********************** ⬇ ************************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** DAME AKE ADO BOOK 3 1⃣ DAME AKE ADO 3 Ma'u tanatafe cikin duhuwa tanata sauri burinta tayi nisa dagidan cikin ranta tana saka bazataje gidan yayyentaba kogidan umma bazata ba domin zasu iyadawo da ita gidan yaya Ahmad shikuma yacigaba da dukanta yana kulleta cikin gidan kamar mayya bata Ankaraba tayi karo Dawani mutum kayanta suka zube yayi taga taga kamar zata fadi Allah daiyasanya bata fadinba mutumin yazabga salati yana kokarin bata hakuri saigabanta yahau bugabawa domin muryan yayan natane hakan yasanya tagintse bakinta batace komaiba tasuri kullin kayanta tawuceshi dasauri cikin ikon Allah aka kawo wuta daidai lokacin da Ahmad kebata hakuri yadan bita da kallo da mamakin jin wacce yabuge din batace komaiba har ya ayyana cikin ranshi ko kurma ce sai kuma ya hango kamar ma'un sace mamakinsa yakara karuwa ganin tanata sauri tayi gaba yafara kwalla mata kira ma'u ma'u jikinta yadauki rawa saboda yagama shigarta tatsaya cak takasa matsawa daga inda take takuma kasa cigaba da tafiya har ya isa inda take tsaye yaleka fuskarta don kara tabbatarwa itace hankalinsa yatashi da yatabbatar itace cikin fargaba yace ma'u inazaki har lokacin taka magana sai idonta dake zubda hawayen tsoro kamar yakara yin magana saikuma yafasa ya kama hannuta kawai yafara tafiya Asma'u tafara binsa tana hawaye SHIKENAN TASHIGA UKKU TASAN YAU MAIRABATA DA YAYA AHMAD SAI ALLAH GASHI GIDAN BABU KOWA BABU MAIKWATAR TA Hakatayita binsa zaro zaro tanarungume dakayanta harsuka shiga gidan suna shiga yamaida gidan dasakta yadatse hakan yakuma yakadamata ciki tafashe dakuka sosai yakalleta harlokacin hannunta yana rike cikin nasa baice komaiba saida suka dangana cikin dakinsu yazaunarda ita gefen kujera yana fadin inazuwa bari nazo yafice yanufi dayan dakin dasauri tamike tafara zagaya dakin tana kuka hannunta bisa kanta tafara magiya don Allah kayi hakuri yaya nadaina wlh bazankara daidai lokacin yazo da zabgegiyar belt saita kuma zabura tafara ihu dakarfi yasanya hannu bisa lebensa yana fadin shishshi kidaina kuka ma'u badukanki zanyiba nadauko ne domin kidakeni kirama dukan danayimiki yanzu nagano illar abinda na aikata Amshi kirama ma'u yamike mata belt din mamaki yacikata tafara ja dabaya domin bata yarda domin batayarda harzuciyarshi abinda yake nufiba kenan tafi yarda yanayin hakan ne domin yasami damar kamata kawai ganin tanaja dabaya yasanya yacabko hannunta gam cikin nasa saitafasa kara jikinta narawa yadamkata belt din yana fadin dagaske nake ma'u badukanki zanyiba kirama dukanda nayimaki indai har zakidaina yunkuri gudowa kibarni ma'u kalamansa suka sata yin sororo tana kallonsa rike da belt ahannunta duk da karamcin shekarunta maganar yayan nata tagirgizata yasakarmata hannu da belt yajuya yazauna akan kujera yana maicigaba da kallonta ki dakeni ma'u kirama don Allah gani nazauna yanda zaki iya dukan nawa bana fatan kikara yunkurin gudowa idan kika gudu nashiga ukku bansan indazan sanya rayuwataba kobakisan Raliya ma guduwa tayi tabarni da aure naba? Tadan zare ido tana mamakin jin abinda yace tadaure tace dagaske Raliya tagudu? Itama dukanta kayi tagudu yaya?yanda tayi tambayar abin yaso yabashi dariya amman yadake yace bandaketaba kinsan halin Raliya ban isama natabataba balle duka banso kema kigudu idan kika gudu kowa bazai yafeminba harda INNATA MAISONA Kirama don natabbatar kinhuce kinji ma'u Tayi murmushi zuwa yanzu hankalinta yadan kwanta ta isa gabansa tadurkusa tamikamasa belt din tanafadin yaya bazan iya dukankaba nasan nice nayi laifin ma kayi hakuri bazan karaba ranshi yayi haske yace shikenan nahakura amman kimin alkawarin bazaki kara yunkuri guduwa kibarniba Allah bazan karaba nadaina bazanyimaka irin abinda raliya tayimakaba Alkawari abune maigirma ma'u kiyi kokarin rikeshi tadaga kai alamar to tana murmushi ya mike tsaye shikenan kinhuce yanzu mikikeson nadafamiki kici ki kwanta ta turo baki gaba da shagwaba yaya kaine kace nadinga yin abu irin na matan aure amman kakibari nakoyi girki daman umma ma batakoya miniba saitace jagwalgwalo nakeyi kuma ai matan aure sune sukeyin girkinsu dakansu nagani yayi murmushi ma'u ko buhun shiririta yakamo hannuta.... DAME AKE ADO part 12. 2⃣ DAME AKE ADO 3 Zanfara koya miki girki dagayau amman bazaki fatara yin girkiba harsai kin iya sosai eh nayarda saranda na iya zanyi bazan kara sabamakaba tafada cikin hanzari shikenan muje kicin din mezamu dafa yanzu tanabiye dashi saida suka nufi kicin din tace danmalele da wainar fulawa Mai manja wannan duk abinci bane kayan kwadayine kuma ni ban iyasuba yanzu dare yayi indomie zamudafa da Albasa muci yabata Amsa Ai itama tanadadi yaya amma ni na iya itabafa sai ansanya awutaba idan akasanyata aruwa tadade saikaga tayi laushi sai aci yakalleta dasauri da mamaki yace waye yace miki haka akedafa indomie ma'u tasami kujera tazauna tana dariya ganin yanda yasaki baki yana kallonta tace amakaranta bording haka mukeyi tunda ba abarinmu mukunna risho kuma akicin ma ba abarinmu sai siniyoyi kawai suke bari tobahaka akeyi bari yanzu nakoyamiki yanda akeyi yafara kokarin bude indomie din yana zubawa acikin tukunya yadauko albasa ya yanka yazuba akai haka rayuwarsu taci gabada gudana kullum ma'u saikara girma take halittun jikinta nakara bayyana shikuma Ahmad sonta da sha'awarta nakara karuwa acikin ransa saidai tsananin tausayinta yahanashi aikata komai akanta hasalima kogado daya baibari sunkwanta da itaba itatana gado shiyana kasa akan leda dafilo yawurgar haka ake baccin kullum tasaki jikinta da gidan domin yabar yaran suna shigomata sutayata hira suyita wasansu irin na yara sannan yana koyarda ita girki hartasoma iyawa saidai abinda yake damunta baiwuce rashin zuwan Ummanta gidan ba gashi tayi kusan wattanni goma sha ukku kuma shi yayan nata yakibarinta taje bayanshi kullum saiyaje yanata lallabata dai akan tayi hakuri yau tunsafe yafice aiki yabata damar tadafa shikafa da miya domin ta iya yanzu amman kadatabari kowane yaro yafara shigarmata kichin zuwa yanzu ma natsuwa tafara shigarta duk wannan shiriritar ta YAR AUTA tafara dainawa ta iya gyara gidanta tsaf kamar bashiba tashare tagoge ko ina girki ma indai bamai wahala bane tana kokarin yinsa iyakacinta dayaran aike kawai kosuyimata wanke wanke dashara wajen karfe bakwai yashigo gidan abunda yabashi mamaki baiwuce yin horn dayayi sama da sau ukku amman ma'u batazo tazo tabudemasa gidanba domin dayayi horn daya biyu ana ukkun zata fallo koyajiyo muryanta tana fadin yaya inazuwa amman yau yayi yafi sau shidda amman baijiyo matsinta ba saiya matsa jikin kofar gidan sosai yatura da hannunsa saiyaji kofar tabude yashigar da mashin dinsa yasami guri ya ajiyeshi ga mamakinsa saiyaga gidan kaca kaca babu gyara kamar yanda yasaba gani Ransa yabaci dayajiyo karar talabijin da alama kallone yadauke mata hankali tamanta da gyara harda budemasa kofarma yayi nufin shiga dakin yajiyo kauri daga kicin danhaka yanufi kicin din dasauri shinkaface akan risho takama harta kusa konewa gaba daya miyar kuma gatacan gefe marfi yabude hangam takaici yakara kamashi me ma'u keyine nashiririta yau agidan? Yasauke shinkafar yakashe risho dasauri sannan yanufi dan falon nasu kobai daki ma'u ba zatasha fada yadaga labulen yana kwalla mata kira ga mamakinsa saiyaga babu kawa dakin sai TV dakefaman babatu itadaya daga sannan hankalinsa yafara tashi da wutar nepa babu ma'u gaban Tv tana kallo lallai akwai matsala MEKEFARUWANE? saiya saki labule dasauri yanufi dakin gado yanacigaba dakiran sunanta ma'u ma'u yadaga labule yanaware ido kozaihangota amman babu ita acikin dakin babu alamunta hantar cikinsa takada afili yace na shiga ukku ina ma'u tashigane ma'u yasake kwalamata kira dakarfi saiyaji kamar sheshshekar kukan mutum abayan gado yashiga cikin dakin dasauri yana cigaba da kiranta gamamakinsa saiya hangota rakube bayan gado ta tattare jikinta kamar wacce akasanya zama ahaka dole mamaki yabaiyana akan fuskarsa ganin yanda take ta hada gumi idonta yayi jajir alamar tayi kuka takoshi sai ajiyar zuciya take ya isa gabanta yana tanbamyarta ma'u lfy meyafaru meyasameki? Saikawai takara fashewa da kuka tanaja dabaya tanafadin don Allah yaya Ahmad kada kadakeni kaine kace bazaka kara dukanaba kome nayi maka narantse da Allah banyi iskanci dakowaba banyi abinda Raliya tayi da sisco ba kakawo kur'ani nadafa mamaki yakara kamashi datsoro ganin yanakara nufarta tana karaja baya jikin lungu yadan dakata da kwantarda hankali yace tsaya ma'u gayamin meya faru bazan dakekina nako rantse da Allah kome kikayi bazan dakekiba kobakisan kingirmaba yanzu ko umma bazata dakekiba balleni gayamin meyafaru? Cikin sheshshekar kuka tana kara tsatstsare jikinta tana kudundunewa tace Amman dai kasan niba yar iskabace ko yaya yadaga kai cikin rawar jiki nasani ma'una salihace ba yar iska bace ba meyafaru wanine yashigo gidan yayi miki fyade ne ma'u kigayamini zan iya zandaukan dukan abinda yafaru akanki nasan kaddara ce kaji harkafara fada tun bangayamaka ba wlh banyi iskanci dakowaba yaya banyi komaiba yafara fusata haba ma'u kisanarda ni meyafaru kigayamini meye menene cikin karaji da ihu yayi maganar maimakon tadawo natsuwarta saima takara gigicewa kamar zatashiga cikin gadon tafashe da kuka maikarfi jikinsa yayi sanyi yagamo yatafka wauta yadubeta yace ok calm down ma'u yi hakuri gayamin tell me menene ? Ganin batada niyyar magana yasanya yafaki numfashinta ya cafke hannunata yadaga cak saita kara fashewa da kuka da ihu takankame jikinta kamar zata suma fadi take wlh banyi iskanci dakowaba yaya narantse da Allah gabansa yadinga faduwa ganin jini guda guda ajikin zaninta da gurin gabadaya hankalinsa yatashi kwarai da gaske takasa cigaba dakuka cikin karaji yace ma'u meye wannan mezangani haka 3⃣ DAME AKE ADO 3 Bajinin al.ada bane irin naku namata ba....... Cikin kuka tace nima dafarko nayi zaton irin abinnan dawasu kawayena keyine mistration idan sanya Auduga da.ake goge hanci shikenan saiya tsaya nikuma dana sanya saiya jike nakoma sanyawa yajike saikuma jinin yadinga zubuwo bayan banyi komai wlh banyi komaiba Abin sai ma yabashi dariya duk da jinin yazuba dayawa yasaki hannunta domin tadansamu natsuwa sannan yafara magana bakomaiba ne ma'u kowace mace dayanda take fara Al.adarta amman zo cire kayanki kiyi wanka saimuje chemist muji ko wata matsalace tayi doguwar ajiyar zuciya da jindadi tama manta da yayanta yana gabanta tafara kokarin cire rigarta da sauri baiyi zaton ganin abinda yaganiba YAUSHE MA'U TAZAMA HAKA ? ASHE TAZAMA MACE CIKAKKIYA BAISANIBA ? Bugun kirjinsa yafara sauyawa sai yakauda kansa dasauri yana kokarin nemo nutsuwa yasanya cikin nutsuwarta cire kayan takeson yi gaba daya yau babu yar kunyar da take nunawa agabansa saboda bata cikin nutsuwarta tadauko wani zaninta tadaura kafin yazubamata ruwa cikin bokiti yasanya mata abandaki tana fatowa yace maza shiga bandaki kiyi wanka batare da yakalleta ba itama bata kula da komaiba tanufi bandakin tanashiga ya shige dakin da bokiti ahannunsa ya fara kwashe kayan nata dasuka baci yayo waje dasu sannan yafice domin siyo mata Audugar mata Har yadawo tana cikin bandakin bata gama wanka ba hakan ya bashi damar gyara dakin yana tsaka da gyara da gyaran tashigo da sallama yadaga kai da sauri yakalleta yana amsawa cikin shagwaba tace yaya nagama amman haryanzu yana zubowa kadan kadan dariya takwace masa yadaga kai yana kallonta waike wacce irin sakaryata ce ne ma'u ? Amshi nan kisanya da pant dinki Aikinsan yanda akeyi ko ? Tadaga masa kai alamar eh tasani yauwa shirya kafin nima nawatso ruwa nima yanzu nadawo nadan gaji ta amsa yafice shima yajuya domin shiga wanka amman zuciyarsa naci gaba da sakawa da kwancewa Ahaka sukaje chemist din wata ma.aikaciyar jinya datake dan taimakawa acikin Unguwa idan dare yayi duk karadin Ma'u kasayimata bayani tayi sai rufe fuska da dariya kawai ta iya Aunty deeja ma'aikaciyar jinyar tadinga dariya tana zolayar ma'u daga karshe tayiwa Ahmad bayanin babu