Monday/24/May/2021. *TUBALI* PAGE 1 NA *AYSHA ALIYU GARKUWA* *Bismillahi rahmanirahim. Alhamdulillah Allah na gode maka da ka bani rai da lfy da damar fara rubuta wannan littafin nawa mai suna. TUBALI* *Ya Allah ka bani aron rai da lfy da konciyar hankali ka bani ikon rubutashi har ƙarshe bisa, lfy al'farmar Annabi da al'ƙur'ani. Allah kayi min tsari da abin hani, ka tsare min hannuna, tunanina, idanuna, al'ƙalamina, yatsuna, da rubuta wani abu da zai zamewa al'ummar Annabi sharri ko ya zama cutarwa ga tarbiyarmu.* GEMBU MEMBILA Taraba State. Wani irin hadari mai masifar ƙarfi da duhu ne, ya yiwa illahirin yankin Gembu Membila ƙawanya tako wani sashi, gabas da yamma kudu da arewa yake ta gangami. Yayinda Ya haɗe da duhun dare mai gauraye da duhun damina. Hakan yasa babu abunda ke tashi a yankin sai wasu irin tsawa da rugugin da aketa yi babu ƙaƙƙautawa, kana kuma wata iriyar iska mai ɗan karen ƙarfi da sanyi ne ke ci gaba da kaɗawa da ƙarfi. A dai-dai ya irin wannan lokacin kuma gaba ɗaya bani Adam mazauna cikin gidaje, sunyi nisan bacci kasan cewar ƙarfe ɗaya na dare ta gota. Wata kyakkyawar mota ce mai masifar kyau da tsadar gaske, wanda take nuni da mamalakinta wani ne ko wane, ta faso kai. Gudu yake shararawa cikin motar tamkar zai tashi sama. Ma’ana gudu irin na ceton rai, shiyasa shi kansa bai san irin tuƙin da yakeyi ba. Gaba ɗaya jikinsa kyarma yakeyi, duk da azabebben sanyin yanayin wurin, da kuma sanyin A/C’n dake cikin motar, amma hakan bai hanashi haɗa fitinanniyar zufa ta fargabar ganin alamun rabuwa da rayuwar duniya ba. Tuƙi yakeyi yana juyowa yana kallon wata zungureriyar tirela dake biye dashi a baya, haikan-ƙadaran. Da nufin bi ta kanshi ya takeshi, ya gane hakane ganin duk inda yayi binshi tirelar takeyi tana binshi. Cikin tsananin tashin hankali yasa hannunshin ya sharce zufan goshinsa, kana yasa hannunshi ɗaya ya ruggume yaron dake bisa cinyarsa, yana karkarwa ganin irin azabebben gudun da sukeyi. Dai-dai lokacin kuma suka iso, kan babban tsaunin dake saman zuzzurfan kwazazzaɓan kogin Gembu wanda yake haɗe da kogin. Numan Adamawa. Dadin Kowa Gombe. kana da binuye. Sannan hanyar tana nan tamkar tafiyar macijiya ziz-za. Wayarshi ya zaro a cikin kiɗima ya fara magana da wanda ya kira ɗin, yana maganar muryarshi na rawa, magana irin ta ban kwana da duniya da barin wasiyya da bada amana. Sun zo gab da Rugar Rumo dake ƙasan hanyar can gefen kwazazzaɓan. Dai-dai lokacin kuma, tirelar nan ta cim mishi. Cikin tsananin mugunta ya danna motar da ƙarfi, ya ingizata, cikin ramin dake haɗe da manyan Koguna wanda zurfinsa ya zarta zaton mai zato. Ji kakeyi k’uuuuuuhhhh, motar ta bada wani irin gigitaccen sauti. Sai kuma ta ɗan tsaya daga gangarawar sabida karon da tayi da wata bishiya hakan yasa bata faɗa ciki kai tsaye ba. Da ƙarfi ya kuma matsowa ganin bishiyar ta ƙare ƙaramar motar. Ingizata yayi ta tafi cikin ramin. Ji kakeyi fuuuuuuhhh zinɗim! Ta faɗa cikin ruwa. Wanda sautin faɗawan yasa mafi akasarin mutanen Rugar Rumo farkawa. Suna al'hini da tausayin sanin duk wanda ya faɗa ciki ya faɗa ƙabarinsa kenan... Shi kuwa mai tirelar wani irin masifeffen dariya mara daɗin amo, yayi kana ya wuce cikin garin dan babu damar yin kwana a wannan wurin. Tuƙin yakeyi wayarshi saƙale a kunne shi yana cewa. "Sir na gama dashi, babushi a duniya. Yayi ban kwana da duniya yanzu zan wuce cikin Gembu kuma zamuje mu kashe matarsa da yaranshi kab". Ɗan jim yayi jin yadda Sir ɗin ke dariyar cin nasara tare da cewa. “kuna kashesu. Sauran cikon 2 million din ku zai shigo hannunku.” Cikin zaƙuwa matuk’in tirelan yace. "Yanzu kuwa". Kana ya katse kiran, ya nufi cikin Gembu a cikin daren da wannan duhun damunar. *************** Bayan wasu shekaru A kamar Ashirin da biyu 22. Kano state. Shiru hall ɗin taron ma'aikatan tashar Arewa 24 TV dake birnin Kanon Dabo yake, yayinda ma'aikatan ke zaune bisa kyawawan kujerun dake zagaye da babban table mai kujeru sama da hamsin. Yayinda gaban kowa goran ruwan Faro mai sanyi ne da kuma Nutrimilk sai maltina da chii exotic, baya ga haka kuma glass cheers cups ne a gefe-gefe. Kana sai abun sautin magana dake gaban kowa, mai ɗan tsawo. Gefen dama duk manyan ma'aikata ne. Kana gefen hagu mabiyansa. Can baya kuma ƙananun ma'aikata. Babban ogansu ne ke musu bayanin canje-canje tsarin aikin da suke shirin kafawa na forkon shekarar. Gyara zamanshi yayi tare da kallon gefen damanshi. Murya ya ɗan gyara tare da cewa. "Ina mai Shirin baƙon mako?." Cikin nutsuwa Jannart Idris Saleh Dakata. Ta ɗago kanta cikin tattausan muryarta mai cike da nitsuwa tace. "I’m here Sir". Sautin daddad’an muryarta ne kuma yasa, mafi akasarin mutanen dake wajen suka juyo suna kallonta. Tabbas Nitsuwarta na daya daga cikin dalilan da suka sa aka bata ragamar wannan shirin. Kasan cewar manyan mutane masu kamala da shahara ake gayyatowa, so ana buƙatar mai nitsuwar da zata martaba musu manyan baƙin su. Cikin kula. Uban gidan nasu yaci gaba da cewa. "Shirin baƙon mako, yana da manufa mai girma, ta samo manyan mutane ta tattauna dasu, su sanarwa duniya nasarorin su da kuma irin ƙalubalen da suka fuskanta domin. Su kasan cewa matasanmu masu tasowa, Maduban gina TUBALIn rayuwarsu ta yadda zata inganta su, tsare kansu da lalatacciyar tarbiya suyi karatun da sana'a domin watan-wata rana su zama abun koyi abun so wa yan baya." Shiru ya ɗanyi tare da kurɓar ruwan Lemun exotic din dake gabansa. Ita kuwa Jannart na'urar maganar dake gabanta take ɗan sa fararen yatsunta wanda sukaji red henna tana sama tana ƙasa dasu a hankali. Yayinda duk saura kuma sukayi shiru. A nitse yaci gaba da cewa. "But now I’m sorry to say Jannart, shirin ya raunata sosai. Yananin tsaron da kike ciki yasa bakya sakewa ki samu ki gayyato mana manyan mutane, shahararrun masu nagartan da zasu burge mutane. Shiyasa shirin yayi rauni mafi akasarin ranaku sai dai aita maimaita program ɗin daya gabata. Wannan dalilin yasa muka samu umarni daga sama. Aka bamu zaɓi biyu." Da sauri Jannart ta lumshe idanunta kana tayi ƙasa da kanta, saboda fahimtar inda kalamanshi suka dosa. In ta gane ana gab da sallamarta daga aikin. Wanda nanne kaɗai duniyar farin cikin ta, in ta shiga cikine kadai take samun ta sake, tayi raha tajita mai eanci babu Escort, ba Yah Junaidu a kusa. A hankali tasa yatsarta ta ɗan ƙara saƙala na'urar dake saƙale a kunnenta wanda shike ƙarawa jinta ƙarfi, yadda take ɗan taune lips ɗin ta na ƙasane ya bawa kyakkyawan Dimple ɗin ta damar lotsawa, yayinda jajayen lips din nata suke sheƙi dan lasarsu da ta ɗanyi. A hankali A'isha Lawal dake gefenta tasa hannunta ta kama nata tana ɗan murzawa alamun bada ƙarfin guiwa. Salman kuwa dake fuskantar ta, idonshi ya rumtse. Da sauri ta buɗe idonta jin shugaban nasu yaci gaba da cewa. “Umarni na forko wannan karon an bamu sunan mutumin da ake son mu gayyato, yazo ayi hira dashi. Domin shi kadai ne zai ɗaga darajar shiri. Sai kuma cewa in har bazaki iya samun dama da lokacin sakewa ki nemishi ba, to dole a sauƙeki kan shirin. A nemo wata ko wani da zasu iya." Cikin nitsuwa ta ɗan kalleshi kana a hankali cikin tsoron rasa aikinta tace. “In sha Allah zan iya". Da sauri ya kalleta. Kai ta jinjina alaman. "Yess zan iya". Kai ya jinjina kana yaci gaba da cewa. "Sai umarni na karshe, dole a nemishi, ya zama next 2 week's dashi za'ayi hira. Kinga kenan yau saura kwana goma kenan.". Asiya ce dake masifar son amsar ragamar program ɗin daga hannun Jannart. Ta gyara zamanta tare da cewa. "Sir waye ne shi? A ina yake?". Cikin ɗan ɗaga sauti yace. *”Dr Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara ne"* Da sauri duk suka fara kallon juna, cikin kaɗuwa Aisha Lawal tace. "Sir Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara, shifa..." Hannunshi ya ɗaga mata tare da cewa. "Na sani, shi ba mutum ne kamar kowaba, ra'ayin shi da banne. Ko BBC bata taba samun nasarar yin hira dashi bako!?". Da sauri kab suka amsa da. Yess! Yesssss!!". Ajiyan numfashin ya sauƙe tare da cewa. "Toh wannan itace nasararmu in har an samoshi. Zai zama mujallar Arewa ce zata taɓa fidda hirarshi da hoton fuskarshi kana, Arewa 24 TV ce zata taɓa haska fuskarshi da surar jikinshi bayan sunanshi daya zama sananne a Africa baki ɗaya. Wannan shine zai ƙara ɗaga darajar shirin. Shin Jannart zaki iya? Ko dai kai tsaye asa Asiya?". Da sauri Asiya tace. "Sir Ni zan iya, tunda bani da wani tsaron nuna isar cewa ni ƴar wanice, aikina shine isata". Mafi akasarin mutanen wurin ido suka zuba mata ganin yadda take mgna tana watsawa Jannart harara. Ita kuwa Jannart glass din idonta ta gyara tare da ɗagowa jin shugaban nasu na cewa. "Jannart zaki iya ko dai yanayin tsaron da mafahifinki ke baki bazai barkiba?". Cikin sanyi da danne fargabarta tace. "Sir zan iya in Sha Allah. A bani kundin bayaninshi". Ajiyan zuciya Salman ya sauƙe jin cewa ta amsa zata iya, baya son rasa abokiyar aikinsa sabida yana jin daɗin aiki da ita. A'isha Lawal kuma ajiyan zuciya ta sauƙe. Shi kuwa MD’n su, wani file mara girma ya tura gaban Jannart tare da cewa. "Gashi sai dai babu komai nashi a ciki, sai sunanshi, da sunan Company's ɗinshi, da garuruwan da suke. Da Hospital's ɗinshi. Da kuma foundation ɗin sa, mai suna Mainasara Foundation." Jin yayi shiru ne yasa ta ɗan kalleshi kana a hankali tace. "Ba phone number ɗinsane, ba picture dinsa? Ba address ɗin sane?". MD ne ya ɗan gyara zamanshi tare da cewa. "Toh Jannart ai da akwai waɗannan abubuwan a ciki, toh da bazaiyi wuyar samuwa ba kuma da bazai zama mutum na musamman ba, kunsa duk abinda yake killace shine special." Sai kuma ta juyo ta kalli mai kula da shirin nasu dake cewa. "Babu number sa, ba hotonsa ba adireshinsa. Kana ko akwai number sa, ko sau 1000 zaki kira da layuka 1000 ma-ban-ban-ta bazata shigaba, sabida yana amfani da App ɗin nan da in dai bawai yayi saving number ki a wayarsa bane, kiran bazai taba shigaba. Kuma koda ya ajiye ya shiga, zaki kira a ƙalla sau goma bazai amsaba, sai dai ace mikin ki ajiye mishi voicemail. Sabida yawan aiyuka da uzurrukan da mahaifinshi ya ɗaura masa yasa bashi da isashen lokacin kansa ma, da yawan mutane suna matuƙar jinjina masa da mmakin kwazonsa, sabida aiyukan sun mishi yawa, kana matashine a tsakiyar dattijai. To shiyasa bai cika samun lokacin amsa kiraba. Sai dai a ajiye mishi saƙo, so nanne zakiji muryarsa, idan abinda ke tafe dake mai mahimmanci ne, kuma kinyi hikimar faɗa mishi number ki to shida kanshi zai kira". Mafi akasarin su ajiyan zuciya mai nauyi suka sauƙe. Cikin karaya Jannart tace. "My Aunty to Ina kikaji duk wannan bayanin?". Dariya Hajia Rabi'ah tayi tare da cewa. "Jannart yar jaridar gaske wato, tuni har kin fara binciken tun yanzu a kuma kaina". Murmushi tayi tare da gyaɗa kai. MD kuma kai ya jinjina sabida gamsuwa da hikimarta da nitsuwarta wurin aikinta. Cikin girma Hajia Rabi'ah tace. "Toh gsky nima wurin PA'nsa na samu wannan bayanin. Ba kuma wurin PA din kai tsaye ba. Akwai ɗan yayata, abokin ƙanin PA'n nashi ne, so nan naji wannan." Cikin sauri ta miƙawa Hajia Rabi'ah wayarta tare da cewa. "Samin number ɗan yayar taki". Murmushi tayi ta amsa tasa mata number. Kana tace. "Sunanshi, Mahmoud". “To” tace kana ta adana number. Shi kuwa MD'n gyara zamanshi yayi yaci gaba da tsara musu sauye-sauyen programs ɗin nasu. Sai kusan ƙarfe shida saura suka tashi a taron. Suna fitowa, mafi akasari suka kama hanyar parking lot ɗinsu dan daukan ababen hawansu. Wani irin kallo mai cike da tsana Asiya ke bin Jannart dashi lokacin da suka fito, a take Escort ɗin ta suka miƙe suka mara mata baya. A hankali ta ɗan juyo jin Aisha Lawal na kiranta. "Jannart! Jannart!!". Juyowa tayi tare da bin tsakiyar hanyar da suka buɗa matan. Da sauri A'isha Lawal ta iso, cikin sanyi tace. "Zaki iya?." Cikin jin tsoron rasa aikinta, ya zama dole taita zaman gidan da yafi na kurkuku muni da zafi. Tace. "Na'am A'isha zan iya, in sha Allah. In ban iyaba naci gaba da zaman gida, Yah Junaid zai k’arasa kurmatani da marukan da yake yayyarfa min a cikin ko wani mintuna, wurin aikin nan shine duniyata, shine TUBALIn ɗan y’ancina, ya zanyi sakacin rasa aikina". Cikin rauni da ƙara yin ƙasa da murya Aisha tace. "Okay Salman yace ince miki in sha Allah zaku iya, kuma zai roƙi a baku cikekken dama, da zai biyoki sai ya tuna waɗannan kattin dake zagaye dake wanda suke shirye da ilkata duk wani na miji in yazo kusa dake". Kai ta jinnina kana sukayi sai anjima. Wasu dalla-dallan motoci ne guda, uku. Ta tsakiya itace a baya. Ta baya kuma ƴan tsaronta, hakama na gaba. Tana baya a zaune. Yayinda driver'n ta ke janta. A haka suka nufi gida tana mai jin tsoron me zata riska a gida, kasan cewar ta wuce lokacin dawowarta. Anguwa ce mai zaman kanta Janbulo tsit anguwar ba hargitsi, da hayaniya, da kwata kamar ba cikin kano ba, sabida manya-manyan gidaje ba irin gidajen kanawa mitsi-mitsin nan ba. A bakin wani tamfatsetsen gida mai ɗan karen girma da kyau, suka tsaya tare da danna hon. Jiki na rawa mai gadi ya buɗe musu. Nan suka ratsa cikin gidan. Suna isa parking space ana kiran sallan magriba. Wanda yayi dai-dai da fitowar Alhaji Idi Sale Dakata daga cikin gidansa tare da zaratan samari uku Junaid Azeez Abdul a bayanshi. Da wani mutum wanda suke kama da juna Barrister Kabir Saleh Dakata kaninsa kenan. Wata iriyar sassayar ajiyar zuciya mai nauyi ta sauƙe fahimtar Yah Azeez zai koma wurin aikinsa dan taga ana sa kayansa a mota, alamun ana idar da salla zasu wuce Airport dashi. Murmushi Barrister Kabir yayi tare da cewa. "Masha Allah, Ammina kin dawo kenan". Da sauri ta matso kusa dashi tare da kaucewa mugun kallon da Yah Junaid ke watsa mata, cikin sanyi tace. "Eh Abba na dawo, ina Aunty Dija". Ta k’are mgnar tana kallon fuskar Yah Azeez d’in da yakeyi mata kallon mai cike da tausayawa, Barrister Kabir kuwa wanda ta kira da Abba Cikin kula da tsananin tausayinta da danne wani abu can ƙasan zuciyarsa yace. "Suna ciki shiga bari muje masallacin". Da sauri tace to. Kana tayi cikin gida su kuma suka nufi masallaci... *Ethiopia Addis Ababa.* Wani kyakkyawan matashine mai wani irin tsabtaceccen kyau mai masifar ɗaukar hankali, matashine mai jini a jika. Wani irin kimtsestsen taku mai cike da nagarta, nitsuwa, kamala, haiba, yakeyi, yana mai fitowa habarar wani kyakkyawan Asibitin. (Tikur Ambess Teaching hospital Addis.) Yayinda wasu manyan likitocin da ƙasar Ethiopia ke ji dasu ke biye dashi a baya, kana da Nurses. Taku yakeyi cikin kamala da haiba, a hankali yake motsa lips ɗinshi bisa dukkan alamu, gajiya ce ta sashi hakan ɗin. Fari ne mai masifar kyau irin farin mutanen ƙasar Ethiopia sai dai fatarsa tana da haske fiye data sauran dake biye dashi a baya bi'ma'ana ya ɗan fisu fari. Yana da wani irin hanci mai ɗan karen kyau, da tsini, idanunsa masakaita masu masifar kyau da fari, irin idanun nan ne da in sun cicciko da hawaye in akwai abu a gabansu kalar idon kan iya komawa haka, wani irin kekkyawan saje ne mai masifar kyau ne kwance lib a fuskarsa yayi mishi ƙawanya, lips ɗinshi ƴan sirara jajaye masu kyau, sai girarsa masu kyau. Wani irin askine mai ɗan karen kyau bisa kansa. Sosai kamanninsa da Dheeraj-Dhoopar suka fito ras hatta tsawonsa da ɗan jikinsa kamar na Dheeraj-Dhoopar ne komansa dai-dai misali. Daga shigarsa zata nuna wanene shi. Wani irin masifeffen Suit ne a jikinsa mai ɗan karen tsada, red colour mai maiƙo, riga da wondo sai ɗigon fari-fari, kana necktei ɗin wuyanshi shima fari sai ɗigon ja-ja'n. Haka takalmanta sau ciki, toms farare ƙira company'n Italy sai harafin R-M da akayi da red color. irin ta matasa. Masu kima da daraja sai agogon hannunsa ƙirar Gucci shima da harafin R.M a gefe da gefe. Shigar tayi masifar mishi kyau da kamala. Taku yakeyi suna biye dashi a baya. Har suka iso inda motocinsu ke jere. *DR. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara kenan.* Cikin nitsuwa ya juyo yana mai miƙa wa Dr Adeym hannu cikin nitsuwa suka ɗan yi mgna, kana duk sauran ma suka bashi hannu. Kana ya shiga mota, Driver'n'shi dake ciki yaja. Suka fita cikin asibitin. Kai tsaye. Hera Addis hotel Ethiopian, suka nufa. A kan hanyarsu ne, suka bi kusa da wani babban masallacin. Cikin sauƙe numfashi ya cewa, Driver'n'shi. "Tsaya". A taƙaice Da sauri yace to. Kana suka tsaya ganin ya nufi cikin masallacin ne suka fahimci me zaiyu. Nan suka mara mishi baya, dan yin sallan isha'i kasan cewar lokacin ta yayi daga nan kuma suka wuce. A hankali ya maida kanshi ya jingine jikin kujerar idonshi ya lumshe tare da motsa lips ɗinshi a hankali yana sauke numfashin gajiys. Yana jin wayarshi na ringing Amman ko idonsa bai buɗeba sabida tsananin gajiya, kayan jikinsa kansu nauyi sukeyi mishi, bacci yakeji da kuma yunwa. Shiyasa bai amsa kiranba. Sai dai cikin zuciyarsa yace. "Sulaiman!!!". Sai kuma ya ɗan mirgina kanshi gefe. Ganin sun iso. Da sauri mutanen dake cikin motar dake biye dasu a baya suka fito ɗaya daga cikin sune ya matso. Buɗe mishi marfin motar yayi kana ya matsa gefe. A hankali yace. "Bismillahi". Numfashin gajiya ya ɗan fesar. Kana ya zuro ƙafarsa woje. Sai kuma ya ɗan kalli Usman PA'nshi dake tattaro System ɗin shi da wayoyinshi. Kana a hankali yace. "Ɗauko small bag ɗin can." Da sauri Usman yace. To. Kana ya ɗauko ɗan jakar leda mai ɗauke da tambarin Edna Mall Addis Ababa Ethiopian. yabi bayanshi suka nufi cikin HOTEL ɗin. Kai tsaye inda masauƙinsu yake suka nufa. Suna shiga ya juyo ya kalli Usman daya ajiye mishi kayyakin nasa bisa kujera. "Sai da safe, bazanci komai ba, kada Sulaiman ya dameka kace zaka zo ka dameni". Yayi mgnar cikin gajiya. Cikin sauri yace. "Okay Sir". Yana mai kunce net ɗinshi yace. "Toh jeka". Toh yace tare da juyawa zai fita. Sai kuma ya ɗan juyo yana kallonshi jin yana cewa. "Ramadan ya kira ɗazu". Kai ya gyaɗa mishi kawai. Ganin haka Usman ya juya ya fita. Yana ganin ya fita, ya matso ya rufe ƙofar. Yana juyowa yana cire Suit ɗin, bisa kujera ya cillata, kana ya cire ta cikin. Sunkuyowa ya ɗanyi yana kunce belt ɗin ƙugunshi. Yana daga tsaye ya zare wando . Yana son sakewa shiyasa yake jin daɗin rayuwar kaɗaici. Sabida yana masifar kunya da suturce surar jikinsa. Ko dan yanayin halittar jikinsa mai gargasa ne, baya son koda Ramadan ne yaga koda damtsen hannunshi bare sharaɓarsa bare aje ga cinyarsa, da tattausan gargasa yayi masu ƙawanya. So Amman in shi kaɗaine yana sakewa, wasu lokutan daga falo yake fatali da kayyakinsa kafin ya shiga bedroom ma daga shi sai boxes zai shiga. Tattare kayan yayi ya wuce dasu Bedroom, bisa gado ya ajiyesu. Kana ya wuce Bathroom. Bayan ya fitone ya kimtsa cikin wasu tattausan riga da wondo iya guiwa farare ƙal. Turare ya ɗan fesa, kana ya ƙara gudun A'C sannan ya koma parlon ya ɗauko ƴar jakar da yasa Usman ya ɗauko mishi wanda yake cike da chocolates kala daban-daban. Masu sanyi a daskare. Sosai ya ci Galaxy Chocolate mai ɗan karen daɗi kamar yadda ya saba ta'ammali da kayan zaƙi. Bayan ya gama ne, kuma yasha tea mara haɗi, wato coffee. Bayan ya kammala ne kuma ya dawo Bedroom riƙe da system a hannunshi. Kashe wutan ɗakin yayi, kana ya kwanta. tare dasa l system ɗinnasa a gaba. Ajiyan zuciya ya sauƙe, Allah ya sani yana jin wani irin nishadi da sanyi na musamman in yana jin wa'azin Dattijon nan, Malam Mai-nasara, yana son tafsir din shi. Baya gajiya da kallon fuskar tsohon. Wannan yasa yake bibiyar shafin shi na You tube inda yake saka tafsiransa. Lallatsa system ɗin yayi. Jim kaɗan sai ga hoton ya bayyana. Fuskar dattijon ya zubawa idanu. Har bai jin abinda ake magana a kai. Sai da yaji iska na ɗan cika mishi ido ne, ya ɗan lumshe idanun tare da sauƙe numfashi, kana ya buɗe su. Kan rubutun dake ƙasan hoton Dattijo ya kuma kalla. Malam Mai-nasara". Cikin sanyi can ƙasan zuciyarsa yake magana. "Ƙarshen sunanmu iri ɗaya. Ni dai nasan Tubalin nawa sunan. Toh shi kuma menene TUBALIn nashi sunan Mai-nasara, menene asalin sunan?". Wa zai amsa mishi waɗannan tambayoyin da zuciyarsa taƙi dena mishi su? Numfashin gajiya ya sauƙe kana ya kauda tunanin yaci gaba da jin tafsir ɗin nashi. Jin bacci zai kwashesa ne yasa ya rufe na'urar ya kwanta yana mai buɗe tafin fararen hannunshi yana addu'o'in. Yana idawa ya shafa ya kwanta. Kano Nigeria. Sulaiman ne zaune bisa kujera matarsa, Sumayya na gefenshi. Da sauri yace. "Ikon Allah". Juyowa Sumayya tayi tana cewa. "Lfy?". Da sauri ya matsota tare da cewa. "Kiji ikon Allah wai Riyyam-nsra, wannan ɗan Ethiopia da nake ce miki yana masifar kama da Rayyern wai zaizo Nigeria". Leƙowa tayi ta kalli fuskar wayarshi, inda yake TIKTOK yana bisa shafin Riyyam-nsra. "Kai gsky kam Ni kaina ina ta'ajjudin kamanni Rayyern da yaron nan, kamar ta ƙazanta". "Uhumm ni kaina na gaza daina mmakin kamanninsu. To amman kin kuma ji wai zaizo Nigeria". Riƙon da tayiwa yarsu ta gyara tare da cewa. "Abban Nihal me abun mamaki don zai zo Nigeria, kasan celebrity’s da yawo kamar jirage". Kanshi ya jinjina tare da cewa. "Sumayyah ba zuwansa Nigeria bane abin mamaki." "Toh menene abin mamakin". Ta tambayeshi cikin kulawa. Juyo mata fuskar wayar yayi. Da sauri ta zsro idonta waje cike da mamaki tace. "Dama H...! 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *TUBALI* NA *AYSHA ALIYU GARKUWA* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ASSALAMU ALAIKUM, Masoyana ma karantan littattafaina, ina mai farin cikin sanar daku, yau d’in nan MON, 18 OCT 2021 za'a fara biyan kud’in samun damar karanta littafin TUBALI akan farashi mai sauk’i Biya 500 k’aramin farashin na k’aramin group, kana sai *Special people Group* akan farashi mai sauk’i 1k kacal babban group a yawan posting babancinsu yake, zaku biya ta asusuna. ACCOUNT NO 0661110170. BANK NAME: AISHA ALIYU GARKUWA BANK GTBank sai ki turo min shaidar biyanki ta wannan numben tawa da nakeyin whatsApp da ita 09097853276. *PLS TAKE NOTE BAND VTU* kada kiyi min VTU ko transfer'n katin ta wannan numben etisalat d’in idan kuwa kikayi wlh babu ruwana dan na fad’i miki. Please and please in dai da hali kada ki turo min katin, kiyi min transfer'n ruwan kud’i ta bank account na, in kuma babu dama to sayi katin MTN sai ki copy number's ɗin katin ki turo min ta whatsApp. Gareku mutanen jamhuriyar Niger ku tuntub’i Mommy akan layinta +22790899076, ta wurinta zaku biya, hoton katin zaku d’auka ku tura mata ta wannan numben a whatsApp, Special people group 1k ne (1000) k’aramin group kuma (500) kacal, Please dan Allah babbar macece mai yara da tarin jikoki da y’ay’an jikoki mu kyautata lafazi da mu'amala gareta dan Allah don in ka girmama iyayen wasu wasu zasu girmama naki🙏🏻... Littafin TUBALI littafine na musamman mai salo na musamman mai cike da abubuwa masu tarin yawa. *Tausayi, Sark’ak’iya, jan hankali, Fadakarwa, Nishad’antarwa, ilimantarwa, al'ajabi, Sa'ar rayuwa, riƙon amana, cin amana, ribar kyautatawa, kana da sassayar soya mai salon narke jiki da zuciya* Ga number wayata da nakeyin whatsApp da ita, 09097853276 idan kina son biyan kudin samun damar karanta littafin TUBALI sai ki biya ta wannan ac no din dai 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA, dan Allah ki biya kafin kiyi min mgn kina turo shaidar biyanki ina gani zan saki a group, in Kuma baki da ac no ko yanayin zaman wani k’asa ko wani luggun ki sayi katin MTN na 1k in special group kikeso ki turo min. In Kuma k’aramin Group kike so ki sayi katin *MTN ki copy number's din ki turo min ta whatsApp number'n na 09097853276 kada kiyi min VTU ko transfer'n katin 9mobile dan layin nada matsala* Za'ayi tsawon mako ɗaya ana biya ina kafin in fara update domin samun sassaucin aiyukan sauraron mutane, za'a fara biya yau *MON 18 OCT 2021. Kana zan fara posting ranar MON 25 OCT 2021 rana ita yau kenan in mai kowa mai komi ya kaimu bisa rai da lfy* 🙏🏻Na rokeki da girman zatin ubangiji in dai kin san zaki sayane dan ki fidda min littafina dan Allah ki bar kud’inki kiji tausayin marainiya, kada ku cutar da marainiyar Allah,😭🙏🏻🙏🏻🙏🏻. Nasan daga yau har zuwa na gama littafin Chart zaimin yawa zai hausawa aiyuka zasu yawaita gareni, amman babu kamar makonni ukun forko zuwa biyar, Please ina neman al'farmar uzuri in kinga kinyi min mgn ban amsa mikiba, na tuba kiyi haƙuri ba raini bane ko wulak’anci face yawan mutane wata k'il ban isa kan Chart naki bane, Amman muddin na isa na kuma bud’e na gani tabbas zan baki amsa in katine zansashi yana shiga zan saki a group in bai shiga kuma in gaya miki, in Kuma ta account kika turamin ina ganin shaidar biyanki zan saki a group, 🙏🏻Dan Allah in kinsan ba littafi ko maganin gyara namu na mata kikeso ba to kiyi haƙuri da min mgn sai na d’an samu salama🤝🏻😘🙏🏻😂. *Sayan na gari maida kuɗi gida sai kinzo* By *GARKUWAR FULANI* 11/15/21, 7:19 PM - Auntyna: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *TUBALI* PAGE 2 NA *AYSHA ALIYU GARKUWA* "Hausa ya keyi fa ko?". Cike da kaɗuwa Sulaiman yace. "Eh abinda ya ban mamaki kenan.” Sai kuma ya kalleta jin tana cewa. "Koda yake ba mamaki wani ne ya rubuta mishi, tunda kaga ai yace. Ethiopia Addis Ababa to Nigeria kano State. Kanawa zan zo muku. Wata ƙil wani ne ya rubuta mishi". Komawa yayi da baya ya jingina bayanshi da jikin kujera. Numfashi ya ɗan fesar tare da cewa. "Kai Sumayyah gsky da mamaki fa. Kalli Comments ɗin mutane fa da amsar da yake basu." Ya ƙare maganar yana shiga comments section ɗin ƙasan video'n da ya saka a shafin nasa. Inda wani Abis Fulani yake cewa. "Eyyeh Riyyam-nsra a Nigeria, kanawa nama fatan isa lfy". Cike da mamaki Sumayyah ta kalli amsar da ya baiwa Abis Fulani. "Ngd aboki na". da alamun musabaha. Sai kuma tayi ƙasa ganin inda wani. Ahmad MG ya fara mgn da zaro ido alamun mamaki tare da cewa. "Riyyam-nsra da yin Hausa, ko mafarki nakeyi". Dariya yayi tare da bashi amsa. "Noh Ahmad zahiri ne". Tofa wannan abun yasa comments ɗin mutane zubowa kamar ruwan sama domin shi dai ɗan ƙasar Ethiopia ne, kalarsa, harshensa, cimarsa, rayuwarsa, komai na canne, bai taɓa koda maganar Nigeria a shafinsa ba, sai gashi yau kuma yayi video cewa zaizo Nigeria, kuma yana rubutu da hausa yana kuma karantawa. Cikin kaɗuwa Sumayyah taci gaba da bin comments ɗin mutane na farko-farko da ya iya basu amsa sabida yawan mutanen. Cikin mamaki tace. "Lah kalli tambayar da wani ya mishi." Amsar wayar Sulaiman yayi. Ya fara duba saƙon da Imran yayi mishi. "Riyyam-nsra kasan Nigeria ne? Ko Ka taɓa zuwane? Ko wannan ne zuwan da zakayi na forko?". Alaman murmushi yasa tare da cewa. "Nasan abu da yawa kan Nigeria". "Da sauri yace gaya min kaɗan daga ci." "Ok kamar me kake son in gaya maka". Da sauri yace. "Ka iya taken ƙasa. Ko rantsuwar al'ƙawarin ƙasa." Cikin lumshe ido, Riyyam-nsra dake kwance a ɗakinsa. Ya rubuta mishi amsa, da bari in baka amsar a video." Take kuwa ya tashi zaune yayi taken ƙasarmu Nigeria ƙasarmu ta gado kana da rantsuwar al'ƙawarin ƙasa. Wannan video da ya saki Yayi matuƙar jan hankali al'ummar Hausawa duniya baki ɗayansu more Especially ƴan Nigeria bama ya kanawa. Da sauri Sulaiman ya fara rubutu. A karo na forko a rayuwarsa da zaiyiwa wani comment a TIKTOK. Rubutu yayi cikin harshen nasara. "Hey Riyyam-nsra you knew much about Nigeria you are a patriot". Yayi mgnar da gayya ne dan ya gano ko dai ɗan Nigeria ne basaja ne da karya yasa yake ciwa ɗan Ethiopia ne, wata ƙil karatune ya kaishi can. Murmushi yayi tare da rubuta mishi amsa. "Baƙon Nigeria dai mai kishin Nigeria amman ni ɗan Ethiopia ne. Sai dai Nigeria ƙasar babban abokina ne da mukayi karatu tare a US." So daga ganin wannan video, akai ta cewa. "Haba shi yasa mana. Nasir Ahmad ne wanda shine abokin nashi ya fito, yanata mishi tsiya a nashi shafin. Nanfa aka gane sanadin zuwansa da kuma inda ya koyi Hausa ras. Ɗan gajeren tsaki Sulaiman yayi tare da cewa. "Wadannan yaran gaba ɗaya TIKTOK ta haukata mana matasa wanda sune TUBALIn al'umma sai gashi kuma muɗin ma suna shirin haukatamu". Dariya Sumayyah tayi tare da cewa. "Dama haka ai Rayyern ɗin ke ce maka, in baka dena biyewa social media ba, zaka rasa lokacin kanka". Kwaffa yayi tare da rufe datarsa kana yace. "Nima fa Ibrahim ne ya sani fara wannan abun sabida, kamannin Rayyern da wannan yaron." Daga nan sukaci gaba da hira kan kamanninsu. Washe gari da safe ranar talata. Gidan Alhaji Idi Sale Dakata. Su kusan shida ne cikin falonshi. Wanda huɗu daga cikin manyan yan kasuwane masu faɗa a ji masu juya sule ta koma million ɗaya ko tako wanne irin halin ƙaƙama ko talaka zaiji daɗi haka ko bazai jiba. Biyu daga ciki kuma ƙusoshin gwamnati ne masu ƙarfin iko daga ta jiha zuwa ta ƙasa. Alhaji Yawale ne ya gyara zamanshi tare da cewa. "Yaron nan fa yanayi mana illa ba tare da mun ankare ba. Gaba ɗaya ya rarake tubalin da mukayi tsawon shekaru muna ginawa muna samun wuri na jawo mana wuri." Cikin tsananin takaici Alhaji Abdu Tababa ne yace. "Tun-tuni nake gaya muku haka. Mu kauda yaron nan a doron ƙasa shine kawai mafi sauƙin mu. Kunaga yadda kasuwan cinsa ke haɓaka, kamfanonin sa suna bunƙasa daga Arewacin Nigeria har ya koma kudanci ya kafu. Uwa uba yanzu duk ƙasashen Afrika yanada rassai. Ya maida kayan abinci da araha tamkar ruwan sama cikin damuna. Duk inda ka shiga a kasuwannin Mai-nasara race, ke cike. A farashi mai sauƙi ta yaya za'ayi a saurari kayan kamfanonin mu". Ɗaya daga cikinsu ne ya miƙe tsaye tare da cewa. "Ni tambaya ta a kullum ma shine menene Tubalin kasuwancin yaron nan? Yaushema aka haifeshi? Sa'an yaran cikin mune fa! Ta ina ya samu Wannan tarin dukiyar da har ya samu damar razana mana kasuwanci ya raunata mana Company's. Yaushe yayi ginin duk a lokacin ɗaya menene Tubalin dukiyarsa da matakan ikonsa!?." Ya ƙare maganar yana kallon Bala Tambari wanda shine shugaban tsare-tsaren ginin masana'antu a gwamnatance, dole sai yasa hannu za'ayi gini ya za'ayi ka bashi izini da damar yin gini a duk inda yake so a ƙasar nan". Cikin takaici Bala Tambari ya fesar da numfashi tare da cewa. "Tsohon yarjejeniya ne, yana da dukkan abin buƙata, yanada sa hannun da suka gabaceni kuma kan tsari suke. Naso in ƙalu balanceshi. Tun shekaru biyar baya lokacin da ya fara gina babban campany dake Nan birnin Kano wanda yanzu yake gab da kammalashi so naga komai da hujja yakeyi. Yaron shegen taurin kai ne dashi, gashi da ɗan banzan tsaurin ido. Kana mgna zai tsira maka waɗannan siraran idanun nashi masu kama da soyayyan gujjiya, tsakar idon ka ya baka amsa da hujjar da baka isa kayi mgna ba". Dr.Lukman ne ya fesar da iska a baki tare da cewa. "Ni ta ko ina ya tosheni A fannin likitancin gaba ɗaya yana bi yana rarake privet Hospitals. Ɗan banzan komai na asibitinsa mai sauƙi kuma ga kula ya za'ayi aje irin namu asibitocin." Alhaji idi Sale Dakatane ya miƙe a fusacen shina kana yace. "Nifa gaba ɗaya ya ta'azzara min campany na na shinkafa. Sannan kafin kace ka motsa sai ka samu ya toshe ko ina. Hegen yaro mai jajayen kunnuwa. Yana nan tamkar Wahainiya, samun ganinshi ma ya zamewa mutun aiki." Dr Lukman ne ya ɗan sauƙe numfashi tare da cewa. "Cikin satin nan zai dawo Nigeria yanzu haka yana Ethiopia yaje, shugaban kasar can da kanshi da manyan likitocin sune, suka karrama shi. Sabida taimakon da yayiwa wasu daga cikin mutanen ƙasar Ethiopia cikin Airport kan hanyarsa ta zuwa US, dan karramashi a matsayin ɗan kasuwan da yafi ko wanne sauƙin farashin kayan masarufi. Kaga yana tafi kuma yazo wai kuma Ethiopia zasuyi mishi wata karramawar. Yaro kamar ɗan ruwa, komai yasa kai sai Nasara". Bala Tambari ne, ya kalleshi tare da cewa. Toh yanzu dole kai zaka nema mana zama dashi. Yana dawowa muna buƙatar shi mu gwada sayan farashinsa. Muyi mishi tayin harƙallarmu yasan irin ribar da muke shigarwa, wata ƙil zai amince mu haɗa hannu in kuma yaƙi tabbas zamu gina mishi gadar zare.". Da sauri Alhaji Idi Sale Dakata yace. "Uhumm ai In Kuma yaƙi amincewa mu haɗa hannu. Toh lokacin wasan zai fara, dan in taurin kaine da gsky da samun ƙarfin iko bai kai. Mai-gaskiya da wasu ba, da muka gama dasu shekaru ashirin da biyu baya ba, danni cinnaka ne ban bar na gida Bama, bare shi baare." Haka dai suka tashi a taron nasu. A nufin sai ya dawo su zauna dashi. A cikin gidan kuwa. Jannart ce ke Tsaye a kitchen, inda take sanye da wani half gown mai masifar kyau wanda ya d’an bayyana fararen legs d’inta, rigar irin mai kauri da kama fatar jiki dinnan ne, wanda hakanne kuma yasa had’add’iyar Surar jikinta dan bayyana, kasancewarta y’ar gayu, Tabbas Jannart macece mai matuk’ar son fashion, shiyasa hatta suturun da take sawa ya banbanta da sauran na y’an Nigeria, saboda sometimes tafi yin shiga irin na wasu daga cikin larabawa, ko kuma shigar mutanen turkey🇹🇷. Tsaye take a kitchine din cikin kuma nutsuwa take aikinta. Yayinda Mom ke tsaye a gefenta. Cikin kula Mom ta kalleta tare da cewa. "Jannart kamar Yayanki ne ke kiranki". Cikin bugawar zuciya tace. "Yah Junaid!?." Da sauri tace. "Eh shi dai". Bugawa zuciyarta ya kumayi, tare dajin wani iri acikin jikinta, saidai kuma babu yanda ta iya, haka ta juya cikin sanyi ta nufi falon. Can tsakar falon ta hangoshi tsaye, saurayi ne, mai murd’addiyar Surar jiki da kuma tarin gashi akansa irin busu-sun nan, duk da cewar kyawun nasa bawani na zarce hankali bane amma baza’a tab’a k’iransa da mummuna ba, wata riga marar hannuce ajikinsa, sai kuma wondon dake jikinsa wanda ya tsaya masa iya guywa. Bisa alamu kuma yanzu ya tashi daga bacci. saboda yanda idanunsa sukayi jazir. Kallonta yayi, tare kuma da d’an cije labb’ansa, still Cikin binta da wani irin mayataccen kallo yace. "Kije ki share min ɗakina". Fuskarta ta d’an b’ata cikin kuma tsanar shiga ɗakin nashi tace. "Yah Junaid breakfast nake haɗa mana". A fusace ya juyo kanta cikin takaicin abubuwan dake haɗe mishi a kanta ya yarfa mata wani irin gigitaccen mari a kan kunneta na dama, saida ya bada wani irin sauti ƙauuuuu! Da ɗan karen ƙarfi. A gigice tasa tafin hannunta ta tallabe ƙuncin ta. Yayinda wasu taurari suka fara gilma mata a gani. In da sabo yaci ace fuskarta ta saba da marukan Yah Junaid Wanda tun tana yarinya take shansu gashi sanadin su, kunnuwanta sun samu matsala jinta ya raunata. Wasu irin hawaye ne masu masifar zafine suka silalo mata. Ba tare da tace komaiba ta juya ta nufi ɗakin shi. Ta yaya zuciyarta zata samu sauƙin ɗan uwanta da take bata da wani sama dashi tunda shine suke uwa ɗaya uba ɗaya amman yafi kowa tsanarta a duniya. Ba shaƙuwa ko tausayawa a tsakaninsu. Sannan mahaifinsu babu ruwanshi ko a gabanshi Junaid zai daketa babu ruwanshi sai yayi kamar baya wurin ma. In Mom tayi mgna ya gwatsaleta yace babu ruwanta sunfi kusa. Wannan ne ya ƙara tsananta zubda hawayen ta. A haka ta fara tattara mishi falon da gaba ɗaya ya birkitashi. Shigowa yayi ya zauna yana mai Binta da ido, duk inda tayi. Wani irin abu yakeji a kanta. A hankali ya miƙe yabi bayanta lokacin da ta shiga Bedroom. Da sauri ta juyo jin shigowarsa. Gefenta ya matso fuska a murtuke hakan ne yasa bugun zuciyarta ya ƙara tsananta. Har kana iya ganin yadda numfashin ta ke fita da yanayin tsoro. Fuska ya kuma murtukewa. Kana yace. "Munafuka, sai kace da gaske haka kike tsoron maza, ji yadda kike tafiya ba bra kina wani karkakaɗa ƙirji irin ke gaki ƴar iska mai son maza ko?." Idanunta ta rumtse da k’arfi cikin kuma ƙunan ran ƙazafin da Yah Junaid ke jifarta dashi murya na rawa tace. "A'a". Cikin haɗe fuska ya daka mata tsawa tare da cewa. "Toh meya hanaki sa bra?". Murya na rawa tace. "Dr. Lukman ne yace in daina sa bra, sabida matsalar numfashin da Athsman ɗina ke jamin. In nasa ya matse min ƙirji sai numfashina yayi ta shaƙewa". Wani irin dogon tsaki yaja tare da cewa. "Ubanki zanci in baki dena raina min hankali ba, matse ƙirjin da ƙatti keyi bai shaƙe numfashin ba sai saka bra ne zai cushe miki numfashin." Fice min da gani!!". Ya k’are maganar a tsawace. Jin hakanne kuma yasa da sauri ta juya ta fita, hawaye na zubo mata sabida raɗaɗin marin daya yarfa mata da zafin kalaman zargi da yake binta dasu. A falo ta samu Mom da sauri ta faɗa jikinta. Cikin sakin sassayan kuka tace. "Mom ki gaya musu wlh ni ba yar iska bace, Meyasa Mom Meyasa Ya Junaid ke jifana da mugayen maganganu, shifa yaya nane..” Jawo hannunta Mom tayi suka zauna bisa kujera, a hankali tasa tafin hannunta tana share mata hawaye cikin yin ƙasa da murya tace. "Na sani Jannart kuma Allah ya sani, ke ba ƴar iska bace. Yaushe ma kika samu sakewar rayuwar duniya kullum kina cikin takunkumi. Ko ina zakije da masu gadinki. Na rasa wannan masifar tsaron na menene kina girma ana ƙara killaceki kamar abun rashin gsky." Cikin shessheƙan kuka tace. “Mom shi Yah Junaid gani yake, su masu tsaron nawa dasu nake iskanci. Daddy Kuma gani yake in ya cire masu tsaron da wasu zanyi iskanci. Wlh na sani Mom bawai dan tsaron lfyata bane yasa Daddy ware min masu tsaro. Shima zargina yakeyi ko Mom?". Jin yadda numfashin ta ke fitane yasa mom gyara zamanta kana ta fuskanceta da kyau. Allah ya sani tana son Jannart tamkar ƴar cikinta. Amman duk yadda zatayi bata burge Alhaji Idi da Junaid, gani suke kamar so take Jannart ta lalace ne don ba ita ta haifeta ba. Cikin kula da tausasawa uƙubar da suke shayar da ita tace. "A'a Jannart Daddynku baya zarginki, shi ya bada masu tsaronkine sabida larurar ciwonki, kina buƙatar makusanci a koda yaushe, tunda abu kaɗan ke tada miki athsman ɗin wanda kinga tun da yana nimoniya, kina girma yana canzawa ya riƙa har ya zama asman shiyasa yake tsananta kulawa a kanki. Sabida abu kaɗan ke tada miki shi. Kuma Yah Junaid ɗinki yana sonki. Ɗan uwa, uwa ɗaya uba ɗaya ya wuce wasa. Sun haɗa da son da Mamanki zatayi mikine da tana raye". Cikin zubda hawaye tace. "Mom kin bani son da ya kamata uwa ta bawa ƴarta, ni banyi maraicin kyakkyawan tarbiyar uwa ta gari ba. Kawai dai basa so nane". Cikin kafeta da ido Mom tace. "Jannart ki yarda dani, tashi muje kici abinci". Cikin nitsuwa tasa hannunta ta share hawayenta kana ta miƙe. Dinning area suka nufa. Suna zama Daddy ya fito da hakama Junaid da Abdul. Nan suka zauna sukayi breakfast. A hankali ta sauke numfashi ganin Junaid ya miƙe ya bar wurin. Sai kuma ta ɗan kalli Alhaji Idi Saleh Dakata. Cikin takatsantsan da girmamawa tace. "Daddy Ina son zanje gidan Aunty Rabi'ah akwai wani aikin da zamuyi a can". Ido ya ɗan zuba mata. Ita kuwa da sauri tayi ƙasa da kanta. Tana tasbihi cikin ranta, da addu'ar Allah ya ɗaurata a kanshi. Juyawa yayi ya fara sauƙa kan steps ɗin tare da cewa. "Kada ki daɗe. Kuma ƙafarki ƙafarsu Sunday." Cikin sabo da hakan tace. "Toh". Kana ta miƙe ta nufi ɗakinta. Mom kuma ta fara tattara kan table ɗin. Wanka tayi cikin nitsuwa da kuma sauri-sauri. Tana fitowa, ta zauna ta tsane jikinta kana ta busar da tattausan suman kanta. Ta shafa mishi mayuka, sannan ta tubkeshi. Mai ta ɗan shafa kana ta Murja farar hoda, tare dasa man baki. Sosai tayi kyau duk da bata cika kwalliya a fuskarta ba. Wasu tattausan riga da wondo pallazo farare ƙal ta zaro, Sai wata doguwar riga budaddiya mai igiya a tsakiya. pantie tasa, kana ta zira dogon wondon daya kasance yayi tightin fatar jikinta. Dole sa bra baya cikin jadawalin rayuwarta sabida larurar ciwonta. Sai dai takan sa rigunan su ɗan matseta. Rigar ta zura irin mai wuyanan nane wato, high neck, naɗe wuyan tayi ta gyarashi. Cib-cib rigar tayi mata a jikinta gwanin burgewa ƙirjinta yayi cas a tsaye babu alamun ronƙofowa bare zubewa. Lafaffen cikinta ya taimaka kwarai wurin bayyana tsayeyyun breast ɗinta. Doguwar rigar kimono blue color mai ɗigon fari-fari'n ta ɗaura saman riga da wondon, cib kuwa kimonon yayi mata ajikinta, inda kuma har ƙasa yazo mata. Igiyoyin dake sarƙafe tsakiyan rigar ta kama ta ɗaure. Hakan ya bawa tsakiyar rigar haɗewa, sama can kan ƙirirjin ta kuma gefe da gefen ya rufu har ya samu damar rufe nimples ɗin ta. Sai kuma tsakiyan bai ida rufuwa ba. Sai kuma can ƙasa ta nan zaka gane riga da wondone a ƙasan doguwar rigar farin mayafi rigar ta dauko tayi Rolling kanta fuskarta ta fito a ciki kamar sifili (0) a ciki. Sosai shigar tayi masifar mata kyau. Wanda kuma sune suturunta na yau da kullum wanda tafi so da jin daɗin sawa, kasan cewar rigunan cikin masu taushine suna buɗuwa dai-dai jikinta. Turare mai sauƙin ƙamshi ta fesa, sanin sa mai tsananin ƙamshin yana da illa ga baliga in zata fita da kuma lfyarta. Wasu fararen takalma sau ciki masu taushi tasa. Kana ta zari babbar wayarta kiran iphone11promax ta fito. A bakin ƙofar shigowa falon tayi kiciɓis da Mom cikin. Yanayin sakin fuska Mom tace. "Kai masha Allah ɗiyata kinyi kyau". Cikin yanayin jin daɗi tace. "Ngd Mom bari inje da wuri in samu in dawo da wuri". "Toh hamzarta ɗiyata, sai kin dawo". Toh tace kana ta fita ta tafi. Tana fitowa harabar gidan Wadannan garadan marasa kan gado suka miƙe baki ɗayansu. A hankali ta matso kusa da Driver'n'. Cikin kula yace. "Jannart yau kuma ina zamu je, naga yau ba ranar aiki bane?". Cikin jin daɗin yadda dattijon ke mata mgn ta mutuntaka tace. "Baba Ado, gidan Hajia Rabi'ah zamuje". Marfin motar ya kama da nufin buɗe mata, da sauri tace. "Baba Ado ka bari zan buɗe". Murmushi yayi kana ya bude mata, ta shiga. Suma sauran suka shiga sauran motocin suka tafi. Suna isa gidan Hajia Rabi'ah. Bayan sunyi parking ta nufi cikin gida su kuma suka zauna a waje. Da sallama a bakinta ta tura ƙofar. Da sauri taja da baya ganin Asiya dake fitowa. Sai kuma ta shigo ganin taja gefe tana hararanta. Da sauri tayi ciki jin Hajia Rabi'ah na cewa. "A a Jannart kin iso ko. Maza shigo daga ciki". Cikin jin daɗi ta shigo. Ta zauna inda Hajia Rabi'ah ke nuna mata. Cikin girmamawa tace. "My Aunty Ina kwana". Murmushi tayi tare da cewa. "Lfy lau Alhamdulillah ya ƴan tsaron ki". Cikin yin gajeren murmushi tace. "Gasu can a tsaye a bakin gate tamkar dogaran sarki". Dariya ta ɗanyi kana ta kalli wani ɗan matashi dake zaune can bisa kujarar Dinning area tace. "Toh Mahmoud ga Jannart ɗin ta iso. Tunda kaƙi bawa Asiya amsa ko ɗaya". Da sauri ta juyo ta kalli inda aka kira Mahmoud. Shi kuwa tasowa yayi ya nufo cikin falon yana mai cewa. "Aunty naga kamar hasadace ke cinta, kuma ma bada ita nai wayaba. Ita kuma wanna sai saiɓi. Kin san tun safe ina nan kin ajiyeni kamar mara aikin yi". Cikin nitsuwarta tace. "I'm so sorry. Ina kwana". Gefe ya zauna kana yace. "Wuni dai tunda 12 tayi". Nan suka gaisa kana Jannart ta fuskanceshu da kyau. Cikin sani makamar aiki tace. "Yaushe jirgin Ethiopia zai diro Nigeria a wanne gari ɗaya Abuja ko Lagos ne?". Murmushi Mahmoud yayi tare da cewa. "Wato zaki nuna min ke yar jaridace, tuni kin fara tambaya da wayo. Jirgi zaki tambaya ko shi?". Kwaɓe fuska tayi tare da kallon Hajia Rabi'ah kana a hankali tace. "My Aunty menene ma sunan nashi?". Cikin zuba mata ido Hajia Rabi'ah tace. "Iyeh wato ma har kin mance sunan nashi. Kin manta cewa sunan nashi ne kawai makaminki." Cewar Hajia Rabi'ah. Ita kuma Jannart takwara kanta tayi bisa kafaɗa kana tace. "Please my Aunty gaya min zan riƙe". "Rayyern". Ta bata amsa a takaice. Ita kuwa ido ta lumshe tare da fesar da numfashi can cikin zuciyarta tace. *"RAYYERN! RAYYERN!! RAYYERN!!!* Ta maimaita sunan sau uku kana ta juyo ta kalli Mahmoud cikin nitsuwa tace. "Mahmoud ranar yaushe zai dawo? Da wanne lokacin jirginsu zai iso daga Abuja ko Lagos zuwa Kano?". Gyara zamanshi yayi kana yace. "J....! free PAGE . 