[11:02PM, 5/5/2017] ‪+234 701 774 4623‬: 🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻 🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀ 🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻 😭 *GUDUNA AKEYI*☝🏻 *VERY INTERESTED AND SHORT* *STORY* *BASED ON HORROR*🤖 *DON'T TURN ON THE LIGHT* *WHEN READING*😅 *THE BOOK OF Nabila* *Page 1 to 10* *Bismillahirrahmanir rahim* ********************** ? ************************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************? ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ? ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ? ************************** Tsakar darene sosai, dan kusan ince kunnenka babu karar dazai jiyo maka, in banda na tsun tsayen dake shawayi sararin samaniya, sai kuma dan botsin dabaa' rasaba,cikin wani yanayi mai tsananin firgitarwa gamida ban tsoro, kabarin ke wani irin girgiza, Kai kace girgizar kasa akeyi, kana yasoma tsatsagewa,wani irin hayaki gamida Kara lokaci 1 suka kaure illahirin makabartan, Sannan dg bisani, wani farin abu ya dan leko dg saman kabari, Wanda zai tabbatar maka dacewa likkafani ne, dan jikinsa duk jini ne,a dai ² wannan lkc km kabarin ya Fara tafiya ta cikin karkashin kasa da gudu, kai kace tseran mota ake,abundai kamar a mafarki Cikin wani irin yanayi na jin kunya Amaryar ke fadin ameen angona, Allah yabamu zaman lfy Gaba 1 su suka shafa adduar da sukeyi,Ahmad yayi saurin juyowa dg kan daddumar dayake ya fiskanci inda amaryar tasa take,zuciyarsa cike da annashuwa da farin ciki, yadan daga kansa sama gamida dubañ agogon dake manne jikin bangon dakin yace," swty nah darefa yayi sosai is tym 4 bed now, dan kusan 2am fah, kada fa mu makara"itadai amarya bata iya cewa komaiba, dan tariga ta gane inda angon nata yadosa, dan ayanxuma banda bugawa ba abinda kirjinta yakeyi, alamar fargaba, ganin bata da niyyar tashi, yasanya Ahmad tashi ya sunkuceta kamar yar baby, baiko direta koina ba sai kan bed, Cikin kissa ya lakaci hancinta gamida fadin wato ke wai mai kunya koh? daga mgn shine kika wani rufe fusa, to yau zanga karshe kunya, gama fadin hakan keda wuya suka ga wutar gidan ta dauke,ga wata isaka da tasoma busawa mai karfin gaske, kamar zuwan sama ne zai sauko,cikin haushi kuwa Ahmad yace NEPA Baku kyauta ba wlh,awannan zafin dan Allah,gaskiya badan dare yayi sosai ba, da generator zanje na kunna,dan bansan zafi wlh, yana rufe baki kuwa sai kuwa gashi sun dawo da ita, da sauri kuwa yace alhdlah,aah Abu kuma yazama kamar wasa su dauke su dawo da ita hk sukai tayi,ganin basu da niyyar barin wutar ne, Ahamad ya yunkura da niyyar tashi ya kashe wutar dakin hade da ac,amma ga mamaki yaji ya jefa kafarsa cikin ruwa tsundum, ya da'da nutsa kafar tashi akaro na 2 yaji dai cikin ruwa take, da hanzari kuwa ya lalumi wayarsa ya kunna fitila dan ganin meye awurin, Ay baisan sanda ya kurma wani uban ihuba, ya haye kan gado da sauri,dan saura kadan ya takewa amarya kafafunta,itama kuwa cikin tsanani kidima da razana ta biyo bayanshi da gudu, hade da fadin" lfy kuwa? menene? Cikin rawar murya gamida karkarwa ahamad ke fadin," jini jinine nagani akasa k'undum kamar rafi,dan kafafuna gaba 1 sun nutse ciki Muje zuwa [11:02PM, 5/5/2017] ‪+234 701 774 4623‬: 🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻 🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀ 🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻 *GUDU NA AKEYI*☝🏻 😭 *VERY INTERESTED AND SHORT* *STORY* *BASED ON HORROR*🤖 *DON'T TURN ON THE LIGHT* *WHEN READING*😅 *THE BOOK OF NABILA* *PAGE 11 TO 20* Gaba 1 amarya tariga ta gama tsora dajin wanan alamarin,musamman ma da taga zahiri da idanunta, tunda gaba 1 bed sheet din duk inda ya taka ya baci da jini, gashi shima Ahmad din da yake shine na miji maimakon yayi wani abu akai, aa kokari yakema idan yasamu dama ya boye a bayanta, dan jikinsa gaba 1 garkarwa yake,dan tsabar razana A hankali sukaji an mur'da kofar 'dakin ,kana wani irin haske mai karfin gaske ya haske musu idanun su, hakan ne yasa dole Ahmad da amaryarsa rufe idanunsu sakamakon karfin da hasken keda shi,gamida k'an k'ame junansu,suna ihun neman taimako,sannu a hkl halittar nan ke tafiya a sandare, km nanade cikin wani farin mayafi, Wanda duk jikinsa kaca² yake da jini,saa'nnan ta jikin mayafin ma jinine ke tsatsafowa, Sai da tazo dai² saitin gadon nasu sannan ta tsaya, gamida duba yazuwa illahirin dakin, kanta kawai halittar nan ta jijiga saiga kayan dakin suna zuba kasa Kai kace bishiya ake girgizawa, Kama dg akwatina,kayan kan mudubi,dashi madubin kansa, agogon bango Kai da duk wani abu da akasan anasawa a cikin bed room,na fashewa ya fashe hk na tarwatsewa ya tarwatse, Cikin wata irin murya mai amo mara dadi hade da amsa kowa, ta Fara din,"wai Kai ango KO?!!!ke km amarya!!! Kabude kunnuwan ka da kyau,shuhaina ce tsaye gaban ka ke mgn,take cikin Ahmad ya fara kadawa,tsoran dayake ciki ya kara karuwa,tunda shi iya saninsa dai duk duniyar nan shuhaina 1 yasani wato tsohuwar matarsa,wadda allah ya amshi rayuwar ta wata 1 daya gabata,amma km ga wani abu mai rikidarwa na fadin itace shuhaina,mgn da tacigaba dayi ne ya