BAZATA By ©Rash Kardam 1 ********************** ⬇ ************************** ********** Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan likitoci fiskan ta sanye take da yar karamar glass wanda ya kara fito da tsananin kyan da Allah ya mata kalo daya zaka mata ka gane irin nutsuwar da take dashi, gata da kyau ga ilimi, tsayuwa nayi sosai na soma kare mata kallo, da farko zan iya ce muku farace sol, tana da manyan ido gasu farare tass! Masu fisgar hankali wato irin idon nan da ake musu lakabi da sexy eyes, tana da dan karamin baki wanda in ka gansu sai sun baka sha’awa, sa’anan tana da dogon hanci kamar pencil, Allah ya hore mata dukiyar kyau ba laifi, gata da hips dinta, san nan bata da wani kiba, ko da na kalli cikinta a dakale yake, wannan zai baka damar gane acikin wasu jerin mata take. Sannu a hankali ta iso gun motar ta ta bude tashiga, ta juta ta kalli gefenta tace sorry Sis Feenat na dade ko amin afuwa, zakin muryanta da salon da take magana ya sani lumshe ido nan take na fara jin bacci, kunna motar tayi ta dau hanyar fita daga cikin ATBU. Cikin nutsuwa take tukinta tayi nisa da Asibitin ABUT kena ta kaarya kwana, ta hango motar Doctor Marsal tana isowa, parking tayi a gefen hanya ta kalli feenat tace sis ina zuwa ga docter Marsal nan bari in mata magana, tafito cikin takunta mai dauke hankalin mai karatu, DR Marsal kuwa da ta hango ta itama parking tayi ta fito suka tsaya suna gaisawa, sun dauki minti biyar suna tsaye, can wata mota ciran frado mai bakin glass ta taho gadan-gadan kansu tayo, Marsal tana hango Motar tace DR Jiddah ki matsa ga dan ne man maganan nan zai fara, Dr Jiddah ta nuna kamar bata gane waye ba tace"waye dan neman magana?". Cikin dariya Dr Marsal tace " kin fini san shi wato share wa kikay"., Cikin ko in kula Dr Jidda tace "wai wa kike nufi?". Dr Marsal tace "waye in ba Doctor M Ghali ba". "Mtss". Ta ja tsaki, aiko kafin ta rufe baki kaji tasss!…… Ya watsa mata ruwan da ya taru a gefen hanya, dake lokacin damina ne, ranta in yayi dubu to ya baci, tsayawa yayi da motarsa ya fito yana dariyan mugunta, ya soma takowa sannu a hankali ya iso inda suke, cikin tsiwa da masifa ta bude baki zata soma zazzaga masa mafifa, ya ciro kudi masu yawa, ya watsa mata tare kashe mata ido daya ya daga mata gira. ya ce"ga wannan kisai omo, ki wanke kayanki, in kuma hakan zai yi wuya to ki barsu a haka zasu dacewa da ke". Ya dan sake wani murmushin mugunta mai tattare da bayyana nasara acikintanya ce" ko da ya ke na sanki gwanar iya wanki ne ba sai kin tsaya bayar wa amiki ba". Ya sake kashe mata ido daya ya juya yana takun isa da mulki gamida kasaita ya fara tafiya yana jin wani nishadi a zuciyarsa ko ba komai yaji sanyi a ransa. Yakuma rama kadan daga cikin abubuwan da wannan Yarinyar take masa. Idan ran Jiddah yayi dari to ya baci har wani daci-daci take ji a lebben bakinta. Bata kaiga karshen bakin ciki bata yi wani yinkuri ba tana fama da radadin abunda ya mata, yazo zai wuce da motarsa ya kara buleta da kurar motar sa, ko da ta juya aiko nan taga jama ita suke kallo, nan taji hawaye, bakin ciki yasoma zubo mata don tunda take a rayuwarta bata taba karo da cin zarafi irin wannan ba. Ko ta kan marsal bata bi ba ta nufi motarta a guje ta shiga tà saki wani kuka tare da tada motar bar gun da gudu, Marsal na mata magana ko tabi takanta. BAZATA By ©Rash Kardam 2 Nan take taji wasu zafafan hawayen bakin ciki sun zomata, da sauri tayi maotar ta, ko kan marsal bata bi ba, motar ta shiga ta tada, da gudu ta bar gun, feenat da taga duk abunda ya faru sani halin kan warta yasa bata ce mata komai ba, amma gani irin gudun da take, yasa feenat tace Jiddah mai kk yi hakane, don wani ya bata miki rai kike son yin wasa da rayuwanki, me yasa kike da saurin daukan zafi akan al’amari, jiddah ko bata ce komai ba kuma bata rage gudun ba, ganin haka yasa ran feenat ya baci, tace tsaya jiddah ma tsawan baza ki rage gudun motar, to ki tsaya in fita miki a mota, ganin ran sis dinta ya baci yasa ta rage gudun, shiru sukayi, a haka suke tafiya, sannu a hankali, har suka iso Zamani Area, ko da suka shigo Area wani katon gida naga sun nufa ba laifi gidan na da kyau dai dai gargwado, horn tayi mai gadi ya bude, zuwa parking spaces tayi ta ajiye morta ta, gi fen na feenat, tana kashe motar ta fito da sauri tayi dakinta, kayan ta cire kafin ta shiga wanka, feenat ko tana shigowa sukayi karo da hajiyarsu, cikin girmama wa ta mata sannu da gida, ta’amsa cikin fara’ah, ya mai jikin ta amsa da sauki, tace Allah ya bata lfy ta amsa da Ameen, nan tace ina Jiddah kuma? tace ta shiga dakinta, tace ok, tayi kitchen, feenat ta wuce nata dakin, kwanciya tayi kan gado don hutawa. Dr M Ghali kuwa ya bude jiddah da kura, ya nufi cikin T.H, ko da yashiga gurin ajiye motoci ya ajiye ta sa kafin ya dauko briefcase finsa ya fito, kallo daya zaka masa kasan yana cikin farin ciki, badan komai ba, sai don yasan ko ba komai ya tusa ma jiddah bakin ciki yau kuma ya tsokaneta gashi a bainar jama’ah, shima ya rama abunda ta masa, cikin kamala yake tafiya har ya isa office dinsa, mutane sai gaidasa sukeyi ya na amsa musu cikin sakin fuska, ko da ya shiga office din sa, ko ina a gyare tsab do Dr Ghali gwanin tsabta ne, gashi ma aboci son sanyi da kashi, kallo daya zaka masa ka gane cikaken dan boko ne da ya amsa sunansa, ya hadu iya haduwa, ko da ya zauna, nima na dan leko ta window office dinsa don in kara kalon wan nan guye din, ko.da na leka na zuba masa ido sosai, zan iya ce muku dogo ne, yana da dan kauri ba kuma wai zamuce mai kiba ba aa, dan da dai de, yana da dogon hanci wanda ya kai daf da karamin bakinsa, ko da yayi murmushi nan na hango fararen hakuransa, fari ne, fuskansa na dauke da annuri sosai, gaskiy Dr Ghali bana wasa bane, don irin saurayinda yan mata suke rubunsa ne:mrgreen:. Wasu file ya jawo ya fara aikin gabansa, ganin haka yasa nima na kara wuta. BAZATA By ©Rash Kardam 3 Aiki sosai yayi kafin ya fara ganin marasa lfy, sai da ya gama iya wanda zai duba su a ranan kafin, ya taso yazo ya kwanta kan resting chair, dake office din ga wani kamshi da yake tashi hade da sanyin A C, ko da ya kwanta lumshe idonsa yayi nan take abunda ya faru tsakaninsa da Jidda ya dawo masa, sai da yagama tunaninsa kafin ya saki wani mugun murmushi, sai kuma ya soma tariyo abubuwan da yasasu rashin jituwa, watani kadan da suka shude wata safiyar monday ya yi lade gun aiki gashi da marsa lfy da zai duba, gudu yayi a mota sosai kafin ya iso asibiti cikin sauri ya dauki briefcase dinsa, sauri yakeyi sosai, ya shigo asibi, ya shiga emergency, da sauri sauri yake hawan stairs, bai lura da wacce take zuwa ba, saiji yayi ya bude mutun, da sauri ya dago sai da yaji gabansa ya bada dam…. Madadin ya bata hakuri sai yakasa, sai wani mugun kalon da yabita da shi tare da cewa ke bakya ganine, cikin tsananin mamaki take kalon sa, tace kodai kai baka gani dai, wani saki ya saki Mtss yayi gaba abunsa, wannan abu ba karamin bata ma jiddah rai yayi ba amma ta share, ta koma cikin pharmacy dinta taci gaba da bada magun gunanta, tunda wan abu ya faru basu sake haduwa ba ita harta manta da shi, sai ranan ga wata maras lafiya tazo gurinta sayan magani, nan ta duba ta kardan sai ta karanta magun gunan, kafin ta dago ta kalli maras lfy tace waya rubuta miki wa yan nan magungunan, maras lfyn tace bansan sunansa ba amma naji kamar suna cewa wai Dr Ghali, haka kurum ana ambatan sunan sai da taji gabanta ya fadi, duba sign din tayi, haka kurum taji rubutum ya burgeta, ta kalli matar tace a kwai maganin da ya rubuta miki kuma zasu miki karfi, baki kai matakin shansu ba don haka zan canza miki da dai dai naki, matar tace to nan ta debi magun guna ta canza mata su, ta tafi matar. Itakuma taci gaba da sabgar gabanta. Ko da matar ta kai ma Dr Ghali maganin cikin bacin rai yace wacece take da daman da zan rubuta magani har ta canza acikin asibitin nan? Wacece ita? Har take gwada bansan mai nake ba? tayi kadan ciki fushi ya ce wa matar tana ina tace tana cikin pharmacy din yace muje, suna isowa bai tsaya ganin wacece ba idon sa ya rufe, Jiddah ko kanta na sunkuye tana latsa wayarta, sai ji tayi ana buga table din gabanta, kee wacece acikin Asibitin nan da har zan rubuta ma gani ki canza, zaki gwada min ban san aiki na bane, wacece ke?, mai kike takama da shi? sai a san nan ta dago kanta don ta ga wanene wan nan, dan rainin sense din dayake mata hayaniya, cike da tsiwa ta dago nan sukayi 2 eyes dashi cikin bacin rai tasoma gamana. BAZATA By ©Rash Kardam 4 Cikin bacin rai tasoma magana, kee sai da ta nuna sa sama da kasa, kafin tace wa ma kake da suna, ko wa kake ma ba damuwa ta bane in san sunan kaba, but kasani baka fi karfin gyara ba kayi mistake dole a fada maka, dole ne, na kuma canza, ko zakayi wani abun ne, cikin bacin rai sai wani huci yakeyi kamar wani kumurcin zaki nan suka tayi kowa da yana fadar abundaya ya zo masa kan kace me sun tara mitane yan kallo masu basu hakuri nayi amma kamar ingizasu akeyi, cikin sauri Dr Marsal da Sophia sukazo, kama Jiddah sukayi suna kokarin fitar da ita daga pharmacy din amma tanaki, shiko sai magana yake yana cewa zaki san kin taba ghali sai na koya miki hankali, zaki gane ke ka ramar maras kunya ne, Dr Samar ne yazo ya janye shi yana cemasa cool down, Dr Ghali, ba girman ka bane, kana sa insa da wata, nan yayi ta dannarsa, to tun daga wan nan rana, rashin jituwa ya shiga tsakanin su duk lokacin da daya yaga daya to sai ya ta kali magana, haka sukeyi kulum. Shigowan Dr Samar ne ya dawo dashi daga kogin tunani da ya fada, amsa sallaman Dr samar yayi, kafin ya tashi daga ki shin gidan da yayi, Dr samar yace masa ya aikin dai yace Alhamdulilah, yace yayi kyau, ya kwana biyi, yace lau, ciki sigar tsokana yace ina mutu miyar ka take ne, cikin nuna ko in kula yace wa kk nufi fa yace, kafini saninta yace, ban santa ba, yace Jiddah man saki yayi Mtss yace kai ka sani, cikin zolaya yace gaskiya ni salon fadan ku na burge ni, daga yayi alamar ko in kula, Samar yace na kwana biyu ban ganta ba, Dr Ghali yace aiko da zu tashigo, mun hadu d ita, yace kayi sana’ar ko, cikin da riya ya bashi lbr abunda ya faru, haka sukayi ta hira kafin suka dawo na bikin Dr Saleem d Suhana, tsara yanda bikin zai kasance haka sukayita hira har lokacin tashi a aiki yayi, kowa ya shiga motarsa suka bar cikin T.H BAZATA By ©Rash Kardam 5 Waye Dr Muhammad Ghali. Muhammad Ghali asalin haifen bauchi ne, iyayensa fulali ne gaba da baya, Alhaji Muhammad shin mahaifin Ghali da Mahaifiyarsa hajiya Zakiyyatu dukkansu fulanine, Ghali shine babban dan Alhaji sai kanensa biyu mata Habiba d Ruky, sun taso cikin tarbiya mai kyau, tare da kulawar junansu da kaunar junasu, family ne mai dauke da farinciki sosai d sosai, ko ni kaina saida familyn suka burgeni, haka rayuwansu ke gudana cikin aminci, wan na shine asalin Dr Ghali. Jidda ko bayan da tafito da ga wanka ta shafe jikinta da mayuka masu kamshi ta gyara jikinta, kananun kaya ta sa ta kwanta, ko da ta kanta taso ta dan samu bacci amma abu ya fassakar don bakin cikin abunda ya mata shi ya tsaya mata a rai, ta dau aniyar saita rama, da haka har sallan la’asar tayi tayi sallah, bayan ta idar ne ta fito falo gani Abbanta ya dawo yasa taje gunsa tasoma zuba masa shagwaba, suna cikin haka Hajiya Muslimah ta fito hannunta rike da kofi ruwan lemune aciki ta miko ma Abba ya sha, suka zauna falo, feenat ma ta fito cikin wankata na riga da skirt sun mata kyau sosai zuwa tayi ta zauna aka soma hira da ita, gaka sukayita hira har mangariba, kafin suka mike kowa yaje yayi sallah, haka rayuwansu ya cigaba da guda na cikin aminci duk wanda ka gani agidan na cikin farin ciki barin Abba da kulum ya kalli yan yaransa Mata da Allah ta basa sai ya gode ma Allah, sai fatan Allah ya kawo musu miji na gari, na amsa da Ameen. Jidda ce sanye cikin shaddarta, purple colour ya matukar yi mata kyau sosai, tafe take ciki takunta mai daukan hankali ga duk wanda ya ganta, zua gun H Muslimag tayi ta rungumeta ta baya tace maa, tace ya aki autar Abba, tace ina son zan dan fita ne, zanje kasuwa inyi sayya tace to kar ki dade tace to nagode, ko da ta fita motarta tashiga tafiya tace cikin hankali tana jin wakar Aashiqui Hum Mar Jayenge. Tana matukar son wakokin Aashiqui sosai kalo daya zaka mata kasan tana cikin ni shadi, wayarta ne ya soma kara, ta daga taga Dr Suhana cikin murna ta dauka ta ce Amaryan next week ba kya laifi cikin murmushi Suhana tace, Sis an fitar da Ashoben fa kina gida ne in kawo miki tace,,,.. Ummmm bana nan na dan fita kasuwa amma ba dade wa zanyi ba tace right, sai kin dawo zanzo. Na sukayi sallama, ta shiga kasuwa sayyaya tayi sosai duk wani abunda ta san tana da bukata, wani abun burgewa komai ta sai ma kanta sai ta sai ma Sis