*ALLURA* _(Ta tono Garma)_ ********************** ⬇ ************************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _1_ Cike da kissa da k'warewa cikin salo mai birgewa ta kalleta tace "Malama Farida, kin tabbatar bayan alak'ar aiki dake tsakaninki da mai gidanki babu wata alak'ar?" Cike da rashin gaskiya murya k'asa k'asa tace "Eh babu." Faffad'ar takardar hannunta ta nuna mata tace "Wannan takardar na d'auke da jerin bayanan kiran wayar dake shiga da fita tsakaninki da Alhaji Sunusi, zaki iya fad'awa kotu akan me kuke tattaunawa haka da a k'alla kullum kukanyi waya sama da sau goma sha biyar?" Rarraba ido ta shiga yi cikin rashin gaskiya tace "Mafi aksari munfi tattaunawa akan abinda ya shafi aiki, matsayina na sakatariyarshi (secr茅taire) yana kirana a waya ko ni na kirashi kan wani abu da yake son umartata ko kuma ni na tambayeshi." Jinjina kai tayi tace "Kina da masaniya akan kowace doka cewa ba'a yarda wata haramtacciyar alak'a na shiga tsakanin ma'aikaci da ubangidansa ba?" Saida ta had'e fuska alamar jin haushin tambayar sannan tace "Eh na sani." Jinjina kai tayi tare da kyab'e baki tana sake had'e hannayenta tana mitsitsikasu tace " Ranar 26 ga watan 11 shekara ta 2020 kinje ofishin Alhaji Basiru, zamu iya sanin me ya kaiki?" Da sauri kamar yanda aka horeta akai tace "Ni banje ofishin shi ba, ban je ba." Cike da son tabbatarwa tace "Baki je ba?" "Eh." Ta fad'a tana sake gimtse fuska, murmushi tayi ta nufi teburinta ta d'auko wasu hotuna ta dawo gabanta ta mik'a mata tare da fad'in "Kin gane wacece a jikin hoton nan?" Tana kallon hoton ta d'ago tana wuk'il wuk'il da ido ta kasa cewa komai, jin shirun yasa ta karb'ar hoton ta juya ta kai wa magatakarda tare da fad'in "Ya mai shari'a wannan duk da tace bata je ba amma ga zahiri nan, a ganinta da kuma tunaninta shigar dare tayi tare da b'atar da kammaninta dan haka babu mai ganeta, amma inda asirinta ya tonu shine akwai cctv cam茅ra a wani kampanin sarrafa leda dake kusa da ofishin Alhaji Basiru inda tanan ne muka samu damar ganinta." Da sauri lauyen dake kare gwmnati ya mik'e yana fad'in "Objection, ya mai shari'a wannan ba hujjar da zata gamsar bace duba da yanzu babu abinda computer batayi, za'a iya had'a wannan hotunan dan ganin an cimma buri akansu." Da sauri ita ma ta kalli alk'ali tace "Babu wannan nufin a tsarinmu, babban mutum ne da aka ci zarafinshi wanda ta kai har iyalinshi na kallonshi da abun, b'ata dare nayi da rana wajen ganin na tabbatar da mai gaskiya dan a mishi adalci ko da kuwa shi kanshi Alhaji Basiru ne." Da hannu kawai ya mata alama da zata iya ci gaba, sunkyyawa tayi tana rik'e da gefen gefen rigarta bak'a ta lauyoyi wacce ta mata kyau, sake juyawa tayi kan budurwar dake tsaye ta taka gabanta yayin da sautin takalmanta ke fitar da k'ara mai dad'in sauraro wacce ke tabbatarwa da mai sauraron an iya sarrafasu, kafeta tayi da ido "Malama Farida a duk sanda wata ya zo k'arshe ma'aikata da dama sukan je poste poste wasu kuma wajen casher na masana'antarku dan samun kud'in aikinsu, amma abu guda dake da d'aure kai shine, sanda ma'aikata ke ta shan gumi da zafin rana da turmutsutsu dan samun hakk'insu, ke kina gida kwance kina hutawa kike jin naki alerte d'in ta account d'in da daga ke sai mai gidanki ne ke da iko shiga ko fitar da kud'i ta asusun, me yasa?" Sunkuyar da kai tayi kamar zatayi kuka ta rasa abin fad'a, cikin muryar rashin wargi tace "Ke nake sauraro malama Farida." A hankali ta d'ago idonta taf da k'walla tace "Kamar yanda na fad'a miki ne babu komai tsakani na dashi, ni ban san komai ba wallahi." Kallonta tayi tace "Ba amsar tambayata kika bani ba." Kallonta tayi kamar ta kifa mata mari dan haushi tace "A kullum yana yaba k'wazona da hazak'ata, hakan ne yasa bana bin layi yayin karb'an albashi na." Wani murmushin takaici tayi tare da juyawa ta nufi inda take zaune, wasu takardu ta bud'a tare da d'auko wasu a takardu, nufa tayi wajenta ta nuna mata wani hoto tace "Kin gane a i'na aka d'auki hoton nan?" Tana d'ora idonta akan hoton take taji tasu ta k'are, rarraba ido ta shiga tana hangen tululen Alhajin dake zauna sai gumi yake shima yana k'yak'yabta mata ido alamar kar tayi magana, juyawa kawai tayi ta nufi gaban teburin da magatakarda suke tana nunawa alk'ali tana fad'in "Ya mai girma mai shari'a wannan hoton tabbaci ne na alak'ar dake tsakanin Farida da ubangidanta Alhaji Sunusi." Mik'awa magatakarda tayi ya mik'e ya karb'a shima ya juya ya mik'awa alk'ali inda ta sake nuna wata takarda ta mik'awa magatakarda tare da fad'in "Wannan takardar ita zata fallasa mana sirrin dad'ewarsu a tare, ba jiya ko shekaran jiya bane bare a danganta alak'arsu Alhaji Basiru, domin kuwa wannan takardar shaidar zubar da ciki ne da aka ma ita Farida da kuma saka hannun Alhaji Sunusi da amincewarshi shekara uku baya." Bayan ya karb'a ya sake bawa alk'ali inda ta ci gaba da fad'in "Bayan rayuwar da sukeyi da kuma aikin zahiri akwai na b'oye wanda ba kowa ne ya sani ba, a duk sanda wani ya so takara dashi a cikin harkarsu ko kuma ya nemi kawo masa cikas a tafiyarshi Alhaji Sunusi ya kan saka Farida ta ribaci mutumin, da irin haka sunyi nasara akan mutane da dama, daga ciki kuma shine Alhaji Basiru." Nuna d'aya Alhajin tayi dake tsaye gefe d'aya cikin damuwa ta ci gaba da fad'in "Tabbas Alhaji Basiru ya bayar da rahoton ingancin kayan da gwamnati ta siya a kampanin Alhaji Sunusi, sai dai abisa tilas ne yayi haka da fin k'arfinshi da akayi." Lauyan gwamnati ne yayi saurin mik'ewa har da buga tebur yana fad'in "Objection, mai shari'a babu ta yanda za ayi ace tirsasashi ne akayi, babban mutum kamarshi da yake cikin tsaro zaiyi wuya hakan ta faru dashi ba kuma tare da an fahimci hakan ba." Kallonshi alk'ali yayi yace "K'orafi bai karb'u ba, muna gaf da jin k'arshen shari'ar ne." Zaune yayi cikin rashin jin dad'i inda ta juya ita kuma tace "Nagode mai shari'a." Kallon Basiru tayi ta kuma kalli Farida tace "Mai shari'a malama Farida tayi anfani da damarta na kasancewarta mace ta ja ra'ayin Alhaji Basiru har ya biye mata, bayan ta samu abinda take kuma sai tayi anfani da hoton data d'aukesu tare saboda daman an shirya hakan, da wannan hotunan ta dinga mishi barazana dole ya saka bayanin da suka dace akan kayan nan, shi kuma tsoron karya rasa mutumci da kimarsa yasa shi rubuta kayan masu kyau ne, wanda gashi yanzu sanadiyar haka gwamnati ta shigar da k'ararshi tana neman tara mai yawa bayan kuma ta koreshi a aikinshi, ya mai shari'a a duba wannan lamarin a bi mishi hakk'inshi, nagode." Ya d'auki tsawon minti biyar yana rubuce rubuce kafin ya d'an tattara takardun gabanshi ya d'ago yana waina biron hannunshi yace "Abisa shedun da duka lauyoyin b'angarorin suka gabatar, kotu tayi dogon nazari tare da fahimtar cewa Alhaji Basiru baya aikata laifin nan bane da son ranshi, uzurin magud'i da *zanba cikin aminci* ne suka haddasa haka da kuma son zuciya, saboda haka kotu ta wanke shi, sai dai zai biya tarar da gwamnati ta buk'ata ba tare da b'ata lokaci ba, dalili kuwa yana da hannu a cikin asarar da gwamnati ta tabka wajen rugujewar ginin da take ginawa, sannan hakan zai iya zama darasi a gareshi ko dan gaba domin kiyayewa." Ajiyar zuciya ta sauke tare da kallon Basiru da shima ya sauke tashi ajiyar zuciyar, a tare suka sake mayar da kallonsu kan alk'alin daya ci gaba da fad'in "Siyar da gurb'ataccin kaya da basu da inganci, tilastawa jami'in gwamnati wajen saka hannu yayin da aka ribace shi da mace, hakan yasa kotun nan ta samu Alhaji Sunusi da laifi dumu dumu, abisa haka kuma kotu ta yanke mishi hukuncin zama a gidan yari na tsawon shekara hud'u tare da biyan tara ta jumallar kud'i million 25. Farida kuma kotu ta yanke mata hukuncin zama a gidan yari na shekara d'aya sakamakon taimakawa da tayi." Gudumar gabanshi ya buga sau uku wanda yasa mutanen ciki mik'ewa, ta k'ofar baya ya shige sannan mutane suka fara fita kowa bakinshi cike da tsegumi, tunda aka kamasu zasu tafi kowa ke hararenta, ko a jikinta sai ma hanzari da take na ganin ta tafi sabgarta ta gaba. Tana barin nan gidan wani alk'ali taje wanda ke ma wasu shari'a a gidanshi akan sulhun bashi, ko da taje nan ma ta samu d'aya lauyen yaje, bata b'ata lokaci ba wajen fito da wasu takardu a jakarta ta ordinateur (computer) d'inta ta shiga mik'awa dattijon tana fad'in " Alk'ali wannan takarda tana d'auke da yarjejeniyar da sukayi kafin gabatar da harkar, idan ka duba zaka ga *Lawan* ya karb'i kaya na million biyar a hannun *Usman*, amma a cikin rubutun da sukayi akwai abinda Lawan ya fad'a cewa ya karb'i kaya a hannun Usman zai rarrabawa mutane, yayi alk'awarin zai biya bayan wata uku, sannan Usman ya rubuta cewa ya amince Lawan zai biyashi bayan wata uku." Wasu re莽u re莽u (r茅cit) ta fito ta mik'a mishi ya karb'a tana fad'in "Wannan re莽u na shaidar kayan daya bawa mutane ne, a shagonshi na samo su a hannun yarenshi, alamu sun nuna ya bawa mutane kayan shima amma ba'a biyashi ko sisi ba." Marairaicewa tayi da cewa "Da wannan nake neman alfarma a wajenka daka saka hannu a sallami mutumin nan, dan ta hakane kawai zai samu damar da zai karb'o kud'ad'en a hannun mutane shima, amma kama shi da akayi aka rufe bashi ne zaisa ya fito da abinda baya da shi ba, sannan shi ma Usman d'an kasuwa ne, kuma kowa yasan k'alubalen da ake fuskanta yanzu a cikin kasuwa, nagode alk'ali." D'aya lauyen da tunda ta fara magana yake hararenta ta wutsiyar ido, baisan a gidan uban wa ta samo hujojjin da yake tunanin duk ya karb'esu ba? Baisan ya akayi ta same su ba har ta gabatar, a tsarin shari'ar wanda ya shigar da k'arar yana so ne a kasa samun belin Lawan, ta yanda a k'arshe za'a d'aga babbar kadarar Lawan d'in ta wani fili daya siya ya kuma tsonewa Usman ido, amma gashi ga dukan alama zasu samu belinshi. Bayan rubutun da yayi ne ya mik'a mata wata takarda yana fad'in "Lauya Faduma an baki belinshi, sai dai yanzu yana da wata d'aya da rabi na biyan bashin." Da farin ciki ta karb'a tana mik'ewa da fad'in "Nagode alk'ali, sai anjima." Tana shiga mota da sauri ta isa commissariat, tana isar da takardar aka bata shi, suna fitowa ta kalleshi tace "Dan Allah Lawan kayi k'ok'arin biyan kud'in nan akan lokacin da aka bamu, alamu sun nuna kamar Usman baya nufinka da alkairi, dan lokacin da naje shagonka bincike yaren sun fad'a min wani lauya ma ya zo yace shine mai kareka, dan haka ka kula sosai kaji." Jinjina kai yayi yace "Insha Allah Faduma, nagode sosai." Saida ta kama murfin motarta tace "Ba damuwa, ina sauri zan je na d'auki yarona a makaranta, ba dan haka ba dana ajeka gida." Murmushi yayi yace "Ba komai wallahi, kije Allah ya kiyaye hanya." Shiga tayi tana tayar da motar tana kallon agogon hannunta, gudu take sosai dan bata so ya jirata sosai. Ai kuwa tana isa bakin 茅cole d'in *Wangari* ta hangeshi a cikin gomannin yara, murmushi ta saki sanda ta paka motar gefe ta sauke gilashi tana kallonshi. A hankali kyakyawan yaron ya shiga duba kowace kusurwa na titin, saida ya tabbatar babu hatsari kafin ya tako cikin nutsuwa. Bud'e motar yayi ya shigo yana fad'in "Ayya sannu da zuwa?" Kallonshi tayi tana tayar da motar tana murmushi tace "Yawwa yarona, Nukoy (Ya kake)?" Da murmushi shima ya amsa da "Leyge (lafiya lau) Ayya." Cikin farin ciki da hira har suka isa quartier zaria 2, matsakaicin gida ne ginin zamani daidai rayuwar mai k'aramin k'arfi, wuri ta samu ta paka suka fita yana rik'e da jakar ordi. d'inta suka shiga ciki, da sallama duka a bakinsu suka shiga inda matar gidan ta amsa musu ita ma da farin ciki. Gaisheta sukayi ita ma tana musu sannu da zuwa, kallonta tayi tace "Ki shiga kiyi wanka saiki fito ga abincinku nan." *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 17:04 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ *Sis Lubabatu* *Maman Abulkhairi*鉂わ笍 Wannan kyautarku ce _Bismillahir rahamanir rahim_ _2_ Da murmushi ta wuce ciki tana fad'in "To Dada (Tanti), yau me kika dafa min?" Kallonta tayi tace "Me na dafa miki ko me na dafawa shalelen angona?" A hankali yaron ya kalleta cikin nutsuwa sosai yace "Me kika dafa min dara nra (masoyiyata)?" Dariya tayi tace "Ka fara shiga ka cire kayan saika zo ka duba da kanka." Shigewa sukayi ciki, a d'an k'aramin falon yana d'auke da d'aki hud'u a kowane b'angare sai ban d'aki daga d'aya b'angaren a nesa da sauran d'akunan. Bayan wasu mintuna ta fito cikin riga da siket na atamfa, masha Allah tubarkallah lallai kaya rufin asiri ne, kyawun Faduma da tsarin hallitarta ya kai matakin da kowane namiji ya kalleta a zahirancenta zai tsaya bawa idonshi hakk'insu. Doguwa ce mai diri da direwa sosai, komai na jikinta daidai yake da ita da tsarin hallitar fuskarta, duk da ba fara bace amma bak'inta mai kyau ne, idan kayi duba da yanayin gidansu da aikinta kasan ba majiya dukiya bane, amma kasancewar al'adarta tsabtarta da kuma kulawa da kanta da take yasa fatarta take wani shek'i da d'aukar ido. Kasancewar babu d'an kwali a kanta kitson kanta ya bayyana, lahaula kawai zata tofa dan gudun baki, gashin kanta bak'i sid'ik mai yalwar gashi tsayi da yawa, gashi kuma yasha kutso k'anana mai bala'in kyau da birgewa ga mai kallo. Zaune tayi tana jawo kwanon da Dada ta aje mata ganin ta fito, tank'washe k'afafunta tayi ta bud'e kwanon, hannu tasa ta fara ci bayan tayi bismillah, *Amjad* ne ya fito shima ya canza kayanshi, zaune yayi ta bashi nashi abincin shima ya bud'e, kallonta yayi yace "Nagode dara nra." Kallonshi Faduma tayi ta jawo kwanon, tana gani tayi murmushi ta kalleta tace "Dada lallai abinda angonki yafi so kika dafa masa." Cikin murmushin ita ma tace "Abinda ke kuma kika tsana ba." Murmushi kawai ta sake yi tace "Humm." Shiru sukayi babu mai magana har saida Amjad ya riga idawa ya tashi yana fad'in "Ayya zanje na kwanta kafin ayi sallah azahar ki tashe ni." Da murmushi a fuska ta kalleshi tace "To." Da kallo tabi bayanshi har ya shige, saida ya b'acewa ganinta ta saukr ajiyar zuciya, ta mayar da dubanta kan kwanon sai taga Dada na kallonta, saida ta kai loma baki ta kalleta tace "Ya dai Dada?" Murmushi ta shiga yi tan girgiza kai na wani lokaci kafin tace "Faduma kenan, saboda k'iyayyar da kike masa fa kika hana kanki cin biski da miyar taushe mai busashen kifi, sai gashi kuma d'anki ya fi son wannan abincin fiye da kowane." Ba tare da damuwa ba tace "Dada Amjad shi ya so wa kansa, saboda ya had'a jini dashi ne shiyasa, ni kuma babu abinda na had'a dashi." Cikin murmushi tace "Gaskiyarki kam." Tana idawa ita ma ta tashi ta koma d'akinta ta kwanta, ordi. ta d'auka tana daddawa dan ci gaba da binciken aikin dake gabansu yanzu da basu da adadi har bacci ya d'auketa. K'arfe biyu ta farka ta d'auro alwala tayi sallah, saida ta d'ora farar lafaya kan riga da wandon data saka sannan ta fito, a falon ta samu Amjad cikin shirin makaranta yana duba littafin makarantarshi, saida ta nufi k'ofa tace "Muje ko." Kallonta yayi yana mik'ewa yace "Ayya tun yanzu? Na shirya ne fa dan karki jirani dayawa, da sauran lokaci har yanzu." Juyowa tayi ta tsaya tana kallonshi tace "Amjad akwai inda zanje ne, idan na barka wa zai kai ka? Muje kawai jiran minti nawa ne zakayi?" Saida ya d'an turo baki yace "Ayya gaskiya ni..." Shirun da yayi yasa ta kallon fuskarshi tace "Uhum?" Girgiza kai yayi alamar ba komai, fitowa sukayi inda Dada ke zaune, kallonta tayi tace "Dada zan kaishi makaranta, daga nan zan wuce office d'in *Aminu* ne." Da fara'a tace "To Faduma sai kin dawo." Amjad ta kalla tace "Angona saika dawo." Jinjina mata kai yayi alamar to, a daidai k'ofar fita suka tsaya ita da shi, hannayensu suka d'aga inda Amjad d'in ne yayi addua'r fita daga gidan "Bismillah, tawakaltu Allahlah, lahaula walaquwata illa billah." Yana idarwa suka fita a tare, a hanyarsu ta tafiya kamar yanda suka saba tana tambayarshi a cikin karatun yan aji shida yana bata amsa, suna isa ta aje shi ya fita ya zagayo ta b'angarenta, kallonshi tayi ita ma tace "Allah ya tsare min kai yaro na, ka maida hankali kan karatunka kaji." Jinjina kai yayi tare da fad'in "Insha Allah Ayya, sai anjima." D'aga masa hannu tayi har saida ta ga shigewarsa kafin ta wuce, bata jima a hanya ba ta isa bureau d'in, kamar yanda yasan da zuwanta kai tsaye ta shiga ciki, bayan sun gaisa ne take tambayarshi akan matsalar da yake aiki kanta danta taimaka mishi kamar yanda shima yake taimakonta, bayan ta duba takardun daya bata ne tare da k'arin bayanin daya mata ta kalleshi tace "Aminu to me ka fahimta a game da shari'ar ne?" Gyara zama yayi yace "A gaskiya akwai abun d'aure kai, da fari meye dalilin da yasa ita tace ya daketa shi kuma ya musa akan haka?" Saida ta d'an buga teburin tace "Tambayar farko kenan, kasan wani abu?" Girgiza mata kai yayi har saida ta d'ora da "Abinda na lura dashi kamar akwai abinda waninsu ke b'oyewa, amma zamuyi bincike mu gano gaskiyar, tunda dole a cikinsu akwai mak'aryaci." Jinjina kai yayi yace "Hakane, to ya za ayi kenan yanzu?" Cikin jinjina kai tace "Ni zan sake bincikawa, amma kana ganin zai yiwu ace mashayi ne kamar yanda matar ta fad'a?" Murmushi yayi yace "Bamu da tabbbas gaskiya, amma bincike ne zai tabbatar mana da gaskiya." Da hanzari tace "Yanzu abunyi to ka je ka samu mijin ku tattauna, ni zanje gidan saina sake duba mana wani abun." Jinjina kai yayi yace "To shikenan." Saida ta saka k'aramar yatsarta a baki tana d'an cirar akaifa na wasu mintoci kafin ta kalleshi daga bisani tace "Ka lura da komai a tsanake ka fahimci yanayinshi, idan ta kama ka mishi tambayar da zata harzuk'ashi kaga shin zai iya duka idan ranshi ya b'ace ko kuwa." Jinjina kai yayi yana fad'in "Angama." Mik'ewa tayi tsaye sukayi sallama ta fita, daga nan hanyar gida ta d'auka tana tunanin abunyi. Saida ta gabatar da sallah la'asar da taga lokacinta yayi kafin ta fito ta kama girki, k'anwar mahaifiyarta *Owwo* na zaune tana had'a turaren wuta da take na siyarwa abun suna hira, zuwa biyar da rabi ta kammala tayi wanka ta shirya, fitowa tayi cikin wata lafaya mai ja da bak'i wacce ta mata kyau sosai, kallonta tayi tace "Dada zan je d'aukar Amjad." Da tausayawa ta kalleta tace "Faduma kina k'ok'ari sosai akan yaronki, Allah ya baki ladar d'awainiya da kikayi dashi, Allah yasa mai tausayinki ne shima." Murmushi tayi tace "Dada kin manta duk kece silar tsayuwata da k'afafuna, Dada kin fini cancantar addu'ar nan." Girgiza kai tayi tace "Kin cancance ta Faduma, dayawa irinki wasu jefar da yaran ma sukeyi, wasu kuma su kashesu da hannunsu, wasu ma kashesu sukeyi tun kafin su haife su." Saida ta d'an numfasa tace "Amma ke kin rabu da iyayenki ma saboda ki tseratar da d'anki, sannan gashi kin bawa komai baya rayuwar d'anki kawai kika saka a gaba, ko soyayya ba kyayi bare maganar aure." Wata irin dariya tayi wacce tasa dumple d'inta fitowa sosai akan kumatunta tare da fad'in "Dada soyayya? Ni Faduma? Haba dai Dada, ya kike maganar soyayya akai na kamar wacce bata san soyayyar ce ta jefa ni halin da nake ciki yanzu ba?" Tab'e baki tayi ta juya zata fita tana fad'in "Sai dai a lahira kuma idan anayi." Da sauri Dada tace "A'a wallahi Faduma ba dani ba, haka kawai zaki ce sai a lahira, maza ai suna suka tara, kuma ba duka suka taru suka zama d'aya ba, ko so kuke mu ci gaba da zama a haka ni dake ana zaginmu a gari ana fad'in na d'aure miki gindi?" Ko juyowa ba tayi ba sai murmushi da ta ci gaba da dokawa har ta fita, cikin nutsuwa da salama ta isa makarantarsu, tana isa yayi daidai da tashinsu kuwa, yana hangota ya zo ya bud'e k'ofar ya shiga ya rufe, kallonshi tayi jin baiyi sallama ba bai kuma gaisheta ba kamar yanda ya saba. A hankali ta shiga fahimtar yanayinshi da kayanshi, saida ta fara tuk'awa sun d'auki hanya tace "Ban hanaka fad'a a makaranta ba?" Sake rumgume jakarshi yayi ya shiga k'yabta ido yana kumburo baki, bata kalleshi ba saboda cunkoson dake akwai na yan makaranta ta ci gaba da cewa "Amjad da kai nake magana, da wa kayi fad'a? Me ma ya had'aka fad'a a makaranta?" Cikin turo baki yace "Ayya yaron ne ya raina ni fa, kullum yana tsokana ta dan ya ga ina k'yaleshi bana biye masa, shine yau fa har da keta min littafina yayi da gangan, shiyasa muka cire raini yanzu ba zai koma ja na ba." Da sauri ta kalleshi tace "Heeyeee Amjad, kana nemana da zaman lafiya kuwa?" Cikin turo baki yace "Yi hak'uri Ayya." Jinjina kai tayi tace "Amma ka kula daka keta kayanka ko?" Saida ya duba wuyan rigarshi daya yage kafin yace "Yi hak'uri Ayya, ba zan sake ba." Cikin kallonshi tace "Idan na hak'ura ubanka ne zai gyara kayan da suka lalace?" Kallonta yayi baki bud'e yace "Ayya dama wanda ya mutu yana dawowa ne?" Jim tayi ba tare data kalleshi na wani lokaci kafin a hassale tace "Kasan da haka kuma kake bani wahala? Yanzu saina siya maka sabbin kaya kenan." A hankali ya sake cewa "Kiyi hak'uri Ayya." Bata tanka mishi ba har suka isa gida, daf da sallah magriba haramar sallah sukayi dukansu. Da dare da k'yar ta samu sukayi karatun awa d'aya tare da Amjad kafin suka kwanta, amma ba baccin tayi ba sai binciken yanda za ayi ta gano gaskiyar mutuwar matar da ita dai take zargin mijinta ne silar mutuwarta, dare yayi sosai bata san sanda baccin yayi gaba da ita ba da gilashi a idonta dan rage hasken ordi. d'inta da kuma takardu duk a gabanta zube. *Faduma kenan*, agogo sarkin aiki, zak'ak'urar lauyar data d'auki aikinta da mahimmanci tamkar yanda take son kasancewar rayuwarta a cikin farin ciki, ta kan hana idonta bacci domin ganin ta zak'ulo gaskiya daga muhallinta ta d'orata a inda ya dace ko da akan wanda ya bata aikin ne, tana da dokoki kafin ta karb'i case d'in ka, idan kuma ta karb'a babu abinda zai hanata kai k'arshenshi. K'wazonta shine sirrin nasararta, hak'uri da dagiyarta kuma sirrin karb'uwarta, bindiddigi da takatsantsan d'in ta kuma sune garkuwar aikinta. dogaro da kad'aita sarkin al'arshi shi kad'ai kuma suka zama linzamin d'aukakarta. Aikinta ba dan kud'i ko suna take yi ba sai dan *so*, tana yinshi ne dan tana son shi da gaba d'aya zuciyarta tun yarintarta har zuwa kawo yanzu girmanta. *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 17:04 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _3_ Da safe Amjad ya shirya cikin riga da wando na islamiyya masu kyau ya d'auki littafi d'aya a hannunshi suka tafi, duk da akwai makarantu a wurin amma tafi gamsuwa da wacce take kaishi yanzu, ko da ta sauke shi kamar kullum sukayi sallama ta juya ta koma gida. Suna zaune tare da Dada suna d'ura turaren wutar data gyara jiya a kwalabe Aminu yayi sallama, da sauri Faduma ta shiga waigawa inda zata ga ko da kallabi da zata d'ora a kai, dan ita ba ma'abociyar saka hijab ce ba idan ba sallah zatayi ba, lafaya sune kayanta ita kuma ba hijabi ake d'orawa akai ba. Kafin ta samu abun d'orawar har ya shigo saboda gidan ba bak'onshi bane, dole ta dakata tare da amsa sallamarshi ita da Dada, k'arasawa yayi yana fad'in "Kina gida ashe?" Ba tare data kalleshi ba tace "Yanzu na dawo, ai na d'auka ba yanzu zaka taho ba." Bai amsa mata ba saboda gaisawar da sukeyi da Dada, bencin dake kusa dasu ya zauna, sai lokacin ta d'aga kai ta kalleshi tana fad'in "Ya ake ciki Ami..n" Bata k'arasa fad'a ba kawai tayi shiru ta sunkuyar da kanta, yanda ta ga idonshi a kanta duk sai taji ba dad'i, yanzu haka duk da kanta k'asa yake amma tana iya jin idonshi akanta, gata ita kuma riga da wando ne jikinta da suka kamata sosai, tana dawowa ta cire lafayar ta rataya kan wayar shanya kaya, ta wutsiyar ido ta lura da yana bud'a jakar daya shigo da ita, da sauri ta mik'e ta jawo lafayar a bayanta ta shiga d'aurawa a daidai nan ya juyo ya kalleta yana mik'o mata wata takarda wacce yake aikin wata k'ara a kanta Faduma kuma tana taimaka mishi kamar yanda suka saba yana fad'in "Duk abinda muka tattauna yana ciki." Saida ta d'aure lafayar ta karb'a tana komawa ta zauna, kallonta Dada tayi kawai tayi murmushi, tana cikin dubawa ya mik'o mata wata takardar yana fad'in "Nayi magana da abokin nan nawa likita, shima dai amsar tana nan, sai kiyi nazari akan duka abubuwan da muka tattauna." Jinjina kai tayi tana ci gaba da kallon takardun, numfasawa tayi ta kalleshi tace "Yanzu bureau zaka koma?" Kao tsaye ya amsa da "A'a akwai inda zanje ne." Jinjina kai tayi tace "Shikenan ba damuwa, nima anjima zanje na ganta muyi magana, amma idan zan tafi zan kiraka saika kaini." Saida ta kalleshi tace "Ba wata damuwa a game da hakan?" Murmushi ya mata sosai yace "Ko da damuwar ma ai kinsan babu ita tunda ke ce." Murmushi ta masa suka mik'e a tare ya ma Dada sallama, bayanshi Faduma tabi har k'ofar gidan yana k'ara mata bayani da baki, cikin mamaki yace "A ganina dai gaskiya banga ta inda mutumin nan ke da kazar kazar d'in duka ba, komai nashi cikin sanyi yake yinshi har da maganarshi ma, duk yanda nake ganin na kai ga zafafa kalamai gareshi dan yaji haushi sai naga duk yanayi d'aya ne a fuskarshi, yanayin tausayin kanshi kamar wani mata-maza." Dariya tayi sosai har tana sunkuyar da kanta hakan kuma ya sa shi kafeta da ido yana kallonta, saida ta d'an tsagaita tace "Tun a karon farko na fahimci matarshi hatsabibiya ce, duba da yanayin jikinta da nashi zai iya ja masa raini a gurinta, amma zaka iya tuna ranar da aka shiga zaman farko ta fad'a a gaban kotu wai dukan da yake mata duk ya farfasa mata jiki?" Cike da tanbaci yace "Eh, na tuna." Jinjina kai tayi tace "Yawwa, yanzu idan kun sake zaman na gaba ka sake tabbatarwa saika nemi ta nuna muku inda ya mata tabo a jiki, bayan nan saika gabatar da duk wannan hujojjin." Jinjina kai yayi tare da amsar takardun data mik'a masa tana fad'in "Insha Allah nima zuwa gobe zan je na ganta, hankalina ya rabu biyu ne shiyasa ba zan samu tafiya yau ba." Gyara tsayuwa yayi yace "Kalamanki na nuna kamar ba zamu shiga kotu tare ba ranar litini." Saida ta juya idonta masu haske sosai tace "Gaskiya ba zamu shiga ba, kaga duka ni da kai kowa yana da aiki, dan haka za dai mu had'u bayan kammala sauraran k'arar." Ajiyar zuciya ya sauke yana mata wani shu'umin kallo yace "In kuwa hakane na miki alk'awarin zan sanar dake wata muhimmiyar magana amma fa idan nayi nasara a kotu, hakan ne kawai zai bani k'warin gwiwa." Murmushi tayi sosai ba tare da kawo komai a ranta ba ita ma tace "Nima nayi alk'awarin fad'a maka wani abu idan har na samu nasara akan wannan shari'a, dan ka taimakeni sosai." "Da gaske?" Ya fad'a yana mai kafeta da kallo, d'aga masa kai tayi alamar eh, murmushi yayi yace "Insha Allah zakiyi nasara ma, ai naga kamar a jininki take tunda baki tab'a fad'uwa ba." Jinjina kai tayi tace "Sanin daka min kenan kafin mu had'u, ci gabana da nasarata kawai ka gani kuma ka sani, amma akwai tarin k'alubale da matsaloli dana fuskanta kafin nayi nasarar haye tsanin." Jinjina kai yayi yace "Hakane, Allah yana tare dake a kullum." Kallonshi tayi ta d'an murmusa tace "Ni zan koma ciki, sai munyi waya." Da kai ya mata alama shima har ta shige ciki yana kallonta, ko da ta shigo ta zauna Dada ta kalleta tace "Faduma anya kuwa Aminu ba sonki yake ba?" Cike da rashin jin dad'i tace "Daadaaa, Aminu ne fa, kinsan shi kinsan yanda muke da shi, abokin aikina ne kawai." Murmushi tayi tace "Duk da haka, amma na fahimci haka ni." Tab'e baki tayi tace "Ai kuwa ya d'ebo ruwan dafa kanshi, dan zai mutu babu aure." Dariya Dada tayi tace "Ke ma kinsan fad'a kike." Kallonta tayi tace "Allah kuwa Dada." Tsawa ta mata tace "Dallah can daina wannan bak'in bakin malama, haka kawai da k'uruciyarki kina neman kashe kanki, aure bashi ne darajar 'ya mace ba, duk da kina ganin baki da matsalar ci da sha ai ko ba komai kina buk'atar garkuwa." Shiru tayi ta ci gaba da abinda take bata tanka mata ba, cikin fad'a ta ci gaba da cewa "Baki ga yanzu duk idon dangi ya dawo kaina ba, tunda mijina ya rasu na gama takaba aka ce na koma gida na k'i, ni nayi hakane saboda anan nake samun abinda zan rufawa kaina asiri, nan nake da mutanen arzik'in da muka saba kusuwanci dasu, a gidan kuma banda tsirfa da tsegumi na kishiyar uwa da 'ya'yanta me zaka tarar, amma duk kallon mai zaman kanta yanzu suke min har suna ganin ni ke koya miki ma." Kallonta tayi tace "Dada karki damu da abinda ake fad'a akan mu, karki manta sanda yan uwan mijinki suka so rabaki da gidan da mijinki ya mallaka miki tun yana raye, dana tsaya miki a kotu cewa ake ai dan muji dad'in karuwanci ne, amma ni ban damu ba tunda ba abinda mukeyi kenan ba." Ajiyar zuciya ta sauke tace "Hakane, amma duk da haka Faduma ki samu wani mutum mai hankali a cikin manemanki mana ki fitar, hakan zaisa ki koma wajen iyayenki kuma su daina fushi dake." Ciki rashin bawa zancen mahimmanci tace "Dada bana da kowa." Girgiza kai tayi tace "K'arya kike Faduma, dattawan arzik'i nawa ne suke zuwa nemanki, amma abun haushi ko fita ba kya yi bare ki basu dama." Cikin gajiya da zencen tace "Dada to taya zan tsaya b'atawa kaina lokaci, kina ganin duk wanda na nuna ma Amjad nace d'ana ne zasu k'ara kulani ne? Ko kuma kina ganin ko da mutum ya yarda zai yarda idan munyi aure na tafi da yarona ne? Ba zasu yarda ba Dada idan ma dan su sameni sun amince anayin aure za'a samu matsala, shiyasa bana son maganar auren nan Dada, dan Allah ki daina min idan kuma Allah yasa zanyi to Allah ya kawo lokacin da alkairi tare da wanda ya dace." Cike da gamsuwa tace "To yanzu naji batu, ni da haka kike fad'a ma tun farko ai da nafi fahimtarki." _________________ Cike dgajuya da maganar da ta k'i ci ta k'i cinyewa ya sunkuyar da kanshi k'asa, babban limamin da suka saka a maganar ne ya sake kallon wani matashin da ba zai gagara shekara *talatin* a duniya ba, cikin jin hushin taurin kai irin na *Mujaheed* ya nuna shi da yatsa yace "To bari kaji Mujaheed, maganar nan na yanketa kuma ta yanku, wannan gidan ya zama mallakinsu *Salima* da *Halima*, tunda sun maka kara cewa zaka iya zama a ciki har sanda ka so to, in kuma kaga ba zaka iya ba ka tattara kayanka ka fice, amma bana son sake jin wata magana kuma a kan gidan nan, ka jini ko?" Cike da iskanci ya wani jijjiga kai yana hararen duk wanda ke d'akin yana fad'in "Ka fad'i haka mana tunda ai na samu labari kai d'in tsohon saurayinta ne, to kar kuga ni kad'ai uwata ta haifa wallahi ban yarda da rabon gadon nan ba, haka kawai sai a tattare duk wani abu mai daraja a bawa yan d'akin *matar so*, ni kuma da aka d'auka shege bare sai a bani wani banzan gida da yan kud'ad'e, tab' lallai ma." Kowa kallonshi yake da mamakin rashin kunyarshi, *Mukhtar* dake ta cika yana batsewa ne a hassale yace "Kai Mujaheed, liman d'in kake fad'awa haka? Wacece yake tsohon saurayinta? In ce dai ba uwata kake nufi ba?" Kallonshi yayi yana tab'e baki yace "Tunda ka sani me ye na saika tambaye ni to? Ita nake nufi mana, ko baka san labarin ba kai?" A sukwane ya mik'e zaiyi kanshi matar mai matuk'ar dattako da rashin son hayaniya ta d'aga mishi hannu cikin sanyin murya tace "Ya isa haka Mukhtar, bana so, karna sake jin maganarka." Komawa yayi ya zauna yana hararenshi tare da yin k'wafa mai k'arfi, liman d'in ne yaja numfashi ya sake kallonshi yace "Ina da iko da zanyi maganin rashin kunyarka, amma ni babba ne kuma mai hankali, k'aramin tsagera irinka bai kai na b'ata lokaci na kanshi ba, amma kamar yanda na fad'a maka zan sake maimaita maka, wannan gida gadon Salima da Halima ne, idan kuma akwai wanda ka isa ka turo ya k'watar maka to ina jira, takardun na hannuna ka aiko shi na gani." Mik'ewa tayi tsaye yana gyara babbar rigarsshi irin ta malamai mai bud'add'en gaba babu wuya sai hannaye kawai bak'a, kallon *Maryama* yayi yace "Mari ni zan tafi, ku ci gaba da hak'uri kamar yanda kika saba, sai anjima." A hankali ta amsa mishi da "Sai anjima liman, mun gode sosai." Kallon wannan matashin yayi wanda har yanzu kanshi ke sunkuye yana ta juya zoben hannunshi, saida ya tsaya gabanshi ya dafa kanshi yace "Ni zan tafi *Hasheer*, kuyi hak'uri kaji? Allah ya muku albarka." A hankali ya d'ago kanshi ya zuba cikin na liman, d'auke hannunshi yayi daga kanshi yana sake kallon idonshi da sukayi matsanancin ja sosai, inda ya kama leb'enshi na k'asa ya cije gam har rawa rawa yake, bai ce komai ba ya sake sunkuyar da kanshi yana d'an jinjina kai alamar to, saida liman ya sauke ajiyar zuciya dan b'acin rai tsagwaronshi ne ya hango a cikin idon Hasheer d'in wanda ke nuni da komai zai iya faruwa ya bar gidan nan a haka. Cikin dubara ya sunkuya ya kamo hannunshi yana fad'in "Muje ina son magana da kai." Saida ya had'e wasu yawu masu nauyi da suka tokare mishi mak'oshi sannan, cikin sanyin jiki ya mik'e ba tare daya had'a ido da kowa ba ya shige gaba ya fita a falon, da tsaki Mujaheed ya bi shi yana fad'in "Aikin banza, banda jan idon me ka iya? Sakarai lusari." Suna fita Maryama ta mik'e tsaye ta kalli Salima da Halima dake zaune da hijabansu tace "Ku tashi ku wuce d'akinku." Da sauri duk suka mik'e suka nufi d'akin nasu, wata uwar harara Mukhtar ya sake watsa mishi yana fad'in "Wallahi ka kiyayi ranar da zamu had'u da kai, saika manta da cewa k'asa nake da kai idan na maka jina-jina." Mik'ewa yayi ya nufo kanshi yana fad'in "Kai ni kake wa rashin kunya? Ko waccen yayan naka me kaga yayi dani? To zanyi maganin rashin kunyarka wallahi." Tsaki yayi yace "Dallah can malam, ai saboda shi baida lokacin ka ne, idan yace zaiyi da kai a k'ank'anin lokaci tarihinka zai k'are." Da sauri ya k'araso yana fad'in "Kai ni zaka fad'a ma haka? Zanyi maganinka yanzu kuwa." A hassale Mujaheed ya shak'i wuyan rigarshi, shima baiyi k'asa a gwiwa ba ya ci tashi kwalar rigar dan duka bai wuce watanni ne Mujaheed ya bawa Mukhtar d'in, jin dukansu sun kawo k'arfi sun kuma matse junansu sosai har idonsu sun fara raina fata musamman ma Mujaheed, dan Mukhtar ya fishi zubin k'arfi hakan yasa yafi jigata, ganin dai shi zai mutu a banza yasa shi cewa "Sake ni to." Wani kallon raini ya mishi yace "Ni ma sake ni." Sakeshin kam yayi yana fizge rigarshi shima yana fad'in "Sake ni to." Sakinshi yayi shima yana murmushi yace "Na fad'a maka ai ka kiyaye, wallahi ranar daka bari na rik'e mak'ogwaronka saina raba wuyanka dashi." Gyara rigarshi yayi ya nufi k'ofar fita yana fad'in "Marar kunyar banza." Cike da borin kunya yace "Kai ni kake fad'awa haka? Zaka gane kurenka yaro." Bin bayanshi yayi shima ya fita yana ci gaba da bubbutai. Tunda suka fita da liman ba komai ya fad'a masa ba sai sake jadadda masa hak'uri da kuma falalar yin shi da ribar da yake janyowa, saida yaga yana sauke ajiyar zuciya kawai idonshi sun fara washewa sannan ya mishi sallama, dawowa yayi cikin gidan ya nufi nashi b'angaren yana jin zuciyarshi na mishi sanyi na kalaman liman. Yana yaye labulen da sallama murya k'asan mak'oshi ya shiga, bai kula da yanda falon yake ba dan tun shigowar farko haka ya same shi, kai tsaye d'akinshi ya nufa da niyyar shan maganin ciwon kai ya kwanta, yana tsaka da neman maganin yaji an shigo d'akin, bai juya ba dan tunda bai ji sallama ba yasan wacece, a hankali bai ankara ba yaji an kwanta a bayanshi ana rumgumeshi ta baya ana fad'in "Abban *Sharfudeen* shine ka shigo baka nemeni ba ko?" Wani murmushin da baisan lokacin da ya zo mishi bane ya kubce mishi, rainin hankalin mutane dayawa yake, abinda ya ayyana a ranshi kenan, shi dai yasan haka kawai *Saudat* ba zata zo inda yake har da wannan salon a banza ba, dan haka ya warware hannayenta data mishi sakata dasu ta baya ya juyo ya fuskanceta, kallon fuskarta yayi sosai tasha kwalliya kam tayi tsaf, shigowar d'azu da rigar bacci tun ta kwanan jiya ya sameta, amma yanzu harta shirya da wani abu kenan, ganin yanda ya tsareta da ido sai kawai gabanta ya fad'i ta sunkuyar da kai, bai daina kallonta ba har saida ta gaji ta sake d'agowa, shagwab'e fuska tayi sosai kalar d'aukar hankali ta marairaice ta kama mab'allin rigarshi tana gyara mishi tana fad'in "Abban Sharfudeen, wallahi na manta ban fad'a maka ba tun jiya wata k'awata ta haihu har yau ake suna, shine yanzu *Murja* ta kirani take tambayata har na tafi? Shine nace mata ni na manta ma amma yanzu zan taho." Gani kawai tayi ya d'anyi wani murmushi mai ban mamaki da saka mutum tunanin murmushi, amma da yake ba hankali ne da ita ba sai kawai ta turo baki gaba tace "In je?" Jinjina mata kai yayi alamar eh, murmushi ta saki ta dafe fuskarshi da hannayenta ta sumbaci kumcinshi, juyawa tayi ta fita da sauri tana fad'in "Saina dawo." Wata ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi tare da dafe k'irjinshi da yaji ya mishi nauyi yanzun, da yasan abinda zai tarar kenan da bai shigo gidan ba ma, zaune yayi bakin gadon ya dafe kanshi da hannu biyu ya ma manta da neman maganin da yake, tunani ya shiga yi na irin yanda Saudat ta mayar dashi a gidan nan, ya rasa me take nema a duniyar nan? Me ta d'auki zaman aure? Ya take girmama al'amarin k'awayenta da fita? Wace irin uwa ce ita? Murza fuskarshi yayi sosai yana jan wani tsaki, fad'awa yayi kan gadon yana kallon sama amma idonshi rufe yana jin yanda kanshi ke sarawa. __________________ Da yamma ta samu ta shirya taje gidan matar nan ta nuna ita abokiyar aikin Aminu ce, ta samu had'in kanta sosai sai dai matar akwai sakin baki, hakan kuma ya samo asali ne saboda son da take dole mijinta ya saketa, daga yanayinta da d'abi'unta zaka san akwai dalili mai k'arfi da take son su rabu da gaggawa, amma tsaf ta gama karantarta har ta mata sallama ta tafi. daga nan asibitin tantali ta tsaya dan sanin wani abu a game da matar nan, ta kuma yi sa'ar samun k'awarta a bakin aikinta, cikin farin ciki suka gaisa inda k'awarta take fad'in "Faduma ana ganinki? Gaskiya matar nan kirkinki yayi yawa." Dariya tayi tace "A gafarce ni k'awata dan Allah, ke fa kinsan komai aiki shine matsalar, ke ma yanzu ba gashi akan aikin na same ki ba, nima yanzu haka wani aikin ne ya kawo ni wajenki." Cikin hararar wasa tace "Oho! Kenan da ban ganki ba idan ba aikin ya biyo ta kaina ba." Cikin murmushi tace "A'a ba haka nake nufi ba, amma na miki alk'awari insha Allahu zanje gidanki, yanzu fad'a min yaushe zan same ki gida." Hararanta ta sake yi tana gyara zamanta kan kujerarta ta nuna mata kujerar da suke fuskantar juna tace "Hum! Ni dai zauna kinji, yau na sanki ne Faduma?" Cikin dariya k'asa k'asa taja kujerar ta zauna tana d'ora jakarta akan teburin tace "Allah da gaske nake k'awata..." Da sauri ta dakata daga maganarta tana juyawa d'akin da taji ana ihu, kallon k'awarta tayi tace "Kuwar me nake ji?" Cikin jimami tace "Wallahi mai nak'uda a ciki, tun jiya muke ta fama har yanzu." Cikin tausayawa tace "Ayya baiwar Allah, Allah ya sauketa lafiya." Sake juyawa tayi inda taga mutane cirko cirko da gani kasan danginta ne, namijin ta kalla wanda taga damuwa sosai shinfid'e akan fuskarshi duk yayi wani iri. Lumshe ido kawai tayi saboda tausayin kanta da taji, lallai rayuwa wasu na samun gatan da sanda zasu haihu uwa da uba da miji da kuma dangi sukan kasancewa tare da kai, wasu kuma basa samun wanan damar. K'awarta ce tayi saurin cewa "Ina jinki Faduma zan tashi ne ga mai cikin nan." D'an zabura tayi ta dawo kanta tana fad'in "Ah yi hak'uri." Cikin nutsuwa ta mata bayanin yanayin data gani da kuma abinda ya d'aure mata kai duk ta tambayeta abinda take son sani, cikin k'warewa da sauri ta mata dalla dalla, kama daga abinda ke iya kawo hakan har yanda ake ganewa da sauransu, cikin jin dad'i ta d'auka a takarda ta saka a jakarta tana fad'in "Nagode k'awata, kije ga aikinki insha Allahu zan zo gidanki." Saida ta mik'e tace "Da gaske zaki zo?" Cike da tabbaci tace "Wallahi zan zo, ni na fad'a miki." D'aga mata hannu tayi ta nufi d'akin tana fad'in "Sai anjima to, ina jiranki." Ita ma tana had'a kayan ta fita, tunda ta fito kanta k'asa yake saboda maza ne a face asibitin dake zama anan, tana shiga motar ta tayar ta bar wurin cikin sauri, tana isa islamiyyar yayi daidai da fitowarsu, bud'awa yayi ya shiga yana fad'in "Ayya." Cikin kafeshi da ido tace "Na'am, ya kake? An gaji ko?" Saida ya mik'a mata takardar hannunshi ta karb'a yace "Na gaji Ayya." Ko da ta duba taga ta biyan kud'in wata ce, kashe motar tayi ta bud'a zata fita tana fad'in "Ina zuwa bari na biya na dawo." Cikin shagwab'a yace "Ayya ki bari har gobe mana, antashi fa yanzu." Saida ta rufo k'ofar tace "Amma ai malaman suna nan." Da kallo ya bita harta shiga cikin nutsuwa, ajiyar zuciya ya sauke, yanzu ne ya shiga shekararsa ta *takwas*, amma tunda ya bud'a ido ita yake gani tare dashi kullum, ita ce kullum ke d'awainiya dashi take hidima dashi, bai tab'a ganin mahaifinshi ba ko jin labarinshi daga bakin wani, bai san ya kammaninshi suke ba dan ko a hoto babu wanda ya nuna mishi, abunda ya sani kawai a game da mahaifinshi shine sunan *Tagur Sugui* sannan ya rasu tun kafin a haife shi. Cikin girmama juna ya mata izinin zama ta zauna suna sake gaisawa, hannu tasa jakarta ta fito da kud'i ta abe mishi gabanshi tana fad'in "Ga kud'in watan Amjad, ya bani takardar yanzu nace bari na biya tun yanzu kafin na manta kuma." Cikin jinjina al'amarin matar nan yana fad'in "Alhamdulillah, Allah ya saka da alkairi, Allah ya biyaki da aljanna." Wani babban littafi ya d'auka ya shiga dubawa a tsanake ya ga sunan Amjad d'in ya kuma mishi alama da an biya, rufewa yayi ya kalleta yace "Madame Amjad yaro ne mai hazak'a da k'ok'ari, ko da baki zo yanzu dama zamu nemeki a lambar wayarki, saboda munga shiru baki zo kan maganar ba kuma baki ce komai ba, sannan gashi lokaci ya matso sosai." Cikin fad'uwar gaba tace "Malam lafiya, me ya faru haka? Wani abu Amjad yayi?" Da mamaki yace "Kar dai kice bai fad'a miki sak'on dana bashi ba?" Da mamaki ita ma tace "A'a, wane sak'o?" Girgiza kai yayi yace "Subhanallahi, har takarda na bawa Amjad ya baki, kuma na fad'a masa baki da baki." Gaba d'aya ta bayar da hankalinta kanshi tace "Malam lafiya? Wani abu ne ya faru?" Girgiza mata kai yayi yace "Ba komai madame, akan gasar musabak'a ne da za'a gabatar dama, hazak'arshi da k'ok'arinshi ya cancanci ya wakilci yan ajinshi, ina tabbatar miki daga shekara bakwai zuwa goma zai iya zama zakara a ciki." Wani farin ciki ne ya bayyana a fuskarta tace "Masha Allah, naji dad'i sosai malam, Allah ya saka da alkairi, yanzu miye abunyi?" Girgiza kai yayi alamar ba komai tare da fad'in "Ba komai madame, kawai dai za'a ci gaba da k'arfafa masa gwiwa ne, sannan ya dinga samu isashen lokacin bita da kuma nutsuwa." Da sauri tace "Naji kace lokacin ya kusa? Yaushe ne? Ni bansan ya akayi bai fad'a min ba." Cikin kallon fuskarta yace "Rana irin ta yau ne fa." Cikin damuwa tace "Lokaci ya matso malam, kana ganin zai iya kuwa?" Murmushi yayi yace "Ni ma na yarda da Amjad bare ke mahaifiyarshi, kin fini saninshi ai, kuma tun sati biyu daya wuce a islamiyyar nan abinda muke ta karantar da masu gasar kenan, dan haka kar kiji komai madame, insha Allahu ba zai bamu kunya ba." Cike da gamsuwa tace "Mun gode sosai malam, Allah ya saka da alkairi." Jinjina kai yayi yace "Ba komai nagode nima." Mik'ewa tayi ta fita ya bi bayanta da kallo, yana jinjina ma k'ok'arinta sosai akan yaronta, shekara hud'u kenan daya santa kullum ita ke zaryar zuwa kawoshi da d'aukarshi, babban abun birgewa a game da ita shine yaronta bai tab'a jiranta na minti d'aya ba, duk da tana aiki sannan akwai yanayi na yau da kullum, amma kullum tana zuwa kan lokacinta, baka tab'a ganinshi yana jiranta ba. Sai dai abinda ya lura a game da ita babu maganar aure a gabanta, tunanin yanda zata kyautata rayuwar d'anta kawai take yi, hakan kuma baya masa dad'i shi kam duba da yanda Allah yayi ta babu tayawa, kyakyawa sosai ga tsarin hallita da zai birge kowane namiji mai ido, ga kuma tsafta da kama jiki, uwa uba kuma har yanzu yarinya ce tunda gaba d'aya shekarunta basu haura *ashirin da uku zuwa da hud'u* ba. Data same shi a mota ta kalleshi tace "Amjad me yasa baka fad'a min maganar musabak'arku ba?" Saida yayi k'asa da kanshi cikin ladabi yace "Kiyi hak'uri Ayya, sanda aka bani takardar ance kowa ya kira mahaifinsa ne, ni kuma sai aka ce na kira Ayyata." Lumshe ido tayi cikin k'unar zuciya kafin ta bud'e ta kalleshi, a hankali cikin taushin murya tace "Amjad kana jin kunyar nuna ni ne a matsayin uwarka? Ko kuma kana kallona ne a tauye shiyasa baka d'aukeni uwa da uba ba?" Girgiza kai yayi yace "Kiyi hak'uri Ayya, naga kowa cewa ake ya turo Abbansa." Cikin sakar masa ido tace "Shiyasa kake jin kunyar turo ni?" A hankali ya sake cewa "Kiyi hak'uri." Tayar da motar kawai tayi suka d'auki hanya bata sake ce mishi komai ba har suka isa gida ana ta sallah magriba. *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 17:07 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _4_ Bacci ya samu daga kwanciyar nan da yayi sai kiran sallah la'asar ne ya tashe shi, saida yayi wanka a gaggauce dan ya samu k'warin jiki kafin ya fita masallaci, yana idar da sallah kuma ya juyo ya dawo dan yunwa yake ji, bai ma fara tunkaren b'angarenshi ba dan yasan babu abinda zai samu na ci daya wuce bredi da sauran kayan da basa iya rik'e mutum na tsawon lokaci. Da sallama ya shiga falon da suka bari d'azu wajen tattaunawa, duk da kan kujera take amma da carbi a hannunta tana ja, k'arasawa yayi ya zauna nesa da ita yana fad'in "Barka da yamma Umma." Saida ta kai k'arshen istigfarin da take sannan ta kalleshi fuskarta d'auke da murmushi tace "Barka Hasheer, ka tashi kenan?" Saida ya d'an murza ido yace "Um Umma, bacci ne ya d'auke ni." Murmushi ta sake sakar masa tace "Ai tunda yan rigimar nan suka shiga suka ce bacci kake." Waigawa yayi ta d'akin Umma yana fad'in "Suna ina ne Umma? Sun dawo kenan?" Jinjina masa kai tayi tace "Ai yanzu suka tafi islamiyya tare da Salima, *Izzadeen* ne ma ya so yaje ya tasheka Salima tace ba zata jirasu ba." Jinjina kai kawai yayi yana shafa cikinshi, shiru ne ya biyo bayan zantawar, kamar babu wanda zai sake cewa komai sai kuma ta kalleshi a tsanake tace "Na zubo maka abinci ne?" Kallonta yayi cike da kunya da kuma rashin jin dad'i ya d'aga mata kai alamar eh, murmusawa tayi tare da girgiza kai ta mik'e tana fad'in "Allah kyauta." Madafa ta nufa tana cike da tausayin babban d'an nata, shekara da shekaru da aure amma har yanzu babu kwanciyar hankali, ba wai kwanciyar hankali na fad'a ba, A'a! Rashin samun kulawar mata, ita kullum a biki take da kuma waya da kallo, in anyi sa'a tana gidan bata fita ba to hankalinta na kan wayarta ko kuma tv tana kallon abinda take so, shiyasa har yanzu ya gagara yin gaba sai baya da yake yi. Abinci ta zubo masa ya zauna k'asa yasa hannu ya ci sosai ya k'oshi, hamdala yayi tare da godiya ga Umma kafin ya mik'e ya fita, saida ya kalli b'angaren nasu da tunanin ko ta dawo yanzu duba da tun lokacin data fita, amma yana yanda ya barshi sai kawai ya fice shima. _______________ Ta idar da sallah magriba tana zaune kan salayar wayarta tayi k'ara, zura hannu tayi ta d'auka tana duba mai kira, da sauri ta mik'e tsaye tana k'ok'arin cire hijabinta jikinta har rawa yake dan ta d'auki kiran, kiran mahaifiyarta ne da a shekara d'aya da k'yar take yin sa'ar samun ta kirata sau biyu ko sau uku, ita ta hanata ta kirata sai indai ita ce ta kirata, dan haka kullum cikin tsumayin ganin kiranta take. Tana d'auka tare da rangad'a sallama aka amsa mata a dak'ile, cikin bege da k'auna tace "Ayya ina wuni, kina lafiya? Ayya nayi ta jiran kiranki sai yanzu kawai kika kirani." Ba yabo ba fallasa daga b'angaren aka amsa mata da "Lafiya lau, yanzu ma na kiraki ne naji yaushe zaki zo bikin d'an uwan naki? Ko kin manta da bikin ne?" Da sauri ta dafe goshi dan har ga Allah yanayin aikinta yasa ta manta ma, a hankali cikin fargaba tace "Ayya bikin har ya kusa ne?" Da mamaki aka amsa mata da "Ban gane ba *Fati*, kina nufin har kin manta lokacin ne? Saboda baki damu da ja min magana ba ko." Da sauri tace "Yi hak'uri Ayya, wallahi n..." Shiru tayi sai kuma tace "Ayya dan Allah fad'a min yaushe ne saina taho?" Ajiyar zuciya taji ta sauke har taji sautin a kunnenta kafin tace "Alhamis ne insha Allah." Ita ma ajiyar zuciyar ta sauke tace "Shikenan Ayya zan zo insha Allahu, ina so na ganki da Abbah ma da sauran yan uwa." Ba wani karsashi a tare da ita tace "Ki zo, amma kar ku zo tare dashi." Tana fad'an haka tayi k'it ta kashe wayar, sororo tayi da wayar a hannu tana kallo, duk jikinta ne yayi sanyi ta zauna bakin gadonta, idonta taji sunyi taf da k'walla amma saita kawar dasu ta saki murmushi kawai ta mik'e ta fito falo. Har suka kwanta bacci ba ko Dada bata wa maganar ba bare Amjad, sai mai aikinta data shiga yi dan yanzu shine mai mahimmanci gerata da bata wasa dashi. ________________ Ana magriba ta shigo gidan a gajiye sosai, mayafin data cire da jakarta duk a saman kujerar data zauna ta diresu, d'an kwalinta ma haka ta aje shi tare da buda datar wayarta, hotunan bikin da suka d'auka ta shiga d'orawa a saman statu, sam tartsatsin girman kalmar Allahu Akbar da ake fad'a a masallacin dake jone a gidan bai fargar da ita ko ya shiga kunnuwanta ya buga a k'asa ba bare ta damu dashi, har akayi aka idar bata san anyi ba saida taji agogo ta alamta mata k'arfe 07:00 na yamma, da sauri ta kashe datar ta d'auki remonte ta kunna tashar da take so a daidai lokacin an fara wani s茅rie da take matuk'ar so mai sunan *Avenida brazil*, kallo ta shiga yi hankali kwance tana jin dad'in kallon sosai. Da gudu yaran suka shigo saboda ganin d'akin bud'e ya tabbatar mamansu na ciki kenan, suna shiga suka tunkareta da murnarsu amma basu kai gareta ba ta daka musu tsawa tana fad'in "Dallah ku min shiru, miye haka? Kun zo kenan zaku hana ni sakewa ko? Daga shigowarku sai tashin hankali? Mtssss." Gyara zama tayi ta nuna musu kujera tace "Maza ku zauna wurin nan, kar naga uban daya tashi, in ba haka ba ranku zai b'ace wallahi." Duk jikinsu ne yayi sanyi babu wanda yace k'ala, inda ta nuna musu Sharfudeen ya nufa zai zauna sai Izzadeen daya nufi hanyar fita, kallonshi tayi tace "Kai baka ji me nace ba kenan?" Juyowa yayi yana kumburo baki yace "Ni wajen Kaka zani." A tsawace tace "Wuce kayi ta tafiya, ai dama an gama hure muku kunne a kaina, je Allah raka taki gona." Tsaki ta kuma ja ta sake mayar da kallonta kan tv, tana cikin kallon wayarta tayi k'ara hakan yasa ta laluba ta d'auka ta d'ora a kunne ba tare data san waya kira ba, daga can b'angaren aka ce "Kin dawo ne?" Jin muryar yasa tasan waye, wani far tayi da ido tana yamutsa baki irin jin haushin nan tace "Na dawo mana, zanyi ta zama can ne?" Daga b'angarenshi yace "Me kika dafa mana?" Cikin jin haushi sosai tace "Wai kai Abban Sharfudeen baka da magana saita abinci ne? Daga kirana ba ko tambayata kina lafiya ko wani abu? Sai tambayar me na dafa kawai, to idan ban dafa ba kuma fa?" Cike da gatse yace "Saina tambayeki me zaki ci na siyo miki." Sakin fuskarta tayi daga d'aurewar data mata tana turo baki tace "Uhum! Komai ma ka siyo mana, wallahi na gaji ne ba dan haka ba dana mana girki." Rasa abin fad'a mata yasa shi kashe wayar kawai, wani haushi da takaici ne ya taso masa, kullum rok'on Allah yake ya k'ara masa hak'urin zama da ita, yana ta hak'uri ne saboda akwai zuri'a tsakaninsu, amma ita ta kasa fahimtar hakan. Shareta kawai yayi har yayi sallah isha'i a waje ya wuce majalisarsu, yana so ya koma gidan amma tunanin abinda zai tarar kawai ke hanashi, saida ya ga lokacin da yake da tabbacin yaranshi suna daf da yin bacci sannan ya d'auki hanyar komawa gidan da siyayyar daya musu. Yasan duk da taji shigowarshi tun daga bud'e gidan har fitowarshi a mota, dan gashi ma Sharfudeen ya tarbeshi da gudu tare da d'an uwan shi, tunda ta dawo har yanzu tana nan yanda take, hana rantsuwa ta shiga ban d'aki tayi fitsari ta dawo, tunda ya kai kallonshi kan teburin cin abinci ya d'auke sau d'aya baya fatan sake kallonshi, dan har yanzu kwanukan abincin safe ne a kai, kujerar kusa da ita ya zauna yana ta magana da yaran, ledar hannunshi ya mik'a musu yace "Ba wa mamanka." Karb'a yayi ya mik'a mata ta karb'a, ba tare data kalleshi ba ta mik'e ta je ta d'auko faranti ta juye, tana zuwa ta aje k'asa ta zauna tana kallon yaran tace musu "Ku zauna mu ci ba zan jira kowa ba dan yunwa nake ji." Suma yaran duk da basa jin yunwa dan sun ci abinci wajen Kakarsu, zaunawa sukayi suka saka hannu tare, saida ya gama mata kallon tsaf sannan ya saka hannu yana fad'in "Sannu." A take ta d'aga ido ta kalleshi tace "Uhum! Sannu." Bud'a ciki tayi sosai ta ci ta k'oshi yana kallonta yana ayyana albarkacin yaranshi ta ci, ba dan haka ba da bai siyo ba saidai ta kwana da yunwa, suna idawa ta d'auke faranti ta fitar waje, wanda ya zuba k'asa bata damu data share shi ba ko tattare wurin da kyau ta d'auki jakarta da mayafi ta nufi d'aki tana fad'in "Sharfudeen kuje d'akinku ku kwanta dare yayi." Da kallo duk suka bita har ta shige ciki, kallonsu yayi a tsanake cikin sanyin murya yace "Kunyi karatu ne?" D'aga kai sukayi sai Sharfudeen daya k'ara da cewa "Munyi tare da aunty Salima." Jinjina kai yayi ya mik'e ya nufi d'akinsu dasu, suna shiga yace "Kuje kuyi fitsari to." Ban d'aki suka shiga da d'aya d'aya suka fito ya canza musu kaya, saida ya musu addu'a sannan ya kwantar dasu ya rufe d'akin ya barsu. D'akinshi ya shiga ya cire kaya ya shiga wanka, ya jima yana tsaftace kanshi kafin ya fito ya shafa mai ya saka doguwar riga ya fesa turare ya tsefe sumar kanshi da ba wani yawa ne da ita ba ya fito ya nufi d'akinta, tunda ya sani ita dai ba zata zo ba, dama daka ganta d'akinshi musamman da dare to kud'i ko sutura ko fita take so. Yana shiga d'akin ya sameta zaune jingine a jikin gadon da waya a hannu da kayan bacci har ta kwanta, sai dai alamu sun nuna ba tayi wanka ba saboda kwalliyar fuskarta har yanzu na nan, cire doguwar rigar yayi ya aje ya kashe wuta, siririn tsaki tayi na jin haushi dan ita ma tunda ta ganshi d'akin tasan me zai faru, aje wayar tayi ta juya baya ta gyara kwanciyarta, tana gungunin "Yanzu yasha min kai, shi kullum baya gajiya da abu guda, haba ni na tsani jarabar nan wallahi." Karaf a cikin kunnenshi abinda ta fad'a, jim yayi kamar zai tashi daga abinda yayi niyya, sai kuma ya ga shi zai cutu dan sati uku kenan babu abinda ya shiga tsakaninsu na mu'amular aure, haka ya daure ya k'ara matsawa kusanta sosai ya kwanta bayanta, hannunshi ya d'ora kan cikin ya d'aga rigar yana shafawa yana sauke numfashi, d'an tsaki taja wanda har ya fito fili tana fad'in "Wai Abban Sharfudeen miye haka?" Saida ya taushe abinda ke taso mishi sosai yace mata "Uhum! Kamar me fa?" Cikin amon murya na rashin tausayi da ladabi tace "Bacci zanyi fa, dan Allah ka kwanta kai ma." Cikin sauke mata wani zazzafan numfashi a fuska yace "Um um! Ba zan iya ba Saudat, ina buk'atarki sosai, kinsan nayi hak'uri ko." Wani tsakin ta kuma yi cikin haushi wanda yasa shi d'aga kanshi ya kalli fuskarta duk da duhu ke akwai, cikin muryar gargad'i yace "Saudat ki daina min tsakin nan, kinsan bana so ko? Bana so ki kaini mak'ura fa, gwara ki zage ki ko ki mareni da ki zauna kina min tsakin nan." A ganinta k'ofa ce da zata sake hassala shi ya bar mata d'akin, sai kawai ta zabura ta mik'e zaune tana fad'in "To in hakane ka koma d'akinka mana ka k'yale ni, ai nima kasan bana son takura." Gyara zamanshi yayi ya zuba mata manyan idonshi masu yalwar gashi yace "Saudat bana son fad'awa halaka, bana son aikata abinda bai dace dani ba, me yasa ba kya tunanin haka?" Kawar da kai tayi irin ko a jikinta ma ba tace komai ba, kallonta ya sake yi yace "Ba zaki ji tausayi na ba kenan?" Kallonshi tayi tana turo baki tace "Kayi hak'uri na yau kawai har gobe, kaga idan ban kwanta da wuri ba ina makara wajen shirya yara." Sauka yayi daga kan gadon yana girgiza kai ya d'auki doguwar rigarshi ya rik'e a hannu ya fita daga d'akin, da harara ta bishi saida ya fita kuma sai taji har ya bata tausayi, da sauri ta lalubo wayarta da ko datar bata kashe ba ta ci gaba da duba sak'onni, tana son Hasheer sosai tana kuma kishinsa, tana jin dad'in zama dashi da kuma son ta ci gaba da zama dashi d'in, kawai dai tana kama jikinta ne saboda karta lalace ta zama baiwar miji, shiyasa ba a cikin shekarunsu *tara* da aure har yanzu take da yaya biyu, magani take sha ba k'akk'autawa shiyasa da Sharfudeen ya shekara *shida* saida Hasheer yayi da gaske kafin ta daina sha har Allah ya bata cikin Izzadeen, yanzu shima zata mishi k'ane bayan ya shekara shida ko bakwai saita tsaya, dan yara uku take da burin haifa a duniya. _______________ *Litini* Da safe ta fito cikin shirinta tsaf na shiga kotu dan gabatar da shari'arta, tayi kyau sosai cikin farar lafaya da bak'ak'en takalmi k'afa ciki masu d'an tudu, Amjad ma ya gama shirinsa tsaf suka karya kafin suka fita Owwo na binsu da addu'a, tana aje shi makaranta kamar yanda suka saba ta gargad'eshi kan maida hankali akan karatunshi da kuma fad'a, mik'a masa abincinshi tayi wanda yake tafiya dashi kafin taga shigarshi ta wuce ita ma. Aminu ne ya kiranta bayan sun gaisa yake fad'in "Nasan yanzu dai kina hanyar zuwa, dan b'ata lokaci ba d'abi'arki bace." Amsa mishi tayi da "Ina kan hanya Aminu, zamuyi waya idan na fito daga kotu, yanzu duk hankalina ya rabu saboda ina tuk'i kuma ga hada hadar jama'a saboda yau lundi (litinin) ce." Shima amsa mata yayi da "Ba komai to ina jiranki, fatan nasara." Kai tsaye ta amsa mishi da "Kai ma ina maka fatan samun nasara, sai anjima." Tana fad'a ta datse kiran, k'aramin ofishinsu ta fara wucewa ita da Aminu wanda sukayi had'in gwiwa, tana fita a mota ta d'auki ordi. d'inta da jakarta ta rataya ta nufi ciki, makulli tasa ta bud'e k'ofar kafin ta shiga ciki, ba wani walallen ofishi bane amma dai a tsaftace yake sai k'amshin turaren jikin Faduma daya zamar mata jiki har ya mannewa ofishin shima kamar yanda yake a motarta d'akinta da duk wani abu da tayi anfani dashi. Rataya jakar hannunta tayi akan wani d'an k'arfe tare da cire lafayarta ita ma ta ratayata akai, hakan ya bayyanar da rigarta iya gwiwa mai tsaga biyu da wandonta da kuma d'an kwalin dake d'aure a kanta sosai, wani coffre ta jawo dake gaban table d'in ta d'auki rigarta ta lauyoyi bak'a da hularta, warwareta tayi daga ninken sai k'amshin turare take kamar na wuta ta saka, cire kallabin tayi ta d'ora hular ta tsaya akan daidai k'ullin gashinta da tayi, duk tsawonshi haka ta laulayeshi ta had'eshi da ribom d'inta, tana kallon madubi ita kanta saida tayi murmushi dan tasan kayan na mata kyau ba kad'an ba. Jawo kujerar tayi tasa wani hanck. ta goge sannan ta zauna, bud'a ordi. d'in tayi tare da d'aukar wasu takardu ta shiga dubawa a tsanake tana tattara komai tana kuma nazartar wasu abubuwa, inda tana yi tana kallon agogon dake saman k'ofar shigowa dan kar lokaci ya wuce mata bata ankara ba. Tana haka har k'arfe 09:30 tayi, had'a kayan tayi duka wasu tasa a jaka wasu kuma a sa a jakar ordi. d'in sannan ta rik'e a hannu ta fito, saida ta kulle sannan ta nufi mota, saida ta juya ta kalli gungun wasu maza da suke gaishe ta ita ma ta gaishesu cikin girmamawa sannan ta shige ta bar wurin. ________________ Duk yanda ya so yayi banza da lamarinta abun ya gagareshi, da k'yar ya samu ya kai daren nan har ya wayi gari yau safiya, tsabar ciwon cikin daya kwana dashi ko sallah asuba bai samu yayi ba, yanzu ma jin kamar zai mutu tsabar wahala ne yasa shi tasowa yana layi da duk'u duk'u ya kawo kanshi d'akinta, baccinta take ta shara babu alamar tayi sallah, bai jira komai ba wajen haye gadon yaja zanin rufar ya shiga ciki, kamar a mafarki taji an birkita ta tare da janye rigarta sama aka bud'e k'afafunta. Duk yanda ta so janye kanta daga gareshi kasawa tayi, kokawa ta dinga yi dan ta k'waci kanta, ba yanda ta iya dole ta zuba mishi ido tana kallo har ya gama abinda yake ya mik'e, bala'i da masifa ta sha shi a safiyar tana ta fad'a wai ya zai mata fyade? Hak'urin ne ba zai iya ba na yau da tace? Hakan yasa ko yara bata shirya suka tafi makaranta ba sai shi ya shiryasu har mai d'aukarsu ya zo, sanda ya rakasu suka fita zai shiga d'akinshi tayi k'wafa tana fad'in "Kawai ku maza kun d'auki mata anfaninmu kenan a gurinku, kenan ba zaka iya zaman aure dani ba idan baka kusanta ta? Hmmm!" Juyowa yayi ya tako ya zo har gabanta ya tsaya, kallon idonta yayi yace "Saudat, ina kiyaye miki gayyato b'acin rai na, ki kiyaye gayyata ta raina ya b'ace a kan ki, ke baki san zafin zuciyata bane sai sanyinta, baki san hushi na ba sai hak'uri na, kar zaman aurena dake ya zama silar da zaki raina ni, wallahi ranki zai mugun b'ace a kan haka." Jinjina kai yayi shima ya shige d'akinshi, shiryawa yayi ya fito cikin farar shadda, duk da a falon ya ganta amma haka ya aje mata kud'i akan cantre teble d'in dake wurin ya fice. *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 17:07 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _5_ Cikin hukuncin Allah kam ta samu nasara a kan shari'ar, ta bayyanar da hujojjin da dole aka d'aure mijin daya kashe matarshi saboda tayi fada da budurwarshi, duk da ba yayi ne da niyyar kisa ba amma dai ganganci ne yayi k'arara. Da farin ciki suka fito a kotun dangin margayiyar da wasu daga cikin mutanen garin suna ta tayata murna da jinjina k'ok'arinta, musamman yanda ta fad'i hatta da salon kwanciyar mamaciyar a sanda ya tureta ta fad'i, shi mijin yayi k'aryar ita ta fad'i da kanta, amma sai Faduma ta nuna wa kotu da ita ta fad'i da kanta zai zama tsakaninta da k'ofa akwai tazarar zira'i d'aya da da 3cm, amma dayake tureta ne akayi da k'arfi shiyasa har ta kai 4cm, hakan ya birge gar alk'alin kanshi ya kuma jinjina mata. Tana daf da zuwa ta shiga motarta taji muryar mace a bayanta tace "Ina tayaki murna, amma kiyi hankali ki kuma yi taka tsantsan." Juyowa tayi ta kalleta, dakatawa tayi da bud'e motar ta kalleta da kyau, ba yarinya bace kamarta dan zata iya kaiwa shekara talatin da d'oriya, cikin halin ko in kula tace "Nagode, sai dai kuma ban sanki ba." Matsowa matar tayi tana murmushi tace "Ina fa zaki sanni tunda kullum illa kike min, Faduma wai me na tare miki ne a duniyar nan." Wani wurga ido tayi tana murmushin rainin hankali tace "Na miki wani abu ne?" Jinjina kai tayi tace "Sosai ma, kin min abubuwa da dama, kuma ki sani daf nake da kasa hak'uri wallahi, dan banga dalilin da zaki dinga shigowa rayuwata ba haka kawai." D'aga maya hannu tayi ta dakatar da ita da fad'in "Dallah dakata malama, wacece ke? Me nayi miki kuma?" Rumgume hannaye tayi tana mata wani shu'umin kallo tace "Zaki sani nan gaba, kawai dama dan na fad'a miki ki kula ne." Juyawa tayi zata bar wurin sai kuma ta tsaya tace "Uhum yawwa, karki manta da sunana daga yau, *Zaleeha*." Wani murmushi Faduma tayi ta gyara tsayuwarta ta nuna ta da makullin mota tace "Kinsan da maganar nan zata iya d'aureki? Kuma kinsan da zan iya gabatar da maganar nan taki gaban kotu a matsayin hujja? Ke ma ki kula da kanki." Mirmushin ta kuma saki tace "Karki damu dani, ai kin gama ruguza min komai ta yanda ban damu da duk abinda zai same ni ba yanzu, ganin bayanki shine kawai burina a yanzu." Ita ma rumgume hannaye tayi tana jinjina kai da fad'in "Kafin na shiga karatun lauya saida na fara neman ilimin addini, kuma a cikin addini na akwai garkuwa da runfuna da dama da irinmu ke fakewa a ciki domin nisanta daga kaidin ire-irenku, ki sani babu abinda sharrinki zai min, dan nayi gwagwarmaya da wanda suka fiki sharri kuma sai ido suka zuba min, dan haka ina baki shawara ki shafa wa kanki lafiya da shiga sabgata, inba haka ba abun zai miki yawa, dan a k'arshe wasan za'a tashi baki ga tsuntsu kuma kin rasa tarkon, idan kuma akayi rashin sa'a kika kaini bango matuk'a, to fa shakka babu *ALLURA ZA TA TONO GALMA*." Da makullin ta sake nunata ta juya ta shiga motarta bata sake bi ta kanta ba ta wuce, saida ta ga fitarta kad'ai ta sauke ajiyar zuciya, girgiza kai tayi a fili ta furta "Wallahi Faduma ba zan k'yaleki ba, ki d'aure min uwata, sannan a dalilinki aka karb'e kasuwancinta aka mata biyan bashi, sannan kinsa an rufe wanda muke daf da shirin yin aure, kuma kike so na barki? Ai k'arya ne wallahi!" Tana gama fad'a ta wuce. Kotun da Aminu ke shari'a ta wuce inda zuwanta yayi daidai da suma suna fitowa, fitowa tayi ta jingina jikin motar tana hangenshi yana nufota baki bud'e, yana zuwa duk suka saki murmushi da sauri yace "Kin cinye ko?" Murmushi tayi sosai ta d'aga masa kai alamar eh, cike da jin dad'i da karsashi yace "Dan haka sai ki fad'a min abinda kikayi alk'awari." Girgiza kai tayi tana murmushi mai birgewa tace "A'a fa ba haka mukayi ba, kai zaka fara fad'a min." Shima girgiza kai yayi yace "A'a ban yarda ba, kawai ke ki fara fad'a." Hararan wasa ta wurga mishi tace "To! To shikenan zan fad'a yanzu." Saida ta kalleshi sosai ta shanye murmushin fuskarta sannan tace "Nagode Aminu, nagode da duk taimakon da kake min, Allah ya biyaka." A take shima duk wannan karsashin da farin cikin suka b'ace, a sanyaye yace "Wai dama abinda zaki fad'a kenan?" D'aga mishi kai tayi alamar eh sannan tace "Sai kuma..." Da sauri yana sake matsawa kusanta yace "Uhum ina ji? Fad'i mana." Ajiyar zuciya ta sauke tana hangen k'ofar shigowa tace "Jiya munyi waya da Ayya, nan da kwana biyu bikin yaya *Barka*, dole zan tafi jibi insha Allah." Ajiyar zuciya ya sake saukewa yaja baya yana dafe k'ugu yana gyara zaman ordi. d'inshi, kallonta yayi a kasalance yace "Faduma bana so ki tafi." Kallonshi tayi amma sai taji kunya saboda kallon da yake mata ta sunkuyar da kai murya k'asa k'asa tace "Kayi hak'uri mana, ai ba jimawa zanyi ba, da zaran an idar zuwa lahadi zan dawo." D'an d'aga kai yayi alamar shikenan tare da fad'in "Tare zaku tafi da Amjad?" Girgoza kai tayi ta kalleshi tace "Ayya tace naje ni kad'ai, kai dai kasan komai." Cike da tausayawa ya kalleta yace "Kiyi hak'uri Faduma, insha Allahu komai zai wuce ya zama tarihi kamar ba ayi ba." Ba tare data kalleshi ba tayi wani murmushi mai kama da kuka na son tahowa tace "Kune k'arfin gwiwata Aminu, ku kuka samar da wannan Faduman, ba dan kai da Dada ba da yanzu bansan wace irin rayuwa nake yi ba." Kallonshi tayi cikin ido tace "Ina godiya ssoai gareka Aminu, bansan da me zan iya saka maka ba? Amma ina fatan ranar da zata zo ka nemi taimako na nima, da gaggawa cikin farin ciki zanyi maka." Girgiza kai yayi yana murmushi ya kalleta yace "Muje to, ke kullum ba kya rabuwa da tuna baya." Ajiyar zuciya ta sauke tana bud'a mota tace "Rayuwa tana koya maka hankali ne idan kana tuna baya." Motarshi ya bud'a shima ya kalleta yace "Zan zo anjima na ga yarona Amjad." Da sauri ta kalleshi ido cikin ido, *yaronshi*? Bata san me yasa gabanta ya fad'i ba daya ambaci Amjad da d'anshi, bata san me yasa ya danganta kanshi da Amjad ba yau? Jikinta ne yayi sanyi saida ya k'yasta mata hannu yace "Ya dai? Ko nayi kuskure?" Da sauri ta kalleshi ta girgiza kai, murmushi ta k'ak'aro tace "Sai ka zo." Bud'a motar tayi ta shiga gabanta na ci gaba da fad'uwa, motarshi na gaba tana baya har suka fita daga wurin, makaranta ta wuce saida tayi jiran kusan minti sha biyar kafin aka sallamesu suka fito, tana hangenshi shi da wasu yara biyu har suka k'araso, gaisheta sukayi ta amsa da sakin fuska, Amjad ma gaisheta yayi da tambayarta "Ayya ya shari'a? Kinyi nasara ko?" Murmushi tayi sosai tana fad'in "Muje saina baka labarin yanda mukayi." Da sauri yace "Ayya ko zaki sauke abokina gidansu?" Kallon yaran tayi kyawawa dasu ga kuma kama ta kalleshi tace "Ba'a zuwa d'aukarsu ne?" Cikin nutsuwa ya shiga mata bayani "Suna da mai adaidaita Ayya tun suna kan hanyar tahowa adaidaitar ta samu matsala sai cikin wata adaidaita ya kawosu ta wani, kuma yanzu na so mu karb'i wayar mai gadi su kira Abbansu ko Ayyasu amma sun ce basu san lambar ba, kuma ina tsoron abarsu anan shiyasa." Wani murmushi tayi ta kalli yaran tace "Ina ne gidanku?" Sharfudeen ne yace "Zarya kusan commissariat sabuwa." Jinjina kai tayi tace "To ku shiga muje." Bud'ewa sukayi da sauri suka shiga baya Amjad kuma a gaba, suna tafe tana bashi labarin wasu daga cikin abubuwan da kanshi ke iya d'auka dangane da shari'ar nan, a hanyarsu taga mai siyar da karas ta tsaya ta siya, bawa kowa tayi ta kalli Amjad tana dariya tace "Na fiku buk'atar wannan saboda ni na fara tsufa, ido sun fara bani matsala." Girgiza kai Amjad ya shiga yi yana dariya yana fad'in "A'a A'a Ayya, ni Ayyata sabuwa ce har yanzu, babu abinda zakiyi Ayya." Dariya tayi suka ci gaba da tafiya hankali kwance har saida su Sharfu suka nuna mata k'ofar gidan, tsayawa tayi tana kallon gidan, lallai inhar kana son jin dad'in rayuwa zakayi fatan ace wannan gida mallakinka ne, babba ne wanda kalar da aka mishi ma mai d'aukar hankali ce da birgewa, kalar ba ko ina zaka ganta ba, dan kalar maron ce mai duhu da mai haske sai d'an ratsin fari kad'an, rufe motar sukayi har zasu wuce suna daga musu hannu tace "A'a ban gane ba." Juyowa sukayi hakan yasa ta mik'a musu hannu tana fad'in "Mu gaisa mana." Dukansu hannu suka bata cike da jin kunya, rik'e hannayen tayi tace "Ban ji wanda yace ya gode? Nasan dai ba zaku ce Amminku ko Abbanku bai koya muku yin godiya idan an muku abu komai k'ank'antar shi ba." Izzadeen da yafi surutu ne yace "Mu Mamanmu kullum bata koya mana." Sharfudeen ne yace "Mun gode Aunty." Murmushi ta musu tace "Ku gaida kowa da kowa." Har zasu wuce tace "Baku fad'a min sunanku ba? Ko ba zakuyi k'awance dani ba?" Dariya sukayi dukansu suka fad'a mata sunan, wani murmushin ta sake yi tace "Sunayenku da dad'i, Allah ya muku albarka." Juyawa sukayi suka wuce kafin ita kuma ta tayar suka shiga kwana dan komawa baya su tafi gida suma. Bayan isha'i sun gama cin abinci suna hira take fad'awa Dada tafiyarta, tambayar Dada tayi "Amma zamu je dake ko Dada?" Tab'e baki tayi tace "Ni Faduma? A'a wallahi kije ko, ni ina nan babu abinda zanje na musu." Murmushi kawai tayi dan tasan dama ba zata je d'in ba, tambayarta tayi ita ma da cewa "Amma da Amjad zaku tafi ko?" Girgiza kai tayi tace "Dada tace na je ni kad'ai, dole zan barshi nan." Girgiza kai tayi cikin rashin jin dad'i tace "Amma dai wallahi *Hadizey* na da matsala, saboda kawai farin cikin wasu sai ki dinga tauye kanki." Tsaki tayi na jin haushi k'ala dai Faduma ba tace ba, har suka gama hirarsu kowa ya shiga d'akinshi ya kwanta. _______________ Duk da ya fita da b'acin ranta amma sanda ya dawo gidan ganin yaran na tare da ita yasa shi kallonta yace "Sannu da gida." Saida ta harareshi ta wutsiyar ido yace "Yawwa." Baiyi zaune ba dan yaga hankalinta na kan kallo ya wuce kawai, duk yaran bin bayanshi sukayi zuwa d'akinshi, inda Izzadeen ke fad'in "Abba yau aunty ta kawo mu gida, tana da kirki sosai da dariya, kuma kaga mai kyau da k'amshi." Juyowa yayi da mamaki ya kalleshi yace "Kai Izzadeen, gidan uban wa kake jin wannan kalaman? Kenan k'are mata kallo kayi?" Turo baki yayi ya kama hannunshi yana k'amk'amewa yace "Ai da gaske ne ko Deen? Ko da muka shiga motarta muka ji k'amshi, kuma duk in zatayi magana sai tayi murmushi." Sharfudeen ne yace "Kuma Abba har addu'a ta mana, kaga ai Mammie bata mana addu'a." Ajiyar zuciya ya sauke yana girgiza kai yace "To wai wacece?" Izzadeen ne yayi saurin cewa "Mamar abokina ce." Hararanshi Sharfudeen yayi yace "K'arya ce Abba abokina ne fa, ya girmeka ai." Shima turo baki yayi yace "K'arya ce abokina ne." Ganin.zasu fara fad'a yace "To naji shikenan, in ce dai kun mata godiya ko?" "Eh Abba." Suka fad'a kusan a tare, cire rigarshi yayi yana fad'in "To ku zauna zan je nayi wanka sai na zo mu ci abinci." Sharfudeen ne yace "Abba ai Mammie bata yi girki ba." Juyowa yayi ya kalleshi sai Izzadeen da yayi saurin cewa "K'arya ce Abba ta gyara mana salade mun ci." Hararanshi Sharfudeen yayi yace "To Abba salade abinci ne, tunda yamma muka ci fa, kuma har cewa nayi muna jin yaunwa tace muje wajen Kaka mu ci." Girgiza kai kawai yayi cike da takaici ya shige ban d'akin, ya jima yana tsaftace kanshi kafin ya fito ya shirya suka fita shi da yaren suna ci gaba da surutunsu, turarenshi ya fara sanar da ita ya fito, amma ita a dole hushi take dashi sai kawai ta k'i kallon inda suke, shima bai kulata ba ya fita tare da yaren suka nufi b'angaren mahaifiyarshi. Da sallama suka shiga dukansu, amsawa Umma tayi tana kallonsu tace "Da yaran nan ka dawo min? Wai ku bana sallameku ba nace sai gobe kuma." Izzadeen ne yace "To ai tare da Abbanmu muka zo." Hararanshi tayi tace "Nasan dai yunwa ta koroka ko?" Sharfudeen ne yace "Eh, idan kika bamu tuwo muka ci sai mu koma wajenmu." "Idan na k'i fa?" Ta fad'a tana kallonshi, Hasheer dai dariya yake yi sai Salima da tayi saurin cewa "Ka ba Umma hak'uri in dai kana son cin tuwo yaro." Wuri suka samu suka zauna cikin ladabi yace "Umma an wuni lafiya?" Da murmushi ta amsa da "Lafiya lau Hasheer, har an dawo?" "Umma na dawo, ya gida?" Amsawa tayi da "Gida lafiya lau." Kallon Salima tayi tace "Je ki d'auko mishi abinci, ko kun ci abinci ne?" Ta k'arashe da kallonshi, girgiza mata kai yayi alamar a'a, tashi Salima tayi take ta d'auko ta kawo musu, zuba musu tayi shi da yaran suka saka hannu, suna cikin cin abinci Mujaheed ya shigo babu sallama da sigari a hannunshi, Salima ya kalli cike da gadara yace "D'auko min abinci na." Mik'ewa tayi tana hararenshi ta wutsiyar ido ta shige, cikin dakakkiyar muryar da babu alamar wasa Hasheer ya kalleshi yace "Karka sake shigowa gidan nan da sigari, iyakar shanka da ita daga k'ofar gida abinda yayi wajen gidan, amma banda cikin gida saboda akwai yara da yanzu ne ake tarbiyarsu, sannan ya zama na k'arshe da zaka sake shigo mana cikin gida babu sallama." Yana gama fad'a ya sunkuyar da kanshi ya ci gaba da cin abincin, cikin sababi da bala'i da d'aga murya yace "Kai! Kai ubana ne da zaka zauna ka tank'washe k'afafu kana kafa min sharud'a, to ba za ayi ko d'ayan ba kayi abinda zakayi, kaga bana shiga harkar kowa a gidan nan ya kamata nima a fita harkata." Kallon Umma yayi cikin raini yana nunata da hannu yace "Kinga ki wa d'anki magana, wallahi saina kakkaryashi babu abinda ya dame ni, akan me zai zauna yana fad'a min haka sai kace ya haife ni, ko dan anga uwata bata gidan ne?" Cikin sanyi ta kalleshi tace "Kayi hak'uri Mujaheed ba zai sake ba." Kallon Hasherr tayi tace "Hasheer babu ruwanka da lamarinshi, nan gidansu ne yana da damar da zai shigo duk yanda yaga dama, tunda baya shiga b'angarenka to kayi zamanka can." D'ago kai yayi ya kalleta da mamaki yace "Amma Umma ba dan ni na fad'i haka, saboda yara ne wanda suka fi sauran d'aukan abu mai kyau da marar kyau." Ba alamar wasa tace "To suma su zauna wajensu mana, kaga basu zo ba bare su gani." Wani murmushin takaici yayi dan yasan tana fad'in hakane saboda maslaha kawai, amma kuma wanda take yi dominshi ba zai gani ba, ai kuwa sautin tsaki suka ji yana fad'in "Aikin banza, wannan duk salon munafurci ne, ni fa ba yau na fara rayuwa dake ba, sai dai ki ma wani wannan makircinki kuma ba dai ni ba." Wani kallo ya masa yace "Mujaheed! Mujaheed! Na rok'eka duk sanda zaka ci zarafin mahaifiyata ka dinga yi bayan idona, kai kasan albarkacinta kullum kake ci, ka daina wani abun mana tunda ba mahaukaci bane kai." A tsawace Umma tace "Hasheer, kayi abinda ya kawoka mana ka koma wajenka." Saida ya had'e abinda ya tokera masa wuya ya cire hannunshi ya mik'e ya fita, suma yaran mik'ewa sukayi suka bi bayanshi, Salima na zuwa ta mik'a mishi ya karb'a yana bud'e kwanon, gaban Umma yaje ya nuna mata yana fad'in "Dubi wannan yar iskar abincin data zuba min, yanzu ko waccen Sharfudeen d'in mai k'aton kai ba sai ya cinye shi ba." Karb'ar kwanon tayi ta mik'e tana fad'in "Bari na zubo maka da kaina." Da kanta ta sake zubo mishi wanfa tasan dole ya ci ya barshi, kawo mishi tayi yana karb'a ya juya ya fice yana magana k'asa k'asa, girgiza kai tayi tace "Zanyi hak'uri kamar yanda ubanka har ya rasu yana fad'a min, uwarka ma haka yayi hak'uri da ita bare kuma ni." Ko da suka shiga kallo d'aya ta masa tasan ranshi a b'ace yake, amma tana kallo suka shiga d'akinshi, bata damu ta ji me ya faru ba bare tasan hanyar da zata bi wajen ganin dariya ko murmushinshi, ita kam matsalarta ma abinci da bata girka ba kuma taga bai shigo da komai ba, dole da taji yunwa ta mik'e taje ta d'ora indomie, tana idawa ta fito da plate shi kuma ya fito d'auke da Izzadeen har sunyi bacci, kallon juna sukayi lokaci d'aya kowa ya d'auke kanshi, d'akinsu ya kwantar dasu ya koma ya kwanta shima. ________________ Kamar kullum ta aje shi a makaranta ta wuce ofishinsu, ta samu Aminu ya rigata isa har tana tsokanarshi dan baya da mata ne yayi sammako haka, dariya ya mata yace "Wacce nake so ce bata so na." Dariya tayi cike da son kawar da zancen tace "Haka dai ka ce." "Hakane mana." Ya fad'a yana kallonta shima, saida ta wuce nata ofishin kamar yanda take kullum ta cire lafayarta ta d'ora rigar aikinta ta zauna. Misalin 09:30 rana tayi sosai Aminu ya shigo da sallama, kai tsaye ya shiga ya tsaya gaban teburin ya d'ora hannayenshi hakan yasa shi d'an rank'wafawa yace "Kina da bak'o fa." Kallonshi tayi tace "Bak'o kuma? Waye?" Ba tare daya d'auke ido daga kanta ba yace "Um ban sanshi ba gaskiya, ya zo d'aukar lauya ne." Wani kallo ta masa mai kama da harare tace "Shine kuma zaka ce bak'o na? Kawai kaji dashi mana, ina da abubuwa dayawa kuma kaga jibi zanyi tafiya." Karkace kai yayi cikin rarrashi yace "Dan Allah mana ki saurare shi, ni ya fara samu ya fad'a min komai, sai nace mishi zan had'ashi da oganniyata, dan matsalar babba ce." Harara ta sake banka masa tace "Aminu bana so fa, yana ina yanzu?" Da ido ya nuna mata yace "Yana waje." Gyara zamanta tayi tace "Shikenan shigo dashi." Murmushi yayi yace "Yawwa ko ke fa." Girgiza kai tayi har zata maida dubanta ga ordi. ya sake tsayawa yace "Ehem! In tambayeki mana?" Da ido ta masa nuni da ina jinki, cike da zolaya yace "Meye sunan masoyiya da harshen tubanci?" Dariya tayi har kumatunta suka lob'a tana girgiza kai, kallonta yayi cike da birgewa yana murmushi yace "Ina jinki mana." Ba tare data kalleshi ba tace "Yau yan mata zasu shiga uku kenan, to sunan masoyiya da tubanci *dara nra*." Wani tattausan murmushi ya saki da sosai take birgeshi duk abinda tayi, musamman tana harshen tubanci saita k'ara kyau, fita yayi ita ma ta ci gaba da murmusawa, ba jimawa taji an k'wank'wasa k'ofar, cikin taushin murya k'asa k'asa yanda ba zakayi tunanin ko na kusa da ita yaji ba tace "Shigo." Bud'ewa akayi amma bata d'aga kanta ba tana ta danna ordi., taji an rufe k'ofar kuma anyi taku biyu zuwa uku, amma kuma sai taji an tsaya ba'a ci gaba da tahowa ba, hakan yasa ta d'aga kai da niyyar cewa a k'araso mana. Sanda sukayi ido biyu wani mummunan fad'uwa ne gabanta yayi, k'arfin harbawar da zuciyarta tayi yasa ta saurin dafe k'irjinta ta furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un." Bata iya rufe bakin ba dan gaba d'aya jikinta ne taji ya kwashi rawa, ba dan a zaune take ba shakka babu fad'uwa zatayi, tuni idonta suka canza lauyi suka yi sirkin ja tare da taruwar ruwa taf idonta, tana ta k'ok'arin janye idonta ta rufe bakinta, tana so tayi dauriya ta b'oye halin data shiga ciki, amma abun ya gagara ta tsareshi da idonta, zufar data gangaro daga goshinta ta sauka d'as saman gashin idonta ne ya tilasta mata rufe idon hakan kuma yasa hawayen zirarowa suka bi tattausan kumatunta, a lokacin kuma tayi nasarar rufe bakinta ta sauke wani irin numfashi mai k'arfin gaske da sauti, hannunta dake rawa ta d'auke daga k'irjinta tasa ta goge hawayen. Gyara zamanta tayi tare da daidaita nutsuwarta ta d'aga kanta, bata yarda ta sake kallon fuskarshi ba ta bud'a baki zatayi magana, kif taji ta nemi muryarta da harshenta ta rasa, da ta bud'a bakin sai taji kamar bata iya magana ba ko kuma bata san da wane yare zata yi magana ba. Da sauri ta tashi har kujerar ta tintsire ta fad'i da sauri har tana hard'ewa ta shige yar k'aramar ban d'akin dake cikin ofishin ta rufe k'ofar, jingina tayi a k'ofar ta fashe da kuka marar sauti, danne muryarta tayi ta d'aga kai sama tana kuka sosai har tayi zaune k'asa ta manta a ban d'aki take, rintse ido tayi sosai tana fad'in "Me yasa na ganshi? Me ya dawo dashi rayuwata kuma? Me ya dawo nema a guri na? Me ya kawoshi garin da nake?" Ci gaba tayi da kukan kamar ranta zai fita wanda ta jima ba tayi ba na hawaye sai na zuciya kawai, kamar an tsikareta kuma saita mik'e tana share hawayen, gaban madubin ta k'arasa ta wanke fuskarta ta d'aga kai ta kalli kanta, girgiza kai tayi tace "Me yasa zakiyi kuka? Me yasa zaki kasa fuskantarshi? Kin manta dashi fa, rayuwarki kawai kike yi, ya lalata miki ita a shekarun baya, karki bari ya sake lalata miki ita a yanzu ma, karki bari ya sake ruguza miki buri mana." Jinjina kai tayi alamar gamsuwa da shawarar da zuciyarta ta bata, goge fuskarta tayi ta gyara kanta sosai sannan ta fito. Tunda ya shigo ya sauke ido a kanta yaji idonshi na mishi gizon ita ce ko ba ita bace? Dan tabbatarwa ya rufe k'ofar ya taka d'aya biyu har uku, yana tabbatarwa ita ce ya tsaya cak, a lokacin kam dan kwananshi basu k'are bare, amma a yanda zuciyarshi ta buga kanshi ya sara daya rasa ranshi, kakkarwar da yaji hannayenshi na yi da k'afafunshi ne yasa shi jimk'e hannayen da k'arfin tsiya, ya so sunkuyar da nashi kan ko dan kunya, amma sai hakan ya zama jan aiki, haka kawai shima ya kafeta da nashi idanun yana kallo, dantse hak'oranshi yayi sosai har saida jijiyoyin hannunshi da goshi duk suka fito, sai k'ullutun mak'ogwaronshi dake ta kai kawo alamar yana ta had'a yawu da k'arfi. Tashin da tayi da sauri ne ya ceceshi wajen sanin lallai yana motsi, dan tana shigewa ta rufo k'ofar shi kuma ya rufe ido, a hankali ya sake bud'esu akan k'ofar, harbawar da kanshi ke yi da rawar da har yanzu k'afafunshi keyi yasa dole ya k'arasa da k'yar ya zauna kan d'aya daga cikin kujeru biyun dake fuskantar wacce ta tashi, duk'e kai yayi ya d'ora akan hannunshi daya d'ora kan teburin, d'aya hannun kuma ya dafe saitin zuciyarshi da yake jin kamar zata fasa ta fito waje. Yana hakane yaji bud'e k'ofar alamar zata fito, da sauri ya d'aga kanshi yana kallon k'ofar, sam bata yarda sun sake had'a ido ba kanta na kan kujerar, sunkuyawa tayi ta d'auke kujerar ta zaunar da ita, saida ta gyara rigarta ta zauna kan kujerar tana janye ordi. d'in ta janyo wani babban littafi, alk'alami ta d'auka ta rik'e ba tare data kalli fuskarshi ba tace "Sannu ko." Wani zazzafan iska ya furzar da k'arfi yana d'auke idonshi daga kanta, wata ajiyar zuciya ya sauke sannan ya sake kallonta yana mai tattaro duka nutsuwarshi da k'arfinshi, da k'yar kamar mai koyon magana ya furta "Sa...nnu." Kallon wuyan rigarshi tayi jin yanda ya amsa da wuya, d'auke idonta tayi daga nan tace "Sunanka?" Kallon mamaki ya mata jin wai Faduma ce zata tambayi sunan shi a duniyar nan? Lallai ma ya fad'a yana jinjina kai, jingina yayi kan kujerar ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya yana kallonta da isa yace "Sunana *Tagur Sugui*." Ba tare data kalleshi ba dai tace "Shekaranka nawa malam Tagur?" Wani murmushin mamakin rainin hankalinta yayi dan yasan da gangan take haka ba abinda ya kamata ta fara tambayarshi kenan ba, amma saiya dake yace "Ina jin yanzu ne zan cika talatin." Karo na biyu da suka sake kallon juna ido cikin ido, kallon bansan iskanci ta masa, gyara zamanta ta sake yi ba tare data daina kallonshi ba tace "Gaskiya zaka fad'a min." *Yawan sharhi yawan rubutu* *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 17:07 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _6_ Murmushi ya mata yace "Talatin da biyar da wata uku da kwana goma sha biyu." D'auke idonta tayi daga kanshi tace "Me ya kawoka?" Cike da isa da k'asaita yace "Lauyar da zata tsaya min nake nema." Kallonshi tayi fuskarta babu alamar wasa tace "Miye matsalar?" D'agowa yayi daga jinginar ya d'ora hannayenshi akan table d'in kamar yanda ita ma nata hannayen ke sama yace "Shari'a ce tsakanina da matata, mun rabu da ita, ina so na karb'i yarona amma ta hana, na nuna k'arfin ikona wajen karb'arshi, shine ta shigar da k'arata take so a karb'ar mata shi." Wani murmushin takaici tayi ganin yanda yake magana da gadara a ciki abinda bata san shi da su ba, girgiza kai tayi ta ci gaba da tambayarshi duk abinda ya kamata ta sani, daga k'arshe ne ta tambaye shi "Yaushe ne za'a saurari k'arar?" Saida ya sake jingina a kujerar yace "Gobe ne." Kallon mamaki ta masa ta aje alk'alamin hannunta tace "Kuma shine sai yau ka zo neman taimako? An fad'a maka lauyoyin basu da aikinyi ne?" D'aga kafad'a yayi alamar oho! Takardar data dinga d'aukar bayananshi ta d'auka ta mik'e tsaye ta zagaya inda yake zaune ta tsaya tace "Malam tashi fita anan ba zan iya ba, kaje ka nemi wani ko wata su tsaya maka." Jefa mishi takardar tayi tana dafe k'ugu da jiran ya tashi, wani shegen murmushi ya dinga saukewa har ya mik'e tsaye, gabanta ya tsaya hakan yasa ta ja baya tana had'e fuska sosai, sake matsawa yayi haka ita ma ta matsa shima ya matsa har ta kai ga bango, a hassale ta kalleshi tana nuna shi da yatsa tace "Tag.." Kasa fad'in sunan tayi dan haka tace "Bana son wannan shashancin, ka fice min a ofishi ba iskanci ne ya kawo ni ba." Zata wuce ta b'angaren damanshi yayi saurin d'ora hannunshi a bangon ya hanata wannan damar, ta d'aya b'angaren ta juya nan ma ya tareta da hannu, yanda kusancin nasu yayi yawa yasa ta duk'awa zata bi ta k'asanshi ta wuce, da sauri shima ya durk'usa ba kuma tare daya d'auke hannayenshi ba, dole ta soka kanta tsakiyar gwiwanta saboda rawar da jikinta ya d'auka zuciyarta na bugawa da sauri, duk yanda ta kai ga danna kanta tsakanin cinyoyinta hakan bai hanata jin k'amshin turaren dake matuk'ar sata jin abubuwa da dama ba. Ba zato ba tammani taji muryarshi a tausashe yace "Ina *ciki na* yake?" Da sauri ta d'ago ta kalleshi take hawaye suka zubo daga kurmin idonta, numfashinta da taji yana neman d'aukewa ne yasa ta kawar da kanta tace "Dan Allah bani wuri ina so nasha iska." Ba tare daya gyara mata ba yace "Sai kin ban amsa ta sannan." Da sauri ita ma tace "Idan ka matsa saina baka." Ajiyar zuciya taji ya sauke da har saida taji sautin iskan a fuskarta, mik'ewa yayi tsaye ya ja baya yana kallonta, da sauri ita ma ta mik'e tayi nesa dashi ta kalleshi tace "Fitar min a wurin nan ko nasa a fitar min da kai." Murmushi yayi tare da takawa ya koma ya zauna kan kujerar yana kallon yatsunshi yace "Amsata nake jira." Ba tare data matsa daga inda take ba ta kalli k'eyarshi tace "Babu wata alak'a data rage tsakani na da kai, abinda ya faru a baya ya riga daya wuce, dan Allah ka fita a nan." Juyowa yayi ya kalleta fuskarshi d'auke da murmushin nan yace "Amsar da zaki bani ita ce zata tabbatar min da akwai alak'ar ko kuma babu." Kawar da kanta tayi ba alamar wasa a muryarta tace "Na zubar, zubarwa nayi saboda banga anfaninshi ba." Da k'arfi ya mik'e daga kan kujerar ya yo kanta yana tsareta da idonshi, cikin wata birkitattar murya yace "Kin yi me? Akan me?" Juyawa tayi zata kalleshi sai taga kuma har ya k'araso kusanta kamar zai daketa, baya taja da sauri tana fad'in "Dan Allah ka fita nace." A tsawace cikin b'acin rai yace "Ba zan fitan ba *Fadu*, indi yini dahanuma gunin gi (Me kika d'auki kanki)?" Kaucewa tayi daga gabanshi ta nufi kujerarta tana fad'in "Harannuru (ban sani ba." Rik'e k'ugu yayi da duka hannayen biyu ya d'aga sama yana huci, ya d'an jima haka kafin ya sauke hannayen ya juyo ya kalleta, matsawa yayi kusa da kujerar daya tashi yace "Faduma na je sau da dama ina tambaya a kan ki, amma babu wanda yake kulani bare ya fad'a min wani abu dan gane da ke, Faduma na damu sosai akan halin dana jefaki, da k'yar na iya sanin cewa ba kya garin nan daga bakin yayanki Barka, ina ta tunanin ranar da zamu had'u zan ganki ne tare da abinda kika haifa, sai kawai yanzu kice min wai kin zubar, me yasa za kiyi haka Fadu?" Dafe kai tayi da hannu biyu cikin matsanancin kuka tace "Dan Allah *Tagur* bana son tuna komai akan bayana, bana so ka fita dan Allah, ni na manta da abinda ya faru, rayuwata nake yi yanzu sabuwa wacce nasha wahala sosai wajen ginata, kada ka sake ruguza min ita da wani tambihinka marar anfani." Shiru yayi na d'an lokaci sai kuma ya duk'a ya d'auki takardar daya jefa mishi, aje mata yayi kan teburin cikin muryar rarrashi yace "Dan Allah ki taimaka ki duba al'amarin nan nawa, sam banyi tunanin ganinki anan ba, a karon farko Faduma na rasaki, na biyu kuma na rasa abinda ya zauna cikinki, karo na uku dan Allah karki bari na rasa wani d'an nawa, karki duba abinda ya faru tsakaninmu Faduma, ki min wannan alfarmar a matsayin wacce aikinki ne dama." Saida ya sake tausasa murya yace "Dan Allah." Da sauri ya fita daga ofishin hakan yasa ta sake fashewa da wani kukan. Aminu da hankalinshi ya kasa kwantawa ganin ya jima a ciki, damuwarshi bata wuce ganin shima matashi ne, kuma ko dan ya dinga kallonta zai iya zama a ofishin, hakan uasa shi kasa zaune da tsaye, yana ganin fitarshi da minti biyu ya shigo da sallama, turus yayi ganin abinda ya jima bai gani ba, da sauri ya k'arasa yana fad'in "Subhanallahi, Faduma kuka? Me ya faru?" Jan kujerar yayi ya zauna yana kallon kanta dan ko d'agowa ba tayi ba, cikin tausasa murya ya sake cewa "Faduma, d'ago ki kalleni mana, kinfi kowa sanin damuwarki damuwata ce, duk abinda zai b'ata miki rai idan ina da iko zan tunkareshi na hana shi fuskantarki, dan Allah kiyi shiru ki daina kukan kinji, d'ago ki fad'a min me ya faru?" Saida ta samu ta saita nutsuwarta ta d'ago kai amma ta kasa had'a ido dashi, goge fuska tayi ta yi tana sauke ajiyar zuciya, a hankali ya sake cewa "Me aka miki Faduma? Wanda ya fita yanzu ya b'ata miki rai?" Girgiza kai tayi ta d'an kalleshi a kakkauce tace "Ba komai." Wani kallo ya mata yace "Ya zaki ci ba komai bayan ga komai ina gani a gabana, Faduma ko dai zaki fara b'oye min wani abu ne? Ni a ganina kamar babu abinda na cancanci ki b'oye min, duba da matsayina a wurinki da kuma gwagwarmayar da muka sha a baya." Kallonshi tayi da idonta har sun fara kumbara, saida ta sake jan majina ta kalleshi da k'yar ta iya furta masa "Shine, Abban Amjad." Ta k'arashe maganar da sake fashewa da wani kukan, waro ido yayi ya juya ya kalli k'ofar ya kuma kalleta baki bud'e yace "Abban Amjad? Kina nufin Tagur?" Jinjina mishi kai tayi ba tace komai ba sai kuka, ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi yayi shiru shima, baisan me zai ce ba banda haushin mutumin da shi kanshi daya mishi iso zuwa wajenta. Suna zaman shirun nan wayar Aminu tayi sonn茅 (ring), ta jima tana sonne kafin ya d'auka yana sallama, jim yayi alamar yana sauraren abinda ake fad'a daga can b'angaren, cikin sanyin jiki yana kallon Faduma dake ta k'ok'arin share hawaye amma wasu na fitowa yace "Alhaji kayi hak'uri, a gaskiya ba zan iya maya dole ba idan ba zata karb'a ba, kuma kaga a k'urarren lokaci yayi magana, dan haka kawai ka fad'a masa yayi hak'uri." Da sauri Faduma ta kalleshi ta mishi alama da hannu cewa za tayi, d'an d'auke wayar yayi daga kunnenshi yana fad'in "Tu es s没re (Kin tabbatar)?" Da kai ta masa alamar eh, mayar da wayar yayi yace "Shikenan Alhaji, tace ba damuwa zata duba al'amarin." Takardar gabanta ta d'auka tana ji yana ci gaba da wayar, suna idawa ta kalleshi tace "Zaka taimaka min Aminu?" Cike da tausayinta yace "Zanyi Faduma, amma me yasa zaki shiga sabgar mutumin nan? Da kin barshi kawai ya nemi wani, kuma a d'an lokaci haka me zaki iya yi?" Mik'ewa tayi tana tattara kayanta ta sa a jaka tace "Karka damu ba zamu rasa abun yi ba insha Allah." Jinjina mata kai yayi yace "Yanzu me zan iya yi miki to?" Saida ta fara tafiya tace mishi "Muje." Mik'ewa yayi ya bi bayanta suka fita, saida ta rufe k'ofar ta kalleshi tace "Kaje ka same shi ku tattauna game da yaron, wane irin rik'o yayi mishi sanda ya karb'o shi, yanayin aikinshi, ma'ana mai tafiye tafiye ne? Idan mazauni ne wane lokaci yake fita kuma yake dawowa? Sannan ya dangantakarshi da yan uwanshi, yana da mahaifiya da yan uwa mata?" Numfashi ta sauke tace "Ni kuma zan je wajen matar nayi magana da ita, ya bani adresse d'inta." D'aga kai yayi ya nufi hanyar ofishinshi yana fad'in "Ba damuwa." Da sauri tace "Uhem Aminu." Juyowa yayi ya tsaya ta sake matsawa tace "Ya baka rahoton lafiyarshi dana yaron, idan kuma babu ya had'aka da likitanshi wanda ya yarda dashi." Jinjina kai yayi ya sake juyawa ya tafi haka ita ma mota ta shiga ta d'auki hanyar gidansu matarshi. _______________ Zaune suke su biyu sune sai wata data fito daga cuisine (madafa) rike da plateau (faranti) da indomie a ciki, ajewa tayi gabansu tana fad'in "Wai daga ina kuke haka uwar d'akina?" Saida Zaleeha ta sauko k'asa ta gyara zama tana cire mayafinta tace "Daga wajen wani lauya ne muke da aka had'amu dashi." Zaune tayi ita ma sai d'ayar data sauko k'asa ita ma tana fad'in "Lauya? Me zakuyi da lauya?" *Atta* ce ta kalleta tace "Lallai ma k'awata wallahi kin manta damu baki san me muke ciki ba, kina nufin duk abinda ake baki sani ba ma?" Duk da mamaki ta kallesu tace "Wallahi ban sani ba, me ya faru dan Allah?" Tab'e baki Atta tayi sai Zaleeha data fara cin indomien tace "Kenan baki da labarin wannan d'an yarinyar yaje har gida ya d'auke *Ridwan*?" Jinjina mata kai tayi tace "Na sani mana ta fad'a min." "To ai shiyasa ta shigar da k'ararshi kotu dan a karb'ar mata shi." Cewar Zaleeha, kallonta *Abeeda* tayi tace "Da gaske K'awata? Me yasa zakiyi haka? Madadin ki karb'eshi ta sulhu? Kuma naga tunda dai d'anshi ne muye ma sai kin b'atawa kanki lokaci, kiyi sabgar gabanki mana." Atta da Zaleeha ne suka kalli juna sai Zaleeha da tace "Ai ba zai yiwu ba, wannan yaron dole ya zauna wurin ko kuma wani mummunan abu ya faru marar dad'i, idan mukayi sakaci to ba wurin Tagur ba har ita kanta akwai wanda zaiyi bugun gaba da hakan ya karb'eshi kuma ya karb'u in fad'a miki." Da mamaki Abeeda tace "Kamar ya? Kina nufin dangin Tagur d'in?" Wani murmushi tayi mai ma'ana tana jefa lomar indomie tace "Hum! Shima da yasan alak'ar dake tsakaninshi da Ridwan da bai yarda ya karb'eshi ba." Da sauri Atta ta rik'o hannunta tana mata wani kallo, da ido sukayi zaurencensu haka yasa Zaleeha zanca magana da fad'in "Ai in fad'a miki wata shegiyar lauya na so had'aki da ita mai shegen wayo da tone tone kamar kaza, to haushi ta bani wallahi saboda dalilinta yanzu haka nake zauna, da yanzu fa ina shirin amarcewa da Alhaji na." Abeeda ce tayi dariya tace "Gaskiya kam ta cuce mu." Jinjina kai tayi tana fad'in "Haba ki barni da ita, ai wallahi saita raina kanta dan saita zubar da hawaye." Atta ce ta kalleta tace "Ke kuwa uwar d'akina me zaki mata? Ki rabu da ita kawai ki shiga wata harkar, idan da rabo sai kiga Allah ya kawo wanda yafi Alhaji." Girgiza kai tayi tace "Um um Atta! Barni wallahi saina gurza mata nima, in kin fad'i haka saboda Alhaji uwata kuma fa? Ba dan Allah ya taimaka ba an shiga an fita aka fito da ita, da yanzu kina jin ina Mama take? Tana d'aure fa a dalilinta, ai wallahi sai na ci uwarta ta gane bata da wayo, shiyasa na tambayi komai a kan ta nasan wacece ita, dan nasan ta inda zan b'ullo mata." Jinjina kai Abeeda tayi tace "Lallai zata shiga uku matar nan." "Ba kad'an ba ai." Cewar Atta ita ma tana saka hannu a abincin, haka suka ci gaba da cin abincin suna hirarsu. ________________ Bata samu Atta a gidan ba sai mahaifiyarta da mahaifinta, tun shigarta gidan ta fahimci matar gidan ita ke sarrafa gidan, alamu sun nuna mijin baya iya wani hubb'asawa a cikin al'amuran gidan, haka ta dinga fad'awa Faduma abubuwa marasa dad'i akan Tagur ka rantse bata da mak'iyi a duniya sama da shi, ko kuma bai tab'a mata wani abun alkhairi ba, kuma duk hakan saboda ya saki 'yarta ne kawai, ita dai har saida taji maganganun matar sun hau mata kai sannan ta mata sallama ta tafi. A b'angaren Aminu ma ya samu wasu bayanai daga gare shi, wajen rahoton lafiyarsa ne yace gaskiya baya da, akwai kuma takardun dale d'akin Atta a lokacin da yayi had'ari ita ta rik'esu, kuma a gaskiya yanzu baya son wani abu da zai sake shiga tsakaninshi da ita, ganin babu wata tsayayyar magana yasa Aminu kiran Faduma dan ya sanar da ita yaji yanda zasuyi, a lokacin ta fito daga gidansu Atta ta d'auk. Bayan ya fad'a mata ne tace "Aminu muna buk'atar rahoton lafiyarshi, saboda ta hakane zamu samu wanda yafi cikakkar lafiyar da zai iya kula dashi, hatta mutanen da yaron zai zauna dasu in so samu ne zamu so musan lafiyarsu da hallayensu, yin sakaci da wannan abubuwan zasu iya janyo lalacewar tarbiyar yaron da wasa da lafiyarshi, hakan ba abinda zamu so bane." Ajiyar zuciya Aminu ya sauke yace "Ya zamuyi yanzu kenan? Dan da fari yace ko zai had'amu da wani likita abokinshi." Da sauri tace "Ba matsala ya had'amu in dai yasan zamu samu abinda muke so." "Ok bari muyi magana." Ya fad'a yana shirin kashe wayar tace "Saurara." Dakatawa yayi yace "Uhum!" A hankali tace "Yana kusanka?" "Eh." Ya fad'a yana satar kallon Tagur da yake danna waya, d'orawa tayi da "Ka sani a speaker zanyi magana dashi." Saida ya saka yace "Zaki iya magana." Aje wayar yayi akan table d'in dake gabanshi yana kallon Tagur, cikin sanyin murya sosai tace "Ina da sharad'i a aikina, in ka amince zan iya ci gaba da aikin, in kuma baka amince mu dakata daga nan." Kallon juna sukayi Tagur da Aminu sai kuma ya kalli wayar, nuna kanshi yayi alamar wai dashi take? D'aga masa kai yayi cike da jin haushinshi dan shi tunda yasan waye shi yake jin kamar ya rufe shi da duka. Kamar yasan me yake tunani kuwa sai ya saki wani murmushin rainin hankali ya d'ora hannayenshi akantable d'in yana kallon wayar yace "Wane sharad'i kenan Fadu?" Cikin fad'a kamar zata cinye shi tace "Karka sake kirana da wannan sunan." Murmushi yayi mai sauti tare da fad'in "To naji na daina, miye sharad'in?" A hankali tace "Sharad'i shine duk wanda zan tsaya ma ina yin aiki tuk'uru wajen gano gaskiya, ina kuma bayyana gaskiyar ko da kuwa laifin zai shafi wanda nake karewa ne, zan tsaya maka amma idan har na lura yafi dacewa uwar ta rik'e d'anta to shakka babu zan koma tsagenta ne na gabatar da abubuwan da zasu nuna cancantarta wajen rik'eshi, ka yarawa?" Cikin murmushi kamar yana gabanta ya kalli Aminu yace "Na amince, amma wai yaushe kika zama lauya ne." "Wannan kuma matsalarka ce." Ta fad'a tana kashe kiran, girgiza kai yayi yana dariya ya ma manta da Aminu na gabanshi ya mik'e tsaye yana fad'in "Faduma bala'i, Faduma rigima, har yanzu tana nan yanda take bata canza ba, hummmummmmhmmm." Wani kallo Aminu ya masa yana harareshi ya mik'e tsaye shima a shagub'e yana fad'in "... *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 17:08 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _7_ "Faduma sarauniyar taushi ce, bala'i da masifarta tana yinshi ne ga wanda bai mata kirki ba." Tsam ya tsaya yana kallon Aminu kallon tuhuma, kallon me kake nufi da abinda ka fad'a? Me kake nufi da taushi? Kai tsaye ya daddala masa harara tare da juyawa ya koma ya zauna, tab'e baki Aminu yayi alamar ko oho, juyowa yayi ya kalleshi yace "Na d'auka can zamu tafi?" Da wata muryar dak'ilewa yace mishi "Na fasa." Ajiyar zuciya Aminu ya sauke ya juyo da kyau yana fuskantarsa, d'ora hannu yayi akan kujerar daya tashi yana kallonshi yace "Ina zan samu likitan? Duk aikin da Faduma ta bani ina cikashi, yau ba zai zama na farko kuma a kan ka ba." Banza yayi da shi yana rubutu da alk'alami a takarda, saida ya gama ya tura mishi takardar gabanshi ba tare daya kalleshi ba, yana ganin haka shima ya d'auka ya duba, ganin adrese da sunan Dr. ne yasa shi juyawa yana sake tab'e baki ya fice. Da wani mugun kallo ya bishi, lokaci d'aya yaji ya tsani yaron da baisan komai a kan sa ba bayan sunansa da aikinsa, yana ji kuma kamar baida mak'iyi sama dashi, fatanshi kawai Allah yasa babu komai tsakaninshi da Faduma, dan har yau har gobe yana *son* Faduma, rashin sanin inda take yasa ya dunfari rayuwarshi ta gaba, amma fa bai manta data baya ba, Faduma ba ta shiga rayuwarshi bane dan ta fita, shiyasa ma yanzu ta dawo gare shi, zai kuma tsaya tsayin daka da jajircewa wajen ganin ya same ta, yasan zaisha wahala sosai da fuskantar matsaloli bila adadin, daga wajenta ita kanta, wajen iyayenta da suke kallonshi mutumin banza marar amana da alk'awari, da kuma nashi iyayen ma zai fuskanci wani k'alubalen duk da ba mai girma bane, amma hakan ba zaisa ya ji tsoro ba ko ya sare, dan babu wannan tsarin a tsarinshi ko kad'an, yanda duka b'angarorin ke tutiya da jin cewa su jinin tubawa ne, haka shima wannan jinin ne ke yawo cikin jikinshi, dan haka sai inda k'arfinsa ya k'are. Ta fito daga wajen malam *Lawali* wanda take tambayarshi abinda ya shige mata duhu, musamman in tana so tasan hukuncin da shari'ar musulunci ta tanada, kiran Aminu ne ya shigo wayarta ta d'auka tana fad'in "Aminu ya ake ciki?" Daga b'angarenshi ya amsa mata da "Faduma d'an rainin hankali ne mutumin nan, yanzu haka fa wajen Dr. d'in ne zan tafi ni kad'ai." Wani murmushi ta feso mai ban haushi tace "Na sani Aminu, manta dashi kawai, yanzu ina ne asibitin saina sameka acan?" Kai tsaye ya amsa mata da "Clinik Alheri." Jinjina kai tayi tace "Ok gani nan zuwa." Datse kiran yayi ita kuma ta shiga wata kwanar da zata bata damar hawa kan titin daidai, duk da ta titin yar kasuwa ta bi ta manta da lokacin tashin Amjad yayi, sam bata mantawa duk yanda aiki ke shan kanta, amma yau na farko ta manta dashi a makaranta ta wuce inda zasu had'u da Dr. d'in ________________ Ko da ta dawo gida mamanta ke fad'a mata yanda sukayi da lauyar sharewa kawai tayi tana fad'in "Ni naji dad'i ma wallahi da bata same ni ba." Cike da gargad'i uwar tace "Wallahi Atta ki tabbatar kun samu tsayayyen da zai tsaya muku, kinga ba zanyi asarar kud'i na dana ranta miki kika d'auki lauya ba, sannan ba zan yarda wannan shegen mijin naki ya rik'e yaron nan ba, dan in haka ta faru mun shiga uku mun lalace babu hanyar samun kud'i daga gareshi." Tsaki taja mai sautin gaske tana nufa d'aki tana fad'in "Wa yace miki ma zai zauna hannunshi ne? Ko baya ma Allah sai Ridwan ya dawo hannu na, ai ina da hanyoyin da zan dawo dashi cikin sauk'i ba tare da an ji kanmu ba, kawai dan insa kotu ta tirsasa mishi barinshi wurina ne, sannan a wajabta mishi d'aukar nauyinshi ta yanda duk wata zai dinga dire min masu gidan rana nayi haka." Saida ta ga shigewarta d'aki tayi murmushi k'asa k'asa tace "Ni ma kuma sai kin dinga biyana ko na dinga rik'e miki shi in zaki tafi yawon iskancin naki, dan yanzu duniya gwamnati ta hana aikin banza, ba zan duba 'yata ce ke ko shi jikana bane wallahi, ah to ba sauk'i a al'amarin." _______________ Sun ji dad'in yanda suka samu ganin Dr. d'in duk da yana daf da tashi daga aiki dan 12:00 ta wuce, ya karb'esu da mutumtawa ganin masu ilimi ne da kuma masaniyar da suka bashi, hakan yasa har ya sake kiran Tagur suka sake magana, saida ya gama wayar ya kallesu da kyau ya duba wani babban littafi ya aje shi gabanshi, dubawa ya shiga yi tsawon mintuna kafin ya tsaya akan wani shafi ya cire gilashin idonshi ya kallesu yana turo musu littafin yace "Wannan dai kusan shine na farko kuma na k'arshe a reccord d'inmu, ba wani mai yawan jinya bane, yana yi sai dai bai son zuwa asibiti, kusan ma idan zazzab'i ya bashi wahala yakan kirani naje gida na dubasa." Numfasawa yayi ya ci gaba da cewa "Babu wata rashin lafiya a tare dashi da akan iya d'auka, kama daga ciwuka masu sauk'in jinya har zuwa ga manya ma, kusan ni ne likitan dake duba har mahaifiyarshi da yan uwanshi mata biyu, da kuma ita kanta matarshi, to amma..." Duk ido suka zuba mishi suna kallonshi da saurarenshi, d'orawa yayi da fad'in "Yaron yana da athma, kuma ta mahaifiyarsa wacce take fama da ita shekara da shekaru, babbar matsalar kuma ita ce shi yaron tashi athmar chronique ce." Kusan a tare ita da Aminu suka sauke ajiyar zuciya, kallonta Aminu yayi yace "Dole ta rik'e yaronta kawai, tunda asim (athma) ciwon da ake d'auka ne, ko uban bai d'auka ba wasu yara dake tare dashi zasu iya kamuwa." Jinjina kai tayi alamar eh, kallon likitan tayi tace "Mun gode daka bamu lokacinka, zamu tafi." Duk mik'ewa sukayi Aminu har ya bud'e k'ofar Dr. d'in yace "Baki ji ba." Juyowa sukayi saiya kalli Faduma yace "Zamu iya yin magana daga ni sai ke?" Kallon juna sukayi da Aminu sai kuma ya kalleshi yace "Me yasa sai daga kai sai ita?" Kallon Aminu yayi fuskarshi a d'aure yace "Saboda zamuyi sirri ne." Kallon Aminu tayi dake shirin magana tace "Shikenan ka jirani.a waje." Dawowa tayi ta zauna sai Aminu daya dinga kallonsu yana hararen Dr. d'in, k'wafa yayi ya fita daga ofishin yana banko k'ofar da k'arfi, kallonshi tayi ganin yana kallon k'ofar da Aminu ya rufo tace "Uhum ina ji." Kallonta yayi ya d'ago daga kujerar yana d'an lilawa da ita ya had'e hannayenshi, cikin nutsuwa yace "Haka kawai naji hankali na yafi kwantawa da na fad'a miki sirrin nan, bansan ko zai miki anfani ba? Amma dai abune daya jima yana damuwa, kuma kullum na tuna da abun na kan jefawa kaina tambayoyi cewa *ya akayi haka ta faru*? *Dama ana iya samu ne*? Daga k'arshe kuma saina jinjina k'udirar ubangiji akan bawan nasa." Wani kallo mai kama da harara ta masa tace "Ban fahimci inda zancanka ya dosa ba har yanzu? Ko zaka iya fad'a min me kake nufi?" Ajiyar zuciya ya sauke ya sake kallonta ya cire gilashinshi yana sake matso da kujerarshi yace "Kin gane ko? Shekara biyar da suka wuce Tagur yayi wani mummunan had'ari, ranga ranga aka d'aukeshi aka kaishi babbar asibiti (H么pital), yayi jinya sosai a block na tsayin wata hud'u, daga baya kuma ya warke lafiya lau aka sallamesu suka koma gida, a ranar da aka sallamesu likitan dake dubashi ya buk'aci yayi magana dani a matsayina na amininsa kuma likita, da kuma d'aya daga cikin shak'ik'anshi, a lokacin daga matarshi sai mamanshi da kuma yayarshi wacce suke uba d'aya *Gomboy*, lokacin da Gomboy tace zata je babu wanda ya hanata, har zamu shiga ofishin sai kuma Atta ita ma tace zata je tunda abinda ya shafi mijinta ne, bamu barta ta shigo ba har likitan ma bai goyi bayan haka ba, a wannan rana ya fad'a mana abinda ya d'aga mana hankali sosai, daga ni sai ita muka san da wannan abu." Gitgiza kai yayi yana d'auke kallonshi daga fuskar Faduma yace "Kuka tayi sosai tana rok'ona alfarmar karna fad'a masa saboda ba zai iya d'auka ba, na kuma gamsu da abinda ta fad'a min naja baki nayi shiru, abun mamaki sai kawai na ga matar Tagur ta zo asibitin nan awon ciki bayan wata shida da faruwar wannan lamari." Wani murmushi yayi yace "Kamar tasan abinda naje tambayarta kenan sanda naje gidan, sai tayi saurin tarata da cewa wai naga ikon Allah ko? To gaskiya na yarda dan ikon Allah yafi k'arfin wasa, na fad'a miki ne dan bansan ko zai miki anfani ba." K'ura masa ido Faduma tayi, kama daga idonshi zuwa labb'anshi duk kallon yanayinsu take, kallon hannayenshi tayi da sula ya had'esu, basa rawa kuma baya yawan motsasu, d'an numfashi ta furzar tana sauke hannunta daga kan hab'arta data tangale, ita ma kamar yanda ya ma hannayenshi tayi tace "Me likitan ya fad'a muku? Ba zai iya haihuwa ba?" Da sauri ya d'aga mata kai alamar eh, jinjina kai tayi ita ma tana cije leb'e, kallonshi tayi tace "Akwai bayanin haka a rubuce? Ko kuma kana da wani abunda zai tabbatar min da haka?" Girgiza kai yayi yace "Gaskiya bana da, amma in kina so zan iya had'aki da likitan." Kyab'e baki tayi tace "Rubuta min, zanje na same shi." K'aramar takarda ya d'auka ya rubuta mata ya mik'a mata, mik'ewa tayi tana karb'a ta kalleshi tace "Amma kana ganin Gomboy ta fad'a mishi kuwa?" Girgiza kai yayi yace "Ban sani ba gaskiya, dan ban tab'a mishi maganar ba, amma dai sanda na ga Atta da ciki da sanda ta haihu ma na dinga zolayarshi, amma sam baiyi alamun ya gane me nake nufi ba." Jinjina kai tayi ta juya zata fita tace "Nagode." Da kallo ya bita har ta fita, wani k'aramin murmushi ya saki, har ranshi ta birgeshi yanda yaga ta dage tana son samun tabbacin lafiyarsu daga bakunan likitoci ba shaci fad'i ba. Yana ganin fitowarta ya k'ureta da ido kamar mai jiran karin bayani, da tuhuma ya tambayeta "Me ya fad'a miki? Faduma ya zaki yarda ku keb'e daga ke sai shi wai zakuyi magana?" Murmushi ta sakar masa cikin rarrashi da zolaya tace "Allah dai ya huci ran oga Aminu, kayi hak'uri kaji ba san sake ba, nasan nayi kuskure." Saida ya sake had'e fuska yana hararen ofishin da suka fito yace "To me ya fad'a miki?" Kallon mamaki ta masa tace "Sirri mukayi fa." "Sirrin nake so naji Faduma." Ya fad'a da k'arfi, a tsorace ta kalleshi jin yanda ya d'aga mata murya yana matsowa daf da ita, d'an ja baya tayi tana juyawa bayanta sai kuma ta kalleshi tace "Dan Allah ka manta da mutumin nan, me yasa ranka ke b'acewa? Kawai fa mun tattauna ne kan abinda muka tattauna tun a gabanka." Girgiza kai yayi yana ja baya yace "Ba gaskiya bane Faduma, amma ki sani koma me ya fad'a miki wallahi bai kai ko rabin abinda ni nake ji a zuciyata a game dake ba." K'aramin murmushi tayi kawai tace "Kaje a motarka, nima zanje na ga wani Dr. ne a babbar asibiti." Da kallo ya bita kawai yana jin shifa ya fara gajiya da wannan abun, kawai zai fito ya fad'i abinda ke zuciyarshi kowa ma ya huta, amma ba zai iya jurar ganin ana kawo mata hari ba. Tana zuwa Eguillage ta samu labarin yau likitan baya aikin safe sai k'arfe 15:00 na yamma zai shigo, da k'yar ta samu mutumin ya mata alfarmar rubuta mata takardar da idan ta dawo anjima zata samu ganin likitan kai tsaye ba tare data jira ba, godiya ta masa ta juya zata koma mota, *Amjad*, shine sunan daya zo mata a rai bazata, da k'arfi ta dafe k'irji ta bud'e baki taja numfashi, da sauri ta shiga lalubar wayarta a jaka, tana dubawa da k'arfi ta furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, 12:58, ina aikin me na manta da yarona?" Da gudu ta nufi mota sam bata kula da yanda ake kallonta ba, tana zuwa ta bud'e da sauri ta shiga taja da k'arfi kamar motar ta k'wace mata, karo na farko a rayuwarta da zata iya cewa tayi gudun ganganci akan hanya ba sai yau. _______________ Ganin 12:40 tayi yasa mai adaidaitar kiranta ya sanar da ita wallahi yana hanyar d'aukosu adaidaitar ta lalace, cikin jin haushi ta balbaleshi da masifa har ta kashe wayar, kiran Hasheer tayi yana d'auka babu sallama ko wani abu tace "Yara nace kaje ka d'aukosu, mai adaidaitar yace ta lalace baije ya d'auko su ba." Wani bak'in ciki ne ya taso mishi a wuya, magana cikin rashin wayo da taunawa da bayar da umarni, k'ittt ya kashe wayar kawai dan da yana gabanta saiya nuna mata bai ji dad'i ba, dan yana tare da abokinshi duk da bai ji ba, amma ai zai iya fahimtar wanda ya kira baiyi sallama ba bare a gaisa, kallon abokin nashi yayi yace "Ina zuwa dan Allah zan d'auko yara a makaranta ne." Cikin fara'a ya amsa da "Ba damuwa, saika dawo." Fita yayi ya d'auki hanyar makarantar, yana zuwa kam ya samu yaran su uku tsaye daga ciki dan mai gadi bai barsu fita ba. Yana shiga daga ciki suka ruga suka rumgume shi suna fad'in "Abba yau da kanka ka zo d'aukarmu?" "Um." Ya amsa musu dashi yana kallon Amjad daga can baya duk ya takure da alama ma hawaye yake sharewa, kallon Sharfudeen yayi yace "Waye waccen?" Da sauri yace "Abba shine wanda Mamanshi ta kai mu gida jiya, shima yau mamanshi bata zo ba tun d'azu yake jiranta." Kama hannunsu yayi yana nufa wajenshi yace "Ayya, ko lafiya?" Suna k'arasawa ya tsaya gabanshi ya dafa kanshi yana fad'in "Sannu ko, mamanka ce bata zo ba?" Ja baya yayi yana fad'in "Ina wuni." Da fara'a ya amsa da "Lafiya lau, muje saina kaika gida kaga rana tayi sosai, ta yiwu wani aikin ne ya rik'e mamanka." Girgiza kai yayi yace "Babu aikin da ke sa Ayya ta manta dani, nafi tunanin ba lafiya ba." Ya k'arashe maganar da sako da wasu hawayen, matsawa yayi kusanshi yana fad'in "Ah haba kar kayi wannan tunanin, insha Allahu babu komai ka yarda da abinda na fad'a maka, muje saina kaika gidan." Girgiza kai yayi yace "Um um ka tafi kawai, Ayya ta hana ni tafiya da duk wanda ban sani ba." Murmushi yayi yana jinjina tarbiyar da yaron ya samu daga iyayenshi yace "Amma ai ni ka sanni tunda ni ne Abbansu Sharfudeen." Girgiza kai yayi yace "Zan jira Ayya na san bata manta dani ba." Ajiyar zuciya ya sauke yana fito da wayarshi ya mik'a mishi yace "To ga wayata saika kira Abbanka, amma ba zan tafi ba har sai na tabbatar kaima ka bar wurin nan." Da sauri ya kalleshi sai kuma yayi k'asa da idonshi cikin share wasu hawayen dake ta mishi malalowa yace "Aba na ya rasu tun kafin a haife, ni ban sanshi ba ma ko da a hoto ne." Yanda yayi maganar cikin sigar tausayi sosai yasa Hasheer jin tausayin yaron sosai kamar zai mishi kuka, dafa kanshi yayi yace "Sannu kaji, Allah ya jik'anshi da rahama." Cikin qhare hawaye sosai yace "Ameen." Sake mik'a mishi wayar yayi yace "To kira Ayyar ka." Jinjina kai yayi ya karb'a yana fad'in "Nagode Obdo (kawu)." Murmushi yayi yace "Sai naji harshenka wani wuri, ba bahaushe bane kai?" D'aga kai yayi yace "Eh, duka iyayena tubawa ne shiyasa nima na zama batube, amma a garin nan aka haifeni kuma anan na tashi." Cike da k'aunar yaron lokaci d'aya ya jinjna kai alamar gamsuwa, yana shirin danna ok Faduma ta kutso cikin makarantar ko rufe mota ba tayi ba ta fita, duk da lafayarta ta sauka daga kanta amma bata damu data gyara ba idonta na kan Amjad, yana ganinta shima ya mik'a mishi wayar da gudu ya k'arasa gareta, rumgume juna sukayi cike da murna, sumbatar wuyanshi tayi tace "Kayi hak'uri kaji yau aiki ne yasha kaina, amma insha Allahu hakan ba zai sake faruwa ba." Shima saida ya sumbaci goshinta ta saukeshi k'asa sannan yace "Na sani Ayya haka kawai ba zaki barni nan ba, amma a yau na tabbatar da cewa Ayyata ce komai nawa." Dariya tayi ta lak'ace mishi hanci tana fad'in " Wannan *Oddonur* (d'ana ne) ne." Rumgumeta yayi shima yana dariya yace "Wannan Ayyata ce." Sai lokacin ta sake kai kallonta wajen su Izzadeen, kamoshi tayi yana mak'ale a jikinta ta shiga gyara lafayarta ta d'ora sama kai suka k'araso. Tunda ya sauke idonshi akan fuskarta gabanshi ya shiga luguden fad'uwa, komai na jikinshi harbawa ya shiga yi musamman gudun jininshi daya ninku, wani abu yaji yana tafiya a hankali yana ratsa duka sassan jikinshi, abune daya jima bai jishi ba ko akan Saudat, wani haske ne yaji ya mamaye zuciyarshi tare da saukar mishi da wata sanyayyar nutsuwa, yanda ta nuna matuk'ar kulawarta akan yaron ya birgeshi, kyakyawar fuskar ta gigita lissafinshi, sanda take sakin sayayyan murmushi kuma ya tafi da duk wata damuwarshi da b'acin ranshi, sanda ta lak'ace hancin Amjad ta fad'ad'a dariyarta sai yaji kamar zai suma, sai kuma ya gasgata abinda yaranshi suka fad'a cewa mai murmushi duk sanda zatayi magana, ya yarda kam a yanzu duba da tunda ta fito a mota hak'oranta basu b'uya daga kallonshi ba. Yanzu haka kuma da take takowa kamar hawainiya cikin tsananin nutsuwa da kamala da kuma aji da k'asaita, vibration d'in da wayarshi tayi dake hannunshi ne yasa shi saurin dawowa hayyacinshi, ba dan haka ba data tsargu da kallon da yake mata, tana isowa shi kuma ya duba mai kiran, d'auka yayi ya d'an matsa gefe dasu ya amsa, lokacin ita kuma ta bawa duka yaran hannu sun gaisa duk yana hangensu, yanzun ma karkace yayi yana tsinkayen fararen hak'oranta, yanda kumatunta ke ta faman lob'awa ne kawai yaji dariya ta sub'uce mishi, maganar da akayi a waya ya fargar dashi yana fad'in "Zan sake kiranka dan Allah." Kashe wayar yayi ya tako a hankali ya matso kusansu, yana zuwa saida ya sauke b'oyayyar ajiyar zuciya saboda wani irin k'amshin turare daya daki hancinshi, k'amshi ne mai dad'in gaske wanda lokaci d'aya ba zaka gane wane irin turare bane, k'amshinshi kamar na wuta amma kuma yana da sanyayyan k'amshin da yake nuna humra ce ko kuma an had'a biyu ne, cikin daddad'an sauti ya tsinkayi sautin tattausan murya cikin sark'ewar harshe mai surkin hausada tubanci tana fad'in "Sai dai ku ku fad'a min ranar da zaku fara zuwa, idan kuka zo na gani saina kai muku shi har gida shima." Ganin ya k'araso ta kalleshi cike da kunya ba tare da sun had'a ido ba tace "Ina wuni." Ba tare daya d'auke idonshi daga kanta ba yace "Lafiya lau." Nan ma bata kalli idonshi ba sai k'irjinshi tace "Nagode da taimakon daka min, naji dad'i da baku tafi kun barshi anan ba shi kad'ai, nagode." Kallon yaran tayi ta d'aga musu hannu tana fad'in "Bye bye, sai anjimanku." Ta juya zasu wuce ita da Amjad taji yace "Nima nagode." Tsayawa tayi ta juyo, karon farko da suka had'a ido, take taji gabanta ya fad'i sai kawai tayi saurin kawar da nata idon tace "Akan me fa?" Wani murmushi ya saki yana ci gaba da kallon fuskarta yace "Jiya sun fad'a min ke kika kaisu gida, nagode sosai." Murmushi ta masa wanda ya tafi da gaba d'aya imaninshi ya saki baki wajen kallonta, a hankali ta furta "Ba komai, ai 'ya'yana ne suma." Kallon yaran yayi yace "Muje." Dukansu suka ranka yaran na gaba su kuma suna baya, jin idonshi a kan ta ne yasa ta tsayawa baya tana tafiya cike da kunya, shi kam kanshi k'asa yake amma yanda take sauke k'afa fa yanda take d'aukewa duk a kan idonshi, lallen dake k'afafunta bak'i da ja dogayen akaifunta data rufesu da jan lalle, yanda lafayar ta d'auru sosai tare bud'ewa duk in ta wurga k'afarta cikin nutsuwa, sai yaji kamar ya tsaya haka yana ci gaba da kallonta. Suna kaiwa kowa motarshi ya nufa, saida ta bud'e zata shiga ya sake fad'in "Sai anjima." Saboda tukara da tayi da kallon da yake mata yasa ta kalleshi kawai ta jinjina kai, bud'a motar kowa yayi ua shiga suka d'aga, duk da tasan gidansu na gaban nasu kuma hanyar d'aya ce, amma yanda duk sanda kallonta ya kai kan motar sai taga idonshi a kanta yasa taji haushi ta canza hanya, saida ya daina ganinta ya dawo cikin nutsuwarshi ya tuna shi fa babban mutum ne, akwai buk'atar ya kama kanshi kar zalamarshi ta fito fili lokaci d'aya. Murmushi kawai ya sake saki shi kad'ai ya zura hannu ya d'auki wayar zai kira wanda yace d'azu, yana bud'e s茅curit茅 d'in lamba ta fito a wayar reras, d'an kallon mamaki yayi alamar bai gane ba, lokaci d'aya kuma ya zaro ido ya bud'e baki, wani murmushi ya saki har hak'oranshi na bayyana, cikin kallon gabanshi da kuma wayar yayi enregistrer (seve) lambar da sunan *Murmushi na*. Wani murmushi ya kuma saki sanda ya kalli sunan, tab'e baki kawai yayi ya aje wayar gefe. *Preety Aisha* *Halima Muhammad* *Momyn Khadija* *Momyn Sultan* *Lubabtu* *Mamar Hassan* (Yagana) Allah ya saka muku da alkairi ya bar min ku. *Yawan sharhi yawan rubutu* *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 17:08 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _8_ Ko da suka isa gida yaran baki bud'e suke fad'a mata "Mama, yau ma mun ga maman abokinmu, kuma tace mu shirya Abbanmu ya kaimu gidanta ita ma saita kawo mana Amjad." Saida ta nufi t. a manger (d/table) d'in tana aje plate d'in hannunta tace "Wacece kuma hakanan?" Sharfudeen ne yace "Aunty mai murmushi." Juyowa tayi dan tambayarshi sai kuma Hasheer ya shigo, kallo d'aya suka wa junansu suka d'auke idonsu, mayarwa yayi a falon ganin yau ya samu gyara daga gareta, sannan yanda ya ga t. a manger d'in ya nuna ta gama abinci, da sauri Izzadeen ya tareshi yana fad'in "Abba ai zaka kaimu gidan aunty mai murmushi ko?" Shima murmushin ya saki ya d'aga masa kai kawai alamar eh, cikin jin dad'i ya shiga murna sai muryarta da suka ji tace "Je ku cire kayanku ku zo ku ci abinci." Da gudu suka nufi d'akinsu, yana shirin shiga d'akinshi tace "Zaka ci abinci ne?" Ajiyar zuciya ya sauke yace "Me kika dafa?" Hararan k'eyarshi tayi tace "In ba zaka ci ba ka bari mana." Juyowa yayi ya kalleta ya d'aga kafad'a alamar shikenan d'in, shigewa yayi d'akin yayi abinda zaiyi ya fito, tana kallo ya fice ya nufi b'angaren Umma, haushi ne ya kamata sosai dan ta b'ata lokacinta sosai wajen girkin nan, in kuma bai ci ba hakan na nuna fa ba zasu shirya yau ba bare ta samu damar samun kud'in ankon bikin k'awarta, tana cikin wannan tunanin yaran suka fito daga d'aki, Izzadeen ne ya matsa yana fad'in "Mama gyara min rigata." Cikin takaici ta fizgoshi ya fad'a kanta ta shiga k'ok'arin b'alla mishi botir d'in, tana gamawa ta nuna musu abincin tace "Ku zauna maza ku ci." Zaune sukayi suka shiga cin abincin cike da jin dad'in yau suna cin lafiyayyen abinci daga hannun mahaifiyarsu. Tunda ya shiga bayan sun gaisa ya zauna yana kallon wayar, yayi nisa sosai Umma kuma na kallonshi ta kasa cewa komai, Mukhtar ne ya fito daga d'akinshi da niyyar fita, ganin Hasheer na kallon waya sai murmushi yake saki yasa shi d'aga murya cikin zolaya yace "Umma ki fara shirin tarban surukarki, dan naga fitilar ta fara kawo haske mai k'yali." Dariya tayi mai birgewa da nutsuwa tace "Yaushe zaka kawota?" Saida ya k'araso kusansu yana kallon Hasheer da har yanzu bai d'ago ya kalleshi ya mata alama da ido yana nuna mata Hasheer d'in yace "Baki lura da abinda na lura dashi ba Umma?" Kallon Hasheer tayi tace "Kai fa yake wa sharri." Kallonta yayi sai kuma yayi saurin kallon Mukhtar, had'e fuska yayi yace "Lafiya?" Dariya yayi yana lek'a wayar yana fad'in "In gani wacece?" Da sauri ya soka wayar aljihu yana fad'in "Mukhtar ina wasa da kai ne?" K'wafa yayi ya mik'e ya kalli Umma yace "Umma ni zan koma, sai anjima." Murmushi kawai tayi ta bishi da kallo har ya fita, Mukhtar kuma na ci gaba da dariya da tsokanarshi wai to ya rufe bakin. Yana fita masallaci ya nufa yayi salla, misalin 02:20 ya dawo gidan ya wuce b'angarenshi kai tsaye, yana shiga ya same su sunata wasa a falon amma ita bata nan, zaune yayi yana tambayarsu "Kunyi sallah?" Kallon juna sukayi sai kuma suka amsa da A'a, umarni ya basu suyi sallah su shirya ya kaisu 茅cole dan lokaci ya kusa, cikin jin dad'in shi zai kaisu suka tafi a guje dan yin abinda yace. Ya jima zaune yana jiransu kafin daga bisani su fito da kayansu da jakarsu, kallonsu yayi yace "Ina mamanku?" Nuna mishi sukayi da fad'in "Tana d'aki." D'orawa yayi da "Kun ci abinci?" D'aga kai sukayi yace "Me kuka ci?" Sharfudeen ne yace "Abba shinkafa muka ci da nik'akk'en nama da miya mai dad'i." Wani murmushi yayi yace "Hum." Mik'ewa yayi yasa hannu aljihu ya fito da kud'i yan goma goma guda uku, mik'awa Sharfudeen yayi yace "Kai wa mamarka." Da gudu ya juya ya nufo d'akin, yana shiga ya same kwance kan gado da wayarta ta hannu, aje mata kud'in yayi kusa da ita yace "Abba yace na baki." Da sauri ta zabura ta mik'e zaune tana d'aukar kud'in da fad'in "Na miye?" D'aga kafad'a yayi yace "Nima ban sani ba yace na kawo miki." Jim tayi kamar mai tunani sai kuma ta sauko da sauri suka fito, tana ganinshi tsaye yana gyarawa Izzadeen rigarshi ta had'e fuska har ta k'araso, bayanshi ta tsaya tace "Kud'in miye Deen ya kai?" Yanda tayi maganar murya a cunkushe shima haka ya amsa mata da cewa "Kyauta na baki." A bazata wani murmushi ya kubce mata dan ba tayi tsammanin kyautar ba, amma da sauri ta basar ta had'e fuska tace "Ba zaka ci abincin bane?" Ba tare daya juyo ba yace "Alhamdulillah." Cikin tuhuma tace "Ina ka ci abinci?" D'agowa yayi ya juyo ya kalleta da mamaki yace "Baki tab'a tambayata ina na ci abinci ba, me yasa yau kike tambaya?" "Saboda ya dace na tambaya." Wani murmushi kawai yayi ya juya zai fita, da sauri ta tare gabanshi tana fad'in "Kaga malam tsaya ka fad'a min fa." Yanda ta tsaya gabanshi yasa shi kallon fuskarta yace "Kau ce min a hanya." Saida ta girgiza kai tace "Ba zan matsa ba saika fad'a min." Cikin yamutsa fuska yace "Wai me zan fad'a miki?" "Inda ka ci abinci." Ta fad'a tana jijjiga, rab'ata yayi zai wuce ta sake shigewa gabanshi, wani dogon tsaki yaja cikin takaici ya daka mata tsawa yana fad'in "Zaki gusa min ko sai na..." Cije leb'e yayi bai k'arasa ba saboda tuna yaran na tare dasu, kallonta yayi cikin matuk'ar jin haushi ya wurga mata harara ya wuceta, ita kam tunda ya mata tsawar nan ta sunkuye k'asa ta rintse ido, saida taji shiru ta d'aga kai sai taga wayam, mik'ewa tayi ta nufi d'aki tana fad'in "Wallahi zaka dawo ka same ni a gidan, kuma ba zan sake dafa abincin ba saika fad'a min inda ka ci." ________________ Ko da suka je gida sallah suka fara yi kafin suka ci abinci, misalin 02:35 Amjad ya shirya tayi sallama da Dada suka fita, tana aje shi makaranta ta wuce babbar asibiti dan had'uwa da likitan nan. Tayi sa'a kuwa bata b'ata lokaci wajen ganinshi ba, ko da ta sanar dashi abinda ya kawota ya sakar mata fuska sosai, sai dai bai bata takardar data buk'ata ba, wata likita ya had'ata da ita suka tafi tare tayi photocopie takardar ta bata jahun ita kuma ta koma mishi da originale d'in bayan ta sake jadadda mata ta k'ara mishi godiya. Ko da ta dawo gida tana shiga da sallama ta sale had'e fuskarta sosai sakamakon ganin *Hindu*, sam matar bata mata ba saboda halayenta, kallonta tayi ita ma tace "Sannu Faduma." "Sannu." Ta fad'a tana zama kusa da Dada, magana bata sake had'asu ba har ta gama siyan turarenta a wajen Dada ta tafi, kallonta Dada tayi tace "Faduma, matar nan bata miki ba ko?" Saida ta tab'e baki tace "Bata min ba Dada, domin ina ganinta tare dasu Alhaji Sunusi wanda akayi shari'a akan shi waccen satin." Murmushi tayi tace "Duk da haka Faduma ki dinga sakar mata fuska kuna gaisawa, ko dan hakk'in mak'wabtaka ma." Sake tab'e baki kawai tayi ta gyara zamanta tana aje jakarta ta kalli Dada da kyau tace "Dada kinsan wa na gani yau? Kinsan wa na karb'i aikinsa yau?" Girgiza kai tayi lokaci d'aya duk ta zaro ido tace "A'a sai kin fad'a." Saida ta sauke numfashi ta kalleta yana jinjina kanta tace "Dada Tagur muka had'u dashi yau." Da k'arfi ta dafe k'irjinta ta k'ara kwalalo ido tace "Wa? Tagur fa kika ce?" Jinjina kai tayi tace "K'warai Dada, Tagur dai da kika sani." Ba tare data d'auke hannunta daga k'irjinta ba tace "Dama yana garin nan ne? Ya akayi kuka had'u? Me ya had'aki dashi kuma?" Girgiza kai tayi cike da rashin karsashi ta kora mata bayanin yanda sukayi, ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi tayi k'asa da idonta da suka cika da k'walla tace "Dada da nasan yana garin nan dana jima da raba Amjad da k'asar nan ko ta wane hali, bana so su had'u, bana so su san suna da juna, musamman dana fara hango wani tasku na shirin fad'awa akan shi, dan inhar abinda hasashena yake nuna min gaskiya ne, to tabbas matar Tagur ta ha'inceshi, Ridwan ba d'anshi bane." Ita ma ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi tace "Lallai kam, ni kaina da nasan yana garin nan dana jima da had'uwa dashi." Da sauri ta kalleta tace "Me zaki masa Dada?" Sama da k'asa ta harareta tace "Godiya." Dariya tayi wacce ta tilasta zubowar hawayen da suka mak'ale tana girgiza kanta, kallonta tayi tace "Shiyasa har yanzu nake jin farin cikin rashin kasancewarki a wurin a waccen ranar." Da sauri tace "K'warai, dan da ina wurin a wannan ranar Faduma da yanzu d'anki maraya ne na gaske." Wata dariyar ta sake yi tasa hannu ta share hawayen, mik'ewa tayi tsaye tana fad'in "Dada gobe ne tafiyata, zan bar Amjad wajenki amma banda k'arfin halin da zan iya fad'a miki cewa na bar miki shi amana ne, dan har ni uwarshi ke kike kula dani, amma bana so ya fita ko ina har zuwa sanda zan dawo." Jinjina kai tayi tace "Karki damu Faduma, insha Allahu zan rik'e miki amana." Dafa kafad'arta tayi cike da jin dad'i da murmushi tace "Nagode Dada." Wucewa tayi d'aki ta bar Dada zaune da tunanin ina ma zata ganshi ido da ido? Hummm! Allah kad'ai yasan me zata mishi. *Zinder* Jiki na rawa ta d'auki butar ta sunkuya tana zuba mishi ruwa yana wanke hannun, saida ya gama ya mik'e daga sunkuyan da yayi yana murza hannayen, d'agawa tayi tana kallonshi cike da kunya da kuma fargaba, saida ya gama ya shafi fuskarshi cikin harshen tubanci yace "Alhamdulillah, Hadizey ni zan fita, saina dawo." Saile sunkuyar da kai tayi tace "Malam, dama..." Shiru tayi saboda gabanta dake ta fad'uwa, dafe k'irjin tayi tana jin yanda yale buga mata, a hankali ta shiga sauke numfashi da k'arfi wanda har ya fahimci hakan, kallonta yayi yace "Ina jinki." Saida ta sake sauke numfashi sau uku kafin ta d'auke hannunta ta sake sunkuyar da kai tace "Dama...na kirata, ta ta..tace tana nan...tafe gobe." Yanda ta dire maganar da sake wani numfashin zaka san girman abinda ta fad'a a bakinta, ai kuwa yanda tayi tsammani ne wanda zai tabbatar maka da dalilin tsoronta, cikin kwakwazo da hawan kai da sababi kamar yana fad'awa duk wanda ke layin ya shiga fad'in "Hadizey! Ni zaki wanda baisan abinda yake yi ba? Ni ne zan kafa doka nace ga yadda za ayi kice ba haka ba?" Saida ya gyara tsayuwa ya juya da kyau yana kallonta da nuna ta da hannu yace "Nace ina buk'atarta ne? Ni na fad'a miki ina son ganinta wajen sabgata? Kiyi sauri ki kirata ki fad'a mata karta zo, in kuma ta zo to ke zaki fita ki barta anan." Da sauri ta d'aga kai ta kalleshi hawaye har sun wanke mata fuska, da sauri ta durk'usa gabanshi ta had'e hannayenta tana fad'in "Dan Allah malam kayi hak'uri ka min rai, na tuba ba zan k'ara ba kayi hak'uri, ina so naga 'yata ne saboda tsawon lokacin da aka d'auka ban ganta ba, na d'auka dama ce ta zo da zan iya ganinta shiyasa na kirata, amma kayi hak'uri tunda baka so zan fad'a mata ta zauna kar ta zo." Shiru tayi ganin shima ya juyar da kai sai cika yake yana batsewa, ci gaba da kallonshi tayi tana godiya ga Allah daya sa ba gida d'aya take da kishiyarta ba, duk da basu da nisa amma dai zaka iya sirri akan abinda ya shafeka, sannan ita dama 'yayanta biyu ne kawai, namijin ne babba sai Faduma k'arama. Shirun da yayi shima fa jinjina abun yake, yana son ganinta bayan shekarun nan da aka d'auka, har k'asan zuciyarshi yake sonta da kuma damuwa akan ta, abinda ta masa ne kawai yake b'ata masa rai da hana shi sukuni, amma shekara tara ai ba kwana tara bace, har yanzu ko mai kama da Fadumarsa bai gani ba. Juyowa yayi ya kalleta yana shan magani yace "Shikenan na hak'ura, ki bari ta zo, amma da sharad'i?" Da sauri ta sake kallonshi tana mik'ewa tsaye tace "Da gaske? Nagode malam, amma wane sharad'i?" D'an basarwa yayi yace "Sharad'in shine idan ta zo gobe washe gari ana d'aura aure zata kama hanya ta koma inda ta fita, kin yarda?" Kallonshi tayi kasak'e sai kuma ta jinjina kai tace "Ba komai na yarda, Allah ya saka da alkairi." Ficewa yayi kawai komai bai ce ba, da kallo ta bishi har ya fita ta sauke ajiyar zuciya tace "Hakan ma ba laifi angode." Juyawa tayi zata koma d'aki tana godiya ga Allah da yasa duk wata hidima da ake ta auren nan a gidan uwar gidanta ake yin shi, kasancewarsu kansu a had'e yake kuma suna zaman lafiya, shiyasa ma duk wani abu da uwa ke yi *Herde* ce ke yin shi kamar d'an data haifa a cikinta, shiyasa yanzu ma tafi ta jin zafin rashin Faduma a gidan nan, kuma shekaran jiya ma ita tasa ta kira Faduma tace ta zo, amma ita tana tsoron tashin hankalin mai gidan, shiyasa dan kar ya musu rashin mutumci idan ya ganta ta zab'i ta fad'a mishi ya sani, inhar yace a'a to sai tayi zamanta, yanzu kuma daya amince taji dad'i sosai. Daf da magriba angon ya shigo da sauri zai shiga d'akinshi da alama akwai abinda ya kawo shi, da sauri ta mik'e daga alwalar da tayi tana fad'in "Kaji labarin zata zo ne?" Ko da yaji haka yasan wa take nufi, tunda abun ya faru mahaifunsu yayi hushi yace baya son sake jin ko da sunanta a gidan nan, girgiza kai yayi yace "Ayya bana son kisa kanki a matsala, kinsan ran Aba zai b'ace sosai, ki hak'ura mana da zuwanta." Harara ta dalla masa tace "'Yar tawa kake cewa na hak'ura da ita? To da amincewarshi zata zo." Da mamaki ya kalleta yace "Ayya da amincewar Abba? Shine ya yarda ta zo?" D'aga masa kai tayi alamar eh, jinjina kai yayi yace "Lallai Abba ya sauko, amma me kika fad'a masa da har ya sauko da wuri haka?" Cikin saurin magana da fad'a fad'a tace "Bana son iskanci Barka, idan ba kayi farin ciki ba ka fad'a min saina sa tayi zamanta." Tsaki taja ta wuce d'aki tana tab'a hujen hancinta daya mata kyau a fuska, bin bayanta yayi har d'akin ya sunkuya yana kallonta tana saka hijab yace "Kiyi hak'uri Ayya, wallahi ina cikin farin ciki sosai, yanda akayi Aba ya amince ne da sauri haka nake mamaki, amma Allah ya huci zuciyarki." Tsayawa tayi daga saka hijab d'in tana kallonshi ta fashe da kuka mai ciwo ta fad'a kan gadon ta zauna tana fad'in "Barka kafi kowa sanin damuwar da nake ciki, kafi kowa sanin banda buri a yanzu kamar naga *Fadima*, tunda ya koreta a gidan da ciki har yau babu wanda ya sake ganinta, ya ma kowa shamaki da ita ya kuma gitta mana tsinuwa da fushinsa, ya rabani da 'yata na tsawon shekaru takwas da watanni, gobe zan ganta, zan ganta insha Allahu, ko da ina d'ora ido a kanta ne na yarda a zare raina." Da sauri ya mik'e tsaye ya dafa kafad'unta ya shiga rarrashinta da kwantar mata da hankali, jin kiran sallah ne yasa shi cewa "To daina kukan Ayya, ki tashi kiyi sallah an kira, nima zanje na d'auki abu a d'aki zan fita." Jinjina kai tayi tana ci gaba da share hawaye har ya fita, tashi tayi ta kabarta sallah tana ta shashekar kuka. *Maradi* Washe gari kamar kullum ta shirya cikin riga wacce ta tsaya iya gwiwarta da wandonta wanda in ba tafiya take ba zaka rantse kace siket ne, takalman data saka masu tsini ya k'awata shirin nata, lafayarta fara tas ta d'auka ta d'ora akai, sallama suka ma Dada suka fita har tana zolayarta ko ta zo su tafi? Ita kuma da tasan halin kayanta sai tace a'a tayi zamanta, tana k'ok'arin fito da makulli a mota ta kai k'ofa bata ankara, da sauri taji ya rik'e lafayar yana fad'in "Ayya addu'a fa?" Tsayawa tayi ta juyo tana fad'in "Yi hak'uri ban manta ba." Gyara tsayuwa tayi ta d'aga hannu ya musu addu'a sannan suka fita, suna shiga mota tayi addua'r hawa abun hawa sannan suka d'aga. A hanya ta kalleshi cikin nutsuwa ganin ya mayar da hankalinshi kan littafinshi, murmushi tayi ta kalli gabanta tace "Amjad." Kallonta yayi yace "Na'am Ayya." Ba tare data kalleshi ba tace "Kana so na?" Wani irin kallo ya mata kamar na mamaki sai kuma yace "Ayya, ke ce rayuwata fa?Ko wanda yake da baba yana son Ayyarsa bare kuma ni dake kad'ai nake da, Ina sonki sosai Ayya." Kallonshi tayi cike da k'auna tace "Zaka iya rabuwa dani?" Girgiza kai yayi yace "A'a Ayya, mutuwa kawai zata raba ni dake, amma Ayya me yasa kika tambayeni haka? Kina jin kamar bana sonki ne saboda ban fad'a miki gasar musabak'armu ba?" Dariya tayi ta girgiza kai tace "Ko kad'an, kai ka tab'a ganin Ayyarka tayi hushi da abinda ka mata har ta hukunta ka abisa son ranta?" A hankali cikin sunkuyar da kai ya girgiza kai, jinjina kai tayi tace "Me ye na fad'a maka ladabin da zaka iya yiwa babban da ka fara had'uwa dashi baka san shi ba?" Saida ya kalli gabanshi ya sauke ajiyar zuciya yace "Idan naga babba na mishi sallama irin ta addinin musulunci sannan na gaishe gaisuwa irin ta al'ada, idan ina zaune ne shi kuma yana tsaye na bashi wuri ya zauna, idan muna zaune dukanmu ni na koma k'asa, idan yana magana karna katseshi har sai ya gama, idan yayi kuskure karna nuna masa kai tsaye na tunasar dashi cikin hikima, idan ya min kyauta karna karb'a sannan na masa godiya, sannan karna yarda da tafiya da mutum komai kamalarshi in dai ban sanshi ba." Murmushi tayi ta jinjina kai tace "Da kyau, Oddonur na ne wannan." Murmushi yayi shima suka ci gaba da tattaunawa irin haka har ta sauke shi, kallon cikin makarantar tayi tace "Ya naga dalib'ai duk a waje kamar lokaci baiyi ba?" Fita yayi ya zagaya ta k'ofar da take yace "Watak'ila lokacin baiyi ba." Kallonshi tayi tace "To wuce ciki." D'aga mata hannu yayi yace "Sai anjima Ayya." Ita ma d'aga masa hannu tayi tace "Ban da fad'a fa." D'aga kai yayi yace "To." Saida taga shigarsa ciki har mai gadin na d'ago mata hannu ita ma ta d'aga mishi dan ba zata iya d'aga murya ba ta wuce, kai tsaye kotu ta wuce dake kusa sosai da makarantarsu Amjad. Tunda ta isa ta tunkari shiga taji gabanta na ta fad'uwa, sai dai ta horar da kanta dole ta dake ta jure tayi banza da duk wanda zata had'u dashi, ai kam tunda ta fito a mota idonsu suka sauka akan ta, cikin tashin hankalin ganinta Gomboy ta kalli dattijuwar kusanta tace ".... *Yawan sharhi yawan rubutu* *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 17:08 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _9_ "Ayya, wai wa nake gani hakane? Kamar Faduma?" Ita ma cikin firgicin daya fi na Gomboy tace "Nima dai abinda nake gani kenan? Duba mana da kyau." K'anwarsa dake danna wayarta hankali kwance kallo d'aya ta mata tayi k'asa da kanta ta tana fad'in "Ita ce, baku ganeta bane ko me?" A tare suka kalleta sai dattijuwar da tace "Ke *Rahila* da gaske? Ya naga ta canza haka kamar ba ita ba?" Haushin tambayar yasa ta jan d'an guntun tsaki tace "To dama zata zauna nan ne babu ci gaba? Shekara nawa kukayi rabon da ku ganta." Muryar Tagur d'in ne ta katse musu maganar da cewa "Muje." Da sauri ta *Hatimi* ta kalleshi tace "Kai Tagur da gaske Faduma ce can na gani?" Saida ya bi inda ta nuna da kallo sannan ya kalleta yace "Eh Ayya, ita ce." Baki bud'e ta shiga jinjina kai tana fad'in "Lallai duniya, yanzu Faduma ce ta wuce ta gabanmu ko kallon arzik'i babu bare gaisuwa." Ajiyar zuciya ta sauke tana sake rik'e jakarta da kyau, Rahila ce tace "To Ayya me kika mata na alkairi da zaki samu wannan girmamawar daga gareta bayan rabuwarku?" A hassale ta kalleta tace "Ke bana son iskanci, ki rufe min bakinki kinji ko." Gomboy ce tace "Ki rabu da ita Ayya, kinsan dama ko acan ita yar tsagin Faduma ce ai, watak'ila asiri ta mata kuma har yanzu bai sake ta ba." Harara ta dalla mata tana fad'in "Aikin kenan, komai sai kince asiri, shikenan ke babu abinda ke iya tasiri a tare da d'an adam saida sihiri? Mtssss!" A hassale tayi kanta kamar zata kai mata duka tana fad'in "In ban ci uban..." Bata k'arasa ba saboda kallon da Tagur ya musu, duk da a gaba take dashi da shekara d'aya, amma kasantuwarshi ya amsa sunan namiji yasa bata haye mishi, tana shakkarshi yana mata kwarjini sosai kamar shi ke gaba da ita, jinjina kai tayi tana jan k'wafa tayi baya tana hararenta. Kallonshi ya mayar kan Rahila yace "Kar na sake jin bakinki a wurin nan, marar kunya kawai." Hatimi ce tace "To me ya kawota nan?" Saida ya tunkari shiga yace "Ni na d'aukota aiki." Da mamaki suka shiga kallon juna, suna son k'arin bayani amma babu mai basu. Wuce yayi suka rufa masa baya sai Hatimi data rik'e hannun Gomboy tana fad'in "Kiyi hak'uri ki k'yaleta har kuje gida, da kaina zan baki tsumagiya ki zaneta." Ba tace komai ba sai kumburo baki da take, ita kuma Hatimi fushin nata ne bata son gani, 'ya'yan kishiyarta ne data rasu ta barsu a hannunta, su biyar ne duka mata Tagur kad'ai ke namiji, da yake Gomboy ce ta tashi a hannunta shiyasa tafi sonta a cikin yaran, tafi shak'uwa da ita fiye da yanda ta shak'u da nata yaron data haifa a cikinta. Suna daf da shiga taji an kira sunanta da "Trozzonur (K'awata)." Da sauri ta waiga b'angaren da taji muryar Atta, da sauri ta k'arasa da murnar ganinsu, tana k'arasawa ta kallesu tace "Trozzonur har kun iso kenan?" Saida Atta ta kalli Hatimi da ita ma take kallonta da mamakin fitsararta yanda take kallonta cikin ido, ko ba komai dai a tsakaninsu yanzu ai ta auri d'anta, amma wai tana kallonta ido cikin ido babu gaisuwa, tab'e baki Hatimi tayi ta shige, hararar da Atta ta banka mata tana jan tsaki Rahila ta gani, zata nufi kanta cike da masifa Hatimi ta juyo tace "Ke muje." Juyawa tayi ta kalleta hakan yasa ta jinjina kai tana cije leb'e, amma ta sani bashi ta ci kuma zata biya. Kallon Gomboy tayi tace "To me zamu jira?" Zaleeha ce tace "Amma sai naga shegiyar lauyar can a gabanku, ina fata dai ba tare da ita kuke ba?" Juyawa tayi ta kalli k'ofar shiga sannan ta sake kallon Zaleeha tace "Wai Faduma kike nufi?" Hindu ce tace "Kin ma santa kenan?" Da murmushi a fuskarta tace "Na santa kuma? Farin sani ma." Kallon Atta tayi tana yamutsa fuska tace "Ai tsohuwar budurwar mijinki ce wacce ya so aura suka rabu." Duk zaro ido sukayi suka kalleta, baki hard'ewa Zaleeha tace "Tagur dai?" D'aga mata gira tayi alamar eh, tab'e baki Hindu tayi tace "Humm-umm! Da gaske wai ko wasa?" Had'e gira tayi tace "Ya zan muku wasa a yanzu? Kunga ku zo mu shiga." Da sauri Atta ta rik'e hannunta tana fad'in "Ke tsaya dallah, da gaske wai ita wacce naji ana fad'a sunyi soyayya har an saka musu rana?" Cike da tabbaci tace "Wallahi ita ce, Faduma ba." Zaleeha ce tace "Yo me yasa bai aureta ba?" Sake tab'e baki tayi tace "Ke sharri fa ta masa, cewa tayi tana da ciki har da kawo iyayenta gidanmu, shi kuma yace bai yarda ba k'arya ta masa, shine aka fasa auren kowa ya kama gabansa." "La'ilaha illalahu, Muhammad rasulullih sallalahu alaihi wasallam." Atta da Hindu suka fad'a a tare, Hindu ce ta d'ora da fad'in "Shi d'in ne yace k'arya ce?" D'aga kai tayi tana kallon Atta da ita ma ta jefo mata magana da cewa"Shima ashe d'an iska ne shine harda cewa wani wai ya gane ni yar iska ce? Amma dai wallahi baya da mutumci." Tsaki tayi tace "Kunga ku zo muje dan Allah." Ta fad'a tana wucewa, har Atta zata bi bayanta Hindu ta rik'o hannunta tana fad'in "Ke tsaya." Tsayawa sukayi suna kallonta, cikin rad'a tace "Nifa ina tunanin anya kuwa yaron nan na Faduma ba shine d'an data haifa ba." Zaro ido Zaleeha tayi sai kuma ta k'ank'ancesu tace "Kuma fa biri yayi kama da mutum, tabbas zai iya yiwu wa, duba da ai ba yanzu bane abun ya faru." Jinjina kai Atta tayi tace "Ashe haukan banza nake, ina ganin na hifi yaron da zai cinye dukiyarshi, ashe yana can da gabjejen yaro wanda ya haifa a yawon ta-zubar d'inshi." Cike da masifa Zaleeha tace "Kai amma maza bakuyi ba wallahi." Kama hannunsu Hindu tayi suka shiga ciki tana fad'in "Dama sun fad'a miki sunyi ne? Ai mu dasu kallon kallo ne, k'iris ya rage mu fara musu jifar shed'an." Kowa ya samu wuri ya zauna shigowar alk'ali ake jira, duk hangenta suke ita yi duk da yanzu ta cire lafayarta ta d'ora rigarta ta lauyoyi da hularta, hayaniya ake tayi ko da alk'ali ya shigo ta k'ofar gabansu duk aka mik'e dan girmamawa, saida ya zauna kowa ya koma ya zauna ana kama jiki tare da yin shiru. Magatakarda ne ya fara aikinsa ta hanyar shelanta rana mai k'ara da wanda ake k'arar, alk'ali ne ya bayar da izinin lauyoyi su gabatar da kansu, namijin ne ya fara gabatar da kanshi kafin Faduma. Shi aka ba dama ya fara gabatar da abinda kenan, saida ya kira Tagur ya masa tambayoyi kafin ya nunawa kotu yaron ya cancanci ya zauna wajen mahaifiyarsa duba da k'arami ne wanda komai sai an masa. Saida ya gama alk'ali ya bata dama ita ma ta mik'e, hannayenta a had'e tana mummurzasu ta kalli alk'ali tace "Ya mai shari'a ina neman alfarmar kotu data gabatar min da malama Atta?" Coke da dattako yace "Kotu ta baki dama." Magatakarda ne ya mik'e yace "Malama Atta Angr Shilli ta fito." Mik'ewa tayi ta isa inda ake tsayawa ta tsaya tana kallonta, cikin yatsina fuska da dubara ta tab'e baki a ranta tace "Hummm!" Maysawa tayi kusanta tace "Malama Atta lafiyarki k'alau?" Cikin jin haushin tambayar ta harareta ta wutsiyar ido tace "Eh, k'alau nake." Lumshe ido tayi ta d'ora da cewa "A gidanku nawa ke rayuwa?" Idonta cikin nata tace "Mu biyar ne, ni da mama da baba na sai yayuna biyu maza." Da murmushi tace "Kina aiki ne na gwamnati ko wata sana'a?" Kai tsaye tace "Bana yi?" D'an sosa gaban goshinta tayi tace "D'anki Ridwan lafiyarsa k'alau?" A hankali tace "A'a, yana da asma." Jinjina kai tayi tana wani murmushin mugunta tace "Malama Atta kinsan da cewa me yasa ba kya sana'ar komai? Ko kinsan cewa kotu ba zata d'auki yaro ta baki haka kawai baki da abinda zaki rik'eshi?" Da sauri kuma kamar wacce ta tuno wani abu sai tace "Au! Yi hak'uri fa, na manta yaron yana da gara ashe." Kallon alk'ali tayi tace "Ya mai shari'a, ina neman alfarmar kotu ta gabatar min da malam Tagur?" Ba b'ata lokaci shima ya hallara gabanta, bata yarda ta kalli idonshi ba, dan sosai take jin ta takura sakamakon kallon da yake mata, saida ta tsaya gabanshi tace "Malam Tagur me yasa kake son karb'ar yaronka a hannun matar da kuka d'auki tsawon shekara shida a tare? Shin baka yarda da ita bane? Ko kuma baka so d'anka yayi nisa da kai ne?" Ajiyar zuciya ya sauke yace "Duka biyun." Kallonshi tayi tace "Duka biyun kamar ya? Ka fad'awa kotu dalla dalla." Lumshe ido sukayi a tare, hakan yasa sukayi saurin sakin sautin gyaran murya shima a tare "Egyhemm!" Da sauri suka kalli juna sai ita da tayi nasarar yin k'asa da nata idon, numfasawa ya sake yi yace "Ban yarda da kalar tarbiyar da zai samu a wajenta ba, sannan ina son ya zauna tare dani dan zaifi samun kulawa." Cikin motsa hannayenta da kwatance dasu tace "Shin akwai wani hali ne da take yi wanda kale ganin d'anka zai iya d'auka?" D'aga kai yayi alamar eh yace "Gaskiya ne." Jinjina kai tayi tace "Wane irin aiki kake?" Saida yayi k'ok'arin saka idonshi a nata yace "Ni d'an kasuwa, kuma d'an kwangila." Saita ta langab'ar da kai tace "Kana yawan tafiye tafiye ba?" D'aga kai yayi yace "Gaskiya ne?" "Kamar ina da ina kenan?" Ajiyar zuciya ya sauke yace "Kamar China, France, Africa ma ina zagayawa sosai." Matse baki tayi tace "Tsawon wane lokaci kake d'auka kafin ka dawo?" Iska ya feso yace "A k'alla wata d'aya ko sati uku." "Kasan yaronka na da asma chronique?" "Na sani, kuma ina bashi kulawar data dace ta b'angaren maganin daya dace dashi." Ajiyar zuciya ta sauke tace "Zan iya sanin rukunin jininka?" Kai tsaye yace "AB+." "Shin ka tab'a wata rashin lafiya data sa aka maka k'arin jini?" Girgiza kai yayi alamar a'a, jinjina kai tayi tace "Kenan baka tab'a doguwar jinyar data kwantar da kai ba?" Jim ya d'anyi kafin yace "Na tab'a yi, amma shima had'ari ne nayi a mota." Kallonshi tayi kamar kallon tana neman inda yaji ciwo tace "Wane lokaci ka d'auka a asibiti?" "A k'alla wata hud'u." "Duk tsawon lokacin ne su waye ke kula da kai? Ko kuma ba ka hayyacinka baka san me ke faruwa ba?" Girgiza kai yayi yace "Na sani, wanda suke tare dani kullum yan uwana ne sai kuma mahaifiyata, sai kuma abokina dake yawan zuwa duba ni." Jinjina kai tayi tace "A rahoton rashin lafiyar babu bayanin wani had'ari ko matsala?" Girgiza kai yayi yace "Gaskiya babu, da akwai kuma nasan da an bamu rahoton." Tarrr ta sauke ido cikin nashi da murmushi tace "Nagode, zaka iya zama." Kallon mai shari'a tayi ta sake neman alfarmar a gabatar mata da Hatimi, tana zuwa ta kasa d'auke ido a kanta ita mamaki ma take bata, sai kuma tsoronta da wani kwarjini da taji yarinyar ta mata, kamar ba ita ce yarinyar nan mai shekaru *sha hud'u* wacce suke ganin tayi k'ank'anta da zama matar d'ansu. Kusan tambaya akan had'arin da yayi ne ta mata har ta tambayeta "Kina nufin har ranar da za'a sallameku babu likitan daya buk'aci ya ga wani? Ko kuma ya bayar da wata takarda ko da ta siyan magani ko? Ko irin yace wani ya zo zai fad'a mishi yanda zaisha maganinshi?" Shiru tayi tana tunani sai kuma tayi saurin cewa "Na tuna, a ranar dai yace yana son ganin d'aya d'aga cikinmu da zasuyi magana, sai abokinshi *Omar* ya tafi tare da yar uwarshi Gomboy." Wani shegen murmushin ta saki jin ta kawo inda take son kawowa, kallonta tayi tace "Me ya fad'a musu kenan?" Girgoza kai tayi tace "A gaskiya babu wanda ya fad'a mana, dan suna fitowa ma Omar yace yaje ya siyo magani, gomboy kuma ta dawo da takardar sallamar." Cikin jin dad'i da tsaiko tace "Hakan na nufin Gomboy ce kad'ai zata iya fad'a mana me ya faru a d'akin ko?" Da sauri ta d'aga mata kai, da wani irin murmushi ta juyo ta kalli inda Gomboy ke zaune tuni jikinta ya d'auki ruwa sai zufa da take. Tana kallon alk'ali duk da ido suka yi zaurance magatakarda ya mik'e ya kirata, wani irin tari suka ji da k'arfi sosai hakan yasa duk wanda ke kotun aka juya inda aka ji tarin, Zaleeha ce ke wannan tari da iya k'arfinta kamar ta k'ware, duk'e kanta tayi cikin dubara ta rufe bakinta da gyale tace ma Hindu da Atta dake kusanta "Wallahi fita zanyi, wannan tonon asirin ba za'a yi shi dani ba na tsaya ana nuna ni ana cewa ni ce k'awarki, shegiyar yarinyar can saita tono mana wuk'ar yankanmu wallahi." Ganin Gomboy ta taso yasa Faduma juyawa tana kallon takardun dake gaban table d'in data tashi, sulalewa Zaleeha tayi ta k'asa ta fita babu wanda ya hanata. Kallon kallo akayi tsakanin gomboy da Faduma, takawa tayi a hankali hakan ya haifar da bayar da sautin takalminta k'was k'was har ta k'arasa gabanta, numfashi ta sauke tace "Malama gomboy ko?" D'aga kai tayi alamar eh, jinjina kai tayi ita ma tace "Ke ce a gaba da Tagur Sugui ko kuma shi ne a gaba dake?" Cikin nutsuwa tace "Ni ce babba, amma duka shekara na bashi." Jinjina kai tayi tace "Cikinku d'aya dashi?" Cikin had'e fuska tace "A'a, Abanmu ne d'aya, amma ni kamar ciki d'aya muka fito haka nake gani." Jinjina kai ta sake yi tace "Kina da aure ne?" "A'a." Yanda ta fad'i maganar da k'arfi zai tabbatarwa da mai sauraro ta hassala, bata damu ba sai d'orawa da tayi da "An ce kina d'aya daga cikik biyun kuka amsa kiran likita a waccen ranar, dan Allah zaki iya fad'a mana abinda kuka tattauna?" Kamar zata rufeta da duka ta kalleta tace "Shari'a ake akan yaro fa ba jin abinda ya shafi iyayen ba." Wani murmushi tayi tace "Amma yaron ba daga iyayen ya fito ba? Dole mu tabbatar da sahihancin lafiyarsu dan musan wanda ya dace ya rik'e shi." Cikin jin haushi ta kalleta tace "Kawai ya bamu shawarwari ne akan yanda zamu k'ara kula dashi, sai magunguna daya ruba Omar yaje ya siyo." D'an had'e fuska tayi tace " Malama Gomboy, ya kamata ki tabbatar duk abinda zai fito daga bakinki gaskiya kike fad'a." Cikin d'aga murya tace "Me kike nufi Faduma? Har yanzu kina jin haushi na ne?" Kallon mamaki ta mata tace "Akan me kike magana? Karki nemi canza mana maudi'unmu, kina bani amsa me kuka tattauna da likitan?" "Gaskiyar kenan." Ta fad'a tana d'auke kai daga kallonta, juyawa tayi wajen alk'ali tace "Ya mai girma mai shari'a abinda malama gomboy take fad'a a yanzun sam bai zo daidai da wanda shi likitan ya bamu rahoto ba, idan kotu ta min izini zan gabatar da rahoton lafiyar malam Tagur wanda na same shine a hannun likitan daya duba shi, wanda ba dan aiki ba ma na so ya zo kotun amma bai samu dama ba." Da hannu cikin dattako yace "Bismillah." Sunkuyawa tayi alamar girmamawa ta nufi gaban table d'in, d'aukar takardar tayi a jakar ordi. d'inta ta k'arasa kusa da magatakarda ta bashi, mik'ewa yayi shima ya juya ya ba alk'ali ya koma ya zauna, yana cikin duba takardar ita kuma cikin d'aga murya tace "Ya mai shari'a wannan rahoton yana d'auke da jinyar da yayi da kuma wata matsala da shi likitan ya fad'a mana sun d'auki tsawon wata biyu suna son shawo kanta amma Allah bai yi ba, daga k'arshe dole basu da wani zab'i daya wuce su fad'a musu abinda ke faruwa, gomboy tana daga cikin wanda likitan ya fad'a ma cewa sakamakon k'arfen daya sokeshi a mara ya tab'a wasu jijiyoyinshi da suke iya isar da maniyi zuwa inda ake buk'ata har ya shiga ta gaban mace ya isa mahaifa, hakan kuma yasa inhar ba wani ikon Allah ba to malam Tagur ba zai iya haihuwa ba har sai in k'asar waje ya fita, kuma a cikin bayanan daya bamu bai fad'a mana yayi wata jinya ba da har ya fita waje bayan kasuwancinshi." Sausauta murya tayi tace "Idan kotu na buk'ata zan iya samun lokacin likitan dan ya gabatar da kanshi da kuma tabbatarwa, amma a zahirin gaskiya wannan shine abinda ya faru, kuma yar uwarsa ta sani amma duk alamu sun nuna daga shi kanshi har mahaifiyarshi bata fad'a ma kowa ba, idan har zata sauk'ak'a mana to ya kamata ta gasgata abinda na fad'a da kuma rahoton nan, ba abinda muke magana akai bane bare mu tirsasa malama Atta ta fad'a mana Ridwan *d'an waye*, sai dai mun san malam Tagur ya barranta daga yaron nan Ridwan, baya da wata alak'a dashi ta nesa bare ta kusa." Ahiyar zuciya ta sauke tace "Nagode mai shari'a." Komawa tayi kan table d'in ta zauna, kururuwar da kotun ta d'auka yasa ta dafe gaban goshinta, wasu matasa ne daga can baya d'aya yace "A tirsasata ta fad'a mana d'an waye? Macuciya kawai." D'aya ne yace "Da tasan wuk'ar yankanta zata tono da bata kawo k'arar ba ai." Cikin tashin hankali da fitar hayyaci Atta ta daka ihu tana fad'in "K'arya ne, wallahi k'arya take sharri ta min d'an shi ne." Gomboy ma dake ta firfita da bakin mayafinta ne tace "Eh k'arya ta fad'a, saboda akwai wani abu tsakaninsu ne." Duk babu wanda ya ankara sai ganin Tagur sukayi ya shak'i wuyan Faduma ta baya da hannu biyu, mik'ewa tayi tana k'ok'arin b'amb'are hannayensa duk ta rufe idonta tana son yin tari amma ya shaketa sosai yana fad'in "Abinda ya faru tsakaninmu har yanzu baki manta ba shine zaki rama, kamar yanda na kunyata ki a waccen ranar shine ke ma zaki kunyata ni a bainar jama'a? D'ana na sunna da shi kad'ai nake da zaki nuna banda alak'a dashi ta nesa bare ta kusa? Za..." Lauyan Atta da magatakarda ne suka kama shi da k'yar suka rabashi da ita, da k'yar alk'ali ya samu suka nutsu akayi shiru bayan ya gama bubbuga table d'in gabanshi da guduma, saida wurin yayi shiru cikin fad'a alk'ali ya kalli Tagur dake ta huci yace "Abisa tozarta lauya da yi mana hauka a kotu zaka biya tara tare da kwana d'aya a gidan yari domin horo, dan a kiyaye gaba." Faduma da har yanzu hannunta ke kan wuya tana shafawa sai numfashi take saukewa, ita kam ba tayi mamaki ba dan tasan waye shi. Muryar alk'ali suka ji ya kalli Gomboy yace "Malama gomboy ga rahoton likita nan ya nuna abinda ta fad'a, shin da gaske ne haka ta faru?" Shiru tayi tana rarraba ido hakan yasa yace "Malama gomboy ki sani kotu bata lamuntar k'arya, za'a iya yafewa wanda yayi hargagi a kotu, sannan ana sauk'ak'a hukunci ga mai laifi idan har ya fad'i gaskiya ba tare da wahalar da kotu ba, amma yin k'arya babban laifi ne." Hannayenta ta had'e tana murzawa idonta cike da k'walla, cikin muryar kuka tace "Gaskiya ne, dan Allah kuyi hak'uri ku yafe min." Wani sabon hayaniyar ne ta tashi, saida ya bubbuga table aka yi shiru, Tagur ne ya kalleta har zaiyi magana sai kuma yayi shiru ya cije leb'e ya damk'e kujerar da yake zaune a kai, Hatimi tuni ta fara kuka tana salallami, daga baya Atta ta mik'e tace "Mai shari'a wallahi k'arya suke yi Ridwan d'ansa ne, Faduma ta fad'i hakane saboda tana kishi dani." Kallonta alk'ali yayi yace "Na k'arshe kenan da zaki sake magana kotu bata baki dama ba, koma ki zauna." Cikin jin haushi tace "To akan me zan zauna a b'ata min suna? K'azafi ta min saboda ita d'in karuwarsa ce har *d'a* ta haifa masa." Da sauri ta dafe kanta tace "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un." Mik'ewa tayi tsaye ta juya ta kalli Atta da tayi maganar, sai kuma taga ba anfanin biye mata ma a kotun kawai, komawa tayi ta zauna sai dai tuni Tagur ya koma kallonta. Duk yanda abun ake tunaninshi ya wuce nan, kamar kasuwa haka kotun ta zama kowa abinda ke ransa yake fad'a, alk'ali yayi bugun table d'in har ya gaji ya kallesu na d'an lokaci, saida ya ga abun baida niyyar k'arewa ya sake bugawa, da k'yar akayi shiru aka koma kallonshi, ganin lokacin yayi yasa alk'ali cewa "Kotu ba zata ja shari'ar nan ba, amma duk da haka ana buk'atar k'arin bayani daga bakin likitan, dan haka kotu ta d'aga wannan zama zuwa 11/10/20." *Yawan sharhi yawan rubutu* *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 17:08 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _9_ "Ayya, wai wa nake gani hakane? Kamar Faduma?" Ita ma cikin firgicin daya fi na Gomboy tace "Nima dai abinda nake gani kenan? Duba mana da kyau." K'anwarsa dake danna wayarta hankali kwance kallo d'aya ta mata tayi k'asa da kanta ta tana fad'in "Ita ce, baku ganeta bane ko me?" A tare suka kalleta sai dattijuwar da tace "Ke *Rahila* da gaske? Ya naga ta canza haka kamar ba ita ba?" Haushin tambayar yasa ta jan d'an guntun tsaki tace "To dama zata zauna nan ne babu ci gaba? Shekara nawa kukayi rabon da ku ganta." Muryar Tagur d'in ne ta katse musu maganar da cewa "Muje." Da sauri ta *Hatimi* ta kalleshi tace "Kai Tagur da gaske Faduma ce can na gani?" Saida ya bi inda ta nuna da kallo sannan ya kalleta yace "Eh Ayya, ita ce." Baki bud'e ta shiga jinjina kai tana fad'in "Lallai duniya, yanzu Faduma ce ta wuce ta gabanmu ko kallon arzik'i babu bare gaisuwa." Ajiyar zuciya ta sauke tana sake rik'e jakarta da kyau, Rahila ce tace "To Ayya me kika mata na alkairi da zaki samu wannan girmamawar daga gareta bayan rabuwarku?" A hassale ta kalleta tace "Ke bana son iskanci, ki rufe min bakinki kinji ko." Gomboy ce tace "Ki rabu da ita Ayya, kinsan dama ko acan ita yar tsagin Faduma ce ai, watak'ila asiri ta mata kuma har yanzu bai sake ta ba." Harara ta dalla mata tana fad'in "Aikin kenan, komai sai kince asiri, shikenan ke babu abinda ke iya tasiri a tare da d'an adam saida sihiri? Mtssss!" A hassale tayi kanta kamar zata kai mata duka tana fad'in "In ban ci uban..." Bata k'arasa ba saboda kallon da Tagur ya musu, duk da a gaba take dashi da shekara d'aya, amma kasantuwarshi ya amsa sunan namiji yasa bata haye mishi, tana shakkarshi yana mata kwarjini sosai kamar shi ke gaba da ita, jinjina kai tayi tana jan k'wafa tayi baya tana hararenta. Kallonshi ya mayar kan Rahila yace "Kar na sake jin bakinki a wurin nan, marar kunya kawai." Hatimi ce tace "To me ya kawota nan?" Saida ya tunkari shiga yace "Ni na d'aukota aiki." Da mamaki suka shiga kallon juna, suna son k'arin bayani amma babu mai basu. Wuce yayi suka rufa masa baya sai Hatimi data rik'e hannun Gomboy tana fad'in "Kiyi hak'uri ki k'yaleta har kuje gida, da kaina zan baki tsumagiya ki zaneta." Ba tace komai ba sai kumburo baki da take, ita kuma Hatimi fushin nata ne bata son gani, 'ya'yan kishiyarta ne data rasu ta barsu a hannunta, su biyar ne duka mata Tagur kad'ai ke namiji, da yake Gomboy ce ta tashi a hannunta shiyasa tafi sonta a cikin yaran, tafi shak'uwa da ita fiye da yanda ta shak'u da nata yaron data haifa a cikinta. Suna daf da shiga taji an kira sunanta da "Trozzonur (K'awata)." Da sauri ta waiga b'angaren da taji muryar Atta, da sauri ta k'arasa da murnar ganinsu, tana k'arasawa ta kallesu tace "Trozzonur har kun iso kenan?" Saida Atta ta kalli Hatimi da ita ma take kallonta da mamakin fitsararta yanda take kallonta cikin ido, ko ba komai dai a tsakaninsu yanzu ai ta auri d'anta, amma wai tana kallonta ido cikin ido babu gaisuwa, tab'e baki Hatimi tayi ta shige, hararar da Atta ta banka mata tana jan tsaki Rahila ta gani, zata nufi kanta cike da masifa Hatimi ta juyo tace "Ke muje." Juyawa tayi ta kalleta hakan yasa ta jinjina kai tana cije leb'e, amma ta sani bashi ta ci kuma zata biya. Kallon Gomboy tayi tace "To me zamu jira?" Zaleeha ce tace "Amma sai naga shegiyar lauyar can a gabanku, ina fata dai ba tare da ita kuke ba?" Juyawa tayi ta kalli k'ofar shiga sannan ta sake kallon Zaleeha tace "Wai Faduma kike nufi?" Hindu ce tace "Kin ma santa kenan?" Da murmushi a fuskarta tace "Na santa kuma? Farin sani ma." Kallon Atta tayi tana yamutsa fuska tace "Ai tsohuwar budurwar mijinki ce wacce ya so aura suka rabu." Duk zaro ido sukayi suka kalleta, baki hard'ewa Zaleeha tace "Tagur dai?" D'aga mata gira tayi alamar eh, tab'e baki Hindu tayi tace "Humm-umm! Da gaske wai ko wasa?" Had'e gira tayi tace "Ya zan muku wasa a yanzu? Kunga ku zo mu shiga." Da sauri Atta ta rik'e hannunta tana fad'in "Ke tsaya dallah, da gaske wai ita wacce naji ana fad'a sunyi soyayya har an saka musu rana?" Cike da tabbaci tace "Wallahi ita ce, Faduma ba." Zaleeha ce tace "Yo me yasa bai aureta ba?" Sake tab'e baki tayi tace "Ke sharri fa ta masa, cewa tayi tana da ciki har da kawo iyayenta gidanmu, shi kuma yace bai yarda ba k'arya ta masa, shine aka fasa auren kowa ya kama gabansa." "La'ilaha illalahu, Muhammad rasulullih sallalahu alaihi wasallam." Atta da Hindu suka fad'a a tare, Hindu ce ta d'ora da fad'in "Shi d'in ne yace k'arya ce?" D'aga kai tayi tana kallon Atta da ita ma ta jefo mata magana da cewa"Shima ashe d'an iska ne shine harda cewa wani wai ya gane ni yar iska ce? Amma dai wallahi baya da mutumci." Tsaki tayi tace "Kunga ku zo muje dan Allah." Ta fad'a tana wucewa, har Atta zata bi bayanta Hindu ta rik'o hannunta tana fad'in "Ke tsaya." Tsayawa sukayi suna kallonta, cikin rad'a tace "Nifa ina tunanin anya kuwa yaron nan na Faduma ba shine d'an data haifa ba." Zaro ido Zaleeha tayi sai kuma ta k'ank'ancesu tace "Kuma fa biri yayi kama da mutum, tabbas zai iya yiwu wa, duba da ai ba yanzu bane abun ya faru." Jinjina kai Atta tayi tace "Ashe haukan banza nake, ina ganin na hifi yaron da zai cinye dukiyarshi, ashe yana can da gabjejen yaro wanda ya haifa a yawon ta-zubar d'inshi." Cike da masifa Zaleeha tace "Kai amma maza bakuyi ba wallahi." Kama hannunsu Hindu tayi suka shiga ciki tana fad'in "Dama sun fad'a miki sunyi ne? Ai mu dasu kallon kallo ne, k'iris ya rage mu fara musu jifar shed'an." Kowa ya samu wuri ya zauna shigowar alk'ali ake jira, duk hangenta suke ita yi duk da yanzu ta cire lafayarta ta d'ora rigarta ta lauyoyi da hularta, hayaniya ake tayi ko da alk'ali ya shigo ta k'ofar gabansu duk aka mik'e dan girmamawa, saida ya zauna kowa ya koma ya zauna ana kama jiki tare da yin shiru. Magatakarda ne ya fara aikinsa ta hanyar shelanta rana mai k'ara da wanda ake k'arar, alk'ali ne ya bayar da izinin lauyoyi su gabatar da kansu, namijin ne ya fara gabatar da kanshi kafin Faduma. Shi aka ba dama ya fara gabatar da abinda kenan, saida ya kira Tagur ya masa tambayoyi kafin ya nunawa kotu yaron ya cancanci ya zauna wajen mahaifiyarsa duba da k'arami ne wanda komai sai an masa. Saida ya gama alk'ali ya bata dama ita ma ta mik'e, hannayenta a had'e tana mummurzasu ta kalli alk'ali tace "Ya mai shari'a ina neman alfarmar kotu data gabatar min da malama Atta?" Coke da dattako yace "Kotu ta baki dama." Magatakarda ne ya mik'e yace "Malama Atta Angr Shilli ta fito." Mik'ewa tayi ta isa inda ake tsayawa ta tsaya tana kallonta, cikin yatsina fuska da dubara ta tab'e baki a ranta tace "Hummm!" Maysawa tayi kusanta tace "Malama Atta lafiyarki k'alau?" Cikin jin haushin tambayar ta harareta ta wutsiyar ido tace "Eh, k'alau nake." Lumshe ido tayi ta d'ora da cewa "A gidanku nawa ke rayuwa?" Idonta cikin nata tace "Mu biyar ne, ni da mama da baba na sai yayuna biyu maza." Da murmushi tace "Kina aiki ne na gwamnati ko wata sana'a?" Kai tsaye tace "Bana yi?" D'an sosa gaban goshinta tayi tace "D'anki Ridwan lafiyarsa k'alau?" A hankali tace "A'a, yana da asma." Jinjina kai tayi tana wani murmushin mugunta tace "Malama Atta kinsan da cewa me yasa ba kya sana'ar komai? Ko kinsan cewa kotu ba zata d'auki yaro ta baki haka kawai baki da abinda zaki rik'eshi?" Da sauri kuma kamar wacce ta tuno wani abu sai tace "Au! Yi hak'uri fa, na manta yaron yana da gara ashe." Kallon alk'ali tayi tace "Ya mai shari'a, ina neman alfarmar kotu ta gabatar min da malam Tagur?" Ba b'ata lokaci shima ya hallara gabanta, bata yarda ta kalli idonshi ba, dan sosai take jin ta takura sakamakon kallon da yake mata, saida ta tsaya gabanshi tace "Malam Tagur me yasa kake son karb'ar yaronka a hannun matar da kuka d'auki tsawon shekara shida a tare? Shin baka yarda da ita bane? Ko kuma baka so d'anka yayi nisa da kai ne?" Ajiyar zuciya ya sauke yace "Duka biyun." Kallonshi tayi tace "Duka biyun kamar ya? Ka fad'awa kotu dalla dalla." Lumshe ido sukayi a tare, hakan yasa sukayi saurin sakin sautin gyaran murya shima a tare "Egyhemm!" Da sauri suka kalli juna sai ita da tayi nasarar yin k'asa da nata idon, numfasawa ya sake yi yace "Ban yarda da kalar tarbiyar da zai samu a wajenta ba, sannan ina son ya zauna tare dani dan zaifi samun kulawa." Cikin motsa hannayenta da kwatance dasu tace "Shin akwai wani hali ne da take yi wanda kale ganin d'anka zai iya d'auka?" D'aga kai yayi alamar eh yace "Gaskiya ne." Jinjina kai tayi tace "Wane irin aiki kake?" Saida yayi k'ok'arin saka idonshi a nata yace "Ni d'an kasuwa, kuma d'an kwangila." Saita ta langab'ar da kai tace "Kana yawan tafiye tafiye ba?" D'aga kai yayi yace "Gaskiya ne?" "Kamar ina da ina kenan?" Ajiyar zuciya ya sauke yace "Kamar China, France, Africa ma ina zagayawa sosai." Matse baki tayi tace "Tsawon wane lokaci kake d'auka kafin ka dawo?" Iska ya feso yace "A k'alla wata d'aya ko sati uku." "Kasan yaronka na da asma chronique?" "Na sani, kuma ina bashi kulawar data dace ta b'angaren maganin daya dace dashi." Ajiyar zuciya ta sauke tace "Zan iya sanin rukunin jininka?" Kai tsaye yace "AB+." "Shin ka tab'a wata rashin lafiya data sa aka maka k'arin jini?" Girgiza kai yayi alamar a'a, jinjina kai tayi tace "Kenan baka tab'a doguwar jinyar data kwantar da kai ba?" Jim ya d'anyi kafin yace "Na tab'a yi, amma shima had'ari ne nayi a mota." Kallonshi tayi kamar kallon tana neman inda yaji ciwo tace "Wane lokaci ka d'auka a asibiti?" "A k'alla wata hud'u." "Duk tsawon lokacin ne su waye ke kula da kai? Ko kuma ba ka hayyacinka baka san me ke faruwa ba?" Girgiza kai yayi yace "Na sani, wanda suke tare dani kullum yan uwana ne sai kuma mahaifiyata, sai kuma abokina dake yawan zuwa duba ni." Jinjina kai tayi tace "A rahoton rashin lafiyar babu bayanin wani had'ari ko matsala?" Girgiza kai yayi yace "Gaskiya babu, da akwai kuma nasan da an bamu rahoton." Tarrr ta sauke ido cikin nashi da murmushi tace "Nagode, zaka iya zama." Kallon mai shari'a tayi ta sake neman alfarmar a gabatar mata da Hatimi, tana zuwa ta kasa d'auke ido a kanta ita mamaki ma take bata, sai kuma tsoronta da wani kwarjini da taji yarinyar ta mata, kamar ba ita ce yarinyar nan mai shekaru *sha hud'u* wacce suke ganin tayi k'ank'anta da zama matar d'ansu. Kusan tambaya akan had'arin da yayi ne ta mata har ta tambayeta "Kina nufin har ranar da za'a sallameku babu likitan daya buk'aci ya ga wani? Ko kuma ya bayar da wata takarda ko da ta siyan magani ko? Ko irin yace wani ya zo zai fad'a mishi yanda zaisha maganinshi?" Shiru tayi tana tunani sai kuma tayi saurin cewa "Na tuna, a ranar dai yace yana son ganin d'aya d'aga cikinmu da zasuyi magana, sai abokinshi *Omar* ya tafi tare da yar uwarshi Gomboy." Wani shegen murmushin ta saki jin ta kawo inda take son kawowa, kallonta tayi tace "Me ya fad'a musu kenan?" Girgoza kai tayi tace "A gaskiya babu wanda ya fad'a mana, dan suna fitowa ma Omar yace yaje ya siyo magani, gomboy kuma ta dawo da takardar sallamar." Cikin jin dad'i da tsaiko tace "Hakan na nufin Gomboy ce kad'ai zata iya fad'a mana me ya faru a d'akin ko?" Da sauri ta d'aga mata kai, da wani irin murmushi ta juyo ta kalli inda Gomboy ke zaune tuni jikinta ya d'auki ruwa sai zufa da take. Tana kallon alk'ali duk da ido suka yi zaurance magatakarda ya mik'e ya kirata, wani irin tari suka ji da k'arfi sosai hakan yasa duk wanda ke kotun aka juya inda aka ji tarin, Zaleeha ce ke wannan tari da iya k'arfinta kamar ta k'ware, duk'e kanta tayi cikin dubara ta rufe bakinta da gyale tace ma Hindu da Atta dake kusanta "Wallahi fita zanyi, wannan tonon asirin ba za'a yi shi dani ba na tsaya ana nuna ni ana cewa ni ce k'awarki, shegiyar yarinyar can saita tono mana wuk'ar yankanmu wallahi." Ganin Gomboy ta taso yasa Faduma juyawa tana kallon takardun dake gaban table d'in data tashi, sulalewa Zaleeha tayi ta k'asa ta fita babu wanda ya hanata. Kallon kallo akayi tsakanin gomboy da Faduma, takawa tayi a hankali hakan ya haifar da bayar da sautin takalminta k'was k'was har ta k'arasa gabanta, numfashi ta sauke tace "Malama gomboy ko?" D'aga kai tayi alamar eh, jinjina kai tayi ita ma tace "Ke ce a gaba da Tagur Sugui ko kuma shi ne a gaba dake?" Cikin nutsuwa tace "Ni ce babba, amma duka shekara na bashi." Jinjina kai tayi tace "Cikinku d'aya dashi?" Cikin had'e fuska tace "A'a, Abanmu ne d'aya, amma ni kamar ciki d'aya muka fito haka nake gani." Jinjina kai ta sake yi tace "Kina da aure ne?" "A'a." Yanda ta fad'i maganar da k'arfi zai tabbatarwa da mai sauraro ta hassala, bata damu ba sai d'orawa da tayi da "An ce kina d'aya daga cikik biyun kuka amsa kiran likita a waccen ranar, dan Allah zaki iya fad'a mana abinda kuka tattauna?" Kamar zata rufeta da duka ta kalleta tace "Shari'a ake akan yaro fa ba jin abinda ya shafi iyayen ba." Wani murmushi tayi tace "Amma yaron ba daga iyayen ya fito ba? Dole mu tabbatar da sahihancin lafiyarsu dan musan wanda ya dace ya rik'e shi." Cikin jin haushi ta kalleta tace "Kawai ya bamu shawarwari ne akan yanda zamu k'ara kula dashi, sai magunguna daya ruba Omar yaje ya siyo." D'an had'e fuska tayi tace " Malama Gomboy, ya kamata ki tabbatar duk abinda zai fito daga bakinki gaskiya kike fad'a." Cikin d'aga murya tace "Me kike nufi Faduma? Har yanzu kina jin haushi na ne?" Kallon mamaki ta mata tace "Akan me kike magana? Karki nemi canza mana maudi'unmu, kina bani amsa me kuka tattauna da likitan?" "Gaskiyar kenan." Ta fad'a tana d'auke kai daga kallonta, juyawa tayi wajen alk'ali tace "Ya mai girma mai shari'a abinda malama gomboy take fad'a a yanzun sam bai zo daidai da wanda shi likitan ya bamu rahoto ba, idan kotu ta min izini zan gabatar da rahoton lafiyar malam Tagur wanda na same shine a hannun likitan daya duba shi, wanda ba dan aiki ba ma na so ya zo kotun amma bai samu dama ba." Da hannu cikin dattako yace "Bismillah." Sunkuyawa tayi alamar girmamawa ta nufi gaban table d'in, d'aukar takardar tayi a jakar ordi. d'inta ta k'arasa kusa da magatakarda ta bashi, mik'ewa yayi shima ya juya ya ba alk'ali ya koma ya zauna, yana cikin duba takardar ita kuma cikin d'aga murya tace "Ya mai shari'a wannan rahoton yana d'auke da jinyar da yayi da kuma wata matsala da shi likitan ya fad'a mana sun d'auki tsawon wata biyu suna son shawo kanta amma Allah bai yi ba, daga k'arshe dole basu da wani zab'i daya wuce su fad'a musu abinda ke faruwa, gomboy tana daga cikin wanda likitan ya fad'a ma cewa sakamakon k'arfen daya sokeshi a mara ya tab'a wasu jijiyoyinshi da suke iya isar da maniyi zuwa inda ake buk'ata har ya shiga ta gaban mace ya isa mahaifa, hakan kuma yasa inhar ba wani ikon Allah ba to malam Tagur ba zai iya haihuwa ba har sai in k'asar waje ya fita, kuma a cikin bayanan daya bamu bai fad'a mana yayi wata jinya ba da har ya fita waje bayan kasuwancinshi." Sausauta murya tayi tace "Idan kotu na buk'ata zan iya samun lokacin likitan dan ya gabatar da kanshi da kuma tabbatarwa, amma a zahirin gaskiya wannan shine abinda ya faru, kuma yar uwarsa ta sani amma duk alamu sun nuna daga shi kanshi har mahaifiyarshi bata fad'a ma kowa ba, idan har zata sauk'ak'a mana to ya kamata ta gasgata abinda na fad'a da kuma rahoton nan, ba abinda muke magana akai bane bare mu tirsasa malama Atta ta fad'a mana Ridwan *d'an waye*, sai dai mun san malam Tagur ya barranta daga yaron nan Ridwan, baya da wata alak'a dashi ta nesa bare ta kusa." Ahiyar zuciya ta sauke tace "Nagode mai shari'a." Komawa tayi kan table d'in ta zauna, kururuwar da kotun ta d'auka yasa ta dafe gaban goshinta, wasu matasa ne daga can baya d'aya yace "A tirsasata ta fad'a mana d'an waye? Macuciya kawai." D'aya ne yace "Da tasan wuk'ar yankanta zata tono da bata kawo k'arar ba ai." Cikin tashin hankali da fitar hayyaci Atta ta daka ihu tana fad'in "K'arya ne, wallahi k'arya take sharri ta min d'an shi ne." Gomboy ma dake ta firfita da bakin mayafinta ne tace "Eh k'arya ta fad'a, saboda akwai wani abu tsakaninsu ne." Duk babu wanda ya ankara sai ganin Tagur sukayi ya shak'i wuyan Faduma ta baya da hannu biyu, mik'ewa tayi tana k'ok'arin b'amb'are hannayensa duk ta rufe idonta tana son yin tari amma ya shaketa sosai yana fad'in "Abinda ya faru tsakaninmu har yanzu baki manta ba shine zaki rama, kamar yanda na kunyata ki a waccen ranar shine ke ma zaki kunyata ni a bainar jama'a? D'ana na sunna da shi kad'ai nake da zaki nuna banda alak'a dashi ta nesa bare ta kusa? Za..." Lauyan Atta da magatakarda ne suka kama shi da k'yar suka rabashi da ita, da k'yar alk'ali ya samu suka nutsu akayi shiru bayan ya gama bubbuga table d'in gabanshi da guduma, saida wurin yayi shiru cikin fad'a alk'ali ya kalli Tagur dake ta huci yace "Abisa tozarta lauya da yi mana hauka a kotu zaka biya tara tare da kwana d'aya a gidan yari domin horo, dan a kiyaye gaba." Faduma da har yanzu hannunta ke kan wuya tana shafawa sai numfashi take saukewa, ita kam ba tayi mamaki ba dan tasan waye shi. Muryar alk'ali suka ji ya kalli Gomboy yace "Malama gomboy ga rahoton likita nan ya nuna abinda ta fad'a, shin da gaske ne haka ta faru?" Shiru tayi tana rarraba ido hakan yasa yace "Malama gomboy ki sani kotu bata lamuntar k'arya, za'a iya yafewa wanda yayi hargagi a kotu, sannan ana sauk'ak'a hukunci ga mai laifi idan har ya fad'i gaskiya ba tare da wahalar da kotu ba, amma yin k'arya babban laifi ne." Hannayenta ta had'e tana murzawa idonta cike da k'walla, cikin muryar kuka tace "Gaskiya ne, dan Allah kuyi hak'uri ku yafe min." Wani sabon hayaniyar ne ta tashi, saida ya bubbuga table aka yi shiru, Tagur ne ya kalleta har zaiyi magana sai kuma yayi shiru ya cije leb'e ya damk'e kujerar da yake zaune a kai, Hatimi tuni ta fara kuka tana salallami, daga baya Atta ta mik'e tace "Mai shari'a wallahi k'arya suke yi Ridwan d'ansa ne, Faduma ta fad'i hakane saboda tana kishi dani." Kallonta alk'ali yayi yace "Na k'arshe kenan da zaki sake magana kotu bata baki dama ba, koma ki zauna." Cikin jin haushi tace "To akan me zan zauna a b'ata min suna? K'azafi ta min saboda ita d'in karuwarsa ce har *d'a* ta haifa masa." Da sauri ta dafe kanta tace "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un." Mik'ewa tayi tsaye ta juya ta kalli Atta da tayi maganar, sai kuma taga ba anfanin biye mata ma a kotun kawai, komawa tayi ta zauna sai dai tuni Tagur ya koma kallonta. Duk yanda abun ake tunaninshi ya wuce nan, kamar kasuwa haka kotun ta zama kowa abinda ke ransa yake fad'a, alk'ali yayi bugun table d'in har ya gaji ya kallesu na d'an lokaci, saida ya ga abun baida niyyar k'arewa ya sake bugawa, da k'yar akayi shiru aka koma kallonshi, ganin lokacin yayi yasa alk'ali cewa "Kotu ba zata ja shari'ar nan ba, amma duk da haka ana buk'atar k'arin bayani daga bakin likitan, dan haka kotu ta d'aga wannan zama zuwa 11/10/20." *Yawan sharhi yawan rubutu* *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 17:08 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _10_ Kamar jiran fitar alk'ali ake aka sake kaurewa da maganganu kowa murya sama, Gomboy ce tayo kan Faduma kamar wata damisa da niyyar damk'arta, da sauri jami'in dake wurin ya shiga tsakiyarsu yana tare ta da hannu, mik'ewa Faduma tayi ta tattara kayanta, wata fizgowa ya mata ya rik'e hannunta gam ya nufi hanyar fita da ita, tana mutsumutsun k'watar kanta kuma jami'in yayi saurin tunkararshi yasha gabanshi, cikin had'e fuska ya nuna mishi wata k'ofa yace "Muje yallab'ai zaka biya tararka, daga nan zamu wuce da kai dan fuskantar hukuncin da kotu ta yanke maka." Cike da gadara da raini yace "Minti biyu, ina so zanyi magana da ita ne." Girgiza mishi kai yayi yana d'ora hannu akan bindigarshi yace "Baka da wannan damar, muje yallab'ai." Da wani irin k'arfi ya tura Faduma ga bangon wurin ba tare daya saki hannunta ba, d'ora d'aya hannunshi yayi akan bangon shima ya k'urawa fuskarta ido, idonshi da sukayi jawur ta kalla tana sauke numfashi wani na bin wani, a hankali cikin amon muryar b'acin rai yace "Ina *d'ana* yake?" K'asa tayi da idonta hakan yasa hawaye silalowa, saida ta sake sauke numfashi tana rarraba ido tace "Ban san shi ba nima, bana da d'a tare da kai, sake min hannu na." A hankali ya sake cewa "Na biyu kenan zan sake tambayarki, karki bari nayi na uku Faduma, ina oddonur na yake?" Saida ta rintse idonta cikin fashewa da kuka tace "Ban sani ba Tagur, ni babu wani d'anka a wajena, ka rabu dani na tafiyata." Wani duka ya kaiwa bangon daya d'ora hannunshi da k'arfi da wata irin k'arajin murya kamar zai fasa wurin yace "Zaki gaya min inda d'ana yake ko saina kasheki a wurin nan? Ya zaki raina min hankali? Ni abokin wasanki nn..." Bai k'arasa fad'a ba Faduma cikin tsoro da zabura akan tsawar daya mata da kuma tafasar zuciya ta d'auke fuskarshi da mari, bata bari ya gama tantance me ya faru ba cikin k'arajin murya ita ma har tana shak'ewa tace "Karka sake, kar bakinka ya sake kiran sunan d'ana da d'anka." Numfashi ta shiga jerawa kamar wacce tayi gudu tana kallon idonshi kamar yanda shima yake kallon nata da mamaki. Duk wurin tsit ya d'auka dan babu wanda ya fita duk an tsaya kallon drama, su Atta ma dake can suna nasu fad'an ita da gomboy dole suka dakata jin k'arar mari. Idonta jawur tana zubar da hawaye ta nunashi da yatsa manuniya tace "Karka sake kuskuren dangata kanka dashi, baka da alak'a dashi Tagur, kamar yanda na fad'a mishi ka mutu kaima ka d'auka ya mutu dan dama babu shi a wurinka, sannan karka sake d'aga min murya dan yanzu ba Fadu daka sani bace." Ko da ta fad'a tasa k'arfi ta ture hannunshi da har yanzu yake jikin bangon ta fita, rintse ido yayi yana jin yanda zuciyarshi ke tafasa, sake dukan bangon yayi ya juya har zai fita sai kuma jami'in ya mishi nuna da d'aya d'akin, da k'arfi ya juya ya wuce shima ya bi bayanshi. A b'angaren su Atta ma fad'a suke sosai ita da Gomboy tana fad'in "Dama kin min shiru ne dan haka ta faru, to yanzu kinji dad'i? Yar bak'in ciki kawai." Tab'e baki tayi tace "Ai ba ni na aikeki yawon iskancin ba, da kin zauna d'akin mijinki ai da haka bata faru ba." Cikin masifa tace "Ke har ni zaki kalla ki fad'a ma haka? Ba gwara ni ba nayi auren ma, ke fa? Kuma naga dani dake ai duk kanwar ja ce." "Eh naji banyi aure ba, amma da aure irin naki gwara na tabbata babu aure, auren da zan dinga zina da aure na wallahi gwara banyi shi ba." Hindu ce ta dakatar dasu da fad'in "Ya isa dan Allah, tsaya kuji." Shiru sukayi sai huci suke suna kallon juna, a hankali tace "Kunga ba fad'a zakuyi ba, mafita zamu nema da zamu lalata shedar da aka kawo yau, kunsan miye abunyi?" Girgiza kai sukayi dan haka tace "Mu nemi likitan, kud'i yake so ko jin dad'i duka zamu iya bashi, indai zai juya mana shaidar da aka gabatar yau d'in nan." Cike da kurantawa Zaleeha tace "Sai ke uwar d'akina, wannan yayi." Kallon Gomboy tayi tace "Ke kika sanshi, zamu je mu nemi rendez vous dashi, zamu sauya mishi tunani." Jinjina kai gomboy tayi tace "Naji wannan, yanzu yanda zan fuskanci yan gida ne matsalar." Hindu ce ta tab'e baki tace "Ke rabu dasu, murje ido zakiyi ki darzawa duk wanda ya nemi yaga miki rigar mutumci, dama can ai farin ki suke gani basu san bak'inki ba, karki sa matsalarsu a kan ki kinji." Jinjina kai tayi kafin suka rankaya suma suka fita. _______________ Yana k'arasa shiga cikin makarantar ashe an sallami yaran nan sakamakon d'aya daga cikin malaman daya rasu, shiyasa aka ce duk su koma gida sai gobe tunda dama yau ba'a karatu da yamma, cike da damuwa ya samu wuri ya zauna yana kallon masu fita, baisan ya zaiyi yanzu Ayyarshi ta dawo ba, littafinshi ya fiddo zai fara karatu sai yaji wata yarinya a bayanshi na fad'in "Kai ba zaka tafi gida ba?" Juyawa yayi ya kalleta, sai yaji kawai gabanshi ya fad'i dan haka ya k'yaleta ya koma karatunshi, matsowa tayi ta zauna kusanshi tana sake fad'in "Ka tashi ka tafi gida, ko d'aukarka ake zuwa kaima?" Kallonta ya sake yi, ita ma kallonshi tayi sosai ita dai tana ganin fuskar kawunta a fuskar yaron, amma k'uruciya ta hana ta gane kama ne suke, a hankali yace mata "D'aukata ake zuwa." Cike da wayo tace "To yanzu wa zai zo d'aukarka? Kaga babu wanda yasan ba za ayi karatu ba." Kallonta yayi yace "Shiyasa na zauna na jira Ayyata." "Amma ai zaka jima anan, ko zaka bini gidanmu?" Kallonta yayi kamar wani babba yace "Me yasa? Ban sanki ba fa." Murmushi ta masa ta nuna masa class d'in dake kusa da tasu tace "Ga class d'inmu nan, sunana *Khairat Aji Sugui*." Da mamaki ya sake kallonta yana murmushi yace "Lah, sunan kakanmu d'aya, ni kuma ga class d'inmu nan, sunana *Amjad Tagur Sugui*, ke ma Abanki batube ne?" Juya harshenta tayi cikin tubanci tace "A'a, Ayyata ce, gaskiya naji dad'i, zaka bini gidanmu?" Jim yayi sai kuma yace "Ayyata ta hana ni tsallaka ko da titi ne idan ba ita ta zo ba, bana so na b'ata mata rai." Cike da yarinta tace "Me yasa Abanka shi baya zuwa d'aukarka?" Da sauri ya girgiza kai bai ce komai ba, mik'ewa tayi tana gyara zaman jakarta a bayanta tace "Kaga ina da kud'i, kuma basu da yawa bare mu raba kowa yaje gida, amma ka zo muje gidanmu in muka je sai driver ya kaika gida, amma karka zauna anan kai kad'ai kaji." Kallonta yayi yana jujjuya kalamanta, shawara ce mai kyau ta bashi kam, jinjina kai yayi ya mayar da littafinshi a jaka ya goya ya tashi, a hankali suke tafiya suna hirarsu ta yara har suka k'arasa bakin k'ofa, mai gadi na ganinsu yace "Ina zaku ba'a zo d'aukarku ba?" Amjad ne yace "Obdo (kawu) adaidaita zamu shiga mu koma, idan naje gida zan kira Ayya saina fad'a mata na koma gida." "Ka tabbata?" Cewar mai gadi, d'aga masa kai yayi alamar eh, hannunsu ya kama duka yace "Muje to na tsayar muku da mai adaidaitar." Bakin titi suka k'arasa suka samu adaidaita, saida suka shiga yaga tafiyarsu sannan ya koma bakin k'ofa. Sun d'an jima a hanya dan can nesa suke, a k'ofar gidan da suka rsaya yasa Amjad kallon gidan gabanshi na fad'uwa, gidan ya had'u k'arshen had'uwa, suna shiga ciki b'angare biyu ne sai wata k'ofa kuma da zaka bi ka isa wani falon mai zaman kansa, shiga sukayi inda Amjad ke ta doka sallama har suka shiga falon. Ita kad'ai ce a gidan da alama bayan mai gadi da suka wuce da wani mutum na wanki, ganinsu yasa ta zaro ido tana fad'in "Khairat, ya na ganki kuma? Ba'a karatun ne?" Cire kallabin kanta tayi ta cire jakar ta jefar a k'asa ta k'arasa gareta tace "Ba ayi Ayya, shiyasa muka dawo." Sunkuyawa Amjad yayi ya d'auke jakarta da kallabin ya aje saman kujera ya kalli matar, ba zata wuce tsarar mahaifiyarsa ba, sai kawai ya zauna k'asa yana fad'in "Legye?" Da sauri ta kalleshi da mamaki, kallon Khairat tayi tace "Khairat waye wannan? D'an makarantarku ne shima na ganshi da tenue (uniforme)?" D'aga kai tayi ta nufi wajen fridge dan d'aukar ruwa, kallon Amjad ta sake yi tace "Lagye?" Cernuma wuna (me ye sunanka)?" Da murmushi cike da kunya yace "Amjad." Kallon kayan Khairat tayi daya d'auke mata, kallon Khairat tayi dake d'aukar ruwa tace "Kinga yanda ake yi ko? Abinda nake fama dake kenan kullum." Kallon matar yayi yana murmushi yace "Dada, idan kina so ta gyara ta dinga d'aukewa ki daina d'auke mata, wani lokacin ma ki takasu da k'afarki zaki ga taji zafi ta d'auke, to gobe ko ta jefar zata dawo ta d'auke dan kar a taka mata kaya." Da wani tsadadden murmushi ta tara masa hannu tace "Zo nan Amjad." Mik'ewa yayi yaje gareta yana shirin sunkuyawa ta rik'eshi, rumgumashi tayi a jikinta tace "Ka koyar dani darasin da zan bi da yarinyar nan, ina mamanka?" Saida ya sauke ajiyar zuciya saboda k'amshin turarenta daya shak'a kafin yace "Dole yanzu Ayyata tana kotu." Waro ido tayi tace "Ayyanka lauya ce?" D'aga kai yayi alamar eh, jinjina kai tayi ta sake shi tana fad'in "Bari na samo maka abinci ko." Da sauri ya girgiza kai yace "A'a Dada, na k'oshi ai bana jin yunwa." Jinjina kai tayi tace "Shikenan, amma anjima zaka ci." Da sauri ya kalleta yace "A'a Dada, ina so na koma gida dan na kira Ayyata na fad'a mata ina gida, yau na mata laifi dole na nemi afuwarta, bata so ina fita daga cikin makaranta, amma yau gashi na fito har na zo wani wuri." Kallon k'auna ta ma yaron, ko ma wacece mahaifiyarshi tasan tayi k'ok'ari wajen tarbiyarshi, taji tana son sanin mamanshi har tayi k'awance da ita, ko ba komai zata k'aru dan alamu ya nuna mutuniyar kirki ce, wayarta ta d'auka tace "Kira Ayyaka saika fad'a mata." Girgiza kai yayi yace "Dada ina kira da lambar da bata sani ba kuma taji muryata, ba zata tsaya saurare na ba zata shiga tambayata, hankalinta zai tashi saboda bata da kowa sai ni." Murmushi tayi tace "Idan na fahimta dai yaron nan yana matuk'ar son mamanshi." Dariya yayi yace "Fiye da yanda take so na." Hararan wasa ta mishi tace "Anya kuwa zaka so ta fiye da yanda take son ka?" Kallonta yayi yace "Zan iya mana, ita nake gani kullum, da ita na bud'e idona kuma da ita nake gauraya numfashi na kullum." Kallon Khairat tayi dake dhan ruwa tace "Ke baki iya bawa bak'o ruwa ba?" Mik'ewa tayi ta d'auko mishi ta kawo tana fad'in "Ayya ina su Haja?" A tak'aice tace "Suna justice (kotu)" Juyowa tayi daga can tace "Ayya saida suka tafi? Har da kawu ma?" "Har dashi mana, ai shine gayyar tafiyar ma." Da sauri ta dawo a tare data d'auko ruwan ba ta zo ta kama hannun Amjad tana fad'in "Yawwa fad'awa Ayyata sunanka da sunan Abanka, Ayya bari kiji sunanshi." Duk ido suka zuba mishi, rarraba ido ya fara yi shi kuma saida *Aisha* tace "Fad'a min naji." A hankali cikin rawar murya yace "Amjad Tag..ur Sugui." Da k'arfi ta dafe k'irjinta da taji ya doka mata da sauri, zaro ido tayi tace "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, d'ansa ne kai? D'an Tagur ne kai?" Duk tsoro ne ya kamashi sai yaja baya kad'an kamar zaiyi kuka yace "Haka dai Ayyata ta fad'a min, amma ban san komai akan Abana ba, dan Allah Dada kisa a kaini gida." Mik'ewa tayi tsaye ta nufeshi da sauri ya sake ja baya yana neman yin kuka, durk'ushewa tayi ita ma tana kukan tace "Tsaya Amjad babu abinda zan maka, ni sunana Aisha amma anfi kirana Aisho, dan Allah fad'a min sunan Ayyanka." Cike da rashin yarda yace "Fatima." Ya fad'a mata hakane dan kaf garin nan da Faduma suka santa, yasan kafin a fahimci wa suke nufi da Fatima zasu wahala, dab'ar ta k'arasa yin zaune tace "Lallai kai d'an Faduma, kamanin mahaifinka da yarenka sun tabbatar min da haka, tabbas kai d'an d'an uwa na ne." Kallonshi tayi tace "Amma ina mahaifin naka? Ka tab'a ganinshi?" Wani kallo ya mata yace "Ya rasu, idan mutum ya mutu kuma ba'a ganinshi." Da wani mamaki ta kalleshi, ya mutu kuma? Abinda ta fad'a masa kenan! Ba zata k'aryata ta ba dan ko ita aka ma abinda aka mata abinda zatayi kenan, murmushi ta k'ak'aro tace "Amma ko a hoto baka tab'a ganinshi ba?" Girgza kai yayi, mik'ewa tayi tana share hawayenta tace "Kana so ka ganshi?" Da sauri ya d'aga kai alamar eh, juyawa tayi ta d'auki wayarta ta shiga dannawa, ba jimawa ta matsa kusanshi tace "Zo ka ga Abanka, kana kama dashi sosai." Matsowa yayi a hankali, karb'ar wayar yayi daga hannunta ya sauke idonshi akan kyakyawan mutumin, wani irin ziiiiiiii yaji abu na ratsashi yana gauraye jinin jikinshi da mamaye zuciyarshi, da sauri sauri yaji zuciyarshi na harbawa, take k'walla ta cika mishi ido, murmushi ya saki a hankali ya furta " *Aba na*" Kallon Aisho yayi hawayen na saukowa kan kumatunshi yace "Shine Aba na? Wacece ke?" Nuna kanta tayi tace "K'anwarsa ce ni, ni nake bi masa, ubanmu d'aya dashi, nan gidansa ne nima ina zauna ne saboda mun rabu da mijina, kuma bana da kowa daya fisu shiyasa." Sake kallon hoton yayi yace "Amma me yasa Ayya ta bata da hotonshi?" Kasancewarta uwa yasa tace mishi "Ayyarka tana son Abanka sosai, ba zata juri ganin duk wani abu daya shafe shi ba, hakan zai sa ta dinga zama a cikin damuwa, ina ga shiyasa ta rabu da komai nashi." Ajiyar zuciya ya sauke yana ci gaba da kallon hoton, kamar yanda mahaifiyarshi ke duhun fata ba sosai haka shima fatarshi take, amma da alama akwai tsafta da kula da jiki, ga wani saje daya keyawa hab'arshi bak'i wulik dashi, maysakaitan idonshi masu sirkin ja da yalwar gashin girar ido. Murmushi ya saki dan shi ma duk da yana yaro yasan kama da mutumin nan ne yayi, kallonta yayi yace "Dada kisa a kaini gida dan Allah, bana so Ayya taje bata same ni ba." Jinjina kai tayi tace "Shikenan, muje sai nasa dreba ya kai ka, da zan so na kaika da kaina, amma Ayya ta bar min gida na kula dashi." Jinjina kai yayi ya mik'a mata wayar, karb'a tayi tana fad'in "Kana son hoton Abanka?" D'aga kai yayi yace "Ina so nayita kallonshi?" Murmushi tayi tace "Shikenan, insha Allahu yau zan sa a wanko maka shi saina ba Khairat ta kai maka." Murmushi yayi shima ta shiga d'aki d'aukar makullin mota ta ba dreba, bin bayanta Khairat tayi wacce ba sosai ta fahimci hausar ba dan hausa ce sukayi ita kuma tafi jin tubanci sosai, tana shiga tace "Ayya, d'an Obdo Tagur ne?" Jinjina mata kai tayi tace "Eh Khairat, amma ki min alk'awarin ba zaki fad'a masa Abansa yana raye ba, kinji?" Baki bud'e da mamaki tace "Lah Ayya! K'arya?" Girgiza kai tayi tace "Ba k'arya bace, zan fad'a masa amma ba yanzu ba." Jinjina kai tayi sai kuma tace "To in fad'awa Haja?" Girgiza kai ta sake yi tace "Karki fad'a, nace miki ni zan fad'a ko." Jinjina kai kawai tayi ta d'auki makullin ta fita, tare suka fita farfajiya ta ba dreba ta nuna mishi Amjad tace "Ka kaishi gida dan Allah, yasan gidan sosai zai nuna maka." Da girmamawa ya karb'a yana fad'in "To Hajia, muje ko?" Ya k'arashe da kallon Amjad, d'aga musu hannu yayi sai Aisho da tace "Ka gaida min Faduma kaji, ka ce Aisho tana gaisheta." Jinjina kai yayi suka nufi wajen mota biyun dake wurin, da kallo ta bisu har mai gadi ya bud'e musu k'ofa suka fita, ajiyar zuciya ta sauke tace "Da mahaifinka baiyi waccen kuskurenka ba da girmanka ya kai a dinga tuk'aka cikin mota irinsu benz, hilux, honda da sauransu." _______________ Tana tayar da motar kwana ta shiga ta tsaya daidai katangar wata makaranta a baya, had'a kanta tayi da sitiyarin motar ta fashe da kuka sosai, kuka take sosai da bubbuga kanta akan sitiyarin, ji take kamar ta kashe kanta ta huta, ba zata lamunci jin sunan Amjad daga bakinshi ba, ba zata so ta zama mak'aryaciya a idon d'an data haifa ba, ba zata tambayi yanda akayi Atta tasan tana da d'a ba tunda har ta ganta tare da Hindu, rashin kunyarshi dai take jinjinawa da har yake iya kallonta wai yace ina d'anshi? Ta jima nan tana kuka kafin ta tayar da motar ta k'arasa makarantar su Amjad, ganin da sauran lokaci yasa ta ciro wayarta ta kira Aminu, yana ganin kiran ya d'auka yana fad'in "Wayyo Faduma ki gafarceni dan Allah, wallahi na so kiranki naji yanda shari'ar nan ta wakana, amma ina bureaux Alhaji ya kirani na zo shago duba wasu kaya da ake sauke masa." Da k'yar cikin dakusashiyar murya tace "Ba komai, yanzu kana shagon ne?" Cikin nutsuwa yace "Eh ina shago, amma yanzu za'a gama saina koma." Numfashi ta sauke tace "Zaka iya samu na gida Aminu?" Cikin sanyin jiki yace "Muryarki ba yanda na saba jinta bane, Faduma ina fatan mutumin nan baya dawo rayuwarki bane dan ya sabunta zubar da hawayenki, me ya faru kuma yanzu?" Saida ta lumshe ido wasu hawayen suka fito kafin tace "Ba komai, idan da hali ka zo gida dan Allah zamuyi magana." Cikin tsananin damuwa da kulawa yace "Fadumaaa! Shikenan zan zo insha Allah da nayi sallah azahar." "Shikenan." Ta fad'a tana yanke kiran. *Yawan sharhi yawan rubutu* *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 17:08 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _11_ Ko da yaje gida ya samu Dada da bak'in dake zuwa siyan turaren wuta, sallamarshi tasa suka maida hankali kanshi, amsawa sukayi inda Dada ta d'ora da fad'in "Kai jikallen, ya na ganka ka dawo? Ina makarantar kuma?" Saida ya kalli matan yace "Ina kwananku." Amsawa sukayi da "Lafiya lau." Sannan ya kalli Dada yace "Dara nra wani malami ne ya rasu shiyasa aka ce ba ayi." "Allah sarki! Allah ya jikanshi, amma waya dawo da kai gida?" Turo baki ya d'anyi yace "Dada dreban wata yar makarantarmu ya dawo dani." Hararanshi tayi tace "Amma kasan Ayyaka bata so ko?" Marairaicewa yayi yace "Karki hassalata mana, idan ta zo zatayi fad'a ki bata hak'uri." Mak'ale kafad'a tayi tace "Um um! In nayi me zaka bani?" Dariya yayi yace "Yau zan siyo miki naman miya." Dariya duk suka saka inda wata daga ciki tace "Ai kuwa shikenan yaro, wannan k'ok'ari haka." Kallonshi tayi tace "Shiga ciki to saika cire kayan." Saida suka gama siya zasu tafi ta mik'e ta rakasu wayarta ta fad'i saman jikinta, duk'awa tayi ta d'auka tana dubawa, k'walla kiran Amjad tayi yana fitowa ta bashi wayar tace "Sa min caji fad'uwa tayi, data mutu sai cajin ya fece ya tafiyarshi." Amsa yayi ya koma ciki da wayar yasa caji da niyyar in ta d'auka ya kira, ta jima bata d'auka ba daya kunna saita mutu sai da lokacin tashinsu yayi, hankali tashe ya sake kunna wayar yayi sa'a ta kama ya aika kira. _______________ Fita tayi daga motar tana daf da shiga cikin makarantar mai gadi ya fito rik'e da buta, murmushi ya mata yace "Kai Hajia ce? Sannu da zuwa." Cikin hange hangen inda zata hangeshi tace "Sannu, ban ga yara ba, har an jima da sakinsu ne haka? Naga yanzu ne 12:00 tayi." Aje butar yayi yace "Hajia wai kina nufin bai je gida ba? Ai kuwa nan tunda da safe ya bar nan yace zai koma gida.". A firgice ta kalleshi baki bud'e cikin fad'uwar gaba tace "Ban gane tunda safe ya bar nan ba? Ina ya tafi? Ya akayi ka bar min yaro ya fita?" Cike da rarrashi yace "Yi hak'uri Hajia, wallahi shi da wata yarinya ya fito nan yace zasu tafi gida, kuma da kaina na tare musu adaidaita suka tafi." A tsawace tace "Wace yarinya? Ina suka bi?" Cikin rud'ewa kamar yanda ya ga tayi ita ma ya nuna mata, hannu ta d'aga kamar zata mare shi sai kuma ta sauke hannun ta juya baya, dafe k'ugu tayi tana kallon masu sarrafa katifa ta siyarwa, yanayin da take ciki ne taji ya nunku hawaye sun sake gabce mata, juyowa tayi ta kalleshi tace "Malam taya zaka bari su tafi, me yasa yarona zai tafi? Wacece ita yarinya? Indai gida suka tafi me yasa suka bi ta nan a mamadin wannan hanyar?" "Hajia kiyi hak'uri dan Allah, amma ke daga gidan kike kuma baya can?" Kallonshi tayi da sauri kamar ta tuno wani abu, da gudu ta nufi mota ta bud'e ta lalubo wayarta, a daidai lokacin kiran Dada ya shigo wayar da alama ma akwai appel manqu茅. Da sauri ta d'auka ta d'ora a kunne tana fad'in "Oui Dada, Amjad ya zo gida ne?" Cikin tattausan muryarshi yace "Ayya ni ne, Ayya kiyi hak'uri na tayar miki da hankali, dan Allah ki zo gida nima tun d'azu na dawo." Kashe wayar tayi ta ma rasa me zatayi, cije leb'e tayi tana jinjina kai, juyowa tayi ta hangi mai gadin tace "Kayi hak'uri, yana gida." "Ya je gidan ko? To Alhamdulillah." Juyawa yayi ya koma ciki ita ma ta shiga mota ta d'auki hanya, tana zuwa gida ta fita a motar ta tunkari shiga ciki da sauri rai b'ace, tunda yaji tsayawar motar ya fito da gudu tarbenta. Tana shiga shi kuma yana fito sukayi karo, rumgumeta yayi da murna, b'amb'areshi tayi daga jikinta taja hannunshi zuwa ciki, Dada dake zaune tana kallo ta wuce dashi d'aki, mik'ewa tayi ta bi bayansu tana fad'in "Faduma dan Allah karki dake shi, saurare ni kiji abinda ya faru." Tunda ta ga bata kula ta ba tasan yau fa abubuwan sun motsa, babu abinda zai hana Amjad gane kurenshi. K'ofar d'akinshi ta tsayar dashi ta kalleshi rai b'ace tace "Yaushe ka fara sab'a umarni na? Yaushe ka fara kunnen k'ashin da har zan maimaita maka magana sau biyu? Ni ce zan fad'a maka ga yanda nake so amma ka kasa yi saboda kana so kaga na tashi hankalina akan ka a tsakiyar titi ina bilayin nemanka kamar wata yar iska?" Yanda ta k'arashe maganar da d'aga murya yasa shi fashewa da kuka ya had'e hannaye biyu yace "Ayya kiyi hak'uri, kiyi hak'uri ba zan sake ba, ba ayi karatu bane shiyasa dan kar na zauna na jiraki na taho." Jinjina kai tayi tace "Yayi kyau, had'e min hannayenka anan ka tsaya har sai na gama tunanin abinda zan maka." Juyawa tayi zata shiga d'akinta yace "Ayya Dada Aisho tace na gaisheki." Da wani irin sauri ta juyo tana kallonshi, yanda ta firfito da ido zai tabbatar maka maganar ta girgiza ta, da sauri ta k'arasa kusanshi ta sunkuya daidai tsayinshi tace "Aisho? Ina ka santa? Ina kuka had'u? Ya akayi ta sanka?" Cikin nutsuwa ya shiga fad'a mata yanda akayi, yana labarta mata komai tana sake shiga d'imuwa da zautuwa, har saida ta kai ta rufe bakinta da hannun hagu tana girgiza kai da ziraro hawaye, numfashi ta dinga saukewa tana kallon k'wayar idonshi, durk'ushe tayi ta rik'oshi tana fad'in "Kuma ka ganshi a hoton?" Jinjina kai yayi yace "Na ganshi Ayya? Amma me yasa ko hoto d'aya ba zaki aje ba dan na dinga ganinshi? Ayya ba dan na gani ba yanzu da bansan wa nake kama dashi ba, ke ma ya kam..." Da sauri ta kuma k'wak'umeshi jikinta duk sai b'ari take tana rawar murya tace "Amjad..., karka yarda da kowa, Amjad ni ce mahaifiyarka ni kad'ai, babu wanda yake sonka sama dani, karka sake yarda da kowa akan maganar mahaifinka, mahaifinka baya raye a duniya baya raye kaji, idan kuma ka bari suka ganeka wallahi zasu rabani da kai, kai kana so a rabaka dani?" Girgiza kai yayi a hankali yace "Ayya su waye zasu rabaki dani?" Kai tsaye tace mishi "Dangin mahaifinka?" Langab'e kai yayi yace "To Ayya idan su suna son rabani dake, danginki fa? Suma zasu rabamu ne?" Hawayen da suka malalo mata ne suka sa ta sake rufe bakinta dan bata so sautin kukanta ya fita, durk'ushe yayi shima yana share mata hawayen yana fad'in "Dan Allah Ayya ki daina kuka? Kiyi shiru kinji." Matsowa Dada tayi ta kalleshi tace "Tashi ka fita waje kayi wasa." Mik'ewa yayi zai fita da sauri Faduma ta kalleshi tace "A'a karka fita, shiga d'akinka ka zauna." Juyawa yayi ya shiga d'akin, tashi tayi ta kama hannun Dada suka shiga d'akinta, saida ta mayar da k'ofar ta rufe ta zaunar da ita bakin k'aramin gadon suna kallon juna, a nutse Owwo ta kalleta tace "Faduma akwai matsala ne? Naga duk kinyi wani iri dake? Me yake faruwa ne?" D'aga kai tayi tace "Dada akwai babbar matsala." Hankali tashe tace "Me ya faru?" Ajiyar zuciya ta sauke tace "Dada yau dai Tagur yasan akwai d'ansa a wuri na, kuma nasan cikin k'ank'anin lokaci zai san komai a game dani da Amjad." Da tsananin mamaki tace "Ya san shi? Ya akayi ya sani kuma?" "Hummm! Dada bana fad'a miki Hindu nan bata min ba? Ko rantsuwa nayi nasan ba zanyi kaffara ba cewa ita ta fad'awa matarshi, ita kuma matarshi haushin na tona asirin baya haihuwa shine ta min wannan tereren a cikin kotu har tana kirana da sunan wai karuwarsa ce ni." Mik'ewa tayi tsaye cikin b'acin rai tace "Karuwa? Wacece ita? Ina zan same ta? Dan an fad'i gaskiya har zata fad'a miki haka?" Jawota tayi ta koma ta zauna tana fad'in "Zauna Dada, ita ba matsalata bace zanji da ita daga baya." Zaune tayi tana huci sai kuma ta kalleta tace "Yanzu miye abunyi? Dan alamu sun nuna sirrin nan da aka jima ana b'oyewa daf yake da fitowa fili, duba kiga ta yanda yau yaje gidan nan, ya kike gani da ya had'u da Tagur ko Hatimi?" Girgiza kai tayi tace "Ba zasu had'u yau ba kam, sai dai nasan zuwa yanzu ya fito, tunda yana da kud'i ba lallai ya kwana a magark'ama ba kamar yanda alk'ali ya umarta." Ajiyar zuciya ta sake saukewa tana kallonta tace "Dada kinga ni da yamma zan d'auki hanyar Zinder, nasan waye Tagur Dada, tabbas ba zai iya bacci ba yau har sai ya nemi inda nake dan ya k'arasa sanin abinda ya fara tambayata a kotu, bana son had'uwata dashi yanzu saboda har yanzu ina da rauni idan na tsaya gabanshi, kin sani k'aramin aikinshi ne ya tara mana jama'a a unguwar nan, shiyasa nake so na bawa Aminu Amjad ya tafi dashi gidansu, ke saiki zauna kafin na dawo koma meye ya faru." A hankali ta kalleta tace "Amma shi Aminu kina ganin ba zai samu matsala daga gidansu ba?" Girgiza kai tayi tace "Dada ba za'a samu ba insha Allahu, karki manta irin taimakon da Aminu ya min, ya zama kamar wani garkuwata ne shi tsaka a filin dagar da babu bil'adam sai bak'ak'en hallitu masu shan jini." Jinjina kai tayi cike da gamsuwa tace "Gaskiya ne Faduma, wannan alfarma ba zata gagareshi ba." Rik'o hannunta tayi tace "Amma Fati ya kamata ki cire tsaron Tagur d'in nan a zuciyarki, kin san shi ya sanki bai kamata ace har yanzu kina shakkarshi duba da abinda ya faru." Wani murmushin takaici tayi tace "Dada, kinsan da yau har fuskar Tagur na mara cikin rawar jiki?" Murmushi Owwo tayi tace "Ni kam nasan sai dai a rawar jiki zaki iya marinshi, amma duk da haka kin min daidai." Mik'ewa tayi tana fad'in "Bari na shiga na shirya Dada, zan had'a kayan Amjad ma." Mik'ewa tayi ita ma tana fad'in "Bari na had'a masa kayan nasa, kije ki shirya kema." Wucewa tayi tana fad'in "Nagode Dada." _______________ Yau ma da safe shi ya kai yaran makaranta da tunanin sake had'uwa da tattausan fuskar murmushinshi, shiyasa ko da mai adaidaitarsu ya zo ya bashi hak'uri yace ya tafi zai kaisu, amma sai dai kash ko da aka ce ba'a karatun kuma ya zauna har kusan lokacin sai yayi tunanin ta yiwu har sun zo sun koma suma, sai kawai suka koma gida ya maida yaran ya aje. Abinda ya jima baiyi ba yau sai gashi yayi, kai tsaye babbar masana'antarsu ya wuce, masu gadi biyu da kayansu iri d'aya ne suka bud'e mishi ya shiga suna gaishe shi, a daidai harabar ajiye motoci ya paka, yana tsayawa masinjanshi ne yayi saurin bud'e masa murfin, saida ya kashe yana sauke ajiyar zuciya kafin ya zuro k'afarsa mai d'auke da takalmi na fata kalar ja mai duhu, k'arasa fitowa yayi yana mik'awa matashin daya zube k'asa yake gaishe shi, kuma wannan ladabin na d'aya daga cikin dalilin da yasa bai d'auki babban mutum ba, karb'ar wani babban littafi yayi mai kama da kundi ya mik'e yana bayanshi shi yana gaba. Duk da rashin maganarshi ga matashin hakan bai sa yaji ba dad'i ba, yanda ya sanshi dama yasan ba mutumin surutu bane, a hankali yake take masa baya har suka isa k'ofar shiga ciki, wani mai gadin ne da irin kayan waccen ma'aikatan na k'ofar, bud'e musu yayi suka shiga yana gaishe dashi shima, da hannu kawai ya amsa yana kallon katafaran kampanin, mutane ne birjik ta ko ina kuma kowa da aikin da yake wanda yasha mishi kai, wanda suka ga shigowarshi ne kawai suke gaishe shi daga inda suke yana amsa musu da kai, a haka har ya shige ofishinshi ya nemi tanfatsetsiyar kujerar dake ofishin ya zauna ta zaman mutum uku, madadin yayi zaune saiya cire takalmin daga k'afarshi ya aje makullin mota ya kwanta yana kallon sama ya d'ora hannunshi saman goshi ido rufe, duniyar tunani ya fad'a, daidai da wucewar kowani sakan (second) fuskarta gifta mishi take, abune mai wuyar fassarawa yake ji a game da ita, *daga kallo d'aya* yaji abun ya shige shi, a yanzun sai yake ji kamar wata jarabta ce a gareshi, duba da Saudat ma daya mata irin haukan son nan yanzu gashi tana gasa mishi aya a hannu, yana tsoron ita ma ta zama hakan kuma ma babu tabbacin zai same ta, ko sunanta bai sani ba bare inda take rayuwa. K'wank'wasa k'ofar akayi tare da turowa aka shigo, duk da yaji amma bai bud'a ko ido ba bare ya ga wanda ya shigo, saida ya k'arasa kusa dashi ya zauna kujerar mai zaman mutum biyu yana fad'in "Elhaj ashe ka shigo? Tashi ka gani to." Numfashi kawai ya sauke yana jinjina lallai Mukhtar baka da hankali, banza ya mishi har saida ya sake cewa "Elhaj." Hannunshi na dama dake kan cikinshi ya d'ago ya k'yastashi ya mishi alama ya tashi ya fita, murmushi yayi yana fad'in "Yau yan arzik'in ke bisa kai kenan?" Tab'e baki yayi ya aje masa takardun daya shigo dasu yace "To idan ka sauko saika duba wannan zanen, idan yayi ko a waya ka kira ka sanar dani, ina so ne na bayar da oda a bugasu, wani boutique ne ke buk'atar atampopin." Juyawa yayi ya fita duk da haka bai bud'a idonshi ba har yaji fitarsa, ajiyar zuciya ya sauke ya laluba hannunshi ya ciro wayarshi a aljihu, sai lokacin ya bud'e ido yana dannawa, lambar ya nemo ya kafe da ido, murmushi kawai ya saki saboda kallon sunan daya saka a lambarta, sai ya danna ok zai kira sai kuma yayi saurin katse kiran. _______________ Ko da suka dawo gidan Aisho ta tarbe su, amma yanda yanayinsu yake ya tabbatar mata da ba lafiya ba, saida ta kawowa Hatimi ruwa tasha cike da kulawa ta kalleta tace "Ayya lafiya? Ya naga duk kunyi sanyi? Ko dai bakuyi nasara bane?" Ajiyar zuciya ta sauke ta kalleta tace "... *Yawan sharhi yawan rubutu* *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 17:09 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _12_ "Aisho ni ai ban ma san me zan cr ba, abun fa in gaya miki duk a yanda bamuyi tunani ba ya zo mana." Da tashin hankalin ta sake kallonta tana fad'in "Ayya me ya faru wai? Karb'e d'an sukay kenan?" Ajiyar zuciya ta sauke ta kalli Rahila tace "Rahila fad'a mata abinda ya faru, ni kam ba zan iya ba." Tab'e baki tayi cike da rashin damuwa tace "Ke d'an fa aka ce ba nasa bane, kuma shaida aka gabatar akan haka." Duk a tare suka kalleta sai dai kallon Aisho kallo ne na tashin hankali da rud'ani, har saida taji wata zufa na karyo mata, kasa furta uffan tayi har saida Hatimi tace "Rahila karki yarda da maganar nan har ki sata a kanki, ni fa ina ganin kamar k'arya ta fad'a dan ta d'auki fansa." Girgiza kai Rahila tayi ta mik'e tsaye tana kallonta tace "Ayya, kina so ki yaudari zuciyarki ne kawai, amma me yasa ita gomboy bata k'aryata ba acan? Ya kamata ku sarara ma Faduma haka, ta rabu da d'anki yanzu babu komai tsakaninku." Ko da ta gama fad'a ta juya ta nufi d'akinta, baki sake ta bita da kallo na mamaki, saida ta ga shigewarta ta jiyo tana jinjina kai da fad'in "Lallai yarinyar nan." Da wani sabon mamakin kasa fahimtarsu Aisho tace "Ayya, kamar sunan Faduma naji ta ambata? Wace Faduma?" Wata ajiyar zuciya ta sake saukewa tace "Faduma dai da kika sani." Jim tayi tana kallonta duk ta kwalalo idonta kamar zata had'eta dasu tana rarraba su, tunanin hirarsu da Amjad ta shiga yi tare da tuna sanda yace mata yanzu dole Ayyarshi tana kotu, hakan na nufin kenan ita ce lauyar da Tagur jiya ke fad'a mata ya samu, amma ya k'i fad'a mata ko wacece bare ta sani. Ita ma wata wawuyar ajiyar ta sauke mai k'arfi tana rufe bakinta gam, suna haka Khairat ta shigo d'akin da yar tsanarta a hannu, tana ganin Hatimi ta ruga da gudu ta fad'a jikinta tana fad'in "Haja kin dawo?" Jiki a sanyaye ta shafa kanta tace "Na dawo Khairatutu, yau kin dawo da wuri ko?" Da sauri ta juya tana kallonta tace "Haja bamuyi karatu ba yau, kuma tare da d'an makarantarmu muka dawo, sunansa Amjad d'an obdo Tagu..." Da k'arfi Aisho tace "Khairatttt!" Da sauri ta juya ta kalli Aisho, nuna mata d'akin Rahila tayi tace "Je ki ga Dadarki a d'aki tana nemanki kuyi kallo a wayarta." Da sauri ta kalli d'akin tace "Dada na ciki?" D'aga mata kai tayi alamar eh, da gudu ta juya ta shiga d'akin tana murna, da mamaki Hatimi ta kalli Aisho tace "Kamar kin katseta zatayi magana ko?" Wani murmushin yak'e tayi tace "A'a Ayya, wani yaro suka zo tare d'an makarantarsu, sai dai nasa Bala dreba ya mayar dashi gida." Cikin basar da zancen tace "Taya ya biyo su da makarantar ba kusa take ba?" Ita ma a haka ta tafi da zancen da fad'in "Wallahi kuwa Ayya." Mik'ewa tayi tana fad'in "Bari na d'ora mana girki." A d'aki kuwa Khairat na shiga da murna ta hau kan gadon Rahila tana cewa "Dada Ayya tace na zo muyi kallo." Da yake akwai shakuwa da soyayya tsakaninsu matsa mata tayi tana fad'in "Zauna nan, amma ya kika dawo daga makaranta da wuri yau? Ko bakuyi bane?" Tana cikin aje yar tsanarta da karb'ar wayar da Rahila ke mik'o mata tana fad'in "Bamuyi ba, kuma ni na dawo gida da kaina yau." A razane ta zaro ido tana kallonta tace "Khairat me? Ke kad'ai kika dawo? Akan me?" Kallonta tayi ita ma cike da yarinta tace "Adaidaita na shigo da kud'in da Haja ta bani, kuma ni da abokina muka dawo Amjad." Cikin sauke numfashi tace "Aboki? Ke yanzu har aboki gareki? Me zai hana kiyi k'awa to?" Mak'ale kafad'a tayi tace "To ai shi d'an obdo Tagur ne, kuma ni ina son shi." Tashi tayi zaune da kyau ta kalleta tace "Me kika ce? Wane obdo Tagur d'in?" A tak'aice hankalinta na kan wasar da take a waya tace "Na nan gidan." Cike da rashin fahimta tace "Wai kina nufin Ridwan?" Kallonta tayi ta turo baki alamar jin haushi tace "Shi Ridwan da Ayyarshi bata barin muna wasa tare saita dinga korata, Amjad fa nace miki Dada." A duburburce tace "Wai waye Amjad d'in?" Da sauri ta kalleta tace "Shiiiii, kar Ayya taji." Mik'ewa tayi tsaye akan gadon ta dafa kafad'arta tace "Kawo kunnenki kiji?" Sororo ta mik'a mata kunnen, rad'a mata tayi cewa "D'an obdo Tagur ne, amma Ayya tace karna fad'awa kowa." Da wani irin mamaki kamar zai kasheta ta kalleta sanda take zama, ta d'auki minti biyar a haka bata motsa ba kafin ta zabura kuma ta sauka daga kan gadon, har zata fita sai kuma ta dawo ta kama hannunta tace "Ke kinsan sunan Ayyarshi?" Ba tare data kalli ko fuskarta ba tace "Faduma." K'ara zaro ido tayi, da wani irin gudun bala'i ta fita a d'akin tana k'wala kiran sunan Ayya Ayya, Hatimi dake zaune tana neman maganinta na hawan jini a k'aramar jakar hannunta taji kiran, cikin fad'uwar gaba ta juya tana kallonta da fad'in "Lafiya Rahila? Gani nan ke." Aisho ma da taji kiran da sauri ta fito daga madafar rik'e da tukunyar da take shirin d'orawa, tana zuwa cikin tashin hankali tace "Ayya kin gani ko? Wallahi gidan nan ana munafurtarmu dayawa, gaskiya ya kamata kisan abunyi wallahi." Cikin nutsuwa tace "Me ya faru Rahila? Wace irin munafurta kuma?" Saida ta dafe k'ugu da hannu biyu tana wani jijjiga da wurga ma Aisho harare tace "To ba gashi nan ba, ita gomboy ta b'oye miki cewa d'anki baya haihuwa sai yanzu da asiri ya tonu a kotu, kuma ni dama tun farko na fad'a miki yarinyar nan Atta bata min ba saboda k'awarta ce sosai, yanzu kuma gashi d'an Faduma Amjad ya zo har gidan nan yau, amma dan munafuci ance wai ayi shiru kar a fad'a miki, to miye in ba munafuci ba?" Rai b'ace Hatimi ta mik'e tayi kanta, tana zuwa ta d'auke fuskarta da mari jikin har rawa yake tsabar tashin hankalin da take ciki da kuma halin da take shirin shiga, cikin fad'a sosai tace "Wace irin maganar banza kike fad'a akan yan uwanki? Kina da hujjar gasgata Faduma akan abinda ta fad'a ne? Ko kuma zaki iya tabbatar min da shi yaron jinin Tagur ne? Na yarda in d'an Faduma ne, amma kiranshi d'an Tagur ban yarda ba, dan haka karna sake ji kinji na fad'a miki." Saida ta sauke numfashi da k'arfi ta nuna mata k'ofar d'akinta tace "Wuce ki bani wuri." Saida ta juya ta kalli Aisho da al'amarin bai mata dad'i ba ko kad'an, dan ita babu wani nufi a zuciyarta akansu, burinta bai wuce saka musu alkairin da sukayi musu ba, hararanta tayi ta sake juyowa kan Hatimi tace "Ayya kika mareni dan na fad'a miki gaskiya ko? Shikenan ba zan sake saka bakina ba, amma ki sani wallahi wata rana zaki nemi yaron nan kina kuka." A hassale ta wuce d'akinta ta rufo k'ofar da k'arfi kamar zata b'alla ta, da k'yar ta koma ta zauna kan kujerar, ganin yanda take lalubar maganinta jikin sai rawa yake yasa Aisho k'arasawa da sauri, d'aukar maganin tayi ta b'alla ta bata tasha, rufe ido tayi ta jingina a jikin kujerar tana sauke numfashi, ganin tana samun nutsuwa tana dawowa hayyacinta yasa Aisho gyara zamanta, kamo hannunta tayi ta bud'a tafin hannunta tana murzawa cikin sanyin murya tace "Ayya, gaskiya ne abinda Rahila ta fad'a." Da sauri ta bud'a ido ta sauke akan Aisho, cikin rashin fahimta tace "Ban gane ba Aisho? Me ye ke gaskiyar?" Sunkuyar da kanta tayi cikin tausasa murya tace "Ayya Amjad d'an Tagur ne, kuma gaskiya ina ganin bai kamata a ci gaba da dagewa kan cewa ba d'ansa bane, dan Amjad kamar Tagur yayi kaki ya tofar ne, sunan mahaifiyarsa da kuma rashin ganin ko da kammanin mahaifinshi ni dai ya tabbatar min da haka." D'agowa ta sake yi da kyau tana kallonta da mamaki tace "Aisho kina nufin da gaske yaron ya zo har nan gidan?" Jinjina mata kai tayi tare da sake labarta mata duk yanda abun ya faru, jinjina kai Hatimi tayi ta kasa cewa komai, ganin ba tace komai ba yasa Aisho cewa "Ayya me Rahila take nufi da abinda ta fad'a? Wani abu ya faru a kotu ne da gomboy ke da hannu a ciki?" Muryar Gomboy suka ji a bayansu tana fad'in "Babu wani hannu na a ciki ni, kar wanda ya sake cewa nayi wani abu ehe!" Kallonta duk sukay a tare, takowa ta ci gaba da yi tana shiga har tsakiyar falon tana tauna chewing-gum da k'ara gyara ma kallabinta zama wanda ta ma d'auri irin na ba mutumcin nan, girgiza kai Hatimi tayi tace "To dama wani yace kinyi wani abu? Amma me yasa sunanki ya fito kuma kika kasa kare kanki?" Cike da rashin kunya tana wani jujjuya ido da juya baki tace "Ya kamata ku gane neman ganin bayanmu take ta ko wace hanya, ko kun manta ina d'aya daga cikin wanda ta tsana?" Mik'ewa Aisho tayi ta nunata tace "Inhar Faduma ta tsaneki to ta tsaneki ne saboda ke ma kin nuna mata tsana tun farkon fara ganinki da ita." Waro ido tayi ta dakata da taunar chewing-gum d'in tace "Ke! Ni tsaranki ce? Sa'arki ce da zaki sa min baki? Dake nake magana? Ki bari nayi da wacce ta isa mana." Da mamaki Hatimi ta kalleta ganin wata sabuwar d'abi'a a tare da ita, girgiza kai Aisho tayi tace "Ya kamata kisan girma kike? Kuma kin wuce lokacin da zakiyi abu a miki uzurin k'uruciya." A k'ufule tayi kanta tana fad'in "Dan ubanki ni kike fad'awa magana son ranki? Uwa d'aya ta haifemu amma an lalata miki tunani, to dan Allah dake ni, dakeni Aisho sai nasan tsayinka ya kai daidai nawa." Ja baya tayi tana tab'e baki da cewa "A'a wallahi, me ya aikeni dukanki, ai ko ba gaba kike dani ba ba zan iya haka ba, sai dai ko zaki dafani ki cinye ba zan fasa nuna miki abinda kikeyi ba daidai bane." Nunata tayi da yatsa ido rufe tace "Wallahi kika sake shiga harkata saina mareki, karki sake min magana kinji ko." Har zatayi magana sai kuma taja baki tayi shiru saboda shigowar Tagur falon kamar an turo shi, yanda ta tsareshi da ido yasa Gomboy ma juyawa da sauri, suna had'a ido ta gama karance yanayinshi, yanayi ne da in ya shigeshi sai Hatimi ta gindaya masa tsinuwa kad'ai yake sauka, yanayi ne da wani lokacin saita rufeshi a d'akinshi kad'ai suke samun sauk'inshi, bai iya b'acin rai ba ko kad'an, baya da dad'in hushi ko fad'a, k'aramin aiki ne ya nemeka da makamai ayita ta k'are kawai, ka kar shi ko ya kar ka. Duk da dama hallitar idonshi akwai launin ja, amma na yanzu saika rantse ba'a tab'a hallitar fari a cikin idonshi ba, ko kad'an babu masokar tsintsiya a fuskarshi tsabar yanda ya had'eta, yanda ya tunkareta yasa ta hantsilawa bayan kujerar da Hatimi ke zaune tana ihu da fad'in "Wallahi Ayya ki shiga tsakaninmu, karfa ya tab'ani babu abinda na masa." Aisho da Hatimi duk da kallo suka bita, Aisho a ranta tana ayyana "Ashe dai gaba da gabanta aljani daya taka wuta, kina gaba dashi amma kina shakkarsa." Mik'ewa Hatimi tayi tana azamar kamo hannunsa, da k'arfi ya sake tunkarar inda take yana sake dantse harshenshi sosai kamar zai cirashi, sake shiga gabanshi tayi tana dafo kafad'arshi tana fad'in "Saurare ni, kalleni nan Tagur." Wani masifaffen girgiza kai yayi da k'arfi, rintse ido yayi sosai ya sake bud'ewa ya kalli Hatimi, tsabar yanda yake ji ba zai iya magana, dan in yace zaiyi magana zai iya datse harshenshi a banza a wofi, dan haka ya fizge hannunshi data rik'e da sauri sauri ya shiga mata maganar kurame yana nuna mata kanshi da gomboy da kumcinshi, sauke ajiyar zuciya tayi tsaf ta karanci abinda yake nufi, tana kuma sake ayyana lallai haihuwa ba wasa bace, dalilin haihuwarshi ta koyi iya karantar kurmanci saboda in bala'inshi ya motsa saita wannan sigar yake iya fad'in wani abun. Wato yana nufin "Dalilinta yau aka mareni, data fad'a mana gaskiya me zai kaini inda za'a tozarta ni? Me yasa zata rik'eni haka? Me nayi mata? Ayya ki matsa daga nan kawai." Sake kamo hannunshi tayi cikin sanyin murya sosai tace "Tagur kayi hak'uri dan Allah ka saurare ni, ni fa magana ta gaskiya ban yarda da abinda Faduma ta fad'a ba, kuma kaima ka fad'a tun a kotu kawai tayi ne dan d'aukar fansa a kan ka, ko ka manta da abinda ya faru ne?" Da sauri gomboy ta d'ago tsaye daga bayan kujerar tana fad'in "Eh Ayya, wallahi ni bansan da maganar ba kawai jinta nayi, taya ma za ace wani wai an fad'a mana, da gaskiya ne me yasa Omar bai fad'a maka ba?" Binda yayi da ido yanda take murgud'a baki, maida kallonshi yayi ga Hatimi tana ci gaba da fad'in "Kayi hak'uri kaji, sharri ne kawai ta maka." Juyawa yayi kawai ya zauna kan kujerar data tashi, sakin hannunshi da tayi ya bashi damar dafe kanshi da duka hannayenshi biyu yana murza kanshi sosai, duk ido suka sakar masa babu mai motsi, ba wanda ya matsa daga inda yake har kusan minti uku, kamar daga sama suka tsinkayi muryarshi yana fad'in "To d'an da aka ce tana da fa? Me ye alak'ata dashi?" Da sauri Hatimi ta zauna kusa dashi tana d'ora hannunta kan nashi tace "Babu, baka da alak'a dashi, ko ka manta ne?" D'agowa yayi kamar wanda ya farka daga mummunan baccin da yayi mafarki ya kafeta da ido, motsa bakinshi ya shiga yi amma ya kasa fitar da kowace kalma, mayar da kanshi yayi k'asa yana ci gaba da murza kanshi, sake d'agowa yayi yana kallon k'ofa yace "Ayya ina son sanin wani abu akan d'an da akayi magana akai?" A hankali ta kalleshi da d'umbin mamaki tace "Me yasa?" Saida ya kalleta kallon basira da tsantsar gaskiya yace "Inhar Faduma na da yaron daya fito a cikinta, to tabbas *tsatso na* ya fito Ayya." Wata zabura tayi ta mik'e tsaye tana kallonshi, kanta ne taji ya sara mata inda gudun jininta da bugawar zuciyarta duk suka canza lokaci d'aya, bakinta bud'e zatayi magana sai kuma ta tafi luuuuu gaba d'aya zata fad'i a wurin, da saurin bala'i ya tareta a jikinshi tare da zubewa durk'ushe, gomboy da Aisho duk da gudu sukayi kanta har Gomboy d'in da take jin bata damu dasu ba, jijjigata suka shiga yi suna kiran sunan Ayya, cikin kuka da fitar hayyaci Aisho ta shiga fad'in "Wallahi duk laifinka ne, haka kawai kun ja mana bala'i mu rasa madafar data rage mana." Wani kallo ya mata tare da daka mata wawar tsawa yace "Kawowa mutane ruwa malama." K'arfin tsawar daya mata ce tasa ta mik'ewa kamar anyi girgizar k'asa, da gudu ta nufi fridge ta bud'a ta d'auko ruwa, ta juyo da gudu zata kai Rahila ma ta fito da taji suna ta kiran sunan Ayya, tana zuwa ita ma ta samu wannan tashin hankali cikin d'aga murya tace "Ku kira likita mana, Ayya." Ta k'arashe da sake jinjina gata, da k'yar ya iya rarumar wayarshi ya kira Omar, ya fad'a musu baya asibiti kuma yana nesa, amma suyi gaggawar kaita asibiti gashi nan zuwa shima, haka kuwa sukayi inda aka karb'eta aka shiga bata kulawa. _______________ Kamar yanda ya mata alk'awari kam tana idar da sallah ya shigo gidan, Dada ce ta mishi izini ya shiga har falo ya zauna, Amjad da yau ko masallaci bata bari ya fita duk gani take kamar idon mutane akan shi suke za'a iya rabata da shi yasa a gida tace yayi sallah yau, yana shigo da fara'a ya tunkari Aminu yana bashi hannu da fad'in "Obdo Aminu, ina wuni." Saida ya rumgumeshi tsam a jikinshi yana sake jin k'aunar yaron kamar yanda kowace safiya da rana yake k'ara durmiya cikin k'aunar mahaifiyarshi, ajiyar zuciya ya shiga saukewa yana sake shak'ar numfashin daya gauraya da turaren dake jikin Amjad, yana ayyana yanda komai na Faduma k'amshi ne zallarsa, komai data tab'a ko tayi anfani dashi k'amshi ne, bare kuma d'anta? Wacce ko abu ta baka to zaka iya kwana uku kana jin k'amshin turarenta jikin abun, wacce har so yake ta shiga motarshi dan yaji wannan ni'imtaccen sanyin k'amshi. Jin yanda yake sake matseshi a jikinshi yasa yace "Obdo ka matse ni fa." Da sauri ya sake shi yana murmushi da fad'in "Ina k'aunarka ne Amjad shiyasa, kasan da haka?" Jinjina masa kai yayi alamar eh, ledar da tun shigowarshi ya aje gefenshi ya d'auka ya bashi yana fad'in "Ga ice cream." Da murmushi ya kalleshi cike da ladabi ya karb'a tare da sunkuyawa yace " Shikkurdinnan (nagode) obdo, Allah ya biyaka." Shafa kanshi yayi cike da jin ina ma ace d'anshi ne? Labulen da aka bud'e ne ya tabbatar musu tana fitowa, duk kallon k'ofar sukayi tare, tunda ya d'ora ido akanta bai iya d'aukewa ba, wata masifaffiyar lafaya ce ta yane jikinta da ita bak'a sid'ik sai k'yalk'yali da take, babu kallabi akanta hakan yasa kitsonta fitowa daga gaban goshin, babu kwalliya a fuskarta ko kad'an sai hoda data dace da fatarta mai duhu, takalmi ma bak'ak'e ne a k'afarta, sai dai shigar bak'in da tayi ya sake fito da ita ne ya mata kyau, duk da bak'a ce ita amma saita zama mai matuk'ar haske a cikin lafayar. Har ta zauna kan kujera d'an nesa dashi da tsadadden murmushi tana fad'in "Aminu har ka k'araso?" Bai iya cewa komai ba dan tunaninshi na wani wajen yayin da kallonshi kuma ke kanta, lura da haka da tayi yasa ta kalli Amjad tace "Oddo ka shiga ciki zamuyi magana da obdonka." Tunkararta yayi yana fad'in "Ayya kinga abinda obdo ya kawo min?" Murmushi tayi tace "Ka masa godiya?" D'aga kai yayi alamar eh, jinjina kai tayi tace "To je d'akinka." Wucewa yayi ta bishi da kallo har ya shige, duk abinda da ake Aminu na k'urewa fuskarta kallo, da yake tana jin idonshi akan ta sai ta k'i yarda ta kalleshi, gyaran murya tayi cikin taushin murya dan ya fargar dashi, ai kuwa d'an zabura yayi tare da sake kallonta, kunya ce yaji ta rufeshi tare da son basarwa yace "Hajiar nan kin fito?" Ba tare data ja zancen da tsayi ba tace "Na fito, ya kake?" Cikin kafeta da ido yace "Yanzu kam da dama dama tunda ban sameki kina kuka ba." Gefen labb'anta kawai ta musmusa tace "Uhummm!" Saida ta fara wasa da yatsunta sannan ta d'ago idonta ta kalleshi tace "Aminu kaga na kiraka ko? Taimako nake nema a gurina? Sanin kai kad'ai ne zaka iya taimaka min yasa na fuskanceka, na sani kana iya k'ok'arinka akaina da abinda na haifa, amma ka k'ara dan Allah akan wanda kayi, ina kuma tunanin wannan shine zai zama na k'arshe da yardar Allah." Murmushi kawai yayi yana girgiza kanshi yace "Ina jinki Faduma? Kinsan babu alfarmar da ba zan iya yi miki ba inhar bata fi k'arfi na ba." Cike da kunya da jan aji ta d'aga idonta ta kalleshi, duk da idonta cikin nashi suke amma tayi nasarar lumshesu wanda hakan yasa yake jin kamar ya tashi da sauri ya rumgumeta, cikin nutsuwa da fitar da kowace kalma daki daki ta shiga fad'in "Kai ba wanda zan b'oye ma abinda ya shafe ni bane, musamman wanda ke da alak'a da tarihina na baya, dan dole a cikik tarihina daya gabata na ambaci sunanka, babu abinda baka sani ba Aminu, a tak'aice dai shari'ar da mukayi yau ba tay ma kowa dad'i ba daga ni har su, hakan ya jawo mana tonon asirin da dukanmu muke b'oyewa, kuma ka sani idan akwai abinda yanzun bana so wani ya sani bai wuce asan asalin waye uban Amjad ba, to amma yau yasan na haihu dashi, hakan kuma barazana ne a gareni, nasan komai zai iya faruwa bayan tafiya ta, shiyasa nake so kafin na tafi anjima na tabbatar Amjad na cikin tsaro inda Tagur ba zai sani ba bare ya je wurin." Daktawa tayi ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi, k'asa tayi da idonta tana wasa da yatsunta tace "Aminu idan da hali ina so ka tafi dashi wurinka ya zauna a can, na maka alk'awarin ina dawowa ba zan shigo gidan nan ba saina je da kaina na d'auko shi." Fad'ad'a murmushin shi yayi yace "Yanzu abinda kike so kenan na miki kika dinga wannan d'an waken zagayen dani? Faduma nasha fad'a miki duk sanda kike buk'atar wani abu da kuma kin tabbatar zan miki ki daina ba kanki wahala, kawai ki kira ni ki min magana cikin umarni da izza, girmanki ya wuce haka a wuri na." Kallonshi tayi da murmushi tace "Da izza? Umarni? Ni da nake nema kuma zan yi izza?" Shima murmushin ya sake sakar mata yace "Konga tashi ki d'auko min kayan yarona mu tafi, wannan ni ai godiya zan miki da kika mayar dani uba cikin sauk'i." Cikin dariya ta mik'e tsaye tana fad'in "Dama ai baka tab'a raba kanka da shi ba." D'akin Amjad ta nufa ta kirashi tare da d'auko kayan da Dada ta shirya mishi, suna fitowa ya karb'i jakar kayan ya kama hannunshi, dafa kanshi tayi tana kallon fuskarshi, shi ma kallonta yayi idonshi har sun cika da k'walla dan Dada ta fad'a mishi zata yi tafiya shi kuma zai tafi da Aminu, cikin raunanniyar murya yace "Ayya me yasa ba zaki tafi dani ba? Ina so naga Ayyarki kema ko sau d'aya fa ban tab'a ganinsu ba." Kallon juna sukayi da Aminu, kallonshi tayi tana mayar da k'walarta tace "Kayi hak'uri Amjad, wata rana zan tafi da kai kaji?" Cike da rashin yarda yace "Ayya ke ma fa ban tab'a ganin kinje ba sai wannan karan, amma shine ba zamu je tare ba? Ayya wai me ya had'aki da danginki?" D'an zaro mishi ido tayi tace "Amjad, bana son tambayar da ba zata anfaneka da komai ba, kaje tare da Abanka dana dawo zan je na d'auko ka." Cikin jin haushi ya fizge kanshi data dafa yana fad'in "Ni ba Abana bane, naga Aba na kuma ina son zuwa wajen yan uwana." Da gudu ya fice a d'akin ta bishi da kallo baki bud'e, hawayen da suka sauko kan kumatunta ne tayi saurin gogewa tana kallon Aminu, girgiza mata kai yayi yace "Karki damu kanki dan Allah, wannan ba wani bane yaro ne." Zaune tayi kan kujerar kamar an turata tana fad'in "Ya zanyi Aminu?" Matsowa yayi kusanta ya ciro enveloppe ya ake mata kan hannun kujerar da take zaune yana fad'in "Kinga tashi dan Allah ki shirya ki tafi, bana so kiyi yamma a hanya fa, ba dan Alhaji na gari ba da tare zamu je na raka ki." D'aga kai yayi ta kalleshi tace "Nagode Aminu, amma miye wannan?" Murmushi yayi yace "Ki min alk'awarin ba zaki bud'a ba har sai kin d'auki hanya?" Rarraba ido ta shiga yi da tunanin abinda ya fad'a, da sauri ya katse mata tunani da fad'in "Karki dami fa ba wani abu bane, wani abu ne da zai baki mamaki sosai in kika gani, amma zai saki farin ciki kuma zaki sake jin kuzarin tunkarin iyayenki." Jin abinda ya fad'a sai kawai ya gama d'aure mata jijiyoyin jiki, tsananin son ganin iyayenta yasa ta jinjina kai tace mishi "Shikenan nagode, amma zan kiraka a duk sanda na ga miye a ciki dan na tabbatar maka da farin ciki na." Murmushi kawai ya mata yace "Allah ya kiyaye hanya Faduma, ki kula mana da kanki kinji." Mik'ewa tayi tana fad'in "Nagode Aminu." D'an guntun tsaki yayi yace "Ki bari mana bana so, ke dai kawai ina so kije lafiya ki dawo lafiya, ina so da kin dawo ki damk'a ragamarki data Amjad ga wanda kike da tabbacin zai kula daku." Wani kallo ta masa mai kama da harara tace "Aminu wai da gaske kake?" Jinjina mata kai yayi yace "Sosai, Faduma kiyi tunani mana, da a k'ark'ashin inuwar wani kike da hankalinki zai tashi ne wajen tunanin inda zaki bar Amjad?" Ganin yana neman janta da wata magana da bata da muhalli a wajenta tace "Hakane, insha Allahu dana dawo zanyi tunanin wannan." Jinjina kai ya sake yi yace "Da yafi dai." Murmushi ta masa tana kallo har ya fita, tana hange har ya kama hannun Amjad dake kwance kan k'afafun Dada yana kuka, tana kallo ita ma Dada tana share hawayen rabuwa dashi kamar zai tafi kenan ba zai dawo ba, duk yanda ta so ya juyo ya kalli d'akin bai juyo ba har suka fita daga gidan, saida ta ga fitarsu tayi wani malalacin murmushi ta furta "Yarona kenan, zuciyar ta motsa ko? Ko rabin ta ubanka baka kamo ba." Juyawa tayi ta shiga d'aki ta gama had'a nata kayan ita ma ta fito, enveloppe d'in daya aje mata ta d'auka, saida taji gabanta ya fad'i dan daga ji bata raba d'ayan biyu cewa kud'i ne a ciki, amma kuma ta kasa yarda kud'in ne saboda tasan yasan bata son kowane namiji ya taimaketa da sisin kwabo, yafi kowa sanin bata karb'ar kyauta daga hannun namiji bare kuma shi, sannan abinda ya fad'a mata yasa tale k'ara jin kamar ba kud'in bane. Tana fitowa ta samu Dada, duk da tasan tana da halin amma bai hanata fito da kud'i a jakarta ba ta bata tace ta rik'e kafin ta dawo, k'in karb'a tayi amma ita ma ta dage, sallama sukayi har Dada ta bayar da gudummuwar kud'i akai ma Hadizey amma ita kam tace ba zata je ba dan cewa ake ita ta d'aurewa Faduma gindi suke iskanci anan. A motar ta ta k'arasa gidan bus d'in na Rimbo, nan ta samu billets ta motar da zata tashi k'arfe 15:00, nan ta aje motarta bayan minti goma suka tashi. A kowane tafiya na motar tana k'ara kusanta ta da garindata bari shekara tara data wuce, ta bar garin tana yar shekara goma sha biyar, yanzu gashi tana shigarshi da shekarunta ashirin da hud'u, duk kusantarta da garin sake shiga matsanciyar fad'uwar gaba take, a kowane gudu na motar tare da gudun jininta yake tafiya, zuciyarta rawa take kamar zata cire daga k'irjinta ta fito waje, bata san me zata tardo ba? Bata san wane irin k'alubale zata samu ba? Bata san wane kallo zasu mata ba yanzun? Tana tsananin fargabar had'uwa da mahaifinta, iya wannan tashin hankalin kad'ai ya ishi bawa kwantawa rashin lafiya, amma haka ta dage da addu'a a bakinta da ambaton Allah ya sauk'ak'a mata komai karta samu abunda take tsammani. _______________ Daf da la'asar ya gama shirinsa ya fito, a karo na ba adadi kenan daya gifta falon amma baya samunta, sauke nashi girman kan yayi ya nufi d'akinta dan sauke nashi hakk'in, bud'a k'ofar kawai yayi da sallama can k'asan mak'oshi yanda ko ita bata ji ba sai shigowarshi kawai, tana kwance kan gado da wayarta a hannu tana dannawa, kallo d'aya ta masa ta d'auke kai daga kallonshi ta ci gaba da abinda take, amma fa har k'asan zuciyarta tasan ya had'u sosai a cikin bak'in boyl d'in daya karb'eshi, babu hula akan shi kuma dama ba mutumin saka hula bane, takalminshi ma k'afa waje ne na zallar fata bak'ak'e wanda suka fito da farar k'afarsa kamar k'afar mace, kasancewar yadin sharshara yasa ake ganin bak'ar singelt d'inshi data kamashi sosai, kuma d'inkin ma irin na zamani ne ya matseshi ya zauna a jikinshi, duk ya fito mishi da k'akk'arfar k'irarshi ta gwarzo kuma ingarman namiji, duk da ba mai tara gemu bane amma sajen fuskarshi ya k'ara mishi kyau da fito da ainihin haskenshi. Kama daga m'ach猫te d'in dake wuyan rigarshi zuwa agogon kamar na gwal saboda yanda suke d'aukar ido suma bak'ak'e. Ganin yanda tayi bata damu saida ya d'an cije leb'en k'asa ya gyara tsayuwarsa, hannun gaban rigarsa yasa hannu ya ciro kud'i, aje mata yayi kusanta inda ta sauke ido akansu, wani bala'in dad'i taji ya ziyarceta, a rayuwarta tana son ganin yana fito da takardar nan mai zanen d'awisu yana mik'o mata, musamman yanzu data gansu har guda biyar reras, duk da tasan tafiya zaiyi amma hakan kamar gobarar titi ne a gareta. Cikin dakakkiyar muryarshi yace "Ki rik'e wannan, ni yanzu zan wuce zinder ne wajen d'aurin auren k'anin abokina Elhaj *Kalli*, amma insha Allahu zuwa gobe zan dawo." Aje wayar tayi ta mik'e zaune tana kallonshi cikin rashin kulawa da jin haushin abinda ya faru tun jiya tace "Allah ya kiyaye hanya, saika dawo." Wani sanyayyen iska ya huro mai fitar da k'amshin spoot yace "Ameen, saina dawo." Ya fad'a yana mata alama da hannu ta matso, saida ta wani waina idonta ta sauko daga kan gadon, hannunta ya kamo tare da rumgumeta jikinta, bai nuna k'yank'yaminta duk da yana da tabbacin tun safe jikinta bai ga ruwa ba, sai ita data shiga nok'ewa kamar tana son raba kanta dashi, ita ma kuma tana hakane dan kar yaji iskan jikinta, saida ya sumbaci kumcinta yace "Ki kula da kanki." Turo baki tayi gaba cikin shagwab'a tace "Ina so zan fita wankin kai gobe kafin ka dawo?" Ba murmushi a tare dashi yace "Sai kin dawo." Ba tace komai ba har ya juya ya fita ta bishi da kallo, yana fita ya juyo a tunaninshi tana biye dashi, amma ganin bata taho ba sai kawai ya girgiza kai ya ficewarshi. Da kallo ta bishi ita ma tana matsanancin jin son shi da kishinshi, ta ko ina mijinta ya had'u kuma sun dace da juna, sai dai ko kad'an bata jin tana wani abu ba daidai ba bare ta d'auri niyyar gyara. Saida ya shiga Umma ma ya mata sallama ta mishi addu'a sosai sannan ya fito, a farfajiyar gidan ya samu dreban dake tuk'ashi indai zaiyi balaguro na jiranshi, da kanshi ya bud'e mishi murfin ya shiga, mai gadi na bud'e musu k'ofa ya fad'a mishi zasu fara d'aukar d'aya abokinshi a gidanshi sai su wuce. A gidan abokinshi mai sunan Alhaji *Adam* suka tsaya, masallacin dake unguwar suka shiga shi da dreban sukayi sallah a jam'i, saida aka idar ana fitowa suka had'e da shi ma Adam d'in ya fito, gaisawa sukayi kafin ya shiga gida yayi sallama da iyalinshi ya fito suka d'auki hanya. ______________ A asabiti kam da k'yar Hatimi ta farfad'o, kuma har lokacin yaran basu daina cecekucen abinda ya faru ba har ya jawo sumarta, musamman da sauran yan uwan su Aisho suka zo ana ta sake biya zancen, a d'akin da suke kamar zasu cinna mishi wuta, ba dan Tagur masifaffe bane shima da sun cinye shi, dan duk a kanshi suke maganar dan sunyi mamakin yanda yace wai gaskiya ne d'anshi, a ganinsu kenan me ya mayar dasu to? Mahaukata ko wawaye da basu san me suke ba...? *Dan Allah duk wanda yasan yana karanta littafin nan yayi comment, labari ne dana jima ina tsara yanda zai kayatar daku, yin shirun nan zaisa na tsame iya masu comment na ware musu gidansu kawai, dan ba ma zan ba kaina wahala wajen tsayawa cireku ba, dan banga anfanin wahalar da kan.