katse masa tunanin da yake yi,"narantse da Allah bazaka kuma jin dadin duniyar nan ba,!!!kuma dukiyar da kake takama da ita bazata amfana maka da komai ba sai masifa!!!!, sai ka zamto gata gabanka amma bazata amfaneka da komaiba,kasani dukkan Wanda yayi tarayya da Kai karkashinta bazan taba kyaleshiba, Kan kace me sai ga amarya na lilo a saman daki, kamar fanka batare da wani Abu ya riketa ba, fadi take" dan Allah Ahmad kaceceni Zan mutu, ta shaken wuyana,pls kabata hkr, ay ganin hakan da Ahmad yayine yasa zuciyarsa ta tunzura,gaba 1 yaji tsoran da yakeyi ya gushe,baisan sanda ya rugo da gudu ba ya tsuguna gaban shuhaina ido cike da hawaye, yana fadin" Dan Allah kirufamin asiri karki kasheta, ki tuna irin kaunar dana nuna miki, alokacin da kowa ya gugeji, nine fa Ahmad dinki, Wanda kika sha fadin babu abinda zan nema a duniyar nan Wanda baza kiyimin ba, sakamakon hallacin da nai miki matatah, Wata uban tsawa ta daka masa, da karfin gaske,shi kansa saida ya razana,amarya kuwa jinta kake yif akasa an saketa ,tuni ta fadi sumamiya,shuhaina ce ke fadin mugu macuci, azzalumi,butulu Insha Allah sai karshen ka ya zamto kowa *GUDUN KA YAKEYI* Muje zuwa [11:02PM, 5/5/2017] ‪+234 701 774 4623‬: 🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻 🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀ 🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻 *GUDU NA AKEYI*☝🏻 😭 *VERY INTERESTED AND SHORT* *STORY* *BASED ON HORROR*🤖 *DON'T TURN ON THE LIGHT* *WHEN READING*😅 *THE BOOK OF NABILA* *PAGE 21 TO 30* *ASALIN LABARIN* Motocine tsala ²na alfarma,wato irin wadda harsahinnan baya ratsata farare kal² ,dan samun irinsu sai wane da wane, su 6 kan kwalta keta faman zabga gudu,babu ko kakautawa, dukkan Wanda ya hangesu kokarin takansa yake, Dan gudun tsira da ransa,basu tsaya koina ba sai a harabar katafaren hpl dinnan dake grin abj, cikin kankanin lkc kuwa maikatan asibitin suka hallara agurin manya da kananan su dan daukar Wanda aka kawo, wato alh Bukar Baba dogon yaro,hamshakin dan oil and gas din da sunansa ya karade koina afadin kasar nan,musamman ta bangaren taimakon addini Da sauri kuwa driver dake tukin motar ya danna wata na'ura sai ga kofar motar ta bude, kana kujerun suka wani lalan k'wasa gamida yowa waje,Kai kace gadon asibiti ne Wanda ake daukar Mara lafian da yake bukatar taimakon gagawa,caraf kuwa likito suka tarbi gadon nasa cikin hanzari gamida shiga dashi cikin asibitin, Kai tasa dakin tiyata aka wuce dashi, dan a wannan Karon ayadda jikin nasa ya tsanan ta baa' bukatar bata wani lkc,can kuwa awaje cikin mota, shuhaina ce keta faman rabzan kuka baji bagani, wato diya 1 tilo ga alh bukar,dan rabon da aganta tayi kuka makamancin nà yau, tun rasuwar mahaifiyarta, shekara 2 kenan data wuce, wannan karon kam dole tayi hawaye dan tuni tagama sarewa da yanayin jikin na abban nata, don tunda take dashi bata taba ganin condition dinsa ya tsananta ba irin na yau,dakyar ta samu tayi controling din kanta saannan ta fito dg cikin car din,gamida nufar cikin hpl din, body guard na beye da ita,wani kayatacen daki da aka warema wayanda hannunsu ya cudi bayansu tanufa,gamida kunna naurar da zata sadata da dakin tiyatar kai tsaye dan gane wa idonta halin da akeci, da kyar² likitocin dake aiki kan alh sukai nasarar tsaida jinin da yayi ta zuba sakamakon tsagewar da hantar tashi tayi,asakamakon kumburar da tayi sanadiyyar ciwon hanta ( Hepatitis) Kuka kam shuhaina tashashi yau, dan hatta body guard da basa Mata mgn sai da dole tasa suyi mata mgn ta hanyar bata hkr,hade da karfafa Mata guiwa samun lafiyar mai gidan nasu DA yardar Allah,bayan kammala tiyatan da kusan awanni 6 ne Dr din dake kula da alh yayi mata waya da tana iya zuwa tagan shi,dan ya farfado, cikin hanzarinta kuwa ta mike taji zuciyarta har ta danyi sanyi, DA aka cema ya farfdo,takuwa nufi cikin dakin, bt wanan karon hana body guard dinta shiga tayi, akwance ta tarar da abban Nata, dan hk Takarasa inda yake dasauri da yar faraarta, koda ganinta shima murmushi ya fara mata,daf dashi tazauna gamida rike masa hannu kam tana fadin" Abba yajikin naka? hope dai kadan samu afuwa yanzu?pls Abba stay wit me dan Allah karka tafi kabarni, kamar yadda mami tatafi, i really need u abba,tana fadin hk wasu hawaye masu dumi suka fara zuba dg idanunta,cikin karfin hl da dauriya abban nata ya matse hannunta da nashi kana yace,akoda yaushe kirika kaddara kodamu ko bamu zaki rayu shuhainà,tunda Allah yana tare dake, kitsare kanki da mutuncin ki, kada kisake kisauka kan tarbiyar da muka ginaki akanta, kanji my baby?akarshe dukkan harkokiñà danake gudanarwa ba Wanda bakisani bà to kikula dan sai kinyi hkr da jamaa',Dan ni rayuwa tazomin karshe shuhaina, kema kuma kinsan kinada irin wannan lalurar tawa (Hepatits)dan hk kikula wajen bin kaidojin da aka gindàya miki,ban yarda ki cutar da wani ta hanyar sanya masa cutarnan ba,musamman idan kin tashi aure,kifito kifada masa gaskiya koda kuwa hakan zai zama sanadiyyar kin auruwar ki,ni kam dama bana jin ajikina Zan tashi, dan likita ya tabbatar min da cewa hantata ta buga,kuka shuhaina take sosai cikin rawar murya take fadin