********************** ? ************************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************? ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ? ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ? ************************** [11:03PM, 10/21/2017] Feedohm馃挒: 馃挧馃挧 *ZAN RAYU DAKE..馃尮* 馃尮馃尮馃尮馃尮 馃尮馃尮 馃尮 漏 *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM馃挒_* 1鈨� Gurin dinner ya cika makil da dunbin jamaa kae da gani kasan bikine na masu naira .yan mata top class ke juyi tsakiyar gurin ....yayin da hall din ke fitar da wani azababben kamshi ..Daga gefe kuwa wasu yan mata ne su biyu ko wace zaune take hankalinta naga wayarta kirar Iphone6 sam hankalinsu baga cikin hall din yake ba ... .... Mc ....ya bukaci babbar aminiyar Amarya yar uwa ga amarya ta fito ... Fitowarta tata ita da Aminiyarta ta saka hall din karadewa da ihu tare da sowa .... Tana karbar abun maganar gurin yayi tsittt kamar daukewar ruwan sama ... daga gefe kuwa wasu dandazon samarine ke ihu...banda "Feenah" ...babu abunda suke fada ..... "Sunana Safeenat Khalid Mudassir" .....ta fada kallon kaf mutanen dake cikin hall din ....kafin ta cigaba da fadin ... "Duk cikin ku nan babu shegen da bai san Engineer Khalid Mudassir ba ...! Hall dinne ya sake karadewa da ihun mutane ...tayi tsit ..kafin ta daure fuska tace ... "na dauka bikine na masu naira sai naga abun ya banbanta ga dangin ango ..dan banga alamun akwae arziki a tare da su ba.. kaf dinsu sanye suke da yadin da bai wuce 20 thousand ba ..kuma a haka dan tsabar rainin hankali aka gayyaci Feena? .... Kanwar ango ta taso a fusace da niyar dauketa da mari don ta gama kuluwa da wulakancin ta ..... Aminiyarta dake kusa da ita tayi saurin rike mata hannu tana hararanta ... wani Ja'irin murmushi Feena ta sake kafin ta aika mata da wani irin kallon tana fadin ..."Barta Maryam ...ki bar shegiya ubanta ya mutu yana nadamar haihuwarta ....! Wurgar da ab din tayi sannan tayi gaba abunta ....ishak abokin ango ya tare da murmushi don tunda ta shigo ta tafi da hankalinshi ..... " Excuse me Feenat .!....ya sha gabanta tare da harde hannayensa ... Wani kallo ta zabga mashi kafin tace ..."what " " Just Few mints Swky ...ina son contact dinki please"..ya hade hannayenshi guri guda dauke da murmushi .... itama murmushin ta sake ...tare da zabga mashi mari ...tayi gaba tana fadin ..."take it boy .". Hall din ya dauki ihu .....har ta fice bai saki inda ta mareshi ba ...!!! Bayanshi yaji an dafa tare da fadin ...."Weldon ...maganinka kenan .. banga amfanin kula macen da bata san darajar bil'adam ba ...next time idan zaka kula wata ka fara duba dressing dinta before ..." Bai jira amsar sa ba ya zagayeshi tare da barin hall din... Amarya kam banda hawaye babu abunda take ....tayi nadamar gayyatar Feenah gurin taronta duk da ita ce babbar aminiyarta amma batayi tunanin zata mata haka ba ...ko ba komae ya kamata ta duba alakar dake tsakaninsu ta yan'uwantaka ....... "Excuse me, ko ma ciki inda na zauna zaka ga hanky ka dauko man trappr dinta a kasa" ..ta fada tare da dalloshi da flash din wayarta ... Yarda motarta bata amsa mata ba haka bai ko kalli inda take ba ya saka hannu da niyar bude motar ... Ji yayi ta fizge keys din tare wurgar dashi kasa ...." Har ka isa ina maka magana ka wuceni ...!! Dan gidan uban waye kae ? ..me kake takama dashi ? ... A fizge ya kalleta ya girgiza kai yana murmushi ...ba tare da yace mata komae ba ya dauki keys din ya shige motar ya barta tsaye rike da mamaki ... Har ya tada motar yaji tana fadin "Wawan banza bakauye "... Da sauri ya ja motarshi ya bar gurin gudun matsala ... A falo ta iske grandmah dinta ta wajen dad ...gaidata tayi fuska Murtuk sannan ta bude fridge ta fito da robar swan ta balle marfin tana sha .... "Safeena manya..ke dae haka halinki yake " ...kakar ta fads tare kallonta tana girgiza kai ... Aunty Fati ta fito daga kitchen rike da katon tray a hannunta ta ajiye kusa da kakar tare da tsiyaya mata lemo a cikin cup ta mika mata... Kakar tace "sannu Fatima Allah ya biyaki kinji ko ..Allah ya jikan Habiba ....!! "Ameen" ta fada dauke da fara'a sannan ta kalli feena tana fadin ... "Safeena har an dawo ? Ba tare da ta kalleta ba tace ..."baki so dawowata ba ko ? ..saboda na tsare maki gidan uba ko ? ..ta dago tare da zuba mata ido tana aika mata da kallon da ke kunshe da tsabar raini .. Kakar tace ..".kaniyarki Safeena ashe baki da mutunci ...matar ubanki kike fadawa wannan maganar ....? "Uwata ce ? ....ta fada ta Fada a hasale..... "Ai kanwar uwarki ce mara mutunci ...matar da tun kina cikin tsumma ta raineki?.ta goyaki ...,ta baki abinci ..ta baki tarbiya ...haba safeena ..! "Ince abincin ubana ke kawowa ? ko daga gidan kaka ta zo dashi ? ..ina jin tun da ya hada mata garan biki bai kuma aiko mata da ko tiyar shinkafa ba ? *FEEDOHM馃挒* [11:03PM, 10/21/2017] Feedohm馃挒: [8/24, 8:27 PM] Feedohm馃挒: 馃挧馃挧 *ZAN RAYU DAKE...馃尮* 馃尮馃尮馃尮馃尮 馃尮馃尮 馃尮 漏 *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM馃挒_* *this page goings to ...Fa'izahbarwa, Safiyya galadanci , Meela Adeel & It'z Ruky....Allah ya barku da Lanto mai dinki ....馃槀馃槀馃槀馃槀馃槀馃槀馃槀* 2鈨� Rike baki tayi tana fadin ...Safeena!!! "Kinga grandy ...idan gulma ta kawoki gaskia ki tafi ...abinci dai na ubanane ...Goyo kuma da kike magana ..ta dauko zani taga idan ban goyata ba ...tarbiyya kuma ai ba da kudinta ta biya man kudin islamiyya ba ...!!ta jefar da robar ruwan tare da shigewa daki abunta ... "Uwaki nace ...kaji man ja'iran yarinya to dan ubanki ki zo na balle maki zanina ki goyatan mu gani mara kirki !! Aunty Fati tace..."kiyi hakuri sae dae Allah ya shirya ....!! Kaka ta amsa da "Ameen Fatima kina kokari ..." � Da sauri tayo baya tare da nuna shi da hannu ..."Kaine dan Iskan nan da na aikeka last gurin dinner beebarh kika zuwa ko ? Da mamaki ya kalleta tare da kauda kai gefe guda yaci gaba da tafiyarshi zai shige cikin falon ... "Wane dan iska ne ya bar wannan abun ya shigo nan gidan" ....ta fada cikin tsawa tare da nuna Abdulmaleek da hannu ... Cak ya tsaya tare da juyowa yana kallonta ...kar dae ace wannan yarinyar diyar oga ce ...tab Albasa ba tayi halin ruwa ba ..... Wani yaji yana fada mata ..."wae Alhaji yace a shigo dashi ..". Cigaba yayi da tafiyarshi ya shige falon da sauri ....itama dawowa tayi cikin sauri ta komo cikin gidan ...tana bala'i ita kadae ... A babban falo ya iske Alhajin zaune saman kujera ...har kasa ya zube yana gaidashi cikin girmamawa .... Cikin faraa ya amsa mashi yana fadin ya zauna da kyau ...girgiza kai yayi tare da dukar da kanshi kasa ... "Abdulmaleek"....Alhajin ya kira sunanshi cikin natsuwa .... "Naam .".. "So nake ka baro office ka dawo gidana ...Driver dake kai Safeeena unguwa shine ta kora ..ni kuma bana so na ta dinga fita ita kaidai ...tunda aikin nan da office din duk dayane ...anan ma kafi samun sauki ..tunda akwae boys quarters da zaka zauna wanda zai fi maka sauki ...amma sae kayi hakuri da halinta ..na yaba da hankalinka shi yasa ma na nemoka ...ina fatan ba matsala ....? : Zufa ta fara keto mashi ta ko'ina ...duk da Ac dake gauraye da. Falon ....a iya saninshi sam yarinyar bata da mutunci duk da sau daya ya taba ganinta ....sannan ko kadan baiyi tunanin itace tayi wannan rashin mutuncin ba .....sannan sam albasa batayi halin ruwa ba saboda mahaifinta mutumin kirki ne ...muryar Alhaji ta katse mashi da tunani da yaji yana fadin ... "Kayi Shiru Abdulmaleek ko kafi son zama can ne? Dagowa yayi a wahale yana fadin " Ba matsala Alhaji nagode sosse" ...shi kanshi bai san abunda yake fada ba Cikin jin dadi yace "Ameen Abdulmaleek Allah ya maka albarka yaji kan mahaifinka ..." A hankali Alhajin ya juya ga Safeena dake tsaye bakin kofa tare da mika mata hannu .... Dan takowa tayi har gabanshi ta zauna bisa hannun kujeran da yake zaune ....tana bata fuska *FEEDOHM馃挒* [11:03PM, 10/21/2017] Feedohm馃挒: 馃挧馃挧 *ZAN RAYU DAKE...馃尮* 馃尮馃尮馃尮馃尮 馃尮馃尮 馃尮 漏 *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM馃挒_* *Devoted to Ummi A'isha馃憣馃徎* 3鈨� Hannunta ya kamo yana karantar yanayin fuskarta sannan yace "Safeena ga sabon driver nan kullun zai dinga kaiki inda kike bukata Bana son matsala wannan karan Safeena" "Abbah da wannan abun zanyi yawo?...ta fada a dakile "Kwarae don na gaji da shashancinki Safeena ki kiyaye ni wallahi bara ta yiyu ki dinga wulakanta duk wanda aka kawo aiki karkashinki ba ...AbdulMaleek ba wae yaro kadae na daukeshi ba aa amintaccenane ...!! Mikewa tayi tana bubbuga kafa tare da turo baki .... "Mene matsalar Safeena? ...Abbah ya tambaya tare da mika mata hannu ... "Bana sonshine kawae Abbah last week fa bikin berbah ya raina man hankali ashe ma da motar Abbah na yake tutiya ni dae ...... Katseta yayi yana fadin ..."Wuce Safeenah ..." Da Sauri ta fara hawan stair tana gunguni ....Bakin part dinta tayi karo da Aunty Fatee wani sakaran kallo ta watsa mata tare da shigewa daki abunta .... � Bayan ya bar Gida direct gidansu ya nufa ...Nana kanwarshi ya iske tsakar gida tana wanke wanke .... "Subhanallah Nana waya baki wannan aikin bayan bakya lafiya? ...ya tambaya a rude tare da matsawa kusa da ita ... "Ni ce nan dan Ubanka ko zaka dakeni ne mara mutunci " ....Inna Sahu ta fito daga dakinta tana fada ... "Me ya kawo na duka kuma Inna? Kawae naga bai dace ba tunda bata lafiya a bata aiki irin haka ..Tashi Nana jeki bara na ida kinji ko !! "Da kyau Uwarta to bana son nakan banza na mata" ....ta fada a harzuke tare da matsowa kusa da Nana... Nana tace "Bandee ka barsa na ida kaji ....Allah na warke " A harzuke ya juya zaya fita wayarshi ta dau ringing har ta yanke ba dauka ba ....Sae da ya zauna saman dakalin gidan sannan wayar ta sake kara karo na biyu ....Sunan Oga da ya gani ya sa shi ya dae dae ta natsuwarshi tare da daukar wayar ... Oga yaji yana fadin "Abdulmaleek kana lafiya kuwa tun dazo Safeena ke kiranka kazo ka kaita saloon baka dauka ba ? "Wallahi Alhaji ban lura da kiran bane amma gani nan zuwa " ...ya fada tare da mikewa ... "Ayyah nima abunda na fada mata kenan amma kasan Safeena da rigima " ....Alhajin ya fada a hankali Dan murmushi yayi yana fadin ..."Afuwan Alhaji gani nan a hanya " " Ok" ...ya fada tare da yanke wayar ... Missed call din ya buda a tunaninshi zai ga irin kira uku ko biyu amma sae yaga sau daya ta kirashi shine har ta fadawa Abbanta ...."huh" ...ya fada tare da gyara mirrow din left hand dinshi ....Cikin mintina 10 ya isa gidan ...ga mamakinshi sae ya ganta zaune ita da wani saurayi bisa carpet a harabar gidan don duk tunaninshi zaya iskeshi tana jiranshi amma sai yaga zancenta take hankali kwance ..... Ba wani dalili kawae yaji gabanshi ya fadi ....a sulale ya idasa gurin da suke zaune tare da fadin "Madam gani" a hankali ... Bata kalleshi ba sae dae saurayin ne ya kalleshi ya dauke kai ....yayi tsawon mintina goma kafin ya sake fadin "Madam Gani fa" "Uwar me zan maka ....". ...ta fada a fusace Yaji ciwo amma ya daure tare da dai daita fushinshi yana fadin "Oga yace kina kirana ..Sorry ni sam banga lokacin da kika kira wayata ba " "Dama taya zaka gani? ..Kwalwa ta tunkushe da tuwan dawa !! .. Shiru ya mata ba tare da ya kalleta ba ...saurayin nata yace "Feenah please ki sallameshi ya zo ya mana tsaye a kai ya bata mana iskar guri !! "JB Barsa yayi ta tsayuwa idan ya gaji ya tafi don banga uwar da zai man ba yanzu lokacin da na kirashi ai bai zo ba ...kawae Abbah ya ja man raini !!! A hankali ya ja kafafuwanshi zaya fita ...sae da ya kai bakin kofa yaji tana fadin " Maleek " ... Duk da yana cikin bacin rai hakan bai hanashi jin dadin sunan daga bakinta ba ...cak ya tsaya ba tare da ya juyo ba ... "Ka jira a waje idan na gama zan duba idan da lokaci sae ka kaishi ...." *_FEEDOHM馃挒_* [11:03PM, 10/21/2017] Feedohm馃挒: *ZAN RAYU DAKE...馃尮* 馃尮馃尮馃尮馃尮 馃尮馃尮 馃尮 漏 *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM馃挒_* *Devoted to Ummi A'isha馃憣馃徎* 4鈨� Abdul Maleek bai bar gurin ba sae da aka kira sallar magrib sannan ya mike yayi alwala tare da sallah a masallacin gidan ...yana fitowa masallaci yaga ta fito raka JB dan kallonshi tayi kafin ta kauda kai tana dagawa JB hannu da wani blwng smile a fuskarta ....Sae da yaja motarshi sannan ta juyo gurin Maleek din ta kafa mashi ido .. "Zaman me kake mana anan ? Ba karamin kona mashi rai tambayar tayi ba ya danne tare da fadin "Ke kika ce na jiraki Madam Zan kaiki saloon ko" "Gidan Uwarka zan tafi da darennan ...kai baka da tunani baka san darajar mace ba ? Common dallah matsa na wuce !! Ta fada kamar idanuwanta zasu fito saboda tsabar harara Shiru ya mata tare da matsawa ya bata hanya ...sae da ta kusa shiga gidan sannan ta dan daga murya tana fada "Gobe by 7:30 ina jiranka karka bata man lokaci sannan ba kiranka zanyi ba idan kaso ka kai 3pm baka zo ba Bllshit .....!! Ko saurarenta bai idasa ba ya shige motar ya bar unguwar ....bakin titi yayi parking tare da kwantar da kanshi saman sitiyarin motar zuciyarshi na bugawa da azabar karfi ....kanshi ya dinga bugawa a jikin sitiyarin ko ya samu sauki amma kamar kara watsa mashi gas ake a zuciyar ...... Sae da yaji ana kiran isha'i sannan ya fita daga motar ya gangara masallacin dake kusa yayi sallah ......Gurin mai sayar da abinci ya nufa ya sayi shinkafa da wake da miya take away biyu sannan ya nufi gida ....Garejin da yake aje motar ya kaita sannan ya taka ya shiga shagon da yake kwana ya watsa ruwa tare da sanyo bakar jallabiya ya dauki take away din guda ya nufo gidansu dashi ... Tsakar gidan yayi duhu Nana kadaece a bakin dan karamin iccen magoron dake a gefe ta kudundune sai rawar sanyi take .... "Nana " ...ya fada a rude tare da dagota ya hadeta da jikinshi ..."Menene Nana? ..ya akai kika fito ke kadae tsakar gidan duk wannan uban sanyi ? ...ya fada tare da dago fuskarta ... Kuka ta sake a hankali tare da kwantar da kanta a jikinshi .."Baddee inna tace wae baran kwana ba a dakinta saboda dazu ka mata rashi kunya " ...ta fada cikin kuka Duk ya rude yana bubbuga bayanta ....Bakinciki biyu suka taran mashi ...."To yi Shiru kinji ko ? Kinci abinci ? ...ya tambaya a hankali Girgiza kai tayi tare da dago kanta ... Ba tare da yace mata komae ba ya zaunar da ita bakin dakin Baffa ya bude mata abinci ...da sauri da sauri ta dinga ci kamar wani zai kwace mata sae da ta cinye sannan ya debo mata ruwa a randa ya mika mata ..... "Kin ko shi ko? ...ya fada a hankali ... Daga kai tayi tana sauke ajiyar zuciya .. "Baffa ya dawone? Zata bashi amsa suka ji sallamarshi ....Tare suka amsa mashi sannan nana tayi saurin karbo buhun dake hannunshi ...Fuska sake yace "Nana ba'ayi bacci ba? "Uhmm " ...kawae tace tare da murmushi ...Maleek ma gaisawa sukayi sannan ya masu sae da safe ya tafi ...Baffa ya bude dakinshi suka shiga tare ...dama ya saba indae yaga Nana tsakar gida to a dakinshi zata kwana ranar saboda bakin Halin Inna Sahu ...... Yar katifarshi ya gyara mata yace ta kwanta sannan ya shinfida buhu yayi sallah tare da kwanciya gurin ko kan ta Inna Sahu baibi ba ... 《《》》 Tunda Safe yayi Wanka ya shirya cikin kananan kaya wando blue sae rigarshi red ...duk da kayan ba masu tsada bane amma sunyi bala'in karbarshi dan turarenshi ya shafa mai saukin kudi tare da kamshi maidadi .. Karfe 7:00 ya isa gidan lokacin masu aikin gidan kowa ya kama aikin gabanshi. ...... Har harabar gidan ya shiga da mota sannan ya zauna saman fararar kujeru yana jiranta .... Wajen karfe 8:15am ta fito sanye da kayan sport zata shiga gym dake kusa da garden din gidan .... Cikin mamaki ya bita da kallo kafin ya mike tsaye ya bi bayanta .... *FEEDOHM馃挒* [8/27, 1:25 P [11:03PM, 10/21/2017] Feedohm馃挒: 馃挧馃挧 *ZAN RAYU DAKE..馃尮* 馃尮馃尮馃尮馃尮 馃尮馃尮 馃尮 漏 *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM馃挒_* *Devoted to Ummi A'isha馃憣馃徎* 5鈨� "Madam"...ya kira sunan a hankali ganin zata shige gym ta barshi tsaye ... Dan juyowa tayi tana kallonshi a murtuke ba tare da tace komae ba ... "Kince karfe 8:00am nazo ko ? ...ya fada yana kallon fuskarta "Da yaushe nace kazo ? "7:30 madam kuma yanzu har pass 8 ....!! "Sae 12:00pm zanyi lecture din sorry ka jirani " ....bata saurareshi ba ta shige abunta .... Ji yayi hawaye na neman zubo mashi da yasan haka wannan shegiyar yarinyar tace da bai yarda da aikin ba .... Babban abunda yafi daga mashi hankali 12:00pm ake tado su nana makaranta ...sam inna sahu bata ba ta kudin mashi sae dae ta bawa yayanta biyu ita kuma indae baije daukarta ba sae dae duk uwar tafiyar dake akwae ta taho kasa ...... A jiyar zuciya ya sake tare da jan kafarshi ya fita ....cikin mota ya koma ya fito da time table dinshi ya duba ...ganin yana da lecture karfe 10 to 12:00pm ya sashi jin dan sanyi sanyi Yana Shiga yar'adua Unversity ya fara ganin course mate dinshi suna shigowa tsayawa yayi ya ragewa mazan hanya sannan suka shiga faculty of law .... Lecture ake masu amma sam hankalinshi baa gurin yake ba ganin 11:15 tayi gashi lecturer din baya da niyar fita tunda dama sae 12....Ishak ya kalla yaga shima danna wayarshi yake abunshi ..... Dan taboshi yayi yana magana a hankali .."Zan tafi please idan zaa yi attendance ka man !! Daga mashi kai yayi ba tare da ya kalleshi ba .....Sulalewa yayi ta kofar baya cikin sauri ya fita ba tare da lecturer din ya ganshi ba ..... Cikin saa kafin 12 din ya isa .....sae da yayi kusan 30mint sannan ta fito sanye da wani farin less mai stone blue sae dan karamin mayafinta blue da karamar jikka a hannunta ..... Duk da bata cika fara'a ba amma hakan ba karamin kyau tayi ba ...... Baya ya bude mata tashiga sannan ya zagaya shima ya shiga ya ja su ....cikin natsuwa yake tukun ta glass din gefenshi yake hango kyakykyawar fuskarta tana latsa waya tare da sakin wani blwng smile dake fito da side dimples dinta ...... Bai lura ba sae dae yaji tana magana cikin fada "back nace maka ...!! Wani uban burki ya taka tare da yin baya a hankali .... "Yauwa yayi nan ..." ta fada tare da balle kofar motar ta fita .... Shima da sauri ya bita ganin abunda zata fitar mawa ....Gabanshi yayi muguwar bugawa ganin Safeena duke gaban Nana tana rike da hannunta tare da sake mata murmushi .... Duk da ba jin abunda suke fada yake ba amma yana ganin bakin nana na motsawa tare da saka bayan hannunta tana share hawaye Bai gama mamaki ba sae da yaga Safeena ta daga Nana cak tare da mannata jikinta tana bubbuga bayanta alamun lallashi sannan ta nufo mota da ita ... Cikin sauri ya koma motar tare da kife kanshi ...wani irin dadi ke ratsashi ta ko'ina ya rasa dalili .... Har sae da ta zauna sossae ta daura nana saman cinyarta sannan ya tada motar ba tare da ya bari Nana ta ganshi ba .... Ta madubi yake kallonsu "Meye sunanki ? ...Safeena ta fada tare da gyarawa nana wuyan hijab dinta daya keshe .... Cikin Muryar Kuka tace "Nana" "Shiii ba nace ki daina kuka ba ....yi shiru kinji ..." ...ta fada dauke da fara'a .... "Oya Nana ba suna bane na gaskia ...meye asalin sunanki !! "Nana Aisha" ...ta fada hankali "Yauwa daga yau idan yayanki bai zo daukarki ba karki kuma masa kuka kinji ko , Ni zanzo na daukeki kullun zan biyo tanan kinji ko...dama duk haka suke !!! Ta fada tare da kauda kanta gefe guda .....da sauri ya kalleta ga mamaki sae gani yayi ta goge idanuwanta da hankyn dake hannunta .... "Wane Unguwa kuke ?....ta fada a hankali "Kofar Marusa!! ..Nanar ta fada tare da kallon Safeena ... "Maleek kofar marusa zamu kai Aisha " ...ta fada har lokacin tana kallon waje .... Baiyi magana ba sae dae canza akalar motar yayi tare da kura mata ido ta madubi ... Dae dae primary suka tsaya da yake motar barata shiga ciki ba ..... Su duka biyun suka fita tana rike da hannun Nana ....fitowa yayi ya zuba masu ido tare da harde hannayenshi guri guda...yana sakin murmushi mai fitar da sauti ... *FEEDOHM馃挒* [11:03PM, 10/21/2017] Feedohm馃挒: [8/27, 9:25 PM] Yar Lukuta馃挒: 馃挧馃挧 *ZAN RAYU DAKE...馃尮* 馃尮馃尮馃尮 馃尮馃尮 馃尮 *_Haske Writer's Association馃挕_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM馃挒_* *Devoted to Ummi A'isha馃憣馃徎* _Gaisuwa mai yawa tare da fatan alkhairi ga duk masoya da ma wadanda basa karantawa ...nagode sossae da kauna ....Ummy Aysha Mrs Maleek ko kuma nace snatcher ....Safeena tace na fada maki idan kin saba snatching din guys to ki daina don Maleek sae Safeena馃槝馃槝馃槝_ 6鈨� Tambayar da ya fara kanshi shin ashe Safeena na da hali mai kyau irin haka ....Baiyi tunanin zaa samu digon tausayi ba haka aranta ..... Hangota da yayi ta fito daga lungun ya sashi kafe ta ido dauke da murmushi a fuskarshi .....tafiya take cikin natsuwa kamar tana jin tausayin taka kasa ....har ta iso kusa dashi bai sani ba ..... Dan karamin tsoki ta ja tare da shigewa motar ba tare da ya sani ba ....ji yayi ta fizgi motar kamar zata bankeshi ........ Kallo ya bita dashi kafin ya tsayar da okada ya bi bayanta baiyi tunanin zata tafi ta barshi ba ....duk da tana ganinshi ta cikin mirrow din motar hakan bai sa ta tsaya ba har sae da takae AlQalam sannan ta shige abunta .....bata gama parking din motar ba ya iso cikin sauri ya sallami mai akodar sannan ya matsa kusa da ita yana fadin ... "Sorry Madam wallahi ban san kin iso ba !! Wani kallo ta watsa mashi lokacin da take kokarin rufe motar ..... "Kana aikin me har na wuce ta gabanka? ....ta fada tare da kafeshi da ido ... ""Hankalina baya gurin ne Madam !!..ya fada kamar me rada .... "Huh ....fada man gaskia ...kana kalleni ko ? ...to fada man ya kaga yanayin tafiyata ...ta burgeka ne ko yaya !!! ....ta karashe maganar tare da wurga mashi keys din .... Shiru ya mata ba tare da ya kalleta ba ...sae ma lumshe ido da yayi a hankali ... "Runtun Zunubi ne Maleek...4:00pm zan fito ...." ..ta juya a hankali ta shige hall din ..... Bayanta yabi da kallo tare da jingina da motar a hankali ...lumshe ido yayi jin har lokacin yana jin kamshin turarenta ..... Cikin motar ya koma ya tada tare da barin makarantar .... � Aunty bilky ta kalla lokaci guda ta daure fuska tana kurbar lemunta a hankali. .... Aunty bilky tace "Wae Fatee haka kike zaune da wannan marar kunyar yarinyar tana kallon mutane a dage .....!! Aunty fatee ta juyar da kai tare da kallom Safeena sannan tace "To ya zanyi Bilkisu sam Alhaji baya ganin laifinta ...kwanaki fa har cewa tayi zata mareni a gabanshi amma ya kasa daukar mataki ",... Aunty bilki tace "Ke Safeena zo !! Babu musu ta taso daga kujeran da take ta dawo kasan carpet a gabansu ta zauna tare da harde kafafu tana kallonsu .... "Ke Safeena ashe baki da mutunci ...dan Ubanki Fateen zaki mara don kina mara kunya ....duka yaushe kika girma ..anan dan ubanki ta gama wahala dake wadda ko uwarki bata maki kalarta ba ...amma!! Cikin sauri tace "Aunty bilki ki bar saka Ummata a cikin tsiyarku gaskia ...!! "An sakata din dan Ubanki ..ke kenan babu wanda ya isa dake ..bakyajin maganar kowa sae ta ubanki ...to wallahi mun gama maki komae tunda har muka hada uba da uwarki ..ko kiki ko kiso Mu uwayenki ne shegiya mara mutunci ....!! Tashi tayi ta shige daki ....drawer ta bude ta fito da turmin zani da rigunan jarirai guda uku da ta saya zata kaiwa Kanwarta ...ta fito dasu falon ..... Bisa kujeran da Aunty bilkin take ta aje sannan ta koma ta zauna tana fadin ... "Aunty bilki inji da ummana ta haiheni baki wuce ki bata turmin zani da rigar jarirai ba ....?? Daga Aunty bilkin har Aunty fatee bude baki sukayi suna kallonta tare da sauraren abunda zatayi .... "To ga kayanki nan na biyaki karki kuma zuwa kice zaki man rashin kirki !! ...tana gama fadin haka ta mike tare da barin falon ..... Tana ji Aunty bilkin na zaginta amma ko ta nuna ta san da ita suke batayi ba..... Gado ta fada tare da sakin kuka a hankali ita kadae ....kamar an tsikareta ta mike tare da daukar Hijab har kasa ta fita da gudu ta wucesu a zaune....har lokacin maganarta suke ..... *_FEEDOHM馃挒_* [11:03PM, 10/21/2017] Feedohm馃挒: [8/28, 9:16 PM] Yar Lukuta馃挒: 馃挧馃挧 *ZAN RAYI DAKE馃尮* 馃尮馃尮馃尮 馃尮馃尮 馃尮 漏 *_Haske Writer's Association馃挕_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM馃挒_* *Devoted to Ummi A'isha馃憣馃徎* *Dear,Sweetheart You're such a lovely,amzing and caring Sister's..we're more than friend's you're sisters frm another mavellous mother ..It's undistpn to have sisters like you ..i gss am the luckiest person in e- world more grease to your hutrs elbow ...UMMIEY XEEY & EXCLUSIVE QUEEN 馃挒馃挒馃挒馃挒馃挒 ..* 7鈨� Fita tayi daga gidan ko mota bata tsaya dauka ba ta fara tafiya kasa har bakin titi sannan ta tsayar da napep ta shiga ....Dutsin safe low cost ta ce ya kaita ...tafiyar minti 10 ta isa gaban wani ma daidaicin gida ta sauka ta bashi kudinshi sannan ta fada gidan. .... Wata yar dattijuwa ta iske tana gurza danyar kubewa a jikinta ta fada tare da sakin wahalallen kuka mai fitar da sauti ... Aje kubewar tayi tana bubbuga bayanta a hankali har tsawon yan mintina kafin ta dago fuskarta tana fadin ... "Menene matsalar Hussainah ?.... "Ummata kaka ...ina missing nata sossae dan Allah ki barni na kashe Aunty fatee ko zuciyata tayi sanyi kaka ....." ta fada cikin kuka .. "Kul Husainah kar na kuma jin kin kira kalmar kisa a bakinki ...ke kika halicceta? ..bana so kinji ko ki barsu da Allah da sannu duniya zata basu kashi ....." Maida kanta tayi jikin kakar tana jujjuya kai a hankali .... "Tashi kije ki zubo cous cous na nan cikin foodflask ki ci kinji ko !! "Na koshi " ...ta fada a hankali "Tashi nace maki ko ...me kika ci ? Kalli cikinki kamar babu yan hanji a ciki !! Sanin gaskia Kaka ta fada ya sata mikewa a hankali tare da cire hijab dinta ta debo abincin dan kadan ta zauna tana ci .... Sae kusan Magrib sannan ta fito da wayarta ta kira Maleek ....ringing daya ya dauka .... Cikin sanyin muryarshi ya mata sallama .... Bata amsa ba tace "Maleek ka zo dutsin safe ka daukeni yanzu" A hankali yace "Madam ina asibiti wani friend dina baya lafiya ..." "Matsalarka ce Maleek ...within 20mints ina jiranka !! ...ta fada tare da yanke wayarta A hankali ya lumshe idonshi don yanzu sam ba ta bata mashi rai ...sannan ya kalli Fahad dake bawa Ahmed abinci yace "Fahad idan ya tashi kace masa na tafi dauko madam amma zan dawo insha Allah " "Ina zaka Maleek ita Madam din barata dubi uzurin da ka fada mata ba ta hawo machine ta koma gida ...!! ...ya karashe maganar tare da jan dan karamin tsoki Fuska Maleek ya bata tare da fadin "to meye naka a ciki? ..kai tace kazo ka dauketa ? "Allah ya baka hakuri " ...ya fada tare da aje bowl din hannunshi ... "Ameen " ..kawae yace ya fice da sauri yana duba watch din hannunshi .... Ko da ya shiga dutsin safen sae da ya kirata yafi 6times sannan ta dauka tace ya jirata kusa da primary din tana zuwa ...... Fitowa yayi ya zauna saman motar yana jiran ta inda zata bullo .....da yake Hijab ta saka sam bai ganeta ba sae da wata mota ta haskata sannan ya gane ita ce .... Sumar kanshi ya shafa don ba karamin kyau Hijab din ya mata ba ...sam baiyi tunanin Madam na saka hijab ba ...ganin motar da ta haskata tayo baya ta tsaya dai dai ita ya sashi saukowa daga saman motar ya isa gurin .... Na cikin motar ne ya fito wani irin kato dashi sae uban ciki bakikkirin sae washe baki yake tare da fadin "Yan mata ina zuwa cikin wannan daren !! Duk da cikin duhu ne hakan bai hanata zabga mashi harara ba tare da zagayeshi zata wuceshi .... Mutumin ne yayi saurin kai hannu zai rikota ....Maleek yayi saurin rike hannun yana mashi wani irin mugun kallon.. Bata fuska yayi yana fadin "Bismillah Madam ".... *FEEDOHM馃挒* [11:03PM, 10/21/2017] Feedohm馃挒: 馃挧馃挧 *ZAN RAYU DAKE馃尮* 馃尮馃尮馃尮 馃尮馃尮 馃尮 漏 *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM馃挒_* *Devoted to Ummi A'isha馃憣馃徎* 8鈨� Dan kallonshi tayi tare da hade fuska tace ''meye haka Maleek……� Bai kalleta ba sae dae wani mugun kallo da ya watsa mata sannan ya juyo yana kallon mutumin da ya fizge hannunshi yana fadin "How dare are you zaka riken hannu"... "Please madam lets go" ya fada yana kallon fuskar safeena har lokacin fuskarshi na daure Dan karamin tsoki taja tare da kallon mutumin na yan mintina lokaci guda ta gama fahimtarshi alhaji SALLAU ne makwabcin su kaka sannan tsohon saurayin aunty fati kafin ta auri Abbanta sannan lokacin da mamanta ke raye tana yawan ganinshi gurinta Muryar Abdul malek taji cikin tsawa yana fadin"Wallahi ko kabar nan gurin ko na maka rashin kirki babu abunda ya shafeni da ko waye kai " mutumin ta kalla sanna ta dauke kai tana murumushi tare da fadin "sorry bai san ka bane shi yasa, Abdul Maleek muje " motar ta fada ba tare da ta jira abunda zasu ce ba Sai da ya ajeta gida sannan ya tafi A bakin kofar shiga falo ta jiyo muryar uncle ABBA KANIN aunty fati yana fadin "aunty na samu aiki a school dinsu feenat duk wani,bakin,cikinki zan fanshe maki soon ,kinsan jiya na hadu da abbanta shegen ko sisi bai bani ba ,baya da guri sae na diyarshi " Yar dariya ta sake tana fadin "kai dama har wani abun kike tunanin samu gurinshi to koni da kake gani,indae ba wannan shegiyar diyar ta saka baki ba bana cin kudinsa yanzu -" "Barsu zata ci uban tane ko makarantar sae ta gagareta zuwa " Yaye labulen falon tayi a hankali ta shigo tare da zama bisa doguwar kujeran tana kallonsu � dan kallon aunty fati yayi ya mata alama da ido sanna itama ta kalli,safeena tana fadin "Feena daga ina haka� BA tare da ta kalleta ba tace "club " Uncle ABBA yayi saurin fadin "safeena yar gidan dad ni bansan me na maki ba ko magana bakyason yi man, tun da nazo nake nemanki dauko abunci muci atare dama ke nake jira daughter nah " A banzace ta kalleshi tace "ko ni baran iya cin abinci da kai ba Uncle Abba" Dan,waro ido yayi yana fadin "kyamata kike daughter ……� "Bana jin zan iya cin abinci da christian kai kuma bana tunanin kana wankan tsarki ……" ta fada ba tare da ta kalleshi ba "KE.. "UNCLE tashi ka fita dallah barata yiyu ba har cikin dare ma kuzo ku cika mana falo da warin katti, taya zaku mayar mana da gida kamar wata college ko wane sakarai yazo ya shiga ba tare da ID card ba ,please find your way ……"ta fada tare da mikewa tsaye tana nuna mashi kofa Aunty fati tace "safeena uncle abba ne fa � "ko granny ne ina ruwana……"ta fada tare da balla mata harara Dan kallonshi tayi tana fadin "Abba kayi hakuri Safeena bata bason mutane ka tafi kawae zamuyi,mag ana ta waya ke kuma Allah ya shirya ki" Dan murmushi takaici ta sake tace "ameen nagode da addu'a AUNTY fati sanna kiyi addu'ar ALLAH ya ganar da barewa uwarta ta fari ko ba komae taji kamshin cutar dake makale da babarta……� Kallon uncle abban tayi da yayi mutuwar tsaye…… ko kadan baiyi tunanin rashin kunyar Safeena ta kai haka ba ,zaiyi magana aunty fati ta nuna mashi kofa tana girgiza kai Safeena kam ko da ta shiga daki bakin gado ta zauna tare da rumtse ido sam duniyar gaba daya ta isheta hoton yar uwarta ke yawo cikin KWAKWALWRTA dafe kai tayi lokacin da ta hango aunty fati tana sako hasanar daga saman benen falon babu imani bare tausayi lokaci kadan hawaye suka wanke mata fuska tana buga kanta a hankali jikin gadon Maleek ko da ya isa gida a bakin kofar dakin baffa ya iske nana lullube da buhu gurinta ya karasa tare da dagata ya zauna sannan ya zaunar da ita saman kafarshi "Badde yau baka zo ka daukeni ba " ta fada a hankali "kiyi hakuri nana kinji wallahi aiki ya man yawa yau ,wa ya maidoki ……� Dan girgiza kai tayi tana washe baki alamun jin dadin tambayarshi sannan tace "baddee sabuwar auntyta ka ganta badde ga kyau ga mutunci cewa fa tayi kullun zata dinga daukoni indae baka zo ba ,baddee ni dae ina sonta wata rana zaka kaini gurinta kaji baddee na " A hankali ya lumshe ido yana kallon fuskarta duk lokacin da zata mashi masifa sannan yace "anya tana da mutuncin nana ……� Bata fuska tayi tana fadin "eh man baddee tana da tausayi sannan tace tana sona kaima badde dole ka sota indae ka ganta " Dan murumshi ya saki a hankali tare da shafa sajenshi idan yace baya son safeena yayi babban sabo duk da ya san ba ajinshi bace amma baya jin zai iya rayu babu ita ,wani irin so yake mata wanda bai san irinshi ba muryar nana ta katseshi lokacin da take fadin "kai baddee muna sonta ko?kuma gobe ko,kazo daukata baran bika ba " Zancen ya katse ta hanyar tambayarta ko ta ci abinci ,girgiza kai tayi tana fito da hakoranta biyu na gaba tana lotsa gefen kumatunta ,Murmushi yayi don ya gane salon murmushi Safeena ne ta kwaikwaya ko baa fada mashi ba yau yasan,nana na cikin farinciki _*FEEDOHM馃挒*_ [11:03PM, 10/21/2017] Feedohm馃挒: 馃挧馃挧 *ZAN RAYU DAKE馃尮* 馃尮馃尮馃尮 馃尮馃尮 馃尮 漏 *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM馃挒_* *Devoted to Ummi A'isha馃憣馃徎* 9鈨� Da yake ta bashi timetable dinshi tun karfe bakwae ya iso gidan , inda ya saba jiranta nan ya zauna ,yauma daga gym din ta fito sanye da blue din jeans sae bodysnk fara fuskarta fayau natural beauty da ka ganta kasan bata da matsalar rayuwa a fuska har ta iso kusa dashi bai sani ba ido ta xuba mashi sannan ta saka kafarta ta take mashi yatsun kafarshi tana kallonshi , kafarta ya kalla tare da kallon fuskarta sannan ya kawar da kai Dan murmushi ta sake mai fitar da sauti sannan ta dan duka tana kallon fuskarshi duk tunaninshi bara ta magana ba sae ji yayi tace "ya dae Maleek me kake kallo haka ……� kura mata ido yayi ya kasa magana sae murmushin da ya sjbuce mashi "Maleek ka daina kallona da mayun idonka please! ya ciwon kan……� Lumshe ido yayi sannan yace "Allhmd madam " "ok muje " ta fada tare da nuna mashi motar tayi gaba ,tsaye yayi yana kallonta ya kasa koda motsi tun daga sama har kasa ya kare mata kallo ,bara ya iya jin zai fita da ita a haka ba...... Saurin shan gabanta yayi ya kwantar da kai yana fadin "Dan girman Allah madam ki canzo tufafi ba dan ni ba ba kuma dan na isa ba wallahi baran iya fita dake a haka ba dan ALLAH madam " ya karashe maganar murya na rawa Kallonshi tayi na yan lokutta kafin ta juya a hankali ta koma cikin gidan , mintina kadan ta fito sanye da doguwar riga maroon daga samanta ta dan matse sae kasan a bude sae karamar hijab baka , bai san lokacin da murmushi ya subuce mashi ba tare da girgiza kai sannan ya bude mata motar ta shiga ya rufe ,shima ya zagaya ya shiga har ya fita da motar harabar gidan bai kuma magana ba sae dae satar kallonta da yake ta mirrow dake gaban motar Wayarta tayi ringing ta dauka tare da langwabe kai cikin shagawaba ta fara magana " baby Allah ban san ka kira ba ,na shiga gym kuma ko da na fito ban duba wayar ba sae da na shigo mota " Gaba daya ya maida hankalinshi gurin wayar da take ji yayitace "da MALEEK mana " Shiru tayi na dan wani lokaci kafin tace " na manta na fada maka Abbah yace ka turo iyayenka zasuyi magana fa ……" Wani wawan birki ya taka wanda har sae da ta buge da kujeran dake kallonta , gaba daya ya juyo yana kallonta a rude Ta dade kafin ta dago tana watsa mashi harara "Maleek neke faruwa ……"ta fada tana dafe kirji don har ga Allah ta tsorata Shiru yayi ya kasa magana sae uwar zufa dake bi mashi fuska maganar tata tayi balain sokar zuciyarshi ............"wae ya turo " abunda kawae yake maimatawa a ranshi kenan Daure fuska tayi ganin yana neman bata mata lokaci "common dallah meye haka?kaka ganin time na kurewa zaka wani tsaya ka juyo kana kallona � ni dince baka taba gani ba ko mai � dallah mallan juya kayi,abunda ke gabanka bombastic villager……" Bai juya ba sae dae ya dan seconds sannan,ya juya a hankali ya tada motar suka ci gaba da tafiya amma sam baya cikin natsuwarshi ......... Yana a jeta makarantarsu ya nufa yana shiga aka fada madhi result dinsu ya fito suka tafi suka duba luckily da first class ya fita sae abokinshi ishak ya fita da snd sae Abbas da ya fita da thrd class .........wani dan notice da aka lika gefe dasu ne suka duba sunanshine a ka rubuta in bolc ABDULMALEEK AHMED ana nemanshi senate ............ Senate din suka nufa sae da ms din yayi interview dinshi sannan ya shiga office din VC din VC din mutumin kirki ya nuna mashi kujera yace ya zauna ,sae da kyar sannan ya zauna cikin dari dari ...... "Meye sunanka�......"ya tambayeshi,cikin harshen hausa "ABDULMALEEK AHMED sir "......ya fada cikin natsuwa "Waye mahaifinka wane gari kake Abdul maleek � "Sir ni dan jahar katsina ne cikin kofar marusa ina zaune da kawunane " "to ina mahaifinka Abdul maleek……� *FEEDOHM 馃挒* [11:03PM, 10/21/2017] Feedohm馃挒: 馃挧馃挧 *ZAN RAYU DAKE馃尮* 馃尮馃尮馃尮 馃尮馃尮 馃尮 漏 *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM馃挒_* *Devoted to Ummi A'isha馃憣馃徎* _Duniya baka gane kana cike da mosaya sae baka nan ......ALLHMD dan lokacjn da na dauka bana nan na fahimci abubuwa da yawan gaske banda bakin da zan gode maku sae dae na roki ALLAH da ya saka maku da mafificin ALKHAIRINSA ......aunty SIS wallahi ke ta dabance ta ko'ina mutunci da kimarki su suke kara maki daraja da daukaka ...UMMI A'ISHA banda bakin maki godiya sae dae ALLAH yabaki abunda kike nema duniya da lahira ...HAJJA CE ,PHERTY ,MAMAN HUDA,FAREEDA NABEEL,MAIJIDDA ,...ALLAH YA KAREKU DA DUKKA KARIYARSHI ,馃挒_ 馃敓 VC yace "to ina mahaifinka yake"...... "Mahaifina ya rasu ,mahaifiyata kuma tun muna kanana ta rasu ina zaune da baffana tare da karamar kanwata ,sannan nike daukar duk wani,abunda ya danganshi karatuna sir" VC din ya masa taaziyya tare da fatan rahama ga dukka iyayen nashi ,sannan ya fada mashi cewa result dinshi tunda suka bude makarantar baa taba samun irin nashi ba don haka makaranta ta dauki nauyin karatunshi duk kasar da yake bukatar yayo masters dinshi tare da offer ta aiki a highcourt dake GRA a matsayin barister , sannan makarantar zata nema mashi alfarmar shigaba da karatunshi duk da yana aiki ..." Nana ta fara fado mashi idan ya tafi wata kasa gurin wa zata ji,dadi � sannan safeena da baya fatan yayi koda one day ba tare da ya ganta ba ya gwammace yayi,ta zama a drivernta ba tare da tasan waye shi,ba... Cikin sanyin jiki yace ya ya gode amma,shi yafison yayi masters dinshi anan zaria idan,da hali , VC din ya amsa mashi tare da bashi wasu files da zai kai high court din yanzu... wajen karfe sha biyu da rabi yaje daukota lokacin ta gama cika fam dae dae ita yayi parking sannan ya fito ya tsaya gabanta tare da harde hannaye a kirji cikin natsuwa yace "am sorry madam ... A tsawance tace " shut up duntolic nonsense , yaushe nace na ka dawo " Duk da yaji zafin zagin amma sae bai nuna ba illa iyaka dsn murmushin da ya sake iya lebe ... Dan wrist dinta ta duba tana fadin "1hour kenan ka kara then i shud minus ten k a salary dinka ............ Cikin salon tsokana yace "Madam t10k tayi yawa please ki ragen mana ......" Harara ta watsa mashi "lets go bullshit ka tsaya kana kallona da mayun idanunka ...wallahi maleek idan kai mayene ka kama mutun bara kai ko ina ba ......... Dariya ya sake a hankali tare da bude mata motar ... komae na safeena burgeshi yake masifarta,salonta,rayuwarta ,da komae nata daban yake a mutane ... 銆娿€嬨€娿€嬨€娿€� JB kam tunda safeena ta fada mashi sakon Abbanta ya kasa rufe baki company dad dinshi ya nufa , yana zuwa ya iske suna meeting a octgon ... zaya shiga messenger din ya yace Alhaji ya hana a bar kowa a ya shiga har sae sun fito ...... Awulakance ya kalli dattijon yace" don kana dakiki sae kuma yace maka har JB idan yazo ka hanashi shiga ko � Dukar da kanshi yayi yana fadin "kayi hakuri Alhaji ya ce kada a bar kowa ...... Bai rufe baki ba yaji saukar maruka har biyu "Wawa daga yau idan na sake zuwa gurin mahaifina ka saka jakin bakinka ka man magana villager ............ Meeting room din ya fada ba tare da wani shamaki ba ...dadad din na ganinshi ya mike tare da bada umarnin a katse meeting ... MG yace "oga meeting dinnan ba is very imprt ka sani ,yana barazana ne ga wannan,company please ka tsaya a ida ...... "JB ya fiye man komae a yanzu ,muje ..." ya fada kai tsaye tare da barin gurin sae da suka je office dinshi sannan suka zauna ya fada mashi komae ...... "wow my son ya kusa zama ango ...mg zan zama grandpa soon am very happy ..."ya fada tare da hugging din JB din 銆娿€娿€娿€娿€嬨€嬨€嬨€� Auwal abbas ne ya shigo yana fadin wae an canza masu sabon lecturer da zai daukesu anatomy sannan ya aiko by 10 zai shigo idan ya shiga kuma babu wanda zai sake shiga ko fita ... A hankali ta kalli maryam dake danna wayarta tace " tashi muje zan siyo PP nawa ya kare " Ido ta waro tana fadin "safeena 9:45 Fa idan ya shigo ya hanamu shiga fa……� "Ajannah zai raba? ta fada tana bata fuska ... "a'a amma ... "look idan bara kije ba ,bani key dinki na tafi,..... *FEEDOHM 馃挒* [11:03PM, 10/21/2017] Feedohm馃挒: 馃挧馃挧 *ZAN RAYU DAKE馃尮* 馃尮馃尮馃尮 馃尮馃尮 馃尮 漏 *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM馃挒_* *Devoted to Ummi A'isha馃憣馃徎* 1鈨�1鈨� Cikin sanyin jiki ta mika mata keys din sam barata ta iya iskancin safeena ba ...karamin tsoki ta ja sannan ta karfi keys din da karfi tana watsa mata harara ...... A zahiranci ba PP zata sawo ba haka kawae tayi ta yawo cikin gari ba tare da sanin inda zata ba bakin round din dandagoro taga Maleek yayi parking ya tsaya kusa da mai recharge card ...I tama parking din tayi bayanshi ta fito ta jingina tare da harde hannu tana kallonshi ...Sam bai san da zuwanta ba sae da ya juyo da niyyar tafiya sannan ya ganta da sauri ya matso kusa da ita tare da sake mata lallausan murmushi "Maimakon ki kirana ni daukoki sae ki fito madam bayan kinsan aikina kenan " ...ya karashe maganar cikin salon soyayyar da bata boyiwa ... Itama murmushi ta sake tare da mika hannu "bani keys din " Da mamaki ya mika mata duk da bai san abunda zatayi dashi ba ...karba tayi tare da balla mashi harara ta juya tana fadin "iskancin da ya kawoka nan ya maidaka bisa okada idan kuma baka da ko sisi ka dabi sayyada akoma gida ......" Sajenshi ya shafa tare da sake lallausan murmushi ya rakata da ido ...yana ganin ta koma a motar da tazo da ita ta bar wannan din a rufe ...sam bata bashi haushi ba din duk abunda zatayi barata taba kona mashi rai ba sae ma kara burgeshi da take ......... Sai kusan 11 ta koma makarantar tun kafin ta shiga hall din ta jiyo muryar Uncle Abba yana fadin "fibroids are most common growth in a woman reproductive system many woman with fibroids have no symptom at ............... To me ya hadashi da fibroids ta fada a ranta tare da kutsa kai cikin hall din ...shigarta ya datse mashi sauran maganarshi wani ja irin murmushi tare da daka mata tsawa "ke ............ "Sir Safeena khaleed dae...... " itama ta fada a tsawance "get out idiot ,ni zaki fadawa sunanki safeena ……� "Mendotic idiots dae sir ...ni dae kai ,kai a tunani lecture din na zo na yi mtsee kai kasan safeena ta wuce nan ,Maryam karbi keys dinki nan gaba menstrual ko menopausal zai maku ........." ka karshe maganar tare da wurga mata keys din A harzuke yace "dan ubanki safeena ni kike fadawa haka ……� Yar dariya ta sake "ashe ma kasan sunana ,good kar ka kuma zagar man uba ,ka duba da kyau a lecture hall muke ,baa falon dad ba da aka saba zuwa maula ,nan baka da hurumin zagina kai ko a,gidan ma ka zageni nima har gida zanje na samu tsohuwa mai dattin kallabi ........." kafin yayi yunkurin bata amsa,ta bace kamar walkiya a fusace ya dauki tools dinshi ya bar wurin ko office,bai shiga ba ya wuce gidansu ......... 