wata matsala daman wasu matan sukanyi haka farkon fara Al'adarsu amma da sunyi saudaya shikenan idan zasu karayi jinin baya zuba kamar na farko tabasu magunguna da shawarwari sannan suka bar gurinta Ahanya ma'u tayi shiru taga inda yayan nata zaikaisu domin taga ba hanyar gidansu sukayiba gamamakinta sai taga kamar hanyar gidansu Ummanta ake nufa tayi shiru dai tashanye murnarta saidai sanda taga sun shiga layin dadi ya cikata harta gaza boyewa sai data rukunkumeshi tana zabga ihun dadi dafari yadan tsorata da yanda yaji ta makalkaleshi har suka faduwa amma da yagano murnar jindadi ce sai ya saki ranshi amman rikon datayi masa yakara tsinka jijiyoyin jikinsa cikin ranshi yafara korafin abin da yarinyar ke masa cikin lokacin yagaza jurewa yana ganin zai iya karya Alkawarin da ya daukarwa zuciyarshi na barin ma'u tazama CIKAKKIYAR MACE Tasan kanta kafin ya tunkareta da wasu Al'amura na aur e 4⃣ DAME AKE ADO 3 Haka yadaure yakarasa kofar gidan yatsaida babur din yana tsayawa tana dira tun bai karasa tsayuwar ba caraf yacafko hannuta ganin tana shirin zubawa da gudu tayi cikin gida ma'u bakida hankali gudu zaki sanya atsakaiyar titi? Kobakisan ke matar aurebace yanzu saiki sanya mukoma wlh kifasa shiga gidan takwantar da kai cike da fargaba domin tasan kadan ne abinda yayan nata zai iya aikatawa tace yi hakuri yaya nadaina bazan komaba yasaki hannun nata yana girgiza kai to kitsaya mushiga tare banason zumudi nagaya miki takada kai kawai takasa cewa komai amman murna da zumudi suncikata tadan daure tatsaya yagyara tsayuwar babur dinsa yakulleshi sannan suka nufi cikin gida yaya Auwalu yana cikin chemist dinsa azaune ya hangosu tundaga nesa yafara wangale baki da fara'a don ganin yanda ma'unsa tazama butikekiya sunagab da shagon ma'u takufce tafalla dagudu tayi cikin gida domin bazata iya jure wannan jan ran da Ahmad kemataba Ahmad yabita dakallo da tsananin mamaki kafin yafashe dadariya yaya Auwalu ma yafito daga cikin chemist din yana babbaka dariya yace Hoo! Autar Umma wai haka take daman haryanzu batayi hankaliba Ahmad? Ahmad yayi dariya dasauki dai haryanzu yaya yamikawa yayansa nasa hannu suka gaisa suna cigaba da dariya subiyun yaya Auwalu yacigaba da magana Rufe chemist yakamani domin yazama dole naje naga AUTAR UMMA don kada umma tayi fushi dani suka sakeyin dariya sannan suka rantaya sukayi cikin gida gaba dayansu bayan yaya Auwalu yarufe chemist din nasa Acan cikin gida Umma da malam suna zaune suna kallo kasancewa akwai nepa labaran karfe tara suke kallo ma'u tashigo aguje ta manta babu ko sallama ta fada dakin tana kwallawa umma kira dasauri suka jiyo suna dubanta don fargaba Umma kam kasa magana tayi sai malam ne yayi karfin halin daka mata tsawa lokacin data iso tafada cinyar ummanta tana dariya Ke asm'u lafiyarki ke halan kinayin haukane ko? Cikin dariyar farinciki tace yi hakuri baba wlh dadine yacikani nadade bangankuba ina yini ..... Umma dai kallon Autar tata takeyi bakinta yaki rufuwa domin takoma wata babbar budurwa malam yadaure yahadiye fadan domin yayi murna daganin autar tasa yace har kullum dai bazaki daina sakarciba ina mijin naki yake kuma tarike baki tana dariya Umma kinji abinda baba yace wai inamijina maimakon yace yayana? Abin yabasu dariya gaba dayansu suka bushe da dariya Umma nashafa kan ma'un dafadin Ho! Autata naga randa zakidaina shiririta wlh dai dai lokacin Auwalu da Ahmad suka shigo ma'u takalli yaya Ahmad tana yar dariya tace yaya bazankara guduba Allah yanzu ma nakagune naga Ummatane yakada kai yana murmushi baice komaiba Auwalu yayi hararar wasa yanafadin nikuwa meye laifina da aki tsayawa agaidani tarufe fuska tana dariya yaya inawuni banacin kwantai yabata amsa umma tana dariya tace duk kin cikamu dasurutu kinhanani gaisawa da dana Manya yaya akayine saigaku da daddare kuma lfy Ahmad yasami guri yazauna yana dan yake yana satar kallon ma'u da tafara raba ido yace lafiya lau munzo kawai gaishekune baba inawuni malam sulaiman ya amsa dasakin fuska sannan ya gaida Umma tashi daga nan akaballe da hira anata dariya Ma'u dadi yacikata tanaji kamar kada takoma gidan mijinta shikansa Ahmad hirar tayimasa dadi jiyake kamar kada yabar gidan iyayen nasa domin hira cikin danginsa da iyayensa tafi komai yimasa dadi malam ne yafara ankara yace kai saiyaushe ne zaku tafi ne naga kuntsaresu sai hira kuke sharba deeje Umma tayi dariya tana fadin nibabu ruwana sutafi mana aiban hanasuba ma'u taturo baki gaba kamar zata fashe dakuka nidai mukwana anan don Allah baba kwana kuma? Malam yatambaya Ahmad yace eh gobe saimuwuce dasafe Auwalu yafashe dadar5⃣ DAME AKE ADO 3 kardai Ace rayinyar nan yakoyama shiriritar ta Ahmad banda hakan kawai saiku kwana gidan bawani dalili yamike tsaye gwara nawuce ni domin naga bakuda niyyar tafiya Aitafiya yazama dole kuwa kutashi kuwuce inji malam itadai Umma murmushi takeyi idan zasu kwana anan haka takeso tasamu damar ganawa da diyarta ta domin tagayamata dukkan abinda takeson gayamata saboda takasa zuwa gidansu duk da tanason zuwa malam ne yahanata yanacewa wai me zatayi gidan yara tunda suna zaune lfy aishikenan haka ma'u tatashi tana kumbura saiga hawaye yazubomata malam ne yahau salati yace Asma'u kuka kuma todayau kindaina zuwa gidannan tunda hakane karka kara barinta tazo Ahmad saita fashe da kuka tana fadin baba kayi hakuri shiyake hanani zuwa ko ina idan natafiyau bansan randa zankara zuwaba Hakan yadace yayi kumuje dan Allah idan muka biyewa shiriritar Asma'u saikukai dare gabadayansu suka nufi kofa banda umma data kamo hannun Asma'u dasauri taja baya dadi yacika ma'u dantayi tsammani cewa zatayi tazauna saitaga tahauta dafada amman cikin nasiha kinajina ma'u yanzu kinga kinzama matar Aure ba iridaya kike darayuwarki tabayaba don haka saikin nutsu kinyi komai yanda yakamata kidaina gudu da tsalle koba ayimiki aureba yakamata kinutsu haka kobakisan kinfara zama budurwaba Tarufe ido tana dariya kunya takamata waidan ma umma batasan Abinda yafaru da itaba yau kenan Umma takatsemata kunyar kinga bude idonki muyi magana kinga babu lokaci tabude idonta tana kallon umman nata Umma taci gaba da magana cikin hanzari yaya batun girki kin iya yanzu kullum idan yayanki yazo natambayeshi sai yace wai kin iya tayi dariya na iya umma na iya dafa indomie da shikafa da taliya rannan har miya nayi Umma tayi ajiyar zuciya haryanzu dai dasauranki zansiyamiki littafin koyon girki zanbaiwa yayanki yakawomiki muje kada sugaji da jiranki sukayi hanyar fita dasauri Umma tanaci gaba dayimata fada saida suka fita waje sannan takalli umman nata tace Umma shikuma yaya bakiyimasa fada kice yadinga barina inazuwa gida sannan yabarni bakoma makaranta dan Allah Umma umman nata tayi shiru damuwa tadan bayyana akan fukarta tace A ah babu maganar zuwanki gida kullum yanzu baikamata kifara yawoba kibari sai nangaba to Umma makarantar kumafa kinsan yayane yakecewa zanzama likita daidai lokacin dasuka iso wurin su Ahmad dake tsaye asoron gidan maganar ta karshe tadoki kunnawansu gabadaya ma'u tayi shiru ganin duk sunzubamata ido sai takama ina ina gaban Ahmad yayanke fadi domin indai ma'u tahadashi da mahaifiyarta akan maganar makaranta tagama dashi domin bazai iyaja da maganar mahaifiyarsaba sam maganar malam takatse musa fargabar dayake ciki kashiga kugaida jibril mana Ahmad yakalli malam dasauri ma'u taturo baki gaba kamar zatayi magana maganar umma takatseta malam ai inaganin yanzu sunyi bacci kosunyi bacci aizasu iya zuwa sutashesu sugaisa dai kushiga kugaidasu malam yabata amsa Ahmad yashga gaba ma'u tarufamasa baya Abin mamaki saisukaga lami tafito daga bayan kyaure soro sumi sumi babu kunya balle tsoron Allah Ashe labe takeyimusu daman tasan kuma idan suka shigo gidan mijinta zaifara nemanta Umma da malam sukabita da kallo lokacin dasu Ahmad suka shiga gidan tanajin hirarsu sanda taji sungama zasu tafi tafito dagudu talabe abayan kyauren bata taba zaton zasu shigo gidanba Lami tawuce sum sum tanufi cikin gidan kaitsaye malam yabita da kallo baki bude Umma kuwa salati tasanya tana fadin oh ni deeje Allah mai iko baka damu da mutumba ammanshi yamaida lamarin rayuwarasa gabadaya akanka malam yadagamata hannu ganin tafara masifa yana fadin kinga ya isa wuce muje ciki mukwanta deeje tayi kwafa tawuce ciki tana huci ta gyada kai malam yabita duk ransa yabaci amman yana kokarin boyAbdullahi yusuf maitama DAME AKE ADO part 13. Asma'u da Ahmad suka shiga gidan suna kwallah sallama jibrilu yafito daga cikin daki yanagoge idonsa dakokarin gano masu sallamar domin akwai haske wutar nepa mamaki yadan bayyana akan fuskarsa yabude baki yana fadin wai wanake gani kamar Asma'u tadan kalli yayan nata tana murmushi nice baba ina yini lafiya kalau Asma'u Ahmad yadan durkusa dasauri yana fadin baba inayini jibrilu yakalleshi dasauri koshi yasauya amman sauyawar ma'u dagirmanta yafi bashi mamaki kwarai dagaske danshi yana dan ganinsa jifa jifa yana Amsa gaisuwar Ahmad yana kallon ma'un kafin yafara kwallawa lami kira saigata ta bullo simi simi cikeda borin kunya yakalleta cikin yanayin tuhuma daga inakike haka kuma lami? Gabadaya suka kalleta suma saitakama susar keya nadan leka wurin dijene nasamo ashana yakada kai yanafadin oho! Malam jibrilu yacigaba da magana ga Asma'u sunshigo gaishemu yamaida subansa ga Asma'u waiyaushe kuka iso gidan nema? Ahmad yace bamujima dazuwaba yamike tsaya bari muwuce dare yayi Allah yatashemu lfy cikin hanzari mlm jibrilu yace Ameen wani irin dadi yacika ransa ganin yanda ma'u tazama sukayi musu sallama suka kuya sukanufi kofar fita daga gidan shikuma yabisu da kallo yana kada kai Lami kuma tabisu dawata uwar harara kamar idonta zaifadi tasaki uban tsaki wanda harsaida yaran suka jiyo ma'un ce tawaiga dasauri amman yayan nata yajata suka wuce malam yamaida kallonsa akan lami kekuwa lafiyarki kike wannan tsaki saikace wata tsaka A a macijiya ba tsakaba tabashi amsa tana murguda baki yakada kai yashige daki yanafadin saikuma kiyi Lami nibacci nakeji Duk wani taimako da dabara Ahmad yakoyama ma'u yanda zata tsabtace kanta tun tanajin kunya hardai tasaki jikinta dashi bata iya boye masa komai domin randa jininma yadauke saida ta taddashi yana kallo tace yaya kasan wani abin dadi kuwa yakada kai yana murmushi yau jinin yadauke gaba daya yayi murmushi ho ma'u waton andaina jinkuyata ma kenan yanzu ko? Shikenan saiyin wankan haila kin iya ko ta isa kusadashi tazauna tana murmushi na iya yaya tun amakarantar islamiyya nakoya mana saidai wanka yanadayawa Akwai wankan janaba Akwai na hailah dana wankan biki dasauransu Toni wanne zanyi kodayake aiduk iri dayane saidai niyace tabambata ko? 7⃣ DAME AKE ADO 3 Yadaga kai hakane kezaki yi wankan haila ne don haka saikice nawaitul guslul haila farillah sannan saiki fara yin wankan tunda kince kin iyako tadaga kai na iya mana itakuma janabar mece ita ta tsareshi da ido tanason jin amsar da zainata shikuma duk yarikice yama rasa mezaicemata ma'u datambayar tsiya take amman bari yayi mata baro baro yahuta kinsanme akeyi idan anyi aure tsakanin miji da mata kamin yakai karshe tace nasani mana wanke wanke da shara ko? Baisan sanda yagashe da dariyaba yace bawannan bane raya sunnar ma aiki ne aure takuma katseshi raya sunnar ma aiki kuma yin sallar dare ko Azimin litinin da Alhamis duk basu bane bari nanumiki raya sunnar ma aiki saiya kamo hannunta yajata jikinsa ya kankameta domin hakan zuciyarsa ta aiyanomasa yayi tuntuni yaturo bakinsa cikin nata jikinta yadauki rawa tsoro yakamata firgici yashigeta takama kokarin kwace kanta dason fasa ihu amman tagaza shida kanshi yaji wani yadarsu azuciyarsa yasaketa dasauri jikinsa amma yana rawa tafara daja dabaya kamin tafasa kuka tanaganin anyin irin wannan amman cikin fina finai wanda aganinta sai yan iska ne sukeyi meyasanya yayanta zaimata haka kunya dafar gaba duk suka baibayeshi waiwane irin rashin hankaline yajagoranci zuciyarshi ya aikata hakan ga ma'u yarinyar dabatasan komaiba yamike ya isa inda ta takure tana sheshshekar kuka ma'u meye abin kuka kuma wai bakisan meye aure