zaka tashi abba, zaka tàshi,Dan Allah kadena ambaton mutua Abba nah!!!,fadar likita ba fadar Allah bace,shidai kawai mumushi ya bita dashi, Dan shi kadai yasan yadda yakeji acikin jikinsa,take anan ya fara wani irin kakafewa,gamida wani irin tari mai karfin gaske,sai gashi jini ya fara fito masa ta hanci da baki, Cikin tsananin kidima tasa body guard dinta da yayi sàurin hanzartawa dan kiran Dr,amman inah ko kan Dr ya karaso har rai yayi halinsa,innalilahi wa innailaihir rajun Allah yajikan alh Bukar Baba dogon yaro itace kalmar da Dr yafada asanyaye,hade da janyo mayafi ya rufeshi, Muje zuwa [11:03PM, 5/5/2017] ‪+234 701 774 4623‬: 🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻 🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀ 🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻 *GUDU NA AKEYI*☝🏻 😭 *VERY INTERESTED AND SHORT* *STORY* *BASED ON HORROR*🤖 *DON'T TURN ON THE LIGHT* *WHEN READING*😅 *THE BOOK OF NABILA* *PAGE 41 TO 50* 🎂🍮🍮🍮🎂 🍬Happy 🍬 ♻°°°°°°•°°°°°°♻brithday to ma ❄ ❄ Swt & lovely🎈 ♻ ♻ son💋 ❄ IBRAHIM KALEEL👩‍👦 A dan zaman da shuhaina tai da Ahmad, sai taji yana matukar bugeta, musamman barkwan cinsa,dan shi badai ka zauna kusa dashi komin bacin ran DA kake baisaka ka dara ba, kasan cewar sa mtm neshi mai rahar gaske,ga km gidadan ci, dan shi a yadda tsarinsa yake kauye tai masa mumunan kamu, Dr ne tsaye kan Ahmad yanata yan rubuce²nsa,gamida kara duba lfyar sa,take km ya juyo da kallansa ya zuwa inda shuhaina take, hade da miko Mata wata takarda,gamida fadin,"wannan takardar dana miko miki ta sallama ce hajjaju,dan ga yadda muka saukin jikin nasa ya dace da mu sallameshi a yau dinnan, dan hk ga magungunan sa nan da zai cigaba Dasha na rubuta asiya, Cikin sakin fuska tace toh tank u Dr, shima yace mata ya gode,kana ya juya yabar dakin,shuhaina ta dubi Ahmad Wanda yayi kicin² da ransa, tace dashi" ya naga ka bata rai,kaida ya kamata Kai murna an sallameka, koba komai zaka tafi inda Kai niyyar zuwa, ko baka son sallamar ne?Ahmad yace aa ni bawai abinda ke damuna ba Kenan,to me yake damunka? shuhaina ta tanbaye shi,nifa daman bagun kowa nazoba, dan bansan kowaba a birni, azabar kishiyar uwace ta koroni dg garinmu,kasan cewata maraya gaba da baya,shiyasa kawai nà yanke shawarar fitowa neman kudi,km tunda Allah yasa na hadu dake, km na fahimci ke mutuniyar kikice nasan dana fada miki abinda ya raboni da gida zaki taimakan,koda da shara ne, Jin kalaman dayayi ne yasa shuhaina amincewar ta taimaka masa, dan koba komai zata taimaka masa gudun kada ya fada ahannun bata gari, dan hk dg hptl gida ta wuce dashi,ta km hadashi da maigadi akan yarika kula dashi bakon tane,ba km ta kawoshi gidanta bane dan yarika mata aiki tana biyansa bane aa, sai dan kawai duk lokacin da take cikin nishadi ya rika 'debe Mata kewa Kwanci dashi Ahmad har ya zama dan gari,kasan cewar duk sanda shuhaina ke less busy tana km shaawar hutawa, takan fita dashi dan yaga gari,dg bisani idan suntashi dawowa gida su biya ta shago saida kayayaki tasai masa kala daban daban,tare da sawa akoya masa yadda zai rika daukar wanka idan yatshi sakawa,dan har waya sai da tasai masa Irin yadda Ahmad ya zama dan gaye,cikin kankanin lokàçi abin har mamaki yake ba shuhaina,kasan cewar duk shiriritar dayake yanzu ya daiñà,ya zama big guy,kyan dà yàke dashi na asalin filani yafito fili sosai,gashi Kannan nasa da yake daukar gyara kusan kullum banda daukar idanu ba abinda yake,hk dan madaidaicin sajen daya bari yayi masa kyau sosai, Duk Wanda ya sanshi abaya ya ganshi yanzu bazai shaida shiba, dan kwata² yazama natsatse gentle dashi, hk ne yasa shuhaina ma taware masa 'daki daban, dan yanzu ba class dinsa bane ya rik'a kwana damasu gadi,yanzu baban abindà ke damunsa bai wace na rashin ilimi ba, dan hk koda ya fadawa shuhaina batài kasa aguiwa ba,ta nema masa elementary school, km cikin yardar Allah da yake yasa abin aransa, sai karatun ya rika zuwa masa da sauki, Irin yadda shuhaina kejin shakuwarta dà Ahmad acikin ranta abin yanzu ya cànxà salo,dan ya kasance matukar batai ido 4 dashiba bata jin da'di,idan kuwa sch ya tafi taringa Allah ² yadàwo,ita kanta ta rasa me hakan ke nufi, kada dai ace sonshi nake,to idan har dagaske Ina sonshi ya zanyi na tunkareshi da wannan mgn, kar dg karshe shima ya zamto *GUDU NA YAKE* Muje zuwa [11:03PM, 5/5/2017] ‪+234 701 774 4623‬: 🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻 🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀ 🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻 *GUDU NA AKEYI*☝🏻 😭 *VERY INTERESTED AND SHORT* *STORY* *BASED ON HORROR*🤖 *DON'T TURN ON THE LIGHT* *WHEN READING*😅 *THE BOOK OF NABILA* *PAGE 31 TO 40* *Happy birthday my lovely son ibraheem Khalil Allah ya raya ka bisa tafarkin muslinci ,yayi maka albarka fidduniya da lahira ameen* bayan kusun watanni da rasuwan mahaifinta,abbuwa suka fara dawo mata dai²,tunda dama akin kamfanin ba bakonta bane, dan tun yana raye bayan kammala jamiarta ,tare suke zuwa km dama yayi hakanne sbd halin rayuwa, yanzu babban abinda yafi damun shuhaina bai wuce na zaman kadaici ba, tunda duk girman gidanan ita 1ke kwana cikinsa, ita