* *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 17:09 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _13_ A can kuma Omar na sauri zai shiga mota dan yaje asibiti duba Hatimi, dama yana uzurinsa ne tare da iyalinshi Tagur ya kirashi, shi kuma yana matse shiyasa saida ya tsaya ya sama ma kanshi nutsuwa sannan, ya nufi motarshi zai shiga daga bayanshi yaji ance "Barka da rana likita bokan turai." Tsayawa yayi ya juyo dan ya gane muryar Zaleeha, had'e fuska yayi sosai dan baya k'aunar tarnak'in da take kawo masa yanzu a rayuwarshi, daga baya Hindu ta tsaya tana kallonsu ita kuma tana zuwa hannu ta kai kan hantsar wandonshi zata tab'a yayi saurin bige hannunta cikin tsawa da b'acin rai yace "Ke wai me yake damunki ne? Baki da lafiya ne?" Cike da kissa da iya hege ta matsa kusanshi tana kashe mishi ido tace "Ban da lafiya mana, wajenka na zo ka duba ni." "To ki ji asibiti, ko gidana asibiti ne?" Ya fad'a yana bud'e k'ofar motar, rik'e murfin tayi tana fad'in "Malam wajenka na zo muyi magana zaka wani tafi ka barni nan, ya iska ce ni da zaka shareni?" Sama da k'asa ya kalleta yace "To da mecece ke? Zaleeha fita a hanyata kinji ko, na fad'a miki ki manta da komai, ni yanzu rayuwata nake tsaftattaciya." Tab'e baki tayi ta mik'a hannu inda Hindu ta mik'o mata waya, karb'a tayi ta mik'a mishi tana fad'in "Aiki zan baka, tukuincin kuma zan biya da wannan hoton." Da sauri ya karb'a yana dubawa, wani fad'uwar gaba yaji tare da tsoro ya firfito da idonshi, kallonta yayi yace "Ina kika samu wannan hoton Zaleeha? Ba kin ce min kin goge komai ba daya shafi ni dake?" Wani shak'iyin murmushi tayi tace "Gogewa dai? Kuma saika yarda dana fad'i haka?" Tana kallo ya goge hoton ya mik'o mata wayar, dariya tayi sosai tace "To sai me? Ai dai kasan haka kawai ba zan tunkare ba alhalin ban kwafi wannan hoton gida gida ba, kaga malam da tsayawa kayi ma ka saurare ni zai fi maka kyau." Tsaki yayi yana jin kamar ya bigeta yace "Ina jinki? Nawa kike so?" Girgiza kai tayi tace "Ko sisi ban buk'ata daga wurinka." A hassale yace "To me kike so? In dai ni kike buk'ata wallahi kinyi k'arya, yanzu kayan nan na Abida ne kawai, kuma kema kinsan haka." Murmushi tayi had'e da tab'e baki tace "Aikin banza, to wane dare ne jemage bai gani ba." Gyara tsayuwa tayi ta had'e hannayenta a k'irji tace "Magana ce akan larurar data samu waccen nakasashen abokin naka, muna so duk abinda zai faru ka fad'i ko a gaban waye cewa baka san da wannan matsala ba, ka fahimta?" Wani kallo ya mata yana gyara tsayuwarshi yace "Ke baki da lafiya wai? Me kike nufi? Wane abokin nawa?" Tsaki tayi tare da kai wa k'irjinshi duka tana fad'in "Omar karka raina min hankali, ba tare da kai aka fad'i Tagur baya haihuwa ba? To maganar ake a kotu yanzu, karka kuskure ka ce baya haihuwa, ka ce kaima baka san da maganar ba kawai kuma likita bai fad'a muku ba." Cikin jinjina kai yace "Nayi k'arya kenan kike nufi?" "To bak'on abune a wurinka?" D'orawa tayi da "Kaga shima waccen likitan yana can zamu gama dashi, abinda zaka yi kenan ka tsira, in ba haka ba wallahi hotunan nan zasu fara ziyartar gidan *Alhaji Saddi*, kuma dai kasan me zai faru idan surukinka ya ga wannan hotunan." Har ta juya zata wuce sai kuma ta juyo, cikin rashin kunya duk da babu mutane a layin irin sabbin unguwa ne da babu mutane sosai, hannu tasa a aljihun gaban rigarshi ta zaro kud'in ciki, duka ta d'auka tasa a jakarta tana fad'in "Raba mugu da makami ibada ne, ko taxi mun shiga ai." Da kallo ya bita ganin zata shiga cikin gidan yasa shi cewa "Karki shigar min gida Zaleeha, ki wuce ki tafi inda zaki je na yarda zanyi abinda kike so." Juyowa tayi ta kauce Hindu ta shige ita ma tana hararenshi kafin tace "In ka isa ka zo ka hanani mana, ko ka shigo ciki ka fito dani." Shigewa tayi ta barshi tsaye, dukan motar yayi cikin jin haushi ya shiga motar, dukan sityarin yayi yana fad'in "Shiiit! Shiiit!" Dafe kanshi yayi yana tunanin al'amarin, wannan shine *gaba kura baya siyaki*! Alhaji Saddi sirikinshi ne kuma k'anin mahaifinshi, mutum ne mai zafi da kuma son kanshi dayawa, shakka babu zai iya kawowa rayuwar aurensu tangard'a inhar abun nan ya fito, dalilin haka kuma iyayenshi da yan uwa zasu iya hushi dashi, auren gida aka musu da Abeeda, yana masifar son yarinyar dan bayan aurensu yanzu ta canza rayuwarshi sosai, sai dai a baya yayi rayuwar holewa sosai da Zaleeha sanda sukayi soyayya, gashi yanzu abun ya zamar mishi matsala, dalilin haka saida ta nemi k'awance da ita shiyasa yanzu har suke zuwa gidanshi kai tsaye, duk abinda zasuyi in suka zo baida bakin hanasu, gashi yanzu zasu sa shi k'arya, wanda in ya yarda yayi nan ma wata matsalar ce, dan in Tagur ya sani sai ya ci namanshi d'anye. Haka ya tashi motar ya nufi asibiti duk ranshi a jagule. Yana zuwa ya sake dubata dan an riga da an bata kulawar data dace, kallon Tagur yayi yace "Wai akayi haka ta faru ne bayan kunsan Mama na da hawan jini? Irin wannan bai kamata yana faruwa da ita ba." K'ala bai ce masa ba sai kamo hannunshi da yayi suka nufi fita, da kallo gomboy ta bisu tana tunanin da son jin abinda zasu tattauna, dan tana tsoron Allah tana tsoron jarabar Tagur, suna fita har ofishin Omar suka shiga amma babu wanda yayi zaune, cike da son dukan cikinshi ya kalleshi kallo mai tsoratarwa yace "Omar me yasa? Banyi tsammanin amincin dake tsakaninmu zai iya barin ka yarda a cutar dani ba, me yasa baka fad'a min Ridwan ba d'ana bane? Akan me zaka yarda a min wannan cin amanar?" Dukan tara tara gabanshi ya fara yi, kallonshi yayi duk yana neman duburburcewa, da k'yar ya saita nutsuwarsa yace "Ridwan ba d'anka bane? Ban gane ba? Wannan wace irin wasa ce kuma Tagur?" Wani kallo ya masa yace "Kai zan tambaya ai." "Nima tambayarka nake, waya ce Ridwan ba d'anka bane? Sam ban fahimci inda ka dosa ba?" Kallonshi yayi yace "Sanda nayi had'ari ba kai da gomboy likita ya fad'a ma ba zan iya haihuwa ba?" Dagewa yayi ya d'ora hannu a k'irji yace "Ba zaka iya haihuwa ba? Inji uban wa?" Gyara tsayuwa yayi yace "Kana nufin bai fad'a muku haka ba?" Girgiza kai yayi yace "Sam ba ayi haka ba, to wai ma daga ina wannan majiyar ta taso ne? Baka iya haihuwa kuma ka haifi Ridwan." Jinjina kai yayi yana cije leb'en k'asa da tunanin Allah ya taimake ku, dan har ya gama shirya yanda zaiyi bisarsu dukansu hud'un, Omar, Gomboy, Uban Ridawan d'in sai kuma uwar hegun Atta, komawa yayi d'akin hankalinshi na dawowa jikinshi. ________________ Atta ma gida ta koma saida ta fara shiga mak'wabtansu ta sa wata yarinya *Nafi* ta shirya tace zata rakata unguwa, ko da ta gama shirinta ta fito duk yanda uwar ke mata magana ina zata je bata saurareta ba, adaidaita ta kaisu babbar asibitin, nuna kanta tayi a matsayin marar lafiya hakan yasa ta samu katin ganin likitan a sauk'ak'e, amma dole tayi sammakon zuwa dan ta samu ganinshi, sam bata ji dad'i ba ta d'auka zasu samu ganinshi, dan haka suka fito rai a b'ace tana tunanin yanda zata sake fitowa da yarinyar da suke son d'ana tarko da ita, duk da ita ma marar jin magana ce, amma basu fito fili suka nuna mata abinda suke so daga gareta ba, wani abun farin ciki shine sun wuce ta bakin babbar k'ofar shiga suka dakata dan motar dake gabansu ta wuce, wucewa motar tayi suka tsallaka titin, can gefe suka tsaya suna jiran adaidaita. Sun tsayar da adaidaita kenan zasu shiga suka ji ana oda a bayansu, tsayawa sukayi suka kalli motar da mamakin ganin motar data fito daga asibitin nan sannan suka kalli juna sai kuma Nafi ta shiga, Atta ma zata shiga aka sake wata odar, tsayawa ta sake yi dan ta fahimci da su ake, kafin tayi wani yunk'urin mamallakin motar ya fito, had'add'en guy ne da kasan lallai yana jin dad'i, wani lallausan murmushi ta saki, a hankali ta furta " *Dr. Rufa'i Bureima*." Kallonshi ta tsaya yi har ya karaso yana fad'in "Sannu?" A hankali ta amsa da "Sannu likita." "Ya gida madame?" Da "Lafiya lau." Ta amsa mishi tana sake tsareshi da ido, likitan da suka zo nema ne haka gabansu? Jinjina kai tayi tana ayyana ko baida lokacin sai sunyi abinda dama ya kawo su. Tunanin dalilinshi na tsayar dasu ta shiga yi, ta rasa yanda zata kwatanta abun ta ko wace siga, bata tunanin dan sunyi zama a asibitin ne har ya iya ganeta ya zo da kanshi dan su gaisa? Katse mata tunani yayi da fad'in "Wannan k'anwarki ce?" Yanda ya nuna Nafi dake cikin adaidaita a take ta fahimci nufinshi ta kuma gano manufarshi na tsayar dasu, wani sakaran murmushi tayi tace "Eh k'anwata ce, ai wurinka muka zo ma, amma mun samu rendez-vous da kai da k'arfe 07:30 na safe." Kafin yace wani abu ta kalli Nafi tace "Ke fito." Fitowa tayi sai mai adaidaitar daya lek'o yace "Ya Hajia ku fa nake jira?" A wulak'ance tace "Tafi kawai mun fasa tafiyar." Tsaki mai adaidaitar yayi ya tayar ya wuce yana gunguni, kallon Dr. ta sake tana watse hak'ora shi kuma sai kallon Nafi yake, tunda ta lura da haka ta wani had'e fuska tana shan k'amshi, ita kuma Atta tana jin dad'in yanda tarkonsu zai kama kurciya cikin sauk'i haka da basuyi tunani ba, kawar da kanta da tayi ne ya ankara dashi yasa shi kallon Atta yace "Madame muje na sauke ku in ba damuwa? Daga nan sai muyi magana ko?" D'aga kafad'a tayi tace "Shikenan muje." Motarshi suka shiga duka suka fad'a mishi unguwar, hanya ya d'auka amma gaba d'aya hankalinshi na kan Nafi, farar fatarta wacce ta k'ara haske na mai, kasantuwarta siririya kamar dai yanda yake son mace ta kasance ko matarshi, haka take duk ta had'a abinda yake so ga mce, shiyasa tun ganinshi na farko da ita yaji ta kwanta masa, musamman shigarta ta wayayyun yan matan zamani ta nuna mishi ita mai ilimi ce da wayewa. Saida sukayi nisa ya kalli Atta yace "Yayarmu baki fad'a min waye ba lafiya ba?" Ajiyar zuciya ta sauke tace "Karka damu zan fad'a maka, muje dai yanzu ka sauke mu." Jinjina kai yayi bai sake cewa komai ba, ta madubi ya hangi fuskar Nafi da kanta ke kallon hanya tayi shiru, murmushi yayi yace "Yayarmu ita k'anwar nan taki bata magana ne?" Juyawa tayi ta kalleta tayi murmushi tace "Tana yi mana, sai dai komai na k'anwata tsada ne dashi." Dariya yayi yace "Yayarmu to ai a shirye nake da biyan farashina ko nawa ne, kawai a fad'a min da azama zan biya ko tayawa babu." Murmushi ta sake yi sai shi da yace "Ya jikin mai gida? Ina fatan dai yayi sauk'i ko?" A tak'aice ba tare data kalleshi ba tace "Mun rabu?" Da sauri ya kalleta da mamaki, sun rabu? Ya maimaita a ranshi, amma sai yayi shiru da tunanin larurar data same shi tasa ta guje shi, kuma ba zai ga laifinta ba dan yanzu kowa na son ganin k'wanshi a duniya, haka kowa yayi shiru har ya isa gidan ya sauke su, suna fita a motar gaba d'ayansu da ido ta ma Nafi alama data shiga gidansu, ba tare data kalleshi ba kam ta wuce ciki wanda hakan ya k'ara birge shi sosai. Kallon Atta yayi yace "Yayarmu gaskiya ina son magana dake? Ya za ayi yanzu?" Murmushin mugunta ta mishi tace "Karka damu likita, zaka iya dawowa duk sanda kake so." "Kamar yaushe?" Da fara'a tace "Ko anjima ma idan kana da dama." Da zumud'i yace "Da gaske? Wallahi zan iya zuwa idan kin bani dama, dan maganar na da muhimmanci dan ta shafi rayuwata." Da murmushin nan a fuskarta tace "Baka da matsala likita, idan ka shirya kawai ka zo zamu tarbeka." Jinjina kai yayi yace "Fatan dai zan samu ganin har k'anwar nan taki ko?" D'aga kai tayi alamar eh tace "Sosai ma." Murfin motar ya kama yana fad'in "Shikenan saina dawo, sai anjima." Ita ma sai anjima ta masa ta shiga ciki, inda ta samu Nafi ta fad'a mata tayi hak'uri ta bata had'in kai sun kusa cin ma gaci ma. _______________ Saida suka sauka kusan magriba sun fito a mota ta mayar da wayarta a jaka ta ga enveloppe d'in da Aminu ya bata, da sauri ta ciro tana bud'ewa, girgiza kai ta shiga yi tana fad'in "A'a Aminu, a'a fa, ya zaka min haka?" D'an guntun tsaki tayi tana mayar da enveloppe d'in kud'in tana sake zago wayarta, ta so kiranshi sai kuma taga anfanin me hakan zai mata, kawai gwara ta bari har ta koma ta same shi. Taxi ta samu ta fad'a mishi zai kaita unguwar cit茅 soraz ne, har k'ofar gidan kam ta nuna mishi ya sauketa, fita tayi dan kar ta b'ata mishi lokaci, amma saida ta ga sun tsaya taji kamar ta juya ta koma, duk sai yaji ta tsargu yanda har saida ta jawo lafayarta ta rufe rabin fuskarta, wata kunya taji tana shigarta na mutanen data rayu dasu, kallon unguwar tayi ba wani abu bane ya sauya sai wasu gidajen wa aka rufe akayi sabbi ko shago, tana kallon d'aya k'ofar gidan na mahaifinsu inda kishiyar mamanta take gabanta ya sake fad'uwa, ajiyar zuciya ta sauke mai k'arfi ta d'auki jakarta ta d'aga k'afa da k'yar ta fara takawa, k'afarta cijewa take tana son yi mata nauyi, hakan yasa tafiyar take yinta kamar wacce aka tilasta, da yake k'ofar a bud'e take wuni dama kawai shiga tayi ba tare da sallama ba dan komai nata ba aiki yake yi ba, idonta kawai take motsawa tana k'arewa gidan kallo hawaye na taho mata tun bata ga kowa ba. Saitin k'ofar d'akin ta tsaya a cikin runfar tole d'in dake walale a farfajiyar gidan, a saninta da gidan babu wannan runfar haka ma babu shafen nan na sumutin, amma yanzu an gyara hakan yasa gidan ya k'ara haske yayi tsaf, ga kuma wani b'angaren da aka kewaye wanda yasha gyara sosai yafi na iyayenta, hakan yasa ta ayyana a ranta ko nan yaya Barka zai zauna da matar tashi?Sake juyawa tayi b'angaren da ban d'aki take, wata shukar tumatir data gani tasa ta sakin murmushi a bazata, tunawa da tayi irin rayuwar da tayi a gidan da yanda shukar nan ta shiga tarihinta ita ma, sake kai kallonta tayi kan d'akin dake rufe na mahaifinta, saida taji wani murd'awar ciki, dan abu na farko daya fara zuwa mata kuma wanda ya zama dhine na k'arshen shigarta d'akinshi sai yau data shigo gidan, wacce ranar da ba zata manta da ita ba, wasu hawaye taji sun sake taho mata kamar an kunna panpo. Aje jakar hannunta tayi tasa tafin hannunta ta d'ora a wuyanta, ta juya da niyyar sake kallon gidan karaf idonta ya sauka cikin na mahaifiyarta dake tsaye a gefenta da buta a hannu da alama daga ban d'aki take kuma alwala zatayi, wata girgiza taji duka k'irjinta yayi, bud'e baki tayi kamar zatayi magana sai kuma kuka ya kasa barinta, d'an baya taja kad'an tana neman durk'ushewa, dan k'afafunta rawa suke mata ta tabbatar ba zasu iya d'aukarta ba, kamar jiri ya kwasheta haka taji ta durk'ushe a wurin ta fashe da kukan daya taho mata da k'arfi, rufe fuska tayi ta hannayenta biyu tana girgiza kai ta kasa cewa komai. Ita ma sakin butar tayi da azama ta k'araso inda take, durk'usawa tayi ta rumgumota jikinta tana fashewa da kuka ita ma mai tsanani, jin d'umin mahaifiya da soyayyarta yasa ta sake narkewa tana kuka daga k'asan zuciyarta kamar ranta zai fita, daddab'ata ta shiga yi cikin kukan tayi k'arfin halin fad'in "Ya isa haka Fati, kukan ya isa haka, farin ciki ya kamata muyi ba kuka ba." Ba tare data tsagaita ba muryarta a disashe ko fita ba tayi har tana tuntub'e tace "Ayya kiyi hak'uriki yafe min, Ayya ina jin kunyar had'a ido dake." Cikin rarrashi da shashek'ar kuka tace "Nace ya isa haka ko? Me yasa zamuyi kuka a wannan lokacin? Fati?" Cikin son kwantar da hankalinta da daina kukan tana jan numfashi ta amsa da "Na'am Ayya." Mik'ewa Hadizey tayi ta tallabota ta mik'e ita kanta k'asa tana ta share hawaye, k'ok'arin kallon fuskarta take amma tana nok'ewa, saida ta tallabo hab'arta tace "Fati fuskarki nake son kallo, ina so na ga yanda kika canza." A hankali ta d'ago tana ziraro hawaye ta kalleta, murmushi ta saki ta tallabe fuskarta da duka hannayenta tana fad'in "Masha Allah yarinyata ce ta girma haka? Fati kin ganki kuwa?" Cikin share hawaye tace "Ayya ke kuma kin rame, baki da lafiya ne?" Murmushi ta sake mata tace "Humm! Fati a cikin 'ya'ya biyu daka mallaka ka rasa guda, kuma kasan inda yake amma an tirsasa maka mantawa dashi, taya zaka iya zama lafiya har kayi kumari?" Wani kuka ta kuma fashewa dashi ta fad'a jikinta tana sake jadadda "Ayya ki yafe min, duk ni na ja miki wannan tozarcin, Ayya nasan kinsha gori da habaici duk a dalili na." Da sauri ta d'agota tana fad'in "Dan Allah kukan ya isa haka, Fati duk habaicin mutane bai dameni ba tunda ni dai nasan wacece 'yata." Hannu tasa ta shiga share mata hawayen tana fad'in "Shiga ciki ki aje kayaki ki zo kiyi alwala, idan munyi sallah sai muyi hira ko? Dan yau babu abinda zai hana ni shafa kanka bayan kinyi kwance akan cinyata." Murmushi tayi wanda ya fito da hak'oranta ta jinjina kai, juyawa tayi ta sunkuya zata d'auki jakarta, k'afafun data gani tsaye a gabanta ne yasa gabanta tsananta fad'uwa, ko a mafarki ta ga k'afafun tasan mai su, dan haka a tsorace da tunanin yanda had'uwar tasu zata kasance ta d'ago tana ja baya, ido cikin ido suka kalli juna amma da sauri ta d'auke na ta idon, durk'usawa tayi bakinta na rawa sosai kamar wacce sanyi ya kama, sunkuyar da kanta tayi tana jran sake shan wani dukan mutuwar daga gareshi. Da kallo fuskarshi zaka gane babu alamar farin ciki da ganinta, amma acan k'asan zuciyarshi ji yake kamar ya tafi a sukwane ya rumgumo 'yarsa, fushi ne kawai yake da ita irin na k'i fad'i da taurin kai, amma fa a zuciyarshi ya jima da yafe mata da kuma tsananin son ganinta, lokuta da dama zuciyarshi na raya mishi ya ziyaraceta, amma kuma yana ganin kamar bai dace ba, dan har yanzu yana sake jinjina girman al'amarin, Faduma ita ce yarinya ta farko kuma ta k'arshe a duk cikin 'ya'yansa goma sha d'aya daya fi so, ba dan ita ce ta farko ba sai dai son dan biyayyarta gare shi, kuma ita ce k'arama a duk cikin mata guda uku da yake da su, sannan ya ga anfanin kasancewarta mace, dan kaf yaransa babu mai tausayinshi sama da ita. Inhar yace baiyi farin cikin ganin wannan mitsitsiyar yarinyar tashi ce ta zama haka ba yayi k'arya, yanda ta girma ta wanke tayi fes ga tsantsar wayewa da kuma al'adarta daya gani tun daga suturarta da kuma jikinta yasa shi jin dad'i sosai. Butar dake kusa da d'akinshi kawai ya d'auka ya fita jin anata kiran sallah cikin sauri ba tare da yace komai ba, yana fita ta d'ago kai ta kalli inda ya tsaya, juyawa tayi ta kalli Ayya da sauri ta matso ta kamata ta mik'e tana fad'in "Kinga wuce kiyi alwala." Cikin muryar kuka tace "Ayya Aba ban ce min komai ba, ina jin tsoron shirun nan." Girgiza mata kai tayi tace "Karki damu Fati, babu abinda zai faru, saida Abanki ya amince sannan na yarda ki zo." Murmushi tayi tace "Ayya da gaske Aba ya amince na zo?" Jinjina mata kai tayi alamar eh, da sauri ta d'auki jakar ta shiga d'akin, dariya ta saki tana k'arewa d'akin kallo ta ko ina, har yanzu dai d'akin yana nan kamar yanda yake, a tsaftace kullum cikin gyara da sauya masa jere, sai dadad'an k'amshin turaren wuta da har ya zama jiki a d'akin, k'asa ta aje jakarta ta cire lafayarta, hakan yasa riga da siket d'inta suka bayyana wanda suka karb'i jikinta sosai suka mata kyau, fitowa tayi ta samu Ayya ma na alwala, kallonta tayi da murmushi a fuskarta tace "Duniya kenan? 'Yar k'aramar yarinyata ce ta zama haka? Ta zama babbar mace, wacce yanzu babu wani k'alubale da zata iya fuskanta na k'arancin shekaru, Allah na gode maka daka sake nuna min fuskar 'yata kafin ka karb'i raina." Saida ta tsuguna inda buta take ta kalleta tace "Ayya nima na godewa Allah, kullum ina jin kamar na zo na ganku, amma ina tsoron Aba da kuma bakin daya gindaya min." Murmushi kawai tayi suka ci gaba da alwala har saida Ayya ta idar ta taso zata shiga d'aki, kusa da ita ta tsaya tana kallonta murya k'asa k'asa tace "Ya yake? Yanzu ya girma ko?" Kallonta tayi da mamakin yanda saida ta sassauta murya sannan tayi tambayar, murmushi ta mata tace "Ayya yana lafiya, ya so na zo dashi amma ban yarda ba dan gudun sab'a umarninki." Juyawa tayi kawai ta shige d'akin tana jin ba dad'i, ita ma tana idawa ta mik'e ta shiga d'akin, inda Ayya ta shinfid'a mata sallaya ta ciro hijab a jakarta ta kabbara sallah, kusan a tare suka idar duk sukayi azkhar da addu'o'i, Faduma na gyara zamanta Ayya ta kalleta tace "A'a ba zama zakiyi ba, tashi maza kije kiga Ayyarki." Shagwab'ewa tayi tace "Ayya ki bari muyi hira, zan je daga baya." Girgiza kai tayi tace "A'a Faduma, tashi maza ki je, ko kinsan a dalilinta ne kika zo garin nan? Banyi tunanin kiranki ba ita ta matsa min na kiraki, kinsan ita ba tsoron hargagin mahaifinku take ba?" Dariya tayi ta mik'e tana fad'in "Shikenan Ayya bari naje." Lafayarta ta d'auka ta d'aura da kyau, hoda ta d'auka ta gyara fuskarta sannan ta fita. *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 17:09 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _14_ Suma suna shigowa garin suka samu tarba daga wajen Kalli da kanshi, masaukin bak'inshi ya kaisu inda acan ma sun samu wasu abokanansu dake nesa duk sun amsa gayyatar daya musu, wanka ya fara yi tare da alwala suka yi jam'i anan cikin gidan gonar, sun idar da sallah zasu koma ciki dan cin abincin da aka tanadar musu Kalli ke fad'in "A gaskiya Adam naji dad'in zuwanku, ban tab'a tunanin zaku zo ba musamman ma dai su o'o." Wani kallo Hasheer ya mishi ta gefen ido ya murmusa kawai, dariya Adam yayi yace "Me yasa ka ce haka? Duba da shi ya kawoni nan." Cikin gurguwar hausarshi yace "Saboda sanda na gayyace shi ya fad'a min yana da sabgogi dayawa ba lallai ya zo ba." Murmushi Adam ya sake yi yace "Sai gashi ya baka mamaki ko?" "Nayi farin ciki kam, kuma nima insha Allahu zan amsa gayyatar walimar daya shirya ta sabon gidanshi." Har suka k'arasa cikin babban falon mai salon arab, abinci suka samu wanda gurasa da gasashen nama suka fi yawa, hira suke sosai sai dai shi kallonsu kawai yake, shi yasan abinda ke damunshi kawai, yanda ya k'urawa Alhaji Nuhu ido kamar baya fahimtar yarenshi yasa Adam zungurarshi, Nuhu daya fahimci kallon da yake masa ne ya tab'e baki yace "Kai barshi ya kalleni, mamaki nake basa na sani, ni wallahi iya gaskiyata na fad'a inhar na samu mata a garin nan sai nayi aure." Cikin zolaya Adam yace "To me zai hana idan Kalli na da k'anwa saiya baka kaga ba sai kasha wahalar nema ba." Duk dariya aka saka inda wasu ke fad'in ai kam haka yayi, Kalli ne yace "Ina da yan uwa mata kam har uku, amma duka sunyi aure." "Ai ba zaka rasa yar uwa ba." Cewar Nuhu, Kalli ne yace "Hakane kam, amma ma fu auren fari muna yin na gida ne, amma in ka shirya zaka iya dagewa har sai ka samu to ba matsala." Cike da tabbatarwa yace "Wallahi zan iya in dai zan samu, yo ina da ira irenku da su Hasheer a hannu ai babu 'yar da zan nema ban samu ba." Wani uban tagumi Hasheer ya zuba yana kallonshi yace "Hmmm! Nima ban sama ma kaina abinda nake so ba bare na sama ma wani." Duk kallonshi sukayi sai kawai ya mik'e tsaye ya nufi d'akin da suka sauka yana fad'in "Kowa yaji da matsalarsa." Cikin d'aga murya Nuhu yace "Lah! Hasheer ni zaka bawa kunya? Kai yanzu meye kake so da baka samu ba?" Ko juyowa baiyi ba bare ya tanka masa har ya shige d'akin, ci gaba sukayi da hira cikin nishad'i da farin ciki. Hasheer kuma a ciki wayarshi ya sake d'auka ya shiga kallon lambar nan, kira ya aika wanda yin hakan ya haifar masa da bugawar zuciyar da sauri sauri, haka kawai yaji duk yanayinshi ya canza har wani gumi gumi yake, kusan har yafi jin sautin bugawar zuciyarshi kan 'dinnn! 'dinnn d'in da wayar ke yi alamar sone (ringing), rintse idonshi yayi ya cije leb'e yana furta "Hasbunallah wani'imal wakil." Har tayi ta gama ba'a d'aga ba, saida yaji tsayawarta ya sauke wata k'akk'arfar ajiyar zuciya? Sakin wayar yayi ta fad'i k'asa shi kuma ya fad'a kan katifar ruf da ciki, bai sake d'agowa ba har kira yaji ya shigo wayar amma halin da yake ciki yasa shi k'asa d'agowa bare ya d'auka, duk da idonshi rufe suke kuma ya danne fuskarshi a tsakiyar pillow bai hanashi hango kyakyawar fuskarta sanda take murmushi ba, sanyayyan k'amshin turarenta har yanzu yana iya hasasho yanda k'amshinshi yake. Yana samun kanshi cikin tsananin tashin hankali in yaji yanda zuciyarshi ke bugawa a dalilinta tunawa kawai, yana shiga damuwa in yaji yanda zuciyarshi ke neman jawo mishi abinda yafi k'arfinshi, yanda ta iya durmiyawa cikin zuciyarshi lokaci d'aya yana tsorata shi, yanda ta dagula tunaninshi da lissafinshi cikin k'ank'anin lokaci yana bashi mamaki, wasu lokutan ma har ya kan tambayi kansa ba matar aure bace kuwa? Anya ba ta auri wani bayan rasuwar uban yaron ba? In kuma bata da auren ta iya yiwuwa tana da masoya, dole ma haka ta kasance dan ba zata rasa masoya ba, to akwai wanda take so a ciki? Wannan tambayar da rashin amsarta ma yana sa yaji kamar zai wa kanshi kuka. Bai motsa daga nan ba saida yaji ana kiran sallah isha'i, tashi yayi ya d'auki wayarshi ya duba kiran da aka mishi, *Umma na* ne ya fito akan kiran da ba a d'aga ba, soka wayar yayi aljihu da tunanin zai sake kira idan ya dawo daga masallaci. ______________ Kai tsaye gida ya wuce dashi, a harabar gidan ya paka mota suka fito, yana rik'e da jakar kayan Amjad d'aya hannunshi kuma ya rik'e hannunshi, ganin yanda yake kalle kalle ne yasa shi yin murmushi yace "Gidan ya maka ne?" Kallonshi yayi cikin jin kunya ya d'aga kai kawai alamar eh, a d'an terrasse d'in wurin suka cire takalminsu tareda yin sallama suka shiga, babban falo ne da d'akuna da kuma mutane ta ko ina, ko dan yana rana ne a k'alla mutanen falon ba zasu gaza goma ba, kuma duk alamu ya nuna yan gidan nan dan kowa harkar gabanshi yake mafi yawansu kuma kwance wasu na cin abinci mata da yara, amsa musu sallamar akayi bayan haka babu wanda yace wani abu, ba tare da sun zauna ba ya kalli wata babbar mace mai manyan shekaru a jiki da fuska yace "Mama ina wuni?" Tun shigowarshi dama take kallonshi dan haka ta amsa mishi da "Lafiya lau Aminu, an dawo?" Takawa ya fara yi zuwa inda take zaune yana fad'in "Na dawo Mama, ya gida." A madadin ta bashi amsarshi sai cewa tayi "Wannan yaron fa daga ina kake dashi?" Cikin tattausan murya Amjad yace "Ina wuni?" "Lafiya lau." Ta amsa tana kallonshi, Aminu ne yace "Mama d'an Faduma ne, Amjad." Da mamaki tace "Faduma kuma? Wacece hakanen?" "Mama abokiyar aikina da nake fad'a miki." Cikin fahimta tace "Ahan na gane." Kallon yaron tayi tace "Sannu yan samari." A hankali Amjad yace "Sannu Mama." Aminu ma kallonshi yayi yace "Kana cin abinci?" Girgiza kai yayi tare da cewa "Na k'oshi." Jinjina kai yayi ya kalli sauran matan iyayen ya gaishesu suma suka amsa duk babu sakin fuska a tare dasu, bai damu ba bare abun ya damesa dan haka y jashi suka wuce wata k'ofar da ita ma ta fita ce kamar dai ta shigowa, suna ratsawa ta cikinta suka wuce wurin girki, daga can waje d'akunan maza suke, sai dai in ba abun hawanka kake son shigowa dashi cikin gidan ba ba lallai asan ka shigo ba, bud'e d'akinshi yayi suka shiga tare da Amjad, lafiyayyar shinfid'ar dake kan gadon ya nuna masa yace "Ka kwanta ka huta, idan lokacin islamiyya yayi saina tashe ka shirya." Girgiza kai yayi yace "Abdo k'arfe uku na ke so na tafi, saboda musabik'ar da za ayi ina so na dinga samun muraji'a ta awa d'aya a cikin makaranta." Murmushi yayi yace "Ayyarka ta fad'a min komai, karka damu ka huta kafin lokacin sai ka shirya mu tafi." Jinjina kai kawai yayi tare da jawo jakarshi yana laluba, wani Alqur'ani ya fito dashi mai kyau wanda ke cikin gidanshi tare da k'aramin littafi na addu'a da wani micro na karanta k'ira'a, zaune Aminu yayi yana kallonshi yace "Kana rik'e Qur'ani kenan?" Kallonshi yayi yace "Obdo ai musabik'ar da zamuyi ta karatun Qur'ani ce, amma ba hadda ba." Jinjina kai yayi yace "Kamar ka bani shi? Dan ya birge ni gaskiya." Da sauri ya rufe Qur'anin yana mayar dashi bayanshi kamar zai k'wace masa, kallon shi yayi yana dariya yace "Ba zaka bani ba kenan?" Girgiza kai yayi yace "Ba zan iya rabuwa dashi ba, Ayya ta ce ta bani kuma ita ma ta fad'a min ta same shi ne sanda ta cinye gasar hadda Alqur'ani da akayi a duk africa." Da murmushi a fuskarshi yace "Ta fad'a maka kenan?" D'aga kai yayi yace "Kai ma ka sani kenan obdo?" Shima jinjina masa kai yayi, gyara zamanshi yayi yana kallonshi sosai yace "Obdo kasan komai game da Ayyata, dan Allah ka fad'a min me yasa bata san nuna min danginta da dangin Aba na?" Gyara zamanshi yayi yana fuskantarshi ya shafa kumatunshi cikin nutsuwa yace "Amjad, ka fahimci Ayyarka kaji, karka shiga tunanin komai idan ba yanda zaka farantawa Ayyarka ba, ita mai k'aunarka ce da kuma son kula da kai, adalcin da zaka mata shine ka sa a ranka kamar ita kad'ai gareka sannan ka zama mai mata addu'a akan samun farin ciki mai d'orewa, kaji ko?" Kafeshi yayi da ido kamar mai tunani sai kuma ya jinjina kai alamar to, mik'ewa yayi ya cire kayanshi saida ya rage daga singlet da gajeron wando ya d'auki towel ya fita dan yin wanka. ________________ Bayan sallah la'asar anan masallacin asibitin yayi sallah, dawowa yayi d'akin ya samu jikin Hatimi da sauk'i sosai, sannan ga yaran duka a tare da ita, kallon Hatimi yayi wacce ke kallonshi tarrr yace"Ayya zan je gida na dawo, akwai abinda kike buk'ata?" Kallonshi kawai take, kamar ba zatayi magana ba sai kuma ta tab'e baki tace "Hummmm!" D'auke kanta tayi daga inda yake, jikinshi ne duk yayi sanyi sai Gomboy daya kalla ya mata alama da hannu yace "Ke zo nan." Kallonshi tayi da garare jin yace wani wai ke! Tasan dai babu abinda zai mata dan haka ta mik'e ta bi bayanshi kamar yanda ta ga ya nufi k'ofa, a k'ofar d'akin ya tsaya tana zuwa ya kalleta da kyau yace "Me kika sani game da ita?" Kallon bi-aho ta masa tace "Wa fa?" K'wafa yayi ta jin haushi yace "Fadu." Tab'e baki tayi tana yatsina fuska tace "Ban sani ba nima, yau ne na k'ara ganinta tun rabuwarku." Gyara tsayuwa yayi ya shiga nunata da yatsa yana fad'in "Gomboy wallahi ki daina wasa dani, baki da wata k'awa sama da Atta a garin nan, tunda har Atta tasan Faduma na da yaro dole ke ma kin sani, ki fad'a min in ba so kike na huce akan ki ba." Saida ta ja baya kamar zata shige d'akin tace "A'a kaga malam kar ka min masifa, ni bansan inda take ba amma dai su nasan sun sani, ka kira Atta ta fad'a maka ko kuma ka je gidansu." Zaro mata ido yayi yace "Ke baki da hankali ne? Atta ce zan je gidansu ko na kirata? Ai duk hanyar da nasan zata iya had'ani da ita ma na daina bi, ke dalilin biyu ne yasa na ci gaba da rik'e waya a hannu na, ba dan haka ba da ni da waya ma har abada saboda tuna ina kiran Atta da waya." Galala ta kalleshi sai kuma ta tab'e baki, wayarta ta shiga dannawa tace "To d'auki lambar Hindu in baka saika tuntub'eta." Saida yayi kamar zai zabga mata mari yace "Wai miye na son sai kin had'ani da yan iskan nan? Ke ba zaki iya kiranta kiji ba?" Yanda ya tsareta da ido yasa dole ta dannawa lambar Hindu kira, hararanta yayi yace "Sa a spika (speaker)." Lokacin su Hindu sun fito daga gidan Omar ta d'auki kiran, ko gaisawa basuyi ba tace "Uwar d'aki na yarinyar nan wai Faduma me kika sani akan ta ne?" Daga b'angarenta tace "Fadumar? Mak'wabtaka muke fa, gida uku ne tsakaninmu dasu." Gomboy ce tace "Kuma da gaske tana da d'a?" "Wace irin tambaya ce wannan? D'a ko saurayi? Yaron daya kusa bawa shekara takwas baya." Kallon juna sukayi da Tagur daya k'ura mata ido kamar zai had'eta, jinjina kai tayi tace "Ok zamu sake waya." Yanke kiran tayi tana kallonshi yace "Ina ne unguwar?" A tak'aice tace "Zarya 2 bayan LDB (Lyc茅e D'an Baskore)." Kamar jira yake sai kuwa yayi fit ya wuce da sauri, da kallo ta bishi har saida ta daina ganinshi, girgiza kai tayi cikin matsanancin jin haushi da k'ara tsanar Faduma, tsaki tayi ta juyo ta dawo d'akin yan uwanta da suke ciki d'aya suna tambayarta lafiya? Babu wacce ta kula dan a k'ufule take da kowa da komai. Yana hanyar zuwa gidan aka kirashi kan wani aiki, bai iya tsallakewa ba dole ya fara nufa can, bayan sun kammala ya karb'i k'wangilar kawo kujerun da aka buk'ata ya d'auki hanya, har wajen aje motoci ya aje motar ya shiga b'angarenshi wanda ke daf da wajen aje motocin, da sauri sauri ya shiga yayi wanka ya fito ya shirya cikin wata d'anyar gezner fara tas, hula ya d'ora fara mai kwalliyar bak'in zare kamar aikin dake jikin rigar, sai agogon dake ta k'yalk'yali ta farin narkakken k'arfen wacce aka shafe da farar zaiba, saida ya feshe jikinshi da turarukanshi Dolby da Couture kafin ya d'auki makullin wata motar ya fito, yamma tayi sosai shiyasa ma daya fita ya fara tsayawa yayi sallah a jam'i har aka idar kafin ya d'auki hanya. Saida ya tsaya k'ofar gidan yayanshi Aji, babban d'anshi ya samu a k'ofar gida tare da abokanshi suna hira, da ladabi ya k'araso wajenshi yana gaishe shi, fuska a had'e ya amsa mishi da "Lafiya lau, Ridwan yana ciki?" Jinjina kai yayi yace "Eh yana ciki." Ba tare daya kalleshi ba yace "Fito min dashi." Juyawa yayi ya shiga cikin gidan, jim kad'an ya fito d'auke da yaron a kafad'a da yake irin yaran nan ne masu k'aramin jiki, ta b'angaren da yake ya bud'e ya amshi yaron ya zaunar da shi kujerar gefenshi, da farin cikin ganin babanshi ya shiga fad'in "Baba, gida zamu koma? Baba ka kaini wajen Haja." Da murmushi ya kalleshi yace "Can zamu tafi ai, kayi wasa anan tare dasu Abdul?" D'aga kai yayi ya shiga fad'in abubuwan da suka yi, shi dai yana saurarenshi yana hango yanda zaiyi da Faduma, tafiya sukayi mai nisa kafin suka isa unguwar, kwana d'aya ta biyu suka shiga inda ya ga yara na wasa, daidai yaran ya tsaya yana sauke gilashin motar ya lek'o kai yace "Sannunku." Duk kallonshi sukayi suna amsawa da yawwa wasu kuma na fad'in ina wuni? Cikin taushin murya yace "Dan Allah tambaya nake gidansu Faduma." Kallon juna yaran sukayi suna magana k'asa k'asa sai kuma d'aya ya kalleshi yace "Faduma lauya?" Da sauri ya d'aga kai yace "Eh ita." Kwanar baya ya nuna mishi yace "Ga kwanar nan baya ka baro, daka shiga gida na farko ne gidansu hannunka na dama." Da murmushin jin dad'i ya jinjina kai yace "Nagode sosai." Juyawa yayi cikin nutsuwa ya sale dawowa ya shiga kwanar, daidai k'ofar gidan ya tsaya yana kallon k'ofar, gidan waye take anan? Ita da wa suke zaune? Tayi aure ko kuwa har yanzu? Kallon Ridwan yayi yace "Ka jira ni anan kaji? Yanzun zan dawo." Da kallo ya bishi har ya fita ya tsaya k'ofar gidan, waigawa yake ko zai samu yaron da zai iya turawa, amma shiru babu kowa a cikin layin, yayi kamar minti uku yana tunanin abunyi, daga k'arshe kawai ya k'wank'wasa k'ofar gidan da kanshi. Jin ana k'wank'wasa k'ofar gidan ya tabbatar mata ko ma wanene bak'o ne, bak'on kuma a ganinta na Faduma, dan ita duk abokan kasuwancinta suna shigowa daga ciki ne bayan sunyi sallama ta musu izini, wasu ma tana sanin zuwan nasu tun a waya kafin su zo, Faduma kuma da ba soyayya take so ba ko ka tambayeta gidansu ba fad'a take ba, sai dai in tambaya kayi aka fad'a maka, shiyasa ta d'auki gyalenta ta fito, sake turo k'ofar tayi dan ko ma wanene yana daga bayan k'ofar ne, tana d'ora ido akan matashin wanda ya had'u kamar wani sabon ango gabanta ya fad'i, d'an sake fitowa tayi ba tare data d'auke idonta akan shi ba, cikin tsantsar mamaki idonta a kanshi kamar zata cinye shi tace "Mafarki nake yi? Ko kuma fatana ne zai cika saboda a duniya ban da buri daya wuce na had'u da kai?" Ya gane matar kam hakan kuma ya haifar masa da samun nutsuwa da kwanciyar hankali, tunda dai tana taren da k'anwar mahaifiyarta ai Alhamdulillah, sake sunkuya kai yayi k'asa bai ce komai ba, jinjina kai tayi ta k'arasa fitowa daga gidan gaba d'aya ta dafe k'irjin tana fad'in "Tagur! Kai da kan ka?" Wata dariya tayi kamar zararriya ta d'aga kai sama tace "Heeeee! Ya Allah, Tagur dai?" D'an d'ago kai yayi shi dariya ma take son bashi, dan kafin ya fara tunkararsu saida ya barbad'owa kanshi hodar rashin kunya da shanyewa sannan, yana kallon fuskarta yace "Ina wun..." Da sauri ta dakatar dashi da yatsa tace "Karka fara, karka fara Tagur, wallahi ranka zai b'ace." Gyara tsayuwa tayi tace "Me ya kawoka gidana? Me ka zo yi nan Tagur?" K'asa yayi da kanshi yana d'an sosa k'eya ya kasa cewa komai, tapa hannayenta tayi tana fad'in "Lallai Faduma tayi gaskiya da tace zaka zo, to amma abinda ban gane ba ni shine me ka zo yi nan dan Allah?" D'aga kai ya sake yi ya kalleta, cikin taushin murya sosai yace "Dada na zo wajen Faduma ne." "Faduma? Me zata maka? Miye tsakaninka da ita?" Fuskarta ya kalla amma ba cikin idonta ba yace "Za muyi magana ne." Mirmushi tayi tace "Ni Owwo? In sake baka dama ka gana da 'yar yar uwata? Ai har abada Tagur, kai yanzu ko kunya baka ji ba har ka zo gidan nan ka kalleni ka ce wai zakayi magana da Faduma?" Saida ta dafe k'ugu tace "To bata nan, sai me kuma?" Da mamaki ya kalli agogon hannunsa ya kuma kalleta yace "Dada ina Faduma taje a wannan lokacin bata gida?" Da mamakin ita ma ta kalleshi tace "Iyeee! To ina ruwanka? Zamanka take ko ka bata ajiya ne?" Wani iska ya d'an furzo kawai ya sake kallonta yana had'e yawu yace "To Dada ina d'ana yake? Shi na zo gani." Da k'arfi ta dafe k'irji ta d'aga murya tana fad'in "Laha'ilaha illalahu, inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, d'anka kuma? Tagur kai ne ke furta d'an ka yau?" Cire gyalenta tayi ta d'aure k'ugu dashi tam ta kuma dafe k'ugun tace "Karka d'auka uwar Faduma ce ni ka ce zaka min fitsara da rashin kunya, idan t'akamar d'an zamani ne kai nima tsohuwar zamani ce, wallahi ka sake bud'a bakinki gabana ka ce wani wai d'anka saina tsinkeka da mari." Satar kallonta yayi, yanda tayi kuma take tsaye a gabanshi ya nuna mishi zata iya marin nashi kam, ko da hakan ya faru dole zai hak'ura ya shanye dan yasan ya cancanci fiye da haka ma, amma fa sai yayi zazzab'i na rashin ramawa inhar ta mare shi. Muryarta ya sake tsinkaya tana fad'in "Tun kafin na maka abinda ba kayi tsammani ba ka b'ace daga k'ofar gidan nan, in ba haka ba kuma duk abinda na maka kai ka siya da kud'inka." Juyawa tayi zata koma ciki tana ci gaba da masifa, k'ofar gidan ta ja ta rufe da k'arfi ta bar shi nan tsaye, kallon k'ofar gidan yayi ya cije leb'en k'asa yana tunanin matar fa ta gurza mishi rashin mutumci sosai, ajiyar zuciya ya sauke yana shigar da leb'en sama a cikin bakinshi ya nufi mota, yana zuwa ya tayar suka bar unguwar amma fa gobe ma zata ganshi gidan nan, ba kuma gobe kawai ba har sai ranar daya ga d'anshi. ______________ Tana fitowa ta tunkarin gidan, tun daga nesa zaka iya gane shige da ficen da ake yi, har ta isa bakin k'ofar ta shiga soron, hayaniyar mutane ta fara mata maraba, murmushi ta saki na jin dad'in yanda kan iyayensu ke had'e, tsabar had'in kansu ne yasa gashi auren yayanta a gidan Dada Herde ake yi, ita kuma acan ka rantse ba gidan sabga bane, sallama tayi k'asa k'asa tana shiga jikinta sai wani b'ari b'ari yake na tsoro, duk da duhu ne amma da yake akwai hasken fitila kowa na ganin kowa, duk kallon k'ofar kowa yayi tare da amsa sallamar ga wanda Allah ya ba ikon amsawa, amma dayawa basu k'arasa amsawa ba sukayi shiru, wasu kuma sun amsa amma dole sukayi sororo. Abu ne da dama tayi tsammanin ganin haka, amma gubar dake tattare da ido ta wuce yanda take tunani, hakan yasa ta kasa motsawa ta tsaya kallonsu ita ma. Yayarta *Zeinaba* ce ta fito daga d'akin da leda a hannu, jin shiru da kuma ganin suna kallon k'ofa yasa ita ma kallon k'ofar, zaro ido ta sake yi da sauri ta matso tana fad'in "Fatima? Ke ce?" Shiru tayi sai kallonta kawai da take, da gudu gudu ta taho ta rumgume Faduma tana fad'in "Faduma, Ayya zo kiga Faduma." D'agowa tayi daga jikinta suka kalli juna, dukansu farin ciki da murna ne ya bayyana a fuskarsu, tab'a ko ina na jikinta ta shiga yi tana fad'in "Faduma ke ce? Yaushe kika zo?" Murmushi tayi kafin tayi magana dattijuwar sosai ta fito daga d'aki tana fad'in "Zeinaba wa naji kina fad'a?" A tare suka kalleta, da gudu Faduma ta k'arasa gareta dan kamar uwa take d'aukarta, rumgumeta tayi tana kukan farin ciki, ita ma kukan ta shiga yi na farin ciki tana fad'in "Faduma ashe kin zo? Ya hanya Faduma? Kin zo lafiya?" D'aga kai tayi ta kalleta tace "Ayya lafiya lau, ya kike Ayya?" D'aya yayarta ma fitowarta kenan daga d'aki tayi sallah, farin ciki sosai sukayi da ganin yar uwarsu, ita ma taji dad'in yanda suka nuna mata farin ciki ba tare da sun nuna sun tuna abinda ya faru ba, sauran yan uwan ma da suka yi mamakin ganinta a farko duk nuna sukayi sun manta aka yi ta gaisawa, d'aki Herde ta shiga da ita suka dinga hira da tambayarta yaronta, yanda ta cika magana akan shi ne yasa tayi murmushi tace "Ayya bari na koma gida na d'auko wayata saina nuna miki shi." Rik'e hannunta tayi tace "A'a 'diyar Ayya, bana so ki tafi gaskiya, ji nake kamar ba zaki sake dawowa ba." Dariya tayi tace "Ayya ni da bikin yaya ne na zo, zan koma fa da an gama sabgar nan." "Zan bari ki koma tunda kina aiki acan, amma yanzu dai babu inda zaki je." Dariya duk sukayi har aka fara kiran sallah isha'i, alwala akayi suka sake yin sallah, su Zeinaba kuma suka fita suka ci gaba da aikin girki na safe da za'a ci bayan d'aurin aure. Daga nan zaune ma kan sallaya hira suka dasa, har Faduma ta tambayeta "Ayya ina su yaya Kalli da yaransu? Duk suna lafiya?" "Lafiya lau suke Faduma, ba lallai yau ki gansu ba musamman ma Kalli, dan tun safe daya shigo bai sake dawowa ba." Dariya tayi tace "Allah sarki, babban wa dama aka ce uba, yana aurar da k'aramin k'anninshi ba." Ita ma dariya tayi tace "Gaskiya kam, dan yace min akwai bak'in da suke zuwa wanda ya gayyata d'aurin auren, amma acan gidan gonar shi ya sauke su." Da mamaki ta kalleta tace "Ayya yaya Kalli yana da gidan gona ne?" Jinjina kai tayi da farin ciki tace "Ai Faduma bayan tafiyarki abubuwa da dama sun faru, Kalli yanzu ai ya zama babban k'usa wanda yake kula da kowa yanzu a gidan nan." Da farin ciki sosai tace "Haba shiyasa naga can gida ma anyi gyara sosai gidan yayi kyau." Dariya tayi ita ma tace "Kinsan nan za'a kawo amaryar ai." Jinjina kai tayi tace "Allah ya saka masa da alkairi, Allah ya k'ara masa bud'i." Da "Ameen." Ta masa ta d'ora da cewa "Ai wani mutumin kirki Allah ya had'ashi dashi wallahi, shine ya had'a da mutanen k'warai dandanan sai Allah ya sa mishi albarka." Gyara zamanta tayi ta d'ora kanta saman cinyar Herde ta d'auki hannunta ta d'ora saman kanta hakan yasa ta fara shafa mata tace "Ayya bani labarinki." Cikin murmushi da kuma k'aunar yariyar ta fara fad'a mata abubuwan da suk faru bayan bata nan, har da labarin data samu ita ma na zuwan Tagur gidan nan amma babu wanda ya kula shi, dan mahaifinta ya hana kowa ya kula shi, haka dai ya gaji da zuwa har ya daina, Faduma na saurare har yayarta *Liya'atu* ta kawo musu abinci ita da Herde, abun farin ciki da jin dad'i Herde hanata saka hannu tayi sai ita ta dinga d'ibowa tana saka mata a baki, har saida tayi k'wallan farin ciki ta kalleta tace "Ayya nasan ba kuyi hushi dani ba, amma duk da haka ina neman afuwarku, nasa kun zubar da hawayen bak'in ciki, nasa kunji kunya kuma an zageku da tarbiyar da kuka min, ku yafe min Ayya." Girgiza mata kai tayi ta sake jefa mata lomar tuwo bakinta tace "Ni baki min komai ba, Faduma akwai k'addara a rayuwa mai kyau da marar kyau, babu komai kinji." Haka ta ci gaba da ciyar da ita har ta k'oshi, ta so tayi kwanciyarta nan sai kuma Herde tace tasan yanzu Ayyarta ma na son jin d'uminta a kusa da ita, kawai ta je can ta kwanta, data nuna mata ma tana tsoron Aba guntun tsaki tayi tace "Ke manta dashi, babu abinda zai miki kinji, wallahi ya fi mu farin cikin ganinki kuma ya fi mu jin dad'i, bak'ar zuciya ce kawai irin ta ubanku." Dariya tayi ta jinjina kai kawai ta musu saida safe ta tafi, a can gefen gidansu ta hangi taron samari wanda yaya ne gareta shi take bi ma shine auta a cikin maza ya tara abokanshi suna girka wake dan farin ciki, wucewa kawai tayi dan sun gaisa a cikin gida daya shiga d'aukar tukunya da kayan da zasuyi anfani dasu. *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 17:09 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _15_ A d'aki ta samu Ayya har tayi shirin kwanciyarta, cire lafayarta tayi ta zauna kusa da ita akan shinfid'a tace "Ayya har kin kwanta ashe?" Mik'ewa tayi zaune tana fad'in "Na kwanta, na d'auka can zaki kwanta ai." "Ai Ayya ce tace na dawo ke ma wai kina son ganina kusa dake." Murmushi tayi tace "Allah sarki Herde, Allah ya saka mata da alkairi, kina ga fa ko gidan ta hanani lek'awa tace zasuyi komai." Murmushi tayi ita ma tace "Ai naga su Dada Mari da su Nana acan." "Ai sun zo nan na tura su can su kama musu wani abun, tunda ni ta hanani ai ba ma zauna haka ba." Saida ta gyara zama tace "Ayya ban ga Aba ba? Bai dawo ba?" Tab'e baki tayi tace "Bai shigo ba tun fitar da tayi." "To ango fa? Ina so na ganshi fa." Dariya tayi tace "Sai dai in zaki jira ne har sanda ya shigo." Shiru ne ya d'an biyo baya na sakanni kafin Hadizey ta kalleta da kyau tace "Zahra ya maganar aure? Owwo ta fad'a min abinda take fama dake kenan, ta fad'a min kina da ma-neman, amma ke ce dai aure baya gabanki sai aiki sai kuma d'anki, me yasa ba zaki so kasancewa k'ark'ashin inuwar aure ba? Haka kike so kiyi ta yawo a gari kina ci gaba da zubar da darajar kanki kina kuma ja mana zagi? Na tabbata ke ma kinsan ba kowa ke miki kallon kamilalliyar mace ba, ba kowa ke kyautata miki zato ba, me yasa ba zaki rufe bakin jama'a ba ta hanyar fitar da gwani ki samawa kanki mutumci da d'anki ma." Yanda tayi maganar a zafi zafi da kuma sanyi sosai yasa Fduma jan numfashi tace "Kiyi hak'uri Ayya, insha Allahu zanyi." Jinjina kai tayi tace "Allah ya tabbatar da alkairi." "Ameen." Ta amsa a hankali, A nutse ta kalleta tace "Gobe fa zaki koma da an d'aura auren nan, alk'awarin dana yi wa mahaifinki kenan." Da mamaki ta kalleta tace "Ayya gobe kuma? Amma ni na so sai ran lahadi na koma fa." Girgiza kai tayi tace "Sharad'i ya gindaya mana kafin ya yarda ki zo, kinga kuma ba zamu k'i bin umarninshi ba." Cikin rashin jin dad'i tace "Shikenan Ayya, amma ta ya zan koma daga d'aura aure?" Kallonta tayi sosai tace "Haka yake so ayi kuma haka za ayi." Jinjina kai tayi a hankali alamar shikenan, kallonta tayi tace "Ki je d'aki saiki kwanta akan gadon, kuma wayarki tun fitarki naji tana ta k'ara." Mik'ewa tayi tana laluba jakarta ta d'auki wayar, wucewa tayi d'aki tana duba lambobin da suka kirata, Dada, Aminu, bak'uwar lamba da cikin sauk'i ta haddaceta akai saboda rashin wuyarta da kuma yanda ta birgeta, saida ta zauna kan gadon ta kira lambar Dada, gaisawa sukayi sosai tare da mata ya hanya? Saidai bata yarda ta mata maganar Tagur ba, saida sukayi sallama ta sake kiran Aminu shima, amma har ta tsinke ba'a d'aga ba sai kawai ta canza kayanta zuwa doguwar rigar audiga mai taushi ta kwanta da tunanin zai sake kiranta. ______________ Yana jin dad'in zaman gidan duk da yau ne ya fara, dan Aminu na tare dashi ko fita zaiyi sai dai ya fita dashi, ko wajen cikin gidan baya barin fita saboda yasan yaran gidansu akwai rashin ji, shi kuma amanar nan daya d'auka baya son ko k'warzane ya same shi, hatta da abincin gidan ba shi Amjad ke ci ba siyo mishi yake lafiyayye tafiyayye daga waje, karatu kawai yake a d'akin da zuwa masallaci tare da Aminu suyi sallah su dawo. Amma duk da haka matan mahaifinshi guda biyu saida suka kai k'ararshi wajen babanshi daya dawo, yanzu haka har sun kwanta shi da Amjad suna karatu mahaifinshi ya kirashi a waya wai ya same shi d'akinshi yana son ganinshi, sam baiyi tsammanin abinda zai tarar ba dan haka ya tafi kanshi tsaye, da sallama ya shiga ya samu wuri ya zauna yana mishi sannu da zuwa. Cikin fad'a Alhaji Mustafa ya kalleshi yace "Aminu wane yaro ne aka ce ka zo dashi gidan shi? D'an wanene kuma daga ina?" D'an kallonshi yayi yace "Alhaji d'an Faduma ne fa ba kowa ba." "To me yake a gidan nan? Ina uwar tashi take?" Sake kallonshi yayi yace "Alhaji tayi tafiya ne shine tace ya zauna tare dani." "Saboda ka isa da kanka kenan?" Da mamaki ya kalleshi amma bai ce komai ba, d'orawa yayi da "Har ka kawo bak'o a gidan nan ka kasa sanar min?" Kallonshi yayi yace "Kayi hak'uri Alhaji, naga yaro ne kuma ba d'aki aka ware mishi ba, sannan gobe ko jibi mahaifiyarshi zata dawo." Gyara zama yayi yace "Naji, yanzu ba wannan ba Aminu, kaga dai duk cikin yaran gidan nan yan d'akinku kawai nake d'aga ma k'afa, kuma saboda mahaifiyarku bata raye ne, akwai abubuwa da dama da na maka wanda ni basu nake so ba, hatta alak'arka da yarinyar nan ni ba son ta nake ba wallahi, amma fad'a min miye tsakaninka da ita?" Kallonshi yayi duk yayi kicin-kicin da fuska ba alamar wasa ko tausawa yace "Alhaji ni sonta nake kuma ita nake so in aura." "Me?" Ya fad'a da k'arfi, sake turo baki yayi irin tab'ara yana jujjuya kai, kallon b'acin rai ya mishi sai kuma ya tuna mahaifiyarshi kawai tausayinshi ya kama shi, soyayyar da yake mishi matsayinshi na d'an fari wanda ya fara gani a matsayin d'a da kuma soyayyar da yake wa mahaifiyarsu, wani iska ya furzar ya kalleshi sosai yace "Aminu." "Na'am." Ya fad'a ba tare daya kalleshi ba, cikin nutsuwa yace "Aminu alak'aka da yarinyar ba yau kuka fara ba, nasan ka fini saninta da halayanta, sai dai kuma ku yara wani lokacin baku san abinda kuke so ko zai iya cutar daku ba, dole sai ana d'oraku a hanya ana nuna muku daidai da ba daidai ba, taya zaka ce ita kake so ka aura? Bayan kasan har d'a gareta ba da aure ba, taya zaku iya rayuwar aure da wacce aikinku d'aya? Duk wani shige da fice na aikin na wanda baka sani ba, me yasa Aminu?" Kallonshi yayi yace "Alhaji nasan wacece Faduma, wallahi ko soyayya ba tayi tunda suka rabu da uban d'anta, mutuniyar kirki ce k'addara ce kawai ta fad'a mata, ni ita nake so na aura saboda ita nake so." "Uhum! K'addara baiwar Allah, komai sai ace k'addara, to bari kaji ni tuni ma mun gama magana da Alhaji Saddi akan zamu had'aku aure da 'yar wajensa k'anwar abokinka *Faruq*." Tuni ya shiga mutsu mutsu da kai yana fad'in "Faruq kuma? Wace daga cikin k'annansa? Ni wallahi bana sonta Faduma nake so." Dak'uwa ya mishi yace "Uwaka kai da Faduma? Na ce uwaku, to ba zaka aurenta ba kaji Aminu, wanda nake so zaka aura tunda naga baka san ciwon kanka ba." Kallonshi yayi kamar zaiyi kuka yace "Alhaji uwata kake zagi? Uwata dake kwance a kabari? Dan bata raye shiyasa ake mana haka ko? Shikenan amana dai ce." Tashi yayi ya fita Alhaji Mustafa kuma tuni ya shiga kiran "Aminu, Aminu dawo nan ka zauna, magana nake maka fa, karka had'a da wanda ke kabari kaji." Ficewa yayi ya barshi nan, wani iska ya furzo yana girgiza kai, a daidai falon ya had'u da matan mahaifin nashi, kallon mai bisa ruwa ya musu ya wuce ko tanka musu baiyi ba, suma kuma suna jira suji yana mishi fad'a ne, amma kamar yanda aka saba basu ji komai ba, duk tab'e baki sukayi kowace ta shiga d'akinta da tunanin gobe za'a tattauna akan matsalar. Yana komawa d'akin Amjad ya kalleshi yace "Obdo an kiraka a waya yanzu." Saida ya nufi inda wayar take kusa da Amjad yana fad'in "Waye ya kira?" Da murmushi Amjad ya kalleshi yace "Dara nra (masoyiya)" Da sauri ya kalleshi sai kuma yaji kunya ta kama shi, murmushi kawai yayi ya d'auki wayar yana satar kallon Amjad, zaune yayi kusanshi yace "Kasan waye ya kira?" Ba tare daya kalleshi ba yana kallon littafinshi yace "Um, Ayyata ce, naga lambar ai." Dafa kafad'arshi yayi yace "Amma ba zaka fad'a mata ba ko?" Dariya yayi ya kalleshi yace "Obdo me yasa ba zaka fad'a mata ba in da gaske kake?" Cakulkuli ya masa yana fad'in "Yaro mai wayo, kai dai kaja baki kayi shiru." Cikin dariya da son kare kanshi yace "Ba zan fad'a ba, amma in ta dawo baka fad'a mata ba ni zan samo ma Ayyata wani miji." Dakatawa yayi ya kalleshi yace "Amjad baka so na auri Ayyarka?" Cikin nutsuwa ya kalleshi yace "Obdo bana jin Ayya zata samu wani wanda ya kaika ma bare ya fika, va zan so na rasaka a matsayin Aba ba." Shafa kanshi yayi yana jin wani dad'i tare da murmushi yace "Ci gaba da karatunka." Mik'ewa yayi ya fita waje, sanda ya sake kira kuma shima haka tayi ta k'ara ba'a d'aga ba har ya gaji ya dawo d'akin, Amjad na kallonshi ya sake cewa "Yanzu nasan Ayya tayi bacci, ba zaka sameta ba." Zaune yayi yana fad'in "Ya akayi ka sani? Kana ganin zatayi bacci haka da wuri." Kallon agogon d'akin yayi yace "Tayi bacci, Ayya data kwanta cikin sauk'i bacci ke d'aukarta." Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi yana kallon yaron, a haka suma har suka kwanta ba jimawa kuma baccin ya d'aukesu. _______________ Da safe an tashi da shirye shiryen d'aurin aure k'arfe 08:00, tun asuba da taji bud'e gida na Aba ya tafi masallaci bata sake jin motsinshi ba, lura da tayi kamar mahaifin nata baya son sake ganinta ne yasa ko da ta shirya ta bar gidan zuwa gidan su Herde, acan kam sosai ta sake cikin yan uwa har ta kan manta da abinda ya faru, cikin d'an lokaci mutane suka gama cika duka gidajen biyu, dan duk wanda ya zo saiya fara shiga wurin uwar ango sun gaisa, daga nan kuma sai ka wuce gidan Herde a ci abincin da aka tanada dan yau d'in dama. Zuwa k'arfe 08:40 gidansu Herde ya sake cika dan har wanda suka je d'aurin auren sun dawo, a lokacin ido sun sake mata yawa, dan daga yanda ake kiran sunanta da yanda wasu ke magana k'asa k'asa ana binta da ido da baki yasa ta tsargu sosai, gashi kuma dama gidansu ba mata ke akwai ba daga ita sai Zeinaba da Liya, ita kuma ita ce auta sai maza kuma da suke gaba da ita, shiyasa duk kai kawonta ke kan mutanen dake wurin wanda suka santa da wanda basu santa ba. Tana aje tiren abincin gaban wasu tsofaffi ta d'aga zata mik'e wata tsohuwa ta kalleta tace "Ke ba yar gidan Hadizey bace?" Komawa tayi ta tsuguna tana kallonta tace "Eh, 'yarta ce." Kallon juna sukayi da wata ta kusanta sannan ta sake kallon Faduma tace "Ai kece Fatima ko?" Da kallon jin haushi da k'osawa ta kalleta tace "Eh." Jinjina kai tsohuwar tayi ta kalli d'aya tsohuwar tace "Bana fad'a miki ba, ita ce." Sama da k'asa ta hararesu ta mik'e ta nufi d'akin Herde, tana shiga lafayarta ta d'auka zata nad'a Liya tace "Fati ina zaki tafi kuma?" Cikin b'acin rai tace "Aunty Liya gida zan koma, dama Aba yace na tafi da an d'aura auren." Rik'eta tayi tace "A'a wallahi, babu inda zaki je Faduma, wuce kiyi wanka ma tunda ai an gama raba abincin ki zo ki shirya." Turo baki tayi tana kallonta tace "A'a fa aunty Liya." Jinjina mata kai tayi alamar eh, cikin shagwab'a ta aje lafayar ta fito dan yin wankan, wanka tayi sosai ta fito ta shiga shiryawa a nutse, Liya ce ta bata wata sabuwar lafayar data siya dan kanta, godiya ta mata ta karb'a dan sakawa, riga da wandon ta fara sakawa wanda suka sun kamata, lafayar ta d'ora akai ta mata d'aurin sahari, dama ba wata kwalliya bace a fuskarta, humra bak'a ta k'ara shafawa a jikin lafayar, fitowa tayi ta samu Herde cikin mutane, cikin shagwab'a kamar yanda ta saba tace mata "Ayya zan je gida na shirya kayana, Aba fa yace na koma da an d'aura aure." Juyowa tayi ta kalleta da kulawa tace "Naji tafi gidan gani nan zuwa, amma ki manta da abinda Abanku ya fad'a." Jinjina kai tayi ta fita a gidan, a k'ofar gidan ta hangi mota da kuma samari biyu a ciki, murmushi tayi dan ko da ta gansu tasan yayanta Barka ne dan abokanshi ne da ta sani, tana k'arasawa ta gaishesu cikin ladabi ta wuce ciki, tana shiga ganin gidan babu mutane a farfajiyar sai d'akin farko kuma a bud'e yasa ta matsawa kusan k'ofar ta bubbuga, daga ciki akae fad'in "Yau naga jaraba, wai bana ce ku jirani kaya zan canza ba." Cikin harshen tubanci tana danne dariyarta tace "An k'i a jiranka malam fito." Muryar da yaji yasa shi fitowa da sauri yana zaro ido, cak ya tsaya sukayi kallon kallo, bushewa tayi da dariya dan ko rigar bai cire ba tana wuyanshi ya fito kamar an shak'eshi, mayar da rigar yayi da mamaki yace "Fatu? Yaushe kika zo? Ke ce?" Hararanshi tayi sama da k'asa ta bangajeshi ta wuce d'akin tana fad'in "Ban sani ba yaya Barka, wai na zo garin nan dan na ganku, amma kai ko damuwa dani ma bakayi ba." Kamar yanda ya saba hannu ya kai ya jawo gammon data ma gashinta yana dawo da ita baya yana fad'in "Ashe dai har yanzu baki fara tsoro na ba, na d'auka zaki canza ai ashe da saura." Wata k'ara ta zabga wacce duk gidan ba wanda bai ji ba tana fad'in "Ayya! Aba gashi na, zai cire min gashi na." Da wasa tayi cike da nishad'in yanayi, amma sai ji sukayi an bud'e labulen d'akin da sauri ana fad'in "Barka rabu min da 'ya fa, karka ji..." Sai kuma aka yi shiru, da sauri suka juya suma a k'ofar, *Aba* ta furta a hankali, bata ma san yana gidan ba ko kuwa yanzu ya shigo, ko ma dai menene farin ciki ya gama mamayeta ganin ashe Aba ya damu da ita har yanzu, ashe har yanzu baya son abinda ya tab'a mishi ita? Murmushin data saki ne yasa Aba da abun ya zo mishi a bazata, kawai ji yayi zuciyarshi ta buga da k'arfi sanda k'ararta ta daki kunnuwanshi, saiya gagara jurewa bai san ya shigo ba bare yasan me ya furta, sakin labulen yayi ya fita daga gidan ya fasa yin abinda ya shigo dashi ma. Kallon juna sukayi da Barka sai kuma suka fashe da dariya k'asa k'asa suna rufe baki, dangware mata kai yayi yace "Shak'iyiya, ashe har yanzu dai Fatu ba'a canza ba?" Turo baki tayi gaba tana fad'in "Ka daina kirana Fatu bana so, in ba haka ba zan rama." Da mamaki ya kalleta yace "Au! Wai dama kin fara nutsuwa kenan? Ai na d'auka ana miki kike ramawa yar gidan Aba." Cikin murmushi tace "Na daina yanzu." Gyara tsayuwa yayi yace "Fatima yaushe kika zo? Ayya bata fad'a min ba." Cikin sauke ajiyar zuciya tace "Jiya na shigo da yamma, kuma yanzu zan koma." Girgiza mata kai yayi yace "Ki bari zanyi magana da Aba ya barki ki k'ara kwana biyu, tunda har mun gano abinda ke zuciyarshi a game dake." Da sauri tace "Da gaske za kayi?" Hararanta yayi yace "Ina wasa dake ne? Ni fa yanzu babban mutum ne, akwai nauyi akwai a kaina da magana d'aya na da matuk'ar tasiri gareni yanzu." Da dariya sosai ta sunkuya ta bashi hannu suka tapa tana fad'in "Yeeeee! Girma ya zo wa su Barkuku." Mik'ewa yayi yana fad'in "Ke! Waye Barkukun? Fatu..." Bai k'arasa ba sai binta da ido da yayi yana dariya ganin har ta fice a d'akin. Sam bata tunanin samun kowa a farfajiyar, dan haka ta fito da gudunta tana dariyar k'eta, shigowar yaya Kalli tare da wasu a bayanshi yasa ta tsayawa tana kallonshi, da ta fahimci dai shine fa kanshi da murna ta k'arasa da rawar jikinta tana fad'in "Yaya Kalli." Shima da murna sosai yayi saurin rik'o hannunta yana fad'in "Fadu, Fadun Abanta." K'wallan farin ciki ne suka taho mata ta d'ora kanta a k'irjinshi kad'an tana share hawaye, kallon fuskarta yayi a harshen tubanci yana fad'in "Kai Fadu Abanta da kuka? Daina dan Allah kinji, fad'a min yaushe kika zo?" D'agowa tayi tana kallon fuskarshi da kamala da girma suka cikata tace "Jiya, yaya Kalli ya kake?" Saida ya rik'o hannunta suka ci gaba da takowa zuwa cikin gidan sosai yace "Kamar dai yanda kika gani Fadu, girma ya zo mun fara tsufa yanzu." Wata dariya ta bushe da ita tana girgiza kai da fad'in "A'a ban yarda, yaya na bai fara tsufa ba har yanzu." D'an dangware mata kai yayi yace "Ina da k'annai kamarku da kuke kamoni a tsayi ba dole ku tsofar dani ba." Dariya suka saka sai kuma sallamar mutanen a baya ta shiga kunnuwanta, a tare suka juya suna amsa sallamar, kallo d'aya ta musu ta d'auke kai daga garesu, maza ne zarata wasu kamar yayanta wasu kuma basu kai shi ba wasu sun fi shi, bata kula da kowa ba ta d'an janye daga jikinshi ta nufi shiga d'akin Ayya dan tasan tare yake dasu, zata shiga kuma Ayya ta fito tana sake amsa sallamar, dole ta tsaya kusa da ita tana jiran su gama saita wuce, suna fara gaisawa Ayya ta kalleta da harare a harshensu tace "Baki iya gaisuwa ba kuma?" Turo baki tayi ta d'an juya kai ta kallesu, sake kallon Ayya tayi a harshensu ita ma tace "Ayya fa sunfi su goma, taya zan iya gaishesu bayan dukansu muharramaina ne?" Cikin sinne kai da mamakin al'amarinta Ayya tace "Humm! Har yanzu ajin na nan kenan?" Girgiza kai tayi ta kauce mata a hanya ta shige d'aki, Kalli ne ya nuna mata su a matsayin bak'in da suka zo mishi, godiya ta musu sosai da addu'a, Barka ma yana fitowa gaisawa sukayi sannan sukayi sallama suka fita tare dashi, har sun kai k'ofa Barka ya juyo yace "Ayya karki bari Faduma ta tafi ina dawowa." Bai san motar wacece ba shi dai ya shiga kawai, saida ya rufe k'ofar yana jin ana tayar da sauran motocin, bai bud'a idonshi ba sai numfashinshi fa yake sauke da sauri sauri, so yake yaji zuciyarshi ta fara bugawa daidai ko zai samu nutsuwar yin wani tunanin, amma sai doka mishi take da sauri har yanzu, numfashin yake sosai amma shima ya k'i daidaituwa, dafe k'irjinshi yayi yana ambatar inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un a k'asan zuciyarshi, har Kalli ya shigo motar tare da Adam a baya suka tayar suka bar wurin, nisa sukayi sosai a tafiya amma ya kasa komai, saida Adam ya dafa kafad'ar shi ta baya yana fad'in "Hasheer lafiya kuwa? Me yake damunka?" Bud'a ido yayi kamar wanda ya farka daga doguwar suma, d'auke hannunshi yayi a k'irjinshi yana sake sauke wata wawiyar ajiyar zuciya, saida yaji komai ya daidaita yanzu sannan ya furzar da iska ya jingina a jikin kujerar, a hankali ya fara tariyo shigowarsu da sanda idonshi ya sauka a kanta, murmushi, dariyarta, sanda hawayenta suka zuba da sanda ta share, lokacin da take shagwab'a a gaban Ayyarta? Hatta da yanda sunan Kalli ya fita a bakinta sai yaji ashe su duk a cikin kuskure da rashin iyawa suke kiranshi, sai yau ne yaji dad'in sunan nashi wanda ada can yake murmusawa in yaji an fad'a. A hankali ya sauke numfashi yana ayyana "Wacece ita? Me yasa k'arfin zuwanta ya zo mishi a haka? Wane irin tasiri ne a tare da ita da sauran mata basu da? Wace irin baiwa ce da ita? Me take yi anan? Ina d'anta?" D'an juya kanshi yayi ya kalli Kalli dake tuk'i, kamar wani sakarai ya saki baki yana kallonshi, tabbas shima bak'i ne ko yace yana da duhun fata, amma ta ta tafi tashi haske, sannan basa kama ta ko wace siga sai had'uwar jini kawai, a hankali ya sake sauke ajiyar zuciya yana kallon gabanshi yace " *Me ta fad'a a lokacin?*" Da sauri suka kalleshi suna had'a baki wajen fad'in "Wacece?" Da sauri shima ya kallesu dan bai d'auka sunji ba, kikkifta ido yayi sai kuma ya basar da fad'in "Yaren ne kawai ya birgeni." Murmushi Kalli yayi yace "Wai Faduma kake nufi?" Cikin tuk'inshi yace "Gaisheku aka ce tayi, amma a ganinta ku ba muharramanta ba taya zata d'aga muryarta akan ku tayi magana dukanku sai ku ji." Dariya yayi yana girgiza kai da fad'in "Fadu Abanta kenan, da alama har yanzu k'uruciya bata saki kanta ba." Wani kallo ya watsa masa mai sa gaba ya fad'i da saka jin mamaki, a hankali ya d'aga labb'anshi ta yanda kamar ba shi yake maganar ba yace " *Ta kyauta min, hakan ya min daidai, ta rufa min asiri, k'uruciyar ta ta kuma ta min yanda nake so*." Da kallo suka bi shi har da shi mai tuk'in, mamaki ne ya bayyana sosai a tare dasu, Adam ne yayi saurin cewa ".... *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 17:09 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _16_ "Wai kana nufin ka kamu?" Duk basu d'auke idonsu ba daga kanshi suna jiran suji amsa, shiru yayi kamar bai san me aka fad'a ba, da wani mamakin Adam yace "Hasheer kana sonta ne?" Madadin ya bashi amsa saiya kalli Kalli yace "K'anwarka ce ita?" D'aga kai yayi yana mamakin Hasheer d'in kafin yace "Wai Elhaj Faduma kake so? In ko hakane da..." Ba tare daya kalleshi ba yace "Ni na fad'i haka? Kar ku fahimci abinda na fad'a ba daidai ba mana." Shiru sukayi sai Adam daya d'ora da "Allah yasa da gaske kake." A hankali ya juyo ya kalle da mamaki, kamar zaiyi magana sai kuma yayi k'wafa kawai ya juya, gidan gonar suka isa inda suka samu abinci mai rai da lafiya suka ci suka sha sai godiyar Allah, bayan haka kuma kowa ya fara tunanin d'aukar hanya musamman wanda suka fi nisa, amma su Hasheer tunaninsu sai sunyi sallah la'asar zasu tafi sai su shiga kafin magrib. Bayan fitarsu Ayya na shiga d'akin ta same ta take fad'in "Yanzu Faduma gaishe da bak'i ma sai abu ya zama aiki?" Cikin shagwab'a tace "Ayya wallahi da nasan ma tare zasu shigo da ban bari sun ganni ba, shima yaya Kalli ko da dai nan gidansu ne ai sai ya fara shigowa shi kad'ai har a mishi izini sai su shigo." Girgiza kai tayi tace "Allah ya kyauta." Wayarta ta d'auka ta kira Aminu, ta d'an jima tana k'ara kafin ya d'auka, gaisawa sukayi sosai ta tambayeshi Amjad yace ya kaishi makaranta, basu wani ja hirar da tsayi ba dan in ba hirar aiki ba basu iya wata hirar ba, ta fad'a mishi saita shigo kafin sukayi sallama. Ayya dake saurarenta kallonta kawai tayi tace "Yana k'ok'ari fa akan ki, ya kamata ki fahimci manufarsa." Kallonta tayi sai dai ba tace komai ba dan tasan babu abinda Dada bata fad'a mata a game da ita, jin ba tace komai ba yasa ta sake fad'in "Fati, ina fatan dai kina kare mutumcinki ko?" Da sauri ta kalleta tace "Eh Ayya." Wani kallon tuhuma ta mata tace "Fati kinsan dai ina da hanyar da zan bi na gane gaskiya kika fad'a ko k'arya ba ko?" Jim tayi tana kallonta cikin sanyin jiki tace "Eh Ayya, wallahi gaskiya na fad'a miki." Shirun daya biyo baya ne yasa Faduma nisawa tace "Yawwa Ayya, na manta ban fad'a miki ba, Amjad fa yana d'aya daga cikin wanda za ayi gasar musabik'a a k'asar nan, ina buk'atar addu'arku Allah ya bashi nasara." Ko kallonta ba tayi ba kamar ba tayi farin ciki ba tace "Uhum! Allah yasa alkairi." Rashin dad'in yanayin yasa ta amsa a hankali da "Ameen." A nutse ta sake kallonta tace "Ayya zan iya tafiya gidansu dada Amina (uwar amaryar Barka) na gansu?" A take tace mata "A'a."Kallonta tayi kamar za tayi magana sai dai kuma a tarbiyar data mata ba zata yarda tayi hakan ba, shiru kamar ba zata sake magana sai kuma tace "Idan kika je gori da habaice habaice ne zaki sha kawai, gwara kiyi zamanki, da zaki ji ta tawa ma da kin zauna a d'akin nan ko kuma kije can cikin gida sanda za'a kawo amaryar, dan kinfi kowa sanin dangin mahaifinki sun fi d'aukar al'amarinki da zafi sama da kowa, saboda suna ganin ni ce nake d'aure miki k'ugu." Kallonta tayi tace "Ayya na daina fad'a fa yanzu, wallahi zan iya sharesu duk abinda zasuyi, amma tunda kin ce haka shikenan, zanyi yanda kike so Ayya." Mik'ewa tayi tsaye tace "Zan shiga ciki Ayya na kwanta na jira yaya Barka naji yanda zasuyi da Aba." Jinjina kai tayi tace "Shikenan, nima zan je can gidan dan hutar da mutane shigowa nan da can, zan rufo k'ofar daga baya dan suna ganin haka zasu tabbatar ina can d'in ga masu zuwa yanzu." Ita ma jinjina kan tayi ta shige ciki ita kuma ta gama shiryawa ta fita ta rufo k'ofar kamar yanda tace. Tana shiga ciki ta cire lafayarta dan ta ragewa kanta nauyi ta kwanta kan gadon, rairan tayi tana kallon rufin d'akin, a hankali take sauke numfashi tana tunanin baya, tabbas karin maganar da aka ce *ko wa ya tuna bara bai ji dad'in bana ba* gaskiya ne, lallai tayi rayuwa a baya wacce zata iya zama izina ga 'yan baya, labarinta zai iya zama tarihi kuma abun koyon darasi ga wasu da dama, wata ajiyar zuciya ta sake saukewa mai nauyi, a hankali ta lula duniyarta ta baya ta shiga dawo da abinda ya faru a rayuwarta ta baya. *Shekara tara da suka gabata* *Shekara* tara da suka wuce a lokacin tana da shekara goma sha hud'u tana daf da shiga shekara sha biyar a duniya, Allah ya yi hallitar jikinta mai girma ma'ana tana da k'iba wanda wasu ke cewa tana da manyan k'assa, tana da ilimi sosai da son karatu da kuma naci kan duk abinda take so, bata da wata rana da take hutawa a cikinta dan kullum karatu take, in ba na islamiyya ba to na boko ne, mahaifinta *Moliya* ma malami ne, in dai yana gidansu ko gidan kishiyar mamanta to tana tare dashi yana k'ara mata karatu, wannan ya k'ara kusanci tsakaninshi da ita da kuma shak'uwa da soyayya, yana sonta saboda son iliminta da kuma saurin fahimtarta, bugu da k'ari tana tausaya ma matsakaiciyar rayuwarsu da wata rana ma fama ake, Herde macece mai baki da k'arancin hak'uri sab'anin Hadizey, sai dai duk da haka suna zaman lafiya da mutunta juna da rufawa juna asiri, duk da ita ce babba kuma mai 'yaya dayawa da maza bata tab'a kallon Hadizey a matsayin kishiya ba, abinda yaranta zasu nemo su bata shi zata umarcesu da su bawa d'aya mahaifiyarta su, tana kuma son Faduma sosai kamar ita ta haifeta, shiyasa ko tana fad'a da Aba wani lokacin ita ta kan shiga tsakaninsu, sannan tana lallab'a Aba da bashi hak'uri da nuna mishi mahimmancin haka. K'wazonta a karatu yasa yayanta Kalli da mahaifin nasu da Barka suka had'a suka sakata wata islamiyya da ake hadda Alqur'ani zalla da hadisai, tunda ta shiga makarantar bara tab'a wasa da damarta ba, abinda ya kaita take yi sosai har malaman kansu suka ji da ita. Kwalliya ta biya kud'in sabulu dan tana cikin shekara ta sha biyar aka saka sunanta a cikin d'alibar da zata wakilci makarantar a gasar Alqur'ani ta duka africa, karatunta ya rub'anya tare da maida hankalinta sosai akan gasar, da fari an fara tantancesu a garinsu kafin a kowace jaha aka ware mata gwaraza biyu aka turasu babban birnin Niamey. Su goma sha shida ne suka papata inda anan kuma aka cire d'aya da zai wuce gaba, Faduma ce tayi wannan nasarar cikin rakiyar babban wakilinsu kuma malaminsu suka tafi k'asar Ghana. Tana zuwa can ta sare ta kuma rasa k'arfin gwiwarta, hazik'an d'aliban data gani da kuma yawansu da yanda tsarin yake yasa taji kamar tace a mayar da ita gida, a lokacin da aka kira sunanta ta zauna kan kujerar da kowane d'alibi ke zama, ta kalli malaman dake gefenta duk hankalinsu kanta, ga masu d'aukar hoto mai motsi ta ko ina, suna d'auka, ga kuma wasu masu kula da gasar dake gabansu duk hankalinsu kanta suma, nik'ab d'in dake gareta a lokacin saida ya jik'e har yana lik'e mata a hanci tsabar hawayen data dinga yi, ta jima tana sauke numfashi sanda aka karanto mata tsakiyar suratul An'am, har saida aka sake nanata mata kafin ta kori shaid'an ta fara karatun cikin rawar murya, siririyar murayr tsoro had'e da rik'akk'en yarenta a harshenta da kuma kuka da take yi saboda taushin ni'imomin da take karwanyowa suka sa muryarta fita fes, yanda karatunta ke fita a lasifika ya wa duk wanda ke kallonta da saurarenta dad'i, hatta da maluman sun ji kamar karsu tsayar da ita, k'ira'ar habs ce take karatun da ta ita, haka Allah ya saukaka mata har ta ido aka mata tambayoyi kan hukence hukencen Alqur'ani kama daga izhari, iklabi, idgam, ikfa'i. Masu son nasara sun kasu kashi uku, wasu su kanyi gasa ne da tunanin nasara tace su, wasu su kan shiga da tunanin ba zan ci ba, wasu kuma su kan je da nufin jarraba sa'arsu ba dan suyi nasara ko su fad'i ba. Kamar yanda ba'a gane mai nasara a jiki, dan ita nasara sa'a ce, sa'a kuma rahama ce ta ubangiji ga bayinsa, da ikonsa da rahamarsa ta cinye wannan gasa yanda ake buk'ata, ba iya iyayenta da yan uwanta tasa alfahari ba, hatta k'asarta ta shiga alfaharin kasancewarta mai d'auke da wannan gwarzuwar shekarar da a k'alla sai bayan wasu shekaru take zuwa. Irin kyaututtukan da ta ci basa misaltuwa, kusan babu abinda bata samu ba, wanda kowa ke bayarwa a bawa wanda yayi na farko, fridge da babur da kud'ad'en da sai an zauna ayi lissafinsu, wasu ma bayan sun tabbatar da mace ce ta ci gasar d'aukar nauyin kayan aurenta sukayi idan lokacin yayi, inda kuma wani babban attajirin ya bayar da kujerar makka ga iyayenta biyu. Ta dawo k'asarta cike da wani irin farin cikin da bata tab'a yin irinshi ba a duk tsawon rayuwarta, tun daga yanda aka tarbeta a filin jirgi har zuwa isarta gidan abun ya so d'imauta tunaninta, ta samu ahalinta cikin farin cikin daya fi nata. Bayan wasu kwanaki komai ya lafa ta bar ragamar komai a hannun iyayenta, hatta da kujerun makka Hadizey tace ba zata tafi ba sai dai Herde ta tafi, ita ma Herde tace ba zata je ba ai Hadizey ce uwar yarinya, a k'arshe sai mijinsu ne ya raba musu gardama ta hanyar tafiya tare da Herde, dan yasan hakan shine zai fi ma Hadizey dad'i, kusan yan uwanta babu wanda bai samu abun arzik'i ba, sai wasu kud'ad'e da Kalli yayi shugabancin bud'e mata asusu a banki aka ajiye mata, babur kuma dole aka bar wa Barka dan shine bai da abun hawa sai kuma wanda take bi ma *Abakar* da bai isa karambanin hawan babur ba. Ta ci gaba da zuwa islamiyya da makarantar bokonta ba tare da wani abu ya sauya ba, sai dai fa yanda Fadumar nan take da wannan k'ok'arin a karatu haka take dashi a wurare da dama, iyayen yara a unguwarsu suna fatan yaransu su zama kamar ita, nutsuwa da hankalinta da tarbiyarta na birgesu, saidai komai na da ginshik'i, na Faduma kuma mahaifiyarta ce. *Zaune* suke k'asa kowace da takalminta ta zauna akan su suna yar karabke (yar cab'e), daga ban d'aki ta fito da sauri ta aje butar ta dawo ta zauna kan takalminta, har yarinyar zata mayar da k'ank'arun a rame Faduma tayi saurin tsayar da ita da hannu, k'are musu kallo ta shiga yi da d'aya d'aya, tab'e baki tayi tace "Da cutata zakiyi *Maryam*? To na ganoki dai malama dan haka ban yarda ba." Waro ido tayi tace "Ke Faduma, wallahi k'arya ce ban cuceki ba, har yanzu suna nan yanda suke." A k'ufule ta kalleta tace "Ni ce zan miki k'aryar? Maryam akan wata carabken banza zan miki k'arya? Kuma ai da gaske ne kinyi cutar, kinga bari ki gani." Ta fad'a tana nuna mata yayan tana fad'in "Wannan mai jan a gabana yake yana kallona, wannan na kusa da yatsanki shine daf da ramin, kawai yanzu saina samu kin canza musu zama, dalla malama ni tashi." Sakin baki tayi tana kallonta dan gaskiya ta fad'a, bayan ta shiga ban d'aki ta canza musu zama yanda zatayi saurin cinyewa, ashe har ta gano, amma saita basar tayi tsaki tana mik'ewa tace "Ai ke haka kike shiyasa bama son wasa dake." Ita ma mik'ewa tayi tana saka takalminta tana fad'in "To kar kuyi wasar dani mana sai me? Mutuwa zanyi ne?" D'ayar ce ta shiga tattare yayan tana fad'in "Ni bari na d'auke yayana mu tafi." K'afa Faduma tasa tayi watsi da yayan tana fad'in "'Yayan banza da wofi, tsakuwar da ko ina akwai." Mik'ewa yarinyar tayi tana fad'in "Ko ina akwai amma ban da gidanku da sai filin." Rik'e k'ugu tayi tana jijjiga tace "Eh saboda gidanmu ba kwandon shara bane bare mu tara tsakuwa." Hararanta yarinyar tayi tana fad'in "Ke tafi can, an dai ji kunya gamdamemiya dake kina wasa cikin yan yara." Da wani irin kuzari ta tunkari yarinyar ta shak'i wuyanta ta danne dam a hannayenta, zubar da sauran yayan tayi ta zaro ido a take ta wahala ta fara k'ok'arin k'watar kanta, Maryam dake tsaye ne ta fashe da ihu tana fad'in "Wayyo! Na shiga uku zata kasheta, Ayyar Fadu." Ta fad'a tana nufa d'akin, a k'ofar suka had'e da Hadizey dake gyaran jikinta, fitowa tayi da d'aurin k'irji dan ganin miye, da gudu ta nufosu ta rik'e hannayenta tana mata tsawa da fad'in "Saketa." Bata musa ba ko gardama take ta saketa tana hankad'ata baya sosai, maida numfashi yarinyar ta fara yi sai kallonta da Hadizey tayi tace "Ke d'auki kayanku ku tafi gida kinji." Tattara kayan sukayi suka fita suna ta hararen Faduma, kallonta tayi a hassale tace "Me yake damunki Fati?" Turo baki tayi gaba tana gunguni ba tace komai ba, girgiza kai tayi cike da takaicin halin Faduma, zaka rantse da Allah cewa yaran k'anananta ne na uku, amma kuma Maryam tana gaban Faduma a haihuwa ta bata wata kusan takwas, amma da yake jikin ba wani ba kuma suna ji da k'uruciya har yanzu basu wuce wasan yara ba, sai dai tafi jin haushin wasar Faduma, dan yarinya ce da babu ta inda Allah ya tauyeta, gabanta cikakke haka bayanta da duk wasu sassa da zasu tabbatar da k'osawar mace, sai dai duk wannan abun basu sa ta fara jin kanta ita ma macece ba, har yanzu ganin yarinya sosai take wa kanta, kuma abubuwa ukun nan sun taka rawa sosai wajen nuna mata kanta yarinya, rashin k'awaye, rashin kalle kalle tv dan basu da ita ma a duka gidajen biyu, da kuma rashin waya, tabbas da tana mu'amula dasu data fara fahimtar ita ma wata ce. Shiyasa ko makarantar boko ta tafi da wanda take wasa dasu, Faduma ma ko yanzu ta samu yar tsana wasa za tayi da ita har ta goya abarta a baya ba ruwanta da kowa. Girgiza kai ta sake yi ta kama kunnenta ta murd'e sosai tace "Ban hanaki wasar banzar nan ba?" Cikin kukan shagwab'a tace "Na daina Ayya, kiyi hak'uri ba zan sake ba." "Kinyi alk'awari?" D'a sauri tace "Na yi Ayya, nayi wallahi." Sakin kunnenta tayi tace "Shikenan, wuce ki cire kayan nan ruwan zafi na nan cikin roba ki zauna." Yamutsa fuska tayi za tayi magana sai kuma tayi shiru dan bata magana sau d'aya ta sake maimaitawa, wucewa tayi tana turo baki gaba, bin bayanta tayi tana kallo har tayi abinda ya dace wanda tasan tana yi, ganin yanda take komai da sauri yasa cewa "Wai saurin me kike? Fita kike so kiyi ko?" A hankali ta d'aga kai alamar eh tace "Ayya zan je nayi wa Ayya girki." Cikin nutsuwa murya a hankali tace "To kammala min gyaran d'akin nan sai ki wuce, ki tabbatar kuma babu inda kika je daga nan." Da sauri ta shiga d'auke robar data zauna ta fitar waje ta d'auke kayan da Ayya ta shafa dilka tayi turare ta fitar suma, ba wani shara da d'akin ke buk'ata, amma haka ta d'auki tsintsiyar ta share iya abinda zata iya, turaren tsintsiya ta kunna ta k'ara goge komai sannan ta shirya, har ta kai k'ofar d'akin tace "Zo nan." Ba tare data kalleta ba tana gyaran akaifunta tace "Miye sharad'inki na fita?" A hankali ta shiga fad'in "Idan nace zan tafi wuri kaza to na tabbatar can zan tafi, idan na fita babu tsayawa a hanya bare shirmen da bashi da anfani, karna kula duk namijin daya min magana akan hanya, amma karna wulak'anta kowa, banda tsalle tsalle da wasar banza saboda ni mace ce mai daraja, banda tafiya ina kalle kalle na kalli gabana kawai cikin kunya da nutsuwa haka shine addini ya koyar, na gaishe da babba idan na gani, sannan na taimaki wanda naga yana buk'atar taimakon, idan nima yafi k'arfina to nayi addua'r Allah ya kawo wanda zai iya na tafiyata, sannan duk inda nake magriba ta min a cikin gida." Satar kallonta tayi ta murmusa kafin tace "Zaki iya tafiya." Mik'ewa tayi tana fad'in "Nagode Ayya." Da kallo ta bita har ta fita, murmushi tayi a ranta ta fad'i "To ko dan na hanata kula samari ne ma yasa har yanzu ko saurayin wasa bata da?" Dariya ta sake yi ita kad'ai tace "Ai sai an kulasu ne sannan za ayi su, to amma gaskiya ban yarda 'yata ta dinga tsayawa kan titi ba, mijinta zai zo har gida ya sameta idan lokacin yayi." Ita ma Faduma a hanyarta ta shiga gidan take tunanin abinda kullum saita maimaita kafin ta fita kamar wani karatu, k'arasawa tayi ta shiga da sallama, ko sallamarta bata amsa ba tace "Yar albarka ta zo yi wa mamanta, hakane?" Dariya tayi tace "Hakane Ayyata, ya zo samun ladar hidimta miki." Cike da k'aunarta tace "Allah ya miki albarka 'yata ta kaina." Amsawa tayi da Ameen ta cire hijab d'inta ta fara aikin gadan gadan, tana yi suna hirarsu ta 'ya da uwa har ta kammala, yanda tasan ana yi haka tayi tsaf ta aje inda ake ajewa kowa ya zo ya d'auki nashi, sallah tayi sannan ta ci abincin ita ma, daga nan ta kwanta ta samu bacci na awa biyu cikakka har lokacin sallah la'asar tayi, tashinta Herde tayi tayi sallah ta shiga wanka anan ta fito, mai ta shafa saita mayar da kayanta tace idan taje gida saita yi shirin islamiyya. Zata fita suka had'e da Abakar ya shigo, dawowa tayi wajen Herde tana kukan shagwab'a tace "Ayya kinga yaron nan ya k'i bani littafina dana arama masa ko? Wai ce min yayi ma ya b'ata baisan inda yake ba." Cikin b'acin rai yace "Ke ban bayarwa d'in, bana fad'a miki in na ganshi na baki ba." Wani kukan ta saka tana fad'in "Wallahi k'arya kake, ni in baka bani kayana ba saina fad'awa Aba, haka kawai ai bani na hanaka zama lokacin da ake darasin ba har ka rasa." Da mamaki Herde tace "Wai Faduma kina nufin baya zama a cikin aji?" Da sauri tace "Wallahi Ayya baya zama, wasu sabbin abokai yayi da basa jin magana, kuma yanzu ma sa.." Nufa kanta da yayi yana harba mata k'afa yasa ta yin shiru tana lab'ewa bayan Ayya, nunata yayi yana fad'in "Allah saina zubar miki da hak'ora, Ayya k'arya take." Ya k'arashe shima da kallonta, cikin fad'a tace "Yanzu kai ko kunya baka ji? K'anwarka har ta riskeka a ajin da kake kuma a hakan kana so ma ta sake wucewa ta barka, lallai baka nema na da zaman lafiya Abakar, bari Abanku ya dawo zan fad'a masa abinda kake yi." Kallon Faduma tayi tace "Kinga je ki canza kayanki kar lokaci ya wuce." "To." Ta fad'a da sauri tana nufa hanyar k'ofa, bata ankara ba ya wurga mata takalminshi k'afa ciki na ball a baya, durk'ushewa tayi ta fashe da kuka dan taji zafi sosai, mik'ewa Herde tayi da gudu ya dan yasan saita rama mata, lallab'ata tayi ta bata hak'uri ta mata alk'awarin saita rama mata in ya dawo, mik'ewa tayi tana share hawaye ta fita, a nesa da k'ofar gidan ta hangeshi tsaye ya juya baya kamar yana hangen wani abu, duddubawa tayi har saida ta samu wani dutsi ta d'auka ta nufeshi, bata tsaya komai ba ita ma ta rusa mai shi a kai sai a k'eyarshi kuwa kuma take ta b'alle da jini, da wani irin bala'i ya durk'ushe ya dafe kanshi sosai yana hawaye. Da gudu ta juya ta nufi gida shi kuma wasu dake kusa suke fad'in "Subhanallahi, ai k'anwarsa ce." Da sauri ya mik'e ya juya ya nufi gidan shima yana share hawaye, cak ta tsaya ganin Hadizey zata shiga d'aki da alama alwala tayi, kallon tuhuma ta bita dashi ta kirata da hannu, matsowa tayi ta tsaya kusanta tana sunkuyar da kai, fuska a had'e tace "Miye na gudu? Faduma nutsuwar kenan? Kina mace kina gudu haka kamar an koroki." Girgiza kai tayi kawai tana rarraba ido, hararanta tayi tace "Miye?" Girgiza kai ta sake yi alamar ba komai, cikin kakkausan murya tace "Faduma!" "Na'am." Ta fad'a tana d'aga kanta, ba tare data daina binta da kallon nan ba tace "Kin dai san na tsani k'arya ko?" D'aga kai tayi alamar eh, dan haka tace "Fad'a min me kike ma gudu?" A hankali tace "Ayya Abakar ne fa..." Bata gama fad'a ba ya shigo gidan a hassale, da gudu ta bige Ayya gefe ta shige d'aki, girmama juna da ladabi yasa ya ja birki bai iya nuna b'acin ranshi ba a gabanta, ganin ya dafe kanshi yasa tace "Halan ta fasa maka kai?" Juya mata yayi yana nuna mata kan, dafe k'irji tayi da sauri ta tsorata tana fad'in "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, jini kake zubarwa Abakar, ita ce ta fasa maka haka ." D'aga kai kawai yayi bai ce komai ba, da sauri ta shiga d'akin ta samu kyakyawan k'yale ta fito dashi, jinin ta fara goge masa amma sai taga har yanzu fitowa yake, idonta na zubar da hawayen tausayin tace "Abakar Kalli na gida ne?" "A'a." Ya fad'a a hankali, kamar zata d'ora hannu akai tace "Wallahi jini ke fita sosai, dan Allah muje na rakaka asibiti da alama sai an maka d'inki dan naga ciwon da zurfi." Da sauri ta koma d'akin ta zari hijabi da k'aramar jakarta, har zata fito ta juya ta kalli Faduma da ke jin komai ta rakub'e ta rasa yin komai, nuna ta tayi da yatsa tace "Maganata dake mai tsayi, karki bar gidan nan har na dawo." Tana fad'a ta fita ita kuma ta fashe da kuka, duk da tasan ba zata tab'a dukanta ba dan Abanta ya hana, amma hukuncin Ayyarta ya kan mata tsanani komai k'ank'antarshi. *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 17:09 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _17_ Saida aka mishi d'inki akai suka siyo magani suka dawo gida, kai tsaye can ta wuce dashi, Herde dariya tayi har da rik'e ciki tana fad'in ta ji dad'i, kuma saita ta sake fad'a ma Hadizey yanda akayi, amma tace sam bata fahimta saita hukunta ta, ita ma kuma tace zata sake fasa mishi kai in aka tab'a mata 'ya, da wannan ta baro gidan ta shigo na ta, tana shiga d'akin Faduma da bata motsa daga inda take ba ta mik'e, ja baya ta fara yi tana sake silalo hawaye tana fad'in "Dan Allah Ayya kiyi hak'uri ba zan k'ara ba wallahi." Gyara zaman hijabinta tayi ta d'auki sallaya ta shinfid'a ta kabbara sallah ko kallonta ba tayi ba, komawa tayi ta zauna ta jingina a jikin kujera tana kallonta tana sallahta cikin nutsuwa, ta jima dan saida ta kammala har azkhar d'in ta na yamma kafin ta gyara zama ta juyo ta kalleta, a hankali ta furta "Kinyi sallah?" D'aga kai tayi alamar eh, a hankali ta sake furta "Zo nan." Inda ta nuna mata ta kalla kafin ta matso da jan k'ugu kusa da ita tana had'a kanta da gwiwa tana b'oye fuskarta a cikin cinyoyinta, kallonta tayi sosai tace "Faduma me ya aikeki fad'a da namiji? Ko yar uwarki mace na yarje miki fad'a da ita ne?" Girgiza kai tayi tace "A'a, kiyi hak'uri Ayya ba zan sake ba." Ajiyar zuciya ta sauke tace "Me yasa baki rama daidai abinda ya miki ba? Ko kin manta da shari'a ma tana rama daidai da abinda akayi ne, idan ka cirewa wani hannu kaima hannu za'a cire maka, idan ka cire hak'ora kai ma za'a cire naka ne, kin manta da hakane Fati?" Wasu hawaye ne suka sulalo mata tace "Wallahi Ayya ban jefa masa da tunanin zan same sa sosai ba, kiyi hak'uri ki ban izini naje na bashi hak'uri, ba dagangan na zubar masa da jini ba." Wata harara ta wurga mata tace "Faduma kina manta wani abu." Da sauri ta kalleta da son tunano abun, kafin ta tuna wani abu tace mata "Me nake yawan fad'a miki akan alak'arki da maza ko da yan uwanki ne?" Da sauri tace "Ban manta ba Ayya, kin ce na daina wasa tare da maza a gida ko waje, karna yarda wani namiji ya tab'a jikina hakan zai sani jin kunya, zai iya ja min zund'en mutane da zubewar darajata." Sassauta murya tayi sosai tace "Ayya ki yarda dani, wallahi ba fad'a mukayi ba kawai daga magana ne saiya jefeni da takalmi shine nima na rama." Ajiyar zuciya ta sake saukewa ta kalli agogo sai kuma ta kalleta tace "Lokacin makaranta ya wuce, gobe da safe sai kiji, yanzu tashi ki d'ora mata tukunyar tuwo." Cike da farin cikin ba'a hukuntata ba ta mik'e tana cire hijabinta ta fita, fitowa tayi ita ma sai dai zaune tayi tana kallon kai kawonta, ta kuma yi farin ciki ganin tana d'aukar duk abinda take koya mata, duk da dai tasan Fati ba daga nan ba dan duk abinda ta fad'a mata sau d'aya to ta haddace shi kenan, yanzun haka aikin take da sauri sauri sai dai cikin wata irin nutsuwa mai birgewa da ban sha'awa, gashi komai a hankalce da lura take yinshi, wanda hakan zai birge ko mace bare kuma namiji, musamman yanda jikinta ke kad'awa gaba da bayan, kafin magriba har ta tuk'e tuwon shinkafarta da busassar miyar kub'ewa, duk yanda tasan mahaifiyarta nayi haka tayi ba tare data ce mata yi haka ba, har wutar ta kashe ta d'ibi wacce za tayi turare a d'aki ta d'auke komai sai wurin ya zama kamar ba ayi aiki ba, lokacin magriba ta kawo kai sosai tabarma ta shinfid'a a inda tasan mahaifinta na zama dan yau yana wajen Ayyarta ne, ba wai ta fad'a mata bane ko tana lissafe da kwanakin, kawai ta lura da yanda tun safe daya shigo suka gaisa ya fita ta ga tana ta gyaren jiki, jog d'in ruwa da kofinta ta aje sannan ta d'auki buta ta zubo ruwa, ta juyo zata kai ta ajiye ya shigo da sallama. Da sauri sauri ta aje butar tana durk'usawa da karb'ar ledar hannunshi tana fad'in "Aba na sannu da zuwa." Dafa kanta yayi da murmushi yace "Yawwa Fadun Abanta, anwuni lafiya?" "Lafiya lau." Ta fad'a tana kallon Ayyarta data taso ita ma, gata dai tsaye gabanshi tana jin yana amsa gaisuwarta amma har ga Allah bata jin ita me take fad'a, sai ma shagala da tayi da kallonta irin karairayar da take da lumshe ido tana wani tattausan murmushi kamar zatayi kuka sai shagwab'a take. A hankali ta sunkuyar da kai tana sakin murmushi, saida taji yasa hannu ya tallabota ta tuna ashe durk'ushe take, kafad'arta ya dafa yana fad'in "Faduna ya ake ciki? Har an taso daga makaranta?" Tare suka kalli juna da Ayya sai kuma tace "Lafiya lau Aba." Bakin tabarma ya zauna ya zage takalminshi yana jawo butar zai fara alwala, kusa dashi ta zauna tana aje ledar data karb'a tana fad'in "Aba ya kasuwa? Kayi ciniki sosai yau?" Kallonta yayi yana nad'e hannayen rigarshi yace "Alhamdulillah Fati na, kasuwa tayi kyau yau shiyasa ma na siyo miki tsire, ai zaki ci ko?" Murmushin jin kunya tayi tace "To Aba kai ka ci ne?" Girgiza kai yayi yace "Ina zan ci Faduma? Bayan ke baki ci ba." Turo baki tayi tace "To Aba kaje ka dawo nima sai tare da kai bai zan ci." Murmushi kawai ya sake yi ya fara alwalar, saida ya idar ya fita masallaci suma sukayi alwala suka kabarta na su sallar. S1ida yayi sallah isha'i sannan ya dawo kan tabarmar ya zauna inda Faduma ke jiran dawowarshi, zaune yayi yana fad'in "To 'yar Ayyoyinta, ina jinki me ke labari?" Hadizey dake zaune gefe akan kujera ta kalleshi tace "Ta fara fad'a maka ta'asar da tayi wa Abakar tukuna." Kallonta yayi ya kuma kalli Faduma da tuni ta sunkuyar da kanta, murmushi ya saki ya kamo hannunta yace "Tunda naga kina sunkuyar da kai nasan kinyi nadama ne ko?" Da sauri ta kalleshi ta d'aga kai tace "Nayi Aba." Wani murmushin ya sake yi yace "Nasan kuma zaki bashi hak'uri ko?" Sake d'aga kai tayi tace "Zan je na bashi hak'uri Aba." Jinjina kai yayi yace "Kuma duk yanda akayi shi ya fara takalarki ko?" Da sauri ta sake d'aga kai tace "Eh Aba, shi ya fara jifana da takalmi." Waro ido yayi sai kuma ya jinjina kai yace "Rabu dashi zan koma gidan ai zamu had'u." Hadizey dake kallonsu ne ta girgiza kai tace "Da laifinta, da kuskurenta, da haukanta kai duk ba damuwa bane a gareka, komai tayi daidai ne ba zaka nuna mata ba daidai ba, jini fa ta fitarwa yaron nan har saida na kaisa aka masa d'inki, amma kuma baka damu ba sai ma wani biye mata kake." Kallon Faduma yayi yace "Ta fita ba da izinina ba kuma shine baki fad'a min ba?" Rarraba ido tayi tsakanin Ayya da Aba sai kawai tayi murmushi ta sunkuyar da kai, jinjina kai yayi yace "Ana neman d'aurawa 'yata laifi ashe ma ke ce k'asurgumar mai laifin." Cikin taushin murya tace "To ai dama zan..." Bata kai ga fad'a ba Barka ya shigo da sallama gidan, amsawa duka sukayi inda ya durk'usa gaban tabarmar yana gaishe da iyayen, saida suka gaisa Faduma ta kalleshi tace "Yaya Barkuku sannu da zuwa." Kallonta yayi yace "Ke Fadu bana son iskanci." K'wafa yayi ita kuma ta mishi gwalo, kallon ledar hannunshi tayi tace "Me ka kawo min ne?" Kallonta yayi yace "Ya akayi kika san ke na kawoka?" Murmushi tayi tace "Saboda yanda ka min magana ne, da baka shirin kyautata min da zaka kirani da Faduma, amma da naga kana min rashin ladabi to zaka min wani abun alkairi ne." Ledar hannunshi ya jefa mata inda Aba ya tintsere da dariya yana girgiza kai, Barka kuma cewa yayi "Ke dai anyi yar jaraba, Aba yarinyar nan ka turata ta zama jami'ar bincike." Da sauri ta mak'ale kafad'a tace "Um um! Ni lauya zan zama Aba." Gwalo ya mata yace "Ana nan dai, ba'a rabu da Bukar ba an haifi Abu." Bata kulashi ba sai ledar data bud'e ta ciro safar k'afar da take masifar son ya siyo mata da kuma hijab mai kyau, mik'ewa tayi ta saka hakan yasa shi sauka sosai kamar zai ja k'asa tsabar tsayinshi, murna tayi sosai ta kalleshi tace "Nagode yaya Barka." Murmushi kawai yayi ya mik'e zai shiga d'akinshi dake k'ofar shigowa, zaune tayi tana mayar dasu a ledar, kallon Aba tayi tace "Aba ka mana addu'a a masallaci?" Jinjina kai yayi yace "Sosai Faduma, ai ku d'in nan kune rayuwata, taya zan iya mantawa daku a addu'ata." Cikin zumud'i tace "Aba me ka rok'a mana?" Cike da gajiya Ayya tace "Aba, Aba, Aba, wai ke bakinki baya ciwo ne? Ki sarara masa mana na d'an lokaci." Gum tayi da bakin tana kallon Aba dake murmushi, hararanta tayi tace "d'auke ledojin nan ki koma d'aki." Da sauri ta had'a kayan zata mik'e ya kamo hannunta, tallabo kanta yayi cikin kunne ya rad'a mata "Karki damu kinji, bari tayi bacci sai muyi hirarmu, ni na b'ata mata rai shine zata huce kan ki dan tasan bana son a tab'a min ke, rabu da ita kinji ko?" D'ago kai tayi ta kalleshi sai suka bushe da dariya, bata yarda ta had'a ido da Hadizey ba har ta shige d'aki, kallonta yayi yana k'ok'arin tsayar da dariyar yace "To amaryata sarauniyar mata, matso nan kusa dani naji me ke damunki ne." Tasowa tayi ta zauna kusanshi tana turo baki gaba, murmushi yayi yace "Har yanzu baki hak'ura ba kenan? To shikenan ki shirya gobe sai ku tafi tare da Fatima." Murmushi ta saki tana b'oye fuskarta tsakanin cinyoyinta, girgiza kai yayi yana wani murmushin, a hankali ta d'ago ta kalleshi tace "A kawo abinci ne?" Numfashi ya sauke yace "Kawo, ina fatan dai Fatina ta girka? Dan yanzu nafi jin dad'in girkinta fiye da ku da kuka koya mata." Wani kallo ta masa sai kuma ta turo baki tana kyab'e fuska ita tayi hushi, dariya yayi yace "Na tuba to d'auko min na ci yunwa nake ji." Cikin shagwab'a tace "Ka kira wacce ta dafa ta kawo maka." Lek'a fuskarta yayi yace "Idan ta kawo kin yarda ta saka min har a baki ma?" Saida ta d'age gira tace "Duk yanda kake so saita maka, tunda ta fini iya dafawa." Dariya ya sake yi yace "Shikenan bari na kirata ta zo ta kwashe ladar ita kad'ai yar albarkar." Da sauri ta mik'e tsaye tana fad'in "Shikenan to na tafi." Bushewa yayi da dariya ya bita da kallo har ta shige d'aki, k'wala kiran sunan Faduma yayi ta amsa da ladabi ta fito, ledar tsiren ya mik'a mata yace "Na ki ne." Durk'usawa tayi ta karb'a tana godiya, d'aki ta shiga dashi ta samu plate ta juye, biyu ta raba dan yana dayawa tasan kawai ya fad'a ne amma ba yana nufin ita d'ayan ba, fitowa tayi ta aje musu plate d'aya saita wuce da d'ayan d'akin Barka, sallama tayi ya amsa ya bata izinin shiga, cikin zolaya ta kalleshi tace "Yeee Barkuku, kai da masoyiyar ce halan a waya?" Mik'ewa yayi zaune yana fad'in "Zan sake kira." Ya kashe wayar, fizgo hannunta yayi yana fad'in "Fadun Aba kin raina ni wallahi, wai me nai miki ne?" Fizge hannunta tayi da k'arfi tana aje plate d'in hannunta da fad'in "Kai dallah dubi abinda na zo mu ci fa." Kallon plate d'in yayi yace "Iye! Halan Aba ne ya siyo miki?" Cikin kuri ta jujjuya ido tace "Eh mana, eh mana, eh mana eh mana eh mana." Dariya yayi sosai ganin yanda take wani rausaya da wak'a, girgiza kai yayi yace "Zauna to." Zaune tayi suna fuskantar juna ta tank'washe k'afafu suka saka hannu suna ci suna hira, saida suka ida ta mik'e zata fita da plate d'in tace "To biyani kud'in tsirena da ka ci?" Hararenta yayi yace "Tausheni ki k'wata." Hannu ta kai zata d'auki wayarshi dake gefe yayi saurin rik'e hannunta ya matse sosai, k'ara ta saki tana fad'in "Aba!!! Hannu na zai karye." Da sauri Aba ya mik'e daga cin abincin ya shiga d'akin, yana ganinshi ya saki hannunta yana hararenta, turo baki tayi jin Aba na fad'in "Barka ban hanaka zalintar yarinyar nan ba? Allah na sake jin kukanta a gidan nan sai ranka ya b'ace." Da mamaki ya kalleshi yace "Aba ba fa kuka bane take, wallahi iskanci ne duba idonta ka gani." Hannunta ya kama yana hararenshi yace "Ubanka take idan ba kuka ba?" K'wafa yayi suka fita a d'akin, kallon da Ayya ke mata yasa ta zame hannunta daga na Aba ta aje plate d'in wajen kayan wanke wanke ta shige d'aki, girgiza kai tayi tana kallonshi, shima kallonta yayi yace "Miye?" Girgiza kai tayi alamar ba komai kawai, dan abun ya fara bata haushi yanda dan Faduma na k'arama yake wani rawar kai a kanta, ba fa cewa akayi ba zai sake haihuwa ba, ko ita yanzu bata cire rai da sake samun haihuwa ba, amma baya son b'acin ranta ko ganin hawayenta. Duk da ita ma a wajenta hakane tana sonta fiye da komai, tana birgeta k'warai da gaske saboda komai na yarinyarta ta, amma hakan baisa ta kasa yin abinda ya dace akan tarbiyarta ba. Daf da asuba ta farka tana ta had'a uban gumi tana dafe da cikinta, sake matse mararta tayi ta rintse ido tana fad'in "Ayya, cikina ciwo, wayyo Allahna Ayya, marata ciwo take." Wani huci ta dinga yi tana sake dafe cikinta da mara, ba kowa d'akin Ayyata na d'akin Abanta sai ita kad'ai, gashi ba zata iya yanda zata tashi hankalinsu ba, haka ta dinga murkususunta ita kad'ai a d'akin tayi kwance ta tashi zaune ta mik'e tsaye ta durk'usa ta rasa yanda zatayi da ranta, sai dai tafi ta'allak'a ciwon da tsiren data ci ne ya lalata mata ciki, gashi kuma bata samu ko shiga bayi ba bare ta tabbatar da haka, saida ta galabaita sosai lokacin an fara kiran sallah, kiran farko taji ana bud'e k'ofar d'akin, zuba ido tayi taga wanda zai shigo, tana ganin Ayya ce tayi saurin mik'ewa zaune tana sake yamutsa fuska, a hankali ta taka har take gabanta tace "Tashi kiyi alwala." Cikin matse ciki da had'e fuska tace "Ayya cikina ne ke ciwo, ki bani magani nasha sai nayi." Kallonta tayi sosai sai kuma ta zauna kusa da ita tana ci gaba da kallonta, a hankali tasa hannu ta gyara mata gashinta dake dunk'ule amma tsabar wahala duk ya barbaje, zufar da tayi duk ta jik'e gashin nata dake gaban goshinta ga kuma yalwar gashin dama, cikin wata sanyayyar murya tace "Fatima Zahra." Cikin muryar wahala ta amsa da "Na'am Ayya." Tallabo fuskarta tayi tana kallon idonta, hawayen da suka gangaro mata ne tasa hannu ta share mata tare da jawo kanta ta d'ora saman cinyarta, gashinta ta ci gaba da gyara mata shi a hankali tana fad'in "Kiyi hak'uri kinji, zai daina insha Allahu yanzu, Fati abinda kike ji yanzu yanayi ne dake sake tabbatar mana lallai fa 'yarmu ta girma, nasan kin balaga ba tun yau na Faduma, amma abinda yanzun ke shirin zuwa miki shine zai sake kaiki wani mataki da kowace mace data amsa sunanta take kai, girma zai sake riskarki ta yanda akwai abubuwan da yanzu dan dolenki ki hak'ura dasu ki kuma kiyaye wasu, Fatima a daidai wannan k'adamin zan fassara miki maganar da nake miki a dunk'ule kullum, yammacin jiya kin maimaita da kanki, yanzu kuma zan fad'a miki abinda nake nufi." Yar ajiyar zuciya ta sauke ta ci gaba da fad'in "Faduma, a yanzu inhar kikayi sakacin da wani namiji ya tab'a ko da hannunki ne to fa ki sani zaki d'auki ciki, shin kina so kiyi cikin haihuwa ba tare da aure ba?" Girgiza kai tayi da sauri, murmushi tayi tace "Da kyau, dan haka sai ki kiyaye keb'ewa da namiji ko waye shi, duk kuma wanda ya nemi tab'a jikinki to ki nuna masa b'acin ranki kwatankwacin wanda kika nuna wa d'an uwanki d'azu har kika rotsa masa kai, dan in bakiyi haka ba zai sa ki jin kunyar iyayenki, yan uwanki da yan unguwarki da ma *'ya'yan da zaki haifa*, dan haka ki kiyaye." Jinjina kai tayi tana rintse ido tace "Insha Allahu Ayya zan kula." Jinjina kai tayi ita ma tace "Ba sai na taimaka miki ba, nasan da zuwan wannan ranar shiyasa na koyar dake komai tun kafin ki risketa, dan a ganina yanayin zai iya fara zuwa miki bama tare, kina makaranta ko islamiyya ko wani wuri, ai kinsan yanda zakiyi ko?" Saida ta d'aga kanta tace "Ayya duk abinda kika koya min bana manta shi, yana zama akai na kamar yanda karatu ke zauna min akai." Cike da jin dad'i ta shafi kumcinta tace "Je ki kula da kanki, zan kawo miki maganin da zai rage miki rad'ad'in, idan kika ida sai ki sha ki koma ki kwanta kafin safe." Mik'ewa tayi ta bud'a wajen kaya, kamar jira ake ta mik'e kam sai taji abu ya biyo k'afafunta mai sanyi sanyi had'e da d'umi, da sauri ta juya ta kalli inda Ayya ke zaune, ganin ta mik'e zata fita yasa ta sauke ajiyar zuciya, matsawa tayi baya ganin jini yasa gabanta fad'uwa, sai kuma ta sake sauke ajiyar zuciya, sabon pant ta d'auka da pad d'in da Ayya ta aje mata dan zuwan ranar, fita tayi ta shiga ban d'aki ta canza na jikinta ta saka, tana dawowa ta gyara inda ya b'ace ta fita ta wanke kayan, shanyasu tayi sannan ta dawo d'auki maganin data aje mata tasha, kwance tayi tana d'an cije baki in ya motso mata, kasancewar Ibu ne tasha cikin sarautar Allah sai taji sauk'i sosai har bacci ya d'auketa bata sani ba. Da safe ta tashi lafiya lau tayi shirin islamiyyarta, d'akin Aba ta shiga da sallama ya amsa sannan ta wuce ciki, gaisheshi tayi kamar yanda suka saba tace zata wuce makaranta, addu'a ya mata tare da bata yan canji, kallonshi tayi tace "A'a Aba ka rik'e kayanka, na ci abinci na sha ruwa ka sa min albarka, ni kam me zanyi da kud'i? Ka rik'e ka k'arawa Ayya kud'in cefanai." Dariya sukayi tare ya sake binta da wasu addu'o'in sannan ta fita, Barka na fitowa zai fita shima yace "Auta jira na fito sai na kaiki." Kallonshi tayi tana tunano maganar Ayya ta jiya, indai ta hau babur jikinta zai iya tab'a nashi, to in fa ta samu ciki? Ko kuwa shi yayanta ne babu abinda zai faru? Girgiza mishi kai tayi tace "A'a kowa yayi tafiyarsa." Da mamaki ya bita da kallo, wacce wata rana take tashinshi da tsiya tace saiya kaita, inba haka ba ya bata makullin babur d'inta ta d'auki dreban da zai rik'a kaita, amma yau ita ce da cewa a'a, lallai ya fad'a yana wuce d'akin da sallama shima. *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 17:10 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _18_ Ko da ta taso yau ta samu Ayya har ta kammala aikinta, dan haka ciren kayanta tayi kawai ta shiga wata sabgar ita ma, bayan tayi sallah azahar ta ci abinci ta kwanta dan ta huta, da yake litinin ce basa karatun yamma yasa Ayya cewa "Zan tasheki da anyi la'asar dan zan aikeki gidansu *Abdul Razaq*." Wani kallo ta mata kamar tace satin fa daya wuce ta je, me kuma zata je yi yanzu? Ba tace komai ba ta kwanta da tunanin zuwanta gidan nan fa yayi yawa, ko dai yana gidan yayan mahaifinta ne amma nisan dake tsakaninsu bai kai ta dinga zuwa ba haka kusan wata ko satittika gashi yanzu duka sati ne a tsakani ma kuma za'a sake aikenta, kuma aiken da ake mata ba wani abun a zo a gani ba, wani lokacin sak'on fatar baki ne ake bata wanda za'a iya yin shi ta waya, da wannan tunanin har bacci ya d'auketa daga nan. Hadizey ma kallonta take har ta ga bacci ya d'auke, mahaifinta da mahaifin Abdul Razaq sun gama magana kan had'a aurensu, kowa ya amince da maganar ita ce da ake ganin kamar da yarinta tare da ita sai ba'a fad'a mata ba, amma kuma Abanta yace baya da tsarin auren dole wa 'ya'yansa bare kuma wacce tafi soyuwa a gareshi, dan haka yake umarta lokaci bayan lokaci ta dinga ziyartar gidan ta yanda ko bata so shi ba zata so zama cikinsu, shi ma kuma haka yana kawo ziyara gidan tare da nuna mata a fili manufarshi. Amma abun dake bata mamaki shine yanda ko sau d'aya bai tab'a wani d'ad'a Faduma a k'asa ba ta yanda har zata hango ko da da burbushin manufarshi, har kyauta yake mata masu kyau wanda zasu birge mace, amma saita wani basar kamar bai mata ba ko ta nuna duk d'aya ita a wurinta. Ajiyar zuciya ta sauke tana tunanin to kodai tubka ne take ta gaba tana warwara da kanta ta baya? Kar a zo tsanin data d'orata na fita harkar maza yasa ba zata iya sanin sirrin zuciyarsu akan k'wayar idonsu ba ko a aikacensu? Jinjina kai kawai tayi tana ci gaba da tattauna abun tsakaninta da zuciyarta. Ana kiran sallah ta tashi kanta dan akwai masallaci kusa dasu sosai, alwala ta fara yi tayi sallah sannan tayi wanka, cikin nutsuwa da kamala ta shirya cikin riga da siket na atamfa ta d'ora hijabin da yaya Barka ya kawo mata, babu abinda ta shafa a fuskarta hatta da hoda ma, nik'ab ta d'auka ta d'aura sannan ta fito karb'an sak'on wajen Ayya, tunda ta ga fitowarta ta k'ureta da ido, saida ta tsaya gabanta ta sauke numfashi tace "Fati duk wannan shirin fa na miye?" Saida ta kalli kanta sannan tace "Ayya ba aikena zakiyi ba?" Zaro ido tayi tace "Dan zan aikeki ne kikayi wannan shigar? Fati, shigar mai kyau ce sosai kuma ta birgeni, amma ki d'an canza kinji tunda gidan baffanki ne zaki je." Turo baki tayi ta juya zata koma d'aki tayi saurin cewa "Kinga d'auko lafaya ki kawo na d'aura miki." Jinjina kai tayi ta wuce ciki, jim kad'an ta fito ba hijab d'in da nik'ab sai lafaya a hannu, karb'a tayi ta shiga d'aura mata tattausar lafayar fara ce amma mai kwalliya sosai, saida ta gama d'aura mata ta kalleta tace "D'auko kayan kwalliya to a d'an shafa ko kad'an." Kamar zata fashe da kuka tace "Ayya ni bana son kwalliya yanzu." A hankali tace "Saboda me?" Shiru tayi dan bata da dalili, cewa tayi "Fatima mace ai yar kwalliya ce, duk kyanki kina buk'atar wannan zanen, haka Allah ya hallicemu kuma ya fad'a mana ma ko a Alqur'ani, mu mata muna da son k'awa mu b'oyeshi ga wanda basu hallata mana ba mu bayyana shi ga wanda suka hallata." Juyawa tayi ta d'auko kayan a hannu ta aje, kujera taja ta zauna suka kallon juna, a hankali cikin nutsuwa ta fara shafa mata hodar data dace da kalar fatarta mai d'an duhu, sannan ta mitsika mata kwalli a ido ta shace mata girar ido data sama, d'an bakin kwalli ta saka mata a baki saita shafa mata man leb'e mai dank'o sosai da k'yali, kallonta tayi ta saki murmushi tace "Haba ko kefa, kin ganki kuwa?" Madubi ta mik'a mata ta karb'a tana dubawa, dariya tayi tace "Ayya nayi kyau?" Cike da tabbaci tace "Sosai ma." Tattara kayan tayi ta shiga ta mayar ta fito, dawowa tayi wurinta tace "To Ayya me zan ce musu?" Mik'ewa tayi tana fad'in "Ina zuwa." D'aki ta shiga ita kuma ta wuce wurin wajen jog d'in dake da k'ank'ara a ciki ta d'auka zata sha ruwa, da saurin bala'i ta lek'o daga d'akin tana fad'in "Kar ki sha, Fati wai ban hanaki yawan anfani da ruwan sanyin nan ba? Ina wanda na nuna miki." Kyab'e fuskata tayi sosai ta aje ta nufi wajen flas d'in shayi, bud'ewa tayi ta d'an tsiyaya a murfin, lipton ne da karanfani sosai a ciki sai zuma, sha tayi ba dan tana so ba saboda gumin dake akwai ta aje, kiranta tayi ta shiga d'akin, ganin sai b'ata rai take yasa tace "Miye kike wani had'e min fuska? Malama saki fuskar nan kinji." Sakin fuskar tayi amma kuma a had'e take, cikin shagwab'a tace "Ayya ana zafi yanzu, amma tun safe kin hanani shan ruwan sanyi mak'oshi har ya bushe nake ji." Girgiza kai tayi ta kalleta a nutse tace "Faduma, ba dan na cutar dake na hanaki ba sai dan lafiyarki, yanzu fad'a min tunda kika fara shan waccen d'in me kika iya fahimta a tare dake ko yanayinki?" Shiru tayi tana rarraba ido tsakanin k'ofar d'akin da Ayya, ta d'an jima a haka kafin tace "Marata nake jin ba nauyi sakayau da ita, sannan ina jin wani irin d'umi a jikina wanda ya banbanta dana yanayin zafin da muke ciki, sannan...idan ina fitsari ma na kan iya ji k'amshin karanfani na fita." Murmushi ta mata mai had'e da dariya tace "Kina da lura Fati, nasan kuma kina ganin jinin ma na fita miki da kyau ba tare da wata wahala ba ko?" Cike da kunya ta sunkuyar da kanta k'asa, dafa kan nata tayi ta d'ago da ita tana fad'in "Faduma ina so ne ko ba ma tare dake ace kinsan matakan kula da kanki, ko aure kikayi na tabbata ba zaki saka kanki a rayuwar bin malamai da bokaye ba wajen neman biyan buk'atar data shafi d'a namiji, fintinkau, ina so naga kinyi fintinkau a gidanki yar albarka." Hannaye tasa ta rufe fuska tana fad'in "Ayya ki bari dan Allah kunya nake ji." Girgiza kai tayi ta mik'a mata ledar hannunta tace "Ki kaiwa Hajia *Kubra* in ji ni, daga nan ki gaishe da kowa da kowa, amma bana so ki kai magriba baki dawo ba, kin gane?" D'aga kai tayi alamar eh tana karb'ar ledar ta fito, tare suka fita a d'akin tana bata kud'in da zata shiga taxi, kallonta tayi tace "Ayya ki rik'e na dawowar tunda ko naje suna bani." Girgiza kai tayi tace "Ki tafi kawai." Wucewa tayi tana fad'in "Saina dawo Ayya." Da "Allah ya kiyaye." Ta bita tana kallo har ta fita. Taxi ta samu ita kad'ai ta d'auketa ta fad'i unguwar, kallon titi take tana tunane tunane har suka dunfari unguwar, suna shiga layin ta ba hawa ba sauka ta ji gabanta ya yanke ya fad'i, da sauri ta dafe k'irjinta tana furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un." Rarraba ido ta shiga yi tana tunanin dalilin dake kawo haka, to ita dai tana jin yara na cewa in ana gulmarka a wani wurin hakan na faruwa, d'an cije leb'e tayi ta lumshe ido tace "Nasan ma su Maryam ne aka had'u ake gulmata saboda fad'anmu na jiya." K'wafa tayi tana fad'in "Na koma unguwar ai har gidansu zanje a mana tsakani." Lokacin kuma hankalinta ya kai kan dandazon samarin dake k'ofar gidan, d'agowa tayi tana ta d'aga kai tana hangensu da tunanin me ke faruwa, cinkoson wurin na matasan da kuma ababen hawa yasa mai taxi tsayawa daga d'an nesa, ko da taji haka ta mik'a masa kud'inshi ta bud'e, a hankali ta zura k'afar hagu sannan ta dama ta fita ta rufe k'ofar. Har yayi shataletale ya juya tana tsaye tana hangensu, gabanta sake fad'uwa yake jikinta har ya d'auki makyarkyata saboda rashin sabo da tsoro, tunanin yanda zata ratsasu ta wuce take, bata tab'a shiga jama'a maza irin haka ba, ganin su kuma hankalinsu kwance sai shewa da dariya suke kawai ta juya da niyyar shanye doguwar tafiya ta zagaya ta baya, dan anan saita wuce ta gabansu sanan ta shiga ciki, ta can kuma saita kai gidan sannan ta kai garesu, ta juya kenan taji an kira sunanta da "Faduma." Tsayawa tayi ta juyo a hankali, a hankali ta sauke b'oyayyar ajiyar zuciya ganin Abdul ne ya tunkarota, shima tunda ya hangota ne jikinshi ya bashi ba zata iya wucewa ta nan ba, dan haka ya zo ya mata jagora dan komawa ta waccen layin tafiya ce mai zaman kanta. Da murmushi ya k'araso gabanta yana cewa "Ina zaki je? Komawa zakiyi ta d'aya hanyar?" Murmushi tayi ta sinne kanta k'asa kamar zata durk'usa tace "Ina wuni yaya Razaq." Wani murmushin jin dad'i da k'asaita ya saki ya amsa da "Lafiya lau, kina lafiya?" Jinjina kai kawai tayi alamar eh, da hannu ya nuna mata hanya yace "Muje ko saina rakaki, kiyi hak'uri unguwarta mu yau ana sabga ne, wani abokinmu zai auri mak'wabciyarmu bahaushiya, to nan ana k'umshi ne suna jiran yan mata." Komai ba tace ba sai kallon hanyar data sake yi, a nutse ya sake ce mata "Wuce mu tafi, ko na d'auko mota na k'arasa dake ne?" Da sauri ta girgiza kai ta fara takawa a hankali tana ta nok'ewa, gefenta yake suna takawa a hankali cikin nutsuwa, kanta k'asa yake tana jin nauyin d'aga kai ta kalli tarin mazan, amma yanda take sake matsawa kusansu hakan ya k'ara haddasa bugawar k'irjinta, sai kuma k'afafunta da take jin kamar zasu kifar da ita a wurin ta fad'i warwas, tabbas tana jin ido a jikinta suna yawo, sai dai na mutane dayawa ne ko kuma na mutum d'aya ne bata sani ba, inhar dayawa ne to kad'an daga aikin gubar ido kenan, idan kuma na mutum d'aya ne to shakka babu idonshi na da wani sinadari daya sa take jin gajiyawa, zata so ko yaya ne ya sarara mata ta hanyar d'an kawar da idon nashi, sai dai tana sake kusanta kanta garesu tana sake shiga wannan yanayin. Cikin k'aguwa da zak'uwa ta d'aga idonta tana son ta lalabo mai mata kallon k'urillan nan, a cikin sa'a kawai idonta suka sauka cikin nashi, kusan a gefe yake jikin mota hannayenshi a hard'e, ya zuba mata ido kamar zai cinyeta. Harara ta so banka masa ta juya masa baki, to amma abun mamakin da al'ajabi saita kasa dauke idon nata daga kanshi ita ma ta bishi da wani kallo da kai tsaye fassara shi zaiyi wuya, saida ta d'an wuce shi kawai tayi nasarar kauce idonta zuwa gabanta, ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi tana sunkuyar da kanta, wanene shi? Wane irin kallo ne haka? Bata san ta kawo k'ofar gidan ba saida ta ji muryar Abdul na fad'in "Fatima yanzu zamu bar nan, ina fata dai ba yanzu zaki koma ba ko?" Juyowa tayi cikin nutsuwa ba tare data kalli fuskarshi ba tace "Gaskiya Ayya tace kar na kai magriba anan ban koma gida ba." Girgiza kai yayi yace "A'a gaskiya ban yarda ba, yau dai kawai Faduma ki bari na sameki a gidan nan mana." Cikin jin kunya ta shiga wasa da ledar hannunta tana fad'in "Yaya Ayya fad'a min zata min in na wuce lokacin data ce." "Fadumaaaa." Ya k'arashe da jan a d'in, sannan ya d'ora da fad'in "Ki bari zan kira dada da kaina na fad'a mata ni na ce ki jira." Kallonshi tayi cikin firgici da tsoro tace "A'a yaya, karka kirata dan Allah, zan iya zaunawa har bayan magriba amma ba sai ka kirata ba." Yanda tayi maganar a nuna a tsorace tayi, amma kuma cikin nutsuwa ta yanda kamar ba ita tayi maganar ba, murmushi ya sakar mata yace "Ko ke fa, amma kullum da kin zo ko hutawa ba kiyi sai ki koma." Jinjina kai tayi ta shiga ciki shi kuma ya fita, da sallama ta shiga inda matan uku da yara duk suka amsa mata, al'amarin na bata mamaki sosai yanda ta ga yanzu suna wani nuna kulawa sosai akan ta, duk da kishiyoyi ne kuma ana samun sab'ani wata rana, amma dai zaman lafiya yafi wanzuwa tsakaninsu, dukansu kuma kowace nuna mata k'auna take yi, hatta da k'anananshi wani girma taga duk suna bata da a baya ba haka bane. Ita dai ledar hannunta ta bawa mamanshi tace inji ta ta mamar sannan tana gaishesu, bata koma ba har saida tayi sallah magriba, amma gaba d'aya hankalinta a tashe yake, ko gidansu Herde bata cika kaiwa magriba ba, sai dai taje bayan sallah amma magriba gidansu take yin ta, tunda tayi sallah hankalinta ya koma gida kuma, tana fitowa daga d'akin Kubra da tayi sallah tace "Dada zan koma gida, dama yaya ne yace na bari har ayi sallah, yanzu Ayya na can na jirana hankalinta ya fara tashi." Murmushi tayi tace "Ai kuwa yanzu dai dan nasan halinta, to kinga bari Izzatu ta fito saita rakaki ki samu taxi." D'an jinjina kai tayi alamar to ta zauna kan bancin dake kusa da Kubra. _______________ Bayan rabuwarsu da ita ya dawo cikin abokanshi, a hankali ya kama hannunshi ya jashi gefe d'aya, saida ya gayyato nutsuwarshi a tare dashi ya kalleshi sosai yace "Abokina wacece wannan? K'anwarka ce?" Mamakin tambayar yasa shi mishi wani bahagon kallo yace "Tagur, ban sanka da bin bayan mace da zance ba, karka fara a kan k'anwata mana." Wani murmushi ya saki yana sauke numfashi yace "Alhamdulillah tunda k'anwarka ce, kai kasan tunda kaga haka to da magana." "Kamar wace kenan?" Ya fad'a yana hararenshi sama da k'asa, jujjuya idonshi yayi yace "Tatsuniyar gizo ai bata wuce ta k'ok'i, kai ka sanni kai tsaye nake abu ba kwalo kwalo, ina sonta." Duk da fad'uwar da gabansa yayi da kuma tashin hankalin daya shiga lokaci d'aya bai hanashi yin jarumtar b'oyewa ba har ya k'ak'aro murmushi ma yace "Da gaske ko wasa?" Wani kallo ya masa yace "Kamar ya wasa? Ka tab'a jin irin haka daga gareni ne?" Tab'e baki yayi yace "Shiyasa ai na tambayeka d'in dan ban tab'a ji ba." Rab'ashi yayi zai wuce ya rik'e hannunshi yana fad'in "Wallahi da gaske nake, ina ganinta naji abinda ban tab'a ji akan kowa ba, take naji k'ararrawa ta buga a zuciyata." Wata dariyar rainin hankali ya masa yace "Kai, dawo hankalinka kaji, k'anwata munyi mata miji ma, kasan mu tubawa auren fari a gida ake mana shi kafin kayi gaban kanka." Tsaki yayi yace "Wannan magana kuma sai dai ka fad'awa wanda ba batube ba, amma kasan nima shine gaba da baya, kuma babu abinda ban sani ba na al'ada." "Oho! Ka sani kuma shine zaka b'ata min lokaci?" Shi ma tab'e baki yayi yace "Kaga na gani ina so ne, kuma insha Allahu yarinyar can zata zama tawa, ka rubuta ka aje inhar ya tab'a faruwa to zan sake jadadda faruwarsa, in kuma bai faru ba to akai na za'a fara." Girgiza kai yayi ya wuce ya shiga mota dan ba zai juri jin zancen nan ba, yana son yarinyar shima saboda tarbiyarta da hankalinta, yasan yayansa zasuyi sa'ar uwa inhar ya aureta, Allah ba zai tab'a masa hisabi tsakaninshi da yaransa ba kan uwar daya zab'a musu, amma ga wani na son masa iskanci akan burinshi da kuma mafarkinshi, yana kallo har suka gama raharsu da yan matan amarya suka shishiga mota suka bar unguwar @ 360. _______________ Tare da Izza suka fito daga gidan bayan sunyi sallama, kuma duka matan kowace da kyautar data mata, saida taga sun dage sosai tana a'a suma suna saita karb'a kad'ai ta amsa, a hankali suke tafiya har suka kawo daf da titin, motar data tsaya gabansu ce yasa Izza cewa "Lah! Kinga ma ga yayan nan." Duk zuba wa motar ido sukayi har ya fito ya k'araso yana fad'in "Fatima haka mukayi dake? Ba dai tafiya ne zakiyi ba?" Sunkuyar da kai tayi tace "Eh yaya, bana so Ayya ta min fad'a, kuma Aba ya dawo gida yanzu dole nasan ya neme ni." Ajiyar zuciya ya sauke yace "Shikenan muje saina sauke ki." Da sauri ta girgiza kai tana fad'in "A'a nagode yaya." Wata harara ya dalla mata yana fad'in "Ke, ina wasa dake?" Da sauri ta sake girgiza kai alamar a'a, nuna mata hanya yayi yace "To wuce." Ledar hannun Izzatu ta karb'a dake ta mik'o mata, kallonta tayi tace "Nagode Izzatu, ki wa su Dada godiya sosai." Da murmushi tace "Fadu! Godiyar nan wai nawa za'a musu ne?" Murmushi tayi kawai ta wuce, da kanshi ya zagaya ya bud'e mata gaba da nufin ta zauna, wata motar ce ta haskesu sosai har saida dukansu suka saka tafukan hannayensu suna kare fuskarsu, daf dasu motar ta tsaya sai k'arar bud'ewa suka ji da rufewa, sauke tafukan hannun sukayi suka kalli inda suka ji ana takowa a tare. Wannan mutumin ne daya mata kallon nan na d'azu, inda Abdul kuma yace "Tagur." D'aga mishi gira yayi yace "Ashe kana nan?" Cikin jin haushi yace "Miye to? Bibiyata kake dama?" Girgiza kai yayi yace "Ko kad'an, zan je gidanku ne dan ka kaini gidansu, sai kuma na ganku anan da alama tafiya zatayi." Yanda ya k'arashe da kallonta yasa ta saurin d'auke idonta akan shi tana fad'in "Ina wuni." Murmushi ya mata yana k'ure fuskarta da kallo yace "Lafiya lau, muryarki da dad'i sosai." D'aga idonta tayi ta kalleshi sai kuma tayi saurin k'asa dasu saboda kallonta da yake shima, takaici ne yasa Abdul d'an sa hannu ya turashi gefe yana k'ara bud'e murfin k'ofar ya kalleta yace "Shiga mu tafi ke." Rab'ashi tayi ta gabanshi zata wuce yasha gabanta, yanda ya tsaya gabanta yasa ta ja baya sosai tana mishi wannan kallon jin haushi, a hassale Abdul yace "Tagur wai miye haka? Sauri muke fa gida zan kaita." Ba tare daya juyo ya kalleshi ba yace "Minti biyu magana zanyi da ita." K'ureta yayi da ido yace "Ya sunanki?" D'aga ido tayi ta kalleshi sai kuma ta sauke su ta shiga motsa baki kamar zata fad'a kuma tayi shiru, cikin wata murya ya sake fad'in "Sunanki me?" Nan ma shiru bata amsa mishi ba sai wik'i wik'i take da ido, cikin muryar gargad'i yace "Dake fa nake." Da sauri ta kalleshi tace "Faduma, Fatima Zahra." Yanda ta fad'i sunan a tsorace da kuma sauri yasa shi sakin murmushi, iskan bakinshi ya huro mata mai d'auke da k'amshin tom tom, d'an kawar da kanta tayi tana jan k'aramin tsaki, murmushin gefen labb'a yayi yace "Fadu." Yanda ya kira sunan ya tilasta mata juyowa ta kalleshi, ba wai dan bata tab'a jin hakan ba sai dan yanda taji hakan ya mata dad'i da dukan zuciyarta a take, saida ya sunkuyar da kanshi sosai cikin wata raunanniyar murya yace "Tunda nake a duniya ban tab'a ganin macen data birgeni ba kamar ki, ban tab'a sanin miye so ba sai yau kuma akan ki, Faduma ina sonki, so kuma na aure, zaki aure ni?" Bud'e baki tayi kamar zatayi magana sai kuma ta kalleshi da kyau, kallon me kake nufi dani ko me ka d'auke ni? Haka abun dama yake ko kuma shine a haka? Taya zai tareta a hanya ya fad'a mata haka kai tsaye a gaban yayanta? Bashi da tarbiya ne ko me? Bata gama tambayar kanta abubuwan al'ajabi a game da mutumin ma Abdul ya tureshi gefe yana fad'in "Tagur bana son iskanci, wace irin rayuwa ce haka? Ya zaka tare yarinya akan hanya kana fad'a mata wani wai kana sonta?" Rai b'ace ya kalleshi yace "Kar hannunka ya sake tab'a jikina Abdul, in har ba kishi kake ba ka barni na jarraba sa'ata." Da k'arfi ya sake tureshin dan ayi duk wacce za ayi har yana kaiwa daf da titi, cikin masifa yake fad'in "Na tab'a jikinka Tagur kashe ni, sanin dana maka kai ba d'an iska bane yasa zan d'aga maka k'afa, ba dan haka ba Allah daka gane shayi tsurar ruwa ne." K'wafa yayi ya juyo zai koma ga Faduma, ganin bata wajen yasa shi sake kallon wurin da kyau, hangenta sukayi ta d'auki hanya har ta tsayar da mai taxi zata shiga, da sauri ya nufi kanta yana fad'in "Faduma, Fadum..." Bai k'arasa ba ya tsaya yana hangenta har ta shiga sun tafi. Juyawa yayi ya kalli Tagur da shima yake kallon motar, hararenshi yayi ya wuce ga motarshi ya shiga ya tayar, kwanar gidan ya shiga ran shi a b'ace ya ci birki a k'ofar gidan da niyyar yin wanka ya je gidan, yau kam sai ya fad'a ko iyayenshi basu shirya ma hakan ba, zai fad'a mata shima dan tasan da zamanshi, amma ba zai bari Tagur ya masa sakiyar da babu ruwa ba, tabbas shi shaidane baya da wani mummunan hali da kai tsaye zai iya aibatashi dashi, inhar ya cancanci a bashi Faduma saboda nagartarshi, to Tagur ma na da wannan nagarta har da k'arin wacce shi baya da ita ma, amma fa wannan lamarin soyayya ne da bai san wannan ba bare ya sadaukar masa da ita, zaiyi yak'i ne har inda k'arfinsa ya k'are sai in ita kawai ta furta *bata son shi*, to anan bai da wani abinda zai iya yi kuma face ya ja baya. Yana ganin ya shiga motarshi shima ya shiga tashi ya bi bayan taxi, gudu yake sosai har saida yayi nasarar shan gabansu sukataka birki, taxi ne ya fara zunduma mishi ashar da fad'in ko mahaukaci ne? Fitowa yayi ya nufo motar ya bud'e inda take zaune, duk ta tsorata sai zare ido take tana sussunkuyewa kamar zata b'oye, fuskarshi a had'e ba alamar wasa yace "Fito." Girgiza kai tayi tace "Babu inda zanje." Kallon mai taxi tayi tace "Malam muje sauri nake." Tsaki mai taxi yayi yana tashin motar da fad'in "Aikin banza, ni na d'auka ma ko wata matarshi ce." Jin haushin maganar mai taxin yasa shi daka mata tsawa da fad'in "Malama fito nace." Zabura tayi ta fito da sauri bata shirya ba tana ja baya, rufe k'ofar yayi ya nuna mata motarshi yace "Shiga muje." A marairaice ta kalleshi zata yi magana, kallo mai d'auke da harara da gargad'in ki kiyaye kanki yasa ta kyab'e fuska ta matse ido k'walla suka fito, sam ta kasa mishi gardama ko ta k'i bin umarninshi, amma kuma ta tsaya bata yi abinda yace ba, mai taxi daya ga dama ba wani nisa sukayi ba kuma ya fara fahimta kamar mata da miji ne sai kawai yaja ya barsu nan, matsowa yayi kusanta yana fad'in "Shiga muje na kaiki gida." Girgiza kai tayi cikin kuka tace "Ni bana so kawai ka barni na tafi gida kafin a nemi ni." Cikin tashin hankali ya kalleta yace "Kinga yi shiru dan Allah daina kukan to, bani hankalin nan kinji." Girgiza masa kai ta sake yi alamar a'a, rik'e k'ugu yayi yana sauke numfashi, yanda take kukan yake kallonta tana k'ara shiga ranshi, murmushi yayi mai ban sha'awa, a duniya yana son shagwab'abb'iyar mace, yana son mace mai saurin kuka kamar dai wannan da kukan ma ya mata kyau, girgiza kai yayi cikin dariya yace "Faaatima." Yanda ya kira sunanta da jan aa yasa ta d'an dakatawa da kukan ta kalleshi, cikin nutsuwa yace "Wallahi da gaske nake ina sonki, Fatima aurenki nake so nayi in kin bani dama, bana so muyi magana anan, ki kwatanta min gidanku mana sai naje na samu iyayenki." Yanda ta zuba mishi ido baki bud'e yasa zaka san gaba d'aya ma bata wani yarda dashi ba bare abinda yake fad'a, jinjina kai yayi yace "Karki d'auka ni wani watsatse ne ko d'an iska, ina da uwa uba da yan uwa duk a garin nan, nayi karatu har matakin bac wanda yanzu haka ma ina jiran kira daga k'asar Canada ne kan samun gurbin karatu acan, sannan nayi karatun addini har nayi sauka ma, kuma insha Allahu ina da burin ci gaba dashi ma. Faduma a karo na farko a rayuwata dana tab'a fad'an kalmar so, dan Allah karki k'ona min zuciyata ta hanyar ce wa a'a, karki farar min da labarin soyayyata da rashin amincewa kinji, na rok'eki ki so ni kema ko kad'an ne, ina so nayi aure nima na zama babban mutum magidanci mai iyali daya san ciwon kansa kuma za'a ganshi da daraja da kima." Wata tattausan ajiyar zuciya ta sauke tana sunkuyar da kanta, me za tace mishi? Me zata fad'a? Me take ji a game dashi? Ko ba komai yasa taji yau ita ma ashe budurwa ce da za'a iya mutuwa a kan ta, babu wanda ya tab'a tarar ta gaba da gaba ya fad'a mata haka, kai ko da ta bayan fage ma babu wanda ya tab'a aika ko da d'an sak'o ya fad'a mata haka, tana yawan jin yan class d'insu suna hirar samarinsu, wasu ma aure garesu wasu kuma an saka musu rana, shine ita ma wannan bawan Allah yau ya tsomata a jerin waccen 'yan matan kuma yake shirin d'aga darajarta zuwa mataki na gaba mai tattare da lada magudaniya. Murmushi ne ya sub'uce mata sai kawai tasa bakin lafayarta ta rufe fuska, sake matsawa yayi daf da ita yana murmushi shima yace "Kenan kin amince? Ko a addinance kunyar da kika nuna tana nuna amincewa da buk'ata ta ne." Da sauri ta kalleshi sai kuma ta sake sadda kanta, a hankali can k'asan mak'oshi bakinta na hard'ewa tace "Zanyi shawara da Ayyoyina." Da mamaki ya kalleta yace "Ayyoyinki kuma? Ayya nawa gareki ne Fatima?" Kallonshi tayi cikin jin kunya tace "Biyu." Jinjina kai yayi yana kyab'e baki yace "Kuma duk su suka haife ki?" D'aga kai tayi tace "Eh, na tashi na ganni tare dasu." Marairaicewa yayi cikin salon barkwanci ya had'e hannaye alamar rok'o yace "Dan Allah Fatima na rok'eki kiyi shawara da zuciyarki, sannan karki kasa tunowa da wannan marayan da halin da zuciyata zata iya shiga sanadiyar k'in amincewarki." Jinjina kai tayi tana jin kamar yana fasa mata kai, cikin sanyin murya yace "To yanzu muje na sauke ki gida." Da sauri ta girgiza kai alamar a'a tana fad'in "A'a wallahi, iyayena sun hana zasuyi min fad'a." Cikin kafeta da ido yace "Faduma, ni da nake son aurenki ai ba zan so abinda zai b'ata miki rai ba, amma ki sani ba wai zan aje ki k'ofar gida bane na juya na koma kamar wani marar gaskiya ba, zan iya shiga har ciki na damk'a hannunki ga Ayya sannan na juya na koma." Da mamaki ta kalleshi shiyasa ya dake yace mata "Kina mamaki ne?" Girgiza kai tayi tace "Dan Allah ka barni na tafi, ina ta k'ara b'ata lokaci." Murmushi ya sakar mata yace "A gurinki ne b'ata lokaci, amma ni tunda nake yau ne naji na fara cin moriyar lokaci na, Faduma ina ji kamar muyita tsayuwa a haka ina kallonki har lokacina ya k'are anan." A hankali ta d'aga kai ta kalleshi, a gaskiya maganar nan ta kayar da ita k'asa, take taji wani bak'on abu na shigarta akan mutumin da taji yaya Abdul ya kirashi da Tagur, jinjina masa kai tayi tace "Sai anjima." Fahimtar ba zata yarda ta tafi tare dashi ba yasa shi tsayar mata da taxi ta shiga, saida sukayi nisa ya bi bayansu dan yana so ya ga gidansu, ya ganta kuma ta shiga zuciyarshi, dama kuma yana cikin jarabar son yin aure, dan haka ya samu mata. *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 17:12 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _19_ Yana ganin inda ta sauka bai tsaya ba ya wuce, burinshi dama kawai ya ga gidan kuma ya gani. A hankali ta shiga tana sakin sallama, da sauri duk suka juyo kanta suna kallonta, da sauri Aba ya nufota yana kama hannunta da fad'in "Faduma me ya tsayar dake?" Ayya take kallo da ke binta da kallon tas har suka tsaya kusa da ita, hannu ta zura zata jawota tayi saurin lab'ewa bayan Aba tana fad'in "Ayya kiyi hak'uri." Cikin b'acin rai tace "Zo nan Faduma, ina wasa dake ne? Zo naji gidan uban da kika tsaya." Kamar zatayi kuka tace "Kiyi hak'uri Ayya dan Allah, kar ki min fad'a ko bari na fad'a miki abinda ya faru, in kika titsiyeni hakan zai sa na miki k'arya." Kallonta Aba yayi yace "Kin gani ko? Ki bita a sannu mana ta fad'a mana abinda ya tsaidata." Maida kallonshi yayi gareta yace "Ina jinki Fadun Aba me ya rik'eki? Na kira gidan suka ce tun bayan magriba kika fito, gashi kuma yanzu har an gama sallah isha'i anan." A hankali cikin nutsuwa tace "Aba dama mun taho ne sai muka had'u da yaya Abdul, shine yace zai kawo ni gida kuma sai ga wani abokinshi ya zo, sun fara magana anan har suka fara fad'a akai na ma, ni kuma sai nayi tafiyata na barsu, na samu taxi na tafi kuma sai abokin nashi ya sake tareni akan hanya, shine fa na dad'e haka." Dafe k'irji tayi da k'arfi tace "Faduma saurayi ya dawo dake gida? Na d'auka wannan na daga cikin karatun dana koya miki kika haddace shi." Da sauri ita ma cikin k'warewar harshensu tace "A'a Ayya, wallahi taxi na dawo bai shiga motarshi." A hassale ta sake yi kanta tana fad'in "To uban me kika tsaya yana fad'a miki? Ina ce na hanaki sauraren uban kowa akan hanya." Sake k'amk'ame damtsen hannun Aba tayi tace "Aba wai cewa yayi yana so na kuma zai aure ni, amma ni wallahi ban fad'a masa komai ba." B'amb'are hannunta yayi daga nashi ya kalli fuskarta yace "Fadun Aba, bana so ki sake tsayawa da kowa akan hanya kinji, duk abinda mutum zai fad'a miki ya zo gidanku inda gaske yake, yanzu shiga ciki kiyi sallah isha'i." Da sauri ta jinjina kai ta wuce tana waiwayen Hadizey dake binta da harara, tana ganin shigewarta tayi k'wafa tana fad'in "Daf kike da daina fita a gidan nan kam yarinya." Girgiza kai yayi cikin sassauta murya yace "Diza, dan Allah ki dinga sassautawa kanki al'amarin yarinyar nan, karki saka mata tsoronki a zuciya mana, hakan zai iya busar mata da zuciya kuma." Da mamaki ta gyara tsayuwa tace "Na sassauta Aban Fadu? 'Yata ce fa kuma mace, idan ban damu akan ta ba wa zai damu da ita? Ka daina ma wannan magana gaskiya." A hankali ya sake cewa "Diza ba wai ina nufin ki daina ba, tabbas ni shaidane kuma Allah ma ya gani kina iya bakin yin ki akan Faduma, amma ki sani tsanani da k'ok'arinki ba shi zai hana Faduma tayi abinda zai b'ata miki ba, kiyi iya abinda zaki iya sauran ki barwa ubangiji, shine mai shiryarwa zai kula da lamarinta, ba wai fata nake ba amma hak'ik'a yau in Faduma tayi wani na rashin ji to babu wanda zai zargeki, sai dai mu kira hakan da *k'addararta* kawai." Cikin sanyi jiki da gamsuwa da abinda ta fad'a ta jinjina kai ta kalleshi tace "Yanzu zaka iya cin abincin?" Murmushi ya mata yace "Kawo min na ci tunda farin cikina ta dawo." Murmushi ta mishi ita ma ta juya zata tafi yace "Diza kenan, ke ce farin cikin gidana kuma *murmushi na*." Kunya ce tasa ta rufe fuska da hannu ta wuce. Kan tabarma ya zauna ta kawo mishi abincin, tana zuba mishi Faduma ta fito tayi alwala ta koma ciki, yana cin abincin Abdul yayi sallama daga k'ofar gidan, gane muryarshi ne da yayi sai ya amsa ya ce ya shigo, har Ayya zata tashi d'auko mishi kujera ya cire takalmi ya zauna kan tabarmar, a nutse suka gaisa tare da tambayar yan gidan? Saida wurin ya d'anyi shiru na yan sakanni kafin Ayya ta mik'e ta shiga ciki, kallon Aba yayi yace "Aba Faduma nace ko ta dawo gida?" Kallonshi yayi shima yace "Eh ta shigo, amma ba da jimawa ba." Jin yayi shiru bai ce komai ba sai ya sake kallonshi yace "Ta fad'a mana abinda ya faru ai, amma wanene wannan yaron?" Cike da kunya yace "Aba wani abokina ne." Jinjina kai yayi bai ce komai ba, shiru na wasu mintoci kafin Aba ya tank'washe k'afafunshi yana kallonshi yace "Abdul Razaq ina ga in ka shirya zamuyi wani abu dan yi wa tubkar nan hanci." Kallon rashin fahimta ya mishi yana jiran k'arin bayani, ci gaba da cewa yayi "In babu takura a ciki me zai hana a saka ranar aurenku da Fati, kaga da zaren an koma makaranta hutun farko da za'a shiga sai ayi biki, idan kana buk'ata matarka zata iya tarewa, in kuma da matsala zata iya zama anan sai ta ci gaba da karatunta, amma fa shawara ce." Abdul da tunda ya fara maganar yake jin kamar ya d'aukeshi ya goya ya taka rawa dashi, wani farin ciki ne yaji yana shigarshi ta k'asa yana yin sama, sunkuyar da kai kawai ya sake yi ya ma rasa me zai ce, shi aka mishi haka ai gata aka mishi ba kad'an ba. Ganin bai ce komai bane yasa Aba sake cewa "Abdul Razaq baka ce komai ba? Ka amince kenan?" Murmushi yayi yana sake k'asa da kanshi yace "Ba komai Aba, duk yanda kukayi ya dace." Jinjina kai yayi yace "Ba takura dai ko? Idan baka shirya ba kayi magana, d'ana ne kai ba zan so na tauyeka ba." Girgiza kai yayi yace "Ba komai Aba, abinda yayi saura ma insha Allahu za'a k'arasa shiryawa kafin lokacin." Jinjina kai ya sake yi alamar gamsuwa yace "Shikenan Allah ya tabbatar mana da alkairi." Da "Ameen." Tattaunawa suka shiga yi kan kasuwa har da abinda ke faruwa ma, sun jima suna hira kafin ya mishi sallama ya tafi bayan ya tabbatar mishi zai kira yayan nashi a waya sai suyi magana, zuciya fal farin ciki ya dawo gida bai kuma iya b'oyewa ba saida ya fad'awa mahaifiyarshi da abokan zamanta ita ma, murna sukayi sosai dan basu tsammin haka yanzu, tun kafin Aba ya kirashi suyi magana tuni ya samu labari a wajen matan gidan a wannan daren, dan haka shima ya ci alwashin kiranshi da sassafe idan Allah ya kaisu. *guguwar data shiga tsakaninsu da wannan shiri na su* Zaune tayi gabanshi tana fad'in "Aba ina kwana?" Cike da kulawa ya kalleta yace "Lafiya lau Fadun Aba, kin tashi lafiya?" Sunkuyar da kai tayi tace "Lafiya lau Aba." Kallon jakar dake gefenta yayi yace "Har kinyi shirin makarantar?" D'aga kai tayi tace "Eh Aba, amma da d'an sauran lokaci." Jinjina kai yayi yace "To ya hadda taki yanzu?" Kallonshi tayi tace "Aba komai na tafiya daidai, yanzu ma mun fara karantun sahihul bukhari." Jinjina kai yayi yace "Masha Allah, to yanzu kinga kamata yayi ki aje mukhtasarul akhdari d'in nan, tunda kinga shi ba hadda ake yin ba sai mu fara bitar sahihul bukhari d'in a gidan." Girgiza kai tayi cikin shagwab'a tace "A'a Aba, zan iya duka, zamu dinga yin shi duka a gida ma." Murmushi yayi yace "To shikenan auta yanda kike so haka za ayi." Rufe fuska tayi alamar jin kunya, lek'a fuskarta yayi yace "Na kawo kud'in kashewa ne a hanya?" Bud'e fuskar tayi ta girgiza kai tace "A'a Aba nagode, kai da zaka fita yanzu." Girgiza kai yayi yace "Allah ya miki albarka Fadu." Da jin dad'i ta amsa da "Ameen Aba." Jakarta ta d'auka ta mik'e tana fad'in "Aba ni zan wuce, Allah ya tsare min kai ya bada sa'a a kasuwa kayo mana kud'i masu yawa." Dariya yayi yace "Fatima me zakiyi da kud'i dayawa? Farin ciki da kwanciyar hankali sun fi dukiya." Cikin nutsuwa tace "Hakane Aba, ni ma ban damu dasu ba, rayuwarka data Ayyoyina kawai nake so naga tayi kyau." Murmushi ya sake yi yace "Allah ya miki albarka." Da "Ameen." Ta sake amsawa ta fita tana fad'in "Saina dawo." "Allah ya tsare." Ya fad'a yana binta da kallo, Hadizey data fito daga d'aki ta kalla tace "Ayya saina dawo." "Allah ya kiyaye." Ta fad'a ita ma tana binta da kallon har ta fita. Mahaifin Abdul ne ya kira yake mishi maganar, nan a waya suka tsayar da rana da saka ranar da za'a kawo kaya, bayan sunyi sallama yake fad'awa Hadizey, tayi farin ciki sosai har da sauke ajiyar zuciya da hamdalah ga ubangiji, burinta d'aya a duniya ta ga Fatima a d'akin mijinta, ta ga tana k'ark'ashin ikon wani bayan sunyi iya yinsu, hakan zai kwantar mata da hankali har tasha ruwa a tsanake. _______________ Kafin mahaifin nashi ya fita ya sallama d'akinshi ya same shi, saida suka gaisa da kyau kafin ya tambaye shi me yake buk'ata? Cikin nutsuwa ya shiga labarta mishi a harshensu "Aba dama akwai wata yarinya dana gani jiya kuma nake sonta da aure, shine nake neman alfarma a wurinka kuje ku nema min aurenta." Hatimi dake zaune bakin gado tunda ta kawo mishi abin kari bata fita ba, da sauri tace "Tagur me kake fad'a? Ka manta muna ta k'ok'arin nema maka had'i ne a cikin yan uwa? To kayi hak'uri mana sai ka samu cikin yan uwa ka aura." Kallonta yayi a hankali yace "Ayya, wallahi yarinyar tana da nutsuwa da hankali, gaskiya ta min Ayya, ta zo a yanda nake so matata ta aure ta kasance." Da sauri tace "To ka bari ka fara auren fari a gida, bayan wasu shekaru sai ka aureta in zata iya jiranka mana, kuma fa kace jiya ne kuka had'u?" Da mamaki ya kalleta yace "Ayya ta zauna ta jirani har sai matata tayi haihuwa biyu ko uku? Ke fa kinsan yanda al'adarmu take, a gaskiya ni..." Cike da dattako Alhaji Sugui ya kalleshi ya aje cokalin hannunshi yace "Ya isa!" Kallonshi sukayi, gyara zama yayi cikin nutsuwa inda dakakkiyar shaddarsa ta fitar da sauti, kallonshi yayi yace "Kana sonta dai?" D'aga kai yayi alamar eh, jinjina kai yayi yace "Ita fa yarinyar, tana sonka ita ma?" Saida ya d'an juya kanshi sannan yace "Aba yarinya ce mai kunya, kai tsaye ba zata fad'a ba." Wani kallon yarinta ya mishi, shi fa har yanzu kallon yaron goye yake mishi, girgiza kai yayi yace "Ina ne gidansu?" Cikin shagwab'a jin zai samu biyan buk'atarshi yace "A cit茅 soraz ne gidansu." Jinjina kai yayi yana sauke ajiyar zuciya yace "Shikenan, zanje, ka shirya da dare saika raka ni, amma da sharad'i Tagur." Da sauri ya kalleshi da razani yace "Sharad'i kuma Aba?" D'aga mishi kai yayi alamar eh, jiki a mace yace "Wane irin sharad'i kuma?" Saida ya nuna masa yatsa yace "In har muka je aka tambayi yarinya bata amince ba ka sani zaka manta da maganar nan, kuma dole zamu had'aka da d'aya daga cikin yan uwa, ka yarda?" Shiru yayi yana turo baki yana gunguni, nuna masa k'ofar fita yayi yace "Tunda baka amince ba tashi ka bani wuri." Da sauri ya d'aga kafad'a yace "Shikenan na yarda." Shima d'aga kafad'a yayi yace "Shikenan, anjima idan na dawo zan kira sai mu tafi." "Zan raka ka dai Aba, amma ni ba zan shiga gidan surukaina ba gaskiya." Ya fad'a yana fita daga d'akin, girgiza kai yayi yana binshi da murmushi, sake matsowa tayi tana fad'in "Alhaji, ya zaka amince da abinda ya zo dashi? Me yasa zaka yi haka?" D'aga mata hannu yayi yace "Shiyasa ai na gindaya masa sharad'i, har yanzu akwai yiwuwar al'amarin da kuma fasuwarshi." Shiru tayi tana jijjiga abun na damunta a zuciyarta sai dai babu yanda zatayi. Daga nan librairie (labrary) ya wuce wajen aikin Abdul, kasancewar shine mai wajen kuma yana zuwa dama yasa kai tsaye ya wuce ofishinshi, ta b'angaren Abdul kam yayi mamakin ganinshi da safiyar nan da ko jimawa basuyi ba suma da bud'e wurin, amma tunda ya sadda kanshi bai d'ago ba yana ji har ya zauna ya zura hannu ya d'auki robar ruwan dake gabanshi yasha, wani numfashi ya sauke yana furzo iska yace "Ya kake?" Ba tare daya d'ago ba yace "Lafiya lau." Tab'e baki yayi yace "Abdul." Numfashi ya sauke ya aje alk'amin hannunshi ya d'ago, sam fuskarshi babu alamar wasa, can k'asan mak'oshi yace "Uhum!" Wani murmushi yayi mai ciwo yace "Abdul tun jiya da na maka maganar Faduma kake wani ciccije min, wai me ne? Ko kai ma son ta kake?" Saida ya kalli idonshi sosai yace "Eh, da matsala ne?" Zaro ido yayi cikin salon shak'iyanci yace "Haba Abdul, kai fa d'an uwanta ne, aurenta ya kamata ka ba wani wanda ka yarda da nagartarshi, amma ba wai kai ka karb'a ba." Shima cikin salon shegantaka yace "Saboda a littafi aka saukar aka ce haramun ne haka? Kaga Tagur nan aiki ne ya fito dani ba shashanci ba, zaka iya tafiya inba aikin ne ya kawo ba." D'agowa yayi daga kwanciyar da yayi bayan kujerar, sosai ya kalleshi cikin fitar da kowace kalma yanda zata shiga kunnen mai sauraro yace "Abdul, *ina sonta*, ina k'aunarta sosai, kai d'an uwanta ne bana so, bana so muyi takara da kai dan nasan zan bigeka ne, ina so ko babu soyayya tsakaninsu ya zama akwai mutumtawa da girmamawa, shiyasa nake so ka bar min ita cikin sauk'i ba tare da mun shiga matakin siyasa ba, dan kasan siyasa a jininmu take saboda mun gada daga iyaye." Wani kallon raini ta masa yace "Inhar ka yarda da kanka har haka, to kenan me yasa ka zo nan? Neman alfarmar na d'aga maka k'afa ko me?" Wani murmushi ya masa mai kama da kuka yace "Tagur inhar kai namiji ka je ka jaraba sa'arka mana, inhar kai mai ilimi ne nasan kasan ba'a neman aure akan aure." Da mamaki ya tambaye shi da "Ban gane ba?" Jinjina masa kai yayi yace "Eh, haukan da kayi jiya shiyasa iyayenmu yanke hukunci d'aura mana aure a hutu na farko da za'a shiga nan da wata hud'u, kaga kenan ka makaro sosai." D'ora hannu yayi akan teburin gabanshi yace "Tagur, Faduma ba kamar sauran kadarori bace da kake tunanin mutum zaiyi sa'ar samunta kuma yayi sakacin barinta ta kubce mishi, zaka iya tafi yanzu." Shiru yayi kamar mai tunani kafin ya sake kallonshi cike da isa da jin kai yace "Saka ranar aurz ai ba d'aura aure bane, muje zuwa ka gani yanda zan canza wasan." Murmushi kawai ya bisa dashi har ya mik'e ya fita, girgiza kai yayi yana masa kallon ko ya fara kwancewa ne? Shima yana fita daga nan unguwar su Faduma ya sake komawa, daga cikin wata kwana ya paka mota, zaman dirshen yayi zaman jiran ganinta, daga inda yake yana iya hango duk wanda zai shiga gidan da wanda zai fita, tun yana jiran ganinta cikin nishad'i har zaman ya gundureshi, kwantar da kujerarshi yayi sosai ya kwanta ya lumshe ido, a hankali bacci ma ya nemi d'aukarsa a wurin, bai fargaba ba kam bacci ya d'aukesa, hasken rana ne daya hasko ta madubin motar ya farkar dashi, bud'e ido yayi ya tashi zaune yana duba agogon motar, 12:14, hamma yayi yasa tafin hannunshi na dama ya rufe baki. Da k'arfi ya zaro ido tare d'auke hannu daga bakin ya ma manta me yake yi saboda hangenta tana daf da shiga gidan cikin kayanta na islamiyya, dogon shud'in hijab d'in ta mai haske har k'asa da bak'in siket, fuskarta kawai kake iya gani, da sauri ya bud'e motar ya fito sai dai tuni har ta shige ciki, rufe ido yayi cikin rashin jin dad'i, dafe k'ugu yayi yana kallon k'ofar gidan, awannin daya d'auka bai samu ganinta ba baya tunanin zata sake fitowa nan kusa dan ya ganta, amma tunda ya ga wani kaya ne jikinta yasan makarantar, sai kawai ya shiga motar ya bar unguwar da tunanin da yamma can zai yada zango. Da misalin 05:30 na yamma ya isa kusa da islamiyyar, daidai da tashin yara k'anana kafin mayan, baifi minti goma zuwa sha biyar ba manya ma suka fara fitowa maza da mata, dokawar da gabanshi ya fara yi ya tabbatar masa da tana tahowa, yana hangenta kuwa ya fita a motar, bata kula dashi ba sai dai gabanta da taji yana fad'uwa yasa ta juyawa, da sauri ta zabura taja baya tana zaro ido, dariyar daya mata ce tasa ta dafe k'irji tana fad'in "Wai Allah." A hankali yayi murmushi yace "Na tsoraki ko? Ki gafarce ni gimbiya Fatima." Jin wani suna daya kirata dashi yasa ta kalleshi ta saki murmushi kawai ta wuce, rarraba ido ta shiga yi tana dubawa ko sauran d'aliban suna kallonta, kar fa yaja a fara nunata da ido, kusan ta had'a ido da cikin yan ajinsu da dama duk suna kallonsu, hakan yasa ta sunkuyar da kai tace "Dan Allah me ya kawoka nan?" Yanda take taka k'afafunta a nutse shima ya dinga d'ora nashi yana kallon k'asa yace "To ya zanyi Fati na, kin k'i bani damar yin magana dake jiya, shiyasa na sake dawowa." Ba tare data kalleshi ba tace "Dan Allah ka daina bina karka ja min magana, wa ma ya fad'a maka ina nan ne?" Murmushi yayi yace "Tare zamu tafi har gidanku." Da sauri ta tsaya ta kalleshi tace "Gidanmu? Kana so Ayya ta kasheni?" Girgiza kai yayi yace "Ai na fad'a miki ban zo dan na b'ata miki lokaci ba, Fatima hankalina ba zai kwanta ba har sai naji kin amince da aure na." Ajiyar zuciya ta sauke ta ci gaba da tafiya, shirun da tayi ne yasa shi cewa "Ba zaki amsa min ba kenan? Shikenan muyi ta tafiya a haka." Kwanar data shiga babu mutane sosai yasa ta tsayawa ba tare data kalleshi ba tace "Dan Allah na rok'eka ka daina bi na, ni fa ban san komai akan abinda kake magana akai ba, karatu nake, yarinya ce ni har yanzu ban isa aure ba." Wani tsadadden murmushi ya jefa mata wanda yasa taji gabanta ya fad'i a hankali yace "A haka? Faduma nima ai yaro ne, karki ganni dogo haka da wannan gwanjin kamar wani inyamuri, wallahi ban fi ashirin da biyar ba." Wata dariya ce ta zo mata da bata shirya mata ba, zata iya rantsewa har ta manta ranar data iya fito da hak'oranta haka a waje akan titi, dan komai nata Ayya ce ke koya mata shi hatta da yanda zatayi numfashi ma in a waje ne. Fararan hak'oranta da suka bayyana idonta kuma cikin nashi idon sanda take dariyar yasa yaji kamar ya d'auketa yasa aljihu ya tafi da ita ya killace, ya bata dariya gaskiya, kuma daga jiya da suka fara had'uwa zuwa yau guy yasa zuciyarta wani tunani da shiga wani aji da bata tab'a samun kanta a ciki ba, hak'ik'a tana ji a jikinta ko bata so shi ba zata iya yarda tayi doguwar rayuwa dashi, saboda ya iya kalamai had'i da barkwanci. Cikin farin cikin ya saka ta dariya yace "Da gaske nake Fatima, kar girman jikina ya baki tsoro, nima yaro ne har yanzu." Murmushi tayi ta sake ci gaba da tafiyarta, da sauri ya sha gabanta ya marairaice ya ya kalleta yace "Fati." A hankali ta d'aga idonta dake d'auke da ragowar kwallin data shafa tun safe ta kalleshi, a hankali yace "Kina so kiga na mutu ne?" Babu fara'a tare da ita ta girgiza mishi kai alamar a'a, langab'e kai yayi yace "To ki amince min mana, in ba haka ba Fati mutuwa zanyi." Cikin rashin jin dad'i tace "Mutuwa kuma? Me yasa?" "Saboda son ki, kuma gida suna shirin yi min auren dole in dai har na rasa wacce nake so, Faduma ki tausaya min mana ki rufa min asiri kamar yanda Allah ya taimake ki." Ba iya k'afafunta bane taji sun d'auki rawa har da zuciyarta da hannayenta, idonta ma taf sukayi da ruwa har suka fara sauko mata kan kumatu. Hankalinshi ne ya tashi sosai ganin tana zubar da hawaye, cikin kulawa ya matso kamar zai share mata yace "Subhanallah, Faduma kuka kuma? Ni na sake ki? Kiyi hak'uri kinji ban d'auka ranki zai b'ace ba." Zuciyarta ce ta sake karyewa tasa hijabinta ta rufe a bakinta ta sake fashewa da kukan, yanda ta hangi tsantsar tashin hankali a idonshi da fuskarshi ya sake girmama mata shi a k'asan zuciyarta, idonshi cike da ruwa kamar zai matso su zubo ya durk'usa gabanta kan gwowoyinshi ya had'e hannaye yace "Dan Allah ki daina kuka Faduma, bana son ganin zubar hawayenki ko da na farin ciki, wallahi da nasan zuwan nan nawa zai sa hawayen haka zuba da ban zo ba, ki gafarce ni kinji." Cikin muryar kuka tace "Dan Allah ka tashi, ni ba kai ka sani kuka ba, zuciyata ne take min wani wuri, gida nake so na tafi." Mik'ewa tayi tsaye yana fad'in "Shikenan to tafi, amma ki daina kukan kinji." Jinjina kai tayi alamar to ta wuce da sauri, saida tayi nisa zata karya kwana sai kuma ta juyo kamar an kirata, tsaye ta ganshi inda ta barshi bai gusa ba, a k'alla saida suka kalli juna na tsawon minti biyu kafin ta juya ta shige kwanar. *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 17:12 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _20_ Bayan sallah magriba yayanshi har gida ya same shi suka sake tsayar da magana, a k'arshen satin suka saka za'a kawo kaya sai a tsayar da rana, tare sukayi sallah isha'i, suna tsaye k'ofar gidanshi dan yau yana wajen Hatimi ne suna sallama mota ta tsaya a d'aya k'ofar gidan, duk da suna hangen tartsetsiyar motar amma basu kula ba, sai ma sallama da sukayi shi ma ya shiga matsakaiciyar motarsa ya bar unguwar. Tare suke a mazaunin baya sai dreba a gaba, kallonshi yayi yace "Nan ne gidan?" Cikin taushin murya yace "Eh Aba." Jinjina kai yayi yana sauke ajiyar zuciya, hannun k'ofar ya kama zai bud'e yace "Muje ko?" Girgiza kai yayi yace "Aba kaje kai kad'ai ina nan ni." Sake girgiza kai yayi ya bud'e, cikin k'asaita ya fito da k'afafunshi har ya fita gaba d'aya, rufe k'ofar yayi ya sake kallon k'ofar gidan, ban da abun yaro da kuma zuciya, taya zai kawo kanshi wannan gidan? Da sauri ya kawar da abinda zuciyarshi ta bijiro mishi dashi yasa sab'a hannun babbar rigarshi, waige waige ya shiga yi cikin sa'a ya ga wani magidanci da alama mak'wabcinshi ne, da sauri ya d'aga mishi hannu yana fad'in "Assalama alaikum, sannu ko?" Juyowa mutumin yayi da girmamawa ganin babban mutum ne yasa shi k'arasawa yana fad'in "Wa'alaika salam." Musabaha sukayi kafin ya nuna masa gidan yace "Dan Allah mai gidan nan nake nema? Ko yana ciki?" Kallon k'ofar gidan yayi ya juya ta b'angaren da masallaci yake yace " Malam Moliya? Eh to, ai kuwa munyi sallah tare dashi da yayanshi yanzun nan, sai dai ko..." Hangoshi da yayi a k'ofar gidan yasa yace "Yawwa gashi can, yana d'aya gidanshi ne ashe." Da mamaki ya kalleshi yace "Gidansa biyu ne?" D'aga kai yayi yace "Eh ranka shi dad'e, ai can d'in gidansa ne na gado kafin unguwar ta zama ta ma'aikata, wannan kuma haya suke, duk da ma dai an so tashinsu daga nan kasancewar unguwar duk ta ma'aikatan gwamnati ne, amma har yanzu babu tabbacin ci gaba da zamansu gaskiya, amma indai zasu samu doguwar k'afa a cikin gwamnatin, to komai zai iya zuwa musu da sauk'i." Yatsina fuska yayi ya jinjina kai cike da gajiya da zancen da bai neme ba yace "Nagode." Ko hannu bai bashi ba ya nufi inda yake hangenshi, shima da tunda ya ga an fito daga motar ya tsaya yana kallon komai, yana k'arasowa suka shiga gaisawa da girmamawa da mutumta juna, cikin dattako yace "Kayi hak'uri na zo maka kai tsaye haka babu sanarwa." Da fara'a yace "Ah ba komai wallahi, Allah yasa dai lafiya, dan gaskiya ban shaidaka ba?" Murmushi yayi yace "Gaskiya ba zaka shaida ni ba, ni sunana Alhaji Sugui Barka Nakiri, d'an kasuwa kuma d'an siyasa, na zo ne da muhimmiyar magana." Cikin murmushi yace "Masha Allah, ai kuwa na tab'a jin sunan nan a cikin gari, haka ma a redio na tab'a cankarshi." Murmushi yayi cikin nutsuwa yace "Hakane." Jinjina kai yayi yace "To dama dawowata daga masallaci kenan, bari na shiga ciki saina samo mana abun zama ko?" Murmushi kawai ya masa dan dole maganar na buk'atar zama, bayan wasu mintuna ya dawo d'auke da kujeru na roba guda biyu, ajewa yayi suka zauna kusan suna fuskantar juna kuma ba sosai ba, ajiyar zuciya ya sauke mai k'arfi yana d'an zare takalminshi d'aya daga k'afarshi, kallonshi yayi sosai yace "Malam na zo ne akan maganar 'yar wajenka Fatima, jiya d'an wajena ya ganta kuma ya fad'a min yana sonta, shine na ce bara na zo naji idan ba'a mata miji ba sai mu san abun yi, ina kuma fatan ba'a mata mijin ba?" K'arashe maganar yayi da murmushi cikin raha, shima murmusawa yace "Gaskiya ne, kuma naji dad'in haka da kukayi, wannan ya nuna ku mutanen kirki ne kuma daga babban gida, sai dai wani hanzari ba gudu ba." A nutse ya kalleshi shima a nutse ya shiga fad'in "Ba zan b'oye maka ba a gaskiya yanzu haka maganar da muka gama da yayana kenan akan ita Fatimar da kuma yaron wajenshi, mun saka musu rana rai da lafiya kawai muke fatan samu daga wajen Allah." Jim yayi yana nazartar mutumin, kud'in shi da matsayinshi basu sa yaji zai uya bashi 'yar ba? Yaji haushi sosai a k'asan zuciyarshi, amma a zahiri saiya nuna ba komai ya dinga murmushi yana nuna yaji dad'i daya fad'a musu gaskiya, haka sukayi sallama har ya koma cikin motar, saida dreba ya ja suka yi nisa Tagur ya zuba mishi ido yana jiran yaji me zai ce, fuska a had'e ya kalleshi yace "Kayi shirin zuwa ganin d'aya daga cikin 'ya'yan yan uwa." A razane ya kalleshi ya gyara zama yace "Aba? Ban gane me kake fad'a ba?" A hassale ya juyo yace "Me ye baka gane ba Tagur? Yaren dana maka ko me?" Shan jinin jikinshi yayi yaja baki yayi shiru, cikin masifa yace "Haka kawai da girma na da komai na ka d'aukoni ka kawoni wani k'azamin gida, dubi mutumin fa? Har na fad'a masa waye ni ya tsaya yana nuna min ya tsayar da ranar auren 'yarsa dan haka saidai muyi hak'uri, mtsss." A raunane ya kalleshi ya dafe k'irjinshi yace "Aba bai amince ba? Da gaske aure zai mata? Na shiga uku Aba, wallahi ina son Faduma." Nuna shi yayi da yatsa yace "Ka sake maganarta saina mareka." Duk'e kanshi yayi ya jinginar a jikin murfin motar yace "Ina son ta, wallahi Fatima zan iya mutuwa akan ta Aba, ka taimaka ka sake mishi magana, Aba kana da kud'i iko da fad'a aji, zaka iya sama min ita da wannan abubuwan, amma ba zan iya hak'ura da ita ba Allah kuwa." Ganin da gaske yake har da kuka yasa shi kallonshi sororo yace "Kai, wai asiri ta maka ne, ya naga ka wani kwarkwarce ne." Da sauri ya fad'a kan k'irjinshi yana cakumarshi yana kuka sosai da fad'in "Wallahi Aba asiri ta min, farko da tafiyarta ta nutsuwa da kunya ta fara sihirce ni, sai kuma fuskarta ta fargaba da tsananin jin kunya, daga baya kuma Aba saita sihirce ni da fuskar kukanta da tsoro, daga baya kuma saita had'a da dariya da idonta dara dara masu hasken zara, Aba ka taimaka ka sama min yarinyar nan kar ciwon zuciya ya kashe ni, kaga ni kad'ai ne namijin daka mallaka, idan baka yi da gaske ba zaka rasa ni nima." Mamakin dake neman kashe shi daga zaune ne yasa shi yin saurin kallon k'eyar dreba yace "Kai Musa wai yaron nan ne kuwa?" Ba tare faya juyo ba yayi dariya yace "Alhaji nima dai mamakin da nake kenan? K'aramin Alhaji dana sani da jarumta da mazantaka." Girgiza kai yayi yasa hannu yana shafa kanshi yace "Lallai ko taurin mutum ya kai dutse mace zata iya narkar dashi fiye da yanda wuta ke narkar da roba." Da suka koma gida suka sanar da Hatimi abinda ke faruwa, sosai tayi ta fad'a ta kuma yi murna da faruwar hakan, dole suka ce tunda dai auren yake so duk da karatu da zai tafi wanda ko da yaushe zai iya samun kira, to ya fad'a a cikin yan uwa wacce ta mishi, sosai Aisho bata ji dad'in yanda ta ga ya damu ba, hakan na nuna mata irin yanda yarinyar ta shiga zuciyarshi ne, amma sauran yan uwanta musamman ma Gomboy tafi kowa murna. Bayan kwana uku suka nema mishi auren 'yar abokin mahaifinshi, wannan had'i ya ma kowa dad'i daga gidan har sauran famille amma ban da shi, kai tsaye kuma a gabansu ya fad'a musu ba wacce yake so bace dan haka ba zata ji dad'in zama dashi ba, Hatimi kuma cewa tayi idan ya isa ya kashe yarinyar randa aka kaita ya gani, da wannan duka b'angarorin biyu kowa ya shirya lefenshi tsaf zai kai ranar asabar da zata zo. ______________ Ganin gobe ne za'a kai kayan yasa Aba yanke shawarar sanar da ita dan kar abun ya zo mata wani iri, saida ta kammala kawo masa haddata na sun gama sunyi addu'a zata je ta kwanta yace "Zauna auta ina son magana dake." Komawa tayi ta zauna jikinta duk a mace tana kallon mahaifin nata, saida ya jingina a jikin bango sannan ya kalleta yace "Fatima." Cikin nutsuwa tace "Na'am Aba." Kallonta yayi yace "A rayuwa, a tsakanin iyaye da 'ya'yansu, akwai hakk'ok'i da ubangiji ya gindaya, wanda kuma duk wanda bai sauke su ba za'a masa hisabi akan hakan, a rayuwarki, tunda aka haifeki har kawo yanzu girmanki, shin akwai wani abu da ni a matsayina na uba na gaza?" Kallonshi tayi da mamaki sai kuma tayi k'asa da kanta tace "Ko da ni butulu ce Aba bakina yafi k'arfin furta kalmar eh akan wannan tambaya taka, zan uya rantsuwa a wannan k'arnin ni ce 'yar data fi kowa sa'ar iyaye." Murmushi yayi sosai yace "Alhamdulillah, Fatima kin yarda na raineki yanda ya dace?" Jinjina kai tayi tace "Tabbas, na yarda Aba." "Kuma kin yarda na baki ilimi mai inganci?" "Na yarda Aba na, ka min wannan gatan ma." Jinjina kai ya sake yi yace "A ganinki yanzu miye ya rage da ban miki ba a rayuwa?" Kallonshi tayi jim tana tunani kafin tace "Babu Aba, a gaskiya ba zan iya tunawa ba." Murmushi yayi yace "Akwai Fatima, akwai abu d'aya daya rage." Da sauri ta kalleshi tace "Aba miye wannan abun?" Numfashi ya sauke yace "Zab'a miki nagartaccen miji, shine abinda ya rage min yanzu, wanda kuma nake fata ko yau na damk'a hannunki cikin nashi, to zan iya zare raina da hannu na ma na bayar idan hakan zai yiwu." K'ank'ance idonta tayi ta had'e goshinta tace "A'a Aba, ni ina nan tare daku babu inda zanje, Aba karki ji na zo maka da maganar wannan shirmen na jiya, shima nasan da wasa yake, dan alamunshi sun nuna d'an babban gida ne shi." Dariya yayi yace "Faduma, ni dai kai a matsayina na ubanki tuni na sama miki wannan daya dace d'in." A.hankali ta kalleshi tace "Aba waye wannan?" Saida ya kalli idonta yace "Abdul Razaq, d'an uwanki." Tsammm! Taji gaba d'aya jikinta yayi, gabanta ya fad'i sosai, kafeshi tayi da ido tana kallo, ba zata iya tantance abinda take ji ba a gaskiya, sai dai tana jin wani ba dad'i haka, yaya Abdul? Ai sam babu alamar soyayya ma a tsakaninsu, me yasa za'a had'ata dashi? Lura yayi tsaf da yanayinta, cikin dubara yace "Faduma, nasan kin amince da zab'ina, dan ban tab'a cewa ga abinda nake so ba kika ce a'a." Da sauri ta kalleshi ta fara girgiza kai, sai kuma ta tsaya cak tana ci gaba da kallonshi kamar an firgitata, hawaye ne suka sulalo mata a fuska da sauri ta sunkuyar da kanta k'asa, cikin tashin hankali ya d'ago daga jikin bangon yana fad'in "Subhanallah, Fati kuka kuma? Miye na kuka to?" Tafin hannu tasa ta rufe baki cikin kuka tace "Aba yaya Abdul, ni ban tab'a son shi ba shima kuma haka, me yasa zaku had'umu aure? Aba dama ba'a farin ciki ne a cikin rayuwar aure? Ko kuma tawa ce zata fara da haka ba kamar kai da Ayya ba?" Lumshe ido yayi yana addu'a akan labb'anshi, addu'a yake Allah yasa ba abinda yake hangowa bane a idonta, Allah ya kub'utar da alk'awarinshi/su, da k'yar ya daidaita zamanshi yayi k'arfin halin kamo hannunta yace "Daina kukan to yanzu, fad'a min baki son Abdul d'in ne?" Bata d'ago kai ba sai shak'ar majina da take tana goge hawaye, kamar an tsikareta kuma saita kalleshi tana sake jan majina tace "Yawwa Aba, ni ban ce bana son shi ba saboda bansan miye so d'in ba, amma dai na so naji abinda nake ji akan wannan na jiyan nan, Aba kasan wani abu?" Girgiza kai yayi a hankali yana kallonta tsaf, saida ta gyara zama ta d'ora da "Aba kana ji, daga jiya zuwa yau da had'uwarmu ya kafa min tarihi, dana tunashi haka zanji nayi dariya ko kuma murmushi, Aba shine mutum na farko daya tab'a kallona ya fad'a min abinda babu wanda ya fad'a min, kuma Aba har cewa yayi zai mutu idan ban amince zan aure shi ba." Yanda ta k'are maganar da fashewa da kuka ne ya sake d'aga masa hankali, jawo kanta yayi ya d'ora kan cinya yana daddab'a bayanta yana fad'in "Ya isa to, ya isa haka bana son kukan nan, kiyi shiru to muyi magana." Da k'yar ta tsagaita kukan nata ta tashi zaune tana kallonshi da sa bakin d'an kwalinta tana share hawaye, Ayya ce ta fito dan kukanta ne taji ya fito da ita, zaune tayi kusanta tana fad'in "Lafiya kike kuka ke kuma?" Nok'ewa tayi dan tasan yanzu ba lallai ta fad'i abinda ke ranta ba, can ma ta fad'a ne dan taga Aba ne, hab'arta ya kama ya juyo da kallonta gareshi, ido cikin ido suka kalli juna yace "Faduma, ba kya son auren Abdul?" Saddar da kanta tayi ta d'an juya ta kalli Ayya dake bayanta, a hankali yace "Kinga ni zaki kalla, ki fad'i abinda ke ranki kinji, babu wanda zai zauna miki da shi haka kuma babu wanda zai sani yi miki auren da ba kya so." Sunkuyar da kai ta sake yi, a hankali ya sake cewa "Faduma, ba kya son auren Abdul?" D'an turo baki tayi tace "Ni Aba ba yanzu zanyi aure ba." Lumshe ido yayi ya bud'e a kan ta yace "Fati kalleni." D'aga kai tayi ta kalleshi ya sake cewa "Kina son yaran nan da kuka had'u...Waye sunansa?" Da sauri ta kalleshi tace "Tagur." Da sauri kuma tasa yatsanta a bakinta ta ciza tana jin kunyar abinda tayi, dakewa yayi yace "Kina son shi?" Sake sinne kai tayi k'asa tana shafa wuyanta tana murmushi, kama baki Ayya tayi na tsantsar mamakin abinda take gani, sai dai ba zata iya magana ba tayi ma zai katseta, rufe ido yayi shima ya dantse leb'enshi na k'asa, a can k'asan zuciyarshi ya furta "Shikenan, ta faru ta k'are." A hankali ya bud'e ido ya kalleta yace "Shikenan tashi kije, zan san abunyi kinji." Da kallo suka bita har ta shige, dafe kai yayi da hannu d'aya ya furzo iska yana sake rufe idonshi, murmushin takaici tayi tace "Ni daka bi ta tawa wallahi da baka tambayeta, shiyasa na so a mata shiru sai an kawo kayan kawai." Kallonta yayi kamar zaiyi kuka yace "Yanzu ba wannan bane matsala, ta inda zan fara fuskantar yaya na fad'a mishi maganar nan nake." A zabure ta kalleshi tace "Me? Ban gane? Wai kana nufin saika fasa yanzu saboda shirmenta?" Da mamaki ya kalleta yace "Shirmenta? Shirme ne ma ta fad'a? Yarinyar data iya fad'a mana daga jiya zuwa yau ta samu farin ciki da wannan yaron shine shirme?" Mik'ewa yayi yasa takalminshi zai fita, da sauri ta mik'e ita ma tana fad'in "Aban Fadu, tsaya ka saurare ki kaji, ka wa Allah karka lalata zumuncinku da d'an uwanka akan yarinyar nan, yaron fa ko saninshi babu wanda yayi, ba a san halinshi ba da gidansu da asalinshi, haka kawai sai a fasa aurenta da d'an uwanta akan shi." Kallonta yayi yace "Waya fad'a miki ba'a san shi ba? Fad'a miki ne ban yi ba kawai dan naga ba anfanin fad'a, har k'ofar gidan nan mahaifin yaron ya zo nema masa aurenta, amma nace an mata miji." "To kuma tunda ka fad'i haka ba shikenan ba sai a tafi a haka?" Nuna ta yayi da yatsa yace "Wannan fa al'amari ne daya shafi makomar 'yata, ba zanyi wasa da ita ba na tauye farin cikinta dan tabbatar da namu farin cikin." Ko da ya fad'a ya fice daga gidan gaba d'aya, ita ma d'aki ta shiga rai b'ace, Faduma na kwance tayi ruf da ciki tasa k'afa ta harbeta tana fad'in "Sai kije ki zuba ruwa k'asa kisha tunda burinki ya cika ko." Da sauri ta mik'e zaune tana kallonta a duburburce, cikin jin haushi tace "Faduma ubanki ya miki komai a rayuwa, ya haifeki ta hanyar aure babban gata ne da wasu bai samu ba, ya raineki cikin soyayya da kulawa, yayi abubuwa da dama saboda ke, amma yanzu kin girma kin zama mutum, alfarma d'aya ce ba zaki iya yi mishi ba a rayuwa?" Sanyaya murya tayi tace "Haba Faduma, kinsan me kika aikata kuwa? Sama da shekara biyu kenan da sukayi alk'awarin had'a aurenku, kwana uku da suka wuce aka fara shirin tarban bak'in da zasu kawo lefenki, gobe goben nan zasu zo Faduma, amma kin juya tunanin mahaifinki, na tabbata ba zai fasa yin abinda yayi niyya ba dan kinsan yana sonki, ba kuma zai yarda ya aurar dake kina kuka haka ba." Girgiza kai tayi ta juya zata fita tace "Kin bani kunya, kinsa naji kamar ba tarbiyyata ba." Tana ficewa Faduma ta fashe da kuka, a take taji nadama na shigarta da kunyar sake had'a ido da mahaifinta, sai taji kamar bata mishi hallaci ba a rayuwa, kuka tayi sosai kamar zata kashe kanta ta kuma zuba idon dawowarshi har ta fad'a mishi ta janye kuma ta amince da auren yaya Abdul, zata nuna masa tana farin ciki sosai da zab'inshi. ______________ Taxi samu ta kaishi har gidan, kamar wanda bai da lafiya haka yake tafiya, ganin motarshi a k'ofar gidan ya tabbatar masa yana nan, yana yin sallama a bakin soron ya amsa mishi, dama d'akinshi k'ofa biyu ne, akwai wata a soro idan yayi bak'o tanan zai shiga ba tare dana cikin gida sun sani ba, sai kuma ta cikin gidan ta babban falon, bud'e masa k'ofar yayi ya shiga yana tambayar "Moliya kaine tafe yanzu cikin dare?" Bai iya amsawa ba sai wuri daya samu ya zauna, jujjuya abun yake data inda zai fara, sai yaji kamar yayi shiru ya koma sai kuma ya ga daya bari har sai an kawo kayan gwara kafin su kawo. Zaune yayi yana kallonshi yace "Moliya, lafiya kuwa? Ya na ganka hakane?" Kallonshi yayi yana matuk'ar jin kunyarshi sosai, sai dai kuma soyayyar Faduma ta wuce komai a wurinshi, bugu da k'ari a bayyane yake cewa auren da bata so ne zai mata, shi kuma ko wacce ba ita ba ba zai yarda ba barz kuma ita, kallonshi ya sake yi a nutse yace "Yaya akwai matsala ne dama." Da mamaki yace "Matsala kuma? Ta me?" Had'e yawu yayi da k'arfi kafin yace "Dama Faduma ce nake fad'a mata za'a kawo kayanta gobe, maganar gaskiya yaya ta nuna min bata son auren Abdul, shine...nace..bari na zo..." Shiru yayi ya kasa k'arasawa, a hankali shima yace "Shine me? Ka zo ka fad'a min a fasa auren?" Da sauri ya kalleshi sai kuma ya d'an kawar da dubanshi yace "Hakane yaya, kayi hak'uri dan Allah ka yafe mana, nasan zaka ji ba dad'i sosai, to amma barin shi yafi alkairi tunda yarinya ta nuna bata so, kuma ba ita ba ko shi ne ya nuna baya so ina ga ba zamu masa dole ba bare mace kuma." Jinjina kai ya shiga yi yana fad'in "Yayi kyau, yayi kyau Moliya, ni zaka kalla ka zauna kana fad'a ma haka? K'aramin mutum ka mayar dani ko me? Ashe dama kai mutumin banza ne? Yanzu saboda 'yar taka tace bata so shine ka zo kake fad'a min? Ko kuma dai uwar 'yar ce ta nuna bata so, dan nasan abinda take so shi kake yi." Girgiza kai yayi yace "Ba haka bane yaya, hasalima kafin na taho ita ma ta so..." D'aga masa hannu yayi yace "Kaga dakata, 'yarka dai ce ko Fatima, to ka sani har abada Abdul ya fita a harkarta ko da ita kad'ai ce macen data rage, ka sani Moliya ka lalata zumuncin dake tsakanina da kai, dan k'aramin mutum irinka bana buk'atar sake mu'amula dashi komai k'ank'antar kuwa." Nuna masa k'ofa yayi yana mik'ewa tsaye yace "Tashi ka bani wuri, karna sake ganinka gidana kaji na fad'a maka." Mik'ewa yayi jiki a mace baiyi yunk'urin tsayawa bashi hak'uri ba dan yasan ba zai saurare shi ba, yana fita ya mayar da k'ofa ya rufe yana ji ya ci gaba da bala'i da kumfar baki yana fad'a, girgiza kai yayi "Allah ya huci zuciyarka yaya, shi aure ai nufi ne na Allah." Da sauri ya taka ya fita daga gidan daf da zai fita shi kuma Abdul ya shigo suka had'e, k'arasa fita sukayi k'ofar gidan suka gaisa cikin mutunta juna, tunda sukayi musabaha bai sakin hannunshi sai jinjinawa da yake, a raunane ya kalleshi yace "Abdul Razaq kayi hak'uri da abinda ya faru kaji, ka sani shi komai nufi ne na Allah, idan har Allah yayi taka ce to duk kewaye kewayen da za ayi a k'arshe zata zama taka, in kuma ba taka bace ka sani ko ana tsaka da d'aura muku agiyar daraja ne sai wani abu ya gifta da zai zama kamar almakashin datsa wannan igiya." Duk da bai kalli fuskarsa ba dai yanayinshi ya canza ya kuma shiga tunanin me yake nufi? D'orawa yayi da "Abdul na maka wata tambaya d'aya? Kuma dan Allah ina so ka fad'a min gaskiya tsakaninka da Allah." Jinjina kai kawai yayi yana sauraronshi, a hankali yace "Abokin nan nawa wane irin mutum ne shi?" Kallonshi yayi da mamaki sosai yace "Aba abokina kuma? Wane abokin nawa?" "Wannan yaron da yace yana son Faduma." Cikin fahimta yace "Oho! Tagur?" Jinjina kai yayi alamar eh, shima d'an jinjina kan yayi yana sauke numfashi yace "Aba indai gaskiya zan fad'a maka, to Tagur mutumin kirki ne, a gaskiya ban san wani hali dake gareshi ba wanda za'a k'i shi domin shi, a iya sanin dana masa dai kawai yana da d'an zafi ne wanda kuma ko ki ina da shi." Jinjina kai yayi ya sake cewa "Nagode Abdul Razaq, ina k'ara baka hak'uri kaji, karka manta komai kaga ya faru to ka d'auka haka shine mafi alkairi, sannan a gaba zaka iya fahimtar dalilina na yin haka, amma dan Allah karka zarge ni kaji." Zame hanunshi yayi ya wuce ya barshi tsaye yana kallonshi da tunanin kalamanshi da jujjuya su, wucewa yayi sai dai tun a soro yaji muryar mahaifinshi na tashi sama had'e data matan nashi musamman ma mahaifiyarshi, ko da ya shiga gidan kai tsaye d'akin ya nufa yana sallama, amsa mishi sukayi ciki ciki inda ya bisu da kallo yana tambayar lafiya, a harzuk'e yace "Yo ina lafiya? Wannan k'aramin mutumin mana Moliya, wai ya zo yana wani fad'a min an fasa aurenka da Fati, kaji sai kace wata yar gwal, to a fasa mana sai me? Ita zata tsofe a gida amma kai aurenka babu fashi a ranar da aka saka za ayi insha Allahu, saika darje ka zab'a a 'yan matan dake garin nan." Wani murmushi ya saki saboda fahimtar abinda ke faruwa, kenan shiyasa yake ta bashi hak'uri? Girgiza kai yayi kawai yana jinjina abun, Tagur? Hummm! A nutse ya kalli mahaifinshi yace "Aba, dan Allah kayi hak'uri kar wannan abun ya zama silar lalacewar dangantakarku, idan Faduma matata ce babu abinda zai hana aurenmu, tunda kaga haka ta faru to ba matata bace, dan Allah kayi hak'uri ba zan zo ace sanadiyar hakan ba aka samu matsala." Cikin fad'a yace "To ya kake so nayi? Dubi fa abinda ya min, gobe fa za'a kai kayanku dangi duk sun sani suna jiran zuwan ranar, sai yanzu yace wani wai a'a." Sake matsawa yayi kusanshi yace "Aba, kai babba ne kuma mai magana d'aya, ka nuna masa da banbanci tsakanin kai dashi, kayi abinda shi ya kasa yi mana ka k'ara d'aga dajararka." A hankali ya kalleshi yace "Me kake nufi Abdul? Me kake so nayi?" Murmushi yayi yace "Aba idan nine a matsayinka wallahi zan nuna masa wannan ba komai bane, zan bi shi da addua'r sanya alkairi sannan na rok'e shi wata alfarma." Kallon tambaya ya masa da neman k'arin bayani, cikin murmushi yace "Eh Aba, sai na ce idan an tashi kawo kayan aurenta ma a zo gidana ni zan tarbi bak'i, sannan a bani d'aurin aurenta tunda nima ubanta ne, Aba idan kayi haka wallahi baka buk'atar yi masa kallon baka kyauta min ba, da kanshi zai tsargi kanshi zai kuma dinga hukunta kanshi da jin kunya marar anfani, ina tabbatar maka Aba ko ido ba zai sake had'awa da kai ba." Shiru yayi alamar yana tunanin abinda yaron ya fad'a, shi kuma kallonshi ya shiga yi da addua'r Allah yasa ya ci nasara, ba zai so zumunci ya lalace kan had'in aurensu ba, tabbas baiji dad'in yanda ya rusa shirin cikin sauk'i ba, sai dai yayi wata magana da ta isa tasa duk wani mai imani da yarda da Allah ne mai yin komai dole ya yarda shi ma, Dan haka yake fatan in alkairi ce gareshi Allah ya tabbatar masa, in ba alkairi bace kuma Allah ya zab'a musu mafi alkairin kowa ya had'asa da rabonshi. Yana cikin tunanin yaji ya dafa kanshi yace "Allah ya maka albarka Abdul, gashi dai ni na haifeka amma ka d'orani a hanya, tabbas idan nayi haka ni ne zan ci yak'in da nasarata." Murmushin jin dad'i yayi da girmama yanda mahaifin nashi yake son kunyata d'an uwanshi, ajiyar zuciya ya sauke ya kalli Ayyarshi yace "Kuma kuyi hak'uri Ayya ku manta kawai." Jinjina kai tayi tace "Mun hak'ura Abdul, amma ka fito da mata gaskiya, kaga ba sai an d'aga lokacin ba sai kayi aurenka a lokacin da aka saka." Jinjina kai yayi yace "Zanyi Ayya, amma ku zab'a min wacce kuke ganin ta dace dani." Da murmushi tace "In dan wannan ne ba matsala bace, insha Allahu zan duba maka wata wacce tafi Faduma komai kaji." Wani kallo ya bita dashi amma bai ce komai ba, shi ya ga abinda ya gani a tare da Faduma, shi yasan me yake ji a kanta, shi kad'ai ya hango irin rayuwar daya tsara ma kanshi tare da ita. Fita yayi ya barsu suka fara tattaunawa akan yan matan dake cikin ahali. _______________ Har bacci ya d'auketa bata ji mahaifinta ya shigo yi musu saida safe ba, baccin ne ya d'auketa kawai amma ba dan ta shirya mishi ba, dan har ta fara tunanin ko ta b'atawa mahaifin nata rai ne shiyasa ma bai shigo ba kamar yanda ya saba. Har tsakiyar dare ma data farka ta shiga ban d'aki tayi fitsari ta fito saida ta sake kallon k'ofar d'akinshi, tabbas da yau a gidan nan ya kwana da sai ta tashe shi a wannan lokacin, d'aki ta koma ta kalli Ayya wacce daga kwancinta zaka tabbatar ba bacci take ba ita ma ko kuma ta farka ne, uwar d'aki ta shiga ta canza pant d'inta da pad sannan ta dawo ta kwanta. Ko da aka idar da sallah asuba ta faki idon Ayya ta fice a gidan zuwa d'aya gidan, yayanta Manu ta had'u dashi zai shiga ya dawo daga masallaci, da mamaki ya kalleta yace "Ke Fatima, daga ina kike? Lafiya dai ko?" Kamar zatayi kuka tace "Wajen Aba na zo." Da sauri ya matso kusanta ya rik'e hannunta yace "Waye ba lafiya? Ina Ayya?" Hawayen da take ta k'ok'arin rik'ewa ne suka taho tasa hijabi tana sharewa tace "Kowa lafiya lau, yaya Manu jiya na yi wa Aba laifi, ban san ya zanyi ba yaya, ka rakani na bashi hak'uri." Cike da kulawa yace "Laifi kuma Fadu Abanta? Me kika yi wa Aba? Naga ai bata b'acewa ke da shi ko?" Cikin shashek'ar kuka ta gajarce mishi abinda ya faru ta fad'a masa, kama hannunta yayi suka shiga cikin gidan yana rarrashinta tayi shiru, d'akin Ayya ya nuna mata yace "Shiga ciki sai ki jirashi ya dawo tunda kinsan yana fita tattaki a wannan lokacin, idan ya shigo saiki same shi kuyi magana." Jinjina kai tayi alamar to ta shiga ciki, Herde na ganinta ta shiga tambayarta ita ma ko wani ne ba lafiya? Saida ta tabbatar mata da lafiya lau sannan hankalinta ya kwanta, cikin nutsuwa kuma ta labarta komai, dariya kawai ta mata amma ba tace komai ba sai ma jiran mai gidan dan taji yanda zasu k'are. Ko da ya shigo ko ta same shi ta duk'a har k'asa tana kuka tana fad'in ya yafe mata ta amince zata auri Abdul, rarrashinta yayi yace ai kuma wannan magana ta wuce, kuka ta ci gaba da yi duk ya yace mata wanda take so zai aura mata, sai ta ji bata son wanda take jin zuciyarta na raya mata, da k'yar ya rarrasheta da taimakon Herde ta koma gida tayi shirin makaranta ta tafi." Bayan kwana biyu suna zaune tare da Hadizey tana mata gyaran salade wani almajiri ya shigo da sallama, a tare suka amsa suna juyawa da kallonshi, saida ya durk'usa ya gaishe da Hadizey sannan yace "Wani ne a k'ofar gida yace wai yana kiran Faduma." Da sauri suka kalli juna sai kuma Ayya ta kalleshi da mamaki dan haka bata tab'a faruwa ba tace "Wani kuma? Wanene?" Girgiza kai yayi yace "Ban san shi ba nima." "Je ka tambaya wanene?" Cewar Ayya, tashi yayi ya fita jima kad'an ya dawo yace "Yace wai Tagur ne." Sadda kanta tayi k'asa gabanta na fad'uwa, jin shirun yayi yawa yasa ta d'aga kai ta kalleta, ita ma ashe ita take kallo kamar tana karantar yanayinta, d'an tab'e baki tayi tace "Tashi kije, minti goma yayi yawa ki dawo." Cire hannayenta tayi a ruwan ta mik'e ta shiga d'aki, zunbulelen hijab d'inta ta sanyo ta fito suka fita tare da almajirin da ba a ce masa komai ba. K'ofar gidan yake jingine a motarshi bak'a k'irar honda wacce a lokacin sai manya da ya'yansu ke iya mallakarta, yana ganin ya d'an d'ago yana saka takalminshi d'aya daya d'an cire ya gyara tsayuwa, murmushi ya shiga doka mata har ta k'araso. "Assalama alaika." Ta fad'a kanta k'asa, zubawa fuskarta ido yayi kawai yana kallo, saida ya ja wasu sakanni kafin yace "Amincin Allah tausayinsa da jink'ansa su tabbata akan ki gimbiya Faduma." D'an murmushi tayi tana satar kallonshi kawai, jin yanda idonshi ke yawo akan jikinta yasa ta sake sadda kanta tana murza damtsenta daga cikin hijabi, cikin taushin murya yace "Faduma ya kike?" "Lafiya lau." Ta fad'a ita ma a tausashe, murmushi yayi yace "Kinyi farin ciki da gani na?" Da sauri ta d'aga kai ta kalleshi sai kuma tayi k'asa da kanta, har ranta tana jin kunyar had'a ido dashi, girman jikinshi yana kayar mata da gaba, a haka kuma yace shekarunshi basu fi ashirin da biyar ba. Wata sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke a hankali ta furta "Ko da gaske ne bai wuce ashirin da biyar ba?" Dariya ce ta kubce mishi yace "Ki yarda dani mana Fati, daf nake da cika ashirin da shida, kinga tunda bai cikata ba kuma banda tabbacin zai cikata shiyasa nake cewa da biyar." Tunda ya fara magana tasa hannu ta rufe fuska, yo ita fa ta d'auka a zuciyarta tayi magana, ashe yaji? Ba tare daya daina dariya ba yace "Fatima magana na zo muyi dake." Sauke hannayenta tayi ta nutsu tace "Ina jinka." Saida ya daidaita tsayuwarshi yace "Fatima kwana biya zuwa shida daya wuce mun zo nan tare da mahaifina neman aurenki, amma mahaifinki ya fad'a mana an tsayar da ranar aurenku da Abdul, nima a gida sun sama min mata yanzu haka, sai dai har yanzu na kasa farin ciki da nutsuwa, yanzu ma ina zaune naji ke kawai nake son gani, shiyasa na zo dan ina son jin wani abu daga bakinki." Shiru tayi tana saurarenshi ita dai, a hankali yace "Faduma, shin ke ma kina son auren nan? Ko kuma ke ma had'in gida ne za'a miki?" Ajiyar zuciya ta sauke ta kalleshi cikin nutsuwa tace "Hakane an tsayar da ranar aurena, amma yanzu babu wannan maganar saboda Abana baya min abinda bana so." Da wani irin sauri ya gyara tsayuwarshi yace "Me kika ce Fati?" Yanda yayi maganar yasa ta sunkuyar da kai tana fad'ad'a murmushinta ta jinjina masa kai alamar eh, matsowa yayi kusanta yace "Faduma akwai wanda kike so ne a zuciyarki? Wane mai sa'a ne wannan?" Hannu tasa ta sake rufe fuska tana dariya, cikin zak'uwa ya sake cewa "Fad'a min mana naji, ina so na had'u dashi ko zan kwashi damshin sa'arshi nima nayi nasarar cabko yarinya kamar ki." A gaskiya yana fasa mata kai dayawa, yana sa taji ta kamar wata ita kad'ai ce a duniyar ko macen data rage, cikin jin kunya tace "Idan ka koma gida ka dubi madubi, duk wanda ya nuna maka ka fad'a masa shi mai sa'a ne." Ko da ta fad'a da gudu ta juya ta koma cikin gida, wani tsalle ya daka tare da kaiwa iska naushi yace "Woooo!" Da sauri ya shiga mota shima ya bar unguwar da gudun tsiya yana jin ko mutuwa ta riskeshi a haka ba damuwa saboda ya cinmma nasara a soyayyarshi, ya kuma ji farin cikin da ake ji a sanda ka samu karb'uwa a zuciyar wacce kake fatan samun yardarta. Ko k'ofa bai rufe ba ya fad'a d'akinshi da gudu, uwar d'akin ya shige ya tsaya gaban madubin coiffeuse, ya iya k'ok'arinshi na son rufe bakinshi amma ya kasa, kallon kanshi yake sosai har saida ya furta "Tagur kai mai sa'a ne." *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 17:12 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _21_ *A gurguje* A hankali soyayya mai tsafta da kyau da k'arfi ta shiga tsakaninsu, basu wani jima ba aka shigar da manya a maganar, su dai kawai sunga manya kuma an tsayar da magana d'aya, amma basu san yak'in suk'urun da aka sha ba kafin haka ta faru, hatta uban da k'yar ya fahimceshi ya amince da buk'atarshi, hakan ba bayan ya kafa masa sharad'in sai in ya amince bayan ya kammala karatunsa zai auri yar amininshi, shi dai tunda zai samu wacce yake so bai damu ba, da sauri ya amince yace ya yarda zaiyi biyayya, amma Hatimi tace sam hakan bai mata ba, yarinyar ce ma bata mata ba ko kad'an, hak'uri Aba ya bata yace ta kwantar da hankalinta hakan ba komai bane, duk da haka bata yi amanna ba. Abun bai k'ara tunzurata ba har saida aka d'auki kayan lefen da akayi da sunan Husna aka tafi kaiwa gidansu Faduma, ganin tarin tilin kayan da kud'ad'en da aka loda sama ya girgiza ta, saida kuma aka dawo daga kan kayan aka fad'a mata komai daya wakana, kama daga unguwar zuwa gidan, kalar mutanen da yanda aka tarbesu, dan su a ganinsu shinfid'ar harkar girma tafi ta fuska. Hakan ya k'ara jawa Faduma bak'in jini a cikin dangin inda aka shiga caccakarta tun babu wanda yasan kamanninta, babu wani tsayayyen dalilin da yasa suka k'i ta, kasancewarta ba ita bace zab'insu ya kawo haka, har saida Tagur ya fara jin ba dad'i a zuciyarshi, yanda mahaifiyarshi ke nuna halin ko in kula akan lamarin bikinshi da zagin Faduma ko da a gabanshi yana damunshi, ba kuma ita kad'ai ba kaf dangin idan ka cire Aisho da Abanshi babu wanda zaka ji alkairi ya fito daga bakinshi akan Faduma, sai dai bayan Ayyarshi da wanda baya iya ramawa babu wanda yake ce wa kule bai ce masa cas ba, musamman Gomboy da sauran yan uwanshi, kullum cikin fad'a suke da gaba saboda ita, hakan kuma yasa Hatimi cewa yarinyar ta asirceshi tun kafin ta shigo gidan ta had'ashi da yan uwanshi. Lokaci na nan yanda aka saka na farko ba'a k'ara ba bare rage ba, tare da kuma auren Abdul da shima aka samu yarinya a dangi aka had'ashi da ita. Duk sati sau d'aya yake zuwa suna zance daga bayan sallah isha'i zuwa k'arfe tara, bata da waya har yanzu kuma ko da ta Ayya bata tab'a jarraba kiranshi ba, bata ma san lambarshi ba bare tayi wannan ganganci a wayar Ayya, duk da tana son rik'e wayar a yanzu data fara d'and'anar zumar soyayya, sai dai iyayenta basu amince ba sun ce idan taje can ya siya mata fiye da waya ma, suna kiyaye duk wani da zai iya sa magana ta biyo baya inhar ba aure suka d'aura musu ba, duk da tarbiyarshi da yanda ya saki jiki dasu yasa sun k'ara fahimtar waye shi, amma ai zuciya bata da k'ashi dole su kiyaye, shiyasa duk ranar alhamis ta kan zama kamar ranar sallah a gurinsu, da taimakon Ayya take shirya kanta cikin sauk'akk'ar kwalliya, zata share gida tas ayi girki na musamman saboda shi dan a cikin gida suke hirar. Ta wani b'angare kuma ta fara karb'ar gyaran jiki daga Ayyoyinta biyu, sam babu wani abu bak'o a gareta bata ji wani gundura ko isa ba, ba dan komai ba sai dan ta saba da irin wannan dama, tunda safe akwai sinadarin gyaran jikin da ake shafa mata tare da had'in turaren jiki na wuta, daga lokacin kuma saita fara fita da nik'ab, da yamma kuma idan ta dawo daga islamiyya za'a mata na yamma banda ranar alhamis kawai dan ta samu shiryawa da wuri. *Juma'a* Ayya da kanta da ya zo daren jiya ta bashi lambarta tace ya dinga kiranta suna magana ta nan, saboda yanzu sati bakwai ne ya rage ayi bikinsu, kuma akwai gyaren da zasu fara mata wanda idan anayi ba'a fita, ta fad'a masa hakane dan ya nutsu, amma maganar gaskiya gyaran ne na musamman wanda ba za'a so had'uwarsu ba. Alfarma ya nema yana so kafin a fara ya kaita su gaisa da Ayyarshi, dan yanzu da zai taho tana k'orafin har yanzu bata san kamanninta ba, jin haka da farin ciki ta yarda ta amince da abinda ya fad'a, dan gaskiya bata tab'a zuwa ba, sai dai tace idan mahaifinta ya shigo zata fad'a masa zuwa safiyar gobe sai suyi waya ta fad'a masa. Shine fa yanzu tunda tayi la'asar take shirin tafiya. Tsaye tayi gaban Ayya tace "Ayya wannan sunyi? Haka ai nayi ko?" Kallonta tayi tun daga sama har k'asa, rantsetsiyar lafayar mai ja da bak'i da walk'iya mai kalar golden, sai takalma bak'ak'e masu d'an tudu da kallabin data d'aura daga ciki bak'i, sai ta d'aga hannunta ne kake iya ganin rigar ciki mai dogayen hannaye ita ma bak'a. Bata shafa komai a fuska ba, sai k'yalli take da shek'i na gyara, ba tayi haske ba amma tayi luwai luwai tayi wani fresh da ita, man leb'e kawai ta sharkata wanda yasa bakin dad'a walwali da maiko. Fuskarta da yanayin damuwa ta kalleta tace "Faduma k'amshin nan yayi yawa, kamar wata gonar lalle." Dariya tayi tace "Wallahi Ayya bai saka turare ba, kawai na jikina ne sai na lafayar da kika turarata." "Na sani Faduma, ji dai nayi kamar yayi yawa ana jinshi ko daga nesa ma." Turo baki tayi tace "Amma Ayya ai baya da k'arfi ko, gashi k'amshin shi mai sanyin dad'i da kwantar da hankali." Cikin ido ta kalleta tace "Shine tashin hankalin ai." Zaro ido tayi sai kuma tace "Ayya kawo wayarki na kira na fad'a masa na gama shiryawa." Da wani mamaki ta kalleta tace "Faduma ki kira shi? Rawar k'afa kike zaki ji gidan surukai? Faduma kin matsu ki ganki a gabansu ne?" Girgiza kai tayi alamar a'a, jinjina kai tayi tace "Yayi kyau, kuma karki manta da kama kanki Faduma, idan zai yiwu karki yarda ki had'a ido da mahaifiyarshi har ki baro gidan." Da murmushi ta amsa da "Zanyi yanda kika ce Ayya." Jinjina kai tayi tace "Zauna ki jira shi ya zo da kanshi, mace da aji aka santa." Jinjina kai tayi ta koma ta zauna kan kujera, a k'alla ta d'auki minti sha biyar kafin suka ji tsayawar motarshi da sallamarshi a tsakiyar gidan, amsawa sukayi Ayya ta fara fitowa suka gaisa, tana ji take fad'a masa dan Allah kar su kai isha'i basu dawo ba, a hakan ma dan Abanta ya amince ne, cike da tabbaci ya mata alk'awarin dawo da ita bayan sallah magriba, fitowa sukayi da kanshi ya bud'e mata mota ta shiga ya rufe. Zagayawa yayi ya shiga ya zauna suka tafi, bata tab'a shiga motarshi ba sai yau, hakan yasa taji kusancinsu yayi yawa, matsewa tayi wuri d'aya tana jin kamar numfashinsu na gauraya dana juna, juyawa yayi ya kalleta yana murmushi, zaiyi magana sai kuma ya d'an cije leb'enshi, lumshe ido ya d'anyi lokaci d'aya kuma ya bud'e ya kalli gabanshi, ajiyar zuciya ya sauke a hankali, ci gaba yayi da tuk'i har sukayi nisa, sai dai yana yawan jan tsaki, ya rasa me yake damunshi ne, shayin da yasha a majalisarsu ne bai karb'eshi ba ko me, mararsa ke k'ullewa tana masa wani ciwo daya saba jin sa da dare musamman idan yayi mafarki. D'an tsaki ya sake ja yana sake dantse leb'enshi, a hankali ya furta "Na shiga uku, wallahi mik'ewa take." 