Compilied By Abubakar Saleh AlQuyraemey Whatsapp Number 08138873799 Visit www.rumbunlabarai.com For More Complete Documents *_Typing✍🏻_* *_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉ _(Hattara matasa)_ *_Bilyn Abdul ce🤙🏻_* *_HASKE WRITES ASSOCIATION_* ```{home of expert and perfect writer's} ``` ( بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ ) Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai. *_ina mai farincikin sake had'uwa daku a sabon littafina akarona goma sha uku, ina rok'on ubangijin al'arshi yabani ikon rubuta abinda zai amfani al'ummar musulmai, yatsare harshena daga fad'ar abinda zai ruguzani nidaku😭🙏🏻._* _ya ubangiji kakai rahama da gafara kabarin masoyina mahaifina, ALLAH ka gafarta masa ka yafe masa da dukkan 'yan uwa musulmai dasuka rigamu kwanta dama.😭🙏🏻_ *I love you so much my dear Abiena.*😭 *_wannan labari ba habaici baneba, bakuma gugar xana baneba, banyi domin kowaba saidan fad'akarwa da tunatarwa, ALLAH yasa afahimceni._* _duk Wanda ya canjamin wani Abu aciki, komin k'ank'antarsa ban yafeba🙅‍♀._ _ALLAH katsareni daga cecekucen social Media🤕._ ____________________ loading... *_Number 1_* ____________________ *_.......NIGERIA_* babbar k'asace katafariya dake yankin nahiyar Africa, itace k'asar datafi kowacce k'asa yawan al'umma da tarin arzik'i a Africa. K'asace data k'unshi yawan k'abilu manya da k'anana. a nazarin masana, sun rairayo manyan k'abilun k'asar ta Nigeria da adadinsu ya haura 400+. Gakuma Addinai daban-daban dasukeda mabiya, saidai Muslim's and Christian's sune sukafi rinjayen mabiya ak'asar. Nageria k'asace dakeda 6angarori guda biyu, wato *_AREWACI DA KUDANCI_*, wannanne yakawo cakud'ewar k'abilunsu awaje d'aya, musamman awasu jihohi na kudancin k'asar da arewaci. saidai akwai wasu manyan k'abilu uku dasuka wawashi kaso mafi yawa nawasu jahohin k'asar. *_"KABILAR HAUSA FULANI"_* Suna da wasu manyan jihohin k'asar dazaka iya samun zallar wannan yare acikinsu, dukkuma girman k'abila tashiga yanki wad'annan jihohin yaren yakan had'iyeta, a wannan ga6arma zan iya cewa yaren Na Hausa Fulani, yacinye mafi yawan k'ananun k'abilu k'asar, Wanda ahalin yanzu sun daina yara yarensu sai dai Hausa, harshen Hausa har manyan k'abilun ma bai bariba, dan bak'aramin k'utse yayiba a yankunan k'asar ta NIGERIA, har wasu sunama iya kallon yaren amatsayin *General language* saboda mamaya dayayma k'asar Nigeria dawasu makwaftan k'asashen k'etare dake jingine da k'asar. *Jihohin:- Kano, katsina, sokoto, gombe.* Jihohine da ainahin yaran Hausa Fulani ke'a ciki. *_KABILAR IGBO_* Shima babban yarene dazai iya bugar k'irji a k'asar yakira kansa mai fad'a Aji, dukda ko Rabin yaren *Hausa fulani* bai kaiba, amma yarene dakeda d'unbin al'umma, saidai yafi k'arfine a yankin kudancin k'asar kawai, a kudancinma awani yanki, amma zaka iya samun wannan k'abila akowanne lungu da sak'o Na k'asar ta Nigeria, saboda yawan kutsa kai dasuke dashi a kowanne yanki na k'asar domin kasuwanci, harma dawasu k'asashen k'etare. *Igbo sunada jihohin:- Anambra, Enugu, Abia, Imo, Ebonyi.* *_K'ABILAR YORUBA_* Yoruba babban yarene ak'asar ta Nigeria shima, Dan zamu iya cewa shima ya mamaye mafi yawan yankin kudancin k'asar, sannan wasu k'ananun yarurruka suna amfani da wannan yare, saboda kusantuwar k'abilunsu da yaren Yoruba, shima yarene mai d'aukeda yawan jama'a, suma babu laifi, sun k'utsa wasu yankuna Na k'asar ta NIGERIA, sannan sun wawashi wani babban yanki mai fad'a aji Na k'asar, Wanda yazama babban birni mai tarihi dasu Kansu yarabawan ke alfahari dashi, Dan k'asar ta Nageria kanta Na tink'aho dashi. *Lagos* *Yoruba sunada jihohin:- kwara, Lagos, Ogun, Ondo, Osun, Oyo, Ekiti, kogi.* _________ Nasan a wannan ga6ar k'ila mai karatu zaiso jin wani d'an 6antare daga tarihin k'asar, hakanne zai bamu damar fahimtar mi labarin littafin *_"SIYASA KO KABILANCI!?"_* yazo mana dashi. Karna jaku da nisa, ga bayani akan Nigeria mu a wani dogon k'arni, bisa ga bayanan masana Dana tattaro, Dan nasan mafiya yawan masu karatu, basuda jimirin bincike ta wannan fannin, alhalin abune mai muhimmanci da yakamata kowanne d'an k'asa yasani. *_NIGERIA AWANI LOKACI._* Turawan Portugal sune wad'anda suka fara harkar kasuwanci a Nigeria, a tashar ruwan dasuka baiwa suna Largo's data Calabar, a k'arni Na 17 zuwa Na 19. Turawa sunringa shigowa da kayayyakin kasuwancinsu suna musayarsu da bayi a wannan lokacin, Wanda shuwagabannin wuraren ne kawai ke mu'amula dasu, kuma suke ribantuwa da kasuwancin nasu. A shekarar 1807 burtaniya ta dakatar da cinikin bayin da akeyi a Nigeria, bayan biyowar yak'e-yak'en mallakar k'asashe, burtaniya takafa wata rindina a Africa ta yamma, a yunk'urin dakatar da cinikin bayi da k'asashen duniya keyi. A shekarar 1884 zuwa 1885 aka gudanarda da wani babban taro a k'asar James, da ake kira da taron Berlin, inda aka kakkasa kasashen Africa zuwa yankuna daban-daban na mulkin mallaka. Bayan taron. burtaniya tasamu yankuna da dama a yammacin Africa, Wanda Nigeriya naciki. Har zuwa wannan lokacin, ikon turawa mulkin mallaka bai k'arasa Arewacin Nigeria ba, yawancin ikonsu ya karkata a kudancin k'asarne, da yankin iko da Legos. A shekarar 1903 turawan sunsami nasarar mamaye Arewacin Nigeria, bayan tafka gumurzu tsakaninsu da sarkin musulmai Attahiru. Turawan mulkin mallaka sun cafke sarakuna kamar sarkin Kano Alu, bayan dayak'i mik'a wuya, inda suka kulleshi a lakwaja. Bayan wannanne kuma turawa suka samu mallakar yankunan biyu da yankin ikko. Shekarar 1914 babban gwamnan jinar Frederick lugard ya had'a yankunan kudu da Arewa aka sakawa k'asar suna. Sunan Nijeriya yasamo Asaline daga kogin neja bayan da a ranar 8 ga watan January Na shekarar 1897, wata 'Yar jarida wadda daga baya Frederick Lugard ya aura, dame flora Louisa Shaw, ta rubuta wata k'asida a jaridar *"The times"* ta England, kancewa yakamata asama k'asar suna Nigeria, wato *"Niger da Area "*, sabili da kogin Neja dayabi ta ta cikin k'asar. Nigeria na makwaftaka da k'asar Benin, ta yammaci Chadi da Cameron, ta gabashi dakuma janhuriyar Nijar da arewaci. Baki d'aya k'asashen da Nigeria ke makwataka dasu France ce ta mulkesu, inbanda arewacin Cameron da burtaniya ta mulka zuwa wani lokaci kafin France ta kar6a. Tundaga wannan lokaci Burtaniya taringa gudanar da mulkin mallaka Wanda keda majalissar dokoki data k'unshi 'yan k'alilan daga cikin 'yan Nigeria. Da tafiya tai tafiya an nad'a wad'ansu 'yan Nigeria dansu shugabanci wasu yankunan k'asar. Wannan yak'ara basu ikon cin gashin kai, sai dai kuma hakan shine ummul aba'isin haifar da rikice-rikicen *ADDINI dana K'ABILANCI* a sassa daban-daban na k'asar ta Nigeria. Bayanda turawa sukaga lamarin yak'ici yak'i cinyewa, sai sukai tunanin sake fasalta k'asar, inda suka kasata zuwa yankuna uku, *k'abilar Hausa fulani* Arewaci, sai *Yoruba* a yammaci, *Igbo* a gabashin k'asar. Kodayake wannan tsarin yaraba 'yan k'asar, to amma kuma kowanne 6angare yasamu k'arfin fad'a aji a yankinsa. Bayanda wad'annan manyan k'abilu uku na Nigeria suka sami karfin mulkar jama'arsu, dandanan sauran k'ananun k'abilun k'asarma suka fara Neman da abasu *'yancin su*, inda akaita rikice-rikice. Domin asamu kwanciyar hankali a shekarar 1954 an cimma wata yarjejeniyar rarraba ikon tafiyarda ayyukan cigaban al'umma da cigaban k'asa, kamar kiwon lafiya, ilimi da dai sauransu, a tsakanin kabilun ko wanne yanki. Itakuwa gwamnatin k'asa ke kulada harkokin tsaro da tattalin arzik'i. Kodayake wannan baikawo k'arshen rikicin ba, har sai da aka kafa wata hukuma 1957 mai suna *Willink minorities commission*, Wanda ta duba k'orafe-k'ofen k'ananun k'abilu a wannan lokacin. A shekarar 1953 Chief Anthony Enahoro ya gabatar da baiwa Nigeria 'yancin kai a shekarar 1957. Sai dai kuma 'yan Arewacin Nigeria basu amince dahakanba, saboda k'arancin kwararrun dazasu tafiyar da harkokin mulki a yankin, dakuma gudun Cewar 'yan kudancin k'asar zasu mamaye harkokin gwamnati. A wannan lokacinne akaita tura 'yan Arewa k'asashen turai musamman England domin yin kwasa-kwasai ta yanda zasu sami ayyukan kamar su akawu da akanta. To domin samin zaman lafiya bisa wannan banbance-banbance ne aka amince da shekarar 1960 da za'a ba Nigeria 'yancin kai. Bayan shafe shekara da shekaru 'yan kishin Nigeriya nata gwagwarmayar kwatowa k'asar 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka na Burtaniya, a k'arshe hak'arsu ta cimma ruwa, inda ranar 1 ga watan October shekarar 1960 Sir Abubakar tafawa 6alewa yazamo prime minister Nigeria na farko ne yakar6i tutar 'yancin k'asar daga hannun governor general sir James Wilson Robertson, wada ya mulki Nigeria daga shekarar 1955-1960. An gudanar da za6en farko a Nigeria, a shekarar 1959, koda yake, jam'iyyar NPC ta Arewa itace tafi samun k'uri'a a za6en, to amma yawan k'uri'ar data sami basu isa ta kafa gwamnati ba, abinda yasata kafa gwamnatin had'in gwuywa tareda jam'iyyar NCNC ta k'abilar Igbo. Bayanda k'asar tasamu 'yancin kai a shekarar 1960 wad'annan jam'iyyu biyune suka kafa gwamnati, inda bisa tsari Sir Ahmadu bello sardaunan sokoto ya kamata ya zama prima minister, amma saiya marawa mataimakinsa baya wato Sir Abubakar tafawa 6alewa, Wanda ya zamo prime minister farko, shikuma Dr. Nmandi Azikwe governor general na farko a Nigeria. A d'ayan 6angaren kuma jam'iyyar action group ko AG ta yarabawa wadda Abafemi Awolowo ya jagoranta ta kasance jam'iyyar adawa. A kwai banbance-banbance addini da al'adu sosai tsakanin hausawan arewaci da Igbo a gabashi da Yoruba a kudancin k'asar. Anyita samun rikice-rikice a gwamnatin had'in gwiwa, Wanda yakai ga rarrabuwar kai tsakanin wad'anda ke cikin gwamnatin. Itama jam'iyyar adawa ta AG ta samu rarrabuwar kai a tsakanin 'ya'yanta inda a shekarar 1962 wani bangaren jam'iyyar *national Democratic party (NNDP)* wadda S.I Akintola ya jagoranta. Rigingimun *SIYASA* sun mamaye gwamnatin wannan lokaci abinda yakai ga kafa yankin yamma ta tsakkiya, wato *Midwestern region* a shekarar 1963 daga cikin yankin yammacin k'asar. Ranar d'aya ga watan October shekarar 1963 ne aka amince da kundin tsarin mulkin k'asar, kuma a wannan lokacinne Nigeria tazama member a k'ungiyar k'asashen renon England ko *Common wealth* kundin tsarin mulkin yasa Nigeria ta koma ga mulkin tarayya dake da shugaban k'asa da mataimakinsa, inda aka za6i Dr Nnamdi Azikiwe a matsayin shugaban tarayya. A shekarar 1963 an gudanar da k'idayar jama'a wadda ya nuna yankin Arewa ne yafi kowanne yanki yawan jama'a a k'asar. Sakamakon k'idayar ya janwo rikici tsakanin yankunan Nigeria, inda jam'iyyar NCNC take ganin anyi hakanne domin kawai aba yankin Arewa k'uri'a mafi yawa a majalissar dokokin k'asar. Bayan da rigingimu sukak'ici sukak'i cinyewa sai sojoji sukayi juyin mulkin farko a ranar 15 ga watan Jenuary shekarar 1966. Dr Nnamdi Azikiwe ; shugaban k'asar Nigeria na farko tsakanin 1963-1966. Sir Abubakar tafawa 6alewa prime minister Nigeria na farko tsakanin 1912-1966. Major general Johnson Thomas Uwunnakwe Aguliyi-ironsi. Shugaban sojan Nijeriya Na farko, ironsi ya kwashe tsawon kwanaki 194 yana k'aragar shugabancin k'asar. General yakubu gawon. General murtala ramat Muhammad. Olusegun obasanjo yayi shugaban k'asar a mulkin soja tsak'anin 13 February 1976 zuwa 1 ga watan October 1979. Yasake zama shugaban k'asar a farar hula a 29 ga mey 1999 zuwa 29 may 2007. Alhaji Shehu Usman Aliyu shagari turakin sokoto, shugaban Nigeria Na farko mai cikakken iko. General Muhammad buhari ya mulki Nigeria daga 31 December 1983 zuwa 27 August 1985. General Ibrahim badamasi babangida IBB, ya mulki Nigeria daga 27 August 1985 zuwa 27 August 1993. Chief Earnest shoneko General Sani abacha, yayi shugaban Nigeria a 1993-1998 General Abdussalam Abubakar, ya mulki k'asar a 9 ga June 1998 zuwa 5 ga may 1999. Alhaji Umaru Musa 'Yar Aduwa, yayi shugaban k'asar daga 29 may 2007 zuwa ranar 5 may 2010. Goodluck ebele Azikiwe Jonathan 2010-2015. Muhammad buhari a yau kuma a mulkin farar hula. ________________ Alhamdullah, wannan shine tarihin k'asarmu ta gado a tak'aice, Wanda keneman k'arin bayani, zai iya kwakwkwaran bincike ga masana, nidai iya abinda ALLAH yabani ikon tattarowa kenan a taskar masanan.😅 *yanzunne labarinmu zai fara kai tsaye*. Plartoar state (jos) Shima jihace data kasance a cikin yankin Arewa, sai dai tanada yawan k'abilu, sannan d'auke take da mabiya addinin Muslim's and Christian's. Wannan yasaka yawan k'abilanci da rikice-rikice a yankin, mafiya yawan rikicin kuma *_SIYASA KO K'ABILANCI!_* ke haddasasu, amma bada wani nisaba saikiga yazama Fad'an *ADDINI*, shiyyasa al'umar wannan yanki ake yawan musu kutse wajen haddasa fad'ace-fad'ace. Jos tana d'aukeda manyan k'abilu kamar haka. Afizere, Afo, Alago, Anaguta, Amo, Ankwel, Bashiri (bashirawa), akwai kuma mafi yawan k'abilar Hausa fulani ma a jihar. *Khadija Isma'il Uba (Amatallah)* Itama tafitone daga wannan k'abila ta Hausa Fulani, wadda sanadin cirani ya tilasta musu maida jihar jos asalin jiharsu ta haihuwa, wadda zasu iya bugar k'irji su kirata k'asar kaka da kakanni.......✍🏻😅👍🏻 *_ALLAH ka gafarma iyayenmu🙏🏻😭_* [1/16, 1:05 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_* *_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡 *_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉ _(Hattara matasa)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* ____________________ *_Number 3_* ____________________ ........Amatallah wai mikike tunani haka? tun d'azun kin saka abinci gaba kina jagwal-gwalasa kink'i kici?. d'ago manyan idanunta tayi tana kallon Amminta, ta janye idanun nata saboda kwalla dasuka ciko, muryarta na rawa tace, "ALLAH Ammi na k'oshine". " Amatallah banason shashanci fa wallahi, mikikaci dakika k'oshin? kofa abincin rana baki masa cin arzik'iba, lauma batafi hud'uba kika ajiyemin kika fita wai kina saurin islamiyya, shine yanzu zaki cemin kin k'oshi kuma........?". "Miya farune kuma?". 'Baban Amatallah dake fitowa daga d'akinsa yay tambayar'. Daga Amatallah har Amminta kallonsa sukayi. Ammin tace, ''abinda kasanine kullum dai, maganar cin abinci". Guntuwar dariya yayi, yak'arasa cikin falon inda Amatallah ke zaune jikin kujera, a kujerar data jingina ya zauna, " haba mamana nikad'ai, ci abincin mana, babufa k'yau zama da yunwa, a haka kikeson zuwa hutun kano gidan Uncle d'in naki kuma?". "Baba zanje, amma ALLAH na k'oshi". 'Tayi maganar tana matso hawayen datake mak'alewa tun d'azun'. " subahanallah mamana, kuka kuma? kinga tashi ki maida abincin kitchen, kizo ga fura dana saya miki lokacin dazan dawo aiki". Murmushi tayi tana share hawayenta, tamik'e da sauri tanufi kitchen da fleet d'in abincin. Binta yayi da kallo yana murmushin shima. Ammi kuma tace, "wallahi kaine ke saka yarinyarnan duk wata ta6arar datakeyi, nidai ina tuna muku halin rayuwa, kuma gidan wani zata". a k'ufule tayi maganar tana shigewa bedroom d'inta. Baba yabita da kallo kawai yana girgiza kai, yasan gaskiya take fad'a masa, to amma bashida za6in daya wuce gatanta tilon d'iyar tasa, wadda tundaga kanta haihuwa tamusu adabo, shekara kusan 19 kenan amma ko 6ari matar tasa bata sake yiba. ajiyar zuciya ya sauke saboda motsin zaman Amatallah akusa dashi. Tace, " baba nad'ako, nagode sosai, ALLAH yak'ara bud'i". "Amin mamana, ALLAH yay miki albarka kinji". ''Amin baba". Hirarsu suke d'anyi itada babanta, dama kullum haka sukeyi, sai dai yau hirar tasha banban data kullum, Dan yau duk akan abinda yafarune d'azun Amatallah take sake tisama baban nata labarin, muryarta kawai zata tabbatar maka har yanzu a tsorace take. Ammi ma fitowa tayi tazauna, har kusan 10:30pm suna hira, kafin su tashi kowa yanufi d'aki yayi shirin barci. Wata sabuwa Amatallah takasa barci, abinda yafaru d'azun yafara dawo mata dalla-dalla, saita ringa ganin su zike tsaye akanta da wuk'a, da sauri ta kunna fitilar d'aki, tashiga kalle-kalle, amma babu komai, duk da haka kasa barcin tayi, sai can cikin dare barci ya figeta. A firgice ta farka ta kwalla wata razananniyar k'ara, saboda mafarkin datayi su zike sunzo har gida zasu kasheta. K'arar tace ta farkar da iyayenta, arazane suka nufo d'akin, tana ganin su tafad'a jikin Amminta tana kuka, jikinta sai rawa yakeyi. Abu kamar wasa k'aramar magana tazama babba, Amatallah takasa barci, takuma hana iyayenta, tun suna d'aukar lamarin wasa har ya fara basu tsoro, Dan Amatallah harda sumanta, kafin asuba kuma zazza6i yama jikinta rijif, maganarta ko fita da k'yau batayi. __________________________ A gaggauce ta taimaka masa ya kimtsa cikin jallabiya Brown mai gajeren hannu, ya d'an fesa turarensa sannan suka sakko falon k'asa, yaran suna zaune suna kallon wani program na yara a wata tashar larabci, duksun maida hankalinsu sosai a tv n. dan har Abbun nasu yak'araso cikin falon basu saniba, jin jina kansa kawai yayi yana kallonsu da murmushi. Matarsa ta ajiye k'aramin kwano mai d'auke da dabino a agabansa, sai ruwa a jug na glass. Kallon dabinon yayi sannan ya kalleta, "no, nifa naci dabino a mota, bani ruwan dai". Ruwan ta tsiyaya a k'aramin Kofi ta mik'a masa, ya kar6a yana mai fad'in " jazakallahu khairan my wify". "Amin Nurrina". Sai da ya shanye tas ya ajiye kofin, yana anbaton " Alhamdullah". Tace, "saura abinci kuma". " okey, had'amin, bara na duba jikin Saifuddeen". Bai jira amsartaba yanufi 6angaran amaryarsa. Tana zaune a falonta, nono take bama Siddiqa, gefenta kuma ga wani yaro zaune yana kuka da Kofi k'arami a hannu, da alama tsaresa tayi dole yake shan abinda ke cikin kofin. Sallamarsa ce tasaka yaron k'ara k'arfin kukansa, itakuma tad'ago kai tana kallonsa da amsa sallamar. Da d'an sauri yak'araso falon, kusada yaron ya zauna, "Saifudden miyafaru kuma da kuka haka? mi kika masa?". A sanyaye tace, " nikam mizan masa dear?, tea kawai nace yasha nabasa magani shinefa yake wannan kukan iskancin, kadai san Saifudden ai". Kar6ar kifin shayin yayi, ya ajiye saman table d'in gabansu, yajawo yaron jikinsa yana ta6a goshinsa da wuyansa, jin zafi zazza6i zau, ya kalleta a k'ufule, "yanzu nan Aneesa kina nufin saima yanzu zaki basa Magani? tun d'azun kin barmin yaro da ciwo ajiki?". " a'a wallahi dear, nabashi Magani tun d'azun, sai dai kasanshi bayason maganin, ina gama bashi yayi amansa, daganan yay barci, Ummansu cema tace nabarsa saiya tashi, kuma tashinsa kenan d'in, amma Dan ALLAH kayi hak'uri". Baice komaiba yafara k'ok'arin cirema yaron rigarsa da wando, ita dai kallonsu take, harya gama ya d'auki yaron yashiga bedroom d'in ta, ajiyar zuciya ta sauke, tacire siddiqa daga jikin nonon saboda tayi barci. Bedroom d'in ta bisu, jin motsin ruwa a bathroom tagane wanka yake masa. Kwantar da siddiqa tashiga k'ok'arin yi. tana zaune a bakin gadon yafito d'aukeda saif daya nad'o a towel. Shima bakin gadon ya zauna nesa da ita, yace, "bani kaya masu kauri". Tashi tayi da sauri ta d'ako kayan sanyi takawo masa. da kansa yasaka masa, ya d'aukesa suka fice batareda yakuma tanka mataba. Binsa kawai tayi da kallo itama. Tasan zaimayi abinda yafi haka, indai akan 'ya'yan sane. A babban falo ya iske Umma uwargidansa ta had'a masa abinci a k'asa kan carpet, zama yayi, ya zaunar da deen kusadashi, kafin ya maida kallonsa kansu Sahib, "Abul-khair kutaso muchi abinci ko. A tare sukace "to Abbu". Umma ta ta6a wuyan Saifudden tana fad'in ''Deen ya jikin? zazza6in ya sauka ko?". Yaron yad'aga kansa yace, " Umma zansha ruwa". "To deeni na". Ruwan tazuba a Kofi sannan tasaka masa abaki, yasha kusan rabi, Abbu yace, " barsa haka, karya cika cikin da ruwa". Batace komaiba ta janye kofin daga bakin Saifudden. tadawo gabansa ta had'a masa abinci Suma yaran haka. Fruits salad yafara sha, idonsa nakan yaransa dakecin abinci a tsanake, babu mai magana, saboda ya kafa musu dokar duk Wanda yake cin abinci yana magana saiya zanesa, shiyyasa ko Ummita k'aramarsu bata surutu in sunacin abin. Ya maida kallonsa kan Umma dake zaune gefe tana canja charnel a TV. "Ku bazaku ci abincin ba?". Murmushi tamasa, kafin tace, "zamuci mana". Bai ce komaiba ya maida kansa ga bowl d'in dayake shan fruita salad d'in. ____________________________ Dole Baban Ama... Sai a gida yayi salla, dan baisan yanda yanayin garin ya kwanaba. Amatallah kam sai gabannin asubahi barci ya d'auketa, ga zazza6i mai zafi daya saukar mata. Bayan sun idar da salla baba ya kalli Ammi dake zaune bayansa kad'an tana azkar, " yakamata ki tada mamana tayi salla saimu tafi asibiti ko?". Kanta ta jinjina masa, sannan ta mik'e. Da taimakon Ammi Amatallah tayi salla, sai rawar sanyi takeyi tana hawaye, manyan idanun nan sunyi luhu-luhu saboda rashin isashen barci, ga kuka datasha. Tana idarwa basu 6ata lokaciba suka nufi asibiti. Alhmdllah garin ya kwana lafiya, saboda 'yan sanda sun kama mafiya yawa daga cikinsu zike. Sun d'an jima a zaune, kafin su sami ganin doctor, saboda halin da Amatallah take ciki doctor ya kwantar dasu za'a mata k'arin ruwa da allurar barci tasamu nutsuwa. _________________________ *_Two days ogo_* Har zuwa yau Amatallah tana hospital, doctor ya rik'esu, saboda firgita da takeyi bata samun isashshen barci, sai dai ayita mata allurar barci. Sosai lamarin yafara tsorata iyayenta, Dan basuyi zaton abin zaiyi tsamari hakaba, duk da sunsan dama Amatallah tanada tsoro sosai, gata da rik'e Abu a zuciya. Ammi taje gida danta watsa ruwa, Baban Ama.. Ne kawai a asibitin, yana zaune kusada gadon da Amatallah ke jinya, hankalinsa nakan waya yana latsawa, da alama wani yake son kira. Amatallah na zaune ta jingina da gadon, dukta rame, sai idanu kwala-kwala, rik'e take da kofi tana shan fura, bata iya cin abinci, daga fura sai tea, duk da dama abincin bai dametaba. Baba yay saurin kara wayar a kunne, kasancewar wanda ya kira ya d'auka. "Assalamu alaika my brother". Daga can aka amsa masa, bayan sun gaisa da tambayar iyaliansu. yace, " ya jikin baba?". Daga can ya amsa da "Alhmdllh my brother, ina my best daughter?". " gatanan a gadon asibiti". "Gadon Asibiti kuma? Miya farune?". " humm, kabari kawai brother, d'iyar takace sai ahankali, sai dai kashigo Mayi maganar, nazata ma wlhy yau zaka shigo mu koma wajen maganin baba". A jiyar zuciya ya sauke daga can yace, "brother ya jikin nata yanzu?". " lah karfa ka tada hankalin ka, da sauk'i Alhmdllh, barama mugama magana nabata kaji, nasan ka da girmama Abu. yanzu yaushe zaka shigo?. "Okey". " kabari kawai, yau nai niyar shigowa wlhy, saboda naga maganin yana aiki, dan kwana biyunnan baba baya Complain d'in ciwon baya sosai, saikuma wani meeting da za'ayi Na kasuwa ya rik'eni, amma babu damuwa insha ALLAH da an gama zan taho, saina kwana kawai". "Kodai ka hak'ura zuwa goben brother? tafiyar dare batada dad'i aii". " no, karka damu, insha ALLAH zanzo da wuri, bazan iya hak'uri banga jikin my best daughter yanda yakeba, batama phone d'in naji muryarta". Murmushi kawai baba yayi yamik'ama Amatallah wayar. kar6a uncle d'inkine. Duk da halin datake ciki sai da tayi d'an murmushi, tanason Uncle M.A a rayuwarta, saboda yanda yake matuk'ar nuna mata kulawa.... Maganarsa ta katse mata tunani. "My best daughter! baki da lafiya amma brother bai fad'a minba? ya jikin naki?". A hankali ta lumshe idanunta, saboda jin dad'in sassanyar muryarsa, tana son muryar uncle d'inta over. tace, " uncle da sauk'i, na warke ai". "Kai my best ban yardaba, kinji muryarki yanda tazama very slowly kuwa?. duk da nasan dama daughter d'ina cool girl ce. anyway koma yaya insha ALLAH yau a jos zan kwana". " Uncle da gaske?". "Insha ALLAH my Darling". " thanks you uncle, please ka tahomin dasu Abul-khair to". "To amma my best daughter school fa? kokin manta gobe akwai? kiyi hak'uri next time insha ALLAH zasuzo miki hutu". Idonta harya tara kwalla tace, " to uncle saika zo, amma ka gaidamin su, hardasu Aunty's da innani da baba dasu anty Nazeefa". " okey, zasuji insha ALLAH, saina zo". Kanta ta gyad'a batareda tayi maganaba ta mik'ama babanta dake kallonta tun d'azun yana murmushi wayar, duk yanajin hirar d'iyar tasa da abokinsa. Kar6a yayi suka cigaba da tattaunawa..........✍🏻 *_Assalamu alaikum_* _please maganar gaskiya a wannan karon bazan turama kowa buk ta PC ba idan nayi nisa, saboda wasu uzurina dana had'a da typing d'in, inkinga kinmin magana kan turomin daga farko ban amsakiba karkiji haushi. idan ba yanzu zaki karantaba, please ki tara, amin afuwa🙏🏻😊._ *Nasa kogi state acikin jihohin Yoruba, wasu suna ganin kamar nayi kuskure.* *akan Sani na rubuta hakan, dukda kogi ba tsagwaron Yoruba bane acikinta, akwai wani yanki Na jihar da Yoruba sukeda yawa kwarai da gaske. shiyyasa kogi tashigo lissfi.* *kogi state tana iyaka da kwara state ne, kwara kuma k'asar Yoruba ne, kunga dolene yarabawa su sami kutsawa cikin kogi state ai, kokuma wasu k'auyikansu su shafi jihar, akwai garin KABBA zamu iya cewa 90% Yoruba ne aciki. So nima bisa binciken masana nake, su sukasan dalilinsu nadaka kogi cikin yankin Yoruba d'in* Wannan shine hujjata, ba kai tsaye nayiba😅👌🏼. (Wad'an da sukamin gyara kuma, kumin afuwa ba gwaleku nayiba, saida nayi bincike nima😊🤝🏻, amma ngd da tunatarwa🥰.) *_ALLAH ka gafartama mahaifanmu🙏🏻😭_* [1/16, 1:05 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_* *_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉ _(Hattara matasa)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_HASKE WRITER'S ASSOCIATION_* ```{Home of expert & perfect writer's}``` *Assalamu alaikum* _nasan zakuyi mamakin fara typing d'ina, so nayi dubu da yanayin buk d'in, dakuma time d'in damuke ciki, idan nace sai new year lokacin zai k'ure saboda sak'on dazan Isar insha ALLAH, kuma za6e yana tunkaromu. sai dai kuma banyi alk'awarin muku typing kullumba gaskiya🙈, ALLAH yasa zaku bani had'inkai._ Love you so much all❤❤😘 ____________________ *_Number 2_* ____________________ .........Matasa ne Kusan su ashirin suka fito daga wani k'aton gida, Wanda kallo d'aya zakamasa kasan mamallakin gidan yagama jik'uwa da Naira. Duk d'insu Matasane da shekarunsu bazasu haura daga talatin zuwa k'asaba. Hayaniyar dasukece taja hankalina Kansu. Wani yadaka tsale yadire yana fad'in "impossible wallahi!!, bamu yarda da wannan shawaranba, a raba kawai abama kowa kasonsa yakama gabansa!!". Wanda alamomi suka nuna shine babbansu yaja birki daga tafiyar dayakeyi, manyan idanunsa dake jajur yashiga juyawa, ransa a 6ace yace, " kaifa zike! Shiyyasa banason harka dakai wallahi, wai kai wakafi iya shegene? dama tun agaban Oga saiwani fa zak'ewa kake, kakama kankafa guy, idan ka kaini bango babu ruwana dawata sanayyarmu ko SIYASAR data had'amu, am telling you saina maka eyane, ka dai sanni aii". A fusace zike ya matso yana hura hanci, "kai gagis karka fad'amin mai d'aci mana, kasanfa bawai zan raga maka baneba, barganin katara wannan sharan yaran naka, dagani harkai Abu d'ayane ya taramu, shine *BANGAR SIYASA*, to kawai tun muna shaida juna karaba mana kud'i da kayan harka kamar yanda Oga yace maka, bamu yarda da wata shawarar sai gobeba, danni da yarana tun yau da daddare zamu fara lik'a posters d'in mai gida. Zuwa dasafe kuma muga tsageran da zai cireta a garinnan." Tsaki gagis yayi, ya fiddo kud'in dami guda daga aljihunsa yana harar zike, Wanda yafara k'ok'arin zaro wuk'a a k'ugunsa, amma ganin gagis ya fiddo kud'in saiya maida wuk'ar yana gyara riga. Tafiya take cikin d'an sauri da sassarfa, saboda hadarin daya gama gauraye garin, yanda sararin samaniya kawai tayi bak'ik'k'irin zai tabbatar maka ruwan yana gab da sakkowa. Wani d'an lungu tabi, dan a ganinta shine zai zame mata shortcut d'in da zataje gida da wuri. Gaban tane yay wata fad'uwa, saboda hango gungun matasan anguwarsu marasa jin magana (su zike), yanda suke hayaniya kawai zai tabbatar maka fad'a sukeyi. jitai kamar takoma da baya, amma babu dama, saboda tazo gab dasu, wasu kuma sun ganta. Ta kuma yin k'asa da kanta tana karanta *"Hasbinallahu wa ni'imal wakil"* a zuciyarta. Harta giftasu babu wanda ya tanka mata acikinsu, saboda hankalinsu nakan kud'in dake hannun gagis yana irgawa, ga kuma kwali Wanda batasan komiye acikiba dake hannun wani. Ta kusa k'ure lungun taji sun saki ihu gaba d'ayansu, waigowa tayi dantaga miya sakasu ihun......? A razane tazaro ido waje, dan ganin gagis kwance a k'asa wanwar, gawani a kansa yana zare wuk'a daga cikinsa. Tamkar Amatallah zata suma dan firgici, ta kwasa da gudu tareda sakin jakkar makarantar ta a wajen, dama daga islamiyya take. Gudu take iya k'arfinta, ga ruwa yafara sauka, gakuma duhun magriba data kawo jiki. Ta gaban majalissar wasu dattijai tabi zata wuce, yawancinsu duk abokan baban tane ma, Baban natama nanne wajen hirarsa, majalissar tasu rumface, shiyyasa duk da ruwan da aka fara suna a wajen, saima shirin sallar magriba dasukeyi, wad'anda kuma basa sallan suna zaune kan tabarmar dake wajen, wasu kuma saman kujerun plastics. A guje tashigo rumfar tana kwala kiran babana! Sun kasheshi, wlhy sun kasheshi....... Tun shigowarta duk suka mik'e tsaye, harda masu alwala, Wanda ke kusada ita yarik'o hannunta, danya fuskanci a rikice take. "K! Amatallah nutsu kifad'a mana miya farune?". "Uncle wallahi agabana suka kasheshi, na rantse nagansu da idona". sai kuma tafashe da kuka, jikinta sai rawa yakeyi. Sukam su zike, gagis ne yakasa kud'in uku, yabama zike da yaransa kashi d'aya, kayan mayenma dake cikin kwali kad'an ya d'ibo. Da sauri Zike yace, " miye kake nufi?". Gagis yace, "abinda kagani, wannan shine Rabon naku, nikuma sauran nida yarana, tunda mun fiku yawa, kuma munfiku iya aiki, shi Kansas Oga baisan kud'in k'ananun kwari bane shiyyasa ya had'amu aiki daku, amma gobe zan masa bayani.... Kafin gagis ya k'arasa maganar wani acikin yaran zike ya caka masa wuk'a, yana ''fad'in aiko zaka fad'a inka mutu". duk sunga Amatallah wannan yasa koda takwaso da gudu wasu suka biyota. Suna ganin tashiga majalissar dattijan nan sukaja birki, basu k'arasoba. 'Daya a cikinsu yace, " o shit!! Banzan yarinyar can fa a gabanta K show yakashe gagis, yanzu yazamuyi kenan? Karta tona mana asiri fa". Wanda ke kusada shi yaja gajeren tsaki, cikin fusata yace, "ta fad'a mana stupid girl kawai, magana d'aya ce, kawai kowa ya kwanta da shirinsa, dan tabbas komai zai iya faruwa..... Bai kai k'arshen maganarba ya hango abokansu guys Na gudu, hakan ya tabbatar musu fad'a ya kaure tsakanin dabarsu da yaran gagis. Basu jira komaiba suma suka kwasa da gudu. Amatallah kam tana kuka tana bama su babanta daya k'araso wajen yanzu dan yin sallar magriba labarin abinda tagani. Duk d'insu sun razana. Kafin su sami damar magana suka hango mutane Na gudu. a take suma suka tarwatse, Baban Ama... Yaja hannunta suma suka bar wajen, suka nufi gida dan Neman tsira. * A tsorace Ammi da ke alwala tad'ago tana kallon Amatallah da babanta. "Lafiya kuwa baban Ama...?". " da sauk'i dai kam....... a ta k'aice yabata labarin abin da yafaru". Ta zaro manyan idanunta da Amatallah ta gada awajenta, tana sallallami da tafa hannaye, jiki a sanyaye tace, ''to ALLAH ka sauk'ak'a mana ". Amatallah da babanta sukace amin. Sallar da baban Ama... Bai fitaba kenan, sai a gida yaja iyalansa jam'i. __________________________ *KANO STATE* Kallo d'aya zaka masa ka tabbatar a gajiye yake Driven d'in, a hankali ya furta "ya sallam". saboda go slow d'in daya hango agabansa, ya sauke ajiyar zuciya, tareda yamutse fuskarsa mai cikeda kwarjini, a gogonsa ya kalla dake d'aure a tsintsiyar hannunsa Na haggu, ya dafe goshinsa dan ganin yanda lokacin sallar magriba ya gabato sosai. Gaba d'aya ransa a 6ace yake, dayasan zai gamu da go slow d'inan daya hak'ura yayi salla kafin ya taho..... Tunanin sane yakatse saboda Ringing da wayarsa tafara. batareda ya d'aukaba ya kai dubansa kan screen d'in wayar. My wife tee.. Yagani 6aro-6aro yana yawo a fuskar wayar, ya d'an furzo iska kad'an daga bakinsa. d'aukar wayar yayi yana k'ok'arin kiranta sai kuma takuma kira. Koda ya d'aga saiya saka Hans free, muryarsa mai matuk'ar sanyi da nutsuwa yace, " Assalamu allaiki Ummu Abul-khair". "Wa'alaikassalam Nurrina, lafiya kuwa har yanzu baka shigoba? ko ka manta kana azumi ne?". Murmushin sa ya saki mai k'ayatarwa, ya kai hannu yana shafa gemunsa daya k'awatu da bak'in gashi dakuma fari d'ai-d'ai (furfura). "Ban manta ba My tee.., wlhy go slow ne ya rik'eni, gashi har an shiga sallah". Ya karashe maganar cikin 6acin rai. A san yaye tace, " sorry Nurri, ALLAH ya kawoka lafiya to". "Amin nagode, su Abul-khair fa? Kundai turasu masallaci ko?". " eh sun tafi shida Sahib". "Saifuddin fa?". " bayajin dad'i, koma islamiyya bai jeba". "Amma shine bata fad'a min ba?". Har zata bashi amsa saiya katseta, " kinga ina zuwa, naga motocin sun ragu". 'Bai jira cewartaba ya yanke wayar'. Motar yay ma key yay gaba, saboda hanya data bud'e, dama dai wani abunne ya haddasa go slow d'in. Cikin mintunan dabasufi 30 ba ya k'araso gida, a k'ofar gida yay parking, yafito yay alwala a nan massalacin k'ofar gidansa, hankalinsa duk yana kan sallar magriba data wucesa, a gaggauce ya gaisa da mutanene dake k'ofar massalacin zaune suna jiran kiran sallar isha'i, ya shige yay sallar magriba, ya idar babu dad'ewa akayi isha'i. Bayan an idar ya tsaya gaisuwa da jama'a makwafta sannan yakoma mota, horn yayi sau biyu. Kusan mintuna 5, aka bud'e gate d'in. bayan ya shige ta maida gate d'in ta rufe. Sannan ta k'araso wajen motar tasa. Yana zaune har yanzu a ciki, wayoyinsa yake k'ok'arin sakawa a aljihu, ta bud'e motar tana fad'in ''sannu da zuwa". "Yauwa Uwargida na, ya gidan?". "Lafiya lau yake". K'o k'arin fitowar dayake yasata matsawa baya, ya fito idonsa akanta, kwalliyar tata tamasa k'yau, haka kullum matan nasa suke cikin kwalliya, kowa burinta tazama gwana awajensa. Murmushi yamata yana kashe ido d'aya, cikin sassanyar muryarsa yace, " kinyi k'yau my tee...". Itama murmushin tamasa, kafin tace, "thanks you Nurrina". Kansa ya jinjina mata, "da akwai kaya a backseat ki d'ebo su". "Okey". Yara ukune suka fito da gudunsu suna fad'in "oyoyo abbunmu!!". Murmushi yasaki, har fararen hakwaransa Na bayyana, idonsa akan yaran nasa, ya bud'e masu hannayen sa, hakanne yabama babbar rigarsa ta blue black d'in shadda bud'ewa. gaba d'ayansu suka shige ciki, ya had'asu ya rungume shima yana fad'in " oyoyo my children's, I Miss you all". Matarsa data gama kwaso ledojin dake kujerar baya tatsaya tana kallonsu fuskarta d'auke da murmushi. Tace, "oya to a sakeshi ko yagaji, kumuje ciki". Sakinsa sukayi su duka, yakama hannun Sahib da Ummita, Abul-khair mai d'an wayon ya kar6i wasu daga cikin ledojin hannun mamansa, suka nufi hanyar k'ofar babban falon gidan. Sahib da Ummita kam sai zabga masa labarin school sukeyi, murmushi kawai yakeyi. Da sallama suka shigo falon, nanma wata matar nagani tsaye a falon, hannunta rik'eda yarinya dake kunshe cikin kayan sanyi. Wannan ya tabbatar min cewa matansa biyu😊. Fuskarta d'auke da murmushi ta k'araso inda suke tana masa sannu da zuwa. Amsawa yayi shima yana murmushin da k'arema amaryar tasa kallo cikin jin dad'i, dan itama cikin kwalliyar take mai d'aukar hankali. (A raina nace, ''wannan ai sai a gaza gane mai girki🤥🤔"). Hannu ya mik'a mata alamun tabasa babyn hannunta. Ta saka masa babyn dabazata wuce 3month ba a hannun nasa. "O, my Siddiqa barci kikeyi?". Yay maganar a hankali yana sumbatar goshin yarinyar. Sannan ya mik'a mata ita, " bara naje Na d'an watsa ruwa Neesa!". Cikin salon kissa tace, "okey Dear". Harya fara tafiya saiya tsaya, ya juyo yana kallonta, " Saifudden fa?". "Jimm tayi alamar tsoro, ta kauda idonta daga kansa tace, " yana barci". "Barci? A wannan time d'in? Halan lafiya?". Yanzunma a cikin jimamin tace, " bashida lafiya". "Shine kika kasa kirana ki sanar min?". bai jira amsarta ba yafara hawa matattakalar benen dake tsakkiyar falon, dama tuni yaran mamansu tajasu sunyi 6angaren ta. Kamar zata fasa kuka tabishi da kallo, tasan haushi yaji, Dan mijin nasu bai had'a matsalar 'ya'yansa data kowaba, yanason yaransa sosai, kodan yadad'e bai samu haihuwarba ne? Oho. Jiki a sanyaye tashige nata 6angaren itama. Tun daga falon k'amshi mai dad'i yabugi hancinsa, ya shak'a ya lumshe idanunsa, babbar rigarsa yafara k'ok'arin cirewa, ta k'araso da sauri ta taimaka masa suka cire tare. Cikin kashe murya tace, " da kanka Nurrina? ". Murmushi kawai yay yana shigewa bedroom d'insa. da sauri ta d'auki babbar rigar tabi bayansa domin taimaka masa yayi wanka...............✍🏻 *_ya rabbi ka gafartama mahaifanmu 😭🙏🏻_* [1/16, 1:05 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_* *_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡 _{home of expert and perfect writer's}_ *_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉ _(Hattara matasa)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* ____________________ *_Number 6_* ____________________ Baban Ama.. ne ya kalli uncle M.A dake zaune gefenshi bayan sun kalla cin abinci, hankalinsa ya maida gaba d'aya agareshi. "Brother ina saurarenka". Uncle M.A ya d'an gyara zamansa, kafin yay gyaran murya kad'an. "hugm!, brother kasan mi nake tunani kuwa? Akwai wani Abu kusan 1year data shige daya d'aga hankalina, dawo da maganar bashida wata ma'ana, amma yanda rikicin ya kasancene yata6a zuciyata. matasan k'asarnan sunada buk'atar mai jagorancin tunaninsu, saboda duk wani Abu da zaije yadawo akansu yake k'arewa, dasu ake amfanin wajen haddasa duk wani rikicin SIYASA KO K'ABILANCI da ADDINI a k'asar nan, sannan kuma sune akafi kashewa, su akafi lalatama rayuwa. (kuma kullum sune cikin k'orafin gwamnati batayi dasu). Al'halin sune suka maida darajarsu can k'asa har kowacce gwamnati idan tazo take tunin k'ask'antar dasu, ni aganina matasanmu sunada hanya mafi sauk'i dazasu jagoranci k'asarnan brother, amma bata hanyar rikicin siyasa ko k'abilanci ko 6angaranci ko fad'an addiniba.......". "Hakane brother, amma tayaya kai kake ganin zasu fahimci manufarmu, kafa tuna cewa matasan namu, ba kowan nensu ke maida hankali akan karatu ba, idanma sunyi sai domin aiki, ta wacce hanya kake ganin yakamata su fahimci sune k'asar?". Murmushi uncle M.A yayi, "yauwa brother anzo wajen, wannan tambayar nakeso kamin dama". " bara kaji brother, tunfa farko mu SIYASA bata kar6i Africa ba gaba d'aya, wlhy sanadin SIYASA komai namu ya LALACE, da bamusan k'abilanciba, saboda kowa yana a 6angarensa, idan kaga d'an wancan k'abila cikin waccan to harkar kasuwancice ta kaisa. amma tundaga lokacin da Turawa sukace ga SIYASA komai namu ya canja salonsa, tundaga lokacinda turawan mulkin mallaka suka bama wasu 'yan k'asarnan shugabancin wasu yankunan kasarnan komai yafara dagulewa, domin hakanne yazama ummul aba'isin haifar mana da rikice-rikicen ADDINI DA K'ABILANCI a sassa daban-daban na k'asar nan, sannan sukazo suka kuma fasaltamu a yankuna kashi uku, yankin HAUSA FULANI, YORUBA, IGBO, wannanma ya taka rawar gani wajen raba kawunanmu. wannan suna d'aya daga tushen matsalolinmu a NIGERIA, Dan sune suke jagorancin duk wani rikicin siyasa ko K'abilanci har yanzun a k'asarmu wlhy, wad'anda suka fara suntafi sunbar baya da k'ura, har kuma yanzun mun rasa samun nagartattun dazasu kawoma k'asar gyara, saima komai dayake k'ara ta6ar6arewa da lalacewa a kullum, daga talakawan har masu mulkin kowa yana buk'atar gyara Kansa da ahalinsa ma farko, to amma baikamata mu maidasu hujjar farko dazata hallakamuba ai. Abubuwa dayawa sun faru a k'asar nan, Wanda maimatasu bashida wani amfani, dan kamar k'ara dagula komaine, a yanzu hanyar gyara kawai yakamata mu fuskanta, shine zai zama NEXT LEVEL namu." Sai baba😜, ammafa inji bilyn Abdul😂. Dariya sukayi suduka, wadda nikaina bansan dalilin taba. Baban Ama yace, "to minene shirinka a next level brother?". " kafa *KUNGIYAR MATASA* domin nusar dasu illar rikicin *SIYASA KO K'ABILANCI, FA'DAN 6ANGARANCI KO ADDINI*, yakamata mu fiddo hanya ta wayarma matasanmu kai dansu san k'alubalen dake tare dasu, sannan suma sufito adama dasu a k'asarsu, kamar yanda sauran k'ashen duniya keyi, duba tsarin CHINA, abin birgewa, mafi yawa matasan sune akan madafun iko, akwai k'asashe daban-daban dasuke cikin wannan tsarin, Amma mufa Africa son mulki yahana mu bama matasan dama, sukuma matasanma idan zakayi dubi tawani 6angaren saika gane basu cancanci madafun ikonba, saboda rashin nutsuwarsu da sanin muhimmancin Kansu. to amatsayinmu Na matasa tayaya zamu kawo CANGI a wannan tafiyar? yanda za'a fuskanci mumafa 'yan k'asane NAGARTATTATU kuma ababen ALFAHARIN al'ummar k'asarmu da yankunanmu, kaga dolene saimun sami had'inkan matasanmu Na KUDANCI DA AREWACI kenan". sai dai inda gizo ke sak'ar tayaya zamu samu hakan ta kasance?, matasan su fahimcemu sukuma k'aunaci Kansu, dan maganar gaskiya SIYASA DA K'ABILANCI tuni sun rarraba kanmu a k'asarnan dama Africa baki d'aya". Baban Ama yasaki ajiyar zuciya kafin yace, "hanya d'ayace brother nake gani". " wace hanyace brother? ". cewar uncle M.A. " masu taimakonmu brother, bawai 'yan yima dukiyar k'asa babakere da handamaba, nidai nabaka goyon baya 100%, saimu fara Neman wad'anda tafiyarmu zatai dai-dai da tsarinsu, kamar mutum 8 ni da kai cikon Na goma, daganan komaima saiya biyo baya". Uncle M.A yarasama mizaiyi saboda Nuna jin dad'in goyon bayan abokin nasa, sai kawai ya rungumeshi yana jero adu'oin fatan alkairi agaresa, shima Baban Ama addu'ar yake masa. Acewarsa shiyadace da wannan addu'ar, tunda shiya k'irk'iro cigaban, Wanda duk da yasan zasu fuskanci k'alubale iri-iri, saboda aikine bamai sauk'iba, musamman idan akayi dubi da yanda k'asar tagama lalacewa ta 6angarori daban-daban Na Siyasa da k'abilanci da Addini, dukda yana hango nasara wataran insha ALLAH. haka sukaita tattauna batun, har aka kira sallar magriba, alwala sukayi suka fita massalaci. _______________________________ "Wai oga wuk'armi kaketa faman wasawane haka kuma tun d'azun?". Jajayen idanunsa yad'ago yana kallonsa, yasa bayan hannunsa ya shafi gefen hancinsa, fuskarsa ata6e tamkar yaga mala'ikin mutuwa akansa, d'auke idonsa yayi yamaida kan madai-daiciyar wuk'arsa maikamada *fad'ama jini nawuce* saboda tsabar d'aukar ido datakeyi Na kaifi, amma dukda haka kaifin baimasaba yake sake wasata. K show bai daddaraba yakuma maimaita tambayar ga Zike. Wani banzan kallo yamasa, sannan ya tofar da yawu, da yare yace, "aikin daka 6ata zaka koma ka gyara, inba hakaba hummm....". Yay shiru batareda ya k'arasaba. K show ya hura hanci gaba, amma baice komaiba. Su manu duk suna tsaye ake wannan dramar, amma basuji mi zike yafad'ama k show ba, saboda da yare yay maganar, k show da zike kuma yarensu d'ayane. Ramzaki dake zaune gefe yana busa taba yajuyo yana kallonsu, cikin harshen turanci yace, Oga sir dangin waccan babynfa? Inason abani kwangilarsu, dama nadad'e inajin haushin old man d'inta, dan nata6a zuwa k'ofar gidan wajen babynnan amma ya koreni, wai shi ba mahaukaci bane dazai had'a jini dani, kasanfa hausawannan akwai shegen k'abilanci da nuna addininsu yafi Na kowa...... Da Sauri manu ya tsaidashi, " kai! Kai Ramzaki, please kama kankafa, karda tabarka tagayamaka hauka ka rainamin yare, kai k'abilar taka basama mutane k'abilanci ne? 'yan kad'an daku sai shegen gadara, wama yasan da k'abilar takune? Iyakarta jos fa, wlhy yanzu zamu kwashi 'yan kallo a wajenan........ Shima katseshin yayi, tareda mik'ewa da sauri yaje yadaki kafad'ar manu, "to kozaka gwadane?". Yay maganar yana hankad'a manu baya. Shima manu duka ya kai masa. Kafin kace me fad'a ya hark'ume, da k'yar sauran matasan suka rabasu. Zike Na zaune yana jinsu, ko kallo basu isheshiba, wuk'arsa yake wasawa har yanzun. K'ala baice dasuba kuma yamik'e ya tura wuk'ar gefen cikinsa, ya gyara rigarsa yay gaba abinsa yabarsu. Da sauri wasunsu suka bi bayansa, akabar manu da ramzaki a wajen, harar juna sukayi kafin subi bayansu sunajan tsaki was juna, kowanne na zage-zage da yarensa. (Nidai bilyn ku nace, " ALLAH ya k'yauta to".) 🚶🏻‍♀da sauri nabi bayansu Dan ganema idona ina zasuje kuma😨?. ______________________________ Zaune take akan abin salla, tunda ta idar da sallar isha'i bata tashiba, Ammi Na zaune akan d'aya daga kujerun plastic namasu jiyyasa. tunkan su shigo k'amshin turarensa yayo gaba. K'irjintane yafara bugawa da sauri-sauri kamar yanda yakeyi koyaushe, hannu tasa ta dafe tana mamakin wannan lamari, aranta tace, miye ma'anar hakan ni Khadija?..... Sassanyar muryarsace ta tadaki kunnenta. Ammi ta amsa sallamarsa tana mik'ewa, tareda musu sannu da zuwa. Shikad'ai ya amsa, Dan Baban Ama waya yakeyi. Ta gefen ido Amatallah ta ke satar kallonsa, ya canja kaya zuwa fara tas d'in jallabiya mai dogon hannu, sai bak'in wando daya lek'o kad'an da silifas d'in babanta a k'afarsa. Kujerar da Ammi ta tashi ta tura masa, ya ajiye ledojin hannunsa kafin ya zauna yana fad'in "sorry madam mun barku Ku kad'ai ko?". " lah babu komai wlhy, kaida kasha hanya ma, kamata yay kayi kwanciyarka ka huta basai kadawoba". Kafin yabata amsa Baban Ama yagama wayar. matsowa yayi inda suke yana dariya, kibari kawai, babu yanda banyi dashiba ya zauna yak'i, wai saiyaga mamana". Yay maganar yana kallon direction d'in da Amatallah ke zaune. duk tana jinsu, saita k'irk'iri addu'ar k'arya, bayan kuma tadad'e da idar da salla. shafawa tayi sannan tataso, kanta a k'asa ta rissina tana gaishesu. Atare suka amsa da tambayarta ya k'arfin jiki?. tace, "Alhmdllh". Uncle M.A yace, ''My best daughter kinci abinci kuwa?". Da sauri ta d'aga masa kai alamar eh taci. Hararta Ammi tayi, " k'arya dai babu k'yau Amatallah, yaushe kikaci abincin?". Kanta tad'ago ta kalli Ammi, idonta taf da kwalla tace, "kai Ammi". " kai Ammin uwar mi?, tashimin anan kafin na bigeki ak'ara miki kwanaki a asibitinnan". Da sauri Amatallah ta haye gadon datake jiyya. Uncle M.A yace, "madam inafa jin kunyarki, naga kin tasomin d'iya a gaba". " haka kullum takeyi wlhy brother, nafad'a mata rashin cin abinci halittane, harma ina mata misali dakai, amma bata d'agama mamana k'afa ko kad'an. Uncle M.A ya kalli Ammi yana murmushi, sorry madam, rashin cin abinci halittace, haka kusan koda yaushe innani kemin, sai dai in baba Na kusa ya kareni ko Maijidda, yanzu haka matsalar kenan nidasu Fateema, kowacce da irin tunaninta, nifa har asibiti innani takaini ina yaro ban mantawa wlhy, wai likita ya dubani banacin abinci, kowani ciwone dani?. Dariya sukayi gaba d'aya, harda Amatallah datayi murmushi tana satar kallon uncle M.A d'in. sun d'an ta6a hira, harya kira Fateema da Aneesa suka gaisa da Amatallah da Amminta, amma kowacce badan ranta yasoba, musamman Aneesa dakejin zafin Amatallah sosai, (koda yake halintane, tanada zafin kishi, akan Alhaji Muhammad d'in😄, saboda auren soyayya sukayi). Sai wajen tara suka tafi da k'yar, akabar Ammi da Amatallah. dukda baba Ama Na fargabar barinsu su kad'ai, saboda halin da Amatallah ke kwana aciki, gefe kuma yanajin kunyar barin abokinsa ya kwana shika d'ai, haka dai suka tafi yana addu'ar ALLAH yasa su kwana lfy..........✍🏻 *_masoya, INA alfahari daku over wlhy_*💃🏻💃🏻 One Luv my fan's🥰 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [1/16, 1:05 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_* *_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡 _(home of expert and perfect writer's)_ *_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉ _(Hattara matasa)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* ____________________ *_Number 4_* ____________________ ........"Haba dan yanzu Ku kun k'yauta kenan? har a kama su zike kusan 2days amma babu Wanda ya sanarmin acikinku?". "To yanzu da ace shi gagis ya mutu fa? Kenan bazaku sanarminba? Kunsanfa yarannan sunada maruk'ar amfani a garemu yanzu, dolene komai k'ank'antar Abu mu tsaya musu....". " sorry sir!, muma bamuji zancenba sai d'azun wani acikinsu Daba'a kamaba yazo yafad'a mana". "Yaza'ayi ku sani kuwa? tunda bakwa maida hankali wajen kula da aikinku. yanzu ina gagis yake?". " sir! Yana asibiti kwance, sukuma su zike suna police station." "Mtsoww!!, aikin banza kawai, yanzu saiku shirya muje mu kar6o su zike, dan sunada matuk'ar amfani a tafiyarmu. Shikuma gagis zuwa gobe sai wasu acikinku suje su dubashi a asibiti". " okey sir!. _(Nace, "hummm, hattara matasa, kun gadai halin 'yan siyasar k'asar tamu, wannan d'an takarar bata gagis dake kwance a gadon asibiti yakeba, a'a, tasu zike yakeyi, dansu sunada lafiyar dazaiyi amfani dasu, shiyyasa zaije da kansa ya kar6osu a hannun police, amma gagis, zai tura wasune daga mutanensa su duboshi, tunda shi bashida amfani agareshi a halin yanzu. to wlhy haka kuke a wajensu, sai zaku musu amfanine suke kulaku, idan kuma rashin lafiya ko wani tsautsayi ya sameku basuda matsala daku🤷🏽‍, bare kuma idan sun d'ane kujerar💺 dasuke nema🤦‍♀)._ _____________________________ "Dear amma dakayi hak'uri da tafiyar nan sai da safe idan ALLAH ya kaimu mana". d'ago idanunsa yayi yana kallonta da murmushi, saboda yanda tayi maganar. cikin tsokana yace " my Neesa kodai bakison kwananki ya gudune?". Hannu tasa ta rufe fuskarta tana 'Yar dariya, "kai my dear! Nidai ALLAH bance haka ba, ai nasan maganin baba zaka amsone". "Tom shikenan my Sweet Neesa, amma ba maganin babane kawai yasani tafiyar yammarba gaskiya, dan Alhmdllh jikin baba da sauk'i, bakamar wata d'aya daya shige ba. Amatallah ce batada lafiya, suna asibiti ma an kwantar dasu". Tuni fara'ar fuskarta ta ragu, babu yabo babu fallasa tace, " ALLAH yabata lafiya". Daganan tamik'e ta hau had'a masa kayansa. Binta yayi da kallo kawai, yad'an girgiza kansa yana murmushi, baisan miyasa dukkan matan nasa suke nuna kishi akan Amatallah ba?, bayan sunsan jinjinar alak'ar dake tsakaninsa da mahaifin yarinyar, sun kuma san babu yanda za'ayi ya iya auren Amatallah, danshi matsayin d'iyarsa yake kallonta, bai ta6a banbanta matsayin Amatallah dasu Abul-khair ba. Sai dai kuma matansa sun gaza gane hakan, ayanzu haka suduka insunga Amatallah d'in bazasu iya ganetaba, saboda tadad'e batazo kano ba. A baya basu nuna kishin Amatallah d'in, amma tun zuwan dayayi jos sati 4 daya wuce kar6o maganin baba, saiya d'auki pictures d'in Amatallah a wayar babanta (abokinsa), shikam harga ALLAH bada wata manufa yayi hakanba, shiyyasa daya dawo yanuna musu hoton dansuga yanda tak'ara girma, shima kusan 3years bai gantaba, suna ganin hotunan suka canja fuska. tundaga lokacin ko maganarta yayi saisun nuna jin haushinsu, yarasa miyasa suke hakan shikam?....... Ta6asa datayine yasashi dawowa hayyacinsa, har yanzu bata saki fuskaba tace, ''gasu Na had'a". Mik'ewa yayi yana fad'in ''to sannu da k'ok'ari, ya d'auki sauran abin dazai buk'ata da tsarabar daya yoma Amatallah yasaka a madaidaiciyar bag d'in data had'a masa kayan. Jakar ya d'auka, yad'ago yana kallonta, tsaye take jikin mirror, tayi kicin-kicin da face, ahankali yatako gabanta, yad'an murmusa kafin ya rungumeta a jikinsa, acikin kunne yaymata rad'a, sannan ya sumbaci la66anta da goshinta yana fad'in "saina dawo". Duk da maganarsa tasaka zuciyarta yin sanyi, amma saita gimtse, batace komaiba tabiyo bayansa, jakar takar6a suka sakko k'asa tare. Babu kowa a falon, yara duk suntafi school. Kallonta yayi yace, ''bara nayi sallama da Fateema". Kauda kanta tayi daga kallonsa, batace komaiba. Gaba yay abinsa, zuciyarsa Na mamakin kishi irin na mata. komin k'ank'antar Abu sai sun nuna kishi akansa, musamman Aneesa tafi fatima kishi. A Falo ya tadda Uwargidan tashi zaune tana kallo, tamasa sannu da zuwa. Amsawa yayi yana zama kusada ita, idonsa akan TV yana kallon film d'in datake kallon. sai kuma ya maida kallonsa kanta. " Fateema zanje Jos ne". "Jos kuma Nurri? Da ranarnan? Ko jikin babane ya motsa?". " a'a, ba jikin baba bane, zan dai kuma amso masa maganin nan ne, daganan naduba jikin Amatallah batada lafiya, sunama Asibiti an kwantar da ita". Dukda maganarsa ta soki zuciyarta amma saita danne, tace, "ayya ALLAH yabata lafiya? Mike damunta haka?". " Uhm to, bandai saniba, d'azu nake waya da Brother shine yake sanarmin." Azuciyarta tace shine kake sauri katafi tunda ga 'Yar Goal. afili kuma tace, "ALLAH yabata lafiya to, a gaida mana dasu". "okey zasuji". Harya mik'e yakoma ya zauna, yakula da yanda itama yanayinta ya canja, amma dayake tafi Aneesa hankali tayi k'ok'arin danne kishinta, yay murmushi yana fad'in "koma abinda zan tuna baza'a baniba?". Kamar zatace bagashi zakaje inda za'a makaba. saikuma ta danne tace, ''to mikake so?". Girarsa d'aya yad'age yace, " komima?". Kumatunsa ta sumbata. Shima haka ya sumbaci nata, sannan suka fito. Aneesa Na falo tsaye, tagama cika fam da haushi, koda suka fito bata kallesuba tayi gaba abinta, binta kawai yayi da kallo, itakam Fateema saita ta6e baki tana Harar bayan Aneesa. Har jikin motarsa suka rakashi, Aneesa tasaka masa bag d'in a gefensa, bayan yatada motar yamik'o musu hannunsa Na dama, d'aya bayan d'aya sukayi musabaha🤝🏻, sannan yace, "abama yara hak'uri nayi tafiya basu saniba, sannan dan ALLAH karna dawo naji abinda zai 6ata raina, Ku kama kanku, insha ALLAH 2days kawai zanyi nadawo". Atare sukace insha ALLAH bazakaji komaiba, ALLAH ya tsare. Yace, " amin to my Sweet wife's". dan son tsokanar su yace, " Amma bakuce na gaida Amaryaba". Kowacce kauda kanta tayi gefe basuce komaiba, dan bak'aramin dukan zukatansu maganar tayiba, ashedai hasashensu gaskiyane?. Da sauri Aneesa tashige ciki tana hawaye.😹 Jiyayi kamar ya kwashe da dariya, amma saiya gimtse, ya kalli Fateema dake tsaye har yanzu yace, "my tee... bud'emin gate to, tunda bazakuce Na gaishetanba, saina dawo". Kanta kawai ta d'aga masa, tanufi gate tabud'e masa, harya fice yana d'aga mata hannu, tamaida tarufe sannan takoma cikin gida zuciyarta Na k'una, dajin tsanar Amatallah. Nikam bilynku Nace, "wannan fa shine gudu a duhu masu karatu🤣🥴". Yana tuk'i yana dariyar abinda matan nasa sukayi, a fili yace, " dama kun kwantar da hankalinku my wife's, Muhammad bashida burin k'ara aure, koma zanyi babu yanda za'ayi Na auri 'yar cikina, Amatallah she is my daughter ". Da wannan tunani yak'araso gidansu mahaifarsa. A k'ofar wani gida yay parking motar, gidane irin ginin da, sai dai ko ina mulmule yake da siminti, tundaga k'ofar gidan har zuwa bangon gidan. Yatura murfin yashiga soron gidan da sallama, karo sukaci da wani saurayi dabai wuce 30years ba. "A ya Muhammad barka da zuwa". " yauwa Jabeer, daga ina haka kuma? bakaje aiki bane?". "Wlhy naje yaya, mantuwa nayi nadawo d'auka, ina yarana? duk suna lafiya dasu Aunty's?". " lafiyarsu k'alau, ya jikin baba?". "A alhmdllhi wlhy, yanzu haka nabaro innani nabashi kunu dayasa a dama masa". " masha ALLAH, jiki yafara sauk'i, bara to nashiga, dan zanje Jos ne". "Amma yaya Muhammad tafiyar yamma?". " to yaza'ayi Jabeer, ai ranar dole sai dole, bara nashiga dai". "To shikenan, ALLAH ya tsare hanya, a gaida mana su Yaya Ismail da iyalansa". " insha ALLAH zasuji". Musabaha sukayi🤝🏻, shi ya shiga, shikuma yafita. Tsakar gidan babu kowa, sai dai a share yake tas, sai kuma k'amshin girki dake fitowa daga kichin d'in tsakar gidan. Kai tsaye d'akin baba ya nufa, tunda jabeer yace innani tanacan. Sallama yayi a k'ofar d'akin, sai da aka bashi izinin shiga sannan yashiga da sallama. Mahaifinsu na zaune a saman k'atuwar katifar da yake jiyya, ya jingina da filuluwan da innani ta saka masa a jikin bangon, yatsufa sosai gaskiya, duk da hadda alamun rashin lafiya data kuma fiddo tsufan nasa, danma 'ya'yansa tsaye suke Kansa wajen kulawa dashi, musamman ma Alhaji Muhammad d'in. Sai dattijuwa itakuma tana zaune a kujera 'Yar tsugunno kusadashi, itama dai babu laifi ta manyanta sosai gaskiya, sai dai jikinta yafi Na baba k'arfi, saboda lafiya da ALLAH yabata, hannunta rik'eda ludayi zata saka a kwanon shan ruwa, da alama tagama bashi kunun. Tunda yashigo tamasa kallo d'aya saita kauda kanta gefe. baba kam murmushi yayi, idonsa akan sa.. Ya tartare malun-malun d'insa ya zauna a k'asa kusada babansa shima yana murmushi, "sannu baba, ina yini?". Ahankali baba yace, " lafiya lau Muhammadu, ya iyalanka?". "Lafiyarsu lau baba, ya k'arfin jiki?, duk da dai yauma naga Alhamdulillahi". Murmushi baban yak'arayi, yace, " gaskiya ne Muhammadu, jiki kam sai dai mucigaba da godema ALLAH". "to Alhmdllh baba, ai mu haka mukeso, ALLAH yak'ara lafiya da tsawon kwana masu amfani". Baba ya amsa da ''amin Muhammadu". Kallonsa ya maida ga innani data kauda kanta gefe tun d'azun, yace, " Innani ina yini". Kuma kauda kanta tayi sannan ta amsa masa. ta tambayi iyalansa. Shima kansa a k'asa yace duk suna lafiya. Batace komaiba tafara yunk'urin tashi. Da sauri yace, "innani dama zan koma jos ne wajen maganin baba, dan naga yanajin dad'insa, daganan kuma zan duba d'iyar Isma'il batada lafiya, har an kwantar da ita a asibiti ma". Yanzu kam sosai ta kalleshi, tace, " subahanallah, badai Khadija ba?". "Eh innani ita". " miya sameta?". "Wlhy nima ban san dai miyake damuntaba, sai dai naje tukunna". Daga innani har baba addu'a suka mata, sannan baba ahankali yace, " amma Muhammadu zakayi tafiyar dare ai". Kallon agogon hannunsa yayi, "baba insha ALLAH kumin addu'a zan Isa da wuri, yanzu dana fita salla kawai zanyi Na d'auki hanya". " to shikenan ALLAH ya tsareka, yakaika lafiya kaji". Amin baba, ALLAH ya k'ara lafiya". Sukace amin. ya fiddo kud'i a aljihun babbar rigarsa, saman katifar ya d'ora, "innani ga wannan kowani Abu zai taso bana nan, insha ALLAH jibi zan dawo". Batareda ta kalleahiba tace, " da kama bar kud'inka, dan Wanda kabada jiyama ko ta6asu ba'ayiba, munada komai agidannan, d'azuma jabeer yayo cefane mai yawa dazaiyi iya kaimu sati". "Duk da haka a ajiye innani, ina Nazeefa da Shehu? Banji motsin suba". "Nazeefa ta tafi gidan maijiddah, zata tayata aiki abokiyar zamantace ta haihu jiya, Shehu kam wai yatafi makaranta yace".. "ALLAH sarki, to ALLAH ya raya, shikuma ALLAH yasa gaskiyane, tunda nasan halinsa. bara naje lokaci Na k'ara tafiya". "Katsaya kaci abinci, naga Ramatu takusa gamawa". Agogonsa Yakuma kalla, ya d'an kwantar da murya, " kiyi hak'uri Innani, gara naje karnayi dare, naci abincima babu dad'ewar nan." "addu'a duk suka masa, yafita yana amsawa, zuciyarsa nak'ara masa dad'i, dajin k'aunar mahaifan nasa. salla kawai yayi ya d'auki hanya. _______________________________ Koda d'an siyasar nan Mr Pam da jama'arsa sukaje police station sai suka nemi ganin d.p.o Bayan ankaisu office d'insa, suka gaisa cikin mutunci, sannan ya mik'a buk'atarsa ga d.p.o nason asaki su zike, da farko d.p.o yaso ya tirje. Amma tunda Mr Pam ya fiddo 'yan dubu-dubu bugun Abuja sai d.p.o ya waske. Mr Pam yay murmushi ganin yanda d.p.o yayi. Ya ajiye kud'in agabansa yana fad'in "Yaya za'a banisu yalla6ai?". " wata 'yar dariya d.p.o ya d'anyi, yasa hannu kan kud'inda Mr Pam ya ajiye, sannan yace, "yanzun kuwa". Daga Mr Pam har yaransa biyu dake tare dashi dariya sukayi. Duk wani ciku-ciku daya dace Mr Pam yayi, yasamu nasarar fiddo su zike. Wad'anda tunda aka bada belinsu suka fito da k'udirin d'aukar mataki akan Amatallah da ahalinta. Su duk zatonsu babantane yamusu shunen 'yan sanda suka kamasu. Shiyyasa suka k'udirci ramawa..........✍🏻 _(wannanfa Shine halin mafi yawan jami'an tsaron k'asar tamu. Shin tayaya za'a samu gyara? bayan masu gyaran suma suna buk'atar a gyarasu, *CIN HANCI DA RASHAWA* yazama abokin kowa a k'asarmu, kuma duk a dalilin *SIYASA KO K'ABILANCI*, zakiga d'an siyasa yayi duk wani shigi da fici wajen samun yanda yakeso, koda bai cancantaba. Zakiga ankama mai laifi awani waje, amma saboda bad'an yankin bane, ba d'an k'abilar bane sai a masa mummunan hukunci, amma idan k'abilarsa ne babba awajen, da 'yan uwansa sunzo sun mik'a sai a fiddashi, komai girman laifinsa, shiyyasa zakuga idan mutum k'abilarsa nada wani babban muk'ami awaje bayajin tsoron shiga kowanne tarko, saboda alfarmar dayake da ita, shin yaya zamu kira matsalolin k'asarnan?, *SIYASA KO K'ABILANCI!?* ne ke jagorancin lalacewarmu🤷🏽‍♀?.)_ *_ya ALLAH ka gafarta ma iyayenmu🙏🏻😭_* [1/16, 1:05 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_* *_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡 _{home of expert and perfect writer's}_ *_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉ _(Hattara matasa)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_Happy Birthday Abba gana, ALLAH yak'aro shekaru masu al'barka da amfani a duniya da lahira👯🏻🔪🎂🍾🍹_* ____________________ *_Number 5_* ____________________ Kusan 5pm ya isa garin jos, damma ba gudu yakeba, yakuma tsaya a garin Mr Ali yayi sallar la'asar, dan yana ganin kafin yashigo gari time ya shige sosai. Baban Ama... da Ammi duk suna a asibitin, Amatallah na kwance, idonta biyu, amma tarufesu, su Aminta ne kawai ked'an hira duk akan ciwonta. Wayar baba tayi ringing, cikin fara'a ya d'auka yana fad'in "inaga brother ya iso kam". " Assalamu alaika brother, halan harka shigo". "Ai ganima a k'ofar asibitin". Cikin zaro ido Baban Ama... Yace, " maimakon kaje gida kawai? dama isowarka nake jira natafi gidan, nazata can zaka wuce?". "Ai bazan iyaba, sainaga jikin my best D.. first brother". " humm, kai da d'iyar taka ba'asan gwaniba ai, bara nazo to nashigo dakai". "Baban Ama... Ya iso kenan?". Cewar Ammi. " eh wlhy, wai gashima a gate d'in asibitin". "Ikon ALLAH, nazatama zai wuce gidane ai". "kinsan halin brother, bara mushigo dai". "To". Duk abinda ake Amatallah na jinsu, amma batace komaiba, saima luf data sake yi a kwance, haka kawai taji gabanta ya tsananta fad'uwa, duk da dama yau Throughout haka ta wuni gabanta na fad'uwa, jitake kamar wani gagarumin abu zai faru da ita, shiyyasa dukta tsangwami kanta......😢 tun kafin su shigo k'amshin turarensa yayo gaba, Amatallah ta shak'a tareda kuma matse idanunta, still zuciyarta nacigaba da bugawa da sauri-sauri. Addu'a tafara karantowa, dan batasan dalilin wannan gudun da zuciyarta keyiba?, kuma tun ganinta Na farko da *_Uncle M.A_* a wancan zuwan hakance tafaru, harya tafi wancan time d'in idan suna waje d'aya koya shigo sai heartbeat d'inta taringayi kamar zata fito, kuma itakam a shekarun baya tana yarinya batajin hakan akansa, komiyasa yanzu kuma?........... Sansanyar muryarsa ce ta katse tunaninta. bayan sun gama gaisawa da Ammi yamatso gaban gadon saitin face d'inta. Yace, "My best daughter! barci kikeyine?". Ya sallam!, tafad'a a zuciyarta. batasan ya zata musalta yanda cool voice d'in uncle M.A ke razana zuciyarta da dukkan magudanar jininta ba, jitake kaf duniya yafi kowa dad'in murya. Babantane ya ta6a k'afarta tareda d'an bubbugawa. Ta bud'e ido ahankali tamkar mai barcin gaskiya, da uncle M.A tafara tozali, yana tsaye agaban gadon kusada fuskarta, sanye yeke cikin Cyan color d'in tattausan boyal, Wanda yasha d'inkin babbar riga, ya kafa hular zanna bukar black akansa da ratsin cyan kad'an, sai bak'in agogo da bak'in takalmi heir cover. Waro ido tayi cikin acting like tana mamaki ganinsa. Tattausan murmushi ya sakar mata. Ta yunk'ura a hankali tatashi zaune tana "lah Uncle yaushe kazo". Still murmushin yakuma yi, kafin yace, " my best daughter yanzunnan nazo kina barci, ya jikin naki?". "Da sauk'i uncle, ya hanya? Yasu Saifudden da jikin baba?". "Everything Alhmdllh my best D..., amma gaskiyafa kin rame sosai, anya kinacin abinci my best?". K'asa tayi da kanta tana murmushi, saikuma tad'an jinjina kai, tamkar wata k'adan garuwa. Tana fad'in ''inaci uncle, katanbayi baba da Ammi ma". Murmushi yayi, sannan ya maida kansa ga babanta, " brother wai miya faru da my Daughter hakane?". "Humm ai Brother inaga muje gida, sai muyi maganar a can, dan yinta anana zai iya zama danger gaskiya". "okey, amma anbata sallamane?". "No basu sallamemuba, inga dai k'ilan zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu, dan kaganta yanzudai normal, sai dare yayi jikin ya rikice, taita firgita, kullum akanta muke kwana babu barci wlhy". " ya salam, abin yayi tsamari haka Dama?". "Brother Amatallah dama haka take da rik'e Abu, shiyyasa kullum nake cikin fargabar irin mijin da ALLAH zai iya had'ata dashi, ba kowane zai iya d'aukar wannan rayuwan tataba gaskiya, so ina tausaya mata". " karkace haka brother, muyi mata addu'a kawai, insha ALLAHU ALLAH zai bata miji nagari ma". "To ALLAH yasa brother". dahaka suka k'arasa motar sa. Har sun shiga motar Baban Ama... Ya hango Ammi Na tahowa da sauri. Kallon Uncle M.A yayi dake k'ok'arin jan motar yace, ''d'an dakata ga Ammin tanan, inaga munyi mantuwar keys d'in gid...... Bai k'arasaba Ammi tak'araso, keys d'in tamik'a masa kuwa tana fad'in "kun manta keys d'in ai. abinci nannan a seatroom Na shirya". Murmushi Baban Ama... Yayi yana fad'in " jazakallahu khairan uwargidana". Hararan wasa tamasa tace, "kuma amarya ba". Duk su biyun dariya sukayi shida uncle M.A, Baban Ama... Yace, " ai nima aure zan k'ara, bakiga brother ma 2 Star ne ba? kilama yana shirin zama 3 ban saniba, gara nadage nayi nima Amatallah tasamu abokan shawara itama". Juyawa Ammi tayi tana fad'in " wace zata auri tsoho?". Dariya suka kumayi, sai da suka fita daga asibitin Uncle M.A yace, "brother mata basa girma akan kishi, wani lokacin har mamakinsu nake, komin k'ank'antar Abu sai yazama Na kishi a wajensu fa". Baban Ama... Yace, ''ai kishi a jinin mata yake brother, babu mai iya rabasu dashi sai dai ALLAH kawai, kana daiji mi Saliha kefad'a yanzun, wai wazata auri tsoho? alhalin zan iyama d'aukar budurwa sa'ar Amatallah". Yak'are maganar da dariya. Uncle M.A ma dariyar yakeyi, " kai brother, yanzu in ance ga budurwa sa'ar my daughter saika aura kuma?". "Ah da guduma kuwa, kana ganin tamin kad'anne?". " hhh kamata yawa dai brother, mumafa balaifi munja kwana a duniyarnan, kusan 47years fa". "Ai brother rayuwa nabani tsoro wlhy, ALLAH dai ya gafarta mana, yau kake gobe sai labarinka, yanzu nan su kawu da mamana Khadija harsunyi 12years da rasuwafa kenan?". " ajiyar zuciya uncle M.A ya sauke, yad'an shafa fuskarsa yayinda k'asan zuciyarsa yay rauni saboda Baban Ama... yata6o masa wani sashen rayuwarsa, cikin sanyin muryarsa yace, "hakane brother sunkai". Yanda baba yaji muryar uncle M.A ta canja saiya canja hirar shima, ya d'akko hirar abinda yay sanadin kwanciyar Amatallah a asibiti. Ahaka suka k'arasa gida, mamaki dukya cika Uncle M.A, cikin damuwa yace, " brother gaskiya ina wata shawara da zuciyata tun kusan 1year data wuce, akan wani rikici dayafaru, danake kallo a labarai sainaga duk matasane a wajen, sannan duksu akafi kashewa, hakan yatada hankalina wlhy, tun lokacin nake juya maganar araina, amma narasa dawa zan tattaunata, kasancewar nasan akwai fuskantar k'alubalen masu dafamin mu tallafi tafiyar. Murmushi baban Ama... Yayi, kafin su zauna a kujerun seatroom d'in, uncle M.A yacire babbar rigarsa shima ya zauna, ruwanda Baban Ama...yazuba a cup yamik'o masa, kar6a yay yasha. "Brother mikake rik'e a zuciya har kusan 1year? In dai ka yarda dani kafad'amin, insha ALLAH ina tare dakai 100%". "Haba brother mikake tunani? ai duk duniya inka cire baba da innani babu Wanda yasanni sama dakai, kama fisu sanin wasu abubuwan akaina, dansu bakomai zan iya yi agabansuba kona fad'a musu, kaikam a sirrin rayuwata miye baka saniba brother?". " tom naji, nayi kuskure, amin afuwa, yanzu fad'amin mike ranka to? Insha ALLAH ina tare dakai". "Alhmdllh brother"....... Katseshi Baban Ama... yayi, bayan yagama zuba musu abincin, yace, "mufara cika tunbinmu, sai maganar tafi shiga to". Dariya suka tuntsure dashi suduka, sannan Uncle M.A ya sakko. ______________________________ " Oga akwai fa matsala gaskiya". Wani yaron zike ne ke magana cikin muryar maye. Zike dake zaune kan dakalin sokawe Na toilet d'in primary school yana busa taba yad'ago jajayen idanunsa yana kallonsa, "matsalar mi manu!?". " oga! Gagis fa bai wullaba wlhy, ance yana general hospital kwance, kaima kasan yana mik'ewa yak'ine kawai zai tashi, ALLAH wlhy". Wata 'yar zabura zike yayi, yacire tabar dayake busawa daga bakinsa, kallon sauran yaransa yayi daduk suke a cake, wasuma kwance suke a k'asa, wasu kuma suna busa wiwi, wasu kuma rik'e suke da roban faro suna shan wani far in abu, ya maida kallonsa kan manu, ''kai waye yafad'a maka?". "Oga ba d'azun ka aikeni gidan Oga Pam ba? natarar wannan shegen d'an koran nasa zasuje wai dubashi a asibiti, harda mai k'aton kannan da ido gulu-gulu kamar Na kasa jan goro a faranti". Dariya duk suka bushe da ita, amma banda zike da hankalinsa ke a tashe, yasan wanene gagis sarai, tashinsa kuma bazai zama sauk'iba a garesu su dukansu, kallonsu yayi, duk suka tsaya da dariyar dasukeyi. Yace, ''kai guys, dolenefa yau d'innan lahira tayi bak'on bawa, am telling you idan gagis yatashi sai kowa yabar jos, kuma kunsani". Manu yamik'e yana tangad'i, " Oga shiyyasa nafad'a maka ai, yanzu hakafa yaransa nemanmu sukeyi, danma Oga Pam yayi gargad'in kar Wanda yayi wani abune, ammafa dayanzu anfara Caskale a garinnan, ALLAH wlhy". yay taga-taga zai fad'i, saikuma yarik'e bango. "Yau Operation biyu garemu, dolane mu k'addamarma tsohon yarinyar can daya had'amu da kwalawa wlhy, sannan Na yayyaga uwarta a gabanta, itama haka, kafin Na wullasu gidan daba'a dawowa". Dariya suka kuma bushewa da ita, yanzu kam harda zike. Yacigaba da fad'in saikuma wancan sauran gawan gagis, har yaransa saina k'are musu tanadi,, yanzu kutashi muje lik'a posters d'in Oga, koba'aso dolene ayisa kokuma lahira tai bak'i wallayi". (Duk cikin harshen turanci suke magana, Dan k'alilanne ma acikinsu kejin hausar, manu nema kad'ai bahaushe, saurankam kowanne dayarensa, kusandai yanda jos ta tara yarurruka iri-iri, wannan yasa aka cakud'e waje d'aya, baka isa cewa wannan yarene tsageraba a jihar, saboda matasansu a cakud'e suke, musamman ma irinsu zike marasa jin magana🙁). Duk mik'ewa sukayi, kowannensu a buge yake, dan sunyi mank'as da kayan mayen da Oga Pam ya basu, wani buhu dake gefe suka d'auka, zike yabud'e yad'ebo posters yana raba musu, saida kowa yasamu sannan suka tafi, kowa yana rik'eda posters da gam na ruwa a hannu. Sai ihu suke suna kirari wa Oga Pam. Jikin pols da bangon gidaje suke lik'a posters d'in, daduk inda yay musu, babu mai hanasu Dan ansan halin tsagerancinsu sarai. ihu suketa zabgawa. "Wuyyyyyiiii huhuuuuuuuu!!!!!, sai Oga Pam ko jiki yay tsami, a za6esa dole ko wlhy uwar gayu tahaifi wani, wuuuuyii huhuuuuuu!!!!!!!. Abinda suketa fad'a kenan, ba yaraba hatta manya gefe suka koma suna kallonsu. duk poster d'in da suka gani cireta sukeyi, inhar bata Mr Pam baceba. Kad'an yarage fad'a ya kaure tsakaninsu da wasu matasan anguwar, wad'anda suka lik'a wasu posters da suke cirewa. amma wani dattijo yamusu magana. ALLAH yasa wad'ancan masu fahimtane, akwai sauran hankali a jikin, saisuka k'yalesu akan zasu had'une koba yauba. Su zike kam filin nasune, haka sukaita bin anguwanni suna lik'e-lik'en fostar Mr Pam.