ba yan uwa kusaba ballanta ta koma gurinsu da zama.tunda asalinsu ba yan kasarnan bane, Dan sunan kasar kawai takeji bt bata taba zuwa ba. Batun yin aure kuwa tana matukar shaawar hakan kodan samun natsuwa da tsirada da mutunci,bt tariga ta gama fahimtar yawancin samarin da suke zuwa wurinta ba dan Allah suke sonta ba,musamman idan tafiya tainisa ta sanar dasu hln da take ciki,wani dg hk bazai Kara dawowa ba,wani km zai daure ya dawo ammafa bazai kara tunkararta da batun yin aure ba Hkn kuwa bakaramin bakanta ranta yakeba ,dan sautari idan abin ya dameta zama take taita rabzan kuka, tunda tasan tariga da tarasa masoya masu santa tsakani da Allah a rayuwarata (mahaifanta)tunda tasan da ace sana raye irin wannan bakin cikin da take ciki bazai dameta ba,farin cikin suma Kadai ya isheta rayuwar duniya, amma yanzu gashi kowa *GUDUN TA YAKEYI* Tun daga nesa motar keta zabga masa horn amma inah ,abinka da Wanda bai san kan yadda birni take ba ,gaba 1 yabi ya kidime kan kwalta,yayi nan yayi nan,ya rasa inda zai dosa,dg karshema tsayawa yayima cak gamida runse idanunshi kam, hade da kankame buhun ledar dake hannun shi,ay kuwa cikin tsautsayi motar ta makeshi da karfi, yayi wani sama ya fadi can gefe, Shuhaina da tunda driver ya fara tukinsa taketa aikin karatun jarida ,batasan me akeba, sai yanxu da taji motar tai wani irin cin birki da karfi,kana tai wani mugun tsayawa a tsakiyar kwalta,cikin sauri tace "subhanallah meke faruwa?cikin kidima driver yasanar da ita abinda yafaru, ay dandanan ta fito waje da sauri ta nufi inda dandazon jamaa' da suka taru, kwance ta tarada shi malala cikin jini, dan hk cikin hanzari jamaa' suka saka matashi cikin mota, driver yaja mota sai asibiti, Koda isarsu harabar asibitin dan sandan da commisorner ya turo dan daukar report din case din har ya iso,tunda tun suna hanya dama ta kirashi ta sanar dashi abinda yafaru,Dan hk cikn sauri ya gama duk rubutun da zaiyi suka shiga hptl din tare,batare da wani bata lkc ba aka shiga dashi emergency,Dan da nan kuwa aka bashi duk wani kulawan daya dace,aka kuma tabbatar màta ba wani matsala, buguwa yayi da dutse kan ya fashe, sai targade daya samu akafa. Ganin yamma tayine sosai gashi km haryanxu bai far fado ba, dan hk shuhaina ta umarci driver daya tsaya gurinshi ita zata wuce gida,bt idan Ana bukatar wani abu yana iya kirata, taciro bandir din kudi ta mika mishi,nan sukai SLM da dr akan sai gobe da safe. Wani tsadaden Swiss les tasaka mai daukar ido, launinsa ruwan hoda ne anmasa ado da rastin syk blue,ya matukar haska kalan fatan jikinta,mayafin data sanya da takalmin dake kafanta hadi da jakarta,sarkar wuyanta,dan kunneta duk launinsu 1 wato sky blue, tayi kyau sosai, dakanta yau take driving abinda rabonta da ace ta tuka mota ta dade,tafe take har ta iso harabar asibitin,Kai tsaye dakin Mara lfyn tanufa ,koda ta tura kofar dakin da shi ta fara arba ya tashi zaune ya jinginar da kansa jikin bango,sai faman kale² yake,take taji zuciyanta yayi sanyi, Dan hk da yar faraarta ta karasa Driver na ganinta yayi saurin mikewa tsaye,hade da fadin ina kwana hjy" gamida karbar ledan dake hannunta,fuska asake ta amsa masa, gamida karasawa inda Mara lfy yake, shi kuwa abinka da dan kauye ,kur ya bita da ido,ko kiftawa bayayi,yana mamakin irin zubin da allah yayi mata,nan fa ya Fara zuba," kai³ Allah mai baiwa,daman da rabon zanga yar india nashigo burni?aradun Allah kamarku 1 da ita yar India nan, namanta sunanta, har kalan kayan ma kuwa,tab kice ni ay gaba takaini rankiya dade" kamar yayafa? Shunaina ta tambayeshi, yace to ay da abinda yafaru dani bai faruba na ganki? daria ce ta kwace ma shuhaina dan dama tunda ya fara baragadarsa take cinta a ciki, Dan hk ta dakatar tashi dacewa," yanzu ni duk ba wannan ba meke damunka yanzu? km ya sunan ka?yace "dafarkon farawa dai nine amadudu jikan yalwa, dan idan baki fadi hk ba a jar kuka garinmu kenan bame ganewa, na 2 km ko inama ni ciwo yake min dan banso ace intafi gida dawuri rankiyadade,dan ko dadin katifan nan bayasa kàbar gun nan ba Tom naji amadudu, yanzu dai ga abinci na kawo maka, dan hk kadaure kadanci ko yayane,dan nasan Mara lfy akwai taurin kai wajen cin abinci, cikin sauri amadudu ya katseta da cewa aradun Allah bandani, kuma koda banyi niyyar cibama sai naci, dan nasan yadda kike dinnan yar gayu km yar india Ay abinciñ gidan ku ba karamin dadi zai yiba,mikon in gani? Koda ya kyalla idanu ya hangi alatun dake cikin ledar, ay dan tsabar dadi kwallace ta gangaro masa, cikin sauri kuwa shuhaina tace masa lfy? ko bakacin shawarma da smoke fish ne? yace niba hk bane, kukan dadi nake, dama ashe nima arayuwa ina da robon cin irin abincin da muke gani manne jikin jarkar mangyada ( OK)? Muje zuwa [11:05PM, 5/5/2017] ‪+234 701 774 4623‬: 🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻 🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀ 🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻 *GUDU NA AKEYI*☝🏻 😭 *VERY INTERESTED* *STORY* *BASED ON HORROR*🤖 *DON'T TURN ON THE LIGHT* *WHEN READING*😅 *THE BOOK OF NABILA* *PAGE 61 TO 70* Tun dg nan soyayya mai karfi ta kullu tsakanin shuhaina