💥💥💥💥💥💥 *_'YAR GADARA_* 💥💥💥💥💥💥 *_NA_* *_MAIMOUNATH O.G_* _(Mahnoor)_ _Wattpad@maimounathog_ *💫DA BAZAR-MU WRITER'S ASS💫* _*~We are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are d best among all....DA BAZARMU MUKE TUN'KAHO.~*_ *_Ya Allah da sunan ka na fara wannan rubutu, ka yarje min in gama shi lafiya, Allah ka bani ikon rubuta dai-dai._* *_Wannan novel din so daya tak zai rika zuwa muku a sati saboda abubuwa sunyi yawa bani da lokaci sosai, masu cewa ina musu yanga da Jan rai akan novel sam ba haka bane ku fahimce ni please_* *************************⬇********************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** *Page 1/5* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.* Zaune take a falon gidan su ta hak'imce kamar wata sarauniya, sanye take da wani matériel pink color mai shegen kyau da tsada duk da a zaune take na gane d'inkin riga da skirt ne sun kama jikinta sosai. Wayar ta k'irar IPhone7 a hannunta tana ta faman dannawa ga kayan sha da na ci a gaban ta bisa table. Tana cikin danna wayar ne ta d'aga murya ta doka kira da cewa'' Atika! Ke Atika kina ina ne?" Yarinyar da aka kira da Atika ta fito daga wani d'aki da gudu tazo ta durk'usa gabanta tace'' gani anty''. Ba tare da ta d'ago ba tace'' ai na ganki ko ni makauniya ce? Ba nace banson in kira mutum so biyu ba? Me kikeyi ne ina ta kira baki amsa ba?" Cikin rawar murya Atika tace'' anty kiyi hak'uri wallahi ban ji kiran na farko ba''. Wannan karon d'agowa tayi ta kalle ta tace'' tashi kije kice ma Idi driver ya wanke min motar nan red color da ita zan fita kice yayi sauri banson b'ata lokaci''. Atika da batayi school ba ina tasan wani red color sai ta tsaya inda-inda tanason ta tambayeta tana tsoron masifar ta. Ganin har yanzu bata tafi ba ta daka mata tsawa da cewa'' Keee!!! Me kike jira kinyi min tsaye a kai?" '' Anty kiyi hak'uri menene rod colo? ban sanshi ba bane". Cewar Atika. Harare ta maka mata tace'' matsalar ku kenan 'yan k'auyen nan komai baku sani ne sai duhun jahilci cike da kai, cewa nayi kice ya wanke min jar mota ta shikenan sai ki fice ki bani wuri banza kawai''. Kalmar jahila yayi ma Atika ciwo amma ba yanda zatayi in da sabo sun saba da masifar ta tun ba yanzu ba. Ficewa tayi taje ta isar da sak'on sannan ta dawo. Zata shige ta sake kiran ta tace mata'' idan kin shiga ki kira min Laure''. Ta amsa mata da'' to''. Sai ta shige ciki tana mai mamakin hali irin na wannan yarinyar duk da dai ta girme ta. Laure ce ta iso inda take tace'' anty gani''. Itama d'in ba tare da ta kalle ta ba tace'' kije ki gyara min d'aki ki fito da kayan wanki ki kai ma mai wanki''. Laure tace'' to anty''. Haka tayi ta kiran 'yan aikin gidan su tana basu umarni suna aiwatarwa cikin gaggawa saboda sun san halin ta bata ragawa kowa. Wata mata ce ta sauko daga stairs ta tako a hankali har inda take zaune ta zauna gami da cewa'' yanzu ke FARHANAH irin wannan rayuwar da kika d'aukar wa kanki tayi dai-dai kenan a ganinki?" Sai a lokacin ta d'ago ta shagwab'e fuska tace'' kai mom me nayi kuma dan Allah?" Hararen ta mom tayi tace'' ban sani, ina jinki kina ta saka yaran nan aiki, shikenan kin dawo basu da hutu ko? Kuma banson yanda kike tafiyar da rayuwar ki komai a gadaran ce kowa bai isa ba a wajen ki, wallahi ki kiyaye duniya ce karki ga dukiyar da Allah ya bamu kice zakiyi amfani da ita ki rink'a wulak'anta mutane nidai ba haka nake ba bansan a ina kika samo wannan halin ba, dan ko shi daddyn ki da ya tara dukiyar ba haka yake huld'a da jama'a ba''. Matsowa tayi ta kwanta akan cinyar mom tace'' humm mom kenan nifa banga abinda nakeyi ba, kawai dai ina nuna musu matsayina da nasu ba d'aya ne ba shikenan fa''. '' Hmmm kedai ki kiyaye dan gidan wani zaki duk kud'in ki shi zai juya ki yanda yakeso''. Tashi tayi zaune tace'' mom kamar ni wani zai juya ni? Tabd'ijam, mom ni kinga a bar wannan maganar ma fita zanyi akwai wasu takardu da zan amso wajen Haulat kinsan monday mai zuwa zan fara zuwa aiki''. Mom tace'' ok to, amma ke da driver zaku je ko? Dan kinsan daddyn ki bai son kina driving da kanki''. 'Bata rai tayi tace'' mom wane driver kuma, wai ni ba za'a barni in sha iska kad'an ba gaskiya ni kad'ai zanje mutum da motar shi ace sai wani driver zai kai shi''. Tana gama fad'in haka ta mik'e tsaye ta k'wala ma Laure kira ta fito da gudu tazo tace'' gani anty''. FARHANAH tace'' yi sauri ki d'auko min handbag d'ina a d'aki ki kai min wajen mota ina jiran ki kuma saura ki tsaya shiririta in ci mutuncin ki''. Da sauri Laure taje ta haura sama dan d'auko mata jakar ta, mom kuma ta rasa bakin magana saboda hali irin na 'yar ta. FARHANAH tazo tayi ma mom kiss a kunci tace'' mom sai na dawo ko bye.....''. Ficewa tayi bata jira abinda mom zata ce ba. Ganinta yasa duk 'yan aikin gidan su mazan suke wani durk'usa mata suna gaishe ta kai kace sunga wani sarki. Hmm Allah ya kyauta. Driving take cikin nutsuwa dan duk iskancin ta bata ganganci a mota. Glass d'un motar ma bak'i ne ba'a ga na ciki a haka har ta isa k'ofar gidan su k'awar ta Haulat da yake tasan da zuwan ta tana isawa aka bud'e mata get ta shiga dan suma su Haulat d'in masu kud'in ne shiyasa ma har FARHANAH ta iya k'awance da ita. Sun d'an tab'a hira tace zata koma gida Haulat tace'' haba k'awata daga zuwan ki zakice wani tafiya zakiyi?" '' Ke wallahi inason in biya ta super market ne inyi shopping kafin daddy ya dawo kinsan yana gari kuma bai son ina driving da kaina yanzu ma sai da mom tayi min na fito''. Haulat tace'' ok to shikenan gashi mom bata dawo daga asibiti ba ai da kun gaisa''. '' No! Karki damu ai muna tare tunda na dawo k'asar next time mun gaisa ki gaishe min dasu duka har da abba ma''. Haulat tace'' to ba damuwa zasu ji insha Allah sai munyi waya kenan?" '' Ok ! Bye''. A haka sukayi sallama ta shige motar ta mai gadi ya bud'e mata gate ta fice. A bakin wani k'aton super market tayi parking gami da fitowa tana taku d'ai-d'ai duk hankalin mutane ya koma wajen ta ita kuma ko a jikinta dan wani b'akin eyes glass ne manne a idanun ta cike da yauk'i ta shige ciki tayo siyaryarta sannan ta fice. Tana tafe tana addu'ar Allah yasa daddyn ta bai dawo gidan ba. Tayi sa'a kuwa bai dawo d'in ba tana parking ta fito daga cikin motar ta kira Idi driver yazo da gudu yana cewa'' gani ranki ya dad'e''. Fuska ta yamutsa ta zuge zik d'in handbag d'in ta ta ciro kud'i ba tare da ta k'irga ba ta jefa mishi suka watse ya tattare su da sauri yace'' ranki ya dad'e me za'a siyo miki?" FARHANAH tace'' ka bud'e kunnuwanka da kyau ka saurare ni dan ban nanata magana''. Idi yace'' to ranki ya dad'e''. Tace'' kud'in nan da na baka nasan kanada buk'atar su dan jikin ka ma ya nuna hakan, inaso idan daddy na ya dawo in ya tambaye ka cewa tare muka fita kace mishi eh shine dalilin da yasa na baka kud'in nan dan baka isa in nemi alfarma a wajen ka ba kana jina ko?" Idi kad'a kai yayi tare da cewa'' naji ranki ya dad'e insha Allah zanyi yanda kika ce''. FARHANAH tace'' good! Da ka kyauta wa kanka, akwai kaya a motar ka shigar min dasu ciki''. Tana fad'in haka tayi tafiyar ta inda ta bar Idi a tsaye yana mai kallon ta. Ita dai wannan yarinyar har abada ba zata canza ba, Allah ya shirye ki ki gane cewa talaka ma mutum ne. Idi driver ne ke wannan maganar shi kad'ai amma fa a zuciyar shi. Nima kaina anty o.g ina yi mata fatan shiriya. ~~~~~~~~~~~~~~~~~~ Bayan wasu kwanaki FARHANAH ta fara zuwa wurin aiki a matsayin ta na Barrister, wulak'anci kuwa sai abinda ya k'aru bare ma yanzu ta samu daddyn ta ya yarda ta fara driving da kanta yanzu tana jinta wata mai 'yanci tunda ko a gabanshi zata iya ficewa da motar. 'Yan aikin gidan su ma sun d'an samu sauk'in fitinar ta dan a can take wuni sai 5pm na yamma take dawowa. A kwana a tashi har akayi wata biyu da zuwan FARHANAH k'asar. Wata ranar saturday da yamma ta fita dan zuwa wurin shan iska wanda daman takan je week-end zuwa week-end idan bata komai a gida. Tazo shiga cikin wurin sai wata bak'ar mota tasha gabanta ta rigayeta shigewa kuma inda take parking motar ta nan akayi parking. A hankali ta furta'' kan uba yau ko wacece wannan sai na nuna mata kuskuren ta, kamar ni za'a shigewa gaba? tabd'ijam''. Dan neman fitina kusa da motar taje tayi parking itama kafin ta fito taga wasu k'arti sun fito daga cikin motar fuskar nan tasu murtuk ba alamun wasa. Bataji komai a zuciyar ta ba ta bud'e ta fito a dai-dai lokacin d'ayan ya bud'e bayan motar nan da alama shine mamallakin motar. A hankali ya ziro k'afar shi waje cikin nutsuwa ya fito wai wai wai ta yaya zan fasalta muku kyawun wannan mutumen, domin kuwa abin da rud'ani. Dogo ne fari santalele bakin shi zagaye yake da gashi wanda yasha gyara haka kanshi ma gashi ne lub-lub a kwance idan ka ganshi sai ka zata balarabe ne, idanun shi manne yake da bak'in glass shaddar jikinshi kuwa mai shegen tsada da kyau maroon color tasha aiki sosai an kashe kud'i a wurin nan. Ai kuwa FARHANAH tana arba dashi ta cire glass d'in ta ganin wannan mutumen ba k'aramin mamaki ya bata ba.......... *Mu had'u next page dan jin waye wannan wanda har FARHANAH ta rikice ko in ce tayi mamakin ganin shi?* *_'YAR MUTAN KAZAY CE👑_* 💥💥💥💥💥 *_'YAR GADARA_* 💥💥💥💥💥 *_NA_* *_MAIMOUNATH O.G_* _(Mahnoor)_ _Wattpad@maimounathog_ *💫DA BAZAR-MU WRITER'S ASS💫* _*~We are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are d best among all....DA BAZARMU MUKE TUN'KAHO.~*_ *Page 6/10* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.* Tabbas shine dan ba zata tab'a mantawa da wannan fuskar ba. Bari mu d'an koma baya muji meye tsakanin FARHANAH da wannan mutumen? *WAIWAYE* FARHANAH sun had'u da wani a cikin jirgi ranar da zata dawo daga Cairo inda sukayi rigima akan wajen zama. Bayan sun shiga jirgi ne ta rigaye shi zama shine yazo daga baya yace'' malama tashi bani wuri nan nakeson in zauna''. Cikin kallon baka isa ba FARHANAH ta kalle shi tace'' what? Baka isa ba''. '' Ke ni kike cewa ban isa ba? Kinsan ko ni waye?" Kai tsaye ta bashi amsa da cewa'' kai banza mana''. Ya harzuk'a zai kai mata mari aka shiga tsakanin su ya nuna ta da d'an yatsa yace'' wallahi ko ke 'yar gidan uban waye sai na d'auki mataki a kanki bari mu sauka''. Itama FARHANAH tace'' hmm kai d'in d'an gidan uban waye da har kake jin zaka iya min wani abu? Baki isa komai ba a wajena banza d'an talakawa''. Kan uban can kayyah to wannan kalmar ta d'an talakawa ta k'ara harzuk'a shi har yana cewa a k'yaleshi ya nuna yarinyar nan ko shi waye, sai ya koya mata hankali. FARHANAH ko a jikinta dan wayar ta ma ta shiga dannawa bata sake kallon inda yake ba. Abin tak'aicin da suka sauka a filin jirgin Kaduna ya nemi FARHANAH ya rasa haka driver ya d'auke shi suka tafi gida. Kunji abinda ya had'a su to gashi yau sun had'e ya kenan? *CIGABAN LABARIN...* Takowa yayi har inda take ita kuma ta jingina da motar ta dan ya matso sosai kusa da ita har tanajin fitar numfashin shi cikin muryar shi mai kama da rad'a yace'' marar kunya meyasa ranar nan kika gudu? Yanzu gashi mun had'u zan iya karairaya ki insa a kaiki bola na karya banza kuma ko kina musu?" Dan ta raina mishi hankali sai ta ture shi tace'' kai malam kai kuma waye? Kai wane irin d'an iska ne?" Jin abinda tace yasa k'artin nan sukayo kansu da ido ya musu magana sai taga sun bar wajen. 'Kara matsowa yayi kusa da ita ya sassauta murya yace'' ai kin fini iya iskanci tunda har zaki iya barin k'asar ki kije wani wajen, sauran maza kawai''. Hannu ta d'aga dan kai mishi mari ya rik'e hannun gam yayi murmushi yace'' har yanzu ba'ayi wata mace da ta isa ta mareni ba musamman irin ki jibeki k'azama dake na rasa waye uban ki a k'asar nan da har kike jin kanki haka''. '' Sake min hannu malam banson iskanci wallahi, ai da gani na ba sai na fad'a maka ko waye ubana ba kai ma kasan nafi k'arfi d'an talakawa irin ka kuma banson in k'ara ganin mai kama da kai ma bare kuma kai mai mummunar fuskar nan''. Sakin hannun ta yayi yana dariya dan yasan ta fad'a dai ne amma yafi k'arfin a kira shi da mummuna. Kallon ta ya tsaya yi sai ta kauce ta shiga motar ta dan ji tayi ba zata iya zama a nan ba gaba d'aya wannan d'an iskan ya b'ata mata rai. Kusan take mishi k'afa tayi ta fice daga wajen shi kuma girgiza kai yayi yace'' yarinya sai GADARA da girman kai na rasa me ta taka har haka, amma zanyi bincike''. Kiran abokan tafiyar tashi yayi yace su tafi kawai shima ya fasa zaman shan iskar. FARHANAH isar ta gida ke da wuya ta shige d'akin ta ta fad'a kan gadon ta sai kuka, mutumen nan yayi matuk'ar b'ata mata rai har ita zai ce ma sauran maza, me yake nufi kenan? Karuwa ya d'auke ta ko me? Waye shi? Waye uban shi a k'asar nan da har yake gaya mata maganganu son ranshi, dole ne tasan abinyi sai ta bincika tasan ko d'an uban waye. Haka tayi ta maganganu ita kad'ai tana kuka sosai wanda rabon tayi kuka irin wannan har ta manta. Bayan isha'i tana kwance har yanzu kan gadon, Atika ce ta shigo tare da yin sallama da k'yar ta amsa mata. 'Karasowa tayi bakin gadon ta tsugunna tace'' anty inji hajiya tace ki fito an shirya abinci''. Shiru bata amsa mata ba sai da ta sake magana ne FARHANAH ta daka mata tsawa tace'' tashi ki fice min a d'aki tun kafin in b'ata miki''. Atika da ta tsorata da yanayin ta ta tashi sum-sum ta fice. Zuwa tayi ta sanar ma da hajiya cewar korota ma tayi. Hajiya da kanta taje d'akin ta iske ta. Zama tayi a bakin gadon tace'' lafiya kike kuwa? Atika tace min kin koreta me yake faruwa?" Wani kukan ne yazo mata, hajiya tayi mamaki matuk'a wai yau FARHANAH ce ke kuka lallai akwai babban al'amari. Jayota tayi jikinta tace'' subhanallahi daughter me ya sameki ne haka? Nasan ba k'aramin abu ne zai saka ki kuka ba''. Cikin kuka tace'' mom shine, wallahi shine''. '' Shi wa?" mom ta tambaya. '' Mom wannan da mukayi fad'a a cikin jirgi har na gaya miki ma a lokacin da nazo ai''. '' To abinda ya wuce ne kika tuna ya saki kuka ko me?" '' A,a mom yau na k'ara had'uwa dashi yayi ta gaya min bak'ak'en maganganu har da cewa wai ni sauran maza ce''. Tana kaiwa nan ta fashe da wani irin kuka mai cin zuciya. Ta sake cewa'' mom wannan kalmar tafi kowace magana muni da kuma zafi a gareni, wallahi sai na d'auki mataki a kanshi''. Mom rarrashin ta ta shiga yi tace'' a,a karki fara ma, shi fa namiji ne, me ya kaiki fad'a da shi ma, kar inji kin sake cewa haka, kema fa nasan halin ki maybe wata maganar kika gaya mishi''. '' Mom babu abinda na gaya mishi kawai d'an iska ne''. '' Uhm hmm ba ga irin ta nan ba, nasan ba a banza ba wallahi, tashi ki wanke fuskar ki muje muci abinci''. Ta kalli mom da jajayen idanun ta tace'' daddy fa?" '' Daddyn ki ya kira ni yace bazai samu zuwa yanzu ba yanada wani taro da zasuyi''. Tashi tayi ta wuce toilet. **** **** **** Bayan wasu watanni, kwatsam daddyn FARHANAH yazo musu da wata magana wacce ta firgita FARHANAH matuk'a. Maganar itace zai bada auren ta ga d'an sarkin garin nan kusan sumewa ma tayi jin maganar a bazata. Mom ta kalleshi tace'' to amma dear wane irin abu ne haka? Aure fa kace? Auren dole zakayi mata ne?" Girgiza kai yayi yace'' ko d'aya, ba haka bane kinsan dai yanda muke da sarki Jafar ko? Bazan iya hana mishi abinda ya tambayeni ba wato auren FARHANAH, da kanshi ya nemi alfarmar nan kuma bazan tab'a hana mishi ba''. FARHANAH ta k'ara rushewa da kuka tana cewa'' shikenan daddy ka daina sona tunda zakai min auren dole, nidai banso mutumen da ban tab'a gani ba zan aura''. Daddy ya kalle ta yace'' look daughter, kinsan dai bazan so b'acin ranki ba, amma sarki yafi k'arfin komai a wajena matuk'ar abin bai fi k'arfina ba ko a ina yake zan nemo in bashi bare ke da na haifa da cikina''. '' Allah d'aya daddy kawai baka sona yanzu''. '' Ki kalli gidan nan da kyau, kinsan dai nafi k'arfin ace saboda wani abu yasa zan bayar dake ga d'an sarkin garin nan ke kinsan haka, nan babu yanda banyi dake ba akan ki fito da miji tunda ke ba yarinya bace shekara ashirin da hud'u(24) ba nan bane so kike a fara zagina ko? To na gama magana ku zauna cikin shiri dan auren bazai wuce nan da sati biyu ba''. FARHANAH fad'uwa tayi nan sumammiya......... *_Toh fa readers su FARHANAH girman kai zai k'aru kenan, har da su suma kuma? Kuzo ceton rai readers hhhhh........_* *_'YAR MUTAN KAZAY CE👑_* 💥💥💥💥💥 *_'YAR GADARA_* 💥💥💥💥💥 *_NA_* *_MAIMOUNATH O.G_* _(Mahnoor)_ _Wattpad@maimounathog_ *💫DA BAZAR-MU WRITER'S ASS💫* _*~We are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are d best among all....DA BAZARMU MUKE TUN'KAHO.~*_ *ASSALAMU ALAIKUM 'YAN UWA INA BARAR ADDU'AR KU MAHAIFI NA YANA CIKIN HATSARI DOMIN HARIN DA 'YAN FASHI SUKA KAI MUSU😭 ALLAH YA SHIGA TSAKANIN NAGARI DA MUGU😭😭🙏* *SA'KON TA'AZIYYA ZUWA GAREKI 'YAR UWAR MU LEEMA NA RASHIN MATAR YAYAN KI ALLAH YAJI KANTA DA RAHAMA YASA ALJANNAH CE MAKOMAR TA, ALLAH YA RAYA ABINDA TA BARI😭🙏* *Banyi niyyar yin typing ba, wallahi sweet smasher ko dan ke kawai zanyi irin wannan comments da kika sambad'o🥰fan's SMASHER dai ita 'yar wajen FARHANAH ce dan k'awance suka k'ulla🤪Ina yinki sweetheart Allah ya bar zumunci😍🤝* *🤔Wai me FARHANAH tayi muku ne haka kowa bai son ta☹irin wannan bakin jini dole a samo mafita. FARHANAH tace wai yanzu ta fara baku ga komai ba ma.....* *Ya ubangiji ka ba antyn mu lafiya(ANTY MEELAT-JAMILA MUSA) Allah ya kare mana ke antyn mu😘 Allah ya kara miki lafiya da sauran marasa lafiya baki d'aya😢😖🙏🙏* *Page 11/15* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.* Mom ta nufi inda take tana kiran'' innalillahi me yayi zafi haka, alhaji dan Allah ka dawo''. Jin abinda mom ta fad'a ne yasa daddy dawowa baya da sauri ya k'araso inda suke yace'' subhanallahi! Bari in kira doctor Shareef yazo ya dubata''. Mom tace'' ai ciwon ta ba na asibiti bane, maganar auren nan ce kawai ta saka ta cikin wannan halin''. '' Yanzu dai duk abar wannan maganar samo ruwa ki yayyafa mata kafin doctor yazo''. Cewar daddy. Atika mom ta kira ta kawo mata ruwa nan aka shafa mata ruwan a fuska ta farfad'o amma cikin. Atika tace'' sannu anty Allah ya baki lafiya''. Hararen ta FARHANAH tayi tace'' fice min da gani magulmaciyar banza me ya kawo ki nan''. Da sauri Atika ta bar wajen dan tasan halin ta yanzu zata zagi iyayenta ma ita kuma abinda tafi tsana a duk abubuwan da FARHANAH take yi musu, sai tayi ta zagin su uwa uba. Mom ta taimaka mata suka haura saman bene ta rakata d'akin ta kafin doctor yazo. Daddy sai safa da marwa yake yana tubka yana warwara dan a gaskiya bai jin zai iya fasa bada ita ga d'an sarki. Doctor ne ya shigo da sallama bayan sun gaisa suka rangaya wajen FARHANAH. da farko zaune take jin alamar za'a shigo yasa ta kwanta lub tamkar mai ciwon mutuwa ita nan wai ciwo takeyi. Daddy ne ya k'araso bakin gadon nata yace'' daughter tashi ga doctor yazo zai dubaki''. 'Kara narkewa tayi daddy ya kalli mom yace'' hajiya mu bashi wuri yayi aikin shi''. Ta amsa da'' to shikenan''. Suna ficewa ba jimawa ta tashi zaune tace'' kaje ka rufe k'ofar inason zamuyi magana da kai''. Mamaki ne ya kama doctor Shareef wai ko dai daman ciwon k'arya ne? Tunda gashi ta tashi zaune ras kamar ba marar lafiya ba. Bai musa mata ba yaje ya rufe ya dawo yace'' ki gaya min meye matsalar ki in dubaki inada patients a asibiti na baro''. Kallon shi tayi a yatsine sannan ta jayo handbag d'in ta dake kan bedside ta ciro damen kud'i ta mik'a mishi. Ba tare da ya karb'a ba yace'' na menene wannan?" FARHANAH tace'' kud'i ne inaso kace ma su daddy na zuciyata dab take da bugawa matuk'ar aka takura ni kan abinda banso, shi kad'ai nake buk'ata a gareka''. Doctor cike da mamakin ta yace'' wai kinada hankali kuwa? Kinsan me kike cewa?" FARHANAH tace'' kaga da hankali na, daddy yake so yayi min auren dole dan haka nakeson ka gaya mishi haka nasan zai fasa, shiyasa na baka kud'i dan nasan ba zaka k'i kud'i irin wannan ba kasan ni ban rok'on mutum ko neman alfarma, kud'i kawai zan bada ayi min abinda nakeso dan haka karka cuci kanka doctor ka karb'a''. Yaji haushin kalaman ta matuk'a lallai zai nuna ma yarinyar nan ba komai ne kud'i ke bayarwa ba. Kallon ta yayi yace'' wallahi badan nine family doctor naku ba da ko sauraren wannan shirmen naki bazanyi ba, ki kalleni da kyau nayi miki kama da mai yunwar kud'i? Kinga tafiyata kin b'ata min time a banza''. Tana kallon shi ya tattare kayan aikin shi ya fice har yakai bakin k'ofa ya juyo yace'' ba komai ne dukiya ke bayarwa ba, ina miki fatan shiriya daga wannan d'abi'ar taki''. Yasa kai ya fice FARHANAH ta cike leb'e lallai wannan anyi mahaukaci wa zai ga kud'i ya bari? Yanzu meye mafita? Ya zanyi da wannan auren da akeson yi min? Waye ma shi wanda akeso in aura? Wai shi yarima ko? To bai isa in zauna dashi ba. Haka tayi ta sambatun ta tana neman mafita a k'arshe dai ta kira k'awarta Haulat tace'' k'awata ina cikin matsala babba dan Allah meye mafita?" Daga d'aya b'angaren Haulat tace'' subhanallahi! Meke faruwa ne k'awata? Fad'a min''. Nan FARHANAH ta zayyane mata komai game da auren da daddy yakeso yayi mata da d'an sarki. Maimakon taji Haulat cikin damuwa sai taji tace'' wow!!! Gaskiya k'awata na tayaki murna sosai''. Cikin fushi FARHANAH tace'' dakata!! Me kike nufi da kin tayani murna? Auren dole fa daddy zaiyi min kike wannan banzar maganar''. '' Haba ke kuwa aure ai abin so ne bare ma yanda shekarun mu ke tafiya kuma yarima fa zaki aure ma'ana mai jiran gado, kai gaskiya zamu sha biki an saka ranar ne ko kuwa?" Haushi yasa FARHANAH ta kashe wayar ta tana buga uban tsaki gami da fad'awa kan gado ita wai ya zatayi ne? Waye zai fahimce ta? Ita fa sam aure ne ma bai gabanta shiyasa bata tab'a ma yin wata soyayya ba da yake ta raina kowa a ganinta duk basu isa ta aure su ba. Haulat dai dariya tayi bayan FARHANAH ta kashe wayar, ita kanta wasu lokutan mamakin k'awarta ta takeyi ayi mutum da tsatstsauran ra'ayi da son girma. Duk da Haulat k'awarta ce amma sam halin su ba d'aya ba tunda Haulat bata raina mutum ko ya yake bare 'yan aikin gidan su har hira suke zama suyi idan FARHANAH taga haka sai tace mata ki zauna kina hira dasu sai kace matsayin ku d'aya. Ita kuma Haulat tace mata ai duk daya muke a wajen Allah babu da abinda na fisu. Sai dai tayi k'wafa ta shiga wani abin daban. **** **** **** Zaune yake a wani katafaran falo mai shegen kyau iya had'uwa ya had'u, kujerun falon kad'ai sun isa abin kallo da gani an kashe kud'i a nan falon kad'ai kenan ina ga sauran wajen. Kai zan so inje inyi tsegumi fa. Wata mata na gani tana saukowa daga bene a hankali take takawa da ganinta kaga cikar kamala ga nutsuwa a tare da ita dan yanayin yanda take takawa kad'ai zai sa ka fahimci hakan. 'Karasowa tayi ta zauna kan kujera ya zamo yazo kusa da ita ya zauna kan kace me tuni an cika gaban su da kayan marmari. Sauran suka fita wasun su suka zauna matar nan ta kalle su tace'' ku bamu wuri zamuyi magana''. Nan suka fara cewa'' an gama ranki ya dade a tashi lafiya, godiya muke''. Ficewa sukayi inda ta maido kallon ta wajen shi tace'' abba na ya akai ne na ganka da yammar nan?" Shagwab'e fuska yayi yace'' mummy wai me naji sarki yana fad'a ne?'' Murmushi irin na manya tayi tace'' hmmm daman saboda wannan ne kazo? To aure za'ayi maka yace dan tuni an samo maka matar ma tunda ka tsaya ruwan ido''. Tsura mata ido yayi har sai da ta gama yace'' wai kamar ni za'ayi ma wani aure? Haba dan Allah ku canza shawara gaskiya bazan auri yarinyar da ban tab'a gani ba''. '' Ai kuwa aikin gama ya gama dan tuni an gama komai nan da sati biyu ka zama ango''. Yarima yace'' dan Allah mummy ki daina wannan maganar, ni ban tashi aure ba''. Kallon tayi tace'' a hakan? So kake sai ka tsufa mata sun ce basu sonka ko?" '' Ah haba mummy ki daina wannan maganar ba, ai nafi k'arfin nan''. Inji yarima *SYDEEK*. Komai mummy bata k'ara ce masa ba ya k'ari magiyar sa akan a fasa auren shi bazai auri yarinyar da bai tab'a gani ba, amma mummyn shi tayi burus dashi. Tashi tsaye yayi ya fice cikin fushi a zuciyarshi yace wallahi duk yarinyar da tayi garajen zuwa gidan nan sai tayi dana sani......... *Sai nan gaba zakuji ko waye YARIMA SYDEEK insha Allah☝* *Tabd'ijam lallai akwai sha'ani nan gaba* *Allah yasa mu fara azumi a sa'a ya karb'i ibadun mu🙏* *_'YAR MUTAN KAZAY CE👑_* 💥💥💥💥💥 *_'YAR GADARA_* 💥💥💥💥💥 *_NA_* *_MAIMOUNATH O.G_* _(Mahnoor)_ _Wattpad@maimounathog_ *💫DA BAZAR-MU WRITER'S ASS💫* *_~We are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are d best among all....DA BAZAR-MU MUKE TUN'KAHO~_* *_INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN😭 KULLU NAFSUN ZA'IKATIL MAUT, DUKKAN RAI SAI YA 'DAN'DANI MUTUWA, SAK'ON GAISUWA GAREKI 'YAR UWA HABIBA IDRIS(Hubbeey) NA RASUWAR KAKAR MÛ ALLAH YAJI KANTA DA RAHAMA YASA ALJANNAH CE MAKOMARTA😭🤲 NI DA 'YAN GROUP HA'DIN KAI MUNA MIK'O TA'AZIYYAR MU GAREKI👏🏻_* *_Ikon Allah wai na kwance ya fad'i🤔 hummm shiru ma magana ce🤐_* *_Kuma kuramen group ina kallon ku aradu duk zanyi maganin ku_* *Page 16/20* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Yarima *SYDEEK* har ya isa part d'in shi ranshi a b'ace kawai yake yana tunanin wai me yayi wa mai martaba ne haka da har yake neman yi mishi auren dole. Haka ya k'ari sak'a da warwarar shi amma ba mafita dan yasan idan mai martaba yayi magana to babu wanda ya isa ya sa shi canza ta. Ya shiga damuwa matuk'a dan shi fa bai wani tashi yin aure ba, to meye ma ake son sai dole yayi aure shi da ba wani mace ba haka kawai a saka mutum a damuwa. Hummm mû dai muna gefe muna jiran caskalewa hhhh. *_WANENE YARIMA SYDEEK?_* Yarima *SYDEEK* kamar yanda kuka ji sunan d'a ne ga sarkin garin wato sarki Jafar sarki mai adalci. *SYDEEK* tun yana k'arami aka kai shi k'asar sudan acan yayi karatun shi na boko da islamiyya, ya zamto yaro mai hazak'a tun yana yaro. Sarki yana ji da d'an nashi sakamakon shi kad'ai ne Allah ya bar musu dan bayan SYDEEK yara biyu matar shi ta haifa amma Allah bai yi zasu rayu tare ba. Sunan mahaifiyar SYDEEK Hajiya Saudat, ta kasance mace mai hak'uri da kawaici saboda ta gamu da fitintinu da dama a wajen kishiyar ta tun kafin sarki ya hau gadon mulki. Sarki ya rabu da ita ne sakamakon kama ta da akayi zata saka ma mahaifiyar SYDEEK magani a abinci dan taci ta mutu shine sanadiyyar rabuwar su. Sarki bai yadda da duk wani abu da zai b'ata ran matarshi ba dan tana tare da shi tun kafin ya zama sarki. *SYDEEK* ya kasance yaro d'an k'walisa dogo ne santalele masha Allah, fari ne mai k'yan fasali tamkar balarabe yake. Gashin kanshi bak'i k'irin mai santsi lub-lub a kwance a kanshi, hancin shi dogo ne, d'an bakin shi zagaye yake da sagen da kullum ake kan gyara shi. Akwai wani hutu da yazo Nigeria 'yan mata sukayi caaa a kanshi kowacce tana nuna mishi so, wasu cousin d'in shi ne ma wata har gidan tazo a sunan tazo yi musu kwana biyu, ita 'yar k'anwar maman shi ce. Duk abinda sukeyi a banza dan ko kallo basu ishe shi ba. SYDEEK irin mutanen nan ne masu wani irin ra'ayi. Yana da abokai wa'yanda suka had'u a can Soudan duk da ba wani shiga harkar mutane yakeyi ba amma su d'in yakan kulasu. Zan iya cewa shekarun SYDEEK bazasu haura 30 ba. Yanzu dai ya dawo gida gabaki d'aya tare da takardar shaidar zama k'wararren doctor na fannin mata wato gynéco. Yanzu dai SYDEEK zaune yake sakamakon likitar shi da ake kan ginin ta shine mai martaba yakeso kafin ya fara aiki ya zamto anyi mishi aure dan cikar kamalar mutum shine aure. Mace kike ko namiji kuyi sani cewa aure shine kan gaba dan haka duk wanda bai da shi ubangiji ya kawo lokacin. *_CIGABAN LABARIN...._* FARHANAH tun lokacin da daddyn ta yace da ita aure ita da yarima ba fashi shikenan sai rashin mutuncin ta ya k'aru kan 'yan aikin gidan sai kace suke da laifin. Kwance take kan gadon ta duk tunani ya baibaye ta ji takeyi kamar ta gudu ta bar k'asar in yaso sai taga wacce zasu yi ma auren dolen. Saurin yak'ice wannan tunanin tayi dan gaskiya duk k'in ta da auren ba zata iya guje ma iyayen ta bare ma yanda suke matuk'ar sonta da k'aunar ta. Juye-juye kawai take akan gadon sai ga Atika ta shigo tare da yin sallama. Bata amsa mata ba kuma sarai taji ta. Itama Atika tasan ba zata samu amsar ba dan sun san halin ta. Atika zuwa tayi bakin gadon tace'' anty ina wuni? Kina buk'atar wani abin ne a kawo miki?" Nan ma shiru taji ba amsa, Atika da nacin magana sai ta sake tambayar ta amma kafin ta k'arasa maganar bakin ta sai jin mari tayi tass-tass a fuskar ta cikin masifa tace'' na kira ki ne? Ko nace miki inada buk'atar wani abu da zaki zo ki dameni da surutun banza, 'yar k'auye kawai tashi ki fice min daga d'aki ko in tashi in tattakaki a nan''. Dafe da kunci Atika ta tashi ta fice tana mai zubar da k'wallah ita wallahi saboda anty FARHANAH aikin gidan nan duk ya fice mata a rai. Ta maidasu tamkar bayin da taje kasuwa ta siyo. Shin shi talaka ko d'an k'auye ba Allah ne ya halicce shi ba? Cikin irin wannan tunanin Atika taje sauka suka had'u da mom bata ma ganin gabanta saboda b'acin rai sai da ta kai ma mom karo sannan ta dawo hayyacin ta tana ba mom hak'uri. Kallon fuskar ta mom tayi tace'' Atika me zan gani haka? Me ya samu fuskar ki har ta kumbura?" Atika bata iya ta bata amsa ba sai tayi k'asa da gudu tana mai yin kuka gwanin ban tausayi. Mom kuwa k'arasawa saman tayi ta shiga d'akin FARHANAH dan tasan bazai wuce ita ce ba. Cikin b'acin rai mom ta k'arasa inda take tace'' me Atika tayi miki ne kika mareta?" 'Dago jajayen idanunta tayi tace'' mom zuwa tayi ta dameni da wani banzan surutun ta wai ina buk'atar wani abu ne? To ni na gaya mata cewa inason abu?" '' Ke fa wannan yarinyar wallahi ki kiyayi rayuwa ke shikenan ba'a miki abin k'warai ko? Ina laifin wanda ya damu da kai? Wai duk akan auren nan ne kike ta k'unci kin kulle kanki a d'aki kin hana kanki sukuni?" FARHANAH dai bata ce komai ba sai mom ta cigaba da cewa'' to ki sani wallahi auren ki da yarima babu fashi dan daddyn ki ma ya kirani yanzu yace ki zauna cikin shiri zuwa gobe yarima zai zo ku gana''. Tana jin haka ta saka ma mom kuka tace'' haba mom wai dan Allah meyasa daddy zai min haka ne? Kodai ya daina sona ne shiyasa yake neman hanyar rabuwa dani''. Tana kaiwa nan ta b'arke da wani sabon kukan har ta ba mom tausayi dan bâ k'aramin abu ne ke saka FARHANAH kuka ba dan taurin zuciya ne da ita. Mom zama tayi a bakin gadon gami da jayota jikinta cikin rarrashi tace'' haba sweet daughter na kina kallon kanki a mirror kuwa? Baki san kin girma kin kai minzalin da ya kamata a ce kinyi aure ba?'' Mom ta cigaba da cewa'' karki manta 'ya mace gajerar rayuwa ne da ita, ana son daga zarar yarinya ta taso a ce tayi aure tun lokacin da auren ke neman ta ba wai sai tazo tana neman shi bâ shi kuwa yana guje mata, kiyi tunani da kyau soyayyar da daddyn ki yake miki ce tasa yake son ya ga kinyi aure''. 'Dagowa tayi daga jikin mom tace'' duk da haka mom ai bai kamata yayi min auren dole ba a bari in zab'i wanda nakeso da kaina''. Kallon ta mom tayi tace'' ina yake shi wanda kike son? Ke da kike ma kowa kallon bai isa ba, nidai shawarar da zan baki itace kiyi amfani da damar ki tun kafin ta sub'uce miki ah to ni d'aga ni in tafiya ta''. Bayan mom ta fita sai ta sake dulmiya cikin wani tunanin kuma to idan ma daddy ya hak'ura da wancen auren in yace ta fito da wanda takeso fa? Wa zata kawo mishi a matsayin mijin da zata aura? Wata zuciyar tace MUHSEEN. Nan take tace kai a,a Muhsin d'in da yaso raina mata hankali tace ya rabu da ita yanzu ta kira shi tace mishi me? Gaskiya sai ma ya raina ta. Muhsin saurayin ta ne wanda suka shekara suna soyayya amma ta hanashi zuwa gidan su wai a lokacin ita bata isa aure ba kar daddy ta ya gansu tare yace zai mata aure. Shi kuma Muhsin har ga Allah da aure yake sonta ko da ya nuna hakan tace bata shirya ba ya k'ara gaba. Yaji zafin rabuwar su dan yana mata son da bai tab'a ma wata 'ya mace ba a duniya. Muhsin d'an wani gomnan jaha ne shi kuma architect ne na k'asashe yayi fice wajen zanen gidaje yanada kud'i sosai shiyasa ma ya samu FARHANAH ta d'an kulashi haka rabuwar su ta kasance ba dad'i. To gashi yanzu da ta rasa mafita har ta fara neman shi a zuciyarta fa amma dan bata jin zata iya kiran wayar shi bai isa ba inji ita fa readers. ***** **** ***** Washe gari yarima *SYDEEK* ne kwance akan katafaren gadon shi knocking akayi a k'ofar d'akin ya bada izinin shigowa. 'Daya daga cikin masu tsaron shi ne ya shigo tare da yin sallama yarima ya amsa mishi cikin sanyin murya. Zuwa yayi tare da durk'usawa k'asa yace'' ranka ya dad'e yarima mai jiran gado mai martaba ne ya aiko d'an aike yace ka fara zuwa ka ganshi kafin ka fita''. Da hannu yayi mishi alamar ya fita yaji. Tashi yayi ya fice yana cewa'' godiya nake na barka lafiya''. Bayan fitar shi yarima ya lumshe ido dan yasan kwanan zancen akan zuwan shi ganin yarinyar da ake son lik'a mishi ne dan tun jiya maman shi tayi mishi maganar kuma sak'o ne daga mai martaba. Da yamma ya shirya cikin dakakkiyar shadda white colour wacce tasha aiki a gaban ta. 'Kamshi kawai ke tashi a jikin yarima kai kace b'arin turare yayi. Ficewa yayi daga d'akin a falo ya isko masu bin bayan shi suna ganin shi suka zube suna kai gaisuwa gareshi hannu ya d'aga musu a tare suka fita suna mai bin bayanshi suna mishi fadanci. Sai da suka kai bakin fadar mai martaba sannan suka ja suka tsaya shi kuma ya shiga tare da yin sallama nan aka amsa mishi 'yan fada sai gaisuwa suke kawowa a gareshi. Da ido mai martaba yayi musu nuni da su d'an basu wuri. Nan suka tashi suna cewa'' mun bar ku lafiya, a tashi lafiya ya sarkin sarakuna Allah ya ja da kwanaki''. Haka suka fice d'aya bayan d'aya. Bayan sun fice ne sarki ya kalli yarima yace'' Habibullah(da haka sarki yake kiran yarima) da fatan dai wannan shirin na tafiya wurin sirikar tawa ne ko?" Sunkuyar da kai yarima yayi cikin ladabi yace'' eh ranka ya dad'e can zamuje''. Jinjina kai sarki yayi yace'' masha Allah hakan yayi kyau Allah yayi maka albarka''. Yarima ya amsa da'' ameen abba, zamu iya tafiya?" Sarki yace'' tashi ku tafi a dawo lafiya jiya ma munyi magana da baban nata''. Tashi yayi yace'' godiya nake a tashi lafiya''. Da kai ya amsa mishi irin nasu na manya. Duk da anyi musu kwatancen inda gidan yake amma sai yarima yace da driver'n ya kai shi guest house d'in can. Driver yayi mamaki yace'' to amma ranka ya dad'e ba gidan su yarinyar zamuje ba?" Kasancewar amintaccen sa ne yake driving d'in sa sai ce mishi yayi'' a,a kaga Sulaiman muje can d'in gaskiya ni ban shirya zuwa wani wurin ba''. Bai mishi musu ba yaja akalar motar zuwa inda ya fad'a mishi....... *_Toh🤔 amma yarima kamar kaso raina hankalin mai martaba🙀 kai da kace zaka je wajen hirar aure shine zaka wazge ta wani hanyar kuma🤨 humm mû dai muna gefe ko ya kuka ce readers?🤷‍♀_* *_'YAR MUTAN KAZAY CE👑_* 💥💥💥💥💥 *_'YAR GADARA_* 💥💥💥💥💥 *_NA_* *_MAIMOUNATH O.G_* _(Mahnoor)_ _Wattpad@maimounathog_ *💫DA BAZAR-MU WRITER'S ASS💫* *_~We are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are d best among all....DA BAZAR-MU MUKE TUN'KAHO~_* *Dubun gaisuwa da fatan alkhairi a gareku masoya na, a cigaba da yin hak'uri damu godiya nake😉* *Page 21/25* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* °°°°^^^A can gidan su FARHANAH kuwa an shirya tarben yarima domin kuwa an tanadi komai abubuwan ci da na sha kala-kala duk dan shi. FARHANAH sai harare-hararen su Atika takeyi wa'yanda ke ta shige da fice wurin shirya abincin wani haushin su takeji. Mom ta fita tare da driver, a cewar ta zataje unguwa ta dawo kafin bak'in nasu su iso. A b'angaren yarima kuwa kwance yake a falon guest house d'in da yasa Sulaiman ya kawo shi. Idanun shi a lumshe da alama tunani yake me zai fad'a ma sarki idan ya koma gida? Dan tabbas mai martaba sai ya tambayeshi wani abu game da zuwan shi gidan su FARHANAH gashi kuma bai ma tafi ba. Wani d'an tunani yayi sai ya bud'e idanu. Gyaran murya yayi sai ga hadiman shi sun shigo har k'asa suka durk'usa yace'' cikin mota akwai book da pencil a kawo min''. Da d'an gudu-gudu d'aya daga cikin su ya tashi yana cewa'' an gama ranka ya dad'e'' a haka ya fita yaje bai jima ba ya dawo d'auke da book da biron ya kawo mishi, sai da ya yago mishi takarda sannan ya mik'a mishi. Rubutu yayi ba mai yawa ba sannan ya nunke ta ya bada umarnin a kawo mishi envelop itama aka kawo ya saka ya mik'a musu sannan yace'' wannan ka ba Sulaiman kace mishi nace ya biya ta super market yayi siyayyar abinda ya dace ya kai gidan su yarinyar nan''. '' To an gama ranka ya dad'e, umarni naka cikawa tamu''. Haka yana mishi kirari irin na sarauta ya fice ya kai ma Sulaiman ya dawo. Har ya gama siyayyar sai ga kiran yarima da hanzari ya d'aga cikin rawar jiki har da d'an ruzunawa kamar yana gabanshi. Umarni yake bashi akan ya had'a da kud'i dubu hamsin(50) yakai. Yace dashi an gama da izinin Allah yayi mishi sallama tare da ajiye wayar. Anya kuwa ya kyauta ma sarki? A ce duk yanda yake nuna mishi so amma yak'i bin umarnin shi? To ya zaiyi shi fa auren ma bai gaban shi. A lokacin da aiken yaje gidan su FARHANAH tana garden zaune tana wani abu akan system d'in ta da alama aiki takeyi. Mai gadi ne ya kira Atika wacce yaga wulgawar ta yace da ita sak'on FARHANAH ne inji yarima yace bazai samu damar zuwa ba. Karb'a tayi ta wuce garden inda FARHANAH take tana aiki tana kurb'ar juice na exotic. Durk'uwasa tayi tace'' anty gashi wai ance inji yarima wani ne ya kawo''. Wani mugun kallo ta bita da shi jin ta ambaci sunan yarima tace'' to shine me? Sai kuma da yake baki da hankali kika kawo min shi nan baki ga inada abin yi bane?" '' Kiyi hak'uri anty''. Hararen ta tayi tace'' uhm abinda kika sani kenan ai, tashi ni ki fice min daga nan''. '' Anty in kai sak'on d'akin ki ko?" Atika ta tambaya. FARHANAH ta bata amsa da'' a,a zo ki d'ora su bisa kaina mahaukaciya kawai kin b'ace min daga nan ko kuwa dai?" Atika tashi tayi ta fice tana gunguni. 'Dakin FARHANAH takai kayan sannan ta wuce aikin gabanta. Gab da magrib mom ta dawo wai go-slow ya tsaida su a hanya. Daga zuwan ta sai da ta tambaya da yarima FARHANAH tace'' kai mom daga zuwa kije kiyi sallah ki huta sai muyi maganar ko?" A haka FARHANAH ta samu ta lallab'a momy ta haye sama sai kuma ta tara 'yan aikin gidan har ma da mai gadi da tace dasu duk wanda yace yarima bai zo gidan nan ba to a bakin aikin sa idan momy ta tambayesu suce yazo kawai. Ya suka iya banda su bi umarnin ta tunda sun saba da wulak'ancin ta. Bayan sun gama cin abincin dare FARHANAH tana kusa da momy a zaune tana danne-danne a wayar ta momy ta kalleta tace'' nifa jira nake a bani labarin zuwan siriki na''. 'Dan murmushin yak'e tayi tace'' kai momy me kikeso in ce miki ne? Yazo mun gaisa amma bai jima sosai ba yace min akwai aikin da yake gaban shi wannan ma dan dai ya rigaya yayi alk'awari ne kuma bai son ya sab'a ma mai martaba shiyasa yazo a yau d'in''. Kuttt lallai FARHANAH kin iya sharo ta irin wannan k'arya haka tabd'ijam inji fulani hhhh. Momy tace'' to ai ba komai tunda yazo kunga juna shikenan daman banson ayi aure ace cikin ku babu wanda yaga d'an uwan sa''. FARHANAH tashi tayi tsaye tace'' momy zan hau sama akwai aikin da zanyi a laptop''. Momy tace'' ok sai da safe kenan?" '' Yes mom, good night!". Har da su kiss tayi ma momy ita gata baturiya toh fa. Ta d'auki tsawon lokaci tana aiki akan laptop d'in ta kafin ta tashi ta shiga toilet. Wanka tayi ta fito taje ta shafe jikinta da lotion mai k'amshi sannan tayi shirin kwanciya. Kayan d'azu suka fad'o mata a rai. Zuwa tayi inda Atika ta ajiye kayan ta d'auko su. Bisa gadon ta haye tare da zazzage kayan cikin ledar. Kayan k'walam da mak'ulashe ne da dai sauran tarkace birjik sai kuma envelop da ta fad'o daga cikin kayan. 'Dauka tayi gami da yage ta sai taga kud'i sun fad'o tare da wata takarda. Takardar ta d'auka ta bud'e sai taga anyi rubutu kamar haka: *_Assalamu alaiki_* *_Nayi miki sallama ne saboda kasancewa ta d'an musulmi amma ba wai dan kin isa ba, na turo miki abinda kika fi so wato kud'i dan nasan shi kikeso shiyasa har kika yarda da auren wanda baki ta6a gani ba. A k'arshe ina gargad'in ki akan aure na dan shine babban kuskure da zakiyi a rayuwar ki dan ban sonki_* *_Yarima Sydeek_* Tana gama karantawa tace'' kan uban can amma wannan yayi mugun raina min hankali ma har ni zai nuna ma kud'i? Waye shi? Lallai kuwa zan nuna mishi ko ni wacece muje zuwa''. Haka tayi ta haukan ta tana maganganu kamar wata mahaukaciya duk ta hargitsa d'akin kayan ta mayar cikin leda. Washe ta kira Atika bayan tazo tace mata'' d'auki wancan ledar kikai cikin shara''. Ta fad'a tana nuna mata ledar kayan jiya. Atika ta bud'e baki cikin mamaki tace'' anty wannan fa kayan nan ne na jiya sak'on da yarima ya turo''. Mugun kallo FARHANAH tayi mata tace'' to uwar tsari ai na fiki sani kiyi abinda nace ko sai na tashi a kanki ne?" Atika d'aukar ledar tayi ta fice tana gunguni mutum sai masifa da *GADARA* ita nan wai tafi k'arfin komai kamar wata mai kud'in duniya. Atika ce ke wannan guna-gunin ciki-ciki yanda bata jiyo ta ba a haka ta fice da kayan. Wayyooo Atika maido ni ki bani aradu in bataso mu munaso ko ya kuka ce fan's? To wai ina kud'in nan kar dai shima cikin shara za'a kai shi? Ya zama dole muje tunar shara ko zamuyi gam-da-katar mu kwashi dubu hamsin hhhhhhh. Atika kuwa tana sauka k'asa ta fice da ledar b'angaren su tayi taje ta nuna ma Laure suka sakaye abinsu ko a jikin su. Yo ai suna da gaskiya wannan ai wulak'anta abinci ne. 'Bangaren yarima SYDEEK ma da suka koma gida labarin k'arya ya sanar musu kan cewa yaje sun gana da yarinyar maman shi har tana tambayar tayi mishi dai ko yace tayi kawai. Kuji yarima da k'arya to a ina ka ganta ne ma har kake cewa tayi? Humm ayi dai mu gani. Bayan wasu kwanaki magana k'arama ta zama babba domin kuwa an gama maganar komai har an kai lefe gidan su FARHANAH kaya na alfarma wanda tsayawa fad'ar su ma b'ata lokaci ne kun dai san ance tuwon girma miyar sa nama. Tun FARHANAH na damuwa har tazo ta daina ta kuma shirya wa mijin da zata aura tsiya kala-kala sai ya gwammace bai zo duniya ba inji ita ba ni ba. An kawo masu gyaran amarya na musamman ana ta gyara FARHANAH ciki da waje tayi kyau ba na wasa bâ duk da bata son gyaran amma idan ta shiga toilet sai tayi ta kallon kanta tana mamakin canzawar ta lokaci d'aya. Ana sauran sati d'aya d'aurin aure aka turo wasu hadimai daga gidan mai martaba wai za'a tafi da FARHANAH can gidan sarki akwai inda aka killace musamman dan ita zata zauna can har lokacin d'aurin aure. Ai kuwa FARHANAH tace sam bata san wannan ba ta yaya za'a ce wai a kaita can tun ma ba'a d'aura aure ba salon mijin ya raina ta ko. Sai da momy ta zare mata ido ga anty Jamila 'yar uwar baban ta suka tarun mata sannan tayi shiru da bakin ta. Shirya ta akayi cikin shiga ta alfarma tare da saka mata alk'yabba. Mutanen da za'a je dasu sune anty jamila da k'awar ta Haulat sune zasu zauna da ita har ranar d'aurin aure kuma za'a dawo da ita gidan su tayi bankwana da iyayen ta. Ana fitowa da FARHANAH hadimai suka d'auki gud'a kamar ranar aka d'aura auren. Cikin wata mota mai masifar kyau aka saka ta anty Jamila su ma suka shiga. Motoci uku ne aka zo dasu d'aya a gaba sai tasu FARHANAH a tsakiya d'ayar a baya cikin nutsuwa motocin suke fita daga gidan su FARHANAH zuwa kan hanya abin gwanin sha'awa....... Ahayyyeee cakas mun kusa caskalewa💃💃💃 _Dan nayi alk'awari ne wallahi zazza6i ke damuna ga ciwon kai kuma_ *_'YAR MUTAN KAZAY CE👑_* 💥💥💥💥💥 *_'YAR GADARA_* 💥💥💥💥💥 *_NA_* *_MAIMOUNATH O.G_* _(Mahnoor)_ _Wattpad@maimounathog_ *💫DA BAZAR-MU WRITER'S ASS💫* *_~We are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are d best among all....DA BAZAR-MU MUKE TUN'KAHO~_* *_Wannan shafin naka ne our Adhyapak JAMILU ADAM DANWAYYE jinjinar ban girma a gareka Allah ya kare ka👍_* *_Fatan alkhairi gareku 'yan uwana d'aliban GARAM MASALA HINDI SCHOOL Allah ya k'ara had'a kan mu🤝_* *Page 26/30* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Motocin basu tsaya ko'ina ba sai a bakin babban gate d'in masarautar inda da zuwan su sarkin k'ofa ya wangame musu k'ofar suka shiga ciki. Masarautar badai girma ba domin kuwa akwai 6angarori da dama cikin gidan ga kuyangi da sauran hadimai sai hidima suke ana ta kai kawo kowa da aikin da yake. Tsayawa fad'in tsaruwar gidan ma 6ata lokaci ne dan abin sai wanda ya gani. Tsayiwar motocin kenan ai kuwa gida ya d'auki gud'a kamar ranar ne ake bikin. 'Bangare na musamman aka kai amarya FARHANAH da 'yan rakiyar ta. Kan kace meye tuni labarin zuwan su ya baza masarautar sarki ma an kai masa labari haka uwargida ran gida wato maman yarima SYDEEK kenan. 'Bangaren da aka kai FARHANAH ya tsaru matuk'a sosai ya birgeta duk da dai ba auren takeso ba. An kawo musu komai na buk'ata ga hadimai suna nasu aiki. Bayan sun huta jakadiyar mama ta shigo wasu bayi na biye da ita a baya d'auke da wasu kaya a rufe da farin k'yalle. Nan suka durk'usa har k'asa suna kwasar gaisuwa tare da musu sannu da zuwa. Su FARHANAH abin nema ya samu dan da k'yar ta amsa musu. Jakadiya tace'' ranki ya dad'e ki zauna cikin shiri yanzu masu miki gyara zasu shigo''. FARHANAH ta kalleta cikin mamaki amma bata ce komai ba sai gyara alk'yabbar jikinta tayi. Bayin nan suka tashi dan fita bayan sun nemi izinin tafiya. Jakadiya tana zaune wasu mutane suka shigo da alama sune masu gyaran. Kayan nan da aka shigo dasu jakadiya ta d'auka ta shiga wani d'aki wanda yake d'aya daga cikin d'akunan falon. Matan suka mara mata baya su anty dai kallon ikon Allah suke ita kuwa FARHANAH ta 6ata rai sai da anty Jamila tace da ita ta saki ranta kuma duk abinda aka umarce ta dayi kar tayi gardama. Wasu hadiman ne suka sake shigowa aka tusa FARHANAH a gaba har cikin d'akin nan da matan suka shiga. Gyara iya gyara FARHANAH ana mata shi ko'ina na jikinta k'amshi ke tashi domin kuwa kullum da kalar turaren da za'a saka mata cikin ruwan wanka. Haka su kuma tasu al'adar take da kansu zasu gyara amaryar su sai ana washe garin d'aurin aure tukun aka maida su gida. FARHANAH fa tayi kyau tayi fes kuma har ta gama zaman masarautar bata ga yariman nata ba shima kuma bai nemi inda take ba dan ko ma yace zai zo d'in ba barin shi za'ayi ya ganta ba. A al'adar tasu haka abin yake. Haka ma maman yarima kullum ta kan aiko musu da sak'on gaisuwa amma basu ganta ba. Momy tayi mamakin yanda 'yar ta ta canza tayi kyau sosai har wani shining take ga k'unshin da akayi mata mai ratsin ja gwanin kyau. Hidima aka cigaba dayi a 6angarorin biyu musamman ma a masarauta ana zumud'in wannan ranar tayi ranar da babban d'an sarki zaiyi aure babu wanda yakai mai martaba da mummy murna dan sun jima suna yi masa fad'an yayi aure amma yayi burus da maganar. Washe gari an tashi da farin ciki kasancewar yau ne d'aurin aure kowa ka ganshi yana cikin walwala daga gidan su FARHANAH har gidan mai martaba sarki Jafar abin dai ba'a cewa komai. Gidan sarki ya d'inke da d'imbin jama'a na nesa dana kusa ga abokan sarki sarakuna mak'otan garin duk sun samu halartar wannan gayyata da aka aika musu kuma sarki yaji dad'i k'warai da gaske. Gidan sarki sai kai kawo akeyi ta ko'ina mazan su da matan su. Ga bayi suma suna ta aikace-aikace. Yarima SYDEEK ne kwance bisa katafaren gadon sa abokin shi Mahmud sai magiya yake mishi akan ya tashi ya shirya lokaci yana tafiya kuma an kusa d'aura auren amma yayi banza dashi. Mahmud ya kama blanket d'in yaja ya bud'e shi yace'' wai meye haka friend? So kake sai kowa yasan halin da kake ciki?" Ido d'aya ya bud'e yace'' ai gara kowa yasan ba son auren nake ba''. Mahmud ya zauna a bakin gadon cikin rarrashi yace'' haba friend meyasa zakayi haka? Karka manta fa dubban jama'a sunzo duk dan saboda kai, sarakai abokan abba duk sunzo suma wallahi baka ga yanda masarautar nan ta cika da mutane ba, ko kana son ka ba abba kunya ne cikin jama'a?" Jin haka yarima ya tashi zaune tare da dafe kai yace'' oh God! Meyasa mai martaba zai min haka ne? Wai ace kamar ni ayi min auren dole kamar wata mace?" '' Sorry friend ka daure ka danne zuciyar ka insha Allah auren ku alkhairi ne tashi ka shirya please''. Bai sake cewa komai ba ya tashi ya shiga toilet. Kafin ya fito tuni Mahmud ya fiddo masa kayan da zai sa dan yau shi yake masa komai masu mishi hidima kuwa suna can falon k'asa sai wasu dake a sama suna jiran fitowar sa. Bai jima sosai ba ya fito ya shirya cikin dakakkiyar shadda blue wacce tasha aiki irin na sarauta sai hula da takalmi suma iri d'aya duk bak'ak'e anyi musu aiki a jiki irin na shaddar yarima ya fito fes farin shi ya k'ara fitowa da ya saka shaddar nan ga sajen shi da ya sha gyara, gashi ya zagaye d'an bakin shi da yasa pink turare ya fesa mai shegen k'amshi sai ya d'auki eyesglass d'in sa ya manna abin gwanin ban sha'awa yayi kyau sosai. Mahmud ya kalle shi yace'' wow!! Ango gaskiya kayi kyau yau zaka fasa taro fa saura alk'yabba ko?" Yamutsa fuska yayi yace'' nifa ka takura min ina laifi da nayi k'ok'arin saka wannan rigar mai nauyi ma kuma kace in sa wata alk'yabba''. '' Ayi hak'uri ranka ya dad'e ai ita zata k'ara maka k'ima da k'warjini''. 'Kasa suka sauko wanda tun daga saman hadiman shi suke kwasar gaisuwa tare da kirari Mahmud ne mai amsa musu dan da alama k'asaitar ta motsa yanda yasha mur d'in nan. Abokan su ma duk sunzo ashe suna can inda ake ke6e musu daman jiran fitowar shi sukeyi. Bayi sai zubewa sukeyi suna kwasar gaisuwa. 'Karfe *2:30pm* aka d'aura auren yarima *SYDEEK* da amarya *FARHANAH* fad'in yanda d'aurin auren ya kasance ma 6ata lokaci ne kun dai sani ba sai na fad'a ba a ranar naira tayi kuka masha Allah jama'a kowa sai sambarka yake abin birgewa ma bayan d'aurin aure aka cigaba da hidimomi kakaki sai tashi yake masu gud'a suna nasu. Har da wasan dawakai akayi su yarima ba dama ya daure dai ana hidima dashi amma zuciyar shi k'una takeyi idan ya tuna wai shi ne yau aka d'ora ma wannan nauyi sai yaji kamar ya saka ihu lallai wannan yarinyar ko wacece zata d'and'ani kud'ar ta duk da yayi mata kashedi amma bata ji ba. 'Bangaren gidan su FARHANAH ma ana ta hidima daga lokacin da labarin d'aurin auren yaje musu ai kuwa FARHANAH ta shiga rusa kuka kamar wacce aka aiko mata sak'on mutuwa k'awar ta Haulat sai aikin rarrashin ta takeyi amma a banza gashi k'awayen su duk sunzo kuma bata son a fahimci wani abu. Bayan magrib akace anzo d'aukan amarya a fito da ita. Daman an shirya ta sai aka kaita falon daddyn ta inda yayi mata fad'a sosai tare da nasiha inda ya saka mata albarka da fatan samun zuri'a d'ayyiba. Momyn ta ma haka tayi mata nasiha su FARHANAH sai kuka akeyi k'asa-k'asa a haka suka fito harabar gidan inda motocin suke jere. Cikin Mercedes Benz mai shegen kyau da tsada nan aka sa amarya da anty Jamila sai sauran 'yan uwa da k'awayen ta suka shiga sauran motocin. FARHANAH tana ji tana gani aka fita da ita daga gidan su yau wani can ya raba ta da gidan ita bata son barin gidan su shiyasa ma bata batun aure ko kad'an. Anyi tafiya mai nisa sannan suka k'araso masarautar nan aka bud'e musu gate motocin suka shiga d'aya bayan d'aya cikin nutsuwa. Ai fa da isowar su gida ya d'auki kururuwa da gud'a ta murnar zuwan amarya. Sauran motocin a wajen ajiyar mota suka tsaya inda motar amarya ta k'arasa har part d'in da aka tanadar mata wanda yake manne da na yarima. An fito da ita cikin taku d'ai-d'ai take takawa inda anty Jamila da wasu 'yan uwan daddyn ta mata biyu suke a tare nan da nan bayi suka k'araso inda suke tare da shimfid'a wani lallausan abu har zuwa bakin k'ofar gidan ta. Ta bisa suka taka suna tafiya har cikin part d'in FARHANAH. 'Kawayen ta ma ba'a jima ba sai gasu sun shigo wajen nasu sai kalle-kalle suke na k'auyenci dan gidan ba k'arya ya tsaru an kuma kashe kud'i. Kan kace me tuni hadimai sun cika su da kayan cima kala-kala sai wanda suke so zasu ci ko sha. FARHANAH dai nata kallo tana ganin yanda suke shigowa suna kawo gaisuwa. Can kuma sai ga jakadiya daga 6angaren mummy tazo musu da sak'on gaisuwa. Wajen 10:00pm suka fara watsewa dan ma sun tsaya kallon wasan da akeyi ne da tuni sun fice babu mai kwana a nan sai dai gobe zasu zo kawo mata wasu kayan. FARHANAH tana ganin suna shirin ficewa ta aza musu kuka ita ba zasu barta a nan ita kad'ai ba. Anty Jamila tace'' kiyi hak'uri FARHA haka aure ya gada daman, kuma gobe insha Allah zamu zo ai kinga nan gidan sarauta ne komai nasu daban yake dan Allah kiyi hak'uri na tabbatar ba za'a barki ke kad'ai ba''. Anty Jamila tana gama fad'in haka tayi waje tana mai share k'wallah haka Haulat ma kuka ta fara gami da ficewa. Bayan sun fita ne ta cire alk'yabbar da take jikinta daman duk ta dameta takeji. Kallon d'akin ta tsaya yi ashe haka yake da girma da tsaruwa wai bedroom ma kenan ina ga sauran wajen. Tafkeken gado ne wanda yasha shimfid'a da zanin gado na alfarma mai kyau, bedsheet d'in milk color ne haka labulayen d'akin ma ga katafaren carpet sai wasu kujeru suma a jere an lailaye su da kilisa abin dai gwanin ban sha'awa. Duk da tsarin ya birgeta amma sai ta ta6e baki cike da bak'in ciki a zuciyar ta tace da ma wanda nakeso ne da zan iya zama haka nan ma ko da auren bai raina amma anzo an had'a ni da wanda ban ta6a gani ba wa ya sani ma ko kuturu ne ko wani musaki. Duk ita kad'ai take wannan maganganun a zuciyar ta. Tashi tayi dan cire wannan kayan masu nauyi da aka jibga mata sai taji ana ta6a k'ofar alamar za'a shigo kuma tana jin maganganu a k'asa-k'asa. Komawa tayi ta zauna a bakin gadon sannan ta bada umarnin a shigo. Jakadiya ce ta shigo tazo har inda take ta durk'usa tana gaishe ta. Amsawa tayi cikin basar wa. Wasu kaya ta ajiye mata tace'' ranki ya dad'e ni jakadiyar yarima ce wato ni na raine shi tun yana k'arami har ya girma zuwa yanzu haka ni nake kula da abincin da yake ci''. Ganin FARHANAH bata ce komai ba sai jakadiya ta cigaba da cewa'' wannan kayan shi gimbiya zata saka muje 6angaren yarima haka al'adar take''. FARHANAH tana jin haka sai ta kalli jakadiya tace'' a gaskiya ni a gajiye nake kina iya komawa ki fad'a masa cewa hutu nake idan yana buk'atar gani na k'ofa bud'e take zai iya zuwa''. Jakadiya ta kalli FARHANAH tace'' ranki ya dad'e ai wannan al'ada ce tun iyaye da kakanni ba'a canza ta kuma ba'a mayar wa da yarima sak'on da ya bayar''. Taso tace wani abu amma sai ta k'yale tayi jim kad'an sai kuma tace'' ok naji zanje amma fa saboda ke sai ki jira ni a falo in shirya''. Jakadiya ta tayi k'asa da kai tace'' uhmm...humm ai da kaina ma zan had'a miki ruwan da zakiyi wanka akwai masu shirya ki a falo''. Tana fad'in haka ta shiga toilet d'in ta had'a ruwan wankan wanda ya sha turaruka masu dad'in k'amshi. 'Kwarai FARHANAH taji dad'in ruwan ga k'amshin da ke tashi a ko'ina toilet d'in ta tsaya kallo ita dai duk da gidan su ma ba baya a kyau ba amma kam wannan nasu na musamman ne toilet d'in kanshi abin kallo ne dan ya birgeta. Bayan ta fito jakadiya ta kira masu shirya ta suka shirya ta tsab sannan suka fita a tare da jakadiya da kuma wasu bayi biyu su suka rakasu har 6angaren yarima. A k'ofar shiga suka iske masu gadin k'ofar yarima ganin su da FARHANAH yasa suka sunkuya suka kwashi gaisuwa sannan aka basu damar shigewa. Part d'in nashi ma katafare ne ya tsaru sosai shima ga fitilu ko'ina suna haskawa sai flower's masu kyau wanda suka sha gyara. A bakin k'ofar babban falon ma da mai tsaru shima ya gaishe su tare da yi musu sannu da zuwa suka shige. A falon ma masu yi masa hidima ne a zazzaune jakadiya tace'' ayi mana iso wajen mai yarima''. 