feenat dinta don tana matukar ji da ita sosai, haka ta gama ta dawo gida, bata dade ba Suhana ta zo ta kawo mata anko din bikin gaskiya sunyi yau sosai, hira sukayi sosai kafin sukayi salama ta tafi, tun daga wan nan rana shirin bikin Dr Suhana sukeyi basa zama sosai sune can sune nan don sune kirjin biki. Sun tsara events din biki bazata yi wani bidi’ah ba, just Walima zatayi ran Friday bayan daurin Aure Sai Dinner da angwaye suka shirya da daddare bayan an dauko Amarya zasu wuce. Dinner komai ya tsaru yanda ya kamata sai jiran satin bikin da fatan kuma Allah ya kaimu na amsa da Ameen. BAZATA By ©Rash Kardam 6 Wacece Jiddah. Alhaji Taneemu Musa hafafen dan garin Kaduna, nane a Abuja Road Magajin Gari, mutum ne mai kamata ga son mutane, ya kasance mutum mai saukin kai ga iya zama da jama’ah da wuya kaga fushin shi kulum yana cikin fara’ah, Yaya biyu Allah ya bashi su na farko Safeenat wanda suke kiranta da feenat mahaifiyar feenat Allah ya mata rasuwa tun suna Kaduna kafin su dawo bauchi, bayan rasuwar maman feenat ne Alhaji Taneemu ya samu transfer daga gun aiki zuwa bauchi, inda anan ya Hadu da hajiya Muslima ya Aureta itace uwar, Hauwa’u wanda suke kira da Jidda, H Muslima macece mai kirki da da’ah ta rike feenat riko mai kyau wanda ko uwarta ne ita yanda zata mata kenan ko kadan bata taba nuna musu ban banci ba, haka suka yi karatu yayinda feenat ta karanci business Administration, itakuma Jiddah tun tasowarta take son karatun Asibiti hakan ne yasa taje tayi karatun medicine dinta a Mai duguri, bayan ta dawo ne ta samu aiko a ATBU Bauchi, tana ban garen pharmacy, haka suke rayuwansu gwanin burgewa ko ina zaka gasu tare, feenat tana da saukin kai kuma bata da wani girman kai gata da sanyi sosai, sabanin Jiddah da take da zafin zuciya abu kadan ta hauro bata son raini kuma bata raina babba don bata son amata, kuma ita bata cika kula sabgar maza ba, ita bata kula kowa damuwar ta takeyi ita, wan nan shine ta kaitacen lbr Jidda. Kwanaki sunja yau sati guda, yaune ranan daurin Auren Suhana da Angota Saleem kalo daya zakayi ma kawaye da angwaye kasan suana cikin farinciki suna taya yan’uwansu kuma abokan aikinsu murna, su jiddah, Marsal Sophia sam basu samu zama ba sune manyan kawaye, yanzu haka sun tafi Zungur, Villa Garden, yara gurin da za’ayi walima sun gayyato Malama Asmart Adam Dan Fulani, ita zata gabatar musu da wa’azi game da rayuwan Aure guri ya tsaru sosai, sun kuma ajiye komai a inda ya kamata, kafin suka dawo gida don yin wanka su shirya don lokaci yayai, haka suka dawo sukayi wanka tare da Sallah la’asar, kafin suka shirya zuwa gun walima gaskiya su jiddah sunyi kyau bakadan ba, ina ce zan tsaya tsara muku kyan da sukayi to zamu kwana mu yini ban gama ba abokan ango ne suka turo motoci aka jidi yan’ walima aka kaisu, bayan sun gama isa, Malama Asmary ta soma yin nasiha gameda zaman Auren duk wanda ke gurin sai da yaji nasihar ta shigesa, a haka sukayi taro aka watse,koda suka maida Amarya gida, kafin azo a kaita gidanta, Jiddah tace zata tafi gida tayi shirin Dinner faga gida zata zo tunda Zindaba Hotel za’ayi haka ko akayi, nan tayi sallama wa Marsal da Sophia ta tafi. Ko da ta isa gida lokacin ana kiran Isha sallah tayi kafin taci abunci, taje dakin Abba da sallamarta ya amsa tashigo, niman guri tayi ta tsuna ta gaida sa ya amsa cikin fara’a, tace Abba nazo rokon Alfarma ne, yace fadi Autar Abba nan tace masa tana son taje Dinner Suhana ne, sai da ya jin jina kai kafin yace Jiddah da bandun yanda kuke da Suhana ba, gaskiya da na hanaki fita banson kiyi nisa baran ma fitan dare banaso, yace amma kije Allah ya kare min ke, kuma kema ko kula da kanki tace in Allah ya yarda yace Allah ya miki Albarka tace Amin, dakim H Muslimah taje ta shaida mata tafiyarta kuma Abba ya barta, itama ba wani so takeyi ba ta amsa mta da sai ta dawo, dakinta takoma tayi wanka ta tsaya tsara kwaliya tayi kyau sosai kafin ta dauko kayan Dinner wani gown ne, Green da ratsin milk bakaramin kyau tayiba, ta dauko humranta ta feshe jikinta dashi, san nan ta sake dauko turarenta, Essences of love ta fesa dan karamin bakinta yaji jan baki, ga man yan idanunta masu fisgan mutum, gaskiya ta zuba kyau sosai, tafito sannu a hankali take tafiya, H Muslima tsayawa tayi tana kallon diyarta gaskita Allah yayi halita agun ga kyau, ko da ta fita motarta tashiga ta tada, ta dau hanyar Zindaba Hotel, tafe take ahankali, lokacintar BAZATA By ©Rash Kardam 7 Cikin sauri ya cimma ta, hannuta ya kama janta yake fiiiii sai cikin motansa ya wurgata, ya ja motar da gudu ya bar hotel, gudu ya keyi kamar zai tashi sama ga zuciyarsa, da ke masa suya tana in gizashi, han yar fadamar mada ya dauka, jiddah ko kuka ta ke mara sauti wanda tayi da nasani abun da tayi ga shi ya baro ta da gun jama’ah, cikin muryan kuka tace, mai na maka ka dauko ni, kasani in kai dan iskane, to ni ba yar iska bane, ka mai dani in da ka dauko ni, ko kallonta baiyi ba sai wani mugun murmushin da yayi na zaki raina kanki, gudu ya keyi sosai ita ko sai zaginsa takeyi, sai da yayi tafiya sosai kafin ya iso kofar wani katon gida mai kyau sosai babba ne, ya na da katon bakin gate mai girman gaske gaskiya gidan ya hadu iya haduwa ba zan iya kwatan ta muku haduwar kofar gidan ba ma, tsayawa yayi ya fito daga motar tare da kulle motar, shi da kan shi yaje ya bude karamar kofar shiga gifan sai da ya shiga ciki kafin ya bude gate din don ba kowa a ciki, dawowa yayi ya shiga motar kafin ya shigar da ita gidan ya sake bude motar ya na fitowa ya kulle, duk yin Jiddah ta fito abun ya ci tura kallo daya zaka mata ta baka tausayi duk da tsiwarta kuwa. Ya na kulle yazo ya ja motar zuwa parking spaces ya ajiye motar fitowa yayi, ya zago ta gefen ta ya bude da key yace ta fito, cikin tsiwa ta murguda baki:roll:ba zan fito ba sai dai ka mai dani in da ka dauko ni, cikin dariyar mugunta:mrgreen: yace in baki fito ba wlh zan dauke ki, wani harara ta wurga masa, tace sai kuma na tsaya ko an gaya maka ni yar iska irinka ne, ganin zata bata masa lokaci yasa ya fisgo hannuta, ya jata da karifi zuwa cikin gidan, suna shiga ya sanya ma kofar gidan key, janta sa sakeyi tana turjewa ya yi cikin falo da ita, ko da ya bai tsaya nan ba sai da ya jata zuwa wani room koka take sosai tana zaginsa tana turjewa, amma bai san tana yiba wai kunu a wani gida. A Zindaba Hotel kuwa koda Suhana da Saleem, da Marsal da Sophia suka ga haka, cikin tsanani tashin hankali suka shiga motocin su kuka bisu amma sam basu ga ko kyallinsa ba, nan hankalin su ya tashi suhana kam kuka ta fara sosai ace a sanadinta haka ta faru da kawarta, zuwa anguwan su, Jiddah sukayi amma an rasa mai shiga gidansu ya sanar, nesa da gidansu sukayi farkin sun tsaya cirko cirko, can Samar yayi ta maza ya ce barin gwada kiran Dr Ghali, ya ciro wayarsa ya danna number Dr Ghali sai ji yayi ana cemasa,d number u try 2 call is switch off, duk number sa akashe nan han kalin su ya tashi, Saleem ya ce, yanzu yaya za’ayi matsawan in iyayenta suka sani to zasu iya shiga tashin hankali, ko zamu kirasu muce musu zata wuce gidan Amarya ne, Samar yace haka baiyi ba, in wani abu ya sameta ai mun daure kan mu don haka inaga mu fada musu gaskiya kawai, Saleem yace kun san wani abu, suka ce a a, yace ku mata duk ku tafi gida ni da Samar inaga zamuje gidansa na Federal Lowcost mu dubashi, ko kuma gidansa na tambari cikin daya biyu, Dr Samar yace yana da gida ma a Fadamar Mada, amma gaskiya ban san gidan ba sai dai photo gidan dana ta gani, Dr Saleema yace nima ya fada min gidan don yace a gine ya saya kuma ban taba kaini ba, haka su Marsal da Suhana Sophia suka dau hanyar gida Sophia ke tuka motar don marsal da Suhana jikin su ya mutu ga kukan da sukaci, Sophia tafisu dauri ya ita dai Adu’ah tsari take karantawa da kuma Allah ya kare Jiddah, idonta ne ya ciko da kwallah:'( haka suka dau hanyan gidansu Suhana da ke State Lowcost, su Dr ta Samar da Saleem, suka yi hanyar cikin federal lowcost, gudu sukeyi sosai ko da sukaje gidan suka kwan kwasa mai gadi ya fito, suka tambayeshi ko Dr yazo nan yace musu aaa, jiki ba kwari suka shiga mota suka dau hanyan tambari, ko da suka iso check point, nan aka tsare su, sujan yace ina zasu je, suka marasa ina zasu ce, can karya ta fado ma Dr Samar ID Card dinsa ya nuna musu yace maras lfy suk Rash Kardam BAZATA By ©Rash Kardam 9 Bata san lokacin da ta fadi kasa sumamiya ba, dariyan mugunta suka sheke da shi, wanda sai da yasa na razana, daukar ta sukayi, suka soma tafiya da ita, sanyin dake gurin shi ya dawo da ita daga sumar da tayi jinta hanun mutane yasa tasaki ihu ta rinkayi gwar gwadon karfinta, tasoma kiciniyar kwacewa amma ta kasa sun mata riko mai kyau, gani turjewa ba zai ficetaba yasa, suma kiciniyar tsugunawa kasa, laluben dutsi take, cikin sa’a ta samu mai girma lokacin sai janta sukeyi, fakan sa tayi ta kwada masa dutsi ta sa gudu, sosai take gudu hanyan titi, tabi sosai take gudun kamar kafar ta zai fita, suma suna binta, sai da sukayi gudu sosai kafin ta iso titi ai nan tasoma ihu ta na neman tai makon jama’ah, sam bata lura da motar police da tayo ta gun ba gudu take sosai, sai jin kiii nayi sunta ka burki cikin zafin nama, aeko nan ta kara sakin kara. Dr Ghali ke kwance a daki da Jiddah ta fita sai faman lumshe ido yakeyi, kamar wanda aka mintsiresa ya mike yana tambayan kansa, anya nayi ma Jiddah adalci? In barta tana mace ta fita kuma ita daya a daren nan ti in wani abu ya sameta nice silla, sai ya tsinci kansa da jin haushin kansa, cikin han zari ya mike ya nufi motarsa, ya shiga sai alokacin ya kunna wayarsa,ya bude gate ya fita, ae ko bai yi nisa ba wayarsa ta soma ringing Dr Samar ya gani cikin hansari ya daga, Dr Samar cikin zafin rai ya soma maga Ghali ka kyauta kuwa ka dauki yar mutane mai zakayi mata a dare ka tafi da ita ka daga hankali iyayenta da mu, ko ka manta ita macece? Cikin sanyin jiki yace gaskita ban kyauta ba, Dr Samar yace tana ina, yace dazu ta tafi, cikin razana yace what? Kasan bata dauko motarta ba adaren nan ka barta tafita yanzu in aka saceta fa?,nan ya kara rikitar da Dr Ghali kashe wayan yayi ya soma gudu dai dai zai bar layin gidan yaga wasu mutane su biyu zasu shiga wani katon gida da alama masu gadi ne, horn yayi wanda ya sasu tsayawa, shima ya fito a motar sa yazo hunzu, ya rusuna ya gaidasu suka amsa yace baba dan Allah ko kunga wata bidur wan yariya ta wuce tanan, dayan yace bamu dade da jin wata yarinya ta fito tana gudu tana ihu da alaman wasu sun biyota, kuma ba mutum daya ba don muryoyisu da yawa, da gabaya kuma muka rinkaji ihu sosai, daga baya kuma muka daina jin ihun, dayan yace Allah yasa dai ba su keta mata haddi ba inji dayan,Dr Ghali ya dafe kansa, da sauri ya shiga mota gudu yakeyi sosai, ya karade duk inda ya duba a fadamar mada, ba alamar jiddah idonsa ya kawo kwalla, tabbas ni ghali na cika azzalumi maras kirki, na cuci Jiddah mai yasa naksa hakuri lokacin da ta juye min multina, wayan Dr Samar yasake kira yace kuna ina yace gamu a dai dai Rank Road zamuzo fadamar Mada, yace nima na fito ina kusa da inda kuke, Dr Samar yace kaga jiddah yace ko daya sai ya basu lbr da wayan nan mutane suka bashi, Samar yace Innalilahi wa inna ilaihi raji’un, wlh ka cuci Jiddah yanzu a wani hali take, Ghali yace gani isoa gunku.Ko da ya iso su Saleem da Samar sun masife shi sosai, kuma yayi dana sani abunda ya aikata ma jidda daga nan suka yanke shawara zuwa su sanar da iyayenta daganan su wuce police station, suyi report, hanyan Federal low cost, Zamani Area suka nufa ga dare yayi gashi suna cikin tashin hankali. Jidda ko jin karar mota yasa ta kara rikicewa ta saki ihu da sauri wani matashin dan sanda ya fito da toci yana haska jidda da take ihu dai dai nan Wayanda suka biyota suka ga yansanda, nan suka juya zasu gudu sauran police dinsuka bisu, gudu sukayi sosai amma basuyi sa’ar kamasu ba, hakan yasa suka dawo, Sajan Nasir yace ke mai yafito dake cikin dare cikin muryan kuka tace Sir kamin afuwa ku kaini gida wlh zan fada muku ko miye don nasan babana yana cikin tashin hankali, yace bazan kaiki ba sai kin gaya min mai ya fito da ke, cikin muryan kuka ta bashi lbr, ya jin jina sannan yace zan kaiki gida, yanzu amma da ga yau BAZATA By ©Rash Kardam 10 Dr Saleema ne ya daure ya bashi lbr abunda ya faru, san nan Sajan Nasir ya daura daga inda suka gamu Abbanta shiru yayi kafin yace ya gode ma Allah da ba abunda ya sameta, kuma daga yau ta bar zuwa biki, san nan yace Jiddah waya gaya miki a na wa namiji irin yanda kk masa shifa tai makon ki yayi duk da bai kyauta ba kema baki kyauta, Allah ya kare naga ba, suka amsa da ameen, sallama suka masa shida iya lansa sukayi cikin gida, Su Samar suka koma mota Dr ghali ya kalle samar yace naga jiddah ta dawo ina fatan ba