馃槑馃ぃ Zinder Cikin dubara ya sake matse k'afafunshi ya ci gaba da tuk'i, yana son janta da hira amma baya so yayi magana, idan ma yayi zai tona kanshi ne, duk da dai ba lallai bane Fati ta iya fahimta, amma dai jin muryarta ma hatsari gareshi a dai halin da yake cikin nan, a haka sai dai ya juya ya kalleta su sakarwa juna murmushi har suka isa, k'ofar gidan da ta ga ya tsaya mai gadi na bud'e musu yasa ta sakin baki ta shiga kallon gidan, indai har nan ne gidansu to tabbas shi babba ne sa'a tayi, ko kuma ta kira hakan da d'aukar dala ba gammo, har suka shiga ciki ya paka motar a wurin ajesu, cikin sanyin jiki sosai ta fita tana k'ara kallon wurin, mota biyu ne a wurin sai ta shi yanzu ta uku, ta d'an juya ta b'angaren da yake ta ga baya nan, da sauri ta shiga waigawa dan ganin ina ya shiga, motsin bud'e motar yasa ta sunkuyawa ashe bai fito ba. Da k'yar ya fito ya mayar da k'ofar ya rufe bakinshi kam a dantse sosai, bai had'a ido da ita ba dan wani zafi yake ji a jikinshi, daga can tsaye ya kalleta yana ta k'ok'arin ya mata magana, k'arfin hali yayi kawai ya d'aga mata hannu alamar ta taho su shiga, takawa tayi zata nufi inda ya nuna mata amma kuma shi yana tsaye baida niyyar tafiya. Kallonta yayi a ranshi yana ayyana ba zai iya tafiya ba, idan ya shiga gaba zata gane bagwariyar tafiyarshi, idan suka jera zata hangi asirinshi, dan sosai ya bayyana kanshi yanda ko makaho zai iya jin inuwarshi, idan kuma ta shiga gaba ba zai iya mata magana da baki cewa ga inda zata shiga ba. Duk'e kai yayi ya d'ora a jikin motar ya sauke numfashi, zuut zuut zuut kawai ake masa daga k'asan nan, kamar dai an gama had'awa dokin tsere siddi da lizami yana haniniya yana jiran umarni daga mai busa ya zuba guje, ganin haka yasa ta zagayowa inda yake cikin tattausan murya tace "Lafiya? Me yake damunka? Baka da lafiya ne? Cike da k'arfin halin ya d'ago yana mata murmushin dole ya girgiza kai, cikin fizgo magana da k'yar yace "Ba...kom...ai, k..arki...damu." Da ido kawai ta bishi dan ko maganar shi sai taji kamar ta wanda bai da lafiya, sake nuna mata hanya yayi yace "Muje." A hankali ta shiga takawa shi ma haka, sai dai bai yarda sun jera ba kuma ba baya yake sosai ba, yar kwanar ta shigawacce ke daf da babbar k'ofar shiga falon, sai dai a kulle take hakan yasa suka tsaya dukansu, gaba ya matsa ya kai hannu ya murd'a, amma sai yaji a rufe gam, baisan da wannan sabuwar d'abi'a ba shiyasa ya lalubo wayarshi cikin wani matsanancin tashin hankalin da shi kad'an yake fuskantarshi ya shiga dannawa lambar Ayyarshi kira, ga wani irin b'acin rai dake ziyartarshi, ita kanta zuciyarshi harbawa take da gudu gudu da sauri sauri, jikinshi har ya fara tsuma yana rawa saboda bala'in da yake ciki. Ana d'agawa cikin dantse harshenshi yace "A..ayya k'ofa a rufe." Hatimi data fahimce shi tsaf tace "Eh mana tunda ba kowa wa zan barwa d'akina bud'e?" Da wani irin mamaki yace "Ba...kowa.kuma? Ayya ina...kuka tafi bayan kinsan yau Fatima zata zo?" Daga b'angarenta tace "Iyee! Tagur wato saboda wata yar talakawa zata zo gidan, shine aka ce ni kuma ba zan tafi sabgar gabana ba? To bata isa ba wallahi, idan zata iya jirana ta jira ni, in ba zata iya ba ta kama hanya tayi tafiyarta mana, ai ba dole ko?" Da k'yar yace "Shikenan,,,, zata jiraki a... b'angarensu Aisho." Wani murmushi tayi mai sauti tace "To ai tare muke dasu, ka samu ko da tabarma ne a d'akin mai gadi saika shinfid'a mata a tsakar gidan ta zauna, dama ai ita ce ta dace da ita ba falona ba." Yanda ta kashe wayar yasa ya bi wayar da kallo, damk'e hannun k'ofar yayi sosai yana sake cije leb'enshi kamar zai hudashi, sunkuyar da kai yayi yana gayyato nutsuwa da tausar zuciyarshi, addu'a yake Allah ya bashi hak'uri kar yayi abinda bai dace ba a gaban Faduma, zuwanta na farko a gidansu karta fara fahimtar waye shi idan yayi hushi, addu'a yake Allah yasa ya iya rik'e kanshi ya samu ya lallab'ata ita ma. A hankali ya saki hannun k'ofar ya juyo yana kallonta, gabanta ya yanke ya fad'i sosai ganin wani irin ja a idonshi, ko yaji aka zuba mishi iya abinda zasu iya yi kenan, cikin dubara ya had'a kalmomin yace "Sun... fita..w..ani..taro..ne, am..ma yanz..zuuu zasss...u dawo, muje...b'angare na..." Yana fad'a yayi gaba abinshi, da kallo ta bishi da tunanin b'angarenshi kuma, yanda ta hangeshi hannunshi dafe akan mararshi, a hankali yake tafiyar yana d'an had'a hanya kamar yasha wani abu, sai taji gabanta fad'uwa kawai yake duk hankalinta bai kwanta ba, amma sai ta bi bayanshi cikin nutsuwa har ta k'arasa, ko da ta isa ma har ya bud'e ya shiga ciki, tsaye tayi k'ofar tana kallon wurin, rumgume hannaye tayi tana jujjuyawa tana kallon gidan. K'arar abu da taji ya fad'i tare da jin sautin k'ara kamar na mutum ya fito daga ciki yasa ta sauri tura k'ofar ta shiga. Yanzu kam ta tabbatar baya da lafiya, tabbas akwai abinda ke damunshi yana b'oye mata ne, da gani kasan fad'uwa ne yayi ko dai wajen zama akan kujera ko kuma kafin ya zauna, da sauri ta k'arasa tare da saka k'arfinta ta janye teburin dake gaban kujerar k'arami na glass mai kyau, duk da laushin carpet d'in da take ji k'afafunta na takawa, sanyin da taji yana ratsata mai dad'in gaske, k'amshin turaren wuta airfreshner da kuma nashi turaren da take ji wanda yasa d'akin mai d'auke da kakkauran labulaye madaidaici ya ni'mta sosai, durk'usawa tayi gabanshi cikin tashin hankali tana fad'in "Yaya, baka da lafiya ne? Me yake damunka?" Dafe goshinshi yayi yana jujjuya kanshi ya kasa tashi zaune, yanda yake ta dantse lebenshi abun ya fara bata tsoro, yanda yake murza mararshi da mimmik'ewa hankalinta ya fara tashi, sake sunkuyawa tayi kusan kanshi tana fad'in "Dan Allah ka min magana, me yake damunka? Dama kana irin hakane?" Hannunshi dake saman goshinshi ya d'ago yana rawa gaf gaf gaf, da k'yar ya iya rik'o hannunta abinda bai tab'a faruwa ba a tsakaninsu, a tare suka ji wani abu da babu wanda ya tab'a jin kwatankwacinshi. Ita kanta da ba sha'awarce da ita ba saida taji wani abu kamar wuta ta ja ta, tare da bugawar zuciyarta da kuma fad'uwar k'irjinta rairass, hannunshi irin mai tsokar nan ne da taushi sosai, sai kuma sanyi cikin tafin hannu, sab'anin shi da yaji wani bala'i ya sake tunzuro mishi, duk da tana da tuwon hannu amma bai da k'iba ta ciki, sai kuma wani sahihin taushi da fitar da wani irin d'umi mai kaiwa har k'wak'walwa. Sake matse hannu yayi sosai yana d'an mumurzashi, cikin rawar da bakinshi ya fara na sanyi yace "Fff...ati..ma, ban...da.. laffffi..ya, i...na..jin kamar...ba zan... zama..mijinki...ba." Zaro ido tayi a take hawaye suka gangaro daga kan fuskarta, kiciniyar gyara zamanta ta shiga yi wanda hakan yasa hawayenta suka sauka akan fuskarshi. Take ya lumshe ido saboda wani yammmmm da yaji tun daga k'asa har sama, hawaye ne masu d'umi da wani sinadarin daya k'ara ma ciwonsa gishiri, saida ta gyara zamanta sosai tana kuka tana kallon fuskarshi, ga lafayarta data sauko daga kanta har zuwa kafad'a, kuma rik'e yake da hannun na hagu da zata iya sawa ta gyara, na dama kuma shine take share hawaye dashi, cikin muryar kuka mai aika sak'o tace "Dan Allah ka bar fad'in haka kaji, ka fad'a min me yake damunka sai na maka addu'a, insha Allahu zaka samu lafiya." Lumshe ido yayi sosai yana sake shak'ar k'amshin dake fitowa a jikinta, ga hannunta da yake ta mitsikawa kamar zai rabata dashi, sai dai ita ma bata damu ba saboda ganin halin da yake ciki, jin bai amsa mata ba bama ya da wannan niyyar yasa ta sassauta murya sosai tace "Ka bud'e idoka ka kalleni mana *Orronurrrr* (rayuwata)." Da sauri kuwa ya bud'e idon, dan yanda ta ja *r* d'in ya masifar tayar masa da tsikar jiki, sake lumshe ido yayi yana tuna yanda abokanshi suka dinga mishi dariya daga ya karb'i kofin shayin dake hannun Misbah yasha, haka suka dinga tsokanarshi suna cewa wai zai angonce yau da duk wacce ta shiga gabanshi, sai Abdul kuma daya b'ata ranshi har ya mishi fad'a kan me yasa yasha shafin hannun Misbah? Shi fa d'an iska ne, izuwa yanzu ya fahimci komai, sai dai yanda zaiyi da kanshi ne abun damuwar yanzu. Wannan shirun da yayi yana tunani yasa ta ga kamar ya daina motsawa, da sauri ta d'ago daga zaman da take tana kallon fuskarshi, ta sa shi gaba kamar wacce zata mishi wankan gawa ko ruk'iya, sanda take lek'a fuskarshi kuma lafayarta ta sauko har ta rufe mishi fuska, bud'e ido yayi ya juyo da kanshi suka had'a ido. Kamar a mafarki ko tatsuniya sai ji tayi ya damk'o damtsenta ya kwantar da ita kan jikinshi. Da wata irin azama tayi fitt ta sauka daga kanshi tana zaro idonta kamar zasu fad'o k'asa, ja baya tayi tana girgiza kai da mishi wani kallon mamaki, da sauri ya tashi zaune ya matso kusanta, ja baya ta sake yi zata mik'e tsaye yayi saurin rik'e lafayarta, yanda jikinta ya kwashi rawa da yanda gabanta ke dokawa yasa kawai ta fashe da kuka, rik'e lafayar tayi ita ma zata k'waci abar ta amma ya rik'e gam, baya baya ta shiga yi tana son k'watar lafayar tana girgiza mishi kai da fad'in "Ka barni na tafi, dan Allah ka bar min wannan wasar, ban sanka da haka ba fa." Da yake falon ba girma bane dashi dan danan ta dangane da jikin bango, ganin ya yo kanta yasa ta saurin nufa b'angaren dama inda k'ofa take, hannu yasa ya tokare bangon haka ya hanata damar fita, duk'ewa tayi k'asa ta had'a kai da gwiwa ta sake fashewa da wani kukan. Yanda ya koma kamar wani kumurci yasa ta sake tsorata, kamata yayi ya mik'ar da ita tsaye yana kallonta. K'arfi tasa ta tureshi amma da yake bai sake ta ba saiya zama har ita saida ta baro jikin bangon, sai gata kwance a k'irjinshi, zata tashi da sauri ya sake matseta a jikinshi yace "Shiiiiiii." Da k'yar ya sake d'orawa cikin wata irin murya mai ban tausayi da kuma tayar da hankali ga mai ita yace "Faduma babu abinda zan miki, d'umin jikinki kawai nake so naji, hakan zai taimakawa na wa jikin na samu k'arfi, inba haka ba mutuwa zanyi." Da sauri ta d'aga kai ta kalleshi cikin rawar jiki da tsoron da bata tab'a shiga irinshi ba tace "Ka daina ba kyau fa haka, karka sa Ayya ta kasheni da raina idan ta gane ka tab'a jikina, dan Allah ka k'yaleni muje ka mayar dani gida." A hankali ya d'ora hab'arshi akan kafad'arta, cikin wani irin salo ya zura duka hannayenshi biyu a cikin rigarta data kama jikinta, zaro ido ta sake yi ta fasa wata irin k'ara, da sauri sosai ya zaro hannayenshi ya kalleta, a take ya damk'o fuskarta ya zura bakinshi cikin nata, hakan yasa kaji d'ifff, tureshi ta shiga yi amma ka rantse mayen k'arfe ne ya had'u da wani mayen k'arfen, duk yanda ta so ture shi ta kasa dan sosai ya matseta a jikinshi yanda har saida ta rasa numfashin da zata ja. Jin yana ta k'ok'arin rabata da rigarta yasa ta sulalewa k'asa dan ta rok'eshi ya barta, amma abun mamaki saiya bita shima k'asan ba tare daya saki bakinta ba, jin zata mutu a banza saboda bata fitar da numfashi kuma bata shak'ar iska, sai kawai tasa duka hannayenta ta shiga yakushinshi ta ko ina, da sauri ya jaye bakinshi daga nata yana jan yaji da fad'in "Ashhhhhhh." A firgice ta juya daga durk'ushen zata rarrafa ta fita, sake damk'ota yayi cak ya d'orata akan cinyarshi, kallon fuskarta yayi yana shafa kumatunta yana fad'in "Kalleni Faduma, ni fa mijinki ne, yanzu ba zaki iya taimaka min ba?" Da k'arfi tasa hannu ta ture shi tana fad'in "Sake ni na tafi gida malam." Hannuta ya kamo ya d'ora kan wuyanshi yace "Faduma tab'a jikina kiji, dan Allah ki taimaka min na daina jin abinda..." Bai k'arasa fad'a ba ya sunkuyar da kai ya dafe mararshi, ganin kamar ya sassauta mata rik'on yasa ta zamewa a hankali daga jikinshi ta sauka daga kan k'afarshi, saida ta mik'e tsaye zata daka da gudu taji ta sake komawa baya ya rik'e lafayarta, daddagewa ta sake yi a kari na biyu ta tartsa ihu, da k'arfin bala'i duk da yasa zata ci ciwo, haka ya fizgota ta fad'i kwance har kanta ya bugu, rufe mata bakin da yayi da hannu yasa k'arar data saki bata fito ba, cikin haushi haushi ya haye kanta ya danne hannayenta yana kallon fuskarta, idonshi akan ta cikin b'acin rai yace "Ke nutsu, ni fa ba iskanci nace zanyi dake ba, Fatima wasa kawai zanyi dake ko naji sauk'in abinda ke damuwa, ko kina so na mutu ne?" Bai bata damar cewa komai ba ya sauka daga kanta yayi cak da ita ya dire kan kujera, ta yunkura zata tashi ya mayar da ita kwance, kuka sosai tasa tana fad'in "Ni dai Allah ka k'yale ni na tafiyata gida, ni ban san haka kake ba da ban biyo ka." Kwance yayi kanta gaba d'ayanshi hannunshi d'aya kuma na saman wuyanta yana shafawa, marairaicewa yayi yana mata wani kallo mai kashe jiki yace "Faduma ki yarda dani, wallahi ba haka nake ba nima, ki taimaka min indai kina so na, in ba kya son na mutu Fati ki taimake ni kinji, ni fa mijinki ne." Girgiza kai tayi tana siraro da hawaye tace "A'a gaskiya, tsoro nake ji ni dai ka k'yaleni kawai, idan Ayya ta gane ka tab'a wallahi zan shiga uku." Saida ya sumbaci bakinta ita kuma ta kawar da kanta yace "Faduma ba zata gane ba, ba zan miki abinda zata gane ba kinji, na miki alk'awari." Kai ta sake girgizawa zata yi magana ya mata wata damk'a da k'arfi yana tusa kanshi tsakiyar wuyanta ya cije leb'e da rintse ido, yanda ya k'amk'ameta kamar zai koma cikin cikinta yasa ta rufe ido, wani iska ya dinga sauka jikinta sanda taji yana furta "Wayyo Allah na Faduma, wayyo marata zan mutu, Ayya, wayyo Allah, la'ilaha..." Saukar d'umi taji a wuyanta hakan yasa ta bud'a ido, cikin rawar murya tace "Orro ka d'aga ni, kana bani tsoro fa." D'ago kai yayi amma kukan daya zo mishi yasa bai iya had'a ido da ita ba, had'a fuskarsu yayi hanci da goshinsu a had'e idonsu ma duk a rufe, hawayenshi na sauka akan fuskarta ita kuma nata na gangarawa ta gefen ido har zuwa wuya, cikin muryar kuka yace "Fa..ti ki taimaka min." Ita ma a muryar kukan tace "Tsoro nake ji Tagur, babu kyau fa hakan, Allah ya hana kuma yana ganinmu, idan kayi hak'uri kwana nawa ya rage ka mallaki abinda yake naka ne dama?" Saida ya sauke mata numfashi mai iskan tom tom yace "Fati ba abinda kike nufi nake son aikatawa ba, d'umin jikinki nake so naji kawai, ina jin haka nasan zan samu lafiya, Faduma wani abu nasha majalisa ba tare da sani na ba, na tabbata shine yake sani jin haka, ina tsoron na mutu idan ban samu taimakonki ba." Shiru tayi tana saurarenshi, hannunshi taji a cikin rigarta, dama ba bras take sa wa ba ita sai kawai ya kai garesu, sake lumshe ido tayi tana tunanin rayuwarshi ne mai mahimmanci gareta ko kuma tseratar da mutumcinta da imaninta? Idan ta ajesu duk gefe akwai abinda ya kamata ta nuna fifikonshi akan duk wad'ancen, *Allah*, ya kamata ta ji tsoron mahaliccinta da kunyarshi, idan har son gaskiya yake mata zai ji dad'in abinda zatayi, idan kuma dama wannan manufar ce tasa shi biyowa da neman aurenta, to tasan za'a fasa aurenta, saidai tana da yak'inin yanda Allah ya kawo mata shi to zai kawo mata wanda ya fi shi bayan tafiyarshi. Juya kanta tayi daidai damtsenshi tasa iya k'arfinta ta narka masa cizo, wanda lokacin yake shirin fito da nononta ya saka baki, baisan sanda ya saketa ba ya d'ago, kallon wajen yayi har jini ya fito, yunk'urawar da tayi da k'arfi da niyyar ta k'arasa ture shi, sai dai ina dama yana zaune kan jikinta ne, k'arfi yasa shima ya kwantar da ita, bai cire mata lafayarta ba sai dai sama da yayi da ita daga k'asa, zaro pant d'inta yayi ya jefar a d'aya kujerar. Gigicewa tayi ta rasa gane me ke shirin faruwa da ita, kwance yayi a jikinta ya sakar mata duka nauyinshi, sautin fitar gwagwaren numfashinsu kawai kake ji, d'an d'agowa yayi ya kalleta ita ma k'yar shi take kallo, a hankali yace "Kiyi hak'uri Zahra." Duk girman jikin nan nashi da k'arfin jarabar dake cin shi bai sarara mata ko d'aya ba, gaba d'aya ya danna kanshi dan ceton rayuwarshi ne kawai a gabanshi a lokacin. Tana jin abu ya ratsa jikinta ya wuce har cikinta ta ciccika hannunta da naman hannunshi tare da jan numfashi. *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 17:12 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _22_ Da sauri sauri ya shiga taimaka mata ta shiga ban d'akinshi ta wanke jikinta ta fito saboda jin k'arar motar su Hatimi, rik'e yake da hannunta har suka fito falon, yanda take taka k'asa kamar mai koyon tafiya da hawayen dake zubo mata har yanzu yasa shi tsayawa gabanta yana kallonta, ajiyar zuciya ya sauke yana shirin kamo d'aya hannunta, da sauri ta fizge hannayenta tana zabga masa harara, sunkuyar da kanshi yayi yace "Naji Faduma, amma dan Allah kiyi hak'uri ki daina kukan nan, Faduma kar a fahimci abinda ya faru dake mana." Wani kuka ta fashe dashi mai cin rai tace "Allah fa ce mana yayi kar mu kusanci zina, kar ma mu kusance ta bare mu aikata ta, shine yau na aikata zina da wanda za'a d'aura min aure dashi, na shiga uku na lalace? Me zan fad'awa mahalicci na? Da wane k'arfin gwiwa zan iya sake kisantarshi? Ta ya zan iya zuwa ma Ayya a haka?" Tana shirin durk'ushewa yayi saurin rik'o damatsenta ya mik'ar da ita tsaye, cikin rarrashi yace "Faduma kiyi hak'uri dan Allah ki saurare ni, su Ayya sun dawo kuma kowane lokaci wani zai iya shigowa nan, dan sun ga motata zasu tabbatar kina cikin gidan nan, dan Allah ki nutsu ki share fuskarki kinji, ni nine zan aureki kuma babu fashi, wallahi ban kawo ki gidan nan da wannan manufar ba, abun ne yafi k'arfina har ya nemi rabani da rayuwata, ki yafe min kinji *orronur*." Cikin kuka tace "Tagur ba zaka gane bane, Ayya tana kula da kowane motsina fiye da yanda take lura da kowane fitar numfashinta, ina shiga gida zata fara kallona daga k'asa har sama, a k'ank'anin lokaci zata fahimci canjin dake baibaiye dani, me zan ce mata idan ta tambaye ni? Na fad'a mata mijin da zan aura ne?" Girgiza kai tayi shi kuma ya juya jin kamar ana tahowa, da sauri ya kalleta yace "Fati wani na tahowa, karki tona mana asiri kinji, ki bari mu fita daga gidan nan sai mu san yanda zamuyi da Ayya." K'wank'wasa k'ofar da akayi ne yasa ta zaro ido ta kalli k'ofar, hannu tasa ta shiga share hawayen gabanta na mugun bugawa, alama ya mata da hannu suka shiga takawa a hankali, d'aga labulen yayi dan k'ofar a bud'e take tun shigowarsu, Aisho ce tsaye tana ganinsu ta saki murmushi ta kalleshi tace "Sannu yaya, mun dawo, wannan ita ce Faduma?" Kallon data ma Faduma yasa ta sunkuyar da kanta tana had'e hawayenta, kama hannunta tayi ta kalleshi tace "Yaya kukan me take? Kaga duk idonta sun kumbura sunyi ja?" Kallon Faduma yayi sai kuma ya had'e yawu da k'yar ya kalli Aisho yace "Am..., ba komai,...kuka kuma?...Wai gida zata tafi, dan na hanata fa take kukan nan." Turo baki tayi ta kalli Faduma tace "Haba dai aunty Fati, bamu ganki ba zaki ce zaki tafi? Kiyi hak'uri kinji mun tsayar dake, zo muje Ayya na jiranmu." Yanda ta jata da sauri yasa Faduma direwa ta tsaya ta k'i gusawa, juyowa tayi ta kalleta ta ga wasu hawaye na silalo mata, zafin da taji ne da tafiyarta yasa ta taisayawa kanta, k'arasowa yayi inda take tsaye yace "Wuce ku shiga ina zuwa yanzu." Girgiza mishi kai tayi alamar a'a, da ido kawai ya mata alamar gargad'i ta wuce kawai, kallon Aisho tayi dake rik'e da hannunta, takawa tayi a hankali kamar mai tsoron taka k'asa saboda k'aya, ganin a haka take buk'atar tafiyar sai yasa Aisho ma binta a hankali suna tafiya har suka shiga cikin falon. Yana ganin shigewarsu ya juyo da sauri ya rufe d'akin, tar ya sauke ido akan kujerar, buga k'eyarshi yayi a jikin bangon yana furzo iska, rufe ido yayi yana sake tunano komai daya faru, sam bai so haka ba, ba yanzu so ba, tabbas yasha shayin amma kamata yayi ace sun sanar dashi komai, Faduma? Ya tambayi kanshi, tabbas abinda ya faru yanzu soyayyarta ya k'ara mishi, sai dai kuma gabanshi fad'uwa yake hankalinshi na tashi, hak'ik'a ya samu gamsuwa a tare da ita da nutsuwa, ya ji fiye da yanda yayi tunani, ya kuma yi mad'aukakin farin ciki daya sameta a yanda dama yake da buk'ata da kuma kyautata mata zato, sai dai bai so karb'ar wannan abun ba a yanzu, ya so ace bayan an d'aura musu aure ne dubbanin mutane sun shaida haka, an kawo masa ita cikin shiri kamar kowace amarya, bayan gabatar da sunna da nafila sannan ya gama ciyar da ita, akan gado mai dajara da kima, a cikin rufaffen d'akin dake zagaye da garkuwar malaikun rahama, bayan ya karanto addu'a sannan ya kai ga shiga wannan k'asaitacciyar gonar. Gashi yanzu akan kujera ya rabata da mutumcinta, a hargitse a gigice a banyyak'e, bud'a ido yayi ya k'arasa kusan kujerar, dole a wanketa, kuma shi zaiyi wannan aikin, dan jini ne mai daraja a gare shi, pant d'inta da bata kula da shi ba akan kujerar ya d'auka, d'akin baccinshi ya wuce dan gyara jikinshi shima. Yana shiga a drowershi ya bud'a a k'asan kayanshi ya aje pant d'in, lashe leb'e yayi yana girgiza kai da sakin murmushi, shi kad'ai yasan kyautar daya tanadar mata a duk sanda ta shigo gidanshi, shi yasan gata da kulawar da zai nuna mata. Cire kayanshi ya shiga yi yana fad'ad'a dariyarshi, shafa sumar kanshi yayi ya furta "Tayi k'ok'ari *jarumata*." Yanda yaje mata da yanda tayi gardama yasa babu sauk'i ko kad'an, amma bata mishi hargagi ba illa hawaye da wani ke bin wani, ko ba komai ta cancanci yabo ta wannan fanni kam, kuma shi da ita Allah ne kad'ai zai raba su. Suna shiga suka same ta zaune kusanta Gomboy ce sai Rahila da a lokacin bata wani san kanta ba, bata yarda ta d'aga kanta ba bare ta had'a ido da kowa, ji take duk wanda ya kalleta yasan me ya faru da ita, yanzun haka ma idon dake kanta haka take ji, duk da tayi sallama cikin disasashiyar muryarta amma sam basu ji ba, Aisho dake k'ok'arin zaunar da ita kan kujera ne ta kalleta ganin ta zauna k'asa, cikin taushin murya tace "Ina wuni." K'afafun Hatimi take kallo daga k'asa tana girgizasu, babu wanda ya amsa kuma bata damu ba, cikin muryar gadara Hatimi ta kalli Gomboy tace "Kin ganta?" Sama da k'asa ta kalli Faduma ta tab'e baki tace "Na ganta Ayya, gata nan wata k'azama da ita." Da sauri ta d'ago kanta ta kalli inda taji maganar, budurwa ce wacce zata iya kiranta da sunan god'iya, dan da ganinta ba yarinya bace, in bata girme ma Tagur ba ba zata rasa zama tsararshi ba, wani abu daya tokare mata mak'oshi ta had'e muk'ut ta sadda kanta k'asa. Tsaki Gomboy tayi tace "Yar talakawa kawai, ai na d'auka dukana zaki zo kiyi." Take Hatimi tace "Wacece ita? Waye ubanta a garin nan da zata yi wannan kuskuren? Ke!" Ta fad'a tana nunata da yatsata, bata d'aga kanta ba bare ta kalli fuskarta, jin haushin hakan yasa ta sake daka mata tsawa tace "Ke! Ba dake nake ba?" Da sauri ta d'aga kanta ta kalli matar, a karon farko data fara sanin kamanninta, a take kuma ta sunkuyar da kanta tana sako hawayen da suka taho mata, saida ta d'an yo k'asa daga kan kujerar sannan tace "Kinga ni ce nan uwar Tagur, sai dai ki sani tun farko naji bana sonki, bana son aurenki dashi saboda baku dace ba, to amma matsalar ita ce irinku dama idan kuka samu yaran masu kud'i ba kwa musu rik'on sakaina kashi, har da jikinku kuna biya malamai dan ku samu biyan buk'atarku, amma kiji nan da kyau, duk abinda kike tak'ama dashi wallahi saina shiga tsakaninki da d'ana, dan bana son ki bana son ganinki tare dashi, kin fahimta?" Da sauri tasa hannu ta fara share hawayenta, zuciyarta bugawa take da sauri sauri, babu wanda zai tab'ata tayi shiru bare kuma iyayenta, amma halin da take ciki da kuma girmamata a matsayin uwar mijin da zata aura, tabbas har yanzu bata janye daga auren Tagur ba, dan tabon daya mata yanzu babu wanda zai iya aurenta ya zauna da ita bai goranta mata ba sama dashi, shiyasa kawai zata rabu da ita ta ci karanta babu babbaka akan ta. Gomboy ce ta k'yasta hannunta tana fad'in "Malama ki tashi ki tafi, mu ma nan da kika gan mu ba k'aunarki muke ba, tun ban ganki ba naji na tsaneki, ya rage naki ki fara aurenshi dan tseratar da mutumcinki, idan kuma saboda dukiya yasa kika sake manne mishi, to shakka babu zamu ja mutumcin iyayenki a tsakiyar titin unguwarku." Aisho da tayi mutuwar tsaye ne ta girgiza kai tace "Haba Ayya, wannan fa bak'uwarku ce, bai kamata ku mata haka ba ko dan mutumcin wanda ya kawota gidan." Dariya Hatimi tayi tace "Mutumci? Ai tunda ya nanik'e ma yarinyar nan na daina ganinsa da mutumci, abu d'aya ne zaiyi ya faranta min na ci gaba da kallonsa kamar yanda nake masa a baya shine ya rabu da wannan bak'ar k'adarar." K'afa d'aya kan d'aya ta d'ora tana tauna shewingum da k'arfi tana k'as k'as k'as tace "In banda rashin sanin ciwon kai da azarb'ab'i da neman gindin zama a dangin miji, jiya daga fad'a miki ana son ganinki a famille d'in shi, yammacin yau saiki wanke k'afa ki biyoshi ku zo, dan mu nuna miki bama buk'atar ganinki muka bar gidan nan, amma dake ke dangin kwad'ayayyi ne kin matsu ki zo kiga me zaki tarar me zaki samu? Zaune kikayi kika jiramu na tsawon awa har da rabi, tirrr dake." Kusanta Aisho ta matso tana fad'in "Tashi Faduma, tashi na rakaki ki koma b'angarenshi kafin ya fito, ban san abinda zasu miki ba kenan da ban jayoki ba." Mik'ewa tayi tana jin k'afafunta sun fara sage mata, k'asanta na k'ara tsananta mata zafi kamar ta kama ruwa da barkono, k'irjinta daya sha matsa yana mata wani zuut zutt zutt, saida ta mik'e tsaye ta fara ganin wani jiri kamar zai kwasheta ya dasa a k'asa, sake jimk'e hannun Aisho tayi ta tsaya cak, saida ta lumshe idonta ta bud'e ta ga waral da kyau sannan ta d'an juya ta kallesu, cikin nutsuwa da ladabi tana wani malalacin murmushi tace "Nagode, nagode da karb'ar da kuka min, hak'ik'a naji dad'i sosai fiye da yanda kuke zato, kuma a yau ne na k'ara tabbatar da gaskiyar mahaifiyata da take ce min, kowane *kare* kukan gidansu yake yi, rashin mutumci da rashin iya girmama bak'o kuka iya, ni kuma godiya tun ban iya magana ba aka lak'aba min ita a bakina na hadda ce." Juyawa tayi suka zasu fita Gomboy ta mik'e ta yo kanta da k'arfi tana fad'in "Ke dakata! Uban wa kike fad'a ma marasa mutumcin? Ni ko Ayya?" Tsayawa tayi ta kuma sare kan cewa dukanta zatayi, amma kafin ta k'araso gareta suka ji muryarshi yace "Karki fara wallahi." Tsayawa tayi tana hararenshi kamar yanda shima yake hararenta da jajayen idonshi da har yanzu basu washe duka ba, dama ba wani jimawa yayi wurin wankan ba dan hankalinshi na kan yar mutane, sannan kuma magriba ta gabato sosai, k'arasowa yayi cikin takon k'arfi yana ci gaba da mata kallon jin haushi, saida ya tsaya gaban Faduma ya sake nuna ta da yatsa yace "Ba wai iya yau ba kawai, ko a mafarkinki karki yarda kiyi kuskuren d'aga hannunki akan *matata*, yin haka wallahi zai zama miki kuskure da zakiyi a rayuwarki mafi muni da saki dana sani, ruwanki ne ki so Zahra ko ki k'ita, ni dai ina sonta kuma mun riga da mun zama d'aya, rabani da ita kamar rabani da numfashi na." Kallon Faduma yayi yace "Muje na kaiki gida tunda abun haka ya zama." Juyawa sukayi suka nufi k'arasa fita daga falon, Hatimi ce tace "Kai Tagur zo nan." Juyowa yayi ya k'arasa kusanta yana kallonta, nuna mishi ciki tayi tace "Wuce d'aki ina son magana da kai, ka bata kud'i ta hau taxi ta koma gida." Girgiza kai yayi yace "Yi hak'uri Ayya ki gafarce ni, daga gidansu na d'aukota na kawota nan, a bisa yarda dani iyayenta suka bani ita na taho da ita, ki jira kad'an na mayar da amanar dana d'auko ta hanyar cika alk'awarin da nayi sai na dawo." Ko da ya fad'a bai tsaya saurarensu ba yayi gaba, suna tsaye anan har suka fita daga gidan suka d'auki hanya, tunda suka d'auki hanya babu wanda yayi magana a cikinsu, banda shashek'ar kukanta da shan majina babu abinda kale ji, sunyi nisa aka fara kiran sallah ya tsaya a wani masallaci yin sallah, fitarshi yasa ta rufe ido ta shiga tunanin wannan al'amarin daya faru da ita yau, ya mata kaca-kaca a cikin gidansu, uwarshi da mahaukaciyar yar uwarshi kuma suna mata wasu maganganun banza, wannan ai shine *ga mari ga tsinka jaka*. Tana cikin tunanin nan taji ya bud'e mota ya shigo, mayar da kallonta tayi kan titi, saida ya kalleta kafin ya tayar suka d'auki hanya, a wani babban shago ya tsaya yace yana zuwa, bata kula shi ba har ya fita tana kallo ya tsallaka titi ya shiga shago, ajiyar zuciya ta sauke ta d'an k'ak'aro murmushin dole, ko ba komai tana son Tagur, da kuma yau a inuwar aure ne babban lamarin nan ya faru tsakaninsu, to shakka babu dalili d'aya ne zai hanata sa boka ya mallake mata shi ita kad'ai shine tsoron Allah, amma tabbas da zata k'ara b'oye abinta ne k'asan a daka ta killace, dan jajirtaccen namiji kamarshi a wannan k'adami abu ne mai wuyar samu. Yanzun ma dai bata ga dawowarshi ba sai bud'e motar taji ya fargar da ita, ledojin hannunshi ya mik'o mata, kawar da kai tayi kamar bata lura ba, murmushi yayi ya shogo da su a hannu sannan ya aje su baya, rufe k'ofar yayi ya kalleta yace "Hushi ake dani har yanzu Fati?" Ajiyar zuciya ya sauke yace "Fatima, ki k'ara hak'uri, zan kai ki gida yanzu amma gidan d'aya Ayyarki, bana jin tsoron asan abinda ya faru tsakaninmu, saboda ina sonki kuma ina son aurenki, tashin hankalina daya da yasa bana son a sani shine, kar su kawo mana tangard'a a tarayyarmu bare tsaiko a cikin aurenmu, hakan ne zaisa nayi iya k'ok'arina naga an d'aura mana auren nan ba tare da wani tasku ba, kinga akwai sauran lokaci hakan zaisa har kiyi istibra'i." Da sauri ta kalleshi saboda fad'uwar da gabanta yayi, kawar da kai tayi tana sauke numfashi kamar tayi gudu, jin ba tace komai ba ya tayar suka d'auki hanya, basu jima ba suka k'arasa k'ofar gidan ya tsaya, kallonta ya sake yi bayan ya kashe motar yace "Kin shirya?" Kallonshi tayi ta kuma d'auke idonta, sunan Ayya Ayya kawai take fad'a a bakinta, wallahi yau saita kasheta ta gane abinda ta aikata, inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, wata ajiyar zuciya ta sauke ta kama murfin zata bud'e, shima bud'ewa yayi suka fita tare ya bud'e baya ya kwashi ledojin ya shige gaba, sallama yayi Ayya ta amsa ta fito da hijab d'inta da carbi a hanu ta gama sallah kenan, gaisawa sukayi sosai ya aje ledojin k'asa yana fad'in su ma sun ce a gaishe su, juyawa yayi ya kalleta ta tsaya a bayanshi tana ta sune kai, sai ta tona masa komai, murmushi ya mata yace "Saida safe ko." Jinjina kai tayi dan kar Ayya ta gane bata amsa mishi ba, fita yayi ita kuma ta duk'a ta d'auki kayan ta nufeta dasu, hakan ya taimaka mata sosai wajen kasa gane asalin tafiyarta, ciki suka shiga Ayya na fad'in "Yaya ziyarar taki ta kasance?" Cike da dubara da son kawar da hankalinta ta aje kayan tana warware lafayarta saboda k'arfin hali tana fad'in "Ayya na gaji sosai, wata k'anwarsa na samu tana gyaran d'akinsu ni kuma na tayata, duk jikina ma ciwo yake." Wani kallon tuhuma ta mata tace "K'anansa nawa ne?" Saida tayi zaune sama kujera tace "Eh to gaskiya bana ce ba, dan akwai wata dana gani kamar dai yayarsa ce, sai guda biyu kuma suma duk mata." Murmushi tayi tace "Bai gabatar miki dasu bane? Amma da alama kamar shi kad'ai ne namiji a gidan ko?" Cikin matse baki ba tare da tayi yanda zata iya ranfota ba tace "Shi kad'ai ne Ayya." Sallah take so tayi amma kuma bata so kai tsaye tace sai tayi wanka sannan tayi, dan a sabonta tana fara gabatar da sallah ne kafin komai, ko daga makaranta ta dawo lokacin sallah yayi saita fara sallah kafin ta cire kayan makarantar, ba kuma zata yarda ta nuna mata ba tayi sallah ba acan, zatayi mamaki har ta sake mata wata tambayar, ita kuma daurewa tayi sosai wajen gyara fuskarta da daita muryarta. Mik'ewa tayi tana "Bara na samu na wanke jikina saboda k'ura." Har zata fita sai kuma tace "Ayya zan iya yin wanka?" D'aga mata kai tayi alamar eh, da kallo ta bita har ta fita tana jinta ta d'ebi ruwa ta shiga ban d'aki, har aka fara kiran sallah isha'i sannan ta fito daga ban d'aki tayi alwala ta shigo d'akin da d'aurin k'irji da hijab d'inta. Ido ta zuba mata tana kallo kamar yau ta fara ganinta, har ta zauna ta d'an shafa man da Ayya ta ware mata tunda aka saka ranarta ta shafa sama sama, mik'ewa tayi dan saka kaya ta fahimci kallon da take mata, gabanta ne ya fara fad'uwa jikinta ya fara wani tsamm tana jin shikenan ta-ta ta k'are, kayan ta d'auka ta saka ba tare data bari hijabin dake kanta ya sauka ba bare ta fahimci tasa wa kanta ruwa na wankan tsarkin da tayi ta shinfid'a sallaya ta sake kallonta, kallon ledojin data shigo dasu tayi tace "Ayya ki duba abinda mahaifiyarsa ta bani." Ba tare data daina binta da kallon nan ba tace "Kafin nan gama sallah zamuyi magana." Tsurewar da tayi yasa taji kamar zawo zai taho mata sai ka taji cikinta ya motsa sosai, cikin rashin gaskiya tace "Lafiya ko Ayya?" Ba alamar wasa tace "Yi sallah." Jinjina kai tayi ta juya tana addu'a a k'asan zuciyarta, haka ta kabarta sallah sam babu nutsuwa tana mai fatan Allah yasa bata gane komai ba kuma ba akan shi zatayi magana ba. Tana idar da sallah ta juyo tana kallonta ta tank'washe k'afafu, ita ma gyara zamanta tayi sosai yanda suke kallon juna, kallon da take mata sam ba zai bata damar yi mata k'arya ba, cikin kakkausan murya tace "Me yake faruwa? Ki fad'a min gaskiya Fatima." Rarraba ido ta shiga yi tana murza wuyanta ta cikin hijab tace "Ba komai Ayya, me kika gani?" Wani sakaran murmushi tayi tace "Tambayata kike me na gani? To bari na fad'a miki abinda na gani watak'ila ki yarda cewa ni uwarki ce." A nutse ta kira sunanta da cewa "Fatima." D'aga ido tayi ta kalleta tace "Na'am Ayya." D'orawa tayi da "Ba haka kika fita daga gidan nan, walwalarki ta canza, karsashinki da kuzarinki sunyi k'asa, sannan kumburarran fuskar kukanki ma ta bayyana haka, Faduma fad'a min me ya faru bayan tafiyarku? Karki sa na fara zarginki a matsayinki na 'yar dana yarda da ita." Fashewa tayi da kuka yasa hijabi ta rufe fuskarta, girgiza kai tayi tace "Har yanzu ban fara tunanin komai a game da kukan ki ba, karki sa na fara mummunan tunani akan ki mana, ki fad'a min me ya faru?" Cikin muryar kuka tace "Kiyi hak'uri Ayya, bansan ta ya zan iya kwatanta miki irin tarban dana samu a gidansu ba." Cikin sauri tace "Sun nuna basu sonki ne?" Da sauri Faduma ta d'ago ta kalleta, wani sayayyan iska ne taji ya ratsa zuciyarta saboda samun mafita, jinjina kai tayi tace "Ayya gaba da gaba fuska da fuska mahaifiyarsa ta fad'a min bata so na, kuma ba da son ranta zai aure ni ba, sun wulak'anta ni tare da cin zarafi na dana iyayena." Wata ajiyar zuciya ta sauke ta dafa kafad'arta tace "A gabanshi suka fad'i haka?" Girgiza kai tayi tace "Da fari baya tare damu, daga baya ne ya shigo sanda yar uwarsa tayi yunk'urin dukana." Jinjina kai tayi tace "Shi kuma me yayi akai?" Kallonta tayi tace "Inhar zai ci gaba da kare min mutumci na kamar yanda yayi yau d'in nan, to Ayya zan iya cewa kisa ranki a inuwa akan lamarina, insha Allahu zai iya k'ok'arinshi akan haka, dan saida ya mata k'wak'waran kashedi kan kiyaye gigin tab'a ni." Murmushi tayi tace "Haka yayi, ya kuma tabbatar namiji ne shi." Dafa kafad'arta tayi tace "Ki kwantar da hankalinki, da sannu zaki ci su da yak'i Faduma, zaki yi galaba akan su da kyawawan halayenki da kyautata musu, mahaifiyarshi kuma zaki siyeta da ladabi da biyayya." Wani kallo ta bi Ayya dashi a ranta ta furta "Lallai kam ya cika namiji, dan ya nuna min haka a zahiri da bad'ini." Kallonta ta sake yi tace "Ayya wajen Ayya nake son lek'awa." Jinjina kai tayi tace "To, bana ce karki jima ba dan in kuka had'u ba kwa rabuwa da wuri, amma dai karki bari taji me ya faru dan kinsan ta ba hak'uri gareta ba musamman al'amarin daya shafeki, duk wanda zai fad'a miki baya sonki to kamar ya tareta ne gaba da gaba yace ya tsani iyayenta da suka rasu, kinga kuwa bata da abokin gaba sama dashi." Murmushi tayi ta mik'e tana jawo mata ledojin tace "Ayya kawo wanda zan kai mata." Juye kayan tayi duka ledojin, ita kanta Faduma saida ta d'an zaro ido, ba atamfa ba shadda ne masu kyan gaske da les wanda ko baka san kud'inshi ba kasan zaiyi tsadar masifa, jaka da takalmi daidai k'afarta har kala uku sai turaruka manya manya wanda wani kwalinshi ma kawai abun kallo ne sai mayuka da sauran kayan kwalliya, babu abinda babu a lefenta shiyasa siyayyar ta bata mamaki, kallonta Ayya tayi tace "Wannan tsaraba ai taki ce ke kad'ai, ni ce zan shafa wannan ko uwar taki?" Ta fad'a tana nuna wani k'aton Pawpaw lotion da man gyaran kai Beckon olives oil dana Carrot d'in shi, dariya tayi tace "Ayya ai zaku iya shafawa dan jikinku yayi kyau ku wa Aba kwalliya." Kallon mamaki ta mata hakan yasa ta saurin bushewa da dariya ta sunkuya ta d'auki wani les mai kalar ruwan powder tace "Ayya bara na kai wa uwata wannan." Tab'e baki tayi tace "Kin manta bata saka les ko kad'an." Da damuwa a fuskarta tace "Kashh! Na manta wallahi, bari na kai mata wannan to." Ta fad'a tana d'aukar shaddar kalar ruwan zuma sai kyalkyali take, ficewa tayi a gidan ta shiga d'aya gidan, Abakar ta samu yana cin abinci, zaune tayi kusan Ayyar tana tambayarta "Autarmu ashe har kin dawo?" Ba wani karsashi a fuskarta tace "Na dawo Ayya." Yanda ta amsa mata yasa ta kallonta tace "Yunwa kike ji?" Kallonta ita ma tayi da mamakin yanda ta fahimta a take, tabbas tana jin yunwa sosai, sai dai bata jin zata iya cin abinci ma cikin farin ciki, k'arfin hali kawai take yi tana taushe abinda ke zuciyarta, amma maganar gaskiya ji take kamar ta k'urma ihu tayi ta kuka kuma ana rarrashinta, sai dai ba zata iya ba ko dan kaucewa kunnuwan iyayenta jin wannan mummunan labari. Saida Abakar ya fita ta bata shaddar, tayi farin ciki sosai da mata godiya wanda ita kuma bata so godiyar ba, d'aki suka koma tana fad'a mata abinda ta fad'a abinda ta samo, bata yarda ta fad'a mata abinda ya faru ba kamar yanda Ayya ta buk'ata, suna tsaka da hira suka ji shigowar Aba, da sauri ta sake lafewa kamar mai bacci, lek'owa yayi yana ganinta yake tambayar wai har tayi bacci ne? Ita ma Herde data iya taya b'era b'ari sai kawai tace eh, cewa yayi ta barta to ta kwana anan saida safe, dad'i taji har ranta dan hakane zai bata damar juyawa son ranta, amma in tana gaban Ayyarta to dole ta kula da duk wani motsinta, dan har yanzu kamar jaririya take mai shan nono, ko cikin bacci ta motsa sai ta samu Ayyarta na kallonta alamar ta rigata farkawa, har sai tayi abinda zatayi ta kwanta sannan ita ma ta kwanta. Gyara kwanciyarta kawai tayi ba jimawa kuma bacci mai nauyi ya d'auketa saboda dama ta saba baccin rana, yau kuma ba tayi ba saboda shirin zuwan gidan daya zama a cikin tarihin rayuwarta. _____________ Ko da ta farka Herde har ta gyara duk wani abu da ake shafa mata a jiki, saida tayi sallah kafin ta zauna ta shafa mata, awa d'aya ta shiga wanka da ruwan d'umi tare da ganyen turare, da taimakon wannan ruwa ta samu ta gasa jikinta dake mata bala'in ciwo tana daurewa ne kawai, saida ta gasa jikinta sannan tayi wanka sosai da ganyen nan kamar wata mai jego, da wani sabon k'arfi ta fito daga ban d'akin tana jin wani irin dad'i a jikinta da jin canji sosai. *Tunda* abun nan ya faru ta canja mishi sosai, ita dai bata sake yarda ko maganar ta had'asu ba, dama ba zuwa yake ba yanzu saboda gyaran da ake mata, sai dai ta wayar Ayya suke waya tunda ba zata ce a'a ba, dan in tace ma a'a za'a tambayeta dalili? Ita kuma tana dashi dalilin amma ba zai fad'u ba, dan haka zata karb'a ta d'ora a kunne tana saurarenshi, haka zaiyi kid'anshi yayi rawarshi har ya kashe ba zai sake jin komai daga bakinta ba bayan gaisuwa, daga um sai um um. Bai ga laifinta ba sai ma tausayinta da yake ji, tana k'ara birgeshi a kowace rana tare da k'ara mata tanadin jiyar da ita dad'i a rayuwarta, a haka har suka sake cinye satinsu shida da kwana biyu. Kwana shida ne ya rage yanzu inda shirye shirye suka kamkama sosai ta kowane b'angare. Kusan yanzu zamanta yafi yawa a gidan Herde, har k'awayenta acan suke suna shirinsu suma, sai dai yanzu bata jin dad'in zaman gidan, ba dan komai ba sai dan hayaniyar daya fara d'auka, ita kuma yanzu ta zama wata iri tafi jin dad'in shiru sai tsargar da yawu idan tayi, sosai take ji da kuma ganin canji a jikinta, amma saita dangana shi da lokacin aurenta dake gabatowa ne, dan haka yanzu ma ko da taga rana ta fito sosai ta fito daga gidan tare da wata k'awarta ta makaranta data zo kawo kud'in ankonta wacce ba wani sabo ne sosai a tsakaninsu ba, kawai dan zata yi aure ne ta rab'eta ita kuma tana buk'atar k'awaye a tare da ita, gidansu ta wuce ita ma ta shigo gida da sallama, a tsakar gidan ta samu Ayya da yayarta da suke uba d'aya suna hira da duba wasu kaya wanda tasan suna da alak'a da bikin nan, gaisheta tayi cike da ladabi ta shige d'aki, kan gado ta wuce ta kwanta inda taji wasu bak'in ma sun shigo wajen Ayyar, sun jima kafin ta ji muryar gwagonta na kiran sunanta da fad'in ta tafi, yawun dake bakinta da kuma wani irin kasala yasa ta jan baki tayi shiru kamar bata ji ba ko wacce bacci ya d'auketa, har saida taji shiru alamar sun tafi. Ayya ce ta shigo tana fad'in "Fati bacci kikayi ne yaya na ta miki sallama baki ji ba?" Tashi zaune tayi tana kama kallabinta dake shirin fad'uwa daga kanta, Kallon juna sukayi sai kuma Ayya ta shiga mamakin yanda tayi musu shiru, ido waje ta kalleta tace "Ke wai ba dake ake magana bane? Me yake damunki wai?" Saukowa tayi daga kan gadon ta fita ta tofar da yawun ta dawo ciki tana fad'in "Ayya yawu ne a bakina shiyasa ban mata magana ba, dan Allah in kina da wani abu ki ban na sa a bakina ko yawun nan sun daina tarar min a baki." Da wani irin k'arfi ta juyo gareta tare da fincikota tana shirin zama kan kujera, wani kallo ta shiga jera mata tiryen tiryen a matuk'ar tsorace, hannu tasa ta dafe k'irjinta da taji yana dokata da k'arfi k'afafunta na rawa alamar zasu kayar da ita, da yatsa ta shiga nuna ta tana son yin magana kuma ta kasa, jin ta kasa cewa komai yasa ta janye rigar Faduma har zuwa cibiyarta, da k'arfi tasa tafin hannu ta danna mararta, ita ma da k'arfin ta buge hannun Ayyar tare da ja baya ta saki wata k'ara. Saida ta fahimci abinda tayi ne sai kuma ta sadda kanta tana kallon mararta da take jin wani zafi tana d'an yarfa hannu da fad'in "Washh, shhhhhh, zafi wallahi." Kamar saukar aradu a kanta taji Ayya tace "Ina! Ban yarda ba." Kallonta tayi sai kuma ta zaunar da ita akan kujerar, durk'usawa tayi gabanta tana rik'e da hannayenta tace "Ke, kin ci abinci ne yanzu?" Yamutsa fuska tayi tace "Ban ci ba Ayya." Da sauri ta mik'e ta k'arasa shiga uwar d'akin, jim kad'an ta fito da wata k'aramar roba da sugar a ciki, ajewa tayi a kid'ime ta nuna Faduma tace "Tashi kiyi fitsari anan." Da wani mamaki ta kalleta duk sai taga kamar ba a hayyacinta take ba, da rashin fahimta tace "Fitsari kuma Ayya? Bana..." Wani d'an banzan mari ta kifa mata a tsawace tana fad'in "Daga yanzu har zuwa lokacin da zan gasgata abinda nake tunani akan ki kija baki ki min shiru." A razane ta dafe kuncinta tana kallonta a tsorace, mik'ewa tayi jiki na b'ari tana kakkarwa ta ja siket d'inta sama ta zare pant d'in jikinta ta tsuguna, duk tana yi ne idonta akan Ayya da ita ma take kallonta kamar zata fad'o da idonta k'asa, da k'yar ta samu ta yunk'uro ya zubo kad'an dan bata jin fitsarin, d'aukar robar Ayya tayi ta k'ura mata ido, cirko cirko sukayi a tsayen nan ita tana kallon robar tana jiran ganin sakamako, ita kuma tana kallon Ayyar da tunanin me take yi? Me kuma yake faruwa da ita? Saida suka minti goma a haka kafin taga Ayyar ta tafi luuuu ta saki robar ta fad'i a k'asa idonta rufe, da azama tayi kanta ta fashe da kuka tana kiran sunanta, jijjiga ta shiga yi tana kiran sunan Ayya Ayya amma sam bata motsawa, a rikice ta mik'e da gudu ta fito dan nemo agaji, sam ta manta da yanda take, haka ta fita a gidan da gudu tana kuka tayi d'aya gidan. Duk.wanda ya ganta a lokacin yasan tabbas da matsala kuma babba, dan Faduma ko zubar da ruwan wanke wanke zatayi da hijab kake ganinta, yau kuma babu kallabi wanda ya fad'i sakamakon marin data sha bare hijab, Herde ta samu da Abakar sai Barka da shigowarshi kenan yana shirin shiga can gidan nasu, ai da gudu suma suka rankayo aka dawo sanda ta fad'a musu abinda ke faruwa. Suna zuwa suka rufa kanta ana ta kiran sunanta, Faduma dake rik'e da hannunta sai murza tafin hannunta take tana kuka, Herde kuma Abakar tasa ya kawo mata ruwa, a hankali tasa hannu ta shafa mata a fuska, jim sukayi suna kallonta, sai kuwa a hankali ta fara kyakyabta ido sai kuma ta bud'esu tana motsa bakinta kamar zatayi magana, akan Herde ta sauke idonta sai kuma ta shiga kallon duka d'akin da mutanen ciki. Sannu suka shiga jera mata ba kamar Faduma dake had'awa da cewa "Ayya me ya same ki kika suma? Har kin tsorata ni wallahi." A hankali ta juya ta kalleta, tuna dalilin sumarta yasa taji da ba bata farfad'o ba, lumshe ido tayi tana so taji ko mafarki ne take, sake bud'ewa tayi akan ta sai taga gata dai a zahiri, rufe ido tayi ta dantse leb'enta na k'asa ta shiga girgiza kai, kamata Herde tayi ta zauna da kyau tana fad'in "Hadizey lafiya? Meya same ki?" Shiru ba tace komai ba har Barka dake sunkuye yace "Ayya lafiya? Ko jiri ne ya kwashe ki?" Herde ce tace "Ba mamaki, halan yunwa kike zama da ita saboda shirye shiryen nan?" Abakar ta kalla tace "Kai je gida a cikin fridge d'ita akwai damammiyar fura ka kawo." Da sauri ya juya ya fita amma saita kasa cewa komai tana kallonsu, tana so tayi magana amma bakinta yayi masifar nauyi, harshenta kamar an d'aureshi da igiyar k'arfe, gaba d'aya jikinta ma bata jin yana motsawa. Faduma ta kalla data kawo hannunta tana sake murzawa tana wasa dashi, k'yar ta dinga mata wani irin kallo mai sa mutum ya ji ya tsargu, dan kallo ne mai ma'anoni dayawa, tambaya da tuhuma tare da fallasa dana sani da kuma tsana had'e da jin cin an ci amana. Ita ma lokaci lokaci ta kan kalli fuskarta sai kuma ta sadda kanta, suna haka har Abakar ya dawo ya mik'awa Herde furar, saida ta k'ara damawa ta k'ara mata ruwa ta bata tasha, juya kai tayi ta d'an girgiza kan ta alamar a'a, da rarrashi Herde tace "Haba ke kuwa sha mana, kisha ko kinji nauyi a cikinki." Sake girgiza kai tayi alamar a'a, kallon Barka tayi tace "Ko ka kira mana taxi mu kaita asibiti?" Da sauri yace "To Ayya." Ya juya zai fita, da hannu tayi alamar ya dawo kar yaje, dawowa yayi suka sake sakata a gaba da tambayar me take so? Ganin dai shirun nata yayi yawa sai ido da take binsu dashi ya fara basu tsoro da d'aga musu hankali, Barka ne yace zai je kasuwa ya d'auko mahaifinsu ya zo, amincewa sukayi dan zasu fi samun kanta idan yana wurin. Ko da ya same shi ya sanar dashi hankalinshi a tashe ya biyoshi suka taho ko kimtsawa baiyi ba, suna zuwa suka samu zama kawai Herde ta gyara mata ta d'ora mata pillow a bayanta, amma har yanzu idonta akan Faduma suke, yana shigowa da sallama Faduma tayi saurin mik'ewa gare shi ta kamo hannayenshi duka biyu tana tofar da yawu a wajen d'akin ta kalleshi tace "Yawwa Aba zo ka gani, Aba Ayya ta." Cikin muryar alhini ya k'arasa shiga d'akin yana fad'in "Me ya same ta ne? Me ya faru?" A tare suka durk'usa gabanta shi yayi irin durk'uson nan na maza ita kuma ta zube gwiwoyinta, a hankali ya zame hannunsa d'aya daga na Faduma ya rik'o hannun Ayya, cikin tattausan murya yace "Diza, kalleni." Kamar wacce ta farka daga doguwar suma haka ta juya kanta ta kalleshi, da k'arfi ta lumshe idonta sai ga hawayen da tun tuni take son yi sun samu fito mata, bakinta har rawa ya shiga yi da k'arfi ta fashe da wani kuka mai cin ran da tab'a zuciyar mai sauraro, d'aya hannun yasa ya rik'o duka nata hannayen cikin tashin hankali yana fad'in "Subhanallah Diza, kuka kuma ke da kanki? Me ye wannan ya kawo miki wannan tarnak'in da har kika kasa maganceshi da fasaharki? Wane irin k'unci ne wannan da har ya saki zubar da hawaye a madadin nutsuwa da kuma addu'a? Haba Diza ban san ki da haka ba, a iya zamana dake na sanki mace mai hak'uri da juriya da kuma shawo kan matsalolinta, fad'a min yanzu me ya faru haka?" Faduma da ita ma take hawayen ta sake dafa kafad'arta cikin rarrashi tace "Dan Allah Ayya ki fad'a mana me yake damunki? Ayya ke ce fa kike fad'a min juriya akan komai, ke ce kika koyar dani idan da hali na dinga maganin matsalolina musamman wanda suka shafeni ba tare dana tarda hankalin wanda nasan zai fini damuwa ya tashi ba, dubi yanda kika tayar mana da hankali Ayya, dubi Abana hankalinsa duk ya tashi." Shafa hannunta yayi wanda ke kan kafad'arta yace "Yi hak'uri kinji Fadun Aba, zata fad'a mana yanzu, ko ma menene na tabbata yafi k'arfin tunaninta ne." Sake kallon Ayya yayi data fara rage jiniyar kukanta yace "Ina jinki fad'a min, ko zamu keb'e ne?" Jin haka yasa Herde da Abakar da kuma Barka mik'ewa zasu fita, Faduma ma mik'ewa tayi dan inhar su zasu tashi dole ita ma ta bisu, da sauri ta kallesu cikin fizgo magana daga bakinta tace "Kkku...zauna, dan Allah." Kallonta sukayi duk suka zauna har da Faduma dake kamar zata koma mata a ciki, dan rabin k'afafunta ma akan na Ayyar suke, kallon Aba tayi tana hawaye tace "Hankalinka zai iya d'auka? Zaka iya hak'uri da k'addararka? Zaka iya jurar saurara? Zaka iya ci gaba da numfashi idan kaji tashin hankalin da ko a tsammani baka tab'a kawo shi ba?" A rikice duk suka kalleta da mamaki, ba kamar Faduma da gabanta ya yanke ya fad'i, sai take tunani to ko dai abun ya alak'antu da ita ne? Dan tunda tace yawu a bakinta tashin hankalin nan ya fara, Aba ne mamakin ne sosai a fuskarshi, sai kuma yayi gaggawar yin murmushin yace "Duk tsananin tashin hankali idan har ina da sauran numfashi ba zai kar ni ba, duk k'arfin zuwan k'addarata zanyi k'ok'ari na rok'i Allah sassauci ta zo min a sauk'ak'e, Diza duk mumuni baya tab'a rabuwa da jarabawa, idan kuwa mumuni ya wayi gari ba'a jarabtarshi to ya binciki imaninshi, annabawa ma an jarabcesu da kalar tasu jarabawar, dubi babanmu annabi Adam tashi kalar jarabawar, aljanna yake amma aka fito dashi sakamakon yin abinda ubangiji yace kar ma suje kusa dashi bare su ci, amma a k'arshe sun je kuma suka ci, dalilin haka aka fito dasu yana addu'a... _乇亘賳丕 馗賱賲賳丕 兀賳賮爻賳丕 賵廿賳 賱賲 鬲睾賮乇 賱賳丕 賵鬲乇丨賲賳丕 賱賳賰賵賳賳 賲賳 丕賱禺丕爻乇賷賳_ "Sannan ki dubi babanmu annabi Nuhu ma, shekara d'ari tara da hamsin yayi yana da'awa amma d'ansa da matarsa haka suka mutu a kafirai, sannan gaba d'aya mabiyan daya samu ma a wata fad'a ta malamai suna cewa mutane tamanin ne, shima a k'arshe Allah ya mik'awa lamarinsa har yana addu'a.. _乇亘賷 兀睾賮乇 賱賷 賵賱賵丕賱丿賷 賵賱賲賳 丿禺賱 亘賷鬲賷 賲丐賲賳丕賸 賵賱賱賲丐賲賳賷賳 賵丕賱賲丐賲賳丕鬲 賵賱丕鬲夭丿 丕賱馗丕賱賲賷賳 廿賱丕 鬲亘丕乇丕_ "Dubi annabi Yusuf, yana d'aya daga cikin annabawan da suka fi kowane shan wahala, kuma shan wahalarsa da jarabawarsa ta fara ne tun daga cikin gidansu akan yan uwanshi, tun yana da k'uruciya yake fuskantar abubuwa da dama har zuwa girmanshi, duk da k'alubalen daya fuskanta sabubba ne na zuwa matakin da yan uwanshi suka guje mishi, amma shima Allah ya nufa da lamarinshi... _賮丕胤乇 丕賱爻賲賵丕鬲 賵丕賱兀乇囟 兀賳鬲 賵賱賷賷 賮賷 丕賱丿賳賷丕 賵丕賱丌禺乇丞 鬲賵賮賳賷 賲爻賱賲丕" 賵兀賱丨賯賳賷 亘丕賱氐丕賱丨賷賳_ "Dubi annabi Ayyub irin jarabawar daya gani a rayuwarsa, 'yayansa da matansa duk suka gujeshi saboda ciwon da Allah ya jarabe shi dashi, babu mai zuwa inda yake, shima ga Allah kawai ya kai kukansa.. _乇亘賷 兀賳賶 賲爻賳賷 丕賱囟乇 賵兀賳鬲 兀乇丨賲 丕賱乇丕丨賲賷賳_ "Kalli annabi Yunus, babu jarabawar da za'a yi wa d'an adam da zata fi wacce Allah ya mishi, kifi aka umarta daya had'eshi, bala'i na zafin cikin kifi, duhun cikinshi da duhun ruwa, ba abinci ba ruwa babu iska mai kyau, kuma a haka ubangiji yace ba dan ya tuna dani ba a wannan lokacin, to hak'ik'a daya dawwama a cikin cikin kifin nan har zuwa tashin k'iyama, amma addua'rshi ta kub'utar dashi da yace... _賱丕 廿賱賴 廿賱丕 兀賳鬲 爻亘丨丕賳賰 廿賳賷 賰賳鬲 賲賳 丕賱馗丕賱賲賷賳_ Ajiyar zuciya ya sauke yace "Addua'r da zanyi anan bai wuce nace _乇亘賳丕 賵賱丕 鬲丨賲賱賳丕 賲丕 賱丕 胤丕 賯丞 賱賳丕 亘賴貙 賵丕 毓賮 毓賳丕 賵 丕 睾賮乇 賱賳丕 賵丕 乇丨賲賳丕 兀賳鬲 賲賵 賱賳丕 賮丕 賳氐乇賳丕 毓賱賶 丕賱賯賵賲 丕賱賰賮乇賷賳 (286)_ _"Ya Allah karka d'ora mana abinda ba zamu iya ba, kai mana affuwa, ka gafarta mana, ka jik'anmu, kai ne majib'incimu, ka taimakemu akan mutane kafirai_, shine kawai zanyi fata, kuma dama Allah yace.. (285) _賱丕 賷賰賱賮 丌賱賱賴 賳賮爻丕 丕賱丕 賵爻毓賴丕._ _"Allah baya d'orawa rai abinda yafi k'arfinta."_ Sakin hannunta yayi yace "Ina jinki fad'a min?" D'aki duk yayi sanyi babu mai motsin kirki, sai Faduma dake ta gyad'a kai sanda yake magana, cikin zubo da hawayen data kasa tsayar dasu ta kalli duk wanda ke cikin d'akin, ganin duk mutane ne da suke da kusanci da Faduma fiye da yanda take da da ita yasa bata b'oye ba ko kun nauyinsu, cikin rawar murya ta kalleshi sosai tace "... *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 17:12 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _23_ "Faduma, Faduma ciki ne da ita." Herde da Barka ne sukayi nasarar fad'in "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un." Saida Herde ta maimaita haka har sau uku, zabura tayi tana dafe k'irjinta taja baya daga kusan Ayyar, zaro ido tayi tana kallon Aba tana girgiza kai amma ta kasa cewa komai, kallonta Aba yayi sai kuma ya kalli Ayya yace "Diza, me kike fad'a ne haka?" Kallon inda Herde ke zaune tayi ta jinjina mishi kai tace "Na sani, kuma gaskiya ce na fad'a muku, tabbas Faduma ciki ne da ita." Da sauri ya sunkuyar da kanshi ya dafe gaban goshinshi yana furta " _廿賳丕 賱賱賴 賵廿賳丕 廿賱賷賴 乇丕噩毓賵賳貙 賱丕 廿賱賴 廿賱丕 兀賳鬲 爻亘丨丕賳賰 廿賳賷 賰賳鬲 賲賳 丕賱馗丕賱賲賷賳貙 丨爻亘賳丕 丕賱賱賴 賵 賳毓賲 丕賱賵賰賷賱._" Bai sake cewa komai ba daga haka ya mik'e ya bar d'akin, da kallon tsoro Faduma ta bishi sai kuma ta kalli Ayya, cikin kuka tace "Ayya wane irin ciki kuma? Ki gafarce ni ba k'aryata ki nake ba, amma wallahi bana da wani ciki." Girgiza mata kai kawai tayi ta shigo k'ok'arin tashi tsaye dan duk jikinta babu k'wari, da sauri Herde ta kamata ta mik'e ta shige uwar d'aki ita ma, saida ta ga shigewarta ta juyo da sauri gurin Herde ta rarrafa ta kama k'afafunta cikin kuka da tashin hankali tace "Ayya, Ayya ki fad'a musu bana da ciki, Ayya wane irin ciki kuma gareni? Ba haka bane kinji." Barka ma da jikinshi yayi sanyi sosai ne ya rasa abun yi fita yayi Abakar ya rufa masa baya, dafa kanta tayi sai dai ta kasa furta kalma ko d'aya saboda tsabar mamaki, bayan mamakin kuma tausayin mahaifiyarta take sosai, wacce ke wani tanadi da buri akan 'yarta k'waya d'aya tak ta ci shi, kulawa ta gidan duniya babu wanda bata mata ba, to ya haka ta faru? Lallai jarabawa ce daga ubangiji, kuma dole su dage da addu'a da rok'on Allah ya basu k'arfin cinye jarabawar nan. Ba tace da ita komai ba har taji bacci na neman d'aukarta daga nan zaune, d'auke kanta tayi daga k'afarta data d'ora ta mik'e, da kallo Faduma ta bita wacce baccin bai tafi ko ina ba dama, har ta fita a d'akin ba ta juyo ba? sai kawai ta fashe da sabon kuka duba da yanda duk suka watse suka barta ita d'aya, babu wanda yace mata komai, hakan na nufin inhar cikin ne da ita abinda zai faru da ita kenan? Zasu juya mata baya ne? Hak'ik'a tasan tayi aikata kuskure, ta kuma cancanci wannan hukuncin, sai dai shine hukunci mafi girma da zasu iya mata ta horu matuk'ar horuwa, dan zuciyarta ma zata jigata sosai. Kaf wunin haka ya zo ma dukaninsu, Aba bai sake zuwa unguwar ba ma bare ya shigo gidan, Ayya tana d'aki ba ci ba sha ta rasa me ke mata dad'i ma, alwala kawai take fitowa ta d'ora ta koma ciki, Faduma na falon zaune har tayi kukan ta gode Allah, babu wanda ya sake kulawa da tsiyarta har dare, daren ma sai fiye da k'arfe goma Aba ya shigo gidan. Lokacin tana zaune kan takalminta a k'ofar d'akin shi dama take dakon jira, amma yanda ya shigo babu sallama da kuma sanyin jiki kamar wani marar lafiya yasa ta kasa tab'uka komai sai kallonshi da ido har ya bud'a d'akinshi ya shige. Kalli ne ya fito daga d'akin wanda Ayyarsa ta fad'a masa komai, yanzu haka abinci ya kawowa Ayyar da k'yar ya lallab'ata ta ci, fitowa yayi ya kalli Faduma dake zaune k'asa yace "Fati ki je ki ci abinci ke ma." Yana fad'a ya fita a gidan wanda hakan yasa ta fashewa da siririn kuka, yanda a da suke kulawa da lamarinta da fifita ta da shagwab'ata yanzu ba haka ba ko ta ce yau, tana kukan ta ji motsi a k'ofar d'akin Aba, da sauri ta juya sai suka had'a ido duk da akwai duhun dare, da hannu kawai ya mata alamar ta zo. Wani sanyi ne ya ratsata da sauri ta mik'e jikinta na rawa ta nufe shi, tana shiga d'akin da sallama ta zauna k'asa kusan k'afafunshi yana zaune kan kujera ya jingina a jikin bayan kujerar kanshi sama, shiru d'akin ya d'auka kamar babu wanda zaiyi magana, a hankali ya d'ago ya sauke kallonshi kanta, saida ya d'ora tsintsiyar hannayenshi kan cinyarshi kafin cikin wata irin muryar alhini da jimami yace "Waye uban abinda ke cikinki?" Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Ta fad'a a zuciyarta tana d'agowa da sauri ta kalleshi, wai da gaske suke ciki ne da ita? Dama abinda zai tambaya kenan? Ta d'auka rarrashinta ne zaiyi kamar yanda ya saba, ta d'auka kukawarsa ce zai bata har ta samu nutsuwa ta dawo jikinta! Yawu ta had'e tare da yin k'asa da kanta, me za tace? Me zata fad'a masa? Tace da wanda zata aura ne? Tayi gaggawa kenan? Lumshe ido tayi hawaye masu zafi suka bi kuncinta, amon muryarshi ta sake ji yana fad'in "Ke nake sauraro?" Bata d'aga kai ba sai ma hannu da tasa a gaban goshi tana murzawa, kamar ta kira mutuwa kuma ta zo a wannan lokacin, da zai fi mata sauk'i akan amsar da zata bawa mahaifinta, ganin bata da niyyar amsa mishi ne yasa shi sake cewa "Har yanzu tausar zuciyata nake da hak'urk'urtar da kai na a kan abinda take raya min na miki, karki sake kaini bango, karki kaini mak'ura, tun muna mu biyu ki fad'a min waye uban cikin dake jikinki?" Yanda yayi maganar a tausashe ne a zahiri, amma a cikin amon muryar akwai wasu sautika masu tsoratarwa a game da sautin, dan haka ta sake sadda kanta k'asa cike da kunya tace "S..hhhi...ne." Da sauri ya rintse idonshi, saida ya dantse leb'enshi na k'asa yace "Gaggawa ko? Gaggawa ko?" Jinjina kai yayi ya bud'a idonshi ya kalleta yace "Tashi kije, da sassafe ki shirya zamu je mu sanar da iyayenshi abinda ke faruwa, tunda dai kinsan a musulunce ba'a aure da ciki, saiya jira idan kika haihu sai a d'aura ko can gidansa ne saiki shayar da abinda kika haifa." Kunya! Nadama! K'yamar kai duk sai ta ji sun baibaiyeta, yanda bai mata fad'a ba ya nuna sun yarda da ita ne kuma sunyi mamakin abun daga gareta, yanda bai nuna mata b'acin rai ba ya nuna kamar babu abinda zai iya yin magana akan shi ne, idan ta b'angaren addini ne yasan tana da sani daidai gwargwado da zai sa ta kwancewa hanya, idan a zamanancen ne baya jin zata iya ballagazar da kanta haka, idan maganar tsaro da saka ido ake baya jin a layin na su ko yace gaba da baya na unguwarsu akwai yarinyar dake samun wannan tsaron, ko da 'yar wani babban k'usa a gwamnati baya jin ya kaisu ba wa 'yarsu matakan tsaro. Haka ta mik'e ta fita a d'akin ta koma na su, har yanzu Ayya ta k'i yarda ta kalleta, yanzu ma tana d'aki kwance akan gado, shiga tayi ta mata saida safe amma bata ko kalli inda take ba, haka ta dawo ta kwanta akan kujera ko katifar fa bata iya shinfid'awa ba saboda bata jin ma zatayi baccin. ______________ Washe gari sun shirya tsaf dan tafiya, Hadizey ta zuba musu ido kawai, har yanzu bata iya magana sai kallo, yana gaba tana baya sai sinne kai take tana kallon k'eyarshi, daga shi har Ayya babu wanda yace mata wani abu, babu mai son ko da kallonta bare su mata magana, har ya fita k'ofar gidan suka had'e da Herde da kwanon abinci, daga ciki ya koma ta gaishe shi ya amsa a dak'ile, kallon mamaki ta musu tace "Ina zaku je haka yanzu Aban Fadu?" Ba tare daya kalleta ba fuska a had'e yace "Gidansu uban abinda ke cikinta." Daga Herde har Faduma kallonshi sukayi, gyara rik'on kwanon tayi tace "Ban gane ba? Me zaku je kuyi?" A hassale ya nuna ta da yatsa yace "Ke dubi! Fita a idona wallahi, karki k'ara b'ata min rai kinji." K'wafa yayi tare da nufa zai sake fita, ita kam dama sun saba ba tsoron hargaginshi take ba, tafi Hadizey sanin mijinta kam dan ita tasan zafinshi tasan sanyinshi, Hadizey kuma saboda mai sanyi ce shiyasa sanyinshi tafi sani, shiyasa ko baccin arzik'i ba tayi ba tana tunanin abinda ke faruwa a gidan, dan tasan in dai zafi zaiyi to Faduma zata shiga tara ne ba uku ba, hakan yasa yanzu ma tayi sammakon zuwa duba su. Kawar da kai tayi ta tab'e baki tace "Allah ya baka hak'uri, daga tambaya." Saida ya wuce ta gabanta yace "Bana so to." Da kallo ta bishi tace "To ka jirani sai na zo mu tafi tare, dama Kalli na nan ta shigo sai ya kaimu ai da motarsa." Juyowa yayi da wani kallo yace "Kije kiyi me? Gayyatar biki ce zamu je ko me? Ya kike neman hawa min kai ne da safiya yanzu?" Had'e fuska tayi ita ma tace "Kayi hak'uri, amma dan Allah karka tafi da yarinyar nan ita kad'ai, ka bari na tafi tare da ita mana." Hayayyak'owa yayi tare da nuna mata hannu kamar zai rufeta da duka yana fad'in "Ke wall..." Bata bashi damar k'arasawa ba tace "To ka tafi kai kad'ai mana ita ka barta." "Saboda a gareni cikin yake? Kina ganin hankali zai d'auka naje kawai na fad'a musu tana can gida da ciki, ba gwaji na likitoci haka kuma babu yarinya? Mtssss! Baki da hankali Her." Sakar mishi murmushi tayi saboda sunan daya kirata dashi tare da cewa "To in hakane muje na raka ka, kaga ko tabbatar musu za ayi ai sai mace tayi ko, amma kai zaka iya ne?" Jim ya d'anyi kamar maganar ta shige shi, juyawa yayi zai fita yace "Muje." Da farin ciki ta juya ta kalli Faduma tace "Kuje bari na kaiwa Hadizey wannan." A hankali ta fita a gidan da mamakin yanda har yanzu taji Aba bai kama sunanta a bakinshi ba, wanda baya magana d'aya biyu ta uku bai saka sunanta ba, a k'ofar gidan suka tsaya gaisawa da Kalli daya dawo daga tafiya daren jiya, bai san me ke faruwa ba shi dai sun gaisa kuma Herde tace ya zo ya kaisu, yayi mamaki kuma har suka d'auki hanya yana mamakin yanda zasu tafi gidansu wanda zai auri Fati, sai dai jikinshi ya bashi ba lafiya ba kawai, har suka isa babu wanda yayi magana, a k'ofar gidan suka tsaya duk suka fito a k'afa, ganin Faduma yasa mai gadin bud'e musu k'ofa dan ya tuna ita ce wacce Tagur ya zo da ita ranar, saida ya mayar da k'ofar ya rufe ya shiga ciki dan yi musu iso, jim kad'an ya dawo cikin girmamawa yana fad'in "Alhaji da kanshi yace na raka ku zuwa masaukin bak'inshi." Nuna musu hanyar da zata sada shi da can yayi yace "Muje." Raka bayanshi sukayi da tafiya kamar wad'anda k'wai ya fashewa a ciki, har ya bud'e k'ofar da yake yana shiga ya share wuri ya goge, k'ofar falon ma ya bud'e musu suka shiga da sallama duk da sun tabbatar babu kowa. Aba da Herde kusan juna suka zauna akan kujera, sai Kalli da Faduma da suka zauna k'asa kusan k'afafunsu, babu wanda ya samu damar wani k'arewa d'akin kallo bare ka kula da tarin dukiyar dake ciki, dan kowa zuciyarshi a cunkushe take, kansu duk na kallon k'asa suka ji bud'e k'ofar da sallama, Faduma ce kawai bata d'aga ba amma dukansu sun kallesu sanda suke shigowa, Alhaji ne gaba sai Tagur da zumud'in ance wai Faduma da iyayenta ne suka zo yasa shi tasowa daga baccin fa yake, dan ya jima yana son ganinta tun ranar da abun nan ya faru bai sake ganinta da ido ba, Hatimi na baya da Gomboy da kula Aisho suna d'auke da farantai na ruwa da lemo da kayan marmari, wuri iyayen suka samu suka zauna cikin gadara da baza izzarsu, Aisho kawai ta iya binsu da ina kwana wacce ita ma ake maganar aurenta yanzu da d'an yayan mahaifinsu Aji wanda aboki ne ga Tagur sosai kuma d'an uwa, amsa mata sukayi da jin dad'i, sun mik'e zasu fita Hatimi tace "Ku zauna ba sai kun fita ba, ai alhalin gidan nan ne ku." Cike da jin dad'i Gomboy ta haye kan kujera daf da Hatimi suna kallonsu da k'yama, sai lokacin suka samu damar gaisawa, Tagur dai idonshi na kan Faduma yana so ta d'ago, sai dai tunda taji gabanta ya shiga fad'uwa da kuma k'amshin rexona da taji ya tabbatar mata yana wurin, kunya take ji sosai da sosai, ji take kamar k'asa ta tsage ta fad'a ciki, ita fa har yanzu Ba a tabbatar tana da ciki ba, shine za'a mata wannan tonon asirin haka? sake kare fuskar ta tayi da hijab ta yanda babu mai iya kallon fuskarta. Cike da haiba Alhaji yace "Aban Faduma sai ga ku yanzu da safe ina shirin fita, Allah yasa dai lafiya ko?" Ba tare daya kalli fuskarshi ba yace "Eh to, lafiya ba lafiya." Had'e fatar goshinsu sukayi da mamaki ya d'ora da "Subhanallah, lafiya ko? Wani abu ne ya faru?" Ajiyar zuciya ya sauke kanshi k'asa yace "Jiya nima bayan fita ta daga gida naje kasuwa, ba jimawa sai ga yayan ita Faduma Barka ya same ni yake fad'a min wai na taho gida da sauri babu lafiya, hankali a tashe na biyoshi muka taho, ko da muka zo mun samu mahaifiyarshi data suma ta dawo sai dai babu magana duk bata cikin hayyacinta, da fari anyi tunanin kaita asibiti sai kuma ta nuna a'a, to shine dai muka sakata gaba ta fad'a mana abinda ya faru." Alhaji da Aisho ne ke ta faman fad'in inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, asha asha! Sai Gomboy da Hatimi dake ta yamutsa fuska suna hararenshi, ajiyar zuciya ya sake saukewa yace "Alhaji ka ganta nan dai zaune Faduma ciki ne da ita." Wani salati Hatimi ta rangad'a tana fad'in "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, la'ilaha illallah, Muhammad rasulullah (S.A.W), ciki?" Ta fad'a tana dafe k'irji, har Kalli a lokacin ne ya sani shima sai yayi mutuwar zaune, da wani uban firgici Tagur ya kalli Faduma ya shiga rarraba ido, ciki? Faduma? Da wani gudun bala'i yaji jinin jikinshi ya shiga artabu yana rige-rigen safa da marwa, Alhaji ma d'agowa yayi daga jikin kujerar yana gyara babbar rigarshi yace "Ciki kuma malam Moliya? Kamar ya? Faduma?" Shiru sukayi babu wanda yace komai hakan yasa shi cewa "To wa ya mata cikin?" Cikin wata sanyayyar murya Aba ya kalli Faduma dake kusan k'afafun Herde yace "Fad'a musu ke." Wani sabon fad'uwar gaban taji har saida yafi muryar mahaifinta dukanta, ga kuma sunan ke daya kirata dashi, dama tuni hawaye take dan sautin baya fitowa ne, amma yanzu saita fashe da kuka ta kasa yin komai, duk daddab'a bayanta da Herde ke yi bata saurari hakan ba, girgiza kai Aba yayi ya kallesu cikin sanyin jiki yace "Dana tambayeta cewa tayi shine." Yanda ya d'an nuna Tagur yasa su juyawa inda yake suka zuba mishi ido, da k'arfi Hatimi tace "Tagur, kai dai?" Alhaji ma gaban kujerar ya matso kamar zai kifo daga kanta yana kallonshi yace "Da gaske ne abinda suka fad'a?" A tsorace ya kalleshi ya shiga rarraba mishi ido, juyawa yayi ya kalleta a hankali ya furta "Faduma." K'in d'agowa tayi bare su had'a ido, k'ureta yayi da ido yana so ta kalli cikin idonshi kafin ya bayar da amsa, ranshi ne ya b'ace a haukace ya kifa mishi marin daya sa jini gabcewa ta hancinshi. Da sauri kowa ya kalleshi, jinin da suka gani take a hancinshi ne yasa Kalli da Aba saurin mik'ewa Aba na fad'in "Subhanallah Alhaji, kar ka dake shi mana haba." Suna daf da kai wa ga Tagur zasu kama shi ya musu wata tsawar data saka su tsayawa suna kallonshi sanda ya furta "Karku tab'a min yaro." Hatimi ma mik'ewa tayi ta nuna su da hannu tana fad'in "Matsalar had'a hanya da matsiyatan nan kenan, shikenan daga k'ulla alak'a daku abisa larura, sai ku wani zo da banzar tatsuniyarku wai ya mata ciki." A hassale Alhaji ya juya kanta da k'arfi yace "Ke! Rufe min bakin ki nan." Juyawa yayi ga Tagur da kamar ba shi aka daka ba idonshi har sunyi jawur, har yanzu Faduma yake kallo wacce ta sake fashewa da kuka sanda taji an mare shi, har cikinta saida taji ya yamutsa da k'arfi, da k'arfi ya shak'o wuyan rigarshi da hannaye biyu ya mik'ar dashi tsaye, kamar wani mahaukacin zaki ya shiga fad'in "Yanzu Tagur lalacewarka har ta kai haka? Da mutumcina da girmana a gari amma zaka nemi zubar min dasu a lokaci d'aya? Me ya kaika tab'a musu 'ya? Ka manta kwana biyar ne suka rage a d'aura aurenku? Ka manta da k'ok'arin da nake ta yi akan karatunka k'asar waje ne? Shine zaka min haka?" Da sauri Hatimi ta matso kusansu tana kallonshi tana kuka ganin yanda ya shak'e mata shi tace "Dan Allah kayi hak'uri Alhaji ka sake shi, ai har yanzu bai amsa cewa nashi bane cikin, kasan fa talakawan nan matsala ne dasu, ta yiwu 'yarsu yar yawon tsiya ce, ta d'auko shine zata d'orawa yaranmu, kai fa kafi kowa sanin d'anka Tagur, sangartarshi da holewar rayuwarshi bai kai shi ga neman mata ba, sai kuma waccen k'azamar?" Ta fad'a tana hararen Faduma, karaf Gomboy tace "Hakane Aba, saurari abinda Ayya ta fad'a, wallahi nasan sharri suke mishi saboda sun ga d'an gidan masu dukiya ne, idan ma gaske ne tana da ciki ina shaidar likita data tabbatar da haka? Kawai sai a zo da yarinya gaba d'aya, idan gaskiya ne a sameku a asibiti mana." Tunda ta fara maganar suke kallonta, duk da Kalli baya da zafi amma yana ji ba dan kar ya taka doka ba da saiya mareta, Aisho ce tayi saurin kallonta tace "Aunty Gomboy waya saka bakinki a maganar manya?" Kallonsu Aba tayi da yayi kasak'e yana kallonta tace "Dan Allah kuyi hak'uri." Sama da k'asa Herde ta harareta taja tsaki tace "Ke kika sake saka mana baki a magana saina daddakaki a gurin nan." Sakin rigarshi Alhaji yayi shi da Hatimi da duk sauran suka zuba mishi ido, Alhaji ne yace "Fad'a min gaskiya Tagur, cikin dake jikinta naka ne?" Tsuru ya masa da ido, kalamanshi na baya ne suka dinga dawo mishi a k'walwa, a gaskiya ta kowace siga ya duba ya tab'a mutumcin mahaifinshi sosai, amma kuma ai shine uban abinda ke cikinta. Cikin lallami Hatimi ta marairaice tace "Tagur dan albarka ai nasan ba kai bane ko? Ni na sani dama kai ba d'an iska bane, wallahi ina alfahari da kai ta wannan b'angaren, karka mata irin iko da kimar mahaifinka, taya zaka yarda ka b'arar mishi dasu lokaci d'aya? Ka tuna da Husna da iyayenta suma masu mutumci, dukanmu mun yarda da kai mun yarda ba zaka iya aikata abinda suka zo mana dashi ba, ka fad'awa mahaifinka gaskiya kaji ko, kar kaji tsoro." Kallonta yayi yace "Ke ki barshi yayi magana da bakinshi, wallahi a dalilinka siyasata ba zata lalace ba Tagur, idan har gaske kai ne mai cikin nan ko, to shakka babu sai nai maka yankan rago, da ba zan iya kallonka da abun kunyar nan daka ja min ba." A firgice ya kalleshi sai kuma ya juya inda Faduma take zaune, da k'arfi yasa hannu ya juyo da hab'arshi yana fad'in "K'anwar uwarka ce da sai ka kalleta, kalle ni nan ka fad'a min gaskiya." Da sauri kamar sub'utar baki yace "A'a." Har Faduma da kanta ke duk'e saida ta d'ago da sauri, cak ta dakata da kukanta tana kallonshi, su Aba ma shi suke kallo kallon rashin fahimta, da murna Hatimi tace "Uhum! Ka gani ko? Na fad'a maka ai dama ba nashi bane." Kallon Aba tayi da hararan Faduma tace "Dan haka sai ku tashi ku tafi ko, idan kuna buk'atar kud'i ko wani abu ku zo kanku tsaye kuyi bara a baku, amma ba ku biyo ta wata hanya ba." A zafafe Herde tace "Dakata malama, mun yarda bamu da kud'i kamar naku, amma mun yarda mun fiku watacciyar zuciya da arzik'in imani, tak'amarki wannan dukiyar da babu wanda yasan ta yanda aka tarata? To ki sani wallahi zata k'are, tunda duk kud'inku baku kai k'aruna ba." A hankali Aba ya kalleta yace"Her, karna sake jin bakinki a wurin nan indai ni ne mijinki, kin fahimta?" Saida ta sunkuyar da kai tace "Na gane Aban Fadu, kayi hak'uri." Baya taja shi kuma ya kalli Tagur yace "D'ana, me kake nufi da a'a da ka ce?" Kallonshi yayi sai kuma ya ga duk iyayenshi sun zuba mishi ido, bakinshi na rawa cikin muryar kuka yace " *Bbb..a, na...wa bane*." Da sauri ta taso ta zo gabanshi ta tsaya tana kallon cikin idonshi, da d'umbin mamaki cikin dakusashiyar murya tace "Me kake fad'a ne haka Tagur? Ba naka bane ba fa kake cewa? Ka manta ne?" Sunkuyar da kanshi yayi daga kallonta ya had'e yawu, girgiza mata kai yayi yace "Faduma ba zan iya ba wa iyayena kunya ba, ba zan ruguza yardarsu akai na ba, ba zan iya lalata makomar siyasar mahaifina ba, kiyi hak'uri, amma ke ma kinsan gaskiya na fad'a." Da k'arfi ta d'aga murya tace "Miye gaskiyar Tagur? Kenan ka zab'i k..." Tureta Hatimi tayi tana fad'in "Dallah can malama, yace ba nashi bane ba shikenan ba magana ta wuce? So kike da k'arfi sai kin sa ya amsa nashi ne? To bari kiji wallahi tausayin halin da kuke ciki ne kawai zai hana ni makaku a kotu, amma ba dan haka ba da sai kin amsa kiran kuliya, kuma sai an miki bulala tamanin na k'azafin zina da kika masa, yanzu ki tarkata min wannan ku fitar mana a gida, har auren ma *an fasa shi*." Da sauri Tagur yace "Amma Ayya ai n.." Alhaji yayi saurin damk'ar hannun yace "Yi mun shiru." Kallon fuskar Aba yayi daya zama kamar mutum-mutumi yace "Malam Moliya magana ta gaskiya ban ji dad'in abinda kuka yi ba, ku sani na amince Tagur ya auri yarinyar nan ne saboda yace min yana son ta, amma ba dan haka ba wannan yarinyar ajinta bai kai ta had'a kafad'a da yarona ba, daga baku yar dama shikenan sai ku shigo da maganar cin zarafi da k'age kawai dan a lalata mana suna, to ni fa dama yarona na mishi mata kuma karatu zai tafi, dan haka maganar auren nan babu ita a yanzu, zai tafi karatunshi idan ya dawo zai auri daidai dashi, duk wani abu da kuka san an kashe na auren nan, duniya da lahira mun yafe muku shi." Kallon Faduma yayi da idonta suka zama kamar magudanar ruwa sai hawaye wasu na bin wasu yace "Idan har gaske ne kina da ciki, to ki nemi uban d'anki a wuni wuri, amma ni d'ana ba d'an iska bane." Juyawa yayi ya kalli i da Gomboy ke tsaye yace "Ke idan sun fita ku wanke min falon nan ku saka masa turare sai rufe min." Da k'arfi ya juya rik'e da hannun Tagur zasu fita, da wani irin kuka mai tsuma zuciya tace "Tagur ka tuna Allah, tabbas abinda ke ciki na nake ne, da ba naka bane da baiyi min tsalle a mara ba sanda yaji an tab'a jikinka, akwai dangantakar jini a tsakaninku Tagur, akwai alak'a mai k'arfi ta d'a da uba, kada kasa ya tashi babu uba Tagur, ba dan ni ba ka kusanceni dan d'anka ya saba da kai, bana buk'atar komai daga gareka ko da ruwan da zan sha ne, kalmar *Eh* kawai zata sa na d'auke maka nauyin zama ubansa, idan ka furta haka a yanzu na yarda ka barni da d'awainiyarsa zanji da hakan ko da zata kaini ga yin dako ne a kasuwa, amma karka tafi ka barni da wannan mummunan pantin na kalmar a'a, na rok'eka Tagur, dan Allah." Tagur ma daya fashe da kuka kallon Alhaji yayi yace "Aba dan Allah ka barni nayi magana da ita? Minti biyu kawai." Jan shi yayi da k'arfi yana fad'in "Wallahi tsine maka zanyi akan yarinyar nan in baka yi da gaske ba." Suna ganin fitarsu ta durk'ushe wurin tana kuka sosai, tausayi da kuma dangantaka yasa Kalli ma share hawaye ya matso kusanta ya mik'ar da ita tsaye, Herde ma da kalaman Faduma suka sa ta kuka da gaske fita tayi daga falon, a hankali Kalli ya fita da ita daga d'akin tana kuka, saida duk suka fita Aba ya d'aga k'afarsa da tayi bala'in nauyi, da k'yar ya fitar da kansa jikinshi duk yayi nauyi zuciyarshi na ta bugawa, Aisho ma kukan tausayi ta mata ta fita a d'akin suka bar Gomboy, tsalle ta daka da murna tana fad'in "Humm! Kuna ganin zan barku hakane? Abanmu na nuna masa soyayya fiye damu, yanzu a haifa masa jikan titi shima ya so shi fiye da komai, tunda sun sa baya da gado hakan zai sa su dinga mishi kyaututtuka na ban mamaki da zasu sa ya dake kowa, dan haka ba zan tab'a barin haka ta faru ba wallahi, gashi nan yan uwana dake ta haihuwa har yanzu babu yaron da Abanmu yake tsananin so, har yanzu cikinsu babu wanda ya ma kyautar fili bare gida, aikin banza." ______________ Haka suka koma gida a wannan mawuyacin halin da fassara shi abune mai kamar wuya, Faduma da har yanzu kukanta ya kasa tsagaitawa haka suka shiga cikin gida Herde na rik'e da ita, sun samu Owwo (Dada) dake aure a Maradi wacce ba'a jima da aurenta ba a lokacin ta zo dan bikin, tare da yayunsu da suke ciki d'aya da kuma uba d'aya, suna ta fito da kaya saboda da yamma zasu je gyaran d'aki, zuwa gobe kuma za'a fara shagulgulan biki, Hadizey dama bata fad'a musu komai ba, tana dai kallonsu da ido tana nuna musu duk abinda suka tambaya da yatsa. Shigowarsu tasa su kallon k'ofar saboda jin kuka, hankalinsu tashe da kuma mamaki suka rufa kansu suna tambayar me ya faru, Kalli daya shigo a bayansu ne yayi gaggawar d'auko tabarma ya shinfid'a k'ofar d'akin Barka ya kalli mahaifiyarshi yace "Ayya zaunar da ita." Kan tabarmar suka nufa Owwo na sake fad'in "Wai me ya faru da ita? Bata da lafiya ne dama?" Zaunar da ita sukayi babu wanda ya bata amsa ba, ruwa ya kawo ya mik'awa Herde ta amsa tana kifa mata a baki, Hadizey na gefe k'ofar d'akinta tsaye ta rumgume hannaye tana kallonsu. Girgiza kai ta dinga yi alamar ba tasha amma Herde tace "D'an kurb'a dan Allah ko kad'an ne." Duk'a kanta tayi ga kofin zata sha, babu wanda ya ga shigowarshi duk a cikinsu, babu wanda ya ankara kawai sai gani sukayi yasa k'afa ya bige kofin, hakan yasa kofin fad'uwa daga hannun Herde ruwan suka jik'a hijab d'in Faduma, a lokacin da wasu ke waiwaiyawa bayan da suka ga k'afar suna salallami, lokacin kuma ya warto hijab d'in ta k'iiiii ya jawota k'asa, kafin kowa yayi wani yunk'urin tuni ya take k'afafunta biyu da k'afarsa, wasu labta labtan tsumagiya ne ya shigo dasu, kamar wanda Allah ya aiko sa sai kuwa ya kama hijabinta ya tattareshi sosai ya manne a jikinta ya shiga tsula mata. Hankali a matuk'ar tashe Kalli yayi kanshi yana had'e hannayenshi yace "Aba dan Allah, Aba karka kasheta, Ab..." Tureshi yayi gefe tare da nuna shi da yatsa alamar ya kiyaye, da gudu Herde ta shiga jikin Faduma ta rumgumeta tana kareta, hakan yasa saida ya zabga mata bulala hud'u a jiki masu kyau, duk da taji zafi daurewa tayi tana k'ara matse Faduma a jikinta, rigarta ya kama ta baya ya rfizgeta da k'arfin da Allah ya hore masa, fad'uwa tayi kwance tana shirin mik'ewa ta koma yaja Fatima zuwa d'akin shi. Mutanen wurin sun gama tsurewa sun rasa me zasu yi, duk sun kame wuri d'aya sun dafe baki sai girgiza kai suke na tausayi da tunanin me yayi zafi haka? Fadun Abanta? Ita ce yau hannun Aba yake dukanta haka? Lallai ko ma me tayi abun babba ne. Suna cirko cirkon nan an rasa me kuzarin tunkararshi suka ji ihunta a d'akinshi, yanda yake dukanta da sautin bulalar zai sa mai sauraro ya zubar mata da hawaye, hankalinsu a tashe Kalli ya kalli (wannan suna na Kalli wani yana bani wahala idan zan fad'i Kalli ya kalli wani馃ぃ), Hadizey yace "Ayya dan Allah kije ku bashi hak'uri, kar Aba ya kasheta fa." Yanda zuciyarta ke kakkarwar tausayin 'yarta da kukan da takr son yi ne yasa ta kallonshi kamar bak'o, ganin kamar bata fahimce shi bane yasa ya dawo inda su Owwo suke yace "Dan Allah kuje ku taimaka mata, wallahi zata iya mutuwa ko ya salwantar da abinda ke cikinta." Dammm! Gabansu duk ya kwanci kwanci ya fad'i, duk a zuk'atansu suka iya maimaita kalmar abinda ke cikinta? Tabbas yanzu kam sun fahimci komai, babbar yayansu ce ta kallesu tace "Kunga koma me ya faru ai ba zamu bari ya kashe yarinya ba, muje dan Allah mu bashi hak'uri." Zasu rankaya d'akin dukansu kuma mak'wabcin nasu ya shigo da sallama a rikice, kamar jira suke duk suka amsa mishi dan a firgice suke, kallonsu yayi yace "Kuyi hak'uri dan Allah na shigo muku gida kai tsaye haka, wallahi ina ban d'aki uwarsu Maryam ke ce min ba lafiya kamar ana dukan wani, mme yake faruwa ne?" Wani wahalallen tari da Faduma tayi ne tana fad'in "Na mutu Aba, na mutu Aba! Zan mutu wallahi, na tuba Aba ka min rai." Da gudu matan suka shiga sai shi ma daya bisu a baya tare da Kalli, suna shiga daidai ya kai mata wani uban k'ulli a ciki, duk'ewa tayi kamar za tayi sujada tana murd'a cikinta tana sake ci gaba da tarin, babu ko hijabin yanzu a jikinta watak'ila ya fita tsabar wahala, dogon gashinta daya sha gyara duk ya warware ya rufe mata fuska, da gudu matan sukayi kanta sai mak'wabcin daya rik'e shi yana fad'in "Subhanallah, malam Moliya me yayi zafi haka shi ba wuta ba?" Cikin rufewar ido da tafasar zuciya yana fitar da shasheka kamar wanda yayi gudu a harshen hausarshi da bai nuna ba yace "Malam Ilyas sake ni, sake ni na kashe yarinyar nan." Kallon Faduma yayi dake ta murk'ususu ya nuna kanshi yace "Ni Faduma! Ni zaki wulak'anta? Ni zaki tozarta ki zubarwa mutumci? Ashe ke yar iska dama ban sani ba?" Fizgewa yayi daga rik'on daya masa yace "Takaici na d'aya da kika rasa wanda zaki bawa kanki sai k'aramin mutum daya zab'i siyasar mahaifinshi akan mutumcinki, me yasa baki bawa wanda zai iya ganin darajar mutumcin naki ba? Har naje gidansu su dinga fad'a min maganar da suka ga dama, k'aramar yarinyar dana haifa tana kallona tana k'aryata ni, akan ki? Akan ki kawai? Me na miki da zafi haka? Yaudara? Cin amana?" Cikin rarrashi Ilyass yace "Dan Allah koma me tayi kayi hak'uri ka barta Haka, ka yafe mata saika ja mata kunne a tsanake, amma haka ai sai ka ji mata ciwo." Da k'arfi yace "Wa! Ja mata kunne? Yarinyar da tayi girman da zata iya iskanci a waje? Ni! Faduma kuma na gama da babinta, wallahi ta daina wahalar dani tunda har yau zan yayeta a matsayin 'yar dana tab'a haihuwa a doron duniya." "Subhanallah." Ya fad'a yana d'orawa da "Haba dai, karka fad'i haka mana." "Na fad'a, na fad'a, Faduma dai ko? Na yafeta taje ta zama zakka a cikin 'ya'yana, bani ba ita har abad..." Hadizey da shigowarta kenan da sauri ta durk'usa tana fad'in "Na rok'e da Allah karka tsine mata, karka lahata min yarinya, k'addarata ce, karka tsine mata ta ida lalacewa, na ji na d'auki alhakin kuskuren da tayi a baya, duk hukuncin da zaka mata ni ka min amma karka tsine mata, ka tuna da tuna da tunatarwar daka mana jiya, me yasa ka kasa zama mai hak'uri kamar annabawan da suka gabata? Me yasa ba kayi koyi dasu sanda shed'an ke tunzuraka yana maka hud'ubar tsiya?" A zafafe yace "Ko ubangiji baya hukunta wani da laifin wani, nayi hak'uri kan k'addarar data fad'a mana, amma abinda ya faru yau ya jawo b'acin raina na jiya, idan ke zaki bisa da saka albarkarki ga wurin nan, amma ni na cireta a cikin 'ya'yan dana haifa, bani ba ita kuma babu ruwana da ita, abunda zan fad'a muku yanzu shine ta tattara nata ya nata ta bar min gida, wallahi kunji na rantse ba zan sake zama a gidan nan da ita ba, dan in ina ganinta ba zan tab'a mantawa da abinda aka min yau ba, hakan kuma zai iya tunzura ni na kasheta da hannuna." A tsorace ta kalleshi tana rufe bakinta da hannu, Herde ma da sauri ta kalleshi tace "Faduman? A gaskiya kayi hak'uri wallahi babbbb..." Marin daya d'auke fuskarta dashi ne yasa tayi d'if dafe da kunci, saida Kalli ya rintse ido dan kamar zuciyarshi ya soka ganin a gabanshi an marin uwarshi, saida ya sunkuya kusanta sosai ya nuna ta da yatsa yace "Kafin ta bar gidan nan ma saina tabbatar bata bar min duk wani abu daya shafeta ba, daga hatta sunanta ko wani abu daya shafeta bana son sake ji daga gareki, wallahi ko a bayan idona haka ta faru Allah ya isa ban yafe muku ba." Da sauri Ilyas ya rik'e hannunshi yana fad'in "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, malam Moliya kanka d'aya kuwa? Ridda tayi ne?" Da sauri Herde tayi nesa dashi tace "Ina fa, ba wani ridda, kawai dan tayi abinda kowa yasan ba dagangan bane, kuskure kawai shine zaka wani yi kamar yarinyar nan bata tab'a yin abun alkairi ba, haba." Yanda yake kallonta yasa ta fita da sauri a d'akin tana fad'in "Na bar maka gidan ma ni wallahi bani cikin wannan jaraba, haba." K'wafa yayi kafin ya kalli Faduma dake kallonshi kamar bata da rai, nunata yayi yace "Ki tabbatar ban dawo na same ki gidan nan ba." Yana fita Ilya ma ya bi bayanshi haka ma Kalli, a hankali ta kalli Ayyarta da ita ma ta kalleta, ta d'auka zata bita da duka ne ita ma amma sai ta matso kusanta ta rumgumeta, kuka take sosai Faduma kuma idonta ma sun bushe murus, tana son sako hawayen amma sun k'i tahowa ga muryarta data disashe sosai. Sun jima haka kafin daga bisani ta d'agota daga jikinta, duk ta zama wata iri kamar ba Faduma ba, fatarta duk ta farfashe tayi bak'i, wani kukan ta sanya tana girgiza kai da fad'in "Faduma dole ki bar gidan nan, sai dai bansan ina zaki tafi ba?" Ajiyar zuciya babbar yayarsu ta sauke tace "Humm! Ni dama mai gidan yana nan saina mishi magana ta koma can, to shi ba kasafai ake samunshi a waya ba saboda matsalar sadarwa." Da ire iren wannan hujojjin duka yan uwan kusan shida suka fake, Owwo ce kawai tace in zata bita ba damuwa su tafi, tun farko dama bata yi saurin magana bane dan kar ace dan suna ciki d'aya, amma tasan duka akwai magana a k'asa da zata fito daga bakunan yan uwan da zaran an watse daga nan, duk da basu da k'warin jiki haka suka shiga had'a mata kayanta da duk abun buk'ata, inda Owwo ta kira mijinta ta sanar dashi kaf abinda ya faru, dake mutum ne mai kirki sai yaji yarinyar ta bashi tausayi tun bai ganta ba, daf da la'asar suka gama shiryawa suka samu motar da zai musu shata su biyu kawai da kayanta, wanda hatta takardunta na makaranta da kayan karatunta saida ta tafi da komai, tasha kuka sosai na rabuwa da iyayenta yan uwa da garin haihuwarta, inda Herde ta so a k'yaleta wai idan ya huce zai hak'ura, sam suka nuna mata a yanzu dai zaifi tayi nesa dashi kafin ya sauko d'in. Daga ranar nan data juya baya ta bar k'asar bata sake waiwayarta ba, ta fara sabuwar rayuwarta a sabuwar duniyarta mai cike da alhini bak'in ciki da k'unci da kuma kuka, babu abinda ta rasa a wajensu Owwo da mijinta, sai dai damuwar da take ciki da cikinta dake ci gaba da girma wanda tasha jinya bayan zuwansu suna k'ara mata tashin hankali, rayuwa ce da ba zata gogu a tarihinta cikin sauk'i ba, hatta da shatin bulalar da tasha akwai wasu ram a jikinta musamman a bayanta haka ma a wuyanta, sanda ta zo garin bata iya hausa ba sosai, amma yau da gobe saita fara kama harshenta har ta iya, mak'wabtansu dai Owwo tace musu 'yar yar uwarta ce da mijinta ya rasu da ciki, kuma babu wanda ya musa haka sai tausayinta da suke ji, tunda yanayinta da fuskarta na nuna hakan suna ganin mutuwar mijin ce ta zautar da ita, haka sukayi k'ok'ari suka cike mata takatdunta a maysayin wacce aiki ya dawo dasu garin nan, dama a can turata ajin gaba ake shiyasa ajinta ya girme ma shekarunta, saida ta fara zuwa makaranta tana karatunta ta fara sakewa. A hankali a hankali ana gungura rayuwar har cikinta ya isa haihuwa, Owwo da mijinta ne suka tsaya tsayin daka har Allah ya sauketa lafiya bayan awannin data kwashe tana nak'uda, kamar shi aka ma haihuwar komai shi yake yin shi, hatta da hud'uba shi ya wa yaro ya bata zab'in sunan da take so, sanda aka tambayi sunan abun yaro ne suka shiga kallon kallo suna kallon Faduma, kallon malamar asibitin tayi tace " *Amjad Tagur Sugui*." Saida ta fita Owwo le tambayarta da mamaki, murmushi ta mata tace "Dada ai d'ansa ne, suna ganin zai zubar musu da kima ne shiyasa sula guje shi, amma fa yaro zai tashi a matsayin maraya, Dada ko da na rasu bana son yaron nan yasan yana da mahaifi bayan sunansa kawai." Ko da tayi sati da haihuwa ta koma makarantar ta hankali kwance, haka ta samu kai k'arshen wannan shekara tare da sakamako mai kyan gaske, duk abinda ke faruwa babu wanda basa sane dashi, sai dai a b'oye suke samun labarin komai dan kiyaye b'acin ranshi, yayin da Faduma da saduwa d'aya tak ta samu Amjad kuma babu aure, sai ga su Owwo masu aure na neman haihuwa ido bud'e, hakan yasa Amjad sake shiga zuciyar Owwo da kuma Khamis, indai yana gida to yaran na hannunshi yana mishi wasa, wasu lokuta har sai yaji kamar ya had'iye shi ya huta, inda yan uwanshi suka fara tsegumi da tashin hankali kan saiya k'ara aure, dama kuma ba son zaman Faduma suke ba, ya dage shima ba zai yi aure ba har saida aka d'auki shekara uku. A lokacin Faduma ta bar Amjad hannunsu an cireshi daga nono bai isa ba, tana shekara ta uku kenan a k'asar Niamey a universit茅 Abdou Moumouni tana karanta abinda ranta yafi so, wanda Barka ya turo musu duka kud'inta dake asusun da aka bud'e mata sanda ta ci gasar nan har da kayan d'akin da *Elhaj Abdur raham Na-kiri* ya d'auki nauyin yi mata idan aurenta ya tashi, siyar dasu akayi duk aka had'a mata aka turo tayi buk'atarta. Labarin rasuwar Khamis saida yasa ta komawa halin data baro a baya, dan tana kallonshi kamar uba, sai dai bata samu zuwa ba saboda lokacin karatu yayi tsanani. Tunda taje Niamey suka had'u da Aminu a lokacin shekara biyu ta rage mishi ya kammala, da taimakon juna suka fara har shak'uwa ta shiga tsakaninsu, sanda ya bar makarantar duk sai taji ba dad'i, dan ya zama kamar wani garkuwarta, amma abinda ke bata mamaki wani lokaci sai ya baro maradi ya zo Niamey wai ya kawo mata ziyara, haka har ta kai ta iya fad'a mishi komai daya shafeta, sai ya zama duk sanda zai je ya kan tafi da Amjad su ganta. Tana shekara ta biyar ta samu gidan wata mace suka saba, hakan yasa har Amjad ya dawo hannunta ta saka shi jardin, a lokacin ta fara d'orashi kan tarbiyarta har ta kammala suka koma gida. *Mu koma labari* *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 17:12 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _24_ Kiran Barka ne ya tasheta daga baccin daya d'auketa mai nauyi, saida ta fara duba lokaci kafin ta fahimci lokacin sallah azahar ya wuce mata sosai, da sauri ta d'auka ta d'ora a kunne tana fad'in "Barkuku nagode maka daka tashe ni." Dariya ya fara sakar mata kafin yace "Ke munyi magana da Aba, yace fa kawai ki tafi, amma ni ina ganin ki jira ya dawo saiki sake mishi magana." Dafe k'irji tayi tace "Ni yaya Barka? Ba zan iya ba, har yanzu fa ko kallon juna bamuyi ba." "To ya za ayi kenan yanzu?" Saida ta sauke numfashi tace "Kawai ka barshi zan tafi da nayi sallah la'asar, amma ina tunanin idan akayi musabik'ar su Amjad zan dawo dashi nan, ban damu dame zai faru ba sai dai na gaji da rashin amsa mishi tambayar da yake yawan yi min ta me ya had'ani da dangina." Da farin ciki yace "Da gaske? Ashe yayi gado dai mai kyau." Murmushi kawai tayi kamar suna ganin juna kafin tace "Bari zan tashi nayi sallah." Tsakar gidan ta fito tayi alwala ta koma tayi sallah, tana idawa ta k'ara kimtsawa ta d'an shafa powder da jan baki mai duhu da lips, kayanta ta had'a a jakar data zo dasu kafin ta fita zuwa gidan Herde dan fad'a musu zata tafi. A k'ofar shiga gidan ta had'e da Abakar wanda basu had'u ba tun jiya data hangeshi da dare, rufe fuskarta tayi irin kunyar nan, shi kuma ido ya zaro yana fad'in "Fadu? Ke! Wai ke ce nake gani?" Turo baki tayi tana hararenshi, bushewa yayi da dariya da farin ciki sosai ya dafa kafad'arta yana fad'in "Faduma, yaushe kika zo? Shine babu wanda ya fad'a min? Amma dai baki da mutumci shine ko ki neme ni." Kamar zata masa kuka tace "Yi hak'uri, ni nace kar a fad'a ma kowa sai mun had'u kawai." Yatsa ya d'ora akan kumcinta yace "Tafi can! Har yanzu baki girma ba ashe, to ya ina mutumin?" Murmushi tayi tace "Yana gida kuma yana kewarku, amma fa ku daina ce min ban girma ba." Hararenta yayi yace "To kin girma ne? D'aga kai tayi alamar eh, lak'ace hancinta yayi yace "Zan yarda ne idan baki sake rotsa min kai ba." Bushewa skukayi da dariya dukansu suka rankaya cikin gidan a tare. Wata nauyayyen ajiyar zuciya ya sauke tare da lumshe ido, shi hakan ma daya ganta ya masa dad'i ba kad'an ba, ganinta cikin farin ciki da annashuwa, da fari ya ganta a cikin gidan, yanzu kuma ya ganta da fara'a a fuskarta, abu d'aya kawai ya rage yaji daga bakin 'yar tasa shine sautinta, yana so yaji sanyayyar muryar k'uruciyarta ta furta masa kalmar nan ta *Aba*, murmushi ya saki saboda tuna duk wani lokaci da take kiran Aba, ajiyar zuciya ya sake saukewa yace " Allah ka yafe min, ka yafe min zunubaina, Allah ka gafarta min abisa fatali da nayi da rayuwar 'yata, hak'ik'a na zalinci kaina kuma na zama butulu, ban rik'e amanar kiwon daka bani ba, Allah ka ci gaba da kareta a duk inda ta samu kanta, Allah ka dawwamar da farin ciki a cikin rayuwarta, Allah ka shirya mata d'anta ya mata biyayya fiye da yanda ta mana." Daga cikin kwanar daya b'uya bai yarda kowa ya ganshi ba ya sake gyara tsayuwa, tunda sukayi waya da Barka ne ya zo nan yana so ya ga tafiyarta, fatanshi wani abu ya rik'eta ta zauna har sanda ta so, idan zai yiwu bai k'i ace ta dawo ba kenan, kawai yace ma Barka ta tafi ne dan kar su gane yana son zamanta. Data shiga ciki da k'yar ta samu ganin Ayyarta da Herde ta fad'a musu yanda sukayi da Barka, Herde ce ta fara cewa "A gaskiya bana son tafiyarki yar albarka." Saida ta rik'e hannunta tace "Ayyata, kiyi hak'uri ki min murmushi, zan dawo tare da Amjad ki ganshi." Kallonta tayi tace "Kinyi alk'awari?" Jinjina kai tayi tace "Nayi." Hadizey ce tace "Yanzu gidan motar zaki wuce?" A nutse ta kalleta tace "Eh Ayya, amma zan fara d'aukar jakata a gida na barota." Herde ce tace "To muje na rakaki sai muyi sallama." Had'e naman goshinta tayi tace "Ayya ke da ke karb'an kud'in biki? Idan aka zo ba'a ganki ba fa?" Dungure mata kai tayi tace "Ja'ira, ai ba karb'an kud'i muke ba." "Me yasa Ayya?" Ta fad'a sanda suke fita, da fara'a a fuskarta tace "Saboda aurenki muka fi tsumayi da yi wa babban tanadi." Kallonta tayi tace "Ayya!!!" Suna fita waje ta kalleta tace "Me? Wai ba kya son maganar aure gaba d'aya?" Hadizey dake bayansu ita ma ta fito tace "Ai abinda ta tsana kenan, bansan me take nufi ba?" A hankali Herde ta kamo hannunta tace "Fadumata, kar kiyi wasa da damarki kinji, mace kike mai k'urarren lokaci, abinda ya faru a baya bashi zai zama hujjarki a gaban Allah ba, ba duk maza suka taru suka zama d'aya ba, ki sake jarraba wani zaki dace ba kamar waccen hamagon ba." Numfashi ta sauke ba tace komai ba, Hadizey ita ma tace "Kuma ki sani Owwo da kika ga ta zuba miki ido nauyinki ne take ji, amma ta jima tana son yin aure, tana samun masu nemanta da aure, amma ta kafe tace ba zatayi aure ta tafi ta barki gidan nan ba ke da yaro kawai, hakan zai sake ja miki rugujewar mutumci, amma idan kuna tare to komai zai faru da dukanku ne, kinga bai kamata ace kin zama wani nauyi daya mata shamaki tsakaninta da rayuwar aure ba." Kallonta tayi tace "Insha Allahu Ayya zanyi, ko dan na sakarwa dada mara tayi aure ita ma, watak'ila ma a d'aura mana auren tare." Dariya Herde tayi tace "Kinga ki ko? Da alama kin mayar da ita kamar k'awarki?" Dariya tayi tace "Dada ai ta wuce k'awata sai aminiya, ban da kowa sai ita kad'ai." Murmushi Hadizey tayi tace "Dan ta ga bata fita da komai ba, kuma a shekaru ma ai bai fi da hud'u zuwa uku tafi ta ba." Da haka suka isa gidan, daga d'aukar jakarta amma saida sukayi zaune suka shiga hira, ta jima tana fad'a musu abubuwan dake faruwa acan, yanayin aikinta da rayuwar da suke, hatta da rigima da akayi akan gidan da suke zaune saida ta fad'a musu, wanda kafin rasuwar Khamis ya bawa Owwo gidan a matsayin tukuicin da zai iya yi mata da ganin yana gaf da barin duniya bai bar mata komai ba, amma daga baya yan uwanshi suka ce gidan ma na cikin gado, farkon fara aikin Faduma akan wannan rigima ce, wanda ta shiga ta fita ta binkito wasiyyar daya bari a wajen wani amintaccenshi, amma shima sai yayi zalinci ta hanyar yin shiru suka had'a baki da wasu daga cikin magadan, tarko kawai Faduma ta masa ya fad'a tsamo tsamo. Saida la'asar ta riskesu hakan yasa suka farga da sauri suka tashi sukayi sallah suna son komawa gidan bikin kar a ga basu nan, tun suna sallah wayar Herde ta fara ring, sua idawa an sake kira ta d'auka, daga yanda suke magana suka fahimci Kalli ne, da murna ta kalli Herde tace "Ayya ki fad'a masa ni zan tafi sai wata rana kuma." Tana sanar dashi yace ma Herde ta mata magana ta jira akwai motar da zata tafi maradi yanzu sai su tafi tare, suna gama wayar ta fad'a mata, ba tare da tunanin wanda zasu tafi tare ba tace "Shikenan Ayya, mma cikin bak'insa ne?" Jinjina kai tayi tace "Ina ga cikinsu ne." Fitowa sukayi a k'ofar gidan suka yi sallama, gidan bikin suka koma inda su Leeya suka fito dan suyi sallama suma. _____________ Babu abinda ya tsayar dasu, Adam tun tana mishi magana su tafi har yayi banza dashi ya fara jin haushi, daga k'arshe ya koma lalaminshi, har sukayi azahar akayi la'asar bai da niyyar tafiya kamar garinsu, sai yanzu ne da Adam ya mik'e daga kan kujerar yace "Kai nagode Allah fa dani ba matalauci bane, wallahi bus zanje na hau, haka kawai ka mayar dani wani sakarai." K'ofa ya nufa ya fita shi kuma ko a jikinshi, dan yasan babu inda zai iya tafiya, drebanshi da suka taho ya tura ya turawa gajeran sak'o kamar haka " *Karka tafi ko ya nemeka*." Yana karanta sak'on lokacin Adam ya k'araso, saida ya dafa motar yace "Qaseem mu je ka aje ni gidan bus na sonef." Ba wani alamar damuwa ko rashin gaskiya a tare dashi yace "Ai kuwa Elhaj motar nan ta d'an samu matsala, amma yanzu zan sake dubawa sai mu je." Saboda yarda dashi da rashin sanin dawan garin sai kawai yace "Shikenan to ina jiranka." Juyawa yayi ya koma ciki, Kalli ya samu ya shigo ta d'aya k'ofar baya daga rakiyar wasu da suka tafi yanzu hakan na nufin su kawai suka rage a dai gidan gonar, zaune yayi inda Hasheer ya bishi da kallo ta wutsiyar ido ya tab'e baki. D'agowa yayi daga jikin kujerar yana kallon Kalli, cikin taushin murya da harhad'a kalaman wanda hakan ke nuna yana jin wuyar maganar yace " *Ina mijinta*?" Kallonshi yayi da mamaki, a ranshi yake ayyana wai me yasa yake mishi tambaya ne a wani tak'aice? Kafin yace wani abu Adam yace "Wacece? K'anwarsa?" Dariya yayi yace "Yaro zakayi magana." Ko kallonshi baiyi ba sai Kalli da yake kallo, da gurgurarren harshenshi yace "Elhaj ai Faduma bata da miji?" Wata irin ajiyar zuciya ya sauke a fili tare da lumshe ido, dan tunaninshi ya fara ashi ko ta sake aure tunda yaron yace babanshi ya rasu, bud'a ido ya sake yi sauke a kanshi yace "Tun yaushe?" Yar ajiyar zuciya ya sauke yace "Tun da cikin yaronta Amjad." Fad'uwa yaji gabanshi yayi yana sake kallonshi da mamaki, ikon Allah Adam ne yayi tambayar da yaji ta zo mishi a rai da cewa "Tun kafin ta haihu kuma take zaune har yanzu? To shekarar yaronta nawa?" Son kawar da zancen yasa shi cewa"Ina jin baifi bakwai zuwa takwas ba, Elhaj zaka min wata alfarma?" Da ido kawai ya bishi alamar yana saurare, cikin taushi yace "Akwai motocin da aka yo odarsu yanzu haka suna kusan shigowa bakin bodarmu, shine nake so kayi magana da Elhaj d'inka, dan wallahi motar daka saka a kawo maka bana son a samu matsala da conteneur d'in da take ciki ma bare ta kai ga motar." Saida ya sake jingina a kujerar ya lumshe ido yace "Wane Elhaj kenan?" Saida ya saki murmushi yace "G茅n茅ral *Wardugu* mana." Wani uban murmushi ya saki mai kama da dariya, bud'e ido yayi kamar mai jin bacci yace "Hummm!' Kallon Adam yayi ya mik'e da sauri yace "Tashi mu tafi, War zai min iskanci fa." Shima murmushi yayi yace "Ka masa laifi halan?" Saida duk suka fita a d'akin suka tunkari mota yace "Kwana uku kenan daya min magana yana so na zanawa matansa atamfar da ban tab'a kwatanta zana irinta ba, amma na manta." Zaro ido Adam yayi yace "Ka manta da al'amarin *Gaishu*? Ah lallai ka ja bala'i." Dariya ya sake yi dan shi ma fa yasan ya taro match yace "Allah zai ci k'aniyarka ya kama bakinka yana kiran matarshi da Gaishu." Duk sun bud'e motar zasu shiga kuma suka ji wayar da Kalli ke yi, jin yace "Ayya yanzu zata tafi? Ba zai hak'ura ta k'ara kwana ba kenan?" Duk mayar da hankalinsu sukayi a kanshi musamman Hasheer da yaji al'amarin kamar ya shafeshi kai tsaye, jim kad'an ya d'auke wayar daga kunnenshi ya kalli Hasheer yace "Elhaj na mu zaku iya wuce min da k'anwata? Garinku d'aya fa." Da ido ya masa alamar eh, d'ora wayar yayi ya fad'a ma Ayya ta shirya zasu be d'aukarta, motarshi ya shiga shima suka bar gidan gonar zuwa gidansu Kalli. Suna isa k'ofar gidan suka same su tsaye su uku, Leeya da Zainaba sai ita suna ta hira da fara'arsu a fuska, kasancewar bak'ar Hilux d'in haka madubanta suke bak'ak'e wulik, gashi kuma a baya yake b'angaren hannun damanshi, dakatawa yayi daga danna wayar da yake yana kallonta daga nan, yanda ta marairaice tana rik'e da hannun kowace daga cikin yayunta, har bubbuga k'afafu take alamar shagwab'a tana rok'onsu suje gasar da Amjad zaiyi. Da sauri ya kalli k'asa tare da girgiza kai ya huro iska, sake kallonta yayi duk da kuwa yaji yana narkewa, Kalli daya fita daga motarshi ya nufesu, ban ma sun d'an jima suna tattaunawa, sai nuna su take da hannu tana so su tabbatar mata zasu je, Kalli kuma sai k'ok'arin turata yake ta tafi kafin su b'ata musu lokaci, saida suka gama sallamarsu sannan ta taho tana ta d'aga musu hannu tana son tare hawayen dake son taho mata, tana zuwa inda hannunta yake ne b'angaren dama, bud'ewa tayi tana share k'wallar da lafayarta, hakan yasa bata kula da akwai mutum a b'angaren ba, cilla jakarta tayi acan ciki ta fara d'ora k'ugunta ta zauna kamar yanda zata zauna a kujera. Yammmmm! D'in da jikinshi yayi yasa shi sakin wayarshi ta fad'a k'asan motar, da saurin tsiya ta mik'e tsaye tana juyawa, ganin mutum ne yasa ta waro ido tace "Subhanallah, kayi hak'uri dan Allah ban kula ba." Kalli ne yayi saurin cewa "Ke da mutane fa, zagaya can b'angaren." Kallonshi tayi kamar zatayi kuka tace "Ban kula bane yaya Kalli, ka bashi hak'uri." Bata jira me zai ce ba ta zagaya tana sinne kai da motsa bakinta alamar rashin jin dad'i da kunya, bud'ewa tayi a hankali cikin sanyi ta shiga tana d'auke jakarta a hannu ta zauna, d'orata tayi akan cinya ta mayar da k'ofar ta rufe, b'oyayyar ajiyar zuciya ta sauke, duk da bata kalleshi ba taji dai kamar baya motsi, gabanta taji yana fad'uwa a hankali, duk jikinta taji yana macewa kamar an mata *allura*, zufa ce taji tana neman tsatsafo mata daga saman goshinta, da sauri ta kai hannunta ta shafa, cikin rawar murya tace "Ina wuninku." Qaseem ne ya juyo yace "Barka da yamma Hajaj." Muryar Adam taji shima yace "Lafiya lau, kina lafiya?" Rintse ido tayi a k'asan ranta tace "Kaico! Duka maza ne, kuma dasu zan tafi har can?" Tayar da motar yayi zai d'auki hanya ta kalli k'eyar dreban, saida ta raunana murya yanda take ganin ba duka ne zasu ji ba tace "Malam mai tuk'i ina fatan dai ka mana addua'r hawa abun hawa ko?" D'an juyowa yayi yace "Eh to Hajaj, bari sai ki koya min nayi yanzu ko." Langab'e kai tayi ta matse bakinta tace "Ba abun kunya bane ko fad'uwa, sai dai matsayinka na namiji ya ci ace ka iya addua'r nan, ko dan fatan sa'a a hanyar tafiya ma." Jinjina kai yayi yace "Nagode da tunatarwa, yanzu saiki fad'a mana ko?" Ganin yana kallonta yasa ta mishi alama da ido cewar ba zata iya ba, da mamaki ya kalleta yace "Me yasa?" Adam ne yayi gyaran murya "Ugyheem ugyheem!" Da sauri Qaseem ya juya gabanshi ya tayar da motar, tafiyar motar ce ta dawo dashi hayyacinshi, da wani irin sanyi kamar marar lakka a jiki ya sunkuya ya shiga lalubar wayarshi, yana d'aukowa ya d'an saci kallonta, gaba d'aya ta tsinka mishi jijiyoyin jikinshi, ta sage mishi komai kamar wani na'ura dake yi da masarrafi. Yanda zuciyarshi le ta bugawa irin dadak dadak dadak d'in nan yasa shi dafe k'irjinshi, cikin nutsuwa kamar wanda aka d'ora ma bakin bindiga aka ce kar ya motsa ya d'an muskuta, jingina yayi a kujerar ya rufe ido yana d'ora wayarshi a kan cinya. Ba wanda ya sake magana sai tafiya da ake redio kawai ke magana, ka rantse bacci yake saboda ya da ko numfashinshi baka jin sautinshi, ita dai hanya take kallo yanda suke wuce sararin filin wurare da bishiyu zuwa titi. Satar kallonta yayi, a hankali ya saisaita kallonshi da kyau, mamakin yanda yake wani kwarkwarcewa idan ya ganta yake, gaba d'aya saiya rasa kuzari ya zama wani iri, d'aga labbenshi yayi da k'yar kamar mai koyon magana yace " *Me..kike ci ne haka*?" Da sauri ta kalleshi, zaro ido tayi dan wallahi sai yanzu ta gane waye, da d'an d'aga murya kad'an tace "Dama kai ne? Abban...Izzadeen ko? Ina wuni." Madadin ya amsa mata saiya mayar da dubanshi ga kujerar da dreba yake yana murmushi, da alamar tsarguwa tare da ita tace "Amma me kake nufi da abinda nake ci?" Wani murmushin ya kuma saki ya d'an kalleta ta gefen ido yace "Naji kina da nauyi ne." Kyab'e fuska tayi ta cinno baki gaba ta kawar da kanta, gunguni ta shiga yi tana fad'in "Ina ruwanka da nauyi na to? Kaji neman fitina kamar shi le ciyar dani." Murmushi yayi mai sauti wanda yasa ta sake kallonshi, yanda ya zuba mata ido ne yasa tayi saurin d'auke kanta tana fad'in "Ina yarana? Suna lafiya?" Jinjina mata kai yayi wanda ita kuma bata san yayi ba dan ba kallonshi take ba, ci gaba suke da tafiya babu wani nishad'i dan kowa a shiru yake, a dame take jin kanta sosai saboda tana yawan jin idonshi saman jikinta yana kallonta, wayarta ta samu ta fito da ita ta kira Kalli, ko da ya d'auka yace "Fadun Aba yane?" Juya harshenta da yarenta tace "Yaya Kalli me yasa ka had'o ni da mutanen nan? Dama kasan duka maza ne ka ce na taho tare dasu? Ni gaskiya ka kirasu ka ce su tsaya zan sauka." Dariya yayi yace "Fadu kenan, ke da yanzu kunyi nisa, ki hak'ura kawai na yarda da su ne ai." A hankali tace "Shikenan, sai amjima." Aje wayar tayi ta kalli hanya, kallonta yayi sai kuma ya kawar da kai yace "Hum! Ni dai nasan ba tsada zanyi ba ehe." Maganarshi dariya ta bata, kallonshi tayi tana murmushin ta sake kawar da kanta, murya k'asa k'asa tace "Idan akwai wanda ya kamata yayi tunanin haka ai ni ce." Shima murmushin yayi amma bai kalleta ba dan hakan na wahalar dashi, murya a tausashe shima yace "Idan ba tsoro ba a fassara mana to, kuma a dinga yin yaren da kowa zai gane." Hannu tasa ta rufe bakinta tana dariya tare da girgiza kai, ganin shiru ba tace komai ba yasa shi d'aukar wayarshi ya tura gajeran sak'o ga wayar Qaseem, sak'on na zuwa ya d'auki wayar ya duba, ajewa yayi tare da yin abinda ya umarta, kunna mp3 dake motar yayi hakan yasa sautin muryar Sheick Ja'afar Mahmud Adam ta karad'e kunnuwansu, bada hankalinta tayi tana sauraron amsar tambayoyin da ake, sauke jakarta tayi k'asan k'afafunta ta gyara zama ta rumgume hannayenta, hannu ya zura ya d'auki jakar ganin kamar a takure k'afafunta suke, hannu ta kai ita ma tace "Ah daka barshi ai, nagode sosai." Ba tare daya kalleta ba yace "Kud'in dakon ne ba zaki iya biya ba?" Murmushi tayi tace "Shi sauk'i ai ko ya yake yana da dad'i." Wani murmushi yayi sanda ya d'auki jakar ya d'ora kan kujerar tsakiyarsu yace "Son kud'i." Murmushi tayi amma ba tace komai ba, Adam da yana jin sautin maganarsu amma bai ji me suke fad'a bane ya juyo yace "Mutanen nan fa baku da kirki, yanzu kenan ko wani abun ake rabo haka zaku mana shiru?" Murmushi tayi tana sinne kanta k'asa, shi kuma hararanshi yayi ya kawar da kanshi yana kallon titi, juyawa yayi jin babu wanda ya tanka masa yana fad'in "Da kyau, zan rama ne Elhaj." Tafiya suke yi suna gudu sosai wanda hakan yasa suka fara jiyo k'amshin garinsu, allon sanarwar da suka wuce wanda ya shaida musu sun shigo garin gazawa ne yasa shi kallon kujerar da Qaseem yake, har zaiyi magana sai kuma ya d'auki wayarshi ya tura masa sak'o kamar haka "Ka rage gudu zuwa 30." Ganin sak'on ya bashi mamaki sosai, sai dai baisan dalilin da yasa yace yayi haka ba, aje wayar yayi kawai ya fara rage gudun kamar wanda zasu tsallake wani had'ari. Kallonshi Adam yayi amma kuma saiya kasa magana yana kallo ya ga me ya faru? Ita ma saida ta d'an d'aga kanta tunaninta ko bakin wata bodar suka iso wajen jami'ai, ganin babu komai kawai tafiyar ce a haka saita share ta jinginar da kanta tana satar kallon mutumin, wani abu ne take d'an lura dashi amma kuma ba wani abun damuwa ba, ajiyar zuciya ta sauke a hankali ta sake matse jikinta kamar mai jin sanyi. Hakan daya gani ne yasa shi saurin d'aukar wayarshi ya tura sak'o da cewa "Kashe ac." Qaseem ya sake duba waya yana tambayar kanshi "Anya kuwa lafiya yake? Me ya samu bakinshi ne haka?" Kashewar yayi, ajiyar zuciya ta sauke mai k'arfi ta kalli Qaseem tace "Malam dreba waye mai gidanka anan?" Ba tare daya juyo ba da sakin fuska yace "Hajia ai dukansu suna bani umarni, amma ga Elhaj d'in nan kusanki." Jinjina kai tayi tana kallon Hasheer da yayi kamar bai ji ba tayi murmushi, kamar daga sama yaji tace " *Me yasa ba zaka umarce shi da baki ba*?" Mamakin yanda akayi ta gani yayi tare da kallonta yace "Da alama gwana ce ke wajen lek'a sirrin mutane." Girgiza kai tayi tace "Na dai canka da kuma lura da abinda ke faruwa." Da wani kallon da babu fara'a a ciki yace "Yar sanda ce?" Murmushi ta masa tace "Eh, kana da mai laifi ne a gida da kake so na maka gaba shi?" Wata dariya ce ta sub'uce mishi tare da juyar da kanshi yana kallon hanya, ita ma dariyar tayi ta kawar da kanta, babu wanda ya sake cewa komai har saida taji tafiyar a haka ta gundureta tace "Malam dreba zaka iya kaimu gida da wuri kuwa?" Juyowa yayi ya kalli Hasheer, da ido ya masa alamar zaka iya, k'ara mata gudu yayi daga nan ma babu wanda ya sake magana har suka shiga cikin gari. Kallonta yayi yace "Ina zaki sauka?" Ba tare data kalleshi ba tace "A gidan bus na rimbo." "Me yasa nan? Kije gida mana." Ya fad'a yana kallonta, a hankali tace "Saboda anan na bar akori kurata." Qaseem ne yayi tsal yace "Hajaj kamar ke? Ai manyan matane ku a garin nan kamar ku ke juyashi ma." Wani kallo ya watsa ma Qaseem, kallon me ya sako bakinka? Bai ji dad'i ba gaskiya, shi fa duk hira da rahar da sukayi ji yayi kamar suna matsayin ma'aurata, akan me wani zai shiga maganarsu? Ko Adam dalilin da yasa bai masa magana ba kenan, saboda baya so ya sake shiga zancensu ko ya jata da hira, yanda ya fahimci me aji ce ita to zai tayata k'ara kaurin zaren ajin nata. Saida ya had'e fuska sosai cikin amon muryar gargad'i yace "... *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 17:13 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ *SADAUKARWA GA* *_ALLURA TA TONO GALMA GRP_* 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _25_ "Tambayarka akayi? Aje ta inda ta buk'ata ta." Juyawa yayi yana fad'in "Yi hak'uri Elhaj." Ba jimawa ya isar da ita wurin, mik'o mata jakar yayi ta karb'a tace "Nagode sosai, Allah ya tsare hanya." Bud'ewa tayi har ta zura k'afa d'aya yace "Abun ba zaiyi dad'in ji ba daga bakina." Juyowa tayi da alamar tambaya ta kalleshi, d'aga mata gira yayi yace "Bana so da kaina na ce ki kawo kud'in mota?" Yar siririyar dariya tayi tace "Kaga kuma ban tab'a biyan kud'in mota ba ni, amma ba damuwa zan biya wannan karan, tunda na had'u da wanda yafi ni son kud'i." Wani murmushi yayi wanda yasa hak'oranshi fitowa, bud'e motar yayi ya fita hakan yasa ita ma ta fita, zagayowa tayi b'angaren da yake tsaye saboda anan k'ofar shiga take, kiraye kirayen sallah magriba da aka fara yasa ta kallonshi a nutse tace "Zan shiga ciki ana kiran sallah, ka gaida min yara." Cikin taushin murya yace "Ba zamu bar nan ba har sai munga tafiyarki." Girgiza kai tayi tace "Kasan kuwa yawon da nake a garin nan? Kar ka min kallon bak'uwar da zata iya b'acewa mana, kuje nagode da kulawa." Tunda ta fara magana yake sakar mata murmushi har ta kai aya sannan yace "Amana Kalli ya bamu saboda ya yarda damu, sai mun sadaki da gida kad'ai hankalinmu zai kwanta." D'aga masa hannu tayi da murmushi tace "Ok, sai anjima." Lumshe ido yayi alamar ya amsa mata, shigewa tayi inda ta isa wajen r茅servation, jim kad'an ta fito ta wuce inda motar ta take, shiga tayi da bismillah ta tayar ta fito. Daidai k'ofar fita nan ta same shi tsaye jingine a jikin motar, kallonshi tayi kallo na tsanake, sai yanzu ne ta ga wani irin kwarjinin mutumin, a gurinta Tagur ne namijin data sani mai irin wannan k'ira ta k'arfi, amma yau sai taga wanda ya dameshi har ya shanye, tunda wannan yafi Tagur tsayi da kuma kaurin jiki, hakan yasa rigar bla boyl d'in dake jikinshi daga saman k'irjinshi zuwa damatsenshi ta matse kamar zata yage. Murmushi ta saki ita kad'ai dan sai take tunanin to wa yaranshi suka biyo, shi dai gashi kana ganinshi zaka san yana da alak'a da irin larabawan nan na Alg茅rie ko kuma fulanin, jawur dashi har gashin kanshi ya laulauye. Amma kuma su Izzadeen basu da wannan hasken nashi da kuma kyawunshi, a ranta ta furta "Watak'ila uwarsu suka biyo." A hankali ta shigo tahowa har ta fito, saida ta tsaya kusa dasu ta d'an sauke madubin ta d'aga musu hannu alamar sai anjima, Qaseem da Adam ne suka d'aga mata hannun suma, ajiyar zuciya ya sauke ganin ta farfara da gudu ta harba motar kan titi, juyawa yayi ya bud'e motar ya shiga a ranshi yana ayyana dama corolla s d'in ce take kira da akori kura, a hakan ma sabuwa fil sai walwali take, shi motar ma birgeshi tayi ta yanda har yaji ba zai kwana ba saiya mallaketa saboda yanda yaga ta wa abar k'aunarshi kyau, suma hanyarsu suka d'auka zuciyarshi cike da k'uncin rabuwarsu, sai dai yau yana cikin farin ciki, kasancewarshi tare da yarinyar data shiga zuciyarshi a d'an k'ank'anin lokaci abun ya k'ayatar dashi, sunyi raha sunyi murmushi da dariya, zai yi addu'a Allah ya nuna masa ranar da zasu zauna haka a matsayin mata da miji. a masallaci suka tsaya sukayi alwala da sallah kafin suka fito, da wannan suka fara aje Adam bayan sunyi sallama suma suka k'arasa maradi stores yayi siyaya saboda yara suka wuce gida. ______________ Tun safe ya ga bai shigo ya gaisheshi ba, bai nemeshi ba saboda tunanin ko ya rigashi fita ne aikin sauri, haka da rana daya shigo cin abinci bai had'u da shi ba dan yasan yana zuwa shi ma, ganin har yamma daya dawo bai ga motarshi ba yasa ya tambaya yana ina? Saude ce tace mishi "Ai tun safe bai fito ba, da aka aika mishi abincin ma cewa yayi baya ci a dawo dashi, har yaron da ya zo dashi ma sai abinci yake aikawa ana siyo mishi sai makaranta idan ya kaishi." Ranshi a b'ace yace "Yo lafiya? Wani abun kuka masa halan? Kunga ni fa bana son haka wallahi, yara marayu dan uwarsu bata raye sai ku dinga musu abinda kuka ga dama." Tsaki yayi ya nufi k'ofar k'uryar falon da zata sadashi da b'angaren samarin yana fad'in "Haba, wannan ai zalinci ne, yaro da gidan ubansa abinci ma ace ba za'a lallab'a shi ya ci ba." Baki sake Saude ta kalli Harira tace "To! Kinga wani ikon Allah kuma." Tab'e baki tayi tace "Shiyasa dama na ce ba zan iya rik'esu ba, tunda na lura yanda uwarsu tafi soyuwa a wurinshi haka 'ya'yanta ma suka fi namu, da alama har yanzu asirinta na tasiri akan shi duk da bata raye." Girgiza kai Saude tayi tace "Harira ku dinga fad'an alkairi akan mutane, matar data mutu har yanzu kina kishi da ita, haba wace irin rayuwa ce?" Juyawa tayi ta shige d'akinta ita kuma ta bita da tsaki da harara. Ko da yaje bai tsaye ko sallama ba ya shiga d'akin, sun dawo daga masallaci kenan Amjad na shan chocolat yana masa rigimar ya kira mishi Ayyarshi, shi kuma baya son kiranta saboda yana so ta samu lokaci sosai da iyalinta, tunda ya ga ko WhatsApp bata duba ba yake jin tana cikin wani yanayi ne, sai dai farin ciki ko akasin haka bai sani ba, wannan fargaban yasa ya k'i kiranta. A tare suka kalli Alhaji daya shigo, a gigice ya zauna bakin gadon yana cewa "Kai Aminu lafiya aka ce baka fita ba yau? Zaman me kake a gida kamar wani mace?" Saida yayi kalar irin shagwab'ar nan ya turo baki gaba yace "Ni ba zan sake fita ba kuma na daina cin abinci ma." Zaro ido yayi yace "Me yasa? Wani kake tsoro a waje? Wanene?" Girgiza kai yayi yace "Ai kai ne Alhaji." Nuna kanshi yayi yace "Ni kuma! Me nayi Aminu? Wai me yasa kake so ne dole sai amanar Allah ta ci ni? Ka barni nayi farin ciki na zauna cikin salama mana." Kallonshi yayi yana danne dariyarshi sosai yace "Saboda ka k'i min abinda nake so." Hararanshi yayi yace "Kai bansan iskanci fa, me kake so ka zama ne wai? Maganar banza kake so ka sani nayi?" Kamar zai fashe da kuka ya kalleshi yace "Alhaji ban sonta ba, ka barni na auri wacce nake so ko kuma na mutu banyi aure ba." Matsowa yayi kusanshi yana fad'in "Kana..." Kafin ya k'arasa suka ga Amjad ya mik'e zai fita, kallonshi sukayi sai Aminu da yace "Ina zaka je? Zauna." Girgiza kai yayi yace "Obdo na ga kuna maganar da bai kamata ace akwai wani a tsakuyarku ba, ka barni na fita hakan zaisa kuyi sirri." Da kallo Alhaji ya bishi sanda ya fice, kallonshi yayi yace "Wannan shine yaronta?" "Shine Aba, kuma tarbiyarta ce." Ajiyar zuciya ya sauke ya kalleshi sosai yace "Aminu da gaske sai ita kake so? Kuma zaka iya aurenta ka zauna da ita?" Ba alamar wasa yace "Alhaji zan iya, da gaba d'aya zuciyata nake sonta, zan mori 'ya'ya idan har ita ce uwarsu." Kallonshi yayi na wani d'an lokaci kafin ya mik'e zai fita yace "Ka nemi abinci ka ci kaji, kar ka uwarka tayi hushi dani." Mak'ale kafad'a yayi yace "Um um! Ni ba zan ci ba sai ka amince." Harzuk'o mishi yayi yace "Dan ubanka idan baka ci abincin ba taya zaka samu k'arfin gudanar da shirye shiryen auren naka da ita." Wata dariya ce ta zo mishi tare da mik'ewa da sauri ya rumgumeshi yana fad'in " *Abba* nagode, nagode sosai Allah ya saka maka da alkairi." D'an dukan bayanshi yayi yace "Ja'irin yaro, wai shima yasan *so*." D'agawa yayi daga jikinshi yana sunkuyar da kai yana dariya, kallonshi yayi yace "Amma ka sani Aminu nayi hakane saboda kai, amma gaskiya akwai abinda na hango maka wanda ba lallai kai ka hangoshi ba." D'an kallonshi yayi yace "Insha Allah Alhaji babu abinda zai faru sai alkairi, ba yau muke tare da Faduma ba, nasan wacece ita da abinda zata iya yi, zaka yi farin ciki da tarayyata da ita insha Allahu." Jinjina kai yayi yace "Allah yasa." Da murmushi ya amsa da "Ameen." Ficewa yayi saida ya kalli Amjad dake zaune bisa dakalin dake zagaye jikin panpo sannan ya wuce. ______________ A k'ofar gidan yace ya tsaya, yana fita ya kalleshi yace "Ka iya tafiya, amma ka tabbatar k'arfe 08:00 na sameka anan." Jinjina kai yayi yace "Insha Allah Elhaj, Allah hutar da gajiya." Juyawa yayi ya tunkari shiga gidan, da sauri mai gadi ya isa gareshi ya sunkuya zai karb'i ledojin hannunshi, d'an janyesu yayi alamar baya so, gaishe yayi tare da mishi an zo lafiya? A tak'aice ya amsa da "Alhamdulillah." Ya wuce ciki, b'angarenshi ya nufi da tunanin me zai tarar, sai dai yana jin hayaniyar yaran a b'angaren Umma. Tun a k'ofar shiga yaji sautin tv wanda ya tabbatarwa kanshi da s茅rie d'in ta ne take kallo Avenida brasil, a hankali ya ci gaba da takawa harya shiga da sallama k'asa k'asa, gabanta ne ya fad'i dan wallahi ita ta manta ko kiranshi tayi taji ya suka je? Ta fara gyara gidan kuma amma da ta ga har magriba ta gabato bai shigo ba shi da yace zai shigo da yamma, saita d'auka halin tafiya ne ba zai shigo ba, sai kawai ta shiga sabgar gabanta ita ma. Mik'ewa tayi tana rarraba ido da kallon d'akin ta rasa ta ina zata fara, da k'yar ta kalleshi dai tace "Sannu da zuwa." Tsaye yayi yana kallonta da d'akin, ajiyar zuciya kawai ya sauke, gyaran salade d'in ne take a cikin tsakiyar falo, bayan dattin da d'akin yayi wanda ko rantsuwa yayi ba zaiyi kaffara ba in yace ba tayi shara ba tunda ya tafi, aje lodojin yayi daga inda yake tsaye ya tako, saida ya zo gabanta ya rumgumota jikinshi, ruf ya rufe idonshi yana sauke numfashi a hankali, tabbas mutum ne shi mai tsaftar gaske, sai dai bai cika k'yak'yami ba shiyasa ba yanzu haka bai ji warin daud'a da zufar dake fita daga gaba d'aya jikinta zuwa kanta dake cunkushe. K'ok'arin raba jikinta da nashi take yi saboda bata so yaji iskan dake fita a jikinta, cikin dubara tayi nasarar raba jikinsu, ja baya tayi kalleshi tace "Na d'auka ba zaka shigo yau ba ai." Ajiyar zuciya ya sauke yace "Kiyi hak'uri, ban kiraki ba shiyasa." Kallonshi tayi a ranta take ayyana kenan shima yana tunanin shine da laifi da bai kirani ba? Tab'e baki tayi tace "Ba komai." Yanda ya k'ura mata ido yasa ta ji ta tsargu, a hankali ya furta "Kinyi sallah ne?" Duk da k'arya ce zata fad'a amma da yake ba yau ne farko ba da saurinta tace "Um." Hanyar d'akinshi ya nufa yana fad'in "Bari nayi wanka sai naje na ga su Umma." Binshi tayi da kallo yana bud'ewa da makulli ya shige da sauri ta shiga tattare kayan, saurin take sosai wajen gyara falon har ta samu tayi shara, d'akinta ta wuce kayan jikinta da kayan baccin dake kan gado ta d'auke ta gyara gadon, ko da ta idar ta fad'a ban d'aki tayi wanka ta d'auro alwala. Tana fitowa ta shirya da sauri ta d'auki sallaya, saida tasa key a k'ofar d'akin dan gudun kar ya shigo tana tsaka da yi. Har ta idar ta fito ta koma madafa ta samu ta k'arasa gyaran salade d'in bai shigo daga wajen Umma ba duk da anyi sallah isha'i. Tare da yaran suka shigo suna hira, zaune sukayi kan kujera yana kallonsu yanda suke ta fito da kayan daya shigo dasu yace tsarabarsu ce, saida suka gama fitar dasu kowa ya shiga d'auka yana fad'in nashi ne nashi ne. K'arasowa tayi ta tsaya gabanshi tace "Na kawo maka abinci ne?" Jinjina kai yayi alamar eh, juyawa tayi dan kawo masa, d'auko kayan tayi ta aza kan k'aramin tebur d'in ta jawoshi gabanshi, saida ta zuba ta gyara mishi komai ta koma ta zauna nesa dashi tana kallonshi. Tambayar kanta take idan abinda ya faru da wata k'awarsu ya faru da ita fa? Mijinta daga zuwa aikin koyarwa wani k'auye yayi aure babu wanda ya sani, Hasheer d'inta yayi haka ai sai ta had'e zuciya ta mutu, ba zata iya rabashi da yar uban ko wacece ba, ba zata iya kishi da wata akan shi, mad'aukakin so take masa da zata iya yin komai a kan sa, daga ciki kuwa harda salwantar da rayuka, ita tasan waye mijinta ta san mafificin sirrinsa, ko na dare d'aya ba zata bari wata ta ga wannan sirrin ba bare har ta ci alfanunshi ita ma, ba zata iya cewa saida ya aureta yayi kud'i ba ko kuma sunyi rayuwar k'unci a baya ba, dama can da nasibinshi ta ganshi, hab'aka ne kawai arzik'inshi ke sake yi musamman bayan rasuwar mahaifinshi, sai dai yanda ta fara zama a cikin gidan nan, yanzu kuma yake wani mahaukacin gini a kusa dasu, ginin daya d'auki lokaci ana tsarashi da kashe mishi milyoyin kud'ad'e kamar ba gobe, ginin da tun ba'a gama ba ake maganar shi a cikin unguwar da ma wasu wurare, ginin da duk wani matashi mai kud'in da yayi niyyar gasa dashi tattalin arzik'inshi ke samun tawaya, ginin da matasan da basu da sisi idan suka gani suke fatan Rabbi ya basu kaso d'aya a cikin ukun shi, ba zata tab'a yarda su koma can ba haka kawai yace zaiyi aure, Allah saita k'ona gidan da duk abinda ke cikinshi, idan ya so ita ma ta mutu. A nutse ya fara cin abincin duk da bashi ya so ace ya ci ba, abu mai zafi sosai da ruwa ruwa ya so, amma ta had'ashi da salade da had'in kabeji da tumatir da k'wai sai farar shinkafa, abun ya masa dad'i a baki sosai, dama kuma baya jin Saudat ta wannan fannin, matsalar bata cika zage damtse ta dafa abinda zasu ba kullum sai randa ta ga dama. ______________ Bayan sallah azahar saida ya sake dawowa ya tura yaro yace a kira masa Faduma a gidan, tunda Dada taji haka tayi mamaki saita fito da kanta, tana zuwa taga shine ta nuna shi tace "Kai Tagur! Dawowa kayi? Maza ka bar nan k'ofar gidan, inba haka ba fa." Girgiza kai yayi yace "Dada dan Allah kiyi hak'uri ki saurare ni, bana zo bane dan tashin hankali, ni Amjad kawai nake son gani na koma." A hassale tace "Ba zaka ganshi ba, nace ba zaka ganshi ba, kai in banda rashin kunya da fitsara har zaka iya kiran yaron nan da yaronka?" Numfashi ya furzar yana had'e abinda ke ranshi, yana jin kunyarta sosai shi yasa baya iya cewa komai ba, amma yana mamakin yanda take ragargaza masifa haka, dan had'uwarshi ta farko da ita sanda yaje gaishe da yan uwan Faduma lokacin babbar sallah ba haka take ba, lokacin ta zo sallah gida ita sanyi sanyi ya ganta suka gaisa, ashe ta iya fad'a da bala'i haka ita ma. Ajiyar zuciya ya sauke ya kalleta yace "Dada nasan da Amjad d'ana ne, ganinsa nake so nayi kawai shima ya ganni, amma fa idan aka kaini bango zan karb'eshi ne gaba d'aya, tunda dai nawa ne kuma kuma kunsan da haka, sannan zan had'u da ita Faduma." Yana fad'a ya bud'e mota ya fad'a ya bar unguwar yana jin haushin komai, yana hangenta ta madubi tana masifa da bala'i tana fad'in ya jaraba karb'arsa ya gani mana. _____________ Kamar yanda ta masa alk'awari kai tsaye gidansu Aminu ta wuce, tunda take sau d'aya ta tab'a shiga gidan duba Aminu sanda yayi rashin lafiya, dan haka da ta zo saita kasa shiga ta kirashi a waya, d'auka yayi ba tunanin tana garin ya mik'awa Amjad wayar yana fad'in "Ku gaisa da Ayyarka." Karb'a yayi jiki na rawa kamar zaiyi kuka yace "... *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 17:13 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _26_ "Ayya kin manta da oddo d'inki ko?" Murmushi tayi mai sauti tace "Maganar nan ba daga zuciya ko tunaninka ta zo ba oddo, labb'an bakinka ne kawai suka fad'a." Shagwab'ewa yayi yace "Amma shine kika shareni." Ita ma cikin shagwab'a kamar zatayi kuka tace "Ni ba shareka nayi ba, yanzu fad'a min ya kake?" A hankali yace "Ayya bana jin dad'i saboda bana tare dake, amma kuma obdo Aminu yana min komai, ina farin cikin zama dashi." Ajiyar zuciya ta sauke tace "Na sani Amjad, nasan zai maka fiye da haka ma indai shine." "Ayya yaushe zaki dawo?" Ya fad'a da sauri, murmushi tayi tace "Ko yanzu kake son gani ma zan iya fito maka a gabanka." Dariya yayi yace "Ayya kenan, da alama kina cikin farin ciki ko?" Walwala idonta tayi tana sake nanata tambayar a zuciyarta, farin ciki kuma? Tabbas tayi farin cikin ganin iyayenta da yan uwa da tarbar data samu, rashin jin dad'in kawai yanda bata canzata ko kalmar a ba da mahaifinta ba, hasalima tunda ta kalli fuskarshi sanda ya shigo gidan basu sake had'uwa ba, hakan yasa zuciyarta cunkushewa duk taji ba dad'i, a gaskiya bata san me ya jawo farin cikin nata ba. Dan haka tace mishi "Da gaske nake Amjad, kana so ka ganni ne?" Da farin ciki yace "Eh Ayya ina so." Da dariya tace "To rufe idonka sai kace obdo Aminu ya fito da kai waje, ka d'aga kanka daga saman bishiyar nan zaka ganni ina maka murmushi." Dariya ya k'yalk'yale da ita yace "Kai Ayya! Tsafi zaki min?" Ita ma dariyar tayi tace "Ba tsafi ba, siddabaru dai." Kallon Aminu yayi dake tsaye yana kallonshi yace "Obdo wai ka kaini waje." Murmushi ya masa ya kama hannunsa yace "Tabbas bazata zata mana." Fitowa sukayi a tare, tana tsaye a jikin motar tana kallon k'ofar gidan, yana ganinta ya daka da gudu ya rumgumeta yana fad'in "Ayyata, ashe kin dawo dama?" Rumgumeshi tayi sosai tana rufe idonta, sumbatar kanshi tayi tana sake mannashi a k'irjinta cike da so da k'auna, k'arasowar Aminu tasa ta d'aga ido ta kalleshi tace "Barka." Da mamaki yace "Ya kika dawo yau kuma? Lafiya?" Numfashi ta sauke tana kallonshi tace "Lafiya lau, ya hidima da wannan jaririn nawa?" Murmushi yayi yace "Nayi iya k'ok'ari na, amma rainonki daban ne Faduma, jajirtacce ne kawai zai iya kwatankwacin yanda kike yi." Dariya tayi wacce ta fito da fararan hak'oranta tana girgiza kai kawai, d'ago kan Amjad tayi tace "To ya zamu tafi nr ko kuma na bar ka har zuwa gobe?" Juyawa yayi ya kalli Aminu, kallon Faduma yayi yana murmushi yace "Ayya kinga baiyi tsammanin tafiyata yau ba, ina so na tafi dake amma kuma bana so yace ban kyauta masa ba, dan haka ki bari na kwana gobe saina koma." Dariya dukansu sukayi sai Faduma data kama bakinta ta matse tana fad'in "Heyyy oddo, halan ice cream wannan bakin ya samu yake sha?" Cikin dariya yana sunkuyar da kai yace "Yana siyo min kayan alatu kam Ayya, amma dai ba dan haka zan kwana ba." Aminu dake ta dariya ne yace "Ka kyauta yanzu kam Amjad." D'aga gira Amjad yayi ya kalleta yace "Kin gani ko Ayya, dama nasan haka zai fad'a." Shafa kanshi tayi tace "To shikenan ni zan tafi, dada na can yanzu nasan tayi kewarmu sosai, dama alk'awarin da nayi cewa nan zan fara biyowa yasa na taho, ka shiga ciki zanyi magana da obdo." Jinjina kai yayi yasa hannayenshi biyu ya jawo fuskarta ya sumbaci kumatunta, d'aga mata hannu yayi ya shiga ciki tana fad'in "Saida safe oddo, ka kula min da kanka sosai, idan kaje zan baka tsarabarka." Cikin tausasawa yace "To Ayya saida safen." Yana shigewa Aminu ya matso ya jingina a motar yana kallonta, ita ma jingina tayi nesa dashi kad'an tana kallon titi tare da rumgume hannaye, ajiyar zuciya ta sauke tace "Aminu naje gida lafiya na samu Ayyoyina kuma sun karb'eni lafiya, haka ma duka yan uwana kamar babu wani abinda ya faru,sai dai Aba ko fuskata bai kalla ba, babu kalmar data shiga tsakanina da Aba, dana so kwana uku ma shi ya hana yace na dawo, shiyasa ka ganni yanzu." Girgiza kai yayi yace "Kiyi hak'uri Faduma, insha Allahu wata rana sai labari, ina tabbatar miki komai zai wuce kamar ba ayi ba, Ana ma na tabbata ba hushi yake dake ba har yanzu, kawai dai bai saki jiki dake bane." Wani murmushi tayi tace "Haka Ayyata ma tace." Cike da son tabbatar mata yace "Hakane mana Faduma, ai babu wanda zai k'i abinda ya haifa." Girgiza kai tayi tana tab'e baki tace "To, zan ci gaba da addu'a har sanda zai juyo kaina." Gyara tsayuwarta tayi tana juya makullin hannunta tace "Ni zan wuce gida Aminu gashi har an idar da sallah, sai zuwa goben idan Allah ya kaimu." Jinjina kai yayi yace "Ba damuwa Allah hutar da gajiya." Bud'e motar tayi ta shiga daga ciki amma bata rufe ta laluba jakarta, enveloppe d'in daya bata wacce ba tayi komai da ita ba ta fito da ita, kallonshi tayi ta fito tsaye ta mik'a masa tace "Kai kasan ba ma haka da kai, me yasa zaka min haka Aminu?" Had'e fuska yayi yace "Ke me kike nufi to?" D'aga masa gira tayi tace "Ka rik'e abunka." Wata harara ya watsa mata yace "Ina wasa dake ne Faduma?" Kusan sakin bakinta tayi tsabar mamaki, har ga Allah sai taji wani shakkarshi, kamar ba Aminun data saba gani ba suke tsokanar juna, lallai namiji zai iya juya mace komai girmanta, duk da dai Aminu zai iya kai tsaran yayanta Manu dan ya girmi Barka, amma kuma a kallo na zahiri zaka iya cewa zata fi k'arfinshi ko kuma ajinshi, dan shi siriri ne dogo amma kuma kyakyawa ne sai duhun fatarshi ma mai kyau, ita kuma tana da kauri da kuma tsayi ita ma. Kasa musa mishi tayi sai komawa da tayi ta zauna tana kallonshi tana turo baki, da kallo ya bita yana d'aga mata hannu ta bar unguwar. _______________ Ya shiga tashin hankali da rud'u sanda yake fad'a masa tabbas Amjad d'ansa ne, da mamaki ya kalleshi yace "Amma Tagur me yasa a baya ka ce ba d'anka bane? Kasan me kayi kuwa?" A hankali ya girgiza kai yace "Nima nasan ban kyauta ba, wallahi a lokacin su Aba nake tsoro, ban san ya zasu kalli al'amarin ba." Cikin jin haushi yace "Amma me yasa baka yi tunanin ita yarinyar ba? Tagur dalilin haka fa ta bar gidansu tayi nesa da iyayenta, me yasa ka zama mai son kanka dayawa? Ka lalata rayuwar yarinya da sunan soyayya, wannan ita ce soyayyar dama? Haka ake so a garinku kai?" A zafafe shima ya kalleshi yace "Wai kake so nayi ne Aji? Kaina a kulle yake kai kuma ka sani gaba da masifa, mafita nake nema yanzu ba wannan masifar ba." Hararanshi yayi yace "Masifa ce ma? Gaskiya ce ni nake fad'a maka Tagur, baka kyauta ba k'arshen rashin kyautata ma kuwa, wallahi ko shakka babu hakk'inta ne ke bibiyarka shiyasa har abinda ya faru a kotu ya faru." Mik'ewa yayi tsaye yace "Kaga ni fa har yanzu ban yarda da abinda ta fad'a ba a kotu." Tab'e baki yayi yana kallonshi yace "Me yasa zata maka k'arya yanzu? Kai a tunaninka in tana son d'aukar fansa a kan ka bata san yanda zatayi bane shiyasa ta fake da wannan shari'a? Kaga Tagur ni yanzu bansan me zan iya yi maka a game da maganar nan ba, abinda nake so da kai shine karka sake zuwa inda take kace wai kana son ganin d'anka." Da k'arfi yace "Me? Kana lafiya kuwa? D'an nawa? Hhhhhh!" Mik'ewa yayi shima ya zagayo ta inda yake tsaye yace "A gaban wa zaka iya dukan k'irji ka fad'i haka? Kasan da ko yaro k'arami zai iya muku alk'alanci akan maslahar nan, Tagur baka da gaskiya, kuma inhar ka ce zaka ci gaba da kiranshi d'anka a yanzu, to duniya ce zata san asalin waye kai, ba ka guji yaron saboda matsayinku da muk'aminku ba, to ka sani kana daf da tonawa kanka asirin daya sa ka k'i karb'ar yaron a waccen lokcin." Daf da shi ya matso yace "Aji, na zo wurinka ne na fad'a maka duk abinda ke faruwa saboda kai d'an uwana ne yayana sannan aminina, amma shawarar nan taka sam bata min ba, daga Amjad sai Ridwan ne na mallaka a duniya, ba zan yarda nayi rik'on al'amarinsu da sauk'i ba." Wata dariya Aji ya bushe da ita ya juya ya koma kan kujerarshi yana juyata yace "Ai kuwa zaifi kyau ka fara neman wani d'an, dan a yanzu dai duk babu naka a cikin biyun nan." Girgiza kai yayi yace "Wallahi ba dan ina ganin girmanka ba da sai na zubar maka da hak'ora, ka sani Amjad da Ridwan duka ya'yana, na ga kuma mahulukin daya isa ya rabani da su." Kallonshi yayi yace "Tagur, karka sa mu fara tunanin had'arin da kayi yasa ka rasa tunaninka, ka bi komai a hankali kaji." Tsaki yayi ya juya zai fita yana fad'in "Ni karka b'ata min rai dan Allah." Har ya kai k'ofa Aji yace "Kaga!"Juyowa yayi yana kallonshi a k'ufule, d'orawa yayi da cewa "Ya kamata ka samu Aba kuyi magana dashi, dan a sai abu ya kwab'e ba sannan ya ji." Hararanshi yayi yace "Me zai hana kai ka fad'a masa?" Girgiza kai yayi yace "Kasan ni ba wani shiri muke ba yanzu tunda muka rabu da Aisho, gaba d'aya ya d'ora min laifin a kaina, shiyasa ni ba wata shiga sabgarsa nake ba sai dole." Girgiza kai yayi yace "Ai laifinka ne, kai ma ka k'i yarda da laifinka ne saboda babu abinda ya dameka daya wuce kasuwancinka da kuma siyasarka." Cike da rashin damuwa yace "To ya zanyi, nema ya zama dole, siyasa kuma kamar numfashina ce, ita na tashi naga anayi a gidanmu." Saida ya dawo baya yana kallonshi yace "Saboda ta zama numfashinka ne yasa ko 'yar daka haifa baka damu da ita ba? Yanzu haka fa Khairat na daf da mantawa da kalar fuskar mahaifinta." Wani shak'iyin murmushi yayi yace "Banda matsala da hakan, na sani dai duk tsiya dole wata rana za'a nemeni saboda ni ne ubanta." Sama da k'asa ya kalleshi yace "Wannan shine tak'amarka? Amma ta kalleka da daraja ma ai da dad'i ko?" Wani murmushi ya kuma saki yace "Wai kai ne zaka fad'a min haka? Kamar ba yanzu bane muke tattaunawa kan abinda ya shafeka, ai gwara ni da sauk'i ma, tunda babu abinda ban ma 'yar ba, kuma ko yanzu da uwarta zata turo min sak'on Khairat bata da lafiya kai ka sani zan ji da lamarin ne." A wulak'ance yace "Eh na sani mana, iyaka dai ka tura mata da kud'i kace tayi duk abinda ya dace, car ta gama rashin lafiyar ta warke ba zaka taka k'afarka kaje ka duba ta ba." Juyawa yayi ya fice a ofishin nashi ranshi b'ace, shi ma da harara ya rakashi yana jan tsaki, sai dai kuma zuwa anjima zaka iya ganinsu kamar basu rabu rai a b'ace ba. Daga nan gida ya wuce dan tunda safe aka sallami Hatimi. Bak'uwar motar daya gani yasa shi nufa b'angaren Hatimi, amma da ya so shigewa b'angarenshi saboda tunda abun nan ya faru bata wani kula shi sai zuba masa ido kawai, sake tura k'ofar yayi yana sallama a bakinshi. Da wata tattausan murya aka amsa mishi, shiga yayi yana kallon matashiyar dake zaune kusa da Hatimi, baiyi mamakin ganinta ba, dan tunda ya dawo daga karatu take bibiyarshi, sarai ya fahimci manufarta akan shi, amma saiya shareta kawai har saida mahaifinshi ya rasu, lokacin da aka mishi maganar aure kuma Gomboy ce ta mishi shugabancin had'a shi da Atta, amma har lokacin bata daina nuna mishi soyayyarta a fili ba, haka kawai zata zo gidan da sunan ziyara, dan wata rana ma har saida sika d'anyi cacar baki da Atta data lura da take-takenta. Mamakin yanda ya ganta a wannan lokacin yake. Tab'e baki kawai yayi ya k'arasa kusan Hatimi dake zaune da pillow a bayanta, saida ya zauna a hankali kusa da ita yana kallonta yace "Ayya ya jikin?" Kafin tace wani abu Husna da idonta ke kanshi tunda ya shigo tace "Ina wuni yah Tag." Kallonta yayi sama da k'asa a k'asan mak'oshi yace "Da dama." Cike da kwarkwasa tace "Ya jikin Ayya? Ashe bata ji dad'i ba? Nima d'azu da safe Aisho ke fad'a min a waya, shiyasa na zo naga jikin nata." Tunda ta fara magana yake kallonta a kaikaice yana yatsina fuska, tana dasa aya yace "Uhum!" Girgiza kai yayi ya kalli Hatimi dake ta kallon Husna tana murmushi yace "Ayya ba kya jin komai yanzu?" Kallonshi tayi a hankali tace "Tagur, me yasa ka mana haka? Me yasa baka fad'a mana gaskiya ba? Kai kasan yanda na tsani yarinyar nan kuwa." Cikin jin haushi ya mik'e tsaye yace "Dan Allah Ayya kiyi shiru, ba yanzu ya kamata muyi maganar nan ba." D'agowa tayi daga jikin kujerar tace "Sai yaushe kenan?" Cikin kumburo baki yace "Ki bari kiji sauk'i tukuna, amma fa Ayya ki daina cewa kin tsaneta dan Allah, ita d'in fa yanzu uwar jikanki ce." Fitowar Aisho rik'e da kwanukan abinci yasa shi juyawa ya kalleta, hanyar fita yayi yana kallonta yace "Ke ki shirya Khirat anjima zamu je gidan obdo." Da ido kawai take binshi duk wani motsi nashi na birgeta, komai na shi tana son shi, tana son shi tun lokacin da aka so had'a aurensu, tana muradin kasancewa matarshi, tana so ta zauna a k'ark'ashin inuwa d'aya dashi a matsayin ma'aurata. K'irarshi ta masu k'arfi da sauk'ak'akk'en kyawunshi, kalar fatarshi mai duhu da gyaran da take samu, karkataccen harshenshi wanda ke d'auke da yare kala hud'u yana birgeta, idan yana yarenshi na haihuwa sai kaji kamar k'aramin yaro na magana, idan yana hausa ma zaka san harshenshi bai gama nuna ba, haka idan yana french ko inglish wanda duk sai kaji ya birgeka. Bak'in leb'enshi take kallo mai fitar da zafafan kalaman wanda zaka rantse mashayin sigari ne, sai dai haka halittarshi take bak'i ne kawai, ga wani masifaffen gemu daya aje had'e da saje da suka haska fuskarshi, ita ma fitowar Aisho ce ta ankarar da ita ta d'an dawo hayyacinta. Tunda taji yace haka ta gane kakan Khairat d'in yake nufi *Bureima* (A baya nayi kuskure wajen saka sunan kakan Khairat, madadin na ce *Aji Bureima* sai nace *Aji Sugui*), sai dai bata san me yasa zaiyi haka ba, ita dai tasan abokai ne shi da yayan nashi Aji, tana tsoron kar dai zai rabata da ita ne? Amma kuma tasan Tagur ba zai mata haka ba, dan haka saida ya fice kafin ta k'araso ta aje kwanukan, kallon Husna tayi data bishi da kallo tace "Husna sauko ki ci abinci." Kallonta tayi tana murmushi tace "Amma shi ya ci?" Hararan wasa ta masa tace "Lallai ma matar nan, kina nufin ba zaki ci ba idan bai ci ba?" Murmushi ta sake yi ta sunkuyar da kanta, dafa kafad'arta Hatimi tayi tace "Zauna ki ci abinci kinji, idan yana buk'ata zaki ga ya nema da kanshi." A marairaice ta kalleta tace "Ayya!" Jinjina mata kai tayi tace "Karki damu kinji." Tab'e baki Aisho tayi tace "Ya kamata dai ki dinga sassautawa kanki soyayyar bawan Allahn nan, wannan ai sai ki kashe kanki." Turo baki tayi tana kallonta tace "Babu ruwanki ke dai, ai ba zuciyarki bace." Jinjina kai tayi tace "Gaskiya kam, to Allah ya bada sa'a." Murmushi Hatimi tayi tace "Karki damu kinji 'yata, insha Allahu wannan lokacin sai yayi abinda nake so, ba zai tab'a tsallakewa ba wannan karan saiya aureki ko baya so." Wani murmushi ta watso mata tace "Da gaske Ayya? Amma naji dad'i." Cike da bata tabbaci tace "Insha Allahu wannan alk'awari ne." D'aga kai tayi alamar to kafin ta d'ora da "Amma Ayya ina tsoron kar yah Tag ya k'i amincewa, dan yanzu ma naji yana wata magana." Girgiza mata kai tayi tace "Kar ki damu da abinda kika ji yanzu, kuma amincewa ma dole ne, indai ni ce uwarsa kam babu abinda zai hana aurenki dashi." Wani far tayi da ido ta huro iska, aje jakarta tayi kan kujerar ta cire hijab d'in jikinta ta zauna k'asa, gyara zamanta tayi ta saka kwanon tsakiya ta fara tsakurar abincin, Aisho dai kallonsu take da mamakin wannan rayuwa tasu, kina mace kina ta kutsa kanki ga namiji, mahaifiyarshi na d'aure miki gindi, har fa abubuwan da yake so take nuna mata ita kuma tana yi, hatta da saka hijab ita tace indai zata had'u dashi ta dinga sakawa, abun takaici kuma kwalliya ta k'i biyan kud'in sabulu har yanzu. ______________ Da farin ciki ta shiga gidan tana sallama, Dada da bata tunaninta da mamaki ta fito daga d'aki tana amsa sallamarta tare da d'orawa da " Wai Faduma ce? Daga ina haka ke kuma?" Dariya tayi tana nufa d'akin tana fad'in "Nice dada, kinyi mamaki ko?" Mamaki fal a fuskarta tace "Yo Faduma ya kika dawo yau ke da kika ce zaki kwana hud'u? Lafiya?" Saida suka shiga ciki ta aje jakarta ta shiga warware lafayarta tana fad'in "Na dawo dai Dada, dama tun kafin na yafi Aba yace musu saida na dawo da an d'aura aure, shiyasa kika ganni yau." Girgiza kai tayi tace "Yanzu Abanki ba zai sauko daga inda ya hau ba kenan? An tab'a rayuwa haka fissabillilah." Murmushi tayi ta nufi hanyar fita tana fad'in "Dada hakan ma fa daya min banyi tunani ba, karki damu wata rana da kanshi zai neme ni." "Allah yasa." Ta fad'a cike da jimami, alwala ta d'auro ta dawo ta kabarta sallah magrib har ana isha'i ma, gaba d'aya tayi sai shaf'i da wutri data bari sai anjima, wanka ta shiga tayi ta shirya a sauk'ak'e, tana fitowa dada ta aje mata abinci, sosai ta ci ta k'oshi dan tana jin yunwa, tana ci kuma suna hira tana fad'a mata abinda duk ya faru, saida ta gama bata labari ta kalleta tace "Allah ya sakawa Herde da alkairi, a gaskiya matar nan yar aljanna ce, da zamuyi koyi da ita tabbas da babu wata kalma ita wai *kishiya* a duniya." Jinjina kai Faduma tayi tace "Gaskiya ne Dada, ko kad'an bata d'aukar Ayyata abokiyar zamanta, mu kuma data haifa kallon yayan data haifa take mana, shiyasa nake sonta kamar yanda nake son Ayyata." "Gaskiya kam, abinda zaku iya yi mata kenan." Shiru ne ya d'an biyo baya kafin tace "To Amjad fa? Kunyi waya ne?" "Eh dada na je can ma, kuma da kanshi yace na barshi can har gobe sai ya dawo." Dariya tayi tace "Da alama Aminu ya sangarta miki shi da kayan k'walam." Ita ma murmushi tayi tace "Nayi tunanin haka nima, dan nasan Aminu zaiyi k'ok'arin ganin ya faranta masa rai ne." Cikin murmushi Dada tace "Dole ne mana, baki ji ance *ma so uwa ya so d'anta ba*, ai mai son tsuntsu shi ke binsa da jifa." Dariya tayi ba tace komai ba ita dai har ta mik'e ta wanko hannayenta ta dawo ta zauna tana shan ruwa, cike da tabbaci Dada tace "Wallahi Faduma gaskiya nake fad'a miki, Aminu yana sonki kuma ke fa kin fahimta kawai kina b'oye sanin ne." Saida ta sauke kofin daga bakinta ta kalleta tana sauke numfashi, a hankali tace "Dada, idan Aminu yace yana so na zanyi maraba da shi, abinda nake gudu kawai shine matsala, Dada bana son wani abu ya biyo baya wanda zai shafi mutumcina, bana son a sake cin zarafi na a karo na biyu akan k'azamtar dake tare dani, Dada a waccen lokacin nayi shiru saboda banda wayo da hankali da kuma zuciyar sanin ciwon iyaye, amma a yanzu dana san miye haihuwa, na d'and'ani zafin nak'uda na kuma lasa zumar dake cikin ni'imar haihuwa, ba zan juri a ci zarafin iyayena ko yarona ba, shiyasa kika ga bana maganar soyayya, nasan aure dole indai ina da rai da lafiya, ina son raya sunnar ma'aiki nima, abinda zai iya faruwa ne kafin faruwar hakan nake dubawa." Cike da gamsuwa tace "Hakane Faduma, kuma nima ban k'i ta taki ba, nasan za'a iya samun kowace irin matsala, amma duba da yanda kuke da Aminu, ya sanki ya san komai naki kuma a hake yake tare dake, ina ganin kamar ba za'a samu matsala daga gareshi ba." Cikin nutsuwa tace "Hakane Dada, nima ta b'angarenshi bana jin za'a samu matsala, amma fa Aminu yana da mahaifi da kuma matar da yake kallo a matsayin uwa, kinga kuwa ba zamu ce matsala ba zata auku ba." Ajiyar zuciya ta sauke tace "To, Allah ya shige mana gaba." "Ameen." Ta fad'a tana jawo jakarta dake nan kan kujerar, wayarta ta d'auka ta d'an shiga WhatsApp dan tun daren laraba rabonta da shiga. _______________ Dukansu yanayin na musu dad'i ganinsu tare suna hira, Umma nutsatsiyar mace ce mai dattako da haiba, nad'in larabawan dake kanta ta sake gyarawa tana ci gaba da jan carbinta tana kallonsu tana ta doka murmushi, rigimar Salima autarta data Mukhtar suna sakata dariya sosai. Sai Halima da ita ma ke ta dariyar tana goyawa Salima baya, shi kuma Mukhtar sai cika baki yake yana fad'in "Wallahi duk ranar da kika kaini bango a gidan nan na fara zundumo larabci ke sai kin raina kanki a gidan nan." Dariya ta mishi tana mishi gwalo tana fad'in "To inba tsoro ba jaraba mana tun yanzu, ko gaisuwa ce muyi da larabci a gani." K'wafa yayi yana jinjina kai yace "Haba ki ci gaba, ai Umma ma tasan na iya shiru kawai take miki." Kallon Umma tayi tace "Wai Umma? Dan Allah idan ya iya me yasa baya yi? Shi fa banfa爻亘丕 丨 丕賱禺賷乇, 爻亘丕 丨 賳賵乇 babu abinda ya iya." Da sauri yace "K'arya ce na iya 賰賷賮 丨丕賱賰, kuma na iya tambayar suna ma 賲丕 丕爻賲賰 da 兀,賷賳 鬲匕 賴亘,兀匕 賴亘 廿賱賶 丕賱爻賵賯,丕賱丨賲丿 賱賱賴 賲卮丕丕賱賱賴." Dariyar da aka tintsire da ita a d'akin ne yasa shi yin shiru yana kallonsu shima, shi fa da gaske k'ok'arinshi yayi, amma sai ya ga har da wannan bai damu da dariyar ba ma yana masa dariya, hararansu duka yayi ya kalli Hasheer yace "Idan abun sauk'i ne dashi kai ma kayi irin nawa mana, kaga malamai zaku wani tsaya kuna min dariya." Umma ya kalla yace "Umma duk laifinki ne da ba kya mana yaren." Girgiza kai tayi tana ta k'ok'arin dakatar da dariyarta tace "Ni ba laifina bane, ku mazan kunfi zama tare da mahaifinku ne yana muku hausarshi shiyasa, matan kuma suna tare dani kullum dole suka iya yarena, amma kaima dan baka da kan fahimta ne shiyasa, yanzu babbanku dake yasa kanshi ai ya iya." Kyab'e fuska yayi kamar zaiyi kuka inda suka sake wata dariyar Salima harda rik'e ciki an ce mishi baya da kai, kallon Hasheer ya sake yi da tuni ya had'e dariyarshi saika rantse ma yayi nisa a tunani yace "To yayi mana, ni ban tab'a jin yayi ba." Kallonshi yayi yace "Idan banyi ba fa?" D'aga kafad'u yayi yace "Sai mu yarda baka iya ba." Murya a dak'ile yace "A tafi a haka to, mai kan kwakwa." Zaro ido yayi yace "Kam bala'i, ni ne mai kan kwakwar?" Jinjina kai yayi yace "Zamu had'e." Halima ce tace "Ai ni Akhi kai nake mamakin ka ma da sam baka ma su Izzadeen, duk hausa ta k'wace harshensu." A kaikaice ya kalleta yace "Nima ai bahaushe ne, mahaifiyata ce kawai balaraba, idan suna so zasu koya da kansu." Kallon Mukhtar yayi yace "Muje mu fara duba aikin nan." Mak'ale kafad'a yayi yace "Kaje kayi kai kad'ai mana inba tsoro ba, ba yanzu ka gama kirana mai kan kwakwa ba?" Dakatawa yayi daga shirin mik'ewar da yayi ya zuba masa ido, da sauri ya mik'e yana fad'in "Muje to oga." Mik'ewa sukayi zasu fita kuma Mujaheed ya shigo, duk tsayawa sukayi sai kallon kallo da aka shiga jefawa juna, lumshe ido yayi ya bud'e akan shi, so yake ya kauce mishi a hanya ya wuce, amma shima ya tsaya kikam ya k'i matsawa, Mukhtar ne yace "Malam matsa mu wuce ko." Nuna shi yayi da yatsa yace "Kai kar ka min iskanci, ni ba da kai zanyi ba sai dai yayan naka." Kallon Hasheer yayi yace "Malam wurinka na zo, maganar kampanin nan yaushe ne za'a rabashi kowa ya kama kasonshi? Dan ni banda ra'ayin aiki a wani kampanin sarrafa atampopi da sauran kayan mata, ayi kasafi kawai aban nawa kason." Wani kallo ya masa kamar mai jin bacci, a hankali ya d'aga labb'ansa da yake matuk'ar jin nauyin d'agasu yace "Matsa min a hanya." Hararanshi yayi ya kauce a hanyar yana fad'in "Na matsa, amma ka sani wallahi saika raba ko ba kwa so, wannan ai zalinci ne, shima Baba banda son zuciya da nuna fifiko, taya tun kafin ka mutu zaka mallaka abubuwa dayawa akan wasu, to ba zan yarda ba ni dai wallahi sai an bani hakk'ina." Suna jin shi babu wanda ya kulashi har suka wuce, ciki ya shigo shima ya kalli Halima yace "Ke d'auko min abincina." Mik'ewa tayi a kasalance ta nufi madafar, ko kallonshi Umma ba tayi ba ita ma har Halima ta kawo mishi ya juya ya fita yana fad'in "Yau ma zaman munarficin da cin nama na ne akayi ko? To ni dai kurwata tafi k'arfinku wallahi jajayen banza." *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 17:13 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃懇鈥嶐煢煈┾€嶐煢煈┾€嶐煢煈┾€嶐煢煈┾€嶐煢煈┾€嶐煢煈┾€嶐煢煈┾€嶐煢煈┾€嶐煢煈┾€嶐煢� *MAKAUNIYA* 馃懇鈥嶐煢煈┾€嶐煢煈┾€嶐煢煈┾€嶐煢煈┾€嶐煢煈┾€嶐煢煈┾€嶐煢煈┾€嶐煢煈┾€嶐煢煈┾€嶐煢� _Masha Allah uwar jaririyata Barka da kammala wannan novel makauniya, tausayi, yaudara da cin amana, wa'azantarwa nishad'antarwa da kuma tsarkakakkar soyayya duk ya taru a ciki, Allah ubangiji ya baki ladar fadakarwa ya yafe kurakurenki yasa muyi tarayya a ladar. Sai mun had'e a k'arshen *Mage* Insha Allah._ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _27_ Sun jima suna aiki a d'akin Mukhtar har kusan k'arfe 12:50 na dare, a gajiye ya kalli Hasheer yace "D'an uwa wallahi fa na gaji haba, kai ma kaje ka kwanta naga har tafiya kayi ka dawo ban ga ka huta ba." Ba tare daya kalleshi ba ya had'e takardun da suka zana wanda ya mishi kyau ya mik'a mishi yace "Ka aje wannan zuwa safe." Karb'a yayi yana zubasu cikin jakarshi dake gefe, a tsanake ya kalli Hasheer daya mik'e yana d'aukar wayarshi zai fita yace "Akhi." Dakatawa yayi ya zuba masa ido, cikin sanyaya murya yace "Me zai hana ba zaka fad'awa Mujaheed komai bane game da kampanin nan? Ina ga bai kamata ace yana ci gaba da kallon kampanin nan ba a matsayin abun gado ba." Guntun tsaki yayi ya juyar da kanshi gefe yace "Barshi kawai, haka nake so ya ci gaba da kallon yana da gado a ciki." Da mamaki ya kalleshi yace "Amma kana ganin haka babu wata matsala? Kaga fa akwai hannun jarin wasu a ciki, kar ya jawo maka matsalar da zata durk'usar maka da kampani." Wani shegen murmushi yayi ta gefen labb'a amma bai ce komai ba, cikin rarrashi yace "Kaga Akhi, dan Allah kayi tunani akan lamarin nan, kasan halin Mujaheed d'an k'waya ne, yai mana terere k'aramin aikinsa ne fa." Ajiyar zuciya ya sauke ya nufi k'ofa bai ce komai ba, saida ya ga fitarshi ya girgiza kai da mamakin shirun da yayi mishi akan muhimmiyar magana. *Juma'a* Gajiyar daya kwanta da ita ta haddasa mishi makara da safe, hatta da yara basu tafi makaranta ba, dan tun ranar da mai d'aukarsu ya zo yace zai neme shi bai sake waiwayarshi ba, dama kuma sai ya tashi ne yake tashin Saudat ta shirya yaran, to kuma tunda mai tashinta bai tashi ba dole hakan ya jawo musu fashi a makarantar yau. A kasalance ya gama shirya duk da kuwa Qaseem ya fad'a masa yana waje yana jiranshi, haka bai sa shi gaggautawa ba saida ya shirya a tsanake. Mai gadi na k'wak'wasa k'ofar Izzadeen yayi saurin bud'ewa dan ganin waye? Mai gadi ne ya mik'o masa makulli yace "Ka kaiwa Elhaj ka ce inji Sammani motar na nan farfajiya ya aje." Juyawa yayi ya k'wala da gudu yana murna dan ya tab'a ce musu zai siya musu motar da za'a dinga kaisu, ya d'auka ita ce shiyasa da murna ya shigo yana fad'awa Sharfudeen dake wasa, da murna suka rankaya d'akinshi dan su nuna mishi, ya gama b'alla machette d'in shi ya d'auki agogo yana mak'alawa suka shigo, da sauri ya juya ya kallesu labb'anshi a had'e, kan gadon Izzadeen ya haye yana nuna masa makullin da fad'in "Aba duba motar da kace zaka siya mana ce aka kawo." Duk da labb'anshi a had'e suke saida ya musu murmushi, saida ya gama saka agogon ya d'auki wayarshi ya sa aljihu da littafin kud'i na banki sannan ya tara mishi hannu ya karb'i makullin, cikin sanyayyan murya yace "Wannan ba taku ba ce, tawa ce." Duk b'ata rai sukayi Sharfudeen yace "To Abba ina tamu? Kai fa kace zaka siya mana." Kallonshi yayi yace "Amma da nace zan siya muku ai nace wani abu kafin nan, wa zai iya tunawa?" Da sauri Izzadeen yace "Abba cewa kayi idan mukayi k'ok'ari a makaranta muka zo na d'aya zaka siya mana." Dafa kanshi yayi yace "Da kyau, dan haka sai ku dage." Turo baki Izzadeen yayi yace "Abba to ai kaga Mama bata koya mana karatu a gida, kuma shi monsieur le coach ba kullum yake zuwa ba, sannan gashi da saurin magana ba ma gane me yake fad'a." Zuba mishi ido yayi yace "A tak'aice dai ba kwa ganewa?" Ajiyar zuciya ya sauke yace "To yanzu ya kuke so ayi?" Suma duk kallonshi sukayi babu wanda yace wani abu, hanyar fita ya nufa duk suka bishi a baya, yana cikin rufe k'ofar d'akin ya kalli Sharfudeen yace "Mamanku bata tashi ba?" Girgiza kai yayi yace "Bacci take, har tashinta mukayi ta koma." Wani murmushi kawai yayi a ranshi yana fad'in "Allah ya ganar dake gaskiya." Saida ya rufe d'akin ya ciro wayarshi ya turawa wani yaronshi sak'o cewa ya siyo abun karin kumallo ta kawo mishi gida, d'akinta ya nufa yaran duk suka rufa masa baya, baiyi sallama ba dan yasan bacci take, ko idonta biyu ma ba cika amsawa tayi ba, ai kuwa kwance take tana sharar baccinta, murmushi ya sakar mata kamar tana ganinshi, babu ta inda Allah ya tauyeta ta b'angaren hallita, komai na ta mai kyau ne da birgewa, gata kuma kamar ba ita ta haifi yara biyu ba saboda har yanzu kamar budurwa take yar caras, amma rashin kulawarta yasa ta ingiza zuciyarshi fara kallon wata kallon ma na so da sha'awa, duk da ita ma ba baya ba wajen kyau da zubin hallita, hasken fata kawai Saudat zata nunawa Faduma, ita kuma Faduma zata nuna mata kumari da kuma tsayin gashi, sai kuma kula da jiki wanda shine mace gaba d'aya. Tattausar ajiyar zuciya ya sauke yana lumshe ido, kad'an ya rage masa ya rasa duk wani lissafinsa sanda ta zauna jikinshi, turarenta da yanda mazaunanta suka dira a k'afafunshi, ba k'aramar juriya da kawar da kai yayi ba, ko d'an haka na bak'on abu a wurinshi, dan rabon da Saudat ta zauna k'afafunshi har ya manta, shima a hakan wai dan shine ke jawota ya d'ora. A can k'asan mak'oshi ya furta " *K'amshi rahama ne*." Iya k'amshinta kawai zai iya yarda ya rayu da ita a hakan indai har in ya shigo gidan zai ji ni'imtaccen k'amshin nan. K'arasawa yayi ya daddab'a kafad'arta, tashi tayi zaune akan gadon tana hamma bakinta rufe, saida ta kalli yaran ta kalleshi, jaye zanin rufar tayi ta sauka daga kan gadon ta d'aya b'angaren tana kallonshi cikin muryar bacci tace "Har ka shirya?" Ido kawai ya zuba mata yana kallo, ganin bai tanka mata ba yasa ta kalli yaran tace "Wai ku baku tafi makaranta bane? Ba ayi ne?" Sharfudeen ne yace "Mama Kabiru ne bai zo ba, kuma Abba bacci yayi shima." Ba tace komai ba ta juya zata shiga ban d'aki yace "Karb'i nan." Tsayawa tayi ta juyo tana kallonshi, kud'i ya mik'a mata yace "Illa zai zo yanzu zai kawo muku abun kari, ki bashi zai baki canji sai ki rik'e kiyi cefanai." Karb'a tayi tana murmushi har hak'oranta na bayyana, ita fa indai zai dinga bata kud'i bata da matsala dashi, kud'in daya bata da zaiyi tafiya ma me tayi dasu, ga wanda ya bata ranar nan ba tayi komai dasu ba, yanzu kuma ta tabbatar zata rik'e canji mai yawa duk da yasan babu abinda suka rasa na kayan aiki, bai jira tace komai ba ya fita daga d'akin yara suka bishi a baya. A farfajiyar ya samu Qaseem da kuma motar da Sammani ya bari, duba motar suka shiga yi tare da Qaseem dake fad'in "Alhaji wannan motar fa? Tayi kyau gaskiya amma ai wannan ba ajinka bace." Ba tare daya kalleshi ba yace "Tambayarka nayi ta dace dani?" Murmushi yayi yace "Allah huci zuciyarka, motar ce ai na gani..." Wani jan harare ya masa yace "Qaseem ban tambayeka ba." Makullin ya cilla mishi yana fad'in "Muje." Ganin ya bud'e gaban motar yasa ya kalleshi yace "Yallab'ai wai da ita zamu fita?" Ko kallonshi baiyi ba ya shiga ya zauna yana ci gaba da duba cikinta, bud'ewa Qaseem yayi mazaunin dreba ya zauna, d'aga mishi hannu yayi alamar ya tsaya, fita yayi ya koma mazaunin dreba da sauri ya fita ya bashi wurin, zaunawa yayi Qaseem kuma ya koma inda ya tashi, saida ya kalli yaran yace "Ku shiga ciki za'a kawo muku abinci." D'aga mishi hannu sukayi suna fad'in "Abba saika dawo." Da ido ya amsa musu suka fita daga gidan, wani sakayau ya ji shi a cikin motar, ko dan ya saba da babba sai yaji kamar ya zama k'arami a ciki, ga wasu abubuwan da suka bashi wahala wanda a yanzu ya saba dasu automatique ne na motarshi, wannan kuma sai ka aikatu da hannunka ko k'afarka, sai dai yana jin farin cikin tuk'ata saboda irinta ce Faduma ke tuk'awa, daidai k'ofar kampanin suka tsaya mai d'auke da babban allon da aka rubuta *risham super wax*, tsayawa yayi nan ya bud'e motar ya zuro k'afa d'aya ya kalli Qaseem yace "Ka wuce can ka ga an d'ora kayan da zasu tafi Cotonou." Jin haka ya fahimci inda yake nufi, da alama yau ranar ta risham fabric ce, dan haka ya fito yana jinjina kai ya koma mazaunin matuk'i, shiga yayi ciki masu tsaron biyu na gaishe shi ya amsa da hannu ya shige ciki. _______________ Da kanta ta damk'a hannun Khairat cikin nashi, saida ta rage murya cikin rarrashi tace "Dan Allah yah Tagur ka dawo min da ita." Hararanta yayi yace "Me kike nufi? Siyar da ita zanyi ne?" A hankali ta girgiza kai tace "A'a, ina dai tsoron ku had'u da mahaifinta ne ya karb'eta." Tab'e baki yayi yace "Ke in zaki bawa kanki lafiya ki ba wa kanki lafiya zaifi, Aji da kike gani ko mutuwa kikayi bana jin zai iya karb'ar yarinyar nan, in ma ya karb'a su Dada ne zai bawa ita, amma shi baya da lokacinta." Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi ta bishi da kallo, bud'e motar sukayi suka shiga suka bar gidan. A hanya ba wata hira data had'ashi da yarinyar saboda tunaninshi na wani wuri, da haka har suka isa gidan suka shiga tare yana rik'e da hannunta, duk da babban gida ne da mutane dayawa, amma da yake kowa da b'angarensa sai ya zama zaka iya shigowa babu wanda ya sani sai wanda ka zo wurinshi, b'angaren mahaifiyar Aji ya shiga da sallama, da yake dattijuwa ce duk ta aurar da yaranta mata yasa babu kowa daga Ridwan a falon sai autarta da ba zata fi shekara sha hud'u ba, a tare suka amsa sallamarshi tana mishi maraba, fara'a ya gayyato a fuskarshi sanda Ridwan ya taho da gudu ya rumgumeshi har ya samu wuri ya zauna, kiran Khairat tayi ta nufi wurinta tana mata magana sai dai duk ta kasa sakin jikinta saboda ba wani sabawa tayi dasu ba, auta ce ta kirata can ma ta tafi amma ba u wani walwala a tare da ita, kallonta yayi sanda take gaishe shi da ladabi ya amsa da sakin fuska yana fad'in "Auta ya karatu?" Saida ta turo baki dan bata so ana kiranta auta sannan tace "Lafiya lau." Kallon dattijuwar yayi yace "Dada ina wuni?" Amsawa tayi nan suka shiga gaisawa sosai har tana tambayarshi mai jiki? Kallon Autar yayi yace "D'auko min kayanshi yau zai koma gida." Mik'ewa tayi dan cika umarninshi dada kuma ta kalleshi tace "D'auke mana shi za kayi Tagur? Me yasa ba zaka barshi ba? Ko har an gama shari'ar ne?" A hankali yace "A'a Dada, ina so ne na tafi dashi gida." Jinjina kai tayi tace "Shikenan, amma kana ganin Atta ba zata iya zuwa can ba? Kaga fa bakinsu d'aya da Gomboy tunda k'awarta ce." Kallonta yayi yace "Dada in ma haukanta yasa ta zo gidan nan karb'arshi ko ita ta bata shi, wallahi zasuyi dana sanin zuwansu duniya." D'aga kai tayi alamar to fa, kallon Khairat tayi ta sake kiranta ta tafi sai nok'ewa take, rik'eta tayi tace "Ya karatu? Ana zuwa makaranta?" D'aga kai tayi alamar eh, shafa kanta tayi tace "Zaki kwana anan?" Shiru tayi ba tace komai ba, nunata tayi tace "Kin ganki yarinyar nan baki da kirki wallahi, yanzu ni d'in ba zaki kwana gidana ba? Yayi kyau yarinya je ki." Ta fad'a tana turata wajen da Tagur yake, kusanshi ta tsaya tana kallon Ridwan, tana kawo mishi kayan ya karb'a ya mik'e ya musu sallama suka bar gidan. ______________ Kamar wani sakarai haka ya haukace kan Nafi, kuma shi da gaske yake son ta take, Atta banda farin ciki babu abinda take yi ganin sun samu abinda suke so cikin sauk'i, jiya da ya zo da dare sun sha hira sosai har da Nafi data ci kwalliya ta d'auki hankalinshi, ita ma Nafi ta saki jikinta dashi daga jiya zuwa yau ne saboda kyautar kud'in daya mata jiyan, duk da Atta ta zabtare rabin hakan bai dameta ba tunda dai ta samu na kashewa kwana biyu, shiyasa ma ta bashi lambarta da cewa zasuyi waya. Yanzu haka tana d'akin Atta zaune ta zana mata abinda zata fad'a, bayan ta gama gaya mishi ne yayi jim kamar ba zai ce komai ba, kusan minti biyu har saida tace "Kana ji kuwa? Ko ba zaka iya yi min alfarmar bane?" Numfashi ya sauke har saida taji sautinshi a kunnenta kafin yace "Ba haka bane yan matana, abinda kika nema ne da wahala, ba wai juya hujjar da zanyi bane matsala, daga baya idan gaskiya ta fito har ni zan shiga matsala." Cikin karyar da muryarta sosai tace "Kenan ba zan samu ba? Auren yar uwata fa ne ke tangal tangal, taya kake tunanin iyayena zasu aurar dani gareka inhar ba zaka iya taimaka mana yar uwata ta koma d'akinta ba ita ma." Da sauri yace "Ban ce miki ba zanyi ba yan matana, akwai matsala ne a cikin yin hakan, amma ba komai zanyi saboda ke saboda son da nake miki." Murmushi ta masa kamar yana gabanta tace "Har kasa naji dad'i, nagode sosai d'an saurayina." Shima murmushin ya mata yace "Ba komai ai girmanki ne, yanzu ya maganarmu kenan?" Yar siririyar ajiyar zuciya ta sauke tace "Karka damu da wannan, insha Allahu ana gama shari'ar nan zan maka magana sai ka zo kaga su Baba." Da farin ciki yace "Kai amma da naji dad'i wallahi, zan jira wannan ranar ta zo saina zuba ruwa k'asa nasha." Da haka hirar tasu ta k'are ta sanarwa da Atta yanda sukayi, da farin ciki ta mata godiya ita kuma ta kira Zaliha ta fad'a mata yanda ake ciki. ______________ Tsaf ya shirya bayan ya dawo daga masallaci sallah isha'i tare da Amjad suka fita zai kaishi gida, suna d'aukar hanya wayarshi ta fara k'ara, cirota yayi a aljihu ya duba, da sauri ya d'auka yana d'orawa a kunne, da girmamawa da ladabi yace "Elhaj barka da dare." Daga b'angaren Hasheer ma amsawa yayi cikin wata muryar dattako kamar wani d'an marayan zaki da cewa "Barka Amin, ya kake?" Da fara'a ya amsa da "Lafiya lau, ya hidima kuma?" Wata tattausan ajiyar zuciya ya sauke mishi a kunne, jim yayi kamar ba zai ce komai ba kafin yace "Amin ka zo gida yanzu ka same ni." Had'e fara'arshi yayi yace "Elhaj lafiya dai ko?" Cikin sauk'i ya amsa da "Lafiya lau." Tabbas yasan ya girmeshi har a shekaru ma, sai dai ba wani girma sosai ba, kawai dai mutumin na da wani irin kwarjini ne da haiba wanda ko babban daya girme mishi zai iya girmamashi, Allah ya mishi baiwa ta arzik'i kuma yana gudanar da ita ta inda ya dace, hakan yasa yake da wani dattako da yin komai a sannu, kamar yanda sarauta a jini take haka nashi arzik'in ya zama wani jinin jikinsa, kai tsaye zaka iya kiranshi da mai girman kai da raina mutane, a bad'ini kuma zaka gane ba haka bane musamman idan ka zauna tare dashi ko da na minti biyar ne. Dan haka yanzu ma kwarjininsa yasa ya kasa fad'a masa uzurinsa kawai yace "Ba damuwa Elhaj gani nan zuwa." Juya akalar tafiyar yayi zuwa gidan Hasheer dan amsa kiran da ya mishi wanda baisan dalili ba. *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 17:13 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _28_ Ganin ya wuce hanyar gidansu yasa Amjad kallonshi yace "Obdo ina zamu tafi kuma? Ko ka manta hanyar gidan ne?" Kallonshi yayi yana murmushi yace "Ba mantawa nayi ba Amjad, an fad'a min yara irinka na tsada ne shine zan siyar da kai kud'in kuma na auri mahaifiyarka." Ya d'auka zai tsorata ne amma sai gani yayi ya fashe da dariya har da k'yalk'yalawa, da mamaki ya kalleshi yace "Wai baka yarda ba ne?" Da k'yar ya tsagaita da dariyar yana kallonshi yace "Obdo, ai kuwa da ka rasa Ayyata har abada, da kud'in daka siyar mata yaro kuma ka aureta?" Tab'e baki yayi yana jinjina kai yace "To idan ka siyar dani ma wa zai baka aurenta?" Mamaki ne kwance fal kan fuskarshi har saida yace "Kai zaka bani aurenta ne?" D'aga kai tayi alamar eh, murmushi yayi mai birgewa yace "Karfa ka manta har yanzu mahaifin Ayyarka yana raye, sannan tana da yan uwa bila'addin." Cikin muryar yarinta yace "Duk da haka ni zan bayar, tunda su basa zuwa inda muke kuma Ayya ma bata zuwa wurinsu, kaga kenan ni kad'ai gareta." Murmushi kawai ya sake doka masa a daidai lokacin da suka tsaya k'ofar gidan, da sauri ya kalleshi yace "Obdo nan muka zo?" D'aga masa kai yayi alamar eh yace "Ka san gidan ne?" Da fara'a a fuskarshi yace "Eh, gidansu abokina ne Izzadeen, ranar ma da ba'a zo d'aukarsu ba Ayya ta kawosu nan gidan." Sauke ajiyar zuciya yayi yana kallonshi yace "Amma yanzu zaka jirani anan na shiga na fito, na zo ganin mahaifinsu ne zamuyi magana, amma ka min alk'awarin ba zaka fad'awa mahaifiyarka na zo yawo da kai ba." Murmushi yayi yace "Nayi alk'awari." Jinjina kai yayi ya bud'e motar ya fita, saida ya sauke gilashi ya lek'o kanshi yace "Obdo ka gaishe min da Izzadeen." Juyowa yayi kawai ya d'aga masa hannu alamar to, da mai gadi suka fara gaisawa yace "Elhaj ai yana ciki ko?" Nuna mishi k'ofar d'akin Mukhtar yayi yace "Yana ciki ma yana jiran zuwanka." Kallonshi yayi yace "Nagode." Ya bud'e mishi ya shiga ciki, saida ya cire takalminshi ya d'an k'wank'wasa k'ofar tare da yin sallama, Mukhtar ne ya amsa da "Bismillah shigo." Tura k'ofar yayi ya shiga yana sake wata sallamar, mik'ewa Mukhtar yayi yana bashi hannu da fad'in "Oga Aminu barka." Murmushi yayi yace "Oga ai bayanka yake Mukhtar, ya kake ya harkoki?" Dariya yayi yana fad'in "Haba oga wasa kake, harkoki gasu nan ba wuya ba dad'i, sai godiyar Allah kawai." Bai ce dashi komai ba ya zauna kujerar dake fuskantar Hasheer dake danna waya kamar bai ga shigowarshi ba, cikin tausasa murya yace "Elhaj ina wuni." Saida ya lumshe ido na sakan biyu sannan ya d'ago dubanshi zuwa kan Aminu dake ta murza hannayenshi, saida ya fara sakar masa da lallausan murmushi sannan yace "Sannu da zuwa." Sunkuyar da kanshi yayi bai ce komai ba, Mukhtar dake tsaye ne ya juya zai fita yana fad'in "To bari na barku ko? Tunda hirar ta manya ce." Murmushi Aminu yayi ya bishi da kallo har ya fita, haka ma Hasheer kallonshi yayi har saida ya fice ya girgiza kai a hankali ya sake kallon Aminu, d'an gyara zamanshi yayi cikin sanyin jiki tare da zura hannu ya d'auki takardun dake gefenshi akan kujera ya mik'o masa, hannu yasa ya karb'a ya kalli takardun ya kuma kalleshi yana jiran k'arin bayani, cikin nutsuwa da dattako ya nuna mishi tarkadun yace "Amin wannan takardun kampani na risham super wax, ka ajiye su a wurinka kamar yanda kake ajiye min duk wani abu mai mahimmanci, sai dai wannan suna da banbanci da wad'ancen." Da mamaki ya sake kallonshi ya kuma bud'a takardun yace "Elhaj miye banbancinsu?" Numfashi ya sauke mai k'arfi kafin yace "Wannan original ne ba photocopie, ka ajiyesu da kyau Amin." A hankali ya kalleshi yace "Yallab'ai me ya taso haka da zaka bani ajiyar wannan takardu haka kuma ba jahu ba? Da wata matsala ne a k'asa?" Shiru ya d'anyi na wani lokaci kamar ba zai ce komai ba, a hankali kuma sai yace "Bana son ajiyesu a wurina saboda komai zai iya faruwa, kasan yaron nan Mujaheed yana ganin kamar risham wax ma na cikin abubuwan da Abba ya mallaka, shiyasa ta fara maganar wai a raba kampanin kowa ya d'auki kasonshi, kuma nasan kasan cewa wannan kampanin nawa ne mallakata, kawai nayi anfani da sunan da Abba yake sawa duk wasu masana'antarshi ne nima..." Shiru yayi ba tare da ya gama fad'an abinda yake son fad'a ba, sai dan gajiya da jan zancen har yayi tsayi haka, numfashi ya dinga saukewa kamar wanda yayi gudu yana kallon tv dake aiki a d'akin. Kallonshi Aminu yayi yace "Ba damuwa Elhaj, insha Allahu zaka same ni mai rik'e maka amana, zan ajiyesu kamar yanda zan ajiye mafi darajar abinda na mallaka a duniya, zan kula dasu kamar yanda zan kula da kai, insha Allahu ba zan bari wani abu na rashin dad'i ya same su ba." Kallonshi yayi yana sauke wani numfashin ya d'an jinjina kai yace "Allah ya tabbatar." "Ameen." Ya fad'a yana sunkuyar da kai, shiru falon ya d'auka na sakanni kamar babu masu rai a ciki, satar kallonshi Aminu yayi ya ga hankalinshi ma na kan tv da remonte a hannu yana k'ara volume sai karkad'a k'afarsa yake dake kan d'aya k'afar, cikin nutsuwa da kunya yace "Elhaj idan ba damuwa zan iya tafiya, ina kan hanya ne?" Da sauri ya kalleshi yace "Ba damuwa Amin, zaka iya tafiya, nagode sosai." Mik'ewa yayi yana fad'in "Sai anjima." Jinjina kai yayi yace "Zamu sake waya." Ficewa yayi sai dai hankalinsa duk a tashe yake sakamakon takardun nan dake hannunsa, amana abu ce mai girman gaske wacce wanda ya d'auketa inhar yasan girma da darajarta to ko ruwa ba zaka sake sha ba cikin farin ciki, musamman ma wannan mai had'arin gaske, dole yayi taka tsantsan dasu fiye da rayuwarsa ma. Yana shiga Amjad ya kalleshi yace "Obdo ka gaishe min da abokina?" Fuskar tausayi yayi yace "Wayyo na manta, kasan wani? Ban gansu a inda na shiga bane shiyasa." Jinjina kai kawai yayi alamar shikenan. Baya suka dawo cikin k'ank'anin lokaci suka iso gidan, Amjad ne ya fara fita daga motar da gudu ya shiga ciki yana sallama, su Faduma dake tsakar gidan tare da dada da farin ciki ta mik'e ita ma ta tarbeshi, rumgume juna sukayi cike da so da k'auna, k'amk'ameta yake sosai yana fad'in "Ayya nayi kewarki." Ita ma k'amk'ameshi tayi tana fad'in "Nima haka oddo." D'agowa yayi daga jikinta ya kalli fuskarta yana dariya yace "Ayyata ta dabance, tunda na fita a gidan nan sai yau dana dawo nake jin wannan sanyayyan k'amshin mai sani nutsuwa da tabbatar min lallai ina kusa da mahaifiyata." Tunda ya fara magana take murmushi har ya dasa aya, hancinshi taja tana fad'in "Wannan oddo na ne." Saida ya sake rumgumeta yace "Wannan Ayyata ce." Muryar dada ce ta katsesu tana fad'in "Tunda ka manta dani ma ka juya ka koma tare da wanda ya dawo da kai, yau ba zaka kwana a gidan nan ba." Da sauri ya d'ago ya nufeta yana fad'in "La la la la, rufa min asiri uwar gidata, ki taimakawa wannan miskinin angon na ki mana, idan ba'a gidanki ba ina zan kwana?" Cike da so da k'auna ta rumgumeshi ita ma kamar yanda ya rumgumeta ya zauna kan k'afafunta d'am, sake matseshi take a jikinta tana jin kamar ta had'eshi ta huta, tana son yaron kamar wata tsoka a cikin jikinta, murmushi ta masa tace "To shikenan na yafe, amma a kawo wani abu ko, dan wannan jakar da naga ka shigo da ita ba iya kayanka bane kad'ai." D'agowa yayi yana ta dariya ya mik'a mata jakar yana fad'in "Kai akwai dai sa ido a wurin nan, ban da abinki mai gida ya dawo daga tafiya bai shigo da tsaraba ba?" Saida ta fara zuge zip d'in rigar tace "Da gaskiyarka kuma fa." Wata leda ta jawo a cikin jakar ta fara dubawa, ido waje ta kalleshi tace "Wannan kayan dad'in kake ci dama tunda ka tafi?" D'aga mata gira yayi alamar eh mana, turo baki tayi tace "Ai kuwa na zuba ido naji ranar da zaka sake komawa gidan Aminun nan, tsaf k'afar mai gidana k'afata nima." Bushewa sukayi da dariya daidai sanda Faduma ke dariyar ita ma tana amsa sallamar Aminu, juyawa tayi tana kallonshi tace "Shigo mana Aminu." K'arasa shigowa yayi yana sake wata sallamar, kujera ta aje mishi sannan ta samu ta zauna inda take a farko kusa da Dada, bata wani takura ba dan riga da zani ne a jikinta wanda suka amshi jikinta d'as, gaisawa suka shiga yi sosai har dada na zolayarshi da cewa haka yayi ta kashewa Amjad kud'i ya barta anan da tuwo miyar kuka, b'ata rai Amjad yayi yace "To wai ba saida na bar miki kud'in cefanai ba har da na siyan naman miya?" Hararanshi tayi tace "Kai ni bana son k'arya, me ya hana ka siyo ka kawo to?" Kallonshi Faduma tayi tace "Ka shiga ciki ka aje kayanka ka samu kayi wanka." Yatsina fuska yayi yace "Ayya yanzu fa saida obdo ya min wanka." Dada da Faduma a tare suka zaro ido Faduma har da dafe k'irji tace "Wanka?" Kallon Aminu tayi da yau ta ga sai wani sinne kai yake yana jin kunya tace "Da gaske kai ka mishi wanka Aminu?" Murmushi kawai ya saki amma bai ce da ita komai ba, Amjad ne yace "Ayya ai kullum ma shi ke min wanka sau biyu." Wata irin dariya tayi mai tattare da abu ya baka mamaki tace "Lallai Aminu shagwab'a min yaro kayi, kaga nan gaba ba zan sake bar maka shi ba." D'agowa yayi yana kallonta yace "Saboda an mishi wankan? Miye laifi a ciki?" Girgiza kai tayi tace "Abun ne naji shi wani iri, kamar Amjad ka tsaya yi mishi wanka, shekara takwas fa, to ni rabon dana mishi wanka ai har na manta gaskiya." Dada ce tace "Gaskiya kam." Kallon Amjad tayi tace "Kai yanzu baka ji kunya ba ka tsaya gabanshi yana maka wanka? Ko dai sai nasa an sake maka sabon yanka ne?" Kuka ya fashe dashi irin na sangarta da jin kunya ya fad'a jikin Faduma yana fad'in "To miye a ciki dan Allah? Ba shi ne zai auri Ayyata ba? Ai in ya aureta ya zama Abana." Da sauri Aminu ya kalleshi sai kuma yayi k'asa da kanshi irin mad'aukakiyar kunyar nan ta kama shi, sai Faduma da tayi shiru jikinta duk yayi sanyi ta dakata daga shafa shin da take, Dada kuma mik'ewa tayi daga kujerar ta kama hannunshi tace "To anji muje nima yau wankan nan zan jaraba maka naga ko zaka ji kunyata." Tirjewa ya fara yi yana fad'in "Um um bana so, wallahi bana son wankanki zanyi da kaina." Marinshi tayi a mazaunai ta sumgumeshi gaba d'aya harda jakarshi tana fad'in "Uwaka ma k'arya take yaro, nima wankan zan maka." Dukansu da dariya suka bisu har suka shige ciki, a tare suka sauke ajiyar zuciya hakan yasa suka kalli juna a tare, sunkuyar da kanta tayi yau kam sai taji wata kunyarshi ta fara rufeta, ga wata uwar kwalliya daya d'auka cikin farar shadda sai maik'o take, ga k'amshin turarenshi duk ya game gidan, dama kuma dogon mutum da iya d'aukar wanka, hakan yasa shi wani irin kyau kamar ka dangwala shi da bredi ka ci. Numfashi ta sake saukewa ba tare data kalleshi ba tace "Nagode Aminu, ka kuoa min dashi kamar yanda nayi tsammani." Saida ya d'an saci kallonta yace "Baki ji me ya fad'a ba kenan?" Duk da mamaki ne a fuskarta amma bata yarda ta kalleshi ba, cikin rashin fahimta tace "Ban gane ba?" Cikin taushin murya yace "In dai har kin amince, ina so na zama Aban Amjad mai kula da duk wasu nauye nauyenshi." Da sauri ta d'ago ta kalleshi, sai kuma taji gabanta ya shiga fad'uwa tsikar jikinta na tashi, da sauri tayi k'asa da kanta tana salatin annabi a k'asan zuciyarta, ji take kamar k'asa ta tsage ta shiga, kunyar abinda ya zo mata dashi ne take, amma sam daya fad'a mata sai ba ta wani ji al'amarin ba sosai, abun a bazata ya zo mata, tunanin abinda zatayi take yi a wurin, tayi soyayya! Wacce ita ce ta jefata a halin da take ciki yanzu, wace irin soyayya ce Tagur bai nuna mata ba? Wace irin kalma ce bai yi anfani da ita ba wajen nuna mata k'arfin son da yake mata? Ama me ya faru daga k'arshe? Abune da ko a mafarki na hikaya bata yi tunanin zai faru ba. Jimawar shirun naya ne yasa shi gyaran murya yace "Faduma." D'an zabura tayi sai kuma ta k'i kallonshi, a hankali yace "Faduma na sani kina tunanin me yasa na zo miki da wannan zancen ko? Kiyi hak'uri ki fahimce ni, Faduma na gaji da jira ne, na kai matakin da na kasa ci gaba da jurewa ne, har yanzu na kasa kallon wata naji irin abinda nake ji akan ki, na d'auka zan iya ci gaba da jira har sanda zanji sauk'in abinda nake ji akan ki, amma kullum zuciyata sake azabtuwa take." Shiru ya d'anyi na wasu dak'ik'u kafin yace "Faduma na rok'eki dan Allah ki amince min ki yarda ki bani zuciyarki, nasan kin jima da jin irin wannan kalaman daga bakin wani na, amma na miki alk'awari Faduma wallahi zan killaceta a filin birnin zuciyata, zan baki dama ki ci gaba da gina soyayyarki a filin naki ne ke kad'ai, d'anki Amjad zan kula dashi kamar yanda zan kula da d'an da zan haifa, indai ina numfashi a doron duniya ke da Amjad ba zan tab'a barin ku zubar da hawaye ba in dai bana farin ciki bane." Gaba d'aya taji ya d'aure mata jijiyoyin jikinta, bata san amsar da zata bashi ba kai tsaye, dan haka ta shiga rarraba ido tsakanin dama da hauni k'asa da sama, har rawa rawa jikinta ya d'auka na girman al'amarin daya zo mata dashi, tana tsaka da tunanin yanda zata mishi magana ta ga fuskarshi a gabanta yana lek'ata, a bazata abun ya zo mata dan tayi saurin rufe fuska da tafin hannunta na hagu tana dariya mai kama da kukan jin kunya. Shi ma dariyar yayi cikin taushin murya yace "Hakan na nufin kin amince min kenan?" Sake fashewa tayi da dariya ta saka d'aya hannun ta rufe fuskarta, numfashi ya sauke har saida ta ji sautinshi kan fuskarta, mik'ewa yayi tsaye yace "Labarin zuciya a tambayi fuska, alamu su nuna Faduma ta amince min, wannan ranar ta juma'a ba zata tab'a fita daga tarihi na ba har abada, bayan ranar da aka haifi fiyayyen halitta (Annabi Muhammad S.A.W) ban tab'a jin wata rana ta shiga raina ba kamar ta yau." A hankali ta d'ago kai ta kalleshi cikin jin kunya, da k'yar ta sauke idonta cikin nashi tashi "Wai kai baka jin kunya ne dan Allah?" Murmushi yayi yace "Wace kunya kuma? Kinga malama ni daga yanzu ma shirye shirye zan fara, dan na fara jin ina k'amshin angaye." Murmushi ta sakar masa mai sauti ta mik'e tsaye, kallonshi tayi tace "Amma ai ni ban ce na amince ba ko?" Had'e fuska yayi yace "To me kika ce kenan? Faduma ya kike so nayi?" Sunkuyar da kanta tayi tana dariya tace "Kayi magana dashi, indai ya amince nima na amince." Da sauri yace "Wanene?" Ganin tsoron daya bayyana a tare dashi yasa ta sakin wani murmushin tace "Amjad mana." Juyawa tayi ta shige d'aki ta barshi nan, tana shiga ta sauke ajiyar zuciya, sam bata jin abun daga k'asan zuciyarta, bata jin irin yanayin da taji a lokacin data amincewa Tagur, sai dai tafi jin shi a matsayin ta sauke wani nauyi data jima tana dakonshi akan ta, tafi karkata alak'ar nan da sakamakon rama alkairi da alkairi, tafi jin a ranta cewa bata mishi butulci ba. Yana ganin shigewarta shima ya juya yana girgiza kai, wani bayyanannan farin ciki ne ya mamaye mishi zuciya, sai yau ne ya tabbatar anfanin so ka so a soka ne, da za'a yarje mishi shi kam da sai ya zabga ihun da zai firgita duk wanda bai fi tazarar tsakanin kl metre hamsin ba, amma tunda haka ba zata faru ba to kam dole gobe ya tashi da azumi na godiya ga Allah ya karb'i addua'rsa. Tunda ta farka da safe sukayi waya da Ayya ta sake fad'a mata gasarsu Amjad zata fara gobe ne, addu'a ta mata sosai ta musu fatan alkairi, sannan ta fad'a mata yanda sukayi da Aminu, shi ma alkairi ta saka mata tare da ja mata kunne ta kiyaye. Suna gama wayar ta shirya ta fito ta samu Dada da Amjad, dama an basu hutun karatu saboda gasarsu, dan haka yau ranar ta zama ta hutu a gare su dukansu. ______________ Wani k'asaitaccen murmushi ya sakar masa tare da cewa "Allah dai ya huci zuciyar g茅n茅ral dinmu, yanzu ya kake so ayi kenan?" Girgiza kai yayi yana kwantar da kanshi jikin kujerarshi yana jujjuyawa ido lumshe, kallon tablet d'in yayi wacce yake ganin duk wani motsinshi, cikin nutsatsiyar murya yace "Hasheer raina ni kayi shiyasa, inba haka ba taya zaka manta da al'amarin orronur?" Murmushi ya sake yi yana d'ora duka hannayenshi akan table d'in dake gabanshi shi ma yana kallonshi ta k'aramar ordi. d'in dake gabanshi k'irar apple yana fad'in "Na ce kayi hak'uri ko, ba da gangan na manta ba wallahi." Ba tare daya d'ago ba ya kalleshi yace "To ya zanyi? Na hak'ura." D'an siririn murmushi ya masa wanda ya fito da dogayen hak'oranshi masu hasken gaske, hakan kuma yasa hancinshi k'ara fitowa sak kamar zai shiga bakinshi yana fad'in "Na ji dad'i daka hak'ura, ba dan haka ba da nasha fad'a." A hankali ya d'ago daga kujerarshi yana girgiza kai tare da yin k'wafa yace "Zan had'u da kai ne, yanzu fad'a min ya maganar waccen aikin?" A lokacin shi kuma ya mayar da bayanshi jikin kujerar ya fara juya ta shi kujerar ya sauke numfashi yace "Karka damu Wardugu, insha Allahu ina nan zan shigo garin naku domin gudanar da aikin nan." Hararan dake d'auke da tambaya ya jefa masa yace "Ka tabbatar?" Cike da tabbaci shi ma ya jinjina kai yace "Insha Allahu." Jinjina kai shima yayi yace " Allah ya yarda, sai na jika kenan?" "Insha Allah." Ya sake fad'a yana jinjina kai, d'orawa yayi da "Ka gaishe min da yarana." Da ido kawai ya amsa masa da to, a haka sukayi sallama kowa ya kashe wayar, k'aramar wayarshi ya ciro ya sake danna lambar ta fito akan screen, d'ora hannunshi yayi kan ok har kiran ya tafi sai kuma yayi gaggawar dakatar dashi ta hanyar yin rejet茅, d'agowa yayi daga kujerar ya d'ora hannunshi saman tarin sumar kanshi dake gaba mai yawa, murzawa ya shiga yi yana tusa hannunshi yana sauke huci kamar wanda ke fad'a. Ba uya zuciyarshi kawai ke rawa ba har da hannayenshi, hatta da k'afafunshi suna karb'an sak'on yanayin da yake shiga ko da sunanta ya kama a bakinshi, bai san miye na musamman a tare da ita ba? Amma dai yana jin abu na musamman a tare da ita idan yana tunaninta, d'ora goshinshi yayi akan teburin ya sauke numfashi, ya jima a haka kafin ya d'ago ya dannawa lambar Saudat kira, bata jima da fara sone ba ta d'aga, kafin yace wani abu tace "Hello." Lumshe ido yayi na wani lokaci ya bud'e, ya d'auki kusan sakan biyar kafin yace "Ya kike?" Saida ta tab'e baki daga inda take sannan tace "Lafiya lau, kai fa?" Kamar mai jin bacci saida ya saki wani masifaffen charme kafin yace "Bana jin dad'i rabin raina, ina so na dawo gida wajenki, amma bansan ya zaki tarbeni ba." Daga wajenta ta amsa da "Tohhh! Haka kake tunani akai na dama?" "Humm!" Kawai ya fad'a yana murmusawa ta gefen labb'a, a hankali yace "Me kika tanadar min idan na dawo?" Cikin rashin kulawa tace "Ban gane me kake nufi ba? Idan wani abu kake so na maka ka fad'a mana, amma ba sai ka nemi fad'a min magana ba." Bud'a matsakaitan idonshi yayi akan k'ofar shigowa, kamar ba zaiyi magana ba sai kuma yace "Allah ya huci zuciyarki." A tak'aice tace "Sai ka dawo." Shiru yayi bai ce komai ba, har zai kashe wayar tace "Uhyemm baka ji ba?" Tsayawa yayi bai kashe ba kuma bai ce komai ba, d'orawa tayi da "Malamin nan fa ya sake magana kan uniforme d'in yaran nan, shine na ce ko zaka wa Illa magana sai ka bashi ya siyo musu?" D'an guntun tsaki yaja dan sai yanzu ya tuna, makarantar da suke zuwa can babu wani karatu sai shirme, hakan yasa shi canza musu wata, sati d'aya kenan yau da aka kaisu kuma aka ce a musu kayan makarantar, amma ya manta sai yanzu, cikin kasala ya amsa mata da cewa "Ba damuwa, zan je da kaina ma saina siyo." Ko da ya fad'a ya katse kiran, aje wayar yayi ya jawo farar takardar dake gabanshi ya d'auki alk'alami ya fara zane akai. Sai dai babu karsashi a tare dashi, gaba d'aya yanzu kasala ce ke baibaiye shi ya kasa aiwatar da komai, baya da kazar kazar wanda bak'on al'amarin daya shigo rayuwarshi ya taka muhimmiyar rawa. _______________ Tsakin da yayi ya fi dubu, yana so yaje amma tunanin abinda zai sake faruwa yake, matar nan yana jin kunyarta, kuma yana ganin darajar Faduma shiyasa baya so ya ci mutumcinta, amma ba dan haka ba daya nuna mata shi ba'a mishi haka. Agogon hannunshi ya cire ya jefa kan cantre tebur d'in tare da kuma jan wani tsakin, da k'arfi ya daki kujerar dake kusa dashi yana fad'in "Wai ina Faduma take zuwa ne ma? Me yasa kullum bata gidan? Kar fa ta lalata rayuwarta." Rik'e k'ugu yayi yana karkad'a kai ya cije baki sosai, sakin murmushi yayi kuma shi kad'ai yace "Kai ba zai yiwu ba, wallahi ba zata yarda ta zubar da mutumcinta ba, Faduma idan haukanki yasa kika kusanci wani kuma...Hummm!" Dantse leb'e yayi sosai kamar zai cireshi yana jinjina kai alamar fa akwai ta, d'an sassautawa leb'en yayi yana fad'in "Wallahi babu wanda ya isa ya rab'eki, ke tawa ce shiyasa har yanzu baki zama mallakin kowa ba, ni ne uban d'anki kuma mijinki na har abada." Da k'arfi ya juyo da niyyar d'aukar makullin mota ya je koma me zai faru ya faru, sai kuma ya sauke ido kan Husna data shigo yanzu d'auke da kwanukan abincinshi na rana wanda bai ci ba har yamma tayi, yana kallonta tayi saurin yin k'asa da kanta, dan gaskiya tsoro yanayinshi ya bata kamar zata saki fitsari, sake damk'e farantin tayi sosai sakamakon rawar da hannayenta suka fara. Ganin bata shigo ba yasa shi daka mata tsawa da cewa "Ke kuma lafiya kika tsaya min anan? In zaki shigo kiyi abinda ya kawo ki shigo, in ba zaki iya ba ki juya ki koma." Da sauri ta shiga takowa tana had'a k'afa wata kan wata duk ta manta kalar tafiyar da Hatimi ta koya mata, akan tebur d'in ta ajiye farantin ta d'ago ta kalleshi, ido cikin ido ta shagwab'e fuska tace "Abincinka ne na kawo maka, ka zauna ka ci dan Allah." Kallonta yayi kallo irin na tsanake, d'an tab'e baki yayi na jin haushi, da fari yanayin data nuna na tsoronshi yasa shi kallonta, amma yanzu data kalleshi ido da ido ya tabbatar mishi tsoron kawai na yanayinshi ne wanda ya taso daga gurbin zuciyarta, amma sam ba d'abi'arta bace, hakan kuma yasa ta sake fice mishi a rai, dan kamar yanda wani namijin ke son farar mace ko mai k'iba, haka shima yake son mace razannaniya kuma matsoraciya mai saurin kuka, yana so idan ya tsaya gaban mace idonshi suka kalli fuskarta nata idon su kalli sararin k'asa, hakan na sa shi jin wani irin dad'i da fasa mishi kai, abinda ya dinga had'ashi da Atta kenan, tsabagen tsagwaron rashin kunya da tarbiya, kallon k'wayar idonshi sannan ta danna mishi duk maganar da ta zo bakinta, ga kuma rainin tsiya data mishi wanda har ta kan iya saka k'afa ta fita inda ranta ke so ko yana gari ma bare baya nan, shiyasa ma ranar data kaishi bango ya wanwanka mata mari a fuska, ita kuma tayi yaji ta d'auka zai bita da lalami, shine har da tsaye tana cika mishi baki ta waya wai ba zata koma ba sai dai ya saketa, dan ya nuna mata bata gabanshi shi kuma ya saketan ya kuma je har gidansu a gaban uwarta yace ta zama shaida ya datse igiyar aurensu sannan ya taho da Ridwan. Tsaki ya kuma saki ya taka zai fita tayi saurin tare gabanshi ta rik'e gefen rigarshi, yana kallonta ta sake yin kalar tausayi tace "A gaskiya ba zan bari ka fita ba sai ka ci abinci, haka kawai yunwa ta kama ka." Harara ya cilla mata yace "Ke! Sake ni." D'an sassauta rik'on tayi amma bata sake shi ba, buge hannunta yayi tare da daka mata tsawa yace "Sake ni na ce." Zabura tayi ta saki rigar ta rintse ido, sama da k'asa ya bita da harara yaja tsaki ya fice a d'akin, da kallo ta bishi ta murgud'a baki tace "Tunda Ayya tace min zaka aureni wallahi dole ka aureni ko baka so." Juyawa tayi ta fita ita ma tana jujjuya baki, rufe mishi k'ofar tayi saboda hangen motarshi da tayi ya bar gidan gaba d'aya da gudun tsiya. ______________ A tsakar gida ta same su suna ta hirarsu ta shirme ita da shi, kallonshi tayi tace "Oddo muje ko." Da sauri ya juyo dan baisan da fitowarta ba, murmushi ya saki yace "Ayya kinyi kyau." Kallon kanta tayi cikin lafayar mai kalar ruwan k'wai da bak'i, sai rigarta mai dogayen hannu bak'a ta kanti simple, babu kwalliya a fuskarta kamar kullum, sai dai kuma yau bata d'aura d'an kwali ba daga ciki, hakan yasa kake iya ganin gashinta sosai, sai dai yanda ta d'aureshi yasa fuskarta yin haske ta fito sar-sar da ita, murmushi ta masa tace "Nagode." Hararanshi Dada tayi tace "Shiyasa na matsu na aurar da 'yata ko hakan yasa ta ji kalmar nan ta kinyi kyau daga bakin wani ba kai ba." Kallonta yayi ya rik'e baki yace "To ke kuma haushi kike ji idan ni na fad'a? Ayyata ce fa? Ko da tayi aure ma saina fad'a ko a gaban mijinta ne." Da sauri ta kalleshi tace "Amjaaaaad." A hankali ya kalleta yace "Kiyi hak'uri Ayya." Lumshe ido tayi tace "Mu tafi." Kallonta yayi yace "Ina zamu je Ayya?" Bata tanka mishi ba sai dada data kalla tace "Dada zamu je kasuwa zan siyo mishi sabon yadin kayanshi na makaranta daya lalata." Da farin ciki ya kalleta yace "Nagode Ayya, daga nan ma sai ki siyo min harda na islamiyya." Kallonshi tayi tace "Amjad kasan ina da kud'i ne? Me yasa zan siya maka sabbi?" Kamar zaiyi kuka ya kalleta yace "Ayya kin manta gobe ne gasarmu, ina so na fara zuwa da sabbin kaya." Matse d'an k'aramin bakinta tayi tace "To muje." Juyawa yayi ya nufi k'ofar d'akin dan d'auko takalminshi masu d'amara, satar kallonshi dada tayi ta kalli Faduma, murya k'asa k'asa tace "Ban fad'a miki ba saboda ban san ya zaki ji ba, amma fa mutuminki ya zo gidan nan." A take ta zaro ido ta juya ita ma ta kalleshi ta ga hankalinshi na kan saka takalmin, matsowa tayi sosai kusanta tace "Yaushe? Ya akayi yasan nan? Me yace kuma?" Duk zuba mishi ido sukayi saboda tahowa da yayi, da sauri tace "Wuce ina zuwa." D'agawa Dada hannu yayi yace "Saina dawo uwar gida." Ita ma hannu ta d'aga mishi tace "Sai ka dawo." Yana fita tayi saurin kallon Dada hakan yasa tace "Randa kika tafi ai bayan magriba ya zo nan, jiya ma da sassafe ya dawo." Yanda ta zazzaro ido zaka gane a tsorace take tace "Me yace wai Dada?" Cikin rashin ba wa abun mahimmanci tace "Me fa zai ce? Hauka ya zo yana min ni kuma na nuna masa iyakar haukarshi, wai ina d'anshi? Ke ki ji min rashin kunya." Wata wawar ajiyar zuciya ta sauke harda dafe k'irji, iska ta dinga hurowa tana kallon Dada ta kasa cewa komai, kallonta tayi da jin haushi tace "Ke dallah ki fita sabgarshi, muna nan dake na ga uban da zai turo ya karb'ar masa yaron, wallahi har ajalinshi zan iya yi." Da sauri ta sunkuya ta dafa hannunta tace "A'a Dada, Tagur da kike gani b..." Bata gama fad'in abinda zata fad'a ba tayi saurin mik'ewa, da gudu ta nufi hanyar fita daga gidan tana fad'in "Dada na manta Amjad na k'ofar gida, ina tsoron ya sakawa unguwar nan ido." Da kallo ta bita sai taji wani tausayinta ya kamata, a yanda ta shak'u da yaron nan da yanda take kaffa kaffa dashi, ya zata yi idan ya rabata dashi? In har ya nuna iko da kud'i tsaf zai rabasu da yaron ko da ta hanyar shari'a ne. Ganin Amjad tsaye yana kallon hanya ya sata dakatawa daga gudun ta dafe k'irji ta sauke ajiyar zuciya, a hankali ta k'arasa ta bud'e motar suka shiga suka bar unguwar. *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 17:13 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _29_ Babban shagon siyar da duk wani abu daya shafi suturar maza suka shiga, mutum biyu suka samu daga can ciki dan haka ta zauna kan bencin dake daga farkon shiga shagon sai Amjad dake tsaye yana kalle kalle, juyowa yaron shagon yayi ya kallesu yace "Barka da zuwa Hajia." Mazan dake akwai yasa ta kasa magana sai da kai kawai ta amsa mishi da sannu, bai damu ba sai ma cewa da yayi "Wani abu ake so?" Shiru tayi tana ci gaba da kalle kalle, kallonta Amjad yayi sai kuma ya kalli mai shagon yace "Eh, t茅nu (uniforme) muke so." Jinjina kai yayi yace "To ina zuwa ko." Wayarta ta ciro ta shiga duba sak'on manhajar sadarwa ta yane (WhatsApp), gaisawa sukayi da Aminu har suna d'an tab'a hira, bata ji takon komai ba bare motsi, sai dai k'amshin turaren daya ziarceta, had'e da dokawar da k'irjinta ya shiga yi da k'arfi k'arfi kamar ana daka, k'amshin turaren zata iya cankarshi a wurin mutum d'aya da zata iya cewa tayi dogon zango na tafiya dashi da kuma musayar yawu, zata rantse shine mutum na farko a duniya data tab'a sakin jiki tayi fira dashi bayan mahaifinta. Zura hannunta tayi cikin lafayarta ta dafe k'irjinta, rufe ido tayi ta shiga furzar da iska tana jin matsanancin mamakin canzawarta daga jin k'amshin da bata tabbatar wanda ta sani dashi bane. Iya ganin lafayar kawai yasa ya k'ure bayan matar da ido, a hankali yake ji a zuciyarshi ko da ba ita bace matar ta samu daraja a gare shi, ba ita kawai ba duk wacce tayi ta'ammali da wannan sturar ma, dan a kaf duniya bayan mahaifiyarshi Faduma ce ta biyu daya ga lafaya na matuk'ar musu kyau da k'ara musu tsari a cikin adonsu, amma sanda ya kalli Amjad duk da bai ga fuskarshi ba ya tabbatar shine, a k'asan zuciyarshi kawai yaji wani farin ciki ya kama shi, amma kuma zuciyarshi harbawa take da wani sauri sauri kamar zata tsere ta barshi, sai kawai ya kasa ko da motsawa bare yayi wani abun. Yaron shagon ne ya juyo kallonshi, yana ganinshi tsaye k'ik'am ya taho da sakin fuska yana wangale baki da fad'in "Elhaj, barka da dare, ai bai kula ba sai yanzu." Juyawa Amjad yayi da niyyar bashi hanya ya wuce, murmushi ne ya bayyana kan fuskarshi da ladabi cikin nutsuwa yace "Ina wuni obdo." Wata budurwar ajiyar zuciya ta sauke dan yanzu kam Amjad ya tabbatar mata fa shine, wani k'ayataccen murmushi ya sakar masa ya dafa kanshi, da k'yar ya d'aga labb'anshi yace "Ya kake?" Da fara'a ya amsa da "Lafiya lau, ina su Izzadeen?" Ba tare daya daina binsa da murmushi ba yace "Suna gida." Saida ya saci kallon Faduma da kamar bata san suna magana ba, kallon Amjad yayi cikin basarwa yace "Kai da wa ka zo nan? Ina mamanka?" Juyawa yayi ya nuna mishi Faduma yace "Tare da Ayyata muka zo." Kallonta yayi da kyau kamar yanzu ya fara ganinta sannan ya kalleshi yace "Me ka zo siya anan?" Cikin taushin murya yace "Kayan makaranta na da kuma na islamiyya." Shafa kanshi yayi ya lumshe ido, kallon yaron shagon yayi da shima yake kallonsu da saurarensu yace "Ka sallame su ne?" Girgiza kai yayi yace "A'a Elhaj, ai basu jima da shigowa ba ma, yanzu za'a sallamesu." Maida dubanshi yayi ga Faduma da har yanzu hankalinta ke kan wayarta d'aya hannunta kuma a k'irjinta yace "Hajia wane iri za'a dubo?" D'auke hannunta tayi ta d'ago kai ta kalleshi, cikin kwantar da murya sosai tace "Kalar fari da maron, sai kuma ja." Jinjina kai yayi ya juya ya koma cikin shagon, kafad'arta Amjad ya dafa yace "Ayya dubi Abansu Izzadeen." Saida tayi kamar bata san da kowa a bayanta ba sannan ta juyo, tana sauke idonta akan shi ta d'an waro ido, aje wayarta tayi gefe ta mik'e tsaye tana fad'in "Lah, ai ban kula ba, shine nake zaune babba na tsaye." Nuna mishi bencin tayi tace "Zauna ko." Tunda ta mik'e tana magana ya shiga kallonta da mamaki, a ranshi ya furta "D'aya da d'aya." Wani sihirtaccen murmushi ya sakar mata ya girgiza kai ya nuna mata wurin yace "Wanene ni a garin nan da zan tasheki kina zaune?" D'an murmusawa tayi ita ma tace "Ina wuni?" Shiru bai ce komai ba haka ya bata haushi kuma, juyawa tayi tana kallon cikin shagon kuma bata zauna ba, yaron shagon nan ya kalleta daga ciki yace "Hajia ai na yaron nan ne ko?" D'aga kai tayi alamar eh, ci gaba yayi da yankawa har ya gama ya saka musu a leda, fitowa yayi ya mik'a mata, karb'a tayi ta mik'awa Amjad ta kalleshi tace "Nawa ne?" Kai tsaye ya bud'i baki yace "Duka ya kama..." Kallon da Hasheer ya mishi daga bayanta ne yasa shi jan baki yayi tsit, murmushi yayi yace "Shikenan ma Hajia." Da mamaki ta d'ago daga k'ok'arin bud'e jakarta da take ta kalleshi tace "Ban gane shikenan ba?" Girgiza kai yayi yace "Eh Hajia, ku tafi kawai ba komai." Had'e fuska tayi sanda ta lura da inda ya sake kallo, wata na bayansu ne ya biya ko? Kallonshi tayi tace "Dan Allah fad'a min nawa ne kud'i na?" Sake girgiza kai yayi zaiyi magana ta d'aga mishi hannu, karb'an ledar tayi tace "Ka rik'e kayanka in dai ba zaka fad'a min ba, da niyyar yi wa yarona hidima na fito da gumina, bana neman tallafin kowa akan hakan." Sake kallon Hasheer yayi sai ya mishi alama da ido, cikin sanyin jiki da mamakin al'amarin matar yace "Takwas ba hamsin ne." Jaka goma ta mik'a masa tace "Ka bani canjina." Dariya ta so bashi kam, sai kawai ya juya ya shiga ciki ya d'auko mata canjin ya dawo, yana bata ta karb'a ta saka a jaka, juyowa tayi fuskarta a had'e sosai, yanda ya gaje hanyar kamar wani d'an boxin yasa ta kallon fuskarshi, cikin kwantar da murya tace "Zamu iya wucewa?" Kallon Amjad yayi yace "Sai yaushe kenan?" Murmushi ya masa yace "Nima ban sani ba, a gaida min su Izzadeen dai." Kallon fuskarta yayi da wani yanayi yace "Ba shiga tsakani bane, ba kuma anyi da niyyar taimaka miki bane." Kallon Amjad yayi yace "Kamar d'a na d'aukeshi, idan har zan iya yi wa Izzadeen kyauta ko d'awainiya ba tare da naji a raina taimakonsa nayi ba, haka zan iya yi wa Amjad ba tare da naji hakan a zuciyata ba, sai dai naji kamar na sauke nauyin da Allah ya d'ora min." Sake kallon fuskarta yayi duk da kanta na kallon k'asa yace "Idan ba'a alfarma ko taimako a rayuwa, idan isarka ta isheka kuma zaka iya da kanka, me yasa motata bata anfane ni a ranar ba har saida kika kai min yarana gida?" Shiru yayi na wasu mintuna kuma bai kauce a hanyar, numfashi ya dinga saukewa kamar an masa dukan tsiya, a hankali ya kauce a hanyar yana fad'in "Ki daina ganin kowane taimako a matsayin an miki shi ne dan kin kasa." Rab'ata yayi ya shige cikin shagon, duk yanda k'afafunta sukayi nauyi da k'arfin hali da na tsiya ta d'agasu ta shiga takawa da k'arfi suka fita. Duk ranshi yaji a jagule bai masa dad'i ba, dan a ganinshi kamar tana wani tunani ne akan shi marar kyau wanda ya janyo ya yi hakan, sai dai kuma ta wata fuskar k'ok'arinta ya birgeshi, amma dai gaskiyar magana bai ji dad'i ba. Yana gama siyan abinda ya kawo shi har ya mik'e zai tafi yaron shagon ya d'auki wayar yana fad'in "Elhaj ka manta da wayarka." Da mamaki ya juyo yana kallon hannunshi, girgiza kai yayi yace "Ba waya ta bace." Juyawa yayi zai fice yayi saurin cewa "Ai kuwa sai dai in ta matar nan ce da suka fita yanzu, dan ita kad'ai ta zauna anan yanzu." Har k'asan zuciyarshi ya so ya share kawai shi ya san yanda zaiyi, amma kuma tunaninshi na takura mishi da ingizashi tare da duba da wasu sabubba, a kasalance yasa hannu ya karb'i wayar yana fad'in "Zan kai mata." Yana fita inda ya paka motarshi ya nufa, saida ya shiga ya zauna ya kalli wayar, aje ta yayi kan kujera a gefenshi, gyara zama yayi ya wa motar key ya fara saita hanyar da zai bi, tafin hannunshi ya kai ya shafi sajenshi zuwa baki, cak ya tsaya yana sake shinshina hannunshi, d'an girgiza kai kawai yayi saboda jin k'amshin turarenta a jiki, duk da bai san ina ne gidan ba amma dai yayi niyyar bin hanyar daya ga tabi a ranar had'uwarsu ta farko dan kai mata wayarta. ______________ Daga nan gida ya fara wucewa kuma tun a hanya ya fara yin sallah magriba da aka fara kira, saida ya idar ya k'arasa gida bayan ya had'a yaran da Mukhtar yace ya kaisu wajen mai d'inki, yana shiga ciki da sauri ya shiga shiryawa saboda ganin wata lamba na kiran wayar Faduma wacce baya raba d'ayan biyu k'awarta ce saboda sunan daya fito akai. A gaggauce ya shirya cikin shadda kalar ruwan sararin samaniya, sai dai k'aramin d'inki ne rigar kad'an ta wuce gwiwarshi, dogayen hannaye ne da ita hakan yasa d'inkin ya karb'i jikinshi, bak'ak'en takalma ya saka wanda suka fito babban yatsarshi na k'afa guda d'aya, bai d'ora hula akai ba dan bai saba sakata ba, yana fitowa yayi daidai da fitowarta daga madafa. Tsayawa tayi tana kallonshi, masifar kyawun da yayi ne ya tabbatar mata da abinda ake fad'a cewa auren kyakyawa tashin hankali ne, tabbas a yanzu data ganshi a cikin shirin nan sai taji gabanta ya shiga luguden daka, take wani fargaba ya ziyarceta yana lullub'eta, ko fa babu wacce ta iya tunkararshi da kalmar so, to dole a kalleshi daga nesa kuma a k'yasa, shagwab'e fuska tayi kamar za tayi kuka tana ci gaba da kallonshi. Hannunta ya kamo ya matso da ita daf da shi yana kallon fuskarta, wani rantsatsen murmushi ya mata yace "Ya dai? Me ya samu uwar yarana har take shirin zubar min da hawayenta?" A marairaice ta kalleshi, sai taji kamar ta fashe da kuka, magana ta gaskiya tana son mijinta, so wanda za'a iya kira da k'ololuwar so, son da zata iya fansar ranshi da nata ran, halayenshi sun mata a rayuwa, wai fa duk yanda take shareshin nan a haka shi kuma yake manne mata, saboda kawar da kanshi har ya manta da maganganun data fad'a mishi safiyar ranar daya turmusheta akan gado, tun lokacin bata sake ganin alamun ko da abun ya dame sa ba, lallai shi d'in mai hak'uri ne. Wata narkakkiyar soyayyar taji ta sake d'igar mata a zuciya, a hankali ta fad'a k'irjinshi ta ruk'umk'ume shi tsaf, ajiyar zuciya ta shiga saukewa a hankali tana shak'ar k'amshinshi, murmushi ya saki yana jiran yaji ta fad'i buk'atarta shi kuma ya cika mata idan yana da hali, amma sai yaji shiru bata da niyyar magana, shafa bayanta yayi yana d'ora hab'arshi akan kanta cikin sanyayyar murya yace "Me yake damunki?" Saida ta k'ara gyara kwanciyarta akan k'irjinshi cikin muryar kuka tace "Ina sonka *Bab*, dan Allah karka rabu dani, ba zan iya rayuwa babu kai ba." Lumshe ido yayi yana sakin murmushi, kamar babu wanda zaiyi magana a ciki, can ya nisa ya sauke numfashi, sake matseta yayi a jikinshi yace "Ni naki ne uwar yarana, babu abinda zai rabani dake har abada, muna tare." Lek'a fuskarta yayi yace "Kinji ko? Ki kwantar da hankalinki." Jinjina kai tayi alamar to, vibration d'in da yaji cikin aljihunsa ne yasa shi d'agata daga jikinshi, hannu yasa aljihu ya ciro wayar, yana dubawa ganin lambar nan ce ke ta kira ya kalleta yace "Zan fita yanzu, amma zan dawo da wuri." Har ya taka zai wuce ta rik'o hannunshi, juyowa yayi ya kalleta, langab'ar da kai tayi cikin taushin murya tace "Ka kula min da kanka Bab." Murmushi ya mata tare da lumshe ido alamar to zaiyi, sakinshi tayi ya fice haka kawai taji gabanta sai fad'uwa yake kamar ta bi bayanshi. Sai dai babu damar haka da kallo kawai ta rakashi. ______________ Daga nan wurin mai d'inki suka wuce ta bashi, ya tabbatar mata ta dawo da safe k'arfe bakwai zata same su duka, dan haka suna barin nan ganin an fara kiran sallah sai kawai ta biya gidan k'awarta likitar nan, sallah kawai tayi suka mata sallama ta tafi saboda shigowar mijin Rafi'a. Duk da bata so ta tafi ba amma ta mata alk'awarin zata sake dawowa nan kusa, a hankali suka k'arasa gida ba tare data ankara wayarta bata tare da ita ba, tunda suka shiga layin gidan ta ga bak'uwar mota da bata tab'a saninta anan ba sai yau, bak'ar benz ce son kowa k'in wanda ya rasa, kasancewar a k'ofar wani gidan take pake sai ba tayi tunanin komai ba, inda ta saba ajiye motar ta tsaya, Amjad ne ya fara fita ya rufe k'ofarsa, fitowa tayi ita ma ta rufe tana kallonshi da cewa "Ina ga fa anjima dare ya k'ara yi zamu fito wankin motar nan, saboda gobe kaje wurin gasar nan a wankakkar mota." Dariya yayi yace "Ayya, karki bawa kanki wahala, ni a haka nake so na tafi, ai dai Ayyata na da motar ma." Dariya tayi ita ma tana rufe motar ta sab'a jakarta sosai a kafad'a, tunkarar k'ofar shiga sukayi gadan gadan, muryar dake shigar da ita yanayin firgici da fargaba ce ta riski kunnuwanta yana fad'in "Sannunku da zuwa." Makullin hannunta ne ya fad'i da wani irin zabura ta dafe k'irjinta sosai tana fad'in "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un." Dan yanda ya kayar mata da gaba abun ya tsorata ta sosai, zazzaro idonta tayi akan shi sosai kamar wacce ta mutu a wuri. Murmushi ya shiga sakar mata yana tahowa kusansu cikin takon k'asaita da izza, saida ya matso kusansu ya kalli Amjad, *kamar yayi kaki ya tofar*, wata muguwar k'aunar yaron ce da ko Allah baya so a tsananta akan bawansa yaji ta dirar masa, a hankali ya sulale yayi tsuguno irin na maza yana ci gaba da kallonshi, tunda yake a rayuwa da wayonshi dai abu uku ne ya sa shi kuka, na fari ranar da aka zo mishi da al'amarin cikin yaron nan, na biyu kuma mutuwar mahaifinshi da baya gari hakan ya faru, ya so ya same shi a raye dan ya nemi afuwarsa akan k'aryar daya masa, sai yanzu daya d'ora ido akan yaronshi, *d'anshi* mallakinshi, tabbas ya sha zubar da hawaye sai dai bana takaici bane, yasha tuhumar kanshi da aibata kanshi tare da turawa kanshi tambayar ina cikin nan? A wane hali take? Sai dai ko a wajen danginta ya k'asa samun amsar ingancin lafayarta ma bare ya samu nutsuwar zuciya. A hankali ya d'aga hannunshi ya kai kan fuskar Amjad, d'ora yatsanshi yayi akan hancinshi ya lak'ata, da sauri ya fashe da dariya ya kalli Faduma yace "Wallahi da gaske ne, a zahiri e Faduma, yarona ne." Kallon Amjad yayi ya fincikoshi a jikinshi ya rumgume tsam yana tutsashi cikin jikinshi kamar zai mayar dashi a ciki, da k'arfi Amjad ya raba kanshi dashi ya koma jikin Faduma ya lafe, kallon bak'on da ya zo da fuskar mahaifinshi yake mishi, wanene mai kama da Abanshi? Abanshi fa ya rasu, ganin haka yasa Tagur tara mishi hannu yace "Zo nan, zo Amjad, zo ka rumgume Papanka." Mak'ale kafad'a yayi a hankali yace "Um um, kai ba Abana bane, Abana ya rasu." Da sauri ya d'aga kai ya kalli Faduma data gama sarewa tana kallonsu kawai, cikin tuhuma yace "Faduma me yake fad'a haka? Hud'ubar da kika masa kenan?" Kafin tace wani abu ya kalli Amjad ya sake tara masa hannu yace "Kaga Amjad, ni ne Abanka ina raye, tabbas akwai dalilin da yasa mahaifiyarka fad'a maka cewa na mutu, amma gani a raye, ka gani ko?" D'aga kai yayi ya kalleta yana sake cakume lafayarta yace "Ayya wai shine Abana?" A tsorace ta kalleshi, haka ta shiga rarraba ido tsakanin d'an da uban, idan ta k'aryata shi zai d'aga mata hankali, idan tace eh kuma zata zama mak'aryaciya a idon yaron data jima tana tarbiyantarshi, sai kawai ta shiga sako da hawaye suka fara tsere akan kumatunta, mik'ewa yayi tsaye ya kalleshi yana fad'in "Ka gani ko? Ni ne mahaifinka Amjad, ita ma ba zata iya k'aryata ni." Tsaf ya sake ta, hakan kuma yasa tayi saurin kallonshi da mamaki, baya yaja sosai daga gareta yana mata wani kallon tambaya yace "Me yasa Ayya? Me yasa kika fad'a min ya rasu?" Bai jira amsarta ba ya juya ga Tagur ya fad'a jikinshi da k'arfi kamar zai kayar dashi baya, da k'arfi shima ya d'aukeshi sama ya matse gam a jikinshi, sumbatar juna suka shiga yi kama daga wuya kai zuwa fuska, dukansu hawaye ne ke fita a idonsu masu kama da yanayi d'aya, cikin muryar kuka Amjad yace " Karanna karanniy (wai da gaske kai ne Abana)?" D'aga masa kai kawai yayi cikin shashek'ar kuka alamar eh, shima a cikin kuka ya sake cewa " Nigey tanihi din barannuma wannan (Me yasa baka tab'a nema ba)?" Cikin kuka sosai yana sake matseshi yace "Ka yafe min Amjad, ban da amsar da zan baka, ka hukuntani duk ta yanda ya maka zan d'auka, amma ka sani ni mahaifinka ba zan iya rayuwa babu kai ba, karka rabani da kanka kaji." Wani kukan kura tayi ta cakumo Amjad daga jikinshi da k'arfin tsiya, yanda abun ya zo musu a bazata yasa tayi nasarar rabasu, rumgumeshi tayi tsam a jikinta tana binshi da kallon tsana da jin haushi, cikin gigitattar murya ta shiga ja baya kamar zai sake kamoshi tana fad'in "Ka rabu damu Tagur, ka tafi daga nan kayi nesa damu, karka sake kiranshi da d'anka, karka min haka Tagur ka rabu dani na rayu cikin salama." Takawa yayi yana matsawa kusanta yace "Me yasa Faduma? D'ana ne fa, baki da ikon da zaki hana ni kiranshi da haka." Da k'arfi tace "Ina da, Tagur wannan d'ana ne, karka sake danganta kanka dashi." Hanyar shiga gidan ta nufa yayi saurin tareta da azama, fashewa tayi da kuka tana k'ara "Dan Allah ka barni na wuce, wallahi ba zan baka yarona ba, Tagur baka da imani da tausayi, ka fiya son kanka dayawa." Girgiza kai yayi yace "Ni fa ba rabaki dashi zanyi ba, ganinshi kawai zanyi, ki barni nayi magana da yarona, wallahi tafiya zanyi na bar miki shi." Kallon rashin yarda ta mishi tana jujjuya kalaman daya fad'a, ganin kamar tana tunani akan haka yayi saurin cewa "Wallahi Faduma babu inda zan tafi dashi, ganawa kawai zamuyi na tafi." Saida ta harareshi tana sake ziraro hawaye tace "Tagur ka sani fa ba d'anka bane, da bakinka ka fad'i haka." Da sauri ya matso yana marairaicewa ita ma ta matsa baya da sauri sai rawar jiki take, cikin taushin murya yace "Wallahi Faduma na san nawa ne, a waccen ranar ma hukuncin da iyayena zasu d'auka yasa na fad'i abinda na fad'a, ki taimaka ki ban yaron nan naji d'umin jikinshi." Girgiza kai tayi cikin kallon mamaki tace "Tagur idan har yau na yarda na baka Amjad kuka yi hira ta d'a da uba, to tabbas ni ba 'yar halak bace kuma na zalinci iyayena da kaina, ita zuciya mai kyautata mata kawai take so, kai kuma da k'iyayyarka a zuciyata na raini yaron, tsanarka kawai ka koya min a lokacin da babu wani karatu dana iya daya wuce saka so da so." Matsowa ya sake yi yana bud'e hannayenshi zai karb'i Amjad, durk'ushewa tayi ta fashe da kuka tana sake k'amk'ame Amjad sosai har saida shi ma ya fashe da kukan, durk'usawa yayi yana kallonta cikin siririyar murya yace "Karki min haka Faduma, dan Allah ki bani minti biyu kawai nayi magana dashi." Girgiza kai ta dinga yi tunda ya fara magana alamar a'a. Ya fi minti sha biyar da zuwa unguwa bayan tambayar da yayi aka nuna mishi gidan, motarta ce ma ta tabbatar mishi da ya zo wajen, sai dai kuma sai ya ci karo da wani al'amari daya sa shi rud'ani da tsayawar tunani cak. In har mijinta ya rasu to waye waccen? Me suke tattaunawa da har girman al'amarin ya iya tsallake fatar baki har sassan jiki ke aikatuwa haka? Me yasa ta finciko Amjad daga hannun mutumin? Me kuma ya faru yanzun da har ya kaita ga kaiwa k'asa haka? Gaba d'aya jikinshi yayi sanyi sosai, in banda d'add'aurewa babu abinda jijiyoyinshi ke yi, yana so ya fita ko dan ya damk'a mata wayarta, amma tunanin kar ya shiga hurumin da bai shafe shi ba yasa ya kasa, dan ya tabbatar ba zai iya lamuntar jurar ganin wannan tashin hankalin da yake iya hangowa a tare da ita ba, to idan ma *uban d'an ta ne*?. Da wani irin sauri ya dafe goshinshi ya furzar da iska, sake kafe wurin yayi da ido yana sauraren yanda zuciyarshi ke ta tsalle tana kai da kawowa, zafi yake ji daga tafin k'afarshi har zuwa kanshi, zuciyarshi wani suya take masa sosai, kukan da yake iya hangowa tana yi ne ke d'aga masa hankali, ya tambayi kanshi dalilin kukan har ya gaji, babban abun damuwar bai wuce tunanin waye mutumin ba? Haka kawai mace mai fara'a da saka wasu murmushi, tashi d'aya daga zuwanka ka birkita mata lissafi ka sata kuka haka. Wani tuk'uk'in bak'in ciki ne ya sake hantsalo masa daga zuciya ya yo sama ta yanda dole yake buk'atar amayar da shi, inba haka ba kam yau kan mai uwa dawabi za ayi. Da k'arfi ya bud'e motar ya zuro farar k'afarshi, saida ya fita gaba d'aya ya mayar da k'arfi ya rufe, takawa ya shiga yi cikin nutsuwa da salo da kuma sanyi, sai dai kana kallon fuskarshi zata fallasa maka sirrin zuciyarshi, zaka san ranshi a b'ace yake ta yanda zai iya aikata komai, makullin motar da wayoyin hannunshi duk ya zuba aljihu. Yana k'arasawa ya tsaya a kansu dan har yanzu suna durk'ushe, ido biyu sukayi da Amjad wanda yasha rumguma a hannunta ko motsin kirki ba yayi, hannu ya zura a hankali cikin nutsuwa da k'arfin hali da tarar aradu da kai ya cakumo...馃槣 *Idan na ga comment sai ku ji ci gaba* *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 17:14 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _30_ Hannu ya zura a hankali cikin nutsuwa da k'arfin hali da tarar aradu da ka ya cakumo Amjad dake jikinta yayi sama dashi ya sab'a a kafad'arshi, kamar wani d'an shekara biyu sai kawai ya lafe a jikinshi yana shashek'ar kuka, bayanshi ya shiga bubbugawa a hankali. Da sauri ta mik'e ta juyo kamar zata kifa a k'asa dan ganin wanda ya k'waceshi a hannunta, tana sauke idonta cikin nata haka kawai ba gaira ba dalili ta ji wata nutsuwa ta zo mata, haka kawai taji ranta yayi sanyi kamar mai ceto ne ya zo gareta, hannu tasa tana share hawaye ta sunkuyar da kanta. Rik'e k'ugu yayi cikin jin bala'i yana kallon Hasheer yana tauna leb'enshi, mugun kallon da yake mishi da jin haushi yasa Hasheer binshi da wani kallon raini, lokaci d'aya kuma ya d'auke kanshi ya mayar kan Faduma, cike da kulawa harshe a tausashe sosai bakinshi na rawa rawa yace "Wa..ye wan...nan?" Kallonshi tayi ta kuma juya ta kalli Tagur, had'e yawu tayi sosai tana tunanin abinda zata fad'a, tsohon mijinta zata ce? K'arya fa kenan, ko kuma tsohon saurayinta? Sannan uban d'anta dake rumgume k'irjinshi a yanzu? Yawun ta sake had'ewa ta kalli Tagur. Da tsananin mamaki ya matso kusanta hakan yasa taja baya har tana neman fad'awa jikin Hasheer, nunata yayi da yatsa yana fad'in "Faduma kunyar fad'a masa kike ji? Kina jin kunya ne ki ce ni ne uban Amjad? Waye shi ma da zai tsaya haka cikin gadara yana tambaya waye ni? Bayan kuma ni ne ya dace nayi wannan tambayar." A zafafe yayi kan Hasheer ya tara hannu zai karb'i Amjad yana fad'in "Malam bani yarona kaji." Ko motsawa baiyi ba sai wani kallo daya jefe shi dashi, sake matse Amjad yayi yana ci gaba da shafa shi, lumshe idonshi yayi jin yanda gabanshi ke ta fad'uwa, kalmar uban Amjad yake ta nanatawa, ba zai iya jura ba! Ba zai iya ba, me yasa Kalli ya fad'a masa mijinta ya rasu? Da bai yarda ya ci gaba da nink'aya a cikin kogin k'aunarta ba, duk da Allah ne ya jarabe shi da ya fara addu'a Allah ya yaye mishi, in kuma mijinta ya rasu wannan kuma uban Amjad ne, to maza nawa tayi tarayya dasu? Da wani k'arfi ya damk'i bayan Amjad saboda wani jiri ya ji kamar zai kifar dashi k'asa, da sauri ya bud'e ido ya kalleta a lokacin ita ma shi take kallo, saida ya mata alama da ido cikin fitar da kowace kalma a muhallinta yace "Wuce cikin gida." Hannu ta mik'a zata karb'i Amjad dan yanayin daya mata magana ba zata iya ce mishi cas ba, a nutse ya sake cewa "Shiga ciki." Cikin shakkarshi ta juya zata shiga ciki, cak ya rik'e hannunta yana kallonta kallon da babu wasa a ciki, dake akwai hasken fitili yasa komai gani ake, rufe idonshi yayi sanda ya kama hannunta tare da danne leb'enshi na k'asa. Baisan asalin wane hali ne ta shiga ba sanda ya rik'e ta, amma dai tabbas yaji hannun nata na rawa alamar tsoro da firgita, sannan yana jin yanda duk tsigar jikinta ta tashi, k'ure fuskarta yayi da kallo a matsanancin kusan da suka samu, hatta da numfashinshi akan ta yake sauka, duk da idonta a rintse suke bakinta na rawa bai hana shi fad'in "Waye wannan Faduma?" D'aga kai tayi ta kalleshi amma ta kasa cewa komai, sake matse hannunta yayi yace "Waye na ce?" Sake rintse idonta tayi hawaye suka zubo mata, juya harshenshi yayi cikin tubanci yace "Nace waye wannan da zai shiga abinda ya shafi ni da ke? Saurayinki ne ko kuma dashi kike rayuwarki ta yanzu?" Da sauri ta kalleshi, hannunta taja tana son k'wacewa, amma saiya sake rik'e shi gam bai bata damar haka ba, kallonshi tayi tana yatsina fuska tace "Sake ni Tagur." A zafafe yace "Ba zan sake ki ba har sai kin fad'a min waye wannan? Inba haka ba wallahi ba iya Amjad zan d'auke daga wurin nan ba har da ke kan ki ma." Zaro ido tayi tace "Kamar ya? Ka kaimu ina?" Kafin ya bata amsa Hasheer ya matso kusansu, cikin sanyin jiki ya d'ora hannunshi kan wuyan hannun Tagur dake rik'e dana Faduma, a hankali a mugunce kamar bashi yayi ba ya matsi wuyan hannunsa, inda ya had'a tare da k'ashin dake tsakanin wuyan hannun da tsintsiyar hannu, wata damk'a ya ma wurin ba ta wasa ba, a haka kuma ya danne wurin sosai yana murzawa, a zahiri kuma saika rantse tafiyar tsutsa yake masa, uwa uba ma ka kalli fuskarshi wacce ya kalli Tagur da ita yana sakar masa murmushi yace "Kayi hak'uri da rashin gabatar maka da kaina, sake ta sai muyi magana." Cikin jin haushi ya kawo hannunshi shima ya damk'i na Hasheer, a hassale ya kalleshi yana zaro ido yace "Ban tambayeka ba, ban damu da sanin waye kai ba, ita nake so naji daga bakinta." Tsaf ya had'e murmushin da yake masa, cikin salon dubara ya lank'wasa wuyan hannun yana neman karya mishi shi, hakan yasa shi rank'wafowa yayi saurin sakin hannun Hasheer. Faduma na ganin haka gabanta ya sake fad'uwa, da sauri ba tare da tasan ma tayi ba ta d'ora duka hannayenta biyu akan damtsen Hasheer tana rarrashi cikin muryar kuka tace "Dan Allah kayi hak'uri ka rabu da shi, ku rufa min asiri kar kuyi fad'a anan." Saida ya kalli hannayen nata, jan lallen duk da ya fara gogewa amma dai ya birgeshi, wani murmushi ya sakar mata ya saki hannun Tagur, cikin sanyayyar murya yace "Fad'a da girmanmu? Ni mamaki ma nake taya da hankalinki kike kula mutane irin wad'annan da tarayya dasu babu abinda zata k'ara miki face zubewar kima." Da k'arfi ya matso yana fad'in "Zubewar kima? Mutane irina? Kasan ko ni waye kuwa?" Kallon mai bisa ruwa ya masa ya d'an tab'e baki, da sauri ta juya tana shiga tsakaninsu da k'arfi tace "K'arya ta fad'a? Na ce k'arya ya fad'a Tagur? Ka fad'a min me mu'amalata da kai ya anfane ni dashi banda zubewar kima da daraja." Dakatawa tayi tana share hawaye, cikin harshen tubanci ta kalleshi a marairaice tace "Tagur tarayyata da kai kimata ce ta ragu da kuma zubewar mutumcin iyayena, k'ok'arinsu na shekara goma sha biyar rana d'aya ka lalata shi, bayan haka kuma sanda sakamako ya bayyana saika sake saka k'afarka kayi patali da sauran darajar data rage musu, Tagur ko sau d'aya ka sake tunani akai na? Ko sau d'aya ne a rayuwarka ta baya kayi tunanin wane hali nake ciki? Ka tab'a tambayar kanka ina nake da cikin dake jikina? Ka tab'a tuhumar kanka da rashin kulawa da sakaci da ka bawa yaron?" K'unar da zuciyarta ke yi da tafasa ne yasa ta saka hannu biyu da iya k'arfinta ta tureshi, yanda abun ya zo masa a bazata yasa shi fad'uwa k'asa, nuna shi tayi da yatsa murya a kausashe tace "Wallahi Tagur na tsaneka na tsani ahalinka, bana son sake ganinka a rayuwata, idan baka fita a hanyata ba to ka sani akan ka ne zai zama na farko dana fara kashe mutum a duniya, ka sani ni da Amjda ba ma buk'atarka cikin rayuwarmu, zan ci gaba da jajircewa da *neman na kaina* dan ganin na ingatta rayuwarsa, ni ba isassa bace amma da taimakon Allah zan ci gaba da kula da tarbiya da kuma rayuwar yarona, na isje shi komai a rayuwar nan ta duniya kuma zan tsaya masa akan komai kamar yanda uba zai tsaya masa." Ba wai Hasheer da duk yaji abinda ta fad'a ba kuma ya shiga matsanancin firgici akan hakan, har Tagur dake yashe a k'asa saida yayi mamakin haukanta, akan d'an shi fa ta masa haka? Kuma a gaban wani k'ato da bai san wanene ba, sannan har take ikrarin wai ta ishi d'anta zata iya tsaya masa akan komai kamar yanda uba zai masa, lallai kam zai shigar da ita hankalinta, zai fahimtar da ita gaskiyar al'amarin, zai ganar da ita sahihiyar maganar daya dace ace ana d'orawa a mizanin hankali, zai tunatar da ita ko a cikin Alqur'ani ma cewa akayi *wad'anda aka haifa ma arzik'in yaron yana tare dasu, ma'ana cin su, shan su, tufatar dasu da lura da lafiyarsu*, hatta da wad'anda suka haifa d'in duk suna k'ark'ashin kulawar uba namiji ne, zai gargad'eta kan wannan k'udiri nata, domin kuwa ci gaba da yak'i akan shi tamkar tana jayayya da ayar Alqur'ani ne. Yasan shi mai laifi ne, amma akwai wanda suka fi shi aikata laifi makamancin haka, dan haka wannan ba hujja bace da har zata kwanto wata babbar b'araka ta raini da shashanci tsakaninsu ba. Faduma kam na gama fad'a a fusace ta tunkari gidan ta shige bata kula da Amjad dake hannun Hasheer ba, abinda ta sani ne kawai in har yayi sakacin daya karb'eshi a hannunshi, to ba shi ba har danginshi sai ta tashi hankalinsu a aiki, Dada na zaune da babban bokoti gabanta tana had'in tsumin humra ta shigo, da sauri ta kalleta ganin yanda ta shigo, cikin kulawa tace "Faduma lafiya? Me yake faruwa ne?" Bata kulata ba sai d'aki data shiga tana share hawayenta, da sauri ta mik'e ta bi bayanta tana gyara d'aurin zanenta tana ci gaba cewa "Ke Faduma, me yake faruwa ne wai? Ina Amjad d'in?" Saman kujera mai zaman mutum uku ta zauna, gwiwar hannunta ta d'ora kan cinyoyinta hakan ya bata damar dafe goshinta da hannu biyu ta duk'ar da kai, numfarfashi ta shiga saukewa a hankali tana son dawowa nutsuwarta, kusanta dada ta zaune ta dafa kafad'arta tace "Fadu, fad'a min ina Amjad? Me ya same shi?" Kafin ta bata amsa taji wata tattausan sallama a tsakar gidan, mik'ewa tayi da sauri gabanta na fad'uwa ta fita tana amsa sallamar, ganin kyakyawan mutumin da kuma Amjad a kafad'arshi yasa ta k'arasawa da sauri tana dafe da k'irjinta tana furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, Amjad, me ya samu Amjad d'in?" Fuskar matar ya kalla mai d'auke da nutsuwa da dattijantaka, cikin sanyi sosai ya d'ago Amjad daga jikinshi sai dai kuma baccin da yake yasa shi rik'e wuyan rigarshi gam da hannu, hakan yasa ya kasa b'amb'areshi daga jikinshi, lura da hakan yasa ta kauce mishi a hanya tana fad'in "Ko ka wuce ciki saika shinfid'eshi." Kallon k'ofar d'akin yayi da take nuna masa, to ba kowa ne? Mijinta fa ita? Kallonta da matsakaitan idonshi masu haske kamar zai tambayeta, ganin haka yasa ta cewa "Karka damu wuce ciki, mahaifiyar tashi ma tana nan zaune." Sake kallon k'ofar yayi a karo na biyu, a hankali ya d'aga k'afarshi ya taka, wata mijirya yaji k'afafun nashi duk sun kwasa, haka ya wuce ciki tare da zage takalminshi cikin nutsuwa kamar wanda baya son motsa jikinshi, jin sallamar a k'ofar d'akin yasa ta saurin d'agowa ta zuba idonta akan mai shigowa. *Bari mu ji ya Tag yake* Tana shigewa ciki ya mik'e a zafafe yana zazzare ido, hannayen rigarshi ya shiga tattarewa yana dantse da harshenshi, ba zai iya magana ba ko kad'an, an kai matakin da zai iya datse harshenshi ya jefar idan yace zaiyi magana, dan haka bai furta komai ba saida ya gama nad'e hannayen rigar tsaf, kallon juna sukayi da Hasheer dake mishi kallon mahaukaci, sam babu nutsuwa a tare dashi, tab'e baki yayi a hankali ya nufi shiga cikin gidan shima, da kallo Tagur ya bishi babu bakin magana, yana ganin shigewarshi ciki da sallama, da sauri ya nufi inda motarshi take, ranshi a b'ace yake, ga da ga yana kallon wani amma babu damar magana, ya dantse hak'ora sosai har saida muk'amuk'inshi suka fito, wani dutsi ya samu a k'asa yana zuwa ga motar ya baza shi a madubin baya, wanda girman dutsin yasa madubin fashewa, ganin bai fashe yanda yake sa ba yasa shi jujjuyawa ko zai samu wani, sai dai a inda yake akwai k'arancin duwatsun, sai yasa k'afarshi ya shiga dukan motar yana ji kamar zai cijeta, sai dai ya gama billinshi shi kad'ai kuma ya bud'e mazaunin dreba ya tuk'a a wani matsiyacin gudun da sai Allah ya kare kawai. *FadHash*馃様 Kasa mik'ewa tayi duk da ta so haka amma bata tashi ba saboda gaba d'aya kanta sara mata yake, gyara zamanta kawai tayi hakan ya bashi damar shinfid'e Amjad kusa da ita, har ya mik'e da nufin juyawa yaji har yanzu hannunshi na wuyan rigarshi tamau kamar ana shirin rabasu ne baccin ya d'auke shi, komawa yayi ya sunkuya ya kama hannunshi a hankali zai b'amb'are, da sauri ta matsa daf dasu har saida damtsen hannunta ya shiga gugar nashi damtsen ta zura hannunta ta d'ora kan nashi tana fad'in "Ina zuwa." Satar kallon hannayensu yayi da suke gugar juna, sannan ya bi hannunshi da kallo wanda ta d'ora nata akai, d'aya hannunta ta zura saman kanshi ta shafa tare da hura mishi iskar bakinta, duk da bacci yake amma saida ya d'an motsa, hakan yasa ta sunkuyawa sosai ta kai bakinta akan goshinshi ta sumbata, a hankali ya sassaura rik'on daya ma rigar Hasheer, kallonta yayi yana kallon ikon Allah, jin ya sassauta rik'on yasa ta saurin janye hannun Hasheer ta soka yatsunta biyu a cikin tafin hannun Amjad d'in alamar ya rik'e nata, ram yayi da yatsunta da sauri Hasheer ya mik'e tsaye, kusancin da suka samu ya so ganin bayanshi, dan sai yanzu ne yaji asalin wani taushin k'amshi na tashi daga jikinta ne ko tufafinta oho! D'agowa tayi ta kalleshi cikin nutsuwa tce "Nagode." Ido kawai ya zuba mata, dan gaskiya al'amarinta yau daya gani ya gama tarwatsa masa komai, bai san ya zaiyi ba? Gashi kuma bai da ikon tambayarta tunda babu komai tsakaninsu. Dada ce ta matso kusanta sosai cike da tausayawa ta dafa kanta, kallon Hasheer tayi da shima ke kallonta tace "Sannu ko bawan Allah." Kallonta yayi amma bai ce mata komai ba, cikin muryar jimami tace "Dan Allah me ya faru ne dasu? Hankalina ya kwansa kwanciya saboda tunanin abinda ya faru." A hankali ya mayar da dubanshi kan Faduma, a lokacin ta dafe kanta sosai tana k'ok'arin zare yatsunta daga hannun Amjad, saida ta janye sannan ta sake dafe kanta da duka biyun, cikin rawar murya sosai tace "Dada kaina ciwo yake, Tagur ya zamar min matsala." Da sauri ta zagaya b'angaren damanta ta zauna kusanta tana fad'in "Tagur ne ya zo? Haba shiyasa na dinga jin kamar hayaniya a k'ofar gidan, wai me ya miki?" Girgiza kai kawai tayi ba tare data kalleta ba tace "Dada me kuwa zai min daya wuce tayar min da hankali." Dafa kafad'arta tayi tace "Ke kuma kika dinga kuka ko? Wai Faduma yaushe zaki daina jin tsoron mutumin nan ne? Yaushe ne zaki d'aga ido ki kalleshi ido cikin ido sannan ki tsinkawa fuskarsa mari? Yaushe ne zaki iya bud'a bakinki ki fad'a masa duk abinda ke ranki wanda ya jima baki amayar ba? Ya ka..." Muryar Hasheer ce suka tsinkaya a matuk'ar tausashe yace "Ga wayarki." Kallonshi duk sukayi sai Faduma data saka hannu ta karb'a tana kallonshi da mamaki tace "Lah! A ina na jefar da ita?" Ba tare daya daina kallon fuskarta ba yace "Shagon Ibrahim." Zaro ido tayi tace "Kai wallahi na cika shiririta, ya akayi ban fargaba ba tun lokacin?" Kallonshi Dada tayi ita ma tace "Ka zauna ko ruwa aka maka ka sha." Wani murmushin yak'e ya mata ya d'an girgiza kai a hankali, kallon fuskar Faduma yayi yace "Saida safe, kisha magani kafin ki kwanta, kiyi nesa da duk wanda yake baki damuwa da ciwon da kai, yin haka shine *zaman lafiyar kowa*, kinji?" A tare suka k'ura mishi ido da Dada, sai kuma suka kalli juna, murmushi Dada ta saki ta sunkuyar da kanta sai kuma ta kalleshi tace "Ya kamata dai ka fad'a mata, a duniya idan tana da hawan jini bai wuce tsinannan Tagur d'in nan ba." Lumshe ido tayi da k'arfi, Tagur? Uban d'anta ne k'anwar mahaifiyarta ke tsinewa albarka haka? Har k'asan zucuyarta bata ji dad'i ba, amma ya zata yi? Shi ya siyawa kansa, bud'a ido tayi ta kalleshi a sanyaye tace "Zanyi insha Allahu, nagode sosai da kulawa." Juyawa yayi zai tafi tayi saurin cewa "Gashi har yanzu ban san sunanka ba kuma muna ta had'uwa?" Cak ya tsaya bai juyo ba, wani kuka kuka yaji yana sha'awar yayi, a gaskiya lamarin na yau ya tab'a shi sosai, har yanzu ya kasa gane dalilin da yasa Kalli ya mishi k'arya cewa mijinta ya rasu? Me yasa? Miye asalin abinda ya faru da ita? Abinda ya kamata ya sani kenan kafin ya yankewa kanshi hukuncin yarje mata ta ci gaba da gina fadarta a zuciyarshi.A hankali ya juyo ya sauke idonshi akan ta, cikin nutsuwa da bawa kowace kalma hakk'inta ya furta " *Hasheer Abdul rahman nakiri*." Zaro ido Faduma tayi ta mik'e da sauri ta tunkare shi, saida ta nuna shi da yatsa manuniya tace "Kai d'ansa ne? D'an shi ne dama? Ikon Allah." Gyara tsayuwa yayi da wani mad'aukakin mamaki yace "Kin san shi ne dama?" Jinjina kai tayi cike da kunya ta sunkuyar da kanta tace "Mutumin kirki ne, a shekara ta dubu biyu da goma sha d'aya, ya d'auki nauyin kayan d'akin wacce tayi ta farko a gasar musabik'a da akayi ta wannan shekarar." Saida ta d'ago ta kalleshi tace "Ni ce ai." Wani sahihin murmushi ya mata yana lumshe ido, da k'yar ya k'ak'aro magana yace "Ashe da garzuwa nake tare." Murmushi tayi ita ma tana sunkuyar da kanta tace "Ashe da babban mutum nake tare? Kayi hak'uri da abinda ya faru d'azu acan shagon." Dada ce ta mik'e tana fad'in "... *Comment...