.MUTUM DA ALJAN Littafi Na Uku (3) Part B. Author: Abdul aziz M Gini Rubutawa : Al amin Ahmed Misau Nickname: Guyson ko shagala Contack me: 08064594218 Gargadi: Ban yarda wani yayi edit na wannan post ba ba tare da izinina ba.. . Labari ya isowa Guyson cewa Face mutum biyo, wato sarki da yarima kamsus tsawon yan dakiku suna tsaye suna kallon yadda ake ta shirye shiryen tafiyar dayansu bai ce uffan ba daga can sai sarki yayi gyaran murya ya dubeshi a cikin murmushi yace'' hakika ka baiwa namrita shawara mai kyau dakace da ita su manta da batun daukar fansa a kaina'' koda jin wannan batu sai zuciyar yarima kamsus ta buga da karfin gaske ya firgita ainun kuma ya kamu da tsananin mamaki kuma yayi shiru baice komai ba sarki ya sake yin murmushi a karo na biyu yace idan namrita da dan uwanta zaihas sun dauki shawararka sun daina farautar rayuwata nima zan kyalesu amma nayi maka alkawarin duk ranar da suka sake yin gangancin kawo min hari a wannan lokaci zan zare musu ruhin numfashinsu wannan shine kashedi na karshe kuma sakone nake baka yanzu ka isar dashi. Alfarma daya zan iya yi musu idan har suka zo gareni bisa lumana zan rokesu gafara bisa abinda na yi na kashe musu mahaifi ba akan laifinsa ba ka sani cewa a ka idar sarauta kisa a wajan sarki ba laifi bane saidai a kirashi kuskure saboda duk harkace ta mulki duk sarki na gari mai cikakken iko da isa gami da kamala baya durkusawa wani ko da kuwa dan uwansa sarki ne' koda sarki Alkasim yazo nan a zancensa sai ya kwalawa wani hadiminsa mai suna kailub kira yace maza ka janyo min dokina nan take kailub ya ruga zuwa inda dokin sarki yake kafin yazo da dokin tuni sauran hadimai sunkimtsa sarki sun daura masa damararsa an kawo masa takalmansa an ajiye a gabansa ya sanya kuma an shirya masa kayan yakinsa a jikinsa koda ganin haka sai shima yarima kamsus ya ruga zuwa nasa tantin ya shiga kimtsawa da sauri nasa hadimin na taimaka masa. Lokacin da sarki Alkasim ya gama shiri ya hau bisa ingarman dokinsa mai launin ruwan kasa ya zauna saiya wuce kan gaba gaba daya miliyoyin jama ar dake cikin tawagar sai suka biyoshi a baya duuuu.... Kai kace mutanen duniyar ne kaf sukayi hijira zasu koma wata nahiyar daban'' wohoho'' hakika masu iya magana sunyi gaskiya da sukace dole ne ace da mijin iya BABA. domin duk wanda yaga sarki Alkasim a wannan lokaci saboda kwarjininsa cika idonsa da kuma irin gagarumar shigar yakin da ya yi dolene ya tsorata da al amarinsa saboda ya zama tamkar zaki Uban dawa kallo daya mutum zaiyiwa sarki Alkasim yaji zuciyarsa ta buga da karfi saboda kirarsa gaba daya irin ta zakice kaida gani kasan cewa dolene ya kasance masifaffen kakkarfa hm Guyson nake magana sarki Alkasim ya kasance dogon mutum mai murdadden jiki cike da kwanji gami da jijiyoyi yana da yalwataccen kirji cike da gashi kuma a fuska ya kasance kyakkyawa abin kwatance amma kusan ko yaushe fuskar tasa a murtuke take tamkar bai taba yin dariya ba tabbas barewa bata gudu danta yayi rarrafe yarima kamsus ya gado mahaifinsa a sura da cikar zati sai dai zuciyarsa bata da tauri irin ta mahaifinsa ma ana yafi sarki Alkasim walwala da annurin fuska kuma ya fishi tausayi gami da jin kai, sai dai suna tsananin kama da junansu tamkar hassan da usaini kawai shekaru ne ya banbantasu