銆娿€娿€娿€娿€嬨€嬨€嬨€� Tana kwance landline din dakin tayi kara ta tabbata babu mai kiranta sae Abbanta,cikin sauri ta dauka tana share hawayen dake neman zubo mata a ido "Abbah ......"ta fada a hankali kamar me shirin kuka "Safeena ki sameni garden yanzu kinji ko " "to "ta fada tare da saukowa daga saman gadon takalmin ta zura sannan ta ja bakin gyalenta ta fita......gefe ta iskeshi ya shingida yana karanta dailytrust ,gefenshi ta zauna tare da lankwashe kafafuwa tana kallonshi ,aje newspaper yayi ya sake mata murmushi kamar ko yaushe "Safeena me ke faruwa � ...ya fada wit serious tlk "Abbah a ina � "Safeena bakya jin maganata ko me yasa bakya da kyakykyawar alaka da dangin maminki safeena ,ko kadan bakya darajasu me yasa ko don kina ganin mamin taki bata rayane � Idonta ya ciko da kwallah tayi saurin damke hannun abbanta tare da kallonshi "Abbah me nayi dan ALLAH ..."ta fada da shagwababbiyar muryarta kallonta yayi na seconds sannan yace "me ya hadaki da Uncle dinki � "Sorry Abbah... " ta fada a hankali tare da goge hawayen da suka zubo mata "To meye na kuka kuma yarinyar Abbanta ……"ya fada cikin sigar lallashi ,har ga Allah idan akwae abunda ya tsana bai euce kukan diyarshi ba duk duniya babu abunda yafi kauna sama da yarinyarshi "Sorry Abbah zagan,man abbana yayi ni kuma baran iya jurewa ba ka yafe man kaji ........." FEEDOHM 馃挒 [11:03PM, 10/21/2017] Feedohm馃挒: 馃挧馃挧 *ZAN RAYU DAKE馃尮* 馃尮馃尮馃尮 馃尮馃尮 馃尮 漏 *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM馃挒_* *Devoted to Ummi A'isha馃憣馃徎* 1鈨�2鈨� "Baki man komae ba Safeena amma ki kyautata alakarki da dangin maminki ji ko ,bara na kira Abdul maleek ya zo na aikeki abukur gidan inna kinji ko idan,kinje ki kwana acan bana son damuwa ......" "to ……"ta fada a hankali tare da gyara zama Wayarshi ya fito ya kira Maleek din da kanshi sannan ya mata fada sabida ya san halinta sarae idan taje Abukur dole sae sun kwabsa da inna suke rabuwa ……kafin Maleek din ya iso yace taje ta shirya Ko minti talatin bai dauka ba ya iso da ganinshi kasan ya wahala bai fito daga motar ba kamar yarda ya saba sae ma kifa kanshi da yayi a sitiyari ……� Zagayawa tayi ta side dinshi tana kallon yanayinshi haka kawae taji ya bata tausayi first time a zamansu ……"Maleek baka lafiya ne?ta fada a hankali tare da leka kanta ta glass din motar Duk da yana jinta amma sae yayi shiru yana sauraren ko zata sake magana a yanayin da tayi……kamar ta sani bata kuma cewa komae ba sae bude kofar da tayi tare da knocking din sitiyarin � Kalar tausayi ya sake komawa ya dago yana langwabe kai kamar yaro karami……dariya ta sake da ta kara kashe mashi jiki ya bude baki yana kallonta "Madam" ya fada cike da shauki duk zaman da suke bata taba mashi dariya irin haka ba Dage gira tayi tana fadin "Yes common bani guri nayi driving din don baran yarda ka jani da irin wannan yanayin ba ,koma wancan side din ka zauna……�"ta nuna mashi gurin mai zaman banza Kallonta kawae yake cike da mamakinta sannan ya tsallaka ya zauna ……bata kuma cewa komae ba har suka fita daga garin ganin ba kara kulashi zatayi ba ya sashi lumshe ido tare da langwabe kai yana tari Saurin kalloshi tayi tana fadin "Abdul Maleek baka lafiyane � Kamar yaro ya daga mata,kai tare da kokarin saka idanuwanshi cikin nata ,bata bari suka hada idon ba tayi saurin janye nata tana fadin "Sorry……�" 銆娿€娿€娿€娿€嬨€嬨€嬨€� Karfe hudu na marece Aunty faty ta shirya ta tafi gidansu dake layout a can ta tarad da aunty zuby yayarta da suke uwa daya suna falo suna fira da hajiyarsu mafi yawan firan ta safeena ce da Abbanta,wanda dama firar kenan idan sun hadu , kusa da zubyn ta zauna tare da jefar da jikkarta tana dafe kai "Wadannan mutanen su suke su saman ciwon kai wallahi , hajiya gaskia na gaji da wannan zaman ki san abinyi ……�" cewar Aunty faty Harara hajiyar ta sake mata tare da fadin "meye kuma ? "Meye ma bai faru ba hajiya , safeena fa aure zatayi da dan former minister abunda kuma bara ya yiyu ba……� Aunty zuby ta katseta "ke tsaya dallah wane former minister,please ki bar wannan batsar taya diyar AISHA zata auri wani dan mininster baya ga namu yayan nan zaune gida? Tabe baki Aunty fatyn tayi tace "ke ma kya gani dae……hajiya kice wani abu mana ga fadila nan ta girmewa safeena bare ma fauzy da rabi kuma su duka babu wanda yayi aure sae safeena?haba hajiya kar dae ace da gaske mutane suke munyi gadon bakin jinin gurinki ? Cikin fusata hajiyar tace "ke dallah rufe man baki ,gidan uwar wa kuka yo gadon bakin jinin?sae ku bari kuga idan tayi auren ya'yanku basuyi ba sannan kuzo ku man tsegumi ……� Kallon juna sukayi tare da kashewa suka dau ihu "Hajiyarmu……�" Aunty zuby ta bude jikkarta tana fadin "kinga yar uwa ga wani sabon hadi daga sabon shehi kya gwada sakawa ogan a kasan pillow kafin hajiya ta warware komae ……�" Bata bar gidan ba sae wajen isha'i ta koma , sam bama tasan safeenar bata nan ba tun da dama ba nemanta take ba sae da ta hadawa Abban safeena komae na bukata sannan tayi wanka ko sallah bata tsaya tayi ba ta shiga part dinshi tare da garin maganin da zuby tabata da zasu rabu ……cikin saa yana toilet yana wanka ta daga pillownshi ta bar bada kadan sannan ta mike ta bar dakin ta koma nata Jin wayarshi na ringing ya sashi fitowa daga toilet din ba tare da yayi alwala ba , bakin gadon ya zauna yana duba wayar ganin safeena ce ya sashi kiranta tare da shigidawa saman gadon yana sauraren yarda ta dage tana zuba shagwaba wae bara ta kwana gidan Inna ba saboda ta mata wulakanci ita gida zata dawo ……� Dariya sossae yake cike da so yana fadin "Haba SaFeenata ke da kakar taki , kinga dare yayi kiyi hakuri gobe da kaina zanzo na dauko ki kinji ko ……�" Cikin shagwaba tace "Abba cewa fa tayi baran kwantar mata a wannan tsohon gadon nata ba ……�" Yar dariya ya sake a hankali ……dif wayar ta dauke girgiza kai yayi ganin chajin shi ya dauke shi bai ma san baya da chaji ba sae yanzu "Safeena � FEEDOHM馃挒 [11:03PM, 10/21/2017] Feedohm馃挒: [3:47AM, 10/18/2017] Feedohm馃挒: 馃挧馃挧 *ZAN RAYU DAKE馃尮* 馃尮馃尮馃尮 馃尮馃尮 馃尮 漏 *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM馃挒_* *Devoted to Ummi A'isha馃憣馃徎* _Assalamu Alaikum dan Allah masu bibiyar littafin *BAKONMU HASKENMU* su gafarceni na daina posting dinshi for some reasons Amma insha Allahu nan gaba zai fito amma bata social media ba sannan kuma bata siffar novel ba ,ko ma tayayane insha Allahu zaku ganshi kuma nasan sae yafi maku dadi fiye da ta novel...._ 1鈨�3鈨� Ita kam safeena tana jin wayar ta yanke ta fara bubbuga kafafuwa kasa tare da turo baki , muryar inna ta jiyo ta shigo dakin tana fadin "Ayi dae mu gani dan uban mutun dama na fada har gida mara kunya zai iskeni anan nima zanci kaniyar mutun" Dan turo baki tayi tana hararanta ta kasan ido tare da barin dakin gaba daya Dariya inna ta sake sannan ta shinfida abun sallah tana fadin "Naga yarda mara kunya zai shigon daki ya kwana tunda nima bada kudin uban mutun na cika na sayi gidan ba" Daga waje Safeena ta bata amsa "ai da yake aikin gwamnati kike ko business da zaki iya sayan wannan gidan " Kamar jira inna take tayi wuf ta fito tana fadin "to mara kunya fada man ubanki ne ya saya man da zaki fadan magana ……� " Ganin idan ta biyewa inna rigimar ba karewa zatayi ba tunda dama tana da cikinta ya sakata langwabe kai tana lumshe idanuwa tace "Haba kakus ni fa ba haka nake nufi ba , kece tunda nazo kinki ki saurareni sae tsiya kike , ni kuma Allah ma ya sani ko lafiya banda ita hakanan nazo gaidake saboda kwana biyu ban ganki ba , amma idan zuwan nawane bakya so to kiyi hakuri gobe da safe sae in tafi ……" Dayake Inna irin mutanan nanne masu masifar son jikokinsu ya saka jikinta yayi sanyi don ta yarda da cewa safeena batta lafiyar , kusa da ita ta matsa tana fadin "Kece Safeena sam baki da mutunci muddin idan mutun ya iskeki gidanku sae ki rufe ido kiyita rashin kunya bayan a zahiri ba haka kike ba ,amma komae ya wuce kinji ko zo mu shiga ki fadan meke samunki sae a aika a siyo maki magani,sannu kinji ko ,haba shi yasa naga duk idanuwanki sun canza Allah sarki……" ta karashe maganar tare da jan hannunta suka koma dakin Sabon tara Inna ta sake mata tana lallabata kamar wani kwae ,a bisa kafarta ma tayi bacci 銆娿€娿€娿€娿€娿€嬨€嬨€嬨€嬨€� Tunda safe mahaifan JB suka samu Abba a gida , da yake yasan da zuwansu sossae yasa Aunty fatee ta shirya masu duk wani abun bukata ,sunyi farin ciki sossae da karramawar da aka masu ,nan take suka bayar da kudin neman aurensu naira dubu dari biyar ,Yayan Abba ne ya yanka masu sadaki naira dubu dari biyar , nan take suka fito suka bayar sannan aka saka masu ranar aure nan da wata biyar ……� Iya rudewa Aunty faty ta rude lokacin da Abba ke fada mata yarda sukayi da mutanen , kasa boye bakincikinta tayi tace"Million daya fa kace Alhaji ,kuma shine zaku bayar da ita kamar kun sayar……�" Dan murmushi yayi yace "Million daya shine kamar na siyar da diyata fati ? "Kwarae kam Alhaji , kaga dae diyar nan amanace kar mu bayar da ita ga mutanen da basu son darajar kowa ba ,don wallahi duk yawancin musu mugun kudinnan basu san darajar kowa ba" "Atunanina fati mutumin nan bai fini komae ba don haka bana tunanin zai wulakanta man diya tunda ya san itama ba daga gidan tsiya ta fito ba ……�" Shiru ta masa tana karkada kai a hankali……mintina kadan ta dauka sannan ta mike ta koma dakinta ,wayarta ta fito ta kira hajiyarsu ta fada mata komae Hajiyar ce mata tayi ta jira zata nemeta ……� 銆娿€娿€娿€娿€娿€嬨€嬨€嬨€嬨€� A Sanyaye ta kira sunanshi ganin zaya tashi motar "Maleek" Zalla soyayya ya juyo yana kallonta ba tare da ya amsa mata ba , so take ta tambayeshi amma sam ta kasa , ta rasa wanda zata fadawa damuwarta cikin yan kwanakin nan , sam Abba yaki saurarenta kullun ta tunkareshi sae dae yace ta jira shi yana aiki idan ya gama zai kirata haka zatayi ta zama amma sam bara ya nemeta ba ……idonta ya ciko da kwalla ba tare da ta sani ba…… Lumshe ido yayi lokacin da kwallar ke fitowa daga kwayar idonta wani irin sonta ke fizgarshi duk da ya san cewa ta kusa mashi nisa ……� Cikin sanyin murya yace "Madam dan Allah ki koma cikin motar muyi magana ,ba dan na isa ba ……�" juyawa tayi da sauri ganin kukan na niyar subuce mata ga mutanen dake kai da komowa a harabar makarantar bayan motar ta fada tare da kife kanta a cinya tana kuka bata san lokacin da take surututai ba tare da kiran sunan Abbanta"Abbana me na maka dan Allah?me ya saka zaka juyan baya bayan kasan kai kadai ka rageman Allah ka jibanci lamurrana ni marainiyace kafi kowa sanin halin da nake ciki ……�" *FEEDOHM馃挒* [11:03PM, 10/21/2017] Feedohm馃挒: 馃挧馃挧 *ZAN RAYU DAKE馃尮* 馃尮馃尮馃尮 馃尮馃尮 馃尮 漏 *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM馃挒_* *Devoted to Ummi A'isha馃憣馃徎* 1�4� Cikin sanyin jiki shima ya shiga motar , kifa kanshi yayi a sitiyarin yana kallon yarda ta matse kanta da cinyoyinta ,wani irin sonta ke fizgarshi a sanyaye yace "Madam dan girman Allah ki bar kukan ki fada man me ke faruwa�" Girgiza kai take a hankali ta kasa magana ,ina ma zata iya da ta fadawa maleek cewa Abbanta ne ke neman juya mata baya ,amma sam barata iya jin zata yarda da wani mutun ba a rayuwarta har ta iya fada mashi matsalarta � "Please Madam dan Allah kiyu shiru wallahi bana jurar kukan mace bare ma naki madam ko bakya lafiyane� Tambayar duniyar nan ya mata taki kulashi sae ma wani sabon kuka da take ……hankali ya tashi motar ya fita daga makarantar direct dutsin safe ya nufa da ita ,bakin gidan Granny yayi parking a iya zaman da yayi da ita yasan nan kawae take zuwa ta samu farinciki ……� Cikin sanyin jiki ya fito ya bude mata motar sae a lokacin ta dago da kanta ta ga inda suke da sauri ta fito ta shige gidan ba tare da tace dashi komae ba bayanta ya bi da kallo tare da lumshe ido Tana shiga gidan ta durkushe a tsakiyar falon tana kuka , Granny dake zaune bisa doguwar kujera ta mike tare da karasowa gurinta ……� "Menene kuma Hussaina ,fada man me ke faruwa �" Cikin kuka tace "kaka shin Abbana bai san shi kadae gareni ba � ko ya manta cewa mamina batta raye ?aka me yasa yake neman juya man baya �" "Me ya maki Hussaina�" "Granny Abbana ya daina sona�"ta fada tana shashshekar kuka "Karyane Hussaina ko ma mene Allah ya fisu , kin fi kowa sanin kece rayuwar Abbanki me ya saka zaki damu ,bana son wannan kukan kinji ko ,tare da Abdul maleek kika zo �" Daga mata kai tayi a hankali tana sharan kwallah "Jeki kira manshi " Ahankali ta mike ta fita ganin ba motar ya sakata dawowa ta fadawa kakan ya tafi …… 銆娿€娿€娿€娿€娿€嬨€嬨€嬨€嬨€� Alhaji khaleed kam tun da ya zauna office ya,kasa tabuka komai ……cikin kwana kinnan ya rasa meke damunshi sam baya kaunar Safeena ta rabeshi amma idan bata kusa dashi sae yaji ita kadae yake bukatar gani ……har ga Allah ya san duk duniyar nan babu abunda yake kauna sama da diyarshi amma ya rasa meke damuwa …… Wasu yan siraran hawaye ke bin kumatunshi yayin da zuciyarshi ke bugawa da karfi,tsoro da fargabar rasa diyarshi yake ,yana sane da yanayin da take shiga yan kwanakinnan……cikin sauri ya janyo wayarshi tare da kiran Abdul maleek don ya tabbata ko wane yanayi take Abdul maleek zai fi kowa sani Ringing daya a na biyu ya dauka tare da barin office dinsu ya fita harabar court din , kamar yana ganinshi ya russuna yana gaidashi Cikin rawar murya yace "Maleek ina safeena tana lafiya dae ko?" Karo na farko daya farawa uban gidanshi karya yace"Alhaji tana lafiya lau yanzu na kaita makaranta na dawo " "Bata cikin damuwa ka tabbata Abdul maleek ……? "Alhaji tana cikin kawayenta ma suna karatu kuma banga alamun damuwa a tattare da ita ba ,Alhaji lafiya ? "Ba komae Abdul maleek dama kawae ina so naji yarda take ne ,Abdul Maleek ba kai safeena unguwa kadae na saka ba harda amanarta na baka don Allah ka kular man da safeena ……�" 《》�《》 Aunty faty kam daga gidan hajiyarsu gidan Aunty zuby ta nufa ,a falo ta iske ta zaune ita da mijinta ,janta tayi daki sannan ta fito da wasu magunguna ta mika mata a hannu � "Kina jina ko ki tabbatar kin saka mashi a ruwan wankanshi na safe sannan ki zuba mashi a abincin da zai fara ci a safiyar gobe……shi da wannan shegiyar diyar sae daga hannu ……�" Dariya ta sake tana fadin "Sae Aunty to ina na safeenar kin san dae sauran wata biyu bikinta ,kuma ni wallahi bana son wannan shegen auren don bara ta yiyu diyar Aisha tayi aure ba ta bar yayanmu zaune ……�" "Ke kau me kika ci na baka na zubana mashi maganar yace sae ana saura sati bikin zaa sakar mata jini kinga kau dole ango ya kora masu yar su a matsayin bazawara ba budurwa ba ……idan akace a hana auren tana budurwa to kinga zata iya samun wanda ya fi wancan tunda dan ubansu kamar a jininsu yake ……�" *FEEDOHM馃挒* [5:06PM, 10/20/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹* 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 © *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM💞_* *Devoted to Ummi A'isha👌🏻* 1⃣5⃣ "Amma Aunty zuby kina tunanin JB din zai rabu da ita ……yana fa sonta kada ya nema mata magani yaki sakinta ……"ta fada a sanyaye Harara ta sake mata"Baki yarda da abunda na fada maki ba kenan ……shi banzane da zai zauna da mace tana bleeding ,kiyi amfani da kai mana ,tunda uwarta ta yi ta barmu itama babu abunda zata iya , ke dae kawae ki zuba man ido ……" Mikewa Aunry fatin tayi ta sabi jikkarta tana fadin "Bara na wuce aunty zuby komae kenan na kiraki ,yauwa hajiya tace ki aika Fadila ta karbo maki sakonki ……" Kusan tare motarta data Safeena ta shiga harabar gidan Abdulmaleek dinne ya fara parking sannan Aunty fatin tayi a tare suka fito da safeenar ,da Sauri aunty fati din ta matso tana fadin "Feena ina kika tsaya tun dazu nake kiran wayarki naji ko kin dawo gida ……" Harara ta sake mata kasa kasa tace "ki godewa Allah da baki sameni ba, don da kin samu da baki samu damar fita ba……" Kwantar da murya tayi tana fadin "haba feena me yasa kike man haka yanzu neman naki ma a waya laifine ……" "kya ji dashi Aunty fatee ,Maleek gobe da safe kaje dutsin safe granny na nemanka ……"ta karashe maganar tare da yin gaba abunta Aunty Fatee ta juyo tana kallon Maleek daya zuba masu ido yana kallon duk abunda suka ,lallae sae yau ya tabbatar da safeena bawae shi kadae bane batta so aa duk wanda ke rabe da ita ne takewa haka ,amma tana da kyakykyawar dangantaka da mutanen da bata da wata alaka dasu …… "Abdul maleek kaga safeena ko, yanzu dan Allah abunda take man ya dace ……? Dan girgiza kai yayi a hankali yana kallonta ,cigaba tayi da fadin "Wallahi Maleek sam safeena bata da halin kirki ,yarinyar muguwace bata da tausayi ,kai kanka jiba yarda duk ka lalace ai lokacin da kazo ba haka kake ba ,ni……" Katseta yayi ta hanyar cewa "hajiya sae Allah ya kaimu ……"bai jira abunda zata fada ba ya bar gurin , ko motar bai tsaya dauka ba …… Daga nan gidan granny ya nufa da yake sun riga sun saba shiga kawae yayi ya isketa a falo tana gyangyadi …… "Yar tsohuwa kuma bacci ake yi " ya fada cike da xolaya "Abdul maleeku ne ,yaushe ka shigo ……" "Yanzu wallahi madam tace kina nemana ……" "Eh aikenka nake son nayi a daura gobe idan Allah ya kaimu ……" "Allah ya kaimu goben ……"so yake ya mata zancen safeena amma yana kunya daurewa yayi ya dukar da kai yana fadin "Hajiya ni ko dan Allah ko kin san meke damun Madam ne naga tana cikin damuwa……" A jiyar zuciya ta sake sannan tace "Abdulmaleeku laifina ne ki bibiyar jikata ……" "Ya laifinki kuma hajiya ……? "Karka damu kaji ko ,na yarda da kai sissae Abdul maleeku idan Allah ya kaimu gobe zan fada maka wacece safeena ,tana rayuwane kewaye da makiyanta ……" Wata yar takarda ta fito dauke da address da number waya a kasan number an rubuta Malam ibrahim daurama ta mika mashi tana fadin "Ga address da number wayar mutumin da zaka nema , zaka karbo man sakone daga gareshi idan kaje ka kira numberta zamuyi magana dashi ……" Karba yayi ya mike yana mata bankwana Ko da yaje gidan bai iske nana a tsakar gida ba ,da yake yanzu tana samun saukin Inna tunda yana kawo kudi da kayan abinci ……Dakin inna ya leka ya gaida ita lokacin har nanar tayi bacci ……kudin cefanen gobe ya bata sannan ya tafi inda yake kwana don so yace tunda safe ya wuce aiken granny …… 《《《《《》》》》》 Baisha wahala gurin gane malamin ba ,da yake sanannene ,bayan sun gaisa ya masa bayanin daga inda yake cikin faraa ya amsheshi sannan ya saka aka kawo mashi fura mai sanyi …… ,shi ganshi ya gamsu da malamin domin yana cike da kamala da natsuwa sannan a falon da aka saukeshi babu komae face litattafan addini da,kamshin miskin dake tashi ……Ga tsantsae kama da yake da granny kamar an tsaga kara ,ko baa fada mashi ba ya san cewa dan uwanta ne,…… Waya ya fito ya kira granny suka gaisa cike da barkwanci yana tambayarta ya safeena,…… Baiji me take cewa ba sae dae yaji yace "In Allah ya yarda babu abunda zai cutar da safeena don Allah ba Azzalumin bawansa bane ,wancan ma da sukayi Allah ya ara masu rana ne kafin ya karbi abunsa ……" Sun dan,jima suna maganganunsu kafin ya kashe wayar yana kallon fuskar Abdul Maleek din yace "Kanaji muna ta surutu ko ……" "aa bakomae wallahi "ya fada fuskarshi dauke da murmushi …… Dan murmushi malamin yayi sannan ya mike ya shiga wani daki ya,fito rike da wani dan karamin littafi na larabci sae wata karamar kwalba kamar almiski ya mika mashi yace ya kai mata …… *FEEDOHM💞* [9:37PM, 10/20/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹* 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 © *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM💞_* *Devoted to Ummi A'isha👌🏻* *_YA ILAHI 🤦🏻‍♀ jama'a ku duba da kyau ba novel bane kawae happy birthday nawa billy ladan amma ba wae yana nufin zan cigaba da typing dinshi ba ……wasu ma wae na badu complete document aa ba document ba decomo😂😂_* 1⃣6⃣ Wajen Karfe 11 ya dawo katsina sae da yaje office yayi signing sannan ya wuce gidansu safeena don yana bukatar kara ganinta kafin ya wuce gidan granny …… Garden ya hangota zaune ita da wani mutumi duk da sun juya baya hakan bai hanashi gane JB bane ……wani abu ya tokare mashi kirji bai karasa ba ya juya da sauri zai fita karo yayi da mutun ya dago yana fadin "Sorry……" "Sorry ……"itama ta fada cikin saurin maganarta tare da dukawa ta dauko mashi,key dinshi da ya fadi …… "Very Sorry ban lura da kai bane kaji ……" ta fada tana kallon fuskarshi Gaba yayi abunshi yana kallon kasa ba tare da ya amsa ba ……ita kam binshi tayi da kallo har ya bar harabar gidan sannan ta sake ajiyar zuciya, ta shige gidan da sauri tana kwala kira "Aunty Fatee……! Aunty fateen ta fito daga part din Abbah tana fadin "wannan kira haka fadila kamar mai shirin cika gidan ……" "Aunty nayi gamo wallahi duk na rude ……" "To Allah ya kyauta ,tukun ma me ya rudaki haka ……" "Wani gentle na gani ya fita daga gidan nan Wayeshi Aunty ……" "Mtsww ke mahaukaciya ce wallahi shine zaki shigo kina kwala man kira haka , to ba wanda ya fita anan sae dae idan da aljan kikayi gamon……" Itama karamin tsakin taja sannan ta zube saman kujera tana kallon labulen dake yayewa a hankali ……ganin safeena ce ya sakata sake jan wani karamin tsakin tana daukar remote…… Kujeran dake facing din fadilan ta zauna ba tare da ta kulata ba ,gyarawa tayi ta kwanta sossae tana danna wayarta …… "Ke bakya iyawa mutane magana dan ubanki ……"fadilan ta fada tana kallonta, "Mtsww ni wallahi na rasa me ke damun hajiyarku ,tana ganin mutane na hauka bara ta iya kaisu asibiti ba ,salon su fara dukan mutane kuma a rasa yarda zaayi dasu ……" ta fada hankalinta na ga wayarta Aharzuke fadilan tace "ke da ubanwa kike ……" Kallonta tayi na yan mintina sannan ta mike ta bar gurin …… 《《《《》》》》 Abdul maleek kam jiki a sanyaye ya karasa gidan granny sakonta ya bata sannan ya zauna ……ba tare da bata lokaci ba ta fara bashi labarin …… *_TUSHIYAR LABARIN……_* Abdul maleeku kamar yarda ka sani sunana Hajiya rabi mijina kuma Alhaji shehu tun lokacin da bai da komae na aureshi har Allah ya bude mashi kasuwa arzikinshi ya fara bunkasa ……ina da kawata aminiya hajiya shafa'u mahaifiyar su Fatee auntynsu safeena kenan ……shafa'u aminiyatace sossae duk wani sirri nawa dana mijina ta sanshi babban kuskuren dayi kenan na sanin sirrin mijina da tayi ,a lokacin bata da gurin zuwa sae gidana ,na mayar da ita kamar yar'uwata na saki jiki da ita yarda baka tunani ……mijina ya san amintar dake tsakaninmu da ita don Haka shima ya sake da lamarinta Kwatsam sae naji mijina na neman auren shafa'u harga Allah ban kawo komae ba a raina don nayi imani matar wani bata auren mijin wata ……bayan lokaci amarya ta tare gidan mijinta na kuma rungumeta kamar da ,amma sae dae ita sam bata daukeni a bakin komae ba face kishiyarta makiyarta ……tana zuwa da shekara daya ta dire yarinyarta mai suna zubaida haihuwar yarinyar tazo da salo iri iri don har ta kai bana daukar diyar sae ace tsinkulinta nake …… Kasan kowa da irin kaddarar da Allah ya daura mashi to ni kaddarata ta rashin haihuwace don sae da nayi shekara 18 da aure sannan na samu haihuwa na samu AISHA,a lokacin Shafa'u tana da yara uku ZUBAIDA ,SARATU,HINDE ,bayan na haifi AISHA ne ta haifi FATEE DASALMANU Wanda ka fi sani da UNCLE ABBA Akokarin maigidanmu na ya hada kanmu guri guda amma sam abun ya gagara kamar yana gini ne ana rushewa AISHA ta tashi cikin tsana da tsangwamar yan uwanta ko kadan basa kaunarta dalilinsu kuwa shine ta fisu kyau sannan ko wa yazo gidan baya da magana sae tatata tana da saurin shiga rai farat daya …… A irin wannan halinne har ta girma cikinsu sannan abun Allah duk ta rigasu samun mijin aure ……wannan auren ba karamin tada hankalinsu yayi ba don na tabbata lokacin ne hajiya shafa'u ta fara neman bokaye …… Amma da yake Allah ya kadarta sae tayi auren to babu makawa akayi shi bayan bikinne da watanni kadan Allah yayiwa mijin namu rasuwa ……a tunanina lokacin kishin zai ragu tunda wanda akeyi domin shi ya rigaya ya tafi amma ashe abun ba haka yake ba lokacin mane duk wani kishi,nawa ya koma gun diyata saboda tana auren masu kudi …… Bayan lokaci kadan zubaida itama ta samu miji bata cika shekara daya ba ta haihu ……sae sabon tsegumi ya tashi cewa Aisha bata haihuwa ,sam daga ni har ita ba wanda ya damu domin haihuwa ta Allah ce haka dangin mijinta basu nuna komae ba dangane da rashi haihuwarta …… Sae da zubaida ta haifi Fadila ,maryam da jamila sannan ALLAH ya bawa AIshata ita ya'yanta yan biyu duka mata…… *FEEDOHM💞* [1:29AM, 10/21/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹* 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 © *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM💞_* *Devoted to Ummi A'isha👌🏻* 1⃣7⃣ Lokacin da AISHA ta haifi su safeena sae zancen ya banbanta hajiya shafa'u ta rude akan itama kyawawan jikoki take so kamar nawa ……sae ta fara tunanin idan diyarta ta auri Abbansu safeena to tabbas itama zata haifi kyawawa , ta manta da mai kyau da mai muni duk na Allah ne …… Alokacin fatee kadae ta rage mata tayi aure sae ta fara bin bokaye a kan lallae Aisha ta mutu fatee ta aureshi …… Ina Zaune gidana Aisha ta sameni tana kuka tace ita kam ta gaji da wannan rayuwa kusan watanta 5 tana bleeding abun ba tsayawa ,sunje asibiti ance ba maganin asibiti ya makamata su nema ba …… Ni da kaina naje daura na fadawa dan uwana malan ibrahim shi yace man asirine a ka mata amma insha Allah zaa magance haka …… Lokacin dana fada mata cewa tayi "Haba Ummi taya zaa ce asiri ya kamani bayan kullun cikin tsarkake addinina nake ga Allah fa nake neman kariya gaskia ba asiri bane kawae ana so a hadani da yan uwana ……" Nace "a Kul Aisha ,don kina tsarkake addininki sae kuma akace Allah bara ya jarabeki ba ?shin lokacin da akama mqnzonmu asiri shi rashin tsarkake addinin ne ya saka ya kamashi ? Aisha ki natsu ko da a masallaci kike kwana Allah zaya iya jarabki ta ko wace hanya ,ki dauka wannan itace kalar jarabawar da Allah ya daura maki ……" Haka ta tafi tana kuka ,bayan kwana 10 da naji shiru sae na tashi naje har gidan na sameta ……tun daga bakin falon naji muryarta cikin kuka tana fadin "Ka sawake man dan girman Allah ALHAJI wallahi baran iya wannan rayuwar kaskancin ba ,baran juri ina matarka ba amma kullun cikin wulakanci su kansu yayan da ka haifa baka kulasu ……" Cikin hargowa yake fadin "Har sae kin bari na sawake maki Aisha ,hanya a bude take kina iya tafiya abunki ……taya zan zauna da mata kamar ina zaune da wani namiji sam wallahi baran jura ba ……ya'ya kuma da kike magana ko yanzu kika tsallakesu na tabbata wadda zata zo zata kula dasu ……" Kasa karasawa gidan nayi na juya jiki a sabule ko gida ban iya komawa ba tasha naje na hau motar daura na iske malan Ibrahim cikin kuka na fada mashi abunda ke faruwa Blackseed ya bani mai da garinshi tare da garin magarya yace na bata ta dinga wanka dasu tana sha man blackseed din sannan ya hada man da pure almiski tare da olive yace duk ta dinga amfani dasu ……sannan ya dauko husnul muslim ya hada man yace ta rike azkar…… Haka na dawo da wannan hadin na wuce gida kafin zuwa safe na kai mata ……sae dae daga bakin kofar na jiyo kukan su safeena hakan ya tabbatar man da cewa aikin gama ya gama …… Ganin tana kuka ga yara duka biyu a hannunta ya sakani karban yaran ba tare da na tambayeta baa sin zuwantan ba …… Kusan watanta biyu Alhaji khaleed bai leko mu ba ,cin yayanshi da matarshi duka yana hannuna ……da na gaji na taka har gidanshi na iskeshi a can na iske Aunty fatee zaune a falo suna fira hankali kwance Lokacin ne na kara tabbatar da abunda malan ibrahim ya fada man ,ina tabbatar maka ban baro gidan ba sae da takardar sakim Aisha a hannuna …… Haka muka cigaba da rayuwa yau da dadi gobe babu ,magunguna kuwa kullun cikin hado mana malan ibrahim yake amma sam abun kamar kara cigaba yake Cikin yan kwanakinne muka samu labarim cewa Abban safeena zai auri fatee ……duk a tunanina zan ga damuwa a fuskar Aisha amma sam abun bai dameta ba sae dae fatan alkhairi da ta masu …… Har akayi bikin Alhaji khaleed da Fatee bai nemi yaranshi ba sannan ni kuma ban nemeshi ba akan maganar yaran …… Bayan Auren da shekara daya ne Allah ya ma Aisha rasuwa ba tare da wani ciwo ba kawae mun wayi garine ta rasu ,daga hajiya shafa'u har iyalenta babu wanda yazo man gaisuwa har yau ……shi kanshi Alhaji Khaleed din bai zo ba sae da aka shekara biyu lokacin su safeena sunyi wayau sossae …… Da kuka yazo ,yana tabbatar man cewa wallahi bai san meke faruwa ba ,Allah ya kyauta na bishi da ita don har ga Allah duk da ba cikin hankalinshi yayi komae ba amma tabonshi na raina …… Yana zaune Safeena da nafeesa suka shigo rike da hannun juna ……da yake ba saninshi sukayi ba ko kallon inda yake babu wanda yayi a cikinsu …… Cike da kunyarsu ya mika hannu zai dauki Nafeesar da yake tafi Safeenar hakuri ……yarinyar ta washe baki zata je amma safeenar ta kabe hannun tana hararanshi tare da janye hannun nafeesar suka koma gurina …… Hakan ba karamin dadi yayi man ba tunda ban hanasu zuwa gurin babansu ba amma gashi safeenar ta hana yayartata …… "Safeena ku zo kunji ko 'dan Allah ku matso naji dumin ku ya'yana ……"ya fada tare da kara mika hannu Cikin maganar da bata cika mata baki ba tace "bala a zo in ba ,Nafeesa um um kalki je ,idan kika je balan yan'maki siwi ina ba ……" Dukar da kai yayi yana hawaye ,sossae naji tausayinshi ya kamani na kalli safeena don ina da tabbacin tunda tace kar nafeesar taje bara taje ba nace "Husaina Abbanki fane ,kuje kunji ko ……" "Balan je ba ……wallahi balan je ba " ta fada tana jiniyar kuka *FEEDOHM💞* [6:52PM, 10/21/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹* 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 © *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM💞_* *Devoted to Ummi A'isha👌🏻* 1⃣8⃣ Cikin sanyin jiki ya kalleni sannan ya sadda kanshi a kasa ,tausayinshi ya kara kamani na janyo hannun safeena ina fadin "Zaki sha siwi husaina ……" "Ni nafeesa zamu sha a tare kaka ……" "Yauwa to indae zaki sha kije gurin wannan sae ya sayo maki kinji ko ……" Kallon nafeesar tayi sannan ta kalli Abban nata dake duke kamar me neman gafara ,Janyo hannun nafeesar tayi ta matsa gurinshi tana kallonshi …… Da sauri ya rungumesu yana fitar da numfashi a hankali ……mintina kadan tayi sannan ta fara kokarin kwacewa daga jikinshi tana dukanshi a baya tare da fadin "Sakeni ka bani siwi in ……kaka yaki bani siwi ina nafeesa sakeshi kema ……" Tun daga lokacin kusan kullun sae yaxo gidan Fatee kam har lokacin sun kulle mashi baki baya iya tabuka komae a kanta da su kaga ya fara ja da baya da lamurransu sae suka zuga fateen ta koma kissa da kisisina tare da kokarin dole sae ya maido su safeenar gidanshi domin zata fi kula dasu …… Alokacin da yazo man da zancen zai karbi yayanshi ban musa mashi ba domin na tabbata safeena ba kanwar lasa bace duk da tana karama sannan duk wanda aka bawa rikon safeena to tabbas indae zai cuceta sae shima ya koka ……matsalata daya kawae nafeesa domin Allah ya zuba mata ruwan hakuri sak mahaifiyarta ce ,don tasha safeenar ta janyo fada a kama nafeesar a daka kuma bara ta taba cewa ba ita bace tayi lafin ……sannan nayi imani cewa yanzu yana kaunar yaranshi fiye da zato …… Da dubara aka dauke yaran daga hannuna aka mayar da rikonsu ga Fatee…… Wata ba hagguwar rayuwa suka soma a wajen fatee ,idan Alhaji na gida zata tarairayesu amma idan baya nan cuta kala kala zata masu ,a lokacin basu wuce shekara biyar biyar ba amma aikin gida babu wanda nafeesar bata iya ba ……Safeena tana samun sauki sossae domin duk abunda zaa mata zata nemi hanyar fanshewa …… Ranar juma'a naje gidan dubasu kamar yarda na saba duk sati …… Tun daga harabar gidan naji fatin na bala'in wae ta aje gwangwanin madara amma Safeena ta zubar dashi …… Ihun dana jiyo ne ya sani hanzarin karasa ciki Nafeesa na gani tana duka da handbell kamar tana dukan wani kato , cikin sauri na karbeta ina fadin "Subhanallah ya haka fateema me ke faruwa ne ……? A harzuke tace "dan uwar yarinyar nan na aje madara duka yau na fasata amma ta zubar man da ita duka ……" "Fateema ai hakuri ake da yara kinji ko ……ina safeenar take ……" na tambaya ina karewa falon kallo ko zan ganta Daga saman benen naji ana fadin"kaka ganinan sarkan ne yaki wucewa ……yauwa ya wuce bara na fito……" Ta fito da gudunta tana harara kasa kasa ko baa fada ba nasan da Auntyn tata take ……kallon nafeesar tayi da har yanzu tana hannuna tace "kiyi shiru Allah ya saka maki tunda Allah ya sani bake kika zubar ba ……" A sanyaye nafeesae tace "Ni na zubar mana ……" "Dalla can ni fa ce na zubar ba na sani ba shine ta kamaki tadaka ai na rama maki don na kwashe sarkokinta duka na zubar a masae ……" Hannu ta daura saman kai tana sallallami kafin ta nufi sama da gudu ta duba inda take aje gold dinta babu komae …… Ina jiyo ihunta na tabbatar da abunda safeenar ta fada gaskiayane ……ko kadan banji haushinta ba kafin fateen ta fito naja jikokina muka bar gidan …… Sun kusan wata gurina da kyar na yarda na bashi su Ko Wata daya baa kulla ba akace man wae nafeesa ta fado daga saman bene kanta ya fashe an kaita asibiti …… *FEEDOHM💞* [7:46PM, 10/21/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹* 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 © *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM💞_* *Devoted to Ummi A'isha👌🏻* 1⃣9⃣ A kidime na iskesu FMC a harabar asibitin na iske Alhajin ya fito a rude ,tun daga lokacin jikina yayi sanyi ,na tareshi ina tambayarshi lafiya "Nafeesa ta tafi Umma ……"abunda yake fada kenan Jiki a mace na karasa dakin da suke a can na iske Safeenar kwance saman jikin yar uwar tata tana kuka ,Su fatee suna tsaye cirko cirko kai da gani jikinsu yayi sanyi Saitin kunnenta ta matsa cikin kuka take fadin "Idan baki tashi ba nafeesa baran,baki sweet dina ba ……kinganta nan a bayana na boye ,ki tashi kinji ……" Tana jin tafiyata ta dago a tsiwace tana fadin "Karku zo nan ,kada wanda ya matso kusa damu ……" "Safeena ……kalleni nice fa " na fada a sanyaye Da sauri ta juyo ta rungumeni tana kuka ……"Kaka nafeesata kalli jini a kanta ……wae Abbana yace bara ta tashi ba ,ai dae zata tashi ko kaka?wasa nake mata zan bata sweet din kaka so nake kawae ta tashi ,tsaya ki gani ……" Komawa tayi kusa da ita tare da rike mata hannu tana fadi "Kinga sweet din tashi na baki to ,bude bakinki na saka maki akwae dadi ……" Sossae na rungumeta ina sauke ajiyar zuciya tausayinta ke ratsa dukkan jikina Atare a ka haifesu rabuwarsu dole tayi mata kunci "Kaka kuma ba ita bace ta batawa Aunty fati gaban mirrow ba ni ce kaka, amma ta kamata ta jehota daga bene……" Maganar ta dakeni sossae nayi saurin dagota daga jikina ina kallonta cike da shakkun abunda ta fada Cikin kyarma nace "me kika ce Safeena ……" "Kaka ba ita bace tawa Aunty fatee laifi ba nice nayi kawae don taga shaidar da tayi mani don ta dinga ganeni a jikin Nafeesa shine tace nice ta kamata ta jeho daga saman bene ……" "Wace irin shaida Safeena ……" na fada a rude Hannun rigarta ta dage ,wani tambarin dutsin guga ya fito sossae a hannun "Kin ganshi kaka tun lokacin da ta man shi ina kuka sae Nafeesar itama ta dauka tayi wa kanta don taji zafin da naji ita ……" Daukarta nayi na fita daga asibitin da sauri ba tare da na furta kalma ko daya ba …… Daddare Abbanta yazo daukarta sam kin bashi ita nayi sannan ban fada mashi abunda ke faruwa ba na barshi akan daga saman benen ta fadk …… Tun daga lokacin rikon safeena ya dawo hannuna Abbanta kuwa kullun yana gidana tare da diyarshi sannan banyi kasa a guiwa ba gurin bata magunguna da addu'o'in kariya daga sammu haka bata da ruwan wanka da ya wuce ruwan ganyen magarya …… Tun tana kankanuwa ake binta da mugunta amma Allah na kareta asiri kuwa ita da kanta idan tana wasa zata kawo man layu tace tsinta tayi tana rami ……sae idan mun kwancesu sae kaga sunan Safeena da rubutun ajami …… Haka muka cigaba da rayuwa har sae da takai shekara 18 lokacin ne na tabbata babu wani mahalukin daya isa ya cutar da ita indae ta fannin zama ne sae dae ko ta asiri domin babu wanda ya wuce shi ,Sannan ne ta koma gidan ubanta …… _*CIGABAN LABARIN……*_ Tunda ta fara bashi labarin kanshi na kasa sae da yaji ta tsaya sannan ya dago a hankali yana kallonta …… "Kaka kina sane da Aunty fatee ta kashe mata yar uwa kuma kika barta ……" Yar dariya tayi tace "to ya zan mata Abdul Maleeku ?zan kasheta ne nima ……" "A'a kaka amma ai akwae hukuma ……" "Kwarae kam akwae hukuma ,shi yasa muka barta da babbar hukuma wacce bata da kudi ko nasaba da zata iya sayen alkalinta ……" Lumshe ido yayi tare da mikewa "Kaka zan tafi nagode sossae ……" "Allah ya kiyaye yau de baran ce ka tsaya kaci abinci ba bare ka cinye man dan wanda na rage na dare ……" ta fada cike da zolaya Dan juyo yayi yana dariya "abun har da gori ……" "Eh mana ,kaje kayi aure ka tsaya kullun kana gaban yar kanwarka kana soke kai kana kiran Madem……" ta karashe maganar tana kwaikwayon yarda yakewa Safeena idan sunzo gida Fita yayi falon yana dariya ,har ya bar unguwar bai bar dariyar Kaka ba ……Sossae tsohuwar take burgeshi duk da jikarta yake wa aiki amma hakan bai hanata fada mashi magana ba …… *FEEDOHM💞* [6:57PM, 10/22/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹* 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 © *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM💞_* *Devoted to Ummi A'isha👌🏻* 2⃣0⃣ Gyaran murya yayi bayan ya kammala lecture din sannan ya daga kai yana kallon gefen da yan matan ke zaune "Safeena khaleed ……" "Yes Sir……"ta fada a hankali tare da kallon matashin lecturer dake tsaye gaban bar din "Meet me in my office now……"ya fada tare da tattara DDs dinshi Gabanta ne yayi bala'in faduwa ta bishi da kallo har ya fita daga chamber din "Akan me zan sameshi a office Maryam ……"ta fada tana kallonta "Nima abunda nake tambaya kenan Feena ,ko kuna da wani issue ne dashi ……" Tabe baki tayi tana parking takardunta da ta zubar a saman kujeran "No……Beside ma ban taba magana dashi ba ……" "Ki je kiji abunda zai ce maki but you shld take care……"ta karashe maganar tana kallon fuskarta "What ever ma i should deal wit it ……ki jirani yanzu zan dawo" "Imagine har kin san ma yanzu zaki dawo……pee!! Bata kuma cewa komae ba ta dauki phone dinta ta fita ……area da office din nashi yake sam babu hayaniya a hankali ta tura kofar office ta shiga dauke da sallama ……yana shingide saman kujera ido a lumshe kamar mai bacci …… Bude idon yayi kanta tare da sake mata murmushi ……itama murmushin ta mayar mashi tana kallonshi "Have a sit Feenat ……"ya fada yana nuna mata kujeran dake facing tashi Sossae ta zauna tare da tallabe kumatunta tana kallonshi ,gaba daya natsuwarta ta maida kanshi …… "You're Suprise na kiraki ko ……" Gyada mashi kai tayi ba tare da tace uffan ba "Ki bar mamaki kinji baby ,as classic as you bai kamata kiyi mamaki ba dan handsome kamana ya nemeki you deserve it ……nasan kullun kina kallon mirrow kuma kinyi nayzing kyawun dake gareki ……" Yar dariya ta sake tana maimaita handsome a ranta ……ta tabbata ko drivernta Maleek ya fishi nesa ba kusa ba …… Ganin tana dariya ya sakashi dawowa bisa desk din dake tsakaninsu ya zauna "Feenat baby ……kinsan rayuwar duniya taimakeni na taimake ka ne ko ……" Yar dariyar ta sakeyi tana kallonshi,bata so ta katse mashi hanzari ta fi son ta kaishi har inda take bukata …… "Feena duk wasu da kike ganin sun fuce da first class da taimakon mu ne ……kema abu mai saukine ki fita fresh indae zaki hau hanya ,ki bani in baki baby ba rowa ,ni nan da kike gani idan na tsayawa yarinya ko VC bai isa ya ta ka ta ba ……" "Kaman gwari gwari Sir yarda zan fahimta……" Yar dariya ya sake yace "kamar wata bakauya ,to ina nufin ki taimakeni na taimakeki kema ,……" "Wane irin taimako Sir , kudi kake bukata ko me ……amma a nawa tunanin ni bana bukatar taimakonka" "Oh Feenat kamar ba wayayya ba ……ok i means mu dinga making love ……karki damu babu wanda zai sani ……" "Good anzo gurin ,ban taba tunanin kai wawa bane sae yau karka manta Safeenat Khaleed ce a gabanka yanzu ……idan ka saba lalata yaran mutane to ni nafi karfin jakkancinka ……" Yar siririyar dariya ya sake yana fadin "Yarinya kina wasa da result dinki ……" "Ko kuma kana wasa da aikinka ba……"ta fada tare da fito wayarta ta kunna Tun daga farkon shigowarta har maganar da sukayi yanzu tayi recording …… Mikewa tsaye tayi tana fadin "Ni ba irin jahilan matan da zan shigo office din mazinaci irinka ba kai tsaye ba tare da na shirya ba ……" A firgice ya mike yana nunota "Ke ni zaki wulakanta wallahi baki isa ba ……" "If you step one hnd I'll chop your leg's ……A Tunaninka zaka karbe wayar ne daga hannuna ……so look here ……"ta fada tare da kanga mashi wayar a fuskarshi …… Recording din da tayine yaga anyi forwarded to GRANNY,MALEEK &Maryam…… "Nasha fada maka ni ba jahilan yarinyar da zan shigo office din mutumin irinka,bace ba tare da na shirya ba ……" Tuni zufa ta fara wanke mashi jikin tsabar tsoro da nadama suka mamaye fuskarshi cikin rudu yace "Ki rufa man asiri dan Girman ALLAH Safeena ki goge wallahi ba yin kaina bane Uncle dinki ya sani dan Allah kiyi hakuri wallahi da kyar na samu aikinnan idan kika nuna wannan abun wallahi licenses na aikina za'ayi cancel dan girman Allah ki yi hakuri……" "I Know Uncle Abba ko ……kayi sharing tears dinka dashi……" ficewa tayi ta barshi a tsaye rike da kai Tana isa ta karbi phone din maryam ta goge recording din Allah ya sota maryam din bata duba text din daya shigo ba ……Har ga Allah batayi niyyar yad'a shi ba ta tura masu recording din don ta kwaci kanta don ta tabbata idan ba haka tayi,ba yana iya karbe wayar da karfin tsiya sannan ya mata abunda yaga dama…… Wayar Abdulmaleek ta kira taji ta a kashe ,sossae taji dadi don dama taga txt din baiyi delivering ba ……bari tayi kawae idan sun hadu ta karbi wayar ta goge tunda ta lura ba cika hawa whatsApp din yayi ba ……Granny kadae ce bata shakkar taganshi saboda ta tabbata barata taba fadawa wani ba ,ita kanta tasha fadawa safeenar cewa karta yarda ta tonawa dan adam asiri komae girman laifin da ya mata …… *FEEDOHM💞* [8:10PM, 10/22/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹* 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 © *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM💞_* *Devoted to Ummi A'isha👌🏻* 2⃣1⃣ Maryam ta kalla da tunda ta dawo take kallonta ,janyo hannunta maryam din tayi tana kara karantar yanayin fuskarta ……cikin sanyin murya tace "Feena me ne ?are you ok……? Dan murmushin dole ta sake ta gyada mata kai tana kokarin mikewa tsaye "Safeena are you sure……kina lafiya "ta sake fada domin har lokacin hankalinta bai kwanta ba da aminiyar tata "Assured Maryam me kika gani ne ……" "Nothing amma ya kukayi dashi ……"ta fada tana kallon gefensu "Oh ni Safeena meye na damuwa ?kinga maryam karki damu dama cewa yayi wae Uncle Abba ya nemi phone dina bai samu ba shine ya kirashi yace ya fada man wae Hajiyarsu Aunty fatee batta lafiya ……" "Kin tabbata Feena?kuma shine sae ya kiraki office dinshi ,kinga ni wallahi sam hankalina bai kwanta ba tunda kika tafi wallahi saura kadan na bi ki sae gashi kin dawo……" "Common ni tashi ki ajeni gidansu hajiyar ma na gaidota, Number Maleek bata shiga……,meye na tashin hankali kamar naje war na horrows ……"ta karashe maganar tana hararanta Kofar gidansu Hajiyar Aunty fatin ta ajeta ,ita kanta maryam din taso ta shiga ta gaidata amma sam safeena taki barinta Daga bakin gate sukayi sallama sannan maryam din taja motarta ta tafi ta barta …… Wani dadi taji da ta jiyo muryar Uncle Abba a falo suna magana da hajiya ,saboda sallamar ta zame mata dole ya saka tayi masu …… Hajiyar ce ta amsa tana kokarin boye kiyayyar dake idonta "A'a Amaryace a gidan yau …Yau ina na kalla nayi sallah?rabon da kizo nan gidan ai har na mata………" "Amaryan Jabir Bala …ko sama da kasa kika hada kika kallah meye nawa ciki ,Allah ma yasa da alwala kikayi sallar………"ta fada tana kallon Uncle Abba Dariya hajiyar ta sake don bata san magana ta yaba mata ba "Kaniyarki Safeena ina kika taba jin anyi sallah ba alwala……" Tabe baki tayi tana kallon Uncle Abba da har lokacin bai tanka ba "Abba ……" Ta kira sunan ba tare da ta sakaya ba "Yeah Abba ko ba sunanka bane ,na lura kiran uncle din da nake maka kamar ina cutar kaina ne, shi yasa na kira sunan da uwarka ta saka maka ……" Tafa hannu hajiyar ta fara tana sallallami "Safeena kanki daya kuwa? Kawun naki kike fadawa haka ,kanin uwarki fane……" "Sorry hajiya nima da haka na dauka amma yanzu na banbance meye yan'uba ……kai na dawo kanka "ta fada tana nuno Uncle Abban da mamaki ya hanashi cewa komae "Last warning karka kuma sa wani kare ya nemi yaga man mutunci ,Idan kuma ka kara nima zan yaga rigar tsohuwa……" "La hauwala Safeena ni ……" hajiya ta fada tana nuna kanta Harara ta sake mata "yana da wata tsohuwa ne bayanke ……? Uncle Abba ya taso yana fadin " Ke baki da kunya ,Barni da ita inci uwarta hajiya ,dan uwarki har gida zaki shigo kiyiwa Hajiya rashin da'a ……" Hajiyar ta tareshi tana fadin "Barta Abba kira man iyayen nata yanzu ……"ta karashe maganar tare da share hawayen munafunci…… Juyawa tayi ta bar masu gidan ,ko ba'a fada mata ba tasan Meeting za'ayi kanta kuma ta shirya tazo sannan duk wani dan iska da yayi niyar takata a gurin zata wankeshi yarda ya dace …… 《《《《《》》》》》 Abdulmaleek kam aikine ya cakude mashi yau, ga Zaria yana son yaje amma bai samu lokaci ba sae dae ya turawa CC dinshi script din ta email dinshi saukinshi ma sun daga mashi duk wani abinda za'ayi a makarantar sae dae a turo mashi ta email sae dae duk wata yakan shiga makarantar sau daya …… Case din da yayi na yau ya bala'in rudashi na wata yar budurwace da bata wuce shekara 18 ba ,ta tari mota a bakin dandagoro bata je tasha ba, zata je garin Charanchi cikin rashin saa duka passingern motar mazane sae ita kadae mace ……sae dae suka fita gari sannan suka sauka hanya suka yanka daji suka mata fyade ,su hudu ne mazan amma babu wanda bai yi amfani da yarinyar nan ba ( _yan uwa mu guji tsayar da mota ko'ina muna shiga kara duk jiran da zakayi a tasha ka jira domin kariyar lafiyar mu……wallahi hakan na faruwa sau tari ……_) Sai da yayi sallar la'asar sannan ya bude wayarshi Number Safeena ya fara nema lokacin tana kwance a daki ita kadae tana kuka ,bata da wani wanda zatayi fira dashi taji dadi a yanzu …… Tana jin wayar na ringing ta kyaleta har sae da ta katse dan kanta ……Muryar Abbanta ta jiyo a falo yana kiran Aunty fatee ……da saurinta ta leko tana kallonshi ,a hankali ya daga ido ya kalli kofar dakinta baiyi tunanin tana bakin kofa ba ,suna hada ido ya mika mata hannu …… *FEEDOHM💞* [2:47PM, 10/24/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹* 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 © *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM💞_* *Devoted to Ummi A'isha👌🏻* 2⃣2⃣ Cikin sanyin jiki take kallonshi da idanunta da suka kawo ruwa,ta kasa gasgata cewa Abbanta ne yau ke mika mata hannu tazo gareshi ……Rabon da ta ganshi kusan wata biyu kenan …… "Common Safeena……" ya fada tare da ware duka hannuwanshi Da gudu ta taho tare da fadawa jikinshi ya maida hannayen duka ya rufe ……shi kanshi ya san yayi missing diyarshi ba kadan ba Aunty fatee da ta fito jin yana kiranta tayi mutuwar tsaye tana kallon ikon Allah ,Ayarda Aunty zuby tace mata shi da Safeena sae daga hannu amma tun baa je ko'ina ba gashi yau rike da ita a kirjinshi …… A haka ya shiga dakinshi da ita yana bubbuga bayanta a hankali ,bakin gadon ya zaunar da ita sannan shima ya zauna "Sorry Safeena ……"ya fada yana goge mata fuskarta "Insha Allahu baran sake nesa dake ba kinji diyata ,wallahi ina sonki ni kaina ban san meke damuna ba kinji ko ,kiyi tayi wa Abbanki addu'a Safeena ……" Kasa magana tayi saboda tsabar farinciki sun dade suna fira Ko Aunty fati bai nema ba haka itama bata shigo ba …… 《《《《《》》》》》 Abdul Maleek ganin bata dauki wayar ba ya sashi bude whatsapp dinshi , Text din da ta turo mashine ya fara budewa da mamaki ganin tunda take dashi basu taba magana ta chat ba ganin audio ne ya sashi ko mawa cikin motar sannan ya kunna yana ji …… "Me ake wa Safeenatah……" ya fada tare da yarda wayar da karfi "Inna lillahi wa inna ilaihir raju'un … …" ya ke fada ganin hankalinshi na neman barin jikinshi " _Uncle dinki ya sani……_ " abunda yake maimatawa kenan a ranshi …… "To wane Uncle din ?