☹ Wata anguwar a tanka musu, wani wajen kuma ayi kamarma ba'a gansuba. Saida suka gama tas sannan suka koma bayan Government primary school inda suka maida dan-dalin shaye-shayensu suka zauna maida numfashi, da hirar tsiyatakun dasukayi a yau d'in, wani suyi dariya. Wani suyi surutu da zage-zage. _____________________________ Tunda suka fita Amattalah ta sauke ajiyar zuciya, gyara kwanciyarta tayi tana tunanin rashin zuwan Sadeeq saurayinta dubata. Kobaiji batada lfy bane? Kokuma yazo tana barci halan?. Gashin wayartama tana gida balle ta kirashi, kuma tanajin kunyar tambayar Ammi koyazo...........✍🏻 *yawan comments, yawan kwazona fa🤔🤥.* One luv my fans🥰🥰 *_ALLAH ka gafartama mahaifanmu._*😭🙏🏻 [1/16, 1:05 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_* *_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡 _{home of expert and perfect writer's}_ *_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉ _(Hattara matasa)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* ____________________ *_Number 7_* ____________________ *_WASHE GARI_* 🤔😭 Abin mamaki washe gari da safe sai ga labarin kisan gagis yafito, anje har cikin asibiti da daddare anmasa yankan rago. Kai tsaye kowa su zike aka zarga, musamman da akasan tushen abinda ya kwantar da gagis asibitin. Humm, amma abin tsoro da ALLAH wadai sai aka nemi su zike aka rasa a cikin jos, Ashe suna gidan Mr Pam yabasu mafaka, bayan sungama tsara masa k'arya da gaskiya akan su gagis sunason 6ata siyasarsane shiyyasa suka kasheshi. Sosai Mr Pam ke hura hanci da banbamin masifa akan k'are Duk wani dayace zai kawoma siyasarsa togaciya dolene a 6addashi, koda kuwa abokan takararsane. A daren ranar yadank'ama su zike makamai masu had'ari sosai, wai surik'e domin kare kansu. sunyi farin ciki sosai da wannan k'yauta, dan aganinsu k'arin k'arfin guwwane agaresu. Nidai nace, "hummm".☹ ____________________________ Tunda sassafe Baban Ama yay shirin tahowa asibitin, danya kar6i Ammi taje tai musu girki. Alhmdllh yatadda jikin Amatallah da sauk'i, jiya kuma firgitar kad'an tayi, sai dai zazza6i mai zafi data kwana dashi, dukda Magani da akabata bai saukaba, haka taita sambatu da kiran sunan Ammi da babanta. Lokacin da babanta yake fitowa saiya ci karo da uncle M.A, babu irin rok'onsa dabaiyiba akan yay kwanciyarsa yak'ara hutawa zuwa anjima amma yak'i, yace suje tare kawai asibitin su kar6i Ammi. Haka suka taho badan baban Ama yasoba. Sun iso Amatallah Na barci, saboda batayi barcin dareba, bayan sun gaisa da Ammi tawuce gida sukuma suka zauna hira. Kusan 9:30 Ammi takirasu akan sutaho tagama. Har lokacin Amatallah Na barci. Ammi tataho sukuma suka tafi, Suna kammala cin abinci suka tafi k'auyen da zasu kar6o maganin baba. Basu dawoba sai misalin 2:38pm. kai tsaye asibitin suka nufo. Amattalah na zaune a kan gadon datake jiyya, abinci takeci tana hawaye, ga likita tsaye agefenta yana kallonta yana murmushi shida wata Nurse, Ammi kuma Na a bakin gadon zaune tahad'e fuska tana fuskantar Amatallah, da Alama itace ta tsareta takeci abincin. Cikin gur6atacciyar hausar likitan yace, "Ametala please mana, stop crying, baka sen kai babba baniba? amma kinama common injection kuka? randa zakaje labour room kuma fa iye?......" Banza Amatallah tamasa, jitake kamarma ta bugeshi dan haushi, shigowar su baba yasaka doctor da Ammi kallonsu, duk suka amsa sallamarsu. Uncle M.A yak'araso da d'an sauri yana tambayar lafiya? Amatallah ke kuka?". Doctor ne yamasa bayani akan sunason mata allurane saboda zazza6i yak'i sakinta, to gashi bataci komaiba kuma, shine yace tad'anci abinci kafin sumata. tace tak'oshi, Ammi ta tsareta saitaci, wannan ne dalilin kukan nata. Babantama dariya abin yabashi, dan haka yay dariya kad'an, can k'asan ransa kuma yanamai jin tausayin d'iyar tasa tilo, sai dai bai San daliliba, tunda safe dasukazo ya kalleta yaji kwalla sun cika idonsa, haka kawai yau yawayi gari da k'ulafucin tunaninta da tausayi..... Ajiyar zuciya yasaki, yayinda ya tsinkayo muryar uncle M.A Na lallashinta. Bai ce komaiba, saima gefen Ammi daya koma ya zauna yana kallonsu cikin wani yanayi, ita kanta Ammi kallonsu takeyi a wani iri. Da lalashin uncle M.A akasamu Amatallah taci abinci aka mata allura. tun tana hawaye har barci ya d'auketa, suduka ajiyar zuciya suka saki, kafin su tashi su fita zuwa gida cin abinci, sukabar Ammi Na gadinta, lokaci-lokaci masu dubiya k'awayen Amattalah da makwafta da 'yan uwan Ammi Na zuwa. ____________________________ Gab da magriba Baban Ama yakira Ammi akan tazo gida tabashi wasu takardu daya bata ajiya. Tayi d'an Jimm kafin tace, "to Baban Ama wazai zauna da ita? gani nake bai dace nabarta ita kad'aiba anan. Ajiyar zuciya Baban Ama ya dauke, kawai saiyaji idonsa yacika da k'walla, zuciyarsa tayi rauni, a sanyaye yace, " karki damu, ga Brother nan yataho wajenta, idan kika d'akkomin saimu koma asibitin tare ni da ke". Kanta ta jinjina tamkar tana a gabansa, tace, "to ganina zuwa". Amatallah na kwance tanajin Ammin ta, jitayi bata k'aunar tafiyar Ammin, bayan Ammi ta yanke wayar Amatallah ta kalleta, hawaye taf da idonta tace, " Ammi ki kwatantama baba inda takardun suke saiya d'auka basai kinjeba". tak'are maganar da zubda kwalla. Kallonta Ammi tayi, tana mamakin miye abin kuka anan? daga dai zuwa d'akko takardu tadawo. Matsowa tayi jikin gadon, ta dafa kan Amatallah tana murmushi, "haba Khadija miye abin kuka to? yanzufa zanje na d'auka masa mudawo, kiringa hak'uri da rayuwa Khadija, wannan k'ulafucin namu dakikeyi ki ragesa, karfa ki manta akwai mutuwa, kuma ke d'iya mace ce, wataran aure zakiyi kibarmu dole, kizama mai hak'uri kinji, komi kike tunani, koya cutar dake, koya sakaki rud'ani, to kisaka *HAK'URI* agabansa, insha ALLAH zaki zama mai riba a duniyarki da lahira.......... Sallamar Uncle M.A ce takatse Ammi........, shiru tayi tareda janye hannunta daga kan Amatallah, ta amsa sallamarsa, ya tambayi jikin Amatallah, tace da sauk'i sannan tafita. Har taje k'ofa tajuyo takuma kallon Amatallah dake binta da kallo itama, jiki a sanyaye tafice zuciyarta na k'una. Kawai sai Amatallah ta fashe da kuka. da sauri Uncle M.A yak'arasa inda take yana fad'in " subahanallahi, My Best miya faru da kuka kuma?". Kasa bashi amsa tayi, tacigaba da raira kukanta. Kusada k'afafunta ya zauna yana lallashinta, shikansa gabansa sai fad'uwa yakeyi, gawata matsananciyar fargaba da yakeji tunda safe, harma zuciyarsa tana raya masa ko jikin babane?. ________________________________ "Ka tabbatar kayi kamar yanda nace, karka bari asamu kuskure fa". "Oga karka damu kanka, kasaka aranka kawai sun wulla, itakuma bab.. d'in tana hospital, hawan k'awara yakamata mumata da daddare". " karka damu, kaje afara wannan aikin first." "Okey sir, babu damuwa". _______________________________ Cikin mintuna k'alilan Ammi ta iso gida, a k'ofar gida sukayi kici6is da baba zaitafi salla, tashiga shikuma yanufi massalaci. Ramzaki dake la6e bayan wani kwano da aka zagaye bishiyar mangwaro yafito, da sauri yashige cikin gidan, babu Wanda ya lura dashi saboda duhun magriba daya fara, gakuma garin da alamun hadari ma. Ko kad'an Ammi bataji motsin shigowaba, tayi alwala tashige ciki. duk Ramzaki Na la6e yana kallonta. sai da yaga tashiga falon sannan shima yashigo cikin gidan sosai. Bayan kamar mintuna biyu ya tabbatar Ammi ta kabbara salla. Sad'af-sad'af yashiga cikin falon. Tabbas Ammi taga shigowar sa cikin falon, amma taza6i cigaba da sallarta, dan duk tunaninta 6arawone, hartayi raka'a d'aya yana tsaye a kanta, kallo yake k'are mata sama da k'asa, duk da gefen zuciyar Ammi ya tsorata, amma ta daure batabama shaid'an damar cin galaba akantaba bare ta sallame sallar. Ramzaki sai da yabari tayi sujidar k'arshe sannan yazaro wuk'arsa daga k'ugunsa, dai-dai lokacin dazata d'ago ya soka mata wuk'ar a gefen cikinta na haggu.😭 Babu shiri Ammi takoma Sujudar datayi niyyar d'agowa, maimakin tayi ihu saita fara ambatar "La'ila ha illallah, muhammadarrasulullah, hazbinallahu wa ni'imal wakil". Wannan shine abinda keta fitowa daga harshenta, har Ramzaki ya zare wuk'ar, yadawo d'ayan gefenta yakuma sokawa. Hawayene masu zafin gaske suka fara kwarara a idon Ammi dake a sujuda har yanzun, Ramzaki nakuma zare wuk'ar saita zube kawai awajen, la66anta dake motsawa suna kalmar shahada har yanzu nake kallo. *_Masu karatu nikaina ina cikin rud'ani, wannan rashin imani har INA.😭_* Ramzaki Na tsaye akan Ammi har tagama shure-shure, numfashinta yakoma fita a hankali..... Dai-dainan baba yashigo gidan, da sauri Ramzaki yakoma bayan labule ya 6oye. Baba yashigo cikin tsokana yana ambatar " Uwargida ran gida! kina ina? Zokiga angon gobe........ Maganarsa ta mak'ale a mak'oshi saboda ganin jini Na mamalowa daga inda Ammi ke kwance, kasa motsawa yayi inda take, yabi jinin da kallo kafin ya maida kallonsa ga Ammi, takawa yayi a hankali har inda take kwance. Da sauri Ramzaki ya kwantar da gallon d'in fetur d'in daya shigo dashi, sad'af-sad'af yafice a falon. Fetur d'in yafara malale falon. Durk'ushewa baba yayi a gaban Ammi, yakama hannunta na haggu data dafe gefen cikinta na dama dashi, a hankali yad'aga hannun, soyake ya tabbatar daga nannne jinin ke zuba ko kuwa?. Idanunsa yazaro, Dan ganin yanda jini ke 6ul-6ula, muryarsa na rawa yashiga kiran Saliha! Saliha!!, ke Saliha!!..........maganarsa mak'alewa tayi saboda ganin hasken huta, yajuyo a sanyaye. Kasa motsawa yayi, yay sagade yana kallon wutar dakeci afalon, tanabin duk inda fetur d'in ya ta6a. ko kad'an baiyi yunk'urin motsawaba, saima matsawa dayayi jikin gawar Ammi ya kwantar da kansa bisa fuskarta ya fashe da kuka.😭 A hankali wutar tafara k'arfi, dan har kujeru sun fara kamawa, duk da zafin wutar na dukan baba yakasa tashi, motsin kirkima yakasayi awajen, jiyake tamkar an d'auresa da igiya. Sannu a hankali wutar ta iso inda yake, tuni numfashinsa yafara sark'ewa saboda hayak'in wutar. Hankalin 'yan anguwa yafara dawowa gidan baba, saboda ganin hayak'i tasaman zinc. Wanine ALLAH ya nuna masa fitowar Ramzaki daga gidan. Ihu yafara yana nuna Ramzaki. Ramzaki naganin haka yakwasa da gudu, hakanne ya tabbatarma da mutane baida gaskiya. nanfa wasu matasa suka rufa masa baya domin kamashi. wasu kuma suka afka gidansu Amatallah dan ganin mike faruwane?. Lokacin dasuka fara shigowa baba harya suma, Dan numfashinsa ya gagara fita, hayak'i ya sark'eshi, wutarma tafara bin kayansa shida Ammi. Ihu mutane suka fara tareda d'aukar botikan ruwan dake tsakar gidan suka fara watsawa k'ofar falon, amma wutarnan kamar sake izata akeyi. Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un. Wutarnan batada niyyar mutuwa ko kad'an, wannan yasaka wasu fara Neman 'yan kwana-kwana. duk da haka kuma anata watsa ruwa, makwafta sai kawo ruwa sukeyi. ****** Jikin Amatallah ne yafara rawa, ta fashe da kuka tana fad'in Uncle babana da Ammina. Dan ALLAH ka kiramini su, inason ganinsu, Dan ALLAH kirasu........ A tsorace Uncle M.A ke kallonta, ga mamakin rawar jikin datakeyi, duk da luguden daka da k'irjinsa keyi shima bai hanashi lallashintaba, ya kalli agogon hannunsa, 7 ta wuce, ana gab dayin sallar isha'i. Cikin sassanyar muryarsa yace, "Sorry my best, maybe sai sunyi sallar isha'i zasuzo kinji". Kanta ta girgiza masa, cikin kuka tace, " Uncle kakirasu, inajin tsoro wlhy, sainakeji kamar wani Abu na faruwa dasu Uncle, kiramin baba to yanzun". Baice mata komaiba ya fiddo wayarsa ya kira number baba, kusan kira 4 bai d'agaba. alamun tsorone suka fara bayyana a face d'insa shima, shikansa jiyake kamar akwai abinda ke faruwar. Zumbur yamik'e yana fad'in "kinga ina zuwa...... Ruk'o rigarsa tayi, "please uncle mutafi tare, Nima zan bika, bazan iya zamaba wlhy inajin tsoro". " haba daughter, kiyi hak'uri naje, kinga bakida lafiya, insha ALLAH yanzunnan zamu dawo tare dasu".... Kanta ta girgiza musa alamar bata yardaba. Ya d'anyi shiru kafin yakuma fad'in "to bara naga likitanki nadawo, saimu tafi". Yanzu batayi musuba ta sakesa. Fita yayi kamar zaije wajen doctor d'in, yana fita wajen motarsa yaje, yashiga da sauri yabar asibitin. Kusan atare Uncle M.A ya iso da 'yan kwana-kwana. jikinsane yafara rawa saboda hango dandazon jama'a a k'ofar gidan brother d'insa, ga jiniyar motar 'yan kwana-kwana a bayansa, fitowa yayi da sauri yana bin hayak'in dake turnik'e da saman gidan. Zufa kawai yaji tafara ketoma jikinsa. Ya kutsa cikin mutane shima yana k'ok'arin shiga cikin gidan. Sai dai hakan ya gagara, saboda zafin wutar dukya gauraye matsakaicin gidan, mutanen dasuke a cikima duksun fito. Jirine ya kwashi Uncle M.A lokacinda kunnuwansa suka jiyo masa furicin wani mutum na fad'in ai Alhaji Isma'il d'in da matarsa suna ciki, wani saurayine akaga yafito daga gidan da.......... Baiji k'arshen zancenba ya sulale awajen yafad'i a sume................✍🏻 Masoya kumin afuwa😭🙏🏻nakasa cigaba da rubutun saboda kuka, wlhy kuma da gaske nake😭 *Ya ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻* [1/16, 1:05 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_* *_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡 _{home of expert and perfect writer's}_ *_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉ _(Hattara matasa)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* _Kina inane *Ummu Basheer!?* maza ki matso kusa, wannan page d'in nakine ke kad'ai, kiyi yadda kikeso dashi dear, ki tabbata kina can k'asan zuciyar bilyn Abdull, ina alfahari dake, ALLAH yacigaba da jagoanci a lamarin rubutunki kema my dear, ya raya manasu Abdul🥰🤝🏻 ke d'in tadabance👍🏻._ *_Happy marriage life Ayush Ilyasu, Ubangiji ALLAH yabaku zaman lafiya da zuri'a d'ayyiba, yasa alkairi da farinciki a rayuwar aurenku🙏🏻🥰🥰😊._* _writer's d'inmu dasuka hallacci bikin suka wakilcemu ALLAH yabar zuminci😄🥰🥰._ Nina naje, Baku ganni bane kawai, INA bayan Maman bobo da sadnaf ne, Ummu abrar ta 6oyeni da hawwer😂, saura kuce k'ayya nayi😓. A tambayi hassy da Ummu Alisha ma ehe😏. ____________________ *_Number 8_* ____________________ Tun Amatallah na sauraren dawowar Uncle M.A har tafara fidda rai, kuka sosai takeyi Wanda yafara dawo da hankalin mutane kanta, sauka tayi daga gadon tafito, duk da bazata iya gane motar Uncle M.A ba hakan baihanata waige-waige ba, amma ko maikama dashi bata ganiba, harabar asibitin tafara zagayawa tana lek'a motocin mutane, a nufinta kozataga uncle d'inta. K show yace, "yauwa Oga kaga babyn can, maybe akwai abinda take nema, kaga tama sauk'ak'a mana aikinmu, basai mun shiga cikiba". Wata dariya zike yayi, ya lashe la66ansa yana gyara tsayuwa. Kad'an ya bigi kafad'ar k show yana fad'in " wannan ai tanada amfani kafin ta wulla itama". Dariya shima k show d'in ya tuntsure da ita danya gane inda ogan nasa yadosa, ahankali yace, "Oga please nima ko sid'one abani inka kammala". " hhhhh kar ka damu k show nawa". Amatallah ta jingina da bango takuma fashewa da kuka, ta tabbata uncle wayau yamata ya gudu. Gani tayi wasu doctors biyu da nurses sunfito da d'an gudu, motar ambulance suka shiga ta asibitin suka fice da gudu. Tsayawa tayi da kukan tabi k'urar motar da kallo, k'irjinta sai kuma dukan uku-uku yakeyi. Su zike dake a la6e har yanzu suna kallonta suka fito, dai-daita Kansu sukayi suka nufota, suna daf da zuwa inda take doctor Joshua yafito yana waige-waigen nemanta, danya zo zai mata allurar k'arfe 8pm ne yaga bata nan, mutanen dake wajen suke masa bayani akan tafita kusan 18munutes, shine yafito nemanta. Can ya hangota jikin wata mota ta tsurama waje d'aya ido tana hawaye, ga wasu samari biyu Na tunkarota. kafin ya k'arasa wajen su zike sun k'arasa, k show ya saka mata handkerchief d'in hannunsa a hanci. Da gudu doctor Joshua ya k'araso wajen yana fad'in "kai! Kai!..... Daga k show har zike sun tsorata, sakin Amatallah sukayi a k'asa, tafad'i yaraf saboda abinda suka shak'a mata. Jikin doctor sai rawa yakeyi, bata su zike yakeba, dan ko kallonsu bai kumayiba har suka fice. Kin kimar Amatallah yayi yakima ciki da ita. A dai-dai nan motar Ambulance tadawo. Innalillahi..... Kawai nake maimaitawa saboda ganin wad'anda aka fiddo daga Ambulance d'in😭. Ammi ne da baban Ama, sai uncle M.A, wanda daka masa kallo d'aya zaka tabbatar a rikice yake,. Har aka shiga dasu baba ciki ban iya Na motsaba daga inda nake, saboda tashin hankali. ___________________________ Su zike na fita da gudu sukaci karo da yaran gagis, wad'anda tundaga bayan gidan Mr Pam suke binsu abaya dama, amma basu saniba. Daga k show har zike a tsorace suke kallon dabar matasan, wad'anda zuciyarsu tarigada tagama bushewa, kowanne rik'e yake da makami mai had'arin gaske. Fitsari kawai k show yafara a wando, Dan yasan babu makawa yau d'innan suma zasu wulla inda suke wulla wasu. Babu 6ata lokaci yaran gagis suka far musu kawai, a cikin mintuna dabazasu wuce 20 ba suka zama labari, tuni yaran gagis suka watse a wajen, sukabar gawar zike da k show kwance jina-jina. ******* Ramzaki kam daya kunnama su Baban Ama wuta da k'yar ya tsira shima daga farmakin matasan anguwar su Amatallah, ALLAH yabashi sa'ar fad'awa d'akin wasu matasa 'yan k'abilarsu. Tambayarsa suka shigayi miya farune?. Ramzaki ya tak'ark'are ya mako k'arya, wai wasune zasu kasheshi saboda sun zagi yarensu ya rama. Tuni matasan suka mik'e suna hura hanci, kafin kace me sunshiga zaro makamai kala-kala a k'ark'ashin katifar d'akin. Wani ramine a k'asan katifar, shak'e yake da makamai kala-kala. Dad'ine yakama Ramzaki, shima yakar6i biyu suka fice........ 🙆🏻‍♀😨 ********* Koda yaran gagis suka bar bakin asibiti sai suka nufi gidan uncle d'in zike, Dan sunyi alk'awarin k'arar da dukkan ahalinsa. Babu maganar Neman ba'asi ko dalili suka haikema Mr Marcel Wanda baijiba bai ganiba da iyalansa, hasalima kullum cikin yima zike fad'a yake a kan rayuwar daya saka kanshi. yakashe kud'i babu adadi akan yayi karatu amma zike yay watsi da maganarsa, sai gashi yau ta sanadinsa anzo har cikin gida an kasheshi shida matarsa da yaransa biyu😭. ____________________________ A asibiti kam lamarin ba'a cewa komai, ALLAH yayima Ammi rasuwa😭. Tunkafin wuta dama tarasu ita, saboda wuk'ar da Ramzaki ya soka mata sau biyu. Baba ma dai lamarin sai addu'a, danba k'aramar k'onewa yayiba, likitoci kusan hud'une a kansa. Uncle M.A yakasa zaune yakasa tsaye, jiyake tamkar zuciyarsa zata fito waje daboda tashin hankali, yana tsaye a k'ofar d'akin da'aka shigadasu baba shida wasu makwaftan Baban Ama d'in, sai kaikawo sukeyi, da jimamin lamarin, abin tamkar wani film. *_washe gari_* A washe gari saiga k'aramar magana tazama babba, domin kuwa ba k'aramar 6arna su Ramzaki sukayi a anguwar su Amatallah ba. 6angaren yaran gagis ma saita kwa6e, dan kisan su Mr Marcel yayan zike tasaka danginsu maida murtani, kafin k'arfe 2pm komai ya cakud'e, sallar azuhur ma tagagari jama'a, sai a gida aka yita.🙆🏻‍♀ _____________________________ Hankalin Uncle M.A yayi masifar tashi, gani yayi inhar yabari suka kai dare a jos to tabbas dagashi har Amatallah d'inma bawai tsira zasuyiba, musamman yanda yaga ana kawo masu raunika asibitin, wasuma sun rasu. abinda kuma yak'ara tada hankalinsa shine bayanin likita akan jiya wasu sunzo sace Amatallah. har zuwa yanzu abunda suka shak'a mata baima saketaba. Da sauri yamik'e ganin su doctor Joshua sunfito daga d'akin da baba ke kwance, har yanzu an hana kowa ganinsu. "Doctor yaya?". Numfashi doctor Joshua ya sauke, tareda fad'in lamarin babu sauk'i Alhaji, zafin wutar hayak'inta yayi mugun ilata lafiyar Alhaji Isma'il gaskiya, amma muna kan aikinmu, zakuma muyi iya k'ok'arinmu akansa". Uncle M.A ya jin jina kansa, muryarsa na rawa yace, ''matarfa?". Shiru doctor Joshua yayi, saikuma yad'anyi murmushi, da sauri yace, " itama dai hakan". bai jira cewar Uncle ba yay saurin barin gurin. Cikin sauri Uncle M.A yabi bayansa yana kiran "doctor!". Harya kama handle d'in k'ofar office d'insa zai shiga ya dakata, saurin maida kwallan sa yayi, haka kawai yaji yana tausayin Amatallah da wannan mutumin dabaisan dangan takarsa da iyayen Amatallah d'inba. Uncle M.A daya k'araso yace, ''please doctor inason muyi magana inhar bazan shiga aikinkaba". "Babu damuwa Alhaji, zaka iya shigowa". 'Yay maganar yana shiga office'. Bayansa Uncle M.A yabi. Bayan sun zauna Uncle M.A yace, " doctor inason tafiya dasu Kano gaba d'aya, kaga garinnan kuma harmutsewa yakeyi, dukda bamuna fatan damuwar da'ake ciki tawuce hakanba, amma sunada buk'atar kulawar gaggawa suda Amatallah, please doctor ka taimakeni". Cikin tausayawa doctor Joshua yake kallonsa, ya gyara zamansa yana jinjina kai, "nabaka goyon baya d'ari bisa d'ari Alhaji, nima ina ganin hakan shine mafita. yanzuna nan zan shirya muku tafiya kawai". Sosai Uncle M.A yaji dad'i, sai godiya yakema doctor. Babu 6ata lokaci komai yagama kammala, aka kai su Ammi cikin Ambulance, dukda itad'in ta rasu, amma doctor Joshua yakasa fad'ama Uncle M.A d'in. Amatallah kan a motar Uncle M.A aka sakata, haka sukatafi zuciyar uncle cikeda rauni, lokaci-lokaci yakan juya ya kalli Amatallah dake kwance a baya tamkar gawa.... ************* Tafiyar Awa 3½ ce ta kaisu garin Kano, kai tsaye asibitin Aminu Kano suka wuce. A cikin gaggawa kuwa aka kar6esu, saboda ansan da zuwansu, tunkan subaro jos Uncle M.A yakira doctor Shu'aibu ya sanar masa zuwansu. Wannan yasaka suka Tatar da komai a ready, su kad'ai ake jira. Amatallah ma anbata gado, Dan har zuwa yanzun batasan ina kanta yakeba. Sai da Uncle M.A yaga komai ya dai-daita sannan yatafi gidansu danya sanarma iyayensa. Yana shirin shiga mota doctor shu'aibu yafito da sauri yana nemansa. hangosa dayayi yana shirin shiga mota yasashi fara kwala masa kira. "Alhaji Muhammad! Alhaji Muhammad!!". Harya saka k'afarsa d'aya ya fito, ganin doctor shu'aibu Na tunkaroshi da sauri sai gabansa yashiga fad'uwa. Doctor shu'aibu yak'araso, "sorry Alhaji Muhammad Labbo! na tsaidaka, so dama....... Sai kuma yay shiru. "Ina jinka doctor, mike faruwane?". Tsayuwa doctor ya gyara, sannan cikin damuwa yace, " sorry Alhaji Muhammad, ko kasan macen tarasu?, kamarma tun kusan a wanni 22 dasuka wuce". A sanyaye Uncle M.A ke kallon doctor shu'aibu, ya dafe kansa dayaji yafara sara masa. Hak'uri doctor yafara bashi, tareda lallashi da masa Nasiha. Uncle M.A baice komaiba yashiga motar, kansa ya kifa a sitiyarin motar yafara hawaye. Kusan mintuna 7 sannan yad'ago, motar ya tada yabar asibitin. ______________________________ Tunda yashigo gidan Innani dake tsakar gida tana alwalar magriba kebinsa da kallo. Jingina yayi da bango, batareda ya saniba hawaye suka fara bin kumatunsa. Da sauri Innani ta k'arasa alwalar, "kai lafiyarka kuwa? Da girmanka kake kuka? Miya faru, yaushe kadawo ma?". Yanda Ammi ta jero masa tambayoyin saiya samu kansa dakuma fashewa da kukan. Shiru Ammi tayi tana kallonsa, jikinta sai rawa yakeyi. Cikin d'an daka tsawa tace, " wai baka jinane?". Share hawensa yayi, sannan yashiga bata labari. Innalillahi ...... Kawai Innani ke iya ambata. Baba na daga d'aki duk yanajinsu, saidai baya iya fitowa sai an fiddoshi, maganar Uncle M.A bak'aramin girgizashi tayiba kuwa. Ana cikin haka saiga Jabeer yashigo shima, nan suka had'u sunata jimamin abin, jabeer ma harda kukansa rurus. Bayan Uncle M.A yashiga sun gaisa da baba, shima yak'ara masa bayani sannan yatafi gidansa danya d'an kimtsa sannan yakoma kar Amatallah ta farfad'o babu kowa a kusa............✍🏻 _Dan ALLAH ina rok'onku Ku ringa turama masu cigiya, saboda ALLAH banida time d'in turama kowa ta PC, amin afuwa saboda uzurina, hakanne zaisa nasan kuna k'aunata😄🥰🥰🥰._ One luv my fans👍🏻 *_ALLAH ka gafartama mahaifanmu😭🙏🏻_* [1/16, 1:05 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_* *_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡 _{home of expert and perfect writer's}_ *_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉ _(Hattara matasa)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_Duk naga comments naku, kuma sun k'ayatar dani gaskiga.🥰🥰sai dai wani Abu yasakani dariya matuk'a, kunsan minene?. Masu cewa Uncle M.A yama Amatallah tsufa😂._* *_Wai miyasa abinda zai iya kasancewa gaske Reader's ba kuson ganinshi a Novel's? Abinda na sani kuka sanine, ko a zahiri mai shekarun uncle M.A ba tsoho baneba, kisamu wani a anguwarku mai d'iyar dazata iya kaiwa 18years, tazam kuma itace d'iyarsa ta Fari ki k'iyasta dashi, ko Wanda yakai shekara 60 yana auren budurwa ai, balle 47years, kuma ko a cikinmu a kwai wad'anda mazajensu suka kai wad'an nan shekarun, my Abdull ma shekarunsa kenan🤣😜._* _mu rubuta abinda azahiri zai iya zama gaske kuce bai daceba, muyi Wanda mu da Ku kunsan bazai yiwuba Ku zagemu kuce muncika k'arya ko🤣._ _koma Yaya dai ALLAH yabar zuminci, Dan mu daku duk munacin amfanin junane, inba mai karatu babu abinda zaisa Marubuci 6ata lokacinsa, hakama inba Marubuci mai karatu bazai samuba littafinba, mun gode sosai, irin Trillion's d'innan🤝🏻🥰🥰😘._ ____________________ *_Number 10_* ____________________ An gudanar da zana'idar iyayen Amatallah a gidan mahaifan Uncle M.A, Innani tasha kuka lokacinda taga gawar Isma'il da matarsa a shinfid'e, lallai duniya batada tabbas ko kad'an.😭 Wandama ya d'aura d'ammara da ita saiya kwance. Babama yashiga rud'ani sosai, dan sai da ciwonsa yayi tamkar zai motsa, sai allurar barci akai masa. Har aka binne su Uncle M.A na kuka, koda suka dawo daga mak'abarta d'akin Jabeer yashige ya kwanta, kuka yake tamkar ransa zai fita. Dolene ka gansa kaji tausayinsa. shima dai daga k'arshe dole allurar barcin Jabeer yasaka akai masa. *_Two days later_* Alhmdllh yau kwanakinsu Baban Ama biyu a k'asa, amma Ammi kwananta uku da rasuwa. Duk da 'Yar Nutsuwa tazoma su Uncle M.A hakan bai hanashi warewa gefe yasha kukaba wani lokacin, musamman inyaje asibiti duba Amatallah da Nazeefa ke zaune da ita, dawata k'anwar Innani, gwaggo Rakiya. Har yanzu Amatallah bata farfad'iba, dan doguwar suma tayi, amma tana samun kulawa daga likitoci sosai. _______________________________ *_Jos_* A jos kam lamari yayi k'amari, k'ank'anin Abu yajawo mutuwar d'aruruwan al'umma da asarar dukiyoyi, abinda yafaru akan SIYASA dalilin wasu marasa jin magana ya rikid'e yazama fad'an k'abilanci da addini. 'Yan jaridu da kafafan yad'a labarai na social media sai baza rahotannin k'arya sukeyi, anrasa jin jinar magana akan dalilin wannan rikici na *SIYASA KO K'ABILANCI!?*. A dalilin hakan kuma wasu gur6atattun matasa masu ruguza zaman lafiya suka kuma tada rikici a KADUNA, ik'irari sukeyi wai ankashe 'yan uwansu dake jihar Jos, dolene suma su d'auki fansa. Ba'awani ja danisaba Kano ta d'auka, babu gaira babu sabar nanma wasu bara gurbin matasan suka haikema wasu k'abilu dake killace awata anguwa da ik'irarin d'aukar fansar abinda akaima 'ya uwansu a Kaduna da jos. Abinda yafaru a kano yabama k'abilun kudancin k'asar suma tada tasu husumar, suka fara kisan 'yan arewacin k'asar a nufin d'aukar fansa😨🙆🏻‍♀. _hum wane irin tunanine da matasan k'asarmune? Mike shiga kanmune? Muke za6ama kammu da k'asarmu irin wannan rayuwar? Wace riba mukeci ko nasara idan mun girmama irin wannan rikice-rikicen dabumuma San tushensuba, karfa Ku manta idan ta rikice da kai da ni duk bazamu shaba, ahalinka da nawa babu Wanda zai tsira, dukiyar k'asarmu zata ruguje, karatunka danawa Dana 'ya'yanmu duk zai zama labari, watak'ilma kaida kazama jagoran fad'ad'a tashin hankalin kaine zaka fara mutuwa ko ahalinka, Ku kalli gagis, zike, k show, dasu aka fara, an tarwatsa ahalinsu da basujiba basu ganiba, Amatallah dabatasan tushen rikicinba an rabata da iyayenta, an tarwatsa mata family saboda son zuciya irinna gur6atattun matasanmu, wad'anda mugun tunaninsu bayasa mu d'aukesu a jerin masu amfani da amfanar da k'asarmu, basuda buri saina haddasa rikicin *SIYASA KO K'ABILANCI!?* Saboda son zuciyarsu, kullum zuciyarsu na karanta musu AMUTU KO AYI RAI ba damuwarsu baceba, da ance an kad'a tambarin SIYASA saikaga jikkunan matasan k'asarmu na rawar Mazarin shirye-shiryen duk yanda takama, basuda zuciyar k'yak'yk'awan fata wa k'asarsu ko nagartar ginata ta hanyar zarran mazatankar samartaka na k'uruciya da ALLAH yabasu. miye ribarka idan an siyeka dawasu 'yan kud'ad'e dankayi jagoranci wajen hallaka ahalinka da k'asarka? Wadda bakada kamarta, bakada Inda yafita, duk Inda zakaje saikazama abin tsangwama da gudu , watak'ilma akiraka d'an ta'adda mai lasisi, bakada damar shan ruwan wata k'asa cikin salama tunda ba k'asarka baceba._ Yanzu haka wad'anda suka baka kud'in duk 'ya'yensu basa k'asarma, sannan su sunada tsaronda babu wani mahalukin daya Isa ya tunkari gefen anguwanninsu ballema yasamu ganin su, amma kai anbaka kud'in siyen ahalinka batareda kayi dogon tunaninaba, basuda Matsala da watsewa ko tarwatsewar k'asar, dan sunada isassun kud'ad'e a ciki da wajen k'asar, sunada lasisin zuwa kowacce k'asa su warwasa batareda an tsangwamesu ba kamarkai daza'a kafama tantin d'akunan tamfol ko buhu ko katako a filin ALLAH ana kiranku da suma *'YAN GUDUN HIJIRA*😭. Abincinma dazakaci ko ruwa saiya gagareka, ballantana maganar lafiyarka ko akasinta. Haba matasanmu, kudawo cikin hankalinkufa, kubar yadda da 'yan jari hujja masu amfani daku wajen amfanuwarsu suna haddasa fad'ace-fad'acen addini ko SIYASA da K'ABILANCI ta sanadinku, ni da ku damuke a arewaci da kudanci duk munada ikon canja mummuna zuwa k'yak'yk'yawa, duk Wanda kagani Asama mune muka kaishi, kuma munada ikon ingizoshi k'asa ayayinda muka fuskanci d'an wawasone akan abinda yake mallakinmu, da wahalhalinmu suke tak'ama da baza riguna da cin zarafinmu suna zare idanu, to muma saimu gyara domun gyaro abinda ke cin dunduniyarmu, mukiyayi saidai RAYUWARMU akan rikicin SIYASA KO K'ABILANCI da wasu tsiraru ke jagorancin haddasa mana domin cimma wani burinsu akanmu, sai matasanmu sunyi gyaran halayensu sannan madafun iko da ragamar k'asarmu zata iya dawowa hannunsu👍🏻. Wannan k'alubalen nakune matasanmu💪🏻💪🏻💪🏻. Amma ta sanadin zaman lafiya a k'asarmu da muhimmin sanin darajar kawunanku, kuyi fatali da duk wani banbancin addini ko k'abila kuzo mu rungumi juna domin kawo sauyi wajen tankad'e da rairayar duk wasu masu rusamu ta k'ark'ashin k'asa, karike na rike ki rike mu rike hannun juna domin maida matasanmu jagorori akan madafun ikonmu💪🏻💪🏻😄. Ta hanyar zaman lafiya da k'aunar junanmu cikin zarrar amsa suna 'yan *NIGERIA* k'asa d'aya, uwa d'aya uba d'aya.🇳🇬 Karmu bari mu ruguje daga ansa sunanmu na 'yan k'asa d'aya dalilin *SIYASA KO K'ABILANCI*🙏🏻😢 Ko shed'ancin wasu jagorori masu nemawa Kansu mutunci kawai👈🏻. a wannan ga6ar dolene masu karatu susojin dangan takar dake tsakanin Alhaji Isma'il Uba da Alhaji Muhammad.🤔 Kubiyo bilyn Abdul domin jin tushen labarin.😊👎🏻 ____________________________ Alhaji Muhammad Ahmad Labbo, shine cikakken sunan Uncle M.A. 'Dane na farko daga Alhaji Ahmad Labbo. Alhaji Ahmad Labbo cikakken basakwace ne d'an kasuwa, kasuwancine yakawoshi garin Kano, a da yakanzo ya sari atanfofi yakoma sokoto, sai dai daga lokacin da tafiya tafara nisa saiya dawo garin na Kano baki d'aya, yasamu shago a kasuwar kwari. A nan Kano ALLAH yahad'ashi da matar aure Zainab (innani). Shekararsu 1 da aure ALLAH ya albarkacesu da haihuwar d'a namiji, Wanda yaci sunan Muhammad (Uncle M.A kenan). bayan Muhammad innani tasake Maijiddah, sai Barirah, (amma ALLAH yay mata rasuwa), sai Jabeer,, Shehu, Nazeefa auta. Gwargwadon iko 'ya'yansu sunsami tarbiyya, sannan sun tsaya tsayin daka domin ganin sun sami ilimin addini dana zamani. Muhammad yarone dayataso k'ark'ashin kulawar mahaifi, dan innani tana kawaici sosai alamarinsa irinna 'ya'yan Fari, bata fad'ar sunansa, sannan kuma bakomaine take sakashi acikiba Amma a k'asan zuciyarta tana matuk'ar k'aunarsa fiyema da sauran 'ya'yanta. Bayan kammala primary d'in Muhammad yadage akan boarding yakeson zuwa, babu yanda iyayensa suka iya suka shiga cuku-cukun kaishi Government secondary school Bichi. A canne ALLAH ya had'ashi da Isma'il Uba Salisu, Wanda rana d'aya aka kaisu makarantar, shi an kawoshine daga Kusada local government dake jihar Katsina. tun daga wannan ranar suka k'ulla alak'ar abota mai k'arfi, suna kiran junansu brothers. Kowa a makarantar ya d'auka 'yan uwan junane makusanta saboda k'auna da tattali dasuke nunama juna. Ko kad'an Muhammad baya k'aunar yaga anta6a Isma'il, haka shima Isma'il d'in, idan aka kama d'aya da laifi, akazo hukuntasa sai d'ayan yay tsale yace shine, dan bayaso ata6a lafiyar d'an uwansa. idan kuwa d'aya bashida lafiya ai saika d'auka dukansune suke jiya. gaskiya akwai k'auna mai k'arfi a tsakaninsu mai kuma ban mamaki. Kafin kace mi duk families nasu sunsan da wannan k'auna tasu. har yazam Isma'il kanzo Kano Hutu gidansu Muhammad, haka shima Muhammad kanje jos ko kusada hutu........ Isma'il Uba salisu shine cikakken sunan Baban Ama, d'an asalin jihar jos ne, Dan anan yataso yaga iyayensa, Su biyu iyayensu suka Haifa, Amina itace babba, sai Isma'il. tun suna k'ananu mahaifiyarsu ta rasu, babansu wanda suke kira da kawu yak'ara auren wata makirar mace mai suna Huzaiyya, takan nuna k'aunarta a garesu agaban mahaifinsu, amma dazarar bayanan tashiga gallaza musu kenan, makircinta yahana kawu fahimtar komai akansu. ana haka ALLAH ya fiddoma da Amina miji, amma fatauci yake zuwa jos shi d'an katsina ne a kusada L.G. wannan yasa koda akai aurenta sai aka kaita Kusada. Tunda Amina tayi aure sai Isma'il yakuma shiga uk'ubar huzayya, wannan yasakashi tada hankalinsa akan shi akaisa wajen 'yar uwarsa Amina. Mahaifinsu bai fahimci komaiba, shi duk tunaninsa Isma'il na kewar Amina ne. Haka ya d'akko Isma'il da kansa yakawoma Amina danufin yayi hutu. Sai dai koda hutun Isma'il ya k'are saiya dage akan bazai komaba, kawu yay lalla6ar duniya Isma'il yace bai komawa. haka dole kawu yabar Isma'il awajen Amina. Mijin Amina ne ya nemawa Isma'il makarantar boarding ta Bichi danya cigaba da karatunsa, tunda yagama primary a jos. Daga wannan lokacinne kuma suka had'u da Muhammad labbo, Wanda yazame masa d'an uwa kuma aboki. Idan anyi Hutu Isma'il yakan fara zuwa kusada ne yay kwana biyu sannan ya wuce jos. Wani lokacin kuma a kano yakeyi gidansu Muhammad, a wani karon kuma su wuce jos shida muhammad d'in suyi acan bayan sunje kano, kokuma kowa yatafi gida, sai bayan kwanki kamar uku zuwa hud'u saiya tafi gidansu d'an uwansa hutun. har lokacin kuma Amina bata haihuba. Ahaka suka kammala karatunsu Na secondary, sun rabu cikin damuwa sosai alokacin, Dan kokad'an basuyi murna da graduate d'in nasuba. Kwanaki bakwai kacal dayin candy d'insu Muhammad yakasa hak'uri yashirya sai jos, sosai Isma'il yay farin cikin ganinsa, hakama kawu. Har zuwa yanzu huzayya tananan da makircinta, amma zuwa yanzu Isma'il baya d'aukar raininta. Haka suka maida Kansu kulum cikin yawo daga Kano zuwa jos, har results d'insu ya fito, suduka sunsami abinda suke buk'ata, wannane yasakasu farinciki. Babu 6ata lokaci kuma aka shiga nema musu makaranta, cikin amincin ALLAH kawu mahaifin Isma'il yay nasarar sama musu a University ta jos. Wannan ne dalilin dawowar Muhammad jos da zama, sai lokaci-lokaci yakanje Kano. Sun fara University babu dad'ewa ALLAH yayma Amina yayar Isma'il rasuwa, sosai rasuwar ta girgiza Isma'il da kawu, hakama Muhammad danya santa sosai. Rayuwar samartakar Isma'il da Muhammad abin sha'awace, dan zaratan samarine masu kulada addini da kare Kansu wajen rud'in zamani da samarinmu ke jefa Kansu. Sun maida hankali sosai akan karatunsu, kuma suna samun nasara sosai. Suna a level two ALLAH yahad'asu da Khadija, yarinya nutsatstsiya itama, tunda Isma'il yaga Khadija yafara k'aunarta, sai dai ya 6oye abin a zuciyarsa da burin saisun kammala karatunsu ya furta mata. Sai dai kash Ashe shima Muhammad ya kamu batareda sanin Isma'il ba, shikam yakasa rik'e hakan a ransa ya furtama amininsa Isma'il. Hankalin Isma'il yatashi sosai, saboda k'aunar Khadija yakeyi sosai, amma haka yayta jarumtar dannewa, yabama brother d'insa kwarin gwiwwa da goyon baya 100%, shinema da kansa ya sanarma Khadija soyayyar da brother d'insa kemata. batawani basu wahalaba ta amince, dandanan soyayya mai k'arfi tashiga tsakanin Muhammad da Khadija. Isma'il kuma yanata yak'in cireta a ransa, dan har k'asan zuciyarsa yagama aminta yabarma d'an uwansa Muhammad ita. Kullum Muhammad kan takura Isma'il akan yakamata shima yayi budurwa, yanda dasun kammala karatu sai ayi bikinsu tare. Dariya kawai Isma'il keyi yace katayani nema brother, nifa har yanzu ban k'yalloba. Suna gab da kammala karatunsu saiga Saliha shima ALLAH yabashi. Muhammad yayi murna sosai, yakuma k'arfafa d'an uwansa. Alk'awalin ALLAH ya cika, su Muhammad sun kammala karatunsu, nanma ansha tata 6urza akan komawar Muhammad kano. Koda Muhammad yakoma gida sai mahaifinsa yajawosa suka cigaba da zuwa kasuwa, ahankali Muhammad ya dilmiya a harkar, ya kware sosai tareda kawo canje-canje masu yawan gaske a kasuwancin mahaifin nasa, kasancewar shi d'an zamanine kuma mai ilimi. Shikam Isma'il yana jos babu abinda yakeyi, lokaci-lokaci dai yakanzo kano, yayi kwanaki ya koma abinsa. A wannan tsakanin auren Isma'il yatashi, ALLAH bai cika musu burinsu nayin aure rana d'ayaba, dan Isma'il ne yafara angwancewa. batun yanda shagali ya kasance 6ata lokacine ma aii.😄 Bayan auren Isma'il Muhammad yakawo musu shawarar sukoma suyi masters nasu, (degree na biyu), 100% Isma'il ya aminta da batun. dan haka suka fara nema a University of Lagos (Lagoon), nanma sunyi nasarar samu kuwa, dan haka suka fara karatunsu cikin nasara. A lokacin Saliha matar Isma'il nada ciki. Rashin auren Muhammad yafara damun Isma'il, dan haka yafara takura masa akan maganar Khadija. Amsar daya saba bashice yakuma maimaita masa, akan yana jiran Khadija ne kamar yanda iyayenta sukace saita kammala karatu ta. "Haba brother, kaikuma saika zauna saita kammala d'in?". Dariya Muhammad yayi, yadafa kafad'ar Isma'il yana fad'in " cool dawn mana my brother, duka kwana nawane yarage? Insha ALLAH baifi watanni 7 bafa kaima kasani". "Haka kullum kake fad'a, amma har yau ni banga wata bakwai d'in zata k'areba, kuma mizai hana kaima baba magana a tsaida rana tun yanzu, bayan ta kammala sai musha biki kawai". Shiru Muhammad yayi yana nazarin maganarsa, zuwa can kuma yace, " gaskiyarka fa brother, kaima kazo da shawara". Babu 6ata lokaci sukayi amfani da shawarar Isma'il aka kai kud'i aka tsaida rana, sai ta kammala karatunta. Watanni bakwai na cika kuwa akasha biki, lokacin Saliha ta haihu d'an baizo da raiba. Wattani shida tsakani saliha yakuma samun wani cikin, amma Khadija dai babu labari. Watanni tara cif Saliha ta haifi d'iyarta mace k'yak'yk'yawa. Muhammad yayi matuk'ar farin ciki, tamkar shi aka haifamawa, komai kuwa Na hidimar sunan baby Muhammad ne yayishi, hatta da suna ma shine yarad'a mata Khadija, sunan mahaifiyar Isma'il, kuma matarsa. Tun daga wannan lokacin Muhammad yad'auki son duniya ya azama Khadija dasuke kirada (Amatallah), komai yagani Na yara saiya siya matashi, kullun firarsa akan best daughter d'in sace. A haka suka kammala degree d'insu Na biyu daga lagos suka dawo gida, Isma'il jos, Muhammad kano. Muhammad yacigaba da kulada kasuwancin baba, kuma har zuwa lokacin ko 6atan wata Khadija batayiba, duk k'arshen wata Isma'il kan d'akko iyalansa suzo kano, kokuma shi Muhammad yaje danasa iyalan.................✍🏻 Kubini bashi a page 11 please🙏🏻😄 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [1/16, 1:05 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_* *_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡 _{home of expert and perfect writer's}_ *_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉ _(Hattara matasa)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_Ku gargad'i mai gina ramin mugunta!! 📻_*😥👈🏻 Wannan gaskiyane *Doctor Alhaji mamman (shata)* ALLAH ya gafarta maka🙏🏻 ____________________ *_Number 9_* ____________________ A k'ofar gida yay parking motar sa, sannan ya kama k'ofar zai bud'e, a rufe take. Shiru yayi yana kallon k'ofar, yasan tunda baya nan bazasu ringa barin k'ofar a bud'eba. Mota ya koma ya d'akko wayarsa. Aneesa yakira. A yangance tamasa sallama. Shikuma ya amsa murya na rawa. Gabantane yafad'i, tacire wayar daga kunnenta ta kuma kallon screen d'in domin tabbatarwar shine kokuwa?. ganin shid'inne yasata maidawa a kunnen. "My dear! Lafiya kuwa?". Ajiyar zuciya ya sauke, a raunane yace, " kizo ina k'ofar gida...... Bata jira yakai k'arsheba tafito da sauri. K'aramar k'ofar gate d'in ta bud'e ta lek'a. A tsaye ta gansa ya jingina da jikin gate, gabanta yakuma fad'uwa, hakan ya kuma tabbatar mata babu lafiya. Takowa yayi ahankali yashiga gidan, ta kalleshi tana fad'in "dear motarfa". Kansa ya girgiza mata yace, " fita zan kumayi". yana maganar yana tafiya. Wannan yasata binsa da sauri itama. babu kowa a falon k'asa, dan haka ya haye samansa, Aneesa na binsa abaya. A kan gadonsa ya zube yana sauke numfashi, Aneesa ta zauna kusadashi tana tambayarsa miyafaru cikin damuwa. Bai bata amsaba, sai dai cewa yayi ''had'amin ruwan wanka". Jiki a sanyaye tamik'e zuwa bathroom d'insa, ruwa mai d'an zafi ta had'a masa, tana niyyar fitowa shikuma yashigo, matsawa tayi yashiga sannan ta fita. Yana wanka yana hawaye, lallai duniya abar tsoroce, jiya iyanzu yana tareda amininsa, amma yanzu gashi awani hali mai rikitarwa, ALLAH sarki Saliha, ALLAH ya gafarta miki😭. Aneesa kam da sauri ta sauka k'asa zuwa 6angaren uwargidanta. A falo ta iskesu itada yara suna homeworks d'in makaranta. Yanda tashigo a rikice yasaka Umman abulkhair saurin kallonta, "lafiya kuwa momyn yara?". " inafa lafiya ummansu.........nanda ta sanar mata abinda ta Sani gameda canjawar mai gidan nasu, da dawowar babu zato babu tsammani da yay musu, alhalin gobene yakamata yadawo. Atare suka fito zuwa d'akinsa. Bai fitoba, dan haka suka zauna zaman jiransa. Babu dad'ewa yafito, sannu da zuwa Fateema tamasa. Batareda ya kallesuba ya amsa yana k'ok'arin shinfid'a abin sallah. Sallar magriba ya gabatar, sannan yay isha'i, duk suna zaune suna kallonsa. Yay addu'a yana share kwallar dake bin kumatunsa. Sosai jikin matan nasa yakuma yin sanyi k'alau, sun k'agara ya idar suji mike damunsa. Ganin yanda suka damu matuk'a yaga baidace yabarsu a duhuba, cikin dauriyar danne hawayensa yaymusu bayani. Daga Aneesa har Fateema kuka suke sosai. Mukullin mota da wayarsa kawai ya d'auka yafita zuwa asibitin, yabarsu Aneesa nacigaba da kukansu. A motama yana driven yana hawaya, yakasa jarumtar danna kukansa, tausayin Amatallah da abokinsa kawai ke nuk'urk'usar ruhinsa. a haka ya Isa asibitin. Jabeer da kawunsu Malam Yakubu ya tarar suna jiran isowarsa. Gaida kawu Yakubu yayi, ya amsa tareda masa ta'aziyya sannan suka k'arasa ciki. Inda aka kwantar da baba sukaje, suduka kallo d'aya suka masa suka fara hawaye. Ba k'aramar k'una baba yasamuba gaskiya, abin ko dad'in kallo babu. barci yakeyi saboda sunmasa allurar barci kozai samu sauk'in rad'ad'in dayakeji. Jiki a sanyaye sukabar d'akin, inda Amatallah take sukaje, tana kwance kamar yanda ya barta. matuk'ar tausayinta ya mamaye zukatansu, Uncle M.A ya kauda kansa daga kallonta saboda hawayen dasuka cika idonsa, d'an yatsa d'aya yasa ya goge sannan yanemi gefe ya zauna. ______________________________ Uncle M.A da Jabeer a asibitin suka kwana. Wajen k'arfe 7:am suna shirin tafiya da gawar Ammi gida dan amata sutura Amatallah ta farfad'o. Da sunan iyayenta ta farka a baki, tana kuka tana kiran Ammi da baba ta. da sauri wata Nurse taje ta sanarma doctor shu'aibu Amatallah ta farka. Dagashi har Uncle M.A a hanzarce suka k'araso. Tana ganin Uncle M.A tamik'e da sauri tana fad'in Uncle ina Ammina da babana!, suna ina dan ALLAH Uncle? ". Rasa mizai fad'a mata yayi, yay tsaye kawai yana kallonta, idonsa taf da hawaye. Doctor shu'aibu ne kawai ke lallashinta. da k'yar yasamu ta tsagaita da kukan. Doctor yamatso kusada Uncle M.A, ahankali yace, " Alhaji Muhammad yakamata mubarta taga gawar mahaifiyarta........ Bai k'arasaba Jabeer yashigo yana hakki, ''yaya! Yaya! Kuzo yaya Isma'il ne, gashi can....... Suduka basuji k'arshen maganarba suka fice da gudu, harda Amatallah dake binsu cikin layin rashin k'arfin jiki. 'Dakin da Baban Ama ke kwance suka shiga. Hannunsa dabai k'oneba sosai yake mik'oma Uncle M.A, yana kiran brother a ahankali. ga numfashin sa Na fita da k'yar. Uncle M.A ya k'arasa da hanzari gareshi, shima hannun ya mik'a masa yana hawaye da fad'in sannu brother....... Dai-dai nan Amatallah tashigo tana tangad'i, kawu yakubu da wasu mutane hud'u suma suka shigo d'akin. K'ara Amatallah ta kwala tazube awajen saboda tozali datayi da babanta. Dukansu kanta sukayi har Uncle M.A daya zare hannunsa daga na babanta. Baisan ya cacumotaba yana kiran Khadija! Ke Khadija!! Please karkimin haka kema dan ALLAH Khadija. Innalillahi wa'inna ilaihirrajiun, ya ALLAH gareka nake, a gareka kuma nake neman taimako......yak'arashe maganar yana fashewa da matsanancin kuka. Shima Jabeer kukan yafara ganin yanda yayansa ke kuka sai kace ba babban mutum ba. Baban Ama ma hawaye yake yana murmushi da kallon abokinsa da d'iyarsa. Da k'yar doctor shu'aibu yasamu ya janye Amatallah daga jikin Uncle M.A. 😭kai jama'a, ALLAH ka gafarta mana.🙏🏻 Kusan mintuna 16 aka samu komai ya lafa, amma Amatallah tana a halin doguwar suma. Uncle M.A ya koma inda Baban Ama yake, saboda kiran sunansa kawai yake. Yanzuma hannunsa yarik'e, ahankali yake iya magana, amma duk suna jinsa sabida shiru da d'akin yayi. _"d'an uwana kaga yanda k'addara tayi damu, tsakanin jiya kawai zuwa yau, mungodema ALLAH brother, danshine mafi hikimar masu hikima akan hakan, mutuwa tabbatacen abune akan kowanne bawa, saidai kowa akwai sanadin tafiyarsa brother, wannan mu shine namu sanadin d'an uwana, duk duniya banida kamarka, dukda inada dangi amma kafisu matsayi agareni, sun kashemin Saliha ta hanyar soka mata wuk'a, awannan halin na isketa bayan dawowata sallar magriba, nikuma sun kunnamin wuta, tabbas nasan yaran da Khadija taganine sukai wannan aikin, brother! Na d'auki hakan a matsayin K'ADDARARMU, ga Khadija nan nabaka halak malak, ita kad'aice tarage mini, babu kuma mai iya rik'emin ita tamkar ni sai kai d'an uwana Muhammad, ba ruk'on Amatallah kawai nakeso kayi nawani d'an lokaciba, sonake ta kasance a gareka har k'arshen rayuwarka. brother inaso yanzunan a d'auramaka aure da Khadija..."_ Wata muguwar zabura Uncle M.A yayi, jikinsa da muryarsa na rawa yace, ''brother mikake fad'ane haka?, haba brother khadija fa d'iyatace, inajinta tamkar su Saifudden ne a zuciyata, karkayi haka dan ALLAH brother, gara kace na aurama j........ _Da sauri Baban Ama ya katseshi cikin hawaye, "a'a brother karkace komai dan ALLAH, inhar nid'in d'an uwankane da gaske, bakuma k'yamar had'a zuri'a kakeyi daniba ka amince da auren Khadija tunda ALLAH bai haramta makaba, karkayi dubi da d'iyatace, kasancewarta a wajen kane kawai zaisaka ruhina nutsuwa a cikin kabarina, inada tabbacin har Abadan bazaka ta6a barinta tayi kukan rashina ni da mahaifiyarta ba, duk Wanda zaisan muhimmancin Khadija ko kulawa da ita bayankane, dan ALLAH ka amince, danni lokuta k'alilanne suka rage a cikin dak'ik'un rayuwata, brother nima mutuwa zanyi, insha ALLAHU tare zaku bunne gawata data matata, bazan rayuba brother, Nika d'ai nasan minakeji, please ka amince dan girman ALLAH da k'aunar dake a tsakaninmu._ Kowa a d'akin kuka yakeyi saboda tausayi. Uncle M.A yana kuka yace, " indai hakan zai sakaka farinciki na AMINCE brother, na amince da auren Khadija dukda ina kallonta a matsayin d'iyata, insha ALLAHU zaka tashi brother, cuta ba mutuwa baceba.......... Kasa k'arasawa yayi saboda kuka daya sark'esa. Baban Ama ya k'ara k'ank'ame hannun Uncle M.A yana fad'in "ngd da amincewarka brother, kasani farinciki, zanbar duniya cikin shauk'in farincikin ganin auren Khadija da ALLAH yabani ita d'aya tilo a duniya, ALLAH yasaka farinciki da kwanciyar hankali a rayuwarku, ALLAH ya hana duk wani azzalumi tasiri akan wannan aure, ina rok'on alfarmar a d'aura yanzunan brother kafin numfashina ya k'are. Kai kawai Uncle M.A ke d'aga masa yana zubda kwallah ***** Kawu yakubu da sauran mutane hud'u, sai doctor shu'aibu da abokan aikinsa doctors kusan 10+, sai Jabeer dawasu mutane k'alilan masu jiyya suka shaida d'aurin auren *_Alhaji Muhammad Ahmad labbo da Khadija Isma'il uba (Amatallah)_* akan sadaki naira dubu 30 da kawu yakubu yabada, bayan Jabeer yayi saurin zuwa ATM ya fidda, kawu yakubu ne wakilin ango, yayinda Baban Ama da kansa yay waliccin auren d'iyarsa tilo Khadija (Amatallah). Ana gudanar da d'aurin aure cikin dariya da tsantsar farinciki, amma nasu Amatallah acikin kuka da tsantsar k'unar rai aka d'aurashi, babantane kawai keyin kuka da murmushi lokaci d'aya. Cikin farin ciki ya k'ank'ame hannun Uncle M.A yana masa godiya, tareda k'ara jaddada masa Amanar Amatallah. Kuka kawai Uncle M.A keyi yana fad'in "brother bazaka mutuba, kabar fad'a domin ALLAH, cuta ba mutuwa baceba brother.... Murmushi mai ciwo Baban Ama yayi, " brother sai dai hak'uri, mutuwa kam tazama tilas, ka tabbatarma Khadija na yafe mata, ALLAH ya albarkaci rayuwarta, yasaka mata hak'uri da juriyar danganar rashinmu, tayi hak'uri da k'addarar data shigowa rayuwarta, watarana sai labari, badan ALLAH baya sonta bane ya d'aukemu, watak'il hakan shine mafi alkairi a rayuwarta, ngdma ubangiji dayabamu damar rayuwa da ita na tsawon shekaru 18, har zuwa yau danaga aurenta, ALLAH yayi mata al ....bar.... ka....... Baban Ama ya k'arasa maganar a rarrabe, ahankali kuma yafara kalmar shahada. Lamarin daya rikita Uncle M.A kenan ya rungume Baban Ama yana kuka mai ciwo da k'unar zuciya...... Jin jikin Baban Ama ya saki yasaka Uncle M.A d'agowa yana girgizashi da kiran Isma'il! Isma'il!!!! Please karka tafi kabarni dan ALLAH, brother karka tafi please......... Yanda Uncle M.A ke kuka da sambatu sai da kowa ya koka awajen, da k'yar aka iya janyeshi akan gawar Baban Ama, aka lullu6eshi da farin bedsheet d'in dake kan gadon. 😭😭😭😭😭 🙏🏻ya ALLAH ka gafarta mana. Mutuwa kenan 'yan uwa, bata kwankwasa k'ofar kowa, babu d'an sak'on isowarta, babu alama ko yanayin alamomin kusantuwarta. Saika gama shagala da duniyar kawai saikajita, babu shamaki tsakanin mutuwa da d'an Adam, koka shirya, kobaka shiryaba saita d'auka, komai girman mulkinka ko dukiyarka ko talauci, komin yawan mak'iyanka ko masoya saika tafi, karki manta, karka manta, karna manta, 😢😓😥😰😭👈🏻, ni da kai da ke da su duk zata iya d'aukarmu yanzunnan, wlhy duk sai mun mutu muma😭😭😭😭😭. Suda suka tafi basuyi sauriba, muda muka rage bamuyi jinkiriba narantse muku😭..............✍🏻 *_Yau kam inason naga comments ruwa-ruwa akan auren Amatallah da Uncle M.A, a kowanne groups, inba hakaba ALLAH bazan cigaba da typing ba sai sabuwar shekara idan ALLAH ya kaimu. Yawan comments d'inku yawan kwarin gwiwwarku gareni, inhar banji k'yashin typing ba, baikama kuji k'yashin comments dabai wuce layi biyu zuwa uku ba gaskiya. Idan kunason naciga, nagani a k'asa🤷🏽‍♀. Dan yanzune labari zai fara😊_* *_YA ALLAH ka gafartama banana._*😭🙏🏻 [1/16, 1:05 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_* *_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡 _{home of expert and perfect writer's}_ *_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉ _(Hattara matasa)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* ____________________ *_Number 11_* ____________________ Rayuwa tacigaba da tafiya musu a cikin nasarori, Isma'il yafara aiki anan jos, amma Muhammad yacigaba da kasuwanci, babu ma maganar Neman aiki a tsarinsa. Kwanaki sunyi saurin zama shekaru, harga Amatallah da shekaru bakwai a duniya, duk hutun duniya kuma a kano takeyinsa, tattali da kulawa mai ban mamamki take samu daga khadija da muhammad, bazaka ta6a cewa ba d'iyarsu baceba, tayi masifar sabo dasu sosai. itama dai mamanta tundaga ita babu wani labari, haihuwar taimusu cak ta tsaya. kamar yanda matar Muhammad itakuma sai a lokacinne ALLAH yabata ciki, fad'a muku murna da farincikin dasukayima 6ata lomacine, amma kam lamarin ba'a magana kam. Watannin cikin Khadija 9 da kwana 9 tafara nak'uda, tasha wahala matuk'a wajen wannan haihuwa, da k'yar ALLAH yabata ikon haihuwar yaro namiji, sai dai tana haihuwarsa koma ganinsa bataiba ALLAH ya d'auke kayansa, ta rasu😭. Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, fad'a muku rud'anin da Muhammad yashiga 6ata lokacine ma, murnar haihuwa tazama kukan rasuwar Khadija da rud'anin da Uncle M.A ya tsinci kansa. yaronma kwanansa uku a duniya yakoma. Halinda uncle M.A yashiga sai da yakaishi ga kwanciya asibiti, kusan tsawon sati biyu sannan aka sallamosa, suka cigaba da masa addu'ar ALLAH yabashi dan gana. Tundaga wannan lokacin rayuwar uncle M.A ta canja baki d'aya, yazama silently, maganama bayasonyi, inkaga maganarsa babane kokuwa isma'il Baban Ama. Shima Baban Ama a 6angarensa lokacinne kawu mahaifinsa ALLAH yamasa rasuwa, wata d'aya tsakaninsa da Khadija, shima kan yashiga rud'ani sosai, Dan yana k'aunar mahaifinsa, shikad'ai ya rage masa, gashi kuma yatafi. Aifa rasuwar kawu takuma rikita Uncle M.A, dole baba yaymasa shiri yabar k'asar, yakoma Ghana da zama wajen wani abokin Baban. Uncle M.A yacigaba da zama a Ghana har tsawon shekara uku, ganin karyayta zaman banza sai kawai yafara karatu na wani cause. A Ghana Uncle M.A yahad'u da Aneesa, anan makwaftan abokin baba take, tunda tagansa tarikice, sai dai takula yana cikin matuk'ar damuwa, wannan yasata d'aura d'ammarar dawo masa da farincikinsa, musamman data samu cikakken bayani akan tarihin rayuwarsa. Tasha matuk'ar wahala kafin tasamu kan Uncle M.A, kafin komai ya dai-daita Soyayya mai k'arfi tashiga a tsakaninsu. Aneesa k'yak'yk'yawace sosai gaskiya, gata nitsatstsiya, ga kuma ilimi, (kunsan dai 'yan Ghana suna karatu sosai), k'yawwawan halayen Aneesa ne sukajawo k'aunarta mai k'arfi a zuciyar Uncle M.A. Sai dai kuma lokacin da Uncle M.A yashirya yazo Nigeria danya fad'ama baba a kai kud'in aurensa saiya tarara an saka masa ranar aure shida Fateema d'iyar kawu yakubu k'anin innani, hankalinsa yatashi, amma bashida yanda zayyi, danshi mutumne dabai k'etare maganar iyayensa, dasunce yayi yakeyi, Dan haka ko'a fuska bai ta6a nuna bayason auren Fateema ba, sai dai yasanarma mahaifinsa abinda yazo dashi shima. Baba yaji dad'i sosai, babu kuma 6ata lokacin aka d'aura aurensa da Fateema, bayan sati uku sukaje Ghana kai kud'i, sai dai iyayen Aneesa basu wahalar dasuba sukace kawai a d'aura auren ya d'auki matarsa, tunda abune ba k'asa d'ayaba, su baba sunyi farinciki dakuma jinjina dattako irinna iyayen Aneesa. A kwana biyu akayi komai aka gama, aka basu amaryarsu. Uncle M.A bai gayama Aneesa aurensa da Fateema ba saida suka iso Nigeria. Ai kuwa Aneesa tayi matuk'ar birkice masa, sai da yasha bak'ar wahala kafin yasamu kanta lokacin. Aneesa da Fateema ba gida d'aya yahad'asuba lokacin, Dan gidanshi da yazauna da Khadija ginin mace d'ayane, kuma bashida k'arfin yin gini, dole yakamawa Aneesa haya anan cikin anguwar, babu nisa da gidansa Inda Fateema take. Dukkan hidimar bikinsa biyu Isma'il ne tsaye, (Baban Ama), Dan zumincinsu nan, duk da yanzu yanayin aiki kansasu yin watanni basuga junaba, amma kullum suna mak'ale da waya. Bakuma ko yaushe iyalansu ke zuwa gidajen junaba, saboda Saliha ta girmi su Fateema, kuma batawani saba dasuba sosai kamar Khadija, amma suna girmamata gaskiya. Baba ya tattara dukkan kasuwancinsa ya mik'ama Muhammad gaba d'aya, yace yacigaba da juyawa kawai, tundaga lokacin uncle M.A yakoma kasuwa baki d'aya, dukda yana wani aiki a nan B.U.K Ubangiji ya sakama kasuwancin hannu, dandanan shagon atanfofi ya bunk'asa, har suka bud'e wani. Shekara d'aya da auren matansa duk suka haihu, amma Fateema Ce tafara haihuwar Namiji, aka saka masa Ahmad suna kiransa (Abulkhairi) saboda sunan babane, Aneesa ma ta haihuwa, sai dai d'iyar batazo da raiba. A cikin shekara biyu Uncle M.A harkar kasuwa takuma fad'ad'a, dan zuwa yanzu sunada kusan shaguna Hud'u, sunada shagon atanfofi, shaddoji, materials, gale, kaya 'yan kanti, dakuma kayan yara, kowanne nau'in sittira kaje saika samu a shagonsu. Zuwa lokacin Aneesa ma ta haihu, Namiji, Wanda yaci sunan Abdul'aziz (Saifudden), sunan babanta. Shekara d'aya tsakani itama Fateema tasake haihuwar Namiji Isma'il (yayma Baban Ama takwara😄), yana cemasa Sahibi, (Sahib) kenan. A lokacinne kuma yagama ginin gidansa daya d'auki tsawon shekaru uku yanayi, ya had'e matansa duka a waje d'aya. Had'uwar Aneesa da Fateema kam bata zama da sauk'iba, Dan rikici sosai akaita sha, Aneesa tanada kishi sosai, bata k'aunar ganin abinda zai ra6uda mijinta ko kad'an😄. Itama Fateema a kwai kishin, amma tafi Aneesa wayau Na 6oyewa. Sai da yaymusu zagir-zagir sannan yasamu sauk'in yawan rikicinsu, daganan aka koma kishin kissa, to duk masu ilimi aka tara, dolene salon kishinsu yayi matuk'ar bigeka gaskiya, Dan kowa sotake tazama star a wajen boss. Zuwa yanzu Fateema Nada 'ya'ya uku, Ahmad (Abulkhairi) Isma'il (Sahib) Ai'sha mai sunan mamanta (Ummita). Aneesa nada biyu, Abdul'aziz mai sunan babanta (Saifudden), Sai Zainab mai sunan Innani (Siddiqa). Shekaru uku dasuka wuce ciyo yasamu baba, kad'an-kad'an abin ya fara masa, tun suna magani a tsaitsaye harya kwanta rijuf, sosai Alhaji Muhammad ke tsaye akan ciwon baba, sunje asibitoci da dama Nigeria amma lamarin sai dai addu'a kawai, ciwon koya tafi saiya dawo, saboda yahad'a da girma, ciwon baba dakuma harkar kasuwancinsa daya bunk'asa, ga aiki yahanashi ziyarar jos, sai dai koyaushe Baban Ama Na hanyar duba jikin baba, wani lokacin suzo da Ammi wani lokacin shi kad'ai, Amatallah kam bata biyosu, tun wani zuwa datayi ita kad'ai Hutu su Aneesa sukayi fad'a a kanta itada Fateema tace bata sake zuwa. Koyaya su Ammi sukayi da ita saitak'i biyosu, in zasuzo saitayi tafiyarta gidan ka kanninta iyayen Ammi, Dan zuwa lokacin tafara zama budurwa, tana secondary kusan js 2, duk da yakamata acema taje SS, amma yawan rikin da jihar jos ke fuskanta yasaka karatun yana samun koma baya a jihar sosai. Kullum zancen Uncle M.A ina best daughter d'insa? yakamata tazo masa Hutu. Amma k'iri-k'iri Amatallah tak'i. Hak'ura yayi yabarta saboda shima ciwon Baban da dawowar nauyin gidansu gana iyali ya gama d'auke hankalinsa, ga kuma aiki dayakeyi duk da ba kullum yake a office ba dai. Kwatsam sai Baban Ama yasamu wani mai Maganin gargajiya, ya d'aukeshi sukaje har Kano domin duba baba, Alhmdllh kuma aka dace, Dan baba nasamun sauk'i sosai da wannan Magani, bayan yak'arene Uncle M.A yazo jos kuma kar6awa baba wannan Magani. Anan yaga yanda Amatallah ta girma, duk saiya rikice da mamaki da al'ajabi, Dan yanzu tana shekara 19, SS 3 kuma a Secondary, sune zasu zana SSCE a wannan shekarar. ya d'aukko hotunanta dan nunama matansa suga yanda ta koma, amma sai kishi ya rufe musu ido, suka fara tunanin ko sonta yakeyi, saboda motsi kad'an yace, "my best daughter". Shikuma kawai mamakin yanda tayi girmane ya tsaya masa a zuciya bawani abuba. amma matansa sun hau sun zauna sonta yakeyi. To kuma ga yanda al'amarin ubangiji ya kasance, Ashe ALLAH ya k'addarata acikin matansa Na aure😭. Wannan shine asalin labarin wad'annan brothers guda biyu. Hummmm koya zata kaya kuma idan matan Uncle M.A sukaji a gaske Amatallah tazama matar mijinsu, kishiyarsu, tabbas a kwai cakwakiya.😄 Ku dai Ku kasance dani bilynku kawai. *_WASA FARIN GIRKI!! My fans_*🤩 Mukoma labari👎🏻 _____________________________ Hankalin Uncle M.A yatashi, yanda yaga rikicin ya fad'ad'a har zuwa wasu jihohin, bak'amin ta6a zuciyarsa lamarin yay ba, musamman daya tuna babu brother d'insa yanzu a doron k'asa, dama a wajensane yasamu kwarin gwiwwar kafa k'ungiyar dazata farkar da matasan, a yanzun kam baisan ta Yaya zai tunkari lamarinba, sai dai insha ALLAH zaiyi k'ok'ari wajen hana kansa rashin k'warin gwiwwar aikin alkairin daya kulla niyya, shawarar da amininsa brother d'insa yabashi itace zata zam jagora wajen k'aiminsa da wanzuwar himmarsa........ Ringing d'in wayarsane yasashi sakin ajiyar zuciya, hannunsa yasa yafara lalubenta a gefensa, Dan kwance yake a kan gado, tunda yadawo sallar asubahi yakuma d'an kwanciya, saboda tunani baya barinsa samun isashen barci, tunanin jikin baba da rashin d'an uwansa, ga kuma Amatallah da aurenta, Dan har zuwa yanzu bata farfad'oba, iyalansa kuma basusan da aurenba. Ganin sunan doctor Shu'aibu yasashi d'aga wayar da hanzari, ko gaisawa basuyiba doctor Shu'aibu ya shaida masa Amatallah ta farfad'o, kuma Alhamdllh cikin hayyacinta, sai dai tanata kuka da kiran iyayenta. Da hanzari ya diro daga kan gadon, jallabiyarsa daya dawo masallaci ya d'auka ya Sanya, ya d'au key d'in mota yafita da sauri. A falon k'asa yaci karo da Fateema dake k'ok'arin had'a break fast saboda yara zasuje makaranta. "A'a lafiya kuwa Nurri? Saurin mikakeyi haka?". Bai ko juyo ya kalletaba yace, " zanje asibiti ne, Amatallah ta farfad'o". Duk da tana matuk'ar tausayin yarinyar, amma sai da zuciyarta ta sosu, taraka bayansa da kallo harya fice daga falon, wani takaici yadaki zuciyarta akan mazarin da mijin nasu keyi. (Wata zuciyarta tace, aiko baikamata kiji haushinsaba, Dan babu Wanda ya cancanci damuwa da lamarin yarinyarnan sama dashi, kiduba halin data shiga mana). A sanyaye Fateema tace, "hakane kuma, ALLAH kabani hak'urin jure duk abinda zan gani". Nace, " to amin uwargida".😊 ******** Uncle M.A a rikice ya isa asibitin, tun a k'ofar d'aki yay karo da gwaggo Rakiya tana kuka, bai ce komai ba yashiga d'akin da Amatallah take. Doctor Shu'aibu Na tsaye kanta, sai Nazeefa dake zaune gefen gadon rungume da ita, kuka takeyi rurus da fad'in a kaita taga babanta da Amminta. A hankali Uncle M.A ya sauke ajiyar zuciya, ya k'araso gaban gadon idonsa akan Amatallah. d'ayan gefen gadon yaje ya tsaya, ya kalli doctor Shu'aibu a raunane. Jin jina masa kai doctor Shu'aibu yayi, tareda masa nuni ya lallasheta da idanu. Uncle M.A ya jinjina kansa, sannan yay k'ok'arin maida kwallar idonsa yana cije le6ensa Na k'asa. Alama yayma Nazeefa ta barta ta fita itama, saboda doctor Shu'aibu shima yafitan. Nazeefa ta zare jikinta daga Na Amatallah, ta sakko daga gadon. Hakanne yasaka Amatallah d'ago jajayen idanunta, tana ganin Uncle M.A tak'ara k'arfin kukanta tana fad'in "Uncle ka kaini naga babana da Ammina Dan ALLAH". Bai ce komai ba har Nazeefa tafita. Sannan ya zauna a bakin gadon kusada ita, hannu yasa ya jawota kusadashi ya rungumeta kawai, tuni idonsa suncika da kwallah, harsun fara taruwa a gefen idonsa. Rud'anin da Amatallah take cikine yahanata mamakin rungumar da uncle yaymata, Dan tunda tafara girma da wayo ya daina rik'e koda hannuntama. jinta a jikinsa yasakata kuma fashewa dawani kukan mai tsuma rai. d'an yatsa d'aya Uncle yasaka ya d'auke hawayen dasuka taru masa a gefen ido, ya k'ara rungume Amatallah sosai ajikinsa, cikin daidaita muryarsa yace, " Khadija! ". Yanda yakira sunantane yasakata tsaigaitawa da kukan, amma bata amsaba. Ya kuma fad'in " Khadija! Kina jina?". Cikin da shashshiyar muryarta ta amsa da "Na'am uncle"..............✍🏻 🤩👎🏻 Inaga maybe gobe idan ALLAH ya kaimu bazaku ganniba gaskiya🥰🥰🥰🥰. Idan kuma naga comments yanzu idan nadawo anguwa nayi muku😂. One Luv my fans🥰 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [1/16, 1:29 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_* *_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡 _{home of expert and perfect writer's}_ *_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉ _(Hattara matasa)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* ____________________ *_Number 12_* ____________________ Shiru yad'anyi Na wani lokaci, kafin yagyara mata kwanciya a jikinsa, murmushi yayi mai ciwo sannan yace, "Khadija duk duniya wayafi kowa a halittun ALLAH?". 