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *TUBALI* NA *AYSHA ALIYU GARKUWA* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ASSALAMU ALAIKUM, Masoyana ma karantan littattafaina, ina mai farin cikin sanar daku, yau d’in nan MON, 18 OCT 2021 za'a fara biyan kud’in samun damar karanta littafin TUBALI akan farashi mai sauk’i Biya 500 k’aramin farashin na k’aramin group, kana sai *Special people Group* akan farashi mai sauk’i 1k kacal babban group a yawan posting babancinsu yake, zaku biya ta asusuna. ACCOUNT NO 0661110170. BANK NAME: AISHA ALIYU GARKUWA BANK GTBank sai ki turo min shaidar biyanki ta wannan numben tawa da nakeyin whatsApp da ita 09097853276. *PLS TAKE NOTE BAND VTU* kada kiyi min VTU ko transfer'n katin ta wannan numben etisalat d’in idan kuwa kikayi wlh babu ruwana dan na fad’i miki. Please and please in dai da hali kada ki turo min katin, kiyi min transfer'n ruwan kud’i ta bank account na, in kuma babu dama to sayi katin MTN sai ki copy number's ɗin katin ki turo min ta whatsApp. Gareku mutanen jamhuriyar Niger ku tuntub’i Mommy akan layinta +22790899076, ta wurinta zaku biya, hoton katin zaku d’auka ku tura mata ta wannan numben a whatsApp, Special people group 1k ne (1000) k’aramin group kuma (500) kacal, Please dan Allah babbar macece mai yara da tarin jikoki da y’ay’an jikoki mu kyautata lafazi da mu'amala gareta dan Allah don in ka girmama iyayen wasu wasu zasu girmama naki🙏🏻... Littafin TUBALI littafine na musamman mai salo na musamman mai cike da abubuwa masu tarin yawa. *Tausayi, Sark’ak’iya, jan hankali, Fadakarwa, Nishad’antarwa, ilimantarwa, al'ajabi, Sa'ar rayuwa, riƙon amana, cin amana, ribar kyautatawa, kana da sassayar soya mai salon narke jiki da zuciya* Ga number wayata da nakeyin whatsApp da ita, 09097853276 idan kina son biyan kudin samun damar karanta littafin TUBALI sai ki biya ta wannan ac no din dai 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA, dan Allah ki biya kafin kiyi min mgn kina turo shaidar biyanki ina gani zan saki a group, in Kuma baki da ac no ko yanayin zaman wani k’asa ko wani luggun ki sayi katin MTN na 1k in special group kikeso ki turo min. In Kuma k’aramin Group kike so ki sayi katin *MTN ki copy number's din ki turo min ta whatsApp number'n na 09097853276 kada kiyi min VTU ko transfer'n katin 9mobile dan layin nada matsala* Za'ayi tsawon mako ɗaya ana biya ina kafin in fara update domin samun sassaucin aiyukan sauraron mutane, za'a fara biya yau *MON 18 OCT 2021. Kana zan fara posting ranar MON 25 OCT 2021 rana ita yau kenan in mai kowa mai komi ya kaimu bisa rai da lfy* 🙏🏻Na rokeki da girman zatin ubangiji in dai kin san zaki sayane dan ki fidda min littafina dan Allah ki bar kud’inki kiji tausayin marainiya, kada ku cutar da marainiyar Allah,😭🙏🏻🙏🏻🙏🏻. Nasan daga yau har zuwa na gama littafin Chart zaimin yawa zai hausawa aiyuka zasu yawaita gareni, amman babu kamar makonni ukun forko zuwa biyar, Please ina neman al'farmar uzuri in kinga kinyi min mgn ban amsa mikiba, na tuba kiyi haƙuri ba raini bane ko wulak’anci face yawan mutane wata k'il ban isa kan Chart naki bane, Amman muddin na isa na kuma bud’e na gani tabbas zan baki amsa in katine zansashi yana shiga zan saki a group in bai shiga kuma in gaya miki, in Kuma ta account kika turamin ina ganin shaidar biyanki zan saki a group, 🙏🏻Dan Allah in kinsan ba littafi ko maganin gyara namu na mata kikeso ba to kiyi haƙuri da min mgn sai na d’an samu salama🤝🏻😘🙏🏻😂. *Sayan na gari maida kuɗi gida sai kinzo* By *GARKUWAR FULANI* 11/15/21, 7:19 PM - Auntyna: *TUBALI* PAGE 3 NA *AYSHA ALIYU GARKUWA* *FREE PAGE* *ƊANƊANO* *NMETTARI enji men nfulɓe* "Jibi". Ya bata amsa a taƙaice yana mai kallon Kyakkyawar fuskarta. Ita kuwa gyara zamanta tayi tare dasa hannu ta amshi cup ɗin ruwan sanyin, da Hajia Rabi'ah ke miƙa mata-ta ajiye shi bisa Stoll din baƙin glass dake gabanta. "Nagode". Ta faɗi cikin nitsuwa, sannan ta kalli Mahmoud dake bin fuskarta da ido. Cikin yanayinta na nutsuwa da kuma bayyana zallan ajinta na y’a Mace tace. “Akwai tabbacin jibi zai dawo? Sannan ta Abuja ko Lagos zasu sauƙa?". Wayarshi ya zaro a al'jihun rigarsa yana mai lallatsata kana yace. “In sha Allah jibi zasu dawo. Dan last night muna tare da Deen ƙanin Usman PA'nshi. Yayi magana da yayan nashi kan jikin mamansu ya tashi, yaushe zasu dawo. Toh nan Usman ɗin ke cewa jibi zasu dawo. Iya abinda na sani kenan, sauran bayani kuma sai dai in tuntuɓi Deen ɗin". Ya ƙare maganar yana sa wayar a amsakuwa yadda duk zasuji. “Hello Deen ya Gida". Cewar Mahmoud. Deen dake zaune gaban mamansu wanda yanzu ya gama magana da Usman ne yace. "Lfy lau Alhamdulillah Mahmoud". "Yah jikin Mama". "Alhamdulillah jiki da sauƙi". Ya bashi amsa yana miƙa mata maganin. Gyara zamanshi yayi tare da cewa. "Yah Usman ɗin yana dawowa ko?". Ɗan gajeren tsaki yaja tare da cewa. "Eh to, zasu dawo, amman sai jibi fa kuma nan ma wata ƙil in sun iso su kwana a Abuja wata ƙil suda nan sai ranar jumma'a". ya ƙare mgnar da sanyi. "Ayyah ba komai ai in dai jikin da sauƙi, jumma'a kamar yaune Allah dai ya dawo dashi lfy. Ka gaida min Mama da jiki Allah ƙara ƙarfin jiki". “Amin Amin". yace kana sukayi sallama. Katse kiran yayi tare da juyowa ya kalleta. Numfashi suka sauƙe ita da Hajia Rabi'ah. Sai kuma tace. "Alhamdulillah, toh Mahmoud ko zaka bani number Deen". Da sauri yace. "A a in fa yasan me kike bincika bazai saurareki ba". Hajia Rabi'ah ne ta amshi zancen da cewa. "Kada ki damu Jannart in sha Allah komai zai tafi dai-dai. Shi Mahmoud ɗin shi zai rinƙa samo mana bayani. Tunda kuna da number’n juna zaike miki bayani, ba sai kin fito kinzo nan ba, tunda fitar naki aikine mai zaman kanshi." Cikin gamsuwa da hakan tace. "Toh shike nan My Aunty, Ngd Matuƙa Allah ya saka da al'khairi". “Amin Amin.” tace Tana mai gudun kada aikin ya bar hannun yarinyar tunda kowa ya ganta dai yasan bawai tana yin aikin dan neman kuɗi ko suna bane, tana yine dan ra'ayin tane gashi du-du watanni huɗu tayi da fara aikin kuma suna jin daɗin mu'amala da ita, so dama sanyin da shirin yayi shiyasa aka canza wanda ke yinsa a baya. Kuma da alamun tana matuƙar jin daɗin aikin. Kiran Salman ne ya shigo wayarta. Da sauri ta amsa tare da karawa a kunne. "Assalamu alaikum". Tace cikin sassayan sautin ta. Daga b’angarensa kuwa murmushi yayi tare da cewa. "Wa alaikissalam, Jannart kinbi diddigin Rayyern d’in? Kuma wane lbri kika samo mana a kanshi? " Cikin yarda da kai tace. "Duk motsinshi na cikin tafin hannuna!". Dariya mai sauti Salman yayi. Hakama Hajia Rabi'ah da Mahmoud. "Karsashi’nki da ƙarfin guiwarki akan aiki yana burgeni Jannart”. Cewar Salman. Cikin sauƙe numfashi tace. "Toh ba doleba Salman, tunda naji ana shirin korata, ai sai inda ƙarfina da hikimata suka ƙare". Cikin wasa yace. "Ke har wani ƙarfi a garreki da dai kin tsaya a hikimar na yarda". Murmushin daya sanya beauty point ɗin ta lotsawa tayi. Haka dai suka ɗan tattauna batun bayan ta mishi bayanin abinda ta ji kan dawowarshi. Saida tayi sallan azahar ne kuma ta fito suka nufi gida. A kan hanyarsu ta komawa ne, Baba Ado driver'nta ya ɗan juyo ya kalleta cikin kulawa yace. "Jannart yanzu dai ciwonki da sauƙi ko?". Numfashin ta ɗan fidda kana a hankali tace. "Alhamdulillah da sauƙi dai zance, amman yana yawan motsa min a kwanan nan kamar yana son tashi." Cikin tausayawa yace. "Toh amman har yanzu babu wani maganin da ake baki sai allurar da akeyi duk watan ne?". Kai ta gyaɗa mishi tare da cewa. "Eh". Numfashi ya ɗan fesar kana yace. "Allah ya sauƙaƙa yasa zakkan jikine al'farmar Annabi da al'ƙur'ani". Cikin jin daɗi tace. “Amin Baba Ado nagode!". A can Ethiopia birnin Addis Ababa, kuwa. Riyyam-nsra ne tsaye gaban wayarsa daya tsaida. Rawa yakeyi da murmushi a fuskarsa. Sai kuma ya kalli gefensa. Wata kyakkyawar budurwa wacce a ƙalla suyi sa'anni. Murmushi yakeyi cikin harshen Hausa yake cewa. "Jibi iwar haka ina hanyar Nigeria, su Zayton kuma sai dai ayi ta aikin zumbura baki. Fan's ku gani, wai kishi takeyi dani". Da sauri ta kai mushi bugu tare da matso ƙwallar idanunta, tana faɗin "Mammy! Mammy!!". Wata kyakkyawar matace mai Kekkyawar sura da jiki da shiga ta kamala, wacce kyan surarta ya iya boye ainihin shekarunta, ta fito daga cikin wata ƙofar da fuskantar inda ya kafa wayar tashi. Ɗan gudu-gudu da tsalle-tsalle yake yana zagaya parlon Zayton na biye dashi a baya. Da sauri yayi tsalle tare da ɗan sakin ƙara yace. "Ohh Mommy". Jin ta ɗan sa hannu ta bugi ƙeyarshi. Tura baki yayi tare dasa hannunshi ya shafa ƙeyar yana mai zazzarewa Zayton ido. Abin gwanin ban dariya da ka gani kasan akwai Kekkyawar shaƙuwa, ƙauna, tausayi, da son juna. Ɗauke wayar tashi yayi ya sake video a shafinsa na TIKTOK. Kun san matsalar su kenan ƴan TIKTOK duk abinda zasuyi ko sukeyi sai sun nunawa duniya, More Especially irin Riyyam-nsra da yayi shuhura yayi zarra da dubban dubatan masoya mabiya, musamman a cikin kwanakin nan da yai mgn da Hausa ya janye mana hankalin matasan Nigeria, domin kuwa ayanzu followers d’insa harsun d’arawa two million. Gane abin da yayi dinne kuma yasa. Mammy matsoshi da kyau ta kama kunnenshi ta ɗan matse. Ƙara ya kuma ɗan saki, wanda yasa Zayton tuntsirewa da dariyar jin daɗi tana ɗaga mishi gira. Ita kuma Mammy cikin ɗan faɗa tace. “Wato kai Riyyam baza ka taɓa canzawa bako, duk motsinmu sai ka bazamu a duniya? Kai kam inaga kana gab da nuna duniya yadda kake kashi ma ko". Hannunshi yake ɗan yayyarfawa tare da cewa. "Afwan Yaah Mammy na tuba, wayyo Hamma Mammy zata tsinke min kunne". Dariya Zayton tayi tare da cewa. "Zai aikata fiye da hakama Mammy ja kunnen da kyau". Hannunshi ya kai ya bugi hannunta tare da cewa. "Yarinyar nan ki shiga hankalinki fa". Fuska ta haɗe tare da cewa. "Waye yarinyar yaro in ka manta in tuna maka nice babba 15 minute nake baka, kaga kuwa dole ace da mijin iya baba, dan 15 minute ba 15 second bane". Sosai Mammy ta saki murmushi suna matuƙar sata nishaɗi da ɗebe mata kewa, da danne mata duk wani ƙuncin rayuwa, Especially in suna faɗa kan girma. Zayton son girma kamar gyambo, 15 minute da take bashin nan ji takeyi kamar shekaru goma sha biyar take bashi. Gefe ta zauna kana suka zo suka sata a tsakiya. Cikin sakin fuska ta shafa kan Riyyam-nsra tare da cewa. "Zoh nan autana". Gwalo yayiwa Zayton tare da ɗaura kanshi bisa cinyarta tuni kuma ya sake haɗa video. Murmushi yakeyi yana yiwa Zaiton signal tare da cewa. "Mammy asamin al'barka". Da sauri itama ta sako kanta tare da cewa. "Mammy ai nice mace, dan haka ya riƙe girman ya matsa ni in kwanta". Cikin yin ƙasa da murya Mammy tace. "Ya isa haka ku bari, Dida na bacci kada ku tada min ita". Toh sukace dan yadda tayi mgnar ba wasa. Bayan ya saki wannan video ɗin ne kuma. Ya gyara zamanshi ya fuskanci Mammy da kyau jin tana cewa. “Riyyam sam hankali na. baya kwanciya da wannan rawan kan naka! Ina jin tsoron kayi nesa dani, gaba ɗaya ka juye ka zama ɗan nanaye, ka zama tamkar mazari duk inda kake sai rawa, sai waƙa, sai haɗa comedy duk inda kake waya na hannu, kai kaɗai a ganka kana dariya ko kana kuka ko kana haɗa fuska ko layi, kai gasu nan dai barkatai, ka zama ɗan Film a fili ka rubuta lbri ka tsara ka bawa kanka umarni kayi shirin. Ga ɗan karen yawo yau kace zaka tafi waccar ƙasar, gobe kace zakaje waccar gashi ka zama babu sirri duk inda kake an sani, shiyasa nake jin tsoron zuwanka Nigeria duk inda kaga mata sai ka bisu da ido". Da sauri ya gyara zamanshi cikin nitsuwa kamar ba shiba yace. "Mammy babu komai sai al'khairi, ki yarda dani bana wani mugun abu, in ke bakya gani na ai Ubangijin talikai daya busan numfashin yana ganina". Uhum tsakanin uwa da ɗa kenan ya gane cewa tana zargin shi ne ko tana tsoron taɓarɓarewar tarbiyarshi. Cikin sauƙe nannauyan numfashin tace. "Wlh badon dole ba, bazaka jeba, amman ba komai Allah ya kaika lfy ya dawo da kai lfy. Sai dai dole ka nitsu ka dena wannan rawan kan". Hannunshi yasa ya kame kanshi kana yace. "Toh Mammy na dena". Murmushi tayi hakama zaitun. Washe gari ranar Laraba, Kano Nigeria. Cikin bacci taji numfashin ta, na fita a cushe, kana tana shaƙan zazzafan ƙamshin turaren sa mai masifar ƙarfi da tafiya da numfashin ta. Idonta ta buɗe cikin wahalar numfashi. Da sauri ta ida buɗe su duka tare da fisgo numfashin ta a wahalce. Sabida ganin Yah Junaid da tayi sunkuye a kanta hannunshi na kan ƙirjinta. Wani irin tsuma da karkarwa jikinta ya farayi, da azaban ƙarfi. Cikin tsananin tsoro da razanin ta yunƙuro zata tashi, tare da furta "innalillahi wa innalillahi raji'un." Wani irin azabebben tsoro firgita kaɗuwa da gigitane suka dirar mata lokacin ɗaya jin yadda yasa hannunshi ya matse ta tare da murtuƙe fuskarshi. Cikin tsananin rawan jiki take zaro ido murya da baki na rawa tace. "Innalillahi Wa’inna Ilaihirraju’un Y... Ya... Yah... Juna..Junaid, me haka!!” Wani irin masifeffen kallo ya watsa mata, tare da kai hannunshi duka biyu kan breast ɗinta, yayi musu wani irin masifeffen kamu wanda yasa ta saki wani irin gigitaccen ƙara, lokaci ɗaya kuma numfashin ta ya fara off and Dawn, ciwonta na gab da tashi. Shi kuwa Junaid wani irin sanyi yakeji a ransa tare da rumtse tafin hannunsa. Mom kuwa dake ɗakinta, ita da Abdul cikin razanin jin sautin muryar Jannart ta miƙe tsaye jiki na rawa, ta fito falo. Dai-dai lokacin kuma Jannart ɗin ta fara wani irin fiffizgewa sabida numfashin ta dake shirin barin gangan jikinta. Wata iriyar fitinenneyar zufa mai cike da zafi, ta fara tsastsafo mata tako wani hudan gashin jikinta. “Hahhhh! Uhhhhhhhh!! Fuhhhhhhhheeeeyyyy!!! M...Mom!" Ta fuzgo maganar da ƙarfi lokaci daya kuma numfashin ta ya dena shiga sai fifita. Jiki na rawa Mom ta kutsa kanta cikin ɗakin nata. Shi kuwa Junaid wani irin fitinenne abu yakeji yana tsirgar masa. Hannunshi ya kirjinta. Tare da yiwa breast ɗin ta wani azabebben riƙon da saida yaji. Gamsuwa shaiɗan cinsa. Kana ya juya ya nufi ƙofar fita. A bakin ƙofar sukayi kiciɓis da Mom. Wani irin mugun kallo ya watsa mata. Ita kuwa Mom wani irin kallon tuhuma take binshi dashi. "Mchewww". Taja wani dogon tsaki ganin bazai bata hanya bane yasa ta matsa gefe. Wucewa yayi tare da cewa. "Sai kiyi ai". Ita dai bata bi ta kanshi ba, ta wuce cikin ɗakin. A gigice ta nufi kan gadon tana kiran ta. "Jannart! Jannart!! Jannart!!!". Ta Ƙarisa kiran sunanta a gigice tare da hawa kan gadon ta jawota jikinta tana cewa. "Innalillahi wa innailaihi rajiun. Abdul! Abdul kazo". Da gudu Abdul ya nufi ɗakin sabida dama yana falo Juinad ne ya hanashi shiga. Cikin ruɗani tace. "Abdul kira min Daddynku. Ka gaya mishi jikin Jannart ya tashi". Da sauri yace. "Toh Mom amman bari in fara kiran Dr Lukman". Ya ƙare mgnar yana kara wayarshi a kunne. Ita kuwa Mom sai jijjiga Jannart daketa kokuma da numfashin ta takeyi. Cikin rauni Abdul yace. "Assalamu alaikum. Daddy". "Na'am Abdul ya akayi ne?". Alhaji idi sele Dakata dake zaune a Office nashi Barrister Kabir Saleh Dakata na zaune a gabanshi. Ya amsawa Abdul da kulawa. “Daddy jikin Jannart ne ya tashi, na kira Dr Lukman kuma baya ɗagawa". Da sauri yace. “Innalillahi Bari in kirashi yanzu-yanzu". Ya ƙare mgnar da katse kiran. Cikin kula Barrister Kabir Dakata yace. "Yaya lfy kuwa? Jikin Jannart ko?". Cikin damuwa yace. "Eh". Miƙewa tsaye yayi tare da cewa. Bari inje mu tafi asibiti". Tuni kafin yayi wata magana ma ƙanin nashi ya fita. Abdul ya kuma kira tare da cewa. “Ga Abbanku na zuwa da likita". Toh yace kana ya katse kiran. Shiru yayi yana nazartar irin son da Ƙanin nashi keyiwa yaranshi, Especially ma Jannart yana mata wani irin so na musamman. So na da ban a cikin yaranshi. Ajiyan zuciya ya sauƙe tare da meda kai ya jingina da kujera. A hankali yake jujjuyawa, yana mai ƙoƙarin kauda tunanin da zuciyarsa ke kawo mishi. Shi kuwa Barrister Kabir yana fita kai tsaye. Asibitin Hamda Ya wuce. Yana mai kiran babban Dr. Yana tafe cikin gudu kamar maiyin doguwar tafiya. Yana isa kai tsaye Office ɗin Dr Sajo ya wuce. Yana ganinshi ya miƙe tsaye tare da cewa. "A a Ƙanina! Ka iso, ko ina mara lafiyar?". Cikin girmamawa da alamun tsohuwar amintaka yace. "Barka dai Yaya Sajo, dan Allah kayi haƙuri mara lafiyar tana gida. Ni kuma daga Campany’n Yays Dakata nake, so kafin in koma gida in ɗaukota komai zai iya faruwa, kasan matsalar cutar athsman shiyasa nace bari in biya mu tafi tare. Dan Allah kayi haƙuri". Murmushi Dr. Sajo yayi tare da fara tattara abin buƙatarsa yana mai tuno amintaka da mutuntakar da ke tsakaninsa dasu a baya. Cikin kuma kula da amintaka yace. "Ba komai ƙanina muje, dama na gama yau bani da aiki". Cikin jin daɗi ya juya ya fita, shi kuwa yana biye dashi a baya. Motarshi suka shiga, shiyasa yake taka motar da kyau. Tsoro yakeji yasan yadda ciwon ke wahalar da ita. A can gida kuwa, gaba ɗaya Mom da Abdul sun rikice. Ita kuwa Jannart tuni ta gama gigicewa ta fita haiyacinta, fuskarta nan tayi jazir. Sai fuzgo numfashin takeyi da ƙarfi. Wayar Abdul ne tai ringing yana ɗagawa yace. "Abba jikin fa ya tsananta". "Subahanallahi Abdul gani nan zuwa yanzu". Toh yace kana ya katse kiran. Suna isa kai tsaye cikin gidan sukayi. Abban na gaba Dr Sajo na biye dashi a baya. Suna shiga Dr. Sajo ya fara aikinsa, allura yayi mata dan samun dai-dai-ta numfashin ta. Allah cikin ikonsa kuma a take ta fara sauƙe ajiyan zuciya, lokaci ɗaya jikinta ya fara sakewa. Sai ga wani irin bacci mai nauyi ya kwasheta... Kusan a tare suka sauƙe ajiyar zuciya baki ɗayansu. Cikin kuma sauƙe numfashi Abba yace. "Alhamdulillah". Hakama Mom. Abdul kuwa shiru yayi yana mai jin tausayin yar uwar tasa. Dr. Sajo kuwa, harhaɗa kayan aikinshi yayi, kana ya kalli Barrister Kabir, gyaran murya yayi tare da cewa. “Ciwonta yayi zurfi a jikinta, kuma bata bin doka da ƙaidar maganin yadda ya kamata". Da sauri Mom tace. "Ai ba'a bata magani Allura kawai akeyi mata duk wata". Cikin mamaki yace. "Allura kuma? Toh wacce iriyar Allura ce duk wata kuma!?." Cikin sanyi Abdul yace. "Gaskiya bamu san wacce iriyar Allura bace". Da sauri Dr Sajo ya kalli Barrister tare da cewa. "Wanne Dr ne yake duba ta?". Numfashi mai nauyi Barrister ya sauƙe kana a hankali yace. "Dr. Lukman ne". Wani irin shiru Dr Sajo yayi tare da alamun nisan nazari. Kana yace. "Ok muje ko Barrister". Toh yace kana suka nufi hanyar fita. Sai kuma ya ɗan juyo ya kalli Mom dake gyarawa Jannart din kwanciyarta, cikin nitsuwa yace. “Kada ki damu, zata samu lfy in sha Allah, sannan zamu canza mata Dr da zai na kulawa da ita da kyau". Kai ta gyaɗa tare da cewa. "Mun gode". A hankali Dr. Sajo ya juyo ya kalli Barrister Kabir dake jan mota, dan medashi asibitin sa. “Ƙanina akwai buk’atar a canzawa Jannart likitan da zaina dubata.” Cikin nitsuwa Barrister Kabir ya ɗan juyo ya kalleshi tare da cewa. "Yaya Sajo meyasa!?". Kafaɗarshi ya ɗan ɗaga tare da cewa. "Noh ba komai, kawai dai ciwonta yanada buƙatar gamayyar likitocin zamani bawai a tsaya kan ɗaya ba, a samo wani shima ya gwada kwarewar sa". Uhum Dr.Sajo bai tuna cewa da babban Lawyer yake mgna ba. Cikin fahimtar wani abun Barrister Kabir yace. "Toh ba matsala in sha Allah za'ayi haka. Amman ina zamu samu likitan?". Da sauri yace. "A wannan mai sauƙine, akwai wani Babban Doctor yarone matashi mai ƙuruciya da sanaiyar ilimin likitanci na juya da yau, kana harna gobe yana bincika yasan aikinsa, mun gamsu dashi, Dr Rayyern Mai-nasara." Da sauri Barrister yace. “Zakayi mana hanyar ganinshi kenan? Dan ance yana da wuyar gani". Ya ƙare maganar yana yin parking. Kai ya ɗan juyo ya fuskanceshi tare da cewa. "Eh to Gaskiya yana da wuyar samu, saboda yawan aiyuka, kuma a wani sashin bashi da wuyar gani, in har kaje Mai-nasara Hospital ɗinsa, muddin dai yana ƙasar, toh zaka ganshi sai dai ko in baya ƙasar, in kuma bakayi sa'a ba, sai a turaka wurin wani Dr ƙaninsa da kuma amininsa ɗin ba shiba, tunda yanzu aikin Company's dinsa sun tasoshi gaba, dole ya samo wasu likitocin bayan shi. Saɓanin da da shi kaɗai ke jan ragamar asibitin. Amman idan nasa hannu na baku takarda zuwa gareshi kuna zuwa shi ɗin zaku gani". Cikin gamsuwa Barrister yace. “Alhamdulillah nagode matuƙa Yayana". "Haba ba komai Kabir yiwa kaine. Yauwa sai kuma batun allurar da akeyi matan nan, abar yi matashi akwai buƙatar in santa, sannan ina son sanin sunan allurar". Ya ƙare zancen yana fita daga cikin motar. Cikin gamsuwa Barrister yace to. Kana sukayi sallama. Ganin lokacin sallan azahar yayine kuma yasa ya nufi masallaci. Koda aka idar da sallah kuwa. Gidan yayan nashi ya koma. Ethiopia. Dr Rayyern Mai-nasara ne. Tsaye cikin wasu tattausan Suit masu masifar kyau da taushi tare da sheƙi. Inda Riga da wondon suit din suka kasance pink color masu dauke da zane-zanen fari, sai kuma neck tie ɗin shi daya kasance fari, yayinda long sleeve dinsa ma ta kasance white, takalmin dake kafansa kuwa pink color ne mai dauke da harafin R-M. Sai kuma Diamond watch din dake hannunsa mai ɗan karen sheƙi da tsada. Wayarshi kirar iphone 12pro max ne saƙale a kafaɗarshi yayinda ya mannata a kunne yana magana. Kana kuma hannunshi ɗaya na riƙe da System ɗin shi. Daya hannunshi kuma na lallatsashi. Bisa alamu aiki mai muhimmanci yakeyi. Ga kuma wani irin masifeffen ƙamshi mai ɗan karen daɗin shaƙa da yake fitarwa. Lallausan Sajenshi nan ya kwanta lib, yayiwa kyakkyawar fuskarsa kawanya sai sheƙi yakeyi. Haka kuma Ɗan madaidaicin bakinsa mai jajayen lips na motsawa a hankali. Yayinda siraran idanunshi suka fito ras, cikin ɗan siririn glass mai ruwan garai-garai, irin na Doctor's daya liƙashi cas bisa karan hancinsa. A hankali ya juyo ya kalli Usman daya shigo cikin alamun shiri. "Sir gani". Usaman ya fada anutse. Da idanunshi yayi masa nuni da jakarsa, yana maici gaba da maganar da yakeyi a wayar. "Uhumm". Yace tare da lumshe idonshi. A can ɗaya sashin kuwa ba tare da damuwa ba Sulaiman yaci gaba da magana. Sabida sanin haka Allah ya halicce Rayyern mafi akasarin lokuta maganar Uhumm, ne ko eh ko hmm koko a'a Bai cika yawan surutu ba, da fari gani suke miskilanci ne, sai daga baya suka fahimci abin da gaskene. Dan muddin za'ayi ta surutu ko hayaniya ko magana da ƙarfi a kanshi ko kukan yaro ko babba, a take idanunshi ke kaɗawa suyi jazir, lokaci ɗaya ciwon kai ke rufeshi larurarsa. Ido ya ɗan juyo yana kallon Usman dake tsaye gefenshi. Yayinda kuma yake jin Sulaiman na cewa. "Wallahi Rayyern ni kamanninku ya daina bani mamaki yanzu sai dai tsoro, Allah ko da yayi magana da hausa ko muryarshi iri ɗaya da Ramadan kuma". A hankali yace. "Hmmm Sulaiman social media ka biyewa ko?". Da sauri yace. "Dan Allah tsaya kaji, yaushe zaku dawo?". A taƙaice yace. "Jibi!". Cikin fidda numfashi Sulaiman yace. “Toh gashi kuma shi yaron yau zai taho Nigeria, ni nai zaton yau nema zaku dawo ince Allah yasa ku haɗu a jirgi kaga zahiri, abu kamar an dama kunu an raba har ɗan makolloto yake dashi irin naka fa". Ɗan gajeren numfashi mai d’auke da gajiya Rayyern ya fesar tare da cewa. "Uhmm, it’s Okay a gaida Baby". Yana faɗin haka ya katse kiran. Sai kuma ga wani kiran ya shigo. Da sauri ya zauna bisa kujerar bayanshi kana ya amsa kiran. Cikin tsananin girmamawa hade da ladabi da biyayya da kuma tarin mutuntaka yace. "Assalamu alaikum". A can ɗaya sashin kuwa, wani kyakkyawan mutum ne mai cikar haiba kamala ne, zaune. Alhaji Bashir Muhammad Mai-nasara kenan, sai Mami mai ɗakinshi dake gefenshi. Kana ɗan matashin ƙaramin ɗansu Dr Ramadan Mai-nasara na zaune gaban Abba'n nasu. Cikin tarin so kula bege da kuma ƙauna, Alhaji Bashir ya gyara zamanshi tare da cewa. "Wa alaikassalam". Cikin jin daɗin jin muryar mahaifin nashi yace. "Abba Barka da safiya". "Barka dai Rayyanu". Ido ya lumshe cike da son mahaifin nashi yace. "Abba kuna lafiya?". "Lafiya lau Alhamdulillah, ga Mamynku da Ramadan wai in tambaya musu yaushe zaka dawo, suna kewarka". Murmushin gefen baki daya bayyana fararen kyawawan haƙoransa yayi, cikin kuma sauƙe numfashi yace. "Nima ina kewarku Abba in Sha Allah yau ina hanya amman Abba kai kaɗai fa". Murmushi yayi fahimtar cewa. "Shi kaɗai yasan yau zai dawo kenan." Ramadan kuwa murmushi yayi sabida jin abinda Hamman nashi ya faɗa. Mamy kuwa Kekkyawar mace mai cikar haiba, murya ta ɗan ɗaga tare da cewa. "Toh me zan dafa maka". Idonshi ya lumshe fahimtar sun jishi kenan. Cikin sanyi yace. "Mamy'na komai ma". Amsar wayar tayi tare da cewa. "Cin zaƙi zai Barka kaci abinda zan dafa maka ko?". Cikin fuskar annuri yace. "Yesssss! Mamy". "Toh shike nan Babana Allah ya kawo min kai lfy". "Amin Amin Mamy". Yace cikin lumshe ido Daga nan sukayi sallama. Kana ya juyo ya kalli Usman kana a taƙaice yace. "Mu je". Da sauri Usman yace. "Sir ina muka nufa?". Cike da mamaki Usman ya ɗago kanshi da sauri ya zuba mishi ido cikin al'ajabin jin yana cewa. "Nigeria". Ya buɗe baki zaiyi magana ya ɗaga mishi hannu tare da nuna mishi ƙofar fita. Haka yasa ya gimtse maganar kana ya ɗauki kayyakin nasu Suka fita. Boke International Airport Addis Ababa Ethiopian.Suka nufa kai tsaye Still Kai tsaye Airport parking suka nufa. Bayan Driver'n'shi yayi parking. Da sauri Usman ya fito ya buɗe mishi, marfin motar. Cikin nitsuwa ya zuro ƙafarsa ta dama waje , tare da sauƙeta ƙasa ahankali, Saidai kuma da sauri ya rumtse idanunshi tare da dafe ƙahon zuciyarshi saboda wani irin m...! 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *TUBALI* NA *AYSHA ALIYU GARKUWA* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 ASSALAMU ALAIKUM, Masoyana ma karantan littattafaina, ina mai farin cikin sanar daku, yau d’in nan MON, 18 OCT 2021 za'a fara biyan kud’in samun damar karanta littafin TUBALI akan farashi mai sauk’i Biya 500 k’aramin farashin na k’aramin group, kana sai *Special people Group* akan farashi mai sauk’i 1k kacal babban group a yawan posting babancinsu yake, zaku biya ta asusuna. ACCOUNT NO 0661110170. BANK NAME: AISHA ALIYU GARKUWA BANK GTBank sai ki turo min shaidar biyanki ta wannan numben tawa da nakeyin whatsApp da ita 09097853276. *PLS TAKE NOTE BAND VTU* kada kiyi min VTU ko transfer'n katin ta wannan numben etisalat d’in idan kuwa kikayi wlh babu ruwana dan na fad’i miki. Please and please in dai da hali kada ki turo min katin, kiyi min transfer'n ruwan kud’i ta bank account na, in kuma babu dama to sayi katin MTN sai ki copy number's ɗin katin ki turo min ta whatsApp. Gareku mutanen jamhuriyar Niger ku tuntub’i Mommy akan layinta +22790899076, ta wurinta zaku biya, hoton katin zaku d’auka ku tura mata ta wannan numben a whatsApp, Special people group 1k ne (1000) k’aramin group kuma (500) kacal, Please dan Allah babbar macece mai yara da tarin jikoki da y’ay’an jikoki mu kyautata lafazi da mu'amala gareta dan Allah don in ka girmama iyayen wasu wasu zasu girmama naki🙏🏻... Littafin TUBALI littafine na musamman mai salo na musamman mai cike da abubuwa masu tarin yawa. *Tausayi, Sark’ak’iya, jan hankali, Fadakarwa, Nishad’antarwa, ilimantarwa, al'ajabi, Sa'ar rayuwa, riƙon amana, cin amana, ribar kyautatawa, kana da sassayar soya mai salon narke jiki da zuciya* Ga number wayata da nakeyin whatsApp da ita, 09097853276 idan kina son biyan kudin samun damar karanta littafin TUBALI sai ki biya ta wannan ac no din dai 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA, dan Allah ki biya kafin kiyi min mgn kina turo shaidar biyanki ina gani zan saki a group, in Kuma baki da ac no ko yanayin zaman wani k’asa ko wani luggun ki sayi katin MTN na 1k in special group kikeso ki turo min. In Kuma k’aramin Group kike so ki sayi katin *MTN ki copy number's din ki turo min ta whatsApp number'n na 09097853276 kada kiyi min VTU ko transfer'n katin 9mobile dan layin nada matsala* Za'ayi tsawon mako ɗaya ana biya ina kafin in fara update domin samun sassaucin aiyukan sauraron mutane, za'a fara biya yau *MON 18 OCT 2021. Kana zan fara posting ranar MON 25 OCT 2021 rana ita yau kenan in mai kowa mai komi ya kaimu bisa rai da lfy* 🙏🏻Na rokeki da girman zatin ubangiji in dai kin san zaki sayane dan ki fidda min littafina dan Allah ki bar kud’inki kiji tausayin marainiya, kada ku cutar da marainiyar Allah,😭🙏🏻🙏🏻🙏🏻. Nasan daga yau har zuwa na gama littafin Chart zaimin yawa zai hausawa aiyuka zasu yawaita gareni, amman babu kamar makonni ukun forko zuwa biyar, Please ina neman al'farmar uzuri in kinga kinyi min mgn ban amsa mikiba, na tuba kiyi haƙuri ba raini bane ko wulak’anci face yawan mutane wata k'il ban isa kan Chart naki bane, Amman muddin na isa na kuma bud’e na gani tabbas zan baki amsa in katine zansashi yana shiga zan saki a group in bai shiga kuma in gaya miki, in Kuma ta account kika turamin ina ganin shaidar biyanki zan saki a group, 🙏🏻Dan Allah in kinsan ba littafi ko maganin gyara namu na mata kikeso ba to kiyi haƙuri da min mgn sai na d’an samu salama🤝🏻😘🙏🏻😂. *Sayan na gari maida kuɗi gida sai kinzo* By *GARKUWAR FULANI* 11/15/21, 7:19 PM - Auntyna: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *TUBALI* PAGE 5 NA *AYSHA ALIYU GARKUWA* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *FREE PAGE NE* *Littafin TUBALI na kuɗine, ki biya 500 in saki a ƙaramin group, ko kuma ki biya 1000 in saki Special Group, wanda cikin mako biyu kacal zamu ƙare part 1. Ki turo kuɗin ta asusuna na GTBank, 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU, sai ki turo shaidar biyanki ta wannan numben whatsApp na 09097853276. Ki saya ki karanta cikin salama ba tare da hakkina a kankiba, in bazaki sayaba ga littatafai nan birjik kamar jompa a Jos sai ki samu na kyauta ki karance salim alin* Kallo mai cike da tarin takaici ya watsa mata, rikitattun idanunshi cikin nata kwayar idanun kasan cewar suna fuskantar juna. Wani irin azabebben zogi lips ɗinshi sukeyi sabida yadda ta bugi gemunshi da goshinta, har hakan yasa lips ɗin suka haɗe da kyawawan haƙorinsa. Zut-zut haka yakeji suna zogi. Da raɗaɗi, wani irin tafasa zuciyarshi takeyi tare da harbawa, files ɗin campany'nsa da yake da matuƙar mahimmanci da suke watse a ƙasa ya zubawa idanu. Wani irin mugun kallo ya kuma watsa mata duk a cikin abinda baifi 5 second ba. Idonshi ya kai bisa hannunta dake shaƙe da kwalar rigarsa ta gefe. Hannunshi na dama yasa ya damƙo hannunta da azaban ƙarfi, kana ya yarfashi. Wanda sanadin fizge hannun nata da yayi kuma wayarshi, kirar iphone 12 pro max dake cikin al'jihun rigarsa ya faɗo ƙasa. Kana ita kuwa Jannart wani irin masifeffen karkarwa jikinta keyi. Yayinda kuma gaba ɗaya hankalinta kecan baya. Sabida masifar tsoron Yah Junaid da ta tabbatar muddin ya ganta sai ya kusan kasheta. Haka yasa gaba ɗaya ma hankalinta baya kanshi, bare taga ta'adin da ta aikata mishi. Tangal-tangal tayi lokacin daya yarfa hannun nata, da sauri ta dafe ginin gefenta tare da gyara tsayuwarta, cikin rashin sa'a ta sauƙe ƙafarta ta hagu kan glasss ɗin fuskar wayar tashi, da tsinin takalminta mai masifar ƙarfi. Saurin yin ƙasa da kansa yayi, sakamakon jin ƙaran sautin fashewar glass din wayarsa, wanda take dauke da screen mai tsada. Idonshi ya rumtse da ƙarfi. Yana mai jin tamkar ya shaƙe wuyanta sai tayi sanyi. Sam Ba ɗaruruwan kudin wayar yake tunawa ba, muhimman abubuwansa dake cikin wayar yake tunawa wanda yasan tabbas zai iya rasa wani abun. Ita kuwa Jannart da sauri ta sunkuyo jin ta taka wani abu kuma tsantsi ya ɗebi ƙafarta. Da sauri ta janye ƙafar tata cikin wani akasin kuma, ta sauƙe tsinin takalmin nata, kan tattausan ƙafarsa dake cikin tattausan takalmin fata, dai-dai kan farcen babbar yatsarshi ta kafa tsinin takalmin tare da sake iya nauyi ta. "Auchhhhhh!!". Ya sake wani irin sauti tare da rumtse idanunshi da ƙarfi, hade kuma da taune lips ɗin shi na kasa dake ta zogi tun buge shi da tayi. Ƙara rumtse idanunshi yayi sabida wani irin, masifeffen azaba da yaji tun daga tsakiyar kanshi har cikin ƙoƙon ranshi, kana ya iso kan babbar yatsar tashi. Da sauri ta kuma janye ƙafarta, tare dayin baya kaɗan tana mai wai-wayen bayanta, alamun sam hankalinta baya gabanta sai baya. Wani irin kallo ya zubawa tarin ɓarnar da tayi mishi,a lokaci ɗaya ta lalata mishi abubuwa da yawa, har lfyarshi bai tsiraba Ta nuƙurƙusashi tamkar wanda yayi karo da tirela. Wani irin nannauyan numfashin ta sauƙe ganin Salman ne ke biye da ita a bayan yana ce mata ke ɗin. Da sauri Salman ya iso garesu. Ganin yadda suke tsaye cirko-cirko. Rayyern ya kalla cikin nitsuwa, tare da fahimtar karo sukayi, cikin sauri yace. "Innalillahi karo kukayi, bawan Allah kayi haƙuri." Ya ƙare mgnar yana sunkuyawa files din ya fara tattarewa, yana mai cewa. "Subahanallahi, wayarka duk ta dare, Jannart garin ya akayi haka". Ita dai Jannart sai numfashin tsoro take sauƙewa, ta gaza cewa komai sabida ganin wani irin mugun masifeffen kallon da yake watsa mata, sai yanzu idonta ya kai ga ta'adin da tayi mishi. Da sauri tayi ƙasa da kanta dan bata da jarumtar da zata iya jurar kallon nan daga kwayar fitinennun idanunshi. Yatsun ƙafarshi ta tsurawa ido ganin yadda suke tsuma alamun tsananin azaba, ga kuma jini da take tsastsafowa. Dib-dab-dib-dab haka taji zuciyarta na bugawa a 170. Salman kuwa cikin yanayin damuwa ya miƙowa Dr Rayyern Mai-nasara Takardun da wayar cikin yanayin jin ba daɗi yace. "Dan Allah da Manzonsa kayi haƙuri bawan Allah". Idonshi ya rumtse da ƙarfi tare da miƙa hannunsa ya amshi takardun da wayar. Sabida Salman ya gama dashi, tunda yace. "Dan Allah da Manzonsa yayi haƙuri, to ya zame masa wajibi kuma dole yayi haƙuri sabida wannan shine mafi ƙololuwar al'farmar da mutun zai nema a wurin musulmi yayi mishi, wannan shine kalaman da Abban sa ke cemasa a mafi akasarin lokuta. Amman badon haka ba yaso ya yarfawa wannan birkitacciyar yarinyar mari ɗaya rak, taji salon yadda tafin shi yake, so yayi ya yarfa mata mari da hannun hagunshi wanda yasan tabbas sai ta saki fitsari sabida ya lura bata iya bada haƙuri ba, kuma bata da nitsuwa. Wani irin juyowa yayi ya watsa mata wani irin kallo da fuska a murtuƙe, "Mchewwwww ". Yaja mata wani irin tsaki tare da yin kwaffa kana ya juya yayi gaba ba tare da yayiwa Salman mgn ba. Cikin kaɗuwa Salman yace. "Jannart ya akayi haka, kinga asarar da kikayi mishi kuwa, nasan tabbas duk yadda akayi kece da laifin karon tunda kin hango mala'ikan ɗaukan ranki, kina gudu kina rawan jiki kina wai-waye kinzo kin mishi ta'adi. Kin kuma san kuɗin wayar nan da kika fasa mishi sarai amman ko a jikinki. Sannan kin tsaya kinyi shiru, wannan wanne irin tsorone kijeyiwa Junaid?” Ajiyan zuciya mai nauyi ta sauƙe, tare da lumshe idanunta a hankali cikin nutsuwarta da ta fara dawowa tace. “Allah ya bashi haƙuri, wlh Salman na rasa ta ina zan fara bashi haƙuri ne, kagafa wani irin kallon da yakemin tamkar zai shaƙeni ya kasheni, tsoronshi naji. Sannan kuma duk tsorona kada Yah Junaid ya ganni, wlh in ya ganni a nan kuma bance zanzo nanba bisa aikina sai ya kusan kasheni, duk allurarsa ta sojoji a kaina zai direta." Cikin takaici Salman yace. "Shike nan ai mun rasa damar farko, dan yanzu dai da wuya in Dr.Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara bai wuceba tun tuni, matsalar ba sanin fuskarsa akayi ba bare ace da mun ganshi zamu ganeshi. Dama dole bincike zamuyi da numbers din motocinsa, da aka bamu zamu ganeshi mubi bayanshi muga gidansu. Kinga har lau dai tsoron Junaid yana hanaki nasara. Har nima ta shafeni." Cikin takaici tace. "Toh ya zanyi?". Kwaɓe fuskarsa yayi tare da juyawa yayi baya. Itama kuwa juyawa tayi tabi bayanshi. Riyyam-nsra kuwa, ɓat RAYYERN da Usman PA suka ɓacewa ganinsa. Gaba ɗaya ya gama zagaye wurin babu su ba dalilin su. Wani irin masifeffen kuka yakeji tun daga can ƙasan maƙoshi sa yana taso mishi. Saboda lokaci daya yaga samu ya kuma ga rashi. Kana layinshi bazaiyi aiki a nanba bare ya kira Mammy ya sanar mata halin da yake ciki. Hakan yasa yake jin wani irin ƙuncin rai. Gefe ya koma ya zauna bisa kujera, tare da maida kanshi ya jingine yana mai jin wasu irin zafafan hawaye na tsastsafo mishi. Da sauri Salman ya nunawa Jannart Riyyam-nsra tare da cewa. “Ikon Allah Jannart ga mutuminki". Juyowa sukayi suna kallonshi. Shidinma kuwa Idanunshi da sukayi ja ya buɗe yana kallonsu. A hankali Jannart tace. "Kai ba shi bane, sai dai ko ƙaninshi". Da sauri Riyyam-nsra ya miƙe tsaye tare da rataya jakarshi bisa kafaɗa. "Assalamu alaikum". Yace yana miƙawa Salman hannu. "Wa alaikassalam". Yace tare da bashi hannu. Sukayi musabiha, cikin sanyi Jannart tace. "Ayyah dan Allah ka cewa yayanka yayi haƙuri, ban sani bane". Cikin fahimtar cewa. Rayyern suka gani suke cewa yayanshi, ya ɗanyi murmushi cikin hikima yace. "Ta ina kuka haɗu ina yake. Ni ya ɓace min ne nasan kuma shima ni yake nema yanzu". Da sauri Salman yace. "Ikon Allah ta nan yayi, to amman ba zuwa za'ayi a ɗaukeku ba". Da sauri ya nufi inda Salman ya nuna mishi yana mai cewa. "Dan Allah kuzo ku nuna min inda yayin". Cikin nitsuwarta tace. "Wani aiki mukazo yi nan Airport ɗin kai dai kawai kayi nan ɗin zaka ganshi." Salman ne ya ɗan harareta irin hararar da har yau bata gano manufarsaba, Bayan Riyyam-nsra yabi tare da cewa. "Na nawa kuma aikin yau dai ai mun rasa damar sai dai mubi mataki na gaba, kuma dan Allah fa yace so muje mu nuna mishi." Dole tabi bayansu. Gaba ɗaya harabar wurin Airport parking din babushi babu alamarsa. Kana sun dudduba gefe-gefen duk bashi, cike da gajiya da son komawa gida Jannart tace. "Kai to ka tare taxi mana ya kaika gida". Dafa motarsu yayi tare da kwaɓe fuskarsa kana yace. "Ai baƙone ni, mu baƙine daga Ethiopia, wani aikine Hamma na yazo yi, shine mukazo tare". “Toh ka kirashi a waya mana". Cewar Salman. Dafe kai yayi tare da cewa. "Toh ai dole sai na sai layin nan ƙasar taku nasa. Shiru sukayi baki ɗayansu, Can dai Jannart tace. "Toh yanzu ya zakayi". Cikin danne tarin damuwarsa yace. "Ku taimaka ku kaini na sayi layi. Sannan sai in nemi masauƙi". Haka kuwa akayi Salman ya amince bayan sun kaishi, ya sayi sim card layin Mtn, yayi register. Tuni lokacin biyar ta gota, A hankali suka fito bakin shagon. Cikin kula da alamun kallon akwai inda Salman ya sanshi yace. "Toh ƙanina yanzu ina zakaje ne?". Jingina kansa yayi da jikin motar kasan cewar, CRV ce tanada tudu. Idonsa ya lumshe tare da fara wassafo dajar shigar dake jikin Rayyern. Kama daga Suit ɗinsa agogon hannunsa takalmansa zoben yatsarsa, uwa uba wayarsa. Da kuma irin takardun da yaga yana ciccikewa da matsayin inda suka zauna. Cikin sauƙe numfashi ya ɗago kansa tare da gamsuwa da tunaninsa yace. "Ku taimaka ku kaini hotel mai kyau, wanda yake anguwar manyan mutane. In na isa na samu layi na ya hau zanyi mishi text ta Email ɗinsa". Da sauri Jannart tace. “Toh ni dai Salman ka medani kafin ka kaishi." Murmushi Salman yayi tare da cewa. "Toh ai sai mun wuce ta inda yake so ɗin ba yace unguwar manya ba, mu kaishi hotels ɗin Nasarawa GRA kawai". Juyowa tayi ta kalleshi kana tace. “Uhum kafa san abubuwan wuraren tsada garesu ko, sannan kai kana ma da kuɗin ƙasar nanne?." Murmushi Riyyam-nsra yayi tare da cewa. "Yess ina dasu, nayi canji tun a ƙasata, kuma in ma bazasu isaba ai zasu amshi transfer ko?." Kai ta gyaɗa mishi tana kallon tarin kamanninsa da wanda tayi karo dashi. Bayan sun shiga motar ne. Baba Ado yaja. Salman na gaba kusa da Baba Ado shi kuma yana gefenta. Cikin hausarsa da bata isasshen inganci yace. "Hotel mai kyaufa". Gyara zama Salman yayi tare da cewa. "Kada ka damu. *Nasarawa GRA* itace unguwar da ta tara kaf manyan masu kudi na Kano,babu wani babban mai kudi ko ɗan siyasa na Kano da ya isa yake ji da kansa dama sauran jahohi da basu da gida a. Nasarawa GRA hatta Government House ma anan yake. Sannan a cikin GRA din akwai manyan layuka da sunayensu *Lamiɗo Creasend* da kuma *Ahmadu Bello way* da kuma sauran ƙana nan layuka. Kana akwai manyan Hotel's din da suke Nassara GRA akwai *Tahir Guest Palace* da kuma *Ni'ima Hotel* da *Green Park* da *Liyafa Hotel* duk wadannan suna cikin Nasarawa GRA ne, kuma manya ne sosai ana ji da su suna da tsada da kuma kyau da inganci, zaka samu duk abinda kakeso a ciki. Yanzu sai ka zaɓi wanne zan kaika, kaga dare ya fara yi mana." Numfashin ya ɗan sauke cikin jin daɗi da gamsuwa da bayanin unguwar da suka shigo ɗin, daga shiga unguwar kasan ta manya ce. "Muje Taheer Guest palace hotel". Riyyam-nsra ya faɗi yana kallon gefen titin garin. “To Alhamdulillah gashi ma mun kusa. ”Salman yace yana mai karya kwanan shiga layin da hotel ɗin yake. Suna shiga bayan yayi parking, Suka sallameshi suka tafi. Salman na cewa. "To sai zuwa gobe zan kiraka in sha Allah inji ko ka gane ya'yan naka. Tunda na amshi number taka ta ƙasarmu". Toh yace tare dayi musu godiya. Suna fita Suka nufi ma'aikatar su ta Arewa 24. Tafiya ce mai ɗan tazara tsakani. Hakane yasa Baba Ado yake gudu. Mintuna kaɗan suka isa. Suna isa suka samu su Sunday a tsaye ƙiƙam to babu salla bare salati sai tsaron Jannart in wata tayi a biyasu makudan kud’in, da su kansu har yau basu gano manufar tsaron da ake bata, fiye da shi kanshi Alhaji Idi Sale Dakata'n ba, ko kanshi bai bawa wannan tsaron ba haka babban ɗan sa dasu Abdul, to ko dan ita macece shiyasa. Cikin hikima Baba Ado yayi parking jikin motarsu. Kana suka fita suka shiga cikin ma'aikatan jim kaɗan Jannart ta fito. Suna ganin ta fito suka mara mata baya. Tana shiga mota Baba Ado yaja. Kana yaja suma sauran suka bishi a baya ganin. Yaja ɗin. *Dr Rayyern* Wani Irin karkarwa ƙafarsa keyi, sosai yatsar ke fidda jini. A haka ya tsaida ɗan taxi ya shiga, ba tare da yace komaiba, mai taxi ɗin yaja. Bayan sun fita Airport ɗin sun miƙa hanyar cikin gari. Kanshi ya jingina da jikin kujerar, wani irin masifeffen zafi yakeji zufa na tsastsafo mishi tako ina, sabida zogin da yatsarsa keyi, ga lips ɗinsa dake raɗaɗi kana ga zuciyarsa dake tafarfasa. Sosai mai taxi ɗin ya dai-dai ta motar tasa bisa titi, a hankali yace. "Sir ina muka nufa?". Shiru yayi tamkar bai jishi ba sabida zogin fashewan farcenshi da yatsarsa su suka buwayeshi. Sai da ya kuma tambaya kana cikin taune lips ɗinsa yace. "Nassarawa GRA". Toh yace kana yaci gaba da driving. Tabbas da AC cikin motar amman bai gamsar dashi haka yasa yaketa haɗa zufa. Suna shiga cikin tsakiyar anguwar Driver'n ya kuma juyowa ya ɗan kalleshi a hankali yace. "Sir ta ina zamu ɓullo?". A takaice yace. "Ahmadu Bello way". To ya Kuma cewa kana sukaci gaba da tafi kan kyakkyawan titin mai faɗi da wadatan tsabta. Tafiya yakeyi a hankali. Yanayi yana ɗan kallon tabka-tabkan gidajen dake shumfud’e na gani na faɗa tamkar abirnin India. "Kayi hannun dama". Dr Rayyern Mai-nasara ya faɗa mishi a hankali. To yace tare da ratsa wa damanshi. Wow yace lokacin da suka fito kan ɗan madaidacin titin, da wani irin tamfatsetsen gida mai tsananin kyau na al'farma yake forkon layin. “Yayi tsaya a nan". ya kuma tsinkayo muryar Dr.Rayyern. Juyowa yayi ya kalleshi kana ya juyo ya kalli tamfatsetsen gidan, na al'farmar da in ya kintata nanne gidansu. Cikin ransa yake tasbihi ga Allah. Tare da juyowa ya kalli shi kana a mutunce yace. "Mai gida in shigar da kai ciki mana, naga tun kan ka shiga yatsarka na zubda jini". Wani irin taɓe fuskarsa yayi,a rayuwarsa babu abinda ya tsana sama da haka, mutun ya shiga harkar sa, sam shi a tsarinsa babu ruwansa da shiga sabgar da bata shafeshi ba, sai dai kuma yana matuƙar son tausayawa sabida shi mai tausayine. Cikin dakekkiyar murya yace. "No ba matsala. Bani da canji ko zaka bani Account number ɗinka inyi maka transfer'n in ba matsala?". Da sauri mai taxi yace. "Okay Sir". Kana ya fara karanto mishi ac no ɗin. Wata ƙaramar waya ya zaro a al'jihun rigarsa ta ɗaya gefen. Ya ɗan lallatsa jim kaɗan ya medata al'jihun. Cikin tsananin jin daɗi mai taxi ya kalli text ɗin Alert daya shigo masa na dubu ashirin. Cikin jin daɗi yace. "Ngd matuƙa Allah ya ƙara buɗi ya jiƙan iyaye". "Amin". Yace kana ya sako ƙafarsa waje, a hankali ya takata. "Shehyytt". Ya ɗan fidda sautin sabida ƙafar tayi tsami, tuni yatsar ta kumbura. Bayan ya fito ne kuma mai taxi ɗin yaja motar ya tafi. Shi kuwa Rayyern a hankali tare da d’an ɗingisa ƙafar tasa ya nufi bakin kekyawan gate ɗin. Kan yatsarsa manuniya yasa ya ɗan ƙonƙosa jikin ƙofar. Da sauri wani kekyawan buzu dake zaune bakin ƙofar ya miƙe tsaye, tare da zuwa ya ɗan tura wani abu, kana ya leƙa da ido ɗaya. Da sauri ya meda abin ya rufe tare da sakin murmushi cikin tsananin jin daɗi ya ja ƙofar ya buɗe yana mai cewa. "Masha Allah, Dr. ya dawo". Da sauri wani kekyawan matashi dake fitowa daga can cikin gidan cikin ya nufi baki gate ɗin cike da farin ciki. Yana cewa. "Alhamdulillah, Abba! Abba!!! Mamy ga Hamma Rayyern ya iso". Ya ƙare mgnar yana mai rungume Dr Rayyern da ya shigo. Yayinda wasu mutanen suka taso da sauri suka iso garesu. "Dakta Barka da isowa lfy". Shine abinda suke haɗa baki wurin faɗa da alamun shaƙuwa da so. Duk da alamun akwai driver' a ciki da kuma mai bawa fulawa ruwa sai kuma mai wankinsu da guga, Sai Baba Mauɗo wannan buzun da alamun mai gadinsu ne, shi. Wani ɗan guntun murmushi yayi tare dasa hannunshi ya shafa kan wannan kekyawan matashi daya amshi takardun hannunshi yace. “I miss you so much my Ramadan". Kana ya bawa Baba Mauɗo hannu cikin kulawa da girmamawa tare dasu Ari sukayi musabaha. Anutse yayi gaba Ramadan na biye dashi a baya. Yayinda Su kuma suka koma wurin aikinsu, suna me farin cikin dawowar Dakta wanda yayi kusan mako huɗu baya nan. Suna ratsa farfajiyar gidan da a ƙalla zai ɗauki motoci 7 zuwa 9 kuma ko wacce bazata matsi ko gogi ƴar uwarta ba. Gaba ɗaya gidan zagaye yake da dogayen bishiyoyin na mijin gwanda, sai sirran Ayaba dake ƙasansu a jere da ƴan guntayen dabino. Kana daga can baya kuma wani ɗan ma dai-dai-cin Garden ne mai masifar kyau, wanda yake cike da itatuwa da tsirrai masu sanyi da ƙamshi. Kana daga farfajiyar gidan akwai wani baranda mai kyau da faɗi, wanda yake da steps. Ata ƙasanshi gefen bishiyoyin an jera fararen kujerun silver hakama a ciki. Kana tura ƙofar zaka riski wani hamshaƙin falo mai ɗan karen girma, Dan fadi da girmawa kuwa AC ma biyu ne aciki. Ta gefen hagun falon gab da bakin ƙofar shigowa kuwa, wani ɗan madaidacin Bathroom ne. Sai kuma gefen hagu, wani