…kar dae ace ya taba madam ?waye shi ?… Madam kadae zata iya fada man "……da sauri ya fada neman numberta Ya kira yafi sau 10 bata dauka ba ,motar ya tada ya juyo ya nufo gidansu Har falon ya shiga amma bai tarad da kowa ba sake tryinh number tayi lokacin ta shigo dakin yin sallar isha'i taga kiran …… Cikin farin ciki har da juyinta tace "Abdul maleek yauwa ina nemanka ……" "Madam ina cikin falonku……" "Good bara na zo yanzu ,am kazo da wyar da kake chat da ita ……" "Yauwa……" bata fi minti biyar ba ta fito kanta ko dan kwali babu ,yanayin da ya ganta ne ya sashi jin dan sanyi sanyi kura mata ido yayi har ta karaso ta zauna kujeran dake kusa da tashi …… "Ka bude whatsapp dinka……"ta fada tana kokarin kunna tv Karantar yanayinta yayi na yan sec sannan yace "A'a Madam amma bara na bude yanzu……" Cikin sauri tace "aa karka bude bani na tura wani abu tukun ……" Juyar da kai yayi sau biyu idan ya fahimceta bata so yaga abunda ta turo ……"to me yasa bayan ita ta turo ,ko bata san ta turo mashi bane ……" Katse mashi tunani tayi ta hanyar mika mashi hannu tace "Bani phone din na tura Maleek……" Ya fahimci gogewa zatayi kuma idan ta goge baya da evidence akan abunda yake tunanin zaiyi akan wannan lecturer …… Murmushi ya sake mata tare da kokarin lalibo wayarshi yana fadin "Bara na fidda maki pin din madam……" Juyawa tayi tana fadin "Quick……" Da sauri yayi copying din audion a private Files dinshi sannan ya maida text din unread ya mika mata …… Mintina kadan ta goge abunda take so ,zata mika mashi wayar taga wata number kamar a dp dinta picture din Fadilar Aunty Zuby ce,fasa bashi tayi sae da ta bude picture din ta tabbatar da Fadilan ce sannan ta bude text din da aka turo ……ba komae bane sae pictures din love da tayi mashi sending wasu ma duk basu bude ba …… Gabanta taji ya fadi sossae ta kalleshi da sauri wanda dama ita yake kallo ……a sanyaye ta mika mashi wayarshi tare da mikewa tsaye "Madam kin tura ko ……"ya fada don ganin yanayinta ya canza *FEEDOHM💞* [8:27PM, 10/24/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹* 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 © *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM💞_* *Devoted to Ummi A'isha👌🏻* _*Aunty Sis* Here is your page All negative material circulating in you body stream be evacuate ,Rebuke every refuge of sickness, May llah destroy the grip and operation of sickness upon your life and our lovely sultee,Any evil power moving through your body loose your hold , May the Merciful be with you through out your life I HEART YOU❤❤❤_ 2⃣3⃣ A sanyaye ta gyada mashi kai tana murmushin yake ……wayar da ta miko mashi ya bi da kallo don ganin mai ya canzata lokaci guda …… "Baran je school ba gobe ……" yaji tana fada lokacin da take kokarin barin falon Kafin ya bata amsa ta wuceshi ta shige daki ……missed call din JB ta gani tana kokarin kiranshi ya kira "Wife ina kika shiga haka……?ya fada lokacin da ta daga wayar "Ina magana da Abdul maleek ne ban san ka kira ba ……" "Baby meye haka ,wa ya kawoshi gurin matana da daddare haka……? ya fada cikin daga murya "Ni ce na kirashi wat ur business dere……?itama ta fada cikin daga murya Sauko da murya yayi kasa kasa yana fadin "calm down baby meye na bata rai kuma to naji i made a mistake na kishin yarinyar da 3 weeks ta zama matana ,shikenan ko ……" Dan murmushi ta sake a hankali ,sannan ta sake jiki suna dan fira sossae …… 《《《《《》》》》》 Hajiya kam duka yaranta ta tara ranar ta da fada masu abunda safeenar ta mata har gidan har kari …… Uwar ashar Aunty zuby ta sake tana fadin" Wuyan yarinyar nan ya isa yanka hajiyarmu har gida ta shigo ta zageki kika ki bari Abba ya karya man shegiya ku barni da ita wallahi har gidan uban nata zan tarad da ita sae naci uwarta tunda bata da kunya……" Hajiya tace " Waya fada maku nima kyaleta nayi ? yanzu haka akwae layar dana karbo gurin boka nan da sati biyu zaa yi amfani da ita ya rage sauran sati daya bikinta kenan zaa zauna meeting anan gidan ,ni da kaina zan kira uban nata nace ya turo man ita ,a kujeran da zata zauna anan zaa aje layar na tabbata bara ta tashi daga gurin ba sae da yankewar jinin da zai zame mata babbar cuta ,dan na yau ba irin na jiya bane wallahi har tsutsa sae ya sakar wa shegiya ……" Aunty Fatee tace "Kai dan Allah hajiya sake fada ko naji dadi ,Yauwa nikam Fadila ta fada maku Tana son driver Safeenar……" Hajiya tace "ke rabu da shashashar wofi ,ina ita ina driver ,banda tana ma banzs ta rasa wanda zata so sae drivern safeena salon sake zubar mana da mutunci ……" Kallon kofa Aunty Fatee tayi sannan ta kalli hajiyar tana fadin "Wa yace maku driver ne kadae ?to wallahi Abbas yaron da nake aike ya fada man cewa lawyer ne babba hakanan yake mata basaja yana nuna shi talaka ne ……" A rude Aunty zuby tace "Da gaske Fatee ……? "Wallahi kuwa bara ma na kara tabbatar maku ……" nan take ta sake kiran Abbas din a wayar kuma ya sake maimaita mata cewa kusan kullun sae yaga Abdulmaleek din cikin high court sanye da kayan lawyoyi har ma yace idan ya kara ganinshi zai dauko masu photonshi ya kawo masu …… Yar dariya hajiyar ta sake tana fadin "kaga shegen yaro da arzikinshi yana boyewa a,a Su fadila an samu miji ga kudi gashi kyakykyawa ko ba komae muna mun samu masu kyau a cikin jininmu ……"ta karashe maganar tana buda。 Aunty Fatee tace "ba nan gizo ke sakar ba Maleek din fa kamar Safeenar yake so……" Harara hajiyar ta sake mata "Daena wannan zancen banzar……Su kadai Allah ke so da zasu dinga samun komae a rayuwarsu……" 《《《《《》》》》》 "Abdul maleek zo nan " ta fada tana ya fitoshi da hannu Ba musu ya matso yana kallon fuskarta " Waya baka Apple wrist din hannunka ……" Dariya ta subuce mashi yana kallonta kasa kasa sam ya manta bai canza kaya ba da zai taho hannunshi ya murza a hankali still fuskarshi dauke da murmushi ,shi kam mamakinta yake kamar wani barawo "Maleek bana son wannan halin da ka fara dauka jibi shaddar dake jikinta ……ina kake samun kudi cikin kwanakinnan ?ka tsaya matsayinka Maleek karka ce zakayi abunda ya fi karfinka ……" "Karfin hali ……wae sata a lahira "ya fada a ranshi Dagowa yayi tare da kafeta da ido yana kara jujjuya maganganunta a ranshi ,cikin sanyin murya yace "Madam oga ne ya bani 100k wannan month din……" "Sae ka rasa abunda zaka saya Maleek sae wannan ?shin babu wanda zaka taimaka mawa a rayuwarka ……Maleek kasan marayu nawane abinci ya gagaresu a yau kadan amma Maleek ka cire 40K sa sayi wrist…kayi tunani Maleek kafin ka aikata abu ……" Maganganunta sun ratsashi sossae yafi karfin minti Goma yana kalllonta yayin da ta dukar da kai tana danna wayarta ,Sae da ta dago sannan ta lura da yarda yake ……mikewa tayi tsam ta bar gurin ta koma can nesa dashi ta zauna …… *FEEDOHM💞* [4:45AM, 10/26/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹* 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 © *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM💞_* *Devoted to Ummi A'isha👌🏻* 2⃣4⃣ Ranar monday Tunda safe Abdulmaleek ya fara ciku cikun yarda zaa soke lincense na aikin wannan lecturer din da Uncle Abba ,gurin CC aka fara turashi ,baisha wahala ba tunda yana da evidence a hannunshi ,nan take ya nuna masu ,sannan yaje court dinsu aka saka mashi hannu sannan ya sake dawowa office din CC din ,within 6 hours akayi cancelling lincense dinsu ma aiki suka koma dasu da wanda yayi secondary school bassu da maraba …… Duk abunda yake sam safeena bata sani ba bare Abbanta da ko maganar bata fada mashi ba …… Tana kwance gida maryam ta kirata lokacin ma suna waya da JB tayi holding taJB din ta dauki ta maryam din "Hello besty…… Cikin farinciki maryam din tace "am very happy besty anyi cancelling lincense na Bashir Mahmoud kuma ana rumour cewa a kan kiran da ya maki ne jiya besty……" Uban tsalle tayi ta diro daga saman bed din ba tare da ta sani ba tace "How comes besty wallahi karya ne ba akan case dina bane sae dae wani abu daban gaskia……" "Na rantse maki da Allah feena kan kiran da ya maki ne ,ke bama shi kadae ba harda Uncle Abbanki wallahi ni kaina am wonder tunda kince man nothing happen ……" "Excuse kina ina yanzu?Let talk serious please……" "Wallahi besty ki……" Katse tayi tana fadin "Nay answer me……" "Ina school Feena……" Cikin sauri ta dauki hijab ta saka ta dauki wayarta Napep ta tsaida ta hau ba tare da ta kira Maleek ba ,inda suke zama ta iske maryam din ba tare da ta bari ko,zama tayi ba ta kama kafadar maryam din tana fadin"That are so fortifd against your story besty ……How comes please let once again assl my ears besty ……" "Kai besty sit down awhile mana wallahi ni kaina i might not believe without the srnsible and true avouch of mine own eyes ……" Ahankali ta zauna tana dafe kai ,"Sam ban san yarda hakan ta faru ba besty wallahi ba da sanina akayi cancelling lincense dinsu ba ……To waye yayi haka besty wallahi na rude who did this ……" Cikin Sanyin jiki tace "Amma Feena baki tunanin Abba ne ?beside ma did he do anything bad to you besty……? "No ba Abbana bane wallahi,……" "To wa kika san ya san ya kiraki think……" "Only you ,Granny and Maleek nawa forwading yarda mukayi ,kuma ke kanki maryam baki san na turo maki ba sae da na dawo na karbi phone dinki nayi deleting text din ,true talk besty Lecturer din ya nemeni da iskanci amma Nayi excping Maryam……" "To bakya tunanin Maleek ne ……" Harara ta sake mata tace "Driverna fa ina ya san hanyar da zaiyi cancelling lincense din wani ,beside ma bai san na tura mashi ba ……" Suna tsaye a gurin Bashir din yazo a rude kamar ya fasa ihu yana tambayarta me yasa ta mashi haka ,rokonta ya fara tayi hakuri ,yayi bala'in bata tausayi cikin sanyin murya tace "Wallahi Sir banda masaniya akan wannan abun ,babu yarda zaayi na saka ayi maka haka kai dan,adam ne ban san iya mutanen dake rayuwa a karkashinka ba yi maka haka na nufin durkushe duk wanda ke rayuwa a kasanka ……" hakuri ta cigaba da bashi kamar zatayi masa kuka …… Tana barin gurin ta tafi gidan granny ta fada mata duk abunda ke faruwa ,Ita kanta mamaki abun yake bata ce ma Feenar tayi ta kira mata Maleek yanzu …… Mintina kadan ya isketa a gidan ,da fara'arshi ya gaida granny yana satar kallon Feenar dake aikin danna wayarta kamar bata san da zuwanshi ba …… Dagowa tayi ta sake mashi harara ganin yana satar kallonta "Kabar kallona da dullos eyes dinka Maleek……" Murmushi yayi mai fitar da sauti yana kallon granny da ta tallabe kunci tana kallonta "Idan bakyaso a kalleki ki shiga cikk mana ……"granny tace Dan turo baki tayi ta jan kallabinta tana fadin "Wallahi granny har da ke kesawa Maleek dinnan yana kara raina ni ……"ta karashe maganar tare da shigewa dakin 《《《》》》 Sauran sati daya bikin Safeena hajiyar su Aunty fatee ta kira Abban Safeena tace lallae ya turota meeting gobe da safe ……Ce mata yayi Allah ya kaimu goben insha Allah zata zo …… Safeenar ya sama dakinta ita da su maryam lokacin suka dawo daga rabon IV ya fada mata cewa gobe taje gidan hajiya zaayi meeting sannan baya son yaji wani abu ya biyo baya ,sossae ya mata kashedi sannin halinta ya tabbata idan taje komae na iya faruwa …… Fuska ta bata tana fadin "Abba to wa zai kaini ……" "Ki kira Abdul Maleek mana ……" Rau tayi da ido kamar zata fasa kuka tace "Abba two days numbershi batta shiga …Abba ka kirashi ko baya lafiya ne please kaji ………" "to meye na bata fuska kuma ……ance maki baya lafiya ?zan kiranshi zuwa gobe ……" ya fada yana kallonta *FEEDOHM💞* [4:30PM, 10/27/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹* 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM💞_* *Devoted to Ummi A'isha👌🏻* 2⃣5⃣ A hankali ta lumshe ido tana goge kananan kwallar da suka zubo mata ……photonshi ke yawo a brain dinta sam batayi tunanin zatayi kewarshi haka ba ……� Wayarta ta dauka ta kurawa ido kamar tana karantar wani abu sannan ta saka hannu a hankali tana danna number shi ,batayi zaton ta riketa a kai ba in ba yanzu ba ……har ta gama ringing bai dauka ba ,wani dan karamin tsoki ta sake tare da saka bayan hannunta tana share kwallah da suka zubo mata …… Wahale tajuyo tana kallon maryam dake rike da wayarta tana latsawa ,zatayi magana kiranshi ya shigo mata……� Sanyayyar Ajiyar zuciya ta sake tana kokarin maida murmushin dake niyar kwace mata ,kamar mai tsoron wani abu ta kanga wayar a kunnenta ……� Hadaddiyar muryarshi taji cikin sanyi yana mata sallama ……� Rufe ido tayi sannan ta amsa sallamar tana fadin "Abdul Maleek……�" Rufe ido yayi da sauri sannan ya bude ba tare da ya amsa ba, kusan minti biyar sannan yace " i'm sick at heart madam……�"yayi maganar kasan makoshi "Wat's wrong Maleek have you had quite Tis ……�"ta fada a hankali "Bana da maganinshi Madam just pray for me ……�" Yar kwallan dake idonta ya gangaro "Maleek kaje asibiti a duba ka man please babu ciwon da baya da magani bare na zuciya ……�" "Not so madam ,i'm too much in the sun ……"Ya fada a hankaki yana dafe da goshinshi ……� "Please Ab……�" katse ta yayi "Nay Madam Nagode da kulawa ina maki fatan alkhairi a rayuwar aurenki ……"katse wayar yayi tare da dafe kanshi da ya dake bala'in juya mashi kamar an tsikareshi ya fara hada kayanshi cikin wata karamar jikkar sannan ya fito ya shiga mota ,gidansu Safeena yaje ya shigar da motar sannan ya dauki jikkarshi a hannu tare da mikawa maigadin keys din motar yace ya bawa Madam da safe da wani karamin kit ……� Tasha ya nufa direct motar zaria ya nema duk da lokacin dare ne hakan bai hanashi samun motar ba ……� Safeena naji ya datse wayar ta sake kuka a hankali tare da fadawa cinyar maryam din ,dan bubbuga bayanta maryam din take tare da fadin "Sorry……" jin ta fara shirune ya saka maryam din cewa "You love him Feenat ……�" Cikin tsawa tace "No I don't love him……he's just my driver nd he's such a kind and humble to me i really missed him……�" Dan girgiza kai maryam din tayi a hankali don sam bata yarda cewa feena din ba din ba son Maleek din take ba……� 《《《》》》� Kamar yarda Abba ya fada mata tunda safe ta shirya cikin riga da zani na atamparta ko kwalliya batayi ba don daga meeting din gidansu maryam zata wuce a can zaayi komai zuwa dare a daukesu akaisu tourist lounge inda zaayi friend's day ……� Tana shiga harabar gidan sae da gabanta ya fada a hankali taja kafarta ta karasa falon da ake meeting din ,kowa ya hallara ita kadae ce babu gefen iyaye daban haka gefensu na jikoki daban ,su fadila ta kallah ko wace tasha kunu kamar basu taba dariya ba ……tabe baki tayi tana Spreading arms dinta sannan ta matsa ta zauna a kujeran da babu kowa a sama ……� Tabe baki ta kuma yi jin uncle Abbah ya bude taro da addu'a tana fadin "Sabon salo ……�" Kamar jira Aunty zuby take ta wani nunota da hannu tana fadin "ki shiga hankalinki Fenna meye sabon salo a ciki � addu'arce baki saba ji ba a bakinshi koko me ciki……�" Cikin dakewa ta watsa mata harara tare da fadin "Ko addu'ar nace ban saba ji ba a bakinshi laifine ……" "Watch ur word's wallahi dama meeting dinnan don ke akayishi sakaran banza mara kunya ……�" cewar Aunty Bilky dake harde kusa da hajiya Tabe baki ta kuma yi tare da sakin dan tsoki tunowa da kashedin da Abbanta ya mata jiya daddare ……� Aunty Zuby tace "Zaki iya fada mana dalilinki na zuwa har cikin gida kiyiwa hajiya rashi kunya Safeena ……�" Ido ta fito waje tana fadin "Me tace na mata ……�" "Kin Fi kowa sanin zagin da kika mata mara kunyar banza……�"cewar Uncle Abbah " Baran ce ban zageta ba tunda ta riga ta fada sae dae nan gaba idan Abbah ya kuma shiga harkana to har gidan zan kuma zuwa na zageta har da wanda tace na mata yanzu zan hada mata ……�" ta fada ba tare da wani shakku ba a fuskarta Cikin sanyin muryar munafukai Aunty fatee tace "Amma Safeena kin kyauta sabida Allah komai Abbah ya maki ai kawunki ne tsakaninku bai kamata ki huce kan Hajiyarmu ba ,ko ba komae ai kakarki ce kema……�" Dariyar shakiyyanci ta saki tana kallonsu daya bayan daya ba tare da tace komae ba ji tayi Uncle Abbah na fadin "Kuma dan Uwar yarinyar nan ……�" "Dallah dakata malan karka kuma zagar man uwa wallahi duk abinda zaku fada zan jure amma banda zagin uwata ……�"ta katse mashi magana tana nunashi da hannu Aunty Zuby ta taso tana fadin "An zageta din dan Ubanki wato ke Safeena baraki taba girmama mu ba a matsayin yan uwan uwarki ba ko ……�" "Me kuka taba mata Aunty Zuby ……" ta fada tare da kafesu da ido daya bayan daya Hajiya kam ko kala bata ce tun da suke maganganunsu sae yanzu da ta dago da niyar magana Aunty bilki ta tsayar da ita da hannu tana fadin "Barmu da ita hajiya Zaki biyamu ne abunda muka maki ke da uwar taki ……" A Harzuke tace "Yeah uwar me kuka mamana a rayuwar banda cuta da zalunci shi kuke so na ramata? no wannan na barku da Allah amma ni wanda kuka man zan iya biyanku na tabbata ku duka baku wuce ku ce kun sayi rigar 1500 ba kun bani well ga kudinku "ta bude jikka ta ciro rapper ta 500 ta zube saman hannun kujeran da take zaune sannan ta cigaba da fadin "ke kuma Aunty fatee bai wuce kice kin man wahala ba wanda nasan karya kike da wayauna na dawo gurinki ,zan iya rantsewa sau daya kika taba man wanka kika wanke man kashi sannan kika goya yar uwata……idan kina bukata ki dauko zani kizo na rama maki goyonki sannan kiyi kashi kiga idan ban wanke maki ba ……�" Bata Saurari kowa ba ta mike zata fita ,jin lema a zaninta ya sata kallon kujeran da ta zauna da sauri ,gabanta ya fadi ganin gurin yayi staining da yawa a tunaninta two week's kenan da gama period dinta ……� Dakewa tayi tare da sake masu harara tayi hanyar fita ,ji tayi su duka sun dauki shewa tare da tabawa ……� Tajuyo a fusace tana fadin "Cikin ku babu dan iskan da baya menstruation so i don't care idan nayi staining a gabanku……then kadan dan iskan da ya kara kirana da sunan diyarshi da na fita daga wannan gidan yau……" Tana jinsu suka sake kwashewa da dariya Fadila na fadin "Dama uban wa zai kiraki da diyarshi a haka ……" Bata kulasu ba ta fice daga gidan makwabtan gidan ta shiga da yake suna gaisawa da budurwar gidan ……Pad ta bata tare da sabon pant ta yi wanka ta canza ,kafin ma ta fito wankan har ta sa washing machine ta wanke mata zanin sannan ta sakashi a dryer ya bushe ta bata ta maida ……� *FEEDOHM💞* [8:33AM, 10/28/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹* 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 © *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM💞_* *Devoted to Ummi A'isha👌🏻* *Bestowed to Aunty Sis💕* _Assalamu Alaikum Dan girman Allah kar warda ta sake bina pc tace na bata book daga farko ,wallahi na gaji sam baran iya ba binku ina baku ba ,shi kanshi copying 20 tis ba abu bane mai sauki ,sannan tun daga farko na fara posting dinshi ban tsallake ko da one page ba a duk groups din da nake sae kuma nayi nisa a dinga saka man wani sabon aiki to gaskia baran iya ba…… idan kina so sae anyi nisa sannan ki fara bin book to kamata yayi kiyi starred dinshi ……kar ki man magana naki tura maki kiga kamar wulakancine baran iya bane gaskia 🤒🤒_ 2⃣6⃣ Party sossae akayi na kece raini amma sam hankalin amaryar baya jikinta wajen 10pm aka gama partyn ……Safeena kin shiga tayi motar JB din duk nacin shi sae dae ya hakura Maryam ta tafi da ita …… "Feena wae lafiya kike ?ki zauna sossae man……" Maryam fada tana kallonta Girgiza kai tayi a hankali tana matse idonta ba tare da tace komae ba …… Kamo hannunta Maryam din tayi tare da damkewa cikin nata "Feenat me ne……? "Am totally comfortless Maryam ……"Ta fada tana kallon window "Fada man mene Feenat ……" Ta sausauta murya tare da kamo hannunta "Ki kaini gidan granny please ina son magana da ita yanzu ……"ta karashe maganar tare da mikewa daga kujeran motar da sauri har tana bigewa …… Shiru maryam tayi ganin idonta ya kawo ruwa kadan ya rage ta sakar mata kuka………dafe gefen cikinta da ke murda mata da karfi tayi ta kwantar da kanta saman cinyoyinta…… Kofar gidan granny din tayi parking ta fito tare da zagayowa ta bude gefen da Feena din take tana kallon yarda take ta uwar zufa duk da sanyin motar …… Dafa bayanta tayi tare da dukar da kanta tana fadin "Sorry besty mun iso ……" A wahale ta dago sannan ta mayar da kanta ta kife a saman cinyarta tana cije upper lip dinta da karfi , tafi kusan minti biyar sannan ta sauko da fararen kafafuwanta da ke sanye da hills red kasa ……a dafe ta fito daga motar tana dafa Maryam ,sae da ta gama saukowa gaba daya sannan ta juya tana kallon inda ta zauna lokaci guda ta kalli Maryam tana share hawaye da bayan hannunta na dama…… Dan murmushi maryam ta sake tana girgiza mata kai a hankali "I'll clean……" ta fada tare da kama hannunta ta rufe marfin motar suka shiga gidan Granny din …… Maryam nayin Sallama granny ta amsa tana fadin "A'a kaga yan albarka Haba shi yasa tun dazu nake jin kamshin amare Allah yasa kayan partyn nima aka kawo man ……" Karasa sukayi falon maryam na fadin "Wani kayan party zaa kawo maki granny? to ki ci su da wanne hakora ……" Yar dariya granny ta yi tare da rufe fridge din ta juyo tana kallonsu ,lokaci guda ta zubawa Feena ido tana fadin "Lafiya kike rike ciki Safeena ……" Bisa doguwar kujera maryam ta daurata ,tayi saurin zamewa tana kallon ta tare da sake kuka …… Idanuwan Maryam itama suka kawo kwallah tana fadin "kar ki kwanta a kasa Feena ……" "Maryam so kike na bata mata kujeru?ki barni a nan tun dazu nake saki aiki Maryam……"ta karashe maganar cikin kuka "Nace maki baran gyara bane Feena?ko nace maki na gaji ne? karki kwanta a tiles akwae sanyi besty……"ta fada murya na rawa Granny ta matso tana fadin "Me ke faruwane Maryam?bata lafiya ne?husaina menene……? Wani kuka ta sake mai ban tausayi maryam ta zame jikinta tare da rungumeta tana fadin " granny period take kuma cikinta na mata ciwo sossae shine tun dazu take kuka……please ki mata magana ta bar kukan……" Dan Karamin tsaki grannyn ta sake tana fadin "Ban san shashancin banza ,ta ci gaba da kukan mana dan kaniyarta ……dallah ku tashi ku bani guri ……kai wallahi ku zo ku fice man daga gida ma tun kafin na sab'a maku……" ta karashe maganar tana nuna masu kofa "Granny cikinta ke ciwo fa sossae ……"cewar maryam "Wallahi zan ci mutuncinku baki daya…… ciwon cikin ne bak'on abu gurinku ko ko me a ciki?Don iskanci sae ku sani gaba da kuka akan Abunda ya zama dole kuyi kuma ku ke yi duk month……Maryam ki jata ku barman falo ko naci mutuncinku ja'irai kawae ……" Kuka Safeena ta sake tana fadin "Granny ba normal jini bane da na saba yi ……" A dan fusace ta jiyo tana watsa masu harara "Die normal ne dan gidanku?wallahi maryam zanci mutuncinki ke da kika kawo man ita ……" Mikewa Maryam tayi tare da kama hannun Feena tana fadin "Besty sorry kin ji ko…… tashi muje daki na hada maki ruwan wanka ki canza kaya wadannan sunyi staining da yawa ……" Mikewa tayi a hankali tana cije lips dinta na kasa tare da dafa Maryam ……a Tare suka kalli inda ta zauna su duka ukkun sam ba kalan jini bane gurin yayi powly black kamar charcoal …… "Safeena ,Maryam me ye haka ku ka kwaso man a falo ……?cewar granny tana bin gurin da kallon mamaki Cikin rawar murya maryam tace "granny tun dazu menstruation din Safeena ya koma haka ,granny ban taba ganin haka ba a rayuwana…… please dama yana komawa black? Shiru tayi kamar tana tuna wani abu ,lokaci guda ta nufi Safeena tare da sa hannu ta juyota tana kallonta "Safeena da karfi da zafi kike jin menstrual din yana fita ko? ta tambaya duk ta rude Gyada kai tayi a hankali tana kallonta ba tare da ta amsa ba ……Rufe ido granny tayi gam tana nuna masu su shiga daki kawae ,haka maryam ta riketa har bakin gado ta zaunar da ita har lokacin idonta na rufe ta dafe gefen cikinta "Sorry Feenat you'll be ok kinji ko besty……"abinda ta fada kenan sannan ta shiga toilet ta hada mata ruwan zafi sannan ta dawo ta kamata ta shiga da ita ……Dan bakin gadon da ta zauna ma har yayi stain,yaye bedsheet din tayi tare da lekawa falo zata tambayi granny din ko tana da katuwar leda ta shimfidawa Safeenar sannan sae ta saka mata bedsheet gudun kar matress din tayi staining ,hango Granny tayi inda suka barta tsaye kamar an dasa ta ……Jikinta ya kara yim sanyi ta matsa a hankali tana fadin "Granny ko kina da babbar leda irin ta cikin buhun sugar haka ……? Juyowa tayi ta kalli Maryam din tare da girgiza mata kai tana fadin "Maryam tun yaushe Safeena ta fara wannan abun? "Granny bayan ta dawo daga gidansu Aunty Fatee meeting tace man ta fara ,kuma ta fada man duka two weeks kenan da ta gama normal period dinta ……shin dama ana irin haka granny she's too unwellfull am scared na rasata ,wallahi tun dazu take kuka ko zamu kaita asibiti ne?tunda da motan mu ka zo ……" Wayar Safeena ce ta fara ringing Maryam ta dauko ganin My Future husby ya sata gane JB ne ta daga cikin sanyin murya tare da sallama "Maryam ina Feenat din ……?ya fada jin ba muryar ta bace "She's too unwell JB ta samu bacci ne ……" "Me ke samunta Maryam?kuna ina yanzu ?i wanna see her please……"ya fada a rude Kallon granny tayi sannan tace "don't mind ta samu sauki har ma tayi bacci zuwa da safe kunyi magana ……" "Please kuna ina? "Dutsin safe gidan granny JB please ba sae kazo ba tayi bacci wallahi ……" Ba dan yaso ba ya hakura yace da safe zaizo ya ganta sannan ta aje wayar ta shiga kitchen ta hado mata coffee ta dawo ta wuce granny har lokacin tana tsaye ……Da kyar ta samu tasha coffee din sannan ta gyara mata inda zata kwanta ,sae da ta tabbatar ta kwanta sannan ta dawo falo gurin granny ta zauna tare da fito da wayarta ta kira Mamanta ta fada mata tana gidan grannyn besty acan zasu kwana 《》《》《》《》 A Hankali yake juyi ci kadae bisa madaidaicin gadonshi zufa ko ta ina ke yanko mashi mummunan mafarki yake akan wata kyakykyawar yarinyar dake ta gudu cikin daji tana kuka ,bayanta wasu irin mugayen halittu ke binta a guje ,dae dae wani katon rami kafarta ta daki wani dutsi ta fadi kasa ,gangarawa ta farayi zata fada cikin katon ramin yayi saurin damko hannunta ya rufeta da kirjinshi ……mugayen halittun dake binta suka zo suka wuce ba tare da sun lura da su ba ……yana ganin sun wuce ya dago fuskarta tare da yaye gashin da ya lullubeta mata fuska yana kallonta …… A firgice ya farka yana kiran "Nana ……" tare da karewa duka dakin kallo ganin rana ta fara shigowa ta windown dakin ya sashi mikewa da sauri tare da leka window, calender dake manne jikin bango ya kalla tare da dafe kanshi ya juya baya "I failed……"hawaye suka gangaro mashi a hankali saman chicks dinshi *FEEDOHM💞* [4:58AM, 10/29/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹* 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 © *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM💞_* *Devoted to Ummi A'isha👌🏻* *Bestowed to Aunty Sis💕* *_Feedohm novella kuna ina wannan page din nakune na baku shi kyauta ……I heart you wollah Allah ya barman ku……🌹_* 2⃣7⃣ Wayarshi dake saman gado ta fara ringing kamar bara ya dauka ba ya matsa cikin sanyin jiki ya dauka ,shiru yayi ba tare da yace komae ba jin wanda ya kira bai magana ba ,kusan seconds 15 sannan ya cire wayar daga kunnenshi yana kallonta har lokacin wanda ya kira yana online ……katse kiran yayi ya koma jikin window ya tsaya yana kallon waje ……yana jin wayar ya sake ringing amma har ya katse bai kalli gurin ba ,toilet ya fada ya watso ruwa sannan ya saka shirt fara da blue din jeans ya fesa turare ya dauki wayar ya fito ……Food palace ya shiga yace a kawo mashi paula deen's coconut potage……yayi kusan 20mints yana juya spoon din ba tare da ya kai abincin a baki ba Karar shigowar message ya sakashi dube wayar yana budawa new number ce …… _" The more u go away from me,I'll closer forward my self to you.……I May not say any word only my heart will tell you're special Abdul Maleek ……"_ Tabe baki yayi ya mayar da wayar ya aje tare da aje spoon din ya kife kanshi…… hawaye yaji suna neman zubo mashi a fuska "I failed ……I Love you Safeena you're my life i can't asse without you Madam please don't neglect me Safeena Wallahi na fi kowa kaunarki *ZAN RAYU DAKE* Safeenah……" Bayanshi yaji an dafa ya dago da sauri yana share hawayenshi wata yar budurwar yaren igala ya gani ta kura mashi ido …… Bata fuska yayi tare da sake mata harara yana fadin "What……? Ganin ba wasa a fuskarshi ya sata juyar da kai sau biyu tana smiling ……"Cutie……"ta fada a hankali …… Karamin tsaki ya sake ya mike ba tare da ya kara bin ta kanta ba ……ji yayi zaria gaba daya ta isheshi bare ma mafalkin da yayi masifar daga mashi hankali …… Girgiza kai yayi baya jin zaya iya komawa garin a daurawa Safeena aure yana garin …better ya bari zuwa monday ya koma lokacin ya tabbatar da ya rigaya ya rasa Madam ……Tafiya yake amma sam hankalinshi baa jikinshi yake ba ……mai motar da ke ta mashi horn ya tsaya tare da fitowa yana bala'i ……wanda yake yin bala'in donshi sam bai ma san anayi ba …… 《》《》《》《》 Ranar Saturday da safe granny ta saka aka kira mata Abban Safeena cikin mintina kadan ya iso a falo suka zauna bayan sun gaisa tace "Safeena bata jin dadi ko za'awa iyayen mijin magana a daga bikin zuwa ta samu sauki ……" A rude yace "Me ke damunta Umma? Iyakar abunda take iya fada mashi ta mashi bayani ,shi kanshi sae da jikinshi yayi sanyi ya kalleta a sanyaye yace "Umma ina Safeena ……? "Tana daki tare da Maryam ,na karbo mata wani magani dazu gurin malan habibu nan makwabtanmu kafin mu gama magana naje daura ……" Numfashi yaja a hankali sannan yace "Idan d'aga bikin ne mafita Umma a kira angon sae a gaya mashi su hakura zuwa lokacin da zata samu sauki ……" "Gaskia kam dan duk yarda kake tunanin abun ta wuce nan don wallahi yau yadda kasan icce haka take komae Maryam ke mata nan da can ta kasa matsawa saboda azabar ciwon ciki ……garama yanzu naga maryam din ta kamata sun shiga toilet tayo wanka ……" Maryam ta fito rike da plate zata kai kitchen har kasa ta duka tana fadin "Abba ina kwana ……" "Lafiya lau Maryama ya jikin Safeena? Rau rau tayi da ido tana fadin "Ba sauki Wallahi Abba……" Mikewa yayi jikinshi na rawa ya shiga dakin ,akwance ya isketa tana kallon sama ,juyowa tayi tana kallonshi hawayen dake makale a idonta suka gangaro lokaci guda ta sake murmushi tana fadin "Abba……me yasa?Abbana mutuwa zanyi,wallahi cikina kamar zaya kone Abbah dan Allah ka man addu'a na samu sauki ……" Da sauri ya matsa tare da riko mata duka hannuwanta yana girgiza mata kai "ki dauki kaddara kinji Safeena ,bara ki mutu ba insha Allahu zaki samu sauki kinji ko ……ba ciwon ciki kawae bane ……" Kuka ta sake tana fadin "Abba kawae ne?jibi Abbah ……"ta fada tana kokarin mirginawa ta sauka daga shinfidar da Maryam ta mata …… Dafe kai yayi ganin gurin kamar wacce ta haihu yanzu, sannan yayi powly black sossae "Karki damu kinji ko ……Allah yana ganinki insha Allahu zuwa ranar monday zan nema maki visa a kaiki india indae bai tsaya ba ……" Gyada kai tayi a hankali tana share hawayen "Abba bana son auren kacewa JB ya hakura Abbana sae na warke ……" "Daina kuka mana ,ko so kike ki karyawa Abbanki zuciya Safeena?bara na kirashi sae a bashi hakuri ……"ya karashe maganar tare da lalubo wayarshi ya kira JB din yace ya sameshi nan dutsin safe yana son magana dashi yanzu …… Cikin mintina kadan ya iso ,a harabar gidan yaga maryam a rude yake tambayarta ya jikin Feena…… "Da sauki "ta fada tana rufe window din dakin granny sannan ta mashi jagora zuwa cikin falon granny …… Cikin Fahimta Abba ya mashi bayanin halin da ake ciki tare da bashi hakuri a dage bikin zuwa ta samu sauki …… A rude ya fara fadin "A'a Abba dan Allah kar a daga mana biki ,ka taimaka man ka bari a daura auren yau wallahi ,ko ya Feena take zan iya rayuwa da ita na rokeka Abbah dan girman Allah ……" "Ka kwantar da hankalinka Jabir bawae baran aura maka Safeena bane a'a wallahi kawae ina sone na sama mata magani zuwa wani lokaci sae ayi auren kaga ko a musulunci bai kamata a baka auren yarinya ba tana dauke da lalura ……" Hawaye ya fara bi mashi fuska yana fadin"Wallahi Abba na yarda zan zauna da ita a haka dan Allah ka barni da ita ……" Duk yarda Abba yaso ya fahimceshi a fasa auren kin yarda yayi ,Granny tace a barshi kawae a daura auren tunda yace ya yarda "Allah ya alkhairi……" addu'a kam ya shata gurin Abba don ba karamin dadi yaji ba shi kanshi yasan idan aka fasa wannan auren ba karamin bakin ciki zai shiga ba ……ya kuma kara tabbatarwa da JB zai rike mashi Safeena da kyau …… Dakin da Safeena ke kwance ya shiga ,tana ganinshi ta mike da kyar zaune tana cije lips ……sam bata bakin ciki idan an fasa auren ko kadan saboda ta san babu namijin da zai zauna da ita da wannan kazantar ,daga jiya zuwa yau tayi amfani da pad yafi 50 amma a banza duk inda ta zauna sai gurin yayi staining …… Rungumeta yayi sossae yana fadin "Feena kina jin Abba na fadin wae a fasa aurenmu? Da murmushin yake a fuskarta ta janye jikinta tana fadin "To meye JB hakan shine dai dai saboda ina dauke da lalular da babu wani namijin da zai zauna dani ko da minti biyar ne ……" "Sae ni Safeena wallahi *ZAN RAYU DAKE* A duk halin da kike ……na bawa Abba hakuri ya bar man ke kar a daga bikin kuma ya yarda ……Safeena indae har aka fasa bikinnan son da nake maki karyane wallahi ……ki sa a ranki ni JB *ZAN RAYU DAKE* Ko da lalurar dake jikinki ta linka wannan sau dubu ……Ina sonki Feena soyayya ta gaskia wacce babu algusur a cikinta ki yarda dani……" Wani kuka ta sake tare da kifa kanta a cinyarshi ……ta rigaya ta yarda cewa Jabir na mata wani irin so wae wuyar fahimta …… Karfe 12:30pm aka daura auren Safeena Khaleed da Jabir ……daurin auren da ya samu halatta dumbin mutane daga sassa na duniya…… *FEEDOHM💞* [4:39AM, 10/30/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹* 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 © *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM💞_* *Devoted to Ummi A'isha👌🏻* *Bestowed to Aunty Sis💕* 2⃣8⃣ _I'll write this in bolc *DUK SHEGEN DA YA KARA KARBAR KUDI AKAN YA TURA LITTAFINA ALLAH YA ISA BAN YAFE MASHI* to you reader duk wacce ta sake bayar da kudi aka tura mata littafina ta karanta Allah ya isa wutar jahannama bal bal🔥🔥 banyi littafina don kudi ba don haka kar wani shege ya kara mayar man da littafi na kudi shegu munafukai suna amfani da basirar wasu suna kasuwanci😡_ "Haba Jabir duka nawa kake da zaka yarda da auren mace da lalura a jikinta……" Mum ta fada a harzuke Bata fuska yayi sossae yana fadin "Mum nace ki taimaka man ne ……ni ne fa nace na yarda kuma ni zanyi mata komae then meye damuwarku akai ……? Kwantar da Murya tayi sanin halin dan nata tace " Amma son yarda dad dinka ya man bayani bara ka iya ba……" "Look mum baki son soyayya bane?ko ba auren so kukayi da dad ba……i can do anything akan Feenatah karku saman ciwon kai please ……" "Ni dae……" "Ki saketa idan ke kika aura man ita ……" ya fada tare da mikewa ya shige daki ya barta zaune , binshi tayi tana fadin"yi hakuri son wallahi na yarda kazo ka zauna kaci abinci……" "Baran ci ba……" ya fada kai tsaye 《》《》《》《》 Su Aunty fatee kam hadadden biki suka shirya na gani da fada duk family da abokan arziki an hadu sae raha ake Inna ce ta kalli Aunty Fatee tane fadin "Fateema ni kam ina diyar taki ? tunda nazo ban ganta ba ……" Murmushi tayi tana fadin "Safeena amarya…… kinga nima inna tun jiya nake kiran wayarta a kashe amma bara na kira maryam nasan suna tare……" Cikin jin dadi inna tace "Kira man yar kusuwa kunya ta hanata shigowa ……" Dariya Aunty fatee tayi tana kiran number maryam ,ringing daya ta dauka tare da sallama ,handsfree ta saka tana fadin "Maryam ina kika kai man diyata duk yau ban ganta ba……" A Raunane tace "Muna gidan granny aunty fatee ……bata jin dadi Abba bai maki bayani ba……" Dafe kirji tayi tana fadin "Subhanallah me ya sameta? Zatayi magana Aunty fatee tace "Ina zuwa maryam ga Abbanta nan naji ya shigo bara naje na sameshi ……" ta katse kiran ta nufi gurin Abban A rude a tare suka shiga part dinshi ko zama baiyi ba tasha gabanshi idonta cike da hawaye tana fadin"Alhaji meke samun diyata? dan Allah ka fada man me ke faruwa da Safeena tun jiya banganta ba yanzu kuma na kira maryam tace bata lafiya……meke faruwane? Rufe ido yayi yana kallonta duk ta birkice jin cewa Safeena batta lafiya tausayinta ya kamashi sossae a hankali ya zaunar da ita gefen gadonshi sannan ya zauna yana fadin "Ki kwantar da hankalinki Fateema Insha Allahu zata samu sauki ……matsalarku ta mata ce to sae ta zo mata da wani irin yanayi ni kaina hankali ya tashi saboda hakan ma yasa ko asibitin nan bai kaita ba zuwa monday idan abun bai tsaya ba sae na fitar da ita india zata samu kulawa sossae……" Cikin kuka tace "Meye abun mata alhaji dan Allah ka man bayani sossae ……" Cikin natsuwa ya mata bayanin jinin dake fita daga Safeena da irin yanayin da yazo mata har sae da ya kai aya sannan ya ja numfashi lokaci guda idanuwanshi suka canza yace "Fateema irin yanayin da Aisha ta shiga shine Safeena ta shiga……" "Na shiga uku Yanzu abunda ya samu Aisha shi ke shirin samun Safeenata ……Wayyo Allah wannan wace irin rayuwace muke ciki Ya Allah ka tausaya man ka bawa diyata lafiya wallahi itace haskena ……"ta karashe maganar cikin kuka sossae Ganin ta fishi shiga tashin hankali ya sashi lallashin tashi zuciyar ya fara lallashinta tare da bata hakuri ta dauki kaddara ,da kyar ya samu ta yi shiru sannan ta mike tana fadin "……Ya Allah ka daukewa diyata wannan ciwon ka dawo dashi kaina……" "Kul Fateema ki daina wannan addu'ar mana kiyi addu'ar Allah ya yaye mata itama ……" "Ya zanyi Alhaji wallahi da Safeena ta zauna da wannan ciwon kara ni,na zauna dashi ……Dan Allah kama izni naje na gano diyata yanzu wallahi baran iya kara minti goma ba ba tare da na ganta ba ……" Lumshe ido yayi tare da gyada mata kai a hankali yana sakar mata wani irin kallo ……kalamanta sun tabbatar mashi da Fatee na son Diyarshi har ga Allah wani girma na musamman ya kara mata a zuciyarshi…… Dakinta ta shiga ta iske Aunty Zuby na tattara kayan da yan bikin suka zubar ,Aunty zubyn ta kalleta tana fadin "Ke kuma daga ina idonki yayi ja kamar an maki duka……" Tabe baki tayi tana fadin" Wannan shegiyar yarinyarce Abbanta yake fada man bata lafiya shine na sake mashi kuka farin ciki dan banyi asarar kudina ba ……shi kuma sae ya shige sossae yana wani jin dadi ina son diyarshi ……" Dariya ta sake tana fadin "Amma