abinda ya sameta, ko kallonsa baiyiba sukayi motarsu suka tafi don ya bata musu rai, gashi ko bacci basuyi ba har 3:20am tabbas ya san bai kyauta ba har su samar sukayi fushi ga baccin dayake ji haka ya tada motarsa ta bar unguwan jiki ba kwari. Jiddah ko tunda suka shiga gida abba yace suje su kwanta, daki tashiga ta watsa ruwa ga kafarta sai zafi yake mata, rabonta da tayi gudu irin wan nan har ya manta,ko da tafito doguwar riga tasa da hijab ta biya salolin da ke kanta kafin ta kwanta bacci tayi sosai, ko da gari ta waye bata tashiba sai kusan 6:40 tayi sallah asuba kafin takoma ta kwanta dake weekend ne ranan sai goma da mintoci ta farka, toilet taje ta wanke bakinta kafin tayi wanka ta sa kaya marasa nauyi tafito falo, ta tarar da Abba da H Musleemah sun fito feenah tana kan dining ta gaida iyayenta kafin taje ta gaida Aunty ta, suka yi breakfast a tare, kafin suka dawo gun su Abba suka zauna Abba ya musu fada sosai, yace ma Jiddah ta kiyaye yin gatsali ma na miji, don tayi sa’an mai kirki da wani sai ya mata rashin mutunci, kuma yace daga ranan ya soke zuwa bikin dare, in ba da wani dan uwanta na kusa ba, san nan yace sa iya tafiya, tun daga wan nan ranan Jiddah take jin wani tsanar Dr Ghali ko kallonsa bata sonyi bare taji sunan sa haka ta karashi weekend din duk jikinta ciwo yakeyi. Dr Ghali kuwa tunda tunda ya koma gidansa, kasa bacci yayi, don in ya rufe idonsa Jiddah yake gani tana masa murmushi, gashi ta tafi ta barmasa kamshinta, sai lumshe ido yakeyi, take ya fara jin wani irin feelings gameda Jiddah, sannu a hankali yake karanto surarta sai wani murmushi yakeyi haka kuru yaji zuciyarsa na tsanani son ganinta, nan take ya tambayi me take nufi kardai na kamu da son Jiddah yace anya yarinyar da bama shiri, can yaga tunani ba zai ficcesa ba ga dare yayi, alwala ya yi ya shimfida salaya ya fara kiyamul lail, haka har aka yi kiran sallaha kafin yaje masalacin da ke unguwar yayi sallah ya dawo, Azkar yayi har zuwa 7:00am kafin ya kwanta bacci, nan ya fara mafarki mai dadi, Jiddah ce tazomasa da wani fulawa mai kyau ga kamshi ta mika masa tana murmushi, cikin fa’a yakarba ya zo dafda ita zai mata rada a kunne ta ju tasoma wani tafiya mai daukan hankali tana karairaya, dai dai nan yaji wayansa na ringing, ya ki bude idonsa amma sam ya bar ganin Jiddah, wani uban tsaki ya daka kafin yadaga, yaji Company MTN ke masa talle Caller Tone, nan yaji wani bakin ciki ya tokaresa, wayar ya kashe ya koma ya sake lumshe idonsa kozaiga Jiddah amma shiru, haka yayita juyi karshe wanka yayi ya saka kanana kaya ya nufi restaurant ya sai abinci bai wani ci na kirkiba don yanzu zuciyarsa ta addabesa da tunanin jiddah har Allah, Allah yakeyi monday su hadu agun aiki yaga kyakyawan fuskarta mai burgewa. Su samar ko da suka isa gida Wayar Sophia Samar ya kira ya saida mata ansamu Jiddah ta fada masu Marsal tace to sukayi sallama suka kwanta suma da gajiya suka tashi, haka akayi yinin biki ba wani amarshi sosai, sabida jiga jigan bikin basu samu hallara ba, sai dai muce SUHANA DA SALEEM, ALLAH YA BADA ZAMAN LFY.asha amarci lfy . Yau take Monday da wuri jiddah ta fita don taso makara, gudu tayi sosai bata dau mintuna masu yawa ba ta isa ATBU, parking motar ta tayi ta fito tana dan sauri, wanda saurin da takeyi yasa duk ilahirin jikinta motsawa, ga can nesa na hangi Dr Ghali ya ha BAZATA By ©Rash Kardam 11 A hankali ya tura kofar sai da ya tsaya kusan na minti biyar, ya zuba ma jiddah ido ko kyaftawa ba yayi, sophia ce ta fito da ga cikin toilet din pharmacy din, karaf suka hada ido da Ghali da sauri ya shigo da Sallamarsa, tana jin kamshin turarensa, ranta ya baci wani tsanarsa takeji yana ziyaran zuciyarta, bata dago tanajin suna gaisawa da sophia, can yacemata Dr Samar yazo nan kuwa tace aa ae yana office, ka duba office dinsa kuwa, cikin inda inda yasoma…..dama….uhumm….ae na dauka yazonan ne, sophia ta gama dagoshi, murmushi tayi, yace barinje na dubashi tace to, yana fita sukayi gamu da Marsal zata shigo pharmacy din, gaisawa sukayi sosai, ya wuce ta shigo, Sophia tace sis Marsal ya kk? Ya aiki tace lau, Marsal tace mai Dr Ghali yazo yi pharmacy? Sophia tace ban sani ba nima,na dai fito daga toilet na ganshi tsaye a kofa tace nikam ina zargin wani abu, sai a lokacin Jiddah ta dago man yan ifanunta ta harari Matsal, Sophia tace, anya Dr ba son Jiddah yake ba, marsal tace na dade da tunanin haka, don ina hango tsananin kaunarta a idonsa, wani tsaki Jiddah tace dan Allah ku bar hadani da wannan dan iskan, Marsal tace ba zaki gane bane guy din ya hadu, ya na da qualities din da za ace kin so shi, sis hararanta tayi tafita ta bar musu pharmacy din, Sophia tace kyaleta zasu dai daita mu na mu ido dariya sukayi, haka sukayita aiki har aka tashi kowa ya nufi gida. Kwanaki sun ja watanni sun tafi sofiya in banda tsana da kiyayyan Dr ghali ba abunda zaka gani a idonta, hakane ma yasa ta daina kula kowa, haka rayuwa tayi ta tafiya duk yanda Dr Ghali yaso suyi mutunci abun ya faskara, kulum Adu’ar shi ta yafe masa. Yanzu duk wanda suke tare ko ba a fada ba sun san yana son Jidda sosai,amma yana wayancea sabida rashin hadin kanta da bai samu ba shine kulum zaman jikin window ko zai ga wucewar ya samu relief a zuciyarsa . Haka suka kasance cikin wan nan hali. Jiddah ce tafito cikin shirin aiki sauri take ta makara sosai, ko da tashiga motarta tayi2 motar taki tashi sam, ga feenat ta fita gun aiki a motarta Abba kuma baya nan shima, gida ta koma ta ajiye key din tafito tashiga a Keke Napep, tashiga tace masa Malam dan Allah kayi sauri na danyi late yace to gudu sukeyi sosai, sun iso dai dai kwanar da zai shigar da kai hanyan T.H sai jin kau…… Kau…. Keke Napep dinsu ya hadu da wani mota wanda sai da yayi sanadin fifowar jidda waje, kalo kayi ma napep din da kyar tayi aiki nan gaba, In banda salati ba abunda ke tashi agun ga jini sai kwarara yakeyi, dai2 nan Dr Ghali ya zo wuce ganin abunda ya faru yasa ya tsaya, yana dubawa yaga Jiddah ce nan take ya rikice, yana kiransunan ta yana hawaye pls Jiddah kar ki tafi ki barni ina tsanani bukatar ki, pls Jiddah dau karta yayi wasu suka taimaka masa da mai napep din su ka dauko shi, suka sasu a motarsa, gudu yayi sosai suka isa Emergency nan take Doctors sukayi caaa kansu sai kusan awa daya kafin wani likita ya fito, yace Dr muna son jini, za amata kari don ta zubar da jini sosai, Dr Ghali yace muje a duba nawa in yayi a dauka, cikin ikon Allah jinin su yazo daya. batare da bata lokaciba aka dau jininsa, aka samata, bayan angama treatment dinta aka kaita single room aka samata ruwa, Dr ta ghali ya zauna ya sata agaba ya zabga uban tagumi, sai da ta samu kusan awa daya kafin ta soma bude idon ta a hankali tana salati, taras ta sauke su kan Dr ta ghali, nan take tasaki wani kuka tacwa, dan isaka ka tafi bana son ganinka so kake ka cuceni ka kawo nan kansa ya dafe kansa. BAZATA By ©Rash Kardam 12 Dan iska ma cuci, ka kawo ni nan ka cuce nine, kansa ya dafe nan take ya fara jin haushin kansa,Jiddah ganin bai fita ba yasa tayi kokarin mikewa wani zafi taji kirjinta da kanta na mata, ko da ta duba gefenta, sai a lokacin taga ruwanda aka sa mata, ko da ta kalli kafarta bendeji ta ga ansamata, nan take ta saki kuka, jin kukanta na tsuma zucoyar sa ba zai iya sauraron kukan ya mike zai fita sai da ya kai kofa ya jiyo ya kalleta idonshi ya kawo kwalla ga wani Sonta da ya ke ji, kirjinsa sai harbawa yakeyi da sauri2 bude kofar yayi dai2 nan ya ga Marsal Sophia da Amarya Suhana sun nufo dakin, kallo daya suka masa, suka gane yana cikin damuwa, gai sawa sukayi suka tambayesa ya me jiki,? Yace da sauki don anbasu lbr irin taimakon da ya mata harda jininasa da ya bayar, dakin suma shig. Dr Ghali yafita harabà asibitin, ya nufi gun ajiye motoci, ya shiga motarsa ya bar Asibitin, don zuciyarsa na masa wani irin suya, gudu yayi sosai kafin ya isa gida dakinsa ya shiga ya kulle kansa, kan gado ya fada yana juyi ga zuciyarsa da ke masa wani irin suya, yace ni Ghali na cuci kaina, yarinyar da na tsana ita nake matukar kauna gashi kuma dai2 itakuma take tsananin tsanata, ya zanyi da zuciyata kwalla ne ya cika idonsa, ya kudiri aniyar sai ya wanke kansa, Hauwa’u na ina matukar Kaunan ki My Jiddah, pla kisoni koda rabin cokali, i’m deeply in love with you My Jiddah, you hrt, my Only, kukane ya kwace masa, tabbas yayi nadama sosai, wanda ni “Rash na saida Ghali yana matukar son Jiddah’ yace Jiddah sai na koyar dake yanda zaki So ni haka yayi ta sanbatu shi kadai har magriba tayi yaje yayi Sallah, sai Isha’i ya dawo shirin kwanciya yayi, yana Adu’ar Allah bama jiddah lfy. Marsal da Sophia suka tura kofar dakin suka shiga, ganin tana kuka yasa suka karasa da gudu, sannu jiddah, ya jikin kuka ta kara saki ta fada jikinsu tana cewa, Ya tafi bana son ganinsa na tsane sa dan iskane, mai satan yan mata, kuka take sosai, Suhana tace waye haka, Jiddah tace Dr Ghali, Marsal tace ai bayanan ya fita, sai lokacin ta bude idonta taga baya nan wani Ajiyan hrt ta sauke, Sophia tace yanzu ki bar zance nan ya jiki tace da sauki, nan suka kira su Abba suka sanar musu Abba yace gashi zuwa yanzu, wayar Feenat ya kira tana gun aiki itama yace taje T.H Emergency ta same su, tace lfy yace Jiddah ce tayi Accident, cikin rudewa tace Yasalam!!! Ajiye file din da take cikawa tayi, kafin ta je ta nimi permission ta fita, gudu tayi kafin ta isa asibiti, ko da ta isa wayar Sophia ta kira ta zo ta kaita room din, rungume sis dinta tayi, ido ya ciko da kwalla, tace sannu sis Allah ya kare na gaba, su Marsal suka amsa da Ameen, Abba sun zo haka suka zauna suna kula da ita, sai magriba su marsal suka tafi tun daga wan nan rana, Jiddah take samun kulawa mai kyau, kullum sai Dr Ghali ya zo dubata batare da saninta ba, kuma ya sai kaya ya bama su marsal da Sophia sukawo, amma vasu taba cewa shi bane, don sanin halinta, satin jiddah daya a asibiti aka sallameta, tayi kyau ta murmuri, sabida samun hutu ba fita rana bare zurga zurga2 sai yan tabon da suka rage mata, haka suka dawo gida kulum feenat ke da wainiya da yar’uwa ta, haka harta warke sosai, ta fara fita aiki, sai yan tabon da basu gama baceawa ba, shima tana shafa musu zuma, tayi kyau sosai fiye da da. Yanzu komai han kali kwance takeyi don harta manta da wani wai shi Ghali, a sabgarta. Ghali in banda wutar son Jiddah ba abunda ya dame shi, kulum ka ganshi yana zaune shi ka dai, sai dai yayita smile, yana tuna jidda, a rin wanan tunanin ranan Samar yazo ya samesa, ya jima a zaune cikin office bai san ya isoba sai murmushi yakeyi sai da Dr Samar ya bugi table kafin ya dawo hayya cinsa, yace ghali wlh kabi a hankali, don sam yarinyan nan bata san kana yi ba, hasali haushinka take ji g BAZATA By ©Rash Kardam 13 Kwanaki sun ja, Jidda ce zaune cikin dakinta kasancewar yau weekend, tana ta danne dane a system dinta, taji kara shigowar mai message ta gmail dinta, sai da ta gama abunda zatayi ta bude sakon, taga bata gane mai sakon ba, ta duba profile din ba wani abunda zata gamusu, sakon ta fara karan tawa kamar haka. Assalamu’alaiki Ya ma’abociyar sanyi da kamshi, farin wata mai haskaka sauran, kyakyawa acikin kyawawa, mutunci kamala fara’a suna dauke a fuskan ki, Hauwa’u tun randa na fara ganin zuciyata ta harbu, da tsananin kaunar ki, Jiddah ke mace daya ne tamkar da dubu, kallo ki na hadda samin farin, murmushin ki kan jefani kogin kauna, tafiyar na sanya ni cikin nishadi, bare ki bude dan karamin bakin har labbanki su motsa, zazzakan muryanki ta fito Ya Allah, kusan suma nakeyi, Jiddah ina matukar kaunanki ki taimaka ki son ko kwatan kwacin kwayan zarra ne, niko zan zameki Zuma mai tsanani zaki, zakuma kiyi Alfari dani nan gaba ina matukar kaunarki. Mai Son ki Tabbas kalamansa sun mata dadi amma sam ita ba soyayya bace a gabanta, wani tsaki taja kafin ta goge sakon. Ta kashe system din koda ta dawo kan gado taji massage ya shigo wayarta, tana budewa taga wani bakon number ya turo mata sako kamar haka. My Jiddah Every time i see a flower ……. I think about u and how much i want to be with u n how much i want to hear ur sweet voice, i luv u Jiddah pla luv me. Urs Lover Boy Ta karanta sakon yafi akirga gaskiya guy din ya iya kalamai amma ba shi bane a gabanta, goge sakon tayi tacigaba da sabgarta, har dare tayi nan taji wayarta na ringing ko da ta dauka, new number tagani da sallamart tasa a kunne cikin wata sassayan murya mai daukan hankali, taji ana cewa Amincin Allah ya tabbata a gareki ma’abociya sanyi da kamshi ga kyan fuska, koda batayi niya ba sai da ta murmusa:) yaciga ba da cewa, My Hauwa ina matukar kaunanki sosai, Son ki yamin “BAZATA” amma nasan ke cikin tsiwa tace kai tsaya malam wai waye ne yake niman takura ma rayiwata, waye ne?? Cikin sanyin murya yace Mai Sonki ne. Wani