gami da tsohon kashi shidai sarki yana da saje mai kauri gemu mai tsawo da gashin baki mai yawa shi kuwa yarima kamsus bash da saje da gemu sai dan siririn gashin baki wanda ya yiwa lebensa da habarsa kawanya abin gwanin ban sha awa kuma ko yaushe yana tattare dogon gashin kansa ya tattareshi ya daure su zube bisa gadon bayansa yan matan kasar birnin misra da yawa sun dimauce a cikin soyayyar yarima kamsus saboda kwarjininsa kyawunsa da kuma baiwarsa ta jarumtaka kai wasu ma saida suka zama kamar zautattu saboda yawan begensa da ambatonsa amma ba a taba samun wacce ta burgeshi ba bare ma yayi soyayya shi kansa a halin yanzu da yaji zuciyarsa na begen jaruma namrita kamuwa yayi da tsananin mamaki har yana tambayar kansa a cikin zuci yana mai cewa akan wane dalili nake tunanin namrita alhalin na sha haduwa da matan da suka fita kyau matsayi da daukaka amsar da ya kasa baiwa kansa kenan a duk lokacin da wannan tunani ya bijiro masa to wai shin yadda naji na kamu da son namrita haka itama al amarin yake a ranta kuwa? Ta yaya zan gane hakan alhalin har yanzu bamu fito kuru kuru mun bayyanawa junanmu komai ba ai ita ce ya kamata ace ta fara bayyana min sirrin zuciyarta tunda ni dan sarkine ita kuwa ba yar kowa bace haka dai yarima kamsus yake ta irin wannan tunani da wasu wasun zuci mara kan gado a duk sa adda tunanin namrita ya bijiro masa. Kamar yadda sarki Alkasim ya fada haka al amarin ya kasance wato tunda aka fara wannan tafiya babu sassauci ba ayada zango sai bayan kwanaki uku uku kuma dare da rana a cikin tafiyar ake hatta abinci akan ababan hawa ake ci kuma ko bukatace ta kama mutum ba a tsayawa a jirashi saidai a barshi a baya ya kawai da bukatar idan ya kammala ya ruga da gudu ya riski tawagar kai ko barci ne ya kama mutum sai dai yayi akan dokinsa ko rakuminsa ko alfadaransa sau tari sai dai kaji tum mutum ya fado kasa daga kan abin hawansa saboda magagin barcin sai dai ya mike tsaye zumbur a firgice ya sake dane abin hawan nasa hm Al amin Ahmed Misau Guyson.. Wani babban abin mamaki shine babu wanda yake jin gajiyar tafiyar a jikinsu har sai an yada zango bayan cikar kwanaki ukun . Haka dai darare suka ci gaba da shudewa har ya zamana cewa saura kwanaki uku kacan a iso birnin sarki masarul anjana wanda ke nahiyar kasar Sin inda aka yada zango a cikin wani babban daji wanda ake kira da suna DARUL SAMJUL. Shidai wannan daji na darul samjul masana matafiya da masu bincike sun tabbatar da cewa babu wani daji mai girmansa tarin ni imominsa da kuma yawan dabbobi babu tamkarsa a duk fadin duniyar nan don haka yana da hadarin gaske saboda babu irin kalar mugayen halittun da babu a cikinsa kai sai mafarauci ya cika babban barde yake iya shiga cikinsa yayi farauta inba haka ba kuwa sai dai a dauko gawarsa a ciki koda aka iso farkon wannan daji sai sarki Alkasim dake kan gaba ya ga dokinsa yayi turjiya yana mai haniniya gami da daga kafafunsa na gaba sama kuma yaja da baya kadan cikin alamun firgici tamkar wanda ya hango wani mugun abu a gabansa ai kuwa nan take sauran dawakai da sauran alfadarai da rakuma sukayi koyi da wannan doki na sarki aka rasa dayansu wanda zai kara gaba koda taku daya ne koda ganin abinda ya faru sai farin ciki ya lullube sarki Alkasim ya bushe da dariyar farin