baki da dama wato kukan farin cikin bakiyi asarar kudinki kike ba ko ……? "To Zuby na bakinciki zanyi ……? Harara ta sake mata tana fadin "Da banci ubanki ba ……yanzu angon ya sani koko? Tabe baki tayi tace " Yace man an fada mashi JB dinma ya dage sae an daura auren ya yarda ……kinga bara naje na gano shegiyar don nace mashi yanzu zanje ……" Dariya ta sake tana fadin "Allah ya kara zafin ciwo……" Da "Ameen " ta amsa ta fita tana dariyar mugunta A falo ta iske granny zaune tana shan kunun tsamiya da alama daga makwabta aka kawo mata shi har kasa ta duka ta gaida ita tare da zama kasan carpet tana kallon kasa …… Wulakantaccen kallo Granny ta watsa mata tana fadin "Su Fateema ne? Hala kunji labarin Safeena batta lafiya? ta fadi maganar da zance biyu A hankali ta ja majina tana share hawayen da suka zubo mata tace "Eh wallahi Hajiya yanzu ma Abbanta ke fada man shine nazo na ganta ……" Ita kam kukan ma dariya ya bata ……ta saki dariya irin ta manya tare da rike haba tana fadin"Ikon Allah har da kuka Fateema……" Salon kukan ta canja tana fadin "Ba dole ba inyi kuka hajiya ……ki duba fa yarinya sae da aurenta yazo ace jini ya balle mata kuma na cuta haba dan Allah ai abun da tausayi ……" Yar siririyar dariya ta kara saki tana fadin "To fa ……ki shiga suna daga ciki ……" Mikewa tayi da sauri ta fada dakin tana goge hawaye *FEEDOHM💞* [5:39AM, 11/1/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹* 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 © *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM💞_* *Devoted to Ummi A'isha👌🏻* *Bestowed to Aunty Sis💕* 2⃣9⃣ Safeena na jingine jikin gado maryam na mata fira kadan kadan suna dariya ……Shigowar Aunty Fatee ta batar da duk wani annurin dake fuskar Safeena kallo daya ta mata ta mayar da ldonta ta lumshe tare da zame hannunta daga na maryam "Subhanallah Safeena garin ya haka ta faru kuma fisabillahi baki kirani kika fada man tsawon kwanakinnan……" cewar Aunty fatee tare da zama gefen gadon Ko kala bata ce mata ba sae ma kwantar da kanta da tayi jikin gadon tana kokarin janye kafarta dake kusa da Aunty fatee …… "Safeena ……" ta kara kiranta tare da kai hannu Ta riko hannunta Da Sauri ta bude idonta tana watsa mata harara" Kar kuskura kiyi wasan ta bani wallahi……" Kwantar da murya tayi "Safeena meye zafi duba ki fa nazo yi ,wallahi tunda naji bakya lafiya hankalina ya tashi ……" Rufe ido tayi tana fadin "Aunty Fatee kenan ki bar duk wadannan jokes din ai'nt a kid wallahi ……Irin abunda ya samu mamina shi ya sameni ,Idan har ciwon da Mamina tayi kune sila to nawa waye sila?stop decieving your self please kawae ki tashi ki bar mana gida tun kafin na maki abunda bakiyi tunani ba……" "Ki saurareni mana……" "I said get out ko bakya da kaine?ta fada a tsawance, Jiki babu kwari ta tashi,ta fita tana waigenta Maryam dake zaune gefe ta kalli Safeena tana fadin "Amma bakya kyauta……"Shiru ta mata ba tare da tace komae ba 《》《》《》 "Wae Fadila waye kike kira haka tun dazu sae uban tsoki kike mana……"cewar hajiyarsu dake zaune tana yankan kumba Tabe baki ta kuma yi tare da sake karamin tsaki tana yatsina fuska"Abdul Maleek ne wallahi tun da nake bai taba daga kirana ba sae dae na mashi text shima baya replying……" "Amma ke sakara ce……Gafara can dallah ni bani numbershi shi din banza ya wahalar man da yar jika……"ta fada tare da mika hannu "Hajiya me zakiyi da Number?ta fada da alamun mamaki "Ke dae ki bani mana ,bani nace ba sannan ki kwantar da hankalinki Abdul Maleek kamar kin samu ne shi din banza……" "ah Hajiya ki daina insulting dinshi mana……" ta fada tana turo baki ……rike baki hajiyar tayi tana mata wani irin kallo ……Spreading arms tayi tana fadin"Yeah ki daina Insulting nashi because I love him……" "Lallae Fadila ……"cewar hajiyar tare da mikewa ta bar falon ……Fitowa ta kuma yi rataye da gyalenta da gani kasan tsofa yayi gardama gurin "hajiya sae kuma ina?cewar fadila da ta bita da kallon mamaki Harara ta sakar mata tana fadin "Gurin tsalli zani na kai mashi wannan number tun kafin ki fara duka idan an zageshi ……" "Ban gane ba Hajiyarmu……" Gaba tayi tana fadin "idan na dawo kin gane……" 《》《》《》《》 Karfe 10:15 ya iso katsina kasancewar tun da safe ya iso ……Gabanshi ke masifar faduwa banda addu'a babu abunda ke fita daga bakinshi , da kyar yaje gida a bakin zaure ya iske inna sahu tana neman aike saboda duk su nana sun tafi makaranta ……karbar Aiken yayi ya sawo mata sannan ya dawo suka gaisa sama sam yana tambayarta "duk yaran na lafiya……" ta amsa da "Lafiya lau ……" kadan kadan suka taba hira duk hankalinshi baya jikinshi so yake ya kira ko Maryam ce yaji yarda suke amma ya kasa ya dauki wayar da niyyar ya kira ya fi sau biyar amma ya kasa …… Sassayar ajiyar zuciya ya sake lokacin da yake mikewa ,kawae ya yanke yaje ya gaido Alhaji kila ya samu saukin radadin da zuciyarshi ke mashi …… A Falo ya sami Aunty fateen zaune tana breakfast har kasa ya duka ya gaidata sannan ya tambayeta ko Alhajin nanan …… Hankalinta ta maido kanshi sannan tace "Yana wanka Abdul Maleek ka jirashi dama ina son muyi magana da kai……" Kanshi na kasa yace "Ina saurarenki Aunty Fatee……" "Yauwa Abdul Maleek dama diyata Fadila ce ta dameni tana sonka kuma kaki kulata ko ta kiraka baka dauka shine nace ta bari na maka magana naji ……" "Ita tace maki da bakinta tana sona?ya fada tare da dagowa yana kallonta "Ita da kanta Mana Abdul Maleek ,kuma wallahi diyata ba mummuna bace idan kana so ma bari na kirata yanzu sae tazo ka ganta ,don tace man baka santa ba……" Murmushi yayi mai fitar da sauti yana fadin "Am sorry to say baran iya soyayya da macen da ta zubar da kunyarta ta ya'ya mata da Allah ya mata tace tana son namiji……" Shigowar Alhaji ce ta katse maganar ya mike da sauri yana mashi barka da fitowa ,ko zama baiyi ba ya nufi hanyar Fita yana fadin "Yauwa Abdul Maleek zo ka kaini tunda gaka kazo wallahi tun dazu Jabir ke man waya don shaf na manta jirgin marece zasu bi na dauka sae na dare ……" Bin bayansa yayi yana fadin "to Alhaji……" a zahiri jin sunan jabir da yayi a bakin alhaji ya saka gabanshi yayi mummunar faduwa ……jiki a mace ya fitar da motar suka dau hanyar fita unguwar murya Alhaji yaji yana fadin "Dutsin safe zamuje mu dauko Safeenar Abdul Maleek sae mu samesu bakin round din dandagoro Kano zamuje ……" Safeena……ya fada a ranshi kasa hakuri yayi ya juya yana kallon Alhajin a raunane yace "Wace Safeenar Alhaji ba tayi aure ba me ya kaita dutsin safe ko acan aka ajeta……" "Tayi aure mana Abdul Maleeku ,Bata lafiyane shine zamu kaisu kano ita da mijin nata zasu fita india a dubata……" Lumshe ido yayi hawaye na bin kumatunshi ya rigaya yayi failing ……da yake Alhajin a baya yake sam bai kula da halin da Maleek din yake ba……kofar gidan yayi parking kafin ya zagayo ya budewa Alhajin har ya rigaya ya fito ya shige yana fadin "Shigo Abdul Maleeku……" Girgiza kai yayi a hankali kamar Alhajin na kallonshi sannan ya kwantar da kanshi jikin gaban motar yana numfashi a hankali……Murya Granny da yaji ta sashi naimo natsuwarshi ya dago da kanshi yana yake…… Maryam da ya hango ya sashi juya masu baya da sauri don ya tabbata tana tare da Safeena Kuma bayajin zai cigaba da rayuwa indae yana kallonta …… "Dole ka juya man tunda baka da gaskia……"cewar granny dake kokarin shinfida katuwar leda a bayan motar …… A hankali ya juyo yana yake tare da maida kanshi kasa don har ga Allah baya jin zai iya kallon Safeena a yanzu da ya tabbata ta mashi nisa……"Ba haka bane granny tafiya ta kamani ……"ya fada da murmushin yake a fuskarshi Zuciyarshi ke neman rusa mashi duk wani plan na kar ya kalleta sam ya kasa jurewa……a hankali ya fara bin kafafuwan mutanen dake tsaye gurin har ya sauke bisa kafar daya tabbata ta Safeena ce …… Sae da ya lumshe idon sannan ya fara kallonta tun daga kasa har ya kai kan kugunta da razanannan kallo ya karasa kallon fuskarta ……Lumshe idonshi yayi yar kwallar dake makale ta fado maida idonshi yayi ksn kugunta domin ya tabbatar da abunda ya gani ……Tabbas idan idanuwanshi ba gizo suke mashi ba uwar tulluwa ya hango a bayan kugunta sannan ga uban kalar da zanin ya sake daga sama …… *FEEDOHM💞* [9:27PM, 11/2/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹* 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 © *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM💞_* *Devoted to Ummi A'isha👌🏻* *Bestowed to Aunty Sis💕* 3⃣0⃣ A razane ya karasa yana kallonta "Wat happen Madam?ya fada yana kallon fuskarta Shiru ta masa tare da janye hannunta daga jikin Maryam ta shiga bayan motar……da ita da Abba ne a baya sae maryam da ta zauna gaba ……bakin fita gari suka hadu da family din JB da Suka yo mashi rakiya wanda har mom dinshi ciki ……Bayan sun gama gaisawa maryam ta koma baya JB din ya zauna gaba tare da juyowa yana kallon Safeena ba wata kunya ya kashe mata ido yana fadin "Babynah ya dae?……You'll be ok kinji ko da munje zakiyi enjoying life dinki better than nan garin,I'll be so caring ……" Lumshe ido tayi tare da kwantar da kanta a kafadar Abba ba tare da tace komae ba ……kallon maryam yayi yace "Sister ya jikin baby? Ita kam kunya ma ya bata gaban Abban zai dinga kira masu wani baby dan murmushi ta saki tana kallon safeena sannan tace "She's ok……" "Good " ya fada tare da juya ya fito da wayarshi yana latsawa……Maleek kam da kyar ya iya controlling kanshi babyn da JB ya fada ya hargitsa mashi kwalwarshi …… Masallacin kankia zuhur ta masu Abba yace su tsaya suyi sallah tukun ……Duk suka fita sae Safeena dake zaune ita kadae ta kwantar da kanta baya ……har Maleek ya gama alwala amma baiga ta fito ba…… Ruwa ya diba a buta ya matsa tare da bude bayan motar "Madam ki fito kiyi sallah……" Wani irin kallo ta watsa mashi tare da maida idonta ta rufe ……Ajiyar zuciya ya sake a bayyane don ko hararan madam abun so ce sannan yace "Sorry Madam na fahimci matsalarki amma kiyi tunani abunda ke jikinki ba normal Pes bane na ciwone kuma Allah bai yafe sallah baga mai irin wannan ciwon indae ta tabbata a normal pes dinta bane kiyi kokari kiyi sallah tunda tana kanshi ko bakiyi ta yanzu ba sae kin ramata……" Dan bude ido tayi tana kallonshi idan bata manta ba malamai suna fadin an dauke sallah ne ga macen dake jinin al'ada ba wae jinin cuta ba ……idan har jinin ya zama na cuta to duk lokacin sallah zatayi tsarkine sannan tayi sallarta…… "Thank you……idan mun isa inda zamu zanyi maleek"ta fada a hankali Murmushi yayi sannan ya mike ya koma yayi sallar lokacin duk sun gama suna addu'a ne sae da ya gama tashi sannan ya dawo suka cigaba da tafiya …… Kusan karfe 3 Suka isa airport din dan restaurant din dake gefe suka zauna amma banda Safeena dake zaune taki fitowa ……JB ya kirashi "Kai zo nan ……" Ko nuna yaji alamun kiran baiyi ba har dae Abbah yace "Abdul Maleeku zo mana……"sannan ya matso tare da dukar da kai gaban Abba "Kazo kaci abinci mana ka ja ka tsaya gefe……"ya fada tare da nuna mashi kujeran dake gefenshi Dukar da kai yayi yana fadin "No Abba koshi sae dae wanda zaa mikawa madam naga bata fito ba ……" Kallon motar Abba yayi tare da juyo da kai yana kallon Maleek din sannan yace "Bara ta ci ba Abdul Maleek tunda zamu fito na tambayeta me take so tace man ta koshi……" "Abba to ko cake na kai mata ……"ya fada a hankali ……Dan murmushi Abba yayi sannan yace "To Abdul Maleeku ka shiga ciki ka dauko mata ka kai mata idan zata ci……" JB yayi saurin fadin "Abba kyaleshi ba wani cake din da zata ci yanzu……" "May be taci Jabir kasan tana da kusanci da shi sossae ya fi kowa sanin abunda zake bukata ……Jeka Abdul Maleek ka zabar mata sae ka kai mata kaga idan zata ci kaji ko……"cewar Abba da murmushi shinfide a fuskarshi Eclair cake ya daukar mata da freshmilk sannan ya nufi motar da addu'ar karta yarfa shi don yafi kowa sanin yarfin madam…… Bude motar yayi ya shiga sossae sannan ya mika mata cake din yana fadin "Madam ga cake……" Dan Murmushi ta saki sannan ta bude idonta tana kallon cake din ……karba tayi tana fadin "Thanks ……"sannan ta aje bayan motar ta lumshe ido "Please madam ki ci yanzu dan Allah ……"ya fada kasan makoshi "Na koshi maleek"ta fada atakaice…… "Dan girman Allah madam ba dan na isa ba……" bai rufe baki ba ta dauko cake din tare da budewa ta kai bakinta tana kallonshi ta kasa kasa ……Tunda ta fara ci ya kafe ta da ido yana jefa mata wani irin sassanyan kallo ……har sae da taci rabi sannan ta dago tana kallonshi ,First time kenan da ta ji kunyarshi a rayuwarta ,saurin maida kanta tayi kasa tare da juyawa ta kalli window …… A wahale yace "Sorry…… Ba tare da ta juyo ba tace "How did you bear when i insulted you so badly without understanding you? Da sauri ya bude mata marfin fresh milk din tare da mika mata ……Idanuwanta cike da hawaye ta juyo tana kallonshi,bai dauke nashi idon ba sae ma salon kallon da ya sake mata …… Muryar JB yaji yana fadin"Kai meye haka why are staring her?common dallah fito malan baka san matar aure bace zata tasa ta gaba da wannan shegen kallo ,Baby what happen? Saurin juyar da kanta tayi ba tare da ta amsa masu ba tana jin lokacin da Maleek din ya bar motar sae da kamshinshi da ya bar mata rintse ido tayi gam tana fitar da kwallah ……tabbas tana son JB amma ta tabbata tana jin Maleek A ranta to idan hakane tana Kaunar Maleek ne tana son Jabir…… Ganin Maryam da Abba sun taso ya tabbatar mata da tafiya zasuyi……shigowa maryam tayi tare da sake bglass na motar ta mika mata zani ta canza sannan ta kamo hannunta suka fito tare ……Da sauri JB ya karbi hannunta tare da rungumota jikinshi …… Juyawa tayi tana neman Maleek amma duk arean babu shi sae kamshin turarenshi da ya cika masu gurin ……Hawaye suka taran mata a ido ta daga kai a sanyaye tana kallon JB shima ita din yake kallo ……cikin salo ya kashe mata ido tare da kanne guda daya ……murmushi ta danyi sannan ta juya tana kallon Abba dake gefenta shima ita yake kallo idonshi cike da kwallah Sae maryam dake kallon kasa ko baa fada mata ba tasan kuka take ,idanuwanta suka ciko da kwallah ……"Abba……"ta fada hade da bata baki zatayi kuka Lumshe ido yayi yana juyar da kai "May God be wit you love……" ya fada a hankali tare da juyawa ya rike hannu Maryam suka tafi ,Wani kuka ta sake tana fadin "Please Abba maryam dan Allah wallahi na fasa zuwa *ZAN RAYU DAKU* Abbana karku barni ……" Ta fada tana kokarin fizgewa daga rikon da JB ya mata……sossae ya kara rungumeta yana shafa kanta har suka shiga waiting room …… *FEEDOHM💞* [3:00PM, 11/3/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹* 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 © *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM💞_* *Devoted to Ummi A'isha👌🏻* *Bestowed to Aunty Sis💕* 3⃣1⃣ *_This page is for you swthrt Aysha hameed🌹 Maryam Auntyn Maleek🌹 Maman hanif🌹 besty firdaws Ahmed🌹 Meenarh parrot🌹 Meela Adeel🌹 Aunty Maijiddah musa🌹Ummi Muhsan 🌹Abdul Maleeku Heart you 💞💞_* A cikin motar suka iske Maleek zaune ya kifa kai a sitiyari har suka shiga ba wanda yace kala jin sun rufe kofar motar ne ya sashi kunna motar suka tafi ……tafiya suke kamar kurame Abba na kallon window gefenshi Maryam na kallon ta gefenta tana fitar da kuka a hankali ……Maleek kam gabanshi kawae yake kallo ba tare da dauke ido ba …… 《》《》《》《》 Da daddare suka isa hotel din dake kusa da asibitin suka sauka tana rungume jikinshi,har suka shiga dakin sannan ya zaunar da ita gefen gadon ya koma yana kokarin shigo da kayansu …… Lokacin da ya dawo tana kokarin shiga toilet da sauri ya matsa tare da rungumota jikinshi ganin zata fadin "Baby bara ki jira nazo na kaiki ba……" Dan murmushi tayi ba tare da tace komae ba ,hancinta ya dan ja yana fadin "Inda kin fadi ba?Karki sake kinji ko zan maki komae kike bukata beside ma me zakiyi toilet din? A hankali tace "Zanyi wankane nayi sallah……" Dan waro ido yayi cike da mamaki "Wane irin sallah kuma baby bayan kina Pes……Common muje na taimaka maki kiyi wanka ……" Shiru ta masa suka shiga toilet din a tare sannan ta kalleshi da raunannun idanuwanta tace "Please ka fita zan iya wankan da kaina……" Spreading arms yayi sannan ya fita tare da janyo mata kofar ……Mintina kadan ta fito daure da towel sannan ta dauki kayanta da pad ta koma toilet din ta saka …… "Bara nima nayo wankan ko baby ……"ya fada yana dan rungumota tare da kissing wuyanta …… Tsigar jikinta ne ta tashi cikin dubara ta janye jikinta tana murmushi ……Shinfida abun sallah tayi shi kuma ya fada toilet din ,Da sauri ya fito yana yatsina fuska "Baby wadancan kayan da kika cire ya za'a maki da su……" A tunaninta ya san dae wankewa za'ayi sannan yana sane da barata iya wankewa da kanta ba ……Shirun da yaga tayi ne yasa yace "Baby zaa zubar dasu ne ko? "Zubarwa JB?Ta tambaya tare da kura mashi ido …… "Yeah baby kinsan dae baran iya wanke wadancan kazantar ba ko?infact ma nayi hating jini ko wane irina kinga kenan sae dae a zubar dasu……"ya karashe maganar tare da fadawa saman gado Gabanta ne ya fadi ta bishi da kallo sannan tace "Amma kasan baka son jini ka yarda da aurena sannan kuma ka biyoni ai da kayi zamanka nigeria mun taho da Maryam am sure zata man duk abunda nake bukata……" "No baby jinyarki ai dole sae muharraminki zan maki komae jinin ne kawae baran iya tabawa ba ……please ki dan shiga ki sakasu cikin leda sae na yardo ina son zanyi amfani da toilet din……" Uwar harara ta sake mashi tare da kabbara sallah abunta ……har ta gama sallolinta yana kwance ya kasa shiga toilet din sae da ta gama addu'a sannan ta dafa bango zata shiga toilet din ……da sauri ya taso yana fadin "Baby nace maki ki bar tafiya ke kadae kada kije ki fadi ……" Banza tayi masa har ya kaita toilet din ya fito yana rufe hanci ,ko da ta zuba a ledar kin bashi tayi ta kama hanya zata je ta zubar kamar yarda yace ……tana masifar don doguwar riga saboda lokacin da Abbanta yaje US ya sawo mata ita amma tana gani ta jefar da ita a cikin GG din harabar hotel din ……ko da ta dawo yana toilet yana wanka Cikin jikarsu ta bude ta fito da katuwar leda ta shifida saman bed din sannan ta kwanta tare da rufe dukkan jikinta ……ya fito yana goge kanshi da towel ganin ta lullube ya sashi karasa bakin gadon ya zauna yana fadin "Baby ba dae har kin kwanta ba bakici abinci ba……"ya karashe maganar tare da yaye blanket din yana kallon bayanta Dan karamin tsoki yaja yana fadin "Gaskia wannan abun bai kyauta mana ba baby da yanzu muna can muna enjoying life dinmu wallahi ……ko da yake sati biyu ne zamuyi kuma assure kafin lokacin kin warke kinga daga nan istabul zamu je muyi honeymoon dinmu ko……? Ba tare da ta juyo ba tace "Waye yace maka sati biyu zan warke ……idan sati biyun yayi ban warke ba fa? "Daina fadar haka man baby ……yanzu dae tashi kici abinci ……" Bata kuma cewa komae ba ta gyara kwanciyarta "Au bara ki ci abincin ba baby ……shikenan ai cikinki ne ni dae baran iya kwana da yunwa ba ……" 《》《》《》《》《》 Bayan sun isa garin Abba yace a fara kai Maryam gida sannan suka karasa cikin unguwarsu kusa da wani mai dama fura Abba yace a tsaya yana so Abdul Maleek dinne ya fita ya sawo mashi sannan ya dawo suka karasa shiga gidan …… Cike suka iske gidan kamar ana wani biki Maleek na rike da ledar Furar suka shiga falon Su Uncle Abbah ne da Fadila anyi rashe rashe kadsn carpet ana cin abinci ……Suna ganin Abban suka mike tare da gaidashi ,daga masu hannu yayi cikin fara'a sannan ya karbi ledar hannu Maleek din yana fadin "Karka tafi Abdul Maleeku yanzu zan fito na baka sako ka kaiwa Hajiyar Safeena" A falon ya zauna tare da fito wayarshi yana latsawa Number Safeena ya kurawa ido yana yawo da hannunshi saman screen din wayar …… Fadila ta kalli Uncle Abba tare da kanne mashi ido sannan ta dauki bottle na swan da cup ta rarrafa kusa da Maleek din tana fadin "Ya Maleek ga ruwa ……" Murmushin yake yayi sannan ya girgiza mata kai yana fadin "Alhamdulillah……" Dan shagwabe fuska tayi tana fadin "Ruwan ma bara kasha ba?Dan Allah kasha kaji……" Kallonta yayi na secs ko baa fada mashi ba ya san sarae ita ce Aunty Fatee ke mashi magana sannan itace ke yawan kiranshi da turo mashi message…… "Ka karba mana ……ta sake fada cikin muryar jan hankali "oh na manta ashe ban zuba maka ba sorry……"ta karashe maganar tana kokarin zuba mashi a cup Samun kanshi yayi da kiran Number Safeena bai damu da iyayin da Fadilan,ke mashi ba ……Cikin saa ringing biyu ta dauka cikin sanyin murya tayi sallama "Madam……"ya fada tare da lumshe idonshi Zaune ta mike jin muryan Maleek din sannan ta kalli gefenta inda taji JB ya kwanta amma wayam babu shi tabe baki tayi ganin baya dakin sannan ta maida hankalinta gurin wayar da taji Maleek na fadin "Madam kina jina……? "Eh ……" ta amsa a takaice "Ya jikin naki? "Am okey……" "Alhamdulillah ……" ya fada tare da yin shiru na yan mintina sannan yaja numfashi tare da fadin "Sleep well madam……ki rike addu'a Nothing will happen to you Madam kinyi duka sallolinki……" Gyada kai tayi kamar yana kallonta tare da goge yan kwallan da suka zubo mata he's such a caring person ta fada a ranta ,jin ya sake yin shirun ne ya sata komawa ta kwanta wayar na makale a kunnenta A hankali tace "You done much to me Maleek……" Katse wayar tayi ba tare da ta jira abunda zaice ba …… Sam ya manta da Akwae mutane a falon sae da ya ga Fadilan ta mike tare da fadawa dakin Aunty Fatee da gudu "Ikon Allah……"ya fada a fili tare da kallon Uncle Abba dake ta faman zuban mashi harara Yar dariya ya sake mai sauti to meye hadinshi dasu Spreading arms yayi ya mike ganin Abban yana saukowa,Kudi Abban ya mika mashi yana fadin "Hajiyar Safeena zaka kai mawa kace ta fara amfani da wannan gurin maganin kafin na shigo ……" Hannunsa ya janye daga karbar kudin yana fadin "Zan bata Alhaji akwae kudi hannuna……" "Ka karba mana ka kai mata ……"Abban yace tare da sake mika mashi Girgiza kai yayi kanshi na kasa alamun bara ya karba ba "Meye haka Abdul Maleeku gardama zan tsaya da kai?ka karbi kudi ta kaiwa hajiya final……" "Afuwan Alhaji in dai ni zan karbi kudinka na kai awa Madam dita magani banga amfanina ba a rayuwarka ……dan Allah kayi hakuri na nemawa Madam dita magani da zufar Aljihuna……" ya karashe maganar muryarshi na rawa Shiru yayi yana kallonshi tabbas Maleek mutunne mai tsananin tausayi da alkhairi shi Kanshi ya yarda da cewa Abdul maleek ya aje diyarshi wani guri na daban a rayuwarshi ……hannunshi ya kama yana gyada mashi kai "Nagode Sossae Abdul Maleeku Allah ya albarkaci rayuwarka……" *FEEDOHM💞* [10:24PM, 11/3/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹* 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 © *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM💞_* *Devoted to Ummi A'isha👌🏻* *Bestowed to Aunty Sis💕* 3⃣2⃣ *_Wannan page din nakine khadija bee bee ta Allah ubangiji ya raya mana ilham da sulteen Aunty Sis💞_* Shiru yayi yana kallonshi tabbas Maleek mutunne mai tsananin tausayi da alkhairi shi Kanshi ya yarda da cewa Abdul maleek ya aje diyarshi wani guri na daban a rayuwarshi ……hannunshi ya kama yana gyada mashi kai "Nagode Sossae Abdul Maleeku Allah ya albarkaci rayuwarka……" Fadila kam dan yalolan gyalenta ta dauko dake aje saman gadon Aunty fatee ta fito tana kuka ……Aunty fateen ce ta biyota tana fadin "Ke fadila lafiyanki kuwa me aka maki kike kuka……? Shiru ta mata ta fita daga gidan ,har ta isa gidansu tana kuka ta fada dakin mamanta ,"Me ke faruwa fadila?Aunty zuby ta fada cikin sauri tare da rungumota jikinta Cikin kuka tace "Mum wallahi sonta yake……" ,"Wacece ya ke so kuma?waye ma fada man kinji fadila……"ta fada cikin lallashi "Mum Maleek mana wallahi Safeena yake so kuma na rantse da girman Allah sae dae ya mutu mu duka mu rasa shi……"ta karashe maganar tare da sake kuka da karfi "To Uban wa yace maki sonta yake?kuma an fada maki ana aure cikin aure ne……Sakara ki kwantar da hankalinki ko jiya Hajiyarmu ta kai numbershi gurin boka kuma ya tabbatar mata da naki ne……" Share hawayen tayi tana kallon Mum din tata tana so ta gasgata abunda take fada ……Tabbas indae Maleek ya zama nata She's the luckiest person a duniyar nan ……Cikin farinciki ta rungumo Aunty Zuby tare da manna mata dan kiss tana fadin "I Love you Mum……" Cikin Wasa Aunty zubyn ta harareta tana fadin "Da kinzo zaki daga man hankali akan abunda kinsan dole ki sameshi ……" "Sorry Mum……" ta fada hadi da turo baki 《》《》《》《》《》 Karar shigowar Message da tajine ya sata bude ido a wahale tare da kallon JB dake kwance bisa doguwar kujera kafafu a hanbare kamar wani sabon arne ……Dan karamin tsoki ta sake tana duba agogon dake makale jikin bangon dakin…… 5:15am ta gani wayar dake haske ta saka hannu ta dauka sunan Maleek ke yawo baro baro a jikin message din da aka turo ……Dan guntun message ne ya turo "Madam ki tashi kiyi sallah……"Lumshe ido tayi sannan ta mike da kyar tana kallon inda ta kwanta sam babu sauki, ta fasa a ranta……duk da kwannansu uku ana treating din ta tare magunguna masu dan karan tsada…… Bango ta dafa da kyar tana hararan JB dake ta uban baccinshi sam bai da kula da addininshi wani abu ya tokare mata kirji ,bata samu sauki ba sae da ta dauki robar lemun dake aje gefen gadon ta wurga mashi a fuska ……duk da ta dakeshi sosae amma ko motsi baiyi ba ……tayi tsoki yafi sau 10 sannan ta shige toilet din da kyar tayi wanka tare da tsarki ta fito tayi sallah ,har lokacin baccinshi yake Kamar ta kyaleshi ta dai daure ta kai hannunta tana dukan pillow da ya daura kanshi a hankali tare da kiran sunanshi"Jabir ka tashi kayi sallah ……" Hannun da take dukan pillow dashi ya rike gam tare da bude idonshi a hankali "Baby kin cika takura……" ya fada cikin muryar bacci Tabe baki tayi tana harararshi ta kasan ido sannan tace " Sallan ne takura? "Baby ai ko karfe 11:59am zan iya sallan asuba tunda baa shiga pm ba ……"ya fada yana kokarin gyara kwanciya Bata san lokacin da tace "In ji wane jakin malamin? "Please Ki barni nayi bacci baby promise da na farka zanyi kin ji ko ……" Banza ta masa ta cigaba da addu'o'in da Maleek ya turo mata …… 《》《》《》《》《》 Duk wani abu da granny zatayi Maleek ne ya fansheta, har ga Allah nema mata maganin musulunci yake iya karfinshi Tun lokacin da granny ta fada mashi cewa ciwon Safeena bana asibiti bane hankalinshi yaki kwanciya…… harta office idan yaje karfe sha biyu yake baroshi ,Duk inda yaji wani babban malami yana gurin……Baya k'ashin kashe ko nawa ake bukata sannan ko Abba bai san me yake ba Iyakarshi da Abban kullun dare zai kai mashi fura sannan su danyi fira kadan ya tafi…… ko yarda baya yi su gaisa da Aunty fatee saboda wani mugun haushinta da yake ji Hajiyarsu Aunty Fatee kam ta dage iya karfinta dole Maleek din ya so Fadilanta ko ta halin kaka…… Yau ma tun da safe ta kira Aunty Zuby tace ta turo mata Fadila su tafi gurin bokan tare ……Mintina kadan Fadilan ta zo ,basu bata lokaci ba suka tafi sae da suka fita gari sossae sannan suka yanke daji ……sunyi kusan tafiyar Awa daya sannan suka isa bakin wani burtu dake gefen wata katuwar kuka…… Tun daga waje suke jiyo ihun mace ……hajiyar ta kalli Fadila tana fadin "Ki kiyayi bakinki Fadila idan mun shiga ,ina sane sarae baki da kunya to wallahi wannan mutumin keras yake jira ya wulakanta mutun ……" Turo baki tayi tana fadin "To ni hajiyarmu ina ruwana dashi ……" "Na dae gaya maki ki kiyaye sosae……" Fitowar matar dake ciki ya sasu tsaida maganar da suke ……Sae da suka bar hango matar sannan suka shiga tare da aje takalmansu a bakin burtun ba tare da sallama ba ……Dan tsamurmurin tsohone fuska cike da furfura gashi bakikkirin sae Uban wari yake …… Yafi minti Talatin yana kallon fadilan sannan ya hade miyau ya juya ga hajiya dake zaune tana kallonshi ……katon bakinshi dake cike da algae ya washe yana fadin " Shegen yaro ya hanaku sakat Shafa'u……" Gyada kai tayi tana fadin "Kwarae kam boka……" Wata katuwar tukunya ya fito daga bayanshi ya aje gabanshi yana yan surutai har tsawon minti goma sannan ya dago yana fadin "Shegen yarone mai tsabar riko da addini ba'a zaune yake ba, uwa uba ruwan ganyen magarya shi ya zame ruwan wankanshi ba lalle bane asiri ya kamashi ba ……" "Haba boka akwae wanda ya gagareka a duniyar nan ……"hajiyar ta fada tare da hade hannunta guri guda Dariya ya sake yana fadin "Ai Allah baya bamu sa'a akan muminan bayanshi sae dae idan yana cikin kaddararsu shine sae ya ara mana dan lokaci kadan akansu amma shi wannan shegen yaro ko kadan baya sakaci da addininshi ……Hajiya Shafa'u yarinyarki ta fitar man daga burtu……" A Rude ta kalli Fadilan,saboda sanin halinshi da tayi sam baya da imani ko kadan duka ta kai mata da karfi tana fadin "Boka ka yafe mata ,ke kuma dan ubanki tashi ki koma mota mara kunya……" Tabe baki tayi ta mike ta bar Burtun, Boka kam tun da ta mike ya raka kugunta da kallo sannan ya juyo yana kallon hajiyar da har yanzu tana rude "Ki shigo daga ciki bukatarki zata biya ……"ya fada yana matse kafafuwa Babu musu ta mike ta shiga inda ya sa jan labule ya katange ,shima ya bi bayanta ……Sae da ya gama lalata da ita sannan ya dauko wani karamin zobe ya mika mata yana fadin "Komae yayi Shafa'u, ki bawa diyar taki wannan zoben ta aje sae tsakar dare ta tashi ta kalli yamma ta daura zoben saman hannunta na haggu sannan tace Zoben zalleni jeka zuciyar Abdulmaleek ka hana mashi sukuni har sae yazo gareni ……idan har taga zoben ya bace to tabbas zaizo gareta a ranar idan kuma zoben bai bace ba to aikin baiyi ba sae ku sake dawowa a canza wani salon …amma a zahiri akwae yarinyar dake cikin zuciyar tashi wadda kuka kawo kwanaki aka ma wannan aikin…… to ita yake so sossae idan asirin shi bai kamashi ba, to ita zamu sakawa hauka ta shiga duniyar ta yarda bazai iya rayuwa da ita ba…" *FEEDOHM💞* [5:10AM, 11/4/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹* 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 © *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM💞_* *Devoted to Ummi A'isha👌🏻* *Bestowed to Aunty Sis💕* 3⃣3⃣ _I love you din banza ki daina astrayed kanki baby rapidly da na bar novel din kin barni……_🌹 Dan jinjina kai tayi sannan ta karba ta fita a mota ta iske fadilan tana chat abunta sae da ta zauna sannan ta harareta tana fadin "Ba kyajin magana ko ,idan da kin ja mana bala'i fa……? "Yo hajiya mayan kallo ne ya wani kurawa kirjina ido sae kallo yake sakaran bai ma san duk ciko bane……"ta karashe maganar tana rufe baki "Mtsew shine sae ki hararashi kuma to wallahi ki kiyayi wancan mutumin ya wuce duk yarda kike tunani……" Ko da suka koma gida zoben ta bata tace tayi amfani dashi kamar yarda boka ya mata bayani…… 《》《》《》《》《》 Dan karamin tsoki ya sake ganin turawan da yan mata yan kasar nigeria dake yawo a harabar hotel din wani uban Feelings ya taso mashi ……Ga mace har mace amma babu amfani "Wallahi na gaji ……"ya fada tare da dunkule hannunshi guri guda A hankali ya sauka harabar Hotel din gurin wata da ke ta zaune kusa da ruwa da alama yar nigeria ce ……kusa da ita ya zauna tare da mika mata hannu …… Kallon uku saura kwata ta mashi sannan ta yatsina fuska tana wasa da ruwan dake gabanta …… Da yake dan duniyane bai bar gurin ba sae da ta saki jiki dashi sossae har tana fada mashi sunanta raliya ita yar kaduna ce karatu ya kawota india ……sossae suka hau fira har ta kaisu da shiga room din da take zaune ……Sae da suka shege ayarsu sannan ya fito ya shiga asibitin gurin Safeena …… Lokacin ta har fito daga dakin da ake treating dinta tana zaune tana jiranshi ……Da sauri ya karasa kusa da ita tare da rungumota yana fadin "Sorry baby wallahi chocolate naje samo maki kuma babu masu dadi……" Dan murmushi tayi tare da mikewa tana fadin "Is Okey ……" Shafu fuskarta yayi yana fadin "Ya jikin naki baby? ya rage sossae……" Dan girgiza kai tayi a hankali idonta ya ciko da kwallah ta kasa magana ……deep kiss ya mata a lips yana fadin "Sorry karki yi kuka kin ji ko ……Very soon zaki samu sauki……" Yana rungume da ita har cikin dakinsu sae da tayi wanka sannan ya kawo mata abinci ya aje ya fita yana fadin "Make sure kin ci sossae baby yanzu zan dawo nima ……" Dan girgiza kai tayi tare da daukar wayarta ta kira granny lokacin suna zaune da Maleek din yana mata bayanin wani magani daya karbo ……Maleek din ta kalla tana fadin "Safeena ce bara na dauka……"dan girgiza kai yayi tare da maida hankalinshi gaba daya ga granny din…… "Menene Safeena daga daukar waya sai kuka koma……"Granny ta fada cikin sanyin jikin Wani irin kuka mai tsuma zuciya ta sake tana fadin "Granny harda tsutsa yau da naje asibiti……"ta karashe maganar cikin wani irin kuka kamar ranta zai fita Shiru granny tayi tana maimata addu'a a ranta bata so ta karyawa Safeenar guiwa ita kanta idonta ya ciko da kwallah a hankali ta mikawa Abdul Maleek din wayar don ta tabbata bara ya rasa abunda zai ce mata ba ……ita kam da ta kuskura ta furta kalma daya to ta tabbata da kuka zata fito…… A sanyaye ya karbi wayar tare da kangawa a kunne ……har lokacin kuka take kamar ranta zai fita lokaci guda yaji zuciyarshi na bugawa da karfi da ace zai iya dauke ciwon ya dawo jikinshi babu abunda zai hanashi yin haka …… "Safeena……" ya kira sunanta karo na farko a rayuwarshi ……Dan sassautawa tayi da kukan jin muryar Abdul Maleek din "Safeena ko wane bawa da yarda Allah ke tsara mashi rayuwarshi wani ya kanyi rayuwa cikin jin dadi daga farko sae a karshe Allah ya sauya mashi da wahala ,wani kam yana tashi cikin tsanin rayuwa daga karshe Allah ya sauya mashi da farinciki ……Safeena ki dauka wannan itace kaddararki ba kuma dan Allah baya sonki ya daura maki ba sae don ya jaraba imaninki ……"Shiru yayi yana sauraren yarda take fitar da wani irin kuka "Dan girman Allah ki bar wannan kukan Madam……"ya fada muryarshi na rawa , jin batayi shirun ba ya sashi fadin "Wae meye amfanin jabir da zai barki kina kuka irin haka,Zan zo Madam wallahi baran juri kukanki ba ni zanzo na kula dake ta yarda bara ki samu lokacin da zakiyi kuka ba……" Cikin kuka tace "No Maleek muma sauran kwana biyu mu dawo ……"daga haka ta yanke wayar Shigowar JB ce ta sata juyowa a hankali tana kallonshi ……Zaro ido yayi da sauri yana fadin "Meye haka nake gani Baby……? Inda taga yana kallo nan ta kalla……irin tsutsotsin dake fitowa daga kasanta ne suka gangaro kasan kafafuwanta ……azababben kuka ta sake tare da kifa kanta saman gadon …… "Kai wallahi baran iya……Tsutsa fa Safeena ke fitowa daga jikinshi ……Kai Bata yiyuwa wallahi Ina Sonki Safeena amma har ga Allah baran iya rayuwa dake ba da wannan abun a jikinki ……zan bayar da ko nawane idan mun koma wani yazo yayi jinyarki amma bani ba……" Da sauri ta dago tana kallonshi da rinannun idanuwanta ……kafada ya daga yana fadin "Yeah Safeena ina sonki amma baran iya rayuwa dake ba a haka ……ni zan biya kudi wani yazo yayi jinyarki harki warke baby ……Sorry……" Bata ga laifinshi ba har ga Allah sannan ta san granny kadae ke iya jinyarta a haka ……Wasu hawaye suka zubo mata data tuna cewa yanzu tsofa ya zowa granny ba komae zata iya mata ba a rayuwa ita kanta granny tana bukatar Kulawa a yanzu ……Maryam fa ……Runtse ido tayi gam tana girgiza kai …… 《》《》《》《》 Karfe biyu Hajiya ta tada Fadila tare da bata zoben ……a hannun haggunta ta daura sannan ta kalli yamman tayi kamar yarda boka ya fada amman zoben still na hannunta bai bace ba …… Kallon hajiyan tayi tace "Hajiyarmu kinga bai bace ba fa……" "Ki sake gwada wa mana kila ba yi daya yake bace wa ba……"hajiyar ta fada kamar bata so wani yaji abunda take fada Cikin sanyin jiki ta sake maimaitawa amma still zobe be bace ba ……kusan kwana sukayi suna abu daya amma zobe na nan daram ……kusan asuba fadilan ta kalli hajiya a hasale tana fadin "Wannan munafukin bokan karya yake babu wani abunda zai iya……" ,"Uban wa yace maki bara ya iya komae ba kaji mara kunyar yarinya fada man,uban,wa ya hada auren duka iyayenki idan bashi ba?wallahi ki kiyayi bakinki ……"itama ta fada a hasale don ko kadan bata kaunar ace bokanta bai iya aiki ba…… Tsaki fadilan ta sake sannan ta bar dakin gaba daya ……Falo ta koma ta kwanta cikin mintuna kadan wahallen bacci ya saceta ……ko sallar asuba ba tayi ba har kusan karfe 11 sannan ta mike ta koma dakin hajiyar tayo wanka ta fito tayi breakfast…… 《》《》《》《》《》 Tunda JB ya gane raliya bai kara kwana daki daya da Safeena ba ……sannan ko ya shigo dakin ya dinga dode hanci kenan wae wari dakin keyi ……Tun bata jin haushin abun har ta fara ……Saboda dae dae gwargwado tana kokarin gyara jikinta duk da abunda ke fita …… Sam ita bama taga amfanin shigowar tashi ba tunda ba wani abu yake tsinana mata ba komae ita zata tashi da kyar tayi abunta bata jiranshi…… Tana kwance kalabar da Maryam ta mata kafin so zo ya shigo rike da leda a hannunshi daga bakin dakin ya tsaya yana kallonta "Baby ki shirya gobe zamu wuce……" *FEEDOHM💞* [9:05PM, 11/4/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹* 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 © *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM💞_* *Devoted to Ummi A'isha👌🏻* *Bestowed to Aunty Sis💕* 3⃣4⃣ Dan kallonshi tayi ta cikin mirrow ta watsar sannan ta cigaba da abunda take ba tare da ta amsa ba "Wae baby sae wani sha man kunu kike ko nayi laifine?ya fada tare da langwabe kai yana kallonta ,Tabe baki tayi tana girgiza kai a hankali sannan ta mike tsam ta koma gefen gado ta zauna tana latsa wayarta……karasa shigowa dakin yayi ya tsugunna gefenta yana bata fuska kamar yaga kashi "Sorry baby wallahi ina sonki matsalar daya ce baran iya zama dake ba a haka ,dan Allah ki gafarceni idan munje gida zan samu wani na biyashi kudi yayi jinyarki har ki warke na tabbata granny barata iya jinyarki ba tunda tsofa yazo haka Abba shima namijine zan samu wanda na aminta dashi sae na maki saki daya na bashi kudi ya aureki yayi jinyarki harki warke sae ya sakeki mu mayar da aurenmu ……" Binshi tayi da ido lallae JB wawa ne na karshe a tunaninshi wane sakarae zai aureta a haka har ma yayi jinyarta ta warke sannan ya saketa kamar wani wawa…… Hannunta ya kamo duka biyun "Kiyi hakuri baby wallahi ba yarda na iya ne bana kaunar jini bare wanda ke fita da tsutsa,Na yarda zan kashe ko nawane don ayi jiyarki baby ki dawo gareni……" Har lokacin kallonshi take cike da mamakin maganganunshi a yarda ta fahimta sam JB ba karamin wawa bane a tunaninshi ita zata yarda idan ta warke ta dawo gurinshi ……nadamar aureshi ta,zo mata ……Cikin dakewa ta gyada kai alamun ta yarda da zancenshi "Amma Jabir wa kake tunanin zai aureni a haka? Yar dariya yayi "Gasunan da yawa baby ,babu abunda kudi bara suyi ba……Ko wannan,driver naki ai na tabbata zai yarda yadda naga ya damu da rashin lafiyarki sannan uwa uba ga kudin da zan bashi ……amma dan Allah karki fadawa Abbanki ni nasan yarda zan ce mashi ……" "Abdul Maleek kake nufi?……ta tambaya tana gyada kai tare da kura mashi ido "Eh shi mana ,na tabbata zai iya jinyarki yarda ya kamata na yaba da kulawarshi……beside ma 10m zan bashi yayi jinyarki sannan nan na kara mashi 10m tare da gidana dake GRA ya sakeki bayan kin warke……yayi ko? Juyar da kai tayi sau biyu bata da tabbacin Abdul Maleek zai yarda ……koda ya yarda ya aureta ta tabbata bara ya saketa ba don ta warke ……Gyada mashi kai tayi alamun ta gamsu 《》 《》《》《》 11:46am Dae dae suka gashi cikin garin katsina gida Abba yace a wuce da ita amma sam tace gidan granny take so , Abban cewa yayi a wuce da ita gidan granny gashinan zai zo a bakin kofar gidan suka iske maryam har ta rigasu zuwa ,da murnata ta bude motar ta kamo Safeena tana tambayarta ya jikin Tabe baki tayi tana fadin "Ke ba sauki……" Ahankali ta gyada kai jikinta a sanyaye sannan ta kamata JB na bayansh har cikin gidan ,A falo suka iske granny kwance saman doguwar kujera bata jin dadi tana ganinsu ta mike da fara'a tana taba hannu "Maraba da yan tafiya,ai ban dauka da wuri zaku iso ba……" Zama tayi kasan carpet tana fadin "Maryam taikaman da ruwa please……" babu musu ta mike da sauri ta bude fridge ta dauko masu bottle biyu tare da cup ta aje daya gaban JB sannan ta dawo ta zauna kusa da Safeena tare da tsiyaya mata ta mika mata tana fadin "Sannu besty……" Suna gaisawa da granny Abba ya shigo Abdul Maleek ya kawoshi ……Hannu ya mikawa JB din suka gaisa sannan ya juya ya gaida hajiya tare da mata ya jiki Sannan ya juya gurin Safeena "Safeena ya jikin……" Bata fuska tayi tana fadin "Abba wallahi ba sauki kamar kara man ciwon akayi da naje can……"ta karashe maganar murya na rawa "To yi hakuri Allah zai baki sauki kin ji ko "ya fada cikin sigar lallashi ,sannan ya juya gurin JB yana fadin "Jabir ya hanya? "Lafiya lau Abba mun sameku lafiya……"ya fada yana kallon Maleek da ya shigo lokacin Hannu Maleek din ya mika mashi suka gaisa sannan ya matsa gurin granny tare da dukawa yace "Hajiya ya karfin jikin……" "Baka da kunya Abdul Maleeku jiya ya mukai da kai da safe ……"ta fada tana hararanshi ,Satar kallon Safeena yayi sannan yace "Ayi hakuri tsohuwa……" "Haba wallahi zaka sameni ne ……"ta fada tana gyada kai ,maryam tayi dariya tana fadin "Haba granny dan kinga mutane zaki dinga daga mashi murya Abdul Maleekun ki fane ……" dariya Abba yayi sannan yace "Ka dauko man wayana ……?gyada kai yayi sannan ya mika mashi tare da zama kasan carpet ya lankwashe kafa …… Cikin Sanyin murya JB yace "Abba dama akwae maganar da nake so muyi da kai ……"ya karashe maganar yana satar kallon safeena wadda itama shi take kallo tana son taji me zai fada "A a ba komae Jabir ina jinka……" Maleek ne da Maryam suka mike zasu fita Abba ya dakatar dasu "ku zo nan Abdul Maleek damu da ku duk dayane……" Babu musu suka dawo suka zauna Cikin ladabi da sanyin jiki yace " Abba dan Allah ka gafarce akan abunda zan fada……" Sosae jikin Abban yayi sanyi yace "Bakomae Jabir ina saurarenka……" "Abban tun lokacin da Mummyna ta samu labarin Safeena bata lafiya ta kafe dole sae na rabu da ita a cewarta baran iya kula da macen dake dauke da wannan ciwon ba ……Abba yanzu maganar da nake jiya ta kirani tace idan ban saki Safeena ba zata tsineman Albarka ,wallahi na rasa yarda zanyi da rayuwata har ga Allah ina son Safeena amma mummyta ta dage akan sae na rabu da ita ……Babban abunda nake tsoro tsinuwar da tace zata man na tabbata zatayi ……" Sanyaye Abba yace "Uwa ta wuce yarda kake tunani Jabir tun ,lokacin da ta nuna rashin amincewarta da auren ya kamata kazo ka fada man ,Jabir tsinuwar Uwa ba abun wasa bace ka kiyayeta ,Duk abunda mahaifiyarka bata so ka kiyayeshi domin samun albarkar rayuwa……har ga Allah bazan zargeka ba kayi man halacci sossae na aurenta da kayi ,Ni kaina mahaifin Safeena na yarje maka daka saketa yanzu Idan matarka ce bayan ta warke zan sake baka ita Jabir ,Allah yasa hakan ya zama Alkhairi sannan Allah ya albarka ce ku baki daya……" A sanyaye ya fito da takarda ya aje gaban Abban sannan ya fita falon da sauri yana dafe kai kamar mai shirin faduwa "Jabir kabi a hankali karka fadi ……"Cewar Abban ganin zai fadi ,sannan ya kalli Abdul Maleek yana fadin "Taimaka Abdul Maleeku ka maidashi gida kada yaje wani abu ya sameshi a hanya ……"Mikewa yayi a sanyaye ya bi bayanshi Abban ya juyo yana kallon Safeena sam babu damuwa a tare da ita hakan ba karamin dadi ya mashi ba "Safeena kinga yarda Allah ya kadarta maki ko,karki dauki wannan a,bakin komae insha Allahu zaki samu lafiya sannan,ba kasar da zaa maidaki ni da kaina zanyi jinyarki kinji ko ki ci gaba da addu'a ……" Gyada kai tayi a hankali tana jinjina munafunci irin na JB wae mum dinshi tace zata tsine mashi saboda masifar karya ,Sannan ta kalli Granny da ta rafka uban tagumi duk abun duniya ya dameta……Ji tayi maryam ta kama hannunta tana fadin "Sorry besty……" *FEEDOHM💞* [3:44AM, 11/5/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹* 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 © *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM💞_* *Devoted to Ummi A'isha👌🏻* *Bestowed to Aunty Sis💕* 3⃣5⃣ Abdul Maleek kam a bakin mota ya iske JB jingine kamar yana jiran wani ,Kallo daya ya mashi ya watsar sannan yace "Alhaji yace na maidaka gida……" "To nagode"ya fada tare da bude frnt sit ya zauna zagayawa Maleek din yayi ya zauna sannan ya kunna motar suka juya ……Sae da suka fita unguwar sannan JB ya kalleshi fuska daure yace "Abdul Maleek ina son ka auri Safeena yanzu……" Wani wawan burki ya taka su duka sukayi gaba tare da dawowa baya suka daki kujerun da suke zaune ……Wani irin kallo yake watsawa JB din kafin yace "Out of sense……" ya kunna motar ya ci gaba da tafiya "Seriously Abdul Maleek zan baka 20m da gida ,ka auri Safeeena har ta warke sannan ka sakar man ita na aureta……" wannan karon birkin da ya taka yafi na dazu don har sae da suka sauka saman hanya,Gaba daya ya juyo yana kallon JB din …… Dafa kafadarshi JB yayi yace "Ka natsu sosae Abdul Maleek na tabbata kudinne suka rudaka haka ,Zan baka fiye da haka in dae kan Safeena ……Abunda nake so ka yarda ka aureta kayi jinyarta yarda ya kamata bayan ta warke sae ka saketa ba tare da ka bari Abbanta ya san ni na saka aurenta ba,Abunda yasa nake son ka aureta Saki uku na mata na tabbata idan dad dina yaji na saketa cewa zaiyi dole na mayar da ita saboda akwae kyakykyawar alaka tsakaninsu da Abbanta ni kuma baran iya zama da ita a haka ba kaga kenan ko yace in maidata auren bara ya yiyu ba ,kai kuma auren kisan wutane zakayi har ta warke saboda idan ta warke nazo nace ka aureta zaa dauki lokaci kafin ta fito kila ma har ka fara jin wani abu game da ita ,dan zaman da zakuyi idan bata lafiya babu abunda zaka ji, aikin kudi kawae zakayi ……" ********************** ? ************************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************? ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ? ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ? ************************** Girgiza kai yayi tare da jinjina jahilci irin na JB a tunaninshi kudi zasu sayeshi ne wae 20m ko yanzu ya tabbata kudin dake accnt dinshi sun lika abunda yake kokarin bashi ,lallae ya yarda komae ilminka na boko indae babu na addini to da kai da jahili duk daya kuke ……ai ko duniya zata hade baya tunanin zaiyi gangancin sakin Madam ba,bayan ya sameta …… A jahilce ya kalli JB din yace "taya kake tunanin zata yarda na aureta……" "Kar ka damu ni zan shirya duk yarda zaayi sae dae ban yarda ka rike ko da hannunta bane da sunan ta birgeka sannan ban yarda tayi kuka ……" Gyada kai yayi sosae yana kallonshi ……a cikin manyan jahilae ya yankarwa JB katon fili ya ajeshi, ji yayi yana fadin "karanto man account numberka na tura maka 10m yanzu zuwa lokacin da zata warke zan baka sauran ,idan kuma baka da account din gobe zanje na bude maka a bank……" Murmushi ya saki mai sauti sannan yakaranto mashi accnt number din "Wane bank ne "Jb ya tambaya……"UBA" ya bashi amsa a takaice…… idan yaki karbar kudin zai iya fahimtar wani abu…… Mintuna kadan Alert ya shigo mashi Sae da ya duba sannan ya tashi motar suka karasa gidansu JB din ,a bakin gate yayi parking JB ya fito da card dake dauke da numbershi ya mikawa Maleek din "Ka kirani anjima by 9:30 zanyi saving numberka ……"daga haka ya wuce abunshi Bayanshi ya bi da kallo tare da tribted dinshi yana fadin "Shugaban wawaye……" A hankali …… Juya kan motar yayi wani farinciki na ratsa shi wani bangare na zuciyarshi kuwa tsoro yake kar Abban ya ki yarda da wannan zancen bogin ba…… 《》《》《》《》 Cup ta mika mashi tana fadin "Alhaji Safeena ta dawo amma bara ta zauna nan gidan ba fisabilillahi, Me yasa baku daukeni a matsayin mahaifiyarta ba……kusan kwana biyu fa kenan duk tunanina zata dawo nan amma shiru……" "Ba haka bane ba Fateema Safeenarce ta matsa dole sae gidan hajiyarta zata zauna ,kuma naga da nan da can duk daya ne kawae fatanmu Allah ya bata lafiya……" "Ameen amma ya mijin nata yace ,nayi tunanin ko gidanshi zata zauna ma……"ta fada cike da son sanin halin da ake ciki Bai kawo komae ba a ranshi ya fada mata yarda sukayi da jabir din ya kara da fadin "Ni kaina nayi mamakin saki ukun dake cikin takardar don duk tunanina bai wuce saki daya ba sae daga baya nayi tunanin kila mahaifiyar tashi tace ya mata haka ……fatana Allah ya sa hakan ya zama alkhairi garemu baki daya……" Hannu ta daura bisa kai tare da sakin kuka tana fadin "Amma dai wannan dan iskan yarone shikenan don bata lafiya sae ya kama ya mata saki har uku Alhaji ……" Ganin abun nata ya koma hauka ya sashi shareta …… Wayarshi ta hau ringing ya kalleta "Dan Allah kiyi shiru zan amsa waya " Tare da daukar wayar ya kanga a kunne …… Daga dayan bangaren JB ke fadin "Abba naje office dinka an fada man kana gida yanzu haka ina bisa hanya zan iya karasowa gidan koko sae kadawo na sameka office din……" *"Ka karaso mana jabir ……" "to Abba" Falo ya sauko ya zauna Aunty Fatee ta biyoshi baya ,Cikin yan mintina Jabir din ya iso har kasa ya gaidashi sannan ya gaida Aunty fatee ya zauna "Ya Abban naka Jabir……" "Lafiya lau Abba yace ma a gaidaku ……" "Muna Amsawa ai jiya munyi magana dashi na fada mashi ba laifinka bane jabir……" Dukar da kai JB din yayi sannan ya saka hannu ya fito da ticket guda biyu tare da mikawa Abban "Abba gashi visa ne na nemawa Safeena zuwa asibitin Madina a dubata to da tare dani na zamu tafi sae Mum dita tace baran je ba ,to Abba kawae sae na maida Sunan Abdul Maleek don na tabbata zai kula da ita sosae ……" "Wane irin abune Jabir taya zaka daurawa mutun wahala ba tare da saninshi ba ,duk da Abdul Maleeku karkashina yake baran iya take hakkinshi ba sannan Abdul Maleeku ba muharramin Safeena bane da zaiyi jinyarta kaje a soke wannan Visar ba mai yiyuwa bace Jabir……" ya fada cikin daga murya Kwantar da murya yayi yana fadin "Abba tun ina can na kira Abdul maleek din na fada mashi kuma ya yarda sosae ,bara ma na kira maka shi……" "Dama ta ya zaiki yarda ,Ban taba sa Abdulmaleek wani abu ba yaki yi man ,wannan karan baran shiga hakkinshi ba ……" "Wallahi Abba ya yarda ,da sunanka zan saka sae yace na sa nashi zai tafi da ita,……"ya fada cikin kwantar da murya "Idan ya yarda shi Muharramintane da zasu tafi a tare har yayi jinyarta? "Abba Safeena bata da aure yanzu , Kana iya ba Maleek din aurenta kafin sun tafi tunda sae sati mai zuwa tafiyar ,Ni kaina na yaba da hankalinshi wallahi babu wanda zai iya kula da Safeena kamar shi ,dole Wanda zai kula da safeena ya zama mai rikon Addini ,hakuri,kyautatawa da juriya Abba ,kuma duka Abdul Maleek yana dasu ,shin Abba kana da wanda zaka tura mai irin wadannan halin yanzu,idan kana dashi lokaci bai kure ba zanje na sake masu wata Visa ,fatana ta samu sauki……" Aunty Fatee dake zaune ta zaburo tana fadin "Wane irin Safeena ta auri da Abdul maleek kuma?kai jabir wannan ba zancen kamawa bane kamar dae bata da yan uwa sae a dauki aurenta a ba driver ,don yayi jinyarta kawae ,Kaga Alhaji ko Uncle Abbah sae su tafi da ita,ko ni da kaina nayi jinyar ta……" *FEEDOHM💞* [5:38AM, 11/5/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹* 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 © *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM💞_* *Devoted to Ummi A'isha👌🏻* *Bestowed to Aunty Sis💕* 3⃣6⃣ Cikin Sanyin jiki Abban yace " Fateema AbdulMaleeku yana da duk abunda jabir ya fada kuma nima zanso na bashi amanar diyata matsalar kawae shin idan na hadashi aure da Safeena suka tafi ban cuceshi ba? Karaf tayi tace "Ai ko ka cuceshi Alhaji, ae sae duniya ta zagemu mun dauki diya da cuta mun lakaba mashi don kawae yana karkashin mu……" Daga mata hannu yayi yana fadin "Fateema dan Allah idan bara kiyi shiru ba ki koma daki tunda babu wanda ya kiraki ……" Mikewa tayi tana fadin "Wannan ai son kaine ,Kuma wallahi bara ta yiyu ba……" Binta sukayi da kallo har ta shige daki tana gunguni sannan JB yace "Abba ba cuta, har kudi nace zan bashi yayi jinyarta amma yace bara ya karba ba sannan na fada mashi indae aka sa sunanshi to zai aureta kafin su tafi yace ya yarda ,Wallahi Abba yaron yana kaunarku yarda baku tunani ……" "Duk da haka jabir sae naji ta bakinshi sannan……ka kira manshi yanzu yazo……" Ko da Abdulmaleek din yazo Abba ya mashi magana cewa yayi ya amince, dama me neman kuka ne aka jefeshi da tsakuwa , Sai dai baiyi tunanin Abban zai amince da wuri ba haka …… Farinciki Sosae Abba yake da Maleek din ya amince gidan granny yaje ya fada mata ,itama kasa boye murnarta tayi ta fara guda tare da hamdala tana kwarara mashi addu'a ……Safeena kam tabe baki tayi da Abba ya fada mata don ta riga ta san dawon garin sannan ta dauki alwashin ko ta Warke Abdul maleek din ya saketa bara ta koma hannun JB ba……Maryam ta janyo hannunta tana fadin "Ke bama zakiyi farinciki ba Allah ya baki wanda yafi Jabir din " Yatsina fuska tayi tace "ke kina farincikine……" Cikin fara'a ta gyada kai"Sosae besty samun kamar Maleek sae an tona kinga dae drivernki ne amma yana da wadatar zuciya gashi dan gayu ga kyau ga ilimi wallahi ba wanda zai ce baya da kudi ……" Kallonta tayi tace "Yana burgeki ne besty" Yar dariya maryam ta sake tace "duk wanda yace Abdulmaleek baya burgeshi yana bakin cikine ……" Yan mintuna ta dauka tana kallonta sannan tace "Za ki iya aurenshi……" Harara ta watsa mata tana fadin "Besty akwae shirme wa yace maki zan iya aure maki miji……" Hannayenta kamo sannan tace "Besty ba shirme bane Indae kina son Maleek na maki alkawarin da mun dawo zaki aureshi……" Duka maryam din ta kai mata a cinya tana fadin "Sae inyi ya da Ahmad……" Dariya Safeenar ta sake tana tsuke baki "Oh na dauka an ture gwamnatin Ahmadi……" Granny ta shigo tana fadin "Mara kunya ana fada maki kina yatsinawa mutane fuska amma kin shigo daki har da kashewa, dama ni nasan a rina ana son dan yaro ana kaiwa kasuwa……" Harara ta sakar mata tana turo baki tace "Ai duk abunda ba dan Allah akayi shi ba watsewa yake da wuri……"ta karashe maganar tare da murguda baki "Ke dae kika sani ……"cewar granny sannan tayi gaba tana Fadin "Ke kuma Mayyarta sae ki tashi ki je gida ki gaido mamanki ga Abdul Maleek nan zaizo ya tafi dake ……" "Kai granny ina ruwanki ……"cewar Safeena "Kyaleta besty ba komae naji ni mayyarki ce ita kam ko Tayya bata da ita bare mayya ……" Langwabe kai Safeenar tayi "Nima ai mayyar taki ce besty you done much to me……" Granny suka jiyo tana fadin "Haba yarinya biye mata, zata tafi ta barki ki zo nan kina man mashau mashau da ido wae ke Safeena bata nan lokacin zanci kaniyarki wallahi ,kuma ki fito ya ajeki gida tunda baku da hankali ku duka……" Tare suka fito tana rike da hannun Safeenar sannan ta zaunar da ita bisa kujera , Abdul Maleek maryam ta kalla dauke da fara'a "Ompo besty……" ta fada cike da zolaya Dan murmushi yayi yana kallon safeena ta gefen ido ……ta wani hade rai kamar NADIYA DA AHMADI…… "Rabu da su Abdul maleeku za suyi bayani ne gaba kadan ……ka biya gidan Malam ka karbo abunda yace zai baka "Granny ta fada sannan ta mike ta koma daki ,Itama Maryam din fita tayi ta bar falon ,Cikin sanyin jiki ya dawo gabanta tare da zama kasa "Madam kinga ikon Allah ko……" Yar dariya tayi tana fadin "Ikon naira dae Maleek ……" Shima murmushin yayi "Kin san komae kenan " Tabe baki tayi tare da juyar da kai "Zuwa gobe zaa daura mana aure kin yarda da hakan ……"ya fada yana kallon fuskarta "Duk cikin aikin kudinne ka tambayi yardata?Bestyna na jiraka a waje da gurinta ka tafi da ka fi burgeni Maleek ,lastly banyi tunanin kudi zasu saye ka ba har ka yarda da irin wannan wahalar ……" Murmushi yayi mai sauti " In dae kece bana tunanin zanyi wahala Madam, zan iya komae a rayuwata akanki……" "Gyara kalamunka Maleek cewa zakayi indae akan kudine zaka iya komae a rayuwa……" Mikewa yayi yana leken fuskarta "A yarda ku ka tsara kenan Safeena ,amma a sannu zaku san waye Maleek da yarda na tsara nawa labarin Madam ,ba irin karen da kuke tunani bane daga ke har Jabir din ……" ya karashe maganar tare da kashe mata ido ……Saurin janye idonta tayi tana kallon kafafuwanshi…… 《》《》《》《》 A hasale hajiyarsu tace " Uban meye amfaninki da har zaki bari ya yarda ,sannan dan kina banza sae ana gobe daurin auren zaki zo ki fada man, Yanzu uwarki kike so inyi……" Shiru tayi tana kallon fadila dake kwance bisa cinyar Aunty zuby tana kuka, Sannan tace "Wallahi hajiyarmu ba yarda banyi ba amma ya amince mashi ……" Aunty Zuby ta harziko tana fadin " Dallah rufe man baki ,ke ba mace bace dan ubanki ,Wallahi bayan a gida hajiyarmu ta haifeki da sai ince masanya aka mata a asibiti,Ke fadila ta fara fadawa matsalarta amma gabanki aka rushe duk wani plan dinmu ,sannan dan kina wawiya ki kwaso shegiyar kafarki kozai kozai kizo kina fada mana ……" Kuka ta saki tana fadin "To ni Aunty Zuby ya kuke so nayi maku ……" "Ubanki muke so ki mana"cewar Hajiya Cikin gunguni Aunty fatee tace "Sae dae kuyi hakuri tunda lokaci ya kure" "Sae dae Uban kowa ya rasa wallahi Aunty fatee" Fadila ta fada cikin kuka hade da daga hannunwa sama…… "Dallah rufe man baki dan ubanki ,Ina kika kai zoben da boka ya baki……"cewar hajiya "Yo ni nasan inda yake" Fadila ta fada Aunty Zuby ta dago kanta a fusace tana fadin "Tashi ki nemoshi dan bura ubanki yanzu mu koma gurinshi……" Sannan ta mikawa Aunty Fatee hannun "Ke kuma ina kudin da nace ki tahowa da hajiya dasu……" Jikkarta ta bude tana gungune ta fito da rapper ta dubu ta mika mata ,Fizgewa tayi sannan ta ciri kusan rabi ta mikawa Hajiyar sauran ta bi fadila daki "Kin ganshi koko" Turo baki Fadila tayi "Yo banganshi ba mummy,ni fa wannan shegen bokan ba abunda ya iya……" Duka ta kai mata a baki "Dallah rufewa mutane baki sakaran banza uban wa ya hada aurena da ubanki idan bashi ba……" *FEEDOHM💞* [5:25AM, 11/7/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹* 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 © *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM💞_* *Devoted to Ummi A'isha👌🏻* *Bestowed to Aunty Sis💕* 3⃣7⃣ 『 *_MEENARH PARROT♣ Wannan page din naki ne kyauta 🌹Don na tabbata ni da ke kadae ne muke_ ™JB💃🏻💃🏻……* 』 Neman duniya sukawa zobe amma sam babu alamunshi a cikin dakin, Hajiya tace su bari zuwa gobe sae a fitar da kayan dakin kila wani guri ya makale …… 『』『』『』『』 Abdul maleek kam ko da ya fadawa Baffanshi abunda ke faruwa fatan alkhairi ya mashi ,Wanda dama ya riga ya sani Baffan nashi baya da matsala ,Nana ma kasa rufe baki tayi don murna har ya fita waje ta bishi da gudu tare da riko mashi hannu ta baya ……"Baddi na zaiyi aure" ta fada tana washe baki Dan juyowa yayi yana kallonta sannan yace "Ko bakya so ne Nana" Saurin girgiza kai tayi tana fadin "Ahh baddi ina so mana ,kaga sai in koma gidanka ko? Murmushi ya mata yana fadin "Jeki ki wa inna aiki kinji ko ……" 《》《》《》《》 *Friday……* Bayan an gama sallar juma'a a cikin masallacin liman ya daura auren *ABDULMALEEK DA SAFEENA* Duk da ba wani gayya Abba yayi ba amma daurin auren ya tara dumbin jama'a wanda ko bikin farko bai tara su ba ,yawancin mutanen duk abokan arzikin Abdulmaleek din wanda harda Justice Ahmed kabir tare da VC na yar adua ……Jabir ma baa barshi a baya ba don har dad dinshi sae da yazo gurin …… Yar walima Dad ya hada aka ci aka sha daga abunda ya sawwaka sannan kowa ya watse dob baiyi tunanin daurin auren zai tara mutane haka ba……JB ne yabi bayan Maleek din ganin zai shiga mota ya barshi ,janyo kafadarshi yayi yana fadin "Ba ka ji ana kiranka ba ne" Lumshe ido yayi yana fadin "Oh JB banji ba wallahi ,ina saurine zan gano jikin madam ne duk yau banje ba……" Wani tukukun bakin ciki ya tokare mashi wuya ,ya dage kafada yana wulla mashi wani mahaukacin kallo "Ban yarda ka dinga shishshige mata ba Maleek ……"ya fada a hankali Murmushi yayi mai sauti "Baka san hakkin mace bane akan mijinta?alright bara na fada maka don bana tunanin unguwarku akwae islamiyya ,Madam tana karkashina yanzu dole na kula da ita yarda ya dace ba tare da na gaji ba ……" bai saurare shi ba ya fada mota tare da bata wuta ya barshi tsaye Kallo ya bishi dashi tare da dunkule hannu yana naushin iska ,Dafa bayanshi da akayi ya sashi juyowa da sauri tare da dukar da kai "Abba ina wuni" "Lafiya lau jabir ,ga Dad dinka can baya yana nemanka kaje ka sameshi ……" Abban ya fada tare sa shigewa motar dake kusa da JB din suka tafi da wasu mutane …… Da kyar ya ja kafafuwanshi ya isa gurin Dad din nashi suka koma gida ,A falo ya suka iske Mum dinshi zaune ita kadae ,Dad din shigewa part dinshi yayi ,shi kuma JB din ya zauna falon tare da sake uban tsoki Da sauri Mum din ta kalleshi tana fadin "Kae da wa Son" Tsakin ya kara saki tare da fadin "Mum wannan bakauyen ne man " Tasowa tayi tare da zama hannun kujeran da yake "Me kuma ya maka? "Mum magana ya fada man ,Don nace kar ya shishige mata ,kuma wallahi sae na dauki mataki bai shani banza ba…… " ya fada cikin daga murya "To ai Jabir dole sae ka kauda idonka zuwa lokacin da zai sakar maka matarka ,ka daure kaji ko,karka damu da ta warke zai saketa…… "ta karasa maganar cikin sigar lallashi Yatsina fuska yayi "Mum yunwa na ke ji fa "……Mikewa tayi ta nufi Darea ta dauko mashi trnks na abincinshi sannan ta dawo ta zuba mashi ,Sae da ya fara ci sannan ta nufi gurin dad dinshi…… 《》《》《》《》 Da sallama ya shiga falon amma shiru babu motsin kowa a ciki ,yayi minti goma a tsaye amma ba wanda ya amsa sallamar ,Dakin da Safeena ke ciki ya leka tare da sallama, idonta na kan wayarta ta dago a hankali tana mashi kallon kasa kasa ,sannan ta mayar da hankalinta ga abunda take …… Da murmushi yake fadin "Madam sallamar ma bara ki amsa ba ko?to ai sallama dolene a amsata indae anyita ……" Harara ta sakar mashi ganin yana kokarin shigowa har da su tura dakin tana fadin "Idan a azuciya na amsa fa?ka bude man daki zafi nake ji maleek ……" Murmushi ya sakar mata yana kashe mata idanu "Yi hakuri sai na kunna maki fanka madam ……"ya karashe maganar tare da kunna fankar sannan ya karaso bakin gadon ya tsaya saitinta fuskarta yana kallonta "Wae meye ne kulle Daki kuma ……"ta fada tana bata fuska ba tare da ta dago ba Hade hannayenshi yayi yana fadin "Allah ya baki hakuri don kada kofar ya dinga kara ne naga ana iska ……" Banza ta mashi tana latsar wayarta ,Ganin ba kulashi zatayi ba ya saka shi zama gefen gadon tare da zare wayar a hankali "Meye haka Maleek "ta fada cikin daga murya Yatsanshi ya daura saman lips dinta "Shiii meye na daga murya Safeena ,ko kema baki san matsayin miji a gun matarsa ba ne?ya karashe maganar a hankali tare da langwabe kai gefe guda Dariya ta subuce mata hadi da watsa mashi harara "Fada man matsayin da kake dashi bayan auren kishin wuta kayi ……" Tabe baki yayi yana kashe mata ido "ko……" Gyada kai tayi still tana hararanshi ,Katse maganar yayi ta hanyar tambayarta "kinci Abinci……? "Shafa kaji ……" ta fada tare da sakin karamin tsoki "Wow ina zan shafa Madam……" ya fada yana kanne ido Hararanshi tayi tare da sauko da kafafuwanta kasa ta mike tsaye tana fadin "Idan ka gaji da zaman dakin ka fito ……" bata rufe baki ba ya dagata cak ya nufi hanyar fita da ita yana fadin " Ina zamu koma to madam ……" Mutso mutso ta fara tana fadin "Ka saukeni Maleek dan Allah ……"Wani wahallen kallo ya watsa mata har sae da ya direta falo sannan …… A sanyaye ta bishi da kallo ganin farar Shaddar dake jikinshi tayi staining sossae daukotan da yayi ……A hankali ta dukar da kanta kasa tana kallon carpet , Ganin yanayinta ya sashi dago habarta yana murmushi "Zan samu clean a ciki madam ……?ya fada saitin fuskarta A Sanyaye ta gyada mashi kai "Sorry Abdul Maleek ,sae da nace ka saukeni amma kaki ……"ta fada idanunta cike da kwallah "Kin sani na daukeki ne dole Madam?karki damu kinji ko zan wanke gurin yanzu,Idan naje gida zan canza kayan dama……"ya fada yana sake mata lallausan murmushi …… Mintina kadan ya fito ya wanke gurin, yana fadin "Ina Maryam da Hajiya ne ? "Sun fita" ta fada a takaice "Ok ,ke kin ci abinci ne……?ya fada babu alamun wasa Dagowa tayi da niyar hararanshi amma ya mata kwarjini tayi saurin mayar da kanta tana girgizawa a hankali "Ok kina cin Kebabs na dauko maki a mota ko akwae abinci a kitchen na dauko maki ……" Yatsina fuska tayi tana girgiza kai a hankali "Wane kike so Safeena "ya fada cikin sigar lallashi ……Saurin kallonshi tayi, Yarda yake magana cikin natsuwa da lallashi kamar ba Maleek ba ,Duk da tasan mai ajine amma yau ya sauya sosaae …… "Safeena……" "A kwae a kitchen" ta fada a takaice Da ya ke ya san kitchen din ya shiga ya zubo mata sakwarane da Miyar egusi da taji danyen kifi sosae a ciki ,Dawowa yayi ya daura mata plate din saman stool din dake gefe sannan ya matsar mata dashi gabanta shi kuma ya zauna a kasan carpet tare da harde kafafuwa yana kallonta…… Ji tayi ta takura ,duk yarda taso ta daure kar tayi mashi magana kasawa tayi "Meye kake kallona haka ……"ta fada lokacin da ta kai lomar sakwaran kusa da bakinta "Yi hakuri ……"ya fada a sanyaye bata kuma cewa komae ba har ta gama cin abincin sannan ya dauke komae ya mayar ya dawo "Na taimaka maki kiyi wanka ……? Dakyar ta taushi bakinta daga bakar maganar da take niyar kwabo mashi…… "Kinyi shiru madam ……" "Nagode idan Maryam ta dawo zanyi ……"ta fada fuska a daure Murmushi yayi mai sauti sannan yace "Ba matsala ,ni zan tafi idan Hajiyar ta dawo kice ina gaidata ……" kafin ta bashi amsa ya bata kiss a gefen kumatunta sannan ya fita da sauri don ya tabbata bara ta iya hakuri ba Dariya yayi lokacin da yaji tana fadin " Da ka tsaya mana wallahi duk da bana lafiya sae kasha mari …… *FEEDOHM💞* [9:01PM, 11/7/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹* 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 © *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM💞_* *Devoted to Ummi A'isha👌🏻* *Bestowed to Aunty Sis💕* 3⃣8⃣ 『 💜💜💜💜💜💜』 *Wannan page din kyautane ga dukka mosayan wannan book din ,nagode da kaunarki gareni*💞 Cikin bacci JB yaji wayarshi na ringing kai hannu yayi ya dauka ba tare da ya bude ido ba "To karamin dan iska shine tun da ka tafi ka gagara kirana ko ,Ga raliyar banzaye ta gama maka amfani ……" Waro ido yayi tare da mikewa zaune tsakiyar gadon yana fadin "Wallahi raliya ba haka bane na dawo gida na iske Dad baya lafiya so hankalina ba kwance yake ba……" Dariya mai sauti ta saki tana fadin "Kar ka gwada man karya JB ……" Cikin kwantar da murya yace "Ba Karya na maki ba raliya ……" ket yaji ta katse wayar ba tare da ya karasa maganar ba ,Tabe baki yayi yana fadin "Wawuyan yarinya zaki tada mutun yana bacci ……" Sannan ya gyara kwanciyarshi ,cikin mintina kadan bacci yayi gaba dashi ……A cikin baccin ne yayi mafarkin Raliyar ta zo mashi cikin wata irin Mummunar siffa tana fada mashi zatayi tafiyar Shekara dari amma da ta dawo zata nemeshi ……Firgigi ya farka yana lalubar wayarshi tare da sake kiran numberta amma switch off ,Yanayin yarda ya ganta tayi bala'in tsoratashi ,A sanyaye ya mike ya fita daga dakin ya koma dakin Mum dinshi ya kwanta sae dae babu alamun baccin da ke tare dashi…… 《》《》《》《》 Ranar da zata su tafi tun da safe Maleek yaje daura gidan Malam ibrahim bayan sun gaisa ne yake fadawa malamin cewa harda tsotsa ke fita yanzu …… A jiyar zuciya malam ibrahim yayi yana fadin _"SIHIRIL NAZEEF kenan Abdul Maleek Shi kalar Wannan Sihiri yana aikine kawai Ga Mata ……Bokane Zai turo Aljani zuwa ga matar Ya kuma umurceshi da ya rika Fitar mata da jini ta gabanta, Shi kuma Aljanin nan take zai shiga jikinta a cen cikin Jijiyar jininta (veins)." _Manzon Allah (Saww) yace:……"LALLAI SHAIDAN (ALJANI) YANA GUDANA A JIKIN DAN ADAM AKAMAR YADDA JINI YAKE GUDANA".……Ma'ana: Yana iya shiga duk inda jinni zai shiga, saboda bashi da gangan jiki da zai hana shi yin hakan. Imamu Bukhari da Muslim suka ruwaito shi (An-Nawaawi, 14/155).……A wani Hadisin Kuma na Imamu Bukhari; Lokacin da Hamma bint Jaash ta tambayi Manzon Allah (saww) game da tsawaitar zubar Jinin (prolonged bleeding) a lokacin haila, Sai Annabi (saww) YaCe, "WANNAN YANA DAGA CIKIN MAKIRCIN SHAIDANUN ALJANNU"……(Imamu At-Tirmidi, da Imamu Bukhari suka Ruwaito Shi).……Imam Ahmad Ya fitar da wani hadisi Cewa, Annabi (saww) YaCe, "FITAR JININ HAILA WANDA YA WUCE QIMA YANA DAGA CIKIN SHAIRIN SHAIDANUN ALJANNU".……(Imam Ahamd da An-Nasa’i suka ruwaito shi).……Duka wayannan hadisan suna nuna mana Cewa duk fitar jinin da ya wuce Qima na haila to akwai sharrin aljannu a ciki Don haka Zan baka Ruwan Zam-Zam dana karanta ayoyin Rukiya a ciki abawa Safeenar ta rika yin alwala da su tsawon kwana 3……Haka kuma ta rika shan wayannan ruwan sau 3 a rana tsawon kwana 3, In shaa Allahu za'a dace.……Sannan idan ka fita ta nemi *HABBUR RASHAD,FIJIL,KUSTUL HINDI ,HABBATUS SAUDA ,GARIN FUREN ALBABUNAJ* Sai a debi cokali uku na kowane a hada da zuma ta dinga sha kullun ……_ "To ina zan samesu malam……?ya tambaya cikin kwantar da kai "Da kaje islamic chemist Abdul Maleeku zaka samesu duka insha Allahu ……" Godiya yayi sannan ya mike suka fita tare har gurin motar Malamin ya rakashi tare da mashi fatan Alkhairi sannan ya dawo …… Sae da ya biya gidansu yawa Baffa bankwana sannan ya biya islamic chemist ya hado duk abunda Malam ya fada mashi sannan ya dawo gidan Granny din, a can ya iske Abba Suna magana da ita …… Bai samu ya mata bayanin ba ……ya tsaya suna magana da maryam tana zolayanshi wae tunda aka ta bashi bestynta bai kuma zuwa ba …… Dariya yayi yana kallon Safeena yace "Ki tambayi bestyn taki idan banzo ba……" Juyawa tayi tana kallonta "Wae besty yazo? Harara ta sake mata tana fadin "Ban sani ba……" "Allah ya baki hakuri besty yau fa zaki tafi ki barni amma shine kike man haka ……"ta fada cikin sanyin murya Dan kallonta tayi taga ta mata kallar tausayi tace "Yazo fa besty mantawa nayi ban fada maki ba sorry……" Shima hararan Safeena yayi "Madam bara ki man magana ba ko? ,ko sae munje can ne ……"ya fada cikin zolaya Banza ta mashi tana fadin "Besty dan Allah ki saka man wancen littafin a jikkana dashi zan tafi ……" Abba yace su fito a tafi ,kuka sosae suke ita da Maryam da Abban yace bara a tafi da maryam din ba ta rakata ……Dakyar aka fidda safeenar daga jikin maryam din sannan suka tafi daga Su sae Abban ……ko A Airport din ma Ko bankwana Abba baiyi da safeenar ba ya juya ya tafi…… Rungumeta Maleek yayi a jikinshi yana lallashinta……Daga bayansu suka ji Muryar JB na fadin " Wane irin iskancine haka Abdul Maleek……" Su duka suka juya cike da mamakinshi ashe har nan ya ya biyosu ,Dan waro ido Maleek din yayi yana fadin "Me ke faruwa Jabir ……? Cikin daga murya yace " Baka san abunda ke faruwa ba kenan ,to saketa karamin mara kunya……" Dafe kai yayi yana leken fuskarta "Oh Sorry madam ,Sorry Jabir ,na manta cewa kayi na kula da ita sossae ,na fahimci laifina bai kamata na barta tana tafiya ba ……" yana rufe baki ya dagata ya daura saman kafadarshi ya nufi Wroom da ita …… "To the hell of you thug fox……"JB ya fada cikin daga murya yana nunashi Duk da yaji zafin zagin amma bai juyo ba sae da ya ajeta sannan ya zauna gefenta tare da dafe kanshi da duka hannayenshi …… Hakanan ta ji bata ji dadi ba ,Ahankali ta dafa bayanshi tare da fadin "Sorry……" Kallonta yayi yana murmushi sannan ya zagaya da hannunshi saman kafadarta tare da daura kanshi bisa dayar kafadar ya lumshe ido …… Suna a haka har a ka kirasu suka mike yana rungume da ita har suka shiga…… A cikin jirgin ma duk wani motsinta a idonshi takeyi har bacci ya dauketa ta kwanto saman kafadarshi …… *MILLENIUM AL AQEEQ MEDINA HOTEL* Anan suka sauka anan gab da fara sallar Magrib ,room 12 floor 2 …… Zaunar da ita saman kujera yayi sannan ya duka yana cire mata takalman kafarta ……Sannan ya dago yana sakar mata wani irin sassanyan kallo , Dole yasa ta saki murmushi tare da kawar da kanta gefe …… Peck ya mata a goshi "Zanje sallah ,I'ld be back soon……" Murmushi kawae tayi ba tare da tace komae ba ,shi kanshi bai damu ba ,godiya ma yake da murmushin da ya samu ,Har ya kai bakin kofa ya juyo yana fadin "Tsara ban me kike so ……" "Addu'a"ta fada a takaice "Wannan dole ce ,banda ita ……abinda zaki ci……"ya fada yana kokarin gyara ID card dinshi dake kokarin tona mashi asiri Dan Waro ido tayi "A mosque din" Gyada kai yayi yana fadin "Yeah ke dae fada" "Nothing……" ta fada tana tabe baki "Sae kin fada " ya karashe maganar tare da dawowa kusa da ita "Fadaman please……" "Bana bukata fa……" ta fada tana bata fuska "Dan Allah ……" Banza ta masa tare da jinginar da kai gefe guda "Tunda bakyaso lemme kiss your lips sae na tafi ……" harara ta sake mashi ,ganin ya zauna saman cinyarta tare da dago kanta ya sata fadin " Pistachio……"da sauri tana runtse ido "And ……? ya fada yana kashe mata ido "Ice cream ……" "Sae me……" "Shikenan ……" ta fada tana murmushi "Good……" ™ *JB😛😛* *FEEDOHM💞* [5:10PM, 11/8/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹* 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 © *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM💞_* *Devoted to Ummi A'isha👌🏻* *Bestowed to Aunty Sis💕* 3⃣9⃣ Yana fita ta mike da kyar ta shiga toilet ,Sae da tayi wanka sannan ta tsaya tana wanke kayanta da su ka baci ,Muryarshi taji yana fadin "Twee……" Tabe baki tayi tana fadin "Sabon salo ……" Jin karar ruwa ya sashi shiga binta toilet din ,Waro ido yayi tare da karbar kayan da ke hannunta yana fadin "Twee meye kike haka……? Kallonshi tayi tana fadin "Me ka gani……" Kamo hannunta yayi yana fadin "Kar ki sake kin ji ko I'ld do anything for you……Bara na kawo maki wasu ruwan kiyi alwala kin ji ko ……" Gyada kai tayi a sanyaye tana kallonshi har ya fita sannan ya dawo dauke da ruwan ,shi da kanshi ya dinga zuba mata tana alwalan har ta gama ya kamata suka fito ,sannan ya shinfida mata abun sallah ……Har ta kabbara sallah sannan ya koma toilet din ya wanke kayan Tare da wanke toilet din sannan ya fito …… Lokacin ta gama Sallan ta daga hannu tana addu'a ,Gefenta ya zauna tare da daga hannun shima har ta shafa sannan ya shafa yana fadin "Ameen……"Tare da janyo ledar daya shigo da ita ya fara budewa …… Duk abunda ta fada shi ya sawo mata sae chocolate da ya hado dashi Pistachio ya bude tare da debo kadan a hannu yana fadin "Oya open,your mouth……" Bata fuska tayi tana fadin "Zan ci da kaina……" "Ban yarda ba bude na baki da kaina……" "Maleek ……"ta fada hankali "Na'am Twee……"ya kwaikwayi muryarta Hararanshi tayi sannan tace "Stop calling me wani Twee baka san sunana ba……" Kashe mata ido yayi yana fadin "Na fi kowa sanin sunanki Twee amma baran iya fadi ba……" "Me yasa? ta fada tare da waro ido "Baran iya kiran matata kamar ina kiran wata cousin dina ba……" "To ni bana so……ka kirani Safeena ……" Bae ce mata komae sae wani sanyayyan kallo da ya bita dashi tare da kara mika mata pistachio din a bakinta ,wannan karon bude baki tayi a hankali tare da runtse ido …… Sae da ya gama bata ta koshi sannan tace bacci zatayi ,daukarta yayi ya daurata saman gado sannan ya dawo ya tattara gurin ya komo ya zauna bisa stool din dake gefen gadon tare da langwabe kai "Twee ina zan kwanta……" Shiru ta masa har sae da ya kara maimatawa sannan tace "Ga kujera a can mana ……" Marairaicewa yayi yana fadin "Wallahi Twee fadowa zanyi ……" A Zahiri ta yarda da fadowar zaiyi don itama,idan bacci ya dauketa saman kujeran dakinta sae dae ta farka ta ganta kasa …… "Ka dauki blanket ka shifida a kasan carpet to……" ta fada ba tare da ta kalleshi ba Kara marairaicewa yayi yana fadin "Twee Allahu ,So kike mura ya kamani ko ,don ba JB bane ko ……" Kallonshi tayi tana turo baki sannan ta matsa can karshen gadon ta kwanta tare da juya baya ……tsadaddan murmushi yayi sannan ya canza kaya ya dawo ya kwanta bayanta …… "Maleek duk can filin ba isheka ba sae ka dawo kusa dani ……"ta fada tare da mikewa tana fadin "Ba matsala bara na koma kasan ni……" Saurin rike bargon yayi yana fadin "Allah ya baki hakurI Twee dan Allah karki koma kasan wallahi zan matsa sosae kin ji ko ……" Da sauri ya matsa can karshen gadon ya kwanta sannnan itama ta kwanta …… 《》《》《》《》 ,Cikin kwantar da Murya hajiyarsu ke fadin "Boka mun nemi zoben mun rasa bayan an ajeshi da asuba ……" "Wannan sakacinku ne Shafa……"ya fada cikin budaddiyar muryarshi Aunty zuby tace "Ba yarda za'ai a taimaka mana boka…Daga baya sae mu nemi zoben ,don wallahi Diyata na can banda kuka babu abunda take tun jiya da ta samu labarin sun bar kasar………" "Za'a taimaka maku idan kun kawo zoben ……ku tashi ku tafi "ya fada cikin daga,murya "A taimaka boka……" Kallon da ya jefa masu ne yasa hajiya mikewa tare da jan hannun Aunty Zubyn zasu fita ,har sun kai kofa yace "Ku dawo……" Cikin kyarma suka dawo suka tsugunna , Aunty Zubyn ya kurawa ido yace "Za'a taimaka bayan kin biya man tawa bukatar……" Hajiya ta kalla ,tayi saurin daga mata kai alamun ta yarda kawae ……Sannan ta kalleshi tace "Na yarda ……" ta karashe maganar kamar zatayi kuka ,da ta tuna warin da ta shaka farkon da ya fara saduwa da ita ……Wanda daga lokacinne bata kuma yarda tazo gurin ba sae yau da fadilan ta takura mata da kuka …… Dariya yayi da karfi yana fadin "Jeki waje ki jirata Hajiya……" Mikewa tayi ta fita babu alamun damuwa a fuskarta ……Kusan minti goma da fitowar tata ta fara jiyo ihun Aunty Zubyn ……Mota ta koma ta zauna tare da lumshe ido har Aunty zubyn ta dawo da idanuwanta jawur …… "Allah ya isa ……"ta fada lokacin da take kokarin shiga motar Dariya hajiyar tayi sannan Aunty zubyn ta tada mota suka bar gurin …… Suna shiga harabar Gidansu suka ga wata yar tsamurmurar budurwa ta fito daga part din Uncle Abba……Tabe baki Aunty Zubyn tayi tana fadin "Ina Amfanin fiddawa saurayi part a harabar gida ……" Kallonta hajiyar tayi sannan tace "Ke ma kya fada in dae Abbah ne ,ya dinga kwaso mata kala kala kenan har garin Allah ya waye,wallahi na fara gajiya kada yaje ya dauko mana wata cuta ……" Kwala mashi kira Aunty Zuby tayi ganin ya biyo budurwar yana bata wani abu da alama kudine ……Sae da ya sallameta sannan ya matso yana fadin "Aunty zuby daga ina haka keda hajiyarmu……" Hararanshi tayi tana fadin "Ina ka samo waccen shegiyar kuma……" Dariya yayi yana fadin "Oh Aunty zuby wallahi ba shegiya bace, Baby ce ……Ziyara ta kawo man yanzunnan ……" Hararanshi ta kuma yi tana fadin "Ka dae kiyayi kanka wallahi ,idan ba haka ba kana zaune cuta zata kasheka ……" Dariya yayi yana fadin "Haba Aunty zuby cuta bata kasheki sae ni ……" Banza ta masa suka shige ciki suka barshi 《》《》《》《》 Tafiya yake amma sam hankalinshi ba a gurin kidan dake tashi cikin motar yake ba …… Solution yake nema ta yarda zai rama rashin kirkin da Maleek ya mashi jiya ……Decision kawae ya yanke bara ya cika mashi kudin shi ba zai mashi wayau ne yace yana jiran wasu kudi ne ,Sai bayan ya saketa shi kuma ya aura sannan ya fada mashi gaskia rungumar da yayi mata ce ta sauran kudinshi ……sannan ko gidan da yake niyar bashi ,takardun fake zai bashi yarda bara su mashi amfani ba ……Wani murmushi ya saki tare da dukan sitiyarin ya ci gaba da bin wakar …… Wasu tsadaddun yan mata suka tsayar dashi ,tun kafin ya tsaya ya kare masu kallo ,dukansu ba na yarwa …… Parking yayi tare da rage glass yana fadin "Yane ……" *FEEDOHM💞* [7:35PM, 11/8/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹* 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 © *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM💞_* *Devoted to Ummi A'isha👌🏻* *Bestowed to Aunty Sis💕* 4⃣0⃣ Wata daga cikinsu tace "Can Fadama zamu ko zaka taimaka ka saukemu……? "Ku shigo ba matsala……" ya fada yana spreading arms dinshi ……tunda suka shiga motar ba wanda ya sake magana har yayi parking sannan suka bude zasu fita …… Wacce ta fara magana ya kalla yana fadin "Excuse……"Dawowa tayi ta zauna tare da dagawa sauran hannu alamun tana zuwa Cikin sigar yaudara yace "Har zaki tafi baki fada man sunanki ba baby……" "Raliyah……"ta fada dauke da murmushi Duk da gabanshi ya fadi na jin sunan hakan bai hanashi sakin murmushi ba tare da fadin "Wow nice name ……Bani digit dinki mana……" Karanto mashi tayi yayi saving da Baby R sannan yace "Me zakuyi anan ? Yar dariya ta saki sannan tace "Munzo mu huta ,ko zakayi joining ne ……" "Wow baby dama kinsan am incomplete wallahi ,Muje kawae ……"ya fada cike da zakuwa…… Bude motar sukayi suka fito tare sannan ta matsa kusa da yan matan ta masu magana ……yanajin suka dauki dariya a tare sannan ta dawo gurinshi ……Receiption suka shiga suka karbi keys guda biyu sannan suka fito …… Room daya yan matan ne ,Sae gudan room din shida Raliyah…… Shafin badala suka bude shi da ita ,kusan Awa Uku suna abu guda sae da hankalinshi ya dawo jikinshi sannan ya duba ya ga bata kusa dashi ……"Baby ……"ya dan kira sunanta ,amma shiru Lekawa toilet yayi yaga wayam babu ita sannan inda ta aje kayanta nan ba babu komae ,bai damu ba dan ya saba da harkar yan mata ……ya tabe baki tare da watso ruwa sannan ya dawo ya dauki kayanshi ya mayar ya leka dakin da yan matan suka sauka ko can ta tafi …… A kulle ya iske dakin shima ,Fitowa yayi waje amma ko alamunsu babu ……Mamaki kwance a fuskarshi don tun da yake harkar da yan mata bai taba samun wacce ta tafi ba tare da ta karbi kudi ba ……"Ke kika sani nonsense ……dama kin tsaya ko kudi kin karba da kin huce takaici ,don ba kara ganina zakiyi ba nonsense ……" ya fada tare da fiddo phone dinshi yayi deleting numbertah …… 《》《》《》《》 "Me ke faruwa Twee ko sun fada maki wani abune da kika shiga ……" Ya karashe maganar tare da rungumota jikinshi Lumshe ido tayi tana fadin "Sunyi duk wani test amma basu gano komae ba Abdul Maleek sae dae sun bani wani magani sunce nayi amfani dashi zuwa one week a gani …… "ta karashe maganar idonta cike da hawaye …… "To Sorry karki yi kuka kin ji ko ……" Gyada kai tayi a hankali tare da kara kwantar da kanta jikinshi "Daki zamu koma ko mu fita ki ga garin……" Girgiza kai tayi alamun aa sannan ta duka tana fadin "Ka yarda ID card ……" Kafin ta kai ga dauka har ya dauke ya mayar aljihu yana murmushin yake …… Ta dade tana kallonshi sannan tace "Bakka da gaskia ne? Waro ido yayi yana fadin "Me nayi Twee? "Babu……" ta fada a takaice Hannunta ya kama suka koma cikin dakinsu ,sannan ya hada mata ruwan wanka tayi ,ya wanke kayan da ta fitar sannan ya dawo ya zauna yana yarfe hannu tare da fadin "Twee ko sannu ko ……" Cikin wasa ta harareshi tare da fadin "Sannunka na account dinka……" "Haka kika fada Twee……? Gyada kai tayi tana tsuke baki "Zakiyi man bayani Twee……" "Kai ma din zakayi bayani ne……" Ta fada dauke da murmushi Tallabe kai yayi yana fadin " What is the screat of your beauty and glamour Twee……" Banza ta mashi ta janyo wayarta tana kokarin kunnawa ……ganin taki kamawa ya sa ta kalleshi a shagwabe tana fadin "Help me wit your Phone Abdul Maleek ……" Damka mata wayar yayi a hannunta sannan ya mike ya kunna Tv ya dawo …… Abba ta kira suka gaisa sossae yana tambayarta ina Abdul Maleeku …… Sae da ta kalleshi sannan ta kawar da kai tana fadin "Baya nan Abba……" "Idan ya dawo ki ce ina gaidashi kin ji Safeena ,sannan dan Allah ki natsu yanzu ke ke kasanshi ba shine kasanki ba ,ki tausasa halshenki kin ji ko ……"Gyada kai tayi a hankali tana kallonshi kasa kasa …… "Zaki gama wayan Twee sae kin fada man dalilinki na man karya……" ya fada yana watsa mata kallo …… Sae da ta gama wayar sannan ta kira Maryam ,itama sun dade suna fira cikin jin dadi ,Cikin Wasa maryam ta dinga zaro mata magana mai cike da hikima tare da kwatanta mata meye asalin so sannan meye shaawa …… Sae da sukayi kusan One houe suna waya sannan ta juya zata mika mashi wayar …… Murmushi tayi ganin bacci ya daukeshi ,sannan ta matsa da kyar ta cire mashi takalminshi tare da safar dake kafarshi ta mayar da kafafuwan saman kujera…… Ta dade tana kallonshi tare da yaba kyawun halinshi ,Ko kadan baya kyamarta shine ke wanke duk kayan da ta bata harta pant shike wankewa duk da tsotsar da ke makalewa jiki amma bai taba cewa a yarda ba ko da ita tace ,Sannan baya jin komae ya kwanta kusa da ita tare da rungumeta har safe haka zai tashi jikinshi kaca kaca kamar shi ke jinin …… Lumshe ido tayi tare da bashi wani matsayi na musamman a ranta ……Sannan a yarda ta fahimta JB ya rainawa hankali ba sakinta zaiyi ba…… *Lemme See su waye a team dina* *TEAM JB……ni dae💞💞* Drop your comment amma yan ™JB kadae 08066598868 ……kar naga ™ ABDULMALEEK Don kun man yawa 😡😡 *FEEDOHM💞* [9:08AM, 11/10/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹* 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 © *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM💞_* *Devoted to Ummi A'isha👌🏻* *Bestowed to Aunty Sis💕* 4⃣1⃣ *Gaisuwarku ta dabance Sisters👄 Sawwama,Pherty,Faxy fashion,Maman khadija,Hafsat mai shariff,Billy galadanci,Safiya huguma,Hajjace,Khaleesat haydar,Asmy b,Maryam kaumi ,Muneera,Sanah Matazu,Mrs splendid,,Parrot,Meela Adeel,Jiddah Aliyu……🌹* Hannunta dake saman kafarshi taji ya kamo tare da bude ido a hankali yace "Why're staring me……" "Me zan Kallah a nan ……"ta fada tana kawar da kai Janyota yayi da karfi jikin tare da kwanto da kanta saman kujeran yana fadin "Zo na gwada maki abunda kike kallo ……" Turo baki tayi tare da mikewa tana hararanshi……Lokaci guda ta dafe kai tare da sakin gigitacciyar kara sannan ta fado jikinshi …… A rude ya mike zaune ya rike dukkan kafadunta "Menene Safeena ,Fada man,kinji meke faruwa ,Bude idonki ki ganni kin ji ko……" ya fada a gigice …… Ganin ta cigaba da yin karan ne ya sashi rungumeta sossae tare da tofa mata addu'a ……Jiyayi dukkan jikinta ya saki tana fitar da lumfashi da karfi…… Duk ya gigice yana kiran sunanta "Safeena…… Rungumeta yayi sossae yana tofa mata addu'a har sae da Lumfashinta ya koma dae dae …… A sanyaye ya dago fuskarta "Menene Safeena……are you Ok?ya fada tare da kura mata ido Still Razanannar kara ta saki sannan ta hankadashi gefe guda da dukka karfinta tare da mikewa daga jikinshi ……Kujeran da suke zaune tayi baya ta fadi dashi baya…… Kafin ya yunkura ta fice daga dakin da gudun tsiya ……Shima binta yayi har sae da ta kusa fita harabar Hotel din sannan ya samu ya riketa da kyar …… Duka take kai mashi ta ko ina amma bai saketa ba……Mutanen dake gurin babu wanda yayi niyar taimakonshi don kowa harkar gabanshi yake …… Dakyar ya samu ya sabata a kafada ya komar da ita dakin tare da saka keys sannan ya direta ……Birgima ta fara a kasa tana wani irin kuka mai cin rai …… Dafe kanshi yayi ya koma ya jingina da bango idanuwanshi jawur ,shi kanshi da zai samu yayi kukan da yafi samun sauki ……Tunaninshi ya tsaya cak lokacin da wani bakin hayaki ke fita daga jikinta …… Kara ya saki yana fito da idanu waje ,Tundaga inda yake tsaye ya kai guiwarshi kasa har zuwa kusa da ita tare da tallabota jikinshi yana girgizata "Nothing will happen to you Safeena ……"ya fada tare da sakin kuka ……Addu'a ya fara tofa mata duk wacce ta fito bakinshi ……Kamar wuta haka jikinta yake