da Ahmad, dan idan kagan yadda suke gudanar da soyayyar tasu ,Kai Kace sun dade dama da fahimtar junan su,dan yana matukar jida ita kamar wata kwai a' cokali, ita ma ana ta bangaren hk take masa,ganin yadda alakar tasu ta sauya salone yasanya yan gulma da muna furci fara kutse cikin lamuran nasu, ta hanyar zuga da hurema ma Ahmad kunne,akan lallai kada yasake ya yarda da wannan ala'marin dan cutarsa zatai,dan da ace lafiyayyace ita ko amatsayin mai gadi ba daukarsa zatai ba,amma ganin tayi kwantai shine ta lallabo ta cuceshi,ta km yaudareshi da tarin dukiyar ta,amma Sam Ahmad ya toshe kunnuwan sa bai kula su idan suka zo masa da zancen ,dan sautari sai sun gama bayaninsu ya fara musu nasiha ma, tareda kokarin sasu a hanya ta gari.shi yasa iri irinsu da dama suke jin haushin sa, tare da karanshi da sunan drivern Hjy ********************** ? ************************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************? ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ? ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ? ************************** Bayan kammala sch din Ahmad ne, shuhaina ta gabatar dashi gaban alh aminu(aminin mahaifinta)amatsayin Wanda zata aura, nan alh ya nuna matukar jin dadin sa afili kasan cewar faruwar wannan alamarin,dan koba komai shuhaina kamar 'yar take gunsa,nan suka dan tatauna tare da Ahmad, harma yama ya kwatanta màsa inda garin nasu yake, hkan yasa yace insha Allah zai tura ayi masa bincike har kauyen su ahmad din,sannan duk sanda ya kammala hkn zai sanar da ita hln da ake ciki, nan taita murna hk shima gogan baa' barshi abaya ba Tunda kuwa alh aminu ya tabbatarwa da shunaina ba wata matsala a dangane da binciken da yayi akan Ahmad, nan take kuwa ta bashi director na kamfanin ta, tare da mallaka masa wasu makuden kuda'de,k'alleliyar mota da dai sauran manya manyan kadarori,dan tsabar murna agun ahmad kuka kawai yasaka ha'de da fadin" nagode² Allah ya jikan iyaye yasa kigama da duniya lfy,yasa idan munyi aure mutuwace kadai zata rabamu badai zugar makiya ba, ta bishi da fadin ameen,amma ita anata ganin ita yakamata tai godiya dan koba komai ya rufa mata asiri,dan samun namiji kamarsa sai antona awannan zamanin Wani makeken part ne mai cike da kayan 'kawa da k'yafewa kasancewar duk cikin parts din dake gidan bakamarsa,dan tsabar haduwarsà ,nan amarya shuhaina da angonta Ahmad suka tare ciki bayan daura auren su,amarci kuwa anci shi ruwa²,sun nuna wa junansu tsantsar yarda kowannen su ke kaunar dan uwansa. *DAGA INDA LABARI YA FARA* *CANZAWA* Bayan kusan wata 6 da aurensu, asannan kusan ragamar company din tadawo kacokan hannun Ahmad,sai abida yace zaa' aywatar, sakamakon matsanancin rashin lfy da shuhaina ke fama dashi,kusan sati 2 kenan, asanadiyyan tashin da jikinta yayi,anyi mgn amma abanza, dan yanzu takai ta kawo Ahmad ya fara gajiyawa ma,dan koda likitoci suka tabbatar masa da matukar anason ta sami kulawà ingantacciya to fa saidai a tafi England,Sam kin amincewa da hakan yayi,wai kawai asarar kudine, ya dan leka dakin da take ma abin naneman gagarasa yanzu,sam yanzu ta fara gundurar sa,sai yanzu yake tuna irin shawarwarin dà aka dunga bashi abaya amma sam yayi burus, so ya rufe masa ido, amma daya tuna irin daular dayake ciki sai yaji sanyi a ransa dan hk ya bude babin sharholiyar sa,ta hanyar fara cin uba naira, Muje zuwa [11:05PM, 5/5/2017] ‪+234 701 774 4623‬: 🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻 🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀ 🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻 *GUDU NA AKEYI*☝🏻 😭 *VERY INTERESTED* *STORY* *BASED ON HORROR*🤖 *DON'T TURN ON THE LIGHT* *WHEN READING*😅 *THE BOOK OF NABILA* *PAGE 51 TO 60* Da hk soyayyar Ahmad ta gama ratsa zuciyr shuhaina,har takai ta kawo bata da wani zabi daya wuce ta fito fili ta fada masa gaskiyar abinda ke damunta,koda kuwa bazai yarda ba Ahamad ne zaune cikin keb'ab'en lanbun dake harabar farfajiyar gidan,yanata bitar ass din da aka basu,kamar dg sama yaga shuhaina tsaye kansa tanata faman yimasa murmushi,Dan da nan kuwa ya mike tsaye shima,gamida shafa keyarsa alamun kunya,aah student karatu akeyine aka gudo nan aka zauna?kazauna mana kacigaba da abinda kake,bansan da kaganni awaje karikà mikewa Cikin sakin fuska Ahmad yace a wlh Hjy wani ass aka bamu mai dan rikitarwa shine nazo nan da yake ba surutu sosai nake nazarin sa, da kyau shuhaina tafadi,saannan suka zauna tare, tace niko Ahmad da zaka Kate min da kadena cemin Hjy wlh, dan bana jin dadi idan kana fadin hk, cike da mamaki kuwa Ahmad yace toh Hjy yanzu idan ban kiraki da hk ba me kike son narika kiranki dashi?dan ni ashirye nake dabin duk wani umarni da zaki bani, dan agaskiya kinmin halacci arayuwata, nima km akullum rokon Allah nake daya nunan ranar da zan saka miki da makamancin yadda kika yimin, Fadin hk da ahmad yayi, take shuhaina daji wani irin madarar dadi ta ratsa duk illahirin jijiyoyin jikinta, dan danan xuciyarta ta Fara gaya Mata da yakamata ki sanar dashi gaskiyar abinda ke tafe dake, tunda dama irin wannan damar kike so, km gashi kin samu Murmushin dadi shuhaina ta sakar masa