ciki a lokacinda kowa ke firgici aka yi tsit ana kallonsa kawai cikin al ajabi kawai kuma sai aka ga sarki Alkasim ya sauko daga kan dokinsa ya tsuguna kasa bisa gwiwarsa guda ya debi kasa ya shinshina cikin hanzari da murna ya juyo ya dubi sarkin yaki da yarima kamsus yace tabbas mun iso dajin darul samjul dajin da na dade ina burin son zuwansa domin nayi farauta a cikinsa maza mu yada zango a nan a kafa tantuna tunda dare ya soma sai gobe da safe saimuyi shirin shiga farauta cikinsa yakai sarkin yaki ka zabo manyan jarumai a cikinmu guda arba in ka shirya mana gasar farauta a cikin wannan daji na darul samjul lallai ka sa kanka da yarima a cikin wannan gasar koda jin wannan batu sai mamaki da tsoro ya kama gaba dayan jama ar dake cikin wannan tawaga sarkin yaki da yarima kamsus ne kadaibasu yi wani gezau ba Saikuma Ni Al amin Guyson. Wanda na kasance Jarumi. Ba komai ne ya firgita jama ar ba face kowa ya dade yaana jin wannan dajin darul samjul ana cewa komai hatsabibancin boka ko mafarauci ko kuma jarumi yana shakkarsa akwai abubuwa masu tsananin wahalar gaske wadanda ba a samunsu sai a dajin darul samjul kuma mutane da yawa sun hallaka a kokarin nemo wadannan abubuwa a cikin dajin kai ance ma komai yawan ayari kona fatake idan sukazo giftawa ta cikin dajin darul samjul to sai kaso biyu cikin ukunsu sun zama gawa kaso dayan ma sai sun kasance zakwakuran mayaka matsafa da jarumtaka sannan zasu tsira kuma duk da hakan ma sai da yawansu sun samu mugayen raunuka a jikinsu ba tare da bata wani lokaci ba aka yada sansani a bakin wannan daji na darul samjul aka shiga kafa tantuna aka shirya kayayyaki sai dai mutane da yawa a firgice suke musamman mata hadiman da aka taho dasu saboda jiyo sautin kukan mugayen dabbobi da tsuntsayen dajin duk da cewa suna can nesa dasu saboda kukane mai irin wani bakon sauti wanda kunnuwa basu saba ji ba bayan an gama kafa tantuna anci abinci ana zaune ana hutawa kowa ya samu nutsuwa yarima kamsus na zaune a cikin tantinsa tare da wadansu kuyangi guda uku suna debe masa kewa daya daga cikinsa na bashi labari mai dadi na ban dariya sai ga sarkin yaki ya shigo cikin tantin nasa koda ganinsa sai kuyangin suka barsu su biyu sarkin yaki ya risina ya kwashi gaisuwa sannan ya dauko wata takarda daga cikin aljihunsa wacce akayi rubutu akan ta da bakar tawada ya mika masa yace ya shugabana wannan takarda na dauke da sunayan jarunamu guda arba in wadanda sarki ya umarceni dana zabosu domin shiga gasar farautar daya ce nau shirya mana a gobe da safe koda jin wannan batu sai yarima ya karbi takardar da sauri ya fara dubawa inda ya fara yin arba da sunan sarki sannan nasa da na sarkin yaki a can karshen sunayen kuma da yaga sunayen wadansu jarumai guda biyu wadanda ake kira RAMJUS DA HATYAN sai ya dago kai ya dubi sarkin yaki cikin mamaki yace saboda me zaka sanya ramjus da hatyan a cikin wannan gasa alhalin suna jinyar raunikan da suka samu a yakin da sarki ya turasu watanni hudu da suka gabata?? Koda jin wannan tambaya sai sarkin yaki yayi murmushi sannan yace. Ya shugabana ai duk sun samu lafiyarsu kuma kowannansu ya amsa min da bakinsa cewar zai iya shiga wannan gasa ba kaga yadda ma suke farin ciki da yin wannan gasar ba yayina yarima yaji wannan batu sai al amarin ya