* *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 17:14 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _31_ "Faduma, ni fa ina ganin gobe da safe zanje ofishin yan sanda na kai k'arar Tagur, zan sa a masa tsakani da yaron nan dan ya barsa ya rayu cikin aminci, idan ba haka ba kuma to fa ki sani wata rana zaki kai Amjad makaranta amma ki je baki same shi ba, tunda dai dole zai dinga fita d'aukar karatu, Tagur kula na fahimtar duk wani shige da ficensa to zaki rasa d'anki." Faduma dake ta mata kallon kwab'a tana mata alama da ido da ankarar da ita tayi ko dan bak'on dake tsaye amma ina bata fahimta ba saida ta dasa aya, jinjina kai tayi tace "Zamuyi magana daga baya Dada." Kallon Hasheer tayi tace "Mun gode fa sosai, a gaida yara." Kallon Dada yayi a karon farko daya mata magana yace "Wai me yake faruwa ne? Ba d'anshi bane?" Saida ta tab'e baki tace "Eh shi ya haife sa." Da wata alamar tambayar ya kalleta yace "In hakane kuma me yasa duk wannan tashin hankalin ke faruwa?" Gyara tsayuwa Dada tayi zatayi magana Faduma ta rik'e hannunta, shiru tayi ta kalleta murya k'asa k'asa tace "Me yasa ba kya so a fad'a masa? Ba saurayinki bane?" Zaro ido tayi ita ma murya k'asa k'asa tace "Haba dada, wannan d'in? Kinga yayi kama da aji na? Ki daina fad'a kar kisa ya wulak'anta ni, mahaifinsa ne mai masana'antun risham da kike ji da gani." Kamar zata cinyeta tace "Amma ai mahaifinsa ya rasu, kika sani ko shine mamallakinsu yanzu." Saida ta juya hatshenta zuwa tubanci tace "Shiyasa na ce kiyi shiru, kar ki sa ya fahimceni ba daidai ba." A tare suka kalleshi, idonshi baya kansu yana ga wayarshi daya ciro a aljihu, sai dai tsaf ya ji me suka ce in banda sanda tayi yarenta, wani nagartaccen kallo ya watsa mata yana tura wayarshi aljihu yace "Ke uwa ce, bai kamata a rabaki da d'anki ba, amma uba kuma ya fiki hakk'in rik'e abunsa, in har kinsan ba akan gaskiya kike ba zaifi ki jefar da makamanki, idan kuma kin tabbatar da gaskiyarki, to ki nemi tsayawa akan hakk'inki, amma dai raba d'a da ubansa ba shine mafita ba." Juyawa yayi yana sake fad'in "Saida safe." Da kallo ta bishi har ya fita, da sauri dada ta kalleta tace "Da kin bari na fad'a masa watak'ila ya taimaka mana, dan ni wannan Tagur d'in ji nake kamar na kashe shi." A marairaice ta kalleta kamar zatayi kuka tace "Dadaaaa! Na san Tagur yayi laifi kuma kuna jin haushinshi, amma hakan ba shi zai goge jininsa dake yawo a jikin Amjad ba, sannan ba shi zaisa sunansa ya canza daga uban Amjad ba, haihuwa wata abu ce da k'arfin dangantakarta ya girmi tunanin mai hasashe, dada haka ma duk namijin da shine ya rabaka da budurcinka ya kan zama na musamman, ko da kuwa ana musamman d'in shi makiri ne, dada har cikin raina nake ji idan kika zage shi, hakan ba dan so bane sai dan wannan alak'ar ta jini data had'a ni dashi da kuma *d'anmu*." Sanyin da jikinta yayi ne yasa ta shafa kumatunta da hannaye biyu tace "Kiyi hak'uri kinji, na fahimceki yanzu kam, watak'ila ko dan ban haihu bane shi yasa bansan girman yanfa ake ji a game da alak'ar ba." Da sauri tasa hannu ta rufe mata baki tana girgiza kai tace "A'a Dada karki fad'i haka dan Allah, ba da wata manufa na fad'a ba nima, Dada ni ba 'yarki bace? Ga kuma Amjad ma jikanki kuma d'anki, ai baki da wanda suka fi mu kamar yanda bamu da wanda suka fi ki." Murmushi tayi ta d'auke hannayenta daga kumatunta tace "Na fahimce ki Faduma, yanzu dai ki d'auke shi daga nan ki shinfid'esa d'akinshi." Girgiza kai tayi tace "A'a Dada, ai yau Amjad tare dani zai kwana, dole na saka k'warara tsaro akan shi yanzu, dan tabbas abinda kika fad'a zai iya yiwuwa." Jinjina kai tayi tace "Gaskiya kam, ai ni da saki bani dama ma da gidansu zanje na samu marar mutumcin Haitimin nan na fad'a mata ta ma d'anta magana ya fita a harkarki, inba haka ba kotu ce zata rabamu dashi." Dariya tayi ta juya ta d'auki Amjad tana fad'in "Ki barsu kawai Dada, bana son wani abu da zai sake nuna min fuskar matar nan." D'aki ta nufa dan shinfid'e shi, sosai ta gyara mishi kwanciya ta shafeshi da addu'a da sumbatarshi, tana fitowa sallah isha'i suka fara gabatarwa da aka d'an jima dayi, suna idarwa abinci suka ci a tare suna ci gaba da tattaunawa har suka ida, kowace d'akinta ta shiga bayan sunyi sallama, sai dai babu wacce tayi bacci a lokacin sai tunanin al'amarin duniya da duba wayoyinsu da sula shiga. Saida dare yayi kafin ta gyara kwanciyarta tana k'amk'ameshi a jikinta tsam har bacci ya d'auketa. Yana shiga tun a harabar gidan Husna ta fito wai mishi barka da zuwa, yanda ranshi ke matuk'ar b'ace yasa ko da ya fito daga motar ko rufewa bai yi ba ya tunkari shiga ciki, da sauri ta bi bayanshi tana fad'in "Yaya Tag sann..." Bai barta ta k'arasa ba ya juyo da wata irin had'add'iyar fuskar razanarwa ya nuna ta da yatsa murya a kausashe yace "Wallahi kika min magana sai na cire harshenki na jefawa kare, in kina da zuciya karki sake shiga harkata." Juyawa yayi a fusace ya shige ciki, da k'afa ya tura k'ofar ta bud'e ya shiga ciki, kujerar daya fara kaiwa kusa da ita yasa k'afa ya ture, labulen dake jikin bango wanda ma'aikata ne musamman sukayi aikin sa shi ya kama da k'arfi ya fizgo shi, har saida wani b'are daga cikin sumiti ya zubo k'asa tare da fad'uwar k'arfen dake cikin bangon, a tsiyace ya k'arasa gaban kujera ya zauna k'asa yana dafe kanshi, a hankali kamar zai fashe da kuka ya furta "Me yasa Faduma? Waye wannan? Miye had'inshi da ita? Wace irin rawa yake takawa a cikin rayuwarta da har yake da damar shiga gidan a sanda ya so? Hatimi ce ta shigo da sauri saboda yanda Husna ta fad'a mata ya mata da yanayinshi yasa ta tabbatar ba lafiya ba, tana shigowa kusanshi ta zauna k'asa ita ma tana kallonshi tace "Tagur lafiya? Me yake faruwa da kai daka shigo haka?" Dubanta yayi sai dai bai ce komai ba, a hankali ta sake tausasa murya tace "Yi hak'uri fad'a min, fad'a min me yake faruwa ne haka? Wa ya b'ata maka rai?" Rintse ido yayi yana cije bakinshi, jinjina kai ya shiga yi kamar k'adangare, ya jima haka kafin ya kalleta, cikin birkitacciyar murya yace "Waye shi? Waye shi da Faduma zata ci mutumci na a gaban idon shi?" K'wafa yayi mai k'arfi yana sake jinjina al'amarin, tsaki Hatimi tayi dan sai yanzu ta fahimci a inda matsalar ta fito, kallo ta mishi mai kama da harara tace "Kai yanzu ko kunya baka ji ba da ka kira sunanta gaba ba? Tagur wai me yake damun kanka ne? Ba zaka fita a sabgar yarinyar nan ba kake nufi ko me?" A zafafe ya kalleta yace "Ayya kamar ya na fita a sabgarta? D'ana ne fa a tare da ita? Hak'uri zakiyi wallahi tunda dai har muka samu k'aruwa ni da ita, Ayya duk tsanar da kike mata dole kiyi hak'uri, Faduma kam uwar jikanki ce." Ita ma cikin fad'a tace "To yanzu daga wajenta ne kake? Kuma akan wa naji kana magana?" D'auke kallonshi yayi daga kanta yace "Wani banza ne mai kama da *Bin ladan*, a gaban shi fa Faduma ta tsintsinka min mutumci na." K'wafa ya sake yi mai k'arfi yace "Wallahi saita gane kurenta, kuma shi ma zai san ya tab'a ni, ba dai ta nuna ita zata iya da d'awainiyar Amjad ba? Wallahi saina nuna mata k'arya take ba zata iya ba, sai na sa Faduma ta zo neman taimako na a matsayina na ubansa, sai na sa ta durk'usa kan gwiwarta sannan ta nemi alfarmata na mata taimako a kan abinda ya shafi yaron, sai ta zubar da hawaye ta rok'e ni na amsa nine uban Amjad." Jinjina kai ya sake yi ya mik'e ya nufi d'akinshi, da kallo ta bishi kafin ita ma ta mik'e tana tab'e baki, a ranta kuwa fad'i take "Ga ka ga wurin nan ai, yanda kake jin batube ne kai mai zuciya, haka ita ma jinin tubawa ce gaba da baya kuma nonon batuna tasha, abu kuma ya had'a da d'anta ina tabbatar maka ba zata yarda tayi wannan zubewar bak'ar tasar ba, sai dai ka kashe ta akan yaronta." _____________ Tun a hanya yake sak'a da warwara, tunani fal kanshi kamar zai fasa mishi kai, sai dai duk tilin tunanin nan a k'arshe a dunk'ule ne yayi zaune daram akan tambaya d'aya, *wacece ita*? Wannan tambayar ce kawai ta sukwani dokin zuciyarshi da son gano ainihin wacece d'in, da wannan har ya isa gida, abun daya sauk'ak'a mishi lamarin shine tarairayar daya samu a hannun Saudat, dama kuma bai samu shiga wajen Umma ba bare ya had'u da matsalar d'aya (Mujaheed), shiyasa kaso mai girman gaske ya washe a zuciyarshi saboda yau Saudat tayi niyyar zama mace kuma ta zama a wannan daren tunda har ta kai kanta turakarshi. Amma a lokacin da yake daf da tura yan sak'wanshi zuwa gonarta domin yi mata ban ruwa tare da samun ran sake samu wasu anfanin gonar, sai tayi saurin zillewa daga gare shi a zabure, da k'arfi ya damk'ota ido rufe yana son kai wa bakin gadar. Da sauri ta girgiza masa kai tana fad'in "A'a dan Allah Bab kar ka zubar a ciki, wallahi magani na ya k'are yau ban sha ba, ka bari zuwa gobe idan na je na d'auko sai kayi yanda kake so." A halin da yake ciki, a daidai wannan k'adamin baya jin kira saboda nisan da yayi, damk'arta yayi da kyau ya zazzage duk abinda ya cure mishi a mara a jikinta, sanyi jikinsa yayi tare da tsatsafiwar gumi, kiciniyar tashi ta shiga yi tana d'an ture shi, d'agata yayi ya kwanta ruf da ciki a gefenta, da sauri ta mik'e ta rarumi rigarta zata fita, da wani irin saurin bala'i ya tare gabanta, juyawa yayi ya rufe k'ofar d'akin da key ya juyo ya kalleta, nuna mata ban d'akinshi yayi ya mata alama kawai da hannu cewa ta shiga nan. Duk da tsyuwarshi a gabanta a haka yasa gabanta fad'uwa, kwarjini da kuma wani tsoronshi, dan ji tayi kamar yau ta fara ganinshi babu kaya, yanda ya tsaya a gabanta haka kamar yan boxin da tale gani a mbc action yasa ta kawar da kanta tana jin kunyar kallonshi, baki na rawa ta furta "Zan...shi.ga ban.. d'aki ne." Sake nuna mata yayi cikin jin haushin ta sa shi magana a yanzu yace "Ki shiga nan kiyi duk abinda zakiyi." Turo baki tayi tana hararenshi ta k'asan ido tana fad'in "Ni a d'akina zan shiga." Rab'ata yayi ya wuce ya d'auki towel d'in shi daya fito daga wanka ya ake anan ya d'aura a k'ugunshi, saida ya taka ya nufi hanyar ban d'akin ya juyo ya kalleta yace "Wallahi kika bar d'akin nan sai ranki ya b'ace Saudat, na fad'a miki." Ya murd'a k'ofar zai shiga cikin masifa tace "Wai me kake nufi ne dani? Kullum anan nake shiga ne nayi abinda zanyi? To ba zan shiga nan d'in ba d'aki na zanje." Takowa ya shiga yi kanta a wani gadarance amma fuskarshi a had'e tamau, ja baya tayi sai da taji ta dangane da sofa d'in dake gefen gadon ta tsaya, cikin muryar fad'a da a shekara baya mata magana da irinta sau d'aya yayi magana, kakkausan murya dake nuna zai iya mata tashin hankali, muryar dake nuna zai iya d'auketa da mari, a d'an tsawace ya nuna kanshi yace "Saudat na miki kama da d'an iska ne?" Da sauri ta girgiza kai dan ya gama tsorata ta, sake tambayarta yayi da cewa "Sakarai kika d'auke ni ko mahaukaci? Kin d'auka ban gane manufarki bane? Kin d'auka haka nake baki sake ban fahimci dalilin da yasa kike son fita daga d'akin nan ba da gaggawa ba?" Kamar zatayi kuka ta girgiza kai tana sake gyara rigarta tace "Wallahi ni babu komai, kawai zan koma d'akina ne." Wani murmushi yayi mai ciwon gaske ya girgiza kai yace "Kina sauri ne zaki fita, kina fita zaki bud'a fridge ki d'auki coka da para kisha saboda ba kya son haihuwa dani." K'wafa yayi mai k'arfi ya juya a fusace ya nufi ban d'akin, duburburcewa tayi tana mamakin ya akayi yasan nufinta? Saida ta ga shigewarshi ta zauna kwaram kan sofar kamar an tura ta, bata sake motsawa ba har ya fito, shirin bacci yayi cikin nutsuwa da sanyin jiki kafin ya kwanta ko kallon inda take bai sake yi ba har ya kwanta abin shi. *Lahadi* Tun asuba da suka tashi suke ta shirye shirye suna kimtsawa, saida ta taya shi yayi wanka ta shafa masa, k'wai da dankalin hausa, ya fara ci zuwa lokacin 07:30 tace zata je ta karb'o kayanshi, tana fitowa ta tarar da abun mamaki, babu motarta babu labarinta sam, duddubawa ta shiga yi tare da kallon komai a tsanake tana son gane wani abu, dafe k'ugu tayi tana tunanin ina motar ta take? Wa ya d'auka? Ta yaya? Ganin tunanin ba zai fisheta ba sai kawai ta taka a k'afa ta isa bakin titi, bata sha wahalar samun d'an sahu ba saboda yau lahadi, dake ba nisa ne da wurin ba dan danan suka isa, tana sauka ta kalleshi tace "In ba damuwa ka jira ni zan shiga na fito sai ka mayar dani." Jinjina kai yayi yace "Ba damuwa Hajia." Shigewa tayi shi kuma ya gyara zama, sai dai kamar yanda tayi ta tunanin zata iya riska hakane ta kasance, dan kuwa bai gama ba yana cikin had'e rigar ne, ranta a b'ace ta juyo ta sanarwa d'an sahun ta biyashi ya tafi, komawa tayi ta zauna tana kallonshi shi kuma yana ci gaba da bata hak'uri, dan yau ya ga fuskarta a had'e sosai ba kamar kullum ba. 07:45 ya kammala ya bata ta cika mishi kud'inshi, da sauri ta fito ta tsaya bakin titi, wani ikon Allah kuma sai sahun sukayi k'aranci, wanda suke wucewa kuma da mutane a ciki, hakan kuma ya samo asali ne saboda rana ta fara yi kowa zai fita sabgar gabanshi, dafe gaban goshinta tayi ta matso wata k'wala, a hankali ta furta "Wa ya raba ni da motata? Lokaci ka jirani kad'an na zama uwa ga Amjad, a lokacin da haka ta faru dani mahaifina ne tsaye a kai na har na fita wata k'asar, Allah kar ka nuna min kasawata a yanzu." Bud'a idonta tayi daga rintsewar data musu tana sauke hannunta, tana juya ta tsayar da idonta a kai saboda ganin sak motarta duk da dai wannan tafi k'yalli, k'ura mata ido tayi har ta k'araso gabanta ta tsaya, sauke gilashin akayi duk da dama ba bak'i bane, fuskar mutumin data gani ta sata sauke ajiyar zuciya ta gyara tsayuwarta, saida ya d'auke hannunshi daga kan sitiyarin yana murzasu yace "Barka." Saida ta matse d'an k'aramin bakinta kafin ta jinjina kai tace "Barka da safiya." Saida ya kalli k'afafunta sannan ya kalli fuskarta yace "Me kike anan?" Wulwula idonta tayi alamar k'aguwa saboda bata da lokacin duk wannan, a hankali tace "Nan na zo karb'an kayan oddo." Saida ya d'aga mata girarsa ta hagu yace "Me kike jira?" Da sauri ta shiga fad'in "Motata ce ta samu matsala, adaidaita nake jira zan koma gida." D'an tab'e baki yayi yace "Muje." Yanda yayi maganar yana kawar da kansa alamar yayi maganar k'arshe fa kenan ya bata mamaki, sai dai bata da lokacin yi masa gardama dan har yanzu adaidaita dake wucewa da mutane a ciki wasu ma maza kake gani, turo d'an bakinta tayi ta zagaya kamar zatayi kuka, da kallo ya bi fuskarta yana d'an waro ido, saida ta shiga ta zauna sosai ya ja motar cikin wani irin salo mai nutsuwa wanda har saida ta bi hannun nasa da kallo mai d'auke da bak'in gashi mai sulb'i. D'an satar kallonshi tayi, ko bata tambaya ba tasan daga gurin motsa jiki yake, kayan jikinsa sun nuna haka, bak'ak'e ne dogaye har rigar dogon hannu gareta, sai takalminshi ma bak'ak'e, duk da zaune yake zaka fahimci kayan sun masa kyau kamar na wani gaishe da sarki. D'auke idonta tayi ta fara kallon motar da kyau, wani murmushi tayi tace "Ba dan babu gaba tsakaninmu ba da sai na ce motata ce hannunka." Da sauri ya kalleta yana murmushi ga maganarta, girgiza kai kawai yayi a ransa ya furta "K'uruci dangin hauka." A fili kula cewa yayi "Ba mamaki ita ce?" Ita ma murmushin tayi tace "To me yasa ka d'auke min?" Saida ya juya ya kalleta yace "Saboda na zama drebanki." Wani faffad'an murmushi tayi tace "Haba dai, wacece ni? Ai ko dan darajar sunanka ba zan yarda haka ta faru ba." D'an juyawa tayi ta kalleshi tace "Sunanka babba ne, *Hahsheer*, d'aya daga cikin sunayen fiyayyen halitta, tabbas suna linzami." Tunda ta fara magana yake murmusawa, shi fa hatta sunan data fad'a sai yaji shi kamar yau aka rad'a masa shi, musamman data soka wata h tsakanin s da wata h d'in, hakan ya masa dad'i sosai, kallonta yayi ba tare daya daina murmushin ba yace "Ke ma, sunanki babba ne, *Fatuma Zahra*." Da sauri ta kalleshi tace "Nagode." Da alamar tambaya ya kalleta, jinjina kai tayi tace "Eh, kai ne na farko daka fara kirana da sunana cikakke a lokaci d'aya." Murmushi yayi yayi sosai yace "Nima nagode." Saida ta kalli titi tace "Akan me fa?" "Da kika tunatar dani girman sunana, hakan zai sa na sake zage dantse wajen koyi da mai sunan." Dariya tayi mai birgewa tace "Allah ya baka iko." Kallon ledar dake kan cinyarta yayi yace "... *Kuyi hak'uri fan's* *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 17:15 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _32_ "Kayan na da mahimmanci hakane da suka fito dake da safiyar nan?" Kallonshi tayi tace " *Babban mutum*, kasan aiki na kuwa? Ko zaka iya sama min wani aiki ne da ba zan iya fita da sassafe ba?" Ba tare daya kalleta ba a nanata a k'asan zuciyarsa, babban mutum? Murmushi yayi yace "Wane irin aiki kike buk'ata?" Ajiyar zuciya ta sauke tace "Ko wane iri ka bani zanyi kuma zanyi biyayya." Ta gefen kumatu kawai ya murmusa bai ce komai ba, a daidai k'ofar gidan ya tsaya cak, hannu ta zura zata bud'e ta kalleshi tace "Nagode sosai." Jingina kanshi yayi jikin kujerar ya lumshe ido kamar zai yi bacci yace "Ya Amjad yake?" Saida ta shagwab'e fuska tace "Yanzu shi yake jirana a ciki, nan da minti talatin yana da gasa, wannan uniforme d'in shine." Bud'a ido yayi ya kalleta ba tare daya d'ago kanshi ba yace "Amma kuma shine baki fad'a min ba? Yarinyar nan kina da kirki kuwa? Waro ido tayi ta bud'e baki kamar k'uda zai fad'a, a bazata ba tare da tunanin maganarta ta fito ba tace "Yarinya?" Had'e goshinsa yayi ya kalleta ba alamar wasa yace "Nayi k'arya? Shekararki nawa?" Nuna mishi k'ofar gidan tayi ta bayan hannu duk ta marairaice tace "Ina sauri fa zan shiga ciki." Kallon gabanshi yayi yace "Ki je ki fito saina aje ki." Da sauri tace "A'a nagode, hakan ma daka man..." Da hannu ya mata alamar tayi shiru ba tare daya kalleta ba, samun kanta tayi da yin shiru baki sake, da yatsa ya sake mata alamar ta shiga ta fito nan da minti goma, da wani matsanancin mamaki take kallonshi, yo ji kamar shi ya aike ta? Har wani umarni yake bata, lallai ma *tsohon* nan, ta gefen ido ta harara shi ta sake kama hannun k'ofar, daga sama taji muryarshi mai yanayin jin bacci yace "Kika sake harare na zan tsiyaye miki ido." Kasa motsawa tayi da ido sai wani farrrrr data shiga yi da idonta hakan yasa gashin gidarta karkad'awa da sauri sauri, motsawar data kasa yi yasa yace "Ki hanzarta, idan kin fito zamu d'ora a inda muka tsaya." Da sauri ta bud'e ta fita tana had'a k'afafu ta shiga ciki, dafe take da k'irjinta har ta shige d'aki, Dada ce ta tarbeta da cewa "Faduma shiru daga karb'o kayan? Ko bai ida ba?" Saida ta zauna kan kujera tana ciro kayan tace "Ke da kika san komai Dada, saida na zaune ya idasa had'ewa." Kusanta Amjad ya zo ta fara taimaka mishi yana saka kayan, Dada ce ta shiga fad'in "Da zaki tafi adaidaita kika shiga ko?" Kallonta tayi tace "Me yasa kika ce haka Dada?" Murmushi tayi tace "Ban ji k'arar mota ba da zaki tafi, yanzu kuma ina jin alamarta a waje." Bata so yin maganar da ita ba yanzu, amma dole ta kalleta tace "Dada mota ta dai bata nan waje, ban ganta ba, alamu sun nuna d'aukarta akayi, dan akwai sawayen takalmi da kuma tayar motar, amma ban san su waye ba." A firgice da al'amarin ta zazzaro ido tace "Motar kuma? Amma Faduma kike zaune haka?" Cikin rashin damuwa tace "To ya zanyi Dada? Zan bi sawayen ne har inda ya tsaya? Na barwa Allah kawai, zan kuma yi bincike akan lamarin." Amjad da shima yake mamakin abun ne yace "Kiyi hak'uri Ayyata, insha Allahu Allah zai baki wacce tafi ta, kuma nasan zaki gano su." Murmushi ta masa ta shafa kansa tace "Allah ya yarda." Saida ya gama b'alla botiran tace "To muje na rakaka, Aban su Izzadeen ne ya kawo ni yanzu ma da muka had'u, yace zai kai ka ka." Da mamaki yace "Abansu Izzadeen?" Jinjina kai tayi alamar eh, Dada ce tace "Kin ce ba saurayinki bane? Amma me..." Da sauri ta kalleta tace ""Dada..., kar ki ce komai dan Allah, wallahi kawai mun had'u da alama daga terrain yake, ni kuma ina jiran adaidaita shine ya d'auko ni." Murmushi tayi tace "A haka dai, mai son ka ai shi ke bibiyar lamarinka." Girgiza kai tayi tace "A'a Dada, a yanzu mak'iyi ma na bibiyarka dan ya kai ka k'asa, mak'iyi kan iya b'ata dare da rana dan zak'ulo abinda zai iya tarwatsaka." Ajiyar zuciya ta sauke tace "Hakane kuma, Allah ya raba mu dasu." "Ameen." Ta fad'a tana mik'ewa, kusan Dada yaje yace "Dara nra (masoyiya) zan tafi, kiyi ta min addu'a kinji." Saida ta rumgume shi tace "Insha Allah d'an gudaliya zan maka." D'agowa yayi daga jikinta ya d'aga mata hannu, ita ma hannu ta d'aga mata tace "Dada sai mun dawo." "A dawo lafiya." Ta fad'a tana kallonsu, suna fita a inda ta barshi ta same shi, gaba ta bud'e ta zauna Amjad a baya, cikin sanyayyar murya yace "Ina kwana obdo." Juyawa yayi ya kalleshi ya bashi hannu suka gaisa, juyawa yayi ya tashi motar suka fara tafiya a hankali, ba tare daya kalleta kamar yanda baiyi yanda Amjad zai ji ba yace "Kin ce motarki ta samu matsala, ina take anan?" Iska ta huro daga bakinta, cikin sayayyar murya ita ma tace "A gaskiya ban ganta ba, an d'auke." Da sauri ya kalleta yana mai rage gudun tafiyarsu, a hankali yace "Ban gane baki ganta ba? Wa ya d'auki motar?" Lab'e baki tayi ba tace komai ba, mayar da hankalinshi yayi kan tuk'i sosai, a sanyaye ya furta "Shi yasa kike tunanin ni ne b'arawonki?" Da sauri ta kalleshi sai kawai ta tintsire da dariya tana rufe fuskarta da hannayenta alamar kunya, murmushi ya dinga saki shi ma tare da sake furta "Shekararki nawa ne?" Kallonshi tayi tace "Me yasa kake son sani?" Kallonta yayi da idonsa masu saka shakkarshi da jin nauyinsa, a gadarance yace "Ina jinki?" Turo leb'en k'asa tayi ta kyab'e fuska ta mak'ale kafad'a tace "Um um." Yanda tayi sak wata yarinyar da bata wuce yar shekara biyu ba ne yasa shi saurin juya kanshi ya kalli gefe, b'oyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da huro iska, a k'asan zuciyarshi yace "Zata iya kashe ni wannan." A fili kuma cewa yayi "Na tabbata baki wuce talatin da takwas ba." Zaro ido tayi da sauri ta kalleshi tace "Talatin da takwas? Ni d'in? A ina?" Ba tare daya kalleta ba yace "Oho, talatin da biyar ne?" Kallon gabanta tayi tace "Ka rufa min asiri babban mutum, gaba d'aya fa ko ashirin da biyar ban shiga ba bare na rufe." Jinjina kai yayi ya juya ya kalleta yace "Lallai yarinya ce ke, tunda gashi cikin sauk'i an miki wayo." Had'e fuska tayi alamar rashin jin dad'i, mayar da hankalinshi yayi kan tuk'i, ashirin da hud'u kenan? Lallai yarinya ce, jikinta ne kawai ya girmi shekarunta, shi ma ba wani sosai ba bare har ya dame wanda ya alak'antu da hakan. A k'ofar makarantar ya ake shi, yanda sukayi sallama da yaron ya birge shi sosai tare da nuna masa irin k'ok'arin da tayi wajen tarbiyarshi, saida ya shige kafin ta shiga suka d'auki hanya, a hankali ta furta "Idan ba damuwa ka ake ni maternit茅 tattali." Ba tare daya kalleta ba yace "Kin fi son shiga adaidaitar kenan?" Kallonshi tayi tace "Ba haka bane, akwai wacce zan gani anan ne." Bai ce komai ba suka ci gaba da tafiya, basu fi minti biyar ba suka isa, ajiyar zuciya ta sauke ta kalleshi tace "Nagode sosai babban mutum, sai ka fad'a min nawa ne kud'ina suka kama?" Murmushi yayi mai birgewa yana kallon gefen titi yace "Ke babba ce, kawai kiyi harkar girma." Murmushi tayi sosai tace "Ina jinn fa kud'i na zasu iya kamawa jaka guda babu dala ashirin goma." Kallonta yayi sai kawai ya bushe da dariya, had'a kanshi yayi da sitiyari yana dariya sosai mai sauti, ganin yanda yake dariyar yasa ta turo baki tace "Da gaske fa nake." D'agowa yayi yana ta k'ok'arin tsagaitawa yana kallonta, jingina kanshi yayi jikin kujerar yace "Kenan kud'i na sun kama 0?" D'aga kai tayi alamar eh shi kuma ya jinjina kai, murfin k'ofar ta kama ta bud'e ta fitar da k'afafunta ta sauke su k'asa, juyowa tayi tace "Nagode sosai." Lumshe ido yayi cikin taushin murya yace "Da godiyar nan me zai hana ki yarje min na kira ki a waya." Da mamaki ta kalleshi da alamar tambaya, kafin tace wani abu ya fahimci haka sai yayi saurin cewa "Saboda ki dinga kirana idan zaki fita." Murmushin yak'e kawai tayi, poshet d'in hannunta ta bud'e ta ciro kati ta mik'a mishi, karb'a yayi sai kuma ta sunkuyo kanta cikin rad'a tace "Amma a kirani sanda kake so na tsaya maka akan wata shari'a." Tana fad'a tayi murmushi ta d'aga masa hannu alamar bye bye ta fice, tana rufo k'ofar ya kalli katin, jinjina kai yayi ganin daga sama an saka *C.N.H.J.N* (chambre nationale des huissiers de justice du Niger).Sai sunanta a k'asa da wani cikakken bayanin da kuma lambarta guda biyu d'aya wacce yake da d'aya baya da ita, sai kuma adresse d'in email d'in ta, murmushi ya saki yana girgiza kai ya tayar da motar yana ayyanawa a ranshi "Lallai Hasheer, wannan karan zuciyarka ta kawo ka inda ba lallai a dube ka ba." Tana shiga daidai da Fa'iza ta fito da kaya sosai a hannayenta tana d'orawa akan moton ta, da gani tasan aikin kwana tayi shiyasa ta k'arasa tana mata dariya da cewa "K'awata ki ce yau an kwashi gajiya." Juyawa tayi tana murmushi tace "Faduma ke ce? Ai ki bari wallahi gashi kam mata uku suka haihu a hannu na jiya." Saida ta tsaya daf da ita suka shiga gaisawa, kallonta tayi tace "Yau kuma me zan miki? Dan nasan dai ba kya zuwa wajena a banza." Hararenta tayi tace "Kinji ki, to jiya da naje ke kika kirani? Ni bana son wulak'anci." Dariya tayi tace "To yi hak'uri, kenan kin zo mu gaisa ne?" Wata harara ta wurga mata tace "Ke fa na lura a dole so kike ki k'ure ni, to kinga wata alfarma na zo nema a wurinki." Dariya Fa'iza tayi tace "Gashi kuwa an zo wurin, to ina jinki." Kallonta tayi sosai tace "Fa'iza akwai wani aiki da nake hari yanzu zan shiga, alfarma nake so ki rok'a min wajen mijinki, ina son ganinshi ne idan zai yiwu akan maganar tsohon jami'insu wanda ya aje aiki Insp. Aji." Kallonta tayi tana murmushi tace "Yanzu Faduma akan wannan ne kika wahalar da kanki kika zo nan? Ai ko kirana kikayi za ayi yanda kike so." Dafata tayi tace "Na sani, amma dai dan ki fahimci girman abun ne." Jinjina kai tayi tace "Karki damu, yanzu haka baya gari amma insha Allahu zan sanar dashi a waya ma, duk yanda mukayi zan kiraki sai na sanar miki." Da fara'a tace "Nagode sosai k'awata, sai naji daga gareki kenan?" Jinjina kai tayi tace "Insha Allah." Sallama ta mata ta fito bakin titin, tun kafin Fa'iza ta fito ma ta samu abun hawa, kai tsaye gida tace a aje ta, a hanya kam tunani take da mamakin yanda motarta ta bar k'ofar gidan nan, ta d'auki makulli da jakarta sanda ta durk'ushe a gaban Tagur, to akayi aka d'auki motar da sauk'i haka? Da wannan tunanin ta isa gida, tana bashi kud'in gidan dake kallon gidansu ta shiga da sallama, daga yanda aka amsa sallamarta da mata maraba zai nuna maka akwai kyakyawar alak'a da fahimta tsakaninsu, tun a soro dama take jin sautin redio na tashi har ta shigo, kuma yayi daidai a tashar gidan redion *ama* suke, dattijuwa ce zaune tana bakace hatsi, sai yarinya k'arama dake wasa a gefenta, kujerar dake fuskarta ta zauna tana fad'in "Mama aiki ake?" Da fara'a ta amsa da "Wallahi kuwa Faduma, antashi lafiya?" "Lafiya lau Mama, ina su Hajara? Duk Sun tafi makaranta ko?" "Sun tafi ba jimawa, ina sarkin wayo (Amjad)?" Dariya tayi tace "Mama ya tafi islamiyya shima, kinsan suna cikin masu musabik'ar nan." Da mamaki tace "Kai dan Allah? Amma Faduma shine babu wanda ya fad'a daga ke har Owwo." Langab'e kai tayi tace "Kuyi hak'uri Mama, wallahi nima saura sati d'aya nasan da gasar, a lokacin kuma aiki ya taso ni gaba banda lokaci, Dada kuma ban san bata fad'a muku ba." Jinjina kai tayi tace "Ba komai Faduma, Allah ya bashi sa'a, ai zan kasa kunne naji k'ira'ar ustazu na." Dariya ta sake yi, a hankali ta rage murya tace "Mama halan Baba har sun fita?" Kallonta tayi tace "Eh to ya dai tafi d'aurin aure, amma na tabbatar zai dawo tunda bai karya kumallonshi ba." Jinjina kai tayi tace "Shikenan dama na zo wurinsu ne, amma idan sun shigo kafin su fita ko Azeema ku tura sai ta kirani." Ta fad'a tana nuna yarinyar nan. Mik'ewa tayi Mama na fad'in "Ba damuwa insha Allahu." Ta juya zata fita sai ga sallamar dattijon, amsa sallamarshi sukayi a tare, matsawa tayi kusa dashi tana fara'a da fad'a mishi inda Amjad yake bayan ya tambayeta, saida maganar ta tsagaita kafin ta kalleshi da ladabi tace "Baba dama gurinka na zo." Da fara'a ya nuna mata k'ofar d'akin shi yana fad'in "To to! To mu shiga daga ciki ko?" Murmushi tayi tace "A'a Baba ba ma sai mun shiga ba, yar tambaya ce zan muku." Jinjina kai yayi ya gyara tsayuwarsa da kyau, a hankali tace "Baba nasan kun fita sallah asuba a yau d'in nan, kamar yanda nasan kuna kai har k'arfe sha biyu na dare baku rufe k'ofa ba saboda su Nura." Gyara tsayuwarta tayi ita ma tace "Shine nake so naji ko daren jiya kafin ku rufe k'ofa kun ga motata anan?" Jinjina kai yayi yace "Tabbas, tare da Nura ma muka rufe k'ofar dan ina tsaye ina jiran shigowarsa, kuma mun barta anan k'ofar gida." Jinjina kai ita ma tayi tace "To da asuba fa da zaku tafi masallaci?" Nan ma jinjina kai yayi yace "Hak'ik'a na ga motar nan a k'ofar gida, kuma har na dawo ma tana nan babu abinda ya same ta, kinsan motar a inda kike aje ta yana zamar min kamar inuwa, ina fitowa akanta idona ke sauka, shiyasa inda tana nan ko bata nan na kan gane da sauk'i, amma da safe dana shirya zan tafi d'aurin auren nan ban ganta ba, hakan yasa nayi tunanin kin fita da wuri yau." Ajiyar zuciya ta sauke ta jinjina kai tace "Nagode Baba, ni zan tafi sai anjima." Da kulawa yace "Lafiya dai ko? Wani qbu ne ya samu motar?" Girgiza kai tayi tace "Ba komai Baba, karku damu." Juyawa tayi ta kalli Mama tace "Sai anjima Mama." Amsawa tayi ita ma kafin ta fice, k'ofar gidan ta k'arasa, wayar ta ta ciro ta shiga duba sawayen motar duk data gani da kyau tana d'aukar hoton su, saida ta idar ta shiga gidan ta samu Dada ma da redionta ta kunna, saida ta wuce d'aki ta d'auko bak'in alk'alami ta dawo ta zauna, a hankali ta shiga zana hotunan tayar a takarda tana fitar da zanensu, a b'angare d'aya kuma tana sauraren karatun sauran yara, har saida ta gama zanawa kafin aka kira sunan Amjad Tagur Sugui. _____________ Ko da ya shiga gidan bata kula da tsiyarshi ba har ya shige, tasan lokacin daya saba dawowa ya wuce, bata ga alamar gajiyar daya saba shigowa da ita ba, sai dai a ganinta ba wani abu bane da zai sa har saita tambayeshi dalilin jimawar, dan haka taja baki tayi shiru kuma dama ranta a b'ace yake dashi na d'uren madarar daya mata, alamu sun nuna mata shi a dole so yake tayi ta haihuwa, ita kuma a tsarinta so take a shekara sha biyar su haifi uku kacal. Ya jima a d'aki yana shiryawa kafin ya fito falon tsaf dashi cikin wasu mahaukatan suit kalar shud'i, duk da dashi take rayuwa amma yana fitowa saida ta shagala da kallonshi, daga bisani kuma saita farga ta d'auke kai, kujerar cin abinci ya zauna ya fara bud'a plate d'in daya gani, cr猫me ne da cips dan haka ya mik'e daga kujerar, cikin nutsuwa hannunshi d'aya cikin aljihu, gabanta ya tsaya gabanta yana kallonta, a hankali kamar mai ciwon baki yace "Mantawa kikayi kika yi anfani da kifi?" Saida ta fara girgiza k'afarta irin ko a jikinta tace "Um um." Zuba mata matsakaitan idonshi yayi yace "Kawai kin sarrafa ne?" "Um." Ta fad'a tana kallon tvnta, jinjina kai yayi a hankali yace "Nagode." Juyawa yayi zai fita tace "Zan tafi asibiti d'aukar magani na." Juyowa yayi kai tsaye yace "Ba zaki je ba, idan cikin ya shiga ki zubar dan Allah." Da mamaki ta bishi da kallo, tasan waye mijinta da kuma abinda zai iya yi, sai dai wanda yayi yau bak'on abu ne a gareta da bata san shi da shi ba, kai tsaye ya gaya mata magana haka, da kallo ta bishi har ya nufi b'angaren Umma, jinjina kai tayi tana huci tare da cin alhwashin fitar ko babu izininshi sai dai duk wacce za ayi ayi. Yana shiga da sallama Umma ce kad'ai zaune da babbar wayarta ta jona 茅couter (eapears) tana sauraren redio ita ma, k'asa ya zauna kusan k'afafunta dake k'asa, sunkuyar da kanshi yayi suka shiga gaisawa a harshen larabci, cikin nutsuwa take fad'in "Insha Allah ina sa ran tafiya Alg茅rie sati mai zuwa, amma ba zan jima ba saboda saurayin Halima jiya yake neman a bashi izini ya zo ya ga manyanta, amma na ce ta fad'a masa yanda mukayi da kai sai ta masa." Murmushi ya saki ba tare daya d'aga idonshi a kan ta ba yace "Umma duk yanda ki kai d'aya ne, amma tunda har kin bani wannan damar, ina ga ko yau ma ya zo ya same ni a gida, zamu tattauna kafin mu kai maganar ga su kawu." Jinjina kai tayi tace "Hakan ma yayi, insha Allahu zan sanar mata." Shima jinjina kai yayi kafin yace "A game da tafiyarku kuma Umma, insha Allahu zan tanadar muku komai kafin lokacin." Murmushi tayi tace "Ka ga ba fa wani abu bane zai kai ni, biki ne zan je dan haka bana buk'atar tarin kayan tsarabar nan daka saba da nake rasa wurin saka su a tafiyata." Dariya yayi kawai bai ce komai ba, a hankali tace "Hasheer." "Na'am Umma." Ya fad'a a sanyaye, d'orawa tayi da "A redion ama yau aka fara gabatar da gasar musabik'a ta yara, daga shekara sha biyar ne zuwa k'asa, kowane b'angare kuma da iya hizib d'in da suke karanta, abinda ya birgeni shine wani yaro da aka fad'i sunansa a cikin yara masu shekara takwas zuwa tara, masu shekaru irin nashi duk suna b'angaren masu hizib biyar ne, amma shi abun mamaki ne sai aka lissafashi a cikin masu hizib talatin, su kansu alk'alan sun d'auka kuskure akayi, amma aka tabbatar a nan jerin yake." Numfasawa tayi kamar yanda shima Hasheer d'in ke yi wanda hakan ya nuna ita ya d'auko wajen rashin yawan maganar nan, a hankali ta d'ora da "Ko bai zo d'aya daga a cikin ukun farko ba, nayi alk'awarin yi masa kyauta mai tsoka, sannan kai ma ina so a ranar k'arshe da za'a fad'i sakamakon ka je sannan kayi masa kyauta, sannan kayi kyauta wa duk wanda suka zo na farko." Jinjina kai yayi cike da gamsuwa da kuma k'auna da godewa Allah daya bashi uwa ta gari yace "Insha Allah Umma na, zanyi duk yanda kika ce." Sunan da aka ambata a redion na Amjad Tagur Sugui yasa Umma saurin cewa "Yawwa to kaji shi nan an kira, ka tsaya ka saurari karatun shi mana." Wani basaraken murmushi ya saki, sai lokacin ya d'aga kai ya kalleta, wata soyayyar Faduma ce yaji ta sake burmawa zuciyarshi, lallai ita ce uwar daya dace ya samowa 'ya'yanshi, tabbas ita ce ta dace dashi a matsayin abokiyar rayuwa. Duk shiru sukayi suka mayar da hankalinsu kan karatun Amjad, a tajwidi dai kam ba zai samu abokin gasa ba, a fitar da kowane haruffa da k'alk'ala haka, hatta da sautinshi yayi yanda ake buk'ata. ______________ Zaune suke a ofishin Aji suna tattaunawa kan abinda ya faru jiya da d'auko mishi motar da Aji yasa akayi kamar yanda ya buk'ata, Hatimi ce ta kirashi a waya ya d'aga, daga b'angarenta da sauri cikin tashin hankali tace ""Tagur, kana ina? Kaji abinda ke faruwa a gidan redio kuwa?" A kid'ime ya kalli fuskar Aji da shima ke kallonshi yace "Me ya faru Ayya?" Da sauri tace "Musabik'a ake fa, shine yanzu Rayya ta kira ni take fad'a min wai taji an kira sunan wani yaro sak sunanka da sunan margayi, shine na kunna nima yanzu na sake jin an ce Amjad Tagur Sugui." Da sauri yace "Da gaske Ayya? Wane gidan station ne?" Kai tsaye tace "Ama." Cikin muryar kuka tace "Tagur ka saurara kaji yanda yaron nan ke karatu, wallahi duk ya karya min zuciyata." K'arashe maganar tayi da kuka, da sauri ya kashe wayar bai kula ta kanta ba ma ya kalli Aji yace "Kana da abun sauraro?" Waigawa yayi bayanshi kan fridge ya d'auko, mik'a masa yayi jiki na rawa ya karb'a ya jona ya kunna, yana kamawa daidai da ya gama har an sallame shi, buga teble d'in yayi ya mik'e tsaye yace "Shitttt!" Kallon Aji yayi yace "Ni zan tafi can, sai munyi waya." Da sauri ya d'ago daga kujerar yace "Ina zaka je kuma?" A tak'aice yace "Can zan je na ga d'ana." Da sauri yace "Ka ga zo, dawo nan Tagur." Dawowa yayi ya tsaya yana kallonshi, a hankali yace "Kar ka je yanzu, ka bari lokacin baiyi ba." A gigice yace "Kamar ya? Ina so naga d'ana." Cikin kwantar masa da hankali yace "Na sani Tagur, amma ba yanzu ba, na tabbata ko ka tafi ba zasu bari ka ganshi ba tunda ba'a ida ba, sannan lokacin tashi nayi Faduma zata kasance a wurin dan d'aukar d'anta." Hararanshi yayi yace "To ya zanyi kenan yanzu?" Nuna mishi kujera yayi yace "Zauna dan Allah." Saida ya gama shan k'amshi da hura hanci kafin ya zauna yana kallonshi, cikin nutsuwa Aji yace "Abinda nake so da kai shine, kayi hak'uri kawai na kwanaki kad'an, Faduma da kan ta zata nemeka ta sadaka da d'anka, yanzu ba mun fara aiwatar da shirinmu na farko ba? To ka jira kaga sakamakon da hakan zai haifar, rashin abun hawa zai sa ta dinga makara wajen kai shi da d'auko shi, na tabbata wannan tsarin ba zai sa ta zubar da makamanta ba, amma da mun shiga mataki na biyu, hummm! Tagur dole Faduma ta nemi taimakon ka saboda bata da mataimaki, tsananin buk'atar kud'i zai sa ta nemi taimakon ka a matsayinka na uban yaro, idan shi ma baiyi ba to dole mataki na k'arshe ne mafita, k'adamin da dole ko tana so ko bata so ta neme ka." Numfashi ya sauke yace "Ka tabbatar hakan zaiyi aiki, yarinyar nan fa nasan ta ba yau ba, taurin kai ne da ita da kafiyar tsiya." Girgiza mishi kai yayi yace "Muka ji da dubbunan mutane ma bare k'waya k'wal d'aya, d'ayan ma mace k'aramar yarinyar kamar Faduma, karka damu abokina." Cikin sanyin jiki yace "To yanzu ina motar take?" Jingina yayi a kujera yace "Karka damu da mota, tuni nasa an fara mata takardun bogi." Da mamaki ya kalleshi yace "Me yasa?" Ajiyar zuciya ya sauke yace "Za'a tafi da ita Niamey, zan sa a canza mata kala da wasu abubuwan, saina bawa *Tahir* (k'ananshi) ita ya ci gaba da hawa." Nuna shi yayi da yatsa yace "Kai zan ci ubanka ma, na fad'a maka abinda nake so ayi da ita kenan? Kawai so nake a ajiyeta har zuwa wani lokaci." Tab'e baki yayi yace "Mahaukaci, kai a ganinka zanyi sake duk wani abu marar kyau da nayi ne ya fito cikin sauk'i, kama san wacece Faduma kuwa a harkar shari'a? Ka bar bala'i yayi bacci kawai malam, amma ko kana so ko baka so abinda zamuyi kenan?" Ganin yanda yake ta hararenshi yasa shi yin dariya yace "Ka kwantar da hankalinka mana, ka sani ma sanadiyar aikin namu har ita tace tana so ka aureta, daga nan ba sai ka siya mata duk motar da kake so ba?" Wani murmushi yayi yace "Ni ko bata fad'a da bakinta ba ma ni zan sake jadadda mata hakan." Murmushin baka da hankali ya masa yace "Anya kuwa Tagur, ni fa sai nake gani da kamar wuya, a gaskiya na fara tunanin anya kuwa Faduma zata iya zama matarka, dan abubuwan da suka faru ya gwada kamar mijinta mai babbar zuciya ne yana ta wani wajen, kawai dai lokaci ne baiyi ba." Mik'ewa yayi a hassale yace "In ban ci uwaka ba Aji ka ce d'an iska ne ni, lallai kai mak'iyina ne kuma baka so na da Faduma, inba haka ba taya zaka fad'i haka? To ka auna a ma'aunin hankali zaka gane duk abinda suka faru sun faru ne saboda ni kad'ai ne mijinta, idan kana gardama me yasa har yanzu bata yi aure ba? Bayan shekara tara sai gashi mun had'u a lokacin da ban da aure ita ma kuma haka, mtssss." D'aukar wayarshi yayi yace "Sai anjima, ka b'ata min rai wallahi." Da sauri Aji da ke ta k'yalk'yala dariya yace "Kai bani abun sauraro na." Ko kallonshi baiyi ba yace "Na k'arfin tsiya ne ka zo ka k'wata." Dariya kawai ya ci gaba da yi har ya fita daga ofishin. ______________ A wajen su Hasheer ma haka abun ya kasance... *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 17:15 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _33_ Kasancewar Umma mace ce mai ilimi da tsoron Allah, hakan yasa ta zubar da hawaye a sanda Amjad ke karatu, Hasheer ma da jikinsa yayi sanyi jin karatun da kuma ganin mahaifiyarshi na zubar da hawaye sai jikinsa yayi sanyi, saida ta tsagaita dan kanta kafin ya mata sallama ya fita. Risham super wax ya nufa, kafin ya fara gabatar da komai Mukhtar ya kira ya shigo ya same shi, a takarda yayi rubutu tare da cakin (check) banki ya nad'e ya bashi yace ya kai gudummuwarsa ce, dubawa Mukhtar yayi sai kuma ya kalleshi da mamaki yace "Me yasa to ka canza sunanka? Baka so asan kai kayi?" Da ido ya masa alamar eh, d'aga kafad'a yayi ya jinjina kai yace "Shikenan zan kai." Juyawa yayi zai fita Hasheer yace "Ba ka kai kula ka dawo ba, ka tabbatar kai ma ka bayar da ta ka." Juyowa yayi yace "Insha Allah." Yanda yayi maganar wai shi a dole balarabe yasa Hasheer murmusawa, a hankali yace mishi "Idan ka dawo ka taho min da abun karin kumallo." Murmushi yayi yace "Wane iri kenan?" Tab'e baki yayi yace "Ko wane iri, amma ka tabbatar wanda zan iya ci ne, inba haka ba d'urenshi zan maka." Dariya yayi ya juya yana fad'in "Abu mai sauk'i, Saudat zan kira ta fad'a min abinda ka fi karyawa dashi." K'ala bai ce mishi ba har ya fita. ______________ Bai b'ata lokaci ba ko da ta kira shi ya iso, saida suka d'auki hanya sannan ta kalleshi tace "Ina kwana?" Da fara'a ya amsa mata da "Lafiya lau, ya kike?" Murya k'asa k'asa tace "Lafiya lau." Jin ta tsaya a haka yasa shi cewa "Ina muka nufa yanzu?" Saida ta kalli titi daga kallon wayar da take, takardun dake saman k'afafunta ta nuna mishi tace "Ina son masaniya ne akan wannan, muje garage d'in su Murtala sai mu duba." Kallonta yayi yace "Amma wai su waye zasu d'auki motar nan? Abun na bani mamaki fa." Girgiza kai tayi tace "Yanzu dai ban sani ba nima, abinda nake son ganowa kenan." Jinjina kai yayi yace "Allah ya bamu sa'a." "Ameen." Ta fad'a kai tsaye, shiru ne ya biyo baya na wasu mintuna kafin ya kalleta yace "Munyi magana da Alhaji, kuma ya amince da maganar mu, yanzu ke kawai nake jira ki bani izinin turo magabata na." Tunda ya fara magana take jin abun wani iri, sai dai ba zata iya ce masa a'a ba, ya mata hallacin da wannan kalmar tayi girma ta fita daga bakinta, ajiyar zuciya ta sauke ba tare da tana jin abun a ranta ba tace "Ni ban da tacewa ai, ka samu Dada kuyi magana, duk abinda ta fad'a daidai ne." Wani farin ciki ne ya mamaye masa zuciya, murmushi ne sosai ya bayyana kan fuskarsa, hakan yasa ma ya kasa cewa komai, har suka isa babu wanda ya sake magana, daga cikin kwana ya paka motar saboda bakin titi sosai da babu fili, fitowa sukayi suka taka a k'afa suka isa garage d'in, gaisawa sukayi sosai a fuskar sanayya kafin shef d'in yace "Hajia Faduma halan le kika rako oga Aminu? Dan nasan dai ke kina kula da motar nan." Dariya sukayi inda Faduma tace "Allah dai ya biya bakinku ta kirana Hajiar nan." Da ameen duk suka amsa mata kafin ta mik'a mishi takardar hannunta tace "Malam Murtala dan Allah tayoyin motar nan nake nema, ko zan iya samun su anan wurinku?" Karb'a yayi yana fad'in "Bari mu gani." Duba takardar yayi, a take ya d'ago ya kalleta yace "Faduma wannan ai marque d'in tayar irin motarki ce corolla, sai kuma wannan marque d'in range rover, gaskiya bamu da su anan, saboda motar ba kowa zaki gani da ita, hasalima anan mu gaskiya kusan d'aid'aikun mutane ne na sani da ita, suma idan kika duba rayuwarsu zaki ga mutane manya matasa masu san kece raini da pantamawa." Kallon Aminu tayi kawai tayi murmushi ta karb'i takardar tace "Nagode sosai." Sallama sukayi suka koma mota, daga nan kuma Amjad suka biya suka d'auka ya k'arasa saukesu a gida. ______________ A yau duk wani mai alak'a da Faduma ko Tagur suka saurari redio sun ji wani abu, daga b'angaren iyayenta kuka sukayi na jin karatun yaron, b'angaren Tagur kuma mamaki ne fal ya cika mutane da dama har Hatimi da wasu daga cikin iyayenshi maza suka dinga d'aukar kiran mutane ana tambayar me ye gaskiyar lamari? Sai dai ba kawunanshi ba har Hatimi bata gaya musu sahihiyar magana dan ita dai a wajenta har yanzu akwai tamtama da shakku. *Litini* Tsaf suka shirya ita da Amjad da Dada suka hau adaidaita, a ama suka aje Amjad tare da Dada dan Faduma tace bata so hankalinta ya karkata kan shari'a wani abu ya faru, daga nan ita kuma justice ta wuce har an zauna kusan kamar ita ta rage, babban abun mamakin bai wuce samun Dr Rufa'i da kuma Omar a kotun ba, sai kawai ta shiga murmushin da ita kad'ai tasan ma'anarshi. Mayar da kallonta tayi kan Tagur da idonshi ke kanta tsam, da sauri ta d'auke idonta dan gaba d'aya gabanta ne ya fad'i tare da hasko mata waccen ranar, b'oyayyar ajiyar zuciya ta sauke, a hankali ta furta "Dada taya zan cire tsoronsa lokaci d'aya, mutumin daya ganni na ganshi ganin da babu wanda ya tab'a mana, mutumin daya je min da k'arfin cin tuwonshi." Wani murmushi ta kum saki kamar zatayi kuka a ranta tace "Baki san girmansa bane Dada? Baki san tsoron daya bani a waccen ranar ba, bana tunanin wani namiji zai iya bani wannan tsoron bayan shi." Shigowar alk'ali yasa duk suka mik'e tsaye, saida ya zauna suka zauna aka fara gabatar da abinda ya tara mutane, kowane motsi na lauyensu da likitocin biyu a hankalce take dashi, hatta k'aryata ta da sukayi cewa a gaskiya wata magana bata had'asu da ita ba abun bai bata mamaki ba, tambaya d'aya ce tak zata musu da zata kifar dasu, zasu raina kansu da kansu su shiga kallon kallo wa junansu da jin kunyar kansu. Saida ya gama tsaf alk'ali ya kalleta yace "Lauya Faduma, ko akwai abinda zaki iya cewa a game da abinda lauya mai kare wanda suke k'ara ya fad'a?" Mik'ewa tayi tana gyara bak'ar rigarta da kyau tace "Ina da ya mai shari'a." Da hannu ya mata alama, takawa ta fara yi gaba ta tsaya, cikin d'aga murya tace "Tambaya d'aya nake da ita anan ya mai shari'a." Da hannayenta ta shiga nunawa tana fad'in "8/10/20 an tashi a shari'a ba tare da an k'ark'are ba, haka kuma kotu bata nemi a gabatar mata da d'aya daga cikin likitocin nan ba ko kuma wani dan bata hujja, abun mamaki! Sai ga likitocin nan dukansu sun zo kotun nan dan bayar da hujja, tambaya ta anan ita ce, *wa ya gayyace su anan*? Bayan ba kotu bace ta buk'aci ganinsu, kasancewarsu anan dukansu a lokaci d'aya duba da yanayin aikinsu, ya ta nuna cewa wani ne ya buk'aci da su zo nan dan su ce wani abu." Cacaniya kotun ta d'auka inda ta juya ta koma mazauninta tana kallon inda Atta, Gomboy, Hindu da Zaliha suke zaune, wata muguwar kallon tsana ta wurga musu kafin ta gyara zamanta, lauyansu ne yayi saurin mik'ewa yace "Ya mai shari'a wannan abu ne mai sauk'i, sanin bincike zai biyo ta kansu da kuma son a kawo k'arshen matsalar a yau yasa nayi tattaki na nemi alfarmarsu kan su zo kotun nan, wanda da k'yar muka samu hakan dan dukansu suna da uzururrukansu." Sunkuyawa yayi yace "Nagode mai shari'a." Juyawa yayi ya koma ya zauna, duba da wasu hujojjin da kuma son ganin anyi daidai da rufe wasu abubuwan yasa alk'ali yanke hukuncin tabbas Ridwan d'an Tagur ne, amma kotu na umartarshi daya mayar mata da yaron tunda k'arami ne har yanzu, a shari'ance ma za'a karb'esa ne idan ya shekara bakwai, tare da k'iyasta abinda za'a dinga bata na kula da yaron. Farin ciki duka sukayi ta b'angaren, sai dai mutanen dake wurin sunata tattaunawa akan wasu batutuwan, da sauri ta shiga had'a kayanta dan ita tana da abinda yafi wannan shari'ar ta Tagur mahimammci, tana d'aukar jakarta da wasu takardu ta nufi hanyar fita, a k'ofar fitar ta same su tsaye, shi da Aisho da Hatimi sai Ridwan dake gabanshi, daga shi har Hatimi kallon bi-aho ta musu, a hankali ta kalli Aisho wacce bata manta yanda ta karb'eta, murmushi ta mata tace "Sai anjima." Da murmushi ita ma tace "Sai anjima Faduma, a gaida min Amjad." Da ido ta amsa mata ta wuce ta barsu, acan kusan k'ofar fita ta same su tsaye suma suna magana, tare gabanta sukayi cike da raini da dariyar mugunta, Gomboy ta tsurawa ido tana mamakin yanda ta kasa sanin ta girma, ita ma kallonta tayi ido cikin ido taja tsaki, sama da k'asa ta harareta tace "Wai ke ga sarauniyar bincike da bin k'wak'wafi, to kinga yanda muka juyar da al'amarin, dan haka sai kije gida kiyi kukan bak'in ciki tunda bakiyi nasara ba." Kallon mamaki ta mata tana wani murmushi tace "Kukan bak'in ciki? Hahahahahahahahah!" Tsagaitawa tayi ta kalleta da kyau tace "Da ba al'amarin daya shafi wannan marar mutumcin bane, ina tabbatar miki da zan tsaya da kyau har saina tabbatar da makircinku, amma ban damu da abinda ya shafeshi ba, dan haka zan barshi ya d'and'ani d'acin da ake ji sanda kake rainon yaron da baka da alak'a dashi, sannan a k'arshe yayi nadamar wulak'anta d'an daya fito daga cikinshi, hakan zai zama babban wa'azi gareshi." Kallon Atta tayi, kallo d'aya zaka mata ka fahimci yar duniya ce ta sakawa a gidan gaba, tab'e baki tayi "Kiyi hanzarin ribantan wannan lokacin, dan cikin sauri za'a harbo jirginki." Dukansu ta had'e ta wurga musu kallon wulak'anci kafin ta rab'asu tayi gaba tana jin suna magana ko a jikinta, adaidaita ta samu ta kaita ama ta samu su Dada, ita ma data fad'a mata yanda sukayi sai tace Allah ya k'ara, gwara ya ji zafi shima a zuciyarshi ai. *Yau* ce rana ta k'arshe da aka gama gasar nan kuma ranar fad'in sakamako, kusan iyaye da yan uwa dayawa suna zazzune wasu kuma a tsaye a cikin filin gidan redion, haka alak'alan da suke jagorantar shirin tare da yara, sai wasu daga cikin mutanen gari dan d'aukar rahoto, ta b'angarensu daga ita sai Dada, daga ciki kuwa sakamakon aka fara fad'a daga k'asa ana yin sama, sannu sannu har aka iso ga sunanshi, shine na farko a jerin wanda aka buga gasar tare dasu, babu wanda yayi mamaki dan abu ne da dayawa sunyi tsammaninshi, sai Faduma da tayi kuka na farin ciki da godiya ga Allah, saida aka fara fad'in kyautar da dama za'a bawa kowane d'alibi wanda ya zo na farko, daga baya kuma suka fara kiran jerin wasu sunayen manyan mutanen da kowa ya bayar da tashi gudumawar tare da ware Amjad kuma, ba dan komai ba su dai k'arancin shekarunshi da sahun da yayi tashi gasar ya birgesu, manyan mutane ne da baki d'aya k'asa ma ala san su, kamar irinsu *Kalla transa est files*, *Alhaji Gago*, *Alhaji Na-kiri est files* da sauransu, a jumulce kuma a fad'ad'e aka soma fad'in abinda Amjad ya mallaka sakamakon gasar. _"Sannan akwai wani Elhaj da bai fad'i sunansa ba shi ma ya bayar da kujerar hajj guda biyu ga yaron da mahaifiyarsa, tare da fili mai girman inci biyar, da kuma jimillar kud'i har cfa million biyu. Sannan akwai wata kujerar hajj ma guda biyu daga Alhaji Idrissa tare da d'aukar nauyin karatun yaron daga nan har ya kammala karatunshi, sai kuma Alhaji Lawali da shi ma dai kujerar hajj ya bayar guda uku d'aya ta yaron d'aya mahaifinshi d'aya mahaifiyarshi, sai kuma tsabar kud'i cfa million d'aya. Haka ma akwai Alhaji Nassiru daya bayar da fridge a bawa wanda yayi na farko a sahun hizib talatin, akwai kuma wani Alhaji daya bayar da makullin mota k'irar hilux, sannan..."_ Tunda aka shiga fad'in abun arzik'in nan take kuka, Dada na ta rarrashi tana bata hak'uri, duk wanda ke kusansu murna suka dinga taya ta suna cewa ta daina kuka, sai dai ina wani kukan dole kuma baya tsayawa idan aka fara shi, dan haka har akayi abinda ya tara mutane aka watse a wurin tana kuka, dan sanda malaminsu Amjad ke mik'a mata wata babbar enveloppe kasa karb'a tayi sai Dada ta karb'a, kallon Amjad yayi ya shafa kan shi yace "Kaje gida ka huta kaji, kana da sati d'aya na hutu kawai." Jinjina kai kawai yayi, ficewa yayi inda suma suka juya suka fita, a cikin ma'aikatan gidan redion ne wani ya jasu a tarwatsetsiyar motar nan zuwa gida. Suna isa kam k'ofar gida ya batse da mutane ana tayasu murna, duk ciki suka shiga inda abu ya koma sabo, suna tsaka da hirarsu wayarta tayi k'ara, da sauri ta mik'e ta shiga d'aki, saida ta zauna ta nutsu sosai tace "Assalama alaikum." Daga b'angarenta ta amsa da "Wa'alaiki salam." A ladabce tace "Ayya ina kwana? Ayya kinji abinda ya faru ko?" Cikin nutsuwa tace "Naji, ina tayaki murna." Cikin kuka tace "Nagode Ayya, Ayya ina Aba? Dan Allah ki bashi waya mu gaisa ko ki rok'a min shi ya bani izinin kiranshi, wallahi ina son jin muryarshi, ina so muyi hira dashi Ayya na fad'a masa abinda ke zuciyata." Shiru tayi kamar bata san me tace ba, ajiyar zuciya ta sauke mata a kunne tace "Ga Ayyarki zakuyi magana." Ana mik'awa Herde ta rangad'a gud'a tana ta murna, cikin shagwab'a Faduma tace "Ayya ki kira Aba ki nema min izinin kiranshi dan Allah." Kai tsaye tace mata "Karki damu ke, zan kirashi." A hankali tace "Ayya, idan bai amince ba wallahi sai na d'auki Amjad mun je can, sai dai idan yanka ni zaiyi ya yankani kawai." Cikin zolaya tace "Ya ma isa? Wa ya isa yanzu ya yanka yarinyata mai darajar milyoyin kud'ad'e." Dariya tayi tana jin zuciyarta na fara washewa, turo baki tayi tace "To Ayyar mai darajar milyoyi, ki rok'a min shi yanzu ina jira." "Karki damu yanzu kuwa." Ta fad'a tana yanke kiran, bata fito ba daga d'akin ta zauna zaman jiran tsumayi, saida aka d'auki minti shida cirr saita kira da wayarta, bugu biyu aka d'aga, da hanzari tace "Ayya ya Aba yace?" Cikin sanyin jiki Herde tace "Ko da na masa maganar ma kashe min waya yayi, nayi ta sake kiranshi ya k'i d'agawa." Kallon madubin dake gabanta tayi, matse idonta tayi tare da had'e kukan daya ke son taho mata, da k'yar ta iya furta "Shikenan Ayya, zan kashe waya." Da sauri Herde tace "Kinga Fadu na, karki kuskura min kuka kinji, ki rabu dashi kawai ki zo tare da d'anki, dama ba Owwo ta mana maganar saurayin da kuka tsayar da magana ba, ki zo kawai kinga sai ayi duk abinda ya kamata." A take taji jikinta yayi sanyi, amma bata nuna mata ba sai ma cewa da tayi "To shikenan Ayya, za muyi waya." Kashe kiran sukayi hakan ya bata damar sakin wani marayan kuka, har ga Allah zuciyarta a cunkushe take, tana so tayi magana da Aba ta fad'a masa damuwarta da farin cikinta, amma ya k'i bata damar hakan, ya zatayi kenan? Ayyarta suna hira amma mafi yawan lokuta titsiye take mata, hakan yasa ba komai take sakewa ta fad'a mata da farin ciki ba. Sosai duk wani da suke da kusanci dashi aka dinga zuwa musu murna da fatan alkairi, wannan kyaututtuka na girma haka duk sukayi kasafinsu yanda ya dace, kowa ya ci albarkacin yaro Amjad banda dangin ubansa kawai.馃ぃ ______________ Tsananin tashin hankali da mamaki yasa Hatimi cewa "To yanzu duk abubuwan nan daya samu uban waye zai rik'e? Wai da gaske ba d'anka ne ba?" A kaikaice ya kalleta yace "To in d'ana ne Ayya sai akayi yaya?" "Ka karb'oshi." Ta fad'a kai tsaye, girgiza kai yayi da irin jin haushin nan yace "Saboda abinda ya samu?" Girgiza kai tayi tace "A'a, amma ai ko dan ilimin yaron sai ka karb'o kayanka." Mik'ewa yayi ya kalleta yace "Ayya, abinda Amjad ya samu ba shi ne a gabana ba saboda na tara dubunshi, d'ana a yanda yake kawai nake son shi." Yana gama fad'a ya juya ya fice ya bar musu gidan, Gomboy dake gefensu tana sauraronsu ne ta tab'e baki tace "Amma Ayya ko dan kasancewarki kakar yaron nan ai ina ga ya ci ace Faduma ta kawo shi gidan nan kuma a baki wani kason, kiji fa kujerun da suka samu, to duk uban wa zai tafi makkar?" Tsaki Hatimi tayi tace "Ita da matsiyatan danginta mana." Dariya Aisho dake gefe ita ma tayi tace "Alhamdulillah Allah, abun farin cikin kuma k'ok'arin akan yaron ne zata girbi abinta ita kad'ai." Hararanta Gomboy tayi tace "Ke bana son iskanci, to sai akayi me?" Ba alamar tsoro tare da ita tace "Sai ya kamata ku ji haushi, Faduma da kuma raina ita ce ta raini yaronku ita kad'ai, babu tallafawarku bare ku ga gazawarta." Mik'ewa tayi ta harareta ita ma tace "Wallahi yaron nan ko ubanshi Tagur saiya ladabtar dashi cikin hikima da nutsuwa bare kuma ke." Ko da ta fad'a ita ma tayi hanyar d'akinta ta barsu. Yana fita daga nan gidan Aji ya wuce ya same shi, lokacin bai ko tashi daga bacci ba saboda jimawar da yayi bai kwanta ba, saida yayi tsaki yace "Kai ka fa fara isata, haba da sassafe haka?" Hararanshi yayi yace "Ka ji abinda ya faru a redio?" Tsaki ya sake yi yace "To kai ka sanni da sauraronshi ne?" A hassale yace "To bari kaji a yanzu dai babu wata barazana da zamuyi wa Faduma da zata shiga matsalar kud'i, sai dai mu nemi wata mafitar kawai." Lumshe ido yayi ya kalleshi yace "Muje mataki na gaba to." Jinjina kai yayi yace "Ah to sai dai haka." A hankali yace "Idan na shirya na fita zan kira ka a waya sai mu san abun yi." Jinjina kai yayi ya fita yana fad'in "Sai na ji ka." _______________ Tunda suka ji a redion sanda aka fad'i sunanshi suke ta kwaroroton abokinsu ne abokinsu, hakan yasa Umma sake tambayarsu suka tabbatar mata, hakan yasa har suka fad'a mata ai Abansu ma ya san shi, muradinta akan yaron yasa ta kiran Hasheer a waya dan ba zata iya hak'urin saiya dawo ba, yana d'aukar wayar cikin kamilalliyar murya tace "Hasheer, da gaske kasan yaron nan da yayi na farko? Izzadeen yace d'an ajinsu ne." Cikin nutsatsiyar murya ya bud'a bakinshi yace "Eh Umma." Murmushi ta saki tace "A gaskiya ina son ganinshi, zaka iya kaini gidansu da kanka?" Jim yayi yana rarraba kalamanta, sai kuma ya saki murmushi yace "... *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 17:15 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _34_ "Yanda kike so Umma na haka za ayi." Murmushi ita ma tayi daga can tace "Nagode, Allah ya albarkace ka." Cikin jin dad'i ya amsa da "Ameen Umma." D'orawa yayi da "Hayaniyarsu Izzadeen nake ji Umma?" Saida ta kalli yaran kafin tace "Su ne da kansu, duk sun lalata min falo da abinci k'azaman wofi." Yar dariya yayi yana lumshe ido tare da juya kujerarshi, jin bai ce komai yasa tace "Ina so na gyara d'aki na amma nasan ko na gyara zasu b'ata, shiyasa na bari sai uwarsu ta dawo idan suka koma b'angarensu saina gyara." Jim yayi tare da bud'a ido, a zuciyarshi ya tambayi kanshi "Ta fita kenan?" Tabbatarwa da tayi ba zaiyi magana ba yasa ta kashe wayar, tana ajewa shima ya aje yana siririyar k'wafa, a ranshi kawai yake ayyana irin hukuncin da zai mata, ba zai d'auki wannan wulak'ancin daga gareta ba, zai iya shanye abubuwa dayawa daga gareta, haka kuma akwai abubuwa dayawa da ba zai iya shanyewa ba, mik'ewa yayi tsaye ya d'auki wayarshi ya fice a ofishin, yana fita Qaseem ya taho da sauri ya bi bayanshi, dama baya so ya bud'e mishi k'ofar mota dan haka kai tsaye ma ya zagaya gurin zamanshi, shima yana shiga ya ja motar a sanyaye har suka fita. A k'ofar gida ya sauka ya kalli Qaseem yace "Ka tafi da motar, bayan sallah isha'i ka zo zamu fita." Saida ya d'aga kai yace "Ok Elhaj." Shigewa yayi ciki hakan yasa babu wanda yasan da shigowarsa a gidan dan ba'a shigo da mota ciki ba, kai tsaye b'angaren ya nufa ya bud'e k'ofar falon, bai kunna wutar ba ya zauna kan kujerar dake fuskantar k'ofar shigowa, k'afa d'aya kan d'aya ya d'ora ko takalminshi k'afa ciki bai cire ba, wayarshi ya zaro a aljihu ya shiga latsawa a nutse, ya jima yana rubutu akai kafin ya kalli abinda zuciyarshi ta umarci hannayenshi da su rubuta, ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi, rufe ido kawai yayi ya tura duk da gabanshi na fad'uwa saboda fargaba, saida ya ga sak'on ya tafi ne yaji fad'uwar gabanshi ma ta nunku, me zatayi tunani? Wace amsa zata maido mishi? Rashin sanin hakan yasa ya kafe wayar da ido yana jiran tsammani kamar wanda ya zana jarabawar da zata tabbatar da nasarar hayewarshi mataki na gaba. ____________ Wayar na hannun Amjad a lokacin yana waya da Kalli sak'on ya shigo, saida sukayi sallama ya fito farfajiya ya kawo mata, suna tsaka da girkin da suka d'ora a manyan tukane saboda ayi sadaka abinci mai rai da lafiya, karb'a tayi tana cire tsaron dake wayar, duk da ta ga bak'uwar lamba ce haka ta shiga dan karanta sak'on. Sak'o ne mai nutsur da tunanin bawa, sak'o ne da duk wanda ya karantashi zai iya sakin murmushi ko da ba dashi ake ba, sak'o ne da zai iya d'aukar ruhi kacokam ya killaceshi a ma'adani mafi tsaro a duniya, sak'o ne daya kwantar mata da hankali had'e da saka mata nutsuwa da tambayar kanta *Waye wannan*? Murmushi ta samu kanta dashi tana jin gabanta na ci gaba da bugawa da matsanancin son sanin ma'abocin amincin nan, kalamanshi sunyi kama dana wanda yake girmamaka, zantukanshi zasu iya saka mai raunin zuciya ya ji girman kai a take ya kama shi, ko sarauta ke hannunka aka nemi izninka kamar haka zaka ji lallai mumkinka babba ne, babban abun farin ciki kuma yanda mai sak'on ya nuna d'anta ma abun karramawa ne a gare shi, hakan ya birgeta sosai ta yanda ya d'ad'ata a k'asa har taji ta mishi muhalli a zuciyarta, dan duk wanda zai girmama mata Amjad to ita ya girmama. _"Aminci, jink'ai, tausayi da albarkar ubangiji su tabbata ga uwa yar baiwa, uwar da kowane *d'a* zaiyi fatan samun irinta a duniya, nutsuwa da salama su baibaiye gabanki da bayanki yake ma'abociya koyi da sunnar fiyayyen halitta mad'aukakiya murmushi da saka mutane fara'a, farin ciki madawwami da kwanciyar hankali su k'ara zagaye mai alkunya da haiba game da nutsuwa, kyakyawar fuska mai d'auke da kyakyawar suffa ga ingantacciyar ruhi da jarumar zuciya su kasance d'auke da kyakyawan murmushi har abada, girmanki da kuma matsayinki da kimar d'anki sun wuce kai tsaye a tunkareku dan tayaku murna, idan zai iya yiwu kaina bisa gwiwukana, ni da mahaifiyata muna neman alfarma a gurin sarauniya kuma nagartacciyar uwa izinin zuwa dan mik'o tamu gaisuwar?"_ Yar dariyar da tayi ce tasa Dada kallonta, ita kanta sai ta samu kanta da sakin murmushi duk da bata san me ya faru ba, aje muciyar hannunta tayi wacce zata juya miya da ita ta shige d'aki, zaune tayi bakin gado ta d'ora hannayenta ita ma, cikin nutsuwa da son auna komai a mizani ta shiga mayar da abinda take ganin zai yi daidai da amsa ga wannan babban mutum mai manyan kalamai haka. ______________ Jin sak'o ya shigo yasa shi saurin bud'ewa gabanshi na sake fad'uwa, tabbas a tsorace yake da tunanin amsar da zata maido mishi, abun mamaki sai ga amsar da ta ci uwar tashi, amsar data gigita tunaninshi, amsar data sashi zabura ya mik'e tsaye yana damk'ar wayar a hannu kamar zai b'arata, da k'arfi ya d'aga kai sama yana fad'in "Yesss, yes, yes." Sake kallon screen d'in yayi, cikin rawar jiki ya sake maimaita sak'on kamar haka _"Ina maka fatan fiye da duk alkairin daka rok'a min gurin Allah, hak'ik'a kai babba ne kuma d'an babban gida, kalamanka sun nuna haka tare da nagartaccen aikin hannunka, kai ne mutum na farko a duniya da yasa naji kaina kamar wata sarauniya, sarauniyar ma ta duk duniya, idan har taa b'angaren ingancin kalamai ne zaisa ka samu izinin zuwa, to fa kalamanka sun girmi amsata har car ma da gidan da zan saukeku a cikinshi, amma a tak'aice zan iya ce wa, na amince ka zo da duk wani mafi kusanci da mahimmanci a gareka, zan tarbeku kaina bisa wuyana."_ ______________ A hankali ya sake dawo mata da amsa marar tsayi da cewa _"Lallai samun izinin amincewa haka cikin sauk'i daga gareki ba tare da nabi ta hanyar alfarma ba, ya cancanci idan na zo na rok'i Ummana ta tayani gode miki."_ ______________ Da saurinta ta mayar da cewa _"A'a fa ka rufa min asiri, kana son zuzutani dayawa, ai duk d'an itaciyar da yayi kyau da gani, dad'in k'amshi a hanci tare da sihirtaccen d'and'ano a baki, to fa tabbas ya samo asali ne daga yar baiwar uwar bishiya, hakan zaisa na rok'eka ka sako min uwata a gabana dan na samun damshi da tabarrukinta wajen inganta tarbiyar yarona ya zama salihi tamkar kai... *babban mutum*."_ _____________ Komawa yayi ya zauna banda dariya da bayyanannan murmushi babu abinda yake, Ummanshi ma ta samu yabo daga gareta, shi kuma ta fasa mishi kai da gunduma gunduman kalamai haka, lallai ta musamman ce ita a duniyar matan na daban, a gajarce ya mayar mata da _"Kin rufe min baki da manyan kalamanki, bansan me zan ce ba kuma, ji nake duk abinda zan furta miki yanzu katob'ara ce zanyi."_ ______________ Murmushi tayi ta tura masa _"Idan ka sanar dani waye kai ma zai wadatar dani da saka ni farin cikin sanin wannan mai babbar zuciya haka."_ ______________ Murmushi ya sake saki ya d'ora da _"Ke da zaki bani lokacin da zan iso gareki, me ye anfanin sanin waye ni ta waya kuma?"_ _______________ A hankali ta mayar masa da cewa _"Ka fini gaskiya kuma, zan tsumayeka da kowane lokaci yayi daidai da son zuciyar yar baiwar uwarmu."_ ______________ Jim yayi yana kallon sak'on, bata san waye ba a yanzu, bata san mahaifiyarshi ba, amma tana girmamata haka, matar da yake tare da ita a matsayin uwar 'ya'ya ma ta kasa girmama mishi uwa kamar haka, to kenan miye manufar aurensu? Girgiza kai yayi kawai ya mayar mata da _"Daga yanzu har zuwa sallah isha'i ki zuba idon ganinmu."_ ______________ A gajarce ta maido da _"Angama ranka shi dad'e."_ Saida ta tura sak'on ta kalli jerin sak'onnin, dafe k'irjinta tayi a hankali a zuciyarta ta tambayi kanta, Faduma lafiyarki k'alau kuwa? Ina jan ajin da kamewarki? Me ya had'aki zuba kalamai haka da wanda baki sani ba? Had'uwar yanzu yanzu kawai kiyi ta sakin zance, me yake damunki? Dafe gaban goshinta tayi tace "Kash Faduma, kinyi sakin baki dayawa." Aikinsu suka ci gaba da yi da taimakon mutane har suka kammala, ilahirin mak'wabta na gabansu da bayansu gefensu dama da hauni babu wanda ba'a aika ma abinci ba. Da magriba bayan tayi wanka tayi sallah, a tsanake ta samu kanta da shiri na musamman kamar wacce zata je wata gasar, sai dai ba tayi kwalluya sosai ba sai powder data shafa, jan baki ta saka a leb'enta na sama mai kalar chocolat, sai na k'asa data shafa masa lips hakan ya fito mata da kyawun bakinta yayi kyau yana k'yalli kad'an. ______________ Yana nan zaune yaji motsin tab'a k'ofa, sanin ita ce yasa shi had'e farin cikinshi ya gayyato fuskar tsoro da furgitarwa ya yafa a jikinshi, k'ure k'ofar yayi da ido yana kallo har ta shigo da mamakin yanda akayi k'ofar ke bud'e, dan tuni gabanta ya shiga fad'uwa da tsoron ko shine ya dawo, hannu ta zura a hankali ta lalubi makunnin wutar d'akin ta kunna, haske na gama d'akin sukayi ido hud'u, wani irin tsinkewa gabanta ya sake yi, kallon da yake mata razanannan kallo ne mai sa a ji fitsari, rawa jikinta ya d'auka bakinta na rawa da son k'ak'alo abinda zata fad'a masa shine ya zama dalilin fitarta babu izininshi. Mik'ewa yayi ya fara takawa infa take, ai da gudu ta juya ta bar d'akin ta nufi b'angaren Umma dan ceton ranta, yana ganin haka ya juya ya koma ya zauna yana k'wafa da jinjina kai. Yanda Umma ta ganeta ta fad'o d'akin saida gabanta ya fad'i, tasan ba lafiya ba tunda ta ganta anan, dan in bata manta ba sati d'aya kenan cirr rabon da suyi ido biyu duk da suna gida d'aya, shima a ranar dan zata fita ne ta shigo ta bata kayan yara da za'a canza musu in sun dawo daga makaranta, sai yau kuma data ganeta yanzu, tabbas ko dai ta masa laifi kula tana tsoron hushinshi dan tasan dai shi ba mai dukan mace bane, ko kuma wani abu take so ya hanata, amma dai yanayinta yafi mata kama dana wacce ba lafiya ba, ganin sun kalli juna yasa ta saita nutsuwarta ta sunkuyar da kai, a hankali ta shiga takawa ta k'arasa kusanta, kasa ta zauna kai k'asa tace "Ina wuni Umma." Umma na da hak'uri sosai da sosai, tana da shanye abu da kai zuciya nesa kamar dai yanda Hasheer yake, saidai ta tsani raini kai tsaye, ko Mujaheed tana hak'uri ne da iskancinshi dan yafi mata kama da mashayi, sannan bata son raba kan yayan mijinta, amma ba dan haka ba tuni ta fita sabgarshi kuma fita ta har abada. Amma Saudat a zahiri take nuna mata bata d'auketa da muhimmanci ba, dan haka ita ma tayi wuri ta ajeta, cike da rashin nuna damuwa ta kalleta sama da k'asa tace "Lafiya." Jin yanda ta amsa mata tasan ba wani sakewa ne zatayi da ita ba, dan haka taja baki tayi shiru ba tace ga abinda ya kawota ba, fitowar su Izzadeen daga d'akin Halima a lokacin yasa ta saki jikinta, da gudu suka k'araso gareta duk suka kewayeta kowa na tambayar me ta kawo mishi, yanda zuciyarta ke tafarfasa ga tunanin yanda surukuwarta ta karb'eta ga tunanin zakin ubansu data baro yasa take jin kamar ta daka musu tsawa su matsa kusanta, amma Umma dake nan ne ta hana ta yin hakan, wayar Umma suka ji tayi k'ara ta d'auka, daga yanda ta amsa a harshen larabci ya tabbatar mata da Hasheer take magana, babu abinda taji bayan kalmar isha'i da kuma insha Allah, dan haka bata gane komai ba sai ma mik'ewa da tayi ta aje jakarta da gyalenta ta shiga d'akinsu Salima. *Isha'i* Suna zaune falon bayan sunyi sallah dan yau kam duk ta gabatar dasu akan lokacin sakamakon zamanta anan, sama sama ne suke d'an tab'a hira, su Izzadeen ne suka fito cikin shiri tsaf dasu da kaya iri d'aya, da mamaki ta kallesu tace "Ku kuma ina zuwa haka? Wa ya shirya ku?" Salima ce tayi tsal tace "Tunda kika ga sun fito daga d'akin Umma ai kinsan ita ta shiryasu." Juyowa tayi ta harareta tace "Tambayarki nayi to?" Umma ce ta fito, tattausan k'amshin turarenta na sandal ya sanar dasu haka, duk kallonta sukayi, ba wani jiki ne da ita ba gata fara sol, tayi ruf cikin jar lafaya ta yane har kanta mai d'auke da dogon gashi, takalminta jajaye masu d'an tudu sunyi d'as a farar k'afarta, Halima ta kalla tace "Zan tafi sai mun dawo." Jinjina kai tayi tace "To Umma, Allah ya kiyaye hanya." "Ameen." Ta fad'a tana kallonsu Izzadeen tace "Muje." Salima ce tace "A dawo lafiya Umma." Saida suka d'auki hanyar fita tace "Allah yasa." A daidai k'ofar b'angaren suka samu mota a pake, dama b'angaren da yake zaune a bud'e yake, yana ganin fitowarsu yayi saurin fitowa cikin ruwan sanyi, bud'e b'angaren da yafi kusa da ita yayi, murmushi ta masa tana kallonsa tace "Shukran." Shima murmushin ya mata, shiga tayi tare da su Izzadeen ya mayar da k'ofar ya rufe, komawa yayi kujerar ta zaman dreba, cikin nutsuwa yaja motar suka nufi k'ofar fita, mai gadi na ganinsu ya wangale musu k'ofar, suna fita ya mayar ya rufe su kuma suka harba motar kan hanya. Tun basuyi nisa ba Umma daga baya da take zaune tace "Hasheer." Cikin nutsuwa yace "Na'am Umma." A hankali cikin harshen larabci yanda yaran ba zasu gane ba tace "Wani abu ya had'aka da mahaifiyar yaran nan ne?" Jim yayi yana kallon titi, sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke yace "A'a Umma." Murmushin gefen labb'a tayi tace "To idan ma dai akwai wani abun kayi hak'uri ka k'yaleta kaji." Shiru kawai yayi bai ce komai ba sai murza sitiyarin da yake a matuk'ar nutse har suka k'araso k'ofar gidan. Da hanzari ya fita ya sake bud'e mata ta fito yaran suka biyo bayanta, kallon k'ofar gidan yayi ya nuna wa su Izzadeen yace "Ku shiga sai ku sanar da zuwanmu." Ai da gudu suka juya suka shiga basu jira k'arin bayani ba, Umma ma takawa tayi zuwa daf da k'ofar, hakan ya bashi damar sauraro bugun sautin zuciyarshi daya fara zanca salon bugawa, tunaninshi bai wuce idan ta fahimci shi ya turo mata sak'on d'azu ba me zatayi? Wane tunani zatayi akan shi? Yana tsayen nan yaji muryar Sharfudeen na fad'in "Abba aka ce ku shigo wai." Da sauri ya kalleshi, Umma kuma kallonshi tayi tace "Bari na fara shiga ko?" Gyad'a kai yayi kawai yana kallo har suka shiga... *Sai litinin insha Allah* *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 17:15 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _35_ Bayan tafiyarsu Salima data hangi Hasheer ya bud'ewa Umma mota ne tace "Kai! Wallahi akhi Hasheer yayi bala'in kyau cikin d'anyar shaddar can fara, kinga kuwa yanda yayi wani shakaf dashi har da hula." Halima ce ta kalleta tace "Da gaske? Hula fa? Akhi d'in?" Cike da tabbaci tace "Wallahi kuwa, kinga yanda yayi kamar wanda zai je zance ko kuma gaishe da surukai." Da sauri Saudat ta kalleta, sama da k'asa ta harareta taja wani mugun tsaki mai sautin gaske, mik'ewa tayi a fusace ta d'auki gyalenta da jakarta ta nufi hanyar fita a d'akin, dan a ganinta duk da Salima ba k'aunarta suke ba to hada ma tsanarta da jin haushinta suke, in ba haka ba ya zata fad'i haka a gabanta? Mujaheed da zai shigo ne shima suka had'u, dama duk yaji abinda ya faru, dan haka ya kauce mata a hanya ta wuce sai kula ya juya ya bi bayanta, saida ta kai daf da shiga b'angarenta yace "Matar yaya." Tsayawa tayi ta juyo, ita dai tasan duk abinda ke tsakaninshi da yan gidan, dan haka ita ma bata shiga harkarsa, saida ya k'araso ya tsaya gabanta yace "Sun b'ata miki rai ko?" D'an guntun tsaki taja ta yatsina fuska kawai, murmushi yayi yace "Kiyi hak'uri, iskanci ne kawai da raina mutane, amma kamar Salima ai k'arya ne ace k'uruciyarta ta kai ta kasa sanin maganar da zata wa mutum zafi, kawai da gangan ta fad'a saboda akwai wata manufa a kan ki." Da mamaki ta kalleshi tace "Manufa kuma? Wace iri?" Wani murmushin ya kula saki yace "Ba sa so kisan komai, amma me yasa ke bakiyi tunanin ina zasu je ba?" Jim tayi ta kalleshi da wani mamakin, hakan ya bashi k'arfin gwiwar d'orawa da "Ya kamata ko farka a baccin da kike, yaudara da cin amanarki da ake ya isa haka, ke ma macece mai hakk'i a gurin mijinta, yana da kyau kisan duk abinda yake faruwa a rayuwarshi a kowane sakan." Gyara tsayuwa tayi jikinta na neman fara kakkarwa tace "Mujaheed me yake faruwa? Dan Allah ka fad'a min abinda le faruwa." Ajiyar zuciya ya sauke yana mata wani murmushin *tarko na ya kama tsuntsu* yace "Ba zaki ji daga bakina ba, in kuwa har zan fad'a miki sai dai in zaki yarda mu zama abokai kuma masu rik'e sirrin juna." Shiru tayi tana kallonshi, jinjina kai tayi tace "Ba damuwa, na amince." Wani murmushi ya sake sakar mata na mugunta tsagwaronta tare da juyawa yana fad'in "Zuwa gobe zamuyi magana." Da kallo ta bishi tana nanata kalaman cin amanarta daya fad'a, me ke shirin faruwa? A gidan nan za'a mata haka? Shine har da kwasar mata yara aka tafi dasu wurin cin amanar ta ta? "Lallai akwai tashin hankali a gidan nan." Ta fad'a tana buyawa ta bud'e d'akin ta shige, a falon tayi zaune ita ma kamar yanda ya mata d'azu, girgiza k'afa ta shiga yi tana jinjina kai na masifa tana jiran ya dawo, ya jima bai kashe ta ba saboda ta fita d'aukar maganinta, sunan maganin daya fito a tunaninta ne yasa ta tuna bata sha ba ma, mik'ewa tayi tabe ta d'auko ruwa ta dawo ta b'alli maganin tasha ta mayar a jakarta ta rufe ta zauna tana ci gaba da girgiza k'afa. ____________ Tayi mamaki sosau ganin yaran, musamman da suka fad'a mata suna tare da Umma da Abbansu. Sanda Sharfudeen ya shigo tare da Umma dake bayansu ta sake shiga mamaki sosai, matar dai alamu basu nuna tana da wasu shekaru over ba, amma kuma babbar mace ce da zata iya haifar yayunta ma bare ita, kallon juna sukayi da tunani iri d'aya a zuk'atansu, ba dan komai ba sai dan lafayar dake jikinsu data zama kala d'aya, duk da ta dattijiwar tafi ta ta tsada da kyan gaske, amma ba zaka gane haka ba inba sani gareka ba akan suturar lafaya, musamman ma daya zama ita ma ta ta sabuwa ce fil sai d'aukar ido take janta ya fita da kyau, takalminta ne kawai plate jajaye masu duwatsu da kalar ruwan zuma kamar duwatsun dake ga lafayar d'ai d'ai a wuri wuri. Kwarjini da haibar data cika matar tasa Faduma sunkuyawa tace "Ina wuni *Ayya*, sannu da zuwa." Da wani tsadadden murmushi ta kalleta lokaci d'aya taji ta kwanta mata a rai, kafin ta amsa mata Amjad da Dada ma duk suka gaisheta, saida duk suka gama kafin ta amsa a wata sanyayyar murya tace "Lafiya k'alau, na same ku lafiya?" Kallon fuskarta Faduma tayi, muryarta ta mata kama data wani data sani, amma kuma a ina? Shine ta kasa tunawa, Dada ce ta musu iso zuwa d'aki ta samu guri ta zauna, kafin su ankara Amjad ya ajiye ruwa da lemu a gabanta, mik'ewa yayi ya koma gefe kusa dasu Izzadeen, kallonshi Umma tayi cikin sanyin hali tace "Zo Amjad." A nutse ya matso kamar yanda ta buk'ata, shafa kanshi tabe tayi sai yayi saurin durk'usawa k'asa, kallonshi tayi ta fad'ad'a murmushinta tare da kai hannu ta shafi sumar kanshi, a hankali tace "Amjad ya k'ok'ari?" A tausashe yace "Alhamdulillah." Kallon inda su Faduma ke zaune tayi dan bata san wace zata kala ba tace ita ce mahaifiyarshi tace "Nasan zakuyi mamakin gani na da kuma tunanin wacece ni? Kakarsu Izzadeen ce, dama sun fad'a min makaranta d'aya suke da yaron, kuma ina d'aya daga cikin wanda suka saurari gasar daga farko har k'arshe, a gaskiya yaro ne mai hazak'a da basira, shiyasa na zo da kaina dan ganinshi ido da ido." Murmushi duk suka saki hakan ya k'ara durmiyata tunanin wacece uwarshi a ciki? Dada ce tayi saurin cewa "Mun gode sosai da wannan karramawa, Allah ya saka da alkairi, ai Amjad yaro ne mai kaifin basira." Murmushi tayi ta kalleshi tace "Masha Allah, Allah ya maka albarka Amjad, Allah yasa albarka a cikin karatunka." D'aga kai yayi ya kalleta yace "Ameen Mamie, nagode, ke ma Allah ya k'ara miki lafiya da kwanciyar hankali." Da mamakin addua'r da yaron ya mata ta sake waro ido ta kalleshi, d'agoshi tayi ta zaunar dashi kuma da ita, jakarta data aje gefe ta d'auko ta zuge zip d'in, wani d'an akwati ta fito da shi ta mik'a mishi tare da fad'in "Wannan wata kyauta ce daga gareni, zata maka anfani." Hannu biyu yasa da girmamawa ya karb'a yace "Nagode sosai Mamie, Allah ya saka miki da alkairi." Murmushi ta masa, juyawa yayi ya mik'awa Faduma hakan kuma ya tabbatar mata ita ce mahaifiyarshi dan ba kama suke ba sai ta wasu hallita shima idan ka k'ure musu kallo, misali yatsun k'afarshi dana hannaye masu tsayi da kyawun fasali da kuma tara zufa a kowane lokacin, hakan yasa hannayensu ke da taushi da laushi da kuma gumi. Karb'a tayi ta kalleta ita tace "Mun gode fa sosai, Allah ya saka da alkairi." Girgiza kai tayi amma ba tace komai ba, abincin da Dada ta aje musu ne ta kallesu tace "Yan samari ku zauna ku ci abincin." Kallon Dada sukayi suka kalli farantin abincin, suna so su ci amma kuma suna tunanin abbansu, Sharfudeen ne ya matsa kusan Umma ya mata rad'a a kunne, kallonshi tayi tace "Kaga ko da tsurfa, to Aban naka me zai shigo yayi cikin mata tunda babu namiji anan?" Mak'ale kafad'a yayi yace "Ya zo mu ci abinci mana, ko kuma muje can waje sai mu ci tare dashi." Faduma dake ta tunani ita kad'ai a ranta cewa to ko dai da Hasheer ne tayi magana a waya? Jin abinda yaran suka ce yasa tayi dariya tace "Da gaskiyarku fa, to kaje ka ce ya shigo ciki mana." Kallonta Umma tayi tace "Ai ba zan shigo ba, tunda gidan matan aure ne taya zai shigo babu izinin wani mai gida a ciki?" Ta k'arashe maganar tana kallon dukansu ita da Dada da suke zaune kan kujera d'aya kamar wasu k'awaye, dan dama irin k'anwar uwar nan ce da wata zaka girmeta ma wata kuma kuyi sa'a d'aya, gata ita ma cikin lafaya take fara mai kwalliyar pilawoyi koraye. D'an kallon juna sukayi ita da Dada sai kuma tayi murmushi ta mik'e tace "Ba komai Ayya, bari a mishi iso." Fita tayi daga falon, ajiyar zuciya ta d'an sauke ta kalli su Izzadeen da suka saka hannu tare da Amjad, mayar da dubanta tayi ga Dada, cikin sanyaya murya tace "Ke abokiyar zamanta ce?" Yar siririyar dariya Dda tayi tace "K'anwar mahaifiyarta ce ni." Jinjina kai tayi tana sake jujjuya abun a ranta ita kad'ai, kallonta ta sake yi tace "Amma ai ita ce mahaifiyarsa ko?" D'aga kai tayi tare da cewa "Eh." Nan ma jinjina kai tayi, mik'ewa tayi tace "Bara a zubo muku abinci?" Da sauri tace "A'a Alhamdulillah, mun ci abinci ma a gida ai, suma dai dan suna yara ne." Dariya tayi ta koma ta zauna tana fad'in "To ko ruwan ku sha." Murmushin yak'e tayi ta sunkuya ta d'auki gorar ruwa ta bud'e ta tsiyaya a kofin tangaran da Amjad ya kawo. *Tana* fita akan k'eyarshi ta fara sauke idonta saboda ya jingina a motar ne ya bada bayanshi, duk da ba wani saninshi tayi ba sosai, amma dai taga banbanci sosai a yau a tare dashi, ba wai manyan kaya ba hula daya saka, da kuma wata lafiyayyar crv honda kamar zatayi numfashi sai d'aukar ido take, tsaye tayi daga inda take tana ci gaba da kallonshi, a tausashe sosai yanda ko kusanta kake sai kayi da gaske kaji me ta fad'a tace "Salam." A tare k'irjinshi da saukar muryarta a kunne suka riske shi, dakatawa yayi daga danna wayar ya kafe k'asa da ido, wani numfashi kawai yaji yana saukewa kamar wanda athim zata kama, da k'arfi ya huro iska ya furzar, a hankali cikin fargaban daya fara jin haushin kanshi na tuhumar dalilin da yasa hakan ke faruwa dashi a kanta ya juyo. Ido cikin ido suka kalli juna, sai kuma tayi saurin d'auke nata idon saboda wani kwarjininshi da kyan da taga yayi, shi kuma kasa d'auke ido yayi saboda ganin ta saka kaya irin na Ummanshi, kyan da tayi mai ban mamaki yasa shi yin murmushi bai shirya ma hakan ba. Yanda ta daskare ta kasa motsawa ya bashi damar fara takowa cikin k'arfin hali har ya zagayo inda take, tsaye yayi gabanta ba tare daya sarara daga kallon da yake mata ba, d'aga kai tayi a hankali ta kalli fuskarshi, kallo irin na mamaki sosai, a hankali ta sake furta "Inji bature yace i dont believe it! Na kasa yarda har yanzu da kai nayi magana a waya." Saida ya sakar mata wani masifaffen charme, cikin murya mai saukar da kasala yace "Saboda dumkum ne ni, wannan kalaman sun fi k'arfi na?" *Mai damagaram*馃槑 D'an siririn murmushi tayi tace "A'a ba haka nake nufi ba, abun dai ne ya zo min wani iri." "Na bayar da mamaki kenan?" Ya fad'a yana kashe mata ido d'aya, da sauri tayi k'asa da kanta tana sakin wata dariya, d'agowa tayi ta kalleshi tace "Wannan ai d'abi'arku ce." Da rashin fahimta yace "Dumkum d'in?" Girgiza kai tayi tace "Bayar da mamakin." Kallon tuhuma ya mata yace "Me yasa kika fad'i haka?" D'an gyara tsayuwarta tayi tace "Ba komai, kawai abinda na lura dashi kenan a tare daku, bayar da mamaki, saka mutum ya ji kamar kar ya mutu, da kuma saka mutum fatan mutuwa." Kallonta yayi yana murmushi yace "Kina magana kamar irin haka ta faru dake? Amma me kikayi fata?" Tab'e baki tayi "Hummm!" Juyawa tayi ta koma tana fad'in "Ka shigo ciki, yara na cin abinci ne." Da kallo ya bita, d'aga girarshi yayi kawai ya sake jingina jikin motar bai shiga ba, ganin bai shigo ba kuma babu wanda ya sake bi ta kanshi, har yaran suka gama cin abinci, Faduma da kanta ta wanke musu hannayensu, hakan yasa Umma mik'ewa tana fad'in "To tunda kun ida sai mu tafi ko." Mik'ewa Dada ma tayi tana fad'in "Har zaku tafi?" Kafin su bata amsa kuma ta juya ta shiga d'akinta, hannun Sharfudeen da Izzadeen ta kama suka shiga d'akinta ita ma, duk basu jima ba suka fito, ledar kanta dake hannunsu mai kyan gaske d'auke da kayan da zasu birge yaro a ciki, wanda tana ajiyarsu ne ba dan Amjad ba sai dan yaran unguwa, dan Amjad bata mishi sabon kayan zak'in nan ba, shiyasa in Aminu ya bashi yake jin dad'i, Dada ma fitowa tayi da wata rantsatsiyar kwalba d'auke da humra mai shegen k'amshi da dad'i fara tas, Umma ta bawa ita ma wanda tasa hannu biyu ta karb'a tana fad'in "Kyauta mafi daraja, kyautar turare na da mahimammci, hak'ik'a zumuncinmu da ku ba zai tsaya iya nan ba." Dukansu dai murmushi sukayi suka rankaya suka nufi hanyar fita, a k'ofar suka same shi tsaye har yanzu kamar wani mai gadi, yaran gurinsu suka nufa suna nuna mishi kayan hannunsu, shi kuma hankalinshi na kan Amjad dake gaishe shi, suna cikin gaisawar Umma tace "To Amjad zamu tafi, sai wani lokaci kuma ko? Amma zan karb'i lambar mamanka sai na dinga kiranta muna hira da kai, dan ni dai nayi miji anan, bana son wad'annan kolayen yanzu." Duk dariya suka saka sai su Izzadeen da basu kula ba ma, hararensu tayi tace "Kinga sarakan shan zak'in, basu ma san wainar da ake toyawa ba." Girgiza kai tayi cike da takaicin irin turban da Saudat ta d'ora yaran, mik'awa Faduma wayarta tayi ta karb'a da girmamawa ta saka mata lambarta, tana mik'a mata ta karb'a tana kallonta tace "Sai anjima ko, gashi dai har zamu tafi mahaifinshi bai dawo ba, na so ganinku gaba d'ayanku dan mu tattauna akan..." Bata gama fad'a ba ta ga Dada da Faduma sun kalli juna, kallonta Faduma ta sale yi da jin kunya sosai da kuma hawaye a idonta, sunkuyar da kanta tayi hakan yasa duk suka kalleta, kallon Amjad tayi sai taga shima uwarshi yake kallo haka ma Hasheer, mamaki ne ya kamata cikin nutsuwa tace "Ku gafarce ni idan na fad'i wani abu ba daidai ba, ko mahaifinshi baya raye ne?" Mayar da kallonta tayi ga Amjad ta dafa kanshi tace "Kar dai kai ma maraya ne kamar 'ya'yana?" D'aga kai yayi ya kalleta sai kuma ya kalli Faduma dake gefe, ita ma a tsorace ya kalleshi da mamaki, yaron da baya jin nauyin fad'an Abanshi ya rasu, shine yau yake kallonta haka ya k'i amsawa da eh, me yake nufi? Yatsa tasa ta share k'wallar data taho mata ta gefen ido, kallon Umma tayi cikin dakusashiyar murya tace "Sai anjima." Da sauri ta shige ciki hakan kuma yasa duk suka bita da kallo, da sauri Dada ta d'aga k'afa zata bi bayanta Umma ta d'aga mata hannu, kallon juna sukayi tace mata "Ki bari zan je, ina kallonta kamar 'yar dana haifa dan bata wuce sa'ar yata Halima ba." Shiga tayi sai Dada data huro iska duk tana jin ba dad'i, Hasheer da ranshi ya gama jagulewa ya rasa me ke masa dad'i jin hayaniyar yaran yake kamar saukar guduma a kan shi, dan haka ya bud'e musu k'ofa yace "Ku shiga ciki ku zauna." Shiga sukayi suna d'agawa Amjad hannu, shima cikin gida ya shige jikinshi duk a mace kamar zaiyi kuka, kallon Dada cike da kulawa ya gyara tsayuwarsa ya rumgume hannaye a k'irji yace "Mun had'u da Faduma zuwanta Zinder, Kalli abokina ne na karatu da kuma kasuwanci, ya fad'a min mijinta ya rasu, amma kuma ranar sai ga wani anan wanda ya amsa sunan uban Amjad, dan Allah *aunty* me yake faruwa ne a rayuwar baiwar Allahr nan?" Kallonshi tayi kallo na fahimta, a girme ya girmeta sosai da sosai, sannan matsayinsu ma ba d'aya ba, amma ya kirata da aunty haka kai tsaye? Gyara tsayuwa ita ma tayi da kyau tace "Tabbas mahaifin Amjad yana raye, wani dalili ne yasa ta alak'antashi da mutuwa, a lokacin mu kanmu bamu yi tunanin abubuwan da ke faruwa yanzu zasu iya faruwa ba, da ni da marigayi mijina mun kwab'eta akan kashe mutumin da ake da tabbacin yana raye kuma a duniyar da muke." Shiru tayi na d'an lokaci kafin ta sake kallon fuskarshi sosai tace "Faduma yarinya ce data tashi cikin tarbiya da kulawar iyayennta mata biyu da kuma soyayyar uba (duk labarin ta fad'a mishi wanda ta sani da wanda Fadumar ta k'ara mata bayan sun dawo garin nan)...A wannan ranar sai gashi mahaifinta da ko fad'a zai mata sai dai ya mata a cikin sanyi, sai gashi ya mata dukan dana tabbatar ya daketa ne dan ta mutu ko kuma abinda ke cikinta ya lalace ya zube, haka muka dawo da ita garin nan har saida tayi jinya saboda bak'ar wuyar da tasha." Numfashi ta sauke ta ci gaba da cewa "Duk wani rashin kulawa da Faduma ta dinga nunawa cikin nan da aikin wahala duk dan tana so ya bar jikinta hakan bai sa ya tafi ba, sai ma girma da yake yana ci gaba da bayyanar da kanshi, gudun zargi yasa muka fad'awa mutane yar yayata ce da mijinta ya rasu akan hanyar tafiyarshi, da haka suka yarda kuma suna bata duk wani gudumuwa data kama daga garesu, ta wani b'angaren kuma tana karatunta shima babu wata matsala, dan ko laulayi cikin bai saka ta ba bare ya hanata walwala, da kud'in data samu na gasarta ta dinga d'aukar nauyin karatunta dan bata yarda ko mai gidana ya taimaka mata ba, da kanta ta dinga yin komai har ta bar garin nan tayi karatunta ta dawo, kuma da cikin kud'in da kayan d'akin da mahaifinka ya d'auki nauyi ya siya mata da aka siyar dasu ne har suka had'a suka bud'e ofishinsu ita da wani abokin aikinta, dashi ta siyawa kanta motar da aka sace mata kwana biyu da suka wuce...wannan ita ce Faduma, wacce yanzu babu abinda tasa a gaba kamar aikinta da kuma rayuwar yaronta, kuma kamar yanda kake gani ita ce tsaye akan d'anta sai taimaka mata da nake ta wasu fanonni, dan ko a unguwar nan cikin yara bata yarda ya fito yayi wasa dasu ba saboda gudun d'aukar abinda bai mata ba, sai dai sanin da tayi cewa yaro yana samun fasaha ne idan yana shiga cikin yan uwansa yara, dole yasa take turashi gidan nan (ta nuna gidansu mama) dan yayi wasa da yara shima ba kullum ba." A gaskiya ba dan tace k'anwar mamanta bace hakan yasa yake kallonta kamar surukuwa, da sai ya zumduma ihu ya daki motar nan da k'arfi, haushin yaron nan! Kam! Cije leb'e kawai yayi, dama abinda ya faru kenan shine ranar ya zo nan yana musu hauka? Lallai had'uwarsu ta gaba ba zata mishi kyau ba, saiya taka wuyan d'an banza ya mutu har lahira. Ita kam ban da wani mugun tausayinta da wata k'aunarta babu abinda ya sake ji, har saida yaji ina ma tana nan gabanshi daya durk'usa ya nemi aurenta, da saiya nuna mata maza suna suka tara, da saiya shayar da ita zuma ya kawo haske a cikin rayuwarta, da ya canza shafin rayuwarta daga wani babin zuwa wani babin, *so*, son ta kuma yanzu ya fara, uban d'anta kuma bai dame shi ba, ba zai goyi bayanta kan ta hana mishi yaron nan ba, sai dai ba zai bari bane ya ci mutumcinta wajen karb'an yaron, sannan ba zai tsaya yace sai ta bashi yaron ba shima, hasalima zai so ya zauna wurin uwarshi, dan alamu sun gwada har danginshi ba mutanen arzik'i bane. Kallon Dada yayi dake sharar hawaye yace "Amma me yasa ke bakiyi aure ba? Zamanku haka ku biyu mata sai yaro zai sa a dinga kallonku a k'ask'ance ana zarginku." D'an murmushi tayi tace "Faduma bata da niyyar aure, ni kuma a gaskiya ba zan iya tafiya na barta ba, wanda muka tsayar da magana yace ana d'aura mana aure zan tare, sannan a gidansa yake so na tare ba anan ba, shiyasa na k'i bashi fuskar turawa wajen magabatana har yanzu, duk da nima suna hushi dani dan ganinsu mun zama masu zaman kanmu ne, amma dai hakan bai dame ni ba, rayuwarsu nake dubawa." Jinjina kai yayi yace "Gaskiya ne, Allah ya saka miki da alkairi, hak'ik'a kinyi zumunci mai girma wanda a yanzu samun wanda zai iya irinshi sai an tona, zaki samu sakamakonki insha Allah." Murmushi kawai tayi ba tace komai ba. *A ciki kuwa* *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 17:16 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _36_ Duk abinda Dda ta fad'a masa shi Faduma ta fad'a ma Umma, sai dai jin labarin daga bakinta yafi komai tab'a zuciya, dan tsantsar gaskiyarta ne kuma da zuciyarta take fad'a tana feso zafin dake dunk'ule a zuciyarta ne, yanda take rizgar kuka ya bawa Umma tausayi sosai har ita ma ta shiga zubar da hawayen, tabbas taji abun a zuciyarta sosai, ta tausaya mata matuk'a tare da aunawa a m'aauni ta daidaita idan da akan yaranta ne wata haka ya faru da ita fa? Tabbas bata ga laifin mahaifinta ba, dan kowane iyaye burinsu ace d'ansu yafi na kowa, matsalar kawai zafin ya d'auka dayawa har yanzu yana hushi da ita, wanda a yanzu kuma take matuk'ar buk'atar soyayyar uwa a tare da ita da uba, amma tana nesa dasu babu wanda ke rarrashinta, babu wanda ya tayata rainon abinda ta haifa a cikinsu, ba dan da taimakon Allah ba Allah ya shirya mata yaron, da yanzu tana shan wahalar yaron na rashin ji da abun ya mata yawa sosai, tunda ita kanta Dada tana buk'atar kulawar wani. Ta wani b'angare kuma ta jinjina mata sosai akan k'ok'arinta, abu d'aya zata iya mata yanzu shine ta sasanta tsakaninta da iyayenta, ta koma gabansu ta samu nutsuwa da farin ciki, ta ji d'umin jikin mahaifiyarta, har ta samu miji tayi aure, amma kafin nan zata fara zama mata uwa na d'an lokaci, zata fara kusantar da ita a jikinta ta ji miye damuwarta ta yanzu, wannan shine taimakon da zata iya yi mata kawai. A hankali ta jawo kanta ta d'ora kan cinyarta tana shafa kanta, cikin muryar jimami da kuka tace " *Teema* kiyi hak'uri kinji ki daina kukan haka, insha Allahu komai zai wuce ya zama tarihi, kiyi shiru kinji ki daina kuka, k'addararki ce haka na fahimta, haka Allah yace Amjad zai zo bata hanyar aure ba, amma ki sani Amjad na da nagartar da yara dayawa da aka samu ta hanyar aure suka rasa, Amjad d'aya ne a cikin dubannin yara Allah ya azurtaki dashi, kiyi shiru kinji ki daina kuka." D'agowa tayi tana ta shashek'a kamar ranta zai fita tana share hawaye tace "Shikenan Ayya, tashin hankali d'aya ne a yanzu, Amjad yasan Abanshi yana raye, Ayya idan fa wata rana ya kalleni yace me yasa na samar da shi ta wannan hanyar? Ayya ban da amsar da zan bashi, hankali na yana tashi sosai idan na tuna haka." Tafin hannu tasa ta rufe fuskarta saboda wani kukan ne ya kubce mata, a gaskiya data kwatanta abun da kanta sai taji babu dad'i, ita ma data haifesu ta hanyar aure, suka rayu da mahaifinsu na tsawon zamani, rasuwarshi bai fi shekara biyar zuwa shida ba, amma wani lokacin sukanyi magana mai d'auke da kewarshi da take sa ta zubar da hawaye ta kallesu kawai, bare kuma ita? Lallai ta fahimci duk abinda take ji a zuciyarta kam. Ganin tasa babbar mace kuka yasa ta sauri share hawayenta ta tallabo fuskar Umma, kallon juna sukayi ido cikin ido ta shiga sakin murmushi tana fad'in "Dan Allah Ayya ki daina kuka akan matsalata, na saba rayuwa da ita a haka, wannan ba komai bane ni a wurina, kiyi hak'uri kinji na saki zubar da hawaye." Yar dariya tayi tace "Kin gani nima ina dariya, gashi har na manta da komai." Kallon tausayawa ta mata sosai, ta sake fahimtar wani abu daga gareta yanzu, bayan tsayawar da tayi kan yaron har da jarumtar b'oye abinda ke ranta ma, wanda hakan shi yafi komai wuya a duniya b'oye sha'awa da kuma k'awa zuci. Ita ma mik'ewa tayi ta mata dariya tace "Zan daina kuka, amma ki tabbatar min ke ma ya wuce a wurinki, ba wai na har abada ba dan nasan ciwon nan naki abu d'aya ne zai warkar miki dashi." Mik'ewa tayi tana sake share fuska tace "Insha Allahu Ayya, ba zan sake ba." Hanyar fita suka nufa tana fad'in "Zamu tafi suna jirana a waje." Cikin nutsuwa suka rankayo suka fito daga gidan, a k'ofar gida suka same su da Dada suna d'an tattaunawa, bud'ewa Umma gidan baya yayi, saida ta juyo ta kalli Faduma ta shafi kumatunta tace "Allah ya albarkace ki Teema, insha Allahu zaki ga da kyau a rayuwarki." D'ora hannunta tayi akan na Umma dake kan kumcinta tace "Nagode Ayya, hak'ik'a ke uwace ta musamman, kasancewarki uwa mace baisa kin hukuntani ko ganin laifina ba bare wautata, naji dad'i sosai da kika fahimceni kika min uzuri." Jawota tayi a jikinta suka rumgume juna, dukansu wasu hawayen suka sake sakowa daga kurmin idonsu, hakan yasa Hasheer kallonsu cike da k'aunar dukansu, sai yaji kamar shima ya rumgumesu dukansu ya tayasu kukan, duk da dai baida tabbacin ta fad'a mata abinda ya sani yanzu, amma yaji dad'in ganin wata fahimta da shak'uwa data shiga tsakaninsu daga had'uwar yau, ko kuwa wannan yana daga cikin siddarun yarinyar shiga ran duk wanda ya had'u da ita? Ko kuma dai d'abi'unta ne masu kyau da suke siye zuk'atan duk wanda tayi mu'amula dasu a lokaci d'aya? Shiga tayi ya mayar da k'ofar ya rufe, kallonta yayi da sauri saita sauke idonta k'asa, cikin wata irin murya a sanyaye sosai yace "Saida safe." Jinjina kai ta fara yi kafin tace "Saida safe." Suna kallo har suka bar k'ofar gidan kafin suka koma ciki, suna shiga d'akin Amjad ta wuce wanda ko da ya shigo dama can ya nufa. Kwance yake ya bayar da baya sai yar shashek'a da yake, cikin tako a hankali kamar mai sand'a ta shiga takawa ta gabanshi, saida ta zauna ta dafa hannunshi tace "Amjad kuka kake yi?" Girgiza kai yayi tare da rufe fuskarshi da pillow, ajiyar zuciya ta sauke tace "Hushi kake dani?" Nan ma girgiza kai yayi alamar a'a, a hankali tace "To me kale yi? Ka d'ago ka kalleni mana." Saida ya ja majina a hancinshi sannan ya yunk'ura ya mik'e zaune, da k'yar ya yarfa suka had'a ido saboda bai so ta ga yana kuka, kallonshi tayi ta shafa kanshi tace "Ka ce ba kuka kake ba? Gashi idonka sun nuna haka." D'aga kai yayi ya kalleta idonshi sunyi ja, cikin murya yarintarshi yace "Ayya, me yasa kika ce min Abana ya rasu?" K'ureshi tayi da kallo sai kuma ta rage kallon ta hanyar sassauta idonta, hannunshi ta rik'o cikin nutsuwa tace "Amjad, akwai wani sirri dake tsakani na da Abanka, kar ka so kaji haka tun yanzu, dan hankalinka bai kai ya d'auki girman maganar nan ba, abinda nake so da kai shine karka sake tambaya ta akan mahaifinka." Cikin ido ya kalleta yace "Me yasa Ayya, ki fad'a min mana, Ayya ina son shiga cikin dangina." A kausashe ta kalleshi tace "Amjad bana son ji na ce, ka kwanta kayi bacci." Cikin kuka yace "Ayya modursan yartunnin (me yasa ba zaki yafe masa ba)? Ayya sammahnu (ina son shi)." A tsawace tace "Amjad!" Kallonta yayi ba alamar tsoro a tare dashi, cikin fad'a tace "Tanihi yakkedini (Ni zaka raina)? Toko haraninji toko tahadin ni Ka san shi ne da zaka fad'a min haka?" Cikin ladabi yace "Kiyi hak'uri Ayya na b'ata miki rai." Girgiza kai tayi ta jawoshi ta rumgume tace "Baka b'ata min rai Amjad, bana dai son magana akan mahaifinka ne." A hankali yace "Ayya zaki iya yi min taimako d'aya, na rantse miki idan kika min shi ba zan sake tambayarki komai ba har abada." D'agowa tayi tana kallonshi da mamaki sosai a fuskarta ta tallabi kamatunshi tace "Haba Amjad, kai fa d'ana ne, ka fad'a min me kake so? Insha Allah zan maka shi a matsayin kyautata nima a gareka na samun nasarar da kayi." Idonta ya kalla yace "Da gaske Ayya zaki min?" Jinjina kai tayi tace "Nayi alk'awari Amjad, fad'i abinda kake so Ayyarka ta maka." Saida ya d'an nok'e kanshi yana kallonta yace "Ayya ki kaini na ga Aba na sau d'aya kawai, ina so naje wurinshi, daga wannan ba zan sake tambayarki ba." Tsura masa ido tayi, inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Me yasa Amjad zai mata haka? Mahaifinshi kuma? Tagur fa! Me yasa ta masa alk'awari kai tsaye? Ajiyar zuciya ta sauke ta feso iska ta duk'e kanta, abu ne mai wuyar tsiya Amjad ya nema a gurinta, ya zatayi yanzu? Ta cika alk'awarin data d'auka? Ko kuma ta k'i amincewa? Hakan zai iya shafar tarbiyarshi ne? Amma ai dama ana d'aukar alk'awarin dan wani lokacin akwai yiwuwar a karya shi, kasa samun amsa daga gareta yasa shi cewa "Ayya ba zaki iya min ba bayan kuma alk'awari kika min?" D'aga kai tayi ta sake kallonshi, tabbas ba dan yana yaro ba daya fahimci tashin hankalin da alfarmarshi ta jefa ta a ciki, daya fahimci yanayinta, daya lura da damuwarta har ya janye haka, amma ya zatayi? Ido cikin ido ta kalleshi tace "Idan kun tashi daga makaranta zan kai ka." Murmushin daya bayyana a fuskarshi ne yasa ta mik'ewa tsaye ta shafi fuskarshi tace "Kayi farin ciki yanzu?" D'aga kai yayi yace "Nagode Ayya ta." D'auke hannunta tayi daga fuskarshi tace "Kayi bacci kaji." Jinjina kai yayi alamar to, fita tayi a d'akin ya bita da kallo har ta fice, kwantawa yayi zuciyarshi fal farin cikin zai had'u da Abanshi gobe. Ita ma tana fita d'akin ta ta shiga ta cire kayan jikinta ta canza dogon wando mai taushin gaske wanda ya sake ta sosai da riga mai k'ananan hannu, saida ta shafa man k'afa mai k'ara laushi kafin ta saka safa ta fito falo, Dada ma fitowa tayi suka ci abincin da basu ci ba saboda zuwan bak'in, anan kuma ta sanar da ita ta fad'a wa mutumin komai, ita ma sanar da ita yanda sukayi da Umma tayi, hakan yasa Dada cewa "A gaskiya mutanen suna da kirki sosai, ga su da sauk'in kai da fahimta." Jinjina kai tati tace "Gaskiya, dan haka kawai naji matar ta kwanta min a rai." Kallonta tayi a hankali tace "Dada gobe zan kai Amjad gidansu Tagur." Da sauri ta kalleta tace "Me? Gidansu kuma? Yin me?" Cikin nutsuwa tace "Dada Amjad ne ya rok'i alfarma a wurina, kuma na masa alk'awarin yi masa shiyasa." Girgiza kai tayi tace "Faduma ban yarda da haka ba, idan kuma ya zama dole zaki kaishi to sai dai mu tafi tare da ke." Girgiza kai tayi tace "Wallahi dada babu abinda zai faru, kar ki dam..." D'aga mata hannu tayi tace "Wallahi ba zaki tafi ke kad'ai ba, ai in kikayi haka ma sai naga kamar kin manta abinda ya faru, haba!" A sanyaye ta jinjina kai tace "Shikenan Dada, zamu tafi tare dake a sabuwar motar Amjad." Murmushi tayi tace "Yanzu ki kayi magana." Murmushi ita ma tayi tace "Amma fa banda fad'a Dada, kar kije ki ta mana masifa." Dariya tayi ta daki cinyarta tana fad'in "Uwaki ma, wato kin mayar dani masifaffiya ko?" Dariyar ita ma tayi tace "Sanin hali ai yafi sanin zane Dada." Cikin dariyar ita ma tace "Kinsan kuwa matar nan tayi tunanin ni da ke kishoyoyin juna ne?" Zaro ido tayi tace "Dan Allah? Haba ina ni ina kishi da Dadata? Ai sai wacce ta shirya da kyau." Hararenta tayi dai haka suka ci gaba da hirarsu cikin nishad'i har dare ya k'ara sosai, kowace d'akinta ta shiga ta kwanta da tunanin duniya kafin bacci ya d'aukesu da tsammanin wayar safiyar gobe. ______________ Tunda suka shiga gidan kowa b'angarenshi ya nufa, suna shiga kam yanda take suka tardata zaune da jiran bala'i, kallo d'aya ya mata ya d'auke kanshi ya nufi d'akinshi, hanzarinta yasa ta kallonsu Izzadeen cikin daka tsawa tace "Kai daga gidan uban wa kuke?" Su ma dama da sauri suka nufeta dan nuna mata kayan hannunsu, dan haka da hanzari suka amsa mata da "Daga gidansu abokinmu." "Wane abokin ku?" Ta fad'a a tsawace, Izzadeen ne yace "D'an makarantar mu ne Amjad, wanda mamanshi ta kawomu gida ranar." Mik'ewa tayi ta jawo hannunshi ta matso kusa dashi tace "Me kuka je yi acan? Ita Umma can ta tafi?" A hankali yace "Eh, wai gasa ya ci shine muka je muka masa murna, harda Abba ma da Umman." "Daga nan ina Abbanku ya tafi?" Girgiza kai yayi yace "Bai tafi ko ina ba." Kallon rashin yarda ta bi yaron dashi, sai kuma ta sake shi ta juya a fusace ta nufi d'akin, tana zuwa ta tura k'ofar da k'arfi ta shiga, bai juyo ya kalleta ba sai ma ci gaba da cire rigarshi, hakan ya zama daga wandon shaddar sai bak'ar singlet d'inshi data kama shi, zaune yayi bakin gadon ya fara cire zariyar takalminshi k'afa ciki da safa, gabanshi ta tsaya ta rik'e k'ugu tace "Daga ina kuke?" Tagumi ya buga ya kalleta, kallo na ya zanyi dake? Kallon me kika d'auke ni? D'an cije leb'enshi kawai yayi bai ce komai ba, sake gyara tsayuwa tayi tace "Kai fa nake sauraro? Ka fad'a min ina kuke je min da yara? Na gaji da wannan munafurtata da ake yi a gidan nan." Sauke tagumin yayi, da wani razanannen kallo ya kalleta murya k'asan mak'oshi yace "Saudat kina lafiya kuwa? Ke kinsan kina da laifi a wurina, amma kuma ke ce tsaye a gabana kike min wannan tambayar, raina ni kikayi?" Turo baki tayi tace "Ba maganar raini anan, kawai ina so nasan ina kuka tafi ne da yara na." Hararanta yayi ya mik'e yace "Ke ma kikayi abinda kike so bare kuma ni da ba zamanki nake ba." K'wafa yayi zai shiga ban d'aki ta tare k'ofar tana fad'in "Duk da haka dai ai ina da yancin nasan me kake b'oye min, ka fad'a min tun kafin na fara zargika?" Wani sakaran murmushi yayi yace "Ki fara mana, Saudat ba sai kin wahalar da kanki ba, ki sani yan mata ne dani a waje buhu buhu, kuma ke baki isa hanani kulasu ba." Tureta yayi gefe ya shige ban d'akin, juyawa tayi ta fara bubbuga k'ofar tana fad'in "Kaga fito, wallahi baka isa ba, ni zaka wulak'anta? To na ga yar banzar data isa ta kula min mijina, wallahi saina hallaka yarinya ko yar gidan uban wacece." Ya d'auki minti ashiri a ciki kafin ya fito tana nan tana zazzaga balainta, hannunta ya damk'a da k'arfi sosai ya nufi k'ofa da ita, saida ya bud'e k'ofar ya wurgata ta juyo tana kallonshi, nuna ta yayi da yatsa yace "Wallahi ba dan na wa mahaifina alk'awarin ba zan tab'a dukan mace ba duk girman laifin da zata min, da yau sai na nuna miki masifarki ta rashin kunya ce." Rufe k'ofar yayi da key ya barta nan, shirin kwanciya yayi duk da ba lokacin baccin shi bane, shiyasa ma bai samu baccin ba sai fad'awa tunani. ______________ Ko da suka shirya tsaf suka fito dan tafiya da makullin sabon motarsu, tana bud'e k'ofar gidan suka sauke idonsu akan motar Aminu, da gudu Amjad ya k'arasa gareshi saboda yana waje ne tsaye ya had'e hannaye, rumge juna sukayi suna gaisawa, saida ta mayar da k'ofar ta rufe ta k'araso da fara'a da kuma mamaki, cikin taushin murya tace "Ina kwana." Kallonta yayi yana kashe mata ido yace "Gimbiya Faduma, kin tashi lafiya?" Murmushi tayi tace "Lafiya lau, ya na ganka anan kuma?" Da murmushi a fuskarshi yace "Na zo kai Amjad makaranta ne, dan nasan baki da abun hawa, daga yanzu kuma har ki samu zan dinga kai shi ne da kaina." Da murmushin jin dad'i ta kalleshi tace "An gide sosai Aminu, sai dai kuma ga motar daya samu ta gasar nan, ina shirin kaishi ne da ita yanzu ma." Jinjina kai yayi yace "Na sani, kawai dai zan rage miki wani nauyin ne." Mirmushi ta sake yi tace "Nagode sosai da kulawa." Bud'e k'ofar gaba yayi yace "Bismillah." Da mamaki tace "Tare zamu tafi kuma?" Jinjina kai yayi yace "Eh mana, tunda kin riga kin shirya ba." Matsowa yayi kusanta cikin rad'a yace "Idan kina gefena zan fi jin k'arfin jikina." Girgiza kai kawai tayi ta shiga ya mayar ya rufe, bud'ewa Amjad yayi shima ya shiga, zagayawa yayi ta b'angarenshi ya zauna suka tafi. Tana jinsu shi da Amjad suna ta hira ta shak'uwa kamar d'a da uba har suka isa, yana sauke shi duk suka d'aga mishi hannu har ya shige, kallonta yayi yace "Daga nan ina muka nufa?" Ba alamar shauk'i a tare da ita tace "Gida zan koma?" Saida yai wa motar key yace "Baki da aiki kenan?" Ajiyar zuciya ta sauke tace "Ina da, amma zan duba a gida." Hanyar gidan ya sake komawa da ita, ba wata hira ta nishad'i da sukayi har suka isa, saida ta fita tace "Idan ba damuwa ba sai kaje d'aukarshi ba, zan je da kaina." Da mamaki ya kalleta yace "Me yasa?" Rarraba ido tayi tace "Zamu fita ne tare da Dada, zamu biya mu d'aukeshi daga nan sai mu wuce." Jin haka ya yarda da ita d'ari bisa d'ari, jinjina kai yayi yace "Ba damuwa, Allah ya kiyaye hanya, sai munyi waya ko?" Jinjina kai tayi tace "Ameen." Shigewa tayi shi ma ya juya ya koma. _____________ Tunda ya tashi al'amarin ya zo mishi bai ko tashi daga kan gadon ba ya d'auki wayarshi, lambar mai sunan *Elhaj Kawu* ya kira, bugu uku ana hud'u aka d'auka da sallama, da zolaya cikin taushin murya Hasheer ya amsa da "Wa'alaika salam kawuna, da alama kayi lafiyayyen karin kumallo mai kyau?" Dariya kawun yayi yace "Bansan me yasa kake son tsokanata ba Hasheer, mantawa kake dani k'anin mahaifinka ne ba kakan ka ba, amma ba komai zanyi hushi nayi aure ko zan huta gorinka." Shima yar siririyar dariyar yayi yace "Kawuna, damuwa da nayi da kai yasa ma yanzu haka na zo maka da wani labari mai dad'i." Daga b'angaren yace "Na me fa? Fad'a min inji d'an yarona." Had'e fuska yayi yace "Bana son haka fa kawu." Dariya yayi yace "Shikenan to na daina, ban labari nasha." Ajiyar zuciya ya sauke yace "Kawu na, wata santaleliyar bazawara na samo maka, baka ganta ba kyakyawa mai nutsuwa da hankali, a gaskiya na maka sha'awarta inhar kana so." Daga b'angaren shi yace "Kutt! Yanzu Hasheer saurayi dani shine zaka wani had'ani da bazawara? Lallai ma yaron nan ka raina ni, ni fa budurwa nake so wallahi." Had'e fuska yayi kamar yana gabanshi yace "Da gaske nake fa ba da wasa ba, mijinta ne ya rasu ita ma, kuma haihuwa ko d'aya ba tayi ba fa." Tab'e baki yayi yace "Duk da haka ni dai bana so." Cikin kaushin murya yace "Kafin ka yanke hukunci ka fara zuwa ka ganta mana." Cikin zolaya yace "Kaga zan zo dai kai na raka ka, na gane ka ai kana son ta ne shine zaka wani fake dani." Cike da k'osawa yace "Na yarda ka shirya sai muje ka rakani." Yana fad'a bai jira yaji me zai ce ba ya datse kiran. Sauka yayi daga kan gadon ya fad'a ban d'aki dan shiryawa, bai yarda ya d'auki lokaci mai tsayi ba ya gama shiryawa cikin k'ananan kaya, geans ne fari wanda ya matse daga k'asa da riga bleue mai dogayen hannu, da annashuwa ya fito daga d'akin, amma yana sauke idonshi akan falon duk fara'a da annashuwar shi sai suka b'ace. Ledojin chocolat da abincin da aka zubar da kwanuka duk a falon ba'a share ba, girgiza kai yayi ya fita ba tare daya damu ya tasheta ba, wajen Umma ya fara shiga suka gaisa kafin ya fito, saida ya ciro makullin ya kula dana renge rover ne ya d'auko ba motar da tafi soyuwa a wurin shi ba yanzu wato corolla s d'in shi ba, sai dai ba zai iya komawa ba sai kawai ya shiga ya bar gidan. Kai tsaye risham wax ya fara wucewa dan ya k'arasa aikin War yana so jibi idan zai tafi ya tai mishi da kayan nan ko ya huta da masifar shi. *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 17:16 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _37_ Har sun shirya sun fito k'ofar gidan sun tunkari mota wayar Dada tayi k'ara, tana dubawa ta kalleta tace "Ayyarki ce." Kallonta tayi ita ma tace "Nasan ta kirane ta tambayi Amjad, amma ba zata iya tambayarshi." Kallonta tayi da mamaki tace "Me yasa kika ce haka?" S1ida ta kama murfin zata bud'e tace "Na sani ne ai, zata ce miki kawai dama dan ku gaisa ne, sai kuma tace yara ana makaranta ko? Shikenan fa." Girgiza kai tayi tana murmushi ta d'aga wayar, kamar yanda ta fad'a bayan sun gaisa ne tace "Kowa dai lafiya ko?" Da fara'a ta amsa da "Lafiya lau kowa, ya wajen naku kuma?" "Alhamdulillah." Ta fad'a a hankali, sai da ta ja minti d'aya kafin tace "Ya yaran?" Dariya Dada tayi tace "Duk lafiyarsu lau, ya tafi makaranta, sai uwar kuma gamu tare zamu tafi d'aukarshi." Cikin d'aga sauti tace "Duk ku biyun?" Ajiyar zuciya ta sauke tace "Eh wallahi, daga nan zamu wuce gidansu Tagur ne, saboda jiya Amjad yace yana so yaje." Saida ta dafe k'irjinta daga inda take, zaro ido tayi tana mik'ewa tsaye da k'arfi tace "Wa! Tagur fa naji kince? Wanda dai na sani?" A hankali tace "Shi fa da kika sani." Cikin fad'a tace "Owwo kuma shine zaki raka ta? Me yake damunku ne? Me ya shiga tunaninku daga ke har ita? Kamar wanda basu da zuciya." Shiru tayi na yan dak'ik'u sai kuma tace "Bani ita." Da sauri ta matsa kusa da Faduma dake cikin mota bata rufe k'ofar ba tana kallon Dada, karb'a tayi ta d'ora a kunne tace "Assalm..." A tsawace tace "Rufe min baki dallah!" Da sauri ta kalli Dada da mamaki sai kuma ta mayar da hankalinta kan wayar, cikin fad'a tace "To bari kiji, ban yarda indai nice uwarki, ba ke ba Tagur har abada, ba d'an ki ba Tagur har abada, ba zan lamunci haka ba Faduma, zan iya hak'uri idan da ace dukan mutuwa ya miki kuma ya sakeki a sanda kike tsaka da nak'uda, amma laifi irin wanda ya aikata yafi k'arfin samun yafiyata, dan haka ko da wasa a cikin haukan mafarkinki karki sake tunanin had'ashi dashi, idan ya miki kukan mahaifinshi ki zare masa ido sannan ko sanar dashi waye mahaifinshi, ki kuma nuna masa gaskiyar ke ce mahaifinshi tunda ke ya sani ba wani k'aton banza ba." "K'itt." Taji an kashe wayar, turo baki tayi gaba tare da huro iska, kallon Dada tayi ta mik'a mata wayar, amsa tayi ita kuma ta mayar da kanta jikin kujerar ta lumshe ido, shiru sukayi babu mai motsi tsawon lokaci, a hankali Dada tace "Faduma ya zamuyi yanzu?" D'agowa tayi tana sake sauke ajiyar zuciya tace "Ya fa zamuyi, mu koma kawai." Fita tayi daga motar ta rufe, da sauri ta kalleta tace "Amma yanzu ai ya tashi yana jiranmu." Kallon Dadar tayi tace "To Dada ki min wani k'ok'ari mana, kije makarantar sai ki d'auko shi, wallahi idan ni na tafi da kaina zai yi ta maganganun da zaisa na rasa abun fad'a masa." Jinjina kai tayi tace "Ba damuwa Faduma, ki koma ciki sai naje da kaina." Jinjina kai tayi ita ma ta bud'e gidan ta koma ciki, ita ma bakin titi ta k'arasa ta samu d'an sahu suka nufi makarantar. Tana zuwa har ciki ta shiga suka fito tare yana ta tambayar Ayyarshi? Ta mishi alk'awarin zasu je wurin Abanshi fa? K'ala bata ce mishi ba har suka shiga adaidaita suka d'auki hanya, ganin hanyar gida ce suka nufa ya fara mata kuka yana fad'in "Ni fa Ayyata tace min zata kaini wajen Abana, me yasa zaki kaini gida? Ni ba zan je can ba." Kallonshi tayi tace "Kai Amjad fita idona, tunda muke da kai ka tab'a ganin b'acin rai na? To ka kiyaye ni." Ko ga jikinshi haka ya ci gaba da kuka har suka isa gida, suna sauka ya fad'a gidan da gudu, Faduma dake soya miya zatayi girki da sauri ta kalleshi tana fad'in "Amjad ya da fad'o mana gida haka babu sallama?" Bai kula da abinda ta fad'a ba sai cewa da yayi "Ayya ba ke kika ce zamu tafi wajen Aba na ba? Me yasa Dada ta kawoni gida?" Ajiyar zuciya ta sauke tace "Mun fasa zuwa Amjad." Juyawa tayi ga aikinta hakan uasa shi juyawa b'angaren da fuskarta ke kallo yace "Me yasa Ayya? Alk'awari fa kika min." Ba tare data kalleshi ba tace "Na maka alk'awari ne sanda nake ganin zan iya, daga baya kuma na fahimci akwai matsala, shiyasa na fasa." Cire jakarshi yayi a baya ya jefar a k'asa da k'arfi, da sauri ta kalleshi tace "Amjad, d'auke min jakarka anan wurin." Buga k'afarshi yayi da k'arfi a k'asa yace "Ayya ni ki kaini wajen Abana, idan ba haka ba zan bar miki gidan nan." Da wani matsanancin mamaki ta kalleshi tace "Amjad ka bar min gidan nan? Kan ka d'aya kuwa?" Cikin kuka yace "To ni ki kaini wajenshi ko ki fad'a min abinda ya miki, na gaji ni gaji na gaji, Abana yana raye amma kin sani ina cewa ya rasu." Mik'ewa tayi tsaye a hassale ta nuna shi tace "Wuce d'aki Amjad, ka d'auke min jakarka a nan ka shiga ciki." Kallonta yayi ido cikin ido, tsayawa yayi da kuka sai cije leb'e da yayi ya kumburo baki, wani irin numfashi ya fara saukewa, yanda yake kallonta babu rusunawa a ciki, da yanda yake numfashi da sauri sauri bakinshi kuma a cije alamar yayi zuciya sosai, rufe ido tayi ta nuna mishi k'ofar d'aki tace "Ka wuce ciki nace ko?" Bai k'yabta ba bai kuma yi niyyar abinda tace ba, hakan ya hassalata ta fad'a a tsawace "Na ce ka wuce ciki Amjad, kar ka b'ata min rai kaji ko." Ikon Allah sai kallo, ban da sauke numfashin da yake ci gaba da yi babu abinda ya canza, tsayuwa ce irin ta ko zaki kashe ni ba zan gusa ba, haushin daya bata ne ya tilasta mata d'aga hannu da k'arfinta ta gaura mishi wani mari da k'arfi sosai. Dada dale tsaye saida ta zabura tare da rintse ido, da sauri ta matso gareta tana fad'in "A'a dan Allah karki sake dukanshi, ki k'yale shi zaiyi." Juyawa tayi ta kalleshi da niyyar magana, amma sai taga yana nan yanda yake babu abida ya sauya, saima ja da idonshi sukayi kamar zai kama da wuta, numfashinshi kuma ya sake canzawa, d'aukar jakarshi tayi ta kama hannunshi tana fad'in "Muje ciki ka ji, bana son taurin kai da kafiya Amjad." Fizge hannunshi yayi da k'arfi ya bud'a baki zaiyi magana, amma kuma gam ya kasa sai wannan hucin da yake, matsowa Faduma ta sake yi tana fad'in "Dan ubanka ni kake kallo haka? Ni kake wa wannan kallon? To idan ma mayu ne dangin uban naka ku ci kanku, zaka b'ace min daga nan ko saina tsiyaye maka ido?" Da sauri Dada ta sake tareta tana fad'in "Haba Faduma ki daina mana." A harzuk'e ta nuna shi tace "Ki fad'a masa ya daina kallona haka nima." Kama hannunshi ta sake yi amma ya cije sosai, aje jakarshi tayi k'asa tana fad'in "Kai ni zaka nunawa zuciyar tubawa? Bari ka gani d'an kutumar uban nan." Cak ta d'aukeshi da k'arfin tsiya ta sab'a a kafad'a, leb'enshi da yake cijewa ne yaji ya samu kafad'ar da zai ciza, ba shiri kuwa ya gantsarawa Dada cizon nan a kafad'a, da wata irin zabura ta direshi k'asa ya fad'o tana rik'e kafad'arta da cewa "Na shiga uku, ya cije ni! Kafad'ata." Da sauri Faduma ta matso tana zuwa ta sake d'auke fuskarshi da wani gigitaccen mari, kafin ya ankara ta murd'e kunnenshi tace "Kana lafiya Amjad? Ni ce zaka wa tsayayya? Ni zaka wa iskanci? Akan banzan ubanka ne zaka cizar min uwa? Akan mutumin da bai son ka ba sai kwanakin da basu fi goma sha ba, Amjad duk abin nan da kake saboda ba'a kai ka wurin shi bane? Kai in banda hauka ma irin naka da kasan waye shi da zaka yi gudun tseren ranka ne tsakaninka dashi, Amjad da kasan waye wannan mutumin da baka yarda ka kalli k'wayar idona ba kana min wannan kallon ba." Shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya, dafa kafad'arta tayi tace "Haba Faduma ya kike masa magana haka? Yaro ne fa, ki rabu dashi dan Allah." Kallonta tayi tana sako da hawaye har sun wanke mata fuska tace "Dada yaro ne? Yaro ne amma yasan ya titsiye ni akan maganar mahaifinshi, ki bari na fad'a masa waye uban nashi ko ya shiga hankali, dan ba zan lamunci wannan sakarcin ba, wallahi duk sanda ya sake min maganar mutumin nan a gidan nan saina karya yaron nan." Kallonshi tayi ta nuna kanta ta hanyar dafe k'irjinta tace "Ba dai ni kake ma wannan kallon ba? Kai ga mai zuciya ko? To kai ne ke haukan ka akan shi, shi ba son ka yake ba, dan a lokacin daya kamata ya rumgumeka shi gudun tsira yayi daga gareka, sanda kake buk'atarshi a lokacin ya barka saboda buk'atar duniya ta iyayenshi, sanda ni da kai muke neman tallafi nesantarmu yayi, kai ba iya soyayya bace kawai bai nuna maka ba, gaba d'aya ma bai yarda da kai bane a matsayin d'ansa, a bainin jama'a ya fad'a kao ba nasa bane bai yarda da kai ba, Amjad in zaka dawo hankalinka ka dawo, ba zan kasa bin umarnin iyayena akan cika burinka kai da mahaifinka ba, ka ji da kyau kuma ka kiyaye, kar ka sake min irin haka." D'aki ta shige ta zauna bakin gado dafe da goshinta, numfashi ta dinga saukewa tana rufe idonta tana girgiza kai, saida ta samu numfashinta ya dawo daidai, a hankali cikin muryar kuka da ban tausayi tace "Me yasa Tagur? Me yasa ka shigo rayuwata? Na rasa gano dalilin haka? Sai dai nasan komai da yake faruwa da sanin ubangiji, ta wata fuska kuma akwai dalilin da yasa Amjad ya zo duniya kafin aurenmu, amma Tagur me yasa ka k'i karb'ansa a matsayin d'a? Gashi har yanzu ina cikin tashin hankali da fargaba da rud'u a sanadiyar wautarka, har yanzu hankalina ya kasa kwanciya, ganin Amjad kullum yana sake jefa zuciyata cikin sark'ak'iyar damuwa, Allah ka nuna min ilimin dake cikin lamarina, Allah ka haska min abinda ke cikin duhu a game da ni da yaro na, Allah ka dubemu da idon rahama ka sauk'ak'a mana tsamarin dake cikin rayuwarmu." Dada ko da ta ga shihewarta ta juya ta kalleshi, kanshi k'asa sai shashek'a yayi kamar zai fashe, dafa kanshi tayi ta sauke ajiyar zuciya tace "Amjad, ka tausayawa mahaifiyarka mana, kasan irin k'alubalen data fuskanta a kan ka? Faduma saboda kai ne bata tare da iyayenta, a shekarunta kamata yayi ace tana kusa da mahaifiyarta tana karb'ar tarbiya da shawarwari akan rayuwa, amma kai ne ka nisanta ta da duk wannan, kuma mahaifinka shine silar haka Amjad, me yasa ba zaka tausasa mata ba? Idan kai ma ka fara bata tsoro da saka mata fargaban had'uwa da kai ta hanyar ritsata da wad'anan zafafan tambayoyin naka, ina tabbatar maka babu abinda zai hana mahaifiyarka hd'iye zuciya ta mutu, dan ba zata iya rayuwa a duniyar da mahaifinka ke raye ba kuma kai kana mara masa baya akan 'kudurinshi da bashi da tushe bare makama, duk da yaro ne kai shekarunka basu kai zantawa da kai akan muhimmiyar maganar nan ba, amma na yarda da k'wak'walwarka da tunaninka, zaka fahimci komai ka kuma bawa Ayyarka hak'uri akan b'ata mata rai da kayi." Juyawa tayi zata shiga d'aki ita ma ya rik'e hannunta, tsayawa tayi ta juyo ta kalleshi, cikin muryar kuka ya kalleta yace "Dada, da gaske Abana yace baya so na a baya?" Wani malalacin murmushi tayi ta jawo shi jikinta tace "Amjad bai fad'a da bakinsa ba, amma aikinsa ya nuna haka." A hankali yace "Kamar ya?" Wani murmushin ta sake yi tace "K'aramin misali! Me zaka iya cewa alak'ar dake tsakaninka da Ayyarka?" Cikin sanyin murya yace "Tana so na sosai, nima kuma ina son ta sosai." A hankali tace "To me yasa ka ce tana son ka? Ta tab'a nuna maka so d'in ne ka ganshi da idonka?" A hankali shima yace "A'a, ina ganewa ne saboda tana min komai, kuma ita na tashi ina gani a kusa dani sai kula ke." Wani murmushin ta sake yi tace "Kenan aikinta ne ya nuna maka haka?" Jinjina mata kai yayi alamar eh, ita ma jinjina kai tayi tace "Idan da Abanka yana son ka, me ya hana ace shine da ita suke tare da kai? Me yasa babu abinda ya tab'a maka da zai nuna yana son ka? Hasalima yaushe ne ya son da zamanka a duniyar nan? Amjad yaro ne kai sosai, ba zaka tab'a fahimtar abinda za'a nusar da kai ba, ba wai muna so dole sai mun nisantaku bane, amma dai zaifi kyau a yanzun kuyi nisa har sanda zaka fara fahimtar hankalin kan ka, dan rabaka da mahaifiyarka a yanzu ba abu bane da zai haifar da d'a mai ido ba." Sake k'amk'ameta yayi ya fashe da kuka yace "Dada bana son rabuda da Ayyata, ki be ki bata hak'uri ta yafe min, kar tayi hushi a kaina har ta zubar da hawaye." Da sauri ya d'ago ya kalleta yace "Dada na d'aga murya akan ta Ayyata? Dada kar na shiga cikin hushin Allah, a Alqur'ani ance kar mu ce musu uff kuma kar mu kyaresu, Dada dan Allah ki ce tayi hak'uri bana son shiga wuta, kije ki bata hak'uri kinji dada." Yanda yake jijjigata da kuka yana rok'onta saiya bata tausayi sosai, d'agoshi tayi a jikinta ta kalli fuskarshi tace "Ka ga Amjad, duk da tare muka rayu da ku a gidan nan, amma babu wanda ya tab'a shiga tsakaninka da Ayyarka, kaje da kanka ka bata hak'uri, tana ganinka zata hak'ura, amma idan nice sai nasha wuya." Kallonta yayi yace "Da gaske?" Jinjina masa kai tayi alamar eh, da gudu ya juya ya shiga d'akin, yana shiga ya same ta dafe da kanta idonta rintse, jin yanda aka shigo yasa ta d'aga kai ba tare da tunanin shi bane, ganinshi ya bata mamaki a lokacin kuma ya sata farin ciki, da sauri ya k'araso ya fad'a jikinta yana qale fashewa da kuka, cikin muryar kuka yace "Ayya kiyi hak'uri ki yafe min, kar kiyi hushi dani Ayya, Allah baya bawa mutum abinda yake so idan iyayenshi na hushi dashi, kuma Allah ya jera mai b'ata ran iyayensa a cikin manyan zunubai, sannan yana had'a hakk'in iyaye da hakk'inshi, a wurare da dama a cikin Alqur'ani Allah yana fad'an a bauta masa shi kad'ai, sannan a kyautatawa iyaye, Ayya kiyi hak'uri kinji ki daina kuka a kai na dan Allah." Cikin kukan ita ma ta k'amk'ame shi tace "Amjad ban tab'a hushi da kai ba, kana da zuciya wasu lokuta, kawai dai ta yau ne ta bani tsoro da kuma mamaki, ka daina kaji in baka so na rasa ka ko ka rasa ni." Jim ya rik'eta yana fad'in "Ba zan rasa ki ba Ayya, ba zaki rasa ni ba ke ma insha Allahu." Cikin muryar dariya tace "Har sai na tsufa?" Shima a yanayin da tayi magana yace "Har sai kin tsufa, kanki duk yayi fari." D'an dukan bayanshi tayi tace "Amjad bana son irin tsufan nan, ka rok'a min rayuwa mai albarka a wurin Allah, ba wai tara shekarun ba ko firgitaccen tsufa ba." Jinjina mata kai yayi yace "Amma ni dai ina so naga tsufanki Ayya, a lokacin ne zanyi iya k'ok'ari na wajen kulawa da ke kema kamar yanda kike kula dani a yanzu." D'agowa tayi ta kalli fuskarshi tace "Zanyi farin cikin ganin wannan lokaci Amjad, amma ka sani ba lallai sai na tsufa ba zaka anfane ni, ko a yanzu ma zaka iya yi ta hanyoyi da dama." Kallon idonta yayi yace "Wane hanyoyi ne Ayya?" Numfashi ta sauke tace "Misali idan na ce kayi to kayi da sauri inhar ba sab'on Allah bane, idan na nuna abinda nake so kayi shi ko da baka so a zuciyarka, idan na ce ka bari ma ka bari ko ranka bai so ba, ni kuma zanyi iya k'ok'ari na wajen ganin ban tauyeka ba ta hanyar d'ora maka nauye nauyen da zasu fi k'arfin zuciyarka ba." Fad'awa yayi jikinta cikin shagwab'a yace "Ina son ki Ayyata." Ita ma rumgumeshi tayi tace "Nima ina son ka oddo." Cikin taushin murya yace "Zanyi duk abinda kike so Ayya insha Allahu." "Allah ya yarda." Ta fad'a tana bubbuga bayanshi, Dada dake tsaye duk gabanta komai ya faru, da k'arfi ta buga hannayenta irin ta basu tsoron nan tana fad'in "Wuuuuf!" Da sauri suka d'aga suka kalleta, dariya sukayi ita ma dariyar tayi tace "Har kun shirya kenan? Wato dai ba za'a tab'a shiga tsakaninku ba." Dariya Faduma tayi tace "To Dada wane mahaukaci ne dama zai shiga tsakanin d'a da uwarsa?" Jinjina kai tayi tace "Gaskiya kam na gani yanzu ma na tabbatar." Mik'ewa tayi tace "Mu je mu k'arasa girkinmu." Dada ce tace "Ya kamata dai, tunda kinga wannan sarkin sarakan zuciyar yana gida sai cin abinci." Dariya duk sukayi sai shi daya kumburo baki yace "Abinda ma zan koma anjima da yamma." Kallonshi Faduma tayi tace "Me zaka je yi kuma? Yau laraba fa." Da sauri ya nufi k'ofa yana fad'in "Daga makaranta ne aka raba mana takardar gayyatar iyayen yara." D'auko takardar yayi ya bata ta karb'a ta duba, d'aga kafad'a tayi tace "Allah ya kaimu yamma lafiya." "Ameen." Suka fad'a shi da Dada. ______________ Ran shi a b'ace yau ma ya shigo saboda yaje makarantar dan duba Amjad sai kuma ya kasa ganinshi sai Dada ya ga ta fito tare dashi, sanin masifaffiya ce ta bakinshi yasa kawai bai bayyanar da kanshi ba bare ya musu magana, falon Hatimi ya wuce kai tsaye dan yunwa yake ji, ba sallama ya shiga ya zauna kan kujera, saida ta sauke wayarta daga kunne ta kalleshi tace "Tagur wace irin rayuwa ce haka ko sallama babu?" Turo baki yayi yace "Yunwa nake ji, me kuka dafa?" Wani shu'umin murmushi ta sakar masa tace "Yunwa kuma shine har da had'e fuska sai kace wani rago." Sake had'e fuskar yayi yana kumburo baki, tab'e baki tayi tace "Humm!" Juya kanta tayi zuwa d'akin da Husna ke ciki ta k'wala mata kira, da siririyar muryarta ta amsa da "Na'am Ayya." "Zo nan." Ta fad'a ita ma da k'arfi, jim kad'an ta fito daga d'akin, yanda yake zaune kan kujerar yasa daga gabanka ba zaka fahimci akwai mutum ba, dan ita daga baya ne ta fito daga d'akin shi kuma a gaba yake, girman kujerun yasa ba kowa zaka iya hango k'eyarsa ba idan ya zauna, saida ta zagayo ta tsaye kusan Hatimi tace "Kinga ki samo mishi abinda zai ci a madafa, yunwa yake ji." Da sauri ta kalli inda ta nuna mata, saida ta ji gabanta ya fad'i, ba wai dan ta ganshi ba sai dan rigar dake jikinta, doguwa ce iya gwiwarta mai siraren hannaye, ta mata kyau a jikinta kasancewarta tana da k'ira mai kyau kuma ba wata mai kumari ba, haka kuma manyan kitson dake kanta sabo dashi shi ma duk ya sauka akan wuyanta, da sauri ta kalli Hatimi tace "To Ayya." Juyawa tayi da sauri ta koma d'akin, ta gefen ido ya bita da kallo, tab'e baki yayi irin babu wani abu daya dame shi, sai dai kuma har k'asan zuciyarshi ya yarda yarinyar bata da wata makusa, kawai dai *abar rai da abinda yake so ne*, idan ma akwai wata makusar bai wuce yanda ita ke shiga jikinshi ba sai kuma rashin kakkauran jikinta, dan gaskiya shi kam yana son mace yar dumur dumur (like Fadumarka ba馃槑, saura naji an min caaa a kai). Kallon Hatimi yayi yace "Ayya ina Ridwan?" Saida ta duba wayarta tace "Eh yau kasan laraba ce suna tashi k'arfe 01:00, da sauran lokaci ai." Bai ce komai ba har Hisna ta dawo ta kawo masa cr猫me da cips, har ta kawo lemu ya mata wani wawan kallo cikin tsawa tsawa yace "Ke! D'auke wannan abun, had'o min shayi." Da sauri ta d'auke lemun ta juya jikinta na b'ari, dan har yanzu a firgice take da lamarinshi a ranar daya mata tsawar nan da saida tayi fitsari a wando tun kafin ta shigo d'aki, shiyasa yanzu duk sai taji bata son ma su had'u, tsoro kawai yake bata, ta so ta koma gida mahaifiyarta tace kar ta kuskura ta zauna har ta ga me zai faru, ita ma kuma dama har yanzu tana son shi, zuciyarshi dai ce ke mugun sa mata shakka a kan shi. Tana daf da shiga madafar taji yace "Saura kuma ki saka madara a ciki." Juyowa tayi ganin har ya d'auke kanshi sai kawai ta shige ciki, shayi na musamman ta had'a masa ta kawo, tunda ta aje ya kalli kofin yanda yake tururi sai k'amshi ke tashi, karanfani da citta ga k'amshin anana da kuma k'amshin sugar mai plavour a ciki na fraise, hakan ya tilasta mishi d'aukar kofin ya d'an kurb'a duk da zafin dake akwai, yanda ya ratsa mak'ogwaronshi ya fad'a cikinshi da babu komai a ciki yasa shi lumshe ido, yayi dad'i sosai da zai iya sa wa mutum yasha shi a haka ma, kallonta yayi wacce ita ma take tsaye gabanshi da tunanin ko zai ce wani abu, saida ya sake kallonta daga k'asa har sama ya ga ta d'aura zane akai ta saka hijab, tab'e baki ya sake yi ya mata alama da ido ta b'ace a nan. Da sauri ta juya zata bar wurin Hatimi dake kallonsu tace "Tsaya ke." Kallonshi tayi tace "Tagur, baka iya godiya bane idan an maka abu?" Kallonta yayi ya lumshe ido, a hankali ya bud'e ya kalli Husna yace "Gode maki." Duk da a tsorace take saida ta mishi murmushi na jin wata sabuwar kalar godiya, a ranta take fad'in "Kai guy nan masifa ne, a haka nake son ka wallahi ko zaka kashe ni." A zahiri kuma cikin taushin murya tace "Ba komai, girmanka ya wuce haka a wurina, idan kana buk'atar wani abu ma zaka iya kirana." D'aga ido yayi ya kalleta, kamar da biyu ta fad'i maganar, amma saiya basar ya d'auke kanshi ya ci gaba da abinda yake. D'akin Rahila ta wuce dan fad'a mata abinda ya faru cikin farin ciki. ______________ K'arfe 04:30 suka fito daga gida, dake yau babu karatu sai ta shirya shi cikin shadda kalar ruwan gold d'inki mai kyau ya amshi jikinshi, bud'e motar sukayi suka shiga suka zauna, kallon juna sukayi hakan yasa Amjad daga hannaye ya karanto musu addua'r hawa abun hawa " 亘爻賲 賱賱賴貙 丕賱丨賲丿 賱賱賴 (爻亘丨賳 丕賱匕賷 爻禺乇 賱賳丕 賴匕丕 賵賲丕 賰賳丕 賱賴 賲賯乇 賳賷賳 貙 賵 廿賳丕 廿賱賶 乇亘賳丕 丕賲賳賯賱亘賵賳) 丕賱丨賲丿 賱賱賴貙 丕賱丨賲丿 賱賱賴貙 丕賱丨賲丿 賱賱賴貙 丕賱賱賴 兀 賰亘乇貙 賱賱賴 丕 賰亘乇貙 賱賱賴 丕賰亘乇貙 爻亘丨丕賳賰 丕賱賱賴賲 廿賳賷 馗賱賲鬲 賳賮爻賷 賮丕睾賮乇 賱賷 賮廿賳賴 賱丕 賷睾賮乇 丕賱匕賳賵亘 廿賱丕 兀賳鬲." Yana gamawa ta kalleshi da murmushi tace "Yau ga ka a motarka." Dariya yayi yace "Ayya motarki ce ba tawa ba." Gwalo ta masa tace "Kai aba wa bani ba, kana ina sanda nima na ci nawa kyautar?" Murmushi yayi kawai inda ta juya kan motar suka d'auki titi. _____________ Ko da yaran suka shigo a tsakar gidan suka samu Umma kan kujera zaune da carbi a hannunta da kuma waya, gurinta suka nufa sai mai adaidaitarsu a baya, da girmamawa ya gaisheta ta amsa a tsanake, takarda ya mik'a mata yace "Gashi daga makarantarsu, wai da k'arfe 04:40 iyayen yara su je." Saida ta fara amsa mishi da ido kafin tace "Insha Allah." Juyawa yayi ya fita, kallon yaran tayi ta bawa Izzadeen tace "Ka kaiwa mamanku, sai ka fad'a mata ta kira Abanku ta sanar dashi, idan baya da dama kuma sai a kira Mukhtar tunda shi ya saba zuwa dama." Da sauri suka juya suka nufi b'angaren na su, suna shiga da hayaniyarsu tasa ta d'ago kai, takardar Izzadeen ya mik'a mata ya fad'i abinda Umma ta fad'a, cikin jin haushi tayi jifa da takardar tace "Ba zan kirashi d'in ba, ita me ya hana ta kira?" K'wafa tayi ta mik'e ta shige d'aki ranta a b'ace tun batun maganar jiya, bata sake sanin me ke faruwa ba ita dai ta barsu daga su sai falon, sun ci abinci? Sun cire kayansu? Bacci suke? Duk bata sani ba ita dai har bacci ma ya d'auketa bayan ta gama da wayarta. Saida suka gama wasarsu a d'akin da yunwa ta fara garasu suka koma wajen Umma, anan suka ci abinci har suka d'anyi bacci, ko da akayi sallah la'asar Umma ta tashe su tasa Salima ta shiryasu, zaman jiran zuwan Hasheer ko Mukhtar tayi ta ga wanda zai tafi dasu, amma shiru babu ko d'aya har k'arfe 04:55. Kiran Hasheer tayi da a lokacin yake tsaye yana duba yanda ake zuba mai na girki a manyan bududuwa, yana d'auka da hanzari cikin nutsuwa tace "Hasheer kar dai ka manta da maganar kai yaran nan makaranta?" A rashin fahimta yace "Umma makaranta kuma? Amma ai yau laraba." D'an dafe goshinta tayi tace "Kashh, kar dai Saudat bata kira ka ba? Yara fa ake gayyatar iyayensu a makaranta, kuma gashi har an haura minti sha biyar a lokacin da suka bayar." Kallon agogon hannunshi yayi bak'a ta fata, d'an k'aramin tsaki yayi yace "Bata fad'a min ba Umma, amma gani nan zuwa." Datse kiran tayi shima ya zura wayar aljihu da sassarfa ya nufi inda motarshi take. Gugu yayi sosai har ya isa gidan, a k'ofar ya tsaya yasa mai gadi ya fito mishi da su suka wuce, duk da akwai tafiya amma dake gudu yake sai gasu a d'an lokaci sun iso, har ciki suka shiga tare da yaran a mota. *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 17:17 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _38_ Suna tsayawa iyayen yara da dama na fitowa daga wani aji da aka tattauna dasu, ganin haka yasa duk yaran dake wasa a wurin kowa ya je ga mahaifinshi, akwai mata sai dai basu fi biyar zuwa shida ba, hakan bai sa taji komai a ranta ba, tana jin alfahari duk sanda ta tsaya kan lamarin yaronta, dan haka bata damuwa ko jin kunya indai akan abinda ya shafe shi ne. Inda ya aje motar nesa da ita ne, amma dake zuciya da harbe harbe har ta harbo mishi wata kibiya data tilasta mishi kallon b'angaren, ganinta kuma ya sanyaya zuciyarshi had'e da sakin murmushin da bai shirya masa ba, ga wani kyakyawan canji daya gani tare da ita, duk da zaune take zai iya fahimtar riga da siket ne ko kuma zane mai shap d'in siket, hijab ne kalar atamfar dake jikinta mai hannaye tana danna wayarta, sai dai kamar kullum babu wata kwalliya ta azo a gani a fuskarta, kallonsu Izzadeen yayi yace "Ku jira ina zuwa." Ko a jikinsu sai ma nufa wajen gungun wasu yara da sukayi, cikin kyakyawan takunshi na nutsuwa da k'arfi k'arfi ya k'arasa, tana zaune kansa sadde tana latsa waya har ya tsaya gefenta, zuba hannayenshi ya fara yi aljihu ya sauke numfashi, cikin sanyayyan murya yace "Barka Hajaj." Da sauri ta d'aga kanta ta kalleshi, duk da taji tsayawar mutum a kan ta amma bata d'auka shi bane, mamaki ne ya d'an kamata a karon farko, sai kuma ta sunkuyar da kanta k'asa ta mayar a waya? D'an cije leb'e yayi tare da cewa "Baki so muka sake had'uwa ba ko? Kiyi hak'uri, k'addara ce ta had'amu." Kallonshi ta sake yi, sai kawai ta murmusa ta sauke ajiyar zuciya tace "Ni dai ban fad'a ba." Da alamar zolaya yace "Kenan baki so gani na bane?" Yar dariya tayi da har hak'oranta suka bayyana, girgiza kai tayi kawai ba tace komai ba, ajiyar zuciya shi ma ya sauke yace "Zaki iya taimaka min dan Allah?" Saida ta had'e fuskarta tace "Wane irin taimako?" Hannunshi d'aya ya ciro daga aljihu ya shafi tarin sumarshi yace "Na zo a makare, hakan yasa ban san me aka tattauna akai ba, zaki iya labarta min komai daya faru?" Wani mamaki ne ya kamata ta bud'e baki tana kallonshi, labarta masa? Wai har ya ga damarta dayawa haka? Ita ta zauna tana fad'a mishi dogon zance haka? Lallai! Mik'ewa tayi tana sake rik'e jakar hannunta, za tayi magana kuma yan k'adangarun dake shawagi a wurin suka nufo kansu, d'an matsawa tayi kusanshi tare da basarwa irin kar ya gane d'in nan. Binsu yayi da kallo ya kuma kalli fuskarta, gimtse murmushin shi yayi ya had'e shi, kallonta yayi yace "Ba zaki iya taimaka min ba?" Cikin nutsuwa ta shiga fad'in "Kayi hak'uri ina sauri ne, amma ga ofishin directeur (principal) can ka k'arasa, zaka ji komai da aka tattauna." Cikin shawagin k'adangarun nan wani ya biyo d'an uwanshi da gudu, a tsiyace tayi bayan Hasheer tana zumduma ihu da daka tsalle, Hasheer da bai motsa ba kawai ya fashe da dariya, duk'ewa yayi yana rik'e ciki tsabar dariya, haushin daya bata ne yasa ta fitowa daga bayanshi tana waigawa, saida ta tabbatar babu komai ta kalleshi tana galla masa harara tace "Miye na dariya kuma?" D'agowa yayi yana tsayar da dariyar yace "Ba komai." Turo baki tayi tana gunguni, saida ya sake gimtse bakinshi yana son yin dariya, dan gaskiya ta sa shi nishad'i sosai, a hankali girgiza kai a ranshi yace "Mata, mata! Ha yallah." Kamar ta ji abinda ya fad'a sai kuwa ta sake had'e fuska tace "Ba fa tsoronsa nake ba, kawai bana so na kashe su ne a gabanka." Lumshe ido yayi cikin fuska ta kamala da manyantaka yace "Ai na gani a idonki." Kallon ban yarda da kai ba ta masa sannan ta juya wajen da su Amjad suke tace "Zamu tafi, sai anjima." Lumshe ido yayi alamar to, dan gaskiya ba tafiyarta yake so ba, da zai yiwu sai ya d'auketa yasa aljihu ta kasance duk inda zai tafi tana tare dashi, gashi yace ma kawunshi zasu je gida, shi kuma baya so ta ga zuwanshi can yayi yawa ko taga zak'ewarshi, hakan yasa shi binsu da kallo har Amjad ya zo suka gaisa, har zai juya ya tafi ya rik'e hannunshi yace "Amjad ka iya rik'e sirri?" Jinjina kai yayi yana murmushi yace "Na iya, musamman ma idan alk'awari nayi zan rik'e." Jinjina kai yayi ya shafa kanshi yace "To ka min alk'awarin ba zaka bari kowa yaji ba?" Jinjina kai yayi shima yace "Nayi kawu." Saida ya d'an lashe leb'enshi sannan yace "Akwai wani kawuna da nake so na kaishi gidanku zai had'u da aunty, amma gaskiya mahaifiyarka tana tsoratani, bana so ta ga na cika zuwa gidan." Dariya Amjad yayi yace "Ayyata ce zakanya ce, ta firgita zaki." Dariya yaron ya bashi har saida ya jawo shi jikinshi suna k'yalk'yala dariya, cikin sanyin murya yace "To idan baka so ta gane ka tafi dani mana." Da sauri ya kalleshi da mamaki yace "Kamar ya? Ban gane ba?" Cikin dariya yace "Ayyata bata saba yin nesa dani ba, da ka tafi dani kaga kana da dalili mai k'arfi na zuwa gidan." Hancin shi yaja da fara'a yace "Yaro mai basira." Cike da k'wanbo na jin dad'i yace "Kan Ayyata ne na d'auko." Da birgewa sosai yaji kamar yace yaron nasa ne har ransa, yana da shiga rai sosai da birgewa, gashi babu wannan wautar da ake cewa ta d'an fari, kuma bai da mahaukaciyar k'uruciya, rik'e hannunshi yayi yace "To ya zamuyi ta barka ka tafi?" Raba hannunsu yayi nufi inda Faduma ke tafiyarta cikin nutsuwa zata k'arasa ga mota yace "Biyo ni muje." Bin bayanshi yayi suka nufeta, suna zuwa Amjad yasa kukan shagwab'a ya rik'e hijab d'inta yana fad'in "Ayya, Ayyata ce wannan." Juyowa tayi ta tsaya tana kallonshi, tana kallonshi ita ma ta turo baki cikin shagwab'a tace "Oddo na ne, ya akayi?" Sake langab'ar da kai yayi sosai yace "To ba abokaina bane suke min dariya wai ban tab'a zuwa gidansu ba, shine nima nace sai na tafi yanzu." Yatsina fuska tayi alamar zancen bai shigeta ba, satar kallon Hasheer tayi sai kuma ta kalleshi tace "Amma me yasa zaka ce musu yanzu? Ka bari har ranar da babu karatu sai na kai ka da kaina ka gaishe da Ayya." Wani luuuu yayi kamar zaiyi kwance a jikinta yana sake turo baki gaba, Hasheer ne ya katse mata tunanin da take yi na ta barshi ko ta tafi da abun ta ta hanyar cewa "Na miki alk'awarin dawo miki dashi lafiya." Tsamm tayi ta zuba mishi ido kamar tana karantarshi, cikin sauk'i zata iya cewa kamar mutanen suna neman kusanci da ita ne, to amma saboda me? Wannan ne kuma zai iya sa ta kasa sakewa dasu musamman ta lura a na son rab'ar yaronta Sosai, bata son yin sake da lamarin daya dangance shi. Lura da yayi shima yasa shi saurin cewa "Karki damu, idan baki amince ba zaku iya tafiya." Juyawa yayi cikin takon k'asaita da sam baya nuna b'acin rai tare dashi ya nufi ofishin directeur d'in, kallon Amjad tayi da yace "Ayya me yasa? Dubi fa su jiya har gidanmu suka zo da kakarsu, Ayya suna da kirki fa mutanen." Wani murmushi tayi ta shafi kumatunshi tace "Yaro ne kai Amjad." Hannunshi ta kama suka nufi mota, tsayar dashi tayi gabanta ta bud'e mazauninta ta zauna amma k'afafunta a waje, bud'a jakarta tayi cikin dubara ba tare data bari ya gani ba, wani k'aramin micro ta ciro na d'aukar sauti da tafiya da na'urar sadarwa, saida ta d'an danna wani bak'in buton ta jawo Amjad ta rumgume, cikin dubara ta saka mishi micro d'in a aljihun gaban rigarshi sannan ta d'ago ta kalleshi, murmushi ta masa tace "Ka je to ku tafi, amma karka yarda ka wuce sallah isha'i, ka ji da kyau?" Da murna sosai ya sake rumgumeta, tana kallo ya tafi cikin nutsuwa har ya isa wajen su Izzadeen, saka k'afafunta tayi ta shiga taja k'ofar ta rufe, wayarta ta ciro cikin k'warewa ta shiga app d'in maps ta daidaita sadarwar ta hanyar jona micro d'in da wayarta yanda zai nuna mata duk inda yaronta zai shiga da kuma duk wani abu da za'a tattauna dashi ko wanda ke kusa dashi. Sanda Hasheer ya same shi yaji dad'i sosai, amma sanda suka d'auki hanyar komawa gida sai ya fara tunanin wurin Umma ko wurin Saudat zai sauke yaro? A bayyane ya furta "Umma dai." _______________ Ko da taje gida Dada ke fad'a mata "Bayan tafiyarki fa Aminu ya zo nan tare da wani abokinshi." Kallonta tayi da rashin damuwa akan zancen tace "Shi kuma mz ya zo yi? Bai kirani ba ai." Murmushi Dada tayi tace "Ba wajenki ya zo ba dama, ni ya zo gani kuma yace ke kika bashi dama." Shiru tayi sai ma danna wayarta da tayi tana sauraron duk wani shirme na yara da su Amjad ke yi da abun sauraronta a kunne, ganin bata ce komai ba Dada tace "Na bashi dama ni dai, kuma har na bashi bayanin komai akan iyayenki, ya tabbatar min da jibi jibin nan zasu tafi dan gabatar da kansu." "Uhumm!" Ta fad'a tana had'e labb'anta wuri d'aya, dariya Dada ta sake yi tace "Kinsan wani abu ma? Wallahi yace yana so bayan sallah k'arama ayi bikinku." Da sauri ta kalleta tace "Wata uku fa?" Hararanta tayi tace "Bai kai uku ba." Tab'e baki tayi tace "A gaskiya ya min kad'an, akwai abubuwan da nake hari kafin lokacin." "Kamar me fa?" Ta fad'a tana kafeta da ido, saida ta cire abun sauraron kunnenta d'aya tace "Dada akwai abubuwa dayawa, zan fad'a miki daga baya." Had'e rai tayi tace "Kinga Faduma dakata, wallahi ko ba kya so sai anyi auren nan, wai ya kike nema ki zama wata k'aramar yarinya ne? Sai kiyi ta nema kina zillewa aure." Kallonta tayi tace "Dada ba fa zillewa nake ba, zanyi amma ba yanzu ba, lokacin da yake buk'ata ne ni bai min ba." Tab'e baki tayi tace "Sai dai kiyi hak'uri kam, dan har na kira Hadizey na fad'a mata yanda ake ciki." Turo baki tayi tana fad'in "Gaskiya ni dai ba yanzu ba." "To sai dai ki koma gaban iyayenki Faduma, dan indai anan zaki zauna to tabbas za ayi aurenki a lokacin da Aminu ke so, idan na matsa miki kuma zaki ga na takura miki ne." Kallonta tayi da mamaki, tunda suke da ita bata tab'a cewa ta koma wurinsu ba sai yau, dan haka ta had'e abinda ke zuciyarta tace "Shikenan Dada na amince, amma ki sani zama tare da ke ai yanzu muka fara, tunda zanyi aure anan nima." Komai ba tace ba har ita ma shiga kasa kunne tana sauraron hirar da suke da alama suna cikin mota ne, duk da akwai hayaniya da motsin kayan jikin Amjad bai hanata jin abinda ke faruwa ba. ______________ Ai kuwa Umma tayi farin cikin ganinshi sosai, haka suka tarbeshi da kulawa kamar wani babban mutum, sai dai kuma wani kallo na tamtama da son yin magana ne Umma ta dinga jin Hasheer dashi, har saida ya d'an fara tsarguwa da hakan amma bai nuna ba, saida ya kalli su Izzadeen yace "Kuje sama d'akin auntynku Salima ta saka muku kallo." Da gudu suka tafi sai shi daya tafi a nutse, cikin kaushin murya yace "Ba zakuyi tafiya ba? Ku ga d'an uwanku fa tafiya yake." Tafiyar sukayi da sauri suka haye sama, kallon Umma yayi dake murmushi yace "Umma lafiya ko? Da wata matsala ne?" Girgiza kai tayi tana yar dariya tace "Ba komai, kasan da safe nake son tafiyar nan dana fad'a maka." Jinjina kai yayi yace "Ba komai Umm, insha Allahu zuwa dare idan na fita zan ciro muku ticket d'in." Ita ma jinjina kan tayi kawai, mik'ewa yayi ya fita dan magriba na gabatowa. Haka Umma dasu Halima suka zauna da yaran, babban abinda ya birgesu a tare da yaron yanda ana kwad'a kiran sallah ya fito daga d'akin, alwala yayi tare da yaran suka tafi masallacin dake jikin gidan. Shima saida yayi sallah ya dawo gidan, tare da yaran suka shiga b'angaren, tunda suka shiga falon ranshi ya fara b'acewa, shi bai ma san daya furta "Wai uban wa ma yake siyo mata salade d'in nan ne?" Kallonshi duk yaran sukayi sai kawai ya d'auke kai, sake kallonta yayi ta baje robobi a gabanta tsakar d'akin tana gyaran salade d'in tana kallo, riga ce jikinta marar hannaye da siket bai wuce gwiwarta ba, kallo d'aya ta musu ta d'auke kai, yaran ne suka k'arasa gareta sai Amjad daya durk'usa har k'asa cikin sanyin murya yace "Ina wuni Ayya?" Kallonshi tayi tace "Lafiya lau." Su Izzadeen ta kalla tace "Daga ina kuke?" Sharfudeen ne yace "Masallaci muka tafi." "Sallah kukayi?" Ta tambayeshi, da farin ciki suka amsa mata da eh, sake kallon Amjad tayi tace "Waye wannan?" Izzadeen ne tace "Mama shine wanda muka je gidansu fa jiya, mamanshi ma..." D'aga mishi hannu tayi alamar yayi shiru, mik'ewa tayi da sauri ta bi bayan Hasheer da tuni ya shige ciki, tana tura k'ofar d'akin yana d'aura towel tamau a kunkuminshi, da kallo ya bita har ta k'araso kusanshi saboda ganin yanda ta wani shigo kamar an tsorata ta, gabanshi ta tsaya a fad'ace tace "Wai miye alak'arka da yaron can da kuma uwarshi? Ina uban shine da bana jin ana sako shi a magana?" Kallonta kawai yake, hannye biyu yasa ya dafe k'ugunshi, cikin nutsuwa da rashin son hayaniya yace "Saudat." A tsaitsaye ta amsa da "Ina jinka." Saida ya lumshe ido ya bud'e yace "Ki daina nema na da fitina, kinji ko?" Sauke hannayenshi yayi daga k'ugunshi ya nufi ban d'aki, da sauri ta bi bayanshi ta zagaya hannayenta ta cabki k'ugunshi hakan yasa ta kwanta a bayanshi, cikin tausasa murya tace "Me yasa baka son tsayawa muyi magana, rabin rai na bana son abinda zai rabani da kai." Hannu yasa ya kwance zoben data mishi a k'ugu da hannayenta ya juyo yana kallonta, tallabo fuskarta yayi yana kallon k'wayar idonta, cikin nutsuwa yace "Rabin rai na, ba sauraronki bane bana son yi, magana ne dake wasu lokuta ke hassala ni, kuma kin.." Bai gama fad'a ba tayi saurin fizge kanta daga gareshi ta matsa gefe dashi ta duk'e, amai ne kawai tayi ya taho mata ba zato, hankali tashe ya sunkuya shima yana tambayarta lafiya? Bata iya mishi magana ba saida ta gama kakarinta, taimaka mata yayi ta mik'e suka shiga bayi, sanin tun wankan safe bata sake wani ba kawai yasa shi cire mata kayan, ruwa ya sakar musu yana kallon fuskarta yace "Baki da lafiya ne dama?" Girgiza kai tayi tana yatsina fuska, lumshe ido yayi ya tofar da ruwan da suka shiga bakinshi yace "Ciki ne da ke?" Da sauri ta kalleshi da manyan idonta, k'asa tayi da kanta tace "Ni ban sani ba." D'an murmushi yayi kawai yace "Insha Allah zaki haife cikin nan a sabon gidanmu, ina ji a jikina gidan nan zai zama matattarar iyalina ne, zai zama kwanciyar hankalina insha Allah." Kallonshi tayi da ido kawai ba tace komai ba, ba zata yarda ba sai likita an tabbatar mata, in shine kam an gama da ita shikenan, zai kuma ga tashin hankali. Da towel ta fito a jikinta haka shima, shiryawa yayi shi kam a tsanake cikin d'inkin shadda mai kyau, wayar da taji yayi da kawu *Abdallah* kawai ta kwantar mata da hankali da taji yace ya zo gida ya same shi sai su wuce, bata tab'a tunanin wani abu mai kama da soyayya zai iya had'ashi da kawun nashi ba, duk da Abdallah shine auta a duk gidan baban su Hasheer, gaba d'aya bai fi talatin da shida zuwa da bakwai ba, dan tare da Hasheer ma sukayi wasar k'asa, shiyasa suke ganewa juna sosai, har ya gama shiryawa ya fita tana d'akin, bayan fitarsu a falon ita kuma ta shiga d'akinta ta canza kaya. A wajen Umma suka samu lafiyayyen girki suka ci suka k'oshi, anan Abdallah ya same su, shi ma k'asa ya zauna inda suke yana kallon Umma yace "Hajia ya kike? Ya fama da mu da yaranmu?" Murmushi tayi tace "Ana ta fama kam, ya gaurancin?" Saida ya gyara zamanshi yace "Hajia gauranci ya kusa karewa fa, ki zuba ido ki gani." D'an tsaki taja tace "Abdallah wai baka jin kunya kai idan kana yawo a cikin gari?" Dariya Hasheer yayi ya kalleshi yace "Kuma Umma a haka fa wai shi sai budurwa yake so, ni a gani na wannan tuzurun sai bazawara." Harara ya dalla masa yace "Allah Hasheer zan raba hanya da kai, tunda dai ba k'aunata kake ba, madadin ka tayani samun wacce nima zan bud'e da kaina, shine sai min fatan ragowar..." Da sauri Hasheer "Ehgyhem ehgyhem." Gyaran muryar da yayi ne ya ankarar dashi yayi shiru, kallonshi yayi yace "Shikenan bari mu fita." Haka suka idar suka tashi, zasu tafi saida su Izzadeen suka so a tafi dasu amma ya k'i, haka sukayi ta d'aga mishi hannu har suka b'ace musu da gani. *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 17:17 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _39_ Saida suka fara yin sallah isha'i a hanya kafin suka tsaya a k'ofar transa mall, Amjad kam duk son shi da ice cream yau an nuna mishi k'arshenshi, dan kala kala daga na k'aramar roba da manya haka Hasheer ya siya mishi, chocolat kam leda leda ya siya mishi su, komai sai dai ya d'aukar mishi gaba d'aya kwalinshi ko ledarshi, shi dai kamar zaiyi kuka yace "Kawu ya isa haka, Ayya fa zata min fad'a, kuma duk rabesu zatayi wa mak'wabta." Ko kulashi baiyi ba yace "Ai aiki ne mai kyau za tayi." Bai k'ara cewa komai ba har suka gama suka biya kud'in masu yawan gaske kafin suka tafi, basu sake tsayawa ko ina ba sai a k'ofar gidan suka tsaya Amjad ya fito, dafa kanshi Hasheer yayi yace "Ka ce k'aramar kakarka ta zo." Da murmushi ya jinjina kai ya juya ya shiga ciki, da wasu kayan a hannu har sun fi k'arfinshi, yana shiga falon da suke zaune ya zube kayan yana sauke numfarfashi, Dada ce tace "Oga har ka dawo? Wannan kayan fa?" Kallonta yayi yace "Masoyiyar ana magana a waje." Da mamaki tace "Da ni kuma? Waye?" D'aga kafad'a yayi yace "Uhum! Nima ban sani ba." Nuna shi tayi da yatsa tace "Kai ban son iskanci, ni wa zai zo nemana yanzu bai sanar dani ba?" Kallonta yayi yace "To wai k'arya zan miki?" "To ka wuce k'aryar ne?". Ta fad'a tana kallonshi sama da k'asa, dariya Faduma tayi da sai yanzu ta cire abun sauraronta da gasgata abinda Amjad ya fad'a cewa mutanen kirki ne, bata ji wani abu da yasa ranta ya sosu ba, bata ji wata kalma da bata mata dad'i ba, sannan yaronta bai yada abinda duk take fad'a masa ba, tayi murna sosai da haka kam, kallon Dada tayi tace "To uwata kije mana ki gani, ni da nake fata ki gama daidaita komai sai a had'a aurena da naki?" Dariya tayi tana murmushi tace "Faduma Allah ya amsa mana." Dariya Faduma tayi tace "Lallai Dadata aure kike so wallahi, yanzu kin shirya aure a d'an lokacin nan?" Tsaki tayu ta mik'e tana yafa gyalenta kan riga da siket d'inta tana fad'in "Shashashar banza, ke ban ci ace kin ban kyauta ba na zaman nan da nayi haka, rashin miji kike ganin abu ne mai sauk'i? Faduma dan baki d'and'ani rayuwar bane." Ita dai murmushi kawai ta dinga dokawa suna kallo har ta fita, kallon Amjad tayi tace "Wa ya kawo ka?" Saida ya matsa kusa da ita yace "Abbansu Izz." "Kuma shi yace ka kira Dada?" D'aga kai yayi alamar eh, wani suka taji a zuciyarta da k'arfin gaske, wanda lokaci d'aya ta d'orashi a mizanin farin cikin samun shi ne take taya Dada, zata so hasashenta ya zama gaskiya, zatayi farin ciki fiye da kowa, zatayi murna ko ba komai ta samu babban gida kuma gidan dattawa, kayan daya shigo dasu ta jawo ta fara dubawa tana zaro ido, sai ma da yace "Ayya wanda zan iya d'aukowa ne fa wannan, sauran na mota." Girgiza kai tayi ba tace komai ba, sai a ranta take ayyana "Yanzu shi saurayin Dadata ne, kamar uba yake gareni ai." Wani murmushi ta saki tana sake fad'in "Shine dalilin da yasa yake neman kusanci dani, ashe iri ya gani yana so kuma ya tabbatar zai samu hayewa ne idan muka jefa mishi k'uri'a." Amjad dai na sauraronta bai ce komai ba, dan ta haneshi da saka baki a duk maganar da bata shafeshi ba ko kuma aka nemi jin wani abu daga gare shi ko da ma akan shi ake tattaunawa. A waje kuwa Dada na fita su Hasheer suka zuba mata ido, dake sun aje motar kusa da gidansu Mama, hakan yasa akwai kusan tako goma kafin ta iso garesu, dama duk a tsaye suke sun rumgume hannaye, Abdallah ne ya sakar mata ido yana kallo, cikin sub'utar baki yace "Kaga tafiya kamar wahainiya." Da sauri ya kalli Hasheer yace "Yi hak'uri d'ana, karka d'auka ina son budurwarka ne." Murmushi yayi yace "Karka damu k'aramin uba, ba ita bace wannan." Da sauri yace "To wacece wannan?" Dada na k'arasowa shi kuma yana fad'in "K'awarta ce." "Assalama alaikum." Ta fad'a da zuwanta, cikin nutsuwa Hasheer ya amsa mata, amma Abdallah hankalinshi na kan fuskarta, gaisawa sukayi sosai dashi har tana fad'a mishi tayi mamaki data ganshi, d'an satar kallon Abdallah tayi dake kallonta ta harareshi, ganin ta harareshi yasa shi cewa "Yan mata dan Allah ya sunanki?" Yatsina fuska tayi ta kalleshi ta d'auke kai tana jan d'an tsaki, kallon Hasheer tayi tana fad'in "Allah yasa dai lafiya?" Katsal Abdallah yace "Lafiya lau yan mata, ina k'awartaki ne?" Kallonshi tayi cike da jin haushi tace "Malam ba sunana yan mata ba." "To me sunanki?" Ya fad'a yana k'ureta da kallo, d'an jujjuya idonta tayi tace "Ban sani ba." Cike da zalama shima yace "To yan mata in sake tambayarki?" Da sauri ta kalleshi tace "Na ce maka ba sunana yan mata ba ko." "To miye matsalarki idan kin fad'a min sunanki? Ba zan daina kiranki yan matan ba to." Ya fad'a har da murgud'a baki, gyara tsayuwarta tayi dan ya kaita bango, dalilin Hasheer ne take shareshi fa dama, a hassale tace "To ba zan fad'a ba, kuma karka k'ara kirana yan mata, dan ni ba yan mata bace ehe." "To tsohuwa ce?" Ta fad'a har da hararenta, ita ma da hararar tace "Ban sani ba." Nunata yayi yace "To wai ko baki da suna ne?" "To ka saka min mana, kaji mutum zaka isheni da jaraba, Allah ka sake min magana saina mareka." Da sauri suka kalli juna da Hasheer dake ta gaggab'a dariya a b'oye, matsawa yayi kusanta yana nuna kanshi da cewa "Ke ni ne zaki mara! Lallai yarinyar nan akwai fitsara, yanzu ki kalli fuskata ki ce zaki mareni? Lallai kam da kin kwana asibiti yau, dan dukan mutuwa zan miki." Cikin son gimtse dariya Hasheer ya dafashi yace "Kaga babana, kayi hak'uri mana mace ce fa." Hararanta yayi yace "Kaji fa wai ni zata mara, ta d'auka zance ina son ta ne, to bana sonki kinji ko, kuma ba wurinki muka zo ba maza koma ciki." Yanda yayi maganar kamar da yar cikinsa yasa ta jin haushi, fashewa tayi da kukan da ita kanta bata san na miye ba, kuka irin na yarinta har da bubbuga k'afafu, juyawa tayi ta koma kamar yanda yace tana share ido da fad'in "Wallahi zaka san ni ka wa tsawa haka, d'an rainin hankali." Cikin d'aga murya yace "Kurwata kur wallahi, kuma ki sani ina da lauya da shaida a hannu kan duk abinda ya same ni ko ba yau ba kece." Saida ya ga shigewarta kuma ya kalli Hasheer yace "Kai baaba, ni fa wallahi tun fitowarta ta birgeni, kuma gashi ta min a yanda nake so, saboda ina son mace da ana mata za tayi ita ma, amma kuma ta wani fanni matsoraciya ce, yanda yar k'aramar tsaka zata sumar da ita." Dariya Hasheer yayi dan tuna mishi yayi da had'uwarshi da oganniyarshi, wato mata akwai wani abun al'ajabi a tare dasu, duk yanda yarinyar ke rikita mishi lissafi, take gigita mishi nutsuwa, take kayar mishi da gaba da saka shi jin fargaba, a haka kuma wai k'adangare ta gani ta mak'ale a bayanshi, bayan kuma shi ma tallafinta yake nema, ido bud'e yake neman agazawarta, zai iya sunkuyawa shima ya nemi alfarmarta ta kula dashi, amma yar k'aramar hallita ta tsoratar da ita, hak'ik'a dole su gode Allah ma da yayi su musulmi, ya zama na a hannunsu wani iko yake mai k'arfin da wanda zai rik'eshi ake buk'atar jajirtacce mai zuciyar dauriya da shanyewa. Bud'e mazaunin baya yayi ya fara ciro kayan Amjad yana fad'in "Na zo dan magana da ita, amma ka b'ata mata rai kasa ta koma a fusace, yanzu zaka sa mutumcina ya zube a idonta." Rik'e murfin yayi yana binshi duk inda yayi da kallo yana fad'in "Kayi hak'uri ni dai yanzu ka fad'a min komai a kan ta, kuma kai ina budurwar ta ka?" Saida ya gama fito da kaya ya bar wasu ya kaiwa su Izzadeen ya rufe k'ofar, kallonshi yayi yace "Kana son ta ne?" D'an kyab'e baki yayi yace "Eh to, bana ce a'a ba, kai kawai ina son ta." "Zaka iya aurenta?" Ya fad'a yana kallon idonshi, d'aga kai yayi tare da cewa "Sosai ma, kai kasan dama ba yan matan bane bana yi, kawai matsololin wasu ne ke rabamu, wasu kuma su ce na cika zafi idan nai wa budurwa fad'a." Hararanshi yayi yace "To banda abunka babana kai da ke neman a aureka, me ya aike ka yi ma budurwa fad'a tun tana gidansu? Yan matan yanzu da ko iyayensu basa musu fad'a." "To naji na daina, yanzu ita wannan ya za ayi?" Ajiyar zuciya ya sauke yace "A gaskiya ba zan fad'a maka komai a kan ta ba, ina tsoron kaji wacece kuma ka watsa min k'asa a ido." Da sauri yace "Wallahi ba zanyi ba, ai shi so d'aya ne, kuma kai kasan akwai amana a tsakaninmu." Jinjina kai yayi yace "Abdallah, wannan ita ce wacce na maka magana a kan ta a waya ka nuna baka so, kamar yanda na fad'a maka mijinta ya rasu ba tare da sun haihu ba, tana rayuwa ne da kyakyawar zuciyar son yan uwa, tare da 'yar yayarta suke anan, gidan da mijinta ya bar mata ne, tana so tayi aure amma ta kasa saboda tana so mahaifiyar yaron nan da muka kawo gida ta fara yi, ita idan a so samunta ne tayi aure ta zauna anan gidan ta yanda dai zata zauna k'ark'ashin ikon namiji, darajar aure zata shafi ita kanta mahaifiyar yaron nan, idan tayi aure ita ma saita tare a gidan mijinta ko da baya duniya ne, shiyasa na maka maganarta saboda har zuciyata na yarda da halayenta da kuma d'abi'unta." Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi, rumgume hannaye yayi yace "Miye sunanta? Kuma kana ganin zata amince dani?" Cikin b'oyayyan murmushi yace "Gaskiya ta fad'a min sunanta, amma ban rik'e ba saboda yana da wuya, amma kai idan ta fad'a maka zaka rik'e, maganar amincewa kula ya rage naka kayi fad'i-tashi har ka same ta in kana so." Duk'awa yayi ya kwashi kayan nan dake k'asa yace "Zuba ido ka gani, ba zan fito daga gidan nan ba sai da zuciyarta, na gano miye matsalarta ita, tana da son girma?." Da kallo shi dai ya bishi har ya shige gidan da rangad'a sallama tun daga k'ofa har ciki. Faduma ce ta amsa tare da saka hijab ta fito farfajiyar, gaisawa sukayi a mutunce ganin bata san shi ba, ba tare daya aje kayan ba ko ya bata yace "Ina yarinyar nan take?" Kallonshi tayi da kyau, had'add'en guy ne masha Allah gashi dogo da shi ga kuma iya d'aukar wanka, duk da hakan ance daga dogon namiji yake, juyawa tayi ta kalli Dada data shigo tana musu rigimar zata ci uwar wani a waje 馃ぃ, shima d'an lek'a kanshi yayi yana hangota zaune kam yace "Ke zo nan." Tasowa tayi a harzuk'e ta taho tana fad'in "Kai har nan ciki ka biyo ni? Malam fitar min a gida kaji." Saida ta zo daf da shi ya sake hangen cikin d'akin yace "Me sunan turaren da nake jin k'amshinshi?" Hararanshi tayi tace "Ban sani ba." Mik'a mata kwalayen hannunshi yayi yana fad'in "Yarinya rik'e min nan." Mamakin data shiga ne ma ya hanata motsawa sai kallonshi, zazzaro mata ido yayi yace "Ke karb'i na ce, yarinyar nan fa kin raina ni." Faduma dake dariya ne ta gama fahimtar komai, sai kawai ta juya ta koma ciki ta barsu, had'e fuska ya sake yi yace "Ke dake nake fa, karb'i nan." Da sauri ta matso dan har k'asan ranta taji abinda ya fad'a bada wasa bane, daddagewa tayi tasa hannaye ta tallabi kwalayen, da k'yar ta rik'esu ba dan nauyi ba sai dan yawa, kallon fuskarta yayi ya sakar mata murmushi, yanda yake rik'e dasu bai sakar mata ba duka yasa ta kalleshi ita ma, da sauri ta d'auke idonta saboda kallon da yake mata yana murmushi, cikin sanyayyar murya yace "Yarinya ina sonki, kuma aurenki nake son yi, ko kina so ko ba kya so zan aureki, amma shawara ita ce ki taimaka ki so ni, hakan shine zaman lafiyarki, duk da ina namiji bana da juriya wallahi, abu kad'an zai iya sani kuka, kinga idan kika so ni shikenan kin ceci yan maza daga zubar da hawaye." Kallonshi tayi kallo na basira da manufa, sunkuyar da kanta ta sake yi duk sai taji kamar ya watsa mata ruwan sanyi a lokacin sunk'urun sanyi, hakan ya haddasa mata jin wani kakkarwa a k'afafunta, d'auke kwalayen yayi dake hannunta ya d'an zurasu daga farkon shiga d'akin, sake tsayawa yayi gabanta yace "Sunana Abdallah Na-kiri, Hasheer abokina ne kuma amini na sannan d'ana, mahaifina ya rasu da jimawa ina tare da mahaifiyata, ni kad'ai na rage a gabanta da bata aurar ba, ina da yan uwa dayawa maza da mata wanda muke uwa d'aya da uba d'aya, sannan ni matuk'in jirgin sama ne, amma fa karki d'auka ban iya tuk'a keke ba, na iya shi ma." Yanda ya k'arashe maganar yasa ta wani siririn murmushi, juyawa tayi zata shige d'aki yace "Baki ji ba?" Tsayawa tayi ta juyo, marairaicewa yayi yace "Baki fad'a min cikakken sunanki ba?" Sama da k'asa ta harareshi tace "Ni ka min yaro gaskiya, ko zanyi aure ba dai da kai ba." Shigewa tayi ta barshi da baki bud'e, kai ta fa ci mutumcinshi, irin wannan darzawa haka? Juyawa yayi yana jinjina kai yace "Ba komai zaki so ni, nima naji ina sonki." Yana fitowa ya samu Hasheer cikin mota, bud'awa yayi ya shige ya tayar suka fara tafiya, kallonshi yayi yace "Ya ya?" Gyara zama yayi cike da izza yace "Tuni an wuce wurin, ai yau ba zata iya bacci ba dole tayi ta tunani na." Da mamaki yace "Wai da gaske?" Hararanshi yayi yace "D'an zan maka k'arya ne?" Girgiza kao yayi yana murmushi kawai, cikin jin haushi yace "Sunanta kawai ta k'i fad'a min." Kallonshi yayi bai ce komai ba sai wayarshi daya d'auka, daddanawa yayi jim kad'an wayar ta fara sone irin ya aika kira, kamar zata tsinke sannan ta d'aga ba dan bata kusa ba sai ganin dama kawai, tana d'agawa tayi shiru, shi ma shirun yayi kamar ba zaiyi magana ba, sai kuma ya nisa yace "Hajaj barka da dare." Cikin wata murya data kusan firgita shi ko dan yana a waya ne ta amsa da "Barrrrkahh." A hankali ya mayar da idonshi daga zarowar daya musu, saida ya sauke numfashi yace "Zaki iya tuna mana sunan aunty?" Saida ta kalli Dada da ita ma take kallonta dan muryar a bayyane take kafin tace "Wai Dada kake nufi?" Saida shima ya kalli Abdallah yace "Ko mijin da zai aureta ma dole Dadar zai fad'a?" Abdallah daya kawar da kai ne yace "Kaji sai kace wani mai koyon magana na tsaya fad'in wani Da..da." Had'e dariyarshi yayi dan kar suji ya harareshi, ita ma dake kallon Dada har yanzu ne tace "Ahan, Owwo." Da sauri suka kalli juna, firgigit ya d'auki wayar dake kusa da giyar motar yana fad'in "Baiwar Allah maimaita naji?" Fahimtar sunan ne zai wahalar dasu yasa ta cewa "Kaga! Owwo, O..wwo, ka gane? Sai anjima." K'itt! Ta datse kiran, aje wayar yayi yace "Amma wannan yar rainin hankali ce, ko jira ma ba zatayi ba mu da muka kira mu kashe." Harara ya dalla masa yace "Girmanta ya isa ai, idan kaji haushi ka huce a kaina, amma tab'a wannan wallahi yanzu zan wurgaka kan titin nan." Zaro ido yayi yace "Ina uban na ka?" Tab'e baki yayi bai ce k'ala ba, dariya yayi ya dafa kafad'arshi yace "Kai na ganoka fa, ina ga yarinyar nan ce ko? Fad'a min gaskiya kai." Kallonshi yayi lokaci d'aya ya d'auke idonshi a daidai ya shigar da motar gidan bus na rimbo, anan ya wa Umma r茅servation kafin suka wuce Kebab, Abdallah ne ya ci abinci shi kuma yasa aka mishi envaler dan zai tafi da shi ne, saida suka ida suka dawo ya aje Abdallah gida, duk yanda yake mishi tsiyar ba zai shiga ya gaishe da Hajia ba yace ba yanzu ba zai dawo, saboda ya baro Saudat bata jin dad'i. Shi kuma yasan kawai Hajiar ce yake guje ma, kuma bai ga laifinshi ba shima da take uwarshi hak'uri yake da ita, yanzu yana shiga zata tuno da laifin daya wuce shekara da shekaru tayi ta fad'a akai, tace ayi kaza an mata kaza an daina mata kaza, kuma ita ba irin tsufar nan ba da za'a ce ta fara gigicewa ne ba. _Ayi hak'uri rashin wuta, na so a samu fiye da haka._ *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 17:17 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _40_ Ko ta aje wayar Dada ta shiga banbami da masifa akan Abdallah, Faduma dake ta dariya har da k'yalk'yalawa take da rik'e ciki, haushin data bata ne yasa ta cewa "Faduma na tab'a zaginki ne?" Ba tare data daina dariyar ba tace "Eh to! Wasu lokuta ki kan d'an tab'a, amma ba sosai ba." K'wafa tayi tace "To ki kiyaye kar kisa na zagi ubanki." Rufe baki tayi da hannu tana fad'in "Shikenan yi hak'uri." Wata k'wafa ta sake yi ta zauna tana jinjina kai tace "Kiji d'an rainin hankali, wai ni zai aura, me zanyi da shi kamar wacce ta rasa zawarawa? Haba zanyi maganinshi." Tsagaita dariyar tayi ta kalleta cikin nutsuwa tace "Dada, me ye laifinshi? Banga wata makusa tashi ba ni dai." Tab'e baki tayi tace "Ni ma ban ce yana da ita ba, kawai bai min bane saboda saurayi ne da baisan ciwon kansa ba, kiji fa yanda yake min magana a tsatsaye." Tasowa tayi daga inda take ta koma kusa da ita, kallo ta tayi sosai tace "Dada ta, a gaskiya indai har da gaske yana sonki, to zan so ya zama mijinki, a yanzu kawai ya nuna mana shi namiji nekuma zai iya umartarki, sannan da alamu yana da barkwanci, hakan zai sa ki dinga farin ciki a gidanki, Dada matsalata da kika baibaiye kanki da ita lokacin shiga farin ciki yayi, idan kika aureshi ne hakan zai faru, amma duk zawarawanki daga mai mace biyu sai mai uku, matsalar kishiya kad'ai ba zata barki kiyi farin ciki ba, duk yandazaki so zaman lafiya dasu dole sai wata ta fand'are ta nuna ba haka take so ba, a gaskiya ni dai ina baki shawara kan wannan d'in." Marairaicewa tayi ta kalleta tace "Wai dan kinji ya fad'a? Da wasa fa kawai yake, kuma ko da gaske ne ba zan iya ba, Faduma gwara matsalar kishiya data dangin miji, ke shaidace har yanzu dangin mijina duk da baya raye amma gaba suke dani, badan komai ba sai dan a ganinsu na mallakeshi shiyasa har ya min kyautar gidan nan." Jim tayi ta sauke ajiyar zuciya, kallonta tayi tace "To amma dada kina ganin ba matsala ni aurena da Aminu?" Yar dariya tayi tace "Faduma indai har sun amince a d'aura to karki damu, wallahi sai Aminu ya zama tamkar yaron goye a hannunki, zaki mallakeshi a tafin hannunki, zaki juya akalarshi yanda kike so, amma fa ba da boka ko malam ba, sirrin nan dai da kika sani." Shagwab'ewa tayi tace "Dada tsoro nake ji fa." Hararanta tayi tace "Ke tsoron me dallah, ni ba da haka ne har aka mallakamin gida ba, da hakane nayi dariya har da k'yalk'yalawa a gida na ba, da haka nayi farin ciki na wuce rasa komai a cikin gidan nan, ki kwantar da hankalinki kinji, Allah dai ya nuna mana lokacin." "Ameen." Ta fad'a a hankali, kayan nan tasa Amjad ya kai d'akin Dada ya aje, ice cream d'in kuma suka sha har ta bashi ya kai wa jikar su Mama, sauran kuma a fridge ta saka, sun jima falon suna hira kafin kowa ya kwanta d'akinshi, Faduma kam sun jima suna waya da Aminu, mafi yawa tsokana ce da kuma hira ta raha suke, har sukayi sallama saida safe. _______________ Saida ya fara bawa Umma ticket d'in kafin ya wuce b'angarenshi, tana dad'in abincin daya taho dashi dan dama wannan salade d'in ne ta gyara da niyyar had'a shi da farar shinkafa, ko da suka ci har sun kwanta kuma sai amai ya hanata bacci, duk hankalinshi a tashe ya d'auketa suka tafi asibitin sallama, duk kulawar da take buk'ata aka bata bayan an tabbatar musu k'aramin ciki ne ke wahalar da ita, k'arfe 12:30 na dare suka dawo gida, bai kuma fad'awa Umma ba suka kwanta da tunanin kar ya tashi hankalinta ita dake shirin tafiya. A wannan dare dai baiya bacci ba ko na sile d'aya, dan da k'yar Saudat ta samu bacci ya d'auketa, ko da yayi wanka ma alwala ya d'aura ya fito, salatul istikhara yayi domin neman zab'in Allah akan lamuran daya saka a gaba, idan yayi addua'r kamar haka "丕賱賱賴賲 廿賳賷 丕爻鬲禺賷乇 賰 亘毓賱賲賰貙 賵 兀爻鬲賯丿 乇賰 亘賯丿 乇 鬲賰貙 賵 兀 爻兀賱賰 賲賳 賮囟賱賰 丕賱毓馗賷賲貙 賮廿賳賰 鬲賯丿乇 賵 賱丕 兀賯丿乇貙 賵 鬲毓賱賲 賵 賱丕 兀毓賱賲貙 賵 兀賳鬲 毓賱丕賲 丕賱睾賷賵亘貙 丕賱賱賴賲 廿賳 賰賳鬲 鬲毓賱賲 兀賳 賴匕丕 丕賱兀賲乇 禺賷乇 賱賷 賮賷 丿賷賳賷 賲毓丕 卮賷 賵 毓丕 賯亘丞 丕賲乇賶貙 兀賵 毓丕 噩賱賴 賵 丕噩賱賴貙 賮丕賯丿乇賴 賱賷 賵 賷爻乇賴 賱賷 孬賲 亘丕乇賰 賱賷 賮賷賴貙 賵 廿賳 賰賳鬲 鬲毓賱賲 兀賳 賴匕丕 丕賱兀賲乇 卮乇 賱賷 賮賷 丿 賷賳賷 賵 賲毓丕卮賷 賵 毓丕賯亘丞 兀賲乇賷貙 兀賵 毓丕 噩賱賴 賵 丕噩賱賴貙 賮丕 氐乇賮賴 毓賳賷 賵氐乇賮賳賷 毓賳賴 賵賯丿乇賱賷 丕賱禺賷乇 丨賷孬 賰丕賳 兀乇囟賳賷 亘賴." Daga ciki kuwa har da kusanta kanshi da yake sake yi da Faduma, ya rok'i Allah idan alkairi ce ita Allah ya bashi ita, idan akasin hakane kuma Allah ya cire mishi son lamarinta, yana idawa daga nan kan sallayar ya d'an jinkirta, sai dai ko gyangyad'i bai fara ba aka kira sallah asuba, mik'ewa yayi ya fita masallacin sai dai ana idar da sallah ya dawo. Saida rana ta hantse sosai ya gama shirya yaran sannan suka nufi b'angaren su Umma, da kanshi cikin nutsuwa da ladabi ya tayata had'a kayanta a jaka, suna yi suna hira a hankali har suka gama, wanka ta shiga shi kuma ya dawo falo ya zauna jiranta, ta d'an d'auki lokaci kafin ta fito a shirye tsaf, anan ta same su a falo suna hira kamar yanda suka saba, duk gaisheta sukayi ta amsa a tausashe, wuri ta samu ta zauna kafin ta kallesu d'aya baya d'aya, tsayar da dubanta tayi kan Mukhtar tace "Mukhtar zan tafi, amma dan Allah bana son fitina a gida, duk abinda Mujaheed zaiyi babu ruwanka da shi, kaji ko?" Jinjina kai yayi yace "Insha Allah Umma, babu abinda zai faru har kije lafiya ki dawo lafiya." Lumshe ido tayi kawai sannan ta kalli Salima tace "Salima, ke ma ki kiyaye, kar ya zo yana miki magana ko da akan abinci ne ki dinga turo mishi bakin nan naki, kinsan ya tsani haka kuma zai iya bigeki, kin fahimta?" Saida ta turo bakin kam tace "To Umma, ai shine ya raina mutane wallahi, sai ya dinga mana magana kamar wani ubanmu." Girgiza kai tayi tace "Ni dai na fad'a miki dan ki kiyaye, idan kuma baki ji ba to ga wurin nan, kinsan ko kasheki yayi babu wanda zai iya tanka masa." Kallon Hasheer da Halima tayi tace "Na yarda daku, ban da matsala daku wajen bawa al'amura baya, amma ina tsoron zuciyarku idan aka kai ku bango, Hasheer! Kai ne babba, dan Allah kayi hak'uri da duk abinda zai faru, sannan ka saka ido akan k'annanka, ka tsawatar musu idan sunyi ba daidai ba." Da ido ya fara amsa mata kafin ya jinjina kai yace "Insha Allah Umma, zamuyi duk abinda kika fad'a." Jinjina kai tayi tace "Allah ya muku albarka." "Ameen." Suka amsa a tare, mik'ewar da tayi yasa duk suka mik'e suma tsaye, Hasheer dake k'asa zaune kusa da ita ta jawo jikinta, cikin nutsuwa so da k'auna ta mishi kyakyawan masauki a k'irjinta, tsam ta rumgumeshi tana bubbuga bayanshi, cikin sanyayyar murya tace "Ku kula da kanku." Cike da shauk'i da k'aunar mahaifiyar tashi shima ya sake kwantar da kanshi a kafad'arta, sai yake jin kamar zai rabu da ita ne shikenan, rufe ido yayi yace "Insha Allah Umma, ki kula mana da kanki, Umma ke ce rayuwarmu, ba zamu iya rayuwa babu ke ba." Jinjina kai tayi tace "Insha Allah." Raba jikinsu tayi ta matsa kusa da Mukhtar, shima rumgumeshi tayi tana bubbuga bayanshi da cewa "Sarkin k'in ji, ka kula kaji." D'aga kai yayi yana sake mak'alk'ale mata yace "To Umma, ke ma ki kula mana da kanki." Taba bubbuga bayanshi tace "Zanyi insha Allah." Sakinshi tayi ta koma kan Halima, ita ma dai bubbuga bayan nata tayi tace " 'Yata mai nutsuwa, ina alfahari dake, ki ci gaba da kasancewa haka kinji ko?" Jinjina kai tayi cikin muryar kuka tace "Insha Allahu Umma, k'arfin gwiwar da kike bani yasa nake yanda kike so." Jinjina kai tayi ita ma kafin ta sake ta, tana isa kusa da Salima ta turo baki tana shagwab'a, jawota tayi ta rumgume tana fad'in "Auta ta mai bani ciwon kai, ki kula min da kanki kinji." Sake turo baki tayi tace "Bayan ma duk gidan nan babu mai sona, saida aka gama rumgume kowa kafin ni." Mukhtar ne yace "Ke nima baki ga hak'uri nayi ba saida aka fara rumgume wani kafin ni ba?" Jan kumatunta Umma tayi sosai tace "Wa ya fad'a miki ba'a son ki? Ke baki san cewa daga ni har yayunki duk muna rayuwa ne saboda ke ba kawai, duk wani tanadi da tattalinmu akan ki ne." Dad'i ne ya kasheta yasa ta sake rumgumeta tana dariya, dungurar mata kai tayi tace "Ja'ira Salima." Su Izzadeen ma rumgumesu tayi ta sumbacesu, Hasheer dake gefe na kallonsu ne ta kalli agogon wayarshi, kallon Umma yayi yace "Umma." Juyowa tayi ta kalleshi tace "Na'am." Cikin ladabi yace "Lokaci ya kusa." Jinjina kai tayi tace "Shikenan muje." Duk tare suka fita farfajiyar, saida Umma ta juya ta kalli b'angarenshi sannan ta kalleshi tace "Saudat bata san zanyi tafiya bane?" Cikin nutsuwa yace "Wallahi Umma bata sani ba, domin jiya bayan na kai muku ticket d'in ma na sameta jikinta yayi tsanani, dan tun kafin na fita bata jin dad'i, tsakar dare ma har asibiti muka tafi, ban tashe ku bane saboda dare yayi." Cike da kulawa tace "Subhanallah, amma ai daka fad'a min Hasheer, lafiya ai uwar jiki ce." Mik'awa Mukhtar jakarta tayi tace "Muje na ganta kafin mu wuce." Bayanta ya bi suka shiga b'angaren tana sallama, kallon falon tayi wanda rabonta dashi ta d'an kwana biyu, d'an murmushi kawai tayi ta girgiza kai, babu kimtsi a d'akin bare gyara kafin ayi maganar k'amshin da zai kwantar da hankali, duk son Hasheer da tsafta ai namiji ne shi ba zai zage damtse ya gyara mata falo ba, d'akinshi ne na kwanciya wannan tasan kam yana gyarashi ko dan ya kwanta yaji dad'i ya samu nutsuwa. Rashin tabbacin halin da zata sameta a ciki yasa ta kalleshi tace "Ko zaka iya mata magana? Ba sai na shiga ba ma." Saida ya sauke yar ajiyar zuciya, dan yanda yasan Umma da son tsafta kam yasan ranta zai mugun b'ace idan ta ga d'akin baccin Saudat, shiga yayi d'akin da sallama, yayi daidai da fitowarta daga ban d'aki, kamata yayi yana fad'in "Ya jikin naki?" Yatsina fuska tayi tace "Da sauk'i sosai, yanzu ma ban d'aki na shiga." "Ba kya jin komai?" Ya fada yana tsareta da ido, girgiza kai tayi, jinjina kai yayi shima yace "Muje falo Umma na son ganinki, zata wuce Alg茅rie ne insha Allah." Ba tace komai ba sai biyoshi da tayi suka fito, jin fitowarsu yasa Umma kallonsu, da mamaki take kallonta har ta k'araso, yanzu haka da wannan fuskar ta ta wacce ke da alamun bacci ta kalli mijinta? Da bakinta da bai da alamar ta wanke shi ta fito? Da kanta haka daya warwatse ta fito wurinta babu d'an kwali? Da rigar baccin doguwa dake shara shara ta fito mata? Duk da a gaban idonta ya zauna k'asa kusa da k'afafun Umma, amma ita saita zauna kan hannun kujera tana fad'in "Ina kwana Umma?" Cikin muryar mijinta ta amsa mata da "Lafiya lau, ya jikin na ki? Ashe baki ji dad'i ba? Sai yanzu yake sanar dani." Da yatsina fuska ta amsa da "Eh wallahi, da sauk'i ma ai, dama amai ne ya sha min kai." Ba tare data kalleta ba tace "Allah ya k'ara afuwa." "Ameen." Suka amsa har da Hasheer, mik'ewa tayi tace "Dama zan wuce na ce bari na fad'a dubaki." Ba tare data mik'e ba ta bita da kallo tace "To Umma sai anjima." Juyowa yayi ya kalleta sanda yake tashi tsaye, sai anjima kawai ta fad'a? Babu Allah ya kiyaye hanya ma? Lallai! Bin bayan Ummanshi kawai yayi suka fita babu wanda ya sake tankawa, suna zuwa da sauri suka d'auki hanya inda Mukhtar ke tuk'i sai Umma da yaran a baya, ita suka fara ajewa cike da kewa da sake binta da addu'a, sannan suka wuce suka aje yaran a makaranta suka koma gida. Tsaf Umma ta canza akalar tafiyarta daga Niamey da zata shiga jirgi ta wuce a sauk'ak'e zuwa Zinder, motar k'arfe 09:00 suka tashi, awa uku da wasu mintuna suka isa garin, ko da ta sauka taxi ta d'auka ita ma inda aka kai ta unguwarsu Faduma, yaro d'aya ta tambaya gidan malam Moliya ya nuna mata, da rakiyarshi tare da d'aukar mata kayan ta iso, karb'an kayan tayi sanda suka zo k'ofar gidan, kyauta ta mishi amma sai ya k'i amsa yace "Ai tunda gidansu Fadun Aba ne ba zan karb'a ba." Da mamaki ta kalleshi tace "Fadun Aba kuma?" Jinjina kai yayi yace "Eh, ai haka yanzu muke kiran Aban Fadu." Jinjina kai tayi ta bishi da kallo har ya tafi, cikin nutsuwa da tausasa murya tayi sallama, Hatimi ce ta fara amsawa wacce suke zaune tare da Ayya suna tattaunawa kan maganar kai Amjad gidansu Tagur daya faru jiya, inda Hatimi ke ta bala'i tana fad'in gwara data taka mata birki, ai da har ita sai tayi hushi da ita, shigowar Umma yasa duk suka nutsu suka mik'e, dan kamalar matar da dattakonta ya isa ya nuna maka kamilar mace ce. ______________ Da kanta ta aje shi makaranta da safe, daga nan kuma ofishinsu ta wuce dan dama da shirin haka ta fita cikin riga da wando yan pakistan, tana fita a mota masinjan dake mata aiki da Aminu ma ya zo da murna suka gaisa tare da tayata murna tayi sabuwar mota, fad'a masa asalin yanda motar ta shigo tayi, addu'a ya sake wa yaron kafin ta kalleshi tace "Yallab'ai Aminu ya zo ne?" Jinjina mata kai yayi yace "Eh ya zo Hajia, sai dai bai jima da shigowa ba shima." Ba tace komai ba ta tunkari ofishin shi, saida ta k'wank'wasa ya bata izinin shiga, dake baiyi tunanin ita bace sai yayi mamaki daya ganta, k'arasawa tayi ta nuna kujerar dake gabanshi tace "Zan iya zama?" Da sauri ya mik'e yana murmushi yace "Ranki shi dad'e, ai wannan tafi k'arfin ajinki sai wannan." Ya fad'a da nuna mata wacce ya tashi a yanzu, d'an sahihin murmushi tayi tace "Um um! Nan ma yayi." Zaunawa tayi kafin shima ya zauna yana washe baki da cewa "Gimbiya Faduma, kin tashi lafiya?" Saida ta d'ora jakarta akan table d'in tace "Lafiya lau, ya aiki?" "Aiki Alhamdulillah, kinsan da na d'auka ba zaki zo ba har nayi niyyar tafiya gidan." D'an yatsina fuska tayi tace "Lafiya dai ko?" Numfashi ya sauke yace "Eh to, lafiya lau." D'aga kafad'a tayi alamar oho d'in nan kafin tace "Dama na zo gurinka ne akan kyaututtukan Amjad, ya kake ganin ya kamata muyi dasu?" Yar dariya yayi yace "Faduma ni kike tambaya kuma?" Babu fara'a a fuskarta tace "Eh mana, nayi magana da Dada tace Amjad bai da uban daya fi ka, shiyasa nake tambayarka dan na yarda da haka nima." Wani murmushi yayi yace "Nagode da wannan karamci, amma a shawarata ajiyar kud'i dai ba zaiyi ba, zai fi ace ana juyasu ne ta wasu hanyoyin." Kai tsaye tace "Kamar wane iri?" Da mamaki ya kalleta yace "Faduma, ke fa mace ce, zaki iya kafa ko da kasuwanci ne kina juyasu, kin fini sanin irin abinda ranki ya ke so a game da harkar kasuwa." Jinjina kai tayi tace "Amma ai kasan ni wannan aiki shine nafi so." Saida yayi jim alamar tunani kafin yace "To me zai hana ki fara siyar da kaya irin naku na mata, kamar hakan zai fi ko?" Jinjina kai tayi ba alamar murmushi tace "Hakan ma yayi, zanyi magana dasu Ayya da ita ma Dada." Shima jinjina kai yayi, saida ya d'ora alk'alamin dake hannunshi kan takarda sannan ya kalleta yace "Faduma akwai wani aiki daya taso min, amma ke nake so ki jagorance shi, dan ni a halin yanzu babu abinda ke gabana sai ganin nayi sama dake na killace a muhallina ina baki kulawar data dace." Kawai dariya taji maganarshi ta bata, duk da taji gabanta ya fad'i amma dai al'amarin bai wani daketa ba har a zuciya, saida ta gyara zamanta tace "Me yasa kai ba zaka yi da kan ka ba?" Matse bakinshi yayi yace "Kamar yanda na fad'a miki hasashena na yanzu, gobe goben nan insha Allah su Alhaji zasu tafi garinku su had'u da su Baba, ni kuma yanzu bansan me yasa Alhaji ke ta d'ora min wasu nauye nauyenshi a kai na ba, hakan yasa hankalina ya rabu gida biyu zuwa uku." Girgiza kai tayi tace "Kai ma ai kasan dalilin, dama ba aikinka yake so ba, shagwab'a ka masa ya amince kake yi, kuma kai ne magajinsa na farko, kaga dole zai fara nuna maka yanda komai yake." Ajiyar zuciya ya sauke yace "Gaskiya kika fad'a, shiyasa ba zan iya fara aikin nan da kaina ba saboda ba a cikin gari bane." D'an zaro ido tayi tace "A ina kenan?" Ido cikin ido ya kalleta yace "Niamey." Wata k'akk'arfan ajiyar zuciya ta sauke tace "Kuma shine ni zaka tura ni? Amma ai kasan bana son aikin da zai sani barin gari, musamman yanzu da idona ke kan Amjad." Cikin rarrashi yace "Kiyi hak'uri kinji Fadun Aba, wallahi aikin nan ke ce zaki iya shi yanda ya dace, kuma Amjad ba gani ba? Miye anfani na idan ba zan kula dashi ba?" Dad'in da maganarshi ta k'arshe ta mata ne yasa ta sakin murmushi tana rufe fuska da tafin hannu d'aya, sai kuma ta kalleshi duk ta marairaice cikin shagwab'a tace "Amma kuma ana shirin kai gaisuwa gidanmu shine zaka tura ni wani gari yin aiki? Kai wane irin ango ne da baya son amaryarsa?" Dad'i kashe shi! Sai yaji kamar ya k'urma ihu daga zaune, dariya ya k'yalk'yala jikinshi har rawa yake yace "A'a wallahi, haba Faduma kinsan yanda nake son ki kuwa, ai kawai tunda ba kya so shikenan, zan kira Abdu shi da ke garin sai ya kula da aikin." Had'e murmushinta tayi, ba haka ta so ba, duk abinda ta fad'a kuma ya masa dad'i zata so ya zama namiji, girgiza kai tayi tace "Ka barshi ma zanyi." Da mamaki yace "Da gaske? Ban takuraki ba kuma?" Matse bakinta tayi ta turo shi gaba tace "Babu." Mik'ewa tayi tana fad'in "Ka had'a min bayanan a rubuce saika tura min su." Jinjina kai yayi ya bita da kallo har ta fita, ofishinta ta bud'a ta shige ita ma, cire lafayar dake kai tayi kafin ta d'auki rigarta har gwiwa ta saka bak'a. ______________ Tana aje shi ko da ya shiga ciki yaji an jawo hannunshi, da sauri a tsorace ya juya yana fad'in "Hasbunallah wani'imal wakil." Da fara'a yace "Amjad ni ne." Zaro ido yayi ya bud'a baki zaiyi magana sai kuma ya kafe shi da ido, kiciniyar k'watar hannunshi ya shiga yi hakan yasa Tagur durk'usawa yana kallon fuskarshi yace "Amjad ni ne, Abanka ne, rumgume ni kaji." Mak'ale kafad'a yayi yana son k'watar hannunshi yace "Um um! Ni ka sake ni na shiga aji." Marairaicewa yayi sosai fuskarshi d'auke da damuwa da alhini ga kuma idonshi da suka cika taf da hawaye, cikin murya kamar zaiyi kuka yace "Amjad, kai ma gudu na kake kamar yanda mahaifiyarka take yi? Amjad ta koya maka tsanata ne kai ma, ni fa mahaifinka ne, suna son su nisanta ni da kai ne fa,e yasa ba zakayi tunanin haka ba?" Kallon tuhuma ya masa yace "Ayyata nasan ba zata min k'arya ba, tace baka so na ko kad'an." Take yayi wani r茅action da dole ya baka tausayi yace "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, Amjad ka tab'a ganin wanda ya haifi d'a a cikinsa kuma ace baya son shi? Amjad wane uba ne ka tab'a gani da ya k'i abinda ya haifa? Sai ni ne zan k'i ka? Akan me? Me kayi min? Ita mahaifiyarka ta fad'a maka dalilinta ne?" Shiru yayi kawai yana kallonsa bai ce komai ba, numfasawa yayi yace "Amjad kai d'ane ne, sab'anin daya shiga tsakanina da mahifiyarka karka bari ya shafi d'aya daga cikinmu, kasan dukanmu muna da hakk'i a kan ka, idan ka tauye wani Allah fa zai iya yin hushi da kai, kar ka ce zaka shiga tsagi d'aya akan abinda baka san ya faru ba, hasalima babu wanda ya tsammani za'a sameka a lokacin, karka yarda suyi anfani da kai wajen saka maka k'iyayyar mahaifinka, kasan ni ne ubanka kuma uba da shi ake ado." Yanda maganganunshi suka fara kama kanshi ne yasa shi cewa "Me kayi wa Ayyata to take hushi da kai?" Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon yaran dake ta shigowa suna nufa ajujuwansu yace "Amjad, yaro ne kai ba zaka gane ba, amma mahaifiyarka tana hushi ne dani ne akan rashin gaskiya." Idonshi cirr cikin nashi yace "Me yasa?" Rage girman idonshi yayi yace "Saboda kawai an zab'a min matar da zan aura a gida." Da mamaki Amjad yace "Saboda zaka mata kishiya?" Da sauri ya kalli fuskarshi, wai shi fa bai san ya aka same shi ba? Sai kawai ya d'aga masa kai alamar eh, d'an numfashi ya sauke yace "Dama Ayyata tana da kishi ne haka? Me yasa ta rabu da kai kuma ta nesanta ni da kai? Duk saboda kishiyar?" Jinjina masa kai yayi yace "Eh hakane, saboda mu kasan tubawa idan kayi auren fari, to sai matarka tayi haihuwa hud'u ko uku kafin ka k'ara aure, ita kuma ko haihuwar farko ba tayi ba, shine fa ta k'i zama saida tasa muka rabu, ashe da cikin ka ni kuma ban sani, nayi ta nemanta a gidansu amma babu wanda ya min magana, shine fa saida aiki ya dawo da mahaifina nan kafin ya rasu, sai gashi Allah ya had'ani da kai a sanda banyi tsammani ba." Kuka ya fashe dashi na gaskiya sosai ya rumgume Amjad a jikinshi, yana cikin kukan yaji muryar Amjad yace "Suma iyayenta suna taya ta kishi ne?" Jim yayi bai d'ago sai a ranshi da yace "Baka sha nonon banza ba, indai a tambayoyi ne zamu kwana anan baka k'are tambayata ba, d'an lauya kenan." D'agowa yayi ya kalleshi yace "Hakane, duk gani suke na sab'a ma al'adarmu." Da sauri yasa hannayenshi ya rik'e damatsenshi yana jijjigashi da cewa "Amjad ina son ka, ina son ka sosai ta yanda zan uya sadaukar da abinda na mallaka a duniya saboda kai, karka gujeni kai kaji ko." Fad'awa yayi jikinshi yace "Nima ina sonka *Aba*." Sake k'amk'ameshi yayi yace "Sake fad'a na ji Amjad, kayi ta kirana da Aba." Cikin muryar yarintarshi yace "Aba, Aba, Aba, Aba." D'agowa yayi ya kalleshi yace "Amjad har yanzu mahaifiyarka tana hushi dani, ya zanyi na dinga ganinka ba da saninta ba?" Shiru yayi yasa yar yatsa a baki alamar tunani, da sauri kuma saiya kalleshi yace "Aba, kaga dai ba zaka je gida ba saboda Ayya, makaranta kuma ita ke kawo ni kuma sai taga shigata, sannan ta fad'awa mai gadi idan na shiga kar ya barni na fita ko wane irin uzuri, ana tashi kuma take zuwa d'aukata, kaga kenan babu hanya ko d'aya." Marairaicewa yayi yace "Kenan ba zan iya ganinka ba Amjad?" Yan hannayenshi ya saka ya tallabo fuskar Tagur yace "Aba kwantar da hankalinka, ni fa d'anka ne." Gyara tsayuwarshi yayi yace "Da k'arfe 10:00 ake fito damu shan iska, yara na fita amma ni mai gadi baya barina, ka dinga zuwa lokacin ni kuma zan fito saina ganka." Da jin dad'i yace "To taya zaka fito?" Cike da yarinta yace "Kaga dai idan na fad'awa mai gadi kai Abana ne zaiyi mamaki dan ance ka rasu, kuma zai fad'awa Ayya ita kuma zata san ka zo nan, dan haka zan dinga shiga cikin yara dayawa saina dinga fitowa." Hannu ya bashi yace "Ban biyar." Shima hannun ya bashi suka bige suna dariya, mik'ewa yayi ya saka hannaye aljihu ya ciro wata chocolat mai girma da kyau ya bashi yace "Je ka shiga aji lokaci ya kusa, zan dawo ma idan goma tayi." Hannu biyu yasa ya karb'a yace "Kuma dai Aba?" Shafa kanshi yayi yace "Amjad burina bai wuce ace tare da kai muke bacci ba a gado d'aya." Murmushi yayi yace "Zai faru insha Allahu Aba." D'aga mishi hannu yayi ya nufi hanyar fita yana fad'in "Saina dawo anjima, ka kula da kanka." Shima hannun ya d'aga masa ya juya ya k'arasa shigewa cike da murna da farin cikin ya ga Abanshi. ______________ Daga yanda suka tarbeta da karramata ya nuna mata lallai Faduma daga babban gida ta fito, babban gida ba wai na arzik'i ko sarauta ko malunta ba da sauransu, na dattijantaka da magana biyu, domin dattijon arzik'i shine idan ya yanke hukunci cikin hushi ya gane yayi kuskure ya dawo ya gyara shi ta hanyar rusa waccen hukuncin, duk da hakan ya haifar da magana biyu amma wannan shine *dattijantaka*, saida sukayi sallah azahar ta ci abinci tasha ruwa ta samu nutsuwa, sannan ta fad'awa Hatimi tana son ganin mai gidan, da magana ta zo kuma duka wurinsu, da d'an mamaki Hatimi tace "Wurin mai gidan? To Allah yasa lafiya?" Wani murmushi ta sakar masa tace "Lafiya lau, akan maganar Faduma ne na zo dama." Ai jiki na rawa tace "Ah haba, bari yanzu na kirashi na fad'a masa yana da bak'uwa, ba ma zan fad'a masa abinda ya kawoki ba ai, kinsan zuciya ce dashi." Yanda ta k'arshe maganar da dariya yasa Umma ma murmusawa, ai kam tana kiranshi a waya tace ya zo da sauri yayi bak'i suna son ganinshi. Dake shi mutum ne indai za'a kirashi daga gida to zai amsa, da hanzari ya shirya ya hau babur d'insa da Kalli ya siya mishi ya taho gida. *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 17:17 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _41_ Zuwanshi ma wata sabuwar gaisuwar ta b'arke kafin ta jadadda mishi abinda ya kawota, jim yayi na dak'ik'u kafin ya kalleta, duk da ta ga kallon daya mata gyara zama tayi tace "Kamar yanda na fad'a muku komai a game dani, dalilin gasar musabik'a da akayi kwana biyu da suka wuce nasan Faduma a zahiri, a lokacin da nake jin karatun yaron ban da addua'r da nake yi kamar Allah ya masa albarka ya sakawa iyayensa da alkairi, ta dalilin jikokina kuma sai muka had'u da ita a zahiri, anan ta bani labarin komai daya faru da ita ko nace da ku daga farko har k'arshe, naji ba dad'i sosai, na tayaku jimamin al'amarin da alhini, sannan kuma na tayaku murna da kuma alfahari." Da sauri duk suka kalleta, sai Herde data jinjina kai irin an zo wurin nan, bata kula da kallon da suka mata ba sai d'orawa da tayi da cewa "A gaskiya nayi mamaki da naji daga bakinta irin hukuncin da kuka yanke a kanta, duk me yayi zafi haka yan uwa?" Kallonsu duk tayi d'aya bayan d'aya ta ci gaba da fad'in "Nuna mata b'acin ranku abune mai kyau wanda zai sa ta shiga hankalinta ko nan gaba sannan ta tabbatar cewa tayi abinda bai dace ba, amma kuma tsatsauran hukuncin na korarta daga gida sam babu tsari a cikinshi." Kallon Aba tayi tace "Wai ka ma yi tunani kafin ka koreta kuwa? Kafin ka ce ta bar maka gida kayi tunanin ina zata tafi? Kayi tunanin wace irin rayuwa zatayi a inda zata samu kanta? Aban Faduma gaba d'aya Faduma nawa nawa take a sanda k'addarar nan ta fad'a mata? A shekarun data fad'a min wallahi a lokacin yarinyata Halima ko jinin haila bata fara ba, amma a wannan shekarun nata kuka koreta daga gida ku kayi watsi da lamuranta..." Ayya ce ta d'ago ta kalleta tace "A'a fa, ni ban koreta ba, kuma sanda abun ya faru na yi ta..." Dakatar da ita tayi ta hanyar fad'in "To me ki kayi? Ke da kika zab'i zama da miji akan rayuwar 'yar da kika haifa? Kinga Hadiza, wallahi da nice ke a matsayin uwar Faduma, yarinyar da nake da tabbacin k'addara ce ta fad'a mata sannan na fi kowa saninta, ba zan tab'a yarda ka korar min 'ya daga gida ba, cikin biyu dole ayi d'aya, ko dai mu zauna tare da ita, ko kuma ni da ita duk mu bar gidan, amma ba zan tab'a zama a gidanka ba alhalin 'yata na wani wurin kuma kin tabbata cikin damuwa take." Sunkuyar da kai tayi ta share hawaye da lafayarta kafin cikin rawar murya ba tare data d'ago ba tace "Wallahi na mata kuka sosai yarinyar nan, na tausaya mata matuk'a kamar zan yanki zuciyata, ina ma kun rumgumi 'yarku a lokacin kunyi imani da k'addarar data same ku, ku tayata rainon abinda ta haifa." Girgiza kai tayi ta d'aga ta kallesu tace "Faduma ta zama kamar ita ce ta haife ku ba ku kuka haifeta ba, kunsan me yasa?" Wani murmushi tayi tace "Saboda k'uruciyarta da yanda akayi ta samu d'anta basu dameta ba, abu d'aya data sani shine inhar ta inganta rayuwarshi to zata ji dad'i, hakan ya jawo k'ok'arinta na kula da rayuwarshi tare da sadaukar da komai na ta wa d'anta da ku kuke ganinshi kamar ba mutum ba saboda ba'a same shi ta hanyar aure ba, yau gashi yaronta ya zama abun alfahari gareta, d'an ta ya zama abun koyi ga sauran yara, Amjad dai d'an Faduma ya zama wanda iyaye da dama ke ta k'ok'arin d'aura ya'yansu akan turbar da iyayenshi suka d'ora shi, abun mamaki kuma ku dake kakaninshi kuna nan cike da jin kunyar ku nuna shi a matsayin wanda kuka sani, ko manzon Allah (S.A.W) da yace muyi aure dan mu hayayyafa, ba taron banza da wofi yake nufi ba, yara irinsu Amjad ne nufinshi a samu ta hanyar aure, kuna ganin Allah zai wulak'anta ne saboda ta masa laifi d'aya tak? Ku me kuka d'auki kanku? Ba kwa sab'a mishi ne ko kuma mahasumai ne? Sai yarinya saboda kun haifeta ta musu laifi d'aya sai ya zama kamar ku kuka halicceta kawai kuyi watsi da ita, to ku sani hakk'inta na akan ku, kuma Allah yasan zuciyarta." Kallon Ayya tayi tace "Ba dan Allah ya shiryar muku da 'yarku ba, kinsan wace rayuwa take yi tare da k'anwarki ne? Ita ma babu miji sannan ba wasu shekaru ne da ita ba, taya hankalinki ke kwance kike tsammanin yar uwarki na kula miki da yar da kika haifa, badan Allah yasa mutuniyar kirki bace ita da kinsan zuwa yanzu ina gawurtar Faduma zata kai?" Girgiza kai tayi cike da takaici ta sake kallonsu dukansu tace "Tunda abun ya faru babu wanda ya zauna yayi magana da ita, daga ku uwayenta mata har shi namijin, babu wani yayanta da kuka tab'a wakiltawa ya je ya zauna da ita, kawai kuna zaune kun zuba mata ido daga nesa kenan tayi duk abinda zatayi, tayi duk rayuwar da take so, ta zauna tunani da bak'in cikin iyayenta ya kasheta." Da sauri Aba ya kalleta wanda idonshi sukayi jajur kamar wuta, jinjina masa kai tayi tace "Tabbas har yanzu Faduma na tambayar kanta iyayenta sun daina son ta ne? Me yasa suka kasa yafe mata kan laifi d'aya data musu? Me yasa suke nuna da ita da banza duk d'aya? Kullum cikin tsammanin kiran mahaifiyarta take, kullum cikin sa ran jin muryar mahaifinta take, amma abun ya gagara." Saida ta k'ara share hawaye tace "Da wane kuke so yarinyar nan taji, da cin zarafinta da yaro yayi ta k'arfi ya keta mata haddi? Ko kuma da wulak'anci da iyayenshi suka mata? Shin za tayi tunani akan k'in amsar yaronshi da yayi ne? Ko kuma za taji da hushi da kuke da ita? Ko kuma rainon yaronta data sa a gaba? Wanda kunfi kowa sanin wahalar dake cikin rainon yaro ga wanda yake tare da duka iyayenshi ma, bare ita d'aya ce uwar uba da kakani da duka dangi gareshi, ita ce cin shi shan shi tufafinshi kula da d'awainiyar makarantarshi da lafiyarshi, yarinyar nan kana kallonta zaka san hankalinta ba kwance yake ba saboda larurar rayuwa, kana kallon fuskarta zaka ga damuwa a bayan murmushinta, amma dake yarinya ce data gaji juriya da hak'uri, wallahi duka shanyesu take da ruwa ta nunawa kowa bata da matsala ko d'aya, inhar zaka zauna da ita na minti d'aya saita saka sakin murmushi tare da jin kana k'aunar ci gaba da zama da ita." "Kunga, ku farka daga baccin nan ku jawo yarinyarku a jiki, d'an data haifa yaro ne da zaku iya yin alfahari dashi, tabbas nasan akwai ciwo kuma kowa burinshi ya ga kyakyawan zuri'arshi mai kyakyawar nasaba, amma ku sani ta hanyar Amjad zaku iya samun ingantattciyar nasabar da bakuyi tsammaninta ba, dan Allah na rok'eku ku yafe mata, yafiyarku zata zama wata babbar rahusa da salama a cikin rayuwarta, yafiyarku zata sa komai ya dinga zuwa mata da sauk'i, yafiyarku a gareta tamkar yi mata bushara da gidan aljanna, sannan ku taya ta sake kare mutumcinta ta hanyar sama mata namijin daya dace da ita, hak'ik'a ba dan kar na shiga rayuwarta ba, da zan iya nemawa babban yarona aurenta, ba dan komai ba sai dan na gamsu da nagartarshi, ni ce uwarshi kuma ni nafi kowa sanin abuna, amma a labarin data bani ta fad'a min akwai wanda suka d'an fara maganar aure dashi, wannan zai sa na ci gaba da mata fatan alkairi." Kallon Aba tayi tace "Idan kuma ba zaka iya yafe mata ba, kana ganin girman laifinta yafi k'arfin yafiya, to muyi komai a rubuce, zan mayar da Faduma 'yata ta har abada, ni zan d'auki nauyin kula da ita da d'anta, zan zama uwa a gareta mai share hawayenta da sauraron damuwarta." Kallonsu tayi dukansu tace "Kun yarda?" Duk kallonta sukayi sai kuma suka kalli juna, da sauri Herde ta girgiza kai tace "Mu ma muna Faduma, idan ma su basu sauko ba to ni dama ba hawa nayi ba, dan haka zan biki mu koma tare na rayu da 'yata, in yana so ya aika min takardata acan." A tare suka kalleta, sai kuma Ayya tace "A'a, ni ce dai zai aikawa takardata bake ba, dan gaskiya na gaji da mishi biyayya ina cutar da zuciyata wajen b'oye k'aunar da nake wa 'yata." Kallonta tayi, ya rasa wani katab'us kamar wanda aka tsotsewa jini, sai dai a zuciyarshi yana ta sake maimaita kalaman Umma, duk da ya jima da yin nadama da kuma yafe mata, amma sai yaji gaba d'aya kamar bai zama uba na gari ga y'arshi ba, tabbas da rumgumarta sukayi suka jata a jiki, amma sai baiyi haka ba bai kuma bawa kowa damar yin haka ba, saboda kawai ya nuna yayi hushi da ita, gashi a dalilin haka k'aramar Fadumarsa autarsa tayi dakon nauyin da yafi k'arfin shekarunta. Kallon Umma yayi cikin wata irin murya yace "Idan kin koma ki turo min ita." Kallonshi sukayi kowa da murmushi a fuskarshi, Herde ce tace "Kana nufin ka yafe mata kenan?" Kallonta yayi sai kuma ya mik'e yana saka takalminshi yace "Idan 'yata ta dawo gareni ku kuma duk zaku bar min gida tunda haka kuke so." Dariya suka kwashe da ita sai Herde da tace "Allah baka isa ba, yo 'yarka ce kai kad'ai? Muna nan da kai ai mutu ka raba takalmin kaza." Murmushi yayi ya girgiza kai yace "Duk cikinku wacece ta tab'a k'ok'arin fahimtar yanda nake ji a game da Fadu na? Har zuwan da tayi nan wacece tayi yunk'urin tilasta had'uwa ta da ita?" Herde ce tace "Amma ai saida aka tambayeka ta sake kwana kace a'a." "To shikenan ba za'a sake latsa mutum ba?" Ya fad'a a hassale, kallon juna sukayi sai kuma sukayi dariya, Umma cikin nutsuwa tace "Gaskiya ya fiku gaskiya, na tabbata hada girman kai da mulki irin na maza ya hanashi jawo 'yarsa a jiki, ku kuma duk sai kuka tsorata kuka bar masa yak'in." Kallon Umma yayi yace "Baiwar Allah mun gode sosai da tunin da kika mana, Allah ya saka miki da alkairi, hak'ik'a alkairin da kika mana babu abinda zaki iya nema a wurinmu ki rasa, yanzu haka ina ji da zaki nemawa d'an ki auren Faduma babu abinda zai hana ni tara mutane a yanzu kuma a d'aura a gabanki, Allah ya biyaki da aljanna." Murmushi tayi cikin nutsuwa tace "Ba komai ai yi wa kaine, Allah ya rufa mana asiri duniya da lahira ya k'ara shirya mana yaranmu." *Ameen ya Allah* Jakarta ta kalla tace "Tashi zanyi na wuce, dan tafiya ce a gabana mai tsayi, amma alk'awarin da nayi wa kaina na shirya tsakanin iyaye da 'yarsu yasa ko 'ya'yana ban fad'awa wa ba na zarto nan wurin." Herde ce tace "A'a Hajia kar ma ki fara wannan magana, ai tashi zamuyi mu shiga gidana ki kwana acan, tunda yau Hadizey ke da mai gidan kinga sai mu barsu." Kallonta duk sukayi sai Aba daya girgiza kai ya juya yana fad'in "Allah ya shiryaki Her." Dariya tayi tace "Ameen Aba Fadu." Shima kallon Umma yayi yace "Duk da haka dan Allah ki mana alfarma d'aya ki kwana anan." Murmushi tayi ta kallesu tace "Ni ba shaid'an bace, zuciyata na da taushi, ba komai zanyi yanda kuke so." A tare duk suka fad'i "Mun gode." _______________ Bata jima da zama ofishin ba Aminu ya shigo da wasu takardu a hannunshi, saida ya zauna ya tura mata takardun gabanta yace "Suna d'auke da bayanan komai na had'a." D'an turesu tayi gefe ta kalleshi tana kuma kallon ordi. d'in dake gabanta tace "Akan me matsalar tace?" Gyara zama yayi yace "Wani yaro ne dake universit茅 a Niamey ya kad'e wata yarinya da mota, da fari hukunma ta tabbatar yaron a cikin maye yake kuma yake tuk'i da rana a gangaci, amma daga baya sai aka canza rahoton zuwa cewa ya samu matsalar birki ne, wanda jami'an da kansu suka duba motar suka bayar da rahoton, mutuwar yarinyar ne ya jawo tashin zancen inda wani yayanta ya tsaya kai da fata sai an bi mata hakk'inta, duk da iyauenta dai suna cewa abar maganar, amma shi yayan nata da kuma abokinshi wanda nima abokina ne shine ya dage akan hakan, shine ya kira yake fad'a min na taimaka na musu wannan alfarmar, amma nasan ke zaki iya aiwatar da komai, dan na yarda dake." Tana cikin daddana ordi. d'in tace "Shikenan zan duba, sai ka ciro min ticket ko?" Murmushi yayi yace "Angama ranki shi dad'e." Murmusawa kawai tayi kuma ba tare data kalleshi ba har ya mik'e, saka hannaye yayi aljihu yace "Munyi magana dasu akan masaukinki..." Da sauri tace "Ka barshi zan kira Mama Aissata, saina sauka acan." D'aga kafad'a yayi yace "Hakan zaifi min kwanciyar hankali gaskiya, dan ba zan yarda ki zauna h么tel ba." Sai lokacin ta kalleshi tana murmushi tace "Wai kishi kake?" Hararanta yayi yace "Da me kike tunani?" Dariya tayi kawai ba tace komai ba ta ci gaba da aikinta, shima dariyar yayi ya juya ya fita, sai dai tana jin yana magana da wani wanda yasa shi sake lek'owa yace "Kina da bak'o Hajiata." Kallonshi tayi sai kawai taji gabanta ya fad'i, irin wannan izinin ne ya nemawa Tagur kwanan baya, ajiyar zuciya ta sauke da k'arfi tace "Ya shigo ciki." Fita yayi hakan ya ba dattijon damar shigowa da sallama, nuna mishi kujera tayi amma sai ya k'i zama, gashi kuma alamu sun nuna mutum ne mai kamala duk da shigarshi bata nuna mai dukiya bane, sake kallonshi tayi tace "Bismillah Baba ka zauna." Girgiza kai yayi yace "A'a Hajia nan ma yayi, ai girmanki ya wuce kina zaune nima na zauna." Da mamakin kalamanshi ta kalleshi, sai kuma ta share tace "Baba zan iya taimaka maka da wani abu ne?" Jinjina kai yayi yasa hannu aljihu ya ciro wasu takardu ya mik'a mata yace "Sak'o ne da babban Elhaj, yace na kawo kuma na tabbatar a hannunki na mik'a shi, daga can gidan redion nan aka min kwatancen gidanki, naje can ban same ki ba sai wata mata ga min kwatancen nan ma shine na zo." Karb'a tayi ta fito da takardar daga enveloppe ta duba, takardar filin da aka bawa Amjad ne sai dai wannan original ce, sam ita bata ma lura da waccen cotocophie ce sai yanzu da ta ga wannan, muryar dattijon ne ta dawo da ita daga dubawar da take sanda yake fad'in "Kuma Elhaj yace idan babu damuwa muje dake ki ga wurin, ki fad'i kalar ginin da kike so a tayar miki a wurin, shago, masana'anta, gida, masallaci...etc." Da mamaki tace "Amma kum..." Bai bari ta k'arasa ba yace "Hajia ki dubi girman Allah ki bani damar da zan faratawa Elhaj rai, wallahi a yanda na fahimta yana d'aukar al'amarinki da girma da mahimmanci, na tabbata zai ji dad'i idan naje masa da sak'on nayi komai daya umarceni, ki taimaka dan Allah kar ki ce a'a." Jim tayi tana ci gaba da mamaki, irin yanda dattijon ya rok'eta tare da had'ata da girman Allah yasa ko shed'aniya ce ita ya ci taji rok'onsa. Wata ajiyar zuciya ta sauke ta d'an d'aga kafad'u tace "Shikenan." Da fara'a yace "Godiya nake Hajia, Allah ya tabbatar mana da alkairi." Mik'ewa tayi ita dai ba tace komai ba, rigar ta cire saida ya fita ta samu ta d'aura lafayarta ta d'auki jakarta da duk takardu masu mahimmanci ta fita, rufe wajen tayi kafin ta nufi inda ta ganshi tsaye, sam ba tayi tsammani a motar zasu tafi ba, amma sai taga ya bud'e mata k'ofar baya ta zuk'ek'iyar motar k'irar Prado, gabanta taji ya d'an fara fad'uwa, shakku ya fara d'arsuwa a zuciyarta da tunanin lafiya kuwa? Sai kawai ta shiga tana ciro wayarta, msg ta turawa Aminu kamar haka _"Bayan minti ashirin ka kira ni, idan ban d'aga ba kayi wani abu._ Tura masa tayi sanda taji dattijon ya shiga mazaunin dreba ya tayar, tvn dake gabanta ta k'urawa ido tana kallo sai dai hankalinta ba anan yake ba, sanyin dake ratsata tana jinshi sai dai baya mata wani tasiri. _____________ Ta gama gyaran gidan tsaf tayi wanka ta shirya cikin riga da siket na kanti tana zauna, manya manyan bokiti ne a gabanta tana duba tsumin humra da tayi na kullacca da wasu sirrikan na wasu itatuwa wanda humra ce ta amare, sallama taji a tausashe sosai amma kuma daf da kamar ana shigowa, amsawa tayi tare da fad'in "Ana zuwa." Ta mik'e kenan taji muryar a cikin gida ana fad'in "Ba buk'ata budurwata, gani ma na shigo." Da sauri ta juya ta kalleshi, baki ta bud'e tsabar mamaki, ido ta zazzaro tace "Kai! Kai ne wai? Me ya kawo ka nan yanzu? Wa ya baka izinin shigowa ciki? Kai baka san halin da zaka iya samun mutnne bane?" Wani shu'umin murmushi ya mata, saida ya k'arasa shigowa ya durk'usa har k'asa yace "... *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 17:17 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _42_ Wani shu'umin murmushi ya mata, saida ya k'arasa shiga ya durk'usa har k'asa yace "Dan Allah yarinya ki aure ni ko na huta, jiya banyi bacci ba ina tunaninki." Ja baya tayi saboda kamar zai rik'e siket d'in ta yayi, harara ta galla masa tace "Bawan Allah anya kuwa baka buk'atar ganin likita, me yake damunka ne wai?" Marairaicewa yayi yace "Ciwon son ki budurwata, kuma daf yake da zama ajalina." Alama ta masa da hannu tace "Mik'e tsaye." Cikin shagwab'a yace "Idan na mik'e zaki so ni?" Wata hararar ta watsa masa tace "Shi so d'in banza ne? Malam mik'e kaji." Tsaye ya mik'e yana kallonta tana kallonshi ita ma, ajiyar zuciya ta sauke tace "Bawan Allah ni..." Bai bata damar k'arasawa ba yace "Ba hakane sunana ba, sunana mijinki, ko ki ce uban yayanki." Nuna shi tayi da yatsa da mamaki tace "Kai! Daga ganin sarkin pawa sai miya tayi zak'i? Ina ce na fad'a maka ni ba ajinka bace." Cike sa shak'iyanci yace "In dau har sarkin pawan ne na gaskiya ai ba zai rasa farauto komai ba." D'an siriri kuma k'aramin tsaki tayi wanda ko gama direshi a muhallinshi ba tai ba ya ma leb'enta wani mahaukacin rik'on da yasa ta yin k'asa da k'arfi da niyyar durk'ushewa, da azama ya rik'o hannunta na hagu ya mik'ar da ita tsaye, saida ya kalli fuskarta yace "Kina ji na da kyau? Karki ganni wani sakarai haka, a rayuwata ina matuk'ar son ganin mace na bani girma, haka Allah ya hallice ni da son girma, ire iren abubuwan nan basa birgeni, zai fi kyau ko da na b'ata miki rai to tsaki da harara karki min su a gaban ido na, dan zan iya kashe ki da mari." Kamar wanda ya gama biya mata karatu sai kuma ya sakar mata baki, a hankali ta bud'e idonta da suka mata jawur suka cika tap da k'walla, kallonshi tayi a ranta tana ayyana irin yanda yau ita ce gaban namiji haka, wanda hakan bata tab'a faruwa ba tun bayan rasuwar mijinta, bugu da k'ari hada mata wani kashedi da ko shi margayi bai tab'a mata ba. Sake kallonshi tayi tana so ta harare shi sai kuma take jin shakkar hakan, sai kawai tayi k'wafa mai k'arfi ta juya zata shige ciki, muryarsa a raunane kamar ba wanda ya bayar da umarni ba yanzun yace "Ke budurwata." Da sauri ta juyo cikin fad'a tace "Malam na tsani a kirani da ke, bana so ka bari kaji." Jinjina kai yayi alamar to yace "Zan daina to, yanzu kawo min kujera wajenki na zo zance." Had'e hannaye tayi alamar rok'o tace "Dan Allah ka rufa min asiri ka fita kaji, dama idon yan anguwar nan a kai na yake, yanzu zasu fara zargin har cikin gida nake shigo da maza." K'ofar fita ya nuna mata yace "Zan fita amma in zaki fito ki same ni?" Cike da k'aguwa tace "To wai a ina ka tab'a ganin anyi zance da safiya haka?" Gyara tsayuwa yayi yace "Shikenan babu inda zanje." Matsowa tayi kusanshi cikin lalami tace "Kana ji? Ka tafi yanzu tunda kaga ina aiki, anjima sai ka dawo nima ina son magana da kai." Da alamar tambaya yace "Kin tabbatar?" Jinjina masa kai tayi tace "Nayi alk'awari." Shima jinjina mata kai yayi tare da juyawa yana d'aga mata hannu, da kallo ta bishi har ya fita daga gidan, ajiyar zuciya ta sauke mai k'arfi tana jinjina kai da tunanin kalar rashin mutumcin da zata gurza masa anjima. ________________ Can cikin Ads ya kaita ya nuna mata filin, sa茂da ta ganshi ido da ido ta tabbatar babban wuri ne kuma da alama ana kula dashi, bugu da k'ari akwai idon jama'a a wurin, sake nuna mata yayi yace "Hajia kinga wuri, kuma Elhaj yace duk yanda kika ce ayi haka za ayi, yanzu kenan wane kalar gini kike sha'awar a tayar a wurin?" Murmushi tayi tace "Eh to baba d fari dai abar maganar yanzu, zan fara tuntub'ar manya na da maganar tukuna, duk yanda mukayi zakuji insha Allah." Jinjina kai yayi cike sa gamsuwa yace "Masha Allah, haka ma yayi gaskiya, duk abinda zakayi yana da kyau ka shawarci manya." Jinjina kai tayi ita ma sanda take ciro wayarta a jaka dake vibration alamar kira, tana ganin sunan Aminu tayi murmushi ta d'auka tana fad'in "Allah sarki Aminu garkuwar Fdauma, kayi hak'uri na tashi hankalinka, wallahi wani abu ne ya d'an so tsoratani." Ajiyar zuciya ya sauke wacce taji saukarta a kunnenta kafin yace "Faduma kina lafiya dai ko ? Wallahi da har zan kiraki na tare dana jira lokacin ya cika ba." Murmushi tayi sosai tana shiga mazaunin da tsohon nan ya bud'e mata tana fad'in "Karka damu, komai daidai yanzu." "Kin tabbatar?" Ya tambaya dan gasgatawa. Cike da tabbaci tace "Sosai ma." Sanyayyar ajiyar zuciya y sak茅 saukewa yace "Ok, zaki dawao yanzu ne?" Cikin taushin murya tace "Eh, gani ma a hanya yanzu haka." "Shikenan sai kin zo." Ya fad'a yana datse kiran, kallon tsohon tayi tace "Am baba, idan babu damuwa nace ku sauke ni a dar el-salam." Da saurinshi yace "Ba damuwa Hajia, ai zanyi farin cikin hidimta miki domin saka alkairin da Elhaj yake mana." Da mamakin kalamansa tace "Ban fahimta baba?" Murmushi yayi yace "Tuwon girma ai miyarsa nama, babban goro sai magogin k'arfe." Ita dai da kallo ta bishi tana jujjuya maganarsa da son kamo zaren, saidai bata fahimci komai b芒 har ya sauketa inda ta bukata sukayi sallama. Tana shiga ta samu damar rubuta sunayen duk wanda take buk'atarsu a kujerun da aka bawa Amjad, sai alka'warin kawo hotunansu domin samar musu da visa. Daga nan ofishin ta koma inda ta fad'awa Aminu duk abinda ya faru yana mata dariya shi kuma, sa茂da lokcain d'aukar Amjad yayi ta tashi ta shirya ta fita. _______________ Cikin rububin yara da taimakonsu Izzadeen ya sulale ya fita, a bayan makarantar ya sameshi kusa da wajen kafintoci, ko da ya isa ya bud'e k'ofar ya shiga yana gaishe shi, amsawa yayi yana kallonshi tare da cewa "Yanzu ya zamuyi Amjad?" Girgiza kai yayi yace "Nima ban sani ba Aba." Matse baki yayi yace "Ko zamuje na kaika wajen Ayyata ne?" Da sauri ya d'aga kai alamar eh tare da fad'in "Dama ranar da muka je da Khairat ban ganta ba." Dariya yayi yana tayar da motar da fad'in "Yau kam zaka ganta." Gudu yayi sosai dan lokacinsu kad'an ne, dan danan kam sai gasu sun isa gidan, bai shiga da motar ba duk da mai gadi ya bude musu babbar k'ofa, da girmamawa mai gadin ya sunkuya yana fad'in "Barka da dawowa Alhaji, sannu da zuwa." Kallonshi yayi yace "Mani, yanzu ni ba mai gidanka bane, ka ganshi nan, magajin gidan nan ne da duk abinda gidan nan ya mallaka." Da sauri ya kalli Amjad yana mamaki, a ranshi kawai yake iya tambayar kanshi garin yaya kuma haka zata faru? Saidai rashin wanda zai bashi amsa yasa shi yin shiru, sai gaishe da Amjad da yayi shima kuma ya giashe shi da ladabi, ciki suka wuce da sallama a bakunansu. Husna da Aisho ne a falon sai Hatimi da gomboy da suke fitowa daga d'akinta, duk kallon k'ofar sukayi tare da amsa sallamar, Aisho ce kawai data sanshi a zahiri tayi saurin mik'ewa ta isa gareshi ta rumgumeshi tana fad'in "Lah! Amjad, kaine a gidanmu yau?" Shima rumgumeta yayi yana tausasa murya da fadin "Ina kwana?" D'agowa tayi tana fadin "Lafiya lau Amjad, ina Ayyanka?" D'aga kanshi yayi ya kalli Tagur dake tsaye gefensu yana kallonsu, cike da tsiwa da rashin mutumci Gomboy ta matso tana fad'in "Ke wane yaron ne kuma kika tarkato mana?" Kallonta tayi saidai kafin ta bata amsa Tagur ya nuna kanshi cikin harshen tubanci yace "Gomboy d'an nawa ne tarkace? Ke mahaukaciyar ina ce? Baki ga tare muka shigo ba?" Sarai ta san komai kuma da gangan tayi dama dan Husna ta samu tabbaci daga gareshi, juya kai tayi alamar kai ka sani d'in nan ta shiga taunar cingam (chewing-gum). Tunda ya fad'i kalmar d'an nawa ta shiga rarraba ido tsakanin Amjad da shi da kuma Hatimi, kama hannunsa yayi ko a jikinshi ya nufi wurin wurin Hatimi dashi yana fad'in "Kaga Ayyata nan." Kallon fuskar tsohuwar yayi da ita ma take kallonshi, ta kasa d'auke idonta daga kan yaron sakamakon k'aunar shi da taji lokaci d'aya ta durkaki zuciyarta ta ratsa duk wata gab'a da sassa na jikinta ta gauraya da jini da tsoka, tunda take da Ridwan bata tab'a jin ko da kwatankwacin haka a tare dashi ba, tambayar data jefawa kanta ita ce *"Miye na musamman a tare da wannan d'in?"