corridor ne mai fadi. Kana shiga wurin zaka ga steps ɗin hawa sama masu faɗi. Can gefen Bathroom din kuma ta gaba, wani kekkyawan Dinning area ne mai dauke da table mai kujeru takwas, sai wani Fridge mai suffar show glass Wanda ke cike maƙil da kayan sha. Sai gefenshi kaɗan washing hand baby ne. Kana ta kanshi ƙofar kitchine ne mai girma, wanda yake ƙawace da Kitchen cabinets and drawers masu masifar kyau, komai na ciki blue color and white ne. Daga cikin kitchen din kuma ƙofar store ne. Daga cikin store kuma akwai ƙofar baya, inda wasu igiyoyin shanya ke jere da kuma inda suke ajiye kamarsu dankali, doya, al'basa, da dai ire irensu. Daga Kitchine din kuwa akwai wata ƙofar da zata ratsa ta cikin wani corridor, mai ɗauke da ɗan madaidacin falo mai 3 Bedroom,s and bathrooms. Sai ɗan Dinning area ƙarami. Can gefen dama kuwa inda benen yake, kana hawa sama kan steps din, kana iya hango cikin falon ƙasa. Tafiya kaɗan zakayi ka riski wani babban falo mai masifar kyau da tsaruwa. Can gefe kuma wani kekkyawan Dinning table ne shirye cikin Dinning area mai sarƙafe da labule mai zirin-zirin igiyoyin dake sarƙafe da duwatsu masu daraja sheƙin Diamond. Kana sai wani Fridge shima kamar show glass kana gefenshi kuma Show glass ɗinne mai shirye da cups, plates, spoons, mug's da dai sauransu. Sai Kitchen dake gefe da store kamar na falon ƙasa. Kana sai Bedroom guda biyu, wanda basa kusa da juna dan a tsakanin su Dinning area da kitchen da store suke. Akwai wata baranda mai kyau ta bayan ɗaya Bedroom ɗin inda nanne ɗakin Dr.Rayyern ɗayan kuma na Ramadan. Ƙasan benen kuma akwai wata ƙofar wanda kana shiga zaka samu wani side ne kuma irin na saman sak, koman su iri ɗaya. Sai can gefen kitchin ɗin falon ƙasan kuma akwai wani kofa wanda room and parlour ne mai kyau da Bathroom a ciki. Daga gefe kuma can akwai ɗaki ɗaya inda masu aiki zata iya zama, amman bbu mai aikin a gidan. Can waje kuma akwai BQ, Boys Quaters. Gefen BQ ɗin kuma wani part ne mai kyau matsakaici a rufe yake su kansu Dr Rayyern da Ramadan Basu san menene a cikin wannan Part ɗin ba. Tsarin gidan dai masha ALLAH. Bisa wannan babban baranda mai steps biyar zuwa shida suka hau. Kana suka buɗe kofar babban falon. Ramadan na mai kiran Abba! Abba!! Yana buɗe kofar suka hango Abba da Mamy, suna sauƙowa daga steps ɗin Dinning area, Wanda ta nan zasu fito side ɗinsu. Wani kyakkyawan mutum ne mai matsakaicin shekaru, mai jini a jiki da tarin cikar haiba da kamala. Ganin Rayyern dinne kuma yasa shi sakin wani irin yalwataccen murmushi, tare da buɗe hannayenshi dake cikin gariyar jikinsa. Da sauri Dr Rayyern ya ƙarasa gabansa. Rungumeshi yayi tsam a jikinsa tare da sauƙe ajiyan zuciya. Mamy kuwa gefe ta zauna bisa kujera ta ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya, cikin haiba da tarin son ɗan nata tace. “Babana wato Abba kawai kayi missing ko". Da sauri ya saki Abba yana murmushi mai cike da farin cikin ganinsu yace. "Na isa Mamy, bakiji me bahaushe yace ba." Da sauri tace. "Me yace". Ta ƙare mgnar tana yiwa Abba kallon tsokana. Matsowa yayi kusa da ita, hannunta ya kamo ya ɗaura tsakiyar kanshi tare da yin ƙasa da murya yace. “Uwa mafi uba koda uban sarki ne". Dariya mai cike da so tayi mishi. Abba kuwa gefenta ya zauna tare da tsareshi da ido. Ƙeyarshi ya ɗan sosa cikin sanyi yace. “Abba bani ne na faɗa bafa, Malam bahaushe ne ya faɗa". Ramadan ne yayi murmushi yana mai jin daɗin, yaga Hamman nashi yana gaban iyayensu, dan nanne kaɗai zakaga fara'arsa ka kuma ji yayi doguwar mgn Especially in da Abba ne. A hankali ya zauna gaban Abban nasu, tare da miƙar da ƙafarsa dake masifar mishi zogi. Ita kuwa Mamy Dinning area ta nufa. Plate ta ɗauƙa cikin show glass din, kana ta buɗe Fridge. Chocolates da sweet ta cika cikin plate ɗin. Kana ɗayan kuma tasa Apple da inibi. sai kuma goran ruwa da cup a ɗaya ta shiryasu, bisa tray'n kana ta nufo falon. Da sauri Ramadan ya matso kusa dashi, tare da zubawa ƙafarsa ido cikin mmki yace. "Innalillahi Hamma Rayyern meya samu ƙafarka?” A hankali ya miƙar da ƙafar tare da motsa ta. Da sauri Mamy ta ƙasaro, Abba kuwa sunkuyowa yayi ya kama ƙafar cikin tashin hankali, ganin yadda yatsar ta haye ta kumbura ga jini har yanzu zuba yakeyi. "Rayyern, meya sameka? Meya faru?". Yayi tambayar a rikice. Kanshi ya ɗan sunkuyar ya kalli ƙafar tasa, kana a hankali yace. "Wata mahaukaciya ce ta takani". Yayi mgnar cikin salonsa na rashin iya ƙarya. "Wacece ita a ina kuka haɗu?". Abba ya kuma tambaya. "Ban santaba, just kawai dai I know mental problem ce, kuma a Airport muka hadu.” Ya bashi amsa, adan takai ce yana mai cije labb’ansa, wanda kuma hakan alamace dake nuna cewar kafar tanayi mishi zafi sosae. Ramadan kuwa da sauri ya miƙe, ɗakinsa ya haura da sassarfa, dan ƙaramin akwatin taimakon gaggawa na likitoci ya ɗauko. Yana sauƙowa ya zauna daɓas a gaban Dr.Rayyern ɗin, kamo ƙafar yayi tare da fara bashi taimakon gaggawa dan jinin ya tsaya. Cikin mmki Ramadan yace. "Sorry Hamma har nail dinka ya fashe, amma Mahaukaciya a airport how? then why akabarta ta shiga airport din?” “Uhmmm” yace dan azaban zafin da yakeji. Da sauri suka ɗago kansu baki ɗayansu. Shi Dr.Rayyern TV dake like jikin ginin ya zubawa idanu. Tamkar zai mannasu jikin fuskar kekyawan Dattijon nan Malam Mai-nasara da aka hasko a tashar Sunnah TV. Ahankali ya janye ƙafarsa daga riƙon da Ramadan yayi mishi. Tare da juyawa ya maida hankalinshi ga TV, yayinda shima Ramadan hakan yayi. Abba da Mamy kuwa idanu suka zubawa Rayyern ɗin. Wani irin kallo Abba yakeyi mishi mai cike da ma'anoni. Cikin haɗe fuska yace. "Kai Ramadan tashi ka kashe tv’n nan". Juyawa sukayi baki ɗayansu suna kallonshi. Fuskarshi dake haɗe ne yasa Rayyern yin ƙasa da kanshi, cikin sassayan sauti murya can ƙasa yace. “Please Abba kayi haƙuri wa'azinshi nada daɗi". Cikin tsawa yace. "Ramadan kashe min TV nan". Da sauri Ramadan ya miƙe jiki na rawa ya kashe TV’n. Shi kuwa Rayyern cikin wani irin rauni da biyayya, ga mahaifin nashi da bin umarnin shi da neman izininshi yace. “Abba kayi haƙuri". Fuska a haɗe yace. "Ramadan zokayi mishi aikin daya dace. To yace kana yazo ya wonke mishi yatsar yayi mishi dreesing ɗin wurin da duk abinda ya kamata. Yana gamawa magriba nayi. Dole suka miƙe sukayi al'wala kana suka nufi masallaci. Jannart kuwa. A hankali ta kutsa kanta cikin falon nasu. Tazo tsakiyar falon kekan tayi kiciɓis da...! In sha Allah zuwa dare in na samu caji zakuga PAGE 6. Littafin TUBALI na kuɗine . By *GARKUWAR FULANI* 11/15/21, 7:19 PM - Auntyna: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *TUBALI* PAGE 4 NA *AYSHA ALIYU GARKUWA* ASSALAMU ALAIKUM, Masoyana ma karantan littattafaina, ina mai farin cikin sanar daku, yau d’in nan MON, 18 OCT 2021 za'a fara biyan kud’in samun damar karanta littafin TUBALI akan farashi mai sauk’i Biya 500 k’aramin farashin na k’aramin group, kana sai *Special people Group* akan farashi mai sauk’i 1k kacal babban group a yawan posting babancinsu yake, zaku biya ta asusuna. ACCOUNT NO 0661110170. BANK NAME: AISHA ALIYU GARKUWA BANK GTBank sai ki turo min shaidar biyanki ta wannan numben tawa da nakeyin whatsApp da ita 09097853276. *PLS TAKE NOTE BAND VTU* kada kiyi min VTU ko transfer'n katin ta wannan numben etisalat d’in idan kuwa kikayi wlh babu ruwana dan na fad’i miki. Please and please in dai da hali kada ki turo min katin, kiyi min transfer'n ruwan kud’i ta bank account na, in kuma babu dama to sayi katin MTN sai ki copy number's ɗin katin ki turo min ta whatsApp. Gareku mutanen jamhuriyar Niger ku tuntub’i Mommy akan layinta +22790899076, ta wurinta zaku biya, hoton katin zaku d’auka ku tura mata ta wannan numben a whatsApp, Special people group 1k ne (1000) k’aramin group kuma (500) kacal, Please dan Allah babbar macece mai yara da tarin jikoki da y’ay’an jikoki mu kyautata lafazi da mu'amala gareta dan Allah don in ka girmama iyayen wasu wasu zasu girmama naki🙏🏻... Littafin TUBALI littafine na musamman mai salo na musamman mai cike da abubuwa masu tarin yawa. *Tausayi, Sark’ak’iya, jan hankali, Fadakarwa, Nishad’antarwa, ilimantarwa, al'ajabi, Sa'ar rayuwa, riƙon amana, cin amana, ribar kyautatawa, kana da sassayar soya mai salon narke jiki da zuciya* Ga number wayata da nakeyin whatsApp da ita, 09097853276 idan kina son biyan kudin samun damar karanta littafin TUBALI sai ki biya ta wannan ac no din dai 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA, dan Allah ki biya kafin kiyi min mgn kina turo shaidar biyanki ina gani zan saki a group, in Kuma baki da ac no ko yanayin zaman wani k’asa ko wani luggun ki sayi katin MTN na 1k in special group kikeso ki turo min. In Kuma k’aramin Group kike so ki sayi katin *MTN ki copy number's din ki turo min ta whatsApp number'n na 09097853276 kada kiyi min VTU ko transfer'n katin 9mobile dan layin nada matsala* Za'ayi tsawon mako ɗaya ana biya ina kafin in fara update domin samun sassaucin aiyukan sauraron mutane, za'a fara biya yau *MON 18 OCT 2021. Kana zan fara posting ranar MON 25 OCT 2021 rana ita yau kenan in mai kowa mai komi ya kaimu bisa rai da lfy* 🙏🏻Na rokeki da girman zatin ubangiji in dai kin san zaki sayane dan ki fidda min littafina dan Allah ki bar kud’inki kiji tausayin marainiya, kada ku cutar da marainiyar Allah,😭🙏🏻🙏🏻🙏🏻. Nasan daga yau har zuwa na gama littafin Chart zaimin yawa zai hausawa aiyuka zasu yawaita gareni, amman babu kamar makonni ukun forko zuwa biyar, Please ina neman al'farmar uzuri in kinga kinyi min mgn ban amsa mikiba, na tuba kiyi haƙuri ba raini bane ko wulak’anci face yawan mutane wata k'il ban isa kan Chart naki bane, Amman muddin na isa na kuma bud’e na gani tabbas zan baki amsa in katine zansashi yana shiga zan saki a group in bai shiga kuma in gaya miki, in Kuma ta account kika turamin ina ganin shaidar biyanki zan saki a group, 🙏🏻Dan Allah in kinsan ba littafi ko maganin gyara namu na mata kikeso ba to kiyi haƙuri da min mgn sai na d’an samu salama🤝🏻😘🙏🏻😂. *Sayan na gari maida kuɗi gida sai kinzo* Masifeffen harbawa da babbar jijiyar bayanshi tayi, tare da bugawan ƙirji a jere-a jere, har sau uku. Rumtse idanunshi yayi da ƙarfi dan bai taɓa jin hakan ba, Wani irin tsuma fatan saman idanunshi suka farayi, kamar shi yake juya su. Kanshi ya jingina da marfin motar can ƙasan maƙoshin sa, ya fara mai-mai-ta. "Hasbunallahu wani'imanwakil, innalillahi wa innailaihi rajiun. Subahanallahi Alhamdulillah". Shiru PA yayi tare da ratsa gefe, yana mai kallonshi. Tsawon daƙiƙu 3 suka ɗauka a haka, kana ya yunƙura ya miƙe tsaye tare da ambaton sunan Allah. Bayan ya fita ne kuma PA ya maida marfin motar ya rufe. Kana Driver'n'shi da gwamnatin kasar ta bashi, da ƴan tsaron shi suka fito suka mara mishi baya. Yayinda PA dinsa ke gefenshi. Saida Suka shiga har cikin iya inda matafiya ne zasu shiga. Kana sukayi musabaha duk suka juya suka tafi. Shi kuwa da Usman PA Suka nufi cikin farfajiyar jirgin kasan cewar an fara cikiyan matafiya. A can ɗaya sashin kuwa. Riyyam-nsra ne, tsaye gaban Mammynsu. Yayinda Zayton ke manne da kanta bisa kafaɗarshi, tana rau-rau da idanu alamun zubda hawaye. Cikin yanayi na rauni da taraddadi Mammy ta kalli Riyyam-nsra cike da jaddawa ta kamo hannunsa ta riƙe da ƙarfi ido cike da hawaye tace. “Kasan manufar tafiyarka, itace burinmu da farin cikin rayuwata. Ka kuma sani ina tsoron duk abinda zai rabani da kai. Riyyam ka sani, kaine GARKUWAta nida ƴar uwarka. Lallai tabbas munada ciwo a zuciyarmu. Ina tsoron kada garin gyaran gira in rasa ido. Kada ban samu baɗiniba in rasa zahiri." Cikin ƙarfin hali da jarunta yace. "Mammy babu abinda zaki rasa, in sha Allah ƙari zaki samu. Da izinin ubangiji. Babu wani abu na duniya da zai miki hijabi da mallakinki". Cikin zubda hawaye Zayton tace. "Mammy kin ganshi ko, shi baya tsoro, kada yaje yayi abinda zamu rasashi". Hannunshi yasa ya share mata hawaye tare da cewa. "Koda zaku rasani sai kun samu madadina". Da sauri Mammy tace. "Kamin al'khairi cewa, zaka kiyaye shiga hurumin da ba naka ba, kayi iya abinda ya kaika ka dawo". Hannunshi ya ɗaura kan nata tare da cewa. "Nayi al'ƙawari Mammy na". Rungumeshi tayi shida Zayton ɗin jin anata neman matafiya". Kanshi ta shafa tare da sa mishi al'barka. Kana shi yayi ciki, su kuma sukayi baya. Yana rataye da jakarsa bisa kafaɗa, yayi matuƙar kyau cikin shigarsa ta matasan zamani. Kamanninsa da Rayyern sun ƙara bayyana matuƙa, kasan cewar irin shigar Rayyern ɗin yayi. Wayarshi ya zaro, ya fara ɗabi'ar tasu ta Tiktokers viewing ya farayi, yana jujjuyawa ƙasan jirgin. Tare da fara, mgn da Hausa. “Assalamu alaikum Al'ummar Nigeria". Sai kuma ya haura ya ajiye wayar bisa steps din marfin jirgin, kana ya dawo baya, ya fara takowa a hankali yanayi yana ɗan rawa, da tsalle. Mafi akasarin mutanen dake bayansa matasane, shiyasa suka tsaya suna murmushin calikancinsa. Yana isa gab da wayan second ɗin daya saita na video na cika. Dan haka yasa hannunshi ya ɗauki wayar kana ya kutsa kai cikin jirgin... Zaune yake bisa kujera no 23 acan sama VIP, kusa da jikin windown jirgin. Yayinda Usman ke bayanshi. Wasu files ya zaro cikin briefcase ɗinsa, tare da biro, a hankali ya sunkuya ya fara buɗe takardun, yana sa hannu a cikinsu ɗaya bayan ɗaya. Shi kuwa Riyyam-nsra tafiya yakeyi yana ɗan dudduba no ɗin kujerun. Yana isa kusa da Rayyern ya tsaya tare da cewa. "Yesss! Kunga ga maƙocina, sarkin aiki har a jirgima aiki yakeyi". Bai ɗagoba kuma baici gaba da rubutun da yakeyi ba sai ƙirjinsa dake bugawa. Jakarsa ya zare a kafaɗarsa ya sakata a mazaunin ta. Wanda haka yasa saida ya matso kusa da Rayyern. Yatsun sawun yaron ya zubawa ido cike da mamakin ganin yatsun iri ɗaya sak da nashi yatsun Har nails dinsu. Da sauri ya ɗan ware idanunshi. Ganin wani ɗan ɗigon tawadan Allah kan tsakiyar farcen babbar yatsar Riyyam-nsra. A hankali ya ɗan motsa kafafunshi dan sai yaga kamar ƙafarsa ce. Shi kuwa Riyyam-nsra zama yayi bisa kujerar dake manne data Rayyern, tare da sauƙe numfashi kana ya lumshe idanunshi saboda wani irin masifeffen bugu da zuciyarsa keyi. Yayinda gaba ɗaya cikin jirgin kuma kowa ya zauna mazauninsa. Tsit kowa ya nitsu. A hankali Riyyam-nsra ya buɗe kwayar idanunshi sabida, Jin alamun an rufe marfin jirgin kana jirgin ya fara ƙugin tashi. Shi kuwa Rayyern har yanzu idonshi na kan kyawawan sawun Riyyam-nsra. A hankali Riyyam-nsra ɗin ya juyo ya kalli gefen da Rayyern ɗin yake. Da sauri ya ɗan sunkuyo da kanshi ganin inda Rayyern ya fuskanta. Janye sawunshi yayi tare da cewa. "Salamu alaikum". Da sauri Rayyern ya juyo sabida muryar yaron sak muryar ƙaninsa Ramadan. Yana juyowa shima Riyyam-nsra yana juyowa ya fuskanceshi. Wani irin zabura Riyyam-nsra yayi tare da zazzaro idanunshi waje, kana ya yunƙuro zai tashi. Da sauri ma'aikaciyar jirgin dake bayanshi ta nufoshi da sauri tana cewa. "Hey Are you okay? please sit down!!” Ta ƙare mgnar da ɗan sauti sabida lokacin jirgin, yake raba tayoyin shi na gaba da ƙasa, anfi buƙatar kowa a zaune. Shi kuwa Riyyam-nsra wani irin masifeffen kaɗuwa al'ajabi mmki da tu'jjudine suka rufeshi, gaba ɗaya jikinshi rawayake. Cikin buɗe baki ya nuna Rayyern da yatsarshi manuniya kana ya nuna kanshi. Da sauri ma'aikaciyar ta sake cewa. "Please I say sit down!." Jin hakanne da kuma ganin yanda yake baya baya. Yasa ya koma bisa kujerar ya zauna. Cikin kaɗuwa da wani irin fuska mai cike da mmki yace. "Tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai, daya haliccemu da kamanni iri ɗaya." Shiru Rayyern yayi yana mai kallonshi da gefen ido. Bai iya shiga sabgar da ba ta saba, a rayuwarsa baya taɓa sa kansa a lamarin da bai shafeshi ba. Da sauri ya juyo jin Riyyam-nsra na cewa. "Ina ma Mammy na ta ganka. Allah mai iko. Inama ace jirgin nan bai tashi ba, da na roƙeka da girman Allah da Manzonsa muje Mammy na taga mai tsananin kama dani." Sai kuma ya kalli sajen Rayyern cikin tsananin farin ciki, so, ƙauna, bege, yace. "In sha Allah nima daga yau zan fara tara saje irin naka". Sai kuma ya matso kusa da Rayyern tare da dago wayarshi. A hankali Rayyern ya ɗan juyo kwayar idanunshi kan fuskarshi ganin alamun zai manna kanshi bisa kafaɗarsa. Fuskarshi ya tsuke tare da tsareshi da ido. Da sauri ya kwaɓe fuska tare da karkata kai cikin turo baki yace. "Na tuba". Sai ya ganshi lammanim ƙaninsa Ramadan sak da yayi haka, dan haka Ramadan kanyi mishi duk sanda ya tsareshi da ido. Ido ya ɗan zubawa lips ɗin shi yana cewa. "Please kayi haƙuri hoto zamuyi zan nunawa Mammyna ne, zata so ganinka". Ya juyo da nufin zaice a a. Kawai sai yaji Riyyam-nsra ya ronƙofo kanshi da kyau. Ya manna kansa bisa kafadarsa. Yana murmushi yayi musu selfie. Sai ya zama suna kallon juna. Kafaɗarshi ya ɗan manna da nashi dan jin bugun zuciyarsu ya dai-dai-ta yana harbawa a tare a tare, dib-dib. Sai kuma ya zuba mishi ido ganin ya taso ya zauna ya juyo ya fuskanceshi da kyau. Hannunshi ya miƙa mishi tare da sallama. Dole ya bashi hannu ya kuma amsa sallama tunda horaswar Musulunci ne. “Sunana Zakariyya amman Riyyam-nsra nakeso a kirani, ni ɗan ƙasar Ethiopia nanne, ban taɓa zuwa Nigeria'n ba sai yau. Dalilin abokina Nasiru Ahmad zanje. Kai kuma fa?". Fuska ya kuma kwaɓewa ganin ya janye hannunsa bai kuma ce mishi komai ba. Cikin yanayin shagwaɓa yace. "Please dan Allah gaya min". A nitse ya juyo ya kalli yaron da yakeji. Sonshi da ƙaunarshi na ratsa mishi jinin jiki da zuciya, haka nan yaji wani aminci na musamman a kan yaron. Cikin tattausan muryar da irinta yakewa Ramadan mgn yace. “Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara". Ruggumeshi Riyyam-nsra yayi tare da cewa. "Nice name. Please Zan iya ce maka Yaya?” Kai ya jujjuya mishi alamun a a. Da sauri yayi rau-rau da idanunshi tare da cewa. "Dan Allah fa, to me zan ce maka". A taƙaice yace. "Hamma Rayyern". Wani irin murmushin jin daɗi yayi tare da cewa. "Hamma Rayyern". Sai kuma ya gyara riƙon da yayiwa wayarsa da tun tuni yake musu video. Kusan a tare suka sauƙe ajiyan zuciya lokaci da jirgin ya gama ɗagawa, yayi sama ya rabu da ƙasar Ethiopia. A hankali ya ɗan juyar da kanshi kana yaci gaba da aikin da yakeyi. Da sauri ya kuma kalli Riyyam-nsra da ma'aikaciyar jirgin nan tazo tana ce mishi lfy kuwa, ɗazu yake ta rawan jiki ta ƙare mgnar cikin yanayin saninsa da son suyi hoto tare. Murmushi yayi tare da nuna mata Rayyern kana yayi ƙasa da murya yace. "Yayana ne zai zaneni wai na cika surutu". Murmushi tayi tare da kallon fuskar Rayyern kana tace. "Ka cika rawar kai, ba kamar yayanka ba." Sai kuma ta ɗan kalli Rayyern tare da cewa. "Sir a rinƙa yi mishi faɗa yaron nan baya jin mgn a TIKTOK". Kai ya gyaɗa mata ba tare da ya kalleta ba. Hoto sukayi da Riyyam-nsra kana tayi gaba. Usman PA kuwa yana can baya. A hankali jirginsu yayi ta keta gajumare, yana ratsa sararin samaniya. Tafiya ta nisa kowa sabgogin gabansa yakeyi. Amman banda Riyyam-nsra gaba ɗaya ya shigewa Rayyern shigewa mai tarin yawa. Ya kuma kasa yakice yaron. Duk yadda yayi sai yake jin zuciyarsa mai raunice a kan yaron. Wani irin son yaron yakeji har cikin ƙahon zuciyarshi. Ga mamakinsa ko yanayin cimar da suka fiso iri ɗaya ne. Domin tunda Riyyam-nsra ya shigo bakinsa bai zauna banza ba, sweet da chocolate ya cisu iri daban-daban. Ya lura yaron bakinsa bai zama shiru. Hoto kuwa yayi musu sunfi hamsin video kuwa sun kai goma. Haka sukaci gaba da keta hazo... A nan gida Nigeria kuwa gidan Alhaji Idi Saleh Dakata. A hankali Jannart ta fara motsi, alamun farkawa daga baccin da allurar ya sa tayi na tsawon. Awanni biyu da rabi. A hankali ta fara motsa fatar idanunta da sukayi mata nauyi. Dai-dai lokacin kuma Barrister ya turo ƙofar ɗakin tare da sallama. A hankali Mom dake zaune gefenta ta amsa mishi. "Wa alaikassalam, Barrister ka dawo". Cikin kula ya gyaɗa mata kai tare da ƙarasowa bakin gado. Ido suka zuba mata cikin tausayawa, ganin hawayen dake bin gefen idanunta suna sauƙa har cikin kunnenta. A hankali Mom tasa tafin hannunta ta fara share mata hawayen. Ba tare kuma da ta buɗe kwayar idanun nata ba, ta fara sakin Shessheƙan kuka. Zama Barrister yayi a bakin gadon, tare da kamo hannunta ya riƙe, cike da tausasawa da kulawa yace. "Sorry Jannart kiyi haƙuri ki dena, kuka dukkan abinda yayi tsananin zaiyi sauƙi". Jin muryar ƙanin mahaifin nata, mafi kulawa a gareta ne. Yasa ta buɗe Idanunta, tare da yunƙurawa, zata tashi zaune. Da sauri Mom ta tallabota, ta zauna tare da jingina bayanta jikin allon gadon. Gyara zama Barrister yayi tare da kallon Mom yace. "Mom Abdul a kawo mata wani abu ta ɗan ci". Da sauri Mom ta miƙe tare da cewa. "Toh". Ta nufi hanyar fita cike da kekyawar niya da zuciya. Shi kuwa Barrister ajiyan zuciya mai nauyi ya sauƙe tare da juyowa ya kalli Jannart data gaza tsaida hawayenta. Murya can ƙasan maƙoshi ta fara mgn. “Abba ƙirjina yana ciwo! Kaina yana bugawa, tunani ya hanani samun sauƙi, na gaza gano Yah Junaid wanne irin ɗan uwane a duniyar nan. Anya kuwa Abba Yah Junaid yana da cikekken hankali da sanin haramcin babban fasadin da yake son ai katawa gareni." Sai kuma hawaye shar-shar, suka soma zubo mata ta kasa ƙara sa mgnar. Shi kuwa Barrister cikin tsananin tashin hankali da kaɗuwa da firgici mai birkita tunanin iyaye na gari yace. “Me kike nufi Jannart wanne irin fasadi kuma?". Murya na rawa ta kalleshi cikin rauni tace. "Abba Yah Junaid fa fyaɗe yake son yamin, a lokuta ma banbanta, yana ƙudirin yi min Fyaɗe, idan na ƙi amince mishi ne, yake yunƙurin kasheni. Abba cewa yakeyi fa zai kasheni in ban amince da shiba. Ya kuma ce muddin na gayawa wani zai kasheni. Wlh Abba zai kasheni. Abba ya zanyi? Ina zan shiga a rayuwata in samu sauƙi, Ɗan Allah Abba ka rabani da gidan nan in ba haka ba Yah Junaid zai kasheni kuma Daddy ba zai hanashi ba". Ta ƙare mgnar cikin tashin hankali. Da ya ta azzara nitsuwar Barrister Kabir saleh Dakata. Wata iriyar fitinenneyar zufa ce mai zafi ta soma tsastsafo mishi. Cikin tuno abubuwa da dama na rayuwar duniya, ya kamo hannunta tare da fuskantar ta da kyau kana yace. "Jannart! Jannart!! Jannart!!!". Ya kirata sau uku duk da amsa mishi da takeyi. Cikin yin ƙasa da murya yace. “In sha Allah, Junaid bazai kashe kiba, da izinin ubangiji sai kin rayu, rayuwa mai Al'barka domin ke ayace, kuma izinace sannan taƙin shaida mai ƙarfi". Hannunta ya kuma riƙewa cikin irin sona uba da ɗiyarsa yace. “Jannart zaki rayu cikin aminci. Domin Ubangijin daya raya Annabi Musa acikin gidan Fir'auna cikin lfy da aminci. Shiya rayaki a gidan nan cikin lafiya da aminci. Ya rigada lokacin ya ƙurewa Magautan, bazasuyi nasaraba, dan sunyi nasararsu tun shekarun baya sun gama nasara, yanzu nasarar tamu ce. Gsky zatayi halinta, in sha Allah zanci gaba da zame miki jigo. Kuma zan nema miki GARKUWA, cikin gaggawa kafin su juyo garemu". Shiru tayi tana jin kalaman ƙanin mahaifin nata, sai dai ta kasa sama musu mizanin da zata aunasu ta ajiyesu ta fahimci manufarsu. Gogewar hausarta batayi surfin ta Ƙanin mahaifin nataba. Cikin ruɗanin da kalamanshi suka saka mata tace. "Abba ni na gaji da zaman gidan nan, dan Allah ka sake roƙon Daddy ya bakani ko zai yarda, in koma gidanka." Cikin sauƙe nannauyan numfashi yace. "Jannart sake roƙar tashi tamkar wasa da rayuwarki ne, kamar dai kusanto da a ...". Da sauri ya haɗiye ragowar mgnar sanin ƙwaƙwalwarta bazata fahimci zancen nasa ba. Ita kuwa cikin sanyi ta zuba mishi ido. Dai-dai lokacin kuma Mom ta shigo da tray a hannunta, cup ɗin tea ne mai kauri, sai soyayyan irish da ƙwai. Cikin nitsuwa tace. "Abba to..". Hannu ya ɗan ɗaga mata tare da cewa. "Ya isa da yamma zan dawo muyi mgn Jannart kada ki kuma yin kuka". Ya ƙare mgnar yana miƙewa tsaye. Kai kawai ta gyaɗa mishi kana ta bishi da ido har ya fita. Bayan ya fita Bathroom ta shiga, ruwa ta ɗan watsa, bayan tayi brosh kana ta fito. Ba laifi ta ji sauƙin sosai numfashin ta ya dai-dai-ta. Tea ɗin kawai ta iya sha. Kana ta koma ta kwanta dan Alllurar bata ida saketa ba. Can cikin bacci taji wayarta na suwa. "Mahmoud". Tace tare da amsa kiran. Nan yake shaida mata cewa. Dr Rayyern Mai-nasara yana hanyar dawowa Nigeria tun safe jirginsu ya taso. Zuwa azahar zasu sauƙa Abuja. Kuma yau ɗin zasu shigo Kano cikin alamun bacci tace. “Toh ya akayi kuma lbrin ya sauya Mahmoud ba sai jibi ba kace?” Gyara zamanshi yayi tare da cewa. "Uhumm kin kuwa san waye Dr Rayyern, mutun yana nan tamkar Wahainiya gane shirinsa ko manufarsa fa wuyane dashi. Ke dai in kin samu dama kiyi ƙoƙarin zuwa Airport da yamma wata ƙil a dace, zan turo miki hotuna Yah Usman PA Yayan Abokina Deen wanda yayisu a bayan motocin Dr Rayyern ɗin so sai ki ɗauki number's ɗin motocin ta wannan hanyar zaki iya samun damar bibiyarsa". Cikin sanyi tace. "Toh Ngd matuƙa". Daga nan sukayi sallama. Salman ta kira yana ɗagawa yace. "Ya jikin namu?". Cikin sanyi tace. "Da sauƙi waya gaya maka?". “A'isha Lawal ce ta gaya min tace ɗazu data kira Mom ce ta ɗaga wai jikinki ya tashi." Ayyah tace a taƙaice kana ta mishi bayanin da Mahmoud ya mata ta ƙara da cewa. "Ka shirya da yamma muje Airport ɗin bari in turoma hotunan". Toh yace kana sukayi sallama. Ƙarfe biyu dai-dai jirginsu ya sauƙa cikin international Airport Abuja. Bayan wasu ƴan daƙiƙu, aka fara fitowa. Mutun kusan 21 suka fito. Kana Rayyern ya sako ƙafarsa ta dama kan matakalan forko. Wani irin sassanyan numfashi ya shaƙa a hankali tare da zuƙan iskar ƙasarshi abin sonshi da al'faharin shi. A hankali ya fara takowa yana sauƙa cikin haiba. Da sauri ya ratayo jakarsa a kafaɗa tare da biyoshi a baya da gudu. Usman kuwa shima jakarsu ya ratoyo kana ya biyoshi a baya. da sauri ya matsoshi. Juyowa yayi jin an riƙe mishi hannun damanshi. "Hamma Rayyern daga nan wanne state ɗin zaka tafi". Ya rasa gane meyasa zuciyarsa ke bawa yaron amanna ko dan kamar da sukeyi ne. Sam bai shiryawa amsa mishi ba kawai yaji lips ɗinshi sun furta. "Kano". Wani irin tsalle yayi tare da cewa. "Yesssss! Nima Kano zan tafi ai". Cike da mamaki Usman ya nufosu har yana tuntube tare da cewa. "Sir wannan fa?". Juyowa yayi ya kalli Usman da salon. Baya son shisshigi. Shi kuwa Riyyam-nsra da sauri ya dawo kusa da Usman hannu ya bashi tare da cewa. "Ni ƙaninsa ne". Baki buɗe Usman ya bishi da ido. Daga nan masallacin cikin Airport ɗin suka wuce, ganin azahar tayi har lokacin yaso zarcewa. Suna idar da salla Usman ya miƙe da nufin fita ya samo abinci. Dan yasan ubangidan nasan bazai buƙaci abinci yanzuba. Juyowa yayi ya ɗan kalli Riyyam-nsra tare da cewa. "Bishi kuje Restaurant". Kai ya jujjuya tare da cewa. "Bana jin yunwa". Kai kawai ya gyaɗa mishi. Nan suka zauna har la'asar tayi. Bayan an idar da sallane kuma, suka koma ciki. Domin shiga jirgin da zai wuce Kano. Ƙarfe huɗu da rabi dai-dai jirginsu ya tashi daga birnin tarayyar Nigeria zuwa Kano ta dabo tumbin giwa. A nan cikin Kano kuwa. Jannart ce zaune cikin motar, Salman kana shi kuma yana gaba gefe. Baba Ado dake jansu. Yayinda sauran garadan dake tsaronta, suke hangame da baƙi a zatonsu tana can cikin ma'aikatar nasu, dan sam basu lura da lokacin da ta fitoba, koda yake Salman ne ya bawa Baba Ado key kana ya jawo motar har zuwa bakin mashigansu ya kawo mishi. Shiyasa suka fita, basu ganeba. Kai tsaye filin jirgin sama na malam Aminu Kano suka nufa. Sosai kuwa Jannart tayi kyau acikin shigar pallazo da kuma tight shirt din dake jikinta, wanda ya bayyana lafaffen cikinta, kasancewar kuma rigar nata na d’an bayyana nipples dinta ne, yasa ta daura wata Navy blue fashion top akan shigar ta ta, wanda tsawonsa ya kawo har guiwanta, Yayinda ak’afanta take sanye da wani navy blue hill shoe, na company’n gucci mai kyau da tsada da uban tsini, akanta kuwa wani had’add’en medium vail ne wanda ya sauko harkan kirjinta. Sam akan fuskarta babu wani kwalliya sosai, saidai kuma hakan bai hana zallar kyawun fuskarta bayyana ba, Yayinda small lips dinta suka sha peach lipstick, acikin jikinta kuwa wani sassanyan k’amshi ne yake tashi. Suna shiga cikin Airport ɗin sukayi paking a Airport parking. Kana suka wuce suka nufi cikin. Bayan isarsu da kamar 5 minute, jirginsu Rayyern yayi sauƙar angulu. Bayan yan daƙiƙu ne kuma matafinyan suka fara fitowa. Da sauri Usman ya matso kusa da uban gidan nashi, cikin yin ƙasa da murya yace. “Sir in kira driver?” Shiru yayi ganin ya ɗan kaɗa mishi yatsarshi manuniya. Shi kuwa Riyyam-nsra da sassarfa yake biye da Usman a baya. A haka har suka fito asalin filin da matafiya kan zauna su jira masu tarbarsu. Kanshi ya ɗan ɗago ya kalli taron mutanen, yatsarshi yasa ya ɗan gyara zaman farin glass ɗin dake idonshi. Gefen lips ɗinshi na ƙasa ya ɗan kamo ya ɗan tauna a hankali. Da sauri kuma ya ɗan juyo ya kalli bayanshi. Inda ya hango Riyyam-nsra can baya yana ɗan tahowa yana waige waige a alamun shi yake nema. Gabanshi ya nunawa Usman tare da yin mgna can ƙasa. "Ƴan jarida ne, zanbi nan, in sun tsareka kaji dasu." Yana faɗin haka, ya ratsa yabi yar siririyar hanyar dake gefen damanshi. Shi kuwa Usman ya nufi hanyar fitan. Jannart kuwa da sauri cikin tsananin razana ta koma bayan Salman tare da yin ƙasa da kanta murya can ƙasa tace. "Innalillahi Salman gacan Hakim abokin Yah Junaid idan ya ganni zai gaya mishi." Sai kuma ta zaro ido jikin tashin hankali ta dafe kirjinta tare da cewa. "Na shiga ukuna tare suke da Yah Junaidu ma gashi can bayanshi". Da sauri Salman ya ɗan kalli gabanshi kana ya juyo. Gaba ɗaya jikinta rawa yakeyi sabida hango Hakim Da Junaidu sun nufosu gadan-gadan. Jujjuyawa tayi. Ganin wata ƴar siririyar hanyar ne gefen hagunta, wacce nan Rayyern yabiyo. Da sauri ta sunkuyar da kanta ta ratsa cikin ƴar hanyar ta ɓacewa ganin su. Nannauyar ajiyar zuciya mai ƙarfi ta sauƙe, tare da ci gaba da tafiya cikin yar siriyar kusurwar. Tana tafiya tana wai-waye da juyawa tana kallon bayanta. Shi kuwa Rayyern, cikin ɗan sassarfa yake tafiya. Saboda so yake kafinma Usman da Riyyam-nsra su fito, ya shiga taxi ya tafi. Tafiya yake yana dai-dai-ta kan files da takardun da yayi ta aikin rattaɓa musu hannu a cikin jirgi. Haka yasa bai lura da gabansa. Ita kuwa Jannart tafiya take tana wai-waye shiyasa bata ganin gabanta. Jin kamar takun wani a bayanta ne kamar ana boyota, kuma yasa ta ƙara saurinta. Dai-dai lokacin kuwa Rayyern ya iso gab da ita. Jin ana ce. Ke! Ke!! Yasa ta juya da nufin zata arta da gudu. Sai kawai ta jita jikin mutum sunyi karo. Goshinta ya bugi gemunshi da azaban ƙarfi. Take files da Takardun hannunshi suka watse. Yayinda ita kuma tayi tangal-tangal ta koma baya zata faɗi ƙasa, da sauri ta rumtse idanunta tare da sakin sauti mai cike da tsoro, hade kuma dasa hannunta da nufin dafe ginin dake wajen, dan kare kanta daga faɗuwa ƙasa. Kawai sai ta kamo kwalan rigarshi ta gefe ta cikin da kuma Suit ɗin dake saman da ƙarfi. Pet-pet haka boturan jikin rigar duk suka ɓalle, kab suka watso ƙasa, hakan yasa gaba ɗaya rigunan jikinshi suka buɗe. Cikin wani irin masifeffen takaici yasa hannunshi ya fisge hannunta dake shaƙe da gefen kwalar rigarshi. Ya yarfa hannun tare da zuba mata wani irin masifeffen....! Kuyi hakuri rashin jina da wuri. Rayyern da ban Riyyam-nsra da ban ai sunayenma ba iri ɗaya bako. Free PAGE ne wannan. By *GARKUWAR FULANI* 11/15/21, 7:20 PM - Auntyna: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *TUBALI* PAGE 6 NA *AYSHA ALIYU GARKUWA* *FREE PAGE ne* *Littafin TUBALI na kuɗine ki biya ki darinki biyar kacal in saki a ƙaramin group wanda bonus ne ga dana na, dan in na gama ya zama Complete 1k ne, saukine yanzu ga Masoyana, asalin kuɗi nai 1k ne, Special Group kuma su post nasu zaifi yawa. 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU, sai ki turo shaidar biyanki ta whatsApp 09097853276. Kada ki bari garabasar ta wuceki, kice sai an gama, Hajia in kuma kinada zakuwa da turo 1k a saukake cikin makonni bibbiyu zamuke gama part-part* Fawal beauty parlor sunai muku albashir da bude gidan Mata wato kigyara da kanki👩🏻‍🦰 da cewa suna gabatar da aiki na zamani kamar su gyaran jiki, spa kenan gyaran fuska wato facial,gyaran Kai, hair style , gyaran kafa pedicure,gyaran hannaye, manicure kitso,lalle ja da bakki,ba'a barsu abayaba suna saida kayan gyaran aure, turaruka,man shafawa, suna kwalliya wato makeup,turaren wuta, humrah,kulaccham dama abunda Baku sanshiba wato maida tsohuwa yarinya akankanin lokaci😄iya kudinka iya shagalinka💃kudai ku hanzarta zuwa ga wannan gida na mata zallah (FAWaL BEAUTY PARLOR) Address: Main gate na fire service jimeta, opp sixty plaza. kada kubari abaku labari😍 munai muku maraba a koda yaushe Mata yan kwalisa mace sai da gyara , yar uwa bora ba sunanki kizama mowar mai🏨 da taimakon FAWAL BEAUTY PARLOR 👩🏻‍🦰da kudinki qalilan kifita sab abunki ki baza kamci mai kama jiki. Gamai buka contact CEO FAWaL BEAUTY PARLOR kan 09033901035 or 08078809930 sai kunzo, our time services from 8:am to 7pm, Monday to Saturday/ Sunday 10am to 6pm🪞🎁🛒🛍️🤝🏻 Da Yah Junaid, wani irin masifeffen tsorone ya rufeta wanda yasa ta fara ja da baya. "Dan ubanki sai yanzu kika dawo? Ina kikaje kika tsaya? Tukun nama ƙarfe nawa ne ƙa'idar tashi aikinki?" Ƙara matsota yayi tare da buga mata tsawa. "Shegiya ƴar iska badake nake mgn bane kina jina kinyi shiruba". Cikin rawan murya tace. "Uh uhm dama gidan Baba Kabir nake". Ta ƙare mgnar tana komawa gefen Mom da yanzu ta iso. Cikin haɗe fuska tace. "Yarinyar nanfa ba isasshen lfy ne da itaba". Juya kai yayi ya watsa mata wani irin masifeffen kallo tare da cewa. "Toh uwar shisshigi". A hatsale Mom tace. "Toh ubana, anyi Shisshigin aikin banza". Ta ƙare mgnar da kama hannun Jannart sukayi ciki. Shi kuwa kwaffa yayi tare da bin bayan Abdul da yazo ya wuce su, bai ce musu ko ƙalaba. Riyyam-nsra ne kwance bisa tattausan gadon ɗakin hotel ɗin daya kama. Tuni yasa sim card ɗin sa na Mtn har ya zauna ras a wayar. Kana yasa katin daya saya tun wurin sayan layin. Mgn yakeyi da Mammy. Yana mata bayanin haɗuwarsa da mutumin nan da suke kama. Harma da haɗuwarsu da su Salman, kana ya ƙara da cewa. "Mammy al'ummar Nigeria suna da kirki, suna da mutunci da mutunta baƙo, naga karamcinsu tun a cikin jirgi. Mammy ina son su ina son ƙasar." Cikin sauƙe numfashi tace. "Yesssss! Riyyam akwai masu kirki, da amana da kawaici. Amman kuma akwai maha'inta azzalumai macuta, ka kula da kanka kayi taka tsantsan." Cikin gamsuwa yace. "Toh Mammy in sha Allah zan kula". Daga nan ta bawa Zayton sukayi ta hira yana mai gaya mata yadda ƙasar take. Zaune suke a falon gidan Dr Lukman. Cikin tawagarsu ta gamayyar kamfanonin jihar da kuma likitoci. Dr Lukman keyi musu bayanin cewa. "Dr Rayyern Mai-nasara ya dawo a yammacin yau, kuma Alhamdulillah dama akwai taron da gwamnatin jiha zatayi damu likitoci a gobe da safe, shine babban dalilin dawowarsa. Toh muna tashi a taron zanyi ƙoƙarin tahowa dashi campany'n Alhaji Idi Sale Dakata, muyi taron jan ra'ayin nashi a can". Cikin gamsuwa sukace eh hakan yayi. Kana sukaci gaba da tattaunawar. Ab’angaren Dr Rayyern Mai-nasara kuwa, kusan atare suka shigo cikin gidan shida Abba da kuma Ramadan, wanda yanzunne dawowansu daga masallaci, domin koda suka yi sallah’n magriba basu fito daga cikin masallacin ba, har saida aka sallame salla’n Isha. Kaitsaye cikin babban falon gidan suka nufa, Yayinda zuciyar kowannensu ke cike da sanyi da kuma salama, musamman ga yanda iska mai dadi ke kad’awa tana ratsa kowani hudan gashi na jikin d’an Adam mai rai. Haka suka shigo falon Abba na gaba, sai Rayyern dake take masa baya, wanda yayi na k’arshen shigowa kuwa shine Ramadan, wanda yake d’an shafa screen d’in wayar dake rike a hannunsa. Ganin shigowarsu ne kuma yasa Mamy dake, tsaye agaban had’add’en dining table d’insu wanda aka k’awatasa da wasu fitinannun royal chairs, ta saki sassanyar murmushin dake bayyana tsananin k’aunarta ga ahalin nata, murya asake tace. “Masha Allah! Our dinner is ready.” Jin hakan da sukayi dinne kuma yasa kasu sakin murmushi, tare da wuce wa dining area din kai tsaye. Ramadan kuwa kulolin da Mamy ta miƙo kishi ya amsa dasu plate and spoos da gorunan ruwa mai sanyi. Kana ya juya ya fita, dan kaiwa su Baba Mauɗo nasu abincin cikin kamala da mutuntaka ya kai musu kana ya dawo. Shikuwa Rayyern da tun fitowarsu daga masallaci, yake tasbihi acikin zuciyarsa, kaitsaye gaban had’add’en fridge’n mai kaman show glass d’in dake dining area din ya nufa, yana isa kuwa ya bud’e murfin fridge’n, tare da d’ansa kansa ya zaro babban ledan chocolate na diary milk , wanda ya d’au sanyi sosai. Maida murfin fridge’n yayi ya rufe, tare da juyowa ya zauna akan d’aya daga cikin kujerun dining table d’in, wanda aka cika saman babban table d’in, da kayan cima kala kala, more especially fruits. Ahankali ya b’are ledan, tare da kai chocolate d’in bakinsa. Fitinannun idanunsa masu d’auke da long eye lashes ya lumshe, adaidai lokacin da yaji d’and’ano da kuma zak’in chocolate din ya mamaye harshen sa, wanda hakan yasa shi sake tura chocolate din abakinsa, tare da soma taunawa ahankali, yana maijin wani irin sanyi aransa, Tabbas aduk sanda yake cin abunda yakeso, yakanji wani irin gamsuwa na musamman, musamman madai duk wani abu mai zak’i, kwarai yanason zak’i sosai da sosai. Abba da Mamy dake zaune kuwa idanunsu kawai suka zuba masa, musamman ma Abba da bayajin dad’in, yawan shan zak’in da Rayyern d’in keyi, always shan zak’i sai kace karamin yaro. Shikuwa Rayyern da har yanzu idanunsa ke lumshe, hakanan yaji ajikinsa cewa akwai k’wayoyin idanun dake kansa, wanda hakan yasa ahankali yad’an ware oily eyes d’insa, masu matuk’ar kyau da daukar hankali. Karab sukayi ido hudu da Abba, hakanne kuwa yasa shi d’an gyara zamansa, tare kuma da yin k’asa da kansa, saboda acikin 2 second din ya fahimci wani irin kallo Abban, nasa keyi masa. Zare chocolate din dake bakinnasa yayi, tare da ajiyewa agefe. Ganin hakanne kuma yasa Mamy da Ramadan yin murmushi, shikuwa Abba plate d’in dake dauke da crispy microwave Patatoe chips, and salad, da kuma onion sauce ya turowa Rayyern d’in gabansa. Tare da cewa. “Maza kacinye wannan.” Plate din da Abban nasa ya turo masa ya kalla, tare da d’an zaro idanunsa, kana lokaci guda kuma ya sanja mood dinsa izuwa shagwab’a, akasalance cikin kuma muryarsa da bakowa kejinta ba yace. “Abba duka wannan zan ci?.” “Eh duka kuma yanzu nakeson kaci.” Abba ya fad’a cikin tsare gida. Ahankali ya saukar da idanunsa k’asa, saboda yanda yaji tone din Abban nasu, yasan abun is seriously. D’aukan plate d’in abincin yayi tare da fork ahankali, yakai abincin bakinsa bayan yayi bismillah. Bai kuwa wani ci abincin sosai ba, ya d’ago kansa ya kalli Mamy dake cin abincinta itama. Cikin muryarsa dake bayyana rashin sabonsa dayin magana mai yawa yace. “Please Mamy na k’oshi da abincin nan ki bani tea.” D’agowa Abba yayi ya kalleshi, still kuma cikin tsare gida yace. “A’a fa yau sai kacinye abincin nan tas, saboda haka babu wani tea din da za’a baka.” Maraitattun idanunsa yad’an lumshe, cikin kuma yanayin dake bayyana tsananin biyayyarsa ga mahaifinnasa yace. “To Abba amma dan Allah abani tea sai in had’a, na tabbata abincin zaifi shiga...” Yanayin yanda ya k’are maganar yana karyar da wuyansa gefe ne, yasa Abban sakin murmushi, cike da k’aunar d’an nasa yace. “Shikenan to na yarda ka had’a da tea d’in.” Jin haka yasa Mamy tashi ta soma kokarin had’a masa tea, kamar yanda ya buk’ata. Shikuwa Murmushin jin dad’i yayi, saboda dama shi yafison ko yaya idan zaici abinci, ya zamana yana mixing abincin da abu mai zak’i, gashi kuma dama shi. Sam baya da yawan cin abinci, sometimes idan yaci chocolate d’insa ya d’aura da bootle water, yakanji sa dai-dai. Had’a masa tea d’in acikin mug Mamy tayi ta mik’o masa, koda ya karb’a bai wuce 3 sipping yayi ba, ya d’ago kansa ahankali ya kalleta. Cikin yanayi da salon maganarsa yace. “Ayyah Mamyna sugar baiji ba dai, please ki karamin.” Idanu Mamy tad’an zaro cikin yanayin mamaki tace. “Rayyern Shugar 3spoon amma kace baiyi maka ba, kai dai kam shan zak’i ya zama maka jiki.” Ta kare maganar tana mai k’ara masa Shugar one spoon acikin tea d’in. Murmushi kawai yayi, batare daya kuma cewa komai ba, ya maida kansa ya cigaba da sipping tea din, sai time to time yake daukan patatoe daya yakai bakinsa, nan ma kuma gudun kada Abba yayi masa fad’a ne. Saida yasha kusan rabin tea d’in, kafin ya d’ago da kansa ahankali ya kalli Ramadan dake cin abinci. “Ramadan ya hospital d’in, ina fatan komai yana tafiya dai-dai ko?.” Ramadan kuwa Jin abunda Hamman nashi ya tambaya ne, yasa shi dakatawa da cin abincin, tare da cewa. “Alhamdulillah Hamma Rayyern komai yana tafiya yanda ya kamata, bayan wannan tafiyar taka ma Ya Sulaiman yana zuwa, tare mukeyin duk wasu abubuwan da suka dace.” Idanunsa ya d’an lumshe ahankali tare da jinjina kansa, Tabbas dama yasan koda bayanan, Sulaiman da Ramadan zasu gudanar da komai yanda ya kamata kana ga sauran Doctor's ɗin, kasancewar dukansu Doctors ne way’anda suka san aikinsu, kuma kowannensu da irin k’warewarsa. Hiran hospital d’in da kuma irin manya manyan ayyukan da sukayi, alokacin da bayanan Ramadan d’in ya shiga yi masa. Yayinda shi kuwa ahankali yake d’an jinjina kansa, alaman gamsuwa, saboda zuwa yanzu bakinsa ya dan fara gajiya da motsawa. Abba da tun d’azun ya kafesu da idanu baya ko k’yaftawa, murmushi ne kawai ke bayyane akan fuskarsa. Yayinda yake yiwa yaran nasa, wani irin kallo mai d’auke da tsananin k’auna had’i da soyayya, Tabbas yanaji aransa cewa yaransa GARKUWA ne, sannan koda bayan ransa da izinin Ubangiji, Zasu ƙarasa ginin TUBALI’n da aka fara ginasa zasu karasa ida ginasa da yardar Allah, akullum a kuma koda yaushe yana alfahari dasu, Tabbas ako ina zaiyi al'faharin cewa. Yay’an nasa jajirtattune kuma masu k’wazo, Lallai watarana Tabbas zasu cimmawa abunda suke so yana jin gamsuwa mai tarin yawa na riƙo da amarsu da Allah ya bashi da basu gamsasshiyar tarbiya. Jin da yayi hirar tasu ta tsaya ne kuma, yasashi Kallon Rayyern tare da cewa. “Rayyan ya tafiyar taka? Ina fata ansamu abunda akeso ko!?.” Kai Rayyern d’in ya jinjina tare da bud’e bakinsa anutse yace. “Alhamdulillah Abba, duk wani abu da muke nema na samu, dama kayan amfanin companies dinmu ne naje sayawo, to kuma ba abunda ban samu ba, nayi ordering Insha Allah kuma soon zasu sauk’a nan Nigeria.” Kai Abban ya jinjina cike da gamsuwa, kana yace. “To kaida kaje US kuma sai gaka a ethiopia’n harda karb’an wani kambun karramawa.” Murmushin daya bayyana fararen haƙoransa yayi, cikin kuma sakewa da mahaifinnasa yace. “To Abba ai acikin Airport na hadu da yarannasu harna taimaka musu, shine fahimtar likitane Ni yasa dole aka wuce dani k’asarsu, Jin dadin ceton ahlin masu muƙamin ƙasar ne yasa sukamin wannan karramawar.” “Masha Allah Allah Ubangiji yaci gaba da taimakawa.” Abba da Mamy suka had’a baki wajen fad’ar hakan. Ramadan kuwa daya kammala cin abincinsa, mik’ewa tsaye yayi tare da d’aukan wayarsa dake kan table d’in, cikin kuma yanayin nuna kulawa ga Hamman nasa yace. “Yauwa Hamma Rayyern bari na amso maka maganin rage zogin ciwo acikin pharmacy d’inmu.” Kai kawai Rayyern din ya jinjina, Yayinda shi kuma Ramadan yasa kai ya fice daga cikin falon. Koda ya fito daga cikin gidan nasu direct Mai-Nasara’s Pharmacy Nig LTD ya nufa, kasancewar kuma pharmacy din bashi da wani nisa da gidansu, hakan yasa bai wani b’ata lokaci ba ya dawo. Shida kansa ya d’auko bottle water marar sanyi, tare da b’are maganin ya bawa Hamman nasa yasha. Bayan Rayyern din yasha maganin ne kuma, ya mik’e tsaye ahankali tare da kallon su Abban nasa, aladabce yace . “Abba ni zanje na kwanta, dan inajin gajiya sosai ajikina.” Kai Abba ya jinjina masa tare da cewa. “To Allah ya tashemu lafiya.” Da “Ameen.” Ya amsa kafun yayiwa Mamy da Ramadan saida safe, kana kaitsaye ya nufi sashinsa, da k’ofar shiga cikinta ke Cikin babban falon a nitse yake tattaki bisa steps ɗin haurawa saman. Ahankali ya murd’a handle d’in had’add’Iyar k’ofar, tare da tura kansa ciki. Wani irin sassanyan k’amshin room freshener daya shak’ane kuma yasashi lumshe idanunsa, wanda suke d’auke da wani yanayi na musamman. Tabbas shi mutum ne maitsanin son k’amshi, wannan yasa aduk sanda yaji k’amshi sai zuciyarsa tayi sanyi. Ahankali ya bud’e idanun nasa, tare da soma bin kekyawan falon da kyawunsa ya zarce tunanin mutum da kallo. Duk da kuwa cewar babu yawan tarkace acikin falon, amma yanayin tsarin falon da kuma kayan dake cikinsa, na millions din kud’i ne ya ƙawatashi. Domin kuwa acikin falon wasu irin had’add’un Roma complete sofa’s ne masu masifar kyau da tsada, wanda sukayiwa tsakiyar falon k’awanya, Yayinda aka cika samansu da wasu irin trow pillows new design, babban abu mafi d’aukar hankali ajikin sofas din kuwa