sake daure masa kai saboda shi dai a saninsa irin raunikan da ramjus da hatyan suka samu ana iya yin shekara guda ana jinyarsa ya za ayi ace har sun warke a cikin watanni hudu kacal?? Kawai sai yarima ya kada kai ya dubi sarkin yaki yace to menene yanayin wannan gasar ina so naji yadda aka tsarata sarkin yaki yayi gyaran murya sannan yace abinda na tsara shine gaba dayanmu mu arbain din zamu shiga cikin dajin darul shamjul a kasa bisa kafafuwanmu mu yi farautar dabbar farko wacce mukayi arba da ita . . Dokar gasar itace ba za a harbi dabbar ba ko kuma a sareta da makami sai dai a kure mata gudu a kamota da karfin tsiya koda mutum ya samu nasarar kamata shi kadai sauran jaruman gasar zasu iya kwaceta daga hannunsa sai dai karfinsa da basirarsa da zafin namansa su kwaceshi ya dawo da dabbar a hannunsa har izuwa nan sansanin namu shine ya tabbata ya lashe gasar koda jin sarkin yaki yazo nan a zancensa sai yarima kamsus yayi doguwar ajiyar zuciya sannan ya dubi sarkin yaki yayi masa dan guntun murmushi yace tabbas ka iya shirya gasa mai matukar wahala aiko sarki da kansa sa ace zata iya bashi nasara a wannan gasa ba wai karfinsa da dabararsa ba sai dai ka manta da abu guda a cikin gasar cikin mamaki da doki sarkin yaki yadubi yarima yace menene abin da na manta dashi? Yarima yace ka manta kace a cikin dokar gasar babu amfani da karfin sihirin tsafi hakanne kadai zai hana sarki dani lashe wannan gasar a saukake yayinda sarkin yaki yaji wannan batu sai yayi murmushi yace tabbas kazo min da babbar shimfidarsa ya kishingida yace inka fita ka toromin kuyangina suci gaba da debe min kewa saboda bana zaton zan iya yin barci da wuri sarkin yaki yace haba ya shugabana kai kuwa menene zai hanaka barcin alhalin baka daya daga cikin masu tsoron wannan daji na darul shamjul? Yarima yace kaga mai daki shi yasan inda yake yi masa yoyo tafi ka bani wuri dajin haka sai sarkin yaki ya juyo da sauri ya fice daga cikin tantinsa fitarsa ke da wuya sai ga kuyangin yarima sun dawo nan dai sukaci gaba da debe masa kewa har saida suka ga barci ya saceshi sannan suka mike tsaye suka fice suka tafi izuwa nasu tantin suna tsegumi da gulma inda daya daga cikinsu ta dubi sauran tace wai shin anya kuwa yarima lafiyayyen namiji ne ko da jin wannan tambaya sai sauran kuyangin biyu suka bushe da dariya sanna guda tace kece bakuwa a cikinmu shi yasa baki san halayansa ba to ki sani mu tare dashi muka taso tun kuruciya yarima bai damu da mata ba kuma bai taba yin soyayya ba mun sha yin barci tare dashi mu kwana daki guda amma bai taba nuna sha awarsa akan dayarmu ba akwai ranar da muka taba yi masa irin wannan tambayar da kikayi mana yanzu amsar da ya bamu itace ya daukarwa kansa alkawari cewar ba zai taba sanin wata ya mace ba face matar da ya aura koda jin wannan batu sai mamaki ya turnuke wannan kuyanga ta jinjina kai tace ai kuwa duk macen da ta auri yarima ta gama dace da samun babbar sa a domin ya tara baiwa mai yawa irin wacce mazaje da yawa basu da ita da wannan kami kuyangin suka rufe hirarsu kowacce ta samu wuri ta kwanta suka kama barcinsu... . Nima kuma da wannan kalami nawa Guyson naji barci ya fara neman zuwa sbd haka nake cewa sai Allah ya kaimu Gobe zamu ci gaba Amma kafinnan... Nidinne dai Al Amin Ahmed Misau