saannan ta dubeshi tace Ahmad kana nufin yanxu dan ka sakamin duk abinda nace zakayi? Kwarai kuwa matukar bai sabawa koyarwar addinin muba cewar Ahmad,nan tace masa nikuwa dama nadade da wani abu cikin raina, km duk duniyar nan banajin akwai mahalukin dazai iya share min hawayena inba kaiba, Da sauri Ahmad yayi saurin dago kansa yadubi shuhaina yace ni km Hjy? nida ba kowan kowaba dame Zan taimaka miki dashi? rangwadar dakanta tayi hade da sakin wani siririn murmushi tace, nasan a iya dan zaman dakayi agidannan nasan kaji lbr irin lalurar dake tare dani Wacce sanadin hakan yasa da dama samari ke gudun aurena,gudun karsu kamu da irin cutar danake da ita, nasan da ace dukiya na bawa mutum daman ya mallaki dukkanin abinda take so, to kuwa dana dade da mallakar miji munyi auren mu, Nan shuhaina ta goge hawayen da ya gangaro Mata kuncinta, ta dubi Ahmad tace inason ka aureni Ahmad, amma kasani bazan maka dole ba,kana da zabi, km dan Allah idan katashi fadamin abida ka zartar kada ka duba irin abida nai mk,dan ni nai maka tsakani da Allah ne,kayi hukncin da bazaka cutar da rayuwar kaba pls, nan ta mike zata bar wajen Ahmad ya dakatar da ita da fadin tsaya my heart basai kinje koina ba dan yanzu zaayita ta kare Abinda ya fada makaramin girgiza zuciyar shuhaina yayi ba,dan jitai gaba 1 tayi mutuwar tsaye dan da'di,hakanne ma yasa batasan sanda ta furta kalman my heart afili ba,yace kwarai kuwa you re my heart desire,dan nima bazan boye mikiba,zuciyata tadade DA kamua da ra'da'din kaunar ki, ban daisan ta hanyar da Zan nuna miki bane, dan ban kai matsayin ba Gameda cutar dake damunki kuwa,suma wadancan masu gudun naki, basu yarda DA kaddara bane, sun dauki canfi ne irin na bature sun sa a ransu, wanda ni sam ba hk bane agurina, da sannu Allahn dayasa miki zai yaye miki insha Allah,karki damu bazan taba gudinki ba, km kisani banyi hk ba dan kwadayin wani abuba dg gareki, kawai hadine dg Allah Muje zuwa [11:06PM, 5/5/2017] ‪+234 701 774 4623‬: 🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻 🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀ 🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻 *GUDU NA AKEYI*☝🏻 😭 *VERY INTERESTED* *STORY* *BASED ON HORROR*🤖 *DON'T TURN ON THE LIGHT* *WHEN READING*😅 *THE BOOK OF NABILA* *PAGE 71 TO 80* Sam yanzu amhad baya kulawa da shuhaina kwata²,ya daina zuwa wajen ta, rabon data sa shi a idanunta ma takusa kwana 4 kenan yau, sai dai Taji motsin shigowar sa ko fitarsa,gashi wani karin bakin ciki duk yan aikin dake gidan ya hanasu shiga part din dà tàke, km kowaye ya tambayeshi Ina Hjy cewa yake tananan lfy hayaniya ce bataso, Kuka kuwa da bakin ciki shuhaina tasha shi, dan yanzu takai ta kawo fitsari da kashi a kwance take yinsu,abinci kuwa daman duk sanda Allah yasa ya shigo dakin,to zai shigo mata da ruwa madara snacks ya ajiye mata daf da ita,idan ta iya ta jawo taci ruwanta,idan ta kasa shi dai baruwansa ,yariga ya sallameta ,sai kuma wani jikon,hakan yasa take matukar nadamar amincewa da Ahmad arayuwarta,ta tsaneshi kwata²,bata kaunar ganinsa ma, Kwance Ahmad kwance kan wani makeken gado a 1 dg cikin guess house din daya siya kwanan nan dan holewa, dg shi sai wani gajeren wando ya balain matse shi,a kuibinshi na hagu wata mace ce fara kanta yasha attachment tawani lafe kan kirjinshi tana ta faman shafa yalwataccen gashin dake kwance a kirjin nashi cike da kirsa, dg kuma ita sai breziya da wani siririn paint,a ban garensa na dama shima hk abin yake, bt ita rike masa shisha tayi gamida zura hannunta cikin gashin kansa gamida hura masa kunnensa time 2 time, shi kuwa zukar shishar yake bt gaba 1 yabi ya kidime dan tsabar dadi, ya manta ma kwata² a wane duniyar yake,cikin kasan zuciyarsa kuwa rayawa yake inama wannan banzar matar tawa ta mutu in gaje dukiyarta? Ashe dama hk masu arziki sukejin dadi? kaga data mutu rayuwa zata dawomin sabuwa in fantama inda nakeso son raina, ay baisan sanda tsabar dadiba dariyar da yake ta fito fili, Murmushi ne ya Kama 1 dg cikin matannan,dan hk ta wani rungumo shi kam, tana wani mgn kasa ² tace" Swt darling,na fahimci dukiya da mata suna kara maka jindadi sosai,dan hk nima ashirye nake da in doraka kan wani mizani dazaka dade iya rayuwarka ana damawa dakai, Cikin hanzari Ahmad ya dubi yace Ashanti ,hade kashe mata kyawawan yes nashi yace "fadamin ko menene Zan aminta dashi lovely nah, dan kinsan Ina matukar jidake duk cikin ciks dina ,cos Ina bala'in son inga sunana ya game koina dalilin dukiyata, Rausayar da kai Ashanti tayi jin irin yabon dayayi mata, gamida tashi cak ta zauna kan cinyarsa, labbanta na gogan nashi tace"dil ne dani km matukar ka aminta natabbatar baza kayi failing ba,bt aharkar akwai rike sirri,Ahmad yace "fada min Ina jinki"Ina harka da wata kungiya dake siyan sasan mutane, kuma harka dasu akwai karuwa sosai,dan idan kaji irin makudan kudin da suke fiddawa wajen siyan haja sai ka rikice, Ashanti ta rungumo Ahmad jikinta sosai, tayadda yana iya filling din boos dinta a kirjinsa,cikin kunnesa take mgn ra'da² ka mallaka mana cikar dake gidanka, akwai muhimman abubuwa da muke bukata dg gareta,tunda Kai kanka bata