'Dayan ya tashi ya haura sama bai jima ba ya dawo yace'' ai yarima har yayi bacci''. Mamaki ya lullu6e jakadiya tace'' to ikon Allah an gaji kenan, to shikenan ranki ya dad'e ke kina iya hawa sama dan in yana bacci ba'a tashin shi amma ke zaki iya zuwa muje in raka ki falon sama''. Ita dai FARHANAH bin ta kawai takeyi dan bata son yi mata gardama ganin matar dattijuwa ce. A bakin k'ofar d'akin yarima jakadiya ta tsaya gami da nuna mata cewa nan ne d'akin nashi ta shiga kawai. Jakadiya tafiya sukayi ita da bayin nan. FARHANAH gaban ta na fad'uwa ta tura k'ofar d'akin a bud'e take amma d'akin da duhu sai fitilar gefen gado mai duhuwa ita ce ke a kunne. Ta hango mutum kwance bisa k'aton gado gashi sanyin AC sai tashi yake kuma ko rufe jikinsa bai yi ba alamar sanyin ma bai damun sa. A hankali ta k'arasa har wurin gadon ta tsaya a bakin gadon tana son ganin fuskar shi amma bata ganin ta saboda d'aya gefen take. Tana nan tsaya kawai sai yarima yayi juyi irin na cikin baccin nan ya juyo face d'in sa inda take. Kusan sumewa tayi ganin wanda ke kwance a gadon a matsayin mijin auren ta....... *Sai hak'uri fa bani da time sosai ne* *_'YAR MUTAN KAZAY CE👑_* 💥💥💥💥💥 *_'YAR GADARA_* 💥💥💥💥💥 *_NA_* *_MAIMOUNATH O.G_* _(Mahnoor)_ _Wattpad@maimounathog_ *💫DA BAZAR-MU WRITER'S ASS💫* *~_We are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are d best among all....DA BAZAR-MU MUKE TUN'KAHO._~* *_Assalamu alaikum fan's nagode sosai da addu'o'in ku Allah ya bada lada._* *Akwai wacce tayi copy na wasu wurare na book d'ina 'YAR GADARA to please banson fitina ki daina kiyi naki inyi nawa hakan sam bai min dad'i ba. Ba sai na kama sunanki ba kinsan kanki so please and please ki rubuta taki basirar🙏* *Page 31/35* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* °°°°°°°Cikin tashin hankali da firgici marar misaltuwa ta fito daga d'akin ko ganin kirki batayi haka take saukowa daga stairs d'in. A bakin k'ofar falon nashi ta tsaya tana maida numfashi gami da dafe k'irji kamar wacce tayi gudu ko taga wani abin tsoron. 'Kofar falon a rufe amma tana dafa ta aka bud'e. Mai tsaron k'ofa ne ta gani tsaye, cikin hanzari ya duk'a ya kwashi gaisuwa ko kallon arziki bata masa ba ta fice. Haka a k'ofar fita part d'in ma masu tsaro ta iske su ma gaisuwar suka mik'a tayi banza dasu ta nufi part d'in ta. Tana shiga d'akin ta gado kawai ta fad'a gami da rushewa da kuka mai tsanani kamar ranta zai fita. Kuka tayi mai isar ta kafin daga bisani ta shiga tunani da zancen zuci. A gaskiya ita dai daddyn ta bai k'aunar ta sam bai sonta yanzu a rasa wanda za'a aura mata sai wannan mutumen da tafi tsana a rayuwar ta. Why? Why? Daddyn ta zaiyi mata haka? Ji takeyi kamar ta kashe kanta saboda tsabar tak'aici da k'unci. Lallai ma yaron nan zata nuna masa ruwa ba sa'an kwando bane, ita tafi k'arfin shi wallahi nesa ba kusa ba, me ma zatayi da shi? Haka FARHANAH tayi ta haukan ta har bacci 6arawo yayi awon gaba da ita. A goshin asuba cikin bacci take jin kamar ana knocking ga idanun ta da sukayi mata nauyi da k'yar ta iya bud'e su. 'Dakin duhu babu haske ko kad'an tayi mamakin hakan dan a iya sanin ta fitilar d'akin a kunne har baccin ya d'auke ta. Tana cikin tunanin ne taji an k'ara yin wani knocking d'in. Ko waye warhaka kuma? Abinda ta ayyana a zuciyar ta. Izinin shigowa ta bada, jakadiya ce ta shigo hannun ta d'auke da wasu kaya a lullu6e da farin yadi mai kyau. 'Karasowa tayi kusa da gadon ta kwashi gaisuwa tana cewa'' ranki ya dad'e an tashi lafiya ko?" '' Ina fa na tashi lafiya tunda kin dako min uban asubanci, lafiya kuwa?" Jakadiya tace'' ai daga cikin gida aka turo ni ko zan taimaka miki da wani abin''. Wani abu FARHANAH ta fad'a a ranta a zahiri kuwa cewa tayi'' nagode ban buk'atar komai a gaskiya ni kin shiga hak'k'ina ma bacci fa nake kika tashe ni''. Hak'uri jakadiya ta shiga bata sannan tace'' gimbiya ai ina fatan kin gane ni nice dai jakadiyar yarima dan ni na raine shi tun yana jinjiri har ya girma duk ni nake kula da lamuran shi''. FARHANAH ta fara gundura da maganar tace'' to wai ma me ya kawo ki nan dan Allah daman haka kukeyi a wannan gidan?" '' Ai gimbiya al'adar masarautar ce duk ranar da d'an sarki yayi aure to washe gari ana zuwa domin d'aukar zanin gadon ku shine shaidar yarima yayi dace da mata tagari''. Kallon ta kawai FARHANAH take yi har ta kai aya duk ta fahimci yanda abin yake ta gano komai. FARHANAH tace'' dan Allah na rok'e ki duk da ban ta6a rok'on wani mahaluki ba to ina d'an ganin girman ki, please ki fita bacci bai isheni ba''. Jin abinda FARHANAH tace ne yasa jakadiya ta tashi tsam jiki a sa6ule ta fita ko kayan da tazo dasu bata d'auka ba ta fice tana mai tunanin yanda zata sanar ma uwargidan ta wannan maganar ta FARHANAH. Ita a kaf tarihin wannan daular bata ta6a ji ko ganin wanda yayi haka bâ sai akan FARHANAH. Jakadiya ta zayyanewa mama komai amma ta d'an yi ma zancen kwaskwarima akan cewar ta tarar da 6angaren nasu a rufe alamar basu tashi ba kuma bata son ta takura musu shiyasa ta dawo. Maman yarima zagaye falo ta shiga yi dan neman mafita akan wannan lamari. Tasan halin yarima da kafiya akan abu maybe ma jakadiya ba gaskiya ta gaya mata ba. Gara asan abinyi tun kafin mai martaba ya tashi. Wayar ta ta d'auka ta kira yarima SYDEEK shi kuwa a lokacin ne ya fito daga toilet yaji wayar sa na ringing. Baiyi mamaki ba dan yasan bazai wuce maman shi bâ kuma yasan kwanan zancen wannan al'adar ce bai so ko kad'an ko da kuwa ace da yarinyar da yake so aka had'a shi bare ma kuma da bai san ma ko wacece ba. Yana tunani har wayar ta katse sai a karo na biyu ya d'auka tare da yin sallama cikin tattausar muryar sa mai dad'in saurare. '' Kana ina ne?" Tambayar da mama tayi masa kenan. Yace'' ina d'aki na mama''. Sai cewa tayi'' to naji ina ita matar taka?" Wannan tambaya kam ta daki zuciyar sa, ina ma yasan inda take? Wacece ma ita? Kuma 'yar waye ita? Anya ma ba mayya bace? Duk yanda yayi mata gargad'in kar ta yadda da auren nan amma ta nac..... '' Wai ba tambayar ka nake bane? Maganar mama kenan wacce tasa ya dawo daga duniyar tunanin da yaje. Cikin d'ar-d'ar yace'' mama...nima ban..san inda take ba". Cikin k'araji mama tace'' what? Me kake nufi da baka san inda take ba?" '' Am so sorry mama wallahi ban ganta ba, kinsan ba zanyi miki k'arya ba''. '' Wai kasan abinda kake cewa kuwa? Kasan dai yanda al'adar gidan nan take ko? Yanzu ya kakeso ayi kenan?" Yarima SYDEEK yace'' dan Allah mama ki daina zancen al'adar gidan nan, wai meyasa k'iri-k'iri ake son maida al'ada addini ne? Wannan al'adar ya kamata ace zuwa yanzu an barta mama''. '' To sarkin tsari tun a da basu bari ba sai yanzu a kanka ko?" Kafin yace wani abu ta katse kiran. Yarima ya cilla wayar bisa katafaren gadon shi a yayin ya dulmiya duniyar tunanin wannan al'adar da har yanzu ba'a daina ta ba. Shi wallahi haushi abin yake bashi. Mama kuwa sai sak'a da warwara takeyi na yanda za'ayi rufa-rufa a kauda maganar zanin gado a yau. Ita kanta al'adar nan ta isheta haka nan to amma babu yanda ta iya ne, gashi babu kyau Allah ma ya hana amma sunk'i su daina. Zatayi iya bakin k'ok'arin ta ganin cewa an bar wannan al'adar. A tak'aice dai dubara akayi dan rufe bakin 'yan masarautar akan cewa gimbiya bataji dad'in jikinta bane shiyasa dan haka za'a d'an d'aga wannan wasa zuwa wani lokaci. Duk da haka dai wuni akayi ana kad'e-kad'e da bushe-bushe abin gwanin ban sha'awa. Sai yamma lik'is 'yan uwan FARHANAH suka watse amma an bar k'awar ta Haulat dan zasu tattauna ne. Zaune suke a falon ta na sama wanda yaji kaya na alfarma komai na falon abin sha'awa ne. Kallon Haulat tayi idanun ta cike da k'wallah abinda ba'a ganin sa akan fuskar ta saï da zancen auren nan yazo mata. FARHANAH tace'' wallahi daddy ya tsaneni bai sona ko k'adan k'awata''. '' Dan meyasa zaki ce daddy bai sonki ya tsaneni?" '' Haba mana ke kuwa ya rasa wanda zai had'a ni aure dashi sai wannan yaron da na tsana duk duniya? Ban sonshi ban k'aunar shi, me zanyi da d'an iska ragowar turawa?" Haulat dariya tayi iya son ranta wanda har yasa ta kular da FARHANAH, hararen ta tayi tace'' ke Allah banson iskanci, ya ina miki zance serious kina min dariya? Nace ban sonshi ko dole ne?" '' Sorry k'awata wai da kika ce ragowar turawa shine abin ya bani dariya wallahi, namiji ai bai zama ragowa sai dai mace''. '' Kina nufin nice ragowar kenan ko?" '' A,a Allah ya kiyaye ma in kira ki da wannan sunan, kawai dai ina son ki nutsu kiyi ma iyayen ki biyayya dan babu abinda zaki saka musu dashi akan soyayyar da suka nuna miki kamar rik'e auren ki hannu bibbiyu''. Saboda haushi ma FARHANAH kasa magana tayi dan ita fa babu yanda za'ayi ta zauna da mutumen da bata so balle kuma wannan da tafi tsana. Bayan Haulat ta tafi ne jakadiya tazo da wa'yanda zasu rink'a yi mata hidima, wanda zasu kula da ita a nan 6angaren ta. Su uku ne aka kawo mata, Shafa'atu mai gyaran bedroom d'in ta da kuma kulawa da kayan da zata saka, da Maryam mai kula da 6angaren abincin da zata ci sai Halimatu itace mai kula da tsaftar falo, idan ya gyaru itace idan ma basu gyara shi bâ to laifin a kanta yake duk da dai masu gyaran falon su ma a daban suke. A dak'ile take kallon su abinda dai taji dad'in sa da za'ayi mata komai dan daman bata wani saba da wahala ba kuma fa duk da haka ta iya girki kawai tsabar girman kai da *GADARA* su suke hana ta shiga Kitchen. Ana gama isha'i sak'o ya iso gareta daga 6angaren yarima cewar ta shirya zasu shiga cikin masarautar dan gaishe da maman shi da mai martaba. Taso ta mayar da 'yar aiken akan cewa bata zuwa sai kuma ta tashi ta shirya tana fitowa taga tuni an fiddo mata kayan da zata saka da komai na buk'ata. Bayan ta saka kayan ne sai ga Shafa'atu tayi knocking, sai da taja aji ta bata izinin shigowa. Tace tazo ta taimaka mata dan ta shirya ne. FARHANAH ta kalle ta tace'' ikon Allah, wai a gidan nan komai mutum zaiyi akan idanun kowa?" '' Kiyi hak'uri ranki ya dad'e ai haka akeyi dan ba'a son ki wahala ne ai''. Gaban dressing mirror taje ta zauna akan kujera Shafa'atu tayi mata k'walliya mai kyau har sai da tayi mamaki ashe ta iya k'walliya har haka? Lallai zasu shirya da wannan yarinyar kuma gashi tana da tsafta. Da aka gama Shafa'atu da kanta ta daidaita mata takalmin da zata saka sai kuma alk'yabba da ta d'ora mata akan leshin da tasa wanda akayi ma d'inkin riga da zani amma rigar tasha aiki a gabanta. Kunnuwan ta manne suke da d'an kunnen zinare, wuyan ta, hannun ta ma haka sai walk'iya take. Tana tafe Shafa'atu na take mata baya. Su o'o an samu abinda akeso daman ita akwai son a bauta mata saboda kallon k'ask'anci takeyi ma mutane ita kowa bai kai bâ haka bai kuma isa ba. 6angaren yarima ma ya gama nashi shirin a bakin k'ofar suka had'u kowannen su da masu take masa baya shima yarima ya sha kaya na alfarma da alk'yabba a jikin sa. Abin mamaki kalar shaddar da yasa blue ce haka itama lace d'in jikin ta blue ne mai aikin pink a gaba. Ita dai tasan ko shi waye amma shi har zuwa yanzu da suka had'un ma bai ga fuskar ta ba kuma bai buk'atar hakan ma. Babban falon mama suka fara zuwa akayi musu iso zuwa cikin falon. Uwargida sarautar mata gishingid'e take bisa kilisa ta ta alfarma, tsaruwar falon abin ba'a cewa komai. Hadiman ma kuwa sai hidima suke ga wasu na a gefen ta kayan ci da sha ne a gabanta wanda ko kallon su batayi saboda bata buk'atar cin su ko shan wani abu a wannan lokacin. Tana ganin su yarima da hannu tayi musu alamu na su fita. Tashi sukayi zasu fice bayan sun gaishe da su yarima su FARHANAH sai shan k'amshi akeyi har yanzu fuskar ta a lullu6e. 'Daya bayan d'aya suka fice suna mai yi musu kirari irin na 'ya'yan sarauta. 'Karasawa sukayi suka zauna a gefe-gefen ta yarima ne ya fara gaishe ta cikin ladabi da girmamawa haka itama FARHANAH tayi kamar yanda taga yariman yayi. Cike da fara'a ta amsa musu tana mai kallon FARHANAH tace'' 'yata kina lafiya? Ya bak'un ta? Da fatan dai ba wata matsala ko?" Cikin sunkuyar da kai FARHANAH tace'' lafiya lau mama ba komai''. Yarima jin muryar yasa ya d'ago kanshi da sauri saboda tunawa da yayi akwai wata mai irin muryar nan da ya sani, wannan fitsararriyar yarinyar. Ina ma zai ganta ne yanzu? Tun a wancan lokacin ta 6ace ma ganin sa wa ya sani ma ko aljanah ce. A rashin sa'ar da yayi ko da ya d'ago ma bai ga fuskar ta ba. Hira suka d'an ta6a yarima yace'' mama mai martaba ya shigo kuwa?" '' Eh yana 6angaren shi ku tashi kuje ku gaisa daman ya tambaya da ku''. Yarima ne ya fara mik'ewa ita kuma sai da mama tace'' 'yata kuje ku gaida abban ku kinji? Allah yayi muku albarka''. Can k'asa ta amsa da'' ameen''. Shima gogan naku ya amsa suka fice. Ita dai FARHANAH bin bayanshi takeyi kamar rak'umi da akala saboda yanayin masarautar yana rikita ta dan parts d'in sunyi yawa. Cikin nutsuwa sukayi sallama ya amsa yana zaune a wani falo na shak'atawar shi ne kafin ya shiga ciki. Falon shima a tsare yake kuma babu mai shigar masa nan sai yarima da kuma matar sa. Ma'ana dai wani bai shiga nan yana son kasancewa shi kad'ai a wurin. Zuwa sukayi suka kwashi gaisuwa cikin girmamawa. Cike da fara'ar sa ya amsa yana cewa'' kuna lafiya ko?" Duk suka amsa da lafiya lau. Sarki ya kalli yarima yace''...... *Kuyi hak'uri da wannan mura ce ta kama ni gashi na jima banyi typing ba.* *_'YAR MUTAN KAZAY CE👑_* 💥💥💥💥💥 *_'YAR GADARA_* 💥💥💥💥💥 *_NA_* *_MAIMOUNATH O.G_* _(Mahnoor)_ _Wattpad@maimounathog_ *💫DA BAZAR-MU WRITER'S ASS💫* *~_We are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are d best among all....DA BAZAR-MU MUKE TUN'KAHO._~* *Page 36/40* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* °°°°°°°Mai martaba ya kalli yarima SYDEEK yace'' Habibullah ka saurareni da kyau kaji abinda zan fad'a maka''. '' To ranka ya dad'e''. Yarima ya fad'a cikin girmamawa har da 'yar rutsunawa ita kuwa FARHANAH a zuciyar ta cewa take humm kamar wani mutumen kirki. Mai martaba yayi gyaran murya irin nasu na manya kuma masu ji da mulki yace'' to Habibullah yanzu dai kasan nauyi ya hau kanka da baka da nauyi ko hak'k'in wani yanzu kuwa Allah yasa kayi iyali dan haka ina son ka nutsu kuyi zaman lafiya da iyalin ka matuk'ar ka sa6a mata to zan d'auki mataki a kanka saboda k'ima ta ne yasa mahaifinta ya baka auren ta kai tsaye ba tare da yayi gardama ba dan haka ka kiyaye''. Sai da ya kai aya sannan yarima yace'' insha Allah zaku sameni da mai yi muku biyayya akan duk wani za6in ku ba za'a samu matsala ba''. '' Masha Allah''. Cewar sarki. Sai kuma ya kalli FARHANAH tace'' 'yata idan yayi miki ba dai-dai ba to ki sanar da maman ku ta gaya min in d'auki mataki kinji ko?" '' To ranka ya dad'e ba komai insha Allah lafiya zamu zauna''. '' Al-hamdulillah naji dad'in jin hakan, Allah yayi muku albarka ya baku zuri'a tagari masu yi muku biyayya kamar yanda kukayi mana''. Dukkan su suka amsa da ameen amma can k'asa kamar basu son fad'i. Ba'a jima ba ya sallame su sukayi masa godiya sannan suka fita. Sai da suka biya ta wajen mama sukayi mata sallama tukun suka tafi. Kowa 6angaren shi ya nufa FARHANAH sai hararen yarima takeyi ta k'asan ido shi kuwa ko a jikin sa yayi hanyar part d'in sa. Da shigar ta bata d'au lokaci mai tsayi ba sai ga wasu hadimai sun shigo da kaya nik'i-nik'i na ban mamaki wai kyauta ce daga gidan mai martaba. FARHANAH dai ikon Allah take kallo haka akayi ta shigar mata dasu ciki. Tsayawa zayyana irin kyaututtukan da aka kawo mata ma 6ata lokaci ne. An d'auki tsawon sati biyu kenan amma ango bai san amaryar sa ba ita dai tasan ko shi waye kuma ta d'auki d'amarar cuzguna mishi har sai ya gaji ya sauwak'e mata wannan k'addararren auren mara amfani. Akwai aure marar amfani ne? Humm lallai FARHANAH ba dama. Allah dai ya kyauta. A wata ranar saturday FARHANAH taji tana son fita shan iska wajen lambu. Shiryawa tayi da kanta dan tace a k'yaleta tayi shirin ta. Cikin shigar atamfa vlisco take amma ta d'ora alk'yabba wacce har ta fara sabawa da wannan yanayin da farko ji take tana matuk'ar takura mata amma yanzu ta saba dolen ta. Tafe suke ita da tawagar ta har zuwa lambun wanda aka gyara kafin isowar ta dan tuni sun san da zata zo wurin. Ba k'aramin birgeta wajen yayi ba domin kuwa lambun a gyare yake abin gwanin ban sha'awa ga flowers masu kyau a wurin idan kaga lambun zaka zata ma ba'a cikin gida yake ba, kamar wani d'an k'aramin daji mai cike da shukoki ne. Zama tayi a wajen da aka tanadar mata ga fruits kala-kala sai wanda takeso za'a bata tana daga gishingid'e kamar wata matar sarki. Ko da yake matar yarima wata rana zata iya zamowa matar sarki. Duk abin nan yarima yana kallon su ta wajen sa dan lambun had'e yake da na wajen sa dan dai wajen yana da girma ne sai kaso mutum zai ganka ma. Shi burin shi d'aya ne shi dai ya ganta, yana son ganin wace yarinya ce wannan mai taurin kai haka. Shima d'in zaune yake tare da mabiya bayan sa. Jarida ce a hannun sa kamar ita yake karantawa amma a zahirin gaskiya hankalin sa na wajen da su FARHANAH suke yasha alwashin yau saï yaga wannan yarinyar. Toh fa yarima nima zan so kasan matar taka ai. Rigiji gabji akwai drama fa. Yarima SYDEEK sai da ya bari suka koma gida tukun ya tashi dan zuwa yaga wannan yarinyar mai son girma da mulki gami da d'agawa. A hanyar duk wata baiwa idan ta ganshi sai ta zube k'asa dan gaisuwa shi dai ba wani son irin hakan yake ba amma ko ya fad'a basu iya dainawa dan tsoro. A haka har suka k'arasa cikin falon gimbiya FARHANAH, hadiman ta ne kawai ke kai kawo tsakanin falo da kuma Kitchen. Zama yayi a d'aya daga cikin kujerun alfarma na falon gami da d'ora k'afar shi d'aya bisa d'aya. Duk suka zo suka kwashi gaisuwa da hannu yake amsa musu kafin daga bisani yayi magana cikin k'asaita da nutsuwa yace'' ina uwar d'akin ku?" Shafa'atu tace'' tana sama a d'akin ta ranka ya dad'e, bari in sanar da ita zuwan ku''. '' No zanje da kaina ki barshi kawai''. Cewar yarima SYDEEK. Kallon wa'yanda suka zo tare yayi nan take suka gane abinda yake nufi saboda sun saba da halin sa yawancin maganar da zai musu to kuwa da kai ne ko idanu tun basu ganewa har ya zamto suna fahimtar sa. Ficewa sukayi waje suna mai masa kirari. Bayan sun fita ne ya tashi tsaye ya hau stairs inda zai kaishi bedroom d'in ta. Bai sha wahalar gane d'akin ta ba da yake yanayin ginin nasu iri d'aya ne sai dai kawai girma da na yarima yafi wannan da kad'an. 'Kofar d'akin da ya gani a d'an bud'e ita ya tura ya shiga cikin takun sa na k'asaita idanun sa manne da bak'in glass. Zaune take a bakin gado ko riga bata saka ba dan yanzu ta fito daga toilet sai taji wayar ta na ringing shine tazo ta zauna. Tawul ne kawai a jikin ta tana danne-dannen ta a wayar ashe text ne Haulat ta aiko mata shine take dubawa, jin anyi sallama da 'yar siririyar murya yasa ta d'ago kanta ai kuwa nan idanuwan su suka had'u da na juna. Yarima SYDEEK ji yayi kamar an duma masa wata guduma a tsakar kai saboda wani sara da yayi mishi lokaci d'aya har sai da ya kame kan yana mai furta addu'o'i. Duk da tuni tasan shine mijin nata amma sai da taji wani shock ya ziyarce ta. Da yatsa ya nuna ta yace'' you! Me kika zo yi a nan?" Kallon shi tayi up and down kallo irin na raini sai kuma ta maida kanta bisa sreen d'in wayar tayi kamar babu wata halitta a d'akin in ba ita ba. 'Karasowa yayi zuwa inda take yace'' ke banson raini ba tambayar ki nakeyi ba? Nace me kika zo yi a nan?" '' Ni kuma ina so, wai ma me kazo yi min a d'aki ne? Ka fice min daga nan malam''. Yarima ya k'ara harzuk'a yace'' wai daman kece matar da aka aura min? Idan kuwa har kece to zan iya cewa mai martaba ya daina k'auna ta kwat-kwata a rasa wacce za'a mak'ala min sai ragowar wasu''. FARHANAH tana jin yace ragowar wasu ta zabura ta tashi tsaye tace'' wallahi k'arya kake kace min ragowar wasu, gaka ragowa har zaka ce da wasu ragowa? Ka kalleni da kyau nafi k'arfin ka nesa ba kusa ba dan haka karkayi tunanin so ne ya zaunar dani a gidan nan''. Murmushi yarima yayi yace'' kin ta6a ganin namiji ragowa? Ai sai dai ayi mace sauran maza ba dai namiji ba, kin gama yawon ki an rasa mijin aure shine aka bada ke sadaka ko?" Wayyooo Allah na kuzo ku ga irin yanayin da FARHANAH ta shiga da jin wannan magana ta yarima. Takowa tayi har inda yake dab dashi ta tsaye tace'' kalleni sama da k'asa kai kasan na wuce a bada ni sadaka wallahi kai dai kace mata ne suka ce basu sonka shine akayi maka alfarma kawai''. '' Kanki akeji kin dai shigo gidan sarauta daman shi kike hange duk da kud'in da na baki amma sai da kika nace akayi auren nan, mu zuba ni da ke''. Juyawa tayi cikin takun ta taje bakin gadon ta zauna tana mai aika masa harare ba tare da tace komai ba. Yarima da son tsokana zuwa yayi inda take ya kalleta sai yayi dariya yace'' duk abinki ba zaki ta6a jan hankali na ba, mata masu kyan fasali ma basu gabana balle ke jibeki dan Allah kai abba ya gama dani''. '' Ka fice min daga d'aki malam''. Murmushin k'asaita yayi gami da sunkuyawa dai-dai fuskar ta ya kama tawul d'in daga gaban ta wajen tsakiyar breasts d'in ta a hankali kamar mai rad'a yace'' mu nan gidan dattako ne ba'a yi mata iskanci dan haka kar in k'ara ganin ki da d'aurin k'irji ba wani birgeni zakiyi ba''. Karaf ta kama hannun sa tare da bigeshi tace'' d'an iska ne kai ai ni nasan haka daman ka wani rik'e min tawul to jikina a k'walelen ka har abada banza kaw.....'' bata k'arasa ba ya d'auke ta da wani irin mari har sai da taga taurari. Dafe kunci tayi tace'' ni ka mara? Kai har ka isa ka mareni? Waye kai? Wallahi sai na rama dan kayi kad'an kaci bulus a kaina''. Tana gama fad'in haka ta d'aga hannu zata mazga masa tafi ya rik'e hannun ta da k'arfi ya murd'e har sai da tayi k'ara su FARHANAH anji maza. Nuna ta yayi yace'' har yanzu ba'ayi wata yarinya da zata d'aga hannu takai min mari ba, baki isa ba kuma ba zaki ta6a kaiwa wannan matsayin ba dan haka ki kiyaye kinci darajar iyayena ne da tuni na 6alla ki ba'a kawo min wargi''. Hannun ya yarfar sannan ya fice ko kallon inda take bai sake yi ba. Kuka wi-wi ta shiga yi kamar wacce aka aiko ma da sak'on mutuwa. Lallai ma wannan ba k'aramin d'an rainin hankali bane, har kamar ita wani can banza zai mara kuma bata rama ba? Yaci bulus kenan ko me? Kai wallahi bai isa ba sai ta rama marin ta. Haka tayi ta kukan ta tana maganganu kamar wata mahaukaciya duk ta hargitsa gadon. Yarima d'an duniya ko da ya ganta ma bai wani nuna alamar mamaki sosai ba a gabanta, amma fa da ya koma part d'in sa tunani ya shiga yi yanda akayi har aka had'a su aure, meye alak'ar mahaifinsa da nata mahaifin? Mu ma dai bamu da amsar tambayar nan jeka wajen gimbiya FARHANAH. Hahahahhh drama a gidan yarima SYDEEK. *** **** ***** Bayan kwana biyu da faruwar hakan jakadiya tazo ma FARHANAH da sak'on gaisuwa daga wajen yarima kuma yace yana buk'atar ganin ta a 6angaren sa. FARHANAH ta kalli jakadiya tace'' inaso ki koma ki gaya mishi cewar ni bani da lokacin tafiya inda yake amma idan ya matsu zai iya zuwa nan''. Jakadiya tace'' ranki ya dad'e ki gafarceni 'yata amma ai ba'a mayarwa da yarima sak'o nasan halin d'ana tunda ni na raine shi''. '' Kiyi hak'uri kinsan ina ganin girman ki yau sam na tashi ne banjin dad'i shiyasa bazan iya tafiya ko'ina ba''. '' Ashsha! 'Yata bari a samo miki magani to''. '' Ki barshi kawai zan samu sauk'i nagode''. Abinda FARHANAH ta fad'a kenan. Duk dagewar jakadiya akan taje ta sanar a kawo mata magani ko a kira family doctor amma FARHANAH tace a,a ita dai bata buk'atar ko d'aya daga cikin su. Haka jakadiya ta fice tana mai yi mata sannu da jiki su shafa'atu ma haka dan suna a gefe-gefen ta. Da kallo tabi jakadiya, ita wannan bata san abinda ke damuna yafi k'arfin asibiti ba? Ai ni matsala ta ita ce zaman auren nan musamman da yarima SYDEEK. Duk wannan maganar fa FARHANAH ce ke yi a cikin zuciyar ta. Ita dai jakadiya bata hak'ura ba dan zuwa tayi cikin gida ta sanar ma da mama akan cewa ai gimbiya bata ji dad'in jikinta ba. Hankalin mama ya tashi ta kira yarima ta sanar masa sai cewa yayi'' to mama ni me zanyi mata kuma?" '' SYDEEK karka yarda raina ya 6ace kaji ko?" '' Allah ya wuci zuciyar ki mama ya kike so ayi?" '' Har ma tambaya ta kakeyi yanda za'ayi? Ba matar ka bace? Ai kai ya kamata kasan duk wani motsi nata da wasu al'amuran nata idan ka cika ni zan fad'a ma abban ka''. '' To shikenan mama dan Allah ki daina fad'an nan ya isa haka''. Katse kiran tayi ba tare da tace dashi komai ba. Tashi yayi ya shirya dan tafiya gano 'yar mulki wato FARHANAH, shi yana komai ne dan iyayen sa amma bâ dan ita ba. Ta k'ofar baya yabi inda zata sadashi da gidan FARHANAH dan tsakanin ba nisa kamar a had'e ne ma suke sai dai lambu ta gefen d'aya. Bai bari kowa ya bishi ba shi kad'ai ya tafi. Bata falon sai hadiman ta kawai suke aikace-aikacen su. Kallon su yayi inda kowacce ta durk'usa gami da gaishe shi. Sama ya nufa inda d'akin ta yake, a kwance lub cikin blanket ya isketa d'akin ba haske sosai dan windows d'in duk a rufe suke sai fitilar gefen gado mai kalar blue. Takawa yayi har bakin gadon tana kallon shi dan fuskar ta na kallon k'ofar shigowa. Fitilar d'akin ya kunna sai ko'ina ya d'auki haske. Sannu yayi mata amma bata amsa mishi ba sai yace'' karkiyi tunanin dan na damu dake ne yasa nazo nan, a,a umarnin iyayena nake bi kinsan ni mai biyayya ne ba kamar ke nake ba''. Tashi tayi ta zauna sannan ta kalleshi sama da k'asa tace'' da waye yace kabi umarnin nasu ai da sai kayi zaman ka, ban buk'atar wani taimako daga gareka dan baka kai wannan matsayin ba''. '' Ki tashi kisa kayan kirki doctor zata zo duba ki''. '' Ban so nace malam wai kai maye ne ko me?" '' Da ni maye tun a ranar da na fara ganinki ba zaki kai labari ba, banson doguwar magana ki tashi ki shirya yanzu zata iso''. FARHANAH tayi k'ememe tak'i tashi ga mamakin ta saï taga ya nufi wardrobe d'in ta ya bud'e ya d'auko mata doguwar riga b'aka ita dai ikon Allah take kallo. Zuwa yayi da niyyar ya d'aga ta sai ta bige masa hannu tace'' kaga banson iskanci ka saba ta6a kod'andd'un matan ka ni nafi k'arfin ka wallahi''. Ajiye mata rigar yayi a bisa gado kafin yayi magana suka ji knocking a k'ofar d'aki. Kallon ta yayi yace'' wallahi ki tashi kisa rigar nan tun kafin ranki ya 6ace ba'a musu dani''. Ficewa yayi ta harare shi ji takeyi kamar ta rufeshi da duka wani irin haushin sa takeji. Tashi tayi taje toilet ta saka rigar sai kumburi take wai ita ce yau wani yake bata umarni lallai zatayi maganin wannan yaron. Hahaha kin makaro FARHANAH mijin naki ne yaro? Hummm bari ki shiga hannun manya kisha labari muna gefe ko ya kuka ce fanz? A tare suka shigo d'akin doctor na biye dashi a baya.......... *To ko ya zata kaya? Zata yarda doctor Sharifa ta duba ta ko kuwa?* *Ba lokaci sosai ku dai ku biyoni da sannu zamu kai ga inda muke son zuwa* *Na raina comments din ku wallahi idan bai muku ba zan koma yiwa 'yan wattpad kad'ai typing* *_'YAR MUTAN KAZAY CE👑_* 💥💥💥💥💥 *_'YAR GADARA_* 💥💥💥💥💥 *_NA_* *_MAIMOUNATH O.G_* _(Mahnoor)_ _Wattpad@maimounathog_ *💫DA BAZAR-MU WRITER'S ASS💫* *~_We are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are d best among all....DA BAZAR-MU MUKE TUN'KAHO._~* *Page 41/45* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* °°°°°°°Yana gaba doctor Sharifa tana bin bayan shi suka shigo d'akin. Gani yayi ta saka rigar da ya bata ta koma cikin blanket d'in. 'Karasawa sukayi har bakin gadon cikin fara'a doctor Sharifa ta gaishe ta amma sai ta amsa a yatsine kamar mai ciwon baki. Doctor ta kalle ta tace'' sannu gimbiyar mu ya jikin naki?" FARHANAH tayi wani fari da idanu tace'' da sauk'i''. Abinda ta fad'a kawai. Doctor tace'' Allah ya k'ara sauk'i, meke damunki?" Shiru tayi sai doctor ta kalli yarima wanda hankalin sa yake kan wayar sa tayi murmushi tace'' please ka d'an bamu wuri mana''. 'Dagowa yayi ya kalli doctor Sharifa yace'' akwai matsala ne a zaman nawa?" '' Gimbiya ce naga kamar tana jin kunyar ka shiyasa''. Humm yarima yace a ranshi, wannan yarinyar ce zata ji wata kunya ta yarinyar da bata iya komai ba sai fitsara. Sai da doctor ta sake mishi magana sannan ya tashi ya fita bai ko waigo inda suke ba. Gwaji tayi mata sai ta kalleta tace'' gimbiyar mu ya kamata ki rage yawan tunani da saka damuwa a ranki, kinga jinin ki ma yana neman hawa dan haka ki kiyaye dan Allah''. '' Ok thanks''. Ta fad'a a tak'aice. Magunguna ta rubuta mata sannan tayi mata sallama ta fice da takardar maganin. A falon sama ta iske yarima yana zaune taje ta zauna itama ta mik'a masa takardar tace'' gashi a nemo wannan magungunan ta fara shan su a yau dan gaskiya matar ka jinin ta yana neman hawa a dalilin yawan tunani da damuwa, meye matsalar?" Duk da sun sama da doctor Sharifa dan ba yanzu suka san juna ba amma ta d'an girmeshi sai dai sunyi school d'aya. Bai jin zai iya fad'a mata wani abu da ya danganci zamantakewar su. '' Yarima da kai fa nake, ko da wata matsala ne?" Maganar ta ce ta dawo dashi daga tunanin da yake yace'' no doctor ba komai sai dai maybe da bata saba da gidan bane, kinsan rayuwar masarauta ba kamar ta kowane irin gida ba ce akwai takura''. Ba dan ta yarda ba tace'' ok! To shikenan Allah ya sauwak'a a nemo maganin yanzu please''. '' Insha Allah''. Cewar yarima. Har zata tashi sai kuma tace'' ni nasan akwai abinda kake 6oye min in ba haka ba meye na nema na tunda kai ma likitane kuma k'wararre a wannan harkar''. Yarima ya kalle ta da lumsassun idanun sa yace'' please doctor mu bar zancen nan dan ba zaki ta6a ganewa ba''. '' Ok Allah ya bata lafiya''. Bai amsa mata ba kawai kyauta yayi mata tayi godiya ta fice. Yarima bai son mummyn sa tasan ba shine ya duba FARHANAH ba dan fad'a zatayi mishi yasan halin ta shi kuma bazai iya duba tan ba. Sawa yayi aka kira masa d'aya daga cikin mutanen sa ya bashi takardar maganin yace yayi maza yaje ya siyo yana nan yana jiran shi. Bayan d'an aiken ya fita ne shi kuma ya koma d'akin da take. Tana kwance dafe da kanta ji tayi yana mugun sara mata. Ga mamakin ta saï gani tayi yazo dab da ita ya zauna yana k'ok'arin ta6a kanta inda yaga ta rik'e sai ta fisge taje can k'arshen gado, bai damu ba sai ya ta6e baki ko a jikin sa. Shiru ne ya ziyarci d'akin kafin daga bisani ya tsinkayi muryar ta tana cewa'' malam ka fice min a d'aki ban buk'atar wani taimako daga gareka sai abu d'aya nakeso shine ka sauwak'e min wannan k'addararren auren naka''. Murmushi mai fitar da sauti yayi yace'' da ace zan iya yin haka da nafi kowa jin dad'i dan nima yanda akayi miki dole haka aka tursasani sai na zauna dake, daman wata daban ce ba ke ba da abin da sauk'i amma sai nayi rashin sa'a wai kece a matsayin matar aure na''. '' Kaga malam ni ba dogon turanci na nemeka ba kawai ka bani takardar saki na ka gani idan zaka k'ara gani na''. Tashi yayi tsaye yace'' kije ki nemi wa'yanda suka k'ulla abin su zasu iya warwarewa ni meye nawa a ciki?" Juya masa baya tayi shi kuma ya shiga zagaye a d'akin yana duba agogon hannun sa magrib ta kusa d'an aiken nan ya jima wallahi shi fa zaman shi d'aki d'aya da wannan yarinyar k'ara tafasa mishi zuciya yake. Knocking akayi da sauri yaje ya bud'e gami da murtuke fuska yace'' wai me ya tsaida shi ne sai yanzu ya kawo?" tambayar da Yarima yayi ma Shafa'atu kenan. Jiki na 6ari tace'' ranka ya dad'e cewa yayi magani d'aya ne yayi wahalar samu amma ya samo gashi nan''. So yayi yace ta shiga ta kai mata sai kuma ko me ya tuna sai ya kar6i ledar magungunan ya koma ciki. Da zuwan sa ya jefa mata ledar bisa gadon yace'' gasu nan idan kinga dama kisha ko ki bari wannan ruwan ki''. Yana fad'in haka ya ficewar sa. Wasu hawayen tak'aici taji sun zubo mata, wai me ya sameta ne da har wani banza yake gaya mata magana bata iya ramawa? Anya ita d'in ce kuwa? FARHANAH ke wannan maganganun ko ince tambayar da bâ amsa. Kwana biyu taji sauk'i ta warware sai taji tana son ta koma bakin aikin ta saï dai ta yaya kenan? Yanzu dole sai ta tambayi wannan mutumen? Wayar ta ta d'auko ta kira momyn ta bayan sun gaisa mama take tambayar ta ya zaman nasu babu wata matsala dai ko? Ita kuma an sosa mata inda yake yi mata k'aik'ayi sai tace'' yauwa momy kin tuno min daman inaso in koma aiki ne tunda na jima a gida''. Momy tace'' ki tambayi mijinki ai ba ni zaki tambaya ba kuma bana jin ma zai amince dan gidan sarauta fa kike da wuya in ana musu zarya idan yak'i amincewa kiyi masa biyayya dan Allah ku zauna lafiya da mijinki kina ji na ko?" '' I can't mom, sai dai ya sakeni na gaji da wannan zaman''. '' Auren ne kika gaji dashi har kike ikirarin ya sake ki? Wai a ina kika d'auko wannan baud'ad'd'en halin?" FARHANAH kuwa tanajin haka sai ta rushe da kukan shagwa6a tana rok'on momyn ta akan tasa baki yarima ya sauwak'e mata auren nan ita ba zata iya ba da auren kulle. Momy tace'' ki saurareni da kyau wallahi kika kuskura daddyn ki yaji wannan maganar sai ranki yayi mugun 6aci dan zai ajiye son da yake miki ne ya hukunta ki ai kinsan halin sa''. Zatayi magana momy ta kashe kiran da ma wayar baki d'aya dan tsananin tak'aici da haushin abinda 'yar ta keyi ita dai halin ta bazai ta6a canzawa ba. Washe gari ta aika ma da yarima sak'o akan zata koma aikin ta gobe sai ya maido mata amsa kamar haka: _Ba'a zuwa wani aiki a tsarin masarautar nan aure kikeso dan haka zaman aure zakiyi ban yadda ki fita ba_ _SYDEEK(Habibullah)_ Tana gama karantawa ta mik'e tsaye tana huci ta shige bedroom d'in ta daman a falon sama suke ita da su Shafa'atu. Kai kawo takeyi a d'akin ta rasa mafita wannan guy d'in fa sai ta nuna masa ainahin kalar ta tukun wai aure ko wa ma ya d'auki wannan a aure? Zan iske shi har 6angaren nasa ai ayi ta ta k'are. Tana gama maganar zuccin nan ta d'auko alk'yabba ta d'ora kan kayan jikinta ta fita tashi sukayi dan yi mata rakiya ta d'aga musu hannu kawai ta fice. A hanya sai gaisuwa akeyi mata ko kallon su batayi kawai ta kutsa kai falon nashi bai nan sai ta nufi d'akin baccin sa. A gishingid'e ta iske shi akan carpet wanda ya sha wani lallausan kilisa mai kyau, k'ananan kaya ne a jikin sa farar T-shirt ce da dogon wando bak'i kanshi a bisa pillow yana daga kwancen ya hango ta a zuciyar shi yace to masifa ko da me aka zo oho. Ko sallama babu tazo ta tsaya a kanshi tace'' malam me kake nufi da hanani zuwa wajen aiki na?" Shiru ba amsa hakan sai ya k'ara harzuk'a ta ta sake cewa'' da kai fa nake dan rainin hankali kayi min shiru''. Tashi yayi zaune ya kalle ta yace'' ni musulmi nake ba arne ba da zaki shigo min d'aki ko sallama babu kamar d'akin ki''. '' Banga wanda zanyi ma sallamar bane shiyasa''. Murmushi yayi yace'' ko da yake mantawa nayi ke da ganinki ma akwai k'arancin ilimi dole a samo miki malamar da zata koyar dake ilimin zaman aure''. '' Wallahi k'arya kake kaji in gaya maka ba daga nan ba kai d'in ne baka isa inyi maka sallama ko biyayya ba, idan wasu na tsoron ka ni ko kallo baka isheni ba''. '' To ba kinga irin ta ba, rashin ilimi kawai ke d'awainiya dake har tausayi kike bani, aiki kuma nace bâ zakije ba in kin isa ga hanya nan''. Haushi ya bata taje ta cakumeshi tace'' Allah baka isa ba sai dai ka sakeni bazan zauna da kai ba, bana sonka ban kuma k'aunar ka ko ana dole ne?" '' Ba'a dole amma ni kika lik'e min aka aura min ke dole nasan dai kece kika ce saï ni wato kinga yaro sabon jini ba kamar ki tsohuwa ba ko?" Wayyooo Allah gaskiya yarima ka gama da gimbiyar taka fa. Hannun ta ya kama ya cire daga rigar shi sai ya haye bisa gado ya k'yale ta a nan tsaye. Nufowa tayi inda yake sai yace'' kika kuskura kika zo inda nake abinda zan miki ko kare bazai ci ba dan haka ki kiyaye ni". '' Idan nazo d'in ka kashe ni yau za'ayi ta ta k'are ko ka sakeni ko kuma goben nan in tafi wajen aiki na tunda ba da kud'in ka nayi karatun ba''. Tana maganar tana matsawa inda yake har ta dangana da katafaren gadon sa k'arfin hali irin na FARHANAH har da hawa tayi bisa gadon zata sake cakumar sa ya rik'e hannayen ta duk biyun ya murd'e tayi 'yar k'ara dan zafin da taji yace'' ke kin rainani ko? Saboda kinga ina k'yale ki ni ban ta6a ganin amaryar da ke kawo kanta turaka ba sai ke wato an saba da bin maza ko?" Wata irin fisga tayi dan jin abinda yace amma ta kasa k'watar kanta yace'' haba yarinya ai baki isa ba''. '' Ka sake min hannu mugu azzalumi kawai''. 'Yar dariya yayi yace'' humm da ni azzalumi ne shigowar ki nan d'akin da tuni sai dai wata ba ke ba, matsalar ki kinkai kanki inda Allah bai kaiki ba saboda ke gaki 'yar masu kud'i to ba komai ne ake nuna *GADARA* da fifiko a kanshi ba tashi ki fice min daga d'aki tun kafin inyi ball dake''. Yana fad'ar haka ya sake mata hannu har da tunkud'a ta tayi baya Allah ya so ta dan gadon babba ne da ta fad'o k'asa. Sauka tayi a gadon tace'' aikin banza in kai namiji ne ai da sai ka sakeni in tabbatar ba da raggon namiji nake ba''. '' Nasan abinda kike nema kuma ba zaki ta6a samu''. Ficewa tayi ba tare da tace komai ita wani irin haushin sa ne takeji kamar ta shak'eshi ya mutu haka takeji a ranta tsana mai tsanani take mishi. Washe garin ranar tana kwance a d'aki Shafa'atu tayi knocking da k'yar ta iya ce mata ta shigo. Da sallama ta shigo d'akin cikin rawar jiki taje ta durk'usa kusa da gadon tace'' anty gimbiya kinyi bak'uwa tana falo''. Anty take ce mata saboda FARHANAH da kanta tace su daina ce mata ranki ya dad'e bata so. 'Dagowa tayi tace'' bak'uwa daga ina?" '' Ai anty cewa tayi kawai inyi miki magana''. '' Tana ina yanzu? FARHANAH ta tambaya. '' Tana nan falon sama''. Wani irin kallo tayi ma Shafa'atu tace'' what? Har falon nan macen da baku san ko wacece ba?" '' Kiyi hak'uri anty naga kamar kunada kusanci sosai da juna ne''. '' Tashi ki tafi ina zuwa''. Tashi tayi ta fice tana godiya kamar wacce aka bata kyautar wani abu kai fadanci baiyi ba wallahi zaman k'ark'ashin wani ba dad'i. Zuwa tayi ta sanar ma da bak'uwar cewa tana nan fitowa. Zata sauka suka had'u da yarima zai hayo sai ta ra6e gami da durk'usawa ta gaishe shi sai da ya wuce ta tashi. 'Bakuwar ce zaune a bisa kujera 2 seater Al-Qur'ani ne a hannun ta tana karantawa a nan falon ta sameshi. 'Karasowa yayi inda take ya kalleta sama da k'asa ita kuma sai da ta kai aya tace sadakallahul azim ta rufe ta d'ago ta kalleshi suna yin ido hud'u tace'' ina kwana ranka ya dad'e''. 'Daure fuska yayi yace'' humm yau kuma sabon fi'ili ne ya tashi? Kin wani d'auko Al-Qur'ani kamar kin iya karantawa har da gaishe ni ko dan nace ki koma slamiyya ne?" Ita dai kallon shi takeyi irin kallo na mamaki shi kuma da yaga ta k'yaleshi tana kallon sa sai ya k'ara da cewa'' kin wani tsareni da idanu d'aukan Al-Qur'ani ba shine iyawa ba''. Kafin tace wani abu sai ga FARHANAH ta fito daga d'aki yarima ya kalle ta ya kuma kallon bak'uwar nan da take zaune ya kasa furta komai kai wai meke shirin faruwa ne yau? FARHANAH tana ganin wacce ke zaune tazo da gudu ta fad'a jikinta tana cewa'' oyoyo......... *Kai readers meke shirin faruwa ne? inji yarima.* *Wacece wannan bak'uwar da tazo musu har yasa yarima ya firgice haka?* *Nima ina son sanin wannan matar dan warware muku abin nan.* A yanzu ne zaku san wacece FARHANAH da ma asalin ta baki d'aya. Wallahi zan iya ajiye rubutun nan dan na raina comments din ku kuma duk zan cire mutane in saka sabbi. *_'YAR MUTAN KAZAY CE👑_* 💥💥💥💥💥 *_'YAR GADARA_* 💥💥💥💥💥 *_NA_* *_MAIMOUNATH O.G_* _(Mahnoor)_ _Wattpad@maimounathog_ *💫DA BAZAR-MU WRITER'S ASS💫* *~_We are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are d best among all....DA BAZAR-MU MUKE TUN'KAHO._~* *_Masu satar fasaha ba zanyi muku Allah ya isa ba amma kuji tsoron Allah ku daina._* *Page 46/50* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* °°°°°°°FARHANAH da gudu tazo ta fad'a jikinta cikin murna take cewa'' oyoyo sister na, wayyooo Allah na dad'i dan Allah yaushe kuka zo?" '' Jiya da dare, cewa nayi bazan fad'a miki ba sai nayi surprising d'in ki''. '' Ai kuwa wallahi kinyi d'in dan ban ta6a tunanin zan ganku a nan kusa ba''. Murmushi tayi cikin nutsuwa tace'' humm kaji ki kamar kin wani damu dani d'in''. '' Sosai ma na damu my sister, I really miss you''. Inji FARHANAH. Shi kuma yarima ganin haka yasa yayi baya ya sauka k'asa cike da tunanin wacece wannan da har yayi tunanin FARHANAH ce? Gashi yayi ta gaya mata maganganu marasa dad'i, zai so sanin hak'ik'anin gaskiyar lamarin dan abin da rikitarwa, ko dai twins ne daman ko kuwa ya abin yake ne? Waye zai amsa masa wannan tambayoyin? Oho maka yarima. Da wannan tunanin ya bar part d'in ta gaba d'aya. Bayan ya fice ne ta kalli FARHANAH tace'' wai akwai wata matsala ne a game da zaman ki ke da yarima?" 'Baya fuska tayi tace'' me kika gani?" '' Zuwa yayi yake fad'ar magana kamar daman ya sanni ko dai ya zata kece?" '' Dan Allah ki daina maganar wannan mutumen tayar min da zuciya takeyi share kawai yanzu dai ina my baby ya baki zo min dashi?" Kallon mamaki take mata tace'' dear akwai matsala kenan amma kika 6oye min ko?" '' Matsalar itace ban son shi ban k'aunar shi kawai haka nan daddy yayi min dole, shine fa guy d'in nan da nake baki labari wata rana idan baki manta ba''. Tace'' Duk da haka dai ai mijinki ne yanzu ya kamata komai ya wuce kiyi masa biyayya dan Allah kinji?" '' Bazan iya ba fa kar ma ki had'a ni da Allah''. Cewar FARHANAH. Ita kuma tace'' kenan kinfi son kuyi irin wannan mugun zaman da hankalin ku da ilimin ku haba dan Allah wallahi zan had'a ki da daddy''. Hannayen ta ta kama tace'' sister ki fahimceni nifa wannan mutumen ne ban so dan ko ganin sa banson yi''. '' Ai kuwa ya zama dole ki dawo kan hanya ki farka daga nannauyen baccin da kikeyi ina laifin yarima wallahi namiji yanada saurin sauka yanzu haka ma duk kece dan nasan halin ki''. Banza tayi da ita a nan tace da ita su shirya suje can part d'in yarima tana son su gaisa ta kuma sanar masa yanda alak'ar su take da FARHANAH amma sai da k'yar ta amince zasu tafi. Nima kam zan so ki fad'a mana ya kuke da FARHANAH? Wace irin alak'a ce har haka? *_ASALIN SU...._* Alhaji Ado mai dala shine mahaifin su FARHANAH da FAREEHA sai mahaifiyar su Hajiya Rabi wacce suka yi auren so ba wai had'i ba. Hajiya Rabi ta auri Alhaji Ado tun bai taka matsayin da yake a yau ba saboda sun sha wahalar rayuwa kafin Allah yayi masa bud'i. Asalin su 'yan Borno ne shi da ita duk 'yan can ne amma yanayin kasuwanci ne yasa suka bar garin borno, kuma sun zauna garuruwa da dama. Sun jima Allah bai basu haihuwa ba dan sai da suka shekara takwas(8) da aure sannan Allah ya basu kyautar 'yan biyu wato FARHANAH da FAREEHA. A lokacin Allah yayi masa bud'i basu sha wahala wajen rainon 'yan biyu sun taso cikin gata da jin dad'i Alhaji ya shagwa6a su sosai sai abinda suke so akeyi musu duk da dai wani lokacin Hajiya tana nuna mishi illar yiwa 'ya mace gata tunda gidan wani zata amma sai ya bad'a ma idanun sa toka yace shi bai da kamar su tunda har ya cire rai da samun haihuwa. (Ba'a cire rai akan haihuwa ko wani abin daban, idan kaga Allah ya jink'irta kar6ar addu'ar ka to tabbas a lokacin ba alkhairi bane a gareka dan haka kowace addu'a da d'an Adam zaiyi Allah zai amsa mishi insha Allah mu cigaba da hak'uri kan al'amuran mu). A yanzu dai Alhaji suna zaune ne a Kaduna dan ya daina yawace-yawace da iyalen sa tunda ya samu arziki fiye da tunanin mai karatu. A yanzu babban d'an kasuwa ne wanda yayi fice ba ma a Nigeria ba har a k'asar waje, yana kutsawa ko'ina a dama dashi, yanada abokai manya-manyan 'yan k'asa da ma 'yan siyasa. FARHANAH da FAREEHA sun kasance masu bambancin halayyya ita FAREEHA bata da matsala dan bata d'auki girman kai ta d'ora a kanta ba, duk da mahaifin su mai kud'i ne hakan bai sa ta zama irin FARHANAH ba dan ita FARHANAH bata kallon kowa da daraja 'yan aikin gidan su ma sun sani dan basu jin dad'in yanda take musu ga kyara ga zagi FAREEHA tayi ta mata magana amma a banza sai dai ta k'yale ta kawai dan tayi nisa bata jin kira. Kowa yasan halin su ba d'aya FAREEHA tana da faran-faran da mutane a yayin da FARHANAH ta zamto mai k'yaliya ko gaisuwa sai taga dama zata yiwa mutum. A lokacin da aka ce za'a fitar dasu waje karatu 'yan aikin gidan su dad'i suka ji saboda FARHANAH, ita FAREEHA bata so tafiyar ba ma amma babu yanda zatayi umarnin daddyn su ne. A wani hutu da suka zo ne ita FAREEHA ta fitar da miji shima a can turai suka had'u d'an Abuja ne sunan sa Adeel iyayen sa masu kud'i ne a lokacin da suka had'u a can shi yaje hutu ne kawai k'asar dan yana aikin sa daman to shine ya ganta yace shi da aure yake sonta kuma yana son ganawa da iyayen ta ya zata a can suke da zama. A haka iyaye suka shiga maganar akayi komai kafin su koma, daddyn su yace FARHANAH itama ta fito da miji sai a had'a su ayi musu auren tace Allah ya kiyaye ita bata tashi wani aure ba 'yar k'arama da ita kuma bata ma ga wanda zata iya aura ba duk mazan basuyi mata ba. Kai jama'a kuji k'arya fa, arziki ba hauka bane yarinya. Karatun likita daddyn su yaso suyi amma ita FARHANAH tace bata so haka kawai kayan k'azanta taje tana ta6a jikin mutane, ita dai 'yar uwar ta sarkin hak'uri ta yarda tayi karatun likita na 6angaren haihuwa ita kuma *'YAR GADARA* ta karanci barrister. A wani hutu ne akayi auren su kuma har 'yan Borno ma sunzo dangin momyn su da na daddyn su, kakannin su biyu da kai biyu sun rasu. Abban Alhaji ya rasu sai mahaifiyar sa ita kuma Hajiya mahaifiyar ce ta rasu da jimawa ma. Bayan an gama shagalin biki aka kai amarya Abuja. Adeel yaso ta koma can turai ta k'arasa karatun ta tace sam bata zuwa ko'ina ta bar mijinta. Kaji masu tarbiyya da sanin ya kamata. Ita dai bata da matsala dan Adeel yana jin dad'in zama da ita tana mishi biyayya da kuma iyayen sa. Bayan shekara d'aya ta haifi d'an ta namiji Fawwaz. Daga nan kuma aka d'auki mai reno ta cigaba da zuwa school a nan Abuja har ta gama karatun ta. Abinka da harkar masu akwai nan da nan aka sama mata aiki a wani asibiti. Yanzu dai sunzo gaida iyayen ta da kuma sauran 'yan uwa, da auren 'yar uwar ta da bata samu tazo ba. Nasan masu karatu zasu ce ya akai FAREEHA bata zo auren 'yar uwar ta, to hakan ya faru ne sakamakon tafiya k'asar Canada da sukayi ita da mijinta da d'an ta, rakiya ce tayi ma oga kan wani aiki da yaje yi a can tace sai dai suje tare bata samu wata matsala daga wajen aikin ta ba. To kunji abinda ya hana ta halartar bikin gimbiya FARHANAH *'YAR GADARA.* *_CIGABAN LABARIN..._* Sai da FARHANAH ta d'auki wani lokaci kafin ta shirya su nufi gidan yarima. A bakin k'ofar aka bud'e musu suka shiga ba 6ata lokaci. Hadiman sa ne kawai a falon suna ganin su suka gaishe su cikin girmamawa suna mai mamakin irin wannan kama da su FARHANAH sukeyi. Kallon su FARHANAH tayi cike da isa gami da izza tace'' ina yake?" Sun gane ko wa take nufi d'ayan nasu yace'' ranki ya dad'e yana sama tunda ya hau bai sauko ba''. '' Ban tambayeka wannan ba''. Cewar FARHANAH sannan ta kama hannun FAREEHA tace'' muje''. Sama suka hau a tare suke takawa ko a falon saman ma bai nan FARHANAH tace su koma tunda bai nan FAREEHA ta kalleta tace'' ai wallahi baki isa ba sai kin shiga ciki kin fad'a masa ina son mu gaisa''. Cike da jin haushi taje ta tura k'ofar d'akin nashi ta shiga ita kuma FAREEHA ta zauna a bisa kujera mai zaman mutum d'aya. A kwance yake a k'asa kamar na ranar sai dai yau da bambanci tunda alamu sun nuna kamar bacci yake yayi pillow da hannayen sa singlet ce da dogon wando a jikinsa, d'akin ba haske sosai hakan ya bata damar takawa a hankali taje har inda yake ta tsaya tana kallon sa tana ta6e baki kamar dole. Shi wannan bai da wurin kwanciya sai a k'asa idan ya fita waje kuma ya rink'a wani d'aure ma mutane fuska k......tunanin ta ya katse ne sakamakon jin muryar sa a hankali yace'' lafiya kika yi min tsaye a bisa kai?" Innalillahi wai mutumen nan aljani ne ko kuwa dai? Yanda ta iske shi saï ka rantse kace bacci yake. Kallon banza tayi mishi tace'' ba zuwan kaina bane sister ce tace tana son ku gaisa in ba dan ita ba kai kasan babu abinda zai kawo ni wannan d'akin''. Murmushi kawai yayi dan Shi lamarin yarinyar nan yana bashi mamaki ita dai a dole tafi k'arfin kowa da komai. Ficewa tayi yabi bayan ta da kallo sai tafiyar yanga takeyi kamar bata son taka k'asa a haka ta fita. Zaune suke falon suna 'yar hira kad'an-kad'an har lokacin da yarima SYDEEK ya fito cikin shigar wani yadi mai laushi ruwan sky, fuska a d'an sake ya k'araso inda suke. FAREEHA ce ta zamo k'asa tana gaishe shi yace'' ah haba tashi ki zauna dan Allah ni ba haka nake ba''. Ta wutsiyar ido FARHANAH ta harare shi dan ta gane da ita yake. Zaman ta ta gyara har da d'ora k'afa d'aya bisa d'aya ta shiga danna wayar ta a yayin da suke gaisawa sosai shi da FAREEHA har yana tambayar ta mijinta tace yana lafiya kuma shima yana nan zuwa wasu ayyuka ne suka tsaida shi. FAREEHA ta kalli FARHANAH sannan ta maida kallon ta wurin yarima tace'' dan Allah ka k'ara hak'uri da halayen ta nasan kaima zuwa yanzu kasan yanda take to wallahi tun muna yara haka ta taso da rayuwar ta amma maybe nan gaba ta canza''. Murmushi yarima yayi yace'' no ba damuwa ai nidai abinda nakeso ta daina irin wannan ji da kai d'in saboda rayuwa bata da tabbas abin ya kai har wasu da suke cikin gidan nan sun san halin ta''. Tsagal FARHANAH tace'' malam da ka bani takarda ta da ba zaka k'ara ganina ba a rayuwar ka dan k'asar ma zan bari saboda kar Allah ya sake nuna min fuskar ka''. '' You see! Haka take duk abinda zai fito daga bakin ta ba maganar kirki bace''. Yarima ne yake ce ma FAREEHA haka. Kallon FARHANAH tayi tace'' please bamu wuri inason muyi magana ni da shi''. Tashi tayi tsaye dan daman duk zaman wurin ya gundire ta tace'' idan kinso kar ma ki bar wajen kinga tafiya ta''. Tana fad'in haka ta kad'a kai ta sauka. '' Dan Allah kayi hak'uri ba sai ka gaya min komai ba dan haka take tunda muka taso Allah yayi ta a haka kowa k'asa yake da ita haka take gani dan haka sai kayi hak'uri da ita har lokacin da zata canza wannan halin nata''. '' Ba komai sister ni tausayi ma take bani wallahi, sai kuma ina so kiyi hak'uri da abinda ya faru d'azu na zata ita ce''. 'Yar dariya FAREEHA tayi tace'' nasan ka zata ita d'in ce ai saboda kamanni da ka gani, ba komai ai rashin sani ne, ni da ita twins ne mu kawai mahaifan mu suka haifa Allah bai sa sun sake samun wata haihuwar ba''. '' Allah sarki ai kamannin sunyi yawa kuma sabon abu na gani dan bâ zata d'auko Al-Qur'ani ta karanta ba sai son girma ita dai ta kishingid'a bisa kujera su kuma suna mata firfita wasu suna fadan ci sai yanda tace shi ake yi ni kuma ina jiye mata halin rayuwa gadon mulki ba haka yake ba yau gareka gobe ga wanin ka yau ina mutanen farkon da suka hau gadon mulkin? Babu su amma ita gani take hakan dai-dai ne a gareta''. A nutse FAREEHA take sauraren shi har ya gama nan dai tayi ta bashi hak'uri akan ya rink'a nusar da ita ko zata canza ta dawo kan hanya dan itama bata son irin rayuwar da 'yar uwar ta takeyi. Yarima ya nuna mata ba komai shi bai da matsala da ita. Nan suka cigaba da tattaunawa har wani d'an lokaci sannan tayi masa sallama ta koma wajen FARHANAH. Gimbiya FARHANAH ba tana zaune tare da su Shafa'atu FAREEHA ta shigo tare da yin sallama suka amsa mata ita dai FARHANAH da k'yar ta amsa mata wai haushin ta takeji. Zama tayi a kujera tace'' magana zamuyi dake''. Bata ce komai ba sai kallon su Shafa'atu da tayi nan take suka gane nufin ta, tashi sukayi suka basu wuri. '' Ba'a nan ba muje sama cikin d'aki''. Cewar FAREEHA. Tashi tayi suka hau sama basu tsaya a falon ba d'aki suka shiga, a bakin gadon suka zauna FAREEHA ta kama hannun FARHANAH tace'' my blood dan Allah ki tsaya ki saurareni kiji abinda zance miki''. '' Uhmm ina jinki, me ya faru kuma?" '' Ba wani sabon abu bane maganar nan dai da nakeyi miki kullum ita ce, dan Allah ki rage wannan fad'in ran da jiji da kai irin wannan rayuwar sam bata dace dake ba, kuma duk naji yanda zaman naku yake ya kwatanta min baki daraja shi ko a gaban talakawan sa kina mishi mugun kallo kuma ko bai gaya min ba nasan zaki aikata hakan sannan gashi na gani da idanu na''. Shiru batayi magana ba sai FAREEHA ta cigaba da cewa'' kiyi sani shi fa miji shugaba ne a gidan sa duk talaucin sa balle ma mutum kamar yarima mai k'ima da daraja a idanun mutane ni wallahi na yaba da hankalin sa, ji fa yanda yake magana cikin nutsuwa dan Allah ke bai birgeki ba? Ace ki samu miji kamar shi ai abin alfahari ne ma dan haka ki nutsu wallahi gidan sarauta kike zai iya k'ara auren shi ko mace nawa yakeso kuma sakin da kike nema bazaki samu ba har abada''. '' Kin gama ko da saura? FARHANAH ta buk'ata. '' Na gama fad'i inji meye matsalar ki da shi mutum nutsatstse?" '' Ai ni na fad'a miki son shi ne ban yi dan bak'in ciki ma har da hanani aiki na bayan da kaya na ya ganni''. '' Ki kwantar da hankalin ki 'yar uwa da sannu zaki so shi insha Allah nidai inason ki bada had'in kai mu samu baby dan naga alamar har yanzu ba wani abu da ya faru a tsakanin ku''. FAREEHA ta k'arashe maganar cikin tsokana. Duka takai mata a baya tace'' Allah ya kiyaye ba dai ni ba''. '' Ke d'in dai yarinya sai maganar zuwa aiki karki manta gidan sarauta kike ba'a musu zarya kiji in gaya miki, ko ni da kika ga ina aikin nan k'warin gwiwar sa sweetheart ne wallahi da ba zanyi aikin nan ba ni nafi son inyi bautar ubangiji na aiki sam bai barin ka ka kula da gidan balle kuma mijinka dan Allah ki canza hali sister''. '' Sannu mai miji naji ashe kin iya wa'azi haka ban sani ba?" Hararen ta FAREEHA tayi tace'' kedai kika sani, wai kin kuwa san yarima har gida yake zuwa gaishe da su momy? Wallahi duk kwana kad'an sai sunje haka momy ta gaya min''. '' Oho masa duk neman wuri ne dai nidai bazai samu ba a wajena''. '' Humm Allah ya shiryeki dai, anjima zamu shiga fada in kai gaisuwa''. Kwanciya tayi a gadon tana cewa'' wash na gaji da wannan surutun naki please bacci zanyi''. '' Time d'in sallah ya kusa karki kwanta''. FARHANAH tace'' to naji sayyada''. Murmushi kawai FAREEHA tayi daga nan wayar ta tayi ringing tana d'agawa taga sweetheart d'in ta ne sai ta sake fad'ad'a murmushin ta tayi picking gami da yin sallama cikin wata iriyar murya mai sanyi da nutsuwa shima a nutse ya amsa mata yace'' matata ya kike?" '' I'm fine but I really miss my husband''. '' Me too, ya su momy da daddy da sauran jama'a?" '' Duk suna lafiya daddy bai k'asar ma''. Gyara zaman shi yayi daman a office yake yaji yana son jin muryar matar sa yace'' masha Allah! Allah ya dawo dashi lafiya ina amarya FARHANAH da yariman ta?" Kallon inda FARHANAH take tayi kafin tace'' uhmm amaryar yarima gâta nan kusa dani ai daman gaya maka zanzo gidan ta so ina gidan ta a yanzu haka''. '' Ok yayi kyau ki mik'a gaisuwa ta ga gimbiyar mu to''. Dariya tayi tace'' insha Allah zataji''. Yace'' ina baby na? Bashi inji ko da k'iriniyar shi ne''. FAREEHA tace'' am sorry yana gidan momy, a lokacin da na fito yana bacci ni kuma sai na k'yaleshi''. '' Ok shikenan zan barki haka nan ina wajen aiki, I will call you later ok?" Cikin shagwa6a tace'' haba sweetheart nifa ban gaji da jin muryar ka ba''. Farin ciki yakeji sosai a kullum yana gogiya ga ubangijin sa da ya azurta shi da mace mai hankali da tarbiya, sai da ya kwantar mata da hankali sannan sukayi sallama. Ajiye wayar tayi FARHANAH tace'' humm uhmm su miji manya ji yanda kike wani shagwa6a kamar yarinyar goye''. '' Ke kinga ki barni inyi kaya na mijina ne fa bani da kamar shi kuma ke daga ganinki sai kin fini shagwa6ar nan har dai ki shiga k'waryar manya zaki bani labari''. Kafin tace wani abu aka kira sallah daman akwai masjid na masarautar so ko mutum yana bacci zai jiyo kiran sallah. Tashi sukayi suka gabatar da sallah'r azahar kafin Shafa'atu tazo ta sanar mata an shirya abinci. Bayan la'asar suka shiga fada dan gaida mutanen fada. Sunje wajen mummyn yarima sannan akayi musu iso suka wuce wajen mai martaba saï saka musu albarka yake. Bayan isha'i yarima da kanshi ya maida FAREEHA gida dan yace bai buk'atar kowa a tare dashi. A hanya ma sai da FAREEHA tayi ta bashi hak'uri akan halayen 'yar uwar ta. Sai da ya shiga ciki ya gaishe su, FAREEHA kuwa da kaya nik'i-nik'i tazo kyauta mai yawa ta samo daga fada. Ko da ya dawo part d'in iyayen sa ya wuce ya gaishe su tukun ya wuce gidan gimbiya FARHANAH. 