'Dan d'agowa tayi ta kalleshi kad'an, sai kuma ta maida kanta a gefen hannunsa, muryarta a dusashe tace, " MAZON ALLAH (S.A.W) Uncle ". Lumshe idanunsa yayi yana fad'in " masha ALLAH Khadija, yanzu yana ina?". Yanzun kam tashi tayi sosai tabar jikinsa, jingina tayi dagadon idonsa Na kanta. "Uncle ya koma ga Ubangijin sammai da k'assai". ''Alhmdllh Khadija, yakikeji darashin kasancewarsa a duniya". Mamakin tambayoyin Uncle suka fara bata, amma saita dake tace, " inajin babu dad'i, amma nayi hak'uri tunda ubangijine ya tsara hakan, ina dai Addu'ar ALLAH ya sadamu dashi a ranar ceto". Kansa yakad'a mata, muryarsa takuma sanyi fiyeda sanyin datake dashi, yakamo hannayenta biyu yarik'e a nasa, "Khadija ke musulma ce kuma mumina, kinsan k'addara da jarabawa, duk wani mumini akwai irin jarabtar da ALLAH kanyima rayuwarsa, wani yabashi dukiya mai tarin yawa, amma bashida lafiya, wani talauci amma yanada lafiya da 'ya'ya, wani ilimi amma sai ya jarabceshi da hatsabibiyar mace ko shi d'in ya kasance hatsabibin, ko cikin 'ya'yansa, wani haihuwace ALLAH bai bashiba, wani ya haihu 'ya'yan sun zame masa fitina, wata macen gidan mijine jarabtarta, wata rashin aure, wata rashin lafiya, wasu kuma saikiga ALLAH ya had'a musu komai Na rayuwa, sai dai kinsan wani Abu?". Amatallah ta girgiza masa kanta. Yacigaba da fad'in kowanne irin matsayi ka taka a rayuwarka inhar bakajin tsoron ALLAH ba to kaifa ba komai baneba, duk k'ask'ancin waninka inya kasance mai tsoron ALLAH toya fika agareshi, ubangiji shika d'ai yasan iya adadin halittun daya halitta masu numfashi a duniya, kuma shine ya tabbatar mana duk sai ya d'and'ana mana mutuwa, wad'anda suka rigamu tafiya ba sauri sukayiba, muda muka rage bamuyi jinkiriba. A wannan ga6ar ina mai baki hak'uri, da rok'onki akan kizama cikin bayi masu ambaton Alhamdullahi ala kulli halin aduk yanayin dasuka tsinci Kansu a rayuwa, ki kar6i jabawarki da hannu biyu dankizama cikin salihan bayi muminai..........." Hawayene masu zafi suka fara zarya a kumatun Amatallah, tabbas bayanan uncle namata nuni akan babu babanta a duniya, ahankali tace, "uncle babana yarasu ko? Karka 6oyemin, kafad'amin, insha ALLAH zuciyata zata iya d'auka, domin ubangiji baya jarabtar bawa da a binda bazai iyaba. namaka alk'awarin kasancewa cikin bayin ALLAH masu hak'uri da kar6ar jarabawa ko wacce iri". Da k'yar ya iya had'iye wani kulutu daya tokare masa k'irji, sannan ya d'aga mata kai a hankali shima hawaye nabin nasa kumatun. Jikinsa kawai tafad'a tasaki kuka mai tsuma rai, hannu biyu ya kar6eta ya rungume, suka cigaba da rairawa a tare, abin gwanin ban tausayi. Sun d'auki tsawon lokaci ahaka kafin Amatallah cikin kuka tace, " uncle Ammina fa?". "Sai hak'uri Khadija, Saliha tama rigayi brother ra..s....u...wa...". yak'arashe maganar da k'yar, saboda wani d'aci dayakeji a zuciyarsa. Sunyi kuka mai isarsu shida ita, kafin doctor Shu'aibu yazo yana lallashinsu, dole akama Amatallah allurar barci danta samu nutsuwa. *_One week later_* Alhamdllh a sati d'ayannan daya gabata abubuwa masu yawa sun faru, ciki harda rud'ani mai rikitarwa da Amatallah ta shiga, dole aka d'akkota daga asibiti aka maidota gida wajen innani. Basu 6ata lokaciba aka dage mata da addu'oin dangana da hak'uri, Alhmdllhi ansamu nasarori kam, Dan addu'a takobin mumini Ce. Nutsuwa tazo mata sosai, sai dai yawan kuka datakeyi, sannan maganama yanzu kam saita wunima batayiba. Kullum uncle Na hanyar gidansu innani. Nazeefa da Innani suna matuk'ar k'ok'ari wajen rage mata kewa da yawan damuwa, hakama jabeer, Shehu kam sai a hankali, danshi dama bayajin magana, zaman gidamma bayi yakeyiba, danma yana masifar tsoron uncle Muhammad d'inne yake rage wani abun. Har zuwa yanzun daga Amatallah har matansa babu Wanda yasan da zancen aurensu, innani da babane kurum sai jabeer da maijiddah suka Sani, ko Nazeefa batasan komaiba. Bayan sati uku da rasuwarsu Ammi cif baba yace yakamata asanarma Amatallah zancen auren, karya zam saita saki jiki kuma akuma maidata ruwa, gamma taji komai yanzun tahak'ura baki d'aya, hakama matan uncle yakamata Susan halin da'ake ciki. Innani tayi na'am da wannan batu, Dan haka aka kira kawu yakubu da doctor shu'aibu, sai Su jabeer kuma. Kowa dai ya hallara. Aneesa da Fateema sai mamakin wanna taro sukeyi, su duk zatonsu akan ruk'on Amatallah ne, anason aza6i wadda za'a bamawa acikinsu, tunda sunsan dolene mijinsu zai cigaba da rik'onta. Fargaba dukta cika Uncle, damuwarsa d'aya akan yanda Amatallah zata kar6i zancen auren ne. Bayan addu'oi da aka gabatar kawu yakubu yamik'e a nutse yafara jawabi tundaga farko har k'arshen abinda ya wakana aranar da Baban Ama zai rasu. Tun jikin Amatallah Na rawa a 6oye harya fito fili, tafara karkarwar rawar sanyi sosai, kuka kam tama nemesa tarasa gaba d'aya. Anty maijiddah dake kusada itace tajawota jikinta tana lallashinta. Idon uncle k'yam akanta, ko k'yaftawa bayayi balle yatuna akwai wasu halittu su Aneesa awajen. Daga Aneesa har Fateema kam mutuwar zaune sukayi, kowacce takasa motsin kirki, har kawu yakubu yagama jawabi yakoma nasiha agaresu. Tashin hankali kenan, Wanda ba'a samasa rana. Wannanfa shine ana wata gawata tazo. Dad'i sosai yakama Nazeefa, Dan aganinta babu Wanda Amatallah tadace dashi kamar yayansu Muhammad, lallai wannan shinefa ake kirada *HA'DIN ALLAH*. har taro yatashi mutum uku basu iya koda tariba, Aneesa, Fateema, garama Amatallah tanata hawaye da rawar sanyi. Ranar kam haka ta kwana rijif da zazza6i mai zafi ajikinta, sai sambatu takeyi dakiran sunan Amminta da baba. Da k'yar innani tasamu tayi barci, dama ita ba had'in auren ba, halinda yarinyar zata tsinci kanta, dakuma yanda zata kalli al'amarinne damuwar. ___________________________ Alhmdllh k'ura ta kwanta, zuwa yanzu jos da Kaduna abubuwa sunfara dai'daita, sai dai bak'aramar asarar rayuka dana dukiyoyi akayiba, lamarin ko k'yan gani babu, abin tashin hankalin abin yafi shafar matasanmu, kusan duk sune aka kashe da raunika kuma ga wad'anda suka rayu. A kudancin k'asarma Alhmdllh komai ya lafa, sai kuma yad'a 6arnar da akayi a kafafen yad'a labarai Na waje dana gida, hanyar samun kud'i kuma ta bud'ema 'yan jaridu. Jami'an tsaroma sai fankama suke, hakama 'yan siyasa abin kamfen dayima jam'iyya mai mulki gugar zana tasamu, muma kammu talakawan ba'a barmu abayaba, sai zabga kalaman ALLAH wadai muke ga gwamnati batareda dubi da mune muka haddasama kanmuba. K'asar duk tabi ta rud'e da surutai marasa kan gado, kowa k'abilarsa da addininsane mai gaskiya, babu mai yarda a jingina masa koda laifi d'ayane, masu tsoro kuwa harsun tattara inasu-inasu sunma k'auyikansu da yankinsu saukar angulu, Na kudanci sunkoma yankinsu hakama arewaci, kowa 'yancin fad'ar albarkacin baki dayake ik'irari dashi tasashi kasa yima k'asar k'yak'yk'yawan fata, saima k'ara Neman hanyar kare kai Dan aganin wasunmu bata mutuba rufa tayi, akwai sauran yak'i agaba, kowa yakoma gidane yasawo sulken yak'i. A 6angaren manyan k'asar kam d'if kakejinsu, kaikace babu sarakunan gargajiya ak'asar, malaman k'asar da pastors sunyi gum da bakunansu basa cewa komai sai sunsami ke6ancewa da mabiyansu a k'uryar lunguna, wasunsu suzama masu tunzura matasan da nuna musu sune masu gaskiya, k'alilan dasuke Na kirki sune masu tsawatarwa da nuna kuskure da illar abinda yafaru. Kowa yazama d'an jari hujja, mutuncinsa kawai yake k'ok'arin karewa da yankinsu, zancen nuna gaskiyar muzama k'asa d'aya al'umma d'aya son zuciya yasa mungina rami duk mun binne furucin bakunanmu, mai k'ok'arin so a gyara saikaji jama'ar yankinsa sun rad'a masa suna *MARA KISHIN KAI*. humm kai da shi mai tada husuma komai yanka albashin had'a rikice-rikice wanene mara kishin kai aciki?. Wlhy idan bamu gyaraba wankin wula tana dab dashirin kaimu tsakiyyar dare mai duhuwar dazamu kasa koda ganin tafikan hannunmu. Da ni da kai duk 'yan k'asane, munada zarrar kawo canji koda ta hanyar tsarkake zukatanmu ne da gyara halayyarmu. Ba gwamnati da shuwagabanni ne kad'ai ke buk'atar gyaraba, hatta damu talakawan masu ik'irarin Neman gyara da hura haccin sai an gyara d'in muna buk'atar gyara kanmu. Taya kakeson k'asarka tazama mai tsafta ta hanyar jagorancin shuwagabanni amma kai talakan k'asar kullum kana tebirin 6arna. Bakasan darajar zuminciba, bakasan muhimmancin addininka da koyi da k'yawawan aiyyukan daya kawo makaba, bakasan wace k'yautatawa yakamata iyalanka su samu daga garekaba, balle ajega zancen makwafta da abokan zamanka Wanda addini ya banbantaku, baka Neman abincinka ta hanyar hallal balle kaciyar da iyalanka suzama nagartattu masu tsafata, kullum harshenka yana kan aibanta 'ya'yan jama'a da zund'en matan mutane, sai hassada da ganin k'yashin cigaban d'an uwanka fal ruhinka. Kina mace kinkasa son abokiyar zamanki balle 'ya'yanta, kullum zuciyarki cik'in k'yashi da bak'inciki take idan mijinki ya k'yautatama iyayensa da 'yan uwansa, kinkasa nutsuwa wajen bautama ubangijinki amma kece sahun gaba agidan uwar gulma ko gidajen Malam tsubbu da bokaye anufin Neman taimako, burinki kullum ace kece sama dakowacce mace a6angaren k'yale-k'yale da kayan k'awa Na duniya, buri dason burga yahanki fad'ama mijinki gaskiya yayinda kikaganshi bisa karkatacciyar hanyar dazata iya kaiku wuta ke da shi da 'ya'yan dakuka haifa, Kana matashi amma kullun burinka akan kayi kud'i kake, ka auri mace ajin farko a k'yawawa kasaka acikin gidanka Na k'awa danta zame maka fure, babu ruwanka da tarbiyyarta ko addininta balle nasabar data fito, jin kanka kake on top kai yanzu kafara zamaninka mutuwa da sauran tak'i a tsakaninku da ita, baka ganin kowa da gashin arzik'i saboda kai ka iya kuma karanka yakai tsaiko, kasani sai dai ka sanar babu mai sanar da kai saboda kasha boko ka k'oshi, da ance kayya kaine sahun farko a masu d'akko makami afara y'ar rere tsakaninka da jama'ar gari, aganinka kai dai-daine bakada matsala da duniya, koyanzu kabarta hankalinka a kwance tunda baka haihuba. Wlhy muji tsoron ALLAH, mufara tuna komu su waye kafin gangar shaid'an tamana tasiri a zukata mu kwashi filin rawa muna tangad'in maye dajin kanmu can k'ololuwar sararin samaniya muna yawo cikin giza-gizai. Kowa yaje inda zashi yadawo akwai rana d'aya tak da za'a baka littafin ayyukanka a hannun haggunka ko damarka, wannan za6in yarage naka. Duk nau'in shed'ancin dakakeji ka gawurta tarihi ya nuna anyi wani kafinka, kuma anshafeshi yazama labari tamkarma bai zoba. To kaikuma asuwa da naka tak'adarancin bazai zama labariba harma ayo Wanda yafika k'warewa. Abin mamaki dukfa da wannan halayen namu amma mukeson samun shugabanni nagari, bayan ALLAH yafad'a mana, dai-dai sugabanninmu dai halayenmu kuma. Tab d'i, ashe kam da sauran kallo😨🤔. Kayi nazari, kiyi nazari, nayi nazari, muyi nazari domin gano illolin takubban shed'anarmu komunada rabon gyarawa kafin randa mala'ikan mutuwa da rundunarsa zasu zagaye sashinmu Dan k'udundunar ruhinmu zuwaga Wanda yayka yayni dama duniyar da abinda ke cikinta. ALLAH ka ganar damu gaskiya koda bazata mana dad'iba, ka tasirantar da ita agaremu, mu kar6eta mukumayi aiki da ita danmu samu komawa ga ALLAH cikin salama😭🙏🏻. _____________________________ "Wai kana nufin bazakayi break fast ba agida dear?". Gyara zaman hular kansa yayi, sannan ya d'auki turare ya fesa, kafin ya juyo sosai yana fuskantarta, cikin sassanyar muryarsa yace, ''sorry my neesa, wlhy ina saurine, dan inada meeting a da lectures k'arfe 12, gashi inason shiga naga jikin baba, nakumaje kasuwa, yau kayanmu zasu iso. Please kimin afuwa mana my sweet". Ya k'are maganar da matsawa kusada ita ya rungumeta a jikinsa. Bakinta ta d'an turo kad'an, cikin d'aurewar fuska tace, " kai dai kanason ganin Amatallah kawai, babu wani duba baba". Lumshe idanunsa yayi yana guntun murmushi, ya d'agota daga jikinsa yana mai zuba idanunsa kan k'yak'yk'yawar fuskarta datasha kwalliya. "My neesa! kina ganin nayi laifi kenan koda ganin Khadija zanje? a tunanina koda babu aurena a kanta ta cancanci irin wanman kulawar daga gareni, karfa ki manta jinin brother d'inace ita. a zatona kodan halin da yarinyar ta tsinci kanta ta cancanci kubar mata ni gaba d'ayama ai". Sosai Aneesa ta zaro idanu waje, " mubar matafa kace?". "Eh mana". 'Yay maganar cikin d'age gira'. Bakinta ta ta6e, cikin matuk'ar hasala tace, " ai wlhy ba haifi d'iyar dazan banmata kaiba, raba dai-dan kama danekiyi tsoron azabar ALLAH ne kawai yasani hak'uri, nifa wlhy harma mamaki nakeyi yanda kayarda da auren d'iyar cikinka, shin baka tunanin kamata tsufane?". Wani abune ya soke zuciyar Uncle M.A, ya kafe Aneesa da idanu ko k'yaftawa bayayi. tabbas maganarta ta mugun shigarsa. bai ce mata komaiba ya d'auki wayarsa da key yafice. Bayansa Aneesa ta raka da harara, yau ko shiga su gaisa da Fateema bai yiba. Sai tashin motarsa kawai taji. Da kansa yabud'e gate ya fice, sannan yafito daga motar ya yarufe, tafiya yake amma maganar Aneesa nakuma tasiri a zuciyarsa, shikansa tunda aka d'aura aurenan abinda ke damunsa kenan, sai yaga kamar an cutar da Amatallah, duk da shikam garas yake jin kansa da lafiya, bai San miyasa maganar Aneesa tamasa zafiba da yawa, bayan shima yasan gaskiya tafad'a. Hannunsa yakai yashafo ma dai-daicin gemunsa, kafin ya furzar da iskar bakinsa yana kuma dafe sitiyari. Ya d'anja lokaci a hanya kafin ya isa gidansu, saboda 'yan makaranta. Babu kowa a tsakar gidan, sai dai yaji kamar alamar mutum a Ketchin. Yasan maybe Nazeefa ce, Dan haka saiya wuce d'akin baba. Sai da yayi sallama, aka bashi izinin Shiga sannan ya shiga. Innani ya tadda gefen baba tana gyara masa rawani bisa kansa data yafa masa, da alama wanka tamasa, kullum da sassafe take masa wanka ta shiryasa, shiyyasa saika taddashi tsaf. Tunda yashigo baba da innani suke binsa da kallo, Dan tabbas sun gano alamun damuwa a fuskarsa, duk da sunsan damuwar rashin isma'il har yanzu bata barshiba, hakan bai hana baba fad'in "Muhammadu lafiya kuwa?." Duk girman d'a agaban iyayensa yarone😊. Dan haka sai Uncle M.A yakuma jin zuciyarsa tayi rauni, zama yayi ya gaida iyayen nasa, da tambayar ya jikin baba?. Tambayar baba yasake mai maita masa. Innani dai batace komaiba, tama kauda kanta daga garesu, tanata ninke kayan baba daya cire, sai dai dukkan hankalinta Na kansu. Yay k'asa da kansa, cikin sanyin muryarsa yace, "baba akan maganar auren nanne, sai nake ganin kamar an cutar da yarinyarnan, musamman idan akayi dubi da shekarunta da nawa". Murmushi baba yayi tareda gyara rawanimsa dayake rufe masa fuska, yace, " miyasa kake wannan tunanin Muhammadu?, ai ba haramun baneba idan mai shekarunka ya auri kamar Khadija, sai dai malamai sukance yin zai iya zama cutarwa ga ita yarinyar zuwa gaba, Dan sanda zaka kai wasu shekarun tsufa ita kuma sannan take tashen k'uruciyarta, kaga zata iya cutuwa saboda kai k'arfinka ya ragu, amma zakaga wani kuma idan ALLAH yabashi lafiya babu abinda bazai iyaba alokacin, (anta6a ma sheaik jafar Mahmud Adam tambayar nan, irin wannan amsar naji kuma yabada) amma ALLAH bai haramtaba, saboda masalahar gudun yad'uwar zinace-zinace yasa malamai sharhantawa". " kai kumama ai shekarunka basukai adamun ba har irin haka". A raunane uncle M.A yace, ''baba shekara 47 fa". Da sauri Innani ta juyo ta kalleshi, baba kuma yay guntuwar dariya. "Muhammadu kai yanzu shekarunka 47?". "eh mana baba, koma nafine?". 'Yaya maganar a raunane'. Yanzun kam ba baba ka d'aiba, har Innani sai da ta murmusa. "Lallai Muhammadu, to ai ko auren namu baima kai 45 ba sai a watan jibi, kuma awatan da aka kawo zainabu gidannan a watan tasamu cikinka, wannan lissafin kane dai kawai". " to Amma baba a takardar haihuwata ai hakane". "Yo Muhammadu takardar haihuwa ba kaine kaima kankaba lokacin dazaka sakandire, koka mantane?. lokacin da aka haifeka zainabu a rogo ta haihu, Dan ana goyon ciki a lokacin, tun cikinka Na wata bakwai akazo aka tafi da ita can, sanda tadawo min nan kanada wata biyu da kwana 26 a duniya, sannan ana arba'in biyu idan mace ta haihu tana wankan jego. "Na dai manta taka mai-mai miya faru karon haihuwarka, amma an haifeka da shekara 1 aka kifar da gwamnatin gawon, Murtala ya hau mulki, sai dai bana mantawa abinda nake ganin zan iya k'iyastashi da haihuwarka lokacin dai an cireka a mama da kwanaki 6 obasanjo yazama shugaban k'asa a mulkin soja ko zainabu?, da wannan kawai zan iya k'iyastawa gaskiya, saika bincika shekarun kagani". Innani tad'an gyara tsayuwarta a jikin bango, batareda ta kalli Uncle M.A ba tace, " hakane Malam dan bazan mantaba har shi ubasanjo ya sauka ba'a dawomana dashiba, har sai da iya ta rasu, dan munma fidda rai akan zai dawo wajenmu, nama haifi maijiddah har da cikin Barirah". "Wannan gaskiyane zainabu, dan haka saika lissafa kaga shekara nawa ya kama, ka had'a da shekaru biyu kafin mulkin shi Ubasanjo d'in". Waya Uncle M.A yaciro a aljihun gabar rigarsa, Dan yau ba babbar riga yasakaba, ya d'anyi danne-danne sannan ya d'ago yana kallon baba, yace, " baba 44 fa kenan". "To shekarunka kenan Muhammadu, kaga kuwa ba kai tsufan daza ace kagagara auren Khadija ba, kumama duk muture maganar shekaru, ai mahaifinta yasan daliln cewa kaine kadace ka aureta, kodan nagartarka, dukda yasan yawan shekarun naka ko. kuma koda shi baiyi hakanba ni zan aura maka ita da kaina, kaine kafi kowa sanin ciwonta, da yadda zaka kula da ita domin kwaranyewar damuwarta, ko Jabeeru ban yarda dashiba akan hakan, sai ka kwantar da hankalinka wajen kula da amanar da Sama'ila yabar maka, ALLAH yay muku albarka". "amin baba". Nasiha baba yamasa sosai, itama Innani tayi tata, sanan yamusu sallama yafito. 'Dakin Nazeefa ya nufa, saboda yasan Amatallah tana can...............✍🏻 🤩👎🏻 *_k'ashin. Mindirik'inku saiya kwanta, kunji baba yace Uncle baikai 47 ba, 44 yake,😂, ammafa kusani d'an 60years ma yana auren 'Yar 17, kuma auren lobayya😜🤣._* Wataranma sainayi novel da d'an shekara 70😏🥴. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [1/16, 1:29 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_* *_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡 _{home of expert and perfect writer's}_ *_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉ _(Hattara matasa)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* ____________________ *_Number 14 & 15_* ____________________ Sosai ransa ya 6aci daganin gungun matasan dake gefen titi, sai ihuce-ihuce sukeyi, daga mai sanda saima wuk'a da katako, kallo d'aya zaka musu kasan mafi yawansu ba'a cikin hankalinsu sukeba, huci ya furzo daga bakinsa kafin Yakuma maida kallonsa Kansu, sai lik'-lik'en poster's d'in wani d'an siyasa sukeyi, kansa kawai ya maida jikin kujerar ya kwantar, hannunsa d'aya dafeda sitiyari, kallonsu yakeyi daki-daki, kai kace TV yasamu. Babu abinda k'asan ransa keyi sai suya da k'una akan halinda wasu MATASANMU suka tsinci Kansu aciki, sun mance matsayinsu a cikin al'umma, basa tunanin gobensu da jibinsa, jiyansu da yau ne kawai agabansu, 'yan siyasa sun maidasu karnikan farautarsu, dakuma sun d'are kujerun mulki sai su ringa kiransu da suna *'yan ta'adda*, bayan kuma sune sanadin wargaza rayuwar Mafi yawan matasan, sun haddasa bak'in ciki a zukatan iyayensu da al'ummar k'asar baki d'aya. Jiyay kewar brother d'insa ta dawo masa sabuwa fil, tamkar yanzune yabar duniya, kwallar data taru masa a ido yasa d'an yatsa d'aya ya d'auketa, har zuwa yanzu yarasa wazai tunkara domin samun goyon bayan kafa k'ungiyar matasa kamar yanda Baban Ama yace suyi. Karaf tunaninsa yafad'a akan abokinsu Sabi'u m Ali, tabbas yasan Sabi'u shima mutumne mai jure gwagwarmaya, kuma tabbas yasan baisan Isma'il ya rasuba. d'an murmushi yayi saboda samun abokin tafiya Na biyu bayan brother d'insa. Bai sake kallon matasan nanba yatada mota yabar titin. Kusan Horn uku yayi sannan Aneesa tazo ta bud'e masa gate. Koda ta rufe gate d'in saita nufo motar, duk da zuciyarta tana cikeda fargabar tarbar dazata samu a gareshi, saboda yanda suka rabu da safe. Motar yabud'e ya fito, ganin yanda take a d'arare dashine yabashi dariya, amma saiya danne baiyiba. yad'an kalli k'ofar falon yaga babu mai tahowa, saiya matsa kusada ita kawai ya rungumeta da manna mata kiss a kumatunta, cikin kunnenta yace, "kinyi k'yau my Nessa". Duk da taji dad'in kalaminsa, hakan baisata daina fargabarba, Dan tasan halinsa akan share Abu yayi tamkar bai 6ata ransaba, saika manta ya hukuntaka akansa. Yatsu biyu yasa ya d'ago ha6arta yana kallon fuskarta sosai, cikin k'asa da murya yace, ''koba'a murna da dawowata gidan da wurine?". Murmushin k'arfin hali Aneesa yayi, ta girgiza masa kai, "a'a wlhy my Dear, abinda nayi makane da safe yake matuk'ar damuna". Murmushin gefen baki yayi kawai yakama hannunta yana fad'in "yarafa?". Tace, " basu dawo islamiyyaba ai". "Okay, to muje ciki, yunwa nakeji sosai, jinake kamarma zan iya cinye abincin gidannan duka yau". Babu shiri Aneesa ta tuntsure da dariya, " kai Dear amma wasa kakeyi ko?". "Hh, ba wasaba fa My Nessa, tunda Na fita drink kawai nasha awajen meeting....." Yakai k'arshen maganar suna shiga falon. Aneesa batasamu bashi amsaba, saboda Fateema data fito daga nata 6angaren cikin kwalliyar d'aukar hankali. Kallonta kawai Uncle M.A yatsaya yi, saboda babu k'arya kwalliyar tata tayi masa k'yau, amma dukda haka yayi hakanne danya bama Aneesa haushi, itama taji bak'in cikin dayaji d'azu da safe. A hankali yasaki hannun Aneesa da mamaki yahanata koda motsi, Dan bahaka sukayi da Fateeman ba, sunyi shiri akan sun daina masa duk wani Abu dazai faranta ransa, amma danta d'auketa sakarai shine taci uban kwalliya ta fito. Uncle M.A daya k'arasa inda Fateema take sai kawai ya rungumeta yana fad'in "woow! my tee.., kinganki kuwa? saikace wata 'yar 22?. d'agota yayi daga jikinsa ya manna mata kiss a bakinta da yasha jan janbaki, harya d'ebo tsaraba shima😉. Kutt, zuciyar Aneesa tamkar ta fashe, ai ko ita dakeda girki bai yaba kwalliyarta haka ba, sannan ma a kumatu yamata kiss, amma Fateema a baki, wannan wane irin wulak'ancine?. Da sauri tabar wajen tashige 6angarenta. Yana ganin ta shige yasaki Fateema yanufi samansa. Binsa da kallon Fateema tayi tana gumtse dariya, sai da taga ya shige sannan tayi dariyar mai isarta, halin Muhammad nak'ara mata sonsa matuk'a, shi mutumne da in matarsa tamasa Abu bazai ta6a 6ata lokacin wajen mata ihu ba, sai dai yabi wata hanyar ya bak'anta miki rai, bata raba d'ayan biyu abinda Aneesa tamasane da safe yarama. ta gallama 6angaren Aneesa harara tana fad'in "'Yar rainin sense, da kin d'aukeni wata sakaraine ko?, azatonki na mince mun had'a kai ko? to Fateema garas take kallonki, bar ganin shekarunmu d'aya, sabodama kin rainamin hankali nun Yanke shawara babu Wanda zaiyi kwalliya shine kika koma d'aki kikayi ko? A nufinki kinbar sakarai anan, haba matarnan tas nake kallonki, shiyyasama naci kwalliyar dataci uban taki, mtsoww, sakarai wadda bata iya danne kishinta ba". Tana gama fad'a ta shige nata side d'in itama. Nace, "lallai Fateema kin burgeni wlhy, mata sai kuma Ku gyara😊". Shikam yana shiga nasa d'akin dariya yayi shima, sannan yashiga k'ok'arin cire kayan jikinsa. Harya fito wanka babu labarin Aneesa, bai damuba Dan yasan yanzu tahau sama. Farar jallabiya yasaka, yad'an fesa turare sannan yadawo falonsa, zamansa yayi dai-dai da shigowar yaransa da gudu su hud'u. Duk kansa auka fad'a suna fad'in "oyoyo Abbunmu". Shima rungumesu yayi cikin farincikin ganinsu, yace, " my Children's oyoyo, andawo islamiyyar?". Atare sukace "eh abbunmu". " masha ALLAH manyan gobe, ALLAH yayi muku albarka kunji, mi'aka koya yau?". Rige-rigen fad'a masa suka farayi, barema Ummita da take bisa cinyarsa. "Kunga afad'a d'ai-d'aya, kungafa banason hayaniya nagaji sosai". yafad'a a kalar tausayi. Suma duk sai suka marairaice suna "sorry Abbunmu". Murmushi yayi, yabi dukkan kumatunsu ya sumbata, sannan suka shiga fad'a masa d'ai-d'ai. Ana haka Aneesa tashigo d'aukeda tire, fuskarta kawai ya kalla yasan tayi kuka, (sai dai a k'asan ransa rayuwarta tana burgeshi, ko kad'an Aneesa batada rik'o, in har zaka 6ata mata rai dazaran tayi kuka kota amayar da maganar to shikenan kuma ta huce). Kallon yaran tayi tace, " kunga, kowa yaje yacire Uniform ko, abar Abbu yaci abunci". Atare sukace to momy. Duk suka fita. Sai da ta tabbatar sun sauka daga benen sannan ta tako a hankali inda Uncle M.A ke zaune yana kallonta. Saman cinyarsa kawai ta zauna, batareda tace komaiba ta had'e bakinsu waje d'aya. Bashida za6in daya wuce kar6arta hannu biyu. 🚶🏻‍♀bara na koma falon k'asa, idan sun dai-daita saina dawo😏. Kusan mintuna 5 sannan Na koma, tararwa nayi tana zuba masa abinci suna dariya. Na rik'e ha6a ina fad'in lallai (mata da mini said ALLAH), kuma gaskiyar Nazeefa, zaman gidannan Sai mai wayo, Dan rayuwa akeyi ta kissa da kishin masu Ilimi, masoyan Amatallah saiku mik'e sosai, dan saikun mata training akan zaman wanga gida da ake kishin 'yan bar.....🤭ban dai Ce komaiba Ba ruwana bara Na tsuke bakina kar masoyan Aneesa da Fateema su caskalani🤐 Da kanta tabashi abincin suna hira cikin so da k'auna, sai da yagama tsaf sannan yay alwala suka sakko k'asa tare, ya tasa 'ya'yansa maza gaba suka tafi masallaci sallan magrib. Saidai sukayi sallar Isha'i sannan yaturo yaran gida, shikuma yatare Napep sai gidansu dukda garin yafara canjawa kamar hadari zai had'u. Nazeefa da Amatallah suna zaune a d'aki tareda Innani, Tuwo sukeci suna hira kad'an-kad'an domin d'aukema Amatallah kewa. Sallamarsa kawai suka jiyo a tsakar gida, Nazeefa ta amsa dad'an k'arfi yanda zai jiyosu. Sai da ya lek'a d'akin baba yaga barci yakeyi sannan yadawo d'akin Innani dayajiyo muryar Nazeefa, nanma sai da yay sallamar aka amsa dabashi izinin shiga sannan yashiga. Idonsa Akan Amatallah yafara sauka, wadda tunda taji sallamarsa gabanta yashiga fad'uwa, sai ma taji tuwon yafita kanta, koda yashiga bata d'aga ido ta kalleshiba. Kusada Innani yaje ya durk'usa yana gaisheta da tambayar jikin baba. Ta amsa tana kauda kai gefe kamar yanda ta saba masa. sunama gama gaisawar tamik'e tafita daga falon. Nazeefa ya kalla dake gaisheshi, bayan ya amsa yace, "Jabeer da shehu fa?". ''Yaya basu shigoba tukunna". " Okay". Cikin d'an rawar murya Amatallah ta gaidashi itama, idanu kawai ya zuba mata batareda ya amsaba. Takuma maimaita gaisuwar a karo Na biyu. Yanzunma bai Amsaba, sai cewa da yay "my best! alk'awarin kenan? tunkan muyi nisa harkin karya?. Cikin dabara Nazeefa tazare jikinta ta fice tabarsu. Cikin muryar kuka tace, " kayi hak'uri Uncle ban karyaba". d'an murmushi yayi tareda girgiza kansa. Sai kuma yataso yadawo inda Nazeefa ta tatashi yana lek'a kwanon tuwon da sukeci. "Uhm my best babu tayine?". d'an murmusawa tayi tace, "a'a to bismillah". gyara zamansa yayi, cikin dai-daita murya dan soyake ta saki jikinta dashi. Yace, "Sai da Na rok'a my best!?". "to kayi hak'uri, bara nakawo maka wani wannan ya k'are". "A'a ngd". Kallonsa tayi, a shagwa6e tace, " uncle fushi kayi ko?". 'Tak'are maganar tamkar zatayi kuka'. Yanda tayi maganar a shagwa6e sai yaji wani iri daban, bak'aramin birgesa tayiba, jiyay zuciyarsa Na kissima masa wani Abu daban, yay saurin fad'in ya salam, kai zuciya ta, mikikeyi hakane? Amatallah d'iya tace. "Kaji Uncle, please mana".... Maganarta ta kuma saukar masa bisa kunne. tsintar kansa kawai yayi da mairairaice murya shima, harda langa6e kai gefe kamar yanda tayi. "Ni dai gaskiya na k'oshi my best". Dariya sosai Amatallah takeyi, shikuma ya kafeta da ido yana kallonta da murmushi. sai da tayi sosai sannan ta daina. " uhm, dama haka kika iya dariya my best?". Hannu tasa ta rufe fuskarta, "ALLAH uncle kaine kaban dariya, shagwa6afa kayi". " lah da gaske? aini bamma San nayi wani abuba. tashi ki wanke hannu kizo muyi maganar School d'in da kikeso". "To". Tafad'a tana mik'ewa d'auke da kwanon. Har taje k'ofa ta juyo, yanda taga yana kallontane yasata k'asa da kanta sannan tace, " uncle tuwonfa?". "Kansa ya girgiza mata sannan yace, " a'a Na k'oshi, wasa nake miki, ban dad'a dacin abinciba ne da naci". Kai kawai takad'a ta fice tana mamakin wannan sabon salon da Uncle kemata a yanzu, tamkar ba Uncle d'in taba, babuma abinda ke takurata kamar yawan kallonta da yakeyi. ******* Ganin yara sun dawo babu shi yasaka Aneesa kiran Abulkhairi ta tambayesa. "Momy bansan ina yajeba, yacene mu shigo gida shi zaije wani waje". Shiru Aneesa tayi tana kallon yaron, k'asan ranta haushi da kishi na cinta. Sallamar Abulkhairi tayi, ta d'auki waya ta kirasa. Amatallah na fita daga falon kiran Aneesa na shigowa, murmushi yayi dayaga my Wife Neesa. d'agawa yayi, cikin sanyin muryarsa yamata sallama. Batareda ta amsaba tace, " dear wai ina kuma kaje a darenan?". Bai iya k'aryaba, dan haka kai tsaye yace, "ina wajen Khadija ne my Neesa". Ai tamkar yadaki zuciyarta da mashi, ta dai daure tace, ''amma a darennan?". "uhm akwai abinda najeyine mai muhimmanci, amma bazan dad'eba zan dawo, kedai kawai kishirya kar6ar tsoho yau, dan dolene mu goga raini ki tabbatar da saurana har yau". Shiru tayi, takasa cewa komai. " hello, bak'ya jinane Neesa? ko harma kin tsoratane?". Dariyar basarwa tayi, "saika zo d'in, nima na shirya". " ko babyna?". "Eh mana". cewar Aneesa. Murmushi yayi mai sauti, dan hartana jiyosa, yace, " my Siddiqa zatayi k'ani ko k'anwa kenan yau".... Da sauri ta katseshi da fad'in ''my dear!, dan ALLAH bar fad'e, wasa nakeyi wlhy, sai ka dawo...." Bata jira cewarsaba ta yanke wayar. Girgiza kansa yayi yana murmushi, A fili yace, ''my Neesa m...... Shiru yayi bai k'arasaba sabida ganin Amatallah tsaye a bakin k'ofa, baisan tashigoba ko kad'an. Itakam bama tadad'e da shigowarba taji yana waya, duk da taji da wacce yakeyi hakan baisa taji komaiba azuciyarta, zama tayi nesa dashi. Shikam duk saiyaji babu dad'i, a zatonsa zatayi kamar yanda su Aneesa ke masa, sai yaga ko'a jikinta. Saima Neman waje tayi ta zauna. Nikam nace, "Hhhh, yo Uncle ita kishin mi zatayi? tunda har yanzu batasan mi akema kishinba🤣 ai da sauran time🤐. List d'in sunayen Schools yabata taza6a, tace itadai kowacce ma ya za6a mata, daga k'arshe dai sai Nazeefa da ya Jabeer ne suka za6ar mata. Kusan 10pm yay musu sallama ya tafi, akan zuwa gobe zai kawo mata form ta cike. ********* Ai ko daya koma gida saida yasha fama da Aneesa kafin su dai-daita. Kishi kumallon mata kenan, bana ganin laifin Aneesa kam, sai dai gaskiya mata kud'an ringa rage zafin kishi, musamman ma agaban miji, dan yana ragema mace daraja wlhy. ko zakiyi kishin kiyi mai aji kamar na uwargida Fateema😉👌🏼. ____________________________ Alhmdllh komai ya kammala gameda exam d'in Amatallah, ta kuma maida hankali sosai a karatun, musamman da taimakon da Nazeefa ke bata sosai, shima Uncle idan yaje gidan yata bata haske kenan akan abubuwan, tunda yasan sirrin jarabawar. kowa k'arfafa mata gwiwwa yakeyi agidan. Baba kuma ya sanarma Uncle M.A yakamata yaje Jos dan Neman dangin Ammin Amatallah, yakamata a sanar dasu komai gameda rasuwar 'Yar uwarsu da mijinta, dakuma aurensa da Amatallah tunda hankali yad'an kwanta zuwa yanzu saboda sojoji aka zuba a jihar jos d'in da Kaduna. Sosai Uncle M.A yayi Na'am da batun, bai kumayi k'asa a gwiwwa ba ya shirya yaje jos. Sosai lamarin ya tsa6a zuciyarsa, yanda yaga gagarumar 6arnar da akayi a jihar sakamakon rikicin da ya afku, har yay sanadin rasa d'an uwansa. A dangin Ammi ma mutane da yawa sun rasu, wasu kuma suna asibiti suna jiyya, nan dai ya kwashe komai ya sanar musu, sunsha kuka sosai, dan dama sunata nemansu, ashema sune farko-farkon rasuwa. Duk sunyi na'am da zancen auren, sun kuma saka albarka, sai dai sun rok'i alfarma ya dawo musu da Amatallah nan bayan ta kammala Exam, sai ayi biki kafin a maidota Kano gidansa. Godiya yamusu, da alk'awarin maido Amatallah d'in, dan aganinsa hakan ma zaisata tad'an rage wani rad'ad'in, takuma dingajin an mata aure irin na kowacce mace. Sosai yamusu alkairi sannan yatafi suna zabga masa albarka da addu'oin fatan alkairi. Su Amatallah sun cigaba da zana jarabawa cikin nasara, ahaka suka kammala NECO & WAEC cikin farin ciki. Har zuwa yanzu kullum Amatallah saitayi kukan rashin iyayenta k'oda a 6oyene saboda kar Innani ko Nazeefa wani yagani, bakamar randa suka gama exam tasha kuka tamkar ranta zai fita, jitake inama Ammi da baba nada rai, suga wannan rana dasukaita buri. Da k'yar ranar aka samu kanta a gidan, harda zazza6i tayi. Satinsu d'aya da kammala exam Uncle M.A da Nazeefa suka kaita Jos wajen dangin mahaifiyarta, tayi matuk'ar farin ciki da ganinsu, sai dai ansha kuka ranar itada dangi, daga baya dai suka sakama ransu dangana tunda kuka bazai dawo da wad'anda aka rasaba. Zamanta cikin dangin mahaifiyarta saiya rage mata wani rad'ad'in, tad'an samu sauk'in k'unar zuciyar datake ciki sosai, gashi kowa tattalinta yakeyi saboda tausayin datake basu. ********** Uncle M.A kam dasu Nazeefa sai suka shiga kewarta, dan d'an zaman datayi yakawo sabo da shak'uwa mai k'arfi tashiga tsakaninsu. Su Aneesa kam da Fateema dad'i sukaji, dan koba komai yanzu yarage zarya gidansu, sai dai yana zuwa kamar yanda yakeyi da, da safe kafin yatafi kasuwa ko aiki, kokuma idan ya taso. A kuma wannan tsakaninne tafiya wani Cause a Dubai na tsawon watanni tara ya sameshi. kuma cikin gaggawa. A daddafe yaje sukai sallama da Amatallah, yakuma sanar mata data shirya Jabeer zaizo akan makarantarta idan result ya fito, amma sai dai tayi hak'uri, k'ilan zata koma Kano da zama fa. Kanta ta jinjina masa tana k'ok'arin maida hawayenta. Shiru yayi yana kallonta, murya a sanyaye yace, "bak'yason Kano ko my best?". Da sauri tace, " a'a Uncle, inaso wlhy". Guntun murmushi yayi kawai, yace, "OK shikenan to, ammafa ba wajen Innani ba wannan karon". Kallonsa tayi, murya na rawa tace, "Uncle ina to?". Shima saiya kalleta da d'an murmushi yace, " gidana, kobak'ya son zama?". Hawayen datake mak'alewane suka zubo, amma batace komaiba. Hannunsa kawai taji akan kumatunta yana goge mata hawayen, muryarsa can k'asan mak'oshi yafara lallashinta. "Kiyi hak'uri Khadija, mu kar6i jarabawar mu da hannu biyu, ni kaina ina cikin rud'ani wlhy, bansan yanda zuciyata zata d'aukeki a matsayin matata ba, bayan kuma matsayin d'iya mafi soyuwa kike dashi agareni, banida wata mafitane akan hakan, saboda alk'awarin rik'eki naima Brother yayinda Numfashinsa yarage k'iris ya k'are daga gangar jikinsa." "Kullum cikin tunanin mafita nake, amma nakasa samowa, ni kaina inajin tamkar mun cutar dake, gashi kuma bakin alk'alami yarigada ya bushe, dan banida damar ruguje alk'awarin danaima brother bayan k'asa ta rufe idonsa. kiyi hak'uri, insha ALLAH komai zai zama labari, lokaci na zuwa dazamu fara kallon kammu ni da ke amatsayin miji da mata kinji". Kai kawai ta iya d'aga masa. Waya mai k'yau ya bata a kwalinta, " ga wannan ki rik'e, nasaka miki Number ta, duk abinda kike buk'ata kobai mikiba ki kirani ki sanar mini, da nayi tunanin kicigaba da zama wajen Innani harna dawo. to sai kuma baba yace hakan bai daceba, gara kawai a kaiki gidan, k'ila kafin na dawo kin saki jikinki, ga 🏧 d'ina nan duk sanda kike buk'atar kud'i saikiyi amfani dashi, Nazeefa zata dawo gidan itama harna dawo, karki yarda wani Abu ya had'aki da Aunty's naki kinji, (duk da ma dai bayan tafiyata d'aya a cikinsu zata Bini) kibasu girmansu kamar yanda na sanki, kuma kicigaba da hak'uri akan duk abinda za'a miki bai mikiba, (duk da dama nasan ked'in mai hak'urice), duk Wanda yamiki wani Abu a cikinsu ki kirani ki sanarmin kinji." Nanma kanta kawai ta jinjina masa. "Yawwa my best D.. , ALLAH yay miki albarka, d'inkunanki nacan Nazeefa takai da duk abinda kike buk'ata, banda wasa da karatu, banda tarkacen k'awaye, ki maida hankali sosai, kuma dan ALLAH kirage yawan damuwarnan kinji ko". Yanzuma kanta ta jinjina. Yace, " kimin magana please naji mana". Yanda yay maganarne yasakata murmushi, ta share ragowar guntun hawayenta, "ngd sosai Uncle, ALLAH ya biyaka da mafificin alkairi, Yakuma Baka nasara akan abinda zaka nema". " amin my best D..., ngd da addu'arki, yanzu miza'a bani dazan ringa tunawa". "Uncle mikake so?". " komai nasamu inaso my best D.." Shiru tayi alamar tunani, zuwa can ta kalleshi, "Uncle kafad'a, ni narasa mizan Baka ai". Murmushi yayi yana kamo hannun damarta. Kallo tabishi dashi dantaga mizaiyi da hannun. Bud'e yatsunta yayi sosai sannan yakai bakinsa tsakkiyar tafin hannunta ya sumbata. Wani yarrr taji ajikinta, harda 'yar girgiza da runtse ido. Ya d'ago yana kallon fuskarta da murmushi. Saurin kama k'ofar motar tayi zata gudu. Yay saurin rik'o hannunta yana fad'in " yazaki gudu baki baniba?". Wata matsananciyar kunya da mamakin sane ya cika Amatallah, a zuciyarta tace dama haka Uncle yake? naga ta kaina. Ba yanda baiyiba amma tak'i juyowa ta kalleshi, ganin bazata juyo d'inba saiya zame gyalen kanta tareda d'an kwalin. Idanu Amatallah ta zaro waje dan mamaki wannan aiki na Uncle..... Kafin takai k'arshen mamakinta taji ya zare pink d'in Ribbon d'in data d'aure tsaka tsakin gashinta daba wani tsawone dashiba. Yana zarewa tasamu ta fice, da gudu tashige gidan kakanninta da yayan Ammi da k'aninsa ke ciki yanzu. tabar Uncle da dariya. Ribbon d'in ya saka a hannunsa sannan ya d'auki d'ankwalin atanfarta data bari ya d'ora a cinyarsa, ya tada motar kawai yatafi, yanamai jin wani nishad'i dashi kansa baisan ma'anarsaba...........✍🏻 🤩👎🏻 *_ALLAH ka gafartama Mahaifanmu😭🙏🏻_* [1/16, 1:29 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_* *_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡 _{home of expert and perfect writer's}_ *_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉ _(Hattara matasa)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* ____________________ *_Number 13_* ____________________ Da sallama ya shiga d'akin. Amatallah dake zaune a bakin katifar Nazeefa tana canja rigar filo da sauri ta juyo tana amsa sallamar cikin rawar murya. jikinta har rawa yakeyi. Shiru yay yana kallonta. Sai yaji babu dad'i ganin yanda yanzu kamar tsoronsa takeji, saima yazo gidan sau uku bata bari sun had'uba, yau ma yasan k'ila batasan yazo ba. Murmushi gefen baki yayi, ya d'an kauda kwayar idonsa daga kanta saboda zanine kawai da vest a jikinta. ''My best D......", sai kuma yakasa k'arasawa, yace, " kintashi lafiya?". Da sauri tace, "Uncle sorry ina kwana". Yanzun ma murmushin gefen baki yayi, kafin ya amsa, ya kuma kallonta kad'an, "bak'ya jin sanyine? Kika zauna haka?". Gaban tane yafad'i, tama manta da kayan dake jikinta, hijjab tajawo da sauri ta saka, wata matsanan ciyar kunya takuma lullu6eta, saita koma ta zauna bakin katifar ta kifa kanta a cinya. Zama yayi bisa wani stool dake d'akin, cikin sanyin muryarsa yace, " yanzu yaya kikejin jikinki?". Bata d'agoba, ta amsa da "naji sauk'i, sai dai yawan ciwon kai". " tunanifa kenan my best?". Kanta ta d'ago, idanunta cikeda kwallah ta girgiza masa kai batareda tayi maganaba. Shima kan ya girgiza mata alamar kartayi kuka. Ta saka hannu ta share hawayen dasuka fara bin kumatunta. Mik'ewa yayi tsaye dan bayaso ta karya masa zuciya, yace, ''inaga zuwa Monday zan nema miki school d'in dazaki koma, anfara Reghestiretion d'in SSCE, koba k'yason ki zana a wanan year d'in sai next year?". Share hawayenta ta shigayi tana murmushi, "a'a Uncle inaso zanyi". Murmushi yayi saboda ganin tana kuka tana dariya, ya matso kusada ita Yakuma k'asa da muryarsa kamar mai tsoron kar a jisu, yace, "kimin alk'awari to". Yanda yay maganar sai bugun zuciyar Amatallah ya k'aru, ta d'ago manyan idanunta dasuka yi d'an ja ta kalleshi. Ya jinjina kai alamar ta amince. " uncle alk'awari kuma?". "Yes my best". " uhm Uncle nami to?". Komawa yayi inda yatashi zaune yasake zama kan stool d'in, "my best inason kimin alk'awari zaki rage yawan damuwa, rashin kwanciyar hankalinki nawane, kukanki yana ta6amin zuciya ainun Khadija, ki daure wajen kar6ar wannan jarabawar tamu, duk sanda kikaji zuciyarki cikin k'unci ki d'auki alkur'ani ki karanta, su brother addu'armu suke buk'ata kawai a yanzu kinji". Kanta ta d'aga masa tana share hawaye, " uncle insha ALLAHU duk zanyi". ''Yauwa my dear, ALLAH yay miki albarka". 'Yay maganar yana mik'ewa'. Amatallah tace, "amin". Agogon hannunsa ya kalla yana fad'in " bara naje to, idan na dawo saimuyi magana ki za6i school d'in da kikeso ko?". "To Uncle, amma ko wacce kaza6amin tamayi". "Shikenan, amma baradai Na dawo d'in". Kanta ta jinjina masa, sannan tamasa addu'ar dawowa lafiya. Yana murmushi ya amsa sannan ya fice. A tsakar gida yatarar da Nazeefa. "Lah Yaya dama kana gidannan?". Murmushi yayi yana kallonta gaidashi tayi, ya amsa yana tambayarta babu dai wata Matsala akan Amatallah ko?. " eh wlhy Yaya tarege yawan kukan bakamar da ba, kuma danaga zata fara tunani sainayita janta da hira danta saki jikinta, amma nakula kamar bata isashen barci". "Nima nalura da haka kam Nazeefa, Dan tama min complain akan kanta yana ciwo". " rashin barcine da tunani Yaya". "Babu damuwa, insha ALLAH zan d'auki mataki, kedai kicigaba da k'ok'ari wajen rage mata yawan tunani da damuwar, a satin nan zan nema mata school dazata zana SSCE d'inta, maybe hakan yad'an d'auke hankalinta". " yawwa yaya, hakan ma yayi sosai". "Yawwa bara na wuce time Na tafiya, yau bazakije school bane?". " eh Yaya. Yau bamuda exam...... Fitowar Shehu daga d'akinsa yana mik'a da hamma, babu zancen rufe baki a tsarinsa, dagashi sai gajeren wando da vest. kallonsa sukayi suduka. Uncle M.A ya had'e fuska yana kallonsa, cikin daka tsawa wadda bata hana muryarsa fita da sanyiba yace, "kai! Shehu!, wane irin iskancine wannan? zaka fitoma mutane tsakar gida da boxer? kamar kai kad'aine a gidan?". Shehu ya yad'an Sosa k'eyarsa yana duk'ar da kansa, " kayi hak'uri Yaya, ni bansan kana gidanba ai". "Lallai kam, wato sai ina gidanne zakayi shigar mutunci? Nazeefa da Amatallah ba k'annenka baneba? kai bakajin kunyar su ganka a haka? to ni abindama nakeson na sani, sai yanzu katashine kokuwa?". Nazeefa tayi saurin " fad'in ALLAH Yaya sai yanzunne yatashi, da asuba babu irin bugun da ya Jabeer bai masaba amma yak'i bud'ewa, hakama innani". Harararta Shehu yayi, amma baice komaiba. Cikin matuk'ar 6acin rai Uncle M.A yace, "wai Shehu mikakeso kazamane kaikuwa? Wannan wace irin rayuwace kaza6ama kanka? gwargwadon iko kowa k'ok'ari yake dakai agidannan kan kazama mutumin kirki, amma gakanan tamkar wanda bakin iyaye ke d'auniya dashi? yanzufa ka kalli agogo kusan 7:30 amma bakayi sallar asubahiba, amatsayinka na matashi mai lafiya, ko baba dake kwance yana jiyya kullum saiyabi jam'i a gida, kaje kayi tayi wlhy, rayuwarkace, idan ka gyara kaine zaka anfana, idan kabari ta lalace asararkace, shekarar k'arshe kake a makaranta amma yanzu haka yau kunada exam, kana kwance kana barci k'ilama ko karatu bakayiba?". " Yaya nafayi, dad'ewama danayi ina karatunne yajamin makara..... "Rufema mutane baki kafin na sa6a maka kammanni wlhy, ina k'ofar gidan su Rabi'u kazo ka wuce kaida abokanka kunata warin sigari, nasan baka ganniba ai, kuma koda na dawo gida kwance na iskeka kana barci zakace wani karatu kayi. walhy Yaya idan yaronan bai tsallakeba wannan karon karka kuma 6ata kud'inka akansa, banza kawai Mara amfani wa kansa bare waninsa". Jabeer ne mai maganar cikin k'unar rai da bak'incikin halin d'an uwan nasu daya biyema abokan banza suna shashanci. "Abinda dama na yanke kenan Jabeer, ka duba shekarun da yaronnan ya d'auka a makaranta, tunfa Nazeefa na ss2 a secondary, gashi harzata kammala degree d'inta tareda dashi, k'ilama takuma barinsa.... ''Dan ALLAH Yaya karkace haka, insha ALLAHU zan dage nabar jami'a wannan year d'in, kodan naga kunyi farinciki, kuyi hak'uri Dan ALLAH, kucigaba damin addu'a". ALLAH sarki, d'an uwa rabin jiki, sai kuma tausayinsa ya kamasu, a raunane Nazeefa tace, " please ya Shehu ka canja mana, kodan k'ok'ari da Yaya Muhammad keyi a kanmu kullum shida ya Jabeer, ga halin da baba yake ciki, ALLAH abinda kakeyin nan yana k'ara saka damuwa a ciwon baba, kai abin baya damunka ne?". ''Ya za ayi ya damesa Nazeefa? tunda duniya da abokan banza na kaimasa yanda yake buk'ata, ALLAH ya shiryeka Shehu, kawuce kaje kai Salla rana na kumayi, ni bara na wuce kasuwa". "Yaya nagama karin kumallo fa, kazauna kaci dan naga yanda kafito da safen nan dawuya idan kayi a gida". "No auta, karki damu, ina saurine yau kayanmu suka iso, gashi zanje office yau, inada meeting da lecturers". Bai jira cewartaba yabama Jabeer hannu sukayi musabaha ya fice. Dariya Jabeer yayi yace, " auta kema kinsan Yaya da abinci aii, nidai bani nawa na d'ora natai aiki". Itama dariyar tayi kawai tanufi ketchin. Abincin kowa ta zuba takaikai musu, sannan ta d'auki nasu itada Amatallah. Baba da innani duk sunajin abinda ke faruwa a tsakanin 'ya'yan nasu. hakama Amatallah tana jiyosu, sai hakan yasata kewar families d'inta, dajin sha'awar inama tanada k'anne ko yayye itama, ko babu komai ai zasu tattauna akan matsalolinsu suji sanyi, wannan tunanin ne yasata kuka sosai. motsin shigowar Nazeefa yasata saurin share hawayen tacigaba da shinfid'a bedsheet a kan katifar. "Anty Nazeefa kin ganni har yau ban gama gyaran d'akinba". Dariya Nazeefa tayi tana ajiye tiren hannunta, "inafa za'a gama mana gyaran d'aki, kunyi bulum keda Yaya a d'aki kamar bakwa gidan kunata shan soyayya". Cikin zaro ido waje Amatallah tace, " kai Anty Nazeefa, soyayya kuma? Uncle nefa". 'tak'are maganar kamar zatayi kuka'. Sosai Nazeefa take dariya, "yo Amatallah ai yanzun yatashi daga Uncle, yakoma miji, ba laifi bane idan anyi soyayyar. Kinsan kuwa bala'in dacewar da kukayi keda ya Muhammad? wlhy karki bari damarnan ta ku6ce miki, ya Muhammad garas yake tamkar wani d'an 30years, yandama yakeda k'aramin jikinnan wasu d'auka suke ma Anty maijidda ce babba, kofa ya Jabeer yafishi jiki. wama zaice ya Muhammad yanada mata biyu, koda yake uku fa yanzun". ta d'agama Amatallah gira. Baki Amatallah ta tura gaba, " Anty Nazeefa kibari Dan ALLAH, nifa ALLAH Uncle d'inane" ta matso hawen dasuka taru mata a ido tunda Nazeefa tafara maganar. Kusada ita Nazeefa ta zauna, ta dafa kafad'arta, "kiyi hak'uri Amatallah, nasan anan gaba kad'an zakiso ya Muhammad amatsayin miji ba Uncle kad'aiba. na tabbata saiya nuna miki soyayya maiban mamaki, dan soyayyar dayakema Yaya Isma'il duk zai tattara yahad'a da wadda yake miki, ya Muhammad yanama ya Isma'il k'auna maiban mamaki, to yakike zaton kuma kasancewarki matarsa jinin masoyinsa ya Isma'il?, gakuma ke kanki dama yanda yake sonki sosai tamkar 'ya'yansa. lokaci kawai muke jira na ganin hankalinku ya kwanta dagake harshi, dan har yanzu duk kuna cikin rud'anine na abubuwan dasuka faru, amma nabaku shekara d'aya zuwa biyu kacal, insha ALLAH sai kunzama abin kwatance a duniyar masoya. Ke dai kawai ki koyi yanda zaki zauna da matansa, dan gidan ya Muhammad zama akeyi namasu ilimi da kissa, kowacce jitake da kanta akan tayi karatu mai zurfi, saiki dage sosai akan karatunki, tunda inada tabbacin yaya bazai barkiba kema, zai maidaki makaranta, fatana dai kirage wannan sanyin naki, dan zama dasu Anty Aneesa sai jaruma, kuma mai wayo. Zan cigaba da baki haske a zaman mu, yanda kema zaki kwaci 'yancinki a hannun mijinki, harma kizama tauraruwa fiyeda kowa a zuciyarsa kinji". Kai kawai Amatallah ta jinjina mata, tasaka hannunta biyu ta share hawayenta, sai dai k'asan zuciyarta tana tunanin yanda za'ayi ta zauna da Uncle d'in nata a matsayin miji, bayan zuciyarta tana girmamashi tamkar mahaifinta, tabbas maganar Anty Nazeefa gaskiyace, babu wanda zai kalli Uncle yace yakai shekarunsa, saboda k'aramin jiki da ALLAH yabasa, baza'a kirashi siririba, hakama bashida k'iba, sannan yana tsaka tsaki a tsawo, ba dogoba ba gajereba kuma........ Girgiza tan da Nazeefa tayi ne yasata sakin ajiyar zuciya. Nazeefa tace, "kinga bar aikin mu karya tukunna ko". " to". Kawai Amatallah tace tamik'e, MacLean da brosh ta d'auka tafita. Nazeefa tabita da kallo a sanyaye, tausayinta na kuma ratsata, a fili tace, "insha ALLAH zakiyi farin ciki a rayuwarki Khadija, nasan ya Muhammad zai kawo sauyi a duniyarki, ALLAH dai yak'ara baki hak'urin jurewa wannan jarabawa tarashin iyaye lokaci d'aya, kuma yakawo mana sauk'in rikice-rikicen dasuke sanadin wargaza farin cikinmu a k'asarnan. ALLAH ma yay miki gata ke, tunda yabarki da Ya Muhammad, a kwai yara irinki masu yawa dasuka shiga halin k'uncin rashin families d'insu ta sanadin irin wannan rikice-rikicen *SIYASA KO K'ABILANCIN*, amma rashin gata damasu tallafa rayuwar tasu yasasu shiga k'angin wahala da tarwatsewar rayuwar tasu suma, ALLAH ka kawomana iyakar wad'annan matsaloli dai." Nace, "amin Nazeefa😭🙏🏻. ____________________________ Tunda yafita sai Aneesa tafad'a gadonsa ta hau rusa kuka, tabbas sunada aiki agabansu, yarinyarnan bama ganinta yakeba a shekarun baya yasuka k'are, kullum zancenta na bakinsa, inaga yanzu ta dawo kusa dashi, tana amsa sunan matarsa kuma. Tunda k'addara ta dawo da Amatallah Kano basu sake samun kan mijin suba, motsi kad'an yana gidansu, dasunyi magana saiyace yaje duba jikin babane, insunyi k'orafi akan Amatallah yace basuda tausayi. Tasan yarinyar nabata tausayi, amma gaskiya tana matuk'ar kishin mijinta, taso ace daga ita sai shi da 'ya'yansu zasu rayu, amma tunkamma tazo gidan saita taras wata tarigata shiga, maimakon abarta taji da zafi d'aya, gashi kuma rana tsaka ankuma aura masa wata, k'aramar yarinya ma, sa'ar k'anwarta ta biyu. Dolene ta d'auki mataki wajen ninka soyayya da kulawar datakema mijinta fiyema data dacan, dan tafison yasota fiye da kowacce acikinsu. jibafa tunda tayi sallar asubahi taketa kaida kawo wajen ganin tahad'a masa break fast mai rai da lafiya, saboda ganin kwana biyu bayacin abinci sosai saboda damuwar dayake aciki tarashin amininsa. (Duk da dama shi bamai yawan cin abinci baneba) Amma dan wulak'anci shine yafice wai sauri yakeyi, yanzu haka kuma yanacan wajen bak'ar yarinyar can. saita kuma rushewa da kuka kuma. Nace, ''bantan uba, Aneesa kinada aiki wlhy🤣, zan bama Xoxo kwangilarki😜". Ita kanta Fateema abin yabata mamaki, ganin yafita cikin fushi ko d'akinta bai kallaba, bayan kuma k'a idarsane duk Safiya zai shiga d'akin wadda ba itace da girkiba su gaisa, hakama idan yadawo aiki zai shigo miki, yaji ya lafiyarki keda yara, da darema kafin a kwanta zai shigo yamiki sai da safe yama yaransa addu'ar barci. Amma yau ko yaran bai sauraraba, saima k'arar bud'e gate da rufewa sukaji. Cikin damuwa tagama musu shirin makaranta ta turasu wajen Aneesa suyi break fast, amma sai suka dawo suna sanar mata momyn batanan, kuma ko Saifudden ma ba'ama shirin school ba. Tashi tayi tafito, ta lek'a 6angaren Aneesa batanan, har bedroom sai Siddiqa dake barci a kan gado, tad'anyi knocking k'ofar toilet amma shiru, saifudden ne kawai kwance afalo lullu6e da towel, da alama wanka aka masa ba'akai ga shiryashiba ma, dan ga uniform d'insa nan a gefensa da manshafawa da turare. Kallon Sahib tayi tace, "Sahib jeka saman Abbu kagani kotanacan tana sharane". " to Umma". Sahib yafad'a yana fita da gudu. Babu dad'ewa ya dawo yafad'a mata tana d'akin Abbu tana barci. "Barci kuma? lafiya kuwa?". fita tayi tana fad'in " Abulkhairi tada Saifudden ka shiryashi ina zuwa". Sai da tayi sallama kusan sau uku sannan Aneesa ta amsa. Fateema tashigo d'akin idonta akan Aneesar. "Momyn yara lafiya kuwa?". Tashi Aneesa tayi zaune, tayi kwafa sannan tafad'ama Fateema abinda yafaru, dan aganinta wannan matsalace dazasu raba tare sukuma d'auki mataki akanta. Fateema tace, " Humm momyn yara kenan, nimafa haka yaymin ranar da yarinyarnan ta farfad'o, gaya mikine kawai banyiba". Aneesa takuma yin kwafa, tace, "Wana mataki kike ganin zamu d'auka? inba hakaba yarinyarnan saitama kiremu daga kan 'yayanmu wataran, dan naga rawar jikin dayake akanta tayi yawa tunkanma tashigo gidan, raina mana hankali kawai akayi, za'ace wani babanta yarok'eshi ya aureta, wlhy dama can son yarinyarnan yakeyi, shima Baban nata ya gane hakanne shiyyasa ya k'ak'aba masa. nifa har mamakin yanda babanku yayarda yama Muhammad wakilcin auren nakeyi, bayan kuma yasan keza'ama kishiya". Duk da maganar Aneesa ta k'arshe ta 6atama Fateema rai haka ta danne saboda kishi na cinta itama, tace, "miye shawararki to akai? Nasan dai Muhammad bazai ta6a sakin Amatallah ba, kodan k'aunar mahaifinta dayakeyi". ''Yo idan shi bazai iya sakintaba, ai ita saimu sata masa bore tace bata sonsa, ai dole dai ya barta ko". " hakane, amma tayaya zamuyi hakan?". ''Muyi tunani na kwana uku, abinda kowa ya yanke saimu tattauna yiwuwarsa mugani kawai, koya kikace?". "Hakan yayi d'in, yara sun shirya, ke suke jira karsu makara". Mik'ewa Aneesa tayi suka sakko k'asa tare, a gaggauce suka bama yara break fast dan mai keke napep d'in dake kaisu makaranta yazo................✍🏻 Nace, " humm, wai Fateema da Aneesa ne yau a inuwa d'aya😂, lallai Amatallah da k'arfinta tashigo💪🏻🤣. 🤩👎🏻 Rashin comments d'inku kesani wannan laziness d'in, buk'atar typing d'ina kullum yana hannunku☹✋🏻, inkun gyaran nima zakuga sauyi a gareni🤷🏽‍♀😏. 🚶🏻‍♀ *_ALLAH ya jik'an iyayenmu😭🙏🏻_* [1/16, 1:30 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_* *_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡 _{home of expert and perfect writer's}_ *_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉ _(Hattara matasa)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* ____________________ *_Number 16_* ____________________ Da gudu ta wuce Furera matar kawunta yayan Ammi dake tsakar gida tana wanke-wanke. "Ke Amatallah lafiya kuwa?". Anty Furera tafad'a a tsorace tana zare hannunta daga ruwan wanke-wanken, ganin tawuce d'aki itama tatashi da gudu ta shige inda Amatallah tashiga harda rufe k'ofar.🤣 Ganin haka da Sadiya tayi matar k'anin Ammi itama saita afka d'akinta ta banke k'ofa harda sakata. Sufa duk zatonsu wasune suka biyo Amatallah d'in, gashi mazan gidan duk basanan sun fita. Tashi Amatallah tayi daga kwanciyar datayi a gadon Anty Furera danjin tarufe k'ofa. ''Lah Anty Furera lafiya kuwa kika rufe k'ofar?". " keza'a tambaya Amatallahi, miyafaru kika shigo gida da gudu haka?". Sai yanzu Amatallah tatuna da yanda tashigo, dariya tashiga tuntsurama Anty Furera, dan ganin jikinta har rawa yake saboda tsoro. Sai da Anty Furera tamata magana sanan ta tsagaita da dariyar datakeyi, "Anty Furera babu komaifa, wai da kina zaton minene?". Ajiyar zuciya Anty Furera tasauke, " kai Amatallahi kin d'auki hak'ina wlhy, kinsan garinan ba lafiya yacikaba, har yanzu a d'ar-d'ar kowa yake, waya biyoki haka to?". Guntuwar Dariya Amatallah tayi, ''kai Anty Furera haka kike da tsoro ashe?, babu komai wlhy, bud'e kiga wayarda Uncle ya siyamin". Amatallah tayi maganar donson kauda tanbayar da Anty Furera kemata. Bud'e d'akin tayi, sai lokacin itama Anty Sadiya tabud'e nata. Fitowa tayi tana tambayarsu ko lafiya taga sun shiga d'aki?". Labari Anty Furera tabata, Amatallah bata bari zancen yayi tsawoba tabasu kwalin wayar suka shiga kallo da yaba k'yanta. *********** Uncle M.A kam haka yabar jos cikin farin ciki da kewar brother d'insa, dan baibar garinba sai da yabiya ta gidan su. Komai ya k'one, da Alama ma ankuma sakama gidan wutane, dan randa abun yafaru gobarar bako ina ta cinye hakaba, amma yanzu harda gidajen makwaftansa, bayan kuma waccan ranar wutar bata ta6a kowanne gidaba, anguwarma gaba d'aya tayi kaca-kaca. Mota yakoma yatafi kawai, wani 6angare na zuciyarsa na tuno masa abinda yafaru tsakaninsa da Amatallah, sai yakanyi murmushi, lokaci-lokaci kuma yakan kama d'an kwalinta dake kan cinyarsa ya shak'i k'amshin. Haryaje Kano ribbon d'inta na a tsintsiyar hannunsa. sai da zai shiga gida yacire d'ankwalin yasaka ribbon d'in ciki ya nannad'e ya tura a aljihu. Yau girkin Fateema ne, dan haka ita tabud'e masa gate. yauma kamar kullum a cikin kwalliya take, hakama yaransa suna gida saboda Alhamis ce babu islamiyya kuma ana hutun boko, itama Aneesa cikin kwalliyar tafito tamasa sannu da zuwa, suduka basusan ma inda yajeba.😜 Da taimakon Fateema yay wanka, sanan ta shirya masa abinci, bai ciba sai da suka dawo sallar Magrib shida yaransa. Suna kammala cin abinci suka fita sallar isha'i, daga can gidan su yawuce da yaran gaba d'aya, suka gaida kakanninsu. Sun dad'e agidan suna hira shida Jabeer da Shehu da Nazeefa, Rabin hirar duk akan tafiyarsace dakuma Amatallah, innani dai bata saka musu Baki sosai, amma tana saurarensu, baba kam tunima yayi barci, dan babu laifi jikinsa da sauk'i. Basu koma gidaba sai da yaga plashing d'in Fateema, dole yatafi shi kad'ai yabar yaran nan, dan dare yayi, kuma duk sunyi barci, gashi a Napep sukazo ba motaba, shima mashin d'in Jabeer ya kar6a yatafi a kai. ___________________________ Gobene takama tafiyar Uncle, duk abinda yakamata ya kimtsa yayisa, abinda ya danganci gidansa dana mahaifansa duk yamik'ashi hannun Jabeer, hakama lamarin kasuwa, dukda akwai yara masu kulada shagunan, amma dole sai da mai kulawa lokaci-lokaci. Abu d'ayane ke damunsa arai dabai samu koda kafa harsashin saba, yarasa wazai fara tunkara da batun? Dan bakowa baneba yakeda zuciyar irin wannan jihadin, musamman ma daya kasance abune da sai an ta6a aljihu. Zuciyarsace tashiga bashi shawarar kiran Sabi'u m Ali. Wayarsa ya d'auka sai dai zuciyarsa na fad'a masa yakira ko karya kira, danya kai tsawon wata 10 rabosa da waya dashi, dama can yafisu k'ok'arin kira a waya dama zumincin dagashi har marigayi. Shawara ya canja, yafara masa test massage. kusan mintuna 15 saiga kira yashigo. Wayar ya d'auka yana k'aramar dariya, Dan ganin Alhaji Sabi'u ne. Sai da ta tsinke sannan shi ya kira. Alhaji Sabi'u na d'agawa Uncle M.A yafara bashi hak'uri kawai. Dariya Sabi'u yayi daga can yace, "ya zanyi daku, kai da Isma'il ko kad'an bakwason zuminci dani na lura". " a'a wlhy, ba haka baneba, amma amana afuwa kanmu bisa wuya". "Hhh shikenan ya wuce aii, ya gida ya iyali?". " duk lafiya lau muke". ''To Alhmdllh". Gyaran murya Uncle M.A yayi, sannan yace, "wlhy maganace a bakina, gashi kuma ban saniba ko kana kano?". " eh ina Kano, ai munma dawo gaba d'aya, zirga-zirgan ta isheni ne". "A lallai na yarda munada laifi sosai a wajenka, yanzu nan har kadawo da iyalinka Kano amma babu labari balle a k'ulla zuminci?". " to nima nayi laifi amin hak'uri, bama su dad'eba, 3month's kenan da dawowar, kaina bisa wuya". Still dariya Uncle M.A yayi, yace, "shikenan to, indai ban takuraka ba zuwa 4:pm insha ALLAH zan shigo, Dan gobe zan bar k'asar ne". " mutumina ina kuma zaka fad'a haka? Halan kaida Isma'il ne?". "A'a, nasan namaka laifi gaskiya, amma Isma'il ALLAH yamasa rasuwa kusan 6month's ago". yak'are maganar hawaye na cika idonsa. A can kuwa Sabi'u ya masifar rikicewa, sai sallalami yakeyi, dole Uncle M.A ya yanke wayar, dan k'ara karya zuciyarsa yakeyi. kusan mintuna goma sannan Sabi'u yasake kira, yamasa ta'aziyya sosai sannan yace babu damuwa yazo su had'u a gida, zai turo masa address d'in inda suke yanzun. Uncle M.A yamasa godiya sukayi salama. Jin gina yayi da kujera ya furzar da huci, a hankali ya furta ALLAH yajik'anku brother, I miss you so Much wlhy. Har Fateema tashigo ta shirya masa abincin Karin kumallo a k'asan carpet bai saniba, ya Lula sosai a duniyar tuna rayuwarsa da Brother d'insa. Ganin shirun yayi yawa Fateema ta k'arasa kusadashi ta zauna. Sai da ta ta6a kafad'arsar sannan ya juyo yad'an kalleta. " haba Nurri tunanin mikake hakane?". "Kansa kawai ya girgiza mata baice komaiba". Shuru tai tana Kallonsa kawai, amma fuskarta ta nuna alamun shiga damuwa. Hannunta yakamo yana murzawa a hankali, cikin sassanyar muryarsa yace, " my Tee... ina tuna brother ne". Tausayi yabata sosai, tasan har Abadan mijinsu bazai ta6a manta Baban Ama ba, Dan ubangijine kad'ai yasan irin k'aunar dasukema junansu. hannu tasa tad'an shafi k'asumbarsa zuwa gemu, sorry Nurrina, kacigaba damasa addu'a, muma duk ita muke jira, ALLAH ya gafarta musu sukuma". "Amin ya rabbi". " please abinci to, karya huce". 'Dan murmushi yayi ya sauka yana fad'in "wayo dai za'amin. yara fa?". " taf ai wad'an nan tuni suka karya tun kana barci". "Tofa lallai, yau kuma ba'a jira Abbu ba?". " hhh aiko dai basu jirakaba, harma mai lesson d'insu yazo". "OK, bara nima kiga na karya, fita zanyi naje nadawo da wuri, sonake yau na yini a gida ina kallonku kawai". " kai Nurri, saikace wad'anda zasu mutu?". "Mutuwarma ai bamuda tabbas d'in rashin zuwanta my tee". "hakane kuma Nurrina". Bayan ya kammala break fast yay wanka, gayu sosai yaci cikin shadda galila brown color mai duhu, yayi k'yau sosai, ya d'ora hular zanna bukar itama brown. Fateema dake fesa masa turare sai k'od'a k'yan dayayi take. Murmushi yayi yana kashe mata ido d'aya, " my tee fesamin turarennan sosai, wata k'ilma nasamo ta hud'u". Daina fosa turaren tayi, ta wani had'e fuska ta juya masa baya. Dariya sosai yayi, har hakwaransa na bayyana, ya rungumeta ta baya yana mata magana a kunne, "my tee... bakwason ta hud'un ne?". Juyawa tayi suna kallon juna, ta d'ora d'an yatsanta saitin zuciyarsa, idonta akan face d'insa, shima kallonta yakeyi yana murmushi, " Nurrina indai ina cikin nan ❤ ban damuba, kayi in dai amaryace, ai kowa da halinsa zai zauna." Rungumeta yayi yana murmushi, "my tee... Karyi kokwanto kinji, kinacan k'asan-k'asan zuciyar Muhammad, babu kuma wata mace dazata iya tureki ko wacece ita kin gane". Dad'ine sosai yakama Fateema, takuma rungumeshi tsam ajikinta tanaji kamar tashige kawai ciki, a hankali tace, " I love you more my Nurri". Shima a hankalin kamar mai tsoron ajisu yashiga jero mata kalamai masu kwantar da hankali, kai kace itaka d'aice matarsa babu wasu. Hakan da Alhaji Muhammad kema matansa yakesa kowacce d'aukar kanta itace mowa, Dan duk matar data kasance tana tare dashi, yakan nuna mata soyayya tamkar ita kad'ai gareshi, shiyyasa suke masifar kishi da juna, kowacce d'auka take anfi sonta da k'aunarta. Shikam yanayin hakane danya saka kwanciyar hankali da farinciki a tsakaninsu, kuma Alhmdllh yaci nasara da salonsa😊. Tare suka sakko falon k'asa, ya shiga 6angaren Aneesa. A falo ya isketa tanama Siddiqa kwalliya, idonta a k'ofa harya shigo dan tunkan ya shigo k'amshinsa yayo gaba, ba k'aramin d'aukar hankalinta kwalliyarsa tayiba. Ta sakar masa murmushi, shima ya maida mata murtani yana zama kusada ita. "Dear irin wannan d'aukar wanka haka? ina zuwa?". " zanje Jos ne wajen amarya". Baki tad'an ta6e badai tace komaiba. "Ko bak'yason najene?". 'yay maganar yana d'aukar Siddiqa dake cinyarta'. "ni a suwa dazan hanaka zuwa wajen matarka?". Kusada ita yamatsa sosai, yasa hannu d'aya ya sak'alo k'ugunta dashi tareda kuma mannata da jikinsa, "ke a matata wadda nake tsananin so mana my Neesa". Kallonsa tayi tana wata dariya ban yardaba. Goshinta da la6annta ya sumbata yana kuma mannata jikinsa da fad'in " kobaki yardaba ne my Neesa?". "Humm dear kenan, zaka wajen wata kuma kanamin dad'in baki, da dai a baya dai na yarda, amma yanzu kam ganganne". Siddiqa ya gyarama kwanciya a cinyarsa yana dariya, " My Neesa kice yanzu ni kinbar yarda dani Ashe?". "Ya zance nabar yarda dakai kuwa, na yarda dakai mana, akan wannan maganar daine kam sai a hankali". " lallai naga ta kaina, to maida wuk'ar, babu inda Muhammad d'inki zaije my lover, zanje cikin garine wajen wani abokina, insha ALLAH yanzu zanje na dawo, sonake yau na kasance daku Ku kad'ai, fitarma danta zama dolene da banyiba". Murmushi tamasa, harda masa kiss a kumatu. "Ya mik'e da Siddiqa a kafad'a, " humm my Neesa kishi". Itama mik'ewa tayi tana dariyar, "yo kaga laifina ne dear?, Kasan kuwa yanda nake jinka kuwa? ba k'aramin danne zuciyata nakeba idan naga wata mace ta ra6u da kai, amma babu yanda zanyi, haka ALLAH ya k'addaramin raba dai-dai d'inka da wasu mata". ta k'are maganar kamar zatayi kuka. Tausayi tabashi, dan shi kansa yasan Aneesa na matuk'ar k'aunarsa fiyeda tunanin mai tunani, shiyyasa shima yake mata uzuri akan wasu abubuwan, murya a sanyaye yana kallon kwayar idonta yace, " I love you so much my Neesa". jikinsa ta fad'a, tahad'ashi shida Siddiqa ta rungume itama tace, "I love you Abadan my Heartbest". Sosai yakuma mannata da jikinsa, yana sakar mata tagwayen kisses a wuya. 🤣ho Uncle Muhammad kazama na......., uhm babu ruwana dai🤭. Lokacin dasuka fito falo tuni Fateema ta shak'i haushi, amma kokad'an bata nuna a fuskaba, saima wani salon kallo datake masa, hakan kuma saiya hasala zuciyar Aneesa, ta kar6i Siddiqa a hannunsa takoma batareda tamasa rakkiyarba. Fateema kuwa taji dad'in hakan sosai, ita kad'ai tarakashi, saida suka gaisa da mai ma yara lesson sannan yayma yara saiya dawo Fateema tabud'e masa gate yatafi. Duk yanda Sabi'u yabashi Address d'in haka yabi. Tarba aka masa ta girma, sai kace Wanda yadad'e da fad'an zaizo. Iyalansa duk sukazo suka gaisa, shima matansa biyu da yara 7, d'ansa namiji na fari harya zama d'an saurayi. Sabi'u yakuma yimasa ta'aziyyar Isma'il, da kuma jimamin wannan rasuwa, dan Alhaji Muhammad sai da yasanar masa duk yanda lamarin ya afku. sosai Alhaji Sabi'u yay ALLAH wadai da wanan hali irinnan 'yan siyasar k'asarmu da matasa, yakuma nuna fushinsa akan yanda irin wad'annan rikice-rikicen kan faru musamman lokacin gabatowar za6e, da an kad'a tambarin siyasa shikenan kowa yana cikin d'ar-d'ar na tsoron afkuwar tashe-tashen hankula na rikicin *SIYASA KO K'ABILANCI* dakan taso a irin lokacin. Da wanan damar Alhaji Muhammad yay amfani wajen sanar masa manufarsa shida Brother d'insa, sai dai mutuwa tai musu gaggawa. 100% Alhaji Sabi'u yabada goyon baya, da alk'awarin shima zai shiga a dama dashi a tafiyar. Alhaji Muhammad yaji dad'i da karamcin abokin Nasu, nan dai suka tattauna abubuwa da dama dasuka shafi k'asarnan kuma suke damunmu, musamman ma yankin AREWACIN NIGERIA. Abubuwan tamkar an shiryasune daga plan A zuwa Z. Rikicin boko haram kamar bazai k'areba, ALLAH dai yakawo mana iyakarshi, bayan kisan gilla da akaima al'ummar arewacinmu, sannan kuma sune ake kira da 'yan ta'addar, sai dai muna murnar samun sauk'in bomb's sai kuma na satar shanu ya shigo, shima abin mamaki a arewaci kawai yake faruwa kuma jama'ar yankin ke amsa sunan 'yan Ta'addar. Zaune bata k'areba fa bayan dak'ile Satar shanu sai kuma Kidnapper's da ayanzu sune ke addabar yankin na arewacin kasar again. Shin wannan lamarin bazai Baku mamakiba kuwa? bakwa ganin abubuwan kamar dama angama tsarasune daki-daki, idan wannan bai tasiriba sai a koma wancan?. Miyasa komai baya faruwa sai'a arewacin k'asar kawai? alhalin bushewar idanun matasanmu batakai ga aikata irin wad'annan manyan ta'addacinba. Ba wai dan ina 'yar arewa nake maganar nanba wlhy, sai sai kawai lamarin kan bani mamaki, yanda kowanne bala'i sun k'are a Arewacinmu. nasan kuma banima kad'ai ba, duk mai hankali yayi wannan tunanin. Shin a ina matsalar takene?. Manyanmu ne?. Talakawa ne?. 'Yan siyasa ne?. Matasanmu ne?. Kokuwa k'ulla mana akeyi dan a ruguzamu😭?". 🙏🏻ya rabbi kayi gaggawar ruguza duk mai son ruguzamu, kamana maganinsa kafin shi yayi namu, kahanashi zaman lafiya kafin shi ya hanamu, kahanashi farinciki kafin shi ya hanamu, kamasa abinda yadace da zalincinsa kafin shi yaci nasarar zalintarmu😭🙏🏻. Ubangiji gareka muke, kuma gareka muke Neman taimako, ya ALLAH karkamana hukunci da halayen wasu wawayen dake cikinmu masu busashshiyar zuciya wajen aikata sa6onka. ALLAH ka zaunar da k'asarmu lafiya, kabamu shuwagabbanni nagari masu k'aunarmu dason cigabanmu.🙏🏻 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*🙏🏻😭 [1/16, 1:30 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_* *_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡 _{home of expert and perfect writer's}_ *_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉ _(Hattara matasa)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* ____________________ *_Number 19_* ____________________ "Assalamu alaiki". 'Amatallah tafad'a yayinda ta k'arasa ga matsiyar budurwar. Cikin d'an murmushi ta amsa mata, tareda bata hannu alamar suyi musabaha. Itama Amatallah saita mik'amata sunama juna murmushi😊🤝🏻😊. Bayan sun gaisa Amatallah ta tanbayeta kotana a department d'in sune?. " eh". ta amsa mata da kulawa. ''Yauwa sister dan ALLAH ko akwai lecture yanzun?". "Yes sister, nanda 15minutes insha ALLAH". " ok ngd sosai". Budurwar ta jinjina mata kai tana murmushi. Har Amatallah ta juya zatabar wajen budurwar tace "amma ke sabuwar zuwace?". Juyowa Amatallah tayi tana gyad'a mata kai. Budurwar tace, "Nasamu friend kenan? sunana Fa'iza Abdul-hakeem Gwarzo". " Nice name dear, nikuma Khadija Isma'il Uba (Amatallah)". "Woow Nice name, sunan mamana kenan". Murmushi kawai Amatallah ta mata. Gurinda Fa'iza ta nunama Amatallah kusada ita ta zauna, nan suka d'an fara hira kad'an-kad'an, dukma Fa'iza ce k'arfin hirar. har dai 15minute's suka cika suka mik'e domin shiga lecture. Farin cikin da Amatallah ta tsinci kanta a ciki 6ata lokacine wajen bayyanashi ma. Tundaga wannan ranar sabo mai k'arfi yashiga tsakanin Amatallah da Fa'iza, itama Fa'iza Ashe matar aurece, harma takusa shekara da d'an k'aramin cikinta ma. Sosai suke maida hankali a karatunsu babu maganar wasa. Yanzu group d'in nasu sunzama su hud'u, Amatallah, Fa'iza, Rita, Goodness, idan ka gansu abin birgewa, duk kuma kusan shekarunsu d'ayane, Rita 'yar Taraba state ce, Goodness kuma 'yar Kaduna ce, amma duk sunajin hausa, barema Goodness, garama Rita kad'an-kad'an takeji, bakowacce kalmar Hausa take ganewa da k'yauba. Komai nasu tare sukeyi, bazaka ta6a tunanin mabanbanta k'abilu baneba, babu raini bare k'yamar juna, idan lokacin Salla yayi su Amatallah sukanje tareda su Rita, saisu sami waje su zauna a wajen masallaci harsuyi su fito. Rayuwar gidan Uncle kam agareta Alhamdllh, bata fuskantar matsalar komai, dan Nazeefa tsaye take a kanta. Itama kuma batasa wasaba wajen kulada abubuwan dasuka shafi gidan. tsakaninta da yaran kam sosai shak'uwa tashiga. Ko waya sukayi da babansu saisun bashi labarin Antynsu, da sweets datake siya musu kullum. Sosai yakejin dad'in hakan, dan yanason maison 'ya'yansa. _______________________________ Akwana a tashi babu wahala wajen ubangijin al'arshi, yau ga Aneesa da watanni hud'u a Dubai, ta murje tayi k'yau abinta, dolene kaganta ta birgeka😜. Yau bayan Alhaji Muhammad yadawo gidan a gajiye, ta taimaka masa yay wanka sannan ya zauna yin bud'a baki, (kasancewar alhamis ne). dukda bawani Cin abincine dashi sosaiba hakan bai hanata had'a masa 'yan abubuwaba wad'anda bazasu zama almabazaranci ba. Yana shan shayi suna hira kad'an-kad'an, acikin hirar tasune yake fad'in "my Nessa kifa fara shiri". Kallonsa tayi cikeda kulawa, " Dear! shirin me kenan?". 