shine, yanda aka k’awata su da wani irin abu mai kaman royal glasses, da kuma ado na musamman, kasantuwar design din Golding ash ne kuma, yasa har wani d’auke ido adon sofas d’in keyi. Yayinda daga k’asan sofas din kuwa aka shumfud’e wani had’add’en Ash colour Austin carpet, mai tsananin taushi da laushi, domin kuwa saboda tsabar laushin carpet d’in, har k’afan mutum kan iya nutsewa idan ya taka. Yayinda aka d’aura wani had’add’en glass Roma table akan tsakiyar carpet d’in, wanda kuma shine ya k’ara k’awata kyau da had’uwar falon, musamman wasu beautiful roses masu kalan gold da aka d’aura asamansa. Acan b’angaren dama kuwa, wani irin makeken tv plasma ne black na companyn Samsung mai matuk’ar kyau da tsada, saboda tsabar girman TV din kuwa, ba a iya mannashi a bango ba, kan wani had’add’en Royal tv stand aka ajiyesa, daga gefe da gefensa kuwa aka zuba wasu glass roses masu kyau da tsada, wanda da zaran dare ya rufa suda kansu, suke bada deference colours na light. Still kuma had’add’un dark and golding ash colour, plain curtains d’in dake sak’ale jikin kowacce door da kuma windows d’in dake cikin falonne, suka k’ara bayyana had’uwar falon, domin kuwa curtains ne masu shegen tsada da aminci, wanda aka k’awata su da had’add’en decoration na d’aukar hankali, Tabbas ko daga iya curtains d’in dake cikin falon ka tsaya, kasan an kashe matuk’ar kud’i, balle kuma aje ga kwalliyar wallpaper din, da akayiwa gaba d’aya jikin bangon falon da ako ina zai amsa sunansa falo. Har lau kuma acikin falon nasa tafiya kad’an zakayi, ka iske wani had’add’en dining area’n da aka k’awatasa da decoration na classic curtains masu kalan grey, sai zazzafan Angel dining table mai d’auke da 6chairs, grey da kuma gray colours, Tabbas ko a iya wajen falon Rayyern ya amsa suna, ya kuma cika hamshak’in falon dake dauke da tsadaddun furnitures. Daga gefen dining area din kuwa wata koface, wanda da’alama kuma nanne kitchine d’insa. Sai kuma wasu kofofi guda biyu dake cikin falon, 2 bedrooms wanda kitchen and dining area ke tsakiyarsu. Sassanyar ajiyar zuciya ya sauk’e a dai-dai lokacin da ya gama, k’arewa had’add’en falonnasa kallo, komai nead babu wani alama ma dake nuna cewar, yakai 4 to 5 weeks baya cikin dakin, kasancewar duk kwanan duniya Ramadan na shigowa yana gyara duk abunda ya d’anyi kura. Rigar suit d’in dake jikinsa ya zare ahankali, tare da ajiyeta akan sofa, ahankali cikin takun dake bayyana gajiyarsa ya nufi d’aya, daga cikin 2 door d’innan da suke d’an nesa da juna. Sauk’e hannunsa akan k’ofar dake b’angaren dama’nsa yayi, wacce takasance itace bedroom d’insa. Koda ya tura kansa acikin dakin kuwa, wani daddad’an kamshi da kuma sanyin AC ne ya bugeshi, still ajiyar zuciya ya sake sauk’ewa, musamman da yaga yanda aka k’awata, original royal bed d’insa da soft bedsheet mai kyau. Kamar dai yanda yaga falon nasa nead, haka ma komai dake cikin dakin, babu wani abu na kushewa acikin bedroom d’in, saboda nan ma wasu royal furnitures ne aciki masu masifar kyau, tamkar dai agidan sarauta haka d’akin nasa yake, saboda komai kama daga kan bed, drawer, dressing mirror, gothic chairs duk masu kalan gold ne, sai kuma curtains din cikin dakin da suka kasance milk colour. D’an sunkuyawa yayi ahankali ya zare takalman dake k’afarsa, batare kuma daya jira komai ba, ya soma kokarin zare long sleeve din dake jikinsa, bayan ya cire rigar ne kuma, ya k’arasa gaban wani medium glass wardrobe, wanda acikinsu ne yake ajiye duk wasu abubuwan buk’atansa marassa nauyi, kama daga kan towel, bathrobe, short neakers, dadai sauransu. Wani nead bathrobe ya d’auko tare da warwarewa ya zura ajikinsa, saida ya gama daure igiyoyin bathrobe din kuma, kafun ya zare wandon suit din dake jikinsa. Kaitsaye bathroom d’insa ya wuce, Lallai ko acikin bathroom dinansa nasha kallo, domin kuwa hatta wajen da mutum zai tsaya yayi wanka na glass ne, daga cikin gurin kuma kana iya ganin komai na cikin toilet d’in, ga wani had’add’en jakuzzie mai daukar hankali wanda cikinsa, ke cike da tsabtataccen ruwa. A yanayin yanda yakejin kansa a matuk’ar gajiye ne kuma, yasa bai wani bata lokaci wajen yin wankan nasa ba, bayan ya kammala wankanne kuma ya dauro alwala, kasancewar haka ya sabarwa kansa, baya tab’a kwanciya babu alwala. Ahankali ya murda handle din bathroom din ya fito, hannunsa rik’e da wani towel, Yayinda gargasan jikinsa kuwa ke jik’e da ruwa, sunyi wani irin kwanciya lub, wanda kuma hakan shiya sake bayyana hasken fatarsa. Cikin yanayin nutsuwar daya zamar masa sabo, ya tsane duk jikinsa, tare da karasawa gaban dressing mirror ya shafa mai ajikinsa, bayan ya kammala shafa maid’inne kuma, yabi jikinsa da wani men body spray mai kamshin gaske. Yana kammala duk wani abu da zaiyi kuwa, ya k’arasa gaban wardrobe dinsa, tare da ciro wani sabon towel ya daura akan waist d’insa, yayi hakanne kuma saboda sometimes yafi jin dadin bacci, idan babu wani kaya mai nauyi ajikinsa, kamar dai towel yanajin dadin bacci da towel sosai. Numfashi ya fesar adai-dai lokacin da yayi amfani da wani remote, wajen yin off na hasken wutan dake cikin dakin. Anutse ya haura saman tattausan gadonsa, tare dakai hannunsa ya kunna two bedside lamp din dake gefen gadon. Ai kuwa yana ajiye kansa akan pillow, yaji sautin kiran waya na tashi daga gefensa, hannunsa yasa yadan dafe kansa akasalance, saboda Allah Yasani kwata kwata at this time bayason damuwa. Idan ya gaji bacci kawai yake so yayi, domin da hakanne kawai zaiji he’s okay. Kallonsa ya mayar ga inda Ramadan ya ajiye masa wayoyin nasa uku, wato samsung da kuma iphone d’insa wacce, mental problem dinnan ta dazu ta kwankwatsa masa da tsinin takalmin ta, wanda dududu yasan kudin takalmin nata bai wuce 10 to 12k ba, amma gashi tazo tayi masa asaran dubu daruruwa sai kuma yar karamar woyar. Jawo wayoyinnasa yayi ahankali tare da ture iPhone d’in gefe, ya dauk’i Samsung S21 ultra din da take ta ringing, ganin sunan Sulaiman na yawo akan screen d’in wayarne kuma, yasa shi picking call d’in. Koda ya amsa sallamar da Sulaiman din keyi masa kuwa shiru yayi, sai shi Sulaeman d’inne, daga can b’angaren yace. “Ya akayi nak’ikk’ira d’ayan layinka akashe, sai yanzu na samu wannan? Ykk fatan dai kana lapia, sarkin rainin hankali shine harda wani cemin ba yau zaka dawo ba, kai dai kam Rayyern naga randa zaka daina miskilanci.” Idanunsa ya d’an lumshe, tare da sauke ajiyar zuciya, kana agajarce yace. “What’s up ai gani nadawo ko?.” Kai Sulaiman ya girgiza domin kuwa idan da sabo ya saba da halin Rayyern Mai-nasara. “Nothing nakiraka na sanar dakai kada ka manta, gobe ne fa taron likitoti da za’ayi hope zaka je ai?.” Sulaiman ya fad’a da kulawa. “Insha Allah.” Still ya fada yana me gyara kwanciyarsa. “Okay to saida safe kurman dole, mitsss mutun baya gajiya ma da shirun.” Sulaiman ya fad’a yana me katse kiran. Rayyern kuwa ahankali ya zare wayar daga kan kunnensa, tare da fesar da wani irin numfashi. "Ashyhhhhh". wanda kuma yayi hakanne saboda zogi da yakejin yatsar k’afarsa nayi masa, duk da kuwa yasha magani, amma dai har yanzu yakanji k’afar nad’anyi masa zogi. Labb’an bakinsa ya cije da d’an k’arfi tare da rumtse idanunsa, lokaci daya ya soma tuna yanda yarinyar tayi masa babban b’arna, kuma wai dan saboda tsabar raini, ko hakuri ta kasa basa dan girman kai, sai wuki-wuki da ta soma yi masa da mayun idanunta. “Mchewww.” Yayi tsuka abayyane tare da cewa. “Da wani dan bakinta kaman na tsuntsu, dama irin wayannan ƴan yaran. Sam ba kai daya garesu ba.” Yakai karshen maganan yana sake gyara kwanciyarsa, tare da sakin kowanni irin tunani ya kama ambaton sunan Allah Acikin ransa, da haka bacci ya d’auke sa, yau ko samun daman duba system d’inshi baiyi ba. Taheer Quest Palace. Riyyam-Nsra ne kwance akan makeken bed din dake cikin d’akin hotel d’in daya kama. 12:30 am kenan amma har yanzu wayarsa kirar iphone 11pro ne ke rik’e ahannunsa, Yayinda yayi kwanciyar nan irinta rub da ciki, gaba d’aya hankali, tunani da kuma nutsuwarsa ya badasu ne ga wayar tasa, Inda yake ta receiving DM da kuma comments na mutane, akan videos d’in daya sake d’azu na shigowarsa Nigeria, inda mutane da yawa kanyi masa message akan cewar, suna matuk’ar son su had’u dashi, ciki kuwa harda y’an mata masu tambayarsa awanni masauk’i yake, domin acewarsu zasu kawo masa ziyara, burin mutane da yawa shine su had’u dashi suyi videos, wasu kuwa zallan kyawunsa ne yake rud’arsu, wanda hakan yasa suke bayyana maitarsu afili, ko kunyar kai da addininsu basaji, amatsayinsu na musulmai, kuma yaya mata, wanda kowa yasani Mace nada matuk’ar daraja, amma Ina wasu matan kam haka suke watsar da kansu kamar shara a bola. Shikuwa Riyyam nsra ayau ya sake tabbatarwa da kansa cewar, mutanen Nigeria nada matuk’ar mutumci da kuma iya karrama bak’o, sannan da yawansu suna nuna masa k’auna k’warai. Bayan ya gama amsa DM na mutane ne kuma yayi posting videos d’insa, wanda yayi musu shida Rayyern, Yayinda a k’asan videos d’in yayi godiya da irin karamcin da Rayyern d’in yayi masa, wayyo Allah ai kuwa kaman jira mutane suke, suna gama watching na videon ya fara samun new comments and DM, wanda shi kansu bazai iya amsasu duka ba, Yayinda mafi yawancin mata kuma suka sake haukacewa, nanfa kowacce ta fito ta fara maganganu kala-kala, harda masu tambayarsa wai dan Allah ko zai had’asu da kyakkyawan yayanshi. Shidai ya gani amma baiyi reply ba. Bakin shi ya dan zumbura gaba tare da cewa. “Wayyo wannan Hamma Rayyern ɗin ya kashemin kasuwa fa, ji duk an shareni sai mgnarsa ake,”. Ya kare mgnar da murmushi Ana Cikin hakanne kuma saiga k’iran Nasir Ahmad ya shigo cikin wayar tasa. Koda ya d’aga hira suka sha inda Nasir Ahmad ya dinga yi masa fadan cewa bai Kirasa ba, da kuma mai yasa zai sauka a hotel, saboda da ace yakirasa da bazai taba bari ya sauka a hotel ba. Hakuri Riyyam din ya basa, daga nan kuma suka ci gaba da hirarsu, ananne Nasir din ke tambayan a Riyyam hotel din daya sauk’a, bayan ya fad’a masa cewa a Taheer ya sauk’a ne kuma sukayi sallama, inda Nasir din ya shaida masa cewar, Gobe Insha Allah zaizo nan Taheer Guest Palace din, ya d’aukesa su tafi gidansu...! Uhummmmm, akwaifa abu a wanga littafin, fatana dai Allah ya bamu aron rai da lfy, mu gama lfy, amman kam ku shirya karatu da murmushi a fuskokinku🤝🏻🥰 By *GARKUWAR FULANI* 11/15/21, 7:20 PM - Auntyna: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *TUBALI* PAGE 7 NA *AYSHA ALIYU GARKUWA* *FREE PAGE ne* *TUBALI littafine na kuɗi, ki biya sannan in saki a Group inda zanke posting, biya 500 in saki a ƙaramin group, ko kuma ki biya 1k Hajia in saki a special Group kisha karatu cike da shaukin da salama hajiata, turo kuɗin ta asusuna na GTBank 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU, sai ki turo min shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276, in kuma babu damar turawa ta banki zaki iya sayan katin mtn ki copy number's ɗin katin ki turo min ta whatsApp na 09097853276* Ahmad na kashe wayartasa kuwa shima ya kashe data d’insa, saboda zuwa yanzu bacci sosai yakeji. Duk da cewar yana iya kaiwa har 2:00 am a online, amma dai yau kam yayi tafiya ya gaji sosai, dole yana buk’atar bacci. Cikin abunda bai wuce 10mn ba kuwa bacci mai nauyi da gajiya ya d’aukesa. Washegari. Ajere suka dawo daga sallan asuba, Abba da Baba Mauɗo suna gaba kana su kuma suna biye dasu da Ari da Hadi. Su a farfajiyar gidan suka tsaya wurin aiyu kansu. Inda su kuma kaitsaye suka nufi babban falon gidan, koda suka k’arasa azaune suka samu Mamy hannunta rike da carbi tana ja, ganinsu da tayi dinne kuma yasa ta sakin murmushi, Yayinda Rayyern da kuma Ramadan suka gaisheta cikin girmamawa. Itakuwa Mamyn fuska asake ta amsa musu, tare da tashi ta had’a musu coffee mai zafi. Domin hakan d’abiarsu ce dukansu, idan suka dawo daga masjid sai sunsha coffee. Bayan sun gama shan coffee dinne kuma kowannensu ya haura side d’insa. Rayyern dai yana shiga bedroom d’insa, kwanciya yayi tare dajan blanket ya rufe jikinsa, bayan ya rufe idanunsa ne kuma, yasoma gabatar da azkhar d’insa na safiya, domin neman kariya daga wajen Allah Mahalicci mai kowa mai komai. Yana cikin yin azkhar dinnasa ne kuma bacci ya daukesa. 7:00 am dai-dai kuma ya farka sakamakon alarm din gefen bed d’insa dake ta kara. Kaitsaye toilet ya wuce tare da Sakarwa kansa ruwa, bayan ya kammala wankane kuma ya fito, inda ya kimtsa kansa cikin wasu had’add’u kuma tsadaddun riga da wando na leather suit navy blue colour, Yayinda long sleeve d’insa ta kasance sky blue, irin mai taushin nan. Tabbas bak’aramin kyau kayan yayi masa ba, Musamman da ya bayyana asalin kwarjini, haiba da kuma cikar zatinsa. Uwa uba kuma ga wani daddad’an kamshin turaren dake tashi ajikinsa. Wasu had’add’un navy blue toms kirar companyn Italy, daya saka ak’afafunsa ne kuma suka sake kawata kyawun Shigar tasa, Yayinda tsadadden agogon dake daure akan tsintsiyar hannunsa keta shining. Ahankali ya gama d’aura navy blue necktie awuyansa, tare da juyawa ya d’an kalli kansa amadubi, Tabbas shi kansa ya gamsu sosai da sosai, da shigar, Dan shigar tasa ta d’aukar hankali ne, musamman ma k’awataccen sajen dake kwance akan fuskarsa, wanda take bak’a sidik mai yawan sheki. Dan kawar da kansa daga Kallon madubi’n yayi, bayan yasa hannu ya d’auki briefcase d’insa, wanda ya saka duk wani abu mai mahimmanci nasa aciki. Kaitsaye cikin takunsa dake bayyana nitsuwarsa ya nufi hanyar fita daga cikin dakin, direct kuma falon k’asa ya nufo. Koda ya fito falon acan kitchine ya hango Mamy tsaye tana aiki. Yayinda Ramadan kuwa ke gefenta yana taya ta y’an wasu aikace aikace-aikacen masu sauk’i da maza zasu iya. Ido ya lumshe tare da d’an takowa zai shiga kitchine din, saidai kuma maganan da yaji Ramadan na fad’a ne yasashi d’an daka tawa. Acikin kitchine din kuwa Ramadan ne tsaye yana ɓarewa Mamy Maggi yana mai cewa. “Please Mamy tunda dai shi Hamma Rayyern yace muku, a fara yi min aure shi ko mgnar kansa ba yi yakeyi ba. To nikam dan Allah da Manzonsa abani dama nayi dan Allah, Mamy kiyiwa Abba magana, nidai gaskiya aure nakeson yi.” Ya kare maganar fuskarsa d’auke da zallar shagwab’a. Mamy dake tsaye kuwa murmushi tayi tare da d’an girgiza kanta, kana tace. “Nidai ba ruwana kayiwa Hamman naka magana, ya gayawa Abbanku cewar ya barka kayi aure, domin Abbanku zaifi saurin aminta da maganarsa.” Sake shagwab’e fuska Ramadan yayi, tare da karyar da wuyansa gefe, kamar zaice wani abu kuma sai yayi shiru. Rayyern dake bayansu kuwa ɗan guntun murmushi yayi, tare da d’an d’aga sautin muryarshi, Cikin kulawa yace. “Don’t worrie Ramadan, Isha Allah zan gayawa Abba cewar kanason aure ya barka kayi aurenka, ku haifa mana babies dozin-dozin ko zamu samu gidan nan zai daina zama shiru.” Juyowa dukansu sukayi suna kallonshi, Mamy kam mamakine ya isheta, sakamakon jin abunda Rayyern din ya fada, wato shi bazaiyi auren ba, saidai yasa ayiwa wani, har yau itakam tana mamakin hali irin na Rayyern, Sam kwata kwata mata basa gabansa, babu wata Mace daya tab’a gani arayuwarsa yace yana so, shidai hakanan yake tana fata Allah ya nuna mata sanjawarsa. Shikuwa Rayyern juyawa yayi kaitsaye ya nufi bedroom d’in Abba. Koda ya isa kofar bedroom din yana knocking, Abba ya bashi daman shigowa, bayan kuma sun sake gaisawa ne, ya bud’e briefcase din dake rike ahannunsa, wasu files ya ciro daga cikin jakar, wanda yayi aiki a kansu tun jiya da yake cikin jirgi, mik’awa Abban files d’in yayi tare da cewa. “Abba ga way’annan files d’in already nasaka hannu a kansu, sannan daga ciki akwai takardun engines din da muka saya a US.” Kai Abba ya jinjina tare da karb’an takardun, cikin kulawa yace. “Masha Allah, yaushe ne zakaje meeting d’in da zakuyi, naji ance harda govenor da ma wasu manya manyan Doctor’s, sannan tare da Ramadan zakaje ne?” Sake gyara zamansa yayi kana aladabce yace. “A’a Abba bada Ramadan zamu jeba, saboda yau suna da aikin da zasuyi anan cikin hospital shida Sulaiman, maganan shiga meeting din kuma 11:00 am daidai ne.” Again kai Abba yasake jinjinawa cike da gamsuwa yace. “Masha Allah To Allah Yabada sa’a.” Da Ameen ya amsa sannan ya mik’e tsaye, atare kuma suka fito shida Abban nasa. Inda suka iske Mamy da Ramadan sun gama jere komai akan dining table. Batare da wani b’ata lokaci ba kuma, suka zauna atare su duka suka soma cin abincin, kasancewar chips and sauce na egg da kuma fruit salad and ketchup Mamyn ta had’a musu, amma shidai yafi k’arfi wajen shan tea. Acan b’angaren Riyyam-Nsra kuwa yau tun tashinsa yakejin zuciyarsa wasai, ga kuma wani irin nishad’i da yakejin kansa aciki, sosai yakejin shaukin Nigeria na shiga jikinsa. Bayan yayi wanka ne kuma ya shirya kansa cikin, riga da wando masu kyau da tsada. Waya da kuma earpiece d’insa ya dauka, kana anutse ya fice daga cikin dakin nasa, direct wajen hotel din ya fito, saboda hakanan yaji yanason zaga unguwar da yake, duk da kuma akwai restaurant acikin hotel din, amma yaji sha’awar zagawa ko zai samu wani difference restaurant dancin abinci. Haka dai yadinga dan tattaki acikin unguwar, har dai ya samu wani had’add’en restaurant ya tsaya anan yaci abinci, bayan ya gama ne kuma ya sake dawowa hotel d’in daya sauk’a, To anan nefa ya samu Nasir Ahmad yazo, cikin farinciki shida Nasir suka rungume juna, tare da zama suka fara hirarsu na yaushe gamo.. Gaba d’ayansu zaune suke akan dining table suna breakfast. Yayinda kowannesu ke gudanar da harkar dake gabansa, amma Banda Junaid daya kafawa Jannart ido, wacce take zaune akan kujerar dake facing nasa. Tayi kyau sosai cikin shigar maroon abayan dake jikinta, wanda ta sake bayyana haske da kyaun fatarta, kasancewar bata saka bra bane kuma, yasa ta jawo mayafin abayan nata ya sauk’a harkan kirjinta. Saidai kuma gaba daya kwata-kwata bata da wata nutsuwa awajen, saboda irin Kallon da taga Ya Junaid nayi mata, kwata-kwata ya hanata sakat, ta kasa koda cin abincin. Daddy ne ya kalleta kana cikin tsananin kulawa da so yace. “Jannart kici abinci mana, kodai jikin naki ne?.” Kanta ta d’an girgiza ahankali, cikin kuma muryarta da yayi sanyi sosai tace. “A’a naji sauki Daddy.” Kai Daddyn ya jinjina. Shikuwa Junaid tsuka yayi azahiri tare da cewa. “Bawani rashin lafiya dake damunta, iskanci ne da kuma zallan rashin gaskiya kawai, munafuka mai fuska da zuciya biyu” Ya k’are maganar yana mai saka k’afarsa ta k’asan dining table d’in ya take ta. Idanunta ta rumtse da k’arfi saboda zafin da taji na abunda ya mata. Duk da cewar Daddyn nasu yaga hakan kuwa, amma baice kala ba saima ci gaba da cin abincinsa da yayi. Abdul ma da tausayin yar uwartasa ya cika masa zuciya kasa cewa komai yayi, domin yasani koda wasa yayi magana, yanzu sai Ya Junaid din yayi kasa-kasa dashi. Momy kuwa zuru tayi kawai tana kallonsu, domin har acikin zuciyarta ta kasa gane wani irin ahali ne take zaune acikinsu tsawon shekara da shekaru, har yau ta gaza gano manufar wasu daga cikin ahalin, abunda zata iya akullum kawai shine saka ido, da kuma jiran ranar da komai zai fito fili Jannart ta samu enci kamar ko wacce ɗiya a gidan ubanta, lokacin ɗaya taji idanunta na cicciko da hawaye sabida tausayin mairaini Jannart. Asashin su Rayyern kuwa anutse duk suka kammala breakfast dinsu, bayan yayiwa su Abba da Mamy Sallama ne kuma, suka fito atare shida Ramadan zuwa compound din gidan, inda ya samu Hadi driver d’insa na jiransa. Ganin ya shiga mota ne kuma yasa Ramadan shima shiga cikin tasa motar. Kaitsaye maigadi ya wangale musu Gatie suka fice daga cikin gidan. Suna hawa titi kuwa kowannensu ya kama hanyar inda zashi, Yayinda Ramadan ya wuce Mai-nasara hospital kaitsaye, shikuwa Rayyern government Hause ya nufa, domin acanne babban hall din da zasuyi taron yake. Gaba d’aya compound d’in had’add’en wajen aciki yake da tarin manyan Mercedes benz, G waggon, da kuma range rover iri da kala, motoci ne duka da suka amsa sunansu ta manyan masu kud’i, Yayinda kuma kowa dake zuwa wajen ya kasance babban Doctor ne maiji da kansa, wanda kuma ya k’ware da sanin makamar aikinsa. Gaba d’aya kowannensu sanye yake da suit ajikinsa, Yayinda kuma suke tafe cikin nutsuwa. Sai-dai kuma ga mamakina duk inda Rayyern ya wuce sai naga wasu daga cikin doctors din na bashi girma, like suna respecting nasa, duk da kuwa cewar wasu da yawa sun fisa shekaru, amma sanin makamar aiki da k’warewarsa yasa suke jinjina masa. 11:00 am dai-dai na cika kuma Gaba d’aya suka hallara acikin babban hall d’in, da tsaruwarsa ta zarce kwatantuwa, wanda cikin mutanen dake zaune awajen kuwa harda mai girma Govenor kano. Nanfa bayan kowa ya zauna suka shiga gabatar da taron nasu, inda d’aya bayan d’aya daga cikinsu ke tashi suyi bayani gamsasshiya, wanda kuma hakan tamkar k’arawa junansu sani ne sukeyi. Alhamdulillah dai sun gudanar da taron nasu yanda ya kamata, inda kowannensu ya fahimci d’an uwansa, bayan anci ansha ne kuma suka rufe taron da addu’a. Koda suka fito compound na hall d’in, kuwa tsayawa gaggaisawa da junansu sukayi. Inda ananne kuma Dr. Lukman ya mikawa Rayyern d’in hannu sukayi musabaha. Bayan sun gaisa d’inne kuma yakeyi masa murnar k’arin nasarar da yake ta samu, da kuma irin cigaban daya samu arayuwa. Dakai kawai Rayyern din ya iya amsa masa, domin magana bata wani fiye damunsa ba kuma ya gaji matuƙa da doguwar jawabin da yayi a likitance. Har ya juya zaitafi ne kuma maganar da Dr. Lukman din ke fada ya dakatar dashi. Inda yaji yana cewa. “Please Dr.Rayyern Mai-nasara idan babu damuwa, muna gayyatanka wani zama da zamuyi yau a Dakata’s Company Nigeria Limited.” D’an juyowa Rayyern yayi ya kalleshi, cikin rashin gamsuwa da kuma nuna shakka ako da yaushe yace. “Ni kuma?”. Da sauri Dr Lukman ya cire idonsa kan idon Rayyern ɗin tare da shakkarsa yace. “Eh”. “Gaskiya bansan da zaman ba, impact ma banida wannan lokacin.” Ya k’are maganar agajarce yana mai duban agogon dake daure atsintsiyar hannunsa, hakanan yake Sam bayason wasa ko kuma raini. Tabbas yana kiyaye kansa wanda kuma hakan d’abi’a ce dake cikin jininsa, awaje d’aya ne kawai zakaga murmushi da kuma fara’arsa, shine idan yana tare da Abbansa, Mamy da kuma Ramadan sai Baba Mauɗo, akasin haka kuwa Sam baya da sakewa da sauran wasu mutane, gentle mutum ne shi kuma straighforward, duk abunda ke bakinsa ya kuma san gsky ne shi yake fad’a, in ya ma daɗi ruwanka in kaji ba daɗi ma ruwanka. Sam arayuwarsa baya ta'ammali da fad’an k’arya ko munafurci, hakan ba d’abi’arsa bace, then ba kuma ya shiga abunda bai shafe sa ba. Lips Dr.Lukman yad’an cije cikin kuma lallab’awa dayin k’asa da murya, yace. “Please Dr. dan Allah karkayi rejecting gayyatarmu, domin kuwa zama ne da za’ayi da shuwagabannin companies masu ci ayanzu, ba kuma wani jimawa za’ayi ba only 1hour ma yayi, dan Allah da Manzonsa Dr. Rayyern Mai-sanara ka samu ka halarta, koda ace na tsawon 30mn ne!!!” Shiru yayi tare da d’an lumshe idanunsa, saboda gaba daya Dr. Lukman din ya kashe masa jiki daya ambaci sunan Allah. Tabbas akan komai idan ka ambata masa sunan Allah to yakanji zuciyarsa ta sake. D’an numfasawa yayi tare da bud’e bakinsa ahankali yace. “Is alright ba damuwa zanje, yaushe ne taron?” Cikin hanzari da kuma Jin dad’i Dr. Lukman yace. “Yau ne kuma yanzu nima can na nufa Insha Allah, ko zamu had’a hanya sainayi maka jagora.” Kansa kawai ya jinjina, batare kuma daya sake cewa komai ba, direct ya nufi wajen motarsa, yana shiga kuwa Hadi driver yaja suka fice daga compound din wajen, ganin hakanne kuma yasa Dr.Lukman ma cikin sauri ya shiga motarsa ya rufa musu baya. Kusan atare kuwa suka iso babban company’n, Dakata wanda yakasance kayan masarufi ake sarrafawa aciki, Tabbas company’n yana da girma kuma yana da kyau ba laifi, saboda ank’awata cikinsa da abubuwa masu kyau. Saidai kuma ga mamakin Rayyern kwata kwata babu wasu ma’aikatan kirki aciki. Haka dai Dr.Lukman yayi masa jagora harzuwa babban d’akin da sukeyin taro. Koda ya shiga gaba d’aya mutanen dake wajen basu wuce su 18 ba, wanda kuma dukkaninsu suna zaune ne akan royal chairs. Yayinda wani babban dogon table, wanda aka cika samansa da kayan drinks yayiwa gabansu k’awanya. Akan daya daga cikin kujerun wajen Dr. Rayyern Mai-nasara ya zauna, wacce kuma ta kasance itace take facing na Barrister Kabir Saleh Dakata. Agefensa kuwa Alhaji idi Sale Dakata ne zaune. A hankali ya juyo ya kalli wani dattijon daya zauna ɗaya gefen nashi, Alhaji Abdu Tababa kenan. Numfashi ya ɗan fesar tare da ɗan kallon Barrister Kabir Sake Dakata. Wanda tun shigowar Rayyern d’in ya kasa d’auke idanu daga kansa, domin hakanan yaji idanuwansa nayiwa Dr. Rayyern d’in Kallon sani, yanaji ajikinsa kamar a wasu shekarun baya masu tsayi ya tab’a sanin the same irin fuskar na, saidai kuma to Fuskar waye? Waya sani mai irin fuskar? Tambayar da bashi da amsarta, bashi kuma damai amsa masa haka yasa ya gaza janye idanunsa kan fuskar Rayyern yayinda yake motsa lips ɗinshi a hakali. Shi kuwaRayyern ido ya ɗan zuba mishi a fakaice yana nazarto abinda ke zuciyarsa . Gaggaisawa sukayi amutumce kafun daga bisani Alhaji Idi Sale Dakata. Ya d’an muskuta ya gyara zamansa. kana yace. “Toh Alhamdulillah domin kusan gabaki d’ayanmu munsan abunda ya taramu da kuma musabbabin had’uwar mu anan wajen. Idan kuma akwai wanda zance baisani ba saidai wannan yaron wanda yazo yanzu.” Ya fad’i maganar yana nuna Rayyern da hannu, cikin isa da gadarar dake bayyana cewar akwai wani abunda keyi masa suya a zuciya. Wanda hakanne kuma yasa Rayyern dago kai, ya soma bin kowannensu da idanu, yana mai karantar labarin dake zuciyoyinsu akan fuskokin su cikin hikima, da kuma haɗawa da ɗan lbransu da ya sani. Shikuwa Alhaji Idi Sale Dakata ci gaba yayi da cewa. “kamar dai yanda kuka sani munzauna ananne saboda mu tattauna akan kasuwancin mu, sannan Rayyern kaida baka sani ba kasani, munyi wannan taronne nagamayyan manya-manyan company’s, saboda akwai buk’atar had’a kawunan mu, domin mu gudu tare mu kuma tsira tare bi ma’ana, mu had’e kasuwanci’n wuri guda mu haɗa hannu ta yadda zamu tsara farashin kayan abinci da sauransu a yadda mukeso..” Ya dire ayar mgnar yana mai kallon. Alhaji Abdu Tababa dake jinjina kai. Kai Rayyern ya d’an girgiza tare da maida fuskarsa ya tsuketa waje d’aya, domin lokaci guda ya dawo asalin Rayyern Mai-nasara dinshi, hazikin matashin da bayajin shakka ko tsoron duk wani magauci’nsa ya rigada ya gama saninsu in and out yasan kowa yana da cikekken bayani kan kowansu. Gyara zamanshi yayi tare da maida bayanshi ya jingina da jikin kujera, Kana ya ɗan juya kanshi hagu da damanshi. Muskutawa yayi ya maida kujerar baya kaɗan kana ya ɗaura ƙafarsa ɗaya bisa ɗaya sabida zogin da yaji yatsarsa nayi mishi dan toms ɗin dake ƙafarsan ya takure yatsar da Jannart ta fasa mishi, cikin zuba musu ido ya sauƙe sassanyan numfashi, tare da cewa. "Kuyi haƙuri". Yayi mgnar cikin mutuntaka da girmama su. Cikin haɗe fuska Alhaji Yawale yace. "A kan me? Me kake nufi da muyi haƙuri? Fito fili kayi mgn yadda zamu gane?". Numfashin mai nauyi ya fesar sabida, sarawar da kansa ya farayi sabida yadda suke mgn da ƙarfi. Cikin nitsuwa yace. “Bana buƙatar had’a hannu daku a cikin kasuwanci na!!!". Ya fad’i hakan in don’t care manner, domin iya gaskiyarsa ya fadi kamar yadda suka nemi ji. Idanu suka zazzaro gaba dayansu. Yayinda Dr. Lukman dake gabansa ta gefensa bisa hagu yace. “Haba Dr.Rayyern ya zaka fad’i haka, agaban mutanen da yawancinsu sun haifeka, at least dai ai ya kamata ka daraja su ko dan sun fika gogewa a harkar tunda tun kan a haifeka suke juya kobo ta zama dubu...” Wani irin kallo da Rayyern din ya watsawa Dr.Lukman d’inne yasashi saurin rufe bakinsa gum, saboda hatta hantar cikinsa saida yaji ta kad’a. “Bazan had’a hannu dasu ba, na fad’a na kuma sake maimaitawa Ni DR. RAYYERN BASHEER MUHAMMAD MAI-NASARA bazan had’a hannu dasu ba!!!” Ya fad’i maganar da muryar dake bayyana iya gaskiya, da kuma zallan rashin tsoro ko shakkar kowa dake wajen. Gaba dayansu shiru sukayi sai Alhaji Ma’aji wanda yake da company'n Ma’aji and Sons ne ya d’an muskuta, tare da fad’in. “Meyasa bazaka had’a hannu damu ba?” Wayarshi ya ɗan zaro cikin aljihunsa kana ya ɗan danna kaɗan sannan ya medata cikin aljunsa tare da cewa. "Awa ɗaya dana baku cikin ɗaƙiƙun rayuwata da Allah ya aramin, kunci 21mn saura muku 39mn, in kuma kun gamane zan tafi." Cikin hatsala Alhaji Yawale yace. "Toh meyasa kace bazaka haɗa hannu da mutane ba". Juyowa yayi ya ɗan kalleshi kana yace. “Sabida tafiyata da taku ba iri ɗaya bane. Muddin muka ce zamu haɗa hannu, dole gefe ɗaya zai rinjayi ɗaya, ta yiwu ku rinjayeni. Ku ɓata min kekkyawan TUBALIn da aka ginamin. Ko kuma Ni in rinjayeni in ruguza muku mummunan TUBALIn da kuka gina tun da daɗewa, in ɗauraku bisa tsarina wanda kuma nasan bazaku lamunci hakaba. Dan haka muyi tafiyar a rabe shi yafi. Domin ni dai a atafiyata talaka nake dubawa. Ku kuma aljihunku kuke dubawa, ni kuma ba haka bace a tawa tafiyar, domin ahar kullum talaka nake dubawa, da rayuwarsu, manoman da suke noma abinci, su yake zuwa ya gagara yafi karfinsu, Yayinda ku kuma kunanan kuna juya abincin da suka noma da wahalarsu, yana zame muku manyan kud’ad’e, Sam baku damu da talakan daya noma abincin ko yaci ya koshi ba, ko bai cika wannan duk ba damuwar ku bace, saboda haka. Bazan had’a hannu daku aci gaba da cutan talakawa ba, domin sudinma mutanene kamar kowa!!!”. Wani irin murmushi mai cike da tarin ma'anoni Barrister Kabir Saleh Dakata yakeyi, yana mai kallon Rayyern ido cikin ido cike da alamun so, da kuma tsoro can ƙasan zuciyarsa. Su kuwa sauran gaba ɗaya a hatsale suke Cikin yanayi hasala Alhaji Idi Sale Dakata yace. “Okay wannan dalilin shi yasa ka zagaya gaba d’aya, kan manyan manoman da ƙanana da suke sayar mana da abinci ka hanasu sayar mana, har sai sun gama sun ware wanda zasu ci kafun su kawo mana mu mu saya?.” “K’warai kuwa hakane, saboda hakkinsu ne kuma guminsu ne, ya zama lallai tilas cutarwar da kukeyi musu ya isa haka, Manoma bawai bayinku bane, domin da ace babusu yau da dukkanku baku kai wannan matakin ba, har yaushe zaku daina ci gaba da cutan mutanen da suke taimakon ku?.” Ya kai k’arshen maganan nasa, cikin wata irin Muryar dake bayyana, cewa a shirye yake da yayi fito na fito da kowanne daga cikinsu, Sam babu alaman tsoron acikin zuciyarsa. Wani irin bak’inciki da kuma k’unci ne suka cika zuciyar Alhaji Idi Sale Dakata, wanda hakan yasa shi hasala, ak’ufule yace. “Indai wannan k’udurin naka ne basai kana da rai da lafiya zaka cika saba, Lallai Tabbas ayi mugani idan zai yiwu!” Cikin tsoro Barrister Kabir Saleh Dakata ya juyo ya kalli yayan nashi Alhaji Idi Sale Dakatan har ya buɗe baki zaiyi mgn kuma, sai yayi shiru ya juyo yana kallon Dr Rayyern Mai-nasara da yayi. Murmushin dake bayyana izzarsa da fito da kwarjininsa, kana ya d’ago ya kalli Alhaji Idi Sale Dakata. Cikin bayyana rashin tsoronsa yace. “Kwarai saida rai da lafiya ake komai, amma kuma abun jin dadin shine babu wani mai rayawa ko kashewa sai Allah, babu kuma wani wanda ya isa yin abunda Allah bai nufa ba, koda wayeshi kuwa.” Sosai Alhaji Ahmed Tambari ya jinjina kanshi, hakama Barrister Kabir Saleh Dakata, fuskarshi suka zubawa idanu. Suna tuno irin kamarsa da ya ƙalubalancu shekarun baya. Dr Lukman kuwa rumtse idanunsa yayi sabida murya Rayyern na tuna mishi wata muryar data gabata. Da ƙarfi ya kuma rumtse idanunshi sabida hatta ɗan maƙolloton wuyan RAYYERN irin na wancan mutumin ne. Da sauri ya buɗe idanunsa jin Alhaji Abdu Tababa na cewa. “Tabbas babu mai rayawa ko kashewa sai Allah amma. Yaro ka san cewa komai akwai sanadi. Toh Lallai watarana za’ayi sanadin da zuciyarka zata tsaya da bugawa ka kiyayi kanka.” Alhaji Abdu wanda yake aboki ga Alhaji Idi Sale Dakata ya fad’i hakan cikin hasala. Shikuwa Rayyern awannan karon dariya yayi harsaida fararen hakoransa suka bayyana, saboda shi gaba d’aya dattijawan ma gani yake kamar basu San mesukeyi ba, domin harya fara tunanin cewa girma ne kawai ya Kamasu. Mik’ewa tsaye yayi ahankali tare da daukar glasss dinsa dake aje bisa table d’in, taku daya biyu yayi ya tsaya tare da juyowa ya kalli Alhaji Idi Sale Dakata. Fuskarsa dauke da wani murmushi mai rugurguza zuciyar magauta yace. “Idan akwai Allah to babu wani wanda ya isa da juyya RAYYERN Mai-nasara dole ya dakatar da Dakata in dai kan sayan k’udiri ne.” Cikin fushi Alhaji Idi Sale Dakata ya buga table din dake gabansa, tare da fadin. “Karya kake yaro, wallahi kai karamin al'haƙine, domin kuwa mun munji da wayanda suka fika tauri da tsaurin ido ma, saboda haka kai ba komai bane.” Still wani irin murmushi yayi Cikin kuma nuna halin ko inkula yace. “Wai tsoro kuke bani ne?". A hatsale Abdu Tababa yace. "Isa muke nuna maka". Ronƙofawa yayi kanshi kaɗan kana yace. "Hmmmm nifa RAYYERN Ina da taurin kai, ni nan Rayyern babu wanda ya isa sakani abunda banyi niyya ba, haka kuma babu wanda ya isa sakani yin abunda zai sab’awa addinina, idan kuma kuna ganin wasa ne to Lallai magwaji ya gwada ya gani!!!.” Ya ƙarashe mgnar da ɗan sauti. Kana ya D’an rank’wafo bisa kan Alhaji Idi Sale Dakata, cikin hade fuska da kuma zafin zuciya yace. “Ina raga muku ne kawai saboda waɗannan fararen gemun dake kan fuskokinku, amma akasin haka hmmm nima zan iya take kowa kuma ya taku!!!” Yana gama fad’in hakan ya juya afusace ya fice daga cikin dakin taron. Dai-dai lokacin kuwa mota k’irar Black Benz ta faka a farfajiyar wajen, ahankali Jannart ta zuro da kwawayan legs dinta waje, wanda suka sha dogon takalmi na al'farma, sannu ahankali kuma itama ta fito daga cikin motar gaba daya. Wata irin fitinanniyar gown ce mai masifar kyau ajikinta. Yayinda ta yane kanta da mayafin rigar, wanda hakan ya fallasa asirin kyawunta mai daukar hankali, daga gefen damanta kuwa Abdull ne ya fito, inda hannayensa ke dauke da wasu manyan basket guda biyu. Domin zuwa sukayi musamman dan kawowa su Daddyn nasu da kuma Barrister Kabir abinci, saboda sun shaida musu cewar suna da taron da zasuyi, shiasa Momy tayi girki na musamman aka kawo musu. Dai-dai isowar Jannart steps din da zata haura zuwa cikin hall din, shi kuma Dr. Rayyern ya fito daga cikin hall din ransa a matuk’ar b’ace ga wani irin masifeffen ciwon kai wanda ihun dattawan nan suka sakar mishi, ga yatsarsa dake zogi dan baima sha mgnin da safe ba. Karab idanunsu suka sark’afe acikin na juna, saidai kuma ganinsa da Jannart d’in tayi ne yasa ta saurin janye jikinta baya. A cikin hall ɗin kuwa gaba ɗaya sun hargitse kowa da abinda ke faɗi. Haka yasa Barrister Kabir Saleh Dakata miƙewa da sauri ya nufo woje yana mai bin bayan Dr Rayyern Mai-nasara. Shikuwa Rayyern kasancewar afusace yake shiyasa ko sake kallonta baiyi ba, direct ya nufi wajen motarsa wanda hakan yasa Jannart ta bisa da kallo. Har saida ya b’acewa ganinta. Yayinda Barrister Kabir Saleh Dakata ma da yanzu ya fito sai binshi da idon yayi. Abdull dake tsaye ne ya kalli Jannart tare da cewa. “Ya dai kinsan sane?” Dan kauda kanta gefe tayi, batare kuma da taja zancen ba tace. “Eh muje kawai.” Jin hakan ne kuma yasa Abdull Sakai. Da sauri suka tsaya ganin ƙanin mahaifin nasu, sai dai hankalinsa baya kansu. Motar Rayyern Mai-nasara ya zubawa ido. Yana mai motsa lips ɗinshi a hakali. Jin muryar Abdul ne ya sashi ɗan juyowa, ya amsa gaisuwar yayi tare da kayan kana yace. Su tafi gida. Daga nan suma suka juya gida. Rayyern kuwa daga Cikin company din direct cewa yayi driver ya dawo dashi gida. Hakan kuwa akayi suka nufo gida kai tsaye. A nan Nassarawa G.R.A kusa. Riyyam-nsra ne ke tsaye ajikin wani tamfatsetsen gate na alfarma. Wanda garin yawon zafaye anguwar da sukeyi ne da tattaki shida Nasir ɗin shi suka gilma ta gidan. nan kuwa Nasir yace. "Riyyam-nsra ya tsaya suyi video a gate ɗin gidan. A hankali yake shafa tarin sumar dake kwance akansa. Ahmad dake tsaye agabansa yana rike da, wayar Riyyam dinne yayi dariya tare da cewa. “Nifa wallahi yanzu kam nagaji da rik’e wayannan, tun d’azun kake cewa zakayi video da waƙar hausa amma ka kasa, sai kace wani bak’o a harkar.” Dariya shima Riyyam din yayi tare da cewa. "Kafa san hausar tawa kar inje bin waƙar bai hauba." Murmushi Nasir yayi tare da cewa. "No kada ka damu zaiyi." Murmushi Riyyam-nsra yayi tare da shafa sumar kanshi kana, ya ɗan ware sawunsa. lokaci d’aya kuma ya nutsu, tare dasa Ahmad yayi start din videon, cikin abubuwansa irin na tiktodians daya saba, ya soma rawa tare da bin wata waka dake tashi acikin wayar, inda yake cewa. “Niba gida ba niba mota ba,". Yayi mgnar yana nuna gidan bayan nashi Kana yaci gaba da cewa. "Bamai tarin dukiya masu yawa ba, Babana shiga gwamna ba, ba shugaban k’asa ba ba kuma member ba". Sosai Nasir yake murmushi yana jinjina mishi sabida yayi masifar kyau da bin waƙar hausa. Cikin karsashin ganin Nasir na jinjina mishi yaci gaba da cewa. "Banje makaranta maitsada ba, banje Dubai ba kuma banje London ba. Gidanmu ba a G.R.A ne ba, ban d’auki selfie nasa Instagram ba. Ko zana zamma saniyar ware wallahi ni baza na zam makaryaci ba!!!” Sosai yake wani irin rawa mai ƙayatarwa yayi masifar kyau. Dai dai lokacin kuwa Motar Dr Rayyern Mai-nasara ta kunno kai dai dai wajen gate din, Yayinda motar Ramadan ma ta kunno kai ta b’angaren hagu, saboda shima yanzun nan shigowarsa cikin layin nasu. Atare suka ci wani irin birki tare da zaro idanu saboda G..... Fawal beauty parlor sunai muku albashir da bude gidan Mata wato kigyara da kanki👩🏻‍🦰 da cewa suna gabatar da aiki na zamani kamar su gyaran jiki, spa kenan gyaran fuska wato facial,gyaran Kai, hair style , gyaran kafa pedicure,gyaran hannaye, manicure kitso,lalle ja da bakki,ba'a barsu abayaba suna saida kayan gyaran aure, turaruka,man shafawa, suna kwalliya wato makeup,turaren wuta, humrah,kulaccham dama abunda Baku sanshiba wato maida tsohuwa yarinya akankanin lokaci😄iya kudinka iya shagalinka💃kudai ku hanzarta zuwa ga wannan gida na mata zallah (FAWaL BEAUTY PARLOR) Address: Main gate na fire service jimeta, opp sixty plaza. kada kubari abaku labari😍 munai muku maraba a koda yaushe Mata yan kwalisa mace sai da gyara , yar uwa bora ba sunanki kizama mowar mai🏨 da taimakon FAWAL BEAUTY PARLOR 👩🏻‍🦰da kudinki qalilan kifita sab abunki ki baza kamci mai kama jiki. Gamai buka contact CEO FAWaL BEAUTY PARLOR kan 09033901035 or 08078809930 sai kunzo, our time services from 8:am to 7pm, Monday to Saturday/ Sunday 10am to 6pm🪞🎁🛒🛍️🤝🏻 By *GARKUWAR FULANI* 11/15/21, 7:20 PM - Auntyna: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *TUBALI* PAGE 8 NA *AYSHA ALIYU GARKUWA* *FREE PAGE ne* *Littafin TUBALI na kuɗine hamzarta ki biya kafin a gama free PAGE in saki a Group, ƙaramin group 500 special Group 1k ne, 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU, sai ki turo min shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276, ko kuma ki sayi katin mtn ki copy number's ɗin katin ki turo min ta whatsApp 09097853276* Ganin Riyyam Nsra da sukayi, domin daga Rayyern har Ramadan kusan atare idanunsu ya sauk’a akan matashin yaron dake tsaye ajikin gate din gidansu. Wanda shima kuma Rayyern din d’ago kansa kenan da zaiyi, ya sauk’e idanunsa akan na Rayyern dake zaune agaban motarsa, inda yake zaune akan kujerar mai zaman banza, ya zauna agaba dinne kuma saboda lokacin daya fito daga hall din taro, na Dakatas company ransa a matuk’ar b’ace yake, wannan yasa bai tsaya wani tantance inda zai zauna dinba, kawai sai ya bud’e gaban motar ya shiga ya zauna. Sam kwata-kwata babu alaman murmushi akan fuskarsa, saima tsananin b’acin ran da yasa fatar fuskartasa tayi jajur, haka ma idanunsa, ga kuma wata yar jijiya da ta bayyana akan goshinsa, sosai yakejin kansa na d’anyi masa ciwo, wanda kuma hakan ya faru ne saboda d’an yawaita magana da yayi yau din, da kuma ihun da way’ancan dattawan suka dingayi masa tsakar aka. “Laaah Hamma Rayyern!!” Riyyam-nsra dake tsaye fuskarsa d’auke da tsananin farinciki da kuma mamakin ganin Rayyern d’in ya fad’a, yana mai d’an matsawa daga jikin gate d’in, kaitsaye ya nufo wajen da motar Rayyer’n d’in ke tsaye. Still fuskarsa dauke da murmushi yace. “Thank God dama zan sake ganinka anan kusa, jiya kun b’acemin a airport nasha wahala sosai awajen neman ku.” Idanu Dr Rayyern Mai-nasara ya lumshe duk da cewar, baya iya jiyo abunda Riyyam d’in ke fad’a, amma ya daiga bakin yaron na motsi kuma ya karanto abinda yake faɗin. Dai-dai lokacin kuwa daga cikin gidan, Baba Mauɗo ya wangale musu makeken gate d’in, wanda hakan yasa direct driver’n Rayyern din ya tura hancin motar ciki. Wulgawan da motar tazo yine kuma yasa Naseer dake tsaye ya sauke idanunsa akan, wani handsome guy dake zaune acikin motar, wanda yake matuk’ar kama da abokinsa Riyyam-nsra. Bakinsa ya wangale cike kuma da tarin mamaki yace. “La Riyyam kalli wani maikama da kai.” Murmushi Riyyam yayi tare da nade hannayensa akirjinsa, yana mai bin motar Rayyern da ta shige cikin gida da kallo. Ramadan dake cikin motarsa kuwa, tun d’azu mutuwar zaune kawai yayi, tare da bud’e ido da baki yana kallon matashin saurayin, da yake ganinsa tamkar hoto copy din Yayansa Rayyern. Lallai Tabbas wannan kamar da yake gani akan fuskar yaron, da kuma ta Hammansa Rayyern ta b’aci. Cike da tu’ajjudi ya k’araso da motarsa zuwa bakin gate din gidan, tare dayin k’asa da glass din motar yana me sake Kallon yaron da har yanzu murmushi ke bayyane akan fuskarsa. Ganin kuma yaron ya dan juya masa baya, ya kuma tare masa hanya ne, yasashi danna horn. K’aran horn dinne kuwa yasa Riyyam-nsra da kuma Naseer juyowa, suka sauk’e idanunsu akan Ramadan dake kokarin tura hancin motarsa cikin gidan. Idanunsu gaba d’aya suka zubawa fuskarsa, Yayinda lokaci daya Riyyam-nsra yaji wani irin abu ya daki kirjinsa, saboda Kallon fuskar Ramadan da yayi, ganin kuma kamar idanunsa na d’anyi masa gizo ne, yasashi sanya tafukan hannayensa yadan mutstsuke su. Saidai kuma yin hakan da yayi ya sake tabbatar masa da cewar, bawai gizo idanunsa keyi masa ba, Lallai Tabbas fuskar wanda ke zaune acikin motar, tana shige da fuskar Mammy ce da kuma ta Zaytoon dinsa. Wani irin mamaki ne ya lullub’esa, Yayinda Naseer kansa shima daya ga kamannin fuskar Mammyn Riyyam dana Zaytoon, akan ta Ramadan dake zaune acikin motar yace. “Allahu Akhbar Allah Mai girma Riyyam kalli wani maikama da Zayton da Mammy’n ka, gacan kuma wani mai kama da kai, kodai y’an uwanku ne sud’in?” Naseer ya kare maganar yana mai kallon, Riyyam wanda tuntuni ya nufi cikin gidan. Ganin hakanne kuma yasa cikin sauri Naseer din rufa masa baya. Riyyam-nsra kuwa yana k’arasa shigowa cikin gidan, Dr.Rayyern Mai-Nasara na fitowa daga cikin motarsa, Haka ma Ramadan. Cikin dan hanzari Riyyam din ya karasa, batare kuma da tunanin komai ba, ya ware duka hannayensa tare da fad’awa jikin Rayyern d’in, ya d’an rungumesa da k’arfi. “Naji dadin ganinka sosai Hamma Rayyern, nanne gidanku?, waye wannan Hamma Rayyern?” Riyyam-nsra yayiwa Dr. Rayyern duka tambayoyin, tare kuma da d’aga hannu ya nuna Ramadan dake tsaye, shima bakinsa d’auke da tarin tambayoyi. Tsumammun idanunsa ya lumshe ahankali, tare kuma da sauk’e wata irin ajiyar zuciya, Tabbas kafun iyanzu yanajin zuciyarsa na matuk’ar tafasa, saidai kuma gashi yanzu lokaci daya yaji zuciyar tasa nayin sanyi. Hannayensa yasanya ya d’an janye Riyyam daga jikinsa, kana ahankali yace. “Eh. kanina ne, Ramadan.” Murmushin matuk’ar mamaki da kuma Jin dadi Riyyam yayi, cikin halinsa na faram-faram da sakewa, ya rungume Ramadan din, kana da d’abi’arsa ta wayewa yace. “Sunana Riyyam-nsra kuma naji dadin had’uwa dakai Hamma Ramadan.” Murmushi mai dauke da wani irin Jin dadi, tare da zallan k’aunar yaron da yaji yana shigarsa alokaci guda Ramadan yayi, cikin kuma nuna zallan farincikinsa yace. “Me too, amma wai a ina kasan Hamma Rayyern dina, da har kuke matuk’ar kama haka?” Murmushi Riyyam-nsra yayi, kana cike da tsananin mamakin sautin muryar Ramadan irin tasa yace. “Acikin jirgi muka hadu dashi jiya, nima nayi mamakin kamannin da mukeyi dashi sosai, amma kuma Allah babu yanda baya ikonsa, saboda haka ne ma ya zama Hamma na!!”