saboda masifar zafin da ya dauka amma hakan bai sakashi sassauta rikon da ya mata ba …… Ganin hayakin bai daina fita ba ya sashi rarrafawa yana rungume da ita ya fito da zam zam din da Malam ya bashi yana shafa mata a dukka jikinta …… Kusan Minti biyar sannan hayakin ya daina fita daga jikinta sae wani uban duhu da fuskarta tayi kamar an shafa mata charcoal…… ,Lumshe ido yayi hawayen dake makale suka gangaro saman goshinta ……Ta dan jan lumfashi da karfi …… "Safeena……" A hankali ta fara bude idonta da suka kada sukayi jawur har ta sauke saman fuskarshi …… Hannunshi ya daura yana zagaye fuskar tata da tayi duhu ,a hankali ya furta "Are you Ok ……"can kasan makoshi…… Girgiza mashi kai tayi a hankali tana nuna shi da hannu tare da kwace jikinta ta koma ta makure jikin bango……A Sanyaye ya bita har jikin bango ,Matsawa ta fara yi tare da sakin kuka tana girgiza mashi kai da hannu …… "Kiyi Magana mana Safeena……"ya fada kamar zaiyi kuka , Kasa magana tayi sae dae kukan da ta sake da karfi tana girgiza kai , "Nine ba kya so nazo gunki Safeena? Ya fada don ya fahimci kar ya matso take nufi Da sauri ta gyada mashi kai tana kuka ……Lumshe ido yayi yana fadin "To yi hakuri ki bude baki ki man magana, sae na tafi kinji ko……" Juyawa tayi ta hade kanta da bango tana kuka ,Asanyaye ya matsa tare da dafa bayanta yana kiran sunanta …… Juyowa tayi ta fara dukanshi da karfi tana turashi ……A sanyaye ya mike ya fara tafiya da baya har ya kai bakin kofa ,sannan ya bude ya fita tare da rufe kofar a hankali ya jingina da ita …… ,Kanshi yayi bala'in daurewa ,Tambayoyine ke zagaye a kwalwarshi wanda ya rasa wacce zai amsa a ciki ,fito da wayarshi yayi ya fada dialing number granny ,Da sauri ya datse kiran yana girgiza kai "No ……" Ganin tsayuwar bara ta mashi ba ya sashi zaunawa bakin kofar har tsawon awa daya ,sannan ya mike kamar an tsikareshi ya fita harabar hotel din yayo alwala ya dawo ,Sae da ya kunna karatun kur'ani sannan ya bude kofar dakin ya shiga kamar barawo …… Karkashin gado ya hangota kwance da alama bacci takeyi ,Tausayinta sossae ya darsu a zuciyarshi ya karasa gurin tare da tsugunnawa ya janyota a hankali ,Har ya fito da ita bata farka ba ,Daukarta yayi ya kwantar da ita saman gado ,sannan ya zauna yana kallon fuskarta da tayi kamar an shafa mata charcoal …… Cikin jikkarsu ya dauko cotton da zam zam yazo yana goge mata fuskar a hankali ,Cikin sa'a duka bakin ya fita ta koma fresh da ita ,Addu'a sosae ya tofa mata sannan ya mike ya rufe dakin ya dawo ya kwanta gefenta ,har lokacin kira'ar sheikh sudais ke fita daga wayarshi …… Rungumeta yayi sosae sannan ya kashe light ya rufesu da bargo…… 《》《》《》《》《》 Uncle Abbah ya shigo falon rike da bakar leda ,Ganin Abban Safeena zaune ya sashi komawa baya ya boye ledar a aljihu sannan ya shigo da sallama …… "Alhaji barka da wuni……" Ya fada harda dukawa Cikin Fara'a ya amsa "Barka kadae Abbah ya gurin su hajiyar ……" "Suna lafiya lau Alhaji sun ma ce a gaidaka……" Mikewa yayi yana fadin "Madallah " sannan ya bar falon ……Mintina kadan Aunty Fatee ta fito tana hararanshi "Kai shine tun dazu hajiya tace ta aikoka amma dan iskanci sae yanzu kaga damar zuwa……" "Ance maku ni banda aikin yi ne……Malama dallah ki karba sannan ki kirata ta maki bayani ……"ya fada yana mazurai Fizge ledar tayi ta juya tana surutai …… "Ke nufinki bara ki bani kudin petrol ba ……" Karamin tsoki ta sake ta wuce ta barsa a gurin ,Shima kwafa yayi ya fita yana fadin "Zamu hade ne wallahi ai kar ta san kar ce……" Sae da ta rufe dakin sannan ta bude ledar ta zazzageta saman gadonta ……Kullin maganine guda biyu a cikin daure cikin takardar nama …… Tabe baki tayi sannan ta dauko wayarta dake jone a jikin socket ta kira Hajiyar …… "Ya kawo hajiya……"ta fada jin hajiya ta dauka "Yayi kyau ,kina ina yanzu ……"hajiyar ta fada "Ina dakina mana ……" "Yauwa magani na karbo maki don na gaji da zaman banza Fatee ,ina amfanin zaman da kike babu da babu jika a gidan ……" Yatsina fuska tayi tana fadin "Kema kya fada……" "Yanzu ga magani nan kulli biyu ki zuba mashi dukansu a abinci ,Ki tabbatar yaci yau dinnan ……" "To na meye hajiya……"ta fada a hankali "Gidanshi na gaskia zai koma……"ta fada kai tsaye A razane tace "Mutuwa hajiya? "Kanin ubankine da bazai mutu ba ……" ta bata amsa kai tsaye ,A sanyaye tace "amma hajiya ko ya mutu fa hakkin takaba kawae nake dashi, meye amfanin hakan ?ba kara na zauna ba ko sato mana na dinga yi ……" "Rufe man baki sakarai ,ai da yake yarda kike banza haka kowa yake ,to bara kinji kina saka mashi yaci ya shure ko motsi bara ya kara ba sannan zaki tattara komae Uncle Abbah yazo ya karba kafin mutane su taro ……" "Safeena fa Hajiya……" "Ta mutu……" ta fada a takaice Yar dariya Aunty Fatee ta saki tana fadin "Yanzu naji batu Hajiyarmu ……"Sannan ta yanke wayar ta shiga wanka ,Mintina kadan ta fito tare da tsantsara kwalliyarta sannan ta dauki ledar ta shiga kitchen da ita …… Da sallama ta shiga dakinshi yana zaune da computer gabanshi ta duka tana fadin "Abban Safeena baka gajiya da aiki……" Dan murmushi yayi yana kallonta sannan yace "Ke kuma bakya gajiya da yawo ko……? Share maganar tayi tana fadin "ka sauko kaci abinci gaskia ……" "Kin hado man da ruwan zafi ko ……?ya fada yana karewa abincin kallo "Kaga na manta wallahi ,Amma bara ns zuba maka abincin sannan na tafi na daura ruwan zafin ……" Da murmushi yace "Thank you ……" Zuba mashi abincin tayi tana fadin "Ka sauko kaci kafin na dawo dan Allah ,wallahi bana son kana zama da yunwa……" Rufe computer yayi ya sauko yana fadin " Na sauko hajiyata ……"Sae da taga ya dauko spoon ya saka a cikin abincin sannan ta fita tana waigenshi da murmushi kwance a fuskarta…… *FEEDOHM💞* [2:17PM, 11/10/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹* 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 © *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM💞_* *Devoted to Ummi A'isha👌🏻* *Bestowed to Aunty Sis💕* 4⃣2⃣ Aje Spoon din yayi ya mike a sanyaye ya rufo dakin ,sannan ya dawo ya dauke duk wani takardunshi masu mahimmanci da kudinshi dake aje ya kai toilet ya rufo da keys ,sannan ya wurga keys din bayan mirrow …… Abincin ya debi rabi ya zuba a leda sannan ya bude glass din window ya jefa bayan gida ,Wayarshi ya fito yana dialing number Safeena amma a rufe ,ta Abdul maleek ya gwada har tayi ringing ta katse bai dauka ba……Rufe wayar yayi ya sakata a pocket na wandonshi sannan ya dube dakin ya dawo gaban abinci ya kwanta kamar matacce …… Turo kofa tayi harda yar wakarta ,ganinshi a kwance ya saka ta tako har gabanshi tana wank girgiza tare da tabe baki "Bikin sallah ……"ta fada tana hambare hannunshi dake cikin abincin Drawer ta bude ta fito da tilin takardu tana fadin "Idan sunje can sun fitar ……"yana ji ta kira Uncle Abbah tace zata bar takardun a falo idan yazo ya dauka …… Sannan ta fita da gudu tana ihu kamar mahaukaciya ……Hawayen da yake dannewane suka gangaro mashi na tausayin kanshi da diyarshi ……Hannun riga ya saka ya goge jin tana taho da masu gadin gidan tana fada masu Alhaji ya rasu…… Kukane kwance a fuskarta kai da gani zakayi tunanin hakan ne a ranta ……"Shikenan Alhajina ,Asirina ya tonu na shiga uku ni,Fateema ……"Abunda take fada kenan tana kallon masu aikin dake tsaye cirko cirko …… A hankali ya fara motsa hannunshi ta yarda zasu gani sossae ,Bala sabon driver tun bayan tafiyar Abdul maleek ne ya zabura yana fadin "Yana motsi wallahi ……" "Ku kamashi akaishi asibiti dan Allah ……"cewar mai gadi tare da nufoshi ya dagashi , Aunty Fatee kam tsaye tayi ta kasa motsi yayin da kukan da take shima ya tsaya cak ,Har sae da su Bala suka fita dashi sannan ta dawo hayyacinta tabi bayansu …… Da yake balan shi ke driving cikin mintina biyar suka kaishi FMC…… Yarda suka shiga asibitin a rude suna ihu yasa akayi saurim shiga dashi emergency…… 《》《》《》《》《》 A wahale ta fara bude idanunta da har lokacin suke jawur ……Daga kai tayi tana kallon Abdul Maleek da idanuwanshi ke lumshe sae dae ba bacci yake ba sae dae karatun Alkur'ani da yake bi a hankali …… "Abdul Maleek……"ta fada kasan makoshi Da sauri ya bude idon yana fadin "Twee are you ok……" A hankali ta gyada kai tare da fadin "Ruwa……" kallon bakinta da ya bushe yayi sannan ya zura hannu cikin dan karamin fridge din dake gefen gadon ya dauko mata bottle din faro ……Yana budewa ta karbi da sauri tare da kallon sama tana shan ruwan …… Sae da ta kusa shanyewa sannan ta saki hannunta kasan gadon tare da sakin sauran ruwan tana fadin "Abdul Maleek……" Kallonta yake cikin tausayawa sannan yace "Na'am Twee ya akai ……? "Headache……"ta fada tana runtse idanu Gefen kanta ya kama yana fadin "To yi hakuri Sannu kinji ko ……" Kuka ta saki a hankali tana fadin "Dukan man shi ake Abdul Maleek da karfi ,kace su daina ……" Rike kan yayi yana tofa mata addu'a har sae da ta fara lumshe ido sannan ya saki yana fadin "Sorry Twee ……" Tabe baki take tana juyar da kan tare da kiran sunanshi bayan duk wani fitar numfashinta ……Bai gaza ba gurin amsa kiranta ,har sae da ta bari don kanta sannan ta koma baccinta ……Kara gyara mata kwanciyar yayi saman kirjinshi yana bin karatun kur'anin cikin natsuwa …… Tunda asuba ya mike ya cire da kayanshi da suka baci yayi wanka sannan yayi sallah ,Yana addu'a ta fara motsi da kai a hankali tana kiran sunanshi ……"Abdul maleek……" Da sauri ya matsa tare da rike mata hannu yana kallon fuskarta da bakinta da ya bushe yayi fari fat ……A hankali yace "Twee menene?ina ke maki ciwo……" Lumshe ido take tana budewa a hankali tare da kiran sunanshi,Kusan minti biyar sannan ta budesu tar saman fuskarshi tana kallonshi ……"Inna lillahi wa inna ilaihirraju'una……" ya maimata mata a hankali Ganin ta amsa ya sashi talloba ya zaunar da ita jikinshi "Kiyi wanka kiyi sallah ko Twee……"ya fada a hankali Noke kafada tayi tana fadin "Abbana Abdul maleek……" "Na kira maki shi……"ya fada cikin sigar lallashi Juyar da kai tayi tana kallon bango ba tare da tace komae ba……Wayarshi ya janyo ya kashe karatun kur'anin sannan ya fara kiran Abban amma wayarshi a kashe …… Kamo Hannunta yayi yace "Twee kinga asuba ce Abba bai bude wayarshi ba ,kiyi hakuri kiyi sallah zuwa safe sai na kira maki shi kin ji ko……" Kallonshi tayi na yan mintina sannan ta sauke kafufuwanta daga gadon tana kokarin mikewa ……kamar an jehota ta dawo tare da sakin kuka tana fadin "Kafana Abdul Maleek ……" Saurin duba kafar yayi amma bai ga komae ba ,ya dago yana kallon yarda ta dage tana kuka bil hakki da gaskia ,Dan murmushi ya sake sannan ya cire jallabiyar da yayi da sallah da ita ya aje tare da daukarta ya kaita toilet din ya aje …… ,,Kamar wasa yaga kafafunta na rawa bayan ya ajeta zai juya ,Saurin tallabota yayi jikinshi yana binta da kallon mamaki "Twee me ke faruwa ne……" Dukar da kai tayi tana share hawayen da suka cika mata ido tare da fadin "Sorry for disrupting……" Saurin kamo hannunta yayi yana kallon cikin idonta "Look Twee karki kuma fadin haka kinji , ko kin manta har kudi aka bani don inyi jinyarki ……? Saurin kallonshi tayi ,ya gyada mata kai yana fadin "Yeah 10m ya bani ,ni kuma zan mayar masa da 20m ya barni na kare rayuwata ina jinyarki ……" Bata san lokacin da murmushi ya subuce mata ba ,jan hancinta yayi yana fadin "Me kike so yanzu ……? Shiru ta masa tana rufe ido "Baki iya wankan ne Twee……"ya fada a hankali "Zan iya ……"ta fada da sauri "Nima bance zan maki ba ai Twee don ban shirya hakan da JB ba……"ya karashe maganar kamar an mashi dole ,Sae yanzu ma yake kara jin takaicin JB da yake neman,ya miyar dashi kamar wani wawa ,wae ya mashi jinya sannan ya sakar mashi ita …… "Ka bude man zip din sae ka fita ,Zan san yarda zanyi ……"ta fada a hankali Lakuce mata hanci yayi sannan ya saka hannu ya juyo da ita jikinshi ya zuge mata zip din ,yana kallon fuskarta …… Dan murmushi yayi tare da shafar digon bakin dake tsakiyar bayanta sannan ya fita daga toilet din …… Da kyar ta samu tayi wankan tana kuka ,Sae da ta daura towel ta sa Pad sannan ta kwala mashi kira cikin muryar kuka don yanzu ba laifi jinin ya rage zuba sosae ,kawae idan ta kwanta baccine take bata jikinta …… "Kuka kikayi ko Twee……"ya fada yana kallon kwayar idonta Shiru ta masa tana turo baki ,Bisa Abun sallah ya ajeta ya dauko mata jallabiyar da ya cire ya saka mata tare da hijab sannan tayi sallan daga zaune don kafafunta basa tsayuwa sosae…… 《》《》《》《》 "Wae kawae sae naga 'ta kwaso na maguzawa ta tankara' _Aunty Sanah matazu ta hanani zagi_ yana motsa hannu ……"cewar Aunty Fatee dake tsaye phydiartric tana waya da Hajiya…… "Sae akae ya kuma ……"hajiyar ta fada cikin,zakuwa A sanyaye tace "Sae na kaishi asibiti……" "Anyi Asararki Fateema wallahi,Na Zubaida dan a gida na haifeki da sai ince musayarki aka man asibiti,Banda kila doluwa bara ki ida karashi ba a dakin……" "Hajiya sae da ba na tattaro masu aiki sannan ya fara motsa hannun ,taya zan karasa shi gaban mutane ……" "Ke ai ya karasaki dan ubanki ……" ta fada tare da kashe wayar tana sababi ita kadae Fadila dake zaune ta kalleta tana fadin "Shi Abdul Maleek din bara ya dawo ba tunda boka yace jiya zata rasu……" A Fusace tace "Sae ki kirashi kiji dan ubanki ,kina ganin wannan banzar uwar taki tana neman ja man asara kina kira man wani Abdul maleek can ……" Tabe baki Fadilan tayi tare da fadin "Ko tashi asarar yake gani ……" hadi da mikewa tabar mata falon Abban kam Yana kwance sanye da Oxygen likitan ya shigo zaya debi jininshi ,wanda kusan sau uku kenan ana shigowa ana dibar saliva dinshi tare da jini …… Bude ido yayi tare da rike hannun Likitan yana mashi alama ya cire Oxygen din ,Da mamaki likitan ya shire yana kallonshi ,Mutumin da aka kawo ake kiran ya mutu amma ya bude idonshi tar yana kallonshi…… A sanyaye Abban yace "Ka fita ka fada masu na rasu……" "A kan me ……? ya tambaya a razane "Haka suke so Doctor……Dan Allah ka fada masu zakaga farinciki kwance a fuskar wadda ta kawoni ……" "Me yasa Kake so ace ka rasu Alhaji " "Karka damu ……"Ya fada a sanyaye "To idan suka bukaci gawarka fa ……"ya jeho mashi tambaya "Sae ku basu wadda a ka nemi mai ita aka rasa……"ya fada kai tsaye Yar dariya likitan yayi yace "Alhaji basu sanka bane da zamu basu gawar wani ,sannan ba abu bane mai yiyuwa ……" Shima dariyar yayi mai cin rai sannan yace "Akan abun duniya suke neman halakani ,abunda ni na tare da gumina ba wani ya bani ba ,matar da ta kawoni ni da kaina naji tana waya da mahaifiyarta akan zasu zuba man magani a abinci na mutu ,shine banci abincin ba sae nayi pretending kamar naci ,sae da ta tara mutane sannan na fara motsi har aka kawoni nan ,Akwae aibu don nace ka fa masu na rasu……" ya karashe maganar murya na rawa Cikin tausayawa yace "I'll prepare anything Alhaji ,Zan basu gawar da aka riga aka nade da likafani ta yarda rufewa kadae zasuyi ……sannan wannan criminal act ne dole a shigar dasu court ……" "Na riga na shigar da kara likita ……" "Good Alhaji ,amma yaushe har kayi reporting ko ka saka wani ya maka hope ka bayar da evidence naka……" Yar dariyar yake ya saki yace "Court dina bata bukatar wani Evidence ,gaban Alkalin akayi komae ,kawae mu jira lokaci ,lokacin da zasu karbi hukuncinsu ……" Girgiza kai likitan yayi cike da tausayi ,sannan ya fita ya sanar da su Aunty Fatee cewa wanda suka kawo ya rasu ,Sannan zasu shirya gawar zasu basu zuwa anjima kadan …… Kafin lokaci kadan Asibiti ta cike da mutane ,masu kuka nayi masu dariya nayi , Ciki har da mutanen JB da family na maryam ,Granny kadae ce bata sani ba …… Idan akace Maryam ba diyarshi bace babu wanda zai yarda a gurin yarda take kuka na fitar hankali ,Mum dinta ce ta fizge wayarta ganin tana neman kiran Safeena gurin tare da fadin "Maryam ba kya son Safeena ne ……" Cikin kuka tace "Ina Sonta Mummy Abbanta ne fa ya rasu ,shine bara a barni na fada mata ba ……" "Idan har kika fada mata a haka Maryam ba kya sonta ,sannan bara ta taba mancewa da Kece kika fada mata rasuwar Abbanta ba……" "To Mummy bani na fadawa Abdul Maleek ko addu'a su mashi dan Allah ……" A sanyaye ta mika mata wayar ,ringing daya ya dauka yana fadin "Munyi fushi tunda sae yau kika kiramu ……" "Abba Abdul Maleek ……"ta fada cikin kuka A rude yace "Me ya sameshi Maryam ……" Kai tsaye tace "Ya rasu……" A Razane ya kalli Safeena dake zaune tsakiyar gado tana game ,Suna hada ido yayi saurin barin dakin ya fita waje tare da yanke wayar …… "Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un " ya dinga maimatawa har ya dawo da natsuwarshi Kamar yaro ya tsugunna bakin kofar dakin yana kuka ……Sae da yayi mai isarshi sannan ya goge fuskarshi ya koma dakin …… Turo baki tayi tana fadin "Da waye kake waya……? Murmushin Yake yayi yace "Da sweetheart dita……" Tabe baki tayi ba tare da tace komae ba ,A Hankali ya matso ya zauna saman gadon tare da janyota jikinshi "Sorry……" ya furta da zance biyu …… "Twee Gobe mu koma gida ko……" ya fada a hankali Murmushi tayi tace "Kaima din ka gaji ko ……" Juyo da ita yayi yana fadin "Kalleni Safeena ……Karki kuma fadin kalmar na gaji a bakinki kin ji ko……" Gyada kai tayi a hankali tana kallon fuskarshi …… Wayarta tayi kara ganin sunan JB ya Sashi saurin kai hannu ya dauka ……ba tace mashi komae ba sae binshi tayi da kallo …… *FEEDOHM💞* [4:05PM, 11/11/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹* 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 © *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM💞_* *Devoted to Ummi A'isha👌🏻* *Bestowed to Aunty Sis💕* 4⃣3⃣ Wayarta tayi kara ganin sunan JB ya Sashi saurin kai hannu ya dauka ……ba tace mashi komae ba sae binshi tayi da kallo tana murmushi …… Kamar jira yake a dauka ya ce "Baby Sorry ……Abba ya riga mu gidan gaskia ki dawo gida gobe……" "To ……" Abdul maleek din ya fada a takaice tare da datse wayar ,yana girgiza kai ……lallae jahilci mugun ciwone da tare suke a haka zai fada mata rasuwar mahaifinta kamar yana fada mata rasuwar mai shagon unguwarsu ……lallae JB Dom ne ya fada a hankali "Me ya fada ……"ta katse mashi tunani "Cewa yayi na dawo mashi da matarshi "ya fada yana murmushin yake "Sae kace mashi me……?ta fada a hankali "To nace masa Twee……"Ya karashe maganar yana yake Itama murmushin tayi a hankali ba tare da tace komae ba …… 《》《》《》《》 Cikin mintina kadan aka hada masu gawar da zaa basu suka tafi ,likitan ya koma yana fadawa Abban cewa akwae wata yarinya dake kuka kamar ranta zai fita a waje …… Yana fadin haka Abban ya gane Maryam ce ,Ce ma likitan yayi ya kira mashi ita a sirrance Family din maryam likitan ya tsaida har sae sa su Aunty Fatee suka tafi sannan ya shiga da Maryam din office dinshi inda Abban ke aje …… Dafe kirji tayi tare da waro ido tana fadin "Abba ko fatalwarshi ……" "Abban dai Maryama ……" ya fada dauke da murmushi tare da mika mata hannu ,Likitan ta kalla taga ita yake kallo dauke da murmushi sannan ta tabbatar da Abban ne zaune …… Da gudu ta matsa kusa dashi tare da tsugunnawa gabanshi ,cikin kuka take fadin "Abba suka ce ka rasu wae ……" "Ban rasu ba Maryam kinji ,amma a gurinki ……"ya fada cikin sigar lallashi "Abba Aunty fatee ma ta dauka ka rasu sae kuka take ,bara na kirata na fada mata ta daina kuka……" "Kul Maryam a gurinki kadae nake a raye kinji ko ……Karki fadawa kowa ban rasu ba ……" "To me yasa Abba" "So suke na rasu Maryam ,shi yasa na basu guri su ci abunda ke cikin duniyar ……" Kamar yarda ya dauki Safeena haka ya dauketa bai boye mata komae ba Kuka ta dinga yi tana "Allah ya isa Aunty Fatee,Me Abba da Besty suka maki ……" Rasuwar ta tara mutane yarda baa tunani ,wasu na bakinciki wasu na farinciki …… Abba kam daga asibitin tasha ya nufa ya shiga motar kaduna…… 《》《》《》《》 《》 Takardun da Uncle Abba ya kai hajiya ta zubesu saman gado tana dubawa…… "Zuby duba man wadannan takardun na uban meye wannan yarinyar ta dauko……"ta fada lokacin da ta daga wata takarda dake kumshe da kudin da companyn ya bayar bashi …… "Wannan ai takardar bashi ce da Alhajin ya bayar……"cewar Aunty Zuby tana hararan takardun…… "Tab ……zo ki gani Hajiyarmu babu ta gida a nan don duk irinsu nake gani ……" Watse takardun sukayi kasa ,amma babu takardar ko da fili a ciki ,daga ta kudin da ya bayar bashi sae ta kudin da aka biyashi ,Ciki har dae da takardun safeena na primary school…… 《》《》《》《》《》 Cikin bacci yaji ana kissing lips dinshi na kasa,kai hannu yayi ya buge bakinshi tare da gyara kwanciya……ji yayi an dallah mashi mari da karfin tsiya ,ya mike a zabure yana waigege rike da kumci …… "Uban waye ya mareni……"ya fada cikin jarumta amma zuciyarshi harbawa take da karfi ,Jin anyi shiru ya sashi mikewa yana waigege ya fita daga dakin …… A falo ya iske mum dinshi tana kallo ,ganin yana waigege ya sata kallonshi da sauri tana fadin "Lafiyarka Son…… " Kai tsaye yace "Ina fa lafiya wani shege ya mareni ina bacci……" Yar dariya tayi tana fadin "Mari kuma JB? to gaskia babu wanda ya shiga dakinka yanzu ……ko dae mafarki kayi……" Tsaki yaja yana fadin "Da Allah ni mum bansan jikina bane?to ba wani mafarki ……mari na akayi kuma wallahi sae na mari kowa na gidan nan yau……" "Allah ya baka hakuri……"ta fada kamar tana tsoronshi Mikewa yayi ya tattaro duka yan aikin gida daga tsofaffi har yara ya dawo falo…… Babu laifin zaune babu na tsaye ya bisu da maruka bibiyu ,bai dagawa kowa kafa ba…… Sannan suka mike suka tafi cike da takaicinshi ,dama kuma idan da sabo sun saba da halinshi…… 《》《》《》《》 "Da gaske gobe zamu tafi gida……"ta fada a hankali tana kallon gefenshi "Eh Twee kiyi hakuri kinji ko ……"ya fada tare da kwantota a jikinshi…… A hankali tace "To me yasa AbdulMaleek……" "Kirana akayi baffa baya lafiya……Ko bakya son komawa mu zauna anan Twee?……" ya fada cikin sigar lallashi…… Girgiza kai tayi a hankali ba tare da tace komae ba ,Wayarshi ta hau ringing ya sa hannu ya dauko ganin sunan Abba a jiki ya sa ya mike a hankali tare da zareta jikinshi ya sauka saman gadon …… Binshi tayi da kallo a sanyaye idanunta suka ciko da kwallah ,Ta saba gabanta yake waya amma daga jiya zuwa yau ya canza gaba daya sae ya fita yake daukar wayar ……Hawaye suka ciko mata a ido ta saka bayan hannu ta share ,wani gefen na zuciyarta ke fada mata ko dae shima ya gaji ne ……Sunan Allah ta furta a hankali kamar yarda taji yanayi tare da kifa kanta a filo ta saki kuka mara sauti …… Yana Dauka yaji muryar Abba ,a kidime yake tambayarshi shi dinne koko wani ne…… "Nine Abdul maleeku……"Abban ya fada cikin sanyin murya "Abba kuma maryam ……" Datse mashi maganar yayi yana fadin "Tace maka na rasu ko Abdul maleeku……? Gyada mashi kai yake kamar yana kallonshi …… Shi kanshi Abban yasan mamaki ne ya hada Abdul maleek din magana …… A hankali ya warware mashi komae,tare da fadin "Ina Maharaja hotel yanzu haka a kaduna……" Sun dade suna magana sannan Abban ya kashe wayar …… Cikin Farinciki ya koma dakin ,Shi kanshi ya godewa Allah da bai fada mata ba ,to da yanzu sae yace mata me kuma ?ya tabbata ko gabas da kudu zata hadu barata yarda ba …… Cikin shauki ya kira sunanta"Safeenah……" Banza ta mashi tana kukanta kasa kasa…… Shima bai tsammaci zata amsa mashi ba ,ya matsa jikin socket ya saka charge sannan ya shige toilet yayo wanka…… ya fito yana yar waka a hankali…… Tsaki ta saki da karfi tare da kara sautin kukan nata ……Ido ya waro cike da mamakinta ya matsa yana fadin "Twee kukan me kike ……" Dago fuskarta yayi ya tsaya yana kallonta ……ganin bilhakki da gaskia kukan take kuma da alama ba yanzu ta fara ba ……don daga yanayin idonta zaka gane ta dade tana yinshi …… "Ya salam Tweena me aka maki……Sorry ki bar kukan ki fada man me ke faruwa?ko na maki laifine……?ya karashe maganar cikin sigar lallashi…… Rungumeta yayi sosae yana lallashinta…… amma taki danka mashi ,lokaci guda duk ya rude idanuwanshi sukayi jawur "Twee bakya lafiya ne " Banza ta mashi ta cigaba da kukanta ahankali…… "Look dan Allah ki man magana kinji Safeena……Me ke faruwa?wani guri ke maki ciwone Twee……? Ganin yana niyyar yi mata kuka ya sakata bude baki a hankali tace "Ka gaji Abdul Maleek……" *FEEDOHM💞* [2:20PM, 11/12/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹* 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 © *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM💞_* *Devoted to Ummi A'isha👌🏻* *Bestowed to Aunty Sis💕* 4⃣4⃣ Ganin yana niyar yi mata kuka ya sata bude baki a hankali tace "Ka gaji Abdul Maleek……" A rude yace "Dame na gaji Twee? Da hannu ta nuna mashi kanta tana kallon kasa…… Kafadarta ya riko da sauri yana kallonta sannan yace a sanyaye "Ni na fada maki na gaji Twee……?har ga Allah baya son wannan kalmar ta gajiya tana fitowa da ga bakinta "Look Safeena ……Wallahi Billahillazi kinji na rantse maki da Allah ban taba gajiya da ke ba……"ya fada a hankali A hankali tace "Ka gaji mana……" Rumtse idonshi yayi da sauri sannan ya bude yana fadin "Kalleni Safeena…… har rantse maki fa nayi ……" Shiru ta masa tana kallon kasa ……dago Fuskarta yayi ya hade da tashi yana kallon cikin idonta ……a hankali yace "Kin yarda ban gaji ba Twee……? Girgiza kai tayi alamun aa ……A sanyaye ya saketa tare da mikewa yana kallonta …… Kayanshi ya fiddo ya saka ba tare da yace mata komae ba ya dauki wayarshi ya bar dakin…… Jikinta yayi bala'in sanyi ta bi bayanshi da kallo…… Bayan mintina kadan ya dawo rike da leda a hannunshi ,ajewa yayi ya dauko plate sannan ya dawo ya juye kebabs din ciki ya mika mata ba tare da yace komae ba …… Kin karba tayi ta mayar da kanta kasa ……ko baa fada mata ba ta san fushi yake da ita tunda bai taba mata haka ba …… Gabanta ya aje mata plate din ya juya da niyar tafiya yaji ta riko hannunshi tare da sakin kuka a hankali tana fadin "Sorry………" A sanyaye ya dawo ya zauna tare da rike kafadunta yana kallon fuskarta ,hannu ya saka ya share mata hawayen sannan yace "Ya isa hakanan kinji ko ,Wallahi bana kaunar wannan kalmar na fitowa daga bakinki ,Dan Allah ki daina Safeena……" Gyada kai tayi tare da kwantar da kanta jikinshi tayi lamo …… "Tashi ki ci abinci kinji ko……"ya fada tare da dago kanta Wayarshi ta fara ringing ya mike yana fadin "Bari na dawo kinji Twee……" Hannunshi ta rike gam tayi rau rau da ido "Dawa kake waya tun dazu kake fita ……?ta fada har da dan guntun hawaye Haka kawae ya samu kanshi da farincikin tambayar da ta mashi ……Shirun da yayi yana kallonta ya sata sakin hannun nashi tare da komawa ta kwanta …… "Abba ne Twee……" ya fada tare da dagota Ba ta kalleshi ba tace "Shine kuma sae ka fita……" "Bude idonki ki kalleni Safeena ,dama shi yasa kike kuka dazu ……?ya fada yana aika mata da sanyayyan kallo…… Bude idon tayi tana kallonshi da fararen idanuwanta wanda ko da tayi kuka mintina kadan zasu juye su koma fararensu …… Tun daga farkon wayarshi da Maryam har zuwa Wayar da sukayi da Abban ya fada mata cikin natsuwa da sigar lallashi …… Abunda yake gudu shi ya faru don kuka ta sake mashi bata yarda ba Abbanta na raye ……Ita bata yarda ba…… "Baki yarda dani bane Safeena?ya fada kamar zaiyi kuka Fuskarshi ta rike da hannayenta tana girgiza mashi kai "Abbana Abdul maleek……"ta ke fadi kamar numfashinta zai bar jikinta "Wallahi Allah yana raye Safeena ……bai ci abinci da ta bashi ba……" "Ni dae ban yarda ba ka kaini gurin Abbana shi kadae nake dashi Abdul maleek dan Allah……" Wayarshi ya dauko ya kira Abban akayi rashi saa,wayar tashi a katse ……Abincin ma kin ci tayi ,Dole ya tafi ya nema masu private jet da zai maidasu gida da safe …… Ko da ya dawo kukan take kamar ranta zai fita ,Kasan carpet ya zauna tare da kura mata ido ,kamar wasa yaji hawaye na bin kumatunshi…… ……A hankali ta sauko daga saman gadon tare da dawowa kusa dashi ta rungumeshi sosae tana fadin "Ina Son Abbana Abdul maleek Shi kadae nake dashi sae granny ……Mamina ta rasu sannan Hassanata ma ta rasu ta barni…… dan Allah ka kira manshi Abdul maleek……" Rungumeta yayi sosae yana kara trying number Abban ,ji da yayi ta shiga ya sashi dagota tare da kanga mata wayar a kunne …… Sun kusa awa biyu suna magana Da Abban,banda lallashinta babu abunda yake ……Dakyar ta yarda ta aje wayar sannan ta kalli Abdul maleek din tace "Anya Abbana ne Abdul maleek ……? Kuka ko dariya ya rasa abunda ya dace yayi ,Ita da ta gama waya Da Shi amma take tambaya ko shine da gaske ……Harara ya sakar mata yace "Bansani ba……" Hawaye ya gani sun taru a idonta ,yayi saurin rungomota yana fadin "Allah ya baki hakuri Twee ,wallahi shine ko anayin muryar mutun sak ne……? Girgiza kai tayi a hankali …… Duk da hakan bai sa hankalinta ya kwanta ba ta mike ta fara hada masu kaya …… "sluggish girl……da cewa nayi Twee tashi kije can ki dawo…… kuka zaki man kice kafarki zai kare……"ya fada yana kashe mata ido Littafin dake hannunta ta wurgo mashi cike da kunya tana fadin "Ai kaine ke cewa bana iyawa ko nace na warke……"ta karashe maganar tana turo baki "Ba wani nan ……Ke dae kawae slothful lady ce……"ya fada yana kwaikwayon muryarta Hararanshi tayi cikin salo da jan hankali sannan ta dan cije lips dinta na kasa ta cigaba da abunda take…… 《》《》《》 "Wallahi zuciyata ke masifar tashi kwana biyun nan……"cewar hajiya tana yatsina fuska "Kisha magani mana Hajiyarmu……"Cewar Aunty zuby tana kokarin daukar gyalenta da ke saman gadon hajiyar ……sannan tta kara da fadin "Bara mu je mu dawo don na lura fadila bara ta barni na zauna lafiya ba indae ba ganin yaron nan ya dawo tayi ba……" Bata fuska tayi tana toshe hanci sannan tace "A dawo lafiya……" 【】 "Boka ka tabbata ta rasu ,kuma yaronnan har yanzu bai dawo ba……"Aunty zuby ta fada dake durkushe gaban boka…… Dariya yayi yana fadin "Ta dade da mutuwa ……don aljanun da muka tura mata ba kanana bane suna tafiya ne da wuta ,duk wanda suka raba sae sun konashi …… Maganar dawowarshi kuma Yarinyar ta shigo mu dubata yau dinnan zai dawo in dae bukatarmu ta biya ……" ya karashe maganar yana kallom kirjin Fadila Su duka biyun suka mike daga tsugunnin da suke suna kallonshi cike da tsaro ……Aunty zuby kam bata tunanin zata yarda boka ya sadu da diyarta ,haka ita fadilar ke ji bara ta yarda wannan kazamin ya rike ko da hannunta…… "Ki jiramu daga waje……"Cewar bokan yana nuna Aunty Zuby Kallon uku saura kwata fadila ta mashi cike da jarumta tace "Idan ta jiramu kayi uwar me dani……" Kafin ta rufe baki Aunty Zuby ta amshe "Fice mu tafi fadila wallahi baran taba yarda wannan mummunar halittar ya kusanceki ba,Har yanzu ina sonki ban shirya kwasar takaici ba ……" Dariya ya saki da karfi yace "Ita Uwar taki da ta yarda na kusanceki bata kaunarki ne ……" Fadila ta bashi amsa cike da tsiwa "Uban me ya shafeka da uwarta ,wannan ita taji zata yarda amma ni tawa uwar bara ta yarda ba ……Dama sae da na fadawa hajiya wannan tsinannen bokan babu abunda zai iya amma ta nace tace ya iya aiki ……Mummy dallah mu tafi tun kafin na kifar da shegun tukwananshi……" Tunda Boka yayi maganar jikin Aunty Zuby yayi sanyi har sae da fadilan ta jata zasu fita sannan ta dawo hankalinta …… Duka dakin ya dauki ihu kamar zaya tsage cikin wata irin murya bokan yace "Jeki yarinya ku tafi ke da uwar taki muga me zaki amfana mata……JELILI ka sakar mata mafi munin cuta har tsawon rayuwarta ……" A fusace Aunty Zuby ta juyo tana fadin "Ta Allah ba taka ba tsinanne……" "Kin san da Allah kika zo nan ……"ya fada cikin karaji…… Dan karamin tulun dake gefen hannun Fadila ,ta juya tare da takeshi da takalminta tana fadin "Na fi karfin ka tsinanne ……" Fashewar tulun yayi dae dae da karar da bokan ya saki tare da yanke jiki ya fadi kasa ……Wani jinine ya fara fitowa daga jikin tulun yana nufar gurin da bokan yake kwance …… Sannu sannu har ya fara mamaye dakin ……Da sauri Aunty Zuby ta fizgi fadila suka bar dakin suka fada mota …… A motar maganar bokan ke ta yawo a kanta ,Kenan hajiya ba santa take ba tunda har ta bari boka ya kusanceta …… Wawan birki Aunty Zubyn ta taka ganin guguwa tayo kan motarsu ……Addu'a ta fara nema amma duka sun bace mata tunda dama ba iyawa tayi ba ……da kyar ta kakaro "INNA NAKAFU MIN RABBANA YAU MAN ABU SANKAM DARIRI……" Cikin dakewa Fadilan tace "Mum karki jira ki tada motar mu tafi kawae aikin wannan shegen bokan ne……" Bata rufe baki ba taji kamar ruwa na fita daga karkashinta da sauri sauri…… A Rude ta saka hannu ta laluba pant dinta lokaci guda tana kallon Mum din a kidime "Muje mum karkk tsaya ……"ta fada cikin tsawa …… Kunna motar tayi zata bi ta cikin guguwar ta wuce ,Kamar an fizge motar daga hannunta haka taji sannan tayi ta juyi dasu cikin daji …… Cikin kidima Fadila ke fadin "Mum kiyi Addu'a mana sannan ki rike motar kin tsaya kina kwalalo ido ……" "ALLAHUMMA INNI A'UZUBIKA MINAL KUBSI WAL KABA'ISI……"Abunda ta fada kenan tare da balle marfin motar zata fita…… *FEEDOHM💞* [12:40AM, 11/13/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹* 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 © *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM💞_* *Devoted to Ummi A'isha👌🏻* *Bestowed to Aunty Sis💕* 4⃣5⃣ ALLAHUMMA INNI A'UZUBIKA MINAL KUBSI WAL KABA'ISI……"Abunda ta fada kenan tare da balle marfin motar zata fita Bala'in da suke ciki bai hana fadilan cewa "Amma mumy kinji kunya duk da bana zuwa islamiyya amma Umman Safeena ta taba fada man addu'ar shiga toilet ce wannan……" Kafin ta rufe baki Aunty Zubyn ta bude motar ta fita ……Har lokacin motar bata daina juyi ba don haka ta bi ta kafar Aunty zubyn ta cigaba da juyi a sama……Kusan minti Talatin fadila na ciki tana ihu Aunty Zuby kuma kafarta tayi daga daga …… Motar ta tsaya cak don kanta ……sannan fadilan ta samu ta fito tana tangyadi tare da kwarara amai …… Bata lura da Kafar Aunty Zubyn ba ta zauna tare da dafa kafar tana rike da ciki …… Ihu Aunty Zubyn ta saki tare da janye kafar da sauri…… Kallon kafar tayi tana fadin "Mumy ai ke kika ja kanki da kin tsaya da kafarki bata ji ciwo haka ba……Amma shine kika fito ki ka baroni wato duk abunda zai faru dani ya faru ko?Allah ya kara ai……"ta fada har lokacin tana amai Juyar da kai Aunty Zubyn tayi tana hawaye ba tare da tace komae ba …… Dakyar Fadila ta mike ta je bakin titi ta samo wani mai mota aka dawo aka saka Aunty Zubyn sannan suka tafi gida …… Tsaki mai motar yayi lokacin da fadila ta fita yana fadin "Haba hajiya kin san kina da matsala kuma sae ki zauna man gaban mota ……" Kallon gurin tayi sannan ta kalli bayan rigarta tare da sakin tsaki " Sae ka aje motar kaga idan ba'a wanke maka ba banza jarababbe sae kace ba cikin jini uwarshi ta haifeshi ba……" Cike da mamaki yace "Daga taimako ……? Bata jira shi ba tayi cikin gida ta bar Aunty Zuby da mai motar ya fiddo ya juya ya tafi yana yaba rashin kunya na fadilan…… Asibiti aka kaita Cewa akai kafar barata ta gyaru ba sae dae a yanketa gaba daya ……A sanyaye hajiyar tace a yanke …… 《》《》《》《》 A kaduna suka sauka …… Sannan suka kira Number Abban ya fada masu room number da yake …… Safeena na ganinshi ta kwace hannunta daga na Abdul maleek ta nufeshi da gudu ta rungume tana kuka …… Shima kanshi Abban kuka yake kamar karamin yaro …… Abdul maleek dinne yayi jarumtar lallashinsu har sukayi shiru ……sannan Abban yace su tafi Katsina su sauka gidanshi …… Ya fada mata inda ya jefa keys din da inda takardun suke yace ta dauke…… shima yana nan zuwa nan da dan lokaci kadan …… Mota daya suka dauka daga ita sae shi a baya …… Hancinta yaja da karfi ganin tunda suka baro gurin Abban bata mashi magana ba …… Yar kara ta saki cike da shagwaba sannan ta kwantar da kanta a kafadarshi tana hararanshi kasa kasa …… "Twee nayi laifine ……? Banza ta mashi ta lumshe ido kamar tana bacci ……Hannu ya saka ya shafi gefen wuyanta a hankali tare da mintsinawa …… "Biyu kenan ……"ta fada bayan ta saki yar kara "Ke ce Twee kinki kulani ……"ya fada tare da kwantar da kanshi saman kanta "Shine sae ka mintsine ni ……"ta fada a hankali "To yi hakuri……" Shiru ta masa ganin driver ya maido hankalinshi kansu…… 【】 Kamar yarda Abban ya fada gidanshi suka sauka harda Abdul maleek ……da yake darene babu koma kofar gidan yana rike da hannunta har tsakiyar falon …… Hannunta ya saki ganin Aunty fatee tana saukowa daga saman benen tana waya ……,Kallonshi Safeena tayi tare da matsawa sosae jikinshi …… Aunty Fateen bata lura dasu ba har sae da ta sauko falon sannan ta lura da safeenar…… tayi saurin datse wayar tana kallon Safeenar cike da tsoro …… "Ke Safeena ke ce ……"ta fada arude tare da nunata da hannu …… Kwantar da kai tayi tana jefa mata kallo sannan tace "Na canza maki ne……" Kuka Aunty Fatee ta saki tana fadin "Baki canza ba Safeena ……" Tabe baki tayi tana kallon Abdul maleek …… Kusa da Ita Aunty Fatee ta matso cikin kuka tana fadin "Safeena Asirin mu ya tonu Allah ya dauke mana Alhaji Safeena kaiconmu Diyata……" "Kaiconki dai Aunty Fatee ……Ubanki ya rasu ……to meye a ciki idan Abbana ya rasu?Allah ya ji kanshi ……"ta fada tare da jan hannun Abdul maleek suka shiga dakin Abba dake bude …… "Shiga ki gani wallahi da gaske nake Safeena ya rasu ……"Cewar Aunty fatee tana jan majina …… Rufe kofar sukayi ……Wani bakin ciki ya tare mata makoshi ganin an watsa komae na dakin da alama takardun ake nema …… Girgiza kai tayi a hankali hawaye suka biyo mata a kumata "Shiiii ……"ya fada tare da daura hannunshi saman lips dinta Hadiye kukan tayi ta koma ta zauna tana kallon Abdul maleek dake kokarin janyo Mirrow …… Aunty Fatee kam suna shiga dakinta tashiga ta kira Hajiyarsu amma har ta kare ringing bata dauka ba ……JB ta kira cikin saa yana kusa da wayar ya dauka "Safeena ta dawo kuma ta warke Jabir ……"Abunda ta fada kenan ta datse wayar sannan ta fito waje …… Fitowa sukayi dauke da jikka A hannun Abdul maleek ……da sauri Aunty Fatee ta tare tana fadin "Ina Zaki da ita Safeena meye kika kwaso ……? "Kudinsa ne da takardunsa ……"ta fada kai tsaye Cikin rudu tace "taya zaki kwashe kudin bayan bake kadae ke da gadonsa ba……"ita kanta Aunty fatee ji tayi kamar an fizgo maganar daga bakinta …… "BARRISTER ABDULMALEEK AHMED……Lauyan Alhaji ina da hurumin da zan kwashe duk wasu kaddarorinshi tare da sa hannun kuto har zuwa lokacin da zaa raba maku gadon……" Abdul maleek ya fada tare da fito ID card dinshi dake dauke da kyakykyawan hotonshi cikin rigar lauyoyi…… Amsar ID card din tayi ta buda ,bata yi mamaki ba tunda dama tasan Barrister ne tun da dadewa ……mika mashi tayi ta juya a sukwane ta koma daki …… Kallon Safeena yayi da ta bude ido da baki tana kallonshi ……kunnenta ya kamo ya rada mata "Duk burga ce Baby ……" Dariya tayi don ta yarda burgarce sae dae ID card din da ya nuna fa? Dakinta ta shiga ta dauko makullin motarta don tun lokacin da maigadi ya batashi tare da takardar da yace Abdulmaleek ya bashi bata kuma bi ta kanshi ba…… Mika mashi keys din tayi suka bar falon …… A Mota ta kalleshi a hankali tace "Ina ……" Katse ta yayi yana fadin '"Ina na samo ID card ko……? A hankali ta gyada mashi kai tana kallonshi …… "Copy ne jiya da muka sauka nasa aka man printing tare da lamination ……"Sannan ya kalleta yana fadin "Muje gidanmu mu kwana ko? Dan murmushi tayi tana gyada kai …… Bayan yayi Parking kofar gidansu ya juyo da murmushi a fuskarshi yace "Kinga gidanmu Madam ……zaki iya kwana kuwa? Hararanshi tayi tare da bude marfin motar ta fita ……bin bayanta yayi har ta shiga zauren ya riko hannunta yana fadin "Sae ki baroni Twee……" Banza ta mashi tana kokarin zame hannunta daga cikin nashi ……a kunnenta ya matsa yace "Sorry……" Fuska a daure tace "Ka gyara maganar da kayi sannan ……" …… Lumshe ido yayi sannan yace " Safeenata zata kwana gidan Baffana ……"ya fada cikin wata irin murya …… Kallon juna sukayi tare da murmushi lokaci guda wanda su kadae suka san fassararshi…… Inna sahu ta karbeta hannu bibiyu ……sae da suka zauna sannan yace bara yaje ya dawo ,Jikkar gaba daya ya aje bayan dakin Baffa cikin kejin kaji sannan ya daura buhunnan taki a sama tare da tsummuna…… Ya Tabbata tuwon dawa inna sahu tayi ……Fita yayi ya sawo mata Chips da Tabouleh gefe guda …… Sannan ya dawo ya iske har Inna sahu ta kawo mata tuwon da miyar kuka tsanwa shar da ita bata fara ci ba ……Suna fira da Nana da tunda ta dawo ta gane Safeenar ta makale mata …… Gabanta ya aje sannan ya zauna yana kallon yarda ta sha kunu tare da janyo langar tuwon ta fara ci ……Bai ga fuskar cewa taci abunda ya sawo mata ba Har taci tuwon ta koshi ba tare da ta kalleshi…… 【】 JB yana kwance da sabuwar yarinyarshi Aunty fatee ta kirashi …… Mikewa yayi zumbur yana kokarin mayar da rigarshi ……Yarinyar da ta riga tayi nisa a bukace take dashi tayi saurin riko hannunshi…… "Baby ina zaka please……?ta fada idonta a lumshe "Sorry baby…… Feenata ce ta dawo yau zanje na ganta ……"ya fada yana kokarin daukar wayarshi "Karka man haka Jabir wallahi a bukace nake kaima ka sani ……"ta fada idonta cike da kwallah …… Hannunshi ya fizge yana hararanta "Meye nawa a ciki ……" "Da kasan zaka man haka da baka tado man da feelings ba ,dan Allah ka taimaka man karka barni haka JB……"ta fada hawaye cike da idonta Kallon uku saura kwata ya mata tare da fiddo kudi cikin wallet dinshi ya aje mata "Duk yarda zakiyi kiyi ki samu natsuwa ……dama na fada maki inada wadda nake so kuma ta dawo …I wishes you all the best baby………" Girgiza kai tayi a hankali tana kallonshi har ya bar dakin sannan ta mike tsaye saman gadon tana girgiza ……Maciji ta koma bakikkirin tare da silalewa ta window ta fita …… *FEEDOHM💞* [4:52AM, 11/13/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹* 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 © *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM💞_* *Devoted to Ummi A'isha👌🏻* *Bestowed to Aunty Sis💕* *SISTER SAWWAMA HERE'S YOUR CHPPY DEAR ENJOY❣* 4⃣6⃣ Gurin Aunty Fatee ya wuce a tunaninshi Safeena tana gidan ,Ko gaisawa basuyi ba ya tambayeta "Ina Feena din ……? Tabe baki tayi tana fadin "Sun fita amma na tabbata gidan hajiyarsu ta tafi ……" Mikewa yayi yana fadin "Bara naje can na samesu ……" bata ce mashi komae ta sae binshi da kallo da tayi …… A gidan Granny ma wayam ya iske don cewa tayi bata san ma sun zo ba …… Wayar Safeenar ya kira amma a kulle…… Ta Abdul maleek din ma a kulle ,karamin tsoki ya ja sannan,ya mike ya fita ba tare da bankwana ba …… Da kallon Mamaki granny ta bishi a ranta take fadin ……Meye ruwanshi da dawowarsu zai rude haka …… A Bakin motarshi yaga budurwar da ya baro ……tsaye tana jiranshi a fusace ya karasa yana fadin "Uban me kika biyoni na maki anan……? Shiru ta masa tana kallonshi …… "Nonsense ……"ya fada tare da bude motar zai shiga …… Rike hannunshi tayi tana fadin "Kaine mutumin da ka fara kusantata Jabir …kuma dole ka aureni…" Dariya ya sake yana fadin "Amma baby baki da hankali taya zan iya auren macem da na kusanta a titi? "Amma kasan kaine mutumin da ka kauda man budurci ko……? "Wannan ba abunda ya shafeni bane Baby na maki dole ne……ko ba ke kika kawo kanki ba……"bai jirata ba ya shige mota ya barta …… 《》《》《》《》 Sae da yayi wanka ya shirya cikin riga da wando sannan ya shigo gidan ……duk tunaninshi bata tashi ba yanzu amma yana kutsa kai ya ganta tana wanke wanke Nana na mata dauraya Bata fuska yayi sosae sannan ya karasa gurin yana hararan Nana ……babu shiri ta mike ta bar gurin …… Kafarshi kawae ta kalla ta cigaba da abunda take ……Ganin tsakar gidan ba kowa ya sa ya Dagota karfi yana hararanta …… Turo baki tayi tana hararanshi kasa kasa tace "Meye haka ……? "Ki wuce ki koma daki ……"ya fada babu alamun wasa a fuskarshi Kallonshi tayi sannan ta dauke kai tare da komawa ta cigaba da wanke wankenta …… Daki ya shiga ya dauko mata hijab dinta tare da jikkar kayansu sannan ya fito yana fadin "Inna mun tafi zan maidata gida ……" Inna Sahu ta fito tana fadin "Da safe haka Abdul maleek ka tsaya a kawo mata koko mana wallahi tun dazu na aika a sawo mata basu dawo ba……" "Hajiyarta ta kirani yanzu idan munje can tayi kalacin ……"ya fada tare da daura mata hijab din saman kafadarta yayi gaba …… A sanyaye ta bi bayanshi ,inna sahu ta biyota tana mata addu'ar a sauka lafiya …… Bayan motar ta bude ta shiga tana turo baki ……Bai ce mata komae ba ya tada motar……Har sae da yayi parking Layout gaban wani katon gida ……Sannan ya juyo yana kallonta na yan mintina "Twee Fito muje ……" Ba ta dago kai ba haka bata tanka ba ……Bude motar yayi ya fito ya dawo bayan ya zauna tare da kamo hannunta …… "Twee Dan nace ki bar wanke wanken shine kike fushi ……"ya fada a hankali Banza ta mashi tana kallon kasa…… "Kin taba yin wanke wanke a rayuwarki safeena ……? Kallonshi tayi a hankali sannan tace "Idan ban taba yi ba sae aka ce maka ban iya ba kuma……? "Allah ya baki hakuri ……mu shiga ciki, Tunda Asuba JB ke kirana ……Na fada mashi yazo nan ya iskeni ……" Kallonshi tayi tare da fadin " Gidan waye nan ? "Gidan da JB ya bani ne Safeena ……"ya fada yana kallonta "Kenan zaka sakeni……? ta karashe maganar kasan makoshi Kallonta yayi na yan mintina sannan ya bude motar tare da jan hannunta suka fita ……Kamar yarinya take binshi tare da kallonshi har suka shiga wani katon falo sannan ya zaunar da ita yana lumshe ido …… Kujeran kusa da ita ya zauna ……Ya fito d a Envelop guda biyu daga cikin aljihunshi ya aje saman hannun kujeran tare da mayar da kanshi ya kwantar …… A Sanyaye take binshi da kallo tare da karewa ilahirin falon kallo……Sam hankalinta baya ga tsaruwar falon yana ga Envelop din da Abdulmaleek ya aje …… Wayarshi tayi kara ya dauka tare da fadin "Kashigo……"a takaice ……Sannan ya juya ya kalleta tare da mikewa ya koma saman hannun kujeran da take …… "Ko kina sona Safeena……? ya fada kamar yana mata rada …… Duk da faduwar da gabanta yayi hakan bai hanata sake mashi harara ba tana fadin "Bana sonka ,idan ka tashi kaman saki dari …Hakan ba zai sa na koma hannun JB ba" Yar dariya yayi tare sa kissing goshinta don ya gano tsatsar kaunarshi a idonta "Sha kuruminki Twee uku kadae zan maki ,amma ki daure ki koma gurin JB kinga kudin da ya bani fa suna da yawa sannan ga katon gida……Dan Allah madam bai burgeki ba…… sae dae ban sani ba ko bakin ciki kike man ……" Karamin tsaki ta saki tare da mikewa tsaye tana fadin "Idan na san wannan abun zakayi da ban biyoka ba ……bani takardar na tafi……"ta fada tana mika mashi hannu Dariya yayi yana fadin "Twee ki bari ya zo man na damka mashi amanarshi a hannu mana……" Bata saurareshi ba ta nufi kofar fita…… bin bayanta yayi yana dariya da envelop din yana fadin "Allah ya baki hakuri Twee ga takardar taki……" A fusace ta fizge envelop din tayi gaba tana kokarin danne kukan dake niyar subuce mata …… Aharabar Gidan sukayi karo da JB ……kamar sakarai ya saki baki yana kallonta tayi wani fresh da ita "Beaut……"ya fada yana shafar sumarshi…… Ganinn hawaye a idonta ya sashi fadin "Meye na kuka Fennat?Ke da ya kamata kiyi farinciki *ZAN RAYU DAKE* yanzu baby……" Kallon da ta watsa mashi ya makale sauran maganar……sae da ta fito titi sannan ta samu abun hawa …… Gidansu Maryam ta nufa kai tsaye…… 【】 "Good Job……"JB ya fada tare da mika mashi hannu…… Murmushi yayi mai sauti sannan yace "Ka ganta ne ……" "Yeah na ganta da takardarta a hannunta yanzu da zan shigo ……Naji dadi sossae Abdul maleek kayi man abunda banyi tunani ba …… " "Eyeh ……Karka damu " ya fada tare da daukar wayarshi yana latsawa "Ina Copy na takardar da ka bata? Envelop din dake aje ya mika mashi hankalinshi naga wayarshi …… Karba yayi ya aje sannan yace "Sae dae kayi hakuri Abdul maleek wallahi kudin da nace zan baka basu samu ba……dama companyn mu na sayar to har yanzu ba'a bamu kudin ba sae zuwa karshen month dinnan zan turo maka ……" Yar dariya ya saki yana fadin "Karka damu" Dariyar mugunta yayi sannan ya bude envelop din ya fito da takarda guda biyu ta sama an yi rubutu dan gutun :【NI ABDULMALEEK AHMED BAWA BAN TABA TUNANIN ZAN IYA SAKIN MATATA SAFEENA BA ……INA MATUKAR KAUNARTA TA YARDA BAZAN IYA RAYUWA BABU ITA BA ……MALAN JABIR GA CHEQUE DIN NAIRA MILLION 20 NAN NA LINKA MAKA KUDINKA…… KA BARMAN SAFEENA MU KARE RAYUWA DA ITA……】 Wata wawar shakara ya wa Abdul maleek din yana fadin "Wallahi baka isa! sae ka sake man Matata ……" Tunkude JB din yayi yana fadin "A tunaninka kowa wawane kamar ka Jabir?Tun ina shekara biyu nake zuwa islamiyya kuma har yanzu ban daina zuwa neman ilmin ba ……Malan jabir ko da na auri Safeena banyi niyar sakar maka ita ba saboda ina mata son da kai baka mata…… kasan meye AUREN KISHIN WUTA?na tabbata amsar bata wuce aa ……to Abdul maleeku yasan me ake nufi AUREN KISHIN WUTA sannan yasan meye makomarsa ……Kana fadin *ZAN RAYU DAKE* amma ka kasa jinyarta na dan lokaci ……a hankan zaka rayu da ita Jabir?Sannan saboda batan basira ka rasa wanda zaka ce ya auri Safeena sae Ni Abdulmaleek ?har ma na maka jinyarta ta warke sannan na sakar maka ita kamar wani sakarai?