'Dan murmushi yayai, dan yasan yanzu zai tsokaloma Kansa rikicinta, ya kur6i shayin yana d'aukar remote dan rage k'aran TV, "my Nessa komawa Nigeria mana". " Dear Nigeria kuma? to saboda mi? kona maka laifine?". Yanda take jero masa tambayoyin saita bashi dariya, amma saiya gimtse baiyiba, ya ajiye mug d'in yajawota jikinsa, a hankali yake mata wani salon da yasata narkewa jikinsa, "my Nessa kinsan dai bake kad'ai bace dani, inada wasu matan ai, kuma sunada hak'k'i a kaina, yazama tilas Na saukeshi kuma, kiyi hak'uri zaki koma ita kuma Fateema saita zo". Wani k'ududun bak'in cikine yahana Aneesa magana, ta danne kukan da yazo mata. Jin tayi shiru ya lek'a fuskarta, " my Neesa!". Idanunta tad'ago ta kalleshi. yace, "miya faru?". Yunk'urawa tayi tatashi daga jikinsa, ranta a 6ace tace, " amma ai Fateemar ba lafiyane da itaba, itakuma d'ayar ai naga makaranta kace tanayi ko". Guntun murmushi yayi yana girgiza kansa, wato Amatallah Ce d'ayar, batada matsayin daza'a fad'i sunanta ita. Hannayenta yakamo ya rumtse cikin nasa yana murzawa a hankali, "hakane My Neesa, saidaifa kin sani Na Sani wanan ba hujja baceba dazan kare kaina a wajen ubangiji, abindama yasa kikaga babu Amatallah a tafiyar saboda haryanzun bata gama sabawa daniba, saboda yanda Auren namu yazo, tana buk'atar nagama koya mata yanda zata saba dani a matsayin miji kafin tasan hakan a aikace, rashin lafiyar Fateema bazai hana tazo gareniba kingane". Hannunta kawai ta zare daga NASA, ta tashi tabar masa wajen. Binta yayi da kallo harta shige bedroom d'insu. Iskar bakinsa ya furzar, ya girgiza kai tareda cigaba da bud'a bakinsa **** Tundaga ranar bai sake ma Aneesa maganar tafiyaba, yanata mata dai shirye-shirye da had'a mata tsaraba. Fateema ma anan tanata shirye-shirye, dan bazataje da yaro ko d'ayaba, Ummita ma anasata a school. Randa Aneesa zata taho ranar Fateema zata tafi. Koda Amatallah taji batun tafiyar bataji komai arantaba, saima tunanin yanda zasu zauna da Aneesa ita kuma, tanata Addu'ar ALLAH yasa itama Tamaka kamar Fateema, sauk'in tama akwai Nazeefa a gidan. Komai Na tafiyar Aneesa ya kammala, ana gobe zata tafi Alhaji Muhammad yasha rikicinta, hakadai ya shareta yanata lallashi. Washe gari su Amatallah sukama Fateema rakkiya har airport, basu baroba saida sukaga tashin jirginsu. yara basu damuba, tunda ga Anty Nazeefa gakuma Amatallah, garama Ummita tad'anyi kuka kad'an dataga Ummanta tashiga jirgi ta barta, saida Shehu yace mata allura Umma zataje sannan tayi shiru. Daga canma Alhaji Muhammad yayima Aneesa rakkiya, baibar airport d'inba saida yaga sun taso, harda kukanta kuwa. Saita bashi tausayi, har yakai ga mata addu'ar ALLAH ya sassauta mata kishinnan nata. Koda su Aneesa suka sauka Jabeer ne yaje ya d'akkota. tunda ta shigo gidan taketa faman ta6e baki, dan ganin fentin da gidan yasha, hakama dasuka shiga falon gidan taga an maido da k'ofar 6angaren bak'i ciki, taita baza ido don son ganin Amatallah, amma komai kama da ita bata ganiba, daga yara sai Nazeefa. Bayan tahuta taci abincin da Amatallah ta girka kafin ta wuce school, saita hau gyaran 6angarenta, (India tsaftace badaga bayaba Matan Na Uncle, dan Aneesa ma tafi Fateema tsafta gsky, dukda itama Fateeman bawai k'azama baceba, sai dai Aneesa irin matannan ne dakomai sunfi sansa k'al-k'al). Bata tambayi kowa Amatallah ba, har yara daketa bata labarin abinda antynsu ke musu, barema Saifudden dake nanik'e da ita. siddiqa ma nata yawo cikin 'yan uwanta danta fara tafiya. Amatallah kam yau lectures d'in yammane da ita, shiyyasa saida tayi girki ta tafi school, basu fitoba sai around 6:pm, a gurguje tamasu Rita sallama tashiga napep d'in dasuka tare mata, dansu a hostel suke, yau kuma Fa'iza ma batazoba, maybe jikintane dan cikinta yafara tsufa. Ana kiraye-kirayen sallar magriba Amatallah ta shigo gida, babu kowa a falon dan haka tashige 6angarenta kawai. hijjab kawai tacire ta tashiga toilet dan d'auro alwala. Koda aka idar da sallar magriba bata fitoba, dan fargabar had'uwa da Aneesa, da akayi sallar isha'i sai kawai tashigama wanka, tana fitowa ta shafa mai kawai tasaka bak'ar jallabiya. Yunwa takeji sosai, bataci abincin ranaba tafita, harta kai k'ofar fita tadawo falonta kuma, tayi haka yafi sau uku kafin tayi ta maula ta fito. Tana fitowa yara Na sakkowa daga sama suda Nazeefa, da gudu suka iso gareta suna mata oyoyo, duk rungumesu tayi tad'auki Siddiaqa da itama tashiga rubibin 'yan uwanta. Sannu da zuwa Nazeefa Tamata, tace, ''badai sai yanzuba?". "A'a Anty Nazeefa, tun magrib nadawo, kuna cikine shiyyasa. Ashe 'yan tafiya sun iso?". " kina fita suna isowa, dan inaga daga kaiki ma ya Jabeer yawuce ya d'akkosu". ''Ayya bara Na shiga Na gaisheta to". "Okey, kishiga tana ciki". Cikeda fargaba Amatallah ta nufi 6angaren Aneesa d'aukeda Siddiqa, d'ayan hannunta kuma tarik'e Ummita. Muryarta nad'an rawa tayi sallama, Aneesa dake zaune a falo tana fiddoma Siddiqa kayanta ta amsa. Shigowa Amatallah tayi, Aneesa ta d'ago ta kalleta, sukaima juna kallon ido cikin ido, kowannensu saida yaji fad'uwar gaba, amma Amatallah saitamata murmushi. Yayinda Aneesa ta kauda idonta, fuskarta kadaran kadahan, ba ad'aureba bakuma a sakeba kamar ta Amatallah. " bismillah ki zauna". Aneesa tafad'a tana zuge zip d'in jakkar kayan Siddiqa. Zama Amatallah tayi a d'ofane saman kujerar kusada ita, ta d'ora Siddiqa a cinyarta, yayinda Umminta ta ra6u da jikinta itama, cikin dauriya tace, "ina yini, kundawo lafiya". " lafiya lau, yamuka sameku?". "Lafiya lau Aunty". Daga nan kuma falon yay tsit, sai dariyar Siddiqa da Ummita kema wasa. Kusan mintuna uku babu Wanda yasake cewa komai, sai kuma Aneesa ta katse shirun da fad'in " ya karatu?". Amatallah tace, "Alhmdllh Anty". ''Masha ALLAH". daga nan kuma suka sake yin shiru, kowa da abinda yake kissimawa a zuciyarsa kan d'an uwansa. Mik'ewa Amatallah tayi tace, " bara mu barku Ku huta ". Bata jira cewar Aneesa ba ta fice. Aneesa tabita da kallo tanamai jin wani irin kishi a k'asan ranta, dukda tafi Amatallah haske da hanci Dan Aneeaa farace, koma nace k'yau, hakan bai hanata jin zafintaba da fargabar had'a miji da ita. Amatallah kam babu komai a ranta, sai dai ta kula halin Aneesa ya banbanta sosai da Fateema, a ranta tace ALLAH yabani ikon zama da kowannenku lafiya nidai. Nace, " amin Amatallah". A canma Fateema ta isa Dubai lafiya, sun rungume juna ita da mijinta cikin kewar junansu, tun a mota yake nuna mata yayi matuk'ar missing d'inta, sai shafa cikinta yake yana kissing wuyanta. Itadai murmushi kawai takeyi da mamakinsa, saikace ba yau wata matar tabar wajensaba. Koda suka isa gida dakansa yamata wanka, yakuma ciyar da ita abinci, daga nan kuma aka koma soyayya🤭, su Uncle fa babu dama, dole matanka suyita tsula kishi a kanka🤥. 🚶🏻‍♀ _____________________________ Abubuwa suncigaba da faruwa, wasu masu dad'i wasu marasa dad'i. Zaman Aneesa da Amatallah dai sai a hankali, babu wani kulawa babu kuma gallazama juna, dan ba gargad'in wasa Uncle yayma Aneesa ba akan zaman lafiyar gidan, yakuma tabbatar mata inhar yaji wani Abu daban ita zai hukunta, tunda itace babba. Itama Amatallah bai k'yaletaba, yamata gargad'i sosai. To Alhmdllh babu dai wani gagarimin Abu daya faru, dan kowaccensu na gudun 6acin rai, kuma ma ga Nazeefa, duk abinda yafaru a gidan takan sanarma yayanta. Rashin zamanma da Amatallah ke samu a gidan saboda makaranta saiya kuma sauk'ak'a wasu abubuwan. Duk ranar asabar kuma suka had'u suduka sutafi gidansu Innani su yini a can. Jikin babama Alhmdllh, dukda ciyone Na tsufa dai. Masha ALLAH zuwa yanzun kam su Alhaji Muhammad baifi sauran 1month su dawo Nigeria ba, kuma Alhmdllh yasamu nasarori sosai akan abinda yaje nema. Yanzu haka kam shirye-shiryen dawowar suketayi. Tunda kwanakin dawowar Uncle M.A yazama 10days Anty maijidda tazo gidan, wasu kayan gyaran fata masu k'yau dana gashi ta kawoma Amatallah, ta nuna mata yanda zatayi kullum indan zata kwanta, sai wasu turarurruka masu masifar k'amshin tsiya, Na wanka dana gashi, ga mayuka masu k'yau da k'amshin tsiya, Sosai tama Amatallah gargad'i akan tadage karta saka wasa a amfani dasu, sannan tace taringa shan fruits kullum safe da yamma, ga Nono shanu mai k'yau dana rak'umi tace tasaka a fright tanasha shima safe da yamma, sai kuma had'in Zuma da kayan k'amshi da mazar kwaila, shikuma da yamma kawai tanashan 3spoon. Godiya sosai Amatallah tamata, dukda bata fahimci dalilin Anty maijiddar Na bata wad'annan kayanba, bakuma tasan ma'anarsu bama, tadai d'auka Na gyaran fatane dakuma murjewar jiki. Duk yanda Anty maijidda tamata bayani haka ta dage sosai. aifa dandanan Amatallah tafara sauyawa, fatarta harwani shek'i takeyi, dama ga bak'inta mai k'yaune, k'amshi kam ba'a magana aii, ko da ga nesa ta giftaka saika jishi, su Goodness k'awayenta kullum cikin tambayar miya canjata haka sukeyi?. Itadai sai dai kawai tamusu dariya bata cewa komai, dan har lokacin basu ta6a sanin tanada aureba, duk zatonsu Uncle datake yawan ambata shike rik'onta dai, Fa'iza cema taso ta d'an d'agota amma saita doje. Fa'izan tace aibabu damuwa, inma tanada auren ai zasu sanine watarana. Aneesa ba wani ganin Amatallah takeba sosai, shiyyasa bata kulada canjawar datayiba, sai dai k'amshin datakeyi kwanan nan yana d'aukar hankalin Aneesa, harma take mamakin ina Amatallah tasamo wannan k'amshin haka?. Sai dai batada mai bata amsa, dodele tai gum da bakinta.🤐 ____________________________ *_RANA BATA K'ARYA_* yauce ta kama ranar dawowar su Uncle k'asarsu ta haihuwa, tunda asubahi Aneesa aka tashi tafara gyaran 6angarensa, saida taga komai yad'au haske da shek'i, hakama tadawo babban falon gidan, 6angarentama haka, Nazeefa dai nata kallon ikon ALLAH, Amatallah ma batasan hidimar da akeyiba, tunda tayi salla takoma barci, sai wajen 7:30 ta tashi tayi wanka, ta shirya kamar yanda Anty maijidda takira ta Umarceta. Bata dade da kammalawa ba Jabeer ya kirata akan tafito yazo d'aukarta. Mamakine ya kamata, dan tasan yaudai babu school, dan Asabar ce. Tana cikin mamakin saiga Nazeefa ta shigo itama cikin shiri. Kallonta Amatallah tayi tace, "Anty Nazeefa tare zamu fitane?". ''Eh". Cewar Nazeefa. " ina zamuje to, ko wajensu innani?". "A'a, kedai kiyi sauri ki shirya, dansu Ya Muhammad k'arfe 5pm zasu sauka, somuke kafin 3 mu dawo kuma. Amatallah batace komaiba tak'arasa shiri ta fito. shiru taji falon, dan haka ta tambayi ina yara?". Jikin motar suka k'arasa Nazeefa tana fad'a mata suna gidansu wajen innani, Aneesa kuma tafita itama. Mota suka shiga Amatallah Na mamakin wannan Abu, ina kuma duk zasuje abar gida shiru haka?, amma koba komai tayi murna, dama batason Uncle ya iskota agidan..................✍🏻 Nace, "humm, Amatallah kenan, zakiyi bayani dalla-dalla-dalla da bakinki😂😜. 🤩👎🏻 One Luv my sweet fan's🥰 *_ALLAH ka gafartama iyayenmh😭🙏🏻_* [1/16, 1:30 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_* *_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡 _{home of expert and perfect writer's}_ *_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉ _(Hattara matasa)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* ____________________ *_Number 17_* ____________________ Uncle M.A bai baro gidan Alhaji Sabi'u ba sai da suka tsara abubuwan masu yawan gaske, harda mutanen daya dace su tuntu6a domin samun had'in kansu a tafiyar. Bayan sun kammala tsare-tsarensu Alhaji Muhammad yaymusu sallama yataho bayan ya ajiyema yara kud'in shan Chocolate's. Daga gidan Alhaji Sabi'u gidansu yawuce ya gaida iyayensa, nanma yad'an dad'e sannan yataho da burin zai koma da daddare. Harya tada mortar ya kashe, waya ya d'auka yafara laluben Number Amatallah yana murmushi. Rabonsa da ita tunda yaje jos, kullum yakira saiyaji wayar a kashe, idan kuma sunyi waya da kawunta kunya yakeji yace yahad'ashi da ita. Cikin sai'a kuwa yau sai Number tashiga. Amatallah na zaune a tsakar gida itada Anty Sadiya da wata yarinyar makwaftansu Asiya tana mata kitso, Anty furera kuma nata kai kawo a tsakar gida tana girkin rana. Game Amatallah keyi a waya hankalinta kwance, jefi-jefi takan saka baki a hirar Asiya da Anty Sadiya. Kirane ya shigo wayar, wannan ne kuma karo na farko da aka kirata, dan ita mantawama take da wayar, tunda Uncle yabata suka gama gani ta kasheta. Bata kuma kunnawaba sai yanzu dataga games a wayar Asiya ta d'akko ta tura da films. Number babu suna, shiyyasa ko kad'an batayi zaton Uncle baneba. d'agawa tayi tareda manna wayar a kunnenta tace, "hello". d'an lumshe idanunsa yayi ya gyara zama sosai da kwantar da kansa a jikin kujerar motar. Amatallah takuma fad'in " hello wanene?". cikin Nutsuwarta tayi maganar. d'an murmusawa yayi sannan yamata sallama cikin sassanyar muryarsa datake matuk'ar so. Bata buk'atar k'arin bayani kam, danta ganesa. saita samu kanta da fargabar amsawa. Sai da Yakuma maimaita sallamar da cewa "My Best! Bak'ya jinane?". " inaji Uncle, ina yini". "Bazan amsaba, dan kinmin babban laifi my best, Wanda kuma kika cancanci hukunci mai girma da tsauri". Amatallah ta marairaice murya kamar zatayi kuka, " wayyo ALLAH na, minayi Uncle?". Daga Anty Sadiya har Asiya baki suka sake suna kallonta da mamaki, su gani sukeyi tana sane takeyi, saboda sungane Uncle d'in tane na Kano, kuma Mijinta a yanzu. Itakam kokad'an ba haka bane, babu wata manufa aranta, sai dai saboda shagwa6ar datakema babanta abayane kawai, saikuma take ganin Uncle d'in kamar shine Baban ayanzun, shiyyasa takan masa Abu tamkar yanda takema babanta, dan ita tama manta dawani batun aurensa dake kanta. Ba k'aramin canja tunaninsa shagwa6ar Amatallah tayiba, saiya samu kansa dakuma narke mata shima, ya manta matsayinta na d'iyar Isma'il brother d'insa, yarinyar da aka Haifa a tafin hannunsa harya rad'a mata Suna. "Uncle please, kafad'amin laifin dan ALLAH?". " Ajiyar zuciya ya sauke, yakuma k'asa da muryarsa sannan yace, "miyasa kika kashemin waya? tunfa dana tafi bakiko nemeniba my best". " kayi hak'uri Uncle. ALLAH mantawa ma nayi da wayan, sai d'azun natuna dazan tura games aciki". "Uyim an manta da Uncle, amma ba'a manta da tura games da Films ba ko? zan ramane ai nima". " wayyo Uncle bazan sakeba ALLAH insha ALLHU, kaji Dan ALLAH". "Shikenan, amma idan kin sake zan hukun taki, kin amince?". Kanta ta d'aga masa kamar yana gabanta, tace, " to Uncle, sai kuma tace uncle katafine? ". "A'a ban tafiba dai tukunna, amma insha ALLAH gobe k'arfe 3pm zan wuce". "Ayya, ALLAH ya kaimu lafiya Uncle, yasa kaje a sa'a kadawo da Nasara". " amin my best daughter, ALLAH yamiki albarka kinji, ya gafartama su brother ". Murya a raunane ta amsa da amin. Sallama sukayi akan zai kuma kiranta anjima Dan yaji muryarta tafara canjawa, bayason jin kukanta ko kad'an. Tana ajiye wayar Asiya ta tuntsure da dariya harda rik'e ciki. Kallonta Amatallah tatsaya yi da mamaki tareda k'ok'arin had'iye kwallan data cika mata idanu. " Asiya lafiyarki kuwa?". "Ah, k'alau nake kuwa, Amatallah irin wannan lobayya haka". " lobayya kuma Asiya? Uncle d'inanefa". "Uhm ai Nasan Uncle d'in nakine nima, ALLAH dai ya kaimu Kano kawai musha kallo, ALLAH da nacema Abba banson karatu a Kano, amma yanzu kodan ke can zanje". Baki Amatallah ta ta6e, tace, " k'yadai ji dashi". Anty Sadiya dai batace komaiba, sai 'Yar dariya datakiyi itada Anty furera. Amatallah bata fahimci duk inda suka dosaba, tacigaba da game d'inta, sai dai k'asan zuciyarta tana mamakin a salon da Uncle ya amsa mata waya yau, sai kuma narke murya yake k'asa sosai, dukda tasanshi shid'in dama k'arshe ne awajen golden voice. Shiru Uncle M.A yayi yanabin wayar da kallo, kai kace acikine zaiga Amatallah ta 6ullo, gemunsa yashafa a fili ya furta " Muhammad mike damunka hakane? d'iyar Isma'il cefa, wadda a tafin hannunka aka haifeta". Ya k'are maganar da fad'in "ya salam!" tareda furzo iska daga bakinsa. Ya dad'e yana sak'awa da kwancewa Kafin yatada motar yanufi gida. *_Washe gari_* Misalin 2pm yasamu rakkiyar matansa da k'annen sa zuwa airport, yara sunsha kuka har saida yamusu wayo sannan. kafin jirginsu yatashi saida yay k'ok'arin kiran Amatallah amma wayarta a kashe, ya kira kawunta kuma yace baya gida wlhy. baiji dad'in rashin samuntaba, haka dai yashiga jirgi suka shilla. Jabeer ya maidasu Fateema gida da yara. Anty Maijiddah da Shehu da Nazeefa suka shiga keke napep suma suka tafi, dama anan sukazo. ___________________________ Tunda Uncle M.A yabar k'asar rayuwa gidansa ta canja salo, sunkoma rayuwar babu ruwan wani da wani, ko wacce harkar gabanta takeyi, idan an had'une dai za'a gaisa kowacce takama tsaginta. Tafiyarsa da kwana biyu Nazeefa ta had'o kayanta tadawo gidan, wani d'aki dake can sama kusada nasa ta gyara. Hakan kam bak'aramin haushi yabama Anresa da Fateema ba, amma babu yanda suka iya, Dan Nazeefa bata raga musu, shiyyasa duk suke shakkarta, ko Fateema dake 'Yar uwarta bata d'agama k'afa. Kullum Jabeer zaizo da safe yaga lafiyarsu, da yammama idan yadawo aikima yakan zo, shima shehu randa 'yan arzik'in ke kansa yana lek'owa, wadda kuma tamasa kallon banza a cikinsu kotak'i basa abinci yamata wankin babban bargo yay tafiyarsa. Anty Maijiddah ma takan lek'o ganinsu. Alhmdllhi jikin baba ma babu laifi, yasamu sauk'i, dukda lokaci-lokaci ciwon kan motsa masa. Kullum ta ALLAH Alhaji Muhammad yakanyi k'ok'arin kiran kowa yaji lafiyarsa, dakuma k'ara nuna soyayyarsa ga matansa, shiyyasa kowacce kejin kanta On top, tamkar ma mijin yafi kulawa da ita da yawan kiranta. Basusan inhar yakira d'aya dasun gama waya zai kira d'ayarba. Harma Amatallah dabawani sakewa take suyi hiraba, bare akai ga zancen soyayya, yakan daiji lafiyarta sukumayi hira kad'an. Hakanne kuma yafara tasirantar da shak'uwa a tsakaninsu, koyaya takan d'an saki jiki dashi, yayinda shikuma kanyi mamakin kansa a yanda yake gaza controlling d'in tunaninsa akan Khadija d'iyar Amininsa, wadda yake mata kallon d'iya abaya, a yanzunkan yafara ganin canjawar wancan matsayi. Datake dashi aransa, dan ko yaushe tunaninta Na mak'ale da zuciyarsa, a da yakan d'auki hakan tausayinta ne dayakeyi, amma a yanzu shi kansa yafara k'aryata zuciyarsa, Ita kanta Amatallah bazatace batajin wani Abu dangane da Uncle d'intaba, sai dai kunya da d'aukarshi a matsayi kamar babanta yagaza ganar da ita har k'agara take ya kirata a waya Dan taji muryarsa kawai, Dan dama can tana bala'in son muryar Uncle d'in nata. Gameda damuwar rashin iyayenta kam tana nan tanayi, kullum ta ALLAH saitayi kukan rashinsu da kewarsu, kuma takan dage wajen musu addu'ar Neman gafarar ALLAH kamar yanda Uncle kullum kan tunatar da ita. Ana cikin haka Result d'insu ya fito, Alhmdllh Amatallah tasamu kaso mai tsoka a WAEC d'inta, NECO ma haka dukda batakai WAEC d'inba, tayi farinciki sosai. hakama Uncle M.A. A kuma wannan tsakanin ne Fateema tafara laulayin ciki, hakanne yasaka Alhaji Muhammad yanke hukuncin Aneesa saita biyoshi, amma za'a bar Saifudden anan saboda school. zatayi wata hud'u tadawo sai Fateema taje, lokacin tasamu lafiya cikinta yayi kwari. Hhhh, tofa abin mema yasamu ga Aneesa dan batasan tsarinsa natayi wata hud'u bane ta dawo, ta d'auka indan ta tafi shikenan sai kuma ya kammala karatu su dawo tare🤣😜. Ai kam tashiga yauk'i da gwalangwaso anama Fatima kallon nice a sama. Duk da hakan ya Sosa ran Fateema saita danne, ta nuna murnarta da tafiyar Aneesa, dan itama batasan cewar Aneesar wata hud'u zatayi ta dawoba, duk ya 6oye musu bai fad'aba. Shiri sosai Aneesa tayi, Jabeer yashiga shigi da fici wajen shirya tafiyar tata. Watansa 1 da sati 2 Aneesa tabi bayansa. Ranar Fateema tasha kuka, dan 100% tagama yadda mijinta yafison Aneesa, ko kad'an bata bari Nazeefa da yaranta sun gane halin datake cikiba, saima ta wayance da laulayin cikine kawai. Nazeefa mutumce mai bin kwaf-kwaf akan mutaneba, wannan yasa itama bata kawo komai a rantaba ta d'auka gaske laulayine ya maida fateemar haka. Tafiyar Aneesa babu dad'ewa aka kammala komai Na makarantar Amatallah, kasan cewar Uncle M.A yanada fad'a aji a B.U.K d'in. Komai ya kammala zata karanci Medicine Amatallah tayi murna sosai, dan kullum burinta kenan ta karanci fannin lafiya, tun iyayenta Na da rai kullum labarinta kenan, Uncle M.A yarigaya yasan da wannan burin nata, shiyyasa ya cika matashi da amicewar Ubangijin al'arshi. Aikam ranar tayi tamkar ta fasa masa dodon kunne saboda murna. Farin cikin data shigane shima ya jagoraci nasa farincikin, har yakejin bashida wata matsala a rayuwarsa dan kullum burinsa yaga farinciki Amatallah baiwar ALLAH, marainiya. Samun makarantar Amatallah kuma yasa aka fara 'yan gyare-gyare agidan Uncle M.A, dan saita tare zata fara school. 6angaren daya ware dama dan babanta idan sunzo Kano su ringa sauka aka gyara, dan shima girmansa d'aya da 6angaren matansa, sai dai shi k'ofarsa ba ai nahin cikin babban falon gidan takeba, tana cikin corridor d'in dazai sadaka da falon ne, wannan yasa Uncle yace a maido k'ofar tadawo cikin falon, sai a toshe waccan. Haka kuwa akayi, Shehu ne yatsaya akan aikin, aka kammala komai tsaf aka sake sabon fenti har waje, dan danan gida ya d'auki haske da shek'i, daka gani kasan sabuwar amarya zata shigone. Fatima bataji zafin kishiba sosai kamar sanda akai aure Aneesa, dan yanzu harda ita akaje wajen had'a lefen Amatallah. Ita da Anty Maijiddah da Nazeefa da Jabeer, sai Gwaggo Rakiya k'anwar Innani, akwatina Hud'u masu k'yau, kuma sun zubo kaya masu k'yau da inganci. Kwana biyu da had'o lefen suka shirya suka kai jos. Ranar Amatallah kam tasha kuka sosai, dan abin Na bata mamaki, wai Uncle ne mijinta, mutumin datake kallo a matsayin babanta, wayyo tasan dasu baba nada rai da hakan bazai ta6a ya faruba, shi kansa Uncle bazai kawo hakan a ransaba, amma yanzu k'addara taragayi fata. Babu Wanda bai zubda kwallaba a wajen, haka akama su Anty Maijiddah shatara ta arzik'i suka dawo Kano a ranar, suna mai jin tausayin Amatallah sosai. An tsaida tarewarta nanda kwanaki goma, ta tare da sati d'aya zata fara school d'inta. Tun kuma daga wannan lokacin ko Uncle ya kira Amatallah a waya bata d'agawa, daga k'arshrma saita kashe wayar baki d'aya. a ganin inta d'aga bazata iya masa maganaba, dan sai a yanzune batun Auren nasu ke matuk'ar damunta, dan ta tabbatar da gaskefa akeyi Uncle yazama mijinta. Abin ya damu Uncle M.A matuk'a, da rashin d'aga wayarsa da Amatallah keyi yana cin zuciyarsa, daga k'arshe ma saiyabar samuntaba kwata-kwata ___________________________ Aneesa na zaune kusada Alhaji Muhammad dake shan fruits salad data had'a masa na bud'a baki, (dan duk litinin da alhamis d'in duniya sai yayi azumi), tsaf take cikin kwalliyar d'aukar hankali, Siddiqa na gefe zaune (danta fara zama) an barbaje mata kayan wasa. Lokaci-lokaci yakan d'ago ya kalleta suma juna murmushi, haka Aneesa keso, takasance daga ita sai Muhammad d'inta, shiyyasa wannan damar data samu take tattalinsa tamkar kwai a cokali, a 6angaren kula da miji daga Aneesa har Fateema kowa kwararrene. Kiran wayarsa da akayine yasaka Siddiqa tsorata harta fashe da kuka. Su duka dariya sukayi, Aneesa ta d'auketa tare da d'akko masa wayarsa ta mik'a masa, dama tana hannun Siddiqa ne tana wasa da ita cikin kayan wasanta, wayar ta fad'a jikintane babu zato kuma aka kira, sai ringing d'in ya tsoratar da ita shine ta razana. Hakanne yabama iyayenta dariya. Har wayar ta tsinke Alhaji Muhammad bai d'agaba saboda dariyar da Siddiqa ta basu, sai da ta tsinke sannan shi ya kira, dama Jabeer ne ya kirashi. Bayan sun gaisa ya tambayi jikin baba da sauran abubuwa. Jabeer yace komai Alhamdllhi. "To masha ALLAH, akwai matsalane?". " eh to Yaya matsalarnan kam Alhmdllhi babu ita, sai sai kawu Hafizu ne ya kirani, wai akan punches d'in Amatallah ne, yace na tura masa Account Number d'ina zai turo kud'in daza'a saya mata anan Kano basai ansha wahalar saye daga can jos ba. shine nace masa to yad'an bani lokaci ina office amma zan kirashi. to shine nakiraka na sanar maka". "ALLAH sarki Hafizu, to in banda abunsa ko dai Isma'il nada rai ai inaga nine maima Khadija kayan d'aki ko, wannan maganarma a barta kawai, dama nayi niyyar maka magana akan zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu kuje kai da maijidda Ku za6o mata duk wani abinda ake buk'ata". " OK Yaya babu damuwa, shi yazan cemasa yanzun kenan?". "Ka barni dashi zan kirasa kawai". " hakan yayi to Yaya". "Yauwa, waifa jiya saina manta na sanar maka inason nafara turo kaya daga nan, muga kuma abinda ALLAH zaiyi". " kai Yaya wlhy nayi farin ciki, dama inata tunani akan kaje garin Business amma banji kana maganar d'ebo mana hajaba, ashe abin na ranka". Dariya Alhaji Muhammad yayi yace, "tom zan turo maka wasu kaya ta WhatsApp ka gani, idan sunyi saina turosu k'arshen watannan mugani koza'a fad'a". " to ALLAH ya tabbatar mana da alkairi Yaya". "Amin Jabeer, ya Shehu fa? yana zuwa kasuwan kuwa?". " da dai yafara wasa kam, amma tunda innani tamasa magana saiya maida hankali da zuwa sosai, kuma Alhamdllh zuwan nasa yana d'auke hankalinsa dan naga kamar shaye-shayen ma yarage". "Alhmdllhi, ALLAH ya shirya manasu baki d'aya". " amin Yaya, a gaidamun Siddiqa da Anty Aneesa". "Ok, zasuji, inka koma gida zan kiraka muyi magana da baba da innani". " shike nan saina koma d'in". Daga nana suka yanke wayar. Duk wayar nan da yakeyi babu Aneesa a wajen, tatashi tunda yafara wayar saboda kukan Siddiqa, har kuma yagama bata dawoba saboda tsayawa lalla6a Siddiqa tayi barci datayi. Har ya kammala shan fruits salad d'in bata dawoba, yashiga toilet d'in falon yay alwala yafita sallar Isha'i a masallaci..............✍🏻 🤩👎🏻 *_ALLAH ka gafartama mahaifanmu🙏🏻😭_* [1/16, 1:30 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_* *_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡 _{home of expert and perfect writer's}_ *_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉ _(Hattara matasa)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* ____________________ *_Number 18_* ____________________ Rashin samun Amatallah a waya yana k'ara damun Uncle M.A, sai yake ganin kamar tana cikin k'unci da damuwane. Yarasa wazai kira yahad'asu. Duk da yakira kawu Hafizu akan pinches d'in Amatallah d'in, yakuma nuna masa koda da ran Isma'il shine ya cancanci yama Amatallah kayan d'aki aii, bare kuma yanzu ma amatsayin matarsa take. Da k'yar kawu Hafizu ya amince, amma dukda haka yace zasu mata kayan ketchin, dole Uncle M.A ya amince da hakan. Duk da bawani gagarumin biki za'ayiba dai sunyi shiri bakin gwargwado. Su Anty Sadiya nata bama Amatallah magunguna, amma saita faki idonsu ta zubar batasha, duk basusan ta6argazar datakeyiba. Ahaka dai yarage saura kwana biyu kacal. Sosai Amatallah ta birkice musu, sai lallashinta kowa keyi daban baki, hardai ranar kaita kam batama da lafiya. Zazza6i sosai da ciwon kai sun addaba mata, harma k'ara narkewa takeyi wai koza'a d'aga😄. Amma saitagama sai kuma shiryawa sukeyi. Ranar daza'a kaita gida yacika da dangi da makwafta, akad'anyi shagali na mata kawai a cikin gida. Da k'yar Anty Furera tasaka Amatallah tayi wanka, babu zancen kwalliya dantak'i amincewa, farar hodama dak'yar tayarda ta shafa. Kusan k'arfe 11am saiga mutanen Kano sunzo d'aukar amarya, sai dai gayyar duk abokan Jabeer ne, kaikace shine angon, saikuma samarin family d'insu da mata kad'an su Anty Maijiddah da Nazeefa da Gwaggo Rakiya, saikuma wasu dangin baba na sokoto, dan sunzo suma. Amatallah tasha nasiha wajen iyayenta, kuka kam ai ba'a magana, dan kowa saida ya tayata ranar, kodan tuna iyayenta.😭 Ahaka aka d'akko Amarya Amatallah sai Kano, (gashi ango baya kusa bare yay lalashi🤭). Kai tsaye gidan Uncle M.A aka wuce da ita, sun iske gida cike taf da dangi na Sokoto dana nan Kano, makwafta da abokan arzik'i, (dan biki sosai sukayi abinsu dukda babu ango), nanfa gida ya rud'e da tarbar amarya 'yar k'amshi, aka rakata har d'akinta. Masha ALLAH na fad'a, dan ganin yanda aka tsara 6angaren nata, lallai Amatallah 'yar gatan Uncle d'inta, komai Pink colour ne da milk kad'an, (Uncle yadad'e da sanin Amatallah nason pink sosai, shiyyasa yace komai Jabeer ya d'auki pink). Aikam Kodai mak'iyi yagani dolene ya yaba, dan komai yayi acan-acan a talauce ba'a sarauce ba. Sunci sunsha Alhmdllhi, duk kuma sun yaba da karamcin da akai musu, musamman ma na Fateema, dan tanata rawar gani gaskiya. Amatallah kam tak'i yarda taci komai sai kuka take. Sai da k'yar Nazeefa da Asiya suka lalla6ata tasha fura da Nazeefa tasayo mata. Da daddare koda Uncle yakira yace Nazeefa tabama Amatallah wayar. Nazeefa batace mata komaiba tasaka mata wayar a kunne kawai, dansu ukune a d'akin, 'yan rakiyarta duk suna d'aya d'akin 6angarentan, Asiya kuma tayi barci saboda gajiyar tafiya.. Saukar Muryarshi kawai taji acikin kunnenta. A zabure tatashi, jikinta har wani rawa yake, azatontama koyana a d'akinne, ganin Nazeefa zaune kusada ita da waya a hannun saita saki ajiyar zuciya. Nazeefa kam dariyama tabata, amma saita gumtse batayiba, tasake mik'a mata wayar, dan Uncle nakan layi bai kasheba, "kar6a mana Amatallah, yanafa jiranki". Kunyar Nazeefa takeji, shiyyasa ta amshi wayar tasaka a kunne. Nazeefa kuma yashiga toilet d'in d'akin. Sallama yasake mata. Dak'yar ta iya amsawa, muryarta na rawa, hawaye harsun fara zirara a kumatunta. Jikinsane yay sanyi, yatashi daga kwancen dayake yafito corridor d'in falon, Aneesa da fitowarta kenan daga ketchin ta had'o masa shayi tabishi da kallon, rantane ya 6aci, ita tamayi zaton Fateema Ce, dan batasan yau Amatallah zata tareba. A kujerar dake corridor d'in ya zauna, muryarsa a matuk'ar sanyaye yace, " My best! kuka kikeyi dan kindawo gidana da zama?". Kanta ta girgiza masa tamkar tana gabansa batareda tace komaiba. Jin bata amsaba, saidai shashshekar kukanta yake jiyowa yace ''kinason nima namiki kukan?". Da sauri tace, "A'a Uncle na daina". " haba Khadija! Bak'yason zama dani?". "A'a inaso Uncle". tayi maganar da fashewa da kuka. " to Amma miyasa kike kuka Khadija!? ". " ba komai Uncle, ina tuna su babane". Ajiyar zuciya yayi, Yakuma raunana muryarsa sosai, "kiyi hak'uri Khadija kinji, badan ALLAH baya sonki bane ya d'aukesu, Kimusu addu'a ba kukaba, su tasuma tayi k'yau, dan koba komai mutuwar shahada sukayi, wannan kad'ai ya Isa muyima su brother murna ba kukaba kinji ko?". " to Uncle zan daina insha ALLAHU". ''Yauwa my best, yanzu ki share hawayenki kinji ko". "To" ta amsa tana share hawayen tamkar yana ganinta. "Yauwa babyna kokefa, yanzu dai fad'amin kobak'yason zama Kano nasa Jabeer yamiki visa ki dawo nan Inda nake?". Da Sauri tace, " A'a Uncle, inason nan, ba makaranta zanjeba?". "Makaranta zakije my best, amma sainake ganin kamar bazaki iya karatunba, saboda damuwar dakike ciki". ''Wlhy Uncle zan iya, inason karatu, indai kukane na daina bazan sakeba". " promise". "Promise Uncle". " tom ngd, yanzu kinci abinci ko?". "Eh nasha fura". " fura aiba abinci bace my best, nasan tunda aka sake tarewarnan bak'yacin abinci ko?". "Inaci Uncle". " kai ban yardaba". "ALLAH kuwa". " to shikenan, yanzu mikike sha'awar ci nasa a kawo miki?". "Babu komai Uncle na k'oshi, furan ya isheni". " kin tabbata". "Eh Uncle, ALLAH kuwa". " shikenan, karna kumajin kinyi kuka, yanzu kitashi kiyi wanka, saikiyi alwala kiyi nafilfili da karatun alku'ani, insha ALLAH zakiji zuciyarki tayi sanyi da salama, kima su brother addu'a, ALLAH yay miki albarka kinji". "Amin Uncle, ngd zanyi to". ''Yauwa my best D.., saida safe ko, zan sake kira bayan kin kammala naji kinbar kuka ko an karya alk'awarin Uncle bawan ALLAH". hannun tasaka tarufe fuskarta kamar tana gabansa, ta saki wayar a kan gadon, dariya yayi ya kashe wayar, dan yanajiyo mutsu-mutsunta kasancewar sabuwar katifa ko ledar ba'a cireba aka shinfid'a bedsheets d'in. Nazeefa ma dake tsaye a bakin toilet dariyar tayi, aranta tana jin sha'awar wannan soyayya ta uncle da d'iyarsa, a ranta tace ALLAH ya daidaita komai cikin sauk'i Amatallah. K'arasowa tayi ta d'auki wayarta, saitaga yakashe, ta kalli Amatallah dake shirin sauka a gadon tayi murmushi. Batace mata komaiba tafice d'akinta. Duk yanda Uncle yace haka Amatallah tayi, ai kam Alhmdllhi tasamu nutsuwa, saigata suna 'Yar hira da Asiya data farka har barci ya kwashesu. Washe gari akayi walima 'yan jos suka koma da yamma, bayan sunje gidansu Uncle sun gaida baba da jiki. Shatara ta arzik'i Uncle yasa Jabeer ya had'a musu, sun tafi sunbar Amatallah Na kuka tamkar ranta zai fita Anty Maijidda da Nazeefa sai lallashinta sukeyi, daga k'arshe dai saida aka kira Uncle yay lallashi da tuna mata alk'awarin datayi Na ta daina kuka sannan tayi shiru, amma sai zazza6i mai zafi ya rufeta, dole jabeer ya nemo mata Magani tasha. ____________________________ Tunda Aneesa ta fuskanci Amatallah Ce ta tare saita hau zum6u-zum6ure wa Alhaji Muhammad. Shareta yayi, yay tamkar baisan mitakema fushinba, saima ya maida hankalinsa wajen yima Siddiqa wasa, da daddare kuma yakira Fateema tabama yaran sukasha hirarsu. yakira Nazeefa tabama Amatallah tace tayi barci, saboda maganin datasha da yamma, da k'yarma tayi salloli takoma ta kwanta. sallama yamata ya yanke wayar. _____________________________ Rayuwa tacigaba da tafiya cikin Nasarori da jarabawa, yau kwanakin Amatallah hud'u agidan Uncle d'inta. Kullum da safe takanje har d'aki ta gaida Fateema, ta taya Nazeefa aikin gidan tana k'ara nuna mata komai yanda zatayi, Dan Fateema bata iya aikin saboda laulayin datake fama dashi, dama ita haka take fama a farkon kowanne ciki. Ita Nazeefa ma hakan dad'i yamata, Dan koba komai Amatallah zata kuma koyon abubuwan dasuka dace sosai takuma kware da wahalaryi kafin mijin nasu ya dawo. Yaran kuwa sun maida 6angaren Amatallah nanne wajen zamansu, itakam jansu takeyi ajikinta sosai, Dan tana kallonsu tamkar k'annenta, kuma hakan Na sakata Nishad'i sosai, saboda ta tashi ita kad'ai kwallin kwal a gidansu, babu Yaya babu k'ani, su Ammine komai nata, shiyyasa shak'uwa tashiga tsakaninsu sosai wadda taketa wahal da ita har yanzun. Uncle kam yana kira a wayar Nazeefa yace abata, wani lokacin dataga Nazeefa da wayar saita shige toilet d'in k'arya, har sai yagaji ya kashe, sai idan Nazeefa ta rutsatane sanan take amsar wayar. Ganin kamar yana takura mata saiya rage kiran, koya kira Nazeefa baya cewa abata. Aneesa kam bayan tagama fushinta ta sakko Dan kanta batareda ya kula da lamarintaba, danshi tausayi da dariya take bashi.. *_one Week ago_* Sati d'aya cif da tarewar Amatallah tafara zuwa school, Jabeer dakansa yakaita a motar Uncle. Sanye take cikin shigar mutunci, dantasha gargad'i wajen Uncle sosai. Atanface siket da riga porpul mai haske da ratsin pink kad'an da bak'i, saita saka pink d'in hijjabi mai hannu iya gwiwa, ta saka d'an abubuwan dabaza'a rasaba a cikin pink d'in lady's bag, takalman tama flat pink, duk da bawata kwalliya tayiba tayi k'yau sosai, sai k'amshin turarenta marar k'arfi dake fita k'ad'an, inba ma kusada ita kakeba bazakajiba kam. Gaba ta bud'e zata shiga Jabeer yace, "a'a shiga baya abinki Amatallah". Kunyace ta kamata, ta duk'ar dakai tana murmushi, a hankali tace, " a'a Yaya Jabeer, kabari Na zauna a gaban kawai, kaiba driver d'ina bane". Murmushi kawai yayi shima, yabud'e mata murfin motar tashiga gaban sanan yatada motar suka fice daga gidan. Motar tayi tsit, babu mai magana acikinsu, Jabeer yamaida hankalinsa ga tuk'i, itakam Amatallah kalle-kalle kawai takeyi tana sauraren redio daya kunna har suka shiga cikin BUK. Tunda suka shigo take addu'oin Neman nasara a rayuwar wannan makaranta dazatayi. Guri Jabeer yasamu yay parking, har Amatallah zata fita yace, "ki kunna wayarki Ya Muhammad yace zai kiraki". Kanta ta jinjina masa batareda ta juyoba. Atare suka fito, Amatallah nata kallon mutane dake kai kawo, wasu 'yan mata da samari wasu kuma samari zalla, wasu 'yan mata zallah, kowa dai da abinda yakeyi. wasu kuma daga cikinsu duksun zuboma su Amatallah idanu, hakanne yasaka Amatallah duk'ar dakai, Dan ita irin mutanen nanne da basu cika son taron jama'a ba. Jabeer ya kalleta yace, " muje". gaba yay tabishi abaya har zuwa wani Office. sai da yayi Knocking aka bashi izinin shiga sannan yashiga Amatallah Na binsa abaya. Mutumin dake zaune a office d'in wanda da alama shine mamallakin office d'in koda ba'a fad'aba, ya fad'ad'a murmushinsa da fad'in "Jabeer kun iso?". Jabeer ya amsashi da " eh yaya Lawan". Ta gefen ido Amatallah ta kalleshi, shima dai zai iya kaiwa sa'an Uncle d'inta. sai dai yafi Uncle k'iba sosai, Dan zaima iya ninkashi biyu..... Maganarsace ta katse mata tunani, ta kalleshi da Sauri saikuma ta kauda kanta, zama tayi kujerar dayake nuna mata. bayan zamanta ta gaidashi a ladabce. Shikuma ya amsa cikin fara'a. Sun tattauna da Jabeer, aka bata wasu takardu tasaka hannu sannan suka masa sallama suka fito. Har department d'insu Jabeer ya rakata, ya d'an mata bayani sannan yamata sallama yatafi bayan yabata 1k, yace bayan sun gama takirashi. Kanta ta jinjina masa tayi godiya. Tafiyar Jabeer babu dad'ewa wayarta tafara wringing, Jakarta tabud'e ta lalubo phone d'in, ganin sunan Uncle saida gabanta yafad'i, d'an wawwaigawa tayi Dan Neman inda zata zauna. A dakalin barandar wajen taje ta zauna, dan taga wajen yanada tsafta, ta d'aga wayar tasa a kunne. Sassanyar muryarsace tamata sallama. Itama a sanyayen tace, "wa'alaikassalam, Uncle ina kwana". " lafiya lau my best, amma mu munshiga yini nan, ya Ku isa makarantar?". "Eh Uncle, harma Yaya Jabeer yatafi". "okay, to babu wata dai matsala ko?". " eh Uncle, komai normal". "To Alhmdllh, saikuma a dage, banda wasa da k'awayen banza please my best! Kinji, banda biyema samari dan ke matar aurece kin sani". Idontane yacika da kwalla, itafa kokad'an batason atuna mata wai tanada wani aure, aurenma Na Uncle d'inta......... " kuka kikeyi ko my best!? ". Da sauri ta share hawayenta, tace, " a'a Uncle ina jinka". ''Imyiim, bagashi naji muryarki Na rawaba". "Uncle murace kawai keson kamani". " kokuma Uncle akeson yima wayo ba, anyway koma dai Yaya kiringa tuna alk'awarin da kikamin na kin daina kuka". Kuma share hawayen tayi, sannan tace "to Uncle, insha ALLAH bazaka sake jiba". " haka kullum kike fad'amin ai, amma kin kasa cika alk'awari". "To kayi hak'uri Uncle, zan kiyaye yanzu. yasu Anty da siddiqa?". " suna gida lfy lau, ni ina school ne". "Uncle inka koma ka gaida minsu". " zasuji insha ALLAHU, yanzu ki samu wata a wajen saiki tambayeta inkunada Lecture by this time kinji". "To Uncle sai anjima". ''Ok bey bey my heartbeat". Da sauri tace, " Uncle!". ''Yace uyim, yayane? kobaki yarda ke heartbeat d'ina bace?". A wani salo yay maganar. Da sauri ta yanke wayar, shikuma ya tuntsure da dariya daga can. Nima dai Na tayaka Uncle🤣, nasan Fans ma zasu tayamu🤩👎🏻. Amatallah tana yanke wayar ta rik'e ha6a tana fad'in "o ni Khadija, dama haka Uncle yake?". Amatallah kad'anma kika gani indai Uncle ne😂. Mik'ewa tayi tana cigaba da juya lamarin Uncle d'inta a zuciya, harta k'arasa wajen wata dake zaune can gefe itama cikin shiga ta kamala, aganinta ita kad'ai ta dace tama tambayar da Uncle yace tayi, dan tun tana waya taga wucewarta har zamanta awajen.................✍🏻 🤩👎🏻 One Luv my sweet Fan's🥰 *_ALLAH yajik'an iyayenmu._*😭🙏🏻 [1/16, 1:30 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_* *_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡 _{home of expert and perfect writer's}_ *_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉ _(Hattara matasa)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* _masoyanmu Amanna afuwa dajin *YAR SARKI CE* shiru, wasu 'yan dalilaine suka kawo hakan, amma insha ALLAH zata cigaba🥰🥰._ ____________________ *_Number 20_* ____________________ Wani Saloon Ya Jabeer yakai su Amatallah, a can suka iske Anty maijiddah, itadai Amatallah sai mamaki take a k'asan ranta. Babu 6ata lokaci wata farar mata tajata wata k'ofa, Ashe cikin gidane, koda suka shiga saita kaita wani d'aki, zani tabata tace tacire kayanta tana zuwa. Amatallah dai mamaki dukya kasheta, amma duk abinda aka sakata babu musu takeyi, tasan Anty maijidda dai bazata cutar da ita ba. Tana gama cirewa babu dad'ewa matar tadawo da kwa6a66en Abu a boket k'arami. Mik'a mata boket d'in tayi, tace, "dan ALLAH karki cutar da kanki, ki tabbatar ko ina Na jikinki yasamu, bayan kin gama murje jikinki saiki shafa wannan shikad'ai a fuskarki wannan kuma bayan kin gama zanzo nasaka miki a gashi. daganan kishiga nan cikin, ta nuna mata wani k'aton bambu da aka saka wani Leda. Kai Amatallah ta jinjina mata. Duk yanda matar nan tasakata haka tayi, abun sai wani masifar k'amshi yakeyi, haka dai tagama murje ko ina najikinta tashiga banbun kamar yanda matar tace, kusan mintuna biyar da kammalawarta matar tayi Knocking k'ofa da tambayarta ta kammala. Amatallah ta amsa mata da eh. Shigowa tayi, taga Amatallah tayi yanda duk tace, taji dad'i, dan haka tafara shafa mata d'ayan abun a gashinta, tana gamawa tasaka bak'ar Leda ta d'aure mata kan, tafice ta barta. Sai da Amatallah tayi kusan awa biyu sannan matar ta shigo tahad'a mata ruwan d'umi da k'amshi, sai wani sabulu tabata tace tayi wanka. Indai tak'aice muku sosai Amatallah tasha gyara a d'akinnan, kusan awa 3 sannan suka dawo ainahin wajen saloon d'in, su Anaty maijidda sai yaba k'yan da tayi sukeyi, Nazeefa harda tatta6ata. Itadai Amatallah murmushi taitayi, ita kanta tanajin canji Na musamman a jikinta. An kuma wanke mata kai aka gyara matashi, sanan aka mata kunshin Jan lallale da bak'i. Dole ka ganta kasan Amaryace, tahad'u sosai abin harma ba'a magana, ga wani sirrin k'amshi Na musamman. Basubar saloon d'inanba saida aka yima Amatallah simple makeup mai burgewa, ba'a cikashi d'inanba yanda zai canja mata kamanni, amma tayi k'yau masha ALLAH. bayan matar nan ta had'ama Amatallah wasu kayan gyaran jikin dazata ringayi a gida suka tafi. Anty maijidda gidansu ta wuce, Jabeer kuma ya maida Amatallah da Nazeefa gida. Kusan k'arfe 3:26pm lokacin, kuma ALLAH yasosu Aneesa bata dawoba. Dawowarsu babu dad'ewa sukaji dawowar Aneesa, itama gyaran jiki taje, takumayi k'yau sosai wlhy, sai shek'i da walk'iya takeyi kamar amaryar itama. Batawani 6ata lokaciba tashiga ketchin, dama kafin ta fita ta tanaji komanta, had'awa kawai zatayi. Nazeefa Ce tafito ta tayata komai, danta hana Amatallah fitowa. Tace baza'a ganta ba a waje sai su Uncle sun shigo gidan. Rashin ganin Amatallah yasa Aneesa d'aukar koma bata gidan, bakuma ta tambayi Nazeefa ba. K'arfe hud'u suka gama komai, suka kuma gyara gidan da bazama kowanne lungu da sak'o k'amshi mai dad'in gaske. Aneesa ta shigo 6angarenta dan tsara kwalliyar tarbar mai gida. Amatallah tana idarda sallar la'asar saiga Nazeefa ta shigo, itace ta zaunar da ita ta gyara mata kwalliyarta datayi alwala wasu guraren suka d'an 6aci. Wani material pink colour da akaima d'inkin sket da Riga Nazeefa tabata, d'inkin yayi 'yau over, gashi yafitar da ainahin Shep d'inta, sannan colour d'in ya haska bak'ar fatarta. Nazeefa tamata d'auri mai k'yau, itadai Amatallah kallon ta kawai takeyi cikeda mamaki, amma takasa cewa komai, ita damuwartama yanda zata had'u da Uncle d'in nata, dan kunyarshi takeji sosai, musamman ma idan ta tuna da yanda yake mata a waya yanzun. Bayan Nazeefa ta gama mata komai hardasu sark'a da abin hannu, ta fesheta da turarurruka masu k'amshin tsiya da shiga zuciyar mai shak'arsu. Hummm, masu karatu, yaufa Amatallah d'inku ba'a magana, ni tsorona ma karta haukatar mana da Uncle fa🙆🏻. Aneesa ma tanacan tana tsara nata gayun, itamafa babu sauk'i, dan wanka iya wanka tayi, ta bulbule lungu da sak'o Na jikinta da k'amshi, dama harda Siddiqa aka tafi gidansu innani. A can kuwa 4:30 nayi su Anty maijidda da yara suka tafi tarbo su Uncle a airport. 5:8pm jirgimsu ya sauka. Uhhm nafad'a lokacinda naga Fateema Na sakkowa jirgi da k'yar, cikinta ya tsufa, tak'ara k'yau da haske ga k'iba, Alhaji Muhammad Na bayanta shimafa ba'a magana, ya murje dakuma kwarjini, sajennan da gemunsa sunkuma yin bak'i sid'ik, sai furfura d'ai-d'ai data k'awata gemun nasa, wadda bazamuce ta tsufa bace sai dai baiwarta da ALLAH yamasa. Da gudu yara sukaje suka tarosu suna ihun Kiran Abbunsu da Ummansu. Alhaji Muhammad duk yahad'asu ya rungume harda yaran Anty maijidda guda uku, bayason su Ce zasu rungume Fateema dantayi nauyi. Tsaye tayima tana kallinsu da murmushi jin dad'in ganinsu. Anty maijidda ta k'araso tana mata sannu da zuwa da tsokanarta uwar biyu. Duk dariya sukayi, aka shiga gaishe-gaishe kafin su k'arasa mota, dole saida suka had'a da taxi dan motar tamusu kad'an. Duk hayaniyar da akeyi a gidan Amatallah Na jiyowa daga d'aki, gabanta sai kuma fad'uwa yake, heartbeat d'inta nak'ara k'arfi, amma takasa fitowa Dan kunya takeji. Uncle kam tunda Aneesa tafito idonshi akanta, bak'aramin k'yau kwalliyarta tamasaba, gadan-gadan shi ta nufa zata rungume amma saiya doje ya d'auki Siddiqa da Umminta, Dan bazai iya abin kunyarnan gaban k'annensa da yaransaba. Lamarin yabama Fateema dariya sosai, danta lura tsaf da nufin Aneesar dakuma abinda mijin Nasu yayi Na gujema manufarta. Nazeefa ma ta lura, ta juya fuska tana dariya. Duk da abinda yamata ya 6ata mata rai, amma saita danne, ta k'araso daf dashi tana masa sannu da zuwa, cikeda fara'a ya amsa mata da kanne mata ido d'aya. ta sakar masa da wani sihirtaccen murmushi kuwa da d'age masa gira. Kallo d'aya tama Fateema tace sannunki. Ran Fateema ya 6aci da rainin wagon Aneesar, ya gida kawai tace itama tayi gaba abinta. Har suka k'arasa ciki yana baza idon son ganin Amatallah amma babu ko k'urarta. Anty Maijidda Na lura dashi, sai kawai tayi murmushi, a zuciyarta tace ya Muhammad Amatallah tawuce arhar ka ganta kai tsaye, saika bita har d'akinta. Dukda daular abincin da Aneesa ta had'a musu bata d'auke hankalin Uncle ba, gaba d'aya hankalinsa nakan son ganin Amatallah, soyake kawai yaga halin datake ciki. Suna cikin cin abinci Fateema ta kalli Nazeefa tana fad'in "Nazeefa wai Amatallah fa?". Da hannu Nazeefa ta nuna 6angaren Amatallah d'in. Uncle datun da suka fara maganar ya d'ago ido yana kallonsu yace, " lafiya dai ko bata fitoba?". Nazeefa tace, "Yaya ban saniba nima, tundai d'azun tana ciki".. Ajiye spoon d'in hannunsa yayi ya mik'e yana fad'in "bara Na dubata to". duk binsa da kallo sukayi, wani haushi yakama Aneesa. Fateema kuma tayi murmushin mugunta, dama danta rama abinda Aneesa tamata ta tambayi Amatallah d'in, Dan tasan dole mijinsu yayi wani Abu akai. Anty Maijidda kam da Nazeefa sai dariya sukeyi a zukatansu. Amatallah da har suka shigo cikin falon tana jiyosu, tana kwance a doguwar kujerar falonta tana game a waya, dukda zuciyarta sai harbawa take da fargaba. game d'in kawai takeyi, amma bawai yana mata dad'i baneba, Rabin hankalinta nakan su Uncle d'in. A hankali yaturo k'ofar falon ya shigo. Ko kad'an Amatallah bataji shigowar saba, sai k'amshin turarensa saboda ta juyama k'ofa baya, kuma a la66ansa yayi sallama yanda bazai yuwu tajiba. Shiru tayi tana hasashe, a zatonta ko tun daga waje k'amshin ke shigo mata. Uncle kam al'ajabine ya kamashi, shiyyasa yakasa motsawa, tunda yake bai ta6a ganin Amatallah da kwalliyaba sai yau. Jin kamar mutum tsaye akanta yasata juyowa cikeda fargaba. da Sauri ta mik'e tana fad'in "Uncle sannu da zuwa, ALLAH banasan ka shi..go..ba ne". Murmushi yayi, ganin yanda jikinta har rawa yake, kai kace taga wani ojuju ne, takawa yayi a hankali har inda take batareda yace komaiba, daga zaune Amatallah tad'an matsa baya kanta a k'asa tana wasa da yatsun hannunta, a kujerar ya zauna shima kusada ita, ai saitaji kamar tatashi ta tsilla a guje. Hannunsa ya d'ora kan yatsun hannunta datake wasa dasu, yanda Jan lallen yay rad'am ne ya burgesa, murza yatsun yayi, hakanne yasaka Amatallah d'agowa tad'an kallesa. Komi ya tuna kuma saiya saki hannun, cikin sassanyar muryarsa yace, " haba my best! Babu fad'a miya kawo gabane? Laifin mi mukayi aka k'i fitowa tarbarmune, ko ba'a murna da dawowarmu mu koma Inda muka fito?". Hannu tasa ta rufe fuskarta dantaji kunya sosai tace, "Sorry Uncle, ALLAH ba haka bane fa, kawai dai". Murmushi yayi mai k'ayatarwa, yasa yatsun hannunsa biyu ya d'ago ha6arta tareda saka d'ayan hannun ya janye hannayenta data rufe fuska, saita rumtse idanunta. "bud'e idon to, kifad'amin kawai dai me? kokuma nayi wani Abu". Tace, "ALLAH uncle inajin kunya". " my best! to miye najin kunyar?, nifa Uncle d'inkine, ko yanzun an daina Uncle d'in dani sai mij......" Bai kai k'arsheba ta waro manyan idanunta a kansa. Shima saiya waro nasa kamar yanda tayi yana murmushi har hakwaransa Na bayyana a fili. Yunk'urawa tayi zata tashi danta gudu ya rik'e hannunta yana fad'in kinga wasa nakeyi, muje kici abinci, kowa ya hallara babu ke, har Fateema Na tambayarki taga bakizo mata sannu da zuwaba". "Uncle azumi nakeyi ai". " azumin me my best? Yaufa Saturday?". Rasa mizata cemasa tayi, dankuwa k'arya ta mullik'a babu wani azumi, tana dai jin kunyar fitane saboda kwalliyarta. Hakanne yasa yagane k'arya take. Mik'ewa yayi itama ya mik'ar da ita tsaye. Ta marairaice masa fuska kamar zatayi kuka, "wayyo Uncle da gaskefa nakeyi". Baima San tanayiba, dan kallonta yake daga sama har k'asa, bak'aramin zama kayan sukayi a jikintaba..... Ganin hankalinsa bama kanta yakeba ta girgiza hannunsa dake rik'eda nasa. Kallonta yayi da sauri, yace, " mikikace my best!?". A shagwa6e tace, "kai Uncle kana nufin baka jiniba ma?". Kasa amsata yayi, yaja hannunta dan yakula inhar suka kai wani lokacin a falonnan zai iya kauce hanya ya aikata abin kunya.... ''Uncle please zanje da kaina, ALLAH zanma ci abinci". Amatallah tayi maganar da sauri dan ganin da gaske soyake ya kaita har falon yana rik'eda hannunta. Baice mata komaiba ya saki hannunta, fitowa sukayi yana gaba tana bayansa, dan haka ta 6oye sosai a bayansa. Fitowarsa yasaka Fateema da Aneesa d'agowa suna kallonsa, kowa da dalilinta na kallonsa da son suga Amatallah d'in. Anty Maijidda tace, " a'a Yaya lafiya dai ko? ina Amatallah d'in to?". Juyawa yay a zatonsa bata biyoshiba, sai ya ganta a bayansa, tana famar 6uya, matsawa yayi gefe yanda zasu ganta yana fad'in ''k'alau take, kunyarku takeji saboda tayi.....". Sai kuma yay shiru ya k'are maganar da 'Yar dariya yana zama a kujerar daya tashi wadda Aneesa da Fateema suka sakashi tsakkiya. Amatallah jitai tamkar ta nurse k'asa dan kunya, Fateema da Aneesa duk sukad'an waro idanu kanta cikin mamaki da ganin k'yan datayi. Aneesa Na mamakin yaushe Amatallah ta koma haka?, Fateema kuma Na mamakin canjawar Amatallah d'in a watanni hud'u. Nazeefa kam cikin nuna kamar batasan da kwalliyar Amatallah d'in ba tace Woow!! Amatallah, wannan wanka yayi, kinfito a amaryarki". Jabeer da Shehu da Anty Maijidda da Uncle duk dariya sukayi, yayinda wani kishi ya tokare mak'oshin Aneesa da Fateema. Amatallah komawa tayi baya da sauri tashige bangarenta. Nanfa duk aka saka mata dariya, harda yaran. Nazeefa tashiga kwala mata kira, amma sai Uncle yace "barta Nazeefa, haka Khadija take da kunyar tsiya". " Yaya ai bataci abincin bafa". " 'Diba ki kai mata kawai, kowama yakamata yay saurin kammalawa yanzu zakuji magrib". Duk da to suka amsa. Nazeefa ta d'iba komai dai-dai misali Dan tasan Amatallah batada cin abinci sosai ta kaimata. Har Nazeefa tashiga ta fito Amatallah bata yarda sun had'a idoba, dariya Nazeefa tayi kawai tafito abinta. Suna mammala cin abinci mazan suka wuce masallaci, Matan kuma sukayi agida. Su Uncle basu dawoba sai da sukayi sallar isha'i. Koda suka dawo basu zaunaba, shidasu shehu da Anty Maijidda suka tafi gidan iyayensu danya gaishesu, harda Nazeefa Dan tace bazata kuma kwanaba kuma, ba lallashin da Uncle bai mataba tace, a'a. Anty Maijidda tace yabarta, gara ta tafi. Saboda yanayin zaman gidan nashi ba mace d'aya bace, idan ta nuna kusancinta da d'aya sai yazama abin magana, sukuma zaman lafiya mai d'orewa sukema gidansa fata. Badan ya soba suka tafi gaba d'aya. Daga innani har baba sunyi farincikin ganinsa sosai, sai dai innani ta danne abinta a zuciya kamar yanda ta saba masa. Sunsha hira, Dan saida baba yace yaje gida ya huta, gobe idan ALLAH ya kaimu yadawo suyi hiran. haka ya tafi badan hira da iyayensa da 'yan uwansa ta isheshiba. Tunda suka fita Aneesa tashige 6angarenta, aka Shiga k'imtsa jiki.😜 Fateema ma 'ya'yanta taja suka shige Nata 6angaren, Dan k'anwarta zaliha tazo Tamata gyara tun jiya da safe. Lokacin daya shigo gidan tsit kamar babu kowa, a tsakkiyar falon ya tsaya yana Mazarin INA yakamata yafara Shiga?, wajen Fateema, ko Aneesa, ko Amatallah?.😂🤐...........✍🏻 🤩👎🏻 One luv🥰 _Dan ALLAH idan mutum ya tambaya daga farko maishi yaringa tura mishi, ku Na tausayimin mana, kodan k'ok'arin muku typing danake kullum, abubuwan sunmin yawa, banason kuma masoyina yaga Na wulak'antasa wlhy ko kad'an, Duk masoyina Na gaskiya nasan zai taimakeni._😊🤝🏻 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*🙏🏻😭 [1/16, 9:01 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_* *_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡 _{home of expert and perfect writer's}_ *_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉ _(Hattara matasa)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_Jiya maganar gaskiya naci dariyar Comments naku over, dan naga zanga-zanga kuka shirya yimin akan kwanan Amatallah jiya😂, especially 'yan Group d'ina da Group d'in party, sai Kundin Haske da Group na Manshat , sai dai network yamin iya shege, amma ngd sosai walhy, ALLAH yabar zumunci, bilyn Abdull Na yinku irin Trillion's d'innan, I love you wujiga-wujiga._*😂😂🥰🥰🥰🤝🏻👍🏻. ____________________ *_Number 21_* ____________________ Yadad'e tsaye yana canki canka, daga k'arshe dai yashiga 6angaren Amatallah, babu kowa a falon sai dai k'amshi mai dad'i dake tashi, tsayawa yay kallon falon, Dan d'azun ta rikitashi bai kalli komaiba, komai yayi k'yau yanda ya kamata, cikin yabama k'ok'arin k'annensa Na za6o abinda yay dai-dai da ra'yinsa shida Amatallah yashiga bedroom d'in. nanma babu kowa, amma ko ina tsaf yake kuma k'al, gadon yasha gyara, ga ta saka filolin a wani style mai k'yau, guntun murmushi yayi kafin yamaida kallonsa ga bathroom inda yake jiyo motsin ruwa alamar wanka takeyi. Juyawa yayi yafita kafin tagama ya dawo. Saiya shiga 6angaren Aneesa. Tana zaune abakin gado cikin wata rigar barci jaa datayi masifar mata k'yau da haska farar fatarta, Siddiqa takema shirin barci, Saifudden Na kwance a gadon haryayi barci. Tsayawa yay kwai yana kallonta danba k'aramin k'yau tamasa ba a rigar barcin, cikin wani salo ta d'ago idanunta tana kallonsa tareda d'an fari. Murmushinsa mai k'ayatarwa yasaki, yataka a hankali zuwa gareta, dai-dai ta shinfid'e Siddiqa a gadon. Ta baya ya rungumeta cikin kunnenta yace, "zaki kasheni da salonki my Neesa". Dad'i ya kamata, ta juyo sosai suna fuskantar juna, sai kawai ta fad'a jikinsa suka rungume juna tsam, tace, " I miss u so much my Dear". "Me too my Neesa". yafad'a yana d'ago kanta, bakinsu kawai ya had'e waje d'aya, yashiga mata wani salo mai rikitarwa. Su duka sun haukace, kai kace yau suka fara ganin juna, sai da Uncle yaga abin zai zarta sannan yacire bakinsa a nata, ya kuma rungumeta da k'yau a jikinsa suna maida numfashi. kusan mintuna biyu sannan yace, " My Neesa kinsanfa yau niba naki baneba, Na Amaryane". Idontane yacika da kwalla, yanzu kam ba zafin kishi bane kawai, harda tsananin buk'atuwar da take ciki, wata hud'u ba wasa baneba, takuma k'ank'amesa kamar mai gudun arabasu, (dukda tana buk'atarsa bazata ta6a cemasa karyaje wajen matarsa ba, duk zafin kishinta bata fatan shiga hak'k'in wata a abokan zamanta). Jin laimar hawayenta a k'irjinsa saita bashi tausayi, yasan yanayin Aneesa sosai, wata hud'u ba wasa baneba kuma agareta, Dan baita6a nisan kiwo basa kusa dashiba kamar haka. Jin yana k'ok'arin d'ago kanta saitayi saurin share hawayenta, koda tad'ago saita masa murmushi, murmushin shima yamata, yasa hannunsa biyu yakamo kumatunta, cikin kuma k'asa da muryarsa yace, "sorry my Neesa, ban fad'a Dan wulak'antaki ba, saidan kawai hak'intane Na sauka a wajenta, kuma namata kwanaki 7 kamar yanda yake a shari'a, amma karki damu zan nema mana mafita idan kin amince". A sanyaye tace, " wace mafitace dear?". Lumshe idanunsa yayi tareda kissing la66anta sannan yace, "zanje Na rok'i Khadija tabamu kwana d'ayannan kawai domin Na kwaranye miki k'ishinki". Ajiyar zuciya tasaki sannan tagyara tsayuwarta tana fad'in " a'a dear, itama anshiga hak'inta kenan ai, nida ita duk Abu d'ayene a wajenka, maganar wadda kafiso wannan a zuciyarka yake, tsananin k'aunarka da kishinka danakeyi bazaisa na jagoranci abinda zaisa katashi ranar kiyama da shanyanyen jiki har Na kaika wuta ba, insha ALLAH zanyi hak'uri har tayi kwanakinta, amma kasani INA matuk'ar Sonka da kishinka, harma nakanji nafi kowacce mace Sonka da kishinka a duniya". Tausayi tabashi, Dan haka Yakuma d'ora bakinsa kan nata batareda yayi maganaba, yashiga kuma nuna mata tsantsar soyayyarta dake cikin zuciyarshi shima. Sunja adadin wasu lokuta kafin Aneesa ta janye jikinta da k'yar, kan gado kawai ta haye ta kwanta tareda juya masa baya. Yasan kuka takeyi, Dan haka baice mata komaiba yajuya yafita jiki a sanyaye. Samansa ya haye, yaje yay wanka da shirin barci. Babu dad'ewa ya sakko. 6angaren Fateema yashiga, takashe komai Na falon, sai fitilar wayarsa ya kunna, d'akin yaran yafara Shiga yaga babu kowa, hakan ya nuna masa suna tareda ita kenan, d'akintama fitilar a kashe take, data wayarsa ya haska ya hangosu a kan gado sun jeru suna barci, murmushi yayi ya k'arasa garesu yana ayyana soyayyar uwa da 'Yaya a zuciyarsa. Duk saida yabisu d'ai-d'ai yama kowa kiss a goshi, Fateema kam harda d'an tsotsar la66anta sannan yama cikinta da wuyanta kisses yamusu addu'oi yafita dukda yasan Fateema tamusu suma yaran tasakasu sunyi. Amatallah tunda tafito wanka taji kamar k'amshin turaren Uncle, gabantane ya fad'i, cikin sand'a ta lek'a falo azatonta yana can, ganin wayam babu kowa tasaki ajiyar zuciya sannan tadawo. Zani ta d'aura tasaka hijjab tayi shafa'i da wutiri, idarwarta kenan tacire hijjabin ta d'ora saman gado, tabud'e Waldrop danufin Neman kayan barci yay sallama, ba k'aramin tsorota tayiba da ganinsa, taja hijjab d'in data cire tasaka da Sauri duk da yama Rigada ya shigo d'in, Yakuma ganta a yanda bata son. Murmushi kawai yayi, ya k'arasa bakin gadon ya zauna. Kanta a k'asa tamasa sannu da zuwa. Idonsa a kanta yace, "yauwa my best! Kin daina kukan tafiyarsu Nazeefa ne?". Kwallace tacika idonta, ta d'ago kad'an ta kalleshi ta duk'ar da da kanta. "Kukan dai kuma?". Girgiza kai tayi da sauri. Zamansa ya gyara yana nunu mata kusa dashi, " zoki zauna naji to". Dukda tanajin kunya haka ta zauna amma d'an Nesa dashi. Idonsa akan yatsun hannunta dake d'aukar hankalinsa yace, "to, ya school?". " Alhmdllh Uncle". "Masha ALLAH, babu dai wata Matsala ko?". Kanta ta girgiza masa da fad'in " eh uncle". "Alhmdllh ai haka akeso, zuwa da safe Na duba Nagani idan da gaskene, yanzu alfarma nazo nema". Cikeda mamaki ta kalleahi, " uncle! Alfarma kuma? a wajena?". Kansa a jinjina mata fuskarsa d'aukeda guntun murmushi. "Alfarmar kwananki nake nemama Aneesa". Ko kad'an Amatallah bata fuskanci inda maganarsa ta dosaba tace, Uncle ban ganeba ai". Shiru yayi yana nazarin tayaya yakamata yamata bayani, sai kuma yamatso kusada ita sosai, hakanne yad'an sakata jin tsoro heartbeat d'inta Na k'ara gudu, kamar zatayi magana saikuma tayi shiru. Duk da ya fuskanceta hakan bai hanashi kamo hannunta ba ya saka a nasa, " uhm INA nufin kibari yau Aneesa ta kwana d'akina". "Wayyo Uncle, ni mizai sakani Na hana Anty Aneesa kwana d'a......." Saikuma takasa k'arasawa saboda maganar Tamata nauyin fad'a. 'Dan murmushi yayi, aransa yace tunda kinsan ma'anar kwana d'akin nawa, a hankali abinda nake nufinma zaki gane ai. a fili kuma yace, "Nasani bazaki hanataba, amma hak'inkine ai". Zuwa yanzun kam Amatallah tagama fuskantar Inda Uncle d'inta ya dosa, amma nauyin maganar bazaisa ta ta6a nuna masa ta ganeba, saima mamakinsa take a zuciyarta dukda shima azancen NASA akwai salon alkunya tunda bai fito kaitsaye ya nuna mata manufarba....... Katseta yayi da fad'in "kinyi shiru Khadija". " Uncle nidai dukda bansan miyasa kake son hakanba Na amince ta kwana wlhy". Tayi maganar a kunyace. Murmushi yayi tareda sumbatar bayan hannunta, yace, "ALLAH yay mini albarka Khadija". Shi duk zatonsa Amatallah da gaske bata gane Inda ya dosaba, Dan kallonsa k'aramar yarinya shataf yake mata. Nidai nace, " hummm Uncle kenan, shekarar Amatallah 20 yanzu ace batasan miye aureba?, bayan yanzun yaramu sai dai addu'a, 'Yar shekara 15 saita baka labarin mi ake a gidan aure tsaf, in kayi wasa takuma fad'a maka komai dalla-dalla, ai waya📱 babu masifar dabata kawo manaba a wannan zamanin, sai dai kawai wad'anda ALLAH ya tsare, amma jeka Facebook kawai kaga ta6ar6arewar tarbiyyar yaranmu.😭 Kama godema ALLA daya baka Amatallah d'in mai kunya, yanda idanun 'yan matanmu ya bushe yanzu suka d'au kunya k'auyanci ai abin ba'a magana, ALLAH dai ka shiryamana zuri'a kawai.🙏🏻 Mik'ewa yayi yana fad'in "tom tashi ki kwanta namiki addu'ar barci". Kanta a k'asa tana cigaba da wasa da yatsun hannunta tace, " Uncle ai bansa Sleeping dress". "Okay, to tashi kisa ka". Shiru tayi kamar bazata tashiba sai kuma ta mik'e ta koma wajen Waldrop d'inta ta ida zaro kayan data fara d'auka d'azun. duk Uncle yana tsaye yana kallonta. toilet d'inta tashiga dan ta Sanka. Murmushi yayi yana shafa gemunsa, a ransa yanajin k'aunar Amatallah da yanda take komanta a nutse, wani lokacin idan tayi Abu yakanga tamkar brother d'insa (to jini ba k'arya baneba aii Uncle). Yana nan tsaye harta fito, kallonta yayi, dukda tasaka Riga da wando na barcin, hakan bai hanata sanyo hijjabin ba a sama. Tsaye tayi a bakin k'ofar kanta a k'asa. Yace, " zoki kwanta mana, ko zakiyi wani abunne kuma?". Kanta ta jinjina masa alamar a'a. "Ta kowa yayi a hankali har inda take, ya kama hannunta batareda yace komaiba, har gaban gadon sukaje sannan ya saki hannunta yana nuna mata gadon da yatsa. Bata yarda ta kalleshiba ta hau gadon ta kwanta bayan ya gyara mata filon. bargo yaja ya lullu6a mata zuwa k'irjinta sannan ya rankwafo saitin kanta daf. ita dai Amatallah kallon ikon rabbani takeyi, da girmanta an maidata baby. Hannu yasa cikin bargon kad'an yafara tattara hijjabin jikinta, a hankali ya furta "d'aga my best a cire wannan hijjab d'in, babu k'yau kwanciya da hijjab, zai iya kawo matsala ga mai barci, kamar shak'e mutum da makamancin hakan". Kanta ta jinjina masa a hankali, Dan yanda ya rank'wafo kanta saitaji kamar zai fad'o mata, har saukar numfashinsa tanaji, taimaka masa tayi yacire hijjabin, kafin ya ida cirewa tayi saurin Jan bargon ta rufe k'irjinta. Yana kallonta, dan haka yay dariya a zuciyarsa kawai. yana gama cire mata hijjabin ya ajiye gefe ya zauna kusada ita a bakin gadon. addu'oi yamata kamar yanda yakema sauran matansa, ya tofa mata a hannu ta shafa itama da wanda tayi, mik'ewa yayi yasake rankwafowa ya gyara mata bargon, sannan yamatso da fuskarsa daf da tata, hakanne yasaka Amatallah saurin rintse ido dad'an k'ank'ame jikinta zuciyarta tana kuma bugawa da k'arfi saboda kusantowarsa garesa sosai. Kiss ya manna mata a goshi da kumatu, sai kuma ya dakata yana kallon fuskarta da yanda take k'ara k'ank'ame ido, yanda tayin saita bashi dariya harya murmusa, yace, " bud'e idon mana my beat ki kalleni". "Ya salam" tafad'a a zuciyarta tareda mamakin wannan lamari na Uncle, tana masa kallon salihi Ashe shima A ne na bugawa a jarida....... Batakai k'arshe. Tunanin taba taji saukar la66ansa akan nata. A zuciyarta tace na shiga tara ni Khadija, Uncle zaka kasheni da kunyarka wlhy. Saida ya sumbaci la66anta sau biyu sannan yamik'e tsaye sosai yana murmushi idonsa a kanta face d'inta. "Sai da safe my Heartbeat! ko kawai nashigo bargon mu kwanta abinmu, mu warware sadaukar da kwanan?". Bargon taja da sauri tarufe har kanta gaba d'aya. K'aramar dariya yayi yamatso kamar zai bud'e mata bargon, murya k'asa-k'asa cikin rad'a kamar mai tsoron ajisu yace, " Ina matuk'ar Sonki keda Salonki my best Darling. goodnight, zan kwana da mafarkinki". Bai jira cewar taba yakama hanyar fita, yamasan bazata ceba d'in, fitilar d'akin ya kashe ya fice, bayan ya kunna fitilar wayarsa. 6angaren Aneesa ya komai, tana nan kwance yanda ya barta, tayi kuka harta godema ALLAH, bai mata maganaba ya d'auki Saifudden ya fita, wajen Fateema ya kaisa, dukda barci takeyi abinta hankali kwance itada yara, haka ya shinfid'eshi kusada 'yan uwansa yamasa addu'a sannan ya koma wajen Aneesa. yanzuma yanda yabarta haka ya isketa, ya d'auke Siddiqa daga gabanta ya gyara mata kwanciya gefe saboda gadon babbane ba laifi. Duk abinda yakeyi Aneesa na jinsa, tun shigowarsa ta farko har d'aukar Saifudden ya fita dashi, ko kad'an batayi zaton Amatallah zata yarda ya dawo wajen taba, anya idan itace zata iya kuwa? sai taji Amatallah ta birgeta..... Ajiyar zuciya ta saki yayinda taji ya rungumeta. Hummm, nayi nan, Dan yau Uncle da neesarsa babu sauk'i.🤐 🚶🏻‍♀ Tumda Uncle yafita Amatallah ta sauke ajiyar zuciya a fili tace, ''kai Namijima sai abarsa, duk yanda kake kallonta a nesa ba haka bane, saika zauna dashi kake gane Natural colour d'insa, wlhy a baya idan wani yacemin haka Uncle Muhammad yake saina k'aryatashi, humm Ashe ya wuce tsammanina ma". Hannu takai ta shafa bakinta, saikuma taja bargo da sauri takuma rufe fuskarta tana rintse ido da fad'in ''wayyo Uncle Muhammad ka kasheni wlhy, yanzu tayaya zan iya kallonka da safe?, shikenan na mutu ni Amatallahin Ammi da baba". Haka taita sambatunta ita kad'ai, hardai barci yazo mata, takuma 'yan addu'oi ta gyara kwanciya.............✍🏻 Ni dai mai d'aukar rahoto nayo waje ina dariya wa shirmen Amatallahin ku😂👍🏻. _Nasan saboda yawan page d'in nan yau har saikun kai jibi kuna karantawa🤭, kusan Read more 7 fa🤣😜, asha karatu lfylfy._ 🏃‍♀ 🤩👎🏻 One Luv my sweet fan's🥰👍🏻. *_ya ALLAH ka gafartama mahaifina._*😭🙏🏻 [1/16, 9:01 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_* *_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡 _{home of expert and perfect writer's}_ *_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉ _(Hattara matasa)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_Hummm, jiyakam ai magana gagarata tayi a kowanne groups, dan jiya kad'an garage nasha Suburbud'a hannunta masoyan Amatallah😆😆, Aneesa zata jamin jaza'i, nibada laifiba😂🙆🏻._* Haba masoyan Ama..., karku damu zaku fanshe ne🥰👍🏻. ____________________ *_Number 23_* ____________________ Koda Uncle ya koma gida ya taradda Fateema kawai a falo, Aneesa kam tana 6angarenta. Gaban Fateema ya k'arasa ya sumbaci Goshinta da cikinta, d'agowa yayi yana dariya da fad'in nabiya bashi my tee... Itama dariyar tayi tana fad'in kafita koba sabulu". zama yayi inda Aneesa ta had'a break fast, batareda ya nemetaba yazauna yaci kad'an kamar yanda ya saba. Fateema kam dad'ine ya kamata, tasan cin abincinnan dayayi bai nemi Aneesa ba saitayi tamkar ta fashe dan haushi. Yana hayewa samansa itama ta tashi tashige 6angarenta, dama da biyu ta zauna falon.😆 ********* Amatallah bayan sun fito lecture suka nemi waje can gefe suka zauna suna sauraren ta. A nutse tabasu labari tana kuka, suma sunayi, aka rasa mai lallashin wani cikinsu, saida sukayi mai isarsu sannan sukayi shiru suna bama Amatallah hak'uri, sosai suka tausaya mata. Itama Rita tace zata basu labarinta gobe. Duk suka amsa da ALLAH ya kaimu. Amatallah tanason tambayarsu maganar da Aneesa ta mata da safe, amma tana ganin kamar suma bazasu fahimtaba, musammanma su Goodness, dan haka tayi shiru da nufin zata tambayi Fa'iza ita kad'ai. Suna fitowa lecture ta k'arshe Goodness da Rita suka nufi hostel, yau basu musu rakkiya ba saboda kowa yagaji. Da wannan damar Amatallah tayi amfani ta sanarma Fa'iza abinda yafaru tsakaninta da Aneesa, dakuma tambayar da Uncle yamata ta 6oye masa. Kallon mamaki sosai Fa'iza kema Amatallah, tace, "dama bakida wayo haka Amatallah?. Wace mace ke sadaukarma kishiya kwananta? Sai dai haihuwa ko lalura wlhy, Lallai bakisan miye kishiba Ashe. Wlhy duk da kike ganina k'aramarnan bana bari kishiya tasamu lagona, bazanyi kishin haukaba kuma bazan raga mata ba". " ban ganeba Fa'iza, kema kinada kishiyane?". Dariya Fa'iza ta mata, "lallaima Amatallah, koda yake duk yandafa muke dake d'inan babu Wanda yasan gidan wani, toni rana d'aya aka d'aura aurena da kishiyata, ni da safe ita da rana, kuma yanada wata matar, saidai tana gidansu, sa6anin dasuka samune yayo auren huce haushi damu mu biyu, yanzu kuma shirin dawowa take an sasantasu". Ba k'aramin mamaki da al'ajabi bane yakama Amatallah, a ranta tace halin maza sai abarsu. a fili kuma tace "amma Fa'iza kunsan da haka kuma kuka aureshi?". " to yazamuyi Amatallah, auren zumincine, da mamana da babansa uwa d'aya uba d'aya, waccan kuma budurwarsace dama, saboda itanema suka rabu da matarsa akan yace zai Aurota ta tada hankalin kowa a families d'in, harya kai gamata saki d'aya saboda sakko iyayensa datayi a haukarta, mamansa kuma tanada zuciya, hakan yasa tace bayan auren dayakeson k'arawa yahad'a dani mu zama biyu, saitaga yanda uwargidansa zatayi d'in, shinefa dalilin dayasa aka d'aura aurenmu rana d'aya, ni da safe ita da azhur, kusan shekara biyu kenan, uwargidan bata kuma wani aurenba, bakiga yanzu duk yanda tafita hayyacintaba, kullum cikin bibiyarsa take tana bashi hak'uri da rok'on ya maidata, dan suna matuk'ar son juna, to shine manya dai suka shiga aka sasanta, yanzuma jibi zata dawo". "Tabb, lallai wasu matan basuda hankali, nifa banga mafitaba ga macen da zata rud'ar da kanta wai dan miji zai sake aure, raini yake kawowa wlhy, kowa yanamaka kallon shashasha, kinga yanzu ta jama kanta daga d'aya anmata biyu, kuma mijin bazai kalleta da darajaba kamar da can?". " wlhy kuwa hakane Amatallah, ALLAH dai ya sassauta mana kishinan, wasu Matan sun Gaza gane kishi cikin SIYASA tafi kawo zaman lfy da daraja wajen miji, kamazo kana hauka kan Namiji baisan kanayiba". "Tokin gani, kuma wlhy kishiyarma indai kina nuna mata komai ba komaiba a fiska koda kina kishinta a rankin saikinga tana shakkarki da tsoron takaki, dan baki bata wata k'ofar dazata rainakiba, kuma mijin bazai ta6a aminta ta raina kiba, kinga ai kin nemama kanji daraja har wajen dangin mijin. yanzu wlhy Uwargidanmu inkikaga yanda take kishinta saita burgeki, amma Aneesa ba a magana, harma mamaki take bani". ''Karki damu Amatallah, zan koya miki wasu abubuwan, dukda shi zama da kishiya basai ankoyama mace shiba, wahalama na sakata ta koya, kamardai yanda ni wahalarce tasani koyon". "Kai dan ALLAH?". dariya Fa'iza tayi, " ALLAH kauwa Amata, ke idan INA Baki labarin gidanmu ALLAH saikice k'arya nake, ai garaku na fahimci kishin masu Ilimi akeyi a gidanku, mu Amaryarmu tafi uban kowa zafin kishi, ga uwargidan itama babu sauk'ice". "To ALLAH ya k'yauta". Nandai suka d'an tattauna, Fa'iza ta ankarar da Amatallah abinda Aneesa ke nufi da maganarta. " kinga daga yanzu kema sauk'i shirya aii, amma dan ALLAH inason tambayarki, kumafa ki fad'amin gaskiya inhar kin yarda dani". "Na yarda dake wlhy Fa'iza, shiyyasama nafad'a miki sirrina ai". Murmushi Fa'iza tayi, sanan taja hannunta suka zauna kan wata baranda, dan dama basukai ga fita gate ba. Kafad'arta ta dafa, " Amatallah shin kinason Uncle d'inki kuwa?". Dariya Amatallah tayi, sannan tace, "gaskiya kikace na fad'a miki kuma zan fad'a miki Fa'iza. lokacin da akai aurenmu dai bana masa son aure, dan kallon uba nake masa, lokacin ga rud'anin rashinsu Ammi, amma tunda na fahimci yanason cikar burina akan karatu, da k'aunar dayakema mahaifina sainaji nafara masa SO irinna aure, Ahankali kuma yaytamin abubuwan dasukaja ra'ayina ta waya, da kuma taimakon shawarwari da k'anwarsa Nazeefa taita bani, saina kuma gane babu Wanda yasan muhimmancina da kuma zaiji tausayina kamarsa, nasan kuma wannan babana ya kalla harya k'ulla wanan auren, Wlhy Fa'iza ina son Uncle har cikin raina, saidai ina masifar jin kunyarsa, musamman idan na tuna alak'arsa da mahaifina". 