bane wannan abin danaimiki shine soyayyar aure bashi bane wannan iskanci ne turawane keyinsa acikin film yadafe kai dadamuwa wai wace irin yarinyace ma'u gata haihuwar birni kuma yar makaranta wadda yakamata ace tasan komai amman ba abinda tasani yagyara murya yana shirin lallabata amman tini tafice daga dakin tanacigaba da kuka yabita da kallo yama rasa mezaiyi washe gari dasassafe yashirya yafice gurin aikinsa yabarmata rubutu atakadda ganin bata tashi daga bacci ba yau basu kwana daki daya ba ma shi falo yakwana don ganin duk tafirgice dashi zuciyarshi fal tunani kamar yanda suka saba kullum saisunyi meeting kafin sufara aiki da manajojin gidan man sannan ayi lisafin abinda ke cikin litar kowa yau mai gidan manne baki daya da kansh yazo wato ALHAJI NURA KWANGILA YAN LEMAN duk ma aikacin dayaganshi sai gabanshi yafadi domin yariga kowa isowa Ahmad kusan nakarashe a shigowa gabansa yayanke yafadi amman daya dubi wayar hannunsa yaga haryanzu bakwai bata karasaba yadanji dadi aransa domin yasan baiyi latti ba bayan duk sun taru babban manaja yasanardasu yabude sabbin gidan mai a legas yanason zai dibi wasu dagacikin ma aikatan suje suhadu dawadanda za adiba sabbi acan suyi aiki natsawon watanni ukku dasu harwa dancan susami gogewa don hakan kowa yakasance cikin shiri sunansa zai iya fadawa 8⃣ DAME AKE ADO 3 Dawannan yayi sallama dasu yatafi kusan kowa bayason sunanshi yafada dan bamaison yayinisa da iyalinsa musamman shi Ahmad dayake da danyar amarya shakaf inazaiwuce yabarta har tsawon wannan kwanakin donhaka afili da cikin ranshi yake addu ar Allah yasa babushi din yanagab datashi daga aiki yaya Auwalu yakira wayarshi bayan sungaisa Auwalu yace idan yatashi daga aiki yabiya tacan gidan ya amsa dato sukayi sallama sanda ya isa gidan yaya Auwalu matarsa hafsa tashiga tsokanar shi tunyana ramawa harbakinsa yayi shiru datafara hadawa da matarsa yaya Auwalu yace kinga hafsa idan zaki taimaki yaron nan kibashi abinda kikace to idan kuma bahakaba yayi tafiyarshi tamike tana dariya tashiga cikin daki minti biyu hafsa tafito daga dakin hannunta rike da bakar leda takaraso wajensu tamika masa Amshi nan kakaiwa ma'u tayita karatu Haus a Novel ne yadan waro ido DAME AKE ADO part 14. yadan waro idoí ½í¸³da mamaki wai kina nufin littafan soyayyane eh sune tunda yayanka yabani lbr halinda kuke ciki da ma'u naga babu mafita bayan wadannan littafan tayita karantawa yakarba yana jijjiga kai cikin ranshi yana fadin NAYI ZATON AI BABU KOMAI CIKINSU SAI HIRAR SOYAYYA MARA KAN GADO AMMAN DAI BA AKIN TA MUTUM Yayi godiya sannan yayi musu sallama zaiwuce danyaga dare yanashirin yimasa lokacin daya isa gidan saiyatarar dayara afalon suna kallo amman yana shiga yaran sukafice domin tun randa yayi musu barin mahaukaciya suke jin tsoronsa yatsaya abakin kofa rike da labule yana kurawa ma'u kallo data kauda kanta gafe tanawasa da yatsun hannuta ma'u baki ganni bane naganka mana sannu dazuwa yafada afili aranta kuwa cewa tayi mezan maka kuma yayi murmushi don shi mailiafine a gurinta yakarasa kusa da ita yamika mata ledar dake hannunsa karbi wannan inji Aunty Hafsa tace kiyita karantawa harkigama dasu duka taleka ledar taware ido duk wannan saikace wata jaka nadai karanta wasu kawai duk yanda kika gani haka zakiyi makika dafa agidan ne dan wake mana dan wake ma'u dawannan daren yatambaita da damuwa babu kyaune cinsa dadare yaya? Tamaida masa tambayarsa A'a banceba zubomin amman kadan tamike tanufi kicin yadafa kai cikin ransa yana Addu'ar Allah yasanya ma'un tasauya sanadin karance karance kamar yadda Aunty Hafsa tafadamasa Washe gari bayan yafita aiki tayi shiru tunani duk yacika ranta domin babu yaron daya shigo mata kusan kowa yana makaranta tunanin kawayenta yafadomata arai tana tuna irin rayuwar dasukayi abaya koyaya suke yanzu ta tambayi kanta acikin zuciyarta idonta ne yaciko da kwalla damuwa fal acikin ranta can sai littafannan suka mata arai tamike da sauri tanufi daki dasauri tadaukosu tazabi daya daga cikinsu tahaye kujera tafara karantawa wasa wasa littafin yayimata dadi hartakasa ajewa koda yan hira tata sukazoma yau bata kulasuba ko Abinci rana bataciba dan bata iya tashi tagirkaba balle wanke wanke ko shara saida taga yayan nata nagab da dawowa sanna tamike tafara gyara gidan soyayyar jaruman littafin tayi matukar burgeta kuma takayatar da ita domin har sunyi aure sunfara gudanarda rayuwar aure nan gurin kam shima tadade tana tunani wannan shine rayuwar Aure kenan ? Har yayan nata yataddata bayan sallar magariba tanata karatu yayi murmushi ganin yanda tagwagwafe yakula batasan ya isoba ma yayi gyaran murya tamike dasauri tanayimasa sannu dazuwa yaya akayi kanwata dadadi kenan littafin ? Dadi yaya kayi wanka kaci abinci nabaka lbr akwaidadi wlh yakada kai kawai yawuce yanacin abinci tanabashi lbr littafin datake karantawa Ranshi yayi wasai domin tafara sakar masa jiki kuma yagane karatun zairagemata da kadaicin makaranta haka yayitajin lbr yana kada kai kwanaki kusan ukku kullum idanyadawo aiki da lbr dazata bashi yau yadawo ransa acunkushe domin yana daya daga cikin wadanda Alhaji Nura kwangila yasanya ayi tafiyar legas dukkan abinda zainisantashi da ummansa da ma'u baya kaunarshi domin kullum kafin yatafi aiki saiyabiya duk da sammakon dayakeyi itakanta umma harta saba don haka kodata idarda sallar asuba bata komawa bacci saita tashi takama aikace aikacen gidan yau ma'u tanata bashi lbr amman sam hankalinshi baya tare da ita har tagano wani abu yanadamunsa tace yayana kobada lfy ne? Dasauri yadago kai yadubeta eh banajin dadi ne ma'u gaba daya yanayinta yasauya zuwa damuwa tamike sannu yayana me zankawo maka? Kwantar da hankalinki nasha magani ma kan yadan fada inasodai inje wurin ummane yanzu Amman dai danizakaje ko? Takatseshi ciki hanzari dasauri yace A ah nikadai zanje yayi dan tunani yanason zuwa da ita amman yasan zuwa da ita din zaisanya sukasa samun natsuwa ganin bashida mafita yadubeta yace bari nakiramiki A'ilon gidan kasa kuyi kallo kinyada dasauri tace eh nayarda kirata..........Am yaya namanta yaufa hajiya tazo takawomaka kaya masu yawa nima haka kuma tace tanagaisheka bari nakawo maka kayan yasan kowace hajiyace hjy Aminansace maisonshi dasauri yace kinga bari nadawo yafice dasauri Acan gidan umman shi tashiga damuwa dajin antura Ahmad legas har tsawon wattani ukku harsaida fuskarta tanuna hakan afili tace babu kuma wani abu daza a iyayi akan dole saikunje din subasuda tausayi ne bausan kanada iyali ba? Malam yayi murmushi afili yace wai yaushe zakiyaye Ahmadu ne Deeje? Abin yabasu dariyaí ½í¸ itada Ahmad din gabadaya tace Au! Hakama zakace malam baka tunanin nisan dazaiyi? Meye abin nisa ga namiji don yatafi legas yanzu idan yasami aiki acan bazaki barshi yajeba kenan? Tayi ajiyar zuciya insha Allahu kozaisamu aiki anan zaisamu malam kadinga yin irin tunanina mana Aitunanin kowa dabanne nasan dai bazasu cinye mikishiba acan yanda yaje guda haka zaidawo guda kiyi masa addu'a dasanya albarka kawai takada kai shikenan yanzu ne tafiyar Ahmad yagyara zama wajen jibi sukace insha Allahu inatunanin kawo ma'u gidanma gobe kafin indawo! Gida kuma akanme? Malam yakatseshi da sauri A ah hakan bazai yiyuba kabarta adakinta tasaba da aure yanzu tazama matar aure dole takoyi juriya irinta mace mai aure yayi danjim kamar bazaiyi maganaba saiya daure yace gidan zaimata girma ne gashi tanajin tsoro kuma akwai kurciya haryanzu atare da ita inaga kamar zamanta zaifi tunda kwanakin dayawa. Maitama DAME AKE ADO part 15. Umma kam tana bayan ra ayin Ahmad amma tagaza cewa komai Don kada malam yayi zaton hada baki sukayi Amman acikin ranta tana addu'ar Allah yasa ya amince din hakan ne kadai mafita malam yace tau shikenan tunda kana ganin hakanne mafita baijima agidanba yayi sallama dasu domin hankalinsa yanakan ma'u daya baro akwai yankallo agidan yabarsu dan haka yatada babur dinsa yanufi gida yana isa yahango kofar soron ansakayota saidai wurin bakikirin kasan cewar andauke wutar nepa yakafe babur dinsa agefe yasauka domin yatura kofar yashiga yatabbatar babu wani abu akan hanya cikin soro saida ya isa cikin soro yafara kokarin kunna yar cocilan din dake hannusa dai dai lokacin dayaji wata uwar kara yarude yafara kallon inda karar kefitowa acikin soron ne daga gefe kuma muryan ma'u ce cikin sauri yace ke menene ma'u nine Ahmad cocilan din dake hannunasa wacce yake kokarin kunnawa tafadi saboda damkar datayi masa tana sheshshekar kuka kamar zata shide cikin firgita yace ke menene meyafaru tana kankame ajikinsa take fadin wlh kamar tafiya akeyi acikin gidan nakasa zauna..........ina A'ilon take? Anadauke wuta kanenta sale yazo kiranta nayita magiyar tatsaya tace wai dukanta za ayi shine nabuya abayan gado saina dinga jin tafiya nagudo nadawo soro naboye cikin kuka take bayanin yakasa cewa komai domin rikon datayimasa tasaukarmai kasala dawani iri shauki da kyar yadake yace shikenan sakeni nashigo da babur dina babu komai tsorata kawai kikayi taki sakinsa takuma kiyin magana har lokacin jikinta rawa yake yakara kwantar da murya yace bari badauko cocilan din tadan sakeshi amman tana gabansa yasunkuya yafara laluban cocilan harya samu yakunna yahaske fuskar ta dariya takamashi ganin tayi miyau da majina yakauda da kai yana dariya Ho ma'u hankalinki saike bari nashigo da babur din nifa tsoro nakeji Allah kuwa yaya yamikamata tocin rike harnashigo dashi haka tatsaya badon tasoba haryashiga da babur din yashige gaba tana biye dashi abaya suna shiga aka kawo wuta yakalleta yana rike da babur din haryanzu yanayinata dariaya togashinan babu komai agidan matsoracya kawai itadai batace komai komaiba yadauki buta yanufi bandaki saita tashi dasauri harda dangudunta yawaigo dasauri malama bandaki zakibini kuma A a tafada dasauri yakuma fashewa dadariya kinga dun Allah kikwantar da hankalinki kiyita addu'a babu komai bari nafito dahaka yasamu yashiga bandaki yanaci gaba da dariya a zuciyarshi daren ranar tana gado shiyana kasa kwance takundundune kamar za ashigo adauketa ma'u akwai kurciya da shiririta yanason yayi maganar tafiyarsa da ita amman yanda take afirgice dinnan yasan bazaisami komai agareta ba don haka ya kyaleta dasafe baijima dafitaba yadawo domin manaja gidan man yace sudawo gida kowa yayi shirin tafiya gobe sannan yadan basu kudaden dakowa zaibarwa iyalinsa ma'u anmike kan kujera anata karatu Allah yasanya takammala aikinta gabadaya tajiyo sallamarsa tadago da mamaki tana kallon kofar dakin tamike dasauri taleko shine din kuwa damamaki tace yaya Ahmad yauhar kadawo dawuri haka 1⃣1⃣ DAME AKE ADO 3 yakada kai banyi aikiba ne nadawo nayi shirin tafiya ne tafiya kuma ta tambaya dasauri kinga shiga ciki kizauna nayi miki bayani babu musu takoma tazauna shima yasami guri yazauna yafaramata bayanin dalilin tafiyar haryakai karashen bayanin tayi shiru dadamuwa kamar zata fasa kuka amman yaya bazan iya zama nikadai agidannanba katafi dani can dan Allah yakauda kai A a bazanje dakeba anan zaki zauna kefa matar Aurece baikamata kidinga yawo ko inaba abinda bajimawa zanyiba darana saikiyita wasa dasu A'ilo idankuma dare yayi saiki kulle gidan kisanya sakata babu wanda Zaishigo ai tadafe kirji dan Allah yaya kayi hakuri wlh bazan iya kwana nikadaiba saidai idan kayarda nadinga zuwa gidansu mairon gidan kasa nakwana yabata ran wasa gidan kuma fa yakwana shikadai babu kowa banyardaba gaskiya dole kizauna kedaya tayi shiru tarasa mezatace ma amman dai idonta yafara zubo da hawaye dasauri yamike yanafadin lalala kada kiyi kuka yar Amaryata tsokanarki nakeyi tashima kishirya kayanki mutafi gidansu umma acanzaki zauna tamike tadaka wani uban tsalle tana ihu yabude baki yana kallonta lallai yariya zakija afasa tagimtse murnar yi hkr yaya nadaina bari naje nafara hada kayana ko ajikinta batajin komai akan tafiyarsa domin damar komawarta ga ummanta tafi komai yimata dadi yana kallonta tafice yana kallonta yafada kujera ya lumshe ido baison rabuwa da matar tashi ayanzu zaman dasukayi nawatannin nan yashaku da ita fiye da tsammani kobabu komai