Guyson sunana kenan MUTUM DA ALJAN Littafi Na Uku (3) Part C. Author: Abdul aziz M Gini Rubutawa : Al amin Ahmed Misau Nickname: Guyson ko shagala Contack me: 08064594218 Gargadi: Ban yarda wani yayi edit na wannan post ba ba tare da izinina ba.. . Labari ya isowa Guyson cewa da wannan kalami kuyangin suka rufe hirar tasu kowacce ta samu guri ta kwanta suka koma barci abinsu,lokacin da gari yaw aye da sassafe bayan anyi kalaci jama’a suka sake taruwa a bakin tantin sarki Alkasim inda aka jere jarumai talatin da takwas wadanda zasuyi gasar farauta a cikin dajin darul samjul , a cikin wadannan jarumai hard a sarkin yako, sauran jama ar tawaga kuwa sunyi dandazo a gefe guda suna jiran fitowar sarki Alkasim ana ta kace nace kowa na fadin albarkacin bakinsa akan wannan gagarumar gasa da za ayi wasu suna mamakine akan daliin da yasa sarki ya shirya wannan gasa alhalin ana kan hanyar zuwa birni n sarki masarul anjana , wasu kuwa suna mamakin yadda aka zabo ,mutum arba’in kacal alhalin ga jarumai nan da yawa wadanda aka taho dasu dubunnan don su nuna jarumtakarsu acan birnin sarki masarul anjana domin su burge gimbiya zulfulaifa ko tayi dariya.Jim kadan sai ga sarki Alkasim tare da dansa yarima kamsus sun fito daga cikin tantinsu. A wannan lokaci duk su biyun sunyi gagarumar shigar yaki mai matukar kwarjini daban sha awa wadansu bakaken rigunan fata matsatstsu masu gajeren hannu suka sanya gami da dogon wando shima na fata matsatstse gaba dayan surar jikinsu ta bayyana a fili takalmin da suka sanyama fata ne dogaye iya guiwa masu madauri kowannansu ya rataya zabgegiyar takobi a bayansa kuma ya saba kwari a bayansa ga baka ruke a hannunsa. Wohoho duk wanda yaga wannan da da uba a wannan lokaci dole ne su burgeshi kuma dolene su firgitashi saboda yasan cewa su biyun kacal zasu iya tashin gari guda domin da gani babu tambaya ansan kura zataci mutum Guyson nake magana sunana kenan dan misau babban abin da zai fi burge mutum shine yadda kamanninsu tsawonsu da kuma kaurin jikinsu da surarsu ta zamo iri daya sak tamkar tagwaye kawai a fuskane za a gane banbancin shekarunsu ba tare da bata wani lokaci ba sai sarkin yaki ya risina ya gaida sarki da yarima kamsus sannan ya dubi sauran jama ar tawagar su ma yagaishesu nan take yayi jawabin yadda za ayi wannan gasa da kuma dokokinta koda jin hakan sai gaba dayan jama a suka kama yiwa sarki Alkasim kirari gami da jinjina ana cewa ai tabbas shine zai lashe wannan gasa sun manta dani guyson a gefe nan fa sarki alkasim yaji wani irin farin ciki gami da girman kai ya shigeshi baisan sa adda ya kama yin murmushi ba yana dagawa jama a hannu a dai dai wannan lokacine yarima kamsus ya hango jarumi Ramjis da hatyan tsaye a gefe daya cikin jaruman gasar suna kallon sarki suna murmushi alamar cewa suna da ja akan cewa babu tabbacin cewa shine zai lashe wannan gasa fiye da shekaru ashirin da biyar baya a birnin misra idan aka yi gasar farauta ramjis ko hatyan ne daya daga cikinsu ke lashe gasar saboda dama can sune 'ya'yan sarkin mafarauta wato gado sukayi ba haye ba ko sau daya sarki Alkasim ko yarima kamsus dayansu bai taba shiga wannan gasa ba don haka yau Al amarin ya zama sabo ba a san yadda zata wakana ba kawai sai yarima kamsus ya baro inda sarki ke tsaye yazo