* Bata tsaya b'ata lokaci na wajen samo amsar tayi saurin shafa kanshi, murmushi ta masa tace "Amjad, kana lafiya?" Da murmushi shima a fuska ya amsa da "Lafiya lau Mamie, ina kwana?" Fad'ad'a murmushinta tayi ta kalli Tagur tace "Daga makaranta ka d'auko shi ne Tagur? Naga kayan makaranta a jikinshi." Kai tsaye yace "Eh Ayya, yace yana son ganinki ne ni kuma na kawo shi." Sak茅 kallon Amjad tayi ta rumgumoshi jikinta ta lumshe ido, sanyayyan numfashi ta sauke tana sake shak'ar siririn k'amshin turaren dake bayan kunnenshi zuwa wuya, sake dagowa tayi tana kallonshi tana jin kamar ta cinye shi ta huta. Husna da har yanzu kanta ke daure ne tace "D'an ka kuma?" A saninta dai lokacin da ake fasa aurensu an zo da maganar ya wa yarinyar ciki, amma tnnda shi yace ba nashi bane sai aka watsar da zancen kuma, to shi kuma wannan daga ina ya fito? Tambayar dake mata yawo kenan. Saida ya harareta yace "Eh d'ana ne, ko da magana ne?" A hankali ta girgiza kai alamar a'a, murmushi Hatimi tayi tace "Karki damu Husna zan miki bayani daga baya." Kallon Aisho tayi tace "Aisho ki kawo masa wani abu ya ci mana?" Da sauri ta mik'e tana fad'in "To Ayya." Da harara gomboy ta bita sai Amjad da yayi saurin cewa "A'a dada ki barshi, na k'oshi ma, komawa zanyi yanzu kafin lokaci yayi." Kallonshi duk sukayi sai Tagur da yace "Hakane Ayya, lokacin komawarsu yayi." Da k'yar ta rabu dashi ko zama basuyi ba Tagur ya jashi zuwa waje saboda lokaci yayi musu. Har waje ta bisu tana rik'e da Amjad tana tambayar yaushe zai dawo, dukansu amsa d'aya suka bata cewar "Zan dawo." Bata gushe daga nan ba har saida taga b'acewarsu daga layin gaba d'aya kafin ta koma ciki cike da so da k'aunar yaron da a baya tana d'aya daga cikin wanda ta sake kambama al'amarinshi suka k'i karb'a, kuma itama hakan ya sake assasa ne daga zugar da d'an uwan mijinta ya dinga mata Alhaji Bureima. Ko da ta shigo ta samu Aisho har ta fara ma Husna bayani, a rikice a kuma gigice ta kalleta tace "Kuma da kanshi ya amsa cewa nashi ne yanzu?" Gomboy ce tace "Da kanshi mana, wani ne zai amsa mishi dama." Kallon Hatimi tayi data shigo yanzu tace "To amma Ayya ya makomata ni kuma? Kinfi kowa sanin ina so na auri Tag." Matsawa tayi kusanta ta dafata tace "Na sani mana Husna, kuma wannan burin insha Allahu zan cika mik shi, ki kwantar da hankalinki kinji." Share y'ar k'wallar data taho mata tayi tace "Shikenan Ayya, amma dan Allah kada ku bari su Hajiata su san da maganar nan, ko da zasu sani dai a bari har bayan aurenmu." Daddab'a kafad'arta tayi tace "Karki damu kinji, ki kwantar da hankalinki b芒 zasu sani b芒." Da kallo gomboy ta bisu tana jan tsaki da tunanin wata hanyar ta sak茅 ruguza Tagur da tsatsonshi. ********************** ⬇ ************************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** ________________ Sanin babu kowa a gidan yanzu yasa shi dawowa, kai tsaye b'angarenta ya nufa, yana zuwa bai nemi izini ba ko yin sallama kawai ya tura k'ofar tare da shigar da k'afafunshi, da sauri ta juya dan ganin wanda ya shigo mata d'aki haka. Rasa katab'us tayi saboda ganin Mujaheed ne, gashi rigar baccin nan ce jikinta har yanzu kuma tana cin abinci, duk da dai ba sosai tasan ciwon kanta ba amma taji ba dad'i, saida ya kawo tsakiyar d'akin sannan yayi sallama, sai tayi shiru kawai bata amsa mishi b芒 ita ma, kan kujerar zaman mutum uku take, kuma a haka ya zauna kan kujerar shima ya gyara zamanshi yanda yake kallonta sosai. Sunkuyar da kanta tayi bata kalleshi ba, cikin sanyin murya yace "Madam antashi lafiya?" Fuska a had'e tace "Lafiya lau." K'ofar d'akin ta ya kalla yace "Har ya fita ne?" Da kai kawai ta amsa mishi da eh, jinjina kai yayi yace "Naji wai Umma ta tafi Alg茅rie?" Cikin mak'oshi ta sak茅 amsa mishi da "Um." Girgiza kai yayi yace "Yanzu saboda Allah Saudat in har gidan nan ana d'auka ta kamar kowa, kina ganin ya dace Umma tayi tafiya ban sani ba?" Cire hannunta tayi daga dambun da take sank'ara ta kalleshi tace "Bai dace ba, amma naga ai kai ne baka shiga sabgarsu." Wani murmushi yayi ya juyar da kai kawai bai ce komai ba, sake kallonta yayi yace "Kinga ni ba wannan ne ya kawo ni ba, wani abun arzik'i na zo miki dashi." Da mamaki ta kalleshi tace "Abun arzik'i kuma? To ina jinka." Sake gyara zamanshi yayi da kyau yace "Zaki iya tuna kampanin madarar da aka bani a cikin gadona?" Jim tayi sa茂 kuma ta d'aga masa kai alamar eh tare da cewa "Na tuna, wanda yake nan kusan mjc." Jinjina mata kai yayi yace "Yawwa shi, to kinsan na canza ginin wurin nasa aka min restaurant, to yanzu haka angama komai da komai ma'aikata ne da zasuyi aiki wurin muke nema, shine nace bara na baki wannan contrat d'in kinga kema zaki k'aru." Da mamaki ta kalleshi tace "To abinda ban fahimta b芒 shi ne, kamar kana so ni na samo maka ma'aikatan da zasuyi aiki a wurin?" D'aga kai yayi tare da fad'in "Hakane, kinsan harka yanzu duk yi min in maka ne, ko yan uwa gareki duk zaki iya kawosu kinga duk za'a k'aru da juna ai." Shirun da tayi kamar abun bai shigeta bane yasa shi saurin cewa "Kema idan kin iya wani abun ai zan iya d'aukarki aiki." Kallonshi tayi tana dariya tace "Gaskiya ba zan iya aikin wahalar nan ba, kuma ma na tabbata Bab b芒 zai barni ba." Hararanta yayi yace "Ke kuma saiki biye mishi duk abinda baya so kema ba kya so, kinfi so komai sai ya miki da kanshi, mota wannan ta hawa ya kasa siya miki ki murza da kanki." Ai kuwa ya sosa mata inda ke mata k'aik'ayi sai kawai ta girgiza kai tace "Shi fa wannan d'an uwan naka har yanzu yana abu ne kamar bai waye ba, da nayi maganar mota sa茂 yace ba yanzu ba, har yanzu d'in ba tayi b芒 bare ya siya min." Da kallon makirci ya bita tare da fad'in "Kinga kuwa akwai wani aiki da zaki min nan gaba, da zaki min shi wallahi saina siya miki motar da duk kike so." Zaro ido tayi baki bud'e tace "Mota fa? Kai zaka siya min?" D'aga kai yayi yace "To miye a cikin mota, ke kinsan kuwa waye Hasheer? Wallahi Saudat mijin nan naki b'oyan kurwa yake miki baya so ki gane waye shi, amma ba k'aramin hamshak'in mutum bane, ya tara k'azaman kud'i fa nake gaya miki." Tab'e baki tayi ba tace komai ba sai d'orawa da yayi da cewa "Kinga yanzu zaki samo min mutanen?" D'aga kafad'a tayi tace "Eh to zan bincika maka mu gani ko za'a dace." Dariya yayi ya mik'e yasa hannu aljihu ya ciro kud'i ya mik'a mata yace "To ga wannan yanzu sai kisa kati ki kira mutanen ko." Zaro ido tayi tasa hannu ta karb'a tana fad'in "Duka wannan?" Gurgiza kai tayi tace "Wannan ai ba wani abu bane." Murmushi tayi tace "Nagode, insha Allahu za'a samu." Gyad'a kai yayi ya fita bai sak茅 cewa komai. ______________ Sanda taje ta d'auke shi bata ga wani canji b芒 daga gareshi daya wuce farin cikin da take iya hangowa a tare dashi, sa茂 kawai bata damu ba suka wuce gida kamar yanda suka saba. Da yamma ankirata a waya kiran da zata iya kiranshi ma-kafin tarihi a gurinta, dan saida suka gaisa take fada mata idan tana da dama ta zo gidansu ta same ta zuwa gobe, har tace zata je sai kuma Umma tace a'a taje aikinta, kasancewar tun a cikin gaisuwarsu da farko take fada mata tana shirin tafiya da safiya, saida Herde tasa baki kafin ta yarda zata je aikin, amma b芒 hakan ta so b芒 duk da dai bata san dalilin kiran ba, amma tafi zaton alkairi ne insha Allah. *Da dare* Aminu ya zo gidan ya kawo mata ticket d'in kamar yanda ta buk'ata, hakan yasa ta kwanta bayan ta gama duk shirin tafiyarta tsaf tare da tunanin barin Amjad hannun dada sai Aminu daya mata alk'awarin kulawa dashi har taje ta dawo. ______________ Tunda y'a shigo gidan ya ga babu wani canji sai ma k'ara hargitsewa sakamakon yaran yau suna nan tare da ita saboda rashin lafiyarta, saida ya d'aga k'afarsa sannan ya tsallaka farantin da yaran suka ci abinci kafin y'a wuce, kusanta ya karasa y'a sunkuya ya... *Allah abun godiya, Allah nagode maka, masoya ma ina godiya gareku, duk batun alkairinku a kaina y'a riskeni, naji dadin tunaninku a kaina, sai dai ina godiya ga jajirtaccen shingena, duk sa saida aka horani amma wannan b芒 komai bane face wani darasi mai zaman kansa, Allah ya barmu tare.* *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 17:18 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _43_ Sunkuyawa yayi y'a sumbaceta a goshi tare da d'agowa ya d'an zauna kusanta, kallon ta yayi ya sake kallon d'akin, a ranshi yake jin tausayin kanshi sosai dan samun cikin nan nata sake tab'arb'arewar al'amuranta ne, ko bata laulayi haka take zama tana kafawa k'azanta wurin zama da gindiya hujjar cewa ciki ne da ita, wannan dalilin na d'aya daga cikin dalilin da suka saka shi cika dare yau din, dan yasan ko ya zo ba wani abun birgewa da zai tarar. Marairaicewa tayi ta kalleshi tace "Sannu da zuwa Bab." Da matsakaitan idonshi kawai ya amsa mata tare da d'an kawar da kanshi, ajiyar zuciya ya fara saukewa kafin ya sake kallonta yace "Ina yara?" Saida ta yatsina fuska tace "Sunyi bacci." Wata ajiyar zuciyar ya sake saukewa yace "Ya jikinki?" Shagwab'ewa tayi tace "Uhumm! Babu dad'i, ni wallahi yau sha'awar hawa mota ma cikin nan ya saka ni." A hankali ya karkato ya kalleta, sai kawai ya d'anyi murmushi ya d'auke kanshi yace "Wani ya zo gidan nan ne yau?" D'agowa tayi daga jikin kujerar tace "Ban gane ba? Me yasa kake tambaya?" Girgiza kai yayi ya yunk'ura a hankali y'a mik'e, d'akinshi ya nufa sai ita ma ta mik'e ta bi bayanshi tana fad'in "Bab, wai dan Allah me yasa ba zaka siya min mota ba? An fad'a min fa kana da kud'in nan ba wai baka da su ba." K'ala bai ce mata ba sai ma cire kayanshi daya shiga yi yana kuma k'ok'arin kiran wayar Umma, yana jin an d'aga yayi saurin jefa rigarshi daya cire kan sofar dake kusa da kofar shiga ban d'aki yana d'ora wayar a kunne da cewa "Umma na." Daga b'angarenta ta amsa da "Hasheer bawan Allah, Hasheer sarkin hak'uri ya kake?" Sanyayar ajiyar zuciya ya sauke yana shafa kanshi yace "Umma na bana da lafiya, kinyi nesa damu na tsawon kwanaki, gashi kuma bansan yaushe zaki dawo garemu ba." Murmushi Umma tayi tace "Kwantar da hankalinka Hasheer, yanzu haka ina Zinder sab'anin na kasance a Niamey kamar yanda kuka sani." Da sauri ya zaro ido yace "Umma Zinder kuma? Amma ya akayi kika je can? Me kika je yi a can kuma Umma?" Cikin taushin murya tace "Hasheer, wani muhimmin aiki ya kawoni nan, bana ce na gama ba dan ina da burin ganin komai ya daidaita, amma dai insha Allah komai ya kusa zuwa k'arshe, kuma na maka alk'awarin sanar da kai komai da zaran na dawo." Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke yace "Shikenan Umma na, amma ki tabbatar min kina cikin aminci." Murmushi tayi tace "Ina cikin aminci Hasheer, mutanen dana sauka wurinsu suna da karamci sosai." "Shikenan Umma, Allah ya tsare min ke." Da "Ameen." Ta amsa kafin ta tambaye shi yan gida kowa lafiya da sauran yara, daga bisani kuma ya fad'a mata shima da safe zai kama hanyar zuwa Niamey, addu'a ta mishi sosai a matsayinta na uwa tare da fatan sa'a. D'auke wayar yayi daga kunnenshi yana bin k'ofar da Saudat ta bi, tunda ya ambaci sunan Umma na saita fita daga d'akin tana turo baki, abun mamakin da bai gane ba shine, haushin ya katse mata hirar data shigo da ita ne ta haanyar kiran mahifiyarshi da yayi? Ko kuma jin haushin bai kula ta bane ya kawo haka? Rashin samun tsayayyar amsa sa茂 kawai ya juya ya shiga ban d'aki dan watsa ruwa. ________________ Kiran Tagur ne ya tashe shi da safiyar nan da budurwar dake gefenshi ko motsawa basuyi ba, a kasalance ya d'auka ya kara a kunne cikin magagin bacci yace "Hello!" Da sauri Tagur yace "D'an rainin hankali kana nan kana baccin na asara ko ? Kai dai Allah ya sawak'e maka wallahi." Tsaki yayi yace "Naji dai, yanzu miye na kirana da safiyar nan?" Da sauri yace "Kasan da jiya na zo da Amjad gidan nan?" Ba tare da bawa abun wani mahimmanci ba yace "Da gaske? A ina ka d'auko shi?" "Daga makaranta mana." Ya fad'a kai tsaye, da sauri ya zabura daga kwancen ya tashi zaune yace "Da gaske? Da kanshi ya biyoka kuma?" Cike da tabbaci yace "Ai shi ya bayar da shawarar yanda ma zamu dinga had'uwa ba tare da sanin mahaifiyarshi ba." Jinjina kai yayi ya d'an cije leb'e yace "Hakan yayi kyau, kaga yanzu ta hakane zaka k'ara samun kusanci da d'anka, sai dai duk da haka zaifi ka samu waya ka bashi saboda kullum ba zai yiwu ku had'u ba, ko ya ka gani?" Jim yayi sa茂 kuma ya yace "Hakane kuma fa, ba damuwa gobe idan mun sake had'uwa zan siya mishi wayar." Da sauri Aji yace "Amma fa ka tabbatar ka siya mishi babbar wayar da zata nuna d'anka d'an gata ne." Murmushi yayi yace "Baka da matsala da wannan Aji, sai anjima yanzu." Kashe kiran kawai yayi da sauri ya shiga neman lambar babanshi, ta jima tana kururuwa ba'a d'aga ba har saida tayi kamar zata tsinke, yana d'auka Aji yace "Aba ina ka shiga ne haka? Ko dai kai ma baka koma gida ba ?" Cikin muryar bacci shima dai yace "Ban kwana gida b芒 Aji, lafiya?" Saida ya gyara zamanshi yace "Haba ko da nace, Aba yau kuma wace kalar hannun ka d'auko?" Cikin fad'a yace "Kai Aji bana son iskanci, zaka fad'a min meke faruwa ne ko na kashe wayata?" Dariya yayi yace "Aba dai ya kamata a fara jin tsoron Allah." D'an tsaki yayi yace "Kaji wai kura ce da ce ma kare maye, kai yanzu nasan wace cikar ce a gabanka ko bayanka." Dariyar shegentaka ya masa yace "Yanzu dai Aba abar maganar nan, kasan me yasa na kiraka yanzu?" "Saika fad'a." Ya fad'a a hankali, a hankali Aji yace "Aba maganar yaron nan na wurin Tagur, yanzu haka fa kaji har ya kaishi gidansu yau, kuma yaron da kansa ne ya sama mishi mafita ta yanda zasu dinga had'uwa, to yanzu dai na ce ya siyi waya babba ya bashi, na tabbata indai Faduma na da hankali zaiyi wuya ace bata ga wayar nan ba da wuri, a lokacin kuma nasan zataji ba dad'i, kaga zata yi k'ok'arin rabasu lokacin ni kuma saina fito da shirina na gaba." Cikin jin dad'i yace "Da kyau yarona, naji dad'i sosai, hakan na nufin mafari ne na k'arshen mutumcin ahalin Sugui kenan?" Girgiza kai Aji yayi yace "Ko kad'an Aba, wannan k'arshen ne, farkon shine samar da Amjad da mukayi, kuskurenmu kawai shine daya fito daga cikin Faduma, amma yanzu wannan karan ba zan rabu dasu ba har sai naga sunan da mahaifin Tagur ya k'wace gareka na siyasa ya sake dawowa gareka a karo na biyu." Da k'arfi yace "Nagode Aji, ka tabbatar min kai d'an halak ne, Allah ya maka albarka." "Ameen Aba." Ya fad'a k'asan mak'oshi, d'orawa yayi da "To yanzu ya maganar waccen d'ayan mai kafirin taurin kai kamar yahudawan farko? Har yanzu yana kan bakanshi ko?" Wani murmushi yayi yace "Aba Elhaj Hasheer duk wani motsinshi akan idona yake, yanzu haka shirinshi na gaba shine tafiya Niamey da zaiyi yau ko gobe, kuma zaije taron bud'e reshen kampaninshi ne acan, sai dai a bayanan sirrin dana samu an tabbatar min da zai had'u da tsohon shugaban k'asa, wanda kafi kowa sanin 'yan jam'iyar adawarmu ne, had'uwa dashi kamar had'uwa da Alhaji Basiru, hakan na faruwa kuma ba makawa saiya mara musu baya, abinda mu ya kamata ya ma mubaya'a." Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi yace "Yaron nan na da matsala, haka lokacin ubanshi na raye ya k'i dangwalawa k'uri'armu, abun takaici kuma shine goyon bayan al'ummar da suke samu duk da basa siyasa, alkairinsu ga mutane yasa suke samun d'aukaka, shiyasa yanzu nake so naga yaron nan ya mana mubaya'a a jam'iyarmu amma ya k'i ko saurarenmu." Cikin nutsuwa yace "Aba kwantar da hankalinka, Hasheer yanzu a tafin hannuna yake, zamu je wani mataki dashi da dan dole yayi abinda muke so." Sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke yace "Naji to, yanzu ya maganar shashashan k'annan naku?" Cikin rashin d'aukar abun da gaske shima yace "Aba maganar Tahir na gama dashi, daga jami'an har zuwa lauyan dana d'auka duk mun rufe bakinsu da tsabar kud'i, ina da tabbacin zamuyi nasara." Cikin jin dad'i yace "Yayi kyau, sannu da k'ok'ari kaji Aji, Allah ya maka albarka." "Ameen Aba, zan kashe waya sai anjima." Sallama sukayi inda dukansu suka sake rumgume yan matan dake kwance gefensu. ______________ Aminu da kanshi ya d'aukota tare da Amjad, makaranta suka aje shi ya fita y'a zagaya wajen Ayyarshi, rik'e hannunta yayi kamar zaiyi kuka yace "Ayya Allah ya kaiki lafiya, karki jima dan Allah ki dawo da wuri." Shafa kumatunshi tayi tace "Insha Allah oddo zan dawo da wuri, ka kula min da kanka kaji." Jinjina kai yayi yace "To Ayya." Kallon Aminu yayi yace "Obdo sai anjima." Jinjina kai yayi yace "To Amjad, saina dawo d'aukarka ko? Insha Allahu zan zo akan lokaci kamar yanda Ayyarka take yi." D'aga kai yayi yace "To mijin Ayyata." Da sauri suka kalli juna da mamaki, sa茂 kuma Aminu yayi dariya ya kalleshi yace "Ka bani Ayyarka kenan?" Dariya Amjad yayi yace "Duk duniya ai banga wanda zan iya bawa Ayyata ba idan ba kai b芒." Tafin hannunshi ya sumbata ya jefa mishi yace "Nagode Amjad, samun k'uri'a daga gareka alamar nasara ce." Da sauri cikin harshen tubanci Faduma tace "Amjad waya aike ki maganar nan? Surutu ko?" Sunkuyar da kai yayi yace "Kiyi hak'uri Ayya." Daga musu hannu yayi yace "Sai anjima Ayyata, Allah kiyaye hanya, ki siyo min abun dad'i." Da kallo ta bishi kawai sai Aminu daya ce "Me kika fad'a masa da kika canza harshe?" D'auke kai tayi tace "Inba ga tsoro ba ka fad'a mana." Murmushi yayi y'a tayar da motar suka fara tafiya yace "Ke inba ga tsoron ba ki fad'a mana." Mak'ale kafad'a tayi tace "Um um, ka daure ka koya kaima." Jinjina kai yayi yace "Ba zan koya ba da kaina, sai dai zan baki wad'anda dole su koya daga gareki." Kallonshi tayi tace "Kamar ya?" Saida ya kashe mata ido yace "Idan mukayi aure kika haifa min yara ai dole su koya a wajenki." Cikin jin kunya tace "Lahh! Kai ma kana wannan tunanin?" Hararanta yayi yace "Faduma waye baya son haihuwa? Musamman dake uwar Amjad, ai in dai zaki dinga haifa min yara kamar Amjad wallahi ko duk sati ne na yarda ki haihu." Da sauri ta rufe fuska tana fad'in "Inna lilliahi wa'inna ilaihi raju'un, ashe duk maza haka kuke, Aminu gaskiya ba kai." Dariya yayi da mamakinta yace "Au na tuba, ayi hak'uri ba zan sake ba." Tab'e baki kawai tayi ba tace komai ba, wata hirar suka ci gaba da yi ya sauketa, saida ya fito ya ga shigarta da tashinsu kafin ya bar wajen cike da mata fatan sa'a. ______________ Duk da bai kwana garin b芒 amma yana shigowa nan gidan ya fara shigowa dan gaishe da iyayenshi, sallama ya shigo da ita a bakinshi da kuma farin ciki, a tare Herde da Hadizey da kuma Umma suka amsa, ganin Ummar ya mantar dashi komai ya k'arasa da mamaki yana fad'in "Uwarmu, ke ce a gidanmu? Ikon Allah." Murmushi tayi cikin nutsuwa tace "Ni ce da kaina d'an albarka, dama nan ne gidanku? Lallai ikon Allah." Da sauri Hadizey ta d'ora mishi kujera ya zauna suna fuskantar juna, gaisawa sukayi sosai inda y'a d'ora da fad'in "Uwarmu yaushe kika zo nan? Elhaj d'in ne ya kawoki?" Girgiza kai tayi tace "Jiya na shigo da rana, kuma tun jiya na so komawa amma suka hana, Hasheer kuma bai ma san na zo nan ba sai daga baya." Da mamaki a fuskarshi yace "To uwarmu lafiya dai ko?" Herde ce tayi saurin cewa "Ashe kunsan juna?" Kallonta yayi da girmamawa yace "Ayya ba kinsan Elhaj Hasheer ba? Abokina kuma mai gidana?" Da sauri tace "Eh eh..na gane." "To ai mamansa ce." Ya fad'a da ladabi, ai fa sai sabon al'ajabi da farin ciki ya tashi da k'arawa juna sani, har suka fad'a mishi abinda ya kawota wanda hakan ya masa dad'i fiye da kowa. Aba ne yayi sallama dan ya dawo suyi ban kwana saboda tace zata koma da tayi sallah azahar, shima zaune yayi da aka fad'a mishi yana jajanta abun, har saida ya kalleta yace "Hak'ik'a alkairinku garemu ya wuce mu gode muku da baki, ni da iyalina a shirye muke da yi muku duk abinda kuka nema a ko yaushe ne." Murmushi tayi tace "Zumuncin daya k'ara k'ulluwa ma wannan kad'ai abun farin cikin m没 ne, Allah dai ya k'ara mana fahimtar juna, ya kuma shirya mana yaaranmu." Amsawa sukayi da Ameen, dama kayanta a shirye suke dan haka ta mik'e tace zata wuce, duk mik'ewa sukayi inda Kalli yace shi zai kaita, har k'ofar gida suka rakata suna binta da addu'a kala kala har suka tafi, juyowa Aba yayi ya kalli su Herde yace "Wallahi ba dan ban san ra'ayinsu akan abinda zuciyata take raya min ba, da nayi wani abu da ni dai zai sani farin ciki." Herde ce tace "Kamar me kenan malam?" Kallonta yayi yana murmushi yace "Kamar ba wa d'anta auren Faduma, dan gaskiya kamalar mutanen ta birgeni." Duk jinjina kai sukayi alamar gamsuwa suka koma ciki. ______________ 04:45 suna jin k'amshin shiga cikin garin dan baifi minti talatin zuwa arba'in b芒 su k'arasa, da sauri ta ciro wayarta dake vibration alamar kira, tana dubawa taga sunan Mama Aissata, d'auka tayi sai dai gabanta fad'uwa yayi saboda yanda taji muryar matar, cikin yanayin alhinin nan take fad'in "Faduma dama na kiraki ne na fada miki Allah ya yiwa mahaifina rasuwa yanzu bayan sallah la'asar, gashi kuma ni har na zo garinmu bansan ya zakiyi ba kuma yanzu." Cikin jimami tace "Ayyah sannu Mama Aissata, karki damu ba komai zan nemi wani masaukin, Allah ya jik'ansu da rahama." Cikin dakusashiyar murya tace "Ameen, da zaki iya sai kije gidan sai dai ba zkaiji dad'in zama ba tunda daga ke sai samarin gidan." Wani murmushin takaici tayi tace "Ba komai mama Aissata zan samu wani wurin insha Allah, dama bamu k'araso ba har yanzu." "Shikenan Allah ya kawoku lafiya." Da "Ameen." Ta amsa suka katse kiran. Ajiyar zuciya ta sauke tare da tunanin abunyi,k'arshe kawai shawara d'aya ta yanke ita ce idan ta sauka zata shiga taxi saita nemi mai taxi daya kaita wani matsakaicin masauki mai tsaro da rashin hayaniya. ________________ Sun idar da sallah azahar har Kalli ya dawo daga rakiyar Umma mota ta tsaya k'ofar gidan, a tak'aice dai iyayen Aminu ne kuma sun samu tarba ta musamman dan dama Owwo ta sanar dasu zuwansu, duk da dai maza ne kuma maganar maza sukayi ta manya, inda suka tsayar d'脿 magana d'aya ta auren Faduma da Aminu wanda shima aka taho dashi suka ganshi ya gansu. Tunda an samu amincewar duka yara yasa Aba yace ba buk'atar jan lokaci da kuma wani tsarabe tsarabe, sadaki kawai shi dai daga gareshi yake nema, lefe kuma yaro ruwansa ya mata tun ananko kuma sai taje gidansa. Da haka zaman nasu kowa yayi farin ciki aka watse bayan Aba ya karb'i sadakin Faduma a wurin mahaifin Aminu jaka d'ari cas lakadan ba ajalan ba inji hausawa. Sati uku kawai suke jira yayi su d'aura musu aure komai ya wuce. ________________ 05:31 cip suka sauka ta fito bakin titi dan neman taxi, watak'ila ko dan magribata ta gabato kuma ranar aiki ce yau yasa kusan duk taxin da suke wucewa da mata a ciki ko yara yan makaranta, saida ta d'an fara takawa saboda ta ragewa kanta tsayuwar, ta sake tsayawa kenan zata d'aga hannu wata bak'ar honda rav4 ta tsaya gabanta, rashin ganin waye a ciki da kuma jin haushi yasa ta dallawa gilashin motar harara da aka rufe da bak'ar leda, matsawa tayi gefe dan neman taxin ta, bud'e k'ofar akayi aka fara zuro wasu jajayen k'afafu masu d'auke da takalmin kampanin clarks England, saida ya gama fitowa kafin ta fahimci waye, fad'uwa gabanta yayi sosai tare da jin k'afafunta sunyi wata mijirya lokaci d'aya, k'asa tayi da kanta tana fad'in "Me kuma ya kawo shi nan? Ko dai aljani ne? Ko kuma *bibiyata* yake yi?" Sanyayyar muryarshi marar hayaniya da kwaramniya ce ta daki kunnayenta yana fad'in "Hajaj barka da tsayuwa." Saida ta fara bud'e bakinta kafin ta d'aga kanta ta kalleshi, saurin kawar da kanta tayi saboda kwarjininshi, cikin sark'ewar murya tace "Da girman kujerarka ranka shi dad'e." Lumshe ido ya d'anyi na lokaci kuma ya bud'e, idonshi k'ar a kanta yace "Ban tab'a sanin cewa ke mafad'aciya bace sai yanzu, ko me mota ta tayi miki da kika zabga mata harara irin wannan?" Da sauri ta kalleshi a ranta tace "Lahh! Ashe ya gani." Amsar daya bata cewa "Na gani, kuma jira nake naji hararar nawa ce kika mana?" Yar dariya tayi wacce ta d'auki hankalinshi har ya bita da kallo, sosa gaban goshinta tayi tace "Eh to, da yake hararar babba ce nayi, darajarta ta wuce muyi lissafinta a hanya." K'aramar ajiyar zuciya ya sauke a hankali yace "Me kika zo yi anan? Yaushe ma kika zo? Me kuma kike jira a tsaye?" Wurga idon da tayi ya tabbatar mishi bata so tambayar ba, d'an muskutawa yayi ya gyara tsayuwarsa ya soka hannayenshi aljihu yace "Ina zaki je yanzu?" A d'an k'ufule ta kalleshi sai dai ba yanda zai gane ba tace "Zanje masauki na ne, ina jiran taxi ne." Da idonshi ya nuna mata motar yace "Muje." Girgiza kai tayi tace "Nagode, zan samu abun hawa ma." Sake gyara tsayuwa yayi yace "Ina wasa dake ne?" Kallonshi tayi saita kasa yi masa gardama, turo baki kawai tayi tana d'an gunguni, cikin taushin murya yace "Me yasa kika zage ni?" Cak ta tsaya daga haramar tunkarar motar, kallonshi tayi ido da bakinta duk a bud'e kamar dai babba ya fad'i abinda hankalin yaro y'a kasa d'auka tace "Lahhh! Yaushe nayi zagi kuma? Ni wallahi ban ce komai ba, ka dinga fad'in gaskiya mana." D'aga mata gira yayi da mamakin kalamanta, wani d'an murmushi ya saki kawai ya bud'e mata kofar, saida ta zo daf dashi zata shiga ta tsaya, nuna shi tayi da yatsa kamar yarinya tace "Ka rantse min da Allah ba zaka siyar dani ba? Kaga fa nan garin ba garina bane." Dariyar da kawai bai shirya mata bace ta kubto ta sanyo mishi kai, ba komai ya bashi dariyar ba sai cewa da tayi ya rantse, kallonta yayi ya girgiza kai yace "Ba zan siyar dake ba, sai dai zaki biyani kud'in dako na har da na waccen ranar." Murmushi tayi ta girgiza kai tana shiga tana fad'in "Wannan ba dai son kud'i ba." Saida ya shiga ya zauna da kyau ya rufe motar, Qaseem ne ya juyo yace "Hajaj barka da yamma." Da yar fara'a tace "Barka malam." Bai sake cewa komai ba daga haka, can k'asa k'asa sosai taji muryarshi yana fad'in "Duk son kud'ina ai bai kai naki ba, tunda har yanzu kin k'i biyana bashi na." Murmushi tayi tace "Zan biya sai sunyi yawa." A tausashe ya sake cewa "Ina zamu aje ki?" Marairaicewa tayi tace "Duk masaukin da kuka san zai iya d'aukar mummanar 'yar lukuta kamata, ku aje ni acan." Da mamaki ya kalleta yace "Ban gane b芒? Baki da wajen sauka ne zaki sauka h么tel?" D'aga kai kawai tayi alamar eh, d'auke kallonshi yayi daga kanta bai ce komai ba tsawon minti biyu zuwa uku, a hankali ya sak茅 kallonta yace "Kinsan g茅n茅ral *Wardugu*?" Da sauri ta kalleshi tace "War? Na san shi mana, ai ina son shi sosai wallahi." Zaro ido yayi yana mata wani bahagon kallo yace "Kina son shi kuma?" Da yatsunta ta dinga nuna tana fad'in "Eh..ina nufin yana birgeni, ina son aikinshi da k'ok'arinshi akan k'asarshi, sannan kuma yarenmu d'aya." Ajiyar zuciya ya sauke tare da furzo iska waje, a hankali yace "To gidanshi zan kaiki ki zauna, zaki fi samun kulawa da tsaro acan, sannan ni kaina zan fi samun nutsuwa." Da sauri tace "Me ka ce?" Jim yayi sai kuma ya girgiza kai alamar ba komai, tab'e baki tayi alamar oho ita ma, cikin sanyin murya tace "Kawai ka saukeni wani wurin, ba zan d'orawa kowa nauyi ba." Kallonta yayi ba alamar wasa fuskarshi a d'aure yace "Wannan maganar mun gamata, zaki sauka acan haka na so kuma za ayi." Yanda ta tsareshi da ido tana mamakin k'arfin haalinshi, duk da dai ya birgeta dan tana son namiji haka, amma kuma ai baya da wani iko akan ta. Jin har yanzu idonta na kanshi ne yasa shi sake kallonta, saida ya fuskanceta da kyau cikin wani irin yanayi yace " *Batuuuul*, ki daina kallona haka kinji, zuciyata na da rauni sosai." Yanda yaja sunan nata da yanda shine farkon daya tab'a kiranta haka y'a mugun birgeta, ga kuma rashin fahimtar zantukanshi da batayi ba, k'asa tayi da idonta cikin shagwab'a tace "Shikenan na daina kallonka, ai na fahimci komai." Da sauri ya kalleta yace "Me kika fahimta?" Kawar da kanta tayi ta sauke ajiyar zuciya tace "... *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 17:18 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _44_ Kawar da kanta tayi ta sauke ajiyar zuciya tace "Nasan idona ne ke tsorata ka, shiyasa baka son ina kallonka." A hankali ya sauke ajiyar zuciya a b'oye, saida yayi kamar ba zaiyi magana ba sai kuma yace "Akwai wani abun al'ajabi ne a tare dasu." Shiru tayi ba tace komai ba kuma bata kalleshi ba, saida ta tabbatar da gaske yake ta kalleshi idonta taf da k'walla tace "Dan Allah babban mutum na rok'eka karka kaini gidan mutane, zan je na nemi wani masaukin." Tunda ta fara magana ya k'ura mata ido yana kallon k'wayar idonta dake ta rawa tana son sako hawaye, ita ma ganin yana kallonta yasa ta jan majina a hancinta tace "Dan Allah fa? Kaji." Da sauri ya d'auke kanshi yana a'uziyya a cikin ranshi sakamakon abinda shed'an ke hasko mishi a game da bakinta, saidai ya ci alwashi duk randa igiyar aure ta d'auresu a inuwa d'aya, to tabbas kafin ta tare dakin shi saiya fara saka hannayenshi biyu ya tallabo fuskarta ya saka bakinta a nashi bakin ya masa tsutsar tom-tom a sanda yake matsananciyar murar dake saka hancinshi yin jajajir. Ganin bai kula ta ba kuma ita hankalinta bai kwanta b芒 sai kawai ta fashe da kuka tsakaninta da Allah, da sauri ya juya ya kalleta har da Qaseem dake tuk'i, yanda take lab'e baki take murza idonta da hannaye ta bude muryarta sai ma ya rasa me zaiyi, dariya? Ko kuma ya fito mata da jajayen ido ne? Girgiza kai kawai yayi yana ci gaba da kallon bakinta dake d'auke da fararen hak'ora tas, a hankali ya furta "K'uruci dangin hauka." Tab'e baki yayi ya jingina a kujerarshi yana kallon titi, basu tsaya ko ina ba kam sai unguwar a茅roport, a tabkeken gidan da suka tsaya mai tarin jami'an tsaro a k'ofar kad'ai saida ya kayar mata da gaba, kasancewar shigowar g茅n茅ral kenan daga tafiya yasa kofar gidan zuwa cikin farfajiyar ya zama kamar wani filin daga, kuma hakan ya samo asali ne saboda rakoshi gida da sukayi sannan suna kusa da filin jirgi. Yanda jam'ian dake k'ofar suka gaisa da Hasheer da yanda suka basu hanya suka shiga ciki ya tabbatarwa Faduma lallai akwai amintaka da sananya sosai tsakaninsu, a farfajiyar suka tsaya wnada yasa ta dole ta dakatar da kukanta, kallon gidan ta shiga yi zuwa sojawan da suka shiga mota biyu suka bar gidan da gudu bayan sun sara ma wanda shine g茅n茅ral d'in. Cikin gamdakatar ya juyo sai kuma idonsu suka had'e dana juna, wata mummunar fad'uwa gabanta yayi tare da jin murd'awar ciki wanda y'a haddasa mata jin mahaukacin fitsari, da sauri ba tare da saninta ba tayi ram da damtsen Hasheer dake kusa da ita, mamaki ne ya kama Qaseem daya fito daga mota, uwa uba kuma Hasheer daya tsaya cak ya juya yana kallonta, hannun nata y'a bi da kallo, d'an girgiza kai yayi ya mayar da kallonshi kan War. Takawa yayi da niyyar tafiya amma Faduma na rik'e dashi, sake kallonta yayi cikin taushin murya yace "Shine fa, War, ko baki tab'a ganinshi bane?" Girgiza kai tayi tace "Dan Allah ka d'aukeni daga nan zan sake wuri, ba zan iya zama gidan nan ba." A hankali yace "Me yasa?" Sai lokacin ta d'aga idonta ta kalleshi, a ranta ta maimaita tambayar "Me yasa ma yake tambayata?" A hankali ta sake satar kallon fuskar Wardugu, gashi dai fari tas dashi amma wallahi fuskarshi babu annuri na hasken murmushi bare ka kawo masa wasa, gashi wani gabjejen k'ato tubarkallah, amma duk da haka bai b'oyuwa a ido ka gane fatar jikinshi mai laushi ce tsabar hutu da jin dad'i da kuma kula da kai. Takowar da War ya fara zuwa garesu ne tasa ta janye hannunta daga Hasheer ta sake komawa bayanshi sosai, yana k'arasowa ga mamakinta yanda ba tayi tsammani ba sai gani tayi sun rumgumi juna, wanda hakan yasa suka sake had'a ido da War saboda tana bayan Hasheer ne, sa茂da suka raba jikinsu suka sake musabaha taji wata karyayyar murya kamar ba tashi ba yace "Da baka zo yau ba, da na sameka har can, daka yabawa aya zak'inta." Murmushi Hasheer yayi ya shafa sumar kanshi yace "Sanin waye kai ya isa ya sani yin abinda banyi niyya ba ai." D'an satar kallon Faduma yayi yace "Mugu, yaushe ka k'ara aure banda labari." Duk da gabanta fad'uwa yake amma da sauri tace "A'a ba matsarsa bace." Tare suka kalleta, fahimtar tana jin tsoronshi yasa ya sake had'e fuska yace "To wacece ke" Rarraba ido ta shiga yi tana kallon Hasheer ko zaiyi magana, shi kuma yana yin tsoro da firgicin nata ya birgeshi saiya tsaya kallonta, ita kam yanda War ya tsareta da ido yasa ta sakin baki tace "Ni fa satoni yayi ban san shi." A tare suka kalli juna sai War daya had'e fuska sosai yace "A ina ka d'auko 'yar mutane? Yaushe ma ka fara wannan harkar ban sani ba?" Da sauri Hasheer ya juya y'a kalleta yace "Kinga Batul fad'a masa gaskiya, wannan ba imani ne da shi ba saina kad'aita ubangiji, zai iya saka wa a rufe ni." Duk zuba mata ido sukayi dukansu, sinne kai tayi tana jin kamar tace wayyo ita wayyo kanta, wata sanyayyar murya ce daga bayan mazan ta ceceta daga wad'annan bijimaye tana fad'in "Shine ka dawo tun d'azu ka k'i zuwa inda nake ko? Ni nayi hushi ma." Dukansu suka juya suka kalleta har da Faduma, matashiyar yarinya ce da shekarunsu ba zasu gagara zama d'aya ba, gashi ita ma doguwa kuma da d'an kakkauran jikinta, saidai duk da Faduma na da duhun fata sai taga tafi wannan d'an haske, sai dai wani shan gaba da wannan ta mata shine, fatarta daga nesa ma kawai abar kallo ce, wani mutsu mutsu take da shek'i da kuma wani walwali mai birgewa, fatar a kwance take sosai da gani kuma kasan akwai laushi da tsantsi. Ga kuma wani bak'in leshe dake jikinta mai kwalliyar kore daya sake fito da kyawun hallita da tsarin fatarta da kuma haibar fuskarta. Tana idasa k'arasowa garesu bata kula kowa b芒 sai wajen Faduma data nufa ta kama hannunta da tsadadden murmushi a fuskarta tace "Sannu da zuwa ko? Sun barki tsaye suna ta miki surutun." Kallon Hasheer tayi tace "Elhaj ya haka? Ka zo da bak'uwa kuma ka barta a waje." Sanyayyan kallo ya watsa ma Faduma, ita ma shi take kallo b芒 ko sararawa, jan hannunta tayi suka nufi cikin gidan tana fad'in "Muje ciki kinji ki huta, kunsha hanya fa." Binta kawai tayi baki sake, Wardugu ne yace "Orronur yanzu nine ko kallo ko? Ai dai nine kika bankad'ar haka? Ba damuwa." Juyowa tayi k'asa da sama ta harareshi tare da juya d'an k'aramin bakinta, murmushi Hasheer yayi dan har zuciyarshi zamansu ke birgeshi, yana fatan samun abokiyar rayuwar da zasu ko da kwatanta irin hakane. Faduma ma kanta saida taji ta birgeta saboda yanda tayi abun. Gogan kam lumshe ido yayi tare da shafa sumar kanshi dake ganin gyara da kud'i, murmushi yayi ya fara takawa a hankali suka bi bayansu, suna shigowa tartsetsen falo Faduma taji bata san ma me zata tsaya kallo ba, komai abun kallo ne a gidan bare d'akin, masu aiki biyu ne ke ta faman gyara wurin cin abinci, d'aya daga ciki ta kalla tace "Ki je mota ki d'auko jakunkunan bak'i." Da girmamawa ta amsa ta fita, Faduma na cikin mamakin yanda suka karb'eta suka shigo a tare, tana d'ora idonta a kansu saida gabanta ya sake fad'uwa, ba dan komai ita d'azu dama ta tsorata da ganin War ne saboda bata tab'a ganin mai irin k'irarshi a zahiri ba, sai kuma yanzu da suka shigo da Hasheer sai taga har tsayinsu ma kusan d'aya, sannan k'irar ta k'arfi ba wani babbanci, illa kawai War k'ananan kana ne a jikinshi, Hasheer kuma bata tab'a ganinshi dasu ba sai ranar data ganshi da kayan sport, shima kuma daga cikin mota ne bata ga ainihinshi ba GABA m d'aya. A hankali ta sauke ajiyar zuciya a ranta tace "Wannan matanku na da aiki, ni kam ina zan iya da k'artin nan?" Tsaye War yayi ya bud'e hannayenshi yana kallon *Agaishat* yace "Ki zo na rumgumeki mana ko naji sanyi a raina." Mak'ale kafad'a tayi tace "Um um, hushi nake dake." D'an yatsina fuska yayi yace "Kizo nace orronur (rayuwata)." Sake mak'ale kafad'a tayi tace "Um um." Zaro mata ido yayi yace "Ni ne um um d'in? Orro ba dai ni ne um um ba? Na kiraki kika k'i ki zo ko?" K'wafa yayi mai k'arfin gaske tare da cewa "Ki zo nan kafin na k'idaya uku." Cikin kukan shagwab'a tace "Zan zo to, amma Wardugu bana son duka, karka dake ni kaji." Wani d'an murmushi yayi yace "Ni ne Wardugu ko? Naji to ba zan dakeki ba, amma wallahi ciki zan miki." Da sauri ta taka ta isa gareshi ta fad'a jikinshi, rumgumeta yayi ya sauke ajiyar zuciya yana fad'in "Ina sonki orro." "Nima haka *sojana*." Ta fad'a kamar zatayi kuka. Tunda suka fara wannan abu Faduma ta saki baki tana kallonsu, Hasheer kam ko a jikinshi sai ita daya k'ura ma ido yana kallonta, murmushi kawai yake ganin yanda take rufe baki dan kunya da kuma zaro ido na mamaki, saida suka rumgume juna ta juya musu baya tana mamaki, juyawa yayi inda zai iya ganin fuskarta yace "Ni ne na satoki ko?" Kallonshi tayi ta girgiza kai, marairaicewa tayi tace "Dan Allah ka barni na tafi, kai da ka zo ka zauna amma banda ni, ba zan iya zama da mutanen da ban sani ba." Saida ya rumgume hannaye yace "K'orafi bai karb'u ba, zama daram anan." Kallonsu War yayi dake mak'ale da juna cikin sanyin murya yace "War karka lalatani mana, miye haka saboda Allah?" Kallonshi War yayi yace "Abinda kake min ne na rama, baka ga komai ba ma." Wani murmushi yayi yace "Kwantar da hankalinka, wannan karan ba anan zan zauna ba." Agaishat ce tace "Ba wannan maganar Elhaj, tunda ya fad'a min zaka zo nasa aka gyara maka d'akin ka." Faduma dai da birgewa take kallon matashiyar, ko ba komai ta birgeta, gashi yanda take magana zai nuna maka buzuwa ce ta usul dan harshenta na gurguri wajen hausar, sannan yanda take fitar da rrrr d'in ma abun sha'awa. Mai aikin ce ta shigo da duka jakunkunansu ta nufi d'akin bak'in da ake ware masa duk in ya zo, dan War baya barinshi ya zauna wani wuri ba nan ba, ganin har da jakarta yasa Faduma da sauri tace "Jakata." Kallonta sukayi sai Agaishat da tace "Za'a kai miki d'aki ne." Nuna Hasheer tayi tace "D'akin da zai zauna?" Da mamaki tace "Eh mana." Juyawa tayi ta kalli Hasheer tace "Ko ba matarka bace?" D'an hararanta yayi cikin mak'oshi yace "Ni na fad'a muku nayi aure ne?" Shima War hararanshi yayi yace "Wannan fa d'an iska ne da kike ganinshi, ba zamu gane gabanshi ba har sai na matseshi." Agaishat ce tace "Kunga yanzu dai magriba ta gabato, kuje kuyi wanka sai muyi sallah, daga nan ma zauna sai muyi hira." War ne ya kalli agogon hannunshi mai kyau yace "Lokaci ba zai ishemu ba, mu fara yin sallah." Juyawa Hasheer yayi ya kalli Faduma yace ma Agaishat "Ki kula da ita fa, dan tace min mijinki take tsoro bata son ko had'a ido dashi." Zaro ido tayi baki bud'e idonta har sun kawo ruwa tace "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Yaushe na fad'i haka? Wallahi kaji tsoron Allah, ka fad'a masa gaskiya kar ka sa ya k'ullaceni." Tunda ta fara magana suke kallonta suna dariya banda War, Hasheer kam nuna kanshi yayi yace "Yanzu nine kike cewa wai naji tsoron Allah?" Rik'e k'ugu yayi ya kalli War yace "Kaji fa wai naji tsoron Allah?" Tab'e baki yayi yace "Indai mata ne ai kad'an ka gani, duk girmanka saika b'ata lokaci wajen bata labarin gaskiya, amma da ka gama sai tace saika rantse da Allah." Agaishat ce tace "To miye a ciki dan kace sai mutum ya rantse? A rantse mana inda gasken ne." Faduma ma turo baki tayi tace "Ni ma ai naga nasiha ce na maka ta kaji tsoron Allah." Jinjina kai yayi yace "Nagode to." War ne yace "Amma ke ba-tuba ce ko?" Jinjina kai tayi tace "Eh yallab'ai." Wata sahihiyar dariya yayi yace "Da kyau, Allah na gode maka, yau gani ga wacce ta iya yarena." Kallon Agaishat yayi yace "Yau mutum saida yaji haushi, kullum kece kika samu su Maryama ku dinga min buzanci a gida, rufin asiri na d'aya ina jin dayawa." Kallonta Hasheer yayi yace "Karki damu Gaisho, muma sai muyi larabci, ai basu iya ba." Cikin jin haushi War ya nuna shi da yatsa yace "Wallahi can kifar da kai ka sak茅 kiranta da Gaisho." K'wafa yayi sai Agaishat da tace "Elhaj fad'a ba komai, ce Gaisho d'in naga mai kifar da kai." Dafe k'irji yayi yace "Yanzu ni kika kunyatar? Haba nagode." Gwalo ta masa wanda yasa Faduma bushewa da dariya, lokaci d'aya taji k'aunar zama da mutunen saboda dad'in sha'aninsu, hak'ik'a akwai fahimtar juna sosai a tsakaninsu. Cikin harshen tubanci ta kalleshi tace " Shuhula hundan dussu, murohi casudu balak, tani unnu indaha nasurde (Rabu dasu, tunda naga ita tana bayanshi, ni yanzu ina bayanka)." Da farin ciki yace "Bidi shikurdunna dudonura, tunda owonni muradu kannurda (Nagode yer uwata, kuma kinga munfi k'arfinsu)." Dariya tayi tana satar kallon Hasheer tace "Unnu owonni yinu tunda hattiri mura bassi (Kuma gashi basa jin me muke fada ba)." Shima hararan Agaishat yayi yace "Ka tagna muro hikti cedde cidi adannura bassi kannurda (Ai ta k'i koyen yarena, amma yarana sun iya)." Ganin Agaishat sai rarraba ido take tana kallonsu yasa tace "Marrat mushi tubusindu hikkuhuri (Watak'ila na koya mata a zaman da zamuyi)." Da sauri Agaishat ta nufeshi tana fad'in "Wallahi ban yarda ba, haka kawai ku saka mu gaba kuna mana yare." Dariya duk sukayi sai Hasheer da har yanzu yake kallon Faduma yana kallon bakinta jin yanda take karya harshen nan yace "Zaki maimaita abinda kika fad'a ne Hajaj." Mak'ale kafad'a tayi tace "Um um." Kiran sallah da aka kwad'a yasa suka ankara, Agaishat ce ta kalli Faduma tace "Muje na nuna miki d'akinki." Har sun nufi hanyar Hasheer yace "Bari zan nuna mata." Juyawa sukayi suka kalleshi, Agaishat ce tace "Kasan inda zan sauketa ne?" D'aga mata gira yayi yace "Ina ne ban sani ba a gidan nan?" Gaba ya wuce sai Faduma data bi bayanshi tana kallon kusurwar da yake shiga da ita, suna shigowa ta wani corridor zasu wuce ya juyo a hankali, bata ankara ba haka bata tsammanin haka daga gareshi sai ji tayi ya rik'e wuyan hannunta ya turata jikin bango, sakin hannunta yayi yasa hannayenshi ya dafe bangon bayanta, hakan da yayi ne ya hanata kowace dama ta numfasawa ma bare motsawa. Gabanta ne ya fara dakan uku uku inda jikinta ya fara d'aukar rawa, kusancin yayi yawa sosai ta yanda taji hawaye sun cika idonta, kasa d'aga ido tayi ta kalleshi sai mutsu mutsu da take da baki, cikin wata dakakkiyar murya yace "Me kuka tattauna dashi?" Cikin rud'anin data shiga da kuma firgici da sark'ewar murya tace "Ni..fa, ba... Komai muka...ce ba... Kkkawai fa..." Kukan data saka ne yasa shi k'ura mata ido yace "Miye na kuka kuma?" Saida ta d'ora hannunta kan k'irjinta sannan tace "Numfashina ke k'wace min...dan...Allah bani iska." D'aga gira yayi y'a janye hannayenshi a hankali har ya matsa daga gefenta, nunata yayi da yatsa yace "Amma fa ki sani sai nasan me kuka fad'a." Cikin jin haushi da tsiwa ta matsa gefe tana nuna shi da yatsa tace "To wai kai meye matsalarka da dole sai kaji abin...." Tsittt tayi sakamakon kallon daya wurgo mata, kallo ne na ruwan sanyi da salama, amma kuma a bad'inance kallo ne da zai kassara gabb'an jikin wanda aka jefa dashi. Sunkuyar da kai tayi ta turo baki tace "Ni bance komai ba." D'auke kanshi yayi yana murmushi ya murd'a k'ofar d'akin da ya tabbatar nan Agaishat zata kawota, da hannu ya mata alama data shiga ta wuce tana satar kallonshi tana kumburo bakin, saida ta zo daf dashi zata shiga yace "Bakin nan yana kusa da fitar da jini." Juyowa tayi ta kalleshi, cike da tabbatarwa yace "K'warai kuwa, Batul naga kin raina ni, ba kya jin wuyar jujjuya min bakin nan mai kama da chocolat." Da mamakinshi ta bud'e baki tana kallonshi tace "Lahhh! Wai kaima haka kake? Ni dama na jima da fahimtar hakan d'abi'ar maza ce." Kallon rashin fahimta ya mata yace "Rashin kunya ko?" Saida ta shiga d'akin ta kama murfin k'ofar tace "Da fitsara ba." Da k'arfi ta rufe kofar tana dariya da sai daga baya kuma ta tambayi kanta ta mecece take? Kallon d'akin tayi wanda babu ce kawai babu a d'akin har da fridge k'arama, alwala ta samu tayi ta fito ta gyara lafayarta ta kabbara sallah. *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 21:37 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _45_ Tana cikin sallah aka k'wank'wasa k'ofar d'akin, jin bata amsa ba yasa mai aikin shigowa tare da jakar kayanta, ajiye mata tayi kusan gado ta juya ta fita, a nutse ta samu ta idar da sallah kafin ta mik'e, cire lafayar tayi kafin ta nufi ban d'aki, sai lokacin ta sake samun damar yi mata kallon tsaf, jinjina kai kawai tayi tana mamakin komai, ba dan Allah ya taimaketa ta tab'a ganin wannan panpon a tv ba da bata san yanda zata kunna shi ba, fitowa tayi ta bud'e drower dake gefe, babu komai a ciki sai towel kala kala manya da k'anana da kuma rigar wanka ta mace data namiji, alamar dai a kowane lokaci shirye suke da bak'i suna kuma maraba dasu. Wani k'aton towel ta d'auko ta warware ta aje kan gado, cikin nutsuwa ta soma cire riga da siket d'in ta har ta gama, d'auka tayi ta d'aura a k'irji, jakarta ta bud'e ta d'auki sosan wanka da sabulu da kuma brush da maclean sannan ta shiga ban d'akin. Ta jima tana wankewa da darjewa tsawon lokaci kafin ta fito, duk da tun shigarta taji wayarta na kuka bai sa ta hanzarta ba, yanzu ma tana fitowa ana sake maido kiran, karasowa tayi ta d'auka tana danna ok saboda ganin Aminu ne, shiru tayi ba tace komai ba sai shine yace "Ranki shi dad'e." A hankali ta zauna bakin gadon tana sauke ajiyar zuciya a hankali, cikin sanyayyar murya tace "Ya kake yallab'ai?" Daga b'angarenshi ya amsa da "Komai k'alau, ina fatan dai kinje lafiya?" A hankali tace "Lafiya k'alau, gani ma har na huta gajiya ina shirin zan fita gidansu yarinyar nan." "Da wuri haka?" Ya fad'a da d'an k'arfi, saida tasa yatsa ta goge ruwan dake girarta tace "Ba fa zama na zo yi ba ko yawan bud'a ido." Ajiyar zuciya y'a sauke yace "Hakane, nima zan so kiyi ki gama dan ki dawo gareni, kinsan fa yanzu kad'an ya rage mu zama miji da mata." Cikin muryar kasala tana lumshe ido tace "Na sani, yanzu dai ka bani minti biyar zan gama shiryawa." Da sauri yace "Ba matsala, ki gaida min mama Aissata." Jim tayi ta kalli bango sai kuma tace "Ba gidanta na sauka ba." A d'an razane yace "Ba gidanta kika sauka ba? To ina kika sauka? Ba dai h么tel ba?" A hankali tace "A'a, ina kan hanyar zuwa take fad'a min mahaifinta ya rasu, nayi tunanin zuwa h么tel saina had'u da wani abokin yaya Kalli, a k'arshe dai shine ya kawoni gidan wani abokinshi na zauna." Da k'arfi yace "Abokinshi kuma Faduma? Ban gane ba?" D'an murmushi tayi tace "Eh abokinshi, ina ga ma ka san shi, ba zaka rasa jin sunan g茅n茅ral Wardugu Marahut ba? Mutumin kirki ne sannan yana da mata." Ajiyar zuciya ya sauke yace "Da sauk'i tunda yana da mata, amma dan Allah ki kula Fadu na." "Insha Allah." Ta fad'a a tak'aice, sai anjima ya mata tare da jaddada mata ta kira Abdu zai taimaka mata kan komai, mik'ewa tayi ta aje wayar ta shiga shiryawa a tsanake, hakan yasa har aka fara kiran sallah isha'i bata gama b芒, tana karasa shiryawa cikin riga da wando kalar shud'i, wandon dama a bud'e yake daga k'asa sai rigarsa k'arama ta ciki da kuma ta sama wacce ta sauko har wuce gwiwa, d'aura d'an kwalin tayi saita ciro hijabi a jakarta tayi sallah isha'i, amma batayi shaf'i da wutri ba ta mik'e ta nad'e sallayar. Cire hijab d'in tayi ta warware d'an kwalin ta yaneshi a kanta, hoda kawai ta shafa sa茂 maik'on man leb'e, takalmi ta saka masu d'an tudu kad'an ta fita tana danna kiran lambar Abdu da Aminu ya turo mata. A hankali take tafe tana amsa wayar tare da bashi kwataccen gidan ya zo ya kaita, duk da shi dai saida gabanshi ya fadi data ambaci Wardugu, amma tunda ita tace saiya daure yace zai zo, amma kam har ga Allah baya son binciken k'wak'wafin nan da za'a gano har hanjin mutum. Babban falon da suke tsaye d'azu ta fad'o, tsayawa tayi ganin babu motsin kowa da tunanin inda zata nufa, daga bayanta taji ance "Hajia tana nan ne." Juyawa tayi ta kalli mai aikin, jinjina mata kai tayi ta bi hanyar data nuna mata, a zatonta hanyar da zata kaita waje ce amma sai gata d'od'ar kan mutane dake zaune akan teburin cin abinci, cak ta tsaya tana k'are musu kallo, sai kuma gabanta ya shiga luguden fad'uwa a hankali dan har Wardugu ma kallonta yake, gashi kuma bata ga wanda take gidan dominshi ba. Agaishat ce ta nuna mata kujera tace "Bismillah, zo zauna mu ci abinci." Da ido ta amsa mata tare da d'aga k'afarta zata taka, k'arar bud'e wata k'ofa yasa su kallon wurin har da ita, Hasheer ne ya fito da waya a kunne alamar yana amsawa, saida Faduma taji tsigar jikinta ya tashi sakamakon nuna mata gaskiyar al'amarin da yayi, abinda take tunanin ba lallai yana da shi ba, amma sai ta ganshi a jikinshi a mummurd'e cikin salama, wato idan ta fahimta kamar ya karanta zancan zucinta ne, shiyasa yanzu ya sako k'ananan kaya wanda suka fito dashi da kad'an War ya fishi, watak'ila yafi shi ne saboda shi sojane ko dan daga. A hankali ta sauke ajiyar zuciya ta d'aga k'afarta ta fara takawa, idonta a kanshi har yanzu kuma shima idonshi tarr suke a kanta yana kallo, inda shima a nashi b'angaren yana ayyana shigar daya ganta da ita ne a yau, bai tab'a ganinta haka ba sa茂 yau, kullum lafaya lafaya sai ranar daya ganta da riga da siket da hijab. Ta mishi kyau fiye da kullum duk da ba kwalliya bace a fuskarta, matsala d'aya itace kallabin k'arami ne kuma dashi ta fito, duk da bai ga bayanta ba amma ya tabbatar ya fito y'a zauna mata a baya daram, tunda alamu sun nuna tana da su, sai kuma tsayayyen k'irjinta da shima yayi tsai yana zare ido ga duk wanda ya kalleshi, ga cikinta daya shafe sosai saiya sake fito da tsarin hallitarta. Cikin sanyin jiki shima ya fara takowa yana zura wayarshi aljihu, inda ta nufa zata zauna shima ya nufa, cikin mutumtawa yasa hannu a hankali yaja mata kujerar da zata zauna, saida ta kalleshi sannan ta gyara ta zauna tana fad'in "Nagode." Bai tanka mata ba sai jan kujerar dake kusa da ita yayi ya zauna shima, a hankali ta aje wayarta akan teburin tana kallon Agaishat tace "Barkanku." Da murmushi ta amsa mata da "Barka, ya gajiya kuma? Da naji shiru na d'auka ko bacci ya d'aukeki." Murmushi kawai tayi sai Agaishat data mik'e zata fara zuba abinci, rik'e hannunta Wardugu yayi ya mik'e tsaye, komawa tayi ta zauna dan ta fahimci me yake nufi, faranti ya d'auka ya aje mata gabanta sannan ya d'auki wani ya aje gaban Faduma, hararan Hasheer yayi yace "K'ato da kai dai bana zuba maka abinci ba." D'an guntun tsaki yayi yace "Ina k'ato ne zan zauna karb'ar abinci daga gareka? Allah ya kiyaye." Mik'ewa yayi ya d'auke farantin daya d'ora gaban Faduma, wani ya d'auko ya d'ora mata yana fad'in "Ka ciyar da matarka malam, nima da kaina zan ciyar da burin..." Duk idon da suka zuba mishi har Wardugu dake tsaye da cokali a hannu, bai yarda ya kalli kowa b芒 a cikinsu sai kawai ya basar yace "K'anwata me zaki ci?" D'aga kai tayi ta kalleshi, wallahi ko dan tana zaune sai ya mata wani kerere kamar zai had'eta tsaf ya sha ruwa, wasu yawu ta had'e tace "Ka barshi ma nagode, zan zuba." D'aga kafad'a yayi ya zauna dan dama baisan ya zaiyi ba, cike da bayar da umarni yace "Zuba min to?" Kallonshi tayi sai kuma ta wurga ido alamar haba ma wannan mutumin, mik'ewa tayi tsaye tana tura kujerarta baya dan taji dad'in tsayawa, tagumi yayi ya zuba mata ido sai Wardugu daya harareshi yace "Anji haushi dai." Cike da shak'iyanci ya shafa sumar kanshi ya masa gwalo, ita da War haka suka zuba musu abinci sannan suka zuba ma kansu, saida ta kammala ta aje masa cokali ta d'auki kofin ruwa ta tsiyaya masa ruwa da kuma wani kofin na tangaren ta zuba lemu ta aje masa, kallon k'wayar idonta yayi yace "Nagode, karon farko zan ci abu daga gareki, daga yanzu tarihi zai fara kafuwa tsakaninmu, ba zan manta wannan ranar ba kamar yanda duk randa rana ta biyu ta zo da zan ci daga gareki saina tunatar dake wannan ranar." Yanda yayi maganar yana kallon idonta ita ma tana kallon nashi, sai taji gabanta na wata fad'uwa a hankali da kuma jikinta daya fara wata kyarmar sanyi, da k'yar ta nutsu ta samu ta d'aga labb'enta tace "Aci lafiya." Mantawa tayi data janye kujerar kawai tayi nufin zaunawa, lura da duk wani motsinta yasa shi saurin fahimtar abinda zatayi, da azama ya zura k'afarshi hakan yasa ta yin zaune daram akan cinyarshi a karo na biyu kenan a rayuwarta. Da sauri ta zabura ta mik'e kamar wacce ta zauna kan k'aya tana kallonshi, shima ita yake kallo cikin dakakkiyar fuska yace "Da kin fad'i, kujerarki na baya." Huci ta furzar ta jawo kujerar ta sauna tana satar kallonsu War da suma suke kallonsu, sake sunkuyar da kanta tayi bata yarda ta had'a ido dasu ba, Hasheer ma guma fuska yayi dan Wardugu ya kawo masa wargi. Shiru wurin sai k'arar cokali suna had'uwa da tangaren d'in faranti, d'an gyaran murya Wardugu yayi yace "Malam har yanzu baka gabatar mana da bak'uwarmu ba?" Da sauri ya kalleshi tare da aje cokalin hannunshi ya d'an ja hancinshi kad'an, kallon Faduma yayi ya sunkuyo kusanta cikin rad'a yace "Ya akayi kika rage nauyi?" Da k'arfi ta kalleshi ta kuma juya ta kalli su Agiashat da basuji me ya faru ba, sake kallonshi tayi da mamaki tana jinjina rainin hankalinshi, tunda dai ko sikeli k'arya ne ace ya gano nauyinta daga yar zaunawar nan da ko dak'ik'a d'aya batayi ba, girgiza kanta kawai tayi ta cunno masa baki tana tunanin sai fa ta nunawa mutumin nan kalar nata haukan. Kallonsu Wardugu yayi yana gyaran murya yace "Sunanta Batulu, k'anwata ce." War da Agaishat kallon juna sukayi sai kuma Agaishat ta kalleshi tana murmushi tace "Elhaj kasan dangantaka kala kala ce, wace irin k'anwa ce ita a gareka?" D'an girgiza kai yayi yace "K'anwa kawai, k'anwa kamar kowa, ko tayi girma da zama k'aramar k'anwata ne? Bata wuce tsarar Halima fa." Kallonshi tayi hakan yasa shi kallonta shima yace "Ko nayi k'arya?" Kawar da kai tayi tace "Ni ban ce ba, kawai dai a dinga fad'in gaskiya tsakani da Allah." Waro ido yayi yana lek'a fuskarta yana fad'in "Ke, kalleni nan." Wardugu ne yace "Kai d'Allah, to gaskiyar ce ka fad'a? Mtsss." Kallon Faduma yayi yace "Dan Allah fad'a mana wacece ke?" D'an gyaran murya tayi ta kallesu tana fad'in "Ni sunana Faduma aikine ya kawoni garin nan, da fari zan sauka gidan mama Aissata wacce na d'an zauna gidanta sanda nayi karatu anan, to sai aka samu matsala mahaifinta ya rasu sai ta tafi k'auyensu, hakan yasa na shiga tunanin masaukin da zan sauka mai tsaro, akan hakane muka had'u dashi yayan nawa, shine fa ya kawoni nan da k'arfin cin tuwo." Tana dasa aya taja numfashi ta sauke, karaf idonsu suka had'u ashe tagumi ya buga yana kallonta, tana kallonshi ya d'aga mata gira yace "Baki kamar chocolat." Da sauri ta kalleshi tace "Tohhh, kana lafiya kuwa?" War ne yace "Ina ya ga lafiya, ai tuzuranci ne ya fara haukatashi." Rufe baki tayi da hannu tana dariya a hankali tace "Da alama kam." D'an kallonshi tayi tace "Allah ya bada lafiya." Agaishat ce tace "Wane irin aiki kike?" Kallonta tayi zatayi magana Hasheer yace "Lauya'atu ce, masu d'aure magana." Kallonshi tayi sai Agiashat da taji tace "Lahh! Ashe ke lauya ce, kinga kuwa dama ina buk'atar lauya, dan lokuta da dama ana tauyeka saboda ana ganin macece ni." K'arashe maganar tayi da satar kallon War da shima ke kallonta, mirmushi yayi yace "Allah sarki, Wardugu d'an Ayya bawan Allah, baya da mai son shi." Murmushi Faduma tayi tace "Ai gida bata k'oshi ba ba'a kaiwa dawa, in kana buk'ata zan fara tsaya maka kai da muke yare d'aya kafin ita." Hasheer ne yace "Ku komai sai kun saka k'abila a ciki?" Turo baki Agaishat tayi tace "Ni naga ma k'anwarka bata sona da k'awance, zanyi hushi da kowa a gidan nan." Dariya Hasheer yayi yace "Ki bata lokaci kinji, zatayi k'awance dake ko tana so ko bata so." Kallonshi Faduma tayi tace "A bisa wane dalili?" D'auke kai yayi yace "Duk ranar dana sake kawoni nan kika mata shekara d'aya." Murmushi tayi tana fad'in "Ina ga zaka fara satar mutane kenan, dan nidai bana tunanin za'a sake samu irin co茂ncidence d'in da aka samu yanzu." Wani shegen kallo ya mata mai ma'anoni yace "Me yasa kike tunanin ba za'a sak茅 samu ba? Ko kina tunanin zanyi sanya ne har ki sake yi min nisa, Batul zaki zauna a k'ark'ashin inuwa da yardar Allah, ina jin haka a jikina." K'uri ta masa da ido tunda y'a fara magana tana kallonshi babu ko motsawa, kalamanshi a matuk'ar sanyaye suke shigarta har ya dasa aya,tabbas kalamanshi nada ma'ana kuma suna da abinda suke nufi, sai dai ba kai tsaye yayi maganar ba, duk da zata iya cewa ya bata satar amsar abinda ke zuciyarsa ne, amma a ganinta kamar abune marar yiwuwa, ba ma wannan ba sam basu dace ba. D'an d'auke kanta tayi ta d'auki cokalin gabanta ta tsakuro abincin, sam kasa jefashi tayi cikin bakinta saboda nauyi da komai y'a mata, su Agiashat ma dake kallonsu a take suka fahimci komai, musamman ma War ya gane abokinshi ma ya kamu da soyayyar yar yarinyar nan, kamar dai yanda shima soyayyar yarinya ta wahalar dashi, sai dai y'a fahimci ita bata d'auki abun da wani mahimmanci ba, ko tana da dalilinta ko kuma tana d'aya daga cikin mata masu jan aji ne da rik'on sakaina kashi ga al'amura masu mahimmanci? Vibration d'in wayarta ne yasa ta saurin kallon wayar ta d'auka, cikin nutsuwa ta d'oran a kunne a tausashe tace "Dada." Saida ya kalleta saboda yanda ta kira sunan a shagwab'e, kasa cire idonshi yayi yana kallon yanda bakinta ke motsawa wajen gaisawa da Dada, har saida ta tambayeta "Kunyi waya da mijinki?" Rau-rau tayi da ido ta sak茅 yin k'asa da murya tace "Dada...da saura fa har yanzu, kinga zan sak茅 kiranki." Daga wajenta tace "Shikenan ina jira, nima bak'o gareni, amma ki tabbatar kin kira Abanki kun gaisa, kinsan yanzu fa ya daina hushi dake, ido rude yake son magana dake, amma yana jin nauyin kiranki da kanshi." Murmushi ne ya bayyana a fuskarta harta manta ta canza harshe tace "Da gaske dada Aba ya daina hushi dani? Karki damu zan kirashi yanzu, amma ke da waye?" Amsa mata tayi da tubanci tace "Wannan yaron ne ruwa tara." Dariya tayi ta kalli Hasheer, da sauri ya kawar da kanshi yana had'e fuska, murmushi tayi tace "Nima ina tare da d'aya yaron anan, zan fad'a miki yanda akayi muka had'u anan." Sallama sukayi ta aje wayar, kallon War tayi da niyyar magana, amma sai gabanta y'a fad'i da k'arfi, tunawa tayi da maganar data fad'a da tubanci, kenan yaji komai yanzu? A hankali ta sunkuyar da kanta tana marairaicewa kamar mage na jin bacci, murmushi yayi ya kalli Hasheer yace "Karki damu ba zan fad'a masa ba." Da sauri tace "Kayi alk'awari?" Jinjina mata kai yayi, da farin ciki ta d'auki wayarta ta mik'e tace "Ku gafarceni, zanyi waya ne." Da ido War ya mata alamar ba komai yana gimtse dariyarsa, tura kujerar tayi baya ta kalli Hasheer dake cika yana batsewa, murmushi ta masa tace "Abokinka yana gidanmu wajen uwata zance." Wani murmushin ta sake yi ta wuce, da kallo ya bita har ta shige ta inda ta fito d'azu. Yana ganin b'acewarta ya kalli Wardugu yace "In baka fad'a min abinda ta fad'a ba War wallahi yau ba zan kwana gidan nan ba, kaji dai na rantse." War dake ta shek'a dariya ne ya tsagaita yace "Allah baka hak'uri, ni yanzu kasan orro tace na rage fad'a da masifa, ba dan haka ba bazan fad'a ba kuma babu inda zaka je." Jinjina kai yayi yace "Naji, fad'a min?" Wata dariyar y'a sake yi yace "Hira take data shafi ahalinta, sai k'arshe kuma da alama an tambayeta kai ko kuma kama da haka, shine tace ita ma tana tare da d'aya yaron, kai fa take nufi." Tintsirewa ya sakeyi da dariya har Agaishat ma, shi kuma juyar da kai yayi y'a cije leb'ensa na k'asa yana jinjina kai. *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 21:37 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _46_ Murmushi kawai ya saki na jin lallai an shawo dashi, amma ba komai *lokaci ne* tayi mai isarta, idan ya fahimta daidai kenan Abdallah yana wajen dada, ita dada ce ta fara kiran ubanshi da yaro, shine ita ma kenan tace gata ga yaron, hmmm/ a hankali ya furta "Zamu kwatse ne yarinya." Zai ci gaba da cin abincin Wardugu ya sake kecewa da dariya, harara ya maka masa yace "Allah War bana son k'ananan iskanci, me ka d'aukeni wai?" Cikin dariya yace "Abinda ta d'auke ka." K'wafa yayi yace "Ita ma zata sauke da kanta idan taji wutar gashinta." Cikin zolaya yace "Sai ranar daka sauke mata duka nauyinka ta gane garjejen basamude ne kai, saiku zauna lafiya." K'wafa yayi yace "Ka barta kawai, saina kai mata har mak'ogwaro ai ta yan..." Bai gama fad'a b芒 Agaishat ta mik'e tana fad'in "Subhanallah, dama haka kuke, tab'." Rik'o hannunta War yayi ya mayar da ita ya zaunar yana hararenta da fad'in "Wane shafi ne a cikin karatun baki biyashi ba?" Da sauri tace "Banda wannan dai da kuke karantawa yanzu, ni duk karatuna bai wuce yanda za'a k'ara maggi ko rage wuta bane da yanda za'a daidaita gishiri." Murmushi kawai sukayi sai War daya kalleshi yace "Hasheer, dan Allah fad'a min wacece ita? Kuma meye a tsakaninku?" Ajiyar zuciya y'a sauke yana kallonshi ya gyara zama da kyau, cikin sanyin murya yace "Wacce nake so ce War, ina sonta har zuciyata da gaba d'aya rayuwata, tunda na fara ganinta ta shiga raina ba tare da sanina ba, kallon fuskarta kawai yana haifar min da farin ciki da nisjad'i, jin muryarta yana saka gabb'an jikina amsawa su kuma nutsu, sai dai kashhh! Ban san ta yanda zan fad'a mata ba, Wardugu wallahi tsoronta nake ji, ina tsoron tunkararta, gabana fad'uwa yake idan na kalli idonta, jikina rawa yake idan ina tsaye gabanta, k'afafuna gagara d'aukata suke idan na jima tsaye a gabanta, banda wata dubara idan ina gefenta, rasa duk wani kuzari nake indai *murmushi na* tana tare dani." Nauyayyen ajiyar zuciya ya sauke, sunkuyar da kanshi yayi yace "Ban san ya zanyi ba, ko fahimta ta ba tayi ba bare na saka ran zata dubeni wata rana, aikinta da kuma rayuwar d'anta ne kawai a gabanta." Da mamaki suka sake kallonshi sai Agaishat da tace "Dama ta tab'a aure?" Kallonta yayi sai kuma yayi shiru, saida yayi dogon nazari da tunani kafin yace "Bata tab'a aure ba, k'addara ce ta fad'a mata ita ma ba'a son ranta ba, fin k'arfinta akayi..." Labarinta ya fad'a musu wanda yasa Agaishat zubar da hawaye, a hankali War ya matsa kujerarshi kusa da ita yana rarrashi, cikin kuka sosai take fad'in "Ta bani tausayi wallahi, musamman yanda duka iyayenta suka k'yaleta, ba uwa a tare da ita ba uba ba uban yaron, amma haka ta raini cikin harta haifeshi shima ya zama abun kwatance, lallai wannan abar koyi ce garemu iyaye." Jinjina kai War yayi yace "Hakane, kiyi hak'uri to ki daina kukan." Fitowar Faduma ce tasa duk sukayi shiru, wacce ta fito da farin cikin yau sunyi waya da Aba bayan shekaru da dama, har ya bud'e baki ya saka mata albarka tare da cewa ya yafe mata, sannan tayi saurin gama abinda ke gabanta ta dawo ya ganta, lallai yau tana cikin farin ciki ba kad'an ba. Ganin fuskar Agishat da hawaye yasa ta tsayawa cikin ladabi tace "Lafiya? Me ya faru take kuka?" Kallon juna sukayi sai War ne yayi saurin cewa "Wai dan yaronmu zasu kwana gidan kakaninsu, shine take wannan kukan, ta saka ran dawowarsu ne yau." Murmushi tayi ta gyara zaman wayar hannunta da yar jakarta k'arama tace "Allah sarki, ko nice ke zanyi kuka, amma a madadin zubar da hawayen, sai na kirasu naji muryarsu sannan na tabbatar suna cikin aminci." War ne yace "To kinji, bari na kira miki su." Murmushi Faduma tayi tace "Amm..ni zan fita, akwai wani abokin aikina da zai taimaka min, yanzu haka yana k'ofar gidan nan zamuje gidansu yarinyar da abin ya faru da ita." Kallonta yayi amma bai ce komai ba, War ne yace "Yanzu kuma? Me zai hana ki bari har da safe?" Girgiza kai tayi tace "Aiki na zo nayi, idan so samuna ne na koma gida k'asa da sati d'aya, saboda akwai wanda rayuwata da tashi suna cikin na juna ne, a kowace dak'ik'a kuma ina jiyo k'amshin had'arin dake tunkararshi." Ido suka zuba mata suna kallo, cike da dattako War yace "Me zai hana ba zaki fitar da tsayayyen jagoran da zai kula da lamarin rayuwar taki ba?" Saida ta kalli Hasheer sannan ta d'auke idonta tace "Na samu ma, lokaci kawai muke jira." Murmushi tayi ta sake rik'e jakarta tace "Ni zan tafi saina dawo." Juyawa tayi bata jira kowa ba, tana fita daga kusurwar ya mik'e da sauri yana lalaba aljihu, da sauri War yace "Kai miye haka? Ina zaka je?" Girgiza kai yayi hankali a tashe yace "Ba mahaukaci bane ni da zan zauna anan ina cin abinci, ita kuma tana can tare da wani a gaban mota, kai ba zai yiwu ba." Da mamaki Wardugu yace "Yanzu akan yarinyar ne kake wannan b'arin jikin Hasheer." Tsaki yayi yana nufa hanyar fita yace "Ba zaka gane ba." *Kwateta da alama Wardugu ya manta da baya fa.馃榿* Cikin d'aga murya War yace "Ka karb'i makullin mota to." Saida suka ga ficewarshi War ya sauke ajiyar zuciya ya kalli Agaishat, cikin sanyin murya yace "Wallahi tausayi yake bani, had'uwata dashi ta farko zaki rantse kice bai aje ko sisi ba, kuma ba komai ya jawo haka ba sai mutanen da suke zagaye da kai ma suna nuna maka k'iyayya da hasada, da kike ganinshi nan fa har gini yayi wanda na mak'aryaci zan iya ce miki in baifi gidan nan ba to babu abinda nan zai nuna masa, amma har yanzu ya kasa tarewa saboda fargaba, ba ma kowa yasan da gininshi bane saboda wani ya wakilta yayin aiki." Cike da jimami Agaishat ta girgiza kai tace "Allah sarki, rayuwa kenan, kowa da kalar tashi jarabawar, shi tashi kenan." D'an tab'e baki yayi ya ci gaba da cin abincin da sam basu maida hankali ba, hatta cire rai da sak茅 jin maganarshi sai kuma yace "Abun takaici matarshi ma bai iya zama yayi sirri da ita, hummm!" Cije leb'e yayi alamar rai ya fara sosuwa kafin yace "Wallahi da yarinyar nan zata yarda ta gane son da yake mata, ni kam dana tsaya mishi ya aureta wallahi." Aje cokalinta tayi tana kallonshi tace "Ai ko yanzu wani yunk'uri zamuyi wajen ganin mun daidaita tsakaninsu." Da mamaki ya kalleta yace "Kamar ya?" Yar ajiyar zuciya ta sauke tace "Kawai mu k'ara kusantasu da juna, hakan zaisa kowa yaji ba dad'i har ita d'in." Kallon anya kuwa ya mata yace "Kuma kina ganin hakanne mafita?" Jinjina kai tayi tace "Zuciyarka ma tayi taushi ta karb'i karatu da ladubban so bare kuma ta mace mai rauni." Hannu ya zura zai kamota ta zille tana dariya shi kuma yana fad'in "Wato ni zuciyar dutse ne dani ko?" Dariya take k'yalk'yalawa tana fad'in "Ni dai ban fad'a ba." K'wafa yayi yace "Zaki zo hannu ne orro, yanzu dai muje mu kwanta." Mak'ale kafad'a tayi tace "Um um, ni bana jin bacci, kuma bak'i fa ne damu a gidan, ba jimawa kasan zasu dawo." Mik'ewa yayi yana fad'in "To ni na fad'a miki baccin zamuyi, so nake kafin yaron nan ya dawo nayi zagaye ko biyar haka." Da sauri tace "Akan wa? Tadb'ijam! Emergency kenan." Murmushi kawai yayi yana girgiza kai ya wuce, a dolenta ta bi bayanshi bata da wani zab'i. ...Tana shirin bud'e motar da Abdu ya zo da ita hancin motarshi ya sanyo kai, b芒 ma wacce suka zo da ita bace dan Qaseem ya fita da ita, inda take tsaye ya paka motar ya d'an sauke gilashi ya zuro kai yace "Muje." Dakatawa tayi ta kalleshi d'脿 rashin fahimta tace "Ban gane ba?" Da ido da kuma baki tare da taimakon hannunshi na hagu ya mata alama da tayi shiru kawai ta shigo in ba haka ba zai mirk'usata, yanda yayi da hannun a k'arshe yasa ta zaro ido, d'an matsawa tayi kusanshi tace "Yallab'ai, nifa ba yawon bud'a ido na zo ba, zanje gidansu yarinyar da aka kad'e ne danyin bincike, kuma shine yasan wurin zai min jagora." Da wata harara harara yace "Ni zan tuk'aki, shi ya mana jagoran." Numfashi ta sauke dake nuna kana hawa min kai ta juya ta kalli matashin tace "Mr. Kayi hak'uri dan Allah ka shiga gaba sai mu biyo bayanka." Murmushi ya mata yace "Ba komai Fatima, muje." Juyowa tayi ta dalla masa harara ta k'asan ido ta zagaya tana kunkuni ta bud'e ta shiga, saida ya tayar da motar ya kalleta yace "Wato na sha miki kai ko? Baki so na hanaki tafiya da k'ato ba ko? Da kyau Batulu." Ya k'arashe da yin k'wafa yana jan motar a hankali, shiru tayi kamar malam ya ci shirwa y'a sha ruwa, ita kam wani tsoro tsoro ma yake bata, gashi tunda suka zo nan ta lura yana yawan magana sosai ba kamar acan garin ba. Ganin shirun kar ya mata yawa saita ciro wayarta tana dannawa, satar kallonta yayi yace "Da manyan namu ake hira ko?" Kallonshi tayi a hankali tace "A'a." Jinjina kai yayi kalar shi fa so yake saita biye masa, hannu ya kai zai karb'i wayar tana ganin inuwar hannunshi tayi saurin janyewa ta kalleshi, jinjina kai ya sake yi yace "Oho! Na gane, da babban ne kike soyayya ko?" Da mamaki ta kalleshi tace "Ni ai bana soyayya." "Sai masifa kenan?" Ya fad'a yana kallon fuskarta, ajiyar zuciya ta sauke ta kawar da kai ta ci gaba da danna wayarta, a hankali yace mata "Yaushe rabonki da nan?" Kai tsaye tace "Ba jimawa." Jinjina kai ya sake yi yace "Ina da ina kika sani anan?" Kai tsaye ta sak茅 cewa "Ko ina." Satar kallonta yayi yana murmishi, wato amsa ce take bashi da jin haushi alamar bata son maganar, idonshi ya mayar kan titi ya sake cewa "Ina kika baro min Amjad? Ai da kin taho dashi." Kallonshi tayi sosai dan ita indai zaka yi maganar yaronta to tana d'aukarka mai k'aunarshi ko da haka bane a ranka, cikin salama tace mishi "Yana wajen dada, zata kula dashi." Jinjina kai yayi yace "Allah yasa." A ranta ta amsa da ameen, ta d'auka an wuce wurin sai kuma yace "Zaki bawa babana mamanki ya aura?" A take ta kalleshi tace "Wa? Mamana kuma?" Ba tare daya kalleta ba yace "Eh mamanki, budurwar babana b芒, ba kin fad'a min yana gidanku zance ba." Juyar da kanta tayi tana fad'in "Oho! Yanzu na gane." D'aga kafad'a tayi tace "Ban sani ba nima, idan tana son shi zan iya bashi ita duk da kima da tsadarta a wurina, idan kuma bata so saiya hak'ura." Murmushi yayi yace "Za ma ta so shi, na yarda dashi ai." Kallonshi tayi tace "Me yasa kace haka?" Ba tare daya kalleta ba yace "Saboda nasan ba zai rabu da ita ba har saiya samu zuciyarta." Murmushi tayi ita ma tace "Shi d'in ya yake da kai?" "Babana ne." Ya fad'a kai tsaye, sai kuma ya d'ora da "Autansu babanmu ne, duk inji d'aya ya bugosu." Da sauri ta kalleshi baki bud'e tace "Tohhhh!" Kallonta yayi fuska a had'e yace "Oh yi hakuri fa, yaro kamata na fad'in haka ko? Na tuba ki gafarceni." Gyara zama tayi tana kallonshi tace "Wai tsaya malam, tun d'azu sai maganar yaro da k'atti kakeyi, me hakan yake nufi ne? Ka fito kayi magana kawai, ni na kiraka da yaro ne?" Kallonta yayi da mamaki yace "To miye kuma na tsarguwa Hajaj? Idan babu rami me ya kawo maganarsa? Ko dai ko dai..." Juya kai tayi tace "Ni ba wata tsarguwa da nayi, na gaji da jin abu guda ne kawai." Hannu ya kai ya kunna mp3 dake motar yana fad'in "To saurari wannan, ni kuma nayi shiru." A daidai kan wata wak'ar Umar m. Shareef ya tsaya ta share hawayenki amarya, ko dan ita d'in ba ma'abociya wannan sauraren bane da kalle kalle, hakan yasa sai bata wani kula ba kawai ta ci gaba da danna wayarta, dake inda zasu akwai tafiya sosai yasa har wak'ar ta zo k'arewa, wani salon wak'ar ya shigo d'aya daga cikin wak'arshi na album d'in tsuntuwa mai taken wasik'a. Bakin danja suka tsaya hakan y'a ba Hasheer damar k'ura mata ido yana kuma bin wak'ar a slowly kamar yanda mai ita keyi, tattausan muryarshi da yanda yake rera wak'ar saiya daki zuciyarta sosai harta d'ago kai ta kalleshi, ido cikin ido suka kalli juna, gagara d'auke idonta tayi duk da kuwa wani irin tartsatsi dake harbinta daga idon nashi. Shi kanshi kasa janye idonshi yayi sai ci gaba da rera wak'ar yana wani lumshe ido kamar shi ya k'irk'ireta, abun jin shi take kamar dasu ake, jin baitukan take kamar dan ita ko dan su aka yinsu, to amma dai ai bai ce yana son ta ba, kai ita bai ma nuna mata ba a zahiri dan haka kawai ta share al'amarin. Odar da aka yi daga bayansu ta dawo dasu daga duniyar da suka lula, cikin nutsuwa ya ja motar suka ci gaba, babu wanda ya sake magana har suka isa k'ofar gidansu yarinyar. Bata kalleshi ba dan duk jikinta yayi sanyi sosai, bud'ewa kawai tayi ta fita ta k'arasa kusan Abdu, tsaye sukayi yana k'ara mata bayanin ga gidan tace su shiga tare, tare suka rankaya da sallama a bakinsu, Hasheer dake binsu da kallo wani dagon tsaki yaja, dama haka aikinta ke had'ata gauraya numfashi da kowane sauna da sakarai? Gaskiya ba abu bane mai yiwuwa wannan, ina ba zai d'auka ba, k'wafa yayi yana jinjina kai da gyara zamanshi dan jiranta. _______________ Suna idar da waya da Faduma dada ta kalleshi shima dama kallonta yake tunda ta canza harshe sai abun ya birgeshi, cikin sanyi sosai yace "Budurwata me kika fad'a? Ince dai ba gulmata kikayi ba ko?" Sama da k'asa ta kalleshi tace "Kana da abun gulma ne dama? Magana kawai nayi." Murmushi yayi yace "To yanzu ya batun soyayyarmu?" Kai tsaye tace "Babu shi, ai na fad'a maka bana da ra'ayin auren matashi irinka musamman kai da baka tab'a aure ba." Matso da kujerarshi yayi gaf da ita sosai yana fuskantarta ya kuma d'ora hannayenshi akan hannun kujerarta, hakan yasa ya tsareta sosai babu wani tazara tsakaninsu, k'urawa fuskarta ido yayi yace "Ni ina sonki a haka, me ye aibun aurenmu to? Duk abinda nake so shi magabatana ke yi min, na miki alk'awarin ba zaki tab'a samun matsala daga gareni ba." Sake kawar da kanta tayi tace "Ka gane mana, ni fa bazawara ce data tab'a aure, kai kuma kace baka tab'a aure ba, taya aurenmu zai yiwu?" A take yace "Ubangiji ne zai iya mana, kinga yarinya kalleni nan." D'an juyo da kanta tayi ta kalli wuyan rigarshi kawai dan ba zata iya klalon fuskarshi ba, cike da nutsuwa da dattako yace "Ki fad'a min tsakaninki da Allah ba zaki so auren saurayi ba inhar a zab'inki ne?" Ajiyar zuciya ta sauke har iskan bakinta mai fitar da k'amshin karamfani ya daki fuskarshi, cikin nutsuwa ta jinjina kai tace "A gaskiya zan so haka, domin kuwa saurayi na aura aurena na fari, bansan matsalar abokiyar zama ba da wani k'unci na rayuwa, tasku kad'an na fuskanta daga danginshi, kuma kasancewarshi jajirtaccen namiji ya tsaya min sosai harna daina samun matsala daga garesu, bayan rasuwarsa ne komai ya sake lalacewa har suke son rabani da gidan nan daya mallaka min." Bakinta kawai yake kallo yanda take maganar cikin sark'ewar hausa da kuma nutsuwa, *jajirtaccen namiji*? Hummmm? Ta dakeshi da magana fa sosai, amma ba komai lokacinta ne, ba tare daya matsa daga gareta ba yace "Budurwata, zaki iya aurena nan da sati biyu zuwa uku?" Fad'uwar da gabanta yayi ne yasa ta saurin dafe k'irji tana kallonshi a firgice, sati uku? Yo ita me tayi? Kai bata ma shirya ba, sunyi zaman nan ne data fad'a mishi ya rabu da ita fa, sai kuma maganar aure? Katse mata tunani yayi da cewa "Ki bani dama naga iyayenki, ko da baki so na ma na yarda, amma zan koya miki sona a cikin sati ukun nan kafin aurenmu, in haka bata faru ba ki fasa aure na." Kallonshi kawai sai taji yau hausar ma data d'an kama tana neman kubce mata, fahimtar haka shima yayi saiya sake cewa "Yarinyata, wallahi aure nake so, na fad'a miki matuk'in jirgine ni d'in, a gurin aikina kullum kafin su yarda kaja mutane sai sun duba lafiyarka, ni kuma sun gano ina fa da matuk'ar buk'atar mace a yanzu, shiyasa suka ban hutun wata uku na zo na samu mafita, yanzu haka na ci wata d'aya da rabi, da tun waccen lokacin na ganoki da zuwa yanzu cikin sati uku ko biyu ne jikinki." Da sauri tasa tafukan hannayenta ta rufe fuska cike da kunya, murmushi yayi yace "Kin amince kenan?" Bud'e fuskar tayi tana turo baki tace "Ni bance ba, haka kawai sai nayi aure da wuri haka." Wani murmushi ya sake yi ya jinjina kai yace "Yarinya kenan, ke kam k'uruciya na damunki." Galala ta kalleshi tace "Wai ku maza me yasa kuke haka? Mace tsofai tsofai sai ku ce mata yarinya." Murgud'a baki tayi ta juyar da kai, wani shak'iyin murmushi yayi yace "Kinga da kina matata ne kika juya min bakin nan, hummm! Da yanzu wani zancen ake ba wannan ba." Rufe bakinta tayi ba tace komai ba, gyara zamanshi yayi ya shige cikin kujerar, katinshi ya ciro ya aje mata kan cinyarta yace "Indai kin amince da aurena to ga katina nan ki tura min da bayanin gidanku, idan kuma baki amince ba ba matsala, sai dai ba zaki sake ganina ba gaskiya, dan bana so na rasa aikina da nake so, zan je neman aure saidai ki sani ke ce wacce ke cikin zuciyata." Ko da ya gama fad'a y'a mik'e ya fita tana binshi da kallo baki sake, saida ya b'ace sannan ta sauke ajiyar zuciya ta d'auki katin, karantawa tayi sosai kafin ta mik'e ta shiga d'aki. Jin motsinta yasa Amjad dake d'aki yayi saurin datse wayar da sukeyi da Tagur, dan tunda rana ya had'a shi da kabceciyar waya kuma yace kar ya nuna ma kowa, duk da ya shiga yanayin rashin jin dad'i amma haka ya karb'a ya masa godiya. Kwance yayi ya bud'a littafin karatunshi a dole shi karatun yake, ai kuwa lek'awa tayi dan taga yayi bacci ko yaya? Kallon juna sukayi tace "Baka kwanta ba dama?" A hankali yace "Karatu nake." Jinjina kai tayi ta jawo masa k'ofar tana fad'in "Bari na rufe gida nima kwance zanyi." Fita tayi ta rufe gidan ta dawo, d'akinta ta wuce tayi shirin bacci ita ma ta kwanta, katin ta d'auka ta saka lambar a wayarta, ta jima tana tunani da sak'a da warwara kafin daga bisani ta yanke shawarar kar tayi wasa da damarta, tura masa komai tayi daya buk'ata sannan ta kashe wayar gaba d'aya saboda kunya ma take ji, tana kuma mamakin yaron nan d'脿 lamarinshi ya wujijjigata k'asa. ______________ Da k'yar dai yau ya samu yaje gidansu Atta dan bata kud'in wata na kula da Raidwan, tunda ta fito ta tsaya bai kula da tsiyarta ba har ranta ya gama b'acewa tace "Malam in kasan babu abinda ya kawoka me ye na aikawa a kirani kuma?" Wani wulak'antaccen kallo ya mata yace "... *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 21:38 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _47_ Wani wulak'antaccen kallo ya mata yace "To ki koma mana marar mutumci." Cikin masifa tace "Au! Nice ma marar mutumcin? Ga ka babbar marar mutumci da zaka zo har k'ofar gidanmu ka nemi fad'a min magana, kaga malam nan fa ba gidanka bane da kake min abinda ka ga dama, anan wallahi saimu casu da kai." Wani shashashan murmushi yayi yace "Kaji yar tasha lamba d'aya, to ni ba da wannan na zo ba." Gyara tsayuwa yayi yace "Ina d'ana?" Harara ta maka masa tace "Yana bacci." Tab'e baki yayi ya saka hannu aljihu ya ciro enveloppe ya mik'a mata yana fad'in "D'ari ne anan, duk wata zan baki haka dan kula min da yarona, ban yarda ki dinga takura min kan k'ananin abubuwa, kuma wallahi Atta idan kika bari wani abu ya samu yaron nan sai na ci ubanki a garin nan." Zaro ido tayi sai kuma ta tuna ai kalar zaman nasu kenan, hararanshi tayi tace "Ai ba kai ka haifar min yaron ba, kuma idan buk'atarka ta tashi dole zan nemeka." K'wafa yayi ya kama murfin motar zai shiga yana fad'in "Ni dai na fad'a miki." Tsaki tayi tace "Da alama yau karuwar bata maka yanda kake so ba shine ka zo zaka tsareni da masifa, can ta matsemaka jarababbe." Da gudu ta zagaya ta shige gidansu yana binta da kallo, cije leb'e yayi ya jinjina kai yace "Zamu had'e wata rana, sai kinyi aman jini, banza ballagaza." Jan motar yayi ya bar k'ofar gidan da tunanin kiran Faduma da lambar da Amjad ya saka mishi a waya, tunanin abinda ya kaita Niamey yake? Shiyasa yake so yaji daga bakinta, amma ba zai kira yanzu ba sai yaje gida ya sauka a mota yayi zaune kan kujera sannan, dan yanzu Faduma tafi k'arfinshi tsoro ma take bashi, dan ko magana ta daina mishi cikin taushi yanzu kuma babu wannan kunyar da rawar leb'en. ________________ Tsaf ta gama d'aukar bayanan iyayen yarinyar da sanin muhimman abubuwa kanta, godiya suka musu suka fito tare da rakiyar abokin yayan yarinyar wanda shine ya tsaya musu, da kuma yayan nata duk suka fito, tsaye sukayi inda ta kallesu tace "Kun san a ina ne yaron yake?" Abdu ne yace "Eh, yana nan a yantala tare da abokanshi suke zaune." Kallonshi tayi tace "Kasan wani Abu a kanshi ne?" Jinjina kai yayi yace "Eh to, bayan sanin cewa shi d'an tsohon conseiller ne Alhaji Bureima Barka, gaskiya ban nemi sanin komai a kanshi ba." Jinjina kai tayi tace "Zuwa gobe da safe zaka kaini gidan da yake." Da mamaki duk suka kalleta sai Abdu da yace "Gidansu kuma? Me zaki je yi acan?" Kallonshi tayi tace "Dole mu tabbatar da gaskiyar yana shaye shaye ko kuwa a'a." Abokin yayar yarinyar ne yace "Yana shaye shaye fa yaron nan, har cod茅ine sha suke." D'aga gira tayi alamar oho tare da cewa "Gobe zamu tabbatar." Abdu ta kalla tace "Ka min wani k'ok'ari ka samo min masaniya akan abokinshi wanda kuka san sunfi kusa sosai." Jinjina kai yayi yace "Shikenan." Hanyar mota ta nufa tana fad'in "Sai anjima." Motar ta bud'e ta shiga tana sauke numfashi, saida ya mata kallon tas sannan ya tayar suka bar wurin, wata ajiyar zuciya ta sauke tace "Wai me yasa ka biyo ni ne? Aikina fa ba kad'an bane." Shiru mata dan fa maganar gaskiya ranshi a b'ace yake, shi dai gardawan nan daya gani tare da ita har su uku sam abun bai kwanta masa a rai ba, ita ma bata sake cewa komai ba har ta dannawa Ayyarta Herde kira, tana d'auka cikin tubanci suka gaisa da farin ciki, cikin jin dad'i tace "Ayyata yau na kira Aba kuma ya d'aga, Ayya kinsan ma me muka tattauna? Aba ya saka min albarka yace Faduna kiyi hak'uri ki yafe min. Kai Ayya ina cikin farin ciki." Ita ma da murna ta amsa mata da "Faduma mu godewa Allah mu godewa matar nan, wallahi ba fad'a ba zagi cikin ruwan sanyi tayi abinda muka kasa yi, gaskiya matar nan Allah ya saka mata da alkairi." Da murmushi sosai tace "Ameen Ayya, zan sake kiranta nima na mata godiya, dan tayi min abinda bansan da me zan biyata ba." "Hakane, amma dai kiyi sauri ki dawo daga aikin nan, dan tuni nan har mun fara shirye shiryen bikinki." Cikin shagwab'a ta turo baki murya a tausashe sosai tace "Ayyahhh! Kamar dai kun gaji dani, a bari na dawo mana sai a saka ranar." Da k'arfi tace "Ke wace ranar da tuni aka saka? La la la la! Kar dai bai fad'a miki ba?" Had'e murmushinta tayi tace "Ayya ban gane ba?" Daga can tace mata "Faduma ai Abanki ya saka rana, kuma wallahi sati uku kacal ya saka a cewarsa me za'a jira tunda kun fahimci junanku." Dafe k'irjinta tayi a hankali ta saci kallon Hasheer dake tuk'i tace "Inna lillahi! Amma Ayya ya Aba zai min haka? Sati uku me nayi a cikinta? Ko gyaran ka茂na banyi ba bare kuma nasan yanda zanyi da Amjad." Sunan Amjad da yaji yasa ya kalleta, saidai tunda ba ji yake ba saiya d'auke kai kawai, cikin nutsuwa da manyantaka Herde tace "Faduma, kar kiyi wasa da damar da Allah ya baki mana, Amjad yanzu d'an gata ne dake da kakani biyu mata da kaka namiji, sannan yana cikin kulawar duka gab'a d'aya danginki, karki damu dashi kinji, yaron nan Aminu Owwo ta fad'a mana komai a kanshi, mun mishi godiya ba adadi akan irin kulawar daya dinga baki ke da Amjad, yana k'aunarki sosai tunda har ya k'uduri aurenki duk da yasan komai akan ki, dan haka dama ce karki yarda ta kubce miki, kiyi addu'a Allah yasa haka shi yafi zama alkairi, kinji ko." Ajiyar zuciya ta sauke tare da gauron numfashi tace "Shikenan Ayya, zanyi yanda kika fad'a, amma Amjad yanzu kakaninshi mata uku ne ba biyu ba, baiwar Allahn nan ta zama Ayyata ta uku yanzu." Cikin farin ciki tace mata "Ta cancanci haka kam, idan kana son ganin karamci kaga matar nan an wuce wurin." Murmushi tayi ta juya ta kalli Hasheer dake tuk'inshi a nutse, kamar dashi take dan bata d'auke idonta daga kanshi ba cikin harshen hausa yanda zai fahimta tace "Ayya bishiya mai dad'i ita ke fitar da 'ya'ya masu zak'i da kuma dad'in ci, duk ruwan k'oramar da sukayi dad'i to daga k'asar da aka hak'osu ne, ita uwa ta gari ita ke haifo da 'ya'ya na gari zuwa duniya, sannan uwa managarciya tamkar k'asa mai fitar da anfanin gona, *haka halinsu yake* Ayya, karamci da karramawa a jininsu yake, zasu dawwama har abada a zuk'atanmu ba tare da mun daina musu add'uar alkairi ba." Herde kam jin abun tayi amma da k'yar ta iya tsintsar wata hausar data fad'a duk da tana kama hausar. Hasheer kuma dake kallonta ya kasa ko k'yabtawa, dad'in dake nuk'urk'usarshi ne yasa har ya d'an saki murmushi, juyar da kanshi yayi bai ce komai ba, datse kiran kawai tayi sai lokacin yace "Wannan wace uwa ce? Ina ma zaki bani kwatancenta dana fansota a ko nawa ne dan na had'a da tawa uwar." Cikin murmushi ta kalleshi tace "Kar ka so kanka dayawa mana, ka bar mana mu ma mu samu tabarraki." Da murmushi yace "K'ari ai baya k'in dad'i." Murmushi tayi tace "Ko da na mari ne kuwa." Kallonshi tayi sosai tace "Ka min wata alfarma mana?" Ba tare daya kalleta ba yace "Uhum! Ina jinki." Cikin shagwab'a tace "Kayi min lamuni duk sanda na koma garinku naje gidanka na gaishe da Ayyata?" Da mamaki ya kalleta yace "Umma wai?" D'aga kai tayi alamar eh, murmushi yayi yace "Ba damuwa, amma da sharad'i?" Cikin fuskar yarinta tace "Lahh! Kai fa babban mutum ne, to na yarda fad'i." Cikin zolaya yace "Ni gidana duk wacce ta shiga bata fita sai mutuwa." Zaro ido tayi tace "Yankan kanun mutane kake? Haba nifa najima ina d'an zarginka, ashe dawalakin goro a miya." Dariya yayi mai sauti yace "Kusan haka, amma ba kowa nake yankewa kai ba, wasu idan gidan yana k'aunarsu to sukan dawwama ne ba fita sai dai suje su dawo, amma suna cikin gidan suna bauta wa mamallakin gidan." Wani kallo ta masa ta d'age girarta sama tace "Wace irin bauta kuma?" Saida ya d'an kalleta yace "Kamar gyaran gida, kula dani da kuma haifo yaran da zasu zama albarkar cikar gidan." Wata dariya ta bushe da ita ta kalleshi tace "To idan kuma mutum baya da k'wan haihuwar fa?" Saida ya kalleta yace "Gidana zai iya zama da kai a haka, zaka kula da mai gidan ne kawai kana masa biyayya." Jinjina kai tayi tace "Wannan sharad'in na shiga gidanka da wuya yake, ka canza wani mana." Girgiza kai yayi yace "Ba zai yiwu ba, haka gidan yake tun iyaye da kakani." Jinjina kai ta sake yi tace "Kenan kuma duk a haka kuka zo duniyar." Murmushin gefen labb'a yayi yace "Kusan haka." D'an kawar da kai tayi tace "Ya zanyi to tunda ina so? Zanje a haka indai zan dinga ganin fuskar Ayyata kullum zan zauna." Kallonta yayi yace "Da gaske?" Da gira ta masa alamar eh, cikin rawar muryar tace "Dan Allah babban mutum ka ban Ayyarka na had'a da nawa ayyoyin su zama uku, wallahi ina sonta har zuciyata saboda tayi mun abinda ko Ayyata data haifeni bata min ba, ina jin kamar babu abinda zan mata na saka mata kamar na dinga kiranta da sunan *mahaifiyata*." A hankali ya ratsa bakin titi ya tsayar da motar, dan a gaskiya abinda ta fad'a kan mahaifiyarshi yasa yaji duk ya rasa kuzari, ta d'aure masa jijiyoyin jikinsa da kalamanta, yaji a ransa dole ma ya dage ya shigar da ita gidansa a matsayin mata, shi zai samu kulawarta, yaranshi zasu samu tarbiyya, mahaifiyarshi kuma zata samu girmamawa. Kallonta yayi bayan ya jingina sosai yace "Zan baki mahaifiyata Batul, amma ke ma zaki bani Ummanki?" Langab'ar da kai tayi tana wutsil wutsil da ido tace "To ai idan na baka d'aya ka lalata min lissafina kenan, daga uku zasu koma biyu." Shima marairaicewa yayi cikin sigar tausayi yace "Idan na baki ita ni ya zanyi *Zahra*? Kinfi kowa sanin me ake nufi da uwa dan har guda biyu gareki, idan na baki ita zan rasa mai kula dani da yi min add'ua, kuma kinsan tasirin dake cikin bakin mahaifiya, ko zaki iya d'aukar wannan nauyin?" Tarrr ta sauke idonta akan shi, magana ce ya mata ta nutsuwa da kuma aiko da wani sak'o, gabanta ya fad'i matuk'a taji wani irin tausayinshi na ratsa jijiya da jinin jikinta, wani abu taji na musamman a kan mutumin daga k'asan zuciyarta yayi sama yana mamaye duk illahirin jikinta. Ita dai tasan yana da mata, amma kuma yace bayan mahaifiyarsa babu mai kula dashi? A hankali tayi k'asa da idonta ta jinjina kai kamar marar gaskiya tace "D'aukar nauyin mahaifiya ya fi k'arfin kaina, da zan iya dana d'auka." Yanda ta sunkuyar da kai yasa shi saka yatsanshi d'aya ya tallabo hab'arta zuwa ga fuskarshi, suna had'a ido hawayen da take k'ok'arin b'oyewa suka gangaro, tausayinshi sosai taji akan abinda ya fad'a, ita tafi kowa sanin rashin kulawar mahaifiya, a hakan dan tana da guda biyu, ina ga shi mai guda d'aya wacce inta tafi shikenan ya rabu da farin ciki kenan. Yatsa tasa ta share hawayen tana jin kamar ta rumgumeshi ta kwantar da kanshi akan k'irjinta ta shafa kanshi tace "Kayi hak'uri kaji, karka damu da wannan, ni ina tare da kai, zan maka duk abinda kake so." Sai dai kashh babu wannan damar, lek'a fuskarta yayi da kyau yace " *Teeti* ke ma uwa ce, a sunan uwa da kuma haihu babu babba ko k'arami, kamar yanda mahaifiyata zata albarkaceni, ke ma zaki iya yin haka, kuma watak'ila add'arki ce zata bini duba da Allah na kallon zuciya ne." Sakin hab'arta yayi ya kamo hannunta na hagu da hannunshi na dama ya d'ora saman kanshi, da sauri ta kalleshi jin hannunta kan tattausa kuma yalwatacciyar sumar dake gaban kanshi. Idonshi sun kad'a sunyi jajir ya kalli fuskarta yace "Ki sanya min albarka *Teema*, kullum Ummana sai ta min haka amma banda yau da bama tare, nasan addu'arki gareni zata karb'u da yardar Allah, ki sanya min albarka kinji." Fashewa tayi da kuka sosai tana son k'wace hannunta amma ya rik'e kuma baisa k'arfi ba, cikin kuka tace "Bansan me zan ce ba, dan Allah ka sake min hannuna, nima sa albarkar nake nema." Girgiza kai yayi bai kuma saki hannunta ba, kallonshi tayi idonta har sunyi ja tace "Me kake so daga gareni?" Da murmushi yace "Addu'arki." Saida ta shak'i iska kafin ta gyara muryarta tace "Zaka samu duk abinda kake so da yardar Allah, ubangiji ya ci gaba da tsareka a duk inda kake." Jin ya d'an saki hannunta da sauri ta janye tana rufe fuskarta da hannu, cikin tsokana yace "To mama tunda an saka min albarka a kalleni a min murmushi mana." Bata san lokacin da dariya ta kubce mata ba ta kalleshi da kukan shagwab'a tace "Bana so fa, ka daina." Murmushi yayi yana tayar da motar yace "A daina zubar min da hawayen nan to, saboda daraja ce dasu marar misaltuwa." Kallonshi tayi sai dai shi bai kulata ba, mirmushi kawai tayi ta girgiza kai tana mai jin wani masifaffen dad'i har k'asan zuciyarta. Tafiya suka ci gaba yi cikin farin cikin har suka iso gidan, suna shiga farfajiyar gida ta fito daga motar kenan kira ya shigo wayarta, duba lambar tayi da babu suna sai dai mai sauk'i ce sosai lambar airtel, d'auka tayi da tunanin abune mai mahimmanci, tana d'orawa a kunne cikin zazzak'ar murya (Yagana sai dai haushi) yace "Amincin Allah ya tabbata a gareki." Cak ta tsaya tare da d'an dafe k'irjinta daya buga da k'arfi, tunanin daya fara zuwa mata shine "Ina ya samu lambata?" Shiru tayi ta kasa cewa komai saida ya sake fad'in "Faduma Bintu, barka da dare." A hankali ta fizgo nutsuwarta tare da sauke ajiyar zuciya, d'auke hannunta tayi daga k'irjinta, cikin rawar muryar dake nuna tana son zubar da hawaye tace "Wa ya baka lambata?" Murmushi yayi daga inda yake yace "Faduma ni kike tambaya wa ya bani lambarki?" Saida ta had'e rai sosai tace "Kai a wa da ba zan tambayeka? Ka haifeni ne?" Wani mad'aukakin mamaki ne ya ziyarceshi har saida ya gyara zamanshi yace "Faduma ni? Ni a uban d'anki, ina da damar da zan samu lambarki kuma na kiraki." Tsaki taja tare da gyara tsayuwarta ta manta da tana tare da mutum tace "Tagur banda lokacin ka, ina da abubuwa masu mahimmanci, dan haka karka sake kirana kaji." Zata kashe wayar yayi saurin cewa "Karki fara Faduma, wallahi karki kashe min waya." Dakatawa kam tayi kamar dole tana saurarenshi, cike da gadara da isa yace "Me kika je yi a Niamey?" Da yanayin mamaki ta yatsina fuskarta tace "Tagur, waye kai da kake min wannan tambayar? Ko Aba da mukayi waya d'azu bai min ita b芒, sai kai." Lumshe idonshi yayi ya furzar da iska kafin ya bud'e yace "Faduma na damu akan ki ne, ina so nasan abinda ya kai ki, Faduma nasan har yanzu kina jin haushina abisa abinda ya faru, Faduma kiyi hak'uri dan Allah ki yafe min, wallahi ba'a son raina ba nima haka ta faru, bansan ta..." Dakatar dashi tayi da fad'in "Tagur." Shiru yayi sa茂 ita data d'ora da cewa "Da kasan yanda nake jin haushinka da baka yarda ka kirani ba, Tagur da kasan irin illar daka min wallahi da baka yarda ka sake tunkarata, da kasan kuskuren irin k'unar daya haifar min da kayi fatan mutuwarka madadin sake had'uwa dani, da kasan irin taskun daka jefa rayuwata wallahi daka zauna kana tsinewa kanka madadin sake bibiyata, amma me rashin kunyarka ya tunzuraka ka ke aikatawa? Har kallona kake kana kiran d'ana da d'anka." Da sauri ya marairaice yace "Faduma ki saurareni dan girman Allah." Ajiyar zuciya ta sauke tana had'e wani nauyayyen d'aci daya tokare mata mak'oshi tace "Tunda ka had'ani da girman Allah ina jinka na tsayin minti d'aya." Da sauri yace "Nagode, nagode Faduma." Saida ya karya murya sosai kamar wanda zaiyi kuka yace "Faduma wallahi ba'a son raina komai ya faru ba, tabbas na k'i karb'an Amjad a lokacin, amma daga baya dana nuna ina da alak'a da cikin sai Ayya ta rufe ido tace sam bata yarda ba, k'arshe ma tsinuwa ta gitta min akan cikin nan kuma Aba ya goyi da bayanta, daga k'arshe ma basu barni na kwana garin ba suka turani karatu, Fadu na yarda nayi kuskure babba, amma wallahi tallahi Faduma ko keta miki haddi da nayi wallahi bansan ya akayi na kasa rik'e kaina ba, Faduma tunda nasha shayi a hannun abokina na rasa duk wata nutsuwa, wallahi nayi k'ok'arin nesanta kaina dake amm..." Cikin zubar da hawaye taja majina sosai tace "Lokaci ya cika, Tagur karka sake kirana indai kana sona da farin ciki." Tana fad'a d'if ta kashe wayar, jimk'e wayar tayi sosai ta durk'ushe ta fashe da kuka. Kaf abinda ta fad'a duk yaji dan yana bayanta tsaye, da sauri ya saka wayarshi aljihu ya k'araso kusa da ita yayi tsugunno irin na maza yana kallonta, yatsa manuniya yasa kamar d'azu ya d'ago hab'arta, girgiza mata kai cike da damuwa cikin sanyin murya mai saukar da nutsuwa yace "A sanin dana yi wa duk mai sunan Faduma jaruma na santa, Faduma lokaci yayi daya kamata ki daina shan wahalar mutumin nan, Fatima kin azabtu dayawa a dalilinshi, kin rasa soyayyar iyayenki na tsawon shekaru a dalilinshi, kuma a dalilinshi ne kika karb'i bulala daga hannun Abanki da ko fad'a bai tab'a yi miki ba, a dalilinshi ne kika rasa morar k'uruciyarki. Shin har yaushe ne Faduma zaki ci gaba da zama kina bauta masa? Sai yaushe ne zaki jefar da k'wallon mangoro ki huta da k'uda? Zuwa yaushe ne zaki kalli k'wayar idonsa ki fad'a masa ba ke bashi har abada? Yaushe ne zaki samu k'arfin gwiwar da zaki ganshi ki watsar a gefe kamar baki ga mutum ba?" Tunda ya fara mata magana take d'an sauke numfashi a hankali inda zafin bakinta ke dukan yatsanshi, d'ora mata yayi da cewa "Fatima ke ba baiwa bace, mutum ce kema mai 'yanci, wannan rayuwar bata kamace ki ba, ki daure ki aje komai a gefe kema ki mori rayuwarki ta hanyar bautawa mahaliccinki da kuma zama a k'ark'ashin inuwar aure." Mik'ewa yayi a hankali tare da kama jakarta hakan yasa ta mik'e tsaye tana binshi da kallo sototo kamar sabuwar hallita, hannu yasa aljihu ya ciro hankc. Cikin nutsuwa ya goge mata hawayen dake kwaranya yana kallon idonta yace "Zubar hawayen nan na fad'a miki bana so, tamkar zubar ruwan dalma ne a birnin zuciyata, duk wanda zai saka saukar hawaye a birnin zuciyata kuma zan iya d'aukan ran ko waye ko da duk duniyar nan tana tare dashi ne." Saida ya soka hanck. D'in cikin aljihu yace "Karki kirawo mishi tsautsayi da gaggawa, kinji?" Zuba hannayenshi yayi aljihu ya juya ya nufi cikin gidan yana fad'in "Muje." Kasa motsawa tayi sai binshi da ido, abinda zuciyarta ta raya mata kawai shine "Anya ba saiya d'aukeni ya shigar dani ba?" Dan k'afafunta kam sun gama mugun sanyi, mutumin nan fa haukatata yake neman yi, ya yake so ne da ita? Shin dama yasan komai a kanta? Ko kuma dai daga abinda ta fad'a ne harya fahimci komai? Ko kuma Ayya ta uku ta fad'a masa komai ba. Kaso dayawa na b'acin ran data shiga taji a take mutumin ya tafiyar mata dashi, kukan data wawuro da niyyar zubarwa ya kwab'ar mata dashi gaba d'aya, a take taji wani k'arfin gwiwa na son ganin Tagur, zata kalleshi ta tata mishi kalar rashin mutumcin da zai dace dashi, sannan ta wuce ta barshi baki sake rik'e da hab'a. *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 21:38 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _48_ Sake juyowa yayi ya kalleta yace "Muje ko?" Da wani irin k'arfi ta d'aga k'afarta ta gusar da ita zuwa gaba, a haka ta ci gaba da takawa har suka shiga ciki, siririyar sallama yayi suka amsa suna zaune kan kujera suna hira, sannu da zuwa suka musu inda War yace "Ka dawo kenan?" Wani kallo Hasheer ya masa yace "Eh, da magana ne?" Tab'e baki yayi bai ce komai ba, cikin nutsuwa Faduma tace "Ni zan shiga ciki, saida safenku." Wardugu ne yace "Ya aikin naki?" Da murmushi ta amsa mishi da "Alhamdulillah, na fara bin al'amarin, zuwa safe zanje gidan da yaron suke zaune,duk da hakan akwai had'ari amma zan kwatanta insha Allah." Jinjina kai yayi yace "Idan kina buk'atar wani taimakon zaki iya yi mata magana saita fad'a min, ko kuma ki sameni kai tsaye ki fad'a." Jinjina kai tayi tace "Nagode sosai, Insha Allah zanyi haka idan buk'atar ta taso." Kallonta yayi yace "Zaki iya tafiya." Da girmamawa ta sake cewa "Nagode, saida safenku." Da murmushi Agaishat tace "Saida safe k'awata." Murmushin tayi mata ita ma tace "Saida safe." Kallon Hasheer tayi kallo mai aika sak'o ta tausasa muryarta sosai tace "Saida safe babban mutum." Bata jira amsarshi ba ta shige ta inda ta fito d'azu, tana shiga d'aki kayanta ta cire, ban d'aki ta shiga da niyyar wanko bakinta ta fito, amma tunawa kalaman bawan Allahn nan gareta sai kawai ta manta saiji tayi ruwa na sauka a jikinta da kayan baccinta data saka, da sauri ta zabura ta janye daga nan, sai kawai ta cire kayan ta sakarwa kanta ruwan d'umi tayi wanka ta fito, wasu kayan baccin ta d'auka ta saka doguwar riga har k'asa mai hannaye iya damtse, shanya wad'ancen tayi a ban d'akin sannan ta fito, ta kashe wutar d'akin tare da hayewa kan gadon ta d'auki waya da nufin kiran Aminu, dan tasan tunda tace zata kira to shi ba zai sake kira ba saboda tsoron kar ya takura mata. Gajeran sak'o ne ya shigo wayarta kamar haka _"Babban fatana bai wuce ace kina cikin farin cidaina a yanzun."_ Murmushi tayi tare da sake nanata sak'on, a hankali ta d'ora hannayenta ta maida da _"Na daina kukan fa."_ Shima murmushi yayi ya maido mata da _"Allah yasa haka, da nafi kowa jin dad'i."_ _"Hakane ma."_ Ta maida a gajarce, a hankali ya maido mata da cewa _"Ki kwana lafiya."_ _"Kai ma haka."_ Ta maida a tak'aice. Kiran Aminun tayi amma abun mamaki sai taji kawai ranta b'acewa yake da yake nuna mata zumud'inshi na zai aureta, sai kawai ta dinga masa magana ba'a yanda ta saba ba tana nuna ta gaji zata kwanta kawai, haka ya barta sukayi sallama ba wani farin ciki ko nishad'i duk da da茂 shi ya so suyi hira ita ce ta k'i. *A wajen* Hasheer ma suna gama wayar ya kira Saudat, tunda ya ga tayi saurin d'auka yasan wayar tana hannunta kenan, shiru babu wanda yayi magana kusan sakanni goma kafin shi yace "Barka da dare." Cikin turo baki ta amsa da "Barka." Girgiza kai yayi yace "Kina lafiya?" "Lafiya lau." Ta amsa kamar bata san maganar ko an sakata dole, tambayar yara yayi suma dai duk ta amsa a hakanan, shiru yayi na wani d'an lokaci kafin yace "Nayi ta jiran kiranki tun tuni, amma sai naga baki da wannan tunanin jin yanda na sauka, na ma sauka lafiya? Duk bai dameki ba." Shiru tayi kamar tana gabanshi sai hararen bango take da turo baki, jin bata amsa ba yasa shi cewa "Na b'ata miki rai ne Saudat? Kina hushi dani ko?" Da sauri tace "Ai kasan dole raina ya b'ace, ina ta maka maganar mota amma ko kulani bakayi ba, wato ga mahaukaciya ma." Ajiyar zuciya ya sauke har saida taji saukarta a kunnenta, cikin kasala yace "Shikenan zan siya, magana ta k'are?" Murmushi tayi tace "Da gaske zaka siya min? Yaushe?" Saida ya girgiza kai yace "Zan siya idan na dawo, kafin nan ki fara shirin tarewarmu sabon gida." Wani dad'i ne ya ziyarceta da sauri tace "Da gaske Bab? Kai amma naji dad'i, dama na matsu mu koma gidan nan wallahi dan nima a dinga kallona babbar Hajia." K'ala bai ce mata ba harta tausa muryarta tace "Amma har da Umma zaka koma can d'in?" Mamakin tambayarta ne yasa shi yin sak'e yana tunanin tambayarta, me take nufi? Ta tambaya ne saboda tayi murna ko kuma bak'in ciki? A hankali yace mata "Eh, da Umma na zan koma." Da k'yar tayi k'ok'arin shanye b'acin ranta murya a dak'ile tace "Shikenan, saida safe." Bata jira taji me zai ce ba kawai ta kashe wayar ta aje tana jan tsaki, cikin jin haushi take fad'in "Ina dalili, mata ke mijinki ya rasu ni kuma kin kanainaye min nawa, komai dai Umma Umma shi kuma, mtssss! Yanzu sabon gidan ma saina tare da hawan jini." Ya jima zaune akan gado yana tunanin rayuwa kafin Wardugu ya shigo d'akin da sallama, dama yasan zai shigo shiyasa bai kwanta ba, amsawa yayi yana aje wayar hannunshi ya gyara zama, sofar dake gefen gado ya zauna yana kallonshi yace "Baka kwanta ba kenan?" Girgiza kai kawai yayi alamar a'a, ajiyar zuciya Wardugu ya sauke y'a kalleshi sosai yace "Hasheer akwai matsala fa." Gyara zama ya sake yi yana fuskantarshi yace "Matsala kuma War? Wace irin matsala?" Cikin jinjina kai yace "Kasan babu abunda ban sani ba, hakan yasa bayan fitarku nasa anbi bayanku, kuma tabbas an gano akwai masu bibiyarku ko kuma nace masu bibiyarka." K'akk'arfar ajiyar zuciya ya sauke yace "Ba zai wuce Aji ba, mtsss! Ban san me yaron nan yake nufi dani ba, so yake saiya kaini bango nayi abinda bashi bane ko me?" Tab'e baki War yayi yace "Ba zai wuce suce suna son ganin bayanka bane tunda bakayi abinda suke so ba, kuma ni hakan ya min dad'i tunda sam mutanen nan babu Allah a gabansu." Wani murmushin takaici yayi yace "Abba fa ya fad'a min komai akan Alhaji Bureima kafin ya rasu, kuma yace ko bayan ransa na had'a hannu dasu bai yafe min ba, ni ko me zai aikeni?" Iska Wardugu ya furzar yace "To yanzu ya ake ciki akan waccen maganar?" Jinjina kai yayi yace "Komai ya daidaita, insha Allahu zuwa jibi zan je mu tattauna da tsohon shugaban k'asa, kuma ina saka ran had'uwa da Alhaji Bassiru." Jinjina kai yayi yace "Hakan yayi kyau, sai kuma maganar bud'a sabon wajen, me ka tsara akai?" Kallonshi yayi yace "Ban shirya komai ba, amma na baka wuk'a da nama ka fad'a min duk abinda ya dace nayi." Murmushi yayi yace "Ba matsala, zuwa gobe da safe zamu san abun yi." Jinjina kai ya sake yi, mik'ewa yayi tsaye yana fad'in "Zanje d'aki orrota na jirana, saida safe gauro." Girgiza kai yayi yana dariya yace "D'an iska dai rairai ne, kuma nima gaba kad'an zan rama." Hararanshi yayi ya nuna shi da yatsa yace "Daga yanzu duk sanda zaka fita zaka fita ne da rakiyar sojojina." Hararanshi yayi shima yace "Sai kace wata mace zan zauna sai an bani kariya, ga yarinyar dake neman d'aga min hankali ma, dole yanzu duk inda zata je k'afarta k'afata." Girgiza kai War yayi yace "Ni dai na fad'a maka, saika kiyaye." Lumshe ido kawai yayi ya bishi da kallo har ya fita, gyara kwancinshi yayi yaja bargo ya rufe, duk awannin da sukayi tare da baiwar Allahn nan ce suka shiga dawo masa a kwanya, saiya samu kanshi da sakin murmushi musamman sanda ta mishi addu'a da lokacin da take son ya bata Ummanshi, da haka har bacci b'arawo ya d'aukeshi bai sani. 07:54 suka shigo tare da War dukansu da kayan sport a jikinsu, yanda suka had'a gumi zai nuna maka motsa jiki sukayi, kallonsu Agaishat tayi dake rik'e da babban faranti da kayan abinci sama zata kaiwa Faduma wacce sukayi aikin tare a madafa ta shiga ta shirya, lura da tayi jiya bata ci wani abun kirki ba yasa take tunanin ko zata fi sakewa idan ita kad'ai ce. Murmushi ta musu tace "Sarakan tsalle tsalle kenan, ba kwa gajiya da wannan guje guje, a haka kuma idan 'ya'yanku sukayi sai kuce su daina." War ne yace "To ai d'an soja sojane." Dariya Hasheer yayi yace "Haka ma matar soja sojace ba." Hararanshi War yayi yace "Inji wa ya fad'a?" Kallonshi Hasheer yayi yace "Ai haka abun yake, hasalima mulkinta yafi naka izza, idan tayi niyya yanzun nan zata hanaka sukuni wallahi." Tsaki yayi yana had'e fuska ya kalli Agaishat yace "Wannan 'yar tatsitsiyar yarinyar? To na gani idan ta isa." Kallonta Hasheer yayi yace "Gaisho kinji, inaga har yanzu War bai fahimci cewa *duk k'aryar kada ta ruwa bace*, amma ina so ki fad'a masa da yaren da zai gane cewa mu maza da bazarku muke taka rawa." _Wanda bai karanta ba ya nemi wannan littafi na *duk k'aryar kada* da kuma *bak'a ce* duk daga marubuciyarmu Sajida._ Wani shu'umin murmushi tayi kawai ta matso kusan Hasheer ta mik'a masa farantin tace "Ka kaiwa Faduma wannan." Da mamaki ya karb'a yana fad'in "Ina take?" Kai tsaye tace "D'akinta mana." Girgiza kai yayi yace "Ba zata fito bane?" Saida ta kalleshi ta saci kallon War tace "Bata jin dad'i ne." A take hankalinshi ya watse da sauri ya nufi hanyar kusurwar yace "Subhannallah, me kuma yake damunta?" Da kallo suka bishi har ya shige, kallon War tayi k'asa da sama ta juya zata wuce, jawota yayi ta fad'o jikinshi ya d'ora hab'arshi akan wuyanta yana fad'in "Ina kuma zaki je? Muje ki had'a min ruwan wanka." Fizge jikinta tayi ta juyo a marairaice yanayin da tasan tana bala'in firgitashi tace "Ayya malam Wardugu, sai dai gashi kuma yarintata tasa Ayyata bata koya min yanda ake had'a ruwan wanka ba, amma kai tunda kana da shekaru ga kuma tarin k'wanji." Ta k'arashe tana tab'a damatsenshi tace "Kaje ka had'a da kanka." A fusace ta juya ta koma d'aki ta barshi nan. Da kallo ya bita yana rarraba ido a ranshi yace "Tofa, Wardugu me ka jawowa kanka kuma?" Da hanzari ya bi bayanta dan dole ya lallab'ata kafin kwana biyu masu zuwa, a haka ma dan yayi sa'a *Walyn* bata nan da gobe zai koma gidanta, shi kuma ba haka yake so ba, tabbas Walyn macece data amsa sunanta kuma ta iya kama jikinta ga tsafta, matsalarta d'aya ce zuwa biyu, rashin bashi mahimmanci da d'aukar al'amarin k'awaye da zuwa biki da mahimmanci, sai kuma rashin damuwa da damuwarshi wanda ta kai ko kusantarta yake sai tai masa rakin tsiya. *Yana* zuwa hankali tashe ya bud'e k'ofar ya shiga, wata irin masifaffiyar k'ara ta kwamtsa k'ara, a tsorace ya saki farantin abincin saboda jin abun kamar daga sama, tsalla idonshi yayi can gaban gadon inda yaji k'arar, da sauri ya k'arasa jin tana fad'in "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, hasbunallahu wani'imal wakil, wayyo cikina zan mutu." Durk'usawa yayi gabanta cikin tashin hankali yana kallonta yanda ta had'a kai da gwiwa yace "Batul, lafiya? Me yake damunki?" A zabure ta d'ago ta kalleshi dan bata d'auka shi bane, da taji zubewar kwanuka ta d'auka mai aiki ce ko matar gidan, dama tasan haka zai faru, tunda ta tashi da asuba taji damuwar saka aurenta ta dawo mata sabuwa da tsananta tunani akan makomar Amjad yasa ta saka ran ganin canjin yanayi, indai zata shiga damuwa sosai to yanayin jikinta kan amsa har ya bijiro mata da jinin al'adarta ko da ba lokacinshi bane, shiyasa ma ta baro Agaishat a madafa ba tare da sun gama aiki ba tayi niyyar shiryawa danta fita ta samu ta siyo auduga, sai dai kashh tsarinta baiyi ba tunda gashi lokacin ya risketa. Cikin fitar hayyaci na rad'ad'in ciwon cikin nan ta kalleshi da k'yar tace "Dan Allah kira min matar gidan, kace ta zo da sauri." Gabanshi ne ya kece ya fad'i, kallonta ya tsaya yi da burin sake tambayarta lafiya? Yanda ta sake matse jikinta sosai ta k'udundune cikin hijabi tana sake fad'in "Dan Allah yi sauri, kayi sauri kaji zan mutu." Girgirza kai yayi da sauri ya mik'e ya fita daga d'akin, Agaishat na jikin Wardugu sai rarrashi yake da 'yar muryarshi har da fad'in "Ni d'in banza da zan musa wannan magana, wallahi kawai na fad'a ne a gabansa, ke fa kinsan yanda muke dashi." Tab'e baki tayi tace "Ai a gabana ka fad'a, da bayan idona ne da sauk'i." Sake marairaicewa yayi yace "Orronur ina kika so na saka kaina, ki tallafa min mana, kinsan bana iya wa sa茂 dai ke." Kallon fuskarshi tayi sai dai kafin tayi magana Hasheer ya k'wankwasa k'ofarsu, da sauri suka kalli k'ofar dan su dai sun san yaransu basa nan, War ne ya taho ya bud'e k'ofar fuska a murtuke, ganin Hasheer ne sai yayi saurin cewa "Hasheer lafiya?" A kid'ime yace "Ba lafiya, ina Agaishat? Ta zo da sauri dan Allah Batul na kiranta." Shima hankali a tashe yace "Me ya sameta? Jikin ne har haka?" Agaishat dake sauraronsu tayi saurin fitowa da mamaki kar dai rashin lafiyar data ambata ce ta zama gaske, ita ta fad'i hakane dan ya kai mata abinci da irin hakane shak'uwa zata shiga tsakaninsu har Faduma ta fahimta, cikin rawar murya tace "Lafiya Elhaj? Tana d'akinta ne?" "Eh tana ciki." Da sauri ta nufi hanyar zai bi bayanta War ya rik'e hannunshi yace "Ka jirata mana, da zaka iya yin wani abu ai da bata buk'aci bak'uwa ba fiye da kai." Dafe k'ugu yayi da duka hannaye biyu yace "Ko me yake damunta? Tana cikin rad'ad'i fa sosai, kamar tana nak'uda." Wata bazawarar dariya War yayi ya dakeshi a kafad'a yace "Sakarai, to ya wuce watanta ne yayi, kai anya kuwa baka haukace akan yarinyar nan ba." Jim yayi alamar tunani sai kuma yace "Kuma fa hakane, kai gaskiya nima dai shashasha ne." 馃槈 _Dama...dama_ Murmushi War yayi yace "Ka zurfafa sosai Hasheer, shiyasa har k'ank'anuwar matsalarta ta d'aga maka hankali ka kasa fahimtar halin da ubangijinsu ya hallicesu ne, garesu kuma ba sabon abu bane face rad'ad'in wata yafi na wata." Kallonshi yayi yace "Ita ma idan ta aureni zata daina insha Allah." Dariya suka bushe da ita daidai lokacin da Agaishat ta fito da sauri ta ratsasu ta shige d'akin, jim kad'an ta fito da sabuwar ledan auduga da kuma plaket d'in magani Ibu. Ta sake wucewa, babu wanda yace mata komai harta shige. Da kanta ta b'alli maganin ta bata tasha kafin ta taimaka mata ta shiga ban d'aki, ta jima a ciki tana tsaftace jikinta kafin ta saka audugar ta fito, zaune tayi bakin gado leb'enta a cije sosai tana rintse ido, tana jin motsin Agaishat tana kai da kawon gyara d'akin na abincin daya zubar, amma bata iya d'aga ido ta kalleta ba harta gama ta dawo kusanta tace "Ya kike ji yanzu? Da sauk'i?" Saida ta saki leb'enta data cije taja numfashi sosai ta sauke shi kafin ta jinjina mata kai tace "Da sauk'i sosai, nagode." Girgiza kai tayi tace "Ba komai, bari na kawo miki wani abincin." Girgiza kai tayi tace "Ki barshi ma ba yanzu ba, anjima zan ci." Kallonta tayi tace "Kin tabbata?" Jinjina kai tayi alamar eh, ita ma jinjina kan tayi tace "Shikenan, bari na barki ki saka kaya." Ba tace komai ba har taji fitarta da rufo mata d'akin. Kwance tayi madadin saka kayan ta dunk'ule, tun yana d'an mata ciwo a hankali a hankali har ya daina gaba d'aya sai kuma bacci ya d'auketa mai dad'in gaske. _______________ Yana ganin sak'onta bai jira komai b芒 ya shigo d'akin Hajiar, tana zaune tana shafa maganin ciwon k'afa dake damunta ya samu wuri ya zauna yana tutturo baki alamar shagwab'a zai mata, kallonshi tayi tace "To auta lafiya? Meya faru ake ta faman turo bakin nan?" Sake turo bakin kam yayi yace "Hajia ni dama na samu wata budurwa ne, kuma ma har mun gama maganar aure da ita, shine nace bari na fad'a miki saiki tura tsofaffin nan gidansu wurin iyayenta." Tunda ya fara magana tayi banza dashi tana ci gaba da shafa maganinta kamar bata san me yake ba, har ya gama bata kulashi ba kuma bata da niyyar hakan, kallonta yayi kamar zai fashe da kuka yace "Hajia magana fa nake?" Kallonshi tayi tace "To ya zance maka? Auta nifa na gaji da shiga sabgar soyayyarka, ka iya samo budurwa kasa mu shiga magana kamar gaske, amma daga baya sai ka zo kace ka fasa, da an tambayeka dalili? Sai kace yarinyar ce ta raina mutane daga yi mata magana ta harareka ko ta maka tsaki, to ina dalili na sake shiga naji kunya, ko su kansu tsofaffin da kake magana akai ba zasu yarda cikin sauk'i suje nema maka aure ba yanzu indai suna da hankali." Kallonta yayi kamar zaiyi kuka yace "Hajia yanzu kenan ba zaku iya yi min abinda nake so ba? Shikenan zan koma na aje aikin nawa dan ni dai ba zan iya hak'ura da budurwata ba." Shiru tayi kamar bata ji shi ba, mik'ewa yayi yana fad'in "Ni wallahi na d'auka ko bayan ranki zaki iya yin fatalwa ki min abinda nake so, ashe ba haka bane." Cikin d'aga murya tace "Auta zan ci ubanka Kabiru fa a gidan nan kana min zancen fatalwa, ni nace ba zanyi maganar ba? Ai kasan ba gane lambarsu ba nake bare na kira, b芒 sai ka jira gari ya waye ba saika kira Kabiru ka bani shi a waya." Ko da ta fara magana yake ta k'yalk'yala dariya a b'oye, juyowa yayi ya dawo gareta ya tsuguna ya shafa k'afarta yace "Yawwa Hajiata nagode, Allah ya saka miki da alkairi, Allah ya barki dani har duniya ta tashi." Bige hannunshi tayi tace "Kai dallah can tafi ka bani wuri, shashasha kawai." Har ya mik'e tace "Kuma wallahi wannan karan aka nemo auren ko kasheka yarinyar zatayi ba za'a fasa ba kaji na fad'a maka." Dariya yayi yace "Hajia ai wannan ma mai hankali ce, tunda ta tab'a aure mijinta ne ya rasu, amma bata tab'a haihuwa ba." Zaro ido tayi tace "Auta me kace? Bazawara fa? Kai yanzu matar matacce zaka aura? Duk 'yan mata sun k'are ne a garin wannan da sai bazawara zaka aura kana saurayi da kai? Ah lallai na yarda haukan tuzurantaka ya tab'aka kaima." Dawowa yayi ya zauna yace "Hajia to miye aibu a ciki dan ta tab'a aure? Ni ita nake so kawai ki goya min baya nayi koyi da sunnar manzo (S.A.W)." Girgiza kai tayi tace "Auta gaskiya ka sake wata, kasan ko dangin ubanka ma suka ji wallahi ba zasu yarda ba." Cikin rarrashi yace "Amma ai Hajia suna tsoronki kuma suna ganin girmanki, inhar kika nuna musu abinda autanki ke so ne fa shikenan, babu wanda zai ce wani abu sa茂 dai daga nesa." Kallonshi tayi tace "Yanzu kai dole sai ita." Marairaicewa yayi yace "Hajia ita ce tayi min alk'awarin kula dake da ni gaba d'aya, ni kuma wacce zata kula dake nake son aura ba yarinya fitsararriya ba, kuma ma Hajia ai wasu 'yan matan saboda ke ce muke fad'a dasu in sukayi magana ta rashin kunya a kan ki." Girgiza kai tayi tace "Allah ya shiryaka auta, sam baka jin yuwar yin zaune ka sharara min k'arya son ranka." Da sauri ya kamo hannunta ya juyo da kanta zuwa kanshi yace "Hajia ba k'arya bace, gaskiya na fad'a miki, in baki yarda ba mareni ki gani." Girgiza kai ta sake yi tace "Shikenan tashi ka bani wuri zanyi tunani." Kallonta yayi yace "Shikenan Hajia, amma dai karki mance da cewa ita ce wacce autanki yake so, rashinta a gareni zai iya jawo min ciwon zuciya." "Allah ya sawak'e auta, ko ni banyi ciwon zuciya ba bare kai, ba dai kana sonta ba?" D'aga kai yayi yace "Sosai ma Hajia." Jinjina kai tayi tace "Shikenan da safe zan kirashi." Sumbatarta yayi a kumatu ya tashi da sauri ya bar d'akin yana jin dad'i. *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 21:38 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _49_ Ai kuwa da sassafe sai gashi d'akinta wanda wani lokacin saita fita taje d'akinshi da kanta dan ganin ko yana nan? Haka zata sameshi yana bacci, amma yau gashi da samako da shigowa nan, wayarta ya karb'a ya kira baba Kabiru ya bata wayar, yana saurarensu suka gaisa har ta nemi daya zo gida ya sameta anjima, da girmamawa ya amsa mata da to kasancewarta matar yayanshi daya rasu, suna idar da wayar ya kalleta yace "Hajia karfa ki manta idan ya zo ki fad'a musu ni a sati uku nake so, ita ma budurwar tawa ta amince." Girgiza kai kawai tayi ta bishi da addu'ar Allah ya shirya, har ya juya zai fita sai kuma yace "Hajia zan fita yanzu naje na samo wanda zasu mana gyaran gidan, kinsan fa saina fara zama da amaryar nan kafin mu wuce can." Rik'e hab'a tayi tace "Tun yanzu auta?" Nuna mata tsintsiyar hannunshi yayi yace "Kai Hajia ai babu lokacin b'ata lokaci, sati uku ne fa kawai, har akwatuna duk zan had'o yau d'in nan." Ita dariya ma ya bata kawai. _______________ Ko dan baccin safe ba d'abi'arta bace hasalima ba zata iya tuna da wayonta ranar data yi shi ba, sai wannan d'in data samu ya mata dad'i sosai har ta nink'aya izuwa duniyar mafarki mai dad'i da aminci, vibration d'in wayarta dake kan gadon yasa ta tashi firgigit tana rarraba ido, saida ta lalubo wayar ta d'ora a kunne ba tare da duba wanda ya kira ba, sai kuma ta dafe cikinta da ta tuna ya mata ciwo d'azu amma yanzu ya bari, cikin muryar bacci tace "Na'am." Abdu ne daga inda yake tsaye yace "Faduma yaron da kika ce na miki bincike akan shi, yanzu haka gani k'ofar gidansu wani abokinshi ya saukeshi a mota, kuma a yanayin daya shiga ciki ina jin kamar a bige yake." Da sauri ta nufi wurin kayanta data saka a drower tana fad'in "Yawwa nagode, zaka iya sanin abokin nashi?" Da sauri yace "Eh nayi tambaya, kuma wanda aka bani masaniya akanshi shine ya saukeshi yanzu, dan an tabbatar min kullum tare suke." Da sauri tace "Da kyau, yanzu ka turo min kwatancen gidan a msg ina zuwa yanzu." "Shikenan." Ya fad'a yana datse kiran, da sauri ta saka riga da zani daban daban ta saka hijab d'inta na sallah ta fito da wayarta a hannu, a zatonta ba zata samu kowa a falon ba, dan haka ta wuce da gudu gudu ba tare data dubi wajen zaman ba, saida ta kusa kai k'ofa yace "Idan kika zubar da hak'ora sisi ba zan kashe ba." Cak ta tsaya ta jiyo da sauri tana kallonsu, duk sai jikinta yayi sanyi ganin dukansu a tsaye amma kamar mazan fita ne zasuyi Agaishat kuma ta rako mai gidanta, kallonshi tayi ta turo baki tace "Ai ina da kud'i nima, ko ka manta har mota ce dani a garinku?" Maganarta dariya ta basu sosai har Wardugu sai gashi yana k'yak'yatawa, Agaishat ce tace "Kinyi gaskiya, kinga kuwa ba za'a goranta miki ba." Wardugu ne yace "Kuma yayanki ma ai yana da kud'i, kuma zan iya kashe ko nawa ne akan ki bare a d'aga mana hanci." Kallon Hasheer tayi tace "To kaji." Tab'e baki Hasheer yayi yace "Wai jiya da kika zo ba kece ke lab'ewa bayana ba kina tsoronsa? Yaushe har kuka fara 'yan uwantaka?" Galala ta kalleshi tace "Lahhh! Wai me yasa ka fiye tashin tashina ne?" Agaishat ce tace "Ke rabu dashi, ai mijina kwarjini ne dashi, nima haka yake kayar min da gabana." Kallonta War yayi yace "Amma duk da haka ai ban tab'a gani a idonki ba, orro na so naga kina d'auki a kaina, na so naga kina rawar jiki idan kika ganni, amma sai kike nunawa kamar ma baki gann ba." Girgiza kai yayi yace "Yarinyar nan fa kin wahalar dani dayawa." Dariya Faduma tayi ta kalli Agaishat tace "Da girman kujerarki Hajia." Dariya suka saka amma banda Hasheer dake kallonta a ranshi yana fad'in "Ai ga wata Agaishat d'in nan, tana fahimtar karatun sala sala, amma ita ta ma bud'e min k'ofa naji dad'in bata bayani ta k'i, ko na d'auko maganar da nake so ta hau kan mizani saita canza mana hira zuwa wani abu daban." Cije leb'e yayi shi kad'ai ya jinjina kai yace "Yaran nan, suna son wahalar da mutane." Kallonshi duk sukayi dan a fili yayi maganar, kawar da kai yayi sai Faduma data mayar da kallonta kansu, saurin da take yasa ta cewa "Nagode yallab'ai, zan fita ne ina sauri sosai." Takowa yayi zuwa gareta yace "Muje na kaiki?" Da ido da baki duk saida suka girgiza tace "A'a, zanje da kaina, naga kamar zaku fita." Kallon War yayi sannan ya kalleta yace "Eh, amma na fasa, idan kika fita ke kad'ai gabana fad'uwa yake." Kallonshi tayi da wata fassara ta daban, muryar War ce ta tsinkaya yana fad'in "Kuje Allah ya kiyaye, idan ka dawo da ita saika sameni acan." Jinjina kai yayi alamar to sannan ya wuce, saidai yayi mamakin yanda War ya goya masa baya madadin ya masa tijara, bin bayansa tayi tana kallon k'eyarsa tana tuna mafarkinta na yanzu, murmushi kawai tayi ta kawar da kanta a ranta tace "Ba zai tab'a faruwa ba, wannan farin cikin yafi k'arfinki Faduma." Ba dan zuciya ma da kai kanta inda yafi k'arfinta ba, me ya kaita hango mata babban mutumin nan a matsayin *mijin aurenta*, ai sam basu dace ba ma da juna tunda ya fita komai da komai, dan ma yana k'ask'antar da kanshi zuwa mataki na k'asa, ba dan haka b芒 a yanda tasan margayi mahaifinsa da yanda ko kwalin sabulu ta d'auka saita ci karo da mai sunan risham ai ganinshi ma ba abu bane mai sauk'i, shine har da nuna mata gasu a k'asar waje da bata san wace k'asa bace wai tana goye a bayanshi da kayan sanyi a jikinsu. Dariyar da abun ya bata ne yasa har sautinta fitowa, juyowa yayi ya kalleta da mamaki sanda yake bud'e motar yace "Hajaj ya dai?" Da sauri ta kalleshi kamar wacce ke gidan biki aka ce d'aga zan duba ajiyata, sai kuma ta girgiza kai tace "Ba komai." Murmushin yak'e ya mata ya shiga ya zauna itama ta zagaya ta zauna, saida yayi baya baya yace "Me kike ma dariya ke kad'ai?" Ajiyar zuciya ta sauke tace "Mafarkin da nayi ne ya saka ni dariya." "Wane iri kenan?" Ya fad'a yana danna hancin motar zuwa waje, yar dariya ta sak茅 yi tace "Sirri ne, ba zan fad'a ba ka min dariya." Kallonta yayi yace "Da gaske ba zan fad'a ba." Kallonshi tayi itama tace "A k'asar waje na ganni, ina rayuwar da ko a mafarkin ba'a tab'a nuna min ita ba sai yau." Murmushi kawai yayi yana tambayar kashi to ko dai mata ne ke da son a fita dasu k'asar waje, shi kam a rayuwarsa baya son fitar nan idan bata zuwa sauke farali ba ko kuma yaje mahaifar mahaifiyarshi, shiru kawai yayi bai ce komai ba saida taji wayarta tayi k'ara alamar sak'o ya shigo, dubawa tayi sannan ta kalleshi tace "Bassora zamu nufa." Bai kulata ba sai ci gaba da tuk'i, madubin dake gabanshi ya daidaitawa zama ya hangi bayanshi, murmushi yayi dan ganin d'aya daga cikin motocin gidan War. Muryar Faduma ce ta dawo dashi tana fad'in "Yallab'ai wai me ka zo yi garin nan?" Ba tare daya kalleta ba yace "Wanda ya tara iyali an jefesa da wannan tambayar? Dako na zo yi." Murmushi tayi tace "Dako ma ai kala kala ne, wanne ka zo yi?" Saida ya saci kallonta yace "Na mutane da kayansu, kamar dai yanda nayi naki kuma nake kanyi yanzu." Bud'e baki tayi da mamaki tace "Lahh! Ni fa bana son gori, a maka ko baka so kuma ace an maka." Dariya yayi bai ce komai ba, saida sukayi nisa ya kalleta ba alamar wasa yace "Ina da had'uwa da tsohon shugaban k'asa, daga nan kuma zan bud'e sabon reshen risham wax." Jinjina al'amarin tayi amma a k'asan zuciyarta, a fuska kuma murmushi tayi tace "Yayi kyau, Allah bada sa'a." "Ameen." Ya fad'a a hankali, kallonta yayi yace "Yanzu fad'a min kema, akan wace matsala kike bincike yanzu da har take had'aki magana da mazan dana gani jiya?" 'Yar dariya tayi tare da kallonshi tace "Wata budurwa aka banke, yaron kuma daya banketa harta rasa ranta yana yanayin buguwa, amma saboda d'an mai kud'i ne shi sai aka canza zancen zuwa wani daban, akan shi nake aiki har nake magana da maza a arha wasu kuma har suna dakona." Dariyar da baisan da zuwanta bane ta taho mishi tare da girgiza kai yana fad'in "Da alama tsoron tsiya ne ya miki yawa, amma ba'a kayar dake wajen maida magana." Kallonshi tayi tace "Nice ma mai tsoron, ni ai bana da tsoro." Girgiza kai yayi yace "Kece Fatima ta farko dana sani matsoraciya madadin jaruma." Turo baki tayi tace "Ni fa babu abinda ke tsoratani." Jinjina kai yayi yace "Uhm! Na gani ai, tunda ranar ma da k'adangare ya biyoni a bayanki na b'uya." Baki sake tace "Lahhhh! Me kake nufi?" D'aga kafad'a yayi yace "Ba abinda nake nufi, gaskiya kawai na fad'a." Tab'e baki tayi cikin muryar yarinta tace "A dai riga fad'in gaskiya tsakani da Allah." Kallonta yayi yana wani murmushi yace "Titi kinsan duk ranar da kika shiga hannu na *zaki gane kurenki* ko?" Cikin k'yalk'yala dariya tace "Taya ma zan shiga hannunka babban mutum?" Jinjina kai yayi yana murmushi yace "Idan kikayi tuntub'e zaki fad'i." Ba tare data daina dariya ba tace "Tunda hakane ba zan yarda na fad'o ta kusurwar da kake ba, sai nayi dama ko hagu." Dariya kawai ya saki marar sauti bai ce komai ba, dan cikinshi ma ya fara mishi ciwo saboda dariyar da take saka shi, bugu da k'ari har yanzu yana mamakin yanda yake zama uban surutu a gabanta, yawan maganarshi da yawan fara'arshi idan yana tare da ita ne, shiyasa yake da burin samunta a rayuwarshi ko dan ta zama farin cikinshi kuma abokiyar hirarshi. A daidai motar Abdu ya paka ta sauka, matsawa tayi kusa dashi tana fad'in "Har yanzu yana ciki ne?" Jinjina mata kai yayi alamar eh, a hankali tace "Nagode sosai Abdu na barka kana ta jira, ka je kawai ni zan shiga ciki." "Ciki kuma?" Ya fad'a yana kallonta, murmushi tayi tace "Karka damu." D'aga kai yayi alamar shikenan, bud'e motar yayi bayan ya tabbatar mata zai k'ara samo bayanai kan abokinshi sai suyi waya. Saida taga tafiyarshi ta dawo kusan motar, lek'o kanta tayi tasa k'arfi ta keta hijabinta a wuyan, kallon fuskarta tayi a madubi dama bata shafa mai ba, gashi yanayin sanyi sanyi har yanzu sa茂 tayi fari alamar a bushe take, kallon Hasheer tayi daya k'ura mata ido da mamaki yana kallo, murmushi ta masa tace "Zan shiga ciki na fito, ba tabbacin fitowata yanzu." Da baki ya nuna k'ofar data kalla yace "Nan d'in ina ne?" "Gidansu yaron dana fad'a maka." Ta fad'a kai tsaye, d'an turo idonshi yayi amma baice komai ba, yana kallonta harta shige ciki sai wata ajiyar zuciya daya sauke, girgiza kai yayi yace "Ya zaki dinga jefa min kanki a had'ari irin wannan? Ina zaune anan kina ciki tare da yan iska? Hmmm!" Ya kama hannun murfin zai bud'e wayarshi tayi k'ara, d'auka yayi ya duba yaga Abdallah ne, wani huci yayi dan yasan in biye masa zaiyi suyi hira awa d'aya ba zata rabasu ba, kuma akan abu guda zasuyi ta maganar saidai yayi ta nanatashi yana sak茅 mishi kwalliya yana fad'a, d'auka yayi yana shan magani dan ya fahimci 'yan maganar basu saman kanshi amma fa dashi saboda akwai wani abu a gabanshi. Sallama ta dinga kwad'awa a harabar gidan da k'arfin, dan a dole take so ta zama wata daban ko da ba 'yar k'auye ba, saida tayi sallama kusan goma sha wani abu kafin daga ciki aka amsa da "Waye wai?" Saida ta d'an tsorata jin muryar a wani irin yanayin mugun bacci da tsananin kasala sak irin muryar 'yan maye, d'an dakewa tayi ta matsa kusan k'ofar shiga falon dan k'aramin gida, saida ta gyara muryarta sosai wajen gauraya hausarta da harshen zarma tace "Yallab'ai bak'uwa ce." Shiru akayi wanda yasa tayi tunanin ko bacci ya sake d'aukar wanda y'a amsa sallamar, duk da alamu sun nuna mata mutum d'aya ne a ciki, wata sallamar ta sake zabgawa da k'arfinta har tana jin mak'oshinta na amsawa, dan rabon data d'aga murya kamar haka zata iya cewa tun sanda Aba yake mata dukan mutuwar nan. A hassale sosai cikin b'acin rai wanda shaye shaye ya sak茅 handasa mishi ya waro labulen daya musu shamaki tsakanin ita da ganin cikin falon, cikin harshen zarman daya kama na zama anan yake fad'in "Mahaukaciyar banza, wacece ke? Uban me kika shigo nema da zaki takura min?" Fararen idonta ta sauke cikin nashi fuskarta a gimtse, data tuna me ya kawota kuma saita saki fuskar ta matso tana had'e hannayenta da k'ak'aro kukan k'arya tana bashi hak'uri da zabarmancin da ita ma ta kamashi tun sanda take karatu data zauna da mama Aissata, a tsawace yace "Me kike nema nace?" Da gurgurin hausa tace "Yallab'ai ka taimake ni kayi min rai kamar yanda Allah ya taimake ka, aiki nake nema ko wane iri ne, shara guga, wanki, wanke wanke, kai ko wane aikin k'arfi ko wahala zan iya yi dan na samu abinda zan ciyar da marayu na." Nunata yayi da yatsa yace "Akan wannan ne kika tasheni a bacci, ke kinsan waye ni kuwa?" Ya fad'a yana tangad'awa kamar zai kifa, durk'usawa tayi tace "Dan Allah yallab'ai ka taimake ni, ko shara ce na maka saika bani abinda zan ci." Rufe ido yayi ruf kamar bacci ya d'aukeshi daga nan, kusan sakan goma a haka tana satar kallonshi kafin ya bud'a ido ya kalleta, nunata yayi da yatsa yace "Shiga nan saiki share...inkin gama ki tafiyarki...karna sake ganinki anan, kin...ji ko?" Mik'ewa tayi ko to b芒 tace ba ta wuce ciki bayan ta cire takalminta, warin daya mata maraba a d'akin ya sake tabbatar mata ko waye shi, bata raba d'ayan biyu cewa har giya wannan yana tab'awa idan ya samu, sigari da shisha da kwalaben cod茅ine da benelin ba adadi a k'asan teburin dake tsakiyar falon. Jin motsinshi a bayanta yasa tayi saurin matsawa gefe ya wuce, wani d'akin ya shiga wanda ta tabbatar bacci ne zai koma, ajiyar zuciya ta sauke na jin dad'in yanda aikinta ya zo da sauk'i, sam bata tsammani haka ba shiyasa ta shiryo da kyau. Girgiza kai tayi, a hankali ta sake nanata sunan a ranta "Attahir Bureima Sugui, k'ane ga Aji, d'an uwa ga Tagur, hummm!" Ta fad'a tana ciro wayarta data soka a cikin rigarta k'asan cibiya, hotunan kwalaben nan ta dinga d'auka kafin ta mayar da wayar ta fara aikin tattare d'akin, leda ta samu ta zuba wasu daga cikin kwalaben da suka d'aure mata kai har da syringe na allura data gani duk ta d'auka, aje ledar tayi daga waje kusa da abun zuba shara. Komawa tayi ta ci gaba da aikin, cikin sauri kam sai ga d'akin ya zama na mutane har warin ya rage, d'akin daya shiga ta nufa da niyyar k'wank'wasa tace ta gama, tana d'ora hannun taji k'ofar ta tafi alamar a bud'e take, har zata dawo sai tayi sallama sai kuma ta girgiza kanta, d'an sake turawa tayi a hankali, kwance ta hangeshi k'asan gado duk da ga gado kuma lafiyayye, shi kanshi d'akin akwai datti sai dai ba kamar falo ba, da sauri ta ciro wayarta wacce ke silent ta d'auki hotonshi, jan k'ofar tayi ta rufe kamar yanda take kafin ta juyo zata fito. Ido hud'u sukayi da Hasheer daya gama waya da Abdallah ya mishi albishir shifa ya samu shiga, sannan ya mishi iskanci mai kyau cewa wai ya barshi a baya yana nan yanata kallan ruwa kwad'o zai masa k'afa, da k'yar ya rabu dashi shine fa ya shigo dan ya samu hankalinshi ya kwanta. Da sauri ta taho bata kula ba kawai ta kama hannunshi suka fito daga d'akin tana mishi alama da yayi shiru, ledar data aje ta d'auka suka fita suka shiga mota. Aje ledar tayi k'asan k'afafunta ta shiga gyara hijabinta dan ya zauna mata a kai sai sauka yake, saida ta gama ta ciro wayarta ta shiga duba hotunan, tab'e baki ta dinga yi tana yatsina fuska, kallon Hasheer tayi dake kan tuk'i tace "Yallab'ai wane likita zaka iya had'ani dashi wanda yasan harkan miyagun k'wayoyi sosai?" Saida ya langab'ar da kai yace "Nawa zaki biya?" Wani iska ta shak'a kafin tace "Nawa kake so?" Kallonta yayi yace "Baki ci komai ba tun safe, na fara sama miki wani abun da zaki ci, daga nan sai ayi koma menene." Kallonshi tayi da kallo na basira, dan ita harta manta da bata ci komai ba ma sai yanzu daya fad'a, marairaicewa tayi tace "Idan na koma gida zan ci, yanzu dai ka fara ajeni a asibitin." Ba tare daya kalleta ba yace "Ashe kuwa ba zaki gama aikin nan daya kawoki ba, dan wallahi in baki ci komai ba babu inda zaki matsa daga nan." Ajiyar zuciya ta sauke tana fad'in "Allah karya kawo ranar da zaka min d'ure." Bai kalleta ba yace "Indai zaki dinga wasa da cikinki abinda zai faru a tsakaninmu kenan nan gaba kad'an." Rumgume hannaye tayi tace "To naji." Kallonta ya d'anyi na lokaci ya kuma kalli gabanshi yace "Haka zaki je asibitin?" Da sauri ta kalleshi tana dariya tace "Nayi kyau ko? A haka na maka kama da wata 'yar k'auyen gwaddoji?" Dariya yayi yana girgiza kai bai ce komai ba, wata k'aramar restaurat ya tsaya, futa yayi cikin nutsuwa ya k'arasa bayan yace mata yana zuwa, da kallo ta bishi har ya shige ciki, ajiyar zuciya ta sauke tana fad'in "Ko miye a ransa a game dani?" Da sauri ta girgiza kai tace "Ina ga fa dan ina k'anwar yaya Kalli ne, shiyasa yake kyautata min sosai yake bani kulawa." Ta jima anan ita kad'ai har ta amsa wayar Abdu ya bata bayanan yaron da inda yake zama da halinshi na neman mata, hakan ya mata daidai dan haka sukayi sallama. Lokacin kuma Hasheer ya dawo ya mik'a mata sandwich d'in daya saka aka had'o mata, karb'a tayi tana fad'in "Shikurdunna (nagode)." Saida ya shiga ya tayar ya kalleta yace "Duk randa kika kaini bango na fara nawa yaren zaki gane kurenki." Murmushi tayi tana k'ok'arin aje ledar akan cinyarta, da sauri yace "Ban gane ba? Cinyewa zakiyi ki bani ledar." Satar kallonshi tayi a ranta tana tunanin yanda zatayi haka kam, bata tab'a yi b芒 tunda take, taya yau zata fara? Wannan b芒 tsarin rayuwarta bane, marairaicewa tayi tace "Zan ci idan muka isa gida." A marairaice ya kalleta yace "Fati yunwa kike ji fa, baki ci komai ba." Zuba mishi ido kawai tayi wanda ya kasa jura ya d'auke idonshi yace "Sai dai na kaiki gida, idan kika cika cikinki saina kaiki duk inda zaki je, daga nan ma kya canza wannan shirin." Turo baki tayi amma ba tace komai ba dan yanda ya had'e fuska ya nuna babu wasa a ciki, tana kallo suka mayar da akalarsu zuwa gida kam. ________________ Yayi kiran duniya har ya gaji haushi kamar zai kasheshi daga tsaye, a k'arshe saida aka fad'a masa ta fita yasa yaron ya shiga cikin gidan ya tashi Attahir ya bashi wayar, cikin hargagi da b'acin rai Aji ya daka masa tsawa yana fad'in "Attahir kai mahaukacin ina ne? Wane irin wawa ne kai? Faduma data shiga gidanka me tayi a ciki?" Cikin baccin da har yanzu y'a k'i barinshi yace "Faduma? Wacece hakanan kuma? Me nayi yanzu?" A razane yace "Ubanka kayi, yarinyar data shiga gidanka ta d'auki sama da awa d'aya a ciki, me tayi a ciki nake son sani?" Yaron dake tsaye gabanshi ya k'urawa ido yana kallo yana lullumshesu, shi har tsoro ma ya bashi dan ya lalata gaba d'aya rayuwarshi, ya jima a haka wai shi tunani ne yake kafin yace "Mai aiki ce fa, neman aiki ta zo na taimaka mata." Da k'arfi Aji ya buga teburinshi yace "Shiiiit!" Datse kiran kawai yayi hankali a tashe ya danna lambar Alhaji Bureima yana fad'in "Da aka fad'a min an ganku tare na d'auka lauyarsa ce ke, ashe ke aka d'auko a wannan case d'in, hummm! Faduma ba zai miki kyau ba al'amarin kam yanzu tunda dani kika had'a hanya." Bureima na d'agawa yace "Aba kasan me yake faruwa kuwa?" Jin yanda yake magana ya tabbatar masa ba lafiya ba, dan haka yace "Me yake faruwa Aji?" Da sauri yace "Aba Faduma ashe ita ce lauyar da aka d'auka zata kare dangin yarinyar nan, Aba yanzu haka har taje gidan Attahir a matsayin mai neman aiki kuma ya barta ta shiga, kasan gidanshi kuma baya rabo da kayan kurb'e kurb'en nan na banza." Cikin tashin hankali yace "Subhannallah! Aji kayi wani abu wallahi kar yarinyar nan tasa a kulle min yaro, in haka ta faru fa saina kasheta da hannu na, to ni dai na fad'a maka." Kashe wayar yayi sai bin wayar da yayi da kallo, kenan shi ya fishi jin zafi? Jinjina kai yayi ya shiga neman lambar d'aya daga cikin yaran da suke bin bayan Hasheer, zai aika kiran sai kuma kiran Aisho ya shigo wayar, cikin tsananin jin haushi ya danna ok ya d'ora a kunne yana fad'in "Ina jinki miye?" Cike da dakiya murya a dak'ile tace "Dama Khairat ce ba lafiya, ina so zan kaita asibiti." A tsawace yace "To ki kaita mana, miye na sai kin fad'a min kafin ki kaita? Zan tura miki kud'i yanzu maza ki kai min yarinya asibiti a dubata." Bai bata damar fad'an komai ba ya datse kiran ya shiga sabgar gabanshi data fi mishi anfani. ________________ Suna zuwa gidan a falo ta samu Agaishat zaune da wasu robobi a gabanta kalar na ice cream amma kuma bashi bane a ciki, dan har takarda ke jikinsu da rubutu, gefe kuma gwangwanin madara ne k'ato sai kofi, da murmushi tace mata "Sannu da gida madame, ke kad'ai zaune?" Da fara'a ita ma tace "Wallahi ni kad'ai, masu aikin duk sun tafi, dama sukan zo ne su tayani shara da goge goge, bayan haka ban yarda su kama min komai b芒 a harkar gidana, jiya ma dan nasan zamuyi bak'i ne harna rik'esu suka kama min girki." Ta birgeta kam dan haka tayi murmushi tace "Yara basu dawo ba?" Girgiza kai tayi tace "Basu dawo ba, idan suna wurin Ayya basa ko tunawa dani." Dariya tayi tace "Shikenan kar zaman kad'aici ya dameki, bari na shiga na fito saina zauna muyi hira, karki ce bak'uwar nan ta cika yawo." Dariya tayi tace "Ah b芒 komai ai, ke da kika zo aiki." Cike da gajiya tace "Wallahi kuma yanzu ma ina son zuwa asibiti, amma tunda dai nace zamuyi hira zan zauna insha Allahu, zuwa azahar saina tafi." Murmushi tayi da farin ciki tace "Naji dad'i gaskiya." Nufa hanyar d'akin tayi tace "Saina fito." Jinjina mata kai tayi kafin ta sake duba robobin dake gabanta, yau kam tana cikin farin ciki saboda ta sake samun nagartattun magunguna daga hannun wanda ta yarda dasu ta kuma yarda da aikinsu. Tana shiga d'aki lambarshi ta nema ta turawa sak'o kamar haka _"Elhaj zaka iya tafiya uzurinka, wallahi duk kasa ina jin kaina kamar wata wacce ta isa, ni na fasa fitar ma."_ Ganin sak'onta yasa shi murmusawa kafin ya maido mata da cewa _"Zan tafi, amma kar kiyi mamakin ganina a gabanki duk sanda kika fita bada sanina ba."_ Dariya ta tura masa sa茂 ya maido mata da cewa _"Da gaske."_ Maidawa tayi ita ma d'脿 cewa _"Na yarda. "_ Ya fara baya baya zai fita daga gidan ya lura da ledar data aje, sake tura mata sak'o yayi cewa " Ledar nan Allah yasa ba shara bace a ciki?" Dariya tayi sosai ta maido da cewa _"Da ita zan tafi asibiti, akanta zan nemi sanin anfanin maganin dake cikinta."_ Jinjina kai kawai yayi bai maida mata ba ya fita daga gidan, yanzu ma kamar d'azu akan babur wani soja yabi bayanshi har yaji ya tsargu. *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 21:38 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃馃馃馃馃馃馃馃馃馃 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 馃馃馃馃馃馃馃馃馃馃 _Lallai wannan littafi ya ci sunansa, domin kuwa da wasa wasa *Najeeba* tayi wuf da zuciyar sarkinmu mai adalci mai damagaram sultan *Shaheed*. Babban darasin dake ciki kuwa bai wuce irin yanda ya kamata 'yan uwa su zama ba, yaya kamar yaya D'ayyab gaskiya a kowane gida za'a so samun irinshi, ko wane uban zai so haihuwar yaro kamar yaya D'ayyab, Allah ya saka masa da alkairi, ni nafi kowa sanin cewa yayanmu ke da wannan halin shiyasa kika sako mana shi a matsayin yaya D'ayyab, Allah ya saka masa da alkairi, Allah y'a bashi yaran da zasu k'aunaci junansu sama da yanda ya so ku, Allah ya dafa masa a al'amuransa baki d'aya. Mai gayya mai aiki, hazik'a a cikin hazik'ai, zinariya a cikin taurari, Allah ya k'ara miki basira da hazak'a da ilimi mai anfani, Allah ya tsare gabanki da bayanki ya kauda idon 'yan bak'in ciki akan ki, ina ji dake, ina alfahari dake, ina tink'aho dake, ina girmama lamarin daya shafeki, kiji dad'inki tawajena ki huta son ranki, sai mun had'u bayan sallah insha Allah._ _*Kwaten Kakar Ejaz ce*_馃憣 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _50_ Tana gama shiryawa ta zauna ta ci sandwich d'in nan kafin ta fito, a falo ta samu Agaishat ta mik'e tsaye, kallon juna sukayi tace "Na ganki a tsaye." Da fara'a tace "Naga rana tayi, shine zan shiga madafa na fara aiki." Jinjina kai tayi tace "Eh gaskiya kam, to muje sai muyi aikin." Madafa suka shiga mai kyau da tsari da girma dan fara aiki, kallon Agaishat Faduma tayi tace "Yanzu ke kad'ai ce a gidan nan? Kuma ba kya jin tsoro idan yallab'ai baya nan?" Dariya tayi tace "Ni kad'ai ce anan, abokiyar zamana tana d'aya gidan." Da mamaki ta waro ido tace "Wai dama kina da abokiyar zama?" Da dariya a fuskarta tace "Eh mana, ke baki ga tsoho ne na aura ba?" Dariya tayi ta sunkuyar da kanta tace "Ba wani tsoho, amma yaranku nawa?" "Biyu, Muhammad da Khalid." Ta fad'a tana rufe fridge data d'auko nama a ciki, hannu Faduma tasa ta karb'a tana fadin "Allah ya rayasu." "Ameen." Tace sai Faduma da tace "Ya zakiyi da naman? Ko na miki marineshi." D'aga kai tayi tace "Eh, abinda zan mishi kenan." Aikin naman ta fara yi inda Agaishat kuma ta fara sarrafa pliwar da zatayi gassashen bredi, Faduma ce tace "Amma me yasa baku zauna a tare ba? Naga dashi kanshi mijinku zaifi samun nutsuwa da farin ciki." Cikin rashin jin dad'i Agaishat tace "Nima na so hakan, amma dana masa magana saiya nuna min ba hurumi na bane, kuma ita ta k'i kwantar da hankalinta, sai kawai na share batun nima." Kallonta tayi tace "Tana da yara ita ma?" Girgiza kai tayi tace "Har yanzu dai ana jiran lokaci?" Ajiyar zuciya ta sauke sanda take saka hannunta cikin ledar safar girki zata fara yamutsa naman tace "Amma a ganina da kin sake jarabawa, rayuwar gaba ake ji b芒 yanzu ba, k'aramin misalin da zan iya baki shine yaranku, idan suka tasa suka ga kanku a rabe yake zasu san da bambamci kuma babu jituwa a tsakaninku, k'arara zasu dinga nuna rashin girmamawa gareta ko da had'uwa sukayi a hanya, ba za'a tab'a samun shak'uwa tsakanin yaranki da nata ba idan Allah ya bata, ya kike ganin idan babu ran mijinku? Ba fatan mutuwa nake masa ba sai dai kowa yasan dole ce, idan ya barku a haka zaku tashi kanku a ware babu had'in kai da k'aunar juna, a matsayinku na wanda suka had'a miji, 'ya'yanku kuma suka fito ta tsatsonshi abun ba zaiyi dad'i ba, duk abinda aka ce ya faru na rashin jituwa tsakaninku babu wanda zai k'aryata, kuma wariyar kan naku zai iya haifar da komai." Sanyin da jikin Agaishat yayi ne yasa ta kallon Faduma kamar zatayi kuka tace "Wallahi Faduma ina tunanin abun nan ni ka茂na, saidai ina tsoron shiga duk al'amuran daya nuna min ba ruwana ne, musamman ma *Walyn* data gama tattare kayanta daga gaban ma'aiki, amma daga abinda kika tunatar dani yanzu yasa naji k'arfin gwiwar sake tunkararshi da maganar ko da ba zai ji dad'i ba." Matsowa tayi sanda ta gama wanke hannayenta bayan ta rufe naman tana fuskantarta tace " *Trozzonur* (k'awata), kin ganni nan a gidan mata biyu na tashi, ko da na bud'e idona mata biyu na gani a kewaye da mahaifina, d'aya mahaifiyata d'aya ma mahaifiyata, duk haka na d'auka da farko sai daga baya na fahimci wacece wacce tayi nak'uda ta haifeni, mahaifina yasha fad'a min yana son had'a kan iyalinshi duk da kansu a had'e yake kuma gidajen suna kallon junane, amma abinda yake fad'a shine yana tsoron mutuwa tasa duka yaren kowa ya kama uwarsa ya manta da d'ayar, amma idan suna gida d'aya babban cikinmu zai tattaramu duk ya rumgume." Idonta taf da k'walla tace "Da gaskiyar mahaifinku Faduma, nima kuma insha Allahu sai inda k'arfina ya k'are yanzu." Da murmushi tace "Hakane, amma ki masa magana ta sigar da zai fahimceki da kyau, banda b'ata rai da saurin hushi." Dariya tayi tace "Ke dai kin fini sanin komai, ni kuma bana da sani akan yanda ake lallab'a maza." Hannun Faduma ta rik'o suna kallon juna Agaishat tace "Ban tab'a yin k'awa ba da zan iya kira aminiyata, gwara ma zuwa na nan ina iya yin hira ta sirri da *Alhinayet*, sai dai ba tsarata bace shiyasa ba komai nake zaunawa mu tattauna ba, amma yanzu daga yanda kika fad'a min gaskiya kai tsaye, sai ina ji ina buk'atar yin k'awace dake." Hannu ta mik'a mata alamar musabaha tace "Faduma zakiyi k'awance dani?" Murmushi tayi tace "Ni kam nayi k'awaye saidai na wasa a lokacin da k'uruciya, yanzu ma ina da k'awaye saidai bana sirri ba, Ayyoyina ne abokan sirrina, amma kwanan baya da suka wuce na fahimci akwai lokacin da kake kasa kallo uwa ka fad'a mata wani abun kai tsaye, duk ni ayyata ta min horon da babu abinda zan iya b'oye mata, amma yanzu nima nayi k'awa ta sirri." Hannu ta bata suka gaisa cike da murna kafin suka ci gaba da aikinsu sunayi suna hira, labarin dramarta da Wardugu ta dinga bata ita kuma tana mamaki tana al'ajabi da dariya da kuma jinjina wani abun. Sai dai wani abun idan ta fad'a mata sai taji ta kwatantashi da yanda Hasheer ke mata yanzu, musamman yanda ta fad'a mata acan yana saka ido kan lamuranta, yana nuna mata kishi a zahiri amma dai bai fito yace ina sonki ba, da wannan har suka kammala suka kai komai muhallinsa kafin suka fito gyara wajen cin abincin, saida suka idar dukansu suka shiga da niyyar yin wanka. Shigarsu ba jimawa War ya dawo tare da Hasheer, dukansu ciki suka shiga suma kowa ya watsa ruwa, misalin 02:00 na rana duk suka hallara kan teburin, Agaishat da Faduma ne suka zuba abincin suka aje ma kowa, saida suka idar sun zauna Hasheer ya buga tagumi ya kalli Faduma da suke kusa yace "Kin iya tuk'a tuwon shinkafa?" Kallonshi tayi ta saci kallonsu Agaishat kafin ta kalleshi tace "Ban iya ba, na dai iya kad'a miya." Jinjina kai yayi yace "Da maburgi ko da ludayi?" Ba tare da sakin fuska ba tace "Da cokali dai." Cikin nutsuwa suka fara cin abincin, wayarta dake kan teburin kamar yanda mazan ma suka aza ce tayi k'ara, ta zura hannu zata d'auka sai kuma kiran ya yanke, dubawa tayi taga sabuwar lamba ce sai kawai ta share, abinda ta sani kawai shine in abune muhimmi za'a sake kiranta. Kallon Wardugu yayi yace "War kasan da babana zaiyi aure nan da sati uku?" Kallonshi yayi yace "Haba dai?" Cikin jimami yace "Bari kawai, kuma fa tare muka je dashi gidan, kawai kasan da abun sa'a ne tuni harya samu shiga gashi zai angonce." Kallonshi tayi da mamaki, amma kuma tunda bai saka da ita ba sai tayi burus, satar kallonta yake yana jiran yaji tayi magana amma tayi kum, sai kawai yake ganin hada rainin hankali da jan ajin tsiya suna damunta. Kallonta yayi yace "Matar nan fa kirkinki yayi yawa, babana zai auri dadarki shine ko ki fad'a min." Cike da al'ajabi tace "Ban gane ba? Yaushe akayi haka?" Zaro ido yayi yace "Au! Baki sani ba ma? Ai kuwa kira dadarki kisha labari, dan zata amarce ta barki." Shiru tayi tana nazarin abun, sai kawai ta share da nufin zata tab'ota idan sun kammala, haka kammala cin abinci suka tashi, fita suka yi niyyar sak茅 yi dan dama Hasheer bai so dawowar ba, saboda shi bai saba komawa gida cin abinci ba, War ne yace Allah ya tsareshi da cin abinci waje bayan ga matarshi. Cikin nutsuwa da rad'a Agaishat tace "Sojana anjima ina so zamu je gidan Ayya? Daga nan sai m没 taho da yaren." Jinjina kai yayi yace "Allah ya tsare, orro?" Yanda ya kira sunanta a kausashe yasa ta cewa "Na'am." Saida ya kama kunnenshi yace "Ko hoda ban yarda ki shafa ba, sannan ki saka nik'ab sannan dreba zai kaiki." Da sauri ta langab'e tace "Lahhh! Ni wallahi da kaina nake so nayi tuk'i." Zaro mata ido yayi yace "Wacece? A garin nan! Mahaukaci ne ni orro, kinga in dai baki yarda ba saidai a bar fitar harna dawo saina kaiki." Marairaicewa tayi tace "Ni da trozzo zamu tafi fa, kuma ita ma tayi tuk'i." Da mamaki yace "Iyeah! Ina kika samu wannan kalmar kuma?" Maida kallonshi yayi ga Faduma dake zaune hankalinta kan tv cikin harshen tubanci yace "Kar fa ki yarda ki koya mata tubanci a gidan nan, nafi so tayi ta zama a haka ina wanketa." Juyowa tayi cike da kunya da girmamawa tayi dariya tace "Kayi hak'uri yallab'ai, trozzo ta ce yanzu ba zan yarda a mata abinda ba zata ji dad'i ba." Kallon Agaishat yayi yace "Me kika bata haka kika asirceta daga jiya zuwa yau?" Hararan wasa ta mishi tace "Da me ka d'aukeni? Ban iya jawo mutum jikina ba?" Jinjina kai yayi yace "Hummm!" Sake marairaicewa tayi tace "Yanzu da dan Allah ka barni na tafi tare da ita." Girgiza kai yayi yace "Gaskiya ban yarda da tuk'inki ba, saidai ko in ita zata tuk'a." Da sauri tace "Eh na yarda." Karaf a kunnen Hasheer dake tsaye bakin k'ofa yana danna waya, zai lek'o ne ya masa tijara sabida tsayawar da yayi sai kuma yaji wannan batun, dukanshi yayi a kafad'a yace "In ka isa War kirani d'an iska, kaji mutum kai, ita aka ce maka ta iya tuk'in ne da zan barta tayi shi a garin nan." Kallon Agaishat yayi yace "Gaisho a hak'ura da tafiyar ko ma ina ne, in kuma ba zai yiwu ba ki bari mu dawo ni saina kaiku." Hannun War ya kama da k'arfi ya jashi suka fita yana fad'in "Haka kawai ina zamana kaja min salalan tsiya, da asaran waccen ba gwara ta duka kadarorina ba." War dake kallon ikon Allah y'a ma rasa me zai ce masa, saida suka shiga mota ya kalleshi yace "Anji kunya dai, ka tsaya k'aramar yarinya zata kasheka da ranka, har fa tsoronta kake, da nine kai tuni na kalleta na fad'a mata komai kowa ya huta." Wani shak'iyin murmushi yayi yace "Nagode Allah da ba nine kai d'in ba, da yanzu kana nan kana zare mata idanu da nuna mata kai k'ato ne." Dukanshi yayi a kafad'a shima yace "Kai tubarkallah, wannan k'wanjin nawa fa yana tsone muku ido." Dariya yayi bai ce komai ba har suka fita daga gidan suna amsa gaisuwar sojan daya bud'e musu k'ofa. Faduma kam daga nan zaune ma ta kira dada, sanda ta tabbatar mata lallai Abdallah zai aika manya tasha mata dariya da tsokanarta, har saida ta aiko mata da ashar kad'ai ta shafa mata lafiya, daga nan ta bata Amjad dake saka kayan makarantarshi Aminu zai zo d'aukarshi, saida yaji tsoro sanda ta mik'o mishi wayar dan a tunaninshi ko ta gane shine ya kirata d'azu da wayarshi, son jin muryarta yasa shi mantawa ya kirata da lambarshi, saida ta fara kururuwa kuma saiya kashe saboda tunawa baida abun fad'a mata. Gaisawa sukayi sosai ta tambayeshi karatu ya amsa da lafiya lau, cikin shagwab'a yace "Ayya yaushe zaki dawo?" Cikin rarrashi tace "Zan dawo nan kusa Amjad, me kake so na zo maka dashi?" Saida yayi tunani ta hanyar fad'in "Ummmmm! Yawwa Ayya ki siyo min takalma na ball da kuma irin kayan nan na sojawa." Bushewa tayi da dariya tace "Amjad kayan sojawa kuma? To shikenan zan siyo." Da sauri yace "Ayya har da bindiga fa." Da sauri tace "A'a bar maganar nan, bana so kaji ko, kayan dai zan siya maka idan na gani insha Allah." "Shikenan Ayya sai kin dawo." Ya fad'a a sanyaye, mik'awa dada wayar tayi sukayi sallama, sosai Faduma ta sake jin k'aunar yarenta domin kuwa gata ga Agaishat amma ta tabbatar bata san da wa kuma akan me suka tattauna ba. Wunin ranar sun sha hira ita kuma dole ta soke fitarta har zuwa dare, girkin yamma ma tare sukayi suka gyara komai, sa茂da sukayi sallah magrib suka shiga dan shiryawa. Faduma ma tunda ta shiga saida tayi waya da Aminu da kuma Abdu a lokacin har anyi sallah isha'i kafin ta fito. Fitowarta daidai da fitowar Agaishat daga d'aki cikin wata d'anyar shadda da aka mata babbar riga, ta kashe d'aurin d'an kwali ya zauna mata, uwa uba sanyayyan k'amshin dake fita a jikinta. Ita kanta Faduma sabida wanda zata had'u dashi yasa dole ta sako riga da siket na kanti wanda siket d'in ke hawan saman rigar k'asan nonuwa, sai rigar da hannayenta suka zo gwiwar hannu, kallabin d'an yalolo ta d'ora akai kalar pink kamar yanda siket d'in yake, duk da tana jin rashin sabo dan kayan idan ta sakasu lafaya take kima musu, amma gata yau a haka sai taji ta wata kala, amma inba haka tayi ba ba zata samu abinda zata je nema ba, suna tsayawa kusa da juna kowa abinda ke ransa ya yi gaggawar fad'a, a tare suka ce "Turarenki ya min dad'i." "Turarenki ya min dad'i." Dariya sukayi jin sun fad'i abu guda, Agaishat ce tace "Kin jiki da tsokana, a duniyar turare ai babu kamar tubawa da barebari." Murmushi tayi tace "Buzaye kuma suka ce ja bamu wuri ba, Allah turarenki ya min dad'i." Ita ma ba alamar wasa tace "Allah nima naki y'a min dad'i, abun birgewa a tare dashi yanda kai tsaye baka gane turaren wuta ne ko na ruwa, sannan yana yanayi da wani turare dana sani *oud zarkah*." Murmushi tayi tace "Indai kina so wannan abune mai sauk'i, idan na koma zan lodo miki shi cike da mota a kawo miki." Zaro ido tayi tace "Ke wawuya, baya da tsada ne?" Dariya tayi tace "Ai kuwa yana da, dan 1litre d'in shi ma jaka arba'in da biyar yake." Sake zaro ido tayi tace "Indai hakane kam zan biya kud'i saiki kawo min, amma idan na siyeshi zan ajeshi mazaunin turaren d'aki." Da rashin fahimta ta kalleta tace "Na jiki ne fa." Dariya tayi tace "Baki gane ba? Da yake ni ina raba turare kala biyu ne, akwai wanda nake shafashi dan mai gidana kawai, akwai kuma wanda zan iya sakawa a jiki ko a kayana na fito." K'ank'ance ido tayi tace "Kice harkar ta manya ce, to wannan karatu yafi k'arfin Faduma." Duka Agaishat ta kai mata ta kauce suna dariya tace "Babu abinda baki sani ba, iya hege ne zaki min na yaran zamani." Lumshe ido tayi tace "Da gaske ni Faduma babu abinda na sani bayan tambaya da bincike da tsayawa gaban alk'ali." Dariya sukayi kafin su tsagaita tace mata zata fita, da rashin jin dad'i tace "Ki bari dreban naki ya zo mana saiya kaiki." Girgiza kai tayi tace "Dreba? Ki rufan asiri kar yaji yasa a d'aureni, inda zanje ne bana so naje da kowa, dan akwai wanda zan had'u dashi ina neman wasu bayanai a gurinshi, a yanda aka fad'a min yaron yake dole sai nayi wani abun da zai d'auki ko da hankalinsa ne kafin na samu abinda nake so." Jinjina kai tayi cike da gamsuwa tace "Shikenan to Allah y'a tsare, sa茂 kin dawo." Fita tayi ita kuma ta samu wuri ta zauna jiran shigowar oga War, tana fita taxi ta d'auketa ta fad'a mata inda zata kaita, sun jima suna tafiya sama da minti talatin kafin suka isa unguwar, bata sha wahalar gane gidan daya kwatanta mata ba mai farin fanti, d'an nesa da wurin tasa ya sauketa ta biyashi, saida ta gyara zaman d'an kwalinta ta d'an fito da rabin gashinta kafin ta k'arasa da tako na rausaya tana jan k'afafu, tana isa samari ne guda biyar kuma daga motocin dake wurin guda biyar zaka san kowa da tashi kenan, ba tayi mamaki ba dan an fad'a mata 'ya'yan manya ne, to dama ko ba'a fad'a ba ga abubuwan da suke sha ai sai masu kud'i. Kashe murya tayi sosai cikin k'warewar harshen french tace "Ina wuninku, Safwan yana fa?" Dake akwai duhu a wurin yasa shi lek'o kanshi daga zaunen da yake ya saka shisha a gaba yana ta hanb'ara, shima a harshen french yace "Gani nan, wacece?" Da k'yar ta sarb'o harshen zarma tace "Da kyau, ka taso ka gani mana." Wani daga ciki ne da harshen hausa yace "Tashi baaba, yarinyar fa ta had'u." A tunaninshi bata jin hausa sai kawai tace "Nagode." Tsuru ya mata da ido sai kawai ya basar, tasowa yayi ya tsaya gabanta k'ik'am, wayarshi ya ciro ya kunna fitila ya haska mata a fuska, dau! Taji hasken a idonta, kawar da fuskarta tayi gefe amma bata hanashi ba, saida ya gamawa fuskarta da bakinta dake ta k'yalli kallo sannan ya kashe, cikin ruwan sanyi yace "Ban ganeki ba, daga ina?" Cikin kashe murya da kakashe ido tace "A makaranta mana, ba zaka ganeni ba saboda shekarata ta farko kenan." Saida ya matso daf da ita kamar zai had'eta yace "To ya akayi yanzu?" A hankali ta d'an ja baya tana fad'in "Zanyi shagalin k'ara shekarar haihuwata ne, kuma ina so nayi babban shagali a wannan shekarar saboda Abbana ya sakar min dala sosai, sanin kune manyan yara yasa *Arkiya* tace na nemeka, dan kai kad'ai ne baka da girman kai a duk cikin abokanka, ina so ka taimaka min wajen zab'a min gurin da za'a rak'ashe da duk abinda ya kamata." Da mamaki yace "Arkiya Bello?" Saida ta sauke ajiyar zuciya jin anyi dace an samu mai sunan kuma ya santa tace "Eh ita." Wani murmushi ya saki yana shafa wuyanshi yace "Angama babbar yarinya, kin kawo kukanki gidan mutuwa, zuwa yaushe ne shagalin?" Saida ta kalli idonshi tace "Gobe, shiyasa ma na zo cikin daren nan." Da sauri yace "B芒 komai ai, mu daren shi muka fi so." Juyawa yayi ya kalli abokan sai kuma ya kalleta yace "Zaki iya biyoni muje na nuna miki wani wuri kiga ko zai miki?" D'aga kafad'a tayi tace "Ba damuwa, muje, nayi tunanin haka shiyasa ban fito da motata ba kar ace saceka zanyi." Dariya yayi yace "A garin nan?" Wata Corolla suka nufa y'a shiga kiciniyar bud'ewa, kallon motar ta dinga yi duk d'脿 akwai duhu kuma taga wannan kalarta shud'i ce, a hankali ya d'ora hannunta ta shafa sai taji wani garji garji, sak alamu ne na an shafa mata fanti marar kyau kuma ga wanda basu iya aikin ba. Yana bud'ewa ita ma ta bud'e suka shiga, nan ma saida ya d'an kai ga jan tsaki kafin makullin ya shiga gidanshi ya tayar. Sigari ya kunna ya zuk'a d'aya zaiyi na biyu yaga ta k'ura masa ido tana kallo, mik'a mata yayi yace "Kina shan sigari ne kema?" A ranta tace "Kam bala'i." A fili kuma girgiza kai tayi tace "Ina so nasha saboda tana birgeni, amma Abba na mugun tsohon d'an k'waya ne shima, shiyasa ko zaune nayi cikin masu shanta saiya ganeni ya min masifa." Dariya yayi yace "Lallai wannan gyatumin naki jaraba ne shima." Cikin murya irinta tsageru da shak'iyanci tace "Ai babba ma kuwa, amma dole gobe zai hak'ura ya barni na mori ranar nan." Saida ya cilla sigarin waje ta madubi yace "Gaskiya ne babbar yarinya, dan mu kanmu sai munyi tatul." Kallonshi tayi a zuciyarta tace "Hmmm! Muje dai." Shiru tayi tana kallon komai dake motar, zuciyarta sai raya mata take anya ba motarki bace? Amma wata zuciyar na fad'in yaushe aka d'auketa da har aka kawota nan aka canza mata kala? Kai ba ma zai yiwu b芒. Hannu ya kai d'an coffre d'in dake rufe yana fad'in "Bari naga ina ya aje min ajiyata." Jawowa yayi sai ya k'i bud'ewa, k'arfi ya kuma sawa ya k'i, cikin jin haushi yayi tsaki yace "Wannan bak'ar mota." Hannu ya sake kaiwa da k'arfi zai mazga mata, a bazata a sanin data ma motarta ba tare da tunanin dubarar zatayi aiki ba kawai tasa hannun hagunta a k'asan ta danneshi sosai saina damar ta jawo murfin, tsaf sai gashi ya bud'e, ita ma baifi watanni ba da Amjad ya lalata mata shi, saita hakane take bud'e shi. Kallon kallo sukayi ita mamakin yanda akayi motarta ta zo nan, shi kuma mamakin yanda ta bud'e mishi a dubarance,abinda ta tsinkaya a ciki ya kayar mata da gaba, ko da bata da masaniya sosai amma ta tabbatar coca茂ne ce, ganin ya tsareta da ido dole ta saki murfin kawai ta d'auke idonta akai, dan ita dai yanzu ta tabbatar kawai ta ta ce ba wani maganar wai k'arfen nasara ba kai kad'ai aka k'era ma irinshi ba. Basarwa kawai tayi ta juyar da kanta sai kuma ta kalleshi tace "Tsohuwa ce?" Saida ya kuma yin tsaki yace "Ta kwana biyu, amma ba wani tsufa bane tayi, kawai wasu abubuwan nata ne ke da wuyar sha'ani kai tsaye." Cike da shak'iyanci tace "To ka siyar da ita ka siyi wata mana Alaji." Murmushi yayi yace "Ni tawa motar Honda ce, wannan ma ta Tahir ce." Cike da basarwa tace "Tahir shine wannan dogo bak'i ko?" Ba tare daya kalleta b芒 yace "Eh shi." Da mamaki ta kalleshi tace "Amma bashi naji jiya a makaranta ana magana ko an kamashi ne ko me?" Dariya ya bushe da ita yace "Wa ya fad'a miki a garin nan ana d'aure mai kud'in na din-din-din? Ai ko kwana baiyi ba acan aka fito dashi." Murmushi tayi tace "Gaskiya yayi kyau, ai na d'auka yana can har yanzu." Girgiza kai yayi yace "Ko kad'an, yanzu haka yana gida yana hutawa, da farko ma abun ya so yayi k'amari ne saboda dangin yarinyar da suka dage sai an bi musu hakk'insu." Cikin sigar jin zance ta gyara zama tace "Wai dama akan yarinya ne duk abun?" Tab'e baki yayi yace "Wata budurwa ce ya kad'e wallahi bayan ya bugu, shine fa ake ta wannan rigimar, yanzu haka yan uwanta sun shigar da k'ara kotu." Cikin kafeshi da ido tace "Amma me yasa yayi tuk'i bayan yana a bige shima? Ai da had'ari sosai." Cikin rashin bawa abun mahimmanci yace "Kuma fa a lokacin muna tare, ya aje ni gida zai tafi gida ne shima abun ya faru." Girgiza kai tayi tace "Ayya, Allah ya kiyaye gaba, ku dinga kula dan Allah." Cike da murmushi yace "Ba yawa babbar yarinya, tsautsayi ne kinsan baya wuce ranarsa, dan a lokacin ko fita bamuda niyyar yi." A hankali tace "Gaskiya ne kam." Sauke ajiyar zuciya tayi ta kalli gabanta tace "Casu kuka je halan?" Murmushi yayi yace "Wallahi wani gidan gona muka je taya abokin murna yarinyar da yake so ta amince zata aureshi." Zaro ido tayi tace "Fita gari? Amma ai da dare ne abun ya faru ko?" Jinjina kai yayi yace "Eh fita gari, da yake tun yamma akayi abun, to mun dawo ne bayan sallah isha'i abun ya faru." Sauya maganar yayi da cewa "Wai ni kam miye ladata idan na miki wannan k'ok'arin?" Saida ta kalleshi cikin shagwab'a tace "Saika zab'a sannan." Da murmushi yace "Samun sumbata daga kyawawan labb'en nan ma masu kama da chocolat ya wadatar dani." Saida taji gabanta ya fad'i, a take kuma sai taji tana sha'awar sake k'urawa madubi ido taga miye a labb'enta da ake dangantasu da chocolat. Basarwa tayi tace "Wannan k'aramin abu, yanzu kake so ko sai zuwa goben?" Da murmushi yace "Ajiye min shi zuwa goben zaifi dad'i." Ta wutsiyar ido ta harareshi tana jan tsaki, a haka dai suka k'arasa wani wurin holewa, ya so su shiga ta hangi wani mutum tsaye tace ai kawunta ne idan ya ganta zata sha mita. Ganin ya tafi da sauri ta sake bud'e wurin ta d'auki hoto a wayarta sannan ta d'auki leda d'aya 'yar k'arama, da sauri tasa a jakarta kafin ta sake duba duk wani wurin ajiya, babu wani abu sosai ko dan suna son canza mata kama, inda ta d'auko coca茂ne din tayi nasarar ganin takardu, saida ta juya ga k'ofar taga bai fito ba kafin tayi sauri ta bud'e. Yana shiga shi kad'ai ya samu ya musu buckin ya fito, da sauri ta nad'e takardar ta zura a jakarta ta rufe wurin ta fuske kawai, kud'in da ya biya ba sune a gabanshi ba a lokacin, hallitarta yake k'arewa kallo da tunanin goben irin casun da zai sha, suna yin gaba kad'an tace ya sauketa zata je siyan robe d'in da zata saka gobe, daga nan ta biya saloon ta samu rendez-vous zuwa goben, a haka dai suka rabu bayan ta karb'i lambarshi, cikin salon shegantaka yace "Wans suna zan saka idan kin kirani?" A ranta tace "Sakaran banza, a wannan yanayin yarda da wanda baka sani ba." A zahiri kuma cewa tayi "Ka saka Le茂la." Da murmishi yace "Suna mai dad'i." Murmushi kawai ta masa har ya bar wurin da cewa sai gobe sannan zasuyi waya. *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 21:39 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _51_ Dama wayarta a silent take saboda bata son kira ya shigo wayarta da zai lalata mata shirinta, saida ta shiga taxi ta fad'i inda zata sauka sannan ta ciro wayar, daidai kira na sake shigowa na karo ba adadi, murmushi ta saki ta danna ok ta d'ora a kunne, cikin yanayin da bai tab'a yi mata magana b芒, cikin amon muryar daya tsorata ta sosai cike da fad'a da masifa yace "Titi kin kyauta, nagode sosai kinji, bayan fita ban sani ba har kin bar sak'o a fad'a min cewa zaki had'u da wani, a k'arshe kin nuna min ni k'ololuwar marar anfani ne a gareki tunda har kika kasa d'aga kirana." Fad'uwa gabanta ya dinga yi, cikin rawar baki tace "Elhaj kayi hak'uri, wallahi ba haka bane, na fita..." Cikin rawar murya kamar mai kuka yace "Titi ki dawo gida dan Allah, zuciyata bugawa take yi da sauri kamar zata tsaya, dan Allah ki dawo." Gaba d'aya saiya kashe mata jiki, cikin murya kamar zatayi kuka ita ma tace "Ina hanya." A hankali kamar mai mata susar kunne yace "Kina cikin k'oshin lafiya?" Da rawar murya tace "Ehhhh." Shiru yayi sai numfashi a hankali da yake sauke mata kuma bai ce komai ba, ita ma sauraren numfashinshi kawai take kamar mai son saita nutsuwarshi, sunyi kusan minti biyu a haka kafin ya katse kiran, ita ma d'auke wayar tayi a kunnenta tana kallon kiran daya mata, kira d'ai d'ai har guda 47, wata wawuyar ajiyar zuciya ta sauke ta mayar da wayar ta aje, takardar nan ta ciro ta shiga dubawa, saida ta gama dubawa sarai ta mayar a jaka ta rik'e hab'a tana tunanin lamarin. Saidai daga bayanan data samu yanzu ga Safwan zuwa wanda ta samu ga iyayen yarinyar jiya ta fahimci akwai sab'anin kalamai, kuma zuwa safe zata koma taji gaskiyar lamarin. A hankali ta dinga takowa tana shigowa falon kamar marar gaskiya, Agaishat ta fara tarbanta ta rik'o hannunta tana fad'in "Har kin dawo? To aikin?" Kallon Hasheer tayi daya juyo da k'arfi yana tsaye rik'e da k'ugu kamar wanda aka shigar da matarsa d'akin nak'uda, wani wurgo mata ido da yayi sai yasa ta sake tsorata, damk'e hannun Agaishat tayi tana sake satar kallonshi, takowa ya fara yi cije da leb'e yana jinjina kai alamar zai iya kifeta da mari ma, bata b'ata lokaci ba wajen bin umarnin da zuciyarta ke raya mata, ai da gudu ta kwasa tayi d'akin daya zama masaukinta tana kwamtsa k'ara da kiran sunan "Wayyo Aba na, Aba ka zo ka taimakeni." Cak ya tsaya idonshi kawai suka iya binta da kallo, sake rik'e k'ugu yayi ya juyo da mamaki inda War yake zaune, sai yaga shima dariya yake har da girgaiza kai, Agaishat ma haka dariyar take ta nufo wajen mai gidanta ta zauna tana fad'in "Ka tsorata ta fa." Sakin hannayenshi yayi ya girgiza kai yana murmushi yace "Kaga muguwa ko, gaba d'aya ta mantar dani abinda nayi niyyar yi." Wani kallo War ya masa yace "Ka je dai yanzu ka lallab'a ka bata abinci ta ci." Cike da gatsali yace "A baki zan bata baba Wardugu?" Harara y'a dalla masa yace "Kai kiyaye ni fa, ka dai san da Ayya bata tab'a yi min k'ane ko k'anwa ba ko? To na samu k'anwa yanzu kuma wallahi saina zaneka a kan ta." Wata dariya yayi kafin yayi magana Agaisha ta mik'e ta had'o abinci ta zo ta bashi tace "A yanzu tana tunanin zaka daketa saboda tunanin ta b'ata maka rai, idan kaje mata da sanyi sosai tare da bata abinci ta ci zata ji a ranta ka damu da ita ne sosai." Karb'an farantin yayi yace "Nagode." Da murmushi tace "Fatan nasara." Juyawa yayi zai shiga War yace "Idan kaine kuma ka sake kifar da abincin, tunda ba kai ke siya ba ai dole ka dinga min asara." Dariya yayi ba tare daya juyo ba yace "Sannu mai kud'in siyan abinci." Cike da kuri yace "Ni ne nan, mai mata biyu ba, Wardugu d'an baiwa ikon Allah." Girgiza kai yayi ya juyo yace "Ka zuba ido ka gani, insha Allahu sai nayi ta biyu da ita ko da garin nan zai b'alle da yak'i ne." Hararanshi yayi yace "Kai yaro ka min ladabi na tsaya maka a aurenta, inba haka b芒 saina b'ata lamarin na zuga iyayenta na nuna musu karsu mata auren fari ba da batube ba." Hararanshi yayi yace "Kar ka min haka War, na rok'e ka kaji." Wucewa yayi ya barsu nan, yana zuwa ya k'wank'wasa k'ofar d'akin a hankali da nutsuwa, lokacin har ta cire d'an kwalinta ta zauna kan gado tana duba 'yar ledar coca茂ne d'in nan, da sauri ta mik'e har ranta tunaninta Agaishat ce tunda taga duka suna falon, tana bud'ewa gabanta ya tsinke ya fad'i har saida ta rufe ido, ganinshi da faranti yasa ta zura hannayenta zata karb'a. Tunda ya zuba ido akan ta ya kasa d'aukewa duk da k'ok'arinshi na son yi mata kallo d'aya irin na shari'a, rab'ata yayi ya shigo d'akin tare da aje farantin kan wata kujerar katako mai kauri sosai, yana d'agowa ita kuma ta wuce inda d'an kwalinta yake zata d'ora a kai, bin bayanta yayi da kallo har saida ya rufe ido. Ashe dai lafayar nan ba k'aramin rufa masa asiri take ba, wannan shiga da tayi ta fito mata da komai, ga wani uban dogon gashi bak'i k'irin da yaga ta dunk'uleshi ya kwanta a bayanta, duk girman siket d'in saida ya nuna faffad'a kuma kakkauran k'ugunta har kana iya hangen yanda yake motsawa. Kamar zai fashe da kuka yace "Yanzu Faduma haka kika fita dama? Ya kike neman kasheni daga tsaye ne?" Wani luuuu tayi da ido baki bud'e, sai kuma ta k'yabta ido tace "Da matsala ne yin hakan? Dalili na mai k'arfi ne na yin hakan." Sunkuyar da kanshi yayi yace "Amma in zakiyi haka ki dinga tunawa dani." D'an lek'a fuskarshi tayi tace "Saboda me? Kana da wani abun da kake son fad'a ne?" D'ago kai yayi ya kalleta yace "Bakina akwai abun fad'a, amma tsoron Faduma nake." 'Yar dariya tayi taja baya tace "Nima tsoronka nake Elhaj, mu tafi a haka kawai." Tarr ya sauke idonshi a kanta da wani firgitaccen kallo yace "Ba zai yiwu ba, dole na killace abinda yake nawa ne, insha Allahu wannan burin zai cika." Kallonshi tayi kawai ta kasa musa mishi ko tace a'a, hasalima sai a can k'asan zuciyarta data amsa da "Allah ya cika maka burinka." Wani iska ya furzar ya kalleta ita ma tana kallonshi yace "Ina kika je?" A hankali tace "Wurin aiki." Numfashi ya sauke yace "Teema kiyi a hankali, akwai had'ari fitarki ke kad'ai, akwai masu bibiyata kuma jiya zuwa yau sun tabbatar ina tare dake, zasu iya yin yunk'urin cutar dake ta kowace siga, ki kula min da kanki kinji?" A nutse ta kalleshi tace "Su wa ke bibiyarka? Kuma akan me suke bibiyarka? Ni kuma me yasa zasu cutar dani?" Wani murmushi yayi mai ciwo yace "Ba zaki gane ba, ke dai kiyi abinda nace kawai, idan zaki fita ni zan kaiki ko ina ne." Saida ya marairaice yace "Dan Allah ki min wannan alfarmar." Ajiyar zuciya ta sauke tace "Insha Allah zan kiyaye." Da murmushi yace "Nagode." Da hannu y'a mata alamar zo, matsowa tayi ya nuna mata bakin gadon yace "Zauna ki ci abinci." Kallonshi tayi tace "Zan ci anjima, yanzu ina son yin magana da yallab'ai." K'ure fuskarta yayi da kallo yace "Zuwa safe zan kaiki wajen likitan da kika buk'ata yau." Da farin ciki tace "Kai amma naji dad'i, nagode sosai." Juyawa kawai yayi ya fita sai d'aukar takardar nan da kuma coca茂ne da tayi tabi bayanshi, a falon suka tardasu sai soyewarsu suke a tsaftace, cike da kunya ta k'arasa ta d'an zauna nesa dasu, Hasheer ne ya kalleta yace "Ki saki jiki ki daina tsoronshi, zo ki fad'a masa abinda kike son fad'a." Da kunya ta mik'e ta fara takawa kamar zata kife ta k'arasa, War daya gyara zama yana kallonta har ta k'araso, takardar hannunta ta mik'a mishi tace "Dama yallab'ai ina so ku bincika min takardar motar nan ne na k'warai ne ko kuma na bogi." Ledar coca茂ne d'in ta mik'a masa tace "Sai wannan dana samu a motar yaran nan, shima ina so na tabbatar coca茂ne ce mai kyau." A hankali Hasheer yace "Coca茂ne?" Juyawa tayi ta kalleshi, a d'an tsorace yace "Batul da masu ta'ammali da coca茂ne matsalar ta had'aki? Tabb'." Ya fad'a yana girgiza kai, War dake ta mamakin samun coca茂ne shi kam abun na neman yafi k'arfinshi ma, yanzu duk irin yanda suke da zuba ido da jajircewa akan lamarin shaye shayen nan abun ma k'ara gaba yake, shi tashin hankalin shine yanda ake ana shigowa dasu? Tabbas dole saida sahalewar wasu manya b'ata gari, to amma su waye? Kuma wace dubara suke aiki da ita wajen shigo da ita? Mik'ewa yayi ya kalleta yace "Ina zuwa." Ta k'ofar fita ya bi suka bishi da kallo, Agaishat ce ta kamo hannun Faduma ta zaunar da ita tace "Ke kuwa ya akayi kika samo abubuwan nan?" Zatayi magana Hasheer ya mik'e shima ya fita, d'akin da War ya ware dan wasu binciken na sirri ya shiga wanda gaba d'aya madubi ne wanda harbin bindiga ma baya fasa shi, ko da ya shiga tuni yayi nisa da cakular na'urar dake gabaanshi, sai wani soja daya duba coca茂ne d'in nan ta wata na'ura mai ijiya dake d'auke da madubin microscope. Tsaye yayi kawai yana kallonsu har War ya mik'e ya k'arasa gaban wani madubi dake da kauri sosai tare da wasu fitilu masu haske kalar sararin samaniya, takardar ya d'ora akai ya k'ura mata ido, da sauri ya jaye yana jan tsaki ya sak茅 komawa kan kujerar daya tashi, sau d'aya ya danna madanni ya shiga duba bayanan da aka turo masa, saida ya gyara zamansa kafin ya shiga kwafar bayanan, yana k'arasawa ya danna enter saiga takarda na fitowa daga na'urar dake gefenshi, mik'ewa yayi ya zage takardar da sauri ya kalli sojan nan yace "Me tace?" Da girmamawa yace "Chef, wannan mai kyan ce." Tara hannu yayi ya bashi sauran data rage a leda, kallon Hasheer yayi yace "Me ka sani akan k'warewar yarinyar nan akan aikinta?" Girgiza kai yayi yace "Gaskiya bansan komai ba, da wata matsala ne?" Girgiza kai yayi shima yace "Babu, kawai zan so nasan k'warewarta ne dan ina son sanin yanda hodar iblis da sauran kayan maye ke shigowa k'asa." Dantse leb'e yayi ya daki tebur d'in dake gabanshi da k'arfi yana sakin tsaki, sojan nan ya kalla yace "Kuyi fitar dare yau, daga k'arfe goba har zuwa asuba ku kama koma uban waye kuka gani, sannan duk gidajen holewar nan ku kai sumame acan kar ku bar kowa." Saida ya buga k'afa da k'arfi ya sara masa da hannu yace "A vos ordre chef." Fita yayi da sauri suma fita sukayi, a zaune suka samesu ya mik'a mata takardun, karb'a tana tana dubawa tace "Nagode yallab'ai." Takardar ta duba, wato takardun k'arya ne aka mata da canza ma wasu abubuwa kammani, kuma ba sabuwa ba. Cikin muryar tashin hankali data kayar mata da gaba yace "Ya akayi kika samu hodar iblis d'in nan? Ina suke zama? Su waye su?" K'ifta ido tayi ta kalleshi sak ya shiga yanayi na soja marar wasa, Agaishat kanta jininta ya dawo kan akaifa dan tasan sun motso, yau Allah zai kareta tasha matsa a d'aki ko ya juya mata baya, cikin rawar murya ta shiga fad'a masa abinda ya faru. Safa da marwa ya fara yi a tsakiyar d'akin, saida ya gama ya tsaya ya kalleta yace "Ki kirashi a waya, kuyi magana kan har yanzu da maganar shagalin nan, ta hakane zamu kai musu cabka." Kallonta yayi fuska a had'e yace "Ki nemi daya turo miki lambar asusunshi, kice zaki mayar masa da kud'in daya biya." Da sauri ta d'aga tace "To yallab'ai." Mik'ewa tayi ta nufi masaukinta, Hasheer ma nashi d'akin ya shiga duk ranshi ba dad'i, dan gani yake kamar War zai jefata a wata matsala ta daban, a yanda ya hau kuma yanzu yace zaiyi magana ransu ne duka zai b'ace k'arshe suyi zuciya da juna, dan hakan ba sabon abu bane dan ma shi bai cika hayaniyar ba. Kayanshi ya cire yayi wanka ya fito d'aure da towel, gaban drowar kayanshi ya tsaya rik'e da k'ugu, d'an tsaki kawai yayi ya jawo wani dogon wando daga k'asa bak'i, bindigar data biyo wandon zata fad'o ne yayi saurin cabkota ya tare cike da salon k'warewa, kallon bindigar yayi ta zallar bak'in k'arfe mai d'auke da alburusai takwas sai nauyi, mayar da ita yayi ya aje kafin ya saka kayan. Data shiga d'akin saita kasa cin abincin kawai ta kira Safwan dan shirin yallab'ai ya fad'a, sun jima suna hira har ya dage ba zai turo mata lambar asusun ba ita ma ta dage saita mayar masa da kud'in, da k'yar sukayi sallama ya turo mata lambar, ganin dare yayi a lokacin kuma Aminu ya kirata saita bari har da safe, sun sha hira sai dai shi yafi janta da hirar sannan ta mayar masa. Mantawa tayi da abincin nan ta kwanta abinta kawai bacci ya d'auketa. *07:20* Ganin bata fito yasa Agaishat samunsu a d'akin motsa jiki, saida Hasheer ya saka rigarsa kafin ta shigo, kallonshi tayi tace "Elhaj Faduma naga har yanzu bata fito ba, nace ko zaka je ka duba ka gani?" Juyawa yayi b'angaren dake da agogo ya kalla, jinjina kai yayi ya nufi k'ofar yana fad'in "Ina zuwa." Fita yayi sai War daya kalleta yace "Ke me yasa baki je kin duba ba? Kinsan a halin da zai sameta?" Murmushi tayi tace "Ai ba zai shiga kai tsaye ba, ni nafi so su dinga kusantuwa kullum hakan zai sa ta shiga hankalinta." Murmushi yayi yace "Orro ta kenan." Cikinshi dake d'auke da six pacs ne ta dan mishi k'ulli tace "A ci gaba da motsa jikin." Murmushi yayi yace "Orro wannan k'ullin naki idan soja za'a kaiki da gudu za'a koroki." Kallonshi tayi a ranta tace "Kai da k'arfi kuma nima saina saka maka k'arfi, ai kamar taliya haka nake a gabanka." 馃槀 _WarAgaishat_ Tun asuba data farka saboda sabida ta sake kama ruwa da ruwan d'umi ta sake pad ta wanke bakinta ta sake komawa ta kwanta bacci yayi gaba da ita, bata sake motsawa sai yanzu da taji an bubbuga d'akin tace "Shigo." Shigowarshi ita kuma tana tashi zaune tana gyara gashinta daya barbaje, da murmushi ta shafa fuskarta tace "Ina kwan..." Bata fad'a ba saboda ganinshi da tayi, a take ta jefi kanta da tambayar "Wai me yasa yake shigo mata d'aki?" Kwanukan jiya ya bud'e ganin abincin na nan yanda yake yasa shi kallon ranshi a b'ace yace "Miye haka? Akan aikin ne kike wasa da lafiyarki?" Wani tsaki yaja ya juya ya fita, ta d'auka yayi hushi kenan sai kawai ta jawo wayarta ta shiga duba lokaci da kuma hotunan data d'auka na jiya, tana ganinsu ta aje wayar ta yunk'ura zata sauka taji an sake shigowa, shine dai d'auke da wani farantin fuskarshi tamau b芒 alamar wasa. Komawa tayi ta zauna ta shiga waigawa inda zata ga kallabi ko hijab, saidai gasu can akan kujerar dake gaban madubi, d'auke waccen farantin yayi ya aje k'asa ya jawo kujerar ya zauna, aje farantin yayi a saman gadon fuska a d'aure yace "Gyara min zamanki." Gane manufarshi da tayi yasa ta cewa "Zan ci Allah kuwa." Wata harara ya mirgino mata yace "Ina wasa dake ne? Batul zan had'a miki jini da majina yanzu." Wata hegiyar k'wafa yayi ya bud'e plate d'in soyayyar doya da k'wai da sauce d'in ta, cokali yasa ya yanko loma ya juyoshi cikin sauce d'in ya nufi bakinta dashi, da mamaki ta girgiza kai alamar a'a, waro ido yayi ya aje cokalin yace "To je ki kurkure bakin ki fito." Da sauri tace "Na yi brush tun tuni, zan ci dai da kaina." Cokalin ya sake d'auka ya nufi bakinta ta kawar da kai, wani kallo ya mata yace "Kinsan Allah? Wallahi d'ure zan miki Batul, ki daina wasa dani fa kamar wani kakanki." Turo baki tayi gaba idonta suka cika taf da k'walla, yana sake mik'o mata ta bud'e baki ta karb'a ta shiga taunawa a hankali, kallon bakin nata yake kamar zai had'e mishi yawu, ita kuma jin idonshi a kanta yasa ta d'ago a hankali, ganin inda yake kallo yasa ta saurin rufe bakinta da tafin hannu tana fad'in "Ni wallahi bana son haka, kawai sai ayi ta k'urawa mutum ido, to k'walelen kare da hantar kura." Wani shu'umin murmushi yayi yace "Wannan hantar da yardar Allah zata zama halalin kare, zai gatseta iya son ranshi." Ita ma a nutse ta kalleshi tace "Idan kuma fa d'aci ne da ita, zata gagari bakin karen nan harya jefar." Ba tare daya daina kallon fuskarta ba yace "Ai mayunwaci baya bambambace wannan, buk'atar maji hajj sallah ne." K'asa tayi da idonta sanda ya sake jefa mata wata lomar, k'arar da wayarta tayi ne yasa ta d'auka saboda ganin sunan dada, da sauri ya fizge wayar yace "Daga yanzu har ki gama cin abinci ba waya." Marairaicewa tayi tace "Ka bani dan Allah, zata had'ani da yarona ne fa." Mik'o mata yayi yace "Ki gaishe min dashi." D'auka tayi sanda kiran yayi daf da yankewa, sallama ta fara yi kafin suka gaisa da harshensu har aka bata Amjad shima suka gaisa, a haka kuma yana bata abincin tana karb'a sam tama manta ya alak'arsu take ta dinga karb'a kuma tana wayarta, saida sukayi sallama ta aje wayar ta kalleshi tace "Na k'oshi fa." Kallon farantin yayi, yasan b芒 dan wayar nan data d'auki hankalinta ba da bata ci kamar haka ba, ruwa ya tsiyaya mata masu sanyi ya mik'a mata, karb'a tayi ta kurb'a sau d'aya ta aje ba dan bata buk'atar ruwan ba sai dan tsaro. Mik'ewa yayi zai fita tace "Idan na shirya fa yanzu zan fita." Jinjina kai yayi yace "Zan kaiki da kaina." Da alamar zolaya tace "Malam ina fata dai ba tunani kake yi zan raba kud'in aikina biyu na baka rabi ba?" Dariya yayi yace "Ke kuma gaki marowaciya lamba d'aya ko?" Girgiza kai tayi tace "Kud'ina ba zasu isheni ba nima, saboda zan yiwa yarona siyayya ta kayan sojawa da kayan ball da sauransu." Murmushi yayi yace "Wannan ba hujjar da zata sa a k'i biyana bace." Murmushi tayi ta bishi da kallo harya fita. Wanka ta shiga amma sai k'walwarta ta shiga hasko mata fuskarshi sanda yake bata abincin nan, a idonshi take hango tsantsar tausayinta da jin k'ai da damuwa na rashin cin abinci da batayi ba, sannan a k'wayar idonshi ta hango abu mai kama da k'aunarta a sanda yake hidimta mata ba tare da nuna k'yama ko gajiya ba, saima wani b'oyayyan farin ciki dake fita shinfid'e akan fuskarshi na aikatuwa da hannayenshi keyi a dalilinta, bud'a idonta tayi ruwa na sauka a kanta bisa hular ledar dake hana gashi jik'ewa, a hankali ta murza sabulun dake hannunta santex ta goga a wuyanta da bayan kunne tana fad'in "Idan ma abinda nake tunani gaskiya ne, hak'arshi ba zata tab'a cimma ruwa ba, ba zan iya auren wani ba bayan Aminu." Ci gaba tayi da wankanta harta fito d'aure da towel babba kad'an ya rage ya sauka k'asa, zata fara shafa mai aka bubbuga k'ofa, da sauri ta d'auko hijab ta saka tace "Shigo." Agaishat ce ta shigo da sallama, murmushi tayi tace "Au! Ke ce dama?" Hararan wasa ta mata tace "Kin d'auka shine ko?" Murmishi kawai tayi ba tace komai ba, cikin nutsuwa Agaishat tace "Dama yayi niyyar kaini gidan Ayya ne, shine nace ko zaki zo mu tafi tare." Jim tayi tana tunanin uzurirrikanta, kafin ta bata amsa cikin zolaya tace "Har da shi fa zamuje, shima zai gaishe da Ayya." Kallonta tayi tace "Lahhh! Ke ma kin iya sharri, nifa babu komai tsakani na da shi, ki daina had'ani dashi kar kisa mutumcina ya zube a wurinshi." Dariya tayi tace "Ba wani nan, shima ai naga take takenshi kamar yana ruwa." Dariya tayi ta juya zata shafa man tace "To nima zan je, shikenan?" Dariya tayi ta fita tace "Bara na fad'a musu to sai m没 jiraki." Fita tayi ita kuma ta ci gaba da shirinta da d'an sauri sauri amma a nutse da hankali, saida ta gama ta d'auki duk abinda zata fita dashi dan ba zata dawo ba har sai taje inda tayi niyya yau, fitowa tayi ta tunkaro falon da tattausar sallama. Tsareta yayi da ido sanda yake tsaye yana waya da Umma, lumshe ido yayi dan sai yanzu ta fito masa a Fadumar daya sani a can garin, cikin lafaya mai kyan gaske ta yane kanta cikinta tsaf, banda hoda da man leb'e babu abinda ke fuskarta. Cike da ladabi ta zauna tana kallon War da cewa "Ina kwana yallab'ai." A hankali ya amsa mata da "Lafiya lau." Agaishat ce tace "Ni baki gaisheni ba fa?" Dariya tayi tace "Ina kwana yallab'iya." Dariya tayi tace "Lafiya k'alau oganniya." Kallonta tayi tace "Kuma?" Hararenta tayi tace "Ba dad'i ne?" Wayar hannunta ta shiga dannawa ta nemo lambar asusun nan, mik'ewa tayi tana fad'in "Yallab'ai ga lambar asu..." Cak ta tsaya da fad'a dan gaba d'aya ta fad'a jikin Hasheer daya taho da niyyar yaji za'a fitan ne ko kuwa, bata kula dashi ba dan kanta na k'asa shi kuma baya tunanin zata kawo masa karo, ido biyu sukayi suna had'e yawu da matuk'ar wuya, a hankali ta raba jikinta da nashi tayi baya sosai idonta kuma na cikin nashi, kallon kin gama lahatani kawai yake mata, amma ya basar yanda ba zata gane komai ba y'a d'auke kanshi. Kallon inda su War suke yayi wanda su hakan ya musu dad'i musamman Agaishat da har saida ta mintsini War a damtse, dakewa kawai yayi ya kalleta kuma ko a fuska bai nuna yaji dad'i ba. K'arasawa tayi da wayar a hannu ta mik'a masa jikinta sai rawa yake tace "Lambar asusun." Da ido kawai ya mata alama ya karb'a, d'aukar lambar yayi a wayarshi ya mik'o mata, Agaishat ce tace "Idan kowa ya gama saimu tafi ko?" Mik'ewa duk sukayi sai Hasheer daya shiga gaba dan dama a tsaye yake, kallonshi take a ranta tana fad'in "Yayi masifar kyau, manyan kaya suna k'ara masa kwarjini." Ta gefenta kuma su Agaishat ta kalla, tana cikin wata atamfa mai k'yalli, duk da ta rufe d'inkin da hijab mai hannaye amma zaka san tasha d'inki mai tsada dan babbar atamfa ce, shi kanshi oga War wata galleliyar shadda ce jikinshi d'anya sharaf sai d'aukar ido take gashi kalar maroon d'in mai kyau, baya Agaishat ta bud'e ta zauna haka Faduma ta zauna kusa da ita, mazaunin mai zaman banza Hasheer ya kama zai shiga War yace "Waye zai tuk'a malam?" D'age gira yayi yace "Kai mana, ina bak'onka ne zan tuk'a ka." Gurgiza kai War yayi ya bud'e mazaunin matuk'i ya zauna da bismillah, cikin nutsuwa da salon birgewa ya juya akalar motar zuwa k'ofar waje. A nutse suke tafiya shi da War na hira data shafesu, Faduma ma da Agaishat suna d'an tab'a hirarsu suna dariya, wayarta ce tayi k'ara alamar sak'o, dubawa tayi ta bud'e ta karanta kamar haka _"Kinyi kyau fa."_ Murmushi tayi ta d'aga idonta ta kalleshi, sak茅 mayar da dubanta tayi kan lambar da har yanzu ko suna bata saka ba ta rubuta ta mayar masa. Dubawa yayi shima ya karanta a hankali cewa _"Kai ma haka, kamar za'a dangwalaka da gurasa."_ Dariya yayi shi kad'ai yana girgiza kai ya maida mata, tana dubawa a ranta ta karanta da _"Wane kalar lemu ya dace a korani dashi kenan?"_ Murmushi tayi ta maida masa ita ma, yana dubawa ya ga _"Wannan wanka ai sai bakwai a raye (7alive). "_ Dariya yayi sosai ya sake tura mata, dubawa tayi ta karanta _" Amma sunan kakanki ne da ni ko? "_ Maidawa tayi ita ma ya karanta da _" Zan binciki nasabata har zuwa kakana na ashirin, watak'ila ayi dacen samun mai sunan Hasheer."_ Gyara zamansa yayi ya sa hannu ya juyo da madubin dake gabanshi zuwa bayanta ya daidaita ya hango fuskarta, kallon idonshi tayi ta cikin madubin sai kuma ta mayar da idonta akan wayar, maido mata sak'on yayi ta karanta da _"Ba haka sunana yake ba, ki koya idan baki iya ba."_ D'an zaro ido tayi sai kuma ta rubuta ta tura masa, dubawa yayi yaga _"Allah na iya, kai da kanka ka fad'a min kuma na rik'e."_ Maido mata yayi cewa _"Ki garda baki iya ba, in kuma kin iya fad'a naji."_ D'aga kai tayi ta kalleshi ta cikin madubi daidai shima ya kalleta, had'e fuska tayi ta masa alamar zamu had'u d'in nan ta cije leb'e, kallon Agaishat tayi da banda kallonta tana murmushi babu abinda take, cikin dubara tace "Ya kike kallona haka?" Girgiza kai tayi tace "Ba komai." Murmushi tayi tace "Kinga ina bitar karatun Al-shama'il Nabiyy ne, ina karanta sunayen fiyayyen hallita ne da suka inganta, kinga bari kiji uku daga ciki." Saida ta kalli madubin nan sukayi ido hud'u dashi, cikin taushin murya da hard'ewa da harshen tubanci ya gama ratsata tace "Akwai *Mukhtaar*, akwai *Ahmaad* sannan akwai *Haasheer*." Take ya lumshe ido, na farko kenan da yaji sunanshi daga gareta haka, k'ara k'aunar sunan yaji a ransa da jin kamar ta sake fad'a har bacci ya d'aukeshi, sak'o y'a tura mata cewa _"Kin cancanci na miki kyautar kwabo."_ Maido masa tayi da _"Halan sunan kakarka ne dani shiyasa kake son tsokanata?"_ Dariya yayi ya shafi sumar kanshi ya maido mata da _"Zan waiwayi asalina har zuwa kakani na na ashirin, a ciki ba za'a rasa mai sunan *'Yar ma'aiki ba*."_ Wata dariya tayi ta maida masa da _"Satar kalamai, shiyasa nake tunanin kai d'in mai yankan kanun yara irina ne."_ Gyara zama yayi zai rubuta amsa War y'a kalleshi yace "Mutumin nan ko d'aureka zamuyi ne?" Agaishat ce tace "Sojana kayi shiru, ba'a katse mutum idan yana sirri da zuciyarsa." Hararanshi yayi yace "Ai shi bai fahimci haka ba." Nan fa gardama ta b'arke har suka isa gidan Ayya amsar da bai bayar ba kenan. *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 21:39 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _52_ Agaishat ce gaba sai War dake bi mata sai FadHash (hmmm, ni dai bana yin ka) kuma a baya sun jera kamar wasu amaren da suka zo godiya, sunkuyowa yayi yanda tsayinsu ya tashi daidai cikin rad'a yace mata "Yara masu k'iriniya irinki sacesu a killace ya kamacesu, kema lokaci na zuwa." Murmushi tayi tace "Kaga dai wajen Ayyar yallab'ai zamu shiga, kuma na tabbata yanda baya son wargi haka ita ma, ka rufa min asiri kar kasa nayi dariya ko shirme a gabanta, dan Allah?" 'Yar dariya yayi yace "Da baki fad'a naji ba da na kiyaye, amma tunda kika fad'a kin shiga uku sau dubu uku." Marairaicewa tayi tace "Haba dan Allah, ina laifi dubun biyu ma." A hankali War dake gabansu ya duk'a ya since takalminshi k'afa ciki, yanda yayi duk sukayi suka ajesu k'ofar shiga falon, da sallama duk suka shiga a bakinsu sai Faduma data had'a da kallon falon tana son gano inda kaskon turaren wutar nan yake irin wanda dada ke had'awa. Dattijuwa ce ta fito daga wani d'akin tana amsa sallama, Faduma saman matakalar ta fara kallo ta d'auka tana zata fito, ikon Allah sai ganin Agaishat tayi ta tafi da sauri ta bud'e hannayenta ta rumgumeta tana shagwab'a da fad'in "Ayya na." Cikin wata irin nutsuwa mai birgewa da kwanciyar hankali ta rumgumeta tana fad'in "Yarinyata, ya kike?" Cikin turo baki tace "Lafiya lau Ayya, ina kwana." Murmushi ta mata madadin amsawa ta mayar da kallonta kan Hasheer, fad'ad'a murmushin tayi ta d'an saki Agaishat ta tara masa hannu tace "Zo yaro na, sai yanzu yaga damar kawoka ko?" Cikin takon nutsuwa da zara zaran k'afafunshi jajaye masu d'auke da dogayen yatsu ya taka lallausan carpet d'in ya k'arasa gareta, sunkuyawa yayi yana rumgume hannayenshi baya, dafa kanshi tayi tana fad'in "Kana lafiya?" Da murmushi yace "Ummu lafiya ta k'alau, fatan kema haka?" Saida ta tallaboshi yayi tsaye duk da ya kereta sosai sannan tace "Indai ina tare daku lafiya ce zatai ta dad'uwa insha Allah." Murmushi ya saki yace "Alhamdulillah." Wardugu ne ya tako shima ya zagaya bayanta ya d'ora duka hannayenshi a kafad'unta ya had'esu kamar zata goyashi ya d'ora hab'arshi a bayanta yace "Ayya kin manta dani ko daga ganin wannan yaron?" D'an dukanshi tayi a hannu tana fad'in "Kasheni wai zakayi Wardugu? Sakeni." Sake kwantawa yayi a kanta yace "Ayya nayi kewarki fa, satina biyu bana garin nan bare na ganki, so nake ma nayi bacci a k'afafunki." Bud'e baki tayi ta kalli Hasheer tace "Kaji shi fa, yau nayi sabon yaron ne zan tsaya kulaka." Agaishat ce ta rik'o hannunta ita ma tace "Amma ai ni kina da lokacina ko Ayya?" Kallonta tayi tace "Ya danganta daga yanda kuka..." Bata kai ga fad'a ba ta tsaya tana kallon Faduma dake ta kallonsu tana murmushi, dan sosai suka birgeta har taji tana kewar ayyoyinta, da k'arfi ta b'amb'are hannayen Tagur tana kallonsu da tuhuma tace "Tare da bak'uwa kuke dama?" Duk sai lokacin suka kalleta suma, Agaishat ce tace "Eh Ayya, tare muke." Nufa wurinta tayi tana fad'in "Amma kirkinku yawa ne dashi, kuma shine kuka barta a bakin k'ofa?" Babu wanda yayi magana da kamo Faduma tayi da duka hannayenta biyu ta zaunar da ita a kujera, sunkuyawa tayi ta tallabo fuskarta dake k'asa, cike da kunya ta kalli fuskarta amma basu had'a ido ba, cikin ladabi tace "Ina kwana?" A nutse tace "Lafiya lau yan mata, ya kike? A hankali tace " Lafiya lau." Murmushi ta saki ta kallesu tace " *Wacece ita*?" Kallon juna sukayi, War ne yace "Ayya yarinyar..." Da sauri Hasheer yace "Ayya tare muka zo, k'anwata ce." Kallonshi tayi daga sunkuyen nan tace "Daga kallonta sai nake jin kamar mun had'a jini ko wata nasaba ta nesa ko kusa, kuma gashi sai na ganta kamar batuba ko?" War ne yace "Ayya ai k'anwa na samu, ki mata yaren kiji." Kallon Faduma tayi da har yanzu ta k'i ta kalleta cikin harshen tubanci tace "Ya sunanki?" Saida ta sake sunkuyar da kanta tace "Faduma Zahra." Murmushi tayi a harshen tubancin tace "Ke k'anwarsa ce?" Tsam ta kalli inda Hasheer yake, sai kawai ta jinjina kai a hankali tace "Eh Ayya." Murmushi ta sake yi tace "Yayi kyau Faduma." Mik'ewa tayi tsaye ta kalli Agaishat tace "Yaranki sun tafi makaranta, da sun taso zaki koma da kayanki." Dariya tayi ta nufo wajen Faduma ta kama hannunta tace "Taso muje kiga d'akina." Tab'e baki War yayi yace "Tsohon d'akinki dai." Turo baki tayi bata kula shi ba suka haye sama inda d'akin nata yake, suna ganin shigewarsu War yayi saurin fad'awa kan kujera yana fad'in "Ayya zan ci duk abinda kika dafa, nayi kewar girkinki." Hasheer kam da sauri ya bud'a fridge yana fad'in "Allah kasa ina da sa'ar samun damun Ummuna." Yana bud'awa ya shiga k'arewa fridge d'in kallo, ganin bai ganta ba yasa ya kalli Ayya dake kallonsu baki sake yace "Ummu ba fura?" Nunasu tayi da yatsa tace "Wai dama ladabin da kukayi ganin yaren nan ne?" Girgiza kai tayi ta matso kusan Hasheer, kunnenshi ta kama ta murd'e sosai tace "Miye batun wani k'anwarka ce? Fad'a min wacece ita?" Rik'e hannunta yayi yace "Zan fad'a miki Ayya, amma da fari sakar min kunnen nan, dan Allah na tuba." Sakinshi tayi ta zauna kusa da War, hakan yasa Hasheer zama kusa da ita sosai suka sakata tsakiya, War kanshi na maman kafad'arta sai hannun Hasheer dake cikin nata, cikin nutsuwa tace "Ina jinka." Kamar zaiyi kuka yace "Ummu wacce nake son aura ce, amma fa ita bata san ma ina son ta ba, Ummu ki fad'a min yanda zanyi na shawo kanta cikin sauk'i yanda dana fad'a mata zata amince min." Wani murmushi tayi tace "To me kake jira da baka fad'a mata ba? Yanzu fa ba'a sanya musamman yan matan yanzu, bare ma wannan kadarar mai daraja, kawai yarona ka fad'a." Marairaicewa yayi yace "Ummu ko ina son fad'a dana kalleta saina kasa, wani lokacin kuma sai naji tsoron kar ta k'i amincewa, saina dinga janta da hira kawai da tsokana." Hannunta ta zura ta shafi kumcinshi tace "D'ana, yau dai kawai ka kalli fuskarta ka fad'a mata kana sonta, kasa a ranka cewa idan bakayi haka ba kowane lokaci wani zai iya d'auke maka ita kuma kana kallo ya tafi da ita, shin zaka so haka?" Girgiza kai yayi yace "Ummu sai inda k'arfina ya k'are a kanta indai ba ita ce tace bata so na ba." A take tace "Ba ma zata fad'a ba, wace 'yar ce zata k'i gwarzona? Ai da gudu ma, duk da dai naga yarinyar akwai nutsuwa da aji, dan samunta a gareka zai zama babbar nasararka ne." Jinjina kai yayi yace "Hakane Ummu, shiyasa kullum nake k'ara sonta." D'an shafa kan War tayi da yayi shiru yace "Manyan duniya me ake tunani?" Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi yace "Ba komai Ayya, tuwonki nake son na ci kawai." Sakin duka hannayensu tayi tace "To ku d'agani na tashi." Hasheer ne ya sake langab'ar da kai yace "Um um, ki zauna haka Ummu, yaje da kanshi." Nuna shi yayi da yatsa yace "Ayya kice ya bari, zan fasawa mutum kai a wurin nan." Saida ya kallesa yace "Ummu ki fad'a masa nima ina da abun daya mallaka." Dariya tayi ta kalli War tace "To kaji dai, yanzu ku d'agani na tashi to." Sak茅 lefewa sukayi a jikinta, cikin fad'a tace "Kunga ku kiyayeni fa, idan kuka kaini bango duk yayeku zanyi na rumgumi 'yan matana dan sunfi dad'i sha'ani." Da sauri suka d'agata a tare Hasheer na fad'in "Ummu na yanzu zaki iya jefar dani ki kama bak'uwa?" Saida ta mik'e ta kalleshi tace "K'warai ma kuwa, tunda naga ta fika nutsuwa da hankali." Murmushi yayi ya sunkuyar da kai yace "A duk duniyar nan Ummu a gidan nan kuma a gabanki ne kawai nake jin kaina k'aramin yaron dake shan nono, idan ina tare dake na kanji duk wasu k'ofofin k'uruciya da shagwab'a sun bud'e min, ko Umma bana mata haka saboda akwai k'annai a gabana, amma anan nakan saki jikina nayi kukan shagwab'a a gaban uwata kuma ta kulani har ma ta share min hawayena." Murmushi ta sakar masa mai k'ayatarwa ta saka hannu cikin sumar kanshi ta murza, tunanin had'uwarsu kawai take da bai fi shekara hud'u zuwa biyar ba, sanda War ya shigo dashi gidan nan da nutsuwarshi sun birgeta, sai kuma Wardugu ya fad'a mata irin had'arin da yake fuskanta, hakan yasa ta tausaya mishi har tayi k'ok'arin ta shiga jikinshi ya sake d'脿 ita, tayi nasara sosai dan ya saki jikin da ita musamman shekara biyu da suka wuce da aka tab'a kawo masa wani hari, hakan ya sake d'aga hankalinsu haka shima kanshi, saita sak茅 rumgumarshi har ya dawo nutsuwarshi, a hakane fa yanzu har shak'uwa irin haka ta shiga tsakaninsu, ka rantse tun daga yarinta amintakarsu ta fara da Wardugu. Dan shi kanshi yanzu Wardugu yana d'aukaka lamarin Hasheer fiye da komai, yana sakin jiki da shi sosai abinda a baya ba yayi da kowa, amininsa d'aya tak *Mu'azzam*, kasancewar baya gari d'aya dashi yasa yanzu amintakarsu kamar taja baya sai ta waya, kafin ya zauna da Mu'azzam suyi sirri d'aya har sunyi da Hasheer a yanzun, haka kuma dama Allah yake had'a bayinsa, idan har suka tuna had'uwar da k'arfin amincin dake tsakaninsu su kansu sai suyi mamaki. *Wannan haka yake.