yakaso sokancinta danya dinga cindariya kawai amman yaya ya iya rabuwa tazama dole Amotar haya taxi suka tafi domin kayan dayayiwa su umma siyayya nakayan abinci da kuma kayan sawar ma'u sunada yawa ma'u kuwa murna takeyi kamar zata shide shidai kawai yake ransa babu dadi Acan gidansu umma ma haka tadinga murna tanajin kamar za asanyata agidan Aljanna umma tana kallonta tana murmushi shikuma jiyake kamar kada yatafi Anan yaci abinci har wajen karfe goma baibar gidanba saida malam yayimasa magana Ahmadu yakamata kaje kakwanta haka domin samun damar tashi dawuri tunda kace sammako zakuyi? Yayi shiru dadamuwa saiyakejin kamar yarabu dasu kenan har abada faduwar gabanshi takaru idonshi yataru da kwalla malam yayi murmushi nason basar dashi Ahmad saikace wani karamin yaro don Allah ka kwantar da hankalinka sai alokacin jikin ma'u yayi sanyi tazubawa Ahmad ido wanda kansa ke kasa itakanta umma kauda kanta tayi gefe don batason ganin fuskar dan nata Cikin rawar baki Ahmad yace naji gabana inazaton babu Alkhairi acikin acikin tafiyar nan tawa gwara nafasa nasamu wani aikin kul nakoma jin wannan maganar Ahmadu tunranda kafadamin maganar tafiyar nan nasanarda yan uwanka mukayita Addu'a saikuma da aski yazo gaban goshi sannan zakace kafasa ban amince dahakan ba sam kaje kayiwa mamanka hajiya Amina sallama tukunna naje dagacan mukayo nan tace agaiaheku muna amsawa maza tashi kawuce ya mike yana kallon ummansa da har lokacin kanta yana kallon wani sashin yace umma zanwuce sai alokacin tawaigo idonta yacika da kwalla tace Allah yakiyaye hanya kakula da kanka Ahmad kakula da Addininka da matsayinka na musulunci aduk inda katsinci kanka Allah yayimaka Albarka kalmarta ta karshe tafi komai dadi agareshi yanzu da agidan marayu yatashi waye zaidinga saiyamasa Albarka kamar haka yayi kokarin goge kwallar data zubomasa yanafadin Amin Umma nagode baba natafi Allah yatsare yakiyaye madinga gaisawa ko awayar yayanka ne 1⃣2⃣ DAME AKE ADO 3 Ma'u tanazaune tamkar andasata gabadaya murnarta takoma ciki saizare idonta takeyi saiyanzu takejin ciwon tafiyar yayanta Ahmad kalamanshi sunsanyayar mata dajiki har kwalla yacika idonta Umma tadubeta tace bazakije kuyi sallama bane? Takalleshi dasauri maganar umma tasanyata mikewa dasauri babu shiri donbin bayan Ahmad dayafice dasauri yana goge idonsa cikin gaggawa tabishi donganin yanufi soro kaitsaye dasauri yaya Ahmad takwalla masa kira sanda ta isa soron taga zaifice yatsaya gami da waigowa da sauri yakalleta ma'u yaya akayine? Cikin dakiya dakokarin boye damuwa yake maganar yaya bamuyi sallama ba zaka tafi naga kamar ranka yabaci yaya dan Allah kayi hakuri idan nayimaka laifi yayi murmushi dajindadi lallai ma'un shi tafara samun hankali da natsuwa ya isa kusa da ita yariko hannunta yanajin kamar yarungumota jikinsa amman gudun abinda zaifaru yasa yadake cikin dakiyar zuciya yace ma'u bakiyiman komaiba amman inajin kewa dakadaicin rabuwa daku naga kamar murna kikeyi domin kidawo gidansu Umma ko? Tasunkuyarda kai kunya tarufeta amman saita girgiza kanta alamar a a bahakabane ba yakura mata ido cikin hasken dayaratso soron yanaci gaba da magana kidinga yiman addu a ma'u naso kamin natafi nasaimiki waya amman banida kudi kudin danasamu nayiwa su umma siyayya nasanyamiki wasu kudi cikin kayanki idan kina bukatar wani abu kidinga siya kada kitambayi umma ko baba kinjiko tadaga kai alamar to yajanye hannunsa daga cikin nata yanadan ja dabaya yace sainadawo ma'u yajuya dasauri yafice ma'u kurawa kofar ido kamar katabishi saiyanzu takejin kaunar mijin nata haka takoma gidan babu kwari balle karsashi ajikinta Gasu Ahmad saidare suka isa garin legas kaitsaye gidan dazasu sauka suka isa dayake amotar kamfaninsu suka tafi gidane irin ginin legas amma babu laifi yanada kyau kowa da dakinsa daban akabashi dakyar suka iya cin dan abinci suka kwanta baccin gajiya washe gari kuma dasafe akakwashesu amotar kamfani akakaisu sabon gidan man maisuna YAN LEMA PETROLEUM & 10 dayake duk sunan gidajen man nasa dayane suntarar da ma aikatan gurin wanda aranar zasu fara aiki babban gidan mai yagina wanda yafi nacan kasancewar shikadai ne dashi alegas kuma nafarko ajahohin kudu kuma ance shine nafarko dayafara ginawa dayake kuma yanada kishin jama arsa HAUSAWA kusan kaso sittin naginin duk hausawane saisauran yarbawa basusha wahalar fara aikinba kasancewar anrage kudin litar dakaso biyu (2%) cikin (100%) saboda gidan man sabone haka yasanya akayita samun masu siya Awannan ranar dakyar Ahmad yasamu dan lokacin yin tunanin ummanshi da ma'unsa kida yakema lokacin dayana aikin mayakan tunodasu jefi jefi kuma aduk yayin dayatuno dasu saiyayi murmushi 1⃣3⃣ DAME AKE ADO 3 KWANAKI sukai tazuwa suna wucewa zuciyoyo nakara shiga cikin damuwa Awannan lokaci ma'u takara fahimta meye Aure meye miji domin yayi nisa acikin karance karance sannan Umma ta ajiye kunya tanayimata bayanin aure meya kunsa menene alfanunsa wannan yake karasanya takara son mijinta idantayi kwance agado saitayita tunaninsa burinta baiwuce yadawoba musamman lokaci da hajiya Amina tazo ta taddata tana karatun littafi tasayomata jaka guda tace ayitayi ananma tasamu abubuwan karuwa dayawa takaicinta daya tunda Ahmad yatafi bata tabakoda jin muryansa ba kullun sai dai yaya Auwalu ko yaya sani yazo yabasu labari yace sunyi waya dashi sungaisa tanaso tace abatashi idanyakira wayar amman vazata iyaba sam sukuma sunkasa karar subata din Ahaka har watanni biyar suka cika zuwa lokacin ma'u takoyi abubuwa masu dama yacika tazama budurwa domin tacika shekaru sha shida kenan gashi kullum umma saita bata kunun daka irin na MUTANEN NIJAR da tukudi tunbata son sha haryazame mata jiki dukkan halittar ta takammala fitowa tazama CIKAKKIYAR MACE Idan tatuno abinda tayiwa mijinta abaya saitayita dariya daganin wautar kanta gaskiya Ahmad tayi kokarin zama da ita shekara daya dawata bakwai amman baiyimata komaiba tatabbatr yayan nata namatukar kaunarta yanzu saidai abinda kedamunta baiwuce rashin dawowarsaba kullum sai umma tayi mita domin ita kanta tagaji amman sai yaya Auwalu yace ba abasu damar dawowabane saidai duk karshen wata yana aikomusu da sako wannan abin shine yake farantawa malam rai kwarai dagaske domin ayanzu kobaifita kasuwaba bairasa abinda yasanya abakinsa Albarkacin darajar iyaye Ahmad yana cikin tsananin damuwa datakura saboda rashin iyalinsa da iyayensa Ayanda Alhaji nura yayi musu Alkawari watanni ukku zasuyi amman gashi harsun shiga watanni shida kuma watan yana neman karewa ba acemusu komaiba hankalinsa duk yatashi haryarasa abinda zaice agayama ummansa da ma'unsa amman dai yasan sunacikin damuwa kwarai da gaske lokacin dasuka cika watanni bakwai yagama fusata baijin komai bayan ya isa ga ahalinsa don haka lokacin da Alhaji nura ya iso gari donya duba yadda abubuwa suke tafiya Ahmad yaji kamar dukkan matsalarsa takare dan haka lokacin da yazauna mitin dasu yakudiri aniyar fadin abinda keransa bayan yayi yabo dajindadin yadda akasamu cigaba da abinda ake bukata ga gidan man yayimusu albishir dasamun karin albashi maitsoka murna dajindadi yacikasu amman banda Ahmad domin yawanci wadanda sukazo kamar basu damu da iyalinsuba dayawa sunsaki jiki suna mu amalarsu harma dasu ajiye daduro! Bayan Alhaji nura yagama bayaninsa Ahmad yadaga hannu yana fadin idan yallabai yabani dama inada maganar da zanyi gabadaya kallo yakoma wurinsa abokinsa isuhu haryadan zunguresa alamar kada yayi magana domin yasan abinda zaice saboda kullum saiyayi masu korafi amman Ahmad baikulashiba Alhaji yakada kai kanada damar yin magana Ahmad yamike tsaye yafara koro bayani yallabai kamar yanda kafada abaya kafin muzo garin nan kace watanni ukku kacal zamuyi amman gashi harmunshiga wata na bakwai kuma watan yanagab da karewa amman babu labarin tafiya gida shine nakeson ayiman bayanin yanda abin yake Rufe mana baki mara kunya kaikadai kake da iyali kobakin magana bakaganin wasu neman aiki sukeyi sun rasa idon su arufe manajan gidan man yafadi haka bayan yakatseshi cikin tsananin bacin rai da masifa Ahmad yace hakane kasan babu wanda ya isa yabaiwa wani aiki idan ba Allah yakaddara ya aminceba DAME AKE ADO part 16. Inaji ajikina aikin danakeyi yanacikin kaddarata sukuma wadanda basu samu ba hakan aka rubuta alittafin kadararsu dan haka zaka iya yanke kowane irin hukunci akaina babu tsoro balle fargaba Ahmad yasake fadar maganganunsa manaja yakara fusata dajin abinda Ahmad din yafada masa batare dawani shakkarsa ko fargaba ba gurin kowa yayi tsuru tsuru cike da tsoro masamman isuhu abokinsa manaja yanuna Ahmad da dan yatsa cikin tsananin fushi da fusata kaikada kasake kayiman rashin kunya daman najima daganin take takenka dan matsiyata ba,za...........kai manaja dakata Alhaji nura kwangila yadoka masa tsawa jikin manaja yadauki rawa yaguntse baki da sauri domin yau dai asirinsa yatonu duk yanda yaso kuma yakare abin yafaskara Alhaji nura yana huci yakalli ma aikatan yace Acikinku waye yasamu manaja damaganar yanaso abarshi anan idan har za adinga bashi alawus din dazairika aikawa iyalinsa? Kowa yayi shiru ana kallo kallo manaja yafara hada gumi jiyake kamar kasa tatsage yashige cikinta saboda tsananin kunya Alhaji nura yabisu da kallo daya bayan daya yace babu sukayi shiru wanda yatabbatar masa da babudin yakada kai cikin takaici Nayi matukar bakin ciki da manaja ya aikata wannan zalunci da sunana tun lokacin dakuka wata ukku nasameshi damaganar komawarku ga iyalinku idan kuma da maibukatar zama ana legas yacigaba zamansa amman sai mutumin nan yace min aiduk kunce anan zaku zauna indai za adinga baku alawus kuna turawa iyalinku nace yaware wasu kudi yadinga baku dukkan sati ashe karyace yashirya min bahaka bane gaskiyar lamarin ba naji dadin wannan maganar dakayi Ahmad inason mutum irinka dabayajin tsoron fadin gaskiya duk dacinta kai manaja katafi gida nadakatar dakai tsawon wata ukku babu Albashi mataimakinka zaimaye gurbinka!!! Kukuma dukan maibukatar tafiya gida saiyafara shiri cikin satinnan saikuwuce sannan albashinku yana nan yanda yake dakarin danayimuku nagode manaja yadafe kai da tsananin tashin hankali dakatarwa wattani ukku babu Albashi dame zaidinga ciyarda iyalinai har wannan lokacin balle kuma kudin dazainemi mata domin duk abinda yake samu jikin matan banza yake karewa Ahmad kam yafi kowa farin ciki saigashi yafara shirya jakarsa domin babu komai acikinta sai tsarabar kayan ma'u isuhu yana zolayarsa yanda yayi magana da babban manaja babu tsoro mutumin da kowa yakejin tsoronsa da shakkarsa baisanarda kowa zai komo cikin satinba domin yanaso yayi musu bazata ne kawai Ranar assabar da daddare suka bar garin legas wajen karfe tara da rabi nasafe suka iso garin kano motarsu natsyawa yaji wani farin ciki yacikashi aranshi umma da ma'un sa kawai yake son gani yana kokarin shigowa gidan yaci karo da Amina kanwar raliya taci kwalliya tayi bilicin kamar wata karuwa gabansa yafadi domin kallota da kamannita sun tunomasa da raliya gabadaya takoma kamar raliya cikin rawar baki tace masa Ahmad sannu da zuwa batare da ya kalletaba ya amsa da yauwa yashige ciki dasaurinsa tabishi da kallon mamaki baki abude gaba daya yasauya yakara haske da kayau kamar bashiba saitakoma ciki dasauri domin tabaiwa babarta labari itada kullum take addu a Allah yasanya jirgin kasa ko mota yatakeshi yamutu koyanfashi sutaresu su harbeshi domin tafara kishi daganin yanda ma'u take komawa kullum kuma agidan ba ada magana saita Ahmad saikace shikadai da aduniya ma'u tana durkushe tana wanke wanke da T. Shirt ajikinta da dogon siket tana yar wakarta tajiyo sallamar Ahmad tadaga kai dasauri da mamaki saita fasa ihu dajindadi tana fadin yaya Ahmad dagaske kaine dan Allah tawurgarda kwanon dake hannunsa tanufeshi dagudu ta kankameshi tana ihu umma dake kicin tajiyo tafito fasauri ta leko dadi damamaki yacikata tayi wurgi da ashana tana fadin Ahmadu kaine da tsakiyar ranar nan kesakeshi mana kinbi kin kankameshi kamar zaki kadashi kunya takama ma'u tasakeshi dasauri shi kam ji yayi kamar sudauwama ahaka 1⃣5⃣ DAME AKE ADO 