. Riyyam ya kare maganar yana me bin Dr.Rayyern da kallo, wanda tuni ya soma tafiya harya kusa isa kofar da zata sada shi da babban falon gidan. Ramadan kuwa idanunsa yadan lumshe tare da sake rungume kyakkyawan matashin yaron ajikinsa, wanda ak’alla shekarunsa baza su wuce 21 to 22 years ba, Lallai yaji matsanancin son yaron ajikinsa, har yakai ga yanajin inama da ace yaron zai zamanto k’ani agaresa, kamar yanda shiya kasance kani ga Hamma Rayyern, Tabbas yaji gamsuwa da yaron acikin zuciyarsa, Yayinda kuma kamannin Hamma Rayyern din dake kan fuskar yaron, yasanya shi jinsa awani waje na musamman a zuciyarsa. Hannun yaron ya kamo kana cikin kulawa yace. “Masha Allah Riyyam-nsra mu shiga daga ciki, domin kuwa na kwad’aitu dason nunawa Abba da Mamy mu mai kama da Rayyern dinsu.” Murmushi sukayi su dukansu, kana Riyyam ya sake rik’e hannun Ramadan k’am acikin nasa, Yayinda acikin zuciyarsa yakejin wani irin nishad’i, ji yake tamkar ba yaune farkon fara haduwarsu ba, yanajin kamar tuntun tuntuni ya sansu, acikin wani bari na jikinsa. D’an juyowa Riyyam din yayi ya kalli Naseer Ahmad dake tsaye, yana Kallon ikon Allah, tare da tu’ajjudin abunda ke faruwa. Alama yayi masa akan ya biyosu, hakan kuwa akayi cikin dan sassarfa Naseer ya rufa musu baya. Dr. Rayyern Mai-Nasara kuwa koda ya karasa cikin falon, direct part d’insa dake sama ya nufa, saboda ayanda yakejin kansa nadan sarawa, ba kuma yason wani abu da zaizo ya dameshi. “Abba! Mamy! Abbana!! ku fito kuga wani abun ban mamaki!!!” Cewar Ramadan dake shigowa cikin falon, hannunsa rike dana Riyyam-nsra. Wanda kuma yanayin maganan nasa ne, cikin dan bayyana sautin muryarsa, ta yanda duk nisan dasu Abban suke zasu iya jiyosa, kasancewar kuma suna daya daga cikin bedroom din kasa, dake cikin falonne yasa, cikin sauri suka mik’e tsaye, tare da soma rige rigen fitowa asalin babban falon, saboda kiran da sukaji Ramadan d’in nayi musu, yadan tsinkar musu da zuciya. Ai kuwa isowar su Ramadan din tsakiyar falon, yayi dai dai da fitowar su Abban. Fitowar daya haifar musu da wani irin bugun zuciya, tare da matsanancin firgici hadi da zallan mamaki. A matuk’ar mamakance had’i da tu’ajjudi, Mamy ta dafe kirjinta tare da sake, ware Idanunta akan matashin yaron da hannunsa ke sark’afe dana Ramadan, wanda idan ba k’arya Idanun nata keyi mata ba, Lallai Tabbas kamannin d’anta Rayyern ne, kwance akan fuskar yaron. Cikin karfin halin daya kasa danne mamaki da tu’ajjudi’nta tace. “Ramadan waye wannan? A ina kasa moshi? Kamar fuskar Rayyern nake gani akan tashi fuskar, ko kuwa dai idanuna ne keyimin gizon hakan?” Murmushi Ramadan yayi, tare da sanya dayan hannunsa ya jawo Riyyam-nsra jikinsa, cikin kulawa kuma yace. “Sam ko kad’an Mamy ba idanunki bane ke yi miki gizo, sunansa Riyyam-nsra, kuma tabbas yana matuk’ar kama da Hamma Rayyern dinmu, sannan Hamma Rayyern dinne ma ya samo shi, domin sun had’u ne a Ethiopia cikin jirgin da zai kawosu Nigeria.” Shiru Mamy tayi tare da kafe yaron da ido. Kamar dai yanda Abba ya kafesa da ido, baya ko k’yaftawa, domin tun Kallon farko da yayiwa yaron ya kasa dauke idanunsa daga kansa. Wani irin bugawa yakejin zuciyarsa nayi, Yayinda wani abu ke tasowa tun daga cikin kasan kafarsa har zuwa tsakiyar kansa, Lallai Tabbas akwai kama aduniya, amma irin kaman Rayyern daya hango akan fuskar yaron tayi yawa. Ramadan dake tsaye kuwa ganin irin yanda fuskokin iyayen nasu, ke cike da zallan mamaki ne yasa shi, sakin murmushi tare da jawo hannun Riyyam-nsra suka k’araso kusa da iyayen nasu. Hannun Mamy Ramadan ya kamo, tare da d’an fad’ad’a murmushinsa, cikin kuma son basu cikakkiyar gamsuwa yace. “Dan Allah Mamy ki kalli Riyyam da kyau, matuk’ar kama sukeyi da Hamma Rayyern dinki.” Juyowa ya kumayi ahankali ya kalli Riyyam, wanda fuskarsa ke dauke da yalwatacciyar murmushi. Shid’inma Murmushin yayi kana yace. “Riyyam wannan itace Mamyn mu, Uwa d’aya tamkar da dubu, wannan kuma shine Abban mu, mahaifin daya kasance Garkuwa kuma jigo ga y’ayansa.” Yak’are maganar yana meyiwa Riyyam nuni, da iyayen nasu shida Dr. Rayyern. Yalwatacciyar fara’a ne ta bayyana akan fuskar Riyyam, Cikin matuk’ar ladabi da biyayya kuma yad’an durk’usa akan guiwowinsa, tare da bud’e bakinsa anutse yace. “Abba da Mamy barkanku da gida, fatan zaku karb’eni kamar yanda su Hamma Rayyern da Ramadan suka amsheni, saboda daga yau Mamy kinzama mahaifiya agareni, haka ma Abba daga yau ka maye min gurbin Mahaifi.” Kusan daina bugawa zuciyar Abba tayi, alokacin da yaji saukar muryar yaron acikin kunnensa, saboda tsananin yanda yaji muryar yaron tayi masa kama da ta Ramadan. Yayinda daga gefe guda kuwa kwakwalwarsa ke neman juyewa, saboda wani irin tsohon tunani mai karfi dake neman dawowa cikin lissafinsa, da sauri sauri zuciyar Abban ke bugawa, musamman ayanzu daya sauke idanunsa akan yatsun kafan yaron. Mamy kuwa da ayanzu taji zuciyarta nayin sanyi, hannayenta tasa ta d’an d’ago yaron, tare da sakar masa murmushi kana cikin tsananin kulawa tace. “Insha Allah Riyyam mun karb’eka hannu bibbiyu kamar yanda su Hammanka suka karb’e ka.” Murmushin tsananin jin dadi Riyyam yayi, sai alokacin ne kuma ya dago kai ya sake Kallon Abban su Ramadan d’in, da har yanzu ya kasa dauke idanunsa akansa. Abban kuwa ganin Riyyam din na Kallon sa ne, yasashi dan sakin murmushi. Ramadan kuwa hannun Riyyam din ya kama suka dawo cikin falon suka zauna, direct gaban fridgen dake cikin falon ya nufa, inda ya d’auko wa su Riyyam din bottle water da kuma fresh milk mai sanyi, ya basu suka sha shida Naseer da ya zama ɗan kallo. Mamy kuwa da kanta ta k’arasa dining table, inda ta had’a musu lunch, saboda tuntuni rana tariga tayi. Ramadan kuwa cike da soyayya yaja su Riyyam da kuma Naseer suka karasa kan dining table d’in. Bayan kuma sun zazzauna ne Mamy tayi serving dinsu, inda ta zuba musu lafiyayyar jalop rice din da tayi, wanda yasha kayan vegetables, da pepper chicken. Turawa kowannensu abincin tayi gabansa, tare dajan kujera itama ta zauna, anan kusa da Abba wanda shima yanzun ya karaso ya zauna. “Rayyern fa ko bai dawo ba?” Mamy ta tambayi Ramadan dake shirin kai loman abinci baki. “Ya dawo amma ya haura sama, na daiga mood d’insa, kamar he’s tried, i think kuma stress din aiki ne.” Ramadan ya fad’a yana mai hadiye abincin dake bakinsa. Kai Mamy ta jinjina cikin gamsuwa kana kuma ta d’ago kanta ahankali ta kalli Riyyam-nsra, fuskarta dauke da murmushi tace. “Masha Allah Riyyam kaiko daga wacce k’asa kake?” Riyyam dake cin abinci gyara zamansa yayi, tare da fuskantar Mamy’n, kana aladabce cikin bagwariyar sausarsa yace. “Ni d’an k’asar Ethiopia ne, acan mahaina da kuma y’ar uwata suke, acan aka haifeni kuma acan na taso nayi rayuwa, nazo nan Nigeria ne kuma saboda, abokina Naseer.” Ya k’are maganar tasa yana me nuna Naseer dake shan Chapman din da Mamyn ta had’a. Mamy kuwa still murmushi tayi tare da soma cin abincinta. A Dai-dai lokacin ne kuwa Rayyern ya soma sauk’owa daga kan steps din falon, wanda ya sake shirya kansa cikin wasu had’add’un riga da wando, na normal jeans. Sai-dai ganin da yayiwa su Abba da kuma Riyyam-nsra akan dining table ne, ya sashi tsayawa tare da zuba musu ido. Abba kuwa da har yanzu baidainajin bugawar zuciya ba, d’ago kansa yayi ya kalli Naseer tare da cewa. “Kai kuma a ina kake, su waye kuma iyayenka?” Jin tambayar da Abban yayi ne yasa Naseer gyara zama, cikin dan girmamawa yace. “Sunan Babana Alhaji Ahmad Dasuki, mu asalin yan Nigeria ne, kuma muna zaune anan cikin garin kano unguwar Rijiyar zaki.” D’an Jim Abba yayi alamun dogon nazari, kana anutse yace. “Sunan mahaifinka Alhaji Ahmad Dasuki, amma gaskiya bangane shiba.” Murmushi Naseer yayi, tare da cewa. “Eh gaskiya bai shahara sosai ba, saboda ba a b’angaren kasuwanci yake ba, saidai Mamana yar gidan Malam MAI-NASARA ce, ni jikansa ne.” Lokaci guda walwalan dake kwance akan fuskar Abba ta kau, take duk wani annuri da murmushinsa suka gushe, badon komai ba kuwa saidan jin an ambata masa sunan Malam MAI-NASARA. Ganin hakanne kuma yasa Ramadan, d’auke kansa daga Kallon Abban nasu da yake, inda ya sauk’e idanunsa akan Rayyern dake tsaye akan steps, wanda shi d’inma kuma Abban nasu yake kallo. Sam gaba d’ayansu basu San dalilin daya sa, Abban nasu baison gani ko jin wani abunda ya shafi Malam MAI-NASARA’n, basusan wannan sirrinba, haka kuma basusan dalilin ba. Kai Ramadan ya d’an sunkuyar ahankali cikin kuma rauni, dayin k’asa da murya yace. “Abba yanzu ma abunda ya dawo dani gida kenan, dazu aka Kai mana Malam Mai-nasara hospital dinmu bashi da lafiya, hypertension and diabetes na damunsa, so akwai buk’atar Lallai lallai Hamma Rayyern ya duba sa, so Ya Sulaiman ya kikkira wayan Hamma Rayyern d’in amma kwata-kwata baya shiga, shiyasa na dawo gida saboda inasaka ran cewa zan iya samunshi, Dan gaskiya jikin Malam din ya tashi sosai!” Fuska Abba ya sake had’ewa tamau, cikin kuma nuna halin ko inkula yace. “Babu inda Rayyern zaije, ai bashi kad’ai bane Babban Dr. acikin garin Kano, akwai Doctors da dama, akaishi wani asibitin mana.” Shiru gaba d’aya falon ya dauka, Yayinda Ramadan ya sunkuyar da kansa k’asa. Shikuwa Rayyern dake tsaye idanunsa ya d’an rumtse, acikin zuciyarsa yana mai tambayar kansa, dalili da kuma hujjar da tasa Abban nasu bayason alak’arsu da Malam Mai-nasara, Tabbas da ace baisan waye mahaifin nashi ba, zuciyarsa zata iya sak’a masa abubuwa da yawa, saidai kuma amma yasan cewa mahaifinnasa mutumin kirki ne, babu yanda za’ayi wani mummunan tunani yayi tasiri acikin zuk’atansu sun san wayeshi mutun ne managarci daya ginasu kan kekkwan tubali nagarta. Idanunsa da suke alumshe yadan bude, tare kuma da karasa saukowa akan steps din, kaitsaye ya nufo dining table din, duk da kuwa cewar har zuwa yanzu yanajin kansa nadanyi masa ciwo. Isowarsa dining table dinne kuma yasa duk suka dago kansu suka kalleshi, Yayinda Abban cikin matsanancin kulawa yace. “Masha Allah Rayyern ka dawo, ya meeting din naku?” Kujerar dake gefen ta Abban nasu yaja ya zauna, kana aladabce yace. “Eh Abba na dawo, meeting kuma Alhamdulillah komai ya tafi yanda ya kamata.” Kai Abban ya jinjina cike da gamsuwa tare da fadin. “Alhamdulillah haka akeso ai akoda yaushe.” Gyara zamansa yayi, kana ahankali cikin kuma yin kasa da murya, hadi da sigar roko yace. “Abba dan Allah kayimini al'farmar samun daman duba Malam Mai-nasara, tunda Ramadan yace yana da buk’atar taimakona sosai, please Abba dan Allah me zai hana bazaka bari naje na dubashi ba!!” Ya k’are maganar tasa cikin k’ank’an da kai. Yayinda Abba kuwa ya dauke nasa kan, tare da sake hade fuskarsa. Ganin hakanne kuwa yasa Naseer zaro wayarsa, ya dannawa lamban Umminsa kira, cikin sa’a kuwa bugu biyu ta d’auki wayar. Saidai kuma irin yanda Naseer din yaji sauti da Amon muryarta ne, yasa hankalinsa tashi. Cikin fargaba yace. “Ummi ya naji muryarki haka? meyake faruwa kodai jikin Malam ne ya tashi?” Daga can b’angaren kuwa cikin sheshshek’an kuka Ummin tace. “Eh Naseer jikin Malam ya tashi sosai, yanzu haka ankaishi Mai-nasara hospital, amma Dr da ya kamata ya dubashi bayanan, gashi kuma yanajin jiki sosai, domin sauran Doctors din da suka dubashi, sun tabbatar mana da cewar jininsa ne ya sauk’a, ga kuma diabetes.” Idanun Naseer ne sukayi raurau lokaci daya kuma suka ciko da hawaye, ahankali yadan share k’wallan da suka zubo masa, kana yace. “Kiyi hakuri Ummi Insha Allah Malam Mai-nasara zai samu lafiya, ki daina kuka muma zamu zo nan asibitin nida abokina Riyyam nsra.” Daga haka kuwa bai sake cewa komai ba ya kashe wayar tasa, ya maida ita cikin aljihu. Sai kuma ya dago kansa ya kalli Abba wanda har yanzu kansa ke gefe. Dan jan kujerar da yake kai baya yayi, tare da mikewa tsaye ya iso har gaban Abban ya durk’usa, cikin muryarsa irin ta masu neman al'farma yace. “Dan Allah Abba kayi hakuri kabar Hamma Rayyern yaje ya duba Malam, yanzu haka Mamana kuka takeyi, kuma tace jikin Malam din ya tsananta sosai, dan Allah Abba kayi mana al'farma, Malam shine duk wani hasken cikin familyn mu, rasashi dai-dai yake da yankewar farincikin mu.” Still Kai Abba ya sake kawarwa gefe batare daya ce komai ba. Ganin hakannen kuma yasa gabaki d’ayansu sukaji zuciyoyinsu sun raunata, babu ma kaman Rayyern da hakanan yakejin duk wani al’amuran daya shafi tsohon acikin jinin jikinsa. Riyyam-nsra kuwa ganin yanda Abban ya kawar da kansa gefe ne, yasashi saukowa daga kan tasa kujerar shima ya durkusa agaban Abba’n. Cikin sanyin da muryarsa tayi yace. “Dan Allah Abba kayi hakuri, kabari Hamma Rayyern din yaje ya dubasa.” Idanu Abba da ransa ke ab’ace ya rumtse, kamar kuma zaice wani abu saiya fasa hade da mikewa tsaye, kana yasa kai ya wuce bedroom d’insa kai tsaye...! Duk wacce batayi anfani da sabulunnan ba anbarta abaya acan karshen bayama kuwa duk Mai tantama akan sabulai nagyaranjiki cewa basa Aiki toh yacire mg's domin kankat ne insha Allah babu Wanda yayi anfani dasabulunmu yace baiyi ba koyaushe mg's sai sanbarka amare da uwargidaye hardama yanmata kuhanzarta kusamu naku ba karya domin bama cika Baki kugwada kubada labari da bakunanku sabulu daya tamkar dubu wadandama basasan using cream sabulun mg's herbal whitening black soap yawadacemuku jikinku zaiyi kyau koyaushe kukasance clean cikin kamshi Kuna glowing koda bakusa turare ba🤗 Kayanmu bana bleaching bn organic ne sunagyarajiki fiye da tsammaninku zaifiddomuku da ainihin natural beauty dinkine Wanda yagwada shi zaitabbar amare kuyi kokari kumallaki mg's domin baruwanku da zuwa adirjemuku jiki zakuga yanda fatarku zata dinga walwali Ina masu pimples Tabo(spot) Sunburn dama dukwani matsalar fata kuyi kokari kunemi soap dinnan before 2weeks zaisharemuku hawaye kuzama abun kwatance Sister's masu nankarwa kuma kunemi soap dinnan Yana rage nankarwa sosai🧖🏻‍♀️duk me shakku tayi kokari tagwada mg's insha Allah bazakiso rabuwa dashi ba Akwai maisa haske Amma kayanmu nafada bana bleaching bn zaifiddomiki d ainihin halittarkine yagoge dukkan dattin jiki Akwai Kuma Wanda zaimiki maintaining skin dinki yasaki fresh fatanki tazama kalar hutu Sannan munada beauty kit wnd yk mayarda fata tadawo tamkar madubi wnd yajaraba shine zai tabbatar Set din yakunshi Abu 6 Soap,body cream,face cream,scrub, cleanser, glow oil Pls bamacika Baki you HV to try it and see for yourself 100%tested nd trusted Beauty kit:11k Soap price:3k Location:kaduna buh munaturawa ko Ina Amma delivery is not free Maiso kindly message 08062991549 Call 08064532391 Note:Babu inda zakusami mg's herbal whitening black soap sai a number dinnan bairiga yakai market b inyakai we will let you know buh as for now wnn numbern ne kawai🙏 Maiso yahanzarta before yaji sold out akwaisu available now insunkare you HV to wait akawo so maiso yahanzarta🙏adade anayi sai gsky🤭🤝 Mg's skincare By *GARKUWAR FULANI* 11/15/21, 7:20 PM - Auntyna: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *TUBALI* PAGE 9 NA *AYSHA ALIYU GARKUWA* *FREE PAGE ne* *Littafin TUBALI na kuɗine ki biya ki karanta cikin salama, special Group 1k ne kana akwai karamin group 500 kacal ne 0661110179 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU sai ki turo min shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276, ko kuma ki sayi katin MTN ki turo ta whatsApp ɗin* Hakanne kuwa yasa suka bishi da kallo dukansu harsaida ya b’acewa ganinsu. Ahankali Rayyern da Ramadan suka dawo da kallonsu ga Mamy wacce itama tayi zugum, da dukkan alama kuma bata da abuncewa. Naseer kuwa mik’ewa tsaye yayi, kana jikinsa amatuk’ar sanyaye ya kalli Mamy, cikin bayyana godiyarsa agaresu yace. “Zan tafi Mamy, mungode sosai da karramawarku agaremu nida abokina Riyyam.” Jin abunda Naseer din ya fad’ane kuma yasa Riyyam ma saurin mik’ewa, tare da cewa. “Naseer jirani mu tafi asibitin tare.” Kai Naseer din ya girgiza tare da kama kafadun Riyyam, cikin sanyi yace. “A’a Riyyam ka zauna, kada kace zaka bini, saboda asibitin Mai-nasara bak’aramin asibiti bane, ko ni da zanje yanzu sainasha tambaya kafun zan iya gano ward d’in da suke, kayi hakuri kaji duk yanda ake ciki zan kiraka awaya Insha Allah ina dai zaka gane hotel ɗin da ka sauka?.” Kai Riyyam yadan jinjina batare kuma daya soba, haka yabar Naseer ya tafi shi kad’ai. Ganin fitan Naseer dinne kuma yasa, Rayyern mikewa ahankali, cikin kuma takin dake bayyana nutsuwarsa, ya nufi dakin Abban nasu kai tsaye. Ajikin k’ofar ya tsaya tare da daura hannunsa akai ya d’anyi knocking. Daga ciki Abba dake zaune akan wata kujera ya jingina kanshi ya rumtse idanunshi ya bada izinin shigowa. Ahankali Rayyern ya tura kofar dakin ya shiga, bakinsa dauke da sallama. Amsa masa sallamar nasa Abban yayi, tare kuma da kafesa da ido. Shikuwa Rayyern anutse ya karaso ya zauna agaban Abban nasa. Rank’wafar da kansa k’asa yayi, sannan aladabce yace. “Kayi hakuri Abba, duk da bansan manufarka ta aikata hakan ba, amma Ina mai rokonka daka bani daman zuwa duba lafiyar Malam Mai-nasara, yau akaron farko yazo hospital dinmu, yana kuma cikin halin buk’atar wanda zai kula da lafiyarsa, dan Allah Abbana kayimin wannan alfarmar, domin kuwa hakkina ne na kula da duk wani marar lafiyar da yazo asibitin mu, aiki na ne hakan, nabawa duk wani marar lafiya kulawa, Dan Allah Abba karkace a’a, domin yin akasin hakan tamkar wulakanta marar lafiya ne.” Idanu Abba ya lumshe, tare da sakin ajiyar zuciya, domin kuwa Tabbas yasan cewar shi ya d’aura Rayyern din, akan turban da duk yanda abu yake, idan aka rokeka da Allah da Manzon sa to zaka aiwatar. Yasani kwarai ya gina ƴaƴan nasa, akan tubalin tausayawa duk wani mai neman taimakonsu. Ajiyar zuciya ya kuma saukewa akaro na biyu, kana cikin tausasa murya yace. “Shikenan tunda ka had’ani da Allah Rayyern, kaje ka dubashi, amma iya taimakon daya kamata kawai zakayi mishi, da zaran yaji sauki kuma, ayau nakeso ka sallameshi banason ya kwana acikin asibitin.” Dagowa Rayyern yayi fuskarsa dauke da murmushin jin dadi, yace “Insha Allah Abba, idan yaji sauki ayau yau zan sallameshi, nagode sosai da wannan alfarmar!” Kai Abban ya jinjina, kana shikuma batare da wani b’ata lokaci ba ya tashi ya fice daga cikin dakin. Direct bedroom d’insa ya nufa, Yayinda ya d’auko wayoyinsa da kuma yan k’ananun abubuwan da yasan dole zai bukata. Koda ya sauko kasa, haka ya samu Mamy Ramadan Riyyam sunyi zugum. Kallon Ramadan din yayi, cikin yanayin saurin da yakeyi kuma yace. “Ramadan zo mu tafi hospital din.” Ai kuwa jin haka yasa Ramadan mikewa cikin sauri, ya marawa Rayyern din baya, kasancewar tuni harya fara tafiya. Koda suka fito cikin mota d’aya suka shiga, ak’agauce kuma Hadi drivern yaja motar suka fice daga cikin gidan. Ak’alla saida sukayi tafiyar 17mn, kafun suka iso babban katafaren Mai-nasara Hospital d’in, wanda aka k’awata gininsa kamar ak’asar turai. Koda driver yayi parking Rayyern baijirayi komai ba, cikin hanzari ya bude murfin motar ya fita. Yayinda Ramadan ya take masa baya. Sulaiman da yanzu fitowarsa daga cikin office dinsa, hango Rayyern din da yayine yasashi k’arasowa da sauri. Rayyern kuwa ak’agauce, batare ma daya bari sun gaisa da Sulaiman din ba yace. “Awani ward aka kwantar da Malam Mai-nasara?” “Emergency ne, amma kuma abisa tunanin ba zai samu ganinka yau ba, yasa Manyan ya'yansa suka daukeshi zuwa wani hospital din na daban.” Idanu Rayyern din ya kankance tare da dafa kansa, dake sarawa da d’an k’arfi yace. “Shitt! Why Sulaiman? Meyasa bazaka ce musu sujirani ba?” Kai Sulaiman yad’an girgiza tare da cewa. “Nakira duka wayoyinka is not available, gashi jikin nasa yana ta tsananta, kuma kaine wanda ya dace ka dubasa, domin mu munyi iya yinmu, yan uwannasa kuma sun kasa hakurin jiran zuwanka, shiyasa suka daukeshi zuwa wani asibitin daban.” Idanunsa da suka d’anyi ja ya rumtse, saboda Sam ba haka yaso ba, hakika yaso ace shida kansa ya duba mutumin. Juyawa yayi ya nufi office d’insa, yana maijin ransa duk a jagule, ga kuma ciwon kansa da a yanzun yake sake karuwa. Koda ya zauna acikin office din, ji yayi gaba daya zaman asibitin ya ishesa, hakan yasa shi tashi ya fito. Anan yasamu Ramadan ma na shirin komawa gida, saboda yasan sunbar Riyyam shikad’ai acan. Kamar yanda suka zo kuwa atare suka koma. Inda Koda suka shigo cikin falon gidan, azaune suka iske Riyyam-nsra kan lallausan carpet din dake malale a tsakiyar falon, agefensa kuwa Mamy ce, Yayinda shi kuwa yake rik’e da wayarsa yana sana’arsa ta chatting. Saidai kuma duk da chatting din yake, amma bakinsa baiyi shiru ba, labarai kawai yake ta bawa Mamy kala kala, wanda kuma duk rabin labaran nasa akan Mammynsa da kuma Zaytoon abokiyar tagwaicin sa ne. Mamy dai itakam zamanta da yaron ya sata nishadi sosai, saboda labarai ne na abun dariya yake bata. Kallon Riyyam-nsra da Mamyn Rayyern yayi, batare kuma da yace wani abuba kaitsaye ya haura sama, saboda so yake yasha magani ya kwanta, ko zai samu relief na headache din dake damunsa. Ramadan kuwa zama yayi suka sha hiransu, kafun daga bisani ya kama hannun Riyyam din, suka haura dakinsa dake sama. Acan b’angaren Jannart kuwa, sunyi waya da Salman. Inda yake shaida mata cewar. Ya samu information akan sunan hospital din su Rayyern din, da kuma yanda za ayi su samu ganinsa idan sunje hospital din. Ajiyar zuciya Jannart ta sauk’e adai-dai lokacin da ta zare wayar daga kunnenta. Cikin kuma halin Kosawa tace. “Yah Allah Kataimakeni, ka had’ani da wannan mutumin, da nemansa yafi na kud’i wahala, mutum shiba Diamond ba amma ace wai ganinsa ya zama aiki, yau shine can Gobe shine nan, wai dole saikabi wasu matakai kafun ka iya ganinsa, babban ma abun takaicin shine Kwata-kwata, ko a social media babu wani information akansa, baya Facebook baya Instagram only Twitter kawai, still kuma a Twitter dinma, babu wani information akansa, ko hotonsa babu.” Yar siririyar tsuka taja, tare kuma da turo dan karamin bakinta gaba, kana ashagwab’e tace. “Idan ma ba munafurci ba da rashin gaskiya. Meyasa yake boye kansa, da har za’ace kwata-kwata babu wanda ya tab’a ganin fuskarsa? A jaridu ko a TV Maybe ma shidin irin ɗima-ɗiman alhazawan nanne masu tafiya da kyar da kuma katon ciki ne, shi yasa yake boye kansa.” Momy dake tsaye abayanta ne tace. “Lafiyarki kuwa Jannart keda wa kike ta tashin k’ananan maganganu?” Juyowa tayi tare da Kallon Momyn kana ta kwab’e fuskarta. “Momy aiki aka bani a office, gashi kuma aikin sai wahalar dani yakeyi.” Ta kare maganar tana me zare earpiece din dake kunnenta. Dan Murmushi Momy tayi hade da cewa. “To Allah Ya baki sa’a, amma dai yanzu kam ki ajiye aikin kitchine dinnan haka kije ki huta, zan karasa dafa pepper meat din da kika fara.” “To Momy.” Tafad’a a sanyaye tare da ajiye baban spoon din dake hannunta. Momy kuwa da kallo ta bita harta gama ficewa daga cikin kitchine din, Allah yasani duk da cewar ba itace ta ta haifi yarinyar ba, amma tana matuk’ar so da tausayinta. Saboda yanda rayuwar yarinyar yake cike da sarkakiya mai daurewar hankali da tunani. Wanda kuma ita kanta haryau ta kasa gano gaskiyar hakikanin abunda ke boye. Jannart kuwa Koda ta fito daga cikin kitchine din, anutse take tafiyar ta batare kuma da ta lura da Yah Junaid dake zaune acikin falon yana shan shisha ba, direct ta wuce bedroom dinta. Dan dauro alwalan sallan Magriba. Junaid dake zaune kuwa da idanunsa yabi manya manyan hips dinta harsai da ta b’acewa ganinsa, (Yana ɗaya daga cikin illolin da sa suturun banza suke jawa ɗiya mace, koda kuwa a cikin gidanku ne). Kafun ya iya rumtse idanunsa, tare da shakawa cikinsa hayakin shisha. Allah Yasani yana matuk’ar so da buk’atar kanwartasa fiye da komai aduniya. Domin akanta yakanji kamar ana ingiza sa kowacce rana. Haka kuma idan dai zai ganta sau dubu da irin shigar data zame mata ɗabi'arta to Tabbas zaiji sha’awarta sau dubu yanayin shigarta ke ingiza lafiyar samartakarsa. Mikewa tsaye yayi kamar zai bi bayanta kuma sai ya fasa, tare da komawa ya zauna ya cigaba da bankawa cikinsa hayakin shisha, duk da kuwa yanajin ana kiran sallan magriba, amma haka yayi biris tamkar ba yaji. To dama sallan bawani damunsa tayi ba. Acan gidansu Rayyern kuwa har akayi sallan Isha suna tare da Riyyam. Wanda kusan atare ma sukaje masallaci sukayi sallan magriba dana isha. Yanzu ma kammala dinner dinsu kenan, Riyyam din ya mike tsaye, tare da duban Abba da Mamy. Cikin girmamawa yace. “Abba Mamy zan koma masaukina, na kuma nagode da karramawarku sosai.” Ramadan dake zaune ne ya rik’o hannunsa tare da fadin. “Haba Riyyam-nsra a daren nanne zaka koma hotel, please ka kwana anan mana, ai duk munzama daya....” Sauran maganan dake bakin nasane ta makale amakoshinsa, sakamakon mummunan kallon da yaga Abba ya watsa masa. Shikuwa Riyyam-nsra da bai lura da Kallon da Abban yayiwa Ramadan dinba, murmushi yayi. Kana cikin nuna godiyarsa yace. “Kayi hakuri Hamma Ramadan watarana ai Zan dawo.” Kai Ramadan din ya jinina, Cikin waskewa kuma yace. “Shikenan ba matsala To muje na saukeka.” Saida safe Riyyam din yayiwa Mamy da Abba, inda suka amsa masa amutumce. Kallon Rayyern dake zaune Riyyam din yayi, kana ya dan rankwafo ya rungumesa, cike da k’aunar Rayyan din da yakeji acikin zuciyarsa yace. “Saida safe Hamma Rayyan.” Kai Rayyern din yadan jinjina masa. Yayinda Ramadan kuwa ya kama hannun Riyyam-nsra din suka fice. Saida suka hau titi ne kuma Riyyam-nsra din yake fadawa Ramadan hotel din da zai kaisa. Yayinda acan gidannasu kuwa , bayan tafiyar su Ramadan din Rayyern tashi yayi ya wuce bedroom d’insa. Wanka yayi bayan ya fito ne kuma ya d’auki system d’insa, ya soma latsawa, Yayinda akai akai yake saka nutella chocolate abakinsa. Agaban babban Hotel din na Taheer Guest Palace Ramadan ya sauke Riyyam, tare dayin exchanging phone number atsakaninsu. Bayan kuma Ramadan din yace da Riyyam Gobe yazo suyi breakfast tare ne, suka sakeyin sabuwar sallama, Yayinda Riyyam kaitsaye ya wuce cikin hotel din. Shikuwa Ramadan juya akalar motarsa yayi zuwa gida. 12:30 am dai-dai Rayyern ya kashe laptop dinnasa, tare da mirginawa ya kwanta akan gadonsa. Wanda daga zaman nasa awajen zuwa yanzu yashanye fiye da rabin Kwalban Nutella chocolate. Idanunsa yadan lumshe saboda yanda yakejin bacci na game cikinsu. Sannu Ahankali kuma ya soma ambaton sunan Allah ahaka har baccin ya daukesa. Acan sashin Riyyam-nsra kuwa, koda ya shiga dakinsa na hotel din, haka ya tarar da komai nead. Wanka yayi tare da zuwa ya fada kan gado, hade da jawo wayarsa ya runguma, bayan ya kunna data ne kuma ya shiga whatsapp sama sama yayi chatting acikin whatsapp din, kana daga bisani kuma ya dawo ta inda yafi karfi Wato Tiktok. Atakaice dai saida yakai kusan 2am yana sheke ayarsa kafun bacci barawo ya daukesa, haka kuwa yayi baccin yabar data d’insa akunne. Washegari. Kamar koda yaushe yauma 7:30 am ya gama shirya kansa tsab, cikin royal high quality black suit, tare da white long sleeve wacce tayi masa kyau sosai. Kasancewarsa mai kyau ne kuma shiyasa komai ya saka saiyayi masa kyau. Ahankali yake saukowa daga kan steps din falon, Yayinda briefcase d’insa ke rike ahannunsa na dama. Mamy dake tsaye tana shirya dining table ne ta dago ta kalleshi. Ɗan guntun Murmushin gefen baki yayi, wanda ya ɗan bayyana fararen haƙoransa, kana cikin nitsuwa yace. “Good morning Mamyna.” Murmushi itama Mamyn tayi, cike kuma da soyayyarsa tace. “Morning My beautiful son, kafito a dai-dai maza zokayi breakfast dinka.” Karyar da wuyansa gefe yayi, tare kuma da duban agogon hannunsa. Muryarsa adan sanyaye yace. “I’m sorry Mamyna yau sauri nakeyi, amma idan Ramadan yazo fita ki hada masa breakfast dinnawa a basket ya kaimin office.” Murmushi Mamy tayi tare da cewa. “To ba matsala adawo lafiya Allah ya tsare ya kuma bada sa’a.” Da “Ameen.” Ya amsa kana cikin jin dadi ya Sakai ya fice daga cikin falon. Dai-dai fitowarsa compound din gidanne kuma, Riyyam da Ramadan suka shigo atare. Cikin sauri Riyyam ya karaso, tare Da dan rungume Rayyern din, fuskarsa dauke da Murmushi yace. “Good Morning Hamma Rayyern!” Idanu Rayyern din yadan lumshe tare dasa hannu ya shafa kan Riyyam din, cikin kuma yanayinsa na rashin sabo dayin magana yace. “Morning Riyyam, Ina fata kunyi waya da Naseer yau, ya jikin Malam din?” Kai Riyyam din ya jinjina tare da fadin. “Eh munyi waya dashi, ya kuma tabbatarmin cewa jikin Malam din da sauki.” Kai Rayyern din ya jinjina tare da cewa. “Okay bani numbern Naseer din.” Yafada yana me mikawa Riyyam wayarsa dan yasa masa numbern Naseer. Ramadan kuwa kai ya jinjina cike da gamsuwar lallai Hamman nasa ya dauki lamarin malam da matuƙar mahimmanci. Hakan kuwa akayi domin cikin abunda bai wuce 1mn ba Riyyam ya sakawa Rayyern din numbern. Ramadan kuwa dake tsaye fuskarsa dauke da dan mamaki yace. “Hamma Rayyern me zakayi da numbern Naseer kuma?.” “Zanje na duba Malam Mai-nasara ne, tunda har Abba ya a mince dana dubasa din, tofa Tabbas saina duba sa, zan kira Naseer din idan basa hospital har gidansa zanje na dubasa.” Rayyern din ya fada in full confidence. Ramadan kuwa Kai ya jinjina cike da gamsuwa, sai kuma suka hada baki atare shida Riyyam wajen cewa suma zasuje gidan Malam Mai-nasara din. Kansa kawai ya kad’a, adai-dai kuma lokacin da yake shiga cikin motarsa yace. “Okay nidai yanzu hospital zan wuce, sai Idan na tashi ne zan biya can gidan nasa, amma idan kuna da chance zaku iya zuwa maybe mu hadu acan .” Yana gama fadan hakan yaja murfin motar ya rufe, batare kuma daya saurari mai zasu sake cewa ba, yasa Hadi driver yaja motar suka bar wajen. Su kuwa Ramadan da Riyyam kaitsaye cikin gidan suka wuce. Koda suka karasa cikin falon Riyyam aladabce ya gaishe da Mamy da kuma Abba wanda yake yanzu fitowarsa daga daki. Cikin farincikin ganinsa Mamy ta amsa, Yayinda Abba ma ya amsa masa fuska asake. Anan kan dining table sukayi breakfast. Bayan kuma sun kammala ne Riyyam da kansa ya gyara wajen, tare da kai plates din da suka bata kitchine ya wanke. Mamy kam cike da mamaki take kallonsa, domin kuwa duk da ta hanashi saida yayi, inda yake bata labarin cewa ai yanayiwa Mammynsa ma, saidai watarana dagangan sai yakiyi dole Zaytoon ce zatayi. Mamy dai itakam dariya kawai takeyi, saboda daga jiya zuwa yau din kawai, zama da yaron ya zame mata sabo. Abba kuwa ido ya zuba musu da inda yake zaune can tsakiyar falon yana nazartar ƙarfin halin Riyyam-nsra da shisshiginsa garesu anya kuwa!?. Ya ɗiga ayar tambaya a kan yaron. Acan hospital kuwa Rayyern bayan yadan duba wasu daga cikin patients dinsa ne, ya d’auki waya ya kira Naseer. Bayan sungaisa ne kuma yake tambayar Naseer din, jikin Malam Mai-nasara. Tofa ananne Naseer din yake fada masa cewar. “Ajiyan ankai Malam din Zanna Hospital, amma kuma an sallamosu Yanzu dai Malam din yana gida, kuma babu laifi jikin da d’an sauki. “ Kai Rayyern din ya jinjina, tare da cewa Naseer din ya turo masa adireshin gidan Malam din zaizo anjima. “To.” Naseer din ya fada cikin minti kadan kuwa ya turowa Dr Rayyern din, da text message na address din gidan Malam Mai-nasara. 12: am dai-dai Rayyern ya kammala duk wani abu abunda yakeyi acikin hospital din. Haka ya fito daga cikin office dinnasa yana taku cikin nitsuwa da kuma zarransa dake kara bayyana kwarjininsa da haiba na cikakken da na miji. Kaitsaye compound din asibitin ya nufa, yana zuwa kuwa ya shige cikin motarsa batare da bata lokaci ba, driver yaja motar suka fice daga cikin asibitin gaba daya. Bayan sun hau titi ne kuma drivern ya juyo yadan kallasa, kana aladabce yace. “Ranka ya dad’e Ina muka nufa?.” “Hausawa sabon titi.” Ya fada atakaice. Tare da sanya hannu ya zare glass din dake manne a idanunsa. A dai-dai wannan lokacin kuwa Ramadan Riyyam da kuma Naseer ne, acikin motar Ramadan din kirar Range rover velar 2019, inda suma kaitsaye suka nufi Unguwar ta Hausawa sabon Titi, wanda suna tafiyar ne kuma bisa jagoran Naseer. After some 20mn suka iso gaban wani gate din makeken gida mai tsananin kyau da girma. Wanda kuma yake nanne gidan Malam Mai-nasara. Horn Ramadan dake driving ya danna. Jin karan horn dinnasa ne kuma yasa maigadi, Dan lekowa ganin dalleliyar motar da yayi ne da kuma Naseer a gaba ne yasashi karasawa da hanzari ya wangale babban farin gate din. Wanda hakan ya bawa Ramadan daman tura kan motar tasa ciki. Wanda shigansu cikin gidan kuwa. yayi dai dai da wani irin masifeffen bugawar zuciyoyin Riyyam-nsra da Ramadan. Kokarin maida gate din maigadin yasomayi saidai kuma ganin wata dakekkiyar motar again BMW ta faso kaine, yasashi wangale gate din. Inda matukin motar ya tura hancin motar ciki. Wanda saukan tayoyin motar acikin gidan, yayi dai-dai wani irin azabebben harbawa da zuciyar Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara yayi. Cikin wani irin matsanancin faduwar gaban da yakeji, da kuma dukan da zuciyarsa keyi ya bud’e idanunsa inda ya saukesu A...! Fawal beauty parlor sunai muku albashir da bude gidan Mata wato kigyara da kanki👩🏻‍🦰 da cewa suna gabatar da aiki na zamani kamar su gyaran jiki, spa kenan gyaran fuska wato facial,gyaran Kai, hair style , gyaran kafa pedicure,gyaran hannaye, manicure kitso,lalle ja da bakki,ba'a barsu abayaba suna saida kayan gyaran aure, turaruka,man shafawa, suna kwalliya wato makeup,turaren wuta, humrah,kulaccham dama abunda Baku sanshiba wato maida tsohuwa yarinya akankanin lokaci😄iya kudinka iya shagalinka💃kudai ku hanzarta zuwa ga wannan gida na mata zallah (FAWaL BEAUTY PARLOR) Address: Main gate na fire service jimeta, opp sixty plaza. kada kubari abaku labari😍 munai muku maraba a koda yaushe Mata yan kwalisa mace sai da gyara , yar uwa bora ba sunanki kizama mowar mai🏨 da taimakon FAWAL BEAUTY PARLOR 👩🏻‍🦰da kudinki qalilan kifita sab abunki ki baza kamci mai kama jiki. Gamai buka contact CEO FAWaL BEAUTY PARLOR kan 09033901035 or 08078809930 sai kunzo, our time services from 8:am to 7pm, Monday to Saturday/ Sunday 10am to 6pm🪞🎁🛒🛍️🤝🏻 By *GARKUWAR FULANI* 11/15/21, 7:20 PM - Auntyna: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *TUBALI* PAGE 10 NA *AYSHA ALIYU GARKUWA* *FREE PAGE ne* *Na kuɗine littafin Special Group 1k ƙaramin group 500 ne kacal, 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU sai ki turo min shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276, ko kuma ki sai katin MTN ki copy number's ɗin katin ki turo min ta whatsApp* Fawal beauty parlor sunai muku albashir da bude gidan Mata wato kigyara da kanki👩🏻‍🦰 da cewa suna gabatar da aiki na zamani kamar su gyaran jiki, spa kenan gyaran fuska wato facial,gyaran Kai, hair style , gyaran kafa pedicure,gyaran hannaye, manicure kitso,lalle ja da bakki,ba'a barsu abayaba suna saida kayan gyaran aure, turaruka,man shafawa, suna kwalliya wato makeup,turaren wuta, humrah,kulaccham dama abunda Baku sanshiba wato maida tsohuwa yarinya akankanin lokaci😄iya kudinka iya shagalinka💃kudai ku hanzarta zuwa ga wannan gida na mata zallah (FAWaL BEAUTY PARLOR) Address: Main gate na fire service jimeta, opp sixty plaza. kada kubari abaku labari😍 munai muku maraba a koda yaushe Mata yan kwalisa mace sai da gyara , yar uwa bora ba sunanki kizama mowar mai🏨 da taimakon FAWAL BEAUTY PARLOR 👩🏻‍🦰da kudinki qalilan kifita sab abunki ki baza kamci mai kama jiki. Gamai buka contact CEO FAWaL BEAUTY PARLOR kan 09033901035 or 08078809930 sai kunzo, our time services from 8:am to 7pm, Monday to Saturday/ Sunday 10am to 6pm🪞🎁🛒🛍️🤝🏻 Akan motar su Ramadan, wanda tuni Naseer ya fito daga cikinta, Yayinda Ramadan da Riyyam ke kokarin fitowa suma. Tsumammun eyes d’insa masu dauke da wasu sinadarai na musamman ya lumshe, tare da sanya hannu ya dafe dai-dai saitin zuciyarsa. “Yah Allah kabani nutsuwa, k’arfi da kuma k’warin guiwa ako da yaushe!”. Yafad’i hakan acan k’asar zuciyarsa dake harbawa da sauri-sauri. Kwata-kwata baisan meyasa agaba d’aya y’an kwanakin nan, zuciyarsa ke yawan harbawa da k’arfi ba. Saidai kuma koma meye yana fatan ya zame masa alkhairi. Bud’e murfin motar yayi ahankali tare da zuro kyakyawan k’afafunsa waje. Dai-dai lokacin da ya gama fitowa acikin motar kuwa, su Ramadan da Riyyam suka k’araso. Riyyam-nsra kuwa da murmushi ya kasa buya akan fuskarsa ne yace. “Laa Hamma Rayyern kaima ka iso?” Kai Rayyern din ya jinjina masa alaman. “Eh.” Naseer kuwa dake tsaye agefe, wayarsa ya zaro tare da dannawa lambar Uncle Mustapha (Kawunsa, yayan mamansa) kira. Bugu daya kacal kuwa Uncle Mustapha ya d’aga wayar. Jin an d’aga wayanne kuma yasa Naseer cewa. “Uncle Mustapha gamu nan cikin compound tare da Dr. Rayyern din dana gaya maka cewa zaizo ya duba jikin Malam.” Uncle Mustapha dake zaune acikin falo, kuwa saurin mikewa tsaye yayi, batare kuma daya katse wayan ba yace. “Masha Allah to Naseer ka shigo dashi mana, ku shigo ku shigo.” Yanayin yanda yayi maganar yana me nufar hanyan fita daga cikin falonne kuma, yasa sauran yan uwansa dake zaune acikin falon suka dan kalleshi. Daga waje kuwa Naseer ne ya kalli Rayyern din, hade da cewa. “Hamma Rayyern mu shiga..” Bai gama rufe bakinsa ma baiyi ba, saiga Uncle Mustapha d’in ya fito, fuskarsa dauke da yalwatacciyar murmushi ya soma takowa inda su Rayyern din suke. Idanu Rayyern da kuma Ramadan suka ɗan zuba mishi. Kamar kuwa yanda suka zuba mishi idanu, haka shima ya zuba musu nashi idon, musamman akan Rayyern da kuma Riyyam, wani irin kallo yake musu mai dauke da mamaki, da kuma yanayi mai bayyana alhini., ciki kuwa harda fuskar Ramadan da yakewa kallon ya taɓa sanin mai irin fuskar farin sani. Isowar Kawu Mustapha’n kusa da sune kuma yasa, duk tunanin da suke suka tsaya cak. Hannu Rayyern ya mik’awa kawu Mustaphan, wanda shima ya mik’o masa nasa hannun fuska asake, sukayi musabaha. Bayan sun gaisa da Rayyern dinne kuma, Kawu Mustapha’n ya bawa su Ramadan da Riyyam-nsra hannu suka gaggaisa. Cikin kuma yanayin dake bayyana zallar farinciki da mutum tawa, Uncle Mustapha’n ya dubi Rayyern, kana atausashe yace. “Masha Allah Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara barkanka da isowa. Cikin ikon Allah Jiya iwarhaka munata fama da neman damar yanda za’ayi muganka, sai gashi kuma yau kaida kanka ka tako k’afarka izuwa inda muke, kai Masha Allah sannunku ku iso mu shiga daga ciki.” Murmushi Rayyern yayi kana anutse yabi bayan, mutumin da ayanzu kawai ya shaida da karamcinsa. Su Ramadan ma rufa musu baya sukayi, Yayinda Riyyam ke tafiya yana k’arewa katafaren gidan kakan abokin nasa kallo, wanda aka matuk’ar k’awatasa, kasancewar kuma gidan nada part-part da yawa ne, shiyasa ya zama kamar wani mention, Yayinda Kota ina dake cikin gidan, aka cikasa da shuke shuken korayen trees. Isowarsu bakin kofar da zai sadaka da babban falon dake cikin gidanne, yasa Rayyern d’an lumshe idanunsa, saboda hakan yaji harbawar da zuciyarsa keyi na sauk’a, Yayinda zuciyar tasa kuma keyi sanyi. Haka kuma yakejin wani irin abu na ratsa cikin tafukan hannaye da k’afafunsa. Kasancewar kuma shike bayan Uncle Mustapha dinne, yasa shiyayi na biyun shiga cikin falon, da girmansa yayi a had’a manya manyan faluka guda biyu awaje daya. Taka k’afarsa ta dama da yayi acikin falon kuwa, shiya sanya shi jin wani irin sanyi na game duk jikinsa. Ajiyar zuciya ya sauke ahankali, wanda yayi dai-dai da sauk’e ajiyar zuciyar Ramadan da kuma Riyyam-nsra suma duk alokaci daya. Kamar kuma yanda Rayyern din yaji azuciyarsa, haka suma sukaji. Shigowarsu cikin falonne kuma, yasa gaba d’aya ahalin Mai-nasara da y’ay’a da kuma jikokinsa dake kewaye dashi, duk suka d’ago kai suna kallonsu. Atake kuwa tsananin mamaki da tu’ajjudi ya bayyana akan fuskar wasu manya daga cikin mazauna falon. Inda suka kafe su Rayyern din da ido, basa ko k’yaftawa, hakan yafaru ne kuma saboda wani tsananin kama da suka hango. Kawu Mustapha ne yadanyi murmushi saboda Kallon da yaga y’an uwannasa nayiwa su Rayyern, wanda kuma shima yasan dalilin da yasa y’an uwannasa ke kallonsu haka. D’an juyowa yayi ya fuskanci y’an uwannasa cikin kuma bayyana farin cikinsa yace. “Manyan bak’i mukayi, domin babban Doctor din da ya shahara, ya kuma yi kaurin sunane da kansa yazo dan duba Malam, Wannan shine Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara.” Yakai karshen maganan yana meyi musu nuni da Rayyern dake tsaye. Ajiyar zuciya suka sauke gabaki d’ayansu tare kuma da had’a baki wajen yiwa su Rayyern din iso. Karasa shigowa cikin falon su Rayyern din sukayi, kana kuma cikin girma da mutumtawa Rayyern ya shiga bawa, manyan mazan dake zaune acikin falon hannu suka soma gaiggaisawa. Kowannensu fuskarsa dauke da murmushi. Bayan kuma sun gama gaisawa da Rayyern dinne, su Ramadan suma suka matso suka gaggaisa dasu. Yayinda Rayyern kuwa ahankali ya sauk’e idanunsa akan fari kuma kyakkyawan Dattijon dake kwance, wanda ayanzu ya soma d’an yunkurin tashi, musamman saboda jin shigowar su Rayyern din. Dattijo ne mai matuk’ar kamala, mutumci da kuma haiba, haka kuma duk da yana da yawan shekaru da y’ay’a, amma hakan baisa tsufansa ya yawaita ba sabida hasken Addini da riƙo da ibada. Idanu Rayyern yadan lumshe tare kuma da budesu alokaci guda, yana me ambaton sunan Allah da ya sauk’ar masa da wata iriyar nutsuwa, acikin y’an mintunonin da basu wuce 5 ba. Su Uncle Mustapha kuwa ganin Malam Mai-nasara dake kishingid’e akan lallausa kuma tattausan sofa, na kokarin tashi zaune ne, yasa cikin tsananin kulawa da kuma kauna suka taimaka masa ya tashi zaune. Idanu Malam Mai-nasara din ya zubawa kyakkyawan matashin saurayin dake dan nesa dashi wato Rayyern. Wanda kuma shima Rayyern din kallonsa yakeyi. Yayinda acikin zuciyarsa yakejin wani irin sanyi, da kuma rauni mai tsananin gaske. Ga kuma wani abu da yakeji na game dukkan mashigan ramin iska dake jikinsa. Yanaji ajikinsa tamkar wata duniya ce sabuwa ya shigo. Yayinda Ramadan da Riyyam dake bayansa suma sukejin thesame irin abunda Hamma Rayyern dinnasu yake ji. Wanda kuma bawai iya sukad’aine sukejin hakan ba, harda shi kansa Malam Mai-nasara, domin kuwa har izuwa yanzu ya kasa dauke idanunsa daga kan Rayyern. Sannu ahankali kuma ya d’aga hannunsa tare dayin alama akan Rayyern d’in yazo kusa dashi. Aikuwa Rayyern din kamar jira yake, cikin nutsuwar da ya zame masa jiki, ya matso kusa da Malam din sosai, hakanne kuwa ya bawa Malam din daman kamo hannun Rayyern d’in ya rik’e acikin nasa. Nannauyar ajiyar zuciya mai sauti suka sauƙe atare shida Rayyern d’in, saboda had’ewar hannayensu waje d’aya shiya haifar da daidaiton bugun zuciyoyinsu. Kai Dr. Rayyern ya d’an rank’wafar cikin kuma muryarsa mai tsananin taushi, dake bayyana nitsuwa da mutumtawarsa ga Dattijon mai tsananin karama a idanunsa yace. “Malam barka da rana, ya ƙarfin jikin naka?” Idanu Malam Mai-nasara ya lumshe tare dajin wani irin sanyi acikin zuciyarsa, wanda lokaci guda ta d’auki soyayyar Rayyern din ta ajiye awani waje na musamman. Tabbas fuskar Rayyern din ta ratsa shi, Yayinda ta kuma so tono masa wasu abubuwa da suka faru a shekarun baya masu yawa. Sake rik’e hannun Rayyern din da kyau yayi, tare da cewa. “Alhamdulillahi jikina da sauki, kaine Dr. Rayyern Basheer Muhammad Mai-nasara ko?” Kai Rayyern ya jinjina masa, tare kuma da cewa. “Eh Malam ni ne Dr. Rayyern Basheer Muhammad Mai-nasara.” Ya kare maganar yana me fadada murmushin dake kwance akan fuskarsa, tayaya ma zai iya boye farincikin da yake ciki ayau din? Bayan gashi ga mutumin da yake matuk’ar so da kauna, fiye da duk sauran Malama’n da yake sauraran wa’azinsu, Dattijon da yake son gani akullum, kana Dattijon dako kallonsa yake acikin tv ko laptop yakanji sanyi acikin zuciyarsa. “Alhamdulillahi! Masha Allah!! Lallai godiya ta tabbata ga Ubangijin talikai!!!” Malam din ya fad’a adai-dai lokacin daya sauke idanunsa akan Ramadan da kuma Riyyam, wanda suke gaidashi. Fuskarsa cike da tsananin mamaki ya amsa musu, tare kuma da dawo da kallonsa ga Rayyern dake zaune agabansa, har yanzu kuma suna rik’e da hannun juna. Rayyern kuwa ganin irin Kallon da Malam din keyi masa ne, yasashi yin ƙasa da kanshi. Malam Mai-nasara kuwa, fuskarsa dauke da mamaki yace. “K’annanka ne?” Kai Rayyern din ya jinjina, cikin halinsa na girmamawa kuma yace. “Eh k’annena ne, wannan Ramadan, k’aramin kuma shine Riyyam.” Idanu Malam Mai-nasara yadan lumshe hade kuma da jinjina kansa, Cikin yanayin gamsuwa kuma yace. “Masha Allah. Allah Ubangiji ya d’ayyabaku ya kuma ci gaba da rayaku cikin aminci dajin dad’i amman Riyyam kuma sunane cikekke!?.” Da “Ameen.” Gaba d’aya falon suka amsa. Kana Ramadan da Rayyern kuma suka ɗan kalli, Riyyam-nsra. Murmushi ya ɗanyi kana yace. "Cikekken sunan *Zakariyyah* ne". Murmushi Malam dasu Uncle Mustapha sukayi, wato sunan gayu ko?. Malam yace cikin barkwanci. Murmushi ya kumayi tare da gyaɗa mishi kai. Gyara zama Rayyern yayi, tare da fuskantar Dattijon, kana atausashe yace. “Malam yanzu inada inane yake maka ciwo? sannan yakakejin yanayin ciwon naka idan ya tashi?” Idanu Malam Mai-nasara yad’an lumshe, tare kuma da tankwashe kafafunsa waje daya. Ahankali kuma yace. “Sau dayawan lokuta nakanji ciwon kaine kawai maitsanani, sai kuma jiri amma ba wani mai yawa ba, baya ga haka kuma sai k’afafuna da idanuna wanda nakejin watarana sunayi min nauyi, da kuma zazzab’i, amma dai yanzu kam Alhamdulillah jikin nawa isashshen k’arfi ne kawai babu.” Ajiyar zuciya Rayyern ya sauk’e, tare da kuma gyara zamansa, kana anutse yace. “Eh kamar dai yadda su Dr Sulaiman