👍🏻Jinjina Fa'iza tama Amatallah, " ammafa kin birgeni, dan kar6ar k'addarar ki dakikayi shine Abu mafi muhimmanci, na tabbata kuma k'addarar alkairice, dawatace saita bijire tace yamata tsufa. Maganar kunyarsa kuma karki damu, daga randa kuka kasance k'ark'ashin inuwa d'aya zaki rage da kanki wlhy, nima nayi wannan kunyar Akan ya Usman, amma yanzun hummm". Dariya sukayi gaba d'aya harda tafawa. Fa'iza tacigaba da fad'in ''yanzu Amatallah akan abokan zamanki zan baki shawara, saifa kin mik'e sosai, inba hakaba su maidaki sakarai har mijinma yacigaba da d'aukarki haka. Ki kama mijinki ram ki rik'e dan yanda kike bani labari nakula mijinku d'anson soyayyane da kulawa da mace, kiyi k'ok'ari kema ki samu rabonki kafin su tsufar dashi kinan kunya na tsutarki. inhar yau yabuk'aci ki kar6i kwananki wlhy ki kar6a, kuma ya buk'aceki karki bijire masa, yanda yanzu ake yayin mutuwarnan". ''Kai Fa'iza ALLAH kinban kunyafa". "A'a ah yarinya zauna kallon ruwa kwad'o yamiki k'afa, yanzu maza tsada sukeyi shiyyasa kowacce mace ke tattali idan tasamu, karki bari kunya tasaki zama bora a gidan mijinki. kuma kin burgeni dabaki fad'amai ainahin abinda Aneesa tamikiba, dan da kanki yakamata ki rama, karki raga mata, intaga keda uwargidan halinku mai k'yaune itama zata fara gyarawa, kinga kun jefi tsuntsu biyu da dutsi d'aya kenan, Ku k'ara daraja da soyayyarku wajen miji, kun kuma gyara halayyar abokiyar zamanku yanda zaku samu zaman lafiya sosai". " gaskiyane Fa'iza, shikenan zanyi amfani da shawarar ki, Aneesa kuma zan nuna mata ainahin Natural colour d'ina, dan nakula kallon shashasha takeminne, batasan Amatallah bata d'aukar rainiba, halin rayuwane kawai ya maidani haka, bana fad'a amma kuma nasan yanda zan zauna dakowanne irin mutum". "ALLAH ko kwanan dakike gani na barmata yahad'a da inajin kunyarsane, kuma itama ina son na gwadata, shiyyasama naje tayata girkin da safe, dannaga yanda zata kar6eni, hakan duk yana cikin dabarun da Anty maijidah ta koyaminne". 👏🏻Tafa mata Fa'iza tashigayi tana dariya, " da k'yau Amatallah, Ashe kemad'in A ce ban saniba". "ALLAH Fa'iza ba wai haka baneba fa, kawai dai bana son rainine ALLAH kuwa, ina son idan na nuna maka girmanka kajashi". " gaskiyane Amatallah, ALLAH yabamu zaman lafiya dai, nima jibi uwargida zata dawo, bansan kuma wane zama zamuyiba da ita". "To ai yanzu kece Uwargida kenan". Dariya Fa'iza tayi sosai, takama k'arfe ta mik'e da k'yar tana fad'in "su Uwargida anji jiki". Amatallah ma mik'ewa tayi tana dariya, "babufa wani aniji jiki, karkima yarda akawo miki raini, kece Uwargida". Haka dai suka tafi suna tsokanar juna, kowa tasamu Napep tashiga. Shawarwarin Fa'iza sunyi tasiri sosai a zuciyar Amatallah, Hakanne kuma yasata d'aukar aniyar ramawa ta cikin ruwan sanyi, a ranta tanajin itama zata shiga a dama da ita, dan tana son Uncle d'inta, tunda tasan zama dashi babu cangi har Abadan saidai mutuwa, to mizaisa tacigaba da cutar kanta Aneesa na kallonta a banza, itafa ta tsani tana ganin mutuncin mutum yanemi zubda darajarsa a gurinta, dama ai bawai batasan kanta bane, kawai kunyar Uncle da kallon uba datake masane yasata komawa gefe, amma yanzu shawarwarin Fa'iza sun maidota hanya d'od'ar, kuma zatayi amfani dasu. " hummm, su Amatallah anji jiki Anfara dawowa hanya🤣, haka masoyanki sukeson ganinki, musamman ma Tawan (miss Xoxo)😂👍🏻 ___________________________ Sanda Amatallah ta dawo gidan ta tarar Uncle bayanan yafita, Fateema kawai ta tarar a falo zaune, yarama suna Islamiyya. Sannu da zuwa Fateema tamata, ta amsa cikin fara'a tana mata barka da gida. Jin maganganinsu ne yasaka Aneesa dake kitchen lek'owa a zatonta Uncle ne ya dawo, dukda cike take da haushin abinda yamata da safe, dan tana ciki har yayi break fast yay wanka yafice bai nemetaba, har yanzu kuma bai dawoba, amma dukda hakan tafitone yanzun tarbarsa danta bama Fateema haushi, sai kuma taga Ashe Amatallah ce. Daga Fateema har Amatallah kallonta sukayi, Amatallah ta d'auke idonta tareda mik'ewa ta kwashi takardunta, saida taje k'ofar 6angarenta sanan tace Anty Aneesa sannu da girki fa". bata jira amsartaba tashige abinta. Ba Aneesa ba kawai harta da Fateema saida ta kalli Amatallah d'in, dan awani salo daban tayi maganar, kuma cikin sanyinta kamar yanda ta saba, inma Baka saniba bazaka ta6a cewa itace tayi maganar ba. Fateema tayi dariya a zuciyarta tana fad'in yanzun za'a fara wasan kenan. Aneesa kam wani k'ududun bak'in cikine ya tokare mata mak'oshi, tama rasa yanda zata fasaara rainin hankalin Amatallah d'in. Koda Amatallah ta shiga d'akinta alwala tafarayi tai salla, danta risketa tana hanya ne. Ko da ta idar bata nemi abinciba, chin-chin d'in dasuka saya a makaranta taci tasha ruwa, sannan tashiga wanka, tadad'e a toilet d'in kafin ta fito, data fito batayi kwalliyaba, d'akinta tasama key dan bata buk'atar ko Uncle ya dawo ya shigo mata yanzun. Game taita bugawa a waya abinta har saida aka kira sallar Magrib, tana jiyo hayaniyar dawowar yara tun 6pm, amma dai bataji alamar Uncle ya dawoba, hakan yamata dad'i kuwa. Alwalar magrib tayo tazo tayi salla, tsakanin magrib da isha'i tayi karatun alkur'ani da azkar d'in yamma, daga nan gaban mirror takoma ta zauna, tanutsu wajen yin simple makeup, takuwayi k'yau d'as. Wasu Pakistan ta saka, rigar sky blue ce, wandon kuma na jins dark blue tayi k'yau sosai, ta taje kamta takuma gyarawa, dama batayi kitsoba, dukda gashinma bawani na kirki baneba, tamkar na (Fatee d'ayyabu Tyw😜) d'an siririn gyalenta shima sky blue tasaka, inba kallon Tsaf kamataba bazaka ta6a d'auka kwalliya tayiba, komai Simple tayishi, sai masifaffen k'amshi datake ta zubawa, wanda sirrin Anty maijiddane da k'awarta mai gyaran jiki😉. Compilied By Abubakar Saleh AlQuyraemey Whatsapp Number 08138873799 Visit www.rumbunlabarai.com For More Complete Documents Uncle kam yanacan wajen Alhaji Sabi'u m Ali suna tsare-tsarenasu, saida sukayi sallar isha'i sannan yabaro gidansa, daga nan gidansu yaje, bai wani zaunaba suka gaisa a tsaitsaye saboda yaje da safe daya fita kafin yaje gidan Alhaji Sabi'u, daga nan gidansa ya zarto. Horn yayi kusan sau 3 sanan su Abulkhairi suka jiyoshi, da gudu suka fito suka bud'e masa ya shigo. Hayaniyarsu Ce ta fiddo Aneesa, cikin kwalliya take kuwa kamar ka saceta ka gudu, tanata k'amshi abinta. fitowarta tayi dai-dai ta fitowar Uncle daga mota. Yaransa duk suka rungumeshi, tarbarsu yayi cikin jin dad'i, yabisu d'ai-d'ai yana sumbatar kumatunsu, suma duk suka sumbaci nashi. Aneesa dake tsaye gefe yayi kamar bai gantaba saita kuma cika fam, amma dukda haka ta danne fushinta tamasa sannu da zuwa. Kallonta yayi ya sakar mata murmushin dake kasheta. Babu shiri itama tayi murmushin, Siddiqa dake hannunta ya kar6a, tafara masa gwarancinta yana dariya shida sauran yaran, ahaka suka k'araso babban falon. kujera ya nuna musu yace su zauna nan su jirasa yadawo, ya zaunar da Siddiqa itama, Aneesa na tsaye yawuceta ya shiga 6angaren Fateema. A falo ya isketa zaune tayi rashe-rashe da k'afafu ta bud'ema kanta fanka, fuskarsa d'auke da murmushi yak'araso gareta. "O my tee... Irin wanan bajewa haka? halan babynane yasaki jin zafi?". "Kabari kawai wlhy Nurri zufa nakeji sosai kamar nayi wanka a ruwa". Kusada ita ya zauna, yad'an rungumeta jikinsa yana manna mata kisses a wuya da la66anta, " my tee hakan ya nunamin babyna yakusa zuwa duniya, ai da kin fara zufarnan nasan haihuwarki ta gabato, ALLAH ya saukeminke lafiya Uwargidana". "Amin Nurrina". Itama ta sumbaci kuncinsa". " thanks my tee". Murmushi tayi batace komaiba. ''Yauwa my tee bara naga Amatallah itama naje nayi wanka, yau ina son zama daku Ku duka". " okey boss sai munji kira". Rankwashi yad'an kaimata, tunkan hannunsa ya sauka a kanta ta tare tana fad'in "wayyo Nurrina sorry please". Dariya yayi batareda ya rankwashe tanba, yace, " matsoraciya kawai, ga tsoro gajan fad'a". Dariya tayi, shima yafita yana dariyar dajin k'arin k'aunarta har k'asan ransa. Tunkan ya fito Aneesa tajiyo dariyarsa, da sauri tashige 6angarenta zuciyarta na suya. Koda tafito saiya Nufi 6angaren Amatallah............✍🏻 🤩👎🏻 One luv my sweet Fan's🥰 *_Ya Rabbi ka kai rahama da gafara kabarin iyayenmu_*😭🙏🏻 [1/16, 9:01 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_* *_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡 _{home of expert and perfect writer's}_ *_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉ _(Hattara matasa)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* Comments naku na k'yatar dani ainun. *_Ummu Ameer, Nana yakaku, maman khalifa, Ummu Ramlat, Layla, Xeecul, mom yasna, m@imun@tu, Maman iman, Jamila fika_* _😨ALLAH ya albarkaceku da yawafa, aradu kozan cika page d'inan bani gama zanoku, ko 'yan group d'ina kad'ai sa cikashi.🥰 inayinku irin Trillion's d'innan wlhy, ALLAH yabar k'auna.🥰🥰❤💃🏻👍🏻._ 💃🏻💃🏻Aneesa ma fa akwai farin blood *_Maimuna ado, and xaujatu_* basa barin a ta6a musu ita😄💃🏻🥰🥰🥰❤ina yinku kuma👍🏻. ____________________ *_Number 22_* ____________________ Kamar yanda yasaba da asubahi yabisu duk ya tada kowacce dantayi salla, yatasa yaransa gaba suka tafi masallaci. Koda suka dawo saiya haye samansa yay kwanciyarsa. Aneesa ma da barcin ta koma abinta, komi tagani kuma saita tashi tafita kitchen had'a break fast. tafara babu dad'ewa Amatallah ta shigo kitchen d'in itama, kallon juna sukayi, Amatallah tace, "ina kwana Anty". Cikeda yanga Aneesa ta amsa mata. Amatallah bataji komai a rantaba, dan har zuwa yanzun bata gama Sanin ma'anar kishinba, tarayu gidansu Amminta ita kad'aice, shiyyasa bata ta6ajin zafi ko haushin wani Abu da Aneesar keyiba, tanama d'aukar hakan kawai a tunanin halin Aneesar ne. Kauda tunaninta tayi gefe, tai murmushi da matsawa kusada Aneesa tana fad'in " Anty mizan tayaki dashine?". Yanzunma a d'age Aneesa tad'an kalli Amatallah, saikuma tacigaba da abinda takeyi, "no kije abinki, sonake yau na had'ama my Dear special breakfast da kaina, kodan na nuna masa godiyata na dad'in daya jiyar dani jiya, ai ba ayi mai miji da banba mai girki daban kingani ". Dukda Amatallah taji duk maganar Aneesa tsaf, sai dai bata iya fassara magana ko d'aya ba a ciki, amma ta fahimci maganace cikin magana tamata. d'an murmushi kawai tamata tace, " OK bara naje to nayi shirin school, dama inada lectures d'in safe". bata jira amsar Aneesa ba tafice abinta. Aneesa taraka bayan Amatallah da harara tana ta6e baki. Nidai nace, " hummmm". ********* A 6angaren Fateema tunda maigidan ya tadasu da asuba taga Saifuddin a d'akinta saitaji wani haushi, wato ita Dan an raina mata hankali shine aka d'akko yaro aka kawo mata dansu su samu su warwasa yanda sukeso. To aii idanma gaskiyane yau d'akin Amatallah yakamata ya kwana ko, kenan Aneesa tayi wani makircin?, ai ko sai tayi mata abinda zata bak'anta ranta yau d'innan basai gobeba. Tayi wata 'Yar dariyar mugunta. Tofa Uwargida ran gida, mikike k'ullama Aneesar kuma?.😆 ********** Tunda Amatallah tabar kitchen d'in takasa manta maganganun Aneesa, datayi k'ok'arin mantawa sai maganar tadawo mata a rai, sai takejin wani gefen zuciyarta yanajin kamar d'acin maganar, haka tagama shiryawa sukuku. Tayi k'yau cikin zani da riga Na shadda oxblood color, zani Rafa sket, saiya fita tamkar sket d'in, hakama rigar Tamata d'as, batawani yi kwalliyaba, fauda kawai ta shafa da kwalli sai lipstick data saka, d'an kwalinma normal d'auri tayi, tana tsaka da kimtsa abinda zata buk'ata a handbag yay sallama. Amsawa tayi a sanyaye, sannan ta rissina ta gaidashi. Tsura mata idanu yayi ganin yanda takeyi komai a sanyaye, tamkar mai tunanin wani abu. "Khadeeja!". Yakira sunanta yana zama kan stool d'in madubinta datayi shafa. Kanta a k'asa tace, "Na'am Uncle". " bakida lafiyane?". Yanzunkam sai da ta kallesa, idonta yad'an Tara kwalla, saboda haka kawai maganar Aneesa har yanzu cin zuciyarta takeyi, tanason tasan ma'anar maganar, Dan yanayin da Aneesa Tamata maganar kawai ya tabbatar mata bamai dad'i baceba......... "Khadeeja!". Yakuma kiranta dad'an k'arfi Dan ganin tatafi wani tunanin, hakan kuma ya tabbatar masa akwai abinda ke damunta d'in. Da Sauri tace, " na'am Uncle, INA jinka". "Kina jina ko kina tunani dai my best, kinga please fad'amin damuwarki, karki 6oyemin khadeeja, yanzu nine Brother, nine Ammi, nine Uncle, kuma nine Miji, duk abinda yadameki nizaki tunkara Na share hawayenki kona kare mutuncinki nakuma kwato miki hak'k'inki kinaji ko". Kanta ta jinjina masa tana had'iye kukan dayazo mata. "Yauwa my Best! to fad'amin kinji, ki d'auka yanzu Nid'in Ammice, nasan dai bazaki iya 6oyemata damuwar kiba ko?". Muryarta Na rawa tace, " ALLAH babu komai Uncle". "Khadeeja ban yardaba, Bahaka muka rabuba jiya da daddare". yayi maganar yana tasowa zuwa gareta. Handout d'in hannunta da bag d'in ya amsa ya ajiye akan gadon, ya d'ora hannayensa duk biyu a kafad'arta, idonsa Na kallon fuskarta. Ita kuma ta duk'ar da idonta tana kallon k'afarsa. Cikin sassanyar muryarsa wadda takuma komawa slowly yace, " waye ya 6ata miki rai a gidanan? Fateema!". Ta girgiza kanta. Yace, "Aneesa!". Shiru tayi. Hakanne yasashi fahimtar Aneesa Ce. Iskar bakinsa ya furzar sannan yakuma cewa ''Aneesa Ce ko? mita miki?". Hawayen datake mak'alewa ne suka zubo a kumatunta, murya Na rawa tace "babu abinda fa tamin Uncle, kawai naje tayata girkine tace nabarsa zatayi, shine naji babu dad'i, gani nake ko wani Abu namatane, tunda kaga da bakanan kullum tare mukeyi da Anty Nazeefa , wani lokacin kuma da ita Anty Aneesar, shiyyasa yanzu datace Na barsa sainakejin babu dad'i kamar wani laifi namata". Iska Yakuma furzowa a bakinsa, kafin yamatso da ita jikinsa ya rungumeta yana shafa bayanta alamar lallashi. Sunkai kusan Minti 3 a haka sannan ya d'agota, hannunsa yasa ya goge mata hawayen kafin yakai bakinsa ya sumbaci goshinta. " ki daina damun kanji Indai akan hakanne kinji my heartbeat, badan kin mata laifi bane, kawai inaga Dan taga zakije school ne, amma zan mata magana, daga yau karki kuma zubarmin da hawayennan masu tsada akan wata a gidannan, kema matar gidace kamar kowaccensu, zankuma tabbatar musu da hakan kinji ko?". Kanta ta d'aga masa alamar to. Yace, ''yauwa my babyna, yimin murmushi mana konaji sanyi". 'Yay maganar yanajan kumatunta'. Hakanne yasata sakin murmushi mai k'ayatarwa. Sumbatar goshinta da kumatunta yakumayi yana fad'in "yauwa kokefa my best". Kunya dukta kama Amatallah itadai. " kinada lectures d'in safene?". "Eh Uncle". " Okay, to k'arasa shirin ki sameni a falo mutafi, idan Na ajiye yara a School saina k'arasa dake". Kanta ta d'aga masa alamar to. shikuma ya juya yafita. Afalo ya iske yara angama shiryasu, zama yayi duk suka zauna kusada shi suna gaidashi, ya amsa yana sumbatarsu d'ai-d'ai a kumatu. Babu dad'ewa Fateema tafito cikin kwalliya, (a raina nace Uwargida kina fama da kankinma bazaki hutaba🤭). Tunda ta fito idon Alhaji Muhammad Na a kanta, sai murmushi suke sakarma juna, mik'ewa yayi ya taimaka mata ta zauna, yanason yad'an sumbaceta amma ga yara, Dan haka yamata magana rad'a-rad'a, "sorry my tee.. My children's na kallonmu". Murmushi tamasa, Dan tasan miyake nufi, yanason sumbatarta ga yara, tasan bazai iyaba. Gaidashi tayi da tsokanarsa ango kasha k'amshi, duk angwancinne yasa aka manta damune?". Wata 'yar dariya yayi, yakuma k'asa da murya Dan kar yara su jisu, " my tee... Nazama abin tsokana kuma? ai na shiga kina wanka, su Abulkhairi basu sanar miki bane?". Itama dariyar tayi, tace, "wasa nakeni Nurrina, ya gajiyar hanya". "Alhmdllh my tee.., ammafa akwai, gashi yau dolene nad'anyi wasu yawo wlhy a cikin gari". " amma dai daka hak'ura kad'an huta yinin yau a gida, zuwa gobe saikayi duk abinda kakeso". "Ai fitar tanada muhimmanci my tee..., Alhaji Sabi'u a matse yake dason ganina, nima kuma dai hankalina na kansa, za6e yakuma gabatomu gab, dolene muyi wani motsi da gaggawa kinga". Kallonsa take cikeda so da k'auna, jin mijinsu take harcan k'asan ranta saboda k'yawawan halayensa... Ahaka Aneesa tafito daga 6angarenta cikin kwalliya ta samesu. ganin yanda suke kallon junansu sai kishi ya kamata, harara ta balla musu. Sarai Fateema ta ganta, amma shi bai gantaba saboda yabata baya kad'an. Dariya Fateema tayi a ranta, da fad'in bakiga komaiba 'yan mata, saima anjima ma kin shiga tarkon dazan d'ana miki. Fitowar Amatallah yasaka Fateema janye idonta daga kansa, ta maida kan Amatallah tana murmushi, " Amatallah kin tashi?". tafad'a cikeda fara'a. Itama Amatallah d'in murmushin tayi, kafin tabata amsa yaran duka sukayo kanta suna fad'in "Antynmu ina kwana!". Kowa na 'Yar rige-rigen fad'a da shigewa jikinta. Duk had'asu tayi ta rungume, ta amsa musu da tambayar sun tashi lafiya?. A tare sukace " lafiya lau antynmu". Daga Uncle har Fateema kallonsu suke suna murmushi, zuciyoyinsu najin dad'in yanda Amatallah keson 'ya'yansu, (masu iya magana kance mai d'a wawa) wannan yasaka Fateema kanji sassaucin kishin Amatallah tunkan ta tafi Dubai,, dan duk wada yaga yanda Amatallah kema yaran yasan har zuciyartane. Guntun tsaki Aneesa tayi tashige kitchen. tana jiyo yanda Amatallah ke gaida Fateema cikin girmamawa, itakuma Fateeman tana amsawa tamkar da biyu. jitai duk tak'ara tsanarsu suduka. Uncle kam dad'ine sosai yakuma kamashi, Dan ganin yanda Fateema take bama Amatallah kulawa, sai yaji takuma girma da kima a idonsa. Yarane kawai sukayi break fast d'in, Amatallah ma tea kawai tasha, danji tayi bazata iya cim ko lauma d'aya daga abinda Aneesa ta girkaba, saitaji ma'anar maganganunta sannan. Uncle baice mata komaiba, danya fahimci haushin Aneesa takeji, kuma tabbas ta 6oye masa ainahin abinda Aneesar ta mata. Aikam ganin shine zaikai Amatallah school ko rakkiya Aneesa bata masaba, baibi ta kantaba shima ya fice abinsa, amma yanason saiya san ainahin abinda taima Amatallah d'in. Amota ma Amatallah tayi shiru, sai shine keta hira da yaransa dake bashi labarin abuwan da akayi bayanan. Wani yayi magana wani kuma yayi murmushi kawai, ahaka har sukaje school d'in yaran. Yaran duk suka fita, shikuma yajuyo yana kallon Amatallah, "my best d'an bani 5minutes naga headmaster d'insu, ai bazaki makaraba ko?". Kanta ta d'aga masa. da fad'in " eh Uncle". Fita yayi yana murmushin miskilancin Amatallah, yadad'e da sanin dama Amatallah miskilace ta bugawa a jarida. Kusan mintuna bakwai saigashi ya dawo suka tafi. motar tayi shiru, shi yana tuk'i yana kallon jama'ar gari da nazarin wasu abubuwa gameda yanayin matasan daketa kaikawo, ko zaiga wani canji dasuka samu a 11month's d'in d'aya d'auka baya k'ar, sai dai baiga wani canjin ba koda k'aramine. Amatallah kuma tayi shirune tana kallon mutane dakuma cigaba da juya maganganun Aneesa, (kusan dai Amatallah wajen rik'e Abu arai). Har gaban department d'insu ya kaita, amma yace bazai fitaba, Dan bada shirin shigowa yazoba. Har zata fita yarik'o hannunta. Juyowa tai ta kallesa, yawani langa6e kai "my best! dama haka ake sallama da miji?". K'asa tayi da kanta tana murmushi. ya murza hannunta. dag'owa tayi tad'an kallesa, shikuma ya d'aga mata gira. da sauri ta juyar da fuska tana fad'in ''kai Uncle". a shagwa6e tayi maganar. "Lallai yarinya, ashe zamu kwana a motarnan kenan? dan yau babu wani Uncle anan". Juyowa tayi tace, " uncle kwanafa!?". "Sa wasa kiga aiki kuwa yau". " wayyo Uncle, ALLAH munkusa shiga lecture, kagama su Goodness can da alama nisuke jira". ''Laifin waye to?". Amatallah tace nashiga tara, wai Uncle ya manta matsayinsa ne agareni. a zuciyarta tayi maganar. Kamar yasan mitake fad'a kuwa yakuma ruk'o hannunta da k'yau, "my best kifa rage kunyarnan, lokaci yayi dazaki fara d'aukar Uncle d'inki a matsayin miji ba Uncle kawaiba, koda yake niyakamata na canja wannan matsayin nawa a gareki". yak'are maganar da sumbatar hannunta. Idonta ta rimtse a zuciyarta tace ya salam. Yana sakinta ta fice da sauri. Dariya kawai yayi yana girgiza kai, ya tada motar ya tafi yanamai jin farincikin yanda Amatallah tafara sakin jiki dashi, yana ganin zuwa yanzu lokaci kad'an zai k'ara mata komai ya dai-daita, ayanda yake gani itama takamu da sonsa kamar yanda ya koyar da ita. Tunda ta fito a motar wasu daga d'aliban suka saka mata idanu, hardasu Fa'iza. K'arasowarta yasaka Rita fad'in "baby ke da waye yau? muntafi tarbanki mukaga ba ya Jabeer bane". Da sauri Amatallah tace, " uncle d'inane". Fa'iza dake zaune da tsohon cikinta tayi dariya, danta kuma gaskata Amatallah nada aure yanzun..... Kafin tayi magana Goodness tace, "Amatallah anya Uncle d'inan ba mijinki baneba?". Harararta Amatallah tayi batareda tace komaiba. Aiko suka saka mata dariya, Fa'iza ta yunk'ura ta tashi dagyar tana kallon Amatallah, " to 'yammata ai yanzu munsan komai, sai a daina raina mana wayo, aini wlhy tundaga yanda kike amsa masa waya nasan yawuce Uncle kawai, yaukuma munga zahiri, dan yanda yarik'e hannunki yana miki wani kallo kad'ai yabamu ams........" Amatallah bata bari ta k'arasaba tarufe mata baki. Rita da goodness suka shek'e da dariya. Sai kawai Amatallah ta fashe musu da kuka, dama ga abinda Aneesa ta mata yanata caccakar ranta. shiru sukayi, saikuma jikinsu yayi sanyi, nan suka shiga lallashinta, suna bata hak'uri. Share hawayenta tayi tace, "kubar bani hak'uri, nifa bakune kuka sakani kukaba, kawai dai yanda auren namu ya kasance da Uncle na tuna. Tabasu tausayi sosai. ganin time d'in lecture d'insu yayai tace Subari su fito zata basu labari. A sanyaye suka jinjina mata kansu, sanan suka nufi lecture................✍🏻 🤩👎🏻 One luv my sweet Fan's🥰 *_ALLAH ka gafarta ma iyayenmu_*😭🙏🏻 [1/16, 9:01 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_* *_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡 _{home of expert and perfect writer's}_ *_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉ _(Hattara matasa)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* _Na gaisheku Aminan arzik'i, *Miss Xoxo and Ayusher Muh'd* kud'in na da banne a zuciyar Bilyn Abdull_ _i love you so much masoyan kwarai😉🥰👍🏻_ ____________________ *_Number 26_* ____________________ Dariya ce takusan kufcema Amatallah amma tayi k'ok'arin dannewa, dariyar tata tazone kam saboda ganin yanda Aneesa take sakkowa daga benen tamkar wadda aka biyo. tayi k'ok'arin kauda kanta gefe tana cigaba da jere kulolin abincin bisa tiren data d'akko. Sai da Aneesa taimata wani kallo sannan ta shige 6angarenta tana murmushin muguntar data shiryama Amatallah itama. Sarai Amatallah taga mugun kallon da Aneesa tamata, amma bai dametaba, tadai nemi tsarin ALLAH daga sharrinta a zuciya, Dan tasan tabbas wannan kallon bazai zamto Na alkairi bane. gyara mayafinta tayi sannan ta d'auki tiren abincin tayi sama, komai cikeda dauriya takeyinsa, amma k'asan ranta ita kad'ai tasan a fargabar datake. Sallama tayi a k'ofar falon batareda ta shigaba. Uncle dake kishingid'e har yanzun inda suka barsa ya amsa yana kallon k'ofar, "shigo mana". Yafad'a yana maida kallonsa ga TV. Sai da tad'a sauke ajiyar zuciya kafin ta tura labulen da tiren tashigo. Batareda ya kalletaba yace, " lafiya naga kin dad'e?". Kanta ta kad'a masa kawai tana ajiye tiren bisa santa table d'in dake tsakkiyar falon. Hakanne yasakashi juyowa ya kalleta, dai-dai itama ta d'ago zata cemasa ga abincin suka had'a ido. Da sauri ta sauke nata. shima janye nasa yayi yatashi zaune yana murmushi, k'arar TV ya rage yana fad'in "sauke k'asa ki janye table d'in, banacin abinci a sama". Nanma batace komaiba ta sauke kamar yanda ya umarceta, k'asa yadawo ya zauna, itakuma ta durk'usa gabansa tana sauke kulolin daga tiren, harzata fara zubawa yace, " zauna da k'yau mana". Still nanma dai bata tankaba ta gyara zamanta tareda tankwashe k'afafunta tafara zuba masa abincin. tuwon alkama ne miyar d'anyen ku6ewa, sai k'amshin kori ketashi mai dad'i (so a 6angaren abinci babu sakarai a matan Uncle, kowacce gwanace😊). "My best! wannan abincin yayi yawa ai, kozaki cine?". Da sauri ta kad'a kanta alamar a'a. Yad'an murmusa kad'an " wai an d'inke bakinne?". A sanyaye tace, "a'a Uncle". " Okay duk jan ajine irinna Amare?". Ba shiri tasa hannu tarufe fuskarta tana fad'in "kai Uncle". " ALLAH kuwa my best!, najiki tsit ne, amma ina ruwan wanke hannu". "Bara Na d'akko na mantane". Baice komaiba, sai dai harta fita yana binta da kallo, a fili yace " ALLAH kenan mai tsara al'amura, shi koda a mafarki yama ta6a tunanin Amatallah a jerin matansa, koda matan NASA keyin kishi da ita abaya wlhy shi bayajin komai a ransa game da ita, kallon d'iya yake mata tamkar su Sahib, amma Ubangiji gagara misali saigashi ya canja al'amura tamkar wani labarin tatsuniyoyi ko finafinai...... Sallamarta ta katse tunaninsa, ta ajiye k'aramar roba data zubo ruwan wanke hannun, zama takumayi tamkar d'azun. "Yauwa babyna sannunku". yafad'a yana saka hannunsa a ruwan. Itadai Amatallah mamaki komansa ke bata, tana mamakin yanda ko kad'an bayajin kunyar kiranta da kowanne irin suna yanzun, jibifa abinda yamata d'azun tamkar ba uncle d'intaba..... Jin hannunta cikin ruwan ta sauke ajiyar zuciya da kallonsa. ido d'aya ya kashe mata, kafin yace, " nasan kema yunwar kikeji ai... "ALLAH uncle a'a, naci abinci d'azun". "Saiki k'ara yanzu ai ko". Babu yanda zatayi dole tasaka hannu kamar yanda yamata umarni sukaci a tare, sai dai a kunyace Amatallah keci, ko kad'an takasa sakin jiki taci Na kirki, sunci kusan fin rabin data zuba taga ya tsame hannunsa yana fad'in "Alhamdllh". Itama saita tsame nata hannun, dama tuni ta k'oshi, tsoron karyay mata fad'ane yahanata cire hannu. Kallonta yayi " badai kin k'oshiba?". Ta langa6e kanta gefe tamkar zata FASA masa kuka tace, "ALLAH uncle nak'oshi, kar cikina yafashe fa". A mamakinta saitaga ya d'ora hannunsa saman cikinta wai zai duba yaga iyakar Girman cikin. Da sauri tad'an matsa baya, shikuma yasaki k'asaitaccen murmushi yana shafa gemunsa, Wanda takula hakan yazame masa al'ada, inhar Abu zai faranta ransa koya 6ata ransa sai ya kai hannu yashafi gemun nan da itama kanta shaidace tasan ya k'ara masa k'yau da kwarjini. " Uncle tunda kaci abincin bara naje Na kwanta, lectures d'in safe gareni gobe". Wani kallo mai cikeda ma'anoni yamata kafin ya kauda Kansa yana murmushi, yakula dama tuni a d'arare take dashi, yabasar da maganar batareda ya bata izinin tafiyarba. "Uncle Na tafi?". Maganarta tasakashi juyowa ya kalleta, Kansa kawai ya kad'a alamar tatafi batareda yayi maganaba. Ai ko cikin hanzari ta had'a kwanukan ta d'auka ta fice. binta kawai yayi da kallo harta kullema ganinsa sannan ya sauke ajiyar zuciya. Amatallah Na sauka tayi hamdala ga ubangiji data kubtar da ita. Nace, "humm". ****** Abinda yabani mamaki koda Na lek'a wajen Aneesa saina taddata hankali kwance, tana zaune a falo tanama Siddiqa shirin barci, harda 'yar wak'ama take rerawa abinta, sai dai kuma baitin wak'ar yasakani fahimtar bata jin dad'i baceba. Lalla6awa nayi Na fito, itama Uwargida Na lek'ata. zaune take ta zuba tagumi tana kallon 'ya'yanta, itakam ban fahimci mike damuntaba. Fitowa nayi itama nabi bayan Amatallah. Na isketa tayo brosh tafito daga toilet, harma ta cire kayanta tasaka riga da wando Na barci pink, wandon iyakarsa gwiwa, sai rigarma batada girma sosai mai hannun shimi, itama dai 'yar wak'arta naji tanayi harta bud'e Waldrob d'inta ta d'akko hula tasaka a kanta kafin ta daka tsale ta haye gadonta, duk acikin murnar Uncle baice ta kwana d'akinsaba..... 😂zakiyi bayani. Uncle kam tana fita shima ya mik'e, TV ya kashe danji yay labaranma sun fita kansa, dama gawani abinda ake nunawa daya Sosa zuciyarsa akan MATASA, fitar Amatallah d'in saita sakashi a kewa, ya saba zama a irin wannan lokacin da matarsa zaune gefensa suna 'yar hirar rayuwa da soyayyarsu. yabar Amatallah ta tafine danya kula takasa sakewa, shikuma baya buk'atar abinda zai k'untata rayuwarta. amma mi saiyaji bazai iya kwana shikad'ai ba gaskiya, bayan kuma ga mata har uku suna amsa sunan halalinsa, bedroom d'insa yashiga ya canja kayansa zuwa na barci, vest ne da boxer, saiya d'aura jallabiya a sama kawai, yad'an fesa turare kafin yashiga toilet yayo brosh, wayoyinsa ya d'auka ya zuba a aljihu, dan shi baya kashe waya sai dai abisa kuskure ko rashin caji. Yakashe komai Na 6angaren nasa yafito. Sai dai yana fara sakkowa daga benen ana d'auke wuta, "ya salam" yafad'a yana dafe kansa. Ya zaro wayarsa daga aljihu ya kunna fitila sannan ya ida sauka, dolenema ya kunna Generator kodan Sahib dabaya k'aunar zafi, koyaya zafi ya isheshi zaitashi yaytama mutane kuka, yaron yanada masifar jin zafi, gakuma Fateema da ciki kansata zufar babu gaira babu dalili. harya kama hanyar k'ofar fita kuma yadawo baya, 6angaren Fateema yashiga da sallama. Amsawa tayi tana cire taguminta da saita kanta gudun karya fuskanci halin datake ciki, yak'araso cikin bedroom d'in idonsa akan yaran. "Wai yanzu kuma su Ummita sun dawo nanne da kwana?". Kallonsa tayi tace, " a'a, kawai dai kwana biyunnan ne, amma zasu koma d'akinsu ai". Kansa kawai ya jinjina, ya matsa kusadasu yana lek'a fuskar kowa, ya gyarama Abulkhairi kwanciya daya dawo bakin kadon sosai wajen murje-murjen barci. "Nikam d'azun Shehu yakawo fetur gidannan?". " kai, anya kuwa, gaskiya banga shehu a gidannanba, sai dai idan kuma bai shigo bane kokuma yakawo ina d'aki, amma ka tambayi Momynsu dai watak'il taga zuwansa". ''Okay, to zaman mikikeyi baki kwantaba?". Guntun tsaki tayi kafin tace, "wlhy hakanan dai". Matsowa yayi kusada ita ya taimaka mata ta kwanta, sannan ya tofesu da addu'a, yabisu d'ai'd'ai ya sumbata kafin yamata saida safe. Yana shirin fita Sahib yafara motsawa yana k'unk'unin kuka, da baya ya dawo ya haskashi, harya fara tara zufa, yanad'an kad'a hannunsa alamar yima kansa firfita. " to sarkin jin zafi, zaka fara ko?" Uncle yay maganar yana sinkuyowa kansa yacire ma6allan rigar barcinsa ya cire masa. Ita dai Fateema batace komaiba tana daga kwance tana kallonsu harya gama. Da d'an hanzari yafita yana fad'in "bara dai Na bincika fetur d'in". 6angaren Aneesa yashiga, har yanzu tana falo zaune, sai dai tagamama Siddiqa shiri tuni, tana kan cinyarta dai har yanzu, idonta a lumshe, dan tunda aka d'auke wuta bata motsaba bare ta kunna fitila, sallamarsa tasata amsawa amma bata kalleshiba dukda haska fuskarta dayayi da fitilar wayarsa kafin ya maida Kallonsa ga Saifudden dake kwance a kujera doguwa, kuma maida kallonsa yayi kanta itada Siddiqa. Fuskarsa babu walwala yace, " shehu yakawo fetur d'azune?". Kamar bazata tankaba, saikuma tace, "ban saniba nima, Dan bai shigo cikiba, amma ka tambayi umman yara mana". Zai k'ara maganama aka maido wuta, ajiyar zuciya kawai ya sauke yace " Alhmdllh" ya kashe wayar yasaka aljihu, Saifudden ya d'auka yay cikin bedroom d'inta dashi, haryaje k'ofa yajuyo yana kallonsa bayan yata6a d'uwawun Saifudden. "Wai sai yaushe zaki daina sakama yaronnan Pampas ne?". Baki tad'an tunzuro, " amma dai kasan fitsari yakemin a gado, kaga dole na saka masa pampas". "Humm amma ai nafad'a miki ki maidashi 6angaren Fateema yana kwana cikin 'yan uwansa, tundasu katifarsu fitsari baya hudawa, tunda bazai yuwu yadinga kwana shi kad'aiba anan". " ammafa dear kasa......." Saikuma tayi shiru bata k'arasaba. Yace, "nasan mi?". Shiru tayi bata tankaba, amma idonta a kansa. Shima shigewarsa yayi ya shifid'e Saifudden, yadawo ya d'auka Siddiqa itama, itadai Aneesa kallonsa kawai takeyi, bai fitoba saida yayi musu addu'oi kamar yanda ya saba. Koda yafito bai kulataba yanufi hanyar ficewa. Da sauri ta ruk'i hannunsa na dama, cak ya tsaya amma bai juyoba, sai kawai tamatsa ta rungumeshi ta baya tareda sakin wani marayan kuka. Shiru yayi yana saurarenta dukda kukan NATA na sukar zuciyarsa, sai kawai ya lumshe idanu, kusan mintuna 3 kafin yasa hannu ya janyeta a bayansa, takuma rik'eshi da k'yau yanda bazai guduba. "Please dear kadaina fushi dani Dan ALLAH na tuba". Kallonta yayi ya kauda kansa, dukda tabashi tausayi bai tankaba yakuma yunk'urin fita. Sai kawai tazube a gabansa takuma sakin kuka. tamau yakuma tamke fuska, " Aneesa bani hanya na wuce" yay maganar a d'an tsawace. "Babu inda zanje Muhammad, sai dai mu kwana anan". Wani murmushi yasaki yana shafa gemunsa, yace "sai dai ke d'in ki kwana anan amma baniba mai amarya, tunda baki shirya fad'amin abinda ya had'aki da khadeeja ba muyita zama ahaka". Dukda maganar ta soki zuciyarta haka ta danne, tamik'e tana fad'in "shikenan zan sanar maka, saikamin hukunci, amma ina fatan hakan bazai sakaka d'aukar wani sabon fushinba?". A tausashe take maganar, kuma dolene tabaka tausayi. Kallon agogon falon yayi kafin ya kalleta, " kibari saida safe, yanzukam barci nakeji" ya kai karshen maganar da kama hannunta zuwa bedroom d'in ta, dama tayi shirin barci, dan haka ya taimaka mata ta kwanta, goshinta ya sumbata yafita yana fad'in "ALLAH yabamu alkairi". Bata tanka mishiba, sai wasu hawaye masu zafi dasuka kwaranyo a kumatunta, tasan babu makawa yau zai angwance abinsa, a fili tace, "ya ALLAH ka sassautamin kishinan dai". ALLAH saita bani tausayi masu karatu😓. Harna amsa da amin Aneesa. Dan zafin kishi bala'ine. Komai na falonta yakashe sannan yafito babban falo, nanma yakashe abinda zai kashe, fitilar kitchen ya hango a kunne, itama ya k'arasa ya kashe tareda jawo k'ofar, saida ya tabbatar komai dai-dai sannan yanufi 6angaren Amatallah. Ba barci takeba, tana zaune tsakkiyar gadon tana karatu, harta kwanta aka maido wuta, shine ta tashi kawai tana bincika takardunta na school, Dan watak'il gobe amusu test. Shigowarsa babu zato sai sallamarsa dataji kusan dab da ita yasakata diriricewa, tafara laluben abundan zata rufe jikinta, saidai babu komai akusa da ita, bargone kuma ta turashi can k'arshen gadon lokacin datayi tsalle. Shikam kallon k'yawun halittar da ALLAH yamata yasakashi manta gabanma wa yakene, saida tafara k'ok'arin sauka daga gadon Dan d'aukar hijjabi sannan ya dawo hayyacinsa. Saurin rik'ota yayi ya maidata kan gadon, shima ya zauna gefen yana kallon takardun data baje a gadon, "dama bakiyi barciba" yay maganar murya a sanyaye kuma yana kallonta. Kasa magana tayi, sai jijjiga masa kai datayi tanata wani takurewa da gyagygyara wuyan rigarta tamkar tamata yawa, alhalin kuma cif take a jikinta tamkar an gwadatama. Murmushi yayi yana hayewa sosai kan gadon, ya tattare takardun waje d'aya yamaida kan drowan gefen gadon ya ajiye. Muryarta na d'an rawa tace, "Uncle ina karatun test ne fa". Hannu yakai yarik'o nata yana wani k'ank'ance idanu, "tunda miji yazo sai'a barshi aii ko, nima wani text d'in zamuyi yanzun aii". Gabanta ya fad'i, ta tuno maganar Fa'iza, gefe kuma tana mamakin dama haka Uncle yake Wai?...." Bata kai k'arshen tunanintaba tajita a jikinsa, sosai jikinta yafara rawa, hannu kawai yakai saman bango kusada fuskar gadon ya kashe fitilar d'akin. Mi cikin Amatallah zaiyi banda k'ara kuuuuuu!!!. Tamkar ya kwashe da dariya haka yaji, amma saiya dake ya gyara mata kwanciya sosai ajikinsa bayan yazame jallabiyar jikinsa ya zauna dagashi sai vest da boxer. Kasa cewa uffan Amatallah tayi, saidai jikinta har yanzu rawa yakeyi, bata k'ara tsorataba saida taji babu alamar kaya a jikinsa, kasa daurewa tayi muryarta na zuga na alamar tahowar kuka tace, "please Uncle ALLAH I...... Bai bari takai k'arsheba ya d'ora hannunsa akan le6enta, acikin kunnenta yace, " ya isa haka, ni barci kawai nazo muyi madam pinky....." 'Dan k'ank'ame jikinta tayi saboda maganarsa tasaka tsigar jikinta yin yarrr. luf tayi bata kuma yunk'urin yin maganaba, taji ya janye hannunta daya d'ora saman k'irjinta ya d'ara yatsansa a bakinta. Shirune ya biyo baya a d'akin, sai k'arar fanka kawai, shi addu'a yakeyi, itakam tunanin da fargabar wannan lamari ga d'unbin mamakin rashin kawaici na namiji sun cika kwalwar kanta, hummm komin matsayin Namiji a wajenka kafin aure, labari yakan koma bayan kazama matarsa, saisu ture Duk wata kunya da karar girmansu a wajenka su nuna maka sunma manta, kujifa Uncle yanzu harda wani cemata madam pinky, saboda komai nata pink har kayan barci kenan, wayyo Uncle zaka kasheni da kunya wlhy........ Cak tunaninta ya tsaya danjin hannunsa indama batayi zatoba da sunan yana shafa mata addu'a, k'ank'ame jikinta tayi waje guda. Yasaki murmushi mai sauti yana janye hannun daga inda ya d'ora. Koda ya kammala addu'ar sai kawai ya rungumeta da k'yau ya lumshe ido batareda yace da ita uffanba. Dan danan barci mai dad'i yay gaba dashi, Amatallah kam sai sak'e-sak'e takeyi, hankalinta bai kwantaba saida taji saukar numfashinsa a hankali alamar barci ya d'aukeshi, addu'a tayi tad'an tattaofa batareda ta shafaba ta lumshe idanu, barci yace muje zuwa......... Asuba tagari Uncle and Ama........ 🚶🏻‍♀nima natafi wajen nawa Uncle d'in😄😜. ___________________________ *Washe gari* Kusan 3:39am ya farka kamar yanda ya saba a kowacce ranar lahadi daren litinin, dakuma laraba daren Alhamis, sauran ranakun kuma yakan tashi tun around 2 randa kuma nauyin jiki da gajiya suka hanashi shikenan, yanda Amatallah ta katantanesa saiyayi murmushi, hannu yasa k'ark'ashin filo ya d'akko k'aramar wayarsa ya kunna fitila ya haska ta, ba k'aramin shigewa jikinsa tayiba, gashi da alama andad'e da d'auke wuta ma, sanyin asuba daya fara busowa yad'an sassauta zafin garin, cikin dabara ya janyeta a jikinsa tareda gyara mata kwanciya yamaye gurbinsa da filo, gani yay tad'an gyara sosai tareda kuma k'ank'ame filon tacigaba da barcinta. Murmushi yakumayi kafin ya fice, shaf ya manta baisa ta ajiye masa kayan tea ba, ALLAH ma yasoshi kowacce tanadashi a kitchen d'in 6angarenta, kitchen d'in falonta yashiga, wanda kowacce tanadashi, saikuma na gaba d'aya Wanda yake a babban falonsu, inda ananne kowacce keyin girki ranar duty d'inta,, haskawa yayi yana son ganin plas d'in tea d'inta da addu'ar ALLAH yasa tana ajiye Hort water kamar sauran, can ya hangoshi a kusurwa, yamatsa yana d'agawa da tunani, ''Alhmdllah" yafad'a yayinda yaji nauyi, nan dai yahad'a shayi mai sauk'in kauri, ya bud'e fright d'inta kota ajiye bread tunda ana ajiyema kowa, kusan uku yagani alamun bata cima ita kenan, saikuma k'ananun cake Wanda da alama ita tasiya kayanta ta ajiye, cake d'in dake nannad'e a ledoji gudun karya bushe ya d'auka guda 2 da ruwa yafito, bedroom d'in ya koma, ya ajiye kayan hannunsa saman k'aramin table d'in fake gaban sofa yawuce bathroom yayo brosh, yana shan tea da cake idonsa akan Amatallah, shikad'ai yasan miyake kissimama zuciyarsa, hardai yagama tsaf yakoma bayi yay alwala, abin salla ya shinfid'a sannan yasaka jallabiyarsa ya kabbara salla. Har aka kira sallar farko yana nafilfilinsa, a lokacin yamik'e yay rakata'ainul fijir sannan yatada Amatallah da k'yar saboda tanada nauyin barci. Ganinsa a d'akin yatuna mata tarefa suka kwana, kanta a k'asa tashige toilet, shikuma yafita yana murmushi. Kamar yanda ya saba d'akin kowaccensu yashiga yatadasu, ya taimakama Fateema tayi alwala saboda nauyin datayi, sannan yatada yara suma da taimakonsa sukayi alwalar, d'akin Aneesa yakoma shima Saifudden ya tadadashi, dukda Aneesa tatashi bata tadashiba saboda tasan shike tashinsu kullum. Dukda k'ank'antar yaransa hakan bai hanashi horonsu da zuwa sallar asubahiba komin sanyi ko ruwa, saidai in bakada lafiya kokuma shima bazaijeba akan wani dalili mai k'arfi, saisuyi agida gaba d'aya, amma dai tilasne saika tashi kayi sallar..............✍🏻 _jiyakam kunjini shiru, dama nasanar daku inada wasu uzurirrika, wlhy da k'yarma nake cire time d'in muku typing, shiyyasa zakuga ko comments d'inku ban tankaba kwana biyu, saima yau nasami damar dubawa, ngd sosai, kuna sakani nishad'i, ina alfahari daku dajin dad'in yanda kukema mahaifina addu'a, ALLAH yabar k'auna, kuma kunan araina daram, shiyyasa nake daurewa nayi typing danna sakaku farin ciki wlhy😄😘._ 🤩👎🏻 One luv my sweet Fan's🥰 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻 [1/16, 9:01 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_* *_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡 _{home of expert and perfect writer's}_ *_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉ _(Hattara matasa)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* ______________________ *_Number 24 and 25_* ______________________ Ta6a k'ofar yay yajita arufe dan haka ya kwankwasa, da k'wankwasa k'ofar da bugawar zuyar Amatallah lokaci d'aya suka kasance, dan tabbas tasan shine, tunda tajiyo hayaniyar yaransa suna ihun murnar dawowarsa. K'ara bugawarsace tasakata mik'ewa dole tanufi k'ofar tana k'ara gyara zaman siririn gyalenta da k'yau. ta bud'e k'ofar cikeda fargabar k'arfa fama kanta gwiwa, sai dai me suna had'a ido da boss jarumtar ta tafara k'ok'arin su6uce mata, matsawa tayi yashigo yana sa6a babbar rigarsa a kafad'a idonsa a kanta yana binta da kallon k'urulla, gani yayi kayan sun kuma k'ank'antar da ita, amma tayi k'yau sosai. Zama yayi a kujerar kusa dashi, wadda ta kasance 2seaters, Amatallah kam tuni ta zube a k'asa tana gaisheshi cikin d'an rawar murya, dan dukkan ALWASHIN ta (Ummu Aysha) dataci bayan barowarta makaranta zuwa yanzu saitaji kwarjininsa ya fatattakeshi. Bai amsa gaisuwarba sai kiran sunanta dayayi cikin sassanyar muryarsa. Ta d'ago manyan idanunta tad'an kalleshi, saikuma ta maidasu k'asa tana cigaba dayin wasa da yatsun hannunta. Yatsun hannun yabi da kallo, wad'anda haryau rad'am suke da zanen jan llalli da 6ak'i, yasaki guntun murmushi mai sauti Wanda har Amatallah d'inma saida tajishi. "My best zonan". ya fad'a yana mik'a mata hannu kamar wata tata🙇‍♀. Batayi musuba tamik'e kanta a k'asa taje inda yake, tana k'ok'arin zama a k'asa yaruk'o hannunta tareda jawota ta fad'o saman cinyarsa. A fili tace, "ya sallam!!, Uncle Sorry". tayi yunk'urin mik'ewa, a zatonta ko asfa kuskure tafad'a kansa. illahirin jikinta duk rawa yakeyi, dan tunda uwarda ta haifeta duniya hakan baita6a faruwa da itaba ko'a mafarki, dukda cud'anya cikin k'abilu daban-daban da Amatallah tayi hakan baisa koda kuskure wani namiji yata6a rik'e hannuntaba bayan mahaifinta da Uncle M.A, shima kuma saida igiyar aure ta tabbata kansu sannan yafara mata hakan, sai dai kuma idan ta mantane......... Kuma mannata dayay da jikinsa yana sauke sassanyar ajiyar zuciyane ya maido Amatallah daga tunaninta, " Uncle please ". tafad'a tana kuma yunk'urin kwace jikinta. A cikin kunnenta yace, " aji tausayin bawan ALLAH mana my heartbeat". Tsigar jikin Amatallah Ce tatashi yarrr tareda yamutsawar 'yan hanjin cikinta Na tsoro. tafara tuno maganar Fa'iza, ta girgiza kai a zuciyarta tana fad'in bazan iyaba Fa'iza, kimar Uncle tawuce zaton kowa a garen.......... Batakai k'arsheba taji wani bak'on al'amarin dayafi Na zama cinyarsa girgizata, rufe idonta datayi yabama Uncle damar k'arema fuskarta kallo har zuwa la66anta da sukasha lipstick sunata k'yalli, kasa hak'uri yayi kamar yanda yaso, sai kawai ya manna bakinsa akai. Saida ya tabbatar yashanye lipstick d'inan tas sannan ya janye bakinsa. Ai da gudu Amatallah ta sauka daga jikinsa tashige bedroom d'inta, bataja birki a ko inaba sai toilet d'inta. jingina tayi da k'ofar tana hakkin gudun datayi da sauke numfashi, ga hawaye sha6e-sha6e a face d'inta. Shikam tana barin jikinsa yabita da kallo, harta shige sannan yay wani k'asaitaccen murmushi maihad'eda guntuwar dariya, shikansa yana mamakin kansa akan zurfafa cik'in k'auna da begen d'iyar cikinsa, abinda ko'a mafarki bai ta6a wanan tunaninba, hargashi yau takaishi ga rashin hak'uri ya aikata abinda shi Kansas kunyar Kansa yakeji, ya lumshe idanunsa yana furzo iskar bakinsa dawani murmushin dayake k'ara fidda ainahin k'yawunsa da kwarjinin kamala da ALLAH ya azurtashi dashi. ganin bazata fitoba kusan mintuna uku yatashi ya fice. A falo Yakuma iske yara suna kallon Cartoon Na larabci, sun maida hankalinsu sosai akan TV, dan haka baiyi maganaba yashiga 6angaren Aneesa. Zaune ya taddata a fallo, sai dai kallo d'aya yamata yagane tasha kuka, zama yay kujerar dake kallonta, cikin tsare gida yace, "lafiya dai ko?". Maganarsa takuma tunzuro Aneesa, tawani turo baki gaba tana kuma d'aure fuska itama, a tsiwace tace, " wai minamaka kake wulak'antani irin haka? miye laifina danna soka? kokuwa wannan shine salon sakayyar dazakamin bayan karaboni da k'asata da iyayena......." Wani banzan kallo yamata, Wanda yasata 6ame bakinta babu shiri, tasan halinsa sarai yatsani raini da rashin tausasa harshe, amma itama rantane yagama 6aci akan abinda yamata da safe bai isheshiba yak'ara mata wani yanzun. Maimakon yabata amsoshin maganganunta se cewa yayai "miya had'aki da Amatallah da safe?". Ranta Yakuma 6aci, shaid'an Na angiza zuciyarta tace, "Woow! dama munafuncina akayi a wajenka shiyyasa kake wulak'antani? itakuma da salon data shigo gidan kenan? kaima miji munafuncin kishiyoyi...." ''Aneesa!! Karfa kibari fushina yakai k'arshe a kanki, ki sanarmin abinda Na tambayeki". a fad'ace yayi maganar, amma hakan bai hana muryarsa fita cikin sanyiba da nutsuwa. Dukda Aneesa takai k'arshe a 6acin ranta hakan bai hanata tsorata da Shiba, tasan halinsa sarai, Duk abinda kaga ya tanka a Kansa, to lallai ya d'aukeshi da girma, amma komi matarsa zata masa Na 6acin rai bata Isa ya mata ihu ba, saidai yayi abinda kema zai bak'anta ranki cikin ruwan sanyi, rabonta dataga irin wannan Fushun a taredashi tun fad'an k'arshe dasukayi da Fateema lokacin daya had'esu gida d'aya, dan lokacinma dukansu gida yace su tafi saiyazo, saida babansa ya hana sannan ya hak'ura saboda gaya masa da sukaje sukayi......... Tunaninta ya katse lokacin dataga yamik'e yafice bai sake cemata komaiba, binsa tayi da kallo ranta Na suya da mamakin Amatallah, lallai zata gyarama yarinyarnan zama a gidannan, wato ita kuma NATA salon had'a fad'a da miji ko, idonta harya kai tsaurin haka, ai ko tayi Na farko tayi Na k'arshe, zata shayar da ita mamaki. Nace ''hummm". Yanzunma yaran basu luraba harya haye samansa, ransa gaba d'aya a 6ace yake da Aneesa, dan harga ALLAH bazai d'auki k'untatama marainiyar ALLAH ba, mahaifinta yabashi itane dan ganin zai iya rik'e masa ita, bakuma zai yuwu wani ya k'untata ta yabariba koda wanene wlhy. kayansa ya cire yashiga wanka, koda yafito k'ananun kaya yasaka bak'in dogon wando da farar t-shirt mai gajeren hannu, yad'an fesa turare yadawo falonsa, saida yabud'e freight ya d'akko ruwa ya d'auki kofi da aka jere a wata 'yar glass drawer sannan ya zauna saman kujera, koda yasha ruwan saiya zame ya kwanta tareda lumshe idanunsa, ba barci yakeba tunanin tattaunawarsu da Alahaji sabi'u yakeyi, dakuma yanda suka tsara abubuwa, ahaka har tunaninsa yakoma kan rayuwar data shud'e, kewar Brother d'insa tadawo masa sabuwa a zuciya, ayanzu abubuwa dayawa suna damun zuciyarsa amma babu Wanda zai sanarmawa, yashare 'yan kwallan dasuka taru masa a gefen ido kafin yakai dubansa ga agogo, 9:34pm, wayarsa ya jawo da zummar kiran Fateema saikuma ga kiranta ya shigo, guntun murmushi yayi sannan ya d'aga, saida tamasa sallama ya amsa sannan tace, ''najika shirune Nurrina, koka fasa ne?". d'an huci ya furzar, kafin yace ''a'a my tee...., yara fa?". "Gasunan harsun gaji da jiranka sun kwanta saboda school". " oh sumin afuwa, tunda sun kwanta kuzo kawai". "Okey". kawai tafad'a ta yanke wayar. Amatallah ya kira, tana ganin kiransa gabanta yafad'i, a tsorace ta d'aga wayar, muryarta har zuga take, kansa kawai yad'an girgiza, yace, " khadeeja kin kwantane?". Sunan daya kirata dashine yasata d'anjin sassauci a zuciyarta, danta kula sai akan muhimmin Abu yake kiran ainahin sunan nata. a sanyaye tace, "a'a karatu nakeyi". Murmushi yayi mai sauti yace, " okay, tom kizo samana yanzunnan". bai jira amsartaba ya kashe kiran. Hannu tasa aka tana fad'in "nashi 100 ni Khadija, mikuma zanma Uncle a darenan?". maganar Fa'iza takuma fad'o mata a rai. _inhar yau ya buk'aci ki kar6i kwananki wlhy ki kar6a, kuma ya buk'aceki karki bijire masa, yanda yanzu ake yayin mutuwarnan._ da sauri tace, " bazan iyaba wlhy Fa'iza, bazan iya had'a shinfid'a da Uncle ba, Na shiga uku ni Khadija, wayyo Ammina". Yanda take safa da marwa a tsakar falon saita bani dariya da tausayi. A can kuwa Uncle itama Aneeaa ya kirata, cikeda tsoro ta d'aga, "ki sameni a sama". Kawai yace ya yanke wayar. Takuma tsorata, dan haka tatafi sukuku zuciyarta Na nadamar abinda tamasa d'azun. Kusan a tare suka iso da Fateema, dan zaman Fateema kenan tashigo, murmushin dayakema Fateema tuni ya d'auke daga fuskarsa ganin Aneesa, bayan ya taimakama Fateema ta zauna kusadashi ya maida idonsa ga TV batareda ya kalli ko sashen da Aneesa takeba. duk da Fateema ta lura da canjawarsa hakan baisa ta fuskanci wani abububa tsakaninsa da Aneesa. Kusan mintuna biyar da zamansu babu labarin Amatallah. Wayarsa ya d'auka yakuma kiranta. tana d'agawa da sauri tace " ganinan zuwa Uncle toilet na shiga". Baice komaiba ya yanke wayar. K'irjin Amatallah Na dukan d'ari-d'ari ta yayi sallama a k'ofar falon. Su duk suka amsa banda Aneesa. "Shigo mana". tajiyo muryar Uncle. Kanta a k'asa tashigo, dan duk taga slifas d'in su Fateema a k'ofar falon. maimakon ta zauna a kujera kamar yanda sukayi saita zauna a k'asa. Fateema tace, " haba Amatallah! tashi ki hau kujera mana". "A'a Anty, nanma yayi, ina yini". Amsawa Fateema tayi cikin fara'a dason k'ular da Aneesa. Aiko ta shak'a🤣. Amatallah ta kalli sashen da Aneesa take tace, "ina yini?". Shiru Aneesa tayi tak'i amsawa tamkar batajiba. Wata uwar harara Uncle ya maka mata, babu shiri ta amsa gaisuwar. Amatallah kam baki ta ta6e, tad'an saci kallon Uncle taga shima itad'in yake kallo, amma fuskarsa babu walwala. Kauda idon tayi azamaryi tana gyara zamanta sosai. Kusan mintuna biyu yayi gyaran murya sannan yamusu sallama. Atare suka amsa masa. Addu'a yayi kafin yafara da abinda ya tarasu. _"Alhmdllh, da farko dai zan fara da muku nasiha akan halin zaman takewar rayuwa. duk yanda karayu dawani mala'ikun ALLAH kan rubuta k'yautatawarka gareshi ko cutarwarka agareshi, kuma aranar kiyama zaimuku hisabi akan wannan zaman tabbas, dan haka akeson ka kasance mai k'yak'yk'awar zuciya akowanne irin hali, karik'e kowa da zuciya d'aya, shi kishi ba hauka baneba, duk abinda kaga ubangiji ya halatta ga bawansa to shiyasan dalilin hakan, inamai gargad'arku dakuji tsoron ALLAH akan cutar da juna koda da mummunan kallone bare magana, nidai harga ALLAH ban auri kowaccenku dan bana sontaba, duk d'inku so iri d'aya nake muku, banbanci yanaga yanayin yanda kowaccenku ta k'yautatamin, dan ita zuciya takan karkatane gamai k'yautata mata. insha ALLAHU kuma nayi alk'awarin kare ma kowaccenku mutuncinta da hak'inta, bance muku nid'in dabanne acikin mazan duniya ko Hausa fulaniba, saidai inamai tabbatar muku zanyi duk wani k'ok'arin samun tazara wajen k'yautatama iyalina tsakanina da sauran maza, dan tabbas kawai kuskure da sauran maza kanyi musamman mazan HAUSA FULANI ma, zakuga namijin bahaushe mafi aksarinsu sun dauka cewa, aure ba komai ba ne face jima'i da tara zuri'a. Hakan ne ma ya sa Yana da wuya ka ga ma'aurata suna sumbatar juna a goshi koh a kumatu, kuma idan ka ga sun rungume juna, toh labari mai dadi ne ya samu."_ _"Yana da wuya ka ga miji yana baiwa matarsa abinci a baki, Idan ka ga hakan kuwa toh ka tabbata matar ce bata da lafiya, shima ba kowanne kema yin wannan k'ok'arinba, wanima yana kallon matar zai tsallake yatafi ga harkokinsa, a ganinsa bashida lokacin zama ya kula da ita ma a haukarsa."_ _"ldan ba a drama ko Novels ba, zai yi wuya ka ga miji ya bude wa matarsa kofar mota ko taimaka mata da rainon yaransu ko ma d'aukar yaron gaba d'aya, wani saiki samu in anmasa haihuwa daga ya d'auki d'an yamasa hud'ubar suna bazai sakeba sai idan yaron yana cikin matsanancin ciwo koya mutu yad'auki gawarsa, amma bawai haka kawaiba danjin dad'i, a tunaninsa raino sai mata, shi nashi kawai yanemo abincine yabasu, babu maganar neman shak'uwa tsakanin 'ya'ya da mahaifi, to mahaifiyarsuma bata samuba bare kuma su yaran"._ _"Abu guda daya da yake sanya magidanci a Arewa ya taba wuyan matarsa shine lokacin da take korafin zazzabi yana damun ta, ba zai kuma kara tabawa ba sai wani sabon zazzabin ya zo, ko fad'a ya had'asu 6acin rai yasakashi shak'e wuyan domin mata hukunci, saikace yasamu dabba ko baiwarsa"._ _"Lokaci daya ne za ka ga miji ya dauko matarsa a hannu, lokacin kuwa shine idan ta fara labour (nakuda) zai kai ta asibiti, ko daren farkonsu yanaji da zumud'in son samun biyan buk'atarsa, kokuma inta mutu ya fiddo gawarta daga asibitin ko d'akinta, hakama yimata wanka ko suyi tare, idan kaga haka sai dai wankan gawarta bayan mutuwarta, shima idan ansamu mai mata shikenan, amma koda wasa bata isa gifta band'akiba idan yana wanka, koda wani Abu ya manta zaice ta kawo masa, kodai tamik'a ta katanga kokuma yad'an bud'e k'ofar kad'an ya kar6a yakoma ita kuma fuskarta Na gefe gudunma karta kalleshi yace batada kunya."_ _"ldan ka ga ma'aurata na zaune a waje da daddare, kada ka dauka tsabar soyayya ce, maganin sauro suka watsa a dakin suna jira warin ya ragu, kokuma 6era yamutu sun kasa zama a d'akin ko zafine, mafi yawama zakaga tabarmar kowa daban"._ _"Yawancin mata idan ka ga sun sayawa mazajensu wani abu kyauta, toh ka tabbatar an kwantar da mazajen ne a gadon asibiti, sannan ne mai tausayi za ka ga ta sayi lemo da ayaba ta kawo masa. ldan ka ga ma'aurata suna tsere-tsere, toh ka tabbata abin tsoro suka gani kowa yana ta kansa, kokuma fad'a suke yanason dukanta ta tsere dan tsoro shikuma yabiyota yana banbamin masifar son kamata yamata hukunci. Amma ba soyayyaba"_ _"ldan ka ga ma'aurata tare sun fito da yammaci suna tafiya, ba wai shawagi suka fito ba, yawanci k'ara za su kai na wani da ya doki ɗan su, kokuma wani Abu tashin hankali ya riskesu kowanne yana gida saisu fito atare domin zuwa. a lokaci daya ne mace ke kallon idon mijinta dab da dab, lokacin da ya nemi taimakon ta don wani abu da ya faɗa cikin idanun sa kokuma ita ya fad'a mata anata idon"._ _"Idan aka yi sa'a miji ya zama mai bawa iyalin sa kulawa, sai ka ji jama'a suna cewa : Ai mijin Hajiya ne, Bawan mata, ko kuma ta gama dashi ko d'ankwali yaja hula, k'arshe ma ka ji ana kiran sa da Mijin tace"._ _"gabaki daya an dauki aure tamkar azaba, abin da ake yin sa bisa turbar soyayya da k'auna da koyi da fiyayyen halitta ANNABI MUHAMMAD S.A.W, idan zaka binciki gidan auren malam bahaushe 99 zaka samu sunbar koyarwar addini sunkoma nasu tsarin Mara 6illewa, shiyyasa kullum matan ke cutuwa da azabtuwa suna kallon gidan auren prison ma yafishi sauk'in zama, da mace tayi watanni biyu gidan miji akai rashin sa'a tasamu ciki a wannan tsakanin to tazama tsohuwa ga mijinta, komin k'ok'arin ta Na gyara masa kanta a d'age yake kallonta, yanzu idonsa yakoma kan 'yan mayan waje kuma, shiyyasa saikiga ka ajiye mace hud'u a gidanka amma idonka bai daina hange-hangen 'yan matan layinkuba, soyayyar tazama ta titice kawai saboda ana d'aukin juna. to tayaya za'a samu raguwar mace-macen aure a arewacin k'asarnan, babu abinda ADDININMU baizo mana dashiba, amma duk munzubar sai yahudawa keyi, yanzun kuma muna k'ok'arin komawa koyi dasu, shiyyasa kuma saikuga soyyayar babu wani tsarin birgewa saboda ancire muhimman abubuwan da Manzon ALLAH yakoyar damu, tunda babu kunya, babu girmama juna a soyayyar d'an boko ko kad'an, a kowane waje gaban kowa zaimata duk abinda yazo kansa koshima yamata don nuna sunason juna, sannan kowannensu yanada 'yanci babu tazarar girmama juna tsakaninsu dazai nuna shi mijine ita matace, to tayaya za'a samu yanda ake buk'ata a ganinku?"._ Suduka ukun suka girgiza kai suna fad'in "babu". Ya nisa yana binsu da kallo d'ai-d'ai, cikin tausasa harshe yace, " to ina rok'onku banason irin wannan makauniyar rayuwar,, kuzo mugudu tare mu tsira tare, Fateema kece babba, kicigaba da rik'e girmanki, idan lamarin gidana ya 6aci kezan fara zarga, haka kuma Aneesa da Khadeeja, karna sake naji wani raini yashiga takaninku da Fateema, dukda ke Aneesa kina ganin kusan shekarunku d'aya, to agidana itace babbarki koda kuwa kin girmeta, ki rik'e girmanki kema Aneesa, dan kina sama da Amatallah, idan kika ringa mata Abu marasa k'yau kece zaki zubar da kimarki a idonta, sannan kekuma Khadija ki Sani daga Fateema har Aneesa gaba dake suke, koda ban aurekiba amatsayin iyaye suke a wajenki, ki kiyayi ma wata rashin kunya a cikinsu, idan naji hakan zanyi matuk'ar 6ata rankine." Gaba d'ayansu kowacce gyad'a kanta tayi alamar amsawa. Yace, "ALLAH yay muku albarka, yakuma bamu zaman lafiya gaba d'aya". Suka amsa da amin. " yauwa sai maganar kwana, daga yau Khadija zata fara kwanakinta bakwai da shari'a ta tsara, saikuma bayan tagama acigaba da kwanakin dazaku za6a a yanzun. nabaku za6i, kwana bubbiyu ko uku-uku ko d'aid'aya? Wannene za6inku?". Duk shiru sukayi alamar tunani, Aneesa tace, "nidai anawa ra'ayin kwana d'ai-d'ai, amma idan ana ganin bibbiyun zaifi shima banda matsala, kwana uku dai yaymin nisa, bazakaga minjin kaba har kwana shida kenan, haba kudai duba lamarinnan". Murmushi kawai Uncle yayi baice komaiba, sai kallon Fateema dayayi alamar tace wani Abu itama. Murmushin mugunta tayi, itama tafison bibbiyun amma danta bak'anta ran Aneesa tace " nikuma a nawa ganin ukun zaifi, sai ka more sosai da mijinka yanda ya kamata kokuwa? amma idan an tsaya a biyun ma banida matsala nima". Wani azababben kallo Aneesa tamata, badai tace komaiba. Nanma murmushi Yayi, yakai dubansa ga Amatallah, wadda tunda aka fara maganar kanta a k'asa tana wasa da bezar gyalenta, tana jinsu sarai, amma aganinta maganar ta manyace, shiyyasa ma tayi k'asa da kanta. "Khadija kefa, bakice komaiba?". Kanta ta girgiza amalar batada abin fad'a. " miyasa? Kema matar gidance aii, kuma kinada hak'k'in fad'in ra'ayinki, fad'i kwana nawa kike buk'ata ke?". Duk da tahowar wani kuka haka ta dannesa, dan batason suga lagonta, murya a sanyaye tace, "Uncle nidai duk yanda su Aunty's suka tsaya yamin, ni dama za'a cireni a ciki nafi buk'atar hakan". A zuciyar Fateema tace gulma kenan yarinya, itako Aneesa bayan ta antayama Amatallah harara tace " munafuka". a zuciyarta. Uncle kam wani k'asaitaccen murmushi yayi yakuma gyara zamansa yace, "ai cirekinnan ba abune mai yuwuwaba Khadija. daga nan ya maida kallonsa gasu Aneesa da kowa haushi ke nuk'urk'usar ranta, yace, " Anyway duk naji za6inku, amma tunda naga kowannenku nada za6in ra'ayi d'aya way not muzauna akansa kawai, inaga kwana bibbiyun yayi OK?". Gaba d'aya sukace yayi, amma banda Amatallah da ko kallonsu takasa yi. Daga nan Nasiha yakuma musu mai ratsa jiki da 6anrgo, sannan suk rufe da addu'a ya sallamesu. Bayan sun mik'e ya kalli Amatallah daketa hanzarin fara fita yace, "Khadija!". Cak ta tsaya zuciyarta na dukan hamsin-hamsin, tajuyo da k'yar amma bata kalleahiba. Murmushi yayi yace, "a kawomin abinci inajin yunwa". Fateema harta saka k'afarta waje taji abinda yace, murmushin mugunta tayi, dan tasan Aneesa ce tayi abincin ba Amatallah ba. Itama Amatallah d'in yawu ta had'iye da k'yar sanan tace, " Uncle Anty Aneesa ce tayi girkin ai". Kallon Aneesa yayi kad'an ya kauda kai dan ganin tacika fam, "uhm koda ita tayi ai kece yadace ki bani d'in ko". Kanta ta jinjina masa kawai tafice a sanyaye. Aneesa har zatayi maganar kuma, komi ta tuna saitayi shiru ta juya tafita rai a 6ace. Wata 'Yar dariyar mugunta yayi ya gyara zamansa...............✍🏻 Mace hummm, Uncle karfa Aneesa ta 🤭babu ruwana dai, baza'aji mutuwar 'yan group d'ina a bakinaba😂😜 🏃‍♀ 🤩👎🏻 *_ALLAH ka jik'an iyayenmu_*😭🙏🏻 [1/16, 9:01 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_* *_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡 _{home of expert and perfect writer's}_ *_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉ _(Hattara matasa)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* ____________________ *_Number 27_* ____________________ Koda suka dawo massalaci Uncle 6angarensa ya koma, dama Amatallah nata addu'ar ALLAH yasa karya dawo. gadon takoma ta kwanta, tajawo filon daya d'ora kansa tana shinshinar k'amshin turarensa daya manne ajiki, tuni tana matuk'ar son k'amshinsa, dan bata mantawa lokacin tana kusan 11years sannan tazo hutu, ta ta6a cewa yabata turarensa tanason k'amshin, lokacin kam dazata tafi yabata, babanta yayta fad'a akan yazai bata turarensa mai tsada haka. Uncle yace ina ruwanka, wannan tsakanin uba da d'iyane. Dole baba yay shiru ya barta da turaren. A saninta da k'amshinnan tasansa tun fil azal, dukda takula yanad'an had'awa dawasu turaren yanzu, takuma baje hanci tana shinshinawa sosai. wani tunanine ya fad'o mata a rai, anya kuwa Aneesa zatayi break fast yau?, ganin batada Amsa ta jawo wayarta da nufin kiran Fa'iza tabata haske, dan tace mata a jiya Amaryarsu zata kar6i miji. Bugu d'aya kuwa Fa'iza ta d'aga. Da kirarin amarya kinsha k'amshi tafara mata. Amatallah tace, "kai Fa'iza banason tsokana wlhy, ni babu wata amarya anan". "Hhhh 'yammata zaki magantu, inba amaryaba miyasa kikaimin wannan kiran sassafen?". " humm bazaki ganebane kawai, nifa tambayarki zanyi?". ''To ina saurarenki". "Yanzu kenan nizanyi girki a gidan". Amatallah tafad'a kamar zatayi kuka. Sosai Fa'iza takeyin dariya, " kai Amarsu irin wannan shagwa6a haka, tuna dai banine Uncle d'inba". Amatallah tafara k'uluwa, tace, "ni inbazaki fad'a minba Na kashe wayata". " sorry amaryar Muhammad labbo" Fa'iza ta fad'a tana danne dariyarta, "yanzu dai kinga inda da had'inkai ai suyakamata sucigaba dayin abincin harki gama kwana bakwanki, amma dai nasan dakamar wahala tunda Aneesa cema mai girkin kawai, Uwargida Na fama da kanta, kawai kije kiyi, kuma wlhy ki matse basira kiyi Wanda zai tada kunnensa sama dan dad'i, kindai San d'and'anon abincin kowacce acikinsu, dan haka kema saikizo danaki salon, tunta ALLAH bai hana mijinku ajiye muku abubuwan buk'ataba dai-dai gwargwadon iko". "Hakane Fa'iza ngd sosai, bara naje nayi komai da wuri, kinsan yau dai Lectures d'inmu duk Na safene". " hakane kam, ALLAH yabada nasara". "Amin saimun had'e a school". Duk suka yanke wayar. (Kunsanfa Amatallah batasan Uncle Na azumiba). Ajiye wayar tayi tafito domin shiga kichin. Tad'an dad'e tsaye tana nazarin mizatayi, Google tashiga tayo searching break fast mai k'ayatarwa, taduba taga alhamdllh sunada mafi yawan abinda ake buk'ata, Wanda babu kuma tabarsa akan zatayi manage kawai ahaka. Dan danan gida yafara d'aukar k'amshi, abinka da kitchen a falo. Daga Aneesa har Fateema suna can sunama yaransu shirin makaranta. Cikin abinda bai wuce 1½ ba ta kammala komai, kamar yanda taga masu gidan kanyi tagyara babban falo ta jere komai a tsakkiya, takoma ta gyara kitchen d'in ta wanke abinda ta 6ata, a gaggauce takoma 6angarenta nanma ta gyara dukda bawani datti kedashiba tunda itama ba zama takeyiba. Sai lokacin ta lura da mug d'in shayi da ledan cake dana per water, kofin ta d'auka tad'an jujjuya da mamakin waye yasha tea?, itadai tasan batashaba, a fili tace, " ko yunwa ta tashi Uncle ne yasha? "Inaga hakane kam". tafad'a tana kwashewa tanufi kitchen d'inta, d'auraye kofin tayi ta maidashi mazauninsa, tadawo takarasa gyaran bedroom d'in, annan taci karo da wayoyinsa, kwashesu tayi ta zube a drowar gefen gadon, su Kansu k'amshin sukeyi, gaba d'aya k'amshinsa yakama komai nasa Na mu'amular yau da kullum. Saida ta tabbatar ta kammala komai sannan tashiga wanka. babu 6ata lokaci tafito tayi shirinta cikin zani da Riga Na atanfa green da ratsin Orange, kayan sunmata k'yau sosai, dansun haska bak'ar fatarta datasha gyara tanata walk'iya da shek'i, bawata kwalliya tayiba kamar kullum, tana cikin d'aura d'ankwali yaturo k'ofar yashigo da sallama. Ta amsa kanta ak'asa batareda ta kalleshiba, har k'asa ta tsugunna ta gaisheshi, idonsa akanta ko k'yaftawa bayayi ya amsa yana guntun murmushi, gabanta yak'araso yasa hannu biyu ya kamo kafad'unta ya mik'ar da ita, "my best! Kin iya gayu fa, koda yake agayama 'yan jos gayu, dama anan 6angaren Ku kwararrrune (sai dai k'arya inji ni......lol🤭😜) jasawa amin afuwa tsokana ce. Ita duk kunyarsa ta isheta, kanta ak'asa tana murmushi dan jin furicinsa. Ya matso da ita jikinsa ya rungumeta, a kunnenta yace, "miyasa bakizo kin shiryani ba? Ko bakiga haka matana su keyi ba?". Kunya takuma kamata, takuma lafewa sosai ajikinsa tana shak'ar daddad'an k'amshinsa, kusan mimtuna 2 ya d'agota yana fad'in " my best karki karyamun azumifa". Yanzun kam sosai ta kallesa danjin furicinsa, sanye yake cikin farar d'anyar shadda wadda tad'au aikin wuta mai masifar k'yau, yaukam babu malum-malum, rigar kuma kad'an ta wuce gwiwarsa, hularsa Brown color tamkar surfanin gaban rigar, (duk a abunda baifi 3Seconds tayi wannan kallonba.....lol😉), ta marairaice fuska a shagwa6e tace, "Uncle azumi kuma?". Gira ya d'aga mata yana murmushi kafin yace, " kin manta yau alhamis ne". Kad'an ta turo bakinta gaba Dan tuna wahalar datasha wajen had'a break fast, wlhy datasan yana azumi baza tayi mai dad'in haka ba. Hannu yasa ya d'ago ha6arta "ya dai? sarkin shagwa6a". Dariya yabata dayace sarkin shagwa6a, ta murmusa har hakwaranta Na bayyana, " Uncle banfa san kana azumiba, natashi naita wahalar had'a break fast ". " ooh my best! Sorry, kaina bisa wuya kinji, amma kiyimin irinsa a bud'a baki zanci kinji. kar6a wannan ki sakamin". ya kamo hannunta ya zuba link d'in hannu yana mik'a mata hannunsa na dama. Dukda tanajin nauyi haka takama hannun tafara k'ok'arin saka masa, danta iya, wani lokacin takan sakama babanta idan Ammi tana busy zai fita. tsaf ta saka masa har yayi mamaki. "My best dama kin iya?". Kallonsa tayi tana murmushi, " Uncle ai ina sakama baba". Shima murmushi yayi tareda kai hannu ya shafa fuskarta yana fad'in ''oo dadys girl ". Dariya duk sukayi. Yace, " k'arasa shirin muje kiyi break nima school d'inku zanje yau". "To Uncle". Fita yayi, itakuma ta k'arasa shirin nata, ta saka hijjab da takalmi tafito, duk suna falo, yara nayin break fast, gaishe da kowannensu tayi cikin girmamawa, kowacce ta amsa cikin danne kishinta, Dan tunda ta fito sukebinta da kallo kozasuga canji a tafiyarta, saidai kuma normal take tafiya babu wani alamun tangard'a. tsaf Uncle duk ya fahimcesu saboda duk yanda suke kallon Amatallah d'in akan idonsane, 6oyayyan murmushi kawai yayi, aransa yace " mikukeci nabaka Na zuba guy's ". Yaran duk suka gaidata, ta amsa cikeda kulawa kamar yanda ta saba. Itama zama tayi taci abincin kad'an, data d'ago saita kama Uncle na kallonta, daga k'arshe dai ta d'auke kanta gaba d'aya data kula duk idon matansa a kansune. Shiko gogan ko a jikinsa. Suna kammalawa suka mik'e, mai napep d'in dake kai yara school yazo, atare suka fito, yaran suka shiga napep sukuma motarsa, Amatallah ta bud'e musu gate d'in dansu Aneesa babu Wanda yamasa rakkiya (kishi ya hana ...lol😂😜). Sunama ficewa Fateema da Aneesa duk sukaja tsaki, saikuma suka kalli juna danjin tsakin nasu yafita lokaci d'aya, basarwa Fateema tayi tad'iba break fast tafara ci, Dan yanzun batada jimirin yunwa. Murmushi mugunta Aneesa tayi, a ranta tace, " muguwa kawai, a fuska tamkar ta kwarai, amma zuciyarki saidai ALLAH. a fili kam tashi tayi tashige 6angarenta. Fateema tarakata da harara😆. Uncle kam tunda suka tafi Amatallah tayi tsit, cikin raba hankalinsa biyu yafara janta da hira, yana kallon jama'ar gari da yara 'yan makaranta, saikuma tuk'i. Amatallah dai nata murmushine, wani lokacin kuma tace, ''eh ko a'a". Bai damuba dan yasan muskilancin ta, ahakanma washi anajin kunyarsa da kimarsane, amma da Jabeer yana bashi labarin yanda suke kasancewa idan zai kaita school kozai d'akkota yaci dariya. Maimakon yawuce makaranta kai tsaye saiya wuce gidansu, batayi maganaba saima dad'i taji, shi kansa yaga farin cikin a fuskarta, murmushi kawai yayi baice komaiba. Cikin zumud'i tawuceshi ta fara shiga gidan. Da shehu tafara cin karo yana alwala a tsakar gida, da alama sai yanzu zaiyi sallar asuba. Cikin tsokana tace, "su Ya Shehu dai baza'a canjaba, k'ara'i dai kullum". Dariya yayi yana mik'ewa, " kece da farar safiya haka Antynmu?....." Bai k'arasaba Uncle shigo, hakan kuma yayi dai-dai da fitowar Nazeefa itama daga kitchen saboda muryar Amatallah data jiyo, rungume juna sukayi suna murna, yayinda shikuma Uncle kema Shehu fad'an k'inyin salla da wuri, harma 8 ta wuce yau. Tare suka shiga d'akin baba, innani ma nacan, sun taddashi zaune innani na bashi kunu, aladabce suka gaidasu da tambayar jikin baba. Baba Yaji dad'in ganinsu a tare kuwa, hakama Innani dukda bata nuna a fuskaba. Baba yace, "Muhammadu idan kadawo aiki inason ganinka". a hankali yake maganar. ''To baba, insha ALLAH dana taso zanzo". Basu dad'eba sosai suka musu sallama suka fito. bayan sun gaisa da Jabeer shima, Dan sanda suka zo yana wankane. Sun tafi da alk'awarin Nazeefa na zuwa weekend d'inan. Yauma ta iske su Rita na jiranta, Dan harma F'aiza tarigata zuwa, ta k'arasa tana tsokanar Fa'iza da wak'ar mai ciki eye ganinan tafe. Duk dariya sukayi, Fa'iza tace, " haba yarinya kema kwana nawane". Hararta Amatallah tayi, tace, "fatan tsiya". Goodness tace, " na arzik'i dai". Dariya duk suka kumayi. Kusan 12 Lecturer d'insu na English bai shigoba, dukma sun fidda rai da zuwansa, wasuma suna k'ok'arin barin hall d'in sai suka hango wani malami na tahowa. Gabatowarsa ta saka wani d'alibi fad'in "kuttt wlhy kowa ya nutsu boss ne da kansa zai mana lecture yau......" Bai gama rufe bakiba Uncle yashigo, mamaki sosai Yakama Amatallah, dama Uncle yanada alak'a da school d'innan har haka? Tasan dai kamar yana aiki anan, amma bata d'auka yana Lectures ba. Mamakinsa yakuma kamata, yayi masifar tsare gida alamun babu wasa kenan, ta tuna Uncle mai yawan fara'a ashe haka yake a waje. Sai dai yanda 'yan class d'in suka nutsu abin yaso bata dariya, musamman idan tayi dubi da yanda aka raina wasu lecturers d'in, bakamar wasu group na samari da 'yammata da ake kira *Gayun zamani* kallonta takai mazauninsu tagansu a nutse kamar basuba. Kallonta ta maida ga Uncle d'in dake magana cikin nutsuwa dakuma kwararren Turanci. Yana bayanine akan zai d'aukesu lecture d'in saboda lecturer mai d'aukarsu yasamu Accident a daren jiya. Nan suka shiga mishi addu'a. Tunda yashigo yaga Amatallah, amma yashare tamkarma baisan da ita a hall d'in ba, saidai tuni Fa'iza dasu Rita suka ga kallon dayake satarta dashi, hakanne yasasu shan jinin jikinsu kodai shine Uncle? dukda Amatallah bata sanar dasu Uncle na aiki ananba. Harya gama lecture d'in yafita sannan suka samu damar tanbayarta, dariya kawai tayi batace komaiba, yayinda Rabin hankalinta ke kan 'yan class d'in dake gulmar Uncle, wani d'alibi harda mik'ewa yaje inda lecturers kan tsaya idan zasuyi lecture ya kwaikwayi salon Uncle d'in, nanfa aka kwashe da dariya, d'alibin yace, "please guys bai burge kuba?". Nanma suka amsa da sosaima ana dariya, wata ma a 'yan matan ta mik'e tana fad'in " aini babu abinda yafi d'aukar hankalina gareshi sai salon maganarsa mai sanyi da takunsa, kai jama'a malamin nan yayi over, inama zan dace da na tsinci tsuntsu daga sama". Nanma dariyar aka Sanya da sakin ihu. Ta kuma kwaikwayon muryarsa yanda yafad'i sunansa, my Name is Muhammad Ahmad labbo, nine zan cigaba da jagirantarku kafin mai d'aukarku yasamu sauk'i....... Salon nata yasakasu kwashewa da dariyar ihu suna kiran saikinyi zee-zee. Ta shafi inda ya d'ora hannunsa ta sumbaci hannunta da fad'in "I love you so much Muhammad mai babban suna". Nanma dai bata sake zaninba ihu sukayi. Dukda wannan Abu dake faruwa Amatallah tayi kicin-kicin da fuska ko sau d'aya batayi dariyaba tunda budurwarnan tafara kwaikwayon Uncle....... Maganar zee takuma katse mata tunaninta, " kai my guys, ammafa bawan ALLAH nan akwai tsare gida, ya matarsa keyi?". Wani yay caraf yace "zee-zee dakin Shiga daga ciki zaki canja manashi". Dariya ta tuntsure dashi, sannan ta rungume hannunta ak'irji tana lumshe ido, " wayyo! ALLAH Da nikam nasamu duniya, saidai kumin addu'ar samun lahira kuma, wlhy da gaske yasace zuciyata sonsa nak......... Amatallah bataji k'arshen zancenba tatashi tafice saboda wani masifar tsanar zee daya turnik'eta, harma da sauran 'yan ajin dake tayata da ihu. Rita dasu Fa'iza suka take mata baya da sauri suna kiran sunanta. Baki zee ta ta6e tana rakasu da harara, kafin ta kalli 'yan ajin tace "tofa kunga wani Sabon salo, ko wata ke sonsa a cikinsu? Tab wlhy Ashe da anyi yak'i a bayaro". Sosai yanzu ihunsu yafi na d'azun, wasu dasuma abinda zee take bai birgesuba suka fara ficewa, wasu kam suma abinda kedamun zee shike damunsu wato son Uncle d'in (basusan tsoho bane......lol😉😜). Da k'yar su Fa'iza suka lallashi Amatallah dake kuka, goodness tace, "ai hankali aka kiya miki, saiki tashi dan kamo mijinki, wazai kallesa yace matansa Uku bare yayi tunanin yakai shekarun dakika fad'a mana, wlhy sisi kardai kiyi sake..... Sosai suka mata fad'a, bakamarma Fa'iza dakejin tamkar ta mangareta. Koda aka tashi lecture d'in k'arshe wajen 2:30 bata nemesaba, dukda kuma yace idan tagama ta kirashi, tafiyarta tayi bayan tasha gargad'i wajen Fa'iza akan kartaje tamasa shirme tunda bashine yace zee tasoshiba, kuma tabata shawara akan abin sharruwa daya kamata ta had'a masa. Tadai tafi tana zun6ure-zum6ure. (Ama...kishi lol😆) _________ Uncle kam baisan wainar da'ake toyawabama shi, saidai idan yatuno yanda Amatallah ke satar kallonsa a aji yakanyi murmushi. Yasamu ganawa da dukkan lecturers d'in, Yakuma kawo musu kudirinsa na kafa k'ungiyar matasa dakuma zawarcin abokan tafiya. Wasu sun bada had'inkai, wasukam sunata 'yan kame-kame saboda sunji maganar hardata kud'i, duk Uncle ya lura dasu. Ya tausasa harsher yana fad'in " karfa hakan ya dameku, bawai tilasne saika zuba kud'inkaba, inhar zuciyarka atsarkake take da nufin son a gyara tafiyar matasan zaka iya bada gudun mawarka, Dama munsaka maganar kud'inne saboda tallafama Matasan dabasu sami koda karatun secondary d'inba, sai Mike ganin Sana'a yafi dacewa su a tallafesu da ita, saikuma wad'anda karatun Nasu ya tsaya iya secondary d'in, sunada buk'ar mu taimakesu domin cigaban karatunsu, saboda wasu sun cancanta amma rashin tallafi yasakasu maida takardunsu kasan jakka sukoma maula ko dabar siyasa ko shaye-shaye, akwai kuma Matasan dasun kammala karatun amma babu aikinyi, bazai yuwu kowanne saiyazama ma'aikacin Gwamnati ba, Dan bazata iya d'aukar kowa aikiba, to kunga saimu tallafa musu da sana'oin hannu dazai rik'e rayuwarsu kodan rage musu rad'ad'i wajen tunzuruwarsu ga aikata ta'addanci, mukuma cire musu ak'idar nayi karatu dolene Nina naga kaina a office. Wad'annan hanyoyin zasu rage ma matasanmu yawan Shiga TARKUNAN 'yan siyasarmu masu gur6ata tunaninsu da kud'i harsuna haddasa mana rikicin *SIYASA KO K'ABILANCI*, kudancinmu sunrigada sunyi nisa a irin wannan taimakon, zakiga mutum d'aya ya d'auki nauyin yara goma karatu, koma fiye dahaka, babu kuma abinda suka had'a, kawai k'auyensu d'ayane. Amma mufa 'yan arewa duk iri-iren wad'annan abubuwan bamayi, kullum burinmu mu Gina k'aton gida, musa tsala-tsalan mata da ma'aikata masu yimusu hidima, saika samu harabar gidan mutum d'aya da mota goma, har yaran gidan k'anana sunada motarsu da ake kaisu yawo, amma gawasu suna cikin wahalar rayuwa bama tausayinsu, idan munga idonsu ko kud'insu sai sun tsaya takarar kansila ko ciyaman ko d'an majalisa ko gwamnan jaha, to sannanne zasuna mana 6arin kud'i kamar basusan ciwonsuba, a wayonsu idan sun hau kujerar mulki sunsan zasu maida fiye da abinda suka watsa mana". "Mun manta damaganar alk'awuran aiki dasukai masa, wannan tunanin namune ya Karya arewacinmu, akowane lamari mune koma baya, yanzu damuna taimakon matasanmu wasu azzalumai sun isa su sami damar haddasa mana tantin ta'addaci a yankinmu? Bakwajin ciwon yanda ake kashe mana matasa ana kama wasu acikinsu ana jinginasu da ta'addancin? Idan kana ganin babu d'anka aciki ko k'aninka, baka tunanin ta6ar6arewar komai har 'ya'yan naka su taso suma sugaza amfana da komai na k'asarsu? Shin bakwa tunanin ba ayanzun matsalar takeba sai zuwa nangaba mun rasa jagororin tallafin arewacinmu, sufa matasannan damuke zuba ido wajen kallon lalacewarsu koma jagorancin lalacewar tasu watarana sune zasu zamto rik'e da k'asar. Shin mikuke tunani akansu idan k'asar tazama a hannunsu? Kuna ganin 'ya'yanmu k'anana zasu shane? Kokuwa yankinmu damu kanmu zamusha? Kufayi tunani akan wannan lamarin, dan duk d'inmu iyayene, kuma yayyane, musan zafin damukeji yayinda mukaga d'aya acikin zuri'armu kangararre, shin bakwa tunanin ya sauran iyaye sukeji suma?. Akiraka mai kud'ine abin birgewa kokuwa ALLAH ya aminta da k'yawawan aiyukanka? Wannene za6inku?!!!". Duk shiru sukayi tamkar ruwa yacisu, saikuma jikkunansu sukayi sanyi da dukkan furicinsa, sunsan tabbas gaskiya yake fad'a, nanfa k'ananun maganganu suka fara tashi k'asa-k'asa. Cikin fusatar 6acin rai Uncle yakwashi takardunsa yafice daga d'akin taron, duk kiran da Alhaji Sabi'u da shugaban makarantar kemasa bai ko waigosuba. Ajiyar zuciya Alhaji sabi'u ya sauke, ya kallesu da kulawa "kuyi hak'uri ransa yarigada ya 6aci sosai, Alhaji Muhammad labbo mutumne mai kishin k'asarsa da yankinsa, mai irin tunaninsane kawai zai fahimci zafi ko bak'incikin dayakeji akan ta6ar6arewar Arewacinmu. Ga form nan duk mai son kasancewa a tafiyar tamu saiya samu shugaban makaranta ya yanka ya cike, naira dubu d'yane kacal, bayan mun mammala samun abokan tafiya kuma saimu fuskanci tsare-tsare nagaba, Dan abin yazo mana a kure, za6e yagabato, somuke kuma mu nunama 'yan siyasar k'asarnan matasanmu sune *KASARMU* dolene kuma a dama dasu tako wane fanni." Daga haka shima yamusu sallama yafice, yarage dagasu saisu. Nan dai sukaita tattauna lamarin, wad'anda sukayi na'am atake suka yanki form d'in. Wasu kuma dai basuce komaiba a kan lamarin.............