………Kasan tsawon shekaru nawa na dauka ina lallashin soyayyarta Jabir?Sannan na sameta cikin sauki na saketa kamar wani mahaukaci sabon kamu?zauna kayi tunani da kyau JB……" Kara shakareshi yayi yana nushinshi da karfi…… "Wallahi sae dae mu duka mu rasata……" abunda yake fada kenan …… Tun Abdul maleek yana kokarin kauce dukan da JB ke mashi har ya fara ramawa ganin abun ba mai karewa bane …… Dambe sukayi sossae kamar bara su rayu ba ……sae da suka daku dan kansu sannan suka rabu kowane ido kamar garwashi…… JB ya nunashi a harzuke yana fadin "Wallahi sae ka sake……" "Wallahi baran saketa ba……" *FEEDOHM💞* [5:35PM, 11/13/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹* 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 © *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM💞_* *Devoted to Ummi A'isha👌🏻* *Bestowed to Aunty Sis💕* 4⃣7⃣ "Mu zuba mu gani ……Waye ubanka a garinnan?me kake takama dashi……?cewar JB din "Ba wanda nake takama dashi sae kaina ……Uba kuma bandashi ,kai kuma da kake takama da ubanka ,zamu gani idan ya isa ya sani sakin Safeenah……" "Safeena tawa ce ,idan ba haka ba kowae zai rasa……" "Kaine ka rasata JB……" A fusace JB ya bar Gidan yana fadin "Kowa zaya rasa wallahi babu wanda ZAI RAYU DAKE SAFEENAH……" Banza yayi dashi ya zube saman rug yana mayar da numfashi ,tun tasowarshi bai taba dambe irin haka ba ……Dan karamin tsaki yaja sannan ya mike ya shiga dakin dake kallon falon …… Toilet din ta bude ya sakarwa kanshi ruwan zafi na tsawon awa saya sannan ya fito ……Allah ya taimakeshi ya aje kaya a gidan ya dauka ya saka sannan ya shigowa da Safeena motarta ya fita da tashi …… Gidansu ya koma ya dauko jikkar da ya aje bayan dakin Baffa sannan,ya kaita bank ya aje ya wuce office dinsu …… 《》《》《》《》 Fadila ta kalli Aunty Fatee tana fadin "ni fa Aunty fati ba lokacin period dina bane amma sae bleeding nake ……" Kallonta tayi tace " Ko dae kin manta lissafine……" Tabe baki tayi tana ware kafada sannan ta kalli hajiya dake zaune gaban,gadon Aunty Zuby tace "Hajiya har kin karbo test din……? Girgiza kai tayi tana fadin "Sunce idan idan,sun fito da result din sister baraka zata kawo mana ……" Da sauri Aunty Fatee tace " Wae hajiyarmu tun yaushe baki jin dadin ni ban sani ba……" Hararanta tayi tace "Dama yaushe zaki sani tunda rabon da na ganki tun bayan rasuwar mijinki kina can kin saki baki ,takardun ma kinki ki nema……" Ta bude baki zatayi magana Sister baraka ta shigo rike da result din ……Aunty fatee ta karba tana dubawa ……lokaci guda ta saki kara tana fadin "CIKI HAJIYA……"Uban kuka ta saki tana cigaba da fadin HIV/AID :Positive HEPATATIS:Positive Shikenan mun shiga uku Hajiya mun lalace …… Yanke jiki hajiyar tayi ta fadi a sume …… A Yashe aka dauketa aka bata gado …… Kusan awa daya ta farka sae dae barin jikinta baya amfani ,a rude Aunty Fatee ta je ta fadawa Nurse din suka shigo tare …… Duk Wani test da zasu mata su kayi suka tabbatar da paralysis ya kama hajiyar …… Ko da ta farka da "Na shiga uku ni Shafa ……Ina na samu Ciki" ta bude ido "Gurin Boka" Aunty zuby da ta farka lokacin ta fada tana kuka …… Aunty Fatee ta saki kuka tana fadin "Muke da shiga uku Hajiyar ace uwarmu da cikin shege……" Fadila kam mikewa tayi ta shiga toilet tare da cire dankwalinta ta linka ta sa sannan ta yarda pad din ganin pad din bata mata wani amfani sannan ta fito ta zuba masu ido suna koke kokensu…… 【】 Safeena kam tana isa gidansu maryam ta iske Mum dinsu a falo…… Da sauri ta tare ta rungumeta tana mata ya hanya cike da tausayi Kuka ya kwace mata ,Mum din ta fara lallashinta tare da bata baki ,don duk a tunaninta Rasuwar Abban nata takewa kuka…… Kwala maryam kira tayi ta fito ……ai kuwa makalkale Safeenar tayi kamar zata kadata ……sannan ta jata dakinta ta rufe kofa tana fadin "Besty karya suke maki Abba na raye na wallahi ……"ta fada lokacin da ta zaunar da Safeenar saman gado Cikin kuka tace "Na sani besty……" Idon maryam din ya ciko da kwallah ganin Safeenar na kuka tace "Baki warke ba besty? *"Na warke"ta fada cikin kuka "Besty so kike nima nayi kukan ,Dan Allah kiyi shiru kin ji menene to? "Abdul maleek ne besty……" Da sauri maryam din tace "Wani abu ya sameshi ……" Takardar ta mika mata tare da komawa baya ta kwanta …… Sae da ta gama karantawa sannan ta kalleta tana fadin "Ashe baki da wayau besty……" Da sauri ta mike tana kallon maryam din …… Daure Fuska maryam ta kuma yi tana fadin "Yeah ban taba sanin baki da hankali ba sae yau Safeena ,da mutuncin Abbanki kike neman ki zubar mashi dashi a idon Abdulmaleek……meye ribarki idan kinyi auren kisan wuta kin koma hannun jabir?Abun kunya ma Safeena har da yardarki ……ya kike tunanin idan Abbanki yaji kinyi aurene idan kika warke ki koma gidan jabir saboda shi,bara ya iya jinyarki ba sae Abdul maleek ko besty ?drivernki dake karkashin Mahaifinki ……to bara kiji wallahi Abdul maleek babban barister ne hakanan ya cigaba da kaiki makaranta ……kuma wallahi Safeena indae har Abdul maleek ya sakeki ki manta da ni maryam a rayuwarki……" Kuka take tana fadin "Wallahi maryam bance ya sakeni ba shi ya bani takardar yanzu ,kuma wallahi banyi niyar na rabu dashi ba haka banyi niyar na aureshi bayan na warke na ya sakeni ba ,Shin banda wayau ne besty koko ban san banbancin SO da SHA'AWA ba Besty ……Abdul maleek ke Sona kuma ina ina sonshi ……jabir kuma sha'awata yake ni kuma sha'awarshi ki fahimceni mana ……" Duk yarda maryam din takai ga daurewa amma ta kasa ,rungume Safeenar tayi tare da sakin kukan itama ,don ko kadan bata son abunda zai shafi kawartata ……duk wani farinciki na Safeena tana fata su rabashi biyu ……haka duk wani bakin ciki,nata tana fatan a rabashi uku ita ta dauki biyu …… Sae da suka ci kukansu sannan Maryam din ta koma tana lallashi Safeena "Dan Allah kiyi shiru wallahi wasa nake baran iya rabuwa da ke ba kinji ……" Shirun tayi tare da kallon maryam din tana fadin "Na sani besty kawae ina kukan,na batawa kawar da tayi Shekara biyar tana raba duk wani,bakincikina ta dauka ,sannan kawar da ta man abunda babu wani mahalunkin da ya kwatanta man shi a rayuwa……Dan Allah ki yafe " Dariya maryam din tayi sannan ta janyo takardar tana karantawa da karfi 【Safeena ko da yarda na aureki banyi niyar na sakeki ba bayan kin warke ,Wallahi na aurekine don na RAYU DAKE Har abada ……Dan Allah Madam ki karbeni a matsayin miji ko da baki son haka wallahi nafi dacewa dake a rayu nafi Jabir Kaunarki nesa ba kusa ……ki yarda dani Safeena ina maki wani irin So mai wuyar fassara na maki alkawarin bara ki taba kuka dani ba……Tun lokacin da na fara ganinki a bikin beeba na fara sonki dabi'unki da komae naki abun burgewa ne gareni safeena……nayi farinciki sosaae da mahaifinki ya daukeni a matsayin driverki sannan nayi bakinciki lokacin da naji zakiyi aure ……Dan Allah KI YARDA DANI Ina matukar kaunar ki Safeena…… ……by 8:00pm zan zo na daukeki mu dawo gida kinji ko ……Much love 】 Fizge takardar tayi ta fara yagawa tana fadin "Wallahi sae na rama……" Dariya maryam din tayi sannan ta mike da debo mata abinci ta kawo mata …… 《》《》《》《》《》 Sae da harka tayi nisa sannan Uncle Abbah ya fara kokarin wando …… Wata uwar zabura yarinyar tayi tare da mikewa tsaye tana kallon PPart dinshi "Kutmar can a hakan da kake kokarin shigata……" *FEEDOHM💞* [4:53AM, 11/14/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹* 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 © *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM💞_* *Devoted to Ummi A'isha👌🏻* *Bestowed to Aunty Sis💕* 4⃣8⃣ Wata uwar zabura yarinyar tayi tare da mikewa tsaye tana kallon PPart dinshi "Kutmar can a hakan da kake kokarin shigata……" Janyota yayi jikinshi yana fadin "Haba Baby kamar wata yarinya da Allah ki tsaya mana wallahi yau set na gold zan baki……" "Uwar Gold zaka bani Abbah ……ka mayar dani yar iska da wannan kazantar zan tsaya ka shigeni lallae baka da hankali……" PPart din ya kallah tare da mikewa zumbur yana kallon gurin ……wasu kurajene suka feso jawur dasu ga gurin ya tsatstsage yana fitar da jini kadan kadan ……Kallon gurin yake a tsorace ,duk da ya san akwae kuraje amma basu kai girman haka ba ……wani farin abu yaga yana kokarin fitowa …… Su duka suka kurawa gurin ido ……Lokaci guda suka mike tsaye ganin karamar tsotsa fara daga tsakiyar gurin ta fito tana yawo saman kuraje …… Gyalenta ta dauka ta fice da gudu tana fadin "Allah ya isa shege ……" Shikam maida wandonshi yayi ya nufi asibiti inda su hajiya ke kwance ……Ya fada masu a rude…… Cikin maganar da bata fita Hajiya tace "Hate ka kaishi a dubashi ……"Aunty Fatee ta mike Ta bi bayanshi ……yayin da Aunty Zuby ta bisu da harara ……fadila kuma kwashewa tayi da dariya…… Sample na gabanshi suka dauka tare sa dinbar jininshi ……da result ya fito HIV/AID kadae ne positive ……sannan nurse din tace basu gano,wata cuta ba game da gaban nashi illa iyaka suna tunanin yawan bin matane yasa gaban nashi yayi haka ……magunguna suka rubuta masu…… 《》《》《》《》 Da kyar maryam ta samu Safeena ta yarda suka je gidan granny wajen hudu na marece …… Fira suka sha sossae da ita…… Anan ne ma maryam ke fada mata abunda su Aunty Fatee sukawa Abban Safeena …… Hajiyar batayi wani mamaki ba don tasan zasuyi abunda yafi haka…… 【】 JB kam tunda ya koma gida ya kasa zaune bare tsaye ,yawo kawae yake tsakanin falo da dakinshi ,ko da mum ta mashi magana ……tsawar da ya sake mata dole ta koma daki kamar wata diyarshi …… Kiran wayar Safeena yayi amma har ta katse bata dauka ba ,wani abu ya tokare mashi lumfashi ,ya koma ya zube saman gado tare da dafe kanshi …… Uban duka aka sake mashi a bayanshi da karfi ,gantsarewa yayi sannan ya mike yana kalle kalle ……Zuciyarshi ta buga da karfi ganin labulen window na dagewa wani iska na fita daga dakin …… Cike da bacin rai ya yaye bargon dake shimfide saman gadonshi yabi iskar da duka yana fadin "Ni zaa wa iskanci ……to wallahi nima ba karamin dan iska bane ,duk shegen da ya kara dukana ya raina uwarshi……" Bai rufe baki ba aka daukeshi da mari ……kamar sabon kamu ya kaiwa iska duka cike da rashin tsoro "Na lura wani salom iskanci zaa kawo man na dukana ,to wallahi bana tsoron ko wane dan Iskan aljani……" Kofar toilet dinshi ta bude da karfi ,ya bi da gudu ya kamota ya rufe yana fadin "Baza'a barta bude ta ba yan iska a rufe nayi raayin ganinta ……" Kamar mahauci ya dinga surutu shi kadae cike da jarumta ……Sae da komae ya tsaya sannan ya mike ya fita daga dakin ……Har aka gama magrin bai bar surutu ba…… Tunaninshi daya inda zai samu safeena suyi magana yanzu ……"Dutsin safe……" ya fada da karfi tare da daukar mota ya fita …… Tun kafin ya shiga gidan yake kwala mata kira kamar zaya tashi sama ……Suna zaune da granny ya fado falon yana haki …… Cikin hargowa yake fadin "Amma Safeena Abdul maleek ya cika babban shege mara alkawari……" Kallonshi sukayi su duka ba tare da wani ya amsa mashi ba …… "Kin tsaya kina kallona ki fito muje ki karbo takardarki ……" "A gurin wa?Granny ta fada har lokacin tana kallonshi …… Fizgo Safeenar yayi da karfi ya mikar da ita ya hadeta da jikinshi ……lafiyayyen mari ta sakar mashi tare da fincike jikinta daga rikon da ya mata …… Cikin mamaki ya ke kallonta dafe da gurin da ta mara "Abunda kika aitaka yanzu ya nuna man kina bayan Abdulmaleek Safeena……?ya fada cikin konar rai "Akwae jahilar macen da zata kwarewa mijinta baya dama ……? ta fada tare da tsareshi da ido Dauketa yayi da mari yana fadin "Ni zaki ciwa amana?wallahi baki isa ba…… ke tawa ce kuma dole ki dawo hannuna ……" Bai rufe baki ba Maryam ta daukeshi da mari tana fadin "Akwae Ubanda ya haifawa Abba ita a family dinku……? Ya daga hannu da niyar ya rama yaji an rike hannun "Karka kuskura ka taba ta wallahi domin shine kuskure mafi muni da zakayi a rayuwarka ……"cewar Abdul maleek da ya shigo yanzu Kamar wani mahaukaci ya shakereshi "Abdul maleek karka tabashi ……"granny ta fada tare zuwa kusa dasu ta nuna jabir "Jabir fita ka bar man gida dan girman Allah……" "Wannan ne gida?ya fada yana watsa mata kallo "Ko ma menene nace ka fita Jabir ……" "Zan fita amma wallahi Sae dai mu duka mu rasata indae har na bar Safeena kowa ma ya barta ……" "Naji ikon Allah jabir kasan kana sonta me yasa ka saketa?Tunda baa maka dole ba ka saketa cewa akayi ta dawo gida a sama mata magani ta koma ,kai kuma kace mamarka tace ka saketa ,to me kake so a maka yanzu jabir.……? Banza ya mata Kamar guguwa ya bar gidan Zama Abdul maleek yayi suka gaisa da granny ……Safeena da maryam suka shige daki abunsu …… Nan yake fada mata da yayi niyar shigar da Aunty fatee kara sae dae rashin shedu ya hanashi saboda Abban bai riga ya ci abincin ba bare a ce an kaishi asibiti an tabbatar da poison suka saka a ciki…… Sae da ya fadawa granny gaskiyar bai boye mata komae ba hatta aikin da yake sannan ya kara da fadin zai tafi da Safeena yanzu …… Cewa tayi,"Ba komae Abdul maleeku fatan mu Allah ya sanya alkhairi cikin zaman ku ……" Sannan ta mike ta samu Safeena da Maryam zaune ,Sossae ta ma Safeenar fada sannan tace ta tashi ta bi mijinta su tafi …… Turo baki tayi tana fadin "Wallahi granny baran bi sa ba ……" Juyar da kai granny tayi tana fadin "Tunda kika taso nake lallashinki Safeena amma wannan karan kaniyarki zanci wallahi ……" Maryam ta amshe "Wannan karan bana bayanki besty ,ki tashi kawae ku tafi ……" Ganin da gaske suke ya sata daukar hijab dinta tana turo baki ta fita ,maryam ta bita har bakin mota tana mata magana amma sam bata kulata ba .…… Bayan motar ta bude ta shiga ,bai ce mata komae ba yama maryam bankwana suka tafi …… *FEEDOHM💞* [4:07AM, 11/15/2017] Feedohm💞: *💧💧 ZAN RAYU DAKE🌹* 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 © *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM💞_* *Devoted to Ummi A'isha👌🏻* *Bestowed to Aunty Sis💕* *49 to 50* Tsayawa yayi ya sayar masu abinci sannan suka tafi ,koda suka iso gidan cewa tayi bara ta fito ba wallahi …… Cikin lallashi yace "kiyi hakuri ki fito kinji Twee kinga dare yayi har 10 fa ……wallahi banyi dan na sakaki kuka ba i want to examine wther you love me or not……" Banza ta mashi tana kallon gefe guda …… Wata mota da yaga anyi yayi parking nesa dasu…… yasa ya waiga yana kallon motar na yan mintuna wadda dama ya lura tunda suka taho ake binsu…… Kallonta yayi sannan ya fita ya bude gate din ya shigar da motar yayi parking…… "Ki zauna anan karki Fito kinji ko?……idan ba ni nazo na bude ba……"ya fada yana kokarin fita daga motar …… Tabe baki tayi ba tare da tace komae ba…… juyowa yayi yana kallonta sannan yayi Kissing dinta a kumatu tare da bude motar ya fita yana kallonta …… Binshi tayi da kallo har ya bude kofae falon gidan ya shiga……Sannan ta lumshe ido a hankali ta kwantar da kanta baya Mutane suka fara dirowa cikin gidan su kusan 12 Ko wane rike da makami…… Tana dagowa gidan ya gauraye da haske A rude ta fara binsu da kallo daya bayan daya…… JB ta hango rike da katuwar bindiga yana nuna masu kofar gidan ……Ganin sun shige cikin falon yasa ta fara kokarin balle kofar ta fito…… Duk iya kokarinta ta kasa ashe ya rigaya ya rufeta ta waje ……Wani irin ihu ta saki da karfi tana dukan glass din motar tare da kwala Abdul maleek kira…… Abdul maleek da tunda ya shiga gidan ya zauna falon hankalinshi bai kwanta da motar da ya gani ba ……Yana jin lokacin da suka diro ya kira wani police officer yana fada mashi…… Uban bugun da aka kai mashi da kasan bindiga ya sashi sakin wayar kasa ……kallo ya bisu dashi har ya tsayar da idonshi kan JB dake harde saman kujera tun zuwansu…… "Ina take ……?JB ya fada da idanunshi kamar garwashi…… "Wacece ……? ya tambaya yana watsa mashi wani fitinanen kallo "Ku fada mashi ko wacece……"Ya fada tare da kallon yaran da suka zo tare…… Su duka suka rufeshi da duka…… duk da yana kokarin ramawa amma sae da suka mashi laga laga …… "Where's she……?JB ya fada cikin tsawa "Yanzu na tabbatar Kai ba namijii bane Jabir !macece cikin kayan maza…… tun da har ka dauka wadannan karnuka aka mace ……"Ya fada a galabaice Yar dariya yayi yana fadin "Kae da kake namiji yanzu sae ka gwada taka jamurtar……" Kafin su ankara ya saka kafa ya farde jabir din har sae da kanshi ya daki tiles da karfi ……Bugu sauran yaran suka rufeshi dashi wasu kuma na yankarshi har sae da suka barshi kwance …… Sannan yasa Yaranshi suka bincike kaf gidan amma babu ita……Har karkashin bed da cikin drawers suka bincika amma babu ita duk wani lungu da sako na gidan sae da suka bincike amma babu ita……Suka dawo suka fada mashi …… Bakin bindiga ya buga mashi yana fadin "Tana Ina……? "Ban sani ba……"ya fada yana dafe da inda aka dakeshi…… Safeena kam wayarta ta lalubo cikin kuka ta fara kiranshi…… Ganin haske ya sa JB ya kai hannu ya dauki wayar "TWEE……" Ya gani bisa screen din …… "Tana kiranka……"JB ya fada yana murmushin mugunta…… Da sauri Abdul maleek ya kai kafarshi ya hankade wayar ta fadi kasa ta tarwatse…… Wani daga cikinsu ya kai mashi yanka a gefen hannunshi na dama ……Dafe gurin yayi tare da sakin karamar kara ya duke don har bone dinshi sae da ya fito ……jini kam kamar an bude famfo …… Wayar JB ya dauka tare da hadewa ya kunna ……tana kawo haske Safeena ta sake kira ……dauka yayi tare da sakata speaker…… "Ki fito daga inda kika boye…" Cikin kuka ta ke kiran sunan Abdul maleek …… Tsawa JB ya daka mata yana fadin "Kina ina nace wallahi idan baki fito ba na zo na nemoki da kaina sae na kasheki sannan na kashe Abdul maleek idan kunso ya RAYU DAKE a lahira……" Kamar ana fizgar lumfashinta take fadin "Kar ka mashi komae Jabir zan fada maka inda nake yanzu ……" Da karfi Abdul maleek yace "No Safeena karki sake ki fada masu……" Yana jin lokacin da ta saki kuka tana fadin "Ina cikin……" Kukan kura yayi ya warce wayar tare da bugata a jikin bango ta yarda barata sake amfani ba …… "Mu tafi dashi oga Zata kawo kanta ……"Wani daga cikinsu ya fada Mikar dashi sukayi da tsiya suka fito dashi harabar gidan jini na fita sosae daga jikinshi…… Tana kokarin kiran wayar JB taga sun janyoshi kayan dake jikinshi kansu sun canza kala …… Uwar kara ta saki tana buga glass din motar da karfi ta yarda zasuji…… Su duka hankalinsu ya dawo gurin tare da sakin Abdulmaleek din sukayo kanta …… Tambayarshi keys din sukayi yace bara ya bayar ba ……Kara yankarshi sukayi……ya tafi kamar zai fadi yayi saurin dafe kofar …… Buga kofar take cikin kuka take fadin "Ka basu Abdul maleek dan Allah……" Girgiza mata kai yayi yana fadin "I Wld'nt Safeena……" "Kuyi ta dukanshi har ya fito dashi ……"JB ya fada tare da juya baya …… Kamar ranta zai fita take fadin "Ka daina Jabir…… na roke dan Allah ka daina dukanshi it griefs JB ……" Jin yarda take kukan ya sa Jabir din juyo wa yana masu alamar dasu dakata sannan yace "Kina sonshi ne? Bata san lokacin da ta dinga daga mashi kai ba tana fadin "Ina Sonshi jabir…… dan Allah karka cutar dashi……" Da sauri Abdul maleek din ya daga kai yana kallonta …… Kallonta JB d yayi da idanuwanshi kamar garwashi sannan ya kalli Abdul maleek din tare da gyara bindigarshi yana fadin "KO WA YA RASA……" Tare da saita Safeenar ya harba……ta cikin glass bullet ya huda tare da nutsewa a kafadarta ta haggu…… Kara ta saki da karfi tayi baya ta daki dayan glass din motar ……zaya kara harbinta Abdulmaleek din ya saka kafa tare da tadiyeshi ya fadi yana dukanshi da karfi …… A hankali yake fadin "You'll pay for this JB ……" Karan motar yan sanda ta su suka bi ta katanga suka dire su dukansu …… Da gudu ya fara laluben flowers din dake gefen motar har ya fito da keys din ya bude ya shiga tare da rungumota yana girgiza fuskarta ……cikin kuka yake fadin "Dan Allah ki tashi Safeena despite the fact you're the light that brighter my heart,you're are everything to me i'm lost without you……" Shigowar yan sandan ya sashi kwantar da ita cikin motar tare da fitowa ya koma driver sit …… Da sauri police ya matso yana fadin "Sorry……Bamu da petrol lokacin da ka kira……" Tsawa ya daka masu yana fadin "If any one of you step one hnds here I'll chop his legs wallahi ……Me zaka man yanzu ?meye amfanin ku?baku da wani amfani a rayuwar yan adam ……aikin kawae sae criminals sun tafi sannan ku zo da uzurinku na banza……Kar wanda ya matso kusa damu bama bukatar komae daga gareku……" Kunna motar yayi ya fita daga gidan ya barsu tsaye cirko cirko…… Tuki yake amma hankalinshi naga Safeenar ……duk bayan seconds sae ya juyo ya kalleta ,har yayi parking cikin asibitin sannan ya fito da sauri tare da balle marfin motar ya daukota ……Sae da ya shiga asibitin sannan ya lura da police din da ya biyoshi ……kallon daya ya mashi ya watsar tare da sakin tsaki da karfi…… Nurses suka karbeta aka shiga da adjoin …… Kamashi wani nurse yayi don ganin ciwon dake cikinji ……da sauri ya dakatar dashi yana fadin "Karka damu dani kaje ku dubata……" Sae da wata nurse ta fito tace mashi an cire bullet din sannan ya yarda sukayi treating dinshi …… Ana fitowa da ita ya bi bayansu har aka shigar da ita wani daki da ke da duhu ……Cewa akayi kar ya shiga amma bai kula kowa ba ya shige tare da zama gefen gadon yana shafa fuskarta …… Kamar karamin yaro ya dinga kuka yana surutai…… 《》《》《》《》 Su JB kam suna barin gidan guest house na babanshi suka nufa ……Kudinsu ya basu suka tafi sannan ya zauna dafe da kai kamar zuciyarshi zata fito saboda masifar bugawa…… Fitilon dakin suka dauke lokaci guda Sannan lalubayen dakin suka fara yayewa yayin da kara ta cika dukka dakin ……Ko gizau baiyi ba ya mayar da kai ya kwantar yana dafe da gefen zuciyarshi …… Wani farin abu kamar gawa yaga ya fara nufo inda yake …… Wayarshi ya fara laluba yana kokarin kunna flash din ……kifar da wayar akayi kasa tare da kifa mashi mari ……dafe gurin yayi yana fadin "Yanzune zaa sha banban don bana daukar duka daga ko wane shege……" "Ko zaka rama yanzu ma……" Yaji maganar na fitowa daga bayanshi …… Murya na sarkewa yace "Fito idan kai babban shege ne kaga idan ban rama ba ,don wallahi bana daukar rainin duka ninan namijin dan iska ne wallahi……" Haske ya gauraye dakin ta ko'ina ……tare da kida kamar ana dukan ganga…… Ta bayanshi aka taboshi…… A hankali ya fara waigowa yana fadin "Yanzu kau zan gwada maku nima shegen kaina ne ……" Dafe wandonshi yayi yana fadin "RABBANA ATINA FID DUNIYA……"Ganin wata mummunar bakar halitta sanye da korayen kaya ……duk hakorinta daya yafi karfin bakin mutun daya ……idanuwanta na fitar da wani irin jini yayin da gashin kanta ke jan kasa…… Cikin wata hargitsartsar murya take fadin "Gani ka rama namijin dan iska……" Jan numfashi yake da karfi ya kasa furta ko da kalma daya har lokacin yana rike da wandonshi da ke kama da an wankeshi…… Matsowa ta fara yi jikinshi yana jan baya har ya kai jikin bango …… Cikin tsawa tace "Ka rama babban shege ko sae na kara maka wani zaka hada ka rama……" Lokaci guda tayi girgiza ta dawo sak Raliya da suka hadu india ……kafin ta sake juyewa ta zama raliyar da yakai Fadama ……sannan ta zame masa yarinyar da ya kora shekaranjiya…… Kallonta kawae yake yana fitar da numfashi yayin da zufa ta wanke mashi jikinshi ,fitsari kam yayi ya kai sau biyar nan take …… Dariyar ta saki da karfi sannan ta kai hannunta zata sake marinshi …… "QUL HUWALLAHU……"Ya fada tare da sulalewa jikin bango yana fizge fizge kamar mai farfadiya…… Dariya ta saki tana fadin "Ka dade kana wa yaudarar yan mata ta hanyar yi masu alkawarin aure amma da zaran bukatarka ta biya sae ka wulakanta ……nima na maka alkawarin aure kuma bama sabawa Jabir……" Wani abu ta hura mashi sannan ta bace bat kamar walkiya…… 《》《》《》《》 Kwana Abdul maleek yayi kusa da Safeena ko nan da can bai je ba ……Haka ya hana idonshi bacci gudun kada ta farka yana bacci …… Bai kuma kira kowa ba har garin Allah ya waye ……haka ya wuni ko abinci baici ba ……yan sanda kuwa sunyi shigowa yafi 10 wae sunzo investigation ne……ko kallon inda suke bayayi don baiga amfanin yan sandan nigeria ba da sae an gama mugun abu sannan ka gansu…… Wajen karfe 6 na marece sannan ta fara bude idonta a hankali,…… A rude yasa hannun ya ida bude mata su yana kiran sunanta "Safeena …… "Kalleni dan Allah kinji Safeena Abdul maleek ……"ya fada lokacin da ya gama bude mata idanun da hannunshi …… *FEEDOHM💞* [2:31PM, 11/17/2017] Feedohm💞: *💧💧 ZAN RAYU DAKE🌹* 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 © *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM💞_* *Devoted to Ummi A'isha👌🏻* *Bestowed to Aunty Sis💕* , *51 to 52* "Bude idonki ki Kalleni kinji Safeena Abdul maleek ……"ya fada lokacin da ya gama bude mata idanun da hannunshi …… Sae da ta maida idon ta rufe da sauri sannan ya tuna abunda yayi bai dace ba "Sorry ……"ya fada a hankali Bude idon tayi tana kallon gefen hannunshi dake nannade da bandage sannan ta saki kuka a hankali tana fadin "JB ne Abdul maleek……Shine ya yankeka ,bayya da imani sae da nace mashi karka yayi amma yayi Allah bara ya barsa ba wallahi mugune……" Lumshe idonshi yayi yana jin kukan nata har cikin ranshi ……Rungumeta yayi sossae yana fadin "Ki bar kuka kin ji Insha Allahu muna cikin kariyar Allah kuma,nima bazan kyalesa ba ……" A Hankali tace "Yana so na mutune Abdul maleek……? Da sauri yace "Ko yana so ko bayya so nothing will happen to you ……" Sae da kalleshi sannan tace "Zai sake zuwa nan Abdul maleek ……Mun tafi gurin Abbana……" "Bara ya zo ba kinji ko……"ya fada cikin sigar lallashi tare da kara rungumeta sossae…… Sun dade a haka sannan ta dago idonta tana kallonshi ……Shima kallon nata yake kafin ya sa hannun ya rufe idonta yana murmushi …… "Menene……?ya fada cikin kunnenta har lokacin hannunsa na saman idonta …… A Hankali ta sa hannunta saman nashi tare da cirewa tana aika mashi da wani irin tsadadden kallo na musamman …… Sannan ta Lumshe ido a hankali tana fadin "Last tima i asked you Abdulmaleek How did you bear when i insulted you so badly without understand you amma baka bani amsa ba am appolozed……" Rungumeta yayi yana fadin "I see your love on me behind every word you say……I love you" Shiru tayi tare da zagaye hannunta da baya da ciwo a jikinshi ……likitan ya shigo yana fadin "Patient dinka ta tashi amma bakayi reporting ba kana nan cikin lovers trcts ko?Ga magunguna nan ya kamata ku samu abu liquit kuci sannan ku sha ku duka sannan kaima ka kwanta ka huta saboda yanayin jikinka……" Langwabe kai yayi yana fadin "Help,me doctor ga kudi ka bada a sawo mata ni bana bukata ……" Sannan ya maida hankalinshi kanta yana fadin "Da na tashi kuka zakiyi ko Twee……?ya karashe maganar yana kallon fuskarta Kadan ta murmusa cike da kunyar likitan …… "Ba wani kai dae ne zakayi kukan idan ka tashi……ya kamata ka kwanta ka huta tunda ta tashi ko……"likitan ya fada tare yin gaba yana fadin "zaa kawo,maku abinci ka tabbata ta ci kaima ka ci dan Allah sannan kusha magani……" "Okey……"ya fada a hankali tare da bin likitan da kallo har ya bar dakin…… Wani Police ya shigo ya zauna yana fadin "Sir ya mai jikin……" Kallon zanci gidanku ya mashi sannan yace "lafiya……" "Zaka iya fada mana cikakken sunan wadda aka harba……" "A'a ……"ya fada kai tsaye "Me yasa?ya kamata ka bamu hadin kai domin gano wadanda suka maka wannan aikin……"ya fada yana kallonshi Wani kallo ya watsa mashi yana fadin " Bana tunanin nan da Shekara goma zaku iya gano su ……please Get out……! "Amma……" Katse shi yayi yana fadin "Baka san kofar da ka shigo bane?alright ka juya lefthand side dinka zaka ga door akwae dan karfe a jiki sae kayi clicking ,idan ya bude sae ka fita ka bani guri……" "Kayi hakuri lokacin da ka kiramu motar mu babu petrol sae da aka kira commissioner ya aiko da kudin sannan……" "Shi yasa nace baku da amfani yanzu……Dan Allah ka fita……" A sanyaye ya fita…… bai damu da abunda Abdul maleek ya mashi ba tunda yasan laifinsu ne da basu zuwa cikin gaggawa …… Nurse ta shigo rike da katon flask dauke da ruwan zafi sae kamar Cler a hannunta da Plates…… "Thank you……"Abdul maleek ya fada bayan ya karba sannan ta juya ta fita …… Chips ne a cikin Cler din ……ya juye yana cije bakinshi saboda hannunshi da ya rike yanzu …… Kallonshi tayi tare da karban Plate din da hannunta mai lafiya ta aje gefe guda …… Zaiyi magana ta daura hannunta saman lips dinshi tana jefa mashi wani fitinannen kallon da yasa shi dauke idonshi da sauri …… "Go nd brush……"ta fada ba tare da ta kalleshi ba …… A Hankali ya mike yana tafiya har ya isa toilet din …… Brush yayo ya dawo yana mika mata hannu alamun ta taso itama tayi …… Hannun nata mai lafiya ta bashi ,ya jata har toilet din tayo brush tare da alwala sannan suka dawo ,suka zauna saman gadon…… Tea din ta ta hada a cup sannan ta kai bakinta ta sha kadan tare da janyewa ta daura saman nashi …… Lumshe ido yayi a hankali sannan ya bude yana kallonta ,cikin sanyin murya tace "Ko da zafi ne……? Murmushi yayi ya hade cup din da hannunta ya rike yana kallon kyakykyawar Fuskarta …… " Kullun kai ke Feeding dina Abdulmaleek……don Allah yau ka barni nayi naka……"ta fada muryarta rawa Sakin hannun yayi a hankali yana kallonta tare da lumshe ido …… Chips din ta debo ta saka mashi a baki ……sae da ya hadiye sannan ya bude ido tare da kama hannunta ya debo wani ya kai bakinta ……Janye idonta tayi daga kanshi tare da bude bakin ta saka tana murmushi mai fitar da ainahin kyawunta…… A haka suka ci abincin har suka koshi sannan ta janyo magani suka sha tare da kwantar da kanshi saman cinyarta tana fadin "Sleep……"kusa da kunnenshi …… Lumshe ido yayi yana shakar kamshinta farinciki na ratsa dukkan zuciyarshi ……Bai san lokaci da bacci yayi gaba dashi ba …… Murmushi tayi lokacin da ta fahimci yayi baccin tare da saka hannunta tana zagaye dukkan fuskarshi a hankali ……Sannan ta cusa yatsunta cikin sumar shi…… "I Love you……"ta fada tare da pecking goshin shi…… Wayarta ta janyo tayi dialing number Abbanta cikin saa ya dauka ,bata fada mashi abunda ya faru ba sae dae tambayarshi da tayi yaushe zai dawo…… "Nan da sati daya Safeena……"ya fada kai tsaye Daga haka suka cigaba da firansu …… Sunfi awa daya sannan ta aje wayar tana kallon Abdul maleek da har lokacin bacci take cikin natsuwa …… Hannu ta kai ta Shafi wuyanshi ,da Sauri ta janye jin jikin nashi kamar wuta ……haka nan taji kwalla na neman zubo mata …… Kwanto da kanta tayi bisa kanshi tana fadin …… "Sorry……Allah sae ya saka maka wallahi……" 【】 Tun suna Asibitin Hajiya tace a zubar da cikin amma likitan yace idan aka kuskura aka zubar dashi to wallahi zata iya mutuwa saboda ciwon dake tare da ita …… Duk da hakan bata yarda ba Aunty Fatee ta aika wani asibitin ta karbo mata wasu taps ta dawo …… Ranar da ta shasu kamar zata mutu amma cikin yaki fita …… Satinsu biyu asibiti sannan aka sallamesu wanda har lokacin barin jikin hajiyar baya amfani…… Aunty Zuby kam keken guragu aka bata ta dinga amfani dashi idan taji sauki ……kuka sosaae tayi da ta tabbata da ta riga ta zama gurguwa……Babban tashin hankalinta da akace hajiya nada HIV ita ma ta san bata rasata tunda kamar yarda boka ke kusantar hajiyar ita ma haka yake kusantarta ……tayi kuka kamar ranta zai fita tare da nadamar rayuwarta ta baya…… Gashi tunda aka kawota asibitin sau daya dadyn su Fadila ya leko ……yanzuma da Aunty fatee ta kirashi tana tambayarshi ko gidanshi zaa maido Aunty zubyn cewa yayi aa ta zauna gidan hajiyar ba sae ta dawo ba…… Fadila ma jini sae abunda ya cigaba tun tana sa ran daukewarshi har ta fitar da rai domin har kananan Tsutsa ke fita wani sani …… Set na gold din Aunty fatee ta sace taje ta sayar dashi dubu dari da hamsin ba tare da kowa ya sani ba taje asibitin zaria aka hado mata magunguna ta dawo …… Sauran kudin kuwa taci gaba da kashewa abunta…… Uncle Abbah ma duk da magungunan da yake sha amma abun yaki sauki ……wani irin jini ke fita daga cikin kurajen sossae ta yarda baya da damar saka wando sae ya baci ga tsutsa da yanzu sae uku ta fito lokaci guda…… Kullun yana zaune da yar shara sae ya daura zani a ciki ta yarda rigar barata baci ba …… Tunda suka koma gida Aunty Fatee ke hidima dasu don dawowa tayi gaba daya gidan da zama kwanansu biyu ta fara gajiya da hidimarsu komae ita ke masu hatta kashi nan hajiyar ke yinshi sae dae ita zata wanke mata …… Saukinta ma da Mijin,Aunty bilki ya saketa wai tana mashi sata Sai ta dawo gida tana taimaka mata … Shima ba komae take iyayi ba sae ta ga dama…… 【】 Ganin har an kwana amma JB bai dawo ba yasa hankalin mum dinshi ya tashi ta sami Dad dinshi ta fada mashi …… A fusace yace "Wae taya zaki takurawa yaro da girmanshi ,Jabir bai isa ya kwana bane a waje ?koko yarone da zaa matsa mashi dole sae ya kwana gida……" Kwantar da murya tayi tana fadin "Ba haka nake nufi ba ,naga bai taba kwana ba har ya yini bai dawo gida ba ……" A Zafafe yace "To yau ya kwana har ma zai kara kwanan sae muga wanda ya isa ya takurawa yarona……" Tabe baki tayi zata juya taji yana fadin "Ki sa ahada abinci sossae zanyi baki daga abuja yanzu ma zan fita na daukosu don a guest house dina zasu sauka……" Banza ta mashi tana gunguni ta fita…… Ko da yaje ya dauko bakin nashi daga airport guest house dinshi ya nufa dasu …… Da yake duhu ya fara ya bude masu falon suka shiga suka zauna ba tare da sun lura da Jabir dake sandare gefen falon ba …… Sai da aka kunno Gen sannan suka ga mutun kamar gunki tsakiyar falon …… Su duka suka mike tana kiran "Ekilisiya……"abunka da ba musulmai ba…… Dad dinne ya isa gurinshi tare da dagoshi a rude yana kiran sunanshi ……Shirun da sukaji ne yasa wani mai karfin hali ya dauko robar ruwa suka watsa mashi …… A firgice ya bude ido yana fadin "Muga dan iska a cikinmu……"yana yi yana karkada kai …… Dad din ya rungumoshi yana fadin "Jabir me ke faruwa……? "Muga dan iska a cikinmu ……"Abunda ya fada kenan tare da angaje Dad din ya ruga da gudu zaya fita daga falon …… Bakin Dad din sukayi namijin kokari gurin kamoshi sannan suka turashi mota aka nufi asibiti dashi …… A Can dinma sai da aka daureshi ya tsaya duk wanda yayi magana ko ba dashi yake ba to shi zai bashi amsa da "Muga dan iska a cikin mu……" Duk abunda zaa mashi akayi sannan aka mashi allurar bacci likitan yacewa Dad din ba maganin asibiti bane ya dace dashi …… A Maidashi gida a nemi wani malami ya mashi addu'a…… Wulakantaccen kallo Dad din ya aikawa likitan yana fadin "Kawae kace bara ku iya ba amma babu abunda yafi karfin asibiti……" Cikin natsuwa likitan yace "Wallahi alhaji ba maganin asibiti ya dace dashi ba……" Dariya dad din yayi ta izgilanci sannan yace "Kamar yarda ubanka ya kashe maka kudi aka baka kwalin wannan aikin haka nima zan kashe kudi ko wane asibiti ne na samama dana lafiya……" Shima kallon Dad din yayi a wulakance sannan yace "Kamata yayi ka kashe kudi a bawa dan naka irin kwalina sae ya nemawa kanshi magani ……asibiti kuma daga nan har Sin ka kai danka dole ku dawo a nemi wanda nace ……marasa mutunci" Daukar Jb din akayi suka tafi gida dashi ……Mum din na ganinshi ta hau ihu da kururuwa kamar diyar arna har sae da Dad din ya taka mata birki sannan ta zagaita tana fadin "Waya maka haka Jabir……? "Muga dan iska a cikinmu……"abunda ya fada yana kokarin bude da idonshi dake rufe ……da yake bata san abunda ke faruwa ba sae cewa tayi …… "Haba Jabir nice mum dinka me ke faruwa haka ?waya maka haka? "Muga dan iska a cikinmu ……" Zata sake magana Dad din ya taka mata birki dole tayi shiru…… *FEEDOHM💞* [3:07AM, 11/19/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹* 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 © *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM💞_* *Devoted to Ummi A'isha👌🏻* *Bestowed to Aunty Sis💕* *53 to 54* Satinsu daya a asibiti aka sallamesu …… Ishaq abokinshi ya kira ya mayar dasu gida …… A Bayan motar suka zauna babu wanda yace kala a cikinsu sae dae kanta na saman kafadarshi…… Tana ganin sun doshi hanyar gidan ta masa wata irin cakuma tana kallonshi …… "A'a……"take fada da karfi tare da girgiza mashi kai …… Matse ta yayi a kirjinshi ba tare da yace komae ba ……har cikin gidan ya shigar dasu sannan ya fita daga motar jin Safeena na kuka …… Ishaq na barin motar ta saki sabon kuka tana fadin "Kar mu zauna anan dan Allah……" Riketa yayi sossae yana fadin "Me yasa Safeena? "Gidan JB ne Abdul maleek dan Allah ko gidan Baffanka ne muje mu kwana amma baa nan ba ……"ta fada tana kuka a hankali…… Shafa kanta yayi tare da kara rungumeta yana fadin "Ba gidansa bane Safeena ……dan Allah kiyi shiru wallahi,bana kaunar kukanki……" "Ban yarda ba dan Allah mu tafi ni dae wallahi dawowa zasuyi……" "Akwae sojojin da aka kawo Safeena babu abunda zai faru da yardar Allah……" Lekawa tayi tana kallon sojan dake tsaye bakin gate din da katuwar bindiga …… Ihu ta sake tare da kara makalkaleshi …… Dakyar ya samu ta yarda da ba gidan jabir bane na Ishaq ne ……Sannan suka fito har lokacin tana rungume jikinshi tana zare ido kamar karamar yarinya…… Bankwana sukayi da ishaq din ya mika masu ledar hannunshi sannan ya fita …… Koda suka shiga falon da sauri ta rufe kofar tare da jingina da ita tana kallonshi …… "Common ……"ya fada yare da janyota ta fado jikinshi…… "Ki saki jikinki kinjo Twee……" "Idan suka zo fa……"ta fada a,hankali… Daukarta yayi ya daga sama yana fadin "Bama zasu zo ba……" Shiru tayi har lokacin tana mazurai ……da wayau ya samu ta shiga dakin tayi wanka sannan suka fito ya jasu sallah …… Ledar Da ishaq ya basu ya bude ya fito da Potato'n chicken bundt dake ciki ya juye masu a plate yana kallonta …… Yatsina fuska tayi tana kallon gefe guda har lokacin jikinta bai koma dae dae ba…… "Eat……"ya fada tare da janyo hannunta ya daura saman,spoon din yana kallon blming face dinta…… Girgiza kai tayi tana lumshe idanunta a hankali tare da jingina da kujera…… "Eat kinji Twee……" "Bana ci……"ta fada a takaice…… "Me yasa?ko bakya sonshi ne……?ya tambaya cikin sigar lallashi Gyada mashi kai tayi alamun Eh …… "To me kike so……?Ya fada a hankali Cikin Salo tace "Awara……" Dariya ya saki mai sauti yana kallonta tare da sake maimata Awaran a fili …… Turo baki tayi tana kallonshi ta kasa kasa …… Still murmushi yayi yana shafa sajenshi sannan yace "Ina zan samo awara