suka shaida min cewa. Hawan jini da kuma ciwon sugar ne ke damunka Malam a binciken da sukayi maka, kuma hakanne. Domin shi yawan ciwon kai da kuma jiri hadi da zazzab’in da kakeji duk alamane na hawan jini, sannan kuma shi yanayin ciwon kan yakan iya sauyawa, domin watarana zakaji ciwon agefen kanka ta b’ari d’aya ne, watarana kuwa zakaji ciwon kan asaman goshinka ne, wanda idan yayi karfi har yakan iya sauk’owa ya rik’e jijiyoyin idanun mutum, wannan duk cases ne da hawan jini kan haifarwa, shi kuwa nauyin da kakejin k’afafu da kuma idanunka nayi da yawan haɗa zufa, suma alamace ta ciwon sugar, wanda kuma suma bako da yaushe ne suke tashi ba, domin zaka iyajin hakan da safe, kafun zuwa rana kuma sai kaji abun ya lafa, baya ga haka kuma zaka iyajin hakan da yamma idan maraice ya rufa, sannan kuma akwai yawan fitsari da zakaji kanayi akai akai, koda kuwa ace baka sha wani ruwa mai yawa ba da jin kamar wani abu na bin jikinka...” D’an numfasawa yayi kana ahankali ya sake rike hannun Malam Mai-nasara daya zuba masa idanu yana mai gyaɗa mishi kai alamun duk abinda ya faɗa hakane. Atausashe yace. “Insha Allah zaka samu sauki Malam, sannan kuma ciwon naka bai wani zama abun tashin hankali ba, saboda mafi akasarin mutane suna samun hakan idan girma ya cimmusu, kamar dai kai ayanzu daka tara manyan y’ay’a da jikoki, akwai kuma magunguna da zan rubuta maka, wanda zasu taimaka k’warai wajen kawo maka Sauk’in ciwon, sannan kuma akwai kalolin abincin da ya kamata ace su zakana ci, saboda zasu bada nasu taimakon sosai wajen Inganta lafiyar jikinka.” Gaba d’aya falon kai suka jinjina cike da gamsuwa akan abunda Dr. Rayyern din ya fad’a. Shikuwa Dr.Rayyern abun rubutu ya ciro daga cikin aljihunsa, tare da wata yar farar takarda. Rubutu yayi asaman takardar bayan kuma ya kammala rubutun ne yayi sign acan k’asan takardar. Alhaji Ibrahim wato babban dan Malam Mai-nasara din dake gefe kad’an ya mik’awa takardar, tare da cewa. “Way’annan sune magungunan da ya kamata yana shansu a koda yaushe, Insha Allah zai samu lafiya nan bada jimawa ba. Karb’an takardan Alhaji Ibrahim din yayi, tare da yiwa Rayyern d’in godiya maitarin yawa. Saidai kuma baikai ga ida godiyar tasa ba, muryarsa ta mak’ale a kasan makoshinsa, sakamakon daura idanunsa da yayi akan sign din da Dr. Rayyern din yayi acan kasan paper’n. Idanu ya k’urawa sign din cike da ɗan mamaki hadi da al’ajabi, ya d’ago ya kalli Baban nasu, wato Malam Mai-nasara da kuma sauran y’an uwansa. Cikin tu’ajjudin da yake ciki dinne kuma direct ya mikowa Malam Mai-nasara din takardan. Aikuwa Malam Mai-nasara na karb’an takardar idanunsa suka sauk’a akan signing din dama salon rubutun kanshi. Cike da mamaki wanda har saida ya kasa b’oye hakan ya d’ago ya kalli Rayyern. Rayyern kuwa da Sam bai fahimci komai adangane da irin Kallon da yaga sunayiwa takardar ba, kwata kwata sam baidamu ba. Saima juyowa da yayi ya kalli Ramadan. Cikin kuma bada umarni yace. “Yauwa Ramadan yanzu amshi takardar sunayen magungunan Malam ɗin kaje ka d’auko masa a pharmacy.” Kai Ramadan ya jinjina tare da cewa. “To.” Cikin abunda bai wuce 2 minute ba kuwa Uncle Mustapha ya miƙawa Ramadan takardar sunayen magungunan. Hakan yasa batare da wani b’ata lokaci ba, Ramadan din ya juya ya tafi, dan d’aukowa Malam din magungunan da zai nasha. Bayan fitar Ramadan dinne kuma, Naseer ya kama Hannun Riyyam-nsra suma suka fice daga cikin falon. Haka kuwa mutanen dake cikin falon suka dinga fita daya bayan daya. Hardai saida falon ya rage daga Malam Mai-nasara sai Rayyern da kuma Uncle Mustapha, Alhaji Ibrahim, da kuma dayan kaninsu mai bimusu Alhaji Abdallah. Alhaji Abdallah’n dinne kuma ya kalli Dr.Rayyern kana cikin sakin fuska yace. “Masha Allah Dr. Rayyern munji dadin zuwanka k’warai, mun kuma gamsu da duk wasu bayanan da kayi mana, amma kafun zuwan ka da har mun gama yanke shawarar cewa zamu fitar da Malam din waje, can k’asar Egypt, Saboda ya samu kyakkyawar kulawa, amma dai yanzu Alhamdulillah tunda ga kanan, domin dama da way’anda zamu gani acan din da kuma kai d’in duk abu daya ne.” Murmushi Rayyern yayi, kana anutse yace. “A’a basai an fitar dashi ba, sauk’i na Allah Ne kuma Insha Allahu zai samu lafiya.” “Allah Yasa.” Duk suka amsa cike da gamsuwa. Yayinda Uncle Mustapha yad’an muskuta had’i da cewar. “To Dr. Rayyern ka fad’amana kud’in maganin sainayi maka transfer ko.” Kai Rayyern d’in ya girgiza, tare da hade kafafunsa waje daya ya tankwashe su. Hannunsa na dama ya d’aura akan na Malam d’in, Cikin yanayin mutumtawa yace. “A a ku barshi banzo nan dan abiyani ko sisin kobo ba, haka kuma duk wani magani dana sa Ramadan ya kawowa Malam banyi hakan dan abiyani ba, Malam mahaifi ne agareku ni kuma Kaka ne agareni, saboda haka komai da nayiwa Malam nayisa ne saboda matsayi da kuma darajarsa, fata na dai shine Allah Yabashi lafiya.” “Ameen Summa Ameen.” Gaba ki d’ayansu suka had’a baki wajen fad’an hakan, Yayinda suka sake shaida mutumci, karamci da kuma kyakkyawar tarbiyar da Rayyern din ya samu, Lallai acikin zuk’atansu sun gamsu da cewar Rayyern d’in mutumin k’warai ne, wanda kuma ya taso a hannun iyayen k’warai. Shikuwa Malam Mai-nasara murmushi ne ya fadada akan fuskarsa, domin kuwa alokacin da yaji Rayyern din ya kirasa da sunan Kaka, bakaramin sanyi yaji acikin zuciya da gangar jikinsa ba, Lallai Tabbas shima ya d’aukesa amatsayin jikansa. Hannunsa na dama ya d’aura akan Rayyern d’in, Cikin kuma yanayin nuna godiyarsa agaresa yace. “Masha Allah Allah Ubangiji yayi maka al'barka Rayyern, ya tsare gabanka da bayanka, ya kuma dauwamar da farinciki acikin zuciyarka da na ahalinka.” Da “Ameen.” Duk suka amsa. Inda Malam din ya sake d’ago Kai ya kalli Yayan nasa, cikin aminci yace. “Tabbas Dr. Rayyern ya gwada mana karamcinsa, saboda haka kamar yanda ya daukeni amatsayin Kaka nima na daukesa amatsayin jikana, zan kumayi masa kyauta da karamci kamar yadda yayi mini, Ibrahim shiga cikin dakina, ka bude wajen da nake ajiye kayana na musamman ka d’auko masa sabbin alkyabba da hirami.” Murmushin farinciki dukansu sukayi inda Alhaji Ibrahim kuwa ya mik’e cikin girmama maganan mahaifinnasu kaitsaye ya nufi dakin Malam Mai-nasara din dake cikin falon. Har yakai bakin kofarne kuma ya juyo tare da Kallon mahaifin nasu, kana aladabce yace. “Malam alkyabba da hiramin guda nawa za’a d’auko masa?” “D’auko masa kala bakwai, saboda zasu fi isansa domin zai saka guda daya acikin kowacce rana, Kaga kenan kala bakwai zasu isar masa har sati guda yana sawa yana tunani.” Kai Alhaji Ibrahim ya jinjina, tare da bud’e kofar dakin mahaifinnasu ya shige. Cikin abunda bai wuce mintuna goma ba, kuwa sai gashi ya dawo hannayensa dauke da manya manyan alkyabba, da hirami irin wanda limaman makka suke sakawa ajikinsu, alkyabbu ne masu kyau da kuma tsadar gaske. Mikawa Malam din Alhaji Ibrahim yayi, Yayinda shikuwa Malam din ya mikawa Rayyern dake zaune, wanda fara’a da kuma farincikinsa ya kasa b’uya. “Wannan kyautace agareka Rayyern domin kuwa nasan zasuyi maka kyau sosai, shigace irin ta kamala.” Kai Rayyern ya jinjina cike da tsananin jin dad’i kuma yace. “Godiya nake maitarin yawa Malam, Allah ya kara arziki da lafiya.” “Ameen.” Malam Mai-nasara din ya amsa cikin jin dadi.” Dai-dai lokacin kuwa Ramadan Riyyam da kuma Naseer suka shigo cikin falon. Karasowa Ramadan yayi ya mik’awa Hamman nasu babban ledan magungunan dake hannunsa. Karb’an magungunan Rayyern yayi, hade kuma da mik’awa Ramadan alkyabba bakwai din daya same su amatsayin kyauta daga Malam. “Kyauta na samu daga wajen Malam.” Yafad’a adai-dai lokacin daya gama mikawa Ramadan din kayan. Idanu Ramadan din yadan zaro fuskarsa cike da tsananin farinciki yace. “Masha Allah Malam godiya muke.” Hararan wasa Rayyern ya watsa masa, kana cikin sigar tsokana yace. “Godiya muke kaman yaya, nawa nefa ba namu ba.” Dariya kusan gaba dayansu suka sa, ciki kuwa harda Malam. Riyyam kuwa jin hakanne yasashi, d’an shagwab’e fuska, tare da matsowa kusa da Malam din yace. “Ayyah Kaka Malam toni Ina nawa alkyabban.” Murmushi Malam Mainasara yayi, tare dasa hannu ya shafa kan Riyyama din. “Kaima taka tananan tana jiranka amma sai ka ƙara girma, yanzu idan na baka yawa zasuyi maka.” Malam din ya fada da matuk’ar kulawa. Aikuwa Riyyam kamar dama abunda yake jira kenan, cikin yanayinsa na sakewa daya zame masa sabo, ya kalli Ramadan tare da cewa. “Yeh za’abani ba za a bawa wani ba.” Ya kare maganan yana meyiwa Ramadan din gwalo. Abunda ya matuk’ar bawa su Alhaji Ibrahim dariya kenan. Shikuwa Ramadan durk’usawa agaban Malam din yayi, cikin sigarsa ta shagwab’a shima yace. “Shikenan na fahimta yanzu wariyar launin fata za’a nunamin, da farko an bawa Hamma Rayyern alkyabba, yanzu kuma an shafa kan Riyyam amma ni ba a shafa nawa ba.” Ayanzu kam Dariya Malam Mai-nasara yayi, har saida hakwaransa suka bayyana, cikin matsanancin kauna da kuma soyayyar yaran da yakeji acikin ransa, ya sa hannu ya dan jawo Ramadan din jikinsa. Kansu ya shafa dukansu tare dayi musu addu’a, domin hakanan yakejinsu acikin zuciyarsa tamkar jikokinsa na gaske. Rayyern kuwa duk abunda kannen nasa sukayi kallonsu kawai yakeyi, bayan kuma ya gama bare magungunan da ya kamata ace Malam din yasha ne, yasa Naseer ya miko masa bottle water marar sanyi. Da kasan ya bawa Malam magungunan yasha. Tare dayiwa su Alhaji Ibrahim bayanin yanda akullum Malam din zaina shan maganinsa. Godiya sukayi mishi sosai, ganin da yayi kuma lokaci yadan ja sosai ne, yasa shi kallon su Ramadan tare da cewa su tashi su tafi. Cikin aminci sukayi wa Malam din sallama, inda Rayyern ya shaida masa cewar zaidawo ya sake dubashi. Koda suka tashi tafiya kuwa har wajen motocinsu Uncle Mustapha da kuma Alhaji Abdallah suka rakasu. Basu koma cikin gidan ba kuma harsaida suka ga tafiyansu Rayyern din. Daga b’angaren su Raayyern kuwa kaitsaye gida suka nufo. Direct Rayyern dakinsa ya wuce, saboda yana son yin wanka, sannan akwai kuma wani aiki da zaiyi a laptop d’insa. Yayinda su Ramadan da Riyyam kuwa, anan falo suka zauna inda Mom ta kawo musu abinci suka ci. Bayan sun gama cin abincinne kuma suka wuce masallaci danyin sallan azahar, ciki kuwa harda Rayyern wanda ya sanja shigarsa zuwan wata farar jallabiya. Jannart. Kwance take akan makeken gadonta, wanda akoda yaushe yake shumfud’e da lallausan bedsheet na alfarma. Irin kwanciyarnan ta rubda ciki tayi, Yayinda ajikinta take sanye da wata baby gown marar nauyi. Lumsassun Idanunta ta ware ahankali tare kuma da sauke wani ajiyar zuciya mai Cike da tarin damuwa. Lallai Tabbas tana da buk’atar y’anci acikin rayuwarta, rayuwar da har yau ta kasa tantance wacce kalar rayuwa ce, rayuwar da kwata kwata babu haske acikinta sai tarin damuwa, kunci da kuma kadaici. Mirgina wa tayi a hankali kana taci gaba da tunani. Yayinda akowanni kwanan duniya da irin kalubalen da take fuskanta, acikin kowanni sa’a kuwa zuciyarta na bugawa da tarin tsananin tsoron abunda zaije ya dawo. Lallai Tabbas tana da buk’atar haske acikin rayuwarta, haka kuma tana da buk’atar abokin rayuwar da akoda yaushe zai debe mata kewa, Sam arayuwarta batasan wani abu Waishi ingantaccen farinciki ba, akullum damuwa kawai da tsoro ta sani. Haka kuma akowani bayan minti guda tsoronta yakan rub‘anya, tare da mummunan bugun zuciya akan abunda Yayanta Junaid ke neman aikata mata. Saudayawan lokuta takan tambayi kanta, cewar shin Ya Junaid wani irin d’an uwane? Meyasa akoda yaushe bashi da fata ko buri saina keta haddinta? Tabbas tunaninta yakan neman watsewa aduk lokacin da ta tuna cewar Ya Junaid din yayanta ne Uwa daya Uba daya. Shin Meyasa Rayuwa take garari da ita? Karar wayarta dake aje bisa bedsite ne ya katse mata duk wani tunanin da takeyi. Ahankali tasa hannu ta share dan guntun hawayen dake kwance agefen Idanunta, wayartata dake ta faman tsuwa ta dauka, ganin kuma sunan Salman ne ke yawo akan screen din wayar yasata picking da dan hanzari. “Y’ar Hutu wato kinanan kina hutawa agida ni kuma kinbarni da wahalan aikin ki ko.” Cewar Salman. Itakuwa Idanunta ta lumshe tare da d’an gyara kwanciyarta. Cikin muryarta da tayi sanyi sosai tace. “Sorry Salman gaba d’aya yau banajin karfi sosai ajikina ne, Impact ma nina fara sarewa da wannan aikin wallahi, I’m tired because mutumin nan kamar bazamu samu daman ganinshi ba.” Murmushi Salman yayi tare da d’an gyara zamansa kana cikin son bata karfin guiwa yace. “No Jannart don’t stress your self, Insha Allah yau zamu had’u dashi, kinsan na samo mana information akansa, so Yanzu dai anjima kishirya muje hospital d’insa, Insha Allah zamu samu ganinsa.” Idanunta dake alumshe ta bud’e tare da sauke ajiyar zuciya. “Thank you so much Salman Insha Allah zan shirya by 3 pm sai muje, zanzo office saimu tafi aboye batare da kowa ya sani ba.” (Hattara garemu iyayen yara, yawan tsaro baya hana yaranmu yin abinda suke so. Tsananta addu'a da jawo yara a jiki yafi tsananta tsaro da zafi), “To saikinzo.” Salman din ya fada tare da kashe wayar. Itakuwa Jannart bayan ta ajiye wayartata agogon dake sakale ajikin Bangon dakin ta kalla. Wanda ya nuna mata 2:30 pm. Zuro kafafunta kasa tayi daga kan bed din, batare da ta tsaya sanya ba kuwa ta shige bathroom danyin wanka. Sanin da tayi cewar basu da enough time ne kuma yasa bata wani bata lokaci awajen yin wankan nata ba. Koda ta fito mai kawai ta shafa ajikinta, sai kuma powder and oil lipstick. Yayinda tabi zara zaran eye lashes dinta da mascara. Bayan kuma ta feshe jikinta da sassanyan body spray ne. Ta karasa gaban Sif din kayanta, inda ta zaro wani dogon wandon pallazo white and white colour roba t shirt wanda yake da ɗan fadi kaɗan ta kasa kuma yazo kusa da guiwarta. Cikin nutsuwa ta sanya kayan ajikinta, tare da daukan wani hill shoe mai kalan blue ta saka ak’afanta, kana kuma ta yane kanta da wani dan vail shima mai kalan blue. Akan tsintsiyar hannunta kuwa wani anklet ta saka mai kyau. Wanda ya sake kawata kyaun kwalliyar tata. Murmushi ne ya dan bayyana akan fuskarta, saboda Kallon irin kyaun da tayi acikin madubi, Yayinda kayan jikin nata kuwa sukayi matukar amsarta tana matuƙar son ƙananan kaya, ta gaza gano illar sasu a ko ina. Tabbas ayau din ko makiyinta bazaiyi mata kallo daya ya dauke kansa ba sosai kam tayi kyau. Wata yar madaidaiciyar handbag blue colour ta rike ahannunta bayan ta rike wayarta ahannunta na dama ne kuma ta juya ta fice daga cikin dakin. Anan Cikin falo ta samu Momy da kuma Abdull zaune. Ganin ta cikin shiri da sukayi ne kuma yasa Momy cewa “A’a Jannart fita zakiyi ne.” “Eh Momy zanje office amma bazan jimaba Zan dawo Insha Allah.” “To adawo lafiya” Da Ameen ta amsa, Yayinda Abdull kuwa yace idan tazo dawowa ta kawo masa abundadi. Da to kai ta amsa masa kana tasa kai ta fice daga cikin falon. Tana fita compound din gidan kuwa, kattin samudawan guard dinta suka tattaso. Har acikin ranta Allah Yasani kwata kwata batason wayanann mutanen da suke tsaronta, saidai kuma babu yanda ta iya. Haka ta shiga mota suka fice daga cikin gidan. Direct Nasarawa G.R.A ta nufa inda anan wajen aikin nasu yake. Suna isa kuwa ta fito daga cikin motar, kaitsaye ta wuce cikin Arewa 24 din ɗan madaidacin ma'akatane, wanda yake kamar irin manyan gidajen nan ne na al'farmar. Sam wurin gidan TV'n bai cika girmaba, dan bazaifi wani gidanba, ma, sai dai zubi da tsarin wurin shine mai tafi da hankalin mai kallo, kota ina ka wulga shuke-shuke ne masu kyau da ɗaukar hankali kamar a kasashen turawa, Gate ɗinsu daya ne ta inda ka shiga ta nan zaka fita, can ciki kuma Office-office. Masu kyau ma dai-dai-ta na al'farmar da hall ɗinsu sai ɗakunan haska shirye-shiryen su. Duk inda ta gilma kuwa sai abokan aikinta sun bita da ido, Yayinda kowa ke yaba irin baiwar kyau da Allah ya bata manya daga ciki irinsu Aunty Fa'iziyya D Sulaiman kuwa ƙuruciyarta suke gani a fili da illar shigarta da ta meda jikinta. Direct office dinsu ta wuce kaitsaye. Inda ta samu Salman da kuma Aysha Lawan suna zaune. Nanfa ta tsaya gaisawa da Aysha kawartata. Acan gidansu Rayyern kuwa. 3:00 am dai-dai ya fito daga wanka, inda ya shirya kansa cikin wani black tracksuit, masu kyaun gaske, da suka matuk’ar amsar jikinsa. Yayinda ak’afansa kuwa ya saka wasu had’add’un sneakers shoe masu kyau da taushi. Bayan ya gama kimtsa kansa ne kuma, ya shafa wani irin fitinannen turare mai tsananin kamshi. Bud’e drawer’nsa yayi. Shiru ya ɗan Tsaya yana mai kallon Alkyabbun dake jere a saman kayanshi. Haka nan yaji yana son gwada sa alkyabbar a jikinsa yaga ya shigar zatayi mishi. Numfashi ya ɗan fesar a hankali inda anutse ya zaro daya daga cikin alkyabbun da Malam Mai-nasara ya bashi. Warware alkyabban yayi tare da soma kare mata kallo baƙace mai kyau irin mai sheƙin nan gefe da gefenta an ƙawayashi da zare golding, kai ya jinjina saboda shi kansa ya yaba da kyau da kuma haduwarta, musamman daya fahimci cewar ba karamin kudi aka saka wajen sayan duk alkyabbun ba fuska ya dan yamutsa dan sun cika nauyi. Addu’an sanya sabon kaya ya karanta, "Alhamdulillahil laxee kasani haxal saubah warazaƙani min gairi hauli minni walaƙuwah". dai-dai lokacin daya ke daura alkyabban akan kayan dake jikinsa. Tare kuma da daukan harami ya daura akansa. Ya Allah! Bakaramin kyau Dr.Rayyern Mai-nasara yayi ba, alokacin daya gama kimtsa kansa Cikin alkyabbar. Kyau yayi sosai da sosai, wanda shi kansa saida ya sake yiwa Allah Godiya daya halittosa amatsayin bil’adama musulmi mai shiga ta kamala. Koda ya kalli kansa amadubi numfashi ya ɗan fesar a hankali saboda yanda yaga ya fito tamkar Limami. Wayarsa da kuma wata yar jaka dake gefen gadonsa, wanda ya kusan cika cikinta da chocolates ya d’auka, tare da rik’e jakan ahannunsa, kaitsaye ya fice daga cikin dakin. Ahankali yake saukowa daga kan steps d’in...! Uhum muje-muje dai sunan wata mota, lbrin yanzu anka fara. By *GARKUWAR FULANI* 11/15/21, 7:20 PM - Auntyna: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *TUBALI* PAGE 12 NA *AYSHA ALIYU GARKUWA* *FREE PAGE ne* *Littafin TUBALI na kuɗine special Group 1k ƙaramin group 500 kacal 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU,sai ki turo min shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276. Ko kuma katin MTN* Fawal beauty parlor sunai muku albashir da bude gidan Mata wato kigyara da kanki👩🏻‍🦰 da cewa suna gabatar da aiki na zamani kamar su gyaran jiki, spa kenan gyaran fuska wato facial,gyaran Kai, hair style , gyaran kafa pedicure,gyaran hannaye, manicure kitso,lalle ja da bakki,ba'a barsu abayaba suna saida kayan gyaran aure, turaruka,man shafawa, suna kwalliya wato makeup,turaren wuta, humrah,kulaccham dama abunda Baku sanshiba wato maida tsohuwa yarinya akankanin lokaci😄iya kudinka iya shagalinka💃kudai ku hanzarta zuwa ga wannan gida na mata zallah (FAWaL BEAUTY PARLOR) Address: Main gate na fire service jimeta, opp sixty plaza. kada kubari abaku labari😍 munai muku maraba a koda yaushe Mata yan kwalisa mace sai da gyara , yar uwa bora ba sunanki kizama mowar mai🏨 da taimakon FAWAL BEAUTY PARLOR 👩🏻‍🦰da kudinki qalilan kifita sab abunki ki baza kamci mai kama jiki. Gamai buka contact CEO FAWaL BEAUTY PARLOR kan 09033901035 or 08078809930 sai kunzo, our time services from 8:am to 7pm, Monday to Saturday/ Sunday 10am to 6pm🪞🎁🛒🛍️🤝🏻 Kafad’anta wanda ya sauk’o ya rufe bayanta. Batare kuma daya sake cewa komai ba, ya juya fuskarsar nan amurtuk’e. Bottle water da kuma phone d’insa ya d’auka, kana ya zo ya wuce ta gefenta. Itakuwa Jannart Idanunta ta rumtse da k’arfi, tare dasa hakwaranta ahankali ta cije lips d’inta. “Duk wata macen da tasan ciwon kanta, bata yawo ahaka kamar yanda ke kikeyi, sannan mata da yawa suna sirrranta kansu, amma ke kina bayyana k’azantarki.” Ta maimaita maganar daya fad’a mata d’in, wanda yasa tajin zafi har acikin zuciyarta, cikin kuma k’unan rai da b’acin ran kalaman nasa da wata iriyar fitinenneyar kunya mai masifar kashe ido da jiki tace. “Waye shi da har yake fad’amin irin way’annan bak’ak’en maganganun, meya gani ajikina haka? Sannan akan me zai rufamin wannan abunnasa me shegen mayataccen k’amshi?.” Ta fad’i maganar tana me d’an zame alkyabba’n ajikinta, dare da juya bayanta ta kalli jikinta, saboda tanason sanin mai ya gani ajikinta da har zai fada mata irin wannan maganan. Karab kuwa Idanunta suka sauka akan jinin, dake jikin farin wandon ta, wanda da alama kuma daga jikinta jinin ya fito. Idanunta tad’an zazzaro waje cike da mamaki da wata sabuwar kunya tace. “What period dina kuma? Innalillahi Wa’inna Ilaihirraju’un Period at this time, Oh My God!!” Ta fad’a da d’an k’arfi, cikin kuma muryar dake bayyana tsananin takaicinta, saboda Sam bata tab’a tunanin period din nata zaizo a irin lokacin ba, kasancewar tasan da sauran lokacin daya rage masa, har na tsawon kwana uku kafun yazo. “But amma why yazo yanzu? Meyasa Meyasa?” Tayiwa kanta tambayar tana me b’ata fuska, domin sam bataji dadin abunba, cikin sauri kuma taja alkyabban daya rufa mata din ta sake rufe jikinta. Lokaci d’aya kuma taji wani irin matsanancin kunya, da takaicin kanta na taso mata, duk da kuwa tasan cewar ba laifinta bane, period dinne ya sanja time wanda ko wacce mace kan iya fuskantar hakan musamman in tashin hankali da tsinkewar zuciya ya riski mutum, amma tayi matuk’ar takaicin ganin jinin period dinta da wani da bata sani ba yayi. Tabbas taji kunya yanzu da wani idon zata sake kallonshi? kuma shi dinma ayanzu wani irin kallo zainayi mata karo na forko a rayuwarta da taji haushin irin shigar da takeyi. “Wata macen da batasan ciwon kanta ba, bata iya ankilta kantaba.” Zuciyarta ta bata amsa atake. Idanunta ta rumtse cike da takaici. Dai-dai lokacin kuwa Salman Ya ware idanunshi a kansu tare da dawo da kallonsa gareta. Fuskarsa dauke da d’an mamaki yace. “Ha’a Jannart lafiya kuwa kizo mutafi mana..” Sauran maganar tasance ta mak’ale, alokaci da yaga jikin Jannart din lullub’e da Al'kyabban, da dazu ya ganta agefen mutumin da har yanzu baisan sunanshi ba. Jannart kuwa fuska tad’an marairaice, kana cikin sanyin jiki ta soma takowa zuwa inda Salman din ke tsaye. “Jannart wannan Al'kyabban fa? Kin sanshi ne?”. Salman din ya tambaya, saboda yayi mamakin ganin ya sawa Jannart din da al'kyabban k’warai. “Shi ne ya bani.” Jannart din ta fad’a kaitsaye, bisa kuma sanin rashin dacewar Salman din yasan gaskiya abinda yasa yasa mata, shi yasa ta fad’a masa hakan, batare kuma da ta bada wata kofar da Salman din, zaiyi mata wata tambayar ba ta soma tafiya. Salman kuwa idanunsa ya zuba mata, yana mai Kallon yanda al'kyabban tayi mata matuk’ar kyau duk da tayi mata yawa, saidai kuma Jin tace wancan mutumin ne ya bata, yasa shi jin babu dadi acikin zuciyarsa. Saidai kuma bashi da ikon bayyana hakan. Ab’angaren Dr. Rayyern kuwa Koda ya fito daga wajen wasan, kaitsaye Inda motarsa ke fake ya nufa. idanun y’an tsirarun mutanen dake wajen ke kansa, duk da cewar kuwa basusan shi din asalin waye bane, amma kallo daya zakayi mishi kafahimci cewa mutum ne mai zarra. Baya ga haka kuma ga tarin baiwar kyau da Allah Yayi mishi. Tun kafun ya karasa isowa Parking lot din wajen kuwa, Hadi driver’nsa ya fito tare da bud’e masa k’ofar motar. Yana shiga kuwa driver’n ya rufe k’ofar, tare da zagayawa cikin sauri ya tada motar. Suna ficewa daga Parking lot din kuwa, su Jannart na isowa. Nanfa kallo kuma ya dawo kan Jannart, domin al'kyabban dake jikin nata ya k’ara bayyana asalin kyau da kuma kawata shigar dake jikinta da jawo hankalin mutanen dake wurin kanta. Murfin motar Salman din ta bud’e, tare da zagayawa gidan baya ta zauna, wanda tayi hakanne kuma, saboda idan sunzo shiga cikin gidan tv’n nasu, kada masu tsaronta su ganta, ko kuma wani wanda yasanta . Salman ma shiga cikin motar yayi, tare da yiwa motar keyi suka fice daga cikin wajen wasan gaba d’aya. Jin sun hau titi ne kuma yasa ta lumshe Idanunta, tare da sauke wata irin ajiyar zuciya mai karfi. Lallai ayau din tana cikin tarin damuwa tsananin kunya da kuma takaicin kanta da kanta. Yayinda acikin zuciyarta kuwa take fatan Allah Yasa. Dr Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara din yazo, kamar yanda wancan yayi musu alkawari, kan. Numfashin ta fesar a hankali tare dayin mgnar zuci. "Allah yasa kada in sake haɗuwa dashi har abadan, wannan kayan kunyar ina zan kaishi." Tayi mgnar cike da kunya. “Idan shi Dr Rayyern Mai-nasara kuma baizo bafa, shikenan na rasa aikina?” Tayiwa kanta tambayar, dayasa duk taji zuciyarta ta Karye. Salman dake driving, wanda kuma tun dazu yake satan kallonta ta cikin madubi ne yace. “Munsamu full confidence din samun daman yin hira da Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara, amma kuma sai naga kamar bakya cikin farinciki, kamar akwai wani abu dake damunki, please ki fad’amin wacce irin damuwa ce haka ke damunki?”. Idanunta dake alumshe ta bud’e, tare kuma da k’ak’alo murmushi ta daura akan fuskar ta. “Ina farinciki mana Salman, Ina cikin farinciki Tabbas, saidai bansan me yasa ba zuciyata keson sanyamin wasu/wasi, Ina fargaban kada ace wancan mutumin raina mana hankali kawai yayi.” Ta fad’i hakan tana me gyara zaman al'kyabban jikinta. Salman kuwa jin hakanne yasashi yin Murmushi, cikin son karfafa mata guiwa yace. “Karki damu Jannart Insha Allah zakiyi hira da Dr Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara, domin na tabbata wancan mutumin da muka hadu dashi awajen wasan polo bazaiyi mana karya ba, Lallai nagamsu akan cewar yasan shi, ki duba da kyau shima ai daga ganinsa ba karamin mutum bane, duk da kasancewarsa matashi amma yayi ruwan mutane masu kamala da dattaku” Maida idanunta tayi ta lumshe, batare kuma da ta sake cewa Salman din komai ba, ta shiga fesar da numfashi ahankali. Domin zuwa yanzu zuciyarta tatafi wani waje na daban. Lumshe idanun nata da tayi kuwa, yayi dai-dai da lumshe idanun Dr Rayyern Mai-nasara, dake zaune acikin motarsa. Gaba d’aya ya yamutsa fuskarsa, saboda yanda yakejin zuciyarsa na d’an tashi kad’an kad’an. Tabbas jinin da yagani ajikin yarinyar ya b’ata masa rai, Yayinda kuma yasa shi jin wani irin takaici had’i da tashin zuciya. Kwata-kwata arayuwarsa bayason ganin wani abu daya shafi jinin sirrin mace shiyasa ya wadata asibitin sa da likitoci mata da zasu iya lura da ɓangaren haihuwa Allah ya sani bai son ganin jini. Ayanzu kuwa idan akwai abunda ke bashi matuk’ar takaici, To bai wuce yanda yarinyar ta jawo ya shiga harkarta. D’abi’arsa ce baya shiga harkar kowa, more especially ma mata, sometimes bayan Uwa mahaifiya yakanji babu wata alaka da zai iya kullawa da wata Mace awaje ta daban, sai gashi bisa dole wata can ta shigo harkarsa. Wanda kuma yayi imani cewa badon sanin rashin dacewar barinta ta tafi a haka da jini ajikinta ba, To da bazai tab’a bata al'kyabbarsa mai matuk’ar daraja da kyau ta sanyawa jikinta dake abude ba, domin ai bashine yace tana yawo haka babu hijab ba. Shidai kam Sauda yawan lokuta yana mamakin, yanda wasu matan ke yawo haka sakaka, babu wata kulawar kirki da suke bawa kansu ina iyayensu?. Yar gajeriyar tsuka yaja, tare da bud’e idanunsa. Dai-dai lokacin kuwa suka iso cikin farfajiyar katafaren asibitin nasa. Anan cikin babban parking lot, Hadi driver yayi parking motar. Yana gama dai-dai-ta parking din motar, kuwa Dr Rayyern ya bud’e murfin motar ya fito, fuskarnan tasa kuwa babu alaman murmushi akanta. Dan Kallon Hadi driver din yayi, kana cikin yanayin dake bayyana, rashin iya tsawaita maganarsa yace. “Kaje gida ka huta idan na tashi zanyi driving din da kaina .” Kai Hadi ya jinjina, kana cikin girmamawa yace. “To Ranka ya dad’e nagode.” Karb’an makullin motar yayi, batare kuma daya sake cewa Hadin komai ba, ya kutsa kansa cikin asibitin. Saboda mood din daya samu kansa aciki ne kuma yasa, ko iya amsawa tarin ma’aikatan dake gaishesa baiyi ba, kaitsaye ya wuce office d’insa. Yana shiga cikin office dinnasa kuwa, ya murzawa kofar key. Saboda ayanda yakejin kansa kwata kwata bayason damuwa. Karasawa gaban dan madaidaicin fridgen dake cikin office din yayi, tare da zaro bottle water mai sanyi ya kafa abakinsa. Bai dauke goran daga kan bakinsa ba kuwa har saida yasha fiye da Rabin ruwan dake cikin goran. Take kuwa ya soma sauk’e ajiyar zuciya, Yayinda yakejin sanyin ruwan na mamaye kirjinsa. Wanda hakan yasa acikin kaso 10 na b’acin ransa, kaso 6 yayi kaura. K’arasawa yayi ya zauna akan wata had’add’iyar leather sit dake cikin office din. Cikin kuma son rage tarin ayyukan dake gabansa, ya jawo laptop d’insa dake kan desktop. Atsanake ya soma shigar da wasu bayanai akan Campany'shi da aketa aikinshi yanzu, wanda yafi duk sauran na jahohin girma. Still kuma time to time yake sauke ajiyar zuciya. Acan b’angaren su Jannart kuwa, daga wajen buga wasan Polo’n, basu wani dau lokaci mai tsawo suna tafiya ba, cikin mintuna kalilan suka iso gidan television din nasu, na Arewa24. Kamar yanda suka fita asace kuwa haka yanzun ma suka dawo asace. Inda Salman yayi parking motar tasa acan baya, inda babu wanda zai gansu. Hakanne kuwa yasa cikin sauri Jannart ta fito daga motar, tare da sanya hannayenta duka biyu ta gyara zaman al'kyabban dake jikinta. Ahankali ta soma tafiya sai-dai kuma taku daya zuwa biyar kawai tayi ta tsaya cak, tare da juyowa ta kalli Salman wanda ya zuba mata idanu baya ko kyaftawa. Murmushin daya kara bayyana kyawun fuskarta tayi, batare kuma da ta fahimci ma’anan irin Kallon da Salman din keyi mata ba tace. “Nagode sosai Salman, nagode da taimakonka, tabbas ka taimakeni awannan tafiyar, saboda nasan cewar badon kaiba dana rasa wannan babbar daman dana samu ayau.” Idanu Salman din ya lumshe, cikin kuma nuna mata girman matsayinta awajenshi yace. “Akoda yaushe bana buk’atar godiyarki Jannart, domin Ina tabbatar miki da cewar kin wuce haka awajena, kamar kuma yanda kikeson aikinki, haka muma mukeson aiki dake, bamason rasaki Jannart, saboda haka duk wani abu daya shafeki ya shafeni.” Ya fadi hakan yana mai bayyana iya gaskiyar abunda ke kwance acikin zuciyarsa. “Bazan iya daina gode maka ba Salman, saboda akoda yaushe kana iya kokarinka wajen bani kwarin guiwa, thanks alot ni zan wuce gida sai munyi waya.” Ta kai karshen maganan nata tana me juyawa, kaitsaye ta nufi wajen da guard dinta suke. Shikuwa Salman da idanu ya rakata, har saida ta b’acewa ganinsa, kafun ya juya ya nufi cikin office d’insu. Yayinda itakuwa tana isa bakin motarta, gaba daya guard dinnata suka mimmik’e, Shashashai duk acikinsu kuwa babu wanda yasan cewar ta fita. Bud’e murfin motar tayi, bayan ta shiga ta zauna ne kuma driver’nta yaja sukayi gaba, Yayinda sauran guard dinnata suka rufa mata baya. Kwata kwata kuwa Tafiyar 40 minute ne ta kawosu katafaren gidansu Jannart din. Inda suna shigowa compound din gidan motar Junaid ma na shigowa. Ganin motar yah Junaid dinne kuma yasa zuciyar Jannart bugawa da wani irin karfi, lokaci daya kuma taji duk fargaba da tsoro ya lullub’eta. Tabbas ita kanta tasan cewar tana matuk’ar tsoron Yah Junaid, wanda kuma hakan ya samo asali ne saboda yawan takurawan da yakeyi mata. Al'kyabban da yake jikinta ta kalla, sanin da tayi kuma cewar idan Yah Junaid din ya gani, zai iya fassarata da wata manufa tasa ta daban, yasa cikin sauri ta zare al'kyabban daga jikinta, tare da sauko da ita ta daura akan waist dinta. Cikin yanayin tsoro da kuma fargaban dake kwance acikin ranta, ta bud’e murfin motar ta fito. Hannunta rike da jakanta ta soma tafiya ahankali. Dai-dai lokacin kuwa Junaid ya fito daga Cikin motarsa, hannunsa rike da karan sigari yana zuk’a tare da tankadi alamun a bige yake yayi tatil da barasa, dishi-dishi yake ganin komai hakan ke sashi tangadin Idanunsa ya dan kurawa Jannart din, Yayinda yakejin kamar ya rufeta da duka, dan tsananin takaicin rashin samun Galaba akanta da bayayi. “Daga Uwar Ina kike?” Ya tambaya cikin kakkausar murya tare da son gano meke daure a kugunta kuma ya kasa. Jannart kuwa da sautin fitar muryar tasa, yasa hanjin cikinta kad’awa Idanunta ta rumtse, kana cikin muryarta dake bayyana zallan tsoronsa tace. “Daga wajen aiki nake.” “Wajen aiki? Munafuka makaryaciya sai yanzune ake tashi daga wajen aikin karfe shida saura? Makaryaciyar yarinya wato kinje kin gama rabawa kattin banza jikinki kin more sun more, shine sai yanzu zaki dawo ko, tafi daga nan wajen kona tattakaki nayi kasa-kasa dake.” Ya fad’i maganar amatukar tsawace da maye. Hakanne kuwa yasa Jannart d’in, Cikin yanayin sassarfa ta nufi cikin gidan kaitsaye, domin tasan ba karamin aikinsa bane yayi kasa kasa da itadin kamar yanda ya fad’a. Sam tasan baya mutumta duk wani abu nata. Yayinda akullum take sake ganin wutar mugunta acikin idanunsa. Duk da kasancewarsa dan Uwanta amma yana muzantata, kwata-kwata babu ruwanshi da cewar ita k’anwarsa ce. Komai yazo bakinsa furta mata yake. Harsai yaushe ne zata tsallake rashin mutumcinsa? Harsai yaushe ne Yah Junaid din zai mutum tata amatsayinta na kanwarsa? Yaushe zai daina gwada mata kiyayya da kuma tozarci? Wasu siraran hawaye masu zafi ne suka silalo daga cikin idanunta, adai-dai lokacin da ta karasa bakin kofar da zai shigar da ita babban falonsu. Hannu tasa ta share hawayen nata, kana ahankali ta murda handle din kofar ta shiga. Rashin ganin kowa acikin falonne kuma yasa ta sauk’e ajiyar zuciya, batare kuma da ta. Nemi Mamy ko Abdull ba, kaitsaye ta wuce bedroom dinta. Tana shiga bedroom din kuwa ta soma rage kayan jikinta, tare da shigewa cikin toilet ta kimtsa kanta. Koda ta fito kwanciya tayi lub akan gado, tana me tunanin yanda halin rayuwa keyi da ita. Sam babu wani farinciki da take samu acikin gidan nasu. Kullum Cikin fargaba da tsoro take, awaje daya kawai takejin dadi, shine wajen aikinta, ananne take yin farinciki batare da wani ya tsangwameta ko ya harareta ba. Idanunta dake dauke da danshin hawaye ta lumshe. Kana cikin sanyin murya tace. “Allah Kazama gatana akoda yaushe.” *Dr Rayyern Mai-nasara.* Ajiyar zuciya ya sauke tare kuma da mikewa tsaye, ahankali ya soma tattare tarin takardun dake gabansa. Bayan ya kammala had’a takardun ne kuma ya d’auki waya da makullin motarsa dake aje akan desktop. Kaitsaye ya fice daga Cikin Office din. Koda ya fito compound din asibitin, bai wani tarar da yalwan mutane ba, kasancewar lokacin magriba ta fara yi. Direct wajen da motarsa ke fake ya nufa. Bayan ya shiga ya zauna ne kuma yayiwa motar key, tare da cillata kan shumfud’add’iyar Titin dake cikin asibitin har zuwa waje. Tuk’i yakeyi cike da nutsuwa, Yayinda ahankali kuma yake bin karatun Alminshawy dake tashi acikin motar. Da fitansa acikin Hospital din kuwa, yanzu ak’alla yakai 18minute, inda kai tsaye ya nufi masallacin Al'furƙan dake Cikin unguwarsu ta Nassarawa G.R.A. Dab da zai shiga cikin layin masallacin kuwa, ahankali ya d’ago kansa ya kalli madubin dake Cikin motar, kasancewar kuma aikin madubin shine bayyana maka wanda ke bayanka, hakan yasa idanunsa suka gane masa wata bakar mota mai tint dake biye dashi. Kawar da kansa gefe yayi tare da ci gaba da tukinsa, isowarsa Cikin layin dinne kuma yasa shi shiga wata kwana. Aikuwa d’aga kan da zaiyi sai yaga wannan motar dake bayansa itama ta shigo kwanan. Idanu ya d’an tsurawa motar, fuskarsa dauke da mamaki, saboda zuwa yanzu ya tabbatar da cewa motar shi take bi. “Bibiyata akeyi.” Ya fad’a fuskarsa d’auke da dan murmushi, ba tare kuma da tsoro ko fargaba ba ya cigaba da tafiyarsa, inda tuni ya d’auki numbern motar dake bayansa din ya rike akansa. Isowarsa gaban babban masallacin Al'furƙan dinne kuma ya sashi parking motar, tare da bud’e murfin motar ya fito, domin zuwa lokacin an soma kiraye kirayen sallan magriba. Fitowarsa daga cikin motar ne kuma yasa, motar dake biye dashi din, yin reverse cikin sauri matukin motar da ba a iya ganin fuskarsa, ya Karkata akalan motar zuwa wani waje daban. Dr Rayyern kuwa ganin wanda yake bibiyannashi ya juya ne, yasa shi sakin Murmushin dake dauke da ma’anoni daban daban. Wayarsa ya maida cikin motar, bayan kuma yayi alwala da bottle water’n da ya d’auko acikin motar ne, kaitsaye ya wuce cikin masallacin. Koda aka idar da salla’n bai fito daga cikin masallacin ba saida ya kammala addu’o’insa kana akayi sallan isha'i sannan ya fito. Daga masallacin Al'furƙan din kuwa kaitsaye gidansu ya nufa. Yayinda acan gidannasu kuwa Abba da Baba Maud’o ne zaune acikin compound din gidan, inda suke hira cike da girmama juna da Kekkyawar mu'amala. Dai-dai lokacinnne kuma Rayyern din ya iso bakin tankamemen gate din gidan. Horn din motar tasa ya danna. Wanda hakan yasa Baba Maudo tashi da dan sassarfa. saurin dakatar da Baba Maudon Abba yayi kana cikin girmamawa sanin tabbas Baba Mauɗo ya girmeshi yace. “A'a Baba Maud’o zauna ka huta, yau bari in taya ni zan bud’e gate din.” Cike da mamaki Baba Maud’o ya koma ya zauna, ganin da yayi kuma har Abban ya karasa jikin gate dinne yasa shi komawa ya Zauna tare da zuba mishi idanu. Kana a hankali ya lumshe su tare da sauke nannauyan numfashin. Abba kuwa bud’e katon gate din yayi, Inda Rayyern ya tura hancin motar tasa cikin gidan, saidai kuma ganin da yayi cewa Abban nasa da kansa ya bud’e gate din gidanne yasa, batare daya kutsa can ciki ba yayi parking motar. Tare da bud’e murfin motar ya fito. Cikin dan girmamawa hade dayin kasa dakai yace. “Abba Baba Maud’o barkanku da dare, amma Abba da ka bari ai na fito da kaina ma zan iya bud’e gate din.” Kai Abban ya girgiza tare da cewa. “A’a ai hakanma baiwuce motsa jini bane, Baba Maud’o ma da kansa yace zai bud’e amma nace masa ya bari, sannunka da dawowa ya hospital din?” Abba Yayi masa tambayar cikin kulawa. “Alhamdulillah Abba,". Kana ya kalli Baba Mauɗo cikin kulawa yace. "Baba Mauɗo gsky ni na gaya maka bana son kana aikin nan naka, zamu Ari ya rinƙayi aikin gadin, wlh bana jin daɗi inga kana buɗe mana gate.” Murmushi Baba Mauɗo yayi tare da cewa. "Rayyanu kenan to me a ciki ai motsa jiki ne kawai”. Kanshi ya jujjuya kana ya kalli Abba tare da cewa. “Ramadan yana ciki ko.” Kai Abban ya jinjina masa, tare da cewa. “Eh shima Ramadan din yanzu ya dawo ya maida wancan bakon yaron masaukinsa.” Dan jinjina kai yayi kana kaitsaye ya wuce cikin gidan. Ahankali ya tura kofar falon ya shiga bakinsa dauke da sallama. Ramadan da kuma Mamy dake zaune acikin falonne suka amsa masa. Cike kuma da farincikin ganinsa Mamy tace. “Masha Allah Rayyern ka dawo.” Kansa ya jinjina tare da cewa “Eh.” “Barka, ya hospital din.” “Alhamdulillah.”ya fada yana me karasowa cikin falon. “Hamma Rayyern sannu da dawowa, tun dazu Riyyam ke jiran dawowanka, amma ganin baka dawo da wuri ba, yasa na maidashi masaukinsa dan yaƙi ya tsaya yaci abinci ma, sai zuba mishi Mamy tayi ya tafi dashi.” Cewar Ramadan Wanda yake Kallon Hamman nasa. Gajiyayyun Idanunsa ya d’an lumshe, tare kuma da gyad’a kanshi ahankali, cikin yanayin kasalan daya saukar masa ya nufi stairs din dazai haurar dashi sama zuwa d’akinsa. Da kallo Mamy da Ramadan suka bishi har saida ya b’acewa ganinsu, kana Mamy taja dogon numfashi tare da sauk’e ajiyar zuciya...! *GARKUWAR taku ce dai MA'AURATA, da masu shirin aure, da masu jego, da yan gayu masu son k’amshi kece raini, da gyaran da zaike maimaita muku dararen forkon kuruciya* Ko kunsan Jikinmu na da sinadaran hormones da suke taimakawa dan’adam akan komai musamman lokacin da mace take mu’amalar aure da mijinta. Mafi akasari wannan hormones din ne ke samun matsala ko su yi sanyi koma su daina aiki kwata-kwata shi ne dalilin da zai sa mace tace bata jin sha’awa ko bata san dadin aure ba. Albishirinku ina da kayan da ke taimakawa wannan sinadaran du dawo aiki tukuru don karkato miki da kimarki wajan mai gida sannan su taimakawa wannan sinadaran hormones dinki su dinka secreting din ni’ima wadatacciya da zata taimaka miki ki gamsu mijinki ya gamsu fiye da tunaninki. Note: Kayana ba sa tsinka ruwan ni’ima suna dai taimakawa hormones dinki ne su tsattsafo da ni’imar musamman wacca cutar sanyi ko dattin mahaifa ya dankarar da su ya hana su yin aikinsu yanda ya kamata. Haka zalika idan kina da kyau ki kara da wanka. Zaki iya amfani da magani na na gargajiya wanda zai gyara miki sex hormones din kullum ki kasance cikin humidify wato cikin damshi mai albarka kamar yanda ake son mace. Yana gyara miki mara. Sai kamshi. Hajiyata daure ki fara amfani da turarena ki ji irin salon kamshin sa salo ne da zai daidaita ki da mijinki ya kankaro miki da kimarki a wajansa. Siyan na gari mayar da kudi gida. Ga masu buƙata ga number' wayata wanda nake whatsApp dashi 09097853276 kimin mgn ta whatsApp in har kin tabbatar kin shirya saya mu dai-dai ta, kayana ba ƙanana bane, shiyasa bana harkan karanta, muddin kinsan baki shirya sayaba Please kada kiyi min mgn ki bari sai kin shirya kuɗinki a hannu, ba ina nufin kayana bana talaka bane, no akwai ƙananan set na masu karamin karfi, banson aimin mgn a ɓatamin lokacin aiyukana a shirme baki shiryaba. Shine karantan da bana so. 0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU. In kin shirya ga number ta ga kuma account number ta wanda in mun gama mgn zaki turo kudin ki, kana insa miki kaya a mota, duk ƙasar da kike kayana zaije gareki, amman fa in kinada dalilin zuwan nasune🤝🏻sayan na gari meda kudi gida. GARKUWAR MA'AURATA By *GARKUWAR FULANI* 11/15/21, 7:20 PM - Auntyna: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *TUBALI* PAGE 11 NA *AYSHA ALIYU GARKUWA* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *FREE PAGE ne* _Littafin TUBALI na kuɗine hamzarta ki biya ki karanta cikin salama special Group 1k ne karamin group 500 kacal 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU sai ki turo min shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276, ko kuma ki sayi katin MTN ki copy number's ɗin katin ki turo min_ *Albishirinku! Ma'aurata, GA GARKUWAR KU nan tafe muku da tsarabobi na musamman gareku ma'aurata daga cibiyar mgnin mata mai taken GARKUWAR MA'AURATA* *NI DAI AYSHA ALIYU GARKUWA. Ina matukar mamakin wani irin lokaci da ya riske mu mai wahalallan fassara. Kullum dai magana daya ce, akan ma’aurata, fada, rashin jituwa, mutuwar aure, akan kuskure kalilan, rashin kula, rashin yi wa juna uziri. Toh wai duk me ya janyo hakan? Na zurfafa a tsananin tunani hakan ya tilasta min bincike mai tarin yawa wanda ya kai ni ga gano inda matsalar take? Shin yar’uwa ke macece amma kin san wacece mace ku? Kin san me ake kira mace kuwa? Mace ita ce matar da take zama iyali a wajan namiji ta zame masa bango, sanyin idaniyarsa, ta zame masa gata da farin cikin rayuwarsa ta zame masa ruwa abar kore ƙishinsa ta zame masa mayafi mai karesa daga gigitar kadaice, ta kuma dorar da mijinta kan turbar gaskiya, ta kashe masa jiki da salonta ta rikita shi da baiwa da ni’imar da Allah ya bata idan har ta san hanyar mayar da kanta sabuwa dal awajanta, wato kullun takasance masa tamkar amarya har ya kasa tantance daren amarcinsu da sauran dararen rakun rayuwar su. Wannan ita ce mace. Ina da wata saukakkar hanyar da zaki zama abar so da kulawa da soyayya a wajan mijinki ta hanya mafi sauki, 09097853276 hanyar ita ce ki gwada amfani da kayana na gyara ki gani, ina mai tabbatar miki da in sha Allahu sai kin dara da murna sai kuma kin gode min. Kayana kaya ne da aka yi shi da zallan itacanmu na gado marasa illa a cikin jikin dan adam musamman mace, kaya ne da suke taimakawa (sex hormones 😍) dinki. Misali kina kallon India😘, hollywood, Asian film🥰 kina ganin yanda mazansu ke nunawa matansu tsananin soyayya kamar su ba su kyautar ransu!? Saboda me hakan? Saboda suna sadaukar da lokacinsu wajan gyara jikinsu da kayan da ke tsattsafo da ni’ima cike da tsukewa, kayan nan kuma ana yinsu ne zallar magungunan gargajiya wanda ba su da illa domin haɗine na ingantattun itatuwa da yayansu. Ina baiwar Allahn da miji ke daure mata fuska babu hirar arziki? Zo ki ji yar’uwa zan baki gumbata da zallar gari wanda aka yi su da nagartattun itacen da ke da matukar amfani a jikin mace. Gubar ciko, gumbar tsalle dole, gubar da ba'a baiwa mai kishiya, garin maɗi, garin mallaka, tsumin goron tula, tsumin tsartai, tsumin maratsi, pala-pala butar sirri, kwanon k’asaitacciyar mace, furar mata madararta gareki Hajia takenta sha yanzu mgni yanzu, Ina mata masu fama da sanyi? Sanyin mara ki zo na hadaki da magani na na sanyi wanda yake wanke mara ya fitar da duk wata cuta da ke samun mazauni a wajan. Ina da ciccibi mai kyau. Ina da hadin amare mai kyau wanda zai gyara yarinya ya kankaro mata kimarta akwai hadin mai jego wanda muke yinsa na asali inada kekkyawan Hadi maida tsohuwa yarinya. Akwai daya bangaren wato *KAMSHI* Kimarki gyaranki da kamshinki Hajia yan mata. Matan da suka gane suka san yanda za su kankaro da mutunci su ne masu amfani da kayan gyara da kuma sanyaya jikinsu da ni'imantaccen kamshi, ina da turaren wanka da na bandaki na daki na jiki da na kaya dana tsuguno kamshin turarena na dabam ne mai sanyaya zuciyar wanda ya shaka ina da kayan kamshi na amarya da na maijego da na uwargida da dukkan macen da take kokarin mayar da kanta mai daraja a idon kowa ta zamo sarauni a idon mijinta, akwai shu'umar humra, sayan na gari maida kuɗi gida, banda karanta yayin gyara Hajia. Zaku iya samun kayyakina a duk garin da kike, zakiyi min mgn ta whatsApp number na 09097853276 domin yin zaɓinki, ko karin bayani, zaki tura kuɗin ta account na 0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU in mun gama mgna zan sa miki kaya a mota yazo duk garin da kike, in baki shirya saya yanzuba Please kada mu wahal da juna ki bari sai kin shirya kafin kiyi min mgn. 