✍🏻 _bara nabi Amarku sarkin kishi🚪🚶🏻‍♀_. 🤩👎🏻 One Luv my sweet fans🥰 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [1/16, 9:01 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_* *_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡 _{home of expert and perfect writer's}_ *_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉ _(Hattara matasa)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* _Gundumemiyar gaisuwa gareku da fatan alkairi *Hafsat Rano, Ummu Hanan (mamana) Mzzdaddy, Maryam wasagu, Aysha Manshat, Maman Shaheed, Ummu Affan (mamana) Bily s fari* na gaisheku nakuma Na gaisheku, inayinku over, ALLAH ya k'ara basira agareku writer's d'inmu🥰🥰🥰👍🏻😘_ ____________________ *_Number 28_* ____________________ Tana cikin Napep kiran Fa'iza yakuma shigowa, d'agawa tayi batareda tayi maganaba. Fa'iza tace, "wlhy Amatullah ina mai baki shawarar karkije gida kina kuka ko fushi, ki saki fuskarki, dama wai haka kike da kishi kema?". " bazaku ganeba Fa'iza, nifa ba kishi baneba". "Oooh to miye?". " humm, mubar maganar kawai". "Shikenan an barta, kiduba Na tura miki wani Abu, amma Dan ALLAH inamai rok'onki ko'a fuska karki bari mijinki da abokan zamanki suga fushi a fuskarki, sannan kinutsu sosai wajen shirya masa abincin shan ruwa, kikuma tanadi kalaman kare kanki a wajensa idan ya tambayeki dalilinki Na tahowa Baku nemesaba". Kitt Fa'iza ta yanke wayar batareda tajira mi Amatallah zata fad'aba. Ajiyar zuya Amatallah ta sauke, ga wata k'aunar Fa'iza nashiga harcan k'asan ranta, tabbas k'awa tagari rahamace ga kowanne bawa, shigowar Fa'iza rayuwarta ALLAH ne kad'ai yasan nasarorin data kawo mata, takanji tamkar ciki d'aya suka fito da Fa'iza. Addu'a taitayi a zuciyarta hartaji abinda ya rik'e mata mak'oshinan ya koma, har sukaje k'ofar gida tana sakin ajiyar zuciya akai-akai, shidai mai napep yanata aikin tuk'insa da saurarenta, ALLAH ma ya taimaketa ba irin masu shegen surutunnan baneba da shiga abinda ba huruminsuba. Kud'insa ta basa kafin ta shige ciki. Babu kowa a falon, sai dai yanata k'amshi mai dad'i. Harga ALLAH bazata 6oyeba tsaftar matan gidan Na birgeta, koyayane bazaka tadda falon a cikin dattiba, shirun gidan ya tabbatar mata yara sun tafi Islamiyya. Bata shiga d'akiba, saita lek'a kitchen, dan tanata tunanin komi yara zasuci idan sun dawo? batayi zaton wani acikinsu zaimata girkin daya zama wajibi akantaba. Sai dai tashiga mamaki yayinda taci karo da kular abinci dakuma fleets alamun anci abinci, tabud'e kular (jallop d'in shinkafa Ce) maidawa tayi ta rufe tana mamakin waye yayi girkin to acikinsu? Koda wasa tamasan ba Aneesa bace. Kasa hak'uri tayi dai, tashiga 6angarenta a gaggauce tayi wanka tai sallar la'asar data risketa a hanya, bak'ar doguwar riga jallabiya tasaka, hula tasa a maimakon d'ankwalin tanufi 6angaren Fateema dannan tafi zaton an taimaketa. A falo ta isketa tanashan fanka, a girmame ta gaisheta, itakuma ta amsa cikin fara'a da k'ok'arin danne kishinta. "Anty Fatee ngd sosai, nabarki da wahalar girki". Fateema ta kalleta tana d'an murmushi, " ayya Amatallah momyn yarace tayi banibama wlhy, taga har yara sunkusa dawowa baki dawo bane". Mamaki ya kama Amatallah, shiyyasa akeson ka k'yautata zato wa d'an uwanka, duk mugun halin mutun tawani 6angaren sai kaga mutumin kirkine, tabbas ita kanta tasani, inhar tacire maganar kishin tsiya Na Aneesa batada wata hujjar zaginta akan mugun hali. fita tayi tanamai jin nauyin zargin datama Aneesa. 6angarenta tashiga a sanyaye, a falon sai Siddiqa fake wasa kawai, tana ganinta tataho da gudu tana gwarancin su Na yara, Dan maganar tata babu dad'i sosai har yanzun, sama Amatallah ta d'agata tana cafewa suna dariya. Ahaka Aneesa tafito daga bedroom ta samesu, (duk mai son d'anka dolene duk zafinsa dakakeji kaji sassauci), Dan haka Aneesa ta kallesu da murmushi a saman fuskarta, zama tayi abinta batareda ta tankaba. Amatallah ta sauke Siddiqa a cinyarta bayan ta zauna, gaisheda Aneesa tayi a girmame kafin tace, "Anty ngd fa da girki, nabarki da wahala ALLAH ya raya su Siddiqa". Murmushi Aneesa tayi, " karki damu da wannan, taimakon juna tilasne agaremu komin kishin damukeji akan juna, kishi daban k'yautatawa daban". "Gaskiyane Anty ngd". daga haka tataso tafito rik'eda Siddiqa. Zamanta tayi a falonta bayan tazubo abinci, tanaci tanabama Siddiqa harsuka gama, daga nan taita biyema yarinyar suna shirme.. A wannan lokacinne kuma Uncle yashigo gidan, bai wani yimusu horn ba yafito dakansa yabud'e gate yashigo, wannan yasa babu wadda tajishi dukda kuma bama wutace ke akwaiba bare ace k'arar TV ta hana. hankalin sune kawai bai jeba, Aneesa ma waya takeyi da mutanen Ghana tun fitar Amatallah. Fateema kuwa tanashan fankarta da ta samu isashshen charge tana karatun addu'in 40rabbana. Itakuma Amatallah shirmensu da Siddiqa ya d'auke hankalinta gaba d'aya, tanason yara kodan tasowa datayi ita d'aya kwallin kwal agidansu, koda suna jos haka zatayita jajubo 'ya'yan jama'a Na makwafta, wani lokacin Ammi taita fad'a tamkar ta ari baki, sai dai Amatallah tabata hak'uri, ammafa gobe babu fashi saikin ganta dad'an wani ta yayibo. Harya shigo falon babu wadda ta fito, shi mamakinema ya kamashi, wai duk matannan biyu babu wacce tasan da shigowarsa, (zatonsa Amatallah bata dawo school ba, shi saima yanzu yatuna ko tanacanma tana nemansa gashi yataho), Ramsa a 6ace yake shiyyasa yay shigewarsa samansa batareda yanemi kowacceba barema Amatallah daya bari a makaranta. Ruwa kawai ya watsa ya saka k'ananun kaya wando dogo da k'aramar Riga, falonsa yadawo yad'an kwanta adoguwar kujera ya lumshe idanu badan barciba saidan son dai yasamu damar yin tunanin halayen mutanenmu masu ban haushi darashin Sanin darajar Kansu da mutuncin yankinsu. Ya jima a kwance yana tunani batareda yasan lokaci yajaba, hardai yafara jiyo hayaniyar yara sun dawo islamiyya. A 6angaren su Amatallah da gaske babu wacce ALLAH yabata ikon sanin shigowar mai gidan, kusan 5:00pm Amatallah tashiga kitchen, lokacin Siddiaq tayi barci ta goyata. Da abincin gida ta fara, tuwon semo.... Miyar Ogbono tayi, Dan komai Na kalolin miya daba'a amfani dasu anan Kano saida Anty furera ta tanadar matashi, musamman miyoyin k'abilunnan da Amatallah duk ta iya mafi yawa aciki, Dan Ammi batayi wasa wajen tsayawa koyama Amatallah kalolin abinciba da aikin gida, wannan yasa batada Matsala akan kowanne fanni Na girki dakuma kulada muhalli (kamar Ammi tasan k'addarar d'iyar tata zama cikin kishiyoyi). Batawani jimaba ta mammala had'a miyarta, sannan ta d'ora tuwo dakuma wani 6angare Na kayan shan ruwan Uncle. Dan danan k'amshi yafara baje gida (had INA had'iyar yawu Nima mai rahoto....lol😋😜) tsaf tagama komai ta kimtsa kitchen d'in, tana mopping yara suka dawo daga islamiyya. Jin suna Neman Abbunsu yasata fitowa daga kitchen d'in, Dan duk iyayensu Na d'akunansu. hayaniyar yarance ma ta fiddo Aneesa. Kusan tare suka fito da Amatallah. Tuni yaran sun arta sama aguje, sunsan Abbunsu yana gida tunda ga motarsa a waje. Aneesa da Amatallah suka kalli juna, Aneesa tace, "dama ya dawo?". Har Amatallah zatace da bata saniba, saikuma taga ai abin kunyanema ita mai girki bata san miji yadawo ba, kuma alamar yaran ta nuna tabbas Abbunsu yadawo d'in. " eh Anty yadawo babu jimawa sosai, yad'an kwantane ya huta". "To, ALLAH yasa lafiya dai, Dan dear baya barcin yamma gaskiya". Cikin son kare kai Amatallah tace, " kansa ke ciwo". ''Ayya shiyyasa, ALLAH yakawo sauk'i. Wai yanzunan k'atuwarnan kika goya haka? bak'ya gudun ciwon k'irji?". Murmushi Amatallah tayi, tagyara zaninta data Goya siddiqa dashi daga sama tana fad'in "lah Anty aibatada nauyi". " lallai kam, sannu da k'ok'ari, aini bama zan iya aiki da yaro a bayaba, Umman yaracema da wannan k'ok'arin". Murmushi kawai Amatallah tayi batace komaiba. Aneesa ma tajuya d'aki abinta. Amatallah kam tsaye tayi tana kallon matattakalar benan, kodai Uncle fushi yakeyi da ita danta taho?. Jitai kwalla tacika idonta, jiki a sanyaye tanufi saman, takula gabma ake da shan ruwa. Baya takoma tad'ibo dabino awani d'an kwano, tad'ora a tire da ruwa da cup, hakan duk yana cikin aikin fa'iza data koyar da ita, da kuma training d'in Ammi dabazata ta6a mantawaba, (kunsanfa duk abinda katashi kaga anayi agidanku mawuyacine kiga kaima Baka aikatashi a gidan mijiba, iyaye saiku kula wlhy saboda 'ya'yanmu masu tasowa).😊👍🏻. A falo ta iskesu shida yaransa, duk suna a jikinsa kowa nabada labarin abinda aka koya musu, sallamarta tasakashi d'ago idanunsa ya kalleta. Koda suka had'a ido saita sakar masa murmushi, hakanne ya sanyaya zuciyarsa daga haushinsu dayakeji. "Sannu da zuwa Uncle". tafad'a murya k'asa-k'asa. Dukda surutun yaran hankalinsa Na kanta, kuma yaji mita fad'a. ya d'auke idonsa akanta yamaida kan Abulkhairi, "Abulkhairi kuje maza a canja Uniform ayi alwala nima ganinan sakkowa mutafi masallaci kunji". Atare suka mik'e suna fad'in to Abbbunmu. Daga shi har Amatallah da kallo suka raka yaran, kowa Na murmushi. Ya maido kallonsa kanta, " my best kinyi k'yau da goyon kuwa". Murmushi tayi kanta a k'asa tace, "ngd Uncle, kadawo lafiya". Still murmushi shima yayi, ya kwantar da kansa jikin kujerar yana kallonta, " ba godiya zakiminba tunda ba k'yautar Siddiqar nabakiba, kawai kema kidage ki haifomin naki". taji kunyar maganarsa, Dan haka ta kauda kanta gefe tana murmushi. Yasa hannu yakamo nata, cikin zolaya yace, ''kokuwa yau zamu samune ma kawai nayi shiri?". Batasan sanda ta dubeshiba tana zaro ido waje, shima yayi yanda tayi, sai suka tuntsure da dariya kuma. Tace, "kai Uncle". Yace, "ALLAH my heartbeat ". Murmushi kawai tayi, shikuma yashafi kumatunta, "Matsoraciya wasa nakeyi, sorry nataho Na barki a school ban nemekiba, 6atamin rai akayine". 'Dan kallonsa tayi da mamaki, har zatayi magana saikuma tayi shiru, gwarama kawai tabarsa a yarigata tahowar. "Fad'i mana". Yayi maganar idonsa akanta. " a Uncle babu komai, gashi can ana kiran salla". "Alhmdllh" yafad'a tareda mik'ewa yashiga bedroom d'insa, babu dad'ewa yafito, da alama alwala yayo da brosh. Zama yayi inda ya tashi, yaci dabino uku yasha ruwa kafin yamik'e yana shafar gefen kumatun Amatallah, "bara naje masallaci babyna". "Adawo lafiya" Amatallah tafad'a a kunyace". Itama sakkowa tayi danyin sallar, ta sauke Siddiqa agadonta tashiga bayi. Su Uncle basu dawoba saida akayi isha'i, zuwa sannan tad'an gyara fuskarta da hoda da kwalli da d'an janbaki kamar yanda Anty maijidda da Nazeefa suka gargad'eta akan bakoda yaushe ake zuwa wajen miji fuska a kod'eba. Ranar dai Uncle yaci girkin Amatallah yana mata Santi, itako sai dad'i takeji tana dariya, daga Fateema har Aneesa babu Wanda ya tanka, yara kuwa suna taya Abbunsune. Yauma a d'akinta ya kwana, tasha kunya kamar jiya, koma nace fiye da jiya, Dan yaukam Uncle kasa barinta yayi harda 'yan wasanni, Wanda ganin ta tsorata yak'yaleta daga baya sukasha barcinsu, dukda yarigata barci ita tsorone ya yanata saida taji yayi. *_5days ogo_*. Kwanakin Amatallah 6 kenan da kar6ar miji, a kwana shidannan ba'a maganar shak'uwarsu, dan koyaya dai tasaki jiki dashi, dama kuma hakan shine fatan Uncle d'in. gashi kuma gobe Fateema uwargida zata kar6eshi ko Aneesa, duk kuma sai Amatallah taji babu dad'i, koba komai tasaba da kwanciyar dasukeyi tare a gado d'aya. Da daddare suna kwance, barci sukeyi hankali kwance, Amatallah Na jikin Uncle ta dabaibayeshi kamar zata shige jikinsa. bugun k'ofane ya farkar da Uncle, ga Amatallah kam hakan bamai sauk'i baneba, saboda shegen nauyin barcinta. Da k'yar yazame Amatallah a jikinsa yatashi gabansa na fad'uwa, tabbas yasan babu lafiya, yakumafi kawo hakan ga Fateema. Ilai kuwa yana bud'ewa yaci karo da Aneesa wadda take a rikice, sai yarfa hannaye take tana safa da marwa. Yana bud'e k'ofar tayo kansa, " dear Umman yarace babu lafiya, ina k'yautata zaton ko nak'uda wlhy......" Abinda yafaru shine tun farkon dare bayan Uncle yashiga sunyi sallama takejin babu dad'i dajin alamomin ciwo, amma harya fita bata iya fad'a masaba dankarya tashi hankalinta, saima ALLAH yakawo barci ya figeta da wuri, acikin barci ta farka da matsanancin ciwo, cikin azaba ta d'akko wayarta da nufin kiransa, saidai takira har sau biyu bai d'aukaba, hakanne yasata maida akalar kiran ga Aneesa. Arikice Aneesa tashigo wajenta, ganin nak'udace ta d'auke yaran d'ai-d'ai tamaida 6angarenta, shine taje ta tado Uncle bayan itama takirasa bai d'agaba. Shikuma ya danne wayarne da filo harta shiga silent bai saniba, wannan ne yasa bai d'aga kiransuba. Har rige-rigen shiga 6angaren Fateema sukeyi itadashi, zuwa sannan kuma Fateema nak'uda gadan-gadan. Aneesa tace dear mutafi asibiti mana". "Neesa kalli agogofa, 2:41am akwai had'ari gaskiya, mudai bata taimako muga ko ALLAH zaisa mudace ta haihu lafiya". Aneesa tayi na'am da hakan, addu'a Uncle yafara tofama Fateema a ruwa, hannunsa rik'eda d'ankwalinta yana share mata gumi. Aneesa kuma Na taimaka mata dawasu dabarun... A wannan time d'inne kuma Amatallah tafarka arikice saboda mafarkin Anty Fateema datayi tana kuka, ta laluba babu Uncle, ai babu shiri ta wantsalo daga gadon, hijjabi kawai ta d'ora a saman kayan barci ta tafito, tundaga falo tafara jiyo nishin Fatima da maganar Aneesa tana fad'in daure Umman yara, insha ALLAH kin kusa. Wani nishi da Fateeman tasaki yasaka Amatallah fashewa da kuka saboda tausayi, saikuma tad'an tsagaita taji kukan jariri ko murnarsu Uncle d'in da haihuwar amma saitaji tsitt, saima gauron numfashi da Uncle yasaki tareda fad'in "Fateema!!"...............✍🏻 🙆🏻mun shiga d'ari, kardai Uwargida.....🤭ba ruwana😓. 🤩👎🏻 One luv my Sweet fana🥰 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻 [1/16, 9:01 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_* *_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡 _{home of expert and perfect writer's}_ *_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉ _(Hattara matasa)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* ____________________ *_Number 29_* ____________________ "A'a dear karka damu tana numfashi, nakula tagajine kawai...... Aneesa batakai k'arshen zancenba Fateema takuma yin wani nishin mai k'arfi saiga jaririya ak'asa tana watsal-watsal, atare suka furta Alhmdllh. Amatallah ma ajiyar zuciya ta sauke, tana dariya tana kuka, Uncle yafito d'aura ruwa da Aneesa ta buk'ata ya ganta tsaye ta jingina da Bango idonta arufe, ganin tana kuka da dariya saita bashi tausayi, yajawo hannunta ya rungumeta yana fad'in ''to kukan ya Isa haka ALLAH ya sauketa lafiya, yaushema kika tashi?". Tana share hawayenta tace, " Uncle tun d'azunne". "To shiga ki taimakawa Aneesa Ku gyarata bara Na d'ora ruwan zafi". " to Uncle ". Tsaf Aneesa da Amatallah sukaita hidimar taimakon Fateema, Aneeaa taima jinjira wanka, Amatallah ta gyara wajen, yayinda Uncle ya taimakawa matarsa shikuma, kafin Safiya komai yayi tsaf, tasha tea ta kwanta itada sargad'ed'iyar jaririya dansu huta. ALLAH ma ya taimaki Amatallah lecture biyune da ita suma duk Na yammane. Da safema bayan sunyi sallar Asuba basu hutaba, saida sukaga yara suntafi makaranta, Uncle kam yana d'akinsa yanata barci tunda suka dawo salla. Ai yara Na tafiya daga Amatallah har Aneesa kowacce takoma gado, dama yara tea and bread suka basu Dan Neman sauk'i. Gidan yayi tsit, mai jegoma barci ta takeyi Na ramuwar kusan kwanaki, Dan tunda suka dawo bazatace ga randa tasamu isashen barciba, kullum rabi da rabine, itadama tafiya nak'udar tsaye, shiyyasa haihuwar takanzo mata da sauk'i kuma randa tatashi. Sai kusan 9 Uncle yafara tashi, shima yau dai kasuwa dama kawai zaije. Yasha mamakin jin gidan tsit, Fateema yafara lek'awa yaga har lokacin barci take daga ita har jinjirar, ya lek'a Aneesa itama, tayi d'ai-d'ai abinta a gado, ta danne Siddiqa da k'afa d'aya alamar k'ila barcin taso hanata shiyyasa tamata haka. Murmushi yayi yafito zuwa d'akin Amatallah, nanma abin yabashi dariya yanda tabaje abinta tana shak'ar barci, kansa ya girgiza kawai. Aransa yace lallai su mata anji jiki yau.😂 Kitchen yashiga abinsa, ya had'a tea da soya kwai uku yad'auki bread yafito, shikam da yunwa yatashi yau, kodan jiya dayasha ruwa bai wani ci abin kirkiba saboda zuwan alhaji sabi'u gidan, bayan tafiyarsa kuma barci ya takurashi dole ya kwanta batareda ya nemi abincinba. Dole yatashi da yunwa kuwa, ga matan nasa yau kowacce taji jiki wajen kar6ar hauhuwa. A falon k'asa yazauna yayi break fast d'insa, kafin yatashi zuwa d'akin Amatallah, har yanzu barci ta takeyi, waya yad'akko yafito babban falo. Baban Fateema yakira kawu yakubu, ya gaidashi a ladabce kafin ya Sanar mass ansami k'aruwa, kawu yakubu yamasa barka da addu'a ga jaririya kafin suzo. Daganan Anty maijidda yakira itama, saikuma Nazeefa Dan bazai iya fad'ama Innani ba, baba kuma bayama iya waya sosai saboda ba'ajin maganarsa da k'yau. Dan danan dangi aka rud'e da farin ciki. Sai wajen 10 daga Aneesa har Amatallah suka tashi, hakama mai jegon kanta, shima hayaniyar su Nazeefa ne ya tadasu, dan danan gida ya kacame da surutu saboda dangi dasuka fara cikashi. Dole Uncle yay shiri yabar musu gidan zuwa kasuwa. Can d'inma manyan kasuwar yasamu suka zauna meeting akan kafa k'ungiyar matasa, dolene kowanne abun alkairi akwai k'alubale acikinsa, a tashin farko Uncle baisamu had'in kan wasunsuba, dukda dogon bayani Na gamsarwa dayay musu, wasuma saisuka fara d'auka Siyasa yakeson shiga kawai, dukda ransa ya6aci haka ya danne, yasamu mutane hud'u kacal acikinsu dasuka aminta da tafiyar tasu, hakanne kuma yad'an rage masa 6acin ransa. Bayan sun kammala yakira Alhaji Sabi'u ya labarta masa yanda sukayi. Hamdala Alhaji sabi'u yayi, yace, "to inaga zuwa yanzun saimu zauna kuma mu tattauna kafin tsare-tsare su biyo baya, yanzu dai munada manyan mutane kusan 10 kenan, kuma kowannenmu babu matsalar rayuwa dazata takurasa yakasa fidda d'an wani Abu Na taimako koda 5k ne kacal aduk wata". " wannan gaskiyane". "Yawwa to saimu zauna kenan a tattauna, insha ALLAH zan shigo wajjen naka zuwa dare nayi barka, daganan saimu tattauna". " babu damuwa Alhaji ngd sosai, saikazo". Daga haka suka yanke wayar. Badan Amatallah tasoba taje makaranta, tasha tsokana wajen su Fa'iza kuwa wai itama insha ALLAH bad'i iyanzu itace zata haihu musu, ai ko ranarma dai zee tasha harara kamar kullum da Amatallah kemata (itako zee batama San Amatallah tana yiba ma😜.) Bayan antashi suka ajiye magana akan ranar asabar zasuzo musu barka, dan gobe Friday basuda lectures ma ko d'aya. ____________________ Washe gari kuma Aneesa ta kar6i girki, Amatallah tashan kallo, kai kace Aneesa zata canja gidanne, saboda shirye-shiryen kar6ar boss. Washe garima Aneesa Nata rawar k'afa, ko kunyar 'yan barka bataji ma, saima shi Uncle d'in take bari da kunyar. Su Fa'iza dasukazo barka sukace kinga yanda ake tattalin miji aii, wlhy kimik'e idanma zaki mik'e, yanzu dai mijin nakune Ku biyu, tunda Uwargida tana jego, nanfa suka shiga fanfata da koya mata abubuwa, su goodness masu ido bud'e kam ai salon yanda ake soyayya iri-iri suka shiga koya mata, Fa'iza tasaki baki tana sauraren ikon ALLAH itada Amatallah, duk da tarigaya tasan yan dama rayuwar k'abilunnan take, baruwansu iyashegensu sukeyi tun suna a waje, saikagama yarinya tabaro k'auyensu tazo takama d'aki a binni wai tazo neman kud'i, kuma bazata ta6a amsa sunan ita karuwa baceba (ALLAH ya k'yauta dai), Fa'iza kam girman Kano Ce, bakomai tasani gameda suba sosai. Haka dai sukasha hirarsu suka tafi. Bayan Aneesa tagama kwanakinta Uncle yadawo hannun Amatallah, tabbas yaga canji a wannan karon, danta rage tsorata idan ya ta6ata, kuma tasaki jiki dashi babu laifi, dukda haka kuma bai nemi komai gareta ba ya had'iye kwad'ayinsa Dan bata lokaci, Duk da kuma acikin muguwar zak'uwa yake da son kasancewa da ita d'in, hakanne yasaka Ama... Sakin jiki dashi sosai, aganinta yabarta bayanzuba, k'ilama saita kammala karatunta🤭(zaki bayani lol😆). *********** Akwana atashi babu wahala wajen Ubangiji, yau kam kwanan Fateema shida da haihuwa, gobene sunan baby, a yau d'inne kuma Uncle zaidawo hannun Amatallah bayan yagama kwana biyu ga Aneesa. Nazeefa data dawo gidan tun haihuwar Fateema ta fahimci babu abinda yashiga tsakanin Amatallah da yayansu, hakkane yasata k'udirin kafa musu tarko yau sudukansu, tasamu Anty maijidda ta sanar mata cewar sutafi plan B akan Amatallah d'in, dukda bata fito fili ta sanarma Anty maijiddah komaiba, amma itama tadad'e da fahimtar Amatallah har yau batasan mijiba, kodan yanda bata kishin matan yayansu sosai kamar yanda su suke kishi da ita. Dawuri ranar Anty maijiddah tazo gidan saboda aikima. Hummm fad'a muku yanda Anty maijidda tagyara Amatallah ranar ai 6ata lokacine kawai, saidaifa hummm!! Ina mai tabbatar muku yau Uncle bai Isa iya control d'in kansaba, gashi dama kwana biyun dayay d'akin Aneesa ma tana Off. Kusan 5pm tashiga kitchen d'inta domin yin girki, Kitchen d'in tsakar gida su Anty maijiddah sunata aikin abubuwan daza ayi Na suna gobe, Dan haka tanufi kitchen d'inta danyin girkin dare, yau kuma ne rana ta farko fazatayi girki a cikin d'inta, ta fiddo tukwane a kwali ta wanke daduk abinda tasan zata buk'ata, kafin tafara had'a miyar Agusi d'inta datasha busashen kifi ga wadataccen naman tantakwashi, tunifa gida ya d'auki k'amshi su Anty maijidda sai fad'i suke Amatallah zaki kashemu da k'amshi. (Nima dai Amatallah zata kasheni da kwad'ayi Anty maijidda😋 lol) Batasanma sunayiba aiki ya d'auke hankalinta, ta had'a lemon kankanarta dayasha madara da kayan k'amshi, ta fere doya mai k'yau ta d'ora, harga ALLAH bazata iya daka sakwarar mutane kusan 15 ba, Dan bayansu Kansu da yara sunkai goma ga kuma Anty maijidda nazeefa sai yayyen Maijego biyu da kanwarta zaliha ga gwaggo rakkiya, ga kuma wata dattijuwa k'anwar Maman maijegon, kuma duk gidan zasu kwana, yayyen fateemar ne kawai tasan komin dare k'ila zasu wuce, Nazeefa Amatallah takira domin Neman shawarar yazatayi. Dariya Nazeefa tayi tana fad'in "amma ke ragguwace, kina nufin Yaya kawai zakiba sakwara? to bamu yardaba". " kai Anty Nazeefa ki tausayamin, ALLAH ba abune mai sauk'iba dakan sakwara". "To Na tausaya miki 'Yar Uncle, yanzu dai dafa doyan saiki d'iba iya wadda zaki daka masa, nikuma sainakai sauran babban kitchen ahad'u adaka gaba d'aya". ''Yauwa Anty Nazeefa ngd, shiyyasa nake sonki". Dariya sukayi gaba d'aya Nazeefa tafice. Zuwa magriba ta kammala komai, suma su Nazeefa sun daka waccan, ta had'ama Uncle abincinsa ta d'auki tukunyar miyar duka ta kaima Anty maijidda. Abincin ta d'auka takai samansa, takuma saka turare kamar yanda Anty maijidda tace mata, saida taga komai yayi dai-dai har ruwan wanka ta had'a masa Dan tasan yana gab da dawowa, ta had'ashi da zafi sosai yanda sanda zai dawo yayi daidai wanka. d'akinta takoma ta shirya itama, dama tayi wankanta tunkan tayi sallar magriba, kwalliya tayi mai sauk'i tayi d'aurinta mai k'yau yanda Fa'iza ta koya mata, (Amatallah duk irin wad'annan abubuwan bata iyasuba, saboda batada k'awaye gakuma yanayin inda ta tashi, barta dai da tsafta ga nutsuwa, amma irin dai iyayi Na 'yammata bata iyaba😄). K'amshi take tamkar tayi 6arin turare a jikinta, kodai mace taji k'amshina nan nata saita firgita balle kuma.....humm.🙈lol Ana kuwa idar da sallar isha'i Uncle yashigo gidan Yarane kawai a falon, dan haka suka iso da gudu suna ihun murnar masa oyoyo, rungumesu yayi yana murnar ganinsu shima, harma da yaransu Anty maijidda, zaliha dake tare da yaran a falon Dan tana fashin salla ta gaidashi, cikeda fara'a ya amsa yana fad'in "autar mama kamar kiyi zamanki tare damu kawai". 'Yar dariya tayi tana fad'in " Yaya aikuma makaranta". "Anya kuwa ba wayo bane?". " ALLAH kuwa Yaya". "Shikenan to na yarda". yay maganar yana nufar hanyar 6angaren Fateema, bayan Sahib ya kar6i ledojin hannunsa yanufi samansa dasu. Ya iskesu Anty maijidda zaune a falon Fateema, Mariya Na salla itada gwaggo rakiya, risinawa yayi ya gaida inna Nafi dake zaune tanama jaririya wanka, su Anty maijidda suka gaidashi suma itada Anty maimuna, sunata d'aura kayan rabo. Anty maimuna tace, " Yaya Muhammad fatin tana cikifa". Murmushi yayi yanufi bedroom d'in Fateema, Anty Mariya data idar ta kalli su Anty maijidda tana murmushi "kai ya Muhammad Na birgeni saboda kunyarsa wlhy". Duk dariya sukayi , Anty maijidda tace kad'anma kikagani Indai ya Muhammad ne. A zaune ya tadda Fateema tana ware kayan fitar suna dayay musu suduka, amma ita kala biyar, sukuma su Amatallah uku-uku itada Aneesa. Murmushi sukaima juna kafin ya zauna kusada ita ya rungumeta yana mata kisses zafafa a wuya, a hankali yace, " I miss you my sweet tee....". Duk da taji dad'in maganarsa hakan bai hanata yin 'yar dariya ba, ''kai Nurrina harda zolaya abin? Kaida keda sabuwar Amarya fil a hannu". Wani k'asaitaccen murmushi yasaki yana shafar gemunsa dakuma manna mata wani kiss d'in, "humm My tee... Amarya daban ke daban ai". Murmushi kawai tayi batace komaiba, 'yar hira sukayi da tattaunawa gameda sunan gobe, yakuma bata za6in sunan datakeson asama baby. " duk wanda kasaka yayi Nurri, nidai nabaka za6i kamar ko yaushe". Yay d'an murmushi yana mik'ewa, "to shikenan ALLAH ya raya Ameenatu". Itama murmushi tayi tace, " Amin Nurrina lallai Anty Mariya zataji dad'in wannan karamci sunan Iya babu zato". Baice komaiba yafita yana dariya. Ya tarar Aneesa da Nazeefa da Amatallah ma sunzo falon, Nazeefa ta gaidashi, Aneesa ma da Amatallah suka masa sannu da zuwa. Fakar idon jama'a yayi ya kashema Aneesa ido d'aya sannan yafice. Tayi murmushi kawai tacigaba da abunda takeyi. Anty maijidda ta kalli Amatallah "madam atashi ko". A kunyace Amatallah tatashi tafita, sukayi mata dariya banda Aneesa da tayi murmushin yak'e kawai saboda kishi, ga Amatallah tasaka hijjabi kan kwalliyarta babu maicewa ga yanda take, sai uban k'amshinta daya baje falon. A hanyar 6angarensa ta iskeshi tsaye yakama k'arfen benen idonsa a k'ofar Falon Fateema. Hakanne ya tabbatarma Amatallah fitowarta ya tsaya jira. Suna had'a ido yad'an sakar mata harara sannan yafara takawa yana hawa. Bayansa tabi tana gumtse dariya................✍🏻 _gaskiya 'yan bauchi state muna matuk'ar godiya da goyon bayanku ga shugaban k'asarmu mai kishinmu baba buhari, nabaku page d'innan k'yauta saboda farincikin dakuka Sani yau, ALLAH ya maida shugaban k'asa gida lafiya da dukkan 'yan uwa dasuka halacci wajen campaign d'in, ALLAH kabamu shuwagabanni nagari🙏🏻._ Bauchi inayinku irin Trillion's d'inan🥰🥰🥰🥰❤❤❤❤❤👍🏻 🤩👎🏻 One luv my sweet Fan's🥰 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻 [1/16, 9:01 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_* *_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡 _{home of expert and perfect writer's}_ *_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉ _(Hattara matasa)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_Special gaisuwa gareku Haskakakku_* _Nana Diso. Pherty xarah. Asmy b Aliyu. Maman khady. Miss Xoxo. Nuceey luv. Zainab bawa. Hafsat rano. Jiddah Aliyu. Kdeey. Slimzy. Khaleesat Haidar. Billy Galadanci. Saffiyya Huguma. Ayusher Muh'd. Ai'sha d'ansabo. Ummu basheer. Ummi Ai'sha. Hajjace. Faxy fashion. Feedhom. Bilyn Abdull (nima Na gaida kaina🤭😂)_ *ALLAH ya k'ara haskakaku!* *HASKE WRITERS ASSOCIATION kenan gaba d'aya masoyanmu* 🥰🥰🥰🥰😘🤝🏻👍🏻 ____________________ *_Number 30_* ____________________ Tashiga bedroom d'insa da sallam, harya fara k'ok'arin cire babbar rigarsa, saida yagama cirewa ya ajiye sannan tace, "sannu da zuwa Uncle". Ya amsa yana k'ok'arin fara cire mafallan rigarsa ta ciki, juyawa tayi tana fad'in " Uncle bara inje, idan ka gama saina daw........" Da sauri yarik'o hannunta tadawo baya, yad'an had'e fuska kad'an idonsa akanta. Maida nata k'asa tayi tana kallon k'afafunsu, duk kuma saitaji babu dad'i, ta marairaice murya kamar zatayi kuka dan ganin ya rik'eta kuma yayi shiru. "Uncle please miya faru?". Ta d'anso bashi dariya amma saiya kanne, yasa yatsu biyu ya d'ago ha6arta. idonsa taga ya k'ank'ance yana mata wani kallon da yasha banban dana kowacce rana, da sauri ta janye daga kallonsa. Yad'anyi gyaran murya. Hakanne yasata dole takuma kallonsa. Girarsa d'aya a d'age yace, " Khadeeja kinason kishiyoyinki su rainaki ko?". Cikeda mamaki tace, "Uncle kamar ya?". " kamar yanda kike nuna halin ko inkula akan mijinki. Haka kikaga su Aneesa namin? Sai dafa akace ki biyoni kika taso, Daba ace ki bizoba ma baki zuwa kenan ko?". Kanta ta girgiza masa alamar a'a. "To miyasa ke bakya koyi dasu? Ina kallonki kamar mai wayo amma ba haka bane ashe". A shagwa6e kamar zatayi kuka tace, " ALLAH uncle inajin kunyane, amma kayi hak'uri bazan sakeba zan canja insha ALLAH". Sai yanzu taga yasaki wani lallausan murmushi yana shafa gemunsa, murya k'asa-k'asa tamkar mai gudun ajisu yace, "Kunyace kawai matsalarki my babie? Karki damu zan canjaki da kaina ma kafin ki canja kanki". A kasalance ta d'aga masa kanta, saboda dukkan illahirin jikinta yamutu murus da salon Na Uncle. Ya d'an murmusa tare da bata sumbata a goshi, ya saki hannunta yacigaba da cire ma6allan rigarsa, itadai Amatallah kanta a k'asa takasa kallinsa. Tsaf ya cire komai, dagashi sai vest da boxer, yatako a hankali zuwa gabanta, duk'owa yayi saitin kunnenta, har tanajin saukar numfashinsa a dokin wuyanta, yace, "indai kunyace yau d'innan zan cireta kowama ya huta". yana gama fad'a yashigewarsa toilet yana wani murmushi mai k'ayatarwa. Rufe k'ofarce tadawo da Amatallah hayyacinta, tabi k'ofar da kallo tana cigaba da juya maganganunsa, sometimes takanyi mamakin Uncle da halayensa, gaba d'aya ya canja mata yanzu, kai tsaye yake mata abubuwa ko kunya babu, maganarsa ta k'arshe tafad'o mata arai, sai kuma taji gabanta ya fad'i. a fili ta furta ''ALLAH yasa ba abinda nake zaton bane". Bata bar wajenba saida taji motsin zai fito ta gudu falo. Baiyi mamakin rashin ganintaba, dan yasan dama bazata tsayaba, d'an murmushi yayi yacigaba da goge jikinsa da k'aramin towel. Amatallah Na zaune afalo ta k'urama TV ido, saidai azahiri hankalinta bama akansa yakeba, yana kan tunanin maganar Uncle ne, dukda wani 6angare Na zuciyarta yana fad'a mata ba haka bane. Jin anjawota yasakata yin firgigit tadawo hayyacinta, da sauri ta kallesa dukda daddad'an kamshinsa ya tabbatar mata shine. baiyi maganaba, sai hijjabinta daya cire. "Kai my best! wai ina kika sami turaren nan mai narkar danine?". Yayi maganar cikin kunnenta. Hannu tasa tarufe fuskarta tana murmushi, ''kai Uncle naka ai yafi nawa dad'i". Ya murmusa a karo Na barkatai tare da kuma jawota sosai a jikinsa yana shinshinar wuyanta, tuni ya fara sakar mata wasu zafafan kisses, daga haka aka koma (abinda Malam ya hanani fad'a🤭). Tunfa Amatallah Na kallon lamarin a matsayin k'arami harya koma fin k'arfin, turarenta, gaba d'aya yagama birkita boss bayaji baya gani, ya mantafa (Khadija ce d'iyar brother), saida ya rud'ar mata dadukkan jiki da.......sannan ya fara Ankara a falon suke, kuma koyaushe cikin yaran wani zai iya shigowa dan k'ofar abud'e take. daga ita harshi tagwayen ajiyar zuciya suke saki, jikin Amatallah sai 6ari yakeyi, ta duk'ar dakai ta kasa kallonsa ko sau d'aya. Shikansa kunyace takamashi, amma saiya Fiske ya sauka k'asa yana fad'in ''sakko kibani abinci yunwa nakeji my best". Yay maganar murya a shak'e tamkar mai Mura. Tamkar Amatallah ta FASA kuka haka ta sakko tazuba masa sakwara dataji daka tayi luk'uy, tuni k'amshi ya gauraye hancin Uncle, harma ya k'agara tazuba ya fara zubama cikinsa.😀😜 Aiko tasha mamakin yanda taga yaci abincin sosai, sannan bai matsa mataba datace ta k'oshi, saiya tura mata Leda d'aya acikin ledojin da Sahib ya kawo. Shiru tayi tana kallon ledar, yad'ago kai yana kallonta, suna had'a ido tayi azamar janye nata tana d'an tura Baki gaba. Yayi murmushi mai sauti yana fad'in "garama kichi yarinya, shikuma bakin anjima kad'an zaimin bayani dalla-dalla". Kuma tunzuro baking tayi, yajawo ledar yana bud'ewa, kazace datasha gashi mai kyau sai k'amshin dad'i takeyi, ga kayan had'i Na musamman tasha na salad, sai yoghurt mai sanyi Na hollandia. Gabanta ya tura yacigaba dacin sakwararsa yana zuba mata Santi. Tun tana gimtse dariya harta fara yinta a fili. dole yashagala a kallonta, harya kammala batakoci lauma d'ayaba akazar, ya wanke hannunsa tare da ture kwanikan gefe ya jawota jikinsa. Da Kansa yaciyar da ita kazan, tun tana basarwa harta saki jiki taci, shima yoghurt d'in tasha babu laifi. Nace, " habawa Ama....sai Uncle yamiki irin ta (Ya khaleel Na *Ciki da gaskiya* ya tsareki kibiyasa kazarsa tamkar yanda Sholly tabiya ya Khaleel itama). 🏃‍♀😂 Bayan sun gama ta tattara wajen, ta d'auki kwanikan zata sauka dasu. Harta kama handle d'in k'ofar yace, "sauran kuma saina biyoki yauma". Shiru tayi batace komaiba, sannan kuma bata fitaba. Harya d'auke kansa yakuma kallonta, " Yaya dai?". Idonta tab da kwalla tace, "Uncle yaufa su Anty maijidda anan zasu kwana". " to saimi yafaru dan anan zasu kwana? hakan Na nufin bazaki kwana d'akin mijinki ba kenan?". Kasa cewa komai tayi. Yace, "minti talatin nabaki kacal, idan zaki dawo kizomin da Lipton". Kallonsa tayi zatayi magana taga yayi kicin-kicin da face. A sanyaye tafice. Tana dire kayan a kitchen Anty maijidda ta shigo, hannunta kawai takama batareda tayi maganaba suka shige 6angarenta. Mamaki ya kama Amatallah data tadda abubuwa saman gadonta, nanma Anty maijidda batayi maganarba tabata Abu a kofi tace shaye. Kar6a Amatallah tayi babu musu ta shanye, tasandai Anty maijidda bazata cutar da itaba, abinkam yamata dad'i sosai, kamar madara kamar waken suya dai, kai tagaza gane minene. Wani d'an kad'an kuma Anty maijidda ta kuma bata, shima dai akwai dad'i, tabata wasu turarurruka kala hud'u, kowanne tamata bayanin inda zata shafashi, (ko kunya Anty maijidda bataji) cewar Amatallah a zuciya....... Maganar Anty maijidda ta kuma katseta, idan kingama ki fesa wannan turaren kuma dukkan jikinki sannan ki saka wannan rigar barci, ga zani nan ga hijjab nan, in kin k'iyi kuma zangane". tana gama fad'a tafice ta barta. Binta kawai Amatallah tayi da kallo, kafin tatashi tafara yin duk yanda tace tayi. Cikin mintuna 20 Amatallah ta had'e, ga wani k'amshi daya kusa bugamin kwanya tana zubawa, (jinai inama ta sanmin nima na birkita my Abdull😉...lol). Zani ta saka da hijjabin dasuma keta k'amshi sannan tafito falonta, tsaye tayi tana tunani, waikuma yanzun dolene tajefa gaban Uncle ahaka? Itafa rigar barcinan kunyama take bata. Kodayake bazata cire zani da hijjab d'inba komi Uncle zai mata. Da wannan tunanin tanufi kitchen, black tea ta had'a masa kamar yanda ya buk'ata, ta d'ora akan k'aramin tire tafito. A falo sukaci karo da Aneesa, kallan kallo akaima juna, Amatallah tawuce batareda ta tankaba. Aneesa ma tashige nata 6angaren rai a 6ace, a ganinta da biyu Amatallah ta mata haka, ga wani k'amshi na masifa daya baje gidan ajikin Ama..... (Hhhhhh🤣 to mita miki Anee? Kodai kishinne ya motsa?😜). Tad'an dad'e tsaye a bakin k'ofa tanata sak'awa da kwancewa, Uncle kam duk yana kallonta ta labule, dan tunda tafara tako steps d'in k'amshinta ya iso masa. Ganin tak'i shigowa yace, "kona kawo miki bargon kwanciya my bes...... Ai bata bari ya k'arasaba ta shigo falon. Kauda kansa yayi yana danne dariyar dake taho masa. Shan tea yake yana satar kallonta, saida yagama tsaf sannan yatashi yashiga bedroom d'insa, mintuna kusan 5 yafito da alamar alwala yayi. Kallonta yayi yace, " shiga kiyo alwala". "Uncle nafayi isha'i har shafa'i da wutirima". " nasani aii, jeki dai kiyi". Bata kuma cewa komai ba taje tayo alwala a toilet d'insa. Yajasu sallah raka'a biyu yad'ora da addu'oin fatan alkairi da zaman lafiya agaresu, da had'in kan iyalansa, yay addu'a mai tsawon gaske akan mahaifinta, harda 'yan kwallansa kuwa, Amatallah kam kuka takeyi rurus harda shashsheka. Bayan sun shafa ya rungumeta yana lallashi da fad'a mata kalamai masu kwantar da hankali, daga nan aka zarce da soyayya saboda kukanta ya kasa k'arewa, jin bakinsa cikin nata kuwa yasata had'iye kukan tilas.🤭 (abinda yabiyo baya kuma Malam yahana fad'a😎). Ganin fa za'ai abin kunya a falo ya cukuykuyi kayarsa sukai d'akinsa. Inason binsu ina tsoron kar garin Neman gira arasa ido, kafinma Na yunk'ura Na tashin najiyo Uncle M.A ya Mirza makulli alamar basa buk'atar kallon k'urilla👀, inba so kuke kuma Uncle yafad'ama Malam Na lek'aba....🤭🙆🏻to mu hak'ura kawai idan Ama... tafito tabamu labari🥳😆, hanyar lafiya a bita da shekara🤩). Koya kukace my guys🤷🏽‍♀?.😜 Kukan dana jiyo na Amatallah da kwala d'an wani ihunta wanda nake addu'ar ALLAH yasa nikad'ai naji banda (Aneesa ko Uwargida fateema🤭🤣), yasani fad'ar shikenan Uncle ya wuce wajen, (Amatallah team yaufa kune aciki su Aneesa a kwana😂) masoyan Anee amin afuwa. 🏃‍♀ Ina nan zaune na zabga tagumi da jiran fitowar Uncle idan yagama ta6argarzar😢. Anja wani d'an lokaci nalek'a da k'yau ta kafar makulli, can na hango Uncle rungume da Amatallah tana zabga kuka tamkar ranta zai fita, shiko babu abinda yake fad'a sai "ALLAH ya albarkaci rayuwarki my Heartbeat, Jazakallahu khairan! Jazakallahu bil jannah Amintacciya ma abociyar kame mutunci da bin dokokin Ubangiji, tabbas nayi k'yak'yk'yawan zato akanki, kumma kin tabbatar min hakan yau, yakuma k'ank'ameta da bata wasu zafafan kisses Wanda yasaka Amatallah tsaida kukanta dole saikuma shashsheka. Cikin kunnenta yacigaba da fad'a mata sirrin zuciyarsa (banajinsu fa😒🤫🙄). Adaren dai Alhaji Muhammad bai bar Amatallah ba saida ya taimaka mata tagyara jikinta tsaf tana zuba masa shagwa6a wadda ke sake dulmiyasa a k'aunarta😻. Yabata sauran yoghurt d'in tasha da Paracetamol sannan ta kwanta. Lalla6ata yaytayi har tayi barcinta tanata sauke ajiyar zuciya lokaci-lokaci. Ahankali yake shafa kanta yana murmushi, ya sumbaci la66anta da goshi akaro na babu adadi " I love you so much my heartbeat, ALLAH ka gafartama brother da Amminki, tabbas ked'in kinzama wani yankin na rayuwata, kin mayemin gurbin brother d'ina, ina miki son danima bansan iyakarsaba". Ya k'ank'ameta ajikinsa yana zubar da hawayen danima bansan fassararsuba sai ALLAH sai kuma shi kansa🤪😶................✍🏻 _kuyi manage da wanan, nid'in nazama sai'a slowly wlhy🙁. ngd da comments d'inku da addu'ar dakukema mahaifina, ALLAH yabar zuminci._😘😘 *_Team Ama..... Today is your day fa🤪👌🏼._* 🤩👎🏻 One luv my Sweet Fan's. *_ALLAH kagafarta ma iyayenmu_*😭🙏🏻 [1/16, 9:01 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_* *_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡 _{home of expert and perfect writer's}_ *_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉ _(Hattara matasa)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* _gaisuwarku dabance kamar yanda kuke na daban agareni,_ *perty novels and Manshat Novels + Nice & cul novella & Kundin Haske, Siyasa ko k'abilaci group 1-2-3, Taskar littatafan Hausa, Home of Novels & House of Novels, MF & J hausa novels* _Inayinku irin trillions d'inan, inajin dad'in comments naku da yadda kuke hira akan wannan buk, ALLAH yabar k'auna_🙏🏻🤪 One luv all😻😻🥰🥰😘. ____________________ *_Number 31_* ____________________ Da asuba kam da k'yar ya tada Amatallah, (to dama yaya lafiyar kura.....🤭 ) dama can Ama.... Ana shagwa6a ballantana kuma yau mai dalili ta samu. Tana bud'e idonta suka had'a idanu, maidawa tayi ta rufe da sauri. Murmushi yayi yana shafa kumatunta, "haba my heartbeat a taimaki Uncle atashi please mana". Baki ta turo gaba tana hawaye, a shagwa6e tace " babu fa wani Uncle nidai, bayan ma......." Saikuma tayi shiru tajuya masa baya. Murmushi yak'arayi ya hawo gadon sosai ya kwanto a bayanta da d'ora kansa bisa dokin wuyanta, cikin kunnenta yace, "shikenan bara to a maimaita irin na jiya tunda babu wani Uncle kikace......" Ai bata bari yakai k'arsheba ta tureshi ta diro daga gadon, wuff tafad'a toilet d'insa. Dariya sosai yakeyi, (daka gansa kasan yana cikin tsantsar farinciki) nishad'in dake kwance saman fuskarsama kawai ya isheka amsa. Sakkowa yayi yafita Dan tada jama'ar gidan. Babu maganar shiga 6angaren kowaccensu, Dan duk da bak'i, knocking kawai yayi musu, yana tsaye har suka tattashi, yacema Aneesa ta tado masa su Abulkhairi, dan a 6angarenta suka kwana. "Kashigo mana, mufa kad'aine sai Nazeefa da Zaliha, kuma suna d'akina su". murya ad'an cinkushe take magar, Dan haka kawai haushi yake bata tunjiya dataga Amatallah zata 6angarensa. Bai damu da yanda tai maganaba yashige, a zatonsa ko mura keson kamata😜, harma tabar falon takoma d'akinta. d'ayan d'akin yashiga yatadasu, sukayi alwala sannan yatasasu gaba suka tafi massalaci, ana idar da sallah aka rad'a sunan baby Ameenatu (sai muce ALLAH ya raya Uwargida). Suna dawowa yashiga d'akin Amatallah, ALLAH yaso Anty maijidda takwashe kayan jiya, ko ina tsaf saidl mayataccen k'amshinta daya rigaya ya mannewa 6angaren. Waldrop yabud'e ya d'akko mata wani less mai k'yau da d'aukar ido, yahad'o da mayafi kalar filawoyin less d'in, ya d'auki takalma flat suma dai kalar gyalen, sannan ya d'ibi kayan kwalliyar saman mirror d'inta da turarruruka, dukda wasuma baisan amfanin suba shidai duk ya had'a mata yafito. A falo suka had'u da Aneesa tafito d'aukarma siddiqa ruwa, kallonsa take shida ledar hannunsa, dakuma kallon 6angaren Amatallah daya fito. yad'anji kunya, Dan haka cikin basarwa ya kalli ledar da d'an d'agata sama sannan ya kalli Aneesar yana murmushi. Harararsa tayi tara6a ta gefensa zata shige kitchen abinta. Da sauri yasha gabanta, "my Nessa ba gaisuwa?". Dukda taji kunya saita dake, batace komaiba ta kauda fuska gefe. Ya marairaice murya tareda d'an langa6e kansa gefe ''haba Neesa ninefa Muhammad d'inki, miyayi zafi ake fushi dani?". Dariya yabata sosai, Dan haka ta murmusa, rissinawa tayi ta gaidashi da tanbayar ya angwanci. Yad'an zaro ido waje ''my Nessa! angwanci kuma?". Haushi yakamata, aranta tace, " Namiji munafuki.." (Bani nafad'aba Neesa ce🤭). Gaba tayi abinta tashige kitchen d'in. Yabi bayanta da kallo yana murmushi har hakwaransa Na bayyana, gwalo yayma bayanta yanufi 6angarensa yana fad'in "baki k'aryaba Nessa, yaukam ni angone mai lasisi". (Hoooo Uncle d'inmu, kana aljannah muna binka da addu'ar fatan alkairi🤩). Aneesa kam saida tayi hawaye a kitchen (duk dama batasan koya angwance d'in da gaskeba) tana son Muhammad harma batasan iyakaba, shiyyasa take kishinsa, itafa ko'a makaranta kishin kar afita yasata kasancewa mai k'ok'arin tsiya, bare kuma Muhammad d'inta, duniyarta, farin cikinta, tanamasa so irin Wanda batama San adadinsaba, ta wanke fuskarta sannan tafito. (Neesa sai dai hak'uri, duk sonsa dakike k'addararki kenan zama da kishiyoyi🤭😆. Sai hak'uri dai. Nina Inason my Abdull d'ina, kuma k'ila saiyamin kishiya😒😢). Ya tarar Amatallah na shirin fitowa, taja baya yashigo, kanta a k'asa ta rissina ta gaidashi. Murmushi yayi kafin ya amsa yana fad'in " ya gajiyarki babyna?". Bata iya amsashiba, saima k'asa data kumayi da kanta. Bai damuba danshi kunyarta kuma tsundumashi a kogin k'aunarta yakeyi. Yakama hannunta suka koma ciki yana tambayar INA zataje?. A marairaice tamkar zatayi kuka tace, "Uncle please kabarni Na sauka, kaga akwai ayyuka da za'ayi, ga breakfast ga......." Baima bari Takai k'arsheba yajawota saman gadon sosai "yo karsuci breakfast d'in Indai saikin sauka kinyi musu, ai idan wani ya ganki a k'asa saidai nanda 12 Na rana", ya rungumeta a jikinsa " kinga muyi barcinmu ma". "Uncle!" tafad'a tamkar zatayi kuka. Hannu yasaka kan la66anta yay mata Alamar zip🤐. Shiru kuwa tayi Dan dolenta, wani salo yafara mata, ahankali tafara lumshe idanu Dan sak'on Na shigarta, jin yana neman canja hanya sai hankalinta yatashi (karfa Uncle yace zai k'arayine nashiga uku ni Khadija), shiru tayi tahau barcin k'arya, dukda zuciyarta Na bugawa da sauri-sauri saboda tsoro, a sannu dai har barcin gaskiya ya kwasheta, dama barcin takeji dauriyace kawai yasata son saukar dakuma kunyar aganta da safe tafito daga 6angarensa. Jin shiru da saukar numfashinta ahankali bisa k'irjinsa yasashi lek'a face d'inta, goshinta ya sumbata Yakuma rungumeta da k'yau yana murmushi da jero mata wasu addu'oin fatan alkairi zuciyarsa, shima babu jimawa barcin yay gaba dashi. Babu wanda ya nemeta acikinsu Anty maijidda, saima hidimar d'aura breakfast dasukeyi abinsu. Garama Aneesa tasoyin magana saikuma tayi shiru. Dasuka kammala breakfast d'inma Anty maijidda tace Nazeefa ta d'auka takai sama. Har Nazeefa tashiga ta ajiye bataji koda motsinsuba, hasalima k'ofar bedroom d'in arufe take. 'Yar dariyar mugunta tayi kafin tafara gyaran falon nashi, a zuciyarta kuma tana addu'ar ALLAH yasa an gamune, sai zabga murmushi takeyi harta kammala, ta saka turaren wuta sannan taja musu k'ofar tafice abinta. A k'asama ta iske su Anty maijidda sunata gyaran gidan, an kora yaran duka waje, 6angaren Amatallah tashiga, tayi mamakin yanda taga mirror d'in a hargitse, batace dai komai tagyara mata ko'ina, ta saka turaren wuta sannan tarufo tafito. Bayan sunyi breakfast kuma suka shiga kujiba-kujibar d'aura girkin suna da duk abinda za'a buk'ata, zuwa lokacin kuma su Anty Mariya yayyen maijego sun dawo, Dan da daddarennan duk suka tafi gida, yanzn kuma suka dawo Dan kama girki. ***** 😀 Koda Amatallah da Uncle basukai 12 ba kamar yanda Uncle yay fata sun kai dai 10 suna barci abinsu, Amatallah ce tafara farkawa,bayan tayi addu'ar tashi barci ta kalli yanda ta kanannad'e jikin Uncle, kai kace zata komane jikin nashi, ta tsurama fuskarsa ido tana kallo, Uncle yanada k'yau dai-dai misali, kuma yanada haske babu laifi, amma bak'ine, gemumsa da zagayayyen gashin bakinsa sune suka k'ara masa kwarjini da cikar haiba, hannu takai a hankali ta shafa gemunda tadad'e tana kwad'ayin ta6ashi saboda burgeta dayakeyi, masha ALLAH tafad'a a zuciyarta, saboda wani laushi da santsi ga k'amshi da gemun keyi, (ba dole yayi laushiba, kud'in da gemunnan ke lashewa aiba Na wasa bane). Tunda tafara ta6a gemunsa ya farka, kokad'an bashida nauyin barci, amma bai nuna mata yatashiba, danya kula tanajin dad'in shafa gemun nasa. Ringing d'in wayarsa yasaka ta janye hannunta da sauri, tayi k'ok'arin janye jikinta amma yak'i bata damar hakan, kallonta takai ga agogon d'akin kafin tadawo da kallonta kansa tana zare idon tsorata da mamakin yanda lokaci yatafi, amma takasa magana bare ta tadashi. Aka kuma kiran wayar, batareda ya bud'e idoba, baikuma saketaba yamik'a hannunsa d'aya ya d'auka, kad'an ya kalli screen d'in wayar kafin yad'aga yasa a kunne yana fad'in "Assalamu alaika". Daga can Alhaji Sabi'u yace, " Alahji Muhammad lafiya naji muryarka haka?". Murmushi Uncle yayi sannan yace, "a barci ka tadani". " barcifa kace? wasa ko gaske?". "Da gaske" yay maganar yana kuma k'ank'ame Amatallah kamar za'a kwaceta🤭. "Lallaikam, kaiko wane aiki ya hanaka barcin dare? Saikace dakai ake abincin sunan". 'Yar dariya Uncle yayi, kafin yace, " mutumina bazaka ganeba ne kawai, yanzudai miya faru?". "Uhhm nakirake dama naji kokana kasuwa, amma badamuwa, idan kafito kakirani inason mu had'une". "OK, saina fitod'in". "An rad'a suna ko? Gashi ko 'Yar walima bamu had'aba". "hhh Alhajina kainane yad'au zafi, shiyyasama ko maganar walimar banyiba, mata kawai suyi nasu, mu munyi namu da asuba ai, baby taci sunan Aminatu". " Masha ALLAH, ALLAH ya raya manasu akan sunna, ya albarkaci rayuwarsu, yasa masu mana addu'ane bayan k'asa ta rufe idonmu". "Amin ya rabbi. Insha ALLAH zuwa 12 zan sameka a office kawai". "okay babu damuwa saina ganka". Kallonta yayi bayan ya kashe wayar, ta lumshe idanunta dan bataso su had'a ido. Murmushi yayi yashiga zagaya yatsansa kan la66anta, murya k'asa-k'asa yace " 'yammatana da guduwa zakiyi ki barni kenan?". Wayyo ALLAH, tafad'a a zuciyarta. Jin bata amsa mishiba ya yunk'ura yatashi da ita a jikinsa, "shikenan tunda bazakiyi maganaba, tashi muje namiki wanka kar 'yan suna sufara jajenki". Babu shiri ta ware manyan idanunta kansa. Ido d'aya ya kashe mata😉, tai azamar janyewa. Sauka yayi itama yakamo hannunta zai saukar da ita ta tirje tana langa6e kai, " please Uncle zanyi da kaina Dan ALLAH". "ban yardabafa my best, dolene nakuma gasaki karkije kina tafiya agane yau......" Hannu tasa ta rufe masa baki tana cewa "kai Uncle". Hannun ya janye yana dariya, " to naji bazan fad'aba, muje Na had'a miki ruwan kawai". Batak'iba wannan tabishi, yahad'a mata dad'an zafi yace "ki daure karki cuci kanki, kisan yau taron jama'ane agidan kinji". Ta d'aga masa kai idonta a k'asa. Kumatunta ya sumbata yafice. Bakuwa ta cuci kan nataba tagasa ko ina yanda yakamata, dan bawani zafi sosai takejiba dai mai cutarwa, tundama Uncle yamata gashi Na musamman da daddaren, amma tanajin jikinta ko'ina yana ciwo, gakuma wani canji Na musamman dukdai ba yanda tasaba jiba. Tadad'e tsaye tana kunyar fitowa da guntun towel d'insa dake bathroom d'in, amma babu yanda zatayi ganin time nakuma tafiya a banza tafito a takure. Babu kowama a d'akin, hakanne yasata sakin ajiyar zuciya, kayanta tagani a saman gado, tayi mamaki sosai, amma haka ta d'auka a gaggauce ta shafa mai da body spry, sannan tashirya tsaf, sosai kayan suka mata d'as ajiki. Bawata kwalliya tatsaya yiba, tana cikin shafa fauda yashigo da sallama, da alama shima wankan yayo a d'ayan d'akin dake 6angarensa inda Nazeefa ta zauna sanda yana Dubai. " hummm my Heartbeat Ashe nasan kala nima, kinyi k'yau kamar Na zauna naita kallonki abuna". Murmushi tayi tace "ngd Uncle". Shima murmushin yayi yahau shirinsa, ko sau d'aya Amatallah bata kalli inda yakeba. " my best zoki za6amin kaya ko". Tad'an kallesa kafin tace "Uncle nikuma?". Gira ya d'aga mata kawai. Mik'ewa tayi tanufeshi, danta tuna (maganar Anty furera). Yana tsaye gaban Waldrop d'in, hakanne yasa yad'an matsa tashigo gaba, kallon kayan ta tsayayi, tsarin komai ya birgeta. Jitai ya sak'alo hannunsa kan cikinta ya rungumeta tareda d'ora kansa akan kafad'arta, itako yazatayi da wannan lamari Na Uncle.... Maganarsa ta katse mata zancen zucin datakeyi. " kifa za6amin kalar naki ehe". Murmushi tayi ta jawo wata sky blue d'in shadda d'anya, tad'an juyo ta kalleshi da nuna masa kayan. Wuyanta ya sumbata yana fad'in ke tadabance my best! kamar yanda komanki yake nadaban". Taji fad'in kalaminsa sosai, Dan haka ta danne kunya ta taimaka masa ya shirya, cikin janfa da wando Na kayan, rigar tawuce gwiwarsa da kad'an, amma sunmasa k'yau ainun, saikace wani d'an 30+ (😆...lol). Tana saka masa ma6allin gaban rigar suna murmushi, tagama tafesa masa turarensa. Yace "saura hula my best". Murmushi tayi ta za6o masa derk blue acikin hulinan data gani birjit. A mamakinsa saiyaga tana karin hular..... (Abinda nakasa iyawa🤭 Ama... Zanzo ki koyamin narigama boss d'ina nima😂) tsayawa yayi kallonta cikeda birgewa. Bayan tagama tamatso kusadashi, yafita tsawo, danhaka yad'an duk'o ta saka masa, tareda dai-daitata da k'yau. Kallon kansa yayi a madubi yana murmushi, " my best ina kika iya Karin hula haka?". "Uncle wajen baba mana, tun ina masa yanacewa baiyiba harna dage Na iya kala-kala". "Masha ALLAH my best!" Yafad'a yana kuma kallonsu a madubin, tabbas yasha ganin karin hularnan akan brother d'insa, ringumeta yayi yashiga bata masu zafi....(😘 kundai gane). Saida tasha dad'ad'an kalamai sannan suka fito falo, dakansa yabata brekfast d'in dasuka gani a falon. Bayan sun kammala kuwa babu yanda baiyiba su fita tare tak'i, yamata kisses yafice tana masa addu'a. Murmushi tayi tareda shafa fuskarta tana fad'in my Uncle I love you so much, lallai ka cancanci kowacce mace ta haukace a kishinka, hummm wani sirrin saidai *RUHI* kawai". Dahaka ta koma bedroom d'in ta gyara, ta tartare kayanta a ledar ta ajiye gefe. Saidaifa wlhy bazata iya fitaba, to dawane idon zata kalli jama'a?. Nazeefa takira wai Dan ALLAH tazo. "Nazo namiki mi? yarinya kima sakko idan zaki sakko, ai gidan babu mutane sosai". " please Anty Nazeefa, ALLAH bazan iyaba inajin kunya". "Meyasa baki biyo mijinkiba, kinga shi gashina yanata gaisawa da dangi, kuma mai hotoma ya Jabeer ya kawo, gakuma 'yan jos nan su Anty Sadiya sun iso yanzunan". " da gaske Dan ALLAH Anty Nazeefa su Anaty furerane?". "ALLAH kuwa, gasuma Suna gaisawa da Yaya a falonki........." Ai tuni Ama....ta manta dawata kunya bare abinda yafaru da ita, dukda tanad'anjin zafi hakan bai hanata sauka dad'an guduntaba, wannan yasa duk kallon k'urillarka bazaka gane mitake cikiba. Ta wuce su anty maijidda Afalo. Duk dariya suka saka mata, har Aneesa kasa daurewa tayi ta dara, (a ranta tana kuma jinjina tsantsar k'uruciyar Amatallah). Anty maijidda tace "k'uruci kenan dangin hauka". Nanma dariyar dai akayi, kishiyar Anty maijidda tace nikam tana birgeni, ko kad'an batada damuwa Amatallah wlhy". Aneesa tayi murmushi tace, " gaskiya tanada hak'uri, tunda babu mai cewa tamasa wani Abu Mara k'yau a gidannan wlhy, ALLAH dai yacigaba dabamu zaman lfy". Gaba d'aya akace amin. Kowa yasan Aneesa tanada kishi, amma macece mai fad'ar gaskiya da mutunci idan taso, gashi bata iya wulak'anta dangin mijiba, ita kowa natane, duk sharrinka wlhy bazakace kazo gidan ta wulak'antaba, ko Fateema datake 'Yar uwarsu jininsu iyaka dai kenan, (kishine dai kam ba'a cewa komai a wajen Aneesa😂). amma kam tanada fada sosai wajen dangin mijinta dana kishiyarta, (zatayi kishi kam dake, amma danginki komai a mutumce)................✍🏻 🤩👎🏻 One luv my sweet Fan's *_ALLAH ka gafartama mahaifanmu_*😭🙏🏻 [1/16, 9:01 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_* *_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡 _{home of expert and perfect writer's}_ *_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉ _(Hattara matasa)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* ____________________ *_Number 32_* ____________________ Amatallah Na shiga ta cikukuye Anty Sadiya dake kujerar farko, "fad'i take oyoyo anutys d'ina, saikuma tasaki Sadiya takoma kan Anty furera da Asiya. Uncle dai murmushi kawai yake zubawa, yaji dad'in ganin Amatallah a farinciki, kullum haka yake fatan ganinta, bayason ta yawaita kukan maraici....... Maganar Anty furera ta katse masa tunani. " uch Amatallah, wai yaushe zakisan kin girmane?". "Babu rana Anty furera". Amatallah tafad'a tana dariya, suka had'a ido da Uncle, gira yad'an d'aga mata. Ta kauda idonta tana murmushin itama. Humm yau Amatallah fa ba'a magana, tana nanik'e da Aunty's d'inta sunata shan hira dabata labarin jos. Suma sunji dad'in yanda sukaga ta murje tayi k'yau, hakan ya nuna musu hankalinta ya kwanta, Alhaji Muhammad yarik'e amanar d'an uwansa, dukda sunga kamar batada walwala sosai, amma jin dad'in ganinsu Na k'ok'arin danne hakan, babu Wanda ya tambayeta damuwarta cikin su, tunda sunsan zaman aure saidai hak'uri, komin San da kukema juna dolene wataran a k'untatama juna, bakomai ake samu 100% ba. Ansha hotuna kafin Uncle yafice sabgar gabansa. Ita ta rakasu d'akin maijego Uwargida, taci gayunta cikin had'ad'd'iyar shadda popul, hakama jaririyar anmata gayu, Ummita tana nanik'e da ita, saikuma wasu daga cikin danginta dake cin abinci, wasu kuma hirarsu sukeyi. Duk suka gaisa a mutunce. Fateema ta kalli yanda Amatallah tayi k'yau cikin kwalliyarta, k'ok'arin danne kishinta tayi kamar yanda ta saba, tayi murmushi tana fad'in Anty yara kinyi k'yaufa, kamarma kece mai jegon". Murmuahi Amatallah tayi, ta 6oye fuskarta jikin Ummita dake kan cinyarta tace ''kai Anty kecema ai sarauniyar k'yau d'in, kinganki kuwa?". Dariya wad'anda ke kusadasu sukayi, abin kuma ya birgesu tamkar ba kishiyoyiba. Aneesa tashigo itama ta cakire cikin less jaa, tayi k'yau sosai, fleets takawo saboda bak'i, itama Fateema saida ta tsokaneta wajen yaba kwalliyarta. Aneesa ma ta danne zuciyarta da kishi tayi murmushi tana fad'in "lallaima Umman yara, bakiga kankiba kenan keda Antyn yara?, karfa Ku rud'a mana Abbun Abulkhairi wlhy". Sosai akeyin dariya a d'akin, kasancewar Aneesa a tsaye take sai kowa yaji maganar datayi. Sosai suka birge kowa, (har nimafa😉, sainaji ina sha'awar kishiya amma ta yini d'aya🤭😂lol). Cikin girmamawa Aneesa tafara gaida su Anty furera....... Amatallah ta katseta dafad'in " Anty Aneesa zafasuzo Ku gaisa". Murmushi Aneesa tayi (saboda taji dad'in wannan girmamawa, damafa Aneesa akwai son girma🤭😆) tace, "to shikenan, bara naje Na jiraku, dama an bani sak'o nabaku keda Umman yara". Atare sukace to, Fateema ta kalli Aneesar tana fad'in mu taso kenan?". "A Ku k'arasa tu kunna, nima akwai abinda nakeyi." Okey. Su Anty Sadiya sund'an dad'e a 6angaren Fateema kafin suje 6angaren Aneesa ma, anan Aneesa ta had'a musu abinci, takumace anan zasuyi sallah. Godiya sukai mata da k'ara yaba kirkin kishiyoyin Na d'iyarsu Amatallah. Aneesa da Fateema da Amatallah kam sunacan saman Uncle, Aneesa tasanar dasu cewa Uncle yace zaizo da bak'ine wai da la'asar, " yakuke ganin zamuyi kenan? Yace yakiraki baki d'agaba Antyn yara". Amatallah tace, "Na manta wayarne a d'akina mukaje 6angaren Anty". " okey, yanzu miye shawarar abinda za'a tanadar musu?". Fateema tace, "kai Abbun Abulkhairi ma dai akwai kwak'ule-kwak'ule, yanzu Dan ALLAH d'azun dazai fita ba'a gabanki Na tambayi kozaiyi bak'iba a jiye musu abinci?, amma yace a'a". Tayi maganar tana kallon Aneesa. " to yazamuyi umman yara, kinsanshi dai ai, yanzu kawai mu nemi solution, Dan yace bak'infa Na kunyane. Antyn yara bakice komaiba fa?". Murmushi Amatallah tayi, "to Anty mizance, Abinne Na Uncle saishi, yanzu kawai inaga ayi jaloff d'in shinkafa mana, ahad'a da tuwon shinkafa ko semo...., tunda ga masa za'a kawo daga idansu Innani kamar yanda naji su Anty maijidda nafad'a. Kobaiyiba?". " yayi kuwa sosai wlhy, akwai zo6oma, dukda muma munada namu mutanen, sai a d'an d'iba kad'an". ''Shikenanto, dama yace shehu zai kawo drinks da ruwa asaka musu k'ank'ara". Cewar Aneesa kenan. Amatallah tace, "to inhakane ahad'a da kunun aya". Fateema tace, " amma har ayi? Yanzufa biyu saura, kumafa 4 yace?". "Walhy har ayi Anty, aigasu Anty Nazeefa ga Asiya duk zasu taimaka mana da aikin". " to shikenan, gasuma Ramla nan, aikin mi sukeyi, duk saisu had'u ai su taimaka muku, (k'annen Fateema ne suma, amma duk da aurensu). Sund'an k'ara shawarta abinda zasu k'ara dashi sannan suka sakko k'asa. Da taimakon su Nazeefa suka had'a abinci da abinsha masu k'ayatarwa, harda suyar kaji, abinka da hannu dayawa dandanan asuka kammala, aka had'a komai a falon bak'i dakecan waje, komai yayi babu yanda za'ayi suji kunya kuma, harda alalan dasukayi Na jama'arsu duk suka d'iba suka ajiye, zuwa sannan gidan kam ya d'inke da jama'a. Su Amatallah duk aka canja kaya, komai tanayinshine kawai, amma jikinta duk babu dad'i, saidai Alhmdllh tana k'ok'arin daidaita tafiyarta, kasancewar dama ita mutumce mai sanyi, komai NATA a nutsuwa takeyinsa, su Anty Sadiya suna 6angaren Aneesa takasa ta tsare. Sai 6angaren Amatallah yazama Na yaran mata, su Nazeefa da k'annen Fateema, dadai yara-yaran matan danginsu, suna falon Ama sunata shan shargallensu ana barkwanci da tsokanar juna. Saigasu Fa'iza Goodness Rita dawasu k'awayensu Na makaranta da'ake gaisawa. Nanfa fili yakuma kacamewa da hira, kokad'an babu Wanda yanuna k'yama gasu goodness kasancewarsu ba addininsu d'ayaba, suma tun suna d'ari-d'ari har suka saki jiki anata hira da dariya. "Amatallah ta kalli Fa'iza cikin tsokana tace, " sannu uwar uku, ALLAH nazatafa bazaki iya zuwaba?". Hararta Fa'iza tayi cikin wasa tace, "a'a uwar 12 ba ukuba, kenifa garau nakejina ko reren gudu saimuyi ehe". " tab dawa zakiyi reren? Aiko zan barki a taku biyu harnaje Na dawo baki motsaba". "Hawaba yarinya, badan karnama Uncle d'inmu asarar sabon babyba danace muyi". " sabon baby a ina?". "A cikinki". cewar Safina wata cousin d'in su Uncle. Aiko nan tsokana tadawo kan Amatallah, ta dage tana kare kanta, nandai Ramla da Bilkisu suka shiga kare mata suma. Sun kacame da surutu wayar Amatallah nata ringing bata saniba. Anty maijidda tashigo tana magana da k'arfi yanda zasuji. " oh ni Hauwa'u, anya kuwa wani najin maganar wani a cikinku? Kunjikuwa yanda kuka cika mana kunnuwa? Amatallah mijinki nata kiranki a wayama baki saniba kenan?". Da sauri Amatallah ta kalli wayar, gata a gefenta amma batajiba, dayake wayar a silent take, kuma ta kifeta, mik'ewa tayi tana fad'in "ALLAH banjiba Anty". " yazakiji kuna wannan zuba tamkar rediyoyi, kizo to". Tsallakowa tayi tafito, Fa'iza da goodness da Rita suka kalli juna suna murmushin jin dad'i, dansunga sauyi ga aminiyar tasu, atunaninsu bazata mik'eba kai tsaye hakaba saita nuna jin kunya, (amma sai sukaga babu kowani alamar hakan tare da ita) basusan dauriya Amatallah tayiba kar ai mata dariya😂, (Dan tak'aru da hirar yaran matan da tund'azun akan gidan aure dama aketa surutun). A waje ta iskeshi shida Aneesa tsaye suna magana, kishi da haushi suka kamata, (ya ita da miji wata dafara zuwa wajensa😏) (Ama... An fara kishi kenan....lol 🤣). Danne zuciyarta tayi ta k'arasa, sannu dazuwa tamasa, ya amsa idonsa akan kwalliyarta data tafi dashi, maganar dasukeyi da Aneesa ya maimaita mata. "Abokainane gasunan kusan su goma, kokad'an banyi zaton zuwan nasuba, saida nafitane Alhaji Sabi'u ke sanarmin sunce zasuzo ganin baby, naji dad'in k'ok'arinku, ALLAH yaymuku albarka kunji my wife's". Atare sukace Ameen, kowa kishi nacinta a zuciyarta, amma a fuska bazaka ganeba, (Aneesa ma anfara k'ok'arin dannewa🤭😜). " yauwa to yanzu saikuma Fateema magana, idan mun kammala cin abincin saikuzo Ku gaisa kenan, akawo Aminatun. Sai daifa bahaka zakuzoba k'attin banza su ganeminku, asawo hijjabai". Daga Aneesa har Amatallah dariya sukai masa. "To ai gaskiyane, danma karsuce, ALLAH da har nik'af zance kusa, kunsan inada kishi, khadeeja Ce kawai bata gama saninaba, amma ahankali zaki fahimci hakan kema"., yay maganar da kanne mata ido d'aya. Murmushi tayi ta kauda idonta akansa. Sarai Aneesa ta gansu, kuma taji zafi sosai, harma saida fuskarta tad'an nuna, amma tayi k'ok'arin waskewa dafad'in ''ALLAH nagaji over". " sorry my neesa". Uncle yafad'a cikin tausayawa, ya kalli Amatallah ma yace sorry my best, nabaku wahala ko?". "Lah babufa komai Uncle, ai alsunan babynmuce, damunyi barci gajiyar zata ware ko Anty?". Murmushin yake Aneesa tayi, ta kad'an kanta kawai, amma mamakin Amatallah takeyi, dama tana magana haka? Dan tuni ta lura Amatallah miskilace. Ciki suka koma, uncle kuma yakoma wajen bak'insa. Kamar bayan 1hour yakirasu duk awaya akan suzo sun gama, kowacce cikin hijjabi tafito, Amatallah ta kar6i jaririyar daga hannun Fateema suka jera abin sha'awa suka nufi falon. Sallama sukayi ak'ofa, saida aka amsa musu sannan suka shiga. A mutunce suka gaisa, Uncle ya amshi Ameenatu a hannun Amatallah yabasu, fita sukayi suka bar musu ita tunda barcima takeyi. Duk saida suka gama ganinta suka saka mata albarka da addu'oi sannan aka maidota da alkairi mai yawa daga garesu. Alhmdllh taro yatashi lafiya, (Fan's barkanku da gajiyafa, lallai kunyima Uncle kara, irin wannan tururuwa haka, harfa gaza lissafoku nayi saboda yawa, to ALLAH yabar zuminci sai, kowa tasha kanwa saboda ciye-ciye damukayi, kar atashi da 2go da safe🤭😆, dansu o e naga har guzurin extra akayi a viva leda😜. Ba ruwana ban dad'i sunaba dai.