'Yan aikin ta duk sun tafi 6angaren su ba kowa a falon sai TV da take aiki ita kad'ai ga fitilu a ko'ina girgiza kanshi yayi ya d'auki remote ya kashe TV d'in sannan ya haye sama. Yana shiga d'akin nata ita kuma tana fitowa daga wanka ta bazo gashi wanda ba kitso daman ta jima batayi kitso bâ saï dai tasa ribbom ta kame shi. 'Daure take da farin tawul tayi kamar bata ganshi ba taje gaban dressing mirror taja kujera ta zauna tana taje kanta, a hankali ya tako har inda take duk tana ganin sa ta cikin madubin. Hannayen sa duk biyun yasa ya dafe jikin dressing mirror d'in ya saka ta a tsakiya gami da sunkuyowa ya d'ora ha6ar sa kan kafad'ar ta yace'' da nayi tunanin gidan ku ne haka ashe ke kawai Allah ya fitar da zakka a gidan ku, 'yar uwar ki yarinya mai hankali da nutsuwa ga sanin ya kamata amma ke sam baki da wa'yannan halaye why? Uhm?" Ture kanshi tayi tace'' kai malam banson iskanci da lalata fa, kai ka saba dole saï ka ta6a mace dan jaraba to ni a hir d'in ka dan nafi k'arfin ka''. Hannayen sa ya goya a baya sannan yayi murmushi yace'' ki daina yaudarar kanki idan ma so kike in ta6a kin ko ince ina sonki sam baki cikin tsarin irin matan da nake so an lik'a min kene kawai na hak'ura dan biyayyar iyaye''. '' Allah ma ya kiyaye in had'a jikina da k'azami irin ka, jibeka dan Allah wai nan kai d'an sarki baka dace da wannan ba''. Bai sake mata magana saï da ya bari ta gama tsab tasa rigar bacci duk yana d'akin kuma bata damu ba dan bai gabanta. Sai da ta gama ta kalleshi tace'' to malam kana iya fice min daga d'aki bacci zanyi ni banson fitina''. Zuwa yayi inda take tsaye tana nuna masa hanyar fita, damk'ar ta yayi ya k'arasa bakin gadon da ita yayi jifa da ita saï kuma ya haye gadon gami da sake rik'ota tace'' wai meye haka? Kai kam maye ne ko me?" Bakin sa ya had'e da nata tana gumtsewa ma saï da yayi nasarar sakata ta bud'e shi ya zuba mata yawun bakin sa kuma yak'i sakin ta dan hancin ta ya rik'e har ta had'iye yawun tukun ya sake ta tana ta k'ak'arin amai da gudu ta tashi ta nufi toilet wai ita a dole saï ta amayar da yawun yarima. Yana tsaye ta fito har da hawayen ta tace'' Allah ya isa tsakani na da kai mugu azzalumi ni zaka zuba ma k'azantar ka salon ka goga min wani ciwon''. Nufar ta yayi yana cewa'' ba daga yawu na tsaya ba zan zuba miki abinda baki isa ki amayar dashi ba''. Yana maganar yana binta ita kuma tana ja da baya........ *_Toh fa ya zata kaya kenan tsakanin FARHANAH da yarima?_* *_Ko dai su yarima ana son angwancewa ne irin wannan mugunta haka?_* *_Akwai match 'yan bayana ku biyoni muga ya zata kaya nayi gaba saï kunzo......🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀_* _NA GAISHE KU 'YAN HANNUN DAMA TA🙌🙌🤝_ *_DAGA AL'KALAMIN MUNATTU NE🖊🥴_* *_'YAR MUTAN KAZAY CE👑_* 💥💥💥💥💥 *_'YAR GADARA_* 💥💥💥💥💥 *_NA_* *_MAIMOUNATH O.G_* _(Mahnoor)_ _Wattpad@maimounathog_ *💫DA BAZAR-MU WRITER'S ASS💫* *~_We are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are d best among all....DA BAZAR-MU MUKE TUN'KAHO._~* *Page 51/55* *_DUNIYA🌍MAKARANTA📚🖊_* _NA YADDA DA WANNAN KALMA👆_ *_ZUWA DA KAI YAFI SA'KO🤷‍♀_* *_YOU HATE ME? PROBLEM TI E NIYEN🤷‍♀🤷‍♀_* *NEVER HATE JEALOUS PEOPLES. THEY ARE JEALOUS BECAUSE THEY THINK YOU ARE BETTER THAN THEM😜* *JEALOUSY WILL EAT UP YOUR GOOD DEEDS LIKE A FIRE EATS UP FIREWOOD🤗* *QUI PARLE DERRIÈRE MOI RESTERAS TOUJOURS DERRIÈRE MON DOS. AH OUI😉* *_SHI GISHIRI DA SUGAR KALAR SU 'DAYA CE BAMBANCIN SU YANA BAYYANA NE IDAN AKA 'DAN'DANA TO HAKA MUTANE SUKE, IDAN HAR KANA JIRAN GODIYA KO SAKAYYA DAGA MUTANE TO BABU SHAKKA ZAKA SHA MAMAKI, MUTANEN YANZU BASU GODEWA UBANGIJIN DA YA HALICCE SU MA BARE WANI. HAKA RAYUWAR SOCIAL MÉDIA TA GADA WASU MASU HANKALI WASU SA6ANIN HAKA, WASU MASU TUNANI WASU KUMA MARASA TUNANI. SHI MAI FUSKA BIYU TAMKAR SHE'DAN YAKE KAMAR YANDA SHE'DAN ZAI CUCEKA TO HAKA SHIMA MUNAFUKI MAI FUSKA BIYU YAKE, DUK ABINDA BAKA GANIN SA DOLE NE YAYI GALABA A KANKA SAIDAI 'KARFIN ADDU'A, WALLAHI DA IN ZAUNA DA MUNAFUKI GARA IN ZAUNA DA 'BARAWO TUNDA SHI SAI NA AJIYE ZAI 'DAUKA. YA ALLAH KA RABA MU DA MASU FUSKA BIYU. AMEEN DAN DARAJAR AL-QUR'ANI MAI GIRMA🙏🙏_* *_NA GAISHE KU 'YAN HANNUN DAMA🙋 TA MUSAMMAN 'YAN GIDANA WATO FORUM INA GAISHE KU KYAUTA NAGODE DA DEDICATION DIN KU ALLAH YA 'KARA MUKU BASIRA DA 'DAUKAKA KU SANI ANTY MAIMOUNATH NA YINKU 'YAN AMANA💞_* *_RANA IDAN TA TAKE SAI MAI WANKI YA SAMU GURBIN SHANYA, IN KA BI'DENI MU ZAUNA IN KUMA KA KYARENI INJA IN BAR MA HANYA......INJI ADO GWANJA🤣🤣_* *_A cigaba da gashi ko ya kuka ce fan'z😆😆🤷‍♀_* Share please🙏🙏 *_"YAR MUTAN KAZAY CE✍🏻👑_* 💥💥💥💥💥 *_'YAR GADARA_* 💥💥💥💥💥 *_NA_* *_MAIMOUNATH O.G_* _(Mahnoor)_ _Wattpad@maimounathog_ *💫DA BAZAR-MU WRITER'S ASS💫* *~_We are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are d best among all....DA BAZAR-MU MUKE TUN'KAHO._~* *Al-hamdulillah na tabbatar sak'o na ya isa inda nakeson yaje d'in, karku manta shi munafurci ba abin yi bane haka ma magulmaci bazai shiga aljannah ba. Allah ka haneni yiwa wani k'yeta🙏* *_DUK ABINDA AKEYI A TAFIN HANNU NA💁 A SOCIAL MÉDIA BA'A MUNAFURCI🤨 A RIN'KA SARA ANA DUBA BAKIN GATARI DAI.......MUNATTU NA KALLON KU...👀👀😉_* *_FAN'S A CIGABA DA GASHI KAWAI...🙅 KUNA SANI NISHA'DI😅🤣_* *Page 51/55* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *<><><><><><>* Yarima yana binta tana ja da baya har suka isa bakin k'ofar toilet ta kama zata bud'e dan ta shiga sai yayi karab ya rik'e hannun nata yace'' gudun me kikeyi? Abinda kikeso ne ai, banson wani jan aji muje kawai in taimaka miki tunda kin jima bakiyi ba''. Tsabar tak'aici idanun FARHANAH sunyi jawur amma batayi kuka ba dan a ganinta zai rainata idan yaga hawayen ta, cikin dakewa take tureshi tace'' kaga malam banson iskanci fa ka fita a hanya ta kuma Allah ya kiyaye in had'a jikina da naka kallar ka k'azami da kai kawai''. Sunkuyowa yayi kan fuskar ta daman hannayen sa ya tokare ginin ya sakata a tsakiya suna jin numfashin juna yace'' baki ma ga k'azanta ba yarinya, had'a jiki dani kuwa ki saka a ranki kamar kinyi dan ma kin samu za'a taimake ki ni ban ta6ayi ba ke kuma fa? So nawa kikayi? Da maza nawa kika tara? Turawa ko b'akar fata? Duk nasan baki da wannan amsoshin dan basu k'irguwa''. Wani irin k'arfi yazo mata ta tureshi da k'arfi amma yarima ko gezau baiyi ba dan namiji da mace ba zasu ta6a zama d'aya ba akwai bambanci sosai. Sulalewa tayi dan tabi ta k'asan shi saï ya d'ago ta da hannu d'aya yace'' ba zaki iya ba yarinya ni ba irin tsofaffin turawan ki bane ni jarumi ne''. '' A hakan? Ai ni baka isheni ba yaro da kai saï fitina da jarabar son ta6a jikin mace, kai nasan da 'yan mata nawa kayi fasik'anc.....''. Bata k'arasa ba yayi sama da ita sai kan gado, zuwan shi kawai ya jefa ta bisan gadon sannan yabi bayanta. Tureshi tayi tana toshe baki dan kar ya had'a bakinsa da nata amma ya kama hannun da k'arfi ya matse ba shiri ta saki tare da yin ihun wahala gashi ya sakar mata nauyin shi dan ya tabbatar mata da shi d'in ba yaro bane yace'' zan nuna miki ni ba yaro bane''. FARHANAH tace'' abinda ka saba kenan a can turai d'in to kaje ga karuwai a ko'ina cikin gari''. 'Kyaleta yayi ya shiga matsar ta lungu da sak'o kuma cike da mugunta yake aiwatar da komai balle ma da ya samu k'irjin ta, ai duk dauriyar FARHANAH sai ta fara hawaye yana ganin hawayen ta yayi murmushi ya mik'a hannu ya kashe fitilar d'akin nan da nan duhu ya gauraye ko'ina.... Duk abin nan fa bakin FARHANAH bai mutu ba sai Allah ya isa take masa tana kai mishi duka a k'irji amma ko a jikin sa sai ma bakin shi da ya kawo kan kunnen ta ya rad'a mata cewa'' meye kike wani fizgewa kamar wata sabuwar amarya? kin fa ta6ayi meye abin tsoron kuma?" A wahalce tace'' wallahi sai Allah ya saka min abinda kayi min mugu azzalumi''. '' Me nayi miki na mugunta? Tun ba'a je ko'ina ba kin fara karaya? aikin yaron ne zan nuna miki''. Zatayi magana ya had'e bakin su waje d'aya ya shiga nuna mata k'warewar shi akan harkar, murzarta yakeyi iya son ranshi wasa ya fara nisa yarima ya shiga kici-kicin cire mata rigar jikinta ita kuma tasa hannuwa biyu ta dafe gaban rigar ganin haka da yayi yasa ya kama rigar ya yaga ta a biyu ya shiga sarrafa albarkatun k'irjinta. FARHANAH anajin wuya amma ta kasa motsawa ma dan k'arfi ya sakar mata kuma babu bakin da zatayi ko da ihu ne balle taji dad'i. Wata iririyar ajiyar zuciya tayi jin bakin yarima akan k'irjinta, tamkar mayunwacin jinjiri haka yake mata FARHANAH bata san a wace duniya take ba bare ma da taji hannun sa a inda bata zato, hannu ta d'aga da k'yar ta kama nashi hannun amma mutumen naku ko aka wai inji 6arawon tagiya. Komai na jikinta yarima ya cireshi sai da yayi mata lakwas tukun ya fara k'ok'arin k'utsa kai cikin fadar ta.... Addu'ar saduwa da iyali yayi sannan ya fara dannawa cikin fadar gimbiya a zaton sa zaiji a key a k'ofar amma ga mamakin sa sai yaji a gark'ame take alamar ba'a ma ta6a shiga wannan fada ba. Yaso ya k'yaleta amma da ya tuna maganar ta na ce masa yaro sai ya cire tausayin ma ya danna wanda daga shi har ita babu wanda bai sha wahala ba tunda duk sabon shiga ne wallahi yayi zaton ita ba virgin bace ashe dai abin ba daga nan yake ba. Ihun wahala FARHANAH ta saki a hankali dan bâ zata iya d'aga ko da hannun ta ba fuskar nan kuwa ruwan hawaye ne ya wanke ta tas, yarima aiki yake tuk'uru ya ma manta da gimbiya FARHANAH yake. *(Ina k'iyayyar dake tsakani? FARHANAH zata daina yi masa fitsara? Zasu daidaita suyi zama irin na kowane ma'aurata? Wallahu a'alam zamu bisu dai mu gani).* In tak'aice muku labari a k'arshe dai FARHANAH sume mishi tayi dan wahalar tayi mata yawa yarima jarumin namiji ne, ba raggon namiji bane kamar yanda take fad'a. Zuwa wani lokaci ya mirgina gefe rabu da ita yana mayar da numfashi can ya tashi zaune gami da kunna fitila yanayin yanda yaga FARHANAH ne ya saka shi a tashin hankali, da sauri ya matso kusa da ita ya ta6a ta yaji bata numfashi ai kuwa ya sauka a gadon yaje ya kawo ruwan sanyi a fridge da ke d'akin ya yayyafa mata nan take ta sauke ajiyar zuciya gami da cewa'' wayyooo Allah na momy kizo zai kashe ni''. Tashin farko da yaji tausayin ta ya d'arsu a zuciyar sa sai wata nadama ta kama shi me yasa ma yayi mata haka? Me ma ya kai shi kusantar ta? Wata zuciyar tace dashi saboda tace maka yaro. Ganin wannan tunane-tunanen bazai yi masa ba ya tashi ya kai glass cup d'in bisa fridge ya dawo dan ya taimaka mata yana kai hannun sa ta bige hannun tace'' don't touch me! Azzalumi'' ta k'arashe maganar cikin kuka. Kan kunnen ta yazo daga bayanta yace'' am sorry ki bari in taimaka miki''. '' Banson wani taimakon ka tashi ka fice min da gani banson in k'ara ganin mai irin kammanin ka ma''. Bai ce komai ba ya dafe kai ya rasa ya zaiyi da ita sai kuma ya d'auki wayar sa ya duba lokaci k'arfe 1am a hankali ya furta ya salam gashi FARHANAH sai kuka takeyi kuma ta hana ya taimaka mata saboda taurin kai irin nata. Tashi yayi ya shiga toilet d'in ta ya tsarkake jikinsa sannan ya kama hanyar fita daga d'akin sai yaji muryar ta tana cewa'' Allah yayi maka abinda kayi min mugu azzalumi i hate you...''. Taja maganar cikin wahala. Girgiza kai yayi ya fice ba tare da yace mata k'ala ba, a falon ta na k'asa ya tsaya yana tunanin abinyi a yanzun yaso kiran mummyn sa sai yaga rashin dacewar hakan, har zai kira doctor itama sai kuma ya fasa yaga itama d'in bai dace ya kira ta warhaka ba duk da bata da miji. Tunanin sa ya tsaya akan jakadiya, ai nan da nan yaje wurinta d'akin ta ya buga can tazo ta bud'e ganin yarima a tsaye yasa tace'' d'ana lafiya kuwa a wannan lokacin?" 'Dan sosa k'eya yayi yace'' uhmm dan Allah taimako nakeso kiyi min''. '' Fad'i ko meye idan har bai fi k'arfi na ba to zanyi maka shi''. '' Nayi 6arna ne kuma ta hana in taimake ta so please kije yanzu dan tana buk'atar taimako''. Jakadiya ta gane komai tayi d'an murmushi tace'' to shikenan ba komai yanzun nan zan tafi''. '' Yauwa nagode sosai''. Inji yarima. '' Ah haba ka daina gode min dan Allah ai kai d'ana ne kuma ai babu abinda zaka nema ba'ayi maka shi ba''. Godiya ya k'ara yi mata gami da ficewa. Da k'yar FARHANAH ta yadda jakadiya ta taimaka mata dan ma dai babu yanda zatayi ne amma irin wannan al'adar har yaushe ace wani zai maka komai dan miji ya kusance ka a ranar farko gaskiya baiyi ba, shi kuma mugun ai zata had'u dashi ne har da zuwa yayi ya tozarta ta. FARHANAH tana kuka jakadiya tayi mata komai irin na al'ada sannan ta fito ta barta a toilet, jakadiya tana tattare bedsheet d'in tana ta murya sai maganar zuci takeyi tana cewa madallah da d'ana yayi sa'ar mata tagari gimbiya ta kawo budurcin ta d'akin mijinta, ninke bedsheet d'in tayi ta ajiye gefe sannan ta shimfid'a wani sabo milk color mai kyau. Yau ko'ina jakadiya ta gyara mata d'akin ya canza kala ga k'amshin air freshner yana tashi, tana gamawa ta fice da zanin gadon a hannun ta. Gimbiya FARHANAH anji dad'in ruwa ank'i fitowa daga cikin ruwan ma, kwance take cikin kwamin idanun ta lumshe amma suna tsiyayar hawaye tak'aici kamar ta kashe kanta haka takeji, wai yau wani can banza ne ya raba ta da abinda tafi so take tanadin sa shekara da dama lallai kuwa ya taro match. Ahayyee cakas kaico FARHANAH na tausaya miki dan babu abinda zakiyi ma yarima ki rama abinda yayi miki, i'm sorry to say miji yafi k'arfin banza ki iya bakinki ko kuma ki k'one yarima dai ya sha lagwada....hahaha kar ta ji ni dai...... 'Kamshin da ruwan wankan yakeyi ne ya hana FARHANAH fitowa daga ciki ga k'asanta da ya dameta da zogi jarababbe mai bin mata kawai ta fad'a a zuciyar ta tana k'ara sakin wani marayan kuka. Lokaci mai tsawo ta d'auka sannan tayi wankan tsarki ta fito tana d'ingisawa tare da cije lips d'in ta saboda rad'ad'in da takeji. 'Dagowar da zatayi sai taga d'akin nata tamkar ba shi bâ, komai an canza gwanin sha'awa amma duk da haka batayi wani murna ba sai ma bak'in cikin da yake cin ta game da abinda yarima yayi mata. Washe gari tuni labari ya baza masarautar kuma an sanar akwai gangarumin wasa da za'a wuni anayi haka al'adar masarautar take. Labari da a lokacin da yaje ma mummyn yarima taji dad'i sosai dan jakadiya ce ta kai musu labarin gimbiya ta cika d'akin ta. FARHANAH kuwa tana cikin blanket ta k'udundune waje d'aya dan saboda sanyin da takejin yana ratsa duk wata ga6a ta jikinta ga kanta da yake mugun sara mata. Tana nan kwance akayi knocking bata iya ta amsa ba sai aka shigo, jakadiya ce ita da Shafa'atu suka k'araso kayan da yake hannun Shafa'atu jakadiya tace'' ajiye su kije ki had'o ma gimbiya abinda zata ci kiyi sauri''. Shafa'atu ta amsa da'' to''. Cikin ladabi dan jakadiya tanada matsayi a masarautar itama, bayan ta fita ne jakadiya taje kusa da gadon tace'' sannu 'yata ya jikin naki?" Cikin zubar da hawaye tace'' ba sauk'i''. '' Ashsha! Allah sarki haka rayuwar auren take 'yata sai kinyi hak'uri a sannu zaki saba''. FARHANAH a zuciyar ta tace da me zan saba? Wannan ma tsautsayi ne da k'addara in ba haka ba wannan d'an iskan bai isa ta bashi kanta ba, kuma ba wani yafewa zatayi ba. Ferfesun kan rago aka had'o mata tare da kayan marmari sai wanda take so zata ci, Shafa'atu tayi mata ya jiki ta fice tukun jakadiya ta tilasta mata ta d'an ci kad'an sannan tasha maganin sai yamutsa fuska take, bayan ta gama jakadiya ta sanar mata cewa akwai masu shirya ta ba jimawa zasu k'araso, ta nuna mata kayan da suka shigo dashi su zata saka in amjima akwai wasa can 6angaren mai martaba. Ita dai da idanu take binta batasan meyasa bata iya yiwa jakadiya musu ko rashin kunya ba. Bayan ta fice ne ba jimawa suka k'araso da k'yar ta iya fitowa falon sama. Kitso da lalle aka fara yi mata ta dawo tamkar amarya kai tafi ma hakan dan ko a lokacin tana amarya ba'a mata irin wannan k'walliya ba tunda ta nuna bata ra'ayi. Da aka gama kuma ta shiga wanka yanzun ma har an had'a mata ruwan d'umi da kuma ruwan wanka mai had'in turare wanda ke zaunawa jikin mutum bai saurin fita. Tana fitowa tayi turus ta tsaya tana musu kallon mamaki FAREEHA ce da Haulat a zaune a d'akin. Taso tazo wajen su da gudu saidai ba hali dan raunin da ke jikinta bazai bari tayi gudu ba. A hankali ta tako har inda suke nan take ta fad'a jikin FAREEHA ta fashe da wani irin matsanancin kuka tana cewa'' sister kin gani ko? Kin ganshi ko? Ya zubar min da mutunci ya tozarta ni ya raba ni da abinda na jima ina tattali......''. Kuka yaci k'arfin ta su kuma sai aikin rarrashi suke da ban baki da k'yar suka samu tayi shiru sai ajiyar zuciya take. FAREEHA tace'' kiyi hak'uri ai duk matar aure daga haka ta fara kowacce saï taji wuyar kafin tazo ta saba dan haka hak'uri kawai zakiyi''. Kallon FAREEHA tayi tace'' ba shi nayi wa tanadin kaina ba, wannan bai isa ya zamo *mijin aure na* ba, wallahi dashi gara ko waye ma in aura dan na tsane shi, na tsane shi meyasa ba zaku gane bane''. Ta k'ara rushewa da kuka. Toh! ikon Allah FARHANAH irin wannan k'iyayya haka ai tayi yawa. *(Ba'a son mutum yayi zurfi cikin k'iyayyar wani, haka ma soyayya ba'a zurfafa ta dan wahala zaka sha)* Sun samu ta shirya cikin kayan da jakadiya tazo mata da su tayi kyau tubarkallah masha Allah! Abin ba'a cewa komai. Masarauta ta kacame da shagulgula FARHANAH sun had'u da yariman ta a wajen taron dan kujerar su ma a waje d'aya aka ajiye kamar yanda akeyi na ango da amarya. Yarima fa sai k'yallin goshi akeyi an kwashi gara ba wasa ba a yayin da ita kuma FARHANAH take aika masa sak'on harara ta k'asan ido bata san cewa ya ganta ba sai ya sunkuyo dai-dai kunnen ta ya rad'a mata cewa........ *Na daina kashe kaina inyi tayi muku readmore dayawa tunda wasun ku basuyin comments idan na gama wannan novel din wallahi wani group zan bud'e masu comments su shiga wa'yanda basuyi kuwa ko sun shiga wallahi waje zanyi da su ko da ciki d'aya muka fito da mutum....* _NA GAISHE KU 'YAN HANNUN DAMA TA MASU BIBIYAR NOVELS 'DINA🙏_ *_'YAR MUTAN KAZAY CE👑_* 💥💥💥💥💥 *_'YAR GADARA_* 💥💥💥💥💥 *_NA_* *_MAIMOUNATH O.G_* _(Mahnoor)_ _Wattpad@maimounathog_ *💫DA BAZAR-MU WRITER'S ASS💫* *~_We are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are d best among all....DA BAZAR-MU MUKE TUN'KAHO._~* *_This page is dedicated to: MARDIYA M.KA'OJE(maman Ahmad), HAUWA SAUDIYA(maman Fairuza), MARYAM ISHAQ(sister na), UMMU BASHEER(sweet sister), BADIYYERT BEAUTY QUEEN(ma chérie), JAMILA MUSA(anty Meelat), HAWWA MUH'D USMAN(real~smasher), HABIBA IDRISS(Hubbeey), HALIMATUS-SADIYA(Leematy)_* *_Wa'yannan mutanen bazan ta6a mantawa dasu ba, 'yan amana ne, masoyan gaskiya ne, tamkar 'yan uwa muke tsakanin mu ba ha'inci ba cin dunduniya ba cin amana saï aminci a tsakani ina jin su har k'asan heart❤ d'ina baki bazai iya fayyace yanda nake dasu ba saidai ince Allah ya d'aukaka zumuncin har abadan, Allah ya gina katangar k'arfe tsakanin mu da shed'anun mutane da aljanu, ba sonku nake ba k'aunar ku nake💘 ban ta6a ganin mutanen da suka san ya kamata ba irin ku. I really luv you....lodi-lodi....💖💘_* *_Zum ma hakkini kandiri kannu rakkenah🤷‍♀_* *Page 56/60* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *°°°°°°°* Sunkuyowa yayi dai-dai kunnen ta ya rad'a mata cewa'' how are you? Hope jikin da sauk'i ko?" Batayi magana ba sai k'afa da tasa ta take nashi k'afar da k'arfi dan mugunta, yaji zafi amma ya dake ya k'ara cewa'' ba zaki ta6a hucewa ba matar yaro''. Kawar da kanta tayi ganin duk abinda take masa bai jin haushi ita kuma ba haka taso ba. Wuni akayi ana kad'e-kad'e da bushe-bushe kai kace yau ne bikin yariman dan wasa na musamman aka gudanar, FARHANAH tasha kyaututtuka a ranar dan daga kan waziri har kan sauran mabiya bayan sa sunyi mata kyauta ta bajinta to bare kuma uwa uba sarki da uwargida ai abin ba'a cewa komai sai sambarka. Taro ya watse lafiya lau Al-hamdulillah komai ya tafi yanda akeso cikin tsari kuma. Daga nan wajen taron gidan mummy aka wuce da FARHANAH, bayan sallah'r magrib su FAREEHA sukayi haramar tafiya gida ai kuwa FARHANAH tace sam bata san wannan bâ, da k'yar ta rarrashe ta tace'' kinga sweetheart yayi text zai shigo yau d'in nan dole inje in san me zan tanadar masa''. '' To shikenan ni daman nasan kun daina k'auna ta ku tafi d'in kawai''. A haka suka rabu tayi fushi sosai ko sallamar su bata amsa musu ba tayi kwanciyar ta inda aka kawo ta wanda bata san dalilin yin haka ba ita dai 'yar kallo ce. Bayan sun tafi ne sai ga mummy da kanta ta shigo inda take ganin ta yasa ta tashi zaune tana d'an cije le6e dan har yanzu bata dawo yanda takeso ba. Cikin sunkuyar da kai ta gaishe da mummy ita kuma sai ta zauna kusa da ita gami da dafa kafad'ar ta tace'' 'yata ki daina jin kunya ta ni mummyn ki ce, ki d'auka ke da yarima duk d'aya kuke a wuri na, idan kuma akwai abinda yake yi miki wanda bakiso ki sanar min in d'auki mataki a kanshi kinji ko?" '' Ba komai mummy''. FARHANAH ta fad'a cikin sanyin murya, da yarima ya biyo halin iyayen sa da ya zama mutumen kirki amma da yake zaman turai yayi duk ya d'auko wasu d'abi'u na iskanci da rashin kunya, duk FARHANAH ce ke wannan maganar a cikin heart d'in ta. Mummy tasa aka kawo mata kayan cima kala-kala kamar a gidan biki dan abin har mamaki yake bata irin wannan k'aunar da suke nuna mata ne ma yasa taji d'an sanyi kad'an saboda cike take da yarima. Sai 9:15pm yarima ya shigo 6angaren mummy a lokacin ta fito daga d'akin da FARHANAH take dan time by time take zuwa dubata da kanta saboda zazza6in da ya rufe ta. Hadiman ta suka gaishe shi sannan suka fita d'aya bayan d'aya dan basu wuri su zanta da d'anta. Yarima kuwa zama yayi gami da cewa'' wash mama nagaji dayawa wallahi''. 'Karasowa tayi tana hararen sa tace'' wai da suna nawa zaka kira ni ne?'' '' Kowanne ya dace da ke mummy na ai bani da kamar ki dan kinyi min komai a duniya, thank you my sweet mum''. Filon kujera ta d'auka ta jefa masa tace'' ni ba ma wannan bâ daman ina neman ka kuma ko da baka zo ba zan sa a nemo min kai''. '' To mummy Allah yasa dai ba wani laifin nayi ba''. '' Tashi kaje matar ka tana wancan d'akin a kwance ba lafiya, waye yace maka ana haka? Kazo ka aikata ma mutane shirme kawai duk kasa yarinya ta fige a rana d'aya kawai''. Kai ya sunne yana sosa k'eya ya na d'an murmushi ya tashi ya tafi d'akin da FARHANAH take. A kwance ya iske ta ga abinci kala-kala ga kuma kayan marmari amma ta kasa ci dan tak'aici. Yana shu'umin murmushi ya k'araso bakin gadon ya zauna gami da cewa'' uhmm sannu amaryar yaro ya jikin naki?" Cikin zubar da hawaye tace'' ina ruwan ka mugu azzalumi me kuma kazo yi nan?" Sunkuyawa yayi dai-dai fuskar ta har suna jin numfashin juna yace'' don't worry wife ai ba zanyi a nan ba sai mun je can''. '' Bazan ta6a yafe maka ba wallahi, kuma sai naje asibiti an cire min dattin da ka saka min a jiki haka kawai ka goga min wata cutar''. Me yarima zaiyi in ba dariya ba abin mamaki shi da bai cika yin dariya sosai ba amma da yake wannan ta mugunta ce har da rik'e ciki yake, bayan ya tsagaita ne yace'' am so sorry dear kin makaro dan dattin da kike magana tuni ya zauna a cikin marar ki ba kuma wani likita da ya isa ya fidda shi dan haka gara ma ki hak'ura''. Tashi tayi zaune gami da cakumo gaban rigar sa tace'' ko kai maye ne sai an cire min k'azantar nan kuma sai ka sake ni''. Ta k'arashe tana mai fashewa da sabon kuka kuma rigar shi tana a hannun ta. '' Auren mu ba saki, karkiyi tunanin cewa so ne yasa na kusance ki, a,a kawai dai na nuna miki ne ba'a raina namiji duk k'anantar sa balle ma ni kinyi kad'an kice min yaro, namiji ba'a nuna mishi *GADARA*, isa, fifik'o, ke kuma duk kinada su, sai d'an banzan girman kan tsiya sai kace 'yar k'aruna, kud'i, mulki duk ba abin tunk'aho bane dan wasu masu arzikin yanzu sun zama talakawa, wasu masu mulkin sun shud'e saboda shi gadon mulki gado ne na aro dole kayi ka bar ma wani dan haka kibi duniya a sannu duk arzikin ku wasu sun fiku''. Tunda ya fara magana take kallon shi saï taji ya d'an birgeta yana magana ne cikin hik'ima da nutsuwa ba wai fad'a yake ba duk da har yanzu tana rik'e da wuyan rigar sa. '' Zaki sakar min riga ne ko sai kin gama kallon nawa?" Wata irin kunya ce ta lullu6e ta sai ta sake shi tana share hawayen ta tace'' baka isa in kalle ka ba, kai waye da har zan kalle ka?" '' Mijin *'YAR GADARA*". Yarima ya bata amsa kai tsaye gami da d'aga mata gira ita kuma ji take kamar ta shak'e shi ya mutu kowa ma ya huta wallahi k'yank'yamin jikinta kawai takeji saboda ta kasa samun sukunin abinda ya faru jiya. Ba tayi aune ba saï jin hawaye tayi suna bin kuncinta shi kuma yarima yasa hank'ici yana goge mata tuni ta dawo cikin hayyacin ta, ture hannun sa tayi tana maka mishi wani mugun harare a dai-dai lokacin akayi knocking k'ofar yarima ya bada izinin shigowa. Wata 'yan mata ce cikin masu hidimar Hajiya(mummyn yarima) ta shigo ta sanar musu sak'on Hajiya tana son ganin su a falo. Hawayen ta goge sannan ta sauka daga gadon tayi gaba yana zaune yana kallon yanayin tafiyar ta yau duk ta zama wata so silent amma dai jikin fa dan bakin kam bai mutu ba. Kafin ta k'arasa tuni yayi saurin tashi ya iske ta gami da jingina a bakin k'ofar ya kalle ta sama da k'asa yace'' wai a haka zaki fita? Kinga irin tafiyar da kikeyi kuwa?" '' Matsa min in fita ni banson iskanci da rashin kunya in ma meye ai kai ka ja gara a gani a san dai kai d'in fuska biyu ce da kai mugu kawai''. Kamota yayi ya had'e bakin su sai da ya tsotse mata baki cikin mugunta sannan ya sake ta yace'' wannan kad'an daga cikin irin muguntar tawa sauran saï anjima''. FARHANAH tace'' Allah ya isa wallahi *an cuceni* da aka had'ani da kai''. Handle d'in k'ofar ya kama ya bud'e suka fita a tare kamar basuyi komai ma saï dai kana kallon FARHANAH zaka gane tasha kuka. A kishingid'e akan lallausan carpet suka iske mama ta sallami kowa saï ita kad'ai, tana ganin su tayi murmushi tace'' daughter sannu zo nan kusa dani". Zuwa tayi ta zauna kanta a sunkuye saï mummy ta tashi zaune da kyau tasa hannu ta kama fuskar FARHANAH tace'' daughter kuka kikayi ne?" Kai FARHANAH ta girgiza mata alamar a,a saï mummy tace'' kamar ya a,a bayan ga fuskar ki ta nuna alamun kinyi kuka sosai, gaya min in wani wuri yana miki ciwo kinji ko? Ki d'auke ni kamar momyn ki karki 6oye min damuwar ki''. '' Ba komai mummy''. Ta fad'a cikin sanyin murya. Mummy ta kalli yarima da hankalin sa yake akan wayar sa kamar bai jin su tace'' son ko dai wani abin kayi mata ne?" 'Dagowa yayi yace'' ni kuma mummy? Gata nan ki tambayeta daman na iske ta tana kukan ta''. Cewar yarima. Mummy ta jefe shi da wani irin kallo wanda ya saka shi nutsuwa ya kama kunnuwan shi duk biyun yace'' sorry mum da gaske nake maybe zazza6in ne ke damunta har yanzu''. '' Duk kai kaja ai kana abu kamar ba doctor ba, kuje 6angaren ku ka sake duba ta in da akwai wata matsalar a sanar min''. Kallon FARHANAH yayi yace'' an gama ranki ya dad'e yanzu kuwa''. Ya k'arashe yana ma FARHANAH murmushin da shi kad'ai yasan ma'anar sa''. Har zasu tashi mummy tace'' kafin nan inaso in gaya maka abban ka yace nan da kwana biyu zaku bar k'asar kai da matar ka dan haka ku zauna cikin shiri gobe ka kaita tayi sallama da 'yan gida''. Murna yarima yake yace'' yauwa mummy thank you amma ni fa da nafison inje ni kad'ai bazan dad'e ba ma''. '' Kai wallahi ka fita daga idanu na kaji ko? Yo ai baka ma isa bane, kuma ba wani jimawa zakuyi ba just two months sai ku dawo saboda bikin bud'e asibitin ka''. Yarima yace'' to shikenan Allah ya baki hak'uri yanda kika ce hakan za'ayi''. Mummy ta kalli FARHANAH tace'' daughter tashi ku tafi dare yana yi karki biyewa wannan mai shirmen ya sameni kamar wata granny d'in sa''. Cikin ladabi tayi mata sallama tayi gaba shi kuma yarima zuwa yayi kusa da mummy cikin murya mai kama da rad'a yace'' mummy nace ba.....kiyi addu'a Allah ya kawo miki jika nan kusa''. Hannu ta kai zata kwad'e shi ya gudu yana dariya. Ita har tayi gaba abin ta dan daman bata son su had'a ko da hanya ce. Kafin ta k'arasa bakin k'ofar ta tuni ya rigaye ta yace'' sannu ranki ya dad'e gimbiya matar yarima ai bai kamata ba ace kamar ki kina tafiya a k'asa ba, ko in sa a kawo mota ne a k'arasa dake ciki?" Hararen shi tayi gami da ture shi tayi shigewar ta shima ya biyo bayan ta har cikin falon a nan suka iske su shafa'atu suna jiran dawowar uwargidan su. Durk'usawa sukayi suna mata sannu da zuwa da kuma tambayar jikin ta, dan tak'aici da hannu kawai ta amsa musu tayi hayewar ta stairs d'in. Yarima ma ya k'araso suka gaishe shi ya basu umarnin duk suje makwancin su ba damuwa, godiya sukayi masa sannan suka fice yaje ya rufe k'ofar falon ya kashe fitilun k'o'ina sannan yabi bayan FARHANAH. 'Dakin ma a bud'e ya iske shi. Shigewa yayi kai tsaye, bata cikin d'akin amma yaji k'aran ruwa a toilet. Saboda tsokana irin ta yarima zuwa yayi bakin k'ofar toilet d'in yace'' a bud'e min in shigo mana''. '' Ko kai maye ne kurwata tafi k'arfin a lashe ta mugu kawai''. Inji FARHANAH. Sai yarima yace'' a,a ba kurwar ki zan lashe ba, kema ai kinsan abinda nazo lashewa''. '' 'Dan iska mai bin mata marar kunya, ba zaka k'ara cin galaba a kaina ba''. '' Karki damu na yau yafi na jiya dad'i fa yarinya karkiyi ma kanki bak'in ciki da wani jan aji dan nasan kinaso''. Wani irin ihun tak'aici FARHANAH ta saki cikin kuka tace'' wallahi sai Allah ya saka min ka cuceni ka cuci rayuwa ta, ba kai nayi wa tanadin budurci na ba''. '' Sai kuma gashi ni na kar6eshi ba''. '' Wayyooo Allah momy na". Abinda FARHANAH ta fad'a kenan. Yarima yace'' indai dan ni kika k'i fitowa to na tafi''. Hararen k'ofar toilet d'in tayi kamar shi ta gani a jikin, fitowa tayi d'aure ta tawul a k'irjin ta... Batayi aune ba sai ji tayi anyi sama da ita yace'' wa na kama? Ashe ke har yanzu da sauran ki baki san komai ba''. Dukan k'irjin ta takeyi tana cewa'' ka sauke ni kaji malam''. Bai ce da ita komai ba ya nufi katafaren gadon ta ya jefa ta a bisa yana murmushi mai cike da ma'anoni masu tarin yawa ya hau gadon gami da kashe fitilar d'akin ya bar mai duhuwa ta bedside drower tuni d'akin ya d'auki wata kala daban gwanin ban sha'awa...... Janyota yayi yace........ *_Need your du'a fan'z wallahi bani da lafiya k'arfin hali ne kawai._* Ku muje zuwa mana🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀ *_'YAR MUTAN KAZAY_*👑 💥💥💥💥💥 *_'YAR GADARA_* 💥💥💥💥💥 *_NA_* *_MAIMOUNATH O.G_* _(Mahnoor)_ _Wattpad@maimounathog_ *💫DA BAZAR-MU WRITER'S ASS💫* *~_We are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are d best among all....DA BAZAR-MU MUKE TUN'KAHO._~* *<><><><><><><><><><><><><><><>* _This page is for you my brothers: *H@SS@N ATK & PRINCE ABD@LL@H*, dubun gaisuwa da fatan alkhairi zuwa gareku, Allah ya saka muku da mafificin alkhairi, amincin Allah yayi ta wanzuwa a gareku Allah ya baku abinda kuke nema duniya da lahira, nagode sosai da k'ok'arin ku a kaina. Ina yinku over💞 Allah ya bar zumunci🤝_ *<><><><><><><><><><><><><><><>* *Page 61/65* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* ********Yarima janyota yayi yace'' haba wa yarinya ai nayi miki nisa wajen hangen nesa duk da dai kince ni yaro ne''. Tureshi takeyi amma ko gezau baiyi ba sai ma k'ara matse ta da yayi tace'' ka sakeni karka cinyeni a d'anya tunda naga iskancin da kukeyi da karuwan ka ne ya motsa''. 'Yar dariya yayi yace'' karuwai na? Wai har kin fara kishi na tun kafin in auro wata amaryar?" '' Ka auro d'ari ma in kaso ni babu ruwana ka fita a harkata''. '' Ni na isa in fita a harkar ki bayan zuwa nayi ma ki k'ara min abin jiya''. '' Allah ya kiyaye ai wancan ma sai Allah ya saka min abinda kayi min''. '' Ai dai bâ haramun na aikata ba ko?" Banza tayi dashi shi kuma sai shige mata yake yi yana son ya ji shi a duniyar maji dad'i amma shi likita ne yasan ba zata iya jurewa ba. Hawayen ta yaji sun zubo mishi a k'irji saboda kanta ya matse a k'irjin sa yace'' wai yaron kike tsoro haka har da kuka?" '' Ka k'yaleni haka nan banson ka ra6i jikina na tsaneka ko anayi dole ne?" Kunnen ta ya d'an ciza yace'' yes! Anayi dole tunda gashi nan anyi mana dole daga ni har ke, na tabbatar kema bâ sona kikeyi ba kamar yanda banjin ko d'igon sonki a raina ba dole mu rungumi k'addara a yanda tazo mana''. Can k'asa tace'' mugu kawai ka sakeni in tafiya ta tunda ka samu abinda kakeso''. Sakin ta yayi ta tashi daga gadon ta d'auki pillow taje kan carpet ta kwanta yayi kamar baiji ma me tace ba sai shima ya tashi ya fice daga d'akin. FARHANAH bata sake ganin yarima SYDEEK ba sai washe gari shima a bakin mota suka had'u da misalin k'arfe 5:00pm dan zuwa yi ma iyayen ta bankwana. A motar ma su biyu ne a baya sai driver da kuma wata motar na bin bayan su har unguwar su FARHANAH, cikin su babu wanda ya yiwa d'an uwan sa magana har suka isa k'ofar gidan, mai gadi ya bud'e musu gate suka shige. A d'akin saukar bak'i aka sauke su suna zaune ne a falon da ya tsaru yasha kaya ba k'arya an kashe naira a nan. FARHANAH ciki ta shiga tana ganin momyn ta sai ta fad'a jikin ta gami da fashewa da kuka momy tace'' to meye abin kuka kuma daga shigowar ki?" '' Momy k'yaleta dan Allah''. Cewar FAREEHA tana mai hararen FARHANAH. FARHANAH cikin kuka tace'' ke kuma ina ruwan ki ai daman bakin ku d'aya ke da shi, mama nidai babu inda zan bishi ya kasheni mugu ne azzalumi''. '' Subhanallahi! Mijin naki kike cewa haka? Kar in sake ji wallahi daddyn ku zai sa6a miki idan yaji wannan maganar duk kuwa da son da yake miki''. '' Momy ki rabu da ita ai ko tana so ko bata so tafiya ta zama dole, dole ne kibi mijinki''. '' Ke ki fita a harka ta wai ina ruwan ki ne?" FAREEHA ta kalli momy tace'' momy wallahi yarima mutumen kirki ne mai sanyin hali ita dai ce mai matsalar baki ga iskancin da takeyi masa ba''. '' Duk dai ku bar maganar nan jeki fad'a wa daddyn ku cewar yarima yana son su gaisa sai ayi masa iso falon nashi''. Tashi FAREEHA tayi tace'' to momy''. Ta wuce part d'in daddyn su FARHANAH sai maka mata harara takeyi. Anyi ma yarima iso wajen daddy sun gaisa cikin girmamawa yarima yake gaishe da daddy, daddyn kan shi yana mai yabawa da hali irin na yarima dan duk zuwan da yake yana isko shi a gida kuma ya lura yaron akwai tarbiyya ga nutsuwa. Mijin FAREEHA ma yazo sun gaisa da yarima sun amshi number'n juna dan yin zumunci. Da zasu tafi momy tayi ma FARHANAH fad'a sosai akan tayi wa mijinta biyayya tayi abinda ya saka ta sannan ta bar abinda ya haneta. Haka a hanyar su ta komawa ma babu wanda ya yiwa d'an uwan sa magana kamar dai yanda suka zo gidan su FARHANAH, ko da suka koma d'in ma kowa part d'in sa ya nufa. Yarima yayi shirin sa na tafiya sai kuma ya tashi yaje part d'in FARHANAH dan ya sanar mata cewa tayi shirin ta da wuri dan k'arfe 2:00pm jirgin su zai tashi zuwa Malaysia. Ko da yaje part d'in ta tana can falon sama kai tsaye ya nufi stairs d'in yana takawa a sannu a hankali cikin nutsuwa gwanin ban sha'awa daman k'ananan kaya ne a jikin sa, jar riga mai ratsin fari sai bak'in wando jeans kayan sun kar6eshi sosai ga wani shu'umin turare da ya fesa ko'ina ya gilma k'amshi ke tashi. Zaune take bisa kujera mai zaman mutum biyu tana danne-danne a laptop d'in ta a yayin da shafa'atu ke mata tausar k'afafuwa a gefe d'aya kuma k'aramin table ne wanda aka d'ora juice da cup glass. Yarima yana ganin ta a zuciyar sa yace humm wannan bâ zata canza hali ba. Isowar sa wajen ne yasa shafa'atu ta dakata da abinda takeyi ta gaishe shi cikin ladabi ta tashi tsaye zata fice sai a lokacin FARHANAH ta d'ago kanta ta kalli Shafa'atu tace'' ina zaki je bayan ga aikin da na saka ki?" Kafin ta amsa yarima yayi mata nuni da ta tafi kawai, sai tace'' godiya nake na bar ku lafiya''. Tana gama fad'in haka tayi saurin sauka k'asa shi kuma yarima ya zauna a kujera mai fuskantar ta kafin daga bisani yace'' wai ke kam wane irin hali ne gareki? Sam baki san darajar mutane ba gaisuwa ma wannan baki iya ba, kedai abinda kika iya shine *GADARA* da nuna isa kamar kinfi kowa wallahi wannan halin ba hali mai kyau bane gara tun wuri ki canza hali''. Duk maganar da yarima yake mata ko kallon banza bai samu ba bare na arziki laptop d'in ta kawai take dannawa. A zuciye ya taso ya d'auke laptop d'in a zaface yake cewa'' I hate ina magana ayi banza dani, ke har kin isa ina miki magana kiyi min banza? Me kika d'auki kanki ne? Duk abinda kikeyi ina k'yale ki ne saboda ke mace ce in da namiji ne yake min haka da tuni an wuce wurin dan bai ma isa ba, kin d'auki girman kai da isa kin d'ora ma kanki dan kinga ina binki a yanda kikeso ko? Ki kiyayeni ina gaya miki''. Ya k'arashe maganar tare da wurga mata laptop d'in ta, cikin azama ta k'ar6eshi dan kar ya kai k'asa. Itama kallon shi tayi da rinannun idanun ta da sukayi mata ja dan tsabar masifa tace'' to malam ai sai kayi maganin abin in ka is....''. Bata idasa ba ya d'auke ta da wani gigitaccen mari cikin fushi yace'' duk iskancin ki na fiki iyawa wallahi ke naki bai ma kai ko'ina ba, ni idan na fara karanto miki nawa daki-daki wannan k'aramar k'walwar ta ki tayi kad'an ta d'auka dan nawa karatun mai wuyar d'auka ne a gareki''. '' Tabd'ijam wannan shine mari na biyu kenan da kayi min, kuma shine marin da aka ta6a yi min a rayuwa ta, ba'a ta6a d'aga hannu an dakeni ba sai kai can wani banza''. Da sauri yayo kanta sai ta baza a guje cikin bedroom d'in ta amma kafin ta rufe tuni ya k'arasa bakin k'ofar d'akin tamkar wanda aka jefo, shiga yayi ya rufe k'ofar da hannu d'aya har da key yasa daman kuma yana rik'e da ita a hannun sa d'ayan. Wurgata yayi bisan gadon sannan shima ya hau gadon gami da matse ta yace'' baki isa ki kira ni da banza ba, ai kece banzar wacce bata san darajar d'an Adam ba bare kuma ni da nake matsayin mijinki, da kike cewa in sake ki wallahi ba dan mai martaba ba da tuni na nuna miki ni d'an halak ne, kuma karkiyi tunanin cewa *so ko sha'awa* ne yasa har na kusance ki, a,a kawai na nuna miki ne ni ba yaro bane kamar yanda kike fad'a, na gaya miki baki cikin tsarin irin matan da nakeso ni da ke ma gara ace *'yar k'auye* na aura marar ilimi tunda ke wayewar ki da ilimin da kike tak'ama dashi duk basu amfana miki komai ba sai ma aiki irin na jahilai da kike yi, ni ban iya fitina ba, ban son yawan hayaniya amma duk ta dalilin ki nake yin su, ki iya bakin ki in ba haka ba in miki abinda har ki mutu tabon bazai goge a zuciyar ki ba''. Ya idashe maganar yana huci ya sake ta. Kuka ta saka tana cewa'' wallahi bazan zauna da kai bâ sai ka sake ni tunda auren ba dole ne ba''. Sauka yayi daga bisa gadon ya kama hanyar fita sai ya juyo yace'' ba zaki ta6a samun abinda kike so d'in ba, ki zauna cikin shiri gobe 2pm jirgin mu zai tashi''. '' Bazan je ba maye mai nacin tsiya kawai''. Bai juyo ba ya girgiza kai ya fice ranshi a matuk'ar 6ace. Washe gari maman yarima ta aiko aka tafi da gimbiya FARHANAH 6angaren ta a can akayi mata shiri na musamman mama kuwa har da kayan mata tasa aka had'o masu kyau da tsada ba irin tarkacen nan ba. Haka daga gidan su ma momyn su ta aiko mata sak'o FAREEHA da kanta ta kawo sak'on ta zauna suka d'an ta6a hira sannan ta tafi dan zuwa wurin mijinta tunda bai koma ba wai ta shirya su koma tare gidan ba dad'i da basu nan ita da babyn shi ita kuma gidan su bai isheta ba amma babu yanda ta iya dole ta shirya gobe su koma. Kafin lokacin tafiyar su yayi mummyn yarima ta had'a su tayi musu nasiha mai shiga jiki kuma tace da yarima ga FARHANAH nan amana idan tayi kukan wani abu to laifin sa ne kuma amana sai ta kama shi, daga nan wajen mai martaba suka wuce nan ma dai sarki nasihar yayi musu da fatan alkhairi sannan yace ma yarima kar su wuce wata biyu saboda sai yazo za'ayi bikin bud'e asibitin sa ya fara aiki zaman ya isa haka nan. Anyi musu rakkiya airport suna zuwa ba'a d'auki wani lokaci mai tsawo ba aka fara kiran fasinja, da aka kira su yarima suma suka shiga jama'ar sarki suna ta musu fatan a sauka lafiya. A jirgi kuwa tsakanin yarima da FARHANAH ba wata magana dan taso ta tashi daga kusan shi ta canza wuri sai ya maidata ta zaunar a Hankali yace mata'' ki nutsu nan ba gida bane idan kika ce zaki nuna isa ke zaki wahala''. Kawar da kanta tayi tak'i ma kulashi ga turaren shi saï hawan mata kai yake ji tayi kamar tayi amai saboda zuciyar ta kawai ke tashi, zip d'in handbag d'in ta ta zuge ta ciro shiwingum(cingam) ta saka a bakin ta saï yamutsa fuska take kamar anyi mata dole. Duk abinda takeyi yarima na kallon ta k'yaleta kawai yayi a zuciyar shi yace Allah yasa yarinyar nan tayi ciki yaga ta iskanci, wata zuciyar tace masa idan tayi ciki zubar da shi zatayi tunda bata sonka, nan take ya k'aryata hakan yace ina ai bata isa ba wallahi. Duk maganar nan a cikin zuciyar shi yake yi. Tarin da takeyi ne ya dawo dashi cikin hankalin sa ya kalle ta yace'' sannu''. Bata amsa ba sai ma sak'on harara da ya samu daga gareta. '' Cin cingam ba d'abi'a mai kyau bace musamman ga matar aure dan haka ki cire ta a bakinki''. '' Idan nak'i fa?" ta tambaye shi. Ya bata amsa da'' sai in cire ta da kaina na, idan kinyi gardama kuwa yanzu a gaban mutane zan danne ki in cire ta''. '' Baka isa ba''. Tana fad'in haka ya kamo ta yayi-yayi ta bud'e bakin tak'i sai ya matse mata hannu da d'an k'arfi sai da tayi ihu a nan ya samu damar cire cingam d'in. Drama a cikin jirgi sai da hankalin kowa ya dawo kansu sannan suka nutsu shi kuwa yarima har da cin magani ya maida eyesglasses d'in sa ya saka. Sun sauka lafiya lau a malaysia sai kuma mu ga irin zaman da zasuyi a nan domin kuwa d'akin kwanan su ma d'aya ne dan a hostel suke kuma d'aki d'aya yarima ya kama dan mugunta....... *Ku biyoni dan ganin irin wainar da zasu toya a k'asar malaysia a gida ma sunyi bare kuma a nan inda ba kowa.* *To wai ko dai su FARHANAH an k'unsa ne ana cin cingam har da su tashin heart🥴🥴* *_I'm sick, need ur prayers😢🙏_* *_AL'KALAMIN MUNATTU NE✍🏻_* _#VoTe #CoMmEnTs #ShArE_ *_'YAR MUTAN KAZAY CE👑_* 💥💥💥💥💥 *_'YAR GADARA_* 💥💥💥💥💥 *_NA_* *_MAIMOUNATH O.G.K_* _(Mahnoor)_ _Wattpad@maimounathog_ *💫DA BAZAR-MU WRITER'S ASS💫* *~_We are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are d best among all....DA BAZAR-MU MUKE TUN'KAHO._~* *°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°* _Duniya mein jo do rukha *(munaafiq)* hoga, qayaamat ke din us ke munh mein aag ki do zabaanein hongi._ *_(Abu Daawood: 4873)._* _Wanda ya kasance a duniya me baki biyu ma'ana munafiki a ranar qiyama harshen wuta biyu zasu kasance a bakinsa._ _Subhanallahi!_ *_(Abu Daawood: 4873)_* *^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^* *_Al-hamdulillah naji sauk'i cikin yardar Allah, nagode sosai da addu'o'in ku Allah ya bar zumunci🤝_* *_Mai rauni kar ta karanta wannan page d'in saboda tsaro🤨 wa'yanda basu da aure suyi hak'uri da wannan shafin😣 matan aure fa gashi🙈 'yan mata ga naku👉😫😝_* *Page 66/70* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* ******Zaune take a bisa kujera ta d'ora k'afa d'aya bisa d'aya tana danna wayar ta yarima ya shigo tare da yin sallama, can k'asa ta amsa ba tare da ta d'ago kanta ta kalleshi ba. Kasancewar a gajiye yake kawai wucewa yayi ciki shima bai sake kallon inda take ba, bayan ya wuce ne ta kalli bayanshi tayi d'an k'aramin tsaki wanda da k'yar ma ya fito. Yarima kuwa yana shiga bedroom d'in direct toilet ya nufa dan yin wanka, ya d'an jima a ciki kafin ya fito d'aure da tawul a k'ugun sa yana tsane ruwan kanshi da k'aramin tawul kuma. Tsab ya shirya ya saka kaya gami da fesa turare yana taje kai wayar sa tayi ringing yana d'auka ashe mummyn sa nan take yayi picking call d'in yana gaishe ta amsawa tayi tare da tambayar ina 'yar ta wato gimbiya FARHANAH take nufi ai kuwa yarima ya zabga mata k'arya yace'' mummy tana bacci''. '' Banson k'arya fa kaji ko, a wannan time d'in ne zaka ce min tana bacci ai nasan lokacin can ko dai bata da lafiya ne?" Kallon agogon hannun sa yayi yaga 1pm a nan sai yace'' eh mummy na fita ne da na dawo tana bacci da gaske nake''. '' Ni duk ba wannan ba ka duba min ita ko dai bata da lafiya ne, duk abinda ake ciki ka kira ni''. '' To shikenan ranki ya dad'e an gama''. Har zai kashe sai kuma yace'' au mummy daman nace bâ...kiyi addu'a Allah yasa baby zan samu''. Mummy tace'' oh ni wai yaushe ka zama marar kunya haka?" '' Sorry mum na daina ki gaida min abba na zan kira shi anjima''. '' Ok to zai ji amma ya kamata itama ka siya mata number'n can dan ta rink'a gaisawa da iyayen ta''. '' Ok''. Abinda yace kenan dan bai son ya k'ara wata magana kuma yayi laifi tunda yanzu FARHANAH ta zama 'yar gatan masarautar a dalilin budurcin ta da ta kawo gidan miji. Fitowa yayi falon a dai-dai lokacin akayi knocking k'ofa yazo ya bud'e dan yasan oder abincin da yayi ne ya iso, amsa yayi gami da yi masa godiya da yaren turanci. Wajen dinning table ya nufa ya ajiye kasancewar akwai komai na buk'ata a d'akin, duk abin nan da yake FARHANAH ko d'agowa batayi ba chating kawai takeyi da k'awar ta Haulat wacce ke yi mata shak'iyanci tana cewa tazo musu da tsarabar baby dai. '' Ga abinci can zaki iya zuwa kici''. Abinda taji yace kenan dan bata ma san yazo daf da ita ba har tana shak'ar k'amshin turaren da ya saka, sai taji sha'awar turaren haka kawai bata san dalili ba har da wani d'an lumshe idanu takeyi. Sai da ya sake mata magana a karo na biyu sannan ne tace'' bani da yunwa''. Wayar hannun ta ya kar6e cikin had'e rai yace'' idan zakiyi min magana ki kalle ni face to face kiyi magana dan nafi k'arfin ki basar dani kuma dole sai kinci abincin nan dan ba zanyi asarar kud'i na ba''. Kallon shi tayi tace'' ai sai ka fad'i kud'in naka ko nawa ne a biya ka tunda kasan ni ba matsiyaciya bace''. '' Baki da kud'in da zaki iya biya na, daga anyi magana sai kice kud'i, nawa ne ma gareki a account d'in naki bare ki rink'a tutiya da su, kud'in ki bai ma isa kud'in pure water ba yarinya''. '' Naji dai abinci ne ba zanci ba saidai kayi asarar kud'in naka, da Allah malam give me my phone kana 6ata min time''. Cikin aljihun sa ya saka wayar sannan yaje ya cika cikin sa da abinci ya bud'e fridge ya ciro yaourt (yogot) ya kwankwad'a ya sha ruwa ya tashi zai fice ciki ta sha gaban sa gami da rik'e k'ugu tace'' kai malam duk abinda kake ji dashi nima haka ka bani waya ta tunda ba kai ka siya min ba''. Bai ce mata komai ba kawai ya janye ta daga k'ofar ya shige ta bishi a baya sai masifa take masa har ya gama shirin sa na bacci ya hau gado yayi kwanciyar sa tare da yin bismillah kafin ya fara karanto addu'o'i ya tofe ko'ina sannan yayi ya shafe jikin sa yaja blanket ya rufa. Duk wannan abun fa FARHANAH tana kallon sa tare da yin masifa ita kawai sai ya bata wayar ta shi kuma ya basar kamar ma bâ dashi akeyi ba, hakan ya k'ara tunzura ta ta fincike blanket d'in da ya rufa tace'' malam da kai fa nake ka bani phone d'ina''. Ido d'aya ya kanne yace'' na k'arfi ne''. '' Ai gani nayi babu ko sisin ka a ciki bare kayi min iko da kaya na''. '' Amma kuma inada ikon hanawa akan mai wayar''. Cewar yarima SYDEEK yana mai k'ara tura wayar k'ark'ashin pillow d'in da yake akai. Hannu ta mik'a zata tura k'asan pillow d'in ya kuwa kama ta ya janyota sai bisan jikin sa har sai da yace'' washsh....zaki karya ni ashe haka kike da nauyi?" '' Ban sani ba, da Allah malam sakar ni kuma ka bani waya ta tun kafin inyi maka ta'asa''. '' Bismillah''. Sake tura hannun zatayi yayi karaf da hannun ya rik'e gam yanda zata ji ciwo nan da nan tayi 'yar k'ara tana cewa'' aiii! Allah ya isa na ban yafe ba mugu kawai''. Kamota yayi ya mayar k'asan shi ya shiga sarrafa ta yanda yakeso ita kuma sai nok'ewa takeyi gashi ta kasa wani motsin kirki sai tace'' d'an iska kaw....''. Bata k'arasa ba ya had'e bakin su. Soyayya mai cike da k'warewa yake nuna mata dan yarima ya iya romancing wanda ita d'in bata isa ma ta iya hanashi ba saboda ya kashe mata dukkan wasu ga6o6i na jikinta bata iya wani kata6us kawai ta zubawa sarautar Allah idanu. Nishi kawai suke futarwa, wani irin abu ne ya zirga mata cikin kwanyar kanta da ma dukkan sassan jikinta jin bakin yarima a bisa k'irjin ta, yanayin yanda yake mata cikin gwaninta ga hannuwan sa basu tsaya wuri d'aya ba sai shafar ta yake lungu da sak'o. Can wasu 'yan lokuta taji ya cire mata rigar jikin ta duk da ba rigar bacci bace amma dai ta shan iska ce ba wani mai nauyi ba. Hannuwan sa yakai a bayan ta ya cire masangalin brezia d'in ta yayi jifa da ita ya sake maida kanshi akan breast d'in ta, cike da mugunta yake tsotsar su kawai dan yasa tayi laushi shi bai ma yi niyyar yi mata wani abu ba amma yanda take mishi magana a *GADARAN CE* ne yasa yake mata hakan dan ya nuna mata ruwa ba sa'an kwando bane. Da k'yar ta iya bud'e baki tace'' ban yafe maka.....maka ba ka daina banso nace...''. '' Yarinya me ma akayi, tun yanzu har kin fara raki''. '' Allah ya isa''. Abinda ta fad'a kenan ta k'ara rushewa da kuka, shi kuma maimakon ya daina sai ma neman hanyar da zata sadashi da fadar ta yake tunda yasan babu wani shamak'i a tsakanin su bare ma da tace masa Allah ya isa shikenan ta k'ara kunna shi. Duk k'ok'arin ta na hanashi shiga jikin ta amma ta kasa dan ya kashe mata jikin da zafafan wasanni tana ji tana gani ya ratsa jikin ta tunda taji ya rad'a mata addu'ar saduwa da iyali tasan ba shakka a yau ma yarima sai yayi yanda yakeso da ita. Wani irin ciwo ya ratsa ta bata son tayi kuka dan kar ya ga damar ta ma amma ina yarinya wace ke ai kuwa sai ta saki wani irin kuka mai cin rai saboda zafin da yake ratsa ta kama daga k'afafun ta har zuwa cikin k'wak'walwar ta shi kuma oga SYDEEK aikin sa yake aiwatarwa cike da k'warewa tare da hik'ima da ya ga tana damun shi da kuka sai ya had'e bakin su waje d'aya ya zamto ya rufe bakin kukan. Hhhhh am so sorry my FARHANAH nidai ta wajenki ce shiyasa ma nake tausaya miki gara kiyi saranda ki kar6i yarima a matsayin miji in ba haka ba kuwa kece zaki wahala saboda da wannan damar zaiyi amfani ya rink'a kwasar gara. Hhhhh caskalewa a d'akin yarima.... Yarima biji-biji yayi mata domin kuwa sai da yakai FARHANAH ko kukan ma ta kasa sai a ciki takeyi balle ma da ya had'e bakin su k'in cirewa yayi aiki biyu-biyu kawai yakeyi yarima d'an duniya kenan. Yaso ko da ya gamsu yak'i rabuwa da ita sai kuma yaji rashin kyautawar hakan tunda ko ba komai shi namiji ne, mace da namiji ba zasu ta6a zuwa dai-dai ba mu mata munada rauni da k'arancin tunani sa6anin namiji shi mai tunani da hangen nesa ne, amma fa wasu mazan...... Sauka yayi a kanta ya koma gefe yana maida numfashi ga wani irin k'arfi da yake jin yanada shi a lokacin bai k'i anjima ya k'ara ba kawai dai ya tausaya mata ne duk da ita bata ganin hakan. Kukan da takeyi ne ya dawo dashi cikin hayyacin sa, ya d'an matsa yasa hannu ya dafa ta kafin yayi magana cikin muryar wacce ta gaji da kukan azaba gami da ture hannun sa tace'' karka saka ta6ani azzalumi kawai Allah ya isa wallahi ban yafe maka abinda kayi min ba''. Zuwa yayi kan kunnen ta yace'' ko baki yafe ba Allah yasan halal d'ina na ta6a ba haramun ba, karki sake min Allah ya isa in ba haka ba kuwa jikinki zai gaya miki ina fatan kin gane?" Mirginawa tayi da k'yar ta matsa daga kusan shi saï kukan ta takeyi har ta bani tausayi, shi kuma yarima tashi yayi ya shige toilet yayi wanka ya fito daga shi saï boxer tana kallon shi saboda akwai lamp na bedside mai bada kala, kawar da kanta tayi ta shige cikin blanket tana zubar da hawaye har da su cije lips saboda rad'ad'in da take jin k'asanta yana mata. Ba tare da yayi mata magana ba yaje ya yaye blanket d'in ya sungumeta sai toilet ba dan taso ba sai dan ba zata iya aiwatar da komai ba dole sai an taimaka mata. Dole tana ji tana gani yarima yayi mata komai sai dai wankan tsarki da tayi da kanta. Kafin ta fito ya gyara bedsheet d'in wanda yasha yamutsa, tana fitowa daga toilet ya ganta sai dafe bango take tana ta cije lips ya nufi inda take ya kamo hannun ta dan taimaka mata sai ta fusge hannun ta tana mai hararar sa, murmushi yayi yaje ya zauna bakin gado yana kallon ta har ta k'araso bakin gadon kuma har a lokacin hawaye bai daina zarya a fuskar ta ba. Hayewa tayi ta kwanta shi kuma yarima sai ya tashi yaje ya had'o mata tea da kanshi ya dawo yaje cikin kayan shi da akwai maganin pain killer da na zazza6i ya koma bakin gadon. '' Ki daure ki tashi kisha tea ga magani''. Abinda yarima yace da ita kenan. Ta amsa mishi da'' bazan sha ba in mutu ma ina ruwan ka''. '' Sorry tashi kisha please''. '' In dole ne sai ka d'ura min''. '' Irin wannan maganganun ne banaso shiyasa nima nake miki abinda bakiso, banson ina magana ana maida min ita a gatsau, ki tashi kisha ko kuma in maimaita double d'in abinda nayi miki''. Cikin kuka tace'' ga hanya nan ka maimaita sai in san ka cika namiji soko kawai''. Idanu ya zaro kamar tana kallon shi dan ta juya masa baya yace'' ni kike ce ma soko? Nid'in''. Juyowa tayi tace'' yes you, and so what?" Ajiye cup d'in tea yayi yace'' ni kuwa zan nuna miki ni ba soko bane yanzun nan kuwa''. Ya k'arashe yana mai hawa gadon sosai.......... *_Wannan yarinya da taurin kai kike🤔 duk abinda yayi miki baki saduda ba har yanzu bakin ki yana kaud'i? Wai yaushe ne bakin FARHANAH zai mutu murus?_* *_Yau mai k'watar ki a hannun yarima SYDEEK sai Allah nidai ba ruwana dake, yarima kayi so uku m.......🤐 shittttt🤫 ayi shiru kawai yarima zai caskale...🤸‍♂🤸‍♂🤸‍♂🤸‍♂🤸‍♂🤸‍♂🤸‍♂🤸‍♂_* _Domin jin dad'in ku nayi wannan amma jikin har yanzu bai k'arasa warwarewa ba amma Al-hamdulillah🙏_ _Wa'yanda basa comments duk na sanku kuma ina nan zuwa kanku ba wayo kuka fini ba....🙄🤨😏_ *_AL'KALAMIN MUNATTU NE✍🏻_* _Comments_ _✔ote_ _Share_ *_'YAR MUTAN KAZAY CE👑_* 💥💥💥💥💥 *_'YAR GADARA_* 💥💥💥💥💥 *_NA_* *_MAIMOUNATH O.G_* _(Mahnoor)_ _Wattpad@maimounathog_ *💫DA BAZAR-MU WRITER'S ASS💫* *~_We are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are d best among all....DA BAZAR-MU MUKE TUN'KAHO._~* *_ASSALAMU ALAIKUM DAN ALLAH WA'YANDA SUKA YI COPY NA TAMBARIN FORUM 'DIN MU KU CIRE KU NEMI NAKU, BANSON FITINA KOWA YA NEMI NASA PLEASE AND PLEASE.