tsaki tayi takashe wayar gaba daya ta kanta, sai me sam bacci yaki daukarta kaman mutumin sai yawo yake mata akanta rutse ido tayi har bacci ya dauketa, tunda ga ranan mutumin nan yasata gabada kamai tun bata so harta dawo jin dadi kalamansa wani sa in ta saurare sa, su dan gaisa haka rayuwa su tayita tafiya. Cikin shirin aiki tanufi office don yau suna da meeting, Ko da ta isa mu marsal da sophia sun zo, jiran time kwai sukeyi su shiga metting, hira suke sosai, sai ga Dr Ghali da Samar su nufo su, Jiddah ta hade rai sai wani kun buri takeyi, ko da suka iso Dr Samar ne yace sanuku ya kk ya aiki suka amsa d lfy, ya kalli sophia yace Sophee pls ki dan kira mana Suhana a waya kice ita da Dr Saleem suyi sauri time din da za’a shiga fa yayi, mun kira wayar Saleem na kashe tace to, ta kirasu sikace gasu a hanya, dogiya sukayi suka wuce sai da sukayi nisa yace ya abokina kaga target yayi ka ganta cikin sauki, murmushi yayi, haka sukayi ta hira har aka shiga meeting duk wasu man yan Doctors din T.H sun hallara hall yacika, sosai kowa ya zauna, bayan wani Dr ne ya bude taro da Adu’a, bayan an shafa, professor Aminu Ilyasu ya mike cikin harshen turaci yake mafana, topic dinsu na yau akan Seminar da zasu je Kaduna 2 da kuma Doctor dinsu biyu da basa shiri, 3 zakuma a wakilci masu zuwa Seminar, sabida basa son in aje a samu matsala, hall din ne ya dan argitse da surutu, kafin ya ce ayishiru, saida gu ya lafa, yasoma bayani yanda seminar zai kasance bayan ya gama ya gan garo kan yan da zasu tafi, nan yasoma da kiran sunan doctors din 1 Aminu Ilyasu 2 Muhammad Ghali 3 Samar da Saleem. Female 1 muna da Hauwa’u Taneem 2 Maryam Sais( marsal) BAZATA By ©Rash Kardam 14 Tace eh Jiddah don da jinin Dr ghali a jikinki, ya miki taimako bana wasa ba, ya kamata ki sau rara masa, cikin firgici jiddah tace what??? mai kikace cikin fushi tace abunda kikaji nace, sophia juyawa tayi dakunta don taji haushi a cikin jama’a jiddah zata na wulakanta mutum kamar Dr Ghali, Jiddah ko jikinta ba kwari ta juyo don ta nufi dakinta, taga ba Dr agun cikin da muwa tayi dakinta, magar sophia ya tsaya mata a rai, ya za’ayi ace da jinin Dr ta ajikinta ita dai tsan ko hug basu tabayi ba, bare hada gado daya da za’a ce da jinisa a cikinta, kanta ya matukar daurewa, taje ta dawo tana tunani amma ta rasa amsa, kuma gashi Sophia da alamun da gaske take maganar don ga shi har fushi tayi da ita, tana cikin haka taji karar message da sauri ta dau wayarta, tasan Lover Boy dinta ne, da sauri ta bude tasoma karanta wa kamar haka, Hello My Jiddah I wl hold u up wen u cant stand, i wl wipe away d tears:'( wen u cry, i wl fight 4 u wen u gv up i wl luv u 4evr nd olways……. pls luv me till end of ur lyf my jiddah . Urs Lover Boy Har cikin zuciyarta taji dadin kala mansa, can ta tuna da abunda ya faru dazu, da sauri ta mike ta fita, dakin Marsal ta nufa, da salamarta, ta tura kofar ta shiga karan ruwa taji da alamar tana bayi, kwaciya tayi akan gadon ta lumshe ido tana tunanin kalaman lover Boy dinta, yayin da wani sashi na zuciyarta ke tunano mata kalaman sophia take takara shiga da muwa, sai da marsal ta dau mintuna tana wanka kafin ta fito, ta hango jiddah kwace kan gado, cikin zolaya tace, ta gidan Lover Boy, ya gajiya murmushi:) ne ya bayyana a fuskarta, alamar jin dadi, tace ya bi lfy, marsal ta tsane jikinta da karamar towel din da ta yafa a kafadarta, ta jawo jakarta ta ciro mayu kanta tafara shafawa, Jiddah ta kalleta tace Marsal maga nakeso muyi, cikin kulawa marsal tace ina jinki Jiddah, ta dan nisa kafin tace ina son in tambaye ki wani abu, marsal tace ina jinki, ta ci gaba da cewa dazu mun fito da Sophia zamu dakina, nan ta lbrta mata yanda sukayi, Marsal tace eh gaskiya ta fada kuma ni na tabbata ghali yayi nadama, kuma yana tsananin kaunarki sosai, don kallo kwayar idonsa zaki gani, cikin damuwa jiddah tace ni har yanzu baki fada min ba ya akayi na samu jininsa a jikina bacin nasan ko hug bamutaba bare har jininsa ya zauna a jikina, Ko dai rike min hannu da yayi ne jininsa ya shiga jikina, marsal dariya tayi sosai tace haba jiddah, ki kwantar da hankalinki duk kin bi kin rude, cikin damuwa jiddah tace dole in rude mana, marsal sai da tasa kaya kafin tazo ta zauna, jiddah tace nifa bana son wulakanci don na zo gunki, marsal tace sorry Haugal, kinsan har na hada muku nickname, mtss ta buga tsaki, tamike zata tafi jidda ta riko ta tace yi hakuri kawata zauna kiji, da kyar jiddah ta zauna, ta soma bata lbr likacin da tayi hatsari da irin da muwar da ya shiga da taimakon da yabata, da kuma rasa jinin da za’a samata ya bada nasa, jikin jidda yayi sanyi sosai, marsal taci gaba da cewa Haugal, cikin hanzari Jiddah ta dago fiskarta da ya canza kala. Dr ghali dakinsa ya koma ya dafe kansa cike da damuwa, oh ni Ghali nayi regret din abunda nayi ma Jiddah, gashi bata Sona, bata son ganina, jiddah ya zanyi da kaunarki da yake damun zuciya ta, jiddah ke ce farin cikina , ke ce abun kaunata, “SANYI IDANIYATA” book by Zee Abuja, Jiddah ke ce mace ta farko dana fara sonki, hawayene ya cika idonsa, harda rusunawa kamar tana gabansa, yace, My Hauw’u pls forgive me, n forget what i did 2 u. U are hrt desire, i luv u more My Sweet Jiddah, nan take jikinsa yasoma kakarwa sanyi ya faraji ga wani tsananin ciwon kan da ya dame sa har yana sassara masa, kan gado ya fada ya ja bargo ya rufe kansa yana wani irin kuka mai ban tausayi yana kiran BAZATA By ©Rash Kardam 15 Jiddah ta daga idonta da ya canza kala zuwa ja, cikin sauri ta tashi jiki ba kwari ta nufi room dinta, kan gadon ta fada, kuka tasoma rusa why me yasa zaka bada jininka a jikina, ke nan yanzu jinina ya gauraya da naka, kuka tayi sosai, tana cewa i hate u Dr, why u do dis 4 me, dafata da taji anyi yasa ta dago marsal ta gani, jikinta ta fada tana kuka, marsal ta rarrasheta, tace kiyi hakuri Dr ba yayi da nufi bane yayi don Allah ne, kuma Jiddah ki kasance mai yafiya “Allah yana son masu yafiya da hakuri har albishir ya ce a musu, lalashinta tayitayi da kalamai masu dadi, harta hakura, amma sam batajin manta abunda Dr ya mata, sai da sukayi Sallah magriba kafin marsal ta fita, saida ta shiga dakin Sophia ta taras tana waya da yan gidansu bayan sungama suka dan taba hira ta mata sallama, ta tafi dakinta, Bayan fitan marsal jiddah ta yi sallah isha’i ta roki Allah ya rage mata irin tsanar da takeyi ma Dr ghali, bayan ta shafa Adu’ah sai da tasha tea kafin ta kwanta tana tunani kala2 har bacci ya dauketa. Dr ghali kuwa zazzabi ne ya rufesa sosai, sai rawan dari yakeyi, Dr Samar ne ya shigo ya gansa haka da sauri ya karasa gun sa ya yaye bargon, yaji jikinsa zafi, da sauri ya koma dakinsa ya debo kayan aiki ya auna sa, sannan ya masa alura , ba a dade ba bacci ya daukesa, ganin halin da ke ciki yasa samar rufe dakinsa ya dawo gunsa ya kwanta a resting chair dakin, bai farka sai kusan uku saura, nan yaji jikinsa ya masa sauki, bayi ya shiga yayi alwala ya biya sallah da ake binsa, tea samar ya hada masa ya sha, kafin ya bashi wasu magain ya sha, ya sanan ya koma bacci da asuba suka yi sallah, bayan sun idar samar ya masa fada sosai, kan ya bar sanya damuwa a zuciyarsa gashi har jinimsa yaso ya hau, ko da sukayi breakfast suka nifi gun seminar, kallo daya zaka masa kaga irin ramar da yayi sosai, sai karan hancinsa da ya fito sosai, su jiddah ma haka suka fito sunsha kyau, suka nufin gun sau ran mota suka shiga suka nufi gun seminar. Jiddah ta kasa sakewa, sosai haka kurum taki son su hada hanya da Dr ghali, haka suka gama seminar suka soma shirin dawowa, sai da sukaje Abuja Road ta gaida yan uwan babanta ita da su Marsal kafin suka dawo hotel din washe gari suka dau hanyar bauchi, tun a hanya ta tura ma Lover Boy dinta sako kamar haka My Only Gani a han yar dawowa, farin cikina, zan so ace kai zan fara tozali da kai don ina muradin ganinka burina mu kasance tare. Ur beloved Jiddah Mesage ne ya shiga wayar sa bayan ya karanta yayi mata reply kamar haka, My Jiddah Jiddah ina sonki ina tsananin kaunar ki but ina tsoron randa zamu hadu karkice baki sona kun fasa. Mai Son ki Ko da takaranta mur mushi tayi ta mayar masa da amsa ka mar haka, My Hrt Kasani Sonka da kaunar ka daga Allah ne ajina yake ina matukar sonka ina kaunarka, ban damu da ya kake ba kai nake so kai nake kauna, kudi ko kyau basa gabana kai ka dai ne a gabana, Sonka d Kaunar ka na tasa a gabana bana jin kira bana wai ge, na baka kaina da zuciya ta . Ur Jiddah Ko da ya ka ranta ya sake turo mata wani sakon My Jiddah Ki min alkawarin cewa in kin gani ko yaya nake bazaki kini ba zaki cigaba da sona a ko yaya nake, kuma duk rintsi duk wuya bazaki juya min baya ba. Mai Sonki Ko da ta karanta murmushi tayi wanda yasa marsal da Sophia hada ido suka kalli juna, marsal kasa hakuri tayi tace wai nikam Jiddah murmushin mai kikeyi ne, tace kwaji da gulmanki, ina tare da Lover Boy ai dole kuka ina Smile:). shewa sukayi suka tafa ta ciga ba da rubu tunta, My Hrt Na maka Alkawari bazan gujeka ba har karshen rayuwa ta ko da ta kasance kai gurgune ko makaho, ko mafi da gaka ni kai nake so kaunar ka ya kamani a cikin zuciyata bazan iya gudunka BAZATA By ©Rash Kardam 16 Duk jikinta rawa yakeyi, bakinta na rawa, idonta ya fara fida hawaye:'(da sauri ta koma motarta tana kuka, da hanzari ya biyota gun motarta, kafin ya karaso tayi ribas sai kura ta tayar ta bar gun da gudu kamar zata tashi sama, ganin irin gudun da takeyi ya razana don gabada ba gudun hankali takeba motarsa ya shiga ya bita hanyar auguwansu, ina tayi nisa sosai ko da ya iso bai ga alamarta ba, tsayawa yayi a kofar gidan, ya tamabayi mai gadi, ko Jiddah ta dawo? Yace tun dazu ta fita kuma bata dawo ba, hankalinsa yakara tashi, gidan su Dr Samar ya nufa cikin tashin han kali, ko da ya isa ya tar yana shi shin fita, ganin Dr ghali yasa ya tsaya kalonsa don baya hayyacinsa gaba daya, da sauri ya rike shi yace Dr lfy mai ya faru? Hannunsa ya kama ya shigar dashi dakinsa, ya zaunar da shi, ruwa ya miko masa maisanyi ya sha, ya ce ya kara masa, sai da ya dan nutsu kadan kafin Dr Samar ya ce mai ya faru na ganka haka? Idon Dr yayi ja yace Samar abunda nake gudu kenan gashi ya faru, Dr Samar yace mai ya faru? Nan ta kwashe lbr komai ya fada masa, Dr samar yace haba Ghali, pls be a man, abu kadan sai ka daga hankalin ka, ka yawaita adu’ah Allah yana tare da mu, in Allah ya yarda Jiddah malakin ka ce, cikin sanyin murya yace Ameen, haka sukayita hira Samar yana lallashinsa har dare yayi kafin suka rabu. Jiddah na jan motar ta, gudu tarinka yi tana kuka, ta nufi gidansu Marsal ko da ta iso horn tarinkayi, harda na hauka, duk mai gadi ya rikice, cikin hanzari ya bude gate ta shiga gidan ajiye motar tayi ta fito da gudu tayi cikin gidan tana kuka, tayi sa’ar ba kowa, a falo, dakin Marsal tayi, tana shiga ta gansu da Sophia sun gama shiri zasu je gidansu Jiddan, jikinsu ta fada ta saki kuka, sosai take kuka duk ta ruda su, sai tambayar ta sukeyi lfy, cikin kuka Jiddah tace Lover asai Dr Ghali ne, ya cucen sai da ya samin sonsa na kamu zai min haka mai na masa da yake shiga rayuwata haka, ajiyar zuciya Sophia ta sauke tace Alhamdulilah na jima ina fatan haka, Allah ya amshi fatana, jiddah cikin kuka ta dago tace Sophia asai ba kya sona ke ma, tayi murmushi tace ko daya naga kun matukar dacewa ne shiyasa, marsal da sophia sukayi ta rarrashinta kuma suka gwada nata tayita adu’ah may be a kwai alkairin da Allah ya boye, sai magriba ta bar gidan ko da ta isa gida sallah tayi ta kwanta, nan feenat ta shigo, tazo kan gado tace sis kin dawo ko ki laiko ni, ko dai lover boy bai miki bane, nan idon jiddah ya kawo kwalla, ta fada jikin feenat ta saki kuka, feenat ta rarrashe ta kafin tace sis mai ya faru? Jiddah tace asai lover boy Dr Ghali ne, feenat tace ghali wanda kukayi ta case kwanaki tace yes, feenat tace wooow amma salon soyayyar ku ta burgeni, munsha rigima Allah ya sanya alkairi, jiddah ta zame jikinta, feenat ta mata nasiha kafin ta mata sallama ta koma dakinta, ta kwace taji karar shigowan sako tasan ghali ne da farko taso ta share amma zuciyarta ta kasa hakan, mika hannu tayi ta dauko wayan ga sakon kamar haka, My Jiddah Ki yarda dani ina tsananin kaunarki, Allah ne ta jarabeni, ki sani in ba ke ba zan iya rayuwa ba, ki tausaya min dan Allah Urs Dr Ghali Har cikin zuciyanta taji tausayinsa amma gan gan jikinta ya kasa yafe masa, haka yayi ta turo mata sako kala2 da ta gaji kashe wayar tayi washe gari kin fita aiki tayi. Dr Ghali kuwa tun da yaga Jiddah bata fito ba han kalinsa ya tashi, ya nufi pharmacy ya samu su marsal bayan sun gaisa yake tambayarta, ya jiddah lfy bata fito sukace suma basu sani ba don sun kira wayarta akashe amma suna ganin lfy ne, hakan nan suka dan yi hira da su marsal har suna