da amfani awajen ka, cos bata iya gamsar min dakai lovely nah,bata kula min da kai, banda kullum taita bata maka rai,ni km kasan baban abinda ban so kenan Tazamar maka kamar pic, ashanti ta fadi hakanne adai dài sanda ta dafe saitin inda zuciyar Ahmad take, sakamakon bugawar da take da sauri ²,ta Kara da cewa cool down my man, kada kaji KO dar aranka, bawanda zai san hakan ta faru I promise you, idan gudun zargin jamaa kake ma, da zarar sun kammala zanyi iya iyawata inga basu taba naman jikinta ba tawaje,kaga ba Wanda zai fahimci abinda ya faru, Dg hk km sai kafara kiran kanka multi billoniar, cikin wata irin daria Ahmad ya Kara janyo Ashanti jikinsa, gamida sunbatarta in and out yace" lallai sai yau natabbàtar da kina kaunar cigabana my Angel, tunda gashi cikin dan zaman da mukai dake kin fahimci matsalolina da inda nasa gaba, hakika idan hk takasance I will never forget you, gaba 1 suka sa dariya gamida mikewa tsaye hade da rungumar junansu suka shige cikin wani secret room Muje zuwa [11:06PM, 5/5/2017] ‪+234 701 774 4623‬: 🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻 🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀ 🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻 *GUDU NA AKEYI*☝🏻 😭 *VERY INTERESTED* *STORY* *BASED ON HORROR*🤖 *DON'T TURN ON THE LIGHT* *WHEN READING*😅 *THE BOOK OF NABILA* *2ñd to the last page* *PAGE 81 TO 90* Kansu tsaye bakojin dar, suka karaso haravar gidan,manyan barada ne su kusan 3sanye DA bakaken kaya,fuskarsu rufe da mask, suka nupi part din da shuhaina take, sun kuwa yi saa ba Wanda ya gansu sakamakon dama tunkan suzo gidan sunriga da sun asirce gidan ta cikin wata tafkekiyar kwaryar tsafi,Wanda zufinta yakusa zurfin wata rijiyar,hakanne ya basu damar ba wanda ya gansu,koda isowarsu dakin da shuhaina take kwance cikin kashi da fit sari,gaba 1su toshe hancinsu sukayi, sakamakon tsabar warin dake tashi, Cikin wani irin yanayi mai kamada mafaki take iya hangensu garara ²,gashi badamar mgn ballantana ta iya tambayarsu ko suwaye km dg inah, dan hk kawai ta bisu da kallo tare da yin adduoin da ya sauwaka acikin zuciyarta Wani dan madaidaicin buzu 1 dg cikinsu ya shimfima ya zauna,kana sauran suka tsaya kansa suka fara wani irin sambatu,kankace me,gaba 1 suka kama wata irin girgiza kaikace electric shock ne ya kamasu,take idanunsu ya canza kala zuwa jah, gashi Kansu dana jikinsu gaba 1 suka wani mike tsaye, dan najikin nasu gaba 1 saida ya hodo ta kayan jikinsu,farcen dake hannayensu da kafafunsu sukai wani zako² ba kyan gani, Bakinsu kuwa sai fitar dawani kumfa ya keyi launin jini² Kai kayi zaton sabulu sukeci, amma duk da hk basu fasa surkullen da sukeyi ba,ana hk dakin ya gauraye da hayaki, gamida wata irin Kara mai karfin gaske, ji kake yif kamar an jefo wani abu dg sama da karfi Kan gado Ganin hk yasa shuhaina dake kwance kara tsorata sosai, Hawaye suka fara zuba dg idanunta, gwanin tausayi, gashi ba bakin yin ihu balle tayi ko wani yaji ya taimaketa,dan dama ko motsi bata iyayi a yan kwanakin nan, Wani dunkulalen abune ya fado kan gadon daf da kafafun shuhaina,mai girman gaske,fuskarsa yanayin ta mutum amma gangar jikinsa irinna miciji, sai wani irin abu ke fita dg bakinsa mai yauki Kore shar kamar kubewa danya,gamida zazare manya ² idanun sa jajaye,hade da Fara matsowa inda shuhaina ke kwance, Ahankali ya fara hawa jikinta gamida sidar fatar jikinta yana zuba mata wani irin ruwa mai yauki ajiki,har yazo dai² fuskarta, ita dai banda salati ba abinda take dan tasan tata ta kare yau,kura mata ido yayi kur, gamida zaro harshensa waje, ya fara lasar mata fuskarta, da yazo dai² wuyanta kuwa gaba 1bakinsa ya bude,hakoransa zako² koraye shar suka bayyana waje ya kuwa soka mata su da karfi a wuyanta, take anan ta fara shure ² dan tsabar azaba, Da karfi yake zukar jinin jikinta dan tsabar dadin da yake ji gamida lumshe manya² idanunsa, su kuma wadannan mutanen da suka ga hk sai sukayi shiru da surkullen da suke, alamun abin nema ya samu,baban cikinsu dake zaune kan buzunsa ya tara wata katuwar kwarya daidai bindin halittar nan, koda taba wurin saiga jini ya fara malalowa cikin kwaryar kamar an bude fanfo, gaba 1 su 3 hankalinsu ya tashi,yawun bakinsu ya tsinke, da sauri kuwa suka kafa kai cikin kwaryar suka fara shan jinin Bayan halittar nan ta gama tsotse jinin jikin shuhaina tsaf, km ta tabbatar ta mutu, ta kuwa zura dogon harshenta cikin bakinta har saida ta tabbatar yaje har cikinta, ta kuwa nanado komai da komai dayake cikin tayo waje dasu da karfi, cikin hanxari wani dg cikin mutane nan ya zagayo gamida mika wata container ta duma ya zuba ciki,lasar wuyan shuhaina kawai tayi saiga tabo inda ta tsosi jinin ya baje bayan sun kammala komai ne,km sukai clearing koina, suka fara surkullen da sukai abaya, wannan halittar ta bace,suma suka fice dg gidan,sai misalin 10am kamar hadin baki maaikatan gidan suka farka, kowa kuwa nata mamakin yadda akai hakan ta kasance Wurin 12pm motar Ahmad ta tsaya dai² bakin gate din gidan, da sauri kuwa mai gadi ya bude mai hade damai sannu da zuwa, dan dama ya sanar musu a kd zai kwana sai washegari zai dawo, Kai tsaye dadin