* Ciki ta shiga ta zubo abinci ta kawo musu, k'asan carpet suka zauna dukansu hannayensu goma suka wanke suka saka biyar, fura ta d'auko a fridge da tasa mai kyau da ludayi, gabansu ta zauna suna cin abincin ita kuma tana damun furar cikin nutsuwa, Wardugu ba ma'abocinta bane haka ita ma, jiya yana fad'a mata Hasheer ya zo ta nemota ta ajiye dan tasan zai nema, da nono take damunta kamar yanda yake so, suna yi kuma suna hira tana sake jadadda mishi kawai yau ya fad'a a wuce wurin, inba haka b芒 ita zata fad'a mata. Dariya yayi yace "Ummu zanyi yanda kika ce, amma da fari zan fara fita da ita taga gari, daga nan saina fad'a mata komai." Kallonshi War yayi yace "Garin me zata gani? Kawai ka ajeta wuri d'aya malam, ka samu wurin cin abinci mai kyau ko wurin shak'atawa mai kyau saika fad'a." Jinjina kai yayi yace "Nagode, zanyi haka insha Allah." Duk da basu ji takon fitowarsu ba amma sautin maganarsu k'asa k'asa wacce kowace ke ji da kanta yasa suka kafesu da ido, kowane gwanar zuciyarshi ya zubawa ido yana jin zuciyarshi na harbawa da k'arfi k'arfi, har suka sauko suna fad'ad'a murmushi. Mamakin yanda suka samesu Faduma keyi, tana tambayar kanta "Wai dama k'arfin alak'arsu har ya kai haka?" Bata yarda ta had'a ido da kowa ba dan dukansu tana ganin girmansu, gaban Ayya ta tsuguna cikin taushin murya da kunya tace "Ayya dama akwai wani aiki da zan fita yi, insha Allahu ina idarwa zan dawo sai mu koma tare dasu." Da murmushi a fuskarta tace "Allah sarki, wane aiki kikeyi?" Hasheer ne yace "Lauyatu ce Ummu, kin ganta nan kullum a hanyar bincike da sake kutsa rayuwarta a had'ari take." Sake sunkuyar da kai tayi dan karta kalleshi tayi wani abun da zataji kunya, kallonta Ayya tayi tace "Allah ya bada sa'a kinji yarinyata, Allah ya tsareki a duk inda kike." Da ladabi tace "Nagode Ayya, saina dawo." Da kallo ya bita sanda take mik'ewa yace "Wannan Ayyar dai ta g茅n茅ral ce babu damar yi mana k'wacenta." Da sauri ta rufe bakinta dan maganarshi dariya ta bata, Ayya ce tasa k'afa ta zungureshi tace "G茅n茅ral tun yaushe na yayeshi na tattara masa kayansa daga gidana, yanzu sune 'ya'yana kai ma bana so ka nemi wata." Girgiza kai yayi yace "Ummu yarinyar nan fa da kike gani k'wararriyar 'yar k'wace ce, daga had'asu da Ummana shikenan duk ta rabani da ita ta juya min baya, yanzu Umma ko kiranta nayi a waya sai tace *ina 'yar albarka*?" D'auke kai Ayya tayi tace "To ga wata ma yanzu, nima yanzu 'yar albarkata ce." Kallon Faduma tayi tace "Zan fara baki lahaula saboda magauta 'yata, bamu san me zasu iya aikatawa ba." Satar kallonta Wardugu yayi sai kuma ya kalli Faduma yace "K'anwata, da gaske zaki k'wace min Ayyata? Ita kad'ai fa gareni." Cikin kafeta da ido Hasheer yace "Nima saida na fad'a mata haka, amma bata bar min ita ba." Satar kallonshi tayi a hankali, da sauri ya kashe mata ido d'aya, zaro ido tayi ta kawar da kanta, girgiza kai tayi cikin nutsuwa tace "Yallab'ai zan baka Abana, saika bar min Ayyar." Dariya sukayi sai kawai yace "Kinga kuma idan kikayi haka sai Abana ya zama biyu kenan." Hasheer ne ya tsareta da ido yace "Batula yanzu ayyoyi nawa kika tara?" Dariya sukayi sai Ayya data girgiza kai, a hankali tace "Guda hud'u, kuma da sannu zan cika guda dozin." Jinjina kai yayi ya sauke numfashi ya kalli Wardugu yace "Har na fara jin tauyin wanda bamu had'u dasu ba, Agaishat kiyi hankali karki bari ta had'u da ayyarki." Dariya Agaishat tayi tace "Ai idan ta gama tarasu ni kuma zan kwashi rabi daga ciki." Ayya ce ta kalli Faduma tace "Kinga, wad'annan da kike gani sai sukai isha'i basu gama zancen nan b芒, ke kuma kina da aiki a gabanki, wuce ki tafi kinji, Allah y'a tsare ya bada sa'a." Sunkuyawa tayi tace "Ameen Ayya, nagode." Kallon Ayya yayi yace "Ayya sai mun dawo, kuma fa karki bashi furata." Da kallo ta bishi tana so taji wai tare zasu tafi ko me yake nufi? Ita ce tace mishi tashi mu tafi? To yaushe? Ikon Allah ta fad'a a ranta tana binshi da kallo, wannan ai jarabta ce babba ma kuwa, zaune Agaishat tayi ta lafe a jikinta sai Wardugu daya watso mata wani kallo ya mata nuni da hanyar d'akinshi dake nan har yanzu, kuma duk randa ya bushi iska saiya tarkatota su dawo nan suyi kwana biyu uku su koma. Gane manufarsa da tayi yasa ta mak'ale kafad'a alamar a'a, d'an marairaicewa yayi yana sake nuna mata, sake dai mak'ala kafad'ar tayi dan haka ya d'an zaro ido, kyab'e fuska tayi tace "Um um, Ayya kin gani ko." Sunkuyar da kanshi yayi sanda Ayya ta kalleshi, ita kuma dariya tayi sai Ayya data girgiza kai a ranta tana fad'in "Allah ya shiryaku, shi waccen ya bi yarinyar, kai kuma daga nan zaune kana kiranta, hmmm." Suna fita ta kalleshi cikin rad'a tace "Elhaj wai me yasa kake so ace kai dreba na ne?" Wata dariya ya kece da ita ya kalleta yace "Dan kina sha'awar fad'a ba sai kin danganta hakan da wani ba, ki fad'a kai tsaye drebana." Murmushi tayi taja lafayarta ta rufe fuska, shiga sukayi suka d'auki hanyar babban asibitin, hira ta nutsuwa da nishad'i da kuma barkwanci ce tayi ta shiga tsakaninsu har suka isa, a bayan mota ya ciro mata ledar, hannu ta kai zata karb'a ya janye yace "Wane ni? Ina tare dake kuma kiyi dakon kayanki." Murmushi tayi kawai kai tsaye suka samu ganin likitan bayan sunyi jiran da bai wuce minti sha biyar ba, zaune sukayi kan kujerun dake fuskantarshi suna kallonshi, cikin kwarewa ya dinga mata bayanin kowane syrup d'in da nashi kalar anfanin, tare da k'arawa da cewa dukansu dai kayan maye ne masu had'ari ga lafiya da rayuwa. Syringe d'in nan ta nuna masa yasa hannunsa mai safar likitoci ya karb'a, kallonshi yayi sosai ya kalleta yace "Ba zan iya gane wace kalar k'wayar akayi anfani da ita ba, amma in zaki iya bani zuwa gobe sai ki samu sakamakon, dan yanzu lokacin da nake zuwa makaranta ne koyar da wasu d'aliban harkar likitanci." Girgiza kai tayi tace "Wannan ba damuwa bane, zan jira insha Allah." Mik'ewar da sukayi yasa shi binta da kallo yace "Ba kowane lokaci zaki sameni ba, ki fara kirana kafin ki zo." Wayarta ta ciro a k'aramar jakarta ta mik'a mishi tace "Ba damuwa, saka min lambar." Da kallo ya bita sai kuma ya kalli likitan, tsaki yaja tare da yatsina fuskarshi ya kawar da kai, bata kulashi ba bare tasan da wa yake, saka mata lambar yayi ta karb'a ta kalleshi tace "Nagode, sai ka jini." Da murmushi ko yace "Sai na ji daga gareki." Saida ya kalli k'wayar idonshi yace "Har abada." Juyawa yayi gareta data kalleshi da mamakin lafiya? Saraf ya karb'e wayar ya fita da sauri ya bar ofishi yana goge lambar, lumshe ido tayi ta tuna bayan 98-36- lamba biyu na k'arshe ma sun zauna mata akai, na tsakiyar ne dai ta lura akwai wata 8 d'in da kuma 3, to zai zama 83 ko kuma 38? Bud'e ido tayi ta sauke ajiyar zyciya ta girgiza kai ta fita. A mota ta sameshi zaune ya had'a kanshi da sitiyari, harta zauna ta rufe bai d'ago ba bare ya kalleta, ganin shiru yasa ta lek'a fuskarshi tace "Yallab'ai." Jim yayi kamar bai ji ba na tsawon minti biyu, a hankali ya shiga d'agowa yana sauke numfashi, saida ya had'e yawu kafin ya kalleta, gabanta taji ya fad'i saboda ganin idonshi sunyi launin ja ga kuma jijiya a kanshi kusa da goshi har zuwa kusan kunne, d'auke idonta tayi saboda tsoron yanayin data ganshi, a hankali yace "Kalleni nan." Juyowa tayi da sauri tana raba ido, girgiza mata kai yayi cikin muryar tausayi yace "... *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 21:40 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _53_ Juyiwa tayi da sauri tana raba ido, girgiza mata kai yayi cikin muryar tausayi yace "Dubeni Teema, wallahi wannan yanayin bak'one a gareni, ban tab'a jinshi bare na sanshi, ki taimaka idan har kin fahimci wani abu ki nema min sauk'i." Had'e hannayenshi yayi alamar rok'o yace "Dan Allah?" K'uri ta masa da ido kamar bata fahimtar yarenshi, saidai banda fad'uwa babu abinda gabanta keyi, ta fara fahimtar abinda mutumin ke nufi, saidai a yanzu sadakin wani ne akan ta, kuma mahaifinta ya yarda dashi ta yanda ba zata sake gigin kawo masa wani ba kamar yanda tayi a baya, dole ta hak'ura ta nuna masa bata gane komai ba, badan bata jin wani abu b芒 a game dashi. Saida ta gama masa kallon tsaf shi ma idonta yake kallo sannan ta d'auke idonta cike da basarwa tace "Idan kana da abunyi zaka iya saukeni anan, zan je yantala ne gidansu yarinyar nan." Wani tuk'uk'in haushi ne ma ya taso mishi, wai duk bayanin nan daya mata ko tausayi ma bai bata ba kenan? Wayarta dake aljihun gaban rigarshi ce tayi vibration alamar kira, Aminu ne sai dai bai fahimci komai ba a game da sunan dan an rubuta *A. Garkuwa* ne (Aminu garkuwa ba, sai Aminu馃拑), cikin b'acin rai ya cillo mata wayar sai kuma ta fad'a mata a wuyan hannu da k'arfi, da k'arfi tace "Aouch!" Yarfe hannun ta shiga yi tana fad'in "Washhhh! Auhhhhh." Bata ankara ba taji tattausan hannunshi ya rik'o nata, juyowa tayi sai gani tayi yana ta busa mata iskan bakinshi a wurin kamar wacce wuta ta toye, a rikice ya kalli fuskarta yace "Ki yafe min dan Allah, ki yafe min kinji, bansan zaki ji ciwo ba da banyi ba." Turo baki tayi ta kalleshi kamar zatayi kuka tace "Ai kasan zata bigeni dama, me yasa baka bani a hannu na ba? Kawai dan likita ya b'ata maka rai sai ka huce a kaina." D'an mamatsa mata hannun yayi yace "Yi hak'uri to na daina hushin yanzu, kiyi hak'uri kinji." Mak'ale kafad'a tayi tace "Um um, saina rama." Shi fa da gaske yake kuma ya d'auka ita ma haka, wayarshi ya ciro a aljihu ya mik'a mata ya zura mata wuyan hannunshi yace "To rama." Sake mak'ala kafad'a tayi tace "Ni ba da waya nake so ba." "To dame?" Ya fad'a yana kallonta, da yatsa ta bubbuga mata hak'oranta, da alamar tambaya yace "Wai cizo?" Jinjina kai tayi alamar eh, wuyan hannun ya mik'a mata yace "Indai kinsan kin yafe min to ciza son ranki." Ganin yanda ya mik'o mata hannun yasa ta yin dariya ta d'auki wayarta dake kan cinya tace "Na hak'ura, ban cika son ganin hawayen babban mutum ba." Kallonta yayi sai shima yayi murmushi yace "Na yarda ke auta ce tunda kin iya jan sharri haka." Saida taja numfashi tace "Gaba da baya ma kuwa." Tayar da motar yayi suka d'auki hanyar yantala cike da nishad'i, tana ganin kiran Aminu amma bata d'aga saboda bata da yaren da zata mishi magana dashi da take ganin mutumin nan ba zai ji ba, a take kuma zuciyarta ta tambayeta "Me yasa kika k'i d'aga kiran saboda shi?" Satar kallonshi tayi, haka kawai dai taji bata so yasan komai a kanta, ba tare da wani dalili ba taji bata so taga murmushi da dariya sun d'auke a fuskarshi, har cikin ranta take jin tana son suyita kasancewa tare, a dalilin zuwanta garin nan har takan manta da wacece ita idan tana tare dashi, saida ta zo garin nan ne take jin kanta ashe ita ma zata iya yin rayuwar farin ciki, had'uwarta da mutumin nan yasa take tuna lallai ita ma budurwa ce duk da an yi wa budurcin nata babbar illa. Dan haka take jin kamar bata son abinda zai shafi farin cikinshi, ba ta son abinda zai gurguntar da mu'amularsu. A k'ofar gidan ya sauketa ya fito shima ya nufi masallacin dake kusa dan yin sallah azahar ita kula ta shiga da sallama, kamar zuwanta na shekaran jiya da dare yau ma ta samu tarba daga wurin mahaifiyar yarinyar sai kuma kakarta dake k'ofar d'akinta zaune, sun gaisa sosai mahaifinta ma ya fito daga ban d'aki suka gaisa da butarshi a hannu, cikin karramawa da harshen zabarmancinshi yace "Madame kin sake dawowa, ya binciken naku?" Ajiyar zuciya ta sauke ta kallesu shi d'脿 uwar tace "Bincike Alhamulillah, saidai akwai wani abu dana gano da yasa dole na dawo wurinku dan samun gamsashiyar amsa." Duk kallonta sukayi da kyau sai mai gidan ne da yace "To to! Lafiya ko? Wace amsa kenan?" Kallonsu tayi da kyau tace "Kun fad'a min 'yarku taje d'aukar karatu ne (lesson) a bayan gidan nan aka kad'eta, alhalin kuma a bassora aka kad'e 'yarku, me ya kaita can bayan kuna ikrarin tana nan daf daku? Bakuyi mamakin jin inda aka bige muku 'yarku bane ko me?" Kallon juna sukayi iyayen sai uwar ta fashe da kuka, cikin jin haushi a harshen zarma ya shiga fad'in "To miye na kuka kuma? Kawai dan kisa ta gane komai? Allah ranki zai b'ace." Rai b'ace Faduma tace "Dakata Abba, aikina nake yi anan, tun kafin na fara d'ora alk'alamina akan matsalarku saida na fad'a muku, bana son k'arya dan in ma anyi ta Allah zai dafa min na gano gaskiya, idan kuma na gano ko kai da nake wa aikin ne na gane baka da gaskiya na kan gurfanar da laifinka a gaban alk'ali, dan haka ku taimaki kanku ku fad'a min gaskiyar magana, inba haka ba to zan d'ora alhakin mutuwar 'yarku akan ku abisa sakacinku da kula da yara, wanda zaku iya fuskantar hushin hukumomi masu kula da hakk'in yara da mata." Kallon dattijon tayi a kausashe tace "Zab'i ya rage naka ka taimaka mata ta fad'a min gaskiya, ko kuma kaje ga sallarka ka barni na tambayeta, dan yanda al'amarin ke dukanta matsayinta na uwa kai baya dukanka haka." Sanyi yayi sosai ya jinjina kai yace "A'a madame dama ba wani abu bane, gaki gata dai zata fad'a miki." Fita yayi yana kurb'ar ruwa a butar hannunshi, gyara zamanta tayi ta kalli uwar ta nuna mata turmin dake kwance k'asa, zaune tayi kanshi tana kallonta duk a d'arare, fuskarta a had'e sosai kamar ba faduma ba tace "Fad'a min me ya faru? Dama kuna da d'abi'ar barin yara fita ne da dare ba tare da saninku ba musamman ma mata?" Girgiza kai tayi tace "A'a, gaskiya ita ba mai son fita bace daga gida ba tare da wani dalili ba." Kafeta tayi da ido tace "To a ranar kun aiketa wani wuri ne?" Girgiza kai tayi tace "A'a." Jinjina kai tayi tace "Shin kun tab'a waiwaiyarta idan ta tafi makaranta dan ku tabbatar can d'in ta tafi?" Shima girgiza kai tayi tace "Gaskiya a'a, dan bamu tunanin zata iya yin wani abu marar kyau." Tsareta tayi da ido tace "To me ya kaita unguwar bassora indai hakane?" Fashewa tayi da kuka tasa hab'ar zaninta tana share hawaye, cikin kakkausan murya tace "Kinga, d'ago ki kalleni ki fad'a min me yake faruwa, dan ba wasa bace ta kawo ni nan, idan kuma ba zaku fad'a ba to zan shiga binciken sanin abinda ya faru da kaina, dan ba zan yarda na baro garina da abubuwa masu mahimmanci ba kuma na koma haka kawai, dan haka ina jinki?" Cikin kuka ta kalleta tace "Mu ma mun shiga tashin hankali sosai sanda aka fa'da mana inda aka samu gawarta, yarinyar da muke tsammanin tana bayanmu kad'an, sai muka jita nesa damu kuma nesa da duniyarmu, ba wannan ne babban tashin hankalinmu ba kamar abinda muka gani a jikinta bayan rasuwarta." Shiru tayi tana ci gaba da rera kuka, ba ko k'yabtawa Faduma tace "Me kuka gani?" Cikin shashek'a tace "D'aya daga cikin malaman dake mata wankan gawa ne ta keb'e dani suka nuna min cikin dake jikinta, ciki kuma bana wata d'aya ko biyu ba, a k'alla zai kai wata biyar a jikinta." Da k'arfi Faduma tace "Ciki kuma?" D'aga kai tayi alamar eh, da mamaki da kuma kad'uwa tace "To wa ya mata cikin?" Girgiza kai tayi tace "Abinda har yanzu muka kasa samun amsarshi kenan? Har yau tambayar da muke jefawa kanmu kenan wa ya mata ciki? Saidai mai amsa manan bata raye bare muji." D'an dafe gaban goshinta tayi ta kalleta tace "Yanzu ke baki san cewa tana da cikin ba saida aka nuna miki?" Girgiza kai tayi a hankali tace "Ban sani ba gaskiya." Ita ma girgiza kan tayi tace "To waye saurayinta wanda kuka sani har kuke barinta tsayawa dashi?" Nan ma girgiza kai tayi tace "Bata da wani tsayayyen saurayi da yake zuwa gidan nan, hasalima ita bata da hayaniya da son tara samarin nan." Girgiza kai tayi irin takaicin nan tace "To k'awaye fa? Wacce suke da kusanci sosai?" Kallon Faduma tayi tace "Ai bana iya ce miki ga wata k'awa da take k'awance da ita ba, ita dai tafi son rayuwar cikin gida tayi zaune d'aki ita kad'ai." Cikin alama da hannunta na hagu take mata nuni da fad'in cewa "Kuma baki tab'a saka ido akan son zaman d'akin nata ba? Ko kuma ki tuntub'e ta kiji matsalarta ko damuwarta?" Cikin sanyin jiki tace "Gaskiya ban tab'a ba, saboda a tunani na kawai rayuwarta ce haka son shiru shirun." Cike da jin haushi Faduma tace "Amma ko a 'yan uwanta ko kuma ke ko wani babu wanda take hira ta sirri ko data shafeta? Ko kuma wani ko wata da take da shak'uwa da sakin jiki dashi ko ita? Inba haka ba taya yarinya kamar wannan kuma zatayi ciki a haka?" Shiru uwar tayi tana d'an nazari na wani lokaci, sai kuma ta girgiza kai a hankali tace "Maganar gaskiya babu, yan uwanta ma bata cika zuwa inda suke ba sai in sune suka zo nan, kuma baka ganin walwala tare da ita bare ka gane farin cikinta na ganin 'yan uwanta, ni kuma kullum tana yi min magana cikin ladabi da kunya, shiyasa ko lokacin fara al'adarta ma sai wajen mahaifiyata na turata, dan bansan taya zan mata bayani ba, sai ma 'yan watannin da suka wuce ne naga tana d'an sakin jiki har tayi hira da *Deen*, hakan yana bani mamaki da kuma jin dad'in akwai wanda take sakewa dashi har tayi dariya." Da sauri tace "Waye kuma Deen?" Da mamaki ta kalleta sai kuma tace "Abokin yayanta, wanda shi ya tsaya mana har aka d'aukoki, da fari mun so abar maganar ne saboda gano akwai ciki jikinta, amma shi ya tsaya mana kai da fata sai an bi mana hakk'inmu." Hannunta tasa ta murza fuskarta sosai ta kalleta tace "Shi d'in tun tsawon wane lokaci kuka san shi?" A nutse tace "A k'alla zai kai shekara shida ko bakwai." "A duk shekarun nan kai tsaye yake shigowa gidan nan ko kuma bayan ya nemi izini?" Idonta ta kalla tace "Kai tsaye yake shigowa amma daga bakin soro saiya tambayi idan yayan nata yana nan." Gyad'a kai tayi tace "Tana da waya ne?" Girgiza kai tayi tace "A'a bata da." Jinjina kai tayi tace "Shi d'in a ina zan iya samunshi?" A hankali tace "Eh to bana ce b芒 gaskiya, amma dai nasan gidanshi a Bassora yake." Tsam tayi ta kalleta, har ranta take jin kamar ta kifa mata mari, ko uta data haifi namiji ba zata mishi wannan rik'on ba bare ita mai mace. Girgiza kai tayi cike da takaici tace "Kin tab'a lalubar jakar makarantarta kiga abinda ta k'unsa?" Girgiza kai dai tayi kamar kowane lokaci tace "A'a, saboda a fili take ajeta kuma ina tunanin kayan karatu ne kawai a ciki." D'ora yatsunta biyu tayi tana shafa karan hancinta, ta d'an jima haka tana tunanin yanda lokaci lokaci takan zazzage jakar Amjad ta dubata bayan yayi bacci, tana samun nutsuwa idan taga bata samu komai ba. Kallonta tayi tace "D'auko min jakarta." "To." Ta fad'a tana mik'ewa ta nufi shiga d'akin, a hankali Faduma ta kalli tsohuwar dake k'ofar d'akin tana ta darzar goro, da alama tana da matsalar ji dan tun ranar ta fahimci yanda suke mata magana da k'arfi. Vibration d'in wayarta ne ya dawo da kallonta kan cinyarta, d'auka tayi taga sunan Safwan, saboda gudun b'atawa yallab'ai War aikinsa yasa ta d'auka dole, daga bangarenshi yace "Babbar yarinya wai ya ake ciki ne? Har yanzu babu labarinki." Cikin salon data sameshi dashi jiya ta d'aga muryarta tace "Yi hak'uri dan Allah Alaji, gamu saloon tare dasu Arkiya da Binta, muna gama wankin kai zan kiraka sai naji kana ina na sameka a inda kake." Da farin ciki yace "To b芒 damuwa ina jira fa, sai naji daga gareki." Cikin zazzak'an murya tace "Da zaka taimaka min ma da fara shirye shiryen wurin nan, kaga saina tura maka kud'in ta asusunka." Da sauri yace "Babbar yarinya, kinsan da alerte d'in da kika min na jiya ya kusa haukatani na kasa bacci, ai kud'in da kika turo sun isa ayi komai a gama." Wurga idonta tayi gefe d'aya da alamar gajiya dan tasan aikin War ne tace "Ba komai bane wannan ai, aci gaba da gashi kawai." D'if ta kashe wayar saboda fitowar mahaifiyar yarinyar, mik'o mata jakar tayi bak'a k'atuwa mai kyau kuma sabuwa, karb'a tayi ta shiga zuge zip hankali kwance tana lalubawa, duk litattafan ciki saida ta cirosu ta bud'ewa da sauri ta rufe, a cikin jakar akwai k'aramin zip dake lullub'e da wata raga ba kasafai ido ke sauk'in ganinshi ba, wanda ake wa taken da *kashe ni ka d'iba*, tana saka hannu ta jawo babbar waya k'irar infinix a ciki, sakin jakar tayi ta kalli wayar ta saki wani murmushin ban haushi. Kallon uwar tayi tace "Kin gani, sakacinki me ya jawo miki yanzu? Yarda da kuma sakankancewa 'yarki ba zata aikata kaza ba yasa kin kasa yin abinda ya kamata akan ta." Jefa wayar tayi akan jakar ta mik'e tana fad'in "Ba zan tsaya bincike da bin dindigin 'yarki data rasu ba, abinda ya kawoni shine a gano gaskiyar a cikin maye aka kashe muku 'yarku ko kuma ba haka ba, ina fatan wannan ya zama izina a kan ki ko dan 'ya'yanki na gaba." Juyawa tayi ta fita cike da takaici tana jin kamar tayi kuka, fitowarta daidai da bud'e motarshi zai shiga sun dawo daga masallaci, zagayawa tayi ta bud'e motar ta shiga motar tana kumburo baki. Gyara zamanshi yayi da kyau yana kallonta yace "Idan baki fad'a min wanda ya tab'a ki a ciki ba, to zaki sa na shiga gidan mutane na rufe kowa da duka." Tintserewa tayi da dariya bata shirya ba, kallonshi tayi tana k'yak'yata dariya tace "Da gaske sai ka dakesu?" Jinjina mata kai kawai yayi yana murmishi ganin Allah ya bashi damar sakata dariya, girgiza kai tayi sanda ya tayar da motar suka d'aga, kallonshi ta sak茅 yi tace "Ka sanar ma yallab'ai yarin nan fa na kirana akan maganar shagalin nan." Ajiyar zuciya y'a sauke y'a kalleta yace "Yaro? Kina jin dad'in kiran namiji yaro ko?" Rufe fuska tayi da hannayenta tace "To ai idan naga yaron ne, kuma naji ance duk maza kamar jarirai suke a hannun mata." K'uri ya mata da ido sai kuma ya jinjina kai yana ciro wayarshi, cije leb'e yayi yace "Zamu gani nan da d'an lokaci, idan kuwa mutum baisa na ji na zama jariri ba, hmmmm! Sai nayi k'uli k'ulin kubra na dallawa mutum harara ta bayan idonshi." Wata dariyar ta kwashe da ita harda rik'e ciki tana fad'in "Dan Allah ya isa haka, karka kasheni da dariya mana." Murmushi yayi dan shi a gareshi hakan ne farin cikinshi, wayar ya d'ora a kunne yana fad'in "War na Agaishat." Amsawa yayi na 'yan dak'ik'u kafin ya sake cewa "Yaron nan d'an k'waya daka mak'ala mata aiki dashi dole ne yake kiranta, ya zatayi dashi kafin raina ya b'ace na ji masa ciwo." Kallonshi tayi saidai shi ko a jikinsa ma, shiru yayi yana sauraron Wardugu kafin yace "War ka tabbata babu matsala?" Tabbacin daya bashi yasa yace "Shikenan kamar yanda ka fad'a, amma aka mata kallon banza akan ka zan rama." Bata ji me yace ba sai dariya da taga yayi yace "To naji masifaffe." Ya datse kiran, ba tare daya kalleta ba yace "Sak'o daga yallab'anki yace ki koma gida idan kin gama abinda kike, anjima kuma zaki had'u dashi saboda maganar shagalin, shi kuma zai cika miki taron da 'yan mata da samari yanda komai zai tafi daidai." Kallonshi tayi tace "Zanyi yanda ya fad'a, amma yanzu akwai inda nake son zuwa." Wayarta ta duba ta kira lambar Aminu, a tsaitsaye suka gaisa ta tambayeshi lambar abokinshi? A take ya lak'aba mata ita akai kafin ta datse kiran ta shiga saka lambar, bata jima tana k'ara ba ya d'aga yana sallama, amsawa tayi cike da haushinshi da sake gasgata zarginta akanshi, fad'a mishi tayi tana hanyar zuwa ya bata kwatancen gidanshi? Bai wani damu ba ya shiga fad'a mata har ta datse kiran suka nufi unguwar. A can k'ofar gidan suka hangeshi sai suka k'arasa ya sauketa, kallonshi tayi kallo na tsanake, izinin shiga ciki ya mata tace "A'a nan ma ya isa, na zo yi maka wasu tambayoyi ne, ina fatan zan samu amsa ta gaskiya da gaskiya?" Jinjina kai yayi yace "Insha Allahu." Tsareshi tayi da ido a yanayin da ko zai mata k'arya to zata gane daga wasu alamomi tace "A gidansu margayiya an fad'a min kusan kai ne kad'ai mutumin data fi sakewa dashi, hakane?" Kai tsaye yace "Hakane gaskiya, dan yarinya ce ita da bata cika son hayaniya ba sosai, nima kuma ina janta da wasa ne da tsokana shiyasa take sakewa dani." Ba tare data daina mishi kallon nan ba tace "Shak'uwar dake tsakaninku takai matakin da zata iya fad'a maka wani abu dake damunta ko kuma ya fasheta kai tsaye?" Gyara tsayuwa yayi yace "Wasu lokuta takan fad'a min abinda y'a shafi karatunta, ko kuma idan ina mata magana kan k'awaye saita nuna min haka tafi son zama ita kad'ai kawai." A take tace "Bata tab'a maka hirar saurayi ko kuma soyayya da wani ba?" Murmushi yayi yace "Gaskiya a'a, bana jin tana dasu samarin nan." "To waya fa? Ko kai ka siya mata?" Ta fad'a tana tsareshi da ido, daga yanda yayi da farko zaka gane bashi da gaskiya, amma saita basar kawai, a duburburace yace "Waya kuma? Ban tab'a ganinta da ita ba? Ni me zai sa na siya mata waya bayan bata ra'ayi?" A dak'ile tace "Kenan sakewarta da kai bai kai ta fad'a maka tana b'oye waya a jakarta ba?" K'yak'yabta ido yayi bai ce komai b芒, d'aga kafad'a tayi tace "A saninka da ita waye ta sani a unguwar nan bayan kai?" Jim yayi sai kuma y'a kalleta yace "Gaskiya ban sani ba." A take tace "Kenan a ranar da aka banketa ma wurinka ta zo akan maganar cikin dake jikinta ko kuma ka mata abinda ka saba yi mata?" Da k'arfi ya kalleta yana zazzaro ido, jujjuyawa y'a shiga yi baya da dama da hauninshi, kallonta yayi ya rufe baki da hannu d'aya yace "Dan Allah ki rufa min asiri, abinda ya faru tsakanina da ita tsautsayi da k'ad..." D'aga masa hannu tayi tace "Ya isa, ba abinda nake son ji ba kenan, abinda ya kawoni shine na tabbatar kai ka mata ciki, ka sani abinda kayi yaudara ce da cin amana da kuma *zamba cikin aminci*, hakan bai dace b芒, ba zan fallasa ka ba ko da a wajen iyayenta, saidai zan musu hannunka mai sanda akan ka, kuma idan nayi niyya kasan zan iya tona maka asiri ta yanda za'a kamaka da laifin fyad'e wa yarinyar da bata kai shekara sha takwas ba, a doka ta k'asar nan kumaj daka sha d'auri a k'alla na shekara goma sha biyar ko kuma talatin." Juyawa tayi ta barshi nan tsaye ta koma mota, da kallo yake binta da son sanin abinda suka tattauna ya ga tana magana a nutse amma kuma da kw'arewa ta kamar ta kai matumin mak'ura, amma ganin tayi shiru idonta kamar da hawaye saiya k'yaleta kawai ya tayar da motar suka d'auki hanyar komawa gidan Ayya. *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 21:40 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _54_ Ko da suka koma sun samesu zaune falo zasu ci abinci akan carpet, kallonsu Ayya tayi tace "Har kun dawo? To ku wanke hannayenku mu ci abinci." Kallon robar Faduma tayi wacce zasu wanke hannun a ciki da kuma alama kowa anan ya wanke, durk'usawa tayi saboda ba zata iya musawa ba, shi kuma tsuguno yayi irin na maza hakan ya sa suke fuskantar juna, tsareta yayi da ido yana kallon yanda take wanke hannayen, a hankali ya saka hannayen nashi ciki shima hakan yasa ta saurin d'ago idonta ta kalleshi, satar kallon su Ayya tayi sai taga babu mai kallonsu, da ido ta masa wuk'il da alamun "Cire mana." Shima da idon ya nuna mata "Um um." K'asan ruwan ta kwantar da hannayenta ta jawosu baya zata janye dan bata son hannayesu su had'u, d'ora hannayenshi kan nata tare da rik'e natan, zaro ido tayi ta bud'e baki kamar tayi magana. Kallon hannayen nasu tayi wanda nashi suka yi jajir a cikin ruwan, nata kuma suka bayar da kalar bak'i mai kyau, saidai tsakanin nata da nashi bata san wanne yafi taushi ba, marairaicewa tayi tare da yin kalar tausayi sosai tace "Dan Allah." Murmushi yayi yana kallonta ya zare hannayenshi tare da sakin na ta hannayen, da sauri ta cire na ta ita ma tana matsawa kusa da Agaishat ta zauna, mak'alewa tayi a kafad'arta ta kasa saka hannun, daf da ita ya zauna wanda sam bata yi tunanin haka ba ganin Ayya ce anan, amma haka ya kutsa y'a shiga tsakiyarsu, duka kowa ya tank'washe k'afafunshi amma banda Faduma da ta tokare k'afarta d'aya ta d'ora hab'arta a gwiwarta, a hankali take tsakurar abincin tana kaiwa bakinta cike da kunya, Ayya ce ta kalleta a nutse tace "Auta ta." Tare da Agaishat suka kalleta, murmushi Ayya tayi tace "Agaishat na bake ba, ki barwa Faduma k'aramtar mana." Turo baki tayi gaba ta mak'ale kafad'a, kallon Faduma Ayya tayi tace "Kiyi sauri ki ci abinci kinji, zamu shiga gyaran jiki yanzu." Da ido kawai ta iya amsawa, amma a ranta tana mamakin gyaran jikin me kuma? Toh ita dai bata sake cewa komai ba saida Hasheer ya kalleta ya d'ebo lomar tuwo yace "Naga kamar kunya kike ji, karb'i na baki." Sake sunkuyar da kai tayi cike da kunya amma bata kalleshi ba, ayya ce tace "Zan fa ci mutumcin mutum kana neman hana min yarinya sakewa a gidan nan." Murmushi yayi yace "Na tuba Ummu." Basu sake magana ba har suka kammala su War suka fita waje su kuma suka shiga d'akin sama, dama b芒 kitso ne akan ta ba, duk kulawarta da jikinta yau sai aka nuna mata gaba ma da gabanta, ayya da kanta ta zaunar da ita ta dinga tsaga gashin nan nata tana shafeshi da wani gangariyar mai dake maganin duk wata cuta ta kai, dan har zafi gareshi idan aka saka amma haka aka shafe mata kanta dashi aka rufeshi da ledar kai. Cire kayanta tayi kamar yanda Ayya ta umarta ta d'aura towel a jikinta, daga k'afafu zuwa hannaye da kuma kafad'u da wuya zuwa fuska aka shafe mata shi da wani abun da ta tabbatar da kurkur a ciki da kuma zuma, sanda aka gama shafa mata Ayya ta koma gefe ta zauna sai cikin masu aikinta data had'awa Faduma ruwan wanka, minti arba'in ta d'auka kafin ta shiga wanka da ruwan d'umi, saida ta fara wanka hakanan kafin ta saka sabulun da Ayya ta bata, had'a shi ne akayi da sabululuka da kuma sauran had'i irinsu dankalin turawa da zuma da kurkur da inibi da kuma ruwan kankana, tunda ta fara wankan taga jikinta na fitar da wani irin datti. Ita kam har kunya taji data ga dattin nan ba wai na daud'a ba, saidai datti ne da zaka ga y'a fita ne kawai idan kayi wanka da wani sabulun mai cire wannan dattin. Ga wani sihirtaccen k'amshi da yake fitarwa wanda tuni jikinta ya d'auka, uwa uba kuma wani sulb'i da taji fatarta tayi a take, daga k'arshe kuma saita had'a harda kanta ta wanke karin ta fito. Fitowa tayi ta zauna kan kujera Ayya ta bata mai ta shafa wani mai taushi sosai da kuma k'amshi sannan mai duhu, saida ta gama shafawa ta zauna mai aikin nan ta busar mata da kanta sannan ta dinga caje mata shi a nutse kamar aikinta ne, saidai yau da gobe ne da Ayya take sa ta tana taimaka mata in zata ma Agaishat gyara, wasu mayukan aka kuma shafe mata kan dasu ta d'aure mata shi tsakiyar kanta ta mau da irin robar yaran nan kafin ta saka mata wani ribom k'arami masu fitowa guda goma sha biyu a leda. Kallon kanta tayi a madubi na tsawon lokaci, lallai ashe bak'inta mai kyau ne da nutsuwa sannan fuskarta ma kyawunta ya kai matakin da zata iya birge kowa, ba kwalliya tayi ba sai ma k'yalli da fuskar keyi na man data shafa, amma a haka wani shek'i shek'i ne take yi kamar k'wan da aka k'yank'yashe yanzu yanzu. Gabatowar magrib yasa su Agaishat yin sallah sai ita kad'ai suka bari da bata sallah a zaune, wata matashiya ce ta shigo d'akin suka gaisa ta zauna tunda basu san juna ba, suna idar da sallah ma akan ta suka sak茅 rufuwa har da wacce ta shigowa yanzu ashe mai kwalliya ce, ita kam har dai ta kasa hak'ura cikin harshen tubanci tace ma Ayya "Ayya ni kam shirin me ake min kamar wacce zata je biki?" Murmushi tayi tace "Muma zamu shirya yanzu, akwai taron da zamu je ne da aka gayyaci duk iyalin Wardugu, kuma kema kin zama d'aya daga ciki tunda har ya yarda ki zama k'anwarsa." D'an murmushi kawai tayi ba tace komai ba, kaya Ayya ta bata ta saka wanda Hasheer da kanshi ta umarta da rakiyar War suka siyo su, gaban madubi Ayya ta tsayar da ita tace "Kalli nan mu gani." Kallon kanta tayi da sauri ta waro fararen idonta ta sauke akan ta, sai taga kawai ta zama wata 'yar tsana, da tace bata son kwalliya shine ita kanta hodar da aka shafa mata harda wata walk'iya take fitarwa, gashi ta dace da kalar faatarta ta kwanta tayi luwai luwai, ga wajen dake bayyana idan kayi murmushi ma ya fita da kyau (contour) da wata hoda mai d'aukar ido, caje mata girarta kawai akayi aka daidaita mata zamanta, sai mascara data k'ara fito mata da gashin idonta yayi zarzar dashi, farin lips da kuma maroon d'in jan baki aka shafa mata saiya had'e da leb'enta ya bayar da kalar natural. Doguwar rigar data saka mai hannaye bak'a da kuma k'aramin kallabinta da aka yane mata kanta dashi a zamanance. Murmushi ta saki tana ji kamar ta zauna haka tayi ta kallon kanta, kai ashe ma kwalliya rahama ce kuma tana k'ara maka kyau duk kyanka, rashin lokaci yasa ko kwalli a ido bata damu data saka b芒 a matsayinta na mace, yanzun ma gashi dai ba'a saka mata shi a cikin ido b芒 sai daga k'asa, gashi idonta sun k'ara fari sosai sakamakon (couleur bleu) da aka saka mata. Kiran Safwan ne ya dawo da kallonta k'asan madubin, d'agawa tayi ta d'ora a kunne a nutse tace "Hello." Daga b'angarenshi yace "Wai babbar yarinya ya hakane? Wuri ya cika ke kawai ake jira." Zaro ido tayi ta shiga rarrabasu tana kallon kanta a madubi, wuri ya cika kuma? Ta ya ya? Wata sani anan? Wata gayyata? Maganar Hasheer ta tuna da yace yallab'ai yace zai cika miki wurin taron da 'yan mata da samari. Ajiyar zuciya ta sauke tace "Gani nan tafe." Bata jira me zai ce b芒 ta datse kiran, kallonta Ayya tayi tana murmushi tace "Muje ko." Da mamaki tace "Amma ayya ai ku baku shirya ba?" Murmushi ta mata tace "Karki damu kinji, ku da茂 ku fara yin gaba, zamu sameku acan." Saida ta kalli Agaishat tace "Ni da ita kawai?" Girgiza mata kai tayi tace "A'a, ke da Hasheer." D'asss! Taji gabanta ya fad'i a hankali, k'urawa Ayya ido tayi kamar yanzu ta ganta, bata san me yasa ba sai taji ta kasa musawa, hakan na nufin dan yarda dashi ne? Ko kuma dan tana jin daban a game dashi a zuciyarta? Hannunta da Ayya ta kama yasa ta kallon hannun nata ita ma, fita sukayi daga d'akin Agiashat na fad'in "Fatan nasara trozzo." Juyowa tayi ta kalleta saita rasa me take nufi, suna fara sauka ta matakalar sukayi ido biyu ita dashi. Sak'e tayi baki bud'e ta ci gaba da takowa a hankali har suka sauko, gabanshi Ayya ta tsayar da ita tace "Ga 'yata na baka amana, ku kula min da ita sosai, yanda na baku ita ta dawo min gida haka, kun fahimta?" Tunda y'a tsareta da ido ya kasa d'aukewa sai wani mus mus yake da ido da baki, wani basaraken murmushi ya saki uwa ya ga mai damagaram yace "Ayya 'yarki tayi kyau, nagode Allah da bata yawan kwalliya, da na zama mai kisan kai." Buge bakinshi Ayya tayi tana fad'in "Shiru, malam wuce min kaji." Kallon Faduma yayi da kanta ke k'asa yace "Muje *murmushi na*." Kallon Ayya tayi ta mata alama su tafi ba komai, a hankali ta fara takawa suka nufi k'ofa a tare, saidai yana gabanta kad'an dan haka ta samu damar kallonshi ita ma, a ranta kawai tace "Yayi kyau yau ma." Dole taja ta tsaya a farfajiyar sakamakon ganin War cikin kakinshi da wasu zaratan sojoji uku a gabanshi suna magana, had'e yawu ta fara yi da k'yar tana kallonsu, saida suka gama magana suka rara mishi suka fita, motoci taji sun tashi a k'alla sunfi guda biyar kuma harda moto ma. Juyowa yayi garesu fuskar nan fa yau babu alamar wasa, Hasheer ya kalla yace "Kun gama shirin ne?" D'aga kafad'a yayi yace "Ta gama." Sa茂da ya d'ora k'afarshi gaba yace "Muje." Juyowa yayi ya mata alama da suje, bin bayansu tayi a nutse a hankali har suka fita k'ofar gidan, renge rover ce bak'a wulik Hasheer ya bud'e mata baya, cikin nutsuwa ta shiga ta zauna ya rufe, zagayawa yayi d'aya b'aren ya zauna kusa da ita sai War a gaba tare da wani soja. A hanya banda kallonta babu abinda yake har taji ta fara tsarguwa, cikin rad'a ya matso da kanshi kusanta yace "A gaskiya *Samha* (mai kyau) kishi nake ji sosai." Tarr ta kalleshi ita ma cikin rad'a tace "Saboda me?" Kyab'e baki yayi yace "Zan fad'a miki da zaren aikin nan ya kammala, insha Allahu." Gabanta taji ya fad'i, zai fad'a mata? Me kenen? Yace yana sonta? A'a fa, ba ta son ji gaskiya, duk tsumewa tayi wuri d'aya ta rasa walwalarta har suka isa wurin, duk bud'e k'ofofin sukayi suka fita, saida ta zagayo Wardugu ya kalleta yace "Ke ki shiga ciki duk suna nan, zamu kalli abinda ke wakana a ciki daga waje, karki damu kinji? Ki saki ranki komai ya tafi daidai." Kamar ta zabga da gudu take ji maganar nan da yake mata, da k'yar ta jinjina masa kai alamar to tana so tayi tambayar ta ina zasu kallesu? Amma yanda yau yake g茅n茅ral d'in babu dama, saida ta d'an kama rigar da hannayenta sannan ta fara tafiya, kallonta yake yana jin zuciyarshi sai sake bugawa take. Tana shiga daga ciki ya rintse idonshi ya bud'e yana jan dogon tsaki murya kamar zaiyi kuka yace "Wallahi Wardugu saboda tabbacin daka bani yasa zan barta tayi aikin nan, ina dalili ta shiga cikin 'yan iska maza da mata a haka suka k'are mata kallo." Dafa kafad'arshi War yayi yace "Kayi hak'uri mutumina, nasan ba zaka ji dad'i ba dama, kishin abinda kake so ai halak ne musamman kai jinin larabawa, ai ku kuka yankewa kishi cibiya, akan matanku ku yanki mutum ba komai bane." Ganin ya mayar da abun wasa yasa shi zabgawa a guje yabi bayanta dan hankalinshi ma a kid'ime yake, tana daf da hayewa saman benen taji an rik'o hannunta ya turata jikin bango, a tsorace ta kalleshi amma b芒 tace komai ba, babbar yatsarshi ya saka kan labb'anta ya shiga goge mata kalar nan data shafa. Zata janye fuskarta ya dira mata idonshi da sukayi jajir yana jin ko marinta ta kama fa zaiyi, shi wallahi ko Saudat da take fita da gyale dan ba yanda zaiyi da ita ne, yasha yin maganar amma ta nuna wayewar kenan, amma ba k'aramin haushi yake ji ba musamman ta cab'a ado sosai. Saida ya goge mata shi tass ya kalli k'wayar idonta, cikin muryar dakiya da sark'ewa yace "Batul ki nutsu ki saurareni, a wurin nan samari ne da zan iya kamalta miki su da dokin tseren da aka busawa usur d'in gudu, ko a me? Ko a yaya? Ko a wane lokaci? Ko a wane hali jiran tab'i da birgewa suka jira, ki rufa mana asiri Batul karki bari wani ya miki kallon sha'awa, kada ki bari wani ko wata su had'a jikinsu da naki, idan kuma ba haka ba." Cije leb'e yayi ya matsa baya zai sauka a benen, da sauri ta sauke ajiyar zuciya tace "Me zai faru?" Juyowa yayi ya kalleta ido da ido yace "Duk zamu ruguntsuma muje kiyama." Sororo tayi tana kallon al'ajabi har ya gama sauka ya fita, juyawa tayi ta k'arasa hayewa ta shiga wurin, wata irin shewa wasu 'yan mata da bata san su ba suka saka suna fad'in "Yeeee! Babbar yarinya ta faso, ga Le茂la nan ta shigo." Duk kowa nutsuwa yayi ya maida hankalinshi gareta, kusanta 'yan matan suka dawo da take kallonsu da son sanin yanda akayi suka kama sunanta na k'arya da Safwan kawai ta fad'a ma, Safwan ma dake cikin wasu fitinannun k'ananan kaya matsowa yayi, ita kam da take k'ara kallon 'yan matan da mamakin shigarsu kamar zasu fito tsirara, a hankali ta kalleshi ta kashe masa ido tace "Alaji nagode sosai, wuri yayi kyau fa." Shafa kanshi yayi yace "B芒 komai ai, kin had'u fa sosai." Murmushi tayi tace "Nagode." Kallon wata wacce tafi zak'ewa yayi yace "Arkiya ku rakata wajen zamanta." Kallon yarinyar daya kira da Arkiya tayi, kenan inta fahimtar k'aryarta ce yallab'ai War ya mayar da ita gaskiya ta hanyar gayyato mata duk wanda ta ambata a labarin, suna cikin tafiya a nutse tana satar kallon kowace kusurwa tana so taga ko kamarori (cam茅ras) suka lak'a ne amma babb abinda ta gani har suka k'arasa. Komai babu abinda ba'a tanada a wurin ba har cake d'in da akayi babba mai sunanta a rubuce, Faduma yau taga abinda yafi k'arfinta, tunda take a rayuwa bata tab'a riskar kanta a irin wannan rayuwa ba, taso kwafsawa sosai sai Arkiya ce ta nuna mata su fa aikin yallab'ai g茅n茅ral suke, k'arar wak'ar dake tashi samari da 'yan mata ana rawa saida ya saka mata ciwon kai, hayaniya saida ta fara saka mata ciwon kai taji so take ta bar wurin kawai. Misalin 12:00 na dare wurin ya sake hautsinewa da warin hayak'in sigari da shisha wata ma a 'yar farar takarda zaka ga mutum ya nad'eta yana sha, hakan yasa rashin sabo saita fara jin ita kanta kamar tasha wani abu, a hankali a hankali ta fara ganin komai na juya mata, gashi tana gani da idonta amma bibbiyu take ganin kowa gifta mata, wani irin zama tayi akan kujerar kamar zatayi kwance, Safwan ne ya k'araso wanda suka gama waya da Tahir yace yaso zuwa Aji ne ya patattake shi da masifa yace babu inda zai je sabida halin da suke ciki, yana zuwa kusanta ya zauna cikin salon iskanci ya d'ora hannunshi kan cinyarta yace "Ya dai b茅b茅? Na kawo miki lemu ne?" Murmushi tayi sai kuma ta jinjina masa kai, mik'ewa yayi a ranshi yana da tabbacin rashin sabo ne yasa hayak'in wurin ya fara droguenta, k'arasawa kawai zaiyi a sauk'ak'e, yana zuwa lemu ya zubo a kofi ya saka wata k'aramar k'waya fara ya kawo mata. A lokacin da wayarta a hannu suna magana da Aminu bata ma san me take fad'a masa ba bare tasan shi me yake fad'a, shi kuma hankalinshi duk ya tashi jin kid'a a inda Faduma take a wannan daren kuma a wani yanayi na daban, sam bai zargeta b芒 saima tunanin ko aikin ne ya jawota zuwa wannan matakin? In kuwa hakane yayi kuskure babba daya turo ta, sai kawai yaji ba zai hak'ura ba gwara ya gane ma idonsa komai, tunda yaji ta saki wayar wani ya mata magana da cewa "Ga abun sha." Ya mik'e ya fara tarkata nashi ya nashi dan barin gari ya kamashi dole shima da asubar fari. Kifa kai tayi ta shanye abun nan tass, yana ganin haka yayi murmushi ya lashe leb'e, mik'a mata hannu yayi alamar ta taso, ba tare da sanin me take yi ba ta dafe kai da hannu d'aya shi kuma ta bashi hannu ya kamata ta mik'e, tafiya suka fara saida ya shiga da ita wata kusurwa k'arama da babu kowa a wurin, had'ata yayi da bango ya d'ora goshinshi kan nata kamar zasu had'a baki yace "To ya b茅b茅? Sumbata zaki bani." D'an kawar da kanta tayi gefe da sauri ya juyo da kanta, sunkuyawa yayi yana neman lalubo bakinta dan y'a had'e da nashi, da k'arfi ta tureshi yayi baya kamar zai fad'i, a hassale ya dawo gareta dan shima saida ya shak'i coca茂ne, duka hannayenta ya rik'e ya had'a da bango yana son dole saiya kai bakinshi a nata, k'ara ta saki lokaci d'aya kuma taji an saki hannayenta sai fad'uwar abu da taji a k'asa ko tace fad'uwar mutum. A hankali ta bud'a lumsasun idonta sai taga Safwan kwance a mugun yanayin da ko ita bata tsamlanin halin da zai shiga y'a kai wannan, k'asa a yashe bakinshi zuwa hanci sai fitar da jini suke, gashi kuma har an d'aure hannayenshi da ankwa, War ne ya mik'ar dashi tsaye ya kama kunnenshi ya murd'e kamar zai cire yana fad'in "Kune ke lala..." Bai gama fad'a ba Hasheer da wani sojan ya rik'eshi tun sanda ya had'awa Safwan jini da majina ya sake kaiwa Safwan wani naushi a fuska har saida y'a kubce a hannun War ya fad'i k'asa, da k'arfi cikin tafasar zuciya ya bi kanshi ya danne mishi wuya da k'afa da niyyar kawai ko shi ko kuma shi. Cikin wata siririyar muryar rangaji da fitar hayyaci Faduma tace "Ya isa haka, kar kuyi kisan kai a gabana, un..ba haka duk saina had'a ku da g茅n茅ral, dan kuwa...ni d'in k'anwarsa ce, k'anwarsa ce ni, uwarmu d'aya, kuma ubanmu da..." Fad'uwa taje yi da sauri ya d'auketa a jikinshi cak yana kallon fuskarta, bai tsaya bin ta kowa ba ya fice da ita a hannunshi, duk gurin ya hargitse da iface iface saboda tuni an kama masu shaye shayen, masu k'aramin laifi kuma sojawan nan sun kewayesu sun sakasu tsallen kwad'i saboda ja musu kunne, wasu matasan kuma da aka samu suna lalubar juna kuma mata dasu aka saka su marin junansu. Kai tsaye ya wuce mota da ita ya kwantar da ita ya karb'i makullin a hannun sojan ya bar wurin, saida yayi tafiya mai nisa ya tsaya a inda babu kowa, dukan sitiyarin motar ya kama yi kamar zai ciji motar ko ita ta masa laifi, saida ya gaji dan kanshi ya dakata ya juya ya kalleta sai motsa baki take, juyowa y'a sak茅 yi ya sa yatsa ya share k'wallar data taho mishi ta gefen ido ya ci gaba, gidan Ayya ya kaita wacce hankalinta ya tashi ganin ya shigo d'auke da ita kamar gawa. *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 21:40 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _55_ Shinfid'eta yayi kan doguwar kujera Ayya tayi saurin nufa wajen fridge dan kawo ruwa, kallabinta daya warware yasa hannu y'a cire mata ya aje gefe, kallon fuskarta yake kamar zai had'eta, so yake ta farka ya fad'a mata shi fa ba zai iya jurar lamarin nan ba. Ruwan da Ayya ta mik'o mishi jikinta na b'ari yasa shi amsa, a hankali ya bud'e ya zuba a hannun, shafa mata yayi a fuska hakan yasa ta juyar da kanta ta bud'a baki tace "Kai...nifa..." Rufe mata baki yayi dan yasan sambatu ne kawai na shirme zai fito a bakinta har zuwa sanda zata dawo hayyacinta, cikin nutsuwa ya tallabo hannunta hagu ya rik'e sosai yana kallon fuskarta, cikin yanayin rauni sosai da kuma son dakewa da juriya murya na rawa yace "Ki tashi Zahra, ki tashi na fad'a miki abinda ke raina ko na huta da dakon kayan nan masu nauyin dake neman kasheni, daf nake da durk'ushewa saboda ka茂na ba zai iya d'auka ba, Faduma bansan wane irin kamu kika wa zuciyata ba? Sam babu sauk'i a al'amarin, bansan taya na zama lusari kuma mai gaggawa akan lamarin daya shafeki ba, idan abun ke ya shafa kai tsaye nakan kasa nutsuwa bare nayi tunanin wani abu, ban cika hayaniya da magana ba, amma fa hakan kafin na had'u dake ne kuma idan ba kya gabana, Faduma kullum fargaba na shine karna fad'i sirrin zuciyata kuma kice a'a ba kya so na, ina tabbatar miki bansan halin da zan shiga ba, zan iya rantsewa ban tab'a jin mugun son wani abu a duniya ba kamar yanda nake jinki, Faduma ki farka na kalli fuskarki na fad'a miki cewa *ina sonki*, ina sonki kuma zan ci gaba da sonki har k'arshen rayuwata, Faduma da wani zai ce min asiri kika min dan na so ki saina yarda, domin kuwa yanda soyayyarki ta shiga zuciyata kuma take sake gayraya da jinin jikina abun yana neman halakani, dan Allah ki tausaya min, ki sassauta min Faduma ko na dak'ik'a d'aya ne." Cike da tausayawa Ayya ta zauna kusa da kan Faduma ta shafa kanta tana kallonshi tace "Kayi hak'uri kaji, na fahimci irin son da kake mata, amma me ya faru? Me ya lalata mana shirinmu haka?" Wata ajiyar zuciya ya sauke yana kallon Faduma yace "Ummuna kamar mahaukaci nake komawa akan lamarin yarinyar nan, idan abu ya shafeta sai naji na zabura na tare kamar Izzadeen ko Sharfudeen ne na gani zasu shiga had'ari, bansan ya zanyi da raina ba." Saida ya sauke numfashi yace "Sun bugar da ita da kalar iskancinku, a bige take yanzu haka, ba'a hayyacinta take ba." Ita ma ajiyar zuciya ta sauke tace "Hasbunallahu wani'imal wakil, Allah sarki baiwar Allah, wannan aiki da had'ari yake." Kallon Faduma tayi tace "Amma ka tabbatar babu wata matsala? Ko zamu kaita asibiti ne?" Girgiza kai yayi yace "Insha Allahu zata farka, babu abinda zai faru, saidai ba lallai ta iya tuna abinda ya faru ba." Jinjina kai tayi tace "To yanzu anan zaku barta ta kwana ko?" Jinjina kai yayi yace "Ta zauna anan Ummu, nima anan zan kwana." Da farin ciki tace "To shikenan, zata iya tashi ne na rakata d'akina? Dan zan so ta kwana dani." Sunkuyar da kanshi yayi yace "Ba zan iya d'aukarta ba Ummu, wanda nayi ma acan dan babu yanda zanyi ne, ku jaraba tashinta ku gani." Mik'ewa Ayya tayi ta fara daddab'ata, cikin wani hargagi na fitar hayyaci da magana irin ta 'yan maye tace "Ku daina tab'a ni na fad'a muku, inba haka ba g茅n茅ral zai...shiga tsakaninmu, ban shiga harkar kowa ba dan haka karku shiga tawa, inba haka ba kuma..tom na fad'a muku...." 馃槀馃槀馃槀 *(G茅n茅ral ne a bakin)* Kaamata tayi da k'yar ta mik'e tsaye sai lauyewa take tana son komawa ta kwanta, shi dai zuba mata ido yayi yana kallo har tana neman rikito masa akai ya matsa baya, dan in haka ta faru wanka ne zai hau kansa na farilla, da k'yar da sud'in goshi Ayya ta shigar da ita d'akin sai cijewa take tana maganganu tana fad'in ta barta ta kwanta, suna shiga d'akin kan gado ta fara da k'arfi ruf da ciki, ajiyar zuciya Ayya ta sauke cike da tausayinta ta sunkuya ta cire mata d'amarar takalmin dake k'afarta masu d'an tsayi kad'an ta aje gefe, ribom d'in kanta ta cire mata shima ta aje kafin taja mata bargo ta lullub'eta sannan ta kunna mata masuburbud'ar sanyi馃榿 (ac) ta fita. Kai tsaye gida ya so ya wuce saboda yasan Agaishat na can na jiranshi, saidai kuma tunanin halin da amininsa ya bar wurin nan shi yafi tsaya masa a rai, dan haka ya karkata akalar motar zuwa gidan Ayya dan tabbatarwa kanshi suna cikin k'oshin lafiya daga shi har yarinyar ta bakinshi, dan a ganinshi yanzu kam kamar shine silar komai, tunda ita ta gama nata aikin harta wuce wannan babin, shine yace ta ci gaba saboda yana son sanin ta yanda ake shigo da kayan nan k'asar nan, yasan kuma ta hanyar yaran zai samu masaniyar da a sannu zata dangana shi da inda yake buk'ata, yana so ko da aikin nan zai zama shine na k'arshe a gareshi ya tabbatar dai yayi nasara. Anan ya sameshi falon zaune k'asan carpet ya had'a gwiwar hannayenshi da cinyarshi kanshi kuma k'asa, duk da shima fa a d'ane yake na darun da suka sha yanzu da yaran nan, zuciyarshi a wuya take sosai, amma tunda yana ganin kamar laifinshi ne kuma bak'onshi sai ya shigo da fara'a cike da zolaya yana fad'in "Yaro ashe nan ka taho, ina Faduma?" D'ago kai yayi ya kalleshi cikin nutsuwa ya nuna masa d'akin Ayya, cikin sanyin jiki ya matsa kusanshi ya zauna daf da dashi ya dafa kafad'arshi yace "Kayi hak'uri kaji, ka kwantar da hankalinka zata farka, buguwa ne kawai tayi kuma kaga bata saba ba, amma insha Allahu zuwa safe zata tashi a Faduman daka sani." Ba yabo ba fallasa yace "Allah yasa." Jinjina kai yayi yace "Tashi mu tafi gida dare yayi." Girgiza kai yayi yace "Ka bani makullin waccen d'akin zan zauna anan." Da mamaki ya kalleshi yace "Ban gane ba? Hasheer gidan Ayya zaka kwana?" Jinjina kai yayi yace "Eh." Girgiza kai yayi yace "Ba zai yiwu ba, wurina ka zo Hasheer kuma kasan gobe da misalin k'arfe tara na safe ne had'uwarka da tsohon shugaban k'asa, sannan akwai shirye shirye a gabanmu dayawa na bud'e kampanin nan zuwa k'arfe hud'u na yamma ko? Dan haka tashi mu tafi." A sauk'ak'e kuma a nutse ya d'aga labb'enshi da k'yar yace "Wallahi anan zan kwana." Dafe k'ugu War yayi irin zaiyi tijarar nan da niyyar ko a kai ne zai d'aukeshi sai kuma Ayya ta fito daga d'akin, kallon tuhuma ta bisu dashi kafin ta kalli War tace "Wannan tsayuwar rashin mutumcin fa? Halan halin ne zaku siyar a daren nan?" Nuna Hasheer yayi yace "Ayya kinji fa wai nan zai kwana, bayan kuma na bashi hak'uri kuma akwai inda zamu je da safiyar goben." Da mamaki tace "Au! Nan da zai kwana yankeshi za'ayi? Tunda nan yake so ya kwana ka barshi mana, ka tafi kai da safe sai ka zo kuje koma ina ne." Kallon Hasheer yayi da kanshi ke sadde kamar baisan sunayi ba, k'wafa yayi ya ciro makullan d'akin ya jefa mishi a jiki ya juya ya fita, cikin d'aga murya Ayya tace "War dama da takalmi ka shigo min d'aki?" Ganin bai kulata ba y'a fita a ranta tace "Ran 'yan maza ya sosu kenan? Zaku shirya zuwa safen." A zahiri kuma cewa tayi "Zan gamu da ubanka ne yaro." Dafa kan Hasheer tayi tace "Tashi kaje ka kwanta kaji, ita ma baccinta take a nutse, zan kula da ita." D'agowa yayi tare da mik'ewa ya kalleta yace "Nagode Ummu." Murmushi ta masa ta bishi da kallo har ya fita, girgiza kai tayi cike da tausayinshi tare da tuna wayarta da Umma d'azu bayan fitarsu, anan take fad'a mata ai yanzu matsalar da yake fuskanta ma harda d'an uwanshi da suke uba d'aya, juyawa tayi ta koma d'aki ita ma dan shirin bacci ta kwanta, saida ta gama tsaf ta kwanta gefen Faduma, sauke ajiyar zuciya tayi dan hakan saiya k'ara mata k'aunar son 'ya mace da jin ina ma ace 'yarta ce Faduma, data damk'a hannunta ga mutum mai kamala karamci da dattako da kuma d'auke kai ga al'amura, da tunane tunanen nan har bacci ita ma yayi gaba da ita. *11:30* Shigowarshi ta biyar kenan bayan dawowarsu daga wajen tsohon shugaban k'asa, duk da yaji dad'i sosai akan samun abinda yaje nema, kuma yayi farin ciki da irin taimakon da dattijon ya masa, saidai akwai wani abu dake damunsa daya kasa barinshi ya nuna hakan, yanzu ma yana shigowa Ayya ya samu ta fito daga madafa, cike da damuwa yace "Ayya har yanzu bacci take?" Jinjina kai tayi tace "Bacci take Hasheer, ina ga ta bugu sosai ne fa, kuma ni ban tasheta ba ko da asuba dan naga ba sallah take ba." A marairaice yace "Ayya ko zaki bani izinin na shiga na gani dan Allah? Idan kuma ba lafiya ba fa mu muna tunanin bacci take? Za'a samu matsala babba." Da hannu ta masa nuni tare da cewa "Bismillah." Da sauri ya nufi d'akin ya tura k'ofar a hankali da siririyar sallama a bakinshi, idonshi akan gadon sai kuma ya hangota kwance tayi rairai ta juyar da kanta sa茂 gashinta da duk ya barbaje, saidai kuma lullub'e rabin jikinta yake da bargo ruf, tsaye yayi yana kallon fuskarta da har yanzu ke d'auke da kwalliyar nan idan ka cire jan bakin daya goge mata, sanyayyan numfashi ya sauke tare d脿 zura hannu aljihu ya ciro wayarta ya aje mata gefenta, dan tunda safe da War ya zo ya bashi ita sakamakon tattare komai da sukayi sun samu mamallakin kowace waya amma banda wannan, shiyasa yayi tunanin ta Faduma ce kuma kam ta ta ce. Juyawa yayi ya fita dan Wardugu ma na waje yana jiranshi zasu tafi wani wuri, Ayya na ganin fitowarshi tace "Tana lafiya?" Cikin sanyin jiki yace "Tana nan dai yanda kika barota Ummu, amma idan muka dawo bata farka ba kawai zanje na d'auko likita ya dubata." Jinjina kai tayi tace "Na goyi bayan hakan." Nufa hanyar fita yayi tace "A dawo lafiya." "Allah yasa." Ya fad'a yana ficewa. *11:41* A hankali ta fara farkawa tana bud'e ido da yin mik'a tare da salati ga Annabi, a gajiye ta tashi zaune tana kallon d'akin, rashin sanin na waye yasa ta tambayar kanta "Nan kuma ina ne?" Babu hoton mutum bare ta d'auki haske, saidai kawai tasan d'akin mace ne macen ma mai shegiyar tsafta da son ado, kuma da alama fad'uwa ce ta zo daidai da zama, son adonta ne ya had'u da masu gidan rana wato kud'i, dan tsarin d'akin da kayan cikinshi had'e da k'amshin da yake fitarwa kawai ya ishi bawa yayi zamansa anan ya rayu, dafe kanta tayi tana son tunano me ya faru da ita? Abinda ta iya tunawa kawai shine jiya wajen shagalin nan, daga zuwanta wurin har sanda Aminu ya kirata ta d'aga, to amma me ta fad'a masa wace magana sukayi? Wannan kuma bata sani ba. D'an tsaki tayi ta d'auke hannunta daga kanta, cikin kalle kallenta idonta suka sauka kan agogo, ganin wannan lokacin sai tayi tunanin agogon ce bata da lokaci tunda dai ta tabbatar ba dare bane, jujjuyawa tayi dan a saninta tana bacci ne da wayarta a gefenta, cikin sa'a ta lalubota ta danna dan duba lokaci. Zaro ido tayi gaba d'aya da dafe k'irjinta, a tsiyace ta yaye bargon ta sauka daga kan gadon tana fad'in "Ni Faduma me ya sameni haka?" Wayarta ta sake dubawa sai tarin kiran da bata d'aga ba na Aminu da Dada da Ayyarta har da ma yaya Barka, ga likitan ne daya kamata ta koma dan karb'o sakamakon nan, tunda yau kawai gareta gobe zasu zauna kotu, bud'e tsaron wayar tayi ta fara neman lambar sai kuma ta tuna ai jiya Hasheer bai bari ta saka ba, to amma ai ta rik'e lambobin illa guda biyu kawai da bata fahimci wacece a gaba ba. Abun mamaki saita kasa tuna komai akan ta bare ta d'ora a wayar ta kira, hakan yasa kawai taji ba tada zab'i daya wuce taje asibitin ta ganshi ko da zata nemi alfarmar a had'ata dashi ne, da sauri ta fita daga d'akin saidai babu kowa a falo, kuma bata ji motsin kowa ba, saidai ta fahimci gidan Ayyar g茅n茅ral ne ta kwana kenan, kallabin rigar jikinta ta hanga saman kujera a aje, da sauri ta d'auka ta aza saman kanta ta juya ta shiga d'akin da aka mata gyara jiya, nan ta samu jakarta amma babu kowa, kawai tana fitowa ta fita bata tsaya komai ba, k'ofar d'akin ta samu takalmin roba da Ayya ke ajewa saboda idan anyi bak'i zasuyi alwala, tana sakawa kam cas a k'afarta saita kalli fuskarta a madubin k'ofar shiga falon, da sauri ta k'arasa gaban panpon dake farfajiyar ta kunna ruwa ta wanke fuskarta kafin ta fita, kurtun dake tsaron k'ofar ma bai hanata ba tunda fita ne zatayi ba shigowa ba. Kallabinta tasa ta goge ruwan fuskarta ta tari taxi tace a akaita asibiti. Sam bata wahala wanen ganin likitan ba dan ma ta sameshi yana kan aiki, nan ya bata r茅sulte d'in tare da mata bayanan da suka kamata, saidai abinda ya lura ita kanta yau ba a daidai take ba, baya ce tana shaye shaye ba dan idonta da hannayenta da yanda take magana zuwa fatar jikinta basu nuna ba, amma dai yau maganarta ta zance da kuma kallonta, haka ta mishi sallama ta baro ofishin duk da ya so magana da ita. Tana fita ta samu wata taxi ta shiga tana saka takardun a cikin jakarta, basuyi nisa ba wani matashi ya tsayar da taxin shima ya fad'i unguwar da za'a aje shi, gaba ya zauna ita kuma tana baya tana ta k'ok'arin kiran Ayyarta amma kiran baya shiga saboda matsalar sadarwa. Suna shiga wani layin unguwar shiru babu mutane kawai yace anan zai sauka, taxin na tsayawa wasu matasa su biyar suka fito daga malafarsu suka zagaye taxin, bud'e inda Faduma ke zaune wani yayi ya finciko hannunta yana fad'in "Fito nan, fitsararriya marar kunya." K'ara tayi tare da fad'uwa kwance wayarta da jakarta duk suka fad'i, da sauri ta juyo tana kallonsu a tsorace, mai taxin ne ya fito yana fad'in "Malam ya dai? Me tai muku?" Wuk'a d'aya daga ciki ya zaro yace "Babu ruwanka, ka kama gabanka ko kuma m没 had'a da kai, matsalarmu da ita babba ce." Yanda duk suka zaburo mishi yasa shi shiga taxinshi ya bar wurin, dan k'aramin aiki ne garesu su parka cikinshi, ganin haka da sauri ita ma ta jawo wayarta da jakarta ta rungume ta mik'e tsaye, baya baya tayi da niyyar ta zuba a guje amma wanda ke gefenta ya tunkud'ota gaba da k'arfi, wanda suka shiga taxin tare ne ya rik'o hannunta da k'arfi yana fad'in "Ina shaidan suke?" A dak'ile ta kalleshi tace "Wace shaida kuma? Su waye ku?" A tsawace ya sake fad'in "Ina shaidun nace? Ke ina wasa dake ne? Bani da imani da kike gani na nan, zaki tattaro duk shaidar da kika had'a a game da matsalar data kawoni nan ki bani, idan ba haka b芒 zan kasheki a wurin nan kuma na kashe banza." Saida ta mishi kallon raini ta fizge hannunta da karfi tace "Ka kashenin mana ka gani, kuma ba zan bayar ba." Da hannun nan nasa mai k'irar rodi bayan hegen tauri ya d'aga shi da k'arfinshi ya galla mata mari, wani suuuuuuu! Taji a cikin kanta tare da jin kamar ana mata kuwa, da k'yar ta d'aga idonta ta bud'e a lokacin ta gane ashe a k'asa ma take kwance ruf da ciki tsabar azaba. A tsiyace ya fizgo jakarta dake kafad'arta ya d'auki wayarta ma, kallon sauran yayi yace "Ku muje kawai, nasan a cikin jakar nan zamu samu komai." Wani daga ciki ne ya sunkuya yana fad'in "Kai wannan fa abun wuyan nata zinare fa." Wani daga ciki ne yace "Uban wa ya fad'a maka?" Saida ya kai hannunshi kan wuyanta ya damk'o sark'ar da Ayya ta saka mata jiya yace "Kai baaba bar wannan maganar Allah, ina gane abubuwa fa." Ya jawo sark'ar kenan daga wuyan suka ji saukar wani marin da kai kasan ko marin aljani saidai haka, dab'as ya fad'in yana sakin sark'ar ya dafe kumcinshi da hannu bibbiyu yana fad'in "Wayyo kunne na, kunne na zai tsinke, wayyo Allah." Da sauri ta kalli Wardugu dake gabanta ya turmushe yara biyu a k'afafunshi ya taushe ya hanasu sukuni sa茂 bille bille suke, a k'ufule ya murd'ewa d'aya kunne yana fad'in "Uban wa ya turoku?" Tauuuu! Suka ji k'arar harbin bindiga, kad'an ya rage a kafad'ar Faduma wannan yasa ta dagewa iya k'arfinta ta saki k'ara tana rufe kunnayenta duka biyu. A razane sosai hankali a tsantsar tashe ya kalli yaron da yayi harbin, sake murd'e mishi hannaye yayi hawaye sharrr a idonshi abinda zai iya cewa rasuwar mahaifinshi ce kawai tasa shi zubar hawaye, had'e hannayen yaron yayi wuri d'aya baki na rawa yace "Kkkka...harbeta? Da alburushin nan ya sameta fa??? Kasheni zakayi?" Hannunshi ya zura a k'ugunshi bayan rigarshi ya ciro bindigarshi, bai tsaya jiran komai ba ya danna kunamar bindigar a hannun da yaron yayi harbi, da gudu Wardugu ya k'arasa ya rik'eshi tare da rik'e bindigar yana fad'in "Hasheer baka da hankali ne? Harbi fa kayi?" Yaron da tuni zugi yasa shi fad'uwa sumamme ya kalla, sauran kam na ganin haka wani daga ciki ne yace "Kai! G茅n茅ral ne fa." Ai da gudu duk suka watse kowa na yin hanyarshi, amma tsabar jaraba saida Wardugu ya k'urewa d'aya daga ciki gudu ya kamoshi, d'aurin goro ya masa ya watsashi a but d'in mota dan dole yasan waya turo su. Da sauri ya nufo wurinta wacce tayi suman zaune tunda taga ya ciro bindiga, take komai nata ya tsaya ta sshiga tunanin me ya had'ashi da ita? Bayan shi ba police ba kuma ba soldat ba, sannan ba wani jami'i da doka ta yarjewa rik'e makami dan kare kansa ba, *waye shi?* ta ambata a zuciyarta kawai. Kallon tsaf ya mata yana share hawayen yace "Batul kina lafiya? Babu abinda ya sameki ko?" K'uri ta masa da ido tana kallo sai hawaye da taji suna mata zarya, lura kamar bata hayyacinta yasa shi fad'in "Me yasa kika fito Batul? Akan me zaki min haka? Shin ban fad'a miki akwai had'ari fitarki ke kad'ai ba?" Ganin bata ko motsawa yasa shi zura hannu zai tab'ata dan ganin tana raye, a zabure ta ja baya tana fashewa da kuka da fad'in "Karka tab'a ni, karka sake tab'ani." Mik'ewa tayi tsaye tana ja baya a tsorace tana kallonshi, tsaye yayi yana binta da fad'in "Batul tsaya, ki nutsu ki dawo hankalinki, kina buk'at.." Hannu ta d'aga masa tace "Shiru!" Nuna masa yaron tayi tace "Hasheer harbi fa kayi? Ka kashe mutum? Dama..." Sai kuma tayi shiru. Da mamaki duk suka kalleta shi da Wardugu daya saka sumammen nan a mota dan kaishi asibiti, a kkid'ime cikin fitar hayyaci tana rera kuka tace _"Hasheer waye kai? Me ya had'a ka da makami? Ko kasan yanda nake kallonka a idona kuwa? Shin ka tab'a tunanin me nake tunani a game da kai? Ni lauya ce da aikina yana had'ani da mutane iri iri, na sani kuma kullum a shirye nake da fuskantar kowane irin k'alubale daga wajen duk wanda yake jin haushina, daga lokacin dana fara jin zuciyata ta fara shak'uwa da kai saina fara tunanin kaine wanda ya dace dani, a hankali nake jin kamar nace *ina sonka*, saboda idan raina ya b'ace kaine ke sakani dariya da kawar da b'acin raina, na d'auka baka san tashin hankali ba a rayuwarka, amma sai yanzu da nayi nisa a tunanin rayuwa da kai, sai na ganka da makami mai had'ari, me yasa? Me yasa Hasheer?"_ Fashewa ta sake yi da kuka ta juya da gudu ta k'arasa kusa da Wardugu dake jikin mota yana murmushi, cikin kuka tace "Dan Allah yallab'ai ka kaini wajen Ayyarka, ina so nayi kuka harna gaji saboda na rasa abinda nake so." Bud'e motar tayi ta shiga baya ta zauna tana duk'ar da kanta, kasa motsawa yayi daga wurin sai kallonsu da yake, War ne ya kanne masa ido kafin ya shiga ya tayar da motar suka bar wurin yana tsaye, saida suka b'ace ya sauke ajiyar zuciya, juyawa yayi ya d'auki jakarta wayarta da sark'ar da yaron ya saki, rataya jakar yayi a kafad'a sam b芒 tare daya sani ba ma, kasa tsayar da taxi yayi haka ya dinga tafiya a k'asa a hankali kamar zararre yana murmushi yana fad'in "Ita ma tana jin abinda nake ji dama? Ashe tana tunanin yin rayuwar aure dani?" Asibiti war ya fara biyawa ya aje yaron nan, sanin waye shi yasa ba'a tsaya wani waya mutu wa ya taso b芒, tunda yace kawai sun kawo masa hari ne shi kuma ya harbeshi shikenan aka wuce wajen, saida aka bashi duk kulawar data dace War ya nemi ganinshi, da sauri Faduma ta mik'e tace "Nima zan je?" D'an tab'e baki yayi ya juya ya tafi, bin bayanshi tayi tana ta sharar hawaye dayawa nata kallonta, wasu na tunanin ma ko ita ce amaryar g茅n茅ral d'in tunda sun ganta bak'a ita ma. *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 21:40 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _56_ Yaron na kwance suka shiga, lokaci k'ank'ane harya zagbe ya fita hayyacinshi, duka zagayawa sukayi ta b'angaren damanshi suka tsaya, fuskar nan a tamke War ya kalleshi yace "Wa ya turoku?" K'yabta ido yayi kamar zai kwamtsa ihu yace "Kayi hak'uri yallab'ai ka yafe min, nima ban tab'a ganinshi ba sunanshi kawai nake ji." A take yace "Me ye sunan?" Cikin rawar murya yace "Sunanshi Aji, ni wallahi bansan komai ba, umarni kawai yake bawa abokinmu ta waya saimu tayashi aikin." Jinjina kai yayi yace "Ina zan samu abokin naka?" Girgiza kai yayi yace "Yanzu bansan inda zaka sameshi yallab'ai, baya zama wuri d'aya." Nan ma jinjina kai yayi ya matsa daf dashi yasa hannu aljihunshi, lalubawa yayi ya ciro duk abinda ke ciki, sigari ce kare biyu sai tabar wiwi a farar takarda, sai ashana da abun goge kunne, d'aya aljihun ya saka hannu ya ciro kayan ciki, k'aramar waya ce sai plaket na wani magani, dubawa Wardugu yayi da kyau ya kalleshi yace "Dashi kuke anfani kuna fad'awa duk wacce ta tarbi gabanku ko?" Girgiza kai yayi yana nuna mishi hannun mai ciwo yace "Wallahi yallab'ai ba haka bane." Faduma dake kallonsu tana fahimtar komai hannu ta kai zata karb'i maganin, rik'ewa yayi ita ma kuma ta rik'e ya k'i sakar mata, kallonshi tayi tace "Zan gani yallab'ai." Lumshe ido yayi ya girgiza kai alamar a'a, dan shi dai a k'anwarsa yake kallonta, kunya ma yake ji taga maganin nan dan yasan saita tambayi anfaninsa, shi kuma b芒 zai iya fada ba, sakar masa tayi ta kalli yaron tace "Maganin miye?" Kallon War yayi hakan yasa bai bata amsa ba, sake kallon War tayi tace "Yallab'ai na miye?" Cike da k'aguwa ya kalleta yace "Maganin nan da zaran kayi anfani dashi zaka d'imauce ka fita hayyacinka, duk macen daka samu zakayi k'ok'arin sauke sha'awarka akanta." Shiru tayi tana tunanin abinda Tagur ya fada mata a ranar, da sauri ta kalli War tace "Yallab'ai dame ake anfani dashi?" Ba tare daya kalleta ba yace "Akwai na ci da abinci, amma wannan a madara ko shayi ne." Darammm! Taji gabanta ya sake fad'uwa, hakan na nufin dashi yayi anfai? Ko kuma wani ya saka mishi bai sani ba? Lallai tana buk'atar sanin haka, da sauri ta juya ta fita hakan yasa War juyawa da sauri ya fita, dan har yanzu ba daidai take ba dole su saka ido akanta sosai. Gadan gadan ta nufi motar ta bud'e Allah yasa ya hangeta ya bud'e mata daga masarrafin dake hannunshi, shiga tayi ta zauna tana ta jijjiga yatsunta da bubbuga k'afafunta tana motsa bakinta, kamar daga sama taji k'arar harbin nan hakan ya tilasta mata saurin dafe kunnuwanta ta saki k'ara da k'arfinta. Da sauri War ya k'arasa yana kallonta, ajiyar zuciya ya sauke dan shi yafi kowa sanin matsalar nan, abun ya zo mata bazata kuma anfitarma wani jini dole ta firgita. Tunda suka fara tafiya War ya ciro bindigogin biyu ya aje cikin mota, dan ita kanta bindigar da yaron yayi harbi da ita saiya san ta ina ta fito? Maganar da yaji Faduma nayi ne yasa shi d'an juyuwa, amma sai yaga ita kad'ai take magana kamar har yanzu a gigice take, kuma ba zaiyi mamaki ba dan k'arar harbin da akayi kawai ya isa ya tunzurata ya gigita mata k'wak'walwa, d'auke kanshi yayi suka ci gaba da tafiya har suka isa gidan. Yana tsayawa k'ofar gidan ta fito ta shiga kamar dai ba Faduma ba kamar wacce akayi yak'i a gabanta, tana shigowa falon Ayya hankalinta tashe dan tunda suka shigo Hasheer ya tambayi ta tashi? Da tace a'a fa shine ya shiga d'akin dan tashinta amma bata nan, hankali tashe suka tambayi mai gadi ya fad'a musu ta dai shiga taxi, a gigice yace su tafi asibiti dan nan kawai tunaninshi ya fara bashi, suna zuwa kuma likita yace ta bar nan dan haka suka fito, cikin sa'a ne fa War yace bari suyi kewaye ta hanyar nan sai su tare duk taxin da suka gani za'a sameta anan. Tana ganin shigowarta tayi saurin rik'o hannunta tana fad'in "Alhamdulillah, Allah nagode maka, Faduma daga ina kike?" Kallonta tayi tsam ido cikin ido kamar yanzu ta fara ganinta, sai kuma ta ruk'umk'umeta ta fashe da kuka a harshen tubanci tana fad'in "Ayya Hasheer ne, ya kashe wani da bindiga, Ayya shima kasheshi za'ayi a dokance, Ayya karsu mishi komai dan Allah, kice musu bashi bane." Dafa bayanta tayi tana mamakin kalamanta, shigowar Wardugu yasa ta kallonshi daga nan tace "Me ya faru Wardugu?" A tak'aice ya fad'a mata abinda ya faru, yana direwa da sauri Faduma ta d'ago tace "Eh Ayya harbi fa yayi, Ayya ya kashe wani kuma akai na ne, Ayya bana so shima a kashe shi." Cikin nutsuwa ta jata zuwa kujera ta zaunar da ita, zata nufi fridge dan kawo mata ruwa ta rik'e hannunta gam tace "Ayya me yasa yayi kisan kai? Me yasa ya kashe shi?" Wardugu ne ya matso daf da ita ya durk'usa yana kallon fuskarta yace "Faduma, bai mutu ba, ba tare dake muka kaishi asibiti ba? Kuma gashi har mun samu bayanai daga gareshi ma, ko kin manta ne." Tarrrr ta zuba mishi ido tana motsa bakinta alamar son tayi magana, amma tana son tuna lallai hakane abinda y'a fad'a, kunnuwanta ne taji sun sak茅 mata amsakuwa na k'arar nan tare da yi mata wani dummmm kamar ana kuwa, sake dafe kunnuwanta tayi k'am ta rintse ido sosai, saida ta d'auki kamar minti d'aya kafin ta d'auke hannayenta ta kalleshi tace "Ina wayata?" _Yan maiduguri, 'yan Nigeria baki d'aya Allah ya k'ara muku kwanciyar hankali a k'asarku, muma haka Niger Allah k'ara wadatamu da kwanciyar hankali. Ameen ya Hayyu ya Qayyum_ Da sallama ya shigo a hankali kamar kazar da ruwa ta daka (馃槢) jakar nan har yanzu tana kafad'arshi duk da lura da yayi ana kallonshi, amma tunda dai ta Fati ce to miye a ciki? Ita kanta zai iya dakonta ya zagaye garin nan da ita bare jakarta da ko kilo d'aya ba zata yi ba, _(Da jakar kwate ce dake aje kud'i ai sai kilo ashirin)_, suna had'a ido tayi saurin mik'ewa tsaye, shima da sauri ya k'araso yana fad'in "Fatima." Ja baya tayi tace "Karka matso, kai mai kisan kaine, har fa makami kake rik'ewa, ni babu ruwana da kai." Da sauri yace "Faduma tsaya ki saurareni." Da gudu ta juya ta shiga d'akin Ayya tana kuka, wata ajiyar zuciya suka sauke tare da Wardugu, kallon Ayya yayi yace "Ayya zan fita yanzu na kai yaron can ofishina, daga nan zan biya wajen likitanki na mishi magana a kanta, ina tsoron wani abu ya shiga kanta." A sanyaye Ayya tace "Gaskiya nima haka, Allah dai ya kareta." Jinjina kai kawai yayi ya fita daga gidan, matsowa tayi kusan Hasheer tace "Yarona kana lafiya? Babu abinda ya sameka dai ko?" Girgiza kai yayi sai jakar Faduma da waya da sark'ar daya mik'a mata, karb'a tayi ya juya ya fita ita ma ta shiga d'akinta, ban d'aki taji motsin ruwa saita d'auka wanka ko wani uzurin take, aje mata kayan tayi kan gado ta juya zata fita, k'ara taji daga ban d'akin hakan yasa ta shiga da gudu tana salati, tsaye ta ganta bakin panpo da doguwar rigar ruwa na sauka akanta, k'arasawa tayi ta kashe panpon ta taimaka mata da kanta ta cire mata rigar, towel ta d'auko ta d'aura mata a k'irji sannan suka fito, zaunar da ita tayi bakin gadon ta d'auki k'aramin towel ta d'aura mata shi akai dan ruwan su tsane, rawar d'ari ta shiga yi bakinta na rawa sosai hak'oranta na had'uwa. Da sauri ita kad'ai ta shiga fad'in "Sanyi, sanyi nake ji sosai, sanyi nake ji, sanyi." Wata doguwar rigar bacci Ayya ta d'auko wacce take sakawa, da dubara ta taimaka mata ta saka, kwantar da ita tayi bayan ta cire mata towel d'in kanta, babban bargo ta d'auko cikin drower ta rufeta ruf tare da kashe pankar dake juyawa kad'an, dan ita ma ba kullum take kunnata ba saboda akwai ac, fita tayi a d'akin ta shiga madafa dan had'a mata shayi mai zafi dan taji dad'i, ga yunwa, ga k'waya, ga firgici, dole abun ya mata yawa ta nemi haukacewa. Abunka ga idan da kud'i da kuma kulawa ga kuma iko, saiga Wardugu tare da rakiyar likita mace suka taho tare, yanda Ayya ta sake mata bayanin abinda ya faru yasa sukayi waya da babban docteur d'in daya turo ta, tana aje wayar ta kalli War da Hasheer da suka tsareta da ido tace "Zamu d'auketa a kaita asibiti." Dafe kai yayi k'asan mak'oshi yace "Oh Allah." Dafashi kawai Wardugu yayi suna kallo Ayya da likitar suka shiga suka kimtsata suka fito da ita, gata dai a tsaye da kyau kuma lafiya lau, amma kuma daka kalli fuskarta zaka fahimci nutsuwa bata tare da ita, sam ta b'angaren da Hasheer yake ma bata bi ba dan sai ya fara tsorata. Shi kuma mamakinshi Wardugu ma dake d'aure da bindiga a k'ugu kowane lokaci bai tsorata ta ba sai shi, amsar ita ce shi jami'i ne kai kuma farar hula, that's why you are civilian.馃ぃ Abu kamar k'arami sai gashi a gurinsu an girmamashi ya zama babba, a hankalce aka shigar da Faduma na'urar da zata hasko komai daya shafi k'ok'on kanta, bata gaza minti ashirin ko sama da haka ba aka fito da ita. Gwajin jini da sauran bincike duk babu wanda ba'a mata ba harda duba kunnuwanta, daga bisani kuma allurar bacci tare da wasu sinadaren da zasu patattaki sauran k'wayar dake jikinta, kwantar da ita akayi kan gado ta samu nauyayyen bacci, a lokacin Agaishat ta zo asibitin, ita da Ayya suka zauna wurinta suna kallonta cike da tausayi. Hasheer kuma gida suka koma tare da Wardugu saboda k'arasa shirinsu na bud'e risham wax, saida sukayi sallah azahar data kubce musu sannan suna shiga gidan, kai tsaye d'akin suka nufa, suna shiga War ya mik'o ma Hasheer bindigarshi yace "Ga wannan, ka ajiyeta da kyau, babu wani bincike akanta dan nayi anfani da alburushin bindigata, saidai ka dinga kula ba haka kawai zakayi harbi ba Hasheer." Wani murmushi yayi yace "Wardugu ai na gama anfani da wannan bindigar kuma har abada, dalilinta ne fa Faduma ke kwance asibiti yanzu, a silarta ne fa yanzu haka bata kallon fuskata, a gaban idonka tace karna sake tab'ata saboda ni mai kisan kai ne, kuma ta d'ora da fad'in ta rasani, ni kuma me zanyi da bindigar nan? Ka rik'eta kawai." Da mamaki Wardugu yace "A'a Hasheer, ba zai yiwu ba haka, kaifa kasan dalilin da yasa aka mallaka maka wannan, badan komai ba saidan kare kanka daga masu bibiyarka, ya zaka ce ka hak'ura yanzu saboda abinda ya faru? Ita ma firgici ne ta shiga kuma zata warware da yardar Allah." Murmushi ya kuma saki yace "Ai shiga firgicin nata shine abinda bana so, Wardugu bindigar nan ba zata sak茅 min anfani ba, idan ma na karb'a yanzu to jefar da ita zanyi." Wata nauyayyan ajiyar zuciya ya sauke yace "A duniya ina tunanin kamar ba za'a samu wanda zai so 'ya mace kamar yanda na so Agaishat ba, Hasheer kana son yarinyar nan sosai, muyi k'ok'arin gama abinda ke gabanmu nan da jibi, ni Wardugu na maka alk'awari sai yarinyar nan ta zama matarka da yardar Allah." Fad'ad'a murmushi yayi yana cije leb'e yace "Idan ka min haka ni kuma, na maka alk'awarin baka d'ana namiji da Faduma zata haifa ka mishi tarbiya sannan ka mayar dashi soja kamar ka wanda zaiyi numfashi don k'asarsa kawai." Da murmishi War yace "Idan kuwa hakane, nima saina tabbatar dana kawoshi gabanka a cikin kakinshi na soja ya kalleka ya buga k'afarsa da k'arfi sannan ya sara maka cike da alfaharin kasancewarsa d'anka." Cike da k'aunar juna suka rumgume junansu suna bubbuga bayan juna, raba jikinsu sukayi kafin War ya fara shiga yayi wanka tuni har sun kama wani zancen dan mantar da su shiga wata damuwa musamman ma Hasheer. *05:30* Yamma sosai suka dawo likitar sanda Ayya ta kirasu ta fad'a musu zasu koma gida, duk tsaye suke sai Faduma dake zaune kan gadon sun hanata tashi, yanzu kam daidai take jin kanta saidai tana tuna sanda Hasheer y'a ciro bindigar nan yayi harbi, har yanzu tambayar bata wuce *waye shi ba?* Likitan ne ya mik'awa Wardugu wasu magani k'waya uku yace "Alhamdulillah babu wata matsala akan ta, da dai bakuyi saurin kawota ba da hakan zaici gaba da faruwa ne, kuma zai iya janyo mata birkicewar k'wak'walwa da zaucewa, yanzu komai ya tafi daidai insha Allahu, wannan ku bata da dare kafin ta kwanta, gobe ma haka sai jibi ma a bata na k'arshe." Hannu y'a bashi suka gaisa yace "Nagode sosai." Girgiza kai yayi yace "Ba komai, Allah ya kiyaye gaba." Da "Ameen." Duk suka amsa kafin Agaishat ta rik'e hannunta suka fita, lokaci lokaci sukan had'a ido ita da shi kasancewar a tsakiya take kuma shi yana zaman banza ne War ke tuk'i, rufe ido yayi yana tuna jiya da zasu tafi gidan Ayya, tana doka masa murmushin nan kumatunta na d'an lob'awa, ina ma zata jaraba yanzu ma da yayi ihu da larabci shi kam. Saidai ina kallon mamaki da tuhuma kawai take binshi dashi, kallon jira nake m没 sauka kasha tambayoyi, jira nake a tsaya ka fad'a min komai. A farfajiyar duk suka fita kowa ya tunkari shiga ciki, kallon juna suka sake yi a karo na ba adadi, saida ta zo daf dashi zata shiga tace "Ka bani mamaki Hasheer." Wucewa tayi gaba da sauri, tana shiga daidai wayarta da Ayya ta aje kan kujera nata kururuwa, d'auka tayi zata d'auka kuma ta tsinke, ganin Aminu ne ga kuma tarin kira da bata san adadinshi ba yasa zata mayar da kiran Ayya ta shigo ita ma, kallonta tayi tace "Faduma hushi kike dashi?" Ajiyar zuciya ta sauke ta kawar da kanta gefe a dak'ile tace "Ayya me ya had'a shi da bindiga? Waye shi a cikin jami'ai? Dama sakarcina ya kai haka na zauna ina wangale baki a gabanshi?" Da sauri Ayya ta rik'e hannunta mai wayar ta karb'a ta aje kan kujera, zaunar da ita tayi suna fuskantar juna sai Agaishat a gefensu, cikin nutsuwa Ayya tace "Faduma kinsan doka ba saina fad'a miki ba, a ganinki mutum nawa aka yarje ma rik'e makami? Bayan jami'ai farar hula ma an yarje masa domin ya kare kansa daga shiga had'ari, to kamar hakane ya faru da Hasheer." Da mamaki ta kalleta tace "Had'ari kuma? Wane irin had'ari yake ciki?" Jinjina kai tayi tace "Faduma wasu mutane kina gninsu ne kawai, amma da zasu tona miki cikinsu saikin mutu dan zulumi, Hasheer babu abinda ya rasa na rayuwa hasalima kullum gaba yake yi mak'iyansa na baya, saidai ya rasa farin ciki da zai iya kira da sunan farin ciki, k'alubalen ya fara ne daga sanda mahaifinsa ya rasu, kampanin risham wax mallakar Hasheer ne wanda guminsa ne ya samar masa dashi, amma kampanin akwai mutane dayawa da suka saka masa ido kuma suke son ganin ya wargaje, daga ciki kuwa harda wanda suke na kusa dashi sosai, kinga akwai k'anensa da suke uba d'aya sannan akwai d'aya daga cikin k'annan mahaifinsa Alhaji Saddi, wannan bak'in cikin da takaaicin wutar da suke hura masa kullum yasa shi kasa samun nutsuwa, har ta kai ga suna aiko masa da 'yan jagaliya suna masa barazana da rayuwarsa, a irin hakane wata rana labari ya zo ma Wardugu kan had'arin daya shiga, ranshi ya b'ace sosai a lokacin yaji kamar zai nik'a naman mutanen nan, da k'yar aka shawo kanshi ya hak'ura, shine fa ya mallaka masa bindiga bayan an tabbatar masa ita a dokance tare da bashi izinin yin harbi ga duk wanda ya kawowa rayuwarsa barazana, Faduma bindigarshi mai lasisi ce ba kara zube take ba, bana jin ya tab'a harbin kowa da ita idan ba yau ba kuma akan ki." Mik'ewa Ayya tayi tsaye ta dafa kafad'arta tace "Karki k'ara masa wani b'acin ran akan wani, ke d'in ganiyar ta musamman ce a wajenshi, hushinki a gareshi zai iya gusar da tunaninshi." Shigewa tayi d'akinta dan samu tayi wanka, ita ma mik'ewa tayi a zabure ta fito farfajiyar gidan sai Agaishat data bita da kallo, tsaye ta hangosu shi d'脿 Wardugu suna magana, k'arasowa tayi a hankali ta tsaya bayansu tana kallon k'eyarshi, cikin raunin murya taji yana fad'in "Wallahi Wardugu saina fad'a mata, kaji fa me tace? Wai na bata mamaki kuma a haka bayan ta bini da kallon tsana." War da yaga fitowarta da ido ya mishi alamar bayanka, da sauri ya juyowa dan gabin menene, sauke idonshi yayi cikin nata suka kalli juna, da sauri ya sak茅 matsowa kusanta yana fad'in "Faduma." Idonta tsaf cikin nashi tace "Na'am." A marairaice yace "Har yanzu hushi kike dani?" Jinjina masa kai tayi alamar eh, kamar zaiyi kuka yace "To me yasa? Nifa saboda ke nayi harbi." Saida ta fara motsa d'an bakinta kafin tace "Saboda baka fad'a min had'arin da kake ciki ba, me yasa Hasheer?" Ajiyar zuciya ya sauke ya juya ya kalli Wardugu dake kallonsu, juyowa yayi ya kalleta a lokacin Wardugu ya bi ta gabansu ya wuce y'a shiga d'akinshi, cikin taushin murya sosai yace "Faduma taya zan fad'a miki k'uncina bayan ni kuma abokiyar hira da dariya nake nema, wacce zata dinga mantar dani damuwata, bana so kiyi tarayya a cikin bak'in cikina." Cikin shagwab'a ta turo baki tace "Amma ai daka fad'a min koda masauki ne da mun nemawa masu son ganin bayanmu a magark'ama, ko kuma mu sak茅 durmiyasu cikin k'unci ta hanyar ganin ci gabanka." Da murmushi da kuma mamaki a fuskarshi yace "Batul, damuwata kike alak'antawa da kanki, Fati jam'i fa kikayi kika ce mu, a madadin kice damuwarka." Wani sanyayyan murmushi ya saki ya sake kallonta yace "D'azu da safe kin fad'i maganar da tasa naji kamar zan suma dan dad'i, na d'auka tsoro da firgici ne, ashe har zuciyarki kema kina sona kamar yanda nake *sonki*." Wani murmushi ta saki tare da rufe fuska da tafin hannunta ta sunkuyar da kai, ta d'an jila a haka shi kuma yana kallonta kafin ta d'ago kanta, suna kallon juna ta had'e dariyarta tace "Hasheer har yanzu baka san komai a ka茂na ba, ni ba kamar yanda kake tsammani bace." A hankali yace "Na sani Faduma, babu abinda dadarki bata fad'a min b芒, kama daga had'uwarku da yaron nan zuwa fara soyayyarku da fasa aurenki da d'an uwanki, har zuwa saka ranar aurenki dashi da kuma...samuwar cikin Amjad." Tunda ya fara maganar ta fashe da kuka marar sauti tana girgiza kanta, d'agowa tayi da sauri tace "Duka ka sani dama? Ashe kana kallona da abun nan kuma kayi shiru." Wani murmushi ya saki yace "Na sani, amma wannan abun bashi yasa nake sonki ba, hallayarki ta gari ce da yanda kike tsaye kan d'anki suka rinjayeni akan ki Faduma, kuma jin labarinki bai k'ara min komai ba sai soyayyarki, zan iya zama dake a kowane irin hali Faduma." Kallonshi tayi tana share hawaye tace "Har yanzu akwai abinda ya kamata ka sani wanda baka san da shi ba." Saida ya matso fuskarshi a had'e yace "Menene shi Fati?" Sunkuyar da kai tayi cikin rawar murya da kuma kunyar kallonshi tace "Hasheer dole mu hak'ura da junanmu, soyayya ba zata yiwu a tsakaninmu ba bare aure, na kuma d'auki hakan a matsayin k'addarata, *rasa abinda nake so*." Yankewa gabanshi yayi ya fadi, hankali tashe ya sake matsowa ya rik'o hannunta yace "Ban gane ba Faduma, ki min dalla dalla yanda zan fahimta." Hannayensu dake had'e ta kalla tana kuka tace "A karo na biyu mahaifina ya sake tsayar da ranar aure, a karo na biyu kuma ba zan sake kawo mishi tangard'a ba." Wata damk'a ya ma hannunta da k'arfi har saida ta zabura ta kalleshi tace "Aouch!" Sassautan rik'on yayi tare da sake matsawa daf da ita kamar zai had'e har sa茂da taji numfashinshi na sauka a fuskarta, fuskarshi take kallo saidai idonshi a rufe sosai ya had'e naman goshinshi kamar wanda kanshi yake sarawa, lalabawa yayi ya kamo d'aya hannunta shima ya rik'e jim, a hankali yake jijjiga hannayenta yana d'an bud'a idonshi, saida ya gama bud'ewa duka ya zuba jajayen idonshi cikin nata dake ta zubar da hawaye, sunkuyar da kanshi yayi sosai yana kallon k'asa cikin radar muryar kuka yace "Dan Allah, Dan Allah Faduma Bintu karki bari su rabani dake, wallahi Fati zuciyata bugawa take da sauri sauri, ina tsoron sonki ya zama ajalina." Kallonshi take sai kuka kawai da take cike da tausayinshi tace "Kayi hak'uri Hasheer, nima bansan ya zanyi ba, kayi hak'uri kaji." Da sauri ya d'ago ya kalleta yace "Batul waye? Waye zai rabani dake? Waye zaki aura? Fad'a min shi naji wanene shi? Me yake tak'ama dashi dani bana da? Nasaba? Ilimi? Kud'i ko kyau?" Fashewa ta sakeyi da kuka ta sunkuyar da kai ita ma tana girgiza kai, da k'arfi ya tallabo fuskarta yace "To fad'a min me yasa ba zaki aureni ba? Ba kya sona ne?" Cikin kuka tana neman sulalewa k'asa tace "Ba haka bane Hasheer, ka fahimceni mana." *Aminu* Tunda suka shigo garin yake ta faman kiran wayarta amma tana k'ara an kasa d'agawa, hankali tashe ya nufi gidan g茅n茅ral Wardugu kamar yanda ta tab'a fad'a masa a waya tun zuwanta, shi da k'yar ma ya kama sunan nashi da taimakon d'an taxin da zai kaishi, dan shi ko a fuska bai sanshi ba tunda ba waani kallon tv yake ba sosai, ya tab'a ganinshi tabbas amma yanzu haka b芒 zai iya cewa gashi ba, shi ma mai taxi gidanshi na farko ya kaishi inda Walyn take, dama kuma baata nan dan haka ba'a barshi ya shiga ba, daga k'ofa suka dakatar dashi suna bincikarsa, katinsa ce ta tabbatar musu shi d'in ba zauna gari banza bane, shiyasa kad'ai suka kwatanta mishi gidanshi na airport, can ma da zuwanshi suka rik'eshi bakin k'ofa suna tambayarshi, saida suka gmasu da hujjar daya basu sannan suka fad'a mishi g茅n茅ral ya fita tun safe, madame ma bata nan saidai bak'uwar tun jiya ta fita basu ga dwowarta ba, lallab'asu yayi da k'yar daya tambayesu inda zai ga g茅n茅ral ko ya samu masaniya akan Faduma, a take suka ce saidai yaje gidan ayya, nan ma kwatancen suka mishi ya sake bazama da tunanin ko zai karad'e garin nan saiya ga fadumanshi. Gidan ma daya zo katinshi ya nuna musu tare da fad'a musu wacce yake nema, a sauk'ak'e kurtun ya barshi ya shiga tunda yaga tana ciki har da g茅n茅ral d'in kanshi. Shigowarshi ne fa ya ga Faduma tun lokacin da Hasheer ya matso daf da ita rik'e da hannunta, kad'an ya rage bai kife a wurin ba, kanshi ne ya shiga juyawa zuciyarshi ta fara dokawa da mugun k'arfi. Faduma dai daya sani, wacce ko rantsuwa yayi ba zaiyi kaffara ba cewa bai tab'a had'a hannunshi da nata ba, bayan gamdakatar na ta mik'o mishi ya karb'a ko shi ya mik'a mata hannunsu ya zoji juna fiye da hakan bai tab'a shiga tsakaninsu ba, amma ita ce a gaban wani, wanin ma Elhaj Hasheer da yake kallo kamar mai gidanshi, hannunta cikin nashi suna kallon juna ita tana kuka kuma ba tare data nemi raba hannunta da nashi ba, bugu da k'ari harda tallabo fuskarta suna abu kamar dai zai rumgumeta a jikinshi. Ba komai a gano ba a idonsu sai tsantsar k'aunar juna, saidai a yaushe hakan ya fara faruwa? Yaushe suka had'u? Me ya had'asu anan ma? Miye tsakaninsu? Wannan amsar ita zai tunkaresu yanzu yaji duk yanda akayi. Suna cikin kallon juna Hasheer na mata marayan kallo da yake saka tusa mata tausayinshi taji kamar ta goyashi a bayanta, cikin mutuwar jiki da nauyin da k'afafunsa sukayi ya d'ago ya tako yana fad'in "... *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 21:40 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _57_ "Sannunku." A tsorace Faduma ta fizgi hannayenta tana kallon inda taji muryar Aminu, sake ja baya tayi gabin sun had'a ido ta shiga zare ido tana kallon Hasheer da kuma Aminu, cikin in'ina d'脿 rashin gaskiya ta shiga murza yatsunta tana bubbugasu kan cinyarta tana fad'in "A...Ami..nu, kaine?...yaushe ka zo? Ya ma..." Shiru tayi dan mak'oshinta taji yana neman bushewa, yanda ta duburbuce da yanda take da yatsunta ya sake tabbatar masa da akwai wani abu, amma a zuciyarsa saiya bawa kansa hak'uri da niyyar gano koma menene a tsanake, murmushi ya saki cike kissa ya mik'awa Hasheer hannu da ladabi yana fad'in "Elhaj barka da yamma." Idonshi akan Faduma yana son yasan amsar tambayarshi, a d'an dak'ile ya kalleshi shi sam kamar ma bai ganeshi ba, mik'a masa hannun yayi da tuni har jikinshi ya fara d'aukar zafi (abunka ga jar fata馃え), k'ala baice ba saima saurin raba hannayensu da yayi ya maida kallonshi kan Faduma. A hankali Aminu ya kalleshi, wani malalacin murmushi yayi tare da juyawa a nutse ya kalli Faduma, idonta na kan Hasheer ita ma amma tana ganin ya juyo tayi saurin d'auke nata, kallon juna sukayi tace "Amma ya ka zo haka kwatsam ba sanarwa? Me ya kawo ka nan?" Ba tare daya daina murmushin nan ba yace "Nayi ta kiranki baki d'auka ba, ni kuma hankalina ya kasa kwanciya, shiyasa na biyoki dan na tabbatar komai lafiya." D'an murmushin yak'e tayi tace "A ina ka sauka?" Girgiza kai yayi yace "Tukuna, ke kika kawoni garin nan shiyasa na fara nemanki kafin komai." Wani murmushin ta sake yi tana satar kallon Hasheer da zuwa yanzu ya fara kallonsu kamar yana kallon wasu aljanu, ganin gaba d'aya sai canzawa yanayinshi yake yasa ta fara tsorata gabanta y'a fara fad'uwa, kallon Aminu tayi tace "Mu shiga ciki ka gaishe da Ayya ko?" Girgiza kai yayi yace "Amma Faduma nan ina ne? Ke da kika ce kina gidan g茅n茅ral, me ya faru jiya muna cikin magana kika aje? Ina ne ma kike a wannan lokacin? Me kuma yasa ba kya d'aukar wayata?" A duburbuce ta shiga fad'in "Amm...Aminu ka gane? Abubuwa da dama sun faru, amma idan muka zauna zan fad'a maka komai." Mayar da kallonshi yayi ga Hasheer da a lokacin yake kallonshi shima, a ransa kawai yake ayyana duk wannan tambayoyin da tuhumar na miye yake mata? Waye shi d'in a gareta? Cikin sakin murmushi Aminu yace "Elhaj ya na ganka nan kuma? Dama kunsan juna ne?" Wani kallo Hasheer ya masaa irin kamar ban fahimcekan nan ba, da sauri Faduma tace "Eh munsan juna, tun acan ne dama muka had'u a dalilinsu Amjad da Izzadeen da suke makaranta d'aya." Tunda ta fara magana yake binta da murmushi, a tsanake yake fahimtarsu sosai da abinda ke zuk'atansu ma, ita kam burinta shine su bar wajen, dan kowane mutum da baiwarsa, idan har ita Allah ya mata nasibin shawo kan matsalar bincike da warwareta, to Aminu kuma tasan wayeshi a game da lura da kowane motsi na mutum, hatta da yatsunta da labb'anta saiya gano yanda suke motsawa da kuma musababbin motsawarsu hakan. Sake kallon Hasheer yayi yace "Elhaj a sanina dai yau aka bud'a reshen risham ko?" Da k'yar ya rufe bakinsa dake bud'e ya lumshe ido ya d'an jinjina masa kai, kallon Faduma ya sakeyi data nuna su tace "Dama kuma kunsan juna ne?" Murmushi ya mata yace "Eh, ai shine Elhaj d'ina, duk sanda zaki ji nace zance gidan Elhaj to shi nake nufi." Jinjina kai tayi alamar gamsuwa, tare da sake cewa "Mu shiga ciki ka gaida Ayya." Kallonta yayi ya jinjina kai cikin hikima ya kalli Hasheer dake tsaye kamar an girkashi yace "Elhaj dama ina tunanin kiranka na fad'a maka an saka ranar aurena, insha Allahu nan da kwana goma sha bakwai za'a d'aura aurena da..." Saida ya juya ya kalleta yace "Da Faduma." A hankali kamar wacce aka kama da kayan mutane tayi tsuru da ido tana kallon Hasheer, rintse idonshi yayi tare da cije leb'enshi na k'asa sosai, wani bahagon murmushi ya k'ak'aro kan fuskarshi wanda kana ganinshi kasan yayi kama dana kuka, kallon Aminu yayi yana son sanin da wane hannun ko k'afar zai fara kaishi k'asa ne kafin wani abun ya biyo baya, saidai zuciya na fad'a mishi ba girmanka bane Hasheer, juyawa yayi ya kalli Faduma dake kallonshi kamar kaje gaban malami da laifuka akanka kuma ya yunkaroka da tsumagiya, kallon daya jefa mata na tuhuma da tambaya yasa ta jinjina kai da sauri tace "Eh, shine..mijin...da zan...aura." Taf da k'walla a idonshi amma a haka y'a jure ya kuma daure ya jinjina kai, shi fa da ita kad'aice a wurin wallahi sai yayi kuka, amma tunda akwai wannan yaron dole ya kama girmansa, murmushi ya sake gayyatowa da tsiya yace "Yayi kyau." Kallon Aminu tayi ta sake nuna mishi shiga cikin falon, da kallo ya bisu yana ambaton sunan Allah a k'asan zuciyarsa, saidai komai na jikinsa ya tsaya cak ya daina aiki, yanzu haka ji yake sai an nemo Wardugu ya d'aukeshi daga nan tsaye (Kwate kiji fa). Gudumar da aka doka masa akai ce tasa shi rintse ido sosai ya yatsina fuska, ya jima haka yana duk addu'ar data zo bakinshi kafin ya bud'e ido, duhu ya gani ko ina ya mamayeshi, b'arin jikinsa yaji yana masa masifaffen nauyi yana rijayarsa zai kayar dashi, wuuuuuu! Ya gani gaba d'aya ana juyawa dashi hakan yasa shi tafiya b'aren damarsa zai kifa, da wani irin sauri Wardugu dake fitowa daga d'akinshi da waya a kunne yana amsawa ya rugo a guje ya taresa ko takalmi babu a k'afarsa, salati yayi a hankali kamar hankalinshi ba'a tashe yake ba, kasancewar shima hamshak'in k'aton ne yasa sai janshi Wardugu yayi ya shigar dashi ciki. _Da Tagurguri ne ai da d'aukarsa za'ayi yaron kirki._馃榿 Suna shiga ciki ya shinfid'esa ya danna kiran lambar likita, da gaggawa ya amsa da gashi nan duk da yamma ce sosai magriba ma ta kawo kai. Faduma ma suna shiga Agaishat ta shiga dan yin alwala sai Ayya data fito yanzu da waya ita ma suna gaisawa da mijin nata uban gwarzon yaronta nata wato *Marahut*, tsaye tayi tana kallon Aminu da mamaki dake d'an sauke jakarshi a kafad'a, gaisawa sukayi sosai kamar sun san juna cikin mutumci da girmamawa, Faduma ce ta kalleta da kunya tace "Ayya wannan sunansa Aminu, kuma shine mijin da zan aura." Kamar saukar mari Ayya taji kalamanta, k'uri ta mata da ido tana kallonta, saida ta saki wayar hannunta kan kujera tace "Faduma dama zakiyi aure shine baki fad'a ba?" Murmushi tayi tace "Ayya ba haka bane? Zan fad'a muku dama ina so harna kammala abinda ya kawoni ne." Sake kallon Aminu tayi daga k'asa har sama, a ganinta dai bashi da wata makusa, matsalar d'aya yayi yaro wanda a shekarun Faduma da wayewarta zasu sha matsaloli da dama da zai kasa shawo kansu. Ayya kasa amsa mishi tayi daga lokacin sai zuba musu ido, to ina Hasheer yake? Ya ganshi ne ko kuwa? Ha Yallah! Faduma kam juyawa tayi ta kalli Aminu tace "Magriba ta gabato, muje kayi alwala kayi sallah, idan ka dawo zamuyi magana." Juyawa yayi zai fita ta tara hannu ta karb'i jakarsa, tare suka fita ta rakashi har bakin panpo, cikin nutsuwa ya shiga gabatar da alwalar, sanda ya fara wanke fuskarshi ne ya samu damar sako da hawayenshi tare da ruwan alwalar, hakan yasa shi jin sanyi sanyi a ranshi, a hankali ya d'aga kai ya kalleta, saidai gaba d'aya hankalinta yana kan k'ofar d'akin can daya tabbatar nan Elhaj Hasheer ya shiga, d'an girgiza kanshi yayi kawai yana sake jadaddawa kansa yin hak'uri da kuma falalarsa, saidai abu d'aya daya k'uduri yi shine gobe ana gama shari'ar nan tare da ita zai juya su bar garin nan, idan suka je tayi abinda zatayi zai sake mayar da ita gaban iyayenta har sanda za'a d'aura aurenta. Ruwan dake hannunshi ya yarfa mata shiyasa ta kalleshi a zabure tana rarraba ido, wani murmushi yayi yace "Na tafi masallaci." Da kai kawai ta amsa mishi ya nufi k'ofar fita zuciyarshi na matuk'ar suya, juyawa tayi jiki a sanyaye ta shiga d'aki ta aje jakar saman kujera, ita ma duk abinda tasan nata ne ta harhad'o dan ba zata sake tsayawa tare da su ba, hakan zai sake rugurguza zuciyarta, tana zaune Agaishat na sallah a falon taga shigowar likita, ganin ya shiga can d'akin yasa ta mik'ewa da sauri ta kalli Agaishat tace "Ina ga fa wani babu lafiya?" Kallonta tayi ta sallame sallarta tace "Waye kuwa bayan Hasheer, Ayya tace min wai mijin da zai aureki ne ya zo." Mik'ewa tayi saidai da gudu Faduma ta fita a d'akin ta fad'a d'akin War, karo ta kaiwa Wardugu dake tsaye bakin k'ofar ya bawa likitan dama dan dubashi, shi kuma yana kwance idonshi a rufe sosai, da sauri likitan da War suka kalleta da mamaki, bata kula da bigewar data ma Wardugu ba sai ma rab'ashi da tayi ta wuce tana fad'in "Yallab'ai me ya same shi?" Wani masifaffen kallo ya mata mai saka mutum jin fitsari yace "Ke zan tambaya ai, tare na barku." Girgiza kai tayi ta k'arasa gaban kujerar da yake kwance ta durk'usa, hawaye ne suka shiga yi mata sintiri a kumatu, Ayya da Agaishat suka shigo suma suna tambayar lafiya? Allura likitan ya ciro ya shiga had'awa yana fad'in "Ya akayi jininsa ya hau haka yallab'ai? Me yake damunsa?" Da sauri ta damk'i hannunsa da yayi zafi kamar wuta tana matsanancin kuka tace "Hasheer dan Allah ka bud'a ido ka kalleni, karka kashe kanka mana akai na, ya kake so nayi idan kai ma dake namiji haka ta faru da kai?" Hannun data rik'e likitan ya rik'o ya kallleta yace "Ina zuwa madame." Sakin hannun tayi tana kallo zai mishi allurar, ko dan bata son allura ko kuma saboda wanda take so ne saida ta rintse ido sanda aka mishi, har yanzu dai idonshi a rufe bare ya kalli wani ko yayi magana. War da wayarsa ke ta kururuwa ne ya d'auka ya duba, shi sai yanzu ma ya tuna ko da suka je aka bud'e wurin nan suka je asibiti d'auko su Ayya, gashi harda manyan mutane a wurin da su suka gayyacesu duk sun barsu can, d'aukan kiran yayi a k'ufule yace "Dan ubanka idan an gama abinda ake kowa ya ci abinda yake so ya tafiyarsa, mai kampanin gashi kwance babu lafiya." Dogon tsaki ya k'are dashi tare da kashe wayar ya mayar aljihu, sallamar Aminu ce tasa kowa juyawa ya kalleshi, d'aya bayan d'aya ya dinga binsu da kallo shima, babu wanda yake mishi kallon mutumci sa茂 ma jefo masa kallon tuhuma da tambaya, Faduma da tana kallonshi ta d'auke kai tana share hawaye, cikin nutsuwa yace "Kuyi hak'uri na shigo muku kai tsaye, naga kamar wani babu lafiya ne shiyasa." Babu wanda ya tanka sai War daya zabga masa kallon mutuwa yace "Waye kai d'in?" Gabanshi yaji duk ya tsinke ya fad'i, sai yanzu ne daya ga fuskarshi ya tabbatar shine g茅n茅ral, sunkuyar da kanshi yayi dan shi tsoronshi ma ya lullub'eshi baisan me zai ce ba, a hankali cikin muryar kuka Faduma ta mik'e tace "Yallab'ai, sunansa Aminu, shine wanda zan aura." Da wani mugun sauri ya kalleshi shima, sai kuma ya sake kallonta ya kalli Hasheer dake kwance, jinjina kai yayi yace "Dole, bawan Allah, mtsssss." Ita kanta a lokacin sai taji ta tsargu dayawa, duk sai taji kamar suna mata kallon maciya amana, sunkuyar da kanta tayi tace "Kuyi hak'uri dan Allah ku gafarceni idan na b'ata muku rai, nagode da taimakon da kuka min, zamu tafi." Rab'asu tayi zata fita War ya tare hanyar yace "Babu inda zaki je har saiya farka." A tsorace ta kalleshi tace "Yallab'ai?" D'aga kai yayi yace "Eh." Kallon Aminu tayi da shima yake kallonta tace "Amma yallab'ai ni banyi komai ba, zamu je mu samu wani masauki ni da Aminu, na maka alk'awarin zan dawo na dubashi." Girgiza kai yayi yace "Ki zauna anan, shima kuma bak'on naki zai zauna anan, duk ina da masaukinku." Rarraba ido ta shiga yi ta kalli War ta kalli Aminu dasu Ayya dake gefe, likitan ne ya d'ago yace "Yallab'ai nayi iya abinda zan iya yi masa, saidai da zaran ya sake irin haka to kar kuyi wasa ku kaishi asibiti kai tsaye, tashin farko jininshi na hawa haka daya fad'i zaai iya janyo masa mutuwar b'aren jiki." Rintse ido tayi hawaye sharrrr suka sake biyo kumatunta, bud'ewa tayi ta saauke akan Hasheer da yanzu rintsewar idon ba sosai ba alamar bacci ma ya d'aukeshi sakamakon allurar da aka masa. Jinjina kai War yayi yace "Insha Allahu za'a kiyaye, yanzu babu wata matsala?" Girgiza kai yayi yace "Insha Allahu babu, kawai dai a barshi ya samu bacci sosai." Sake jinjina kai yayi suka fita tare da likitan, saida yaga tafiyarshi kafin ya kalli kurtun nan yace "Daga yanzu har sanda zan baka umarni a gidan bak'in nan guda biyu babu fita bare ayi maganar shigowa, idan kuma tsautsayi yaja maka fitarsu to kwananka ya k'are." Bai tsaya komai ba ya nufi masallaci shima dan gabatar da sallah. Duk jiki a mace suma suka fita daga d'akin sai Faduma da Aminu da suka tsaya gefen d'akin Ayya ya zauna kan farar kujera ita kuma kan dakalin dake zagaye da flowers, shiru tayi tana kallon yatsunta tana wasa dasu, maganarshi ce ke mata yawo akai da yace _"Dan Allah, Dan Allah Faduma bintu karki bari su rabani dake , wallahi Fati zuciyata bugawa take da sauri sauri, ina tsoron sonki ya zama ajalina."_ A hankali ta sauke ajiyar zuciya hawaye suka silalo mata, cikin sanyin murya ta furta "Ya zanyi nima Hasheer?" Tsawar da Aminu ya daka mata ce ta dawo da ita hayyacinta, da sauri ta kalleshi tana share hawayenta tana fad'in "Na'am, Am..Aminu." Girgiza kai yayi cikin jin haushi, na takwas fa kenan yana mata magana, amma tayi nisa a tunani bata ma san ya nai ba, kallonshi tayi a d'an tsorace tace "Kayi hak'uri dan Allah, ina wani tunanin ne, me kace?" Girgiza kai yayi ya tsareta da idonshi masu sirkin ja yace "Faduma me ke tsakaninki da Elhaj Hasheer?" A diririce ta kalleshi tace "Amma Aminu ba na fad'a maka ba, babu komai tsakaninmu ai kawai taimakona yayi." Ba tare daya rage kallon nan ba yace "Kin tabbatar?" Jinjina kai tayi tace "Eh." Shima jinjina kan yayi kafin yace "Me yake faruwa a game da binciken nan? Wane irin had'ari kike fuskanta?" Ajiyar zuciya ta sauke ta shiga fad'a masa abinda ya faru daga daren jiya zuwa yau, a k'arshe ta d'ora da cewa "To fa shine Abansu Izzadeen yake k'ok'arin kwantar min da hankali, amma bayan wannan babu komai." Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke yace "Kiyi hak'uri Faduma zumud'in son na aureki ya mantar dani had'arin da zaki iya fuskanta sakamakon aikin nan, kiyi hak'iri kinji." Girgiza kai tayi da sauri tace "Ba komai." Jinjina kai yayi yace "Yanzu ya zamuyi?" Cikin rauni sosai tace "Mu jira ya farfad'o saimu bar nan komai dare, zan tafi tare da kai mu samu wani masaukin, zuwa gobe zamu gama abinda ya kawomu saimu koma." D'aga kai yayi yace "Abinda na zo da niyyar yi kenan, Allah ya kaimu goben." "Ameen." Ta fad'a a hankali, shiru sukayi babu wanda ya sake magana, sun jima haka kafin ta mik'e tace "Zan shiga ciki Aminu." Jinjina kai yayi alamar to, tana shiga su Ayya na zaune ba wata hira a tsakaninsu suma, ido suka zuba mata harta zauna basu daina kallonta ba, a hankali ta fara jin tsarguwa da jin tana son barin gidan nan, dan gani take kamar suna kallonta mai laifi, saidai babu damar fita tunda umarni ne na g茅n茅ral. Har sallah isha'i suna zaune sai ma Wardugu daya dawo tare da yaran da aka kaisu can gidan, kallonsu Faduma tayi da mamakin yanda duk sukayi kama da mahaifinsu, musamman ma dai Muhammad, hatta tafiyarshi k'arfi yake sakawa kamar wani bijimin namiji, sai Khalid ne ma daya cika miskilanci amma fa akwai zuciya da jarabar fad'a. Kamar dai kullum yanzu ma hakane tuni Faduma ta siye zuciyar yaran da jansu a jikinta, babban abun birgewar shine da yaren tubanci suke hirarsu, dan Wardugu baya musu wata hausar da ba yarensu ba, haka ita ma Agaishat tana musu nata yaren buzancin shima ya zauna a bakinsu daram, zuwansu kad'ai yasa ta saki jikinta suke shirme kuma a nutse take sake d'orasu kan hanya, suna haka Ayya ta mik'e tana amsa waya cike da ladabi da kuma girmamawa harda fad'in "Da girman kujerarka." Da kallo Faduma ta bita tana son tasan waye kuma, amma da taji Agaishat tace "Ayya a gaishe min da Abu." Saita tabbatar da mahaifin War ne kenan, to amma baya gari ko? Ta tambayi kanta, sun ci gaba da hirarsu kuma wayar Agiashat ma tayi k'ara, d'auka tayi saidai daga yanda kai tsaye umarni ya bayar tasan har yanzu a kume yake, kallon Faduma tayi sanda ya aje wayar tace "Trozzo oga na nemanki a d'akinshi." Dammm! Taji gabanta ya fad'i, wallahi ita har yanzu tsoron bawan Allahn nan take ji, wani kallo daya mata d'azu kamar zatayi zawo a jikinta, mik'ewa tayi tana salati a k'asan zuciyarta rik'e da hannayen yaran, kallonsu tayi tace "Ai tunda yace ke to ke kawai yake son gani." Saida ta dafe cikinta daya juya mata tace "To dan Allah trozzo ke muje ki rakani, wallahi a tsorace nake." Murmushi tayi tace "Karki damu fa babu abinda zai miki." Girgiza kai tayi tace "Wallahi ina jin tsoro, idan ya kifeni da mari fa?" Dariya tayi tace "Ai duk tsumewar g茅n茅ral da b'acin ranshi baya dukan mace, da matarsa ce ke k'ark'arinta idan kin b'ata masa rai ya miki hawan k'awara saikin gane kurenki." Murmushi Faduma tayi ta girgiza kai tace "Ku dai matan aure ba'a magana daku saikun kauce layi, komai yana da zaurencensa a gurinku." _Haka dai k'anwata ta ce._馃榿 Fita tayi tana addu'ar Allah ya rabasu lafiya, bata ga Aminu anan ba sai kawai ta wuce kai tsaye, da sallamar da ka rantse shak'eta akayi take yinta can k'asan mak'oshi sosai, shima a mugun dak'ile ya amsa mata tare da cewa "Shigo." Kamar wacce ta sato kaza a hijabi haka taketa tattare hannayenta cikin rigarta doguwa, nuna mata kujerar dake kallonshi yayi, tsinkewa gabanta ya sakeyi amma haka ta daure kanta a k'asa ta zauna tana satar kallon Hasheer dake bacci har yanzu, gamewa tayi wuri d'aya tana murza hannunta tana jiran taji me zai ce. Cikin tsumammiyar muryarshi ta b'acin rai da dak'ilewa yace "... *Sorry* *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 21:40 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _58_ Cikin tsumammiyar muryarshi ta b'acin rai da dak'ilewa yace "Da gaske za'ayi aurenki?" D'an d'aga idonta tayi ta kalleshi sai kuma ta saukesu k'asa baki na rawa tace "Eh yallab'ai." A k'ufule yace "Kinsan da haka me yasa baki fad'a mana ba ko kuma shi? Dan musan halin da ake ciki." Sunkuyar da kai ta sak茅 yi k'asa ba tace komai ba, cikin fad'a da tijara yace "Miye bawan Allahn nan ya nema a gareki mai wuya? Soyayya ce fa, idan kinsan ba kya yi me yasa kika sakar masa fuska tun farko? Ko dama burinki ki kasheshi ne?" Da sauri ta d'aga kai ta kalleshi hawaye na gangaro mata, girgiza kai tayi ta kalli Hasheer da baisan me ke faruwa ba tace "Wallahi yallab'ai nima ina sonshi, saidai duk son da nake masa baikai wanda nake wa iyayena da suka kawoni duniya ba, hak'ik'a shi dasu sune rayuwata a yanzun, kuma dukansu kowa da huruminshi, zan iya bayar da rayuwata akan shi, amma bana so na sake b'atawa iyayena akan d'a namiji." Table d'in daya shiga tsakaninta dashi na glass ya rantab'awa hannu da k'arfin sababi ya mik'e yana fad'in "D'a namiji? Ke kinsan waye ni kuwa? Waccen d'a namijin daya lalata miki rayuwa daban Hasheer ma daban, ko a suna da halayya da kama ta yanayi basuyi kama ba, akan me zaki had'asu wuri d'aya? Kuma inace kema d'a namijin kika haifa? Shin zaki ce baki da yarda akan d'anki ne?" Tunda ya buga table d'in k'afarshi ta gurd'e yayi k'asa kayan samanshi suka zube, kanta a k'asa tana fatan Allah ya shigo da wanda zai shiga tsakaninta da bawan Allahn nan ita dai, cikin d'aga murya yace "Dake nake magana, ki fad'a min gaskiya ba kya jin yarda da yaronki?" Cikin rawar murya tana kuka tace "Na yarda da Amjad sosai yallab'ai, bana jin zai iya yin abinda bai dace ba, badan ni na haifesa ba saidan saninshi da nayi." Rik'e k'ugu yayi da hannu d'aya ya nuna mata Hasheer dake kwance yace "Irin yardan da kika wa d'anki irin wannan yardar nake da akan Hasheer, Faduma ki bashi dama ya aureki wallahi na baki tabbacin ba zaki tab'a zubar da hawayen bak'in ciki ba, idan kuma haka ya faru ni nan Wardugu Marahut na yarda ki fad'awa duniya ni mak'aryaci ne." Kawai fashewa tayi da kuka ta kasa c茅wa uffan harya gaji d'脿 jin rera kukan ya zauna jiki a mace yace "Tashi kije." Mik'ewa tayi da sauri zata fita, cikin dakakkiyar murya yace "Ji nan da kyau, idan har wani mummunan abu ya sameshi, b芒 ke ba saboda mace ce ke kuma Uwa, amma wallahi duk namijin da zaki aura sa茂 nasa kin gagara zama dashi, inhar Hasheer bai sameki ba babu uban da zai aureki yaji dad'i." Karrrr ta masa da ido tana kallo, sai kawai ta juya ta fita da gudu. Yau dai gidan Ayya ya zama kamar gidan da aka kawowa hari, haka Aminu ya kwanta a d'akin bak'i yana jin kanshi kamar an tsareshi ne, ga tunanin abinda ya gani ya kuma san dole wani abu ya tunkarosu. Faduma ma haka ta kwanta a tsohon d'akin Agaishat sai Ayya ma a d'akinta, Agaishat War da yaransu kuma sun nufi nasu gidan, haka gidan kowa ya kwanta saidai babu wanda ya samu bacci kaf a cikinsu, Ayya na tunanin halin da Hasheer ke ciki, tana shawarar ta sanarwa da mahaifiyarsa ko tayi shiru? Saidai tana tausayinshi sosai musamman da taga soyayyar na neman tafiya da rayuwarsa. A wajen Aminu ma haka bai rintsa b芒 tunani ne kala kala fal a ranshi, shawara yayi ya sake yafi sau dubu, saidai daga k'arshe ya samu mafita tsayayya wacce yake son tsayawa akanta ko da me hakan zai haifar, dan shima yana son Faduma kuma zai tabbatarwa da duniya shima masoyinta ne na hak'ik'a, babu mahalukin daya isa ya rabashi dashi, tunda har mahaifinshi ma yayi k'ok'arin yin haka amma bai ji ba, dan haka shima a shirye yake da duk abinda za'a fad'a a fad'a zai d'auka. Faduma baiwar Allah ta ci kuka kukan halin da Hasheer ke ciki, ta rasa ina zata saka kanta har tsayawa tayi gaban ubangijin al'arshi dan kai kukanta akan halin da take ciki, amma kuka y'a ci k'arfinta k'arshe sai sujadar ta dinga yi bata iya fad'ar komai a baki sai a zuciyarta. Hasheer ma hakane a wurinshi, tunda ya tashi ya sak茅 shiga wani tashin hankali, tunaninshi ya tsaya cak baya iya tuna komai, yana so yayi kuka da gaske saidai hawaye sun cije sun k'i zuwar masa, gashi yayi kiran Umma ko zaiji sanyi a ransa saidai wayar bata shiga, a k'arshe lambar Faduma ya nemo ya kafe da ido yana tunanin abunyi, jin zuciyarsa na neman bugawa sai kawai ya tura mata sak'o gajere kamar haka _"Ki daure ki sha maganinki, sannan kar kiyi kuka, dan Allah."_ A lokacin da taga sak'on kuka ne kam ya hanata maido masa da amsa, hakan ya k'ara tashin hankalinshi sosai da tunanin ko dai Aminu nada nasaba da rashin maido masa amsar? Tana can tana bacci yanzu? Da tarin amsoshi fal a ranshi da kuma sake jadadda wai shine suka had'a yarinya d'aya da wanda yake kallo kamar k'aninsa Mukhtar kuma ma'aikacinshi, da wannan shima har asuba ta gabato yayi alwala yayi nafilfili kafin yayi sallah subah. *07:00* Agaishat ce ta aiko mata sak'on kayanta danta samu ta shirya kan lokaci, cikin shirinta ta fito cas a lauyarta cikin kamala da nutsuwa inda ta d'aura lafaya fara sai rigarta bak'a ta aiki a sama, k'asa ta sauko cikin nutsuwa, Ayya na zaune a falon da carbi ta durk'usa har k'asa tace "Ayya ina kwana?" Kallonta tayi cike da birgewa dan shigarta ta mata sosai tace "Lafiya lau Fati, antashi lafiya?" Da murmushi yak'e tace "Lafiya lau." Sake kallonta tayi a tsanake tace "Faduma kinsha kuka, idonki har sun kumbura." Sake sunkuyar da kai tayi tace "Ayya rayuwa ke zuwa da haka, shekaran jiya warhaka ina bacci cikin nutsuwa da salama, misalin bakwai da rabi Hasheer ya sameni har d'aki ya bani abinci da kanshi." Zuciyarta ce ta karye sai hawaye sharrr, sunne kai ta sak茅 yi tace "Sai yau na sake tabbatarwa ya min illa sosai, yau naji ina ma dana farka na gansa a gefena, ina ma yana nan tare damu yana kallon fuskata, ina ma tare dashi zan fita a mota yana sakani dariya da tsokanata..." Fashewa ta sakeyi da kuka, cike da tausayi Ayya ta dafata ta zaunar da ita kusa da ita kan kujerar, a tsanake ta kalleta tace "Faduma tunda kina sonshi kema me zai hana ba zaki bashi dama ya aureki ba?" Cikin share hawaye tace "Ayya zanfi kowa farin ciki idan aka ce babban mutum zai zama mijina, managarci ne daya fito daga tsatson managarciyar uwa, ko dan hallacin mahaifiyarsa akaina na sulhunta tsakanina da mahaifina da a baya baya kallon ko fuskata tsayin shekaru takwas zan so ace na saka d'anta farin ciki, saidai Aminu ma wani babban mai hallacin ne da watsar dashi yafi k'arfin iyawata, Ayya a dalilin Aminu nayi karatu cikin salama ba tare da kowane k'alubale ba, a dalilin Aminu ne na zama lauya har nake alfahari da aikina, dalilin Aminu yarona yake walwala kuma har yake rawa ma da bazarshi." D'aga kai tayi ta kalleta tace "Ayya a kowane lokaci Aminu yakan shiga gaba ne ni kuma na bishi a baya saboda tunanin kare min had'arin da zan fuskanta, taya zan iya kallonsa nace bana son sa? Bayan har ya biya sadakina kuma an karb'a." Girgiza kai tayi alamar ba zata iya ba, jinjina kai Ayya tayi tace "Fatima na fahimceki a matsayina na wacce aka haifa, saidai a matsayina na uwa ban ga dalilin da zaisa kiyi auren saka hallaci ba, Faduma inhar abinda ya miki dan Allah yayi banga abinda zaisa shi damuwa dan kince b芒 kya son shi ba, Faduma auren mutumin da baka so ba abu bane mai sauk'i kamar yanda kike d'aukarshi a yanzu, zaki iya k'arar da rayuwarki ba tare da kin tab'a jin wata rana da soyayyarshi ta shiga zucuyarki ba, ko zai dinga lasar k'afarki ya zama kujerar da zaki dinga zama, wallahi idan har zuciyarki bata son shi to fa ba zaki so shi ba, hak'ik'a kyautata na jawo so, saidai ba kowane lokaci ba musamman idan an riga da anyi auren, wanin da zuciyarki ke so ne zai zama shamaki ga duk wani abun alkairi da mijinki zai miki, a k'arshe zaki tashi babu ladar saima tarin zunubi, dan idan baki sonshi duk k'ok'arin na ganin kin kyautata masa wallahi Faduma wata rana sai kin gaza kin hassala akan shi, ko dai kiyi furucin da zai karkare wani kaso na ladarki, ko kuma kiyi aikin da za'a rubuta miki zunubi, ko da kuwa ta hanyar k'iya masa ne akan shinfid'arsa, dan wata rana zaki ji ya isheki ya dameki da buk'atarsa, ko da kuwa ba mai yawan buk'atar bane, har sai ankai lokacin da kai tsaye ba zai kiraki ki zo garesa ba. " Sake kallonta tayi sosai tace " 'Yata, a ganina zaifi kyau ki fad'a masa gaskiya, dan inhar farin ciki yake nema a cikin aure, to babu wani farin ciki a cikin auren matar da wani take so ba kai mijin nata ba. " Ajiyar zuciya Faduma ta sauke, ta gamsu sosai da abinda ta fad'a, amma ta ina zata fad'a ma Aminu bayan kuma tace masa babu komai, a hankali ta kalli Ayya tace "Ayya b芒 wannan ne damuwata ba yanzu, yanda zanyi naga Hasheer nake tunani?" Murmushi tayi tace "Abu mai sauk'i, kinga abun karin kumallonsa nan mai aiki ta ajiye kasancewar Wardugu bai yarda su shigar masa d'aki ba, dama ina tunanin tashi ne kuma kika fito." Murmushi tayi sosai tace "Nagode Ayya, bara naje na dawo." Aje jakarta tayi anan ta d'auki babban farantin ta fita zuciyarta na dakan tara tara da tunanin abinda zai faru, tsaye tayi a bakin k'ofar tayi sallama a matuk'ar sanyaye, shiru taji ba'a amsa ba, wata sallamar ta sake yi a karo na biyu nan ma shiru, a karo na uku ta sake wata sallamar, jin shiru yanzu ma sai ya d'an tashi hankalinta ta fara tunanin ko babu lafiya, wata zuciyar ta tambayeta "Idan fa jikin ne ya sake tashi? Wane hali yake ciki?" Kafin ta samawa kanta amsa sai kawai ta tura k'ofar jikinta har b'ari yake ta shiga, gigigigigi! Farantin hannunta ya shiga yi kayan na neman zubewa, cak ya d'auke farantin daga hannunta cikin dakiya ya sunkuya ya aje shi k'asa sabida table d'in saida ya tashi ya ganshi a tarwatse (Tambayi Wardugu ikon Allah). Ci gaba yayi da goge ruwan jikinshi da knaramin towel d'in, d'ayan kuma mai d'an tsayi daya wuce gwiwarsa yana zaune d'aram a k'ugunsa, wani jiri take ji yana d'ibarta kamar zai kifar a k'asa. Ashe dai zab'en tumun dare tayi, shima dai kayane rufin asirinsa da bai cika saka k'anana ba, amma fa wasa wasa shima gabjejen rigiji-gabji ne, kai ita fa tsoron irin hallitar nan take _(Kwate muje na baki lbrina ni da malaminmu馃ぃ)_, har yanzu jikinta taji bai daina b'ari ba. Fuska a had'e, a matuk'ar d'aure a yanayin da sam bata sanshi dashi ba ya juyo kanshi ya kalleta, murya a d'aure tamau yace "A littafi mai tsarki ma cewa akayi ku koma idan kukayi sallama ba'a amsa muku ba kuma ba'a baku izinin shiga ba to ku juya, hakan shine yafi alkairi gareku." K'afafunta da taji suna mata wani karrrrr yasa ta saurin zubewa ta duk'a a wurin kamar mai gaisheshi, kanta a k'asa kuma ba tace komai ba, d'auke kai kawai yayi ya juya ya shige uwar d'aka, da kallo tabi faffad'an bayanshi har ya shige, kasa tashi tayi a wurin sai kallon yatsunta take da babu zobe ko d'aya sai fari na azurfa wanda Aba ya bata tun sanda ta cinye gasar nan. Ba tare data tashi daga nan ba taji motsin fitowarshi, kafin ta ganshi kuma sai turarenshi ya sake sanar da ita hakan, d'aga kanta tayi gaba d'aya suka had'a ido, saida gabanta ya sak茅 fad'uwa saboda wani kallo da yake mata irin kallon da War yayi mata jiya, k'arasowa yayi kusanta ya tsaya da wayarsa a hannu yace "Me kike jira anan? Kina buk'atar wani abu ne?" D'aga kanta tayi sosai ta kalleshi sai kuma ta fara mik'ewa a hankali, saida ta tsaya da kyau sannan ta sake kallonshi murya na sark'ewa tace "Ina...kwa..na?" A gatsali yace "Lafiya lau na tashi, zaki iya tafiya, nagode da kula." Galala ta kalleshi kamar zatayi kuka tace " *Hash*..." Da sauri ya d'aga mata hannu yace " *Fad*..., kinga dan Allah ki fita anan, mijin da zaki aura fa yana gidan nan, bana so ki jawo k'ananan iskanci a gurin yaro." Nuna mata k'ofa yayi yace "Fita." Juyawa tayi tana sako da hawayenta zata fita, har ta kai k'ofar sai kuma ta tsaya ta juyo, da sauri ta sake dawowa gareshi ta tsaya tare da ciro alk'alamin dake gaban rigarta ta aiki, kamo lallausan hannunshi tayi ta bud'e tafin hannunshi, d'an rubutu tayi kafin ta saki hannun ta kalleshi tana hawaye tace "Wannan shine abinda zai rage maka a game dani, idan har na tafi ba lallai m没 sake had'uwa ba Hasheer, amma ka tuna wannan sunan zai zauna daram a zuciyata dama kaina, kuma ka sani ina sonka so mai tsanani." Tana fad'a ta juya da sauri ta fita, kallon tafin hannunshi yayi sai yaga rubutu ne kamar haka *FadHash*, (grp allura yau zamu shiga uku mu yan FadTag), baisan sanda ya saki wayarsa ba ya fita da sauri, hangenta yayi zata shiga d'akin Ayya yace "Batul." Tsayawa tayi ta juyo da sauri, da sauri ya k'arasa ya tsaya gabanta ko takalmi babu a knafarsa, ido cikin ido ya kalleta da yanayin data sanshi dashi yace "Indai kina sona to me yasa zaki auri Aminu? Saboda hallacin daya miki?" Murya a karkace tace "Bayan haka Hasheer mahaifina ya shiga maganar, ina da yak'ini akanka fiye da yak'inin dana samu lokacin soyayyata da Tagur, saidai ina jin kunyar kallon mahaifina na nuna masa ga wanda nake so." Cikin tsareta da ido yace "Kenan kin zab'i zama da Aminu akan ki fad'awa mahaifinki ba kya son shi? To wane adalci kika wa kanki kenan? Shin kin tabbatar Abanki zaiyi farin ciki da aurar dake ga wanda ba kya so?" Jim tayi tana kallonshi, tabbas yayi maganar da zata iya dubawa, dan ko ranar da sukayi waya da Aba y'a sake fad'a mata cewa _"Faduma har yanzu ina sonki fiye da kowa a cikin 'ya'yana, farin cikinki shine nawa farin cikin, bak'in cikinki kuma shine bak'in cikina, zanyi iya k'ok'arina wajen ganin na k'arasa sauran rayuwar data ragemin da bautar ubangiji na shi kad'ai da kuma kyautata miki da nuna miki tausayina a fili."_ Ajiyar zuciya ta sauke ta kalleshi carrr a ido tace "Hak..." Ayya ce ta katse mata magana ta hanyar lek'owa ta mik'o mata waya tace "Gashi ana ta kiranki, da alama ana gaggawa ne." Karb'a tayi tana duba lambar da babu suna, danna ok tayi ta d'ora a kunne tana kafe Hasheer da ido, cikin sanyin murya tace "Hello." Daga can b'angaren aka ce "Faduma Moliya, lauya mai zaman kanta haifaffar garin Zinder amma a yanzu mazauniya Maradi, uwa ga Amjad Tagur Sugui d'a d'aya da kowa ke rububin samu, kwana sha shida ya rage a d'aura aurenki da abokin aikinki Aminu Mustafa, yanzu haka kina Niamey wurin wani aikin da zaki tabbatar da kaini k'asa, sannan kina rayuwa ne a gidan g茅n茅ral Wardugu Marahut karan farko kin zauna a gidanshi yanzu kuma kina gidan mahaifiyarsa daya fi so da k'auna, Hasheer Abdulkareem Na-kiri kusan a tare kuke tunda kuka shigo garin nan, yanda kike rayuwa da yanda kika dage saikin kinga bayanmu yasa ni tambayar kaina to ko dai kin manta da Amjad ne? Yana ina yanzu haka? Me yake yi? Yana cikin k'oshin lafiya? Ni inada duk wannan amsoshin, amma ke fa?" Wuru wuru ta shiga yi da idonta ta rab'a Hasheer ta wuce tana dafe da saitin zuciyarta data fara mata wani mugun bugu b'al b'al b'al, a razane kuma a kausashe tace "Waye kai? Ina Amjad yake? Me kuke so daga gareni?" Wata dariya akayi daga b'angaren aka ce "Dad'ina dake saurin fahimta, hujojjin da kika tara nake buk'atarsu yanzu, bana so su tunkarin kotun nan ko da wasa, domin kuwa alk'ali *Gukuni* ne zaiyi wannan alk'alancin, shi kuma dattijo ne da baya tsoron kowa da kuma komai, indai har baka da gaskiya kuma hujja ta, bayyana haka, to zaka je gidan maza ko kai shugaban k'asa ne." A kid'ime Faduma dan ita bata san ma waye alk'alin ba tace "Ina yaro na? Karka cutar min dashi dan Allah, zanyi abinda kake so." Murmushi akayi mai sauti tare da fad'in "Da kin kyautawa kanki, yanzu ki tabbatar kin had'a duka hujojjin dake hannunki, ki fito bakin titi ke kad'ai akwai motar da zata tsaya gabanki, ki bawa wanda ke cikin komai, kin fahimta?" Da sauri ta juya zata shiga d'aki tana fad'in "Na gane, na fahimata sosai, dan Allah karku cutar min dashi." Cike da gargad'i aka ce "Ki buda sadarwar yanar gizo gizo zaki ga sak'o na jiranki." Cikin harshen tubanci yace "Faduma kar kiyi k'ok'arin raina min hankali da wasu dubarunki, karki kuskura g茅n茅ral ko Hasheer bare wannan sakaran Aminun wani yaji, idan ba haka ba wallahi d'anki Amjad zai mutu." Cak ta tsaya sanda take fitowa daga d'aki Ayya da Hasheer sai biyarta suke suna kallonta dan sun tabbatar ba lafiya ba, a hankali cikin muryar kuka tace "Dan Allah na rok'eka karka kashe min shi, zanyi duk abinda ka ce." K'ittt taji an datse kiran, da sauri ta bud'e jakarta ta shiga lalubar takardu, tana cirosu ta jefar da jakar ta sake rik'e wayarta ta nufi hanyar fita, Hasheer ne ya rik'o rigarta yace "Me yake faruwa?" Kai tsaye tace "Ba komai, ina zuwa yanzu." Fizge rigarta tayi ta juya, Aminu ne y'a fito daga b'angaren bak'i cikin shirinshi shima, ganinta a gigice yasa shi mamaki da cewa "Faduma lafiya?" Girgiza kai tayi tace "Ba komai, zan dawo yanzu." Ta kai bakin k'ofa duk suka zaburo suna sake tambayar lafiya? Juyowa tayi tace "Dan Allah ku kwantar da hankalinku, idan na dawo zan sanar daku komai, indai har kuna sona to ku zauna a gida kar wanda yayi tunanin wani abu, komai yana lafiya, ku yarda dani." Tana fad'a ta juya ta wuce ta barsu nan, Hasheer da Aminu kallon juna sukayi sai Hasheer daya juya a fusace ya shiga d'aki dan neman wayarshi ya kira War, danya lura sosai kamar barazana ce aka mata da Amjad. *Maradi* Wajen amarya dada da ango Abdallah komai na tafiya daidai, dan an bashi aurenta kuma ya karb'a, yanzu haka shirye shirye kawai sukeyi wanda hakan ya d'auke hankalinta sosai wajen gane wane hali Amjad yake ciki, shi kuma yanzu har fashin zuwa ya tab'ayi saboda sunje yawo shi da Tagur, kullum suna manne a waya suna hirar d'a da uba (dole ne Tagurguri na), a hakane jiya da dare Bureima ya samu labarin tsohon daraja Gukuni ne zaiyi shari'ar yaronshi, hankali a tashe a gigice ya kira Aji, dan in basuyi da gaske ba za'a kulle mishi Tahir kulluwa ta har abada, dan babu abinda zai hana yasha d'auri, k'wararan hujojji daga zak'wak'urar lauya zuwa ga alk'ali Gukuni, ai inhar kasan waye shi dole hantarka takad'a in kasan baka da gaskiya. Ko da ya sanar dashi ya lallab'a shi yace zaiji da komai, shi kuma sai gashi takanas ta kano yaje gidan saboda makircin da yake d'auke dashi. Dukansu sun d'auka ganin Khairat ne ya zo da bata da lafiya, shima kuma daya ga sun d'auka saiya barsu a haka, Khairat taji dad'in ganin Abanta harta kasa barin jikinshi har tayi bacci. Maganar gaskiya kam yaji lallai 'yar nan daga garesa ta fito, dan soyayyar da yake mata ma daban take, ga kuma ita kanta Aisho daya samu cikin riga da siket na leshe, maganar tsafta kam dama k'arya ne yace bata da ita, k'amshi yace ja bani wuri, dan haka a yau yaji duk sun gama d'auresa da tuna masa baya da kuma wata alak'a mai k'arfi da tasirin gaske da ba'a mantawa data shiga tsakaninsu, saida yaje tafiya ne suka tsaya k'ofar gida shi da Tagur suna sallama. Cikin makirci ya tambayeshi "Wai ya Amjad yake ne?" Da tsadadden murmushi a fuskarsa yace "Aji komai lafiya, jiya muna tare da Amjad ko aji bai shiga ba muna yawo, kusan babu entreprises d'ina da ban nuna masa ba, mun ci abinci tare, mun sha abun sha a tare sannan munyi nishad'i." Murmushi yayi yace "Gaskiya naji dad'i, yanzu saura ku kwana tare kenan?" Jinjina kai yayi yace "Shine ya rage, kuma shima ya kusa faruwa insha Allah." Kallonshi yayi da kyau yace "Ai da zaka iya ma da gobe ka d'aukosa ya kwana anan, tunda kaga jibi babu karatu ba zai fita b芒, kuma ga dukkan alama Faduma ta kusa dawowa da zaran ta kammala shari'ar nan gobe." Da mamaki ya kalleshi yace "Shari'a? Dama aikine ya kaita can? Amma ya akayi ka sani?" Duburburcewa yayi ya shiga kame kame yana fad'in "To kai kuwa banda abunka, maganar duniya tana b'oyuwa ne, nima wani ne ke fad'a min ko aiki taje yi" Share zancen kawai yayi yace "In kuwa hakane gaskiya gobe zan d'aukoshi, ni matsalata da Faduma da bata saurarena." Cikin jin dad'i yace "Yawwa hakan yayi, kawai ka d'auko d'anka tunda kana da iko dashi, ai wuri ta samu shiyasa har take nuna maka kamar ita ta ma kanta cikin, amma fa kaji da kyau ko shari'a zaka iya yi da ita akan d'anka." Jinjina kai kawai yayi yace "Insha Allahu zaiyi wannan hutun kwana biyun a gidan nan, karka damu." Hannu ya bashi yana fad'in "Ko da ta nemeka ma ka nuna mata sam baka san inda yake ba, dan kasan ta sani ba makawa zata zo har nan ta d'aukeshi, dan bata wasa akan lamarinshi." Nan ma sake jinjina kai yayi har suka rabu. *Kasancesar* dada zata je Katsina siyayya yasa ta kawoshi makaranta tunda wuri ta aje shi ta wuce, bayan ta tabbatar mishi zata kira Abdallah ya d'aukeshi, saidai tuni Amjad ya kira ubansa a waya ya fad'a masa yana makaranta, yana zuwa shi kuma ya d'aukesa da fad'a masa cewa "Karya damu da rasa darasi da zaiyi, ranar litinin zai kawoshi da kanshi saiya fad'awa malaman wani uzuri ne ya rik'eka." *Niamey* A gigice ta k'arasa bakin tintin ta tsaya tana kallon kowace mota ta wuce, a k'arshe dai bak'ar mota ta tsaya aka d'an sauke glass kad'an aka mik'o mata hannu, mik'a musu tayi gaba d'aya saidai banda wayarta, suna karb'a suka ja motar da gudu ko lamba babu. Tana saman hanyar dawowa ta shiga manhajar sadarwa ta yane, hotunan Aamjad ne aka turo mata da kayan makarantarshi zaune da waya yana game, lumshe ido tayi ta sauke numfashi tace "Allah ya tsare min kai." Da sauri ta k'arasa gidan ta samesu cirko cirko, kallon Aminu tayi tace "Aminu, babu maganar aikin nan yanzu haka, mu gaggauta barin garin nan dan gida babu lafiya, idan kuma baka tashi ba to ni zanyi gaba." Hankali tashe yace "Wai me yake faruwa ne Faduma?" Saida ta nufi shiga d'akin Ayya tace "San sanar da kai a hanya." Tana shiga duk abinda ya rage nata ta d'auko ta fito, kusan Ayya ta k'arasa tace "Ayya ba haka ya kamata muyi sallama ba, saidai bana da wani zab'in, insha Allahu ba zan manta daku ba, kuma wata rana zan kawo muku ziyara." Fuskarta babu alamar jin dad'i tace "Shikenan Faduma, Allah ya yarda, Allah kaiku lafiya." "Ameen." Ta fad'a tana d'an fad'awa jikinta, d'agowa tayi ta saketa ta juya, mik'a hannu Aminu yayi ya karb'i jakarta shima harya d'auko tashi, gaba yayi bayan yace musu "Sa茂 anjima." Kallon juna sukayi da Hasheer daya fito bayan ya kira War, kallo ne dake matuk'ar galabaitar da dukansu yake kuma aika sak'on dake cikin zuk'atansu, a hankali a tausashe sosai tace "Sai anjima babban mutum." Tana fad'a bata jira me zai ce ba tak'arasa bakin k'ofa, suna tsaye suna kallon mai gadin cikin sanyayyar murya Hasheer yace "Bud'e musu." Bud'e musu yayi dan shi dai ko dan yana bak'o ne oho, amma shi a ganinshi kamar uwa d'aya ta haifi mai gidanshi da kuma Hasheer, basu wahala wajen samun taxi ba suka nufi gidan bus dan ba zasu rasa ba tunda har yanzu takwas bata k'arasa yi ba. Sa茂da suka bar unguwar Wardugu ya zo gidan a tsiyace a @360, da sauri y'a kalli Hasheer yace "Tana ina? Su waye suka kirata?" Wani sakaran murmushi yayi yace "Ta tafi, shikenan kawai." Juyawa yayi ya shiga d'akin War ya bishi sai Ayya data bisu da kallo cike da tausayi. *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 21:41 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _59_ Tun kafin su k'arasa gidan bus ta kira dada a waya, cikin nutsuwa murya a sanyaye tace "Dada ina Amjad?" Owwo dake tsaye suna jiran mota ta shirya tashi tace "Amjad ai makaranta na aje shi, wani abu ya faru ne?" Girgiza kai tayi kamar tana gabanta tace "A'a, saidai Amjad baya makaranta, an kirani a waya yanzu har ana min barazana da rayuwarsa, gani nan shigowa garin insha Allahu." Hankalinta idan yayi dubu ya tashi, a gigice tace "Amjad d'in? Ina yake to? Su wa suka d'aukeshi?" Ajiyar zuciya ta sauke tace "Nasan inda yake, idan na zo zan fad'a miki." Cikin tashin hankali tace "To kinga na fasa zuwa katsinar nima, dama zanje siyayya ne dan lokaci gabatowa yake, kema jiya nayi ta kiranki dan naji ko da wani abunda kike so amma shiru, zan koma gida na jiraki ki zo." A hankali tace "To dada, sai na zo." Tana fad'a ta yanke kiran a lokacin sun k'araso, Aminu ne ya isa ya yankar musu ticket sunyi sa'ar samun bus da zata tashi yanzu, basu tsaya komai ba suka d'auki hanya. Wata 'yar leda mai d'auke da cake mai kyau a ido da kuma babban robar lemu 5 alive Aminu ya mik'o mata yace "Komai baki ci ba har yanzu, ci wannan." Kallonshi tayi da idonta da har sun gaji da kumbura, d'An murmushi ta masa kawai ta karb'a dan maganar gaskiya tana jin yunwa, saida ta fara ci kuma saita fara tambayar kanta "Ko me yake yanzu? Ya akayi abubuwa suka canza musu haka kwatsam? Me yasa ta kamu da son shi ita ma?" A hankali taja majina tare da mayar da hawayen dake son taho mata, mayar da kallonta tayi kan titi ta rufe lemun ta daina sha, ta b'angaren Amjad hankalinta kwance yake, dan koma waye ya turo mata hotonan yayi babban kuskure bai kuma santa b芒 farin sani, tunda har yayi kuskuren turo mata hoton da ta iya hangen farar kujera da fararen labulaye da kuma teburin cin abinci a bayanshi ma fari sol da kujerunshi, tasan waye yake matuk'ar son kalar fari, tasan waye ke da son mallakar d'akin da aka k'awata da farin abu, dan haka tasan d'anta na cikin k'oshin lafiya, idan ma wani abu ya sameshi to tasan wa zata tuntub'a. *Niamey* Kiranta daya gani ba k'akk'autawa yasa shi mayar mata da kiran duk da jikinshi na fama da mugun zazzab'i, kamar dama jira take tayi wuff ta d'auka, saida yaji mamaki ganin ta d'auka da sauri haka, ajiyar zuciya ya sauke zaiyi sallama kawai ta fashe da kuka tace "Babe dama abinda kake yi kenan? Abinda ya kaika garin nan kenan? A gaskiya ka bani mamaki fiye da zatonka, wallahi ban tab'a tunanin kana neman mata ba saida naga zahiri, shine kuma harda goyon bayan Wardugu da mamansa ma har kuka tare da ita a gidanta, shikenan naji idan ka dawo kawai ka kai min takardata gidanmu, danni ba zan iya zama da kai ba, ciki ne idan na haife kaje ka d'auki abunka." Tunda ta fara magana ya rufe idonshi yana sauraronta yana jin kamar tana matsa tsawa a kai, gashi kukan nata na tab'a zuciyarshi ga kuma tashin hankalin data kunno masa, b芒 tare daya bud'e ido ba murya k'asan mak'oshi yace "Kina ina yanzu?" Cikin kuka tace "Gani ina had'a kayana zan bar maka gidanka bebe." Da sauri ya bud'a ido yace "Dan Allah Bab karki tafi, ki bari zan dawo yau komai dare, zamuyi magana akai." Cikin kuka tace "Wallahi ka ji na rantse saina tafi, ni zaka zauna kana ci wa mutumci a gari da karuwa, wata bak'a da ita mummuna da bata kaini komai ba, amma da ita kake tozartani." Girgiza kai yayi yace "Bab duk yanda zan kwatanta miki ba zaki gane ba, ki bani dama na zo na fad'a miki abinda yake faruwa mana." Cikin dakiya tace "Duk abinda zaka fad'amin saida ka sameni gidanmu." K'ittt ta datse kiran, d'auke wayar yayi daga kunne ya kalli Wardugu, cikin jimami yace "War ina ga zan bar garin nan yau, na so nayi zamana anan har sanda zan samu labarin aurenta, saidai ba zan zauna anan nayi biyu babu ba, babu Faduma *murmushina*, sannan na rasa Saudat *cikar kamalata*." Kallonshi kawai Wardugu yayi baice komai ba, to shi bai san me zai ce ba, matarsa matarsa ce baisan tsakaninsu ba, dan y'a tashi hankalinshi saboda zata masa yaji shi yasan wacece ita, dan haka ba zai hanashi lallab'a matarsa ba, kamar yanda ko shine ba zai kasa lallab'a tashi matar ba, amma fa idan Agaishat d'insa ce. Shiryawa kawai yayi rana patsal patsal yace zaije gidan War ya d'auki jakarsa ya wuce, sallama y'a wa Ayya suka tafi War da niyyar ya had'ashi da d'aya daga cikin jami'anshi su tuk'ashi har gidanshi, tunda washe garin ranar da suka zo Qaseem ya koma da motar da cewa sa茂 bayan sati d'aya zai dawo d'aukarsa, a motocin ma saiya zab'i waccen ranshi ke so kuma ya tafi da ita har abada, matsalar kawai baya da karsashin da zai iya tuk'i har wani gari. *Maradi* Ko da suka shigo ta kira Dada tace ta fito bakin titi zasu d'auketa, haka kuwa akayi anan adaidaita sahu ta d'auketa dan tuni tace Aminu yaje gida karya damu kawai, ya tafi gidan saidai da kalar tasa damuwar shima, makarantarsu Amjad suka fara tsayawa suka shiga har ciki, shugaban makarantar suka gani ya musu izinin shiga da kuma zama, kasancewar ya santa dan ita ce komai daya shafi yaron yasa shi sakin fuska yana fad'in "Madame kinga kuwa yau d'in nan nake tunnain kiranki dan mu tambayeki muji ko lafiya me yake damun Amjad." Saida ya zauna kan kujerarsa ya aje wasu takardu ya ci gaba da cewa "Dan yau naga bai shiga aji ba jiya ma haka, gashi a kwana uku da suka wuce idan aka fita hutun mintin talatin yakan yi lattin dawowa aji, Allah yasa dai lafiya?" Magana kawai yake amma Faduma tayi sular zaune tana kallonshi, Amjad dai nata? A hankali ta kalli dada ita ma cikin tashin hankali race "Wallahi babu ranar da Aminu baya kawoshi makarantar nan, kuma da kanshi yake maidashi gida." Wani iska ta furzo ta kalli shugaban makarantar tace "Kuyi hak'uri dan Allah, dayake bana gari nayi tafiya, inaga ya tafi wajen dangin babansa ne, amma daga nan can zanje na d'aukoshi." Jinjina kai yayi yace "Ba damuwa madame, saidai a k'ara saka ido akan shi sosai, dan gaskiya malaminsu na math har ya min k'orafi cewa ya rage bawa darasi hankalinshi, kamar yana raba hankalinsa gida biyu, kasancewarshi yaro mai k'ok'ari ya bamu damar saurin gano wad'anan matsalolin, ina fata za'a kiyaye?" Jinjina kai ta sak茅 yi tace "Insha Allahu za'a kiyaye, hakan ba zai sak茅 faruwa ba." Da godiya duk suka fita a hanya dada tace "Amma wannan aikin Tagur ne ko?" Wani murmushi tayi tace "Shine mana, kuma daga nan can zamu je kamar yanda na fad'a." Cikin jin dad'i dada ta cije leb'en k'asa tana jinjina kai, dan har yanzu a zuciyarta akwai wani buri guda uku da take da shi take kuma fatan cika shi yau d'in nan. Adaidaita suka sake tara ta fad'a musu gidan kamar yanda ya tab'a fad'a mata sanda yaje mata da aikin nan, dan duka saida ta tambayeshi har wajen aikinshi ma, kamar tasan wannan ranar zata zo kam. Dake babu irin mahaukacin tsaron nan suna fad'awa mai gadi su k'awayen Aisho ne ya bud'e musu, ai kuwa gadan gadan suka tunkari ciki kowace fuska a d'aure da kuma jin masifa, dan babu waccen zuciyar ba'a wuya take ba. Dada ce ta fara kutsa kai falon tana fad'in "Yawwa ina marasa mutumcin gidan nan suke?" Ko dan yana yammaci ne kusan har gomboy da bata cika zaman gidan ba da Rahila da bata cika zama falon ba ita ma tana zaune, kamar shigowarsu ake jira kuma sai aka fara kiran sallah magriba. Gomboy ce ta kallesu da rashin mutumci sosai tace "Marasa mutumci kuma? Ke kuma wacece? Mahaukaciya ce ke?" D'as d'as d'as Dada ta taka ta tsaya tsakiyar falon, cire lafayarta tayi daga saman kai ta sokata a k'ugu sannan ta kalleta tace "K'amar fitsararriya, bake kika kawoni gidan nan ba, shi waccen babban shaid'anin nake nema." Mik'ewa tayi tsaye ta tunkarota cikin ballin bala'i tace "Ke wanene shaid'anin? Wai wacece ke da zaki shigo har gida kina mana isk..." Tatsssssss! Dada ta d'auke fuskarta da lafiyayyen mari, a tsorace Faduma ta kalleta sai sauran mutanen da duk suka mik'e da mamaki, dafe k'ugu dada tayi ta kalli gomboy data dafe kumci ido rufe tana fad'in "Kai kai kai kai!" Kallon fuskarta tayi tace "Ke ce gomboy?" Da mamaki Faduma ta kalleta, Aisho ce tace "Baiwar Allah ita ce Gomboy, lafiya kika mareta? Me tai miki?" Jinjina kai tayi cikin gadara tace "Nagode, dama a gidan nan mutum uku nake da burin marin fuskarsu, ta farko Gomboy, ta biyu Hatimi, saina uku Tagur, yana ina shi?" Cikin rawar jiki Hatimi ta d'ora hannu a kumcinta tace "Yanzu yarinya saiki mareni? Wacece ke? Me nai miki to?" K'asa da sama ta harareta tace "Cas kuwa zan yankeki da mari, amma ai kin gane wannan ko?" Kallon Faduma duk sukayi sai kuma Hatimi tace "Eh, kamar Faduma ko?" Cikin rashin kunya tace "Cire kamar, ita ce da kanta, ina Amjad yake?" Gomboy ce ta shak'i wuyan rigarta tare da d'aga hannu ta kasheta da mari ita ma, cikin jin zafi ita ma ta shak'i wuyan nata rigar tare da sake gaura mata wani marin, a bazato kawai dada ta kwashi k'afafunta ta zubar a k'asa tare da haye ruwan cikinta, taushe hannunta tayi da gwiwarta hakan y'a bata damar sake sauke mata wasu marukan a fuska tana fad'in "Ni zaki wa iskanci, dama a cike nake dake na fitsarar da kikayi a waccen ranar." Da sauri Aisho ta matso zata rabasu Faduma ta d'aga mata hannu tace "Barsu Aisho, mutanen gidan nan naku basa gane yaren mutane, ina so na fita a rayuwarku amma d'an uwanku na jawoni ciki, akan wane dalili?" Ta fad'a da k'arfi cikin d'aga murya, daga bayansu suka ji tagur yace "Bani nake jawoki cikin rayuwata b芒, rayuwarce ta sake jawomu ta had'e saboda ganin dacewar hakan." Da k'arfi Dada tayi suka daga kan Gomboy da har ta had'a mata jini da majina a fuska tayi kanshi, da k'arfi Faduma ta rik'o hannunta suka kalli juna, giegiza mata kai tayi alamar a'a, sakin hannunta tayi ta matsa gareshi tana kallon Amjad da idonsa suka raina fata yana lab'ewa a bayanshi, fuskar nan ta mahaifiya ta yab'a a fuskarta ba alamar wasa tace "Zo nan." D'an lek'owa yayi ya kalleta, cikin harshensu tace "Nace zo nan." A hankali ya shiga takowa gabanshi na fad'uwa sosai hawaye har sun fara wanke masa fuska, ita kuma sake had'e rai take duk da dai taji dad'in ganinshi cikin tsadadden sutura mai kyan gaske ga kuma kama da ubanshi data fito fili sak. Yana zuwa ta rufe ido ta kaud'e fuskarshi da lafiyayyen marin da duka d'akin saida ya amsa. Da k'arfi ya saki k'ara a lokacin Tagur ya sukwano ya nufo kanta, da sauri ta d'aga kai ta kalleshi ta dakatar dashi da hannu tace "Karka kuskura kace zaka shiga tsakanina dashi, wannan d'ana ne." Kallon Amjad tayi tace "Amjad yaushe ka fara sab'a umarni na?" Girgiza kai ya shiga yi cikin kid'ima a harshensu yana fad'in "A'a Ayya, kiyi hak'uri ki min rai." Kunnenshi ta fizga da k'arfi ta juyar da kallonshi zuwa ga Tagur tace "Ban fad'a maka la fita sabgar mutumin nan ba? Me yake baka dani bana baka da har zaka fara wasa dani?" Wurgashi tayi gefe guda ya fad'i k'asa ta matsa daf da Tagur tana kallon idonshi tace "Me kake so ka koya masa a haka? K'arya da raina ni a matsayina na mahifiyarsa? Akan me zaki shiga rayuwar yaro ka nemi lalatawa? Shekara nawa kasan na b'ata ina tarbiyarshi, lokaci d'aya ka shigo rayuwarshi kana neman ruguza mishi rayuwa, jiya da yau ka hanasa zuwa makaranta, a aji har an fara fahimtar akwai abinda ke d'aukar masa hankali, me kake nufi Tagur? Burinka ka tarwatsa rayuwarshi kamar yanda 'ka ma tawa rayuwar? To baka isa ba, Amjad d'ana ne kuma baka isa ka rabani dashi ba, wallahi na rantse maka idan ka sake had'a hanya dashi saina zama ajalinka idan ya so nima a d'aureni." A fusace ta juya ta nufi inda Amjad ke zaune k'asa yana kuka, finciko hannunshi tayi ta mik'ar dashi tsaye, a rashin sa'a wayar aljihunsa ta fad'o, d'auka tayi da sauri ta kalleshi tace "Wannan fa? Ta uban waye?" Saboda ya gama tsorata da sauri yace "Aba ne ya siya min." Juyawa tayi ta kalli Tagur ta d'aga wayar da iya k'arfinta ta jefa masa sai kuwa a goshi ji kake kamatsss (馃槀), a hassale tace "Bama buk'ata, sanda muke buk'atar taimakonka baka taimaka mana ba sai yanzu da muke tsaye kan k'afafunmu." Fizgar Amjad tayi suka kai daf da Tagur, kallonshi ta sakeyi tace "Ko sau d'aya ne ka gwada sanin darajar d'an adam da kuma d'abi'unsa." Tsaki taja tare da hararenshi sama da k'asa, har sun kai k'ofa Dada na masa gwalo tana haraarenshi, a hassale ya d'auke hannunshi daga goshinshi dake fitar jini yace "Amjad d'ana ne, kinsan haka nasan haka kowa ma dake nan ya san haka, dan haka zan karb'esa ta k'arfin ikona, tunda har kin kasa fahimtar haka ta lalama, to ki shirya amsa kiran alk'ali dan zan karb'i d'ana ta hanyar shari'a." Wani malalacin murmushi tayi ta kalleshi da kyau tace "Banyi musun Amjad d'anka bane, amma a dokance ma Amjad zai zama d'ana ne, Tagur ina zauna ina jiran sammacinka idan har ka cika d'an halak, ni Faduma moliya zan tsayawa kaina a gaban kowane alk'ali ne a fad'in duniyar nan akan yarona Amjad, kaji da kyau." Tana fad'a ta juya suka bar gidan zuciya na tafasa, Gomboy dake kwance ce iskanta suka motso dan dama ta jima dasu, haushin abinda ya faru ga jini da Faduma ta fitar masa sannan ta k'ara da cewa idan shi dan halak ne, hakan ya masa zafi sosai. Su Aisho nata k'ok'arin rik'eta ya taho a fusace ya turesu, had'e hannayenta yayi duka biyun ya shiga marin kumatunta yana fad'in "Zaku kwanta? Zaku kwanta nace? Kwanta..." Haka gomboy ta ci bak'ar azaba har saida Hatimi ta mata hawaye babu wanda yace k'ala har ta zube kwance kamar gawa shi kuma ya fita, sam y'a manta da sallah magriba na saman kanshi haka ya tunkari ofishin Aji dan fad'a masa abinda ya faru da kuma tabbatar masa zai kai k'ararta. Sanda ya shiga ofishin suna waya da Bureima, yanda ya shigo kai tsaye yasa shi saurin aje wayar dan dama yana nuna masa basa shiri sosai da mahaifin nashi saboda rabuwarsu da Aisho, kuma haka kowa dangi ya d'auka, amma a b'oye alak'arsu suke ta d'a da uba harda wacce ma abokin banza da abokin banza ne ta kamace. Duk abinda ya faru ya fad'a mishi a hassale, shi kuma cikin farin cikin hak'arsu zata cimma ruwa ya sake zugashi ai karya yarda ta raina masa hankali ma shi da yaronsa, da wannan suka rabu bayan ya tabbatar mishi shi zai had'a shi da lauyen da bata isa ta ja dashi ba. _______________ Suna zuwa gida k'ofar d'akinshi ta nuna mishi tace "Kama min kunnuwanka a wurin nan har sanda zan fito." Baiyi musu ba yayi abinda tace sai Dada data bita d'aki tana fad'in "Faduma kiyi hak'uri dan Allah, nima da laifina haka ma Tagur, amma banda baida laifi yaro ne, kawai yana son kasancewa da ubanshi ne, kuma kinga baisan komai ba dole ya yarda da duk abinda ya fad'a masa akan ki." Juyowa tayi da sauri tace "Dada nima ban ce yana da laifi ba, babban takaicina shine yardar da na masa, na yarda Amjad ba zai iya aikata kuskure mai girma irin haka ba, amma dubi abinda ya min." Wani kallo dada ta mata tace "Faduma, Amjad ne kike kiraranta laifinsa haka kamar wani babba? Ko dai akwai abinda yayi bayan wannan?" Shiru tayi tana kallon dada sai kuma ta fad'a kan knaramin gadonta tare da sauke ajiyar zuciya, har ga Allah in gaskiya zata fad'a zafin daga zuciyarta yake tasowa, kuma ciwo ne da yayi kama da irin ka rasa wani abun nan ranka a b'ace matuk'a, a hankali ta girgiza kai tace "Ba komai Dada." D'aga kai tayi ta kalleta tace "Yanzu ya maganar shirye shiryen?" D'aga gira tayi tace "Abdallah ya sakoni gaba Faduma, wal'ahi mutumin nan rugimarsa kamar ta d'an da aka cire daga nono, kinga dai shiga kiyi wanka ki fito zaki sha labari." Mik'ewa tayi tana murmushi tace "Ai babu labarin da nake son ji kamar yanda akayi mutumin nan ya warci zuciyarki, abun nan ya ban mamaki, yaron da kike fad'in zaki ci..." Da sauri dada tace "Rufa min asiri Faduma, ai yaron nan d'anyen kai ya nuna min ya fini, ke haukanshi ya dame nawa ya shanye." Dariya kawai ta shiga yi tana cire kayanta dan shiga wanka, d'orawa Dada tayi da fad'in "Kinsan da jibi zamu bar garin nan tare dake, dan su kawu sun ce maza mu koma can indai ba muna so mu nunawa mazan namu mun isa da kanmu ba." Kallonta tayi tace "Jibi dada?" D'aga mata kai tayi, cike da damuwa tace "Amma fa kinji me na fad'awa Tagur, wallahi sai nayi shari'a dashi tunda ya raina mutane." Cikin rarrashi tace "Faduma shari'a idan aka tashi yi ai ko a ranar zaki zo kuma ki koma." D'an kyab'e fuska kawai tayi ba tace komai ba sai fita da tayi falon ta shiga ban daki. ________________ A wurin Aminu ma ko da yaje gida a gaggauce ya shirya yayi sallah, bai jira ba da kanshi ya sameshi bakin babbar kasuwa sukayi magana, sanda ya fad'a mishi abinda ke tafe dashi sai yaji jikinsa yayi sanyi ya tsorata da irin son da yake ma yarinyar, kuma abinda ya fad'a masa yana niyyar yi idan yayi shi ko shi dake ubanshi zai gane shayi ruwa ne bare kuma shi, domin dai a matsayinsa na d'an kassuwa yasan waye Abdul Rahaman Nakiri da kuma babban d'ansa Hasheer. Saidai kawai ya tayasa da addu'a dan mutum in yayi nisa baya jin kira, amma fa yana jin d'an marayan nan nashi. Da sassafe ya dokawa Mukhtar kira a waya, saida suka gaisa cikin zolaya kamar yanda suka saba kafin yace "Mai gida wani taimako zaka min, lambar g茅n茅ral nake nema abokin Elhaj?" Cikin zolaya Mukhtar yace "Kayya sire, sojan mazan fama zaka ce, in baka da gaskiya zaka had'u da Wardugu nemi audigar mata kayi k'unzugu, dan in bakayi zawo ba kayi fitsari a wando." Dariya Aminu yayi sosai yace "Wannan kirari haka shi kad'ai?" Cikin fara'a yace "Ai indai wardugu ne yafi haka, kai mutumin nan fa ina ga baifi sau uku dana tsaya gani gashi ba, dan wallahi mugun tsoronshi nake ji." Cikin ajiyar zuciya yace "To yanzu zaka samo min, ko kuma na nema a wuni wurin?" Da fara'a yace "A'a kai ma zan samo ai." A hankali yace "Amma fa karka bari Elhaj ya sani." Da sauri yace "Baka da damuwa ai." Da haka sukayi sallama ya masa godiya, a k'alla an samu awa biyu kafin ya tura masa lambar ta sak'on sms, sak'on godiya ya sake tura masa kafin ya saka lambar ya kirashi saidai a zuciyarshi banda bugu babu abinda take yi. Sanda ya sanar dashi abinda ke ranshi a game da faduma, Wardugu yaji ina ma yaron nan yana gabanshi ne da sai ya hau saman benen da yafi kowane tsayi sannan su rikito tare duk sun mutu, saidai a hankali ya dinga kwantar ma kansa da hankali harya samu nutsuwa ta dawo masa, yayi na'am da abinda ya fad'a ko dan ganin hakan shine maslaha tunda ya riga ya biya sadakinta, ko a addinance haramun ne wani yace zai nemi aurenta. Cikin mutumtawa sukayi sallama War kuma ya kira Umma ya sanar da ita, dan kamar yanda Aminu ya fad'a yana jin nauyin tunkarar Hasheer da maganar Faduma, shima Wardugu hakane a wurinshi, dama albishir d'in aurenta zai mishi wannan saiya tunkareshi. Sanda Umma taji labarin nan ita kanta sai abun ya jijjigata, amma sai bata nuna ba a fili ma farin ciki ta nuna na ganin kyautatawar Aminu da bai nuna halin k'urciya ba sunyi wa juna terere, duk da tasan Hasheer nada halin girman da b芒 zai shiga shirginshi ba, ita ma a cewarta zata tuntub'i manyanshi wanda zasu iya tsawatar mishi da ba ita mace ba, dan alamu sun nuna wannan matsalarce ta kai kunnen matarshi har ta masa yaji. *Zinder* A tare Aba da yaya Kalli da yaya Manu dasu Barka suka kalli Alhaji Mustafa da kuma dattawan biyu, kallon da Aba y'a ma Kalli yasa shi sunkuyowa cikin kunne ya masa rad'a, jinjina kai yayi kafin ya kalli Alhaji Mustafa, a ransa kawai yake ayyana duk da shine ke da 'ya mace amma zaiyi yanda suke so saboda zaman lafiya, maganar aikin Faduma tunda haka suka ce to ta barshi har abada, d'aura aurenta kuma da suka buk'ata zuwa gobe da azahar shima ba matsala sun d'auka, cikin dattako shima yace "Mun amince, Allah ya tabbatar mana da alkairi." Da farin ciki suka amsa da "Ameen." _______________ A wajen Faduma tun jiya tasha hira da Dada akan abubuwan da suka faru, sun jima suna hira kafin ta zauna da Amjad ma ya fad'a mata komai daga farko har k'arshe, girgiza kai kawai tayi na takaicin tunanin inda k'walwar Tagur take, shi fa ta lura irin mutuanen nan ne kamar alawar dank'o, inda aka jasu can sukeyi babu nazari. Daga nan take ta fara tunani akan matsalar data tunkarota yanzu kam, dan ya zama dole tayi nasara sannan ta haska mishi duhun dake gabanshi. Daga yaya Barka har Abdul sai gashi tayi waya dashi tana neman k'arin bayani akan waccen ranar data wuce shekaru tara kenan, inda ta sake tabbatarwa kanta Tagur baya da hankali shine data kirashi a waya da safiyar nan, yana d'auka yace "Kin gane ba zaki ci riba ba kenan kin dawo muyi sulhu." Cikin dakiya tace "Ba wannan magaanar Tagur, ai shari'a dani da kai akan Amjad daga nan har bayan duniya zan iya tunda ina da masu tsaya min." Wata dariya ya mata yace "Masu tsaya miki? Ke d'in? Su waye wad'anan?" Wani murmushi tayi tace "Amma dai ai kasan alk'ali Gukuni ko? Sannan kasan waye g茅n茅ral Wardugu? Haka kuma kasan mai masana'antun risham? Kabi a hankali Tagur." Cikin sanyin jiki yace "Su d'in menene d'inki?" Cikin shak'iyanci tace "D'aya kakana, d'aya yayana sai kuma saurayina." Shiru yayi yana sauraronta, tabbatarwa da tayi ta d'aureshi sai tace "Ranar da zanje gidanku a waccen ranar bayan 'yan gidanku akwai wanda ya sani ne?" Cikin dakakkiyar murya yace "Babu." Kai tsaye tace "Alhaji Bureima yana cikin masu farin cikin aurena da kai ko kuma a'a?" A dak'ile yace "Yana son abinda nake so, shi yake tayani lallab'a iyayena akan su barni na aureki." A bazata dan ta bugi cikinshi dan daga bayanan data samu a baya ta fahimci akwai wani abu tsakanin saurayin nan daya bashi shayi da kuma Aji, a hankali tace "Baka san gaskiyar ba, ka tuntub'i ayyarka ta fad'a maka wanda ta fad'a ma zan zo gidan a ranar nan." Jin baice komai ba yasa ta cewa "Ka daure ka kirani idan kunyi magana da ita." Datse kiran tayi shi kuma ya aje wayar ya tashi ya shiga bangarensu yana kiran Hatimi. Wannan shine ya tabbatar mata kan Tagur yafi guda d'aya domin kuwa sake kiran nata yayi bayan ya matsewa Hatimi wuri ta fad'a masa gaskiya, farin ciki ga Faduma bak'in ciki ga Tagur. Sun idar da waya ne Dada ta shigo da k'atuwar leda ta aje tana fad'in "Kinga wannan wani ya kawo yanzu wai inji Elhaj wai aba wa Amjad." Da sauri ta sauko daga kan kujerar ta shiga zazzage ledar, kayan sojawa ne kala kala na yara masu kyau da takalma na ball da sauran kayan yara, murmushi ne ya kubce mata tace "Allah sarki babban mutum, ni har na manta da kayan nan ma, ashe shi bai manta ba." K'wala kiran Amjad tayi dake d'aki ko islamiyya bata kai shi ba, nuna mishi kayan tayi ya shiga murna da yi mata godiya. Kiran Kalli ne y'a shigo wayarta ta d'auka suka gaisa, a tsanake cikin harshen tubanci yace "Zuwa gobe da safe duk abinda kike ki barshi ki taho akwai dreba da zai zo ya d'aukeki, kin gane?" Kamar zatayi kuka tace "Amma yaya Kalli..." Dakatar da ita yayi yace "Karki ce komai, hakan mijin da zai aureki ya buk'ata, dan baya son wani abu da zai kawo muku rud'ani, ni kuma Aba ne ya wakiltani na fad'a miki." Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi tace "Shikenan, Allah ya kaimu goben." Aje wayar tayi tana turo baki ta fad'awa dada abinda ke faruwa, ita kam farin ciki tayi ganin zasu bar garin nan tare in ya so kuma su dawo tare domin tarewa d'akin mazajensu. *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 21:41 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _60_ Misalin 07:30 ciff dreban ya zo ya d'aukesu bayan an d'orawa wata motar kayan su na anfani, motarta ma d'auketa akayi Kalli yace zaisa a kai mata ita idan mijinta ya so hakan, wannan karan tafiya harda Amjad, yana kwance jikin dada faduma da waya a hannu tana ta k'ok'arin tambayar duk wani data san zai iya bata amsa akan abinda ya shafi Tagur da ahalinsa, saidai fa dauriya kawai take amma gabanta fad'uwa yake, hirar dada da angon nata ne ma ke sakata nishad'i da murmushi ko ta girgiza kai. ________________ Tun daren jiya daya shigo ya so yaje gidansu, amma zazzab'in dake neman zama jikinsa ya hana masa sukuni sai kuma yara da suka baibayeshi suna murnar Abansu, shi dai bai hantaresu ba bare kyararsu, kallonsu kawai yake da ido yana tuna sune silar had'uwarshi da ita, gashi abu k'ank'ane ya zama babba haka, soyayyarta na neman halakashi, baisan ya zaiyi bane da rayuwarsa, haka kawai yake jin abun yana k'aruwa madadin raguwa, shidai ya yarda Allah ne yake saka so a zuk'atan bayinsa, kuma shi kawai ke iya cirewa a sanda ya so, badan haka ba daya cire ko dan ya sararawa kansa, tunda dai zatayi aurenta ita ma, kai ko dan 'ya'yansa da matarsa ma dole ya cire dan karya shiga hakk'insu dayawa. Wanka kawai yayi bayan ya had'asu da tsarabarsu ya rakasu wurin Salima dan ya bar Halima da saurayinta a k'ofar gida ta masa rakiya. Da safe yayi ta kiranta amma bata d'agawa, duk da ciwon da kanshi keyi ga zafin jiki haka ya shirya tare da Qaseem ya kaishi gidan, ba laifin gidan ba zaka kirashi tsoho ba, saidai ba sabo bane ba kuma babba bane, abun takaici shine daya shiga ciki suka gaisa da mahaifiyarta a mutumce take fad'a mishi wai bata nan ta tafi asibiti, tunda ya tambaya wace asibiti tace bata sani ba yasan da had'in bakinta, sallama ya mata kawai ya fita ita kuma ta bishi da harara da gunguni na ganinshi kamar mai zalintar 'yarta. Har k'ofar gida aka saukesu, fitowa sukayi suna kallon k'ofar gidan, dada ce ta kalli dreban tace "Ka jirani na fito saika kaini gidanmu nima." Murmushi Faduma tayi suka shiga ciki da sallama dan dama ba soro ne a gidan ba, da gudu da kuma shewa da murna aka tarbesu har suka kasa gane su waye ma, su ma farin cikin suka shiga yi kawai saida suka sakesu daga rumgumewar da suka musu kafin suka kalli juna, a hankali Faduma ta fara murmushi a fuskarta dan ta gane wasu wasun kuma kama kawai take gani, bayan aunty Aleeya da aunty Zeinab, matar Kalli *Rashida* sai matar Manu da bata santa ba da kuma matar Barka da sauran yarensu. Ta gefe d'aya kuma iyaye ne bayan ayyoyinta biyu sai yan uwan ayyarta dukansu hud'un da kuma Nana surukuwar Barka da sauransu. Masha Allah sun ga tarba da tsantsar farin ciki a fuskokin kowa, har dada kanta ta kasa tafiya duk anan suka zauna kamar za'a had'e juna, Amjad kamar za'a cinyeshi, daga 'yan uwan nata zuwa iyayen da suke tsokanarshi da mai gidansu har Aba kasa b'oye k'aunar da yake ma yaro yayi saida ya nuna, wasa wasa dai haka suka k'arar da lokacinsu da hira cikin nishad'i da farin ciki, sai yamma lik'is suka fara barin gidan har da dada ma, sannu sannu sai gidan ya zama shiru daga ayyoyi biyu sai Faduma sai Amjad da Aba ya jashi zuwa masallaci cike da alfahari. Yayi murna sosai yanda tunda suka fita duk wanda ya tsaya yana gaisawa dashi sai yayi saurin gaisheshi a ladabce, kuma baya k'urawa mutum ido yai ta kallo sanda suke magana, hakan ya burgeshi sosai har ya tuna da zuwan matar nan mai dattako data shirya tsakaninshi da 'yarshi. Ta samu damar yin wankan tsarki ta gabatar da sallah isha'i, sun ci abinci kwano d'aya da yaya Barka da Aba da kuma Amjad, daga bisani suka sha hirarsu suma har suka kwanta babu wanda yace mata ga abinda ke faruwa. *Asabar* Tunda suka tashi yaran wajen yaya Kalli suka warci Amjad sukayi gaba, ita dai mamakin hidindimun dataga anayi kawai take, har rana ta take sosai saida taga gidansu ya fara cika da dangi fiye da zuwansu jiya, a k'arshe dai Herde ce ta mata umarnin shiga d'akin matar Barka ta zauna acan, yanda akace tayi haka tayi saidai gabanta fad'uwa yake har yanzu. Bata san meke faruwa ba saida 12:00 rana taji muryar Kalli a tsakar gidan yana maganar d'aurin auren k'anwarsa ne nan da awa biyu, saida ta suma a wurin na awa biyu kafin hayaniyar mutane ta dawo daita hayyacinta. K'arfe d'aya da rabi na ranar Asabar anguwar su Faduma ta fara d'aukan harama, mutanen anguwar sit茅 Soraz na ta b'ib'ilowa ta waje waje suna samun matsuguni a wajen da aka kawata da shinfid'u na alfarma da kujeru sosai, kai kana ganin irin yanda aka k'awata wajen da runfuna har biyu tafka tafka na tarbar baki dan su samu mafaka a k'asan runfunan zaka gane bikin nan na 'yar gata ake yi. K'arfe d'aya na ranar jiragen sojoji suka ringa sauka har k'waya uku, sai kuma jirgin yawon daya sauke jama'arsa. Cikin wata dakakkiyar shadda kalar ruwan sararin samaniya ya fito daga d'aya daga cikin jiragensu fuskarsa d'auke da bak'in gilas. Bai zame ko ina ba sai gaban abokinsa abokin aikinsa kuma ya ja ya sara masa kamar yanda shima ya sara masan hakan yasa suka saki murmushi a tare kafin su gaisa da juna. Irin tarin sojojin daya ga ya zo dasu du an tsatsare hanyar kamar wani shugaban k'asa zai sauka ya saka shi sakin murmushi a fili yace "Kar dai ka ce min kun tsayar da shige da ficen al'ummah dan kawai zamu shiga gari?" Kansa ya shafa yace "Haba oga, ai ko motar wa ta fito a yau zata yi hak'uri mu jera kwanon tafiar nan mu je har inda muka dosa dan kuwa k'asa muke da ita ba wani ba!" Wani murmushin yayi masa sannan ya kai dubansa wajen jirgin da mutane ke ta fitowa wad'anda zasu sauka a nan kenan. Walyn ce ta fara fitowa, Hajia Walyn kenan cikin kwalliyar nan da aka saba sai walwali ake hannunta rik'e da tafkekiyar wayarta har ta idasa sauka. Ayya ce ke ta k'ok'arin gyara lafayarta tana magana tana d'an juyawa baya hakan ya saka shi k'ure wajen da take d'an juyawa bayan da ido dan ya san da cewa itace zata fito. Ai kuwa saida ya k'ara kallonta, sai kawai yake ji a k'asan zuciyarsa wannan lafayar da ta saka aka kawo mata daga saudiya zata lafe mata a wad'annan kayan nasa ta saka shi a uku. D'an gyaran murya yayi ya kai dubansa wajen dakarun mazan dake tsaitsaye bayan sun sara masa. Fuskarsa tamke a ransa yana ayyana 'yan k'wal uba duk da kayan soja zaku masu dirar mikiya k'ofar gida haka kawai?. A fili kuwa saiya k'ara had'e fuskarsa sosai ya d'aga muryarsa dake dake ya basu umarnin kowa ya je cikin mota su fara tafia. Da gudu gudu kowa ya nufi matsuguninsa a cikin motocinsu, shi kuwa ya rage muryarsa sosai ya ce "Aboki, hak'uri fa zakayi ni zan tuk'a Hajia gaskiya." Murmushi yayi ya mik'a masa key d'in dalleliyar motarsa yana nuna masa ita fara k'al sai walwali take abinta. Juyawa yayi ya k'arasa wajensu, su ukun a tsaye , yana isa da dabara yake kallonta k'asa k'asa, ai kuwa shi dai ya ha kayansa a fili dan kuwa a rayuwarsa baya son lafayar nan ta lafata a jikinta ta shiga duban jama'a. Motar ya nuna masu yana k'ara tamke fuskarsa, Ayyah ta kalli fuskar tasa da kyau ta yatsine tata ta daga k'afarta ta nufi wajen motar. Baya suka shige Ayya da Walyn wace bata yi zaton shi zai tuk'a su ba, saida ta ga fuskarsa tamke ya nunawa Agaishat gaba sannan ta yatsine bakinta (Mai hali馃榿). Tuk'i yake yana gannin yanda aka tsatsare hanyar nan sosai kama tun daga aeroport na garin Damagaram suka ringa ratsawa suka biyo ta Post, suka gangara da motocinsu suka d'auki hanyar wajen rond point, haka suka dirfafa suka d'auki hanyar tashar Agadez suka mik'a a babar hanyar dake kaika cit猫 Soraz har suka k'arasa. Tunda anguwar ta d'auki jiniya jama'a suka k'ara zuba ido dan ganin me ya kawo masun garin wajen? Ai kau sun ga tarin taron dakarin sojoji, nan da nan yayunta da mahaifinta suka mimik'e suma suna kallon mutanen sai gyagyara kujerun zama suke abinsu ama kuma ba wanda ya zauna suna jiran Wardugu ya fara fitowa. Kansa ya gyad'a a hankali yace "Ayya, yanzu fisabilillahi a haka zata shiga cikin gidan ne? Dubi fa lafaya ta nad'a fa." Ayya ta kama hab'arta da mamaki da yaren buzancin data koya a wajen su Agaishat da Alhinayett tace "Wardugu ka kiyayeni na rantse maka, to lafaya ba itace sutura ba? Ai ita lafayar ta saka ita 'yar uwarta ba lesh ta saka ta yi makup ba? Kana iya kulleta a motar har ta suma kafin a gama d'aurin auren!" Agaishat dake k'ik'ifta ido ta saci kallonsa ta ga yana zabga mata harara sai ta sada kanta k'asa sosai tana tunanin halin kishin Wardugu, shi yasa fa ta k'i saka shada ko lesh ta fito sannan fuskarta ba kwalliya ko dis daidai da turare mai sasaukan k'amshi ta saka dan kiyaye rigimar uban gidan nata ama da alama ya shak'a, ita kam ba zata biyan shi ba. K'asa k'asa yace "Gaishu na gode, ba dai ba ni? Ba dai ni ba Gaishu? Shine kika d'ad'ame abin kika fito ko? Na rantse maki sai na maki ciki a yau!" Fuskarta ta takwakwafe tana kallonsa ya bud'e masu motar Ayya ta fita tana tura baki haka ma Walyn tana amsa wayar k'awarta da zata zo su gaisa, da sauri Agaishat ta kamo hannunsa cikin nata tace "Yi hak'uri Abul Umi, ba zan kuma ba ka ga fa ba d'aurin da baka so ba na yi, karka min ciki yanzu na rok'e ka." Murmushi yayi ganin yanda ta shagwab'e fuska, a ransa ya ayyana matsoraciyata, sai kuma ya kanne mata ido d'aya ya fita ya zagaya ya bud'e mata k'ofar. A gaskiya duk an cika da mamakin irin kulawar da bak'ar mace ke samu a gaban wannan tsadaden gayen, gasu dai tafiar harda uwar gidansa, sai dai irin yanda du motsinta na kan idanuwansa ke bayar da mamaki, hakan kuwa ba komai bane sai rayuwa ta fahimta dake tsakani, biyaya , sadda kai, zubar da kai a gaban miji ba kasawa bane, hakan da Agaishat ta kama ne ya saka Wardugu baya iya kaucewa idanuwansa a kanta, aljihunsa na kanta, lokacinsa na gareta, a haka har suka shige cikin gidan kafin shi kuwa ya nufi wajen mahaifin Faduma. Abin mamaki irin tarbar da Mahaifin Faduma ya yi masa, sosai Wardugu ya rage tsayinsa kansa sade sannan ya mik'awa mahaifin Faduma hannu sukai musabaha kafin ya amsa masa gaisuwar hanya da iyali. Wani murmushin ne ya ringa saki ganin tarin jama'ar da suka halarta daga b'angaren angon da suka zomawa kama daga oncles d'insa, da abokanansa, da yan uwansa na jini duk da ya san akwai gayyar auta a ciki, amma jama'ar sun faranta ransa. Ido hud'u sukai da Aminu dake tsaye cikin dakakkiyar shada yana fitar da annuri a fuskarsa yana sakin murmushi, shima murmushin ya sakar masa yana jin girman yaron a ransa, lallai yaron ya ciri tuta mai karfin gaske kuma halayensa sun saka yaji shi har k'asan zuciyarsa. Harama aka fara, du wa'inda suke da ruwa da tsaki a harkar d'aurin auren suka marmatso, kai harta yan gulma sun matso sun kasa kunne dan ganin wai ma da waye za'a d'aura auren nan mai tarin jama'a masu fad'a a ji a Niger? irin wad'annan dakarun sun saka da yawa shan jinnin jikinsu, da yawa sun kasa sun tsare gannin k'waf suke son yi gannewa idanuwansu, wai shin Fadumar da ta shekare shekaru bata gida ne ta ciro tutar nan ta dawo har mahaifinta yayi wannan taro dominta har Allah ya tara mata kasa ta hanyar tara mata tarin jama'a haka??? A lokacin da marok'i ya d'aga muryarsa ya ringa sanar da a nutsu za'a gabatar da d'aurin aure a lokacin ne Faduma ta kifa kanta a gefen kafad'ar Agaishat ta fashe da wani irin kuka mai cin rai har tana jin zuciyarta zata buga, da k'yar take janyo numfashinta tana k'ara yin wani hak hak hak tana taune leb'enta muryarta cen ciki ta k'ara damk'ar hannun Agaishat dake murmushi tace "Agaishat kar su d'aura, kar su mallakawa wani ni bayan yana raye, Agaishat kar su tarwatsa min zuciyata, mutuwa zanyi Agaishat wallahi." K'ala ba tace mata ba sai shafa kanta da tayi tana jin kamar ta tayata kukan ita ma, Umma da ita ma ta biyo jirgi ta zo yau tana gefenta, hannunta ta rik'e tana matsawa saidai babu wanda yace mata komai, Walyn dake ta b'ata rai tana yatsina fuska ita an zaunar da ita wani banzan d'aki da ko ac babu, hararansu take da wutsiyar ido tana jiran k'awarta ta zo ta kwasheta suyi gaba, dan ba zata zauna kallon takaicin nan ba, ba ma kamar Agaishat data ga tana ta nanik'ewa yarinyar, ko dan kalarsu d'aya ce tarin bak'ak'e oho (Kakale dan Allah fada min sunan matar nan a voice naji). Rugugin muryoyin maza ne suka ji sun amsa da *Fatiha*, hakan ne yasa Faduma damk'e hannun Umma sosai ta sake tusa kanta jikin Agiashat tana fad'in "Shikenan Agaishat, sun halakani, sun kasheni a tsaye, me yasa iyayena suka kasa bani damar sake ganinshi kafin su d'aureni da igiyoyin wani? Na shiga uku ni Faduma." Jawo kanta Agiashat tayi ta d'ora kan cinyarta tana daddab'ata kawai, a na biyu ma suka ji an sake shafa fatiha haka na uku, muryar sank'ira suka ji yana kwaroroton "Alhamdulillah, aure ya d'auru tssakanin *Faduma Bintu Moliya* da kuma angonta *Elhaj Hasheer Abdul rahaman Nakiri*, Allah ya basu zaman lafiya..." Da sauri ta d'ago ta tsare Agaishat da ido, me zasuyi 'yan d'akin sai kawai suka bushe da dariya har da k'anwar Umma da suka taho tare Hajia *Marfu'a*, wata irin nutsatsiyar kunya ce tasa ta mayar da kanta cikin lafayar Agaishat tana saka kukan shagwab'a, duka Ayya ta kai mata tana fad'in "Ja'ira, da ana so ake kai kasuwa." Girgiza kai tayi a hankali tace "Faduma yaron nan d'an albarka, daga shekaran jiya da kuka taho zuwa jiya ya shiga ya fita har saida yaga an d'aura auren nan naki da wanda zuciyarki take so, shima ya fahimci babu farin ciki a cikin auren matar da kake da tabbacin bata sonka, bugu da k'ari kuma kasan wanda take so." D'agowa tayi da sauri tace "Ayya ina Aminu? Ina so na ganshi idan da hali." Murmushi Umma tayi tace "Nima zan so haka, bari nasa Wardugu ya turo mana shi." Ayya ce tace "Kafin nan ta nemi izinin mijinta dan ya lamunce mata magana da wani." Dammm! Taji gabanta ya fad'i, Hasheer? Wanda suka rabu kwana biyu da suka wuce? Cikin jin kunya ta sunkuyar da kanta tana jiran taji inda zasu tsayar, Herde ce ta shigo da farantin abinci tare da wata tana ta rangad'a gud'a suka aje suka fita. ______________ Yau dai kawai Allah ya yassare mishi samun kuka na gaskiya da gaskiya, ba kuma komai ya janyo haka ba sai ganin Mukhtar cikin shiri kuma yace mishi zaije d'aurin auren Aminu Zinder tare dasu kawu Kabiru da kawu Saddi, yayi tunanin me ye na ujilar sai an aurar da ita haka? Me yasa aka rage yawan kwanakin kuma? Sai kawai ya kifa kanshi a sitiyarin motar daya fi so yanzu Corolla yasha kuka ya gode Allah, daga nan kuma gidansu Saudat ya nufa dan wallahi neman wacce zata rarrasheshi yake ido bud'e. Duk da baiso ba amma dake mahaifinta dattijo ne haka ya mushi iso zuwa d'akinshi, da kanshi ya turo masa Saudat ta same shi anan, da mai hankali da lura ce k'arara zata hango tashin hankali da tallafin da mijinta ke nemanta, saidai ina baki ma ta shiga botsarewa ita a dole ya b'ata mata rai, idonshi jajir dasu sun kumbura haka ma hancinshi tsabar murzashi da yake, amma bata lura duk da wannan ba sai zama da tayi akan kujera kusa da inda yake zaune. Ganin haka da kuma neman agajin wani da yake yasa shi sake matsowa kusanta ya d'ora kanshi a kafad'arta, cikin muryar kuka da tausayi da tsuma zuciya ya shiga fad'in "Bab kiyi hak'uri ki dawo gareni, karki bari a rabani dake kema, wacce kike b'ata ranki domin bata san muna wahalar da kanmu akan ta ba, Bab ta min nisan da duk saurina ba zan iya kamota ba, yanzu haka tana daf da shiga k'arknashin inuwar wani, zata zama mallakin wani a k'ark'ashin ikon wani, banda dabarar da zan iya aiwatarwa ta zauna gefena har k'arshen rayuwa, kud'i na da duk iko da alfarmar da na ke da sun kasa sama min ita a matsayin mata, Baba na rasa ta kenan rasawa ta har abada, ki tayani da addu'a kawai na manta da ita, na sake sabuwar rayuwa mai farin ciki ko da babu ita, Bab zuciyata azalzalata take yi tana rura min wuta mai rad'ad'in gaske, ya zanyi da raina? Ya zanyi Bab? Ki fad'a min ya zanyi yanzu?" Ya k'arashe yana fashewa da kuka marar sauti, jikinta yayi mugun sanyi tare da jin wani abu d'脿 ma ta kasa fassara shi a take, bata kai ga fara lissafin abinda take tunani ba wayarshi ta shiga kururuwa, bai d'aga ba har saida ta tsinke, jin an sake maido mishi yasa shi cirowa wayar da niyyar kasheta gaba d'aya, ganin Adam ne yasa yaji ba zai iya tsallake kiransa ba, d'auka yayi kamar almara kawai Adam ya shiga fad'in "Kai malam wai kana ina ne kai? Ya za'a d'aura maka aure kuma baka wurin? Yanzu kana ina?" Cikin wofantar da zancen yace "Zan sake kiranka dan Allah." K'it ya yanke kiran, har zai kashe wayar kuma sai kiran Wardugu ma ya shigo, yana d'auka shima cewa "Barka abokina, ina tayaka murnar mallakar wacce kake so, yanzu ka shirya ina nan zan zo garin na sameka, jibi kuma su Ayya da Umma zasu taho maka da amaryarka." Da mamakin kalamnsa yace "Wai me yasa kuke son tsokanata? Wace irin wasa ce wannan?" Dariya War yayi yace "Kai malam ka shirya kawai kafin na zo, a gidan abincin daya fi kowane a garin nan zaka mana oda, dan ina tare da manyan bak'i kuma a jirgi zamu iso." Zunbur ya mik'e yace "Wardugu dan ubanka ka fad'a min gaskiya? Me ya faru dan Allah?" Cikin k'yalk'yala dariya yace "Wallahi aurenka aka d'aura yanzu da Faduma, gamu a wurin baka jin hayaniya? Ai yaron nan jiya ya kira ya fad'a min yace ya bar maka ita, dan ya lura kafi shi sonta sannan kafi shi buk'atar aurenta, saboda ya sanka yasan abubuwa da dama akan ka, kai yaron nan fa ya mana babban taimako, badan shi ba da watak'ila mu ci uwarmu wallahi, dan yanda yarinyar nan ta shigeka ina ga saita kaika k'abarinka ta baroka." D'auke wayar yayi daga kunnenshi ya damk'eta sosai, gabas ya kalla a take yayi sujadar godiya ga Allah, mik'ewa yayi ya juya inda Saudat take ya rumgumeta tsaf yana bata wani zazzafan sumba a bakinta, ya jima haka kafin ya raba jikinsu yace "Ki shirya dan Allah anjima zan zo na d'aukeki da kaina zuwa sabon gidanmu, kar kice a'a Saudat." Da sauri ya saketa yana fad'in "Ina zuwa, zanyi bak'i ne." Ficewa yayi ya barta galala tana kallonsa da mamakin meke faruwa? *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 21:41 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _61_ A cikin wata runfa gefen masallaci ya samu Alhaji Mustafa zaune tare da wani dattijo, yana zaune akan kujera ya duk'ar da kanshi ya rufe fuska da hannayenshi ya fashe da kuka kamar yaro, dafashi mahaifin nashi yayi yace "Aminu idan kasan ba zaka iya ba me ya aikeka yin abinda yafi k'arfinka?" Girgiza kai yayi ya d'ago ya kwantar da kanshi saman cinyarshi yana fad'in "Zan iya Alhaji, kawai dai k'irjina ne yake min ciwo, ka min addu'a dan Allah komai zaiyi daidai." Daddab'ashi ya shiga yi yace "Aminu ba zan iya kallonka a wannan halin nan, da zaka amince dana nema maka auren yarinyar nan, wallahi da nan da sati biyu sai kayi aure kaima ko hakan zai rage maka rad'ad'i." Da sauri ya d'ago kanshi yace "Na amince Alhaji, na amince wallahi ka aura min ita, zan maka biyayya ba zan sake bijirewa umarninka ba." Cikin farin ciki ya sake daddab'ashi yace "To shikenan naji, yanzu share hawaye ka daina kuka, muna komawa gida zan samu Alhaji Saddi da maganar." Jinjina kai yayi yana shashek'ar kuka sai dattijon nan da yace "Kayi k'ok'ari yaro, Allah ya biyaka da aljanna." "Ameen." Alhaji Mustafa ya amsa da murmushi a fuskarsa. _______________ A gefe guda ya damk'awa Kalli enveloppe mai shak'e da kud'ad'e yace "Wannan shine sadakinta, a bawa yarinya abunta ta moreshi ta hanyar data ga dama, na bayar a cikin mutane k'asa da hakane saboda gudun abinda hakan zai jawowa abokina." Karb'a Kalli yayi da girmamawa ya masa godiya tare da fad'in "Insha Allahu zan kaiwa Aba sai su bata da hannunta." Gyara tsayuwarsa yayi jikin mota yace "Idan ka shiga ka turo min Ummanmu dan zamu wuce yanzun." Amsawa yayi ya shiga cikin gidan, sanda yaje ya fad'awa Umma Ayya ce tace yaje ya fad'a masa ba zasu fita anan ba har sai sun shigo sun biya kud'in ganin amarya, sanda aka fad'a masa wani murmushi ne yayi yace "Banda abun Ayya ina zamu je ganin amarya babu ango? Ta hak'ura mu samoshi tukuna." Kiranta yayi a waya nan fa ta dage ai dole awa yarinya abinda ake ma kowace mace, Faduma da lokacin tana kewaye ne cikin yan uwa sai k'awayenta na yarinta su Maryam da suka zo da 'ya'yansu hud'u sai mai guda uku. Dole a k'arshe ya nemi rakiyar wasu daga cikin abokansu harda Kalli daya dage shi fa ba zai shiga ba, saida Wardugu yace zai ci uwashi fa kad'ai ya shiga gaba. Sallamar zataran matasan masu fad'i aji, mulki, iko, kud'i, ilimi da kyawu kawai yasa duk matan gidan maida hankalinsu garesu, saida aka gaisa aka wa juna barka kafin suka nuna musu d'akin da suke. Wardugu wata uwar fuska ya caka ya saka gilashin nan bak'in ba alamar wasa, shi fa badan farin cikin da yake na samun wacce abokinshi ke so da me zai kaishi cikin yara k'anana馃槑, Faduma na zaune can k'uryar su Ayya da Umma da Dada sauran mutanen, tuni Walyn ta fara gatsinar baki tana taunar cingam, kallo d'aya ya mata ya d'auke kanshi ya shiga lalubar inda fitilar tashi take, addu'arshi bai wuce ace bata nan ba, saidai harya gama kalle kallenshi bai ganta ba domin kuwa darar amare mai kalar ja cikinta suka shige ita da Faduma tunda taji zai shigo dan karya mata cikin nan a cikin mutane. Da k'yar aka samu cikin mazan wani yace "Ina amaryar take to?" Maryam ce tace "Zaku ga amarya idan kun biya." A hankali Wardugu ya juya ya kalli wanda yayi maganar, labb'enshi kawai ya motsa yace "Ka biya to." Murmushi yayi ya zura hannu aljihu yana girgiza kai, dan dole ya biya inba haka ba yasha matsa (Jikan Hajia na biyu kenan Ammar ikon God), 'yan jaka bobbiyu ne kalar shud'i shar dasu har turiri suke ya mik'a mata, hannunta saida ya shiga rawa dan kud'in sun wuce tunaninta, a k'alla tasan zasu haura jaka hamsin. Ganin ya biya yasa shi cewa "To sai muga amarya ko?" Mik'ewa tayi da niyyar bud'e rufar Faduma, sai kawai Wardugu yace "Kar kiyi." Wannan umarni daya bata ko Ayya saida hantarta ta yamutsa, kallon mazan yayi yace "Al'adace kuma kunyi, m没 tafi kawai, haka kawai ku gama kalle masa mata tun shi banga fuskar annurinta ta amarci ba, k'artin banza daku." Dariya aka kwashe da ita tuni Kalli ya juya ya fita a harshen tubanci yana fad'in "Allah ya shiryaka Wardugu." Har zasu fita Abdallah ya kutso kai d'akin yana fad'in "Yo ban gane ba, duk taron nan nine aka tsana da ba'a gayyaceni ba?" Lumshe ido War yayi, yana jin dad'in zama kusa da Abdallah saboda nishad'i, saidai anan harkar girma yake so suyi komai a hankalce. Tunda taga shigowarshi ta dunk'ule dan bata so ya nuna ya santa ma, amma ina suna had'a ido yace "Ke budurwata zo nan." Daga can ta dallo masa harara ta d'auke kanta, nuna kanshi yayi yace "Ni kika harara? Ni dai ko? Zamu had'u a gidanmu wallahi sai nai..." Wardugu ne ya rufe masa baki da tafin hannu, Agaishat ma satar kallon Abdallah tayi jin wani kamar mijinta, murmushi kawai tayi ta sake sinne kanta a dara. Kallon Umma yayi yace "Uwar gida sarautar mata, kinga dai k'ok'arina nata jawo miki girma." Hararenshi tayi tace "Wai kai bakinka baya ciwo ne? Kayi shiru mana harda surukuwarka fa a wurin nan." Dariya yayi yana kallon su War duk suka fice sai shi kad'ai yace "Kinga budurwata nan bayanku, kinga fa ranar aurenmu aka fara sakawa, amma gashi d'ana zai sake rigana angoncewa, amma ba komai zamu taddosu insha Allah." Duk saida suka sake kallon Dada data had'a kai da gwiwa cikin kunya, addu'arta bata wuce ya fita ya bar d'akin ba, juyawa yayi yana fad'in "Amarya zamu had'e a partyn larabawa (arabian night)." Da sauri Umma data aika kira ta kalleshi tace "Zakuyi?" Jinjina mata kai yayi yace "Insha Allahu, ai dole mu casu a bikin nan, bayan nan ma akwai shagalin tubawa da za'ayi." ______________ Sanda ya shiga motar rasa abunyi ma yayi, wayarshi ya k'urawa ido yana tunanin wanda zai fara kira, Ayya ce ko Umma ko kuma Batul? Yana cikin kallon wayar sai Umma ta raba gardama ta hanyar kiransa, da sauri ya d'auka yana dariya mai kama da kuka yace "Umma na, Umma na ashe kin zo?" Cikin nutsuwa a harshen larabci tace "Na zo Hasheer." Ajiyar zuciya ya sauke yace "Umma kunyarki nake ji." Murmushi yayi tace "Babu maganar jin kunya, yanzu dai abinda nake so da kai shine gobe zaka zo nan tare abokanka kiyi godiya, ni da ayyarku zamu wuce gidan hakimin sarkin damagaram mu kwana biyu acan, zuwa jibi insha Allahu zamu tafi da ita, sai kuma maganar party da waye da naji Abdallah na magana, bana so, kar a fara." Cikin girmamawa da ladabi yace "Insha Allahu Umm na, yanda kike so haka za'ayi." D'orawa tayi da "Sannan Saudat, kayi k'ok'ari ka kwantar mata da hankali kafin na zo, sai kuma izini da Faduma ke nema a wajenka tana so zatayi magana da Aminu?" Darammm! Yaji gabanshi ya fad'i, a hankali ya furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un." Aminu? Lallai yai masa abinda ba kowa ya masa ba, kai tsaye zai iya cewa rayuwarsa ya ceto daga fad'awa halaka, a hankali cikin taushin murya yace "Ba komai Umma na, na amince." Cike da dattako tace "Mun gode, zamuyi waya." Yanke kiran tayi ta kalli Ayya tace "To, mun samu izinin, yanzu 'yata zata iya magana dashi?" Dariya Ayya tayi tace "Abu mai sauk'i." Murmishi sukayi kawai kafin suka tura a wa Aminu magana. ________________ Yana aje wayar ya shek'e da wata dariya yana dukan sitiyarin yace "Wai nine na bayar da umarni akan Faduma? Ni Hasheer ni aka nema izini kafin tayi magana da wani?" Murza motar yayi ya bar k'ofar gidan ya nufi wajen cin abincin da zai tanadawa su g茅n茅ral kafin su iso. Yana barin nan da ranar nan tsaka Zaliha da Atta suka zo gidansu, tambayar Saudat sukayi aka nuna musu d'akin mahaifiyarta suka shiga da sallama, bayan sun shiga sun gaisa ne cikin makirci Zaliha ke fad'in "Ashe har an d'aura auren, to Allah yasa alkairi ya baku zaman lafiya." Cikin rashin fahimta tace "Ban gane ba? Auren wa aka d'aura?" Atta ce ta zaro ido tace "Lahh! Kar dai kice baki san an d'aura auren ba?" Cikin jin haushi tace "Wai auren wa kuke magana akai?" Zaliha ce tace "Allah sarki kiyi hak'uri, dama munji an d'aura auren mijinki ne d'azu a damagaram, kenan baki da labari?" Da k'arfi ta mik'e tsaye ta dafe k'irfi tana kallonsu tace "Mijina? Hasheer d'in?" Kallon juna sukayi da jin dad'in samun labarin auren nan daga bakin bazawarinta Saddi, kallonta sukayi Atta tace "Sosai ma, wai baki sani ba dama?" Rik'e kanta tayi daya fara sara mata tace "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, Hasheer d'in ne yayi aure." A fusace ta nufi k'ofa zata fita da sauri Zaliha ta tarota tana fad'in "Ke tsaya kiji." Cikin d'aga murya tace "Me zan tsaya naji? Na d'auka cin amanata kawai yake da bak'ar yarinyar nan, ashe ma har aure yayi ban sani ba? Wallahi ko ni koshi ne a garin nan, shi harya isa?" Zaunar da ita sukayi Atta na fad'in "Kinga, idan baki iya kama b'arawo ba to ke saiya kamaki, kinsan ma me ya faru? To bari kiji da kyau." Gyara zama sukayi ta ci gaba da fad'in "Shi wannan munafikin Aminun lauyan mai gidanki, duk iskanci da tuggu da tsiyar na gareshi, domin kuwa shi zata aura nan da kwana sha biyar, sai kawai yace ai mijinki yafi shi sonta kuma ke baki iya kula dashi ba, dan haka ya bar masa ita dai bak'ar da kike magana akai, wannan yarinyar da kike gani nakiya ce mai k'arar da ahali, tunda ta shiga rayuwar tsohon mijina gaba d'aya gidansu ya rikice, har yau shi da mahaifiyarsa da yar uwarsa ba wani shiri suke ba saboda ita, dan haka kema rabaki zatayi da mijinki kamar yanda ta rabani da nawa mijin." A gigice ta kalleta idonta a waje tace "Kin santa kenan? Ita ce Faduma wacce ta haihu a waje?" Da sauri tace "Ita ce, ai d'an data haifa ma na mijina ne, kin ganni yanzu akan titi ina gantali." Wani murmushi tayi mai ciwo tace "Mujaheed ya ban labarinta, amma bata isa ba, ni ba zata rabani da mijina ba wallahi, kuma ba ita data aurar min miji ba har wanda yayi sadaukarwar saiya shiga uku, ba dai ya had'a mijina da wata ba, shi a tunaninshi zai samu kamilalliyar budurwa ya aura?" K'wafa tayi tare da mik'ewa tsaye tace "Wallahi bashi ba aure har abada." Zaliha ce ta tab'e baki tace "Ai abinda ya faru yasa k'anin mahaifin mijinki zai d'aura masa aure da *Zulfa*." Wata dariya tayi tace "Wallahi bai isa ba, ba zasu d'aura auren nan ba." ______________ Falon Ayya ta samu Aminu zaune yana jiran shigowarta da Amjad saman k'afafunshi suna hira k'asa k'asa, yana ganinta ya saki murmushi yana fad'in "Amarya kinsha k'amshi." Cikin darar da aka rufeta da ita ta kalleshi ta samu wuri ta zauna, had'a ido sukayi da Amjad take ya fahimci ma'anar kalli ya fita, k'asa ta kalla dan kunyar had'a ido taji dashi tace "Aminu ya haka? Me yasa kayi haka?" K'uri ya mata da ido na wani lokaci sai kuma yayi murmushi yace "Haka Allah ya tsara Faduma, ina miki fatan alkairi, Allah ya sanya alkairi." Ba tare data kalleshi ba tace "Amma Aminu..." Cikin sanyin murya yace "Faduma, dan Allah mu bar maganar baya ta wuce wannan, duk abinda nayi dan Allah nayi shi ba dan wani ba, na so aurenki ne saboda ni kaina bansan yaushe kuma a wane lokaci na kamu da sonki ba, zanyi farin cikin aurenmu kawai idan kika aureni kina mai farine cikin haka, amma ayi aurenmu ke zuciyarki na gurin wani, abune da ba zan iya jura ba shiyasa nayi hakan, Elhaj Hasheer kamar mai gida na d'aukeshi kuma yaya, taya zan aureki bayan yana sonki kuma kema shi kike so bani ba? Wace irin rayuwa zamuyi kenan? Na tauyeki ta hanyar tirsasa miki zama dani? Ko kuma na mayar dake bazawara a sanda bakiyi tsammani ba? Duk hakan ba burina bane shiyasa nayi haka, ina da yak'ini akan Elhaj wallahi zaki fi farin ciki da aurenshi fiye dani." Mik'ewa yayi yana kallon k'ofa yace "Na barki lafiya." A hankali ta d'aga kai ta bishi da kallo harya fita, ajiyar zuciya ta sauke tana jin ba dad'i, hak'i'k'a tana rayuwa ne a yanzun saboda wanda take so aka aura mata, amma fa Aminu ma taji ba dad'i dan da gani kasan juriya ce kawai da k'arfin hali. Duk da ba biki su Ayya suke yi ba amma masu zuwa yi musu barka ma kawai sun cika gidan, haka har la'asar ta riskesu, bayan sunyi sallah ne su Umma suka ce zasu tafi masaukinsu, dreban daya kawo su Faduma ne ya kaisu gidan hakimin sarki, saidai Agaishat anan aka barta tare da Dada su zauna wurin Faduma. _______________ Da la'asar su Wardugu suka sauka garin, a sabon gidan ya tarbesu tare da wasu abokansu daya rasa yanda akayi suka ji batun auren nan, a kad'an sai gashi gidan ya tara majiya k'arfi sama da guda arba'in, sun ci sun sha musamman nama dai da aka mayar kayan banza an kawo gasashe an ci soyayye (馃槒 Hmmm! Aci dai in rowa abar so ce), su kam suna wurin nan har sallah magriba kafin suka rabu ya rage daga ango sai aminin ango da Abdallah dake ta Hasheer tsiya, fad'i yake wai ya kaishi wajen bokan daya kai sunan Aminu? (馃槀nima grp Allura ku fada min sunan bokan da kuka hadani dashi nayi musayar sunan nan?) shi kam banda murmushi da shafa sumar kanshi babu abinda yake, k'arshe dai daya damesu da surutu Wardugu ne ya d'auki takalmi ya jefa masa ya bar gidan shima, lokacin kawai suka samu damar tattaunawa kan abunda ya faru, ya k'ara jinjinawa Aminu sosai saidai a gaskiya a yanda yake jin Faduma baya jin idan shine zai iya wannan sadaukarwa, saidai kawai ya masa addu'a da fatan Allah ya kawo ranar da zai saka masa da alkairi shima. Shiryawa sukayi cikin wasu manyan kayan suka tafi gidansu Saudat, wannan karan mahaifinta suka gani kai tsaye kuma Wardugu ya kwatanta masa abinda ya faru, dake mutum ne mai nutsuwa shi sam baiga wani abun d'aga hankali a ciki ba sai ma addu'a daya ta kwaronyo musu tare da mishi alk'awarin gobe ya zo ya d'auki matarsa kamar yanda ya nema saboda yana so daga nan tayi sabon gida. ______________ Suna zaune d'akin shiru suna d'an tab'a hira sama sama, Dada na mak'ale da waya a kunne ita da mutumin, Agaishat ma tana ta k'ok'arin kiran nata gwarzon, kira na biyar kenan amma baya d'agawa, aje wayar tayi tace "Wani abun yake mai mahimmanci, yanzu da nice ya kira haka ban d'aga ba sai nasha mitar tsiya." Dariya Faduma tayi tace "Rayuwarku gwanin sha'awa, aini nayi mamakin daya amince ki kwana anan ma shi yayi gaba." Dariya ita ma tayi tace "Ai kafin ya amince saina nayi kuka kuma Ayya tasa baki, amma duk da haka fa nayi sa'a tunda yana da hanyoyin da zai hanani a sauk'ak'e." Kiranshi ne ya shigowarta sanda suka baro gidansu Saudat, nunawa Faduma tayi tace "Bari kiga idan ban d'aga ba yanzu kiji me zai ce." Suna kallo har kiran ya katse ya sake maidowa, 'daukar wayar tayi tace "Cewa zaiyi na masa wulak'anci dan na samu abokan hira, a k'arshe yace ciki zai min." Dariya Faduma tayi tana kallonta ta d'aga ta saka a amsakuwa, kamar rubuta mishi tayi sai kuwa yace "Orro nine nake kira a k'i d'aga min har saita yanke? Ni ko? Saboda an samu gulma anayi, nagode kiyi yanda kike so, dan kinga bama kusa shiyasa zaki wulak'antani, amma wallahi muka had'u ciki zan miki." Cikin dariyar mugunta ta cireshi a amsakuwa ta d'ora a kunnenta tace "Idan baka min b芒 fa? Ka yarda na tuhumeka?" Cike da mamaki yace "Iyeee! Lallai ma orro, ni ko?" A hankali yace "Ina amaryarmu? Kuna kula mana da ita dai ko?" Saida ta kalli Faduma tace "Mu ma ina angonmu?" Cikin bala'i yace "Angonku orro? Ku fa kika ce? K'aton zaki had'a da kanki? Ke ina ruwanki da shi?" _Kwate iya mana dashi dan Allah, Wardugu zai sa min ciwon kai kamar waccen d'ayan dan gidan Hajia._ *Washe gari* tun asuba da suka tashi babu wanda ya koma kwana, masu shara nayi masu goge goge nayi, har gari ya waye wasu suka fara shiga ban d'aki suna wanka. Dada da Agaishat da Faduma tare sukayi karin kumallo a d'aki, hakan ya k'ara musu shak'uwa da wata sabuwar zumunta, inda Agaishat tace "Wallahi sai nake jin kamar nayi zamana anan, acan fa bana da k'awaye kamar haka da nake zaunawa dasu muyi hira." Dada ce tace "Ki k'ara kwana ko biyu mana, ko kuma ki bari ku tafi tare dasu Ayya." Zaro ido tayi tace "Kai! Ai ko a k'ugu ne Watdugu ya d'aurani mu koma, tun d'azu fa munyi waya yace suna saman hanya, ai ba zai yarda ba." Murmushi Faduma tayi tace "Banga laifinshi ba, ki barshi ya mori k'uruciyarsa kafin lokacin ritayarshi yayi." Dariya sukayi sai Agaishat da tace "Ke kuwa wannan anya ba zakiyi masifa ba." Had'e fuska tayi tana hararenta tace "Wace irin masifa kuma!" Murmushi dada tayi tace "Zaki fara fahimta yau idan angonki ya zo." D'an tsaki tayi tace "Ku dai tsofaffin matan nan haka kuke." "Ke ma kuma kin shigo sahu ba." Cewar Agaishat. Ko da rana tayi Dada ta musu sallama ta tafi dan ita kanta abubuwa ne a gabanta, suna nan kuma mota uku suka tsaya k'ofar gidan aka shiga fitowa, Umma da k'anwarta ce da kuma Ayya sai matar hakimi data taho tare dasu saboda kara, Herde data shigo tunda safe ce ta shiga kawo musu wurin zama da kuma matar Barka, bayan duk sun zauna gaisawa aka sakeyi kafin Ayya ta jadadda mik'o musu godiya na karamcinsu a garesu, suma sake fad'a musu sukayi babu komai kafin suka gabatar da abinda ya kawosu. Marfu'a ce ta kalli Herde da kyau cikin sark'akk'iyar hausarta tace "Bayan godiya zamu nemi alfarma a wurinku, ko daga ina kuma ko nawa ne gyaran jikin amarya mun d'auki nauyinshi akanmu zamu biya, sai lefenta insha Allahu nan da sati d'aya za'a gama had'a mata kayanta a kawo mata, kamar yanda addini ya tanadar haka mu wajenmu mukeyi, idan kuna buk'ata zaku iya yi wa 'yarku kayan d'aki badan komai ba saboda al'adar nan munga abun na zama na gori idan ba'ayi ba, saidai karku tsawwalawa kanku domin kuwa a sabon gidan da zata tare babu abinda zata nema ta rasa, sai kuma wannan..." Ta fad'a tana d'aukar kwalin dake gabanta na sark'a, mik'a ma Herde tayi tace "Wannan k'aramar kyauta ce daga mahaifiyarshi zuwa ga amaryarmu." Wani kwalin ta sake mik'o mata tace "Wannan ma dai daga wata mahifiyar tashi." Ta fad'a tana nuna Ayya, sannan ta mik'a mata wani d'an gida mai kyau na agogo tace "Wannan daga gareni." Matar hakimin nan dake cikin shiga ta sarauta wata baiwar dake bayanta ta tarawa hannu ta mik'o mata kwalin tanfatsetsiyar lafaya tace "Wannan daga gareni ba yawa." Herde hannunta ne taji yana rawa tayi saurin zube kayan saman cinyarta, godiya ta shiga yi musu sosai suna mata godiyar suma, a hankli Umma tace "Zan iya ganin Faduma?" Nuna mata d'akin tayi tace "Tana ciki, bismillah." Cikin nutsuwa da shigarta ta tafaya ta shiga d'akin da sallama bayan ta cire takalminta a k'ofar, dama tunda taji shigowarsu ta zunbula hijabinta har k'asa akan riga da zanin data d'aura simple d'inki, takurewa ta sakeyi tana amsa sallamar da mata sannu da zuwa cikin girmamawa, zaune tayi kusanta suka gaisa a nutse sosai. Jakarta ta bud'e ta ciro wata sark'ar k'afa masu kyau guda biyu kala d'aya, mik'a mata tayi tana fad'in "Karb'i wannan, wannan abun da kike gani na k'afa ne, mamata ta bani shi sanda ta aurar dani, sanda muka aurar da *Meena* haka kawai na k'i yarda na bata, yanzu kuma ina ajiyarsa ne dan na bawa Halima ko Salima, amma jiya bayan d'aura aurenki sai naji a raina ke ce kika dace dashi, ko ba komai nasan zaki fi d'aukarsa da daraja, anan naga wannan sark'ar ta k'afa mata basu cika anfani da ita ba, hasalima sai ake ma duk wacce tasaka su wani kallo na daban, amma ita wannan kwalliyar tun zamanin fiyayyen hallita (S.A.W) mata suna anfani da ita, dan ko a k'issar Nana Aisha (R.A) da aka anbata har a Qur'ani ma wacce aka mata k'azafin zina akwai hadisai da suka nuna sark'ar k'afarta ce ta b'ata shine dalilin komawarta har tagawar ta tashi ba tare da ita, kinga kenan suna anfani da ita, dacewarta shine ka saka a d'akin mijinka ka yi tafiya ta birgewa tayi sauti a k'afarki yanda hankalin mai gidanki zai koma kanki, amma ba kiyi anfani da ita ba dan ki d'auki hankalin wasu, kin fahimta?" Saida Faduma ta sauke ajiyar zuciya kafin ta jinjina kai tace "Nagode Umma, kuma insha Allahu zan kula da ita kamar yanda zan kula da kaina." Murmushi tayi tayi shirin mik'ewa tana fad'in "Ki kula da kanki, mu zamu koma." Da kai kawai ta amsa mata, tana kallo harta fuce kafin ta kalli sark'ar mai kyau ta tsantsar zinariya irin ta da wacce babu algus. *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 21:41 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _62_ Faduma na sallah walaha a d'akin Khadija matar Barka Agaishat kuma da littafin hisnul muslim tana karatu suka ji sallamarsu, babu wacce gabanta bai fad'u ba hakan kuma bai rasa nasaba da k'uratowar wani mai matuk'ar mahimmanci a garesu kusa da su, mik'ewa Agaishat tayi ta aje littafin tana fad'in "To fa sun zo, ina zan shiga?" Sallamewa Faduma tayi ta mik'e da k'aton hijabinta tana fad'in "Wai ke kuka saba kenan? Ni ina zan lab'e?" Dariya Agaishat tayi tace "Ni nasan halin kayana ne, idan har yasan ina nan zai shigo babu ruwanshi." A hankali cikin nutsuwa suka ji muryoyinsu dana su Ayya suna gaisawa a tsanake a kuma mutumce harda Aba da baiyi nisa b芒, jim suka ji kamar babu kowa a wurin sai muryar Kalli data shiga kunnuwansu yana fad'in "Ina amaryar take Ayya?" Cikin nutsuwa Ayya ta nuna mishi k'ofar tace "Yanzu ta shiga zatayi sallah." Aba ne ya nufi hanyar fita yana fad'in "Ka masa iso mana sai su gaisa." Muk'ut tayi ta had'e yawu, da Hasheer zata gaisa yau a matsayin miji da mata? Tsare Agaishat tayi da ido dake kallonta tana mata dariya, muryar Kalli suka ji yace "Ayya ina Agaishat?" Zaro ido tayi tace "Tofa, zai cabko ni." Duk da ba sautin takunsu suke ji ba amma daga yanda gabansu ya tsananta fad'uwa sai suka tabbatar suna nufosu, duburburcewa sukayi suna neman mafita, da sauri Agaishat ta d'aga hijabin Faduma ta shige ciki ta jata da k'arfi suka zauna kan kujerar zaman mutum uku, Faduma na ganin haka ita ma saita saka fuskarta cikin hijabin sukayi shiru sai numfashi da suke saukewa kamar sunyi gudu. "Assalama alaikum." Suka fad'a a tare, shiru sukayi sai Faduma da taji jikin ya d'auki rawa, jin ba'a amsa ba da kuma tabbatarwa suna ciki yasa suka bawa kansu amsar cewar miskilan ne a kansu, bud'a labulen War yayi ya cire takalminsa ya fara shiga, a bayansa Hasheer ya shiga cikin nutsuwa, kallon juna sukayi sai suka sake kallon abun kamar wani buhu, a hankali Wardugu ya zauna yana fad'in "Zauna." Shima guri ya samu ya zauna yana ci gaba da kallonta, tuni ya gama gane abarshi daga k'afafunta da suka fito masu kyawun fasali da zara zaran yatsu, cikin hamshak'iyar murya Wardugu yace "Gaishu nine fa na zo, ba zaki d'ago ki kalleni ba?" Kimmm tayi kamar jin shi, kallon Hasheer yayi ya kanne masa ido yace "Ni kam ka gane taka matar anan ne?" Girgiza kai yayi cikin wata tattausan murya a nutse yace "Ko kad'an, amma taimakeni na cirota anan." Cikin nuna ba wasa Wardugu yace "Nima bansan inda tawa take ba, amma abinda zai faru anan shine, kawai mu rufe ido mu d'ora hannayenmu, duk wacce kowanenmu ya tab'a to matarsa ce ko da ba tasa bace." Da saurin bala'i Agaishat ta d'ago tana bilinbituwar fitowa a hijabin tana fad'in "Kamar ya?" Inda Faduma ma ta zuro kanta ta fuskar hijabin tana fad'in "Lahhh!" Saida suka had'a ido dasu sai kuma kunya ta kamasu suka sunkuyar da kai, murmushi sukayi suna girgiza kansu a hankali, hannu Wardugu ya mik'a mata yace "Zo." Saida ta shagwab'e fuska kmar zatayi kuka ta d'an mak'ale kafad'a, mik'o masa hannun tayi ya mik'ar da ita, zaunar da ita yayi kan kujerar dake daf dashi yana kallon fuskarta, magana suka shiga yi k'asa k'asa har saida ya kalli Hasheer da idonshi ke kan gimbiya Faduma ko motsawa baya yi yace "Kai." D'an kallonshi yayi saidai hankalinsa na can, girgiza kai yayi ya mintsineshi a damtse yana fad'in "Jarababbe, daga ganin yarinya ka wani k'ura mata ido, to mu zamu fita mu barku, idan kaine kuma wanka ya kamaka a gidan surukai." Sunkuyar da kai yayi ya d'ago ya kalleshi sanda suka mik'e, Agaishat kam tuni ta rufe fuska da hijab d'inta, kallon zan kamaka ya mishi yace "Wardugu ka cini wasan nan, na yarda mun tashi d'aya da banza, amma ka sani sai mun had'u a inda baka isa ka d'aga kai ka kalleni ba zan rama." D'aga hannu yayi kamar zai mareshi yayi saurin kaucewa yana dariya k'asa k'asa, so ne yake ya jashi bala'i suyi a gaban manya,shi kuma baida lokacin nan a yanzu a halin da yake ciki, saida suka fita yana jin suna musu zasu tafi su dawo saita dawo suyi sallama suka fita. Tasowa yayi daga kan kujerar ya tunkareta, gabanta kam tuni ya sae shiga daka da sauri sosai kamar zai fito, gabanta ya tsaya tare da yin tsuguno irin na maza ya d'ora hannayenshi a nata ya shiga wasa dasu yana kallon fuskarta, kanta k'asa ta k'i d'agawa sai ma lumshe ido da take tana jin kamar ta rintsesu, sahihin k'amshin turarenshi da kuma numfashinshi dake d'an kaiwa a fuskarta zuwa idonshi da take ji a jikinta, duk sun gama d'aureta ta yanda take jin ba zata iya d'aga kai ta kalleshi ba, ga kuma abinda Wardugu ya fad'a ya fita ya barta da kunya. A hankali yace "Hmmm! Kwana biyu da suka wuce ma me kika fad'a?" Had'e yawu tayi bata d'aga kanta ba bare ta amsa, ci gaba da wasa yayi da hannayenta yace "Kin ce ba zamu tab'a aure ba, mu hak'ura da junanmu waye...waye...to yanzu me ya faru?" Saida ya saka tafin yatsunshi ya d'ago hab'arta ya kalleta yace "Gani gaki a matsayin mata da miji." D'an kawar da kanta tayi ta sak茅 sunkuyar dashi saboda kunya, sake kamo hannunta yayi yace "Batul kin min laifuka da dama wanda kuma na zo ne da niyyar hukuntaki, dan ba zan iya yafe miki ba kamar yanda zan fad'a miki laifukan dan karki kalleni a matsayin marar adalci na hukuntaki akan laifukan da baki san dasu ba." Da yatsun hannayenta ya shiga mata lissafi yana fad'in "Na farko shine kama min zuciyata da kikayi ba tare dana shirya ba, na biyu bibiyata da kika dinga yi har saida na shak'u dake, na uku juya min baki da kuma gunguni, na hud'u zauna min a k'afafu da kikayi har sau biyu, na biyar kasa fad'a min an tsayar da ranar aurenki, na shida kallona da kikayi babu kaya, saina bakwai kuma na k'arshe shine kirana da kikayi da yaro." Ajiyar zuciya ya sauke yace "Zahra dukansu saina rama, ko ki yarda ko karki yarda, zab'i biyu zan baki masu sauk'i da zasu sa na yafe miki." D'an kallonshi tayi a hankali hakan yasa shi cewa "Zab'i na farko shine ki sumbaceni, zab'i na biyu kuma ni na sumbaceki, na uku kuma baki da zab'i idan har baki d'auki d'aya daga ciki ba, shine zaki tare gidanki yau d'in nan." Ba tare data kalleshi ba kanta a k'asa sosai tace "Zan iya kare kaina? Dan ina da ja." Murmushi yayi yana hangen bakinta dake motsawa, a hankali yace "Zaki iya, amma banda son kai." Jinjina kai tayi a hankali cikin nutsuwa da sanyin murya ssosai tace "Laifi na farko ba nice na kama zuciyarka, Allah ne ya saka maka sona saboda nima ya saka min, laifi na biyu nima da fari na d'auka bibiyata kakeyi, sai jiya ne na fahimci cewa alak'ar da zata shiga tsakaninmu ce ubangiji ya dinga haddasa mana had'uwa, laifi na uku ba dagangan na juya maka baki ba kuskure ne, laifi na hud'u ban gani ba sanda na zauna maka k'afafu, laifi na biyar nima fargaba ne ya hanani sanar da kai saboda bansan ya zakaji ba, laifi na shida ni ban kalleka haka kawai ba saidan tsorata da nayi, laifi na bakwai kuma na k'arshe ni ban ce maka...kawai dai laifin na Dadata, kuma babanka ya ci alwashin hukuntata." Wani sauk'ak'ak'en murmushi yayi yana d'an d'auke idonshi daga kan bakinta yace "Kamar yanda babana ya ci wannan alwashin, haka nima na ci shi akan ki kuma zan tabbatar dashi." Sake nutsar da kanta tayi tace "Kayi hak'uri to." Girgiza kai yayi tare da d'ago hannunta na dama ya d'ora labb'enshi akai ya sumbata, tsammm ta rufe ido saboda har kwanyarta taji saukar abun, tafin k'afarta taji yayi wani ziiiiii take tsigar jikinta duk ta tashi, lek'a fuskarta yayi yana mataccen murmushin mugunta yace "Ya dai Hajaj, kinji wani abu ne?" Kanta kawai ta iya girgizawa a hankali, cikin tsareta da ido yace "Fad'a min to, me ya tsorataki da yasa kika shigar min d'aki babu izini?" Bud'a baki tayi zatayi magana sai kuma ta kasa, idonta taji duk sun cicciko daf take da sako hawaye, murmushi ya mata yace "Jikina ne...ya tsorataki? Ko kuma...dai rashin lafiyata?" Girgiza kai tayi alamar a'a sai kuma ta jinjina alamar eh, wani murmishin ya kuma saki yace "Duka biyu kenan?" Mik'ewa yayi tsaye gabanta, tallabo hab'arta yayi yace "Dubeni, nifa yanzu naki ne, mallakinki Faduma, babu shamaki a tsakaninmu, karki tsorata dani kinji." Lumshe idon da tayi yasa hawayen da take ta rik'ewa suka taho, wani murmushin mutuwar ya sake yi mata tare da sunkuyawa, cikin wani mahaukacin salo da al'amarin da yafi k'arfin tunaninta ya lumshe idonshi ya saka harshenshi akan hawayen da suka taho mata, sake rintse ido tayi sosai tana jin jikinta na d'aukar wani zazzab'i da mijirya, tana ji yana lashe hawayen nan da harshenshi mai d'umin gaske. Saida ya d'auke mata su tsaf ya kalli fuskarta, cikin rikitacciyar murya yace "Tun ranar da kika juya min bakin nan naci alwashin hukuntashi ta hanyar..." Wuf yayi da bakinta ya shiga tsutsa a tsanake a ladabce a sanyaye, bata aiwatar da komai ba sai aukin hawaye da kakkarwa. Shi kanshi jikinsa ya gama mutuwa da kuma kunnuwa, manyan kanya sun karb'i sak'on tare da killaceshi a masauki mai kyau, jikinsa ya amsa ya yarda ya had'u da mace yau, dan an kwana biyu rabon da ya bawa dokinshi abincinshi 馃檲, wata tsuma yaji y'a fara dake tasowa tun daga k'asa tana kaiwa sama, saida ya gaji dan kanshi yaja leb'enta a cikin nashi yana raba bbakinsu a hankali yana kallon fuskarta, akin leb'enta yayi yana 'yar dariya ganin hawaye kamar an bud'e panpo, matse d'an bakin yayi yace "Na huce na yau, sai kuma na gobe idan na zo." A hankali ta bud'e ido tana saurin sunkuyar da kanta, so take ta mik'e ta bar wurin amma ya tsare wurin da girmanshi, kai ita sa茂 yau taga abinda yafi k'arfinta, ashe dai maza basu da kunya, a gidanmu? Daga d'aura auren? Kamar yasan me take tunani ya sake durk'usawa yace "D'abi'unmu kike tunani ko?" Hannaye tasa ta rufe fuskarta tace "Ni dan Allah ka fita, kar kasa Ayyata ta kalleni wata iri mana." Wani basaraken murmushi yayi yace "Zan fita, amma ki fad'awa Umma gidana kike so a kaiki kai tsaye, dan tace saikin fara zama a gidanta na sati biyu, ni kuma..." Shiru yayi ya mik'e yana kama hannayenta yace "Muje ki rakani, dama dana shigo baki gaisheni ba." Zaro ido tayi tace "Rakiya kuma? Ni d'in? Ayya ba zata bari ba." Kama hannunta yayi yanda ya gauraya yatsunta da nashi ya jata yana fad'in "Ko lahira nace zan tafi dake a yanzu babu mai hanani Samha, dan haka kowa cewa yake ki bini sau da k'afa." Suna daf da fita a d'akin ta cije tace "Ni wallahi kunya nake ji, baka ji me yallab'ai ya fad'a ba? Haka kawai na fita ana kallona, kaje dan Allah, biyayya zan maka amma ba daga yau ba." Da mamaki ya juyo yace "Ba daga yau ba? Sai yaushe kenan zaki fara min?" K'yak'yabta ido ta shiga yi hakan yasa shi cewa"Bari na tambayi Ayya naji sune suka fad'a miki haka ko kuma wannan karatunki ne." Da sauri ta rik'o hannunshi tana fad'in "A'a dan Allah." Kallon juna sukayi ya d'an had'e fuska, a hankali tace "Shikenan zan maka biyayya iya iyawata, zan d'ora k'afata a inda ka d'auke taka bada hanzari ba, fatana kawai ka jani a hankali yanda ba zan gurd'e ba." Murmushi ya sakar mata mai kashe jiki ya tallabi fuskarta yace "Batul, ki kwantar da hankalinki, insha Allahu indai nine na miki alk'awarin ko da kin gurd'e zan zama ina gefenki ba zaki kai k'asa ba da yardar Allah." Da kunya ta sunkuyar da kai tace "Allah yasa." "Ameen." Ya fad'a yana rumgumeta a jikinshi, wani tatsssss! Taji kamar wutar lantarki ta jata, sakin baki kawai tayi tana jinshi yana shafa bayanta, saida ya d'ago tayi saurin juyawa da k'aton hijabinta ta koma d'akin, da kallo ya bita yana murmushi harta shige uwar d'aka, girgiza kai yayi ya juya ya fita bayan ya musu sallama suka fita shi da Kalli. _Cakwakiyar yanzu zata soma insha Allah, idan mukayi duba da abubuwa kamar haka:_ _Idan har Alhaji Saddi k'anin mahaifin Hasheer ne? Kenan Aminu zai auri cousin d'in Hasheer ce, kuma fa wannan Alhaji Saddi shine littafinmu ya fara da kawo mana shari'arsu a kotu wanda Faduma tayi sanadiyar da aka kullesa, sannan shine bazawarin Zaliha kuma uba ga Nadia matar Omar abokin Tagur._ _Sannan a gefe d'aya Husna tana son auren Tagur saidai bata san iyayenta su san matsalarsa ta rashin haihuwa._ _A ina Saudat ta samu labarin Faduma da Hasheer a wani garin? Sannan me zata shirya da zai hana auren Aminu?_ _Ga Hasheer, ga Wardugu, ga Aji da kuma mahaifinsa, shikenan Faduma tasha wahalar banza kenan akan aikin nan?_ _Tagur ya ci alwashin shiga kotu da ita, ita ma kuma ta karb'i tayinsa da hannu biyu, ga kuma auren Hasheer a kanta, taya haka zai faru?_ _Shin a k'arshe ya makomar Amjad, waye zaiyi nasara a cikinsu, *Uwa* ko *uba*?_ _A k'arshe kuma ga *Faduma* ga *Hasheer* ga kuma *Saudat*, wace wainar zasu toya a gidansu?_ ```Duk zamu san haka bayan watan azumi insha Allah.``` *Yan Uwa anan zamu tsaya insha Allahu domin gabatowar wata mai alfarma watan ibada da bautar Allah, muyi k'ok'ari duk wani shirme da abinda ba zai anfanemu ba mu ajeshi domin samun falalar wannan wata, Allah ya nuna mana zuwanshi lafiya ya kuma sa zamu azumceshi har k'arshenshi, Allah ya ara mana rai da lafiyar bauta masa, sai mun had'u bayan sallah insha Allah.* _*Ayi ibada lafiya.*_ *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 21:41 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _63_ Suna fita Faduma ma da rakiyar cousine d'inta suka shiga gidan Herde inda suka 'yan uwan nata wanda sune kamar k'awayen a ynzu suka tsiri wasannin da dole ne a bikin tubawa, ko da kuwa k'aramar bazawara ce ke. Akan tabarma duk mutanen suke uwaye da yara da yan mata, an saka musu kid'a irin na guitar mai iyawa na taka rawa a tsakiyar filin, d'aki ta wuce kai tsaye bayan sun gama rangad'a mata bud'a wasu iyayen harda karin kud'i suka mata. Sun d'auki minti talatin anan taji sallamar Agaishat, Dada dake tsakiyar fili tana rawa tana d'aukar selfie dan turawa Abdallah ta tsokani rigima ce ta fara ganinta, dakatawa tayi saboda kunyarta tare da nuna mata d'akin Herde tace "Tana ciki, ashe har kun dawo?" Da fara'a a fuskarta tace "Mun dawo, kuna ta shagali ashe." Dariya kawai tayi ta bita da kallo sanda take shiga d'akin, sallamarta tasa Faduma d'agowa daga sunkuyar da kan da tayi tana amsawa da mamakin ganinta, tun kafin ta zauna tace "Ya kika dawo yanzu? Ai na d'auka fitar soyayya ce." Dariya tayi tana zama daf da ita tace "Bari kedai, nima haka nayi tunani, sai kawai gani nayi ya kaini gidan hakimi inda su Ayya suka sauka, ashe Anna ta ce ta zo ita ma, saboda jiya bata samu damar zuwa d'aurin auren ba, shine fa ta biyo jirgi yau ta zo." Zaro ido tayi da jin mamakin mutanen a ranta, suna da kirki dukansu da kuma kara, yanzu aurenta daya zo kwatsam shine aka ma taron da aka tara jiya, kuma abun birgewa duk Wardugu ne yayi ruwa yayi tsaki a lamarin, gashi yanzu harda surukanshi ma duk bai bari ba? Lallai ta yarda shi d'in babban mutum ne. Da sauri tace mata "Ina Anna taje?" Saida ta cire hijabinta tace "Tana nan wajensu Ayyarku, tare muka taho ai, amma yanzu zaki ganta ta shigo nan." Gyara zama tayi tana dariyar mugunta tace "Na matsu ta shigo ko na samu k'arin Ayya." Harara ta dalla mata tace "Annata tafi k'arfinki trozzo, ki ma canza tunani." Dariya tayi tace "Har mu gani." Da gudu Dada ta shigo d'akin a tsorace ta rufe wayarta tana fad'in "Abdallah ne ya had'a ni da mijinki, dan Allah karb'a ki bashi amsa, ni gabana fad'uwa kawai yake, na gagara samun nutsuwar yi masa magana." Dariya Agiashat tayi tana karb'ar wayar dan tasan gogonta ake nufi, tana karb'a tace "Sojana, soja mazan fama." Wani murmushi ya saki daga inda yake yace "Ta kasa min magana ko? Ai dagangan nayi a yaren da zata tsorata." Takwaf takwaf tayi da fuska a harshen buzanci tace "Bana so fa, ka tsorata mana uwa, yanzu me kuke so?" Saida yayi ajiyar zuciya yace "Muna so ne mu sani duka al'adar bikin tubawa zasuyi ne?" Cike da zak'ewa tace "Duka zamiyi, haka naji suna fad'a, ai wannan dole ne a mata tunda ita ma 'yar gata ce." Wani murmushin makirci yayi yace "Zasuyi, amma ke ai ba kya wajen." Take ya yanke kiran tare da mik'awa Abdallah wayarshi, kallon Hasheer yayi dake gefe yace "Duka zasuyi, kuma dama nayi tunanin haka, batuba ce dole kayi d'amarar yin duk abinda muka saka ka yaro." Wani murmushi Hasheer yayi yace "Zanyi komai a kanta War, kai dai kawai ka min jagora izuwa kowace al'adar." Muryar Abdallah suka ji a bayansu yana fad'in "Haba yarinya, ba dai ni ba, ai dai nine kika turowa hoto kina rawa, nace a bari kuma kika ce sai anyi, ba damuwa zan kamaki a hannu na." Kamar wasu 'yan biyu a tare suka girgiza kai suka juya suka ci gaba da tafiya inda Wardugu ke tuk'i a nutse sosai zasu k'arasa guardian d'in Kalli, dan zuwa safiya Hasheer zai koma haka ma Wardugu. ________________ Tana mik'awa Dada wayar ta amsa ta fito ita ma tana ci gaba da tsokanar Abdallah, ganin haka yasa Agaishat d'aukar ledar data shigo da ita fara mai kyau kuma babba ta mik'a mata, karb'a Faduma tayi da mamaki tace "Miye?" Da zolaya tace "Duba ki gani." Bud'ewa tayi sai kuwa ta fara cin karo da wannan turaren da sukayi maganarshi a Niamey, da sauri ta ciro tana dubawa da fad'in "Kai kai kai, wai kina nufin ni kika kawowa?" Dariya tayi tace "Gudunmuwar da zan iya baki kenan, turare a matsayinki na batuba." Wani kallo Faduma ta mata tace "Amma ai kema jiya naji kun gaisa da Ayya da harshen tubanci." Dariya tayi tace "Eh hakane, kinsan Anna ta ce batuba, mahaifina shine buzu, a haifemu a garin timiya mun gairma acan Annarmu ma yaren buzanci take mana, shiyasa yaren kawai mukafi iyawa..." Wani abu da Faduma ta hango shine tana maganar amma kuma tana had'e kuka da k'arfin tsiya tare da sinne kanta tana son b'oye hawaye, dafa kafad'arta tayi tace "K'awata, lafiya? Kin tuna wani abu ne?" Girgiza kai tayi tare da fashewa da kuka tace "B芒 komai." Cikin damuwa ta aje ledar gefe ta sake matsawa kusanta sosai tace "Ya zaki ce ba komai, dan Allah ki fad'a min kinji, kinga yanzu ni babu abinda zan b'oye miki, musamman ma da kika san komai akan Amjad." Cikin share hawaye ta d'ago kanta tace "Faduma kowa a duniya da jarabawarsa, ta wani takan girmi ta wani ne, sanda naji labarinki na miki kuka sosai tare da tausaya miki matuk'a, saidai ki sani murmushin da kike gani a fuskata mijina ne a samar min dashi, badan haka ba watak'ila ina rayuwar k'ask'anci a wani yankin, Faduma ke k'waya d'aya kika haifa, amma mu mahaifiyarmu mu biyar ta haifa abisa k'addararta." Gabanta ya tsinke ya fad'i ta kalleta ido waje, zufa taji ta tsatsafo mata da k'yar tace "Agaishat, me kike nufi?" Jinjina mata kai tayi tace "Tabbas, mu biyar, amma ba kamar yanda kike tunani bane." Kallon Faduma tayi da kyau tace "K'awata mun tashi a wani k'auye dake yankin Agadez da ake kira timiya, muna rayuwa tare da uyayenmu duka biyu, saidai mahaifinmu..." Tsaf labarin tarihinta ta fad'a mata, Faduma bata samu damar kuka ba sai hawaye kawai, a rayuwar nan? Lallai kaji dubu, duk da bata ganta ba amma tana ganin kammaninta a idonta, ta matsu ta shigo ta ganta, dole tayi fama da jin jiki mana, rayuwar aure ba tare da aure ba kuma bada saninka ba, har kayi ta hayyayafa haka? Rarrashin juna suka shiga yi da ban hak'uri tare da addu'ar Allah ya datar dasu da kyakyawar k'addara. Suna haka Anna tayi sallama cikin gidan, da sauri Faduma ta d'auki darar da aka rufa mata tun jiya kafin a d'aura aure wanda da k'yar cousine d'inta suka bari iyaye suka rufeta, kuma dama haka al'adar take, fuskarta kawai ta bari suna kallon k'ofar dan jin Dada na wa Anna iso zuwa d'akin. Da wata sallamar ta sake shigowa a bakinta, a tare suka amsa da fara'a sai Faduma da kanta ke sadde k'asa, har ta k'arasa kusa da ita ta zauna hakan yasa suka sakata tsakiya bata d'ago ba, tallabo fuskarta Anna tayi tana murmushi a harshen tubanci tace "Yarinya kyakyawa tubarkallah, Allah ya baku zaman lafiya." D'an d'ago idonta tayi tana murmushin yak'e amma bata amsa ba saboda kunya sai cewa tayi "Ina kwana Ayya na." Da murmushi tace "Lafiya k'alau." Agaishat ce tace "Anna kinga kafin ki zo cika min baki take wai zata rabani dake, amma gashi ta k'i ko da had'a ido dake." A hankali ta kalli Agaishat tace "Ba cika baki bane, hak'ik'a tayi nasarar rabaki dani, domin kuwa tunda na sauka a gidan hakimi nake jin k'awayena suna yabonta, a take naji ta shige min rai nima." Shagwab'ar da fiska tayi tace "Anna ke ma?" Jinjina mata kai tayi tace "Tabbas." D'an satar kallonta Faduma tayi ta mata gwalo, hararanta Agaishat tayi tace "Malaminki ya ci kud'inshi, kin raba Elhaj da Ummanshi, kin raba min miji da Ayyarshi, yanzu gashi nima kin rabani da Annata." 