3 Amman dai yadake ya ajiye jakar hannunsa dasauri ya isa ga ummansa yadurkusa yana gaisheta umma tadinga kallonsa cikin farinciki dajin dadi tana amsawa jitakeyi kamar tagoya shi abayanta don dadi ma'u kuwa tsaye tayi tanata kallonsa gaba daya yayan nata yasauyamata yini akayi damurnar dawowar Ahmad su ma'u ankulle cikin daki sai hada kaya takeyi gaba daya zaman gidan umma datake doki yanzu ya isheta domin shagwabar datakeyiwa umma da yanzu duk tadaina kuma tanason gwada irin abinda take koyo alittafi agidan mijinta musamman girke girke data kware yanzu akanyinsu umma tashigo dakin daukar wani abu tahango ma'u anata hada kaya dariya taso kwace mata amman saitadake tace Asma'u menene kikeyi haka kuma? Babu kunya tace Umma kayana nake hadawa koba yanzu zamu komabane ? Umma tarike haba damamaki tana kada kai Au har zaman gidan namu ya isheki kenan? Ma'u tarufe fuska kunya takamata tana dariya umma tayi murmushi aisaiki huta da hada kaya domin bayau zakukomaba saigobe anje angyara gidan tafice tabarta murnar ma'u takoma ciki taturo baki gaba shikansa Ahmad abinda yake bukata kenan yakoma gidansa yakebe damatarsa kohira suyi amman yaya ya iya da hukunci ummansa dole yayi shirin kwanciya adakin gwaurayen gidan amman ba sukwanta da wuri ba anatashan hira dasafe kamin kowa yafito ma'u tasalara wankata sanda umma tafito domin dama koko taci karo da ita anata shafa hoda da fesa turare umma tatabe baki nashiga ukku Asma'u badai nan shirin tafiya gidan mijinki kikeyi haka da sassafe ba? Malam yadaga labule yana kallonsu bayan yadawo daga masallaci yayi murmushi tolaifi tayi kenan kefa kikaimata gori kullum yaukuma saikidamu Amman dai tabari ayi karin kumallo ko? Shima Ahmad tun da sassafe yashirya yabaiwa kowa tsarabarsa sai tamatarsa kawai yabari acikin jakarsa Umma da malam sunata zolayar ma'u da Ahmad dasuketa hada kayansu suka fice suna dariya shatar mota taxi suka dauka har kofar gidansu gidan yayi futu futu cike da tsananin kura kamar anyi shekara ba ashiga cikiba ma'u tacire gyalenta tasakale ajikin igiya tafara karewa gidan kallo tana tunanin ta inauadace tafara gyarawa ne? Ahmad yabita da kallo tunda yadawo yake mamakin irin girma da cikar da ma'u tayi saikace yayi shekara rabonshi da ita kamar ance takalli inda yake tajuya tanafadin yaya ta ina zanfarane takasa karasa maganar saboda irin kallon dayakemata tadauke kanta dasauri domin yamzu tasan irin ma anar kowane irin kallo shima yadanji kunya amman saiya dake yace wannan aikin yafi karfinki kekadai ma'u dole saina taimakamiki bari kigani saiya fara kokarin cire kayansa yana ajiyewa shima akan igiya yarage daga shi saigajeren wando da singileti tasanya hannu suka cigaba da aikintare saikarfe hudu sannan gidan yadawo hayyacinsa yanda suke bukata sunyi butu butu da kura shiya fara shiga toilet yayi wanka bayan yafito yasanya kayan da yabari akan igiya yafice domin yaje yasiyo musu take away saboda yamma tayi babu damar yin girki ayanzu yana fita itama ma'u tafada wanka bayan tafito tafara gyara jikinta dayin turare masu kamshi domin Umma wannan karon batayi sanya gurin hada mata kayan kamshi da gyaran jikiba wata kila tahimci har lokacin ma'u budurwa ce ita kamin kace wani abu gidan ya dauki wani irin kamshi maidadi dasanyaya zuciya tafara duban kayan da yayan nata yakawo mata tsaraba dukansu kananan kayane saikuma rigunan bacci saikuma kayan gyaran gashi kala kala da mayuka komai maikyau tasan yayan nata danayune amma batayi tsammanin ya iya zabe kamar hakaba saiyanzu da idanunta suka ganemata tama rasa wanne kaya yakamata tasanya domin kowanensu yanada tsananin kyau daga karshe dai ruwan idonta yakare akan wani dogon siket mai roba da alama idan akasanyashi zaikama jikin mutum rigar kuma maikama jikice kwarai dagaske koda tasaka kayan sun Amsheta kwarai da gaske kitson kanta shikune don haka yadace da kwalliyarta kasancewar tanada gashi tayi dauri dawani gyale kitson yafito tatsakiya yasauka abayanta tasanya wani dogo dankunne wanda shima yanadaga cikin kayan dayayan nata yasiyomata bayan tagama tsantsara kwalliya takoma falo tana kallo domin ankawo wutar nepa alokacin saibayan sallar magriba Ahmad yashigo gidan domin yabiya tawurin abokinsa ishak sungaisa sannan yayi yanbiye biyensa dai bata damuba domin bayan kallon datakeyi yan matan unguwar su A'ilo sunata shigowa dagaisawa suna murnar dawowarsu kaitsaye falonsa yanufa domin can yaji motsinta baifita da babur dinsaba domin yasan shima yana bukatar gyara saiwashe gari zaikaishi aduddubashi tukunna hakan yasanya ma'u batasan yadawoba saida yashigo dasallama tadago kanta dasauri ta kalleshi saitamike daga zaunen datake tanufeshi tanafadin sannu dazuwa yayana ta amshi kayan dake hannunsa tanufi cikin daki domin ajiyewa Ahmad yabita!da kallo komai najikinta juyawa yake yabude baki saikace wani sauna ANYA KUWA WANNAN MA'UNSA CE BASAUYAMASA ITA AKAYIBA ? Batasan yanayiba harya isa yazauna jikinsa yayi sanyi abinda yakeji gameda ita yadinga dawo masa ko acan legas yayi fama da irin wannan matsalar saidai yadinga dagewa da addu'a donkada shaidan yayi galaba akansa komai na ma'u yasauya cikin dan wannan lokaci kodayake kokamin yatafi yafara fuskantar wasu yansauye sauye atare da ita amman basu kai nayanzuba tamike tashiga kicin tadauko babban faranti tajuye musu Abinci dayayimusu take away takawo gabanshi ta ajiye yaya sauko muci nifa yunwa nakeji yasauko yanafadin nima haka Amman dai abaki zaki bani ko mamata? Tayi dariya takauda kai kunya tarufeta azuciyarta cewa tayi mezaihana nabaka nagwada yanda Alhaji bashir yayiwa fauziyya akanka ( TACIKIN LITTAFIN SAWUN GIWA) Amman afili bazata iyaba yayi murmushi yafara cin abincinsa yadinga janta dahira yanabata lbr abinci ikko itama tanabashi lbr abubuwan dasuka faru ahaka harasuka kammala cin abincin dukkan hankalin Ahmad yanakan ma'u ayau dai yake zaton dauriyarsa takare idan bai isa ga matarsaba komai zai iyafaruwa gareshi Ita kanta ma'u tanajin tanajin wani abu yanayawo akanta duk lokacin datakalli mijin nata domin tacika tayi dankam babu wata damuwa kota kwabo aranta amman kowa yarasa yanda zaitunkarar dan uwansa Ma'un ce tafara gudowa dakin baccinsu tasanya kayanta don akwai rigunan bacci kala kala don haka tazabi daya maikyau tasanya duk da dukkan rigunan anahango komai na mutum idan yasanya itakuma bazata iya yarda yayanta yaganta ahakaba donhaka tahaye gado takudundune ciki bargo shima baiwani jima afalo ba yabiyo bayanta saiya taddata agado kudundune ya isa kusa da ita yazauna daga gefen gado yana fadin ma'u sanyi sanyi kikejine haka? Kinga bude naga yanda rigar tayimiki dukkan kayan dabasuyimiki kyauba canzasu za ayi tayimin kyauma Allah yaya............A ah sainagani da idona bari nagani yafara kokarin janye bargon tana rikewa da yar kissa amman sai da yacire yazubawa halittar matarsa ido WAIDA GASKE DAMAN HAKA MA'UNSA TAKE? Takara kudundunewa zuciyarta nacigaba da bugawa tabbas dai abinda take karantawa cikin littafi zaifaru akanta duk da batasan awane hali yakeba shi mijinta jikinta yabata yakura mata idone don haka takara matse jikinta gabanta yanaci gaba dafaduwa yayiwata yar doguwar ajiyar zuciya yamike tsaye yace taso ma'u tayi shiru batayi maganaba kuma bata motsaba harya dan juya yafara tafiya amman saiyasake waigowa yace ma'u kina jinafa daure tashi kiyo Alwala zangaya miki abinda zakiyi bayan kinyi Alwalar Tayunkura kamar kifanya harlokacin jikinta yana nannade tarike zanin yana kallonta yakada kai yayi murmushi yawuce tayi ajiyar zuciya bayan tahango inuwarsa yagama ficewa tadafe kunci takara maida hannunta ga kirjinta dayake bugawa tayi dan murmushi sannan tamike tafito yana tsakar gida kusa da bandaki yana daura Alwala Tarakube tana jiran yakammala yayi kamar baigantaba yana gamawa yashige falo sai tanufi bandakin tashiga tajima tana sakawa da kwancewa kukan wata mage datazo wucewa daga kan soron ne yabata tsoro tashige dakin da sauri yana zaune akan sallaya ya tankwashe kafafunsa yayi shiru amman amman bakinsa yadan motsi alamar lazimi yake ta isa kusa dashi tatsaya daga bayansa yaji alamun shigowarta don haka yamike da kansa yadauko hijabin sallarta yamika mata batare da yakalletaba yace sallah zamuyi raka'a biyu ma'u yashige gaba yana kokarin tayarda sallah tabishi abaya ta tayar baija dogayen suroriba yayi sallama yajuyo yakama kanta yafara karanta addu'a ALLAHUMMA INNI AS'ALUKA KAIRAHA WA KAIRA MAJA BALTAHA AKAIHIM WA'AZUBIKA INNI SHARRIHA WA SHARRIHA WA SHARRA MA JABALTAHA ALAIHI " yayi dan shiru bayan yakammala addu'ar yana kallonta cikin kwantarda murya yace ma'u nasan kin iya farillan addini dasuka kamata kisani ko akwai wani abu dabakisaniba? Ma'u tagirgiza kai kawai yasake yin murmushi yace ma'u ai bangane mekike nufiba kibude baki kisanarda dani eh ko a'a zakicemin shine zanfahimta kuma harnagamsu eh nasani tafada da sauri yace yauwa nasan haka tashi kije kisanya rigarki dakikasanya dazu kikwanta baijira jin abinda zataceba ya mike yafice yanufi kicin dinsu yaduba yayi sa'a akwai kalanzir donhaka yadora ruwan zafi kadan yadafa shayi yasanya koren ganye shayi yashanye karamin kofi sannan ya nufi dakin yayi sa'a akwai wutar nepa fanka kada dakin nasu yanda takwanta dazu haka ta kwanta yasanya hannu yakashe kwanfitilar dake dakin yakarasa gadon yakwanta daga gefe inda yake yanajin sautin ajiyar zuciyar ma'u yadan matsa gab da ita yanadan gugar jikinta amman baishafetaba sai yace saiyace ma'u bani lbr dame dame yafaru bayan tafiyata? Tayi shiru takasa magana saidai faduwar gaban nata yadan ragu yacigaba damagana ahankali dai dai saitin kunnenta tunda kinki bani lbr bari nabaki mawa lokacin da akace andaura aurena dake sainaga abin kamar wasa kamar shiririta harna tare dake banajin komai akanki saikulawa ta kanwata sannu ahankali damuwa da tunaninki yafara shiga raina lokacin dazan tafi legas nayi tsammani nadamu darabuwa dakene domin sabo da shakuwa data koma shiga tsakaninmu saidai bayan naje nagano kaunarki ne nagaskiya yashiga zuciyata yayi dan shiru yana murmushi shidaya cikin duhu wani shauki da bakon abu nasake shigarsa yadan kara matsawa jikinta yakamo hannunta yarike kam cikin nasa yafara wasa dashi yace ma'u babu abinda nakeso aduniya yanzu bayan Allah da manzonsa da kuma Ummata kamarki tsikar jikinta tatashi yarr! Tadinga jin wani abu yanashigarta wanda bazata iya fasaltashi ba tadinga jin kamar tajuya tarungume mijinta amman saitajiyo tafukan hannunsa sun saki hannunta sunfara kaikomo cikin jikin jikinta yacigaba da magana cikin kunnenta bantaba zaton zanyiwa ma'una irin wannan soyayyarba kigayamin ma'u mekimeji akaina yanzu domin tunda nadawo naga wani abu akwayar idonki kuma gangar jikinki kamar tana nunamin wani abu nayadda.............yasake kasa da murya yana cikaba da magana ma'u kinyi wayo kinsan meye Aure kin amince nazama miji agareki nagaske ba suna ba kibarni nafara raya sunnah dake afarkon duniyata kibarni naji abinda kowa yakeji acikin aurensa ma'u yakankameta ajikinsa kamar zaimaidata cikinsa itakam tagaza cewa komai domin yayimata dukkan abin zaikashemata jikinta dazuciyarta tagamsu da amsar mijinta takaranta littafan soyayya masu dama amman bata taba karanta irin wannan soyayyar da mijinta ke gwadamata ba cikin Duniyar shauki tajiyoshi yana cigaba da sambatu da rokonta bakice komai ba ma'u kibani dama dan Allah ki amince nazama miji agareki da gaske cikin rawar baki da kyar tafurta na amince yayana domin tafuskanci yanagab da shidemata Allah mai iko kawai Ahmad yake iya ayyanawa cikin ransa Hmmm ni abdullahi kam sai ma'u other wise sai dae ku tsintoni a sambisa DAME AKE ADO part 16. 