tsokanan sa haka abun ya kasance, gaskiya sunji dadi wan nan hadi na Haughal, har cikin ran doctor yaji dadin sunan ya musu salama ya nufi office dinsa, Jiddah ko sai da ta kwana biyu bata fi BAZATA By ©Rash Kardam 17 Jiddah ta mike a razane, tana girgiza kai, alamar aa, Abba da h muslima tsaya sukayi suna ganin ikon Allah, Abba yace Jiddah zauna idonta da ya soma zubar da hawaye ta zauna, tace Abba dan Allah ja taimakr ni wlh bana so ba na, cikin tsanani mamaki Abba yace jiddah har ak wai abunda zan saki, ki kauce min kuka ne ya kwace mata, yace to Jiddah ki sani ba makawa ai anyi auren nan, da gudu ta nufi daki tana kuka, feenat ma kuka ta somayi ma Abba akan dan Allah ya janye wlh jiddah tananda wanda take so, tsawa ya dakamata itama barin falon tayi tana kuka, ko da taje dakin Jiddah taji ta akule, dakinta takoma tana kuka sosai, ta tausaya ma kan war ta don tana matukar son ghalinta, mai yasa Abba xai yanke hukuncin nan, Jiddah ta shiga daki sam ta ki bude kanra ko abunci ta ki ci haka ta kwana da gari ya waye ba irin bugun da feenat batayi ba amma fir ta ki budewa, Abba ko da ya tambaya akace taki fitowa, yace a rabu da ita, H Muslima ta shiga tashin han kali don yau kwanar jiddah2 a daki bata fito ba abba kuma yaki nuna da muwarsa, ko da ya dawo ta masa maganar jiddah fushi ya kamayi da ita, ganin haka yasa ta nufi dakinsa ta dauko extra key tazo ta bude fakin jiddah nan ta ganta kwance kasa tayi amai bata hayyacinta da gudu ta koma falo ta kira Abba ama ko ya kulata feenat ne tafito cikin rudu suka nufi dakin dauko ta sukayi suka nufi asibiti, ko da suka kaita emergency, aka shiga da ita, Abba ko daya ga anfita da ita hankalinsa ya tashi mota ya dauko ya bi bayansu ko da ya iso an shiga da ita emergency, da gudu feenat taje gunsa tana kuka ta rike kafarsa, tace abba na dan Allah ka yi ma Jiddah afuwa, ka tausaya ma halin da take ciki, cikin sanyin murya Abba yace Safeenat na riga na ma Alhaji alkawari yaya zanyi, cikin kuka safeenat tace baba ka janye batun Jiddah ni na amince abasa ni kuka takeyi sosai mai ban tausayi, da sauri abba ya daga ta yana sanya mata albarka, H Musleema har ranta taji dadin abunda feenat ta mata ba’a dade ba likita ya fito yace ulcer ce ta so ta kamata sabida rashin cin abinci, nan aka kai Jiddah ward din da aka kautarta an daura mata ruwa, bata farka ba sai rana, tana bude ido ta ganta asibiti kuka ta saki nan feenat da H Muslima har rige rige dukeyi na zuwa gunta, da sauri feenat ta rungumeta tana cewa sis matsan ina raye, zan yi iya yina Abba ba zai miki Auren doleba, sis kiyi shiru Abba ya janye batun aurenki wani ajiyan zuciya ta sauke, haka suka yita bama jiddah kulawa har saida ta kwana uku, aka sallameta ta warke sosai ko da suka dawo saida taroki abba ya fiya ya hakura, tun daga ranan su H Muslima suka fara shirye2 na bikin feenat, duk da cewa ba ta san waye ango ba amma hakan bai da meta ba ita dai zatayi Auren biyyane. Dr ghalikuwa aikin sa yakeyi cikin kwanciyan hankali bayi da wata matsala.tunda ya samu Jiddah sa kulum suna makale a waya, haka yan gidansu ma in suna waya da dad dinsa yace yau kusa dawowa don yana son surprise dinsa hakan yasa ghali ala2 su dawo shi da Jiddah kuwa abun sai ya ba ma mai karatu mamaki irin love din da suke sha wani sa’in har nake kwatantasu da Romieo n Juliet ko masoyan cikin film din Ashquie wato Arohi Keshaf Shirke da Rahol jekal, abunsun gwanin burgewa, ko ni sai da na yaba da ghali don gwanin soyayya ne haka kwanaki sukayita ja yau ya rage saura 1 month Dr Ghali ya dawo murna gun jiddah da ghali ba’a magana. Alhaji Muhammad Ahmad bakara min lefe ya jigga ba yayi kaya nagani na fada na nuna ma sa’a ranan Asabar Abba yazo yace ma H Muslima su shirya yau za akawo kayan Feenat. Yau Jiddah da su H Muslima basu ga ta zama ba kaya su ka shirya maiji da lfy, nan suka gama suka kimtsa ko ina nan gidan yan uwan H Muslima da makwabta suka shigo karban kaya, feenat da jiddah kuwa sun fita unguwa, Jiddah tun suna mota taji gabanta na faduwa sosai da sosai, haka sukaje unguwan suku2 da ita sai dab mangriba suka dawo ko da BAZATA ********************** ⬇ ************************** ********** Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** By ©Rash Kardam 18 Gidan Alhaji Taneem da gidan shirye2 na biki akeyi ba kadan ba, Abban su Jiddah kayan daki bana wasa ya sai mata ba ya hada kaya bakan2 ba, sai lailaya Feenat yakeyi, sabida irin biyyan da tamasa, komai sai feenat don tunda Jiddah taki umar ninsa ya dan janye mata, H Muslima ba karan gyara take ma feenat ba, haka duk wani abu mai kyau in tagani zata sai ma feenat, Jiddah ma kudi tacire sosai sukaje kasuwa da Jiddah suka zabi kaya kai gsky feenat ta ga gata bana wasa ba, ga wani kyau da takara don tana samun gyara na musan man fatarta tayi kyau luwai2 gwanin burgewa. Gidan Alhaji Ahmad Muhammad suma shirye2 sukeyi bana kadan ba, don Dad yana ji da dansa, ga murnan dawowansa ga biki wanda hakan yake don haka Habeeba ya kira da Ruky yace baya son lbr ya isa kun Son dinsa, yace su shirya zasuje gd Auntyn sun suji mai zatayi sai su sanar masa da murna suka amsa, shirin zuwa gidansu feenat suka farayi duk jikinsu na rawa, zasuje suga Auntyn su, wanka sukayi sosai suka sa kaya iri daya bakara min kyau sukayi ba, yayan gd H Zaks kenan, driver ne ya dauke su ya kaisu, ko da suka je feenat kadai suka samu a gd, tamusu tarba mai kyau suka zauna suna hira ta kawo musu drinks ana cikin haka sai ga Jiddah ta shigo, ganin baki yasa ta zauna a falo aka shiga hira da ita, nan su Beeba da ke kusan sa’ar Jiddah tace Aunty Jiddah da man maganar Event muka zoyi tunda angon baya gari, haka kurum Jiddah taji faduwar gaba, cikin dauriya da tace ina ga zamuyi Dinner da walima kawai ya isa ko ya kk gani, sukace haka za’ayi, jiddah in sun hada ido da Ruky sa i taji gabanta yayi mumunan faduwa don tana kama sosai da ghalinta har yanayi murmushin su, da kasaitan maganar kaman na sarakai, san nan kuma bata da yawan surutu kaman na ghali, take taji yarinyan ta burgeta, su beeba sai dab magriba suka tafi gida suna jin dadin tarban da Feenat da Jiddah suka musu abun gwanin burgewa, ko da sukaje gida sun yaba ma feenat, Ruky tace ni Aunty jiddah ta fi burgeni inama da ita bros zai aura, beebah tace nikuma banga aibun aunty feenat ba haka sukayita hira har abba ya shigo suka masa bayani yaji dadi yace da kansa zaije yaga diyarsa, H Zakiyya ma taji dadi da yanda taji halin surkanta sai fatan Allah ya basu zaman lfy. Su Jiddah nanya sai shirin biki, Dad da kanshi yazo ya kawo kudin su walima nan yace Abba ya kira masa yaransa su gaisa, hajiya muslima ya kira yasa ta kira masa Jiddah da feenatu, hijab suka saka suka fito, bayan sun gaisa ya ciro kudi ya mika ma musu dake Jiddah itace akusa ta mika hannu zata karba, rass kake ji yanda kirjin feenat ya buga, sai da ta razana, don wan nan mutumin sunyi tsananin kama da Dr ghali kamar an tsaga kara, har sai da Abba yace lfyrki kuwa, da sauri ta amsa tayi godiya ta suka tafi, bayan tafiyan Dad da kwana 5 ya aiko ma feenat da kati da zata raba na aure, katin yayi kyau sai a lokacin tasan sunan angonta Muhammad Ahmad Muhammad har cikin ranta taji tana son sunan ya burgeta, sai ta fara tunanin wani irin zama zasuyi shi bai taba ganinta ba itama bata taba ganinsa ba, gashi auren biyya zasuyi dukkansu, wata zuciyar tace to wani irin zama zakuyi kenan, nan taji tafara tausayin kanta, tun daga ranan aka fara shirye2 na biki gashi kwanaki sun ja yau saura sati biyu biki gashi Dr ghalin Jiddah ma saura sati biyu ya dawo, Jiddah sai murna takeyi gashi dai2 bikin feenat dinta duk wani abun da zasu bukata kama daga ashobe duk sun tana da jiddah kwanan nan sai yawan faduwar gaba takeyi don har yar rama sai da tayi, H muslima ta bayeta tace ba komai, dole ta kyaleta, suka ciba da shirin biki ga shi kwanaki ya karato yau saura kwana 4 ayi walima ran jumma’a a daura Aure kuma jumma’ah da daddare ayi dinner da kai amarya, duk su Jiddah sun dawo busy ga Dr ya kusa fawo wa abun ya mata kashi 2, yan uwansu na kaduna duk sun zo yan uwan maman feenat sun zo suma sun taka nasu rawar g BAZATA By ©Rash Kardam 19 Haka tayita tunani kala2 duk wani abunda ya dace anyi sun gyara a harabar gidansu zasuyi walima tunda yana da girma, tun ranan laraba suke shiri ran alhamis zasuyi walima, a harabar gd su, yakama ranan Dr ghali zai diro ranan jumma’a daga india jiddah na cikin farin ciki, sunje gyaran gashi gawani mayen lallen da aka masu, kai mai karatu kar kiso kiga Jiddah tamkar itace amaryan feenat tayi kyau itama, Yau alhamis duk ina kaduba a gidan fararen kurune an gara ko ina komai yayi kyau sai jiran lokacin walima afara, sunje sun gayyato Malama Juwairiya ita zata gatar musu da lectures agun, Dad din feenat kuwa sai da ake gobe aure ya kira su Dr Samar ya sanar da su kuma ya gargade su, kada su sanar masa, Dr samar bakaramin tashin hanlai ya shiga sai ka dauka shi za’a masa Auren, gd ya dawo ya shiga daki ya zabga tagumi, a xuciyarsa ina ma da Abba zai yarda ya hada auren Jiddah dana Dr Ghali ya zamana mata 2 ya aura, sai a lokacin ya duba katin yaga ansa Safeenat Taneen sai da yaji wani faduwar gaba, wannan irin sunan feenat dinsa, don tun randa sukaje gidansu Jiddah da tabata Allah ya jarabce sa da so feenat, don ya yanke shawaran Dr Ghali na dawowa zasu samu Jiddah da maganar, haka yayi ta tunani kala2. Da yamma yan walima har an soma taruwa, amrya tayi wankanta cikin wani uban materia orange da golden, ta kawo lifaya shima orange da golden tayi kyau sosai, Jiddah ko tasha material ita maroon da golden colour, tayi kyau ba kadan ba kai ka dauka itace Amaryan, tasha kyau ba kadan ba, sai da aka cika suka fita, tun fitowarsu jama’a suke zuzuta kyan amaryan don su sun dauka jiddah ce duk da feenat ma ba baya bane gurin kyau, gsky Amare sai son barka, nan na hango su Sharrefa anfiti sai daukan amare photo akeyi, su pinky lady ansha gayu kamar ba gobe, sannu a hankali suka tako har zuwa gun kujerun su, bayan sun zauna Malama Juwairiya ta soma gabatar da wa’azi abun gwanin burgewa, sai 6:00 aka tashi angun wa’azi walima yayi kyau sosai, haka suka koma gida agajiye, sallah sukayi suka kwanta, Jiddah ko na makale da Dr ghali suna waya, tace My luv nayi missing dinka da yawa har mafarkinka nakeyi, yace my Jiddah ina don da na dawo za’azo ayi maganar Aure kinga mun huta kulum muna tare don bazan gaji da kallon kyakyawan fuskanki ba, jiddah sonki da kaunarki a jinina yake ina matukar kaunanki, ur ar my lyf, n u ar my happiness, cikin murmushi:) tace Dr ta i a tsananin kaunarka sonka a jinin jikina yake yabi jiki da tsoka, hira sukayi sosai, sai da dare yaraba sukayi sallama, washegari suka tashi anata shiri, don bayan sallah jumma’ah za’a daura Aure, Abba ya gyara gidan da ghali zai zauna kusa da nasa abun gwanin burgrwa ayi ma feenat jere dakin ya zuba kyau sosai, sai karfe 12:00 yan jere suka dawo sunata zuzuta kyan gidan, karfe daya da rabi bayan an idar da sallah jumma’ah dubban mutane masu fada’aji da hannu da shuni suka shaida daurin Auren Ghali da feenat, Dr samar kam kasa zuwa daurin Auren yayi don yana taya abokinsa jimami, gashi baima san wacece amaryan ba, ko yatake sai Allah, karfe 7 na dare jirgin su Dr Ghali ya dawo ya siyo tsaraba ma Jiddah bana wasa ba kama daga kan turaruka lesuna shadda ubansun, masu kyau, Abba ya kira samar yace yazo ya samesa ko da yazo, ya baza wasu kaya masu kyau, sosai da sosai ya basa wata sabuwar mota yace kaje ka dauko sa a Airport ka wuce dashi gidanku zan kirasa awaya, sanan ka basa wananan katan yasa karfe 9:00 za’afara dina a Zaranda hotel sai ka kaishi banson ka sanar dashi komai ina son zan masa “BAZATA” ne Dr Samar jiki ba kwari ya bar gun dad yanufi Airport, ko da yaje shi yana isa jirginsu ya sauko nan bai dade ba Dr ghali ya fito, Dr ghali yayi kyau har yar kiba yayi ya kara murjewa ya kara haske cikin fara’a ya iso ya mika ma Dr Samar hannu s BAZATA By ©Rash Kardam 20 Jiddah ta tafi luuuuu da sauri ghali yayi kanta amma ina kafin ya karasa ta zube kasa sumamiya, cikin tashin han kali ya dauketa yana wani irin kuka mai ban tausayi, sambatu yake yi kala2 ko da yasata a mota sai alokacin ya tuna key na hannun Dr samar ya juya kenan ya gansa da su feenat da marsal da sophia a rikice, zuwa yayi ya kwace key din motar yayi ciki da gudu, su feenat kafin su shiga ya tada motar dole yasa suka shiga motar marsal da sophia suka rufa musu baya T.H suka nufa, Alhankalin Dr ghali in yayi dubu ya tashi yana tuki yana kallon jiddah, pls kar ki tafi ki barni kece rayuwata, bazanji dadin rayuwa in bake ba, lyf is nothing with out yhu my Jiddah, yana isa dauko ta yayi ko rufe motar baiyiba ya nufi emergency da ita, nan likitoci suka karbeta shikam ya