'Yar dariya Faduma tayi da kunya hakaan yasa Anna cewa "Kin gani, inba fitsara ba a gabana kike fad'in wai mijinki." Girgiza kai tayi lokacin da Agaishat ta rufe fuska alamar kunya, cikin nutsuwa Anna ta d'an jawa Faduma kunne da nusasheta zaman rayuwa tare da jadadda mata hak'uri akan sabuwar rayuwar da zata samu kanta a ciki, sun d'an jima kafin ta mik'e tace zata koma gidansu Ayyarta suyi sallama saita wuce, tare suka fita da Agaishat ta rakata ita kuma ta shiga duba turarukan da Agaishat d'in ta kawo mata tana jin dad'i sosai. ________________ Ko da Anna ta koma ta samesu a d'akin uwar gidan hakimi na alfarma, Umma na danna carbinta ta hannu sai Ayya dake gyaran farce Marfu'a na cin tuffa suna hira a nutse, saida suka jima suna hira har sukayi sallah azahar kafin Anna ta kalli Ayya cikin nutsuwa tace "Sai naji kamar kuna maganar tafiya da yarinyar gobe?" Ayya ce tace "Eh hakane, gobe zan rakasu su wuce da ita, idan na kwana biyu acan saina d'auki jirgin komawa gida." Jinjina kai tayi sai kuma tace "Amma me yasa ba zaku barta anan ba, ku bawa iyayenta damar kimtsata da kansu, sannan ita kanta zataji dad'i duba da yanda auren ya zo kwatsam, ina ga ai babu abun gaggawa a ciki ko?" Kallon Umma Ayya tayi ita ma ta kalleta, da ido sukayi zaurence kafin suka kalleta a tare, Ayya ce ta gyara zama tana aje abun gugar akaifar hannunta k'asa tace "A gaskiya bamuyi tunanin haka ba, amma gashi kin tunatar damu, ko ba komai ita ma budurwa ce kuma mai gata, hakan zai basu damar da zasu cika al'adarmu." Jinjina kai tayi irin to ko kufa tare da d'orawa da fad'in "Abinda ya kamata kenan, dama ance sati biyu ne bikin ya rage a yanda yake a tsare da farko, kunga nan da sati biyu sai amaryarku ta tare bayan kun turo angonta da abokanshi d'aukarshi, hakan shi zai tabbatar da an cika sharud'an al'adarmu, dan m没 fa ko bazawara ce indai ba babba to ana mata yanda aka wa budurwa ne." Ayya data san komai ce tace "Tabbas haka yake, kuma insha Allahu zamu gabatar da komai yanda ya dace." Matar hakimi ce ta muskuta tana fad'in "Kenan yanzu zaku tafi ba tare da ita ba?" Marfu'a ce tace "Hakan abun dai ya nuna a yanzu kam, to amma maganar gyaran jiki da muka d'auki nauyi fa?" Cikin dattako da nutsuwa Umma tace "Wannan ba matsala bace, tunda dama ko can aka tafi zamu basu damar kula da ita da kansu ne, tunda muna cikin duniyar da yarda tayi k'aranci ne, kawai zamu bar musu duk abun buk'ata saimu tafi, idan Allah ya kaimu sati biyun sai ta tare d'akinta kai tsaye." Anna ce tace "Gaskiya naji dad'i sosai da kuka d'auki shawarata duk da kasancewata mai k'arancin shekaru a cikinku." Dariya sukayi sai Ayya data d'an harareta tace "Ke ce mai k'ananan shekarun? Lallai ma?" Dariya suka sake saka mata dan yanda Ayya tayi abun, d'aukar abin gyaran farcen tayi ta ci gaba da gyaran akaifunta a nutse hannayen dake d'auke da tanfatsa tanfasan zobuna na zinariya kamar zasuyi magana. Ayya ce ta kalli Umma tace "Ban tambayeki ba? Kina ganin kuwa matarsa ba zata bayar da matsala ba? Duba da yanda lamarin ya kasance." Ajiyar zuciya Umma ta sauke cikin sanyin jiki tace "Dole zata bayar da matsala, dole nasan Saudat zata mayar min da yaro kamar mahaukaci." Matar hakimi ce tace "Tabbas zata ji zafi, amma ai kamata yayi tayi hak'uri tunda an riga an d'aura, kuma mijinta yana so kinga ai bata da wata dabara." Ayya ce tace "Kawai ki saka masa ido shi da ita d'in kiga me zai faru, kardai ki yarda dalilin kishinta tasa d'anki ya nemi zaucewa, idan kika ga haka zata faru ki rumgumi abunki ki samar mishi da nutsuwa." Murmushi Anna tayi tana d'an girgiza kai, hakan yasa matar hakimi ma yin dariya tace "Gaskiyarki uwar g茅n茅ral, dad'i na dake bakya son wasa, ke da kika zauna ma da Walyn kuma ta biki bare wannan da na tabbatar bata kai Walyn komai ba." Murmushi Umma tayi tace "Humm! Ba zata kai Walyn ba kam, saidai kuma ita ma tana ji da kanta sosai, tana ji da kwalliya da kyau da son ado, kawai rashin sakar mata kud'i ne yasa Walyn zata fita k'yalk'yali da ji da kai, shima kuma dan yana taka tsantsan ne saidai zuwa yanzu bana jin zai ci gaba da tauye iyalinshi saboda b'adda kama." Ayya ce tace "To Allah ya sanyaya mata, amma dai ta kiyaye dan bama d'aukar rainin matan 'ya'yanmu gaskiya." Dariya sukayi haka suka ci gaba da hira cikin nishad'i da farin ciki. _________________ Har dare 'yan matan suna wasannaninsu d'脿 nishad'i kafin kowa ya watse bayan raka amarya gida, tare da agaishat d'脿 dada, amma suna ganin duka iyalin Faduma zaune akan tabarma sa茂 suka wuce d'aki ita kuma ta zauna anan. Kamar yanda al'adarsu ta tsara haka suka gabatar ma Faduma da kyaututtuka na birgewa, duk da iya kud'inka iya shagalinka ne amma dai sunyi k'ok'arin wadatata da ado na zinariya wanda a al'adarsu shine gatan da zasu iya yi mata, tayi murna da duka kyautuka dan sunyi mata bajinta, godiya ta musu harda hawaye inda suka shiga rarrashinta. Daga bisani kuma Aba ya mik'a mata enveloppe d'in sadakinta, saida ta karb'a tace "Amma Aba ku rik'e a hannunku, ni babu abinda zanyi dashi." Murmushi yayi yace "Fadun Abanta, ni ma fa ina d'aya daga cikin masu son a dinga bawa 'ya'ya mata sadakinsu, tunda su ke morarshi, amma ya zaki goyi bayana nayi kura da shan bugu gardi da kwasar kud'i? Sam ba dani ba, Allah ma cewa yayi sadakinku bana iyayenku ba, ganin damarki ne ki dinga siyen ashana kina k'yastawa har kud'in su k'are, haka ma ganin damarki ne kiyi abinda zai anfaneki, mu dai fatanmu Allah ya baku zaman lafiya." Saida ta share hawaye ta kalli Yaya Kalli tace "Yaya kud'in nan suna da yawa fa? Ina zan kaisu? Kuma gashi ka dage kai da fata kai zaka min kayan d'aki." Murmushi ya mata yace "Million goma ne, sunyi komai daidai ruwa ne daidai tsaki, a wajensu da kuma wajenmu wannan ba komai bane, muna da yak'inin zaisan ya auri batuba, kamar yanda nake da yak'inin zaki san kin auri bahaushen dake da sirkin jinin larabawa a jikinshi." Sunkuyar da kai tayi a ranta tana maimaita goma? Goma fa? Amma dai da gayya suka mata haka ko? Suna so suga ta rikice ne kawai. A nan ta sanar dasu komai dake faruwa, tsaf ta kwashe komai ta fad'a musu daga had'uwarta da Tagur ta farko har ta k'arshen ma da kuma tayin daya mata ita kuma ta karb'a, ran Kalli ya b'ace sosai har saida yayi kamar zai daketa a wurin yana tuhumarta akan me zata tsaya ma b'ata lokacinta akan shi? Me yasa tun farko bata sanar dasu ba? Shi kam da tuni ya rufesa rufewa ta har abada, da k'yar Manu da sauran 'yan uwan suka tausheshi kafin Aba shima ya nuna sam shima baiji dad'i ba, dan da ace zai ganshi ido da ido da sai ya tsinke fuskarsa da mari, saidai akwai wata magana da tayi data sakashi duba lamarin shine da tace *uban d'anta*, hak'ik'a ko dan Amjad zasu iya d'aga masa k'afa ayi komai a mutumce, shiga kotu akan maganar nan zai ja musu terere na jama'a, duk da shi wannan bai dameshi ba amma su dole su duba mutumcinsu dana 'yarsu da kuma shi kanshi yaron. A k'arshe dai sun ce ta masa magana basa son ayi shari'ar a cikin mutane, suna da damar da zasuyi shari'a gaban alk'ali saidai a bayan fage, taji dad'in shawararsu dan ita batayi tunanin haka ba, taso kawai ta biye masa duk inda za aje aje kawai. *Washe gari* Har ga Allah sun tashi da shirin raka amarya gidanta ba da wata zugar mai yawa ba, saidai abun farin ciki zuwan su Umma gidan da safiyar nan da kuma fad'a musu zasu bar amarya har nan da sati biyu, sosai Ayya tayi farin cikin jin haka saidai bata nuna a fuskarta ba, sai kuma wasu mak'udan kud'i da Umma ta bayar dan cika alk'awarin data d'auka na d'aukar nauyin gyaran amarya, godiya suka musu sosai tare da musu addu'ar Allah ya tsare, inda Herde ta basu tabbaci zasu kula musu da amanarsu dan yanzu sun fisu iko da ita. Haka suka tafi da farin cikin karamcin mutanen da kuma kawar da kansu ga abun duniya, dan sun lura duk girman kyautar da zasuyi bata wani d'ad'asu a k'asa bare suyita rawar jiki, dukansu a jirgi suka koma k'asarsu har Anna ma data koma tun daren jiya, Agaishat ma bata so rabuwa da Faduma ba amma haka suka rabu, saidai taji dad'in turaren da ita ma ta bata wanda tace ya mata dad'i. Suna fita daga gidan Dada ta shigo d'akin da sauri a harshen tubanci tana fad'in "Faduma, Faduma kinsan me?" Faduma dake jiran ace ta fito harta cika fuskarta da hawaye ta d'aga kai ta kalleta, da murna Owwo tace "Sun tafi, sun yarda ki zauna anan har nan da sati biyu." Da sauri ta sauko daga kan gadon tana yaye hijab d'inta k'ato tace "Da gaske dada? Sun amince?" Jinjina mata kai tayi tace "Sun amince, har ma sun tafi." Wani tsalle ta daka harda rumgume Owwo tace "Kai amma naji dad'i, gaskiya sun kyauta min." Ita ma da dariya ta rumgumeta tana fad'in "Nima naji dad'i, kinga fa kenan tare zamu bar garin nan a matsayin masu aure, sannan zai zamana ranar da Ayyarki zatayi bikinta ne zamu tafi." Da murna sosai tace "Hakane fa dada, a ranar za'a d'aura aurenki." Murna suka dinga yi saboda farin cikin d'aga tafiyar nan, haka ma Ayya da Herde suka fara shirin kimtsa yarinyarsu daga gobe da zata shigo. _______________ Saudat dai ta koma sabon gidansu abisa tilastawar mahaifinta, ta koma inda ta tara mishi zugar k'awaye da 'yan uwa, shi dai duk dan a zauna lafiya haka ya wadatasu da abinci da abin sha suma, saida suka gama pacakarsu son ransu da iface ifacensu sannan suka tafi. Saidai ya lura da wasu sabbin k'awaye da tayi Atta Zaliha da kuma Hindu, Gomboy ma bata halarta bane saboda har yanzu bata ji sosai saboda bak'ak'en maruka da tasha hannun k'anin nata sai kumatunta da suka kumbura sukayi duhu abu ga fatar mai. Da dare Umma taje gidan tare da Marfu'a suka samu Saudat, saidai ran Umma ya b'ace ganin Saudat na mata kallon raini harda d'ora k'afa d'aya kan d'aya tana kalkad'awa, da k'yar saboda sanin ya kamata ta fara fad'in "Sadaut mun zo ne muyi magana akan al'amarin daya faru, nasan zaki ji ba dad'i za kuma ki jijjiga, ki sani mu ma dukanmu haka abun ya zo mana, shi kanshi Hasheer baisan da lamarin ba sai bayan an d'aura auren, da wannan nake rok'onki da kiyi hak'uri, nasan zafin da ake ji idan aka ce an maka abokiyar zama, tunda nima na d'and'ani zama da ita, amma idan kikayi hak'uri kika kawar da kanki komai saiya wuce, kusan zan iya cewa kamar ba'a miki adalci ba na rashin sanar dake, amma kamar yanda na fad'a abun kai tsaye ya zo babu shiri, kiyi hak'uri dan Allah ki zauna da mijinki lafiya da kuma abokiyar zamanki, idan kikayi haka zaki ci riba marar misaltuwa." Shiru tayi ta d'aga kai ta kalleta, ita ma k'arrr take kallon idonta tana jijjiga k'afarta, ganin bata da niyyar cewa komai yasa ta cewa "Saudat shi aure da kika gani..." Mik'ewa Saudat tayi da wayarta a hannu tana fad'in "Umma nagode da nasiha, zan shiga ciki na amsa kira ne." Juyawa tayi ta nufi kusurwar da zata kaita sabon d'akinta da yau take jinshi kamar wuta, gidan da take tunanin shigowa ita kad'ai, sai gashi bayan uwar da zata biyo baya harda kishiya, hmmm! Su zo d'in kawai ta fad'a tana shigewa d'akin. Marfu'a cikin jin haushi da d'aga murya kasancewarta irin masu babban muryar a harshen larabci tace "Dama haka? Me yasa baki fad'a min ba dan nayi zamana kar naga wannan takaicin, mtsssss!" Mik'ewa tayi a hassale ta fita Umma ta mik'e ita ma tabi bayanta, ko kad'an abun bai dameta ba, babban farin cikinta shine d'anta ya mallaki wacce take da yak'inin zata faranta masa, dan ta gaji da ganinshi cikin yanayin damuwa da sanyi kamar wani marar kuzari da shiru shiru. Saida ta tabbatar sun tafi ta fito tana fad'in "Aikin banza aikin wofi, ke a haka aka miki taki kishiyar ne? Sai ni da aka raina za'a min haka, wallahi duk sai kun gane kurenku." Zaune tayi kan kujera da wayarta a hannu, su Izzadeen ne suka shigo da gudu suna wasa, a tsawace tace "Maza ku wuce d'akinku ku kwanta, bana son hayaniyar nan." Da sauri suka nufi d'akin nasu, ta danna kira a wayar sai kawai taji kuka ya kubce mata, kashe kiran tayi ta jefar da wayar kan kujera ta fad'i zaune ta fashe da kuka. Sama da awa uku ta d'auka a wurin nan tana kuka tsakaninta da Allah, har takai ta tsaya sai shashek'a da take kamar zata mutu ido sun mata sumtum murya ta dishe. Mai gadi da Qaseem ne suka aje akwatina a k'ofar d'akin suka juya suka koma, da tausassan sallama ya shigo a bakinsa yana jawo wasu daga cikin akwatinan, amma ganin Saudat zaune tana kuka kamar zata mutu yasa shi sakin akwatinan ya k'araso da sauri, cire takalminshi yayi bakin carpet d'in mai kalar ruwan k'wan da maroon kamar yanda kusan komai na gidan kalarsa kenan, zaune yayi k'asa kamar yanda take ya kamo hannunta ya tallabo fuskarta da hannu d'aya yace "Subhannallah! Bab, me ya sameki haka? Lafiya?" Fizge fuskarta tayi a hassale ta mik'e ta d'auki wayarta ta juya a k'ufule ta shige d'akinta, girgiza kai yayi ya mik'e ya bi bayanta, yana shiga zaune ya sameta akan kujerar dake gaban madubi, durk'usawa yayi ya rik'o hannayenta yace "Bab, ki fad'a min me ke faruwa mana? Kinsan damuwarki nima damuwata ce ko?" Da wani babban kallo ta bishi tace "Allah ko? Ai na gani, b茅b茅 damuwata damuwarka ce amma shine ka kasa nuna min haka a aikace? Yanzu abinda ka min kayi min adalci kenan?" D'an sunkuyar da kai yayi yana kallon hannayenta yace "Na sani Bab, amma kiyi hak'uri kinji, nima a bazata abun ya zo min." Da k'arfi ta d'aga murya tace "A bazata? Yarinyar da kuka kwashi kwana hud'u tare a wani gari, shine zaaka ce aurenta ya zo maka a bazata." D'an girgiza kai yayi hakan yasa tace "Nan miye baka fad'a min ba? Nuna min kake ta maka nisa zatayi aure, ashe duk munafurci ne ana can ana d'aura maka auren da ita ni kuma ka zo kana raina min hankali, to b茅b茅 kaji da kyau, wallahi ba zan zauna da karuwar nan ba, yarinyar data gama yawan tazubar a titi harta haifi yaro a waje, yarinyar dake raba mata da mazansu ni saina zauna ta rabani da kai." Mik'ewa tayi ta koma kan gado ta zauna tana share hawaye, mik'ewa yayi ya zauna bakin gadon ya sake rik'o hannayenta, sake kubcewa tayi tace "B茅b茅 babu dad'in bakin da zaka min, zama ne da yarinyar nan ba zan iya ba, kawai kasan yanda zakayi dani." Kallon idonta yayi cikin son tausar zuciyarshi yace "Yanzu ya kike so ayi Bab?" Cikin tijara tace "Ko dai ka saketa shikenan mu zauna lafiya, ko kuma ka nuna min kafi sonta a kai na ni kuma ka sakeni, amma zamana da ita a gidan nan sam ba abu bane mai yiwuwa." Wani murmushi yayi mai ciwo yace "Na saketa bab? Amma kina ganin idan nayi haka nayi adalci?" Ita ma kallonshi tayi tace "Ni kenan ka min adalci haka? B茅b茅 ka min adalci dan Allah?" Girgiza kai yayi ya jawota jikinshi ya rumgume yana fad'in "Na sani bab, ko kad'an ba'a miki ba, shiyasa ma muke baki hak'uri, kiyi hak'uri ki yayyafawa zuciyarki ruwan sanyi, dan Allah karki d'aga hankali har hakan ya jawo miki matsala, kin dai san halin da kike ciki." Girgiza kai ta shiga yi tana cakumar rigarshi da babban sauti take fad'in "Bebe ba zan iya ba, wallahi ba zan iya hak'uri ba, zuciyata tafasa take kamar zata fashe, k'irjina ciwo kawai yake min, ka taimake ni b茅b茅 dan Allah karna mutu." Daddab'ata ya dinga yi yana shafar kanta da d'an kwalin ya fita yana fad'in "Ya isa Bab, karki d'aga min hankali mana, kiyi hak'uri kiyi ta ambaton ubangiji a ranki, komai zai zo miki da sauk'i insha Allah." Cikin kuka tace "B茅b茅 karuwa fa ce, karuwa ce harda d'an shege ta aje fa, wallahi ba k'arya nake ba ka bincika zaka sani, yaronta fa shine abokinsu Izzadeen, kuma k'arya take fad'a wallahi mahaifinshi yana raye, b茅b茅 karka had'ani kishi da 'yar bariki ba zan iya ba." Tunda ta fara magana ya lumshe ido yana sauraronta, kalmar karuwar d'aci take masa sosai, amma ya zaiyi a yanzu daya wuce saurare, tallabo kanta yayi ya kalli fuskarta duk ta fita hayyacinta, cike da tausayinta ya had'a bakinshi da nata ya shiga sumbatarta a sanyaye sosai, ta so ta kubce daga gareshi saidai ya hanata damar haka, tun tana tureshi da k'arfi harta daina sai a hankali ta shiga tureshi tana rera kuka mai sautin da baya fita. Wasa tayi wasa tayi nisan zangon da dukansu babu wanda keda k'arfin halin iya dakatarwa, saidai Saudat kuka take kamar dai yau ne daren farkonsu, babban abinda ke zuwa mata a lokacin bai wuce tunanin yanda duk wannan salon na gwarzon mijinta da kuma tsarinshi mai rikita bawa had'e da wuyar mantawa, sabonshi mai sakata k'ara narke mishi, mai mata zuwa d'aya tak tasan ya zo da kanshi da kuma kayan aikinshi, shine yau aka d'aura irin igiyoyin da aka d'aura musu wanda suka hallata mata ganin mafi k'ololuwar sirrinshi. Lallai zata mutu idan wannan ranar ta zo, had'a shinfid'a da wata akan shi, ta sanshi ya santa har ma su dinga kwana a tare, lallai mutuwa zatayi idan haka ta kasance. Sanda yayi niyyar tashi daga kanta da k'arfi ta jawoshi ya fad'a kanta, da hanzari ya d'an d'agata dan baiyi tsammanin haka ba, shiyasa ma ya fad'a mata da duka k'arfinshi, shi kuma baya son abinda zai shafi cikin dake jikinta, shiyasa yanzu ma sama sama ya caccaketa, a da yana tanadin harta haihu saiya huce takaici, amma yanzu takacin ya koma kan Batul, ita yake so ya wa ragargazar wulak'anci ta bambamce uban d'anta da kuma future uban 'yayanta, yanke masa tunani tayi ta hanyar fashewa da wani kukan tana fad'in "Babe dan Allah dan Annabi ka min rai, karka had'a min kanka da kowa, wallahi mutuwa zanyi idan kaje ga yarinyar nan, karka min haka b茅b茅 karna rasa raina." A hankali ya gyara kwanciyarshi kan gadon ya sake jawota jikinshi ya matse tsam, cikin kunne ya rad'a mata "Matar dana fara so a rayuwata Saudat ce, ita ta fara haifa min yaron daya zama sanyin idaniyata, a dalilin Saudat nake shiga duk inda wani babban mutum kuma magidanci yake shiga, saida na fara sanin Saudat nasan miye so, had'uwata da Saudat na fara sanin ta-kamata da karamci, saida na sameki ne hankalina ya gama cika kamilalle, Saudat ita ce arzik'ina kuma aljannata, Sa'adatu sa'ar mata, Sa'adatuna fara mai farar zuciya da farar aniya, ina sonki Saudatuna, ina k'aunar fiye da yanda nake son kaina, shigowar wata rayuwata bashi yake nuna zan daina sonki ba, ke daban, ita ma daban, kowace da huruminta a zuciyata, sanin duk wani namiji zai iya bawa kowace matarshi matsayin daya dace yasa Allah ya hallata mana auren fiye da d'aya, ki nutsu uwar 'ya'yana ki aje hankali, ke kike mulkin gidana kuma ke zaki ci gaba da yi har bayan raina, kada kiyi abinda zai bud'e k'ofar raini tsakaninki da 'yar uwarki, ba zan lamunci a raina min martabata ba, duk wacce tace zata miki kallon mai bisa ruwa ni kuma zansa k'afar wando d'aya da ita." D'auke bakinshi yayi a kunnenta ya sake rumgume yace "Ki kama girmanki kinji, a matsayinki na wacce tafi kowa sanin Hasheer, a matsayinki na wacce take da sani akaina fiye da mahaifiyata ma ta wani b'angaren, a matsayinki na wacce tasan ciki da wajena, sannan kiyi alfahari kasancewarki matata ta fari, kisa wannan kawai a zuciyarki kiyi farin ciki, idan kika min haka ni kuma zan tabbatar dana kaiki matakin da a duniyar nan dai tamu babu wani mahalukin daya tab'a yi wa uwar gidansa wannan gatan." A gaskiya idan taji bata ji sanyi a zuciyarta ba k'arya ta shirga, taji ya fasa mata kai sosai kuma dama ta sanshi ba daga nan, mutumin soyayya ne kawai dai itace d'in sa茂 a hankali shima saiya jefar da makaman ya huta, amma fa iya kalamai ga Hasheer na daga cikin abinda yaja ra'ayinta akan shi harta daina kula kowa sai shi, uwa uba ga kuma k'ask'antar da kai a gaban mace, shi dan ya rok'eki ko yace kiyi hak'uri ba komai bane a gurinsa, ga kuma tausayi da yi wa mace uzuri, shiyasa ta so mallakarshi ita kad'ai, amma da alama k'addara ce ta riga fata. Wannan dare haka sukayi a manne da juna tana ajiyar zuciya da shashek'a shi kuma yana aikin rarrashi, ko baccin kirki dukansu basu samu ba saida sukayi sallah asuba tare, bayan sun idar ne ya sake janta suka koma gado, ba jimawa bacci ya d'auketa dan ta jima rabon data samu baccin mai kyau da dad'i. Baiyi bacci ba sai tunanin abubuwan dake ta faruwa haka, har saida rana ta fito ya mik'e da kanshi ya shirya yara cikin kayan makarantarsu ya kira Qaseem ya kaisu tare da cewa ya sama musu abu su ci a hanya, akwatin nan ya shiga dasu d'akin ya aje mata, yasan irin kayan daya zuba mata dole ya birgeta dan shi yasan wacece Saudalarshi, saida ya jere mata su guda takwas ya cire doguwar rigarshi ya watsa ruwa kafin yayi shirin fita zuwa gaishe da su Umma da suka dawo yana so yaji ya labarin murmushinshi me ake ciki. Murmushi yayi shi kanshi sanda zuciyarsa ta fad'i haka, a ransa yake ayyana "Banda abun Saudat, da fa wani ta aura ba ni ba da yanzu kina jinyar mijinki ne, to amma bata fad'uwa dole ayi shiru saboda tsaro." _Mata b芒, zama damu dole, in baka zauna da mata ba ka zauna da k'anwa ko yaya, in haka bai faru ba akwai 'ya, idan shima ya gagara to fa akwai kankat, wacce ta silarta ne ma ka zo duniyar *uwa*, da girman kujerarmu._馃拑 Tsaf ya gama shiryawa ya zauna gabanta ya sumbaci goshinta tare da shafa kanta, har zai mik'e ta rik'e hannunsa suka kalli juna, murmushi ya sakar mata tare da fad'in "Barka da tashi sarauniyata." Lumshe kumburarrin idonta tayi kawai ta masa yak'e, saida ta tashi zaune ta gyara zamanta tace "Fita zakayi ne?" Sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke yace "Eh rabin raina, zan d'an fita ne amma ba jimawa zanyi ba zan dawo." Cikin kallon tuhuma tace "Ina kenan?" D'an satar kallonta yayi shima yace "Wajensu Umma zanje." Tab'e baki tayi tawar da kai tana fad'in "Hummmm!" Murmushi yayi bai ce komai ba shima. Cikin rashin kulawa tace "Kaje, amma ka fara saukeni asibiti zan ga likita na yau." Da mamaki ya kalleta yace "Likita kuma? Meye matsalar?" Yatsina fuska tayi tace "Maganar aurenka ta jijjigani sosai b茅b茅, shiyasa jinina ya hau fiye da yanda kake tsammani, zanje ganin likitan ne kamar yanda ya buk'aci ganina yau." Wata iska ya furzo ya kalleta yace "To ki shirya saimu tafi tare, idan na ajeki saina wuce kafin ki kammala na dawo saimu dawo gida tare." A hankali ta shiga saukowa daga kan gadon, da kallo ya bita yanda take komai a sanyaye harta shiga ban d'akin, mik'ewa yayi ya fita daga d'akin da wayarshi a hannu, k'ayataccen falon ya zauna dan jiranta yana duba tashoshin da yasa aka kaama mishi don kallon shi da kuma yara. A k'alla saida ya kwashi minti hamsin da biyu zaune harya manta ma da jiran wani yake, da sauri ya duba agogon hannunshi, ganin lokacin yasa shi zabura yana aje remonte d'in hannunshi yana fad'in "Har lokaci ya tafi haka? To shirin me take?" Zai nufi d'akin kuma ta bud'e k'ofar ta fito, sanyayyan kallo ya bita dashi harta k'araso gareshi, batayi kwalliya ba saidai ta shige cikin wata had'add'iyar shadda riga da siket ta d'ora mayafi akai, saida ta k'araso tana gyara jakarta tace "Mu tafi ko, saidai kuma ban ci komai ba." Idonshi akan fuskarta yace "Bab da kin aje mayafin nan, dubi kayan sun fito da jikinki sosai, ki taimakeni kinji." Wani kallon gatsali ta masa tace "Uhum? Kaga kuma harna saba gaskiya, kuma naga ai munsha yin maganar nan da kai ko? Kawai ka barni haka nake son fita." D'an girgiza kai yayi tare da d'auke kai daga gareta yace "Me zaki ci nasa a kawo miki?" Cikin yatsina fuska ita ma tace "Ni indomie zanci , zan dafa da kaina kawai." Da kallo ya bita sanda take shiga madafar, cikin takaici ya sake girgiza kai ya koma ya zauna, tunanin taurin kai irin na Saudat yake, a matsayinshi na namiji yana da wasu d'abi'u da a gaskiya rashin samun wanda zai tafiyar dashi a yanda yake so babbar matsala ce, yana da son daya fad'a sau d'aya tak ace to ko shikenan, akwai lokacin da ma mulkinshi ke hawa, yana da yak'inin bashi da gaskiya, amma kuma a haka yake so ace kayi hak'uri, wannan d'abi'a ce da kusan kowane namiji yana da ita, rashin sanin haka zai janyo maka samun matsala da kace-nace a zamanka dasu. *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 21:41 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _64_ Ta d'auki sama da minti ashirin kafin ta fito da farantin indomie da safaffen k'wai, k'asa ta aje ta zauna ta jawo farantin gabanta, saida ta saka hannu ta kalleshi tace "Zaka ci?" Girgiza kai yayi alamar a'a, ko a jikinta kam sai ci gaba da cin kayarta hankali kwance, ganin kamar dagangan take son sa shi makara saiya basar daga kallonta ya shiga duba sak'on da Wardugu ya turo masa, girgiza kai kawai ya shiga yi da mamakin yanda ya cimma nasarar nan da kuma farin ciki da son isar da sak'on wajen amaryashi. Bai ma kula da sanda ta gama ba ta tsaya gabanshi, saida yaji muryarta tace "Muje." Kallonta yayi kafin ya mik'e ya shiga gaba ta bi bayansa, saida ya kulle falon kafin ya cire makulli d'aya a cikin uku na k'ofar ya mik'a mata d'aya yana fad'in "Ki rik'e wannan a wurinki." Kallonshi tayi sororo, tunawa da waccen gidan sanda aka kaita makulli uku ya bata shi ya d'auki d'aya dake masu hud'u ne, amma yanzu ya d'auki d'aya ita d'aya kenan waccen d'aya? Fizgar makullin tayi ta shige gaba ta barshi nan yana kallonta da mamaki, 'yar k'aramar k'wafa yayi kawai ya wuce, so yake daga yanzu har sanda zai tabbatarwa kanshi ya mata adalci yayi hak'uri da duk abinda zatayi, zai daure ya had'e komai har sai ya gamsu a ranshi yayi iya iyawarshi a kanta, dan duk yanda auren nan ya zo masa a bazata tabbas an shiga hakk'inta, dole a lallab'ata a kuma saurari kukanta, bai dace a k'ara mata zafi kan zafi ba. Ita kanta saida ta tsaya kallon sabuwar hilux d'in daya bud'e mata mazaunin kusa dashi a gaba, had'e yawu tayi kafin ta shiga ta zauna, har k'asan ranta tasan fa ta shigo gari, dan harda tana cikin juyayi a jiyan nan fa da taga k'awayenta da 'yan uwa nata santi a kan gidan, a take ta fara d'aga hanci tana hurashi sama tana musu kallon mai bisa ruwa, ginin ne yayi ba k'arya kuma a yanda ta san shi da taka tsantsan batayi tsammanin zai iya kece mata raini ta hanyar gwangwaza mata wannan k'ererren gidan ba. Suna fitowa daga wajen pakin d'in motocin suka ci karo da mai aiki maji k'arfi yana ta sharar dattin da aka wa gidan na jiya, gaishesu yayi har k'asa kasancewarshi matashi ne, da kulawa Hasheer ya amsa banda Saudat data kalleshi ta d'auke kai, k'arasawa sukayi nan ma mai gadi ya ja musu k'ofa ta b'angaren hagu, gaishe su yayi shima kafin suka bar gidan. Asibitin kud'i suka nufa, har zai fita tare da ita tace "A'a b茅b茅, ka barshi ni zan shiga ciki, idan buk'atar ganinka ta taso zan kiraka a waya." K'ala bai ce ba sai kallon gabanshi da yayi kawai, harta bud'e murfin ta kalleshi tace "Baka ban komai ba." D'an kallonta yayi tare da saka hannu aljihu yace "Nawa kike buk'ata?" D'aga kafad'a tayi tace "Ko nawa ma." Murmushi yayi a ranshi yana fad'in "Saudat da kud'i sa茂 Allah." Shi kanshi bai k'idaya ba ya mik'a mata sabbin fitowa daga banki jajir da su, har ga Allah saida ta d'an murmusa ganin kud'in nan a hannunta da bata san nawa bane shi ma kanshi wanda ya batan, karb'a tayi tana had'e fuskarta dan karya gane tare da k'udurawa a ranta, tunda dai har y'a ci amanarta to ya fara kashesu kenan har sai aljihunta ya cika, ficewa tayi tana fad'in "Kar kayi saurin tafiya, zan shiga naga ko zan samu ganin likitan da wuri." Shi dai ido ya zuba mata kawai, ya zaiyi to dama? Ya kalleta kawai yaga iya gudun ruwanta, wayarshi ya ciro ya ci gaba da dannawa, Umma ya kira ya tambayeta kwanan bak'i ta amsa da komai lafiya, sannan ta tambayeshi yaushe zai shigo, fad'a mata yayi ya kawo Saudat asibiti, sai kawai ta bisu da addu'a ta kashe wayar. ________________ Su ma yau da farin ciki da kuma hidima suka tashi a gidan, duk da uwar Zulfa taso kawo tangard'a dan ita takaicinta d'aya yaron nan har an fara magana tsakanin iyaye ya nuna baya so yana da wacce yake so, yanzu dan tayi aure da wanda take so ita ma shine za'a sake dawo wa da 'yarta shi? Amma da Saddi ya zare mata ido saita rasa yanda zatayi daya wuce hak'uri ta kalli ikon Allah. Tun safe Omar ya kawo Nadia gidan suna ta kai da kawowa, ita ma kuma tuni ta gayyaci k'awayenta dan su zo tarban kayan k'anwarta da za'a kawo, kuma dayawa sun amsa gayyata ta hanyar tabbatar mata da zasu zo. _________________ Sosai Aji ya sakankance da lamarin har ma da tsarabar saka ido akan auren Faduma, su Safwan da aka kama basu dameshi ba saboda a tunaninshi ya rufe kowace k'ofa da zata kawo masa barazana, hatta da lokacin da aka d'aura auren a kunnuwanshi ya sauka, saida aka gama komai ya kira Tagur a waya, cikin shashantar dashi da mayar da shi gaula yace "Tagur ban gane ba, na d'auka kace Faduma taka ce, ya kuma ka bari aka aura mata wani?" Lokacin yana saman hanya yaja birki da k'arfi yana fad'in "Ban gane ba Aji? Me kake fad'a haka?" Shima a rashin fahimtar yace "Kamar ya baka gane ba? Kana so kace baka san an d'aura aurenta bane ko me?" Da sauri ya fito daga motar ko rufewa baiyi ba yana fad'in "Fadumar? Uban waye ya auri matata? Wane d'an iskan ne ya auri uwar d'ana? Bai san ko ni wa bane? Kai wallahi ba zai yiwu ba." Tab'e baki yayi daga inda yake yace "Ai kuwa ya yiwu, tunda yanzu haka tana gidan iyayenta a matsayin matar wani, sati biyu kuma zata tare gidan mijinta." Duka ya kaiwa motar yana fad'in "K'arya ne! Aji kaji na rantse maka da Allah wallahi babu inda zata je, Faduma? Tawa ce, koma uban waye dole ya saketa." D'orawa yayi da "Fad'a min waye shi? Me yake ji dashi? Waye ubansa a garin nan?" Da mamaki Aji yace "Me zakayi Tagur? Karfa ka janyowa kanka rigimar da tafi k'arfinka." A tsawace yace "Babu ruwanka, idan na jawo ka koma gefe ka yi kallona." Sake tab'e baki Aji yayi a ranshi yace "Dama nace maka zan durmiya ne muyi nink'aya tare da kai a matsalar?" A zahiri kuma cewa yayi "Tagur wannan harkar fa ta manya ce, wallahi wannan karan saidai mu zuba ido muyi kallo, domin kuwa *sawun giwa* ne ya take na rak'umi, kuma wannan karan Faduma ta kece raini ta d'auko *d'awisu* a cikin tsintsiye, ita ma babbar yarinya ce badan kai daka lalata mata komai ba, amma kuma kasan hausawa sun ce *babban goro* sai *magogin k'arfe*." Kamar zai fasa wayar da iya k'arfinshi yace "Zaka fad'a min abinda na tambaya ko saina kashe ka? Dan ubanshi goron ya ci uwarshi." Dariya Aji yayi daga inda yake ta samun nasarar kaishi bango, cikin nutsuwa yace "Hasheer Abdul rahaman Nakiri, babban d'a ga mamallakin masana'antun risham, jigon talakawa da gajiyayyu, jagoran 'yan kasuwa manya da k'anana." Duk yanda Tagur ke cikin tashin hankali bai hanashi fahimtar gaskiyar da Aji ya fad'a ba cewa sawun giwa ya take na rak'umi ba, duk yanda yake da k'i fad'i amma dai zuciyarsa ta karaya ya kuma saduda, dan daga can k'asa ta raya mishi cewa "Kai ba kowa bane aka had'aka dashi." Amma sai yace "Zai gane bashi da wayo tunda ya had'a hanya dani." A wajen Aji ma cewa yayi "Ko kuma kaine zakayi wayon yanzu ba tunda zaka shiga sabgarshi." Bai gama fahimtar komai ba yaji ya datse kiran wayar, d'aukar hanya yayi a sukwane ya nufi gida dan fa ba zai yiwu ba. ________________ Ta jima ciki har saida ya kirata a waya, tana d'auka yace "Bab ya dai? Ina fata dai ba jikin bane?" Cikin shagwab'a kamar zatayi kuka tace "B茅b茅 har yanzu jinina bai sauka ba fa, amma gani nan fitowa saika mayar dani gida." Da mamakin jin k'arfin halin Saudat yace "Ban gane na mayar dake gida ba?" Cikin yanayin sangarta tace "To miye baka gane ba? Angama dubani kuma an rubata min magani, gani nan fitowa yanzu." Jim yayi yana tunanin kalamanta kafin ya datse kiran, kusan minti goma kafin ta fito cikin nutsuwa da jakarta a hannu da takardar magani mai d'auke da tambarin likitar, bud'ewa tayi ta shiga ta zauna sai langab'ewa take ta mik'a mishi takardar maganin, karb'a yayi yana dubawa kafin ya saka aljihu ya tayar suka tafi, ganin ya d'auki hanyar komawa gidan gadan gadan yasa ta cewa "B茅b茅 maganin fa?" Ba tare daya kalleta ba yace "Idan na ajeki saina siyo." Turo baki tayi tace "Um um, salan ka manta da lafiyata idan ka had'u da Umma ko?" Kallon mamaki ya mata tare da cewa "To ya kike so ayi yanzu?" Cikin shagwab'a tace "Kawai ni muje tare ka siya ka bani, in ya so saika tafi." K'aramar ajiyar zuciya ya sauke ya juya akalar motar, ya gama fahimtar so ne take tayi abinda zaisa a fara nunashi da baki, dan rashin zuwa ya gaishe da bak'in nan zai ja masa abubuwa maras dad'i, duba da tun lokacin da suka zo amma hidimarsu jiya ta hanashi tafiya ganinsu. K'ara gudun motar yayi sosai wanda hakan yasa shi isowa 17 portes, kai tsaye pharmacie 17 portes ya nufa dake jikin likitar tattali, ya cire d'amararshi zai fita tace "B茅b茅 jirani mu tafi tare." Kallonta yayi yace "Saboda me? Ke ma yanzu ba k'in shiga kikayi dani asibiti ba." Kamar zatayi kuka tace "To ai da dalili ne, ni kawai zan bika, idan mukayi sa'ar samun k'awata a ciki zata mana sauk'i fa." Wani banzan murmushi yayi a ranshi yace "Ni na fad'a ina son sauk'in kuma?" A zahiri kuma c茅wa yayi "Muje." Tunda ya lura rigima ce take nemanshi da ita, dan yace a'a tace saboda yayi amarya ne, a hankali suka shiga takawa har suka shiga ciki, su biyu suka samu akan aikin yau mace da namiji, saidai ta layin namijin akwai mutum har biyu, bayan wani dattijo ya tsaya dake gaban macen tana neman canjin da zata bashi, tana mik'a masa ya matsa gaba yana ciro takardar da mik'a mata. Karb'a tayi tana k'are masa kallo da kuma hangen Saudat ta wutsiyar ido, saida ta d'an taune leb'enta na k'asa ta shiga kakkane masa ido tace "Bonjour monsieur." Satar kallon Saudat yayi kafin yayi murmushi ya amsa mata da ido, takardar ta duba kafin ta juya dan d'auko maganin tana fatan Allah ya d'orata akan bawan Allahn nan daya gama had'uwa mak'ura, juyowa yayu ya kalli Saudat yace "Bab ba ita ce k'awar taki ba?" Tsaki taja tana kawar da kai ba tace komai ba, d'auke kanshi yayi shima yana girgiza kai, jim kad'an ta dawo da magungunan a hannunta ta aje saman teburin daya musu shamaki a tsakani, saida tayi danne danne a na'urar dake gabanta kafin ta kalleshi ta fad'a masa kud'in, hannu yasa aljihu ya ciro ya mik'a mata, karb'a tayi ta fara k'ok'arin zaro canji, da hannu ya fara mata alama kafin ya d'aga bakinshi a nutse cikin tattausan murya yace "Ki barshi." Da sauri ta kalleshi, duk da tayi tsammanin haka amma yanda ya mata magana ya d'ad'a a k'asa gaskiya, bata san lokacin data saki murmushi ba tare da d'an sunkuyawa ta duk'ar da kanta tace "Merci monsieur." Leda ta d'auka ta saka masa ta mik'a masa, yana karb'a ya juya suka fita inda ta bishi da kallo kamar zata jawo shi, suna shiga mota ta kalleshi tace "B茅b茅 dama haka kake sakin fuska ga kowace mace? Shiyasa wacce karfar ma ta mak'ale maka." Gyara zama tayi tace "Wallahi kaji na rantse, inhar kasan neman mata kake ka sakeni na koma gidanmu, dan duk randa asirinka ya tonu Allah saina zama ajalin..." Tafin hannu yasa ya rufe mata baki, girgiza mata kai yayi cikin sanyin murya yace "Kowace kalma dake fita daga bakunanmu akwai mala'ikun da suke rubuta mana ita, kuma zamu sameta rubuce akan littafinmu, kisan me zaki dinga fad'a da bakinki Bab, kar kiyi maganar da zata yanka wuyanki." Fizge bakinta tayi daga hannunshi tana fad'in "Ni ka mayar dani gida, kuma karuwar daka aura ba zan zauna da ita ba, dole kasan yanda zakayi dani wallahi." Tayar da motar yayi yana d'an cije leb'enshi na k'asa, hanya suka d'auka saidai babu mai magana in banda sauke numfashi da suke, a k'ank'anin lokaci ya kawota gidan kuma daga bakin k'ofa ya tsaya, bud'ewa tayi ta fita ranta a b'ace duk da ba yanzu ta so su rabu ba, saida yaga shigewarta tana dallawa mai gadi harara dake mata barka da dawowa kafin shima ya tayar yana girgiza kai. _______________ Yau ma da gudun tsiya ya shiga gidan bayan yayi odar data firgita duk mutanen gidan, Husna dake farfajiyar gidan tana amsa waya ne taga shigowarshi, tun daga yanda ya fita a motar ya tunkari b'angarenshi ta tabbatar ranshi a b'ace yake, ajiyar zuciya ta sauke a zuciyarta take raya "Ko me ya faru kuma yanzu? Kullum shi da bak'in rai yake shigowa gida." D'an tsaki tayi ta aje wayar bayan sunyi sallama ta bi bayanshi, a hankali ta k'arasa tura k'ofar tana mai rarraba idonta zuwa inda za ta hange shi, ganin baya falon ya sa ta k'arasa shiga baki d'ayanta, sai da ta zo tsakiyar falon kusa da k'aramin teburin dake tsakiyar ya fito da sauri daga uwar d'akinshi, cak ya tsaya yana bin ta da tuhumammen kallo daga k'asa har sama, a tsawace kamar zai fasa d'akin yace "Me ya kawo ki nan?" Zabura tayi ta shiga rarraba ido tana kame-kame, wata tsawar ya sake daka mata yace "Na ce me kike min a d'aki?" Da sauri ta rintse ido tare da fad'in "Yaya Tag dama..." Da k'arfi yace "Dama me?" Kamar zata fashe da kuka tace "Dama na ga ka shigo ne kamar ranka a b'ace, shi ne..." Shiru tayi ba ta k'arasa ba dan haka yace "Shi ne kika zo ki titsiye ni ki ji damuwata ko? Tun da ke ce uwa ba." Da sauri ta girgiza kai alamar a'a, nuna mata k'ofa yayi a hassale yace "Fita anan kafin na same ki anan?" Da sauri ta juya dan jikinta har rawa yake saboda tsoro, har ta kai k'ofa kuma ta ji maganarshi kusa da ita alamar ya taho shi ma yana fad'in "Idan ma kina da abun yi mai mahimmanci ki je kiyi, ban da lokacin duban wata 'ya mace a yanzu bayan uwar d'ana da na ke paputukar ganin ta dawo gareni." Da sauri ta juyo ta kalleshi, duk da bata iya tsayawa suyi dogon zance da shi, amma haka ta ji k'arfin gwiwar fad'an abin da ke ranta, sai da ta d'an ja majina kad'an kamar wacce ta yi kuka kafin tace "Ni ma ba ni na siya ba, Allah ne ya d'ora min son ka a zuciyata, ba na kishi da uwar d'an ka na fari a duniya, kamar yanda na ke jin ni ma uwa ce ga d'an ka Amjad, zan iya zama da kai duk adadin matanka, in dai ni ma zaka kulani a matsayin matarka." Sama da k'asa ya haarareta tare da jan dogon tsaki ya rab'ata ya wuce ya na fad'in "Iska na wahalar da mai kayan kara." Da kallo ta bi shi har ya koma ya shiga motar sa ya sake barin gidan, jiki a mace ta jawo k'ofar falon ta rufe mi shi da makullin da ya manta bai waiwaye shi ba kafin ta wuce b'angarensu. _________________ Da sallama a bakin shi ya shiga falon ya na cire takalmi a k'ofar, Salima ce ta amsa dan ita ce kawai a falon tana goge-goge, da ladabi da kuma fara'a a harshen larabci tace "Akhi, sabahul-khair." Sai da ya fara lumshe mata ido kafin ya amsa a tausashe da cewa "Sabaha-nur." K'arasawa ya yi a nutse ya zauna kan kujerar ya kalleta yace "Ina Umma?" Da sauri ta aje abun gugar hannunta ta matso kusanshi ta na fad'in "Akhi ina amarya? Umma ta na ciki, dan Allah nuna min ita ko a wayarka ne, na matsu na had'u da ita." Kamar yau ya fara ganinta haka ya k'ureta da ido ya na kallo, d'an girgiza kai ya yi alamar k'osawa da zancenta kafin yace "Ki fara sanarwa da Umma na zo, sai ki zo na nuna miki to." Turo baki ta yi ta mik'e ta na bubbuga k'afa ta shiga d'akin Umma da sallama tare da k'wank'wasawa, bakin gado ta samu Umma zaune sai Marfu'a dake kan kujerar gaban madubi suna tattaunawa kan lefen da za'a yi, amsa sallamarta su ka yi dukansu kafin tace "Umma akhi ya na falo." A sanyaye ta jinjina kai alamar to, juyawa ta yi ta fita ita ma Umma suka mik'e suka biyo bayanta, ta na zuwa daf da shi ta zauna tace "To akhi nuna min? Umma ta na zuwa yanzu." Wani charme ya sakar mata ya na murmushi yace "Ba na da hotonta, amma zan samo miki." Wani kallo ta sake sakar masa ta mik'e ta na gunguni, da 'yar dariya ya bita ya na fad'in "Ina Halima?" Juyowa ta yi tace "Ta tafi islamiyya." A nutse ya sauke mata idon shi da alamar tambayar, ke fa? Sunkuyar da kai ta yi ba tace komai ba, sai kawai ya rabu da ita ba sai ya tsananta ba, tun da ta na zuwa kullum kenan dalili ne ya hanata zuwan yau. K'arasowar su Umma da sallama ya saka shi saurin sauka daga kujerar ya zube k'asa ya zauna, sai da suka zauna dukansu ya d'aga kai ya kallesu, a mutumce kuma a ladabce suka shiga gaisawa musamman ma auntyn ta shi Marfu'a da aka jima ba'a had'u ba. Wata hirar suka shiga tab'awa kamar babu abinda ke gabansu a lokacin, sun d'auki kusan minti ashirin kafin Umma ta sako zancen da shi dai ya fi masa dad'i, jin yanda ake ciki akan lamarin amaryarshi ba. A sanyaye ta shiga fad'in "Na san ka na cike da mamakin yanda na ce ma ka mun taho kuma ba tare da Faduma ba kamar yanda aka shirya da farko, hakan ya faru ne sakamakon shawarwari da mu ka samu; sai mu ka ga barinta acan shi ya fi, mahaifiyarku (Ayyar Wardugu) ta k'ara mana bayani akan al'adunsu, kuma sun tabbatar mana da dole ne a yi wa yarinya tunda dai ita ma jinin tubawa ce gaba da baya." Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi, sai da ta ja numfashi sosai kafin ta d'ora da cewa "Za ka zage ne sosai wajen yin duk abinda al'adarsu ta tanadar, sai dai kamar yanda na fad'a ma ka ba na son wani shagali daga gareka, kuyi komai a nutse dan Allah." Sunkuyar da kai ya yi yace "Insha'Allah Umma, za'a yi duk yanda ku ke buk'ata." D'an d'aga kan shi ya yi ya kalli fuskarta yace "Ni kai na Wardugu ya fad'a min wasu abubuwa da ya kamata ayi, sai dai Umma maganar d'aukar amaryar nan kamar ya mana tsauri ko?" Murmushi ta yi ta na girgiza kai tace "Bai yi mana ba, 'ya fa aka wanke aka bamu ba tare da mun sha wahala ba, sai jiran tsawon dare ne ba za ka iya ba?" Marfu'a ce ta d'ora da "Bayan kuma har k'amshin mutuwa ka fara ji a dalilinta." Dariya suka mi shi inda ya sunkuyar da kan shi ya na shafar tarin sumar da ke kan shi ya na murmushi shi ma, wa ya fad'a musu? Ya san dai ba za ta wuce uwarsu ba (Ayya). Umma ce tace "To ka ji, dan haka za ku iya tafiya da yamma kafin magrib kun shiga garin, sai ku zuba mu su ido kuga abinda za su yi har su gama ja mu ku rai su fito mu ku da amarya." Wani murmushin ya kuma yi yace "Allah ya sa kar ayi abun fad'a a wurin nan." Da mamaki Umma tace "Abun fad'a kamar me? Ban gane ba?" Girgiza kai ya shiga yi ya na fad'in "Umma har da rikitaccen ubana fa za'a d'aukowa amarya a ranar, kar ya saceta su gudu ai." Tab'e baki ta yi ta na murmushi tace "Babu abinda ya isa ya yi a wannan ranar." Gingina kai ya sake yi ya d'ago yace "Shikenan Umma, insha'Allah..." Bai kai k'arshen maganar sa ba Meena ta rabka saallama, ganin Hasheer kuma ya sa ba ta jira amsar kowa ba kamar yarinya ta taho da gudu-gudu ta na fad'in "Akhi ango, ashe zan sake ka anan?" Daf da shi ta zauna ta na cire hijab d'inta da nik'ab ta na ta murnar ganin shi. Girgiza kai ya yi a hankali yace "Ba ki girma ba har yanzu Meena, me ya ke damunki?" Cikin shag'waba ta shiga kyab'e fuska ta kalli auntynsu tace "Aunty kin ji fa? Wai ban girma ba." Dariya ta yi tace "To kin girman ne?" Sake turo baki ta yi sai Salima da ta fito daga d'akin Umma ta gama gogewa, da wata irin murnar ganin juna suka daka tsalle suna ihu suka rumgume juna, girgiza kai duk su ka yi suna kallonsu da mamaki. Sai da ya tashi tafiya suka tsaresa sai ya nuna musu amarya, duk yanda ya so zille musu ya kasa dan Meena akwai kafuwa da iya zance, k'arshe dai kiran wayar Faduma ya yi dan su gaisa ta waya, sai dai hakan bai samu ba sai kururuwa da wayar ta yi ta gama ba'a d'aga ba, hakan kad'ai ya sa suka rabu da shi ya fita a gidan. *Barkaanmu da sallah* *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 21:42 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _65_ *Zinder* A b'angaren amarya tun asuba da ta tashi ba ta sake komawa ba, d'akin Aba suka tare ita da Amjad da Barka suna ta shan hira cikin raha da k'aunar juna, Ayya da Khadija ne ke aikin had'a abun karin kumallo a tsakar gidan. Har kusan 07:30 Ayya ta shigo da sallama d'auke da farantin kwanukan abinci, wanda sallamarta a d'akin ya yi dai-dai da sallamar Owwo tsakar gidan, Khadija ce ta amsa suka gaisa a mutumce dan ita ma kamar uwa ta ke a gareta. Fitowar Ayya ya sa suka sake gaisawa ta na tambayar "Ina amarya?" Nuna mata d'akin ta yi tare da fad'in "Tana ciki, har kin k'araso kenan?" Sai da ta je daf da d'akin ta aje k'atuwar ledar da ke hannunta tace "To ai ba ma tsaya sanya ba, sa'a fa mu ka yi da aka bar mana ita." Murmushi kawai ta mata ganin ta shiga d'akin da sallama, dukansu ne suka amsa mata da sakin fuska suka kuma gaisa a tsanake, zaune ta yi a inda Aba ya nuna mata ta na hararen Amjad da cewa "Kai! Sauko mi shi a k'afafu mana; sai ka karya shi?" Mak'ale kafad'a ya yi yace "Ai dai kakana ne ko?" Tab'e baki ta yi tace "A fad'awa wanda ba shi da kaka." Gwalo ya mata yace "Ni dai ga nawa anan, ban ga na wasu ba." Nuna shi ta yi da yatsa tace "Kai! Ka kiyaye ni, zan kifar da kai a wurin nan." Dariya su ka yi sai Aba da ya d'ora da fad'in "Owwo dama haka kike takura min shi? Ki barshi ya walala mana, ai sabon shiga ne shi a harkar kakanin." Wata dariyar suka kuma yi sai Faduma da tace "Aba da ka rabu da su ai, ganinmu ne ya sa zasu fara safiyarsu da haka, amma nan bayan idanmu soyayya suke kamar babu gobe." Dariya su ka yi hakan ya sa dada mik'awa Amjad hannu tace "Taso na ji ya ka kwana d'an gidan dada? Na ga duk nema ake a saka mana ido ma." Mik'o mata hannun ya yi tare da d'agowa daga cinyar Aba ya fad'a cinyarta, ruk'umk'umeta ya yi cikin rad'a suka shiga gaisawa, kallonsu Aba ya yi ya na hango tsantsar shak'uwa da soyayyar da ke tsakaninsu. Cikin farin ciki yace "A gaskiya Owwo kun shagwab'a yaron nan." D'agowa ta yi ta kalleshi tace "Duk da haka kuma da kallo kawai muna isar masa da sak'on gargad'i ko tuhuma kuma ya ankare da wuri." Cike da gamsuwa yace "Allah ya saka m没 ku da alkairinsa, k'ok'arinku akan wannan yaron Allah ne kad'ai zai iya biyanku." Farantin abincin ya jawo yace "Ku gyara mu ci abinci." Dada ce tace "Har da ni?" D'an hararanta ya yi cikin tsokana yace "Ke d'in ba iyali na ba ce? Malama saka hannunki ke ma." Dariya ta yi duk suka mik'e suka wanko hannayensu, zaune su ka yi gaba d'aya suka saka farantin tsakiya, Faduma ce ta zuba musu kafin Aba ya saka hannunshi sai dada sai kuma Barka kafin Faduma da Amjad. Ko da suka ida suka wanke hannu dada ta shiga d'aki su ka yi magana da Ayya, dan haka Faduma na shigowa tace "Muje to." Kallonta tayi tace "Ina?" Saida ta d'auki ledar nan tace "Gidan Herde." Ba ta mata musu ba ta bita suka tafi sai Amjad da suka fita tare da Barka zai kai shi gidan yaya Kalli zai wuni acan. Suna shiga d'akin ta fara kalle kalle, amma ba ta yi magana ba har sai da dada tace "Cire kayanki." Herde ce tace "Ke ma ai cirewar za kiyi." Murmushi tayi tace "Ni kullum cikin gyaran jikina na ke, ita ce dai agogo sarkin aiki ba ta da wannan lokacin, da k'yar ma take zuwa salon gyaran gashinta, ita dai ki barta da tayi wanka ta shafa mai ta shafa turare." Sai da ta fara ciro kayan cikin ledar nan tace "Shi yasa na ke so na fara darjeta da hannaye na kafin sab'a ma kai na." Dariya Herde ta yi tace "Lallai wannan uwa idonki a tsaye yake." Kallon Faduma ta yi tace "Cire min rigarki." Da mamaki ta kalleta tace "Rigata kuma Ayya?" Ba alamar wasa tace "Eh; rigarki." Turo baki ta yi ta na karkace kai hakan ya sa Herde jawota gabanta ta zura hannayenta bayan rigarta ta jaye zif d'in, k'asa rigar ta yi ta fad'i ita kuma ta shiga k'ure mata kallo, ganin ta kare k'irjin da hannayenta ya sa dada cewa "Haba wai Faduma me ye haka? D'auke hannunki mana." Cikin shagwab'a tace "To dan Allah kawai sai na bud'e k'irjina kuna kallo, laifin me ya yi ne?" Dak'uwa Herde ta mata tace "Amma dai kin san kin tab'a shayarwa ko?" Sake turo baki ta yi a hankali ta d'auke hannayenta, cirrr suke kuma irin kaurarren nan ne masu cika hannu, duk da fatarta bak'a ce amma su suna da d'an haske mai kalar ja, sai kan nasu da shima yake da d'an duhu da fad'i kad'an. Herde ce ta kalli dada tace "Ba mu da matsala da su, sai dai duk da haka ina buk'atar su fi haka tsayawa da k'afafunsu." Jinjina kai ta yi tace "Ya za mu yi kenan?" Fita ta yi daga d'akin ta na fad'in "Garin hilba kawai ya ishemu." A nutse suka fara mata abinda ya kawosu, mai (stella, mai gurguwa馃榿) da aka had'a shi da wasu tame-tamen aka fara labta mata shi a jiki, farfajiyar gida suka fito inda akayi d'an rami aka saka gwangwanin madara a ciki da garwashi, sai iccen magarya da aka jik'asu a ruwa bayan an wankesu aka saka a cikin gawashin, kujerar tsugunno aka d'ora mata ta zauna aka rufeta da bargo ruf, kasancewar ba shayarwa take ba ya sa ko bras ba'a saka ma ta ba. A hankali turirin yahak'in ke shiga jikinta da fatarta,sannu sannu take jin ya na ratsata tana had'a uban gumi. Saida Herde ta tabbatarwa kanta da yanzu komai ya yi kafin ta d'auke mata bargon, wanka ta shiga da ruwan d'umi inda ta darji jikinta da subulun da aka had'a da kalar sabululuka da wasu daga cikin kayan itatuwa dangin kankana da inibi da kuma zuma had'e da zallar madara peak, dan dama tun da akayi maganar aurenta da Aminu suka had'a shi suka aje. Ita kanta sanda ta gama wanka sai ta ga wani datti ya fita a jikinta kamar ba ta tab'a wanka ba, tana fitowa ma ba ta saka kaya ba dan wannan matakin farko ne, kuma in ba ta manta ba irin wannan gyaran aka mata lokacin da aka saka ranar aurenta da Tagur, shi ya sa yanzu ma ko raki ba ta yi ba bare k'orafi. Wannan karan kuma kurkur da caf茅 had'e da lemun tsami da madara aka linde mata jikinta da shi, daga bisani bayan angama ta sake komawa kujerar nan ta zauna aka rufe ta da bargo, tana hakane wayarta ta shiga kururuwa, dada ce ta d'auka tace "Lamba ce babu suna." Daga cikin bargon tace "Nawa ne k'arshen lambar?" Saida ta duba tace mata "Sipili (0) sipili (0)." Fahimtar waye ya sa ta cewa "Idan kiran ya tsinke ki kashe wayar gaba d'aya, zan sake kira daga baya." Kamar yanda tace haka ta yi ta aje mata wayar d'aki, yanzu ma dai kamar farko gumi ta dinga yi har ya na mata tsiyaya a k'asa haka ma bargon nan ya yi sharkat. Yanzu ma wanka ta sake yi da ruwan d'umi kafin ta shiga d'aki ta shafa man da dada tace mata a cikin farar roba, a lokacin ita ma ta shiga cikin na ta bargon ta fara jib'i (zufa). Misalin 11:40 suka kammala dukansu, Faduma da wayarta a hannu ta na son sake kiranshi kamar yanda tace amma kuma sai ta ji ta kasa, to me za tace ma sa? Sai kawai ta share ba ta kira ba ta sake kashe wayar saboda jin wata kunyarshi ma take sakamakon tuna had'uwarsu ta jiya. Tana tsaka da tunanin nan ta ji Herde na fad'in "Ke Owwo ki ji tsoron Allah, yanzu ke zaki lalata mana al'ada, kinfi kowa sanin mu dai tubawa ba ma irin wannan ko?" Dariya Dada ta yi tace "Na sani, tun da aurena na farko haka kuka barni; saida na je na nemawa kai na, yanzu ma ai ba wani laifi ba ne tunda duk abinda na had'a naturel ne." Girgiza kai ta yi ta tab'e baki tace "Ni dai da kin bar min 'yata haka, na yarda da wannan sirrin da na ma ta da kuma wanda aka ma ta na farko ma." Ita ma girgiza kai ta yi tace "Um um! Ai dole na k'ara mata da wannan, dan kishiyarta haifaffar maradi ce, ni ma kuma a maradin na san wannan sirrikan, dan haka zan mata dan ta zama zara ita ma a gurinshi." Herde kam abun mamaki ya ke ba ta sosai, to ita in ba yanzu ba bata tab'a gani ba, tasan dai ko za ka yi sai ka je gidan amma ba yanzu ba. Jin ba tace komai ba ya sa dada kallonta, kallon Faduma ta yi da ke kallonsu ita ma ta k'yabta ma ta ido alamar za ta tsokani Herde, kallon Herde ta yi cikin raha tace "Ai ke ma ba zan barki haka ba, dole Aban Fadu ya san cewa a gidanki aka yi gyaran amare, dan sai na miki had'i na musamman kin sha." Mik'ewa ta yi da sauri ta na fad'in "Inna lillahi wa'inna ilaihi rahu'un! Owwo haka ki ka zama ba kunya? Wannan dai ba d'abi'ar batuba ba ce." Fita ta yi daga d'akin suna jin ta na fad'in ita ba za ta iya ba ta tafi gidan Hadizey, fitarta kuma ita ta bawa dada damar zazzage kayan cikin ledar nan har da blender ta kam ta taho,nan fa ta shiga markad'a kankana ta saka zuma da garin raihan da peak suka raba biyu ta bawa Faduma, karb'a ta yi ta na fad'in "Ni fa wallahi dada kunya na ke ji, idan fa Ayya ta fad'awa Ayya abinda m没 ke yi" A take dada tace "Ta kashe ki to, ke in ma basu yarda aka gyara ki sosai ba ai sai Allah ya tambayo su, dubi fa kud'in da aka bayar na gyaran jikinki kawai." A hankali ta d'an kurb'i kad'an, wani gard'i ta ji tare da dad'i a baki, sai kawai ta kifa kanta ta shanye tas ta aje kofin, dariya dada ta yi tace "'Yar banza an ji dad'i ko?" Rude fuska ta yi wai ita kunya, yanzu ma ta na kallo ta markad'a dabinon da ya jik'a sosai tare da kanunfari ta tacesu sannan ta sake zuba wata peak d'in suka sha, Faduma har ta d'an kishingid'a dada ta mik'o mata wani dunk'ulallen siga (sugar) bashi da girma kuma haskenshi k'arai-k'arai yake har guda uku tace ta yi ta tsutsa har ya k'are. Ita dai daga nan kwance ta dinga tsutsar shi har bacci ya rideta a wurin. *Maradi* Lafiya lau cikin farin ciki ya isa ma'aikatarshi dake mallakinshi (risham wax), bai damu da rashin d'aga wayarta ba har sanda ya sake kira aka ce a kashe, dan ya na da matuk'ar uzuri a rayuwa. Sai dai farin cikinshi ne ya koma bak'in ciki sanda ya yi wani fitinanne kuma gigitaccen bak'on daya dagula masa lissafi, sanda aka fad'a mi shi ya na da bak'o farin cikin shi ya sa bai tambayi waye? Ko me ya kawoshi ba? Kawai ya b芒 wa sakatarenshi damar shigo da shi. Ya na jin bud'a k'ofar ya d'ago ya zuba masa ido, matashi ne da ba zai wuce tsarar Mujaheed ba, babu alamun talauci ko k'azanta a tare da shi, hasalima mutum ne mai d'aukar ado kasancewar shi dogo kuma mai ajiyayyun suffofi na k'arfi. Ya masa kallon sani da farko amma rashin tuna a ina kuma me ya tab'a had'asu? Sai kawai ya share zancen ya masa izinin zama a kujera biyun dake gabanshi. Cikin nutsuwa da isa da k'asaita Tagur ya zauna ya na k'are ma Hasheer kallo, k'afa d'aya ya d'ora kan d'aya ya na wani malalacin murmushi, sai dai har zuciyarshi ya gama tsinkewa da lamarin nan, tun daga k'ofar ma'aikatan wurin nan har zuwa ciki ya nuna mi shi babu makusa a wurin wanda zai zo, ganin girman wurin da dubannin ma'aikatan da ke ta aikinsu irin fasalin tsarin wurin da ma manyan injina (enginer) aikin dake wurin ya sa shi shan jinin jikinsa. Gashi yanzu a cikin ofishin shugaban wurin, shugaban ba wai mai wakiltar mai kampanin ba, a'a! Wannan shi ne mamallakin wurin baki d'aya, ofishin bai da wani girma na azo a gani, amma tsarinshi da tak'aitattun kayan ciki wanda kusan komai na gilashi ne ko bak'ar robar dake da inganci, a can gefe doguwar kujera ce ta zaman mutum uku da kuma k'anana masu zaman mutum d'aya sun saka ta tsakiya, sai wani k'aramin tebur wanda ke tabbatar maka tafiyayye ne tare da kujerun. Sai babban Allon dake bayan kujerar mai d'auke da ayatul kursiyu kamar dai wanda ke bayan Hasheer d'in mai d'auke da suratul falak'. Kallon da suke aikawa junansu kamar za su ci kansu, Hasheer na kallon Tagur ne da mamakin rainin hankalin da mutumin ya zo mi shi da shi, dan haka a nutse kuma a wahalce ya d'aga labb'ansa masu matuk'ar tsari da su ka zama shamaki da fararen hak'oransa yace "Waye kai?" Yanda ya tsare shi da ido da wani kakkausan kallo ya sa shi gyara zamansa, dan sosai Hasheer ya masa kwarjini a ido, wani malalacin murmushi ya saki tare da shafo sajenshi yace "Ba za ka shaida ni ba dama, ni ma kuma ban gama shaida ka ba sai yanzu." Ba tare da ya daina bin shi da wannan mummunan kallon ba yace "Me ke tafe da kai?" Saida ya d'ora enveloppe d'in da ke hannunshi akan teburin kafin yace "Magana ce akan matata da ka aura." Da wani sakaran mamaki Hasheer ya kafeshi da ido ya na son nazartarshi, a tsanake yace "Matarka?" D'aga masa gira ya yi yace "Eh, matata, wacce ka aura kwana biyu da suka wuce." Sai lokacin Hasheer ya samu damar d'an kawar da kallon shi daga kan Tagur ya d'an ja k'aramin tsaki, sosai ya nutse a cikin lafiyayyar kujerarshi ya na d'an juyawa da ita, wani kallon raini ya masa yace "Alamunka bai nuna wanda yake ya kubto daga gidan mahaukata ba, da sai na yi k'ok'arin ganin na had'aka da likitan k'wak'walwa." Numfasawa ya yi yace "Ban san ko b'atan kai ka yi ba har ka zo nan? Da tunanin ka zo inda ka ke son zuwa." Wani sakaran murmushi Tagur ya yi ya na kallonshi sosai yace "Ban yi mamakin jin haka daga gareka ba, amma dai ka sani matar da zan aura Faduma ita ce matar da ka aura, sannan uwar d'ana." A take ya lumshe ido ya na maimaita "Uwar d'ana." D'an bud'e idon ya yi ya kalleshi a kaikaice yace "Me ya kawoka nan?" Cike da shak'iyanci yace "Ba na zo bane dan na ce ka sakar min matata..." Yatsa manuniya ya nuna shi da ita a hassale sosai yace "Ya zama na k'arshe da za ka sake kiranta da sunan matarka." Yanayin tsoro ya yi cikin izgilanci yace "To fa! Na ji na daina." Enveloppe d'in gabanshi ya d'auka ya turo mi shi zuwa gabanshi yace "Wannan ne dama ya kawo ni, matarka ta karb'i tayin da na mata na shiga shari'a akan d'anmu, ta d'auka da wasa na ke shi ya sa har ta yi nesa da shi, amma kai a matsayinka na mijinta za ka iya isar da sak'on gare ta." Mik'ewa ya yi tsaye ya na gyara zaman rigarsa ta baya ya na kallon shi yace "Ko kuna so, ko ba kwa so dole ku yarda ni ne uban d'anta na fari. Kuma ko da auren soyayya ku ka yi da Faduma ka sani ita ma kuma ka tuna mata, ni ne dai na farkon da ya fara isa a duniyar al'ajabinta har na yi nasarar riskar ni'imarta, mun gauraya ni da ita gaurayar da har yanzu kai da ke mijinta ba ku yi ta ba, da wannan nake alfahari kuma na ke tutiya a cikin rayuwar Fadu." Tunda ya mik'e dama Hasheer ya sunkuyar da kan shi ya fara aikin gabanshi, amma kalaman da ya fara fad'a suka saka shi dakatawa ya na sauraronshi, amma daga bisani sai jikinshi ya fara tsuma ya na kakkarwa, ta yanda har alk'alamin hannun shi ya kubce bai sani ba, k'in d'ago idonshi ya yi saboda ya tabbatar da sun canza kalar launi, duk yanda zuciyarshi ke tafasa da yanda jijiyoyin kan shi suka mik'e bai sa ya kalli Tagur ba, dan zai iya zama ajalinshi ba tare da sanin ko da sunanshi ba. Saida ya ji fitarshi kad'ai ya yi saurin dafe k'irjinshi ya rufe idonshi da hannunshi da har yanzu ke rawa, da k'yar ya saka d'aya hannun ya dafe kanshi dake mugun sara masa da k'arfi, duk kuma wannan tashin hankalin da ya shiga bai hana shi nanatawa a zuciyarshi ba cewa "Duniyar al'ajabinta? Ni'imarta? Gauraya? Sannan ya na alfahari." Kamar an turashi bayan kujerar haka ya kwanta bayanta ya rufe ido ya na ta sauke numfashi da k'arfi sosai, jilawa a wannan yanayin ya kasa katab'us ya sa shi danna d'an madannin dake kad'an daga k'asan teburin wanda ya alamtawa sakataranshi da ya na nemanshi da ujila kenan. Sakan k'alilan ya shigo da sallama tare da k'wank'wasawa, a hankali ya k'araso gabanshi ya tsaya ya na karantar yanayinshi, ba tare da ya bud'a ido ba ya nuna masa fridge d'in dake wurin, da sauri ya nufeta tare da bud'ewa ya d'auko ruwa ya kawo mi shi, sai da ya bud'e robar ya mik'a masa ya karb'a da k'yar ya kafa bakinshi ya tsiyaya. Ajiyar zuciya ya shiga saukewa kamar gudu ya yi, saida ya kusan d'aukar minti biyar a haka kafin ya bud'e ido ya kalleshi, da hannu ya masa alamar ya tafi shikenan. Juyawa ya yi ba musu ya fita, enveloppe d'in nan ya kalla da tunanin ya bud'e ko ya barta? Wata zuciyar ta k'arfafa masa gwiwar bud'ewa, d'auka ya yi ya bud'e ta ya ciro takarda ya fara karanta, sammaci ne daga kotu kuma da gaggawa za'a zauna dan kwana d'aya tak tsakanin yau da ranar da za'a zauna, ninke takardar ya yi ya shiga tunanin lamarin a tsanake. Ya jima anan ya na tubka da warwara kafin ya kira wayar yaya Kalli, bayan sun gaisa ne a tsanake ya fad'a masa abinda ya faru a gajarce, ran yaya Kalli ya b'ace sosai da tuhumar me ya sa sai Hasheer zai kai wa? Amma daga baya ya sanar dashi suma sun san da maganar da kuma shawarar da suka tsayar, hakan ya sa zuciyar Hasheer samun nutsuwa, amma sai yace "Ka ga kuma ni ba ta sanar da ni komai ba, amma zan turo maka da takardar sai ka bata." Da haka su ka yi sallama ya nuna masa ba komai sai ya ji daga garesa. Duk da haka saida ya kira Wardugu ya fad'a masa halin da ake ciki, bud'ar bakinsa cewa ya yi "Ya zo har ofishinka? Ya baka wannan sammacin kuma ya fita lafiya k'alau?" Wani d'an murmushi ya yi ya na tunanin to ina ma kaji abinda ya fad'a min? Da kenan ni kai na ban tsira ba. Jin bai amsa shi ba ya sa yace "Kaga Hasheer ba na da lokacin tsayawa saurare da kallon wannan takaicin, Faduma dai yanzu matarka ce, idan ka yi niyya ka barta ta shiga shari'a da shi, idan ba ka yi niyya ba babu wanda ya isa ya tursasaka, amma..." Sa茂da ya ja numfashi ya ci gaba da cewa "Amma fa ban yarda ko kallon banza ka tsaya d'auka daga k'aramin yaron nan ba, Hasheer kai fa namiji ne, Faduma kuma yanzu matarka ce mallakinka iyalinka, kare mutumcinta ya na wuyanka ne, ko maganar banza karka lamunta ya fad'a mata bare kuma kai yace zai kalleka ya fad'a maka marar dad'i, idan har haka ta faru ni na baka dama ko a gaban alk'ali ne ka kalleshi ka datse masa harshe, shari'a daga nan har a busa k'aho za mu iya da uban duk da ya tsaya masa, amma ka nuna masa matarta ce ita yanzu, kuma kai ne ke da iko da abarka." Hasheer kam ban da murmushi babu abinda ya ke dokawa a fuskarshi, ba wai maganar Wardugu ko shi da ya bi ta zuciyarshi d'azu da ya yi ajalinshi, amma sai ya k'arfafa kan shi ya cije sosai bai yi aikin alawadai ba. *Zinder* Da yamma bayan Herde ta sake darjeta kamar dai yanda aka mata da safe yaya Kalli ya shigo gidan, bayan sun gaisa ya bata wannan takarda da yanzun nan sak'onta ya iso mi shi, kuma kamar yanda Hasheer ya nema bai fad'a mata daga wurin wanda ta fito ba, tun daga nan Herde ta fara fad'a inda ita kuma ta shiga zulumin ta ya zata kirashi kawai ta fad'a masa za ta shiga kotu shari'a? Da wannan tunanin har dare ya risketa ba tare da ta yi tunanin ta inda za ta fara ba. A hakan ma dad'inta d'aya shine anan garin ne za su shiga shari'ar. *Maradi* Kwance ya ke akan doguwar kujerar ya na danna wayarsa, a matuk'ar matse ya ke da ya ji kiranta ya shigo wayarsa amma har yanzu shiru, sai ya yi kamar zai kira kuma sai ya fasa ya ci gaba da abinda ya ke yi, ya na jin hayaniyar yaran amma bai kulasu ba, fitowar Saudat ce tasa shi kallon k'ofar. Saida ta k'araso ta zauna kusa da shi da plate d'in gyd'arta mai sugar a hannu tana watsawa baki, d'an murmushi ya k'ak'aro mata yace "Umma Sharfudeen kenan." Wata harara ta dallo masa tare da fad'in "Ya akayi?" Kallonta kawai ya yi da mamaki bai ce komai ba, mayar da hankalinshi ya yi kan wayar shi ya na ci gaba da kallon lambar murmushin shi, har ya fara mantawa da ita a b'angaren shi ya ji tace "Ina lauyan na ka Aminu?" A tsagaice ya kalleta ya yi jim, kamar ba zai yi magana ba sai kuma yace "Wani abu ya faru ne?" Girgiza kai ta yi tace "A'a, ina so ne na gan shi na ji dalilin da ya sa ya sadaukar ma ka da matar da zai aura? Bayan kuma yasan ka na da mata." D'auke kan ta tayi daga kan shi tace "Sai dai kuma ko dama can ya na jin haushi na." Wani shak'iyin murmushi ya yi bai ce komai ba, satar kallonshi ta yi ita ma kafin ta d'ora da cewa "Kuma kai yanzu farin ciki ka ke da ya ma ka sadaukarwar nan ko? Ba ka tunanin ya ma ka halin d'an adam? Kasan fa ya na da sani sosai akan ka kuma shi d'in amintaccenka ne, ko ni ban da masaniyar da shi ya ke da akan ka ta b'angaren sabgoginka da abubuwan da ka mallaka." D'an tsayawa ya yi daga latsa wayar da ya ke yace "Bana tunanin Aminu zai ci min amana, da zai iya hana ni farin ciki." Tab'e baki ta yi tace "Ni kam da zan baka shawara kakarb'a, wallahi da sai na ce ka gaggauta karb'ar duk wani abu da ke mallakinka a wurin shi, dan mutum bashi da tabbas, mace kuma da ka ke gani tana da tasiri sosai ta yanda za ta iya k'ulla gaba tsakanin k'asa da k'asa ma bare kuma tsakaninka da d'an korenka." Shiru ya yi alamar ya na tunanin abinda ta fad'a daga bisani kuma sai ya sauke ajiyar zuciya, jin bai tanka mata ba ya sa ta kallonshi tace "Da alama akwai wani abu mai mahimlanci a tsakaninku ko?" Kallonta ya yi shi ma sai kawai ya yi murmushi ya d'auke kan shi yace "Akwai muhimman takardu na a hannunshi, amma kar ki damu zan karb'o su." "Hmmmm!" Ta fad'a tare da sake d'auke kanta daga kan shi, murya a dak'ile tace "Yaushe amaryar za ta tare?" Kallon ta ya yi yace "Nan da kwana goma sha biyu." Mik'ewa ta yi kawai ta shige d'akinta ya na binta da kallo, wayarshi ya kalla da tunanin ko dai shi ya kirata ne, sai kuma wata zuciyar ta kwab'eshi ya fasa, haka dai ya ajiye wayar ya biyewa yaranshi suna ta shirmensu har dare ya yi kowa ya kwanta. *Ina godiya da comment da addu'o'inku mutane na, a ci gaba da gashi.*馃拑 *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 21:42 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _66_ Saida ya gama shirin kwaanciya tsaf ya haura kan gadon a nutse, jawo bargon yayi ya rufa tare da juyawa b'angaren da take, a hankali ya zura hannunshi na dama ya d'ora kan mararta, a zabure ta mik'e zaune tana juyowa inda yake da cikin b'acin rai tace "Malam lafiyar tab'ani?" Da wani mamaki ya kalleta da jin cewa ta yi masa tambayar rainin da babu wanda ya tab'a ma sa ita, kuma hakan baya rasa nasaba da rashin sanin zafin zuciyarshi da ba ta yi ba. Amma yanzu ma sai ya yi k'ok'ari sosai wajen had'e b'acin ran da ya wuni da shi wanda Tagur ya k'unsa mi shi, d'an rusuna idonshi ya yi yace "Kawai dai ina son jin d'umin jikinki ne." Sauka ta yi daga kan gadon ta na kallonshi tace "Lallai ma! To a me ka d'auke ni ne? Wacce ba ta da zuciya? To ba ka isa ba wallahi." Hannu ta sa ta fizgi wayarta ta nufi hanyar fita ta na fad'in "Bebe ka gama wulak'anta ni, a sannu kuma zan nuna ma ka kuskurenka." Jingina ya yi a jikin gadon ya rumgume hannaye ya na kallonta har ta fita, ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi ya d'an girgiza kan shi, wayarshi da ya aje gefenshi ya laluba ya jawo, lambar ya sake nemowa sai dai ba zai iya kiranta a yanzu ba, dare ya yi. A hankali ya mayar da wayar ya aje ya yaye bargon ya zuro k'afafun shi a hankali ya sauko, ya mik'e zai nufi toilet da niyyar d'auro alwala ya ji k'arar shigowar sak'o a wayar. Zura hannu ya yi ya d'auki wayar ya duba, a take murmushi ya sub'uce masa tare da yin zaune kan gadon, a hankali ya sake bin sak'on da kallo kamar haka _"Duk da dare ya tsala, amma ina fatan ban shiga lokacin da ba nawa ba. "_ Shafa sumar kan shi ya yi ya na murzawa, to mi ye ma na murmushi anan? Kar fa ka zama sakarai akan yarinya k'arama. Abinda zuciyarshi ta raya mi shi kenan, a hankali ya d'ora zara zaran yatsunshi ya shiga mayar mata da cewa _" Duk da dare ya tsala, amma ban gushe ina jira da d'aukin son ganin kiranki ba. "_ Ya d'auki ak'alla minti d'aya kafin ya ji sak'o ya shigo ya duba, sak'o ne kamar haka _" Ina neman afuwar *saraki*, nasan na yi laifi sosai, amma kuma zuciyata na fad'a min an shigar dani hannun mai *halin girma*, d'abi'arsa ce hak'uri, halinshi kuma yafiya, da wannan na ke ji har raina ba'a tauyeni ba da aka damk'a ragamata hannun *sadauki na*_." Wani lafiyayyen numfashi ya sauke inda murmishi ya kasa barin fuskar shi, wani wuuuuu ya ke ji kan shi na hawa saman gajimare, wani irin farin ciki ne ya ke jin na huda zuciyarshi, a b'angare d'aya kuma wani felek'e ya ji zai iya yi a gaban ko waye saboda kalamanta, sai kawai ya danna kira a lambar dan ba zai juri tura sak'on ba, kad'an ya rage ta sa farin ciki ya mi shi kamun kazar kuku har ya rasa tunnain shi ya jefa wayar wani wurin. Sanda kiran ya shigo sai d'脿 ta tashi zaune ta sauke numfarfashi, a hankali ta d'auka ta d'ora a kunne ta yi shiru, shi ma da fari shirun ya yi kafin daga bisani a hankalce cikin muryar da za ta iya saka mai ran bacci yace "Hasken idaniya ta Zarha, barka da sha min k'amshi tare da ja min aji." D'an murmushi ta yi mai sauti a nutse tace "A gafarce ni, a karon farko kar ka sa na ji a raina kai d'in ka na da mita ne, sha ma ka k'amshi ai ya fi k'arfin aikin Zahra." Murmushi ya yi shi ma tare da gyara zamanshi ya kwanta kan gadon ya na shafar k'irjin shi a cikin riga yace "Ba zan mi ki mita ba, dan na gama fahimta da yarinya shakaf aka had'ani tarayya, dole sai ina hak'uri, idan ba haka ba kuma numfashi na ya dinga min barazana kenan na son ganin ya bar gangar jiki na." Murmushi akan fuskarta tace "Tunda haka ka ke kallo na ni kuma ba zan gaza wajen nuna ma ka d'abi'a irin ta yara masu shekaru irin nawa ba." A hankali yace "A shirye na ke da d'aukar kowace irin hauka indai ta k'uriciyarki ce." 'Yar ajiyar zuciya ta sauke sannan tace "Ina son za mu yi magana idan ka na da lokaci *ranka shi dad'e*?" A sanyaye yace "D'aya a cikin ukun lokacina na ku ne iyalina, za ki iya d'ibar wanda zai isheki zan kasa kunne na saurari buk'atarki, amma kafin nan ina yarona?" Murmushi ta yi na jin dad'i tace "Ya yi bacci a d'akin Aba." Cikin d'ar d'ar tace "Magana ce dama akan Amjad, ni da kuma mahaif..." Da sauri ya katse ta dan wallahi idan ta fad'a jinin shi hawa zai yi a take, a d'an gatsau yace ma ta "Za ki min wata alfarma?" A sanyaye ita ma tace "Kai da kaya ai duk mallakar wuya ne, ka fad'i buk'atarka kawai, insha'Allah za ta zama k'ararra indai hakan ka ke so." Saida ya d'an yi murmushi a sauk'ak'e kafin yace "Mu bar maganar nan har zuwa gobe da safe." A ladabce tace "Yanda ka ke so raka shi dad'e, Allah ya kaimu goben." Ajiyar zuciya ya sauke har ta na jin sautinta ya d'ora da cewa "Fad'a min halin da ki ke ciki yanzu?" Da rashin fahilta tace "Kamar ya? Ina cikin farin ciki." Saida ya sake narkaka muryarshi yace "Kina kewata ne?" Da sauri ta rufe fuskarta da tafin hannu kamar ta na gabanshi, jin shiru ba ta amsa ba ya sa shi cewa "Kin tuna sumbatar jiya? Ina son sake mi ki irinta *Fatiti*, ya za ayi?" Shiru ta sake yi ta na rarraba ido kamar suna kallon juna, wani tattausan murmushi ya yi yace "Kar ki damu *Fadma*, zan yi hak'uri na jure har nan da sati biyu, a lokacin kuma zan had'e sumbatar sati biyu na yi mi ki ita a lokaci d'aya." D'an gyaran murya ta yi ta shiga kame-kame tace "Am..da... Yallab'ai, saida safe ko?" Wata 'yar dariya ya yi yace "Sa茂da safe, amma ki sumbace ni tukuna..." Fizge wayar ya ji anyi wanda ya sa shi juyawa da sauri ya na kallonta, bai san da shigowarta ba ko kad'an, kamar wacce za ta had'eshi tsabar fitini da b'acin rai, cikin tsananin tashin hankali da fitar hayyaci ta buga wayar a k'asa ta na fad'in "Wallahi Hasheer ba ka isa ba, a cikin gida na? A gidan ma har d'aki na kuma akan gadona? Lallai na sake yarda da aka fad'a min karuwa ce ita ce, to bari kaji ba zan d'auka ba wallahi, ni ba zan yarda da wannan wulak'ancin ba, dan haka ban damu ba idan ku na son cinye junanku a waje, amma gidana kam wallahi na wuce wannan matsayin rainin." Rik'e k'ugu ta yi ta na sauke numfashi ta na zubar da hawaye. Da k'yar ya sauko da k'afafunshi ka rantse bashi da lafiya, dan komai a sanyaye yake yin shi kamar marar Lakka a jiki, kallon ta ya yi a tsanake ya kuma kalli wayar, lashe leb'en k'asa ya yi da tunanin me zai mata? (Jikan Hajia dai saida ya yi tsayuwar rashin mutumci sannan yace "A biyani wayata, ko kuma ubanki ya biya ni馃槑 Allah ka shirya mana bawanka). Mik'ewa ya yi a sanyaye ya nufi wayar ya sunkuya ya d'auka, ganin yanda tayi ratsa-ratsa ya sa shi juyowa ya kalleta ya nuna mata wayar yace " Me ki ka yi haka? Saudat kan ki d'aya kuwa?" Da mamaki ta matsa kusan shi tace "Ban da hankali Hasheer, na ce ban da hankali ka yi abinda za ka yi, 'yar iskar ina ka d'aukeni da za ka zauna d'akina ka na hirar iskanci da karuwar..." Da sharb'eb'en yatsansa ya nuna ta ran shi a b'ace yace "Kar ki sake kiranta da karuwa, ba ita ba ce kinji na fad'a mi ki." A harzuk'e kamar za ta had'e shi tace "Na fad'a karuwa ce, inba karuwa ba me ya sa ka d'auketa tun daga garin nan har Niamey? Sakatariyarka ce ita ko mataimakiyarka? Ko kuma matarka ce a lokacin da ku ka yi tafiyar?" Wani iska ya furzo y'a na d'auke fuskarshi daga kan ta, k'wafa ya yi mai k'arfin gaske saboda tuna nasihar mahaifinshi ta cewa kar ya sake ya tab'a dukan mace duk yanda za ta kai shi k'ololuwa wajen b'ata masa rai. Sannan Umma ma ta jadadda masa ya yi hak'uri da duk abinda zata masa yanzu, kishi ne! Juyawa ya yi zai bar ma ta d'akin kawai tasha gabanshi ta na fad'in "Bebe me nai maka ka daina so na? Me ya sa ka daina so na yanzu?" K'urawa fuskarta ido ya yi ya na kallonta ya na ji kamar ya gyara tsayuwa ya fara lissafa mata sakacin da ya jawo dalilen da suka sa shi fara kallon mata a waje, sai kuma ya d'auke kai kawai yace "Har yanzu ina son ki, kuma ba zan daina son ki ba." Ficewa ya yi da sauri ita kuma ta fad'i d'abas ta fashe da kuka sosai ta na fad'in "Mutuwa zan yi bebe, mutuwa zan yi ka raba min kan ka da wata, cikin nan ma zubar da shi zan yi wallahi dan banga anfaninsa ba." Cak! Ya tsaya tare da dawowa d'akin, durk'usawa ya yi ya shafa fuskarta ya na kallonta yace "Bab ki daina, ki daina fad'an za ki zubar da cikin nan kinji, kiyi hak'uri tashi ki kwanta." A gigice ta kalleshi tace "To ka saki yarinyar can idan ba ka so na zubar da cikin nan." Kallonta ya yi tsammm! Kamar ba zai ce komai ba, sai kuma ya girgiza mata kai yace "Wannan ba adalci bane, ciki nawa, ke ma kuma tawa ce, sannan Faduma ma a yanzu mallakina ce, dukanku ina son ku, kuma babu wanda nake son tauyewa hakk'i akan waninsa." Mik'ewa ya yi ya kamo hannunta ta yi tsaye, cikin dakushewar murya tace "To ni ka sake ni na koma gidanmu, b茅b茅 ba zan iya zama da kishiya ba, musamman da ka nuna min kalar na ta karuwancin a d'akin baccinmu." Lumshe idonshi ya yi jim kamar wanda bacci ya d'auka a wurin, sai kuma ya bud'esu fes a kan ta ya sauke numfashi yace "Ki je ki kwanta." Hanyar fita ya yi ya na fad'in "Sai da safe." Ya na juyawa ta sake fad'uwa da k'arfi kamar 'yar bori ta na fad'in "Shikenan tafi, wallahi sai na zubar sai dai ka kasheni, kashewa ma ta nawa dan ka gama kasheni tunda ka k'ara auren nan, dama munafurci ne daga kai har Aminun, had'in baki ne tsakaninku dan kar na fahimta, amma ku sani yanda ku ka d'aga min hankali kuma na ku sai ya tashi, wallahi sai kun ciza yatsanku tsabar tashin hankalin da za ku fuskanta, tunda Aminu ya had'ani da k'unci da fitina shi ma sai ya had'u da daidai shi, ba zan tab'a bari ya yi rayuwar aure ba, ba zai tab'a samun nutsuwa ba har abada, da ni ku ke zancen." Iren iren sambatun nan ta dinga yi har dare ya tsala ba ta san lokacin da b'arawo bacci ya yi gaba da ita ba. *Da safe* A shirye ya fito cikin shadda d'inkin zamani wanda ya kama jikinshi, a falon ya same ta zaune da wayarta a hannu, k'ala bai ce mata ba ya nufi d'akin yaran, samunsu ya yi suna ta k'ok'arin shirya kansu da kansu, taimaka musu ya yi a gaggauce dan lokaci ya yi, fitowa su ka yi ya na rik'e da jakunkunansu a hannu, tsaye ya yi gabanta yace "Ina abincin su?" Wani irin kallo ta watso mi shi tare da girgiza k'afa tace "Ban dafa ba." Idonshi a kan ta yace "Kamar ya ba ki dafa ba? Haka za su tafi makarantar?" Cike da raini tace "Wannan kuma matsalarku ce, in kai za ka dafa, in kuma siya musu za ka yi duk ya rage na ku." Wani malalacin murmushi ya yi yace "Ba matsalarki ba ce hakan?" Cike da tabbaci tace "Ko kad'an bai shafeni ba, in kuma za ku zauna jira har amarya ta zo to." Girgiza kan shi ya yi ya kalli yaran yace "Muje." Bin bayanshi su ka yi suka fita, da kan shi ya tuk'asu a k'aramar motar da ya siya saboda su k'irar 4matic, saida ya siya musu abinda za su ci a hanya kafin su ka wuce ya aje su. Ya na aje su saida ya tsaya ya samu sabuwar waya mai kyau da tsada ya siya kafin ya isa ofishin shi. *Zinder* Suna karin kumallo tare da Aba da Barka aka kira wayarta, ta na ganin lambar sai da gabanta ya fad'i, saida ta tsinke aka sak茅 kira na biyu kafin ta tattaro kuzarinta ta d'aga ta kara a kunne ta na kallon Amjad da ke cin abinci a nutse. Shiru ta yi sai shi ne daga b'angaren shi yace "Faduma kenan, sai kawai na ji kin yi aure ko?" A harshen tubanci tace "Eh, ka na da matsala da hakan ne?" Cikin shak'iyanci yace "Sosai ma, kin manta da na fad'a mi ki ke matata ce? Akan me za ki auri wani?" Cikin jin haushi tace "Saboda shi na ke so, kuma na gane shi ne namijin da ya dace dani, namiji mai zarra da sanin ta kamata, namiji mai addini da ilimin mutumta d'an adam." Wata dariya ya yi yace "Faduma ni ki ke fad'awa haka? Ke har kin manta ni da za ki dinga fad'a min haka?" A hassale tace "Na fad'a Tagur, na fad'a ka kashe ni, ka ga ni yanzu matar wani ce, kar ka kuma kirana a waya dan ba zan d'aga ba, ka fita a rayuwata tunda ba ka da anfani a gareni, d'ana gashi nan za mu shiga kotu ta yanke mana wanda zai zauna da shi, dan haka ka manta dani." Cikin jin zafi shima yace "Ba zan fita a harkarki ba Faduma, ke wallahi ki ka yi wasa ba za ki tare a ko ina ba sai gida na, Amjad kuma zai zauna dani ne tunda ni na mi ki cikin shi." Mik'ewa ta yi a hassale ta na fad'in "Idan ka isa ka yi abinda ka ga dama, wallahi Tagur da na je gidanka a matsayin mata gwara na mutu ba aure, ko kuma kai na yi ajalinka tunda dabba ne kai." Cikin kwaratsi yace "Faduma ni ne dabban? Dabba fa ki ka ce? Amma dai kin san duniyar nan babu wanda zai nuna min saninki ko?" Wani wawan tsaki taja tace "Aikin banza, tak'amarka kenan, amma ka sani Tagur wallahi ba ka cika namiji ba, ko abinda ya faru bai sa naji lallai kai namiji bane mai zarra, dan haka ka jira ka gani zan nuna ma ka sakamakon da mijina zai haifar a lokacin da ya zo gareni, in kuma ka na da iko dani ka hana faruwar hakan." Zai yi magana Barka da suke saurarenta ya karb'e wayar da sauri ya d'ora a kunne, cikin k'unar zuci yace "Kai shashasha da bai san ciwon kansa ba, kai jahilin ina ne? Da mace ka ke tsayawa ka yi cacar baki? Me zai hana idan isarka ta isa ka same ni ko kuma mijinta, banza lusari d'an daudu kawai, bari kaji, wallahi ka sake kiranta a waya kafin ta bar gidan nan, na rantse maka da Allah sai d'an nan ya zama maraya, dan sai na ma ka kisan wulak'anci, banza kawai." Aba ne ya mik'e shi ma ya nuna masa ya bashi wayar, bai bashi ba dan a lokacin Tagur ke fad'in "Barka ni ka ci wa mutumci haka akan k'anwarka? Ka sanni ka kuma san waye ni, indai ina numfashi a doron k'asa wani namiji bai isa yaje duniyar Faduma ba, wallahi ba za ta tare a gidan ba sai dai ku kasheni." A harzuk'e yace "To shikenan mu zuba." Shima a dake yace "To mu zuba mu gani, ni da ku shege ka fasa." K'it! Ya kashe kiran hakan ya sa Barka kallonta a zafafe kamar zai daketa yace "Za mu zauna zaman jira mu ga me zai yi, k'ark'arinta dai ya yi abunda wasu tubawan ke yi, yace zai d'auke ki ya gudu da ke, to mu zuba m没 gani wallahi sai na ciro mak'ogwaron yaran nan na jefar." Cilla mata wayar ya yi ya fita duk da Aba na son magana da shi, ita ma a zafafe ta d'auki wayar ta fita a d'akin Aba ta shiga d'akin Ayya. A sannu sannu abinda ya faru ya fara riskar 'yan uwanta, ai fa kowane zuciyata ta zo iya wuya duk sai suka rufe ido suna neman fitina a duk inda take, kowa abinda yake fad'a shine "Su Tagur zai wa iskanci? Ya manta su ma jinin tubawan nan ne da zai nuna mu su iya shege? To su da shi shege ka fasa, Faduma na jira ya zo ya d'auketa kamar yanda wasu ke yi." Kalli ne ya fara zuwa gida da sharb'eb'iyar wuk'a ya same ta a d'akin, yanda ya shigo ne ya tsorata ta har ta zabura ta mik'e ta na fad'in "Yaya Kalli?" Ido ya zaro mata yace "Ke! Fad'a min inda zan samu Tagur? Dan ubanshi mu zai wa iskanci?" Cikin i'ina ta kalli wuk'ar hannunshi ta girgiza kai tace "Yaya Kalli ban san a ina yake ba, me za kai masa? Dan Allah ku yi hak'..." "Ke!" Ya daka mata tsawa da iya k'arfinshi, nunata ya yi da yatsa yace "Duk ke ki ka ja mana wannan k'ask'ancin, tun farko da kin fad'a mana sanda ku ka sake had'uwa acan, da tuni na yi maganin yaron nan." Juyawa ya yi ya fita a d'akin, a tsakar gida Ayya da gabanta ke ta fad'uwa ne tace "Kalli wai yanzu ba za ku hak'ura ba kenan? Ku bari har ya sameku da kan shi mana." Girgiza mata kai ya yi yace "A'a Ayya; kawai ku bar mu da shi zai gane kurenshi." Juyawa ya sake yi a fusace zai fita sai kuma ya tsaya ya na lalubar wayarshi da ke k'ara, ya na cirota saida gabanshi ya fad'i, a k'asan mak'oshi ya furta "Wardugu kuma?" Da k'yar ya danna ok ya d'ora a kunne, ai kuwa abunda yake tsammani ne ya ji, dan ya na d'auka a harshen tubanci Wardugu yace "Kalli me yake faruwa a garin nan? An fad'a min an ganka da makami." Kallon wuk'ar hannunshi ya yi sai kawai ya yi murmushi, wato kenan duniya dai idon mutane akan ka ya ke? Hmmm! Cikin saurin magana na b'acin rai yace "Yallab'ai akwai matsala fa, wai wannan d'an iskan yaron ne yake mana barazana da Faduma ba za ta shiga d'akin mijinta ba, so yake ya nuna mana shi batube ne, to ko mantawa ya yi mu su wanene? Shi ne na ke so na kawo k'arshen iskancinshi." Shiru ya yi, shiru ne na son k'wato natsuwarshi da ke son barin shi, matuk'a ranshi ya b'ace har ya ji zuciyarshi na tafasa, cikin rikitacciyar muryar da ta saka Kalli d'an tsorata yace "Matar ta amini na? Wani zai d'auke?" A tsawace yace "Ku barshi!" Saida Kalli ya d'auke wayar a kunnenshi saboda yanda muryar ta dakeshi, d'orawa ya yi da "Dan girman Allah ku barshi ya d'auketa, ya shiga da ita duk duniyar da ya ke ganin mahulukin bai kai cen ba, amma ku rubuta ku aje ni Wardugu sai na samo shi kuma na yanka wuyanshi." K'it! Ya kashe kiran, jiki a sanyaye Kalli ya k'arasa fita ko juyowa bai yi ba. Wardugu kam suna gama waya Hasheer ya kira da tunanin ko yasan me ke faruwa, zaiyi farin ciki idan aka ce bai sani ba, dan shi dai a sanin da ya ma Hasheer mutum ne mai hak'uri, amma fa aka kai shi bango ya na yin abinda zaka d'auka b'arin mota ne, ya kan rikice ya gigice ya kuma birkitawa abokin gabarsa lissafi, musamman abinda ya shafi Faduma da ta ke da tasiri a rayuwarshi yanzun. Ya na d'agawa suka fara gaisawa, daga kuma yanda suka gaisa ya tabbatar ma sa bai san komai ba, sai kawai yace "Ka san me ke faruwa ne ta b'angaren amaryarka?" A hankali yace "Amaryata kuma? Lafiya? Wani abu ya faru ne?" B'oyayyar ajiyar zuciya ya sauke yace "Ba komai, ina so na ji komai lafiya ne?" D'an murmushi ya k'ak'aro yace "Komai lafiya lau." D'orawa ya yi da "Yaushe ne zaman kotun nan?" A hankali ya amsa masa da "Gobe." D'innnn! Ya datse kiran alamar shi kad'ai ya san me zai faru goben. Wayar ya bi da kallo kawai bai ce komai ba sai ma tunanin kiran Faduma. Ya na kiranta ta d'aga suka gaisa tare da k'ok'arin b'oye damuwarsu, dan kowa baya yanayin farin ciki, bai bata damar doguwar magana ba sai izinin da ya bata kan ta je kotu, taji dad'i sosai tare da mi shi alk'awarin kare kanta, da haka su ka yi sallama ba wata hirar soyayya kamar yanda suka saba. *Da yamma* suka kama hanyar tafiya Damagaram dan riskar shari'ar nan a gobe, kuma kamar yanda ya buk'ata wannan karan ba su taho da Gomboy ba duk da taso tafiyar, sai Aisho kawai da Hatimi da kuma Husna da tace ta na so ta zo ne dan ta ga gida. A hanyar ne yake fad'a ma Hatimi "Ayya kamar yanda na fad'a mi ki, ana gama shari'ar nan kar ku k'ara minti d'aya a garin nan, ku bar nan da gaggawa ni zan same ku daga baya, ko ta wane hali Amjad zai dawo hannunmu da kuma *uwarshi.*" Da tashin hankali duk suka kalleshi, da k'yar Hatimi tace "Tagur ban gane ba? Me ka ke nufi har da uwarshi?" Kafin yace wani abu Aisho ta yi saurin cewa "Yaya Tagur ba dai d'auketa ka ke da niyyar yi ba?" Bai kula ta ba kamar wanda bai ji ta ba, Hatimi ce ta sake cewa "Kai magana ake? Me ka ke shirin aikatawa ne?" A k'ufule yace "D'auketa zan yi, ni Faduwa za ta wa gorin iko akan ta, ni za ta faffad'awa magana saboda ta yi aure? To wallahi da auren na ta zan d'auketa na ga uban da ya isa ya karb'eta a hannu na." Cikin kid'ima Aisho dake baya zaune tace "A'a yaya Tagur, dan Allah ka rufa mana asiri ka fita a harkarta, na ji magana k'asa k'asa a wajen Gomboy akan mijin da ta aura, ban san ko matarsa k'awarsu ce ba, amma dai da alama mijinta babban mutum ne dan ya na da alak'a da g茅n茅ral Wardugu, kuma kafi kowa sanin waye Wardugu, sannan su kansu danginta su ma dai kamar su jinin tubawa ne ke yawo a jikinsu, wallahi abinda ka ke shirin aikatawa zai iya jawo salwantar rayuka da ba'a san adadinsu ba." Hatimi ce ta jinjina kai tace "Gaskiya ne, ka saurari abinda ta fad'a ma ka, indai za ka ji ta tawa to abar maganar nan, ba kai ba Faduma Tagur, ba na so ka halattawa kan ka ita ta hanyar haram, muyi k'ok'ari mu ga mun samu Amjad sai kawai mu juya inda mu ka fito." Da wani irin k'arfi ya cije leb'enshi tare da danna oda da k'arfi sosai, da sauri duk suka kalleshi sai Hatimi da ta shiga dukan damtsenshi ta na fad'in "Saki bakinka, saki leb'enka na ce dan ubanka kar ka ji wa kan ka ciwo." _(馃槑 Maza ba, ba kamar waccen ruwan sanyin ba, sullutun wofi.)_ Bai saki leb'en ba ita dai har ta gaji ta rabu da shi, babu wanda ya sake magana sai sauke numfashi, inda kuma Husna take hasko kan ta a matsayin matarshi ta na sauke shi idan ya yi irin wannan b'acin ran, haka dai suka k'arasa tafiyar ta su ba dad'i ba wuya. *Talata* _Ranar kotu_ Kuka ta yi sosai kafin ya yarda ya tsaya saurarenta, sai da ta gama bayaninta tsaf cikin sanyin jiki ya kalleta yace "Na ji Ayya, zan hak'ura kamar yanda ki ka ce, amma ki sani ba zan hak'ura ba idan kotu ta rabani da Amjad, ba zan hak'ura ba Ayya." Ko da ya fad'a ya yi gaba ya na fad'in "Ku biyo ni muje, lokaci ya kusa." Bin bayanshi su ka yi ita da Aisho jikinsu a mace da fatan Allah ya tsare ya kuma kai su lafiya. *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 21:42 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _67_ Sosai ta yi mamakin ganin danginta masu d'umbin yawa da sunan za su rakata kotu, ba wannan ne abun tashin hankalin ba kamar yanda zaratan matasa ne suka fi yawa wanda za su tafi ne da shirin ko ta kwana, *a mutu* ko *a yi rai* duk dan kareta, ga kuma su yaya Manu da yaya Kalli da su Barka har da Abbakar ma ba'a bari a baya ba. Girgiza kai kawai ta yi sanda ta k'are mu su kallo, ba za ta mu su magana ba dan ba za su saurare ta ba, haka ta rik'e hannun dada gam suka d'auki hanya a motar yaya Kalli, sai Amjad da ke tare da Abdul (wanda aka so had'a Faduma da shi)da kuma Barka. *Farfajiyar Kotu* Tank'am wurin yake da bil'adam da kuma tarin motoci tuli guda, amma fa a cikin motocin akwai wanda suka bambamta a kalarsu da kuma matuk'a motocin, dan kuwa motoci ne irin na shiga sahara (rai-rai) masu d'an banzan gudu, ma su tuk'insu majiya k'arfi ne da ke nuna sun san kan motocin ko kuma dai sojojin b'oye ne (馃槑 Wardugu ya yi halin). Dayawa daga cikin mutanen harkokin gabansu suke da ke nuna ba sa kula da abinda ake, sai dai tunda Faduma ta shigo take lure da kuma hankalce da cewa lallai mutanen nan *b'adda sawu su ke*, gabanta kuma ya shiga fad'uwa na tunanin abinda suke shirin aikatawa, dan ta na ji a jikinta ba lafiya ba; kuma komai zai iya faruwa a wurin. Kusa da k'ofar shiga ciki suke tsaye ya hard'e hannaye ya matse fuska a cikin bak'in gilashi, Amjad na ganinshi da gudu ya fizgi hannayenshi dake rik'e da su Barka ya tunkare shi, da sauri Barka ya yi niyyar cakumo Amjad sai kuma Faduma ta yi saurin rik'e hannunshi ta girgiza ma sa kai. Da gudu ya fad'a jikin Tagur da ya rage masa tsayi ta hanyar durk'usawa da gwiwarsa d'aya, rumgume juna su ka yi sosai cike da k'aunar junansu da kuma soyayya tsakanin d'a da uba, sun jima haka inda su Faduma su ka yi cirko-cirko su na kallonsu, d'agowa ya yi daga jikinshi ya kalli Hatimi dake shafa kan shi tace "Amjad ya kake?" Saida ya fara jinjina mata kai kafin yace "Lafiya lau, ina kwana?" Da murmushi ta amsa da "Lafiya lau." Kallon Aisho ya yi da ita ma ke murmushi yace "Aba ya ku ka zo nan kuma? Kun zo kallon shari'ar Ayya ne?" Tsam! Ya yi da mamaki da alamar tambaya, bud'a baki ya yi yace "Ayya..." Sai kuma Hatimi ta yi saurin katse shi da cewa "Eh Amjad, abinda ya kawo mu kenan." Murmushi ya yi sosai yace "Za ku sha kallo, dan na san Ayyata za ta yi nasara, babu lauyen da ke bugeta a harkar nan." D'aga kan shi ya yi ya tsinkayi Faduma da suke d'an nesa kad'an, wani malalacin murmushi ya yi yace "Za mu gani." Mik'ewa ya yi ya na sake rik'e hannun Amjad gam a na shi hannun, Barka ne ya k'arasa gabanshi da fuska a had'e sosai ya tarawa Amjad hannu yace "Muje." Zuro ma sa hannun ya yi ya rik'e, ya jashi sai kuma Tagur ya sake rik'e shi g shi ma, shi ya ja shi haka shi ma Barka ya ja shi, wani kallon makirci suka aikawa junansu Barka yace "Rigimar ka ke nema kenan?" Fuska a dake sosai yanayin da babu wasa yace "Rigima a jininmu take, idan ka shirya ni ma a shirye nake akan yarona." Cikin muryar gargad'i Barka yace "Sake shi Tagur." Shi ma a irin yanayin nan yace "Ba zan sake shi ba, ka karb'esa da k'arfi mana idan ka isa, ko ka d'auka wannan zugar da ku ka yi za ta hana faruwar abinda na yi niyya ne?" Gyara tsayuwa ya yi sosai ya na shu'umin murmushi, zai yi magana da sauri Aba yace mi shi "Kai Barka, sake mi shi yaron ka gani, idan shi jahili ne ai mutane ba jahilai bane, mun san me mu ke yi m没." Sakin hannun Amjad Barka ya yi ya dawo ya tsaya ya na hararen Tagur, shi kam ko a jikinshi, sai ma mayar da hankalinsa da ya yi kan Amjad. *08:00* dai-dai duk mutanen suka kasance a zaune a cikin makekiyar kotun sauraren shari'ar da ta shafi harkar iyali da sulhu wa jama'a, abune da bai cika faruwa ba ka ga mutane cike a kotun, amma shari'ar ta yau ta d'auki mutane da dama kuma duk dangi ne da suka nuna sai anyi komai gabansu, dan ba su san me zai faru ba idan sun juya baya, hakan kuma ya samo asali ne daga ikrarin da Tagur ya yi akan Faduma na ba za ta shiga d'akin mijinta ba. Amjad ne kawai bai shigo ba kamar yanda Faduma ta so, sai dai ya na tare da Kalli da kuma Abdul da ke jin haushin Tagur sosai na rabashi da yarinya mai ilimi, gashi yanzu ta mu su nisa dukansu d'in. _Za ku ga na nuna Faduma za ta tsaya ma kanta a kotu, saboda hakan shine ya min daidai a tsarina, a dokar k'asa ma hakan zai iya faruwa, sai dai akwai matakai masu tsauri da lauya zai bi bayan faruwar wani abun mai girman gasken kafin ya samu damar tsayawa kan sa da kan sa, domin taya dokarmu ci gaba da wanzuwarta ya sa bai bi matakan ba, dan shi kan shi kafin kasan matakan idan ba karatun ka ke ba babban aiki ne, dan haka za mu tak'aita domin nishad'i._ Lauyen da ke b'angaren Tagur ne ya mik'e ya gabatar da kan shi kafin ya zauna, jim wurin ya fara d'auka kafin alk'ali ya kalli b'angaren da suke yace "Lauyen wanda ake k'ara?" Cikin sanyin jiki da gyara zaman lafayarta mai kalar bak'i da kore ta d'an matsa gaba, takarda ta mik'awa magatakarda ya karb'a ya mik'e ya bawa alk'alin, dubawa ya yi a tsanake kafin ya d'ago ya na gyara gilashin shi yace "Za ki iya, bismillah." D'an sunkuyawa ta yi tace "Nagode mai shari'a." Zaunawa ta yi in da alk'ali ya koma kan lauyen cen, mik'ewa ya yi cikin karsashi da d'aga sautin muryarshi yace "Mai girma mai shari'a, wannan shari'a ta mu ba ta da wani tashin hankali bare sark'ak'iya, magana ce akan yaro da ake neman raba shi da ubansa, wanda hakan kowa yasan ya sab'awa k'a'ida, da wannan koken ne malam Tagur ya zo gaban wannan kotu mai alfarma dan ta bi mi shi hakk'insa, abisa wannan mu na da hujjar da ta tabbatar da wannan yaro na sa ne, kuma babbar shaidarmu ita ce uwar yaron da kan sa." Alk'alin ne yace "Miye hujjar ta ku?" Gyara tsayuwarsa ya yi ya na juyawa inda Faduma ke zaune ya nuna ta yace "Hujjata ta farko ita ce Faduma Moliya, wacce ita ce uwar yaron da ake rigima a kan shi." D'an shirun da ya biyo baya ne ya sa alk'ali yin alama da hannu alamar ta taso, magatakarda ne ya mik'e ya sake jadadda mata, mik'ewa ta yi a sanyaye kuma a tsanake ta k'arasa cikin tsakiyar kantar ta tsaya, lauyen ne ya k'arasa gareta inda alk'ali ya tambaye ta cikakken sunanta, saida ta amsa mishi ya ba lauyen damar tambayarta, cikin d'aga murya yace "Malama Faduma, tambaya uku kawai zan mi ki, da fatan za ki amsa min su ba tare da tsaiko ba?" Da wani shak'iyin murmushi tace "Insha'Allah." D'ora hannunshi ya yi a kan kantar yace "Amjad d'an ki ne na cikinki?" Cike da tabbaci tace "Tabbas Amjad d'ana, ni na haifi abu na." Jinjina kai ya yi yace "Da kyau, shin da gaske Tagur Sugui ne mahaifinsa?" Nan ma cike da bashi tabbaci tace "Tabbas, Tagur Sugui ne mahaifinsa, kuma ba na jin ya na da wani d'a a duniya bayan Amjad da na haifa." Da mamaki yace "To idan kin yarda shi ne ubansa, me ya sa ba za ki bashi d'an shi ba? Ke ki huta, shi ya huta haka ma d'an ku ya huta ta hanyar samun ingatacciyar rayuwa." D'ago idonta ta yi ta sauke a kan shi, cikin jin haushin maganganunshi tace "Saboda haihuwarsa kawai ya yi, amma bai zama uba a garesa ba." D'an tab'e baki ya yi yace "Kamar ya?" Wani sakaran murmushi ta yi tace "Tambaya uku ka ce, ka gama zagayenka." Wani kallo ya mata na mamakin raini da isarta kafin ya kalli alk'ali yace "Nagode ya mai shari'a, tambayar kenan, sai dai ina rok'on kotu da ta duba lamarin nan da kyau, ita kanta ta tabbatar mana shi d'in d'an sa ne na cikinsa, dan haka ban ga dalilin da zai sa ta nemi raba su ba, domin kuwa da uba kowa ke amsa sunanshi." Da hannu alk'ali ya masa alamar zai iya zama sannan ya kalli Faduma ita ma yace ta zauna, dukansu zaune su ka yi inda ya shiga rubutu kusan minti d'aya kafin ya d'ago ya kalli Faduma yace "Akwai abin da za ki iya cewa ne?" Mik'ewa ta yi ta na gyara rigarta tace "Ina da ya mai shari'a." Da hannu ya ma ta alama tare da cewa "Bismillah." Mk'ewa ta yi ta k'arasa cikin takon nutsuwa da takalminta dake fitar da sauti d'aya bayan d'aya ta tsaya tsakiyar wurin gaban magatakarda, had'e tafukan hannayenta ta yi wuri d'aya ta shiga mitsitsikasu, a hankalce kuma a d'an d'age kamar yanda k'aidar aikin take ta fara da fad'in "Ya mai girma mai shari'a kamar yanda abokin aikina ya fad'a ne, a yau wannan kotu ta karb'i gayyatar shari'a mai sauk'in gaske, domin kuwa abun a bayyane yake ta yanda duk mai hankali ya masa kallon basira zai fahimci ba matsala bace da za ayi jayayya akai." Cikin d'aga sauti sosai tace "Mai shari'a Amjad da ake magana akan shi ba ta hanyar aure aka haife sa ba, *k'addara, tsautsayi*, *sakaci* da kuma *rabo* su suka kawo shi duniyar nan, sai dai babu sakacin iyayena a ciki ko d'aya, domin ni shaida ce a kan tarbiyar da suka bani, ni ma kuma idan har za mu duba abun ta fuskar k'addara, to ba zan ce da sakaci na ba sai dai na ce rabo ne kawai, dan duk abin da ya faru ba da son raina ya faru ba, fin k'arfi ne da kuma cin zarafin mata da mu ke fuskanta a kowane lokaci." Sake d'an muskutawa ta yi tace "Akwai tarin hujjoji da dalilai da zan gabatar wanda su ne suka zama katanga tsakanin Tagur da Amjad, haka kuma ina da tarin tambayoyin da na ke son gabatarwa a yau d'in nan, mutum na farko da na ke son fara jin wasu amsoshi daga bakinshi kuwa shi ne *Tagur*." Da hannu ya yi alamar bayar da izini sai magatakarda da ya mik'e ya sake jadadda abin da alk'alin ke nufi. Jiki a mace sosai inda gabanshi ya shiga dukan tara-tara ya taso ya k'arasa, kallon juna su ka dinga yi da ma'anoni da dama, sai da ta tsaya gabanshi tsaf ba tare da sun daina kallon juna ba, cikin muryar da ta k'ara kayar masa da gaba tace "Malam Tagur, za ka iya fad'awa kotu kai wane irin mutum ne, ma'ana dama halayyarka ce ribatar 'yan mata sannan ka yaudaresu? Ko kuma k'arancin shekaruna a waccen lokacin ya sa ka shiga rayuwata ka min wayo?" Da wani mad'aukakin mamaki ya kalleta, shi ne Faduma za ta ma wannan tambayar? Bayan ta san shi bai tab'a soyayya ba sai a kan ta. D'an gyara tsayuwa ya yi ya na kallonta yace "Ban tab'a soyayya ba, ban tab'a yaudara ba." D'an murmushi ta k'ak'aro ta d'ora gwiwar hannunta kan kantar da ya ke tsaye tace "Sanda labarin soyayyarmu ya isa gidanku, za ka fad'a mana yanda iyayenka su ka karb'i al'amarin?" Cikin taushin murya yace "Da fari ba su amince ba, amma daga baya sun amince har aka fara maganar aurenmu." Idonta tsam a kan shi tace "Kenan ka na so ka ce ba a samu wata matsala ba a game da hakan? Kowa ya yi amanna da ni a gidan?" D'an sunkuyar da kan shi ya yi sai kuma ya saci kallon Ayya, kallon Faduma ya yi yace "Ayya ta da kuma yayata ce kawai basu amince, amma dai rashin amincewar ta su bai hana komai ba." Jinjina kai ta yi tace "A lokacin da aka saka ranar aurenmu, da kanka ka nemi izini a wajen iyayena kan cewa zan je na gaishe da mahaifiyarka, hakane?" Shi ma jinjina kai ya yi yace "Hakane." Sake jinjina kai ta yi alamar gamsuwa tace "Ranar juma'a ne ka zo har gida ka d'aukeni mu ka je gidanku, me ya faru da shigarmu?" K'yak'yabta ido ya yi ya na kallon alk'ali da kuma ita, cikin rashin gaskiya yace "Am..., ko da mu ka je ba m没 samu kowa a gidan ba, sai na kira Ayyata ta ce sun fita amma za su dawo ba jimawa, dan haka mu ka shiga ciki mu ka jirasu." D'auke hannunta ta yi daga kan kantar ta d'anyi baya ta na kallonshi tace "A ina kenan mu ka zauna jiransu?" A sanyaye yace "A b'angarena, cikin falona." K'ure shi ta yi da ido tace "Me ya faru a lokacin?" Wani mummunan fad'uwar gaba tare da jin kad'awan kayan ciki ya saka shi dafe cikinshi, zazzare ido ya fara yi ya na kallonta kallo na ki taimaka min, ki bar tambayar nan dan Allah. Kamar ta san me ya ke tunani sai kawai ta saki murmushin jin dad'in ganin yanda ya gigice tace "Za ka iya zama malam Tagur, idan buk'atar ganinka ta taso zan neme ka." Tuni ya bar wurin ya na addu'ar "Allah ma ya mantar dake sunana har mu tashi daga zaman nan." Kallon alk'ali ta yi tace "Ya mai girma mai shari'a, ina neman alfarmar kotu da ta gabatar da malam Moliya a gabanta? Domin amsa wasu tambayoyi." Kamar dai kowa shi ma a inda ake tsayawa ya tsaya ya na kallon fuskar 'yarsa Fadun Aba, ita ce yau ga ta ga shi zai amsa tambayoyi daga gareta akan aikin da shi ya ke tunanin ba za ta iya ba, ya ke ganin kamar shirme ne cen ma na yarinta. Gyara tsayuwa tayi hannayenta a had'e da ladabi tace "Malam Moliya bayan ka samu labarin ina d'auke da ciki a jikina ba tare da aure ba, a matsayinka na uba namiji wane mataki ka d'auka?" Numfasawa ya yi yace "A sanda na samu labarin ban yi fushi ba, dan hakan zai sa na d'auki mataki cikin yanayin b'acin rai, amma a tsanake sai na ga zai fi kyau mu samu shi iyayen yaron mu fad'a masa, duba da a lokacin kwana uku ne ya rage aurenku, tunda mun yarda ba'a aure da ciki, kuma al'amari mai girma irin wannan bai kamata a b'oye mu su ba, ko ba komai aka fad'a mu su an dakatar da auren za su tambayi dalilin dakatarwar, ban yi k'asa a gwiwa ba mu ka je gidan mu ka same su mu ka sanar da su halin da ake ciki." Cikin sakin fuska tace "Wace irin tarba ku ka samu a gurin mutanen?" Girgiza kai ya yi yace "Ba a tab'a cin zarafi na irin na ranar ba, ban tab'a jin an k'ask'antani kamar wannan rana ba, na shiga damuwa sosai da tunanin k'ananan mutanen da Allah ya had'amu tarayya da su, a gaskiya..." Da saurin lauyen nan ya mik'e yace "Ina da ja ya mai shari'a, wannan ma abu ne da ba zai yiwu ba ai, ta ya za ta kawo mana mutane daga gidansu bayan sun rubuta labarinsu? Sannan su zaunar da mu anan su na fesa mana shi." Wani kallo alk'alin ya masa yace "K'orafi bai karb'u ba." Kallon Faduma ya yi yace "Ci gaba." Murmushi ta yi ta d'an sunkuya tace "Nagode mai shari'a." Kallon Aba ta yi tace "Idan na fahimce ka kamar iyayen yaron ba su yarda da abin da ku ka je mu su da shi ba?" Gyad'a kai ya yi yace "Hakane, sam ba su yarda ba musamman ma mahaifiyarsa, dukansu mamaki da kuma al'ajabin abin da yaron ya yi su ke, har su ke ganin d'ansu ba zai iya aikata wannan mummunan aiki ba." D'an lumshe ido ta yi tace "Nagode malam Moliya, za ka iya zama." Kallon mai shari'a ta yi tace "Nagode mai shari'a." Juyawa ta yi ta koma ta zauna ta na dallawa Tagur hararar tsana, alk'ali ne ya tambayi d'aya lauyen idan ya na da tambaya ko abun cewa? Mik'ewa ya yi yace "Ina so zan yi wata tambaya ga malam Moliya?" Magatakarda ne ya mik'e ya sake kiranshi ya fito, bayan ya tsaya gabanshi ne yace "Malam Moliya ka ce sanda ku ka fad'a mu su suna mamaki jin yaronsu ne ya aikata wannan abu?" Cike da tabbaci yace "Eh, hakane." Jinjina kai ya yi yace "Idan hakane kenan ya nuna ba halinsa ba ne, tunda har iyayensa su ka yi inkari akan faruwar lamarin." Kallon cikin idonshi ya yi yace "Dama yaronsu zai zauna ya na fad'a mu si duk wani abu da ya ke aikatawa ne a waje? Ko kuma tare da shi suke yawo da za su zama shaida kan kyawawan d'abi'unshi?" A d'an hassale lauyen yace "Tambaya ka maido min kai ma madadin amsa." Gyara tsayuwa ya yi yace "Shin miye zai gagarin yaron da suke daf da aurar da shi a lokacin? Yanda zai kusanci macen? Ko kuma yanda zai mata cikin?" Dayawa daga mutanen kotun dariya su ka saka har Faduma kan ta sai da ta sunkuyar da kai ta na murmushi, Tagur kam d'an kawar da kan shi ya yi haka ma *Hasheer* sai da ya dara, dan ya na kallon komai da ke wakana ta k'aramar tablet d'in shi a ofishin shi, wanda Barka ya kira shi ta hoto mai motsi (appel vid茅o, vid茅o call) ya na kallon komai tarau, a duk wani motsinta k'ara birgeshi yarinyar ta ke, shigar da tayi ta birgeshi sosai dan ta kare mi shi abin da ya ke halalinsa, yanda ta ke gudanar da aikinta ya birgeshi sosai, hakan ya sa ma har ya buga tagumi ya na kallon komai da ke wakana a wurin. Sai da alk'ali ya bubbuga gudumar gabanshi kad'ai ya samu aka tsagaita dariyar, hakan ya sa lauyen komawa ya zauna sai alk'ali da ya ba wa Aba umarnin zama, ya jima ya na rubuce rubuce kafin ya d'ago yace "Akwai wani mai sauran bayani?" Faduma ce ta mik'e tace "Za mu iya cewa shinfid'a mu ka yi, idan kotu ta amince zan so na gabatar da Ayyata Herde,wacce ta na d'aya daga cikin wanda aka je gidan su yaron a wannan lokacin." Wani murmushi ya saki, lashe leb'enshi na k'asa ya yi ya na sake kallon bayanta ta tablet d'in ya na fad'in " *Gimbiya Zahra* rigima, ban da abinki uban yaronki ki ke kira yaro." Wani murmushin ya kuma. A wajen Tagur ma wani kallo ya wurga mata a zuciyarshi ya na fad'in "Wai me ya sa Faduma ke son wulak'anta ni? Ni ne ma take kira yaro kamar wani d'an da ta haifa." Tuni kotu ta bata dama inda ta tsaya gaban Herde da kallo d'aya za ka mata kasan a tsorace ta ke, sai da ta je daf da ita ta rik'o hannunta cike da kulawa tace "Ayya ta ki nutsu, tambaya kawai zan mi ki ke kuma ki bani amsa." Jinjina mata kai ta yi alamar ta ji, ita ma d'an jinjina kan ta yi kafin tace "Malama Herde da ke a ka tafi gidansu a waccen ranar, mun ji daga bakin malam Moliya cewa iyayenshi ba su amince da abinda a ka je mu su da shi ba, shin za mu iya sanin me ya faru ta b'angaren yaron? Ya amince ko kuma shi ma kamar iyayensa bai amince ba?" Sai da ta girgiza kai tace "Ai ko kad'an bai amince, hasalima shi ne babban shed'anin, dan cewa ya yi ba na shi bane." Murmushi Faduma ta yi tace "Nagode Ayya ta, za ki iya zama." Gyara tsayuwarta ta yi har sai da ta zauna kafin ta nemi ganin Tagur, sai da ya ji kamar ya nutse k'asa ko yace babu inda zai je, a take ya fara jin matsananciyar nadamar kawo maganar nan kotu, da ya sani da ya hak'ura sun yi ta jayayyar a gida har ya samu wani kamashon da Amjad zai iya kiranshi da Aba, gashi Aji da ya fara maganar zuwa kotu, ya dinga tirzashi kan a zo dan a bashi yaron shi, shi bai ma zo kotun ba bare ya kalleshi ya ji dad'i. Sake tsayawa ya yi gabanta a karo na biyu suka shiga kallon juna, cikin kafeshi da ido da alamar b'acin rai tace "Da gaske ne abin da Herde ta fad'a? Ka amsa da cewa cikin nan ba na ka bane?" Tarrrr! Ya kalleta cikin ido, amma sai ya yi saurin d'auke na shi, dan wal'ahi kaf ta zaro idonta ta na kallonshi da su kamar ta na son tsorata shi, abun mamaki kuma duk kusurwar da ya kalla shi ake kallo kallon jiran amsar da za ta fito daga bakinshi. Sunkuyar da kai ya yi ya ji ba zai iya bayar da amsa ba gaskiya, amma sai Faduma tace "Malam Tagur kotu na saurarenka." Sake sunkuyar da kan shi ya yi a hankali ya d'aga labb'enshi yace "Hakane." Cikin son k'ureshi tace "Hakane ka amsa ba na ka bane kenan?" Jinjina kai ya yi kamar mai kuka yace "Hakane." Da sauri ta juyo wajen alk'ali ta na fad'in "Shikenan, komai ya zo k'arshe ya mai girma mai shari'a, dama wannan shari'a mai sauk'i ce kawai ya so wahalar da mu ne, amma ko a addinance d'an da aka haifa ba ta hanyar aure ba na uwa ne, ana jingina shi ne da mahaifiyarsa ba mahaifinsa ba, duk da zai iya amsa sunan ubanshi amma dai a hakan ma alfarma aka ma ka, sannan idan m没 ka yi duba da abin da ya faru anan, malam Tagur ya yi ikrarin wannan ciki ba na sa bane a lokacin da ya ke d'an tayinshi babu wanda yasan me za a haifa, sai yanzu ne da ya zama mutum zai fito ya kalli mutane yace d'an sa ne? Tsabar rashin kunya har ni zai iya shigar da k'arata a kotu kan d'an da ni na san wahalarsa, wannan wane irin cin zalin ne da cin mutumci?" Juyawa ta yi kan Tagur da ke tsaye, duk da hawayen da ke zuba a idonta haka ta shiga fad'in "Da fari ka rabani da mutumcina ta k'arfi da yaji, a gidanku an ci mutumcina an wulak'antani duk saboda kai, mahaifina ya koreni a dalilin k'ask'ancin da ka ja min ya yi fatali da lamaruna, ya min bulala ya zageni ya koreni daga gidansa duk a kan ka, duk da na yi karatu kuma na samu aikin da na ke so, amma na jingine rayuwar jin dad'i da morewa a gefe saboda kula da yaron ka, lokacin da ya kamata ace ina gaban mahaifiyata ta na d'orani a hanya, amma saboda kuskurenka sai na kasance ina neman yanda zan yi na inganta rayuwar yaro, na yi samari da dama da suke fitowa da sunan so na kuma da gaske, amma tunanin yaronka da ke tare dani ya sa ban bud'e wannan k'ofar ba bare har wata rana a gorantawa yarona ko kuma ni. Shekara d'ai-d'ai shekara tara na d'auka a haka, na yi fad'i-tashi da dama saboda Amjad, ana kallo na karuwa a gari saboda d'an da ba'a san ubansa ba, a haka kuma har ka kalleni ka ce min wai zan karb'i sammaci daga kotu?" Cire takalman k'afarta ta yi a harzuk'e ta duk'a ta d'auka ta jefa ma sa ta na fad'in "Tagur kan ka d'aya kuwa?" Da sauri alk'ali ya bubbuga gudumar nan hakan ya sa ta dakatawa ta jawo takalman ta saka, saida ta share hawayenta ta saita nutsuwarta ta juya kan alk'alin, cikin sauke numfashi da magana a sanyaye kamar mai neman alfaa ta shiga fad'in "Mai girma mai shari'a, yaron nan da ake magana da shi wallahi ko sau d'aya bai tab'a ciyar da shi ba, dai-dai d'脿 k'wayar zarra ba ta tab'a shiga bakin Amjad ba da sunan mahaifinsa ne ya kawo, haka ruwa ma bai tab'a shan wanda a dalilinshi ne su ka samu ba, idan har Tagur ya tab'a mallakawa Amjad takalmi d'aya gashi a gabana ya fito ya fad'a, a tsawon wannan shekarun da aka d'auka bai tab'a anfanarmu da komai ba, sunanshi kawai ya ji a gari, amma bai san waye ya siya masa ragon da aka yanka masa sunan da shi ba, mai shari'a Tagur Sugui bai tab'a sanin cewa akwai yaron nan a doron k'asa ba idan aka cire wata d'aya baya. A hakan ne ya ke da dama da ikon da zai iya shigar da k'ara ya na son ya k'waci yaron nan a ba shi." Girgiza kai ta yi ta na sauke numfashi ta kalli Tagur da kanshi ke k'asa ya na share hawaye, ita ma hawayen ta share tace "Tagur tunani ne ba ka da, shi ya sa makusantanka ke ma ka yawo da k'wak'walwa, ka mata ya yi ka fara da tambayar ya Amjad ya rayu a doron k'asa ba tare da ka sani ba? Wace irin rayuwa d'ana yayi kafin na san da shi? Ta ya aka ciyar da shi? Wa ya shayar da shi da kuma tufatar da shi? Ilimin da Amjad ya samu waye ya tsaya ma sa haka? Su waye k'ashin bayan da su ka zama jigo ga tarbiyar da ya ke d'auke da ita." Sake matsawa ta yi gabanshi tace "Shin duk kasan amsar wannan tambayoyin?" Fashewa ya yi da kuka tare da saka tafukan hannayenshi ya d'ora glshinshi akan kantar da yake tsaye, cikin kuka ita ma ta kalli alk'ali tace "Mai shari'a ga k'anwar mahaifiyata nan shaida ce, sannan shi kan shi yaron ya na waje dan ba na son ya san a kan shi m没 ke wannan zaman, na gama magana indai akan yarona ne, abu d'aya da zan rufe da shi shi ne idan ana tamtama akan irin kulawar da na bawa Amjad, ana iya gabatar da shi anan, ban da fargaba ko d'ar-d'ar akan duk jarabawar da za a ma sa da za ta bayyanar da nagartarsa musamman ta b'angaren addini, *ni* Faduma Moliya na yarda idan har aka samu nak'asu a cikin makin da ya cancanta ya samu, to *na barwa Tagur Amjad har abada*." _Shari'a fa ta yi zafi._ *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 21:42 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _68_ Shiru kotu ta d'auka in banda sautin kukan Hatimi da kuma Herde, sai wanda suke matsar k'walla ba tare da sauti ba, komawa ta yi ta zauna ita ma ta na ci gaba da share hawayenta kan ta a sadde, an d'auki tsawon mintuna a haka kafin alk'ali ya d'ago ya fara da fad'in "Bayan dogon nazari da duba da hujjojin da duka b'angarorin biyu su ka gabatar, wannan kotu za ta yanke hukunci dai-dai da abin da ya dace. Duba da wasu abubuwa da kotu ta lura da su kamar haka." Takardun gabanshi ya fara dubawa ya na fad'in "Na farko kamar yanda mu ka sani d'an da aka haifa ta hanyar da ba aure na uwa ne, duk da a maslaha da kuma kyautatawa ta d'an adam bai haramta idan uwar ta yi sadaukarwa ba. Abu na biyu kuma shi ne malam Tagur ya riga da ya amsa tun farko cewa wannan cikin ba na shi ba ne, hakan na nufin ya koresa daga garesa ne, da ta hanyar aure haka ta faru akwai matakan da za mu bi kafin mu sake jingina ma sa yaron shi, amma tunda babu wannan darajar hakan zai sa ba za mu tirsasa kowa ba. Abu na uku kuma shi ne tunda aka haifi wannan yaro na rana d'aya bai san da wahalarsa ba, duka nauyinshi mahaifiyarsa ce ta d'auka. Duba da wannan ne kotu ta yanke hukuncin cewa yaron nan Amjad *mahaifiyarsa ce* za ta ci gaba da rik'e shi, dan ita ce da shi kuma ita ta dace ta ci gaba rik'e, sai dai kotu na umartar malama Faduma da ta ware wani lokacin ko da sau d'aya ne a wata da yaro zai dinga ganawa da *mahaifinsa*, tunda tun farko da sunan shi a bayan sunan yaron, haka kuma kotu na umartar malam Tagur daga yau za ka fara d'aukar nauyin wannan yaro, cin shi, shan shi, suturarshi, kula da lafiyarshi, karatunshi da sauran buk'atu na yau da kullum, wannan dole ne ko kuma hukunci ya hau kan ka...sanadiyar b'ata ma ta lokaci akan abin da ka ke da tabbacin ba ka da gaskiya a kai, da kuma tsayar da ita gaban shari'a a kan yaron da ta yi d'awainiya da shi, shi ma kotu na umartarka da ka biya malama Faduma tsabar kud'i har70 000 (jaka d'ari bakwai) kotu." Zunbur Hatimi ta mik'e ganin alk'alin har ya mik'e shi ma ta na fad'in "A'a dan Allah kar ku mana haka, ku taimaka ku ce yaron nan ya zauna a hannun mu, wallahi ina son Amjad ba zan iya rayuwa babu shi ba." Aisho ce ta mik'e ta rik'eta amma sai neman fizgewa ta ke, har alk'alin ya fita bai kula da tsiyarta ba sai Faduma da danginta da suka mik'e, da sauri ta tunkari Faduma ta cakumota a jikinta ta na kuka ta na fad'in "Faduma, Faduma ki duba lamarin nan, dan Allah ki bamu Amjad kin ji, na mi ki alk'awarin kulawa da shi wallahi." A wulak'ance Faduma ta fizge jikinta daga na ta ta k'arasa gaban Tagur da ke zaune ya na ta kuka, tab'e baki ta yi tace "Tagur da ka na da lissafi da na bar Amjad a hannunka, amma ba zan yi haka ba domin kai kan ka ba ka san masoyanka na gaskiya ba." Sake rik'o lafayar Faduma Hatimi ta yi tace "Wallahi za mu kula da shi, ki bani shi ni zan kula mi ki da shi kin ji, na rok'e ki Faduma?" Wani sakaran murmushi ta yi ta kalli mutanen da ke zagaye da ita, duk su na tsaye tare da ita ne dan kare lafiyarta, kallon Herde ta yi tace "Ba zan yi mamaki ba idan har ki ka fini son Amjad, domin kuwa *ki na d'aya daga cikin wanda su ka zama silar samuwarshi a gaggauce.*" Cak! Kukanta ya tsaya ta shiga binta da wani kallo, mik'ewa Tagur ya yi da sauri idonshi sunyi jawur ya kalli Faduma yace "Me ki ke fad'a Faduma?" A shashance ta juyo ta kalleshi tace "Eh, haka na fad'a, Ayyarka ita ta taimaka ma ka ta hanyar taka muhimmiyar rawa har ka hayake min da k'arfi." Da wani sabon mamakin duk mutanen wurin su ka shiga kallonta, Tagur da jikinshi ya d'auki b'ari gabanshi sai bugawa ya ke, ga kan shi tuni ya fara sara mi shi ne ya yi k'arfin halin cewa "Ban gane me ki ke so ki fad'a ba? Ki min dalla dalla." Gyara tsayuwarta ta yi ba ko alamar damuwa tace "Daga ranar da ka fara tunanin turo min sammacin kotu, a lokacin ni kuma na fara bin diddigin duk wani abu da ya shafi wanda ya san ka ma, Tagur na san abubuwa da dama akan ka da kuma mutanen da ke tare da kai." Numfashi ta sauke mai nauyi tace "Ka yarda da na fad'a ma ka ba ka haihuwa Tagur, matar nan Atta kud'inka kawai ta ke ci a banza, aurenka da ita ma yer uwarka Gomboy ce ta had'ashi saboda ta fi kowa sanin k'awarta ba mutuniyar arzik'i ba ce, Aji da ka ke gani ka ke kuma d'aukarshi aminin da ba ka da kamar shi, sam ba da zuciya d'aya ba ya ke zaune da kai, ya na nuna ma ka babu komai tsakaninshi da mahaifinshi saboda rabuwarsu da Aisho, amma kullum su na manne da juna suna shirya makircin da zai durk'usar da kai, Tagur mutanen nan biyu sun fi ka sanin Amjad *d'an ka ne*, domin kuwa a ranar da zan je gidanku mahaifiyarka ta sanarwa Alhaji Bureima zan je, shi kuma ya sanar da d'an sa Aji cewa zan zo gidan, da haka su ka shirya ma ka mummunan tarkon da ka fad'a a ciki, sun umarci mahaifiyarka da ta bar gidan har sanda aikinsu zai kammala, ita a yanda su ka fad'a mata shi ne za su yi magani na dan ganin aurenmu bai yiwu ba, amma su kuma sai su ka zagaye su ka samu abokin ka Misbah, inda ya yi anfani da maganin da ke rikita lissafin namiji idan ya yi anfani da shi, Abdul ya tabbatar min shi ne ya neme ka da shayin, kuma ya fad'a min ya ma ka fad'an me ya sa ka sha?" Girgiza kan ta tayi ta ci gaba da cewa "Tun kafin na san ina da ciki Bureima ya sanar da mahaifiyarka cewa za mu iya zuwa mu ku da wannan tatsuniyar, dan haka su ka hure mata kunne kan cewa kar ta amince dan ba na ku bane, da wannan ne fa har mahaifiyarka ta yi abin da ta yi, kuma umarninsu ne ta bi wajen tilasta mahaifinka ya d'auke ka a k'asar nan a d'an k'ank'anin lokaci dan a mantar da kai ni." Kallon fahimta da jin k'ai ta masa tace "Tagur ka daina yarda da kowa a rayuwar nan cikin sauk'i, sannan ka dinga shawara da zuciyarka wajen yanke hukunci, ka kuma daina yin abu da kai ba tare da ka yi nazari akan shi ba, ina so rayuwar d'ana ta inganta fiye da tawa rayuwar, ina so ya zama ka na kula da shi da lamuran da suka shafeshi da gaba d'aya iyawarka." A hankali ta fara takawa za ta bar nan amma sai ta tsaya cak saboda ganin *Aji* ya shigo wurin tare da zugar matasan da dama Faduma ta san zaman wani su ke, tashin hankalin shi ne Amjad na hannunshi ya rik'e gam da alama kuka ya ke, duk hankalin mutanen ne ya watse inda Barka ya manta da wayar da ya ke d'auka da ita ya zura aljihu yace "Ina yaya Kalli?" Cikin siririyar muryar Amjad yace "Sun ji mu su ciwo..." Mari Aji ya kifa ma Amjad hakan ya sa shi yin shiru ya na kallon shi a tsorace, da sauri ta zabura za ta nufeshi Tagur ya rik'e hannunta, girgiza mata kai ya yi sanda su ka kalli juna, cikin muryar kuka yace "Ba aikin ki bane wannan, na wa ne." Sakin hannunta ya yi zai tunkari Aji ya nuno sa da bindiga yace "Kar ka matso nan, yau sai na kasheta na kasheka kai ma kad'ai hankalina zai kwanta, wallahi ba ta isa ta tarwatsa mana iyali ba." Hatimi ce ta fito daga bayan Faduma tace "Tarwatsa iyali ai kai ka fara Aji, yanzu me tai ma ka kuma? Sai yaushe za ka bar yarinyar nan ta huta ne?" Ita ma nuna ta ya yi da bindiga idonshi jajir da alama ya sha wani abun na maye yace "Ke rufe min bakin ki, wannan yarinyar ita tasa g茅n茅ral Wardugu ya d'aure min d'an uwana, yanzu haka an yanke masa hukuncin zama gidan yari shi da abokananshi, dan haka ita ma sai ta mutu haka kai ma da ka zama silar shigowarta rayuwarmu." Kallon Tagur ya yi da kyau yace "Dama kai na jima ina jin haushinka, mahaifinka ne ya k'wace sunan da mahaifina ya yi a cikin harkar siyasa, arzik'inku ya rub'anya na mu haka ma ikonku, to yau zan harbeka a wurin nan na kawo k'arshen lamarin nan." Cikin tashin hankali Aisho ta shigo gaban Tagur tace "Aji dama abin da ke ranka kenan akan mu? Dan Allah ka aje makamin nan ko dan 'yarka Khairat?" Wata tsawa ya mata ya na fad'in "Ke rufe min baki, can ke da 'yarki ku k'arata, ni dama ba auren soyayya na yi da ke ba, aurenki ya na d'aya daga cikin irin muzgunawar da na fara ma ahalin Sugui." Baya Tagur ya yi da ita ya na kallonshi yace "Ka kasheni Aji, amma kar ka kuskura ka tab'a min yaro na, shi kad'ai gareni a doron duniya, ba zan lamunci ganin cutuwarshi ba." Wata dariya ya b'abb'aka ya shiga fad'in "Shashasha marar tunani, ka ji da kyau in fad'a ma ka, na tsaneka Tagur kuma na tsani zuri'arka, shi ya sa na so nesanta da wannan fitinannen yaron, mahaifina ne ya tunatar da ni cewa indai ka na ganin maradi haka ma Amjad, to ba shakka wata rana za ku had'e, shi ya sa na shirya ma wannan had'arin da tunanin ka mutu kowa ma ya huta." Duk wurin tsumewa aka yi ana sauraronshi, Tagur da tuni jiri ya deb'esa kifewa kawai ya yi a wurin a fad'i sumamme, Aisho da Hatimi da wasu daga cikin dangin Faduma ne suka rufa kna sa, Faduma na kallonshi sai dai hankalinta na kan Amjad. Sallalami aka dinga yi sai Aisho da ta kalleshi tace "Aji ka bamu hanya mu kai shi asibiti, zuciyarshi ta na harbawa har yanzu." Dariya ya sake fashewa da ita ya na sake babbake hanyar yace "Mutuwa a sauk'ak'e, ki barshi kawai ya k'arasa a haka ba sai na tab'a shi ba bare alhakin ya hau kai na." A sukwane Faduma ta yi kan shi hakan ya sa Barka ma bin bayanta da Aba ya na kiran sunanta, a hassale ta tara hannu tace "Aji ka ban yarona, idan ni ka ke neman kashewa gani, amma ka rabu da yarona." Sama da k'asa ya kalleta yace "Ke ce silar faruwar abubuwa da dama, daga cikin wanda ya fi tsaya min a rai shi ne d'aure k'ane na, kuma d'aurin da aka ma sa ba na da hanyar da za a fito min da shi cikin sauk'i sai ya kammala shekarun da aka d'iba masa, shi ya sa zan kashe ki dan na huce takaici na." Kallonshi kawai ta ke, bata san akan me ya ke magana ba dan ba ta san Wardugu ya yi ruwa ya yi tsaki ba har sa茂da aka yanke mu su hukunci. Gyara tsayuwa ta yi ta d'ago hannu za ta lallab'a shi, wani ingarman soja ne a bayansu ya daki kan Aji da wata k'aramar bindiga bak'a mai nauyin gaske, hakan ya haddasa ma sa fad'uwa a wurin ya na sakin bindigar hannunshi, kafin yaran da ke zagaye da shi su ankara duk sauran sojawan nan da Wardugu ya sa su ka yi shiga cikin kaya na farar hula su ka rirrik'esu. Bindigar da ta fad'i ya zura hannunshi d'aya zai d'auko, amma da azama Barka ya sa k'afa ya cillata gefe tare da shak'o wuyan Aji ya mik'ar da shi tsaye, wani mahaukacin mari ya kifa ma sa ya na lalubo mak'ogwaronshi dan ya rik'e, da sauri sojan nan ya ciro Aji a hannun Barka ya na fad'in "Yi hak'uri, kar ku damu da wannan, yanzu za mu tafi da shi, kuma wannan hukunci zai hau kan shi dan aiken g茅n茅ral ne." Cikin k'araji Aji ya shiga neman kubcewa ya na fad'in "Ku sake ni na kashe su, ku rabu da ni, kar na mutu ban d'auki fansa ba." Tauuuuuuuu! Faduma ta sake d'auke fuskarshi da marin da har ya sa ya rintse idon shi, ita kanta sai ta ji hannunta na wani zut zut zut tsabar zafi, idonta jajir ta nuna shi tace "Allah ya isa tsakanina da kai Aji, wallahi sai Allah ya bi mi hakk'ina, ka sani ba kai ka keta min haddi ba, amma a bad'ini kamar kai ma ka na d'aya daga ciki, Allah ya isa mugu azzalumi." Hannun Amjad ta kama ta kalleshi cike da tsana tace "Ka sani Amjad da ku ka zama silar zuwanshi duniya, zai zamar mu ku uk'uba da tashin hankali, kuma ka tuna da wani abu; Amjad *batube* ne gaba da baya, kafin kowa sanin waye batube a doron k'asa, kirkinsu, karamcinsu, nagartarsu, da kuma muguntarsu." A sukwane ta fice a wurin sai su Barka da dada da suka bi bayanta,sun juya da shi za su fita kenan Aisho ta tari gabanshi, ita ma wani mari ta watsa mi shi ta nuna shi tace "Ka sani ni ma zan shigar da k'ararka dan a mana tsakani a game da Khairat, kai ne mahaifinta amma ban lamunce mata ta kiraka da Aba ba ko ba na numfashi." Juyawa su ka yi su ka fita da shi duk ya fara gigicewa dama ga abun maye da ya shigo da shi, ana fitowa farfajiyar nan su ka samu tashin hankalin da ya fi na ciki, dan kuwa taron dangi Aji da yaran shi suka wa su Kalli da Abdul suka k'wace Amjad a hannun su, hakan ya sa su ka ji mu su ciwo sosai tuni an nufi babbar asibiti da su. Nan su ka rufa m没 su baya su ma dan su ga halin da su ke ciki, haka ma Tagur a motarshi Aisho ta tuk'a su ka tafi. Da zuwansu ma aka karb'i Tagur aka shiga da shi urgence, inda su yaya Kalli kuma tuni su na bloc, sun fi awa d'aya su na jiran tsammani kafin aka sanar da su jikinsu da sauk'i, sai dai akwai karaya sosai a jikinsu da kuma ciwukan da aka m没 su d'inki a kai. Duk sai da suka sauke numfashi kafin Faduma ta furta "Alhamdulillah, Allah na gode ma ka." Herde ce ta dafa ta a kafad'a tace "Mu je gida ki samu ki huta, kinga ko karin kumallo ba ki yi ba fa." D'an murmushin yak'e ta yi kawai ta na rik'e da hannun dada da na Amjad suka juya, ta d'akin da aka shigar da Tagur su ka bi sai Amjad ya kalleta yace "Ayya." Kallonshi ta yi ba ta ce komai ba, a marairaice yace "Ayya zan iya ganin jikin Aba?" K'uri ta masa da ido ta na kallo, sai kawai ta saki murmushi ta juya ta kalli Aisho da ke tsaye, k'arasawa ta yi kusanta suna kallon juna tace "Ba a fito da shi ba har yanzu?" Cike da jimami tace "Eh, suna ciki har yanzu." Ajiyar zuciya ta sauke ta juya ta kalli Amjad tace "Ka ga har yanzu likitocin ba su fito ba, mu je ko? Anjima idan mu ka dawo duba jikin su yaya Kalli sai ka gan shi." Kamar zai yi kuka ya jinjina mata kai alamar to ha wuce gaba, duk rufa ma sa baya su ka yi har su ka shiga mota su ka d'auki hanyar komawa gida babu mai magana." Da tafiyarsu ba jimawa likitocin su ka fito, allurar bacci su ka mi shi amma wani ikon Allah ya k'i baccin, idon shi tar a kan su ya na kallonsu ya na fad'in "Ku kira min Ayya, ku nemo min yarona Amjad, ku ce Faduma ta zo ina son ganinta, Aji kuma mai rabani da shi b芒 a hallice shi a duniyar nan ba." Ganin dai zai wahalar da su kawai su ka fito su ka kalli Hatimi da ta yamutse kamar ba ita ba suka ce "Ki je ya na son ganinki." Da sauri ta mik'e za ta shiga sai kuma infirmi猫re d'in tace "Wanene Amjad? Da kuma Faduma?" Da sauri ta kalli likitar kamar ba ta gane hallintarta b芒, sai kuma ta fashe da kuka tace "Amjad jikana ne, d'an shi ne da aka raba shi da shi ta k'arfi da yaji, Fadumar kuma uwar d'an ce amma yanzu ta yi aure, wannan masifa da me ta yi kama?" Tab'e baki likitar ta yi kawai suka wuce su ka barta ta shige tare da Aisho, tunda ta shiga idonshi ke kan ta ya na kallon ta tsam, sai da ta tsaya gaban gadon tace "Tagur ya jikin na ka?" Ba tare da ya rusuna kallonshi gareta ba yace "Ayya me ya sa ki ka cutar da ni? Me nai mi ki?" Sake fashewa ta yi da kuka ta girgiza kan ta tace "Tagur ba na yi bane dan na cutar da kai, a lokacin shad'an na kad'a min k'ararrawa ne, sai na ji ba na son had'a zuri'a da Faduma dan ba 'yar kowa ba ce ita, amma ka yi hak'uri ka yafe min ka ji." Girgiza kai ya yi ya na hawaye yace "Ayya kin gama kasheni da raina, raba ni da Faduma da ki ka yi kin gama rabani da duk wani farin ciki na, na so ta kamar zai cinyeta, na so ta zama uwar 'ya'yana mai tarbiyarsu, amma kin min bak'in cikin mallakar kamilar mace mai addini, kunya da ladabi, yanzu gashi duk ta dalilinki ne mu ka samu Amjad ba a inuwar aure ba, a dalilinki ne har yau na zo da maganar nan kotu mu ka sha ruwan kunya." Kuka su ke yi sosai na nadama da bak'in ciki, d'an kallon Aisho ya yi yace "Aisho ki gafarta min, ki yi hak'uri da abinda zai faru, amma ki sani shakka babu idona idon uban 'yarki sai na kasheshi, wallahi sai na yi ajalin Aji." Cikin k'unar zuci da takaici tace "Yaya Tagur idan har ban kama ma ka kisan shi ba ai ban zama 'yar halak ba." K'wafa ya yi mai sautin gaske tare da jinjina kai, ya jima a haka sai kuma ya fashe da kuka ya na fad'in "Ina ma babu auren kowa a kan ta yanzu, wallahi da na tsaya a gabanta ta mareni da takalminta ko hakan zai sa ta yafe min ta aureni, Ayya ina son Faduma so na gaskiya, wallahi ina son rayuwa da ita." Babu wanda ya tanka ma sa dan su na so a bar maganar kar yai ta harzuk'a a kwancen nan, suna haka cirko cirko da su har Husna ta shigo a gigice saboda wayar da su ka yi da Aisho ta fad'a ma ta su na asibiti, ta na shirin k'arasawa gare shi ya nunota da yatsa yace "Idan ban cire kan ki ba Allah ya tsine min, me ya kawo ki nan?" Tsayawa ta yi ta na kallonshi da mamakin y'a na kwancen ma, da k'arfi ya daka mata tsawa da cewa "B'ace min da gani malama." Kusa da k'afafun shi ta tsaya amma ba ta fita ba sai hawaye da ta fara ta na kallon Hatimi da ke ta kuka, bai sake kulata ba haka su ka ci gaba da zama. *Maradi* Suna gama waya da Saudat da ta fad'a mata komai ta aje wayar gefe, gyara zamanta ta yi a kan kujerar ta kalli Alhaji Saddi da ke gefenta, sannan ta kalli Gomboy da kuma Hindu tace "Ka gani ko Alhaji, wallahi yaron nan ya raina ma ka hankali, wato sai da ya gama karuwancin sa da Faduma, dan bai same ta ba shi ne zai auri Zulfa, gaskiya ya raina ma ka hankali." Gyara zama ya yi shi ma cikin saurin magana yace "Yanzu dama yaron nan ba yaron kirki ba ne, ni zai ha'inta?" Da sauri Zaliha tace "Bari ma ka ji, ka ga takardun da ku ke nema na kadarar Hasheer, wallahi ta na wurin shi yanzu haka." Da sauri ya kalleta sosai yace "Da gaske?" Cike da tabbaci tace "Sosai ma." Hindu ce ta gyara zama cike da kwarkwasa tace "Kun san me na yi tunani a kai?" Duk girgiza ma ta kai su ka yi hakan ya sa tace "A tunani na fa kamar auren nan shiri ne, sanin kan ku ne cikin sauk'i Faduma da Aminu ba za su rabu ba tunda sun saba harka tare, idan mu ka yi duba da takardun da ke hannunshi na Hasheer zai iya zama akwai abin da su ke buk'ata su ma, sa hannunshi ko kuma wata takardar, ganin ba za su samu ta sauk'i ba shi ya sa Faduma ta shiga jikinshi har ta bi shi babban birni ta samu zuciyarshi da karuwanci, ka ga yanzu tunda sun yi aure za su samu abin da su ke so, 'yarka kuma wallahi za ta yi rayuwar bak'in ciki da k'unci ne, dan ina tabbatar ma ka wata rana sai ya kwanta da Faduma a cikin tsakiyar d'akin baccinta kuma babu abin da za ta iya yi." Wasu wawayen ajiyar zuciya su ka sauke sai Gomboy da tace "Tabbas ma hakane, tunda ai farko da yarinyar aka so had'a shi amma ya k'i, sai da ta kwab'e mi shi sannan ya amince." Zaliha ce tace "Ke ba ma wannan ba, ai abun a duba ne ta yanda Faduma su ka had'e da Hasheer a can garin, ya fi k'arfin ace had'uwa ce ta *gamdakatar*." Jinjina kai kawai ya shiga yi kafin ya kalli Hindu yace "Yanzu uwar d'akin me ki ke ganin ya kamata ayi?" Saida ta fara mi shi fari da ido kafin tace "Abu mai sauk'i, muzguna ma ka suka so su yi ai, kai ma kawai ka rama tunda ka gane nufinsu." Da mamaki yace "Kamar ya kenan?" Kallon Zaliha ta yi tare da d'ora k'afa d'aya kan d'aya ta mata alama da ido, ita ma da idon ta amsa mata kafin ta kalleshi tace "Alhaji na, abu ne mai sauk'i, kawai ka tseratar da 'yarka daga makurcinsu ta hanyar dakatar da auren." Jinjina kai ya yi alamar gamsuwa yace "Hakane kuma fa, dan abin d'脿 zan iya yi kenan." Kamar yanda su ka tsaro abun su tun kafin su zo gidan gonarsa, haka su ka tafiyar da tsarinsu a tsanake, Gomboy ce tace "Ai da ni ne kai Alhaji, wallahi sai ranar d'aurin auren, ana daf da d'aurawa ma zan ruguza taron, kuma babu abin da zai faru." Wata dariya ya nuna ta da hannu yace "Wannan ma shawara ce mutuniyar, dama kinga nan da sati ne d'aurin auren ranar talata, sai a yi ta ta k'are kawai." D'an tsaki Hindu ta yi tace "Saboda ma sun raina ka har da neman alfarmar a d'aura auren nan kusa, hummm!" Dariya ya sake yi yace "Ki barsu kawai, ai yanzu gashi manyan hajiyoyina kun saitani a hanya ta yanda zan darza nawa kalar rashin mutumcin." Duk dariya su ka saka sai Zaliha da ta matsa daf da shi ta shafo kumatunshi tace "Wa ne mu Alhaji, ai kai ne a gaba mu na bin ka a baya." Da haka su ka yi ta tattaunawa su na raina masa hankali, wani abun sai su yi kamar basu sani ba ko kuma yanzu ne ya zo mu su a kai, da haka har suka rabu kowa fa da k'udurinshi a cikin zuciyarshi akan d'an uwanshi. Tuni Barka ya datse kiran nan ya saka wayar aljihu shi ma ya shiga tashin hankali da firgici, ya san ba lafiya ba ku ya na tsoron wani abu ya faru a wurin marar kyau, kiran duniya ya ma Barka amma wayar na silent saboda za a zauna zaman nan bai kuma cire ba, haka ya kira wayar Faduma ta yi ta kururuwa ita ma a banza dan a gida ta barta kuma ta na vibrations ne, sai da ya kira Wardugu hankali a tashe ya ke fad'in "Wardugu ba lafiya, yanzun nan zan d'auki hanyar Zinder, matata...wardugu kar wani abu ya samu Batula." Wardugu da ke a tsume tsabar b'acin rai ne ya d'an sassauta yace "Kar ka damu kan ka ta na lafiya, yayanta Kalli ne da wani Abdul kawai suka samu rauni, amma Faduma ta na cikin kariyar ubangiji da kulawata, kuma na ma ka alk'awarin matarka za ta tare a gidanka lafiya lau." Tsayawa ya yi daga safa da marwan da ya ke yi a tsakiyar ofishin ya sauke ajiyar zuciya, numfasawa ya yi yace "Nagode sosai War, amma me ya faru a wurin?" A dunk'ule yace "Idan mu ka zauna zan fad'a ma ka komai da ya faru." D'innn! Ya yanke kiran, d'auke wayar ya yi a kunne ya kalleta, sai kuma ya yi murmushi yace "Wardugu ikon Allah." *Zinder* Da rana suka koma asibiti dan ganin majinyatan, sosai ta zubar mu su da hawaye na tausayin halin da su ka shiga dalilinta, amma sam nuna ma ta su ke ba komai bane hakan, hakk'insu ne ai kare lafiyarta da mutumcinta, sai da matar yaya Kalli ta fara bashi abinci a baki kad'ai ta tsagaita kukan tace "Amjad mu je na raka ko?" Mik'ewa ya yi sai Kalli da ya kalleta yace "Ina za ku je?" Sai da ta yi alamar rashin gaskiya tace "Yaya shi ne da ma ya ke so ya ga Abanshi." Da mamaki cikin fad'a yace "Ban gane ba? To sai aka yi..." Kallon da Herde ta mi shi ne ya sa ya yi shiru, jin babu wanda yace komai ta juya su ka fita sai kallo da suka bi ta da shi kawai. Kallon Herde ya yi yace "Amma Ayya me ya sa ki ka dakatar da ni?" Ba tare da ta kalleshi ba a nutse tace "Babu abin da za ku yi da ya wuce hak'uri, dan Tagur ya riga da ya mu ku *illa* tunda ya fara zama uban *d'anta*, d'an ma wanda ta ke masifar so, ka ga kuma ba ku isa ku cire mata soyayyar d'an ta ba, haka kuma ba ku isa ku gogewa yaron soyayyar uban shi ba ta yanda zai d'auke kai daga shiga sabgar uban, dan haka ayi hak'uri kawai." Su na shiga d'akin da sallama a bakinsu, idonta cikin na shi su ka fara sauka, amma da sauri ta d'auke na ta ta mayar kan Husna da ke zuba abinci a plate, amsa ma ta su ka yi da sakin fuska, Hatimi kam tuni ta tarawa Amjad hannu ya je gareta har ta rumgumeshi a cinyarta, Aisho ce ta mik'e kan kujerar ta ta na fad'in "Faduma zauna." Kallonta ta yi da mirmushi tace "A'a ki barshi ma, ai yanzu za m没 wuce." Sunkuyar da kan ta ta yi dan sosai take jin idonshi na yawo a jikinta, hakan kuma ya sa ta ji ta tsargu da kallon, ta na kallon k'asa ta ga ya mik'o hannu ya kama Amjad, ya na zuwa ga Abanshi ya haye jikinshi ba tare da tunanin kwance ya ke ba, rumgume juna su ka yi kamar za a raba su, hakan ya sa Tagur ya shiga sauke numfashi a hankali idonshi a rufe ya na shak'ar k'amshin turaren yaron, wanda ba zai yi kaffara ba idan yace *Blaze* ne, ba tare da y'a d'ago daga jikinshi ba su ka shiga magana k'asa k'asa, babu mai jin me suke fad'a ita dai har ta fara k'osawa da tsayuwar, ganin ba su da niyyar rabuwa ya sa ta d'ago kai ta kallesu. Da sauri ta d'auke idonta daga kan su dan a take ta ji shed'an ya shiga zuciyarta ya na k'awata ma ta su a ido da matsanancin son ina ma ma'aurata ne, da d'ansu ya more rayuwa kam. D'auke idon da ta yi kuma sai ta sauke akan Husna da ta mayar da ita kamar tv, lallai tasan ita kyakyawa ce, amma kuma duk da bak'in Faduma ta fita kyau nesa ba kusa ba, domin kuwa tana da abun da ya tasirantu wajen fito da sahihin kyawun fuskar ta ta, k'aramin bakinta mai d'auke da labb'a matsakaita masu kalar chocolat, dogon hancinta da ya fito da kurmin ido ta ya kuma saitu har zuwa bakin na ta, ga kuma manyan ido masu matuk'ar haske kamar madara, bak'in kuma idan ta kalleka da shi sai ka ga kamar ruwa ruwa a ciki ko kuma za ka fad'a. A hankali Faduma ta furta ma ta "Sannu." Ita ma a harshen tubancin ta amsa da "Sannu, ki na lafiya?" Amma shan k'amshi na Faduma sai kawai ta d'an ma ta murmushi ta amsa mata da kai alamar lafiya lau, k'ara k'ura ma ta ido ta yi sai kuma ta tuna da Ayya ke fad'a ma ta ta dinga jan aji dan Tagur na son haka, sannan ta dinga kama kan ta ban da yawan surutu, sannan ta zama mai tsoro da saurin kuka ko ba abun kuka ba ne. Ita dai ta na wannan tunanin ta ji Faduma tace "Amjad mu tafi, ana jiranmu a waje." D'agowa ya yi daga jikin Tagur su ka kalleta, kallon fuskar Tagur ya sake yi yace "Aba ina so na kwana tare da kai anan? Kaga zan taimaka ma ka da abin da ka kasa yi." Duk kallonshi su ka yi, sai kawai Tagur ya ji zai yi kuka ya yi saurin sunkuyar da kan shi, cikin muryar kuka yace "Ka tafi Amjad, zan zo na gan ka idan mahaifiyarka ta amince." Juyowa Amjad ya yi ya kalleta, ita ma shi take kallo sai kuma ya juya ga Tagur, tallabo fuskarshi ya yi da k'ananan hannayenshi ya na shirin fashewa da kuka yace "Aba in ga fuskarka, kuka ka ke? Me ya sa ka ke kuka to? Ka daina ka ji ni zan ce Ayya ta kawo ni wurinka, ka daina kuka dan Allah." Wani kukan ne ya sake kubce mi shi kawai ya ruk'umuk'ume Amjad a jikinshi ya na kuka sosai, d'akin shiru ya d'auka babu mai numfashin arziki ma bare motsi, cikin tashin hankali da damuwa ya na kuka shi ma ya shiga kiciniyar d'ago kan shi ya na fad'in "Aba ka daina kuka dan Allah, ni ne na b'ata ma ka rai? To ka yi hak'uri kar ka ce ba na jin maganar, ka ga ma na tafi to daina kukan." Ya fad'a ya na saukowa daga kan gadon, hannunshi Tagur ya rik'e hakan ya sa yace "Aba ka hak'ura? Ka yafe min?" Jawo shi ya yi jikinshi ya shiga sumbatar fuskarshi, da k'yar ya tsagaita kukan ya kalli fuskar Amjad su na kallon juna yace "Amjad ka kula da kanka ka ji, kar ka manta da ni mahaifinka, ina son ka ina k'aunarka, na sani na zalinceka kuma na d'auki alhakinku, amma...ni ma k'addarata ce ta zo a haka, sam ban tab'a tunanin cin zarafin mahaifiyarka ba, amma mak'iya na su suka jawo komai, ka yi hak'uri ka ji ka yafe min dan Allah? Ka rok'a min mahaifiyarka ma ta yafe min duk laifukan da na ma ta." Sororo ya kalleshi yace "Aba me ya sa ka ke magana haka? Wani guri za ka tafi ne?" Girgiza mi shi kai ya yi yace "A'a Amjad, amma dai na san ba da jimawa ba zan mu ku nisa, zan mayar da kai maraya na asali, dan ba zan juri rasa Ayyarka da kuma kai ba a lokacin guda." Da sauri Faduma ta mik'o hannu ta fizgi Amjad ta na fad'in "Amjad mu je." Hannunshi na cikin na Tagur hakan ya sa saida ta fizgeshi da k'arfi kad'ai ta raba hannayensu, fashewa ya yi da kuka da tunanin ko dai mahaifinshi zai mutu ne? Ko kuma wani wurin zai tafi ya bar shi ko kuma su za su tafi bai sani ba. A k'ofar d'akin su ka tsaya ta saki hannunshi ta na kallonshi, sunkuyawa ta yi tace "Amjad mi ye na kuka?" Cikin share hawaye yace "Ba Aba ne ba bai da lafiya, ina jin tsoron kar ya mutu ya barni." Ajiyar zuciya ta sauke ta na kallon fuskar yaron, ya za ta yi? Ta tambayi kan ta, girgiza kai ta yi ta mik'e tsaye ta na ci gaba da kallon shi, dafa kan shi ta yi tace "Albarkata za ta kasance a tare da kai insha'Allah, ka sani ina k'aunarka fiye da yanda kowa ke k'aunarka Amjad, ba wai iya son ka kawai na ke ba, ina mugun son ka ne da gaba d'aya zuciyata." Kamo hannunshi ta yi su ka dawo d'akin ta bud'e k'ofar, sakin hannunshi ta yi da gudu ya k'arasa ya sake mak'alewa jikin Tagur da Husna ta tsaya kan shi ya ci abinci ya dage ba zai ci ba, sake rumgume juna su ka yi da farin ciki. *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 21:42 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _69_ Tsaye ta yi ta na kallon su tace "Wacece ni da zan raba *d'a* da *uban sa*? Rashin imani na bai kai can ba, duk da ka cancanci hakan amma ba zan yi ba, zan yi wannan sadaukarwar da fatan Allah ya yafe mana laifin da mu ka aikata, Tagur ka rik'e yaronka hakan shi ne kwanciyar hankalin mutane dayawa, rok'ona d'aya gare ka shi ne kar ka yi wasa wajen tarbiyarsa, dan Allah ka d'ora a inda na tsaya akan Amjad, idan har ka yi alk'awarin yi min haka, to ni kuma ka sani *na yafe ma ka duniya da lahira*." Kallon Aisho ta yi da murmushi tace "Na yarda da ke Aisho, ki daure ki taya d'an uwanki kula da yaronsa, insha'Allah ke ma za ki samu miji na gari kiyi aurenki." Husna ta kalla tace "Na samu labarin irin soyayyar da ki ke ma sa, ki yarda za ki zauna da shi da zuciya d'aya dan ki raya sunnar ma'aiki, hak'ik'a 'ya'ya su ne jin dad'in wannan rayuwa, amma idan ki ka saka Allah a lamuranki, zai iya dubanki ya saka mi ki, dan *wani hanin ga Allah baiwa ne*." Kallon Tagur ta sake yi tace "Soyayyarta ta gaskiya ce a gare ka, ba na jin za ka samu wacce za ta so ka a yanzu fiye da ita, ka bata dama ta shiga rayuwarka, watak'ila akwai haske da canjin da za ta kawo ma ka." Kallon Amjad ta yi ta tara ma sa hannu ya taho, shafa kumatunshi ta yi tace "Wannan oddo na ne." Shi ma da dariya ya shafi kumatunta yace "Wannan Ayyata ce." Idonta cike da hawaye tace "Zan bar ka wajen Abanka Amjad, fatana d'aya shi ne kar ka manta duk abin da ka koya daga gareni, sannan ka yi biyayya wa mahaifinka da duk wanda sabuwar rayuwarka za ta had'aka da su, ka ji?" Kafin yace wani abu tace "Sannan ka rage zafin zuciyar nan, ba na so ka ji ko?" A tare su ka kalli juna, shi sai ya ji kamar da shi ta ke, ita kuma a zahirin har shi d'in ma ta na so ya rage tunda zai zauna da d'anta yanzu, wani k'asaitaccen murmushi ya saki tare da lumshe ido alamar "Zan yi yanda ki ke so." Sakin hannun Amjad ta yi ba ta jira komai ba ta durk'ushe ta rumgume shi, sumbatar kumatunshi ta shiga yi da goshinshi kamar za ta cinye mi shi fuska. Kukan da ya k'wace ma ta ne ya sa ta mik'ewa da gudu ta bar d'akin, rufo k'ofar ta yi da k'arfi ta jingina a bayanta ta na kuka. Da sauri ya yi hanyar zai bita Aisho ta rumgumoshi jikinta ta na daddab'a shi, kuka yafara ya na fad'in Ayyar shi Ayyar shi, girgiza kai Tagur ya yi ya jingina a bango ya na fad'in "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un." Wani irin kuka Hatimi ta fashe da shi mai tsuma zuciya ta shiga fad'in "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, wannan musiba da me ta yi kama? Allah ka kawo mana mafita a cikin lamarin nan, ga soyayya tsaftattaciya, amma wani abu da ya gifta ya hana uwa zama tare da d'an ta, wannan shi ake kira da *'kaddara ta riga fata*, dan ban zurfafa ma ta k'iyayya ba da watak'ila yanzu yaron nan a d'akinku na sunna ku ke rainonshi." Ajiyar zuciya Tagur ya sauke yace "Ba zan sake jayayya da Faduma ba, dan duk in na yi fad'uwa na ke, a k'arshe kuma har da tsarabar barazanar bugawar zuciya, a kullum shari'a da ita *allura* ce ke *tono galma*." Tun hanyarsu ta komawa Herde ke tambayarta lafiya? Ayyarta kuma ko kallon inda ta ke ma ba ta yi ba har suka isa gida, dama dai yanzu gidan Herde ta ke saboda gyaran jikin da su ke yi, dan haka su na shiga ta wuce d'aki ta ci gaba da kukanta, yau kam dada kad'ai ta samu gyaran jikin, amma Faduma har dare ya risketa ta na kuka, saida Aba ya shigo tare da yaya Manu su ka sakata gaba su na lallab'a ta yi shiru, a lokacin Ayya ta dawo daga asibiti tab'e baki ta yi ta kallesu tace "Wallahi ku ma dai da matsala ku ke, to tasan ba za ta jura ba ta bar mi shi yaron? Ku rabu da ita mana ta yi kukan." Aba ne ya juyo ya kalleta yace "Kinga babu ruwanki malama, in ba za ki tayamu lallab'a ta to yi shiru da bakinki." Nuna kanta ta yi tace "Ni dai? Allah ya tsareni, ku da ku ka ji za ku iya to." Herde ce tace "Ni fa Allah zan kori mutum daga gidana, haba jama'a, yarinya na kuka a ce ba za a lallab'ata ba, autar ta mu?" Juyar da kai Ayya ta yi ta na fad'in "Ba wata auta, k'ane ma zan ma ta duk ku huta wallahi." Kallonta su ka yi kamar wacce ta ci kud'in bashi, ita kam ba ta san maganar ta fito ba, Aba ne ya yi murmushi yace "Ai dai sai na je wurin mutum ko? To ina nan tare da Fadumata yau." Kunya ce ta sa ta rufe fuska da hijabi, shi kan shi Aba sai ya daka fuska saboda kallon da Manu da Faduma ke masa, Herde ce tace "Ko an yi wa Faduma k'ane mu dai ita ce autarmu." Aba ne ya kalli Faduma yace "Fadun Aba, idan kin san ba za ki jura ba to me ya sa ki ka baro ma sa yaron?" Saida ta share hawaye cikin shak'ewar murya tace "Aba saboda *aure na* ne, na bar wa Tagur Amjad har abada, ina so na mayar da hankalina kan mijina, ba na son ko sau d'aya ya ji ba dad'i a game da Amjad, ina ji a wurin mutane su na fad'in yanda namiji ke da kishi, wani ko d'an da ka haifa da wani ya gani sai ran shi ya b'ace, shi ya sa na ke son toshe duk wata k'ofar da za ta iya shigo da zargi ko rud'ani tsakani na da shi, bare kuma har ta gayyato min b'acin ran shi." Saida ta sako wasu hawayen ta rik'o hannun Aba tace "Aba na, kai ma namiji, ka kamalta min yanda za ka ji idan kai ne Hasheer?" K'ura mata ido ya yi ya na kallo da mamaki, fahimtar kallon da ya ke ma ta ya sa tace "Eh Aba, ina so ne na k'ara fahimtar girman abun, hakan zai sa na d'auki dangana na hak'ura mu zauna nesa da juna da Amjad." Ajiyar zuciya ya sauke ya na murmushi ya kalleta yace "A lokacin da na ke ganiyar k'uruciyata, duk abin da iyayenku ke buk'ata wanda sai an siyo shi to ni na ke siyo m没 su, ba dan komai ba saboda na tsani na ga matata ta mik'a abu wa namiji shi kuma ya karb'a, ko da hannunsu bai tab'a na juna ba ina jin haushi sosai, Fadun Aba zan iya raba duk girman kadarar da na mallaka a duniya tare da wani ban damu ba, amma akan *iyalina*, sai in da k'arfi na ya k'are." Murmushi ta shiga dokawa saboda jin dad'in d'an labarin nan, kallon yaya Manu ta yi da yace "Ni fa gaskiya na ji dad'i da ki ka bar mi shi yaron nan, dan har yanzu akwai abin da zai dinga had'aku da shi, wanda ni a gani na idan ni ne mijinki ba zan jura ba, amma kinga haka hankali kwance, idan ki ka buk'aci ganinshi zai kai mi shi k'ofar gida ne ya yi tafiyarsa, idan ya tashi tafiya kuma ya d'aukesa ba tare da bakinku ya had'u ba." Jinjina kai Herde ta yi tace "Gaskiya kam, hakan da ki ka yi ma ya yi kyau, tunda ba ki san mijinki wane iri ba ne a game da kishi." Da haka su ka ci gaba da hirarsu har ta fara sakewa kamar ba uta ce mai kukan nan ba. Har su Aba su ka koma na su gidan haka ma yaya Manu, shirin kwanciya su ka yi ita da Herde su ka kwanta abun su. *Maradi* A wurin ajiye motocin ya tsaya ya sake kiran lambarta da fatan ta d'aga, cikin sa'a kuwa ta d'aga ta na doka sallama a sirance da fad'in "Aminci da rahama da albarkar ubangiji su tabbata ga babban mutum, *mijin Faduma sarkin hak'uri*." Tafin hannu ya sa ya rufe bakinshi saboda ya na so ya d'an had'e ma ta fuska, amma kuma dariya ke son taho mi shi k'arfi da yaji, da k'yar ya gimtse bakinshi yace "Ina fatan mu yi tarayya a cikin wannan rok'on na ki, *matar Hasheer* sarauniyar jan aji." 'Yar dariya ta yi tace "Tuba na ke ranka shi dad'e." Cikin muryar alhini kamar zai yi kuka yace "Faduma me ya sa ba ki d'aga wayata ba? Kin san tashin hankalin da na shiga kuwa? Me ya sa Dan Allah?" Jikinta ne ta ji ya yi sanyi, sai ta ji ina ma a gabanshi ta ke, da a halin da ta ke cikin nan sai ta yi k'undunbala ta fad'a budadd'en k'irjin nan na shi, shi kuma ya ma ta babban gata ta hanyar saka hannayenshi ya rumgumeta ya shiga daddab'ata. Sai dai ba su kusa bare haka ta faru, saida ta tausasa murya sosai tace "Ka yi hak'uri babban mutum, ban fita da wayata bane, kuma su yaya Kalli wani tsautsayi ya same su suna asibiti kwance, amma yanzu komai ya daidaita, insha'Allah amaryarka na da lokacinka yanzu." "Da kenan ba ki da lokaci na?" Ya tambaya ya na kafe wuri d'aya da ido kamar ita yake kallo, a hankali tace "A'a ba haka ba, ina nufin isashe." Ajiyar zuciya ya sauke yace "Ina Amjad?" Saida ta ji gabanta ya fad'i, a nutse tace "Amjad ya na tare da ubanshi." Lumshe ido ya yi bai ce komai ba, har saida ta kalli wayar ta ga kiran na tafiya, ita ma shirun ta yi har saida yace "Can zai kwana kenan?" Had'e yawu ta yi tace "Can zai kwana a yau da gobe da jibi har kullum ma, na bar mi shi Amjad ne kawai." Da mamaki yace "Kamar ya? Amma ai ba haka hukuncin ya kasance ba? Me ya sa za ki bar mi shi yaron nan?" A d'an dak'ile tace "Saboda na yi aure, kuma bauta zan zo na yi ba rainon yaro ba." Cikin d'aga murya yace "Faduma! Me ya sa za ki yi wannan tunanin? Amjad da Izzadeen duka d'aya ne a wuri d'aya, zan..." Da sauri tace "Dan Allah mu bar maganar Amjad, idan ka na son ganinshi ai sai ya kawo ma ka shi." Numfashi ya sauke yace "A gaskiya ban ji dad'i ba, ba kuma zan kasa fad'a mi ki haka ba tunda ba tsoronki na ke ji ba." Murmushi ta yi tace "Allah huci ran Allah biya muradi." Dariya ya yi yace "Wai kakanki ki ka mayar dani ne? Ni ne ma Allah biya muradin?" Dariya ta yi tace "To na janye biya muradin, idan na ce ranka shi dad'e fa?" Da 'yar dariya ya amsa mata da "Ya dad'e tare da na ki." Da haka suka sha hira kafin su yi sallama, ya fito ya nufi cikin gidan, da sallama ya shiga amma ba ta iya amsawa ba, idonshi na kan yaranshi da bacci ya d'aukesu a k'asan carpet,ita kam ta na rik'e da waya ta na ta aikin latsawa, ba ta kalleshi ba bare ta kula da tsiyarshi, cire takalminshi ya yi ya taka carpet d'in dan ya d'auke su, amma sai y'a ji ya taka abu da ya ke da tabbacin shinkafa ce, lumshe ido ya yi ya bud'e tare da kallon k'afar ta shi, ai kam dai ita ce an ci ba a share ba, girgiza kai ya yi ya kalleta yace "Sai yaushe za ki tattare abincin nan?" Ba tare da ta kalleshi ba cike da raini tace "Sanda ka bani umarni." D'auke kan shi ya yi yace "To taimaka ki share dan Allah, kar ki lalata sabon gidanki da, wuri mana." D'agowa ta yi ta bishi da harara tace "Gidana fa ka ce? Ai a da ne ka ke fad'a min haka na yarda, amma ban da yanzu da na san waye kai, shara kuma ba zan yi ba sai ka bari har amaryarka ta zo sai ta kwashe." Wani malalacin murmushi ya yi yace "Haka ki ka fad'a?" Saida ta yamutsa baki ta kalleshi tace "Haka na ce." Jinjina kai ya yi alamar shikenan, d'auke yaran ya yi da d'ai-d'aya ya shinfid'esu d'akinsu, bai kalleta ba ya wuce d'akinshi ya yi wanka ya yi shirin bacci, ya jima a d'akin kafin ya fito falon ya sake samunta zaune yanda ya barta. Zaune ya yi kan kujera ya na sauke numfashi yace "Taimaka min da abinci hajia? Yunwa na ke ji." Sauko k'afarta ta yi da ke kan kujera cike da masifa tace "To fa! Wato ita karuwar ta ka iskanci da soyayya kawai ta iya? To ban dafa abinci da kai ba, sai ka ji idan ta shigo gidan ta dafa ta baka." Lumshe idon shi ya yi ya na d'an murza gaban goshinshi alamar daidaita nutsuwarshi, ya jima haka kafin ya mik'e daga kan kujerar ya kalleta yace "Idan kin gama da wayar to ina jiranki d'akina, ko kuma shi ma kin barwa amaryar?" A hassale cikin takaici tace "Eh d'in, na barta ta je ta cinye ka." Wani murmushin iskanci ya ma ta ya nufi d'akin, cikin masifa ta fara fad'in "Allah na tuba to wane dare ne jemage bai gani ba? Shekararmu tara ba abin da ban gani ba ban kuma san shi ba, ita yanzu ai ragowa ce za ta tarar." Juyowa ya yi a nutse yace "Hakane, amma kin fi kowa sanin madarar da na b'arar jiya ba ita na ke b'arar wa gobe ba, sannan kin san mijinki kullum da salon da ya ke zuwa da shi, a haka ita ma za ta mori ta ta k'uruciyar har ta haifar da sakamako mai kyau." Juyawa ya yi ya shige hakan ya sa Saudat fashewa da ihu ta mik'e tsaye ta na cilli da k'ananan pillown da ke kan kujerar. Haka lamarin gidan ya ke ci gaba da tafiya babu dad'i ko kad'an, babu alamar canzawa daga wajen Saudat, ta zauna ta yi karatun tanutsu ya gagara, hasalima nunawa ta ke ita ce aka ma laifi, dan haka kawai za ta yi yanda ta ga dama. A kullum kamar jira ta ke ya ma ta magana kan abin da ya shafi kula da gida ko yara ko kuma shi sai tace ya jira amaryarsa ta zo, shi kuma a kullum ta fad'i haka babban buri ya ke ci na koya ma ta hankali idan amaryar ta shi ta zo. Ta b'angarenshi da Faduma kuma sai son barka, hello! Kawai za ta fad'a ma sa a waya sai ya saki murmushi, dan shi kan shi hello d'in sai da ta ma sa kwalliya ta musamman ta zaneshi da tajwidi da mai kyau jafin ta ke furta ta, dan sosai take d'aukar darasin da ayyoyinta uku ke koya mata, dan Ayyar g茅n茅ral ba ba'a barta a baya ba, ta manhajar yane (WhatsApp) kawai take koyar da ita laduba da farillai da kuma sunnoni na magana da miji. Babban abin da ta fi fad'a ma ta shi ne ta zama mai matuk'ar lura da yanayin mijinta, hakan zai bata damar fahimtar yaren da za ta mi shi magana da shi, idan ki ka fahimci 'yan tsumewa ne a kan shi, to bi shi a sauk'ak'e, dan kad'an ya ke jira ya ce kinyi ba dai-dai ba. Idan kuma ki ka ga da shan k'amshi ya tashi ma'ana 'yan mulki ne a kan shi, sai ki wasa kalamanki wajen gwarzantashi da kurentashi, ta yanda ko kallon idonshi ma kar ki yi tsabar girmamawa. Idan kuma 'yan fushi ne a kan shi, to ki kiyaye yawan magana, dan abu kad'an ne zai harzuk'ashi ku samu matsala. Akwai ranar da za ki ga yanayin shi gaba d'aya na son kad'aicewa ne da shiru, to shi ma ki mik'o mi shi na shi salon ta hanyar tak'aita magana da k'amsasan kalamai. Idan yanayin farin ciki ya hau kan shi kuma, to za ki iya ma sa duk shirmen da ya zo kan ki, za ki ga ya had'iyi saboda yanayin da ya ke ciki, amma kafin haka sai ki fara nuna ma sa na ki farin cikin ya fi na shi, kafin ki ma sa k'uruciya. Sosai Ayyar g茅n茅ral ta fad'a ma ta abubuwa da dama, kuma duka ta fi magana a kan karantar yanayi, komai ta na ce ma ta ne "Ki karanci yanayin mijinki ki san mijinki wani irin mutum ne, idan girmamawa ya fi so daga gareki, to ki girmama shi kamar za ki ma sa bauta, ki zama baiwarsa kamar zai takaki ya wuce, ta hakane ke ma zai bud'e mi ki k'ofar zuciyarshi, k'ofofin jin dad'inki, k'ofar arzikinshi da kuma k'ofar *aljannarki*." "Idan kuma ki ka gane shi d'in mai son barkwanci ne da nishad'i, sai ki zama kamar joker a gabansa, ki zamar ma sa kamar allon kallonshi na tashar boomerang. Idan kuma mijinki d'an soyayya ne, to ki zage ko da ta hanyar karantawa ne a labarai, wajen ganin kin zama zak'wak'ura a fannin iya soyayya." "Ka da ki bar komai, ki koyi komai, iya girki, iya kwalliya, iya magana, tsaftar jiki da ta muhalli, iya fari da ido da kuma karairaiya jiki, iya saka kaya da za su d'auki hankalin mijinki, iya shinfid'a a gado...da na ce iya shinfid'a ba wai iya d'ora zanin ba, ina nufin iya tuk'a mijinki ta hanyar da duk ki ka tabbatar ba ta sab'awa shari'a ba." "Sannan abu mai mahimmanci, a matsayinki na wacce ki ke da abokiyar zama, ki yi iya k'ok'arinki wajen ganin kin b'oye duk wani sab'ani da zai shiga tsakaninku, ko dukan tsiya ya nad'a mi ki a d'aki, idan ku ka fito ki ma sa murmushi tare da addu'ar Allah ya tsare mi ki shi, a hakan fa kin *jefi tsuntsu biyu da dutse d'aya*, shi za ki bar sa da zulumi da tunanin girman lamarinki, kishiyarki kuma za ta zauna zaman jiran ranar da za ta ga sab'ani a tsakaninku, sannan za ki hana ma ta kwanan farin ciki, dan ganin b'arakarku zai sa ta yi murna." "A k'arshe kuma zan fad'a mi ki da ku yi hak'uri da junanku, shi da za ki zauna domin shi sai kinyi hak'uri da shi, domin akwai lokacin da za ki ga duk soyayya da farin cikin da ake ciki, zai iya rufe ido ya yi kamar bai san ki ba ya tabka mi ki halayyarsu. Sannan kishiyarki ma ki yi hak'uri da ita, ki ba ta girmanta a matsayinta na wacce ta ke gaba da ke a shiga gidan, da haka na ke mi ki fatan alkairi, zuwa gobe da safe kuma zan fara da koya mi ki salon yanda za ki dinga kallonsa da kuma yanda za ki ma sa magana." Da irin haka Ayyar g茅n茅ral ta ke d'orata akan mizani mai kyau ta na ma ta tankad'e da rairaya ta na saita ma ta kalamanta da kallonta. Ta b'angarensu da dada ma sha'aninsu su ke kurb'a idan su ka shige d'akin Herde, haka ita ma Herde gyara irin na al'ada ta ke ma Faduma wacce duk duhun fatarta sai da ta yi sharrr da ita, wani irin yelow-yelow ne da y'a gauraya da fatarta ya bayar da wani kalar sirikin haske mai kyau da d'aukar hankali da birgewa, fatarta na nan mai duhu amma ta kwanta ta yi lumi-lumi, ga kuma k'amshi na fitar hayyaci da ya damb'are a jikinta kamar da shi aka haifeta, ita kan ta haka za ta dinga shinshinar tafukan hannayenta saboda k'amshin na mata dad'in shak'a a hanci har lumshe ido ta ke. Hankalinta kuma a kwance ya ke dan tun washe garin ranar nan da Tagur da su Hatimi su ka zo sunyi magana ta fahimta sosai, duk da dai ba wani sakin jiki aka yi ba sosai, dan idan su sun manta da wuri haka, su kam abu ne mai wuya su manta yanzu, dan haka kana ganinsu za ka gane yak'e kawai ake wa juna. Ya b芒 su hak'uri tare da nuna mu su nadamarshi, sannan ya ma ta alk'awarin kulawa da Amjad fiye da yanda ta yi. Gaskiyar da ta hango a idonshi ya sa ta jin dad'i har zuciyarta ta kuma saki ranta suka sake sallama da Amjad dan za su wuce maradi ne a lokacin. Aminu ma ana daf da angwancewa, domin kuwa *awa goma sha d'aya* ta mi shi tsakani da amsa kiran magidanci, yanzu haka su na hanyar komawa gida ne sun dawo daga wurin kamun amarya, su hud'u ne a motar, amininshi da shi, sai kuma Salima babbar k'awar amarya da kuma amarya, babu mai hira sai waya da mazan ke yawan amsawa akai akai, da haka har su ka sauke su gida dan Salima ma anan ta ke kwana tunda aka saka amarya lalle. Su na shiga kowa wanka ya fara yi dan a yi shirin bacci, da hanzari Abeeda ta d'auki abinda za ta iya d'auka ta m没 su sallama dan Omar na k'ofar gida ya na jiranta za su wuce gida, cikin farin ciki da hirar bikin nan su ka k'arasa gida su ka shirya bacci su ma, tsautsayi ko kuma mu ce tashin hankali, Zulfa ce ta kirata a daren nan, ganin haka sai ta d'aga ta na fad'in "Amarya ya akayi?" Cikin sangarta Zulfa tace "Dan Allah ni ki hau en ligne (online) ki turo min hotunan da ki ka d'auka a wayarki, dan na ga sun fi kyau." Dariya ta yi tace "Saboda hakane dama ki ka kirani? To na ji zan tura mi ki." Datse kiran su ka yi ta hau dan tura ma ta, ganin lambar Zaliha ma ta turo ma ta da sak'on hotuna ya sa ta saurin shiga da tunanin ko wasu hotunan ne na biki tunda yanzu haka duk tare su ka rabu, dan har mamaki take yanda suke mata kara su ke halatartar duk taron da akayi. Ta na bud'e hotunan ba ta san waye ya riga k'asa ba, ita ce? Ko kuma wayar...? Jirin da ya d'ebeta ya sa ta fad'i k'asa hannayenta biyu dafe da kai, a zaunen ma da ta ke sai ta ga ana ta juyawa da ita neman kifewa ta ke, ta zura hannu za ta lalabo gado dan ta rik'eshi da kyau ya zama togaciya da kaiwarta k'asa kwance, sai kuma ta ji k'arar ruwa a ban d'akin, da sauri ta zabura ta kalli k'ofar kamar yanzu ne ta san da zamanta, hakan ya bata damar dawowa hayyacinta, da wani irin k'arfi ta mik'e ta shiga kai da kawowa a tsakiyar d'akin, sai kuma ta zari mayafinta ta bud'a wajen kayanta ta d'auko k'aramar akwati ta dinga saka kayanta a ciki, saida ta cikata pam ta rufe ta sauke k'asa, zagayowa ta yi ta d'auki wayarta sai kuma ya fito, cak su ka tsaya kallon kallo, k'are ma sa kallo ta yi d'aure da towel a k'ugu, wani mahaukacin tsaki ta ja ta nuna shi da yatsa tace "Allah ya isa tsakani na da kai, fasik'i kawai." Wayar ta d'auka ta koma kan akwatin ta jata k'iiii za ta fita, da hanzari ya tako ya na fad'in "Abeeda lafiya? Me ya ke faruwa ne?" A hassale ta juyo tace "Kar ka sake kiran sunana." K'wafa ta yi ta bud'e k'ofar d'akin ta zare makullan, falo ya bita ya na fad'in "Abeeda wai me ya faru ne? Ina za ki je kuma yanzu a daren nan?" Ba ta tanka ma sa ba har ta kai k'ofar fita, tare gabanta ya yi ya had'e fuska yace "Tambayarki na ke ina za ki je?" Hararanshi ta yi tace "Gidan uba na zan tafi, ai kasan ba nan aka haifeni ba, ko kuma nan gidan ubana ne da ba zan barshi ba?" "To me aka mi ki?" Ya fad'a ya na jaddadawa da hannayenshi, tsaki ta yi tace "Kai ka fi kowa sanin abin da ka ke aikatawa a b'oye, mamaki na d'aya yanda ka kasa neman ko wace irin mace a duniyar nan sai k'awata." Hannu ta sa ta tureshi a gabanta ta sa makullin da niyyar fita, rik'e makullin ya yi yace "Babu inda za ki je kin ji na fad'a mi ki, ki koma ciki muyi magana." Da k'arfi tace "Magana? Da kai d'in? Lallai ma!" Hannu ta kai za ta karb'i makullin ya daka mata tsawa da cewa "Na ce ki wuce ciki ko." Da muryar da ta fi ta shi k'arfi tace "Ba zan wuce d'in ba Omar, wallahi ka matsa ka bani hanya ko kuma yanzun nan na ma ka ihun kwarto." Nuna k'irjinshi ya yi da babu riga yace "Kwarto? Ni d'in? To ki yi dan Allah." Ai kuwa baya ta ja yanda muryarta za ta fita da kyau, iya k'arfinta ta sa tace "Wayyo Allah, jama'a kwarrrrrr..." Bai bari ta k'arasa ba ya yi wani tsalle ya rufe ma ta baki da hannu, cikin tashin hankali ya kalli fuskarta duk ya k'walalo ido yace "Abeeda ba ki da hankali ne? Me ya ke damunki ne wai? Ki saurareni mu shiga ciki mu yi magana, dan Allah?" Girgiza mi shi kai ta yi dan ta kasa motsawa daga rik'on da ya mata, hawayen da su ka fara sauko ma ta ne ya kalla, cak ya d'auketa har da akwatin da ke hannunta, hakan ya jawo ta shiga kiciniyar k'wacewa ta na ta bille-bille ta na so ya sakar ma ta baki, a falon ya direta tare da rufe k'ofar da makulli ya sokashi a tsakiyar towel d'in k'ugunshi, kallonta ya yi yace "Ki zo ki d'auka in ke jaruma ce." A ladabce ta kalleshi, ta san waye Omar farin sani? So ya ke ta je d'aukar makullin a wannan wurin ya tumurmusheta a banza, watak'ila ko dan ya na likita akwai abin da ya ke anfani da shi, amma zuwanshi d'aya ma ya na kayar ma ta da gaba bil-hakk'i da gaskiya. Sai kawai ta ma kan ta karatun tanutsu ta zauna kan kujera ta d'ora k'afafunta sama ta rakub'e kamar wata marainiya. Ganin haka sai ya k'arasa kusanta ya zauna ya na kallonta cike da tausayi, to shi ya zai ce ma ta? Ya tabbata aikin Zaliha ne, dan ita ke da hotunansu tun na waccen rayuwar, ba zai yarda wannan gangancin na Zaliha ya kashe mi shi aure ba, ya na son matarsa kuma ya na son zama da ita, sai dai kuma Alhaji Saddi ya san da maganar nan zai mi shi d'anyan kai, zai mi shi hauka sosai har ma ya nemi raba aurensu ko da kuwa da shari'a ne, bai san me ya sa ya ke zafafawa ba sosai? Ko kuma dan shi ma ya san harkar barikin, ya san k'abli da ba'adi na cikinta shi ya sa, dama kuma an ce *wanzame ba ya son jarfa*. Kallonta ya yi sosai a nutse yace "Abeeda ki yarda da ni mijinki kin ji, ki saurari abin da zan fad'a mi ki, wallahi Allah wannan hotunan ba na yau bane sun jima, Abeeda kafin aure na da ke na yi rashin jin magana da wannan yarinyar Zaliha, amma wallahi daga sanda aka d'aura mana aure na tattara komai na watsar na rumgumi sabuwar rayuwata, ki taimake ni Zaliha mu bar maganar nan kar ta fita, ni dama nasan Zaliha ta shiga jikinki ne saboda wani abu, in ba ki manta ba lokacin da na gan ku tare na mi ki fad'an me ya had'a ki da ita? Ki ka ce min k'awarki ce, na nuna mi ki ba na son ki da k'awance da ita, amma sai ki ka fara damuwa da nuna ba ki ji dad'i ba, sai kawai na zuba mi ki ido." Sake sassauta murya ya yi ya kamo hannunta yace "Abeeda ki na so na?" Shiru ta ma sa ita dai ta na tsoron tankawa zuciyar ta motsa ya dalla ma ta mari, jin ba ta amsa mi shi ba sai kawai yace "In dai ki na so na Abeeda kar ki je gida, wallahi idan ki ka je Abbanki zai raba aurenmu ne, na san kuma ba za ki so a rabamu ba." Ba tare da ta kalli fuskarshi ba tace "Ni na fi son ma a rabamu, ba zan iya zama da kai ba." Da mamaki ya kalleta yace "Abeeda kin fi so mu rabu?" "Eh." Ta fad'a ta na cunno baki, mik'ewa ya yi tsaye ya ciro makullan ya bata yace "Gashi to ki tafi gidan dan Allah, amma ki sani ki ka kaini bango wallahi sai na fad'i abin da har hawan jinin mahaifiyarki sai ya tashi, kuma kafin ki yarda a rabamu ki fara tambayar mamanki wane irin zama ta ke da Abbanku." Cilla ma ta makullan ya yi ya shige d'aki ya na gunguni, jin haka kuma sai jikinta ya yi sanyi sosai ta rasa kuzari, agogon gabanta dake jikin bango ta kalla, *12:26* na dare fa kenan, sai kawai ta hak'ura har da safe sai ta tafi, amma ba ta tashi daga nan zaune ba har asuba ta risketa, ita b芒 kwana ba ita ba sallah ba bare salati. *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 21:42 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _70_ Tunda ya tashi da safen nan wata muguwar gajiya ya tashi da ita saboda aikin da ya sha daren jiya, kasancewar bai da tsari na ajiye mata biyu a rayuwarsa ya sa duk girman gidan nan daga b'angaren Saudat sai kuma b'angare da ya ware na shi. B'angaren Saudat shi ne a tsakiyar gidan, amma na shi ya na daga daman b'angarenta ne kusa da gurin ajiye motoci, duk da a ido za ka d'auka girmansu d'aya, amma a zahiri na Saudat ya fi girma da yawan d'akuna, sai dai a yanda Saudat ta horar da shi zama da ita ya tilasta mi shi yin madafa a b'angaren, tunda dai ita ba gwanar girki ba ce sai ta yi niyya. Bai tabbatar da anfanin b'angaren nan ba sai jiya da Kalli ya kira shi a waya ya ke sanar ma sa za a turo kayan Faduma da kuma masu gyaran d'aki, tunda dama ya san da haka amma bai gama yanke in da za ta zauna ba, sai da ya dawo cikin dare ya shiga kiciniyar d'auko sabbin kayan da ya zuba a b'angaren ya na turasu wani d'akin da ke cikin falon, kasancewar d'akuna hud'u ne sai madafa da ban d'aki da ke wajen falon, dan duka d'akunan akwai ban d'aki. Jiya ne kawai Umma ta tabbatar ma sa da Aminu ne zai auri Zulfa, ya yi mamaki sosai amma kuma ya yi farin ciki, duk da ba ya shiga sabgar gidan sosai ya ji a ranshi zai jawo yarinyar a jiki ya ma ta ta lallami kan ta zauna da mijinta. Hakan ne ya sa shi sammakon tashi ya shirya dan halartar d'aurin auren. Ta k'ofar da ya shigo ya tabbatar ma ta kenan a b'angarenshi ya kwana? Sai dai wani irin tsumewa da ya ma fuskarshi ya sa jin lallai fa yau da tsutsotsi aka tashi a kai, to amma dai tunda ba dukanta ya ke ba hakan ba shi zai hanata darza mi shi ba idan ya shiga harkarta, bai tambayi yara ba dan ya ji sanda Qaseem ya d'aukesu, makullin b'angaren ya ciro ya mik'a ma ta fuskar nan a had'e tamau yace "Anjima bak'i za su zo kawo kaya, ki min alfarmar ba su makullin b'angaren can." D'agowa ta sake yi sororo ta kalleshi, d'auke kan ta ta yi ta na girgiza k'afa tace "Ba damuwa, ajiye a nan." Kallon in da ta kalla ya yi, ajewa ya yi kawai ya nufi hanyar fita, to tunda dai ba abun kari ta ke dafa mi shi ba bare ya tambaya, ya lura tunda su ka dawo gidan nan take sammakon tashi, amma na banza da wofi sai da ta girke akan kujera babu aikin fari bare na bak'i. Ita ma ta d'auka zai ma ta maganar tafiya wajen d'aurin auren, amma da ya k'yalleta sai haushi ya sake kasheta. *Masjid* Da isar shi taron ya samu duk a hargitse, dama k'ofar gidan ne za a d'aura auren a masallaci, da k'yar ya shiga cikin jama'ar ya yi nasarar kai wa ga Abdallah da ke ta fad'a kamar zai daki wani, d'an dafa kafad'arshi ya yi ya juyo da sauri, da ido ya tambaye sa da "Me ya ke faruwa?" Gyara tsayuwa ya yi da kyau ya nuna cikin masallacin yace "Wannan k'aton banzan ne mana zai mayar da mu k'ananan mutane, haka kawai ana shirin d'aura aure ya ce wani wai ya fasa bayar da yarinyar." Lumshe ido ya yi tare da sauke numfashi, a hankali ya bud'e ya fara takawa a matuk'ar sanyaye ya nufi cikin masallacin, dangin Aminu ne har da mahaifinshi da shi kan shi Aminun da ke can nesa da su ya na kallonsu, sai kuma Alhaji Saddi da su Kabiru da liman a tsakiyar masallacin, tsaye ya yi kansu, duba da ba za su fahimci yaren da zai mu su ba ya sa shi d'aga labb'enshi da k'yar yace "Miye?" Da sauri Saddi da Kabiru suka juyo, wani kallon raini Saddi ya ma sa jin wai su ne ya ke tambaya da miye? A d'an hassale yace "Auren ne na soke, an fasa ba za ayi ba." Idonshi carrr cikin na shi duk da su na tattare da gajiya da buk'atar hutu, haka ya shige sakar mi shi kallon da duk da ya na k'anin ubanshi sai ya ji kamar zai sunkuya ma sa, a tsaurare yace "Me ya sa?" Cikin fad'a ya d'auke idobshi daga na Hasheer ya shiga fad'in "Kai kafi kowa sanin me ya sa, akan me zan yarda 'yata ta auri wannan fasik'in da ya gama tambad'ewarsa da matar da ka aura? To idan kai ka aureta saboda idonka sun rufe, ni nawa a bud'e suke dan haka ba za ayi ba." Tunda ya fara magana Hasheer ke bin duk wani motsinshi da kallo, kallo ne na kalle ni mana cikin ido ka fad'a, kallo ne na wallahi na tsaneka Saddi, kallo ne da ke nuna Saddi ka yi wasa zan kwab'e anan mu daku. Bai gama bin shi da kallon nan ba cikin muryar kuka Aminu yace "Wallahi wallahi Abba ban tab'a iskanci da ko wace mace ba a duniya, bare kuma Faduma da ko hannunta ban tab'a rik'ewa ba, ka yarda da ni na rantse ma ka." Wani kallo ya wurgawa Aminu da ya sa shi jan baki ya yi tsit, sunkuyar da kan shi ya yi hakan ya sa Hasheer kallon Saddi yace "Ai dai ba za ka ba shi 'yarka ba ko?" Hayayyak'o ma sa ya yi yace "Eh d'in, na ce ba zan bayar ba, na ga kuma idan uban wani ne ya haifa min 'yar." Kabiru ne ya kalleshi cike da takaici yace "Ba uban da ya haifa ma ka 'yar, ka je ka cinyeta idan za ka iya mana me ya dame m没, amma ka sani yaron nan ya kubce ma ka wallahi a k'arshe za ka had'a 'yar da mai irin halinka ne." Ya juya zai fita Saddi yace "Kabiru ni ka ke ci wa mutumci cikin mutane? To insha'Allah hakan ma ba zai faru ba, sai dai bak'in ciki ya kashe mai bak'in ciki." Hannun Kabiru Hasheer ya rik'o su ka kalli juna, a nutse cikin fitar da ko wace kalma yace " *Za'a d'aura auren nan*." Sakin hannunshi ya yi ya k'arasa gaban Aminu ya tsaya, kamar wanda zai firgita shi da yanayinshi yace "Ka san Salima?" Kallonshi ya yi gabanshi na fad'uwa yace "Eh yallab'ai." Ba tare da ya rusuna kallon nan ba yace "Za ka iya aurenta?" Da sauri ya sake kafeshi da ido, kasa amsawa ya yi sai kallonshi kawai da ido, hakan ya sa Hasheer sake murtuke fuska yace "Bani amsa?" Da sauri ya d'aga kan shi alamar eh, a take ya juyo ya kalli Kabiru yace "Kawu za mu d'aura mu su aure yanzu, bai kamata mu bari sunan danginmu ya lalace ba a dalilin wannan abun." Zaune kawai ya yi da ke nuna su ma su zauna, tuni masu ruwa da tsaki su ka zauna su ka fara gabatar da abin da ya tarasu kowa da farin cikin halin girma da matashin ya yi, Saddi kam fita ya yi a masallacin ya na fad'in "Aikin banza, dama burinsu kenan ai su kassaraka." Kamar da wasa sai kuwa aka d'aura auren Aminu Mustafa da Salima Abdul rahaman nakiri, shelar da san-k'ira ya shiga yayatawa ta sa duk mutanen cikin gida aka shiga kallon juna ana mammaki, kowa tambayar kan sa yake "Salima kuma? Da ita aka d'aura auren?" Tun maganganu na tashi sannu sannu har kwaramniya ta fito daga babban falon inda Umma da Marfu'a su ke zaune, mutane ne su ka cika falon har ya tunbatsa saboda ganin k'wam su ma, mahaifiyar Zulfa ce ke fad'in "Wannan abu dama shirya shi aka yi, akan wane dalili za a d'aura auren nan da Salima? Me ya faru da Aminu zai mana haka?" Shigowar Alhaji Saddi ne ya sa shi daka ma ta tsawa yace "Rufe min bakinki a wurin nan, farin ciki ya kamata ki yi da Allah ya kub'utar da 'yar daga halaka, ita kuma da akayi bugun k'irji aka ba shi ita to ga su ga shi, sai me?" A k'ufule ya yi hanyar d'akinshi sai Hajiarsu da ke zaune saboda k'afafu tace "Kai Saddi lafiya? Me ya faru a wurin d'aurin auren?" Kallonta ya yi ba ladabi a ciki yace "Ba komai Hajia." Zai fita a d'akin dan a rikice Yale Hasheer da Abdallah su ka shigo, wani kallo su ka sakarwa junansu mai nuna sam babu fahimta a tsakaninsu, k'in kauncewa ya yi a hanyar hakan ya sa Abdallah kaucewa da tunanin Saddi ya wuce ta nan, dan ya fahimci yau Hasheer da yan sababi ya tashi a kan shi, kuma duk wanda ya taroshi zai iya jawa kan shi zuciyarshi da komai son ka na son nesanta kan ka da shi sai ka ji ka jigata. Shi ma Saddi k'in wucewa ya yi hakan ya sa duk suka tsaya a hanyar, daga inda ya ke tsaye ya d'ago idonshi ya saukewa mutanen falon, had'a ido su ka yi da Umma da ke bin shi da kallon kar ka min haka, d'auke kan shi ya yi cikin wata dak'ilalliyar murya yace "D'aurin auren Zulfa ne ya tara kowa a nan, kuma ba a d'aura da Zulfa ba saboda haka mahaifinta ya so, wanda ya ji zai iya taya ni murna ya je gidan Umma na, zan wadataku da abin da za ku ci ku sha saboda godiyar Allah." Ya na gama fad'a ya kalli Umma, da idon shi ya ma ta alamar mu je, da ke ita ta raini abin ta kuma abin da ya yi d'aya ne a cikin d'abi'unta sai ta fahimci me ya ke nufi, kallon Marfu'a ta yi su ka fara takawa, Hajia da ke zaune ne tace "Kunga ku taimaka min na tashi, me zan zauna na yi a nan nima." Dan ita dama Saddi ta da haifesa ne, amma sam kamar ba uwa ta ke gare shi ba, kuma dama indai mutum ya sa kan shi harkar mata, to komai ya na iya yi har da wulak'anta uwa ma, su Umma ne su ka kamata ta shi sai ga Salima ta fito daga d'akin Zulfa da kuka. A tare su ka k'arasa fita ta na tambayarsu wai da gaske ne aurenta aka d'aura, jin kukan ta a bayansu ya sa ka shi dakatawa ya juyo, hannu ya mik'a ma ta har ta k'araso gare shi, kwantar da ita ya yi a jikinshi ya shiga daddab'ata, cikin muryar dattako da neman nutsuwarshi yace "Salima kin yarda ni yayanki?" Cikin shashek'ar kuka ta d'aga mi shi kai, d'agota ya yi daga jikinshi yace "Kuma kin yarda ba zan iya cutar da ke ba?" Nan ma kai ta d'aga mi shi ita dai, jinjina kai ya yi yace "Dan haka ki share hawayenki, insha'Allah auren nan zai zama silar farin cikin ki, na yarda da Aminu d'ari bisa d'ari, na san shi sosai na san waye shi, ba zai cutar da ke ba Salima, dan Allah ki yi hak'uri kinji ki min biyayya, na yi bugun k'irji da ke ne saboda na yarda da tarbiyyar da ki ka samu, Abba ma ya bar min amanarku ne saboda sanin zan iya tsayawa akan lamarinku, ki daina kuka kin ji." Hannu tasa ta na share hawayen ta na ajiyar zuciya, d'an sake rab'ata ya yi jikinshi yace "Yanzu m没 je gida, sai ki zauna ki fad'a min me ki ke buk'ata." D'aga ma sa kai kawai ta yi alamar to, juyawa su ka yi ta na jikinshi za su fita, Mujaheed ne ya shigo tare da abokinshi, hararan Hasheer ya yi tare da jan tsaki ya kalli Hajia yace "Yanzu Hajia abin da yaron nan ya yi ya kyauta? Kawu fa uba ya ke a garemu, amma ya kunyata shi a bainar nassi." Kallonshi Hajia ta yi tace "Ba zan yanke hukunci ba har sai na ji me ya faru." Tab'e baki ya yi yace "Wannan ai sam ba ka nemawa yarinya daraja ba, kawai tsabar iya yi da neman a sani, kamar kai..." Yanda ya janye Salima daga jikinshi tare da damk'a ma ta wayarshi a hannunta ya sa Abdallah saurin matsawa kusanshi ya rik'o hannunshi, kallonshi ya yi a marairaice yace "Dan girman Allah kar ka biye ma sa, abin da ya ke nema kenan." Cikin muryar k'ufula da k'araji yace "Dan Allah ka barni na d'aure yaron nan na zaneshi ya gane cewa a gaba na ke da shi." Umma ce ta yi saurin cewa "Hasheer." Bai juya ya kalli inda ta ke ba dan ya san da idonta kawai za ta aika ma sa da sak'on, cikin sanyayyar murya tace "Gida na ke so ka kaini, zan iya samun wannan darajar?" Rintse idon shi ya yi y'a sauke ajiyar zuciya har guda uku alamar ya saita nutsuwarshi, karb'ar wayarshi ya yi a hannun Salima ba tare da ya juyo ba yace "Mu je." Bin bayanshi duk su ka yi har Abdallah ma da shi dai ya ke son ya ga tafiyarsu lafiya, shi ina zai yarda su caskale anan ya na ango da tsautsayi ya gifta a kan shi ya ji masa rauni, ai gwara su yi nesa idan ya so ya ci uwar shi, tunda ya raina mutane. A hankali mutane su ka fara sulalewa, wasu ma da sun ga wani zai fita sai su tambaye shi ina ya nufa? Idan ka ce gidan Hajia Maryam sai mutum yace jirani, idan kuma ba can ka yi ba sai a nemi kwatencen gidan dan aje a goge mak'oshi. Su na daf da isa gidan wayarshi da ke aje ta shiga kururuwa, ya na dubawa Kalli ne, d'auka ya yi ya saka a amsakuwa bai ce komai ba ya na saurarenshi, kasancewar su na gida yanzu an sallame su ya sa muryarshi babu alamar wanda ya yi jinya, cikin nutsuwa yace "Elhaj barka da safiya?" A dake yace "Barka." D'orawa ya yi da "Dama yaran nan ne da su ka tafi da kayan nan su ka kira su ke fad'a min basu ga inda za su saka kayan ba." Da mamaki ya yatsina fuska yace "Wai har sun zo ne?" Da d'an murmushi kamar su na kallon juna yace "Eh elhaj, kasan anan aka ma ta siyayyar kayan a babban shagon nan transa mall, wanda za su ma ta gyaran kuma a nan suke dama, sannan ka san akwai gyaran d'akin Owwo ma da idan sun gama nan za su yi, to shi ya sa su ke so suyi su gama da wuri." Wata sakaran ajiyar zuciya ya sauke yace "Ina zuwa." Yanke kiran ya yi da shiga neman lambar Saudat dan ya ji me hakan ke nufi? Sai kuma muryar Umma a bayanshi tace "Ya akayi ba ka bar mu su inda za su ajiye kayan ba?" Cikin k'warewa a harshen larabci yace "Umma wallahi na bar wa Saudat makullen, ban san me ya sa ba ta basu ba." Sai kawai ya ji ran shi ma ya b'ace, to me take nufi? Ajiye wayar ya yi da k'arfi ya na jan dogon tsaki, wata irin kwana ya d'auka ya d'auki akalar zuwa gidan, Umma na ganin haka a ranta tace "Na shiga uku ni Maryama, wa ya tab'a shi yau da dole ya ke neman abokin fad'a?" Da sauri ganin yanda ya ke tuk'i tace "Hasheer ka kwantar da hankalinka, ba na son tashin hankali fa ka sani." Bai tanka ma ta ba sai kan shi kawai da ya d'an jinjina ma ta alamar to. *Bayan fitarshi* Bai fi minti sha-biyar da fita ba mota ta tsaya aka shiga sauke kayan ana shigowa da su, da taimakon mai gadi aka shigo da su dan shi ma ya san da zuwansu, tun ba su k'arasa ba kuma matan da za su yi gyaran su ka zo gidan su ma, su dai su na kallo har aka gama jibge m没 su kayan a nan farfajiya ba su ce komai ba, sai dai su ka ga su na shirin tafiyarsu ne d'aya daga ciki tace "Ina ne za a saka kayan? Ai da ciki ku ka saka mana su." Matashin ne yace "Wallahi mu ma mun tambaya sai mai gadin yace bai sani ba, kuma ya yi ta sallama a falon uwar gidan amma shiru ka ke ji kamar ba mutum." Wata daga ciki ne tace "To kunga ku kira mana wanda zai iya fad'a ma na inda za m没 yi da kayan, dan mu na da aiki a gabanmu." D'aya ce tace "Gaskiya kam, dan yarda ce ta kawo mu wurin nan, ba dangin iya bare na baba, Owwo ce ta wakilta m没 saboda zaman mutumcin da aka yi." Wayarshi ya fito da ita ya kira Kalli ya fad'a ma sa, shi ne shi ma ya kira Hasheer ya sanar da shi yanda ake ciki. Su na zaman jiran an ce mu su mai gidan na nan tafe Saudat ta fito da farar riga da wandon jikinta ba ko kallabi sai wayarta a hannu, k'are mu su kallo ta yi na wulak'anci da tsana da k'yama kafin tace "Wai ku ne ku ka kawo kayan nan?" Mai taushin cikinsu ce ta amsa da "Eh, mu ne." Sake yatsina fuska ta yi ta kalli kayan, duk da a rufe suke amma sai ta kallesu tace "Kunga; ku d'auki tsummokaran kayan nan ku fitar min da su a gidana, nan gidana ne ba zan zauna da ko wace 'yar iska ba, idan ba haka ba kuma za ku ga rashin mutumci." D'aya daga ciki ne ta kalleta sama da k'asa tace "Wannan kuma sai ki bari har shi mijin na ki ya zo sai ki fad'a ma sa, amma ba mu ba tunda har ya bamu umarnin zuwa mu gyara ma sa d'akin amaryarsa." Kallonta Saudat ta yi tace "Ke! Kalleni da kyau, kinga na yi kama da wacce za ta zauna da kishiya? To mijina nawa ne ni kad'ai, ban ga shegiyar da ta isa ta ce za ta yi kishi da ni ba wallahi." Cike da gatsali d'aya tace "Za m没 gane hakan ne idan ki ka bayar da dama wata ta shigo gidan ta kasa k'wace shi a hannunki, amma daga haka mu kam ba za mu gane ba." Gyara tsayuwa ta yi tace "Kunga ba wasa na ke mu ku ba, zan baku sak'o ku fad'awa iyayen karuwar nan, idan har su na son ta to kar su kawota gidan nan, dan cikin uku za ayi d'aya, ko dai na kasheta da tsinin wuk'a, ko kuma na kasheta da bakin bindiga, ko kuma na yi anfani da gubar da za ta kassara duk wata gab'a mai anfani a jikinta, idan har ban yi haka ba ku ce ni ba 'yar halak ba ce." Bushewa su ka yi da dariya biyu daga ciki har da tab'a hannu d'aya kuma tace "To wa ma ya sani? *Abu a duhu*." Wata gogaggiya ce tace "Ke idan kin isa ki b芒 wa Faduma fili a cikin gidan nan ta shigo ku gwada mana, yak'ini ne na ke da ko kin fita kyau ba za ki fita iya ado ba, idan kin fita hasken fata ba za ki fita iya kawo annuri a fuskar mai gidanku ba, ai idan kin isa sai ki bari a kula mijin na ki, ta hakane za mu gane k'warewarki a kan shi, amma ba ki zauna anan ki na fad'a mana haukan banza da wofi ba." Matsowa ta yi gaban matar ta na fad'in "Ni ki ke fad'awa haka? To ba zan bari ta shigo d'in ba, ko kun d'auka ban san cewa wannan tubawan shegen asiri ne da su ba, in dai har za su rab'ar ma ka miji sai sun rabaka da shi." Dariya suka sake tintsirewa da ita, hakan ya hassalata ba ta b'ata lokaci ba wajen d'auke matar nan da mari ta shak'i wuyanta cikin k'araji ta na fad'in "Ni sa'arku ce? Mahaukaciya ku ka d'aukeni ko me? Zan kasheki yau a gidan." Duk da sun ji shigowar mota bai hana su k'ok'arin rabasu ba, da k'yar su ka yi nasarar b'amb'aresu matar na fad'in sai ta rama marinta, da k'yar su ka rik'esu suna huce suna aikawa juna zagi. A haka su ka k'araso a k'agauce ko pakin motar bai yi ba, su na zuwa ya kalleta ran shi a b'ace yace "Mi ye haka Saudat?" Cikin d'aga murya ta kalli matar tace "Ka tambayeta ita ka ji, dama ka yi aure ne da ka ci zarafi na?" Juyawa ya yi ya kalli mai gadi da ke tsaye ya na kallonsu, da ido ya mi shi alamar "Bar wurin nan." Da sauri ya juya ya koma bakin k'ofa, cikin taushin murya Umma ta kalleta tace "Haba ke kuwa Saudat, ya za ki zubar da k'imarki haka a gurin bak'i daga zuwansu? Ba ki san me..." A kid'ime, a gigice, a hassale ba tare da tunanin me hakan zai janyo ma ta ba ta dakawa Umma wata tsawar da ko Izzadeen da ta haifa zai ji ta har ranshi tace "Dakata min malama, b芒 da ke na ke ba, da shi na ke yanzu, ina..." Wani lalataccen d'an iskan mari ya datsa ma ta a fuska, k'arfi da girman marin ya saka ta kaiwa 'yar k'aramar tukunyar flewers d'in da ke zagaye a cirodor wurin, bugu da k'ari kuma ta fad'o kusa da k'afafunshi, gigita da kid'ewa da shiga matsanancin tashin hankali da rad'ad'i had'e da azabar da ta ji su ka saka ta rangad'a ihun da kafatanin unguwar duk mai dogon ji a lokacin zai ji ta, jini ya gabce ma ta ta baki saboda dantse harshenta ta yi da hak'oranta a bazata, hakan ya sa abun ya zo ma ta da k'arfi har jini ya b'alle ma ta, ga kuma ta hancinta ma da wani jinin ya shigo malalowa tuni farar rigarta ta b'ace da jini. Sunkuyawa ya yi ya na kallon fuskarta idonshi kamar garwashin wuta, duk jijiyoyin jikinshi sun mik'e tsabar b'acin rai, nunata ya yi da yatsa cikin gigita yace "Uwa ta? Saudat mahaifiyar ta wa?" Da k'arfi ya mik'e ya d'aga k'afa da niyyar yin k'wallo da ita, da sauri Umma ta matso ta na fad'in "Kul! Wannan ba halinka ba ne Hasheer." Dakatawa ya yi ya aje k'afar, tukunyar da goshinta ta buga d'azun ya sa hannu ya nausheta, watsewa ta yi dan dama b芒 wuyar mutuwa ne da su ne. Duk kowa kama jikinshi ya yi su na satar kallonshi, b'alle botir d'in rigarshi ya yi na sama ya dafe gaban goshin shi, cikin muryar k'araji kamar mai kuka yace "Yanzu hankalinki ya kwanta Saudat? Kin yi farin ciki da hakan ya faru? Wai ke sha-sha-shar ina ce?" Cike da tsoro Umma ta dafa kafad'arshi da niyyar ta lallab'ashi ta samu ya bar gidan, amma sai ya juyo a hassale kamar zai had'eta ita ma ya na nuna ma ta Saudat ya na fad'in "Umma kullum yarinyar nan fad'a ma ta na ke ta kiyayi gayyato b'acin rai na, ina kwatanta ma ta a tsanake ta daina min hawan k'awara ta yanda za ta turani bango, akan wani dalili ne Saudat za ta raina ni har ta nemi raina min uwata? Ni na raina iyayenta ne?" A sukwane ya sake juyowa kan ta ya durk'usa gabanta ya rik'i gashinta ya na kallon fuskarta da ta kumbura ya na fad'in "A karon farko kin dinga cin zarafin macen da ke da kima da daraja a idona, ko sau d'aya ba ki tab'a fahimtar yanayin da na ke shiga ba a duk sanda ki ka kirata da karuwa, idan na ce zan hukuntaki da waccen laifi bai mi ki adalci ba, shi ya sa na dinga had'e duk abin da ki ke min ina zuba mi ki ido, sai yanzu kuma ki nemi taka min uwa, matar da ko uban da ya haife ni ba zan lamunci ya ma ta wannan tsawar ba." Sakin gashinta ya yi da k'arfi ya mik'e tsaye ya na fad'in "Me ki ke ji da shi da ya sa ki ke tunanin ba zan iya rabuwa da ke ba? Kyanki? Surarki? Ko kuma hasken fatarki? To in dai su ne Saudat ki rik'e tsiyarki ba na so, ina so ki sani ni Hasheer kin same ni a kan dai-dai, kuma na sa hannu biyu na karb'i gayyatar rashin mutumcinki, zan kuma nuna mi ki yanda na ke nawa b'acin ran, banza kawai da ba ki san ana d'aga mi ki k'afa ba." Juyawa ya yi kamar zai fita sai kuma ya dawo ya tsaya, nunata ya yi yace "Ranan ba ki na fad'in Aminu ba zai samu kwanciyar hankali ba? To ki sani an d'aura ma sa aure da Salima, kuma a ranar da za a kawo min amarya a ranar shi ma za a kai mi shi ita gidanshi, idan kin isa Saudat, idan ki na so ki nunawa duniya ke mai kishina ce, dan soyayyarki da Allah ki hana mu shiga duniyar matanmu, a ranar da Faduma za ta shigo gidan nan a ranar zan je gareta, ki had'e zuciya ki mutu ko kuma ki sha maganin b'era." A sukwane ya shiga falonta dan ya tabbatar makullin ya na inda ya barshi, ai kuwa anan ya same shi ya d'auko ya fito, matar da duk su ka tsume ka rantse wani mummunan hatsari ne ya faru a gabansu ya mik'awa makullin, bai kula kowa ba ya shiga motarshi ya bar gidan kamar wani zakin da zai fita farauta. Wata hamshak'iyar ajiyar zuciya Umma ta sauke ta na kallon Saudat, yanda ta lura da yanayinta sa茂 ta tsinci kan ta da yi ma ta addu'ar "Allah ya sa bai lahanta mi ki ji ko ganinki ba." A zahiri kuma girgiza kai ta yi tace "Saudat wannan ita ce ranar da na ke guje mi ki ta riskeki ki na hannun Hasheer, ni na haifeshi na fi kowa sanin waye shi, hak'ik'a bai bar komai daga d'abi'ata ba, duk hak'uri na da sanyina shi ne ya d'auko, sai dai ki sani ana kai mu k'adamin da idan mu ka harzuk'a, wallahi Allah kad'ai ya ke gyara lamarin, a yanzu ba zan yi fushi da ke ba dan zaman gidan nan zai iya fice mi ki a ranki, amma shawara d'aya da zan baki shine, ki nemi sabi dabarun shawo kan miji ta yanda Hasheer zai iya waiwayarki, Saudat ko kad'an Hasheer bai iya fushi ba, bai iya d'aukar abu da zafi ba, bai iya sakin lamarin da ya tsawwala ma sa b'acin ran shi da sauk'i ba, wallahi a kad'an ki kwashe shekara d'aya kafin ki yi nasara ya fara karb'ar gaisuwarki, shi ya sa ni kaina mahaifiyarsa na ke kiyaye warto wannan b'oyayyar zuciyar ta sa." Juyawa ta yi jiki a sanyaye tace "Allah ya kyauta." Marfu'a da ke cike da farin ciki ne ta amsa da "Ameen." Kallon matan nan Umma ta yi ta nuna mu su b'angaren tace "Ga b'angaren can, dan Allah ku yi hak'uri da abin da ya faru, ku ci gaba da aikinku, idan na koma gida za a kawo mu ku abinci." Fita su ka yi suma kamar an tsomasu a ruwan zafi su ka bar gidan, su ma dai a sanyaye su ka nufi b'angaren da gudanar da abin da ya kawo su, duk da sun ji dad'in yanda ya nuna bai d'aukar a raina ma sa uwa, ya birgesu da ya yi maganin marar kunyar nan, ya birgesu da ya zama mai kawar da kai bango ne aka kai shi yanzu ma, amma dai yanda abun ya kasance da yanda su ka ga farar fuskar Saudat ta yi kamar babur ne ya yi kwatantanwa da ita ya jefo a k'asa, sai abin ya b芒 su tsoro kuma. *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 21:42 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _71_ A gaskiya ba iya wulak'anci da mutumcinta kawai ya yaga ba, har da k'ask'antar da ita bayan ya nausheta da maganganu masu zafi, tunda take a rayuwa ba ta tab'a jin tozarci irin na yau ba, tunda ta ke dashi bai tab'a ma ta ko da kwatankwacin haka ba, ita kam ina za ta saka kan ta? To wai me ma ta yi ne da zafi haka? Maganar da ta wa Umma? Tabd'ijam! Wayarta ta raruma a k'asa ta dafa bangon wurin ta shiga lalubawa ta mik'e, da jan k'afa da lalabe ta shiga d'aki, tabbas duk maganganunshi na k'arshe da kuma na Umma akan kunnenta suke, amma na farko da ya yi kam ba ta san me ya fad'a ba. Ganinta ne ma ya ke neman bata matsala ga wani matsiyacin ciwon kai da ya sauko ma ta, tambayar kan ta ta yi "Wai dama haka ya ke da zafi? Haka ya iya marin fuska? Ta ya ma ya iya d'aga labb'ensa ya shiga furta ma ta kalamai haka masu kama da saukar ruwan annoba?" Da k'yar ta k'arasa kai kan ta d'aki ta shiga ban d'aki ta wanke fuskarta, kallon kanta ta yi ta ga yanda ta zanca kama a lokaci d'aya, k'wafa ta yi mai k'arfi da ke nuna babu nadama a cikin zuciyarta, fitowa ta yi ta d'auki wayarta ta shiga neman lambar Zaliha, cikin sa'a ta same ta kam ba tare da ta jira sun gaisa ba tace "Zaliha ina ake zubar da ciki?" Da k'arfi Zaliha daga b'angarenta tace "Ciki kuma? Zubarwa za ki yi?" Da k'arfi tace "Eh, zubar da shi zan yi ya jima bai kasheni ba." Tab'e baki ta yi irin ohon nan! Kafin tace "Indai kina da kud'i to ki shirya ki saka rana da lokaci, abu ne mai sauk'i wannan." Cikin jin haushi da k'araji tace "Ke karki d'aukeni mahaukaciya mana, ina da kud'i kuma yanzu na ke son a zubar min da shi." Duk da ta ji haushi ita ma amma sai tace "Ba damuwa, bari na kira likitar na ji idan Dr. D'in na su na nan." Yanke kiran ta yi ta shiga neman lambar Fa'iza, ta na d'agawa ita ma take tambayarta "Dr. Ya na asibiti ne?" Amsa ma ta tayi da "Eh to! Yanzu dai ina maternit茅 tattali, amma nan da minti talatin zan je asibitin sai na gani ko?" Amsa ma ta ta yi da "Ok ba damuwa, nagode." Kiran Saudat ta yi ta fad'a ma ta tare da cewa "Ki zama a cikin shiri, zan waiwaiyeki a ko wane lokaci." A cikin mintin da bai gaza talatin ba Zaleeha ta kirata ta ce ta shirya ta same ta asibitin dks, ba b'ata lokaci Saudat ta canza kayanta ta fita ranta a b'ace da tunanin cikin nan shi ne farin cikin shi, dan haka za ta zubar ya jima bai kasheta ba. Duk da hakan na faruwa ne ba da son ran ta ba, dan ta tab'a kwatanta yi mi shi magana ya fatattaketa ya nuna ma ta ai asibitinshi ce, dan haka in za ta iya aiki ta yi in ba za ta iya ba ta kama gabanta, tun daga ranar sai ta ja baki ta yi shiru. Yanzu ma tunda su ka zo ita ta mu su iso wajenshi, ba ta san me ya kawosu ba ko kad'an da b芒 ta taimakawa Zaleeha ba, dan dama su na mutumci ne tunda aka tab'a zubar ma ta da ciki a asibitin, Fa'iza ita ce tsaye a kan ta har aka sallameta, shi ya sa suke gaisawa jefi jefi ta waya, yanzu ma dai bayan an kammlawa Saudat aikin ita ya bar wa alhakin kula da ita, hakan ya sa ta shiga b'acin rai da jin haushin matar, domin kuwa dalilin da ta fad'a na zubar da cikin shi ne "Mijina ne ba ya son haihuwa, kuma idan na bari ya san da cikin nan to zai min kishiya ne, ni kuma bana so ko kad'an." Wayarta ta ba wa Zaleeha tace "Ki kira min lambar mamana gata nan ki fad'a mu su na yi b'ari." Ba musu ta yi abin da ta sa ka ta, hankalinsu ya tashi sosai da suka samu labari, da sauri mahaifiyarta ta zo asibitin da rakiyar mahaifin Saudat d'in, duban d'akin mahaifiyar ta yi da kyau ta kalleta ita ma ganin fuskarta a wani kumbure ga shatin yatsu duk ta jigata tace "Me ya seme ki Saudat? Ko had'ari ki ka yi? Ya ban ga mijinki ba?" Rufe ido kawai ta yi ta sauke ajiyar zuciya, Zaleeha ce ta yi saurin cewa "Ba hatsari ta yi ba, ku shi ma bai sani ba, ni ma hanya ce ta d'aukoni na biya gidan, shi ne fa na sameta a wannan halin." Bud'a ido ta yi a hankali hawaye na sulalowa, tunawa ta yi da d'an tayin cikinta da aka nuna ma ta, wani tausayin shi ta ji ya na son lullub'eta, lallai ba a banza Allah ya sa ko wane yaro ke rayuwa a cikin mahaifar mahaifiyarsa. Saida ta ja majina ta kalli mahaifinta tace "Fad'a mu ka yi da shi saboda amaryarsa, marin da ya min ne ya tilasta min fad'uwa, daga nan kuma marata ta fara ciwo shi ne sai jini." Mahaifiyar ta gyara mayafi za ta fara zazzaga mahaifin ya yi saurin cewa "Gaskiya ki ka fad'a?" Cikin kuka tace "Eh Abba, wallahi gaskiya ce." D'aga ma ta hannu ya yi yace "Ko da gaskiya ce ki ka fad'a Saudat, na tabbata kin kai Hasheer bango ne, ai ba yau ku ke tare ba, duk yanda aka yi maganar auren nan ce ki ka saka a ranki ki na tayar ma sa da hankali." D'an tsaki ya yi ya kalli uwar ya nuna ta yace "Kar na ji bakinki a wurin nan." K'wafa ya yi ya ciro wayarsa a aljihu, lambar Hasheer da ya ke da tabbacin zai d'aga ya kira. A lokacin ya na kan hanya sai da ya yi pakin ya tsaya ya d'aga, muryarsa babu walwala a ciki, ba y'a tare da karsashi ko kad'an, a mutumce su ka gaisa bayan ya yi k'ok'arin b'oye damuwarsa. Jim! Ne ya biyo baya kafin mahaifinta yace "Ka na da labarin matarka ta na asibiti?" A take ya lumshe idonshi ya sake cakumar sitiyarin motar ya rik'e gam, numfashi ya sauke mai nauyin gaske kafin yace "A'a, me ya faru?" Cikin dattako yace "Ga ta nan asibiti kwance, ta yi b'ari ne." Sake jimk'e idonshi ya yi ya na dantse hak'oronshi ta yanda har daga waje za ka ga muk'amuk'inshi su na motsawa, had'a kan shi ya yi da sitiyari cikin takaici da k'unar jin me ya sa saida Saudat ta yi abin da ta kai shi bango ya d'auki matakin da za ta wahala a rayuwa? Me ya sa ta yi abin da har ya iya d'aga hannunshi a kan mace? Marin da ya ma ta sam bai dace da fuskar mace ba, namiji ne zai iya d'aukarshi har ya gane sak'on me ake so a isar. A hankali yace "Wace asibiti?" Amsa mi shi ya yi da "Nan ne ads asibitin dks." D'an tsaki ya yi a ran shi a fili kuma yace "Ina zuwa." Saida dattijon ya kashe wayar kafin ya aje wayar shi ma, ta yi b'ari? Duka ya kai wa sitiyarin ya na mai jin haushin jin kalmar nan, tabbas ya na son haihuwa so mai yawa, amma fa son da ya ke mahaifiyarsa ya fi wanda ya ke ma haihuwa, dan haka ko yanzu ta d'aga murya a kan matar da shi ko idonta ba ya kallo a tsatsaye ba tare da rusunawa ba, to ba zai b'ata lokaci ba wajen yi ma ta dukan da sai ta nemi k'wayayan haihuwarta ta rasa ma gaba d'aya." Duk da yace ya na zuwa, amma fa ba hakan na nufin zai waiwayi lamarin Saudat a yanzu ba, kai shi ji ya ke ma ta fita a rayuwarshi yanzu, kima da darajarta duk sun zube a idonshi, dama ta jima ta na wulak'anta ma sa yaranshi, ba ta basu cikakkiyar kulawa, dan haka *gaba da gabanta*, yanzu ba zai iya jura ba. Qaseem ya tura asibitin da kud'i ma su yawa da yasan za su ishe su duk wata d'awainiya, daga nan kuma ya rufe babinta ya shiga wata sabgar, gidan shi ne dai bai koreta ba, idan ta ga dama ta dawo ruwanta, idan kuma gidansu ta wuce daga can duk matsalarta ce, ko ba ya da wata matar a yanzu shi zai iya hak'urin zama babu ta, bare kuma ya samu *sanyin idaniyarshi*. Kamar yanda yayi alk'awari bai yarda b'acin ran nan ya mantar da shi ba, dan kuwa mutanen da suka taru gida sai da aka wadatasu da gasashen nama zuwa kayan ciki da aka gasasu a cikin takarda a nad'e, sannan aka wankesu da isashen lemu mai sanyi. Duk da ban bakin da ya ma ta, amma bai sa ta daina kuka ba, da ta tuna fa yanzu aure ne a kan ta sai kawai ta fashe da wani kukan, tun Halima da Meena su na rarrashi har su ka fita wajen hidimar mutanen da ka rantse dama ranar an saka ma ta lokaci, haka su ka dinga fama da jama'a har kusa da magriba kafin su tsagaita. Bayan sallah isha'i ya shigo gidan tare da Mukhtar a bayanshi, daga Meena sai Marfu'a da kuma Hajia su ka rage, k'arasawa su ka yi falon su ka zauna su na gaisawa ya wunin yau? Ya kalli Meena da niyyar tambayar ta ina Salima? Sai kawai Hajia ta kalleshi ran ta a b'ace tace "Kai Hasheer, yanzu abin da ka yi ya dace kenan? To me hakan ke nufi? Ko dai dama kai da shi d'in kun yi shirin *ban gishiri* in ba ka *manda* ne?" A sauk'ak'e ya kalleta sai kuma ya lumshe idonshi ma su d'auke da gajiya, shiru ya ma ta a k'alla na tsawon minti biyu, daga bisani kuma ya kalleta cikin sanyi yace "Ba haka bane, an fasa auren Aminu ne saboda akwai hannun wasu da ba sa son ya yi auren, Aminu kuma ya min hallaci tunda har ya iya mallaka min *murmushi na*, shi ya sa ni ma na ba shi wacce na ke da tabbacin za ta za ma alkhairi a gare shi." Duk da ta gamsu amma sai tace "To me ya sa ba za ku dinga saka lokaci ba? Sai kawai ku dinga yin aure kwatsam kamar wa su 'ya'yan roba, idan ni ban da kimar da za ku dinga fad'a min, to ku dinga shawara da mahaifanku mana." Shiru ya yi dan ya riga da ya gama maganar nan, jin bai tanka ma ta ba ya sa ta cewa "To ai yanzu yarinyar na can ta na kuka, sai ka je ka rarrasheta." Kallon Umma ya yi da ita ma tunda ya shigo ta ke kallonshi, da hannu ta mi shi alamar ba komai kawai, saurareta ke dai. Mukhtar ne ya mik'e yace "Bari na je na rarrashi autar Umma, ai ba a barta ta yi ta kuka ba." D'akinsu Salima ya wuce Hasheer na kallonshi, sai da ya ga shkgewarsa ya kalli Umma yace "Umma ku yi hak'uri da abin..." Da sauri ta girgiza mi shi kai tace "A'a Hasheer, hakan Allah ya tsara, ba komai ka ji ko, ka bar min komai a hannu na insha'Allah komai zai tafi dai-dai, kamar yanda ka fad'a acan za ta tare nan da kwana hud'u." Da sauri ya waro idonshi ya na kallonta, kenan ta rik'e hakan ma a ran ta? Wata irin k'aunar Umma ya ji ta sake dirar ma sa a zuciya, zai zo ya yi dattako irin mahaifiyarshi, Hajia dai na kallonsu dan tasan surukar ta ta ba daga nan b芒 wajen karamci da dattijantaka, kallon Umma ya yi yace "Umma ni zan wuce gida, zuwa safe ku gama tunanin abin da ku ke buk'ata, idan na shigo sai ku fad'a min." Da kai kawai ta amsa mi shi, mik'ewa ya yi shi ma da kai ya mu su sallama, wanda ya fahimta ya fahimta wanda bai fahimta ba kuma bai amsa mi shi ba. Hajia ce ta bi shi da fad'in "Idan ka fita ka turo min autana ni ma ya mayar da ni gida." A can k'asan mak'oshi ya amsa da "Uhum." Ya na shiga mota ya kira Abdallah ya fad'a ma sa, kai tsaye gida ya wuce ya yi pakin, mai gadi ne ya kawo ma sa makullan b'angaren, dan da su ka gama gyara shi su ka bawa, karb'a ya yi ya fito jiki a mace ya bu'da b'angaren. Wata ajiyar zuciya ce ta kubce mi shi saboda wani sihirtaccen k'amshi da ya dake shi, ya na son turare kuma ya yi aiki da turaruka bila'adadin, amma k'amshi bai tab'a fizgarshi irin na yau ba, a hankali ya shiga kallon d'akin, ba wata hayaniya ya yi sosai ba amma tsarinshi zai birgeka, dan komai a wurin kala biyu ne, idan ba maron ba to somon. Kujerun kansu ma su kyau ne da birgewa k'irar royal, sai carpet da ya yi kala d'aya da k'ananan pillow da ke kan kujerar, fridge da ba za ta wuce k'ugunshi ba, ga kuma teburin cin abinci mai d'aukar mutum takwas, sai allon bango da agogo, abu mai birgewa sosai da zai saka kallon wurin shine kwabar glass guda uku da aka cika ta mak'il da kwalaben turaruka, na ruwa da na wuta. K'arasawa ya yi gaban kwabar kamar wani dolo ya shiga kallo, abun kamar wanda aka mu su gorin turare, fari, kalar ruwan k'asa, ja, bak'i, yelow har da kalar shud'i, wani kamar dunk'ulen sugar, wani kamar tauraruwa, wani kamar tsinken sakace, wani ma doron zabuwa ne da shi, kai abun ma dai shi ya so ya fi k'arfin tunaninshi, a hankali ya mayar da kallonshi kan tv, su kam na shi ne su na nan ba a cire ba. Haka ya gama kalle kallenshi ya wuce duka sauran d'akunan ya na dubawa har da madafa, ita kan ta an gyara an zuba kayan aiki a ciki da kwanuka. D'akin baccinta ko kuma d'akin baccinsu ma ya k'ayatu, sai dai wannan turaruka da har gaban madubi suka cika wurin sun soma bashi mamaki, har saida ya ji ya tambayi kansa "To duk yaushe za ayi anfani da su?" Sai kuma ya yi murmushi yace "Lallai auren *batuba*, na auri batuba tare da k'amshi." Rufe d'akin ya yi ya bud'e d'ayan, zaro ido ya yi waje da sauri ya furta "Tohh! Me mutanen ne su ke nufi ne? Ni fa Faduma kawai na aura ba k'yale k'yale ba, zan iya zama da ita ko tsirara aka kawo min ita." Ajiyar zuciya ya sauke ya shiga k'arewa d'akin kallo, a take za ka iya cewa d'akin hutu ne aka yi, watak'ika ko dan sun san ya shafi jinin larabawa ne, ko kuma dai dan su ma tubawa su na da kamanceceniya sosai da larabawa musamman ma na Tchad, shi ya sa su ka yi wannan shirin, domin kuwa salon arab ne da pillownsu cike da d'akin farare sol, sai k'aton carpet mai kwalliyar fari da bak'i, sai kayan kallon da ya ke da tabbacin da su su ka zo, sai kuma manyan tukane farare masu walk'iya guda hud'u inda aka d'ora d'aya a kowace kusurwa, labulayen da aka saka ma masu kauri ne da tsada su ma farara tasss da su, abun kam ya birgeshi dan a take ya hango kan shi a k'asan carpet d'in kwance akan k'afafun Faduma ta na shafa kan shi yayin da hannunshi ke kan tulelen cikinta. 馃槒 _Kai kauce._ K'arasa shiga kawai ya yi da niyyar ya had'a mu su kayan kallon, dan ya ga basu had'a ba tunda ba aikinsu bane, sai lokacin ya kula da wata yar wadar fridge mai kama da kujerar zama, murmushi ya kuma saki a ranshi ya na ayyanawa "Lallai a shirye za ta zo, ko duk wa ya mata wannan siyayyar?" *Aji'ssss馃榿* Tashin hankali wanda zai iya kira da tashin hankali ya gani a rayuwarsa, girmansa da matsayinsa bai tab'a barinshi ya hangowa kansa wannan wak'i'ar ba, daga kotun nan da aka d'aukeshi da manyan motocin nan na shiga sahara aka sojawan nan su ka dinga papara gudu su na kutsa rai-rai da kowane irin gumurzu, shi dai ya san sun yi tafiya mai tsayin gaske kafin ya ji an dakata, ya na daga cikin boot ya ke jin maganganu amma bai san me ake fad'a ba, bai kuma san su waye ba? Bud'e boot d'in ya ji anyi hakan ya b芒 iskan Allah shigowa inda ya ke kwance kamar dabba. Bai gama bud'e idonshi dan ya ga a ina ya ke ba kawai aka rufe mi shi ido da bak'in k'yalle, ya ji an d'aureshi kuma tabbas mutum ne ya d'aukeshi a kafad'a, sai dai ya san koma wanene ya mi shi wannan d'aukar ya san ba k'arami ba ne, duba da shi ma d'in ba wani karen tsintsiya bane. Matakala ya ke jin ana hawa amma kuma ba wacce ke sada mutum da sama ba, in zai canka dai-dai tabbas k'asa ake yi da shi, shi dai bai tamtamce ba ya ji an jefashi kamar wani kayan wanki ya had'u da bango, saida ya yi k'arar wahala sai kuma ya yi shiru saboda jin an rufe k'ofar. *Tunda* al'amarin ya faru hankalin Bureima ya tashi matuk'a, babban tashin hankalin kuwa shi ne rashin sanin inda Aji ya ke, sauran yaran da aka kama duk an fad'a mi shi an kai su prison, amma d'anshi ne kawai babu a cikinsu, tun abun na kamar wasan yaran har ya fara tuntub'ar duk lambobin da ya ke ganin zai iya samun wani rahoton, amma magana d'aya kowa ke fad'a ma sa ita ce "Wallahi baya nan, babu ma mai kama da shi yallab'ai." Ganin abun ba na nutsuwa b芒 ne sai ya fara tuntub'ar manya kan a tambaya ma sa g茅n茅ral Wardugu ina ya kai mi shi yaron shi? Babban mutumin da a k'asa ake girmamawa ya samu Wardugu, amma ya k'ura ma sa ido har ya gama maganar shi su ka yi sallama bai ce k'ala ba. Saida kiran tsohon shugaban k'asa ya riskeshi ne saboda mutumcin dattijon ya sa Wardugu cewa "Idan ya na son ganin yaron sa ya zo da kan shi." Abin da ya fad'a kenan ya yanke wayar. Ya d'auka abun arzik'i ne haka ya shirya ya kawo hanyar Niamey. *Ofishin Wardugu* Kallon juna su ke kowa da abun da ke ran shi, Bureima kam burinshi d'aya ya bar wurin nan lafiya, batube ne shi gaba da baya, amma fa a cikin tubawan ma duk wanda ya san Wardugu ya na shakkarsa. Bud'e k'ofar da aka yi ta saka su kallon k'ofar a tare, Aji ne duk ya fita hayyacinshi ya lalace ya bushe, dan da alama bai cika samun ruwa ba y'a na sha sosai bare ayi maganar abinci, turoshi sojan ya yi ya juya ya fita bayan ya sarawa Wardugu. Da sauri ya k'arasa gaban Bureima ya rik'e k'afarshi cikin damuwa yace "Aba ka fitar da ni a nan, ka d'aukeni mu tafi Aba, wahala za ta kasheni." K'ura ma sa ido ya yi ganin kamar ba d'ansa ba, sai idonshi ma da ya ga kamar ba ya gani sosai, kuma d'akin duhun da aka saka shi ne ya jawo hakan, dan tun ranar bai sake ganin rana ba sai yanzu da aka kawo shi nan. Juyawa ya yi ya kalli Wardugu kallo na ka taimaka dan Allah ka rabu da yarona, cikin muryar rarrashi ya langab'e kai yace "Dan Allah Wardugu ka min rai, ka yi hak'uri ka k'yaleshi, ya tuba ba zai kuma ba." A hankali, a nutse, a sangarce ya mik'e tare da cire hular kakin shi ya aje kan teburin, cikin takon k'asaita da tayar da hankalin mak'iyi ya shiga takowa inda su ke ya na cire d'amarar wandonshi, kallon Aji ya ke da mayatattun idanunshi, saida ya tsaya gabanshi ya yi tsugunno irin na maza, cikin murd'add'iyar murya yace "Kalle ni nan." Da sauri ya kalleshi ya na mitsitsika idonshi dan bai cika gani ba sosai, duhu ya fi gani madadin haske, cikin muryar nutsuwa yace "Waye ni?" Da sauri kamar zai yi kuka yace "Kai g茅n茅ral ne." Lumshe ido ya yi yace "Ka san sunana?" D'aga mi shi kai ya yi alamar eh, a dak'ile yace "Me suna na?" Cikin muryar galabaita yace "Wardugu." Cikin wata razananniyar tsawa da har Bureima saida ya d'an mik'e sai kuma ya zauna yace "Cikakken suna na za ka fad'a min?" Da sauri cikin kid'ima ya cik'e cikinshi yace "G茅n茅ral Wardugu Marahut." Wani k'asaitaccen murmushi ya yi ya sake lumshe ido, bud'ewa yayi a kan shi yace "Ka san ma'anar Wardugu?" Shiru ya yi ya shiga wulk'ita idonshi alamar tunani, hakan ya sa Wardugu mik'ewa ya rik'o hannunsa a nutse, saida ya gyara belt d'in nan na hannunshi yanda ba zai fita daga hannunshi, ya sa ka k'afarshi ta hagu ya take k'afafun Aji, a gaban Bureima ganin idonshi, kamar al'amara kamar aikin aljanu, sai kawai Wardugu ya d'aga d'amarar nan ya shiga tsugawa Aji kashi a gaban ubanshi ya na fad'in "Kai marar kunya? Kai ne ba ka son zaman lafiya ko?" 馃ぃ *Kwate ta, ya yi halin fa* Tunda Aji ya ke a rayuwa bai tab'a shiga nadamar rayuwa ba kamar yau, shi ba yaro ba, shi ba mace ba, amma haka Wardugu ya ke shek'a mi shi belt a jiki inda shi kuma ya samu kan shi da sakin ihu ya na fad'in "Na tuba! Na tuba Wardugu, ka min rai, ba zan k'ara ba wallahi, ka yafe min, wayyo Allahna na mutu." Lallai sai yau ya tabbatar da wata magana da ya tab'a tsinta a gidan tv Wardugu na yi, sanda ya kama wasu yan boko haram ya na bayanin cewa duk wanda ya sake ya shiga hannunsa, to hak'ik'a sai mutum ya manta cewa shi d'in hallitar namiji ce ya yi ihu kamar mace, ai kam dai gashi ya gani, a hakan fa bai harbi kowa ba, bai kashe d'an kowa ba, amma gashi ya na ihu da neman taimako. Saida zuciyarsa ta tabbatar ma sa da cewa yanzu Aji ya ladabtu da bulalarka, a hankali ya sake shi ya share gumin gaban goshinshi, sake rik'e d'amarar ya yi da kyau ya juyo kan Bureima dan ya kora ma sa k'wak'waran kashedin kar ya sake ganin shi anan, ko kuma ya takura ma sa da neman yaronsa ta hanyar had'ashi da manyan mutane. Amma abun mamaki baya nan, Bureima baya nan ya b'ace a wurin, wani shak'iyin murmushi ya saki ya juyo kan Aji ya nuna shi yace "Wannan shi ne ma'anar *Wardugu*." Cikin muryar ingarman soja ya kira yaronshi da ya tabbatar ya na bakin k'ofar, amsawa ya yi shi ma da k'arfi ya na shigowa, nuna mishi Aji ya yi yace "A mayar da shi can." Amsawa ya yi da "A vos ordre chef." Nufa ya yi kan Aji ya na rik'e dariyarshi, shi fa ba Aji bane ya ba shi dariya, dan sun sha ganin irin haka ba yau ne farko ba, yanda Bureima ya fita a ofishin ne har ya na karo da shi ya b芒 shi dariya, da gudu fa ya fita ya na sab'a babbar rigarshi hula a hannu, ya na tafe ya na waiwaiye ya na fad'in "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un." Shi a ganinshi ko aikin shad'anu ne, ko kuma shi ma zai samu rabon tashi bulalar ne, tsofai tsofai da shi ya sa kashi a hannun d'an cikinsa ai abun ba kyau, shi ya sa ya hutashesa d'aukar alhakin tsufa ta hanyar sulalewa. *Allah ya bar min yan Allura, gingina gareku.* *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 21:42 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _72_ Kallon jiran k'arin bayani ne ta ke ma sa had'e da kallon tuhuma, tunda ya lura da haka shi ma sai ya sunkuyar da kan shi yace "Umma b芒 ta da lafiya, ta na gidansu tun ranar da abun nan ya faru." Cikin d'an fad'a fad'a tace "Yanzu kuma Hasheer shi ne ba ka fad'a ba? Ko me ta ma ka ai tsakaninku ne, ni ina ruwana da za ka sakani a ciki? Ai sai ka fad'a min ni na je na ganta." Sake sadda kan shi ya yi k'asa yace "Ki yi hak'uri Umma, ni na manta ne ma tun ranar da suka sanar min?" Cikin hararnshi tace "Saboda ka na zumud'in amarya ne har ka manta da uwar gidanka?" Girgiza jaii ya yi a hankali alamar a'a, d'orawa tayi da "To kaga ni ba dani ba, ka je ka dubo matarka dan har yanzu ta na da hakk'i a kan ka, ko kuma ka saketa ne ban sani ba?" Girgiza kai ya sake yi alamar a'a, cikin taushin murya yace "Umma zan je, amma kinga yanzu tafiyar nan ce gabana, idan na dawo sai na tafi." Jinjina kai ta yi tace "Shikenan, Allah ya kaiku lafiya ya dawo da ku lafiya." Da "Ameen." Ya amsa ya na mik'ewa, kallon d'akin Salima ya yi ya kalli Umma yace "Umma ba zan iya ganinta ba ko kad'an?" Saida ta had'e fuska tace "Ko kad'an, na fad'a ma ka suna cikin aiki ne, ko da ba ka sameta gidan ba sai ka sameta gidanta ai." D'an murmushi ya yi ya na fad'in "Umma da girmana zan je gidanta?" Zaro ido ta yi ta kalleshi tace "Au! Haka ka ce? Ka manta mahaifinku shi ya ke raka 'ya'yansa gidansu, ko ka manta da kanshi ya raka Meena d'akinta ne, dan ban titsiyeka ba na ce sai ka sadata da d'akinta?" Dariya ya yi da sauri ya fita a d'akin dan kar rigimar ma ta motsa tace dawo haka za ayi ma, mik'ewa ta yi ta koma d'aki inda Marfu'a ta tub'e Salima ta na mata gyaran k'arshe, har ta yi wani jawur da ita a haka ma aka barta za ka iya k'ura ma ta ido ka na kallo ba tare da ka gaji ba. *Ranar biki* A gidansu Mama mak'wabtan su Faduma a maradi aka d'aura auren dada, tsofaffin sun ji dad'i sosai na wannan karamci da mutumci da suka mu su. A can kuma biki su ke sha sosai dan har su Ayya yau su ke na su bikin, Faduma dai na d'akin Herde ita kunya ce ma ta rufeta wai ana bikinta bayan ga ta gidan, da haka har su ka yi waya da Hasheer ya ke fad'a ma ta gasu fa a kan hanya, hakan ya sa gabanta tsinkewa ya fad'i har tace "Hanyar ina?" Da wani murmushi ya amsa ma ta da "Hanyar garinku mana, zan je d'aukarki da kai na." Fashewa ta yi da kuka da gaske ta na fad'in "Wayyo Allah, yanzu wai rabuwa zan yi da Aba na? Shikenan ni Fati zan zama marainiya." Lumshe ido ya yi a hankali yace "Rigima ko? Ba damuwa bari na shigo, idan ki ka zo gidana za ki maimaita da bakin ki." Cikin turo baki tace "Ka yi hak'uri, ni ba komai na ke nufi ba." Aunty Leeya ce ta fizge wayar ta na fad'in "Daga yanzu har sanda za ku had'u babu magana ko ta waya." Tunda ta karb'i wayar ta sa a jakarta ba ta bata ba ita ma kuma ba ta nema ba, haka su ka yi ta rak'ashewarsu su na bikinsu a nutse bikin 'yar gatan Abanta da Ayyoyinta. *05: 30* na yamma motoci k'irar hilux su ka shiga tsayawa a k'ofar gidan, komai cikin dattako da girma ake yin shi, kamar yanda aka gama tsara komai mace goma za su tafi, biyar a wurin Faduma biyar a wurin Owwo, kuma abin da ba su sani sai yanzu shi ne satar jirgi aka d'auka, ba wai a mota za su tafi ba, hakan ya sa matan da za su tafi shiga wasi-wasi da jin d'ar na shiga jirgin, Herde ce kawai babu wannan a tare da ita dan sun tafi saudia sanda aka bawa Faduma kujerar hajj, kace-nacen da aka tsaya ya sa har 06:00 ta mu su dai-dai kafin matan su ka fito. Amma fa akwai abu d'aya da ya saka angayen shiga rud'u shi ne rasa amarya Faduma. Kafatanin gidan Herde da gidan Hadizey an yi nema bata nan, matan hakan bai dame su ba dan al'ada ce b'oye amarya, sai dai su ma basu san ina ta b'oye ba bare su fad'a, tun abu na kamar wasa har aka yi sallah magrib aka gama babu ita babu labarinta. Hasheer da hankalinshi ya gama watsewa ne su na waya da Wardugu yace "Wardugu har yanzu ba a san ina ta ke ba, ta ya za m没 zauna anan jiranta? Ka na ganin ba wata matsala?" Cikin son kwantar ma sa da hankali yace "Babu wata matsala, ka kira wayarta ka ji ta na ina?" A wahalce yace "Ina yi ta kiranta Wardugu, tana kururuwa amma ba a d'agawa." Cikin rarrashi yace "Ka gane? Kar haka ya d'aga ka hankali, al'ada ce kowace mace ta na yin haka, idan ba ka yi wasa ba za ku iya kai asuba wurin nan." A sanyaye yace "Wardugu in dai ta na cikin k'oshin lafiya wallahi ko shekara zan yi a nan ina jiranta." Murmushi ya yi yace "To Allah ba da sa'a, ni ma haka na yi lokacin aure na da Walyn, 09:00 na aika motoci, amma sai daf da asubu aka kawota gida na." Murmushi shi ma ya k'ak'aro yace "Amma dai na san da ka zo wurin da ka nemota." Murmushi shi ma ya yi yace "Kai ma yanzu satar amsa zan ba ka, ku duba inda a tunaninku ba za ta kai can ba." Da d'an mamaki yace "A ina kenan?" Murmushi ya yi yace "Ta na gidan nan ba ta fita ba, akwai in da ake ganin mutum ba zai zauna anan ba, to ta na wurin." Da sauri ya katse kiran ya na juyawa ya kafe k'ofar gidan da kallo, duk sun yi cirko cirko musamman ma mazan, kowa sai safa da marwa ya ke ya na shafar sumar kai, sake kiran wayarta ya yi a daidai lokacin Leeya ta fito da wayar ta na nunawa su Herde ga wayarta nan, d'auka ta yi ganin babu suna sai kawai yace "Kina ji na?" Da sauri tace "Eh, ba mai wayar ba ce." Da sauri shi ma yace "Na sani, Hasheer ne." Da kunya da kuma ladabi tace "Au! Ina wuni?" A tak'aice yace "Lafiya lau, a gidanku d'aki nawa ne a ciki?" Da mamakin tambayarsa tace "Uku ne bayan ban d'aki, d'aya na Aba, d'aya na Ayya sai kuma na Abbakar." A hankali yace "Duka kun duba bata ciki?" Cikin muryar alhini tace "D'akin Aba dama a rufe ya ke da kwad'o, d'akin Ayya kuma an duba har k'asan gado bata nan, na Abbakar kuma dama ba makulli gare shi ba, kaga kenan ba za ta b'uya a ciki ba." A dake yace "Wa y'a fad'a mi ki? Je ki duba a ciki, tana nan." D'an kallon Herde ta yi da ke kallon ta ita ma, sai kuma tace "To shikenan." Mik'awa Herde wayar ta shiga ciki, ya na hangensu daga nan ya saki murmushi a ranshi yace "Wannan dalilin ne dama ya sa Wardugu nema mana alfarmar duk sanda mu ka zo za a bamu umarnin tashi? Hmm!" Wata irin gud'a Leeya ta yi daga ciki dake nuna farin ciki, dan dama tubawa na da al'adar gud'a a kowane yanayi mabambamta, akwai gud'ar da ana yinta za ka san ba lafiya ba. Tuni matan da ke waje su ka rankaya cikin gidan su na amsar gud'ar suma tuni suka cika unguwar, yara ne ke fad'in an ganta an ganta, daga in da yake ya cije leb'e yace "Zan hukuntaki abisa haka Teema." Basu bata damar sake ganawa da mahaifiyarta ba bare mahaifinta, duk da sun gana sosai tun kafin zuwansu, hakan ya haddasa ma ta kuka mai tsananin gaske, amma yanzu ma da za su bar ta da ta je ta rumgume su. Motar su ka dannata tare da Herde da aunty Nana, sai sauren matan da za su tafi su ma su ka shiga aka tayar ana bin su da addu'a. A hanyarsu ta isa filin jirgi Abdallah ke sanar ma Hasheer "Ni fa wallahi nan da minti biyar idan ba ta fito ba fad'awa zan yi cikin gidan na nemota da kai na, haba dan Allah tasan tanadin da na mata kuwa a daren nan take son sai na b'ata lokaci a nan." Dariya Hasheer ya yi shi ma ya d'orashi a hanya kafin ya datse kiran, ko da su ka isa can sai da su ka jirasu kusan minti ashirin kafin su ka iso su ma. Hangenta ya ke daga in da take zaune kanta a k'irjin Herde sai rarrashi ta ke, murmushi kawai ya ke saki ya na ji ina ma za ta juyo ta kalleshi? Da ido kawai zai fad'a mata abinda za ta fahimceshi, ko ba ta yi shiru ba za ta mi shi murmushi. *A gurguje* Amare sun sauka lafiya cikin hukuncin Allah, inda nan ma motoci ne su ka taresu aka nufi da kowace gidanta, ba wani abun a zo a gani da aka yi dan al'adarsu haka take, bak'i dai duk gidan Umma aka samu mu su masauki bayan sun ci mai kyau sun sha mai kyau. Gidan ya yi shiru a lokacin d'脿 ya shigo, dama su Izzadeen su na gida wajen Umma, dan haka kai tsaye b'angaren ya wuce cike da zumud'i, saida ya fara shiga d'akin da har yanzu kayan nan su na nan yanda ya watsasu ya kasa gyarawa ya yi wanka ya shirya ya fito. Da sallama ya jawo k'ofar ya shiga ya mayar ya rufe, tsayawa ya yi ya na k'are ma ta kallo cike da tausayin yanda ya ganta, ba yarinya b芒 ce, ba kuma budurwa ba a zahiri, sannan ba jahila ba bugu da k'ari ta na da wayewar zamani, amma ba tayi halin wasu 'yan matan ba, ba ta yi azarb'ab'bi ba ta na nan yanda aka kawota, lafayarta ce fara tas marar kwalliya, ta had'a kai da gwiwa sai shashek'ar kuka ta ke, k'arasawa ya yi a hankali ya zauna kusa da ita ya na kallonta, cikin nuna tashin hankali yace "Subhanallah! Titi kuka ki ke saboda an kawoki gida na?" Wata shashek'ar ta yi ba ta ce komai ba hasalima ko d'agowa ba ta yi ba, ba tare da ya d'auke idonshi daga kan lallen da aka ma ta ba na tukunya yace "Na d'auka farin ciki za ki yi, ashe dama ba so na ki ke ba." Ba ta d'ago kan ta ba haka b芒 ta tanka ma sa ba, ajiyar zuciya ya yi y'a zuro hannayenshi ya tallabo fuskarta, rintse ido ta yi hakan ya sa gashin idonta da ya harhad'e ya kwanta ruf a bayan fatar idon ta k'asa, d'an k'ok'arin k'wace fuskarta ta shiga yi amma sai ya k'i bata damar hakan, a hankali yace "Kalleni." Sake lik'e ido ta yi ta fashe da kuka marar sauti, yanda bakinta ya d'anyi fad'i ne ya sa shi k'urawa bakin ido, cikin rikitacciyar murya yace "Ki na so ne na mi ki irin na ranar can?" Da sauri ta girgiza kai, murmushi ya saki ya na k'arewa fuskarta kallo da hannayenta da suka bayyana, ya na mamakin yanda a sati biyu ta yi wata iri d'anya shakaf da ita, sai wani irin shek'i fatarta ke yi ta na d'aukar ido, ga k'amshi na daban da ke tashi jikinta wanda sam bai ji irinshi a duk cikin turarukan nan ba da suka rigata isowa gidan. Cikin farin ciki yace "To mu je mu yi alwala." Jinjina mi shi kai ta yi alamar to, amma kuma ba ta motsa ba, mik'ewa ya yi tare da rik'e hannunta har ya fara shiga ban d'akin, tsaye ta yi amma kanta a k'asa ta na dai jin kiciniyar shi ya na alwalar, har ya kammala ya kalleta yace "Bismillah." Ba ta motsa ba saida ta ga ya fita ta shige ciki ta rufo k'ofar, wata wawuyar ajiyar zuciya ta sauke ta bud'e idonta akan ban d'akin, d'an bud'o ido ta yi da kyau a ranta ta na ayyana "Duk wannan ban d'aki ne?" Saida ta gama kallo ta samu ta kama ruwa ta yi alwala ta fito, ta na zuwa ta samu ya shinfid'a sallaya, daga yanda ya tsaya gabanta ya sa ta d'an komawa gefe kad'an ta tsaya bayanshi ita ma, juyowa ya yi ya kalleta ya na murmushi yace "Alarammiya ko za ki ja mu ne?" Girgiza kai ta yi cikin sauke ajiyar zuciya, kafeta ya yi da ido yace "Amma ai ki na da hadda, za ki iya ke ma?" A tak'aice karo na farko ta bud'a bakinta tace "Na manta nima." Zaro ido ya yi yace "Hadda?" D'aga ma sa kai ta yi alamar eh, girgiza kai ya yi ya na murmushi ya juya, cikin nutsuwa ya kabbara sallah tare da shiga suratul nisa'i bayan fatiha, a suratun nisa'i ma saida ya shiga tsakiya tsumdum inda ake maganar yanda za ayi saki da kul'i, dagangan ya saki aya ta gaba da za ta yi magana kan shayarwa ya shiga ayar gabanta, jin da gaske k'arshenta zai kai ya sa Faduma d'an yin gyaran murya cikin nutsuwa da cewa "Ughum." Shiru ya d'anyi na dak'ik'un sakanni sai kuma ya d'ora, sake gyaran muryar ta yi, amma ya nuna sam bai fahimta ba sai kawai tace "Subhanallah." Dakatawa ya yi ya na ji a ranshi shi kam ta ma cinye jarabawarta ta wannan daren, kawai mataki na gaba za su je bayan ya ciyar da ita, dan wata nutsuwa ya ji ta na tsarga ma sa da jin cewa lallai yanzu ya more mata, ai komai munin mace inda ta samu addini a rayuwarta to ta gama komai, dan da iliminta za ka ji dad'in rayuwa, da wannan ilimin za ta kula da kai da yaranka. Komawa baya ya yi a sannu sannu har su ka kammala raka'arsu biyu ba wata mai tsayi ba. *02:45* A tsorace ta farka daga baccin da ya fara gigin d'aukar ba jimawa, mugun tsoron shi da ya d'arsu a zuciyarta tunda ya shigo ma ta d'akin da singlet ya sa ta shan jinin jikinta ta kasa sakewa ta kwanta, haka ya yi rarrashin duniya amma ta ce ba ta jin bacci, zaune ya yi a bakin gadon ya na latsa wayarshi, kallonta kawai ya ke ya na dariya, wai ita fa tsoronshi take? Sai dai ya kalleta kawai ya bushe da dariyar tausayinta, dan har mamaki ta ke bashi kamar ba mai surutun nan ba idan ta yi niyya. Shi ne fa ya na ganin bacci ya d'auketa a kan kujerar gaban madubin ya d'aukota ya dawo da ita kan gadon. Mik'ewa ta so ta yi sai kawai ya ma ta runfa da k'irjinshi, kallon idonta ya ke son yi ita kuma ta rufesu sai bakinta da ya d'auki b'ari, cikin murmushi yace "Bud'a idonki." Girgiza kai ta yi sai ma jikinta da ya k'ara kwasar rawa, a take k'wak'walwarta ta fara hasko ma ta waccen ranar, ranar da ta samu kusanci da namiji irin haka, ranar da aka ma ta k'arfa-k'arfa aka rabata da komai, sanda ya zura hannunshi zai warware ma ta lafayar jikinta, a lokacin kuma ta tuna sanda Tagur ya ratsata ya wuce, da wani irin k'arfi ta tureshi tare da daka ihu ta na fad'in "Ahhhhhhhh! Ka rabu dani." Ganin za ta mik'e kuma alamu ya nuna duk a tsorace ta ke ya sa shi saurin komawa kan ta ya rumgumeta tsam a jikinshi, tallabo kan ta ya yi da hannunshi ya d'ora bakinshi dai-dai kunnenta ya furta "Zahra *ni ne*, mijinki ne, ki nutsu." Dakatawa ta yi daga mutsu mutsun da take sai dai ya na jin jikinta na ta rawa kamar wacce zazzab'i ya kama, idonta a rufe sosai leb'enta na rawa hawaye na silalowa ta furta " *Kar ka yi*, kar ka min komai, tsoro na ke ji." Sake mannata ya yi a jikinshi yace "Shiiiiiii! Babu abin da zai faru da ke kin ji, kwantar da hankalinki." D'an hura ma ta iskan bakinshi ya yi a fuskarta yace "Kayan nan na ke son rage mi ki, sai ki yi bacci kin ji." Jinjina ma sa kai kawai ta dinga yi alamar to, ta na ji ya warware ma ta lafayar har ya cireta gaba d'aya ya rage riga da zanin da aka bata ta saka ne, tallabota ta ji ya yi ya zare ma ta zip d'in rigarta, ta sama ya zage ma ta rigar hakan ya sa kunya kamata duk da idonta a rufe suke kuma ta na da bras, rik'e rigar ta yi gam sai kawai ya sakar ma ta, k'asa ya yi da hannunshi ya since d'aurin da ta ma zanin a bayan k'ugunta. Sinne kanta ta shiga yi ta na girgiza kai ta na hawaye, tallabo fuskarta ya yi ya na kallo yace "Binta, halak d'in ki ne yau, ki yi biyayya ga ubangijinki ta hanyar faranta min raina." Nok'ewa ta sake yi ta fashe da kuka ta na rufe fuskarta, rumgumota ya yi jikinshi ya saka yatsu biyu ya b'alle ma ta bras d'in, saida ta k'ara lumshe ido ta d'an damk'i hannunshi da ke kan cinyarta, a hankali ta ji ya kwantar da ita shi ma kuma ya hau ruwan cikinta ya jawo lallausan bargo ya rufesu ciki kirip. Sosai ya yi aiki da ilimi da hikima wajen mayar da ita babbar mace a farlance da kuma sunnance, kai shi dai yau ba dan kar a ga wautarsa ba da sai yace budurwa ya samu a bar sa, ya gode Allah sosai da ya d'auke hankalinsa da tunanin wani ya rigashi isa wajen, ya gode Allah da ya samu murmushinsa a haka, hakan ya tabbatar ma sa za ta tabbata a *murmushin na sa*. A hankali ya ci gaba da saka kayanshi ya na kallon yanda take ta shashek'ar kuka, murmushi ya saki da shi kad'ai ya san ma'anarsa, gaskiya yanda ya ga tsoro da fari a tare da ita da kuma matsancin rud'u, ya d'auka za ta ma sa billi ta tara ma sa jama'a, amma abun mamaki da birgewa shi ne yanda ta iya d'aukeshi tsaf ba tare da raki ko hargagi ba, hasalima idonta a rufe su ke tana b'oye kan ta a k'irjinshi, sai dai ta yamutsa fuska kawai ko ta cije leb'e, sa sam ba ta nuna ma sa gajiyarta ba ko ta ce wayyo ko wash, duk da ya bita sannu sannu amma ya san ta yi juriya, ya san ta yi k'ok'ari da ta daure, dan sosai su ka sha gwagwarmaya wajen isa bakin gab'a, hallitarta da k'aramta ga kuma gyara da ta samu, shi kuma ta shi hallitar da rik'iwa...