🤫🤐🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀. To gida yayi lafiya, daga masu gidan sai Nazeefa da zaliha, sai anty maijidda da Anty badiyya yayar fateema itama Dan ba'a nan Kano take aureba, a jigawa, (yau tazo da safe, sikuma zuwa jibi ta koma. saikuma Anty Sadiya da Anty Furera da Asiya 'yan jos, saikuma inna Nafe. Kowa yayi laushi, da k'yar suka tak'ark'ara sukad'an share falo akayi morphing, wanke-wanke kan ko kallon arzik'i bai samuba, a babban kitchen suka killace kwanukan kawai, Yarama dakansu sukai wanka, suka kwanta, Dan suma sunyi laushin. Da k'yar Amatallah ta tak'ark'ara tadafama Uncle cus-cus, Dan bazata ita bashi sauran jagwalgwalon mutaneba. Dama su Anty Sadiya suna 6angaren Aneesa, tace annan zasu kwana, Anty maijiddah kuma da Anty badiyya zasu kwana 6angaren Fateema sai inna Nafi. Nazeefa Asiya zaliha suna 6angaren Amatallah. Abincin ta kinkima takai falonsa, da k'yar take taka step d'in saboda jikinta yak'ara tsami, harwani zazza6i takeji, ga bakinta d'aci yake mata, Uncle baikai ga shigowaba, Dan ba'a dad'e dayinma isha'iba, sukansu gajiyace tasaka kowa Neman makwanci bayan yayi salla. Duk abinda yake buk'ata ta ajiye masa danufin shikenan bazata dawoba, a 6angarenta zata kwana wajensu Nazeefa. Takuma tako step d'in dak'yar tadawo, wanka tashiga tayi da ruwa mai zafi sosai, tagasa jikinta da k'yau kozataji sassauci. Su Nazeefa duk suna baje a gado, Asiya Na waya da saurayinta, Zaliha da Nazeefa kuma charting sukeyi. Bawani dogon shiri tayiba, komai bata shafaba tasaka wando da Riga masu kauri, tad'an saka tirare. gadon tanufo tana fad'in "hajiyoyi a matsamin". Da mamaki Nazeefa da Zaliha suka kalleta, zaliha tace, " Anty Ama....ina kenan (dukda zasuyi sa'anni da zaliha Anty take cema Amatallah). "Nan mana..." Amatallah ta nuna gadon. Cikin zaro ido zaliha takuma fad'in ''yayanfa?". Hararta Amatallah tayi, "ni malama Ku matsa Na kwanta, ALLAH barci nakeji". " hhhh aikuwa badai a gadonnanba". Cewar Nazeefa tana k'ara bajewa sosai yanda Amatallah bazata samu wajeba. Asiya data katse wayar saboda mahawarar tasu itama tace, "lallaima Amatallah, ke in ance ki kwanta anan saiki kwanta? Shikuma bawan ALLAH fa......" Har Amatallah zatayi magana wayarta dake saman madubi tashiga 'Yar tsuwwa alamar kira. Juyawa tayi ta d'auka, ganin Uncle ne ta tunzuro baki gaba. Hakanne yasakasu Nazeefa kwashewa da dariya. "sai'a tattara atafi kiran boss". Cewar Asiya. Hararta Amatallah tayi kafin tad'aga kiran tasaka a kunne. " wai ba'asan nadawo bane? Kokuwa ba'a yayinane?". Uncle yay maganar cikin sassanyar muryarsa wadda taratsa 6argo da jinin Amatallah". Bubbuga k'afa Amatallah tashigayi ak'asa, cikin shagwa6a tace, "kai Uncle da bak'ifa". "ayaaa kina nufin saboda bak'i bazakizo ki tarairayeniba? Nifa bazan iya barci nikad'aiba my best, a tausayama bawan ALLAH mana". Yanda yay maganar a mariraice saiya bata dariya, ta to she baki tanayi k'asa-k'asa. "Oh dariyama kikemin ko?". Da sauri tace, " ALLAH uncle a'a, ammafa su anty furare fa........ "Karkimin k'arya, nasan suna 6angaren Aneesa, aina lek'o d'akin naji nagasu Nazeefa ne kwance akan gado, Dan haka nabaki 10minute's, kokizo da arzik'i konazo dakaina wlhy agabansu Na cicci6eki babu ruwana".... d'iff ya kashe wayar. Tamkar Amatallah ta FASA ihu haka taji. Tana zin6ure-zin6ure tasaka hijjabi yatafi, su Nazeefa suna mata dariyar wai dole a amsa kiran boss ko jiki yay tsami. Fita tayi tana balla musu Harara, tabugo musu k'ofar da k'arfi. Aiko suka kwashe da dariya, har tafara taka step tana jiyosu sunayi. Nimafa bara nayi kad'an Ama.....🤣, fans kuma kuyi 'Yar kad'an😂 Dan kar musa Ama..... Ta fashe, naga tacika fam🤭😂😜)................✍🏻 🤩👎🏻 *_ALLAH kajik'an iyayenmu_*😭🙏🏻 [1/19, 8:33 AM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_* *_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡 _{home of expert and perfect writer's}_ *_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉ _(Hattara matasa)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* ____________________ *_Number 33_* ____________________ Da sallama ciki-ciki tashigo falon nasa, baya nanma, tasan yana bedroom maybe. Zamanta tayi afalon tana tura baki gaba, kusan 2minutes bai fitoba tayi kwanciyarta a doguwar kujerar, agajiye take over, dan haka barci yad'an fara figarta. K'amshin turarensa daya cika mata hanci yasata bud'e idanun kad'an ta sauke akan fuskarsa, bud'e idon tayi sosai tana kallonsa. Ya sakar mata murmushi yana zama gefen kujerar datake kwance, "anya kuwa amaryarnan tawa ba raguwa baceba?". yay maganar yana shafa fuskarta da hannunsa na dama, na haggun kuma yad'orashi akan hannayenta dake saman cikinta. Tad'an lumshe idanun takuma bud'esu a kansa tana turo baki. " shagwa6a namiki k'yau my best. yanzu dai ya kikejin jikinki?". "Kwalkwal tayi da ido tana niyyar masa kuka, " ALLAH Uncle duk babu dad'i, bakinama d'aci yakemin". "Ayya sorry my best duk na girmane, inji yaya d'acin bakin yake". Yay maganar yana manne bakimsa kan nata. (Humm, Uncle wayo kenan🤪). Kusan mintuna 3 yana k..... nata, tuntana d'an dojewa hardai ta barsa yayi yanda yakeso, yad'ago yana kallonta da murmushi, " nimafa naji d'acin bakinnan my best, kodai muje muga doctor Shu'aibu? Amma bara nakumaji kad'an". Yamatso zaikuma had'e bakin nasu. da sauri ta yunk'ura ta tashi "Uncle wannanfa wayone wlhy". Ya tuntsure da dariya yana sakkowa k'asa kan carpet, itama murmushi takeyi tana zuba masa abinci. " my best! My best!! Wato kin gane wayo nake miki kenan?". "ALLAH kuwa Uncle ai na ganoka". ta tura masa abincin gabansa. " shikenan my best tunda kin ganoni, matso muci abincin". "No Uncle Na k'oshi, barci nakeji wlhy, nagaji". Yanda tayi maganar saita sakashi narkewa, ya jinjina mata kai kawai danya kasa magana. Tace, " Uncle naje Na kwanta?". Kai ya d'aga mata yanamai lumshe idanunsa da shafa gemunsa. Mik'ewa tayi tana neman k'ofar fita, da sauri yace, "my Best wai ina kike nufin zuwa?". " k'asa mana Uncle". Shiru yay kawai yana kallonta da hango zallar rashin wayonta, kusadashi ya nuna mata yace, "dawo ki zauna nabaki magani kisha kafin ki tafin". Batayi musuba tadawo ta zauna, azatonta maganin zai bata da gaske. shiru babu mai magana acikinsu, har yagama cin abincin, kwanikan yamatsar gefe yana fad'in Alhmdllh, ya kalli Amatallah dake gyangyad'i. Ya murmusa tareda jin tausayinta a zuciyarsa, yasan harga ALLAH tagaji d'in. TV ya kashe daduk kayan wutar, ya haska fitilar wayarsa ya sauka k'asa, Generator yaje ya kashe, ya maida NEPA dukda babu wutar, amma in case koda an kawo suna barci basai yatashiba. Amatallah da barci ya d'auka batama san ya fitaba, ya tadata tareda kama hannunta suka tafi bedroom d'insa, batace masa komaiba saboda barcin dake idonta, ya zaunar da ita abakin gado yabata magani tasha tana yamutse fuska, kafinma ya ajiye ruwan hannunsa hartayi kwanciyarta, gyara mata kwanciyar yayi yafara mata tausa ahankali, wani barci mai dad'i ya d'auke Amatallah saboda dad'in tausar datakeji. Saida ya tabbatar yamata yanda zataji dad'in barci sannan yabarta, yaymusu addu'ar barci ya rungume kayarsa. Nima akorikurar k'afafuna najawo zuwa wajen nawa boss d'in🤫. _washe gari_ koda Uncle yafita masallaci itama Ama... Saita sakko k'asa abinta, taredasu Nazeefa tayi salla, babu Wanda yace mata k'ala, bata koma barciba tanufi kichin Dan neman abincin Karin kumallo. Bata dad'eba Anty maijidda tashigo ta taimaka mata. Lokacin dasu Uncle suka dawo masallaci shida yara yaji motsi a kitchen amma baiyi zaton Amatallah bace, Dan haka yawuce samansa, wayam yagani alamun ta gudu, yay guntun murmushi kawai. Su Nazeefa suka fito suma suka fidda wanke-wanke, Anty badiyya da Aneesa kuma suka fara k'ok'arin tsaftace gidan, ganin haka su Anty furera kuma suka hau yimasu Sahib wanka. kasan Cewar aikin kowa Yakama saiya yimusu sauri, Dan danan suka kammala, gidan ya dai-daita. Bayan sun kusa kammala girkin, Dan kad'an ya rage Anty maijidda ta kalli Amatallah tana fad'in "yauwa maza kije kiyi wanka, kafin kidawo na had'ama mijinki saiki kaimasa daganan ki gyara masa 6angarensa, karnaga k'afarki a k'asa sai idan ya sakko zai fita". Amatallah tace " to Anty". Harga ALLAH tana kallon Anty maijidda ne tamkar Ammi agabanta, Dan ko'a shekaruma zasuzo d'aya da Ammi, ita kanta Anty maijiddan Dan d'anta nafari namijine kuma yarasu, Na biyunma namijine, amma da macece k'ilama tana shirin aurarwa kam. Duk yanda ta umarceta hakan tayi, dama yau tanason zuwa makaranta, tayi kwalliyarta cikin gown d'in atanfa, d'inkin Yamata k'yau, simple kwalliyarta tayi tamkar yanda ta saba, tad'an fesa turare sannan tafito. A falo ta iske su Anty maijidda tana zubama yara abinci, su Nazeefa ma suna zaune suna karyawa, gajiya tahanasu cin abincin dare, shiyyasa suka tashi da yunwa. Kitchen tashiga ta d'akko tiren abincin da Anty maijidda ta had'a mata, yaukam saitaji batajin kunyar kowa yaganta Dan zataje wajen mijnta. A hankali take taka step d'in tamkar bataso, tayi sallama a k'ofar falon kafin tashiga dukda ba'a amsa mataba, falonma babu kowa, ta ajiye tiren, falon tahau gyarawa batareda tashiga bedroom d'inba. Duk Uncle najiyo motsinta daga ciki, yana wankane. Tana shiga bedroom d'in yana fitowa, juyawa tayi da niyyar fita tabashi waje ya shirya yace, ''hii". Cak ta tsaya amma bata juyoba, k'arasowa yay gabanta yana kallon yanda rigar ta zauna ajikinta d'as, "my best shirinafa? Wazai mini?". Kad'an ta kallesa ta janye idonta dan ganin dagashi sai towel, murmushi tayi tana d'an Susar wuyanta alamar kame-kame, " Uncle ina kwana". Amsawa yayi yana murmushi, ya kama hannunta suka k'arasa bakin gadon, dolenta ta ajiye kunya gefe ta taimaka masa kamar yanda ya buk'ata, yay gayunsa cikin lemon green d'in boyal, yauma itace tamasa karin hula ta saka masa akansa, ya rungumeta yana fad'in "Thanks my heartbeat". Itama ahankali tace, "I... love... you my Uncle". Da d'ai-d'ai tafad'a tamkar mai koyan magana. Da sauri yad'ago kanta yana kallon fuskarta, "my best really!?". Tana murmushi ta d'aga masa kanta. Kuma rungumeta yayi yana fad'in Thanks you so much my heartbeat, I love you more". yakuma d'ago fuskarta yana bata tagwayen sumbata, yaukam Amatallah taga ikon ALLAH itadai, tana kallon Uncle d'in nata nadabanne acikin maza. Bayan sun kammala breakfast tace masa yau zataje makaranta. Yace ta hak'ura tunda dai su Anty Sadiya basu tafiba sai yamma. Baikuma dace tafita ta barsuba ai, gobe saitaje idan ALLAH ya kaimu da rai. Hakan dole ta hak'ura, aikam yini guda sukasha hirarsu, sai k'arfe biyu sukayi shirin tafiya, tabasu alkairin da Uncle yabata, itama tahad'a da nata, Fateema ma ta had'a musu kayan suna, Aneesama ba'a barta abayaba, tare suka fita dasu Anty maijidda, sukaje suka gaida su Ammi sannan Nazeefa tarakasu tasha suka hau mota. Gida kam yazama dagasu sai su, su Anty badiyya ma da inna Nafi suna kammala suyar Nama suka tafi. Amatallah da Aneesa suka kuma dagewa suka k'imtsa gidan tsaf, daganan Ama... takoma gefe tana kallon Aneesa data kasa zaune takasa tsaye saboda yau miji a hannunta yake. Duk abinda Aneesa keyi Amatallah k'arin ilimine a wajenta, tsaf take k'ara karantar komai da nazarinsa, tanaji a ranta itama lokaci yayi daza'a dama da ita. (😉lol.) ************ Alhmdllh, su Uncle sun sami hallarar inda zasu gudanar da meeting d'insu. Su 12 suka halarci wajen, dukda ba iyakarsu kenanba, akwai wad'anda suka yanki form kusan su 26, to amma su sun ware kan nasune amatsayin shugabanni wad'anda zasu tattauna akan kafa k'ungiyar, dukansu masu ilimine, kuma babu Inda zasu shiga ba'a dama dasuba a k'asar. Alhaji Sabi'u ya gudanar da addu'oi kafin su fuskanci abinda ke gabansu. An tattauna da mahawara mai zurfin gaske, sukace dole Uncle ne zai shugabanci k'ungiyar, Dan shine yafi cancanta da hakan, kodan k'ok'arinsa da k'yak'yk'yawar manufarsa. Ya nuna musu shifa baya buk'atar shugabancin, Dan haka abama Alhaji Sabi'u ko Alhaji Murtala mai daura. An dad'e ana tata6urza akan sudai shid'in sukeso, kuma harsu Alhaji Murtalan. Dolen dole Uncle ya kar6a wannan shugabanci, Alhaji Sabi'u mataimakinsa, saikuma Alhaji Murtala mai daura sakatare, saikuma wasu muk'aman dasuka biyo baya irinna ma'aji da dai sauransu. Tun anan suka fara wasu tsare-tsaren, kamar yad'a manufarsu ga matasan dakuma jawo hankalin masu zuciyar taimako domin zuba sadak'atujjariya a bitalmanin k'ungiya, saikuma bud'e wasu businesses k'anana dazasu tallafi k'ungiyar wajen samun kud'in shiga dadai sauransu. Anan take kowannensu yay alk'awarin bada gudunmawa dai-dai k'arfinsa, dan haka aka bama ma'aji damar bud'e Account da sunan k'ungiya dan a fara zurara kud'in dasuka tara, ansama k'ungiyar sunan *_YOUTH AWARENESS FORUM_*, bayan ankawo sunaye daban-daban dai suka tsaya akan wannan d'in. Uncle dake jawabi yabisu da kallo d'ai-d'ai yana murmushin jin dad'in had'in kan daya samu nasu, bayan yayi doguwar godiya agaresu yad'ora da fad'in "to Alhmdllh 'yan uwana, yanzufa saimunyi hak'uri da juna, muji muk'iji, mugani muk'i gani, karmu d'auka wannan yak'in namu zai zama mai sauk'i, dolene zamu fiskanci k'alubale daga matasan Kansu, dan basu ganin irin wad'annan abubuwan a yankinmu, sannan akwai marasa son gaskiya dazasu fara sukarmu, musammanma jam'iyun siyasa, amma wannan bawai damuwa baneba, dan mud'in bawai 'yan siyasa baneba, amma munason mukawo sauyi akan yanda siyasar kejan ragamar rugujewar matasanmu damu kanmu, inhar kace zaka tara al'uma koyin wani Abu mai k'yau da amfani arayuwa dolene kayita fuskantar k'alubale, wani mai dad'i, wani maicin zuciya, wanima harkaga yata6a iyalinka. abu nagaba shine mu tsaftace harshenmu, muringa sanin kalmomin dazasu fito a cikin bakunanmu, danfa ayanzu komai namu zaizamto abin ajiyewa ga 'yan jaridu dakuma al'umma, sai lokacin damuke hangen nasa ayi amfani da wannan a 6ata mana suna kocin zarafinmu. Saikuma mu kammu muji tsoron ALLAH karmu kasance munafukan juna kokuma fidda wani sirri Na k'ungiyarnan, yin hakan zai iya zama illa agaremu, muyi hak'uri da juna domin ALLAH, duk Wanda ya sa6ama wani yakirasa ya sanar dashi a fiskanci juna tunda mud'in ba yara baneba. a yanzun kiranyenmu zai farane daga kan matasa masu shaye-shaye, dan anfi samun nasara akansu wajen haddasa rikice-rikicen *SIYASA KO K'ABILANCI*, yanzu dai gashi an kad'a tamburan siyasa, kuma naga gangar shaid'an tafara aiki a jikkunan matasanmu, dan haka zama bai ganmuba kenan, zuwa nanda kwana uku saimuyi zama Na musamman akan wannan matsalar, mu tattauna da duba hanyar data kamata mubi koya kuka gani?". Gaba d'aya sunyi ma'am da zancensa, sunkuma yabama k'ok'arinsa, Alhaji sabi'u ma yatashi yay jawabi, daganan kowa daki-daki yayi nasa, kafin taro yatashi cikin addu'ar samun nasarori da fatan alkairi waa juna..............✍🏻 _kuyi manage da wannan, ban yini a gida baneba._ 🤩👎🏻 One luv my sweet fan's *_ya rabbi ka gafartama iyayenmu_*🙏🏻😭 [1/19, 8:33 AM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_* *_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡 _{home of expert and perfect writer's}_ *_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉ _(Hattara matasa)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* _gaisuwa da fatan alkairi, *Dan mom and Sani Ilyasu*_ 🤝🏻👍🏻👍🏻 ____________________ *_Number 34_* ____________________ Rayuwa tacigaba da tafiya cikin Nasarori da fuskantar k'alubale irinna rayuwa, wani mai dad'i wani akasin hakan, zuwa yanzu kam Amatallah tashigo gari, itama tazama 'yar hannu, yanda matan Uncle ke taku d'ai-d'ai da rawa da bazarsu haka itama takeyi, rayuwar gidan takoma ta competitions, kowa so take tazama gaba a zuciyar maigidan. Iya k'ok'ari Uncle yanayi akan matan nasa, k'yautatawa iya gwargwado yanama kowacce, baki isa kisan wadda yafi soba a zuciyarsa, dan kowacce takasance agabansa nuna mata yakeyi babu ya ita, wannan yasa kowacce takejin kanta on top. Duk abinda zakiyi mara k'yau agaresa bazaiyi gulmarki agaban 'Yar uwarkiba, sannan bazaici mutuncinkiba, Indai kun ke6e dagake saishi zaiyimiki kam, hakan yabada taimako Na musamman wajen hana kawoma juna raini a tsakaninsu, saidai kowacce tana tsantsar kishin mijinta, musamman ma Aneesa dabata iya 6oyewa, a salon iya taku kuwa sai Amatallah ta nunama Fateema bata iya komaiba, Dan ko agaban maigidan Amatallah bata ta6a nuna kishi ga 'Yar uwarta, har mamaki yakeyi, wani lokacin yakanyi wani Abu danyaga ko zata nuna 6acin ranta amma ko alamar hakan baya ta6a gani (dukda kuma tanajin haushin amma saita danne) wannan duk Anty maijiddah Ce ke d'orata a network😀. Sukansu su fateemar abin nabasu mamaki, Aneesa takansha yima Amatallah abu amma koda afuska bata nuna mata tasan tanayi balle ma ta 6ata ranta, duk sun rasa gane lagon Amatallah. Duk hanyar da Fateema zatabi ta 6atama Aneesa rai tasanta, amma takasa samun Na Amatallah, salon yarinyar Na bata mamaki da d'aure kanta, gashi kota k'udiri k'untatama yarinyar saita karya mata tanadinta ta hanyar son 'ya'yansu datakeyi, yanda Amatallah kema yaransu bazaka ta6a d'auka yaran kishiyoyinta bane, yanzu haka mah-mah (Aminatu) saita wuni a hannunta inhar batada makaranta. Amatallah kuwa dukda tana kishinsu hakan baisa ta d'auki damuwar k'untata musuba a zuciyarta, gaba d'ayama hankalinta nakan karatunta, ta dage sosai kamar yanda kullum Anty maijidda da Nazeefa ke bata shawara, ita saima suyi Abu sau nawa batasanma sunyiba, harkar gabanta takeyi basu isheta kalloba, a salon kulada mijikam hummm, sukansu sunfara zama 'yan kallo, to kullum Fa'iza tsaye take akan Amatallah wajen koya mata salo-salo Na kissar kama miji, hakama Anty maijidda, gasu Anty furera agefe, kowadai tausayinta yakeji, ga maraici ga zama da kishiyoyi wad'anda suka girmeta nesa ba kusaba. Nasarorikam ana samunsu fiyeda zaton mai tunani, Dan Uncle koda bai fito ya fad'aba musan Amatallah takafa bishshiyar gamji a zuciyarsa, wadda tasaki rassa da 'ya'ya tako'ina😉🤪. Fa'iza ta haihu kusan wata hud'u kenan, su Amatallah ansha sunan baby (Munirat). Fa'iza ALLAH ya raya mana to. A 6angaren Uncle ma abubuwa suna tafiya akan nasarori, yanzu haka suna rik'eda matasa masu yawa kusan 50 wad'anda shaye-shaye yafara ruguza rayuwarsu, suna kar6ar magani da horaswa akan wasu sana'oi. Saikuma masu lafiya wad'anda ayanzu haka suketa cuku-cukun sama musu wajen aiyuka a 6angarori daban-daban, sunkuma bud'e islamiyya daza'a ring a koyar da matasan ilmin addini da dabaru Na rayuwar, dukda k'arancin kud'i dasuka fara fuskanta hakan bai hanasu fara fad'ad'a ayyukan nasu zuwa wash local governments ba, musamman akan matasa 'yan shaye-shaye da had'a daba ta 'yan gani kasheni. Wad'annan nasarorinne suka maida Uncle d'in busy sosai, ga iyali ga ciwon baba dukda Alhamdllh akwai sauk'i, ga harkar kasuwancinsa da Aikinsa, idan kagansa dolene ka tausaya masa har wata rama yayi ta yawaita zirga-zirga. K'alubale kam suna fuskantarsa musamman wajen manyan k'usoshin k'asar, wasu suna ganin kamar wata jam'iyyar siyasa sukeson kafawa a kaikaice, suna yawanjin sukarsu da akeyi a gidajen redio ko talabijin musamman in ana hira dawani d'an siyasa. Kokad'an hakan baya damunsu, saima alkairi yake zamo musu, Dan yakansa wasu masu nagartatattun halaye Dason cigaban k'asar da kishinta sukan kawo Kansu cikin tafiyar domin a dama dasu suma. aifa kafin kace mi sai manufofinsu suka fara fitowa fili, ayanzuma basai sunyi kiranyeba matasan dakansu suke kawo Kansu saboda suma fatarar babu da yawon tazubar ya ishesu, masu kwalayen result a akwati saisuka fara lalubowa suna kakka6ewa danufo ofishin dasu Uncle d'in suka bud'e domin kar6ar k'orafe-k'orafen Masan, masu raunin kasuwanci ko rashin madafa ma gaba d'aya suma suka fara tururuwar gangamin shigowa wannan k'ungiya. Hummm hakanfa bak'aramin shankan su Uncle lamuran suka faraba, sunyi kiranye kuma an amsa harma amsawar tafi k'arfin bitalmaninsu, Dan ayanzu babu abinda sukafi buk'ata samada zunzurutun kud'in Shiga a tafiyar tasu. A 6angaren Islamiyya kam tagama cika mak'il da matasan da suke damuwa da raunin ko k'ishirwar rashin ilimin addinin Nasu su Kansu, malamai kuma magadan annabawa sunyima lamarin caffar fisabilillahi, dansu ajiye wasu daga cikin ayyukansu sun d'aura d'ammarar yad'a ilimi ga matasan koda hakan zai kawo mana raguwar wasu masifun, kullum nasiha da wa'azi maishiga jiki da 6argo shi Malaman kan zazzaga bayan kammala karatu a ajujuwanin dasuka kasance uku kacal, duk suncika harma sun batse ana Neman tallafin k'arin wasu. Tofa ahankali lamarin wannan k'ungiya yafara haskawa, taurarinsu suka fara haske, dattijai da iyaye mata suka fara d'okantuwa daganin 'ya'yansu a tafiyar suma, hakama k'ananu 'yan siyasa masu Neman madafin iko da jama'a suka fara shirin k'utse cikin wannan k'ungiya danufin samun mabiya a matasan, saidai kuma tuni su Uncle sukayi tsawar datasaka masu rawar k'afa a 'yan siyasar ja baya koyin likimo Dan tsorata da gargad'in su Uncle Na ik'irarin Suba 'yan siyasa baneba. Hakan kuma sai yaso zama k'ilu zata jawo bau, Dan masu ri6a66iyar zuciya kuma suka sami abun fad'a da kayayatu akafafen tazo mujita irinnan talabinjin rediyo da yanar gizo. Kunnan uwar shegu su Uncle sukayi da kowa, tamkarma basusan anayi dasu baneba, sai suka bar karnika NATA haushinsu sukama sunata aikinsu dukda bitalmali Na neman agajin tallafin wasu 'yan kud'ad'e a tafiyar. Amma abin birgewa su Uncle basukai wani k'orafi ga wani shahararre komai mulkiba, sai suka duk'ufa wajen baje hajarsu a kasuwa dawasu 'yan abubuwa dazasu kawoma k'ungiyar kud'in shiga koda babu yawane, aka kuma had'a hannu da matasan dasuka sami wasu k'ananun sana'oi a hannu ko aikinyi tasanadin k'ungiyar, haraji aka yankama kowannensu Na naira d'ari biyar akowane k'arshen sati, da wannan kuma za'a tallafi 'yan baya masu tasowa suma. A wannan tsakanin ba'a cewa komai akan Uncle da sauran shugabannin k'ungiyar, Dan kowanne yaji ajikinsa, hattada kasuwancin wasinsu saida yad'an girgiza musamman ma Uncle daya maida komai nasa Na taimako, to ALLAH dai gafurin rahimun yacigaba da rik'e k'ungiyar da ikonsa dukda k'alubalen kud'i dasuka tsinci kansu. a yanzu dai haka dole sun ajiye ranar ashirin gawata domin zaman meeting akan k'ungiyar da fatara irinta kud'i datake fuskanta, yazamana dole su k'yalla idanu wajen lalubo mafitar kubta koda cigaban cimma manufofinsu da burukansu. Yau takama Juma'a, kuma Amatallah ce da miji, dukda Aneesa ma tanata ahirye-shiryen ziyartar k'asarta ta haihuwa Dan ganin gida da danginta (Ghana). Bayan sun fito daga lecture ta k'arshe Rita da goodness sukayoma Amatallah da Fa'iza rakkiya dansu sami abun hawa. Tafiya suke suna zabga hira tamkar ba kusan a tare suka yiniba, Amatallah Na rik'eda muneerah wada tad'an fara woyo masha ALLAH. Sund'an dad'e tsaye kafin su sami abin hawa, kasancewar yau juma'a anata hada-hadar masallaci. Bankwana sukayi dasu goodness kafin kowacce tashiga napep tanufi gidanta. *********** Kusan atare suka iso da yara wad'anda aka d'akko daga makaranta, duk suka rungumeta suna mata oyoyo, itama cikin farinciki ta rungumesun kafin ta tasasu gaba su shiga cikin gidan. Babu kowa a falon, gidan shiru kamar babu mutane, watak'il matan gidan barci sukeyi kowasu uziri acikin d'akunansu. Yaran kowa yashige 6angaren Uwarsa, Amatallah ma jakka da takardun hannunta kawai ta ajiye ta cire hijjab tashiga kichin Dan Neman abincin rana. Tana tsaka da girki Fateema tashigo kitchen d'in, gaisheta Amatallah tayi kafin tace, "ina mah-mah?". " mah-mah tana barci aunty yara, ya makaranta?". "Wlhy Alhmadllh". Ruwa Fateema ta d'auka tafita, a bad'ini kuma bawai d'aukar ruwanne yakawotaba, tazagayone taga mi Amatallah ke girkawane, Dan tasan yau maigidan zai dawo hannunta, agida kuma zaiyi lunch saboda inya dawo sallar juma'a baya sake fita kuma. fita tayi tana d'an ta6e baki, caraf kuma suka had'a ido da Aneesa da fitowarta kenan daga 6angarenta, itama da alamar gulmarce ta fiddota, (hakan yazame musu tamkar al'adar gidan, ranar girkinki sauran matan idonsu nakanki, kowa sotake taga yanda kikayi idan mijin yadawo nata tamasa mafiyinsa😆). Kauda ido Fateema tayi tashige 6angarenta batareda ta tankama Aneesar ba, itama saitaja guntun tsaki tanemi kujera ta zauna a falon. Amatallah kanta Fateema na fita tarakata da harara dafad'in magulmata anfara ma mutane lek'en asirinne, aiko k'afafunku sagaji babu maiganin mizanyi saiyaje kula. Hohoho matan Muhammad Ahmad Labbo! Kuna shagalinku wlhy🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀😂. Har Amatallah tagama girkinta babu wadda tasake lekota, hakan kuwa yamata dad'i, tana tsaka da gyaran kitchen d'in tajiyo horn d'in boss, bata fitaba Dan tasan bama zai shigo da motar cikiba tunda zai sake fitane. Bata kuma jiyo horn d'in nasaba kuwa sai takun tahowarsa, ta ajiye moper d'in hannunta ta d'auraye hannun dad'an goge fuskarta tagyara zaman d'ankwalinta sannan tafito, a falo suka had'u harya shigo, har yanzu Aneesa Na zaune afalon. Ko kallo bata ishi Amatallah ba tanufi mijinta suna sakarma juna murmushi. Ta kashe masa ido d'aya yayinda sukazo gab da juna, murmushin yakuma mata, tawani kashe murya can k'asa yanda komin kusancinka dasu bazakaji mitaceba, tace, "barka da dawowa my jaan!". Kad'an ya rankwafo ya sumbaci la66anta, kafin yace, "yauwa my heartbeat!". Harga ALLAH Uncle baiga Aneesa ba, Amma Amatallah tanakan Sani, itama hannunsa takami ta sumbaci tsakkiyar tafin hannun. Ya wani narke mata yana fad'in my best karki kaini k'asa a falonnan fa". Jakar hannunsa ta kar6a tana wata shu'umar dariya, tai wani far da ido tajuya tana taku d'ai-d'ai, bayanta yabi da kallo kafin yafara takawa shima. Aneesa da zuciyarta keneman fitowa ta danne da k'yar tace sannu da zuwa dear?". Da sauri yakalli sashen da akayi maganar, cikin d'an kame-kame yace, " my Nessa dama kina falonnan?". Wani murmushin takaici tayi tace, "a'a yanzu nazo". tana gama fad'a ta harari Amatallah tabar wajen. Amatallah ma Harar tata tayi batareda tabari Uncle yaganiba balle Aneesar, suna had'a ido dashi kuma tasaki murmushi, " Uncle kafayima Anty Aneesa laifi". Yad'an yamutse fuska yana kallon Ama...., "laifinmi my best?". Step d'in tafara takawa tana murmushin mugunta dafad'in " saika shigo". Binta yayi da kallo kawai, a zuciyarsa yace zaki kasheni da salonki khadeeja, ked'in tadabance...... Fitowar yaran yasashi maida hankali garesu, harsunyi wanka anmusu shirin masallaci, duk suka gaidashi ya amsa cikeda so da k'aunarsu. ''Yauwa my sweet children's ku zauna kar Wanda ya6ata jikinsa naje nima nayi wanka karmu makara salla, ina Ummah?". Sahib yace, ''Abbu tana wanka". "OK, to nima bara naje nayi ko". A tare sukace to " Abbu ". Tunda yashigo falon mayataccen k'amshin turaren da Amatallah ke saka masa yabugi hancinsa, shak'a yayi ya lumshe idanu kafin yak'arasa bedroom d'in. A toilet yajiyo motsinta, dan haka yafara cire babbar rigarsa. Yana ajiyewa tafito itama, k'arasowa tayi inda yake, kowanne idonsa akan d'an uwansa, yana k'aunar yarinyarnan harma baisan iyakaba, sometimes idan tana Abu saita ringa d'ebe masa kewar Brother d'insa... K'ok'arin cire masa bottles d'in rigarsa datakeyine yasashi dawowa hankalinsa, tamkar wani yaro haka ya koma mata, itace tamasa komai hatta da wankan da shirin masallacin cikin milk color d'in shadda, ta fesheshi da turare, shidai kallonta kawai yakeyi, 'Yar k'arama da ita sai wayon tsiya, abaya yana ganin kamar Amatallah zatana cutuwa agidan saboda k'ank'artatrta da k'arancin wayo, amma a yanzu yakula koda za'a cuceta saidai tawani fannin amma bawajen kulawa da mijiba, ta kowanne fage tagama kwarewa, har yana mamakin tamkar wadda ake koyamawa, dukda har yanzu salonta Na nuna kunyarsa tana nan tanayin kayanta, (wadda kunyar tata nakuma sakashi a shauk'in k'aunarta) dan idan 'yan kunyar nakanta takan masa Abu tamkar ranar suka fara had'uwa amatsayin miji da mata, shikansa saiyanjin kamar ranar aka kawo masa ita........ Yanata zancen zuci har tagama kimtsashi tsaf. "Kayi k'yau my Uncle". tafad'a tana shafa fuskarsa. Hannun yarik'e ya sumbata, kafin yajawota jikinsa ya rungume tana shak'ar dadd'an k'amshinsa. Cikin sassanyar muryarsa yace, " ALLAH yamiki albarka khadeeja, yajik'ansu brother kinji". Tana murmushi ta jinjina masa kanta, kafin tad'ago tana kallon fuskarsa, "my lollipop bara nabaka ko fura kad'ansha mana? banason kafita da yunwa". Yanda ta narke masa haka shima ya narke mata, " no my heartbeat karmu makara fa, idan nadawo naci abinci kawai....." Bata bari ya k'arasaba ta tashi daga jikinsa tana tura baki gaba. Saurin rik'o hannunta yayi ya maidota baya yana fad'in sorry my beat karki fushi, haba Amintacciya 'ya daga ALLAH, banito nasha ko kad'anne". Tad'an kalleshi tana turo baki gaba, a shagwa6e tace, "really?". Gira ya d'aga mata kawai danya kasa magana. hannunsa takamo suka fito galo, ta zaunar dashi a kujera sannan tad'iba furar a frighte d'insa tasaka suga kad'an ta motsa, kusadashi tadawo, (hummm) mai makon ta zauna gefensa saita zauna a cinyarsa tana kashe masa ido d'aya. Wani lalataccen murmushi ya sakar mata, ya sak'alo hannunsa a k'ugunta, " my beat karfa kimin Squeezing da kaya nida zanje masallaci". Kofin furar tasaka masa abaki tana 'Yar dariya. amma batace komaiba. Haka taita basa furar saida ya shanye bai saniba, ta ajiye kofin a Center table tana fad'in Uncle kafa shanye tas". Bakinta ya sumbata, "yazanyi tunda 'Yar shagwa6a ta turkeni". " wato Uncle turkekama nayi ko? Shikenan munyima fad'a karka kumamin magana harka dawo masallaci ehe. Da sauri yakamota yana dariya, ya manne bakinsa kan nata. (Hummm dagananfa.....babu ruwana🤭). Da k'yar tasamu ya saketa yafice yana kashe mata ido d'aya da d'aga mata yatsun hannunsa biyu alamar bye bye. Gira ta d'aga masa itama tamasa alamar I love you da hannunta. Tsayawa yay cak yana kallonta, harya d'an juyo zai dawo takoma bedroom d'insa da gudu tarufo k'ofar, tasan inhar ya kamata bakinta saiyaci k'aniyarsa, gashi time d'in masallaci nakuma k'urewa. Sauka yay yana murmushi, dakumajin k'aunar Amatallah dake Shiga jininsa da 6argo. har yanzu yaran Na falo inda yabarsu, Shiga yay 6angaren Fateema suka gaisa, sannan yashiga wajen Aneesa itama, dukda tanata shamasa k'amshi bai damuba danyasan laifinsa. Yana masallaci amma dukkan tunaninsa naga Amatallah, burinsa kawai a idar Yakoma gareta............✍🏻 _Ama.... kina zamani, walla banga laifinkiba,😉 murd'a kanbunki dak'yau karki saka wasa🤸🏻‍♀😻🤸🏻‍♀._ 🤩👎🏻 One Luv my sweet fan's *_ALLAH ka gafartama iyayenmj🙏🏻😭_* [1/19, 10:20 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_* *_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡 _{home of expert and perfect writer's}_ *_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉ _(Hattara matasa)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* ____________________ *_Number 35_* ____________________ Kafin su Uncle su dawo masallaci Amatallah tagama had'a abinci a falon k'asa data kuma gyarawa ta kunna turaren wuta. wanka taje tayi, tsaf ta d'auki gayu cikin wata light popul d'in atanfa da ratsin pink sai bak'i kad'an ajiki, yauma dai kwalliyar bawata mai yawa bace, amma tayi d'as da ita, tasha d'aurinta mai k'yau, ga k'amshinta mai rikita Uncle dasu Aneesa yana tashi ajikinta. Zamanta tayi a falonta ta kira matan kawunta hafizu da kawu hamza Anty furera da anty sadiya sukasha hira abinsu, saikuma ta kira Asiya, suna tsaka da hirane tajiyo horn!. tashi tayi da sauri tana fad'in "ke 'yammata shugana yadawo sai munyi waya next time". bata saurari dariyar da Asiya ke tuntsura mataba ta yanke wayar, d'aukar k'aramin gyalenta tayi tasaka sannan tasaka takalminta flat kalar gyalen, saika rantse budurwace zata fita (😉lol). Gate d'in tabud'e yashigo sannan tarufe, motar tasa tanufo cikin takunta Na nutsuwa da sanyi, yara harsun fito, shikam yana zaune yana kallonta ta madubi yakasa ko kwakwkwaran motsi saida ta bud'e masa k'ofar, murmushi suka sakarma juna, ahankali ta furta "welcome sir!". kasa amsata yayi, saiwani mayen kallo dayake binta dashi, badan yaransaba da babu abinda zai hanashi rungumeta a wajen, yakan rasa tantance watafi wata iya ado acikin matan nasa? Dan kowa gwanace a dressing. ganin yana k'ok'arin fitowa tamatsa baya kad'an, wayoyinsa yamik'o mata sannan yafito, yara suka kwashi ledojin fruits da chocolates d'in da aka siyo musu sukai ciki. Ganin yaran sun shige yakai hannu zai kamota ta zille tana dariya, shima dole yadara yana fad'in " my best! rowar kanki kikemin? babu damuwa zan rama ai". Dariyarta tacigaba dayi tai gaba abinta, shima sai yabi bayanta yana murmushi. A faloma wasu taurarin yaci karo dasu, Dan tuni Fateema da Aneesa ma sunfito, kowacce cikin kwalliyar d'aukar hankali da birgewa, atare suka masa sannu da zuwa, ya amsa cikeda shauk'in ganinsu cikin ado, kowacce saida yakashe mata ido d'aya tareda mata alamar jinjina. duk sukayi murmushi kowacce najin kanta on top da tunanin itace zinariyar gida😀. Kallonsu yayi yace, "bara nad'an rage kayannan ko?". yay maganar yana k'yaftama Amatallah idon. Murmushi tayi dantasan miyake nufi. Saida yafara hawa steps d'in sannan tabi bayansa, suna shiga falo ya rungumeta, Dan yakasa hak'uri. " humm Uncle kai d'innan ko! ALLAH bakada dama". Yay guntuwar dariya da jawo hannunta suka zauna a kujera, tana saman cinyarsa "my best minayi kuma?". " humm babu komai, ai abin bana fad'a baneba. mika rok'omin a masallacin?". Kansa yad'aga sama alamar tunani, saiya kaleta yana k'ayataccen murmushi, "k'anwa na rok'o miki, naga gidannan kowa yanada k'anwa bandake, sainaga ba girmanki bane hakan, gara nayo amarya ta hud'u kema kisami 'Yar k'anwa ko? dama wata yarinya tanata bina a bayar...". 6ata fuska tayi kafinma ya k'arasa, ta yunk'ura zata tashi daga jikinsa.. Rik'eta yayi da sauri yana dariya, " ooh my best! Inakuma zakije? aiban gama fad'aba, Dan harda twins Na rok'o mana masu kama da brother". Murmushin takaici ta sakar masa, cikin dakewa tace, "Su Aunty's fa suna jiranmu da yara". Kuma fashewa yayi da dariya tareda k'ank'ameta ajikinsa yana fad'in oh god, my best! Kishinki mai ajinefa, kina burgeni over wlhy". Mintsininsa tayi a hannu tana fad'in "waya gaya maka kishi nakeyi?". ya saketa da sauri yana fad'in "Uchh!, my best wannan muguntarfa?". Yanda yayi da fusaka saiya saka Amatallah fashewa da dariya tana mik'ewa a jikinsa tace, " saika taho ". Yana kiranta amma ko waiwayensa batayiba tafice abinta. Kansa ya jingina da kujera yana murmushi, da shafa Inda ta mintsinesan, dan yaji zafifa, ahankali ya furta "oh my Khadee ked'in Special ce acikin mata". Can kuma Amatallah data fita dariya takusa kasheta, ganin idon Fateema da Aneesa duk yana hanyar saman, murmushi tayi ta k'arasa cikin falon, " Sorry my Aunty's mun shanyaku, wlhy Uncle". Fateema dai murmushi takaici tayi, Aneesa kuwa saitaja siririn tsaki tana kauda kanta gefe. Murmushi Amatallah ta kuma yi tafara had'a abincin a babban fleet, Dan yau tare takeson suci abinci su duka har yaran. Daga Aneesa har Fateema kallon mamaki suke mata, mizatayi da wannan abincin?..... Shikansa Uncle dake sakkowa kallonta yakeyi, ya canja kayansa zuwa dogon wando Na jeans da blue d'in T-shirt. Yana gama sakkowa tana gama zubawa, ta sakama kiwa cokali sannan ta kallesu, ''to bismillanku, Sahib, Saifudden Abulkhairi kutaho ina Ummita?". "Anty taje fitsari". Cewar Saifudden. Abulkhairi yace, " lah Anty, yau harda Abbu dasu momy zamuci abinci?". Kanta tad'aga masa tana murmushi. "Yau kuma tare family zamuci abinci kenan?". Uncle yay maganar yana zama. Amatallah tad'aga kanta alamar eh, kafin tace " wai musami albarkacin juna Uncle, suma yara suyi farinciki sunci abinci da iyayensu, kumama cin abincin tare yana k'ara dank'on k'aunar juna da zuminci mai k'arfi". "Gaskiyane my best! ALLAH yayi miki albarka". " Amin Uncle". Fateema da Aneesa dai sai sukaji gingirin, Dan sudai basu ta6a wannan tunaninba. duk suka danne kishinsu suka nuna goyen bayansu akan abinda Amatallah d'in tayi. Uncle yaji dad'in goyon bayan Nasu kuwa, shima duk yasaka musu albarka. yanajin dad'in idan wata acikinsu takawo shawara mai k'yau kowani Abu yaga sun taru sun bata had'inkai, bawai kishi yasasu gwaletaba. Abin sha'awa da birgewa sukaci abinci tareda 'ya'yansu a nuse kamar yanda suka horar dasu, family ya had'u abin zaakk'yau😉🤩. Bayan sun kammala Amatallah ta gyara wajen, daga nankuma sukayi zaman hira, yaran sunata wasansu sukuma suna hira su hud'u. dolene kagansu su burgeka, gasu cikin kwalliya, kuma kowa a nutse take hirar babu hantarar juna ko habaici wa juna irinnan kishiyoyi, dukda kuma kowacce kishin nacinta a zuciya, amma duk suka danne suke hira cikin son faranta ran mijinsu, shima kuwa cikin kulawa da soyayya yake amsawa kowaccensu, babu nuna wata tafi wata, nunawa yake duk matsayinsu d'ayane a zuciyarsa. *_(Wlhy Ma'aurata munada matuk'ar gyararraki a gidajen aurenmu, wani fannin saikaga laifin maigidane wajen tarwatsewar zaman lafiyar gidansa, saboda rashin adalci namiji agaban abokiyar zamanki saiya dizgaki da nuna tafiki matsayi a gunsa, hakan ba daidai baneba, inhar maza zasu gyara zaman takewar gidajensu suyi adalci wlhy sai ansami raguwar zafin kishi Na mata, Dan wani abun mazanne ke haddasashi ga zamantakewar matan, zakiga wata Uwargidan tanada sauk'in kai, to amma mijin yagama 6atata ga amaryar tunkan ta shigo gidan saboda son zuciyarsa, kunga koda ta shigo bazataga darajar uwargidanba, to mijin yanuna uwargidan tagazane shiyyasa ita yakawota, kokuma ita amaryar yadinga munafuncinta ga uwargidan Dan kawai yanason uwargidansa Dason faranta mata, saiya fara gulmar iyayen amarya akan kayan d'akin ko gararta ko kud'in daya kashe a aurenta kokuma yace iyayenta suka manna masa ita Dan anga yanada hali Kodai yayta 6ata amaryar itama ta hanyoyi dadama, koya zama MUNAFUKIN MATA a tsakaninsu hakan ba daidaibane, wlhy maza kusani akwai hisabi, kuma duk Wanda ya gagara adalci a tsakanin matansa aranr lahira zai tashi 6arin jikinsa shanyayye, kuma babu makawa sai an antayashi a wutar jahannama, idan kuma bak'in cikinka yasaka mace bin malamai da bokaye wlhy kaima Kanna da wani tsagi Na zunubi aciki, bawai inabin bayan mata su aikata bane, amma mafi yawan mata sukanbi malan tsubbu ko bokaye saboda rashin adalci da k'untatawar mazajensu, saikiga suna Neman hanyar 'yancinsu, wlhy maza kuji tsoron ALLAH. Tawani fannin kuma laifinmu ne mu matan, wai Dan muna kishiyoyi bazamu zauna hira da junaba, inma anci sa'a an zauna d'in zakiga mafi yawa hirar habaicine da gugar zana, shin wannan kishine kokuwa jahilci?, nifa azatona kishi shine gogayya wajen k'yautatama miji da Neman soyayyarsa shine kishi, bawai shirme tsakanina da kishiyaba, kawai muzuba competition kowacce ta nemama kanta 'yanci awajen Wanda ya ajiyemu, bawai mu zauna hassada wa junaba, Dan kishin yanzun hassada tafi yawa acikinsa wlhy, nabaku Assignment ku gwada salon kishin su Ama.... Kugani wlhy koda kad'anne aciki, na tabbata kobayan babu raina saikun tunani, Dan kishi baya hana abama abokiyar zama hak'inta Na matsayin 'Yar uwa musulma, akwai hak'k'in k'yautatama juna tsakaninku, akwai Na mutunta juna, wlhy karkuyi zaton ALLAH bazai muku hisabi akan zamantakewa ba kawai, kafinma azo kan cutarwa ga juna nabin malamai da bokaye, muguwar kirsa dan kawai miji ya tsani abokiyar zamanki wannanma zalincine babba, idan ance kiyi kissa bawai ana nufin ki cutar da 'Yar uwarki wajen 6atata wajen miji ba, hakan ba daidai bane, kowa tata ta fisheta kawai, kinemi fadarki Na nemi tawa, amma babu dalilin 6atanci da juna. ALLAH yasa mudace yakuma shiryemu baki d'aya, komai dai zamuyi mudinga tuna mutuwa mai zuwa babu d'an aike, kwanciyar kabari da tambayoyin cikinsa gaskiyace, sannan kuma Ubangiji yatanadi wuta da aljanna, kuma kowacce zata samu mazauna cikinta, sai muyi hattara karmu bari kishi aikin banza ya kaimu wuta, wanima kishin abin kaitaima maiyinsa kukane, dan mijinma zakiga wata bai damu da'itaba balle yasan muhimmancin kishinsa datakeyi, kullunma mahaukaciya yake kallonta, wlhy mata musan inda kemana k'aik'ayidai mu Sosa, dawanan shirmen kishin damuka maida jinin jikinmu gara muduk'ufa ga ubangiji domin ku6uta daga azabarsa, saifa ka shuka alkairine zakaga alkairin🤷🏽‍♀, shawara tarage gamai shiga rijiya🙅🏼)._* Basu bar falonba saida aka kirayi sallar La'asar, yatasa yaransa gaba suka tafi masallaci, sukuma su Ama...kowacce tanufi d'akinta dantayi. Koda aka idar da sallah saiya kwashi yaran suka nufi gidansu, tashin motarsa kawai su Amatallah suka jiyo. Hakanne yabama Amatallah damar shiya abincin dare, harta kammala tadawo falo inda Fateema da Aneesa suke zaune suna hira, zama tayi itama suka cigaba dayin hirar atare, dukdai bata wuce hirar rayuwaba da abinda ba'a rasaba. Uncle kam yana gidansu, su Abulkhairi sunata wasansu, shikuma suka tattauna akan maganar auren Jabeer da Nazeefa, harma baba yace shima Shehu kawai idan yanada matar aure a hannu ayi gaba d'aya a huta kawai. Uncle yace shikenan, hakanma yayi d'in, ALLAH ya tabbatar da alkairi. Nace amin. Saida akayi sallar isha'i suka shigo gidan, yaran kowannensu yay d'akin uwarsa, Uncle kuma yashigo d'akin Amatallah. Zaune ya isketa kan abin sallah tana addu'a bayan ta kammala karatun alkur'ani mai girma. ya zauna saman doguwar kujera suka shafa tare. juyowa tayi tana kallonsa, "Uncle sannunku da zuwa, sai yanzu ake ganinku?". Ya had'e hannayensa a waje d'aya " tuba nake my best!. Babane yarik'eni akan maganar aurensu Jabeer". "Lah Aure zaiyi ya Jabeer d'in?". " uhm, harma da Nazeefa da shehu". Tad'an zaro ido waje "da gaske Uncle?". " insha ALLAH my heartbeat ". " masha ALLAH, ashe munada shan biki kwanannan". Murmushi yamata yana d'aga kansa da lumshe ido. Tashi tayi tanad'e abin sallar da maida alkur'anin inda yake tana kuma nuna farincikinta, ta cire hijjabin tafita dan kawo masa ruwa. Babu dad'ewa tadawo, center table tajawo gabansa ta ajiye jug d'in data had'a kunun aya mai matuk'ar dad'i, kallonsa tayi yana kishingid'e a kujerar yana danna wayarsa, da alama wani Abu mai muhimmanci yakeyi. Bata katseshiba, bayan ta zuba masa a k'aramin cup saita zauna kusadashi kad'an a kujerar. d'agowa yayi ya kalleta suka sakarma juna murmushi, yad'an shafi kumatunta ya maida hankalinsa kan wayar. Batace dashi komaiba tad'an kwanta a jikinsa tana kallon abinda yakeyi, sak'onni yake amsawa a WhatsApp, da alama wad'anda suka shafi k'ungiyarsune. Kusan mintuna 15 ya d'auka yana amsa sakwannin sannan yakashe datar yazauna da k'yau. Kallon Amatallah yayi datuni tatashi daga jikinsa takoma kujerar gefensa tana game a wayarta. "My best badai fushi kikayiba ko?". Murmushi ta sakar masa, " Uncle miye abin fushi, suma sunada buk'atar lokacinka koyaya aii, nakawo maka abinci nan?". "Wayyo my best ni zanma iya cin abincinnan kuwa? Har yanzu cikina yakasa sauka". Langa6e kanta tayi gefe, " yanzu nan Uncle duk wahalar girkinnan danasha bazakaciba kenan?". Ya had'iye kunun ayar daya kur6a kafin yamik'a mata hannu alamar tazo. Babu musu tataso tazo, kusadashi ta zauna tana zun6ure-zun6ure, ya ajiye kifin kafin yajawota sosai a jikinsa, "sorry babyna mikika dafa to?". " tuwo miyar d'anyen karkashi". "Humm har kinsa yawuna ya tsinke my best, namiki alk'awarin da safe ki d'umama min zanyi break fast dashi". " da gaske Uncle?". "Yes my best". Daga nan tasaki jiki sukaita hirarsu cikin so da k'auna, sai wajen 10 yatashi zuwa 6angarensa. hannunsa tarik'e tana marairaice face. " ya yadai my best? ". " Uncle please mu kwana anan mana". Yay murmushi "tofs my best!, nan kuma? d'akinafa shi laifinmi yayi yau?". " nidai babu laifin komai, kawai anan nake sha'awar kwana". Yaja hancinta yana fad'in "hakan yayi my best, k'ilama ki samo mana twins yau....." "Kai Uncle nifa ba yanzu ba?". " kamarya ba yanzu ba?, sai yaushe kenan my best? " "Uncle saina kammala karatuna, duk yaushe muka shiga level 2". Shiru yad'anyi kad'an yana kallonta, ya sauke numfashi da d'ago ha6arta suna kallon juna, " my best kodai kinashan wani abune dan karki samu ciki? Please karkimin haka Dan ALLAH, inason ganin 'ya'yanki jinin brother d'ina danawa cakud'e awaje d'aya my best please ". Jikin Amatallah saiyayi sanyi, ta maida kanta ta kwantar a k'irjinsa " Uncle wlhy bana shan komai, banma ta6a tunani irin wannanba, kawai dai ALLAH bai kawo baneba, dama kaji nace inason saina gama karatu nafad'ane kawai wlhy, bawai har zuciyata bane, amma kayi hak'uri idan na 6ata maka rai". Murmushi yakeyi yana shafa bayanta a hankali, yaji dad'i sosai da ba wata kwaya takesha saboda gujema cikinba, ya sumbaci kanta yana fad'in ''ngd Khadija, bakimin kaifin komaiba, ALLAH yabamu masu albarka da tarin alkairi a yau d'innanma nake fata". Kuma cusa kanta tayi a jikinsa tana dariyar jin kunya, shima sai yayi dariyar kafin yasaketa yace tom ina zuwa, kiyi k'aton shirin k'ar6ar jikokin brother insha ALLAH. hannu tasa tarufe fuskarta shikuma yafita yana dariya...............✍🏻 Nima Uncle kad'an bani kunyafa🙈😆😜 _'yan Kaduna state nabaku wanga page k'yauta, saboda tarbar da kukaima baba buhari, kun burgeni ainun wlhy._ 😻😻😻😻😻❤❤❤❤❤👍🏻😀 🤩👎🏻 One Luv my sweet fans😻 *_ALLAH ka jik'an iyayenmu_*😭🙏🏻 [1/19, 10:28 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_* *_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡 _{home of expert and perfect writer's}_ *_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉ _(Hattara matasa)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* ____________________ *_Number 36_* ____________________ Da safe haka Ama... ta tashi jiki duk yana ciwo, ba k'aramar murza tashaba wajen Uncle a daren jiya, hakadai ta tak'ark'ara tayi break fast mai sauk'i, shikuma ta d'ind'uma masa tuwon, bayan ta kammala gyaran kitchen d'in da babban falo tayi wanka a gurguje tanufi samansa, tashinsa kenan a barcin daya d'an koma bayan sun dawo massalaci, toilet tawuce ta had'a masa ruwan wanka. Ya langyare mata akan bazai iya yi da kansaba, shi jikinsa ciwo yake masa, "jiya duk kin bani wahala my best". Idanu Amatallah tazaro waje, " Uncle wato nimace nabaka wahalar ko? nan k'asusuwana sai ciwo sukeyi tamkar naje noma, shine zaka dawo da abin kaina ma". Dariya yamata, "oh babyna zo namiki tausa saiki warware gaba d'aya". " wad'in? tabd'i, Uncle ni zakama wayo? ai idan ka ganni lahira kaini akayi, ni yauma nayafe kwannan wa Anty Fateema, ta had'a uku kawai". "Lallai yarinya kinma Isa, yau ma muna tare yini guda, namaso ace girkin naki yakama asabar da lahadine, humyim dakin fad'ama jama'ar jos". Cikin dariya tace, " Uncle!, koda yake ni kama tunaminfa, Anty Aneesa na wucewa nima zan had'a kayana sai jos, wata biyu zanyo". Wani kallo yamata na idan na kamaki saikin fad'i dawa kike. yashige toilet yana murmushi da cije le6ensa na k'asa. Itama dariyar tayi tahau gyaran gadon, kafin yafito tagama gyaran bedroom d'in tsaf takoma falo yafito, bai katse mata aikintaba yayi shirinsa da kansa, k'ananun kaya yasaka, Dan babu inda zaije, yana gida cikin iyalinsa yau. Cikin nishad'i sukayi break fast atare yau ma, daganan suka fito harabar gidan shan iska, yara suna wasan 6uya tareda Amatallah, Uncle da su Aneesa suna musu dariya, abinne ya burge Uncle yashiga shima, ganin haka Fateema da Aneesa suma suka shigo, akabar Siddiqa tanama Mah-mah wasa. Fateema ta d'aurama Uncle k'yallen a fuska aka rufe masa ido, daganan kowa yanemi wajen 6uya, Uncle kuma yafara lalubensu, daga bayansa Aneesa taja rigarsa, yajuyo da sauri yakai hannu zai kamata ta zille tana dariya, Amatallah ma ta ta6a hannunsa, itama ta zille masa, Sahib yazo gabansa yana fad'in "Abbu gani ka kamani". da sauri Uncle yajuyo inda yake shima, amma Sahib ya gudu, Dariya suketa masa suduka, shikuma yana bin sautin dariyar amma yakasa kama kowa, daga k'arshedai ya damk'i Saifudden, nanfa suka saka masa tafi da ambatar an kama Saifi! an kama saifi!!. Handkerchief d'in Uncle yacire yana dariya shima, Saifudden aka d'aurama sa, kowa ya matsa, shima ta6asa sukaitayi suna guduwa da dariyar yanda yake laluben san kama wani, Abulkhairi yazo ta6ashi ta baya ALLAH yabama saifudden ikon damk'oshi, shima aka d'aura masa, Abulkhairi baisha wahalar damk'e Aneesa ba shima, yahau dariyar yakama momy Yakama momy, su Uncle na tayashi da tafi, itama Aneesa aka d'aura mata, aiko da k'yar takama Ummita itakuma, Ummuta koda aka d'aura mata dawayo tad'an d'aga kad'an tana gani da ido d'aya, tashin farko ta damk'o Amatallah, itama aka d'aura mata, itama tafi shan wahalar kafin ta damk'o Fateema da Sahib lokaci d'aya, akadai d'aurama Fateema, sunta zagaya gida ana dariya Sam ta kasa kamo kowa, sai can tarutsa Uncle dayaja mata d'an kwali tayi azamar kama damtsen hannunsa...😂 Haka suka yini cikin nishad'i, daga wannan wasa su koma wancan har lokaci yaja, kowa yagaji suka shige ciki aka zube a falo ana maida numfashin gajiya. Amatallah tashiga kitchen ta had'a abincin rana, daganan kowa yad'an watsa ruwa saboda zufar dasukayi wajen wasa, sai bayan sallar la'asar Uncle yad'an fita zuwa gidansu. Yau ma haka suka kashe juna da soyayya shida Amarsa. Washe gari suka yini gidansu Innani suduka har yaran, koda suka dawo da daddare miji yakoma hannun Fateema, itama haka taita shagalin damk'e kayanta, Yakuma kar6eta tamkar ba ranar yarabu dawata macenba, ya nunu mata soyya mai tsayawa arai da tattalinta tamkar itakad'aice gareshi. Washe gari Monday, yara da Ama..... Duk suka tafi makaranta, shima Uncle yafice harkokin gabansa, kasuwa yafara zuwa ya gaggaisa da jama'a da duba yanda komai ke tafiya, sannan yad'an Shiga B.U.K, bai dad'eba yafito danufi tafiya, Amatallah ma batasan yazoba, tanacan sunata hirarsu dasu Rita bayan sunfito lecture a gajiye sunad'an hutawa kafin ashiga wata. Harya bud'e mota yaji ana masa sallama a bayansa, juyowa yayi batareda ya rufe k'ofarba. Yad'an had'e fuska Dan ganin yarinyar datake Neman takura rayuwarsa a kwanakinnan (zee), inhar zaishigo b.u.k saitazo wajensa, dukda bata fito fili tace tana sonsaba take-takenta sun nuna masa hakan. Canjin fuskarsa baisa tadamuba, ta gaisheshi cikeda ladabi. Amsawa yayi yana tambayarta ya karatu. Tace, "Alhmdllh ya iyali?". Bai amsaba yace, " yau ma tambayarce?". Murmushi tamasa tana gyaran tsayuwa, "eh to kusan haka, amma tayau tasha banban data ranar sir". " lallaikam, gashi kuma ni INA saurine" yay maganar yana kallon agogon hannunsa da gyaran babbar rigarsa ta farar shadda. "Babu damuwa sir, in ban takurakaba kawai kabani number d'inka, koda ta test message ne saina turo tambayar". Yad'an kalleta kad'an, sanye take cikin gown ta material bak'i da d'igon Fari, sai siririn gyalenta Fari data yafa akanta, doguwace babu laifi, sannan tanada haske sosai, kuma yakula 'Yar gayu ce, ko magana a yangance take yinta, zata iya Girman Amatallah koda da shekara uku ne ko biyu, kauda idonsa yayi batareda ya tankaba, ya d'akko card d'insa d'aya yabata sannan yashige motar. Cikin salonta tace, " INA godiya da wannan karamci, daka mini". Wani murmushi kin gundireni yamata yatada motar yatafi. Ta sumbaci card d'in tana wani lumshe idanu da shak'ar k'amshinsa daya mannewa card d'in sannan tabar wajen tana mai addu'ar ALLAH ya mallaka mata bawan ALLAHn nan. Nace hummm. Alhaji Sabi'u dake zaune gefensa Wanda soyayya tarufe idon zee ko ganinsama ita batayiba ya kalli Uncle d'in yana 'Yar dariya. "Mutumina kodai ta hud'uce?". Uncle yakuma dafe sitiyarin da k'yau yana murmushi, ''haba Alhajina ai ka tausayamin kaima, inani ina mata hud'u? Uku nan sun isheni, ni banima da kud'in aure a yanzu balle inda zan ajiye matar, kawai dai yarinyarce nima naga take-taken nata auren suka dosa". " a kawai kashiga kaima, indai kud'in aurene matsalarka ALLAH zai kawo". "Hhh lallaikam Alhaji Sabi'u, to aini yanzuma babu wani gurbi da wata mace zata samu a zuciyata, matana sun mamaye ko ina da ina, harma bana kallon matan dawani fasali, kainema yakamata kashiga ta uku kawai wlhy". " a to tunda abin kaina zai dawo abar maganar kawai". Dariya sukayi gaba d'aya suna cigaba da tsokanar juna har suka kai inda zasuyi meeting d'in nasu. Kusan kowama ya hallara su ake jira. babu 6ata lokaci suka fara abinda ya tarasu. Sun tattauna akan abubuwa masu yawa dasuke damun k'ungiyar sannan suka koma kan neman hanyar samun kud'in shiga, kowa yana kawo shawararsa. Alhaji Murtala yace, "toko zamuci bashin bankine mu kafa wasu sana'oi kafin muga abinda ALLAH zaiyi". "Amma Alhaji murtala bama tsoron gudun Matsala nan gaba? Idanfa adadin maida kud'in yayi bamu sami yanda muke soba akwai matsala kenan". " ito dakuma wannan, to'ai munada sauran kud'i mizai hana muduba wani kasuwanci mai saurin kawo kud'i". "Wannan shawarar tayi kam, toga wata hanya danake d'an shakkar fad'arta da". " wace hanyace? Kafad'a kawai kanka tsaye Alhaji Isa". Nisawa yayi kafin yace, "kwangilace dama ta gwamnati, tun kwanaki governor yamin maganar amma nad'ank'i bashi had'inkai saboda wani dalilina, to yanzu mizai hana mu kar6a amatsayin k'ungiya, ni dama banason amsane alokacin gudun gutsiri tsomar 'yan siyasar k'asarnan". Uncle ya jinjina kai yace, " yayi sosai, yanzu saikamasa maganar kenan?". "Shikenan, saimuje a k'ungiyane to, zan sama mana damar ganinsa kenan". " okey shikenan to". (Alhaji Isa sirikine ga governor, shiyyasa yakeda lasisin ganinsa cikin kwanciyar hankali akuma duk sanda yaso, yak'i kar6ar kwangilar ne abaya saboda gudun surutai na jama'a, shima kuma ALLAH yaymasa rufin asiri dai-dai gwargwado, kuma yana bada muhimmiyar gudunmawa akan k'ungiyar, da kud'insa dakuma aikin kai da kai dasuka saka Kansu). Sun dad'e suna kuma tattauna wasu hanyoyin kafin su tashi kowa yakoma kan harkokinsa. Uncle dai kasuwa ma yakoma. *********** *Bayan sati d'aya*. Wannan karon kam a d'akin Fateema yagama kwanakinsa saikuma Aneesa ta kar6esa, randa zaibar wajenta ne kuma ranar tafiyarta Ghana, dayake anma yara hutun school, shiyyasa tatafi harda Sahib da saifudden da Uncle dazai mata rakkiya ya kwana biyu ya dawo. Suntafi sunbar Fateema da Amatallah da kewa, duk saida suka had'a tsaraba suka bata ta kaima danginta. ta nunamusu jin dad'inta da godiya agaresu, shima Uncle yaji dad'i sosai, da kumajin k'aunar matan nasa sosai a ransa. Sunsha hira harda Nazeefa data zo Dan tayasu zaman kwana biyu kafin Uncle ya dawo. Dangin Aneesa sunji dad'in ganinta, dan haka aka musu tarba ta musamman itada boss d'inta, sai haba-haba akeyi dasu. Kwannan Uncle biyu kuwa ya dawo bayan ya zagaya dangin Aneesa yamusu alkairi dai-dai k'arfinsa, yabarota itada Saifudden da Saheb da Siddiqa, yasha dai shagwa6a randa zai taho wajen Nessar sa, haryaji tamkar karya taho ya barta. Hakadai yataho cikeda kewarsu. yakumazo ya iske wata tarbar ga Amatallah wadda ta mantar dashi kewar Aneesa. Rayuwa tacigaba da shurawa, da gari ya waye sai dare yayi, saikuma wata safiyar. Ansaka ranar auren Jabeer da Asiya k'awar Amatallah, ashe dama tun a wajen bikinta suka jone, Amatallah tayi murna sosai, koba komai tasamu 'Yar uwa akusa, Nazeefa ma an saka tata ranar da saurayinta Mubarak, sai shehu da zaliha k'anwar Fateema, wata 5 kacal indan munkai da rai. Governor yabasu damar ganinsa ranar Monday 11am, dan haka suka tsara masu zuwan su 5 kawai. Uncle, Alhaji Sabi'u, Alhaji murtala, Alhaji Maina saikuma shi Alhaji Isa d'in. ********* Sun sami tarba mai k'yau daga governor dan yanajin dukkan ayyukansu na alkairi, kuma duk d'insu yana musu kallon mutane masu mutunci da sanin mutuncin jama'arsu, sunci abinci a tare kafin sushiga abinda ya kawosu. Governor yayi murmushi tareda jinjina musu "tabbas kun burgeni sosai, kuma ina marhabin da wannan k'udiri naku, nakumayi alk'awari taimaka muku nima nasaka hannu a tafiyar domin cigabanmu muda yankinmu, wannan taimakon bata fuskar SIYASA zanyishiba, zan yishine amatsayina nad'an k'ungiyar, kuma atake anan nima za'a bani form nacike dan zama a member na k'ungiya". Atare sukayi na'am da nuna farincikinsu. Yacigaba da fad'in " ga shawara, mubar maganar kar6ama k'ungiya kwangila domin neman kud'in shiga, dan hakan zaibama wasu damar yad'a farfaganda na nuna k'ungiyar SIYASA ce, bayan kuma naji mafi yawan bayananku na nuna kuba 'yan SIYASA bane, bance kud'in dazan bada zasu rik'e k'ungiyarba, amma zasu taimaka sosai wajen tallafa k'ungiyar takafa wasu sana'oin dazasu ringa kawo kud'ad'en shiga, sannan nayi alk'awarin saka matasan wannan k'ungiya a guraben aiki masu yawan gaske, dakuma guraben karatu awasu jami'oin arewaci da kudanci, wad'anda basuda buk'atar karatun kuma zamu tallafa musu da jari a gwamnatance, ina fata kun gamsu da hakan". Duk mun amince mai girma gwamna, fatanmu ALLAH yashige mana gaba, yakuma cigaba da dafa maka acikin ayyukanka na alkairi, ALLAH yayta kawo mana shuwagabanni irinku masu zuciyar zinari a k'asarnan". Dariya governor yayi, "Alhaji Muhammad Ahmad Labbo kune yakama ayi addu'ar yawaitarku acikin al'umma, dankune zinarai masu zuciyar diamond, da yankinmu sunada irinku tuntuni daba a sami damar kassaramu irin hakaba, ALLAH yak'ara muku tsawon rai da lafiya". Duk suka amsa da amin, Uncle dai 'Yar dariya kawai yayi, azuciyarsa yace amin d'in. Kafin subaro suka bama governor form yacike, shima saida yabiya naira dubu d'aya kamar kowa, sannan yarubuta musu zunzurutun kud'in na gudunmawarsa, suka rabu akan yana jiran takardun matasa d'ari biyar, dan nema musu aiki, damasu neman gurbin karatu, saikuma masu sana'oin hannu. Sunyi godiya sosai da k'yak'kyawar addu'a agareshi, suka baro gidan cikin d'unbin farinciki da yabama halin dattako irin na wannan governor. ****** Watan Aneesa guda tadawo Nigeria, cikeda abubuwan tarin alkairi daga family nata, tsaraba kowa da sunansa. Daga Fateema har Amatallah sunyi kewarta, dan haka ranar dawowarta sukai mata tarba ta musamman, itama tayi kewar tasu, abin sha'awa suka rungume juna cikin nuna d'okantuwarsu. Mai gayya mai aiki kam aibama a maganar irin kewar Aneesar dayayi, ranar kam su Ama... Sai suka zama 'yan kallo dan Aneesa a sabuwar amaryarta tazo.😉 Rayuwa tacigaba da shurawa, su Uncle matsalolin sun ragu musu, dan yanzu sunada kud'in a hannu, ga governor yacika alk'awarinsa na tallafawa matasan da guraben aiki dana karatu, sai k'ananun sana'oi na hannu, wad'anda kuma sukeda sana'oinsu aka kuma musu wani tsari na taimakonsu, kafin kace mi ayyukan wannan k'ungiya sun ratsa birni da k'auye, harsun shiga wasu jihohin arewacin k'asarnan, inda su Uncle suka wakilta amintattunsu dake a jihohin. Abin kunya abin bak'in ciki sai wasu many an k'asar 'yan SIYASA da wasu yankuna na K'ABILUN kudanci suka fara sukar wannan KUNGIYA, da kiranta 'yan rajin raba kan matasan K'ASA, hakan baita6a damun su Uncle ba, dan ayyukan nasu sunfara fad'ad'a zuwa wasu yankunan na KUDANCI, dukda basu samun goyon baya sosai agaresuba, sukan nuna K'ABILANCINSU akan manufofin k'ungiyar kai tsaye. Saidai kuma abinda zai birgeka matasan dake cikin halin hau na rayuwa sai suka dunga danno kai abinsu, suka ajiye maganar wata SIYASA ko K'ABILANCI agefe guda, Kan kacemi suma 'yan kudancin sun fara k'arfi acikin k'ungiyar. Hakan bak'aramin tada hankali wasu 'yan SIYASA yayiba, dan yanzu matasan dasuke sakawa a BANGAR SIYASA da basu kwayoyin maye da makamai sunfara gagararsu, ganin matasanma yafara musu wahala, ba'a cika k'ofar gidansu neman MAULA, bare su sami damar hura hanci da watsa ma 'yan tsaki tsaba. Idan sun taro matasan nan sukuma saisuyi can, sunce yanzu sun daina dafama k'artin banza baya, su turasu sai mota tatashi ko d'ani a gagara basu, saima akoma ana zaginsu da fad'a masu suna 'YAN TA'ADDA, to wannan lokacin yawuce yanzu. Alhamdullah anyi za6e lafiya kuma angama lafiya, dukda zuwa yanzun su Uncle basu gama samin kammala kan matasanba suma sun taka rawar gani a za6en, dan sun nusar da matasan wad'anda yakamata su za6a dansu tallafa musu. Hakan kuwa ya razana 'yan siyasar, dan haka bayan duk sun d'are muk'aman sai suka fara jan matasan a jikinsu ana basu wasu manyan muk'amai. Hakan yabama su Uncle damar cigaba da yad'a manufofinsu dakuma dunk'ule matasan a waje d'aya, suma Kansu gwamnatocin sunyi k'ok'arin bama su Uncle wasu muk'amai amma su Uncle d'in suka nuna basa da buk'atar hakan, su aikinsu dabanne. 'Yan siyasarfa sun fara canja takunsu akan matasan k'asar dan sun kula zuwa yanzu kan matasan yagama waye, bakowanne raini zasu d'aukaba, kuma suna son komawa za6e nagaba, Wanda take-taken matasan yana k'ara ankarar dasune akan sushiga hankalinsu, inba hakaba kuma su antayoka k'asa daga kujerar taka. A gurguje please😎. *_3 years ago_*...............✍🏻 🤭🙆🏻😂 Karfa kuyi magana🤐🥴 🤩👎🏻 One luv my sweet fans. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻 [1/21, 6:14 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_* *_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡 _{home of expert and perfect writer's}_ *_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉ _(Hattara matasa)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* ____________________ *_Number 37_* ____________________ Duniya mai gudu da sauri. da dare yayi saikiga gari yawaye, sai marece, duniya nata zabga gudu tamkar iskar guguwa. Abubuwa da dama sun faru acikin shekara ukunnan, ciki harda auren su Nazeefa, yanzu haka Asiya matar ya Jabeer ta haihu d'anta Namiji Ahmad suna kiransa da sunan (Farhan) itama matar Shehu Zaliha ta haihu d'iya mace Hafsat, Nazeefa ce dai ALLAH bai kawo dawuriba, saima yanzu takeda cikin. *_Gidan Uban gayya kuwa Uncle_* abubuwan sai sanbarka, dukda ansamu marasa dad'i damasu dad'inma, sunan sunata kishinsu kamar yanda suka saba, tattalin mijinsu kam sai abinda yay gaba, haka shima soyayya yake nuna musu tamkar babu gobe, Aneesa ma tasake haihuwar d'anta Namiji Abubakar Sadiq, harma yayi wayo abinsa. Amatallah dai har yanzu babu labari, tunma abin baya damunta harya d'an fara damunta, badan tana samun hantara daga mijin ko abokan zamanta ba, a'a tana burindai itama taga jinintane, tananan tanata karatunta, saidai yanzu kam daga ita sai Fa'iza da Goodness wadda sanadin zama dasu Amatallah d'in takar6i musulinci awata ranar juma'a data gabata, shekara d'aya kenan, tace d'abi'un su Amatallah Na matuk'ar burgeta, tunda suke tare basu ta6a nuna k'yama agaresuba, sun d'aukesu tamkar 'yan uwa Na jini, gasu sunyi aurensu suna gidajensu kuma suna karatu, hakan na matuk'ar birgeta (Dan Fa'iza ma takuma haihuwar d'a Namiji Salim) tunranda Goodness (Aysha) takar6i musulinci Rita tafara jabaya dasu, daga k'arshema tadaina shiga cikinsu kwata-kwata, wai karsu mata tsafin dasukama Goodness itama tazama Musulma, sunta jawota ajiki da nuna mata sufa basu tilasta Goodness tabi addininsuba, kuma ba tsafi sukai mataba, ALLAH ne kad'ai ya k'addara tanada rabon hakan, amma Sam Rita tak'i fahimtarsu, bilhak'k'i tana a kan bakanta Na asirine yasa Goodness komawa addinin musulunci, (wa'izubbillah). Lokacin dasukaje level 4 aka rarrabasu fannoni daban-daban na karatun likitanci, sai Rita takuma nisantarsuma gaba d'aya, da Amatallah da Fa'iza da Aysha (Goodness) fanni d'aya suka d'auka, sun zarce medicine 6angaren mata (Gynecologists), Rita kuwa saita koma 6angaren ido (optometry). A yanzu haka su Amatallah suna cikin asibitin AMINU KANO TEACHING HOSPITAL suna cigaba da karatunsu, tsakaninsu da Rita hello hii ne, shima saita gadamar amsa musu, tamafi jin zafin Aysha (Goodness). Itakam ko'a kwalar rigarta, harkokinta takeyi, dukda ta fuskanci matsaloli sosai ga danginta saboda musulinta datayi, daga k'arshedai wasu daga ciki suka fahimceta, amma sunce dolene tabar family d'insu, tundaga nan tadawo Kano ta sanarma su Amatallah, Amatallah tasamu Uncle ta sanar masa komai, dakansa ya buk'aci ganin Goodness, bayan yakumajin tabakinta yace ta tattaro kayanta tadawo wajen innani, bayan yama iyayensa bayanin komai gameda ita, baba yace tadawo nan gidan dazama tunda dama su kad'aine yanzu a gidan, sai gwaggo rakiya data dawo tana d'ebe musu kewa, (dama mijinta yarasu tuni, yaranta mata kuma biyu duk sunyi aure). Wannan shine silar dawowar Aysha (Goodness) gidansu Uncle, Innani tarik'eta tamkar 'Yar cikinta, duk wata hidima kuma Uncle namata tamkar su Nazeefa, dukda haka takanje Kaduna ta gaida danginta, kuma wasu basa sakar mata fuska har yanzun, bata damuwa kokad'an, saima addu'a datake musu ALLAH ya ganar dasu suma, dan Islamiyya Uncle yasamar mata take zuwa, agida kuma innani Na kuma tunasar da ita, gakuma su Amatallah agefe suma suna bada tasu gudunmawa, sosai hankalin Goodness ya kwanta taketa karatunta dakuma rik'e addininta Na islama, Dan batada matsalar dangi tunda gasu Uncle sun kwaranye mata wannan bak'in cikin. A 6angaren k'ungiyar su Uncle kam saidai muce Alhamdullahi, Dan tazama gawurtacciyar k'ungiya datake gogayya da manyan k'ungiyoyin duniya, sunyi k'arfi a arewa fiyeda zaton mai tunani, ayyukansu sunshiga lunguna da sak'o Na birni da k'auyika, hakama kudancin, dukda suna fuskantar ra'ayin rik'au Na *SIYASA KO K'ABILANCI* hakan baisa sun nuna gajiyawarsu da kiranye ga matasanba, sunkuma cigaba da tallafama matasan sosai. Zuwa yanzu Kungiyar ta wawashi wasu manyan masu fad'a aji nak'asar, tundaga kan malamai har zuwa attajirai da wasu k'usoshin gwamnati, dukda haryau suna kan ak'idarsu ta suba 'YAN SIYASA baneba, dan komin k'arfin mulkinka Baka Isa kazo musu ta fuskar SIYASA su kar6ekaba, SARAKUNAN GARGAJIYA ma ba'a barsu abayaba, dama sune sukafi cancanta suzamto a tafiyar k'ungiyar, Dan ta hanyoyinsune za'a iya gamsuwa da zak'ulo matasan da tallafa musu. Nasarorin k'ungiyar sunkuma ha6akane ta dalilin wani tsari da Uncle yazo dashi Na kowanne matashi daya samu tallafi daga KUNGIYAR ya taimaki matasa uku dabasu sami tallafinba, koda ta silar masa hanyane nasamun tallafin k'ungiyar, idan kuma kai k'arfinka yakai ka taimakeshi da aljihunka. Wannanfa takuma kawo haske da dakuma tallafawa lamarin matasan, shaye-shaye da dabar siyasa sunfara zama labari (dama mafi yawa talauci ke sanyasu aikatawa), ga islamiyoyi Na addini da Matasan suketa sauke alkur'ani da fahimtar wasu littatafai, harma abin ya ha6ak'a, kungiyar suna fidda matasan zuwa k'ashen SAUDI ARABIA domin k'arin fad'ad'a ilimin addinin, (to wani abun dayawa jahilci nakawoshi, musamman matasan Na yanzu da ilimin boko yafi tasirantuwa a ransu fiyeda Na addinin) to Alhamdullh, sanadin wannan taimako Na bud'e islamiyoyi saiga abubuwa dayawan gaske sun canja salo, tarbiyyar matasan da kulada tarbiyyar k'annensu, biyayyarsu ga iyayensu dama dattijai Na sama dasu, (lallai ilimin addini haskene, kuma shima daza'a tsayama Matasan k'asarnan saimun samu sauk'i wasu abubuwan Dakuma gyararrakin gidajen aurenmu dasuke da rauni yanzu). 😂Baku tambayeni labarin zee ba?. Tunda tasami Number sa tafara addabarsa da yawan message, yana gani amma baita6a maida hankalinsa ba, yasha kuma shiga bayaro tazo ta gaisheshi, bawani sakar mata fuska yakeba, amma hakan baisa tagaji da bibiyarsaba. Dayake wahala bata ishi zee ba kusan shekara uku kenan tanata k'ok'arin yad'a manufarta, dukda tanada d'unbin samari masu sonta, amma ita zuciyarta Uncle takeso. zuwa yanzu kuma yakan d'aga waya idan ta kirashi, shiba k'aramin yaro baneba, shiyyasa bai ta6a hantarartaba kocin mutuncinta, da wannan damar zee take amfani tana kuma cusa kanta gareshi. Duk abinan dake faruwa Amatallah bata ta6a ritsasuba balle kuma su Aneesa dake gida, zuwa kuma lokacin Zee tasan Amatallah matar Uncle ce, harma yanada wasu matan, amma dukda haka bataji sonsa yaragu a rantaba ko kad'an. Nidai nace humm.