1⃣8⃣ DAME AKE ADO 3 Haryakai ma'un ga matsayin dakowace mace keshiga wato CIKAKKIYAR MACE ba ma'un kadaiba shikansa yasha wahala domin tare suka bare junansu akwali amman ma'un tabashi mamaki domin tayi matukar dauriya don haka harbacci yadauketa tana kan kirjinsa yanashafar gashin kanta dajin dadi cikin ransa gami dayima Allah godiya dayanufeshi dayin Aure harya dandani zakin dakecikin Aure gajiya da kasala suka taru sukayi musu rubdugu dan haka sunkusan makara shine yafara tashi yadora ruwa yashiga wanka kafin yafito daga wanka an idar da sallah amasallaci baiji dadin hakaba amman yasan Allah zaiyafemasa tunda ba daniyya ya aikata hakan ba saida yafarayin sallah sannan yagirka ruwa maidimi yanufi dakin har lokacin ma'u tana bacci domin tasha matukar wahala dabata taba shaba cikin rayuwarta cak yadauketa kamar yar bebi sai asannan tafarka tanajinsa takara maida idonta tarufe domin kunya tagama rufeta yayi murmushi kawai baice komaiba cikin faffadar robar daya kusa cikawa da ruwan zafi yatsundumata aciki bayan cire dan yalolon zanin dake jikinta tayi doguwar ajiyar zuciya sanda ruwan yafara ratsa jikinta amman har lokacin idonta yana rufe takasa budewa yayi murmushi yajuya yabarta abandaki tayi wanka tagasa jikinta saitaji kwarin kijinta kafin karfe 8 nasafe yayi Ahmad yagama yimusu komai nakayan karin kumallo saida yayi dagaske taci domin kunyarsa tahanata sakat shikam dariya kawai yakeyimata da tsokanarta ranar haka nan suka kareshi cikin nishadi dajindadi gami da soyayyar juna Aranar tare suka fita siyayyar kayan abinci dayake akwai dankudi ahannunsa harda karamin cooker gas yasiyamata yayikuma yimata siyayyar kayan kwalliya dana shafa dai dai karfinsa Rayuwar Ahmad da ma'u tazamo abin sha'awa domin kullum soyayyar junansu kara karuwa take yi acikin ransu sun saba da juna sun shaku da juna Ahmad ya iya soyayya yakuma koyarda da ma'u soyayya da sonsa domin idan yafita aiki ta kagu yadawo donma dai karatun littafi yanadan dauke mata hankali kadan BAYAN SHEKARA BIYU Ma'u tazama CIKAKKIYAR MACE data iyarike mijinta zuwa wannan lokaci duk wata halitta da kira ta kammala fitowa Allah yayimata maitsananin daukar hankali musanman tsarin jikinta da akecewa maikirar kalangu Ahmad yakasa gano sirrin matarsa daga karshe yabaiwa zuciyar amsa kawai Allah ne yahalicceta hakan 1⃣9⃣ DAME AKE ADO 3 Yautana zaune tana gogewa mijinta kayanda ta wanke masa tajiyo sallamar maryam maryam taga labule tashigo tana fadin komatar gidan batananne ma'u tamike dasauri tana ihu farin ciki tarungume maryam suna tsallen cikin farinciki ma'u tayi murmushi tana fadin naji dadin ganinki maryam nayi zaton ai kinmanta danine wace ni kinsa makaranta ke hanani zuwa amman yanzu tunda munyi candy ai harsaikin gaji dani kamin nasamu Admission! Admission kuma maryam ma'u tatambayeta cikin da sanyi jiki maryam tabata amsa da eh kinsan babana yanason nacigaba da karatun kamar sauran yayyena dadamuwa ma'u tace kinji dadi daman nice ke niyanzu saizaman gida bansan ahalin danakeba koda ace candyn ma nayi toda da dansauki anangidan ma'u maryam tayini har saida tataya ma'u girkin dare ita ma'un tana sha'awarta ta kammala karatunta ita kuma tana sha'awar ma'u nayadda tayi sa'ar Aure duk da mijin nata bamai hali bane amman suna cikin rufin asiri saigab da sallar magriba maryam tabar gidan amman tatafi tabar zuciyar ma'u damiki wanda tayi niyar amayar dashi yau kota huta kamar yanda Ahmad yasaba dawowa yauma hakan yadawo yakaraso cikin gida yakafe babur dinsa sannan yajanyota jikinsa yamatse gaggawar tameye bayan takaceni kaikadai bamai gutsirarma to meye danna taba kayana kuma za'adamu bar maganar haka jekacire kayanka kayi wanka tukunna harsaida yaci abinci yakoshi suna falo suna kallo sannan ma'u tabijiromishi da abinda keranta alokacin kanta yana kan cinyarsa yana wasa da gashinta suna cikin nishadi yadaga kai ta kalleshi tace yaya akwai wani abu dake damun zuciyata inason gayamaka amma bansan yadda zaka dauki abin ba ya lakace mata hanci yana murmushi yaushe muka fara yar haka dake ma'una kiboye abu aranki yasanya miki ciwon zuciya idan narasaki mekike tunanin zaisami rayuwata? Tayi murmushi saika sake wata matar yargayu tayi kara saboda mintsilinta dayayi wacce mace ce zata auri mutum irina? Idan narasaki nima narasa kaina bayan su abba babu wanda zaikara bani matat aure har abada.........ya isa haka bazan mutu bama saikarigani da shekara ashirin daya yakuma mintsininta yana dariya tasanya ihu tazame tanafadin kai yaya wlh ka iya mugunta mugunta ko gaskiya yaza ayi nayarda na mutu nabarki har shekara ashirin da daya wato wani ya auremini ke ko? Naki wayon rana daya zamu mutu nida safe keda yamma yanda yake maganar babu dariya yasanya tafashe dadariya tana fadin kaji yaya kamar kaleka littafin kadararmu kasan komai nidai bazanmutu dawuriba gaskiya Anji anbarmiki duniya kiyi gadinta amman gayamin abinda kikeboyewa kona samu kwanciyar hankali don har kindagamini hankali yanzu yaya inason cigaba da karatu ne! Gabadaya annurin fuskarsa yadauke kamar baitaba dariyaba hakan yakara haifar mata dafaduwar gaba amman saitaji yace karatu kuma kamar yaya? Tana kallonshi har lokacin tace karatun boko mana dankaga abokan karatuna harsunyi candy nikuwa inata zaman banza wannan kalmar karshen tashigeshi harya kalleta dasauri yana koma maimaita maganar zaman banza fa kikace ma'u zaman auren ne yakasance zaman banza tawayance dafaduwar gaba tace bahaka nake nufiba yaya wai inanufin inazaune haka babu komai ga abokan karatun nawa harsunyi candy yayi shiru yanasauraronta kamar bazaiyi maganaba yakamata kigane shi aure yanagaba da komai garayuwat ya mace sannan inada karfi da halin dazan iyarikeki kiyi karatu amman ayanzu lokaci yakure bazan iya kallonki kinafita kullum dasunan karatuba wasu nagane mini mata dan haka kicire maganar karatu cikin kundin burikanki yanagama fadin haka yamike tsam danufin ficewa cikin dakin amman maganarta tahanashi fita haba yaya kada kazamto irin mazan nan masu daukar mace tamkar baiwa kaima kanayin abinda kakeso yakamata kabani dama kosaudaya ne arayuwata gaskiya banida burin dayawuce ganin nayi karatu yawaigo baki bude jin kalaman dasuke fitowa daga bakin ma'unsa kamar wadda tarubuta cikin littafi tana karantowa amman saiyaga bahaka shidin take kallo kyar kuma tanacigaba dazakulo abinda keranta yaso yakyaleta tacigaba da maganarta amman saiyakula kamar batacikin natsuwarta danhaka dasauri yadakamata tsawa yanafadin kikame bakinki inhar nine mijinki bazakiyiba har abada! DAME AKE ADO part18. don haka kisanya wannan aranki inakuma gargadinki dakar kikara yimin irin wannan zancen dagayau!!! Yanufi kofa dasauri yafice yana huci wani malolon takaici yataso yatokare zuciyar ma'u WANNE IRIN MIJINE ALLAH YABATA MAIKISHIN TSIYA DASON KANSHI KUMA YASANI SARAI KARATUNNAN AKWAI ALFANU ACIKI AMMAN YARUFE IDO YAHANATA DON YANA TAKAMAR YAFI KOWA KISHI saitafashe dakuka takaici da bakinciki cikinta yahautsine kirjinta yakama zafi don bakinciki tarike ciki tana murkusu tana kuka shikam yariga yafice baimasan abinda kefaruwa da itaba can taji amai yatahomata tayunkura tamike dagudu tanufi tsakar gida kafin ta isaga rariya tuni aman yacimmata tatsuguna anan tafara kelayashi tanadafe ciki dakirji kamar zaibiyo hancinta yafito waje takeji yashigo dauke da maganin dasauro daya siyowa yahangota durkushe tana amai yakidime yanufita dasauri yana tambayarta abinda yafaru yaya akayi ma'u? Meyasameki lafiya? Duk yarikice yarude bata iyacemasa komaiba saboda aman datake yamike yanufi robar ruwa yadebo ruwa cikin buta yanufeta yafara zubamata akanta don tajigata da aman sannu ma'u meyakemiki ciwo kuma yanzu? Takada kai muryarta adashe tana fadin babu komai saidai tashin zuciya kadan kadan zaidaina shima garin yaya kikafara aman ma? Tarintse ido bansaniba nima yayi shiru yana kallonta datausayawa saiya mike bari nasamomiki magani a chemist din sister deeje yafice da sauri itakuma taji wani sanyi yanashigarta tajanyo bargon dake gefe ta dukunkune yadawo dauke magunguna ya ajiye ya dauko ruwa yabude abinda ta lulluba dashi ya tallafo kanta yana fadin ma'u tashi kisha magani batayi musuba ta amsa tafara sha har tahadiye duka ya maidata yakwantar ya mike yafita dakayan itakuwa takara kudundunewa domin har lokacin akwai zazzabi ajikinta yanacan yanakokarin dauraye kayan databata yakuma jiyo kakarin amanta yabazamo dakin dagudu yasameta tana durkushe agaban gado ta amayarda dukan magungunan datasha yadafe kai dadamuwa kamar zaifasa ihu ya isadai yagyaran wurin ya dauko kayan yajibge akan wadancan na waje yadawo yadauko dan ruwa yana bawa matar tashi yafasa wanke kayanma yarungumeta akirjinshi yana shafa kanta da lallashi domin dabaiyi mata masifarba da bazatayi aman har hakaba hakanan suka kwana tana aman tayi yakai sau 4 cikin dare danhaka tun asubah yafara shirin kaita asibiti karfe bakwai sunfice yaso yakaita nakudi amman kuma babu kudi ahannunsa domin wata yafara nisa don haka dole na murtala muhammad yakaita Dayake sunfita dawuri sunyi sa ar ganin likita dawuri akarubuta musu magunguna harda karin ruwa da kuma gwajin fitsari harwajen karfe 3 suna asibitin saida ruwan yakare tas! Saidai harsannan Ahmad baisan abinda kedamun matarsaba donhaka dazasu tafi yasamu wata ma aikaciyar jinya yamikamata korafi yana fadin sister don Allah mekedamun matata dazu ina rude bantambayi likitaba gashi yatashi yanzu ma aikaciyar jinya tayi kamar bazata amsaba datayi ido hudu da Ahmad saitagaza yin musu domin shi mutum ne maikwarjini da haiba dawuya kakalli tsakiyar idonsa kayimasa musu bayan tagama karanta abinda kerubuce ajikin katin ta kalli ma'u tana dariya tana fadin inatayaki murna kinkusa zama mama sam ma'u batafahinci komaiba Ahmad yadan fahimta amman duk da haka sai yasake kallon ma aikaciyar jinya dasauri sister waikinanufin ciki ne da ita tayi murmushi tace kacire kalmar wai tamika masa katin tana murmushi Allah yaraba lfy ma'u kam kunya duk takamata kamar tanutse agurin takauda kanta gefe tana murmushi Ahmad yakuramata ido yana kallonta yama rasa wane irin farin ciki yakamata yayi yadan kalli mutanen dake kai dakomowa banda gudun baki daya suri matarsa yayi rawa da ita sannan yakaita har bakin titi inda zasushiga motar amman dai yadaure yariko hannunta kawai yanata wage baki tamkar mai tallan makilin yace ma'u maiyasanya kika boyemin wannan farin labarin bata iya kallon fuskarshi ba dankunya nima fa bansaniba yaya zaikara magana ta katseshi yaya muyafi gidan mutane suna kallonmu sannan kuma yunwa nakeji wannan abin data fada yasanya ya dan natsu yakama hannunta suka nufi titi shatar adai daita sahu yadaukar musu harkofar gida daman yadan tsaya yasaimata take away dan haka suna shiga gidan yafara shirya mata shi agabanta yace tacinye tas sannan tayi sallah Allurar da akayimata natsaida aman sunyi aiki ajikinta batajin aman ko tashin zuciya a yanzu dan haka tadanci abincin dayawa Ranar dai kowurin aiki Ahmad baijeba sai waya yayi yasanarmusu matarsa batada lfy agayawa manaja yacigaba da kula da ma'u kamar zai lasheta BAYAN WATA TARA kwanci tashi bawuya awurin Allah domin zuwa wannan lokaci cikin ma'u haryashiga wattani tara dukkan wata kulawa dagata tanasamunsu awannan ciki Kamar ranshi haka Ahmad ketattalin cikin nata jama'a kuwa kowa yasan ma'u nada ciki tunyana watanni 4 musamman hjy da Umma sune abokan neman shawararsu Kullum sambayajin kunyarsu indai akan cikinne ma'u takanyi mamaki yanda Ahmad ke tsananin son haihuwa kamar yayi hauka akan kula da cikin aikima don ance anabukatarashi awajenne dole shiyasa yake kyaleta yatafi yau tana kishin gide akan kujera tana kallo tayi wata irin kiba cikinta yafito sosai Ahmad yashigo falon da sallama hannunsa dauke da manyan ledoji guda biyu ta yunkura da kyar tanakokarin mikewa gamida Amsa sallamar yakaraso kusa da ita da sauri yanafadin kinga bance kitaso kitareni ba cigaba da hutawarki nagode DAME AKE ADO part 19. 