kasa komai sai kuka yakeyi wai shi dad zai masa auren dole, kuma yar Jiddah uba daya nana yaji wani irin kuka ina feenat ba zan iya zama dakeba don bazan iya miki adalciba, jin an dafa shi ya juwa Dr Samar ya gani da feenat da su marsal nan yaji wani haushin feenat yakeji da har ta amince aka daura aurensu, Dr Samar shima hankalinsa a tashe yake don yana tsananin son feenat bana wasa ba ga kirjinsa da ke bugawa da sauri2 sai adu’a yake furtawa na neman kariya. Aunty Maryemer da su Habeeba suka kira dad suka sanar masa, hankalinsa yayi tashi sosai number ghali ya kira yaji a kashe, nan ya kira na Dr samar yashiga yana dagawa yace suna T.H dad na kashe waya ya kira number Abba ya sanar masa, hankalinsu a tashe suka nufo asibiti, Ko da suka iso har an fito da jiddah tana bacci lokacin, cikin tashin hankali H Muslima ta ke tambaya mai ya faru, shiru sukayi nan ghali ya soma kuka, ko ba a fada h muslima ita tagane shine mijin feenat. Cikin tashin hankali tayi gunsa tana cewa mai ya samu jiddah dan Allah ka fada min kukan da ghali keyi ya farkar da jiddah tana bude ido taga iyayensu nan tasaki kuka mai ban tausayi ghali yayi kanta bansan lokacin da ya rike hannunta ba pla my jiddah kiyi shiru kece macen dana ke so kuma bazan taba son wataba kece uwar yaya na Jiddah ina kaunarki i luv yhu, kai ta ke gir giza masa alamar aa, yace jiddah bazan taba iya adalci ma wata mace ba in bakebe ke na fara so zuciyata ketake kaun…..tass tass kakeji dad ya kife shi da mari yana huco kana da hankali agabana kuma ga matar ka nan kasata kuka karya kake feenat itace zabin mu dole ka bi kayi kadan, Abba yace ma Samar mai ke faruwa nan Dr Samar ya basu lbr Jiddah da ghali, yana gama wa Abba yace Jiddah kinyi kadan aure an daura kuma baza war2 ba kin ki bin umurni na sai yanzu dayake wanda kike so to baki isa dad yace ghali zama da feenat dole ko ka gamu da fushina, feenat da kuka ya ci karfinta ta yi gun Abba tace Ababa dan Allah kayi hakuri yasa keni Jiddah ta aureshi wlh suna son juna, yace kee ina kara jin wan nan magaran sai na saba miki wuce mutafi sumu2 ta wuce dad ma yace ma ghali su tafi shida samar suka fito ghali sai tangadi yakeyi kamar zai fadi suka shiga mota gidansu samar suka wuce dad da Abba suka tafi akar H Muslima da Jiddah. Ko da suka fita H Musleema ta soma fada ma Jiddah kin ga ilar kin bin umar nin iyaye ina jan kunnen ki da ki yihakuri yanzu kinga irin halarcin da feenat ta miki kar ki daga mata hankali a gidan mijinta ki rungumi kaddara ta iya yiwuwa Allah ya kawo miki sassauci a al’amuranki, idon Jiddah ceke da kwala:'( tabbas tasan nasihar mamanta hakane ya zama dole tayi nisa da ghali ta barsu suyi rayuwansu da feenat, ta kali H Muslima tace Ummah ina ga zanyi nisa da su feenat hanya daya da zan samu sassauci, h musima tace ina zakije? akiyan zuciya tayi tace zan fara ciku2 na tafiya karin karatu duk inda na samu admission zan tafi inyi masters dina kawai a gun amma zan bari sai komai ya lafa don yanzu Abba na fushi dani sosai, h muslima tace aure fa, jiddah tace sai bayan komai ya lafa zan dawo kafin nan nasamu wanda muka dai2 sai ayi maganar BAZATA By ©Rash Kardam 21 Sai da sukayi kuka mai isar su, ghali ne yace Samar feenat ta kace dole in bar maka feenat, Samar yace no ka bi umarni iyayenka cikin muryan kuka ghali yace bana ki musu ba amma su tausaya mana Jiddah itace zabina itace rayuwata, sam ba zan iya zama da feenat a matsayin mata ba, bazan iya mata adalci ba, ina tsoron kar Allah ya kamani da laifin ban yima iyalina adalci, haka sukayi ta jimami, sai kusan 1:00 suka kwanta duk sun kasa bacci ko wanne da abunda yake sakawa a zuciyarsa. Su Abba ko da su ka isa gd dakinsa yayi, feenat ma dakinta tayi, tana shiga sallah tayi ta fara kai kukan ta ma Ubangiji, tana rokon Allah ya kawo mata mafita, don ita ko kadan bata son gani Jiddah cikin tashin hankali,haka shafa ta kwanta bacci. Su Jiddah haka ta kwanta, ko da gari ya waye misalin karfe goma aka sallame su, don jikinta da sauki daman firgicin da tashiga ne, haka suka dawo gd, ko da ta koma dakinta tayi ga gidan da yan biki, wanka tayi ta sha tea, ta zabga uban tagumi, feenat ne ta turo kofa ta shigo kallo daya tayi ma Jiddah idinta ya ciko da kwala:'(, sam jiddah bata san an shigo dakin ba, sai da feenat ta dafata san nan ta dawo hayyacinta, ganin feenat ne yasa tayi yaken da yafi kuka ciwo, feenat jiddah ki kwantar da hankalinki ghali na kine bazan iya zama da wanda kukeso ba, Jiddah ta girgiza mata kai alamar aa, jiddah tace sis ki bi Mijinki kiyi masa biyya kisani Allah ne ya jarabce ni sanadin kin bin umarnin mahaifina, nayi nadama kuma na gane kure na, nan kuka ya kwace mata, tace sis na hakura da ghalu, feenat tace aa ina sis ba zaiyuwa ba, ganin sunki sasanta kansu yasa feenat na kuka ta bar mata dakin, tana zuwa dakinta kuka tayi sosai, Jiddah kam duk ta rame yini daya, ta kuma fauwala ma Allah komai. Dr ghali ko da gari ya waye sukayi sallah, kalo daya zaka musu kaga irin raman da sukayi, sai karfe 10:30 suka fito asibiti suka nufa, nan suka tara da an salami Jiddah, Dr ghali yace su je gidan Dr Samar yace baa’ayi haka ba, kana da Auren yarta kaje duba kanwa Abba da Dad baza suji dadi ba, yanzu muje gidanku muji mai ke tafiya, ko da sukaje suka tarar da sauran yan biki nan abokan wasa suka fara tsoka narsa angon feenat ransa ya kara bacci, da zai juwa Dr Samar ya rikesa, falon Mum dinsa sukaje, koda suka isa, habeeba suka gani tafito daga dakinsu, ganin yanda wanta ya dawo idonta ya ciko da kwala, ta juya da sauri tayi dakin mum dinsu, sai da ta share hawayenta kafin tashiga dakin tace wa Mum ga su bros sun zo, jiki ba kwari H Zaks ta fito, fiskanta dauke da fara’a suka gaisa da Dr Samar ghali ya gaidata ta amsa, nan ta musu nasiha sosai, ghali yace ina dad tace dad baya nan ya fita, Ruky ta kira, ki kawo musu abinci sai da ta kawo mum ta tasa su gaba sai da sukaci, ganin mutane yasa suka mata sallama gidan su Samar suka koma, ghali kwanciyayi yana tunane2 dinsa, ghalu ko ya zabga uban tagumi abun duniya ya ishesa, haka sukayi har dare duk sun dawi so silent, bayan magriba Dad ya kira Samar yace su zo da ghali su sameshi a gidansu feenat, sai da sukayi isha’i wajan karfe takwas kafin suka isa gidan ai ko su dad ma lokacin su ka shigo da Abba a kasan carpet suka zauna cikin biyayya suka gaida su Abba suka amsa H Muslima ne ta fito suka gaisa da dad, Abba yace takira masa feenat da jiddah, bata dade ba, suka zo tare suma guri suka zauna a kasa kusa da H muslima, cikin ladabi suka daida dad, Abba ne ya fara da Adu’ah kafin suka sha, san nan ya kira sunan ghali da feenat ya musu nasiha sosai ya kuma ce ma ghali ya rike matarsa da amana, cikin muryan kuka ghali yace Abba banaki umurnin ku ba, feenat sam bata dace daniba Dr Samar shi ya dade yana sonta, tun randa ya fara ganinta dad yace kaji min yaran “ZAMANI” book by Sheedat Y Abbas, waza ku mayar yaro zaman Aure ba fashi, Dad yace ghali ban yarda ba inji kasaki feenat BAZATA By ©Rash Kardam 22 Ko da suka fita dad da Abba suka rakosu feenat sai kuka taketayi, motar su Samar dad yace tashiga Samar ya kaisu, gidan baya tashiga ghali da samar a gaba, samar yaja mota suka bar gidan Dad na bayansu, sai da Samar ya kaisu har cikin gd kafin ya musu sallama yaja motar ya koma gd da kyar don wani zazzabi ne yake neman rufeshi, ko da ya isa gida ruwa ya watsa ya yi alwala ya gatar da sallah nafila, adu’ah yayi sosai na Allah ya bashi hakuri da dangana bayan ya shafa ya kwanta. Ghali ko gidan yashiga daki na farko yaga kaya sosai nan ya gane na feenat ne dayan daga gado sai sif, shi yashiga ya sa key, feenat na ganin yashiga daki daya itama tashiga wanda ya fara lekawa taga kayanta nan tagane dakinta ne, kulle kanta tayi itama kuka tayi sosai ganin kukan bashi bane mafita yasa ta dauro alwala ta fara sallah, ko da gari ya waye ghali bai bi ya kanta ba ya fita gidansu samar ya koma, samar na ganinsa yace mai yasa yagito yuwar haka, wani mugun kallo ya masa wanda yasa Samar jan bakinsa yayi shiru suka shiga ciki, sai da suka karya kafin suka fita zuwa cikin gari basu suka dawo ba sai dare bayan isha, ghali yace shifa ba zai koma gida ba, nan Samar yasa shigaba yayi ta masa nasiha wanda dole yasa ya mike ya karbi key din motar ya nufi gida. Feenat bata fitoba sai kusan shabiyu rana idonta ya kumbura dosai, store tashiga ta dauko indomee ta dafa da ruwan tea tasha daki tasake komawa ta kulle kanta sai da yanma tafito ta sake dafa indomee taci takoma dakinta, ghali bai dawoba sai kusan 9:00 yana zuwa dakinsa ya wuce wanka yayi ya kwanta sam ya kasa bacci sai tunanin Jiddah sa yakeyi, tundaga wan nan rana haka rayuwansu feenat ya kasance sam bata bari su hadu da ghali shima bai damu da ya ganta ba duk wanda yasan ghali ada in ya ganshi yanzu sai yayi da gaske ya ganesa, yayi duhu duk gayunsa ya rage, yara ge yawan magana baya son shiga mutane. Jiddah itama duk rayuwanta ya canxa ta dawo shiru2, bayan kwana biyu da faruwan abun, taje gun professor Aminu Ilyass ta masa bayani tana so ya tayata, niman Admission ita a kowani kasa ne tana so, nan yakarbi copies din ta kardunta, yace taje duk yanda tayuwu za tajishi, da murna ta dawo gd, yunda ga ranan tafara fita aiki sai dai ko kadan taki su hadu da ghali, Yau tafito gun aiki bayan antashi tabi winti market ta karbi dinkinta, tafito kenan taga wani katuwar Jeep tatsaya a gabanta da sauri ta kauce tashiga motarta, ta tayar ta bar guri aeko sai taga mai motar yana binta, gudu tarinka yi shima ya kara ko da ta leka ta madubi sai taga motar har biyu suke binta dan haka taki bin hanyan gida ta nufi gidansu Sophia ko da ta iso kofar gidan ta ajiye motarta tafito kenan taga wani matashin saurayi fari sol kyakyawa da shi, ya nufota cikin fara a Sallama ya mata wanda yasa dole ta amsa masa, tazo zata wuce yace malama dan girman Allah ki saurare ni kiji mai zance maki, cikin sanyi jiki tatsaya yace Malama dan Allah meye sunan ki, kafin ta masa magana sai ganin ghali tayi yana huci yazo ya shake saurayinan yace kai baka da hankali ne matar nawa zaka tsaya da ita dan iska, ran jiddah ya baci tace kai ghali mai ya maka kasani, ni yanzu ba malakinka bane kayi hakuri ka fita a rayuwata, bana sonka bana soka, ghali kai mijin yata ne meye gamina da kai, ghali mtss tazo kusa da wan nan saurayi tace kayi hakuri kaji dan anjima kazo kasameni, shiko ya dauka gidansu ne cikin jin dadi ya tafi, ghali ya tsaya don tsananin mamaki, Jiddah ki ge fensa tabi ta wuce zuciyarta namata wani irin radadi tana shiga gidan su Sophia kuka tasaki a daki sophia don ta san bata kyauta ma ghali ba tayi hakan ne don ya rabu da ita ya zauna da feenat lfy, ko da sophia taga tana kuka rarrashinta tasjiga yi da kyar tayi shiru kafin sophia ta tan bayeta meye ta sanar mata, sai da ta dan huta kafin ta wuce gida, tana isa wanka tayi ta huta tukun tashiga kitchen ta taya Ummanta girki, bayan sungama ne tazo BAZATA By ©Rash Kardam 23 Jiddah tashiga basu jima ba,jirgin su jiddah ya daga, tafiyan awa uku 3 sukayi ya kaisu UK, ko da suka sauka a Jirgi nan ta hango abikin prof Aminu shi yazo ya dauketa, ka sancewar lokacin yamma ci ne yace ko zata je gd sa, batayi musu ba ta bishi, ko da ya kaita sallah tayi tayi wanka, tana zaune taji ana kan kwasa kofar, hijab tasa taje ta bude, ya miko mata leda godia tayi ta karba yajuya ya tafi, ta rufe kofar ko da ta bude taga abinci ne a ciki, haka ta zauna taci, sai a san nan ta kira su Abba ta sanar musu ta isa, san nan ta kira su Marsal da Sophia ta sanar musu, tukun na ta kwanta ta huta har sai da akayi magriba ta tashi tayi sallah, sai da tayi isha’i kafin ta watsa ruwa tazo ta kwanta, da gari ya waye ta shirya cikin doguwar riga baki da ratsin golden tayi rolling, tana fitowa suka gaisa da shi nan yabata kayan karyawa ta karya, bayan sun gama suka fito motarsa suka nufi makarantar, ko da sukaje basu wani dade ba ta kamla komai, nan a ka kaita hostel, tundaga wan nan rana jiddah ta dun kufa karatu baji ba gani, ta mayarda kanta bussy, sabida bata sontunani ya ada beta, sam Jiddah bata da sai wata Nusaiba Mustapha Katsina, da suka hada kai nasu yazo daya don Nusaiba a kwai girma ma mutum da anin karamci, hakan yasa suka hada kawance duk da cewa Nuceeyluff yar masu kudi ne sosai hakan bai samata girman kaiba. Wacece Nuceey Alhaji Mustapha Katsina shine mahaifin su Nuceey, A Mustapha ya kasance yana da Mata daya, hajiya Maryamer, da yara uku, na farko shine Aslam Sai Nusaiba, sai Autarsu Zee wanda yanzu take SSS2 INTERNATIONAL SHOOL ABUJA, makaranta da sai ya yan wane da wane, A Mustapha na tsananin son Aslam da Nuceey sosai gasu da hankali ga ilimi, duk abunda suke so shi za’a musu hakan baisa tarbiyar ya wargajeba, Aslam ya gama karatun shi a UK shima, yanzu