shuhaina ya nufa, yana yar dariyarsa,ya taradda ita kwance kamar Kai mata mgn ta amsa, amma inah rai yayi halinsa,a sàñnan ne yaji alamun msg ya shigo wayar sa, kodaya duba wani mahaukacin alert ya gani, ay baisan sanda ya fasa ihuba da karfi,dan dadi, ya kuwa saurin rufe bakinshi gudun kar wani yaji ya dagata gamida duba koina a daki bt baiga wata a lamar tonan asiriba, dan hk ya dakko wasu kaya masu kyau yasa mata,ya cana zanin gadon shima,ya kwashe na kashin dake jikinta da bed sheet ya kulle a leda, ya feshe koina da turare,sannan yà nufi harabar gidan yana kuka Muje zuwa [11:06PM, 5/5/2017] ‪+234 701 774 4623‬: 🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻 🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀ 🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻🏃🏻‍♀🏃🏻 *GUDU NA AKEYI*☝🏻 😭 *VERY INTERESTED AND SHORT* *STORY* *BASED ON HORROR*🤖 *DON'T TURN ON THE LIGHT* *WHEN READING*😅 *THE BOOK OF NABILA* *THE LAST PAGE* *PAGE 91 TO 100* *Godia* mai tarin yawa ga dukkan masoyana musamman wadanda suka nuna kaunarsu da wannan buk din nawa ngd² Allah yabar kauna *Bazanmanta daku ba wato* _______=======__________ *Asy kaleel* *Jidda Aliyu* *Ummi Garkuwa* *Allah yabar zumunci* Dan danan gida ya hargitse da kuka,media da sauran kafofin yadda labarai duk sun sami abin yayatawa,hk ciki da wajen gidan yacika tap da jamaa',kowa na jajanta wannan alamari, masoya da abokanan hudarta banda kuka ba abinda suke, dan agaskiya sunyi matukar bbn rashi, dan shuhaina yarinyace mai ganin girman duk Wanda ke kasanta, bata da wulakanci Sam, ga abin hannunta kwata² bai rufe Mata ido ba, samun madadinta kuwa awajensu ba karamin bban abu bane, Kuka Ahmad yake yi sosai kamar ransa zai fita,bayan da suka dawo dg makabarta ,dan anyi lalashi amma Sam hawayen dake kwarara dg idanunsa sunki tsayawa,kowa kuwa tausayin sa ya kamashi matuka, sakamakon kwata² auren nasu baifi wata 8 ba, wato ana tsaka da more amarci,amma gashi mutuwa ta shiga tsakani, ganin hln daya keciki ne yasanya aka rakashi cikin gida, wala Allah koya dan samu dan natsuwa, amma inah su basusan gaba 1 shi haushin kowa yake jiba, dan jiyake inama yanada yadda zaiyi dasai ya tarwatsa dondazon jamar da suka taru,dan irin uban kudin da akasa shi ya fitar a account ba karamin bata masa rai yayi ba Ta window ya leko yake hangen jamaa',yadda kowa ya ware ciki yanata kwasar abinci, banda katon² din ruwa da soft drinks din da aka dunga fita dashi dg gidan Kai kace biki akeyi,km fa duk agadon sa ake kwasar wannan ganimar,takaici ne ya turnike shi ya saki wani uban tsaki ,kawai yaje ya mayar da kofa ya kulle dan tsabar bacin rai, hade da fadin" duk ubanku zakuci mayunwata kawai,dan mgn ku zanyi, dg yau bamai sake zaman min akofar gida,sadakar 3 data 7 ma ayi a masallaci Bayan kamar makonni Ahmad da ashanti soyayya mai karfi ta dinke tsakanin su,amma gudun kar mtn sufara zarginsa ya sanya suka tattara suka koma Lagos da zama na wucen gadi, a can gun aiki km yace ganin gida zashi,idan kaga kuwa yadda suke muamala da juna kai kace sababin amare ne,dan kwata ² ya sabawa tsarin koyarwar muslinci, Kudi kuwa suna cin ubansu, dan adan zuwan da sukayi har ya siyanma Ashanti wata jibgegiyar car yar yayi, duk kuwa abinda tace tanaso komai tsadarsa zai siyan mata,iyayenta ma sun kwashi nasu rabon wurin Ahmad,dan anasu hidimar harda gida yasai musu, banda bakin aljihun daya sakar musu, da yake ba musulma bace, amma sun tsara akan cewa bayan auren su, kowannen su zai zauna ne kan addinin sa batare da takura ba ********************** ? ************************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************? ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ? ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ? ************************** *Back to story* _____===_____ Cikin wata kakausar murya shuhaina ta cigaba da fadin" KO kazaci bansan kane kasa a kasheni ba? km kisa ta hanya mafi azabtarwa, wai duk dan abin duniya, to kasani inada damar dazan kasheka amma bazan aikata hkn ba, so nake gaba 1 duniya sai tasan abinda ka aikata, ita km waccan azzalumar, ta nuna inda Ashanti take kwance, sai na dan dana mata azaba daidai da yadda tasa aka min, daga hannu shuhainà tai sama ,sai ga wani dogon gatari ya bayyana ta kuwa dago ashanti sama ,ta buga mata dai² saitin zuciyarta,take ta fara wani irin k'araji sai ga jini ya fara fita ta hanci, kunne, baki da idanun ta,ganin hakan da Ahmad yayi ne take ya susuce ya zare, ya fita waje da gudu yana sanbatu gamida ihu cikin daren,nan shuhaina tà bace abinta Layi ² Ahmad yakebi cin sanbatu irin na hauka yana bada lbr abinda yayiwa matarsa, banda jifa da tsinuwa kuwa bà abinda yake sha gurin jamaa', kowa *GUDUN SA YAKEYI* an km tsaneshi, duk kuwa da cewa ya riga ya zama mahaukaci tuburan,hmm wannan shi ake kira rasasa², gà dai duniyar ya tara amma ba damar morarta,kaico Allah ka tsaremu da aikin danasani ameen Dukiyar shuhaina data rage km, alh aminu ya tatara yayi Mata sàdaka dasu da zummar Allah yakai ladan kabarinta. *TAMMAT BIHAMDILLAH* ______=========______ *Nabila maman Kalil* ke muku fatan alkairi,mu hadu book nagaba.