da Ummi keta faman ƙwalamata daga falo.        Cikin kumbura fuska da ƙunƙuni take faɗin, ‘Kai Ummi wannan kira kamar makauniya, ai ba kowa ne ya jamin wannan makararba sai Yah Ammar, duk da yasan zanje makaranta harda min gargaɗin karna koma barci sai gashi bayan dawowarsu massallaci ya tsareni sai na haɗa masa indomie wai nafi kowa iya dafawa........’       “Tanee! Tanee!!”.     Ummi ta sake ƙwalama Hibbah kira again. Ƙoƙari amsawa take cikin zazzaƙar muryata tana tattare tarkacen abinda zata buƙata a cikin bag ɗinta mai zubin school bag. Daga can ta sake faɗin, “Auta kina kallon agogo kuwa?!”.         Saurin ɗaukar bag ɗin tayi da gyalenta tayo waje da hanzari. Tun kafin ta ƙaraso tsakkiyar falon Yah Umar ya wullomata harara cikin faɗa. “Wai ke kullum sai kin makara kin makarar da mutane hankalinki ke kwanciya a gidan nan ko? Tun kina zuwa secondary halinki kenan, yanzu kin fara jami'ar ma baki canjaba”.        Fuska ta kumbura tana tura baki, ta ajiye bag ɗinta da gyalen a saman kujera tana ƙarasawa dining ɗin inda duk suke zaune har Ummi, dan haka suke cin abinci a tare duk safiya da dare. Cikin shagwaɓar data saba da tsiwar da bata barin bakinta tace, “Kai Yaya Umar naga dai Yah Ammar ne ya sakani makara, sakanifa yayi na dafa masa noodles”.         Yah Ammar dake kujerar gefenta yana ƙoƙarin fara cin indomie ɗin data dafa masan ya zubomata uwar harara shima yana faɗin, “Dama can kin saba makararki yarinya zaki wani jingina dani”.        Baki ta sake buɗewa zatayi magana Yah Usman dake duba wasu takardu dake gabansa a dining ɗin shima ya watso musu harara ita da Ammar ɗin, “Dalla malamai karku cika mana kunne kuma ko”.      Ummi dake turama Hibbah kofin kunu data zuba mata tace, “Ai inda sabo sun saba, Ammar da Tanee basa taɓa zama waje guda basu isheka ba, sai kace suna ganin hanjin junansu. Nikam babu mai barina da ciwon kai kowa yayi ya gama ya kama gabansa”.        Baki Hibbah ta kuma cikawa da iska tana duban Yah Muhammad da Yah Abubakar masu kareta. Yaya Abubakar dake hidimar haɗama kansa shayi yayi murmushi, “Auta yada kallona kuma? Nimafa yau gashi kina neman makarar dani bayan nace da wuri zan fita”.        Cikin shagwaɓar da takema yayun nata saboda so da ƙaunarta da sukeyi ta ce, “Yaya kaima ko?” ta faɗa tana maida dubanta ga Yah Muhammad da ke ta faman latsa wayarsa. Ƙaramar dariya yayi tunkan tace komai, ya ajiye wayar tasa yana amsar kunun da shima Ummi ta zuba masa dan kusan halinsu ɗaya da Muhibba shima bai cika son tea ba. “Kinga autan Ummi manta da kowa ki karya, yau da kaina ma zan kaiki makaranta bazakibi Ammar ba, maza lokaci na sake ja”.     Jin Yah Muhammad yace da kansa zai kaita makaranta yau ya saka bakinta washewa. Ta kalli Yah Ammar abokin tsamartata tana masa gwalo. Kusan duk sai da sukai murmushi kowa na girgiza kansa cike da mata kallon so da ƙauna.      Basai an faɗa ba, yanda ƴan uwata da Ummin su kema Hibba a gidan zaisa kowa fahimtar ita ɗin ƴar gata ce kuma shalele. A kullum kowa burinsa yaga farin cikinta. Koda laifi tayi suka zaneta ko mata faɗa daga baya sai su koma mata nasiha da lallashinta har sai sunga ta koma rayuwata ta ƙiriniya da rashin ji suke samun nutsuwa. Sai dai kuma a ɓangaren Abba da sauran matansa sam ba haka bane. Sun tsani Muhibbat tamkar ita kaɗaice ƴa a gidan. Hakama sauran ƴaƴan gidan duk basa sonta. Kafin Hibbah takai haka kullum tambayata mi sukai musu? Amma babu mai bata amsa a tsakanin Ummi da yayunta guda biyar. Sai da tayi hankali ne zuwa yanzu take ɗan fahimtar wasu abubuwan duk da dai ba wani ya taɓa zama ya sanar da ita gaskiyar dalilinba har zuwa yanzun.      Itace farkon kammalawa, ta miƙe tana faɗin, “Alhmdllh”.          Yaya Abubakar ya dubeta da kulawa cikin lallashi yace, “Auta ki dingacin abinci ko zaki ƙara girma fiye da haka dan ALLAH, ke kowa na girma yayi ƙiba banda ke, makarantar nan kamar ƙara tsiyayar dake take ma”.       Murmushi tayi cike daso da ƙaunar Yayun nata masu sonta. Tace, “Yah Abubakar duk wannan ƙatuwan dana zama, da kaɗan fa Yah Ammar ya fini tsaho”.     Harara Yah Ammar ya galla mata da faɗin, “Tunda nine marainin wayonki ko? bar ganin Ummi a wajen, na tashi ɓarar dake zanyi ALLAH”.          