🙏_* *~__________________________________~* _Daga wannan page d'in har zuwa end mallakar ka yayana *HASSAN ATK* nagode sosai da kulawa, shawarwarin da kake bani ina godiya sosai, ka cancanci yabo ina yi maka fatan alkhairi😍 Allah ya baka abinda kake nema duniya da lahira, Allah ya bar mana kai mu caskale musha shoki😆💃 Allah ya bar zumunci🤝 kuma fa karka manta ana kyawun tare for💖ever💞_ *~__________________________________~* *Page 71/75* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* °°°°°°°Yaye blanket d'in yayi ai kuwa FARHANAH tana ganin haka sai tayi wuf ta mik'e zaune ba tare da ta shirya ba tace'' wai meye haka? Me kake shirin yi ne?" '' Jarumtar zan nuna miki tunda kince min soko duk da nasan k'arya kike kice ni sokon namiji ne tunda har na iya saka ki kuka''. '' Yo meye kai d'in in ba soko ba? Ai ni a nan banga namiji ba kamar mace haka kake a idanu na saboda ko d'igon tsoron ka babu shi a cikin zuciyar nan tawa''. Ta idashe maganar tana mai ta6a wajen. '' Humm naji to". '' Ai daman inason kaji ne tunda ba sak'o na aiko maka ba kai tsaye nake magana da kai jarababbe kawai''. Kalmar jarababbe ita ta janyowa FARHANAH wata wahalar ko ince azaba domin kuwa yarima danne ta yayi ya shiga kiciniyar cire mata riga ita kuma tana k'ok'arin hanawa. Taurin rai irin na FARHANAH ban ta6a gani ba, maimakon ta bashi hak'uri amma tak'i a ganin ta zubar da aji ne idan na rok'eshi dan ita a tsarin ta wani d'an Adam bai isa ta bashi hak'uri ko neman wata alfarma ba sai dai ta nuna maka kud'i. Idan baku manta ba haka tayi wa doctor'n gidan su ma. Tuni yarima ya yaga mata rigar da yaga kafin ya cire d'in ma 6ata time ne, murzarta ya shiga yi son ransa har da k'yeta a al'amarin nashi tunda ba da wasa yake aika mata wasannin ba. FARHANAH ta rasa abinyi saboda yarima wasu irin hot kisses yake yi mata a kowane lungu da sako na jikinta, bakin shi da ya dasa kan k'irjin ta shi ya haifar mata da wata muguwar kasala ta kasa hanashi dan bâ ma zata iya ba. Yanda kuka san k'aramin yaro idan yana jin yunwa haka yarima ya dawo sai tsotse ta yake ko a jikinsa wata muguwar sha'awar ta yakeji wanda ya rasa dalilin yin hakan shiyasa ma yakejin dad'in abin har da su lumshe idanu a yayin da gimbiya FARHANAH ke zubar da hawayen tak'aici ga zafin da breast d'in ta suke mata saboda tsabar matsa da tsotsar da yarima yake musu musamman na yau yafi ma na can Nigeria. Cikin wata irin murya tace'' wayyooo...momy help me..aiii ka daina min banso d'an jaraba...''. 'Dagowa yayi ya had'e bakin su waje d'aya dan bai son ta katse masa jin dad'in sa. Hannun sa d'aya yakai kan marar ta yana shafa itama ta kai nata hannun ta rik'e nashi sai kai take juyawa gashi ba damar magana saboda yarima ya hanata kata6us babu yadda ta iya sai yanda yayi da ita. Jin alamun hannun sa na yawo gudun kar ya je mata har inda bata so shiyasa ta d'an yunk'ura dan ya d'auke hannun sa sai ya cire hannun ya mayar kan breast d'in ta yayi gefen ta amma fa k'afar shi ta dama ta danne nata k'afafun wanda bata isa tayi babban motsi ko k'watar kanta ba. Hannun sa yawo yake a k'irjin ta ya shiga zagaye d'an yatsan shi akan breast d'in su FARHANAH tun ana jin zafi sai kuma taji sauk'in abin daga haka ya sake maida hannun k'asan ta yana shafar marar a cikin kunnen ta ya rad'a mata cewa'' ya isa haka nan ko in kai ga wurin da zaki san ni ba raggo soko bane?" Kawar da kanta d'aya 6arin tayi tana ta cije lips wata mahaukaciyar yunwa takeji kamar taci babu ga tashin zuciya shima ya addabe ta amma sam yarima yak'i sakin ta dan jaraba irin tasa. Inji ita ba ni na fad'a ba. Kanta ya kama ya sake juyowa da ita 6arin da yake zai had'e bakin su ta fisge tana cewa'' karka sake had'a bakin ka da nawa dan k'yank'yamin ka nakeyi gashi duk ka saka inajin kamar inyi amai''. Yarima yayi murmushi mai sauti yace'' haba wa yarinya kawai ki fad'i gaskiyar ki ma kinji yawu my sweet shine zaki wani ce haka''. '' Allah ya kiyaye duk abinda ya fito daga jikin ka k'azanta ce kuma duk abinda ka saka min sai yaje asibiti an fitar min dashi''. Janyota yayi sosai zuwa gareshi ya kara bakin shi kan kunnen ta yace'' wallahi ba'a yi wani doctor a duniyar nan da zai cire miki abinda kike kira k'azanta dan ya rigaya da yabi jinin jikinki kawai ki jira sakamako dan ku tabbatar ni ba irin kucakan mazan da kika saba bi bane''. Kuka ta fashe dashi tace'' Allah ya isa na, karka sake ce min na bi maza, kuma k'arya kake kace min haka dan da mutunci na kai ka zubar min dashi, babu wani d'a namiji da ya isa ya ra6i jikina ko inyi zina dashi''. '' Sai gashi ni kuma na samu a bonus''. Cewar yarima ita kuma sai kukan tak'aici takeyi na irin maganganun sa. Tana cikin yin kukan ne tari ya turnik'e ta sai ta tashi zaune tana son ta mik'e dan zuwa toilet tana gumtse baki, yarima ya kunne fitilar gefen gado yaje kusan ta yace'' yadai? Me ya faru?" FARHANAH ba bakin magana shi kuma yarima ya lura da bata iya tashi ne amma dan taurin kai ba zata ce ya taimaka mata ba, sauka yayi daga gadon ya d'auke ta yakai bakin toilet ya bud'e mata tana shiga zai bi bayan ta sai tayi saurin rufe k'ofar har da sa key. Amai tayi ta kwaranyawa da k'yar ya tsaya gashi ta wahala sosai saboda yunwar da takeji tunda daman bata ci komai ba duk da tanajin yunwar kawai dan yarima ne ya kawo abincin take bak'in cikin ci. Kin yiwa kanki yarinya ba gashi ke kika wahala ba, namiji fa ba ruwan sa *(Akwai masu cewa ko amarya za'a kai gidan mijinta kar a bata abinci sosai, to dan me? Injiwa? Me zai hana taci ta k'oshi? Wallahi idan mace na jin yunwa matuk'ar namiji ya nemeta a lokacin to kuwa dole tasha wahala, wannan soki burutsun zance ne kici abincin ki iya son ranki dan ko kici ko karki ci ango dai sai......)* na k'yale kar in ba su o'o tsoro......... Wanka tayi da k'yar tana hawayen wahala ta fito daga bayin yarima yazo inda take ya kama ta bata iya hanashi rik'eta ba saboda jikinta ba k'arfi sosai ji takeyi kamar iska zata d'auke ta. Bakin gadon suka k'arasa ya zaunar da ita shima ya zauna gami da kallon ta yace'' are you ok?" Da mugun kallo ta bishi ba tare da tayi magana ba kafin daga bisani ta k'ara hayewa gadon ta shige cikin blanket shi kuma ya tashi ya fita. Tea mai kauri ya had'o mata dan wancan na farko yayi sanyi. Da k'yar tasha sai yatsina fuska takeyi kamar yana bata magani a haka har tasha mai d'an yawa dan daman yunwa takeji. ***** **** **** ***** A cikin 'yan kwanakin da suka biyo baya FARHANAH sam bata jin dad'in jikinta kawai tana k'ok'arin 6oye ma yarima ne. Bata da aiki sai kwanciya ga kasala jikinta ko'ina ciwo abin dai ba sassauci, duk k'arfin halin da takeyi sai da abin ya kai ta da kwanciya. Yau ma da misalin k'arfe 10:30am tana kwance a falo idanun ta a lumshe tana jin wayar tana ringing amma ko kallon inda take batayi ba dan yau ta tashi da jiri komai a kasalance takeyin sa yarima kuwa tun safe ya fita cikin gari. Har wayar ta tsinke bata d'aga ba a dai-dai lokacin yarima ya shigo tare da yin sallama, a ciki ta amsa yanda ba zaiji ba tayi kamar bata san ya shigo falon ba. 'Karasowa yayi inda take ya nufa, yana zuwa ya zauna kusa da ita gami da dafa wuyan ta yaji sanyi bata da zazza6i amma tabbas yasan akwai wani abu dan yanzu ta zamo so silent duk masifar ta ta ragu. Cikin taushin murya yarima yace mata'' sannu''. Bata amsa masa ba sai tashi da tayi ta zauna tare da kallon shi, shima d'in ita yake kallo da gira yayi mata alamar yadai? Sai ta kawar da kai tace'' banson k'amshin turaren nan naki please tashi a kusa dani''. Bai tanka mata ba sai ma tsura mata idanu da yayi yaga ta k'ara haske tayi kyau jikin ta har shek'i yake gwanin ban sha'awa, ya kuma maida kallon shi kan k'irjin ta nan ma yayi 6ul-6ul duk sun ciko, hannu yakai kan k'irjin ta saï ta bige hannun tace'' wai meye haka? To duk jarabar ka ka k'yaleni dai''. Murmushi yayi mata mai cike da ma'anoni yace'' humm yarinya kin kamu tashi muje in duba ki inga me yake saka ki yawan kasala da baccin nan''. '' Ban buk'ata ni lafiya ta k'alau''. '' Are you sure?" '' Yes''. Ta bashi amsa. '' Ni kuma ban yarda ba dole sai na duba ki tashi mu shiga ciki''. '' Nace ban so ko dole ne? Yau ni naga jaraba da nacin tsi....''. Bata k'arasa ba ya dalle mata baki yace'' kin cika taurin kai, akan kalmar jarababbe meye nayi miki? Hukuncin bai isheki ba ko?" '' In ka isa ka d'auki mataki mana ance maka jarababben ko k'arya nayi?" Murmushin mugunta yayi har da cije lips d'in sa yake yayi mata kallon zan kamaki ne. '' Me zaki ci ne a kawo miki?" '' Banjin yunwa''. Ta fad'a a tak'aice. '' 'Karya ne kina jin yunwa kedai kice girman kai ne bazai bari kice ga abinda kikeso ba, kuma ya kamata ki ajiye komai muyi rayuwa irin ta kowanne ma'aurata ba wai dan muna son junan mu ba, a,a sai dan kawai mu bi umarnin iyayen mu suma su san munyi musu biyayya''. Ko kallon shi batayi ba ta tashi zata fice sai jiri ya d'auke ta da kad'an ta kai k'asa yarima ya tare ta ta fad'o kan jikinsa. 'Daki ya kaita ya shimfid'e ta ya ciro kayan aikin sa ya gwada ta jinin ta normal ne sai dai tana tare da yunwa, saura gwaji d'aya wanda zaiyi mata amma bai tunanin zata yarda, dole ne ya zare mata tasan shine gaba da ita idan ya biye mata abin ba zaiyi kyau ba. Fita yayi yaje ya had'o mata abin karyawa dan yasan batayi breakfast ba saboda taurin kai. Sai da ya nuna mata ba wasa cikin al'amarin sa sannan ta d'an ci kad'an yace da ita taje ta shirya zasu fita zuwa asibiti saboda bai zo da wasu kayan ba sai ta nok'e tak'i ma kallon inda yake. Tsawa ya daka mata'' keee!!! Ina binki kamar wata uwata banson iskanci kinji ko? Ki tashi kiyi abinda na saka ki if not zakiyi mamakin abinda zan aikata miki''. Ganin ba wasa a fuskar sa tsam ta tashi taje ta d'auki doguwar bak'ar riga ta shiga toilet sai kumburi take shi kuma yana bin bayan ta da kallon yana mai ayyana musabbabin ciwon nata, na dad'e yana zargin ciki ne gareta dan duk wasu alamu na mai ciki sun nuna a tare da ita sai dai bai san ya zata d'auki al'amarin ba saboda ganin irin k'iyayyar da takeyi masa. Ta d'an jima a toilet d'in kafin ta fito sanye da rigar maimakon ta saka hijab sai ta d'auki veil d'in rigar ta laulaya a kanta kuma gashi d'an k'arami duk abinda takeyi yarima kallon ta kawai yake. Ficewa tayi daga bedroom d'in ba tare da ta kalli inda yake ba, a falo ya iske ta tana zaune yaje kusa da ita ya kalle ta da kyau yace'' a haka zaki fita?" '' Eh! What's your problem?" '' Saboda matar aure kike in kin manta in tuna miki''. '' Aure? Kai kasan wannan haka nayi niyyar fita, nifa a gaskiya kana takura min''. '' Dole ne in takura miki in kuma tunasar dake nauyin da yake kanki tunda ke baki sani ba''. Bata sake magana ba shi kuma ya koma ciki yayi ta binciken kayan ta ko zai samu hijab amma babu duk mayafai ne suma d'in ba wani girma garesu sosai ba, haka dai ya d'auko mata mai d'an dama a cikin su ya fito. Jefa mata yayi yace'' ace kina musulma 'yar musulmai amma babu hijab cikin kayan ki, anya kuwa ke mutum ce kamar kowa? Wai ko dai kina da shafar aljanu ne? Abubuwan da kikeyi sam ba irin na mutane masu hankali bane, tashi muje''. Yana maganar yayi waje ta tashi ta bi bayanshi sai kumbure-kumbure take. Wani clinic suka je abin ka ga masu kud'i kuma clinic daman harkar kud'i ce ba wasting time nan da nan akayi mata dukkan gwaje-gwajen da ya kamata suna jiran result. Ba'a jima sosai ba result ya fito doctor yace su biyoshi office d'in sa nan suka bishi a baya. Kujerun gaba da table ya nuna musu yace su zauna. Bayan sun zauna ne sai doctor ya bud'e takardar..... *_Sanin abinda result d'in ya k'unsa sai mun had'e next page da izinin Allah, ina busy ne kwanakin nan sai kuma gashi ciwon idanu wanda daman ina yin sa lokaci zuwa lokaci so kuyi maleji da wannan_* *_Gaskiya zanyi kwana biyu banyi typing ba saboda tafiya ce ta kama ki idan da hali zanyi ko a can in kuma babu to sai kunyi hak'uri, nagode sosai Allah ya bar zumunci🤝_* *_AL'KALAMIN MUNATTU NE✍🏻_* *_'YAR MUTAN KAZAY CE👑_* 💥💥💥💥💥 *_'YAR GADARA_* 💥💥💥💥💥 *_NA_* *_MAIMOUNATH O.G.K_* _(Mahnoor)_ _Wattpad@maimounathog_ *💫DA BAZAR-MU WRITER'S ASS💫* *~_We are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are d best among all....DA BAZAR-MU MUKE TUN'KAHO._~* _KYAKYKYAWAR ZUCIYA, SANIN YA KAMATA, MAGANA CIKIN NUTSUWA....👇👇_ **************** *_FOR YOU:_* *_DEAR YAYA:_* *_H@SS@N ATK_* ********************* *_Assalamu alaikum 'yan uwana mata masu aji ina kuke? Ga company'n ORIFLAME yazo muku da k'ayatattun mayuka masu inganci da nagarta, mayuka ne masu gyara jiki wanda zakiyi fes dake har oga ya kasa gane ki🤣 ORIFLAME yazo muku da FEMWASH ba ruwan ki da cushe-cushen maganin mata irin na wannan zamani, ga kuma su PURE SKIN, LOVE NATURE: man gashi mai kyau da dai sauran su....idan kina da buk'ata just contact me yanzu ki koma 'yar d'agwas, idan ma sana'ar yi kike nema to kin samu garzayo campany'n ORIFLAME💃💃💃💃 #SUPER AWOOF....SUPER YOU😘👍_* *Page 76/80* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* Doctor Hisham ya bud'e takardar jim kad'an ya d'ago kanshi yana murmushi ya mik'a ma yarima hannu yace'' Congratulations! My friend, matar ka tana d'auke da ciki na wata biyu''. Cikin jin dad'i yarima ya zaro idanu yace'' doctor are you sure?" '' Yes! Of course, ka kusa zama daddy insha Allah''. '' Thank you so much doctor''. '' You are welcom''. Yarima har da sujjada yayi a k'asa saboda tsananin murna daman shi yana da son babies ko dan shi kad'ai ya taso a gidan su, lallai su mai martaba zasu ji labari mai sweet. Doctor ya kalli FARHANAH yace'' madam ina tayaki murnar samun baby, Allah ya inganta''. Hawaye suka gani sharkaf a kuncin ta wani na bin wani, basuyi aune ba sai kawai suka ga tayi luuuu zata fad'i k'asa yarima ya taro ta cikin zafin nama. Ashe sumewa tayi yarima ya rikice yana cewa'' doctor help me please suma tayi''. Doctor ya kira nurses aka kaita wani d'akin nan da nan suka rufar mata da k'yar numfashin ta ya dawo normal kuma har a lokacin tana zubar da hawaye wanda nidai bansan na meye ba. Bayan ta farfad'o d'in duk fita sukayi sai yarima kawai shima sai da doctor Hisham yace dashi ya fito ana son ta samu hutu amma yak'i fita dole suka barshi a ciki. Bayan wasu 'yan lokuta FARHANAH ta fara motsawa tana d'an juya kanta tare da saka hannu d'aya ta rik'e kan da alama yayi mata nauyi ne ko kuma ciwo yakeyi. Ganin haka ne yasa yarima ya tashi daga kujerar da yake ya k'arasa bakin gadon ya zauna kusa da kanta ya kamo hannun ta ya rik'e yace'' me kike so? Me yake miki ciwo ne? Ko kanki ne yake ciwo?" Idanu ta bud'e tarr sai akan fuskar sa, kallon shi kawai takeyi kamar yau ta fara ganin shi tana son tuno wani abu, sai can ta tuna cewa fa doctor yace wai tana d'auke da ciki, cikin ma na yarima, to ta yaya hakan ta faru? Tana kallon ina ma har ta yadda ciki ya shige ta? Kuma cikin ma na yarima? '' Hey! Tunanin me kikeyi?" Fusge hannun ta tayi tace'' ina ruwan ka''. '' Humm kinga yanda Allah yake al'amarin sa ko? Bamu son juna gashi Allah yayi zamu had'a jini''. '' Idan har tunanin ka wannan cikin zai sa in so ka ko in haife shi to ka fidda wannan a cikin zuciyar ka dan bazan haifi wannan shegen cikin.....''. Kafin ta k'arasa ya d'aga hannu zai kai mata mari sai kuma ya mayar gami da dukan hannun sa d'ayan yana cewa'' no!!! Karki sake ki shegan ta min d'a, naji baki sona amma ciki ya rigaya da ya shiga babu kuma wanda ya isa ya fitar dashi face wanda ya halicce shi, idan kika k'ara shegan ta min yaro wallahi zan baki mamaki, marar tunani kawai''. Tashi yayi ya fita daga d'akin zuciyar sa na mai yi masa suya saboda tsananin 6acin rai ko gaban sa bai gani sosai ikon Allah kawai ya kai shi office d'in doctor yana mai dafe kanshi da yaji yana mugun sara mishi. Da k'yar ya k'arasa kujerar gaban office d'in ya zauna bai ce komai ba haka doctor ma da yake rubutu ya tsayar ya shiga kallon shi kafin yace'' friend, me ya faru na ganka cikin wannan halin?" '' Ba komai ka sallame mu mu tafi ta tashi''. '' Good! Haka akeso muje in k'ara ganin jikin nata''. A tare suka fita daga office d'in dan zuwa d'akin da FARHANAH ke kwance. Tana kuka suka iske ta doctor ke tambayar ko wani abin nayi mata ciwo ne? Tayi banza dashi a yayin da shi kuma yariman ya kawar da kai, doctor duk yana lura dasu biyun yasan akwai wani abu a tsakani but wannan ba hurumin sa bane dan ance mata da miji sai Allah zasu daidaita koma dai meye. Daman ya rubuta maganin da zasu siye sai ya basu sallama tare da mik'awa yarima takardar yace'' wannan maganin shi za'a siye ta rink'a sha so d'aya tak a rana amma fa ka tabbatar sai taci ka k'oshi tukun tasha maganin ok?" '' Ok!''. '' Yauwa Allah ya k'ara mata lafiya''. '' Ameen! Thank you". Ita kuma uwar gayyar tana zaune bakin gadon sai kumbure-kumbure takeyi na tak'aici da bak'in ciki. Har suka je masaukin su babu wanda ya yiwa d'an uwan sa magana kowa najin haushin kowa a cikin su. _(Kai jama'a irin wannan zama ina amfanin sa? Gara a raba auren ai tunda yarinya bata ra'ayi, amma zan nema masa 'yar cakwai tunda ke baki so irin wannan yaro d'an kwad'as wacece zata k'i shi? Hahaha....)._ Abinci sosai yasa aka kawo musu kala-kala saboda FARHANAH dan ta samu taci tasha maganin, nan ma sai da yayi da gaske kamar zai dake ta sannan taci tasha magani ta kwanta duk jikinta a mace ba k'arfi. Lumshe idanu tayi gami da d'ora hannun ta a kai tana d'an yamutsa fuska yarima ya matso kusa da ita sosai yace'' meke damunki yanzu? Ko kanki ke miki ciwo?" '' Kafi kowa sanin abinda ke damuna ai''. '' Baki fad'a min ba ya za'ayi in sani?" '' Wannan cikin shine babbar matsala ta, ta yaya zan reni cikin wanda ban so?" '' Ta yanda kika sameshi?" ya bata amsa. '' Ni kuwa sai na zubar dashi''. '' Baki isa ba, babu kuma wani mahaluki a nan duniya da ya isa ya zubar da wannan cikin, dan haka ki daina ma maganar nan''. Cikin kuka tace'' Allah ya isa tsakani na da kai, ka cutar dani''. '' Allah ya isar ki bata min komai tunda Allah ma yasan ba zina nayi ba, ta hanyar aure aka sameshi so wallahi nidai na gaya miki karki kuskura ki sheganta min ciki''. '' Uhmm''. Cewar FARHANAH gami da juya mishi baya sai yace'' time d'in sallah yayi ki daure ki tashi kiyi ko daga zaune ne''. '' A iya sani na ba dan kai nakeyin sallah'r ba, dan haka ka k'yalenik''. '' Ba dan ni kikeyi ba amma hak'k'i ne a kaina ya zama dole in kula da komai naki ciki kuwa har da addinin ki tunda a k'ark'ashin iko na kike''. '' Bazanyi ba''. '' Karki bari raina ya 6ace ba dan kina mace ba da baki isa ma ina fad'a kina fad'a ba, kina cin darajar iyaye ne da kuma wannan cikin na jikinki, duk duniya ban ta6a magana aka mayar min da ita ba sai ke''. Tashi zaune tayi zata masa fitsara ya daka mata tsawa'' ki tashi nace!!! Zan mugun sa6a miki fa''. Sum-sum mutuniyar taku ta shige toilet yarima yana kallon ta cike da 6acin rai idanun nan sun kad'a sunyi jawur kamar gauta saboda tsabar 6acin ran da ya tsinci kanshi a ciki. Kafin ta fito ya dafe kanshi yana karanto addu'o'i sannan ya samu nutsuwa kad'an, sam bai iya 6acin rai ba yanzu zai iya haddasa masa wani ciwon. Bayan ta fito shima ya shiga, sai da yayi wanka sannan ya d'auro alwala ya fito. Ko da ta ida sallah'r a nan ta kwanta shi dai ficewa yayi falo bai ma kalli inda take ba. Bai jima sosai a falon ba wayar sa tayi ringing yana dubawa sai yaga mummyn sa ce, d'an murmushi yayi ya d'aga yace'' assalamu alaikum my lovely mum''. '' Wa'alaikas-salam! Humm yau kuma ta nan ka 6ullo?'' '' A kullum sunayen sukan canza musamman ma a yau da nake d'auke da albishir mai dad'i but sai an bani tukwici''. '' Naji zan bayar a fad'a min me ya faru?" '' Au sorry mummy na kuna lafiya ko? Yasu abba? Ya fama da jama'a?" '' Humm! Kai dai ka sani duk muna lafiya lau komai fine da izinin Allah''. '' Masha Allah!". '' Ina sauraren ka, ina 'yata ne?" '' Uhm 'yar ki tana cikin d'aki maybe ma tayi bacci''. '' Toh! Kullum bacci? Lafiyar ta k'alau kuwa? Ko dai kana yawan damun ta ne?" Tambayar ta d'an bashi kunya amma sanin wacece mummyn sa yasa bai damu sosai ba dan su ba ruwan su basa 6oyewa junan su sirri. Kai ya shafa kamar yana gabanta yace'' ah no! Wane ni kawai dai bata jin dad'in jikinta ne yanzu muka dawo daga asibiti''. '' Ya Salam! Me ya sameta haka?" '' Kin kusa samun jika fa''. Da k'arfi mummy tace'' what? are you serious son?" '' Yes! Mum da gaske nake''. [24/11 23:53] Mahnoor💎: Babu abinda mummy keyi sai godiya ga ubangiji har da hawayen ta na farin ciki kamar an kawo mata labarin matar yarima ta haihu. Sai da yarima ya gaji yace'' mummy ya isa haka nan ai''. '' Barni in gode ma Allah da wannan kyautar wanda babu wanda ya isa ya bamu idan bâ shi ba, idan ta tashi zan kirata a wayar ta''. '' Ok mummy shikenan, a gaishe min dasu abba kunya ta hanani fad'a masa''. '' Oh! Wato nice ba'a kunyar kenan ko?" '' No! Ba haka bane kawai dai naga gara in gaya miki sai yaji daga gareki''. '' Humm sarkin tsara zance naji zan bar ka haka nan ka kula min da ita sosai idan ma laulayin zai dameta ku dawo gida kawai''. '' To mummy bye''. A haka sukayi sallama kowannen su cikin farin ciki. Bayan ya ajiye wayar ya tashi ya koma d'akin dan ganin halin da take ciki duk da dai yasan tana bacci time d'in da ya fito. Tun daga bakin k'ofar yake jiyo sheshshek'ar kukan ta da sauri ya tura ya shiga, tana zaune a bakin gado waya takeyi da alama kuma d'aya daga cikin 'yan gidan su ne. Cikin kukan take cewa'' sister ni tawa ta k'are nasan ma mutuwa zanyi wai ciki ne dani bansan ta yaya hakan ya faru b....''. Kukan da takeyi ne ya hana ta k'arasawa ko me FAREEHA tace mata sai kuma ta sake cewa'' ai daman nasan kin daina k'auna ta, kowa ya kasa gane halin da nake ciki, na gaya muku banson wannan mutumen amma aka dage gashi nan ya cuceni ya had'a ni da aiki zan zubar da wannan ku6ar dan kamar ku6a hake nake kallon wannan cikin''. FAREEHA tace'' wai ke me yake damunki ne haka? Cikin sunnah kike ikirarin ki zubar? To ai yanzu ko cikin shege mai zubar dashi sai wanda bai da imani kisan kai fa? Haka kika koma?" Bata kai ga yin magana ba taji hucin mutum a kusan ta kamar wata guguwa haka ya k'araso wurin nata d'agowar da zatayi sai taga yarima fuskar nan murtuk babu ma alamar dariya ko wasa, ga idanuwan sa da suka rine tsabar 6acin rai wanda ita kanta sosai taji ya bata tsoro dan bata ta6a ganin sa a irin wannan halin ba................ *_Toh fa? Ko wane irin hukunci ne zai d'auka akan wannan matar tasa oho🤷‍♀ ai ita taja🤥 nidai bazan tsaya kallon fad'a ba har aje a gwabjeni haka kawai......._* *_Ku biyoni muga ya zata kaya tsakanin yarima SYDEEK da gimbiya FARHANAH......🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀_* *_Ga wannan bâ yawa saboda ku kawai nayi masoyana amma dai ban cika hawa online ba saboda ina k'auye kuma bansa ranar dawowa ba🙄🤥🤥_* 🤸‍♀🤸‍♀🤸‍♀🤸‍♀🤸‍♀🤸‍♀🤸‍♀🤸‍♀ *_AL'KALAMIN MUNATTU NE✍🏻_* *_'YAR MUTAN KAZAY CE👑_* _Comment_ _Vote_ _Share_ 💥💥💥💥💥 *_'YAR GADARA_* 💥💥💥💥💥 *_NA_* *_MAIMOUNATH O.G.K_* _(Mahnoor)_ _Wattpad@maimounathog_ *💫DA BAZAR-MU WRITER'S ASS💫* *~_We are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are d best among all....DA BAZAR-MU MUKE TUN'KAHO._~* *_FOR YOU:_* *_DEAR_* *_YAH HASSAN_* *_ATK_* *_FAN'S A CIGABA DA YIN HAK'URI DANI DAI ABUBUWAN NE SUKAYI YAWA BAN SAMUN DAMAR YIN TYPING AMMA NI KAINA NA MATSU IN GAMA WALLAHI, MAK'IYAN FARHANAH TACE KU CIGABA WAI HASSADA GA MAI RABO TAKI CE INJI.......🤣🤣🤪🤪_* *Page 81/85* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* °°°°°°°Yanayin da ta ganshi kad'ai yasa tayi sanyi ta rasa ma me zata ce ita kuma FAREEHA sai hello! Hello! Take cewa. Wayar ya amsa daga hannun ta ba gardama ta sakar mishi saboda duk jikinta yayi sanyi ta kasa ta6uka komai, muryar shi ta tsinkaya suna gaisawa da FAREEHA. '' Sister'n mu ya kike? Ya baby da oga?" '' Lafiya lau Al-hamdulillah! Da fatan kuma haka''. FAREEHA ta bashi amsa sai ya mayar mata da cewa'' to ya Nigeria?" '' Gata nan muna sha, yaushe zaku zo?" Sai da ya d'an kalli inda FARHANAH take zaune sannan yace'' in two weeks insha Allah kafin lokacin jikin gimbiya ya d'an warware''. '' Ok! To Allah ya bata lafiya, zan barku haka nan sai wani lokacin, bye''. '' Ok! Thank you sister'n mu, bye-bye!". Nan sukayi sallama da juna ya kashe wayar tare da kallon FARHANAH, ita mamaki takeyi yanda yarima ya sakaye zancen 6acin rai sukayi hirar su da sister FAREEHA kuma ko zancen ta basuyi ba, wato ma ita aka ware ko? Oho miki ai halin ki ne yaja miki. Ajiye mata wayar yayi ba tare da yace komai ba ya tashi ya fita falo, ita dai FARHANAH kallon mamaki take bin shi dashi wai shin fuska nawa ce dashi? Yanzun nan fa yazo a tunzure amma gashi har ya saki fuskar sa duk da dai ba wai ya sakar mata fuskar bane. Cikin dare FARHANAH yunwa ta addabe ta sai murk'ususu take yarima yana ji yayi forget da ita kamar bai ji daga k'arshe ma tashi yayi ya fice daga d'akin ya koma falo yayi kwanciyar sa bisa kujera three seater. FARHANAH kuwa ganin hakan da yayi sai taji wani irin 6acin rai wato ma har da bar mata d'akin me yake nufi da hakan? Ko da zata mutu ba ruwan sa kenan? Tabd'ijam ai kuwa wallahi ba zaiyi baccin nan ba. Tana gama zancen zucin nan ta tashi ta iske shi har can falon, tsaye tayi masa a dai-dai wajen kansa tace'' nifa yunwa nakeji''. Shiru ya biyo baya kamar bai ji ba nan kuwa duk yana jin ta, k'ara harzuk'a tayi tace'' malam da kai fa nake kuma nasan kana ji na kayi min shiru''. '' Fitar min a kai''. Maganar da yarima yayi kenan a tak'aice. '' Oh! Haka ma zaka ce? Wai me ka d'auke ni ne?" Sai da ya tashi yaje ya kunna fitilar d'akin ya dawo ya kalleta yace'' yanda kika d'auke ni''. Ganin zai 6ata mata lokaci sai ta wuce Kitchen tana ta gunguni da zumbura baki murmushi yayi kawai tare da komawa ya kwanta a kujerar. Bata jima ba ta fito daga Kitchen d'in hannun ta rik'e da plate da alama indomie ce ta dafa, ko kallon inda yarima yake batayi ba ta shege d'aki. Tashi yayi ya bi bayan ta, yana shiga ita kuma tana zama a k'asa, zuwa yayi bakin gadon ya zauna ya kalli abincin da gani ta cika masa yaji saï ya d'auke plate d'in daga gaban ta yace'' ba zaki ci wannan yajin ba salon ki hallaka min baby''. Idanun ta cike da k'wallar bak'in ciki tace'' ka bani abu na, ina ce nan nace maka yunwa nakeji amma kayi banza dani shine na nemi abinci na zaka amshe, mik'o min''. '' Ba zaki ci ba fa, ki nemi wani abin kici amma banda wannan yajin''. '' Ok! Well! Ni dama ai buk'ata ta in rabu da wannan cikin kuma yunwa zata iya rabani dashi ai shikenan na huta ma''. Jin zancen zubewar ciki ne yasa yarima ya tashi ya fita yaje ya sake had'a mata wani abincin ya kawo mata. Bisa gado ya haye ya kwanta yana cewa'' kiyi ki gama ki kashe min fitilar d'akin nan ban son haske''. Bata tanka masa ba abincin ta kawai take ci. Bayan ta gama Kitchen ta mayar da plate d'in tasha ruwa sannan ta dawo tabi lafiyar gado, sai yanzu take jin dai-dai gaskiya yunwa masifa ce. Bata k'ara wani juyi ba har sai da taji yarima yana tashin ta asuba tayi. Da k'yar ta iya bud'e idanu saboda wani irin bacci ne yake cin idanun ta, kallon shi tayi suna yin ido hud'u sai taja blanket zata rufe kanta ya rik'e yace'' a,a ki tashi idan kinyi sallah ki kwanta''. Bata tanka mishi ba shima d'in ya fita sha'anin ta yaje ya shimfid'a darduma ya tada kabbara duk tana kallon shi kawai sai ji tayi wani iri a zuciyar ta ta rasa meyasa har ta tsaya take kallon sa kuma wani abu na ta6a heart d'in ta, Allah dai ya rufa mata asiri. Yaye blanket d'in tayi ta sauka daga gadon ta nufi toilet tayi alwala ta fito, nesa dashi ta shimfid'a nata dardumar tayi sallah har ta gama yana zaune da Al-Qur'ani a hannun sa yana karantawa cikin nutsuwa da zazzak'ar murya tamkar wani balarabe ne yake karatun dan tar-tar yake bin karatun sa kowanne yana bashi hukuncin sa. Gado ta koma ta kwanta ba jimawa bacci ya d'auke ta, ya jima a wurin kafin yace sadakallahul azim ya rufe Al-Qur'anin yakai ya ajiye inda ya dace shima ya haye gadon. Cikin wasu 'yan kwanaki da suka biyo baya FARHANAH ta shiga cikin wani hali wanda ta kasa gane kanta sam wani irin feeling takeji gashi yarima ko da wasa bai nuna yana buk'atar wani abu daga gareta bare har yaje mata ko ra6ar jikin ta bai yi ita kuma a ganin ta ai da kunya kuma sauke kaine tare da zubar ajin ta idan har ta nemi wani abu a wajen sa bare ma wannan..... Yarima yana lura da duk wani abu da takeyi kuma ya ganeta yayi banza da ita sai ma ya koma falo yayi kwanciyar sa. Yau ma da misalin k'arfe 11pm yana kwance a falo tazo tayi tsaye tace'' wai meyasa zaka bar ni a d'aki ni kad'ai kamar wata mayya, to ni tsoro nakeji ina mafarkin abin tsoro''. Ba tare da ya d'aga kai ya kalleta ba yace'' a gidan ku da wa kuke kwana?" '' Ina ruwan ka da gidan mu, zancen nan nakeyi ai bazan iya kwanciya a d'akin nan ni kad'ai ba''. '' Ni kuma gashi a nan nake da niyyar kwanciya so ya kamata kije ki kwanta kawai me zai sameki?" Juyawa tayi ta tafi ba tare da tace masa komai ba, yarima kuwa dariyar k'yeta ce fal a cikin sa cikin zuciyar shi yace yarinya zaki ma dawo kan hanya ne. Tashi yayi ya tafi d'akin tana ta juyi bisa gado ta rasa abinda yake mata dad'i wai yau ita ce ke son namiji ya ra6eta lallai wannan cikin zai jawo mata raini gaskiya. Toilet ya wuce jim kad'an ya fito duk tana kallon sa ta k'asan ido wai ita mai wayo kamar tana bacci. Zuwa yayi ya hau gadon ya kwanta tare da juya mata baya, sai da yayi addu'o'i sosai tukun ya shafa a jikin sa tare da lumshe idanu. Cikin bacci yaji ta cakumo shi wai tsoro takeji shi dai murmushin mugunta yake mata yana mamakin hali irin na FARHANAH ace mutum shi sai isa da izza da kuma nuna shi wani ne ita gani take babu wanda ya isa ta nemi abu a wurin sa sai gashi tana neman abinda babu wanda zai iya bata shi idan bâ shi d'in ba. Sai k'ara shige masa take tana cusa kanta cikin k'irjin sa, yarima kuwa iya hak'uri yayi har ya kai da ya kasa wata muguwar sha'awa tazo mishi daman abinka da an dad'e ba'a had'u ba, nan take shima ya shiga lalubar ta...... Yana shafar ta ita kuma sai ajiyar zuciya take saukewa tana mimmik'e mishi kai daga k'arshe ma sai ta shiga bashi taimako suke romancing juna, yarima fa ya rikice sai shafar ko'ina na jikin ta yake. Hannun sa ya tura cikin rigar baccin ta yana shafo albarkatun k'irjinta tare da d'an matsa su ita kuwa sai gantsarewa take yarima dariya fal a cikin sa lallai ciki babu abinda bai saka mata, wata ya sa mata sha'awa wata kuma ya saka mata tsanar namiji ma gaba d'aya taji bata buk'atar ya kusance ta. Wasa yayi nisa inda a hankali yarima ya cire mata rigar jikinta daman shi babu riga a jikinsa, kasancewar an jima ba'a had'u ba da k'yar ya samu ya shige ta har sai da tayi 'yar k'ara ya rufe mata baki da nashi bakin..... Sun d'auki wasu lokuta suna murzar juna har yakai da FARHANAH ta fara gajiya tana son ture shi amma ta kasa duk ya sakar mata k'arfi ni kuwa nace su yarima ko an manta da d'an tayin cikin ne ake murzar ta haka? Cikin kasalalliyar murya da k'yar tace'' bana so ka k'yaleni hakaaa''. Taja maganar abin tausayi dan bai mata da wasa ba. Bai ce mata komai ba saboda ji yake ma tana k'ara kunna shi gashi ta k'ara zamowa sweet ko dan cikin da gareta ne? Shi dai jinta yake kamar yau ya fara tarawa da ita. Duk ture shin da takeyi amma a banza ko gezau baiyi ba sai da yaji ya gamsu d'ari bisa d'ari sannan ya mirgina gefe wani gauron numfashi ta saki jikinta duk yayi sanyi ta kasa ta6uka komai sai hawayen da take zubar wa duk ita taja ma kanta wannan wahalar daman kwanciyar ta tayi ita kad'ai gashi duk ya wahalar da ita a banza, inji ita FARHANAH fa ni ba ruwana. Hannun sa taji akan k'irjinta kafin ta ture hannun tuni ya matso inda take ya rungume ta ya rad'a mata'' idan bai isa ba in k'ara dan ki tabbatar i'm a man''. Kanta ta kawar tace'' Allah ya isa na wallahi sai na had'a ka da mummy, mugu kawai''. Murmushi yayi mai fitar da sauti yace'' ni me nayi? Laifin ki ne ai, ke kika je har inda nake kika gayyato ni ke abin ya dama ni bai dameni ba, taimakon ki kawai nayi''. Fashewa tayi da kuka ya lalubo bakin ta ya had'e da nashi ya hanata yin kukan. A hankali yake shafata a haka ya samu tayi bacci ya tashi ya shige toilet yayi wanka ya fito yaso tayi wankan sannan ta kwanta to amma yasan gajiya ce kuma ba'a son ana yawan damun mai ciki musamman idan tana bacci tunda shima doctor ne yasan dai-dai da akasin hakan. Fitilar d'akin ya kunna ya hau gadon ya zauna yana kallon fuskar ta bakin nan a tsuke na tsiwa a hankali yace rigimammiya kawai. Yau sun kusan su makara wajen yin sallah'r asuba sakamakon wani bacci na mamaki da ya d'auke shi wanda ya kasa gane me hakan yake nufi. A gurguje yayi alwala ya tashe ta itama amma da k'yar ta tashi saboda duk illahirin ga6o6in jikinta ciwo suke mata, mik'a tayi har zata yaye blanket d'in sai taga ashe fa ba kaya a jikinta nan take ta rink'a tariyo abinda ya faru a daren jiya, wai ita ke taya shi har suna romancing juna, me yake shirin faruwa da ita ne? So? No! Ba sonsa take ba, ai kuwa da so bai mata adalci ba, ita dai tasan tanajin wata muguwar sha'awa shine kawai amma bâ wai so ba. Rigar ta ta janyo ta saka sai tayi kamar zata tashi sai ta koma ta zauna tana yatsina fuska yarima yana lura da ita har sai da ya gaji yace'' wai ba zaki tashi kiyi sallah'r ba? Kina ganin time yana shigewa, kina son wasa da addinin ki''. Harara ta bankad'o masa ta cunno baki ta tashi da k'yar tana wata irin tafiya kai kace first night d'in ta ne, tana gunguni ta shige toilet shi dai da idanu yake bin ta. Wanka tayi gami da d'auro alwala tazo ta saka doguwar riga abaya bak'a tayi sallah. Bayan ta gama ne ta koma gadon tayi kwanciyar ta. Duk wunin ranar a rigima sukayi shi wai haushin sa takeji dan ya tara da ita shi kuma abin dariya yake bashi kamar ba da sonta akayi ba hasali ma ita ta nuna tana son ba wai shi bâ. Da misalin k'arfe 2:34pm mummyn sa ta kira shi dan tunasar dashi lallai-lallai su tabbatar sun taso a jibin. Bayan sun gaisa ne mummy take tambayar ina 'yar ta gimbiya FARHANAH sai yarima ya kalli inda take zaune dirshan a k'asa tana hararen shi yace'' mummy 'yar rigima dai, gâta nan sai wani rigima da shagwa6a takeyi kamar wata k'aramar yarinya''. '' A,a nasan halin ka me kayi mata ne?" '' Nothing mummy, kawai rigima ta tashi da shi yau wanka ma ni nayi mata''. Iyyee amma dai yarima baka da kunya inji FARHANAH take cewa a cikin zuciyar ta. Mummy ta amsa da cewa'' bani ita inda ta gaya min gaskiyar al'amarink''. '' Ok! Mummy gata nan''. Yana gama maganar ya mik'a mata wayar ta kara a kunnen ta cikin sanyin murya tace'' mummy ina wuni?" '' Lafiya lau 'yata, kuna lafiya dai ko? Injin babu wata damuwar bai matsa miki ko?" Kunya ta kama FARHANAH cikin dakewa tace'' a,a mummy lafiya lau muke''. '' To me ya faru naji yace kina rigima? Ko wani abin yayi miki dai? Ki gaya min karki 6oye min nima mahaifiya nake a gareki''. '' Uhmm...humm mummy..dam..''. Yarima ya kar6e wayar yace'' mummy yasu mai martaba?" '' Suna lafiya, wai meyasa ka amshe wayar? Baka da gaskiya ko?" 'Yar dariya yayi gami da shafar sajen sa yace'' no mummy ba komai fa wallahi trust me''. '' Hummm ai zaka zo ne nan ka iskoni ka maidani kamar wata kakar ka ko?" '' Sorry dear mum zuwa dare zan kira abba mu gaisa, kafin nan a mik'a mana gaisuwar mu fada''. '' Naji dai ja'iri kawai''. Nan sukayi sallama gwanin sha'awa yanda sukeyi kamar ba d'a da uwa ba, akwai fahimta sosai a tsakanin su. Ajiye wayar yayi ya kalle ta yace'' me kikeso ki gaya ma mummy?" '' Abinda kayi min zan gaya mata''. Ta fad'a ba tare da ta kalleshi ba. Murmushi yayi wanda yake k'ara ma fuskar shi kyau yace'' da kuwa kin k'ara kar6ar wani hukuncin''. Kallon up and down tayi mishi tace......... Nima nace mu had'u a next page.....🤣🤸‍♀🤸‍♀🤸‍♀🤸‍♀ Ku tayani da addu'a in rink'a muku typing kan lokaci😢😒 _Su yarima dai an kwashi gara jiya....🤭🤭🤣_ *_AL'KALAMIN MUNATTU NE✍🏻_* _Share_ _Comments_ _Vote_ *_'YAR MUTAN KAZAY CE👑_* 💥💥💥💥💥 *_'YAR GADARA_* 💥💥💥💥💥 *_NA_* *_MAIMOUNATH O.G.K_* _(Mahnoor)_ _Wattpad@maimounathog_ *💫DA BAZAR-MU WRITER'S ASS💫* *~_We are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are d best among all....DA BAZAR-MU MUKE TUN'KAHO._~* *_FOR YOU:_* *_DEAR_* *_YAH HASSAN_* *_ATK_* _ASSALAMU ALAIKUM FAN'S WASUN KU SUN 'DAUKA NICE *MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE*, TO BA HAKA ABIN YAKE BA BARI IN BANBANCE MUKU, NI *ANTY MAIMOUNATH O.G* DASHI NAKE USING A LITTAFI NA ITA KUMA GA👆WANDA TAKE AMFANI DASHI, DA FATAN KUN FAHIMCI WANNAN TA'KAITACCEN BAYANIN NAGODE🤝_ *Page 86/90* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* °°°°°°°Kallon up and down tayi mishi tace'' bismillah ai ba tsoron ka akeyi ba ehee''. Ta fad'a tare da murgud'a masa baki shi kuwa murmushin mugunta yayi yace'' yarinya zaki zo hannu ne kinyi bayani da kanki''. '' Baka bani tsoro ko d'aya, masu nuna tsoron ka ma wautar su nake gani dan ni banga abin tsoro ba a jikin ka''. Tasowa yayi inda take kafin ta tashi ya cafko ta ya kwantar da ita akan carpet d'in yana cewa'' bari in nuna miki abin tsoron a jikina''. Yana magana yana kiciniyar cire mata riga, hannu tasa ta kare k'irjin ta dan tasan halin sa yanzu zai ce ka murje mata su ita kuma a gaskiya bata so saboda zafin da sukeyi mata dan ba k'aramar matsa suka sha ba jiya a hannun yarima. '' Allah nifa ban so ka daina min, wai dole ne? Nace ban so ka rabu dani''. 'Dan yatsan shi ya d'ora bisa la66an ta yace'' shiiiittt! Karki katse min hanzari salon kuma ki raina ni kice min solopiyo ko?" FARHANAH dai kiciniyar k'watar kanta takeyi tana cewa'' nace maka ban so, ban so ko ana dole ne?" Gira kawai ya d'aga mata alamar eh ana yin dole sai kuma yakai bakin shi kan nata yayi mata wani irin light kiss mai ratsa ga66an jiki, tuni su gimbiya FARHANAH an shiga wani yanayi wanda a da bata san kanta da wannan abin ba, har da wani lumshe idanu tayi. Iskar bakin shi ya busa mata akan fuskar ta sai ta d'an bud'e idanun, 'yar dariya yayi yace'' yadai yarinya ko har kin kamu ne?" Murgud'a baki tayi tace'' kamuwar me zanyi? Ni babu abinda naji daga gareka saboda baka da abinda zaka birg.....'' bata k'arashe ba ya had'e bakin su waje d'aya ya shiga aika mata zafafan sak'onni masu wuyar karantawa bare ma ta fahimci inda sak'on ya dosa. Hannun sa ya d'ora bisa breast d'in ta ya d'an matsa nan take tayi wata irin ajiyar zuciya amma still bakin su har yanzun yana a had'e waje d'aya. Yarima d'an duniya sai da ya tabbatar ya kashe mata jiki da rikitattun wasannin sa tukun ya k'yaleta ya tashi zaune inda ita kuma ta kasa ma tashin domin kuwa duk illahirin jikinta ya mutu murus ta kasa tantance a wane yanayi take. Gefe ya koma yana kallon ta banda murmushin mugunta babu abinda yake yi dan tuni ya harbo jirgin ta, cikin nan ne ya maida ta mai yawan buk'ata amma saboda taurin kai ita ba zata nuna tana son abu ba sai dai in shi zai je gareta ta kuwa kar6eshi hannu bibbiyu sai bayan komai ya lafa ta rink'a hura hanci tana cin magani kamar bata so akayi. Juya kanta tayi gefe d'aya sai ji tayi yace'' tashi muje muyi wanka haka kawai kin jawo min yin wanka ina zaman-zamana''. Ba tare da ta kalleshi ba tace'' me nayi da zanyi wani wanka? Kai dai da Allah ya d'orawa jaraba kaje kayi''. Tashi tsaye yayi yace'' ni kike ce ma jarababbe? Humm shikenan ba zan ce miki komai ba, but wanka ya zama dole dan wallahi k'arya kikeyi kice ba kiji komai ba gashi ko tashi kin kasa saboda kasala''. Yana fad'in haka yayi gaba abin shi ko waiwaye baiyi ba ya shige d'aki, toilet ya nufa dan tsaftace jikinsa saboda a magana ta gaskiya so yayi ma ya zarta hakan amma ya bar ma dare. ***** **** ***** Yau sun tashi da shirin komawa gida sunje sunyi siyayyar tafiya suna tafe suna fad'a musamman ma yarima da yaga tana ma wani magana a wurin kuma har da mishi murmushi nan yarima yayi kicin-kicin ya ja ta suka fice daga store d'in daman ma'aikacin wurin ne, masifa yayi ta mata sai cewa tayi'' ni ka daina min masifa tunda ni ba 'yar ka bace''. '' Amma dai ke matata ce kuma a k'ark'ashin iko na kike dan haka ki kiyaye wallahi kinci darajar cikin da yake jikinki da sai na koya miki hankali tunda na lura yayi miki k'aranci''. Bata sake magana da ganin yanda ya juye ya koma yariman shi sak, kamar bai ta6ayin dariya ba a duniya tuni ya rikid'e ya koma yariman da ta sani a baya *(Na ko gode yarima JININ SARAUTA ba wasa ba, a duk inda kake sai ya nuna, daman wasu ayyukan suke bayyana zahirin ko kai waye).* Har suka zo gida fuskar shi tamau a d'aure ba walwala sam a tare da shi, yarima, FARHANAH kuwa duk sai jikinta yayi sanyi kamar ta bashi hak'uri sai kuma wata zuciyar tace da ita haba dan Allah ina ajin naki duk yake ko kin manta koke wacece? Kin manta matsayin ki ne? Kin manta cewa namiji bai isa ki rusuna mishi ba? Da wannan zancen zucin ta basar da maganar bada hak'uri( shed'an mugu ne sai dai mu nemi tsari daga shi, duk wannan hud'ubar ta shed'an ce fa tunda yasan idan ta bada hak'uri shikenan ta fita a laifi amma k'ememe ya hanata). Washe gari jirgin su ya d'aga zuwa gida Nigeria, ko da suka sauka tuni anzo d'aukan su, motocin gidan sarki su uku ne suka zo cike da 'yan tarben su da masu tsaron lafiyar su. Kowa yayi murnar dawowar su sai wage baki sukeyi, Sulaiman shine driver'n yarima dan haka motar shi suka shiga, motar su yarima itace a tsakiya d'aya a gaban su sai d'aya a baya, cikin nutsuwa suke tafiya har suka k'arasa gidan sarki. Mai tsaron k'ofar yana jin sunzo ya wangale musu gate suka shige one by one. Haba ai tuni gida ya rikice da murnar dawowar su har wata 'yar k'warya-k'waryar liyafa aka shirya musu specially dan jin dad'in zuwan su kuma daman tuni fada tasan da samuwar cikin da FARHANAH tayi, ita dai saï ikon Allah take kallo. A washe garin ranar da suka zo ansha shagali a masarautar abin sai wanda ya gani, lallai kam yarima d'an gata ne a dalilin soyayyar da akeyi masa ne har ta shafi ita kanta gimbiya FARHANAH. Tun ranar da suka zo rabon da FARHANAH ta saka yarima a idanun ta domin kuwa ya daina shigowa 6angaren ta sai abun ya fara d'an damunta, me yake nufi da ita ne? Ko dai taje part d'in sa ta gani ko bai da lafiya ne, to amma a ganin ta idan tayi hakan kamar ta zubar da ajin ta ne. Humm lallai ana wata irin rayuwa a nan, duk wannan fad'in ran kud'i ne ya kawo hakan? Meye abin duniyar da duniyar kanta ma? Har yanzu baki san rayuwa ba FARHANAH. Wasa-wasa fa yarima ya kai sati d'aya basu ga juna ba shi da FARHANAH, tun tana daurewa har abin ya fara damunta sosai, duk yanda taso ta yak'ice tunanin sa amma abun yaci tura, kwance kawai take a d'aki sai tunanin yarima takeyi tana ta sak'a da warwara ta yanda zata 6ullowa al'amarin, ya zama dole ta ajiye komai taje gareshi, da wannan tunanin ne ta tashi ta saka alk'yabbar ta dake a gefen ta daman a shirye take dan bata jima da sauka k'asa ba duk da dai bata cika zaman falon ba ma yanzu saboda yawan kasalar da ke damunta. Fitowa tayi cikin takun ta na isa da k'asaita tana taka matattakalar dan saukowa ga takalmi mai tsini a k'afar ta cikin rashin sa'a ta kurd'e nan take ta fad'i a wurin ta wullo zuwa falon k'asa wata iriyar k'ara ta saki kan kace me tuni jini ya fara ambaliya. Hadiman ta suka rikice da gudu shafa'atu ta nufi cikin gidan su mama wato hajiyar yarima taje ta gaya musu abinda ke faruwa. Ai kuwa hatta mummyn yarima ba'a barta a baya ba tuni sunyo part d'in FARHANAH, su mai martaba basu san me ake ciki saboda suna fada. Ganin yanayin da take ciki ne yasa mummy da gaggawa ta d'auki wayar ta dan kiran yarima sai gashi ya shigo cikin saurin sa ashe tuni yaji labari an gaya masa, abu a cikin masarauta ba mai 6oyuwa bane domin kuwa kan kace me labari ya baza ko'ina sarki ma bayan an tafi da FARHANAH shi da dogarawan shi dasu waziri suka take musu baya. Likitoci ne birjik a kanta sun duk'ufa dan ceto ran FARHANAH dan ko motsi batayi sun hana yarima shiga amma yace ina sam wallahi bazai yiwu ba saidai ayi komai a gaban idanun sa, yaso yasa hannu a lamarin amma doctor'n ya dakatar dashi ganin bai cikin hayyacin sa. Da k'yar suka samu ta farfad'o amma idanun ta har a lokacin suna a rufe lumfashi ne kawai ke fita a hankali da alama bata ma san inda kanta yake ba. Yarima ya kamo doctor yace'' doctor gaya min ya matata da baby na suke? Please ka gaya min". Doctor dafa kafad'ar yarima yayi yace'' calm down friend, mun samu mun ceto rayuwar matarka, muje office zanyi maka bayani''. Haka yarima ya bishi a baya kamar wani zautacce, bayan sun zauna ne doctor ya kalleshi yace'' am sorry to say, cikin jikinta ya zub....'' bai bari ya k'arashe ba ya buga table d'in gaban shi yace'' no!! No!! Doctor karka ce min nayi loosing baby na, ina son baby na please....'' ya kasa magana yau fa yarima ya rikice wai har da hawaye yakeyi. Ko da labari ya riski masarautar kowa Jikin sa yayi sanyi kuma sun tausaya ma yarima matuk'a dan ya k'wallafa rai akan cikin nan sosai. Sai da mai martaba ya saka shi a gaba da nasiha da ban baki ya d'an saki shima ba sosai ba. Kwana biyu a tsakani FARHANAH taji sauk'i tunda ta samu labarin babu cikin jikinta sai itama ta shiga damuwa saboda a yanzu babu abinda takeso da gani irin taga ta haihu da yarima dan wani irin sonshi ne yake d'awainiya da ita duk da dai bata furta mishi ba. Wannan damuwa ta saka mata zazza6i da ciwon kai mai tsanani ko falo bata fita tana cikin d'aki sallah da cin abinci kawai yake tashin ta daga gado duk da dai abincin ma bâ wani dad'in sa takeji ba, ga yarima yayi wuyar gani bare ma yanzu da ake shirye-shiryen bikin bud'e asibitin shi bai samun zama sosai kuma yaji cewar bata da lafiya daga bakin mahaifiyar shi dan ita a zaton ta ma ya sani a yanda tayi mishi maganar FARHANAH ce masa take ya jikin matarsa yace da sauk'i amma bai ma sani ba. Yau ranar lahadi ya kasance ranar hutun duk wani ma'aikaci yarima yana kwance bisa gadon sa ba bacci yake ba tunani yake yana son yaje yaga ya jikin nata sai wani sashe na zuciyar shi yana masa gargad'in ya share ta kawai har sai ta nutsu tayi hankali, maybe ma tana sane ta fad'o dan kawai ta 6arar masa da ciki, cikin da duk duniya banda son Allah da manzon sa sai iyayen sa babu abinda yake k'auna irin sa gashi yanzu ta zubar mishi da kayan shi saboda taurin kai da rashin k'aunar shi. Humm yarima a da ne yanzu fa zuciyar FARHANAH cike take da so da kuma k'aunar mijinta ta kasa furta mishi ne sakamakon kunyar sa da takeji. Tana kwance har a lullu6e ma da blanket damuwa ce tayi mata yawa wanda sakamakon hakan ne zazza6i yak'i barin jikinta duk da 'yan aiken da mummy take aiko mata dan ganin lafiyar ta, wuni suke suna zarya a tsakanin 6angarorin nasu. Kamar a cikin mafarki ta juyo k'amshin sa wanda ya rigayi sallamar shi dan k'amshin turaren sa shi ya fara kai mata ziyara kafin taji yayi sallama da wata irin murya mai sanyi da nutsuwa. Tamkar ta taka rawa haka taji sai dai ba zata iya ba ta gimtse sallamar ma k'asa-k'asa ta amsa da muryar ciwo ga wasu 'yan siraren hawaye da taji lokaci guda sun zubo mata. 'Dakin da d'an duhu shiyasa bata ankare ba sai kawai ganin shi tayi ya k'araso bakin gadon ya zauna yace'' sannu ya jikin naki? Ban san baki da lafiya ba''. Wani irin tak'aici ne ya ziyarci zuciyar ta saboda tsananin haushin maganar shi, wai bai san bata da lafiya ba, me wannan man d'in yake nufi ne wai? Inyi loosing babyn shi har yana tambayar bai ma san bani da lafiya ba? Lallai.... Lallausan hannun sa da taji akan wuyan ta shi ya katse mata maganar zucin da takeji tare da haifar mata wani irin abu wanda ta kasa gane ko meye. Jin zafin da jikinta yayi ne yasa ya janye hannun sa cikin sauri yace'' me yasa baki kirani a waya kin gaya min baki da lafiya ba sai a wurin mummy naji? Wannan ba hali mai kyau ne ba ki canz.....'' bai kai aya ba wayar shi ta katse mishi maganar da yake son furtawa. Wayar ya ciro a aljihun sa ganin mai kiran ne ya saka shi yin murmushi kad'an yayi picking yace'' assalamu alaiki''. Jin alaiki yasa gaban FARHANAH ya tsinke ta saké nanatawa alaiki? Kenan mace ce ta kira shi ko? Wacece wannan? *_TIR'KASHI....RIGIJI GABJI😳 KO DAI YARIMA DALLELIYAR BUDURWA YAYI NE FARHAT BATA SANI BA?_* *_Amsar tambayoyin kaf d'in su suna a gaba ku biyoni ni nayi gaba......🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀_* *_Zaku d'an jini shiru na kwana biyu sakamakon sim d'ina da zan cire in saka a sabuwar wayata, kunga typing sai na saba da wayar kenan tunda har whatsapp zan sake komai sabo dal zanyi🤣 ah to tunda gashi yarima ma yayi sabon kamu.......🤭_* *_Bani da lafiya, ku sakani cikin addu'o'in ku🙏_* *_NA GAISHE KU 'YAN HANNUN DAMA TA🙌🙌_* *_'YAR MUTAN KAZAY CE👑_* 💥💥💥💥💥 *_'YAR GADARA_* 💥💥💥💥💥 *_NA_* *_A.MAIMOUNATH O.G.K_* _(Mahnoor)_ _Wattpad@maimounathog_ *_Al-hamdulillahi na dawo lafiya lau saidai nayi loosing komai nawa kamar yanda kuke gani hatta no dina yak'i yin whatsapp saï da sabon sim na bud'e kuma insha Allah zan cigaba daga yanzu har zuwa k'arshe da izinin mai duka._* *_FOR YOU:_* *_DEAR_* *_YAYA HASSAN_* *_A.T.K_* *Page 91/95* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* ******Hannun sa ya d'auke ya cigaba da amsa kiran wayar yace'' wato kice munada bak'uwa kenan ko?" Daga can ta amsa masa da'' eh mana brother, hutu na d'auka a wajen aiki na specially dan kawai inzo in ganka''. Murmushi yayi yace'' ok! Can't wait saï kinzo, Allah ya kawo ki lafiya, ki gaishe min da 'yan gidan''. '' Ok to bye-bye''. Da haka sukayi sallama ya saka wayar a aljihun sa ya kalli inda FARHANAH take kwance tana hawayen tak'aicin sa ko ince kishi yana bid'ar hallaka ta. Nayi hausar 'yan wani gari. Hhhh..... Cikin maganar shi mai kama da rad'a yace'' wato ke rayuwar ki duk a kuka zata k'are ko? Me akayi miki ne? Ko dai ciwon ne ke damunki?" Daga inda take kwance ta jefo masa wata uwar harara gami da kawar da kanta d'aya gefen saï yayi murmushi yace'' a gani na cikin da baki so ya zube to ai shikenan, maybe ma ke kika zubar dashi ban sani ba''. Wata irin juyowa tayi gami da tashi zaune tace'' wai me ka d'aukeni ne? Nifa bâ irin kucakan 'yan matan ka can bane dan nasan abinda nakeyi tunda da ilimi na ka ganni''. Jin kalmar 'yan mata saï abin ya bashi dariya ya kuma gane inda duk wannan borin nata ya dosa, dan ya k'ara hauda ta cewa yayi'' uhm..humm ai naga alamar ilimin naki bai miki wani amfani bâ shine ma yasa nayi tunanin k'ara aure tana iya yiwa ita amaryar tanada hankali da kuma ilimin da kike maganar kinada shi ni kuma banga alamun hakan a gareki bâ''. Cikin kuka tace'' saï me dan kayi aure? Waye ya damu da kai har da kake wani hura hanci kake fifik'a''. '' Ke nifa mai tsada ne, bâ zaki gane hakan bâ saï kinga amaryar ki, tana nan zuwa in two days zata zo ta gaishe ki''. Batayi magana bâ ya tashi tsaye saï kuma ya d'an rank'ofo kan gadon yanda zataji yace'' please uwargida ki rik'e girman ki dan Allah karki nuna mata irin wannan halayen naki dan ita bata d'auki dukiya a bakin komai ba duk da tanada su fiye da tunanin ki''. Ya k'arashe maganar gami da shafo hawayen fuskar ta ya sake cewa'' bari in duba ki inga abinda yake damunki''. Hannun nashi ta bige tace'' banso rabu dani''. '' Na isa ma? Humm so kike mummy tayi fushi kenan? Ke ai 'yar gatan ta ce''. Da k'yar ta yadda ya duba ta daga k'arshe ya aika a siyo magani. Bai bar d'akin ta ba saï da ya tabbatar da tasha maganin tukun ya fita. Yana fita ta fashe da wani irin kuka mai cin rai damuwa tayi mata yawa dan ma cikin magungunan har da na ciwon kai saï da tasha sannan ta d'an ki sauk'i. Me yarima yake shirin aikata mata ne? Aure zai k'ara? A ina ma to yaga yarinyar har tasan gidan su? To kodai can daman suna tare bata sani bane? Wallahi bâ zata iya sharing mijinta da wata bâ, Allah ya gani tana sonshi sosai son da ita kanta bata san time d'in da ya shigeta ba, tayi iyaka bakin k'ok'arin ta dan ganin ta hana faruwar hakan amma abin yaci tura ta kasa hak'ura. Fashewa ta k'arayi da kuka tana d'auko wayar ta ta bugawa 'yar uwar ta FAREEHA tana picking saï taji FARHANAH tana kuka tana cewa'' sister i can't tolerate it, wallahi bazanyi iya b....'' muryar ta ta sark'e har da tari tana mai cigaba da kukan ta abin tausayi. Cikin tashin hankali FAREEHA tace'' innalillahi! Wai me ya faru ne haka da har kike neman kashe kanki? Ke bâ zaki hak'ura kuyi zaman lafiya da mijinki bâ ko? Allah d'aya zan had'a ki da daddy ince ga abinda kikeyi a gidan mijin''. '' Sister bâ abinda kike tunani bane, wai fa aure yace zai k'ara''. Ta fad'a cikin sheshshek'ar kuka. '' Aure? Shi wa? FAREEHA ta buk'ata. '' Yarima mana, nidai bazan iya zama da kishiya ba, bazan iya sharing mijina da wata can kucaka ba''. '' Wai daman shiyasa kike kuka ko kunya bakiji? Kishiya kika ma kuka? To ai yarima da gaskiyar shi zai zauna ne da ke kad'ai kina mishi abinda kika ga dama saï kace ke kad'ai ce mace? Ni ina bayan yarima d'ari bisa d'ari tunda ya bi ki amma baki gani ai saï ki zauna ya auro wata ta k'wace shi''. '' Yanzu saboda Allah sister maimakon ki bani shawara saï kiyi ta gaya abinda ranki yaso?'' '' To me kike so ince miki ni? Ai wanda akeso shi ake kishi to ke kuma kince bai isa ki so shi bâ dan haka banga abin tayar da hankali ba''. '' Injiwa? Ina sonshi mana, saï son ya kasheni ne sannan zaku gane, wallahi ina sonshi mijina fiye da yanda baki tunani saidai ni bansan yanda zan nuna mishi ba, na kasa sister ya zanyi?" Zuciyar FAREEHA fari k'al dan farin cikin jin wannan maganar, lallai FARHANAH ta shiryu, saï kuma taji mugun tausayin 'yar uwar tata yana shigar ta musamman ma ta taji tana kuka gashi ba lafiya ce da ita ba. FAREEHA tace'' yanzu dai ki daina kukan nan share hawayen ki 'yar uwata kinga ba lafiya ce dake ba, ki kwantar da hankalin ki mû bi komai a sannu kinji?" '' Ok!" abinda FARHANAH tace kenan. Nan suka d'an tattauna ta mata nasiha sosai dan halin su ba d'aya ne ba ita FAREEHA tanada hankali da hangen nesa ga nutsuwa, ita kuma FARHANAH isa ce tayi mata yawa da *GADARA* komai nata nunawa take ita dan ta isa ne za'ayi mata abu. Wannan kenan........ ****** **** ***** Saï ana washe garin bikin bud'e likitar yarima sannan ta iso. Tafe take cikin nutsuwa a hankali take murza sitiyarin motar kid'a ne ke tashi a cikin motar har ta isa k'ofar gidan, horn tayi cikin masu tsaron k'ofar ne d'aya ya lek'o ganin motar ma yasa ya gane ko wacece da hanzari ya koma ya bud'e mata gate ta shiga. Parking taje tayi inda ake ajiye motoci kafin ta fito tuni wani daga cikin hadiman gidan yazo da gudu ya bud'e mata k'ofar mota ta fito. Wow!!! Abinda na fad'a kenan ganin wacce ta fito daga motar lallai akwai sha'ani tabd'ijam iyyyeeee wacece haka? Masha Allah! Gaida ta yayi cikin isa tace'' lafiya, ga key ka fito min da bag d'ina yana booth saï kayi min locking car d'in da kyau ka kai min ciki''. Ta fad'a tare da jefa masa key d'in bai bari yakai k'asa ba ya tare saï ya fad'o hannun sa. Cikin isa take takun ta masu hidimar masarautar saï durk'usawa suke suna gaishe ta dan sun san halin ta sarai. Humm ni kam nace saï kace wata sarauniya ko gimbiya? Irin wannan nuna isa haka? Humm nayi shiru dai bari muga wacece ita. A haka har ta k'arasa part d'in su mummyn yarima ta shiga falon tare da yin sallama. Amsa mata akayi, mummy tana zaune da hadiman ta suna hira dan ita bata da girman kai irin na matan saraki ko kaga matar sarki tace a wani matsa mata k'afa ko makamantan su, a,a ita dai suna mata hidima da duk abinda ya shafi ayyuka duk sunayi, wasu su zauna kusa da ita wasu kuma suna aikin gidan. Mummy ta fad'ad'a murmushin ta ganin yarinyar tace'' oyoyo my sweet daughter kece a garin?" Da gudu ta k'araso gami da fad'awa jikin mummy tana cewa'' wallahi kuwa mum, i really miss you so very much''. Kafin ta bata amsa ta kalli wa'yanda suke tare da ita a zaune tace'' ku bamu wuri zamu d'anyi hira da daughter''. Sannu da zuwa sukayi mata sannan suka wuce d'aya bayan d'aya. Kayan ta ne aka shigo mata dasu tare da bata key d'in ta mummy ta bada umarnin a kai mata sama a d'akin da ta saba sauka. Kan kace me an cika gaban su da abubuwan ci da su fruits. Mummy tace'' daughter HASINA ga abinci kici nasan dai kina tare da yunwa''. '' Uhhh to kad'an ba, dan ban jima da cin cake ba fa''. '' Uhmm cake abinci ne? Har yanzu kina nan da k'in cin abinci ko?" HASINA tace'' no mum ai yanzu ina ci bari ai zaki gani''. '' Ok! Amma fa yau kinyi mana surprise dan baki kira kince kina zuwa ba, saï dai kuma in yayan ki kika kira ban sani ba''. '' Uhm na kira shi amma ban fad'a masa ranar ba dan in baku mamaki''. '' Ai kuwa da anyi babu ke dan gobe ne za'ayi bikin bud'e likitar yayan ki''. Dafe k'irji tayi tace'' what? Haba mum shine ko ya gaya min?" ta tambaya cike da shagwa6a. Toh fa.... Mum tayi mata hararar wasa tace'' ah to wannan kuma tsakanin ku ne ni babu ruwana, yanzu dai tashi kije kiyi wanka idan kin huta saï muyi hirar d'azun nan ma munyi waya da maman ki itama bata sanar min zaki zo ba''. 'Yar dariya tayi tace'' laah ai itama d'in bata sani ba daga can wajen aikin ma d'an hutu ne na one week na d'auka na gaji da aikin nan ne wallahi, kuma fa daga zuwa na mama ta koro ni wai ai ban fad'a mata zanzo ba, ni kuma nace to a bani key d'in mota ta wacce take a nan gidan in tafi shine fa ta bani wai inzo wajenki ita bata iyawa dani''. '' To ai saï hak'uri indai harkar aiki ce, maman ki kuma rabu da ita kishi take, tashi ki tafi nasan dai an shirya miki komai''. Amsawa tayi tana dariya ta tashi ta haye sama, mummy ta kai duban ta inda take cike da tausayin yarinyar. Tausayi? Tausayin me kuma? A yanda naga yarinyar na rawar kai ai na zata bata da wani abin tausayi a tare da ita kenan kallon kitse nake ma rogo? *_WACECE HASINA?_* HASINA Alhaji Tanimu mai canji shine ainahin sunanta ta, kamar yanda kuka ji abban ta mai kud'i ne sosai fiye da tunanin mai karatu, shahararren d'an kasuwa ne kuma yana harkar siyasa ma. HASINA 'yace ga k'anwar mummyn yarima kamar yanda na fara fad'a muku a can baya, nace daku daman tana zuwa gidan su yarima saboda 'yar k'anwar mummy take. HASINA ta taso cikin gata na kowane 6angare wato na uwa da uba, sunyi ita k'ok'arin su dan ganin cewa tayi karatu saboda haka ne ma yasa taje U.S tayi karatun lauyer. Sakamakon yawan tafiye-tafiye da abban HASINA keyi ne sukayi hatsarin jirgin sama ya kama da wuta Allah ya masa rasuwa. Sunyi kuka sosai ita da maman ta, a sanadin hakan ne yasa maman ta wato hajiya Maryam ta fantsama business a yanzu haka k'asashe take zuwa saboda harkar kasuwanci kuma ta samu alkhairi da dama tunda daman abban HASINA ya bar musu dukiya. HASINA ta gama karatun ta tazo aka d'auketa aiki amma Abuja take da zama a yayin da maman ta take Kaduna inda dai su yarima suke. HASINA taso yarima kamar ta mutu ko ince har yanzu tana sonshi tunda ta kasa fiddo miji tayi aure, mummyn yarima ma taso su had'a zumuncin nan amma yarima firr yak'i yace shi ba yanzu ba. Ganin haka ne ma maman HASINA tace a k'yaleshi in bai so kar ace za'a had'a su ta k'arfi dan ko anyi auren ba wani dad'in zama da juna zasu ji ba shiyasa ma aka bar maganar but HASINA kam tana son yarima ko sunanshi aka kama saï taji sanyi a ranta. Toh fa! Ya abin yake kenan? Zaman ta a Abuja shi ya rage mata damuwa na yawan tunanin yarima da takeyi shi dai yace ba wai ya tsaneta bane, a,a da auren ne kawai bai son ta amma dai so na 'yan uwantaka yana yi mata shi. Wannan shine labarin HASINA 'yar k'walisa a tak'aice. Hhhh kai nice fa na saka mata sunan ganin lank'wai d'in nata yayi yawa. *_CIGABAN LABARIN...._* Washe gari aka bud'e likitar yarima inda akayi shagulgula sosai jama'a da dama sun samu halartar taron abin dai saï sambarka masha Allah komai ya tafi cikin tsari kamar yanda akeso. Yanda aka tsara ginin asibitin ya birge kowa kuma maimakon a saka SYDEEK saï aka sa HABIBULLAH HOSPITAL. Komai ya k'ayatar dan an zuba ma'aikata masu k'wazo da ilimin abin. A wajen taron yarima yaga HASINA amma yayi kamar bai ganta ba, ga gimbiyar tashi a kusa dashi ko magana batayi saboda kishi had'e da haushin sa sun hana mata komai. Yarima bai samu kanshi ba saï da k'yar bayan taro ya watse zasu shiga gida sai abokin sa ya jawoshi gefe yace'' kayi a hankali dai, meye na gudun ai mun gane inda zaka nufa jarabar ta motsa ko?" Lallai yayi masa iskanci amma ganin dogarai da jama'a yasa yace'' nagode zamu had'u ne wallahi''. Dariya yayi masa shi kuma yaci magani kamar bai ta6a dariya ba har da bak'in eyes glasses a manne a fuskar shi alamun ba wasa kenan. A gajiye yake aiwatar da komai nashi saboda hayaniyar da ya shiga yau, kanshi ne yake sara mishi dan ciwo da k'yar ya iya yin wanka ya fito ya saka kaya sai kawai ya kwanta duk da yunwar da yakeji. Zakuji nace yunwa, to yarima bai ci komai a wajen taron nan ba dan shi mutum ne mai k'in yarda duk da an saka tsaro ta kowanne 6angare, abinci da dai sauran su. Abu yakeso marar nauyi idan zai samu gashi fitar ma so takeyi tafi k'arfin sa, tashi yayi ya zauna a bakin gadon had'e da dafe kanshi a hankali yace'' oh God!". Wayarshi ya d'auko yaga lokaci ya fara tafiya sai ya kira number'n mummyn shi bayan tayi picking ne ya gaishe ta tace'' lafiya kuwa kake kirana warhaka?" '' Mummy i'm hungry please help your son''. Yarima ne ya fad'a cike da shagwa6a wai ko zata ji tausayin sa, sai ji yayi tace'' ka kiyayeni fa, ina matarka ne da kake kirana dan yunwa? To karka sake min haka ban son shirme''. '' Allah ya baki hak'uri mummy, shikenan tunda kin daina sona bari kawai in kwana da yunwar''. Jikinta ne yayi sanyi tace'' to wai bâ nace kasa matarka ta kawo maka ba? Nifa kaga wajen mai martaba zanje dan haka ka nemi mafita tun wuri''. Bata bari yace komai ba ta kashe wayar ta dan kar ya cika ta da surutu ita kuma wajen sarki zata je. Ohh! Kuji su mummy ma other room za'aje wato dai zuwan bashi da babba bashi da yaro......hhhhhh ah to ni kuma da tsegumi ji nakeyi kamar in bita inga soyayyar manya........ Yarima ya rasa yanda zaiyi sai kawai ya yanke shawarar kiran FARHANAH Allah yasa ma yanada number'n ta. Kira yayi har ta tsinke ba'a d'aga ba sai a karo na uku yaji ta d'auka, ita dai zuciyar ta cike da tunanin ko waye warhaka? oho. Kafin tace wani abu tuni muryar shi ta daki dodon kunnen ta wanda shine ya bata amsar tambayar ta na ko waye. Da wata iriyar murya yace'' assalamu alaikum''. Bata amsa ba dan muryar shi ba k'aramin tafiya tayi da ita ba, ashe haka yake da zak'in murya a waya? Tunanin ta ya katse ne a dai-dai inda yace'' hello! Kina jina kuwa?" Ta mayar masa da'' wa'alaikumus-salam, please who is?" Kuji FARHANAH da iskanci kuma fa ta ganeshi kawai dai mai hali bai barin halin sa inji hausawa. Murmushi yayi mai sauti wanda yakai ma dukkan sassan jikinta har ya haddasa mata wata muguwar kasala, yace'' kizo ina neman ki idan ba zaki damu ba''. '' Har na fara bacci fa ka tashe ni". FARHANAH ta fad'a cike da shagwa6a had'e da kissa''. Yarima yace'' karki damu ai ba zaki dad'e''. Kashe wayar tayi ba tare da tace masa komai ga wata irin kasala da takeji sakamakon muryar yarima da taji, sai taji ta yau tafi ta kowane lokaci zak'i, a take kishi ya turnik'e ta da ta tuno da maganar shi ta amarya, da gaske ko kuwa? Oho. Tashi tayi ta sauya rigar jikinta zuwa abaya bak'a sai ta d'auki hijab ta saka, daman yanzu ta fito daga bathroom kawai dan ta mishi *GADARA* da isa ne yasa tace har ta fara bacci. Turare ta fesa tare da d'aukar wayar ta ta fita gami da rufe k'ofar d'akin. Ta baya tabi inda zai sada ta da cikin gidan yarima kai tsaye ba tare da wani ya ganta ba. Falon a bud'e tana kyautata zaton shi zai bud'eshi dan ba'a barin sa haka, wane mutum. Shiga tayi ta rufe k'ofar a mamakin ta gani tayi TV a kunne ba kowa fitilar d'akin ma mai duhuwa kawai aka bari, ta6e baki tayi ta haye sama gabanta yana d'an bugawa kad'an-kad'an. Tura k'ofar d'akin nashi tayi daga nesa ta hangeshi kwance a k'asa bisa carpet yayi rigingine, wato shi wannan kwanciyar k'asa ce ke birgeshi ko? Abinda FARHANAH tace kenan a cikin zuciyar ta. Sallama tayi a can k'asan murya amma yaji ta sarai bai waiwayo ba ya amsa mata d'akin ba wadataccen haske ta k'arasa inda yake ta zauna a k'asan itama tace'' ina wuni?" Yayi matuk'ar mamaki fa tabd'ijam tunda take a gidan nan bata ta6a gaishe shi ba sai yau kuma har da su zama? Anya FARHANAH da ya sani ce kuwa? Humm...... Yana dafe da kai yace'' lafiya amma ba lau ba, please ki taimaka ki sama min wani abin da zan ci yunwa nakeji ban ci komai ba yau duk hayaniya tayi min yawa kaina yake min ciwo''. '' Kamar me kenan?" '' Salad zaki had'a min shi kawai nake ganin zan iya ci''. Tashi tayi tsaye tace'' ina Kitchen?" Shima ya mik'e tsaye ya fita ta bishi a baya suka fita ya nuna mata Kitchen d'in ya koma d'aki. Aljannar duniya kenan Kitchen d'in ma gwanin sha'awa komai a tsaftace kamar ba namiji ne keyi masa girkin ba. Ta sakankance tana aikin gyara salad duk da ta iya amma abu ne wanda ta jima batayi ba shine ma yasa ta d'au lokaci tana gyaran. Wani plate mai d'an girma ta d'auko ta yayyanka salad d'in da sauran kayan had'in sa tayi masa ado kamar ba ci za'ayi ba, wani plate d'in irin sa ta d'auko ta rufa akan wancan juyowar da zatayi dan d'aukar hijabin ta sai ganin mutum tayi a bakin k'ofar Kitchen daga ciki ya hard'e hannayen sa bisa k'irjin sa ita kawai yake kallo. Cikin hanzari ta warci hijabin ta saka tana mai hararen shi tace'' shine zaka zo kayi ta kallo na ban sani ba?" Murmushi yayi yace'' nayi laifi ne dan na kalli matata?" '' Me ma ya kawo ka Kitchen kamar wata mace?" Baiyi magana bâ ya fita itama ta d'auki salad d'in ta bishi a baya suka haura sama inda bedroom d'in sa. Tana ajiyewa ta kama hanyar tafiya sai yace'' ina zaki je?" '' 'Dakina in kwanta bacci nakeji" Ta bashi amsa. '' Nan ma ai d'akin ki ne ko a cikin daji kike?" Juyawa tayi zata fita taji k'ofar a gark'ame ta rasa ya akayi sai ta juyo ta kalleshi yana cin salad d'in sa ko a jikinsa, cewa tayi'' ka bud'e min in fita''. '' Zaki iya bud'ewa da kanki ai''. '' Ka bani key d'in to''. '' Kinji ki da neman magana key kika gani a hannuna? Kizo ki kwanta a nan idan ma zaki kwanta dan babu inda zaki je cikin daren nan''. Saboda gardamar tsiya har ya gama bata daina mitar ya bud'e mata k'ofar ba shi kuma bai ce ko uffan ba har sai da ya gama yaje cikin bathroom ya tsaftace bakin sa ya dawo ya fesa turare daman kayan bacci ne a jikin sa, fridge d'in d'akin ya bud'e ya d'auko gorar ruwa ta faro ya kwankwad'a sannan yaje inda take cak ya d'aga ta sai gado..... Tana masa magiyar ya sauke ta amma yak'i sai da ya dangana ta da gadon tukun ya kashe fitilar d'akin ya kwanta kusa da ita ya shiga addu'o'in sa wanda suka zame masa jiki ita kuma FARHANAH tayi shiru tana sauraren abinda zai biyo baya. Can taji yasa hannu ya rungumo ta ta baya, wato bayanta na kallon gaban sa saï yasa hannu yana shafar jikin ta ita kuma duk ta takure gabanta sai fad'uwa yake kamar yau suka fara kwana a tare, ta rasa dalilin wannan abu. Ba tare da yace da ita uffan ba yake aiwatar da komai nashi amma dai cikin sanyi yake bin al'amarin. Can wasu 'yan lokuta ya juyo ta ya rad'a mata cewa'' tsoron me kike ji ne haka duk kin takure kanki?" FARHANAH ba magana saï raba idanu takeyi a cikin duhu shi kuma ya cigaba da sarrafa ta cikin k'warewa da nutsuwa kuma. Hannun sa ya tura cikin rigar ta wanda ya haddasa masa jin wata irin kasala da shiga wani yanayin daban, a yau komai ya canza takeji kamar ma bai ta6a yi mata komai ba. Tun FARHANAH tana nok'ewa kai har dai ta bada kai bori ya hau, tuni sun shiga romancing juna cikin nuna tsantsar soyayya. Sai da komai ya lafa ne yarima ya mirgina gefe d'aya yana fitar da wani irin numfashi kai kama da na wahala. Yau rasa me yake damun sa ne tun daga ciwon kai na d'azun har yanzu abin yake son ya zame masa ciwo dan har wani zazza6i-zazza6i yake ji wanda ya kasa tashi ma yayi wanka. FARHANAH ma tana d'aya gefen tana kukan ta a hankali yanda ba'a ji a cewar yarima ya nuna mata k'yeta tunda yasan bata da lafiyar kirki amma yazo yayi mata haka. Toh kuji wata magana kuma? To yo shi baki lura da nashi jikin? Humm.... Duk su biyun sun kasa tashi, to ko me yasa hakan? Wai meke shirin faruwa dasu ne? Me hakan yake nufi? Amsoshin suna cikin next page insha Allah, ku cigaba da yin hak'uri dai..... Anyi biki lafiya lau an watse lafiya amma jina shiru da kukayi shine bak'i garemu wanda suka zo wurin auren, to shine bamu samu zama ba suna fita gari. Yanzu fa sabuwar waya ce zan iya yi muku readmore 10 ma🤓😎 amma ku biyoni dai.....🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀ *_'YAR MUTAN KAZAY CE👑_* 💥💥💥💥💥 *_'YAR GADARA_* 💥💥💥💥💥 *_NA_* *_A.MAIMOUNATH O.G.K_* _(Mahnoor)_ _Wattpad@maimounathog_ *💫DA BAZAR-MU WRITER'S ASS💫* *_~we are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are d best among all....DA BAZAR-MU MUKE TUN'KAHO.~_* *_Assalamu alaikum 'yan uwa da abokan arziki ina yiwa dukkan d'aukacin masoya barka da sabuwar shekara Allah ya maimaita mana yasa mun shigo ta cikin sa'a, Allah ya bamu lafiya da wadata gami da kwanciyar hankali a k'asashen mû baki d'aya, ameen!!!_* *_Bazan ta6a mantawa daku ba yanne na HASSAN ATK & ABDUL-RAHMANE IBRAHIM dubun gaisuwa da fatan alkhairi zuwa a gareku, Allah ya kare ku a duk inda kuke, godiya nake🙏👍_* *_ALLAH YA HUCI ZUCIYAR KA YAYANA, KWARAI NA YABA DA 'KO'KARIN KA AKAN POSTING, A CIGABA DA YIN HA'KURI HAKA RAYUWAR TAKE🙏😞_* *_HAPPY BORNDAY TO ME🎂 I'M SO...SO...SO HAPPY FOR MY SELF💃💃💃💃 AL-HAMDULILLAH ALA KULLI HALIN, DOLE IN GODEWA MAHALICCI NA NA WANNAN BABBAR RANA DA YA NUNA MIN🙏🙏_* 🎂🍧🎂🧁🍡🍨🍦🥧🍿🍰🍹🎂 *_FOR YOU:_* *_DEAR_* *_YAYA HASSAN_* *_A.T.K_* *Page 96/100* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* ******Yarima bai samu ya tashi ba sai da goshin asuba jikinsa duk yayi masa nauyi wata irin kasala yake ji da k'yar ya yink'ura ya tashi zaune tare da yin mik'a yana salatin Annabi gefen da FARHANAH take ya duba sai ya ganta a kwance ta d'an buntsuro bakin ga busassun hawayen ta nan akan fuskar ta, murmushi kawai yayi ya tashi ya wuce bathroom. Ya d'an jima kafin ya d'auro alwala ya fito ya saka doguwar riga yayi raka'atanul fajri sai yaje wurin gadon ya d'an yaye blanket d'in ta motsa gami da bud'e idanun ta da k'yar, ganin shi yasa ta juya fuskar ta gefe d'aya sai yace'' ki tashi time d'in sallah ya kusa ni zan tafi masjid''. 'Kara k'udundunewa tayi tace'' ka rabu dani''. '' Raguwa kawai, idan na dawo baki tashi ba zan k'ara abinda kike gudun''. Jin abinda yace ne yasa ta tashi zaune sai ta tuna ashe ba riga a jikinta, da sauri tasa blanket ta rufe k'irjin ta shi kuma 'yar dariya yayi ya tashi ya fice daga d'akin ma baki d'aya. Yanda take tafiya kai ka rantse yau ne ta fara sanin wani d'a namiji har da d'ingisawa takeyi ta shige toilet. Yana shigowa d'akin tana kwanciya a gado, shima kai tsaye ya wuce gadon ya kwanta sakamakon wani irin ciwon kai da yakeji da kuma zazza6i. Yanayin yanda taga ya canza lokaci d'aya sai abin ya tsorata ta, tashi tayi zaune tana kallon shi yanda yake karkarwa sai ta tashi ta kashe A.C da yake aiki a d'akin ta dawo kusa dashi tace'' me ya sameka?" Da k'yar ya bud'e baki yace'' karki damu zazza6i ne da ciwon kai zai daina idan nayi bacci''. Batayi magana ba ta koma d'aya 6arin ta kashe fitilar sannan ta kwanta gami da runtse idanun ta itama d'in jin zazza6in takeyi amma bata da ciwon kai. Cikin bacci taji yarima ya rungumota sosai ya matse ta a jikin sa ba shiri ta farka ganin halin da yake ciki ne yasa ta rikice zata tashi zaune amma ya k'ank'ame ta ba zata iya k'watar kanta ba saï ta fara hawaye ta rasa ya zatayi dashi gashi da alama banda zazza6in akwai abinda ke damun sa. Murya k'asa-k'asa tace'' ka sakeni''. Shima murya can k'asa yace'' please ina buk'atar taimakon ki karki bar jikina sanyi nakeji sosai''. '' To ka sakeni inje in fad'a wa mummy a kira doctor''. '' No! Karki fad'a mata zanji sauk'i''. 'Kin sauraren sa tayi ta fincike jikinta ta tashi gami da k'ara rufa masa duvet d'in ta shiga bathroom a gurguje ta watsa ruwa dan ita kam zazza6in yayi mata sauk'i zafin jikin ma ya sauka, duk ta rikice ganin yariman a wannan halin. Lallai d'an Adam ba wani abu bane nan da nan Allah zai iya canza shi a duk lokacin da yaso gashi dai yarima duk kuzarin sa ya kasa ta6uka ma kanshi komai. Mummy ta kira a waya ta gaya mata halin da yarima yake ciki, ba'a d'auki lokaci mai tsawo ba mummy ta k'araso part d'in yarima itama bata jima ba saï ga doctor ya k'araso shima. Duba shi yayi ya rubuta mishi maganin da ya kamata a siye saï yarima yace'' doctor itama da zazza6in ta kwana a rubuta mata maganin''. Kunya sosai gimbiya FARHANAH taji har da su sunkuyar da kai tana wasa da d'an yatsan ta saï mummy ta kalleta tace'' subhallahi! Ashe dukan ku ba lafiya? To Allah dai ya sauwak'e irin wannan ciwo na lokaci d'aya''. Mummy ta kalli doctor tace'' doctor me yake damun shi ne? banji kace komai ba''. 'Yar sosa kai yayi yace'' ranki ya dad'e zanyi mishi bayanin komai yanda zai fahimta amma ina buk'atar a bamu wuri''. '' Ok! Ba damuwa bari muje daga waje, ka rubuta mata itama saï a bada a siyo magungunan''. '' To insha Allah yanzu kuwa ranki ya dad'e''. Saï da ya gama rubutawa ya mik'a musu zasu fice doctor yace'' ai itama matar tashi zata tsaya a nan su biyu zanyi ma bayanin''. Jin abinda doctor yace ne yasa mummy ta sak'a wani abu a zuciyar ta amma ta basar tace'' ok to shikenan ka kula min da su please ban son abinda zai ta6a min 'ya'yana''. '' Insha Allah za'a kula da su''. Ficewa tayi a falon sama ta zauna ita kad'ai tazo daman dan tace kar wacce ta biyo ta ko mai martaba ma bai san abinda ke faruwa ba. Doctor ya buk'aci FARHANAH da ta zauna, zama tayi a bakin gadon tana jiran bayanan doctor. Doctor yace'' to kai ya haka? Da matar ka amma naga kana ciwon marasa aure, ma'ana ka tara sha'awa dayawa ne shi ya haddasa maka wannan ciwon har ma da ita d'in''. Wayyoo!! FARHANAH kamar ta nutse a k'asa dan kunya yarima kuwa d'an duniya cewa yayi'' duk laifin ta ne, ta cika son jiki da langwa6ewa ni kuma ban cika takura ma mutum akan abinda bai buk'ata ba''. Dariya doctor yayi yace'' to ya zama dole ku nemawa kanku mafita yanzu duba kaga halin da kake ciki fa''. '' Insha Allah za'a gyara, kace kar inyi sakaci kenan''. Yarima ya fad'a da 'yar zolaya ita dai kunya ta hanata ko da k'wak'wak'waran motsi. Shi dai doctor dariya yake mishi, allura yayi mishi yace'' ya kamata dai ka kula da kanka kai ma fa doctor'n ne kasan duk abinda ke ciki amma kana wasa da lafiyar ku duk''. '' Zan gyara''. Yarima yace a tak'aice. Hannu ya bashi sukayi musabaha ya fice da akwatin sa na likitoci. Mummy yayi ma sallama ya tafi bayan an cika masa aljihu da naira. Kafin yamma jikin yarima yayi sauk'i dan har falo ma ya fito yana zaune suna waya da abokin sa Mahmud HASINA ta shigo falon tare da yin sallama ta k'araso ciki ta zauna a kujerar kusa dashi daman shi kad'ai ne FARHANAH taje part d'in ta hadiman sa kuma basu zauna ba. Saï bayan da ya gama ne suka gaisa yake tambayar ta 'yan gida da kuma wurin aikin ta ita kuma tana amsa mishi cikin kissa da kisisinar da bai ma san tanayi ba dan ba kallon ta yake ba. FARHANAH ce ta shigo falon tare da yin sallama, yarima ya fara amsa mata kafin HASINA ta amsa da k'yar kamar wacce akayi ma dole. Yanda ta gansu a zaunen nan saï ya d'an ta6a mata zuciya amma ya dake tazo ta zauna tana tambayar shi jikin sa yace yaji sauk'i. Falon yayi tsit kafin daga bisani yarima yayi gyaran murya ya kalli FARHANAH yace'' kinga wannan cousin d'ina ce 'yar k'anwar mummy ce a Abuja take aiki sunan ta HASINA''. '' Ok! Sannu da zuwa ya gida?" Cikin basarwa HASINA tace'' yauwa sannu, gida lafiya''. Toh fa! Biyu ce ta had'u kenan kowacce naji da kanta. HASINA tace'' sweet yaya ina son zamuyi magana da kai''. '' Ok to ina jinki Allah yasa dai lafiya''. '' Secret ne mu biyu nakeson muyi maganar''. Satar kallon FARHANAH yayi saï yaga itama d'in su take kallo idanu cike da tsantsar kishi tare da tuhuma''. Yarima yace'' ok ki bari anjima zamuyi kafin nan na k'ara warwarewa dan har yanzu banjin k'arfin jikina''. Kafin tace wani abu tuni FARHANAH ta taso kusa dashi ta zauna cikin shagwa6a tace'' honey muje daga ciki ka samu ka huta nasan dai ka gaji da zaman nan''. FARHANAH ta k'arashe tana mai tashi tsaye tare da rik'o hannun sa alamar ya tashi su tafi. Yarima yayi mamaki matuk'a da jin wannan kalmar ta honey a bakin ta saï dai ya gane abinda yasa tayi hakan saï cewa yayi'' ke da kika yi bak'uwa kuma zamu barta ita kad'ai?" '' Ai ita ba bak'uwa bace, 'yar gida''. Ta juya ta kalli HASINA tace'' sorry dan Allah ana buk'atar ya huta sosai ne''. Kallon up and down tayi mata tare da mik'ewa tace'' yaya saï mun had'u anjiman kenan ko?" '' Insha Allah, ki jira ni karkiyi bacci da wuri dai''. Zuciyar HASINA fari k'al tace'' ba zanyi ba see you later, bye-bye''. Saï da ta fice ne sannan FARHANAH ta sakar masa hannu ta koma ta zauna gami da kawar da kanta tana cika da batsewa, abin ya ba ma yarima dariya wato su mata ko ba'a nuna maka so kishin nan sai ya tona musu asiri gashi nan k'iri-k'iri yaga kishin sa a tare da ita. Shima zama yayi yace'' yadai gimbiya ta? Na zata cewa akayi mu shiga daga ciki ko?" '' Ban rik'e ka ba ai kana iya tafiya''. Tashi tayi tana shirin barin wurin ya kamo ta ta fad'o a jikinsa ya matse ta a tare sukayi ajiyar zuciya yarima har da lumshe idanu yayi kafin ya bud'e ya kafe ta dasu, shiru yayi na d'an lokaci sannan yace'' meyasa kike son azabtar da zuciyar ki akan abinda takeso ne? Meyasa kike son wahalar mana da zukatan mu haka?" So takeyi ta tashi daga jikin sa amma ta kasa saï tace'' ban san akan me kake maganar ba, sakeni zanje insha magani''. '' Ai nine maganin ciwon naki kamar yanda doctor Habib yayi mana bayani ko kin manta in tuna miki?" yarima ya tambaye ta yana mai d'aga mata gira, nan take taji wata irin kasala ta baibaye ta dan ba zata iya kallon yarima cikin ido ba yana mata wani k'warjini wanda a can baya bata san yanada shi ba, saï kawai ta mayar da kanta zata kwantar akan k'irjin sa ya d'ago kanta tare da had'e bakin su waje d'aya yana aika mata wasu sak'onnin....lolz 'Kwacewa tayi tace'' ka manta a falo muke ne?'' '' Uhmm ban manta ba, ai babu mai shigowa ba tare da ya nemi izini na ba''. '' Nidai ka rabu dani zan koma 6angare na''. '' Saï kinyi min wanka kin shirya ni tukun zaki tafi kinsan wajen tad'i zanje''. Fizge jikin ta tayi ta tashi ta fice tsabar tak'aici yasa ta fara hawaye da k'yar ta k'arasa part d'in ta ta inda babu mai ganin ta. Hadiman ta suna ta hidimar su an shirya abinci a dinning da yake magrib ta kusa su kuma bayan isha'i suke zuwa 6angaren su. Suna mata sannu bata iya amsa musu ba saï hannu kawai da ta d'aga musu ta haye upstairs ta nufi d'akin ta. Gado ta fad'a gami da fashewa da wani irin matsanancin kuka, wato dai yarima da gaske yake auren zaiyi ko? Kuma da alama wannan cousin d'in nashi ce tunda har sun ajiye maganar zasu had'u anjima, zan iya barin wata ta shigo fadar yarima kuwa? Zan iya yarda yarima yayi tarayya da wata 'ya mace bayan ni? Bazan iya ba, wallahi bata isa inyi sharing mijina da ita ba...... Haka gimbiya tayi ta sambatun ta har saï da taji an fara kiran sallah a masallacin masarautar sannan ta tashi ta shige bathroom tayi wanka a gurguje ta d'auro alwala ta fito. Bayan ta gama sallah'r ne ta kira momyn ta suka gaisa tana tambayar daddyn su momy tace'' da safen nan yaje Dubaï''. '' Yauwa bari in kira shi ya kawo min abaya ko guda uku ne''. '' Wai ke me zakiyi da kaya ne? Duk irin kayan da gareki basu isheki ba?" Baki ta cunno tace'' haba momy kaya yana ma mutum yawa ne? Nidai inaso gaskiya''. '' Uhm kanki akeji ya mijin naki da su hajiya? Fatan dai babu wata matsala ko?" Shiru tayi tana tunanin ko tace mata yarima zai k'ara aure saï kuma ta basar tace'' a,a wallahi momy babu wata damuwa lafiya lau muke''. '' To madallah haka akeso Allah ya k'ara wanzar da zaman lafiya a tsakanin ku''. '' Ameen momy sai na sake kira, bye''. '' OK! Bye''. Bayan ta ajiye wayar ne taji wani irin tuk'uk'i idan ta tuna yanzu haka yarima yana can tare da wannan yarinyar mai shegen rawar kan tsiya''. Hummm gwano bai jin warin jikinsa ashe? Yau FARHANAH ke ce ma wata mai rawar kai? Ita kuma fa? Bata fi kowa rawar kai ba kuwa? Uhmm..... Bayan isha'i FARHANAH tana zaune a bisa carpet kasala ta hanata fita falo ta ci abinci duk da yunwar da takeji ta rasa ma me yake mata dad'i a rayuwar ta. Haka nan dai ta k'ok'arta ta mik'e tsaye tana ninke darduma taji an rungume ta ta baya, k'amshin turaren sa kad'ai ya isa ta gane shi shiyasa ma tayi ajiyar zuciya ba tare da ta waiwayo ba shi kuma ya sak'alo hannayen sa takan cikinta ya d'ora ha6ar shi bisa kafad'ar ta. Babu wanda yayi magana a cikin su har na 'yan dak'ik'u kafin yarima ya rad'a mata cewa'' yah Sayyada nazo ayi min rakkiya wajen hira''. Hannu tasa ta cire nasa hannuwan taje bakin gado ta zauna ba tare da tace masa komai ba. Takowa yayi inda take ya zauna shima yana mai k'are mata kallo yanzu ta zama so silent ba tsiwar nan irin ta da abin har mamaki yake bashi, ashe zata iya yin sanyi haka? Ba zata iya d'aukan tsawon lokaci tana kallon shi cikin ido ba saboda kasalar da hakan yake saka mata, a idanun sa akwai wasu abubuwa masu cike da tasirin karyewar zuciyar ta wanda ba zata jurewa hakan ba, kallon shi mai cike da ma'anoni da dama ga wani irin k'warjini da yake mata kuma. Hannu yasa ya tallabo ha6arta yace'' madam babu magana ne? Me yake faruwa ne? Ko dai jikin ne?" Baki ta turo kafin tayi magana yakai mata kiss a bakin yasa hannu d'aya ya shafo cikin ta yace'' da alama wannan cikin ba'a bashi hak'k'in sa ba ko? Nasan kina tare da yunwa tashi muje kici abinci''. Tashi yayi tare da mik'ar da ita tsaye da kanshi ya saka mata hijab akan bak'ar rigar da take jikinta ya kama hannun ta suka fita, a falon sama suka yada zango daman a nan aka shirya komai na buk'ata kuma tuni su Shafa'atu sun fice tun lokacin da yarima ya shigo ya basu umarnin tafiya. Abincin take ci amma ji takeyi kamar tana cin magani saï yamutsa fuska take kuma duk yarima yana lura da ita saï yayi murmushi yace'' yadai? Ko babu dad'i ne?" Girgiza kai tayi tace'' kawai ban jin yunwar ne''. Tasowa yayi ya dawo kujerar gefen ta ya kalle ta tace'' ki daina damuwa akan abinda bai kai ya kawo ba, kiyi sauri zamu je cikin gida mu gaishe su daga can ma tad'i zanje''. Ya k'arashe maganar cike da zolayar ta saï ta d'an harare shi tana mai bige masa hannun sa dake yawo a jikinta tace'' to ni ina ruwana saï me dan kaje tad'in?" '' Humm saï ayi ta min kuka mana ba gashi ba tun kafin inje d'in ma ana kukan''. '' Waye yayi kukan?" '' Gimbiya ta mana''. Ya fad'a yana d'aga gira. '' Uhmm ko a jikina me ma zai sakani yin kukan?" '' Kishi''. Ya fad'a mata kai tsaye. Banza tayi masa dan ta lura shima d'in akwai shi da son jan zance. Bayan sun gama ne taje ta d'an gyara jikinta suka fice. Saï da suka je wajen mai martaba suka gaishe shi sannan suka dawo wajen mummy a nan ma sun d'an jima kad'an dan saï wajen 10pm suka yi mata sallama suka fita. Har suka tafi FARHANAH bata ga HASINA ba a wurin kuma taji dad'in hakan dan ganin yarinyar k'ara mata damuwa yake wanda ta rasa dalilin hakan, kishi ne dalili, haka wata zuciyar take fad'a mata a duk lokacin da tayi wannan tunanin. Zata shige 6angaren ta yarima ya hanata suka fice nashi part d'in tare da ba masu gadin wurin su rufe ko'ina shi ya shiga saï gobe, nan suka yi musu fatan tashi lafiya suka shige ciki yana rik'e da hannun FARHANAH. Upstairs suka haura kai tsaye saï a bedroom d'in sa suka tsaya ya rufe k'ofar har da key ya dawo inda take tsaye tana kallon shi ya kama hannun ta suka zauna a bakin gadon kafin yace wani abu wayar shi ta d'auki ruri ya ciro ta daga cikin aljihun gaban rigar shi, sunan HASINA ya gani saï ya d'ago ya kalli FARHANAH da ta kafe shi da nata idanun, murmushi ya sakar mata sannan ya d'aga kiran tare da yin sallama, cikin shagwa6a HASINA tace'' yaya shine ka barni ina ta jiran ka ko?" Dafe kai yayi yace'' sorry kinga na manta ashe kince mû had'u ko?'' Tak'aici yasa ta kashe wayar tare da yin jifa da ita nan take ta fashe da kuka, meyasa yarima yake mata haka ne? Meyasa yake son azabtar da zuciyar ta haka? Shi bai san har yanzu tana son shi bane? A dalilin shi ne har yau ta kasa ba wani d'a namiji k'ofar zuwa wurin ta duk da tarin masoyan da gareta, manyan mutane da 'ya'yan manya duk sun nuna mata so son ma irin na aure amma sam tak'i sauraren su duk saboda shi amma gashi yana nuna mata halin ko in kula dan yayi aure, ita gara Allah ya d'auki ranta ma ta huta gaba d'aya. (Wa'iyazu-billah! Akan d'a namiji zakiyi irin wannan furuci? Wannan kalma bata dace da duk wani kullihin musulmi ba, hakan babban kuskure ne, ya kamata d'an Adam ya kar6i duk irin k'addarar da Allah ya d'ora mishi, Allah yasa mû dace....Ameen!!!) Jin ta kashe ne yasa shima yarima ya sauke wayar ya kalli FARHANAH yace'' madam saï muyi shirin bacci ko? Har yanzu ban jin jikina a dai-dai nasan kuma kema haka abin yake a gareki Allah yasa baby na samu''. Ya fad'a yana shafo marar ta. Hannun ta ture tace'' ban so ni ka daina min''. '' Ank'i a daina ni da jikina sai a hanani ta6ashi?" '' Jikin ka?" '' Yes! Jikin ki mallaki na ne dan haka inada damar yin komai da naga dama dashi, tashi ki canza kaya''. '' Malam ka manta nan ba d'aki na bane?" '' Na fiki sanin hakan ai, duk wani abu da zaki buk'ata akwai shi a nan d'akin maybe ma yafi na d'akin ki''. '' Banga alama ba''. Ta fad'a tana mai kawar da kai. Yana nufar bathroom yana ce mata'' ki bud'e wardrobe d'in can ki gani mana zaki sha mamaki''. Yana shigewa ta tashi taje wurin wardrobe d'in ta bud'e shi ai kuwa tasha mamakin dan cike yake da kayan mata musamman na bacci kala-kala gasu nan. 'Daya ta za6o mai kyau milk color mai santsi kafin ya fito ta saka ta haye gadon ta kwanta gami da rufa ta juya bayan ta d'aya 6arin. Kafin yarima ya gama shirin kwanciya har bacci ya d'auke ta, feshe jikin sa yayi da turaruka sannan yazo ya kashe fitilar d'akin ya kwanta bayan yayi musu addu'o'i. Rungume ta yayi gami da lumshe idanun sa, ji yayi ta d'an motsa da alama bata da nauyin bacci tunda har taji ya ra6eta shiyasa ma ta motsa d'in. Kanshi ya cusa a wuyan ta yana mai shak'ar k'amshin jikin ta mai tayar da hankalin mutum gashi yaji jikin ta da d'an zafi daman yasan bata jin dad'in jikin ta yanda yaga ta zama silent d'in nan. Kafin wani lokaci tuni jikin ta ya d'ume da wani irin zafi saï shigewa cikin jikin yarima takeyi saboda sanyi takeji marar misaltuwa. Tashi yayi ya kashe A/C dake d'akin sannan ya koma ya kwanta ya d'ora kanta bisa k'irjin sa yasa hannun sa d'aya yana mai shafar bayan ta ita kuma saï mutsu-mutsu takeyi wanda ya rasa ko na meye, ko kuma zazza6in ke damunta. Cikin muryar rad'a yace mata'' tashi kisha magani zafin jikin nan yayi yawa''. Nok'ewa tayi dan bata son tashi daga k'irjin sa wanda yake yalwance da gashi mai santsi abin sha'awa kunsan shima fa gashin nan baiwa ce saï wanda Allah yaso yake mallaka masa. Tashi yayi ya zauna ya kunna fitilar bedside drower fitilar mai duhuwa ce dan bata da haske sosai amma irin mai colors d'in nan ce saï canzawa take. '' Ya zama dole fa kisha magani ke kanki gashi zazza6in ya hanaki bacci''. '' Ka barshi please gobe zan sha''. '' Bazai yiwu ba tsaya ma ki gani''. Yana fad'in haka ya rabata da jikin sa yaje ya d'auko maganin zazza6i ya kawo mata tare da ruwa, ba dan taso ba tasha saï yamutsa fuska takeyi. '' Raguwa kawai''. Cewar yarima ita kuwa saï ta cunno baki ba tare da tace mishi komai ba. Fitilar ya sake kashewa suka kwanta ba dad'ewa bacci ya kwashe su duka. Asuba tagari....... Da asuba yaso makara zuwa masjid a gurguje yayi alwala ya nufi masallaci. Har ya dawo FARHANAH bata tashi ba baiyi mamaki ba saboda maganin zazza6in har da wanda zatayi bacci ya had'a mata dan yaga zazza6in yana damunta sosai. Zuwa yayi bakin gadon ya zauna yana mai yaye blanket d'in ya shafo fuskar ta saï ta d'an bud'e idanun ta tare ma mayarwa ta rufe saï yarima yace'' hey! Wake up time for prayer karki makara har na dawo daga masjid fa''. Tashi tayi jiki ba k'wari ta sauka ta nufi bathroom, saï da ta watsa ruwan tukunnan tayi alwala ta fito taga yarima zaune da laptop a gaban sa a maimakon ace ya kwanta. Da ta gama saï ta kwanta a nan bisa dardumar ko meye dalili? oho mata. Yarima ya d'ago kanshi ya tsinkaye ta a kwance kuma duk ta takura kanta saï ya tashi yaje inda take ya d'ago ta yace'' ya jikin? Ko shine yake damunki?" Girgiza kai tayi alamar a,a shi ko da yaji haka sai mik'ar da ita tsaye yace'' to muje ki kwanta a gado bana son wannan kwanciyar da kikeyi a k'asa''. Batayi mishi gardama ba ya kama ta suka k'arasa gadon ta hau ya rufeta da duvet shima ya bita a baya sukayi kwanciyar su. Basu tashi da wuri ba sai kusan 9am har ya manta cewa zaije asibiti ma, a gurguje ya shirya har zai fita ya dawo ya mata wani irin light kiss a kunci gami da shafar kanta yace'' Allah ya baki lafiya wife''. Yasa kai ya fice har da waiwayen ta yake. A falon k'asa ya iske hadiman shi suna ganin sa nan suka zube suna gaishe shi ya d'aga musu hannu kawai ya fice, a can wajen ajiyar motoci ya iske Sulaiman driver'n shi daman shi yake jira ganin yarima yasa ya durk'usa tun kafin ma ya k'araso, ko da ya k'araso gaida shi yayi tare da bud'e masa back seat ya shiga suka bar masarautar domin kuwa yana son duba wasu patients da akayi ma aiki ranar friday duk da dai yana kira dan jin jikin nasu. FARHANAH kuwa ba ita ta tashi ba sai da taji wayar ta tana ruri da k'yar ta ciro hannun ta daga cikin blanket d'in tayi picking ba tare da tasan ma mai kiran ba. Jin muryar 'yar uwar ta yasa ta tashi zaune tace'' an tashi lafiya? Ya my boy?" '' Lafiya lau muke, ya naji muryar haka lafiya dai ko?" '' I'm fine sister kawai dai yanzu ne na tashi daga bacci''. Cikin zolaya tace'' uhmm hmm ai kaji manya ba, wato kice nice ma na tashe ku ko?" '' Kin jiki da son magana, da wa kika tashe mû?" '' Ke da mijinki mana''. '' A,a ni kad'ai ce ai shi ya fita''. Har ga Allah ita dai bata san ma inda yaje ba''. '' Ok! To yayi kyau da fatan zuwa yanzu dai babu wata matsala ko?" '' Uhmm akwai mana''. '' To me ya faru kuma?" '' Wata cousin d'in sa tazo gidan kuma da alama akwai wata alak'a a tsakanin su yanda take wani jin kai da kisisina kamar ta samu wani mijinta Allah sai kin gani ma''. Murmushi FARIHAH tayi dan daga ji tasan 'yar uwar tata ta fad'a son yarima sai cewa tayi'' ki saurareni da kyau, karki sake ki nuna wata damuwa har ita yarinyar ta gane ko kuma shi kanshi yariman, shi namiji ta ruwan sanyi ake bi dashi kinga baki da tabbas kawai zato ne kikeyi dan haka karki sake tun yanzu ta rainaki, me wata 'ya mace zata nuna miki? Allah ya baki surar da zaki iya jan hankalin mijinki da ita to meye kuma abin damuwar a nan?" '' Humm sister haka kawai naji tsanar yarinyar tare da kishin ta saboda shi fa tazo garin nan''. '' Au daman ba a garin ma take ba?" '' 'Yar nan ce mana 'yar k'anwar mummyn sa ce amma ita Abuja take da zama''. '' Kedai kiyi abinda nace miki, kibi mijinki dan Allah kar wata magana ta 6atanci ta shiga tsakanin ku, shi namiji ba'a nuna mishi isa ko *GADARA* duk dukiyar ki ko isar ki dole a k'ark'ashin sa kike dan haka ki dage wajen siye zuciyar mijinki yanda zai zamo babu wata k'ofar da zai saka wata 'ya mace a ciki sai ke''. '' To shikenan zan barki haka tashi zanyi in nemi abinda zanci yunwa nakeji''. '' Ai kaji manya ni kam ina wajen aiki''. '' Allah ya taimaka a gaishe min da oga kuma ki shafa min kan baby na''. '' Insha Allah, bye''. Ajiye wayar tayi tana sauke ajiyar zuciya maimakon ta tashi sai ta janyo pillow d'in da yarima ya kwanta ta rungume tana shak'ar k'amshin turaren sa wanda yak'i barin d'akin ma har inda ya kwanta duk k'amshin ne. A nan toilet d'in sa tayi wanka ta maida rigar ta ta jiya sannan ta fito tare da kulle d'akin ta sauko k'asa. Wata k'ofa ta nufa ta baya ta inda ba za'a ganta ba har ta shige part d'in ta. 'Dakin ta ta nufa ta canza kaya sannan ta fito falon k'asa inda aka shirya mata breakfast ta zauna taci sai ta koma falo cikin hadiman ta suna hira su kansu sunga sauyi sosai a tattare da gimbiyar nan tace ma Shafa'atu taje d'akin ta ta d'auko mata maganin ta. Da sauri-sauri ta nufi sama dan cika umarnin uwargidan ta. Suna 'yar hirar su ne suka jiyo sallamar wasu hadimai akayi musu iso suka zo suka zube suna kwasar gaisuwa aiko su mummy ta aiko su da wani sak'on wanda a rufe yake da wani farin yadi FARHANAH tace da Shafa'atu ta kar6a takai mata bedroom d'in ta. Nan gimbiya tace musu ayi ma mummy godiya kafin taje. Bayan la'asar FARHANAH taje part d'in su mummy a lokacin bata ma falon sai ta zauna a nan akaje aka sanar mata da zuwan gimbiya FARHANAH. Mai aiken tazo tace da gimbiya hajiyar na nan zuwa. Kafin mummy ta sauko sai ga HASINA ta fito tana tsinkayar FARHANAH sai ta canza tafiya zuwa ta yanda a haka har ta sauko tana cikin shiga ta riga da skirt na atampa hannun ta d'auke da hand-bag wanda suke iri d'aya da takalmin k'afar ta masu tsini, k'arasowa tayi falon tana wani yatsina fuska kamar wacce taga abin k'yama tazo ta zauna nesa da FARHANAH ta d'an kalli inda take tace'' sannu ko?" FARHANAH ta kawar da kai tace'' yauwa''. Suma mutanen wajen suka gaishe da HASINA da k'yar ta amsa musu sai kace taga kashi sama-sama take kallon kowa na falon, ita dai FARHANAH ikon Allah take kallo ashe akwai wacce ta fita iyawa. Hahaha....baba ma da baban sa kenan..... A haka mummy ta sauko inda ta iske suna zaman kurame kafin ma ta zauna tace'' a,ah ya haka? Naga kuna zaune baku yin hira?'' Sannu da saukowa hadiman suka mata sai daga baya suma su FARHANAH suka gaishe mummy tace'' 'yata ya jikin naki? Mijinki ya sanar dani bakiji dad'i ba''. Kanta a k'asa tace'' da sauk'i mummy''. HASINA kuwa a sace ta harare ta yanda kowa bai gani ba dan ko ita uwar gayyar ma bata san anyi ba. Mummy ta kalli HASINA tace'' to daughter sai ina kuma? Naga kinyi shirin fita''. '' Zanje gida daga can zan tafi asibiti wajen yaya akwai maganar da zamuyi dashi''. '' Ok! Ki gaishe min da maman taki sannan kuma kinsan dai ba da wannan d'an veil d'in zaki fita ba ko?" Shagwa6e fuska tayi tace'' kai mum me veil d'in nan yayi ne? Naga a mota zan fita ai''. '' Kafin kije wajen motar mutane nawa ne zasu ganki a hakan? Wannan ba mutuncin gidan nan bane ki suturta jikinki dan Allah''. Tashi tayi tana bubbuga k'afa ta haye sama da sauri ita wai an takura mata a ganin ta fa. Bata jima ba ta sauko tace'' to mum gashi na canza ai yayi ko?" '' Yauwa ko ke fa''. '' Mum sai na dawo a huta lafiya''. '' A dawo lafiya banda tuk'in ganganci dan nasan halin ki''. Dariya tayi ba tare da tace k'ala ba tasa kai ta fice. Mummy ta dawo da kallon ta wurin FARHANAH wacce tak'aici duk ya dabaibaye ta wato ma yarima nema yake ya raina mata hankali ko? Me yake nufi da gayyatar wannan har office d'in sa? Ni kuma tunda ya fita ko kirana baiyi bâ bare yasan ma ya nake ko? Humm.... Mummy ta kalle ta tace........ *_Mu had'e a shafin gaba insha Allah_* *_Idan na gama littafin nan ina ganin zan dakata da typing saboda na raina comments d'in wasun ku....._* *_Ina gaishe ku 'yan hannun dama ta🙌👍_* *_'YAR MUTAN KAZAY CE👑_* 💥💥💥💥💥 *_'YAR GADARA_* 💥💥💥💥💥 *_NA_* *_A.MAIMOUNATH O.G.K_* _(Mahnoor)_ _Wattpad@maimounathog_ *💫DA BAZAR-MU WRITER'S ASS💫* *_~we are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are d best among all....DA BAZAR-MU MUKE TUN'KAHO.~_* *_AL-HAMDULILLAH IDON YARO YAYI SAUK'I AN SHAWO KAN MATSALAR MASU ADDU'A NAGODE SOSAI ALLAH YA BAR ZUMUNCI🤝* *_MAIMOUNATH OUSMANE GAGARA KIARI SHINE CIKAKKEN SUNAN GA MASU TAMBAYAR MA'ANAR👉🏻O.G.K_* *_FOR YOU:_* *_DEAR_* *_YAYA HASSAN_* *_A.T.K_* *Page 101/105* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* ******Mummy ta kalle ta tace'' 'yata jikin naki da sauk'i ko? Naga har yanzu kamar kina tare da damuwa''. Murmushin k'arfin hali ta k'ak'aro tace'' naji sauk'i mummy bâ wata matsala''. '' Masha Allah! Haka nake son inji, na aika miki da sak'o ina fatan kin gane duk yanda zakiyi amfani dasu ko?" Har ga Allah bata san me sak'on ya k'unsa ba kawai cewa tayi akai bedroom d'in ta a ajiye, saï murmusawa tayi tace'' eh mummy duk na gansu kuma na fahimta''. '' Yauwa 'yar kirki dan Allah karkiyi wasa dasu dan sunada kyau sosai wata amintacciya tace nasa ta kawo min su, ku yaran yanzu baku da kula sosai shi kuma namiji saï kana gyara''. Saï yanzu ta gane abinda mummyn ta aika mata nan take wata irin kunya ta lullu6eta saï tasa hannuwan ta duk biyun ta rufe fuskar ta. 'Yar dariya mummy tayi tace'' ki daina jin kunya ta nima mummyn ki ce ba zancen kunya a tsakanin mu kinji ko?" '' To mummy''. Hira sukeyi jifa-jifa har zuwa wani lokaci kafin tayi mata sallama ta koma 6angaren ta. Yarima kuwa a gajiye lik'is ya dawo gidan saboda aikin da ya tarar a asibiti yau har tiyata yayi wa wani tsoho abin tausayi saï wanda ya gani. Wanka yayi ya samu ya d'an huta kafin sallah'r magrib yana cikin d'akin sa har saï da aka kira sallah tukun ya fito ya fice masjid. FARHANAH a tunanin ta yarima suna can shi da HASINA nan kuwa duk yau bai samu kanshi ba dan ya wuni yana aiki an sanar masa yayi bak'uwa amma bai samu damar ganin ta ba kuma yasan dai bazai wuce HASINA ba. Da ya dawo daga masjid 6angaren mummy yaje suka gaisa sannan ya wuce part d'in FARHANAH, ita kuma a lokacin tana zaune ta tusa kayan da mummy ta aiko mata tana bin su dallah-dallah kowanne a rubuce yake ji takeyi kamar tana a gaban mummyn saboda kunya. Sallama d'auke a bakin shi ya shigo d'akin saï tayi saurin rufe kayan ta mayar dasu bayan ta gami da amsa masa sallamar shi a ciki-ciki dan haushin shi ta wuni tana ji. Fuska a washe ya k'araso ya zauna a bakin gadon ta d'an kalle shi tace'' ina wuni?" '' Ban ganshi ba, baki da kirki fa ace mijinki ya tafi wajen neman na halak amma ko ki kira a waya kiji ya nake?" '' Idan ni banyi ba ai anyi maka a wani wajen''. '' Anyi min? Wa kenan?" '' Ka fini sani ai''. Ta fad'a tare da murgud'a mishi baki. Dariya yayi yace'' humm sarkin kishi to maida wuk'ar ni babu wacce na gani yau, ya jikin naki?" '' Humm! Da sauk'i''. '' Me kike 6oyewa ne? tunda na shigo naga kin 6oye shi a bayanki, ko dai ba'a son in sani ne?" '' Eh! Ba'a so ina ruwan ka ne wai''. '' Da ruwana tunda kika ce haka kuwa saï na gani''. Tasowa yayi yazo ta bayan ta ya rik'e hannuwan ta duk biyun sannan ya s'auko kayan ya koma bakin gadon. Bud'e su yayi kowanne yana kallo tare da nazarin su kafin ya juyo ya kalle ta yace'' uhmm! Madam kice gata ake min ko? Shine kike wani 6oyewa? To amshi kayanki wannan karon har tukwici zan bayar''. FARHANAH ta kasa k'wak'wk'waran motsi tsabar kunya yarima ya kama ta da kayan mata a hannu dumu-dumi yanzu fa saï yayi zaton daman can tana shan su. Baki ta cunno gami da hararen sa tace'' kaga nifa ba nawa bane sak'on sister ne hajiya ta bayar gobe a kai mata''. '' Ok to bari inje in amso namu rabon dan kar ayi banda mû, muma fa muna son muji dad'in ko ya kika ce?" Ya tambaya yana d'aga mata gira. A shagwa6e tace'' nidai ba ruwana, kai yanzu ko kunya bakaji saï kaje?" '' Kunya? Kunyar wa zanji? Mummy ai mai ganewa ce itama zata so d'anta yaji dad'i''. Banza tayi masa ta tattara kayan takai cikin drower ta ajiye bata kalli inda yake ba tazo zata wuce toilet ya kamo ta ta dawo ta zauna kusa dashi yace'' dan Allah ina son ki duba girman ubangiji karki sake zubar min da ciki, hakan yana bak'anta min rai sosai wallahi''. Kallon mamaki tayi masa tace'' ciki? Ciki kuma? Ni bani da komai kaga ka rabu dani''. '' I know ba za'a rasa ba ma nidai rok'on ki nayi idan ma baki sona ne to ki reni cikin kuma ki fad'a min nawa zan biyaki ladan renon ki please''. Tausayi ya bata saï kawai ta fashe masa da kuka har da sheshshek'a shi kuma ya janyota jikin sa ya shiga rarrashin ta har da bubbuga mata baya kamar wata 'yar baby saï ta k'ara shigewa jikin sa tana mai shak'ar dad'and'd'an k'amshin turaren sa mai tsayawa a rai. Sun d'an d'auki lokaci a hakan har saï da tayi shiru dan kanta kafin ta zamo k'asa cikin wata irin murya wacce bai santa da ita ba ta fara cewa'' dan Allah kayi hak'uri ka yafe min dukkan laifukan da nayi maka a baya, wallahi bazan sake ba na tuba kuma tsakani na da Allah ba ni na zubar da cikin jikina ba tsautsayi na fad'o daga stairs kaji abinda ya faru, duk da na nuna ban sonka amma naji d'acin rabuwa da cikin nan saboda a yanzu bani da wanda nakeso saï kai.....'' ta kasa k'ara wata maganar sakamakon kallon da yarima yake binta da shi saï ta sunkuyar da kai sosai shi kuma ya d'ago ta ya zaunar a kusan shi yana share mata hawaye. '' Alhamdulillahi! Nagode ma Allah da ya nuna min wannan rana, na yafe miki kuma nima kiyi sani ina sonki kamar yanda kike sona saï dai na ajiye hakan a raina ne saboda naga kinyi nisan da duk abinda zan fad'a miki ba saurarena zakiyi ba shiyasa na k'yaleki har wani lokacin, gashi lokacin ya riskeni a bazata, yau dole muyi celebrating wannan rana, yanzu dai tashi muje kici abinci karki bar baby na da yunwa''. Hararen wasa tayi masa tace'' wai waye yace maka ciki gareni?" Gira ya d'age yace'' kin manta matsayina a likitanci ne? To zan gaya miki amma ba yanzu ba saï munje can''. Batayi magana ba ita dai saï kallon shi take ashe dai yanada sauk'in k'ai idan ka zauna dashi kawai dai rashin fahimta ne tun farko da babu shi a tsakanin su. Wayarshi ce ta katse mata tunanin ta d'agawa yayi yana amsa wayar, ya d'an jima yana waya kafin suyi sallama ya kalle ta yace'' ki sameni a part d'ina''. Kai kawai ta iya d'aga mishi tana bin shi da kallo cike da k'auna, gaskiya tayi sa'ar miji ita kanta tasan hakan, a can baya tayi wauta wacce ta hanata gano kyawun mijin nata d'aya tamkar da dubu. Ta kira shafa'atu ta taya ta shiryawa, Shafa ta taimaka mata wajen yin k'walliya domin kuwa ta iya k'walliya sosai shiyasa ma suke shiri da FARHANAH kuma gata da tsafta. Bayan tasha k'walliya Shafa'atu ta d'auko mata alk'yabba saï ta yatsina fuska tace'' no ki bar wannan kayan nauyin please, ni fa a dole nake saka ta ko da can''. Shafa'atu ta rusuna tace'' ai kuwa zakiyi kyau sosai a cikin ta ranki ya dad'e''. '' Ki barshi kawai saï wani lokacin, kinga yanzu dare ne ba ma zan bi ta hanyar da za'a ganni ba, ta k'ofar baya zan bi''. '' An gama ranki ya dad'e, kina buk'atar rakiya ne ko kuwa?" FARHANAH tace'' a,a kiyi zaman ki amma idan kinga ban dawo ba ku rufe k'ofar falo''. '' To shikenan, yanda kika ce hakan za'ayi insha Allah''. Taku takeyi cikin k'asaita a nutse har ta dangana da falon k'asa na yarima wata irin fad'uwar gaba ne ta risketa sakamakon hango HASINA da tayi a zaune kusa da kujerar yarima. Dakewa tayi ta musu sallama yarima ya kalle ta sannan ya amsa amma ita HASINA yi tayi kamar bata ji ba har saï da yarima yace'' bakiji sallamar bane?'' '' Uhm banji ba, wa'alaikumus-salam''. Yanayin yanda tayi maganar ne yasa FARHANAH ta a zuciyar ta tace ke k'aramar 'yar iska ce baki iya komai ba ma tukun tsaya ki gani. Kai tsaye wajen yarima ta nufa daga zuwa saï ta hau kan cinyar sa ta d'an kwanto dai-dai wajen kunnen sa ta rad'a masa cewa'' idan kun gama ina bedroom d'in ka ina jiran ka yau da alama ka gaji zanyi maka tausa''. Tana gama fad'in haka ta mik'e tare da manna masa kiss a baki tare da kashe masa ido d'aya tace'' i'm waiting my husby''. Baki bud'e HASINA take kallon FARHANAH da take takun ta cikin isa tana taka upstairs, su yarima kam anyi suman wucin gadi dan ya ma rasa nutsuwar sa yanda tayi mishi maganar sosai ta tafi da nutsuwar sa, da k'yar ya iya saita kanshi ya dawo da kallon sa inda HASINA take yace'' uhumm ina jinki me kikeso kice min?" Itama da yake 'yar duniya ce saï ta nuna abin bai mata zafi ba ta waske fuska da walwala had'e da shagwa6a tace'' nace ba..uhmmm..daman nace yaya ya zancen auren mu ne? Dan Allah ka tausaya min bani da wanda nakeso idan ba kai ba''. Numfasawa yayi yace'' sister Hasy daman can na gaya miki ki cire zancen aure a tsakanin mû, ke kanki kinsan ba tun yau ba bani da ra'ayin auren zumunci da inada shi da na aure ki, kuma ni ban ta6a miki son aure ba face so irin na 'yan uwan juna, so ban son ki kawo rud'ani cikin zumuncin mû please ki bar wannan maganar ma''. Kuka ta saka mishi yayi ta rok'on ta amma sam tak'i sauraren shi daga k'arshe ma tashi tayi ta fice tana kuka kamar wacce aka kawo mata sak'on mutuwa. Yarima ya dafe kai a zuciyar sa yace wai a hakan ma kenan ina ga kuma mutum yayi mata biyu? Itama FARHANAH bai san me zai tarar a wajen ta ba dan ya lura tanada kishi sosai yanzu ma dan taga HASINA ne yasa tayi masa haka, ko ya masu mata biyu, uku da kuma hud'u sukeyi? Ina shi kam bazai iya tara mata su saka masa ciwo ba. Tashi yayi jiki a sanyaye ya haura sama cike da tausayin HASINA yasan tana son sa sosai to akasin da aka samu shi bai ta6a jin ko da d'igon sonta a zuciyar sa ba da zai iya auren ta da yayi amma ya kasa hakan bare yanzu da yake da matar sa kuma gashi sun fara samun kwanciyar hankali a zaman nasu. Zaune take a bakin gado tana latsa wayar ta saï murmushi take da alama tana jin dad'in abinda takeyi nufi na chatting d'in yana mata dad'i ko ma da waye take. Sallama yayi ta amsa masa a can k'asa ba tare da ta d'ago ta kalleshi ba, a ranshi yace to ai ga irin abin da nake gudu. 'Karasawa yayi ya zauna kusa da ita yace'' madam dawa ake hira ne haka naga ana ta murmushi?" 'Dagowa tayi tace'' friends''. Wayar ya amsa a hannun ta ya ajiye a gefe tare da kama hannuwan ta duk biyun ya had'e da nashi yace'' saï dai naga kin canza fuska kuma nasan hakan yanada nasaba da ganin HASINA a falo, please karki sa wani abu a ranki babu komai tsakani na da ita kinji?" Kallon shi tayi cikin ido saï kuma ta kawar da kanta gefe batayi magana ba, hannu yasa ya juyo kan nata yace'' kiyi magana dan Allah shirun nan ne ban so, ina son ki fad'a min duk abinda ke ranki''. '' To ni me kakeso ince? Babu komai a tsakanin ku shine take min wani irin kallo kamar taga kishiyar ta?" Maganar ta ba ma yarima dariya dan haka ya kasa rik'ewa saï da ya dara wanda hakan ya k'ara k'ular da FARHANAH tayi kicin-kicin da fuska saï yace'' sorry ai kece da abin dariya, wai kishiyar ta kamar da gaske zaki iya zaman kishiyar tunda gashi daga ganin yarinya kin wani rikice''. Ya fad'a yana mai lak'uce mata hanci. Mata da miji saï Allah nan yarima yayi nasarar saka ta a walwala tuni ta manta da zancen wata HASINA ita da kanta ta taimaka mishi yayi wanka sannan suka kwanta. 'Bangaren HASINA kuwa da kuka sha6e-sha6e ta shiga falon a lokacin kuwa mummy tana gishingid'e saboda ta gaji da zaman, ganin HASINA ta shigo da kuka yasa ta sallami kowa ta tashi ta haye sama kai tsaye ta nufi d'akin HASINA dan jin dalilin wannan kukan. A bisa gado ta iske ta kwance tana rusa kuka duk ta yamutsa komai na gadon. Mummy zuwa tayi ta zauna tace'' daughter me ya faru ne kika shigo da kuka?" Tashi zaune tayi cikin kuka tace'' mum yarima ne wai bai sona bazai aure ni ba''. Janyota mummy tayi ta shiga rarrashin ta akan tayi hak'uri ta daina kukan haka kar kanta yazo yana ciwo amma ina kamar ana k'ara ma wuta petur mummy tace'' ina ce an wuce wannan maganar me kuma ya tayar da ita yau?" '' Mummy ni shi nakeso please kisa baki dan Allah''. '' Ah! Ni babu ruwana a zancen ku, kuje ku daidaita kanku idan ya amince zaiyi ta biyu dake shikenan ba wata matsala''. 'Kara rushewa tayi da kuka tace'' haba mum! Haba-haba! Kina ji fa nace miki yace bazai aure ni ba, idan kika saka baki zai yarda''. Rarrashin ta mummy tayi tare da bata baki akan ta hak'ura kawai da yarima tunda ya furta bai ra'ayin auren ta to gara ma kar a tursasa masa dan kar azo ana dana sani. Washe gari HASINA ta tattara kayan ta tayi gaba tana mai fushi da mummy kuma ko mai martaba bata ma sallama ba tayi tafiyar ta a cewar ta mummy ma ta daina sonta kamar na maman ta, kowa ya tsaneta saboda anga ita marainiya ce. Allah sarki! Wannan kalma ta *MARAICI* kalma ce mai ban tausayi ina tausayawa duk marayu a fad'in duniya saboda *MARAICI* ba k'aramin abu bane, Allah ka bamu ikon taimakawa *MARAYU* ameen!!! Lokuta na gudu, awanni da kwanuka sai shud'ewa suke kwanakin rayuwar mû sai k'ara raguwa suke, bayan sati uku akwai wata rana yarima suna kwance da FARHANAH a d'akin sa ya tashi zaune ya kalle ta sai yayi murmushi tace'' wai lafiya kake wani murmushi kamar wanda akayi ma bushara?'' '' Haka kawai idan na kalle ki sai inji nishad'i, kamar ba mû bane masu fad'an nan a baya ashe dai ana sona ake wani basarwa da jan aji''. 'Karamin pillow ta jefe shi dashi tace'' Allah ka daina ban son ana tuna min wannan lokacin''. '' An gama ranki shi dad'e gimbiya ta yarima''. '' Humm! Naji dai''. Tace masa. Komawa yayi ya kwanta yayi dai-dai da yunk'urin amai da FARHANAH tayi da gudu ta nufi toilet. Yarima yana ganin haka ya doka hannu a bisa gado yace yes!!! Abinda nake jira daman, nasan ba haka kawai kika k'ara haske ba yarinya nayi winning, Allah ya inganta min. Yana gama maganar ne ya tashi ya nufi toilet ya iske har ta gama tana wanke fuskar ta. Sannu yayi ta jerowa wa'yanda basu da adadi, kai shi kansa ya tausaya mata yanda yaga ta koma lokaci d'aya, d'an Adam ba komai ne ba a wajen Allah mû dai ne muka maida kan mû wani abin..... Bayan ta gama tsaftace bakin ta ya kama ta suka fito daga toilet d'in. Kwanciya taje tayi har lokacin tana maida numfashin wahala dan amai bai da dad'i ko kad'an. Idanun ta ta lumshe gami da dafa cikin ta yarima ya hayo gadon ya d'ora hannun sa akan nata wanda ta d'ora a cikin yace'' yadai gimbiyata? Cikin ciwo yake ne?" Kai kawai ta girgiza masa sai ya k'ara cewa'' ko kina son wani abu ne?" Sai a lokacin ta bud'e idanu cikin k'asa da murya tace'' tea kawai nake so''. Yarima yace'' ok! An gama yanzun nan zaki sha tea''. Allah ma yaso shi akwai jug na ruwan zafi da komai na buk'ata a d'akin a kuma d'aya 6angaren tunda k'aton bedroom ne yanada komai nashi na buk'ata. Bayan ya had'a mata tea tasha ya d'auko kayan aiki wai zai duba ta ai kuwa tace ina bata san wannan ba ita lafiyar ta k'alau. 