Babban Doctor ne A Asibitin Abuja san nan yana da Asibitinsa na kansa Nusaiba Clinic, shirin da sukeyi da Nuceey yasa baya wata biyu uku bai je gun Nuceey ba, kimai nasu gwanin burgewa, a irin ziyaran da ya ke kaimata watara na yaje UK bai sameta ba tana school sai ya bita school din ko daya je yasamu suna lectures, tsayawa yayi suka gama, Nuceey da Jiddah suka fito daga lectures, tare suka jero suna tafiya cikin nutsuwa, tunda suka fito yake bin Jiddah da kalo, gsky yarinya ta hadu sosai take yaji ya kamu da sonta, ko da suka iso cikin ladabi Jiddah ta gaida shi, ya amsa da gara’a Nuceey tace bros yaushe kazo yace yanzu nazo, Nuceey ta nuna masa Jiddah ama tsayin aminiyarta, yaji dadi sun danyi hira kafin Jiddah ta musu salama ta koma hostel, Nuceey da Aslam suka nufi gidan Nuceey da ke UK, tun daga wan nan rana da Aslam yaga Jiddah ya fara sintiri tsakanin 9ja da UK, nuceey kuwa saida ta san tanda ta janyo Jiddah ta dawo gidan ta da zama haka sukayita ratuansu cikin jin dadi da kaunar juna. 9ja Tun bayan tafiyar Jiddah ghali komai ya sukur kuce masa ya dawo kamar ba ghali, ya rage gayu da yawan magana, Anwar kuwa duk bayan kwana uku sai ya ziyarci Sophia san nan ya karbi number jiddah yana yawan kiranta suna gaisawa sosai, hakan yasa yace ma Jiddah yana son yaje ya gaida babanta, ko kadan bai kawo mata zancen Aure dai je ba, ganin ya nuna mata gaisuwa ne na haka kurum sai ta amince masa, Anwar yayi shiri sosai yasa man yan kayansa ran Asabar da daddare yaje ya gaida Abba Jiddah, sun dade suna hira nan Abba yace ai Jiddah ta bani lbrka, kuma na yaba da hankalinka dan haka katuro min magabatan ka, Anwar cikin murna ya ya nufi gd ya sanar da magabatansa, nan suka zi suka samu Abba yace ba matsala suje su shirya su zo ayi aure, suka bashi goron tambaya da minti, Abba cikin murna ya karba, nan ya raba ma yan uwa, hakan yasa aka kai ma feenat, ran da taji maganar tayi kuka sosai, bayan kwana biyu da faruwar maganar Auren Jiddah, ghali ya je gidansu ya s BAZATA By ©Rash Kardam 24 Cikin razana yace what??? nan take idonsa ya canza kala dishi2 yasoma gani, ruky ce ta kwana kara, nan ya dawo hayya cinsa, cikin hanzari ya bar falo ya nufi kofar fita, habeeba ce ta biyo bayansa amma ina kafin ta iso shi har yata da motarsa ya isa gate mai gadi ya bude masa, da gudu ya bar gidan, tun daga wan nan rana abun duniya ya kara ya ishi ghali, kulum adu’arsa Allah ya dawo masa da Jiddah ta dawo malakinsa. Gidan su Jiddah kuwa iyayen Anwar sun zo an kawo sadaki Abba ya sa biki 3 month nan sukayi sallama, Jiddah tun randa ta samu lbr ta kara shiga damuwa fida kulum kulum sai tayi kuka, yanzu kam tasan ta rasa ghali, kulum haka, daga karshe tasa ma zuciyarta dan gana da fatan Allah yasa hakan shiyafi Alkairi, ko kadan bata fada ma Nuceey abunda ke faruwa ba, sai dai ta rame hakan ne yasa Nuceey ke yawan tambayarta me ke faruwa tace ba komai, Nuceey har tagaji ta hakura ta zuba mata ido . Ghali bai kara rudewa ba sai da ya samu lbr sa bikin Jiddah nan ya daina fita aiki ya kule kansa a gida ko abincin kirki ya daina ci yau kusan kwanansa 4 a daki baya fita, feenat ce tafito zata kitchen, nishi sama2 tarinka jiyowa daga dakin sa, da farko shatewa tayi taje ta girka abincinta, ta hau dining ta ci, tazo da taje daki taji wani nishi mai karfi da ghali ya saki da sauri tayi hanyar kofar dakin ko da tura tashi a kulle, idonta na zubda hawaye tayi dakinta da gudu ta dauko wayarta Abba ta kira don bata da number yan gidansu ghali, cikin kuka take sanar masa, yace gashinan zuwa, dad yakira ya sanar masa, ba a dade ba Abba ya iso ko 3 minutes baiyi da shiga gidan ba dad ya iso, ko da suka tura kofar a kulle suka jita, dad ya rasa yanda zaiyi, sai can ya tuna da extra key dinsa na gidan da sauri ya ce ma Abba bari yazo, Gida ya koma ya dauko keys din suna zuwa suka bude dakin nan suka ga ghali kwance a kasa ga jini a gefensa, idonsa sun kafe, feenat kara ta saki ta raza na sosai, Abba da dad suka daukosa Asibiti suka nufa da shi Emergency nan aka shiga da shi, bai bayan 1 hours Doctor ya fito yana goge gumi da sauri Abba da dad suka nufo shi, doctor yaya, yace ku kwantar da hankalinku, cikin ikon Allah mun samu ceto rayuwansa zuciyarsa ta samu matsala a kwai abunda yake tsananin so, dad da Abba sukayi hamdala, nan aka fito da shi zuwa dakin da za’a bashi gado, haka suka yini a jikinsa, ghali bai farfado ba sai washe gari da safe lokacin Abba da H Muslima sun zo ga Mum dinsa da Dad dinsa, sam batu ya farayi kamar tababe, Jiddah wlh ina tsananin sonki, pls kar ki Auri kowa nine masoyin ki na gaskiya haba hauwa’u na kizo gare ni ina bukatarki, Abba ya ji tausayinsa H Muslima kam idonta kwala:'( yaciko da shi, Hajiya zakiya hawaye ke zuba a idonta, Abba yace ghali na maka Alkawari in ka warke zan Aura maka Jiddah likita ne ya shigo nan yaji sambatun da yakeyi, yace gsky zan baku shawara ku Aura masa yarinyan da yakeso in bahaka ba rayuwansa na cikin hatsari, jikin dad yayi sanyi sosai likita ya masa aluran baci yace in Allah ya yarda zai farka cikin hayyacinsa, Abba ya kali dad yace ghali in ya warke zai saki feenat ya auri Jiddah, kawaici irin na mutanen da yasa dad yace sam bara ayi haka ba Abba yace ai fa ya ro ba zai cutu ba, da ga karshe dad shiru yayi amma yaki amincewa, Abba ya bar H Muslima ya tafi akan da yamma zai zo, haka ko akayi da yamma da ya dawo ya samu ghali ya farfado sai dai ya rame, gha ruwan da aka sama sa, abba ya gaisa da dad su H musima da Mum suka masa sannu da zuwa, ga feenat a gefe itama ta rame, ghali ganin Abba yasa ya soma zubar da hawaye Abba yace ghali ka share hawayenka, ina son yanzu ka sauwake ma feenat zan aura maka jiddah nan Dad yace baza’ayi haka ba, ran Abba ya baci yace Alhaji in na isa da ghali ina son ka barni inyi iko a kansa, nan yace ma ghali ya sauwake ma feenat, feenat nan take taji gabanta na faduwa duk da BAZATA By ©Rash Kardam 25 Abba ya ce ba damuwa, kuma na jidadin hakan Allah ya sanya Alkairi, Anwar ya amsa da Ameen, Anwar ya samu Maryam Salis(Marsal) da farko ta ki sai da Sophia tayi ta lalashinta kafin ta amince, iyayen Anwar da Abba sun zo sun samu magabatan Marsal ansayar da rana daya za’ayi da na Jiddah, haka suka rabu cikin farin ciki, su Marsal Amare an soma gyaran jiki shirin biki sukeyi sosai don ko ba komai suna masu farin cikin Jiddah zata Auri gowaninta, Anwar da Marsal soyayya sukeyi mai burgewa kai kace sun saba tun tuni, marsal har mamakin kanta takeyi irin yanda take nuna ma Anwar tsan2 kulawa da soyayya, su marsal sabon shiga, a soma luv . A ban garen ghali kuwa gyaran gidansa ya shiga yi don yana son su zauna da Jiddah sa a gidansa na fadaman mada, in da ya fara kaita lokacin da suke rikicinsu, gyara sosai ya sa ayi don har tsarin gidan ya dan canza zuwa wani salo, ghali yanzu hankali ya soma kwanciya har ya soma murmurewa, burin shi kawai ace yau an daura, don shi yana ga binta can zai bazai iya jiran sai ta dawo ba, wooo nikuma nace su ghali dan dauki, yanzu an samu Jiddah mun huta da rigima, wani lokacin in yana zaune shi kadai sai dai kaga yana murmushi, karasa na meye shidai ya san mai yake tunawa. Jiddah da Nuceey zau ne suke a kofan hall sun fito daga lectures, Nuceey ta kalli Jiddah tace wai ni kwana biyu mai ya faru na ganki cikin farin ciki, Jiddah tace Nuceey wlh na rasa mai yasa, haka kurum nake jina cikin nisha di kuma walwla na ya karu, Nuceey cikin sigar tsokana tace kodai mun samu ango ne, Jiddah ta harereta tace agogo ne ba Angoba, dariya sukayi gaba daya kafin suka shiga motar Nuceeyluff suka nufi gida suna yar hiransu abun birgewa, komai nasu tare sukeyi sun hada kansu kai kace yan’uwa ne na asali, ko da suka koma abinci suka girka kafin suka watsa ruwa suka ci, wayar Nuceey ce yai ringing tana daukowa taga an rubuta dan uwa, da murna ta daga bayansun gaisa sunyi hira, yace ta ba ma Jiddah nan ta mika mata sun gaisa ya tambayeta karatu tace Alhamdulilah, sun danyi hira sukayi sallama, haka rayuwan su Jiddah da Nuceey a skul ya kasance cikin farin ciki ga kokari ba sa wasa da karatu. Dr Samar ya samu feenat suma sun dai2 kansu,kasancewar feenat bata da iddah tun da ghali ko dakinta bai taba shiga ba, bare ya kusance ta, shima ya turo magaba tansa, sannu a hankali Samar ya ko yarda feenat sinshi wanda ya kasance kulum suna tare a waya, ko tana gun aiki suna tare wata shakuwa sukayi na musamman, hakan suka shiga shiri ba wasa, kwanaki sunja tau biki saura wata daya, iyayen Dr Samar sun kawo kayan Aure gsky yayi kokari sosai don ya zage damtse ya mata kayan kece raini, sai fatan Allah yasa ayi damu. Amarya marsal da Ango Anwar suma an kai kaya komai sai son barka abun gwanin burgewa, Amare sai shiri sukeyi. Abba yasa an kwaso kayan feenat ya sa ma H Muslima ita kuma ya sai mata sabi wanda suka fi na da kyau, ko kadan ba wanda ya fada ma Jiddah maganar Autenta, haka sukayita shi, gali ko dubai taje ya hado lefen Jiddah H Zakiyya ma tayi kikari don da ya dawo ta karamasa kayan sai na saura 3 day biki aka kai lefen Jiddah yan uwa sun yaba ko ni kaina sai da na sara ma ghali don ya kashe kudi kamar bai san zafinsu ba, feenat da taga kayyan sai da ta tsorota dob kayan sai ka sha mamaki, haka sukayita shiri Amare sun sha gyara Musan man H Muslima ta sa aka dauko sis Mamu ta gyara amare, don sis Mamu ba wasa wajen gyara tun daga nesa in ka hango su har wani kyali sukeyi. Rana bata karya, yau jumma’a da yazo dai2 da 26/ feb/ 2016 Duban jama’a suka halarci daurun Auren Muhammad Ghali Ahmad da Amaryarsa Hauwa’u(Jiddah) Taneemu, Samar Abdallah da Amaryansa Safeenat Taneemu Anwar Kabir da Amaryansa Maryam Salis(Marsal) Bayan daurin Aure angwaye suka wuce hotel don gabatar da liyafa, tun gada nes BAZATA By ©Rash Kardam 26 Ta bude baki zatayi ihu ya sanya bakinta a nasa, duk tsiwan jiddah yau ba halin yi bakinta, ya gamu da gamonsa, idonta ta runtse sai hawaye da ke bin fiskarta don tara hanyan yin ihu ga jikinta sai rawa yakeyi, tayi2 ta kwace kanta ama ta kasa, sai yanzu take raina kanta, yau ta gane karfin ta ba daya da ghali ba, can da bara ta fado mata cizo ta ganzara masa a harshe ba shiri ya sake ta da gudu tayi daki key tasa ma kofar tajin gina tana mai da numfashi, sai numfashinta ya dai2 kafin tasaki kuka mai tsuma zuciya daman ghali dan iskane, yana auren feenat zai zo ya bata min rayuwa mai na masa da zai takura min haka, da karfi tace Allah ya isa min dan iska macucu, kawai, can ta tuna da 9ja da sauri ta debi kaya kala 2 tasa a jakarta na hannu sai E passport dinta ra dauka, bude kofar tayi a hankali ta hango gali na kan 3 seater ya lumshe ido hijab dinta sa ta rike ta kalmi a hannu rarrafe ta kara yi don karya ganta sai da ta kai kofa, yaji kamar alaman mutum yana bude ido ai ta fita da gudu ta bar gdn kafin ya risketa tayi nisa don gudu takeyi tsakaninta da Allah ko data ga ta bace masa taxi ta shiga zuwa shool din su, ko da taje, dakinsu na da ta nufa, guri wata frd dinsu, Myer nan ta ce dan Allah tana son ta tai make ta ne, Airport takeso taje tayi booking, din jirgin da zai je 9ja Myer tace ban 5 minutes barin yi wanka mu je, sai da tayi yan kwaliya kafin sukaje duk wani shirin da ya kamata tayi tayi gobe da Karfe 9:00 zashi na safen su a 9ja kum 4:00 dinsu kenan, ko da tadawo makaranta gurin Myer ta zauna sai dare sukayi sallah sukaci abinci kafin suka kwanta. Ghali kuwa ya nimeta ya gaji ko da ya dawo gd mai gadi hana shi shiga yayi dole yasa ya nimi taxi ya koma gdn abokin prof Aminu bai boye masa ba, tun da daman ya san matar sa ce, nan yace zanzu gashi dare ya somayi ka bari gobe muje skul, bayida zabi dole ya hakura, da asuba su ghali suka tashi sukayi Sallah nan suka sake kwanciya baci barawo ya dauke su sai 9:20 suka farka, wanka sukayi sukayi breakfast suka fita. Jiddah ko gari na wayewa wanka tayi sama2 tayi breakfast suka wuce Airport, basu dade ba aka sanar jirginsu zai tashin nan da 5 minutes, basu dade ba tayi bye tashiga jirgi suka lula sararin samaniya, kafin Myer ta dawo skul cike da kewar kawarta, tana idowa cikin hostel sukayi karo da Aysha suna tare da wasu mutane guda biyu, nan tace ga Myer din ido ta zaro:oops:lfy, da sauri ghali yace dan Allah jiddah na ke nema, myer tacea ai Jiddah yanzu na dawo daga rakata a Airport ta tafi 9ja yau kai ghali ya dafe why jiddah, Myer tace mai ya faru, cikin hanzari yace ni yayanta ne kuma Mijinta, Myer tace miji kuma Jiddah daman tana da Aure ne, bai tsaya bata amsaba yayi gaba, abokin prof, yace suje Airport ko da sukaje akace jirgi ya tashi sai gobe da yamma amma lagos zai sauka yace ba matsala. nan ya gama komai kafin suka dawo gd, haka ya kwana suku2 yana tuna jiddah sa da irin yanayin da ya ganta, sai yayi wani murmushi wanda shi ka dai yasan mai yake faruwa, da gari