inda su ramjis ke tsaye ya dubi ramjis yace tayaya kuka samu lafiyar jikinku da sauri haka har kuka iya shiga wannan gasa? Koda jin wannan tambaya sai ramjis da hatyan suka yi yar dariya sannan ramjis ya dubi yarima cikin murmushi yace tabbas ya kamata ace mun samu wata bakwai zuwa takwas muna jinyar jikinmu kafin mu sake fita yaki ko farauta amma saboda an shigo fagenmu na farauta dolene mu fito don kada a yi mana gori ko kuma a kwace mana matsayinmu da muka gada tun iyaye da kakanni koda jin haka sai yarima ya gyada kai yace gaskiya ne kun burgeni amma kuma kunyi ganganci domin ko yaya aka fama wannan rauni naku shi kena9 an dawo daku baya don sai kun sake maimaita watannin da kuka shude na warkewa idan ba zaku damu ba ina son ku kwaye min raunikan naku na gani kafin yarima ya gama rufe bakinsa tuni ramjis da hatyan sun janye kafar wandonsu sai5a tabon manyan sara akan cinyoyinsu shi ramjis akan cinyarsa ta hagu aka yi masa wani lafcecen sara shi kuwa hatyan akan kaurinsa ne na hagu gashi dai duka raunukan an dinkesu kuma saura kiris wajan ya gama kamewa amma akwai alamun cewa idan aka fama ciwukan zasu iya dawowa sababbi koda yarima yaga wadannan raunuka sai ya cika da mamaki kuma ya fara tunani a cikin ransa cewa abin fa da yake zargi ba haka bane ba wani abu yarima ke zargi ba face yana tunanin cewa ramjis da hatyan basu bane ba a zahirin suuka shiga wannan gasa jaruma namrita da dan uwanta jarumi zaihas ne suka juye izuwa kamanninsu to yanzu dai gashi ya duba da idanunsa yaga kuma basu bane domin ida sune din da dole ne ya ganesu saboda wannan rauni da suka samu tsawon watanni hudu da suka gabata kafin yarima ya dubi su ramjis ya sake cewa wani abu sai sukaji an busa kahon tafiya farauta sarki Alkasim ne ya fara wucewa gaba yana sauri sauri gudu gudu ai kuwa sai yarima ya ruga gareshi ya take masa baya koda ganin haka sai ramjis da hatyan ma suka bisu da sauri.... Sannan sarkin yaki da sauran jaruman gasar mutum talatin da shida, duk wanda ya dubi wadannan jarumai arba in a lokacin da suka durfafi dajin Darul Samjul yaga irin surarsu kwarjininsu da kuma makaman yakin dake jikinsu sai yayi zaton cewa zasu iya hallaka gaba dayan mugayan halittun dake cikin dajin to amma fa ga wanda yasan dajin kuma yasan irin mugayen abubuwan hadarin dake cikinsa yasan cewa ba zasu iya ba da shigarsu sarki Alkasim farkon dajin Darul samjul sai kowannansu ya nutsu hatta shi kansa sarki Alkasim kuwa domin shine ma ya fara rage karfin gudunsa yana nazarin gefe da gefensa da kuma gabansa saboda tunanin cewa ko yaushe wani mugun abun zai iya kawo musu hari, nan da nan kuwa kowa yayi koyi dashi domin baiwa kai kariya dajin yayi tsit a cikin safiyar ba a jin sautin komai face na kananan kwari da tsuntsaye komai jarumtakar mutum gami da dakewar zuciyarsa idan ya shigo cikin wannan daji na darul samjul dole ne zuciyarsa tayi rawa saboda yanayin hatta bishiyoyi da irin duwatsun dake cikin dajin wadansu iri ne na musamman wadanda idanu basu saba gani ba sai da su sarki Alkasim suka shafe kusan rabin sa a suna tafiya a cikin dajin ba tare da sun ga wata dabba ko guda daya ba face kwari irin su kunamai, macizai da sauransu dai Al amarin da ya sa kowa ya fara kosawa kenan har aka fara tunanin cewa anya kuwa