2â£2⣠DAME AKE ADO 3 Tayi murmushi waton kayimin haramiyar wannan ladanko yaya? Yafara kokarin fito dakayan dake ledojin dayazo dasu takatseshi yaya dakafara cin abinci kafin kayi komai ko? Bari nadaukomaka tasake yunkurawa zata daukomasa yayi saurin dakatar da ita dakata ma'una naga alamar dai sokike saikintashinnan dole toni akoshe nake Akoshe kake yaya? A ina kaci abinci kuma ta tambaya yanayin fuskarta yafara sauyawa zuwa damuwa yalakucemata hanci kada kiyi kuka matata kanwata daga gidan hjy nake bawatace tabani abinci ba itacema tabani wannan kayan wanda tatara newai yace nakawomiki tadan saki fuska tana dariya naga kayan hajiyar? Wannan tawace ninasiyosu wannan kuma na hjy ne tayi shiru tana kallon ledojin duka saitayi murmushi tanuna ledar dayace nashine kayan yayi dariya ya ajiyemata gabanta taja ledar tafara duban kayan tana fadin nasan mijina dan gayune yafi hjy iya zabe tafara daga kaya yaya kayan sunyi kyau ka iya zabe wlh amman kamar sunyi yawa ko? Inji wa? Yarinya da ace kudine dani wlh da akwatima zanciko dakayan dana ko diyaya to wai ya akayi kasami biyu ganaka gana hjy aida daya ya hakura daya yasiya? Wasu kudine damuke karamin dashe akahadamin yau awurin aiki shine naje kasuwa nayo siyayyarnan saina yanke shawarar naje nanuwa hjy abinda babu saitayamin nakaro to inazuwa tanaganina takama fada akanme dazan siyo banyi shawara da itaba domin itama tasiyo nata kayan daga karshe dai tahadoni danata kayan tace saina kara ma'u tayi dariya gaskiya tafada wlh akan cikinnan kazama wani babban mara kunya ko agaban umma da abba bakajin kunyar maganar cikinnan yayi yake yana fadin ma'u kenan laifina kikagani? Idan banyi daukin cikinnanba meya kamata nayi dokinsa kada kimanta fa shine dan uwana jinina kuma tsatsona Nakasance babu wani wanda yazamto munhada wata alaka ta daga jini awannan duniyar abinda zaki haifane kawai zaizamto min haka idonsa yataru da kwallah inason kihaifamin yara guda guda ashirin ma'u yanda zanraya sabuwar zuri'a daga bangarena nima tunda banida kowa awannan duniyar sai mahaukaciya mahaifiyata data rasu da ace tarayuma data iya zamemin abar kallo kokuma takaini wurin babana dayayimata cikin shege har akahaifeni tasanya hannu dasauri ta toshemasa baki tana kada kai..dan Allah yaya kadaina wannan maganar saikawai yafashe daí ½í¸­í ½í¸­yadora kansa akan kafadarta yana kuka sai itama tarasa abinda yakamata tayi masa sai kawai itama tafashe da kuka yayi sauri yafago ido yana kallonta yajanye jikinsa yi shiru ma'u kuka baikamace kiba kefa yargata ce kinada uwa da uba da yayye da kuma miji kuma yayanki nikuma banida kowa daya kasance jinina saiwannan abin dake cikinki ya isa haka yaya idan basokake kadagamin hankaliba yayi shiru yana ajiyar zuciya kalamanta sunratsa zuciyarsa cikin kunnensa tace gobe zanje awo yaya za ayine? Zankaiki idan angamamiki saikiwuce gida idan natashi daga aiki sainabiya tacan nataho dake saiwajen karfe biyu takammala komai da komai na awo tatako dakyar tanufo bakin kofa saitakejin duk jikinta yayi nauyi yanzu da kyar ta isa bakin titi tasami shatar mota tashiga hargidansu tabiya mai motar tashiga soro saitaja tatsaya turus dafargaba danganin Raliya abakin kofar gidansu tana waya hankalin Raliyan yayi kanta itama sukayiwa juna kallon kallo kowace mamaki yabayyana akan fuskarta ganin yar uwartata dauke daciki Amman Raliya bayan mamaki harda tsananin takaici da kishi domin bayan tadawo yaji lbr Ma'u aka aurawa Ahmad saikuma taganta kwasam da ciki babu zato babu tsammani ma'u kuma tana mamakin gani Raliya da ciki tsoho bayan tasan ba aure ne da itaba KOCIKIN SHEGE TAYO NE? Raliya ce taja dogon tsaki tajuya cikin gidansu da sauri Lami tana zaune akan benci tayi tagumi tashiga tana kwalamata kira Lami! Lami!! Lami!!! Dakarfi lami dake zaune tadago ido yakalleta dasauri cikin fargaba bakin cikin duniya duk ya isheta tace yaya akayine kike kwalamin kira haka? Ta isa gabanta tazauna tana haki tace yarinyarnan ma'u ce tashigo yanzu naganta da ciki kuma cikinma tsoho waikina nufin har ciki tasamu da mijina Lami tatabe baki bagashinan idonki yanunamikiba Raliya? Wlh koganinki bana kaunaryi Raliya nagama kuri dacika baki akanki amman kidawomin da wannan abin kunyar dawanne ido zankalli duniya da makiyana masuneman gazawata suyimin dariya? Raliya taturo baki gaba tana kumburi haba Lami saunawa zangayamiki banyi iskanci dakowa ba wannan cikin na Ahmad ne kwanciya yayi nayi zaton yafadi tuni saicikin wattanan yatashi idanke bakiyarda cikinsa bane waye zaiyarda dani harya kwatarmin yancina? Malam jibril yashigo fakan fakan ransa abace domin baikaunar kolekowa gidan don baison ganin Raliya da cikin da shege ajikinta wanda yakejin kamar yaharbeta yakashe abinda ke cikinta yanason yagayawa dan Uwansa amman baisan yadda zaidauki abinba donhaka yaja bakinsa yayi shiru amman bakinciki yanajan ransa da zuciyarsa yadebi ruwa yazuba abuta yanufi bandaki da sauri Lami tafito daga cikin daki da sauri tafara kwalla masa kira Malam! Malam!! Baiko kalletaba yashige cikin bandaki abinsa lami taja tatsaya turus tarike kugu tana masifa amman wannan wulakanci ne inaimaka magana kayi banza dani tozaka fito kasameni inatsaye inajiranka ai Raliya tafito daga cikin daki tasamu guri tazauna itama Malam jibril yafito daga bandaki yadurkusa yafara Alwala Lami tayi kansa dasauri malam waiko cutar rashin jice tafara shigarka bansaniba? DAME AKE ADO part 20. Yadaga kai afusace Allah yakiyaye saidai kiga wannan bala'in akanki badainiba! Nima din bazata sameniba aniyarka tabika ashe kanaji kayimin banza? Naga kasauya hali dalokacin shigowa gidannan tunda yarinyar nan tadawo kaki zama kaji damuwarta saifishi da kumburin dakakeyi malam yakuma fusata yadago kai yakalli lami damuwarme zanyi bayan wacce nagani manne ajikinta? Aikome yasameta kece kikasaimata da kudinki saita haifamiki shegen kiraineshi bahaka daman kikebukataba? Lami tadaga masa hannu idanunta cikeda masifa tsaya tsaya malam kadaina kiran cikin diyata da shege domin wannan cikin bashege bane da wlh da Ubansa!!! Malam jibril yamike tsaye dasauri yafasa Alwalar yana fadin Au! Kokindaura mata Aurene bansaniba? Wato tayi aure akan aure kenan laifi biyu akanta babu batun aure akan aure auren nan dai guda daya shine akanta haryanzu na Ahmad kuma cikin nasane yasan dahakashi.......malam jibril yafashe dadariya yana kallon lami wacce tafara kuluwa da irin dariyar dayakemata yace wlh nayarda lami bakida hankali yarinyar dabata tare da mijinta tsawon shekaru tatafiyawo amman tasamo cikin shege kice nasane? Ta ina yayimata cikin kokuma tawayar salular zamani? Komeye cikinsa ne idankuma bakayarda ba saikaje kayi tambaya akanhaka tunda tabar gidansa daciki tafita wanda yakwanta mata sai awadannan watanni yatashi kuma shikansa yasan tanadauke dacikin kuma kowa yasan ciki yana kwanciya acikin addininmu dagurin likitoci zamani donhaka dole ya amsa indai bazaka kwatarmata yancita ba nuzanyi duka kotun dake duniyar nan nashiyar shigarta domin kwatarma diyata hakkinta!!! Yatsaya yana kallonta kyar yanda tadage tanazuba bayani yayi kama dana masu hankali saidai kuma yana tantama tabbas mace kanyi shekaru da ciki kuma tahaihu daga baya indai dagaske Raliya daciki tagudu kuma Ahmad yasan da haka tobabu makawa wannan cikin nasane yadire butar dake rike ahannunsa yakarasa kusa da Raliya dake zaune tana kallonsu yace ke Raliya kisanarda ni gaskiya shin dagaskene kintafi da ciki ajikinki daga gidan Ahmad kokaryace kika shirya kawai? Takarkace baki wlh baba da gaskene wannan cikin na Ahmad ne domin yasan dashi tunkamin natafi ninayi zaton yazube ne danaga yadaina girma saikuma dagabaya cikin wattannin nan naga yana tashi idan kuma shi Ahmad din yamusa muje har asibiti agwada agani za'aga jininsa ne acikina malam jibril yayi shiru hankalinsa yadan soma kwanciya idan hakane lallai yasamu mafita yatsira daga daga abin kunyar dayake tunanin yashiga abaya yakada kansa shikenen bari naje masallaci nadawo saimuyi maganar dayaya inazuwa yadurkusa yakarasa Alwalar yafice daga cikin gidan Raliya tatashi tashige dakin ranta yayi fes domin abinda tatsara yatabbata babu kuma wanda ya isa yakaryatata su ma'u sunacan basusan wainar da aketoyaba sannan umma takibata hadinkai sujajanta abin sai sabgoginta takeyi ma'u takagu mijinta yazo yadauketa kosasami damar tattauna matsalar Raliya dashi Malam sule yadawo daga sallar magrib yanufi gida da casbaha ahannunsa yana lazimi yajiyo kiran dan uwansa daga bayansa yana fadin yaya! Yaya!! Yaya!!! Malam sule yaysaya cak gami dajuyowa yakalleshi har yakaraso inda yake yamike masa hannu suka gaisa malam sulemanne yafara magana inakashiga ne jibril kwana biyu banaganinka? Malam jibril yashafa keya wlh yaya inawurin yanbuge bugena daman inason muyi wata muhimmiyar magana ne dakai malam sulaiman yace to to! Mukarasa wajen dakalin can saimu zauna suka nufi wani dan tudu dake kofar gidan suka zazzauna dukansu malam sulaiman ya kalli malam jibril yace masa inajinka meyafaru ne? DAME AKE ADO part 21. Malam jibril yagyara tsayuwa yana tunanin ta inda yadace yafara bayanin nasa canyanisa yace yaya kasan Raliya tadawo gida bayan kwana hudu dasuka wuce kuwa? Malam sulaiman yadan yazabura yace Raliya kuma! Yayi wata doguwar ajiyar zuciya yakara dacewar masha Allahu yaushe tadawo kenan? Yau kwananta 6 malam jibril yabashi amsa yana in ina haba malam jibril amman kakasa sanardani tun randa tadawo din? Amman babu komai tunda kasanar dani yanzu amman kokaro bantabaci da itaba cikin wadannan kwanakin datayi dinba malam jibril yaja doguwar ajiyar zuciya yaya inadan fargabar yanda zanfada maka zuwan nata ne saboda abinda ketattare da ita wato Raliya dai tadawo daciki tsoho kuma.............malam sulaiman yazabura darudani yace cikifa kace jibril!! Ciki dai juna biyu na haihuwa? Ciki nahaihuwa yaya wannan nema dalilin dayasa bakasa sanarda kai harsaida nasami hujjar da zangayamaka don nasan hankalinka zaitashi matuka idan harkaji cikin nata nashege ne amman dayake da ubansa shiyasa nasami karfin guiwar iya tunkararka har nasanarda kai yanzu har lokacin bakin malam sulaiman yanabude tsananin damuwa akan fuskarsa cikin takaici yace Aure kakoma dauramata ne bansani ba dayasanya cikin nata yazama mai uba bashegeba jibrulu? Yanda yake maganar yasanya gaban malam jibrilu faduwa har yaji yanashakkar fadin abinda yayiniyar fadadin saida malam sulaiman yace kaifa nake saurare kacemin cikin nata yanada uba kagayamini waye uban nasa? Malam jibril yagyara zama yace kasan lokacin dabatar gidan mijinta da aurensa akanta baisaketaba.....yayi dan shiru yana kallon malam sulaiman domin yaga yanda yadauki maganar saiyaga yanutsu tsaf yana sauraronshi yacigaba dabayaninsa donhaka malam yaci gaba dabayaninsa koka manta haka yaya? Malam sulaiman ya girgiza kansa tare da fadin A'a banmantaba inasane dacewar Raliya tagudu daga gidan Ahmad batare da yasaketaba injin har izuwa wannan lokacin ma akwai Auren Ahmad akan Raliya Amman duk ba wannan bane yanzu inason naji yanda tasamu ciki halattace ne jibrilu malam jibrilu yagyara zama yana duban yayan nasa eh kafin tabar gidan shi Ahmadu din da ciki ajikinta kuma shi Ahmadu ma da kanshi yasan dashi towai cikin kwanciya yayi saiwannan karon yatashi shine tadawo gida don ashaida tahaifar masa abinsa tabashi malam sulaiman dai yayi shiru yana sauraren jawabin malam jibril saiyaji kamar yashakoshi don bakinciki yarufeshi da duka yarasa dalilin dayasanya kanin nashi yamaida kansa kamar tababbe mara hankali idan yana wani zance yadai daure yace bari natambayeka jibrilu tsawon watanni nawa mace takeyi idan mijinta yasaketa? Dasauri malam jibril yace wata ukku ne yaya malam sulaiman yakada kai itakuma macen da tagudu daga gidan mijinta tsawon shekara biyu ko ukku ma wanne hukunci ne akanta? malam jibril yayi shiru yana juya tambayar sannan yace wlh bansan irin hukunci daken kanta ba saidai ko idan malamai sunyi jawabi malam sulaiman yace to! Idanhakane kaga baikamata kaitsaye kadanganta cikin dake jikin Raliya dana Ahmad ba domin basakinta yayiba balle tace kwanakin iddarta suncika kuma tare daciki ba.......yayi shiru yanakada kai amman bari nayi shiru nafara jin tabakin Ahmad domin shi ne hakkin komai ke hannunsa konaje wajensa Amman idan kashiga gidan kagayawa Raliya tazauna cikin shiri kafin Ahmad din yakaraso malam sulaiman yamike yacema dan uwansa nasa bari nashiga daga ciki sai anjima yajuya yashige cikin gida batare dayaji abinda dan uwan zaikata cemasa ba malam jibril yabisa da kallo gwiwarsa dajikinsa gaba daya sunyi sanyi saiyamike azabure kamar wanda akatsikarawa allura