yanzu Twee……" Ware Hannayenta tayi tare da bude manyan idanunta tana kallonshi …… Murmushi ya kuma yi sannan ya mike yana fadin "Bara naje na bayar a sawo maki ……" Bata ce mashi komae ba har ya fita sae dae gabanta dake faduwa da karfi …… Har ya bar falon ta bishi da gudu tare da rungumeshi ta baya tana fadin "Na fasa ……bana son Awaran dan Allah ka dawo……" Hannunshi ya sanya ya zagayota tare da rungumeta jikinshi yana kiran sojan dake tsaye bakin gate din …… Lamo tayi jin hannunshi na yawo tsakiyar bayanta …… Sojan ya baiwa kudin ya sawo mata sannan ya dauketa cak ya shigar da ita falom tare da zaunar da ita saman kujera …… "Me kike tsoro……?ya fada tare da tsareta da manyan idanuwanshi …… Dukar da kai tayi tana fadin "JB……" Kai tsaye Kallonta yayi na yan mintina sannan yace "Baya lafiya ai……" Da sauri ta kalleshi tana girgiza mashi kai alamun bata yarda ba…… Hannunta duka biyun ya riko yana kokarin saka idanunshi cikin nata amma taki yarda ……Yar dariya yayi mai sauti yana fadin "Da gaske baya lafiya jiya Ishaq ke fada man yanzu haka kamar ciwon hauka yake fama dashi ……" Da sauri tace "Allah ya kara ……" Hannunshi yasa tare da buge bakinta yana hararanta …… Turo baki tayi tare da dafe inda ya buga tana shefa mashi hararan kasan ido…… "Allah ya baki hakuri……amma komae mutun ya maka idan kaji baya lafiya addu'a kake mashi kinji Safeena……" Turo baki tayi tana fadin "Shine fa……" Da sauri ya katseta yana fadin "Ko da Aunty Fatee ce Safeena……" Da sauri tace "Allah ya kyauta wallahi ……" Kanne mata ido yayi yana fadin "Ko……? "Uhm……"ta fada a takaice …… Sallama akayi tare da bashi ledan awaran sannan ya dawo ya juye …… Zata saka hannu ya janye plate din yana hararanta ……"Ki barni nayi aikina……" Shiru tayi tare da kallon kasa fuskarta dauke da murmushi …… Sae da ya gama bata awaran sannan suka,mike ya rufe kofar falon suka shiga dakin dake kallonshi …… Katon gadone a ciki an gyarashi kamar wata sabuwar amarya …… Brush sukayo sannan ya sata tayo alwala sukayi nafila tare da kwanciya …… Janyota yayi ya rungume kamar zaa kwace ta har sae da yaji bacci ya dauketa sannan ya mike ya kunna fitilan wayanshi yana kare mata kallo…… Ya dade yana kallonta tare da kyalla mata photo kala kala sannan ya,kashe wayar ya janyota ya rungume tare da rufesu da bargo…… 【】 JB kam iyayen kudi dad dinshi ya kashe aka fitar dashi india …… Cewa sukayi wai kwalwarshi ce ta samu matsala don haka suka dinga banka mashi allurai kala kala na kwalwa…… Amma ba wani cigaba da aka samu sae dae ci baya tunda alluran da suke mashi sun fara effecting brain dinshi …… Hakanan sai dae aga yana fizge fizge kamar mai farfadiya baya ga surutun da hat lokacin bai daina ba…… 《》《》《》 Abba kam tun da Safe ya hawo motar haya ya dawo katsina …… Abdul maleek ya kira lokacin da suka iso yace yazo ya daukeshi…… Safeena na wanka ya zame ya fita ba tare da ta sani ba ……Sae da ta fito ta nemeshi bata ganshi ba sannan ta shiga zagaye gidan tana dubawa …… Don tsaruwa ya tsaru Sae dae bai shigar mata rai ba tunda ta san ba nasu bane …… Ita tama fi son su bar gidan su nemi nasu koma ko da daki dayane da toilet su zauna don bata tunanin Abdul maleek din zai koma Cikin gidajen Abbanta ya zauna…… Ko da ya dauko Abban nan gidan ya wuto dashi …… Lokacin da suka shiga falon tana kitchen tana dube dube har ta bude wata yar kofar da ta gani a gefe ashe tulun kayan abincine a ciki …… Maidawa tayi ta rufe tunda ta san ba nasu bane ta fito tana kakkabe hannu …… Tsalle daya tayi ta iso gaban Abban tare da rungumeshi …… Kafin su gama gaisawa Abdul maleek ya shiga kitchen din ya daura masu ruwan zafi sannan ya soya kwai…… Tana jin kamshi ta mike ta shiga kitchen din tana waro ido "Waya sa ka taba masu kaya……"ta fada tare da jan kunnenshi…… Kashe mata ido yayi yana fadin "Allah ya basu hakuri……Zan biyasu idan na samu kudi……" Cikin sanyin murya tace "To dole sae mun ci abunda bamu dashi……" Ganin yanayinta yasa shi janyota jikinshi yana fadin "Sorry ……Sun ce nayi amfani da komae ne fa……" Shiru ta masa tana kallonshi …… Janyeta yayi daga jikinshi ya bata ta kaiwa Abban…… Sai da suka koshi sannan Abban yace su taso su tafi …… Da "To……"Abdulmaleek ya amsa …… Safeena kam waro ido tayi tana fadin "Ina? "Gidansu Fateema……"Abban ya fada kai tsaye…… *FEEDOHM💞* [5:26AM, 11/19/2017] Feedohm💞: *💧💧 ZAN RAYU DAKE🌹* 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 © *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM💞_* *Devoted to Ummi A'isha👌🏻* *Bestowed to Aunty Sis💕* *55 to 56* Daga Safeena har Abdulmaleek suka kalleshi lokaci guda a sanyaye sannan Abdul maleek din ya shiga daki ya fito da hijab din Safeenar a hannu suka fito…… Babu wanda yace ma wani komae har suka bar gidan sannan suka dauki hanyar zuwa gidansu Aunty Fatee …… A bakin gate din gidan sukayi Parking kusa da inda wasu masu aikin kawo yashi suke juyewa…… Kai tsaye Abban ya kutsa kai cikin gidan ba tare da fargabar komae ba ……Daga harabar gidan suke jiyo muryar Aunty Fatee tana bala'in an dauke mata set na gold dinta kuma sae an biyata …… Murya Fadila suka jiyo tana fadin "To Uban Wa zai maki sata a gidan Aunty Fatee……" Kai tsaye tace "Ubanki ……"sannan ta cigaba da hargowarta…… Sallamar Abban ya sata juyowa a sukwane tana kallonshi tare da nuno shi da hannu tana fadin "Khaleed kai ne ……" Murmushi yayi wanda yafi kuka ciwo sannan yace "Nine Fateema kinyi mamakine……? Uban ihu ta saki tare da dafe kai tana fadin "Wallahi karya ne ba kai bane ……Hajiyarmu fito ki ga Khaleed wae shine bayan nasan karyane ya mace…… Kece Shaida ya mutu Ni ce Shaida, Zuby ma shaida ce Abbah ma Shaidane ka mutu……" Babu mai iya fitowa cikinsu sae Uncle Abbah da ya fito daure zanin atampha yana kallon Abban ……Sannan ya koma da gudu tare da garkame kofar dakin yana fadin "Fatalwa ……wallahi fatalwace hajiya bani hijabi na shige Hajiyarmu……"da karfi…… "Shine Aunty Fatee Abbana ne ,ko kin dauka ya mutu ne da gaske……?cewar Safeena dake tsaye tana kallonsu …… Dariya Aunty Fateen ta saki tana fadin "Ni ce Shaida ……kai wallahi malan habu ma shaidane kuma Malan bala ma shaidane ya mutu……a'a a'a ya mace nace maku ya mace ……"ta karashe maganar cikin sautin waka tare da fara soshe soshe tana wurga idanu…… Salati Abban ya dauka tare da binta da kallon ……Zuwa tayi gabanshi ta kai hannu zata kamoshi ……yayi baya da sauri yana nunata da yatsa yace "Akul fateema karki kuskura ki tabani……" Itama baya tayi tana wurgawa Safeena kallon da ta fara tsorata da ita ……tayi bayan Abdul maleek ta boye tana ware idanu…… Daga falon ta fita tana fadin "Malan habu shaidane Khaleedu ya mace ……haka liman ma shaidane ka mace ……"Bin ta sukayi a baya Abban na salati amma kafin ta fita gidan ta gama cire kayan jikinta tsab tana fadin …… "Nace maku ya mace tunda sae da na barbada mashi a abinci daga baya ma na juye mashi duka don yayi saurin mutuwa……Kai har Nafeesa na kashe, nace maku ta mace……" Motar dake kwaso yashin ce tayi gaba da ita tare da bi ta samanta ta wuce …… Ihu Safeena ta saki ganin kwalwar Aunty Fatee a tayar motar tare da kankame Abdulmaleek kamar numfashinta zai fice …… Cikin Sauri ya kaita mota sannan ya dawo yana fadawa Abban zaije ya maidata gida ya dawo…… Mutanen gurin kam salati suka dauka bayan motar ta daki bango ta tsaya……na ciki ya fito amma ko kwarzane babu a jikinshi …… Yan hanjin cikinta yashe saman hanya ……haka hannuwanta ko wane ya kama gabanshi ……haka a ka tattarata aka shigar da ita gidan don babu maganar zuwa asibiti…… Cikin Yan mintina labarin mutuwar Aunty Fatee ya karade ko'ina a lungun …… Hajiya kam suna cikin gida babu kafafuwa, banda ihu babu abunda sukeyi…… Liman aka aika yazo amma ba'a sameshi ba wai yaje kauyensu …… haka ladanin unguwar shima baya jin dadi …… Abban ne ya taimaka aka mata wanka tare da sallah ,shima dukka mutanen basu cika sahu daya ba …… Da yan k'warorin mutane aka tafi da ita makabarta …… Bayan anyi kabarin da za'a sakata ne aka ga kananan kunamu jawur kwance a cikin kabarin…… Hankalin mutanen yayi bala'in tashi har ma wasu suka fara sabewa suna barin makabarta…… Abban ne ya jajirce yace su taimaka a sake wani kabarin…… Haka aka sake gina wani kabarin amma the same abunda aka gani ana farkon shi aka gani ana biyu…… Sai da aka gina kabari kusa biyar amma duk wanda aka gama ginawa kunamu za'a gani a ciki …… Wani dan dattijo yace a saka a haka saboda idan zasu gine dukkan makabartar to da alama abunda zasu gani kenan…… Haka aka kamata aka saka cikin kunamun ……Sannan suka juya a sanyaye cikin tashin hankali suka tafi …… Basu fita makabartar ba kabarin Aunty ya kama da wuta…… Cikin kidima suka juya suna kallon tashin hankali …… Abban bai san sadda kuka ya kwace mashi ba yana fadin "Wallahi indae Alhaki na ne Fateema na yafe maki duniya da lahira ……Allah ka tausayawa wannan baiwar taka dan darajar Fiyayyen halitta……" Ruwa Aka fara kawowa da kasa ana kokarin kashe wutar amma ko alamun mutuwa batayi ba …… Lokaci guda wutar ta tsallake kabari biyu dake kusa da na Aunty fateen ta kama ana uku sannan ta kara tsallake kabari Biyar ta kama ana shiddah ……Duk da makabartar zagaye take da ciyawu busassu hakan bai shafi sauran kabarurrukan dake zagaye da makabartar ba …… Kusan Awa uku wutar naci yayin da mutane ke zagaye da makabartar har saman gini……ruwa kan har firefighter sun zo amma a banza sae da suka gaji suka zubawa sarautar Allah ido……Wasu hotuna suke dauka wasu kuma video sukeyi wasu kam kuka suke cike da tashin hankalin da basu taba gani ba…… A hankali kuma wutar ta dinga baya har ta mutu kurmus dan kanta……sannan mutanen suka fara tafiya cike da al'ajabin tare da tambayar wace mata aka kawo me take aikatawa haka? 《Wa iya zubillah……Wallahi tallahi baku bina bashin rantsuwa abunda ya faru kenan akabarin wata baiwar Allah kuma ni,ganau ce ba jiyau ba ……Muji tsoron Allah mu gyara aiyukanmu domin karshenmu……》 Cikin mintina dukkan unguwar da kewayanta an dauka cewa an kai wata mata kabari amma kafin a fito kabarinta ya kama da wuta…… Da labari ya isa gurin su Hajiya karku so kuga tashin hankalin da suka shiga har dasu Fadila da Uncle Abbah …… Lokacin ne Hajiya tayi kukan da ake kira kuka tare da nadama mai tarin yawa ……haka Aunty Zuby wadda dama ta rigaya ta yi nadama amma ranar sae da ta gwammace da ba'a haifeta ba har ta ga wannan bala'in …… Abban ma kuka yayi cike da tausayinta tare da kwarara mata addu'a ……Dan zaman makokin da akeyi ma mutanen kin zama sukayi wadanda suka zauna ma suna jin abunda ya faru suka mike suna fadin ko an zauna ma babu abunda zaman zai mata …… Haka duk suka watse suka bar Uncle Abbah da Abban Safeena durkushe …… 【】 Abdul maleek kam yayi niyar da ya aje Safeenar ya dawo amma ta kankameshi tare da sakin kuka tana dafe kai …… Tambayar duniya ya mata ta fada mashi meke damunta amma taki magana sae zabura take tana kara kankameshi …… Ya tabbata tsoro taji don ko ba'a fada mashi ba yasan bata taba ganin mutun a haka ba …… Addu'a ya fara tofa mata a hankali yana rungume da ita har sae da ta fara dawowa natsuwarta sannan ya dinga maimaita mata Inna illahi wa inna ilaihir raju'un a hankali tana maimaitawa…… Kin barinshi tayi ko nan da can ya tafi tana jikinshi har dare ……sannan ya kira Abban ya fada mashi …… Abban cewa yayi kar ya damu shi har ya wuce gida ma…… Haka suka kwana ko magana ta kasa yi sae zare idanu take kamar mage,…… Kwanansu biyu a haka sannan ya samu ta saki jikinta dashi…… 【】 Tana kwance jikinshi ya zagayeta da hannunshi yana karanta mata wani english novel mai suna tears drops at the sun set…… Dukkan hankalinta ta maida akan littafin tana saurarenshi cikin natsuwa har da su lumshe ido…… A je littafin yayi yana fadin "Meye date yau……? Dan turo baki tayi tana fadin "19 Nov 2017 mana……" Lumshe ido yayi tare da matseta a jikinshi …… Dagowa tayi tana kallonshi tare da shafar sajenshi tana murmushi …… "Menene……?ta fada a hankali Waro ido yayi ya tabe baki sannan ya janyeta ya mike ba tare da yace komae ba ……yatsina fuska tayi tana Spreading arms dinta a hankali tace "Kai ka sani ……"a hankali Juyowa yayi yana kashe mata ido yace "Ko……? Tsuke baki tayi ta gyada kai sannan ta mike ta dauki littafin ta koma saman one siter ta zauna tana fadin "Thank God nima na iya karatun……" Dariya yayi mai sauti sannan ya shige daki yana girgiza kai…… *FEEDOHM*💞 [9:21AM, 11/19/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹* 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 © *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM💞_* *Devoted to Ummi A'isha👌🏻* *Bestowed to Aunty Sis💕* *56 to 57* Sae da yayi wanka sannan ya fito sanye da kananan kaya sai kamshi yake zabgawa yana waka a hankali " *ZAN RAYU DAKE* Zan mutu dake *ABADAN* Dani dake zamu zauna……" Kallo daya ta mashi ta yatsina fuska tana turo baki sannan ta cigaba da kallon littafin don ba karantawa take ba …… Kusa da ita ya matso tare da dukowa ya mata kiss a fuska yana kashe mata idanu ……"Twee zanta fita……" Turo baki ta kuma yi tare da dagowa tana kallonshi sannan tace "Zan je ……" Ido ya waro yana fadin "Ina……? "Inda zaka ……"ta fada a hankali Murmushi yayi mai sauti yana kallonta sannan yace "Alright bara na dauko maki hijab ,dama JB zan gano kema ya dace kije ki ganshi……" Ya karashe maganar tare da kafe ta da ido …… Da sauri ta dago ido tana kallonshi tare da fadin "Sae ka dawo Allah ya kiyaye ka yo man tsaraba……" Dariyar mugunta yayi yana fadin "A'a Twee ki taso muje ……" Turo baki tayi sannan ta cigaba da duba littafin ba tare da tace komae ba …… Lakuce mata hanci yayi tare da kissing kumatunta sannan ya fita yana waigenta…… Mintina kadan ya dawo shida wata yar kyakykyawar budurwa a bayanshi …… Cikin Fara'a ta tari matar tare da bata ruwa …… Sannan ta dawo saman hannun kujeran da yake ta zauna ta kashe murya tana fadin "Wannan fa?ban santa ba……" Kallonta yayi suna hada ido ya kashe mata ido "Zata maki kunshi ta wanke maki kai ta maki kitso……"ya fada tare da kamo hannunta Waro ido tayi tana fadin "Kitso fa kace? Gyada mata kai yayi yana tsuke bakinshi "Bana so gaskia……"ta fada a shagwabe……Saboda har ga Allah bata kaunar kitso Cikin wata irin murya yace "Ni kuma ina so ……Dan Allah kiyi danni kin ji ……? Gyada kai tayi tana mashi murmurshi na musamman tare da komawa gurin budurwa suka fara fira …… Mikewa yayi ya fita ya basu guri…… Kunshin zallah bakin lalle yarinyar ta mata mai shegen kyau kamar an daura zanen…… Sannan ta wanke mata kanta tare da yaryara mata kitso two step kanana kanana ……wanda suka sauko har tsakiyar bayanta …… Wani masifar kyau tayi kamar ba ita ba …… Kusan magrib sannan aka gama ta shiga daki ta kirashi tace yarinyar zata tafi …… Cewa yayi ta tafi kawae ya rigaya ya sallameta ……ko da ta dawo yarinyar tana tsaye bakin kofa zata tafi ……tace ta jirata ta fito…… Yan kayan kwalliya ta kara mata dasu banda 5k da ta bata sannan budurwar ta tafi kamar ta sude dob murna……don Abdulmaleek din 20k ya bata…… 【】 Sai bayan isha'i ya dawo tana zaune falon sae kamshi take …… Sae dae da ganin fuskarta kasan fushi take …… Dariya yayi bai ce mata komae ba ya dauketa cak ya nufi da ita upstair din gidan wanda tunda suka zo bata taba gigin hawa ba…… Lamo tayi har ya bude wani daki mai duhu ya shigar da ita tare da dagata sama yana juyi da ita …… "Ka sake ni……" Cak ya direta kasa ……kai hannu tayi tana lalubarshi ganin dakin babu haske ko kadan tare da kiran sunanshi a hankali …… "Dan Allah ka kunna haske ……"ta fada kamar zatayi kuka Jinshi tayi bayanta yana kokarin zage zip din rigarta tayi saurin rikewa tana fadin "Meye kake yi haka ……" Shiru ya mata tare da kamo duka hannunta ya matse a arms dinshi sannan ya sabule mata rigar ta kasa …… Bai ankara ba yaji hannunshi na yawo a dukka gabobin jikinta …… Wuyanta ya fara kissing a hankali har ya gangaro shoulders dinta ……yayin da hannunshi ya kasa zama guri guda …… Kukan da ta sakine ya sashi lumshe ido tare da matseta a jikinshi ya bar duk abunda yake sannan ya saka mata wata doguwar riga da iyakarta guiwa……Sannan ya daura mata crown dake salki sossae…… A jiyar zuciya ta saki tana fadin "Meye kake yi haka Abdu ……"kasa fadin sunan tayi saboda nauyin da taji ya mata …… Hasken da ya gaurayen dakin ne ya sata waro ido tana bin bangon dakin dake blming da *Happy Birthday to my Princess……* Kallon jikinta tayi tare da kankame hannunta a hankali ta ware hannunta tana juyi a hankali tare da fadin *I Love you* da karfin karfe…… Fitowa yayi daga cikin labule ya dagata sama yana juyi da ita sae dariya take ……Sannan ya shige da ita wani dakin dake ciki wanda ke dauke da katon gado kadae……Sae katon cake din dake gefe guda shima an rubuta sunanta a jiki…… Kallonshi take irin kallon da bata taba mashi ba sannan ta ware hannayenta tana lumshe mashi ido…… Cikin Zarra ya,tako har ya iso ya shige jikinta ta mayar da hannun ta rufe tare da daura bakinta saman wuyanshi …… Tsawon mintinsu goma a haka sannan ta jiyo kara da karfi kamar fashewar wani abu …… "JB ……"ta fada tare da fadawa saman gado ta janyoshi ta makale …… A kunnenta ya rada mata "Baloon ……"tare da cije kunnen a hankali…… Duka ta kai mashi tana niyar tureshi ……Duka nauyinshi ya sakar mata tare da kafeta da ido cikin salon soyayya…… Lumshe ido tayi a hankali har sae da ya gangare daga jikinta sannan ta bude tana kallonshi a hankali …… "Ki shiga kiyi alwala ……"ya fada ido a lumshe …… Bata san lokacin da tace "Bana sal……" Da sauri ya bude idonshi yana kallonta tare da janyota ta fado jikinshi…… Hannu yake niyyar sakawa a pant dinta tayi saurin rike hannun…… "Cire man hannunki daga jikina……"ya fada ido a lumshe …… Turo baki tayi kamar tayi kuka tace "Zan fa yi alwalan dan Allah karka saka ……" "Uhum ……"Ya fada tare da hade hannunta guri guda …… Kukan da ta sakine ya sashi yin dariya tare da sakinta ta mike…… Mintina kadan ta fito Sannan shima ya mike yayo wanka tare da alwalan …… Prayer mat ya shinfida sannan ya mika mata sabuwar hijab har kasa ya jasu Isha'i Daga nan sukayi raka'a biyu …… Sannan ya juyo ya dafa kanta tare da jero,mata addu'o'i…… Ita kam sai zare idanu take kamar mage har ya gama ya dauko wani katon tray ya aje gabanta…… Kajine ciki masu rai da lafiya sae kamshi suke sae Fresh milk gefe guda tare da dabino da inibi…… Ganin babu wasa ya sata karban abunda yake bata tana yatsina fuska ……kadan taci ta kauda kai shima dabinon kawae yaci ya mike ya kauda komae ya dawo ya mikar da ita yana fadin "Good ……naga yau bara ki iya komae ba sae na maki ……" Shiru tayi har lokacin tana zare idanuwa …… Toilet ya kaita tayo brush sannan suka dawo… Takurewa tayi sossae tana raba idanu Sai da ya canza kaya sannan ya miko,mata wani Glom night Pink riga da wando ……bata dauki kayan ba sae kara takurewa da tayi tana kallonshi…… Kwanciya yayi tare da janyota yana fadin "Haba Twee ki saki jikinki mana ba abunda zan maki fa……"… *FEEDOHM💞* [9:26AM, 11/19/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹* 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 © *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM💞_* *Devoted to Ummi A'isha👌🏻* *Bestowed to Aunty Sis💕* *58* A sanyaye ta dago tana fadin "Da gaske……" Hararan wasa ya sakar mata yana fadin "Da da muke tare na taba maki wani abu ……? Girgiza mashi kai tayi da sauri tana murmushi sannan ta mike …… "To kin gani ……tashi ki sa kayanki ki taho muyi baccin mu ko?ya karashe maganar yana kashe mata ido…… Murmushi tayi ta mike ta koma toilet zata canzo kayan ……dariya yayi a hankali yana mamakin Safeena……Ta canza kamar ba ita ba ta koma wata yarinya …… Tabe baki yayi yana fadin "Dama yarinyarce tunda yaune ta cike 20years dan dai Allah ya mata bakine……" "Me ka ce……?ta fada lokacin da ta fito Murmushi yayi yana fadin "Cewa nayi bacci zanyi tunda kinki fitowa hakanan ……" Yatsina fuska tayi sannan ta hawo gadon tare da kwanciya saman jikinshi …… Kashe hasken yayi ya mayar da ita kasanshi yana kallon yarda take wurga idanu cikin duhu …… "Ba fa haka muke kwanciya ba……"ta fada kamar zatayi kuka A Wahale yace "Ya mu ke to?yana shafa skin dinta "Ni ce ke kwanciya a sama……"ta fada a hankali Dariya ta bashi amma ya danne ya hade bakinsu guri guda yana tsotsa a hankali cikin kwarewa ta yarda bara ta ji zafi ba …… Tun tana mutsu mutsu har tayi lagwas tana karbar sakonshi …… Ba tare da ta sani ba ya rabata da duk wata sutura dake jikinta……hannunshi kam kyarma suke sun kasa tsayawa guri guda…… 【】 Duk yarda Dad din JB ke tunanin abun ya wuce haka dole ya tattaroshi ya maidoshi gida … Babban malami ya saka aka nemo mashi yazo …… Rukiyya ya fara mashi cikin Saa Raliyar tayi magana da kakkausar murya tana fadin irin yan matan da ya yaudara yana lalata masu rayuwa har ya kawo kanta …… Hakuri malamin ya bata,…… amma sae cewa tayi barata hakura ba ta riga ta aureshi…… Da kyar da addu'o'i aka samu ta fita daga jikinshi …… Sae dae alluran da aka dinga mashi sun taba mashi kwalwa ta yarda ya koma kamar wani Dolo… Saboda har miyau yake fita daga bakinshi…… 【】 Sae da asuba sannan Abdulmaleek ya dawo hayyacinshi ……Safeena ya kallah dake gefe tana baccin wahala da kananan hawayen kwance a fuskarta sannan lokaci lokaci takan saki ajiyar zuciya…… Janyota yayi ya rungume yana kwarara mata albarka ,don har ga Allah baiyi tunanin zai sameta budurwa ba idan yayi la'akari da jinyar da tayi …… Sai dae masha Allah cikakkiyar budurwa ya sameta,mai dumbin ni'ima……Godiya yayiwa Allah sannan ya kwantar da ita gefe guda zaya tashi …… Kankameshi tayi sosae tana kuka cikin bacci tana fadin "Bana So Ka Daena dan Allah ……" Lumshe ido yayi tare da hura mata iska a fuskarta ,ai kuwa tayi shiru kamar ruwa ya cita…… A hankali ya zame jikinshi daga rikon da ta mashi ya shiga wanka sannan yayo alwala yazo yayi sallah tare da komawa ya hada mata ruwan wanka ya dawo…… Kunnenta ya dinga tsotsa a hankali har ta bude idanunta ……ganinshi da tayi ya sata saurin mayar da idon ta kulle tare da juya baya …… "Sorry na amshi laifina……"ya fada a hankalin Banza ta mashi kuma dama yasan barata kulashi ba …… Daukarta yayi ya kaita toilet din ya sakata cikin ruwan dumi …… hannunshi ta rike da sauri zata mike ya mayar da ita yana fadin "Sorry……" Tun tana jin Zafin har ta koma jin dadin ruwan…… Sannan ya fita ya barta ……kusan minti talatin ta gasa kanta sannan tayi wankan tsarki tare da alwala da brush ta fito …… Ko kallon inda yake batayi ba…… Murmushi yayi mai sauti yana fadin "Morning Twee ya jiki ……" "Oho……"ta fada a takaice tare da canza kaya tayi sallah…… anan ta kwanta bacci ya kwashe …… Zuwa yayi ya mayar da ita saman gado sannan ya rufeta ya fita ya nema masu abun kalaci…… Ko da ta tashi da kuka ta tashi kamar yarinya haka dinga mashi shagwaba yinin ranar ,gashi duk inda zata sae dae ya goyata…… sannan taki yarda su koma upstair din tunda suka sauko ……… Ya koma kamar wani yaronta nan da can ma bai isa yaje ba sae lallabata yake kamar kwae …… Ranar ya sake tabbatar da wacece Safeena gurin rigima …… Da daddare ma cewa tayi barata kwana a daki ba a falo zata kwanta saman one siter …… "To ……"ya ce mata yana murmushi Sae da tayi bacci sannan ya mayar da ita daki suka kwanta A haka suka cigaba da rayuwarsu gwanin ban sha'awa lallaba yake kamar kwae ya katange mata duk wani bakin ciki ya maye mata da Haske…… sae dae har lokacin bai fada mata aikinshi ba sae dae da safe idan zaije office yaje ya tafi wani guri 【】 Hajiya kam ana can ana renon cikin da ko yaushe take sa ran haihuwarshi …… Aunty Zuby ma an koma ga Allah kullun ana rike da carbi haka Uncle Abbah tunda Aunty Fatee ta rasu ya tattara duk wani iskanci ya aje gefe…… Fadila ma ba laifi tana kokarin kwatantawa sae dae matsalan bata da damar ta rabi mutane sae su dinga kyamarta tare da hatararta wae wari take …… Sae ma ta daina shiga cikin mutanen kwata kwata OGA JB ma an samu lafiya sae dae har lokacin kamar wani dolo zaka ganshi saboda aluran da aka dinga mashi a india …… Duk da an mayar dashi amma a banza saboda kwalwar ta rigaya ta tabu da yawa saboda alluran da aka mashi babu cutar a kwalwarshi…… *8 MONTH……* Girgiza kai yayi kamar ya mata kuka yana fadin "Idan haka masu ciki suke da bala'i ko wallahi mu bani maza……" Kwace wayarshi tayi daga hannunshi tana hararanshi tare da tura mashi abinci tana fadin "Allah sae ka cinyeshi tunda ban aikeka ka ciyo abinci gidan granny ba……" Langwabe kai yayi tare da kwantar da murya yana fadin "Haba Twee dan Allah ki rufa man asiri in ba so kike cikina ya fashe ba……" Karar wayarta ya katse mata maganar da tayi niyar yi ta dauka tana fadin "Besty jiya fa nan kika bar IV din zaki bawa su Hauwa'u da Aisha Sada Raddah ba……" Tabe baki maryam din tayi tana fadin "Ke dallah share wadannan tsamayen me suka iya inba suzo su cinyewa mutane abinci ba……wallahi ko jiya naji ana gulmar zainab din gidansu wae ta kusa takaita Abbansu da shegen ci……" Dariya Safeena tayi tana kallom Abdulmaleek daya aje spoon din ya tallabe kai yana kallonta ta ta watsa mashi harara ……Zatayi magana maryam tace"Kinga kin cikani da magana ban fada maki dalilin kiranki ba ……" "To fada man Bestie……" Kai tsaye tace "Kinyi Sabuwar Uwa ……" "Ban gane ba……" Dariya maryam tayi tana fadin "To hajiya ta haihu gobe ma suna babu wanda suka fada mawa nima makwabtansu na jiyo……" Abdul maleek ta kalla taga har lokacin ita yake kallo ta sakar mashi murmushi tana fadin "Zan kiraki anjima bestie……" Katse wayar tayi sannan ta tallabe kumatunta tana kashe mashi ido ……Shima idon ya kashe mata tare da kanne daya …… Tasowa tayi ta dawo saman cinyarshi tare da sagalo hannayenta a kafadarshi …… "Kace na rufa maka asiri ka koshi ko?ta fada cikin kunnenshi "a'a bara na cinye kawae……"ya fada tare da janyo plate din don ya fahimci akwae abunda suke shiryawa da Maryam din …… Janye plate din tayi tana fadin "Tunda ka koshi kuma ai shikenan tashi mu tafi na baka labari……"ta fada tare da mikewa ta kama hannunshi …… Daki ta ja shi ta kwantar dashi saman gado sannan ta daura kanta saman cikinshi ta kwanta …… "Kasan me ke faruwa?ta fada a shagwabe "Uhumm"shima ya fada yana wasa da kalabarta data sauko…… "Dazu maryam ta kirani wae Hajiya ta haihu……"ta karashe maganar tana dariya "Allah ya raya……"ya fada a hankali "Kuma har gobe suna ……sae ka kaini goben ko? "Uhumm"ya fada Turo baki tayi tana fadin "Bangane Uhumm ba……" "Allah ya baki hakuri me kike so ayi……"ya fada yana fitar da lumfashi a hankali "Ka fada man da yaushe zamu je ……" "Wae Gidan hajiyar……? "Eh mana……" "Daga nan ma kina iya mata addu'a Allah ya raya……" Turo baki tayi kafin tayi magana ya mirginota tare da hade bakinsu guri daya …… Bata ja lokaci ba ta cigaba da mayar mashi da martani cikin kankanin lokaci suka lula duniyar masoya…… *FEEDOHM💞* [8:59PM, 11/19/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹* 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 © *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM💞_* *Devoted to Ummi A'isha👌🏻* *Bestowed to Aunty Sis💕* *59* Sanye take da doguwar riga blue ta shadda wadda taji aikin hannu na pink din zare,rigar ta karbeta sosae ta yarda sai kayi tunanin a jikinta aka dinka ……Cikinta ya fito tsam dashi sae ya kara mata wani kyau na musamman……Wayarta ta dauki ringing a hankali ta kalli gurin ,ganin number Maryam ya sata saurin dagawa tare da sallama "Haba bestie ya tun dazu nake jira naga kin kirani mu tafi suna amma har yanzu shiru ko bara kiyiwa su Aunty Zuby kara bane ……"ta fada tana dariya Dafe kai tayi tana dariya "Oh Bestie bara naje na sameshi naga yana falo kila ya barni don jiya cewa yayi wai gulma zai kaini……" "Ya dai kamata gaskia don ku ya dace ace tun safe kuna gidan ……"ta fada tana dariyar mugunta "Bana son iskanci maryam……" "Allah ya baki hakuri Bestie amma naga matsayinku na jikoki ya akai ace tun safe kuka je……" Dariya ta kwashe tare da yanke wayar ,sannan ta dauki dankwalinta tare da zura plat shoes dinta pink ta fita ,Zaune ta sameshi sanye da jallabiyya fara yana duba wani karamin littafi da taga zane abun shari'a a jiki …… Tabe baki tayi ta isa gurin tana fadin "Mutun sae janye janye……,Ni gaskia na gaji……"ta karashe maganar hade da turo baki…… Dagowa yayi ya na sakar mata wani fitannanen kallo bai taba sanin ciki yana wa mata kyau ba sae a kan Safeenarshi… mika hannu ya janyota ya zaunar da ita bisa cinyarshi ,Hannu ya kai yana shafa gefen wuyanta a hankali sannan ya fara goga hancinshi a bisa wuyanta a hankali yana shakar sanyayyan kamshim dake fitowa daga dukka gabobin jikinta ……Hannun nashi ta rike idonta a lumshe "Yaune fa ake sunan hajiya ……"ta fada kamar an fizgo maganar daga bakinta ,ita kanta dariya ta saki bayan ta fadi maganar …… Manyan idanuwanshi ya zuba mata ba tare da ya kyafta ba kafin ya lumshesu a hankali …… "Kayi shiru ,Dan Allah ka kaini……" ta fadi maganar a shagwabe…… Bude idon yayi tare da sakin murmushi mai sauti "Yeah hakane,kinga ni na manta wallahi kara da kika tuna man amma idan kinje me zakiyo……? Ya karasa maganar tare da kissing wuyanta Dan murmushi tayi wanda iyakarshi a lips dinta ,amma a zuciyarta ba haka bane…… "Zan gano baby……"ta fada tare da kare lafewa jikinshi "To kiyi hakuri idan naki yazo ba sae ki gani ba Twee……?ya fada cikin sigar lallashi "Dan Allah……"ta fada kamar zatayi kuka "Nima dan Allah kiyi hakuri Twee ki zauna gida kin ji ko ……"ya fada cikin sigar lallashi Harara ta balla mashi tare da sakin kukan shagwaba lokaci guda ta mike daga jikinshi tana fadin "Wallahi nima baran sake zuwa asibiti ba………" Hannuwanshi ya hade guri guda ya zuba mata ido tun lokacin da ta fara maganarta har ta kai aya sannan ya saki ja'irin murmushi yana fadin "Allah ya baki hakuri Madam……" Banza ta mashi ta koma ta zauna saman rug tana kallonshi tare da hade kai da guiwa tana kuka a hankali …… Murmushi yayi ya mike ya shiga dakinta ya dauko mata hijab sannan ya dawo ya tsugunna gabanta tare da dago habbarta "Sorry tashi mu je……"ya fada cikin kunnenta…… Juyar da kai tayi tana turo baki tace "Na fasa……" Dariya yayi yana fadin "Yauwa Twee Allah ya maki albarka kinga sae muyi zamammu gida na goyaki ko……" Duka ta kai mashi tana goge hawayenta sannan ta mike ta fizgi hijab din ta saka taje bakin kofa ta tsaya tana hararanshi …… "Kuma kin ce kin fasa Twee……"ya fada cike da zolaya Murguda mashi baki tayi tana fadin "Zan je fa……" Dariya yayi mai sauti tare da dagata sama yana juyawa ……bai ajeta ko ina ba sae cikin mota ……Sannan ya zagaya shima ya shiga ya zauna suka fita…… Maryam ta kira tana fadin "Na fito ki shirya yanzu mu biyo mu daukeki ……amma wallahi bara ki bini hannu biyu ba dole ki nemi Rigar da atampha ki baiwa Kakata……" Kwashewa da dariya sukayi sannan ta kashe wayar tare da kallonshi ta marairaice tana kafta ido tana fadin "Dan Allah muje a sayar wa Mamata riga……" Dariya ta bashi sossae ya tabbata ba hakanan zata gidan ba …… Juyawa sukayi suka siyo kayan yarinya masu kyau set 5 sae atampha Exclusive guda daya tare da swiss shima daya…… Gidansu maryam sukaje ya daukota ……a mota yana jin sai iya shege suke amma yayi banza dasu ……sae dae idan yaji abun nasu yayi yawa ya dago ya sakewa Safeenar harara …… Kuma hakan bara ya sa tayi shiru ba sae dae ta dan turo baki tana hararanshi ta kasa kasa sannan ta cigaba da maganarta…… Yana parking kofar gidan ta juyo tana washe baki tare da pecking kutamunshi tace "Sae dare zaka zo ka daukemu ko ……ko kuma kayi zamanka idan mun tashi ga maryam nan sae mu samu napep ya kaimu ko ……" "Ki shiga ku fito ina jiranku……"Ya fada yana kallon wayarshi…… Zaro ido tayi tana kallonshi sannan tace "Amma ai……" Kallon da ya mata ne ya sata yin shiru tare da saddar da kai kasa…… "Ki je ku gaisa ki fito nace……"ya fada a hankali tare da kallonta…… Idonta ya ciko da kwallah tace "Dan Allah ka barni sae anjima……" Dauke kai yayi daga fuskarta ganin hawayen ya gangaro sannan ya bude baki a hankali yana fadin "Tana jiranki Safeena……" Juyawa tayi ta fita ba tare da ta dauki kayan ba ta fita …… Ta iske maryam har ta shige gidan ta barta …… Wani kululu ya tsaya mata wuya duk shirin da sukayi da maryam ya rushe kenan hawaye taji sun kwace mata ta sa hannu ta share tare da juyowa ta kalleshi tayi gaba …… Kwala mata kira yayi amma ko ta juyo,dauko kayan yayi ya biyota dasu …… Kafin ta shiga gidan ya tareta tare da janyota jikinshi ……Kuka ta saki da karfi tana kokarin janye jikinta……Lallashinta ya fara amma ta ki yin shirun …… Zuciyarshi ta karya ya dubeta a sanyaye yace "Sae daren zaki tafi Safeena……? Gyada mashi kai tayi tana kukan…… "To kiyi hakuri kinji ko……Zuwa daren zan dawo na daukeki amma dan Allah ki kula Safeena bana son wani abu ya taba lafiyarki……" Wani yaro ya kira ya bashi kayan yace ya shiga dasu …… "Take care Twee……"ya fada a hankali tare da pecking goshinta sannan ya juya …… Hakanan ta ji ya bata tausayi ……tayi saurin kamo hannunshi tare da zagayeshi da hannunta …… "Sorry yanzu zan fito mu tafi kaji ko……"ta fada a hankali Dan murmushi yayi yana kallon fadila da ta fito ta tsaya tana kallonsu …… Kusa da kunnenta ya fada mata "Kiyi zamanki kinji ko……babu komae amma ki kula……"ya karashe maganar tare da janyewa daga rikon da ta mashi …… Kallonshi tayi tare da kallon inda taga ya kalla sannan ta juyo tana dan murmushi …… "Mu shiga sae mu fito tare ka ji ……wallahi na fasa zaman tunda bakka so……"ta fada cike da shagwaba tare da zare takalmata ta dage kafar da sauri ta daura saman tashi …… Da sauri ya kalli kafar yana fadin "Menene?me ya samu kafar……? Jujjuyar da kai tayi tana fadin "Kamar an tsireni naji fa……" Dukawa yayi ya daura kafar saman cinyarshi yana dubawa sannan ya dago cike da tausayawa yace "Sorry twee nayi maki addu'a amma banga komae ba……" *FEEDOHM💞* [12:32AM, 11/20/2017] Feedohm💞: : 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹* 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 © *_Haske Writer's Association_* ( _Home of expert & perfect writers_ ) *_NA_* *_FEEDOHM💞_* *Devoted to Ummi A'isha👌🏻* *Bestowed to Aunty Sis💕* *END……* GODIYA TA MUSAMMAN *Haske writer's Asso💡* *Feedohm novella* *Taskar billy galadanci* *Zauren biebie isa* *Duniyar makaranta* *Home of novels* *Pherty novels* *Hajjace novel group* *Ladies worlds* *Exclusive angels* *Novels lgdes* *Asy khaleel novels* *Khadija candy novels* 🤝🤝🤝🤝 *The page is Whisticall to* *Aunty Ummi A'isha😘 Aunty Sis😘My Swt Mum Mizz Zozo😘 Bestie Firdaws😘 Aisha Sada 😘Hauwa'u Sada😘 Salima Sada😘 Jeeddah Aliyu򖁁😘Asiya Usman😘 Meela Adeel😘 Meenarh parrot😘 Hajja ce😘 Pherty😘 Nucy luv😘 Faxy fashion😘 Safiya huguma😘 Billy Ladan😘Queen mermue😘Muneera😘Sawwama😘Hafsat mai sherrif😘Slendid😘 Maman khady😘Aunty maijiddah😘Billy galadanci😘 Sofie Galadanci💧Wadanda ban ambata ba matsayinku na dabanne😘* Murmushi ta masa tare da janye kafar tata daga saman jikinshi "Yanzu zan fito……"ta fada a hankali "Allah ya maki albarka to……"shima ya fada yana murmushi Da Ameen ta amsa sannan ta juya gurin Fadeela da har lokacin ta kasa wucewa …… Kallo daya ta mata ta tausaya mata barema da taje kusa da ita taji kalar warin da take fitarwa …… "Ki Sameni gida ki karbi magani ……"ta fada Hankali Bayanta fadilan ta juya taga ko da wata take amma taga ba kowa…… ,sam batayi tunanin Safeenar zata kalleta da idon rahama ba bare har ta mata magana…… A Sanyaye tace "Nagode Safeena dan Allah kuyi hakuri abun……" Katseta tayi tana fadin "Ya rigaya ya wuce……"Sannan tayi gaba abunta …… A Tsakiyar gadon hajiya ta hango Maryam dauke da jaririyar tana ta dariya wadda su biyu suka san fassaranta …… Kallon Aunty Zuby tayi tana fadin "Ya jikin? Aunty Zubyn ta sunkuyar da kai cike da nadama ta kasa amsa gaisuwar Safeena …… Tabe baki tayi tana fadin "Allah ya kawo sauki……"sannan ta juya tana fadin "Meye sunan babyn ? " *Fateema* ……"Maryam ta fada tana dariya …… Itama dariyar Safeena tayi cike da shakiyanci sannan tace"Duba man da wa take kama……" "Wannan Aunty Zubaida ce ……"cewar Maryam tare da daure fuska …… Haka suka karaci shakiyancinsu babu wanda ya kulasu a ciki ko wane kunya da tsoro ya hanashi tankawa Hajiya ma sadda kai tayi tana kuka sannan suka mike suka fita suka iske Abdulmaleek din…… 【】 Tun da daddare take jin ciwon amma bata fadawa kowa ba har sun fara bacci ta mike zumbur tana kuka …… Maida ita yayi ya danne ya dauka rigima ce kawae ……Sae da yaga abun nata nayine sannan ya mike yana lallashinta …… Ganin kamar zata mutune ya sashi kiran Dr bala wanda ke duba ta ya tambayeshi ko yana asibitinshi …… Dr Balan yace wallahi yana nan General hospital wani aiki yake amma su zo nan sae a dubata …… Ba dan yaso ba ya kaita General din saboda ko kadan bai taba zuwa asibitin ba kuma yana ji, yarda mutane ke kukan ana wulakanta mutane acan don tana ta government …… Suna zuwa Dr Balan yace a shigar da ita labour Room sannan yaja Abdulmaleek din saboda maza basa shiga cikin …… A rude Abdulmaleek din ke tambayarshi ko za'a kula da ita sosaae …… Ce mashi yayi wallahi ba matsala za'a kula da ita bara ya kira Sister Aisha zata fi kula da ita sosaae tunda tana da sauki kai …… Number Sister Aisha a rufe ……Sae yace mashi kar ya damu …… Labour Room…… Tunda aka kai Safeena aka jibe babu wanda ya tabata sae ma nurses din komawa da sukayi suka zauna suna firansu …… Macen dake kusa da gadon Safeenar ce ta zabura ta fado tana ihun neman taimako……Cikin Sisters din wata ta taso a harzuke tana fadim "Ke dallah jakar banxa zaki dingawa mutane ihu kamar diyar arna baki kije islamiyya ba kike son gwada mana ……! Matar cikin magagin nakuda tace "Dan Allah ki taimaka man Sister……" Tsawa ta daka mata "In taimaka makin ubanki kin san baki iya jure azabar haihuwar wane shege ya kaiki ga mijin…Ka gane man yan iskan mata marasa da'a kauyawa dasu zasu ishemu da ihu kamar mu muka masu cikin,Wallahi na fara gajiya da iskancin masu haihuwar na Sister meelah…" Sister meela ta tabe bakinta tana fadin "Keni wallahi shiyasa bana taba ko wace shegiya idan ta haihu don kanta idan ma ta rasu ita ta sani……Haka kawae akwaso maka kazanta kazo kana saka hannunka?ko wane shege da ya tashi haihuwa sae ya kwaso jiki yazo nan don sunga ba'a kashe kudi……" Wani ihu Safeena tayi jin yaron na fitowa tare da silalowa daga saman gadon ta fado kasa … Ai kuwa nurse din ta iso a fusace tare da kifa mata, mari tana fadin "Ji beki banza zaki kashe yaronki a banza a wuhi ……" Yaron ne ya fado kasa tare da mahaifa amma sae da nurse dinnan tayi kusan minti talatin tana zaginta sannan ta yanke mata cibin aka gyara yaron …… Wae kuma saboda masifar rainin wayau sae zuzuta kyawun yaron suke…… Safeena na jinsu har ta samu ta dawo dae dae ……sannan ta kalli ta kusa da ita da har yanzu take yashe a kasan tiles tana birgima babu wanda ya kulata cikin nurse din…… Abdulmaleek aka mikawa yaron bayan an gyara shi…… Huduba ya mashi tare da rungumeshi kamar wani zai kwace mashi yana tambayar Safeena …… Har ta kawo bakin kofa ta wa Nurse din magana ……matsowa Sister tayi tana fadin "Yaronki mai kyau gaskia da alama ke ya biyo……" Dariyar takaici safeenar tayi tana fadin "Ko……? Kafin nurse din ta bata amsa ta dauketa da lafiyayyen mari tana fadin "Marin da kika man ne ina cikin labour Saboda tsabar jahilci da rashi tausayi ……" Baki nurse din ta bude zata yi magana ……Safeena ta sake sauke mata wani marin tana fadin "Wannan kuma na zagin da kika man ne ……Rashin iya aiki kuma ki jira karshen ki banza wawiya……" Ta wuce ta barta sake da baki …… Da hannu daya ya dinga driving yana rike da yaron da hannun daya sannan duk bayan yan seconds zai juya ya kalli Safeena da wani irin fitinannen kallo…… Sae dae kawae ta mashi murmushi tare da kawar da kai…… Suna Isa Gida ya fara kiran mutane yana fada masu …… Cikin yan mintina gida ya cika da yan uwa da abokan arziki…… Shi kanshi sae da yayi nadamar kiran mutanen domin gidan gagaran shi shiga yayi daga baya Safeena ma gaisuwa kadae ke hadasu…… , Ita kanta ranar Suna sae da tayi mamakin kudin da aka kashe tare da tambayar kanta ina Abdulmaleek ya samesu…… Cikin wani hadadden Less Coffee ta hade tayi masifar kyau ta nufi dakinshi jin shigowarshi gidan don tun jiya da safe rabon da ganshi……kuma tana so ta gwado mashi kudin Da Abba ya aiko ayi hidimar suna…… Tun kafin ta shigo yaji kamshin turarenta dan haka ya tsaya bakin kofa …… Dasallama ta shiga yayi saurin janyota tare da rufe kofar yana kissing dinta ……janye jikinta tayi tana hararanshi tare da fadin "Meye haka Abdulmaleek ……? "Love ……"ya fada tare da kashe mata ido Zama tayi bakin gefen gadon ya bita ya tsugunna tare da dafa guiwata yana leken yaron "Kin bani abunda banyi tunani ba Safeena kin mayar da Abba Safeena…kin kawo man wani sauyi na musamman a rayuwa Ina matukar Kaunarki ,Bana jin zanyi amfani indae bana tare da ke safeena ……kece duk Silar wani farincika tunda lokacin da fara ganinki na tabbatar da *ZAN RAYU DAKE* cikin salama…,bana da bakin gode maki sae dae Na maki addu'a ……Ina karama Allah godiya da ya bani ke Safeena samun mace kamarki ba abune mai sauki ba na maki alkawarin *ZAN RAYU DAKE* Cikin ko wane hali don Allah duk runtsi karki barni Safeena……You brighten my day Safeena with the sound of your voice, you bring so much laughter and love, you are everything to me and I was so blessed when Allah sent you here for me I Really Love you……." Lumshe ido tayi tana fadin " Nima *ZAN RAYU DAKAI……* Komai wuya Abdulmaleek kaine ka haska man rayuwata ka soni lokacin da kowa ke guduna ka Rayu dani duk da cutar da nake dauke dani ……bana fatan na butulce maka Abdulmaleek kaine Zuciyar Safeena ko bayan raina zan tafi da zuciya……" Shiru yayi suna kallon juna sannan yace "Sunan dan mu *ABDULMALEEK……* Waro ido tayi tana kallonshi dauke da murmushi sannan ta lumshe su a hakali…… "Kin yi farin ciki……"ya fada tare da kashe mata ido… Gyada kai tayi a hankali tana lumshe idonta…… Mikewa yayi a gabanta tare da daukar yaron ya maidashi saman bed…… Dagota yayi tsaye ya rungumeta sossae jikinshi cikin kunnenta yace "Proove……" Kallon fuskarshi tayi sannan ta saka tongue dinta a bakinshi tana juyawa a hankali cikin salo da kwarewa…… A hankali ta dago idanun su duk sun canza tana kallonshi Murmushi tayi tare da zagaye hannunta jikinshi tana fadin "Abdulmaleek ka kashe kudi da yawa ina ka samoshi……" "Allah ya bani……" "Ba haka ba Dan Allah kar kayi abunda yafi kar……" Katse tayayi "Bai fi karfina ba safeena karki damu ……" ID card dinshi ya fito ya aje mata tare da mata bayani sossae a kanshi …… Dukan wasa ta kai mashi ya kauce yana dariya tare da janyo kunnenta yana rada mata kalamai masu dadin gaske …… *Alhamdulillah* *Alhamdulillah* *Alhamdulillah* Nagode wa Allah da ya bani ikon kamalla wannan littafin kura kuren dake ciki Allah ya yafe mana …… Masoya nagode da dumbin soyayyarku Allah ya albarkaci Rayuwarku gaba daya ……💞💞 Sai kun jini a sabon littafina *ABUN DA KE BOYE……* Sadaukarwa ga mai rabo😹😹 08066598868 *FEEDOHM💞* ********************** ? ************************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************? ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ? ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ? **************************