🤝🏻🥰😘 Daga taku AYSHA ALIYU GARKUWA *(GARKUWAR MA'AURATA)* Sautin takun takalminsa dasu Ramadan sukaji ne kuma yasa su maida hankali zuwa gareshi. Idanunsu gaba daya suka zuba mishi, tare da had’a baki gaba dayansu suka ce. “Masha Allah! Tsarki ya tabbata ga sarkin daya halicce mu ya kuma halicci Hamman Rayyern dinmu.” “Innalillahi kai Hamma Rayyern kayi kyau sosai, wallahi kamar daga Saudiya kazo.” Cewar Riyyam-nsra daya hangame baki da hanci yana Kallon Rayyern d’in. Shikuwa Rayyern karasa saukowa cikin falon, yayi ganin Abba da Mamy zaune ne kuma yasashi, d’an rusunawa ahankali yace. “Mammy a bani Bootle water mai sanyi.” Mamy da ita kanta ta yaba da tsananin kyawun da al'kyabban jikin nasa tayi masa ne ta saki murmushi, tare da fadin. “Masha Allah Rayyern kayi kyau, wannan suturar tayi maka kyau, Lallai kuwa ashe Rayyern din nawa ya kerewa sa’a.” Ɗan guntun Murmushin yayi, Cikin kuma alaman jin kunyar yabonsa da Mamyn nasa tayi yace. “Nagode sosae Mamyna.” Abba daya kafe Rayyern din da ido kuwa baya ko k’yaftawa, fuskarsa cike da mamaki yace. “Rayyern wannan shigar fa yaushe ka fara ta? sannan a ina ka samo alkyabba mai tsananin kyau haka?” D’an sunkuyar da kansa k’asa yayi, tare da kama y’an yatsun hannunsa ya soma murzawa. Sam arayuwarsa shi bai iya k’arya ba, impact ma arayuwarsa babu abunda yafi tsana kamar k’arya, bayayin k’arya bakuma yaso ayi masa. Duk da kuwa yasan Abban nasu bazai so abunba so gskyar da zai fada ba, amma ya zama dole ya gaya masa gaskiya, saboda karya ba d’abi’arsa bace. “Kayi hakuri Abba Malam Mai-nasara ne ya bani kyautan Alkyabbu guda bakwai.” Idanu Abba ya kankance cikin kuma nuna rashin jin dadin hakan ya kawar da kansa gefe. Ganin hakanne kuma yasa Rayyern d’in, ya d’an rank’wafar da kansa. Kana cikin sigar ban baki yace. “Kayi hakuri Abba, idan bakason shigartawa sainaje na cire.” Ajiyar zuciya Abban ya sauk’e kana ahankali yace. “A’a ni Bance Banason shigarka ba, kayi kyau Tabbas kuma shigar alkyabba shigace da take da matuk’ar mutumci, gashi kuma ta bayyana tsananin haiba da kwarjininka, saidai amma ka kiyaye nan gaba bafa na son wata alaƙa a tsakaninku.” Kai Rayyern din ya jinjina kana cikin girmama zancen Abban nasu yace. “Nagode Abba kuma Insha Allah zan kiyaye.” “Shikenan.” Abban ya fad’a atakaice. Riyyam-nsra kuwa cikin kasa kosawa da Kallon yanda Hamadan nasu yayi kyau yace. “Please Hamma Rayyern Ina zakaje.” “Polo.” Ya bawa Riyyam din amsa a taƙaice kuma dai-dai lokacin da yake kokarin fita daga falon. Da sauri Riyyam din ya tashi yabi bayansa, yana me fad’in. “To Hamma Rayyern tsaya muyi video dan Allah.” Ramadan dake zaune ma mik’ewa tsaye yayi yabi bayansu. A compound din gidan suka tsaya, inda Riyyam sarkin tiktok ya saita wayarsa ya soma yi musu video dukansu uku. Harda sa musu wata y’ar wak’a, shidai Rayyern Kallon Yaron kawai yakeyi, domin a wuni biyu kawai da sukayi da yaron, ya fahimci wani abu, da kuma irin d’abi’a da yaron yayi shura akai. Saidai kuma baisan Meyasa ba yakejin yaron acikin zuciyarsa hakan yasa yake kasa yakiceshi. Gama k’arasowarsu compound din gidan kuwa, yayi dai-dai da fitowan Baba Maud’o daga cikin d’an madaidacin Part ɗinsa dake gefen gate. Yana fitowa dinne kuma ya sauk’e idanunsa akan Rayyern, dake sanye cikin al-kyabba. Wani irin tsayuwa Baba Maud’on yaji zuciyarsa tayi, take kuma wasu irin abubuwa suka shiga dawowa cikin tunaninsa. Saidai kuma Ina ayanzu kwakwalwarsa bata da wani buk’atar amsar kowani irin sak’o, wannan dalilin yasa zuciyarsa ke cigaba da bugawa da harbawa a hankali. D’an matsowa kusa dasu Baba Maud’on yayi, tare kuma da sauk’e idanunsa akan Riyyam wanda keta faman bin wak’ar Justin Bieber me suna (Peaches) dake tashi awayarsa. Idanu Baba Maud’o ya tsurawa yaron baya ko k’iftawa, Yayinda zuciyarsa ke cike da zallan mamakin, kamannin Rayyern dake kwance akan fuskar yaron. “Baba Maud’o barka da yammaci.” Cewar Rayyern. Wanda maganan nasa ne kuma yasa Baba Maud’o dawowa cikin tunaninsa. Murmushi ne ya bayyana akan fuskarsa, duk da kuwa cewar rabin fuskartasa arufe take, amma hakan bai hana Rayyern din gane cewar Baba Maud’on murmushi yayi ba. “Yauwa Barka dai Rayyern, yau kuma inazaka je haka naga kayi shigar da ta bayyana kyau da cikar haibarka.” Murmushi Rayyern din yayi, tare da dan matsowa kusa da Baba Maud’on kana yace. “Wurin wasan polo zanje Baba Maud’o". Kai ya jinjina alamun gamsuwa. "Shin ko akwai wasu abubuwan buk’ata naka da suka k’are, idan nazo dawowa saina sayo maka.” Rayyern ya tambayeshi cikin mutunta ma'aikatan gidan nasu. Again Murmushi Baba Maud’o yayi, cikin kuma Jin dadin kulawan da su Rayyern din sukeyi dashi yace. “A’a Alhamdulillah ayanzu kam bana buk’atar komai, saidai nace kayi kyau sosai cikin wannan shigar, amma baka daura hiramin naka dai-dai ba, Bari na gyarama irin yanda samarin makka suke saka nasu.” Murmushi Rayyern din yayi, kana ya matso Baba Maud’o d’in ya gyara masa sakun hiramin. Riyyam-nsra kuwa da d’an mamaki ya kalli Hamma Rayyern dinnasu, tare da cewa. “Hamma Rayyern waye wannan mutumin, naga jiya da nazo banganshi ba.” “Sunansa Baba Maud’o.” Ramadam ya bashi amsa. Saurin jinjina Kai Riyyam yayi, kana ahankali ya matso kusa da Baba Maud’o din. Fuskarsa dauke da murmushi yace. “Rawanin da kasa akanka zuwa fuskarka yayi kyau sosai Baba Maud’o, Dan Allah Hamma Rayyern kuzo mu d’auki hoton selfie tare dashi, saboda Idan na koma Ethiopia zan nunawa Mammyna, na kuma bata labarin yanda wasu daga cikin yan Nigeria sukeyin shigarsu.” Ya fad’i hakan saboda baisan cewa Baba Maud’o’n shigar buzayen Niger 🇳🇪 yayi ba. Kamar yanda ya buk’ata kuwa matsowa Rayyern da Ramadan sukayi, inda suka saka Baba Maud’o da Riyyam din atsakiya. Hakanne kuwa yasa Baba Maud’o da Riyyam din ke iya jiyo sautin bugun zuciyar kowannensu, saboda yanayin yanda sukayi kusan ci sosai da juna, domin Riyyam dan sarkin son jiki, har rungume Baba Maud’on yayi ajikinsa. Yayinda Ramadan ya karb’i wayar Riyyam d’in, yayi musu hoton selfie har kala biyu. Bayan ya mikawa Riyyam din wayarsa ne kuma, Rayyern ya juya ya shiga motarsa, driver’nsa yaja suka fice daga cikin gidan. Ramadan da Riyyam kuwa zama sukayi dab’as Akan wani dan dogon Bencin da Baba Maud’o ke zama, haka kuwa suka sa Baba Maud’on agaba sunata hira, musamman Riyyam daya bud’e baki ya dinga shararawa Baba Maud’on labarai kala-kala, wanda duk rabinsu na abun dariya ne. *Arewa 24 TV* Jannart ne da Salman ke tafe acikin babban corridor din, da zai sadasu da compound din gidan tv'n nasu. Anutse Jannart take takunta, Yayinda time to time take Kallon fuskar wayarta dake rike ahannunta. Salman dake biye da ita kuwa, idan hankalinsa yakai dubu to duk akanta yake. Baisan meyasaba hardai idan Jannart tana waje, baya tab’a iya dauke kansa daga gareta, koda kuwa yaya baya iya gajiya da Kallon tafiyarta mai kama data hawainiya. Yayi Imani azuciyarsa cewa Jannart macece ta gasken gaske, ko acikin mata irinta basu da yawa. Isowarsu jikin motarsa ne kuma yasa Jannart fakon idanun guard dinta ta shige cikin motar, kana cikin sauri tace. “Please Salman kayi sauri mubar nan, Domin idan wayannan kattin suka ganni dakai ina mai tabbatar maka cewar akwai matsala.” “Nikuwa nasan da cewar akwai matsala ai Jannart, abu mai sauki ne ma su samin bindiga akaina su harbeni, tsoron da ake baki agidanku ko Gwamna iyakaci.” Salman din ya fada adaidai lokacin da yake ta da motar suka bar wajen. Suna hawa titi kuwa Jannart ta sauk’e ajiyar zuciya tare da fad’in. “Allah Yasa dai mudace mu samu ganinsa yau, amma mutum dan ya zama richest man shikenan kuma ganinsa saiya zama wahala.” Shidai Salman murmushi kawai yayi kaman zaice wani abu kuma saiya fasa. Kaitsaye suka nufi Mai-nasara Hospital. Tafiyar mintuna kad’anne ya kawosu bakin kofar katafaren asibitin. Kasancewar kuma ba ashiga can Cikin hospital din da mota, matuk’ar ba emergency bane, yasa Salman parking motar anan babban parking lot na asibitin, wanda shi kansa ya kusan kwatan wata karamar unguwa. Bud’e murfin motar Jannart tayi ta fito, tana me k’arewa kyau da had’uwar asibitin kallo. Lallai privet Hospital ne daya amsa sunansa, saboda daga ginin asibitin ma kasan ba kananan billions aka kashe masa ba. “Mai-nasara Hospital! Lallai asibitin ya had’u.” Jannart din ta fad’a tana me Kallon Salman. Shima Salman din kallonta yayi, tare da cewa. “To Kema da bakinki kin fad’a, yanzu kiyi imagine tayaya za ace kinsamu ganin mamallakin wannan wajen acikin sauki? karki manta kuma bawai iya Hospital dinnan ya mallaka ba, yana da companies, bama a iya Nigeria ba, wallahi Jannart wannan mutumin *Richest Man* ne na k’arshe.” Kai Jannart d’in ta jinjina, domin ita kanta ayanzu ta yarda da hakan. Kaitsaye kuma suka kutsa cikin asibitin. Acan b’angaren Rayyern kuwa kaitsaye Wajen buga wasan polo suka nufa. Koda suka isa wajen da haduwarsa da kuma kyawunsa ya darawa kwatance. A parking lot driver’nsa yayi parking. Bayan ya fito daga motar nasa ne kuma kaitsaye ya nufi cikin wajen. Da kwata-kwata babu mutane acikinsa. Duk da tsananin girman wajen kuwa, amma bakajin motsin komai saina tarin dawakai da kuma tsirarun masu kula dasu. Wanda kuma hakan ya faru ne saboda zuwan Dr.Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara, kasancewar idan har zaizo wajen To yakan biya mak’udan kud’ad’e ne, ta yanda ranar baza'a amshi kuɗin wasuba, harsai yayi wasansa ya gama ak’alla na tsawon awa 2, bayan ya tafi ne kuma sauran jama’a zasu dawo su cigaba da harkokinsu bawai kuma yana haka dan isa bane, sai dan sosai hayani kan iya sa mishi ciwon kai, yana kuma jin daɗi wasan polo a jikinsa. Shigarsa cikin babban wajen wasan buga Polo dinne kuma yasashi, zare alkyabban dake jikinsa ya ajiye, tare da wayoyinsa harma da y’ar bag din da yasaka bottle water mai sanyi aciki. K’arasawa yayi wajen tarin dokunan da akeyin wasan dasu, tare da zab’o wani farin doki, wanda mafi yawanci idan yazo shi yake hawa. Batare da wani bata lokaci ba kuma ya dale saman dokin tare da rik’e Sandar buga k’wallon nasa ya soma sukuwa, tare da gabatar da wasan. Mai-nasara hospital. Salman da kuma Jannart dake tsaye abakin k’ofar office d’inne suka tsaya suna Kallon juna. Salman ne ya gyara tsayuwarsa tare da cewa. “Please Jananrt mushiga mana, kinfi kowa sanin irin wahalan da muka sha, kafun mu samu aka nuna mana wannan office din, wannan ita kadaice daman mu ta karshe, kada muyi wasa da ita.” Kai Jannart ta jinjina kana asanyaye tace. “To.” Knocking kofar Salman yayi, inda Dr Sulaiman dake zaune akan wata hamshakiyar kujera ya bada izinin shigowa. Hakanne kuwa yasa suka kutsa Kai suka shiga bakinsu d’auke da sallama. Amsa musu sallaman Sulaiman yayi, tare da dago kansa ya kallesu. D’an Kallon juna suka tsayayi na tsawon sakanni, kafun daga bisani Dr.Sulaiman din yace. “Bismillah’nku.” Ya kare maganan yana meyi musu nuni da wasu kujeru guda biyu dake gabansa. Yayinda kuma acikin mintuna kadan na Kallon daya musu, ya fahimci cewar sudin ba marassa lafiya bane. Zama sukayi akan kujerun daya nuna musu d’in, Salman ne ya mik’awa Sulaiman din hannu suka gaisa, Yayinda ita kuma Jannart ta gaidashi da sassanyar muryarta, wanda har hakan yasa shi kasa jurewa saida ya dago ya sake Kallon ta, Yayinda azuciyarsa yake mamakin jin ta gaishe shi da Hausa, domin sam baiyi mata Kallon y’ar Nigeria kuma maijin Hausa ba, kasancewar yanayin kamannin ta da kuma shigarta da tsarinta dabanne, bawai irin normal mata da kowa ya sani bane, ita din akwai abu na musamman atattare da ita, wanda kowanni irin Namiji idan ya kalleta saiya gane hakan. “Meke tafe daku? Ko kuma patient kuka kawo?.” Salaiman ya tambaya. Jin hakan ne yasa Salman d’an gyara zama, tare da fuskarta Sulaiman d’in, kana atausashe yace. “Sunana Salman Aliyu, wannan kuma abokiyar aikina ce sunanta Jannart Idi Sale Dakata, Mu y’an Jarida ne, ma’aikata Tashar Arewa24.” ID Card d’insu suka zaro tare da nunawa Salaiman daya zuba musu ido. Salman ne ya cigaba da cewa. “Munzo nanne bisa dogaro da kuma fatan, dacewar samun ganin Dr.Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara, Dan Allah Dr. Idan akwai taimakon da zakayi mana, ka taimaka muganshi, wallahi ganin nasa nada matuk’ar muhimmmanci, musamman ga Jannart.” Ajiyar zuciya Sulaiman ya sauke, tare da maida hankalinsa ga Jannart, domin kuwa idan har abunda tunaninsa ya basa gaskiya ne, to Lallai ya kamata ace ya taimaka musu. Domin ya raya aransa cewa aiki aka basu domin su tattauna da Dr.Rayyern d’in. Zamansa ya gyara kana anutse yace. “Babu damuwa tunda dai harkunzo nan Insha Allah zaku gansa, duk da cewar ayanzu baya cikin hospital d’in, amma Ina da tabbacin inda zaku sameshi, saidai kuma ganin nasa ba shine ba, dan Ina da tabbacin ba lallaine Dr. Rayyern ya amince kuyi hira dashi ba, saboda aduk k’asarnan babu wani gidan Jarida daya tab’a amincewa sukayi hira dashi.” Idanu Jannart ta d’an lumshe ahankali, Yayinda ajikinta takejin Wannan shine last chance dinta, akasin haka kuwa zata iya rasa aikinta, wanda kuma shine ke sata acikin farinciki. D’an cije labb’an bakinta tayi, kana cikin siririyar muryarta tace. “Please Dr. I need your help please!! Banason nayi losing job d’ina!!!” Takai k’arshen maganan muryarta araunane. Wanda hakan yasa Dr.Sulaiman Jin tausayin yarinyar, saidai kuma har acikin zuciyarsa yayi mamakin, Jin tace bataso ta rasa aikinta. Domin yasan kamarta dinnan ba ace daga gidan talakawa ta fito ba, Sam Kwata-kwata ma batayi kama da hakan ba bare kuma waye bai san sunan mahaifintaba Alhaji idi Saleh Dakata. Sake gyara zamansa yayi, tare da cewa. “Badamuwa zan taimaka muku Insha Allah, yau Wednessday kuma duk ranan wednessday at this time Dr. Rayyern yakan je wajen wasan Polo, ba kuma ya barin wajen sai 5 na yamma, saboda haka zan baku Andreas din wajen, zakuma ku iya zuwa kusa meshi. Wani irin sanyi Jannart taji acikin zuciyarta, Yayinda Salman kuwa yayiwa Dr.Sulaiman din Godiya. Shikuwa Dr. Sulaiman a paper ya rubuta musu adress din wajen, tare kuma da yi musu fatan nasara. Godiya sosai sukayi masa kafun sukayi masa sallama, cikin hanzari suka fito daga cikin asibitin. Direct wajen da motar Salman din ke fake suka nufa. Suna shiga kuwa ya tada motar suka nufi wajen buga wasan Polo’n kaitsaye. Tafiyar da bata wuce ta 20mn sukayi ba, sai gasu abakin kofar babban mashigar wajen wasan Polo’n da yake duka a unguwa ɗaya ce. Bayan kuma Salman yayi parking motar ne suka fito, direct mashigan wajen suka nufa. Amma sai guard din dake tsaron wajen suka dakatar dasu, had’e da cewa bazasu shiga ba, anyi clossing wajen na two hours, suje anjima su dawo. Rau-rau Jannart tayi da ido, Yayinda Salman kuwa ya zaro ID card d’insa ya nuna musu, cikin sanin makamar aikinsa kuma yace. “Mu y’an Jarida ne, ankuma tabbatar mana da cewar mutumin da muke nema yana cikin wajen nan, please dan Allah kubari mugansa, abune na gaggawa.” Dan Kallon juna guard din sukayi, kaman zasu hanasu kuma sai suka matsa musu alaman su shige. Aikuwa wani irin sanyi Jannart taji zuciyarta tayi, cikin sauri kuwa suka sakai suka wuce cikin wajen. Y’an tsirarun mutanen dake wajen suka soma wuce wa, ganin kuma kamar babu alaman yalwan mutane awajenne yasa sukayi tsaya, saboda su kansu basu San ta Ina zasu fara nemansa ba. Jannart dinne ta kalli Salman kana zuciyarta akarye tace. “Anya kuwa Salman kana ga zamu sameshi anan wajen?” Shiru Salman din yayi, alamun nazari dai-dai lokacin kuwa wani ma’aikacin wajen yazo gilmawa ta gabansu. Salman dinne ya tare mutumin, tare da cewa. “Dan Allah Malam muna tambaya ne,". "Allah yasa na sani." Ya basu amsa yana kallon Jannart. Numfashin gajiya Salman ya sauƙe tare da cewa. "Please Dr. Rayyern Basheer Mainasara muke nema.” Idanu sauran ma’aikatan wajen da sukaji abunda Salman din ya fada suka zuba musu. Shikuwa wanda Salman din ya tambaya, kansa ya girgiza cike da mamaki kuma yace. “Dr. Rayyern Bashir Mai-nasara kuma anan wajen? gaskiya bana tunanin hakan, saboda muma bamu sanshi ba, sunansa kawai dai mukeji, amma dama yana zuwa nan dinne.” Baki Jannart ta cije tare da sanya hannayenta ta kama waist dinta. Cike da takaici tace. “Again na sake rasa damata.” “Calm down Jannart, mu k’arasa can cikin wajen mu duba ko zamu dace.” Salman ya ce mata. Fuskarta ta kwab’e saboda zuwa yanzu ta fara gajiya da gantalin neman mutumin tunda shi ba kuɗi bane. Amma da yake ta San wannan din shine last hope dinta, hakan yasa tabi bayan Salman suka shige cikin inda ake gudanar da asalin wasan Polo din. A dai-dai lokacin kuwa Rayyern yayi nisa acikin wasan nasa, sai sukuwa yakeyi akan doki cike da k’warewa da jin daɗin yanayin wurin shiru ba hayani ba mai takura mishi. Yayinda kuma ya kasance shi kad’ai ne awajen yake sashi karsashi. D’an shigowa su Jannart da Salman sukayi Cikin wajen, Saidai kuma ganin da sukayi babu kowa awajenne yasa Jannart jingina bayanta da jikin wani k’arfe. Akasalance tace. “Salman zuwa yanzu Tabbas inaji ajikina cewar na kusa rasa aikina, wannan ɗan is ɗin mutumin ba saukin ganine dashi ba, kalli wajen nan fa babu kowa sai wancan mutumin daya bamu baya yana ta sukuwa akan doki shima ɗaya kamar mara aikin yi.” Takai karshen maganan nata tana me Kallon bayan Dr Rayyern, da yake nesa dasu sosai. Dan kallonta Salman yayi cikin kuma son k’arfafa mata guiwa yace. “Karki damu Jannart Insha Allah zamu hadu dashi, Yanzu dai mukarasa wajen wancan mutumin sai mu tambayeshi koya San wani abu dangane da wanda muke nema.” Still fuskarta ta kwab’e tare da cewa. “shikenan muje.” Hakan kuwa akayi inda suka k’arasa shiga can cikin wajen wasan dake malale da koriyar ciyawa mai cike da damshi. Suna kara kusantan cikin wurin wasanne kuwa Rayyern din ya juyo da akalar dokinsa. Sai-dai kuma Sam baisauke idanunsa akansu ba. Idanu gaba dayansu suka zazzaro, Yayinda Jannart kuwa cike da mamaki tadan matsa bayan Salman. Tana fadin “Laaa Salman wannan mutumin nefa da na fasawa waya a airport, wayyo Allah Salman nikam kazo mu gudu, tun kafun ma ya ganmu.” Kai Salman din ya girgiza tare da cewa. “Mu gudu kuma Jannart? saikace marasa gskiya muje dai ki bashi hakuri dama ai aranar baki bashi hakuri ba, daga ganinsa ma Babban mutum ne watakila ma zai iya taimaka mana muga Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara din.” Fiki-fiki tayi da idanunta, kana adan tsorace tace. “Shikenan muje.” Nanfa suka nufi wajen Rayyern d’in. Dai-dai lokacin kuwa Rayyern dayake matuk’ar gudu akan doki, batare daya d’ago ko waiwaye ba ya taho aguje. Kaitsaye kuma direct inda su Jannart d’in ke tsaye ya nufa. Gadan gadan. Su Jannart din kuwa kansu basu ankar ba, saida dokin ya kusan zuwa gab dasu. Wani irin k’ara mai cike da tsoro da firgici Jannart ta saka da karfi, tare kuma da daura hannayenta akanta ta rumtse Idanunta k’am, domin ta gama sadak’arwa akan cewar dokin ya nuk’urk’usheta ma angama lokaci ɗaya numfashin ta ya fara fizgan firgici. Domin hatta Salman dake gefenta shima yayi surrender. Rayyern kuwa Sam bai Ankara ba saida ihun Jannart din ya shiga dodon kunnensa, wanda hakan yasa cikin sauri ya dago kansa. Ganin yana gab da bi ta kansu ne, yasashi saurin. Damƙe igiyar linzamin dokin da ƙarfi ya tsayar dashi cak. Saboda ganin macen da yayi agabansa ne kuma ya sashi dirowa daga saman dokin. Bayan ya juyashi. Wani irin dogon tsaki yaja. Tare da Kallon Salman wanda keta sauk’e ajiyar zuciya, kana ya watsawa Jannart din dake gabansa wani kallon da yasa cikinta ya murda ya haɗe da numfashin dake sauya salon fita da shiga. Cikin tsuke fuska yace. “Bakwa ganine, yanzu idan da nabi takanku fa?” “Kayi hakuri dan Allah!” Salman ya fad’a asanyaye. Itakuwa Jannart sai ayanzu ta bud’e idanunta, Yayinda gaba daya jikinta ke kakkarwa. Hannu tasa ta dafe ƙirjinta. Rayyern kuwa y’ar gajerar tsaki yaja, batare kuma daya sake ce musu komai ba ya juya ya nufi inda kayayyakinsa suke. Yana zuwa kuwa ya zauna akan wata kujerar silver mai daukar mutun uku, Sunkuyowa yayi tare da bud’e jakan daya shigo da ita ya zaro bottle water, b’alle murfin goran yayi, kana ya soma zubawa akan tarin sumar dake kansa wanda yake jin zufa na tsastsafo mishi. Jin da yayi baisamu gamsuwa bane kuma yasashi karkad’a gashin kannasa dan yadda ruwan zai taɓa fatar kansa, wanda hakan yasa har ruwan dake kan nasa ya watsu akan fuskar Jannart. Salman dake tsaye kuwa dan matsowa yayi, tare da gaishe da Rayyern d’in. Batare kuma daya dago ba ya amsawa Salman d’in atakaice. Idanu Salman yayiwa Rayyern dake tsaye, alaman ta gaishe shi. D’an k’aramin bakinta ta turo gaba tare dasa hannunta ta goge ruwan daya watsa mata, kana asanyaye tace. “Ina wuni.” Shiru yayi bai amsa taba, tare dayin kamar ma baijita ba. “Ina wuni.” Jannart d’in ta sake fad’a akaro na biyu. still shiru yasakeyi kamar baijita ba. “Kibashi hakuri.” Salman dake tsaye ya fada kasa-kasa. Karamin bakinta ta sake turowa, cikin kuma wata irin murya mai kama da shagwab’a, sakalci, sanyi da kuma tsoro tace. “Kayi hakuri please, ranan nayi maka b’arna amma bada sanina nayi hakan ba, Dan Allah da Manzonsa kayi hakuri.” Idanunsa yadan lumshe saboda jin ta had’asa da sunan Allah da Manzonsa ne kuma, yasashi gyaɗa mata kai alaman yayi. “Nagode.” Ta fad’a asanyaye. Shikuwa Salman ganin hakanne ya sashi dan matsowa, cikin neman alfarma yace. “Dan Allah ranka ya dad’e tambaya mukeyi.” D’ago Kai Rayyern din yayi ya kalli Salman din afakaice. Batare kuma dayace komai ba ya maida kansa k’asa tare da ɗaukan ɗan karamin towel ɗin dake gefe ya fara goge suman kanshi zuwa wuyanshi da fuskarshi da sajenshi da ruwan ya jiƙa. Salman kuwa ganin hakanne yasashi Kallon Jannart, wanda gaba d’aya mood dinta ya sanja,tun lokaci da taga kamar dokin zai takesu ta soma sakin wani irin numfashi sama-sama a hankali. Wanda da dukkan alama kuma tsoritan da tayi dazunne yakeson tayar mata da ciwon ta. Sanin yanda ciwon keyi mata idan ya tashi ne kuma yasa, Salman din cewa. “Subahanallah Jannart ciwonki ko?.” Kai ta gyaɗa mishi cikin jawo ajiyan zuciya da take son yi. Cikin kula ya nuna mata gefen Rayyern dan babu wata kujerar a nan kusa dasu. "Maza ga waje ki zauna.” Ya kare maganan yana meyi mata Nuni da d’an gefen Rayyern, wanda kuma dama wajen zaman daya rage din bai wuce na zaman mutum daya ba sabida ya ajiye tarkacensa a wajan zaman mutun ɗaya gashi kuma a ɗaya wojen. Jannart kuwa kasancewar dama ta gaji da tsayuwa kuma ga numfashin ta dake fizga ne yasa, batare da ta musa ba ta zauna awajen sanin in ta zauna zai iya dai-dai-ta. Shikuwa Salman ƙara matsosu yayi. Tare da sake maimaita maganarsa ta dazu. “Dan Allah ranka ya dad’e tambaya mukeyi.” “Inaji.” Rayyern din ya fada agajarce, nan ma saboda yaji Salman din ya hadashi da Allah ne. "Dan Allah wani mutum muke nema". Uhum ya kuma cewa a taƙaice. Gyara tsayuwa Salman yayi tare da cewa. " Sunan shi Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara. Shi muke nema, munje Hospital d’insa ne aka tabbatar mana da cewa Lallai-Lallai yana nan, shine muke tambaya dan Allah koka sanshi?” Ad’an fakaice Rayyern din ya kalli Salman, saidai kuma cikin halin nuna ko inkula yace. “Meyasa kuke nemanshi me zai muku? Wa yace muku yana nan?.” Jannart dake dan haki ne taja ajiyan zuciya ta fizogishi da ɗan ƙarfi kana tace. “Mitssss mutun sai rashin gsky, gaba ɗaya ya wahal damu." Ta wutsiyar idonshi ya ɗan kalleta a fizge. Ita kuwa ci ga da cewa tayi. "Nemansa kawai mukeyi, wallahi daga yanzu kuma ni nagaji, Dan bazan zauna inyi ta neman wani can ƙato baƙi mummuna mai ƙaton tumbi ba dan yayi kuɗi yana jin kansa waya masan TUBALI kuɗin nashi ko na haram ne shiyasa yake tsoron yin ido huɗu damu ƴan jaridu. Kada ya gaza amsa mana tambayoyinmu." Numfashin ta fesar a hankali jin ya dai-dai ta. Salman nata jujjuya mata kai ina bata ganiba bare tasawa bakinta linzamin. Tsaki ta ɗan ja tare da ci gaba da cewa. "Mutumin nan ya wahalar damu sosai, na farko dai shiba kudi ba, amma na lura kudi yafi saukin samu akanshi.” Alama Salman ya mata akan tayi shiru, da yin gyaran murya. hakanne kuwa yasa tayi shirun. Shikuwa Rayyern tunda ta fara maganan yake kallonta ta wutsiyar idanunsa baki cai-cai. Salman kuwa gyara tsayuwarsa yayi, tare da fadin. “Mu yan jarida ne kuma ma’aikatan tashar Arewa24, munzo nanne domin samun daman yin hira dashi, Lallai kuma muna da buk’atar ganinsa. Domin rashin samun tattaunawa dashi ɗin, dai-dai yake da rasa aikin mu.” Fuska Rayyern din yadan tab’e tare da cewa. “Uhummm.” Atakaice. Jin hakanne kuma yasa jikin Salman yin sanyi, still cikin yanayin dake bayyana damuwarsa yace. “Dan Allah In dai kasan hanyar da zanbi wajen ganinsa ka taimaka min, Banason rasa aikina, inason aikina sosai, Dan Allah Idan ka sanshi, ko kuma kasan inda zan sameshi ka fad’amin, domin da wannan aikin kad’ai na dogara, dashi ne kuma nake ciyar da iyalaina da iyayena, dan Allah ka taimaka kada in rasa aikina.” Tabbas Salman ya karyo lagonsa tunda ya hadashi da Allah da kuma nuna masa aikin shine mafogararsa, Idanunsa yadan lumshe ahankali, batare kuma daya kalli daya daga cikinsu ba yace. “Naji badamuwa amma dai yanzu kam bayanan, Zan gaya masa idan ya amince shikenan, zan kawoshi har cikin tashan Arewa24 din kuyi mishi duk tambayar da kukeso.” Farinciki da tsananin jindadi ne ya lullub’e cikin zuciyar Jannart da Salman. Cikin bayyana zallan jin dadi Salman yace. “Mungode sosai ranka ya dad’e, mungode kwarai, saidai amma dama ka sanshi ne?” Kansa ya jinjina tare da cewa. “Eh nasanshi uban gidanane zan gaya masa Insha Allah kuma zaizo zan roƙeshi in gaya masa uzurinka bisa tausayawarsa kan kada ka rasa aikinka da kake kula da ilanka zaizo in Sha Allah.” Murmushi Jannart dake gefe tayi, tare da lumshe idanunta saboda wani irin sanyi da taji acikin zuciyarta sai kuma ta ɗan gyara zamanta. Shikuwa Salman cikin tsananin jin daɗi yace. “Sir! Nagode! Nagode!! sosai!!! Dan Allah kayi mishi magana, ni kuma zan tsumayeka har zuwa nan da y’an wasu kwanaki, wallahi Banason rasa aikina yau kuma saura kwana takwas za'ayi hirar dashi ranar Alhamis na sama.” Kai Rayyern din ya jinjina, tare da sake cewa. “Insha Allah zaizo.” “Ka tabbatar zaizo?” Jannart da nutsuwa ya dan fara sauka azuciyarta ta fad’a. Dan juyawa yayi ya watsa mata harara, cikin zuciyarsa kuwa cewa yayi. “Oho bansani ba shegen baki.” Salman da farinciki ya cika zuciyarsa kuwa, cewa yayi. “Mungode sosai amma dan Allah in ba matsala ka bamu numbern ka saboda idan zaizo din musani.” Kansa yadan girgiza, cikin kuma rashin sabonsa da yawan magana yace. “No kai dai ka bani taka numbern.” To Salman yace Cikin gaggawa kuma ya bashi numbernsa. Mikewa tsaye yayi fuskarsa cike da farinciki yace. “Alhamdulillah Jannart taso mutafi Insha Allah yanzu kam na samu full confidence.” Yayi maganar yana me soma tafiya, saboda tsananin farincikin da yake ciki kuwa bai majira Jananrt dinba. Jannart kuwa ganin Salman din ya soma tafiya ne yasa ta mik’ewa tsaye itama. Tashin nata kuwa yayi dai-dai da juyowan Rayyern inda ya sauke idanunsa Akan bayanta. Da sauri ya rumtse idanunshi da ƙarfi tare da kame jikinsa sabida yadda yaji tsikar jikinshi na mimmiƙewa yana tashi tsaye. Sabida a bunda ya gani ajikinta. Yadda yaji tsikar jikinshi na tashi ne ya kuma sashi buɗe idanunsa. Damatsan hannunsa ya kalla gaba ɗaya tattausan gargasar jikinsa ta miƙe tsaye. Ita kuwa Jannart taku ta farayi da nufin bin bayan Salman wanda haka yasa ta ƙara matsowa gabanshi tana takun dake juya kyawawan mazaunanta. Fuskarshi ya kuma yamutsawa. Tare da saurin kawar da kansa gefe. “Meye haka?” Ya fad’a azuciyarsa yana mai jin kamar ana tsikarinsa Jannart kuwa da batasan komai ba, ahankali ta soma dan takawa. "Ta yaya mace zata kasa sanin ranakun al'adar ta? Ko ta kasa kimtsa kanta har ya fito ya ɓata mata sutura?". Yayiwa kansa tambayoyin a jere. "Miteeeew". Ya kuma jan gajeren tsaki. "Daga nan zuwa parking lot mutun nawa zata sa suga jininta, maza nawa zasu ganta a haka, yanzu ita in an barta wai mai hankali ce ko? Waɗanne irin iyayene gareta da zasu barta kara zube da irin wannan shigar, na tabbatar da suturarmu ta hausa fulani tasa baza'a gane lalacewar kayan jikinta da wuriba kamar wannan tsukekken farin wondon pallozo ɗin ko ya ɓata mata jiki hijabinta zai kareta." Yayi kalaman a saman harshensa. A hankali ya ɗan juyo ya kalleta tana mai ci gaba da tafiya. "Ko ba komai musulmace yana da kyau ta suturce kanta". Ya faɗa yana kallon yadda take jujjuyawa tamkar Wahainiya. Sai-dai bai wuce taku goma tayi ba zuwa sha biyu. Taji muryarsa ta ratsa dodon kunnenta. Inda yace “Stop.” Cikin wata irin kakkauran murya. Aikuwa cak ta tsaya saidai kuma Sam ta kasa juyawa ta kalleshi. Shikuwa Rayyern fuskarsa ya sake had’ewa, tare da yamutsaawa dan ji yake tamkar zaiyi amai kana ahankali ya juyo ya kalli alkyabbar shi dayake gefenshi. A hankali yasa hannunshin ya d’auki alkyabban. Ya tashi tsaye kana ya fara taku a nitse. Har lau bata juyoba kuma bataci gaba da tafiya ba. Salman kuwa juyowa yayi ya zuba musu ido. Kauda kansa gefe yayi lokacin daya kara taku ɗaya ya iso kusa da Jannart ɗin. Ƙara matsowa yayi kusa da ita yana mai ware alkyabbar. Kanshi ya ɗan ronkofar cikin yamutsa fuska yace. “Duk wata Macen da tasan ciwon kanta, bata yawo a haka kamar yanda ke kike yi, sannan mata da yawa suna sirranta kansu, amma ke kina bayyana kazantarki in kika sani nayi amai bazan yafeba.” Cike da mamaki ta ɗan juyo yana kallonshi. Hakan ya zama kamar irin hirar masoyane irin ana kallon juna nan. Wani saurayi ne dake can ta bayane yana kallonsu ta cikin raga, Ya zaro wayarsa da sauri ya fara ɗaukar su hoto, domin ya gano ƙanwar Junaidu ce. Shi kuwa Dr Rayyern Mai-nasara harara ya watsa mata tare da cewa. "Mitssssss Ni ki dena kallona ko in tsokale idanun". Ya fad’i maganar yana me zagayeta tare da dago alkyabban ya d’aura mata akan K...! Fawal beauty parlor sunai muku albashir da bude gidan Mata wato kigyara da kanki👩🏻‍🦰 da cewa suna gabatar da aiki na zamani kamar su gyaran jiki, spa kenan gyaran fuska wato facial,gyaran Kai, hair style , gyaran kafa pedicure,gyaran hannaye, manicure kitso,lalle ja da bakki,ba'a barsu abayaba suna saida kayan gyaran aure, turaruka,man shafawa, suna kwalliya wato makeup,turaren wuta, humrah,kulaccham dama abunda Baku sanshiba wato maida tsohuwa yarinya akankanin lokaci😄iya kudinka iya shagalinka💃kudai ku hanzarta zuwa ga wannan gida na mata zallah (FAWaL BEAUTY PARLOR) Address: Main gate na fire service jimeta, opp sixty plaza. kada kubari abaku labari😍 munai muku maraba a koda yaushe Mata yan kwalisa mace sai da gyara , yar uwa bora ba sunanki kizama mowar mai🏨 da taimakon FAWAL BEAUTY PARLOR 👩🏻‍🦰da kudinki qalilan kifita sab abunki ki baza kamci mai kama jiki. Gamai buka contact CEO FAWaL BEAUTY PARLOR kan 09033901035 or 08078809930 sai kunzo, our time services from 8:am to 7pm, Monday to Saturday/ Sunday 10am to 6pm🪞🎁🛒🛍️🤝🏻 *By* *GARKUWAR FULANI* 11/15/21, 7:20 PM - Auntyna: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *TUBALI* PAGE 13 NA *AYSHA ALIYU GARKUWA* *FREE PAGE ne* *Littafin TUBALI na kuɗine ki biya kafin ki karanta cikin salama da aminci special Group 1k ƙaramin group 500 ne kacal 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU sai ki turo min shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276 in Kuma baki da halin turawa ta account sai ki sayi katin MTN ki copy number's din ki turo min ta WhatsApp 09097853276* Fawal beauty parlor sunai muku albashir da bude gidan Mata wato kigyara da kanki👩🏻‍🦰 da cewa suna gabatar da aiki na zamani kamar su gyaran jiki, spa kenan gyaran fuska wato facial,gyaran Kai, hair style , gyaran kafa pedicure,gyaran hannaye, manicure kitso,lalle ja da bakki,ba'a barsu abayaba suna saida kayan gyaran aure, turaruka,man shafawa, suna kwalliya wato makeup,turaren wuta, humrah,kulaccham dama abunda Baku sanshiba wato maida tsohuwa yarinya akankanin lokaci😄iya kudinka iya shagalinka💃kudai ku hanzarta zuwa ga wannan gida na mata zallah (FAWaL BEAUTY PARLOR) Address: Main gate na fire service jimeta, opp sixty plaza. kada kubari abaku labari😍 munai muku maraba a koda yaushe Mata yan kwalisa mace sai da gyara , yar uwa bora ba sunanki kizama mowar mai🏨 da taimakon FAWAL BEAUTY PARLOR 👩🏻‍🦰da kudinki qalilan kifita sab abunki ki baza kamci mai kama jiki. Gamai buka contact CEO FAWaL BEAUTY PARLOR kan 09033901035 or 08078809930 sai kunzo, our time services from 8:am to 7pm, Monday to Saturday/ Sunday 10am to 6pm🪞🎁🛒🛍️🤝🏻 Yayinda acikin ranta take fata da kuma burin ganin auren d’an nata, Tabbas tana matuk’ar son ace mata Rayyern dinnata yayi aure, domin kuwa ko babu komai zai samu macen da zata kula dashi, Wanda zata jib’anci duk wani al’amuransa, kama daga ci da sha zuwa farin cikinsa kula mishi da tsabtan muhalinsa ko Ramadan ma ya huta. Sai-dai kuma amma ya zata yi, tunda duk sun fahimci cewar ba son auren yake ba, baya shiga harkar mata, balle harsu saka ran cewar watarana zai samu wacce zata yi mishi. Ido ta zuwa Ramadan wanda kiran wayarsa da akayi yasa ya miƙe ya nufi Dinning area, bisa kujera ya zauna. Bisa alamu duk. Raihana ce ta kirashi budurwarshi. Rayyern kuwa yana isa cikin bedroom din, kayan jikinsa ya rage tare da shigewa cikin bathroom ya sakarwa kansa ruwa. Idanunsa ya lumshe adai-dai lokacin da yaji Sauk’an Sassayan ruwan showern akan fatar jikinsa. Haka yakejin wani irin nutsuwa na musamman na sauk’ar masa. Ahankali kuma yakejin duk tarin gajiyar da yayi yana sauka. Atsanake ya kammala wankan nasa, inda ya fito daga shi sai towel dake daure a kugunsa, ad’ayan hannun nasa kuwa mini towel ne Wanda yake tsane jikinsa dashi. Bayan ya kammala ne kuma ya Shafawa jikinsa wani had’add’en mai, tare da men spray mai dadin kamshi. Sabin riga da wandon da ya ciro daga cikin drawer d’insa ya sa. A hankali ya fito dan sauƙa ƙasa, coffee yake so ya ɗan sha. Yana fita falo kuwa ya samu Abba da Ramadan a tsakiyar falon da alamun mgnar Aure Ramadan yakeyiwa Abba. Shi kuwa Abba idanu kawai ya zubawa Ramadan yana kallonsa, ya sani a zatonsu bai damu da mgnar auren Rayyern bane. Shi kuwa yasan sunada babban buri da manufa da shi yakeso yaga Rayyern ya cimmawa, so ganin bai damu da harkar mata bane yasa ya zuba mishi ido, tunda shi nuna musu yake baima san me akeyi da maceba shi kanshi yasan aiyukan daya ɗaurawa Rayyern sun mishi yawa sunfi ƙarfin shekarunsa kawai ƙarfin hali ne da ƙwazo da jarunta yasa yake iya leading komai yadda ya kamata, amman ya rasa lokacin kansa, yana son ya sashi ya saki aikin asibitin ya fuskanci kasuwanci su, to kuma yasan likitancin shine burinsa badon hakaba ai da sai ya bawa Ramadan sashin asibitin duk da dai yanzuma shi bai cika zuwaba. A hankali ya ƙara so kusa dasu. Ganin haka ne yasa suma suka miƙe suka karasa kan dining table danyin dinner. Shidai Rayyern kamar kullum baiwani ci abincin kirki ba, ya tashi tare dayi musu sallama ya wuce side d’insa. Yana shiga kuwa ya murzawa kofar tasa key. Toilet ya koma ya sake dauro alwala, bayan ya fito ne kuma ya sanja kayan jikinsa izuwa payjamas mararsa nauyi. Wata yar jaka da yake ajiyan chocolate d’insa ya dauko, tare da bud’e cikin jakan ya dauki babban ledan chocolate na milka & oreo, bayan ya Bare ledan ne kuma yasa chocolate din abakinsa, tare dayin switchoff na wutan dakin ya kwanta. D’an mirginawa yayi, kana ya dauki wayarsa dake aje akan gadon. Sak’onnin Email da ake turo masa ya shiga dubawa atsanake, time to time kuma yake lumshe ido saboda yanda yake jin dadi da kuma zakin chocolate din na game bakinsa. Ya dauki sama da 30minute kuwa yana duba sakonnin, inda yake replies na wasu sakonnin da suka zama dole, sauran sakonnin kuwa da basu da buƙatar amsa sharewa yayi tare da kashe datansa ya ajiye wayar. Yana gama shanye chocolate din nasa kuwa, ya daura kansa akan pillow tare da jawo blanket ya rufawa jikinsa. Addu’an kwanciya bacci yayi, kamar kuma yanda ya saba yi akowacce rana, haka yau dinma Yana me ambaton sunan Allah bacci ya daukesa. 10:30 pm. Jannart. Sake had’e jikinta waje d’aya tayi, tare da rungume dan k’aramin pillown dake Manne akirjinta. Ak’alla yanzu kusan mintuna 20 kenan da takeson bacci ya dauketa amma ya kasa, duk yanda takai ga rumtse Idanunta kuwa, To wasu kalan tunani ne ke bijurowa cikin k’wak’walwarta. Yayinda ƙamshin turaren dake fita ajikinta Yana me Ratsa cikin hancinta ya hana ta sakat. Akasalance kuma cikin yanayin shagwab’a takai hannun ta dake kamshin turaren zuwa kan hancinta, Sam batasan taya akayi kamshin dake jikin al'kyabban nasa ya kama jikinta ba har hakaba. Gashi asanadiyar kamshin gaba daya ta kasa bacci, Wanda kuma batasan dalilin hakan ba. Ajikinta takejin wani iri aduk sanda kamshin turaren nasa ya daki hancinta, har wanka tayi wai ko zata daina jin kamshin amma babu wani abu daya sanja. “Oh Allah wannan wani irin jarababben kamshi ne haka daya kasa barin jikina?, Wani irin kamshi ne da shakansa ke haifar min da bugan zuciya, Yah Allah nidai kasa nayi bacci yanzu, Dan wallahi nagaji, daga saka al-kyabba kawai sai kamshin mai al'kyabban ya manne min.” Ta kai karshen maganan tana me sake kankame jikinta waje daya. Tare kuma da rumtse Idanunta da karfi, acewarta wai ko bacci zaizo ya dauketa. Domin ita kanta ta kasa tantance hakikanin abunda kamshin ke bata, nutsuwa ne ko akasin haka. Sai-dai koma meye tayi imani cewar kamshin nada matukar daɗi shaƙa da sanyaya rai . Haka kuwa ta dinga juyi akan gadon nata, har sai wajajen 11 pm kafun bacci ya dauketa. *Washegari.* Kamar yanda ya saba kowacce rana, haka yau dinma ta kasance masa. Saidai kuma kwalliyar tasa tayau ta banbanta dana sauran ranaku. Saboda kalan suit din nasa nayau Maroon ne, sai kuma milk colour long sleeve wacce ta kasance aciki. Yayinda ya saka wa kafansa wasu tsadaddun takalma masu matukar kyau da daukar hankali. Yayi kyau matuka, musamman ga fuskarsa, Domin kuwa Lallausan bakin sajensa ya kwanta lub, haka ma gargasan saman idanu dana giran sa masu daukar hankali. Agogon rolex daya daura akan tsintsiyar hannunsa ne kuma ya k’ara bayyana kyaun adon nasa. Hakika Rayyern kyakkyawan matashi ne Wanda ya hada abubuwan so dana burgewa, komai nasa na dabanne, shiyasa abune mawuyaci Namiji ko Mace suyi mishi kallo daya su dauke kai. Ahankali yake saukowa daga kan steps din falon, Yayinda gaba daya Rabin hankalinsa ke ga agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa yana Kallon lokaci. Abba Mamy da kuma Ramadan da suke zaune akan dining table ne duk suka d’ago suka kalleshi. Abban ne kuma ya danyi gyaran murya, tare da cewa. “Rayyern agogo sarkin aiki ka fito.” Jin abunda Abban ya fad’a ne kuma yasa shi ɗan lumshe ido tare da longobar da kai bisa kafarsa. Cikin kuma yanayin dake bayyana tsananin kaunar iyayen nasa yace. “Abba Mamy barkanku da safiya.” “Yauwa barka dai Rayyern ka fito ko, dama yanzu nake da shirin kiranka, Domin tun dazu na gama breakfast kuma naga yau baka sauko da wuri ba, yanzu fa wajen 8 ake nema.” Cewar Mamy dake kokarin hadawa Ramadan tea. “Eyyah Mamy yau ba hospital zanje ba shiyasa ban sauko da wuri ba, inason naje na duba aikin company’n mu da ake ginawa ne, tun jiya engines din da nayi order a us suka iso, To yau inaso naje naga ya yanayin aikin yake tafiya, Domin na fiso daga ansa engines din abude company’n saboda mutane su amfana tunda an gama komai na gini haɗa enginer's ɗin ne kawai ya rage kuma yau za'a fara.” D’an tsagaitawa da maganan nasa yayi, tare dajan kujera ya zauna. Cikin sanyi kuma yaci gaba da cewa. “Mamy da yawan matasa acikin Nigeria’n nan sunyi karatu, amma suna fama da matsalan rashin samun aikinyi, hakan kuwa shi yake sa wasunsu su shiga aikata abunda bai dace ba, yana da kyau ka inganta rayuwar na kasa dakai, da kuma mutanen dake neman taimako, wannan dalilin yasa zan d’ebi ma’aikata da yawa na zuba su acikin company’n saboda su samu hanyar da zasu na cin abinci da kuma biyan buk’atunsu ko Abbana?.” Kai Abba da Mamy harma da Ramadan suka jinjina, cike kuma da tsananin gamsuwa Abba yace. “Duk wani tunaninka dai-dai ne Rayyern, wannan yasa akoda yaushe nake alfahari dakai, Allah ya dafa muku akan duk wani abu da kukeso ku cimma kaida d’an uwanka.” Da “Ameen.” Suka amsa su dukansu. Nanfa Mamy ta had’a masa tea da soyayyen k’wai hadi plaintain yaci. Bayan ya kammala ne kuma yayiwa iyayen nasa sallama, inda shida Ramadan suka fito atare. Bayan sun shiga motocinsu ne kuma Baba Maud’o ya taso zai bud’e musu gate. Da sauri Rayyern ya kira Hadi yace ya buɗe musu gate. Toh yace kana ya buɗe musu. nanfa kowa yayi hanyarsa, inda Ramadan ya nufi hospital dinnasu, shi kuwa Rayyern kaitsaye ya wuce inda ake ginin new company d’in. Adai-dai lokacin daya mik’i titi ne kuma ya maida hankalinsa ga tukin da yakeyi. Hakanan kuma yaji ajikinsa tamkar akwai wani abu dake faruwa. Kansa yad’an d’aga Ahankali ya kalli mirror. Karab kuwa idanunsa suka Sauk’a akan motar dake biye dashi abaya. Idanunsa yadan kankance tare da maida kallonsa ga numbern dake jikin motar. Wani irin murmushi yayi, a lokacin daya gane cewar motar da take bibiyarsa daren jiyane ta biyosa yau ma. Kansa yadan jinjina, still ba tare da tsoro ko fargaban komai ba ya ci gaba da tukin, saidai lokaci zuwa lokaci yakan dago kansa ya kalli motar dake bibiyartasa ta cikin mirror. Adai-dai wannan lokacin kuwa a gidan su Jannart gaba dayansu zaune suke akan babban dining area’n da aka kawatasa da abubuwan burgewa. Dady Momy Abdull da kuma Jannart ne kecin abinci, Yayinda shi kuwa Junaid gaba daya hankalinsa ya maidashi ne ga Jannart. Da yake watsa mata wani irin kallo, mai kama da na kiyayya da kuma tsananin jin haushi. Ita kuwa Jannart lura da tayi, da irin Kallon da Yayan nata ke watsa mata ne yasa ta kasa koda d’ago kanta. Badan kuma tanajin yunwa ba haka take ta tura abincin acikin cikinta. Junaid kuwa tsaida idanunsa da yayi akan d’an karamin bakinta dake tauna abinci ne, yasashi sakin kwafa. Tare da cije labbansa, kana acikin zuciyarsa yace. “Wallahi nayi rantsuwa duk ranan dana kama yarinyar nan ahanuna, bazan kyaleta ba sainaga bata numfashi, ko mutuwa zata yi kuwa bandamu ba saina sauke duk wani abunda nakeji, shegiyar yarinya mai kama da aljanu, kullum wutar sha'awarta take huramin ajikina, wutar kuma da har yau na kasa kasheta.” Hmmm ya sake yin k’wafa tare da watsa mata hararan, daya sa hanjin cikinta kad’awa. Saurin kawar da kanta gefe tayi, tare da ajiye spoon din dake hannunta. Hakanne kuwa yasa Dady dake ankare da ita, d’agowa ya kalleta tare da cewa. “Jannart kwana biyunnan me yake damunki ne wai, ina lure dake ko abincin kirki kin daina ci.” Jin tambayar da Dadyn yayi mata ne, kuma yasa tadan sunkuyar da idanunta kasa, tare da soma wasa da yatsun hannunta, cikin sanyin daya zamar mata sabo tace. “Babu abunda yake damuna Dady, kawai dai Ina kewar gidan Abba Kabir ne. Dan Allah Dady kabarni naje, nayi maka alk’awarin bazan jima ba zan dawo, Dan Allah...” Ta k’are maganar tana me karyar da wuyanta gefe. Yayinda lokaci daya kuma Idanunta suka cicciko da hawaye. Shiru Daddyn nasu yayi baice komai ba ak’alla har na tsawon mintuna 5. Hakanne kuwa yasa zuciyar Jannart karyewa, saboda tasan abune mai sauki Daddyn ya hana ta zuwa, tunda dama bayan office daya yarje mata zuwa, bai sake yarje mata zuwa ko ina ba. Komai zatayi dole saida izininsa, hatta shopping Idan zatayi dole saida amincewarsa zata je. “Shikenan kije amma kada ki jima, kwata kwata 3hours na baki, Sannan kuma kafarki kafar su Sunday, ban amince ki taka k’afarki a wani waje ba Idan babu su.” Dadyn ya fad’a cikin kakkausar murya. “Nagode Daddy kuma Insha Allah, zan kiyaye.” Ta fad’i hakan cikin farinciki, saboda bata tab’a kawo aranta cewar zai barta ba. Batare kuma da ta jira komai ba ta mike tsaye, tare da nufan dakinta kaitsaye. Inda Junaid ya bita da Kallon takaici kasa-kasa, Domin Sam baiso Daddyn nasu ya bata izinin fita ba. Yaso ace ta zauna agida yaudin, ta yanda zai sake kai Mata Hari, da kuma dana mata tarkon da ba zata tab’a iya tsallakewa ba. Acan b’angaren Rayyern kuwa, duk da yasan cewar ana biye dashi amma tukinsa yake cikin nutsuwa. Ahaka har ya kawo bakin babban katafaren company’n nasa. Wanda asamansa aka rubuta. *MAI-NASARA NIG LTD* An kuma yi rubutunne da manyan haruffa, Wanda komin Nisan inda mutum yake zai iya karantashi. K’aran horn din motar daya danna ne kuma yasa masu gadin babban companyn su biyu suka had’a karfinsu wajen bud’e babban gate din mai matukar girma. Cikin k’warewa ya tura hancin motar tasa cikin companyn, Yayinda yake Kallon motar dake biye dashi abaya, Wanda shigansa Cikin company’n ya sata juyawa ta koma. Wani irin murmushi dake d’auke da ma’anoni daban daban yayi, bayan ya gama daidaita parking ne kuma, ya bud’e murfin motar ya fito. Inda atsanake ya soma karewa babban company’n nasu kallo. Company ne mai girman gaske, Wanda Idan mutum yace zai zagaye duka cikinsa, sai ya share sama da awa biyar yana yawo bai isa karshen saba, Domin kuwa hawa hawa har bakwai akayiwa babban ginin company’n, ko wani hawa kuwa girmansa ya zarce tunanin mutum. Haka kuma company ne da aka k’awatasa da ginin zamani, had’i da shuke shuken flowers masu kyau da burgewa. Tabbas anyiwa company’n tsari mai kyau, da burgewa, Domin duk da girmansa, saida aka k’awata ko ina da abubuwan more rayuwa na zamani. Ahankali yake taka k’afafunsa tare da nufar Cikin company’n yana mai son danne tunanin son sanin menene Tubalin dukiyar mahaifin nasu tabbas bakwai zarginsa yakeba amman yana son sanin tubalin dukiyar, sai dai yasa a ransa tabbas ya kusa tambayan Abbansu. Ganinsa da ma’aikatan wajen suka yi ne kuma, yasa suka dinga rusunawa suna gaishe sa. Inda shi kuma ya dinga amsa musu fuskarsa asake, saidai ba wai sakewa irin Wanda zata saka wasu daga cikinsu su rainashi ko suga zallar saukin kansa ba. Sakewace irin Wanda take bayyana, basu matsayinsu da yayi amatsayinsu na y’an Adam. Domin ko Allah Da kansa yace ya karrama y’an Adam. Duk inda ya wuce kuwa kansa yake jinjinawa, saboda yanda yaga ma’aikatan dake saka engines din na saka komai akan tsari mai inƙanci. Kaitsaye babban katafaren office d’insa dake can sama ya nufa bayan ya gama duba wuraren da ake kafa na'urorin sarrafa shinka yayinda Engineer dake jagoranci aikin ke biye dashi a baya. Yana nunnuna mishi komai kai tsaye Office nashi ya nufa. Wanda already anriga da Anyi setling komai dake cikinsa, ank’awatasa da abubuwa masu kyau da burgewa Office din babbane mai yalwan kayan ƙawa. Koda ya shiga cikin office din suit din dake jikinsa ya zare, tare da zama akan hamshakiyar kujerar da musamman take mallakinsa. Wayarsa dake cikin al'jihunsa ya zaro. Tare da kunnata kaitsaye ya saka numbern wannan motar da acikin kwana biyun take bibiyarsu. Bayansa ya jingina da jikin kujeran, tare kuma da Dan lumshe Idanunsa. “Road Safety.” Ya fad’a cikin sanin makamar inda daya nufa. *Jannart.