Dariya duk suka sanya masa, dan da alama da haushi yake maganar. Hibbah tai masa gwalo da ɗaukar bag da gyalenta ta fice da gudu saboda ganin zai miƙe, tasan kuma kanta zaiyo. A ƙofar fita falon taci karo da Abba. Tai saurin komawa baya jikinta naɗan rawar kaɗuwa. Dan duk da rashin tsoro na Muhibbah a rayuwarta tana matuƙar jin tsoron Abba tun tana ƴar ƙarama. Hararar da yake wulla mata ya sata sake sata duƙar da kanta idanunta na tara ƙwalla.         “Wane kalar shashanci ne kuma haka? Da girmanki amma kullum lalacewa al'amuranki ke ƙarayi saboda ke ƴar ido ce!!”.         Sam Hibbah bata son tsawa, shiyyasa da zaran Abban ya mata ita take rikicewa, yanzu ɗinma duk sai jikinta ya hau ɓari, muryarta na rawa alamar tahowar kuka tai saurin faɗin, “Kayi haƙuri Abba bansan ka tahoba ALLAH. Ina kwana”.          Ciki yay batare daya amsa mataba yana jan tsaki. Hibbah ta bisa da kallo wasu hawaye masu zafi na sakko mata bisa ƙyaƙyƙyawar fuskarta. Ido suka haɗa da Yah Usman. Ya girgiza mata kansa alamar kar tai kuka. Dan tun tsawar da Abban yay mata duk hankalinsu ya dawo kansu.      Suma koda suka gaishesa bai amsa musu ba. Sai faman mazurai yakeyi. Basu sakebi takansaba duk suka kwashi kayayyakinsu sunama Ummi sai sun dawo. Itako amsa musu take da fara'a tamkar batasan da zaman Abban a wajenba ma.         Yah Muhammad ne ya kama hannun Hibbah da ko motsi ta kasayi har yanzun. Sai da sukazo har wajen motarsa yasa handkerchief ya share mata hawayenta batare daya ce komaiba. Sauran ƴan uwansa ma kuma bai basu damar cewa komai ɗin ba. Sai umarnin yin addu'ar fita gida kamar yanda suka saba yay musu.       Suna kammalawa kowa ya hau abin hawansa. Yah Muhammad da Hibbah. Abubakar ya ɗauka Usman da Umar a motarsa dansu basu da mota har yanzu sai mashina. Ammar ma ya hau mashin ɗinsa lifan shi kaɗai tunda yau Hibbah tabi babban yaya...........✍ _BONANZA, BONANZA, BONANZA 20% OFF ZAFAFA PAID BOOKS, OFFER ENDS ON 31st DEC 12AM INSHA ALLAH!_ _ASSALAMU ALAIKUM!!_ _ZUWAGA MASOYA, KUMA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR._ _KORAFI YA KARBU, DAGA YAU LARABA 29 GA WATAN DECEMBER IN SHAA ALLAH, ZUWA 31 GA DECEMBER RANAR JUMU’AH KENAN. BISAGA KORAFI DA NEMAN RAGE KUDIN ZAFAFA NA DUBU DAYA KAN LITTAFAN BIYAR, IN SHAA ALLAHU, KORAFIN KU YA ISA GARE MU. KUMA MUN AMINCE. ZAMU KARBI 800 GA LITTAFAI BIYAR DIN DA KUKE BUKATA, A MAIMAKON DUBU DAYA NA BOOKS BIYAR. YAU LARABA ZUWA JUMU’AH KARSHEN WATAN DECEMBER KENAN. ZAMU RUFE KARBAR 800 KUDIN ZAI KOMA DUBU DAYA KARFE 12 NA DAREN RANAR JUMU’AH INSHA ALLAH._ _GA WATAN JANAIRU (3st JANUARY, ZAMU CIGABA DA KARBAR DUBU DAYA KAN LITTAFAN BIYAR._ _A KUMA 1 JANUARY DINNE IDAN ALLAH YA KAI MU, ZAMU FARA SAKIN PAGES DIN LITTAFAN NA KUDI, WATO PAID PAGES👏🏼👏🏼NA BOOKS DIN._ _LITTATTAFAN SUNE: *DABI’AR ZUCIYA (FALL IN LOVE)* NA SAFIYYAH HUGUMA_ _*HALIN GIRMA (GLAMOROUS LOVE)* NA HAFSAT RANO_ _*DEEN MARSHALL: (INTENSE LOVE)* NA MAMUH GEE_ _*SO DA ZUCIYA (A LOVE SO BEAUTIFUL)* NA: NANA HAFSAT MSS XOXO_ _*TAKUN SAAKA(LOVE IN TIME)* NA: BILLYN ABDULL._ _KAI DAGA JIN SUNAYEN KASAN ZA’A SHA GWAGWARMAYA A KUMA KARU DA DARUSSAN DA ZASU KOYAR, NA FADAKARWA DA NISHADANTAR WA HADI DA TACACCIYAR KAUNA MARAR GAURAYE_ _DOMIN KASANCEWA CIKIN MABIYA LITTAFAN ZAFAFAN SAI A TUNTUBE MU TA.👇🏾_ *_WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_* *ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA* *_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_* *GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi* *JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE* *_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_* *_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_* *_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_* *_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_* *_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_* *DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL* 2👉🏾400 3👉🏾500 4👉🏾700 5👉🏾1000 *Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin* 6019473875 MUSAA ABDULLAHI SAFIYA keystone bank Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 08184017082 *IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU* 09134848107 *_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽 #team zafafa biyar *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*. *************************⬇********************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ **************************