wannan gasar zata yiwu? Watakila sai dai a fasa gudanar da gasar a koma da baya zuwa can sansani tunda gashi lokaci na tafiya ba a hadu da wata dabba ko guda daya ba A cikin wannan hali ne kwatsam aka hango wata irin dabba ta musamman ta tunkaro tun da sarki Alkasim yazo duniya bai taba ganin irin wannan dabba ba bare kuma sauran jaruman wadanda shekarunsu sun gaza nasa dabbar tana yanayi da zaki amma tafi zaki tudu da fadi kuma tana da gajeren kahonni guda biyu a tsakiyar kanta masu kauri da tsini, kirjinta a cike yake da gashi mai tsawo har yana sharar kasa a kofatun hannayanta da kafafunta akwai zarazaran farata masu kaifin tsiya saboda nauyinta idan tana tafiya sai kaji kasa na rawa tamkar takun toron giwa da farkon sa adda dabbar tayi arba dasu sarki Alkasim sai taci gaba da tunkarosu ba tare da shakkar komai ba amma da taga cewa suma kara tunkarota suke babu shakkar komai sai ta tsaya cak ta zuba musu idanu aka fara kallon kallo'' chai kaji manyan jarumai masu dakakkiyar zuciyar yaki ehm nidai guyson wajan yaki bana nan sbd haka bari na matsa gefe Wohoho idan maza da maza suka hadu a sannan ne ake sanin waye jarumi kuma waye matsoraci tabbas dasu sarki Alkasim din da kuma wannan dabbar kowa ya sha jinin jikinsa yasan cewa ya gamu da gamonsa idan ka dauke sarki Alkasim da yarima kamsus ,ramjis da hatyan gaba dayan sauran jaruman a firgice suke tunda akayi arba da wannan dabbar domin kowannansu da kyar yake iya daga sawayansa yana ci gaba da takun kafafunsa haka dai su sarki Alkasim suka ci gaba da durfafar wannan dabba ita kuwa tana tsaye kyam a inda take tana kallonsu kawai ko motsi batayi. Koda dabbar taga cewa saura baifi taku goma ba kacal a tsakaninsu sai ta yunkura cikin bakin zafin nama ta juya da baya ta falfala da azababben gudu na kwatance nan mafa su sarki Alkasim suka bita aka kasa mugun tsere hakika masu iya magana sunyi gaskiya da sukace ba a sanin maci tuwo sai miya ta kare. Ana fara yin wannan azababben gudu ne aka fara barin jaruman gasar a baya domin gudu ne na kare iyawarka ko nace kare kukanka, Al amin Ahmed Misau Guyson Sunana kenan shugaban zauran labarai page sai da aka shafe sa a uku ana falfala gudu ga dabbar a gabansu suna hangota itama tana waigensu tana ganinsu amma sun kasa cimmata ita kuma ta kasa bace musu da gani A wannan lokaci gaba dayan jaruman gasar sun sare sun zube kasa suna haki kamar ransu zai fita saura mutum hudu kacal biye da dabbar basu sare ba saboda bakin nacinsu da juriyarsu ba wadansu bane ba wadannan mutane hudu face sarki Alkasim , yarima kamsus, ramjus da hatyan saikuma guyson me rubuta labarin duk sa adda sarki Alkasim ya waigo bayansa yaga yarima dasu ramjis da hatyan na biye dashi basu sare ba sai ya cika da mamaki domin shi a zatonsa ba zasu iya kawowa haka ba suna wannan tseren gudu alhaliin dukkaninsu babu wanda ya ke amfani da karfin sihirin tsafinsa, kawai suna amfani ne da tsagwaron horon da suka samu na gado dakuma juriya da jarumtaka Abu dai kamar wasa har saida yarima dasu ramjis suka hada kafada da sarki amma an rasa mutum daya da a cikinsu wanda zai iya cafke wannan dabba a wannan lokaci tazarar dake tsakaninsu da dabbar bai wuce taku biyar ba babban abinda ya dugunzuma hankalinsu shine ko kadan babu alamar gajiyawa a