😎 ******* **** ****** Yau takama Alhamis, girkin Fateema ne kuma, kusan 5pm Uncle yakira Amatallah tana Asibiti. Cikin kwantar da murya tamasa sallama, ya amsa cikeda shauk'i. Ta marairaice murya tamkar zatayi misa kuka "Uncle ALLAH yau nayi ti6is saboda gajiya". "ayya my heartbeat sorry kinji, gashi banida damar miki tausa yau, saboda nimai tsadane a gareki". Kukan shagwa6a tasaka masa tana bubbuga k'afa da fad'in "hakama zakace ko? shikenan munyima fad'a babu ruwana dakai daga yau, kuma wlhy nima namaka tsada yau harma sati biyu". Aysha da Fa'iza suka tsaya kallon ikon ALLAH, itakam tama manta dasu a wajen. Daga can Uncle yace, " rufamin Asiri my best, wasafa nake miki, nimai arhane koda yaushe agareki, sati biyu, aikafin kigama fushin natafasa Na k'one a tunkunya". "Garama ka tafasan, ni karma ka sake kirana sai anjima". " please my best na tuba, barama Nazo da kaina na d'aukeki idan kin gama". "Aini ko kazo bazan bikaba, Aysha zanbi wajen Innani zan kwana ma". " wayyo babie na, kinaso namiki kuka kenan? koda yake nima saina kwana tsohon d'akin jabeer nima". "Anty fateen fa?". " sainace mata kece kika jani". Dariya Amatallah ta k'yalk'yace dashi, tace "ALLAH ya shiryeka Uncle, nidai babu ruwana wlhy". "Nima ai babu ruwana d'in. yanzu kin gama nazo mu wuce? dan ina kusada asibitinku". " wai da gaske". "Eh mana, nazo wajen wanine". " to saika zo, ina jiranka". "Okay babyna saina zo". Daga haka suka yanke wayar. Aysha da Fa'iza suka saki baki suna kallonta, suka ce " lallai baby kina wutafa, lamarin naku yana bada citta walhy". Far tayi da idanu tace "ya ranku babies?". " fari tas". cewar Aysha. Fa'iza tace, "ni wlhy shekara hud'u daya wuce akacemin Amatallah zata zama haka zan k'aryata fa, ni yanzuma malamar taki kinfini gogewa a harkar". Amatallah da Aysha suka saka dariya, Aysha tace, " muma dai ALLAH kabamu mijinnan mushiga daga ciki". "Amin baby, amma wlhy kibama doctor Yazeed dama, gayennan yana sonki over amma kinata yankwanashi". ''Ba haka bane Ama....., wlhy inajin tsoron kishiyane, kuma matarsa ance batada kirki". " ke 'yammata kar rashin kirkinta yadameki wlhy, kibada kai bori ya hau kawai, zamu bida itane tayi mubaya'ar zaman lafiyar dole, bakiga Anty Aneesar gidanmu yanzu tayi sanyi ba, ai yau da gobe tawuce wasa". ''Wlhy gaskiyarki Amatallah, Amaryarmu tunda taji mijinmu na Neman ta hud'u takama kanta, Uwargida kam aidama tayi sanyi tuni wlhy, ai yanzun an daina yayin kishin HAUKA, kowa tata ta fisheta akeyi". "To shikenan, kubari dai zanma Innani maganar da Uncle, yanda sukace saimu k'ara tattaunawa, Ama... Kid'an farama Uncle maganar". "Okay ALLAH ya tabbatar mana da alkairi to". Atare suka amsa da amin. Suna 'yar hirarsu har Uncle ya iso. Bayan sunje sun gaida shi Ama.. tamusu sallama tashiga mota, Uncle yace "Aysha keba gida zakijebane?". " gida zanje Uncle, zamu samu Napep yanzu insha ALLAH". "Ku shigo to na kaiku bakin asibitin, Dan time d'in shan ruwa yakusa, sai anjima zan shigo gidan, idan kuma zakibimu to?". Da sauri Amatallah ta k'yafta mata ido wai tace eh". Murmushi Ayshan tayi tace " to Uncle". Baya suka shiga, a wajen asibiti Fa'iza tashiga napep yabiya kud'in sannan yanufi gida dasu Ama..... Motar tayi shiru, Uncle nata tuk'insa, Amatallah da Aysha suna d'an hira jefi-jefi akan aikin yau d'in, Uncle najinsu amma baice komaiba har suka Isa gida ana kiraye-kirayen magriba. Fateema tafito cikin kwalliya da d'okin tarbar mijinta, amma saitaci karo dasu Ama... nafitowa a motar itada Aysha. Kallonsu kawai tayi batace komaiba, amma taji zafi a zuciyarta. Shikansa Uncle yakula bataji dad'iba Dan fuskarta ta nuna hakan. Su Amatallah kam ko a kwalar rigarsu, gaisheta sukai suka shige ciki abinsu suka barta da mijinta. Cikin fara'a ya tarbeta, yafito yana fad'in "yarafa my tee!". "Basu dawoba suda momynsu". Fara'arsa yarage yana kallon agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunsa, " mtsoww nifa banason irin wannan rayuwar, shiyyasa banson wani birthday d'in banzan nan, ankira magriba amma suna gidan mutane?". "Kayi hak'uri, wlhy nasan itama hankalinta na gida". Baice komaiba yamik'a mata wayoyinsa, " bara naje nayi salla ni". Tace, "adawo lafiya". Ciki takoma abinta, bataji motsin su Amatallah ba tashige 6angarenta, dan gaskiya taji haushin ganin Amatallah da Uncle tare, ga yarinyarnan data fara zargin kodai mijinsu sonta yakeyi? yo haka kawai dan yarinya ta musulinta sai a maidata tamkar wata jininsu, (nace hummm, kardai kishi ya rufe miki ido fateema). Su Amatallah ma basusan tanayiba, Dan suna shiga Aysha tashiga wanka, Amatallah tazauna tana sauke numfashi dajiran fitowarta itama tasamu tayi, dan tanama fashin salla ne, shiyyasa Aysha tafara shiga danta sami damar yin salla akan lokaci. Har Uncle yadawo sallar magrib Aneesa da yara basu dawoba, ransafa yafara 6aci, bayason shirme irin wannan, yanzumma anfi k'arfinsane, wai d'iyar su shehu ce ke birthday d'in cika shekara biyu, shine Aneesa ta kaisu dan Amatallah batanan, itakuma yakamata taje d'in tunda itace k'arama kuma kamarma za'a iya cewa k'awar Zalihance. A falon k'asa ya zauna yakira Number Aneesa amma tak'i shiga, itadai Fateema tanata had'a masa kayan bud'a baki a d'arare, dukda abin na damunta a rai, tun bayan tafiyarsa masallaci kuma itama take kiran Number Aneesa network ya hanashi wucewa. Tsaki yaja yad'auki ruwa yanasha. Da wayo Fateema tanufi 6angaren Amatallah. fitowarta wanka kenan itakuma tashigo, Aysha kuna na zaune inda tayi salla tana karatun alkur'ani. "Antyn yara munga idi". " kamarya Anty?". "Wlhy momy naketa kira awaya tak'i shiga, kuma Abbunsu yafara fad'an rashin dawowarsu, shima yagwada wayarta tak'i shiga, narasa misuka tsayayi har dare haka?". Amatallah tace, " mun banu, Anty Aneesa ta manta da yandama yayarda suje Birthday d'inan? bara nima na gwada kiranta to". Amatallah ma takira tak'i shiga, tace, "bara nakira zaliha to". ''Yauwa, ni wlhy tunanin nanma bai zominba, yo dukna rud'e kirata muji........" Maganar Fateema tamak'ale saboda sallama da Amatallah tayi alamun Zaliha ta d'aga. bayan sun gaisa taimata Happy Birthday d'in Hafsa d'in dabata hak'urin rashin zuwanta sannan tace Su Anty Aneesa fa? basu taho bane?". "Yanzu suka taho Anty Ama..... wlhy Haneefa ce yarinyar Anty Mariya ta d'auki su Ummita da Siddiqa wai suka tafi gidan k'awarta can k'asan layinmu, gashi tabar wayarta agida, munrasa yanda za'a kirata tadawo dasu, kuma babu wanda yasan gidan. ALLAH yasa Yaya baiyi fad'aba dai?". "A'a baiyiba, tunda dai suntaho shikenan, ALLAH yakawosu lafiya". "Eh sun taho, ya shehu mane yarakosu saboda yaran sunmata yawa gashi ba motar gidaba". " wlhy kuwa, shikenan a gaidamin hafsa, sainazo cin cake". Dariya zaliha tayi suka yanke wayar. Ta fad'ama Fateema duk yanda sukayi, hamdala Fateema tayi, tace, "ALLAH ni tsoronma fita nakeyi, ran Abbunsu a 6ace yake, shirya mu tafi tare". Ido Amatallah tazaro waje, " Anty Fatee ke kina tsoronsa bareni kuma?". Karki damu saka kaya kedai, idan mu biyune k'ila ya sassauta. Aysha najinsu, tayi murmushi cikeda sha'awar wannan family, ita kanta a d'azun taga fuskar Fateema ta nuna rashinjin dad'in ganin Uncle ya kawosu, amma gashi yanzu sun had'u suna magance matsalar data shafi kishiyarsu, rayuwarsu na birgeta. Doguwar riga tasaka kawai tad'an shafa fauda tasaka turare suka fito, yana zaune inda fateema tabarsa, yad'ago ya kallesu, ransa a 6ace yake amma kwarjininsa ya shanyeshi, duk sai tsoro yakama Amatallah, ta la6e bayan Fateema tana satar kallonsa. Kauda idonsa yayi daga kansu kawai, a d'arare Fateema tace, "kozakayi wanka tunda gasunan tahowam......" Wata harara ya jefeta dashi wadda tasakata kame bakinta ta maida kanta k'asa. Hakan yakuma bama Amatallah tsoro, dama Uncle ya iya fushi haka? lallai takuma yarda bayason abinda zai ta6a 'ya'yan nan nasa....... Tunaninta ya katse saboda shigowar yara da gudu, daga Amatallah har Fateema ajiyar zuciya suka sauke, kowa yafurta alhmdllh a hankali. Dukansu jikin Abbunsu suka fad'a suna masa oyoyo, abin mamaki sai Amatallah taga yaware yana musu dariya, Aneesa tashigo a d'an tsorace, Dan tunda taga motarsa a harabar gidan jikinta yay sanyi k'alau. Su Amatallah duk sukai mata barka da dawowa, ta amsa tana nuna musu Uncle da ido, da hannu Fateema tamata alamar itadai tayi shiru. Barka da gida tamasa, ya amsa kamar bata masa komaiba, (itama tasan bazaice mata komanba agabansu Ama....., saiya ke6e dagashi sai itane zataga 6ancin ransa). Shehu yashigo d'aukeda Abubakar, zama yayi ya gaida yayansa dasu fateema, kamar babu komai sukad'an ta6a hira sannan yamusu sallama yatafi. Shima sallar isha'i suka fito da yaran. Baidai sha ruwaba sai bayan isha'i daya dawo yay wanka............✍🏻 *_wayata tagajine, iskanci takemin, ALLAH dai yasa nasamu na k'arasa buk d'inan, shiyyasama nabar chart d'in dannayi manage, ngd da comments d'inku da addu'ar dakukema mahaifina, duk ina gani saidai babu damar amsawa, typing d'inma a wayar my Abdull nakeyinsa wani lokacin wlhy, dan wayata dana cika danne-danne saita k'ame🤣._* 🤩👎🏻 One luv my sweet fans *_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻 [1/24, 2:15 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_* *_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡 _{home of expert and perfect writer's}_ *_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉ _(Hattara matasa)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* ____________________ *_Number 38_* ____________________ A wajen shan ruwanma bai nemi kowaccensu ba, harma mai girkin kanta, tareda yaransa sukaci daganan ya zauna sauraren shirmensu. Aneesa tasan tanada laifi shiyyasa tak'i fitowa, Amatallah kam firarsu sukesha da Aysha hankali kwance, tasan ba itace da mijinba, abincima yana tafiya salla dama ta d'ebo musu, Fateema kam zamanta tayi itama ta sharesa. Sauraren surutun yaran kawai yake, amma hankalinsa nakan matan nasa, yasaba ko yaushe indai yana a gida duk suna gefensa, yau kuma yalura sunma had'e masa kai sun barsa shida yaransa..... Wayarsa dake wringing ta dawo dashi hayyacinsa, Innani yagani ajiki, da mamaki yad'aga dan saiya had'a watanni bata kirashiba inba shine ya kirataba. A ladabce ya gaisheta, ta amsa tamkar yanda ta saba, ta d'ora da fad'in ya yaran. "Lafiya lau suke Innani, ya baba?". "Yayi barci, Aysha ce bata dawoba, shine abin yadameni nace bara na nemeka, danna kira warta bata zuwa". ''Kiyi hak'uri Innani, wlhy naje d'aukar Khadija saita biyomu akan idan nasha ruwa zanzo gidan saina maidota, tokuma saina iske Aneesa basu dawo daga gidan Shehu ba hankalinna yatafi can, amma yanzu zan maidota". ''Alhmdllh, dama ni damuwata kar wani Abu ya samarmin yarinya, amma tunda tanan shikenan dama kun bari saida safe kawai, tunda dare yayi har tara fa, yaushe kukazo ka koma, nifa banason yawon darennan". " to shikenan ALLAH ya kaimu goben a gaida gwaggo". "Zataji". ta fad'a tana yanke wayar. Ajiyar zuciya ya sauke kafin yamik'e yanufi 6angaren Amatallah. Tunkan yashigama yafara jiyo dariyarsu, yashiga falon da sallama, film ya iske suna kallo, da sauri Aysha tace, " sorry Uncle, nataso kagama?". "A'a Innani tace ki kwana anan, amma ki kirata dantata kiranki wayar tak'i shiga". " to Uncle". Bedroom d'in Ama...... yashige, hakan yasata mik'ewa dole tabi bayansa, ta iskeshi a bakin gado zaune. d'an nesa dashi ta zauna. ya kalleta fuska babu walwala, "saboda 'Yar uwarku tamin laifi kuka had'e kai kuna fushi dani?". Ama.... ta d'an zaro ido waje, " Uncle fushi kuma?". "Eh mana, bagashi kunbarni nida yaranaba kowacce ta dawo d'akinta". " nidai Uncle wlhy bahaka baneba, kawaidai ganin karna bar Aysha ne ita kad'ai, amma kayi hak'uri". Baice komaiba yamik'e ya fice, yaran yacema suje su kwanta gobe akwai school. Duk suka amsa da to, samansa ya haye shima. Shigowar Siddiqa da saifudden yasaka Aneesa tambayarsu ina Abbunsu?, Saifudden yace "momy yafi d'akinsa". " umma fa?". "Itama tana d'akinta". Sakasu tayi suka kwanta, taima Abubakar shirin barci sannan ta d'an kuma fesa turare tafito, 6angaren Fateema taje, itama isketa tayi tanama yara shirin barci. " Umman yara alfarma nazo nema, dan ALLAH bara naje nabama Abbunsu hak'uri, nasan lattinmu yajawomin laifi". "Hakan yayi, dama yanzu zanje nace kozakije kibasa hak'uri, naga muduka ukun haushinmu yakeji, yatasa yaransa gaba ya share kowaccenmu". " kuyi hak'uri, nasan nina jamuku". "Wlhy kibarma zargin kanki, kinsan halinsa dai akan yara, kijedai naji sunce yatafi 6angarensa". " okey ina zuwa". A bedroom ta samesa yana shirin barci, sallamarta kawai ya amsa yacigaba da abinda yakeyi. A bakin gadon ta zauna harya kammala sannan tace, "dear!". " uyim". yace batareda ya kalletaba. Tace, "dan ALLAH kayi hak'uri, nasan namaka laifi tunda nasa6a lokacin dakace mu dawo, wlhy Hanifa ce ta d'auki su Ummita suka fita, gashi tabar wayarta kuma babu Wanda yasan gidan". Kallonta yayi cikeda takaici, " amma shine kika gagara kirana ki sanarmin? inda nasan Baku tahoba aizan biya na d'akkoku kamar yanda na kaiku, saboda tsabar kin rainani shine bakiyi hakanba ko?". Shiru tayi tana kallonsa, tama rasa ta ina zata farane, danta kula yakai mak'ura a 6acin rai. Matsawa tayi kusadashi sosai, ta marairaice murya tamkar mai kuka, "dan ALLAH kayi hak'uri dear, wlhy ba raini bane, naga kayi azumi ne karmu shiga hak'inka, ka yafemin hakan bazai sake faruwa ba wlhy, kuma nikad'ai namaka laifin banda 'yan Uwana". " bandasu amma kuka had'emin kai?". "Bahaka bane wlhy dear, maybe su Baka fahimcesu bane, kayi hak'uri to". Tausayi tabashi yanda yaga dukta damu, harda guntun hawayenta. " shikenan na hak'ura ki kiyaye gaba, karki kuma min irin haka, inhar hakan takuma faruwa ki kirani ki sanarmin, miye amfanin wayar, dan baki ta6amin hakanba kuma yasa na hak'uran". Cikin farinciki ta rungumeshi tana godiya, saikuma tasakeshi da Sauri tace sorry". Murmushi kawai yayi ya d'aga mata kai, takuma masa godiya tafita. Ganin yanda tafito ya tabbatarma Fateema komai ya daidaita, dan haka tashiga itama, (dama tasan mijinsu yanada saurin sauka afushi inhar zaka nuna masa nadamarka) saikuma tad'anji haushi, kar Aneesa tagama rurrungume mata miji tana nan. (Abin dariya masu karatu🤣). Itama dai saida yamasa k'orafin sun had'e masa kai, hak'uri tabashi tacigaba da tattalin mijinta, shima kuma yabada kai bori ya hau. Amatallah kam tun fitarsa tabishi da kallo, a fili tace, "ALLAH ya huci zuciyarka Uncle". daga nan tafito suka cigaba da hirarsu da Aysha, dukda lamarin Uncle d'in na caccakar mata rai haka ta danne. ********* Washe gari Da safe sai Amatallah taga da d'an sauk'i kamar ya sauka, hakanne yasa tasaki jikinta kad'an, amma jiya da damuwar fushin Uncle ta kwana, tsaf yalura da yanda takeyi agabansa, shareta yayi danta bashi dariya. Koda suka gama break fast bata yarda sun jirashi akan sufita tareba, da wuri tace sutafi itada Aysha. Lokacin daya fitoma sun dad'e da tafiya. ALLAH yasotama ranar Aneesa ce zata kar6i girkin. Haka rayuwar gidan take tafiya musu cikin kwanciyar hankali da annashuwa, idan kuma wani damuwar ya gifta a fuskanceta a yanda tazo. Wata safiyar laraba kuma Nazeefa tatashi da nak'uda, Uncle mijinta yafara kira, dan haka yatafi a rikice daga kasuwa. Nazeefa tasha wahalar haihuwarnan kafin ALLAH ya sauketa kuma, dan harma sun fara shirin mata cs. tasami d'anta namiji k'ato mai kamada babansa. A ranar daga makaranta Amatallah suka wuce itada Aysha, a can suka iskesu Fateema itada Aneesa. sunta santin baby kuwa, Amatallah harda kuka tayi a 6oye da addu'ar itama ALLAH yabata. Uncle yazo kusan 5pm ya d'aukesu, dankar yara su dawo islamiyya basa nan, kallo d'aya yayama Ama.... yaji ajikinsa tayi kuka, dan ita koyaya tayi kuka sai manyan idanunta sun nuna. bai tambayetaba suka tafi, dama ranar girkintane, dan haka ta zauna a gaba, Aneesa da Fateema suna baya, mah-mah da Abubakar ma suna gaba wajen Amatallah. Tausayinta yakuma kama Uncle d'in, ganin yanda taketa luguyguyta Abubakar da Mah-mah, koma saka baki a hirarsu batayi saboda yaran gaba d'aya sun d'auke hankalinta. Suna zuwa gida mai napep d'in dake kai yara school yana isowa, ya d'akkosu daga islamiyya. Tare suka shiga cikin gidan. Da daddare bayan sun gama cin abinci da 'Yar hira yace yaran suje suyi shirin barci su kwanta. Kafin yashige yaje yayma Aneesa saida safe yayma su saifufden addu'a kamar yanda yasaba yafito, itama Fateema yashiga yayma yaran addu'a. Amatallah tagama tsaftace jikinta da baje ko wanne lungu da sak'o na jikinta da k'amshi, duk a sanyaye takeyin komai, dan rashin haihuwarnan tata na damunta, musamman yau dataga babyn Nazeefa ma. A sanyaye tashigo bedroom d'in nashi, haryama kwanta danya gaji da jiranta. Hannu yamik'a mata alamar tazo gareshi ganin ta tsaya a bakin k'ofar. Idonta harya cika da kwalla ta taka a hankali zuwa gaban gadon, shiya kamo hannunta yajawota tafad'o jikinsa. Rungumeta yayi sosai, a cikin kunanenta yace, "my heartbest waya ta6amin kene?". Ai tamkar yazugata saita rushe masa da kuka kawai. Dama yasan za'a rina dan tund'azu batada walwala koda ana hirama. Bai hanataba ya barta tayi kukan sosai yana shafa bayanta a hankali, alamar lallashi, saida tayi sosai sannan yad'ago kanta ya manne bakinsa kan nata kawai, yafara mata lalashin dazatafi gamsuwa dashi. Saida hankalinsu yadawo jikinsu sannan yashiga mata kalamai masu sanyi da ratsa 6argo. " haba my best fad'amin matsalarki please, nine Uncle nine baba nine Ammi nine miji kuma kinji?". Kanta ta d'aga masa, murya a raunane tace, "uncle maganar haihuwarnan bata damunkane?". Shiru yay danya rasa mima zaice mata, zuwa can yace ''ki kwantar da hankalinki khadeeja, insha ALLAH baki tare da kowacce matsala, Amma ranar Monday ki shirya saimuga doctor mana". " Uncle inajin tsoro wlhy, inajin tsoron kar ace bazan ta6a haihuwaba........." Da sauri yarufe bakinta, ''insha ALLAH zaki haihu, sainaga jinin brother d'ina da nawa cakud'e a waje d'aya da izinin ALLAH my best, ki d'auka komai akwai lokacinsa, watarana sai labari, kikama sani ko nayi ajiya wannan watan". yay maganar cikin tsokana yana shafa shafaffen cikinta. Kanta takuma cusawa a k'irjinsa tana 'Yar dariya. Yayi dariyar shima yana sumbatar Sumarta da fad'in kokefa, amma da anatamin rowar fara'arnan dake yalwata farincikina da annashuwata nima. Kuma k'ank'amesa tayi tana fad'in kai Uncle". "ALLAH kuwa my Dee....." ***** ******* ***** Ranar Asabar d'in week d'in Abulkhairi yashiga layin yara masu zana jarabawar fita daga primary, shima zai wuce secondary insha ALLAH A wannan year d'in, yaron yagirma, kamanninsa da Uncle suna kuma fitowa sosai, hakama Sahib shima yaron yayi girma, dan dakad'anma Abulkhairi zai fishi tsawo, yamafi Abulkhairi wayo. A ranar Monday d'in kuwa Amatallah ta zabgama Uncle wayo dankar suje asibiti, dan itafa tsoro takeji taje ace akwai matsala. Dukda yaganota haka ya k'yaleta, dama shimad'in bayason aje asibitin. Agurguje please😫 Rayuwar tacigaba da tafiya ahaka, yau fari gobe tsumma, yau dad'i gobe hak'uri, ansha sunan yaron Nazeefa, (Sulaiman). su Amatullah kam anata karatu, dukda tanada damuwa azuciyarta bata bar hakan yazama silar raunanar karatunta ba, kullum Fa'iza da Aysha cikin kwantar mata da hankali suke da nuna mata muhimmancin hak'uri da yarda da k'addara. Hakama 6angaren danginta su kawu hafizu, koda yaushe sukayi waya yakan k'ara kwantar mata da hankali. Shikansa Uncle d'in duk abinda zai kwantar da hankalinta da kauda mata damuwar rashin haihuwar yanayi. ganin yanda duk suka damu sai itakuma tafara rage nuna tata damuwar, tama d'auke tunaninta daga wajen gaba d'aya, ta duk'ufa gayama ALLAH kukanta dayawan azumi, sadaka dadai sauransu. To Ama..... ALLAH dai yasa mudace😢🙏🏻. ****** ****** ****** "Wai lafiyarki kuwa Ama......?" "K'alau Fa'iza, mikika ganine?". " kawai tun jiya nifa wani sukuku nake ganinki, tamkar wata mara lafiya". Kanta ta kwantar jikin kafad'ar Aysha tana jan k'aramin tsaki, "kibari kawai, nifa jikin nawane ma duk babu wani dad'i, kuma babu inda yakemin ciwo wlhy". Da sauri Fa'iza tace, " tin yaushe kika faraji?". "Yanaga kin wani tsorata? bafa wani abu bane". Cikin dariya Aysha tace, " aimu fatanmu yazama wani abun, nifa wani k'yauma naga kinayi kwanan nan hajiyata, miye sirrin?". Duka Ama... takai mata, Aysha ta goce da sauri tana dariya. "To miye na dukanta? ba gaskiya tafad'aba? baby ALLAH yasa abinda muke fatane dai, amma koni wlhy naga kin k'ara k'yau, maganace dai kawai banyiba". " uhm kuma daina wahal da kanku, ni banida komai, kawai inaga malaria keson kamani dai". Dariya suka mata, akadai bar maganar ahaka, kowa kuma ak'asan ransa yana addu'ar ALLAH yasa abinda suke fatane😊. Kwana biyu dayin wannan maganar Ama.... ta tashi da zazza6i mai zafi, gashi ranarma Uncle ba d'akinta yakeba, yana wajen Aneesa. Har zasu fara break fast babu Ama...., dayake weekend ne. Uncle ya kallesu yana fad'in wai Khadija fa?". Aneesa tace, "Wlhy nibanga tafitoba tun d'azun, Siddiqa ma tashiga tafito tace barci takeyi, tona d'auka ko gajiyace tahanata tashi da wuri". Fateema ma tace, " ni wlhy kwana biyunnan ma sainaga kamar Auntyn yara batajin dad'i sosai". "Nima nad'an zargi hakan, harma Na tambayeta amma tacemin babu abinda ke damunta, bara dai Na dubata kawai". Sukace to............. Manage please😎 One luv😻😻😻 [1/25, 12:25 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_* *_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡 _{home of expert and perfect writer's}_ *_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉ _(Hattara matasa)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* ____________________ *_Number 39/40_* ____________________ Tundaga falo jikinsa yafara sanyi, dan babu alamar tayi gyara, da sallama yashiga bedroom d'in, babu amsa, ya kalli gadonta, tana k'udundune a bargo tarufe har kanta, da sauri ya k'arasa ya yaye bargon. "Khadija lafiya kuwa? da uban zafinnan kika lullu6........" Maganarsa ta tsaya a mak'oshi saboda yanayin daya ganta, ga jikinta zafi zauu, har wani huci ke fitowa. "Ya salam my best!" yafad'a yana zama gefen gadon, hannu yakuma kaiwa a wuyanta ya ta6a, tarik'e hannun da sauri tana rawar sanyi, "Uncle please bar ta6ani, hannunka sanyi". "dama bakida lafiya amma baki fad'aba Khadija? kuma har tadaki nazo nayi da asuba". " Uncle sannan zazz6in ya saukane, banyi zaton zai dawoba da safe". "Dashi kika kwanama kenan?". Kanta tad'aga masa tana wani lumshe idanu dakuma dunk'ulewa waje d'aya saboda bargon daya cire mata. Tashi yay yashiga bayinta, yahad'a ruwa maid'an zafi sannan yadawo, ya taimaka mata tasakko tanata rawar sanyi da fad'in "Uncle please kabarni Na kwanta, ina ganin jirine". " Sorry my best! Bara namiki wanka kiji d'an k'arfi saimuje Asibiti". Tirjewa tayi tana tura baki gaba, "nidai Uncle basai munje asibitiba, danasha parasitemol zan warke". " to naji shagwa6a66iya, muje dai ayi wankan first ". Da kansa yamata wankan, ya taimaka mata suka fito, a bakin gado ta zauna, ya d'akko Vaseline ya shafa mata, tanata langa6e masa itafa jiri take gani, hakadai ya lalla6ata yasaka mata doguwar riga bak'a. Fita yayi itakuma takoma ta kwanta harda jan bargo takuma lullu6a, taji dad'in wankan, dan ciwon jikin saitaji yaragu harma da zafin. Yana fitowa suka hau tambayar miya faru da Ama.... d'in?. "Batada lafiya Ashe, zazzabi takeyi, Aneesa had'a mata break fast d'inta". Sun nuna jimamainsu akai, Aneesa ta had'a break fast d'in ta d'auka da kanta domin kai mata, Fateema da Uncle sukabi bayanta. Da k'yar tatashi tasha kunun bayan su Fateema sunmata yaya jiki, ta amsa dak'yar tana tambayar ya yara suka kwana. Uncle yayi yayi tatashi suje koda camix ne tunda yau babu aiki amma tak'i, itadai yabata perasetimol tasha kawai. " nifa bazan baki maganiba kai tsaye, nasani ko ALLAH ya share kukanmu ne, kokuwa salon nama kaina ganganci". Baki ta turo masa tana matso hawaye, "amma Uncle kofa masu tsohon ciki sunasha, kuma babu abinda yake musu, tunda a asibiti muna badawa aii". Shiru kawai yayi yana kallonta, yama rasa mizai cemata, daga k'arshe dai saishi ya hak'uran, yabata tasha takoma ta kwanta. Zazza6i dai yak'i sauka, saidai jikin ya huce yakuma dawo, ba Uncle ba hatta su Aneesa duksun damu, dan tasaba ranar weekend sunta shagalinsu da yaran agida kafin su tafi islamiyya, su Kansu yaran duk sunyi sukuki. Da daddare dai abinda batason dole akayi, Uncle yakira doctor Shu'aibu yadubata, gudun karya bata Magani suyi 6arna yace tayi gwajin tsinke. gwajin farko ya nuna mumsami baby💃🏻😀. Murna wajen Uncle ba'a magana, babu kunya ya rungumeta a gaban Doctor Shu:aibu, Ama..... kam hawaye kawai takeyi, dukda tad'an dad'e tana zargin cikine dama, soboda aikintane, (dan kunsan doctor Ce fannin mata insha ALLAH anan gaba kad'an zata zama kwararriya💃🏻). Su Fateema Kansu dai murna sukeyi, kodan k'aunarda Ama....kema 'ya'yansu dolene su tayata farincikin samun NATA itama, kuma ko kad'an basuji kishin farin cikin da mijinsu ke nunawa akan cikinba. Doctor Shu'aibu yace, "dama nasan itama tasan tanada, kawai dai ta 6oye mukune". " Uncle ya kalli Ama..... yace, "wai haka my best!?". Kanta ta 6oye cikin bargo tana murmushi. Duk sai sukayi dariya, Uncle yaraka Doctor sannan yadawo suka cigaba da farimcikinsu. Ranar dai dole Aneesa tayi sadaukarwa na kwananta ga Ama....., Uncle yakwana a wajenta saboda jikinta. (Anee kin biyamu kwannamu😂😜). Hummm kafin kacemi maganar cikin Ama....Yazagaye dangi makusantansu, har 'yan jos an gwargwad'a musu, murna dai ba'a magana, 'yan dubiya su Anty maijidda dasu Asiya su Nazeefa mai jego, ita Ama... Kunyarsuma takeji, duk kuma d'okin son samun cikin saiya 6uya yanzu da'aka samu d'in. Babama yayi murna, hakama innani, dukda bata fito ta nuna a filiba, amma takanas shehu yakawota tazo ta duba Ama..... Amatullah nashan wahalar cikinnan, dan laulayi takeyi sosai, dolene kaganta Tabaka tausayi, dukta rame sai uban haske data k'ara, dukda kasancewarta bak'a. Girki dai su Fateema sun sauke mata, saidai ta kwana da miji, wataranma idan abin yay tsanani hakura suke da kwanan Nasu ya kwana a d'akinta, tanashan k'arin ruwa kam tamkar wata gallon🤭, kullun cikin zirara mata akeyi. To Ama...ALLAH yaraba lafiya. *********** Kwanci tashi babu wahala wajen Ubangiji, ga Ama.... cikinta yashiga wata na 7, yafito d'as kuma yamata k'yau, tanata karatunta hankali kwance, dan Alhmdllh tunda cikin yashiga wata na 5 tasamu sauk'in laulayin, saidai abinda ba'a rasaba, harma taje jos tayo sati biyu acikin d'an hutun dasuka samu, tazaga dangi sosai dukda ba wannane zuwanta Na farkoba, har anguwarsu taje ta gaida makwafta dasuke mutunci dasu kafin rasuwar su baba, dukda ma wasunsu sun rasa rayukansu a lokacin wancan rikicin, wasu kuma sunbar garin gaba d'aya, har kuka tayi dataga kufan gidansu, Dan tuni Uncle yanemi shawarrata akan ayi masallaci ko islamiyya awajen, domin ladan yadinga kaiwa ga iyayenta, takuwa amince, yasa akayima wajen gyara bayan an rushe, masallaci akayi k'arami da islamiyya mai aji hud'u k'anane amam, sai Bohol da akayi mutanen anguwar NATA d'ibar ruwa, dama basudashi. Wani son Uncle Yakuma ratsa ruhinta saboda wannan hidima dayay ga mahaifanta, (kowa yasan anason sadaka mai gudana ga mamaci). a zuwanne takejin labarin d'aure Ramzaki da akayi, saboda kashe wani da Mr Pam yasa sukayi, kuma aka kamasu, koda sukace shine yasakasu aka kirashi saiyace shibaima ta6a ganinsuba ballantana ya sansu, k'arya suke masa, hakanne yasa aka kaisu Court, hukuncin shekaru 25 aka yanke musu a prison. Amatullah dai jitayima INA itace alk'alin , da ratayesu zata sakama ayi take anna, amma hakanma tayi farinciki koba komai zai d'and'ani azabobi kafin yaje waken ALLAH kuma. Satinta biyu tadawo Kano ta koma school aka cigaba da bugawa. Rayuwar gidansu nanan yanda take, saidai 'yan canje-canje daba'a rasaba, amma sunan akan tattalin mijinsu da kishinsa, kuma hakan bai hanasu k'yautatama junaba. Haka shima mijinsu mai gajiya da basu soyayya mai tsaftaba, kowacce gwargwadon iko yana nuna mata tattali da soyayya, yana k'ok'arin adalci a tsakaninsu, wadda yafi so kuma yabarma zuciyarsa. Maganar K'UNGIYARSU kam saimuce Alhmdllh, yanzu haka suna k'ok'arin had'a wani gagarumin taro na k'asa, domin wayarma matasa dakai a kan za6en dake tunkaro k'asar, Wanda bai wuce saura kwanaki k'alilanba a gudanar dashi. Sai dai kuma a wannan tsakaninne wani Abu Mara dad'i yafaru😢, shine Rasuwar baba, adaren juma'a ranar alhamis kenan jikinsa yay tsanani, hankali tashe Innani takira Uncle kusan 1pm, harma ya kwanta, dan ranar a d'akin Amatallah yake, suna tsaka da barci tana kwance a jikinsa, yayinda hannunsa ke rungume da cikinta, da k'yar ya iya lalubar wayar a k'ark'ashin filo, batareda yaga mai kiranba yad'aga dafad'in "please wanene?". Muryar data daki kunnensa tasashi wartsakewa babu shiri, innani yajiyo tana fad'in " maza kazo gida Muhammadu jikin babanku ya rikice". A firgice ya wuntsilo daga gadon, haryana bigema Ama.... cikinta, Wanda zafinne yasata farkawar dole tana fad'in "wayyo ALLAHNA". ina Uncle bai sauraretaba, sorry kawai yace mata yafice da sauri. Dukda azabar da Ama... keji haka ta tashi zaune da k'yar, mamaki yacikata, tabbas babu lafiya, dan ko juyi zatayi cikin barci saiya farka, kuma zai taimaka mata ta juya cikin lalla6awa, amma yanzu ji yanda ya maujeta bai kulaba, sakkowa tayi tafito tana d'an cije baki, dan har yanzu inda ya bigeta bai daina zafiba, yaran cikinta sai motsawa yakeyi alamar shima yaji zafin maybe (😂lol). Tana fitowa falon yana fita shikuma a rikice, ya canja kayan barcinsa zuwa farar jallabiya, hakan yakuma rud'ar da Ama... ta tada su Fateema duk ta sanar musu. Jigum-jigum sukayi, kowa yana sak'e-sak'e da tunanin mike faruwa? dukda wani 6angaren tunaninsu yana kan babane k'ila, saboda jiya jikin nasa yad'an motsa har sukaje suma suka gaidashi. Kasancewar titi babu motoci sai tsilli-tsilli yabama Uncle damar zabga gudu, lokacin dayaje gidan lamari ya 6aci kam, danba baba ba hattada Innani tafita hayyacinta, Aysha sai kuka takeyi, hakama gwaggo Rakiya. Dole adaren suka tafi asibiti, sai daifa babu tsumi babu dabara, kafin asubahi rai yayi halinsa😭, ALLAH ya d'auke kayansa. Mutuwar data zamema Uncle ta uku dabazai ta6a mantawa da itaba, duk yanda yaso ya daure ya rarrashi su Innani yakasa, shima kansa yakifa akan gawar yafashe da kuka😭. 😭hakanne nima yasani kukan, danna tuna da rasuwar nawa mahaifin😭, ALLAH ka gafarta musu, ka yafe musu, muda suka bari ALLAH ka d'auki ranmu muna a masu imani da tsonka ya rabbi, ya ALLAH ka k'ara mana soyayyar manzon ka tsaftatacciya a rihinmu😭. Marayu ALLAH yabamu hak'uri kunji, inayinku a duk inda kuke.😭🤝🏻. To anyita ta k'are, baba yatafi ya barsu Uncle, yanzu shine babban wa, shine kuma Uba. Washe gari misalin 10am akayi jana'izarsa wadda ta tara d'unbin Al'umma, kodan d'ansa yatara, dan matasa dama dattijan sunta tururuwar halattar wannan jana'iza domin nuna hallaci ga Alhaji Muhammad Ahmad Labbo. A kwana Ukun data gabata ba'a cewa komai, dolene kaga Uncle dasu Ya Jabeer subaka tausayi, barema su Nazeefa da Shehu da Anty maijidda, hakama su Amatullah duksun jigatu, amma Yaya za'ayi da ikon rabbi, saidai hak'uri. ALLAH sarki Innani, mace mai hak'uri da k'ok'ari, tasha jiyya harta tsawon shekaru kusan 7, ALLAH yabata ladan jiyyar datayi ta adalin mijinta dattijon kirki mai yakana da dattako. ******* ******* ******* Tun bayan rasuwar baba abubuwa sukaima Uncle cak, Yakoma sai a hankali, kasuwama yadaina waiwayarta, wajen aiki kam danya zame masa tilasne, sauk'in sama ba kullum baneba, K'UNGIYA kanta tasan jagoranta yazama abin tausayi, dole sai Alhaji Sabi'u ne yacigaba da tafiyarda shugabancin kafin komai ya daidaita. Su Kansu matsansa saidai Addu'a suke binsa dashi, amma komai nasa yayi sanyi. Ahaka dai yauda gobe har zuciya tafara sanyi da hak'un dangana, yafara komawa kan harkokinsa dakuma jan 'yan k'annensa a jiki, yakuma ninka kulawarsa ga mahaifiyarsu Innani, wadda ayanzu itace Uwa Uba kuma, itama kanta dukta fita hayyacinta, ga girma na tsufa. Cikin Amatallah yashiga watanni na tara kenan, haihuwa yau ko gobe, dolene kaganta tabaka tausayi, gawata kumbura datakeyi, Uncle dukya d'aga hankalinsa, koda yaushe cikin kiranta yake a waya, a d'an tsakanin dole tad'an jinkirta dazuwa Asibitima, tasamu Hutu harsai ta haihu. Idan tana zaune haka zaita mammatsa mata k'afafu, idan kuma bayanan Aneesa ko Fateema zasuyita matsa mata, saikuma in yara sundawo makaranta, Amatallah tazama 'Yar gata, ai babu abinda zatacema ALLAH sai godiya, itadai ana gudun KISHIYA ita k'aunar nata takeyi, da godema ALLAH dayasa sune abokan rayuwarta, idanma taji mace nafad'in batason KISHIYA saitace amma bakida wayo wlhy, ai KISHIYA abar soce, ta 6angarori masu yawan gaske, mai dogon nazari da hangen nesane kawai zai fahimci hakan, musamman idan ALLAH yabaka mai hankali da sananin yakamata, amma inka samu mai burin korarka aika Shiga tara (🙁 ALLAH karabamu da irinsu to). Ranar wata talata da rana kusan 1pm Amatallah tana kwance barci yad'an figeta wani azababben ciwon Mara ya tasheta kuwa, aiko a firgice tatashi tana kuka dakiran Ammi da baba. Fateema na kicin tajiyo kukanta, a rikice tazo 6angarenta, halin data isketane ya tada hankalinta, tashiga rambad'ama Aneesa kira, itama a guje tazo. Basu wani 6ata likaciba suka memo taxi sai asibiti. Suna isa aka shiga bama Ama.... taimakon gaggawa. Ganin anshiga da ita suka sami damar kiran Uncle suka Sanar masa, mintuna k'alilan saigashi ya iso shida Shehu, isowarsu kuma babu dad'ewa ALLAH ya sauki Ama..... lafiya, ta sunkuto baby girl d'inta, saikuma ga baby boy babu zato. Nanfa murna da farinciki mara misaltuwa ya kaure, kafin kace mi labari ya karad'e dangi makusanta. Ganin ta sauka lafiya zuwa yamma aka sallesu suka tafi gida tareda dangi dasukazo tayasu murnar wannan haihuwa. Uncle baki yak'i rufuwa dan dad'i.😃.............✍🏻 Uncle nima bara na tayaka to😁😁, nasan masu karatuma zaru tayamu.💃🏻 One luv😻😻. [1/25, 4:04 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_* *_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡 _{home of expert and perfect writer's}_ *_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉ _(Hattara matasa)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* ____________________ *_Number 41/45_* ____________________ Uncle bai samu damar ke6ewa da Ama... ba sai dare, yashigo d'akin da sallama, gwaggo Rakiya tana zaune a falo tagama sakama macen kayan sanyi dan shirin barci, ya gaisheta tamasa barka, dan d'azun bata samu damaba saboda su Nazeefa Asiya Fa'iza Aysha zaliha dawasu dangi na familyn su Uncle duk suna a d'akin, sai yanzu daduk suka tafi, yarama da k'yar aka lalla6asu suka kwanta, amma da suka nanik'e da baby's. Bayan zun gaisa ya d'auki babyn daketa barcinta, kallonta yake farinciki nakuma ratsashi dan copy d'in Amatallah ce awajen, sosai yarinyar ke kamada Uwarta, bedroom d'in yashiga inda ya tadda Ama... Na waya da 'yan jos, zama yay a bakin gadon ya d'auki Namijin yahad'a duk ya rungume a jikinsa, yanamaijin k'aunarsu tana kuma ratsashi dashiga 6argomsa tamkar sauran 'ya'yansa. Bayan ta kashe wayar tace, "sannu Uncle". Fuska d'auke da murmushi yace, " kece da sannu my heartbest, ALLAH yaymiki albarka". A kunyace Amatallah tace "amin Uncle". Tasowa yay yadawo kusada ita bayan ya kwantar da yaran, ya rungume ta yana bata zafafan kisses, tareda kuma sanya mata albarka. Ita harma yabata kunya, tace, " Uncle jegofa mukeyi". Murmushi yayi yana kuma sumbatar wuyanta, "nima ai jegon nakeyi my besty". " Uncle kaid'inan ko! Hummm". Yaja kumatunta kad'an, "nid'in minayi?". " a'a babu komai, ai abin bana fad'a baneba". Dariya yayi yana fad'in "idan lokacin fad'ar yayi zaki fad'ane, wane suna kikeson nasama yarana?". Ta murmusa tana kuma lafewa a jikinsa tace, " duk Wanda yamaka yamin nima Uncle". "Shikenan my best, Brother kawai da Ammi". Ta kalleshi da sauri, " Uncle har sau biyu? Sahib ai ya isa, kar kuma abin yay yawa". "Tab lallai yarinya, ko duk yaran gidannan zasu zama sunan brother bazasumin yawaba wlhy, kinsan kuwa yanda sunan keda daraja agurina, nama saka nagama, barama namusu hud'uba kawai". Kasa cewa komai tayi, sai binsa kawai takeyi da kallo tana hawayen farinciki dak'arin jin k'aunarsa a ruhinta da 6argo, itakam mizatama Uncle tabiyashi da wannan d'unbin k'auna dayakema mahaifinta, ai saidai taita K'AUNARSA har k'arshen numfashinta itama kawai.😢 A kwanaki 7 d'inan ansha abubuwa, 'yan barka kullum cikin cika gida suke, su Nazeefa Asiya Zaliha Fa'iza Aysha kullum suna gidan, Innani ma tazo taga jarirai. Ranar suna kam mun rak'ashe mun kwalle abunmu, munci rangam iyakar k'arfinnmu, kad'an yarage Cikin Xoxo yafashe🤭, saida na 6oye kular abinci ta tsagaita, amma su o e sai aka 6oye a bayan murfin k'ofa dankar in ganta nahanata😜, yara sunci sunan Ammi da baba, *ISMA'IL & SALIHA* za ana cemusu *RAYYAN & RAIHANA* to ALLAH ya raya 'yan duguy-duguy iyalan baba. Washe garin suna 'yan jos sukaso wucewa da Ama.... Saidai babu Dama saboda karatunta, daga k'arshedai gidan Innani takoma kamar yanda Innani tabuk'ata, Uncle dukda baisoba haka ya hak'ura, dan bashida damar jayayya da mafaifiyarsa. A can Amatallah tacigaba da jego, ga kulawa ta musamman tana samu wajen Innani da gwaggo Rakiya, hakama Anty maijidda tasaka k'aimi wajen gyarata, acewarsu batada maimata saisu, hakama 'yan Jos ba'a barsu abayaba, kullum suna mak'ale da waya akunne. Su Fateema kam duk k'arshen Sati agidan suke yini, hakadai sukaita wankan hankalinsu a kwance. Watanta d'aya dawasu kwanaki Uncle ya ta'azzara dole suka tarkatota suka maido masa. Hummm fad'a muku yanda Uncle ya ragargaji soyayya 6ata lokacine, ammafa anshata tamkar babu gobe, yaransa sunata k'ara wayo, Ama.... bata wani shan wahalar raino, sanda tana gidan Innani da zama tsakaninta dasu sai bada nono, idan zasuje makaranta ta d'auki d'aya Aysha ta d'auki d'aya, yanzu kam tunda suka dawo gida Fateema da Aneesa da yara sune 'ya. Raino, tsakaninta dasu sai idan sunyi kukan yunwa kozasu kwanta barci. Ahaka aka shiga rugumniyar za6e. Kwanakin taron su Uncle kuma yarage kwana Uku kacal. zasuyine a Abuja dan matasan K'ASAR na 6angarori biyu suke son gani. Tun ana saura kwana biyu taron matasa suka fara turutwar tafiya birnin tarayya Abuja, kowa burinsa kar ayi babushi.😃🤝🏻. Ana gobe taron kam ai Abuja da'd'im tayi da matasa, abubuwa dayawa saida suka tsaya na harkar kasuwanci dawasu abubuwan. Washe garin taron kam hummmm, ai d'an adam ba'a cewa komai, saima ka d'auka duniyar suka tara a wajen kawai saboda yanda MATASAN KUDANCI DA AREWACI suka amsa wannan kira. Su Uncle sai aranar suka isa abujar da sassafe kuwa. Zuwa k'arfe 10 na safe taron yafara gudana.🤩👎🏻 Tunda su Uncle suka hau munbarin taron yake bin matasan da kallo, kawai saiyaji kwalla sun cika masa idanu, shin dama zaiga wannan ranar a rayuwarsa? ko a mafarki baita6a tunanin zai tara matasan dasuka haura hamsinba, amma ga sama da dubunnai a gabansa, hawayen dasuka cika idonsa suka fara gangarowa saman kumatunsa. Alhaji Sani dake kusadashi yad'an bubbuga kafad'arsa yana murmushi. juyowa Uncle yayi yana kallonsa, shima fuskarsa d'aukeda murmushin, yasa handkerchief yana goge hawayen...... Maganar Husain Abubakar d'aya daga cikin matasan masu fad'a aji a k'ungiyar ya d'auki hankalinsu. cikin harshen turanci yake maganar. (Amma ni zan fassara muku da hausa😜). "MATASANMU!!!". suka amsa da ihu. Yakuma fad'in " MATASANMU!! MATASANMU!!!!". tamkar zasu fasa birinin Abuja haka suka amsa wannan kira cikin d'aga hannu da kuwwar ihu. "Lallai Mun yarda MATASANMU suna buk'atar gyara a k'asarmu, amsa kiranku kawai ya tabbatar mana da hanakan, muna muku barka da zuwa wannan taro, da godiya ta musamman ga amsa wannan kira namu, MATASANMU!! abin alfaharinmu, kune k'asar, inhar babu Ku babu k'asa, kun AMINCE da hakan?!!!". Cikin Ihu sukace " Eh!!!!!!!!". "Kun Amince kune K'ASARMU?!!!". " Eh!!!!!!". "Kun Amince zaku had'a hannu wajen rik'eta dakawo zaman lafiya!!?". " Eh mun amince!!!!". "To Alhmdllh, muna godiya da wannan goyon baya, bara nabama shugaba kuma Uban jagoran wannan tafiya da jajircewar ganin munzama ababen Alfaharin, wato *_Alhaji Muhammad Ahmad Labbo!!!"._* Gaba d'aya suka hau ihu da sowa, duksun d'okantu dason ganinsa. Uncle yatako cikin nutsuwarsa zuwa gaban Munbarin, nanfa ihu yak'aru, suka shiga d'aga masa hannu da raira wak'ar girmamawa agareshi. Shima d'aga musu hannayensa duk biyu yakeyi, fuskarsa Na fidda Annurin murmushi da tsantsar farinciki ganin matasan nan. Da k'yar aka samu suka lafa da ihun dasukeyi, Uncle yay gyaran murya yana kuma daidaita tsayuwarsa da gyara zaman babbar rigarsa ta farar shadda akan kafad'a. Cikin sassanyar muryarnan tasa yaymusu sallama. Suka amsa. Saikuma yay shiru yana binsu da kallo, dandanan hawayen suka kuma cika masa ido, yasaka handkerchief yana goge guntayen hawayen dasuka fara k'ok'arin zubo masa a kumatu, nanfa gurin yay tsit idanunsu duk suna kansa, jikinsu yayi sanyi ganin yana sharar ido alamar kuka kenan, ahankali muryarsa tafara ratsa sifikan, " Nagode muku, nagode sosai, bansanma yanda zan nuna muku farincikina ba, amma tabbas ko ayanzu nabar duniya NACIKA BURINA, tabbas wannan shine CIKAR BURINA, KUN CIKA MINI BURINA na tsawon shekara da shekaru, banida abinda zan biyaku dashi, banidashi........ yakasa k'arasa maganar saboda kuka daya tokare mak'oshinsa (nace jama'a dama maza Na kuka irin haka😨?). Kukan Uncle yasaka matasan dayawa kuka, Dan aganinsu sune yadace suyi kuka bashiba, kodan ceto rayukansu dayayi a mafi yawan had'ararruka, ya canja musu gur6atattun ayyukansu da zaman banzan dasukeyi. Dak'yar Uncle yasamu ya daidaita kansa ganin yakarya zukatan matasan, yagoge fuskarsa yana murmushi. yagyara zaman Microphone's d'in da'aka jera kala-kala, Na 'yan jaridu. Yace, "kun shirya!!!!". Cikin matsanancin d'okamtuwa suka amsa da " eh!!!!!". Yakuma fad'in "da gaske MATSAN K'ASARMU sun shirya canja KANSU DA K'ASARSU!!!!?. " nanma suka amsa cikin matsanancin ihu". Uncle dasu Alhaji sabi'u suka tuntsure da dariya. _"Shin MATASANMU zaku yarda acigaba da amfani daku wajen BANGAR SIYASA!!!?"_ "A'a bazamu aminceba!!!!!!!!". _"MATASANMU Zaku kuma yarda abaku KAYAN MAYE domin Baku KU'DI kuyi bangar SIYASA ko wani TA'ADDANCI!!!!!!!!!?."_ " A'a bazamu aminceba!!!!!". _"MATASANMU zaku kuma yarda acigaba da Amafani daku wajen haddasa rikice-rikicen SIYASA KO K'ABILANCI ko fad'an ADDINI ko 'BANGARANCI!!!!!!?._ "A'a bazamu amince ba!!!!!". _" MATASANMU zaku kuma yarda ku ringa keta HADDIN abokan jinsinmu MATA ta hanyar yimusu FYA'DE ko zama KIDNAPPER'S ko FASHI da MAKAMI ko asakaku CIN ZARAFIN wani saboda KU'DI!!!!?"._ Nanma suka Amsa da bazasu aminceba. _"Inhar dagaske MATASANMU sunyi alk'awarin daina wad'annan gur6atattun ayukan dake ruguza K'ASARMU to ina buk'atar Ku tabbatar min da hakan a ZA'BEN dake tunkaromu, yakamata amatsayinku Na 'yan ADAM kuyi nazari akan yanda rayuwar talakan K'ASARMU ke tafiya. Nigeria babbar k'asace maifad'a aji a yankin Africa, k'asace mai tarin K'ABILU da ADDINAI, haka Ubangiji yaso ganinmu, wani bayajin yaren wani, amma kuma saiya dunk'ulemu a k'asa d'aya. Shin munfi ubangijin sanin dai-daine da mukeson rarraba kammu??, Ku koma Ku bibiyi ASALIN TARIHIN k'asarmu Nigeria, kuga yanda magabatanmu sukasha wahalar gwagwarmaya wajen kafa k'asar da kwato mana 'yancinmu, amma maimakon hakan abin bak'in cikin sai muka bari wannan wahalar tasu tatafi abanza, SIYASA taraba kawunanmu, nuna 'BANGARANCI da K'ABILANCI yahanamu zama tsintsiya mad'aurinki d'aya, WAY!!!!? kowa K'ABILARSA kawai yake kallo da gashin arzik'i, miyasa mukema juna kallon hadarin kaji?, manyan K'ABILUN K'ASARNAN sune HAUSA FULANI, YORUBA, IGBO, amma zakaga babu wata gagarumar jituwa atsakanin wad'annan k'abilun, kowanne jiyake shine agaba kuma dolene abisa, ko dolane yazama wani ginshik'in k'asar, amma kumafa bazamu iya had'e kai waje d'aya domin gyaran k'asarba, shin tayaya sauran k'ananun k'abilun zasuyi koyi damune?"._ "Shin kunsan miyasa hakan ya gagara tunma farko?". Suka Amsa da A'a. Tsayuwa Uncle yagyara yana share gumin fuskarsa, yacigaba da fad'in..... _"bakomai baneba face tsabar son MULKI da son tara dukiya, wlhy wlhy da wannane manyan k'asarmu suka rarraba kawunanmu, kowa buk'atarsa yazama SHUGABA, sannan idan yasami shugabancin bawaifa mu TALAKAWANNE agabansuba, ALJIHUNSU shine agabansu, damuwarsu shine su HADDASA MANA BALA'I su tattare IYALANSU subar K'ASAR da k'ud'inmu, yanzu inason namuku wata tambaya, tsakaninku da ALLAH kuma nakeson kubani amsa, nasan kashi 90 Na MATASANMU dake wajannan Government Schools mukayi karatu ai!!?"._ Suka shiga amsawa da eh hakane hakane. _" Shin kunta6a ganin wani d'an Governor ko Minister ko d'an Majalissan jiha kona datta6ai ko wani hamshak'in k'usar gwamnati a MAKARNTARKU ne ta gwamnati?"._ Gabad'a gurin ya kaure da ihun cecekuce. Saida akayi magana suka tsagaita. Uncle yacigaba da fad'in.... _"BANGAR SIYASA dasuke sakaku akwai 'ya'yansu? ko'a wajen Campaign baka ganin 'ya'yansu, wanima saiya gama shugabancin bakaga d'ansa ko d'ayaba, to basa k'asar, sunacan k'asashen TURAI suna karatu, idan sundawo k'asar kuma saidai ka hangesu A manyan motoci suna wucewa kan titi, shin wai mu 'ya'yan TALAKAWA bamusan kammu bane ko bamusan muhimmancin rayuwa baneba!!? idan Su badamuwarsu matasolinmuba mizai hana mu toshe duk wata hanyar dazasu sami Damar shugabantar tamune_." "Shin zamu iyane?". Suka amsa da sosaima kuwa.!!!!!!!!!. _"Alhmdllhi, kusanifa komai sukazama mune sila, dan haka awannan karon MATASANMU mu tabbatar musu da mune k'asar, mu tabbatar musu da lokacin amfani damu yawuce, mu tabbatar musu da yanzu munsan ciwon kanmu, mu tabbatar musu da dolene adama damu. ta hanya d'ayace hakan zata faru shine daina yarda ana amfani damu wajen aikata ta addanci, mutashi mu nemu Na kanmu, mudaina zama dogaro da gwamnati, akwai sana'oi k'ananu dayakamata MATASANMU sunayi domin kare mutuncin Kansu, kwad'ayin aiki da burin sainayi kud'ine ke ruguzamu, dashine suke samun galaba a kanmu, idanfa munyi haratu bashine ke nufin dole samun sami aiki a k'aton office's ba, shi karatu anayinsane domin k'ara nemawa kai martaba da kima aduk inda katsinci kanka, mudaina Shaye-Shaye, dan shima yana ruguzamu da tasirantuwa wajen maidamu baya, MATASANMU dan ALLAH muringa fad'ama kanmu gaskiya kafin wani yafad'a mana, mu gyara kafin a gyara mana, mu canja kafin a canjamu, mu yima kammu hisabi kafin ayi mana, mu tsaftace kammu kafin a tsaftacemu, rayuwarmu tamuce, idan ta lalace mune mukayi asara, wlhy duk sonmu da gwamnati ta gyara sai muma mun gyara d'in, duk Wanda kaji ankira da suna WANE to wlhy badaga kwance ya tsinto sunanba, saida yasha wahalhalun rayuwa, SHUWAGABANNINMU fa suna zuwa dai-dai da halayenmu ne, to Ashe samun tsaftataccen shugabanci da dawwamammen zaman lafiya dayake a hannunmu, idan muka gyara kammu shugabannin kansu tsoron 6atamana zasu dingaji, dansai kazama nagarine zamu za6eka mu kaika inda kake kwad'ayin, Ku gyara dan aza6e nagaba sonake naga MATASANMU ne governor's, kune Senate's president, kune house of Rives kune Minister's kune kune kune........!!!!".🙋🏻‍♂😁_ Gaba d'aya wajen yarud'e da ihun sowa, fad'i suke "ALLAH yaja zamaninka, yak'ara maka lafiya da yawancin kwana.......". Saikuma suka koma wak'ar girmamawa agaresa (Ku saurara zan reromuku wak'ar kuji😂😜🚶🏻‍♀). 'Daga musu hannu kawai Uncle yakeyi, bakinsa yakasa rufuwa saboda jindad'i da farincikin ganin wannan rana mai tarin tarihi a history nashi😁😁😁✋🏻✋🏻✋🏻✋🏻. Da k'yar sukayi shiru Alhaji Sabi'u shima yay nasa jawabin cikin girmamawa, dukdai gargad'ine akan karsu bari ayi amfani dasu wajen haddasa rikice-rikicen za6e, kowa yaza6i za6insa cikin lumana, kuma suza6i mutumin kirki bawanda zaiyi amfani da mulkiba ya ruguzasu suda k'asar baki d'aya, suyi amfani da shawarwarin shugaban wannan k'ungiya Alhjai Muhammad Ahmad Labbo, kada subari kud'i su rud'esu, dansu kwana kad'an zasu k'are, mutuncinsu dana k'asarsu kam yacigaba da sauka kenan harta koma babu abin moruwa, suduba gobensu da jibinsu bawai yau d'insuba, shima yagudanar da nasiha mai ratsa jiki, wadda tasaka matasan jinjinama k'ok'arinsa da yin na'am da wannan nasiha. d'aya bayan d'aya shugabannin sukaita jawabi da nasiha ga matasan. Taro yatashi lafiya Alhmdllh, su Uncle dole suka kwana Abuja dan sun kuma gudanar da taro isu-isu Na manyan k'ungiyar Na jihohin Nigeria baki d'aya. Su Amatullah duk a NTA suka kalla live. kafin kacemi taron yazagaye kafafen yad'a labaran social media dana redio's television's, Jaridu, bawai a Nigeria kawaiba harma da k'asashen k'etare. Dayawan 'yan SIYASA kam lamarin ya tsoratasu, tabbas matasan da gaske sukeyi gyara suke buk'ata 100%, gakuma sarakunan gargajiya Na kudanci da arewaci sunbama wannan k'ungiya goyon baya 100%................✍🏻 🤩👎🏻 One luv😻😻😻😻✋🏻 [1/25, 5:58 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_* *_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡 _{home of expert and perfect writer's}_ *_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉ _(Hattara matasa)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* ____________________ *_Number 46/50_* ____________________ Alhmdllh wannan lamari yakuma k'ara fiddo kimar Uncle a idanun duniya, nanfa wasu manyan k'ungiyoyin duniya na matasa suka fara gayyatarsa domin zama Na musamman, harma dawasu shuwagabannin k'asashe. Uncle yazama babban gwaska, tauraro abin alfarin MATASANMU da k'asarmu, kowa burinsa yayi mu'amulla dashi, dolensa ya ajiye aikin dayakeyi a bayaro, dan nauyi yamasa yawa sosai, ga iyali ga aikin al'umma. Dukda wad'annan nauye-nauyen hakan bai hanashi cigaba da tattalin iyalansaba, saima abinda yay gaba, suma kuma suna tattalinsa dabashi kulawa, kowacce tana kishinsa da k'ok'arin kafa babbar fada a zuciyarsa. Duk d'insu yana yabama k'ok'arinsu da jinjinama halin dattakonsu, dan kishinsu shine yakamata asamu akowanne gidan aure, saidai yasan wani zafin kishin yakan had'a da zalincin wasu mazan🙁🙄. ALLAH dai ya shiryesu Uncle. ************** Ana gab da za6e sukasha binkin Aysha da Dr yazeed, Wanda Uncle ne komai a bikin, duk wata hidima daya kamata iyaye suyi shine yayma Aysha, kuma baigazaba wajen zuwa takanas ya fad'ama danginta komai, harma da rok'onsu wasu sushiga lamarin auren, koba komai dai d'iyarsuce, kimarsa da halin dattako yasakasu nad'o gari zuwa bikin, tabbas jikinsu yayi sanyi daganin Goodness (Aysha) bata rasa komai Na rayuwaba, saima d'aukaka da ALLAH yak'ara mata, ga miji ga karatunta mai yankeba, Wanda fatansu tasha wahala sabida rashin tallafinsu, a haukarsu hakan zaisa tadawo addininsu, shiyyasa suka koreta, to Ashe Na kwarai basa k'arewa, saigashi ALLAH yaymata nasibi da samun wasu dagin masu k'aunarta. Bata nuna musu komaiba, saima kar6arsu da nuna musu har yanzu sunada muhimmanci a rayuwarta, dan ba'a canjama tuwo suna. Su Ama.... Sune amarori k'irjin biki. Ahakadai taro yatashi lafiya, amarya tatare gidan mijinta, Innani harda hawayenta Na rabuwa da Aysha, dan harga ALLAH tana k'aunar yarinyar har cikin ranta. To shatu ALLAH yabada zaman lafiya da zuria d'ayyiba.😻🤝🏻 ************ Za6e yagudana cikin lumana da kwanciyar hankali kamar yanda su Uncle sukayi fata, Alhmdllh kuma ansamu biyan buk'ata daga matasan wajen za6en shugabanni Na gari masu kishin k'asar dason cigabanta. Sannan matsan dayawa sunsami wasu fannoni Na madafun ikon k'asar , kamadaga ministers, Commissioners, da wasu fannoni daban-daban Na muk'amai😁👍🏻. Saimuce ALLAH yatayaku rik'o😻. ******* ****** ******* Yau takasance Juma'a, tunda Uncle yadawo sallar juma'a shida yara bai sake fitaba, sukayi Lunch gaba d'aya kamar yanda yazama doka yanzu agidan, duk weekend tare sukecin abinci suda yaransu. Sallar La'asar tasaka taron firar watsewa, Uncle da yara suka tafi masallaci su Aneesa kuma kowa tashige d'akinta. Da sauri Amatullah tak'arasa gaban gadon ganin Raihana dake barci Na neman sakkowa, tatashi tuni, kasancewar yarinyar tanada matuk'ar hak'uri ko kuka batayiba, tagaji da wasa agadon shine tafara k'ok'arin sakkowa, ALLAH ma yakawo Ama... d'in datasha k'asa. Dungure mata kai Ama... tayi tana fad'in "mamana dakin fad'o Aida kinjamin masifa wajen Uncle nasan bawai zai ragamin baneba". Kamar Raihana taji mi Ama... ke fad'a saita ta6e Baki tana niyyar yin kuka, rawa Ama... tafara mata tana rera mata wak'a kamar yanda take musu itada Rayyan idan suna rigima. Tuni Raihana tayi shiru takoma 6alle Baki tana dariya, Ama..... ta sauketa tana dariyar itama, yauwa Ammi Uwa mai dad'i, zauna kiyi wasa nayi salla kafin Rayyan yatashi shima, yau inada Shiga kitchen". Idar da sallarta babu dad'ewa tajiyo kamar ana magana sama-sama daga babban falo, kuma tamkar muryar Aneesa. Cire hijjab tayi ta d'auki Raihana dake wasa a k'asa tafita (dan tuni yaran sunama rarrafe). " momyn yara lafiy......." Maganar Ama... takatse lokacinda idonta ya sauka akan zee-zee dake zaune itada Rita dawasu 'yammata biyu Wanda duk Amatullah ta sansu amma ta manta sunansu. Aneesa ta katseta da fad'in "kokin sansune Auntyn yara?". Sosaima kuwa, aiduk school mate d'inane, ''amma lafiya kuwa Rita?". Yatsine fuska Rita tayi tana wani taunar cingom, a yangance ta nuna zee. Ama.... Ta maida kallonta ga zee d'in, ''Zainab lafiya?". Saida Zee tamata wani kallon sama da k'asa sannan tace, "maigidan nazo nema". Fateema dake fitowa tace, " maigidan kuma? shikam Nurri miya had'ashi da wad'annan masu kamada kilakin?". Daga zee har muk'arabanta babu wacce ta tanka, saima taunar Cingom sukeyi, jikake k'ass! k'ass!! k'ak'as!!!. Saida suka gama shan k'amshinsu sannan d'aya daga cikin 'yanmatan biyu tace, "Amaryarku ce tazo gaisheku ". Kallon juna Aneesa da Fateema da Amatullah sukayi, Aneesa sarkin rashin hak'uri tafara lailayo musu zagi. K'in tankawa sukayi, saima cigaba da iya shegensu sukayi. Ana haka maigidan yadawo, kallon matan nasa dasuka tsareshi da idanun tun shigowarsa yayi, " lafiya kuma kukam?". Aneesa Ce ta nuna masa su zee tana k'ara kumbura baki. Gabansa yafad'i, azuciyarsa yace yarinyarnanfa ta gundureni, yanzu abin yakai harma gidana..........? Fateema ta k'atse tunaninsa, "Nurri waisu waye sune?". Kallonta Uncle yayi, sannan ya kalli yaransa dake tsaye cirko-cirko suna kallon iyayensu da wad'annan bak'i dabasu san kosu wayeba. " Abulkhairi ja k'annenka kuje tsakar gida kuyi wasa, kar Wanda yadawo sai an kirasa". "To Abbu". Suna fita Uncle ya kalli su Zee. " miya kawoku gidana Zainab?". Kanta ta sunkuyar k'asa tana wani murmushi, "nagane kusan 2weeks baka picking calls d'ina shiyyasa nace bara nazo naga lafiya". Tsayuwarsa yagyara sosai, hannayensa zube cikin aljihun blue d'in jallabiyarsa, ya fiddo d'aya yashafa gemunsa sannan ya maida, cikin sauke numfashi yace, " k'alau nake, kawai ayyukane sukamin yawa, ngd". Yana gama fad'a yanufi samansa batareda yakuma kallon kowacce acikinsuba, harsu Amatullah d'inma. Wani mayataccen kallo zee tabishi dashi, yanda ma yake taka steps d'in benen kawai abin birgewane, harya kai k'arshe kuma bai juyo ya kallesuba. Su Aneesa suncika sunyi FAM, shin me mijin nasu yake nufine? Budurwar tasace kenan da gaske?. Ai bak'inciki hana Amatullah maganama yayi, saita juya 6angarenta kawai. Aneesa ce tafara masifa, "to gayyar tsiya arna a idi sai a tashi abar mana gida ko, tunda bana gado baneba". Su Rita zasuyi magana Zee ta hanasu, tamik'e tsaye tana fad'in " kutashi muje, karku wani damu kanku, kwana nawane nazama matar gidan nima, kowacce shegiya acikinsu saita bar gidan da k'afafunta, dan nikad'ai nakeson kasancewa da abin sona, duk d'unsu basukai matsayin Na had'a kishi da sub....... Dukan da Aneesa takaima bakinta yasakata yin shirun dole, tadafe baki "kai kai nikika dakarma baki?".... " andaki bakin naki, Ku kama gabanku ma kafin mu jigataku a falonnan''. Cewar Fateema. Kwafa su Zee sukayi suka fice. Fasifa k'awayen nata suka hau yi bayan sun fita, akan miyasa bata bari sun koyama matannan hankaliba. Tace, "kubarsu, lokacinsune, daga sanda nashigo gidan babu mai sake yin tari acikinsu, kudai kusaka ido kusha kallo." Dariya suka shek'e da ita damata jinjina. Koda su Zee suka fita sai Aneesa da Fateema suka nufi saman Uncle, a zaune suka iskeshi hankali kwance yana searching tasha a TV, sallamarsu kawai ya amsa batareda ya kallesuba, dan yasanma miya kawosu. Fateema tace "wai yanzu nan Nurri wannan kuma wacece?". Kallonta kawai yayi ya kauda kansa, Aneesa takuma maimata masa tambaya, " Dear maganafa mukeyi! Wacece wannan kilakin?". "To mikukeso Na fad'a muku? Nace ba abinda kuke tunanin bane, kumin kallon mayaudari, kokuwa nace sona take ni bana sonta ku kirani mak'aryaci, inama mai baku shawarar karku tasirantar da abinda bakuda ilimi akansa a zuciyarku. Babu wacce ta tanka masa acikinsu, sukayima ficewarsu suka barmasa falon. Kallo kawai yabisu dashi, ya sauke ajiyar zuciya ta 6acin rai, tabbas lokaci yayi dazai takama yarinyarnan Zainab birki akan haukarta, tunda har tsaurin idonta yakai ta kwaso k'awaye tazo masa gida wajen iyalansa, harma tadunga musu furuci mara k'yau, (dan yana jiyo duk abinda yafaru bayan barinsa wajen), iyalinsa sune mutuncinsa, martabarsa da dukkan sirrinsa, bazai lamunci wata ko wani ya raina masa suba ko 6ata rayukansu, yayi kwafa yana jingina kansa jikin kujerar da lumshe idanu. Yakai tsawon lokaci yana tunani awajen kafin ya sakko k'asa, babu kowa a falon, yarama suna tsakar gida suna wasa, ya kalli 6angaren Aneesa yaga arufe, Fateema ma a rufe, saiya nufi Na Amatullah. Tunda Ama... tajiyo k'amshin turarensa ta ajiye Rayyan datake bama nono tashige bathroom, tanajin Rayyan d'in ya fashe da kuka amma bata kulaba tarufe bayin. Da sauri Uncle ya k'araso ya d'aukeshi, jijjigashi yafraayi yana fad'in "oh my brother na, waye yasaka kuka? Ina Antyn tajene?". Rayyan yayi shiru tareda lafewa jikin babansa, sai ajiyar zuciya, zama yay falon yana jiran fitowarta, amma bulum, mamaki yakamashi, yatashi yalek'a bedroom d'in babu kowa, sai Raihana a kan gado data koma barci, zama yayi abakin gadon yana jiran fitowarta, nanma shiru kakeji. Ama.... kuwa zamantama tayi a toilet d'in tana charting hankalinta kwance, duk kuma bidirin da Uncle keyi tana jiyoshi. tashiyay yafara knocking d'in k'ofar bathroom d'in, amma shiru kakeji. mamaki yakamashi, kodaima bata d'akinne? wannan tunaninne yasakashi ficewa da Rayyan a hannu, tsakar gida yafita inda yaran ke ball, zama yay yana kallonsu da tunanin lamarin matan nasa fal a kansa, wato dai sun had'e masa kai kenan, yay murmushi da k'arajin k'aunar matan nasa a ransa😊. Kiran Sallar magriba tasakashi tasa yaran maza gaba suka tafi masallaci kamar yanda yasaba, yabama Ummita Rayyan suka koma falo itada Siddiqa da mah-mah. Jin sunfita masallaci Ama.... tayi sallah sannan tashiga kitchen nata, tadafa cus-cus. taimaza takai masa nasa ta sakko kafin su dawo. Koda yadawo bai nemesuba, yaransa yatasa gaba suka tafi falonsa, acan sukaci abinci sunata masa hirar makaranta, shikuma yabiye musu, dan yau sune abokan hirar tashi. Saida yaga wasunsu sun fara gyangyad'i sannan yatashesu, yarakosu k'asa, kowa yashiga d'akin mamansa, shikuma yashiga 6angaren Ama.... domin kaimata Rayyan da shima yay barci. Kwance ya taddata tana bama Raihana nono, wadda keta d'aga k'afa d'aya tana wasa dashi saboda dad'in shan nonon datakeji. Kallo d'aya Ama... tayi masa ta kauda kanta, guntun murmushi yayi, ya sauke Rayyan dake a kafad'arsa saman gadon, baimata maganaba yabud'e dirowar yaran ya d'akko kayan barcin Rayyan ya fara saka masa, sai lokacin idon Raihana yakai Kansa, sakin nonon tayi da sauri ta rarrafo wajensa tana murnar ganinsa (yanda Uncle yake tattalin yaransa da yawan d'aukarsu yasa sukayi mugun sabo dashi, zakiga duk k'iwar da yaronsa zaiyi dawuya shi yayi masa), d'aukarta yayi yafara cillata sama tana dariya shima yanayi, sai Rayyan kuma yasaka kuka shima a d'aukesa. dariya Uncle yayi tareda zama yajawoshi jikinsa shima yana fad'in "jealous ko my Sweetheart". Amatullah dai duk tana jinsu amma tayi kamarma batasan sunayiba, shirin barcinta kawai tayi tazo gefen gadon ta kwanta. Shima shareta yayi, saida yaga ya lalla6a yaransa sunyi barci sannan yatashi ya fice. Mintuna k'alilan yadawo bayan ya shishshiga sashen su Aneesa yayima yara addu'a yafito bai kula kowaccensuba. Shi dariyama suke bashi wlhy. Idon Ama.... biyu, tanajin sanda ya shigo harya kashe fitilar d'akin ya hawo gadon. 6oyayyar Ajiyar zuciya tasaki, shikam yayi tashi a fili yana fad'in " I miss you my heartbest". Shiru tamasa. Acikin kunnenta yace, "wai duk kishinne ginbiyata? kinsan ko matan duniya sun k'are babu abinda zanyi da yarinyar can, yakamata Ku shedeni aii, amma keda 'yan Uwanki kun had'e min kai kunata fushi dani". "Fushinmi zamuyi dakai, namu ALLAH ya sanya alkairine aii, miye namu danzakayi amarya". Sassanyan Murmushi yayi yana shafa kanta, ganin kalaman baki bazasu mataba yakoma salon dazata fahimcesa. (🏃‍♀nayi nan). Bayan wani d'an lokaci Na koma, saina taras Uncle Na lallashin Ama... dake kuka, yabata labarin tundaga farkon had'uwarsa da Zainab (zee) har zuwa yanzun, yak'are damata kalaman kwantar da hankali da lallashi, ya tabbatar mata itace autar mata a gidansa har Abadan insha ALLAH. cikin dai hikimarsa ya shawo kanta harta yarda dashi da bashi hak'uri. Yay dariya da kuma rungumeta yana mata daddad'an kalamai. Hakama Aneesa saida yakoma d'akinta ya lallashi abinsa, damata bayani dallah-dallah akan zee kamar yanda yayma Ama...., itama Fateema hakan yamata, duk suka gamsu da komawa tattalin mijinsu tamkar da, amma saida suka saci number zee a wayar Uncle suka had'a kai su uku bayan sun kirata sun saka Hans Free suka mata tatas da gargad'i mai zafi akan mijinsu. Hakanne yasaka zee kiransa tana kuka dafad'a masa abinda matansa sukai mata, yana k'ayataccen murmushi yana saurararenta, saida takai k'arshe sannan yay k'aramar dariya yana gyara zama a kujera (dayake a kasuwa yake). Cikin sasaanyar muryarsa dake kashe ga6o6in Zee😜 yace "To kinga ai saikiji gargad'insu kifita hanyar mijinsu, nidai babu ruwana, tuni na sanar dake banida burin k'ara aure, matana sun isheni, dan haka kisama zuciyarki salama ki sami miji kiyi aurenki, nabarki lafiya inakuma baki shawarar karkiyi gigin sake zuwa gidana, Dan babu ruwana idan matana suka miki wani Abu, nid'in mijin hajiyoyine😆, ALLAH yabamu alkairi.😝 Tundaga wannan ranar zee tafita harkar Uncle, bata sake kiransaba balle turo masa messenges. Haka kuma rayuwar tacigaba da turawa. 3years later😜🤣 ALLAH mai girma da d'aukaka, yau gasu Ama... ana bikin yayesu amatsayin manyan likitoci kwararru, bakunansu sunkasa rufuwa saboda tsabar farin ciki, hakama Na danginsu wad'ada sukayi tururuwa halattar taron. Ciki hardasu Uncle da matansa duka, Anty maijiddah Nazeefa zaliha Asiya su aunty Firera da mazansu su kawu Hafizu, matansu Alhaji Sabi'u da dangin su Fa'iza, harda dangin Su Aysha (goodness) wad'anda ayanzu sun sakko suna ziyarar 'Yar uwarsu itama tana ziyaryarsu, harda d'anta Muhammad (Wanda taima Uncle takwara😄) suna kiransa Yaseer. Angudanar da taro cikin sha'awa da birgewa, tareda kar6ar k'yaututtuka dasu Ama.... suka samu, Uncle jiyake tamkar ya had'iyeta saboda dad'i da k'ara sonta, Dan har yanzu Ama.... tana cikin k'uruciyarta, yanzunema take kuma kilewa tana zama hamshak'iyar mace, ga 'yan yaranta su Rayyan abin sha'awa, sunyi girma sosai da wayo, har sun shiga school tuni, tundagasu kuma bata sakeba, koda yake Fateema ma da Aneesa shiru, tundaga Abubakar Aneesa ma bata sakeba, hakama Fateema tunga mah-mah. Sunsha hotuna tamkar babu gobe, harda Innani da gwaggo Rakiya wadda su shehu suka matsa tilas sukazo suma, Nazeefa da Zaliha da Asiya ma duksun sake haihuwa tuni. Tarodai yatashi lafiya cikin farinciki da annashuwa, kowa yakama gabansa. Su Uncle suka nufi gida inda acanma Uncle yahad'a liyafar cin abinci saboda farantama Amatullah rai, anci ansha an gyatse kuwa, lamarin sai sambarka. *_Kishi kumallon mata🤣_* Tunda su Fateema sukaga Amatullah tafara aiki sukayi tsalle suka dire akan suma aiki zasuyi, kowacce ta kakka6o takardunta daga k'asan jaka. Uncle yay dariya sosai sannan ya had'e fuska. "Amma lallai bakuda hankali, ai kuda aiki saidai Na gidana, idan kun manta bara Na tuna muku to, alokacin dana aureku babu wacce ta shekara a gidana Na tuntu6eku akan kozakuyi aiki?, ince kowaccenku nunamin tayi batada ra'ayi, Ku kulawa dani kawai kukasa agaba, ban gajiyaba nakuma muku hannunka mai sanda akan Sana'a, nannama kukayi kunnen uwar shegu dani, saikuma yanzu dan kunga Khadeeja kuma kuce saikunyi? to idanfa ba 6acin rai kuke nemarwa gidanmu ba kuma ajiye wannan maganar mucigaba da rayuwarmu, itama data nuna batason aikin ko karatun bazan bartaba, amma tun farko ta tabbatarmin hakanne burinta, shiyyasa nabata goyon baya wajen cikarsa, Ku kama kanku, mud'in ba yara baneba balle kuce, yanzu inada k'aton saurayin yaro dake shirin kammala Secondary, banason shashanci, dan haka kutashi ku bani waje". Haka suka tashi kowacce ranta a jagule da Dana Sanin k'in amincewarsu tun farko, dayanzu suma sunzama manyan hajiyoyi da ake damawa dasu, amma sukaima Kansu sakkiyar da babu ruwa, gashinan suna zaune Ama... tafara karatu harta mammala tazama hamshak'iyar likita abin alfahari ga mata😆😜. Bayan kwana biyu suka bashi hak'uri ganin yanata faman fushi dasu. Shima saiya hak'ura, harma ya k'ara musu da k'yautar jari akan suyi kasuwanci, harda Ama.... itama yabata kamar yanda yabasu dukda dai bawasu kud'i masu yawa baneba. Tundaga lokacin kowacce takama kasuwancinta, Amatullah kan su kawu hafizu tabamawa akan sucigaba da juya mata anasu kasuwancin, itakuma tarik'e aikinta kawai tunda batada matsalar ci ko sha balle sutura, mijinsu yana iyakar iyawarsa wajen sauke wannan hak'in nasu. Humm, idanfa kukaga Amatullah dolene takuma birgeku yanzu, tayi k'iba ta murje, daka ganta kaga mata hamshak'ai masu aji, gata da k'ok'arin taimakon mata akan kowanne fanni, kullum cikin basu shawarwari takeyi ta yanda zasu tattali Kansu da yaransu, gata da sauk'in kai da tausayin marasa lafiya, koyaya kake Ama... bata k'yamatarka, dantace ai itama talakance, mizaisa ta k'yamaci 'yan uwanta talakawa, gata da taimako, Rabin albashinta duk kan marasa lafiya mabuk'ata suke tafiya, 'yan yaranta abin sha'awa, kullum cikin godiya takema ALLAH dayabata su da miji irin Uncle, Wanda ayanzu shine duniyarta, shine babanta shine Amminta, shine Uncle d'inta shine kuma miji shine dangi shida danginsa, takowanne fanni sun kare mata mutuncinta da nuna mata k'auna da d'unbin tausayi saboda rasa mahaifanta wad'anda kullum cikin musu addu'ar Neman gafara take dayin sadaka domin ladan yakai garesu, itakam babu abinda zatacema ALLAH sai godiya, danya canja mata rayuwa fiyeda zaton mai tunani, kullum cikin ambaton ALHAMDULLAH take✍🏻👌🏼. 😁 Tonima dai bilynku nace ALHAMDULLAHI. _ina godiya ga UBANGIJIN Al'arshi daya bani ikon fara wannan littafi da kammalashi cikin Aminci, Abinda nafad'a dai-dai ALLAH kabani lada, wanda nayi kuskure ALLAH ka gafarta mini._ _Kulum ina k'ara rok'on masoyana akan su kasance masumin gyara yayinda sukaga kuskure a buks d'ina, insha ALLAH zan kuma fahimcesu da ganin k'imarsu, ina ganin darajar Wanda zaicemin Na gyara kuskurena, Dan haka karkuyi sanya Dan ALLAH, gyaran kuma yazamto ta k'yak'yk'yawar hanyar dazan fahimta, Ngd da k'aunar dakuke nunamin, nima ina matuk'ar k'aunarku wlhy._🥰 Naso buk d'innan yafi haka fad'ad'a, amma matsalar wayata yasakani tilas Na datse labarin iya nan, kumin afuwa, ina kuma fatan iya hakanma zai gamsar daku da amfanar daku. _Babbar nasarata shine Ku tasirantu akan abinda yake mai k'yau a labarinnan, sannan kuyi watsi da kuskurena kasancewar nid'in 'Yar adamce Azija.😇, ina kuskure, bakuma komai nasaniba._ *_Tawan Miss xoxo ina godiya agareki, ked'in tadabannce a zuciyar Bily, babu abinda zance sai ALLAH yabar mana zuminci._*🤝🏻😽😻😻 _Masu min comments kullum dama mahaifina addu'a batareda gajiyawaba kuma ngd sosai, ina alfahari daku, matsalar wayata bazai bari Na lissafokuba, amma kuna k'asan raina, kuma bazan manta dakuba, zuwa nan gaba kuma zan tabbatar muku da hakan.😊🤝🏻👍🏻._ *Bilkisa Ibrahim musa (bilyn Abdull).😊* 🤩👎🏻 Marubuciyar... _Rashin sani!!_ _Auren k'addara ko biyayya!?_ _K'anwar uwace ko kishiyar uwa!?_ _Ni da Aminiyata!!_ _Nawaff!!_ _Ban saketaba!!_ _Abdul-maleek bobo!!_ _karayar arzeek'i!!_ _Ciki da gaskiya!!_ _Sanadin bikin sallah!!_ _Sabon Al'amaree!!_ _Kukan kurciya.....!!_ _Siyasa ko k'abilanci!!?_ _Wanda bai karantaba ya nema a kasuwar social media🤣, karku bari ayi babuku😉😄👌🏼._ Ngd sosai. One Luv😻😻😻😻😻😻😊👌🏼. *ALLAH ka gafartama mahaifanmu dadukkan sauran 'yan uwa musulmai dasuka rigamu kwanta dama, ALLAH ka jagoranci al'amuranmu akan wannan za6e dake tunkaromu, Rabbi ka azurtamu da shuwagabbani nagari masu zinariyar zuciya, ALLAH karkabama dukkan wani azzalimin shugaba damar hawa kujerar da suke kwad'ayi, ALLAH yasa ayi lafiya a gama lafiya batareda tada rikicin SIYASA KO K'ABILANCI ba, ALLAH ka d'aukaka Nigeria yarmu.* NIGERIA is One Nation One people.🇳🇬😊👍🏻👌🏼 *_HATTAR MATASANMU👈🏻👉🏻, Idan k'asarmu tarikece kune👉🏻, idan anyi tsaftataccen za6e kune👈🏻, Dan da k'arfin samartakarku da wautarku ake amfani wajen tada rikice-rikice yayin za6e, inkunk'i bada had'inkai amfaninkune, dan kowa rai yayma dad'i BARAN MAI SHINE🙁🤝🏻._* _masoyana saikuma bayan Sallah k'arama idan munkai da darai, ALLAH ya had'amu da alkairi, kushirya da k'yau, zandawo muku da sabon salo insha ALLAH😉, buk d'ina nagaba hummmm bara dai nayi shiru🤭😂, kuma karkuce komaifa🤫🤗._ *_NEXT LEVEL_*😬🥰😍 Compilied By Abubakar Saleh AlQuyraemey Whatsapp Number 08138873799 Visit www.rumbunlabarai.com For More Complete Documents *_BILYN ABDUL CE🤙🏻_*😻😻😻😻😻😽😹.