'Yar dariya yayi yace'' yau naga patient da gardama, kice ba za'a dubaki ba bayan gashi baki da lafiya''. Har idanun ta sun kawo ruwa tace'' Allah ni ban jin wani abu daman yunwa ce kuma nasha tea''. Kayan aikin ya kawar gefe yazo ya rad'a mata cewa'' haba wife d'an tayin nawa ne baki son in gano?" Ture kanshi tayi tana murmushi tace'' ni ba wani d'an tayi lafiya nake''. Komawa yayi ya kwanta kusa da ita ya d'ora hannun sa akan cikin ta yace'' haba wa yarinya ki yarda na iya aiki kawai''. Kunya ma taji ta wannan maganar tashi, ashe dai duk shiru-shirun sa na banza ne? Ashe yana magana haka?" Humm yo me nufin ki? Namiji ne fa.....hhhhh. Hannun ta ture ya sake maidawa, a haka har bacci ya d'auke su hannun sa na kan cikin ta........ Bayan wasu kwanaki cikin FARHANAH dai ya tabbata daman yarima bai cire rai ba yasan tanada ciki dan daga ka kalli FARHANAH zaka hango wani sihirtaccen kyau da ta k'ara wanda hakan zai baka damar gane me ta k'unsa...... FARHANAH safiyar yau duk bata jin dad'in jikinta kai tun dare take k'orafin ita fa wani iri takeji sam ba dad'i yarima yace mata ai haka ne daman mai ciki bazai yiwu tace ta kasance cikin lafiya kullum ba, kai duk d'an Adam ma ai hakan take dole wata rana kaji ba dai-dai ba a jikin ka. Duk da kasalar da takeji ta tashi ta shiga toilet kafin lokacin kiran sallah'r la'asar yayi. Bata fi 2 minutes da shiga ba naji ta k'wala wata irin k'ara mai razanarwa wacce duk 'yan aikin ta ma sai da suka jiyo, tuni su Shafa sun garzaya sama da gudu dan ganin abinda ke faruwa da gimbiyar tasu...... Da k'yar suka samu nasarar bud'e k'ofar toilet d'in, abinda suka gani ya matuk'ar razana su, FARHANAH ce kwance cikin jini ko numfashi batayi....... *MEKE SHIRIN FARUWA DA FARHANAH KENAN? ME YA RAZANAR DA ITA HAKA HAR TAYI 'KARA WANDA YA JAWO MATA WANNAN FA'DUWAR?* HUMM READERS INAJIN FA TSUGUNNE BATA 'KARE BA, AKWAI *LAUJE CIKIN NA'DI*, WANNAN AL'AMARIN ABIN DUBA NE🙀 INA YI MUKU TUNI DA HASINA FA TA BAR MASARAUTAR CIKIN FUSHI AKAN YARIMA BAI YARDA ZAI AURE TA BA, TO KO DAI TANADA NASABA DA ABINDA YA SAMI FARHANAH? BA RUWANA *ZATO ZUNUBI....* *YA YARIMA ZAIYI IDAN WANNAN MUMMUNAN LABARIN YA RISKE SHI?* AMSOSHIN DUK SUNA A NEXT PAGE INSHA ALLAH! *Basan ce zan ajiye typing ba saboda wasun ku basuyin comments, zan k'ok'arta in k'arasa labarin amma idan na gama wannan labarin zai sha banban, basai nace komai bâ zaku gani a aikace.....* *_'YAR MUTAN KAZAY CE👑_* 💥💥💥💥💥 *_'YAR GADARA_* 💥💥💥💥💥 *_NA_* *_A.MAIMOUNATH O.G.K_* _(Mahnoor)_ _Wattpad@maimounathog_ *💫DA BAZAR-MU WRITER'S ASS💫* *_~we are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are d best among all....DA BAZAR-MU MUKE TUN'KAHO.~_* *_Yin typing a kullum, gaggawar posting ba shine abin duba ba, ah'ah ana son yin typing cikin nutsuwa da sanin me mutum zai rubuta da kuma ingancin sa, mai rubutu ya kamata ya nutsu yasan me zai rubuta, idan na rubuta hakan zan fad'akar ko kuwa? Dole sai mai rubutu yayi taka tsan-tsan da hangen nesa saboda gudun abinda kaje yazo, fatan kun fahimceni😊 dan haka rubutu yuuuuuuuhhh ba shine abin duba ba🤨_* *_FOR YOU:_* *_DEAR_* *_YAYA HASSAN_* *_A.T.K_* *Page 106/110* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^* Haka Shafa ta nufi inda FARHANAH take kwance cikin jini ko motsi batayi Shafa ta shiga girgiza ta tana kuka amma FARHANAH ko gezau dan bata ma san anayi ba, su Shafa'atu sun rasa me zasuyi mata ta maido numfashi sai kawai d'ayar ta gudu taje 6angaren su mummy ta sanar. A rikice mummy tazo kai tsaye sama ta haura, itama ganin yanda FARHANAH ke kwance cikin jini sai ta k'ara rikicewa da k'yar ta iya kiran yarima yazo shima a rikice ya sure ta ko kunyar mummy baiji ba da kanshi ya saka ta a motar kuma yace bai buk'atar driver a halin yanzu. Abin ka da masarauta komai babu sirri cikin sa tuni labari ya sami kowa har fada anje an fad'i komai shi kanshi sarki ya shiga damuwa nan suka rankaya aka bi bayan yarima da motoci. Yarima kuwa tunda ya cilla motar sa waje ikon Allah ne kawai ya kai shi asibitin dan gudu yake na fitar hankali tunda bai cikin hayyacin sa. Yana shiga harabar asibitin tuni an kawo gadon d'ora marasa lafiya dan tun yana hanya ya sanar musu a shirya masa komai yanada patient. Suna shiga motocin su mai martaba suma suka shigo asibitin. Yarima yak'i kowa ya dafa masa mata yace da kanshi zai duba ta, babu abinda d'ayan doctor'n baiyi ba akan ya bar aikin a hannun sa tunda bâ cikin hayyacin sa yake ba amma furrr yak'i sai hak'ura yayi ya tsaya gefe ko da zai nemi wani taimakon. Cikin girmamawa aka ba mai martaba wurin zama dogarai suna daga k'ofar waje daga ciki kuwa su Galadima da Waziri ne sai sauran wasu 'yan fadan, lallai yarima d'an gata irin wannan taron haka? Iya wahala sun sha kafin ta kawo wani gauron numfashi ta saki gami da k'ank'ame hannun yarima duk da idanun ta a rufe suke amma da alama har yanzu tana cikin firgici kuma ba a banza ba akwai dai abinda ta gani, ga wasu hawaye dake ta fitowa daga rufaffun idanun ta amma bata iya ta bud'e su ba. Idan kunga yarima a lokacin zaku iya yi masa kuka ma saboda tausayin halin da shi kanshi ya shiga bare kuma ita uwar gayyar FARHANAH wacce ba'a san meye musabbabin wannan abu ba. Yarima tunda yasan cikin FARHANAH ya zube babu abinda yake furtawa a zuciya sai innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Ya Allah ka kawo min d'auki cikin lamurana, haka yayi ta furtawa har zuwa wani d'an lokaci kuma sai yaji FARHANAH ta saki hannun sa alamar bacci ya d'auke ta kenan. Fita yayi daga d'akin zuwa waje inda su mummy suke, yana zuwa yaje ya kusa da mummy ya durk'usa yana cewa'' mummy wannan ma nayi loosing, mummy bansan me yake faruwa dani ba, bansan me nayi ba da har na cancanci wannan abu,zanyi bincike akan abinda ke faruwa da matata, mummy wallahi akwai wani abu a k'asa ba a banza cikin jikin ta ya zube ba....''. Ya fashe da kuka mai cin rai abin tausayi wai yarima ne yau yake kuka. Da k'yar suka rarrashe shi yayi shiru suka tambayi ya jikin nata yanzu yace ta samu bacci, ya kalli Shafa'atu tare da bata umarnin taje gida ta d'auko wasu kayan a canza mata dan na jikin ta sun 6ace. Har ana abu d'aya domin kuwa FARHANAH daga ta farka to fa ba lafiya sai ta k'wala k'ara mai firgitarwa tana neman wurin la6ewa kamar dai wacce taga abin tsoro sai anyi mata allurar bacci sannan ta koma baccin. Yarima duk ya fita a hayyacin sa gashi sai yana jin yunwa amma ba damar neman abincin ma to mata ba lafiya gata nan dai an rasa kan abin bare ma yasan ta ina zai fara. Mai martaba da mummy suna gida amma waya kan waya suke yi masa dan jin halin da ake ciki, yanzu dai ya yanke shawarar a nan asibitin zasu kwana har zuwa safiya yaga abinda Allah zaiyi. Ciwo yak'i dare haka abin yake domin kuwa FARHANAH cikin dare ta tashi ta shiga zabure-zabure kamar wata ta6a66iya abu fa yaci tura har sai da aka kira malam Umar yazo asibitin dan yayi mata addu'a. Malam Umar shine amintaccen malamin sarki dan kusan zan iya ce muku a tare suka taso kuma sarki bai ta6ayin abu ba tare da ya nemi shawarar malam Umar ba, malam Umar malami ne masanin Al-Qur'ani sosai, dan a iya tsawon zaman su na baya ma malam Umar ya kasance babban amini ga sarki mai 6oye duk wani sirri da ya shafi mai martaba har kawo yanzu shiyasa sarki ya d'auki amana ya damk'a masa. Ko da yazo ma wurin gadon ya wuce, kallo d'aya yayi mata sai yayi murmushin yak'e tare da girgiza kai yace a kawo masa ruwa a wani abu. Yarima da kanshi ya d'auko ruwan a cup ya kawo masa yace'' gashi malam''. Ya amsa yana ce masa'' a yaushe ne wannan abu ya faru?" '' A yau d'in nan ne malam, dan ni lafiya k'alau muka rabu da ita kawai saï labari ya riskeni akan ta yanke jiki ta fad'i a bayi wanda shine sanadiyyar zubewar cikin...''. Sai kuma ya kasa k'arasawa saboda wani irin d'aci da suya da zuciyar sa keyi masa. Malam ya gane shi sai yace'' ba komai ranka ya dad'e karka damu Allah zai bata lafiya insha Allah''. Kai kawai ya iya d'aga masa ya koma ya zauna. Malam ya jima yana tofa addu'o'i a cikin ruwan kafin daga bisani ya yafito yarima da hannu shi kuma ya taso sai malam yace'' gashi wannan a bata tasha a kuma shafe mata jikin ta da sauran insha Allah zata samu sauk'i''. '' To shikenan malam nagode sosai Allah ya bar zumunci zanzo gidan idan na samu nutsuwa''. '' Karka ji komai ni mai jiran zuwan ka ne a kowane lokaci dan haka zamuyi ta yin addu'o'i matarka zata tashi''. '' To shikenan a gaida gida''. '' Zasu ji da yardar Allah''. Yana fad'ar haka yasa kai ya fice shi kuma yarima yaje kusan FARHANAH ya zauna yana jiran ta tashi ya bata maganin ko da bata so zai d'ura mata shi dan ya gaji da ganinta a cikin wannan halin. Sai goshin asuba allurar baccin ta sake ta, zumbur ta tashi zaune a lokacin yarima yana kan sallaya tunda ya gama nafilfilin sa bai tashi daga wurin ba. Cikin sauri ya taso gami da d'auko maganin yazo ya mik'a mata bata amsa ba sai kallon shi da tayi kamar wacce bata san shi haka ta nuna. Ya nufi bakin ta da cup d'in cikin ikon Allah sai yaga batayi gardama ba tasha ya shafe mata jiki cikin k'ank'anin lokaci ta shiga yin atishshawa ba k'ak'k'autawa kafin ta saki wata ajiyar zuciya sai ta kalli cikin d'akin ta maida kallon ta ga yarima tace'' husby kamar a asibitin ka muke, meke faruwa ne dani?" Yarima ya furta'' alhamdulillah! Ba komai wife baki d'an jin dad'in jikinki ne shine muka zo gobe insha Allah zamu koma gida''. '' To amma...amma dai..ni a iya sani na fa toilet na shiga dan yin wanka sai..sai..sai...'' ta kasa k'arashe maganar, yarima yace'' ban son ki tuno komai a yanzu ki kwanta ki huta, in Allah ya kaimu muka koma gida nasan zaki iya tunawa da duk abinda ya faru''. Zata sake magana ya tare ta saï ta koma ta kwanta tare da rufe idanun ta shi kuma ya rufe ta saï ya tashi ya shiga toilet yayo alwala yazo yayi raka'atanul fajri kafin mai kiran sallah a masallacin asibitin yayi. Washe gari suka koma gida daman Shafa'atu ma a asibitin ta kwana dan ita ta wanke duk wasu kaya da FARHANAH ta 6ata. 'Kwarai fada bata ji dad'in lamarin nan ko kad'an ba saboda zubewar cikin wannan na FARHANAH gashi dai suna matuk'ar son suga yarima ya tara yara tunda su Allah shi kad'ai ya basu to gashi abun yana ta zuwa da tangard'a. Cima mai kyau aka girka daga 6angaren su mummy aka kawo mata sai wanda takeso shi zata ci. FARHANAH bata san ma babu cikin jikinta ba har sai da suka zo gida ta shiga toilet taga alamun jini ya zubar mata a lokacin ne ta gane sai ta fashe da kuka har zuwa wani lokacin sannan ta k'yale tayi wanka ta fito. Fuskar nan duk a kumbure riga da zani kawai tasa sai lotion da ta shafa tasa lipstick tazo ta zauna a bakin gado kenan Shafa'atu ta shigo tazo ta durk'usa tace'' ranki ya dad'e ga abinci nan kala-kala an aiko daga cikin gida ki fito kici ko kinji k'warin jikin ki''. Lumshe idanu tayi ta bud'e kafin tace wani abu yarima yayi knocking gami da shigowa. Shafa tashi tayi ta fice tana mai gaishe shi kai a sunne dan girmamawa. Takawa yayi har inda take ya zauna sai kawai ta fad'a jikin sa tace'' wallahi ba laifi na bane, bansan ya akayi cikin jikina ya fita ba, nidai nasan na shiga toilet daga nan...'' yarima ya dakatar da ita yace'' na sani baki da laifi, tashi muje kici abinci yunwa kike ji na sani, daga baya zamuyi maganar''. Ba tare da tayi mishi musu ba ta tashi suka fito falon sama inda an jera musu komai akan dinning daman yarima yaso ya sallami su Shafa'atu to gashi dai tun kafin a kore su sun kama gaban su dan sunsan idan ya fito d'in cewa zaiyi su wuce 6angaren su shiyasa ma suka fece. Ganin bata ga kowa ba yasa tace'' ina su Shafa'atu?" '' Sun gudu mana''. Ya fad'a yana mai yi mata murmushi. '' Gudu kuma? Akan me?" '' Akan sun ga mijinki yazo mana, kuma ai yaci ace sun saba daman, ya kamata daga na shigo su bamu wuri yanda zamu shak'ata muma''. 'Kyaleshi tayi tare da zama a d'aya daga cikin kujerun dinning d'in ta bubbud'e komai ga ferfesun kayan ciki sai k'amshi yake tuni taji yawun ta ya tsinke. Kallon shi tayi tace'' me zan zuba maka a ciki?" '' Wanda zaki ci nima shi zanci''. '' Shinkafa da ferfesun kayan ciki ni zanci''. '' Ok! Zuba min shi nima''. Zuba masa tayi ta ajiye a gaban sa ta zuba nata sukayi addu'a tare da yin bismillah sannan suka fara cin abincin suna korawa da juice na peneapple da d'anyar citta sai zuba k'amshi yake. Basuyi magana ba har sai da suka gama, a tare suka maida komai Kitchen tukun suka dawo kai tsaye bedroom d'in ta suka shige tare da rufewa. Toilet ta shiga tayi brushing ta fito shima ya shiga kafin ya fito ta canza kaya zuwa rigar bacci ruwan k'asa mai sul6i ta sauka har wajen k'aurin ta ta tafi gado ta kwanta dan har yanzu cikin nata ba wani k'arfi sosai kawai dauriya ce takeyi Da yarima ya fito ya iske har ta lumshe idanun ta alamar bacci ke son d'aukar ta shi kuma gaskiya yana son jin abinda ya faru da ita haka har tayi irin wannan razanar amma kuma bai son takura mata saboda yanayin jikinta bari dai ya bar ta ta huta ko zuwa gobe ne. Zuwa yayi ya kashe fitilar d'akin sai ta kan bedside drower ya bari yazo ya hau gadon shima amma bai kwanta ba har sai da ya tabbatar ya tofe gabas da yamma, kudu da arewa da addu'o'i sannan ya tofe mata jikinta ya shafa mata sannan shima yayi ya shafa ya kwanta zai kashe fitilar sai yaga ta bud'e idanu yace'' au wai daman ba bacci kikeyi ba?" Girgiza kai tayi ta tashi zaune ta kalleshi tace'' a,a kai nake jira ai maganar zamuyi''. '' Tabbas ina son jin komai saboda zuciyata cike take da k'una na halin da na tsince ki a ciki musamman irin firgicin da naga kinayi, but kinga dare yayi ki kwanta ki huta ko gobe ne zamuyi maganar karki damu''. Baki ta zum6uro tace'' nidai a,a gara muyi a yanzu ba komai ai naji sauk'i''. Janyota tayi ya kwantar da kanta a k'irjin sa yace'' sure?" Ta d'aga masa kai alamar eh, sai yace'' ok to shikenan ina jinki me ya faru? Kuma me kika gani a toilet d'in wanda ya haddasa miki fad'uwa?" Tashi tayi ta gyara zaman ta tana fuskantar ta tace''........ *Mû dai ya kamata ki fad'a mana abinda kika gani a toilet ehee ni na k'agu inji....* *Wallahi na daina wahalar da kaina wajen yi muku dogon typing tunda bâ wani comments kukeyi sosai ba, ace wai group d'in da nakeji dashi a rasa mutum ko 20 ne da zasuyi comments sai 'yan tsirarun mutane kawai, hakan ba k'aramin bak'anta min rai yake ba, zan bud'e wani group musamman dan masu comments na gaji da yin aikin banza, ni da nake 6ata time d'ina inyi typing banji wuya ba sai ku only comments zai gagare ku?* *Masu comments sannunku nagode Allah ya bar zumunci🤝* *_'YAR MUTAN KAZAY CE👑_* 💥💥💥💥💥 *_'YAR GADARA_* 💥💥💥💥💥 *_NA_* *_A.MAIMOUNATH O.G.K_* _(Mahnoor)_ _Wattpad@maimounathog_ *💫DA BAZAR-MU WRITER'S ASS💫* *_~we are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are d best among all....DA BAZAR-MU MUKE TUN'KAHO.~_* *_FOR YOU:_* *_DEAR_* *_YAYA HASSAN_* *_A.T.K_* *Page 111/115* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *°°°°°°* FARHANAH ta tashi zaune tana fuskantar yarima tace'' a lokacin da na shiga wanka ban kai ga cire kayana ba saï naji motsi kamar a bayana saï na waiwaya banga komai ba ina k'ara waigowa gabana saï naga wata k'atuwar mage mai manyan idanu tana nufo inda nake ina ja da baya tana k'ara nufo ni na rasa ya zanyi ina ta d'aga mata hannu ko zataji tsoro ta gudu amma ko a ka dan a k'arshe ma saï naga tana canza kala zuwa wata halittar daga nan ban k'ara sanin abinda ya faru ba saï tashi nayi na tsinci kaina a asibiti ban kuma san ya akayi cikin jikina har ya...ya..zub.....'' kasa k'arasawa tayi saï ta rushe da kuka gami da fad'awa jikin yarima. Rungumeta yayi ya shiga bubbuga mata baya alamar rarrashi bai yi magana bâ saboda zuciyar sa cunkushe take da tunani kala-kala yana son gano wani abu a cikin wannan al'amari, waye yake son kawo musu rud'ani a cikin gidan su? Meke shirin faruwa ne haka? Waye ya mishi wannan aika-aikar? Bazai ta6a barin wannan maganar ba saï ya bincika yaga ko waye kuma saï ya d'auki mummunan mataki akan duk wanda yake da sa hannu a cikin lamarin insha Allah. Kuka takeyi abin tausayi da k'yar ya iya cewa'' is ok daina kukan haka nan shiyasa naso muyi maganar a wani lokacin ba a yau ba, kinga kin tuna kin kuma shiga damuwa ni kuma shine ban so''. '' Ina son kasan gaskiyar abinda ya faru ne dan karka k'ara zargina da zubar maka ciki da kake zaton na farkon ma ni nayi shiyasa nace muyi maganar a yanzu dan in wanke kaina wallahi *bani da laifi* am sorry husby''. Ta k'ara fashewa da wani kukan wanda har yasa yarima ma yaji wasu hawayen na bin kuncin sa. Saï da ya goge yace'' waye ya had'a miki ruwan wankan? Akwai wacce ta shiga toilet d'in nan kafin ki shiga wankan? A lokacin da zaki shiga kinyi addu'a kuwa?" '' Shafa'atu kawai ta shiga ta wanke min bayin ta saka turare shikenan saï ta fito, a lokacin da zan shiga gaskiya na manta banyi addu'a ba''. '' Ai kinga irin ta nan sam baki damu da addu'o'i ba wanda sanin kanki ne addu'a *takobin mumini* ce a duk halin da ka tsinci kanka ka kasance kana mai addu'o'i dan ko abu zai sameka to kuwa zai zo maka cikin sauk'i amma sam kina wasa da addinin ki, dole ne fa ki maida hankali dan na tabbatar ke ba jahila bace kinyi karatun addini kawai rashin maida hankali ne dake''. Daga jin yanda yake magana zaka san cikin 6acin rai yake yin ta saï ta tashi zaune ta kama hannuwan sa tace'' kayi hak'uri dan Allah bazan sake mantawa ba wannan ma rabon hakan zai faru ne sorry kaji mijina?" '' Uhmm naji ki kiyaye dai, mu kwanta bacci nakeji kema kuma nasan kinaji''. Kwanciya sukayi ya kashe lamp na bedside drower ya rungume matar sa suka yi baccin su. Washe gari yarima ya tara ma'aikatan FARHANAH yace su fad'a masa gaskiyar abinda ke faruwa a gidan nan waye ya shiga toilet d'in FARHANAH yayi wani abin, kowacce jiki na 6ari saï tace ita bata ma shiga d'akin ba tunda wasu basu ta6a shiga d'akin ta ba ma su 6angaren kula da abinci ne saï kuwa Shafa ita ce mai shiga lungu da sak'o na cikin d'akin. Yarima ya kalli Shafa'atu yace'' ke ki fad'a min gaskiya a lokacin da kika shiga toilet d'in baki ga komai ba?" Jiki na karkarwa tace'' wallahi Allah banga komai ba ranka ya dad'e''. Tsawa ya daka mata yace'' keeee!!! Fad'a min gaskiya dake ne aka had'a baki dan a kashe min mata ko? Waye ya baki wani abu ki saka mata a bayin?" '' Innalillahi! Wallahi bazan ta6a cutar da gimbiya ba, babu wanda na had'a baki dashi Allah wankin bayin kawai nayi na fito''. '' Ku tashi ku bani wuri zan bincika da kaina idan na samu d'aya daga cikin ku na da sa hannu a ciki to wallahi kwanan ta ya k'are cikin gidan nan dan saï na rufe ko ma waye, ku tashi ku 6ace min da gani''. Har rige-rigen tashi sukeyi jiki na 6ari dan tsoro daman suna tsoron yarima sosai dan bai cika fara'a ba idan ya gansu bai wasa ba'a kuma yi masa wasa shiyasa suke shakkar sa fiye ma da mai martaba. Suna fita ya koma ya kwantar da kanshi bisa hannun kujera ya shiga tunanin ta inda zai fara da wannan lamari, duk iya tunane-tunanen sa bai samu mafita ba saï ya tashi zaune ya furzar da iskar bakin sa cike da tak'aici har idanun sa sun canza kala saboda tsabar 6acin rai, a haka FARHANAH ta iske shi gami da zama kusa dashi ta kalle shi saï taga duk ya canza ya hargitse. Dafa shi tayi tace'' dan Allah ka saka ma ranka hak'uri akan wannan abin muyi hak'uri kawai a bar zanc....'' bata k'arasa ba ya katse ta ta hanyar daka mata tsawa yace'' what? Me kike cewa ne? Kinada hankali kuwa? In hak'ura fa kika ce? Ban son jin kalmar hak'uri a cikin wannan maganar''. Ita kanta ta tsorata da yanayin sa ganin haka ne ma yasa ta tashi ta bar wurin ba tare da ta k'ara cewa ko da uffan ba dan tasan tunda ya hau dokin zuciyar nan ba sauraren ta zaiyi ba. 'Daki ta shiga ta hau gado ta fara rera kukan ta kamar wacce aka ma dukan tsiya a haka yarima ya isko ta yayi tsaye bisa kanta bata ma san ya shigo d'akin ba tunda kanta ta saka tsakanin gwiwoyin ta take kukan. Kamar daga sama taji yace'' kukan me kikeyi?" Duk da ta d'an tsorata amma saï ta dake tak'i d'ago ko da kanta bare tayi magana saï ya k'ara cewa'' ba dake nake ba? Me akayi miki kike kuka?" Cikin kukan ne tace'' ba kai bane kake min tsawa dan ka tsaneni saboda kawai ciki ya zube shikenan saï ka rink'a ganin laifina bayan na fad'a maka abinda ya faru''. Zama yayi yace'' ba zaki gane bane, ni nasan a halin da nake ciki kawai dai ina k'arfin halin mantawa ne amma bazan iya ba dan saï na bincika yanda abin nan ya faru ke kuma kina min zancen wai mû hak'ura, haba dan Allah gudan jinina fa nake gani yana bin k'asa ba so d'aya ba, kinsan yanda nakeji kuwa?'' '' Allah ya huci zuciyar ka nidai ban son tsawa kuma ina son ka rage damuwar nan mû bi komai a hankali har a samu *bakin zaren* please''. Kamo ta yayi ya lak'uce mata hanci yace'' sarkin shagwa6a wannan 'yar maganar ce har zata saki kuka dan kawai ki k'ara tayar min da hankali''. Zatayi magana ya had'e bakin su waje d'aya ya shiga aika mata sak'onnin sa masu cike da ma'anoni daban-daban itama ba'a barta a baya ba nan ta shiga taimaka masa dan ta mantar dashi damuwar da yake ciki. Sun d'auki lokaci a haka kafin ta zare bakin ta a nashi tace'' anya yau kaci abinci kuwa?" '' Sarkin wayo saï yanzu kika tuno dan kawai ki katse min jin dad'i na''. Rufe fuska tayi tace'' kai kaji ka da wata magana''. Murmushi yayi yace'' ai gaskiya na fad'a kuma kin san nayi hak'uri ma yau kwana nawa kenan?" '' Kwanan me? FARHANAH ta tambayeshi cike da tsokana tayi kamar bata fahimce shi ba. Cije lips yayi yace'' yarinya zakiyi bayani idan na kama ki, wato ma har tambaya ta kikeyi ko? Allah ya baki lafiya kiga aiki da cikawa''. Cikin k'asa da murya tace'' ameen''. Kallon ta yayi yace'' muje part d'ina''. Idanu ta zaro tace'' yin me kuma?" '' Aikin lada''. Ya amsa mata kai tsaye. Batayi gardama ba ta tashi suka fita had'i da rufe k'ofar d'akin. A yau ma cikin dare yarima ya kasa yin bacci saboda tunani da yayi masa yawa yana son gano wannan abu wai mage a toilet to ta ina magen ta shigo? A iya sanin sa da masarautar nan banda halittu irin su talo-talo da zabbi da su jimina da dai sauran su amma bai ta6a ganin mage a gidan nan ba to ya akayi ta shigo gidan har a toilet d'in FARHANAH? A gaskiya wannan lamarin abin dub....ta6a shi da FARHANAH tayi shine ya katse masa tunanin da yake. 'Kara matsowa tayi ta shige jikin sa cikin murya irin ta masu bacci tace'' me kakeyi a zaune warhaka? Tunani ko?" Girgiza kai yayi yace'' ba komai ki koma ki kwanta''. Nok'e kafad'a tayi gami da tashi zaune ta kunna fitilar gefen gado tana mai murje idanun ta da sukayi mata nauyi dan bacci ta kalle shi tace'' dan Allah ka daina yawan tunani dare fa mahutar bawa aka ce, dan me zaka takura ma kanka har haka? Dan Allah mû kwanta''. '' Ki kwanta ai nima zan kwanta nace''. '' Ba wani kayi min wayo dai ko? Ni bazan iya bacci ba idan baka tare dani''. Gira ya d'aga mata yace'' really?" 'Boye fuskar ta tayi akan k'irjin sa dan taji kunyar maganar da tayi. Murmushi yayi mai fitar da sauti yace'' ah haba yarinya ba wata kunya da zakiji kawai fad'a min gaskiya kema kinyi missing....''. Bai k'arasa ba saï ya k'yale kuma. Shiru na wasu 'yan dak'ik'u sukayi saï kuma yace'' to kashe wutar mû kwanta''. Kashewa tayi suka kwanta ya rad'a mata yaushe ne za'a fara kar6a ta?" 'Kin yin magana tayi saï ya d'an cije ta a bakin kunnen har saï da tayi 'yar k'ara wai taji ciwo tace'' kai-kai shine zaka cije ni?" '' Ke kika ja ai, ina jiran amsa ta, naga alamun an warke amma ana yi min rowa ko?" Cizon shi tayi a k'irji yace'' ashsh ni kika ciza haka? Bari kiga in rama nima''. Batayi aune ba taji ya manna bakin sa a nata. Wasannin ma'aurata suka gudanar yarima duk ya kashe mata jiki da wasannin sa masu wuyar fassarawa amma iya wasan kawai ya tsaya da yaji ya rage zafi saï ya rungume ta kan kace me tuni bacci ya d'auke ta shi kuma yarima kiss yayi mata a bacci cike da k'aunar ta ya tashi ya nufi toilet dan tsarkake jikin sa. Alwala ya d'auro yazo ya fara nafilfilin sa dan yasan baccin ba wani d'aukar sa zaiyi ba. Yana bisa sallaya ya tsinkayi FARHANAH tana motsi tana ta jujjuya kanta can kuma saï ta saki wata irin k'ara ta tashi zaune tana dafe k'irji da sauri yarima ya ajiye carbin hannun sa ya taso yazo wurin ta yana tambayar ta me ya faru? Kamar wacce tayi gudu haka take shek'a saï ta fashe da kuka tace'' wata mata ce take ta bina da wuk'a wai saï ta kashe ni, kuma banga fuskar ta ba, cikin daji ta bini tana cewa saï ta hallaka mû daga ni har kai tana daf da caka min wuk'ar ne na tashi''. Gadon ya hayo ya rik'e ta yace'' to daina kukan haka nan ya isa babu abinda ta isa tayi mana da izinin Allah koma ki kwanta''. '' Wallahi bazan kwanta ni kad'ai ba haka kawai tazo ta kasheni''. '' Kinga irin abinda nake gaya miki ko? Baki da lura kan addinin ki gashi yanzu jikin ki ma ba tsarki kikayi bacci ai dole ki rink'a firgita da mugwayen mafarkai, tashi kije kiyi wankan kizo kiyi nafila''. Kallon shi tayi tace'' ni kad'ai zanje toilet d'in? Tabd'ijam saï dai muje tare gaskiya''. Kama ta yayi suka tafi a tare kuma tace dole saï yana tsaye a kusa da ita zatayi wankan. Ganin ta cire rigar jikin ta ne yasa shima ya cire tashi rigar suka shiga kwamin ruwa saï da ya ta6a 'yan wasannin sa da ita sannan suka yo wankan suka fito. Washe gari kasancewar juma'a ce kuma yarima ya kan dad'e wurin mai martaba a fada saboda kar6ar gaisuwar bak'in da suke zuwa dan haka yasa ma wuni guda FARHANAH bata saka shi a idanun ta ba, rabon ta dashi tunda yayi shirin juma'a bata k'ara ganin sa ba. Ta d'an damu na rashin sa a kusa da ita saboda shak'uwar da sukayi a 'yan kwanakin nan yana mak'ale da ita sai gashi yau yak'i yazo gareta. Tana zaune a falo tare dasu Shafa'atu suna mata hirar d'ebe kewa amma fa hankalin ta sam bai wurin su, jim kad'an sai ta kalli wayar ta ko zai kira ta amma shiru kake ji har bayan la'asar babu yarima babu labarin sa. Sama ta koma ta shirya suka fita bayan gidan wajen lambu, wurin gwanin ban sha'awa ko'ina flowers ne sunyi kore sharr dasu wajen an k'ayata shi sosai da kayan alatu na more rayuwa ga wata iska mai dad'in gaske dake kad'awa tare da fulawoyin wurin kamar bâ a Nigeria kake ba idan har ka tsinci kanka a wurin nan, ga swimming fool a gefe shima wani tank'ameme dashi kamar a turai kai nidai wannan wuri naso in kasance nima ace ina cikin sa. Wata kilisa mai kyau aka shimfid'a ma gimbiya ta hau kai ta zauna ga kayan cima da suka zo mata dashi wato fruits nake nufi. Duk da wurin yayi mata dad'in zama saboda iskar da ke ratsa mata jiki amma dai tana tare da 'yar damuwar rashin ganin yariman ta. Sai ana daf da za'a kira sallah a masallacin gidan tukun suka tattara suka koma ciki. Kusan 9:30pm yarima yayi ma FARHANAH text wai ta sameshi a 6angaren sa yanzu. Baki ta ta6e a zuciyar ta tace sai kace ya wani damu dani, wata zuciyar tace mata ya kamata kiyi masa uziri tunda gidan nan gidan jama'a ne kuma kinsan daman duk juma'a yana zuwa fada ga aikin sa na asibiti maybe ma can ya wuce daga fadar. Da wannan tunanin ta shirya ta tafi amma fuska ba walwala har ta k'arasa d'akin sa. Turus tayi ta tsaya ganin yarima kwance da kayan da ya fita dasu ko takalmin k'afar sa bai cire ba, ta jima tana kallon sa kafin tayi masa sallama ta shigo ciki. Har ta k'araso inda yake bai motsa ba har ta zauna a bakin gadon tace'' sannu husby, ya naga ko cire takalmi bakayi ba? Lafiya?" Ba tare da ya tashi ba yace'' yauwa, gajiya ce kawai ta hanani yin komai shiyasa na kira ki please help me wife". Baki ta cunno kamar yana kallon ta amma batayi magana ba, hakan ne ma yasa yarima d'an juyowa ya kalle ta duk ta had'e fuska sai yace'' me ya faru kuma naga kina ta wani 6ata fuska?" Kawar da kanta tayi gefe guda tace'' ba komai''. Tashi yayi zaune yace'' a,a ban yarda ba fad'a min abinda ke damunki''. Cikin sigar kissa da shagwa6a tace'' ba kai bane kaje kayi zaman ka duk yau ban ganka ba fa''. Shafo fuskar ta yayi yace'' shine matsalar?" Kai ta gyad'a kamar wata k'aramar yarinya haka ta zame mishi. Kiss yayi ma kuncin ta yace'' sorry wife ai nine ma ya kamata inyi fushi ba ke ba''. Kallon shi tayi tace'' dan me?" '' Good question! Saboda tunda na fita baki kira kinji ya nake ba, kinga ai nine ma zanyi fushin ko?" '' To yi hak'uri nayi kuskure gobe bazan k'ara ba, bari in taimaka maka kayi wanka ko?" '' Ok baby, thank you!". Ita ta cire masa komai na jikin sa ya rage daga singlet sai dogon wando. Kallon ta yayi yace'' ya haka madam? Sauran kuma waye zai cire su?" Ido ta zaro tace'' kaiii! Haba dai kai kuwa kar dad'in yayi maka yawa mana, idan kaje toilet ka cire kayan ka bazan iya ba ehee". Lak'uce mata hanci yayi yace'' zakiyi bayani yarinya dan kinga na saurara miki kwana biyu shiyasa kika raina ni''. Dariya tayi ta kama kunnuwan ta tace'' tuba nake ranka shi dad'e ko wankan ma sai inyi maka ai''. '' Muje to ai da kuwa kin taimaka dan yau na gaji sosai''. Suna mak'ale da juna suka nufi toilet d'in. Sosai suka 6ata lokaci kafin su fito, da kanta ta shafa masa mai da komai ita tayi masa suka fita falo dan yaci abinci. Bayan ya gama cin abincin ne suka zauna hira a falon a yayin da yake aiki a laptop ita kuma tana kwance kusa dashi tana kallon TV suna 'yar hira a haka har ya gama suka koma bedroom. Kaya suka canza zuwa na bacci sannan suka shige blanket, FARHANAH dan tsokana har da juya ma yarima baya shi kuma ya rungumo ta ta bayan ya shiga shafar ta gami da rad'a mata cewa'' Allah yau dai baki isa kiyi baccin nan ba sai an sallame ni''. Yanayin yanda yayi mata maganar ne ya kashe mata jiki, wani irin yarrr taji abu ya tsirga mata a dukkan jikin ta sosai ya tafi da ita sai ta wani nok'e tana basarwa, ji tayi ya cije mata kunne sai tayi 'yar kara tace'' washsh da zafi fa, ka k'yaleni bacci nakeji''. Hannun sa ya tura cikin rigar ta yace'' yau babu bacci dakon baby nake so in baki, dan haka ki ma daina zancen baccin nan''. '' Nidai na gay...'' bata k'arashe ya datse sauran maganar ta sakamakon wani bak'on yanayi da ta tsinci kanta a ciki..... Sosai suka raya wannan daren har ya kai FARHANAH ta fara rakin ita fa ta gaji bacci zakayi a sannan ne ya saurara mata sukayi wanka gami da kwanciya bacci amma fa yarima bai daina jagularta ba har bacci yayi awon gaba dasu...... *Mû had'u a next page akwai sauran chakwakiya fa, akwai drama nan gaba ma ku biyoni dai a sannu zan warware muku komai....* *_'YAR MUTAN KAZAY CE👑_* 💥💥💥💥💥 *_'YAR GADARA_* 💥💥💥💥💥 *_NA_* *_A.MAIMOUNATH O.G.K_* _(Mahnoor)_ _Wattpad@maimounathog_ *💫DA BAZAR-MU WRITER'S ASS💫* *_~we are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are d best among all....DA BAZAR-MU MUKE TUN'KAHO.~_* *°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°* *_RAYUWA tana koya maka SO....!!!_* *_YAU da GOBE na koya maka WA KAKE SO...!!!_* *_MATSALOLIN_* *_RAYUWA_* *_Na koya maka WA KE SON KA...!!!_* *_ALLAH ka had'a mu da MASOYA NAGARI...!!!_* *_AMEEN...!!!_* *_DUNIYA🌎_* *_MAKARANTA...📖🖊_* *°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°* *_FOR YOU:_* *_DEAR_* *_YAYA HASSAN_* *_A.T.K_* *Page 116/120* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *****Da asuba da k'yar ya 6an6areta a jikin sa saboda wani irin shige masa jiki da tayi kamar wacce take tsoron kar wani abu ya kama ta. Alwala ya d'auro ya saka doguwar rigar shi ta sallah, a gurguje yayi raka'ataynul fajri dan kar a bar shi jam'in sallah'r asuba. Zuwa yayi bakin gadon ya yaye blanket d'in ya shafo fuskar ta, laushin hannun sa da taji ne ya farkar da ita daga nannauyen baccin da takeyi. Idanu ta bud'e da k'yar ta kalle shi sai yayi mata murmushin nan nashi mai tsad'a wanda ba kowanne mutum ne ke da damar ganin sa ba yace'' baccin ya isa haka a tashi time for prayer, zan tafi masjid''. Juya masa baya tayi tace'' ni bacci bai isheni ba idan ka dawo sai ka tashe ni inyi''. Bai sake mata magana ba ya fice dan kar yaje ya makara idan ya dawo zai saka ta tashi ko ta k'arfin tsiya ma dan shi ya tsani yaga ana wasa da sallah. Bayan ya fita ne FARHANAH ta tashi jiki a sanyaye ta shige toilet dan kar ma yarima ya isketa kwance batayi sallah ba fad'a zaiyi mata sosai a yanda ta sanshi ba wasa da addinin sa kuma a yanda ya fice ba tare da ya k'ara mata wata maganar ba idan ya dawo ba zasu kwashe ta da dad'i ba. Kafin ya dawo ta gama sallah amma kasala ta hana ta koma gadon saï kawai tayi kwanciyar ta a nan wani bacci mai dad'i ya d'auke ta. Yarima yana dawowa ya hangeta a kwance bisa pray-mat saï ya girgiza kai gami da yin murmushi yasan gajiya ce dan haka saï yazo ya d'auke ta yakai bisan gado tare da cire mata hijab saï a lokacin ta bud'e idanu gami da turo baki tace'' me kake shirin yi ne haka? Ina bacci na mai dad'i zaka wani d'auko ni''. Hancin ta ya lak'uce yace'' raguwa kawai ko gaisuwa babu kin tsare ni da tambayar me zanyi miki, to aikin lada zamuyi''. Ba shiri ta tashi zaune tace'' a,a na tuba dan Allah, ina kwana to''. '' Lafiya lau amma wannan bai hanani yin abinda nayi niyya''. '' Please husby kayi hak'uri wallahi na gaji kai ma kasan da haka fa''. Ta k'arashe tana shagwa6e fuska. Fitilar d'akin ya kashe gami da kwanciya ya jawota jikinsa ya rufesu da duvet ya sunsuna wuyan ta cikin muryar rad'a yace'' ina son ne in baki ajiya da wuri dan haka ki zamo jarama tunda kina tare da jarumin maza''. Kanta ta kawar gefe d'aya tana ta faman kumbura baki kamar yana ganin ta ita dai gaskiya ba zata iya wannan nacin na yarima jiya ma da yaya ya barta tayi bacci da yanzu zai wani ce k'arawa zaiyi in haka ne ba zata k'ara zuwa d'akin sa ba tunda wahalar d....... Hannun sa taji cikin rigar ta bisa marar ta shine abinda ya katse mata tunanin da takeyi. '' Ya Allah kasa nayi ajiya a nan''. Abinda taji ya fad'a kenan yana shafar marar ta wanda hakan ba k'aramar kasala ya haddasa mata ba, yanda yake yawo da hannun sa akan marar ta da haka tayi bacci bata san ya aka k'are ba. Kusan 10pm wayar sa ta tashe su sakamakon ringing d'in da takeyi ba k'ak'k'autawa da k'yar ya mik'a hannu ya d'auko ya kara a kunnen sa ba tare da ya kalli screen d'in wayar ba cikin murya irin ta mai bacci yace'' assalamu alaikum''. Daga d'aya 6angaren aka amsa masa gami da gaishe shi nan take ya gane wannan kiran daga asibiti ne kawai, ai kuwa hakan ne dan sanar masa akayi ana buk'atar shi a asibitin cikin gaggawa an kawo wata tiyata kuma dole saï yana nan za'ayi aikin nan. Kallon inda FARHANAH take yayi ashe ta farka saï sukayi ido hud'u ta kwantar da kanta akan cinyar hannun sa tana faman shafa masa gashin k'irjin sa saï ya lumshe idanu ya bud'e su yace'' sorry wife an tashe ki ko? Inada emergency a asibiti dole saï naje yanzu aka kira ni dan haka zanyi wanka in tafi kiyi kwanciyar ki''. '' Haba dan Allah baka ci komai ba zaka fita?" Murmushin gefen baki yayi yace'' don't worry wife zanyi breakfast a can ai na saba irin wannan fitar''. Tashi tayi zaune tana gyara zaman rigar ta da duk ta yamutse saboda kwanciya. Ita ta taimaka masa ya shirya ya fice a gurguje. Da kallon tausayi ta bishi tana tunanin a yaushe ma zai samu damar cin wani abu bayan idan yaje d'in ma aikin opération ne ke jiran shi tasan ma da yunwa zai wuni kawai, Allah sarki mijina Allah ya baka ladan aikin ka ya kare min kai.....ta fad'a daga k'arshe tana mai k'ok'arin tashi ta fita taje taga abinda zata saka ma cikin ta dan saï k'ugi yake mata dan neman d'auki. Shiru har zuwa yamma yarima bai dawo ba kuma tana ta kiran wayar sa tana ringing amma no anwser duk ta damu tana son jin ya yake yaci abinci ko bai ci ba? To wa ma zai bashi abincin? Wata zuciyar tace da ita nurses mana na asibitin maybe su suke kai abinci har shima su bashi. Nan take taji fad'uwar gaba, nurses kuma? To meye ma zai had'a shi da wasu nurses haka kawai suna kalle mata miji tabd'ijam ita fa macece mai tsananin kishi dan haka taji wani irin 6acin rai da kishin mijinta ya turnik'e ta. Kasa zama tayi ta tashi tayi wanka akayi mata rakiya zuwa cikin gida wajen mummyn yarima gara taje can ko tunanin zai mata da sauk'i duk da dai su Shafa'atu suna tare da ita amma hankalin ta na kan mijinta gaskiya dan ko Shafa'atu ma ta lura da gimbiyar tasu kamar tana cikin damuwa har tambayar ta tayi ko da wata matsala ne saï tace ba komai. Iso akayi mata zuwa falon mummy a yayin da su Shafa'atu suna kai gaisuwa suka fice waje tare da wasu matan da ke zaune wajen mummyn. Zama tayi cikin ladabi ta gaishe da mummyn saï wani sunkuyar da kai takeyi wai ita kunyar sarakuwa. Mummy ta kalle ta tace'' ya 6angaren naku babu dai wata damuwa ko? naga kamar kina cikin damuwa meke faruwa ne?" Kalar tausayi tayi duk da tana jin 'yar kunya amma ta dake tace'' yarima ne tun safe ya tafi asibiti har yanzu shiru, na kira shi amma baiyi picking call d'ina ba''. Murmushin manya mum tayi taji dad'in yanda FARHANAH ta nuna kulawar ta ga tilon d'an nata saï mummy ta dafa kafad'ar ta tace'' karki damu 'yata yana nan lafiya lau, nasan aiki ne yayi mishi yawa da zai tafi ma a hanya ya kira yake gaya min dan bai samu damar shigowa ba yace kiran gaggawa ne, so karki samu damuwa zai dawo insha Allah''. Kunya ta lullu6e FARHANAH saï ta k'ara k'asa da kanta har da su rufe fuska tana murmushi, mummy ma murmushin tayi tace'' nagode sosai da irin kulawar da kike ma mijinki, kuma ina son ki k'ara akan wanda kikeyi Allah ya baku zaman lafiya na har abada''. Cikin mak'oshi ta amsa ameen d'in wai ita nan kunya takeji. Gabanin magrib tayi ma mummy sallama ta fice a inda su Shafa'atu suke jiran fitowar ta nan suka rankaya suka tafi. Saï bayan isha'i tukun yarima ya shigo gidan ma baki d'aya, duk da gajiyar da yayi saï da ya wuce cikin gida wajen su mummy saboda ko da safe bai samu sun gaisa ba saï a waya. Mummy korar shi tayi tace'' tashi ka tafi duk ka saka yarinya a damuwa na rashin zuwan ka, kuma har kiran ka tayi amma baka d'auka ba tun d'azu tana nan zaune''. Kai ya d'an sosa yace" wallahi mummy duk yau ban samu kaina ba dan wuni nayi ina aiki ko office d'in ma ban zauna ba kuma wayar tana office a lokacin da zan shiga tiyata na ajiye ta, saï kuma da na tashi na wuce wajen malam''. '' Ah to saï ka tanadi abin fad'a mata saboda naga alamar damuwa a tattare da ita, lafiya kaje wurin malam?" '' Eh lafiya lau daman jiya ne da na kira shi a waya yake cewa inje in kar6o wasu addu'o'i shine''. '' To madallah Allah ya taimaka ya kiyaye kuma, tashi ka tafi wurin matarka ka rarrashe ta da kyau''. Dariya yayi ya fice ba tare da yace komai ba, itama mummyn murmushi tayi tare da girgiza kai, hummm yaran zamani. Yarima saï da yayi wanka ya gama komai nashi tukun ya wuce 6angaren FARHANAH. Falon shiru ba kowa saï TV dake ta aiki ita kad'ai, sama ya haura a inda ya iske ta a falon sama tana gishingid'e a bisa carpet ita kad'ai ce saboda ta sallami su Shafa'atu tun d'azu. Ganin shi bai sa ta tashi zaune ba saï ma lumshe idanun ta da tayi tana jin wani irin kishin mijinta bata san a ina ya wuni ba, abincin wa yaci? Duk bata sani ba. Har ya k'araso bata tashi ba saï ya zauna a k'asan shima gami da tallabo kanta ya d'ora akan cinyar sa yace'' haba madam ko murnar gani na ba'ayi? Da alama bakiyi kewata ba kamar yanda nayi''. Farr da idanu tayi tace'' humm sannu da zuwa, a ina ka tsaya ne dan Allah? Har warhaka kuma na kira ka a waya baka d'aga ba, ina ka shiga?" '' Duk wannan questions d'in na ni kad'ai ne? Irin wannan tambayoyi da wanne zan fara?" '' Nidai ka amsa min tambaya na''. '' Ina asibiti ai kinsan dai bazan wuce can ba ko?" '' Humm Allah yasa, to wa ya baka abinci a can? Ba dai nurses ba?" '' Kamar kuwa kin sani akwai nurse Sadiya tanada kirki ita take kawo m.......'' bai k'arasa ba tayi wata irin zabura ta tashi zaune tace'' what? Kana nufin kullum ita ke kawo abinci?" '' Yes! Ai tana k'ok'ari sosai''. 'Bata fuska tayi tace'' daman nasan babu wani asibitin da ka wuni kace dai ga zance ya bayyana kanshi. Dariya yayi sosai na yanda take nuna kishin ta a fili, hakan da yayi saï ya k'ara tunzura ta har da hawaye wai ya maida ta mahaukaciya ma kenan. Baiyi magana bâ kawai d'aukan ta yayi ya nufi cikin d'akin ta, kan gado ya ajiye ta sannan ya koma ya rufe k'ofar ya dawo kan gadon ya hau yace'' madam kukan me kikeyi ne haka?" Baki ta buntsuro tace'' ba kai bane kaje kana cin abincin wata can daban''. Hancin ta yaja yace'' sorry da wasa nake miki fa, kina tunanin a ko'ina ne zanci abinci? Ai ni ban cin abincin wasu saï wa'yanda na sani, abinda baki sani ba inada kuku a can musamman dan yin abinci saboda an hanani cin abincin waje''. Tashi tayi zaune tace'' to meyasa aka hanaka cin abincin waje? Waye ya hanaka kuma?" '' Manta kawai zaki sani nan gaba a yanzu ba zaki gane ba''. Hawayen idanun ta ta goge shi kuma yarima dariya yayi mata yace'' uhmm kukan ya k'are yanzu hankalin ki ya kwanta ko?" '' Eh mana yaushe zan yarda wata tayi min k'wacen miji''. '' Kwantar da hankalin ki ba wannan a gaba na yanzu''. Zata sauka ya rik'e ta saï cewa tayi'' toilet zan shiga fa''. Sakin ta yayi ya koma ya kwanta yasa tafukan hannuwan sa k'asan kanshi yana kallon sama har da lumshe idanu alamar yana wani tunani. Sanyin ruwa yaji a fuskar shi wanda ya tabbatar masa cewa ta fito daga toilet d'in. Ido d'aya ya bud'e saï tayi murmushi tace'' tunanin me kakeyi ne?" '' Naki''. Ya fad'a a tak'aice yana mai jawota ta jikin sa saï tace'' wayyoo sorry bari in saka riga kaga fa tawul ne a jikina''. '' A dai-dai kenan, kinga ba saï nasha wahalar....'' bakin sa ta toshe da nata tana aika masa wani irin hot kisses tare da sabon salo na daban..... Sun d'auki tsawon lokaci a haka kafin ta cire bakin ta a nashi amma da k'yar. Su maigida yarima tuni idanu sun canza kala an zak'ulo masa fitina, cije lips yayi yana jan numfashi da k'yar. Dariyar mugunta FARHANAH tayi masa ta tashi da sauri ta nufi wardrobe dan saka riga. Zata bud'e wardrobe taji anyi sama da ita har saï da taji tsoro ta saki k'ara ya toshe mata baki da nashi. Da hannu d'aya ya kashe fitilar d'akin sannan ya lullu6e su da duvet, nauyi ya sakar mata cikin murya can k'asa yace'' wa kike ma dariya?'' '' Wayyoo husby ba da kai nake ba fa''. '' Uhmm zakiyi bayani yanzun nan''. Zatayi magana ya hanata ko da motsin kirki ne sakamakon wasu sak'onnin da ya fara aika mata wanda dukkan sassan jikin ta ke kar6ar su ba tare da gardama ba...... Sosai ya gwada k'warewar shi akan harkar duk iya rakin ta bai k'yaleta ba saï da ya gajiyar da ita likis tukun ya mirgina ya koma gefe. Iya wahala yau kam tasha ta duk ga6o6in jikin ta sun tashi a aiki saï kace yau ne ta fara sanin d'a namiji, yarima da gayya yayi mata wannan muguntar dan kawai tayi masa dariya shine ya rama ta hanyar da yasan ita d'in ba zata iya ramawa ba. Can zuwa wani lokaci ya mirgino inda take ya rungume ta cikin jikin sa ya rad'a mata cewa'' ko mû maimaita ne?" Kai ta shiga girgizawa alamar a,a saï kuma tace'' duk muguntar nan da kayi min bata ishe ka ba zaka ce a maimaita''. 'Kara shigewa yayi jikin ta hannayen sa yasa akan k'irjin ta yana shafawa can kuma yakai hannun sa d'ayan a marar ta yana shafawa yace'' Allah ka azurtani da baby''. Ko k'ala bata ce masa ba tana jin yanda yake wasa da hannuwan sa a jikin ta tayi banza dashi duk da dai k'irjin ta yana mata d'an zafi saboda yarima bai musu da wasa ba. Wata wawiyar ajiyar zuciya ta sauke jin bakin yarima kan k'irjin ta.... 'Kank'ame shi tayi tana fitar da numfashin wahala da k'yar ta iya fizgo magana tace'' please na tuba haka nan dan Allah bacci nakeji''. Bai mata magana bâ saï da ya gama sha'anin sa sannan ya rabu da ita. A tare sukayi wanka suka kwanta...asuba tagari sabbin masoya...... *Karku manta nace muku akwai chakwakiya nan gaba karku ga kamar ba komai hummm da SAURAN KUKA nan gaba zamu ga waye a BAYAN FAGE yake aikata musu hakan.....* *_'YAR MUTAN KAZAY CE👑_* 💥💥💥💥💥 *_'YAR GADARA_* 💥💥💥💥💥 *_NA_* *_A.MAIMOUNATH O.G.K_* _(Mahnoor)_ _Wattpad@maimounathog_ *💫DA BAZAR-MU WRITER'S ASS💫* *_~we are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are d best among all....DA BAZAR-MU MUKE TUN'KAHO.~_* *_DOMIN MAGANCE 'KURAJEN FUSKA👇_* *1-RUWAN KHAL* *2-ZUMA* *3-MAN ZAITUN* *_Zaki dora tukunya a wuta ki zuba ruwan khal da zuma da kuma man zaitun d'in idan yayi zafi saï ki k'ara d'an ruwa kad'an ki juya sosai sannan ki wanke fuskar ki ki sami auduga ki rink'a goga had'in a fuskar ki musamman wajen da yake da k'urajen, Allah yasa mu dace, Ameen!!!_* *NOTE: Ki guji yin amfani da hannun ki wajen fasa k'urajen fuskar ki, hakan yana k'ara yawan su da sanya fuskar ki ta k'ara ca6ewa, a kiyaye.* *_FOR YOU:_* *_DEAR_* *_YAYA HASSAN_* *_A.T.K_* *Page 121/125* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* ******Kwanci tashi asarar mai rai, lokaci saï tafiya yake kwanakin mû suna k'ara ragewa an samu sati uku sai FARHANAH ta fara langwa6ewa duk ta rasa me yake mata dad'i ga wata muguwar kasala dake addabar dukkan ga6o6in jikin ta har yakai idan ta kwanta a wuri bata son motsawa duk yarima yana lura da ita a zuciyar shi cewa yake yarinya kin kamu kawai. A wata rana ta laraba da dare tana kwance a d'aki ya shigo yana ganin ta ya saki 'yar dariya ya k'araso ya zauna a kusa da ita daman a k'asa take kwance wai k'asan yafi kan gadon dad'in kwanciya( humm yanzu kika san wannan kenan). Kallon ta yayi yace'' sarkin kwanciya wai ke baki gajiya da kwanciyar nan ne?" Kalar tausayi tayi tace'' Allah ni kaina ban son kwanciyar nan amma kasala take sani in kwanta dan Allah nemo min wani magani mana gaskiya ni na gaji haka nan''. Yarima bai shirya ba ya tuntsure da dariyar k'yeta har da rik'e ciki, ita dai FARHANAH kallon shi takeyi da mamaki ashe daman ya iya dariya haka? Fuska ta 6ata tace'' to meye abin dariya kuma? Allah yanzu haka ma wata cutar ce ta sameni ban sani ba''. Saï da ya tsagaita dariyar cikin dauriya yace'' sorry maman baby babu wata cutar da gareki saï alkhairi''. '' Wane irin alkhairi kuma a cutar kasala? Haka d'azu su Haulat ma da suka zo tayi ta min iskanci wai nayi haske kamar mai yaron ciki nace mata bani da komai har da gardama take min''. '' Kina mamakin maganar ta ne?" '' Ban gane me kake nufi ba". '' Ke yanzu baki jin wani sauyi a jikin ki?" '' Haba sauyi saï ya kasheni? Baka ganin yanda na koma duk na wani canza kamar bani ba''. '' To addu'a ta ce Allah ya kar6a''. '' Wace addu'a?" Hannu yakai ya shafo marar ta yace'' ba za'a rasa baby na a nan ba, duk alamu sun nuna ko da ban duba ki ba, but bari in duba ki in k'ara tabbatar da abinda nake zargi''. '' Wai kana nufin ciki gareni?" '' Yes! Ko baki so?" Tashi tayi zaune gami da fad'awa jikin sa tace'' ina so mana, ina son inga na baka babies kamar yanda kake son yara nima zan so in baka su husby''. Kanta ya shafa yace'' insha Allah zamu samesu dayawa ma kuwa kamar dozin''. Idanu ta zaro tace'' dozin kuma? Saï kace wata kaza?" '' Karki damu ai kina tare da gwarzon namiji sharp-shooter kuma ai kin gane ko''. Ya k'arashe yana mai d'aga mata gira. Gwajin fitsari yayi mata kuma ya tabbatar da abinda yake zaton. Yarima har da sujjada yana mai godewa Allah da wannan baiwar da yayi masa gashi dai yana bashi da wuri kawai Allah ne bai nufa sunzo duniya ba. Murna a wurin shi abin ba'a magana har da d'aukar ta yana juyi a tsakiyar d'akin itama dariyar murna takeyi har da hawayen ta tana mai addu'ar Allah yasa wannan d'in mai zama ne. Sabuwar kulawa da tarairaya a wurin yarima ji yake kamar shi zaiyi mata tafiyar k'afar ta ma, waya kuwa idan bai gida saï ya wuni yana kiran ta yace ya take? Bata jin komai? Ba wata matsala? Me take da buk'ata....da dai sauran maganganu irin na kulawa idan ya dawo gida kuwa haka zai kanainayeta ya hanata sakat wai kar tayi motsi da k'arfi saboda babyn sa ya kai ma ko aikin da zaiyi a system saï yaga tayi bacci sannan zaiyi. Wannan cikin yak'i sanar ma da kowa, babu wanda yasan da shi saï FAREEHA wacce yarima da kanshi ya kirata yake sanar mata FARHANAH na da juna biyu amma yana son ya zama secret tayi musu murna sosai tare da addu'ar Allah ya inganta. Cikin FARHANAH yanada wata biyu kwatsam wani bak'on al'amari yazo musu ba wani abu bane face zuwan Hajiya Halima tare da d'an ta Kasim. *WACECE HAJIYA HALIMA?* Hajiya Halima wacce aka fi sani da mama fulani tsohuwar matar sarki ce wacce ya saki a can baya, idan mai karatu bai manta ba na fad'e ta a farkon littafin, saboda mugun halin ta da kuma kama ta da akayi tana zuba magani a abinci shine mak'asudin rabuwar su da mai martaba kuma mummyn yarima SYDEEK tasha wahala sosai a zaman su da ita. Bata da mutunci bata da imani takan azabtar da duk wanda tayi niyya haka ta shimfid'a mulkin ta son rai har Allah yasa suka rabu. Shi kuma Kasim d'an ta ne a cewar ta d'an sarki ne amma abin ba haka yake ba domin kuwa da wani suka haifeshi hasali ma sarki bai sameta a budurwa ba duk da itace matar sa ta farko haka aka rufe maganar dan kar mutane su rink'a zund'e abin kunya ne ace cikin masarautar nan amarya bata kawo budurcin ta ba shiyasa ma aka rufe maganar....wannan kenan..... *Cigaban labarin....* Abin mamakin shine maimakon ayi ma mama fulani kora ko ma a kama ta a rufe a masarautar saboda irin abubuwan da tayi ta aikatawa a baya saï kawai sarki yace ya dawo da ita kuma 6angare na musamman aka ware mata part d'in ta wanda yasha kayan alatu da komai. Abin ya ba fada mamaki amma kuma babu damar yin magana kowa saï dai yabi d'an uwan sa da ido basu san meke damun sarki ba da har ya k'ara yarda da azzalumar matar nan ba. A zuba mata komai kan bayi da hadimai abin saï wanda ya gani, haka Kasim shima saï fiffik'a yake wai shi d'an sarki ne mai jiran gado, sarki saï wani rawar jiki yake a kansu abin fa ba na lafiya bane. Labari yaje ma mummy ne a lokacin da mai martaba ya sanar mata cewa yau fulani ce dashi saï mummy ta kalleshi tace'' ranka ya dad'e wace fulanin?" '' Fulani nawa kika sani? Hajiya Halima to, ta dawo tana cikin masarautar nan kuma na maido ta a matsayin matata''. Mummy duk da ta shiga rud'u amma saï ta tattaro duk wata nutsuwar ta tace'' masha Allah! Hakan yanada kyau, Allah ya tabbatar mana da zaman lafiya''. '' Ameen!". Ficewa yayi daga d'akin ita kuma ta bi bayanshi da idanu tana wani tunani a kanshi, anya kuwa sarki lafiyar shi k'alau? Fulani? Tabbas akwai wani abu, a banza fulani ba zata dawo ba kawai akwai shirin da tayi akai, ko ma meye to Allah ya fi ta. Yarima dai ko da yaji labarin bai wani damu ba amma ita FARHANAH duk ta damu kanta har yarima ya gane ya saka ta a gaba yake tambayar ta me yake damunta saï ta kalleshi tace'' babu abinda ke damuna saï dawowar fulani gashi ance har da d'an ta tazo wai tana son ya hau gadon mulki''. Murmushin yak'e yayi yace'' shine damuwar ki? Sarauta? Ai ni daman can sarauta bata birgeni ga hanya nan yayi bai dameni ba''. Hannuwan shi ta kama tace'' ya zaka ce haka bayan kai ne ya kamata ace ka hau gadon mulkin nan?" '' Mû canza wata hirar ban son kina tayar da hankalin ki akan wannan d'an abin, kinga ba ke kad'ai bace''. '' To shikenan Allah ya kyauta''. '' Ameen''. Ya amsa mata. Daga nan kuma suka canza hirar kamar yanda ya buk'ata, faranta ran juna sukayi suna manne da juna suke kamar kar su rabu. ***** ***** ***** Mama fulani tuni ta fara gudanar da mulkin ta wanda mutane suke kallon hakan da mulkin zalinci dan bata ganin kowa da mutunci tun can baya ma basu ji dad'in ta ba ko kad'an. Shimfid'a mulkin ta tayi tana cin zarafin duk wanda taga dama ga d'an ta Kasim shima d'in saï azabtar da bayi yake, masu hidimta musu ma basu tsira ba, gashi duk abinda sukeyi sarki yak'i yace ko uhumm kuma babu wanda ya isa yayi magana ma. Saboda yanda take wahalar da bayi da masu hidima wasu sun so guduwa amma babu hanya dan ko'ina a tsare yake babu wanda ya isa ya gudu. Mummy tun bata damuwa da lamarin har abin yazo ya fara damunta domin kuwa mai martaba ya canza ko magana tayi masa bai d'aukan hakan da wani muhimmanci tun tana bin shi da maganganu ko zai dawo cikin hankalin sa amma shiru wani lokacin maganar ma baiyi. Hakan ba yana nufin mai martaba yana mata wulak'anci bane a,a ko d'aya babu wannan a tsakanin su saï dai kawai ya canza ne yanda bai ganin laifin mama fulani duk da irin mulkin mallakar da take shimfid'awa a masarautar, zata zartar ma da mutum hukunci ko da baiyi komai ba tasa a azabtar da mutum, tana d'aukan bayin gidan tamkar wasu dabbobi tsananin wahala da k'unci duk suna fuskanta idan an gaya ma sarki saï yace tanada hurumin da zata azabtar da duk wanda taga dama matuk'ar yayi ba dai-dai ba, saï dai su ko basuyi komai ba ma azabar suke sha. Duk wannan abin dake faruwa yarima yana sane kallon kowa yakeyi shi dai bai son abinda zai 6ata ran mahaifiyar sa ko a wulak'anta ta to alhamdulillahi Allah bai sa hakan ta faru ba kuma bai fatan faruwar hakan. An samu wata d'aya da dawowar mama fulani kwatsam saï kuma wani abin ya sake faruwa, abin kuwa shine yanda yarima yaje wurin mai martaba amma saï ya canza masa fuska gaisuwar sa ma da k'yar ya amsa masa, ba yarima ba hatta fadawan sunyi matuk'ar yin mamakin wannan abu dan ba k'aramin abu ne ba ace yau sarki zai iya d'aure ma yarima fuska? Yarima da babu kamar shi a wajen sarki dan saboda shi kad'ai ne d'an da ya mallaka a duniya. Humm na manta ashe fa ance Kasim ma d'an sa ne, to kenan shima gadon mulkin yake jira? Jiki a sanyaye yarima ya wuce cikin gida yaje yace da mummy yana son yin magana da ita. Kallon matan tayi suka ce'' mun barku lafiya, a tashi lafiya''. Duk suka fice saï mummy ta dawo da kallon ta ga yarima tace'' me ya faru? Ya na ganka haka kamar baka da lafiya?" Yarima ya nisa yace'' mummy mai martaba ne....mai martaba ya canza min mummy bansan me nayi masa ba daga can nake na gaishe shi ko kallo na yak'i yi mummy meke faruwa ne a masarautar nan''. Yarima ya k'arashe maganar shi idanun sa na tsiyayar hawaye. Mummy tayi ajiyar zuciya tace'' daina kuka share hawayen ka, kuka ba shine mafita ba dan abban ka saï addu'a kawai ce zata k'wato shi daga hannun azzaluman nan''. Kai ya d'ago cikin sauri ya nanata'' azzalumai mummy? Su waye?" Mummy ta bud'e baki zatayi magana kenan suka jiyo takun mutum a cikin falon, kasancewar suna kusurwar falon a zaune shiyasa basu ga ko waye ba. Waiwayawa sukayi su gani ko waye ke zuwa garesu, mama fulani ce cikin shiga ta alfarma ansha wani dakakken lace mai shegen kyau da tsada, wuyanta, kunnenta, hannayen ta duk zagaye suke da zinare tun daga nesa take walwali kasancewar bata wani saka alk'yabba ba. Cikin takun isa da k'asaita ta tako har inda suke a yayin da hadiman ta ke biye a bayanta. Suna k'arasawa inda su mummy suke saï mama fulani ta kalli hadiman ta nan take jiki na 6ari suka bar wajen suna mai buga mata kirari ita kuma tana hura hanci da kumburin wuya ita gata matar sarki. Duk da su yarima a k'asa suke zaune bisa lallausan carpet ita kuwa fulani a kujera mai zaman mutum biyu ta zauna tare da d'ora k'afa d'aya bisa d'aya ta musu kallon sama da k'asa sai ta tuntsure da dariya kafin daga bisani ta tsagaita ta kalli mummy tace''....... *Tab me zata ce? Wannan matar daga gani zatayi iya shege😕😏* *Meke shirin faruwa ne tsakanin yarima da mai martaba?* *Waye duk mak'asudin wa'yannan abubuwan dake faruwa? Yarima zai cigaba da zaman masarautar nan kuwa?* *Me mama fulani tazo ta gaya musu?* *Amsar wa'yannan tambayoyin suna a page mai zuwa insha Allah* *To bari inyi nan kafin mama fulani tasa a k'wamusoni.....🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀* *_'YAR MUTAN KAZAY CE👑_* 💥💥💥💥💥 *_'YAR GADARA_* 💥💥💥💥💥 *_NA_* *_A.MAIMOUNATH O.G.K_* _(Mahnoor)_ _Wattpad@maimounathog_ *💫DA BAZAR-MU WRITER'S ASS💫* *_~we are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are d best among all....DA BAZAR-MU MUKE TUN'KAHO.~_* *_AMFANIN GANYEN NA'A-NA'A DA MAN TA👇👇👇👇👇_* *1- Idan kan mutum na ciwo a samu d'anyen ganyen NA'A-NA'A a shafa a kan insha Allah za'a dace.* *2-Amfani da NA'A-NA'A na magance fitowar k'urajen fuska, idan kuma ga masu k'urajen ne za'a shafa man NA'A-NA'A a wurin da k'urajen suke za'a samu s'aukin abin musamman ga masu OILY SKIN.* *3-Masu fama da matsananciyar mura su rink'a shan cokali 2×3 a wuni na MAN NA'A-NA'A insha Allah za'a dace.* *_Insha Allah zan cigaba da bayani akan ganyen NA'A-NA'A haka kuma masu fuska da k'uraje ina zuwa kanku akwai sauran bayanai wanda zaku bi dan magance wannan matsalar._* *~______________________________~* *_FOR YOU:_* *_DEAR_* *_YAYA HASSAN_* *_A.T.K_* *Page 126/130* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* ******Mama fulani ta kalli mummy tace'' sannun ki Hajiya Saudat uwargidan sarki Jafar, naga baki zo kinyi min sannu da zuwa ba shine nazo mu gaisa''. Mummy ta kalle ta tace'' fulani meyasa kike son shiga rayuwa ta ne? Me nayi miki ne haka? Dan Allah kiyi harkar ki inyi tawa ban son fitina kema kinsan haka''. Dariya fulani tayi tare da mik'ewa tsaye tace'' inaso ki rubuta ki ajiye a cikin kundin tarihi, saï na kassara rayuwar ke da d'an ki, a zaton ki zan bar miki wannan daular ne? Kinyi k'arya dan na dawo kuma sai na wulak'anta rayuwar k.....'' bata k'arasa ba yarima ya daka mata tsawa yace'' keee!! Karki sake kice zak....'' shima d'in bai kai ga idasawa ba mummy ta d'auke shi da mari ya dafe kunci yana kallon ta idanun sa sun kad'a sunyi jawur kamar gauta dan tsananin 6acin rai. Mummy tace'' yaushe ka zama haka? Irin tarbiyyar da na baka kenan? Yaushe ne ka canza halin ka?'' Cikin rawar murya yace'' mummy amma kina k....'' katse shi tayi da cewa'' amma me? Rashin kunya zakayi mata? Itama uwa ce a gareka dan haka kar in sake jin wata magana ta fito daga bakin ka, nice ya kamata inyi da ita ba kai ba''. Fulani tace'' hehehe!! Saudat kinyi kad'an kice zaki kara dani, dan ni nayi miki zarra nesa ba kusa ba, ba ma zaki gane ke banza bace a gidan nan saï nan gaba''. Kafin mummy ta bata amsa yarima yayi saurin barin wurin zuciyar sa na tafarfasa dan in ya cigaba da tsayiwa a wurin zai iya sa6a maganar mahaifiyar shi. Bayan ya fice mummy ta tako inda fulani take tace'' fulani da da yanzu ba d'aya bane, tabbas a da kin wahalar da rayuwa ta amma yanzu ba zaki iya yin komai a kaina ba dan na rigaki nace Allah, ni ban iya fad'a da masifa ba, naga ke kuma haushin karnuka kawai kika iya so idan kin gama zaki iya ficewa''. Fulani zatayi magana mummy ta haye upstairs ko waiwayen ta batayi ba. Fulani ta cije baki tace'' Saudat wallahi dani kike zancen zaki ga abinda zanyi a masarautar nan''. Mummy dai tana jin ta ta k'arasa hayewa ta shige bedroom d'in ta. Yarima kuwa saï da ya tattaro duk wata sauran nutsuwar sa tukun ya shiga inda FARHANAH take. Tana ganin sa ma tasan da matsala saboda idanun sa kawai zaka kalla kasan da wani abu. Kallon ta yayi yace'' muje bedroom d'in ki''. Tashi tayi suka shiga d'aki daman a falon sama take a kwance su Shafa'atu kuma suna k'asa suna 'yan aikace-aikace. Suna shiga yasa ma d'akin key suka je suka zauna a bakin gado FARHANAH ta kasa hak'uri tace'' wai lafiya kuwa husby?" '' Ina son in tambayeki tsakanin ki da Allah, zaki iya zama dani ko da bani da komai bani da kowa? Ko da kowa ya gujeni zaki iya zama dani?" '' To wai me ya kawo duk wannan maganganun? Meke faruwa ne dan Allah ka sakani a cikin duhu fa". '' Kedai ki amsa min''. Sai da ta kwanta a jikin sa tace'' zan iya zama da kai ko da ace baka da komai da kowa, zan zauna da kai ko da ace baka da abin da zaka ciyar dani, ba wani abin ka nakeso ba ni kai nakeso kai ma kasan haka dan Allah ka daina shakku akan soyayyar da nake maka''. '' Ina son mu bar garin nan ne''. Cikin sauri ta d'ago kanta ta kalleshi tace'' akan me? Meyasa zamu bar gari?" '' Kawai so nake mû bar masarautar nan da kuma garin na wani lokaci, gobe zamu tafi da naso muje Sudan but bai yiwa saboda yanayin da kike ciki zamu je Abuja saï dai ban son kowa na masarautar nan ya sani''. Kuka ta saka masa tace'' ashe daman ba son gaskiya kake min ba, ashe ba zaka iya fad'a min matsalar ka ba har kana kirarin barin mahaifar ka saboda matsala amma ka kasa fad'a min to shikenan nagode''. Ta k'arashe tana mai tashi daga jikin sa zata sauka k'asa ya kamo ta saï cewa tayi'' ka rabu dani''. '' Kiyi hak'uri ki daina kukan nan please kinga zai iya cutar abinda ke cikin ki da ke kanki''. Kallon sa tayi da jajayen idanun ta tace'' abinda yake cikina dai, abinda ke cikina shine kawai kafi damuwa dashi dan baka damu dani ba da ka damu da baka 6oye min abinda ke faruwa ba, dan haka ka k'yaleni kawai''. Can nesa da gadon taje ta zauna a k'asa ta shiga rera kuka har hakan ya jawo mata sark'ewar wani abu ta fara tari daga nan kuma saï ta gudu toilet ta shiga kela amai da sauri yarima ya iske ta cikin bathroom d'in, yana rik'e da ita saï sannu yake mata har ta gama suka fito da k'yar take maida numfashi tsabar wahala. Bayan sun zauna yace'' kin gani abinda nake gudu dan Allah ki kwantar da hankalin ki''. '' Hankali na bazai ta6a kwanciya ba matuk'ar ina ganin ka cikin wannan halin''. '' Zakiyi mamaki idan nace miki yau mai martaba ya juya min baya, daga wajen sa nake da k'yar ya amsa gaisuwa ta na rasa me nayi ma abba da har ya tsaneni rana kai tsaka, shiyasa naga bazan iya zama ina kallon hakan ba gara dai in d'anyi nisa kad'an dashi har Allah yasa ya dawo yanda yake a da''. '' Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Yanzu abba ne zai tsaneka? Ta yaya hakan zai faru?" Murmushin yak'e yayi yace'' ba komai karki damu zai canza nasan dai na wani lokaci, kinsan Allah yakan jarraba bawan sa ta kowace irin hanya, ni kuma ga irin tawa jarrabawar mahaifina bai son ma gani na''. '' To me mummy tace? Ko bata sani ba?" '' Ta sani daga can ma nake itama mama fulani ta k'ara 6ata min rai maganganu na 6atanci zallah takeyi akan mahaifiya ta bazan jure irin haka ba''. FARHANAH ta yamutsa fuska tace'' nifa wannan mama fulanin ban yadda da ita ba, akwai wani abu a tattare da dawowar ta, kaga daga zuwan ta duk tsarin masarautar nan ya canza saï wulak'anta mutane sukeyi ita da d'anta''. '' Rabu dasu duniya ce Allah ya fi su, anjima bayan la'asar zanzo da kaina zan had'a miki kayan da zaki tafi dashi sauran kayan buk'ata zamu siye a can''. '' To wai hostel zaka kama a can d'in? Ya maganar aikin ka? Kasan fa sunada buk'atar ka a asibiti''. Murmushi yayi ya shafi fuskar ta yace'' munada gida a can, maganar aiki zan damk'a komai a hannun doctor, ni hakan ma zai bani damar yin honeymoon d'ina daman banyi ba''. Hararen wasa tayi masa gami da ture hannun da dake yawo akan cikin ta tace'' kaji ka da wani zance wai honeymoon, ko honeymoon d'in yaushe kuma?" '' Ban more angwanci na ba mana, kedai kawai ki shirya d'aukan larura ta''. Ya fad'a yana mai d'aga mata gira d'aya. '' Uhmm please ka daina wani raha muna cikin wani hali ya kamata fa muyi wani abu ko in sanar ma da daddy?" Nisawa yayi yace'' no! Ba saï kin fad'a masa ba, kawai abinda nace d'in nan shine solution, mû bar garin nan na wani lokaci yanda zamu samu damar yin rayuwar mû inda babu takurawa bare sa ido, kinsan komai na masarauta bai 6oyuwa ai kema kinsan haka idan kin manta in tuna miki''. Ya idasa cike da zolaya. Nan take ta tuno abinda yake ma saï kawai ta tsinci kanta da jin kunyar shi ta sunne kai tana murmushi saï ya jawota jikinsa ya rad'a mata cewa'' kin tuna? Ko dai in tuna miki?" Hannu tasa taja gashin k'irjin sa har saï da yayi 'yar k'ara yace'' yarinya duk taraki nakeyi saï na fanshe duk abinda kikayi min''. '' To ni me nayi maka? Daga shafar k'irjin ka shine laifi?" '' Uhmm kika shafa ko kikeso ki nakasa ni in munje can in kasa aiwatar da komai''. Ohh ni yarima ashe shima kunyar bata wani ishe shi ba? Ko kad'an ma kai bashi da ita tun can daman dan basuyi sabo bane. Tana cikin tunanin taji hannun sa cikin rigar ta, saurin rik'e masa hannun tayi tare da marairaicewa tace'' me kake shirin yi ne? Kana kallon lokaci kuwa?" Kwanciyar sa ya gyara akan cinyar ta har da lumshe idanu yace'' uhmm yarinya ba wani wayo da zakiyi min saï na rama abinda kikayi min''. Yarima ya fad'a yana shafar marar ta, ita kuma ya sanya ta a wani hali saboda numfashin shi dake sauka bisa kan cibiyar ta. Ana haka suka ji an doka kiran sallah nan take FARHANAH a hankali ta furta'' alhamdulillah!". Ashe muryar ta ta fito saï ji tayi yarima yace'' baki dai tsira ba dan akwai dare''. Tashi yayi ya shiga toilet d'in ta ya d'auro alwala ya fice da sauri. Itama d'in toilet ta tafi amma saï da tayi wanka tayi alwala saboda zafin da takeji wanda ta rasa dalilin haka, gashi dai ba wani zafi akeyi ba kuma ga A/C a d'akin amma duk a banza. Bayan ta gama sallah tana zaune akan darduma tana 'yan addu'o'in ta Shafa'atu ta shigo dan sanar mata abinci na jiran ta. Kallon ta FARHANAH tayi ta mata alamu da hannu akan tana zuwa dan duk da batayi magana bâ tasan abinda ya kawo ta kenan. Shafa'atu ta fice waje, ita kuma ta shafa fatiha ta tashi tayi simple makeup daman abaya ce a jikinta saï kawai ta saka hijab ta fita. A falon k'asa yau taci abinci, A yayin da take ci ita kuma Shafa tayi sama dan gyara d'akin. Bayan la'asar FARHANAH taje cikin gida wajen mummy dan gaishe ta sannan ta gaya mata abinda yarima yake shirin yi dan ta tabbata mummy bata san da wannan zancen ba. Iso akayi mata ta shiga ciki bayan ta gaishe da mummyn su kuma hadiman ta suka gaida ita FARHANAH. Shiru FARHANAH tayi gali da sunkuyar da kanta k'asa bata san ta ina zata fara ma mummy bayani ba. Mummy da take lura da ita sai ta kalli matan tace ina zuwa sai ta tashi ta kama hannun FARHANAH ta mik'ar da ita suka haura saman d'akin ta. Suna shiga kai tsaye bakin gadon mummy suka nufa amma suna zuwa FARHANAH ta zame ta zauna a k'asa. Mummy ta kalleta tace'' 'yata taso ki hau bakin gadon bai komai magana nakeso muyi''. Tashi tayi cikin jin nauyin ta ta zauna a bakin gadon sai mummy tace'' 'yata d'ago kanki ki kalleni, ni mahaifiyar ki ce duk abinda ke damunki ki gaya min zanyi miki maganin abin in dai har bai fi k'arfi na ba kinji''. 'Dagowa tayi ta kalli mummy tayi d'an murmushin yak'e ba tare da tace komai ba, sai mummy ta kama hannayen ta tana mai k'are mata kallo, sai yanzu ne taga yanda ta canza sosai tayi wani haske fatar ta tayi fresh duk wasu alamu na mai juna biyu sun bayyana a tattare da ita. Mummy tayi murmushi tace'' 'yata baki da lafiya ne naga duk kinyi fari kuma kin d'an rame? Ko dai yarima ne yake miki abinda baki so?" FARHANAH ta girgiza mata kai alamar a,a, sai mummy tace'' to fad'a min damuwar ki matuk'ar kin d'aukeni a matsayin mum d'in ki''. Ta d'aure da ta jijiyoyin jikinta ya ta iya dole ta gaya mata tunda daman abinda ya kawo ta kenan. Cikin sanyin murya tace'' mum yarima ne d'azu yaje yace min wai in shirya kayana zamu bar garin akan wani d'an dalili shine nace bari inzo in gaya miki ko kunsan da tafiyar". Mummy ta nisa tace'' a,a ko d'aya bai gaya min ba amma bari in kira shi inji akan me zai ce ku bar gari''. A wannan lokacin kuwa yarima yana can tare da doctor mataimakin sa yana nuna masa duk wasu mahimman abubuwan da za'a nema a asibitin yace masa zaiyi wata 'yar tafiya ne insha Allah bazai jima ba. Nurse ce tayi knocking ta shigo ta gaishe su sannan tace'' ranka ya dad'e kayi bak'o''. Sanin ko waye yasa yace da ita tace masa ya shigo. Mahmud ne abokinsa ya shigo sallama d'auke a bakinsa suka amsa yaje ya ba kowa hannu suka gaisa yarima ya nuna masa kujera ya zauna sai yarima ya kalli doctor'n yace'' excuses me d'an bamu waje ina zuwa zan k'arasa maka bayanin komai''. '' Ok ba damuwa na barku lafiya''. Ya fice ya barsu a nan Mahmud ya kalli yarima yace'' wai mutumena ya akayi ne naga ka kirani lafiya kuwa?" Hararen sa yarima yayi yace'' wato kenan bazan iya kiran ka ba sai da wani dalili ko?" '' A,a wannan kiran kawai yabi daban da na sauran''. '' Kamar ka sani wallahi akwai 'yar matsala ko ma ince maka babba''. '' Subhanallahi! Meke faruwa?" Nan yarima ya zayyane mishi komai ya kuma fad'a masa yau da dare gidan shi zasu zo su kwana jirgin k'arfe 8am zasu bi dan zuwa Abuja dan tuni yayi booking iirgi, kuma ya sanar masa da cewa bai son mutane su sani shiyasa ma zasuyi fitar dare a masarautar saboda idanun mutane. Mahmud ya tausaya ma yarima sosai kan wannan sabon al'amarin dan juya bayan mahaifi ba abu ne mai sauk'i ba fatan shi Allah ya kawo musu d'auki akan lamarin ya kuma daidaita tsakanin su dan yasan idan ba wani abu ne ya faru ba da wuya ace mai martaba ya juya ma yarima SYDEEK baya, d'an da ake nuna masa gata fiye da kowa. Kai duk wanda yake bayan wannan lamarin Allah bazai ta6a barin sa ba dan akwai nau'in zalunci a ciki. Yana cigaba da gaya masa yanda abin zai tafi kan tsari sai mummy ta kira shi a waya akan lallai ko me yakeyi ya bari yazo gida, ya tambayeta lafiya kuwa? Tace masa lafiya yazo dai tana son ganin sa ne. Kallon Mahmud yayi yace'' mummy ke nema na gashi ban gama abinda nazo yi ba asibitin but zanje gida dole sai na dawo asibitin kai kuma zan kira ka''. Shafar gemun sa yayi yace'' a gaskiya nima fa ya kamata in shigo daga ciki''. Mahmud ne yayi wannan maganar. Yarima ya kalleshi yace'' ka shigo ina?" Hararen sa Mahmud yayi yace'' nima in shiga sahun ku mana''. Dariya yarima yayi kana yace'' a,a zauna idan na haihu zan baka 'yar ka aura''. '' Kuji mugu duk ina zaune? Lallai baka sona, to kwanan nan zan 6ullo nima maybe ma matata ta rigayi taka haihuwa raggo kawai''. '' Kaii!! Waye raggon? Humm lallai to bari kaji my FARHA na d'auke da baby na kawai na 6oye hakan ne saboda abubuwan dake faruwa a cikin masarautar''. '' Hakane kuma to Allah ya bar muku wannan ya inganta shi''. '' Ameen! Friend thank you''. Daga nan suka fita ya kulle office d'in ya gaya doctor cewar ana neman sa ne a gida zai dawo. Fatan dawowa lafiya yayi mishi suka fice shi da Mahmud suna 'yar hirar su irin ta abokai. Ko da yaje gida direct can wajen mummy ya nufa dan jin abinda ke faruwa. Ya iske su ita da FARHANAH a yayin da ita FARHANAH ke zaune kusa da mummy ta tirke ta saï taci ferfesun kayan ciki wanda yaji had'i sosai na musamman kuma, gashi dai ya had'u amma FARHANAH ta kasa cin abin kirki saboda cikinta da takejin ya cunkushe mata ta kasa gane mishi. Da sallamar ya shigo suka amsa mishi ya nufi inda suke, daga zuwan sa kawai ya zauna tare da saka hannu cikin plate d'in ferfesun yana cewa'' mummy barka da yamma''. Hararen shi tayi tace'' rik'e gaisuwar ka ban so, ya haka zaka wani saka hannu ba'a maka bismillah ba?" '' Mummy ayi hak'uri yunwa nakeji ne kuma naga ita tana ci a yangance shiyasa zan kama mata, to wai ma me nayi ne mummy ake cewa ba'a son gaisuwa ta?" '' Baka ma san me kayi ba ko?" '' A,a mum a gaya min''. Yarima ya fad'a yana kai ferfesun bakin sa. '' Cire hannun ka a ciki ga abinci can kaje kaci wannan nata ne nasa akayi mata''. Kallon mummy yarima yayi yace'' ah lallai kice wannan na musamman ne, to ko dai wani abu aka saka ba'a son in sani?" '' Kai ni ban son shirme ka tashi a nan nace''. Hannun sa ya cire yana tand'ewa yace'' amma dai gaskiya wannan ferfesu yaji had'i''. Babu wanda yace dashi komai sai yaje kusan mum ya rad'a mata cewa'' mum a had'a mata kayayyaki sosai kinsan honeymoon zamuje''. Bige shi mum tayi tace'' oh ni hajiya Saudat yaushe ka zama marar kunya haka? To ni bâ abinda yasa na kira ka kenan ba, je kaci abincin magana zamuyi''. Yamutsa fuska yayi yace'' na k'oshi ma''. '' Me kaci ne da har ka k'oshi? Wuce kaci abinci nace''. Sum-sum ya nufi dinning area inda yake tsab a shirye tank'amemen wuri ne abin sha'awa ga cima sai wanda ka za6a. Bayan ya gama ne mum ta tusa su a gaba suka nufi sama. Suna zama mum ta kalleshi tace'' naji abinda kake shirin aikatawa ko gaya min bakayi ba kana ganin ka kyauta kenan ka tsallake garin nan ba tare da na sani ba?" Marairaice fuska yayi yace'' mummy bâ haka bane ai kinsan dole ne ma ki sani wallahi nayi niyyar fad'a miki shine ita ta rigani tazo ta fad'a''. Ya k'arashe maganar yana mai hararen FARHANAH, itama ta rama har da murgud'a mishi baki, sai yace'' mummy kin gani fa harara ta takeyi har da murgud'a min baki''. '' Tayi ai ramawa tayi kai ma ba hararen ta kayi ba? Ko ka zata ban gani ba?" FARHANAH tayi murmushi gami da yi masa gwalo. '' Ni kike ma gwalo kuma? Humm yarinya tara ki nakeyi ai na gaya miki bari ki shigo hannu''. Gyaran murya mummy tayi tace'' duk ka bar wannan maganar ni ban amince da tafiyar nan ba gara ma ka fasa''. '' Na shiga uku mum rufa min asiri har nayi booking fa, dan Allah kiyi hak'uri ina son barin wannan garin ne dan in samu nutsuwa''. '' To wai a wane dalili ne ma zai sa ka bar mahaifarka kaje wani wajen ka zauna? Aikin naka fa?" '' Mummy kinfi kowa sanin halin da ake ciki bazan iya jure ganin fushin abba a kaina ba, inajin kamar wani abin nayi masa''. '' Babu abinda kayi masa abban ku ya canza hali tun zuwan fulani kuma addu'a itace kawai mafita ba wai ka bar gari ba''. '' Inada hik'imar yin hakan mum kedai kiyi ta mana addu'a ina so bayan magrib inje wajen malam ma''. '' Wai matar taka da yaron ciki zaka d'auke ta kayi tafiya da ita?" Saurin d'agowa sukayi duka dan mamakin maganar da tayi. Murmushin manya tayi tace'' kuna mamaki ne ya akayi na sani ko?" '' Eh wallahi mum dan ban sanar ma da kowa ba''. '' Uhmm to ai ka kyauta kuma gashi na sani d'in, Allah dai ya inganta, babu wata matsala a tafiyar taku?" '' Babu insha Allah''. '' To ya kamata idan zakaje gidan malam ku tafi tare ka kaita gidan su tayi musu sallama''. '' To shikenan mum nagode da kika amince, yanzu dai asibiti zan koma akwai wasu abubuwa da zan ba doctor Sadik daman ina can naga kiran ki''. '' Kana ganin zai iya tafiyar da asibitin nan? Kar fa abubuwa su lalace kuma". '' Insha Allah ba zasu lalace ba ai doctor yana k'ok'ari wajen yin aikin sa kuma su ma sauran ma'aikatan duk babu mai lalaci tunda ana biyan su yadda ya kamata akan lokaci kuma''. '' Allah ya taimaka yayi jagora''. Duk suka amsa da ameen, nan yayi musu sallama ya fice. Yarima sun gama tsara komai a asibiti ya dawo ya shirya suka fice gidan su FARHANAH anyi mishi tarba ta kirki daga nan yace zaije ya dawo sai ya d'auke ta. Ya fice dan zuwa wurin malam, ya iske shi a inda ya zayyane ma malam komai da yake faruwa tunda idan baku manta ba na sanar daku cewa malam amintaccen sarki ne dan haka duk damuwar su ya sani. Shawarwari sosai malam ya bashi tare da k'ara mishi wasu addu'o'in yace dashi su dage da addu'a dan wannan lamarin akwai sihiri a cikin sa. Goma ta arziki yarima yayi ma malam sannan sukayi sallama ya tafi. Gidan su FARHANAH yaje ya d'auke ta bayan sunyi musu sallama akan gobe zasu wuce Abuja amma basu ce da wata matsalar ba. Sai da dare yayi kowa ya nemi wurin da zai ajiye hak'ark'arin sa dan hutawa kunsan ance dare mahutar bawa to haka abin yake, yarima yana bisan barandar d'akin sa yana hangen ko'ina dan haka sai da yaga k'afa ta d'auke ya sauka ya d'auki kayan sa yaje ya saka a mota yaje 6angaren FARHANAH har ta fara bacci ma ya tashe ta akan dole dan yasan illar yin hakan ga mata masu juna biyu. Sun shirya kayan su da duk abinda zasu buk'ata sannan suka fice daga masarautar bayan yarima ma yaja kunnen sarkin k'ofa yace kar ya sake yaji wata magana a bakin sa in ba haka ba zai koreshi, a nan yayi masa alk'awarin insha Allah bazai fad'awa kowa ba ya kuma yi musu fatan alkhairi suka fice. Kai tsaye unguwar su Mahmud suka nufa inda daman tuni yana can yana jiran k'arasowar su. Horn yarima yayi wasu 'yan mintuna akazo aka bud'e ashe Mahmud d'in ne da kanshi ma dan yanzu bai da gate-man yace sai yayi aure tukun. Yarima ya danna kan motar cikin gidan ya nufi rumfar ajiye motoci yayi parking suka fito a dai-dai lokacin Mahmud ya k'araso inda suke yana musu sannu da zuwa. Ya kalli FARHANAH da duk tayi laushi yace'' gimbiyar mu ranki shi dad'e anzo lafiya?" '' Lafiya lau al-hamdulillah! Ina wuni''. '' Lafiya k'alau, kuzo mu shiga daga ciki''. '' Wato ni ba za'a gaishe ni ba ko?'' Ya kalli FARHANAH yace'' duk kece sila, kece kika amshe min aboki daman mum ta yadani tuni''. 'Yar dariya aka saka kafin daga bisani su wuce ciki. Ba laifi gidan ya tsaru shima dan yanada girman shi ga flowers ko'ina abin sha'awa. Ko a cikin falon ma ko'ina fes kamar da mace a gidan nan ma sai da yarima yayi masa shak'iyanci yana ce masa gida gashi fes sai dai bai cika gida ba tunda ba iyali, shi kuma Mahmud yace'' kwantar da hankalin ka friend kafin ku dawo nayi sadaki kuma zakuyi mamaki dan surprising d'in ku zanyi ku duka har da madam''. '' Humm Allah yasa to''. '' Ameen ya Allah, yanzu me kuke da buk'ata? akwai komai sai d'an abinda ba'a rasa ba''. '' Kaga mu nan a k'oshe muke kawai a bamu d'aki madam bacci takeji''. 'Dakin da zasu kwanta ya nuna musu gami da yi musu asuba tagari shima ya wuce wani d'akin wanda yake d'an nesa da nasu. Washe gari da wuri suka tashi tunda jirgin safe ne zasu bi, breakfast sukayi a gidan sannan suka fita shi Mahmud shine yake driving d'in su amma a motar sa dan yarima yace masa wannan motar da suka zo da ita bai son a ganta a waje tunda an san motocin gidan su, kuma ya bashi key d'in motar ya ajiye a wurin sa har zuwa ranar da zasu dawo. Da zuwan su ba jimawa aka fara kiran fasinjoji inda aka zo kan su yarima nan sukayi musabaha da Mahmud sannan yayi musu fatan sauka lafiya suka tafi yana d'aga musu hannu. Ana gama kira jirgin ya tashi, wani abu na yarima a lokacin da jirgin zai d'aga sai da ya dafe cikin FARHANAH wai kar ya girgiza, ita dai FARHANAH murmushi tayi masa. Sai da jirgin ya saitu sosai a sararin samaniya tukun ya d'auke hannun sa a inda ita kuma ta jinginu da kafad'ar sa tana mai lumshe idanu alamar bacci...... *Muna yi muku fatan sauka lafiya yarima da FARHANAH, Allah kuma ya daidaita tsakanin ka da mahaifin ka🤲* *Kwana biyu nayi busy ne shiyasa kuka jini shiru kuma gashi wasun ku basa comments, amma karku damu ana zuwa wurin....🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀* *_'YAR MUTAN KAZAY CE👑_* 💥💥💥💥💥 *_'YAR GADARA_* 💥💥💥💥💥 *_NA_* *_A.MAIMOUNATH O.G.K_* _(Mahnoor)_ _Wattpad@maimounathog_ *💫DA BAZAR-MU WRITER'S ASS💫* *_~we are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are d best among all....DA BAZAR-MU MUKE TUN'KAHO.~_* *_Albishirin ku mata masu aji, 'yar uwa matso kiji👂kin dad'e kina neman sana'ar yi amma baki san ta inda zaki fara ba? To ga dama ta samu campanyn ORIFLAME yazo mana da mayuka ingantattu da sauran abubuwan buk'ata da duk abinda ya shafi fata, uwargida da amarya ki siye man ORIFLAME kiga yanda zaki canza fatarki tayi shinning har oga ya kasa ganeki😅😘 idan kuna buk'atar yin register a tuntub'i wannan no d'in👉🏻👉🏻👉🏻 +227-88-05-90-26, karki sa sanyi a lamarin domin kuwa akwai garabasa a wannan watan ga duk wacce tayi siyayya a campanyn ORIFLAME, ORIFLAME yace kuyi kyau, kuyi kud'i, kuji dad'in rayuwa👌'yar uwa meye matsalar ki? Karyewar gashi ne💇🏿 akwai mafita ki nemi(LOVE NATURE) Kisha mamaki, idan ma laushin fata kike nema to ki nemi(LOVING CARE) 'yar uwa zaki ga yanda oga zai rikice😆😂😉, ina masu fama da infection, warin gaba? Duk abin yazo da sauk'i ku nemi(FEMINELLE) shine kankat dan duk wata matsalar gaba kinyi bye-bye da ita, a siye a gwada 'yar uwa sai na jiku....💃💃💃💃💃💃_* *_NA'A-NA'A_* *4-Ga mata masu ciwon mara na al'ada a nemi ganyen NA'A-NA'A a tafasa ana sha za'a dace.* *5-Ana had'a NA'A-NA'A sa zuma a rinka sha domin tana k'arfafa jiki da saka kuzari, kuma yana saka lafiyar hanta ta rinka aiki da kyau.* *^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^* *_FOR YOU:_* *_DEAR_* *_YAYA HASSAN_* *_A.T.K_* *Page 131/135* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* ******Su gimbiya FARHANAH an samu jikin miji anyi lub sai kwasar bacci akeyi shi kuma yana ta aikin kallon fuskar ta ko ya ta motsa sai ya gyara mata kwanciya wasu na kallon su cike da sha'awa na yanda yake tarairayar matar sa. Sai da jirgin su ya sauka a garin Abuja sannan yarima yayi kissing kuncin ta a nan ne ta bud'e idanu da k'yar yau kam tasha bacci ba laifi. Kallon shi tayi sai yayi mata murmushi tare da kama karan hancin ta yace'' sarkin bacci to munzo tashi ki wartsake mu fita''. Tashi tayi zaune gami da yin mik'a, Subhanallahi! Ai yanayin yanda tayi mik'ar ne ma wai ya tafi da yarima sai ya sunkuyo dai-dai kunnen ta yace'' ke rufa min asiri irin wannan mik'ar ai sai ki jawo inyi abin kunya a gaban jama'a''. Kallon rashin fahimta tayi masa ya gane sai yace'' tashi mu fita nasan dai driver yana jiran mu idan munje gida zaki gane abinda nake nufi''. A tare suka fita yana rik'e da hand-bad d'in ta da hannu d'aya, d'ayan hannun sa kuma yana sak'ale da nata. Ikon Allah irin wannan soyayya daga baya aka fara amma har sunfi wasu masoyan usulin ma. Tuni an fiddo kaya kuma driver har yazo dan ya jima ma a airport d'in yana jiran su. Yana ganin yarima ya taho da sauri ya kawo gaisuwa cikin girmamawa har da sunne kai yake daga nan suka gaisa da yariman sosai dan akwai fahimtar juna a tsakanin su. Ya gaida FARHANAH itama ta amsa masa fuska a sake sai yarima ya maka mata harara wai nan kishi yakeyi abin sai ya bata dariya ma. Kayan su Ado driver ya saka a bayan mota sannan ya jasu suka nufi unguwar asokoro inda nan ne gidan nasu yake. Kasancewar asokoro unguwa ce ta masu kud'i dan haka ba zaka ga wani k'aramin gini ba sai tsararru da kuma yanda unguwar take a nutse babu irin surutu ko wani abin daban irin na wasu unguwannin. Gidan su yarima ya tsaru, daga bakin gate zaka san ba k'aramin kud'i aka kashe a nan ba, wani kallon ma sai an shiga ciki. Gate-man ya wangame musu k'ofar sakamakon horn da yaji nan take driver ya shiga daga ciki, direct parking space yaje yayi parking sannan ya fito da sauri ya bud'e ma yarima ya fito zaije ya bud'e ma FARHANAH saï yarima ya dakatar dashi yace'' Ado barshi wannan aiki na ne karka damu kawai kai dai bud'e booth ka fiddo kaya''. '' An gama ranka ya dad'e''. Cewar Ado yana mai 6arin jiki. Haka shima Isiya mai gadi yazo yayi musu sannu da zuwa. Tsarin gidan yayi k'warai ya birge FARHANAH ko'ina a tsare kamar a turai abin dai gwanin sha'awa. Suna tafe hannayen su sark'e da na juna ya kalleta yace'' duk kin gaji ko?" Kai ta d'aga mishi tace'' wallahi kuwa ji nake kamar a k'afa nazo nan d'in''. Yana mata dariya har suka k'arasa bakin k'ofar shiga falon da yake akwai 'yar tazara a tsakani kasancewar gidan ba k'arami bane. Ko da suka shiga ma wata duniyar ce daban saboda tsaruwar da falon yayi ga labulayen d'akin maroon ne masu 'yar walk'iya a jiki tsab komai fes kamar da mace a gidan. A nan falon ta zube a k'asa bisa lallausan carpet d'in d'akin yace'' ya haka? Wai a nan zaki zauna ne?" '' To ina kakeso in tafi? Allah na gaji bari in huta sai muje''. Zama yayi kafin yayi magana ado driver yayi sallama a bakin k'ofar yarima yace ya shigo. Kayan su ne yake shigowa dasu har ya gama sai yarima yace masa'' Ado please zo kayi mana take-away a inda nakeyin nan kaji?" '' To maigida insha Allah''. Ya amshi kud'in ya fice sai ya dawo da kallon sa wajen ta yace'' to tashi muje kiyi wanka kafin a kawo abinci kinga gidan babu abinci saboda na sallami kukun tun wani zuwan da nayi''. '' Ai ni mamakin tsaftar gidan da yanda yake a tsare nakeyi''. '' Why?'' yarima ya tambaye ta. '' To gida sai kace da mace a ciki ko'ina fes anyi mooping anyi komai ba wani datti''. '' Gyara shi sukeyi ai aikin su ne tunda biyan su nake kinga kuwa dole ne suyi aikin kud'in su''. '' Uhmm lallai yayi kyau''. Shi ya kama ta suka haura sama dan kimtsawa. FARHANAH tana yin wanka ta 6ingire bacci yarima kuwa ya sauka k'asa a lokacin shi kuma Ado yazo ya kawo aiken da akayi mishi. Bayan ya fita ne yarima ya ciro wayar sa a aljihu ya kira mummy ya sanar mata sun sauka lafiya ta tambaya da 'yar ta FARHANAH saï yace'' mum wai bacci fa tayi ko abinci bata tsaya ci ba ta gaji ne''. '' Ah to tanada gaskiya ta huta kasan mai juna biyu sai gajiya da wuri dan haka dan Allah kabi yarinyar nan a hankali naga yanda kake 6arin jiki ai ka gane nufi na ko?" Kashe wayar yayi yana murmushi ba tare da ya iya bata amsar ba saboda kunyar da mum ta saka shi. Kai ya sosa shi kad'ai yana wani irin shu'umin murmushi wanda na kasa gane ko na miye. Ya kira Mahmud ma ya gaya masa shima d'in sai da yayi masa shak'iyanci suka yi sallama. 'Kyaleta yayi saï da aka kira sallah'r azhar tukun ya tashe ta saï mik'a takeyi idanu duk sun k'ank'ance mata yace'' wannan bacci ko isar ki ma bai yi?" '' Haba bari kawai ko nayi idan na tashi sai inji kamar ma banyi ba''. Idanu ya zaro yace'' kaii a,a baby kar muyi haka da kai mana ni da nazo yin honeymoon na biyu ya zaka rink'a saka mummyn ka bacci''. Magana yake yana shafar cikinta. Hannun sa ta kama ta cire akan cikinta tace'' ka cika abin dariya, to wai dawa kake maganar?" '' Ah kinji ki da baby na mana, tashi kiyi sallah sai kici abinci ni zan tafi masjid''. '' To sai ka dawo, a dawo lafiya''. '' Ameen maman baby''. Ficewa yayi ita kuma ta bishi da kallo tana murmushi. Bayan tayi sallah ne ta d'auki wayar ta ta kira 'yar uwar ta wato FAREEHA idan mai karatu bai manta ba nace muku ai a nan Abuja suke da zama. Bayan ta d'aga ne FARHANAH take sanar mata sun fa shigo Abuja d'azu, FAREEHA tayi murna sosai tace mata a wace unguwa ce zasu zo anjima da yamma, tace da ita asokoro amma ta bari idan yarima ya dawo zai mata kwatancen gidan. Hira sukayi sosai a wayar kafin suyi ma juna sallama kamar kar su rabu. Fita tayi taci abincin saboda ba zata iya jiran yarima ba dan wata mahaukaciyar yunwa takeji. Tana ci ya shigo tare da yin sallama hannun sa d'auke da ledoji da alama daga can ya wuce yi musu siyayya ne. Tashi tayi zata amsa yace'' a,a yi zaman ki kici abinci na hutar dake''. '' To ina Ado na ganka da kaya a hannu?" Shi ya kawo har nan k'ofar falon ni nace masa ya bani ya koma kar ya shigo min falo ya kalle min mata''. Dariya FARHANAH tayi ba tare da ta k'ara cewa uffan ba taci abincin ta shi kuma ya wuce yakai sauran abubuwan fridge da sauran abubuwan da zasu buk'ata. Da ta gama takai Kitchen sannan ta dawo ta zauna ta kalli yarima a inda yake zaune tace'' na kira sister tace anjima zasu zo bari in kira ta ka kwatanta mata gidan''. '' Uhmm wato har kin kira ta kin sanar mata zuwan mu kenan? Ai da saï ki bari idan mun gama amarcin mu sai mu nemesu ko?" Zama tayi kusa dashi tace'' hummm wai amarci lallai''. '' Eh kina mamaki ne? Amarci zamu ci a karo na biyu''. Shiru tayi tana tunanin yanda zasu kwashe da yariman anjima dan ta lura bazai barta ta wani huta ba ita kuma wallahi bata jin yin komai kai kwata-kwata ma bata son ya ra6eta da sunan yin wani abu. Ji tayi suna gaisawa da FAREEHA yana mata kwatancen wurin tace bata gane sosai ba dan ba wurin zuwan ta bane amma zata sanar da mijinta sai suzo d'in, nan sukayi sallama ya ajiye wayar. Bayan sallah'r isha'i su FAREEHA suka zo gidan a bakin k'ofar sukayi horn mai gadi ya lek'a sai da yayi ma mijin FAREEHA tambayoyi sannan ya bud'e musu suka shiga bai lura da FAREEHA a motar ba da bâ zaiyi wannan tambayoyin ba saboda fuskar ta ma ta isa ta bashi amsar tambayoyin sa. Ba k'aramar murna sukayi ba na ganin junan su nan take suka rungume juna cike da kewar juna FARHANAH tace'' miss you so much dear sis''. '' Nima haka 'yar uwa''. Nan yarima suka gaisa da Adeel mijin FAREEHA suka rankaya ciki aka bud'e sabon shafin hira a nan FARHANAH take ce ma FAREEHA ina suka bar mata babyn ta Fawwaz sai FAREEHA tace'' yana can gidan su mamie''. Mamie take kiran mahaifiyar Adeel matar tana son ta sosai jinin su ya had'u. FARHANAH ta kawo musu drinks da ruwa, bayan sun sha sai FARHANAH ta ja FAREEHA suka tafi sama. Bayan sun zauna ne FAREEHA ta kalli FARHANAH tace'' sister Allah ya inganta muku wannan cikin yasa ya fito lafiya dan naga alamun ciki ne dake''. Marairaice fuska tayi tace'' ashe kowa ma yana ganewa inada ciki, wai har yayi fitowar da za'a ganeshi?" '' Kinji ki da wata magana yo shine me dan an gane? Cikin shege kikayi ne?" '' Ba haka bane kunya nakeji wallahi''. '' Kunyar wa kikeji a nan garin? Ince nan daga ke sai mijinki ne ko? To waye zaki ji ma kunya? Dan Allah ki daina wata irin magana kamar wata wacce bata waye ba''. '' To shikenan na daina ranki shi dad'e, naga ke har yanzu shiru ba'a samo ma baby na k'ani na''. '' Humm dramar da muke sha kenan ni da abban shi wai nice nak'i in haihu saboda ina zuwa aiki shi fa abin ya ishe shi me da me kedai maganganu kala-kala ni kuma sai dai in bashi hak'uri''. '' To ki daina shan magani mana ai ya kamata ace yanzu anyi masa k'ani''. '' Kinga shi fa bazai gane bane na gaya masa na daina sha wallahi yanzu ya kai wata biyar ma amma bai yarda dani ba''. '' Kiyi ta kwatanta masa har ya gane''. Dariya tayi tace'' mutuniyar yanzu komai normal ne ai ke da yariman naki ko?" Murmushi tayi tace'' uhmm sosai ma baki ga yanda ake tarairaya ta ba kamar ya had'iye ni dan so''. '' Masha Allah! Haka nake son inji daman''. Nan sukayi ta hira har kusan 10pm sannan sukayi musu sallama suka tafi kamar kar su rabu haka sukeji. 'Dan uwa mai dad'i babu ya kamar d'an uwa a duniya. Drama a lokacin da akazo kwanciya domin kuwa yarima ya nuna yana son a bashi hak'k'in sa ita kuma FARHANAH saï nok'ewa takeyi dan bata so bata ma jin sha'awar ya ra6eta da sunan yin wani abu. Da k'yar ya samu kanta shima bayan komai ya lafa ne ta saka mishi kuka har da shesheshek'a kamar yau ne daren ta na farko, shi yarima abin ma mamaki yake bashi. Bayan ya fito daga wanka yana goge jikinsa da tawul yaga har a lokacin kukan takeyi sai ya tako har bakin gadon ya zauna ya kalleta yace'' wai meke faruwa ne?" Batayi magana ba ta tashi taje bathroom. Da kallo yabi bayanta ya rasa me yake damunta shi dai yasan bata ta6a yi masa haka ba tun lokacin da suka shirya amma yau gashi har tana masa kuka dan kawai ya kar6i hak'k'in sa, ai yayi ma k'ok'ari yaushe rabon shi da ita? Duk uzirin da yayi mata bata gani ba? Riga ya saka ya yana son yayi nafilfilin sa amma sai ta fito yaji dalilin wannan abu. Fitowa tayi tawul d'aure a k'irjin ta saï cika take tana batsewa kamar wacce akayi ma wani laifi, duk yana lura da ita har tazo ta ra6a ta kwanta ba tare da tasa riga ba. Sunan ta ya kira cikin muryar da bata isa tak'i amsa masa ba ta amsa mishi da'' na'am''. Yace'' tashi magana zamuyi''. Ba musu ta tashi zaune ya kalleta yace'' wai ba tambayar ki nakeyi ba akan abinda yake damunki?" '' Babu komai''. Ta bashi amsa. '' 'Karya kike fad'a min abinda ke faruwa''. Baki ta cunno tace'' ai kaine ina ce maka ban so amma bakaji ba''. '' Meye baki so?" '' Bana jin sha'awar ne shiyasa''. Jinjina kai yayi yace'' akan abinda yake halali na ne kike wannan kukan? Yau ne na fara kwanciya dake? Wani hali ne kike son fitowa dashi ko me?" Matsowa tayi kusa dashi ta fad'a jikin sa tana hawaye tace'' dan Allah ka yafe min ba laifi na bane kawai haka nakeji a zuciyata ba dad'i please forgive me husby''. Cireta yayi daga jikin sa ya tashi tsaye yace'' karki damu na fahimta kwanta kiyi baccin ki''. Kwanciya tayi amma bata yarda in ya hak'ura ba ganin yanayin fuskar sa. Ke6ewa yayi ya shimfid'a darduma ya kabbara sallah, tun tana kallon sa har bacci ya d'auke ta. Washe gari yarima bai nuna mata komai ba a haka suka wuni cikin gidan suna zaune a falo suna hirar su sallah ko cin abinci kawai ke tashin su a wurin. A yau da dare kuwa lokacin bacci yana yi yarima ya d'auko laptop d'in sa bayan ya kashe fitilar d'akin ya zauna a inda yake kwanciya ya kunna systèm d'in sa FARHANAH tana kallon sa ta kasa ce masa komai dan shima bai ce da ita komai ba. Tana a gefen sa shi kuma hankalin shi yana kan laptop har ta fara hamma sai ta d'ora kanta a kafad'ar sa tace'' ya kamata fa ka bar aikin nan mû kwanta bacci nakeji''. Ba tare da ya kalleta ba yace'' zaki iya kwanciyar ki ina aiki ne kuma inaso sai na gama shi kafin nan in kwanta''. Shagwa6a ta fara mishi tana d'an shure k'afa kamar k'aramar yarinya tace'' bazan iya ba sai akan k'irjin ka zan iya bacci''. 'Dagowa yayi ya kalleta bai ce komai ba ya mayar da kanshi kan aikin sa. FARHANAH jikinta ne yayi sanyi me yarima yake nufi? Wai ko dai fushi yayi ne? Indai haka ne ai kuwa da ta shiga uku bata son abinda zai 6ata ran mijinta. Cikin muryar rad'a tace'' dan Allah kayi hak'uri nasan haushi na kaji akan maganar jiya, wallahi ba yin kaina bane kai kasan bazan ta6a hanaka kaina ba dan kuwa mallakin ka nake ka fahimceni please''. Barin abinda yakeyi yayi ya d'ago yace'' ba fushi nakeyi dake ba kawai dai zan k'yakeki ne tunda kin nuna baki ra'ayin kasancewa dani''. Kuka ta fara ya dakatar da ita yace'' karki ma soma, me akayi na kuka a nan? Kinsan a halin da kike ai zaki iya cutar da kanki da kuma abinda yake cikin ki''. 'Kyaleshi tayi ta juya masa baya ta rufa da blanket har kanta ta rufe cike da jin haushin halin sa na kafiya akan abu. Shima aikin sa ya cigaba da yi har zuwa wani lokaci sannan ya rufe yayi musu addu'a sosai tukun ya kwanta. Kwanaki biyu a tsakani yarima ya share FARHANAH da wani batu na buk'atar sa bai ma nuna mata yanaso tun abun bai damunta har tazo ta fara damuwa dan gani takeyi kamar Allah zai kama ta da laifi tunda gashi fushi yake mata akan hakan amma yak'i nunawa haka yasa ta yanke shawarar ita zata bashi hak'k'in sa ko da zai ce bai so ne dan ta fita a hak'k'in shi. Hakan kuwa akayi cikin dare ta mirgina kusa da shi ta d'ora kanta bisa cinyar hannun sa a yayin da hannun ta ke yawo akan k'irjin sa tana wasa da gashin dake kwance lub a k'irjin. Yana jin ta yayi burus da ita, ganin ya k'yaleta ne yasa ta d'an cijeshi a cinyar hannu sai ya d'an motsa ba tare da yace mata komai ba. Haushi yasa ta fara mishi kuka tana k'ara shigewa jikin sa sai a sannan ne yasa hannu ya rungumo ta ya shiga rarrashin ta cikin murya irin ta mai bacci yace'' meya faru kuma?" '' Ba kaine ba kake ta fushi dani baka kulani so kake Allah yayi fushi dani?" '' Am sorry ba haka bane ai bazan ta6a yin fushi dake ba, na fahimce ki da farko ma nine banyi tunani ba a matsayi na na likitan mata, so dan haka karki damu bana fushi dake matata''. Had'e bakin su tayi waje d'aya ta shiga nuna mishi tsantsar soyayya cike da k'warewa yau yayi mamakin ta na yanda tazo masa da wani salon na daban. Abinka da an jima ba'a had'u ba tuni oga yarima ya rikice mata suka dulmiya fagen ma'aurata wanda ke cike da tarin lada da ni'imomi daban-daban abin sai wanda yayi auren shi kawai zai fad'e ta...... Iyyee su yarima fa an murji FARHANAH dan ma yana tausaya mata saboda abinda ke jikinta haka ya k'yaleta ba dan ya gajiya da ita ba. Da asuba FARHANAH a firgice ta tashi tana shafar cikinta yarima ya tashi shima yana kiran me ya faru? Duk da sanyin A/C na d'akin amma FARHANAH saï zufa take, yarima ya kunna fitilar bedside drower ya kama ta yana jijjigawa yace'' kiyi min magana mana me ya faru?" '' Mafarki nayi wata mata ta biyoni wai sai ta farke min ciki ban isa in haifi abinda ke cikina ba''. Yarima ya jinjina kai yace'' Subhanallahi! Tashi muyi sallah munyi maganar daga baya''. A tare suka shiga toilet d'in dan sosai ta tsorata da wannan mafarkin, wacece wannan mai son ganin bayanta? Me tayi mata ne? A ranar haka FARHANAH ta wuni mak'ale da yarima bata yadda ya barta ko dai-dai da second d'aya ba ko wanka a tare sukayi a yau d'in nan, gani take kamar matar zata sake zuwa mata a gaske ma. Bayan la'asar suka fita shan iska can bayan d'aki wajen lambun gidan a nan yake k'ara tambayar ta yanda mafarkin yake ta zayyana mishi sai ya nisa yace'' kinga fuskar matar?" Girgiza kai tayi tace'' a,a fuskar ta a rufe da wani bak'in yadi hannun ta d'auke da wuk'a tana ta surutai wasu ban ma rik'e su ba''. '' Ahan fad'a min cikin wa'yanda kika rik'e''. '' Cewa takeyi ban isa in haifi wannan cikin ba sai taga bayan mu daga ni har kai da duk ma wasu masu goya mana baya da dai maganganu kala-kala''. '' Ba komai bata isa tayi mana abinda Allah bai mana ba, insha Allah babu abinda zai faru kedai karkiyi wasa da addu'o'i kamar yanda na gaya miki''. '' Insha Allah''. Suna hirar su cike da nishad'i dan sun ma manta zancen mafarkin sai sukaji sallamar Ado yarima yace'' Ado ya akayi ne?" '' An wuni lafiya? Ya gajiya?" '' Lafiya lau mai sunan daddy na''. Cewar FARHANAH saï yarima ma ya amsa masa. Ado yace'' ranka ya dad'e kayi bak'uwa''. Yarima yayi jim yace'' bak'uwa kuma? Wacece?" '' Wannan 'yar uwar taka''. Gaban FARHANAH ya fad'i kafin yarima ya bashi amsa tuni ta taho inda suke tana cewa'' Ado meye naka na zuwa fad'a masa ai ni ba bak'uwa bace a gidan nan''. HASINA ce ansha ado ana taku d'ai-d'ai cikin k'walisa da karairaya sai wani yauk'i take daga zuwan ta ta jawo kujera d'aya ta zauna kusa da yarima gami da d'ora k'afa d'aya akan d'aya. Yarima ya kalli Ado alamar yana iya tafiya, godiya yayi mishi ya tafi. Yarima ya maido hankalin sa kan HASINA yace'' me ya kawo ki nan? Ya akayi kika san ina garin ma?" Dariyar mugunta tayi ta kalli inda FARHANAH take sai kuma ta maido kallon ta kanshi tace'' haba kai kuwa sweet meye na tayar da Hankali haka? Dan kawai nazo in kawo gaisuwa ta?" '' Baki bani amsar tambayoyi na ba ai''. '' Kawai jikina ne ya bani kazo garin shiyasa nazo mu gaisa tunda kak'i nema na''. '' Wannan ba hujja bace dan nasan k'arya kike fad'a miki akayi''. '' Ko ma ya ka d'auka, so yasu mum da kowa''. '' Lafiya''. Yarima ya fad'a a tak'aice. Sai ta kalli FARHANAH tace'' uhmm kinga na manta ashe bamu gaisa ba, sannu matar yaya''. FARHANAH tayi murmushi mai cike da ma'anoni da dama tace'' kinga ni kuwa ban ma san kinzo ba dan ban ganin kowa a gabana idan ba mijina ba, idan ina tare dashi babu kowa a tsari na saï shi saboda shine tauraro mai haske dukkan illahirin inda nake shiyasa bâ bazan iya ganin wata ba''. Iya harzuk'a tayi har da su huci tace'' keee!! Ki iya bakin ki ni ba sa'ar yinki bace dan nafi k'arfin ki wallahi''. '' Ballagazar mace ita ke bin namiji duk inda yaje, al-hamdulillah na taka matsayin da baki isa ki taka ba, ba kuma zaki ta6a takawa ba, na shiga inda baki isa ki shiga ba, kinsan ina ne? Zuciyar yarima na shiga zuciyar mijina inda yasa babban makulli ya kulle babu wata da ta isa ta k'ara shiga wannan k'ofar forever and ever, so am so sorry yarinya a k'ara gaba''. Kuturun uba amma FARHANAH ta gama dake HASINA ashe kin iya magana haka? HASINA ta tashi tsaye tana nuna ta da yatsa tace'' kiyi hankali dani dan ba kanwar lasa bace ni''. '' Na gama magana ta bana cacar baki akan abinda ya rigaya ya zama mallaki na ni kad'ai''. HASINA tace'' ki jira yarina''. Fuuuuu ta bar wajen tana ta maganganu duk abinda sukeyi yarima yana zaune yana kallon su ko uffan bai ce musu ba. Tana barin wurin FARHANAH ma ta tashi ta nufi cikin gida ba tare da tayi ma yarima magana ba. Bin bayanta yayi da kallo yana murmushi ya girgiza kai yana ayyana lamarin mata. Sai da ya d'an 6ata lokaci a wajen kafin ya tashi ya nufi cikin gida dan sai da ya kira mummyn sa yaji lafiyar ta sarki kuwa bazai ma kwatanta ba saboda ya kira shi sau d'aya da suka zo amma mai martaba bai d'aga wayar ba haka tayi ta ringing ba'a picking sai yarima ya hak'ura da kiran kawai zasu cigaba da addu'a har Allah ya dawo dashi cikin hayyacin sa. FARHANAH kuwa ana d'aki ana kuka wani haushi da kishin yarima ne ke cin ranta, abinda ya k'ara harzuk'a ta ma da yak'i biyo bayanta yayi zaman sa a can wato gata mahaukaciya sun maida ta wawuya bata san abinda takeyi ba ko? Idan ba haka bane ya akayi HASINA tasan sunzo har ma tasan nan gidan alhali ba mace ke da akwai ba kenan tun can daman sun saba had'uwar su a nan ko? Take shaid'an ya ayyana mata wani mugun abu cikin zuciya idanun ta sukayi bak'i k'irin bata ko ganin gabanta ta sauko daga gadon ta nufi wardrobe tana kuka tana ciro kayan ta daga ciki a haka yarima ya isko ta. Wajen ta ya nufa yana fad'in'' Subhanallahi! Wife me zan gani haka? Ina zaki kai kayan? Kuma kukan me kikeyi?" Juyowa tayi ta mishi wani irin kallo zai kama ta cikin k'araji tace'' don't touch me!!! Karka sake hannuwan ka su ta6a jikina, har ni zaka yaudara yarima?" Cike da mamaki ya nuna kanshi yace'' nine mayaudarin?" '' Eh kai ne mayaudarin sai me? Me zaka iya yi min? Kasheni zakayi ko me?" Murmushin yak'e yayi ya dunk'ule hannun sa d'aya ya kai ma d'ayan hannun duka ya kalleta tuni idanun sa sun fara canza kala dan kar yayi abinda zaiyi dana sani sai kawai ya bar d'akin gaba d'aya yaje falo ya zauna. Tunani ya shiga yi me FARHANAH take nufi da kalmar yaudara? Tana nufin yaudarar ta yayi yana son HASINA ko kuwa me take nufi? Idan kuwa haka ne ya zama dole yaje ya warware wannan tufkar kar abin yayi nisan da zai kasa yin komai. Tashi yayi ya koma d'akin har lokacin kuka take tana had'a kayan ta cikin bag, zuwa yayi ya kama ta tana tirjewa sai ya d'auke ta ya kai bisa gado tana ta shure-shure sai da ya daka mata tsawa sannan ta tsagaita yace'' wai me ya sameki ne haka? Hauka kike baki ga a halin da kike bane? Ko so kikeyi ki illata kanki ne?" Cikin kuka tace'' abinda ke cikina shi kake yiwa ba dai ni ba, da zai zube ma da na huta da fitina kaje wacce kake son ta haifa maka''. '' Ke tsaya kiji maganar da zan gaya miki, ban son hauka da shirme kinji ko? Daman akan HASINA ne kike haukan nan? Zance ni da muke zaune tazo? Nasan da zuwan tane?" '' Ka sani mana, ya akayi tasan kana nan? Daman can kun saba had'uwar ku a nan malam babu abinda zaka fad'a min kawai''. Idanun sa sun k'ank'ance yace'' kinsan Allah kinci darajar k'auna da kuma abinda kike tare dashi, nifa mace bata min irin haka, ba'a ta6a min irin abinda kike min ba, ya ina son fahimtar dake abu amma kina botsare min''. Batayi magana bâ ya sake cewa'' nasan cewa zakiyi ya akayi tasan gidan nan to karki manta HASINA cousin d'ina ce kusan ince miki zaman ta tayi shi ne a gidan mu kuma yanda akayi tasan nan ana yin meeting a gidan nan na family kuma duk yin da za'ayi tana zuwa, ni kuma nan da kike gani bamu ta6a zama wajen meeting d'in nan ni da ita bâ tunda ban zauna a k'asar ba, idan ma zancen so kikeyi inaso ki sani ban ta6a son HASINA da zuwan in aure ta ba saï dai son 'yan uwantaka na jini wanda wannan kuma ba'a iya k'ark'are shi dan cikin jini yake, shiyasa ma da kuke fad'an ku ban saka muku baki ba ita tanayi ne dan kawai kiji haushi ai tasan da ban sonta, da ina sonta da na jima da auren ta tun kafin in sanki ma, dan haka karki k'ara ce min mayaudari na tsani wannan kalmar a yau da wani ne ya gaya haka wallahi saï ya mutu yana dana sani, ni da ga yak'in da yake gabana abbana ya juya min baya maimakon ki tayani mu samu kan al'amarin saï ki 6ullo min da wani abu ni ban san waye ya gaya mata muna nan ba, ko ki yarda ko karki yarda''. Yana kaiwa nan ya tashi zai fita saï tayi saurin saukowa ta kama hannun sa ta durk'usa a k'asa zatayi magana ya d'aga mata hannu ya janyeta gefe ya fice yana huci saboda yanda ranshi ya 6ace. ******** ***** Abu k'arami ya zama babba dan tsawon sati guda aka d'auka yarima bai shiga harkar FARHANAH zai kawo mata komai na cima da duk abinda take so amma babu fuskar yin hira saï dai ya kunna laptop d'in sa yana aikin sa ko ya kira can Kaduna ya rink'a tambayar doctor Sadik yanda al'amura ke tafiya. FARHANAH da abin ya ishe ta saï ta kira mummyn yarima tana kuka take gaya mata abinda duk ya faru nan mummy ta bata hak'uri bayan sunyi sallama ta kashe saï ta kira yarima tana mishi fad'a akan abinda yayi shima ya zayyane mata komai har mayaudari take ce masa wannan kalmar ita tafi komai bak'anta mishi rai. Mummy tace'' nidai ko meye ma ka rink'a hak'uri ita macece mai rauni ko me ta gaya maka ai kishin ka ne yasa ta gaya maka ya kamata ka kiyaye 6ata mata rai kaga halin da take ciki, kar in sake jin irin haka ku shirya kanku kaji ko?" '' Allah ya huci zuciyar ki shikenan ya wuce insha Allah''. '' Yauwa ko kai fa Allah yayi muku albarka''. '' Ameen mummy, ya abba yake har yanzu dai babu wani cigaba ko?" '' Humm ai lamarin har tsoro yake bani amma ba komai insha Allah komai yayi farko zaiyi k'arshe muyi ta addu'a dai''. '' Insha Allah muna kanyi ma''. Nan sukayi sallama ya tashi yaje ya iske FARHANAH tana kwance idanu a jeme alamar tayi kukan ta ta gaji har bacci ya d'auke ta, nan take tausayin ta ya kama shi, toilet ya wuce yaje ya watsa ruwa ya fito ya haye gadon saï da yayi musu addu'o'i ya shafe mata jikinta shima yayi tukun ya shige blanket d'in. Janyota yayi ita kuwa kamar daman jira take saï ta shige jikinsa tana mai nanuk'e mishi abinka da ya kwana biyu shiru tuni ya fara lalubar ta bata hanashi ba nan suka shiga faranta ran juna suna murzar junan su son rai, cike da so da k'auna suka raya wannan dare. Washe gari FARHANAH ta nemi gafarar yarima shi kuma yace ya yafe mata dunya wal akhira ya wuce daman rashin fahimta ne. Bayan wasu kwanaki Haulat ta kira FARHANAH bayan sun sha hirar su ne daga k'arshe take sanar mata cewa jibi za'a kawo kud'in tambaya gidan su. FARHANAH cikin murna tace'' ke dan Allah k'awa wai da gaske?" '' Yes! Da gaske nake kuma auren ma ba zai wani jima ba za'ayi shi''. '' Wow!! Am so happy for you dear, gaskiya naji dad'i k'warai to a ina mijin yake?" '' Au wai bai gaya muku bane? Ai kema kin sanshi''. '' Waye? Ba'a gaya mana ba''. '' Amma my Mohan bai kyauta ba na zata ma ya sanar muku fa''. '' Wai waye Mohan?" Dariya Haulat tayi tace'' Mahmud dai abokin yarima''. Idanu a waje kafin ta kashe wayar ta nufi falo da sauri-sauri take taka stairs d'in yarima ya hangota da sauri ya taso ya tarbeta yana cewa'' meye sauri haka har kije ki fad'o?" '' Wai yanzu Haulat take gaya min cewa za'a kai kud'in tambaya gidan su kuma Mahmud naka shine mijin nata kuma bai gaya mana ba''. Murmushi yarima yayi yace'' daman saboda wannan ne kike gudu haka? To ya gaya min so nayi inyi surprising d'in ki to saï dai na manta ashe Haulat zata iya 6ata min shiri''. '' Gaskiya naji dad'i sosai wallahi abu yayi kyau''. Ana haka azumi ya kawo kai saï shirye-shiryen tarben shi akeyi gadan-gadan, mummy taso su yarima su koma gida suyi azumi a can yace sam bai da wannan ra'ayin yafi son yayi zaman shi a nan Abuja maybe ma sai FARHANAH ta haihu a nan. Ba dan mummy taso ba ta k'yaleshi dan tasan irin halin da yake ciki dole ayi masa uzuri juyawar bayan uba ba wasa ba saï dai muyi addu'ar Allah ya daidaita lamarin nan. Ana azumi saura kwana biyu Ado ya kawo musu siyayyar kayan azumin su wanda yarima ya aike shi da ya siyo tunda FARHANAH yanzu bata wani laulayi lafiya lau take ta kuma ce da kanta zata rink'a yin abincin su ba zata bari wannan ladan mai tarin yawa ya wuce ta ba. A yau ne aka tashi da azumi wanda dubban jama'a suka d'auka saï fatan kaiwa lafiya da kuma lada. FARHANAH bata wani saka lalaci haka take zagewa tayi musu abinci da kayan bud'a baki kala-kala abin har mamaki yake ba yarima ashe ta iya aiki haka? Ganin kitse yake ma rogo ashe? A da zai iya rantsuwa ma idan har ta iya kunna ko da gaz-cooker ne saï gashi ta bashi uban mamaki. Hhhhh su oga yarima an kwashi girki mai dad'i kenan. Yarima ya bada umarnin a siye kayan azumi a raba ma k'auyika mak'otan su har da gidan surukan shi an kai. Shi aikin lada karkayi la'akari da wai mutum yanada shi a,a duk wanda Allah ya cida ka bashi lada zaka samu bare kuma a cikin wannan watan mai albarka mai alfarma. A wannan watan na azumi su yarima da mummy da duk wani mai son ganin walwalar su sun duk'ufa addu'a ba dare ba rana dan yarima kullum tsayiwar dare yake har lokacin k'iyamullayli yayi basu gajiya da addu'a ba haka a can 6angaren su mummy ba suna ta faman addu'a ga malam yana yi a nashi gefen dan ya lura aminin nashi asiri ne kawai yayi tasiri a kanshi. Kamar yanda aka raba kayan shigar azumi haka wannan karon ma an raba kayan sallah al-hamdulillah jama'a saï sambarka suke ma mai martaba da ahalin sun zata shine ya aika musu basu san mai martaba bai cikin hankalin sa ba. Ana gobe sallah a masarauta ana ta shiri anyi anka sosai ake hidima dan zuwan gobe. Su FARHANAH ma sunyi shirin su saï jiran lokaci kawai a yanzu kam cikinta ya fito sosai dan yakai wata bakwai har da wasu 'yan kwanaki amma dai bai hanata yin komai ba, kuma cikin ikon Allah ta daina yin mafarkin da take saboda k'arfin addu'a(Al-hamdulillah). Yau ta kama ranar sallah wanda duk inda kaga musulmi to yana cikin walwala da farin cikin zuwan wannan babbar rana wanda ba kowane musulmi zai ganta ba, wani za'a fara azumi dashi Allah bazai nufa a gama dashi ba, haka rayuwar take, kenan idan Allah ya nuna maka farkon ta da k'arshen ta saï ka gode mishi. Su FARHANAH sunyi yawon sallah daga gidan su FAREEHA ma yawo suka wuce yarima ya kaita wurare kala-kala wurin shak'atawa ita kuwa ga tsufa ya doso ta saï dariya yake mata dan tace kayan ma basuyi mata kyau saboda cikin jikinta. Kwanaki kad'an bayan sallah saï kwacam a fada sarki yana zaune saï aka ga ya mik'e da sauri kan kace me tuni yayi luuuu yakai k'asa. Subhanallahi! Subhanallahi! Subhanallahi! Haka kawai 'yan fada suke furtawa duk sun rikice aka tallabi mai martaba akayi hanyar part d'in sa........ *Ana wata ga wata, turk'ashi!!!!* *Kuzo muje d'akin mai martaba mu gano abinda ke faruwa.......🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀* *_'YAR MUTAN KAZAY CE👑_* 💥💥💥💥💥 *_'YAR GADARA_* 💥💥💥💥💥 *_NA_* *_A.MAIMOUNATH O.G.K_* _(Mahnoor)_ _Wattpad@maimounathog_ *💫DA BAZAR-MU WRITER'S ASS💫* *_~we are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are d best among all....DA BAZAR-MU MUKE TUN'KAHO.