ya waye haka suka dan zaga gari sai yamma abokin Prof ya kaishi Airport ya nufo 9ja. Jiddah ko tana sauka a kano ta sake shiga mota zuwa bauchi sai 9:20pm, ta samu samu isowa bauchi masu motar ta kara musu kudi suka kawota har kofar gd, gate ta kwan2 mai gadi ya bude yana ganinta yace Amarya kece yau a gari ya hanya,? cikin daurewan kai tace Amarya kuma, kafin ya bata amsa ta shiga gd lokacin duk sun kwanta daki umma ta taje ta kwan2 ta bude ta fito ko data ga jiddah ido ta zaro:oops: lfy kika dawo? Dai2 Abba ma fito dga dakinsa jikin H Muslima ta fada ta saki kuka mai ban tausayi, duk sun rude lfy mai ya faru? cikin kuka ne take cewa umm…. Dan…is..kan … Nane ya bini, cikin rashin fahimta Abba yace waye ya biki, ghali, mtss abba ya ja tsaki yace kije dakinki kwanta gobe zamuyi magana idonta na hawaye tayi daki, hmmm wato abba ya BAZATA By ©Rash Kardam 27 Washe gari Sophia tazo sunyi girki sosai, kafin sukayi wanka, sunyi kyau sosai, karfe 1:00 jirginsu Nuceey ya sauka a Abukar Tafawa Balewa Airport, Jiddah ta sanar ma ghali zuwansu, don haka ita da sophia sukaje su biyu kowa a motarta ko da suka isa, sun samu har jirginsu ya sauka, fasinjoji sun fara fitowa, Nuceey ce a gaba sai Aslam sunyi kyau sosai, Zee da Mum da Dad dinsu suma sun jero tare, Jiddah da sauri ta taje rungumeta, Aslam ko tun da ya sauko ya daura idonsa akan sophia ya kasa saukewa gsky ta hadu haka kurum ya ji ta burgesa, jiddah cikin ladabi tazo ta gaida mum d dad, sai Aslam cikin sakin fuska ya amsa, sophia ma tazo ta gaidasu, daga nan suka dunguma zuwa motarsu, sai gida. Koda suka isa H Muslima da murna suka tarbesu kai ka rantse sun dade da sanin juna, Abba gd ya dawo shida dad suka zauna a falon Abba hira sukayi sosai, Aslam da su Jiddah a falo, tun da sukazo idonsa na kan sophia, haka sukayita hira cikin raha bayan sunyi sallah ne suka dawo falo gabadaya akayi yan gaishe2, daga nan dad yace zasu je hotel shida Aslam sukama daki , haka akayi. Da daddare, ghali ya zo ya gaida su mum sai a lokacin Nuceey ke tambayar waye nan jiddah ta bata lbr, nuceey ta tayata murna, sun jima suna hira, kafin ya musu salama, h musima tace jiddah kitashi ki raka ghali mana, cikin jin kunya ta mike ta fito, ko da ta iso yana cikin motarsa, daga waje ta tsaya tana masa sallama, rai ya hada yace bana son miki in bazata shigo ba, ganin ya hada rai yasa ta zaga tashiga motar tana shiga ya kulle motar ya kashe wutar motan, tace masa miye haka bai tanka mata ba ila hannunta ya kama yasa nashi cikin nata,tsikan jikinta taji ua tashi yarrrr, cikin sauri ta dagi ido zata mishi magana ya mannata da jikinsa, cikin salon wanda ni kaina ban taba sanin ghali ya iya irin wan nan muryan ba sai ranan yace My Jiddah kin ga yanda Allah yayi ikonsa ko, kin dawo malakina, jiddah ina sonki kece farin cikina, pls Jiddah ki soni, fiskanta ya dago ya ga ta lumshe ido, bakinsa ya cikin nata duk wani kokarinta ta kwace kanta ta kasa jikinta ba kwari sai da yayi son ransa ya gaji kafin ya sake ta, cikin rada ya ce ki kulamin da kanki nan da 2 weeks muna tare, kauda fiskanta tayi, tace gobe zamu fita da Nuceey san nan ina son zamuje gidan su sis feenat da Marsal, kuma zan shiga ATBU, yace ba koma Allah ya kare, pls ki sanya hijab don kinsan da, da yanzu ba daya bane, tazo zata bude kofa hannuta ya rike yace i love you Jiddah, sai da tafita kafin tace me too, hannu ya daga mata alamun tanufi cikin gd jiki ba kwari. hira su kayi sosai, Nuceey da Jiddah a daki daya Zee da Mum suna daki daya, ko da gari ya waye tare sukayi aikin breakfast, bayan sun karya wanka sukayi, kwaliya nuceey tayi sosai jiddah batayi kwaliya sosai ba, suka nufi asibiti suka fara zuwa, pharmacy suka nufa sophia nan da marsal sun gaisa da ganan sukaje office din prof Aminu, nan suka gaisa, prof tun da ya ga nuceey yaketa aiki isar mata da sakonsa don ya kamu sosai, bayan sun fito suka gamu da ghali, sun gaisa da su, yazo ya rike hannu jiddah ko kumya bayaji, jiddah ko kamar ta nutse kasa, yace ma su nuceey bari ya raka su cikin pharmacy bayan ya rakasu yaki sakin jiddah nan marsal da sophia sukayita tsokanarsa, hannu ta ya ja zuwa office dinsa, ya kulle, jiddah ta zaro ido:oops: miye haka, hannu ya daura a kan bakinsa alamar tayi shiru, zuwa yayi kusa da ita ya zauna a kusa da ita kan resting chair ya zare hijab din kanta, ta rike tace miye haka Dr yace bana son wan nan sunan, fuska ta marai raice ka bari bana so pls, wani murmushi ya mata mai dauke d sakonni kala2, hannu ya sa a fuskanta ya soma shafawa, hannun sa yasa ta baya ya soma zuge zip din rigarta da sauri ta rike cikin rada ya ce jiddah mai yasa kike son hanani abunda Allah ya halasta min, ko kina son ki shiga fushin ubangiji, kai ta girgiza masa alam BAZATA By ©Rash Kardam 28 Cak ya dauketa, ya haura da ita steps din, nan kaji hall ya dauka da ihu da sowa, sai da yaje kujerun da aka tana dar musu kafin ya ajiyeta ya zauna, gsky amare sunyi kyau, ko Rash sun burgeni, sannu a hankali aka soma guda narda biki, nan aka bukaci amarya da ango su fito fili, hannu ya rike tare da janyota jikinsa suka sauka a hankali, Jiddah kam kunya duk ya isheta, DJ ya sake kida, nan ghali ya soma takawa jiddah kam tana tsaye ganin bata da niyar rawa, ya kama kugunta nan suka soma rawa, hall ne ya dauka da ihu, nan aka soma musu liki, feenat da Samar suka sauko, sai Marsal da Anwar, Sophia da Aslam sai kuma Nuceey da Aminu, abun sai wanda ya gani don sun matukar burgewa, sosai da sosai, liki kam sun sha, masoya sun taka sosai, sai 11:00 suka gama dinner, daga nan aka fito, ghali da jiddah suka nufi gdan su, kawaye aka mayar dasu gdajen su, gsky gidan jiddah ya tsaru bazan iya kwatanta muku ba, Abba sunyi kokari, bayan Angwaye sun rakasu suka musu Adu’ah da fatan Alkairi, bayan fitarsu ghali ya umarci Jiddah da tayi alwala, suyi sallah, dakinsa ya nufa, wanka tayi kafin ta daura Alwala ta fito batayi wani kwaliya ba tasaka dogon riga da hijab don yin Sallah, shima dai wankan yayi yasanya jallabiya, yasameta, bayan sun idar da sallah yama yan tambayoyi game da Addini ta bashi amsa, Adu’ah niman zaman lfy da zuri’ah ta gari ya musu, tana amsawa da Ameen, bayan sun gama ya dauko musu kaji da fresh milk jiddah taci tace aa yace ta karba taci taki, jalabiyarsa ya cire ya rage daga shi sai gajeren wando da best, duk kunya ta ishi jiddah, hannu yasa ya zare hijab dinta, ta sunkuyar da kanta, kasa yasa abakinsa ya yaga sai da ya dan tauna kafin ya matso kusa da ita ya janyota sai da ta kwata ajikinsa kafin yasa mata abaki kin budewa tayi shiko bakinsan yaringa turawa nata dole yasa ta karba, haka yayita mata sai da ya tabbatar ta koshi kafin shima ya ci bayan sun gama ya kwashe kayan ya kai kitchen, yana zuwa ya ganta inda ya barta, daukanta yayi zuwa kan gado wutar :idea:dakin ya kashe, a hankali ya soma rabata da kayan jukinta nan fa ta rike tasoma bashi hakuri cikin rada yake cemata haba my Jiddah meyasa kike son hanani abunda Allah ya halasta min ko so kike Mala’iku su tsine miki har wayewan gari, kai ta girgiza alamar aaa, rigar ya cire mata sannu a hankali ya rabata da jiddah sai boye jikinta take, wasani yasoma mata, wanda yasa jikinta mutuwa, nikam ganin abun yafi karfin gulmana yasa na ja musu kofa na fito sai da safe in leko BAZATA By ©Rash Kardam 29 Ghali bai saurara ma jiddah ba sai asuba, yau ya mayar da jiddah cikakiyar mace, Albarka kam yau tasha shi, roka roka sambatu kam ba’a magana don nikam na dauka ghali ya zautu ne tsaban Santi yau ghali harda kyautar gida Ma jiddah da asuba taimaka mata yayi ta gyara jikinta bayan yaje Masalaci yayi sallah ya dawo itama tayi nata kwanciya suka sakeyi sai goma suka farka lokacin an kawo musu breakfast, wanka sukayi kafin suka karya tayi kwaliyarta cikin atamfanta brown da ratsin silver colour tayi kyau sosai da yamma nuceey sukazo da Sophia nan sukayita sokanarta, hira sukayi sosai sai alokacin sophia ke ba ma jiddah lbr sun hade da Aslam fa Nuceey kuma da Aminu, jiddah tayi murna sosai, sai magriba, suka mata sallama don Nuceey washe gari zasu koma kaya ta hada musu sosai kafin suka tafi Jiddah sai da satiyi 2 weeks suna cin amarci kafin ghali ya dau hutu suka soma shirin komawa UK don ta karasa karatunta, sai da sukayi sallama masu Abba da gdansu ghali kafin suka dau hanya, ko da suka isa Uk rayuwansu mai dadi cike da kulawa sukayi satinaa biyu ya dawo 9ja. Nuceey kuwa soyayya tayi karfi tsakaninta da prof har iyaye sunshiga ciki. Haka sophia da Aslam bikinsu yanzu Saura 3 month soyayyan su suke sha sosai abun gwanin burgewa, Jiddah da kuwa ta kara kyau da kiba ga haske, ghali duk karshen wata tana kawo mata ziyara, kamar kulum yanda ya saba yau ma yazo hutun karshen wata, da murna ta tarbesa ta masa duk abunda tasa ba, abinci suke ci cikin kulawa da kaunar juna, Amai ne ya taso ma jidda da sauri tayi toilet, sosai tayi amai wanda ya galabaitar da ita, jikinta ba kwari ghali ne ya gyara gurin kafin ya kamota suka dawo daki ta canza mata kaya suka nufi asibiti, bayan yan gwaje2 da akayi likita ke shai da mu tana dauke da juna na wata3 murna gurin ghali da jiddah ba’a magana haka suka dawo gida yayi ta ririta ta, bayan yagama weekend dinsa zai koma yace ta kula da kanta sosai ga exams ya kusa, ta raka shi har Airport saidata ga jirginsu ya tashi ta dawo, haka sukayita karatu su batan wata daya suka soma rubuta final exams dinsu wata daya sukayi suka gama lokacin cikinta na 6 months, suna dawuwa 9ja suka soma bikin su Sophia da Nuceey haja akayi biki tana da ciki, ga cikin yayi girma2 duk wanda ya ganta sai yace jiddah kodai 2 zaki haifa kamar bacikin fari ba yayi gima sosai, sunyi biki lfy an kai sophia Abuja yayin da Nuceey aka kawota bauchi, haka rayuwa tayita tafiya, Feenat ta haifi yarta kyakyawa mai kama da ita, yarinyan taci Sunan Hameedah, Marsal kuwa namiji taifa aka sanya masa Dalhat yaran ga kyau haka rayuwa tayita tafiya. Yau Alhamis jiddah ta tashi da matsanacin ciwo mara, ghali duk ya rude, kasa mata komai yayi ya dauke ta sai asibiti, basu dade da zuwa ba Jiddah ta haifo yan biyuta mace da namiji, kan kace me asibiti yacika da yan uwa, da yamma aka sallamesu, haka sukayita shirin suna ghali yasai kaya kamar na hauka, ranan suna Saniya ya naka da rago yara sunci sunan Amatulhaleem da kuma Abdulhaleem, anyi shagali sosai, kowa ya watse haka rayuwa yaci gaba da wakana, cikin jin dadi da kulawa. Kwanaki sunja yanzu yaranta sunyi wayo sosai. BAZATA By ©Rash Kardam 30 7yrs later Haka rayuwa ta kasance musu cikin jin dadi Jiddah ce cikin motar ta sabuwa dal, tashi Asibitinta mai suna Haughal Clinic, gsky asibitun ya tsaru bazan iya bata lokaci gurin fada muku irin kyan dayi ba Asibiti ne na kudi amma ban gare biyu, akwai gurin fisabililah, gamarsa kaefi magani kyauta kaga likita kyauta, abun gwanin burgewa, office dinta tashiga taga marasa lfy ta ruta musu magani, kafin tafito ta nufi gidanta da ke ta bayan asibitin tun daga nesa zaka ga an rubuta HAUGHAL HOUSE da manyan harufa, sai kayi tafiya mai nisa akan kwalta din da ya malalu kafin ka iso gate din gidan, horn tayi mai gadi ya bude, nan AmatulRasheed da AbdulRasheed yan shekara 4 suka fito da murnasu suna mata oyoyo, Amatulhaleem da Abudulhaleem suka fito suma rike da hannu Nana Safiyya yar auta suka mata Wlc, falo suka dun guma, nan Dr ghali ya fito shima, yace madam ya hanya ya aiki tace Alhamdulilah, a shagwabe tace Abban su, na gaji tausa ni zakamin, yace zan miki da sharadin cikin kaguwa tace ina jinka yace kin amince in karo…… Murmushi tayi ka karo mai hhhhh a sai dai yar rainon yara don ghali na jiddah ne ita kadai har abada. ********************** ⬇ ************************** ********** Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** Alhamdulilah anan nakawo karshen littafina mai suna BAZATA. SADAUKARWA na sadaukar da littafin nan ga Sister kuma yar’uwa na, Hauwa’u da Mijinta Ghali Haughal . Allah ya bar mutare da so da kauna KUNA RAINA Sadiya Abdullahi Nusaiba Mustapha(Nuceey Aisha S Mazoji Furtuhatu khair Deeja Abdullahi Fateema Fanta Autar Hajiya Zee Hauwa’s Maryam Salis(Marsala Safeenat S Bello( feenat Sophia Kakus Habiba ina kaunarki Pinky Lady Hauwa’u Aisha S A. Da saurasu bazan samu daman lissafa sauran ba, kuyi hakuri kuna rauna masoya na abun kaunata ina tsananin sonsu da kaunarku Allah ya barmu tare ya bar so da yarda. JINJINA GA YAN GROUPS DINA Zaujin Nuhr Rash Kardam Hausa Novels Marmue Home Of Novels Duniyar littafi Hausa Novels Hausa Novel Group World Writers Association Ladies Vision Ladies Novels World Khaleesat Haiydar Novels, Facebook Ina gaida ku masoya na Facebook Da duk wasu group din da na sissafa sai mun hadu a safin littafina masu suna YAR AMANA Da MARAINIYA Ta ku a kullum mai kaunarku ®WWA® Rashida A Kardam