wajan dabbar su kuwa dukkaninsu sun fara gajiya da yin haki alamar cewa nan da wani lokaci zasu iya sarewa ko da suka fahimci hakan sai dukkaninsu a lokaci guda suka daka tsalle sama suka diro akan dabbar kowa ya kai mata cafka kaico bala'i ba a sa masa rana kuma ita masifa ba a san farkonta ba bare karshenta koda wannan dabba taji an cafketa ta gaba da bayanta sai ta fara kokarin kubuta nan fa aka ruguntsuma da azababben fada atsakaninta dasu sarki Alkasim ta rinka kai musu suka da kahonninta cizo da hakoranta gami da yakushi da faratanta da kafafunta su kuma suka rinka gocewa suna gabza mata wannan naushi iya karfinsu amma sai gashi tana shanye dukan nasu tana makesu suna faduwa kasa amma sai dai kaga sun mike zumbur cikin bakin zafin nama gami da jarumtaka a iya gwagwarmayar da wadannan jarumai hudu sukayi a duniya basu taba haduwa da dabba mai karfin wannan ba domin duk sa adda .ta dako tsalle ta kawowa dayansu bangaza da kirjinta idan ya goce duk abinda ta doka da kirjin take yake ratattakewa ya rugurguje ko da kuwa abin ya kasance dutsene ko bishiya. Ganin wannan al amarin yasa sarki da yarima suka fusata ainun suka kara zage damtse suna amfani da dukkan karfinsu akan dabbar ramjis da hatyan kuwa sai suka dan ja da baya suka zuba musu idanu suka samu damar hutawa amma sai haki suke ta faman yi kamar ba zasu iya ci gaba dagumurzun ba Lokacin da dabbar taga sarki da yarima naso suyi mata illah saboda kai mata mugun naushi da bugu suke ta ko ina har tana faduwa kasa in ba don ma tana da mugun zafin nama ba da tuni sun yi mata lugudan da zata kasa tashi sai ta shammaci yarima kamsus ta doki gadon bayansa da kanta take yarima ya kurma uban ihu sakamakon tsananin zafi da zugin da yaji kashin bayansa ya karye sai gani aka yi ya kife kasa da ruf da ciki Koda ganin abinda ya sameshi sai sarki Alkasim ya fusata ainun ya cafi makoshin dabbar da hannayansa biyu ya kauta kasa ya danne kuma ya shaketa iya karfinsa nan fa dabbar ta fara kakarin mutuwa koda taji tabbas zata rasa rayuwarta sai ta fara saran jikin sarki da faratan hannayanta da kafafunta nan fa jikin nasa ya rinka darewa jini na tsartuwa sarki ya rinka kurma uban ihu saboda mugun zafin da yake ji ga jiri na dibarsa amma saboda bakin naci yaki yarda ya saki dabbar saboda fusatar da yayi, abinda ya ayyana a ransa kawai shine sai dai suyi ragas shi da wannan dabbar tunda babu mamaki mugun dukan da tayiwa dansa zai iya zama sanadin ajalinsa. Lokacin da ramjis da hatyan suka ga halin da sarki da yarima suka shiga sai suka kalli junansu nan take suka daka tsalle a lokaci guda suka kama wuyan dabbar da hannayansu a sama suka murdeshi nan take dabbar ta sulale kasa matacciya, shi ma sarki alkasim ya fadi kasa a matukar galabaice jiri na dibansa da jan jiki ya isa inda yarima yake kwance ya mirgino fuskarsa sai yaga ashe da ransa amma ya kasa mikewa ne saboda mugun dukan da dabbar tayi masa a gadon baya sarki yasa hannunsa ya shafi kasusuwan bayan yarima sai yaji babu wanda ya karye tsabar buguwace kawai tasa ya galabaita nan take ya saki murmushin farin ciki............... ! Nima kuma Guyson na saki murmushin ajiye typing ANAN NE KUMA LITTAFI NA UKU YAZO KARSGE SAI MUN HADU A CIKIN LITTAFI NA HUDU DOMIN JIN CIGABAN WANNAN KASAITACCEN LABARI