馃槑 Ya na gama saka kayan tsaf ya d'an sunkuya ya daddab'ata yace "Fati." Ba tare da ta amsa ko ta juyo ba ta tashi zaune ta na dunk'ulewa cikin hijabinta, kallon fuskarta ya yi da ta fara kumbura saboda kuka, a gaskiya ba dan ya yi alk'awarin cika duka al'adun nan ba, da yau kam bai ga mai fitar mi shi da mata waje ba, musamman da tasha aiki tuburan ta karb'i horo daga gareshi mai gajiyarwa, ba dan alk'awari ba da sai ya kwanta gefenta ya na daddab'ata har ta yi nauyayyen mai bacci mai dad'in gaske, to ammaa ya zai yi? Dole ya k'arasa tunda iya na yau ne kawai. A hankali ya kama hannunta yace "Mu tafi." Cike da kunya ta k'i yarda su had'a ido sai kallon k'asa da take har ta sauka su ka fita a d'akin, bai saki hannunta ba har ya bud'e mota ya zaunar da ita, shiga ya yi ya tayar su ka bar gidan inda mai gadi ya bisu da addu'a da mamakin ina za su tafi haka da asussuba? Bai yi wani gudu dan ba nisa ne dasu Umma ba, a k'ank'anin lokaci ya tsaya cikin farfajiyar gidan, a tsorace ta kalleshi cikin muryar da ta sha kuka tace "Nan zan zauna?" D'aga ma ta kai ya yi tare da gira yace "Eh, haka al'adar ta ku take, kinga ke kuma ba a garin nan ki ke ba, kuma a k'aida a na kai mace ne gidansu, shi ya sa aka ce na kawo ki nan tunda su Ayyarki (Herde)su na nan." Wata nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke ta sunkuyar da kai ta na tunanin ya za ta fara shiga gidan? Bayan k'afafunta sunyi sanyi zama kawai take iya yi, yanda aka tallabe ma ta k'fafun nan aka dinga hak'arta ya sa k'afafunta ba sa d'aukarta. Ta na cikin tunaninta ta ji ya bud'e mazauninta, da sauri ta d'aga kai ta kalleshi sai gani ta yi ya durk'usa gwiwarshi d'aya a k'asa, d'aya kuma ya tokareta kamar yanda jajaayen nan ke neman amincewar mace dan ta auresu, ta na tsaka da mamaki ya taro tafin hannunshi na dama kusa da inda k'afarta za ta sauko yace "K'afarki *gimbiya Faduma*?" Da sauri ta bud'e baki irin malakin nan, sai kuma ta rufe ta girgiza ma sa kai, da ido ya ma ta alamar "Maza d'ora min k'afarki anan?" Da sauri ta sake girgiza kai kamar za ta yi kuka tace "A'a, ba zan iya ba babban mutum, ba zan ji dad'i ba." Nuna kan shi ya yi ta hanyar d'ora hannunshi a k'irji yace "Ni na fad'a, haka kuma na ke so a yi, indai ni mijinki ne." Tsatsareshi ta yi da idonta kamar za ta had'eshi da su, a hankali ta cire takalminta plat ta zuro k'afar dama a hannu har ta d'ora akan tafin hannunta, rik'e k'afar ya yi ya d'ora akan cinyarshi ya saka hannu aljihu, sark'ar k'afa ya ciro mai kyau guda biyu, d'ayar ya d'aura ma ta a k'afar sannan ya kamo d'ayar ma da niyyar d'aura ma ta, da sauri ya kalleta ganin sark'ar da Ummi ta b芒 ta, d'aga kai ya yi ya kalleta da mamaki yace "Wannan ai kamar sark'ar..." Sai kuma ya yi shiru ya na ci gaba da kallon k'afar 'yar d'agwas da ba za ta gaza d'aukar lambar takalmi talatin da takwas zuwa da tara ba. Hannu ya sa zai b'alle sark'ar ta yi saurin janye k'afarta ta na fad'in "A'a." D'agowa ya yi ya kalleta kallon ina jin ki, sunkuyar da kai ta yi tace "Kar ka cire min dan Allah, Umma ce ta bani ita, kuma na ma ta alk'awarin kula da ita har abada." Wata ajiyar zuciya ya sauke tare da murmushi ya sake kamo waccen k'afar ya sak'ala ma ta gudar, hannu ya zura ya d'auko takalmin da ta bari a motar ya aje ma ta k'asa ta saka, mik'ewa ya yi tsaye tare da kamota ta fito, nan ma hannu ya sa aljihu ya kamo hnnunta na hagu ya saka ma ta yan hannu na zinariya ma su guda hud'u, haka ma hannunta na dama sai da ya saka ma ta, sannan ya saka ma ta zobe d'aya d'aya a kowane hannu. Aljihun gaban rigarshi ya sa hannu ya ciro tartsetsetsiyar sark'a zai saka ma ta ta yi murmushi ta na sunne kai, d'an lek'a fuskarta ya yi yace "Ya dai?" Sake sinne kai ta yi tace "Na d'auka kud'i ko takarda da alk'alami a ke ajewa a aljihu, ashe harda shagon kayan k'yale-k'yale ma na mata." Jawota ya yi jikinshi ya rumgume tare da saka ma ta sark'ar yace "To ya na iya na auri batuba, an fad'a min dole na kawoki gida da asuba da kyautar da ki ka cancanta, an fad'a min wannan shi ne k'arshen kyauta mai daraja da zan iya baki a ganta da girma." D'agowa ta yi daga jikinta ta na sunkuyar da kai tace "Nagode, ka min kyauta duk da ban kawo ma..." Rufe ma ta baki ya yi ta hanyar had'a bakinshi da na ta da k'arfin da ke nuna maganar ce ba ya so ta fita a bakinta, da wani irin salon mugunta mai tafiya da numfashi ya shiga tsotsan bakinta har da tukuicin cakumar tattausan bayanta ya na matsawa da d'an k'arfi, ta na so ta fizge kan ta amma sai rik'eta ya ke k'am a jikinshi, d'an baya ta ja da k'arfi hakan ya tilasta mi shi fizgota da k'arfi ta fad'a k'irjin ba shiri har saida ta saki siririyar k'ara. Hakan ne ya sa shi sakin bakinta ba tare da ya raba jikinsu ba, saida ya kalli tsakiyar idonta duk da akwai duhun subahi, saida ya had'e fuska yanda za ta fahimci girman lamarin, saida ya k'ara matse damatsenta sosai har ta na matse fuskarta kamar za ta yi kuka sannan ya bud'a bakinshi cikin dakusashiyar murya yace " *Kar ki k'ara*, ina da *kishi sosai*." Raba jikinsu ya yi ya kalleta yace "Kin fahimta?" Da sauri ta jinjina kai dan ita dai tsoro ne ya bata ma, ga wani ciwon da taji ya dad'a k'ara mata a jiki, ga kuma k'afafunta da take jin su na rawa sosai ba lallai ta shigar da kan ta d'akin can ba. *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 21:42 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _73_ Sakinta ya yi ya ma ta alamar ta wuce, a hankali ta shiga takawa ta na jin k'afafunta na ma ta wani karrrr! Haka ta daure ta shiga k'arasawa ko juyowa ba ta yi ba, saida ta shiga falon da sallama ta ji ya tashi motar ya fita a gidan. Herde ce a falon da alama alwala ta yi za ta shiga d'akin da aka sauke su, ai da kukan shagwab'a ta k'arasa gareta ta rumgumeta, da sauri Herde ta d'ago kanta ta na fad'in "Fadun Abanta, har kin zo? Shi ne ya kawoki ko?" D'aga ma ta kai kawai ta yi ta sake kwantawa kan kafad'arta, murmushi ta yi ta na kallon fuskarta tace "To mi ye na kuka kuma? Muje d'aki na jie ya faru? Kinyi sallah ne?" Girgiza kai ta yi su ka juya za su shiga d'aki Umma ta fito ita ma, ganinsu ya sa ta k'arasowa da fara'a ta na fad'in "La-la-la! Faduma ke ce ashe? Na ji k'arar mota dama na yi tunanin shi ne." Da wata irin matsananciyar kunya ta sadda kan ta k'asa ta durk'usa har k'asa tace "Ina kwana Umma?" Da fara'a ta k'arasa ta mik'ar da ita tsaye ta na kallon fuskarta da ta sha kuka tace "Haba dai Faduma, ke fa 'yata ce, ba na son haka kin ji, kar ki k'ara." D'an d'aga idonta ta yi saboda jin muryar da ta yi magana da ita sak ta Hasheer, bambancin kawai shi namiji ne ita kuma mace, kallon Herde ta yi tace "Ku wuce ciki ku yi sallah." Cike da kunya ta shiga takawa tare da Herde da ke ta jawota a jikinta har suka shige, su na shiga ta gaishe da su aunty Nana da Leeya da aka taho da ita, ta ji dad'in ganin yer uwata dan haka ma su na gama sallah su ka mak'ale da juna ta na kwance kan k'afafunta, hannu ta d'ora a kan ta ta na shafawa har ta ture lafayar kan ta, da sauri ta zabura ta mik'e zaune ta na hararenta murya k'asa k'asa tace "Dan Allah mi ye haka?" Da mamaki Leeya tace "Mi ye haka kamar me?" Saida ta saci kallon su Herde tace "Sai kin nuna mu su kai na a jik'e ya ke da ruwa." Basarwa ta yi ta nuna b芒 ta fahimta ba tace "Ban gane ba? Wani abu ya samu kan na ki?" Komawa ta yi ta kwanta a k'afafunta tace "To fad'a mu su na yi wankan tsarki mana hankalinki ya kwanta." Dariya Leeya ta yi kafin ta d'ora hannunta ta shiga cire ma ta sark'ar nan da yan kunne da duk abin da ya saka ma ta, mik'awa Herde ta yi da hannu biyu tace "Ayya ga kyautar 'yarki." Da sauri ta karb'i ta na washe baki, ta na amsa ta zube gabansu da su aunty Nana, wata uwar gud'a su ka saki irin ta amare cikin farin ciki, su na tsaka da gud'ar Dada ta shigo d'akin da sallama ita ma. Faduma bata san lokacin da ta saki dariya ba a b'oye, yanda ta ga Dadar ya bata dariya sosai, hakan ya sa dada nunata da yatsa tace "Faduma zan ci uwarki fa." Shiru ta yi da bakinta ta na b'oye dariyar, ratsasu ta yi ta shige ta zauna sai kumburo baki ta ke, saida ta gama kallonsu tsaf tace "Duk ina kwananku?" Amsa ma ta su ka yi da kulawa, Leeya ce ta d'an zura hannu ta d'aga lafayar kusa da hannunta, jawo hannun Dadar ta yi ita ma ta shiga cire ma ta na ta tsarabar, nan ma gud'a aka yi da jin dad'in yanda su ka samu maza ma su kara da karamci haka, duk da babu wacce ke tare d'脿 budurci amma su ka mu su kyautar ban girma haka? Da sallama Halima ta shigo d'akin hannunta d'auke da babban faranti, gaishesu ta yi a ladabce ta hangi Faduma ta sake fad'ad'a murmushinta tace "Ukhtee ya ki ka kwana?" Cike da kunya kamar ta na gaban Umma tace "Lafiya k'alau." Kofofin da ke kan farantin ta shiga d'auka da d'ai-'daya ta na mik'a mu su, karb'a su ka yi wasu na bin ta da godiya wasu kuma da addu'ar albarka. Ta na fita su ka fara shan abin da ke cikin kofin, madara ce kindirmo mai sanyi da inibi a ciki, tsabar yanda ya ma Faduma dad'i ya saka ta lumshe ido, Herde kam cewa ta yi "Haba shi ya sa duka gidan kowa jajir da shi uwa nuna ranar, ashe tunda asuba su ke farawa da shan madara." Dariya aka yi sai dada da tace "To ai gidan ma su abun ne, madarar nan ma na tabbata cikin abubuwan da su ke sarrafawa ne." Da irin haka su ka dinga hira cikin nishad'i, Faduma kam a matse take da su keb'e da dada dan ta san akwai magana bakinta, shigowar Halima biyu ta na sake kawo mu su cake da kuma tsiren nama zalla had'e da tumatir da albasa, a hakan fa ashe kafin abun karin kumallo ya k'arasa ne ake mu su wannan tanadi. Ana kawo mu su abun kari duk had'amar mai had'ama sai da suka barshi, ko ba su ga kan akuya ko ragon da aka yanka ba sun tabbatar wannan nama wata dabbar ce aka yanka, ga gurasa da ta amsa sunanta had'e da shayi da yaji citta da na'a-na'a, su na k'oshi kam Nana ta kalli Faduma tace "Kinga to zo na since mi ki kitson nan m没 shiga sabo." Dama guda shida ne a kan ta, da k'yar ta bud'e kan dan ita kunya ta ke ji a ga kan ta da lema, cikin sa'a kuma kan ya bushe sai abin da ba'a rasa ba kawai, nan Leeya ta since ma ta kafin su ka shiga kitso, dada ma kwance na ta tayi mai kitson da ta kira ta zo nan ta sake ma ta sabo. Da ke sun fara da wuri sai gashi ko da k'arfe 02:00 ta buga na rana an gama, dan k'anana aka mu su mai kyau da birgewa, musamman Faduma da tafi dada tsayin gashi nesa ba kusa ba. Sallah su ka yi sun zauna za su fara cin abinci da aka kawo Halima ta shigo ta kalli Faduma tace "Ukhtee Umma na son ganinku ke da auntynki." Da murmushi ta jinjina mata kai kawai ta mik'e tare da dada su ka fita, har d'akin Umma ta mu su iso su ka shiga da sallama, ba su k'arewa d'akin kallo ba dan Umman na ciki, guri ta nuna mu su suka zauna kafin ta mik'e za ta fita ta nuna mu su kwanon da ke rufe tace "Ku hanzarta ku cinye wannan, ayyar g茅n茅ral ce ta aiko mana shi, had'i ne mai kyau a jikin mace da ke jimawa a jikinta, a k'alla haihuwa ce kawai ke karya tasirin maganin (tukunya kenan, kwate馃槹), Salima ma ga na ta nan za'a kai ma ta." Dada ce kawai ta yi murmushi tace "To, mun gode sosai." Da murmushi kawai Umma ta fita dan ba su damar ci d'in a tsanake, ta na fita dada ta jawo kwanon ta bud'e ta saka hannu, dahuwar ta dahu sosai ga k'amshi sai dai za ka ji d'and'anon magani a bakin ka, kallonta Faduma ta yi tace "Dada na ta fa ki na ta kumbura kamar ubanmu ya mi ki laifi, shi ne kuma za ki sake wani d'uren?" Kallonta ta yi ta nunata da yatsa tace "Ke bari ma kiji wallahi, wannan yaron na gama auren shi har abada, ki tsaya min kawai na kai k'ararshi a raba aurenmu, ke ba zan iya jarabar yaron ba sai ya kasheni." Tunda ta fara magana ta ke dariya ta na rik'e ciki, cikin jin haushi ta kalleta tace "Ke dubi ido na, wallahi tunda na je gidan nan ban rintsa ba, abu d'aya kamar kukan tsohuwa, wai shi dole ya more tunda ya yi aure, kuma ina rainashi ina ce ma sa yaro." Tsaki ta ja da yin k'wafa ta na fad'in "Ba sai na koma gidan b芒." Cikin dariya Faduma tace "A'a wallahi za ki koma, ubanmu ai ko nan zai shigo ya kwasheki." Da sauri Dada ta kalleta ta d'aga lafayarta ta d'an zame rigarta k'asa, hakan ya ba nononta damar fitowa da babu bras tace "Dubi yanda nono na ya yi, a tsaye suke cirr kafin shekaran jiya, amma ji har sun fara sujada, ga ciwon bala'i da suke min." Jinjina kai ta yi irin haba d'in nan ta ci gaba da cin naman nan, a hankali Faduma ta sa hannu tace "Dada sharrin gyaran da mu ka yi ne, gashi kuma za'a k'ara mana wani." Da sauri kuma ta kalli Dada tace "Dada, wai dama haka abun ya ke ba dad'i sam, amma shi ne har da b芒 wa kai wahala na gyara." D'an k'aramin tsaki ta yi hakan ya sa dada bushewa da dariyar bak'in ciki tace "Fadu da alama an ji jiki ke ma, ai na tausaya mi ki wallahi, da naga ni kaina wahalar da na sha kuma yaron nan bai kai girman mijinki ba, hmmm! Da wahala fa." Kallon dada ta yi tace "Ba za ki daina kiranshi yaro ba kenan?" Yatsina fuska ta yi tace "Ke rabu da shi." Haka su ka ci gaba da hirarsu cikin nishad'i su na dariya har su ka gama, basu bar d'akin ba dan yanayin d'akin da ni'imtaccen k'amshi da sanyinshi ya sa shi yi mu su dad'i su ka zauna, dan Faduma har tunani ta ke a cikin d'akin ayyar g茅n茅ral da ayyar mijinta wacece ta fi son ado da k'amshi? Abu d'aya da za ta ce kawai shi ne dattijawa ne na mutumci da su ka haifi yaran da suke huce mu su takaici, sun tara dala su ke kuma kashewa iyayensu babu jin takaici. _________________ Yaye bargon ya yi ya d'aukeshi cak ya nufi ban d'aki da shi, ya na jin ya aje shi zaune akan watar ya bud'e ido, su na had'a ido ya mik'e ya na dariya da gudu ya fito daga ban d'akin, da gudu shi ma ya biyo shi ya na kiran "Amjad, Amjad ka tsaya fa, lokaci ya yi." Hanyar fita ya nufa ya na fad'in "Um um! Ka kamoni." Har falo suka kai ya na bin shi da gudu su na dariya, ya na kusa da fita ya rik'oshi ya sake d'aukarshi gaba d'aya, ban d'akin ya maido shi ya cire mi shi kaya shi kuma sai dariya yake ya na shafo k'asumbar Tagur ya na fad'in "Aba idan na dawo daga islamiyya za mu je a mana aski, gaskiya ba na son gashin nan na ka irin na 'yan adaidaitar zamani ne." Dariya Tagur ya yi yace "Yanda ka ke so haka za ayi yarima, Allah ya dawo damu lafiya." Sake ya jawo wuyan Tagur ya manna mi shi sumba yace "Ameen Aba." Ya na cire mi shi wando ya juya baya ya na rufe 'yan kayanshi shi ma wai kunya, dariya Tagur ya shiga yi dan har sun saba a kwanakin nan da su ka yi tare, shak'uwa sosai ta shiga tsakaninsu mai ban mamaki, ya ji dad'in yanda uwa ta gari ta zama tushen tarbiyyar Amjad, dan da wannan tarbiyyar ne sanda ya ke kukan Ayyarshi har ya kwatanta ma sa ta yi aure, ta auri wani ba shi ba, ya yi hak'uri ya zauna tare da shi, amma hakan ba ya na nufin ya rabu da Ayyarshi ba. Tsaf yaron ya fahimta har ya bud'i baki yace "Allah ya sa ayyata ta yi farin ciki, nasan Abansu Izzadeen zai kula min da ita sosai, kai ma Aba yaushe za ka yi aure?" A hankali y'a amsa mi shi da "Zan yi Amjad." Hakan ya sa ya kwantar da hankalinshi suke rayuwarsu ta farin ciki, a kwanakin nan kuma ya k'ara zurfafa soyayyar da ya ke ma yaron har ya na jin ya fara zama numfashin shi ta yanda ba zai rayu ba babu shi. Dukanshi ya yi a d'uwawu ya na fad'in "Juyo mana, ni fa ubanka ne, kunya ta ka ke ji?" K'in juyowaa ya yi ya mak'ale kafad'a yace "Um um! Aba na fad'a ma ka ayyata ta daina min wanka, ka barni zanyi da kaina." D'aukarshi ya yi cak ya saka a cikin bahon wanka ya na fad'in "Ayyarka ta daina ma ka ne saboda ta ga ka fara girma, ni kuma ko aure na ma ka ba zan daina yi ma ka wanka ba." Dariya Amjad ya yi cike da kunya ya rufe fuska, ruwa ya fara zuba mi shi a jiki ya na fad'in "Ka na son auren kenan?" Da sauri ya girgiza kai yace "Dada za ta yankeni da wuk'a idan na kula mace, ta ce fa ni ne mijinta." Dariya ya yi yace "Ai bayan dada ma sai ka auri mace uku, Amjad ina son ganin zuri'ata daga tsatsonka, kai kad'ai na mallaka a duniya, idan ba ka yi aure ka hayayya fa ba zuri'ata ba za ta yi yawa ba." Kallon fuskarshi ya yi yace "Aba zan yi to, in dai ka na so zanyi." Murmushi ya yi ya sumbaceshi yace "Allah ya raya min kai Amjad." "Ameen." Ya fad'a su ka ci gaba da wankan, sai da ya shafeshi da mai ya saka mi shi sabbin kayan da ya d'inka mi shi b芒 adadi, b'angaren Hatimi su ka nufa ya dinga b芒 wa Amjad abinci a baki, hakan kuma ba k'aramin b'ata ran Gomboy ya ke ba, ita har yanzu tunda suka dawo ba su fad'a ma ta magana tsayayya ba, kawai sun ce ma ta sun taho da Amjad ne zai kwana biyu, basu fad'a ma ta yanda shari'ar ta kasance ba, sai ma wani canji daga Tagur d'in, duk da dama ba shiri suke ba, amma yanzu ko kallonta ba ya yi, ko magana ta yi da ta shafeshi sai ta ga ya yi kamar bai ji ba. Su na kammalawa su ka mik'e suka fita Hatimi ta bisu da addu'a da murmushin ganin iyalinta. Shi kan shi daurewa kawai yake yana k'yale Gomboy, kuma abu d'aya tak yasa ya shareta shi ne maganar Faduma a asibiti, duk da Amjad ta fad'awa, amma a ganinshi shi ma zai rik'e maganarta ta zama alkairi a gareshi, duba da yana da tabbacin zuciyarshi ce Amjad y'a yi duk da bai ga salonta ba, dan haka ya d'auri niyyar yin banza da lamuranta ya yi watsi da ita, amma ya tabbatar za ta nemeshi tunda ya na ma ta rana sosai a rayuwa. _________________ Da wani irin takon k'asaita kamar d'awisu ya shiga da sallama ya na biye da k'aninta da ya mi shi jagora, fuskarsa a d'an sake ya samu ya gaishe da mamanta duk da dai a fuska ta nuna mi shi akwai magana a bakinta, haka ya mik'e ya shiga cikin falon ba tare da ya yi sallama ba, dan shi fa ya zo ne saboda Umma ta ce ya zo, kuma sai yanzu ne yake ji a wurin k'anin Saudat d'in ai Umma ma ta zo da safe, amma dan rashin mutumci mamanta ba ta mi shi maganar ba, alamar dai ta na ganinshi da laifi kenan. Saida ya zauna kan kujerar da yaron ya aje ma sa, wayarsa a hannunshi da makullin mota ya d'an saci kallonta, ta k'ara yin haske ta kuma d'an rame dama ba mai jiki ba, gashi har yanzu fuskarta akwai tambarin da ya kafa ma ta na tarihi ya k'i goguwa, yanda ya gan ta kamar dai mai jego ya sa shi jin wani tausayinta kamar zai rufeshi, da sauri ya d'auke kan shi daga kan ta, a wani dak'ile a kakkauce yace "Ya jikin?" D'an muskutawa ta yi da niyyar gyara zama, amma matsalar jinin da ke ma ta zuba har yanzu da kuma ciwon da mararta ke yi ya sa ta d'an yatsina fuska ta cije leb'e, sunkuyar da kan ta tayi ta na dafe da mararta, duk akan idonshi har zuciyarshi kuma ya na jin kamar ya tallabota ya rarrasheta, amma zuciyarshi ba ta saukowa da wuri idan ta hau sama, sai kawai ya sake yin burus da ita. D'agowa ta yi da idonta da su ka fara rikid'a za ta yi kuka ta kalleshi tace "Ina yarana?" A dak'ile ya amsa mata da "Su na wajen Umma." A hankali ita ma tace "D'azu Umma ta zo nan ta ce su na makaranta ne, kuma ta ce bata san da na yi avortement sai jiya." Shiru ya yi irin kamar bai ji ba, ita ma shirun ta yi ta na satar kallonshi da mamakin wani masifaffen kyau da ya d'and'asa, wallahi sai taji kamar ta fad'a k'irjinshi ya rumgume ta hanashi fita. A take kuma zuciyarta ta tuna ma ta ai amaryarshi jiya ta tare, kuma ya baki kalmarsa cewa a ranar zai isa gareta, dan haka ya je har an wuce wurin. Wani matsanancin kuka ne ya kubce ma ta da ita kan ta bata san sanda ya taho ba, hakan ya sa ta dafe mararta ta na murk'ususu da jujjuyawa har ta kwanta kan katifar, kallonta ya shiga yi kamar tv da mamakin to me aka ma ta? Girgiza kai kawai ya yi ya mik'e cikin hassalalliyar murya yace "Kinga, ba abin da ya kawoni kenan ba, sai anjima." Ya fad'a ya na fita daga falon, da kallo ta bi shi har y'a fice sai mahaifiyarta da ta shigo da sauri ta na fad'in "Lafiya? Wani marin ya kuma zuba mi ki?" Cikin matsanancin kuka tace "Mama amaryarsa ta tare, ki dubi yanda ya yi watsi da lamarina fa, wallahi gidan zan koma na ga komai a kan idona." Cikin hassala uwar tace "Tashi ki koma to, ni dai babu ruwana kinji na fad'a mi ki." Fita ta yi ta bar ta hakan ya sa Saudat mik'ewa da nufin shiga ta had'a kayanta, amma ciwon marar nan ya hanata dole ta zauna sai dai da niyyar ko mai dare ta ji sauk'i sai ta koma gidan. _______________ 08:34 Abdallah ya sallamo gidan cikin raha da barkwanci kamar yanda ya saba, duk suna d'akin da aka saukesu ana mu su kwalliya dan komawa d'akunansu, da k'yar Faduma ta tsaya ake ma ta kwalliyar dan b芒 ta saba ba, ranar ma da ta tsaya aka ma ta dan ta na gaban ayyar g茅n茅ral ce. Tsaf aka fito da su cikin kwalliya mai birgewa a cikin nad'in lafaya mai shegiyar kyau da tsada, ta Faduma kalar ja ce mai duwatsu sai dada da ta saka kalar ruwan k'asa ita ma mai k'yalli, fitowarsu falon ya sa shi d'an yin shiru ya na kallon dada da ta sunkuyar da kai ta na hararenshi ta k'asan ido, hannun Faduma ta rik'o tace "Wallahi ki fad'a mi shi ba zan iya aurenshi, na fasa kawai ya sakeni." Dariya ita dai ta yi ta na b'oye fuskarta ita ma har su ka k'araso, duk sunkuyawa su ka yi su ka zauna kan kujera, kallonsu Umma ta yi tace "Masha Allah amarena, kun ga yanda ku ka yi kyau kuwa? Allah ya tsareku." Da "Ameen." D'akin aka amsa, a nutse Umma ta kalli dada tace "K'anwata, kin ga mijin nan na ki?" Ta fad'a ta na nuna Abdallah da ke ta kallonta ya na son ta d'ago, d'orawa ta yi da cewa "Sai kinyi da gaske, ni dai dama ba aure na ke da shi ba, dan haka dabarun zama da shi kawai zan koya mi ki." Wani murmushi ya yi yace "Idan kun gama zan iya tafiya da amarsu ta? Akan hanya na ke fa." Kallonshi duk aka yi da mamaki sai aunty Nana da tace "To ba kai za ka tafi da ita ba, mu za mu rakata." Wani murmushi ya yi yace "Ai da na so hutar da ku ne, kun ga yanzu dare ya yi, kuma ga hanyar gidan babu kyau, sannan da safe ku ka ce za ku koma, gashi kuma ni kad'ai na zo duk abokaina sun shiga gidajensu su ma, babu motar da za ta kai ku ma bare ayi maganar dawowa, sann..." Yatsina fuska Umma ta yi alamar gajiya da zancen tace "Kai dallah, haba wannan surutu haka." Kallon su Herde ta yi tace "Kunga, dan Allah ku bar mi shi matarshi suyi ta tafiya, inba haka ba za ku kwana a nan ba ku san abun yi ba." Dariya su ka yi sai wata dattijuwa da tace "Ai na ga alama, kawai su tafi mu sai m没 raka Faduma." Da sauri dada ta d'ago tace "A'a wallahi, ya tafi na je daga baya." Zaro ido ya yi yace "Ke!" D'agowa ta yi ta kalleshi hakan ya sa shi nuna ma ta k'afarshi ya na mitsitsikata yace "Kinga nan? Nan ne aljannarki, ki ka yi wasa zan take na hana ki shiga." Turo baki ta yi ta na gunguni, kallonsu Herde ya yi yace "Yarinyar nan ta raina ni, tun farkon had'uwarmu da haka mu ka fara, haba." Kallonta ya yi yace "Tashi mu tafi malama ko na d'aukeki a kai." Sake lafewa ta yi jikin Faduma ta na mak'ale kafad'a, ita fa wallahi aka takura su tafi su biyu sai tayi kuka, ita kad'ai tasan irin azabar da bawan Allahn nan ya gana ma ta jiya, ya canza ma ta salon kwanci ya fi kala ashirin, ya zo ma ta ba k'akk'autawa har sai da ya saka ta manta da salon karatun ta shiga d'aukar sabon darasi, zuwa d'aya ya ma ta amma ya dame zuwa na tsawon shekaru da su ka yi da su ka yi da mijinta. Kallon Faduma ya yi yace "Ke 'yata mik'o min ita nan." Cikin jin kunya ta kalli dada da ta mak'ale a bayanta, kafin ta yi wani yunk'uri yace "Wai ni kin ma gaisheni kuwa?" A tare su ka kalleshi, dada tunaninta da ita ya ke 'yan mulki ne zai nuna ma ta, ashe da Faduma ya ke dan d'orawa ya yi da cewa "Ni fa baban mijinki ne, ko shi ya ganni gaisheni ya ke." Sunkuyar da kan ta tayi tace "Ina wuni?" Wani murmushi ya yi yace "Ai da duk'awa ki ka yi zai fi armashi." Ba tare da jin nauyi ko wani abu ba ta zunbule daga kan kujerar ta duk'a tace "Ina wuni?" Umma da dada kam baki sake suke kallon Faduma, Umma ce ta yi saurin cewa "Lallai ke ma kin iya taya b'era b'ari, ai za ki shiga uku da shi kam, dan wannan da ki ke gani bai san surukuntaka ba." Gwalo ya ma Umma yace "Kawai dan na ce ba na aurenki shikenan ki ke bina da bita da k'ulli, to zan maidake d'akinki amma sai na mori amarci na." D'an tsaki ta yi ta kawar da kai cike da rashin son hayaniya tace "Allah ya tsareni." Takawa ya yi ya je har gabanta ya sa hannunshi ya kamo na ta, ta na ganin haka ta kalli su Herde tace "Herde ki fad'a ma sa za ku kaini, ba haka al'adarmu take ba, kuna kallo zai ruguza mana tsari." Dariya su ka shiga shek'a ma ta dan yanda idonta su ka yi daf take da yin kuka, ganin dai babu mai taimakonta kawai ta fashe da kuka tsakaninta da Allah wanda ko jiya da za'a kawota ba tayi ba, girgiza kai Umma ta yi ganin har sun fita a d'akin ta na kuka tace "Allah ya baki hak'uri da juriya, baiwar Allah ta ban tausayi." Faduma kam tuni idonta ita ma suka raina fata ta shiga rau-rau da ido, a hankali Herde ta jawota jikinta ta na daddab'ata, hakan ya sa Umma yin murmushi cike da k'aunar matar nan Herde, dan duk zaman lafiyar da aka samu a gidan nan yau ita ce silarshi tunda ita ce babba, da tayi niyyar d'aga hankalinta ko da b芒 ta gidan da akwai wani abu na rashin jin dad'i da ya gifta tsakani. Da haka Faduma ma aka kawo mu su motoci su ka sake rakata gidanta, anan kam har sai da suka k'ara ma ta nasiha sun jima musamman Herde, da k'yar suka rabu ita kuka ita ma Faduma kuka, domin kuwa shak'uwace ta 'ya da uwarta, soyayya ce ta uwa da 'ya. Ko alama yau ba ta yarda ta ci abun da ya shigo ma ta da shi, har sa茂da ya marairaice yace "Batula, idan ba ki ci ba zan yi kuka." Girgiza ma sa kai ta sake yi tace "Na ci abinci gidan Umma, na k'oshi sosai." Ajiyar zuciya ya sauke yace "To ni ki bani na ci, yunwa na ke ji." A raunane ta kalleshi, to ya za ta yi? A hankali ta zura hannunta ta d'auki cokali ta tsakuro kad'an ta nufi bakinshi, murmushi mai sauti ya saki yace "Ki kalleni mana, ko dama ana bayar da abinci ta kumatu ne?" Da sauri ta kalleshi sai ta ga wajen kumatunshi ta nufa, dariya ta yi kanta a k'asa ta nufi bakinshi, saida ya rik'o hannunta ya kai cokalin bakinshi, kallon fuskarta yake sosai yace "Kin tuna ranarmu ta farko a gidan War? Na fad'a mi ki wata rana zan ci daga gareki, kuma na yi alk'awarin tuna mi ki idan ranar ta zo." Sakin hannunta ya yi ta sake deb'owa ta kai bakinshi ya na fad'in "Yau ga shi Zahra ta na bani abinci da hannunta, muna matsayin mata da miji." Ita dai ba ta ce komai ba haka ta dinga ciyar da shi har yace ya k'oshi, kakkauran sanyayyan madara ta tsiyaya ma sa ta mik'a ma sa a ladabce, mik'ewa ta yi ta d'auke kayan ta nufi madafa, duk da k'ofin a bakinshi ya ke saida ya bita da ido ya na ha'diyar yawu tare da madarar, bai tab'a ganin lafayar da ta kama jikinta irin ta yau ba, ga ta kuma wani irin yadi ne mai rawa rawa, hakan ya haddasa kad'awar jikinta tare da lafayar, nutsutsen k'ugunta ne ya shiga juyawa a hankalce ya nai ma sa bye bye. Ta na dawowa ta sake neman wuri ta zauna, kallonta ya yi yace "Fati ba kya jin bacci ne? Mu je mu kwanta ko?" Da sauri ta girgiza kai tace "Ba na jin bacci, sai anjima." Wani murmushi ya saki ya na jin dad'i na kasheshi saboda ganin tsoron nan a tare da ita, dan hakan shi ke k'ara tabbatar ma sa lallai Zuhra ta sa ce, mik'ewa ya yi ya kama hannunta yace "Mu je mu kwanta kinji, ba ki na so na kai ki kiyi sallama da su ayyarki ba?" Da sauri kam tace "Eh, ina so." Da murmushi ya k'arasa shiga da ita d'akin, wuri ta samu ta zauna shi kuma ya d'auki towel ya wuce ban d'aki, ta na nan zaune ta na rayawa a ran ta cewa "Yau fa komai jarabarka za ka shafa min lafiya, ba zan iya d'aukarka ba yau kam." Jin fitowarshi da sauri ta kalli k'ofar kamar marar gaskiya, ai da sauri ta d'auke kan ta tana tarin da babu shiru, da sauri ya k'araso gabanta ya kamo hannunta ta yi tsaye, d'an bubbuga bayanta ya shiga yi a nutse ya na fad'in "Sannu ko." Jinjina kai ta yi alamar amsawa, k'ureta ya yi da kallo sanda ta yi shiru kamar mai karanta wani abu a fuskarta, yanda babu sarari a tsakaninsu gashi ba kaya a jikinshi, sai ta zama wata yar tsirit a gabansa ko 'yar cikinsa, kasa d'aga kai ta yi ta kalleshi sai a ranta da take fad'in "Wallahi shi ma kamar yallab'ai War ne, shi ya sa aka ce babu kyau fariya, na d'auka ba zan iya zama da irin k'artin nan ba." Wuk'il-wuk'il ta yi da idonta dan a take ta tausayawa kan ta, hannu ya kai kan k'ugunta zai kunce k'ullin lafayarta, da sauri ta ja baya ta na kallonshi, shi ma kallonta ya yi hakan ya sa aika ma ta sak'on "Batula ki fita idona in rufe." Ita ma da idonta ta aika ma sa da rarrashin "Ka yi hak'uri babban mutum, b芒 na so." Yar ajiyar zuciya ya sauke ya nufi wajen kayanta, wata rigar bacci ya d'auko ya kawo ma ta fuskarshi a tamke yace "Maza ki canza min kayan nan." Yanda ya yi maganar da yanayin fuskarshi ya sa ta karb'a ta juya ban d'aki ta shige, gaban madubi ta k'arasa ta shiga cire duk shirin nan, saida ta yi wanka sosai ta wanke kwalliyar nan ta tsane jikinta da towel kafin ta saka rigar da niyyar idan ta fita za ta shafa mai. Ta na kallon kanta a madubi da k'arfi tace "Inna lillahi..." Da kyau ta shiga kallon kan ta da mamakin dama rigar da ta saka kenan? Ta ya za ta fara fita da wannan rigar hannaye kamar zasu tsinke, tsayinta iya cinyoyinta ko gwiwa ba ta kai ba, uwa uba kuma a gaban wajen nonuwa shara shara ne duk ana ganin komai. Juyawa ta yi da kyau hakan ya bayyana ma ta k'ugunta da ya fito kan rigar ta zauna ma ta a k'ugu ta yi d'as gwanin sha'awa. Ta na tsaye ta na tunanin mafita, sai kawai ta d'auki lafayarta ta daidaita za ta d'aura. Shigowar shi ta saka ta saurin durk'ushewa k'asa ta na rufe jikinta da lafayar, a hankali ya k'araso gabanta ya d'agota ya na kallonta, karb'e lafayar ya yi daga hannunta, kallonshi ta yi kamar za ta yi kuka ta girgiza ma sa kai, shi ma girgiza ma ta kan ya yi tare da kama hannunta, rik'e rigar ta yi daga gaba ta na jan kamar za ta k'ara ma ta tsawo, suna fitowa ya sulala ya kashe hasken fitilar mai k'arfi ya rage sai siririn, kwantar da ita ya yi ya ga bargo ya rufeta ya kalli fuskarta yace "Yi bacci lafiya." Ganin ya zagaya d'aya b'angaren sai kawak ta sauke ajiyar zuciya ta na mai jin dad'i da zai k'yaleta, gefenta ya kwanta shi ma ya rufe kuma daga shi sai towel d'in nan, ita dai jininta akan akaifa ya ke tayi shiru amma idonta a rufe, ta sakankance da cewa bacci za ta yi yau kam, hakan ya sa ta tuno da dadarta, a hankali ta saki siririn murmushi a cikin bargon a ranta ta na fad'in "Allah fidda a'i daga rogo, dada yau ma za a sha matssss." Ba ta fad'i kalmar dai-dai ba sakamakon jin mutum a samanta ya ma ta runfa, jaye bargon ya yi ya kalli fuskarta da tuni ta sake lik'e ido, a hankali ya sa hannu ya shiga shafar kitsonta da ya mi shi masifar kyau a ido yace " *Fadjimata*." Jin ya yi shiru ya sa ta amsawa da "Umm!" B芒 tare da ya daina shafar kan ta ba yace "Zahra ina son ki sosai, ina son ki fiye da yanda ki ke tunani, ni kaina lokuta da dama na kan zauna na shiga tambayar kai na dalilin da ya sa aka jarabceni da son ki, amma sai na rasa gane dalili, Fati ki bani dama na ci gaba da shiga rayuwarki, na mi ki alk'awarin kawo haske a cikinta." Sannu sannu ta d'an bud'a idonta ta sauke a kan fuskarshi, dan daga jiya zuwa yau an ma ta wahayin hanata kallon idonshi, cikin nutsuwa da taushin murya tace "Nagode, ni ma kuma haka." Wani murmushi ya saki yace "Fati b芒 na son shirun nan na ki, magana ko ya take indai daga bakinki ne ta na saka ni farin ciki." Jinjina ma sa kai ta yi alamar to, lak'ato hancinta ya yi yace "Akan me ki ke godiya?" Cikin sanyin murya tace "A kan son da ka ke min." Cikin tsareta da ido yace "To me ki ke nufi da ki ka ce kema haka?" "Ahhuhhh." Numfashin da ta sauke ya sa ka shi d'an d'agata kad'an, saida ta sake saisaita numfashinta kafin tace "Ni ma dai haka na ce." Da alamar tuhuma yace "Ke ma ki na so na sosai kenan?" D'an bargon ta jawo ta rufe fusskarta cikin kunya, murmushi ya yi yace "Batula ke matsoraciya ce, amma ba raguwa ba, hakane?" Turo baki ta yi cikin shagwab'a ta d'aga kai alamar eh, d'orawa ya yi da "Za ki iya nuna min hakan yanzu?" D'aga kai ta sake yi alamar eh, jinjina kai ya yi yace "Bari na gwada na gani to." A hankali ya shkga sab'ule hannayen rigar har ya cire ma ta su, k'asa ya yi har ya rabata da rigar, cikin nutsuwa shi ma pant d'in ya zareshi, sake ma ta runfa ya yi ya na kallon fuskar tsoronta kamar za ta gigice, hannu ya kan k'irjinta dake cike pam ya shafasu, wani yanayi ne ta ji tare da lumshe idonta. Sam ba ta hanashi ba yin wasa da ita ba, sai dai ita ce ta mi shi kwance ta na sauraronshi, kunya ta ke ji soosai ta na girmama al'amarin maza, dama haka suke? To wai su ko yau ku ka had'u aka d'aura mu ku aure sai su zo gareka? Shin ba sa da k'yamk'yami ne? Ya gama nune ma ta jikinta tas, ta rasa duk wani kuzarinta tsabar yanda ya juyata ya d'aga ma ta hankali da wasu irin salo ma su rikita tunani, tsabar mamakin lamarinshi kawai ya saka ta yin jugum, har kunnenta bai bari ba saida ya tsotse ya zura harshe a ciki, cibiyarta haka saida ya ma ta tsutsa ta musamman, hatta da tafin k'afarta saida ya dinga sumbatarsu ya na saka yatsun a bakinshi ya na tsotsawa. Lallai inba aure ba wa? Inba igiyar aure ba wa zai had'ata da wannan babban mutum haka ya na ma ta wannan abu? Ai ko karuwanci ne su ke zai yi wuya ya kai harshenshi cikin bakinta ma, aa yanzu sai gashi har harshenta saida ya rik'e ya yi ta lagu...馃槑 wallahi kar ku ce na fara iya hege ni ma. Kallon juna suke ya na son d'auke hankalinta da kalamai dan ya samu shiga a sauk'ak'e ba tare da ta ji ba bare har ta zubar da hawaye kamar yanda ta yi jiya, cikin nutsuwa da wata rikitaciyar murya ya shiga rad'a ma ta a kunne "Ba na manta had'uwarmu ta farko, a take zuciyata ta buga dalilin ganinki, sassan jikina suka amsa, idaniyata su ka isar da sak'on wa sauran gabb'aina da cewa gata nan, ita ce wannan wacce ka ke jira, ita ce *murmushin fuskarka* sannan kwanciyar hankalin gidanka, a take na rad'a mi ki sun..." Cak ya tsaya saboda jin ta rik'e hannunshi, kallon juna su ka yi ta na mi shi kallon a'a fa, tunda ta ji hannunshi a k'asanta ya na ta dai-daita wani abu da ya ke son tura ma ta gabanta ya shiga luguden daka, ta na jin ya d'auki hanya b芒 ta san lokacin da ta rik'e hannunshi ba ita ma. Cikin zolaya yace "Ki ka ce kuma jaruma ce ke? Amma shi ne za ki hana ni tabbatarwa." A hankali ta saki hannunshi ta sake k'ura ma sa ido, d'auke idonshi ya yi dan in y'a ci gaba da kallonta zai iya jin tausayinta ya rabu da ita, haka ya ci gaba da d'orata akan hanyar amma kuma ya k'i shiga, wannan barazanar na jiran tsamani ya sa ta jin zufa na tsatsafo ma ta, kamar wacce ke jiran sakamakon jarabawarta haka ta tsareshi da ido kamar yanda shi ma ya ke kallonta jefi-jefi. Sai dai tsoron nan dake kan fuskarta ne ke birgeshi, shi ya sa ya ke ci gaba da yi ma ta wannan k'walelen. Dan in ya yi kamar zai shiga har wani shid'ewa take saboda jin abun kamar hannun mutum, tunaninta da kuma nutsuwarta sun ta'allak'a ne da son sanin ta yanda al'amarin nan zai kasance, ta ya ya abun nan ke shiga jikin mutum? Ta ya ya kuma ake haifo d'an mutum? Lallai wasu kayan sai amale, wani al'amarin kuma dole ya sa ka ji tsoron mahallicinka. Ya na danna kan shi ta waro duka idonta ta bud'e bakinta ta bank'aro kamar za ta tashi zaune, da sauri ya rarumi bakinta ya shiga tsutsa a hankali ya na sauke ma ta numfashi a cikin baki saboda halin da ya samu kan shi a ciki na shiga wani ni'imtaccen d'umi mai saka mutum jin wata ingantacciyar lafiya na shigarshi, d'umi ne mai sirrin gaske da shi dai in aka barshi da zab'inshi to zai yi ta zama a ciki ne bai fito ba, ga wata irin mannewa da yake ya na jawo kan shi ana rik'eshi abun kam sai godiya, *tabbas akwai bambamci*, sai dai sanin sirrin kuma ya fi k'arfin tunaninshi. _(Sirrinmu, tukunyarmu da kankanarmu)._馃拑 _Ku nemi sirrin tukunya da sanin sirrin kankana._ *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 21:43 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _74_ Tun fa jiya da dare take gidan, kuma ta na nan ya shigo kuma ta tabbatar da ya ga d'akinta a bud'e, amma dan kuturun wulak'anci shi ne ya shige wajen amaryarsa ya shareta, lallai Hasheer ba ya nemanta da zaman lafiya ko kad'an. Gashi har gari ya waye k'arfe 09:00 ta buga dai-dai amma shiru bai fita ba, to wace tsiyar ya ke? Shin ita ba ta jin ya gundureta ne? Namijin har wani abun a ninik'e ma sa ne? Hummmm! Za su fito ne ai za su kwatse. *A wajen su kuma* soyayya ce mai tsafda da gudana ke wanzuwa cikin salama da tausasawa da girmamawa, dan Faduma tunda ta yi sallah asuba ba ta koma ba, saida ta kammala girki da turare gidan kafin ta yi wanka ta cancad'a ado a cikin riga da siket na atamfa da suka mata tsaf a jiki, wajen d'aurin d'an kwali ne ma ta so samun matsala saboda rashin iyawa da sabo, amma haka ta daure ta kwab'a zara buhari, sai kuma ya ma ta kyau saboda walyar gashin da ta d'aure da babban ribom. Ta jima a gaban madubi ta na bitar kalaman ayyar g茅n茅ral da dadarta kafin ta iya aro jaruma ta ajiye kunya a gefe ta k'arasa gaban gadon, sunkuyawa ta yi kusa da kan shi ta saita bakinta daidai kunnenshi ta rad'a mi shi "Idan na yi daidai da son raina, zan so *mijin Faduma* ya tashi domin ya nemawa kan sa abinda zai ci, da yardar Allah yunwa ba za ta samu mafaka a cikin *mijina* ba." Duk da bai ji daga farko ba dan a lokacin bacci ya ke da gaske, amma daga inda take fad'in mijin Faduma ya jita sarai, bud'e ido ya yi ya shiga sakin murmushi, mik'ewa ta yi ta na kallon fuskarshi ita ma, saida y'a tashi zaune ya na ci gaba da kallonta, sai kawai ya sauko da k'afafunshi ya tallabe hab'arshi ya yi tagumi ya na kallonta. Tsarguwa ta yi da kallon hakan ya sa ta durk'usawa har k'asa kanta a sadde tace "Barka da tashi ranka shi dad'e, fatan dai banyi laifi ba?". Ba tare da murmushi ya bar fuskarshi ba ya girgiza kai ya na kallon yanda ta durk'usa har k'asa ba tare da jin nauyi ba, cikin sanyayyar murya yace " Laifinki ma ai yafi k'arfin hukunci, dan haka ki yi duk abin da ki ke so Zuhra." Sake sinne kai ta yi tace "Godiya na ke da samun lamani daga bakin wanda ya isa da ni." Mik'ewa ta yi ta mi shi nuni da ban d'aki tace "Zan iya samun alfarmar raka ka?" A kasalance ya mik'e ya na fad'ad'a murmushinshi, a gaskiya fa zai iya mutuwa indai abin da za ta dinga yi ma sa kenan, zuciyarshi ba za ta iya rik'e wannan farin cikin ba. Da kan ta ta bud'e k'ofar ta ja baya alamar ya shiga, saida ya kalli ban d'akin ta sha wanki tas sai k'amshi ke tashi kamar ba bayi ba, muryarta ce ta dawo da kallonshi kan ta da tace "A fito lafiya, ka d'auki lokacinka ranka shi dad'e, girmanka ne." Jawo k'ofar ta yi ta rufe hakan ya saka ta sauke ajiyar zuciya, kai ta yi k'ok'ari fa sosai da ta iya furta masa kalaman nan a yanzu, nufa kan gadon ta yi ta shiga gyarashi a tsanake ba tare da ta canza darar ba dan tun daren jiya aka canza, ta na idawa ta sake feshe d'akin da turare ta d'auko kaskon wutar mai aiki da lantarki ta dawo da shi nan. Kayan da zai saka ta so ciro ma sa saidai babu kayan shi a nan d'akin, sannan ba ta san ina za ta samu makullin d'akin da take jin ya na shiga ba daga shekaran jiya zuwa jiya. Bai wani jima sosai ba ya fito da d'aurin towel a k'ugu sai k'arami a wuyanshi ya na goge kan shi, kallo d'aya ta ma sa ta d'auke kan ta, dan gaskiya kallonshi a haka ya na wahalar da ita da saka ma ta wani fad'uwar gaba. Yanda ya tsaya gabanta kamar dai shekaran jiya ya sa yau ma kan ta a k'asa, saida ya gama goge ruwan tsaf ya na kallonta yace "Za'a iya taimakawa a saka min kayana Hajaj?" Wuk'il wuk'il ta shiga yi da ido tsakanin k'irjinshi da kan shi, d'an jinjina kai ta yi alamar to, kama hannunta ya yi suka fita a d'akin, a jikin k'ofar d'akin ya bud'e makullin suka shiga, yatsina fuska ta yi ta na fad'in "D'akin waye wannan?" Ba tare da ya juyo ya kalleta ba yace "D'akin mijin Faduma mana." Nuna d'akin ta yi tace "A haka?" Sai kuma tace "Amma me ya sa ba'a gyara ba?" Juyowa ya yi da murmushi yace "Zan gyara." Wata 'yar harara ta ma sa tace "Kafin na zo gidan ko?" Tsayawa ya yi daga d'aukar kayanshi a wadrob yace "Me ki ke nufi?" A hankali tace "Zan gyara." Wani kallo ya ma ta mai aiko da sak'on "Kamar ki ce za ki fara." Kallon shi kawai ta yi har ya d'auko kayan ya dawo inda ta ke tsaye, nuna ma ta su ya yi yace "Wannan sun mi ki? Dan babu inda zan je yau ina gida tare da ke." Karb'an kayan ta yi ta warware, d'an rik'e hab'a ta yi tace "Ka fara sakawa tukuna sai na gani." Murmushi ya yi ya karb'i wandon tare da zame towel d'in jikinshi, juya bayanta a tare suka wakana da fad'uwar towel d'in, dafe k'irjinta ta yi tana zazzaro ido tace "Haka su ke dama, d'abi'arsu ce hakan." Hannunshi ya lakayo ta k'ugunta ya jawoya ya had'a da jikinshi ya na murmishi, tunaninshi kenan da babu komai a ciki ya za ta yi? Tsoro kamar farar kura, d'ora hab'arshi ya yi ya lumshe ido saboda turarukanta yace "Me ya sa ba ki son kallon mijinki ne wai *matar Hasheer*? Ki na da wani da ya fi ni ne?" Girgizz kai ta yi da sauri alamar a'a, dan haka ya d'auke hab'arshi ya na juyo da ita yace "To karb'i saka min." Rufe ido ta yi ta karb'i wandon, rik'o duka hannayenta ya yi yace "Ba fa za ki saka min kaya ki na *makauniya* ba." Kyab'e fuska ta yi kamar za ta yi kuka kuma idonta a rufe, cikin shagwab'a tace "Allah ni dai ba zan iya ba." Jawota ya sake yi jikinshi ya rad'a ma ta a kunne "Ko dai ni ma k'aton ne kamar yallab'ai g茅n茅ral?" Da sauri ta jinjina kai alamar eh, sai kuma ta girgiza alamar a'a, dariya ya yi yace "Shikenan, zan kira yallab'ai na fad'a ma sa kin kiramu da k'arti." Da sauri ta bud'e ido a raunane tace "Dan Allah kar ka fad'a ma sa, ba na son ya mareni a fuska." Sai kuma ta rufe ido ruf, hakan ya sa shi shafa fuskarta yace "Wa ya fad'a mi ki na aureki ne dan na bari wasu su mareki? Ai idan War ya mareki ni da shi sai mun hau sama ta bakwai za mu fad'o k'asa." Wani k'ayataccen murmushi ta saki amma idonta a rufe, sakin hannunta ya yi ya saka wandon kafin yace "To bud'e idon ki ga na mi ki a haka?" Bud'ewa ta yi a hankali ta kalleshi, sai kawai ta ji kunya ta sunkuyar da kai tace "Ai ina sonka ne a duk yanda za ka zo min." Karb'an rigar ya yi ya na fad'in "Amma ki na kunyar kallona ba." A sanyaye tace "Shi ma zan daina insha'Allah." Saida ya saka rigar yace "Za ki daina mana da zaran kin d'auki ciki." D'ago kai ta yi ta kalleshi baki bud'e da irin mammakin nan, sai kuma tace "Da wuri haka? Aiki fa na ke." D'an had'e fuska ya yi yace "Batulu wa ye ya fad'a mi ki za ki ci gaba da aiki?" Sororo ta kalleshi, amma maganar ayyarta da tace akwai lokacin da namiji zai yi magana ta umarni ko yankakken hukunci, kai tsaye a lokacin karki nuna ma sa ba haka, bi shi ku je a angama kawai. Ba ta ce mi shi komai ba ta na kallonshi har ya saka rigar, wani murmushi ta saki ganin yanda kayan suka ma sa kyau, wandon daidai gwiwarsa ya ke da kad'an ya sauko, rigar kuma mai botira a wuya da hannayenta akan damtse, kala garesu sosai tare da hoton damisa a rigar da kuma wandon. Ta na kallo ya k'arasa gaban madubi ya caje sumar shi tare da shafa wani lallausan lotion mai kama da madara kafin ya fesa turare, agogo ya d'auka ta roba k'arama kalar shud'e kamar dai kayan, saida ya d'auko takalmi na fara plat kamar silipas ya saka kafin ya k'araso gabanta. D'an jan numfashi ta yi hakan ya sa shi murmusawa ya bata agogon, karb'a ta yi ta shiga d'aura ma sa da jin wani irin dad'in ganin mijinta uban ado ne, ya birgeta fa sasai, a yanda Ayya ta koya ma ta aiki a tsanake sai ta ga wanda ya dameta kuma ya kurb'e, komai a sanyaye ya yi shi har ya kammala, fitowa su ka yi daga d'akin rik'e da hannun juna, kan teburi ta mi shi iso ya zauna ya na duba wayarshi, saida ta aje mi shi plate a gabanshi ya d'ago ya kalleta, murmushi ya saki ya sake kallon wayarshi, fizge wayar ta yi ta na zama kujerar daf da shi ta na d'aukar cokalin plate d'un da fad'in "Elhaj yanzu lokacin cika min cikinka ne, idan ka idar na baka wayar." Murmushi ya yi yace "Ba wani sauk'i kuma?" Girgiza kai ta yi alamar a'a, d'ibar abincin ta yi ta nufi bakinshi, bud'ewa ya yi ta jefa mi shi lomar, lumshe ido ya yi yace "Um! Dad'i." Kallonta ya yi yace "A ina ki ka koyi girki? Na ga kullum ki na yawan bincike ne da tambaya." Da hannu ta mi shi alamar yi shiru, da ido shi ma ya yi alamar na yi, shi ma cokali ya d'auka ya fara saka ma ta a baki, kallonshi ta yi tace "A karo na biyu ka saka min abinci a baki na, bayan ka ciyar da ni a gidan yallab'ai War." Murmushi ya yi su ka ci gaba da ciyar da juna har saida suka tabbatar sun k'oshi, mik'ewa ta yi ta fara tartare kayan za ta d'auke ta kalleshi tace "Yallab'ai ka je ka d'auko mana yaran nan mana, ba na son zama gida shiru haka." Girgiza kai ya yi yace "Ayi hak'uri Hajaj, amma sati biyun nan da zai zo ya wuce na ki ne, ni kaina babu inda zan je ai muna tare." Zaro ido ta yi tace "Sati biyu fa? Ai ya yi yawa, ni dai gaskiya ka d'auko min su, haka jiya Umma ma sam b芒 ta bari mun gaisa da su ba, sai ta ce za su cikani da hayaniya." Jinjina kai ya yi yace "Hakane, dan haka sai nan da sati biyu za su dawo." Marairaicewa ta yi kamar za ta yi kuka tace "Dan Allah ka kawo min su, ka ga za su d'ebe min kewar Amjad." Ajiyar zuciya ya sauke ya kalli fuskarta yace "Shikenan, amma b芒 ni zan je d'aukarsu ba, zan kira Mukhtar ya kawo su." Murmushi ta yi tace "Hakan ma ya yi, Allah ya saka da alkairi." Da kallo kawai ya bita sanda ta nufi madafa, saidai ta na bada baya ta shiga tambayar kan ta "Ya yake yanzu? Me ya ke yi? Wace irin rayuwa ya ke a gidan?" Da rashin wannan amsoshin ta gama d'auke kayan wurin ta kimtsa, falon ta same shi ta zauna gefenshi ta na d'an kallon tvn, hannunta ya kamo cikin na shi ya na sakin murmushi, sai dai ba ita yake kallo ba kuma hankalinshi na kan waya. _________________ Tsaye ta yi kan ta k'ik'am ta tara hannu kamar yanda ta saba in ta na buk'atar kud'i tace "Ayya bani kud'in zan je karb'ar d'inkuna na." D'ago kai ta yi ta kalleta cike da jin haushi, sam yarinyar ta fice ma ta a rai, haihuwa ai daban ta ke, a da kam ta na son yarinyar da 'yan uwanta kamar yanda ta ke son na ta 'ya'yan, amma jin makircin Gomboy akan d'an ta k'waya d'aya tak namiji, sai kawai ta fita a ran ta ta yi wuri ta aje ta. Cikin wofantarwa tace "Bani da kud'i nima, amma ki je ki tambayi Tagur." Mayar da kan ta tayi k'asa ta ci gaba da jan carbinta, ita kuma mamaki ne ya hanata motsawa, Hatimi ba ta tab'a ma ta haka ba, kamar katin zarar kud'inta haka ta mayar da ita fa, shi ne yanzu ta ke fad'a ma ta ba ta da kud'i. Jinjina kai ta yi da ke nuna "Mu je zuwa." Kafin ta kalleta tace "Ina Tagur d'in ya ke?" Ba tare da ta d'ago ba tace "Ya na b'angarenshi." Ba ta jira komai ba ta wuce ta na gyara siririn kallabin dake kan kafad'arta, dama kuma ba damuwa ta yi da duk shigar da ke jikinta fita take, kai tsaye ta bud'a d'akin bayan ta d'anyi gajeruwar sallama da cewa "Salam." Zaune ta same shi shi da Amjad da littafi a hannunsu da alama karatu su ke, tab'e baki ta yi ganin sai wani dariya suke. Ya ji sallamarta sai dai bai d'aga kan shi ba kamar yanda bai amsa ba, Amjad ne ya amsa la ta har da tukuicin "Ina kwana dada?" Kallonshi ta yi ta kwad'a ma sa harara ta ja tsaki ta d'auke kan ta, Tagur ta kalla ta rik'e k'ugu da hannu d'aya tace "Kud'in d'inki za ka ban, na ce Ayya ta bani ta ce na zo na same ka." Lumshe idonshi ya yi, nauyayyen numfashi ya shiga saukewa ya na mai k'arfafa kan sa, da k'yar ya bud'a ido ya d'ago da kyau ya kalleta, wallahi da kafin hud'ubar Faduma ne da ta kalli Amjad tace "Ka rage zuciyar nan, ba na so." Shi kam da sai ya murd'e hannunta har ya ji k'ashinta ya goce kafin ya saki, wani iska ya furzo ya sunkuyar da kan shi ga littafin yace " Ba na da kud'i." Da mamaki ta yi saurin zaro ido ta kalleshi, sai kuma ta k'ank'ancesu tace "Ban gane ba ka da kud'i ba? Ka ga malam kai dai kasan ni ba matsiyaciya ba ce, yanzu ma dan na tattara duk kud'ad'e na ne na bayar a saro min kaya daga Cotonou ya sa na ke nema a wurinka, in za ka bani ka ban kawai ni kar ka b'ata min lokaci." Sake d'agowa ya yi ya kalleta, d'an ja baya ta yi ta juya ta kalli k'ofa ta yanda ya na mik'ewa za ta fita a guje, d'auke kan shi ya yi ya kalli Amjad da ya k'ura mi shi ido, murmushi ya sakar mi shi yace "Mu ci gaba?" Jinjina kai ya yi alamar eh, shi ma jinjina ma sa kan ya yi ya aje littafin gefe yace "Ina zuwa." Kallonta ya yi yace "Mu je daga waje." Da sauri ta fita dan ita dai tasan ba fitar arziki b芒 ce, a k'ofar b'angaren su ka tsaya sai dai nesa take da shi, kallon gargad'i da b'acin rai ya ma ta yace "Gomboy, ki fita a sabgata nan gidan, da fari na yi hak'uri na d'auki dangana kan abin da ku ka min, na barku da Allah da ya halliceku, amma ki sani ba zan sake hak'uri ba ki ka kaini bango a karo na biyu. Sannan ki fad'awa Atta ta daina turo min sak'on wai Ridwan ba lafiya, ba abin da ya shafe ni da lafiyarsa ko rashin ta, ni dai na samu d'ana jini na mallakina, dan haka can ku k'arata da matsalarku, kud'ina da ku ka ci na farko ki sani kun ci halak malak dan ni ne na baku kuma a rashin sani, amma yanzu idona ya bud'e a dalilin 'yar albarka, dan haka b芒 ni ba ku kuma haka babu ku babu ni." K'ofar ya murd'a zai shiga sai kuma ya tsaya yace "Sannan Amjad, ki sani nan gidan ba gidan Aba ba ne, gidana ne da na gidana shi da kud'ina, dan haka duk wanda ki ka gani gidan nan dalilina ya ke zaune, a yanzu kuma gidan nan *na Amjad ne*, domin kwana uku yau da na canza sunan duk wata kadarata da sunan Amjad, ka da ki k'ara yi ma sa tsaki ko harara, dan wallahi sai na k'ona fuskarki." Shigewa ya yi ya barta tsaye ta na mamakin lamarin nan, me ya faru a kotu? Ya san komai? Lallai dole ta kiyaye kafin ta hassalashi, dan kuwa tsaf zai kasheta ya birne gawarta. _______________ Kwance take a k'fafunshi da doguwar rigar kanti iya gwiwa da ya tilasta ma ta sakawa, hannunshi guda akan k'irjinta ya na ta murzawa sai bakinshi da ke saman kan ta ya na sumbata, idonshi a lumshe cikin sanyayyar muryar yace "Yarinya, ko dai za mu koma ciki ne?" A hankali ta girgiza kai dan iya matsar nan ma da ta ke sha ta isheta, d'an bud'a idonshi ya yi da su ka yi jajir yace "Yarinya, ko dai guduna ki ke? Dan Allah yanzu ke ba kya jin dad'in da na ke ji?" Girgiza kai ta sake yi murya a raunane tace "Ba na jin wani dad'i ni sai dai wahala, mugu kawai." Tintsirewa ya yi da dariya yace "Ai laifinki ne, ke ce ki ka ce wai na mi ki yaro ba za ki iya aurena ba, ke in ba ma rashin kunya irin ta ki ba, ni za ki kalla ki ce na mi ki yaro?" Yunk'urawa ta yi ta mik'e zaune ta na hararenshi tace "An fad'a d'in, ko yanzu ina kan bakana kai yaro ne." Fizgota ya yi jikinshi ya kwantar da ita ya ma ta runfa, cikin dakakkiyar murya yace "Ke, kalleni." D'an kallonshi ta yi ta na kakkaucewa tace "Ka daina kirana da ke, ba na so nima." Saida ya d'ora labb'enshi a wuyanta yace "Zan daina, amma yanzu mu je d'aki to." A raunane ta kalleshi tace "Na gaji wallahi, ka bari har da dare mana, *hubbi* ka sarara min haka." Cikin sumbatarta yace "Ai ina so ne na fayyace mi ki zare da abawa, ba na so ki na min kallon yaron." Kamar za ta yi kuka tace "Na gane ai, na sani wallahi kai ba yaro ba ne, na tuba ka ji? Na daina daga yau." Cikin tsareta da ido yace "Kin tabbatar?" D'aga kai ta yi tace "Allah kuwa na daina." Saida ya daidaici bakinta yace "Kin ga fa nan da sati uku zan bar garin nan, amma ki sani ba zan barki ba yarinyata, dan wallahi babu mai rabani da ke yanzu, na riga da na ga wurin *hutuna*." Jinjina kai ta yi dan su rabu lafiya tace "Ni ma ba zan yarda ka barni ba ai, ton pied mon pied ( k'afarka k'afata)." Sumbatarta ya fara yi tare da sake zura hannu rigarta, saida ta rintse ido dan ciwo kawai suke ma ta tsabar murza da suke sha. ________________ Tun suna zaune da k'ugunsu har ba ta san lokacin da ya maidota k'asa ba ya d'ora kan shi a ruwan cikinta, hannunshi kuma har yanzu ya na cikin na ta hannun ya na ta murzawa, idonta a rufe suke bacci na son awon gaba da ita, kamar daga sama su ka ji kukan yara da k'arfi sosai. Da sauri ta zabura ta na neman mik'ewa tsaye tana waigawa, rik'eta ya yi yace "Batulu ya dai? Idan hari aka kawo haka za ki dinga rawar jiki wajen fita?" Kallonshi ta yi tace "Indai har rayuwarka za ta tsira to zan yi hakan." D'an dungure ma ta kai ya yi yace "Kuma sai aka fad'a mi ki zan yi farin ciki da hakan?" Mik'ewa ya yi zai fita ta mik'e ita ma dan ta bi bayanshi, juyowa ya yi yace "Ki zauna zan duba, kukan su Izzadeen ne." Jinjina ma sa kai ta yi alamar to, komawa ta yi ta zauna shi kuma ya fita da takalminshi a k'afa, tun farfajiyar ya ke kallo sai dai bai ga motar Mukhtar ba da yake da yak'inin shi ya kawosu, abun mamaki shi ne jin kukansu a falon Saudat, da mamaki ya nufi falon ya na tambayar kan shi "Me su ka ma ta kuma daga zuwansu?" Dan shi dai tun jiya ya ga k'ofar a bud'e, amma rashin lokacinta ya sa ka shi wucewa kawai. A hankali ya tura k'ofar ya shiga cikin nutsuwa, juyowa ta yi ta kalleshi, haushin shi, takaicin shi, tsanarshi ne duk suka mamayeta, dama haushinshi ne ta fara hucewa akan yaran, a gaskiya ba dan ta na tsoronshi ba yanzu, wallahi da sai ta sharara ma sa mari a fuska ko za ta rage zafi, kai ta tsaneshi yanzu saboda amaryar da ya yi, tun jiya ta na gidan amma bai kula da tsiyarta ba. K'wafa ta yi mai k'arfin tsiya ta na jefar da bulalar hannunta, ta ma rasa dalilin da ya sa ya ke ta k'ara kyau har wani ja ya k'ara yi, hmmmm. Zaune ta yi kan kujera ta na cike da jin bala'i duk da jikinta ba k'wari ne da shi ba, saida ya tsaya gaban yara ya kallesu yace "Lafiya?" Da sauri Sharfudeen ya mik'e ya rumgeme shi ya na tsagaita kukan da fad'in "Mama ce ta dakem." Sake lafewa ya yi jikinshi saboda hararar da ta watso mi shi, Izzadeen ya kalla da har yanzu ke durk'ushe yace "Me ya sa ba kwa jin magana? Baku san mamanku ba ta da lafiya ba ne? Ku daina damunta kun ji." Cikin kuka Sharfudeen yace "Abba ba laifi mu ka yi ba, kawai dan za mu je wajen maman Amjad shi ne ta hanamu kuma ta dakemu." 'Yar ajiyar zuciya ya sauke ya mik'awa Izzadeen hannu ya taso, shafa kan su ya yi yace "Shikenan to, ku wuce d'akinku." Jiki a sanyaye su ka nufi d'akinsu su na share hawaye, ko ba komai sanyin nan da aka mu su ma sun ji dad'in shi. Suna shiga ya kalli fuskarta fuska a had'e cikin muryar da babu wargi yace "Me ya sa ki ka dakesu dan za su tafi wajen Fati?" Cike da rashin tauna magana tace "Saboda na tsaneta, ban ga dalilin da zan bar 'ya'yana su je wajenta ba, ba zan yarda a rabani da su ba kamar yanda aka rabani da kai." Gyara tsayuwarshi ya yi ba alamar tausasawa shi ma yace "Ko ki so ta, ko ki k'i ta, Fati dai matata ce kuma ina son ta a haka, yara kuma nawa ne haka ma gidan nan, dan haka ke ba ki isa ki raba min kan gida ba, yara za su tafi wajenta duk sanda su ke buk'atar hakan, ke ko ita ce ta nuna ba ta son su rab'i inda take wallahi za ta ji a jikinta, bare kuma yanzu haka sun zo ne dan ita ta buk'aci hakan, dan haka ki kiyaye." Juyawa ya yi zai fita, har ya kai k'ofa ta mik'e ta bi shi da kallo tace "A kan 'ya'yan nawa za ka min iko? Wallahi ba ka isa ba, in haifesu a cikina? Ni kuma indai ni ce uwarsu ba za su je wurinta ba, haka kawai." A hankali ya shiga takowa ya na mai bin fuskarta da kallon mamaki, ta na ganin haka sai gabanta ya shiga fad'uwa da tunanin ko ya na duba kumcin da zai fara fallawa mari ne, da sauri ta fad'a kan kujera ta had'e jikinta kan ta cikin gwiwarta ta k'amk'ame sosai. Har ga Allah hakan dariya ma ta ba shi ganin abin da ta yi, wucewa kawai ya yi d'akin yaran jim kad'an su ka fito tare da su, saida ya tsaya kan ta ya tura yaran yace su tafi gashi nan, k'yasta ma ta yatsu ya yi yace "Ji nan, zan nuna mi ki ba a banza Allah ya hallici uwa da kuma uba ba, zan tunatar da ke ba haka kawai aka kira namiji da uba ba, dan haka zan tafi da su, kuma wallahi ki ka yi wasa a can za su tare da zama." K'wafa ya yi ya wuce bai sake kulata ba, saida ta ji fitarshi ta d'ago kan ta sosai ta na bin su da kallo, ita a cikin gidan nan? Lallai fa akwai matsala. *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 21:43 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _75_ Ya na shiga ya ji hayaniyar yaran a d'akin, kallon k'ofar d'akin ya yi ya ganta a bud'e, a nutse ya k'arasa d'akin ya na kallonsu, zaro ido ya yi ya na kallonta yace "Fati, me ki ke yi haka?" Juyowa ta yi hannunta rik'e da allon baago tace "Gyara za mu yi Elhaj, za ka kama mana ne?" Murmushi ya sakar ma ta ya na soka wayarshi aljihu yace "Sosai ma, tunda matar Hasheer ba ta jin magana, ina zan yarda ki yi wannan aikin ke kad'ai, salon Wardugu ya kulleni ku rasa ina ya ajiyeni." Dariya ta yi tace "To bismillah, ka ga dama za mu anfani k'wanjinka ne ta wannan fannin." Mantawa ya yi da yaran na nan ya jawo k'ugunta ya had'a da na shi goshinsu had'e da juna yace "Au! Anan kawai anfaninsa ya ke? Yanzu duk k'ok'arina na jiya ba ki gani ba? Lallai yau kam ki shirya dan babu shakka sai na kawo mi ki a wuya." Dariya ta shiga k'yalk'yalawa ta na neman sub'ucewa shi kuma ya rik'eta gam ya na naman sumbatarta, cikin dariya ta rad'a ma sa a kunne "Yaran nan fa na kallon mu." Da sauri ya saketa ya na kallon b'angaren da suke, abun mamaki tsaye suke cirko cirko su na kallonsu su na dariya, kunya ce ta lullub'e dukansu sai kawai su ka basar su na d'auke kallonsu daga kan su, kallonshi Faduma ta yi tace "Idan ka san abin da za ka min kenan ka fita a gidan." Mak'ale kafad'a ya yi yace "Um um! Ina nan tare da ku." Kallon yaran ya yi yace "Ko ku na so na fita na barku?" Girgiza kai su ka yi da sauri su na dariya su dai, kujera ta kama ta kallesu tace "To ku zo m没 tura." Da gudu su ka taho suka kama ma ta, turawa su ka shiga yi su ka fito da ita falon, za su shiga d'akin shi kuma ya tura d'aya a cikin kujerun mai zaman mutum uku, sororo Faduma ta yi ta na kallonshi ta na k'yak'yabta ido, da hannu d'aya fa ya ke turo kujerar d'aya hannunshi kuma da waya ya na amsawa, saida su ka kauce ya hanya ya wuce sannan su ka ranka d'akin, ganin yaran sun shiga da sauri ta dawo ta sumbaci kumcinshi ta baya ta koma d'akin da gudu. Da kallo ya bita da wayar a kunne ya na sakin murmushi da girgiza kai, a sanyaye kuma a tsanake su ka yi aikin gyaran d'akinshi, wanda a k'arshe kujerunshi sai a nan falon ta sama mu su matsuguni, falo d'aya da set biyu na kujeru kenan, dan ita kujerunshi ma sun fi birgeta dan na shi farare ne k'arr da su, 11:27 suka kammala saida ta ma yaran wanka da kan ta ta shiryasu cikin kayan da ya d'auko mu su a d'akinsu, sannan ita ma su ka shiga wanka tare bayan sun had'a yaran da kayan ciye-ciye. Ba ta d'auka za ta iya ba, amma sai adalin mijinta ya koya ma ta a tsanake ta yanda har ta iya tsayawa a gabanshi su ka yi wanka a tare, hakan ba k'aramar cire ma ta kaso mafi yawa ya yi ba daga kunyarshi da har yanzu ta ke dakonta, tsaf su ka shiga cikin wani sabon shirin su ka fito, ya so kiran Qaseem ya kawo mu su abinci, amma ta ce gwara ko macca ta dafa da dai a siyo, haka kuwa a kayi inda ta mu su kwad'on macca (ordeuvre). *Yanayin* sanyin la'asar d'in ya yi dad'i, ya na bayan gidan tare da yara su na ta k'iriniyarsu ta fito sanye da hijab, a tausashe ta kalleshi da ladabi tace "Yallab'ai zan je na ga jikin aunty." Da sauri ya bud'a idonshi ya sauke a kan ta, Saudat ta ke nufi? Iska ya furzo ya sake kallonta yace "Ki bari anjima sai mu tafi tare." Duk da ba haka ta so ba amma sai ta had'e tace "Angama ranka shi dad'e." Juyawa ta yi za ta koma ciki dan ta kama aikin gabanta, sai kuma ya lura da kamar ba ta ji dad'i ba, sai kawai ya kalli Izzadeen yace "Je ka raka Ummanku wajen mamanka." Da sauri ya nufeta ya na fad'a ma ta, juyowa ta yi ta kalleshi hakan yasa shi sakar ma ta murmushi, kanne ma sa ido ta yi tace "Godiya na ke." Ya na kallonsu har su ka b'ace ma ganinshi, shi dai fatanshi su dawo lafiya, Saudat ba nutsuwa gareta ba a kwanan nan, bai san me ke damunta ba? Duk ta gigice ta zama marar aji da nutsuwa. Tun a k'ofar shiga Faduma ke kallon dattin da ke k'ofar, duk da ba sosai bane amma a ganinta sai ta ji ba dalilin da zai sa a zauna da shi, duba da ba yara gareta 'yan kuci-kuci ba da duk dabararka wani abun sai ka gaza, ko Izzadeen ya isa ka saka mi shi ruwa a bokiti da abun guga ya goge ma ka terrasse d'in nan. Bud'a labulen su ka yi su ka shiga da sallama ta na mai satar kallon falon, ba ta ji k'amshin turare ba sai k'amshin salade da ya sha man gyad'a, za a ci ko kuma an gama ci ma, ba kowa a falon sai plate da ya nuna a ciki a ka ci salade da kuma abun bredi ga ledar chocolat da cingam (chewing-gum) da bidon lemu, kai a tak'aice dai datti kawai, duk sai ta ji jikinta ya yi sanyi, ba komai ya zo ma ta a rai ba sai tunanin in har haka matar take, dole ce ta sa mijinta k'ara aure, in kuma ita za ta yi aiki da abin da ta koya daga wajen ayyoyinta na daga tsaftar muhalli, tsaftar jiki, kula da mai gida, to tabbas *Hasheer zai zama na ta ne ita kad'ai*, za su iya kaiwa k'adamin da lallai sai an ce ta asirceshi, za su kai matakin da zai daina kula uwar gidanshi kuma uwar 'ya'yanshi, ba fariya ba ce take ko kuma yarda da kan ta ne ya sa haka, abu d'aya da ta sani shi ne ita zuciya ta na son mai kyautata ma ta, sannan namiji d'an kulawa ne da riritawa, duk k'azantar namiji ya na son ke mace ki yi tsafta, musamman na su mijin da kwana biyu rak ta fahimci waye shi, yanda ya ke d'aukar ado kamar wani d'awisu, yanda ya ke killace duk abun anfaninshi zai saka ka raina kan ka. Bud'a k'ofar da suka ji ya saka ta saurin d'ago kai ta kalli mai fito, a tare gabansu ya yanke ya fad'i, sai dai kowace na da dalilin na ta fad'uwar gaban. Duk da ba shiri ne a jikinta ba, riga ce doguwa a jikinta ta tsadadden leshe da kuma tsadadden d'inki, babi kallabi a kan ta sai gashinta da ya bayyana, jikinta babu alamar datti ko kad'an, sai dai abun da ya saka gaban Faduma fad'uwa bai wuce ganin kyawun Saudat ba da kalar fatarta, a take ta ji ta tambayi kan ta "Ya aka yi Hasheer ya kalleni?" Ta san ita ma kyakyawa ce daidai gwargwado, sai dai Saudat ta dameta ta shanye gaskiya, sannan ga ta fara sol irin farin nan da idan ya na samun gyara ya ke d'aukar kalar yelow ya yi kyau. Tartsetsiyar iPhone d'in da ke hannunta zai nuna ma ka 'yar zamani ce ita ma, yanayin shigarta da fuskarta za ta fallasa ma ka ita d'in wayayya ce, amma fa a sanin zahiri kenan. _(A to, dan kyan d'an maciji ne)_ Ba komai ya haddasa ma Saudat fad'uwar gaba ba sai ganin nutsatsiyar kamilalliya kuma fuskar tausayin Faduma, babu dai kwalliya a fuskarta ita ma, sai dai a take ta hango wani b'oyayyen sirrintaccen kyau da sai ka ma ta kallon basira za ka gano shi, d'an leb'enta na k'asa mai fad'i na sama kuma tsukakke, siririn hancinta har baki da kuma dara-dara idonta wanda da kad'an farin ya fi bak'in girma. Tabbas bak'a ce, sai dai a yanzu da ta ga kalar fatar Faduma sai ta ji ta na kallon ma su kiran Faduma bak'a da mahaukata, domin kuwa ba su gano ni'imatacciyar farar fatarta a bayan bak'ar ba, a zahiri kam bak'a ce ba wai irin bak'i wulik ba, musamman yanzu da ta samu gyara wani b'oyayyen yelow ya shiga a cikin bak'ar ya sirka shi ya bayar da kalar da za ta saka ka kallonta, wannan sirrin ya kayar ma ta da gaba sosai. Takowa ta shiga yi ta na ci gaba da kallon fuskarta kamar yanda ita ma ta ke kallonta, da k'yar Faduma ta k'ak'aro murmushi tace "Sannu aunty, ai mun shigo mu na ta sallama shiru ashe ki na ciki." Sake murtuke fuska ta yi ta dafe k'ugu ta tsaya k'ik'am gabanta ta na binta da wulak'antaccen kallo tace "Wacece ke?" D'an muskutawa ta yi ta kalli Izzadeen da shi ma ya ke kallonta, kallon Saudat ta yi ta na murmushin yak'e tace "Aunty Saudat sunana Faduma, ban san da zuwanki ba sai d'azun nan, shi ya..." Hannu ta d'aga ma ta tace "Dakata malama?" Shiru ta yi ta na kallonta da mamaki, gyara tsayuwa ta yi ta aje wayarta kan kujera tace "Me ya kawoki nan? Gulma da kinibibi? To bari kiji yarinya, ni ba irin sakarkarun matan nan ba ne, asirinki ba zai tab'a tasiri a kai na ba, wallahi ki ka sake shigowa b'angaren nan sai na karya mi ki k'afa, ki zauna a inda ki ke na zauna inda na ke, kin fahimta?" K'asa ta yi da kan ta ta na sauke ajiyar zuciya da zaro idonta, a hankali ta mik'e tsaye zuit hakan ya sa tsayinsu daidaituwa a kan daidai, kallon cikin idonta ta yi ba tare da rusunawa ko ladabi ba, dan ta fahimci ba wacce za ta girmama kai tsaye ba ce, d'an tab'e baki ta yi tace "Asiri?" Girgiza kai ta yi ta sassauta murya saboda yaron dake zaune tace "Ban san shi ba, aunty Saudat zan ba ki shawara, kar ki fara min irin haka tun yanzu, dan rashin d'aukar haka zai sa na mi ki abin da za ki ciji yatsa, ki kwantar da hankalinki mu zauna lafiya, ko kuma dai ki matsani a bango na kwanto mi ki kurar da za ta kai ki k'arshe." Cikin ladabi ta raunana murya tace "Ki yi hak'uri aunty Saudat, Allah ya baki lafiya." Juyawa ta yi ta kalli Izzadeen ta tara mi shi hannu tace "Mu tafi ko?" Da sauri ya b芒 ta hannun da shi dai da za ta zama mamanshi da ya yi farin ciki, fizgo hannunshi Saudat ta yi hakan ya sa Faduma juyowa da sauri, juyowarta tare da d'auke wutarta sakamakon marin da Saudat ta wanka ma ta a fuska lafiyayye tafiyayye d'an zamani daga hannunta, da sauri ta dafe kumcinta ta na kallon Saudat, baya ta yi da Izzadeen ta sake zaro ma ta ido tace "Na mareki, akwai abin da za ki yi?" D'auke hannunta ta yi daga kumcinta ta yi murmushin yak'e tace "Ba zan rama ba, dan ba zan yarda na zama kamar ke ba, ko ba komai ina so na yi daraja a idon mijina, kinga idan mu ka yi fad'a ai kimata da darajata za su zube, hakan zai sa ya fara tunanin ni ma dai karyar ce." A hassale ta nuna ta kan ta tana fad'in "Ni ce ma karyar? Ke ni ki ke kira da karyar?" Juyawa ta yi za ta kama hanyar madafa da sauri ta na fad'in "Ai kuwa za ki ga aikin karyar, har cikin gidana za ki shigo ki fad'a min magana." Da kallo ta bita har ta shige madafar, sai kawai ta sauke ajiyar zuciya ta girgiza kai ta sake kama hannun Izzadeen tace "Mu tafi." Ya na tafe amma ya na waiwayen bayanshi har su ka fita, a farfajiyar gidan ta kalleshi tace "Ina fatan dai ba ka da surutu?" D'aga kan shi yayi ya kalleta da alamar tambaya a fuskarshi, jinjina ma sa kai ta yi tace "Ina nufin ba za ka fad'awa Abbanka ba ko?" D'aga ma ta kai ya yi alamar eh, murmushi ta ma sa tace "Yawwa yaron kirki." Murmushi ya yi na jin dad'i su ka ci gaba da tafiya, basu ankara sai da ta zo daf da ita ta ji takun tafiya a bayanta, hakan ya sa ka ta saurin juyowa dan ta tabbatar ita ce, ta d'aga tab'aryar kenan ita kuma ta juyo Allah ya bata sa'ar rik'eta gam a hannunta, kallon juna su ka shiga yi sai kuma Saudat ta shiga kiciniyar k'wacewa ta na fad'in "Ba ni ki ka kira karya ba? Za ki gane baki da wayo." Da duka k'arfinta ta saka ta karb'i tabaryar ta na daka ma ta tsawa da fad'in "Dallah malama ya isheki haka." Cak Saudat ta tsaya ta na sakin tab'aryar hannun Faduma, Izzadeen ne ya ruga a guje dan shaidawa Abbanshi, ita kuma tuni ta nunata da yatsa tace "Sai yanzu ne na gane ba iya karya ba ce ke, ke tattariyar rik'akk'iyar jaka ce, yaushe rabon duniya da fad'a na had'a jiki? Ke dama baki san yanzu mata sun waye sun yi ilimi sun daina fad'an had'a jiki da kishiya ba, dan wata ta wannan hanyar ma za ta cutar da ke? Akwai buk'atar ki koma makaranta, dan ni da fari kallon mai ilimi na mi ki." Sa茂da ta sake matsowa daf da ita tace "Kar ki k'ara gigin tab'a lafiyar jikina, mijina ne kawai ke da wannan lamunin." Sakin tab'aryar ta yi kusa da k'afafunsu ta juya za ta koma ciki, saidai tahowar su Hasheer ya saka ta d'an tsayawa, Saudat kuma cikin hargagi da jin zafi ta matso ta sake finciko hijbinta tace "An tab'a ki, ki yi abin da za ki yi, karuwa kawai 'yar iska, ko kin d'auka ban san wacece ke ba? To kaf ina da tarihinki a hannu na, saida ki ka gama barbad'arki da gantal..." Wurga ma ta idonshi da ya yi ya saka ta saurin sakin Faduma tana had'e maganarta, a gaskiya sai yanzu ta fara jin nadamar yanda ta bari zuciyarta ta kamu da tsoronshi haka dalilin mari d'aya tak da ya kifa ma ta, ba dan haka ba yau da sa茂 sun ga tashin hankali a gidan nan. A hankali ya kalli Faduma da ta sunkuyar da kan ta, cikin nutsuwa yace "Fatima." A sauk'ak'e ta d'ago ta na fad'in "Na'am." Da ido ya ma ta alamar wuce ciki, saida ta fara lumshe ido alamar "Angama oga." Sannan ta saki murmushi tace "Umarninka abun cikawata ne, angama ranka shi dad'e." Juyawa ta yi ta nufi b'angarenta, yaran ma bayanta su ka bi, sai da ya ga babu koma ya kalleta ya tab'e baki, d'an k'aramin tsaki ya ja ya wucewarshi ya bi bayansu shi ma. Kamar za ta tashi sama haka ta juya ita ma ta koma b'angarenta, a madafa ya same ta tare da yaran ta na tambayarsu matakin karatunsu a islamiyya, saida ya faki idon yaran ya d'an daki mazaunanta, da sauri ta juyo sai kuma ta ji kunya ta sunkuyar da kan ta, hab'arta ya tallabo yace "Ta hassalaki ko? Ki yi hak'uri kin ji." Girgiza kai ta yi tace "Ko kad'an, ba komai ai ni ban rik'e ta ba." Shafa kuncinta ya yi ya na murmushi yace "Ashe ke ba mafad'aciya ba ce kamar yanda na yi zato." Kallonshi ta yi ta na murmushi tace "Kasan wacece Faduma kam a kan fad'a?" Da kallo mai kama da harara ya bita yace "Ko ma wacece ni dai ban damu ba, zan yarda ne kawai ranar da ki ka yi fad'a da ni har ki ka zubar min da hak'oran gaba." Bushewa ta yi da dariya cikin nishad'i ta ja baya ta na tattare siket d'in kayanta na kanti tace "Kar ka kauce dan Allah ka ga yanda zan ruguza ma ka fuska." Da k'arfi ta kawo ma sa shura kamar za ta bugi kan shi, sai kuma ta zille ta hanyar fad'awa k'irjinshi ta na dariya, tsamm ya rumgumeta a jikinshi ya na k'yalk'yala dariya, a hankali su ka raba jikinsu inda ya kalleta yace "Me za ki dafa mana?" Saida ta waina idonta kafin tace "Nama kawai na fara gyarawa, da wani abun da ka ke sha'awar ci ne?" Ganin yaran sun fita daga madafa ya sa ka shi kwantawa a bayanta ya na rik'e k'ugunta yace "Ki min abun mamaki kawai, amma kar ki manta da kakata, ina so ta zama ta farko da za ta fara cin abincinki, kinsan fa ta na kishi da ke sosai, dole ki yi yanda za ki shiga jikinta, dan kuwa k'orafi ta ke ni da auta duk mun auri tubawa." Siririyar dariya ta saki tace "Indai wannan ne zai farrak'amu, to zan shirya tsakaninmu yanda za ta tabbatar batuba ce ni." Sumbatar kuncinta ya yi yace "Shi ya sa na ke son ki." D'ora kan ta ta yi a bayanshi ta na shafo sumarshi tace "Ni ma haka." Sakinta ya yi ya tsaya da kyau a kan k'afafunshi yace "Yanzu da me zan iya taimaka mi ki?" Koren tattasai manya manya guda uku ta mik'a mi shi da wuk'a akan faranti tace "Wannan za ka taimaka ka gyara min." Cike da jin fa zai iya ya aje akan desk d'in wurin yace "K'aramin aiki, ya ki ke so a mi ki da shi?" Ba tare da ta kalleshi ba tace "K'ananan yanka." Saida ta fara d'ora tukunyarta ta kula da shi, dariya ta yi ta matso za ta karb'a ya kauce ya na fad'in "Babu ruwanki, ki yi aikinki na yi nawa, ladar kuma yanzu ake min bak'in cikin samu Batul." Girgiza kai ta yi tace "Zan nuna ma ka ta yanda zai ma ka sauk'i ne kawai." A hankali ya mik'a ma ta, ya na ganin yanda ta yi a d'ayan ya yi saurin karb'a ya na fad'in "Abun ma babu wuya." Ita dai aikinta ta ci gaba da yi a tsanake su na hira jifa-jifa, saida ta ji yace ma ta "Gashi Hajajju na gama, a kawo kud'in aiki." Kallonshi ta yi tace "Kai dai bawan Allahn nan akwai son kud'i, yanzu d'an aikin nan ma sai na biya?" D'aga ma ta gira ya yi, hakan ya sa ita ma ta d'aga mi shi girar ta kanne ido d'aya tace "Zan biya, amma sai da daddare." Saida ya aiko ma ta da kallon da ya kashe ma ta jiki yace "Kin tabbata za ki biyani? Kar fa ki min wayon da ki ka saba min duk sanda na tuk'aki a mota." Murmushi ta yi ta na wanke hannunta a gaban panpo tace "Idan ma ban biya ba ai yanzu gkdanka na ke, a cikin dare wani zai san lokacin da ka mitsikeni ne ka fanshe kud'inka." Dariya ce ta kubce mi shi ya juya zai fita ya na fad'in "Idan na zauna kusa da ke zan mutu dan dariya." Da sauri ta bi bayanshk ta jawo rigarshi ya dawo baya, a d'an tsorace ta kalleshi tace "Ina za ka tafi?" Da ido ya ma ta nuni tare da fad'in "Wanka zan yi." Zaro ido ta yi ta rik'o tafukan hannayenshi, saida ta d'aga k'afafunta yanda za ta riski kunnenshi dan ya fita tsayi kafin ta rad'a ma sa a kunne cewa "Ka na so ka ja mana babbar asara ne? Bayan ka yi aiki da koren tattasai shi ne za ka shiga ban d'aki." Sauke k'afafunta ta yi daga d'agawar da ta m没 su ta sake tsayawa gabanshi yar firit, kallon juna su ka yi ta murje ido tace "Haka kawai za ka kasheni, bayan ina son na haifa ma ka yan dagwai-dagwai." Tintsirewa ya yi da dariya ba tare da ya tab'a jikinta ba ya cabko bakinta a cikin na shi, da sauri sauri ya shiga tsutsa dan maganar da ta ma sa a kunne duk ta tayar ma sa da hankali, wani yam yam yam ya dinga ji a jikinshi. Tun ba ta kula ba bare ta taimaka ma sa har saida ya ci k'arfinta ta rik'e kan shi da kyau, saida ta ji k'afafunta na rawa za ta fad'i ta yi saurin janye jikinta ta na sunkuyar da kan ta, ganin haka kawai sai ya juya da sauri ya bar madafar ya na had'a k'afa, da k'yar ya kai kan shi d'aki ya na b'oye abin da baya so ta gani, yanda komai ya mik'e d'in nan tsigar jikinshi ta tashi, idan ta gan shi a yanayin nan za ta iya tsorata da shi, dan haka bai yarda ta gani ba ya baro ma ta madafar. _________________ Tunda ta kira waya ta na kuka tace Umma ta tura ma ta Halima hankalinta ya tashi, amma b芒 ta nuna ma ta haka ba cikin nutsuwa tace "Salima lafiya? Wani abu ya faru ne?" Cikin shashek'ar kuka tace "Umma kawai ki turo min 'yer uwata, ba na da lafiya ne." Sanyayyar ajiyar zuciya Umma ta sauke, ko ba komai hakan da ta ji ya kwantar ma ta da hankali tare da b芒 ta yak'inin 'yarta ta je a yanda ya dace, Halima na shirin tafiya makaranta Umma tace ta gaggauta ta tafi, cikin ba ta so ta turo baki tace "Umma 茅cole zan tafi fa yanzu, me zan ma ta idan na je?" A tsanake cikin rashin hargagi tace "Halima haka kawai za ta ce ki ji ne? Ta na buk'atarki ne saboda ba ta da lafiya." Turo baki ta yi tace "To Umma ba ga aunty Marfu'a ba, me zai hana ta tafi?" K'ura ma ta ido ta yi ta na kallonta, kallo ne na gama magana, in za ki tafi ki tafi, in ba za ki tafi ba ke ki ka sani. Da sauri ta koma d'aki ta canza kayanta ta fito, za ta wuce Umma tace "Zo nan." A hankali ta taho ta tsaya gabanta, kallonta ta yi tace "Ki saki ranki Halima, ki nutsu idan kin je ki taimakawa 'yar uwarki, ba ta da wacce ta fiki, ke ki ka fi cancanta da ki san sirrinta, ni na haifeta, sannan Meena na gaba da ke, amma duk da haka tace ke ta ke buk'ata, me ya sa?" Jiki a sanyaye Halima ta sunkuyar da kan ta, hakan ya sa ta mik'a ma ta ledar hannunta tace "Idan ki ka je ki ma ta anfani da wannan da ruwan d'umi, ta gasa jikinta da kyau." Jinjina kai ta yi ta na karb'ar ledar alamar gamsuwa, fita ta yi a farfajiya ta samu drebanta, fad'a mi shi ta yi inda za su nufa cikin ladabi kuma ya amsa ma ta da angama, tun a hanya ta ke ta tunanin abin da Umma ta fad'a, ko da dai ba yarinya ba ce ita tasan me ya faru? To amma dama abun na k'amari haka har sai antona ma ka asiri? (Wuce nan ma yarinya), kuma fa jiya sunyi yawa da ita da daddare tace za ta je ecole ita ma, kenan bayan sun yi yawar abun ya faru? Da wannan tunanin ta k'arasa gidan ta fita ta ce ma dreban ya je ta kirashi idan ta tashi tafiya. Ciki ta nufa da sallama, matsakaicin gida ne k'aramar villa mai kyau da ta dace da zaman ma'aurata masoya mata da miji da 'yan 'ya'yansu, da sauri ya fito yanayinshi kawai zai nuna ma ka a rikice ya ke ya na fad'in "Yawwa Halima, k'araso mana." Jiki a sanyaye ta shiga ta na sake wata sallamar, amma sai gaba ya ke yi ya na nufa d'akin vaccin Salima, tsayawa ta yi bakin k'ofar saida y'a juyo yace "Shigo mana, gata nan ai." A hankali ta shiga gabanta na fad'uwa ta na d'ora idonta akan gadon da ya nuna ma ta, rintse idonta ta yi sai kuma ta bud'e ta sake kallonta, da sauri Salima ta rarrafo daga kan gadon ta na fashewa da sabon kuka ta rumgume Halima da ke tsaye bakin gadon. A tsanake ta kali daren dake kan gadon, babu wani datti a kan ta da zai nuna wani abu ya fari, sai dai Salima ce kawai ka na kallonta zaka ga ta zube lokaci d'aya gashinta a warwatse, a hakan ma dan ya na da mugun tsayi da sulb'i, sai k'aramar rigar da ke jikinta shara-shara, muryar Aminu ce ta dawo da ita daga tunanin da ta tafi, murya ce ta wanda ya yi kuka kuma yanzu ma ya ke shirin yin kukan, a dak'ile a gigice a d'imauce ya kalli Halima yace "Halima dan Allah ki tayani bata hak'uri, ni ma ba a son raina haka ta faru ba yanzu yanzu wallahi tsautsayi ne, amma duk ta damu kan ta sai kuka ta ke, da k'yar ta bari na taimaka ma ta ma ta yi wanka, amma kuma har yanzu kuka ta ke ta na cewa ba ta son gani na." Ita wallahi kunya ya bata, to ita wacece da ya ke fad'a ma ta haka? To wai ba ya jin kunya ne da ya k'i barin gidan kafin ta zo? Kai ita yau ta ga ikon Allah, cikin sanyin murya tace "Ba komai Amin, abin da ka yi ai shi ne abin da ya dace." A marairaice kamar a ce ma sa asss ya fashe da kuka yace "Hakane, amma ba a wannan lokacin ba, akwai lokacin da na ma ta tanadi ne, Halima har yanzu Salima yarinya ce k'arama, ba na so ta tsorata da ni." Gumm ta yi da bakinta dan wannan gaba kad'an zai fad'a ma ta yanda abun ya faru, a hankali ta ci gaba da shafa bayan Salima da ke shashek'ar kuka, sun jima haka babu wanda ya ce wani abu, saida Halima ta kalleshi a kunya tace "Zan taimaka ma ta, dama Umma ta turo ni." Jinjina kai ya yi alamar to, sai kuma ya k'urawa Salima ido, kamar ya jawota ya mayar a cikin cikinshi ya ke ji, wata masifaffiyar k'aunar yarinyar ce ta huda zuciyarshi daga k'arfe 06:30 zuwa yanzu 07:58, sai yanzu ya tabbatar da aka ce *wani hanin gaAllah baiwa ce*, hak'ik'a Allah ya musanya mi shi da ma fi alkairinshi, a yanzu da yasan Salima ya tabbatar shi ne mutum na farko da ya fara kai ziyara a cikin aljannarta, sai kawai ya ke jin matsanancin kishin ko ma waye ya rab'a jikinshi da na ta, wanda da Faduma ce ba lallai ya ji haka ba, ko kuma dai zai iya kamuwa da kishin mutumin da ya banzatar da ita ya wofantar da ita, lallai Allah shi ne Allah, mai kyauta da k'ari, ya rabashi da Faduma sai ya ba shi Zulfa, ita ma aka yakiceta daga jikinshi aka bashi matar shi abar son shi Salima, yarinya shakaf da ko shekara goma sha bakwai ba ta shiga ba. Ya na fita daga d'akin Halima ta zauna bakin gadon ta tallabo fuskarta su na kallon juna, yanda jan fuskarta ta k'ara yin ja ta kumbura sai ta tausaya ma ta, a salamce tace "Me ya sa ki ke kuka haka k'anwata? Bayan kinsan abu ne da dama dole ya faru? Salima da k'arfi ya mi ki ne?" Cikin son dakatar da kuka tace "Bai min da k'arfi ba, kawai dai na tsorata ne a yanda ya zo min, sannan bai shiga da sauk'i ba, ina jin fa saboda na yi yarinya ne shi ya sa ya ketani gaba d'aya." 'Yar dariya Halima ta yi ta shafa kan ta tace "Ki yi hak'uri kinji, ki daina kukan nan ki na ga mijinki duk da d'aga hankalinshi saboda ganin ke ma ki na kuka, ki bari kinji." 'Daga kai ta yi alamar to kafin tace "Shi ma har kuka ya yi da ya ga ina kuka kafin zuwanki, kuma da kan shi ya min wanka da ruwan zafi, amma har yanzu jikina ciwo ya ke." Sake shafa gashinta ta yi tace "Yanzu ma ruwan zafin za ki yi anfani da su inji Umma, bari na tashi na d'ora." Jinjina kai ta yi kawai ta bita da kallo, fita ta yi inda zai sadata da madafa, Aminu ta samu a falo ba ta gan shi ba saida ta ji yace "Ta daina kukan Halima?" Da sauri ta juyo ta gan shi zaune kan kujera, d'aga ma sa kai ta yi a hankali tace "Eh, ta daina." Ya na ganin fitarta ya dawo d'akin da sauri, saida ta zabura ganinshi hakan ya sa shi saurin zaunawa akan gadon, kamo hannunta ya yi ya na kallo kamar na jarirai yace "Kin daina kukan beby?" Kallonshi ta yi da idonta kamar na barbie ta d'aga ma sa kai, tallabo fuskarta ya yi da kyau kamar zai had'a bakinshi da na ta ya na fad'in "Ki daina kuka kin ji, wallahi ba na da juriya akan abin da na ke so beby, ki taimaka min na zama namiji ni ma." Gyad'a ma sa kai ta shiga yi alamar to, sumbatar kuncinta ya yi yace "Beby kin same ni, na zama na ki ke kad'ai, ina son ki Salima, ke ma dan Allah ki so ni, kin ji?" Ya fad'a ya na sunkuyar da kan shi, d'ass ta ji abu mai lema akan cinyarta, ta na dubawa ta ga hawaye ne alamar kuka ne ya ke kenan, da sauri ta yi k'arfin halin d'ago kan shi cikin shashek'a tace "Shikenan to ka daina kuka, ni ma na daina, zan yi yanda ka fad'a." Da sauri ya yi ram da hannayenta ya na k'ure fuskarta da kallo yace "Salima ki ce ke ma ki na so na, ki so ni ko da kad'an ne dan Allah, ki killace min kanki ki zama tawa ni kad'ai." Jinjina ma sa kai ta shiga yi ta na zubo da hawayen da taji sun kasa tsayawa kuma ba ta san na miye ba, shigowar Halima d'akin ta tsaya turus ta na kallonsu ya saka shi saurin mik'ewa ya fita falon, da kallo ta bishi ta na fad'in "Anya kuwa na iya zama da abun kunyar nan?" K'arasowa ta yi ta zauna ta na kallon Salima tace "Gashi ke ba ki tafi makarantar ba, ni ma kuma ban tafi ba a dalilinki." Turo baki ta yi tace "Na tashi da asuba fa na gama komai, na shiga cikin kayana na makaranta na same shi d'akinshi dan na gaishe shi, dan tunda na zo kowa a d'akinshi ya ke kwana, har na gaisheshi na fito bai daina kallona ba, ina shigowa d'aki na d'auki jakata zan zauna falo na ci abinci na jira lokacin tafiyata, dan ya ce zai kaini da kan shi, sai kawai ya shigo d'aki ni dai na ganshi ba kamar yanda na saba gashinshi ba, sai yace min wai baya son jin k'amshin turaren nan na jikina, indai har fita zan yi to kar na fita da shi, na juya zan canza hijabina da na saka ma turaren kawai na ji ya rumgume ni, daga nan fa kawai sai mu ka zo a wannan matakin." Dariya Halima ta k'ara yi tace "To ai wannan shi ne girman Salima, yanzu kin ga ni ke gaba da ke, amma auren da ke kan ki yanzu ya sa kin fi ni daraja da mutumci a idon ma su daraja, matakin da ki ka hau kuma zai iya fizgo shekaruna ya damk'a mi ki a hannu, Salima bugu da k'ari kin samu nutsuwa yanzu da salama tunda kin wuce wannan matakin, mu 'yan baya sai fargaba da zulumin yanda za ka je wa mijin, da kuma yanda na ka daren farkon zai kasance, ki duba ki ga ikon Allah maganar aurena akhi ya tsayar fa, wanda ake jiran k'arshen hutu ya zo a yi, ko a tunani babu wanda ya tab'a kawowa a had'a da aurenki, amma sai gashi yanzu ina gidanki zaune." Jinjina ma ta kai ta yi alamar gamsuwa tace "Hakane, ke ma insha'Allah k'arshen hutun na zuwa za a yi bikinki da yaya *Saif*." Cikin zolaya tace "Zuwa lokacin ai da tsohon cikinki ma." Da k'arfi tace "Ciki kuma? Da wuri haka?" Hararenta ta yi tace "Wane irin da wuri? Wata biyar ne nan gaba fa." Zaro ido ta yi tace "Ukhtee, ni fa ba zan yarda na yi ciki yanzu ba, ni ba zan sake yarda ba gaskiya ciwo ke akwai." Mik'ewa ta yi ta fita ta na dariya, jim kad'an ta shigo da bak'in bokiti ta nufi ban d'akin Salima, saida ta ji fad'uwar gaba saboda ganin kayan Salima a wanke a shaye zanin gado da pant d'inta, a babbar roba ta juye ruwan sai dai ba duka ba ta d'an sirka ma ta, sauran kuma a butar k'arfe ta juye ma ta su kafin ta fito ta taimaka ma ta su ka shiga, sai da taa fito kafin ta cire rigarta ta fad'a ruwan ta zauna, sosai ta rintse ido k'walla na dararo ma ta, amma da aka d'an jima sai ta daina jin zafin kuma sai k'amshin karanfani kawai. Ta na fitowa Halima ta kawo ma ta abun karin ta ajiye ma ta, a lokacin Aminu ya shigo ya na fad'in "Ya jikin na ta Halima?" Halima dai b芒 ta kalleshi ba tace "Da sauki." Da k'yar ta yi dubara ta saka doguwar riga dan tsaye ya ke bai fita ba, ta na zaunawa za ta fara cin abinci ya zauna ya karb'i cokalin yace "Bari zan ba ki da kai na." Ba ta iya mi shi musu ba sai Halima da ta mik'e ta fita, a hankali ya ci gaba da b芒 ta abincin ya na gyara ma ta gashinta da ke d'an dawowa gaba, Halima ce ta sake shigowa da babban kofi na roba a hannunta, kallon Salima ta yi tace "Kin gama ne?" Da sauri ta d'aga ma ta kai alamar eh, mik'a ma ta had'in maltina da peak had'e da kanunfari a ciki da kuma markad'add'en dabino ta yi wanda aka zuba garin raihan a ciki (Had'in martaba kenan), dad'i ya sa Salima kifa kan ta saida ta shanye tas ta na jin sanyin na ratsata, hamdalah ta yi hakan ya sa Aminu cewa "To kwanta ki huta kin ji." Saida ya gyara ma ta kwanciya kafin ya mik'e ya fita, a lokacin Halima ta d'an k'ara gyara ma ta d'aki ta ma ta turare kafin ta shiga dan girka m没 su abincin rana dan ta gama da wuri ta bar gidan. _Masu neman k'arin bayani akan garin tukunya, ku sani ba gari ne mai sauk'in samu ba da ake fad'anshi ga kowa a kuma kowane lokaci, sirri ne mai matuk'ar mahimmanci dans rik'e jikin mace tsakanin haihuwa da haihuwa, duk mai buk'atar garin ta tuntub'eni ko kwateta (Sajida) duk inda ka ke za'a aika ma shi da yardar Allah, sannan akwai turare na ruwa da sabulun gyaran fata._ *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 21:43 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _76_ Ta jima zaune tare da yaran suna wasarsu ta na kallonsu ta na amsar wayar wanda ta ke kira, tunda ya tafi sallah magriba tare da yaran ya turosu gida shi bai shigo ba, hakan ya bata damar jimawa su na waya da dada, sun sha hira sosai ta na fad'a ma ta gamonta da auta, ita dai dariya kawai ta ke ma ta, sai daga bisani ta fad'a ma ta Saudat ma ta dawo, amma b芒 ta fad'a ma ta na su gamon ba, dan in ta fad'a ko yau ba ta zo ta rama ma ta marinta ba, to shakka babu duk randa ta zo sai ta mareta ko da bayan idon Faduma ne. Suna yin sallama wasu daga cikin k'awayenta na yarinta ta kira irinsu Maryam da su Izza, daga baya kuma ta kira k'awarta ta yanzu Fa'iza, sun gaisa sosai kafin ta ma ta k'orafin yaushe za ta zo gidanta, ta bata tabbacin za ta zo ranar da b芒 ta aiki a asibiti dan su jima su na hira, anan ta b芒 ta kwatencen gidan kamar yanda ta buk'ata tare da tabbatar ma ta idan ta tashi zuwa za ta kira ta fad'a ma ta. Ganin dai zai d'auki lokaci sai kawai ta zubawa yaran abinci su ka ci, wanka ta mu su ta saka mu su kaya marar nauyi, cikin nutsuwa sai bacci ya fara d'aukar yaran, dan yau kam sun ji a jikinsu sun samu kulawa, su kansu yanayin ne ya mu su dad'i inda iskan ac ke hura mu su iska har baccin ya d'aukesu. D'an fitowa ta yi farfajiyar da wayarta a hannu ta na neman kiran lambarshi, sai dai ba ta kai ga aika kiran ba ta ga Mujaheed ya fito daga b'angaren Saudat ya shiga motarshi ya fita, tsaye ta yi ta na mamakin wanene shi? Ba ta san shi gaskiya, sai dai ya ma ta kama da zubin k'ira irin na Mukhtar, shi ma a wunin da su ka yi gidan Umma ta gan shi har suka gaisa, to wanene waccen? Ta sake tambayar kan ta. Fita kawai ta yi daga lambarshi ta shiga duniyar WhatsApp dan ganin me ke faruwa, a cikin sak'onnin da su ka dinga shigo ma ta har da na wani da ta saka ma sunan *idon gari*, tun za kafin ta shiga shari'ar nan fa ta nemi wasu bayanai a gun shi, amma shi ne sai yanzu ya maido ma ta amsa, cikin nutsuwa ta dinga sauraren abin da ya turo ma ta, kamar za ta mutu tsabar mamaki da firgici, ta jijjiga sosai ta kuma shiga kokonto da tunani mai zurfi, ta na cikin yanayin ta ji k'arar bud'e k'ofa, ta na d'aga kan ta ta hangeshi a cikin takon nutsuwa duk da k'irarshi ta k'arfi, amma ya na takawa kamar ba ya son taka k'asa. Da sauri ta aje wayar akan ginin corridor ta tunkareshi da fara'a a fuskarta, shi ma murmushin ya shiga sakar ma ta har su ka rumgume juna, ba tare da sun raba jikinsu ba har suka nufi d'akin bayan ta d'auki wayarta. *Washe gari* Ita kawai suke jira a gurin cin abincin, ta na fitowa d'auke da lemu ya kalleta kamar zai yi kuka cikin shagwab'a yace "Batul yunwa na ke ji, ki zuba min abinci ko na yi kuka." Da dariya ta k'araso ta na fad'in "Idan mutum ya yi kuka yanzu saboda yunwa ai ya nuna an saba dama, kuma babu wanda ya isa ya hanamu dariya ni da yara na." Kallonsu ta yi sai dariya su ke tace "Hakane ko?" Duk d'aga ma ta kai su ka yi harda cewa "Eh." Zaune ta yi ta shiga zuba mu su abincin da sauri sauri ta kalleshi tace "Amma dai kasan ka cinye abincinka yanzu anjima ba ka da wani ko?" Marairaicewa ya yi yace "Sai na je gun Umma na ta bani wani na ci, kuma ma ai ni ban tab'a jin yunwa da safaffe irin haka ba." Wani makirin kallo ta mi shi tace "Me ya janyo hakan kenan?"Saida ya kashe ma ta ido yace " Yak'in duniya na uku, wanda ya wakana a farfajiyar dajin soyayya, a k'arknashin kukawar k'auna, cike da tallafin k'orama had'e da taimakawar sumba." Dariya ta shiga k'yalk'yalawa ta na zuba abincin, da k'yar ta mik'awa yaran da su dai ko a jikinsu tunda ba su fahimta ba, shi ma mik'a mi shi ta yi ta na fad'in "Ka ce duniya ta zauna lafiya, tunda jejin ya samu isashen ruwa daga wadatacciyar k'orama." Lumshe ido ya yi ya na murmushi, da hannu ya ma ta alamar matso, d'an duk'o da kan ta tayi cikin rad'a yace "Hankalin komai a kwance ya ke, sai dai wannan turaren na ki ya kan d'aga min hankali dayawa, ba na so ki d'auka ni jarababbe ne." Dariya ta shiga yi ta kalleshi tace "Idan ma kai d'in shi d'in ne, ka sani Batul za ta iya da hakan, dan dama hakan na d'aya daga cikin nauyin da ke kai na." Kallon k'auna ya bita da shi yace "Da gaske?" Cike da tabbaci ta d'aga ma sa kai alamar eh, jinjina kai ya yi ya fara cin abincin yace "Za mu gani, wacce har yanzu kunya ta k'i barinta." Da murmushi tace "Zan daina, nan gaba kad'an." Mayar da hankalinta ta yi kan yaran su ka ci abinci, odar da Qaseem ya dinga yi ne ya saka su mik'ewa da sauri su na d'aukar jakarsu, mik'ewa ta yi ita ma ta rakasu bakin k'ofa ta dinga d'aga mu su hannu ta na mu su addu'ar Allah ya tsare su kuma kula sosai. Dawowa ta yi su ka ci gaba da nishad'insu da raha har suka kammala cin abincin, mik'ewa ya yi ya kama hannunta yace "Mu je." Binshi kawai ta yi har su ka isa falon Saudat, sun sameta zaune ta rasa me ke ma ta dad'i, ganin yaranta ko wajenta basu tafi ba ya sakata zubar da hawayen bak'in cikin da ya mata yawa. Ba ta amsa sallamarsu ba sai ma share hawayen da ta yi, zaune Faduma ta yi shi kuma ya zauna kusa da Saudat, da k'yar ya had'e abin da ke tsakaninsu ya taushe ya kuma b'oye dan kar Faduma ta fahimta, d'an d'ora hannunshi ya yi a kan cinyarta ya kalleta da kulawa yace "Lafiya Umman Deen?" K'uri ta ma sa da ido ta na kallo, a ran ta take ayyana "A gaskiya ba dan shakkarka da na ke ji yanzu ba, wallahi da sai na mu ku hauka a gidan nan." A zahiri kam d'an janye hannunshi ta yi daga k'afarta ta girgiza kai cikin dakusashiyar murya tace "Ba komai." D'an tab'e baki ya yi yace "Haka kawai ki ke kuka?" Cikin jin haushi ta d'an murgud'a baki tace "Ba na jin dad'i ne." Gyara zamanshi ya yi yace "To ku saurare ni, zan yi magana da ku ne mai mahimmanci." Harara ta wurga mi shi, wato zai mu su wannan bak'in bayanin yake nufi? A gaskiya ba za ta iya saurara ba, dan haka ta mik'e tsaye ta na dafe mararta tace "Marata ciwo ta ke, zan shiga ciki na sha magani na." Ba ta jira amsar kowa ba ta juya za ta shige, kallonta ya yi sai kuma ya kalli Faduma ya ma ta murmushi yace "Fati, mu tafi ko?" Murmushi ita ma ta ma sa tace "Idan haka shi zai faranta ran ka ba." Mik'ewa ya yi ya matsa kusanta ya kama hannunta, juyawa su ka yi za su fita Saudat ta juyo ta na kallonsu, ranta a matuk'ar b'ace tace " *Hasheer*." Cak ya tsaya ya juyo ya na kallonta, ba ta fiya kiran sunanshi haka kai tsaye ba, dan haka ya yi mamaki, amma sai ya d'aga ma ta gira ya na murmushi yace "Ya dai uwar gidana, da matsala ne?" Cikin gatsali tace "Ina son magana da kai ne." Wata ajiyar zuciya ya sauke ya kalli Faduma, sakin hannunta ya yi da ido ya mata alamar "Je ki ina zuwa." Amsa mi shi ta yi da ido ta hanyar lumshesu sosai da d'an rusuna kan ta alamar "Angama ranka shi dad'e." Saudat da ke kallonsu haushi kamar zai kasheta, ita ta rasa wane iskanci ne su ke yi da ido, haka jiya ma ta ga ya ma ta da ido ita ma ta amsa, takawa ya fara yi hakan ya saka ta kallon Faduma ta ja tsaki tace "Sai a bamu wuri ko? Zan gana da mijina, ko kuma za ki hana ne?" Wani murmushi ta yi kawai ta sa kai ta fita ta na mai jin dariya ma za ta kubce ma ta, to ita da ta yi niyya ai da ta hana, tsoron Allah ne kawai ke saka ka d'aga k'afa akan wani abun. Su na shiga a bakin k'ofar ya ja ya tsaya ya na aika ma ta kallon jin haushi, suna had'a ido gabanta ya fad'i sai kawai ta marairaice dan kiyaue sake d'aukar irin mahaukacin marin nan, cikin muryar shagwab'a tace "B茅b茅 wai me na ma ka? Ka daina kulani gaba d'aya, ko ka daina so na ne yanzu?" Lumshe ido ya yi ya d'an bud'e a kan ta, saida ya gyara tsayuwarshi sosai yace "Me ki ka min ki ke tambaya ta? Ba komai to, amma ki sani inhar wannan ce d'abi'arki to ni ma sabon halina kenan a kan ki, Saudat ke ba ki isa na kwanta ki jani a k'asa ba, kin gane?" Ko da ya fad'a ya juya sai kuma ya tsaye ya sake juyowa ya kalleta, cike da shak'iyanci yace "Ko dai matsalar kud'i ce? To kar ki damu zan aiko mi ki anjima, idan kuma kayan abinci ne matsalar shi ma zan kawo mi ki, amma za ki iya dafa iya bakinki kawai, tunda yanzu amaryata ta zo za ta dafa min ni da yarana mu ci, hasalima sai mun zab'i wanda ranmu ya ke so." Fita ya yi ya barta nan tsaye ta na kukan bak'in ciki da takaici, kamar ta kama da wuta haka ta ke ji, kamar ta samu kan ta ta ciza ko za ta ji sauk'i. *Bayan kwana biyu* Tun ranar da ya fad'a ma ta magana har yanzu ba ta sake ganinshi da idonta ba, sai dai ta hangi motarshi za ta fita daga gidan ko kuma ta shigo, shi ko a waya baya kiranta bare sak'o, tun a ranar dai ya aiko Izzadeen ya kawo ma ta kud'i, sai gashi kud'in kansu sun bata haushi duk da yawansu. Yaranta ma haka ta na ji tana gani sun k'aura a wajen amarya, sai dai ta ga wulgawarsu suna wasa, sai dai su shigo da gudu su d'auki wani abu a cikin kayan wasansu ko na buk'atarsu su fita, ba ta so ta hanasu ya ma ta k'ansk'ancin da ya ambata ta hanyar rabata da su gaba d'aya, shi ya sa ta kawo ido ta zuba ta na kallo, gashi Umma ce kawai za ta iya magana a saurareta, sai dai kuma ta na jin kunyar Umma kuma ita ma tasan ba za ta kula ta ba. ...Har ranar girkinta ta zo kuma ya dawo b'angaren, amma sai ya dinga ma ta kisan mummuk'e daga tsaye, a d'akinshi ya ke kwana haka ma yaran a na su d'akin, a kwana biyun kowace safiya ya kan bata kud'in cefanai, amma sai yace ta dafa ita kad'ai, shi kam tunda amaryarshi ta zo zai ci a wajenta. Amma fa bai tab'a cin abinci a wurin Faduma ba, ita ma ya na fad'a ne dan ya tunatar da ita abin da ta sha fad'a mi shi, na ban dafa ba, ka juia amaryar ta ka ta zo saita dafa ma ka. Bata tab'a kula mi shi ba dan tsakaninta da Allah tsoronshi ta ke, saai ya fita take zubewa ta sha kukanta ta yi ta kumbura ta na jin kamar ta kashe Faduma, dan inhar za ta samu damar da za ta karta kam sai ta yi aiki da damar, sai dai ita ma d'aureta. *A* hankali ta k'arasa bakin d'an k'aramin kogin nutson (swiminpool) jikinta duk a mace, dan yanzu kam ta rasa kuzarinta ma, Faduma ta samu tsaye ita ma a wurin ta na kallon ruwan ta na amsa wayar Abanta, cikin nishad'i da farin ciki su ke wayar ta na jin kewar mahaifinta. Kamar daga sama kawai Saudat ta sa k'arfinta ta turata baya ta fad'a a cikin ruwa, ji ka ke tamjam tare da k'walla k'ararta a lokaci d'aya data karad'e gidan, a gigice ta shiga paputukar fito da kan ta sai dai b芒 ta iya ruwa ba, ina ma ta gansu bare ta koya? Hakan ya sa ka ta fara gabalaita ta na nitsewa a ciki duk da k'ok'arinta na son ta kawo bakin gab'a. Sanin inda ya barota yanzu da kuma jin k'ararta ya sa ka gabanshi tsintsinkewa ya fad'i, a firgice ya mik'e da gudu ya fito hankalinshi na d'ugunzuma, ya na hangenta a ruwan nan da Saudat tsaye ta dafe k'ugu ta na fad'in "Jira na ke ki k'arasa na bar wurin, shegiya la'ananna." Bai jira komai ba wajen fad'awa ruwan ya tsamota a jikinta, bakin gab'ar ya fara kwantar da ita kafin ya fito shi ma shaddarshi sharkaf da ruwa, girgiza fuskarta ya yi sai dai idonta a rufe su ke, a hankali ya d'an tausa cikinta amma b芒 ta motsa ba, sunkuyawa ya yi sosai ya sa yatsa biyu ya rufe ma ta hanci sannan ya saka bakinshi cikin na ta ya hura ma ta, da k'arfi ta sako tari tare da ruwa a bakinta, tari ta shiga yi har ya taimaka ma ta ta zauna da kyau ta na zubar da ruwan bakinta, kallon juna su ka yi ganin idonshi jajir ya saka ta sadda kan ta k'asa. Juyawa ya yi ya kalli Saudat sai kuma ya kalleta, a dak'ile yace "Me ya had'aku?" Girgiza kai ta yi tace "Ban sani ba, ban san komai ba." Sake juyawa ya yi ya kalli Saudat da ta fara ja baya, mik'ewa ya yi da azama zai rik'ota ya matseta a hannunshi ya tambayeta me ya faru? Amma da ta lura da ba za tasha ba sai kawai ta ruga a guje ta yi b'angarenta, da kallo ya bita, mamakin yanda ta ke gudun nan, to yanzu a ganinta idan bin ta zai yi za ta tsere ma sa kenan? Gudun da ya ke da tabbacin tako uku zai yi ya kamota, tsaki kawai ya yi ya juyo kan Faduma da ke shirin mik'ewa, taimaka ma ta ya yi ya na kallon jikinta da ke tsamo tsamo da ruwa, kamata ya yi zai nufi da ita b'angarenta ta d'an juya ta duk'a ta d'auki wayarta da ta fad'i a k'asa sanda za ta fad'a ruwan. Haka rayuwar gidan ke tafiya, ba su cika had'uwa ba ko a farfajiya, dan tunda Faduma ta gane mi ye nufin Saudat a kan ta sai ta zab'i zaman b'angarenta dan b芒 ta so ta kai ta bango har ta nuna ma ta zuciyarta, ba ta so ta rasa kimarta a gurin mijinsu, ba ta so su tayar ma sa da hankali. Sai dai duk da jarabarta akan saka ido da bincike, ta kasa gane babu shiri tsakanin Hasheer da Saudat, dan lokuta da dama haka zai dinga karb'ar waya a gabanta kamar ya na magana da ita, wani lokacin kuma zai ce ya tafi can su gaisa kamar da safe ko da dare, hakan ya sa ba ta fahimci komai ba, yaran ne ma ke bata mamaki duk yanda za ta ce su tafi wajen Ummansu su gaisheta sai su nuna basa so, har su kan fad'a ma ta ita dukan mutum take kuma b芒 ta ma mutum dariya da wasa, a haka har suka kwashe kwana *goma* da tarewarta gidan nan. ________________ Duba da za ayi kwana uku babu karatu ya sa Tagur shiryawa tare da Amjad suka tafi Zinder, sun yi mamaki k'warai da suka gan su tare, hakan ya ma Aba dad'i har ya kasa b'oyewa, sai dai shi ma ya gama yarda Tagur ya gama cinye wannan wasar ta su tunda har shi ne uban yaron da su ke matuk'ar so, dan yaro ne abun so ko dan wayonshi da hazak'arshi. Ayya ce dai da Herde ba wani sakar ma sa fuska suke ba, dan su kad'ai suka san me suke ji a ransu a game da shi, tabbas dan yafewa sun yafe sai dai har yanzu suna tuna rayuwar 'yarsu, amma duk da haka sun yi farin ciki da ya juya ya barshi nan ya kuma fad'a mu su dama nan d'in ya kawoshi, nan da kwana biyu zai dawo ya d'aukeshi da kan shi. ________________ Cikin ladabi ta shiga matsa mata k'afafun, ita ma a kunyace take fad'in "Ya isa haka wannan 'ya, nagode da d'awainiya kin ji, Allah ya mi ki albarka." Da murmushi tace "Ameen Hajia, nagode nima, Allah dai ya baki lafiya." Murmushi ta yi ita ma cike da k'aunar surukar ta ta tace "Ameen." D'orawa ta yi da fad'in "Wai ina autan ya ke? Tun safe ban ji motsinshi ba." Da kunya tace "Hajia kinsan yana ta shirye shiryen tafiyar nan, ni ma tunda ya fita sallar asuba ban kuma ganinshi ba." Ta na rufe bakinta ya na sallama d'akin, amsa mi shi sukayi da kulawa har ya k'araso ya zauna, da mamaki Dada ke kallonshi ganin kayan motsa jiki a jikinshi, kuma ba da su ya fita ba, kallon ta ya yi shi ma yace "Yarinya kawo min ruwa mai sanyi." Saida ta d'an cilla ma sa harara ta mik'e ta nufi fridge, kawo ma sa ta yi ta tsiyaya ta mik'a ma sa, kallonta ya yi da idonshi na gajiya yace "Ba durk'usawa za ki bani ruwa haka? Ni tsaranki ne?" Da wani mahaukacin mamaki ta kwale baki ta na kallonshi, d'an rufe bakin ta yi ta durk'usa ta mik'a ma sa, karb'a ya yi ita kuma ta mik'e ta koma kusan Hajia ta na tausa ma ta k'afafun, sai da ya shanye tas ya kalleta yace "Zo nan." Sunkuyar da kai ta yi a zuciyarta ta na fad'in "Wallahi bawan Allahn nan ya kaini bango." Ta na zuwa ya bita da kallo tsaye kuma? Sunkuyawa ta sake yi ta na jinjina lamarin Abdallah, ikon da ya ke ma ta Kenan a gidan nan, in ba ta yi ba kuma ta sha matsa a ciki, kofin ya mik'a ma ta yace "Aje a k'asa." Wani murmushi ne ya taho ma ta ba ta shirya ba, ta aje a k'asa? Shi ya sa ya kirata dama? Hmmmm! Karb'a ta yi a hankali ta aje, kallonshi ta yi tace "Da wani abun da ka ke so kuma?" Girgiza kai ya yi a kasalance alamar a'a, mik'ewa ta yi za ta koma ta zauna yace "Ke je ki had'a min ruwan wanka." Hajia ce ta yi saurin cewa "Kai auta lafiyarka k'alau kuwa? Kaga wannan haukan na ka ke had'a ni da kai fa, ba dan ma tana yarinyar kirki ba kai ka isa ka juyata ne? Tunda safe take d'awainiya dani yarinyar nan, shi ne yanzu za ka bi ka addabeta." Lumshe ido ya yi ya na shafar sumarshi yace "Yo Hajia ba ikon kenan ba? Ita ai tasan waye ni." Kallon juna su ka yi da dada da za ta fita, haya d'aya ce da tasan za ta huce ita ma, sai kawai ta sassauta murya tace "Ni ban sani ba autan Hajia, yaushe ma ka girma?" Da sauri ta fita a d'akin amma duk da haka saida ya bi ta da gudu ya na fad'in "Ke! Ni ne ma yaushe na girma? To idan na mi ki ciki za ki sani." Girgiza kai Hajia ta yi ta na murmushi, ko ba komai yanda ta ga bazawarar ta kawo canji a rayuwar yaronta hakan ya mata dad'i. Haka shi ma ta b'angaren jikan na ta Hasheer ta na ganin nutsuwa a tare da shi, haka ma ranar da suka zo nan tare da Faduma da yaran ta yi murna sosai, musamman da yaran su ka dinga fad'a ma ta abin da ta ke musu, sai ta ji ta na mamaki da kuma al'ajabin yarinyar, dan ba kasafai aka fiya samun ma su son uba kuma su so 'ya'yanshi ba a yanzu. _________________ Vibrations d'in wayarshi ne ya tasheta a baccinta, da k'yar ta b'amb'are kan ta daga jikinshi sabida rik'on da ya mata, yunk'urawa ta tashi zaune za ta daddab'ashi sai kuma ya farka shi ma, ganin haka sai ta sauka daga kan gadon ta na gyara yar yaloluwar rigar baccinta ta shiga ban d'aki, wani irin fitsari ne ta ji ya cika ma ta mara duk da b芒 ta jima da kwantawar ba, dan Hasheer kam darzar amarcinshi ya ke a kan ta ba k'akk'autawa, a cikin ban d'akin ta ji muryarshi sosai cikin tashin hankali ya na fad'in "Kinga Salima saurare ni ki nutsu ki fad'a min abin da ya ke faruwa, ina Aminun ya ke yanzu? Me ya sa me shi?" Da sauri ta gama abin da take ta fito ta na kallonshi ya na k'ok'arin saka kaya ya na sauraren Salima na fad'in "Akhi dukanshi su ka yi, wai takardu zai ba su shi kuma ya k'i, shi ne su ka yi k'ok'arin tab'a jikina shi kuma ya dinga fad'a da su, akhi ina jin tsoron kar ya mutu, wallahi akhi ni ma ina son mijina." Saida ya zari makullin mota zai fita yace "Babu abin da zai samu mijinki, gani nan zuwa sai a kaishi asibiti kinji, ki daina kukan nan." Da sauri ta shiga gabanshi ta na tsareshi da ido tace "Lafiya? Me yake faruwa?" D'an matsawa ya yi da ita gefe ya na fad'in "Fati babu lokaci, ina zuwa yanzu, zan fad'a mi ki." Kafin ta yi magana har ya fita daga d'akin, da kallo ta bishi da addu'ar Al'ah ya sa lafiya ya kuma tsare ma ta shi. Gudu ya ke sosai har ya isa gidan kamar yanda Umma ta fad'a mi shi a kwatence kwanan baya sanda zai turo mu su kayan abinci, tunda Aminu bahaushe a al'adarsu kuma haka ake, bud'e ya samu k'ofar gidan sai kawai ya shiga hankalinshi a tashe, a tsakiyar falon ya same ta zaune gabanshi ta d'ora kan Aminu a cinyarta ta na ta rizgar kuka, tabbas ya daku dan kuwa jikinshi kaca-kaca ya ke da jini, a hankali ya furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un." Da sauri ya k'arasa kusansu ya na durk'usawa da tallabo Aminu jikinshi, gyara zamanta ta yi ta na fad'in "Akhi ya mutu ko? Shikenan sun kashe shi, akhi dan Allah mu kai shi asibiti ka ji." Kallonta ya yi yace "Su waye?" Girgiza kai ta yi cikin kuka tace "Ban san su ba nima, kawai ya shigo ne zai rufe k'ofar gidan su ka shigo mana." Mik'ewa ya yi ya na fad'in "Karki damu zai tashi, mu je asibiti." Da sauri ta mik'e tare da kama hannayen Aminu da nufin suyi talla-talla su kama shi, amma sai ta ga Hasheer ya yi fit da shi sun dunfari hanyar fita, ya d'aukeshi shi kad'ai d'aukar da take ganin ko ita ta yi girma a yi mata ita, bare kuma mijinta da ita dai a wurinta ya amsa sunan namiji. Da gudu ta bi bayanshi ta na kuka, ta na kaiwa ya saka Aminu a baya zai shiga mazauninshi, kallonta ya yi yace "Ina za ki je haka?" Da sauri tace "Asibiti." Matsowa ya yi kusanta ya kama hannunta yace "Salima, ko da mijinki ba zai yi rai ba ki kare mi shi *sirrinshi*, ke fa ki ka fad'a min akan ki ne ya yi fad'a saboda za'a wargaza mi shi sirrinshi." Jinjina ma sa kai ta yi alamar gamsuwa kafin ta koma cikin falon da gudu, ta na cikin gudun ta ji ta taka k'aramar kwalba a cikin kofin glass d'in da ya mutu sanda suke fad'a, b芒 ta tsaya ta kula ba kawai ta shige ta canza kayanta da hanzari ta fito su ka wuce, saida ta shiga mota ta d'ago k'afarta ta d'ora a cinyarta ta na dubawa, da kulawa ya kalleta yace "Lafiya?" A marairaice tace "Kwalba na taka." Ci gaba ya yi da tafiya har suka isa asibiti babba, da kulawa aka karb'eshi aka shiga bashi kulawar da ta dace, Salima na zaune akan banci ya durk'usa kan gwiwarshi ya kamo k'afarta, ganin kwalbar ya sa shi kallonta yace "Autar Umma, za ki daure ko?" D'aga kai ta yi alamar eh, murmushi ya k'ak'aro ma ta yace "Idan ma ba ki daure ma dariya zan mi ki." Ita ma d'an murmushi ta k'ak'aro ta rintse idonta, a hankali ya dinga zage ma ta kwalbar har ya yi nasarar cire ma ta, da sauri ta lank'wasa k'afarta tare da bud'a ido, murmushi ya mata yace "Shikenan, yaushe autar Umma ta zama jaruma haka?" Kallonshi ta yi kamar za ta yi kuka tace "Tun ranar da akhi ya had'ani da nagartaccen mijin da babu irinsa a duniya, namijin da ke damuwa da damuwata, ya na kuka da kukana, ya na zulumi da tashin hankalina, hakan ya bani k'arfin gwiwar zama da shi da kuma zama jaruma dan kiyaye shiga tashi damuwar." Mik'ewa ya yi ya zauna kusa da ita ya dafa kafad'arta yace "Hakan ya yi kyau, yanzu kin tabbatar ni ma kamar uba nake a gareku? Ba zan tab'a zab'a mu ku abin da zai cutar da ku ba." Jinjina kai ta yi ta sunkuyar da kan ta alamar kunya, bai bar asibitin ba duk da an fad'a mu su majinyacin na samun sauk'i, kuma babu ko da targad'e bare karaya, saida aka yi sallah azuba kad'ai ya bar asibitin da alk'awarin zai turo ma ta Umma, da safe kuma zai dawo ya sake duba shi. Shigowarshi kenan gidan ya tunkari b'angaren Umma saboda yunwar da yake ji, kuma ya na da tabbacin zai samu abin da zai sa a cikinshi, shi ya sa ma ya shiga kan shi tsaye da 'yar k'aramar sallama, Umma da Marfu'a na zaune akan sallaya da carbi a hannayensu su ka amsa mi shi suma a sanyaye, a tsatsaye ya kalli Umma ya na harare harare yace "Zan samu abinci ne a nan?" Ajiyar zuciya ta sauke kafin tace "Ba za a rasa ba kam, a samo ma ka ne?" "E." Ya fad'a da rashin kunya, a nutse ta shiga mik'ewa ta na tattare lafayarta har ta shige madafa, kallon da Marfu'a ke mi shi cike da mamakin halin yaron ya sa ka shi kallonta yace "Ya dai?" Jinjina kai ta yi alamar haba d'in nan yaro wuri ka samu tare da yin k'akk'arfan k'wafa ta d'auke kan ta daga kan shi, fitowar Umma ya sa ya tarbeta ya na karb'e plate d'in da kofi, saida ya fara kurb'a sanyayyar madarar kafin ya saka ya tsakuro naman ragon da aka yi mi shi manyan yanka ya kai bakinshi, juyawa ya yi zai fita Umma tace "Mujaheed me ya hana ka kwana a gida ne? Sai fa yanzu ka ke shigowa." Juyowa ya yi yace "To! To ina ruwanki? Ki na da matsala da hakan ne? To wajen budurwata na je, sai me?" Girgiza kai ta yi ta juya a hankali ta koma kan sallayarta, ya na kaiwa bakin k'ofa Hasheer na bankad'o k'ofar da k'arfi, da sauri ya ja baya dan ya tsorata sosai, suna had'a ido kawai Hasheer ya saka hannunshi na dama ya cabki wuyan Mujaheed, shak'a irin wacce ke hanaka had'e yawu bare ka shak'i iska ko ka maido shi. Hakan ya haddasa mi shi sakin plate d'in abincin da kofin madarar da yawunshi har tsinkewa suke saboda zalamarsu, a take idonshi suka d'auki launin ja wanda dama sigari ta gama lalatar mi shi da su, hannayenshi ya d'ora akan hannun Hasheer ya shiga daddab'a hannun alamar ya yi saranda ya sake yi. Da wani irin salo da k'arfi ya juyashi ya had'a da bangon daf da k'ofa, cikin tsananin tashin hankali da b'acin rai yake fad'in "Akan me Mujaheed? Me ya sa ka ke son ganin bayana? Me ya sa ba za ka hak'ura da maganar takardun nan ba? Wurin nan mallakina ne gumina ne, akan shi ne ka ke neman mayar min da k'anwa k'aramar bazawara? To gwara na kasheka kowa ya huta, tunda ka kasa gane ina d'aga ma ka k'afa ne." Tuni Umma ta tsaya bayanshi ta d'ora hannunta a kan na shi a tsanake cikin taushin murya tace "Hasheer, sake shi dan Allah." Ba tare da ya kalleta ba ya shiga jijjiga Mujaheed kamar kazar da aka tsamo daga ruwan zafi ya na fad'in "Umma ki barni na kashe yaron nan, me ya sa ya ke min iskancin nan? Dan ina k'yaleshi ne kuma yasan ki na tsaya ma sa." D'auke hannunta ta yi daga kan shi tace "Ni ce fa na ke ma ka magana, ka sake shi ka fad'a min me ya faru?" Saida ya jawo Mujaheed gaba hakan ya bashi damar gwara kan shi da bango da k'arfi har ya bayar da sautin k'umm! K'asa Mujaheed ya zube sumamme dan tuni ya nemi numfashinshi ya rasa, fad'uwar da ya yi a rashin sanin ya suma cikin jin haushi Hasheer ya sa k'afa a daidai mararshi ya mi shi wani kutuhun馃榿 arzikin, bai shirya dawowa ba amma dole ya dawo a gigice ya na sakin k'arar da har Umma ta dafe kunnuwa ya na fad'in "Wayyo! Wayyo Allah, mafarki!!! Hasheer zai kash..." Sai kuma ya yi shiru ganin Hasheer tsaye gabanshi, da rarrafe cikin gudun ceton rai ya yi bayan k'afafun Marfu'a da ke tsaye ita ma ta na kallonsu, a fusace ya juya kan shi ya na nunashi da yatsa yace "Bari ka ji, daga yau ka sake bibiyata akan takardun nan sai na ma ka abun da ko a tarihi ba ka tab'a ji ba, ka fita a rayuwata idan kai d'an halak ne, sannan karka sake shiga harkar Aminu dan yau d'in nan zan karb'i takarduna a hannunshi, idan kuma kai da banzan Saddin kun isa ku tsageru ne, to ku tunkareni ku karb'esu da k'arfin cin tuwo." Juyawa ya yi zai fita ya na fad'in "D'an iska kawai." Har ya kai k'ofar ya juyo ya kalli Umma yace "Umma Salima na asibiti babba tare da mijinta a nan urgence." Ficewa ya yi ya barsu tsaye, saida su ka d'auki minti biyu kafin Umma ta juya, dariya ce ma ta so sub'uce ma ta ganin tsageranta Mujaheed ya had'a kai da gwiwa ya na satar kallon k'ofa, girgiza kai ta yi tace "Na k'aro ma ka abincin ne?" Da sauri ya d'aga kai yace "Eh *Umma*." Da mad'aukakin mamaki ta kalleshi jin yau ya kirata da Umma, abu ne mai wahala a gareshi kam, madafar ta nufa ta na addu'ar Allah ya sanyaya ma sa zuciyar nan, duk da dai tasan da haka ta faru to an kai Hasheer bango ne, amma ta fi so idan ya tashi zuciyar ya yi komai a hankalce a tsanake. Ta na kawo mi shi wani Marfu'a har ta tattare waccen da ya zube, mik'ewa ya yi ya karb'a ya na fad'in "Nagode Umma." Hanyar fita ya kama ya na fad'in "Saida safenku." Marfu'a ce cikin harshenta da babu hausar da kyau tace "Ai safiya ta yi, ko ba ka gani ne?" Jiyowa ya yi ya kalleta a d'an tsoarace, sai kuma ya kalli Umma yace "Umma, dan Allah ki zo mu je ki rakani b'angarena, tsoro na ke ji." D'an murmushi ta yi tace "Tsoro kuma? Na me?" Rarraba ido ya yi sai kuma yace "Kar ya dawo ya kasheni kamar yanda ya fad'a." Sunkuyar da kan ta tayi kafin ta kalleshi tace "Ka je babu abin da zai faru ka ji, ba zai dawo ba, ni na fad'a ma ka haka." Girgiza kai ya yi cikin rashin yarda ya matso daf da ita ya durk'usa yace "Dan girman Allah Umma mu je ki rakani, da na shiga d'akina na kulle sai ki dawo, kin ji Ummanmu, dan Allah Ummana." Zaro ido ta yi sai kawai ta kama hannunshi da babu plate d'in tace "Mu je to." A tare suka fita hakan ya sa Marfu'a shek'ewa da dariya, d'aki ta koma ita ma dan ta ci gaba da shirye shiryenta, dan ta na daf da komawa nan da kwana biyu ita ma. Saida ya shiga ciki ya rufe da makulli kafin ta baro wurin ta na dariya, ta na zuwa ta shirya a gaggauce ta tafi tare da Marfu'a sai Halima su ka bari, za su fita su ka had'e da Mukhtar ya dawo daga motsa jiki, tambayarsu ya yi su ka fad'a mi shi kafin yace "Idan na yi wanka zan fita na je na subashi." Jinjina kai su ka yi sai Marfu'a da tace "Yau dai abokin fad'anka an mana maganinshi a gidan nan." Hannunta Umma ta kama za su shiga mota dan dreban dama ana idar da sallah yake zuwa, dariya Mukhtar ya yi ya na fad'in "Aunty wai Mujaheed ki ke nufi? Wa kuma ya tab'o yau?" Ta na daf da shiga mota tace "Hasheer mana." Zaro ido ya yi yace "Elhaj kuma, kai lallai ya tsokano tsuliyar dodo, wa ya fad'a ma sa ni da Hasheer d'aya ne?" Jinjina kai ya yi ya bisu da kallo dan har sun d'auki hanya, ciki ya shiga da niyyar ya tsokano Mujaheed ya ce mi shi ya zo neman labarin abin da ya faru, dan in su ka yi fad'a ya gaya mi shi magana. ________________ Zaune ta ke a kan kujera k'afafunta masu d'auke da sark'a sun bayyana da kyau a cikin dogon wandon da ta saka da rigarshi, ba ta yi kwalliya ba saboda rashin sanin halin da mijinta ke ciki, bud'a k'ofarshi ya sa ta tashi da sauri ta tarbeshi, rumgume juna su ka yi sai dai wata cakuma ya shiga ma ta dake nuna ranshi b'ace ya ke, a yanda ya yaho gidan nan sanyi ya ke nema, mahutarshi ya ke so ta rarrasheshi ta saukeshi a matakalar da ya hau, rintse idonshi kawai ya yi sosai ya na sauraren yanda k'amshin jikinta ke ratsa hudar hancinshi, ya gode Allah sosai da abun nan ya faru ya na d'akin Faduma ne, dan da a d'akin Saudat ya ke watak'ila ta k'ara hassala shi. Cikin nutsuwa ta d'ago kan shi ta na saka idonta a na shi tace "Wa ya tab'a min *zaki na*? Ba na son ganin yanayin nan a fuskar *jajirtacce na*, dan Allah ka min alfarmar sako min da murmushinka, hakan zai sa matar Hasheer gudanar da wuninta a cikin farin ciki." Marairaicewa ta yi tace "Dan Allah?" Murmushi ya yi ya sake jawota jikinshi ya bata kyakyawan rumguma ya na sauke numfashi, lura da ba zai ce ma ta komai ba ya saka ta jan shi zuwa ciki, taimaka ma sa ta yi ya yi wanka ya fito ta tayashi shiryawa, ba ta yarda ta tambayeshi komai ba sai ma madafa da ta shiga ta k'arasa aikinta. *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 21:43 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _77_ Cikin matsanancin kuka Saudat tace "Ki yi hak'uri Fati ki yafe min, wallahi na d'auka kawai ki na son rabani da mijina ne da yara na, amma yanzu na fahimci gaskiya, dan Allah ki rufa min asiri." Rik'o hannayenta ta yi tace "Ba komai aunty Saudat, ni dama ban rik'eki da komai ba, kuma sirrinki insha'Allah zai zama kamar nawa, zan tayaki b'oyeshi dan nasan babban mutum ba zai so jin haka ba." D'agowa ta yi ta kalleta tace "Da gaske Fati? Kuma ki na ganin hakan babu matsala? Ina tsoron Hasheer wallahi, dan ya na son haihuwa sosai, ban san ya zai ji ba idan ya ji maganar nan? Ina tsoron ya sakeni, ni kuma ba zan iya rayuwa babu Hasheer ba, Fati ina son shi sosai." Cike da tausayi Faduma ta sake jinjina hannayenta tace "Aunty Saudat wa ya fad'a mi ki ma za m没 bari ya ji? Ai za mu yi shiru ne da bakinmu." Kallonta ta yi da ido a kumbure tace "Da gaske Fati?" Jinjina ma ta kai ta yi alamar eh, murmushi ta sakar ma ta tace "Nagode." Girgiza kai ta yi tace "Ba komai, kar ki damu." Sakin hannayenta ta yi tace "Zan koma b'angarena, dan ya tafi masallaci ne kafin ya dawo." Jinjina ma ta ai ta yi alamar gamsuwa ta na kallonta a kunya ce, juyawa ta yi da gaba d'aya k'arfinta za ta fita, cak ta dakata sakamakon ido biyun da su ka yi da shi, da alama ya jima a nan kuma babu wanda ya farga da shi, idonshi sunyi jajir kamar zai fashe da kuka. A hankali cikin takon rid'arwa ya shiga takowa da d'an sauri ya na k'are ma Saudat kallo, baya ta shiga ja ta na rik'e da kafad'ar Faduma ta na fad'in "Bebe ka saurareni zan ma ka bayani, wallahi ba abin da ka ke tunani ba ne, Fati ki fad'a ma sa ba..." Shiru ta yi saboda danganewa da ta yi da kujera a bayanta, ba ta san lokacin da ta wuntsila ta kan ta ba ta fad'a tare da Faduma da ta ja ta da k'arfi su ka fad'i tare, duk k'ara suka saki mai razanarwa tare da kiciniyar tashi, zagayawa ya yi hakan ya sa ka shi ritsasu babu tsimi ba dabara, a kan kujerar Saudat ta shiga b'oyewa bayan Faduma ta na kare fuskarta ta na fad'in "Fati ki bashi hak'uri dan Allah kar ya dakeni, wallahi ba dagangan na yi ba, kuskure ne da tsautsayi." A hankali ta sake sauke idonta akan fuskarshi, cikin marairaicewa da rashin sanin waye shi ta shagwab'e fuska tace "Abban Izzadeen, dan..." Da wata irin k'ara ya daka ma ta tsawa ya na fad'in "Shiru!" Duk sandarewa su ka yi dan kamar saukar aradu suka ji a kan su, da k'arfin tsiya cikin salon k'eta ya kama kunnen Saudat ya murd'e ya sunkuya daf da fuskarta ya ma ta alama da yatsanshi alamar ta yi shiru sakamakon k'arar da ta saki, cikin kid'ima ya nuna kan shi yace "Saudat cikin na wa ki ka zubar? Cikina Saudat? Cikin sunnar da Allah ya bamu ki ka je ki ka zubar?" Sakin kunnenta ya yi ya d'aga hannu da niyyar ya k'ara ma ta wani marin ko ta kwarkwance sai kuma Faduma ta yi saurin sakin k'ara, dan ji ta yi kamar ita ce zai mara, tsayawa ya yi ya maida dubanshi kan ta ya sauke hannun, dafe k'ugu ya yi a raunane ya na kallonta yace "Faduma har ke ce za ki taimaka ma ta a b'oye min wannan sirrin? Dama zaman da mu ke yi da ke kenan? Shin wannan ba kishiyarki ba ce wacce ku ke fad'a? Shi ne har za ki taimaka ma ta ta ci gaba da rufeni ta na cuta min, a gaskiya ban tsammaci haka daga gareki ba." Kallon Saudat ya yi a d'an hassale yace "Ba dai ni ba Saudat? Ni ki ka wulak'anta ki ka wofantar wa da zuri'a? To ba damuwa nagode, amma ki sani ba zan iya zama da macen da zahiri za ta nuna min k'iyayya haka ba, a gaskiya Saudat kin fice min a rai, kawai ki je gidanku n..." Wani kuka Faduma ta fashe da shi ta kalleshi tace "Haba babban mutum, wannan ba halinka ba ne, sam abin da ka ke shirin yi ba karamcin da Umma ta koyar da kai ba ne, a gaskiya idan ka saketa ni ma bin ta zan yi." Tarrrrr! Ya sauke ido a kan ta, to me ta ke nufi? Ya tambayi kan shi, ajiyar zuciya ya sauke cike da nadamar hukuncin da zai d'auka yanzu, a gaskiya ya na son ta kuma zai iya yin komai dominta, amma Saudat ta gama fita a ranshi gaba d'aya, amma fa akwai magana d'aya tak da ta yi da tasa zai fasa hukuncin nan shi ne ambatar sunan Umma, zai janye hukuncin saki d'ayan da y'a yi niyyar yi ma ta, amma ba shakka dukansu za su d'and'ana kud'arsu, dan babu dalilin da zai sa su mi shi wannan iskancin, to me ya m没 su da zafi haka? Ta mi shi laifi d'ayar ta tayata rufe mi shi, zai yi hukunci kuma ta baibayeshi da sunan mahaifiyarshi ta hanashi, k'wafa ya yi a ran shi ya kallesu da kyau ya gyara tsayuwarsa. Saida ya shiga nunasu da yatsa yace "Ba dai kun had'e min kai ba? Ni za ku tozarta ko? To ku je kuyi abin da ranku ya ke so, me ku ke ji da shi? Me ya sa ku ke tunanin ba zan iya rayuwa babu ku ba? To dan Allah ku rik'e duk abin da ku ke ganin na ku ne kuma shi ne silar farin cikina." K'yasta hannu ya yi yace "Za ku san dani ku ke." Nuna Faduma ya yi yace "Ga ki ga ta ai." Fita ya yi daga d'akin ya barsu zaune duk sun dakatar da kukansu, da sauri Saudat ta kalleta tace "Fati, yi sauri ki je ki bashi hak'uri, ke wallahi ba ki san shi bane, a 'yan kwanakin nan ne kawai na fara sanin zuciyar Hasheer, sam abun babu kyau wallahi, bai kamata laifi na ya shafeki ba, ki bashi hak'uri ni kuma zan hak'ura na zauna a haka har sanda zai hak'ura dan kan shi." Jiki a sanyaye ta na jin gabanta na fad'uwa ta mik'e tsaye, ba tare da ta kalleta ba tace "Ki barshi kawai, zai sauko ne, a gaskiya ba zan bari aurenki ya mutu ba." Mik'ewa ta yi ta na fad'in "Amma Fati..." Da hannu ta dakatar da ita tace "Kar ki damu kawai, zai sauko ne, dama yau ya wuni cikin damuwa, wannan damuwar ce ya sauke mana b'acin ran ta, ba shi hak'uri yanzu babu abin da zai sauya sai ma tunzura lamarin." Jinjina kai Saudat ta yi tace "Shikenan, amma dai ina jin tsoro wallahi, kuma idan na ga ya mi ki irin hushin da ya ke min, to gaskiya zan sanarwa da Umma ta shigo cikin maganar, dan ita kad'ai za ta iya tank'waso ma na shi." K'ala ba tace ba sai fita da ta yi daga d'akin zuciyarta na raya ma ta ta bi mijinta, ita ma Saudat da kallo ta bita sai dai kuma a can k'asan zuciyarta tausayin kan ta dana Faduma ne ya kamata, inda ta ji Faduma ta samu wata daraja a idonta, dan a dalilinta ne yanzun ta ke zaune gidan nan da aure, da tuni ta na d'aki ta na harhad'a kaya za ta bar gidan. Ta na shiga kai tsaye d'akinshi da sallama da kuma sand'a, dan ita abun da ya faru yanzu tsorata ya yi ainun, kamar jiranta ya ke dama sai kawai ya d'ago daga sunkuyawar da ya yi ya na neman abu a coffre d'in gefen gado, a tsawace ya nuna ma ta k'ofa yace "Malama fitar min a d'aki." Yanda ta bud'e baki alamar mamaki ya sa ka shi cewa "E, ki fita na ce." D'an rufe bakinta ta yi ta sauke numfashi tace "Amma ni me ye laifi..." Lumshe ido ya yi yace "Faduma ki fita na ce, ki je ku yi abin da ku ke so." Wani numfashi ta kuma saukewa tace "Ka yi hak'uri Aban Izzadeen, mun tuba." Sake nuna ma ta k'ofa ya yi yace "Ki fita." D'an d'aga kafad'a ta yi alamar shikenan, juyawa ta yi ta bud'e ta fita ya bita da kallo, dafe k'ugu ya yi ya shafi sumar kan shi yace "Ha Yallah! Da burin na rumgumeta na shigo gidan, me ya shiga tunaninta haka da za ta taya Saudat b'ata min rai?" D'an tsaki ya yi ya kalli k'ofar yace "Kuma ke ma daga cewa ki tafi sai ki tafi kawai, ba za ki matso ki rumgumeni ba, ke ce fa nutsuwata Fati." Zaune ya yi bakin gadon cikin rashin kuzari ya ma rasa me zai yi. Haka a wurin Faduma duk da ta ji ba dad'i amma sai ta ke gani kamar laifinsu bai kai yanda ya d'auki abun hukuncin ba, da haka dukansu har suka kwana a d'aki daban-daban, amma fa babu wanda ya yi bacci mai dad'i, gwara Faduma ma ita ta rintsa idonta, amma farkawar da tayi ta fi goma, sai ta ji kamar sauro ya cijeta kuma ba shi bane, sai dai ta ja tsaki ta gyara kwanciya ko ta juya, tasan ta na kewar mijinta sosai. Haka shi ma ta b'angarenshi sam bai ma rintsa ba, takaicin zubar da cikin da Saudat ta yi, da kuma kad'aicin rashin kasancewa da murmushinshi, ya saba bacci a gefenta hancinshi na shak'ar mi shi k'amshin da har ya zama jikinshi mai tausasa mi shi zuciya, lallausan fatarta ya k'udunduneta a cikin jikinshi har su yi bacci, rana tsaka kamar an shiga tsakaninsu yau babu hakan. Ko da ya shigo daga masallaci ta na cikin riga da siket na kanti gashinta a d'aure da ta kwance, ganin ya nufi d'akinshi ba ko kallon inda ta ke yasa ta cewa "Barka da safiya Elhaj?" A dak'ile kuma a kauce yace "Barka." Da kallo ta bishi har ya na daf da shiga ciki ya tsaya yace "Kar ki jira ni cin abinci, ki ci kawai." Shigewa ya yi dole ta zuba mi shi ido kawai, tunkarar d'akin ta sake yi tunda yanzun nan zai koma hannun Saudat, ba za ta so su rabu a yanayin nan ba, sai dai ta na zuwa k'ofar rufe ta ke da makulli, hak'ura ta yi ta dawo kawai inda ta d'an tsakuri abincin kafin ta shirya ta kai wa Saudat na su dan ta ga yaran ba su shigo ba. Ba ta zauna ba ta dawo zaman jiran ta ga fitowarshi, sai dai har bacci ta yi a cikin kujera kafin ta ji bud'e k'ofarshi, da sauri ta tashi zaune ta yi kukan kura ta nufeshi, amma da gaske sai y'a kauce ya na d'aga ma ta hannu da nuna ma ta bakinshi akwai ruwa sannan ya na sauri, wani murmushi ne ta ji ya taho ma ta, wato duk yanda aka yi yasan ta na jiranshi shi ya sa ya gumtso ruwa a bakin na shi, da kallo ta bishi sanda ya ke ficewa da sauri tace "Zan iya zuwa gidansu Umma?" Da yatsu biyu ya ma ta wani fit-fit alamar tafi, da sauri ta sake cewa "Da wace motar zan tafi?" Da hannun hagu ya ma ta alamar "Duk wacce ki ke so." Da mamaki ta kalli hannun na shi, ya aka yi ya iya yare haka da hannu? Ita ma ta d'an fara koya saboda yanayin aikinta, ta na ganin wata rana zai iya had'ata da kurma, hakan zai sa sa茂 dai suyi yaren hannaye, girgiza kai kawai ta yi ta na murmushi tace "Ka d'auki lokacinka malam Hasheer, idan Faduma ta so ku shirya za ku shirya ko ba ka so ba." Ciki ta shige ta d'auko hijab d'inta da jaka da enveloppe d'in da babu komai a cikinta da makullin motarshi k'aramar 4matic ta fita bayan sunyi sallama da Saudat. Ta na zuwa gidan kam kamar yanda ta yi tsammani babu kowa sai mai gadi, tunda ya fad'a ma ta babu kowa tace "Mujaheed fa, ya na ciki?" A ladabce ya amsa ma ta da "Eh ya na ciki, tun asubar jiya da y'a shigo bai fita ba." Jinjina kai ta yi ta nuna wani b'angare tace "Can ne b'angarenshi?" "Eh." Shi ne abin da ya fad'a ma ta kenan, a nutse ta tunkari b'angaren ta na girgiza makullin motar hannunta, k'wank'wasawa ta yi daga ciki yace "Waye?" A nutse tace "Faduma, matar Hasheer." Jim kad'an aka bud'e k'ofar, kallon juna su ka yi da kyau, wani malalacin murmushi ta yi ta kauce tare da shigewa d'akin ba tare da y'a ma ta izini ba, kallon tsaf ta shiga aikawa d'akin da sai warin sigari ya ke, kujera t samu ta zauna sanda ya ke fad'in "Me ya kawo ki nan? Mijinki ne ya turoki?" Kallonshi ta yi ta tab'e baki tace "Ni na aiko kai na." Zaune ya yi a kujera shi ma dake kallon ta ta yace "Me ki ke so?" Aje jakarta ta yi k'asa ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya tace "Sulhu, na zo sulhunta tsakaninka da 'yan gidan nan ne, b芒 na son ganin rigimar da ke faruwa a tsakaninku, ina so ka manta da maganar kampanin risham wax." Wani banzan kallo ya ma ta yace "Ke kuma a suwa? Wacece ke? Au! Shi ya kasa shi ne ya turoki kenan ki ma sa yak'i?" Ita ma wata dariyar ta yi tace "Kai kasan waye mijina kuwa? Ai idan da cikar aikin ya ke nema da kan shi zai yi, ina so abi komai a tsanake ne." A hassale yace "To ba zan hak'ura ba, wannan kampanin shi ma a cikin gadonmu ya ke, ba zan yarda a tauye min hakk'ina ba." Girgiza kai ta yi tace "Mujaheed wannan ba hakk'inku ba ne, na d'an uwanku ne shi kad'ai, girman zuciyarshi ta isa ta sa ya bar mu ku wannan mallakin na shi, na tabbatar hanyar da ka biyo ce ta saka shi k'in aminta da hakan, Mujaheed mutanen nan su ne kai, akan me ba za ka rik'esu ba kai ma?" Cikin hargagi yace "Saboda dalilin mahaifiyarsu ne uwata ba ta cikin gidan nan,ita ta raba mahaifina da mahaifiyata, akan me zan rik'esu masoya?" D'auke k'afarta ta yi cikin fad'a ita ma da saurin magana tace "Wacece d'in ta rabasu? Waya fad'a ma ka a dalilinta su ka rabu? Amsa min tambayata." Cikin idonta ya kalla yace "Mahaifiyata ce, ta fad'a min mahaifina ya fi son Maryam a kan ta." Tsaki ta ja mai k'arfi tace "Aikin banza." Mik'ewa ta yi tace "Kasan wacece mahaifiyarka kuwa? Kasan wacece *Rakiya Laminu Arzika*? To bari kaji idan ba ka sani ba." Gyara zamanta ta yi da kyau tace "Mahaifiyarka gogaggar wayayya ce da idonta suka bud'e sakamakon mu'amula da k'awaye, babbar k'awarta *Badiya* da ba sa rufe sirrin junansu tsakaninsu, ba ta auri mahaifinka ba saida ta tabbatar mai kud'i ne, kuma ta aureshi ne saboda kud'inshi da burin samun babban rabo a gidanshi, ba fa rabon haihuwa ba sai rabon duniya ma'ana kud'i ko kadara, ba ta yi nasarar samun komai ba saboda mahaifinku ba irin sakarkarun maza bane, bugu da k'ari akwai tsayayyar mata a kan shi mai tsoron Allah, hakan ya sa a zaman aurensu sun samu matsaloli da dama, a ciki kuma har saida mahaifiyarka ta yi nasarar raba Umma da mahaifinku, Umma tasha wahala sosai dan saida suka kwashi shekara biyar tana shan wahalar gidan nan, ko kulata baya yi bare ya shiga sabgarta, a haka aka haifeka skaanci ya sake tashi, sai dai Allah ba azzalumin bayinsa ba ne, shekararka biyu da haihuwa mahifinka ya saki mamanka sakamakon tsohon saurayinta da ya gansu tare a masaukin bak'i (h么tel)." Tab'e baki ta yi ta yatsina fuska tace "Da haka ne ka ke ikrarin ita ta raba iyayenka? Matar da tunda suka rabu mahaifinka ya karb'eka ya direka gaban Umma take kula da kai, tare da Mukhtar ta raineku kuma babu wani bambamci data nuna a tsakaninku, a hakane ka raina matar da kai d'in da d'an halak ne da ko 'ya'yan da ta haifa su ka b'ata ranta sai inda k'arfinka ya k'are." Komawa ta yi ta shige cikin kujerar tace "Mujaheed sai yaushe zakayi hankali? Me yasa ba zaka taimaki 'yan uwanka ba wajen ganin kun cika burin mahaifinku na son ganin kun zama yara abun kwatance kuma masu had'in kai, kayi tunani akan sunan masana'antunku kawai ka gani, dan tabbatar da had'in kanku mahaifinku yayi anfani da sunanku da kuma nashi sunan, a sauk'ak'e shine ka d'auki *R* dake k'arshen sunan Hasheer, sannan ka d'auki *I* dake ta biyu a haruffan sunan Halima, sai harafi *S* dake farko a sunan Salima, sannan ka had'a da harafin *H* a harafi na biyar a jerin sunanka, sai kuma harafin *A* a harafin farko na sunan mahaifinku, ka tara duk wannan da harafin *M* wanda shine na farko a sunan Mukhtar, idan ka had'asu zai baka *RISHAM*, wannan shine burin mahaifinku kuma mafarkinshi, amma ka biye wasu masu son ganin bayanku suna d'oraka a turbar da ba zata b'ille ba, Mujaheed ko banza wad'anan 'yan uwanka ne da baka da kamarsu, uba d'aya yafi k'arfin wasa kamar yanda kasan babu wanda ya tab'a siyo uba, sannan uwa na haihuwar yaro amma rashin uba yasa a kirasa da shege ko kuma maraya, ya kamata ka farka hakanan Mujaheed, ka gane 'yan uwanka sune naka kuma mutanen nan suna sonka domin Allah, da basa san zama da kai suna da yanda zasuyi da kai ku raba hanya, kuma wallahi hanyar ta rabu kenan har abada, amma basuyi haka ba suke zaune da kai kana musu abinda kaga dama, dubi baiwar Allah Umma, idan maganar alak'a za'ayi bata had'a komai da kai face kasancewarka d'an mijinta kawai, amma a haka kake mata duk wani kalar iskanci kuma take shanyewa, akan me? Wallahi da nice ita ba zan d'auka ba, amma dake ita ce kaga ta d'auka harta shanye, me ya kamata ka saka mata dashi?" Mik'ewa tayi tana kallonshi ta sauke ajiyar zuciya tace "Kayi tunanin abinda ya kamata ka saka mata dashi." Jakarta ta d'auka ta ciro enveloppe d'in nan ta aje akan k'aramin teburin tace "Wannan sune takardun da ku ke nema, idan har zuciyarka za ta yi sanyi ne idan ka samesu to gasu nan, Hasheer ya mallaka ma ka su duniya da lahira, yace abu d'aya kawai ya ke son ji daga gareka shi ne ka kirashi da sunan *akhi* kamar yanda sauran 'yan uwanshi ke fad'a, idan kuma har ka canza to wannan takardun nasan zaka damk'asu hannun wanda ya dace, na barka lafiya." Ficewa tayi a d'akin ta barshi jugum yana kallon takardun nan, bai tab'a jin abinda yake ji a yanzu a game dasu ba, lallai ta tunasar dashi sosai, kuma ya gane kawai wasu ne suka dinga anfani dashi saboda biyan buk'atarsu. Haka ma ya yi wauta da ya dinga yarda da abin da mahaifiyarshi take fad'a mi shi a kan su, duk ita ta hure mi shi kunne ta nuna ba masoyanshi bane su, duk da ko ya ga yanayinta yasan dole a samu kuraikurai da dama a game da ita d'un, sai dai ya yi al'ajabi sosai ta yanda Faduma ta zayyano mi shi tarihin rayuwar mahaifiyarshi haka, a ina tasan cikakken sunanta haka? Sunan babbar k'awarta? Zamanta a gidan nan da kuma dalilin rabuwarsu, a gaskiya ya ji kunya ta kama shi sosai, kuma ya yarda da Aji yace idan har aiki ya had'aka da ita to ta na ma ka binciken k'wak'waf ne, kamar yanda maye ke gani har hanjinka haka ita ma za ta gano komai a kan ka. Zunbur yayi ya mik'e da enveloppe d'un a hannu ya d'auki makullin motarshi ya bar gidan, bai zame ko ina ba sai risham wax dan ya tabbatar acan zai sameshi. Babu wanda ya hanashi shiga a lokacin kamar yanda Mukhtar ke da izinin shiga ko ina haka shi ma, da sallama tare da bud'e k'ofar ya shigo a sanyaye, Hasheer da ke zaune a kujera mai zaman mutum uku ya d'ago dubansa ya na dakatar da hannayenshi daga danna keybord d'in ordi., da mamaki ya ke kallonshi har ya tsaya gaban tebur d'in da ya m没 su tsakani, bai sauke idonshi a kan shi dan shi sallamar ma da kuma ganinshi a nan duk sun bashi mamaki, bai tabbatar da Mujaheed d'an shaye shaye ba ne saida ya aje enveloppe d'in akan tebur ya fashe da kuka yace "Akhi." Zaro ido ya yi ya d'an mik'e tsaye daga inda yake yace "Mujaheed, wani abu ka sha yau ma? A sanina dai sigari ka ke sha da shisha, dama ka na anfani da syrup ko k'waya?" Da sauri kuma sai ya zagayo inda ya ke ya durk'usa, hannu ya kai ya d'ora a kan wuyanshi da nufin ko zai ji zafi jikinshi, a tsanake ya kalleshi yace "Jikinka babu zafi, lafiya? Me ya ke faru?" Wani kukan ya sake fashewa da shi ya rik'o hannayen Hasheer yace "Ka yi hak'uri d'an Uwa ka yafe min, na cutar da ku dayawa na zalinceku, dan Allah ka yafe min kai da Umma, wallahi ba iya kampanin nan ba kawai, ko na wa kason ka ke buk'ata zan mallaka ma ka, dan matarka ta tunatar dani a duk duniyar nan ban da wanda suka kai ku bare su fiku." Mamakin da ke neman halakashi daga durk'ushe ne ya sa shi mik'ewa tsaye da Mujaheed, kallonshi ya ke sosai kafin yace "Matata kuma? Wace matar ta wa? Wai me ka ke magana a kai ne? Me aka ma ka?" D'ago kai ya yi yace "Ba komai, takardunka ne na dawo ma ka da su, ka yi hak'uri akhi." Da dai mamaki a fuskarshi yace "Takardu kuma? Wane takardun?" Kallonshi ya sake yi yace "Takardun kampanin nan, wanda ka b芒 Faduma ta kai min har gida saboda ka na son yin zumunci da ni." Tsaii ya kalleshi da kyau tare da fahimtar inda yaren ya dosa, jinjina kai ya yi ya na sakin murmushi, a hankali cike da shauk'i da k'auna had'e da tausayi ya jawo Mujaheed a jikinshi ya rumgume tsam, ya na jin haka ya sake fashewa da kuka ya na sake fad'in "Ka yafe min akhi, na tuba ba zan k'ara ba wallahi." D'an bubbuga bayanshi ya yi yace "Ba komai k'ane na, na yafe ma ka har abada, ni ma ka yafe min abisa komai." Da k'arfi ya rumgume Hasheer da kyau ya na kukan nadama, su na haka Mukhtar ya shigo da sallama, amma ganin abun mamaki sai ya tsaya ya na kallonsu, takowa ya shiga yi ya na fad'in "Kai kai kai! Yau wace rana ce wannan?" D'agowa Mujaheed ya yi ya kalleshi, hararenshi Mukhtar ya yi yace "Miye ka ke kuka kamar mace?" Nunashi ya yi da yatsa ya kalli Hasheer yace "Akhi ka gani ko? Kukan ma ba zai barni na yi cikin salama ba." Duk dariya su ka yi sai Hasheer da ya kalli Mukhtar yace "Ka ga bana son iskanci, ka yi abin da ya kawoka ka fice a nan." Matsowa ya yi ya na aje takardun hannunshi a kan tebur yace "Ni ma rumgume ni za ku yi, ba ni ne autanku ba?" Cike da shak'iyanci ya fad'a jikin Mujaheed, hakan ya sa Hasheer jawosu gaba d'aya ya rumgume a jikinshi, cikin muryar kuka Mukhtar yace "Na yi farin ciki sosai, Allah ya k'ara had'a kawunanmu." "Ameen." Suka amsa sai Hasheer da a zuciyarshi yace "Ita ta min wannan yak'in, duk da ni ne babba ban tab'a tunanin samun kan matsalar ba a sauk'ak'e kamar yanda ta yi, tunani na idan na dage dole za su hak'ura tunda ina da takardu na k'warai, ashe ba haka abun ya ke ba, *murmushi na* ta yi aiki da k'wak'walwarta ta kuma tabbatar da d'orewar *mirmushin ahalin nakiri*, ina son ki Batul." A ofishin nan suka sha zamansu su na hira da raha abun gwanin birgewa, dukansu sun ji dad'in yanayin tare da jin sanyin zuciya, har azahar su na tare su ka ci abinci kafin suka wuce asibiti ganin jikin Aminu, sosai Umma ta yi mamakin ganinsu tare, amma da Hasheer ya tsaigunta ma ta komai a yanda ya fahimta sai ta ji surukuwar ta ta ta k'ara samun daraja a wajenta. Cike da nadama Mujaheed ya nemi afuwar Aminu da ke zaune ya na kallon Salimarsa ya na jin dad'i, shi ma dai nuna ma sa ya yi ba komai kafin suka mu su sallama su ka tafi, Umma ce ta bi bayansu tare da Marfu'a dan su aje su gida, abun farin ciki da sauri Mujaheed ya bud'ewa Umma b'angaren da za ta zauna ta shiga, dakan shi ya tattare ma ta hijab d'inta dogo sannan ya karb'i tuk'i a hannun Mukhtar, saida ya shiga zai tayar yace "Rana ta farko da zan fara tuk'a uwata a mota, kuma insha'Allahu zai zama na k'arshe kenan da wani zai tuk'a min uwata, saidai ko larura idan ta fi k'arfina." Duk hakan ya mu su dad'i musamman Umma da ta bishi da addu'a, Mukhtar kuma zolayarsa yake wai shi kad'ai zai kwashe ladar? Haka suka isa gida cikin raha da annashuwa. _______________ Cike da kunya ya kalli Hatimi ya sunkuyar da kai yace "Wallahi Ayya da gaske na ke, ki mu su magana indai za ta amince, Ayya Amjad ya fara matsa min akan na yi aure." Da farin ciki fal fuskarta tace "Tagur wannan ai mai sauk'i ne, Husna ta na sonka sosai, na tabbata ba za ta k'i amincewa ba ko da ma an sake fad'a ma ta larurarka." Cike da jimami yace "Zan so haka nima Ayya, dan ita ce matar da Faduma ta min sha'awar aura." Wayarta ta d'auka ta na fad'in "Ai kuwa bari ka gani, yanzu zan kira na fad'a ma kawunka." Jinjina kai ya yi ya mik'e ya na fad'in "Idan sun amince kinga za mu yi tafiya d'aya kenan, neman aure da d'aukar Amjad daga hutun da na kai shi." Dariya ta yi tace "Gaskiya kam, dan kwana biyu da baya nan duk gidan ya min girma, ba naa jin k'iriniyarsu shi da Khairat." 'Yar dariya ya yi bai ce komai ba ya fice, to me zai ce ma ta? Shi da ya ke kwana da yaron tunda ya zo, tunda ya kai shi can kuma ya daina yin baccin sai sallar dare ya na nan gafarar ubangiji akan laifukanshi. Da zafi zafi suka daki k'arfe ta hanyar shigar da manya a lamarin, sam Husna ba ta yi wani d'ar-d'ar ba ta amince da buk'atar neman aurenta daga wajen Tagur, maganar Faduma ce ta rik'e ta zamar ma ta wani karatu da take yawan biyashi har ya zauna ma ta a kai, ta yi yak'inin gaskiya ta fad'a ma ta dan Allah zai iya duba zuciyarta ya bata haihuwa a sanda babu wanda ya ke tsammani. Amma a daren ranar sai Gomboy ta kira maman Husna a waya ta fad'a ma ta baya haihuwa fa, nan fa uwar ta dire akan ba za a yi ba sai dai kome zai faru ya faru, Husna ta yi kuka kamar za ta mutu, dan kulle kan ta tayi a d'aki da ta ga uwar ta ta bata jin rarrashinta da magiyarta akan ta taimaka ta yarda. *Kwana uku* dai babu abin da ya sauya har saida dai Aban Husna ya ga zai rasa 'yarsa a banza, amincewa ya yi a matsayinshi na babba kuma babu mai ja, dan haka aka ci gaba da shirye shirye da jiran lokaci. A lokacin kuma Amjad na wajen mahaifinshi ya ci gaba da karatunshi da kulawar k'anwar mahaifinshi da kakarshi da kuma riritawar mahaifinshi. __________________ Sukuku ya ke yau duk tunani da damuwar rashin Batul a kusa da shi ta gama dameshi ta shanye, gashi dai har ya yi kwana biyu a d'akin Saudat, wanda ita kam ko gaisuwarta ma ba ya amsawa harkar gabanshi kawai ya ke, kwana d'aya ya yi yanzu a d'akin Faduma kuma safiyar gobe zai koma hannun Saudat, hakan ya sa duk baya jin dad'i, da k'yar yake magana da Wardugu a tablet d'in shi yake fad'in "Wardugu ka taimaka ka fito mu su da yaronsu, wallahi Alhaji Bashir ya min magana a kan hakan, sannan Adam ma duk ana bibiyar wanda suka sanni dan na ma ka magana." Yatsina fuska ya yi yace "Kai rabu da shi, ai ba zai yarda ya tunkare ni ba kai tsaye." Kallonshi ya yi da idonshi da suka rine su kayi ja yace "To wai me ka ke mi shi ne? Ina yake Wardugu? Idan ka kashe shi ka fad'a mu su mana su huta su bishi da addu'a." 'Yar dariya ya yi yace "Ban kashe shi ba, horonsu shi ne suke ci gaba da zama a cikin zulumin dakon son sanin inda yake, shi kuma na shi horon shine ko rana ma sai da amincewata zai kalleta." Girgiza kai ya yi ya kalleshi da kyau yace "Wardugu ba ka da imani." Shafa k'asumbarshi ya yi cike da shak'iyanci yace "Sai na kad'aita ubangijina." Sake girgiza kai ya yi yace "Allah ya shiryaka to." Had'e fuska ya yi yace "Ya na ga ba ka koma gida ba har yanzu? Me ka ke a ofishi a wannan lokacin?" Ajiyar zuciya ya sauke yace "Ba komai, aikine ya rik'e ni, amma yanzu zan tafi." Hararanshi ya yi yace "Idan fa na samu ka na wa k'anwata iskanci zan ci uwarka Hasheer." Dariya ya yi yace "To ita wacece da ba za'a ma ta iskanci ba?" A hassale yace "Ita a k'anwata, wallahi Hasheer ka fita idona in rufe, idan ka kuskura ka sakata kuka saina k'wak'ulo idonka na damk'a ma ta a hannunta." Tab'e baki ya yi yace "Da kai da ita dama dangin mayu ne, ita ta cinye min zuciya da kuzari na da bulaliyata, kai kuma burinka ka cinye min idona." Dariya Wardugu ya yi yace "D'an iska dai bai ji dad'i ba, haka ka lalace dama?" Shafa sumar kan shi ya yi yace "Dole na lalace ma na tunda ina son haiho d'an da zaka min rainonshi, idan ban yi ba ina zan samu d'a kamar Wardugu." Cikin dariya da nishad'i na kasancewa da aminin na shi yace "Hasheer fito kai tsaye ka ce kai Wardugu lalatacce ne ma na, tunda ka samu k'aramar yarinya ka na auna mata nauyinka." Shi ma dariyar kawai ya ke amma bai ce komai ba, a tare suka girgiza kai da murmushi a fuskarsu, haka ma a tare suka fad'i "Saida safe." Lumshe ido sukayi alamar amsawa kafin kowane ya kashe kiran, saida ya mayar da tablet d'in a cikin gidanta ya saka a coffre d'in dake ofishin ya mik'e, duk wani muhimmin abu ya kauda y'a je a ma'ajiya b'oyayya kafin ya d'auki makullin mota ya nufi gida. Ya na son kasancewa da ita kamar zai mutu, sai dai baya so ya sauko yanzu daga inda ya hau, amma fa ya na tamtama da kokonta anya zai iya akan Faduma kuwa? Da wannan ya shiga gidan zuciyarshi na dokawa da sauri sauri, ya na shiga b'angaren yayi saurin yin k'asa da kanshi sakamakon ganinta cikin wata arniyar rigar yajuju wa-majuju. *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 21:43 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _78_ Da sauri ta tunkaroshi sai kawai ya kauce ya na sauri kamar zai zuba a guje ya shige d'akinshi, saida ya rufe k'ofar ya sauke wata balagaggar ajiyar zuciya ya dafe k'irji yace "Na shiga uku, me ta ke nufi? So ta ke ta karya min alkadarina?" Girgiza kai ya yi kawai ya shiga cire kayan jikinshi, a sauk'ak'e ya shiga tuna farkon shigowarshi da yanda ta taho da saurin nan, d'angalallar rigarta data matse d'amammen k'irjinta suka shiga d'agawa a nutse, lumshe ido ya yi ya girgiza kai yace "Gashi kuma na ce su rik'e abin da ke jikinsu da suke ganin shi ne farin ciki na." Dantse leb'enshi ya yi da k'arfi yace "Hasheer ba kayi ba wallahi." Yau ma kamar jiya kad'an ya d'an ci iya kayan marmari kawai, ita dai ba ta zafafa lamarin ba, bin shi take a sauk'ak'e kamar yanda ayyoyinta suka koya ma ta, tabbas a yanda ya ke botsarewar nan ta ce za ta bashi hak'uri zai ci gaba da hawa ne sama, amma idan aka kwana biyu ta tabbatar sun galabaita sai ta lallab'ashi da k'arfinta. A haka har dare ya yi ta kwanta bacci, tun kafin baccin ya d'auketa ya shigo, saidai yanda ta ganshi ya tabbatar ma ta yau ma kamar jiya sallah zai yi, dan haka ta rufe idonta dan ta san ba kashe hasken fitila zai yi ba. Shi ma bai kulata ba ya kabbara sallahshi kawai dan ita ce za ta samar mi shi da nutsuwa, matsalar kawai k'amshin d'akin ne ke masifar birgeshi shi ya sa ya ke zab'ar ya zo nan ya yi sallahr ya na shak'ar k'amshin dan ya samu nutsuwa. Matsancin fitsari ne ya tasheta a baccin mai dad'i, da sauri ta sauka a kan gdon da nufin shiga ban d'aki, ganinshi tsaye ya na sallah ya saka ta kallon hanyar, tambayar kan ta tayi "Yau kuma me ya sa ya karkata sallayar haka ta yanda ta ke kallon k'ofar shiga ban d'akin?" Ajiyar zuciya ta sauke ta nufi gaban madubinta, turaren d'aki ta d'auka a robarshi ta da ta tabbatar ya yi tsayin zira'i d'aya ta d'ora a gabanshi, da sauri ta wuce tana dafe mararta da take jin kamar za ta fashe. Rigar jikinta kalar pink ce, dama kuma shara-shara take komai a fili, da kad'an tsayinta ya sauka akan cinyoyinta, haka kuma siraren hannaye ne da ita, duk da ba yadi bane mai kama jiki amma dake rigar ta kama jikinta sai ya zama duk juyawar mazaunanta ana gani wanda ta saka sabon pant bak'i. Bai kalleta da wata manufa ba, kawai shi dai ya ga za ta wuce ta gabanshi ne hakan yasa shi d'an k'yarta idonshi ya kalli giftawarta, rabon ayi kenan, tsautsayi da rabon b'acewar sallarshi kawai shed'an ya sake tayashi d'aga idonshi zuwa sama kad'an, anan ne fa y'a had'u da sittin saba'in, tafiyar da take da sauri ta neman inda za ta tsuguna ta kwarara fitsarinta ya taimaka sosai wajen tsinkewar dokinshi, ai kuwa tuni linzamin dokin ya fara dukan iska har kamar zai baroshi ya fito waje. Tabbaci ya samu na bugawa a jarida na b'acewar sallarshi, dan a take wanka ya hau kan shi amma hakan bai sa ya ji sauk'i a lamarin ba, tabbas sai yanzu ya sake tabbatar da hadisin da manzon Allah (S.A.W) yace idan ka na sallah kar ka bar mace, bak'in kare, da yara su bi ta gabanka, yau shi ne shaida a kan haka dan ya gani a aikace kam. Fitowa ta sake yi a nutse ta nufi hanyar fita daga falon, bai yarda ya kalleta ba sai dai giftawar da tayi ta sa karatunshi ya sub'uce mi shi, sam sai ya rasa ina ne ya ke. A falo ta zauna bayan ta d'auko ayaba da mangoro ta sha abun ta sosai ta na tunanin anya lafiyarta k'alau kuwa? Ta cika ci yanzu da rashin juriyar yunwa, ga rashin hak'urin fitsari KO kad'an, dan har ciwon mara ya ke saka mata idan ba tayi ba, saida ta ji sun isheta ta mik'e ta mayar, yoghourt ta d'auka mai kauri da sanyi tasha ta k'oshi sannan ta rufe, kuskure bakinta ta yi a madafa kafin ta dawo falon, har za ta kashe fitila sai kuma ta barta ganin shi ya kunna bayan ta kashe ta kwanta, dawowa ta yi ta kwanta abun ta ta shige bargo ta rufe ido. Kamar daga sama ta ji mutum ya mata runfa sai dai bai sakar mata nauyin shi ba, bud'e ido ta yi hakan ya basu damar kallon juna da kyau, wani had'e fuska ya yi irin kama jikin nan yace "Batul ni ne sa'an wasanki ko? Ni tsaranki ne da za ki dinga kirana haka da babbar murya? Wato gayyatata ki ke yi ko? To dan Allah gani ki cinye ni, ki yi yanda ki ke so dani kinji, marar kunya kawai." Ya fad'a ya na dungure ma ta kai, baki bud'e ita dai take kallonshi ta kasa fahimtar komai, ta na cikin kallonshi ya sauka daga kan gadon ya kashe fitilar ya dawo, zare doguwar bak'ar rigarshi ya yi ya hauro kan gadon kan ta ya na fad'in "Gani to, bismillah ko malama Zahra'u, ai dai kin shirya d'aukata ko? Kin shirya da kyau dan d'aukar hukuncinki? Zan hukuntaki abisa taimakawa 'yar uwarki a kan zubar min da ciki, sannan na hukuntaki da laifin shareni da ki ka yi, dan hakan tabbaci ne na baki damu da ni ba, ni kuma a tsarina ya zama dole a gareki ke ma ki *ji ni har ran ki*, Fati dolenki ki *so ni* fiye da yanda ki ke son kan ki, idan ba haka ba kuma na mi ki alk'awarin mutuwa a kan ki." Zaro ido ta yi, sai kuma ta yi luuuuu! Da su sakamakon had'a bakinshi da ya yi da nata ya shiga tsutsa a sauk'ak'e. A hankali komai ya gudana suka nuna wa junansu sunyi kewar juna, Faduma kuma sai daren nan ne ta fahimci ashe ita ma sala-sala take d'aukar karatun da yake biya mata ta na saka shi a kan ta, tsaf su ka yi wanka suka shirya kan su. Kwance take a k'irjinshi hannayensu sark'e da juna, shiru kamar babu wanda zai yi magana, can kuma sai tace "Ka hak'ura kenan?" Wani murmushi ya saki idonshi a rufe yace "Umm! Amma ke kawai." A sanyaye ita ma tace "Me ya sa ita to?" K'asan mak'oshi yace "Laifinta ya fi na ki girma." A raunane tace "Ka yi hak'uri babban mutum, a sanina da kai ka na bawa komai baya ne, halin k'aramta ba d'abi'arka ba ce." Shiru ya yi haka ita ma ta na saurare ta ji me zai ce, sun jima haka kafin yace "Zan yi tunani a kai, yanzu fad'a min na isheki haka? Ko da saura?" Shigewa tayi k'irjinshi kawai ba tace komai b芒, a haka kuma komai sai bacci ma da ya d'auk'eta, shafa kan ta ya ci gaba da yi ya na sakin murmushi, a k'asan zuciyarshi ya furta " *Hutuna*, *nutsuwata,* *murmushi na*, a kullum farin ciki ne zai dawwama a gareki." Har ya gama shiryawa ya juyo zai fito ita kuma ta shigo, da rawar jiki ta rik'o hannunshi tana kallon tsakiyar idonshi tace "Babban mutum, ka taimaka min dan Allah ka rufa min asiri, wallahi ina so, ina so sosai, zan iya mutuwa ma idan ban samu ba." Da mamaki ya shiga rarraba ido ya na kallonta kafin yace "Mi ye ki ke so Batulu? Fad'a min shi na ji kinji, zan samo mi ki." Saida ta sake kafeshi da ido tace "Wallahi tuwon hatsi na ke sha'awar ci." Galala ya kalleta baki bud'e, shi fa ya d'auka son shi ne ya ma ta yawa har zai kashe ta, ashe ba haka ba ne. Sai kawai ta bashi dariya, murmusawa ya yi yace "Tuwon hatsi? Kin iya noma ne dama?" Kyab'e fuska ta yi ta girgiza kai alamar a'a, cikin tsareta da ido yace "To kin iya girbe hatsin ne? Ko kuma kin iya shik'a?" Sake girgiza kai ta yi tace "Ko d'aya ban iya ba, babban mutum da gaske fa na ke ma ka." "Ni ma da gaske na ke." Ya fad'a ya na tsareta da ido, d'orawa ya yi da "To za kiya surfa hatsin na kawo mi ki, kuma ai kin iya tuk'a tuwo ko?" Fashewa ta yi da kuka tsakaninta da Allah ta na sakin hannayenshi tace "Shikenan Faduma marainiya, da Abanki ne da yanzu ya sama mi ki tuwon hatsin nan." Juyawa ta yi za ta fita ya rik'o hannunta, kakkafeta ya yi da ido yace "Me ki ke ji a jikinki?" Girgiza kai ta yi tace "Ba na jin komai, ni kawai tuwo nake so na ci, ka kai ni gidan Umma sai ta koya min to." Nazartarta ya ke sosai ya na bawa kowane harafi dake fita daga harshenta muhalli mai kyau, saida ta dasa ayya ya shafo kumatunta yace "Karki damu kin ji, Qaseem kawai zan kira ya kawo mi ki." Cikin jin dad'i tace "Yawwa to kirashi." D'an d'aga gira ya yi irin mamakin nan na zumud'in ta, wayar ya ciro a sanyaye ya kira Qaseem ya fad'a ma sa, ayyukan dake gabanshi ya sa shi yi ma ta sallama ya wuce b'angaren Saudat. Da sallama a k'asan mak'oshi ya shiga, da sauri Saudat da ta ci kwalliya ta mik'e ta na fad'in "Wa'alaikas salam, sannu da zuwa Aban Izz." Saida ya k'arasa tsakiyar falon ya na shak'ar k'amshin turaren ruwan da ta yi, ba laifi yanzu ya ga ita ma ta d'auki hanyar gyara, sai dai wallahi har zuciyarshi zai kulata ne saboda tunin da Faduma ta ma sa, zai so ya kasance mai halin girma a cikin iyalinshi, ba dan haka ba Saudat ya yi niyyar yin shekara d'aya cir da ita babu kulawa. Numfashi ya sauke ya d'an kalleta ya na mik'a mata kud'i yace "Ki dafa abin da ki ke so." A sanyaye ta karb'a zuciyarta na suya, sai yaushe zai bata girki ne ita ma? Tabbas ya raba musu kwana kuma ta na girki amma fa baya ci ko kad'an, juyawa ya yi zai fita har ya kai bakin k'ofa ya jiyo ya kalleta yace "Anjima za ki iya dafa min farfesun kifi?" Wata b'oyayyar dariya ce ta kubce ma ta bata sani ba, da zumud'i tace "Me zai hana Bab, insha'Allah za a yi yanda ka ke so." D'an lumshe ido kawai ya yi ya juya ya fita, da farin ciki ta shiga taka rawa dan ko bai fad'a ma ta ba hakan na nufin zai sauko ko kuma ya sauko ne, dan haka yau kam zage damtse ta yi sosai wajen gyaran b'angaren nan har da d'akinshi ma, sam b芒 wai ba ta iya aikin ba ne, lalaci ne dama irin na 'ya'yan yau, dan haka aikinta ta yi cikin kuzari da karsashi, ko da yara ke dawowa daga makaranta har ta gama da komai. *12:20* na dare gidan ya yi shiru, ya na tsaye gaban panpo ya na sauraren saukar ruwan a jikinshi ya ji an rumgumeshi ta baya, d'an bud'a ido ya yi da sauri tare da d'ora hannunshi d'aya a kan hannayenta, d'ora kan ta tayi a kan bayanshi cikin muryar tausayin kan ta tace "Bab dan Allah ka yi hak'uri ka yafe min, na gane kuskurena wallahi ba zan k'ara ba." Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi tare da jawota ya dawo da ita gabanshi suna kallon juna, kallon mmamaki da son had'iye komai ne ya ke mata kawai ya fuskanci gaba, d'an murmushi ya k'ak'aro ma ta yace "Ba komai, na hak'ura." Turo bakinta tayi gaba tare da kwantawa akan k'irjinshi ta na k'ara rumgume shi sosai, shi ma rumgumetan ya yi sosai ya rad'a ma ta "Kin yi kewata ne?" D'aga kai ta yi alamar eh tare da cewa "Sosai ma, Bab ina son ka sosai, ba zan iya rayuwa babu kai ba, wallahi da gaske na ke fad'a ma ka." Wani murmushi ya saki na jin dad'i, ko ba komai a ce shi ma akwai wanda zai iya mutuwa a kan shi ai nasara ce, d'ago kan ta ya yi a hankali ya had'a bakinshi da na ta idonsu a rufe saboda saukar ruwa a fuskarsu. Daga nan wasar ta canza suka baro ban d'aki aka dawo gado mai daraja, sosai suka nunawa junansu kulawa da shauk'insu, cikin salama da sanyin zuciya bacci ya d'aukesu kowa na jin sakayau a ran shi. *08:15* ya kirata a waya ta same shi a nan, tunda ta shigo falon sai ta ji zuciyarta na tsitsinkewa, yanda ta ga kusancinshi da Saudat d'脿 kwalliyar da Saudat ta d'auka sai taji kamar za ta yi kuka. K'arasawa ta yi ta zauna ta na kallonshi tace "Barka Elhaj." Ba ta jira me zai ce ba dan wani haushi haushinshi ta ke ji ma da b芒 ta san dalili ba, Saudat ta kalla tace "Aunty barka da safiya." Da fara'a ta amsa ma ta da "Barka Fati, antashi lafiya?" Murmushin yak'e ta yi tana zama tace "Lafiya lau." Abinci Saudat ta zuba mu su suka fara ci, kan ta a k'asa ya ke ta na jin yanda zuciyarta ke yamutsawa, sai muryar Saudat ta ke ji k'asa k'asa suna magana, da sauri ta mik'e ta na kallonsu tace "Zan koma ciki, na manta zan kira Ayya." Ba ta jira cewar kowa ba ta gaggauta d'aga k'afarta ta bar falon ta na jin kamar za ta fashe da kuka, saida ta je b'angarenta ta zaunata na maida numfashi, a hankali kuma ta tambayi kan ta "Me ke damuna?" Wata zuciyar ta fad'a ma ta "Dan kin gansu tare ne." Girgiza kai ta yi tace "Idan hakane kam zuciyata b芒 ki min adalci ba, ta ya za ki bari shed'an ya shiga cikin ki ya min wasa da hankali? Matar nan da mijinta na sameta da yaransu, me ya sa zan bari kishinta ya rufe min ido?" Ajiyar zuciya ta sauke tace "A'uzu billahi mina shaid'anin rajim." Wayarta ta lalubo ta danna kiran Ayyarta dan ta samu wasu shawarwarin a game da matsalar da ke neman tunkarota. A wunin ranar kam ta samu bak'uncin Dada tare da yayar Abdallah da ta zo yi ma ta bankwana za su tafi Niamey, sosai su ka yi jimamin rabuwa har da kukansu kamar kar su rabu, sai dai auren kenan mai raba 'ya ma da iyayen da suka haifeta bare dangi. *A gurguje* Duk irin k'alubalen da aka fuskanta a baya sai gashi yanzu sun kau, ta ko ina farin ciki ne ke faruwa da kwanciyar hankali idan ka cire sab'ani na yau da kullum da akan samu a dalilin zaman tare. Ta b'angaren Aji ne kawai ake k'unci da zulumi na rashin sanin halin da ya ke ciki, dan fa Wardugu ya kafe ya k'i cewa kowa komai a game da lamarin shi. Amma hatta da Tagur farin ciki ya ke a sabuwar rayuwarshi, yaronshi Amjad da suke tsaye tsayin daka kan tarbuyarshi, da kuma matarshi Husna da ke kwana da tunanin yanda za ta faranta mi shi rai, zamanta da Amjad ma sai san barka, dan kamar daga cikinta ya fito, babu wani abu da take nuna mi shi bayan k'auna da kulawa, hakan ya sa yanzu Amjad ya rage kewar Ayyarshi dan Allah ya bashi wata. Wajen Mujaheed ma haka abun yake, Umma har tsoro yake bata wani lokacin, ko motsi zai yi sai ya kalleta ya tambayeta Hasheerere ko mace ba ta nuna mi shi zaman gida yanzu, hatta da madafa wani lokacin tare suke shiga ko da shayi za ta dafa, a hakan ma bayan ya tsatsareta da lallab'a har ta yarda ya d'auko ma ta mai aiki, dan Umma ba ta son mai aiki a gida, a hakan ma ta yarda ne dan Halima ita ma ta yi aurenta, ko ba komai shara da guga za ta so a tayata. Hakan ya k'arawa Mujaheed kima a idon Hasheer da ma wani d'a daya fito daga tsatson Umma, sannan ya k'ara mu su kwanciyar hankali. A gidan Hasheerere (馃槬 na fad'a a yankani) ma haka abun ya ke, a nutse cikin salo kishin matan ya ke gudana, walwalar gidan ta dawo, farin cikin ma bayananne ne, sannan annurin gidan daban ya ke, mijin hankalinshi a kwance, yara nutsuwarsu a zaune take wuri d'aya. Sun had'a kan su sosai ta yanda yanzu komai tare su ke yi, dalilin haka ya sa Faduma shi ga cikin mutanen Saudat uta ma ana dama wasu harkokin da ita, duk da dai tana fad'in ita ma fa 'yar gari ce. *Laulayi*, shi ne kawai ke azabtar da ita daga tsaye, ba ciwon ciki bare ciwon kai, ciwon mara ne shi ma ba kullum ba sai tashin zuciya, ta na ci ta k'oshi sai dai inda matsalar take shi ne, idan har zuciyarta ta raya ma ta abu kaza ta ke so, to fa dole a nemoshi komai sanyi, komai zafi, komai ruwa da iska kuma komai dare da asubanci, a hakan fa ita dan ta na rage wasu abubuwan, dan ba komai ne take fad'a ba saboda Ayyarta ta mata kashedin kar ta zama wawuya kamar gara a gaban miji, dan ta na da ciki ta since zane ta bud'e k'afafu ta dinga had'iyar komai, shi ya sa take d'an taausar kan ta wani abu. *Bayan wani lokaci*: Kwance ya ke kan doguwar kujerar da gajeran wando tree quater sai riga t-shirt inda ya tada kan shi da cinyar Saudat, idonshi a rufe bacci ma ke son d'aukarshi, sai sautin karatun yaran da yake ji suna yi Saudat na gyara m没 su, wanda hakan ke masa dad'i sosai har zuciyarshi, wayarshi dake kan kujera ce ta yi k'ara alamar shigowar sak'o, duk da bai bud'a ido ba bare ya kalli wayar yasan ita ce, ita ta saba aiko mi shi da sak'o na gaisuwa ko addu'a, barka da safiya ko yamma har ma da saida safe, lalubawa ya yi ya jawo wayar ya bud'e idonshi, saida ya cire tsaron wayar kafin ya dira a kan sak'on, da k'arfi ya zaro ido bayan ya karanta tare da mik'ewa zaune, kallon Saudat ya yi sai yaga hankalinta na kan Sharfudeen tana duba mi shi littafinshi, a hankali ya sake kallon sak'on ya shiga nanatawa _"Elhaj barka da dare, ka taimake ni ka min rai ka siyo min aduwa."_ Wata dariya ya bushe da ita yana shafa kan shi, girgiza kai ya yi sanda Saudat ke fad'in "B茅b茅 lafiya?" Girgiza mata kai yayi ya mik'e yana fad'in "Ina zuwa dan Allah, zan fita ne yanzu zan dawo." Kallon da ta sakar mishi ya sa ya koma ya zauna ya rik'o hannunta yace "Bab karki d'aga hankalinki, Fati ce ke buk'atar wani abu, kin amince na tafi?" Murmushi ta ma sa tana mai jin dad'in yanda yake kwatanta adalci a tsakaninsu, cikin fara'a tace "Sai ka dawo b茅b茅, Allah ya tsare." Mik'ewa yayi yana fad'in "Ameen, me kike so na taho mi ki da shi?" Dariya ta yi tace "Abin da ka taho mata da shi." "Ba zaki iya shan abinda za ta sha ba." Ya fad'a sanda yake fita, b'angarenta ya nufa da takon karsashi, tsaye ya sameta sai safa da marwa take a tsakiyar falon, tun yamma take son aduwar nan amma saboda gudun shiga hakk'in yar uwarta yasa tayi shiru. Kallonshi ta yi kamar wacce ke jiran tsammanin wani sakamako ta ga likitan da zai sanar da ita bayanin, yana k'arasowa kamar yanda ya saba mata yanzu ma saida ya tallabo fuskarta ya sumbaci goshinta kafin ya sunkuya sosai ya sumbaci tulelen cikinta masha Allah daya shiga watan haihuwa, d'agowa yayi ya kalli tsakiyar idonta yace "Batul, yau kuma rigima ake nema na da ita? Dan mutum yasan ba zan iya dukanshi ba ko?" Marairaicewa tayi tace "Orro, dan Allah ka taimaka min ka samo min aduwar nan naji ta a bakina ina tsutsa, ji nake kamar zan shid'e fa idan ban samu ba." Rumgume hannaye yayi yace "A'a fa Zahra, yanzu ina zan samu abun nan?" Sake shagwab'ewa tayi tace "Ni dai kawai a samo min, ga kasuwa babba, ga kasuwar sonita." Cikin gatsali yace "Amma ai yanzu duk sun rufe, wa zan samu a can?" D'an ja baya ta yi ta taka kujerar bayanta tayi tsaye tace "Na diro k'asa kake buk'ata?" Kallon fuskarta yayi, wato yau fitina take ji ba, girgiza mata kai yayi yace "A'a dan Allah, rufa min asiri Batulu alk'awari na d'auka a kan cikin nan tun ban aureki ba, cikin nan na Wardugu ne." A hankali ta sauko bayan ya rik'o hannunta, saida ta tsaya da kyau yace "Matar Hasheer, ki taimaki mijin Batul mana ki barni yau dai nayi bacci cikin salama, kinsan nemana da fitina me yake haifarwa ko?" Kamar za ta yi kuka tace "To kawai ka samo min aduwa ni." Sunkuyar da kai ya yi ya rik'e k'ugu yace "Allah sarki Hajia, Allah ya jik'anki da rahama (hajiar Abdallah an tafi kudu ashe), kinga da tana nan fa da duk wannan wak'i'ar ban shigeta ba." Cikin shagwab'a tace "To ba ga Umma ba? Ai ba zata rasa ba." Harara ya cilla mata yace "Ke uwata tsohuwa ce da za ta ajiye karikican nan?" Sai kuma ya shafi sumar kan shi yace "Har fa zawarawa ta fara, dan ma na hana ne." Da mamaki ta kalleshi tace "Ka hana kamar ya?" Turo baki yayi yace "Eh d'in na hana, abokin Abana ne kawai ya fito wai zai aureta, ni kuma na ce a'a ban yarda ba, a bar min uwata ta huta haka." Da sauri ta rik'o hannunshi tace "Yawwa na tuna, muje wajen Mama." Ko da ta ce mama ya fahimci wacce take nufi, ta tsohuwar unguwar da suka zauna ba, dan haka yace "Kawai sai na je na k'wank'wasa mu su k'ofa na ce ke kika aikoni karb'ar aduwa? Allah ya kiyaye." Zaro ido tayi tace "Au! Wai ba za ka je ba kake nufi?" Saida ya rumgume hannaye ya murgud'a baki yace "Eh d'in, ai ba tsoron mutum na ke ba, tunda ba haihuwata mutum yayi ba." Tallabo fuskarshi tayi dan ta lura yana jan ta da magana ne dan ya mantar da ita maganar aduwar tace "Mijin Batul, muje tare to, sai na karb'a da kai na." Girgiza kai yayi yace "Je ki canza kayanki to." Da sauri ta juya ya bita da kallo ya na girgiza kai, wayarshi ya jawo ya turawa Saudat sak'on cewa zai kai Faduma gidan mama su karb'o sak'o yanzu zai dawo, addu'ar data maido masa yasa shi murmushi, lallai Batul ta saita masa rayuwarsa da gidansa da iyalinsa, da fari har mamaki yake idan Saudat tayi wani abun, amma yanzu ya daina mamaki ma. Fitowar Faduma tasa shi soka wayar aljihu yana kallonta, a kan labb'enshi ya furta "Kutumar can! Wato bala'i kawai take so mu yi." Lafaya ce ta saka sai kuma ta mata yanda tasan baya so, duniyar Allah ya tsani a sa lafaya a ciro hannu d'aya waje yanda wasu keyi, ta saman wuya a ke zuro hannun hakan yasa zaka ga damtse ma a waje. Bayan ta fito da damtsen saida ta saka wacce yadinta ke bin jikinta, hakan ya bayyanar da cikinta sosai ya fito, yanzu da yayi magana kuma fad'a zata fara yi, abun takaicin kuma cikin harshenta na tubanci, hakan zai sa ba zai san me ta fad'a ba bare ya mayar da martani, girgiza kai kawai yayi ya na tunani ya bita kawai su rabu lafiya, ai daga mota babu inda zata matsa. *Yasin na gaji, za mu kawo k'arshen allura insha'Allah a shafi na 80.* *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 21:43 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _79_ Suna d'aukar hanya ya kalleta yace "Binta, amma dai kinsan ba zaki shiga gidansu mama da wannan lafayar ba ko?" Wani kerere ta kalleshi tace "Saboda me?" Yanda ta jefo mishi tambayar saida yayi saurin kallonta, sai kuma ya girgiza kai yace "Saboda bana so, zaki zauna a mota mama ta fito kuyi abinda za kuyi, amma ni ba mahaukaci bane ki shiga gidan nan da maza a ciki a haka." Gyara zama tayi cikin gwamutsa yaren hausa da tubanci tace "Kamar ya? Wai me kake nufi dani ne? Miye na kallo a jikina to da zasu tsareni da ido da k'aton ciki haka, shikenan ni babu damar watayawa sai an babbake ni." Juyar da kan ta tayi tana turo baki, k'uri ya mata da ido yana kallo harta gama, sai ta bashi murmushi ma kawai yana girgiza kai, saida suka isa k'ofar gidan ya rik'o hannunta gam yace "Ba k'aton ciki ne jikinki ba, cikina ne *Siddiqa*, a jikinki kuma komai na kallona, amma idona kawai ke da damar wannan hangen, idan kika yarda wani a cikin gidan nan ya karkata kallonshi zuwa gareki, to tabbas za ayi makoki a gidan nan zuwa wayewar gari." Marmad'a masa ido ta shiga yi farfarfarfar tana turo baki, a nutse yace "Kin fahimta?" D'aga kai tayi alamar eh, jinjina kai yayi ya saki hannunta yace "Muje." Girgiza kai tayi tace "Zan kira mama ta fito nan sai ta bani idan akwai." Wani shu'umin murmushu yayi ya fita yana ayyana "Wa ya fad'a miki barno gabas take?" A nan mama ta samesu har tana tambayar me yasa basu shiga ba, ita dai bata ce komai ba sai tambayar ta akwai aduwa? Ba su yi sa'ar samu ba a gidan mama dan abu ce yanzu da ba'a cika aiki da ita ba, tunda ya ji abun da mama ta fad'a yasa ka shi kallon Faduma ya kalli mama yace "Mama, dan Allah to ki mata nasiha sosai, yanzu nan zata saka ni neman abar nan ne, ni kaina wallahi na jima rabon da na ganta." A hankali mama ta kalleta tana dariya tace "Faduma, ai za ki hak'ura ko?" Turo baki tayi tace "Zan hak'ura mama, amma fa idan ya siya min ice cream." Murmushi ya yi ya kama hannunta yana fad'in "Abu mai sauk'i, muje." Ba tare daya juyo ba yace "Saida safe Mama." Da kallo kawai ta bisu ita dai, haka kawai ta ji jikinta ya bata Faduma ta kusa haihuwa daga yanzu zuwa lokaci kad'an. A mota kam suna fita hanya ya d'auka ta ali d'an sofo, dan a wannan lokacin *Bouzou city* ne kawai ya zo mi shi a ran shi, cikin nishad'i suka k'arasa wurin bayan sun sha tafiya, a k'ofar gurin ya paka ya kalleta yace "Ina zuwa ko?" Turo baki tayi tace "Um um! Ni ma ina so na shiga ciki, ban tab'a zuwa ba fa." D'an girgiza kai yayi yace "Tanadi nake mi ki, idan kika haihu zan kawoki tare da yaronmu." Sake mak'ale kafad'a tayi alamar a'a, lumshe ido yayi yace "To gyara hannun lafayarki, kuma wallahi karki saki jiki ki dinga min tafiyar nan kina jan k'afafu kinji na fad'a miki." bud'ewa ya yi ya fita ya zagaya ta inda take ya bud'e mata, kamo hannunta yayi ta fito duk da fitilar mashin d'in data haskesu a lokacin, cikin nutsuwa suka shiga takawa zuwa ciki, d'aga kai ta yi tana kallon hasken shud'iyar fitilar data birgeta, kasancewar wurin madubi ne ya birgeta sosai, dan daga nan kana hango abubuwa da dama musamman lumtsuma lumtsuman cake d'in da aka ma kwalliya aka jeresu a cikin wani gurin na gilashi. A k'asa k'asa suka ji maganar manyan matan da suka tsaya gurin da moton, hakan yasa Faduma juyowa da sauri dan abunda kunnenta ya jiyo mata shi ne " *Kyakyawa* dashi." Juyowar da tayi kuma sai tayi saurin dafe k'ugunta daya rik'e, d'an cije leb'e tayi tana furzo iska har suka shiga ciki, duk da sanyin wurin sai gashi tana tsatsafo gumi daga goshinta, inda suke tsaye manyan matan suka tsaya su ma a bayansu, Hasheer kam harkar gabanshi yake, saida aka mik'o mi shi ice cream d'in daya buk'ata ya sake kamata za su juya, da sauri d'aya daga cikin matan wata tace "Sannu." A tare suka kallesu, tsaf ta gama musu kallo cike da jin haushi da tsana, dan shigarsu zata nuna maka marasa jin magana ne, tubarkallah gasu manya manya uwa dawakai, ciwon da take ji ne ya sake taso mata wanda yasa ta sake damk'ar hannun Hasheer ta rintse ido, shi kam kallo d'aya ya musu zai watsar da su, sai kawai fuskarshi ta sauka a kan coll猫gue d'in shi, da mamaki ya k'ak'aro fara'a cikin d'aga harshe da k'yar yace "Charifa Abba?" Dariya ta yi tana mai sake waro idonta tace "Lahh! Hasheer Abdul, dama kai ne?" Duk a tare suka saki murmushin yaushe gamo, sai dai hannunshi da Faduma ta matsa da k'arfi yasa ka shi kallonta, takawa ya fara yi ya kalli Charifa yace "Ina zuwa ko?" Da kwarkwasa ta amsa da "Ba damuwa." Jan ta ya fara yi amma saita cije wuri d'aya tana binshi da kallon ban haushi da mamaki tace "Ka na zuwa fa ka ce? Ka dawo ka musu me?" D'an satar kallonta yayi yace "Muje mota, k'awata ta 茅cole." Kamar wacce ya sokawa mashi a zuciya sai kawai ta fizge hannunta ta ja baya tana rintse ido tace "Ban ji ba, k'awarka fa ka ce? Dama har k'awaye ne da kai mata?" Tsaye yayi yana kallonta, sa'a d'aya bayan su da su Charifa babu kowa sai masu hidimar wajen, hannu ya zura zai kawota ta zille tare da juyawa ta kalli matan, nunasu tayi da yatsa tace "Ku ji nan da kyau, wannan yafi k'arfinku, mijina ne kuma ba ni kad'ai yake da ba, akwai yar uwata a gida ita la, wallahi yafi k'arfinku." Saida ta dire kafin kunnayenta suka jiyo me ta fad'a, sai ta tsinci kanta da mamakin kan ta akan abunda ta yi, wannan duk kishin ne? Anya kuwa bata zak'e dayawa ba? Ya tayi haka kai tsaye kamar wata jahila? A take ta fahimci rashin bayyanawa da basayi a gida shi ya jawo mata haka, sai dai zata gyara yanda ba zata dinga sakin hankali ba. K'awar Charifa ce ta harareta tace "To kaji, ke kuma haka na ki salon yake? To dan yana da biyu a gidan ai ba'a haramta mi shi wasu ba, guy kamar na ki tsaf zai ji da guda hud'u Hajia, dan nasan ire-irens..." Cikin fitar hayyaci da zafin ciwo kawai Faduma ta kasheta da wawan mari, a tare suka rintse ido dan ita fa k'arfin halin ne take, a sukwane ya rik'ota ya juyo da ita gabanshi gabanshi yana fad'in "Batula, miye haka wai? Ya za ki zubar min da mutumci?" Kallonshi tayi da idonta da suka canza launi tana d'an lumshesu, dantse leb'enta take a hankali tana cizawa, cikin harshen tubanci ta shiga fad'in "Eh bana da hankali, wallahi baka isa ka kula kowa ba kai ma, dan baka jin kunya har ni zaka kalla kace ma wai k'awayenka, to ba kai ba k'awa muddin ina..." Da sauri kuma ta cakumo rigarshi ta sulale k'asa yayi azamar tarota jikinshi, k'amk'ameshi take tana fad'in "Hasbunallahu wani'imal wakil, la'ilaha illa anta subhanaka inni kumtum mina zallumin." Su Charifa kam ganin haka saita matsa tace "Wantan haihuwarta ne?" A kid'ime ya amsa da "Eh watanta ne." K'ok'arin kamata ta shiga yi tace "Ka kaita asibiti mana." Gyad'a mata kai yayi alamar to tare da tallabo fuskar Faduma, kallon fuskarta yake sosai yace "Fati na, kalleni nan, fad'a mine kike ji?" Sake cakumoshi tayi tace "Ciwo...ciwo na ke ji, zafi ko ina, ka sakeni na ci uwar yarinyar, me yasa ka kulasu a gabana? Zan *kasheka* mijin Batulu idan na haihu, wayyo bayana." Fit ya d'aauketa daga ita har cikin suka fita a wurin, gidan baya yayi dubara ya kwantar da ita kafin ya d'auki hanya, clinique hamdala suka tsaya inda ya sake d'aukarta sukayi ciki, da ganin haka likitocin suka taimaka mi shi suka d'orata a gado aka shiga da ita ciki. Sam ya kasa yarda da haihuwa ce ta ke ji, daga fitowa nan aduwa sai fad'a sai kuma haihuwa. Zaune yayi a kan kujerar k'arfe yana jiran tsammani, duk da mata da mazan da ke gefenshi wanda suma mai haihuwar garesu, sam bai kula da tsiyarsu ba bare ya tuna tree quater ne jikinshi fa, wata likitar mata ce ta fito da sauri ta tsaya kanshi tace "Elhaj, matarka haihuwa ce za ta yi, ina kayanta suke?" Mik'ewa yayi a duburburce yace "Haihuwa? Ban sani ba, kawai fa mun fito ne." Cikin sauri tace "To ya za ayi yanzu? Daf take da haihuwa ita, kayanta muke buk'ata." Wata dattijuwa ce dake zaune a gefe tace "Ga namu kayan to a mata anfani dasu, tunda mu yarinyar gata can a farfajiya ma tana kai da kawon da kuka sakata." Da sauri ta matsa ta karb'i kayan da tsohuwar ta mik'o mata ta juya ta koma, a sanyaye ya kalleta yace "Nagode mama." Murmushi tayi tace "Ba komai d'an nan." Komawa yayi ya zauna yana jawo wayarshi a aljihu tare da d'an cire takalminshi daga k'afafun, da k'yar ya rarumi lambar Umma ya danna mata kira, yana fad'a mata kam da saurinta ta amsa da g芒ta nan zuwa, abu na ikon Allah ko minti biyar basuyi da gama waya ba likitar nan ta dawo tace "Elhaj barka, madame ta sauka lafiya an samu d'a namiji, yanzu zamu k'ara mata ruwa saboda zazzab'i ne a jikinta." Takarda ta mik'a mishi tace "Ga wannan saika siyo ko." Ya manta da ina yake take ya zube gwiwoyinshi ya kai k'asa yayi sujada ga Allah ta godiya, saida ya d'ago ya karb'i takardar da gudun tsiya kamar yaro ya fita yana dariya, bai san baya da takalmi ba, hasalima ya manta da babu su a k'afarshi tsabar zumud'i da farin ciki, har ya shiga mota ya nufi pharmacie Bourja bai kula ba. Sai lokacin daya fita zai shiga ne ya ji ya taka tsakuwa a k'afafunshi, rintse ido yayi sai kawai yayi shahada ya fad'a pharmacie, yana zuwa aka bashi abinda ya buk'ata ya dawo, zuwanshi yayi daidai da tsayawar motar Mujaheed tare da Umma da Mukhtar, da farin ciki akan fuskokinsu suka rumgume juna, cikin tsokana Mukhtar yace "Ina sabon yaron nawa yake ne? Ina so na zama na farko da zai d'aukeshi dan na samu tabarraki na yi aure nima." Mujaheed ne ya dungure masa kai yace "Tafi can dan Allah, na fad'a maka ai sai nayi aure ko za kayi kai ma." Harara ya galla masa yace "Ka ji ubana, kawai saina jiraka har sai kayi sannan." A tare Hasheer ya dungure musu kai yace "Gidanku, ni ne dai mai yin auren ko? To kuka takurani ba zanyi ba." Mukhtar ne yace "Ah haba dai kai ma wasa ka ke." Mujaheed kam cewa yayi "Kayi hak'uri yaya ka rufa mana asiri, kai kafi son k'annanka suyita yawo a gari kamar wasu sakarkaru?" Dariya sukayi sai Umma da tace "Malam muje ka nuna min inda 'yar mutane take na ga halin da take ciki." D'umguma sukayi ciki inda a gabansu duk aka k'ara mata ruwan, Umma dake rik'e da jaririn ne yana ta kuka ta yi kamar zata sakeshi k'asa tana fad'in "Kai inba ka rufe min bakinka ba zan jefar da kai, ragon banza kai daga dirowarka ka ishemu da kuka, bayan ma ka zo mana a wani gadarance." Dariya suka saka sai Mujaheed da yayi azamar rik'oshi yana fad'in "La-la-la! Umma rufa mana asiri mana, sabon yaron." Hasheer ne yace "Yaron Wardugu ba, Umma ki rufa mana asiri kar kisa ayi sunanshi bana tare da ku." Dariya suka sake, cikin nutsuwa Umma ta kalli Faduma da bacci ke son d'aukarta tace "Ai alhamdulillah, naji dad'i sosai wallahi da labarin haihuwar kawai muka samu, kinsan raguwa ce ni ina iya zuwa nan ke kukan nak'uda ni kukan tausayi." Murmushi kawai ta yi babu wanda yayi magana saboda Hasheer dake waya da Wardugu, cikin tsananin farin ciki Wardugu yace a tura masa hotonshi ya gani, bayan sun gama ya kira Saudat ita ma da mamaki ta kasa gasgatawa, maimaitawa take "Faduma ta haihu fa? Ba ka ce gidan Mama zaka kai ta ba? Dama bata jin dad'i shine bata fad'a min ba?" Cikin nutsuwa a wannan dare haihuwar Faduma ta karad'e ko ina na ahali da makusanta bayan mahaifinshi ya rad'a mi shi sunan mahaifinshi wato *Abdul Karim*, kowa murna da farin ciki har Amjad ma da ya so tayar da hankalin Tagur sai ya kawoshi ya ga k'annanshi, da k'yar suka lallab'ashi tare da Husna wacce ta mishi alk'awarin zasu zo tare da safe. A asibuti suka kwana tare da Umma kafin da sassafe aka sallamesu bayan tabbatar da suna cikin k'oshin lafiya Mujaheed ya kaisu gida. Saudat ce ta fito da katifa a falon aka mata shinfid'a tuni kuma ta d'ora musu ruwan zafi, saida Umma ta fara wanke yaron tas aka gasa mishi jikinshi, mai aka shafa masa na ruwa kafin aka saka mishi kayan da suka dace da yanayin wurin da suke masu maganin sanyi, kasancewar a lokacin Dada na garin tunda ta zo rasuwar Hajia bata koma, hakan yasa da kanta ta shiga taya ta wankan haihuwarta ta farko kamar yanda ita ta tayata a na biyu ba duk da a lokacin bata san kan abun ba, saida ta fara gasa jikinta bayan siracin da tayi kamar zata mutu, ga ruwan zafi da bagaruwar data zauna a ciki kafin suka fara wanka. Ai fa sun sha daru sosai a ban d'aki inda suka rikice suka shiga fad'a a harshensu kamar kaji, dan Faduma sai yanzu ne ta san ciwon jikinta, dan sai taji wannan haihuwar kamar tafi ta Amjad ciwo da wahala, duk da Allah ya sauk'ak'a mata sosai dan a d'an lokacin data haihu zaka gane haka. Suna gamawa suka fito ta shafe jikinta da man d'umi ta saka doguwar rigar atamfa ta d'ora k'aramin hijab a kai, lafiyayyen farfesu da soyayyen dankalin turawa da had'add'en shayi da madara Umma ta girke mata ta ce ta cinye tas, tun tana ci tana murmushi tana jin dad'i, har ta fara ci tana yatsina fuska amma saida ta cinye tas, maganin da aka rubuto mata dada ta bata tasha, a hankali ta ji wata nutsuwa na sauko mata tana bin illahirin jikinta, duk da mak'wabtan da suka fara shigowa yin barka bai hana bacci d'aukarta ba dan a maganin akwai mai saka bacci sosai. Alhamdulillah jego take cikin kulawar uwar mijinta, dan kullum Umma tana gidan tana rumgume da yaron da take tsananin k'aunarshi har zuciyarta, sunan da aka saka mishi tana girmamashi, dan haka take kiranshi da Elhaj ko Abba, wani lokacin ma a gaban Hasheer sai dai tace *shi*馃榿, amma fa a zahiri tsiya take mi shi tana nuna bata aurenshi sai ma ya saketa, tana d'aga mishi k'afa ne dan yana da babban suna. Haka ma Herde tun a washe garin ranar ta zo taya 'yarta zaman jego, ga kuma Dada da kullum suke shan tak'addama da Abdallah kan ta fa dawo kafin ya sameta garin nan, dan dama bayan rasuwar bai so ya tafi ya barta ba ita tace mishi ta ji kamar ciki ne da ita, shiyasa ya k'yaleta a gidansu dan k'anwar Hajia na nan da kuma babbar 'yarta. Uwa uba kuma Saudat da har birge mutane take irin yanda take kulawa da lamarin duka gidan, ta kula da lamuran Faduma dana yaronta, ta kula dana yaranta sannan ta had'a da lai gidansu, dan abincinshi ma kullum daban take dafa mishi dana bak'i, hakan ya k'ara mishi soyayyarta shi kan shi ya sake ganin girmanta. Ana haka har akayi suna abubuwa suka rage, dada ta koma bayan tabbatar mata da akayi a likita tana da cikin wata hud'u, Herde ce dai zaune da yarta tana kula da ita da yaron, Umma kuma idan bata lek'o yau ba gobe za ta zo. *Bayan sati biyu* Saida ta waiga ta kalli Herde ta tabbatar bacci take cikin sand'a ta shige d'akinshi ta rufo k'ofar, ajiyar zuciya ta sauke ta k'arasa gabanshi har ya gama cin abinci ta na kallonshi ya na gyara zaman towel d'inshi ya fito daga wanka cikin rad'a tace "Abban Aba ina ka je haka? Kasan k'arfe nawa ka shigo gidan nan? Me ya faru ne?" Murmushi kawai ya mata ya girgiza kai yayi gaban madubi, bin bayanshi tayi tana sake fad'in "Elhaj magana na ke, wani abu ya faru ne a wajen?" Yatsa yasa a cikin kunnenshi ya k'wak'ule tare da kallonta yace "Bana jinki fa da kyau, d'aga murya." Turo baki tayi gaba sai kawai tasa hannu ta zare towel d'in da k'arfi tana fad'in "Wal..." Bata fad'a ba ai tayi baya luuuu zata fad'i saboda haka kawai ta tsorota da ganinshi kamar yau ta fara ganinshi, ta d'auka yana da boxer (inji 'yan lanjeria) a ciki ashe hakanan ya fito surundunshi guda, da sauri ya bita suka fad'a kan gadon yana kallon fuskarta, cike da shak'iyanci yace "Ni na aikeki? Gashi za ki suma a banza a wofi wajen neman fitinar tsiya, Batul na gayyaceki d'akina ne, shin Ayyarki ba ta raba mana d'aki ba kuma ke ma kika amince da haka saboda ba kya son kiyi ta haifa min yara? Yanzu k'addarar wane yaron ne ta turo min ke d'akina?" Zaro ido tayi tace "Ban gane ba?" Da alamar oho yace "Miye baki gane ba? Bari kiga ni dalla dalla zan miki." D'an kwalinta ya cire ya jefar, hannu ya kai a k'ugunta yana lalubar zariyar zaninta, da sauri ta rik'e hannun tace "Aban Elhaj kar ka min haka, kayi hak'uri ka ji, indai d'akin ka ne na daina shigowa Allah." Girgiza kai yayi yace "Yaushe rabona da ke? Na lura ke ko irin na baki tausayin nan ma ban tab'a gani a fuskarki ba bare ki kawo min agaji da 'yan tsotse tsotse ko..." Herde data farka ne ganin bata falon sai yaron yasa ta rikicewa ta tak'ark'are tace "Faduma." Zazzaro ido tayi sai kuma ta d'aga murya zata amsa kawai ya taushe mata baki yana girgiza mata kai, k'walalo ido tayi tana girgiza kai ita ma, d'auke hannunshi yayi ya d'ora bakinshi tare da kamo harshenta ya saka a bakinshi ya shiga tsutsa, hakan yasa dole tayi shiru sai "Um um um um." Da take fad'a. Sosai ya zabgeta a wannan dare ka rantse da Allah haushinta yake ji ko baya da wata matar, dama tsautsayin nan ne yasa ya dage dole ta karb'i aiki a yau, ashe yasan me ya shirya mata ita kuma da rawar kai ta kawo kan ta, babban abinda yasa tayi sanyi ta koma saurarenshi bai wuce yanda taji yana mata muryar kuka da sambatu yana k'amk'ameta ba, hakan ya mata dad'i musamman a sambatunshi daya rantse mata cewa uta ce hutunshi kuma nutsuwarshi. Ta yarda dan tasan ta karb'i gyara a wurin Dada kafin ta tafi wanda take wa kanta a b'oye, Umma dai kazi take aiko mata kowace safiya ta tukunya, Herde kuma siraci take mata sosai da gashin k'asanta ana turarashi, hakan yasa ita kanta ta ji a jikinta ta gama had'uwa a sati ukunta da haihuwa. Tana jin ya fito daga ban d'aki ta murje ido ta shiga kuka tana fad'in "Ya kake so na kalli Ayya yanzu? Na shiga uku ni Faduma ayya za tace ban da kunya, za tace na lalace wallahi." Tab'e baki yayi yace "Idan baki min shiru ba fa k'arawa zanyi malama, to idan ban samu wani yaron yanzu ba kinga Wardugu yace da shekara d'aya zai d'auke waccen, ya zanyi kenan?" Shiru tayi ta mik'e ta shiga ban d'akinshi ta tsarkake kanta, saida ta fito ta saka kayanta ta nufi k'ofa, cikin sanyayyar murya yace " *Fatoom*." Juyowa tayi da murmushin yanda a kullum yake canza mata suna ta kalleshi, cikin so da k'auna yace "Na baki kaina da zuciyata, ki jani a hankali kar na yi garari a cikin gari, dan Allah?" Dariya tayi tare da mi shi gwalo tace "Sai naja." Da sauri ta fita tana rufo k'ofar, shi ma dariya yayi yana girgiza kai ya lumshe ido, a nutse bacci ya d'aukeshi mai dad'in gaske daya jima bai samu irinshi ba. *Bayan shekara biyar* Bata ankara ba taji ya jawota ya zaunar akan cinyarshi yana fad'in "To yanzu fad'a min ina jinka." Da sauri ta kalli tablet d'in dake gabanshi, zunbur tayi zata tashi tsaye ya sake rik'eta, rufe ido tayi alamar kunya hakan yasa Agaishat da ita ma aka tilasta mata zama a k'fafun tace "Trozzo, idan ma zaki bud'e idonki ki bud'e ne, yau fits..." Sai kuma tayi shiru abin ta, kallonta Wardugu yayi yace "Fitsararru?" Girgiza kai tayi tace "A'a, ban fad'a ba." Kallon Hasheer yayi yace "Yanzu dan kaga nayi shine kai ma sai kayi? Baka tsoron daga haka tsarki ya kama ka?" Duk sunkuyar da kansu sukayi sai Hasheer daya tab'e baki yace "To sai me? A gidana nake ai, ba gidanka ba, kai daga nan nasan tsiyar da kake yi." Dariya Wardugu yayi yace "Ni ustaz d'in? Bana komai ni tambayeta ka ji." Faduma da kanta ke k'asa ne tace "Dan Allah tunda hirar manya ce kuke yi kunga mu yara bata shafemu ba, ka barni naje na k'arasa kimtsa gidana." Da sauri Agaishat tace "Wallahi nima haka." Wardugu ne ya kalleta yace "Kenan mu tsofaffi ne?" Da sauri ta d'aga kai ta kalli wayar tace "A'a ko kad'an, shi nake nufi." Kallonta yayi tare da mintsininta a ciki yace "Ni kika raina kenan da kika ga gadon bacci na?" Zabura tayi ta girgiza kai tace "A'a." Agaishat ce tace "K'awata, dan Allah yaushe zaki zo?" Yanda kan ta ke sunkuye matuk'ar kunya take ji ta kalli wayar, tana jin kunyar Wardugu sosai da mugun kwarjini, ganin ba ta d'aga kanta kawai ya sake tsamukinta a ciki, ba shiri ta zabura tana kallon tablet d'in tace "Gobe." Da sauri tace "Gobe? Da gaske za ki zo gobe?" Kallon Hasheer tayi da yayi kamar bai ji ta ba, a sanyaye tace "Mijin Batul ka fad'a mata mana." Kallonta yayi da alamar rashin fahimta yace "Me fa?" Ajiyar zuciya ta sauke dan ta lura dai baya so ta je inda d'anta yake shi ma kuma ya hana ya zo inda suke, dan ya cika alk'awarin nan da ya d'auka ma Wardugu, tuni shi ma Wardugu yake tsaye a kan Aba wanda suke shirin turashi makarantar sojoji ta yara, sa'arta d'aya yanzu tana da *Rayyadun* da kuma *Affan*. Kallon Agaishat yayi yace "Za ta zo, zan kawota da kaina." A hankali tace "Allah ya kawoku lafiya." Wardugu ne yace "Kafin ku je mu zamu zo." Farin ciki Agaishat ta fara hakan yasa Hasheer cewa "To zamu rigaku." Marairaicewa tayi ta kalli Faduma tace "Faduma ki masa magana kar ya taho, tunda muke bai tab'a cewa zai kaini ba sai yau, kar ya min asarar zuwa garinki mana." Hararenta yayi yace "To da kika fad'a mata ita ta isa ta sani ne? An fad'a miki tsoronta nake ji?" Kallonshi duk sukayi a wayar har ita ma, had'e fuska yayi ya kalli Wardugu yace "K'arya na fad'a War?" Girgiza kai yayi shi ma yana sake tamke fuska yace "To me aka isa a mana dama?" Kallonshi Agaishat tayi tare da mik'ewa kan k'afafunshi ta kalli Hasheer tace "Dan ina ganin girmanka ne Elhaj." Kallon Wardugu ta sake yi tace "Uhummm!" Juyawa tayi ta shige d'akinta, Faduma na ganin haka dama ta gaji da zama, mik'ewa tayi ita ma ta kalleshi tare da hararenshi ta juya baki, kallon tablet d'in tayi tace "Yallab'ai dan ina jin kunyarka ne." Sake kallon Hasheer tayi tace "Hummm!" Saida suka ga shigewarsu sai kuma suka kalli juna, wani basaraken murmushi Wardugu ya shinfid'a a fuska yace "Yaran nan." Tarrr suka kalli juna da Hasheer kamar suna karanta zuk'atansu, a tare kamar yanda yawancin lokuta sukan had'a baki suka ce "Saida safe." Saida kowa ya mik'e yana d'aukar tablet d'in shi kafin Hasheer yace "Na tafi rarrashi." Wani murmushi ya kuma saki yace "Auren batuba kenan." Hararanshi yayi yace "Ko kuma auren buzuwa ba." A tare suka sakarwa kansu murmushi tare da yanke kiran kowa ya nufi d'akin yarinyarshi dan zazzage mata rashin kunya domin su basu damar morar tasu k'uruciyar su ma. *Washe gari* cikin farin ciki ta tashi tayi duk abinda ta saba ya zamar mata jiki, yau dake lahadi Hasheer ma bai fita yana gida, yaran kuma duk sun tafi islamiyya sai Saudat da Faduma zaune suna ta hirarsu abun sha'awa, dan dama ko ka samu matsala da miji kana b'oyewa a irin wannan ranar har sanda zaku shirya. Kamar daga sama aka banko k'ofar d'akin aka shigo da k'arfi har suka juya dan ganin waye, da sauri ta mik'e saboda fad'uwa da gabanta ya shiga yi na ganin yanayinshi, kayan makaranta ne a jikinshi idonshi jajir alamar b'acin ran nan da bata son gani a gareshi, gadan-gadan ya tunkarota wanda hakan yasa jin tsoron d'an nata kamar ba daga cikinta ya fito ba, baya ta ja tana sake kallon yanayinshi, cak ta tsaya sanda ya kawo gabanta shi ma ya tsaya suna kallon kallo, a razane take kallon wannan yaron nata d'an shekara tara wanda a yanzu yake da sha hud'u a duniya, tsayinsa da girman jikin duk na ubanshi ne, hakan yasa duk tsayinta a yanzu sai suka tsaya kai da kai suna kallon juna. Hasheer da Saudat kam 'yan kallo suka zama suna mamaki, yaron dake shigowa da sallama ya gaishesu da girmamawa, har gidan nan yake kwana tare da yaransu, yau shi ne ya shigo musu haka kamar an koroshi. Suna cikin tunanin nan tambayarshi ta dawo dasu hayyacinsu sanda ya d'aga labb'enshi cikin tsananin firgici da jimami da kuka yace " *Ayya, da gaske ni shege ne, ba da aure kika haifeni ba*?" Da wani irin k'arfi ta rufe bakinta ta zazzaro idonta, d'aya hannunta kuma cikinta ta rik'e da taji gaba d'aya saida kayan cikinta sukayi sama kafin suka fad'o k'asa a hargitse, Hasheer da Saudat ma mik'ewa sukayi, Saudat kam tausayin Faduma ne ya ziyarceta a lokacin, Hasheer kuma bayan tausayi da mamakin a ina kuma Amjad ya jiyo haka? Saida wani azababbe kuma fitinannen kishi ya taso mi shi, dan gaskiya maganar nan tana tayar masa da hankali fiye da tunanin mai tunani, yana jin haushi ya ji komai ya tsaya masa kamar an dakatar da rayuwarshi. Komawa yayi ya zauna yana dafe kan shi da yaji ya sara masa. Cikin tashin hankali ya zube gwiwoyinshi k'asa yana kuka sosai ya rik'o hannun Faduma yace "Ayya dan Allah ki amsa min, da gaske ne ko kuma k'arya ce aka fad'a min, Ayya kinga dai ban tab'a tambayar me ya faru tsakaninki da Aba na ba, yau dai ina so ki fad'a min gaskiya karki b'oye min komai, ni dai a sani na Abana ya fad'a min kun rabu ne saboda zai mi ki kishiya." (Illar yi ma yaro k'arya kenan, har abada zai rik'e abun yana kuma kallonka da shi.) A gigice ta d'auke hannunta daga bakinta ta sake ja baya, cikin kuka kamar zata shid'e tace "Amjad wa ya fad'a maka maganar nan? Me yasa baka tambayi Abanka ba?" Mik'ewa yayi da sauri ya sake matsawa kusanta yace "Ayya Abana sam baya so ina mishi maganarki, kuma ke kika koya min fad'ar gaskiya komai d'acinta, shiyasa nake so ki fad'a min gaskiya da kanki." Fashewa ta sake yi da kuka tace "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, Amjad ba zan iya ba, ka je ka tambayeshi." Cikin d'aga murya yace "Ayya ke zaki fad'a min, ni kawai ki fad'a min komai Ayya, idan ba haka ba babu inda zan je." Satar kallon Hasheer tayi, tsaf ta karance yanayinshi me yake koyar da ita, tafi kowa saninshi a kan kishi, kallon Amjad tayi tace "Amjad gida, zamuyi magana anjima." Cikin tsawa kamar ya manta a gaban wa yake yace "Ni kawai ki fad'a min waye ni? Ko kuma dai shegen ne da gaske kamar yanda aka fad'a?" Kama hannunshi tayi da niyyar barin d'akin, amma sai ya mata irin tsayuwar nan ta gagara da kafuwa da zuciya, dole ta sakeshi ta zube gwiwoyinta a wurin ta fashe da matsanancin kuka, tsaye yake k'yam yana kallonta, ita ma kuma bata ce mi shi komai ba har suka jima a haka, sake durk'usawa yayi yace "Kenan Ayya da gaske ne? Shege ne ni? Ayya ba da aure kika haife ni ba dama?" K'arasa yin zaune yayi ya fashe da kuka sosai yana girgiza kai yana fad'in "A kullum idan ana bayar da kyakyawan misali, ni da uwata nake bayarwa saboda a wajena ita ce tsarkakakkiya, idan ana maganar nagarta a idona mahaifiyata ce nagartacciyar baiwa, a wajena babu mai cikar kamalar da ta kai Ayyata. Ashe ban sani ba na yi wa ayyata laifin da har ta hukuntani ta hanyar samar da ni ba ta ingatacciyar hanya ba, ayya me yasa? Me na miki? Dukanki yaranki kin haifesu da aure, sai ni kawai kika ware kika mik'ani hannun ubana, Ayya kinsan me hakan yake nufi kuwa? *Ni*, *zuri'ata* duk zamu kasance a knask'ance, a wulak'ance saboda wannan tabon, ayya me yasa kika kasa min gatan da kika wa sauran 'yan uwana?" _Ko dan kaucewa wannan tambayar daga bakin 'ya'yan da muka haifa, yana da kyau mu k'ara tsare mutumcin kawunanmu 'yan uwa mata, ba zaka fahimci girman tambayar ba sai ka haihu. Allah ya karemu da zuri'armu._ Cikin tsananin kuka Faduma ta dinga girgiza mi shi kai ta rik'o hannayenshi da k'yar kanta a k'asa tana mai jin kunyar kallonshi tace "Amjad kayi hak'uri, na sani dama komai daren d'ad'ewa wannan ranar zata zo, hakan yasa duk sanda na tuna na kan sake shiga tashin hankali fiye da ranar da nasan ina d'auke da cikinka, wallahi ba laifina bane, Amjad kuskure ne da kuma k'addara, ko kad'an banyi gaggawa a cikin lamarinka ba, kuma ba'a son raina haka ta faru ba nima bani da yanda zanyi ne, ka yafe min kaji Amjad kar kayi hushi dani, kuma idan ba ka yarda ba ka tambayi mahaifinka zai fad'a maka gaskiya, duk da shi ma ba'a son ranshi bane haka ta faru, daga ni har shi babu wanda ya tab'a aikata haka da gangan, Amjad ka yafe mana kaji, kar ka k'ullaceni dan Allah ni mahaifiyarka ce." Tsagaitawa yayi da kukan tare da mik'ewa yana jan majina yace "K'addara Ayya? Wace irin k'addara?" Mik'ewa tayi jikinta na rawa ta sake rik'o hannunshi tace "Amjad ka yafe mana kaji, idan baka yarda dani ba ka samu mahifinka ka tambayeshi zai fad'a maka, amma dan Allah kar ka mishi magana cikin b'acin ran nan ko da rashin ladabi, hakan zai sa kuyi fad'a dan shi la zuciya ce da shi kaji." Girgiza kai yayi zai fita ta rik'eshi gam, juyowa yayi ya kalleta hakan yasa ta marairaicewa tana sako hawaye tace "Hushi kake dani? Ba zaka yafe min ba?" Girgiza kai yayi tace "Ayya ke fa kika haifeni, kuma kin bani ilimin daya koyar dani girmama mahaifiya da d'aukarta da mad'aukakiyar daraja, ni kuma me zai sa na yi hushi dani? Kamar dai ba mai neman albarka ba." Da k'yar ta k'ak'aro murmushi tace "Da gaske?" D'aga mata kai yayi alamar eh, jinjina kai tayi tace "To ka tafi gida, dan Allah ka sassautawa kan ka kaji." Jinjina kai yayi yana sake share hawayen fuskarshi, sakin hannunshi tayi tana kallo harya fita yana share hawaye a fuskarshi. Saida ta ga b'acewarshi sai kawai ita ma ta fita da sauri ta nufi b'angarenta tana wani sabon kukan. ________________ Bai zame ko ina ba sai gidan, a farfajiyar ya aje gallelen babur d'in da Tagur ya siya masa ya tunkari b'angarensu, Khairat ya ci karo da ita ta fito daga falon wacce take yawan fama da ciwon athim, bai yarda ya had'a ido da ita ba sai ita data shiga k'ok'arin lek'a fuskarshi, tsaki yayi ya rab'ata zai wuce ta sake tare gabanshi tace "Yah Amjad ko kallona ba zaka yi ba? Wani ne ya tab'oka a waje halan?" Cikin dakusashiyar murya yace "Kauce min a hanya Khairat." Mak'ale kafad'a tayi tace "Um um, saika kalleni." A zabure ya d'ago kanshi yana daka mata tsawa da fad'in "Ki kauce min na ce ko?" Cikin tsoro ta kauce da sauri shi kuma ya wuce tare da jan tsaki, da kallo ta bishi ta tab'e baki tace "Ban yafewa duk wanda ya b'ata min ranka ba wallahi." Yana shiga Husna kawai ya samu zaune irin zaman nan na kana jiran wani y'a shigo da farin ciki fal a fuskarta, tana juyowa suka had'a ido ta mik'e da gudu ta rik'o hannayenshi da murna tana fad'in "Amjad albishirinka?" Ba fara'a a tare dashi yace "Goro." Da zumud'i tace "Fari ko ja?" Saida y'a sauke numfashin k'osawa yace "Fari." Sakin hannayenshi tayi ta nuna mishi takarden hannunta tace "Na dawo daga asibiti, kuma an tabbatar mun ina da juna biyu." Baisan sanda dariya ta sub'uce masa ba saboda har zuciyarshi ya ji farin cikin abun, dan Husna tamkar uwa yake kallonta ita ma, tun yara k'arami take fad'a mishi ya tayata da addu'a Allah ya bata haihuwa, yau kam gashi ta tabbata, sai ya manta da b'acin ranshi kawai ya kalleta yace "Ayya ina Aba?" Da zumud'i tace "Ni ma shi nake jira, na fi so sai ya shigo zan fad'a masa." Jinjina kai yayi yace "Allah ya fito min da sabon k'anena lafiya." Da 'yar dariya tace "Ameen." Dafa kafad'arshi tayi tace "Yanzu ka shiga ciki kayi wanka saika sauko ka ci abinci." Lumshe ido kawai yayi alamar to ya shige ciki, kayanshi ya cire ya shiga wanka, yanda ruwan masu sanyi ke sauka jikinshi haka yaji wata nutsuwa na zuwa masa a hankali, a take ya sakawa zuciyarsa salama tare da sake d'amarar kyautatawa mahaifiyarsa, ba dan komai ba saidan a shekarun nan na shi ya ci karo da abubuwan al'ajabi kala kala, hakan yasa yaji cewa lallai mahaifiyarshi a haka ma *gata* ta masa da ba ta zubar da cikinshi ba, ko kuma ta jefar bayan ta haifeshi, ko kuma dai ta kasheshi da kan ta, a yanzu kuma ya fahimci dalilin da yasa mahaifinshi ya mishi waccen k'arya, akwai lokacin da shekarunka basa d'aukar wani tunanin na ka, daya fad'a masa a waccen lokacin zai iya tashi da damuwar hakan da k'unci da rashin walwala, zai rasa sukuni a cikin yara har ya dinga kallon kanshi kamar daban yake dasu. Amma a shekarun shi na yanzu zai nemi taimakon Allah ya dafa masa wajen d'aukar wannan k'addarar tasa da hannaye biyu ya rumgume a barsa, yasan ba zai rasa kyakyawan rayuwa ba, yana da uwa da uba, yana da kakanni a raye, alhamdulillah mahaifinshi na d'orashi kan harkoki da dama bayan tarin kud'ad'e da kadarar daya mallaka mi shi, sannan ga kyakyawar *kanwarshi Khairat* dake nuna mishi k'auna a fili da bad'ini, tana nuna idan ba dashi ba kamar zata iya hek'awa.馃榿 *Oga Hasheeru* A wajenshi kuma... *Alhamdulillah* 03/06/2021 脿 21:44 - Kwate: 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *ALLURA* _(Ta tono Galma)_ 馃懇鈥嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈煈┾€嶁潳锔忊€嶐煈� *LABARI* _SAMIRA HAROUNA_ *Jinjina gareki* _HAKEEMA (MOM TEEMA)_ *SADAUKARWA GA* _*SAJIDA*(Bab)_ _*Maman Noor & Teema*_ _*RAHIMA* (Princess)_ _*FATIMA* (Kakale)_ _*Hassan Mahaman Nagodi*(Famille)_ 馃挮鉁� *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*馃専 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_馃 鈽� *[ T.M.N.A]* 鈽� 馃摉馃枈锔� https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ _80_ *K'arshe* 馃敋馃敋馃敋馃敋馃敋馃敋 Bata tab'a tsammanin sanyi dage gareshi ba, amma yana shigowa saiya shiga rarrashinta da nuna mata tayi hak'uri, hakan ya sanyaya mata zuciyarta sosai data samu madafar data fake a ciki, hakan yasa yana fita ta d'auki wayarta ta sake kiran Amjad, dan tana tsoron abin da zai faru irin b'acin ran nan data gani a tare dashi, a lokacin ya fito daga wanka ya d'aga yana sallama, amsawa tayi tare da fad'in "Amjad kana lafiya? Ina fata dai babu abin da ke faruwa?" Ajiyar zuciya ya sauke yace "Ayya komai lafiya, babu abin da ke faruwa." Cikin rashin yarda tace "Ka tabbatar?" Cike da tabbaci yace "Na tabbatar Ayya, da na zo ma ban samu Aba a gida ba, sai Ayya da ta min albishirin zan samu wani k'ane." Ajyar zuciya ta sauke tace "Kai amma na ji dad'i sosai, ka ce ina mata murna." A hankali yace "Zan fad'a mata." Ita ma cikin rad'a tace "Amjad, wa ya fad'a maka maganar nan? Fad'a kayi da wani aka maka gori?" Saida ya zauna bakin gado yana sauke numfashi yace "A'a Ayya, ban yi fad'a da kowa ba, zan taho gida ne dai na had'u da dada Gomboy, ita ce ta sanar dani komai." A sanyaye ta maimaita da "Gomboy?" "Eh, ita dai Ayya, ban san me yasa bata so na ba? Ta tsaneni gaba d'aya." Ya fad'a shafar sumar kan shi, cikin rarrashi tace "Tunda ka fahimci haka sai ka san irin zaman da zakayi da ita a gidan nan." A hankali yace "Insha'Allahu Ayya." Murmushi tayi kamar tana gabanshi tace "Sai anjima." Shi ma murmushin yayi yace "Sai anjima Ayya." Da haka suka gama wayar, d'akin Hasheer ta shiga ta sameshi zaune dafe da kan shi, dan sosai ya danni zuciyarshi yayi k'arfin halin sakata murmishi, amma har yanzu wasu kamalai na mishi yawo a kai, *shi ma ba'a son ranshi bane! Daga ni har shi babu wanda ya tab'a aikata haka da gangan!*, d'agowa yayi yana kallonta har ta k'araso, kama hannunshi tayi ya mik'e tsaye tana fad'in "Mijin Batul hushi yake dani ne?" A hankali ya girgiza mata kai alamar a'a, murmushi tayi tace "To a min dariya mana." Kanne mata ido d'aya yayi yace "Nawa za ki biya?" _(Aminoi 2 kenan)_ Lumshe ido tayi ta d'aga k'afafunta dan ta kamo tsayinsa ta mik'a mishi bakinta tace "Sumbace ni to." Dariya yayi tare da d'aukarta yana juyawa da ita, hakan yasa kaso mafi girma na damuwarshi ya tafiyarshi, fad'awa yayi da ita kan gadon yana fad'in "Zan iya baki abinci?" Saida tayi kamar tana tunani tace "Ina jin zaka iya." Dungure mata kai yayi yace "Matar Hasheer kenan, matar da babu irinta a duniya." Tallabo fuskarshi tayi suna kallon juna tace "Ina son ka mijin Batul, ina k'aunarka, ka sauya min rayuwata daga k'unci zuwa farin ciki, Allah ya vani ikon faranta maka rai har k'arshen rayuwata." Had'a goshinsu yayi wuri d'aya yace "Kin riga da kin gama faranta min rai *Radiya*, saidai fatan mu kasance a haka har abada kawai." Sumbatar junansu suka shiga yi a tsanake cikin so da k'auna, sun d'auki lokaci mai tsayi dan har akayi sallah zuhur basu duniyar mutane, sai daga baya suka yi wanka suka rama sallah a tare kafin su fito suka nufi falon Saudat, sun sameta da yaran sun dawo sun ci abinci, wayar Faduma ce tayi k'ara alamar kira, tana d'auka ta d'an yi shiru kafin tace "Ka tabbatar?" Jinjina kai tayi ta kashe kiran, kallon Hasheer tayi tace "Mijin Batul muje mu dawo mana." Hararanta yayi yace "Ina kuma? Ke ni babu inda zan tafi dake, muna fita kina zubar min da mutumci a idon abokaina." Baki ta saki ta kalli Saudat ta kalleshi tace "Yanzu kishin naka ne zubar da mutumci, wallahi zan fad'awa aunty abin da ya faru." Murmushi yayi ba tare da kunyar yaran ba ya kamo hannunta ya d'ora kanta a k'irjinshi yana shafawa yace "Haba matar Hasheer, yi shiru mana ba sa茂 kin fad'a ba." Saudat ce tayi dariya tace "Halan wani abun ka yi a waje? Yer uwa zo fad'a min naji." Cikin dariya Faduma tace "Aunty bari har ya fita zan fad'a miki." D'an tsamukarta yayi a baya hakan yasa ta yin zullo tana sakin k'ara, yaran ne suka kwashe da dariya sai Izzadeen da yace "Dan Allah Abba ka sakar mana uwa hakanan." Dak'uwa ya mishi yace "Kasan me take shirin janyo min kuwa?" Daddagewa tayi ta gartsa masa cizo a k'irji a dole ya saketa yana dafe gurin yana binta da kallon mamaki yace "Lahhh! Haka kike dama?" Saida ta gyara zaman lafayarta tace "Ko fad'a za ayi ai ba za'a fi k'arfinmu ba tunda muna da hak'ora." Saudat ce tace "Da farata ba." Girgiza kai yayi yace "Fad'an mayu kenan." Dariya sukayi daga d'an ne sa ta sake cewa "Mijin Batul muje mana, Allah wani abu ya faru zan nuna maka." Da kallon shegantaka ya bita yace "Akwai citta a lamarin?" Jinjina kai tayi tace "Har da yaji." Da ido ya mata alamar "Muje to." Murmushi tayi ta bi bayanshi tana fad'in "Aunty sai mun dawo." Daga Saudat har yaran da"A dawo lafiya." Suka bisu, a hanya kam fira suke ta soyayya da kauna da raha har suka isa wani gidan gona dake daf da shiga goulbi maradi, a bakin k'ofar suka tsaya suka sauka, mai kula da wurin suka saamu bayan sun gaisa Faduma tace "Ai Alhaji yana ciki?" Da fara'a yace "Eh yana ciki, ku wuce." Ya fad'a yana kauce musu a hanya, hannun Hasheer ta kama suka shiga ciki, wurin yalwace yake da bishiyoyin mangoro da lemun tsami da goba, a k'ark'ashin wata inuwar suka hangesu zaune, murmushi ta saki suka k'arasa suna k'are musu kallo. "Assalama alaikum." Sallamarsu tasa duk suka zabura tare da mik'ewa tsaye, waro ido yayi yace "Ke me ya kawoku nan? Hasheer dama ka san da gidan gonar nan ne?" Tab'e baki yayi yana k'arewa su Hindu kallo yace "Da na sani ai da tuni nayi wani abu a kai." Gomboy ce ta gyara kallabinta tace "Faduma me ya kawoki nan?" Ita ma tab'e bakin tayi ta kallesu dukansu kafin tace "Na fita a rayuwarku Gomboy, kuma na so komai ya tsaya daga nan, sai dai bansan me yasa kuke ci gaba da bibiya ta ba, kun dage sosai na son ganin bayan farin cikina da ahalina, shiyasa na zo dan na tambayeku wani abu." Cike da izgilanci Hindu tace "Tambaya kuma? Tambayar ce har sai kin zo nan zaki mana ita!" A tsatsaye ta kalleta tace "Saboda mahimmancinta ne." Sake k'are musu kallo tayi tace "Wai baku da aikin yi ne da za ku yi bayan saka min ido? Ko kuma babu wani abu daya muku saura ne a rayuwarku daya wuce bibiyar farin ciki na? Da k'ok'arin da kuke na ganin kun ruguzani, me zai hana ku mayar da hankulanku wajen d'aukar maganin rashin lafiyarku tun kafin tafi k'arfinku?" Kallon kallo suka shiga yi musamman Alhaji Saddi daya fara rarraba ido, Zaliha ce tace "Magani kuma? Wace irin rashin lafiya aka fad'a miki muna fama da ita?" Wani malalacin murmushi tayi tace "Kuna nufin bai sanar daku ba? Ai kam bai kyauta ba." Kallon Saddi tayi tace "Kawu, shin na fad'a musu ne yanzu ko kuma na bari zaka fad'a musu? Kaga yanzu sai muje gida mu fad'awa matan naka na gida dan suma su fara d'aukar nasu magani." Da sauri ya matso gabanta yace "A'a! A'a dan Allah, karki je, zan fad'a musu, kar ki fad'a dan Allah kiyi hakuri." Had'e fuska tayi ta d'auke kanta daga kanshi ta kalli Gomboy dake kallon Zaliha tana tambayar ko lafiya? Cikin gargad'i tace "Da tsayawa fad'awa yarona hanyar dana sameshi, me yasa baki mayar da hankalinki wajen ganin kud'ad'enki sun fito wanda kika ba wa *Tassi'u* ya saro miki kaya daga Cotonou ba? Kinsan waye shi? Kinsan a uk'ubar da yake ciki wacce har tasa Allah ya d'orashi a kan ki ya wawuri kud'inki yayi gaba?" Murmushi tayi tace "Idan na canka daidai sai dai nace miki ki hak'ura kawai, dan kin tabka asara babba." Nunata tayi da yatsa tace "Izuwa yanzu nasan taki ta k'are dan kin rasa komai da kike da shi, abu d'aya ya rage miki a yanzu shi ne *d'an uwanki Tagur*, ki nemi gafararsa ki so shi tsakani da Allah, ki daina yunk'urin ganin bayanshi da zuri'arshi, dan yanzu shine kawai madafar daya rage miki, babban abinda kike hassada dashi bai wuce kyaututtukan da mahaifinku ya dinga mishi ba sanda yake raye, Gomboy ko a yanzu da za'ayi lissafin abinda Tagur ya dinga miki ke da 'yan uwanki na tabbata ya kashe fiye da abinda ya mallaka a wajen mahaifinku, cin ku, shan ku, muhalinku da suturarku, kud'in kashewa shi kike tarawa hannu, shin wannan da yake miki *ubanki ne shi* ko tsoronki yake ji?" Girgiza kai tayi ta sauke numfashi tace "A yanda na samu labari har yan uwanki dake aure har yanzu yana d'awainiya da su, ko haihuwa d'aya daga ciki tayi abinda uba ke yi wa 'yarsa na al'ada ku Tagur ne yake yin shi, amma kuma wnnan bai isa ya siya mishi soyayyarku ba, idan aka cire Aisho dukanku kuna son ganin ci bayanshi ne, a yanzu da kika rasa na ki Gomboy waye zai miki? 'Yan uwanki da kuke matuk'ar kishi junanku da jin haushin kawunanku? Ko kuma banzayen samarinki ne zasu tsaya a kan ki har k'arshen rayuwarki? Ko kuma dai bara zaki shiga yi bakin titi?" Murmushi tayi tace "Idan har lissafina yayi daidai, Tagur ne yanzu ma gatanki, kuma ki sani Amjad d'in da b芒 kya so shi ma wata rana zai taimaka miki inhar ba mijin aure kika samu ba." Kallon Hasheer tayi ta kalli Saddi tace "Babu abinda rayuwar nan zata anfaneka da shi, a labari an fad'a miki Alhaji ya mutu da bak'in cikinka, a gaban idona Hajia ma harta mutu bata kula ka, wace irin rayuwa ce ka saka kanka haka? Ya kake so 'ya'yan daka ha茂fa su ji tausayinka? Ko dan wannan ya kamata ka gyara." Kama hannun Hasheer tayi dake hararen Saddi suka juya zasu tafi, k'asa da sama ya kalleshi yace "Wallahi ba dan k'yamarka da nake ba da saina sharara maka mari, dan ubana ma da bak'in cikin halinka ya mutu." Wucewa sukayi cikin takon nutsuwa su kuma suka bisu da kallo jiki a sanyaye, saida suka ga fitarsu suka fara tuhumar kawunansu musamman Saddi, nan fa asiri ya tonu cewa yana mu'amula da dukansu a b'oye ne, hakan yasa Zaliha yi mishi hauka harta rotsa mishi kai tana fad'in "Dama shi yasa kullum kake min hanya hanya a kan aurenmu, har zaman yari kayi amma na jiraka ashe iskanci kake da k'awayena, Allah ya tsine maka albarka shege tsinannen haihuwa." Da haka fa suka kusa kashe kawunansu a wurin saidai tashin hankalin Gomboy yafi na kowa, dan ita harda kud'in da take da tabbaci ta rasa kenan, dan Faduma ba zata fad'a mata magana babu cikakkiyar hujja ba, hakan yasa ta d'auki hanyar gida da tunanin durk'usawa ta bawa Tagur hak'uri da Hatimi kai har Amjad ma. Faduma kuma suna shiga mota sai suka tintsire da dariya, hannu ya bata suka tapa yana fad'in "Lauyata, yaushe zaki koma bakin aiki?" Turo baki tayi tace "Bayan kuma ka hanani, kullum hanya hanya kake min." Jawota yayi suna kallon juna yace "Yanzu ba gashi mun zo aikin ba, duk da baki saka bak'ar rigar nan amma kina yaji 'yan matana." Dariya suka bushe da ita inda ta kashe mishi ido tace "Ai kaine silar bud'ewar k'wak'walwar." Girgiza kai yayi yace "Da abarki na ganki dama." Cikin kunne ta rad'a mishi "Amma yanzu tafi kaifi tunda ta samu tatacciyar madarar jan balaraben *Yar ma'aiki.*" Jan hancinta yayi yace "Ke ko, ko dai sunan kakanki ne dani?" Saida ta waina idonta tace "Zan binciki tarihina har zuwa kakana na ashirin, ba za'a rasa samun mai sunan *Hasheeru* b芒." Dariya ya mata mai kyan gaske yace "Idan kika samo sunan ki fad'a min zan biya da abu mafi daraja." "Kamare fa?" Ta tambaya tana kafeshi da ido, cikin zolaya yace "Kamar na galla miki mari." Zaro ido tayi tace "Lahhhh." Sai kuma ta rufe bakinta tace "Ko dai ni d'in sunar kakar ne ban sani ba?" Saida ya sumbaci kumcinta yace "Zan waiwayi tarihina zuwa kakani na na asirin, da k'yar na tsalleka ban samu mai sunan *Bintu* ba." Cakulkuli ta masa hakan yasa shi sakinta ya gyara zamanshi, tayar da motar yayi suka d'auki hanya, gidan Umma suka tsaya dan gaisheta, abun farin ciki kuma shine samun su Meena da Salima da kuma Halima sun zo ganin mahaifiyarsu, kowace kam da yaranta hakan yasa gidan kaurewa da hayaniya wanda a da baka jin haka, ta so ya barta amma yace sam su koma gida a ci gaba da bayar da himma, dan yana sha'awar ganinta da sabon ciki. ________________ Saida Gomboy tayi kamun k'afa da Aisho wacce ta auri abokin Tagur kafin Hatimi ta saurareta, shi ma Tagur da k'yar ya yafe mata kafin aka ci gaba da rayuwa, a wata safiya kuma sai ga babban bak'o *Aji*. Da k'yar Tagur ya gane shi saboda muguwar ramar da yayi ga bak'i kamar zunubi, idonshi kawai kake gani da dogon wuya uwa na barewa, abinda ya tambayeshi shi ne "Tagur dan Allah ina Aisho take da Khairat?" Saida ya gama hararenshi tsaf ya yi k'wafa yace "Tana gidan mijinta." Gaba yayi ya barshi nan bai sake saurarenshi, duk magiyarshi da kukan da yake bai tsaya ba haka yayi gaba dan baya jin zai iya yafe masa kam. Da sauri ta shiga k'ok'arin kwance goyon *Muhsin* d'an Saudat kenan na biyu bayan Sharfudeen tana d'aga murya da fad'in "Abba ka sakeshi, da kai nake magana fa." Da gudu Saudat ta k'arasa ita ma ta rik'eshi tana lallab'a da fad'in "Sake shi yaron kirki, sake shi muje na baka alawa." Faduma na isowa ta fizge hannunshi tana fad'in "Wannan ba gaba yake dake? Sa'anka ne da zaka ci kwalarshi haka?" Kallon Sharfudeen tayi tace "Kai kuma kana tsaye k'anenka zai rik'eka haka dan naman raini, me yasa ba zaka kwad'a mishi mari ba?" Kallonta yayi galala, har ga Allah baya iya ma k'anin nan na shi, kamar mai cin naman dabbobi haka, k'arfi ne da shi kamar shari'a, idan ya shak'eshi sai yaji ya kasa motsawa, shi ya sa shi dai kam baya ma son ya zo gidan hutun nan, dan abu kad'an yake had'asu ya tumurmusheshi. Saudat ce ta kama hannun Abdul Karim tace "To ai kinsan baya fad'a babu dalili, tsokanarshi yayi." Girgiza kai tayi ta juya ta koma d'aki saboda haushi, tunda ya zo hutun nan bacci ma gagararta yake, tunda shi ba makaranta yake zuwa a nan ba, hakan yasa ko yara na mak'wabta suka daina shigowa, ba wai k'eta gareshi ba kawai dai abu kad'an ne ke sa shi ya matseka. In banda girman kai da miskilanci babu abin da ya aje yaron, suna dawowa falon Hasheer dake zaune hankalinshi kwance ya saki murmushi, zaune tayi kusanshi tana d'aukar Muhsin ta kalleshi tace "Dariya ma kake yi? Ba zaka raba su ba kana kallo zasu mayar mana da gida filin yak'i." Gyara zama yayi yace "To ya zan yi?" Da sauri tace "Kawai ka maida shi gidansu, haba yaro sai jaraba." Wani kallo ya watso mata yace "Ban gane ba? Kinsan da idan War ya ji kina fad'in haka idan ya d'auki yaron nan sukayi gaba wallahi sai kin zubar da hawaye kafin ki sake ganinshi." Turo baki tayi gaba sanda Saudat ta shigo rik'e da hannun Abba tace "To ka fad'a masa ya ja masa kunne mana, hutu fa ya zo ba fad'a ba." Saudat ce tace "Amma dai idan ba'a tsokaneshi ba ai ba zaiyi ba ko?" Kallonta tayi tace "Aunty, kina d'aure masa gindi fa." Hasheer ne ya kalli Abba yace "Abbana zo nan." Tahowa yayi cikin takon d'aukar hankali dake yana cikin kaya na fati masu kyau, gasu dumur dumur kuma sak ubanshi Hasheer a kama, yana zuwa ya tsaya gabanshi Hasheer ya kama hannunshi yace "Wa tab'a uban masu gida ne wai?" Kamar wani babban mutum, numfashi ya fara saukewa tare da kallon Faduma, sai kuma ya lumshe ido ya bud'e ya kalli Hasheer, da yatsa ya nuna masa k'ofa alamar Sharfudeen, kafin ya nuna kan shi kamar wani kurma sannan da k'yar ya furta "Wargi yake kawo min." Baki sake Faduma tace "Iyeeeeh! Wato kai ga wanda yafi k'arfin a kawo masa wargi ko?" Dariya Saudat tayi tace "To a kan me za'a kawo masa wargi?" Hasheer kam shafa kan shi yayi yana murmushi y'ace "Shi kuma me yasa zai kawo ma ka wargi? Bai san cewa ko ni dake ubansa taka tsantsan nake ba saboda kai ne ubanmu." Ajiyar zuciya ya sauke cikin murya k'asa k'asa yace "Ka fad'a masa ya daina, ko na karyashi." Dariya sukayi sai Hasheer da yace "Dolenshi ma ya daina, dan ubana ba abokin wasan kowa bane." Saida ya yatsina fuska cikin harshen larabcin daya d'auka ga Hasheer wanda sosai ya basu mamaki yaron yace "Aba, ni ka mayar dani wajen Abana, na fi son zama a can." Zaro ido yayi shi ma da larabci yace "Me yasa Abbana? Wani abu muke ma ka da baka so a nan?" A hankali ya girgiza kai yace "Kawai a nan ba'a koyar da komai, can kuma Abana ya kaimu ana koya mana karat茅 sannan yana koya mana rik'e bindiga." Tsuru suka mishi da ido sai Faduma da a harshen tubanci tace "Shi yasa ka iya salon mugunta ashe, to Allah ya kyauta." Kallonta yayi cikin fitar da kowace kalma a hankali shi ma a harshen tubancin daya koya wajenta da wajen Wardugu yace "Ai yana koya mana yanda zamu kare kanmu ne, Ayya kema zan koya miki." Waro ido tayi tace "Wa? Kai dai kayi, ni me ya had'ani da fad'a." Cikin turo baki Saudat ta jawo hannunshi da harshen french tace "Shi ne koya yake maka yaren da ban iya ba." Murmushi yayi mai ratsa zuciya cikin harshen french yace "Mama, ai duk yaren da zasuyi na iya, ke ma zan koya miki." Shafa kan shi tayi tare da rumgumeshi cike da k'aunar yaron kamar daga cikinta ya fito. *Alhamdulillah* *Alhamdulillah* *Alhamdulillah* _Allah nagode ma ka daka nuna min k'arshen littafin nan lafiya, masoya nagode sosai da goyon bayanku._ _Wanda suka bani gudummuwa ina godiya sosai, Allah ya k'araana k'aunar juna da fahimtar junanmu, Allah ka yafe kuraraina, lada kuma Allah kasa muyi tarayya a cikinta baki d'aya, ma'assalam._ *TAB'A KA LASHE*馃槣 *Ammar & Hamna return* Yanda ta bud'o k'ofar ofishin ne ya saka shi saurin d'aga kan shi, ganinta ya bashi mamaki sosai har yayi k'asa da gilashin fuskarshi dan tabbatarwa, girgiza kai yayi yana kallonta harta zauna kujerar gabanshi, kallon tsaf ya mata da mamakin yau kenan rigima take ji, shi yasa ta fito da gyale da kwalliya a fuska, ba ma wannan ba shi fa bada izinin shi ta fito ba, bai sans zata zo ba sai ganinta yayi. Ture na'urar gabanshi yayi ya d'ora hannayenshi da kyau cikin muryar nan dai ta shak'iyanci yace "Uwata *Hamna* daga ina ake?" Saida ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya ta gyara zama tana kallonshi tarr tace "Daga gida mana, ya aikin?" Jinjina kai yayi yace "To da izinin wa kika fito?" Tab'e baki tayi tace "Labari na samu ka d'auki sababbin ma'aikata a asibitin, kuma an fad'a min duk 'yan mata, kullum sai su ci ado su fesa turare suna shigowa ofishinka suna maka kwarkwasa, shi yasa na zo na ga yanda tsarin ke tafiya." Da wani kallon ya zanyi da ke ya bita? Kallon me kike nufi da ni? K'wafa yayi yace "Kenan ni ne yaronki?" D'auke kai tayi tace "A'a." Jinjina kai ya sake yi yace "Yayi kyau, yanzu tashi ki koma gida, kuma Hamna duk uban daya kalleki ya yaba kwalliyarki Allah ya isa, sannan ki shirya idan na zo zaki fad'a min uban daya baki izinin fita." Mik'ewa tayi ta koma gefe tace "Babu inda zan je fa, *Ammar* na zo kenan sai naga abinda ke faruwa a nan." Jingina yayi a kujerar yace "Hamna ni zaki wa iskanci, shin gantalalle kika d'aukeni ko me? Na fito daga gida na baroki shine ke ma kika fito." Cikin daka tsawa yace "Gidan uban wa kika baro min yarana?" Zabura tayi kamar za tayi kuka tace "Ammar suna gidansu Umma." Mik'ewa yayi ya nufeta yana fad'in "Oho! Har can kika je dama? Ki ce yawon shik'a ne kike? To yanzu ai kin zo ganin me ke faruwa ne ko?" D'aga kai tayi tana k'ara takurewa tana rufe fuskarta, dan mari ne kawai bata so tasha a fuska, jinjina kai yayi ya koma gaban tuburin ya jawo fax d'inshi ya d'auka tare da danna wasu lambobi, ana d'agawa yace "Same ni a office ?" Aje wayar yayi ya kalleta yace "Hamna a gabanki zanyi soyayyar, idan baki hana faruwar hakan ba ke ba uwar *Shureim* ba ce." Jijjiga kanta tayi tace "Ni kuma Ammar in ban ci uwar yarinyar ba ka ce ba sunana Hamna ba." K'wank'wasa k'ofar aka yi yace "Oui." Shigowa tayi matashiya ce kam cikin ado na ban mamaki da k'amshi na fitar hankali, zaune yayi kan kujerarshi ya nuna mata gabanshi yace "Zauna." Saida ta juya ta kalli Hamna data matso gabansu, ita dai tasan matarshi ce bayan haka bata san komai ba, a hankali ta ja kujerar ta zauna tana sunkuyar da kai, dan haka bai tab'a faruwa ba hasalima bai sakar musu fuska, idonshi a kan fuskarta y'a nuna mata Hamna yace "Ke kika ba wa wannan mahaukaciyar damar shigowa nan?" Da sauri ta kalleshi ta kalli Hamna, sai kuma ta girgiza kai tace "Kayi hak'uri yallab'ai, dan na ga..." Sai kuma tayi shiru, a zabure tayo kanta da niyyar shak'arta, da azama ya mik'e ya rik'eta gam a jikinshi, kallon yarinyar yayi yace "Kawo min allurar bacci, na gaya miki bata da hankali." Da sauri ta tashi ta fita, Hamna kam kubcewa take son yi tana fad'in "Ammar ni zaka tozarta a idon yarinya, ni ce mahaukaciyar? Kuma kake fad'a a gabanta?" Cikin rashin damuwa "An fad'a d'in, inba mahaukaciya ba wa zaiyi abinda kika yi? Ke albarkacin uwayenki nake rage miki fa." A hassale tace "Kar ka raga d'in, sake ni Ammar." Shi ma a hassale yace "Ba zan sake ki kija min asarar kayana masu mahimmanci ba." Ba alamar wasa tace "Amma ka daina kula kowa mana sai mu zauna lafiya." A harzuk'e yace "Na k'i d'in, shikenan saina tsaya tare da ke har abada kamar rai, ke wai ko uwa d'aya muka fito ne? Kiyi zuciya ki daina kulani mana." Girgiza kai tayi tace "Ba zan iya ba Ammar, kamar yanda kai ka fara sani na, haka nima ni na fara saninka, zamu tabbata a haka ko baka so." Sama da k'asa ya harareta yace "To sannu uwata *Sa'ada*, umarni ne ko shawara?" Jijjiga ta sake yi tace "Sakeni Ammar." Sake matseta yayi yace "Na k'i d'in, jikanyar Hajia mahaukaciya kawai." Kallon idonshi tayi tace "Amma dai kasan idan ban yi fad'an nan ba zan iya suma ko?" Hararanta yayi yace "Ki sumar mana, uban wa ya hanaki?" Wata uwar k'ara ta saki da gaba d'aya asibitin ta amsa tq tafi luuuuu, har ga Allah ta d'auka zai rik'eta ne,馃ぃ amma abun ka ga hegen mutum kawai ya saketa gaba d'aya ta tafi rikicaaaaa, wata k'arar ta saki dan ta ji zafi sosai a jikinta da ma kanta data bugo, bud'a ido tayi ta kalleshi daga kwance tace "Ammar ashe kai mugu ne? Shi ne ka sake ni na fad'i." Da shak'iyanci yace "Au! Dama b芒 suma kikayi ba? Ai ban sani ba." Da sauri yarinyar ta shigo rik'e da allura ta aje d'an farantin a kan teburinshi ta shiga had'ata cikin k'warewa da rawar jiki, da sauri Hamna ta mik'e tana gyara kallabinta tace "Ke! Kin ga..." Bai bari ta fad'a ba ya sake cakumota jikinshi ya mata wata matsa kamar d'aurin goro ya kalli yarinyar yace "Hanzarta dan Allah." Ai kam da sauri ta nufosu za ta mik'a mishi, cikin salon k'eta ya janye gyaleta hakan ya bayyana damtsenta a fili yace "Yi mata." Cikin billewa Hamna tace "Ammar kar kayi, kar ka min allura bana so." Dafe kanta yayi sosai ya rad'a mata a kunne "Ni na kawoki? Ba zanyi asarar allurar nan ba, gobe ki sake zuwa tayar min da hankali." Sake rik'eta yayi gam yace "Yi mata ke." Matsawa tayi ta samu tattausan damtsenta mai tsokar gaske ta luma allurar ta bultse mata ita, fashewa tayi da kuka sanda zafin ya ratsata tace "Ammar ban yafe ba, ka sani ba zan tab'a barin kowace mace ta rab'eka ba, tunda har yar uwata ta rasu saboda akwai k'addarar aurenka a kai na, wallahi babu wacce ka isa ka kula bayan n..." Langab'ewar da kanta yayi yasa shi sakin murmushi, cimak ya d'auke ta ya shinfid'e kan gadon da yake duba masu jinya, gyara mata gyalenta yayi yana kallon fuskarta, shafa kuncinta yayi yace "Idan dai ba a k'addarata aka rubuta min k'ara aure ba, Hamna ba ke ba kishiya da yardar Allah, amma ba zan fad'a miki haka baki da baki ba, dan buru'ubarki zata fi k'arfi na." ********************** ⬇ ************************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** *A ci gaba???*馃ぃ馃ぃ馃ぃ *sowi* 馃弮鈥嶁檧锔忦煆冣€嶁檧锔忦煆冣€嶁檧锔忦煆冣€嶁檧锔忦煆冣€嶁檧锔忦煆冣€嶁檧锔