yanufi cikin gidan kaitsaye babu ko sallama yafada gidan yayi wuri wuri da ido baiga kowa atsakar gidan ba saiyajiyo muryarsu cikin daki saiya juya dasauri yafada cikin daki suna zaune suna zance suna sake sakensu nabanza sukanshi yashigo dakin kamar anjehoshi gabadaya suka dago kai suka kalleshi cikeda mamaki dafargaba lami ce tayi karfin halin fara magana malam lfy babu ko sallama? Yadubi raliya kekuma nazo inason kikara gayamani gaskiya abinda kecikinki nawaye don wlh idan kika maidani karamin mutum sairanki yabaci fiye da yanda kiketsammani kinji nagayamiki ko? Raliya tazunburo vaki gaba ranta abace tace nifa gaskiya nafada wlh cikinsa ne idankuma yamusa nayarda musanya Alkur'ani ayi rantsuwa wanda yayiwa wani karya Allah yatona asirinsa tun a duniya malam jibril yayi shiru yana kada kai alamar ya yarda da abinda tace shikenan sai kizauna cikin shiri dan yanzu Ahmadun zaishigo Raliya tana kallonsu kawai tanata Addu'a cikin zuciyarta akan Allah yasanya Ahmad ya amince har ya amshi cikinnata wayarta tayi ringing dasauri takalli jakarta dakegefenta da sauri saitazura hannunta tadauko tamike tayi kofar fita daga dakin tana danna wayar gaba dayansu suka bita da kallo ganin yanda tafice bata kula da nauyin dake jikintaba Hello Rukky babby ya akayine? Dagacan bangaren Rukky tafashe dadariya tana fadin babby kin makale kinki kiranmu ko? Waime ake cikine akan dankadafen daya makalemiki ne? Raliya tamakale jikin bandaki tana hango gidan taga babu kowa saita ce shegiya saiyau kikanemeni to yaudai za'afara shirin yaki ba'ayi komaiba amman nifa nadan fara shakka kamar bazai amshi cikinnanba......kebanza ce kada kikaraya koki batamana shiri boka yatabbatar mini da lallai saiya amshi cikin nan idan kika fara karaya kuma yaya Za'ayi yayarda ya amsa? Raliya tayi ajiyar zuciya tace bakiji yanda akeyimini tambayoyiba kamar ina gaban mala'ikan kabari masu tambayar tashin hankali ne keduk natsorata wlh Rukky danasani danake kitaho dani? Aida shiri yaruguje domin suna ganinmu tare zasu yarda ribar bariki kikaci harkikasamu ciki kedai kiyi yanda boka yace kidaura layar akancikinki kuma kikuskure bakinki daruwan rubutun dole kowa yayarda fatana dai dazarar kinhaifemasa cikin ki ajiyiyemasa kidawo harka karki yarda sukara kullaki cikin gidannan maikama da akurkin kaji Raliya tace karki damu kawata bari ai itace gadonmu cinmu kuma shanmu bari nakoma sainakira ki dakarin bayani akan anda muka yi dasu takashe wayar tana murmushi amman lokaci guda murmushin dake fuskarta yadauke saboda ganin yayanta musa datayi yafito daga bandaki yanamata wani irin kallo babu ko tantama yaji duk abinda suke tattaunawa dakawarta cikin waya tayi mutuwar tsaye tama rasa meyadace tayi yadaka mata harara yana fadin sakarya kinyi asara raliya amman dasannu zaki gane shayi ma ruwane wlh yakada kai yafice talafe ajikin bango cikinta na hautsinawa tana zare idanu ta shiga ukku amman idan yasan wata aibaisan wataba Acan gidan malam sulaiman ma'u zaune akan tabarma tanacin tuwonta suna fira da ummanta dake gefe ma'u takalli ummanta tace Umma baki kula baba yashigo cikin damuwaba? Kohirar dayasaba yi dani yau baiyiba dakyarma ya iya amsa gaisuwata yashige cikin dakinsa umma tace nagani mana watakila saiyau yasami lbr abinda raliya tazo dashi daman kinsan cikin maganarta yakeyi fitowar malam sulaimance takatse musu hira gabadaya yaran suka kama kallonsa suka fara kokarin gaisheshi yana amsawa hannunsa yana rike da tabarma katuwa Ahmad ne yayi sauri yakarbi tabarmar da kehannunsa cikin girmamawa ya shimfida malam sulaiman yazauna yana kallonsu daya vayan daya kowane daga cikinsu yasha jinin jikinsa domin ganin halinda mahaifinsu keciki bayan angama gaisawa malam sulaiman yaja numfashi yadubi salisu yace kai salisu jeka wajen jibrilu kace yazo shida maidakinsa da raliya salisu yamike dasauri don cika umurnin mahaifinsu can malam jibrilu yashigo lami da Raliya nabin bayansa harda Amina ma'u dasauran yan uwanta sukabi raliya da kallo wacce tazundumo katon hijab kamar gaske Amman Ahmad yakasa kodaga kansa balle yakalleta saboda bakinciki da takaici Abin mamaki saiga raliya na kallon Ahmad dayake akwai hasken wutar nepa tanason tagano yanda yakoma shin yacigaba koyakoma baya? Takasa dauke idonta daga kansa malam sulaiman ya kallesu daya bayan daya sun zazzauna yayi gyaran murya ya kurawa malam jibril ido yafara magana yauwa kamar yanda yafaru dazu jibril yakirani akan maganar Ahmad da Raliya wadda nayi munwuceta abaya amman yau yadawo dawata sabuwar magana wacce yadace kujita daga bakinsa banawaba domin masu salon magana sunce waka ga bakin mai ita tafi dadi yawaigo yakalli malam jibril yace jibrilu kafadamusu irin abinda kagayamin dazu malam jibrilu yayi wuki wuki yana kallon mutane wajen shikansa yanada shakki akan abinda zaifada dil ballesu yanajin kamar ana izashi lallai saiyafada ya kallesu yace eh to akan maganar cikin raliya ne daman wai DAME AKE ADO part 22. Gabadaya suka kalleshi da mamaki jin abinda yace Umma kam har tsaye tamike tana fadin kan Uban can! Wannan wace irin maganace mara kan gado haka? Lami tayi caraf ta'amsa daman batazatayi kan gado awurinkiba deeje amman mu awurinmu agurinmu tafi maganar shahararren malami tasiri kikarkade kunnenki dakyau kiji kaimeye haka ne wannan wane irin hauka ne waye yasanya bakinki acikin wannan maganar? Malam sulaiman ne yadoka musu tsawa tahanya fadin wannan maganganu shi kuwa Ahmad baki yasa yana kallon ikon Allah sai yake ganin abin kamar shirin film din nan ma'u kam mutuwar zaune tayi zuciyarta har ta fara raya mata miyagun abubuwa kar dai mijin nata zagayawa yake yi gurin raliya sunawatsewarsu batare da tasaniba? Koda yake ai ance baisaketaba matarsa ce kenan indai hakane kuwa lalle yaci amarnata wani tukuki yataso yatsayamata awuyanta mai daci daciwo tadinga kallon mijinta wanda shikuma yake kallon Raliya da mamaki da takaici gabadaya guri akayi tsit! Kamar mutuwa ce tagifta amman fuskar kowa tanuna abinda ke zuciyarsa afili malam sulaiman ne yacigaba dacewa kaci gaba da bayaninka malam jibrilu malam jibrulu yakalli Raliya wadda ke sunkuyarda kanta kamar tanutse akasa tana kara matsa layar dake jikinta wadda takeganin itace zatayi magana ayadda da ita babu tantama ke Raliya gayamusu suji daga bakinki mana Raliya tafara ina iana tana zare idanuwa daman..........cikin jikina............Lami ta amshe meyekike wani ina iana kifito kifadi gaskiya kada kiji shakka ko tsoron wani Raliya tadan samu kwari gwiwa tace cikin dake jikina na Ahmad ne shine ubansa " Ahmad yamike agigice yana fadin nikarya kike mini wallahi karya kike!!! Malam sulaiman yakalli Ahmad wanda jikinsa yadauki rawa yace Ahmad samu wuri kazauna karnakoma jin bakinka Umma takalli da tsananin mamaki domin tanaganin malm din kamar yanagoyamusu baya ne Ahmad dasauran yan uwansa suka rinka kallon babansu da tuhuma suna ganin komahaukaci yasan tayanda zaiyi wannan ashari'a balleshi malam sulalman yamaida kallonsa ga Raliya yace kicigaba dabayaninki muna sauraronki Raliya tadanji karfi gwiwa tana zaton tanazaton harta fara gamawa da malam dinne tace tunkafin nabar gidansa da ciki natafi kuma yasani shikuma cikin yakwanta nayi zaton yafadi amman saicikin watannin nan naga yatashi shine nace bari nadawo nagayamasa yasani akasake yin shiru dai anakallonta tana inda Umma tanajin kamar tayi zage zage ko ta huce saikwafa takeyi Lami kuwa saigyada kai takeyi tana fadin hakane kam!! " Auwalu yadaga hannu dasauri yace baba dan Allah inason inyi magana malam yace indai Raliya da Ahmad ne bakada ikon cewa komai wannan maganace datashafesu suka dai yakalli Raliya kikace kin kammala bayaninki ko tace eh nagama amman wlh baba cikinsa ne kuma yasani!!! Malam sulaiman yakalli Ahmad dake zaune baki bude kamar andasashi kai kaji dukkan Abinda tafada shin dagaske kafin raliya tatafi daga gidanka akwai cikinka ajikinta? Gaba daya akamaida ido kansa Ahmad yadukar da kanshi kasa yana kada kai yafara magana Abba kuyi hakuri da abinda zanfada dolece tasanyani fadinshi wallahi tallahi tunda aka daura aurena da Raliya ko magana maidadi bantabayi da itaba balle wata harkar aure tashiga tsakaninmu bantaba kusantar raliya amatsayin mamataba wallahi!!! Umma tayi doguwar ajiyar zuciya cikin ranta tana hamdala ga Allah sauranma duk ajiyar zuciya sukayi Raliya kam fashewa tayi dakuka bakinciki da takaici ta tabbatar shegen bokan nan yacikudinta ne abanza tunda gashi aiki baiyiba amman baridai takara jarrabawa cikin kuka tace Ahmad kaji tsoron Allah wlh wannan cikin nakane karya kikeyi bansan komai game dashiba! Cikin kuka tacigaba damagana wlh kaine cikinka ne donka auri ma'u ne kaki amsa .....musa yashigo da sauri yana fadin karya kikeyi munafuka bacikin Ahmad bane wannan gaba daya idanuwan kowa yakoma kansa ana kallonsa damamaki kamar daukewar ruwan sama kukan Raliya yadauke tafara ware ido lami kuwa fusata tayi tacika tabatse tadubeahi cikin fushi tace ubanka ne yasako bakinka cikin wannan maganar? Idan bakakiyayeniba sainayima baki tsakanin miji damata babu wanda yasan tsakaninsu sai Allah musa yacigaba da magana batsoro balle shakka lami kozaki tsine mini sainafadi gaskiya tabbas wannan cikin bana Ahmad bane domin najiyo hirarta da kawarta dazu ina bandaki alokacin tazo kusa da bandaki batasan inacikiba suke tattaunawa akan maganar cikin nan yakwashe labarin dukkan abinda yaji suna tattaunawa awayar itada kawarta yasanarda su Raliya takara rudewa kunya duk tacikata kamar kasa tatsage tanutse cikinta Umma tadaga hannu sama tana fadin Alhamdulillah yau SAKAYYA tabayyana ga SHEGE yatabbata a inda ake ambatonsa kullum!!! Lami kuwa wuki wuki tayi cike da tsananin kunya tana muzurai RALIYA TAGAMA CUTARTA ! Shi kam malam jibril fashewa yayi dakuka yana fadin kincuceni Raliya kinzubarmin da kima!! Allah ya isa banyafemiki ba!!! Allah ya..............."malam sulaiman yadaka masa tsawa yana nunashida dan yatsa kai rufemin bakinka ahaka ma bakayimata bakiba ta aikata wannan shedanci inakuma ga kayimata bakin? Kabarta kawai duniyace ta isheta riga dawando Ammandai yaya saika hanani la'antar wannan yarinyar wacce keyawon duniya da aurenta? Malam sulaiman yace aimaganar aure ta kare kai Ahmad saketa yanzunnan duk da daman tasaku Ahmad yaji wani farinciki yabaibayeshi wanda baitaba jinsaba atsawon rayuwarsa NI AHMAD NAJANYE DUKKAN IGIYOYIN AURENA AKAN RALIYA HAR ABADA Raliya taja baya atsorace sannan tafashe dakuka maikarfi lami kuwa kamar tasanyama gidan fetur dawuta sukone gabadaya kowa yahuta tatashi tafita fuu suka bita da kallon mamaki malam sulaiman yayi murmushi kawai don lami bazata sauyaba itakam ma'u tunanita akan ace Raliya tacigaba da kasancewa matar Ahmad ne da yaya zatayi da rayuwarta? Ahaka suka isa gidansu batareda wani yayiwa wani maganaba Ahmad yajima akan gado yana game awaryasa amman ma'u batashigo dakinba yamike tsye san da ya ankara da jimawarta bata shugoba yafito falon yajiyo muryarta tana amsawa da kyar muryarta kasa kasa yashigo falon da sauri ma'u kina ina? Can bayan kujera yajiyota tana fadin gani nna yaya cikina da bayana zasucire ya isa gurin datake dasauri yana salati yatarar da ita kankame jikin kujera tahada uban gumi sai kada kai takeyi kamar tahadiye kunama cikin fargaba yace yaya dai ma'u lafiya meya faru cikin karfin hali tace tun agidansu umma naji cikina naciwo Ahmad yamatsa gabanta sosai yafara kokarin tayarda ita zaune komota zan nemo muje asibiti? Yaya bazan iya tashiba wani abu yarikemin kafa wash! Innalillahi wayyo yaya.........!!! Ahmad duk yagigice yasaketa ya ma rude yarasa mai zaiyi yanufi kofar fita yana fadin bari na kirawo babar A'ilo karkafita kazo na mutu a gabanka yaya......ka zodon Allah!!! Yadawo dasauri da tsananin tashin hankali ya runguneta gaba daya yafita daga cikin hayyacinsa labarin yanda mahaifiyarsa tahaifeshi kawai keyawo aransa yanzu idan ma'u ta mutu yaya zaiyi da rayuwarsa? MUHADU ALITTAFI NA HUDU ********************** ⬇ ************************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ **************************