~_* *LITTATTAFAI NA MASU FITOWA👇👇👇👇👇* *°°°RAYUWAR SABREEN°°°ZAMBA CIKIN AMINCI°°°SARK'AK'IYA°°°SA'IN SA°°°ALA'KAR MU DASHI* *^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^* *DUBUN GAISUWA DA FATAN ALKHAIRI ZUWA GAREKU 'YAN GIDANA NA WATO 'YAN DA BAZAR-MU WRITER'S ASSO, GAISHE KU NAKE KYAUTA RUWAN ALLAH, KUNA CIKIN AIKI NA A CIGABA DA GASHI INA ALFAHARI DAKU🥰👍* *_FOR YOU:_* *_DEAR_* *_YAYA HASSAN_* *_A.T.K_* *Page 136/140* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *ABUJA* FARHANAH ce kwance bisa cinyar yarima duk ta shagwa6e tana nuna mishi alamar tana son su ke6e yau da kanta take nema tun safe ta azalzaleshi shi kuma yarima tausaya mata yakeyi dan zata iya samun wata matsalar idan yace zasu tayin abu d'aya ya rasa me ya hau kanta duk ta birkice yau. Kanta yake shafawa alamar rarrashi yace'' kiyi hak'uri mana ko zuwa dare ne, wai ko dai wani abu kika sha ne?" Baki ta turo tace'' ni babu abinda nasha, kenan laifi ne dan na nemi abinda nakeso?" '' Ba laifi bane amma yanayin ki zaki duba ni likita ne kinada rauni a wani wajen ban son mu yawaita abu d'aya aje a samu matsala ki bari da dare duk yanda kikeso za'ayi madam''. Ya fad'a yana mai manna mata kiss a baki. Tashi tayi zaune tace'' haka ma zaka ce kenan?" '' Uhmm haka nace dan tseratar da lafiyar ki dana babyn, ke ba zaki gane bane ba wai banso bane ke kinsan nafi kowa son hakan hak'uri kawai nakeyi saboda yanda kike''. Bata k'ara magana bâ saï ta d'auki remote ta canza tasha gami da sauka k'asa bisa carpet ta maida hankalin ta kan TV shi ma yarima wayarshi ya d'auka ya shiga dannawa dan ya lura rigima kawai take nema, cikin 'yan kwanakin nan saï yawan fushi abu kad'an zai sata fushi yasan hakan na zuwa ga duk mace mai ciki. ***** ***** **** A Kaduna kuwa masarauta tana cikin tashin hankali saboda wannan fad'uwa da sarki yayi gashi har ruwa an yayyafa masa shiru, duk sun rikice sarkin fada yace a kira doctor yazo ya duba shi wannan ba abin wasa bane. Mummy kuwa cewa tayi'' nifa a gani na wannan lamarin malam ya kamata a kira ba wai likita ba ko ya kuka gani?" Kafin ayi magana fulani ta harari mummy tace'' wace irin magana ce wannan? Me malam zaiyi masa? A kira doctor kawai shine mafita''. Dayawa sunfi gamsuwa da shawarar mummy amma sunce a kira duk su biyun. Fulani tace'' to ai ni a gani na bazai wuce hawan jini ba dan haka doctor kawai za'a kira''. '' A iya zama na da mai martaba bai da hawan jini''. '' Ke kika ce, kenan bazai iya kamuwa da ciwon ba tashi guda?" '' Allah ma ya kiyaye mishi da hawan jini''. Sarkin fada da galadima suka fita dan kiran doctor mummy kuma ita ta kira malam a waya tana fad'a masa a halin da ake ciki. Haka aka tsaya kan mai martaba wanda har zuwa lokacin bai farfad'o ba duk hankulan mutanen wajen ya tashi, ita kuma fulani saï bambamin fad'a takeyi wai ank'i abi shawarar ta saboda an raina ta babu wanda ya kulata har lokacin da doctor ya k'araso, kusan a tare suka iso shi da malam. Iya gwani babu wanda doctor baiyi ba amma bai gano wata matsala a tare da mai martaba ba, malam yace a kawo mishi ruwa a kwano. Da sauri aka je aka kawo ya shiga tofa addu'o'i a cikin ruwan tsawon lokuta sannan yace a kwantar mishi da mai martaba kowa ya matsa daga wajen su koma gefe. Ruwan addu'ar ya fara yayyafa masa bakin sa d'auke da wasu addu'o'in, minti biyu a tsakani mai martaba yayi wata irin k'ara gami da fisga ya mik'e zaune da sauri yana salati tare da kiran yarima. Al-hamdulillah abinda kowa yake furtawa kenan mummy murna kamar taje ta rungumi mai martaba amma ba halin yin hakan, fulani kuwa saï muzurai takeyi shi dai sarki babu abinda yake furtawa saï d'an shi ina d'an shi yarima. Saboda 6atan basira irin na fulani saï ta fice da sauri kowa ya kalli bayanta su mamakin matar nan sukeyi. Basu gama tsinkewa da lamarin fulani ba saï da suka ga ta dawo hannun ta jaye da Kasim ta shigo taje har gaban sarki tace'' ranka ya dad'e gashi nan''. Kallon ta yake kamar yana son tuno wani abu saï can yace'' keee!!! Wa ya kawo ki nan? Me kika zo yi nan? Wannan ba d'ana bane yarima HABIBULLAH nake nufi bani da wani d'a bayan shi''. Toh fa! Ana yinta yau. Mai martaba ya kalli malam yace'' malam wai me yake faruwa ne naga duk kunyi cirko-cirko a tsaye? Kuma ina tambayar d'ana ba'a amsa min ba?" Tausayin sa yasa mummy ta fashe da kuka gami da ficewa daga wurin. Tashi yayi saï bi bayanta malam yace'' ranka ya dad'e ka kwantar da hankalin ka duk za'a maka bayanin komai''. '' To meyasa hajiya take kuka?'' '' Ba komai yanzu dai ka huta saï muyi maganar''. Ya nuna su fulani yace'' wannan matar me tazo yi masarautar nan?" '' Ranka ya dad'e ai matar ka fulani itace ka maido a karo na biyu kuma''. '' Ni? A,a ba dai ni ba, haba malam me zanyi da mace irin fulani? Annoba ce a gareni kai ka sani ba saï na gaya maka irin zaman da mukayi ba''. '' Toh! Wannan lamarin fa saï an zauna anyi magana a kanshi''. Kafin malam yayi ma fulani magana tuni ta kama hannun Kasim sun fice tana ta maganganu kamar wata mahaukaciya. Sarki ya bada umarnin kar a bari fulani ta bar masarautar nan a saka idanu sosai a kanta har saï an gama binciken abinda ya maido ta masarautar nan, kuma a nan take yace a bashi takarda ya rubuta mata saki amma ba'a kai mata ba har saï an gama komai. Kowa ya fice yana jinjina lamarin nan da abinda ya faru a yanzu a fada game da fad'uwar sarki kenan akwai lauje cikin nad'i. Allah sarki yarima duk abinda akeyi basu da labari suna can da gimbiyar sa. Yanzu ma suna zaune a garden suna shan iska FARHANAH saï yatsina fuska take yarima ya kalleta yace'' yadai wife?" Girgiza kai tayi tace'' ba komai kawai ji nayi cikina ya d'an k'ulleni''. '' Tashi muje ciki in duba lafiyar baby na, kuma ki ma daina shan wannan abubuwan kar suyi miki yawa''. '' Laah! Daga cewa cikina ya k'ulle saï ace dubani za'ayi? Humm lallai ana ji da babyn nan''. Jayota yayi daman suna a k'asa bisa wani lallausan kilisa mai kyau, light kiss ya manna mata a kunci yace'' ina sonki matata''. Ta mayar mishi da'' me too husby na''. '' Kin gama mallake ni saï yanda kikayi dani yanzu, duk dak'ik'a d'aya na bugun zuciyata yana bugawa ne akan k'aunar ki''. Dariya tayi mishi tace'' uhmm ai nima ka gama mallakeni da komai nawa ya zama naka, i love you so very much mijina''. Wani irin dad'i ne ya ziyarci zuciyar yarima cikin jindad'i yace'' really?" '' Yes of course!". '' Thank you wife, kin cancanci tukwici, ko daman kinsan kina bina wani tukwici?" Kallon mamaki tayi mishi tace'' tukwici? Na yaushe kenan?" Saï da yayi murmushin tsokana sannan ya kawo bakin sa kan kunnen ta yace'' na ranar da muka zama abu d'aya, kin manta ranar?" Tureshi tayi tana murmushi har da rufe fuska saboda kunyar da ya saka ta dan ta tuna ranar da yake nufi saï ta turo baki tace'' Allah ka daina bana so ka cika tsokana''. '' Ba tsokana bace kin cancanci a baki tukwicin ne ai, kinga su mummy sun tura nasu can gida nawa yayi saura, a wancan lokacin nasan ko na bayar ba amsa zakiyi ba shiyasa nayi ta ajiyar sa a wurina''. '' Ka daina tuna baya, wai da gaske kakeyi?" '' Ai zaki ga zahiri daman tukwicin a nan garin yake tare dashi nake yawo ko'ina saboda in killace shi ina tarairayar shi kamar yanda nake miki a yanzu, kin zama k'adara mai tsada wanda ba kowa ne ke samun irin ta ba''. '' Kai mijina kana fasa min kai dayawa fa''. '' Ba fasa kai bane, ni kad'ai nasan yanda nake jinki a cikin 6argo na, k'aunar ki tabi dukkan illahirin jijiyoyin jikina ya kutsa ko'ina, yanzu kece gimbiya ni na zama bawan ki saï yanda kika ce''. Dukan wasa ta kai mishi tana dariya. Haka yarima yayi ta zuba mata kalaman soyayya masu ratsa zuciya tare da gamsar da wanda ake fad'a dan shi d'in. Yarima yayi over wajen gwadawa mace soyayya duk da a da baiyi ba amma yanzu da ya d'and'ana sai yaji ashe can da masoya wayo sukayi masa. Hhhh su yarima fa an zauce akan abokiyar fad'a....au ashe fa yanzu komai ya zama tarihi..... ****** **** **** A masarauta fa mai martaba ya rikice da neman yarima sai tambaya yake ina d'an shi yarima? Ina yaje bai sani ba? Amsar dai ya kasa samu har abin ya kai mishi iya wuya ya titsiye mummy yace ta fad'a masa gaskiyar abinda ke faruwa dan shi sun barshi a duhu yana ji a jikin sa kamar wani abin ya faru, ji yakeyi ma kamar duk a mafarki abin ke faruwa. Mummy ta sanar masa da cewa yarima sunje Abuja shi da matar sa, sarki yace'' Abuja kuma? Me yaje yi Abuja warhaka?" '' Ba komai kawai cewa yayi hutu zasuyi su dawo''. '' Hutu kuma? Tun yaushe kenan?" '' Kafin a fara azumi''. Mummy ta bashi amsa. '' Kafin azumi? Shine kuma duk bani da labari? Hajiya yaushe kuka zama haka? Ashe zaku iya yin abu ba tare da sani na ba?" Hak'uri ta bashi tayi mishi bayani a tak'aice yanda zai fahimta tunda ta lura a wancan lokacin bai cikin hayyacin sa. Waya ya d'auka dan kiran yarima saboda yace shi bazai iya zama babu yarima a kusa dashi ba. Allahu akbar! Sai da mummy tayi hawaye dan farin cikin jin wannan maganar ta sarki, lallai mai martaba ya dawo dai-dai. A 6angaren su yarima kuwa a lokacin yana toilet FARHANAH kuma tana zaune a k'asa bisa carpet tana cin popcorn dan kwanakin nan shine abincin ta shi kawai yake birgeta shiyasa ma yarima ya bada aka siyo mata dayawa. Wayar sa dake bisa bedside drower ta fara ringing ba k'ak'k'autawa har ta tsinke aka sake kiran FARHANAH dai tana zaune ko motsawa batayi ba. Kusan sau biyar aka kira a na shida ne yarima ya fito daga toilet d'in d'aure da tawul yana cewa'' wife ana kiran wayata baki picking''. 'Dagowa tayi ta kalleshi tace'' humm me ya kaini ganin abinda zai buga zuciya ta, maybe ma wata yarinya ce ke kiran ka''. Murmushi yayi ya nufo inda take yazo ya zauna a bakin gadon ya mik'a hannun sa zai d'auko wayar yana cewa'' jan magana ko?'' Kafin ta bashi amsa an sake kira, sunan da yake kan sreen d'in wayar ne yasa gaban shi ya buga saboda tsananin mamaki abban shi ne, abban shi ne yau ya kira shi? Saurin d'agawa yayi dan kar ta tsinke, sallama yayi mai martaba ya amsa sai kuma yarima ya gaishe shi cikin ladabi kamar yana gaban shi haka yake mishi magana. '' Meya faru ka tafi Abuja a wannan lokacin?" Tambayar da mai martaba ya jeho mishi kenan. Ya rasa abin fad'a sai da ya k'ara maimaita mishi tambayar sannan yace'' abba kayi hak'uri kawai hutu ne na d'auka muka zo''. '' Wannan ba magana bace, ko a nan zaka iya hutawa ba sai kaje Abuja ba dan haka karku wuce gobe ku dawo gida ina son ganin ka''. '' Abba lafiya dai ko? Meke faruwa ne?" '' Ba komai kawai ina son ka dawo gida ne, ya za'ai ka tafi wani wuri ba tare da sani na ba?'' Hak'uri yayi ta bashi kafin daga bisani suyi sallama, shi fa yarima magana ta gaskiya bai shirya komawa gida ba, nan yafi dad'i daga shi sai matar sa dan sai yanzu ma ya gane cewa kawai sarauta ma batayi ba ta wani fannin, baka da 'yanci ko kuma komai naka sai an sani bâ wani sirri sai kowa yasan duk halin da kake ciki, ga wasu gardawa dake bin mutum ko'ina babu gaira ba dalili. Ajiye wayar yayi ya kalli FARHANAH itama shi take kallo tana murmushi tace'' bâ sai kace min komai bâ abba ne ya kira ka yau?'' '' Shine''. Ya fad'a a tak'aice. '' Al-hamdulillah! Mun gode ma Allah, lallai addu'a *TAKOBIN MUMINI* ce bâ zata ta6a fad'uwa k'asa ba''. Yarima yace'' wai cewa yayi fa mu tafi gida a goben nan, ni kuma a gaskiya naso sai kin haihu mu koma''. '' Gaskiya a,a mu koma, nima nafi son in haihu a can cikin dangi da abokan arziki''. '' Au wato ke baki jin dad'in zama dani a nan d'in kenan?" '' A,a ban ce bâ, nidai gara mu koma, kuma ai tafiya ta zama dole tunda abba ne ya fad'i, fad'ar maganar shi bâ wai shawara bace a,a umarni kawai zai bamu mû kuma mû aikata hakan''. Bai mata magana ya tashi yaje ya nemi kaya ya saka ya dawo ya d'auki laptop d'in sa ya fice daga d'akin da alama fushi yayi ita kuma FARHANAH dariyar mugunta ta bishi da ita, amma fa yanda bâ zaiji bâ tunda taga jinin sarautar ya motsa yanzu wannan sai ta kwantar da kai tayi rarrashi tukun ya sauko. Tashi tayi ta kai sauran popcorn d'in ta bisa fridge ta fita falo inda ta iske yarima yana aiki a laptop d'in sa, kallo d'aya yayi mata ya maida kanshi ga abinda yakeyi. Girgiza kai tayi tana murmushi da kuma mamakin hali irin na yarima, wani lokacin sai ya koma mata yarima na da sak dan ko dariya sai yaso yakeyi. Da k'yar ta fahimtar dashi nufin ta bâ wai bata jin dad'in zama dashi bane, nan da nan aka shirya kunsan miji da mata sai Allah. ******* **** **** A 6angaren sarki kuwa yana ajiye wayar ya shiga fad'a yana cewa'' yanzu hajiya har yarima zaiyi tafiya wani wajen amma ba'a sanar min ba?'' '' Kayi hak'uri''. A harzuk'e yace'' wai idan nayi magana sai kuce inyi hak'uri kuma kunk'i fad'a min abinda ke faruwa dan inaji a jikina akwai abubuwan da suka faru wanda na kasa gane ko meye ku kuma kuna 6oye min, a banza yarima na bazai bar masarauta bâ ban sani ba''. '' To ranka ya dad'e ai cewa nayi kayi hak'uri komai ya huce shikenan''. '' A wurin ki ko? Kina gani har da wannan annobar fulani ta shigo min masarauta babu wanda ya d'auki wani mataki a kanta amma ni zanyi maganin ta insha Allah''. Dad'i kamar ya kashe mummy tunda ta gane komai na jikin sa ya karye duk sihirin jikin sa ya zama tarihi. Tashi yayi ya fice ita kuma mummy a nan take zaune tana tunanin wannan abu, tana k'ara godewa Allah da ya tak'aita abin haka nan saboda yarima da take tausayawa. Bayan isha'i mai martaba bai fad'a ma kowa inda zai tafi bâ yayi fitar sirri shi kad'ai, gidan malam ya nufa. Ganin shi ya bâ malam mamaki sosai saboda mafi yawanci kiran shi yakeyi yaje can masarauta amma yau sai gashi yazo da kanshi to lallai kuwa akwai matsala. Cikin girmamawa ya tarbeshi suka shiga daga ciki, d'akin sa suka shiga bayan sun zauna aka gaisa sai mai martaba ya kalli malam yace'' malam meyasa kowa yake 6oye min abinda ya faru? Ina ji a jikina akwai wani abu amma ank'i sanar dani''. Cikin ladabi malam yace'' ranka ya dad'e wani abin ne ya faru yanzu? Ni zuwan ka ma ya bani tsoro tunda baka saba yin haka ba ai da saï ka kira ni ni inje''. '' Ba komai ka ajiye maganar sarauta a gefe, yanzu ina maka magana ne a matsayi na na aminin ka, ina so ka bani amsar tambaya ta kana gani fa har HABIBULLAH ya gujeni ya bar garin, meke faruwa ne har haka?" Malam ya jinjina kai cike da tausayawa yace'' kwantar da hankalin ka yarima bai gujeka ba, hasali ma sai da yazo har nan ya sanar min tafiyar su''. '' Kenan har da kai kuka goya mishi baya ya bar gida?" '' Ba haka bane tabbas akwai abubuwan da suka faru tun daga zuwan fulani gidan komai ya ta6ar6are''. Daga nan malam ya kwashe komai ya sanar ma da mai martaba, tak'aici har sai da yayi hawaye ya share yace'' Allah ya isa tsakani na da fulani, taso gur6ata min rayuwa tana so ta watsa min iyali gashi d'ana har yana gudu na, wallahi ban ma san anyi ba ji nakeyi kamar wani bacci mai nauyi ne nayi na tashi''. '' Haka ne ba komai kuma ina so karkayi wasa da addu'o'i a lamarin nan kai ma kayi sakaci sosai ai irin ku baku wasa da addu'o'i ko dan mulkin da ke kanku, rayuwa ta 6aci yanzu ko talaka bai tsira ba bare mai matsayi irin naka''. '' Insha Allah, nasan da kwanakin baya nayi rauni wajen yin addu'o'i na bansan ya akayi ba kawai wani irin bacci yake d'auka ta''. '' Komai ya wuce yanzu Allah dai ya kiyaye gaba kuma yarima karka damu zai dawo insha Allah''. Jim yayi kafin ya tashi tsaye yace'' fulani da Kasim da duk wani mai hannu a cikin wannan al'amarin sai na hukunta su hukunci mai tsanani yanda ba zasu ta6a sha'awar yiwa wani ba''. '' Abi komai a sannu ranka ya dad'e''. Cewar malam. Rakiya yayi mishi ya tafi shi kuma ya dawo gida yana mai jinjina wannan lamari, amma yaji dad'in aminin shi ya dawo yanda yake. ****** **** **** Yarima ne kwance bisa gado sai juyi yake ga tunanin maganar mai martaba ga wata muguwar sha'awa da yakeji wacce ya rasa yanda akayi abin ya dameshi ga FARHANAH tayi nauyi sosai gaskiya yana tausaya mata sai dai kuma bai jin zai iya bacci a haka gara ko zafi ne ya rage. Mirginawa yayi yaje kusa da ita ya shiga shafarta a hankali yana sunsunar wuyanta, kamar a mafarki taji ana shafata, motsawa tayi zata juya sai taji mutum a jikinta, idanu ta d'an bud'e akwai hasken fitilar gefen gado ta 6angaren yarima. A kunne ya rad'a mata cewa'' sorry maman baby na tashe ki ko?" '' Uhmm lafiya bakayi bacci ba?" Marairaice mata yayi yanda zataji tausayin sa yace'' wallahi na kasa baccin ne a taimaka min mana da wani abu''. Shafa sajen fuskar sa tayi tace'' kayi hak'uri zuwa asuba please bacci nakeji sosai''. '' Rufa min asiri wife a matse nake ba dan haka ba kema kinsan ban son takura miki a yanda kike d'in nan''. Juyowa tayi tace'' to kashe fitilar can''. Hannu ya mik'a ya kashe kamar yanda tace sai kuma ya juyo gami da rungumar ta, had'e bakin su tayi tana mishi wani salo na daban shima yana taya ta. Yanda take mishi ne ya rikitar dashi daman abinka da wanda yake a matse, tuni ya cire mata rigar jikin ta ya shiga sarrafa albarkatun k'irjin ta wanda suka cicciko suna a tsaye babu alamar rankwafawa, bakin sa ya kai kan d'ayan ya shiga tsotsa kamar wani jariri haka yake sha a yayin da hannun d'ayan ke kan d'ayan breast d'in yana murzawa a hankali duk ya fice a hayyacin sa musamman ma da FARHANAH take yamutsa masa sumar kanshi tana mishi tafiyar tsutsa wanda hakan ke k'ara ingiza wutar sha'awar shi ke k'ara ruruwa. Sarrafa juna suke cikin k'warewa yarima bi yake da ita a hankali yanda ba zaiyi wata 6arnar ba saboda tsohon cikin da gareta. Yaso ya tsaya a iya wasan amma ya kasa jurewa ji yake kamar ranshi zai fita a jikin sa dole sai da ya dangana da fadar ta amma sai da yasan ya kusa kawowa sannan ya shige jikinta yanda bazai jima ba bare ya wahalar da ita........... Hakan kuwa akayi bai wani jima ba ya mirgina gefe yana maida numfashi ga wani irin sanyi da yakeji kamar ma zazza6i ne yake son rufeshi sai rawar sanyi yake. FARHANAH ma an d'an ji jiki saboda wata irin damk'a da yarima yayi mata a yayin samun nutsuwar sa abin har tsoro yake bata, yau me ya sameshi haka ne? Sai kace wanda bai ta6a kusantar mace ba, duk ya rikice mata ko da yake daman yace ya kasa bacci kuma sha'awar ce ta hanashi baccin. Kusanto ta yayi ya rungume gami da ja musu blanket a hankali cikin rawar murya ya rad'a mata cewa'' Allah yayi miki albarka wife, nagode''. Kanshi ta shafa tace'' ameen! To meye abin godiyar kuma jikina mallakin ka ne sai yanda kaso haka zakayi dashi, ka daina gode min tunda ya zama dole idan kanada damuwa kazo gareta dan sauke ta saboda baka da wani wajen da ya wuce wuri na''. Bai ce komai ba ya shige jikinta kan kace me tuni jikinsa ya d'ume da zazza6i wankan ma yau ya kasa tashi yayi sai kusan kiran sallah asuba sukayi wankan yayi nafilar shi yana zaune a bisa darduma zazza6in da d'an sauk'i duk da bai sha magani ba......... Mu koma Kaduna a fada muga irin hukuncin da za'ayi ma su fulani. Washe gari sarki ya tara 'yan fada yasa a kawo fulani da Kasim nan fada sai ta fad'i laifin ta da kanta sannan a yanke mata hukunci dai-dai da abinda ta aikata. Mummy taso ayi abin a sirrin ce a cikin gida mai martaba yace sam gara ayi a bainar jama'a kowa yasan halin ta da ma wanda bai santa ba ya santa. Mummy ta bar maganar sarki yace itama tayi lullu6i tazo fada ayi a gaban ta tunda yarima yak'i zuwa da yaso ayi a gaban shi to gashi bai zo ba. Malam ya shiga maganar yace da sarki'' a,a ranka ya dad'e bai dace ba, ka k'yaleta tayi zaman ta a gida duk abinda akayi ai zata sani'' '' To shikenan amma tayi kiran yarima ya biyo jirgin yamma ko ni inje in taho dasu''. '' Zan gaya mishi dole ma yazo ai tunda kace''. Inji mummy. An taho dasu fulani fada sai zazzare idanu sukeyi munafukai, cikin kakkausar murya sarki yace'' keee!!! Fulani ina so insan ya akayi kika shigo cikin gidan nan har kika yaudari kowa kikeyin abinda da kika ga dama, d'ana na cikina na nuna ban son ganin sa ya akayi haka? Ina zargin da sa hannun ki a duk abinda ke faruwa cikin masarautar nan''. Shiru tayi kamar bâ zatayi magana ba sai da sarkin fada ya mata tsawa yace'' ba dake ake ba? Sarki bai magana biyu amsar ki ake jira''. Fulani ta kalli sarki tace'' idan na bud'e baki nayi magana akan duk abinda ya faru to tabbas za'a sha mamaki saboda bani kad'ai na aikata aikin nan ba har da k'anwar matar........ *Bata k'arasa ba alk'alami na ya fad'i k'asa da naji tace kanwar matar...😳😳 wai matar wa take nufi? Sarki ko wa😳😳🙆🏻 rigiji gabji ana sha'ani a duniya😳😳😳 kai abin ya d'aure min kai😣 ku fa readers?* *Duk wacce bata halarci fada ba to ta garzayo kar ayi ba ita ni na dad'e a can.......🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀* *Sai da nayi typing komai na whatsapp d'ina ya goge naji ciwo da haushi😣😰* *Na gaishe ku 'yan hannun dama ta🙌* *_'YAR MUTAN KAZAY CE👑_* 💥💥💥💥💥 *_'YAR GADARA_* 💥💥💥💥💥 *_NA_* *_A.MAIMOUNATH O.G.K_* _(Mahnoor)_ _Wattpad@maimounathog_ *💫DA BAZAR-MU WRITER'S ASS💫* *_~we are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are d best among all....DA BAZAR-MU MUKE TUN'KAHO.~_* *Sak'on ta'aziyya zuwa gareki 'yar uwar mu d'aya daga cikin forum d'in mu wato AMEENA. ADULLAHI(AUTAH) na rashin yayanki da kikayi Allah yayi masa rahama yasa aljannah ce makomarsa, Ameen!!!* *_Al-hamdulillah! Sak'on taya murna gareki anty HASSANA ATK Allah ya kara basira da hazak'a🤲 ina yi miki fatan alkhairi a rayuwar ki, Allah ya k'ara daukaka, ina yinki irin sosai da sosai😍👌_* *ARADU NA GAJI NIMA😟 KAI YA 'DAU CHAJI🤦‍♀* *_FOR YOU:_* *_DEAR_* *_YAYA HASSAN_* *_A.T.K_* *Page141/145* *END* *END* *END* *'KARSHE!!!* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* ******A fada anyi tsit ba mai motsi ma ana jiran aji abinda zai fito daga bakin fulani. Ganin bata k'arasa ba ta tsaya sai aka tsawatar mata akan ko ma ita da wacece suka aikata ta fad'a ko yanzu a zane ta a nan gaban kowa. Jin haka yasa fulani tace'' ni da hajiya maryam ne muka aikata komai, duk abinda ke faruwa da sa hannun ta itama dan a tare muka aiwatar da komai''. Hajiya maryam? Kunsan wacece hajiya Maryam kuwa? 'Kanwar mummyn yarima wato maman HASINA kenan, kaiiii jama'a duniya ina zaki damu? Bari dai muji yanda abin yake. Sarki yace'' keee! Fad'i ma mutane gaskiya wace hajiya Maryam?" '' Wacce ka sani k'anwar matar ka, idan kuna musu a kira ta tazo nan ta musa a gabana idan ta isa''. '' Keee!!! Yanzu ba matar sarki kike ba, ba'a yi ma sarki magana a gatsau kamar kin samu wani sa'an ki''. Sarki da duk jikin sa yayi sanyi ya bada umarnin aje azo da hajiya Maryam nan fada. Nan da nan aka d'auki mota har guda biyu dan zuwa kawo maman HASINA. Su mummy dai basu san abinda ke faruwa ba sai an gama zasuji labarin komai, labarin da zai girgiza ta matuk'a, 'yar uwar the same parents ta k'ulla mata tuggu, lallai *mutum mugun icce* ne. Ko da suka je sunyi sa'a ne kawai amma tana shirin barin garin ko ince k'asar ma shirin tafiya Dubaï takeyi dan sun tarar ana saka jakar ta a mota dan zuwa airport. Ganin su sai da taji fad'uwar gaba shikenan tata tazo k'arshe me ya kawo dogarai gidan ta? Me tayi ne ma?" Amsar tambayoyin ki suna a can fada kedai bisu kawai. Bayan sun gaisa suka isar mata da sak'on fada ta daburce tace'' me ya faru? Me akayi ne?" 'Daya daga cikin su wanda babu annuri ko kad'an a fuskar sa cikin muzurai yace'' ke mu kawai umarni aka bamu na tafiya dake ba yanke hukunci ko amsa tambaya ba, dan haka shige muje idan kinje kyaji abinda ke faruwa''. Ta tsorata da yanayin su kuma taga babu wasa a cikin lamarin sai ta shiga suka bar gidan a guje. Driver da mai gadi tsaye sukayi baki bud'e suna kallon ikon Allah, ko me uwargidan su tayi ne? Oho ku bita kusha duka kuma....hhhhh. Basu 6ata lokaci ba suka isa fada tana gaba suna biye da ita a baya har cikin fadar sarki. Ganin fulani a zaune yasa k'irjin ta ya tsananta bugawa kamar zai fito waje''. Tsawa aka daka mata nan take ta zauna jikinta na k'yarma. Akace fulani ta maimaita abinda ta fad'a d'azu a gaban hajiya Maryam dan taji da kunnuwan ta. Kafin ma a maimaita maman HASINA cikinta ya d'auki kuwwa kamar ta sako fitsari takeji saboda tsananin fargaba. Fulani ta k'ara zayyane musu komai hajiya Maryam sai zare idanu take na rashin gaskiya ga kunya duk ta lullu6e ta sarki kallon ta kawai yakeyi tunanin sa idan hajiya taji wannan abu ya zatayi kenan? Wannan abu dame yayi kama? Hau ne? Son zuciya ne ko me? Bari dai muji yanda abin yake. Mai martaba yace da hajiya Maryam tayi bayanin abinda ta sani akan wannan al'amarin. Hajiya Maryam duk ta tsure bata ta6a jin kunya da dana sani a rayuwar ta irin na yau ba. Tsawa aka daka mata sannan ta fara cewa'' wallahi bani da laifi duk laifin fulani ne, mun had'u da ita a wani store ne a can Dubaï nayi mamakin ganin ta a Dubaï tunda bansan tana business ba, nan muka gaisa ta fara jana da hira tun ina d'ari-d'ari da ita har na daina a gani na tana so ta k'ulla huld'a dani ne saboda a cuci 'yar uwa ta saï gashi abinda na gudan ya faru a k'arshe, daga nan hostel d'in da ta sauka muka je ina can har zuwa dare duk a lokacin bata min wani zance ba a game da gidan nan sai bayan mun dawo gida Nigeria ita ta nufi Kano ni kuma nazo nan Kaduna''. Jim tayi kowa ita yake saurare wuri yayi tsit. Cigaba tayi da cewa bayan dawowar mu da kwana uku ta kira ni tace dani tana son komawa gidan mai martaba amma sai na taimaka mata itama zata taimakeni yarima ya auri 'yata tunda tasan tana sonshi, nace mata sai nayi shawara, bayan kwana biyu HASINA 'yata ta kira ni tace yarima yana mata wulak'anci kuma yace bazai aure ta ba sai abin ya d'an 6ata min rai amma ban nuna mata ba kawai cewa nayi tayi hak'uri tunda ba'a aure dole, muna gama wayar da ita na kira fulani nace da ita na yarda matuk'ar yarima zai auri HASINA sai dai ban san ta yanda zan taimaka miki ba tace dani tana buk'atar wandon sarki amma boxer na ciki ko wane iri ne tunda ita tana shiga gidan sai ta fake da cewa wurin yayar ta taje. Abin ya d'an tsorata ni saboda ban san yanda za'ayi in samo boxer na sarki ba sai cewa tayi insan dubarar da zanyi dai matuk'ar ina son ta taimaka min nima. A ranar banyi bacci ba kwana nayi ina tunanin hanyar da zan bi in samu wannan wandon. Washe gari tun wuri na shirya na fita dan zuwa gidan hajiya Saudat wato yayata, muna zaune muna hira sai naje da ita muje in gaishe da sarki a lokacin ya shigo gida dan hutawa. Munje amma yana can k'uryar d'akin shi sai hajiya tace bari taje ta gani idan ba bacci tayi ba sai tayi min iso mu gaisa. Bayan taje ne ta dawo ta tabbatar min cewa bacci yake suka fita dan komawa can 6angaren hajiya. Suna zaune sai aka kira hajiya a waya ta tashi ta fice daga wajen hakan ya bani damar komawa cikin d'akin har k'uryar d'akin na shiga na bincika na d'auko wandon na boye a cikin jaka ta saï nayi maza na fita naje na zauna kamar bani ba. Hajiya tana dawowa nace da ita zan koma tace dani da wuri haka? Nace mata eh akwai wasu kayana da aka kawo zanje in gani, haka na sharara mata k'arya na fita jiki na 6ari. Ina zuwa gida na kira fulani na gaya mata abin nan ya samu, a ranar tazo Kaduna sannan ta koma a ranar tace in bata lokaci insha mamaki nidai ban san me tayi da wandon ba wallahi gâta nan duk ita ta rud'eni da maganganun ta na k'arya tace dani yarima zai auri 'yata amma har yanzu shiru. Salati kawai 'yan fada keyi na al'ajabin wannan abu lallai mutum mugun icce ne wallahi. Waziri yace'' ke fulani fada mana duk abinda ya faru, ya kuyayi da wandon nan? Kuma a ina akayi hakan?" '' 'Kasar niger naje dashi dan ayi ma mai martaba asiri ya maidani in mallake shi sai yanda nayi dashi kuma ya kar6i Kasim a matsayin d'an da ya haifa saboda inaso shi Kasim d'in ya hau gadon saraut....'' bata k'arasa ba nan suka hayyak'o mata suna cewa'' turr da halin ki fulani gadon mulki kuma baki isa ba dan mai martaba bashi da wani magaji bayan yarima SYDEEK''. Sarki ya dakatar dasu yace da fulani ta cigaba sai kuma me ya faru? Nan ta cigaba da tona ma kanta asiri ta yanda taje wajen malamin tsubbu har sai da ma yayi amfani da ita sannan ya yarda zaiyi mata aikin, shikenan tace tanaso sarki ya tsani d'an shi yarima ya nuna ko ganin sa bai son yi in da hali ma tanaso daga yarima har mahaifiyar sa a koresu daga masarautar, to sai dai bata samu galaba akan hajiya Saudat ba wato mummyn yarima saboda mace ce mai rik'o da addini bata wasa da azkar na safiya da yammaci. Waziri ya kalli hajiya Maryam yace'' to ke ya akayi kika yarda da matar da bata son 'yar uwar ki har ki had'a hannu da ita a cuci 'yar uwar ki haka? Ke wace irin mace ce?" Cikin kuka da nadama tace'' wallahi a lokacin bansan yanda akayi har na amince da ita ni da naji tace zata taimaka min yarima ya auri HASINA shiyasa har na yarda daman inajin haushin yanda yak'i ta ya auri bare ba, dan Allah kuyi min rai karku bari hajiya taji, sharrin shaid'an ne da hud'ubar wannan muguwar matar''. Cikin tsawa fulani tace'' kee!! Daina kira na da muguwa, ke har akwai wanda ya kaiki mugunta ke da kika ci amanar yayar ki ciki d'aya''. Nan suke ta tone-tone a tsakanin su sai da aka tsawatar musu, sarki ya bada umarnin a kai a tsare fulani tare da Kasim gami da yi musu horo mai tsanani ta yanda ko gobe akace tayi ma wasu irin haka zataji shakkar yi bare kuma sarkin gari. Sai hajiya Maryam itama zata kar6i nata hukuncin na had'a baki da sukayi dan a cuci sarki. Hannu ta d'ora a kai ta shiga rera kuka sarkin fada yace a ingizasu zuwa inda za'a tsare su. Fada ta jinjina wannan lamari haka cikin gida tuni labari yaje kunnen mummy jakadiya ce taje ta zayyane musu komai dake faruwa a fada. Mummy suman zaune tayi da jin akwai sa hannun 'yar uwar ta ciki d'aya, ita ke son kassara mata rayuwa take neman tarwatsa mata gida? Lallai duniya abin tsoro ce. A ranar mummy wuni tayi bata ci komai ba dan tak'aici. Su yarima kuwa sai yamma lik'is suka samu isowa FARHANAH anyi nauyi sosai tafiya ma da k'yar akeyin ta. Labarin yayi matuk'ar girgiza su musamman yarima da ya d'auki hajiya Maryam tamkar uwar da ta tsuguna ta haifeshi, yana son matar nan fisabilillahi amma jin labarin nan ya ruguza komai nan take yaji ya tsane ta ji yake kamar yaje ya rufesu da duka ko zai samu sa'ida a cikin zuciyar shi. A washe garin ranar HASINA ma tazo kuma da k'yar aka k'yaleta ta shiga ciki saboda a yanzu an k'ara wasu masu tsaron wa'yanda basu ma santa ba bare su san matsayin ta a nan gidan. HASINA tayi kuka har ta gode Allah sam bata ta6a zato ko tunanin maman ta zata iya yin abinda tayi yanzu ba. Ta nemi da su gana da maman ta, nan ma da k'yar aka bari saboda kawai tana mahaifiyar ta ne. Su duk biyun aka fito dasu wato fulani da hajiya Maryam saboda yarima ma yace yana buk'atar ganin su. Cikin wani falo aka tafi dasu inda yarima, FARHANAH da kuma mummy suke a zaune saï kuma ita kanta HASINA. Bayan sun zauna ne yarima ya kalle su yace'' ku fad'a min yanda akayi cikin matata yake zubewa dan ban yadda daku biyun nan ba, tunda naji labarin abubuwan da kuka aikata nasan da lallai kunada hannu a cikin zubewar cikin matata''. Fulani tace'' bansan komai ba game da zubewar cikin matarka dan ni ko da nayi asiri ba wannan ne a gabana ba tunda ban ma san tanada cikin ba''. Ya kai duban shi wurin hajiya Maryam yace'' kema baki sani ba ko?" Gabanta ne ya yanke ya fad'i ganin tun kafin yaji komai ma yana mata magana a haka kai tsaye, yariman da yake matuk'ar girmama ta tamkar ita ta haifeshi amma gashi saboda *SON ZUCIYA* da *SON KAI* yasa kowa zai rink'a ganin bak'in ta. Tuni hawaye ya jik'a mata kunci kowa ita yake kallo saï HASINA tace'' mama please karki ce min kinada hannu a ciki dan Allah''. Ta k'arashe tana mai durk'uso a gaban ta. Cikin muryar kuka hajiya Maryam tace'' dan Allah ku gafarce ni, FARHANAH ki yafe min tabbas inada hannu a ciki dan nice ma nayi asirin da cikin FARHANAH yake zubewa kum....'' bata k'arashe ba mummy tace'' innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Mafarki nakeyi ko a farke nake? Kuce min ba gaskiya bane k'arya ce, Maryam me nayi miki ne kike neman kassara min iyali? Kunnuwana sun kasa d'aukar abubuwan da akace kin aikata a gareni''. '' Mummy barta ta k'arasa''. Cewar yarima. Ya kalli hajiya Maryam yace'' uhum daga nan kuma saï me ya faru? Ya akayi? Waye yayi miki wannan aikin?" '' Kayi hak'uri dan Allah, wallahi sharrin shaid'an ne da son zuciya yasa na aikata hakan, nayi haka ne dan HASINA tazo ta fara haihuwa a gidan shiyasa naje akayi mata asiri wanda zai sa daga ta samu cikin a firgita ta cikin ya lalace, cikin ta na farko ma duk nice, nice nasa aka tura mata iska taje mata a siffar mage, cikin nan na k'arshe shine ban samu na iya zubar dashi ba saboda bokan yace bazai iya ba kuna ta addu'o'i sosai shiyasa ma na hak'ura gashi babu wani tak'amaiman maganar auren ka da HASINA amma har so nayi in raba auren ku duk ban samu wannan damar ba, dan Allah ku yafe min''. Ta k'arashe cikin kuka. Tana k'arashewa mummy kuwa tari ya turnik'e ta nan take ta fara wani irin tari mai firgitarwa, duk suka yi kanta cikin tashin hankali yarima ya kama mummy yana girgizawa kawai saï tayi d'ib numfashin ta ya d'auke nan su FARHANAH suka fara kuka haka maman HASINA da ita kanta HASINA, umarni yarima ya bayar akan aje a kawo masa kayan aiki. Yarima ya jima akan mummy kafin ta dawo da hankalin ta, tashi tayi zaune tace a kawo mata ruwa nan aka kawo tasha ta kalli yarima tace'' kace musu su fita ban son ganin su a gabana''. Kallon mama yayi yace'' wallahi kinji na rantse miki da Allah idan wani abu ya faru da mahaifiya ta zan jingine dangantakar dake tsakanin ku in hukunta ki hukunci mafi tsanani, kin cutar dani, kinyi min tabon da bazai ta6a gogewa ba, ban ta6a jin tsanar wani mahaluki a duniyar nan irin ki ba, kin cika butulu, 'yar ki kuma ko matan duniya suka k'are bazan ta6a auren ta ba, ki jik'a ki sha kayan ki''. Ya kalli inda fulani tayi tsuru-tsuru yace'' kema nasan irin hukuncin da zansa ayi miki, kin cuceni kun kusa rabani da abba na, me nayi muku ne a rayuwa?" Shiru ba amsa babu mai motsi saï sautin kuka ke tashi a d'akin, HASINA ma cikin kuka tace'' mama kin bani kunya kinyi abinda ban ta6a tunanin zakiyi ba, ni nace miki ina son in auri yaya SYDEEK ta hanyar asiri? Duk son da nake mishi bazan ta6a yi masa asiri ba, idan ma asirin ne ni ya kamata inje in nema ai ni ba yarinya bace, mama me zaki ce da duniya irin wannan cin amanar da kikayi ma mum? Na yafe ki, na tsaneki bazan k'ara kallon ki a matsayin uwa ba''. Tana kaiwa nan ta fice daga falon da gudu tana kuka na fitar hankali. Nan yarima yasa aka tura k'eyar su zuwa wurin da ake tsare dasu kafin a yanke musu irin hukuncin da za'a musu. A ranar nan mummy batayi bacci ba haka mai martaba yayi ta bata baki akan ta share maganar nan kar tasa ma kanta wani ciwon akan abin nan da ya faru, an sani da ciwo amma ta danne zuciyar ta, komai na duniya mai wucewa ne, haka suka kwana yana ta rarrashin ta daga nan aka wuce duniyar ma'aurata.....su mai martaba ba dama ashe ana shan soyayya a 6oye bamu sani ba? Hhhhh kar yarima yaji dai.... A 6angaren su FARHANAH na haka ita kuma tayi ta rarrashin nata sahibin saboda duk ya fice a hayyacin sa, tunanin irin hukuncin da zaiyi ma wa'yannan mutane yake. A ranar nan dai babu wani bacci mai dad'i da yarima yayi duk da lalla6a shin da FARHANAH takeyi. Itama HASINA haka ta fice daga gidan, direct hostel ta nufa taje ta kama d'aki na kwana d'aya, taci kuka a ranar har ta gode Allah, bata ta6a tunanin maman ta zatayi irin haka ba, gashi ta jawo rugujewar zumuncin su domin kuwa taga yanda mummy da yarima suka fusata sosai akan lamarin nan. Da safe tayi booking jirgi k'arfe 2pm ta bar hostel d'in, ko gidan su bataje ba ta tafiyar ta Abuja, to wurin wa zataje ma a gidan? Humm ai batajin zata k'ara zuwa gidan nan ko da tazo garin. Bayan wasu 'yan 'yan kwanaki da faruwar abin yarima yasa a bautar da Kasim, yanzu ya zama abin tausayi ya zama bawa kai gara ma wani bawan dashi yanda ake azabtar dashi ga babu abinci mai dad'i saï marar kyau. Fulani duk ta fige ta fice a kamannin ta saboda tsabar wahalar da take sha, d'akin da take ko kare aka ajiye zai jigata bare d'an Adam kuma duk wannan umarnin na yarima ne mai martaba yace ba ruwan shi ayi musu duk hukuncin da ya dace. Hajiya Maryam wato maman HASINA, itama fa tana shan wahala dan babu rok'on da batayi ba akan yarima yayi hak'uri ya k'yaleta haka nan ta tuba amma k'ememe yak'i yarda ko kallon ta yayi bare tasa ran zai amince da maganar ta. Mummy matar kirki tana ganin yanda ta koma saï cewa tayi ita ta yafe mata a sake ta taje kawai amma saï da aka sha fama kafin yarima ya yarda a sake ta dan saï da mummy tace da mai martaba yasa baki dan Allah, shi dai sarki cewa yayi ba ruwan sa a ciki dan ta cancanci kowane irin hukunci, ta zubar mishi da ciki ba sau d'aya ba ba biyu ba. Kafin yarima yasa a saki Hajiya Maryam saï da yayi mata gargad'i gami da kashedin ko ciwon kai matar shi ta k'arayi saï yasa an d'aure ta anyi mata hukunci mafi muni a rayuwa. Fulani idanu sun raina fata saboda tsananin azabar da suke sha a masarautar nan yasa ta zabge ta dawo tamkar mai ciwon HIV idan kuka ganta ba zaku shaida ta ba. Saï Kasim shima ya zama kamar wani mahaukaci ga wani uban gashi ya tara fuskar nan ba kyan gani ga tashi azabar da yake kar6a a kullum saï da yayi dana sanin zuwa garin ma ba masarautar ba. ***** ***** ***** Bayan wasu 'yan kwanaki FARHANAH ta tashi da nak'uda a ranar wata alhamis, ana kaita asibiti ba jimawa ta haifi 'yar ta mace sak kama da yarima yarinyar masha Allah ga kyau ga k'iba, 'yar ku6ul6ul da ita gwanin sha'awa, murna wurin jama'ar masarautar nan ba'a ma cewa komai bare shi uban gayya wato yarima. Kasancewar lafiya lau ta haihu ba wata matsala saï aka sallame su daman a asibitin yarima ne ta haihu. Suna dawowa gida yarima ya damk'a ma FARHANAH key na gida da kuma wata dank'areriyar sark'ar gwal mai shegen kyau da tsada, FARHANAH ba bakin magana saï kuka takeyi dan murna, yarima yace da ita'' tukwicin budurcin ki ne da na baby na, hak'ik'a kin bani farin ciki marar misaltuwa, bazan ta6a manta ranaku biyu a duniya ba, kinsan ranakun da nake magana akai kuwa?" Girgiza mishi kai tayi alamar a,a, saï yace'' ranar da na kar6i budurcin ki da kuma yau, bazan manta dasu ba har abada wife, ina son ki matata''. Kunya tasa FARHANAH rufe fuskar ta da tafin hannayen ta tana murmushi yarima yace'' ban son gulma fa, meye abin kunya ke da gashi kin kawo mana baby? Ai kunya ta k'are kuma''. Yarima dai yana nan mak'ale da FARHANAH da kuma babyn su har saï da mummy tazo ta kora shi tukun. Labarin haihuwar FARHANAH ya karad'e dangi kaf su mumyn ta saï murna akeyi amma ta kasa zuwa ganin baby. Pictures akayi ta masa FARHANAH ta tura mata ta kuma turawa FAREEHA itama tana can tana nata laulayin cikin amma ba irin mai tsananin nan ba dan bata wani yin amai saï dai kasala da zazza6i da dai abinda ba za'a rasa bâ kunsan mai ciki. Tunda akayi haihuwar nan ake hidindimu a gidan ba kama hannun yaro, ana kashe naira a nan wurin, ana sauran kwana biyu suna FAREEHA tazo sosai su FARHANAH sukaji dad'in zuwan nata. Ranar suna ta zagayo aka rad'awa yarinya sunan mummy amma suna kiran ta da mamie. Ana gama biki washe gari ma FAREEHA ta koma Abuja saboda aikin ta. FARHANAH sun samu kyaututtuka da dama ta kowane bangare sarki ma yayi mata kyauta mai tsoka haka mummy waziri ma ba'a barshi a baya ba, kai a ranar ba'a cewa komai dan abin saï wanda ya gani. Taro ya watse lafiya lau su FARHANAH sunje wanka da k'yar yarima ya yadda saï da mummy tasa baki tukun, ita kuma FARHANAH dan taje mumy taga 'yar ne shiyasa take son tafiyar ma amma yarima saï wani kumbura fuska yake yana hura hanci wai sam bata damu dashi ba, ita dai nata bada hak'uri ne. Bayan tafiyar su FARHANAH gida yarima bai je ba bai kuma kira ba wai fushi ne yake, FARHANAH duk ta damu saboda ko ta kira shi bai picking, saï da suka samu kwana goma da tafiya sannan ya kai musu ziyara. A wani k'ayataccen falo aka sauke yarima tare da cika mishi gaban shi da kayan marmari irin na alfarma. FARHANAH kuwa tana can d'aki bata ma san abinda ke wakana ba saï da Laure taje ta sanar da ita zuwan yariman. Abin ya bata mamaki, zai zo amma bai kira ta a waya ya sanar mata ba, wai me yarima ke nufi da ita ne? Saï da tayi mishi yanga tukun ta shirya tsaf kamar bâ mai jego ba ta d'auki mamie ta fita. A zaune yake bisa d'aya daga cikin kujerun falon, wayar hannun sa kawai yake dannawa har ta k'araso gami da yi mishi sallama. 'Dan d'agowa yayi cikin basarwa ya amsa amma me yana arba da ita sai ya 6ige da kallon ta, kamar wacce aka sauya masa ita, tayi wani kyau har da fari ta k'ara, tun yanzu ma kenan ina ga in ta gama wankan nan? Ai saï ta zautar dashi, irin wannan kyau haka? Maganar da tayi masa shi ya dawo mishi da hankalin shi, FARHANAH ta mik'a masa babyn ya kar6a yana mai kallon 'yar shi cikin so da k'auna, godiya yake ma Allah da ya mallaka mishi mata da 'ya a lokacin da baiyi tunanin haka ba. Addu'a ya tofa mata sannan yayi mata wani light kiss a d'an k'aramin bakin ta mai kama da nashi, saï FARHANAH tace'' mijina har yanzu fushin ne? Ka manta damu ko kira bakayi kuma ko ni na kira ka baka d'agawa why?" Kallon ta yayi yace'' humm ko dai ke kika manta dani ba, nan k'iri-k'iri kika nuna son rabuwa dani''. Idanu ta zaro tace'' nii!! A,a wallahi ai ban isa ba ma, kai dai ne kak'i tsayawa ka fahimce ni, kayi hak'uri in nayi laifi a gafarce ni''. '' Ba komai ya wuce, yanzu ya jikin naki? Ya baby na tana shan mama da kyau kuwa?'' FARHANAH jin haka saï ta cinno baki tace'' tana sha mana, wato da babyn ka kawai ka damu ko? Yanzu an daina yayi na". '' No! Ba haka bane ai ita k'arama ce dole saï ana kulawa da ita sosai, kishi zakiyi da babyn?" Kai ta d'aga tace'' eh gaskiya ina kishi tunda daga zuwan ta ta amshe min soyayya ta''. 'Yar dariya yarima yayi yace'' humm wife kenan! Ke da naga har k'iba kika k'ara tun daga yanzu alamar hankalin ki a kwance yake ni kuma kin barni da tunanin ki, ni kad'ai nasan yanda nakeji duk dare''. Tashi tayi taje kusa dashi ta ha'esu shi da mamie ta rungume tace'' nima fa ina kewar ka mijina, zuciya ta gangar jikina cike suke da kewar mijina dan dai babu yanda na iya ne kaga *WANKAN GIDA* abu ne na al'adar malam bahaushe idan kayi hak'uri yanzu zaka ga mun gama mun koma ai''. Hannun sa d'ayan ya rungumo ta shima yace'' amma dai kwana arba'in is too much anya zan iya jurewa kuwa? Da a can kike ma ai zan rage zafi amma a nan bazan iya ba kunyar mum nakeji shiyasa kika gudo nan d'in''. FARHANAH dai ganin yarima duk yayi wani iri saï ta tausaya masa ta shiga rarrashin sa nan aka ajiye baby suna nunawa juna kulawa ta hanyar romance su yarima fa an fara sakin hanya kukan mamie ya dawo dasu cikin hayyacin su. Yarima ne yayi saurin d'auko ta ya mik'a ma FARHANAH cikin dashewar murya yace'' kar6i ki bata abincin ta''. Itama duk kasala ta rufe ta a haka ta amshe ta gami da ciro mama wanda suka k'ara cika gashi kamar bata haihu ba tsaye suke gwanin sha'awa amma fa a wajen yarima ba ni ba, ah to hhhhhh..... Cike da sha'awa yarima yake kallon su a lokacin da zata saka ma mamie a baki, ai kuwa tana cafkewa tayi 'yar k'ara gami da cire maman nan take mamie ta fashe da kuka. Yarima ya 6ata rai yace'' wife meye haka? Abincin nata zaki hana mata?" Kallon shi tayi kamar zatayi kuka tace'' husby wallahi zafi suke min idan ta kama''. '' Au daman kullum haka kike mata? Ashe ma yunwa ta shige ta saboda wani shirme naki, oya saka mata ina kallo''. '' Allah zafi kamar raina zai fita nakeji''. Ganin abin nata saï da rarrashi yasa ya matsa sosai kusa da har suna gogar jikin juna yace'' oya saka mata zanyi miki maganin zafin har tasha ta k'oshi, ke ko tausayin 'yar ki bakiyi?" Sake saka mata tayi a baki raf ta kame abinta saï da FARHANAH ta sake yin k'ara yarima ya shiga shafa saman nonon yana cewa'' sorry dear ki daure idan tana sha zaki daina ji, kinga fa yanda suka ciko saboda baki bata tasha to zai saka miki zazza6i''. Da wayo da rarrashi baby tasha mama, yarima ba kunya da ya tashi tafiya yace da mum a kula da FARHANAH bata son ba baby abincin ta''. Mum tace'' ai kullum haka muke fama da ita, yaushe zan yarda da wannan shirmen nata?" Murmushi yarima yayi gami da sunkuyar da kai yana godiya wai saï da yayi maganar yaji kunya. Humm lallai yarima. Saï da ya cika su da kud'i ya fice bai gana da daddy ba saboda bai ma gari yaje Abuja wani taro. ***** ***** ***** Yau da gobe tafi k'arfin wasa domin kuwa su FARHANAH har sun gama arba'in tayi 'yar k'ibar ta ba can ba dan tace bata son zama k'atuwa, baby ma tayi k'iba jajir da ita sak kamannin yarima tar sun k'ara bayyana a tare da ita. Yarima bai wani bari sun zaga dangi ba ya azalzale su suka tarkata suka koma gida. A ranar yarima kukan da yayi ma FARHANAH abin har kunya ya bata dan wani irin shauk'i yakeji, ga wata ni'ima da ta k'arayi a ranar kam ta kusa ta zautar da yarima haka yake kukan dad'i yana sambatu. Basu rintsa sosai ba a ranar saï soyayya ake gudanarwa, kowa yana nunawa d'an uwan sa yanda yayi missing bare ma yarima. Washe gari FARHANAH tana shirya baby ta ba Shafa'atu tace kar su tashe ta bacci zatayi. Ai kuwa hakan akayi baccin ta kawai take shara har yarima ya dawo ya iske baby a hannun Shafa'atu ya kar6e ta ya haye sama. A lokacin da ya shiga FARHANAH tana motsi alamar tana son ta farka. Murmushi yayi yaje bakin gadon ya zauna yana shafar fuskar ta yace'' wife wake up mana baccin ya isa haka tashi ga baby tazo''. Juyi tayi ba tare da ta bud'e idanun ta ba tace'' please k'yaleni inyi bacci na mana ai kasan laifin ka ne duk ka gajiyar dani kamar yau ne ka fara sanin mace''. Dariya yayi yace'' yanzu ma k'ari nazo a bani, wai ashe mata idan sun haihu har k'ara musu taste akeyi?" Hararen shi tayi cikin wasa gami da tashi zaune tana hamma tace'' wani irin bacci ke cin idanuna''. '' Allah yasa nayi ajiyar second baby ne''. '' Wayyoo Allah na ka kashe ni, ina zan iya? Ni fa a gaskiya yanzu ma ya kamata mu d'auki mataki kaga baby k'arama ce ina tsoron...'' bata k'arasa ba yace'' kar ma ki fara wannan banzan tunanin, ni ina son babies dayawa dan haka karki kawo min zancen tsarin iyali''. Ganin ya d'an fusata yasa ta tashi ta wuce toilet ba tare da ta k'ara cewa komai ba. Har ta fito yana zaune da mamie a hannun sa yana mata wasa, mai ta zauna dan ta shafa saï yace'' kinga zo ki bata tasha sannan ki shirya''. Juyowa tayi tace'' naga ba kuka takeyi ba ai ka barni in shirya ko?" '' ko bata kuka ai da gani yunwa takeji kawai hak'uri ne da ita''. Dariya FARHANAH tayi tace'' wacece mai hak'urin? Ai halin ka ta biyo sam bata da wani hak'uri da tana jin yunwar tuni zata 6are baki tana kuka duk ta ishi mutane''. '' Uhmm to yi sauri dai ni nafi son inga baby na tana sha tana k'oshi sosai''. Da haka FARHANAH ta samu ta shirya tukun tazo ta amshe ta ta bata nonon tuni yarinya ta cafke nono ta fara zuk'ar kayan ta. Yarima kuwa waya ya ciro yana ta d'aukar su a hoto dan sun bashi sha'awa FARHANAH saï murmushi akeyi shima ya bada wani style d'in na daban. Bayan tasha a tare suka fita gida mummy suka nufa Shafa'atu ke rik'e da babyn har part d'in mummy. Bayan sati biyu da dawowar FARHANAH aka kai lefen Haulat k'awar ta har an saka rana sati uku kacal wai saboda shi Mahmud d'in k'arin karatu zaije k'asar chad. Kasancewar lokaci ya k'ure yasa ake shirye-shirye a gaggauce Haulat an shiga yi mata gyaran jiki tun ranar da suka kawo lefen da dare aka soma yi mata gyara. Su FARHANAH k'irjin biki abu nasu maganin a kwa6e shiri suke ba kama hannun yaro an fito da anko kala biyu na shadda da kuma atampa duk ba kuma jabbu ba na k'warai masu qualities. Ranar kamu FARHANAH can ta wuni saï shak'iyanci take ma Haulat ita kuma tana binta da eh dai taji. Ranar saturday aka d'aura auren Mahmud da Haulat akan sadaki dubu d'ari biyu, d'aurin auren ya samu halartar d'umbin jama'a daga ko'ina kasancewar Mahmud yaro ne mai yawan fara'a ga kyauta kuma gashi d'an dangi. A ranar aka kai amarya gidan ta saï 10pm yarima ya d'auki FARHANAH suka fice haka sauran k'awayen su ma duk abokan ango ne suka mayar dasu. A wannan ranar ango Mahmud ya darji amarci ba wasa ba, su Haulat anci wuya ba 'yar kad'an ba kunsan mutum tuzuru kamar Mahmud gashi kuma a shekarun sa bai ta6a kusantar zina ba to kunga kenan idan ya samu mace mai k'watar ta saï Allah. ****** ***** **** Bayan an gama bikin Mahmud sarki yace zaiyi murabus yarima ya maye gurbin sa nan kuwa yarima yace sam bai san zancen bâ shi bai da ma ra'ayin hawa gadon mulki. Babu yanda ba'ayi ba yarima dai firrr yak'i yadda saï aka had'a da matar shi FARHANAH aka ce ta saka baki maybe ya yarda ko ta dalilin ta. Da dare suna kwance tana shafar k'irjin sa shi kuma yana wani lumshe idanu sosai sak'on yake kai mishi saï ta kira sunan sa a hankali tace'' mijina''. '' Na'am matata''. Ya amsa murya cike da kasala, saï tace'' anyi maka maganar kujerar sarauta amma kak'i yarda wai meyasa?" Kallon ta yayi yace'' sarauta? Ke kuma me ya had'a ki da zancen nan?" '' Kai ka had'a ni tunda ina auren d'an sarki ai kuwa maganar sarauta ta zama tilas''. '' To bani da ra'ayi ne kuma ban son zancen nan please''. '' Haka dan Allah yanzu har akwai abinda abba zai nema a wurin ka amma ya gagareshi? Ai abba bai cancanci haka a gareka ba''. Tashi yayi ya zauna yace'' wai ke kinsan abinda ake nufi da sarauta? To idan har na kar6i kujerar nan saï fa dole na k'ara aure bi ma'ana saï nayi miki kishiya''. Dumm k'irjin ta ya buga a zuciyar ta saï da ta nanata aure? Lallai a gaskiya ina kishin mijina to amma kuma *UMARNIN IYAYE* fa? Dole ta hak'ura ya k'aran kawai wallahi tunda bata da za6bi in saka. Kafad'ar ta ya dafa yace'' yadai? Kin amince?" Kai ta d'aga mishi saï yace'' ok! Ba damuwa abin ma yazo da sauk'i daman akwai wata yarinya da akayi min tallah'r ta nace ban k'ara aure so yanzu zan aika gidan su kawai aje ayi maganar a gama komai ko ya kika ce?" Wasu hawaye ne suke shirin zubo mata a kunci kawai tashi tayi da sauri tayi hanyar toilet yarima ya shiga guntse dariyar shi sai da yaga ta shiga yayi dariya yanda ba zata ji ba yace yarinya tun daga yanzu ma kenan ina ga kuma kin ganni ina shirin shiga d'akin ta, gashi kin nuna kishi tun a yanzu, hhhh gara dai....... Bata fito ba sai can da jimawa idanun nan jawur alamar taji kuka sosai. Yarima yana kallon ta yace'' wife kuka kikayi dan zanyi aure?" '' A,a me ka gani?" '' Humm ba gashi nan ba duk idanun ki sunyi ja, kefa kika matsa min sai na kar6i sarautar nan kinga kuwa k'arin aure ya zama dole kuma ke nakeso ki za6a min matar''. '' A,a gara dai ka nemo da kanka zaifi''. Bai ce da ita komai ba ya tashi ya kamo hannun ta suka dawo bakin gadon yana kallon ta cikin shauk'in k'auna ita kuma sai kawar da fuska takeyi. Hannu yasa ya juyo da fuskar tana fuskantar sa yace'' kallan ni cikin ido in fad'a miki wani abu''. Kasawa tayi sai ya kai bakin shi kan nata ya shiga kissing d'in ta cikin k'warewa da nuna tsantsar soyayya, tun tana basarwa har itama ta fara taimaka masa suna tsotsar bakin juna zama ya gagaresu sai ya kwantar da ita ya d'ora k'afar shi d'aya akan cinyar ta hannun sa yana kan breast d'in ta yana shafa su. Su FARHANAH fa ana kar6ar sak'on oga yarima suk yasa ta birkice taji babu abinda take buk'ata a wannan time d'in face taji shi a cikin jikin ta. 'Kara hayewa sukayi kan gadon suka k'ara dulmiya duniyar maji dad'i nan yarima ya cire mata zip s'in rigar ta ya sa6ule ta gaba d'aya ya cire tashi ma sai ya rufesu da blanket gami da cigaba da abinda yakeyi cikin jin dad'i da kwanciyar hankali tuni ya mantar da ita zancen kishiya. Can sai da suka jiyar da junan su dad'i sannan suka sarara yarima ya kalle ta itama d'in shi take kallo ya kai bakin sa kan kunnen ta yace'' irin haka kikeso muyi da amaryar ki?" Ya tambaye ta yana mai kai hannun sa kan breast d'in ta sai ta bige hannun gami da juya masa baya. Kan wuyanta yake sunsunawa tare da goga mata sajen fuskar sa duk ya hanata sakat da ta6e-ta6en shi ga hannun sa da yak'i zama wuri d'aya sai yawo yake dashi a jikinta ya sake rad'a mata cewa'' babu amsa ne wife? Allah dai ya bani wata babyn da wuri, ina son yara dayawa fa''. Murmushi tayi ta juyo inda take fuskantar shi, hannayen ta ta sak'ala akan wuyanshi ta sake had'e bakin su waje d'aya tana aika masa hot kisses shima tuni ya biye mata ya shiga wasa da ita suka k'ara jiyar da junan su dad'i a karo na biyu a yanzu kam FARHANAH tayi lakwas jiki ba k'arfi yarima jarumi kuma sadaukin namiji ne bai gajiyawa ko kad'an haka Allah ya bashi k'arfin sha'awa. Washe garin ranar mai martaba ya turo kiran FARHANAH da yarima, ba 6ata lokaci suka tafi. A k'ayataccen falon shi na cikin gida suka iske shi gishingid'e yana hutawa shi kad'ai ba kowa. Zama sukayi tare da gaishe shi cikin ladabi, ya amsa musu cike da fara'a dan suna bashi sha'awa yanda suka shirya kansu kamar ba auren had'i ba. Tashi yayi zaune gami da gyaran murya irin na manya ya kalli FARHANAH yace'' 'yata ya muke ciki game da maganar mu ta jiya?" 'Kasa da kai FARHANAH tayi tace'' ranka ya dad'e na fad'a masa bai ce komai ba''. Kallon yarima yayi yace'' to HABIBULLAH ya akayi ne? Meye matsalar ka da kujerar sarautar nan?" '' Kayi hak'uri ba komai bane face aikin asibitin nan, jama'a da dama suna buk'atata kuma ni a yanzu gaskiya nayi k'ank'anta da zama kujerar nan, bazan iya ba ayi min afuwa idan na fad'i abinda ba dai-dai ba''. Murmushin manya yayi yace'' ba damuwa na fahimce ka ku tashi kuje abin ku Allah yayi muku albarka''. Suka amsa da ameen sukayi mishi godiya suka fita. Gidan mummy suka shiga bayan sun gaishe ta suka fice. Bayan sati su Haulat suka zo yiwa su FARHANAH bankwana dan gobe zasu tafi inda Mahmud zai k'aro karatun sa, amma fa ansha artabu kafin ta yarda da barin aikin ta sai da yayi mata alk'awarin da sun dawo zai sake nema mata wani kuma shekara d'aya ne zasuyi su dawo. Washe gari kuwa jirgin su ya d'aga sai fatan Allah ya sauke su lafiya asha amarci lafiya. ***** ****** **** *BAYAN SHEKARA BIYAR* Rayuwa ta mik'a zaman lafiya ya wanzu a wannan masarauta domin kuwa tuni an sallami su fulani tare da musu gargad'in ko mai kamannin ta aka gani a garin nan sai an kama ta an gark'ame, itama kam ta tsorata sosai. Yanzu FARHANAH an zama manyan mata domin kuwa ta k'ara girma amma dai yaran ta biyu kacal bayan mamie ta sake haihuwar namiji mai sunan Jawad shi kuma sai yayi kama da FARHANAH. maman HASINA ta gane kuran ta yanzu an sasanta ita da mummy daman sharrin shaid'an ne ko itama mummy tayi mamakin wannan abu ashe dai har da asiri ne akayi mata ta fita a hankalin ta ba yin kanta bane. HASINA tayi auren ta ta auri wani yaron minister suna can zaman su a Abuja kuma zumunci sosai akeyi tsakanin ta da FARHANAH kamar komai bai ta6a faruwa ba. Haulat ma da d'an ta Isma'il yanzu haka kuma ciki ne da ita. Tunda yarima yaji wannan labarin ya azalzali FARHANAH wai gashi nan tasa wasa Haulat zata sha gabanta. Shikenan fa ya uzura mata kullum abu d'aya ai kuwa basu cike wata ba ciki ya shiga saboda yarima ya bada wuta sosai. Zaman lafiya da kwanciyar hankali sai k'ara wanzuwa yake a tsakanin su ga alkhaira da cigaban da yarima ke samu. Bayan wata tara FARHANAH ta sake suntulo musu d'a namiji wannan kam yarima ne yayi winning dan yaro dashi yayi kama. Anyi suna yaro yaci sunan Abdallah haka taro ya watse kowa sai sambarka yake. A can Abuja ma FAREEHA da HASINA suna ta zumuncin su gwanin sha'awa. Kowacce mijinta na alfahari da ita. A zaune suke a falo yarima ya saka yaran sa uku tare da FARHANAH ya rungume su yana cewa'' ina sonku iyalai na, hak'ik'a kune farin cikin rayuwa ta, bazan ta6a mantawa dake ba uwar 'ya'ya na''. Itama FARHANAH tace'' nima ina alfahari da kai uban 'ya'ya na ina sonka sosai fiye da tunanin mai tunani, Allah ya bar mu tare dunya wal akhaira''. '' Ameen ya Allah matata''. Cewar yarima yana mai kai mata kiss a kunci....... *************************⬇********************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** *TAMMAT BIHAMDILLAH* *NAN NA KAWO 'KARSHEN WANNAN NOVEL MAI SUNA 'YAR GADARA DA FATAN YA 'KAYATAR YA KUMA ILMINTAR DAKU MASU KARATU, INA SONKU MASOYANA NA NESA DANA KUSA* *SPECIAL THANKS TO:* *YAYA HASSAN ATK & YAYA ABDUL-RAHMAN IBRAHIM (PRINCE)* *BAZAN MANTA DAKU BA HAR ABADA ALLAH YA SAKA MUKU DA MAFIFICIN ALKHAIRIN SA🤲* *KURA-KUREN DA NAYI A CIKI ALLAH KA YAFE MIN BA DAN HALI NA BA🤲* *AL-HAMDULILLAH ALA KULLI HALIN🙏🙏* *_'YAR MUTAN KAZAY CE👑_*