* Tsaye take agaban dressing mirror dinta, Wanda gabansa ke cike da tarin kayan kwalliya. Yanayin yanda take sanye da towel ajikinta ne kuma, yake bayyana cewar fitowarta daga wanka kenan. Atsanake take shafawa lallausan fatar jikinta mai, Yayinda zuciyarta ke cike da nishadi da kuma zumudin fitar da zatayi yau din. Kasancewar tayi missing din gidan Abba Kabir din sosai. Bayan ta gama shafa mai din ajikinta ne kuma, ta murza powder akan fuskarta, hade da gogawa red lips dinta shining lipgloss. Sai kuma kajol da mascara da ta saka, Wanda suka kara fitar da kyaun fuskarta. Batare kuma da ta sake goga wani abun akan fuskarta ba, ta k’arasa gaban wardrobe dinta, Inda ta zaro wani had’add’en doguwar rigar material, wanda yasha dinkin fitted gown Wanda yana ɗaya daga cikin kayan da Barrister Kabir ke dinka mata, da Mom. Koda ta sanya rigar ajikinta, kuwa ba karamin kyau yayi mata ba. D’an kunnen gold marar nauyi tasa akunnenta, tare da daukan wani siririn mayafi ta yafa akanta. Bayan ta zura half cover shoe akafarta ne kuma ta dauki wani baby hand bag Wanda yayi shige da kalan kayanta ta rik’e Agogon dake sak’ale ajikin Bangon dakin ta kalla, ganin da tayi kuma lokaci na tafiya ne, yasa agurguje ta dauki wayarta ta fice daga cikin dakin. Koda ta sauk’o afalon k’asa ta samu Momy. Ganin yanda Jannart din tayi kyaune kuma yasa Momyn sakin murmushi, cikin nuna kulawa tace. “A'a Jannart yau wacce rana ansaka kayan hausawa.” Murmushi Jannart din tayi, tare da karasowa inda Momyn ke zaune, ashagwab’e tace. “Momy kayan baimin kyau ba ko?.” Dariya Momyn tayi had’e da cewa. “Ya miki kyau mana sosai Jannart, ai yama fi miki kyau akan kowanni kaya.” Murmushin daya bayyana fararen hakwaranta tayi, cikin yanayin dake bayyana jin dadinta tace. “Nagode sosae Momy na, in sha Allah zan koyi saka irinsu.” Cikin jin daɗi Mom tace. "Kai Alhamdulillah da naji daɗi haka kuwa Boɗɗo na". Sassanyan murmushi tayi tare da lumshe idonta kana tace. “bari naje saina dawo.” Kai Momyn ta jinjina tare da cewa tagaishe da Abba Kabir din da kuma matarsa, da yaransa. Da “to.” Jannart din ta amsa, kana tasa kai ta fice daga cikin falon. Tana fitowa compound din gidan kuwa ta samu Baba Ado driver da guard dinta na jiran ta. Domin tuntuni Daddy da kansa ya Gaya musu cewa Jannart din zata fita. Yayinda kuma ya jaddada musu kulawa da ita. Kamar Koda yaushe kuma tana shiga cikin mota, guard din nata ma suka shishshiga cikin tasu motar, tare da rufawa motar da Jannart din ke ciki baya. Jin da tayi sunhau titi ne kuma yasa ta d’an jingina bayanta da jikin kujeran motar, tare da lumshe idanunta. Ahankali take sauk’e ajiyar zuciya, Yayinda ayau din takejin kanta tamkar sakakkiyar tsuntsuwa. Lallai watarana tana fata da burin samun yancin kanta, watarana tana fatan yin yawonta ita kad’ai batare da wani ko wata sun bibiyeta ba, haka kuma watarana tana fatan sauyawar rayuwarta gaba d’aya. Yayinda kuma har acikin zuciyarta watarana take fata dason sanin kullin dake ƙule Cikin rayuwarta kamar yadda Barrister Kabir yasha faɗa mata. Shin Meyasa Daddy’nta ya sanya mata tsaro maitsanani har haka duk da kuwa tana gamsuwa da irin soyayyar da yake nuna mata, ɗari bisa ɗari. Meyasa Yah Junaid ke bibiyanta da munanan halaye? Da mugun manufa. Yaushe ne canji zaizo cikin rayuwarta? Yaushe ne zatayi farinciki kamar kowa? Yaushe zataji kanta amatsayin Mace mai y’anci? Lallai watarana zuciyarta kan gaya mata cewa Sauyin rayuwa zaizo. Sai-dai yaushe zaizo? Da wani dalili zai taho a wanne yanayin duk bata sani ba. Wani irin numfashi mai dumi ta fesar, adai-dai lokacin kuwa suka iso kofar madaidacin gidan Barrister Kabeer dake nan Nassarawa G.R.A Wanda kuma isowarsu gidan yayi dai-dai da shigowar sak’o cikin wayarta. Jin alaman shigowan Sakon da tayi ne kuma yasa ta d’ago wayartata ta duba. Ganin sakon da aka rubuta mata dinne kuma yasa ta. Jin wani irin bugun zuciya maitsanani. Idanunta ta rumtse da k’arfi, cikin kuma muryarta da ke bayyana tsoro had’i da firgici Ta...... *GARKUWAR taku ce dai MA'AURATA, da masu shirin aure, da masu jego, da yan gayu masu son k’amshi kece raini, da gyaran da zaike maimaita muku dararen forkon kuruciya* Ko kunsan Jikinmu na da sinadaran hormones da suke taimakawa dan’adam akan komai musamman lokacin da mace take mu’amalar aure da mijinta. Mafi akasari wannan hormones din ne ke samun matsala ko su yi sanyi koma su daina aiki kwata-kwata shi ne dalilin da zai sa mace tace bata jin sha’awa ko bata san dadin aure ba. Albishirinku ina da kayan da ke taimakawa wannan sinadaran du dawo aiki tukuru don karkato miki da kimarki wajan mai gida sannan su taimakawa wannan sinadaran hormones dinki su dinka secreting din ni’ima wadatacciya da zata taimaka miki ki gamsu mijinki ya gamsu fiye da tunaninki. Note: Kayana ba sa tsinka ruwan ni’ima suna dai taimakawa hormones dinki ne su tsattsafo da ni’imar musamman wacca cutar sanyi ko dattin mahaifa ya dankarar da su ya hana su yin aikinsu yanda ya kamata. Haka zalika idan kina da kyau ki kara da wanka. Zaki iya amfani da magani na na gargajiya wanda zai gyara miki sex hormones din kullum ki kasance cikin humidify wato cikin damshi mai albarka kamar yanda ake son mace. Yana gyara miki mara. Sai kamshi. Hajiyata daure ki fara amfani da turarena ki ji irin salon kamshin sa salo ne da zai daidaita ki da mijinki ya kankaro miki da kimarki a wajansa. Siyan na gari mayar da kudi gida. Ga masu buƙata ga number' wayata wanda nake whatsApp dashi 09097853276 kimin mgn ta whatsApp in har kin tabbatar kin shirya saya mu dai-dai ta, kayana ba ƙanana bane, shiyasa bana harkan karanta, muddin kinsan baki shirya saya ba Please kada kiyi min mgn ki bari sai kin shirya kuɗinki a hannu, ba ina nufin kayana bana talaka bane, no akwai ƙananan set na masu karamin karfi, banson aimin mgn a ɓatamin lokacin aiyukana a shirme baki shiryaba. Shine karantan da bana so. 0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU. In kin shirya ga number ta ga kuma account number ta wanda in mun gama mgn zaki turo kudin ki, kana insa miki kaya a mota akai miki state ɗin da kike, Duk ƙasar da kike kayana zaije gareki, amman fa in kinada dalilin zuwan nasune TA *D.H.L Office*🤝🏻cikin mako ɗaya kayanki zai isa duk ƙasar da kike, sai dai akwai ɗan tsada cajinki da zasuyi sayan na gari meda kudi gida. GARKUWAR MA'AURATA By *GARKUWAR FULANI* 11/15/21, 7:20 PM - Auntyna: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *TUBALI* PAGE 14 NA *AYSHA ALIYU GARKUWA* *FREE PAGE NE* *Littafin TUBALI na kuɗine ki biya kafin ki karanta dan Allah special Group 1k ne karamin group 500 bane kacal 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU sai ki turo min shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276, ko kuma ki sayi katin MTN ki copy number's din ki turo min ta WhatsApp na 09097853276* Ta buɗe idonta ganin sunan Yah Junaid na bisa screen ɗin wayarta ne yasa, ta fidda numfashin a hankali tare da cewa. “Innalillahi wa'inna'ilaihi rajiun Yah Junaid Kuma?”. Cikin tsoro ta buɗe text ɗin dai-dai lokacin kuma mai gadin gidan Barrister Kabir ɗin ya buɗe musu gate. Suka kutsa ciki. "Dan ubanki ina kiranki bazaki amsa ba. Maza ki ɗaga ko in ɓaɓɓllaki in mun haɗu". Cikin ƙarfin hali ta zuge zip ɗin Baby hand bang din ta cilla wayar kana ta zuge ta rufe. Da sauri Aunty Dijat tace. "Lah Hafiz ga Aunty Jannart tazo". Ta ƙare mgnar tana nufar inda motarsu Jannart tayi parking. Hafiz kuwa da sauri ya juyo jin ance Jannart, cikin ware ido ya nufi motarsu a guje yana cewa. "Oyoyo my Aunty, Hafiza ga Aunty Jannart tazo". Murmushi mai cike da jin daɗi Jannart tayi kana ta ƙarisa fitowa tare da ware musu hannayenta. A guje suka abka jikinta su duka biyu. Cikin jin daɗi da son yaran ta ɗaga Hafiza da bazata wuce 7 year's ba. Ruggume ta sukayi duka suna farin cikin ganinta. Cikin kula, so, ƙauna, da tausayawa Aunty Dijat ta iso garesu fuska ɗauke da murmushi tace. “Oyoyo Aunty Jannart, yau munji daɗin mu kin tunomo”. Cike da happy tace. "My Aunty kullum kuna raina". Hannu tasa ta amshi Hafiza tare da cewa. "Zo nan kada ki karya min ƴata maza mu shiga daga ciki." Aifa tana faɗin haka Hafiz ya ɗiba a guje yayi cikin gida. Ita kuwa Jannart juyowa tayi ta kalli Baba Ado dake gaisawa da Aunty Dijat. Ita kuwa Aunty Dijat kamo hannun Jannart tayi suka juya suka nufi cikin gida. Cikin murmushi ta juyo ta kalli Baba Ado dake cewa. "Jannart muje ne ko mu jiraki". “A'a Baba Ado ku jirani Awa uku Daddy ya bani". Kai ya jinjina mata, kana ya koma wurin mai gadin gidan. Su Sunday Kuma suka tsaya tamkar gumakan taɓo. Daga bakin falon Hafiz keta rabkawa Barrister Kabir kira. "Abba! Abba!! Kazo ga Aunty Jannart tazo". Da sauri Ya miƙe tsaye, tare da katse wayan da yakeyi wanda kuma dama akan wani case ne da zasu shiga gobe, Cike da farin ciki ya fara tako steps ɗin sauƙowa men falon su. Ita kuwa Jannart Murmushin jin daɗi takeyi wanda ke bayyana tsantsan jin daɗin da take ciki. Ita kuwa Aunty Dijat kitchen ta nufa. fruits masu sanyi ta ciko mata plate dasu. Kana da Bootle water. Tana isowa Abba na ƙarasowa. Kujerar dake gefenta ya zauna tare da sakin murmushi yace. "Hafeeza zaki karya min cinyar ƴa ko". Murmushi tayi tare da ɗan zamowa kaɗan tace. "Abba ina yini". "Lfy lau Alhamdulillah Jannart ya jikinki!?”. Barrister Kabir ya faɗa cikin kulawa. Yana mai kallon matarsa dake nuna tsantsan so ga Jannart murmushi yayi tare da cewa. "A'a Khadijah kin mance Jannart ne da Asman kika kawo abu mai sanyi". Ita kuwa Jannart a hankali tace. "Abba nayi sauƙifa zan iya cin komai". Kai ya jujjuya tare da cewa. "A a ban yardaba". Da sauri Hafiz Wanda zai iya kai shekaru goma sha shida yace. "Abba yau kawai a barta taci". Ina tuni Aunty Dijat ta juya kitchen. Pepper chicken da yanzu ta gama aikinshi da zafinshi ta ɗebo, mata tare da haɗa mata tea mai zafi. "Yauwa ci wannan bari su kuma na sa miki innabi da tufa ɗin a ruwa zasuyi ɗumi zuwa anjima sai kici". Murmushi tayi tare da cewa. "Ngd matuƙa my Aunty". Haka nan sukayi ta nan-nan da ita tamkar suyi mata numfashi. A can MAI-NASARA NIG LMT kuwa. Dr Rayyern Mai-nasara ne zaune cikin nitsuwa yake duba bayananan da hukumar Road Safety, Suka turo mishi akan number motar daya tura musu. Dan neman ƙarin bayanin. Sanin waye shine yasa nan take suka turo mishi sunan mamalakin motar. "Alhaji Idi Saleh Dakata." Shine abin daya mai-mai-ta kan lips ɗin shi. Numfashin gajiya ya ɗan fesar kana a hankali ya kuma ci gaba da ganin jerin jadawalin numbers ɗin motocin da suke mallakinsa kab. Ido ya lumshe tare da meda bayanshi ya jingina jikin kujerar a hankali. Ya fara jujjuya kujerar, cikin sanyi ya fesar da numfashi mai sanyi tare da cewa. "Uhummm!”. Kana ya gyara zamanshi tare da ajiye wayar da tunanin waɗannan tsoffin gefe. System ɗin shi ya jawo ya ci gaba da aikin daya shafi Campany'shi na neman ma'aikata... Yah Junaid kuwa yau ji yake tamkar ya kashe Jannart in ya kamata sabida, video'nta da Ushe ya turo mishi lokacin da Rayyern ke samata al'kyabbar. “Wato dai shegiyar nan tasan maza tasan garɗinsu, ni takeyiwa tereren bankaɗa in na taɓata. Yau kuwa tabbas sai na caccakaki shegiya ƴar iska mai idon cin maza. Yoh dama ya za'ayi wannan zuƙeƙeyiyar. Tarwadan kyau ta zauna babu masu lasarta". Kwafa yayi tare da ƙara yi mata text cewa yana kiranta fa. Dan shi masifar feelings yasa ya mance da cewa bata nan ma. Gashi ya leƙa falo yafi sau uku Mom na zaune... A gidan Barrister Kabir kuwa. Hira sosai Aunty Dijat da Jannart Da Abba dasu Hafiz sukeyi sunci sun Sha, sun kaiwa su Baba Ado ma, dan Aunty Dijat matar kwaraice. Kiran sallan azahar da akayi ne, yasa Abba miƙewa shida Hafiz suka shiga sukayi al'wala bayan sun fito suka nufi masallaci. Abba na cewa. "Ku tashi kuyi salla, ko”. To sukace. Bayan sun fita Aunty Dijat ta miƙe tare da cewa. "Muje muyi salla ko Jannart". Kanta a sunkuye tana yiwa Hafiza kitson kalba ƴan ƙanana a tarin gashin ta tace. "Nayi". Tayi mgnar a hankali kana a gajarce. Murmushi Aunty Dijat tayi tare da cewa. "Oho kinyi da mutanen Makka kenan". Cike da kunya tasa tafin hannunta ta rufe fuskarta cikin tsananin kunyar an gane tana fashin salla. Ita kuwa Aunty Dijat murmushi tayi tare da wucewa Bedroom ɗin ta... Bayan tayi sallan ne kuma ta fito ta sameta suna kitson. Kitchin ta wuce Fruits ɗin ta kawo mata. Kana ta zauna gefenta tare da miƙa mata fork. Dai-dai lokacin Abba da Hafiz suka shigo. Cikin kula Abba ya kalleta kana yace. "Yauwa Jannart ku taso muje mall ku ɗan zazzaɓi abin da kukeso ko". Cikin jin daɗi tace. "Abba muna kitso komai ma aka kawo mana muna so". Ya gane manufarta bazatace bazata jeba, amman ta bashi mgnar a dunƙule sanin tanada hujjar faɗin haka yasa yace. "Daddy zaiyi faɗa ko?". Kai ta gyaɗa tare da gyara zaman kan Hafiza bisa cinyarta kana tace. "Kuma nan ɗin ma awa uku fa ya bani. Gashi yanzu naci biyu saura ɗaya". Hannu ya miƙa wa Hafiz tare da cewa. "Toh ba matsala kuyi kitsonku bari muje yanzu mu dawo, kada Daddy ya haɗa hardani ya tsire”. Kai ta jinjina, har sunje bakin ƙofar fita kuma ya juyo cikin kulawa yace. "Toh me da me kikeso in seyo miki?”. Kai ta ɗan ɗago ta kalleshi tare da yin murmushi tace. "Abba kayan hausawa". Cikin gamsuwa yace. "Masha Allah Ina ga dai ɗiyata ta canza salon shiga ko”. Cike da kunya tace. "Eh Abba naga waɗanan can ɗin basu da rufin asiri kamar namu. Yauwa Abba da hijabai". Ita dai Aunty Dijat murmushi kawai takeyi. Shi kuwa toh yace kana ya fita. Nan sukaci gaba da hira su kuma. Da sauri Jannart ta ɗago kanta ta kalli Aunty Dijat jin abinda take cewa cikin hirar tasu. "Uhm Jannart yanzu kam komai ya dai-dai-ta ai ko?”. “Me ɗin fa My Aunty?". Ta tambaya cikin rashin fahimta. Gyara zama Dijat tayi ta fuskance ta da kyau kana a nitse tace. "Kamar ci gaban rayuwarki mana, yanzu kin gama karatu, har kin fara aiki yanzu wata shida kenanfa da fara aikinki. Toh yanzu kuma sauran miki me!?”. Ido ta ɗan jujjuya kana a hankali tace. “Ohon musu”. Tayi mgnar a hankali. Cike da mamaki Dijat tace. "Su waye ɗin?”. A hankali tace. "Daddy da Yah Junaid mana”. Ganin yadda Aunty Dijat ta zuba mata idone, yasa ta ɗan muskuta kana a hankali taci gaba da cewa. “Ban sani ba kam yanzu kam, sai kuma yadda Daddy yace ai!". Numfashin mai nauyi Dijat ta fesar kana a hankali tace. "Uhmm Jannart kenan shin ke baki da tsarin kankine a kan komai na rayuwarki. Dole sai abinda Daddy ya faɗa?”. Da sauri ta gyaɗa mata kai alamun Yesss haka ne. Apple ɗin data ɗauka ta ɗan ɓantara kana a nitse tace. “Har auren ma, in baice kiyiba bazakiyi ba”. Tada Hafiza tayi ta zaunar da ita gefe dan ta ida Mata kitson. Cikin sanyi tace. "Eh mana”. Ta bata amsa da ɗan guntun murmushi, kana ta ronƙofar da kanta tace. “Toh My Aunty Aure kuma! Ni kuma zanyi aure ne?”. Da sauri Dijat tace. "Mun shiga uku bazakiyi aure ba?”. Nannauyan numfashin ta sauƙe kana tace. “Yoh Ni na sani ne ai sai yadda Daddy da Yah Junaid sukace, Kuma ma ni ban taɓa tuno aureba, tunda basuma taɓa yimin mgnar aureba toh ni wake sona ma”. Cikin tsananin tausayawa yadda ake juya rayuwar ƴarinyar ya zama bata tsarawa kanta komai ma sai abinda su Junaidu suka tsara mata, a takaice ma suke juya motsin rayuwarta. A hankali tace. “Toh wai babu mai zuwa gunki ne? Wanda kuke soyayya ko mgnar aure”. Ta kuma jefowa Jannart tambaya. Inabi ta tsinka tasa a bakinta kana a hankali tace. "Ni kuma wa zaizo wurina, wayema ya sanni. Nifa da zan samu Yah Junaid yayi aure ya bar gidanmu da shike nan wlh bani da matsalar komai a rayuwata zanci gaba da zama a gidanmu a haka har gaban abadan. Ko kuma ace na dawo nan da bani da sauran damuwa a duniya wlh Ni banma san menene soba bare kuma soyayya bare batun aure.” “Tirkashi”. Shine abinda Dijat ta faɗa kana ta ture Hafiza daga jikin Jannart ɗin sannan a hankali tace. "Uhmm koda yake ba mmki. Toh dama ya za'ayi kiyi soyayyan waya isa ya isoki da kalmar so, yadda aka haɗaki da waɗannan bakaƙe kafuran ƙattin samudawan nan da ko yaushe suna biye dake tamkar inuwa. Ina ai dama yana cikin manufar tosheki da akayi tako ina da gayya sabida kada wani ya kusanceki.” Ta ƙare mgnar wasu siraran hawaye masu zafi na silalo mata. Wanda haka yasa tuni itama Jannart idanunta suka cika da ƙwalla. Cikin zubda hawaye Dijat taci gaba da cewa. "A yadda Allah yayi miki cikekkiyar halitta mai nagarta wace ko mace ƴar uwarki bata gajiya da ganinki. Ta yaya za'ace namiji kuma zai gaza sauƙe idanunshi a kanki da manufar so da ƙauna. Toh ko nan wurin Abbankin adadin maza nawane suka zo da kansu dama waɗanda suka turo iyayensu kam sonki da neman aurenki wanda suke bada tabbacin tsoro ke hanasu fuskantar ki”. Hannu tasa ta share hawayenta kana a hankali tace. “My Aunty dole ne sai nayi aure? Ni kawai farin cikin rayuwa nake son samu”. Cikin sanyi tace. “Jannart duk wani farin cikin ƴa mace yana cikane in tana gidan mijinta kuma tayi dace da miji na gari. Haka kuma duk farin cikin ƴa mace baya cika in batayi dace da miji na gari ba”. A hankali tace. "My Aunty Kenan dai dolen-dole saida aure farin cikin ƴa mace yake cika!?”. Cikin sauƙe numfashi Dijat ta riƙo hannunta kana ta fara zaiyyano mata ni'imomin dake cikin aure da matsayin zaman aure dama manufar aure a musulci...” Ramadan ne zaune a ƙasa kusa da kujerar da Mamy ke zaune. Wayarsa ce saƙale a kunne a karo na bakwai ya kira Riyyam-nsra sai ace mishi yana bisa waya. “Yanzuma bata shiga bako?”. Mamy ta tambaya cikin kula. "Uhum inafa ina ga dai ko dasu Zayton yake waya da Mammynsu. Tun ɗazu waya taƙi ƙare wa". Ramadan ya faɗa yana zura wayarsa a aljihu. Gyara zama Mamy tayi tare da cewa. "Toh Allah dai yasa lfy, kagafa yau ko breakfast baizo yaci ba, gashi yanzu har azahar ta gota bai kuma zoba". Kai ya ɗan jingina da kujera kana yace. "Bari in nayi wonka, kafin in wuce asibiti sai in biya in kai mushi abinci.” Da sauri Mamy tace. "Yauwa yafi kam”. Da sauri suka kalli Abba da shigowarsa kenan cikin haɗe fuska yace. "Har ke ɗin ma, shisshigewa lamarin da bai shafeki ba kikeyi, to ya za'ayi in iya control ɗin yaranki da yimin yayuɓe-yayuɓe suna kawo min cikin gida. Toh me ruwanku dan bai zoba!?”. Shiru sukayi baki ɗayansu Saida ya tsagaita Ramadan ya ɗan longoɓar da kai tare da cewa. "Afwan Yah Abba”. Kai ya gyaɗa kana ya wuce falonshi na ciki. A bakin gate kuwa Usman PA ne ya shigo da motarsa bayan Hadi ya buɗe masa. Da sauri ya nufi wurin Baba Mauɗo bayan ya fito. "Barka da yamma Baba Mauɗo”. Cikin kulawa Baba Mauɗo yace. "A'a Barka dai Usmanu! Kwana biyu shiru tunda kuka dawo bana ganinka ka bar Rayyanu shi ɗaya lfy dai ko?”. Cikin son dottijon yace. “Lafiya lau Alhamdulillah Baba Mauɗo, wlh da muka dawo ne Mama, ba lfy ashe ba ciwone matsalar ba, wai tayi kewan ƙannenta tofa dole ranarda muka dawo washe gari ta sani muka tafi Gombe bamu dawo ba sai jiya da dare da yake bamu taso da wuriba”. Cike da kulawa yace. “Masha Allah. Allah ya bada ladan ziyara, sai kuyi ta haƙuri damu, iyaye in an fara girma tamkar yara ake zama. Allah yayi muku al'barka”. Amin Amin yace. Kana ya nufi cikin gida. Da sallama a baki shi ya tura ƙofar falon. Da sauri Ramadan yace. "Wa alaikassalam, Yah Usman mutanen Gombe Kun dawo kenan". Murmushi yayi tare da cewa. “Oyoyo Ramadan Alhamdulillah”. Sai kuma ya juya. Da sauri Usman ya nufi inda Abba ke tsaye rusunawa yayi tare da gaidashi. Cikin kula Abba yace. "Usman kwana biyu shiru”. Cikin girmamawa yace. “Wlh kuwa Abba sai jiya muka dawo”. Ya faɗi haka tare da juyawa ya kalli Ramadan dake miƙo mishi hannu. Musabiha sukayi kana ya kalli Mamy cikin mutuntaka yace. "Barka da yamma Mamy". Barka dai tace tana mai nunawa Ramadan Fridge alamun ya kawo masa abin motsa baki. Da sauri kuwa Ramadan ya nufi Dinning area juice and bootle water ya kawo mishi. Kana yace. "Yah Usman bari in haura sama in ɗan watsa ruwa”. Toh yace. Kana ya haura. Shi kuwa Abba ne ya dawo tsakiyar falon. Mamy kuwa abinci ta kawo mishi. Kana ta nufi Bedroom ɗin ta. Yanaci suna hira da Abba. A can tahir hotel kuwa. Riyyam-nsra ne zaune bisa kujerar dake gefe. Video call yakeyi da Mammynsu cikin sauƙe numfashi yace. "Alhamdulillah Mammy duk abinda muke zato hakane, wlh kuma duk abinda ya tsananta tsawon shekaru yana gab da sauƙaƙa. Sai dai ta ina? Ta yaya? Da yaushe? Zamu fito da manufarmu ta yaya za'a fahimcemu?”. Ido Mammynsu ta limshe sai ga wasu irin zafafan hawaye kana a hankali tace. "Riyyam-nsra nima kaina bani da sanin tudun dafawa Kuma zuciyata ta ƙara kwaɗaituwa da tsatsonta. Ta ina? Ta yaya? Yaushe? zamu samu nasara". Cikin ƙarfin hali yace. "Mammy keda kike da Riyyam-nsra, kada ki damu ki bada yaƙinin ki a kaina in sha Allah zan kusanto miki da nesa kusa dake cikin aminci". Yadda yayi mgnar with full confidence ne yasata sakin sassayan murmushi. Riyyam-nsra akwai ƙarfin hali da yarda da kai, idon ta ita nema da bazaima je Nigeria'n ba amman bisa ƙarfin halinshi yaje. Kai ta jinjina mishi tare da yin murmushi, ganin ya sata farin cikine yasa shi cewa. "Ina Deeda tsohuwa da Zayton?”. Cikin sanyi tace. “Sun tafi asibiti". Ya buɗe baki da nufin yin mgna kenan kuma wani kiran ya shigo ɗaya wayar tashi. Da sauri yace. "Yauwa Mammy sai anjima zamuyi mgn”. Kan ta fargama ya katse kiran. Kana ya amsa wannan kiran wanda shima video call ne. Wata iriyar fitinenneyar miƙa yayi tare da zaro harshensa ya ɗan lashi lips ɗin shi. Sabida gamo da katar da yayi da wata kekkyawar baby mai cikar haiba kalar Ethiopia'n Girl's Tana mishi Ethiopia'n dance. Wanda take jujjuya mishi ƙirjinta da karkaɗa mishi su da karya kafaɗu irin dai rawar su nan ta sai kaci ka ƙoshi kan ka iya yinsa. Ido ta jujjuya mishi tare da tsagaita wa da rawar kana cikin yin ƙasa da murya tace. "I miss you very very very so much sweetheart”. A hankali ya miƙe ya koma bisa gado. Idanunshi da suke juye sabida ganin ɗaya daga cikin abokan masha'arsa da suka haɗu sanadin TIKTOK cikin sanyi da kasalar wani irin masifeffen feelings da ya ziraro mishi kamar zai tsinke mishi jijiyoyin jiki yace. "Nace muzo Nigeria kika ƙi, sannan kuma kina son tarwatsa min kwanya da begenki”. Cikin iya shege ta zame wuyan rigar ta ta ɗanyi ƙasa dashi. Kana tasa hannunta cikin rigar ta zaro mishi... Tare da cewa. "Lollypop"....! Ɗaga nan sukaci gaba da lalatacciyar hirarsu, haka yasa Ramadan nata kira bai amsawa. A can gidan Alhaji Idi Saleh Dakata kuwa. Cikin hatsala Junaidu ya leƙo falon yana mai rabkawa Jannart kira kamar zai yage bakinsa. "Jannart! Jannart!! Jannart!!!". Ya ida kiran da ƙarfi wanda yasa. Mom dake Kitchen ta leƙo cikin taɓe fuska tace. "Menene kake ta ihun kiran wacce bata gidan ma, sai ka tafi gidan Abbanku ai”. Kwaffa yayi tare da watsawa Mom ɗin harara kana ya nufi Part ɗin Abbansu dan sai yanzuma ya tuno cewa bata gidanma. Yana isa bakin ƙofar falon. Dr Lukman da Alhaji Abdu Tababa suna isowa suma da alamun yanzu suka iso. So kusan a tare suka shiga. A falon suka samu Daddy wanda dawowarshi kenan shima nan suka zauna. A gidansu Rayyern Mai-nasara kuwa, Ramadan ne ya fito riƙe da foodflakcs mai kyau. Usman na bayanshi. “Eh ba asibiti ba yake Campany ya tafi tun safe bai dawo bama”. Ramadan ya bawa Usman amsa wanda ya biyoshi da nufin zasu tafi asibiti. Numfashi Usman ya sauƙe tare da cewa. "Toh ni kam bari kawai in wuce can inda yake ɗin”. Toh yace kana shi ya nufi hotel ɗin da Riyyam-nsra yake. Shi kuma ya wuce campany. Yana isa da mai a dai-dai-ta sahun ya tsaida shi bakin gate ya sallameshi. Kana ya shiga cikin kamfanin. Mai napep ya juya. Kasan cewar duk ma'aikatan wurin sun san PA duk wanda yasan Dr Rayyern Mai-nasara zai iya saninshi da PA hakan yasa kai tsaye ya wuce Office ɗin sa. Cikin gajiya ya ɗago kansa ya kalli ƙofar Office ɗin da ake bugawa cikin sauƙe numfashi gajiya yace. "Yesss coming". Cikin nitsuwa PA ya turo ƙofar. Numfashi ya fesar tare da meda bayanshi ya jingina da kujera tare da kallon Usman murya can ƙasa yace. "Sai yau?”. Murmushi yayi tare da cewa. "Wlh kuwa sai yau fa". Ya ƙare mgnar yana ƙoƙarin zama. Sai kuma ya tsaya ganin uban gidan nasa ya miƙe tsaye. Hannunshi yasa ya tattare system din ogan nashi da wayarshi kana yabi bayanshi dan tuni ya tafi. Da sauri yabi bayanshi. Bisa. libta ya hangoshi tanayin ƙasa dashi, da sassarfa ya mara mishi baya. A haka har suka sauƙo hawa na biyu. Suna sauƙa yayi maza yabi bayanshi ganin ya nufi hannun damanshi. Tafiya mai ɗan tsawo sukayi kana suka isa wani wuri mai ɗauke da manya-manyan store's masu masifar girma da faɗin gaske. Wanda sun kai goma sha biyu. Gaba ɗaya a rufe suke tsayawa ya ɗanyi kana ya juyo ya kalli PA tare da cewa. "Muje ƙasa". To yace kana yabi bayanshi. Suna sauƙa ƙasan kuma wasu stores ɗin suka samu kamar na sama. Sai dai waɗannan su anata loda buhunan shinkafa shanshera ne buhu-buhu". Kai ya gyaɗa cikin gamsuwa kana suka sauƙo ƙasa gaba ɗaya. Inda suka nufi can gefen baya wani ƙaton hall ɗin cike da enginer's anata kafasu da haɗasu babu ƙaƙƙautawa. Cikin nitsuwa yace. "Lokacin salla yayi abar aiki aje ayi sallan la'asar”. To sukace cike da jin daɗin kana suka bar aiyukansu. Kana suka firfito. Shi kuwa yayi gaba PA ya mara masa baya. Suna isa parking lot Usman ya buɗe mishi mota gefen baya. Kai ya jujjuya mishi kana ya shiga gaba mazaunin driver'n kana ya nunawa Usman gefenshi. Yana son yayi tuk’i da kansa ne dan sanin akwai masu bibiyarsa. Ana buɗe musu gate ya fita a nitse. Karatun ƙurani ya saki sautin muryar Sheykh Jabeer Habibullah Nuruddeen Joɗa, (GARKUWA) Sassanyan sautinsa mai sauƙar da nitsuwa ya saki. Kana ya saita hancin motar bisa titi ya fara takata a guje. Dan so yake su samu jam'i sallan la'asar a Masallacin ƙofar gidansu. Ana tada iƙama suna isowa. Da sauri sukayi al'wala kana sukabi jam'i Allah yasa ba'a kere musuba. Ana idar da sallan suka shiga cikin gida. Tare da Abba da Baba Mauɗo, Hadi, Ari da Ramadan da Riyyam-nsra wanda suka juyo tare. A bakin gate Usman ya zauna wurinsu Baba Mauɗo. Su Ramadan kuwa a babban falon suka zauna. Shi kuwa Dr Rayyern Mai-nasara bayan Abbansu yabi har falonsu na ciki. Gefenshi ya zauna tare da sauƙe numfashin gajiya kana ya kalli Abba dake cewa. "Ya ka samu aiyu kan?”. Cikin nitsuwa ya tonƙoshe sawunsa kana a hankali yace. “Alhamdulillahi komai na tafiya dai-dai da izinin ubangiji. Shinkafar nan ma da muka saya ta manoman Adamawa can wajajen Gurin ta iso, kuma shinkaface mai kyau da in ganci dan Jamila ce sai kuma mahanga kaɗan ita tafi kyau a barta a ɗaya.” Uhumm yanzufa wasan zai fara daga PAGE din gobe. *Albishirinku! Ma'aurata, GA GARKUWAR KU nan tafe muku da tsarabobi na musamman gareku ma'aurata daga cibiyar mgnin mata mai taken GARKUWAR MA'AURATA* NI DAI AYSHA ALIYU GARKUWA. Ina matukar mamakin wani irin lokaci da ya riske mu mai wahalallan fassara. Kullum dai magana daya ce, akan ma’aurata, fada, rashin jituwa, mutuwar aure, akan kuskure kalilan, rashin kula, rashin yi wa juna uziri. Toh wai duk me ya janyo hakan? Na zurfafa a tsananin tunani hakan ya tilasta min bincike mai tarin yawa wanda ya kai ni ga gano inda matsalar take? Shin yar’uwa ke macece amma kin san wacece mace ku? Kin san me ake kira mace kuwa? Mace ita ce matar da take zama iyali a wajan namiji ta zame masa bango, sanyin idaniyarsa, ta zame masa gata da farin cikin rayuwarsa ta zame masa ruwa abar kore ƙishinsa ta zame masa mayafi mai karesa daga gigitar kadaice, ta kuma dorar da mijinta kan turbar gaskiya, ta kashe masa jiki da salonta ta rikita shi da baiwa da ni’imar da Allah ya bata idan har ta san hanyar mayar da kanta sabuwa dal awajanta, wato kullun takasance masa tamkar amarya har ya kasa tantance daren amarcinsu da sauran dararen rakun rayuwar su. Wannan ita ce mace. Ina da wata saukakkar hanyar da zaki zama abar so da kulawa da soyayya a wajan mijinki ta hanya mafi sauki, 09097853276 hanyar ita ce ki gwada amfani da kayana na gyara ki gani, ina mai tabbatar miki da in sha Allahu sai kin dara da murna sai kuma kin gode min. Kayana kaya ne da aka yi shi da zallan itacanmu na gado marasa illa a cikin jikin dan adam musamman mace, kaya ne da suke taimakawa (sex hormones 😍) dinki. Misali kina kallon India😘, hollywood, Asian film🥰 kina ganin yanda mazansu ke nunawa matansu tsananin soyayya kamar su ba su kyautar ransu!? Saboda me hakan? Saboda suna sadaukar da lokacinsu wajan gyara jikinsu da kayan da ke tsattsafo da ni’ima cike da tsukewa, kayan nan kuma ana yinsu ne zallar magungunan gargajiya wanda ba su da illa domin haɗine na ingantattun itatuwa da yayansu. Ina baiwar Allahn da miji ke daure mata fuska babu hirar arziki? Zo ki ji yar’uwa zan baki gumbata da zallar gari wanda aka yi su da nagartattun itacen da ke da matukar amfani a jikin mace. Gubar ciko, gumbar tsalle dole, gubar da ba'a baiwa mai kishiya, garin maɗi, garin mallaka, tsumin goron tula, tsumin tsartai, tsumin maratsi, pala-pala butar sirri, kwanon k’asaitacciyar mace, furar mata madararta gareki Hajia takenta sha yanzu mgni yanzu, Ina mata masu fama da sanyi? Sanyin mara ki zo na hadaki da magani na na sanyi wanda yake wanke mara ya fitar da duk wata cuta da ke samun mazauni a wajan. Ina da ciccibi mai kyau. Ina da hadin amare mai kyau wanda zai gyara yarinya ya kankaro mata kimarta akwai hadin mai jego wanda muke yinsa na asali inada kekkyawan Hadi maida tsohuwa yarinya. Akwai daya bangaren wato *KAMSHI* Kimarki gyaranki da kamshinki. Matan da suka gane suka san yanda za su kankaro da mutunci su ne masu amfani da kayan gyara da kuma sanyaya jikinsu da kamshi, ina da turaren wanka da na bandaki na daki na jiki da na kaya dana tsuguno kamshin turarena na dabam ne mai sanyaya zuciyar wanda ya shaka ina da kayan kamshi na amarya da na maijego da na uwargida da dukkan macen da take kokarin mayar da kanta mai daraja a idon kowa ta zamo sarauni a idon mijinta, akwai shu'umar humra, sayan na gari maida kuɗi gida, banda karanta yayin gyara Hajia. Zaku iya samun kayyakina a duk garin da kike, zakiyi min mgn ta whatsApp number na 09097853276 domin yin zaɓinki, ko karin bayani, zaki tura kuɗin ta account na 0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU in mun gama mgna zan sa miki kaya a mota yazo duk garin da kike, Kana duk ƙasar da kike zan iya aika miki kaya ta D.H.L amman yana da ɗan tsada, in baki shirya saya yanzuba Please kada mu wahal da juna ki bari sai kin shirya kafin kiyi min mgn. 🤝🏻🥰😘 Daga taku AYSHA ALIYU GARKUWA *(GARKUWAR MA'AURATA)* By *GARKUWAR FULANI* 11/15/21, 7:20 PM - Auntyna: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *TUBALI* PAGE 15 NA *AYSHA ALIYU GARKUWA* *FREE PAGE ne kuma suna gab da karewa* *Baiwar Allah Hajia yan mata uwar gida, 🙏🏻😭 ROK’EKU DA GIRMAN ALLAH DA SOYAYYARKU DA MANZON ALLAH DA DARAJAR IYAYEN DA SUKAYI SANADIN ZUWANKU DUNIYA, DAN ALLAH KADA KI KARANTA MIN LITTAFINA IN KINSAN BAKI BIYA, DAN GIRMAN ALLAH DA ZATINSA DA RANA TA KARSHE DA MUKE TSUMAYI KADA KU FITAR MIN DA LITTAFINA DAN KUN BIYA 1K KO 500 WANNAN KUDIN KARANTAWA KUKA BIYA BA KUDIN MALLAKAR SA BANE, DAN ALLAH DA ISARSA BAYIN ALLAH KADA KU FITAR MIN DA LITTAFINA KADA KU KARANTA IN KUNSAN BAKU SAYABA🙏🏻🙏🏻😭😭😭😭 wlh duk wanda yamin hakan bazan yafe hakkina* _Ki biya 1k in saki a special Group, ko kuma ki bada 500 in saki a ƙaramin group wanda bonus ne wa fans na kullum PAGE ɗaɗɗaya asalin kudin littafin 1k ne in gamashi in ya zama Complete 1kne. Turo kudin damar karanta Littafin TUBALI ta asusuna na GTBank 0661110170 AISHA GARKUWA ALIYU, sai ki turo shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276 in ba halin biya ta account kuma ki sayi katin MTN ki copy number's din ki turo min ta WhatsApp dina_ Kai Abba ke jinjina masa cikin tarin gamsuwa kana a nitse yaci gaba da cewa. "Kuma mun samu al'kama aciki sosai kusan buhu dari bakwai”. Gyara zama Abba yayi tare da cewa. "Ita al'kamar ba duk stores din hawa na biyu ita bane, bazatayi yawa ba?”. A hankali ya ɗan kalli Abba tare da cewa. “A'a bazatayi yawaba Abba sabida abubuwan buƙatunta da yawa, ita za'a sarrafa ayi fulawa kana a juyata ayi Sufageti da makaroni da indomie sannan za'a barta ita ɗaya ma. Kuma yanzu anfi ta'ammali da irin abincin kana zamu fidda buhunan don buƙatun cikin gida kamar su hidimar ababen biki da masu ƙananan sana'o'in duk suna buƙatar fulawar”. Gyara zama Abba yayi fahimtar yana tare da gajiya da yunwa ne yasa shi cewa. “Je kaci abinci kayi wonka zamu ƙarasa mgnar gobe da yamma”. Kai ya gyaɗa kana ya miƙe ya fito. Kai tsaye side ɗin sa ya wuce. Wonka yayi mai rai da lfy ya shafa mai. Kana ya zaro. Wasu tattausan yadin voyel mai masifar taushi mai gidan dara-dara baƙi ne mai sheƙi ya saka. Wanda yayi masifar mishi kyau farar fatarshi ta ƙara bayyana a ciki matuƙa gaya. Wasu tattausan toms yasa Nevy blue masu masifar kyau kana ya kafa hular zanna bukar itama Nevy blue mai ratsin Black da royal blue. Sajenshi ya konta lib sai sheƙi yakeyi tamkar yadin jikinsa fararen ƙananan kayan dake jikinsa suka ƙara haska kalar kayan inda ana iya ganinsu kaɗan ta dara-daran wani sassayan turarensa ya fesa. Kana ya zari wayarsa ya zura a al'jihunsa kana ya nufo falon. Cikin zumuɗi Riyyam-nsra yace. "Wow Masha Allah, Hamma Rayyern dama haka kayan hausa fulani keyi maka kyau tubar kalla kai duk kayan da kasa sai sunyi maka kyau”. Ya ƙare mgnar yana ƙoƙarin ɗaukarsa hoto. Da sauri yasa hannunshi ya shafa ƙeyarsa lokacin da Rayyern ya ɗan ɗaka mishi mari cikin tura baki yace. “Dan Allah ɗaya kawai”. Bai kulashi ba. Sai juya da yayi ya fuskanci Mamynshi, hannunshi ya ɗaura kan cikinsa yana shafawa tare da kallon Mamy kana ya longobar da kai. Murmushi Mamy tayi tare da miƙewa ta nufi Dinning table saninsa yasa ba sai yayi mgna ba take fahimtarsa. Bayanta yabi yana kallon Ramadan tare da cewa. "Me kakeyi a gida”. Cikin tsoron kada ya korasa asibiti yace. "Na gaji ne Hamma Rayyern kuma Dr Imran da Yah Sulaiman da Dr iley duk suna can”. "Shine kuma yanzu Sulaiman yake cewa inje ana buƙata ta?”. Kai ya ɗan shafa tare da fara inda-inda. Shi kuwa tsaresa da ido yayi tare da nazartarshi kana a hankali yace. "Kada ka zama maƙaryaci!”. Da sauri yace to. Wayarsa ce ta kuma ringing ganin Sulaiman ne yasashi miƙewa tare da buɗe Fridge Chocolate masu yawa ya ɗiba daskararru kana ya zaro goran ruwa da sauri haka yasa bai san wanda ya daskare ya ɗaukoba. Cike da mamaki Mamy ta bishi da ido jin yana cewa. "Mamy sai na dawo ana nemana a asibiti, Mamy abu mai ruwa-ruwa nake so in na dawo”. Kai Riyyam-nsra ya jujjuya kana a hankali yace. "Allah sarki Hamma Rayyern sam baya samun hutu, lokacin cin abinci ma rasawa yakeyi bawan Allah. Dan Allah Hamma Ramadan muje ka tayashi”. Kwaffa Ramadan yayi tare da dungure mishi ƙeya kana yace. “Dan Allah Barshi shi baida wani uzuri sai aiki ni kuwa ina fama da uzurin soyayya. taso mu tafi kaga Auntynka yaro”. Ai kuwa da sauri ya miƙe. Shi kuwa Dr Rayyern Mai-nasara yana fitowa Hadi da PA suka miƙe. Da sauri yace. “Noh Hadi bari. PA mu tafi”. Da sauri PA yace “Toh”. kana yabi bayansa. Yana shiga motar yaja. Hadi kuma ya buɗe musu gate, suka fita. Saida suka fita sun hau titin da zai kaisu Mai-nasara Hospital ne ya ɗan miƙawa PA goran ruwan alamun ya buɗe mishi. Amsa PA yayi tare da cewa. “A daskare yake fa”. Hannu yasa ya amshi gorar ya ɗan jijjiga tare da jan tsaki sam rabinsa duk a daskare yake. Aje goron yayi kana ya ɓalle ledan Chocolate ɗinsa ya fara taunawa da yawa-yawa sabida azabebbiyar yunwar da yakeji. A nitse ya zurawa motoci uku dake bayansu idanu. Binshi sukeyi gadan-gadan kamar masu niyar takashi. Da sauri yayi kwana ya shiga hannun damansa. Ga mmkinsa sai gashi sun biyoshi a guje har na gaban na gab da buga mishi motarsa. Cikin ransa yace. “Okay!!!” sai kuma ya juya hagu da gudu. Cikin nitsuwa yace. "PA ko zaka sauƙa!” Da sauri PA yace. “A'a muje in ba matsala, naga motocin nan binmu sukeyi fa, ba halin tsayuwa”. Kai ya gyaɗa mishi kana ya juya akalar motarsa dan canza hanya. Sabida sanin ana buƙatarsa a asibiti in ba don hakaba zai tsaya yaji dasu. So amman ganin duk inda yayi suna biye dashi kamar inuwa ne yasashi juya akalar motarsa kai tsaye titin da zai kaishi Jan bulo ya nufa. Ganin haka ne kuma yasa motocin nan uku suka tsagaita da binshi. Gaba ɗaya ransa ya hatsala ya tafasa sabida yadda suka sashi dole ya fasa zuwa inda akeda buƙatarsa da neman taimakonsa ya nufi inda baya son zuwa. Wani irin masifeffen tsaki yaja tare da taka motarsa ƙirar B.M.W. fara kal mai masifar kyau da sheƙi. Takata yakeyi a fusace. Kai tsaye layin gidan Alhaji Idi Saleh Dakata ya shiga. A hasale yake danna horn babu k’ak’k’autawa wanda hakan yasa mai gadin buɗe masa gate ɗin jiki na rawa. Yana buɗewa kuwa ya kutsa kai. A can gidan Barrister Kabir kuwa. Cikin tsoro Jannart ta kalli wayarta inda ta samu miss call 17. 13 daga ciki na Yah Junaid ne biyu na Daddy ɗaya kuma Salman ɗaya Hajia Rabi'ah. Murya na rawa tace. "My Aunty zan tafi kawai kinga har yanzu Abba bai dawoba ga Daddy ma nan yanata kirana ga kiran Yah Junaid goma sha". Ganin yadda jikinta ke rawane yasa cikin sanyi tace. “Toh gsky kam harda kiran Daddy kam kije, in ya dawo zaije yaji ko lfy". Ledan da take miƙa mata ta amsa tare da cewa. "Nah shiga uku kinga yanzuma ga Yah Junaid yana kira”. Ta ƙare mgnar tana nufar woje, Dijat na biye da ita a baya. Tana fita sakarkarun suka muƙe da sauri ta shiga mota jiki na rawa Baba Ado yaja jin yadda take ce mishi. “Baba Ado mu tafi mu tafi, awa uku Daddy ya bani gashi har biyar nayi.” Ajiyar zuciya Dijat ta sauƙe lokacin da suka fita. Jiki a mace ta koma cikin gida. Su kuwa a 360 suka nufi gidan. Cike da Mamaki Usman yake kallon Dr Rayyern Mai-nasara daya fita cikin motar fuska a murtuƙe yacewa mai gadin. "Ina Ubangidan naku?”. Cike da mamaki mai gadin ya kalleshi kana ya juyo ya kalli ƙofar babban falon Alhaji idi Saleh Dakata wanda daga nan bakin gate ana iya hangoshi. Baya buƙatan ƙarin bayani sabida yadda mai gadi yayi ya tabbatar masa ogan nasu na ciki. Kana kuma ga tarin takalma alamun da mutane a cikin. Cikin wani irin taku mai cike da haiba ya nufi falon. Yana zuwa yasa yatsunshi biyu ya ɗan bugi ƙofar. Da sauri duk suka juyo suka kalli ƙofar Junaidu dake baƙin kofarne yasa hannunshi ya buɗe dai-dai lokacin kuma shima ya turo ƙofar. Ganin Dr Rayyern Mai-nasara na kutso kai cikin falon ne yasa Junaid matsowa tare da cewa. "Kai lfy ina zaka je waye kai!?”. Ya ƙare mgnar yana tsare gaban Dr Rayyern Mai-nasara din. Wani irin kallon daya hautsina hanjin cikin Junaidu. Rayyern ɗin ya watsa mishi, tare dasa hannunsa ya dafe gefen kafaɗun Junaid da yatsu biyu kana ya tureshi da ƙarfi, har saida ya bugi gini kana yace. "Matsa yaro ba wurinka nazoba wurin tsohonka nazo”. Ya ƙare mgnar yana nufan cikin falon gadan-gadan. Wani irin kallon mamaki shakka mai haɗe da tsoro Alhaji idi Saleh Dakata, da Alhaji Abdu Tababa, da Dr Lukman suke mishi kamar idanunsa zasu faɗo ƙasa. Da karfi ya jawo kujerar dake gefenshi kana yasa ƙafarshi ya tureta guuuu ta tafi har gaban Daddyn Jannart cikin rashin tsoro ya zauna bisa kujerar tare da jawota ya motso shi da kyau suna fuskantar juna cikin kakkausar murya yace. "Meh hakan! Me kake nemana kana tura waɗan can karnu kan naka nemana, gani gabanka, ka gaya min me kake buƙatar inyi maka da kake sawa ana bibiyata. Nace me kake son inyi maka!!!”. Ya ƙare mgnar da masifar ƙarfi tare da buga santer table ɗin dake gabansa har saida cups ɗin saman suka kwanta suka gangara ƙasa. Kana hakan yasa duk suka kame jikinsu da zazzaro idanunsu. Da sauri Alhaji Idi Saleh Dakata ya ɗagawa Junaidu hannu dan ganin ya yunkuro zai kama Rayyern. Shiru sukayi baki ɗayansu, shi kuwa Rayyern cikin tafasan zuciya yace. “Da ka barshi ya isoni ai.” Yayi mgnar yana tsare Daddy da idanu. “Mitssssss”. Yaja wani dogon tsaki tare da cewa. “Ina da aiki mai mahimmanci ka sani na baroshi nazo nan dan inji uzurinka sannan kayi shiru kana zaro min jajayen idanu kamar na (DUJI) to wlh hawainiyarka ta kiyayi Ramata. Kada kasa in juyo kanka na wuni ɗaya wlh zaman kasar Kano zaifi karfinka. Ya za'ayi ina girmama furfurarka kana kaucewa, to muddin baka kiyayeni ba tabbas zaka rasa gemun naka gaba ɗaya.” Da sauri ya juyo ya watsawa Dr Lukman wani kallon da yasa shi jin zufa tun daka cikin naman jikinsa dan masifar tsoron da idanun Dr Rayyern Mai-nasara din ya bashi. Cikin sauri yayi ƙasa da kanshi tare da cewa. "Yaro man kaza lallai ka bimu a hankali dan wlh in kace zaka ja damu to wlh. Ko na'urar jin bugun zuciya ka dena riƙewa.” Wani irin gigitaccen tsawa ya dakawa Dr Lukman har saida ya miƙe tsaye dan firgita. Da yatsa ya nuna shi kana ya jujjuyata sannan yace. "Mu zuba Ni da kai magwaji ya gwada ya gani”. Sai kuma ya kalli Alhaji Idi da Alhaji Abdu Tababa da suka zuro mayun idanunsu suka kafesa da ido suna masu nazarin wanne irin kisa ya kamata su yiwa yaron nan ne mai shegen taurin kai ko wani irin illa mafi muni za suyi masa rayuwarsa. Cikin gargadi ya nunasu da yatsa kana yace. "Wlh idan kuna cin ƙasa, to ku kiyayi ta curi. ina mai tabbatar muku in baku kiyayeni ba zaku shiga uku. Tun wuri ka gayawa waɗan can karnukan naka su dena bina, in kuwa ba hakaba zaka rubta rami. Kada ku mance na gaya muku. Idan nace zan taka mutun bashi da GARKUWA a kaina zan takashi domin tsakanina daku faɗane tsakanin gsky da ƙarya.” Gaba ɗaya jikinsu tsuma yakeyi. Yayinda Junaidu kuma zufar tsoro ta keto mishi. Dai-dai lokacin kuma motocinsu Jannart suka shigo gidan. Da sauri ya juya ya fita sabida hango sun da yayi kasan cewar ƙofar a buɗe take. Yana isa wurin Jannart na fitowa kasan cewar ta bayanta yazo bata san ya isoba. Wani ƙauuuuu taji lokacin daya yarfa mata wani irin masifeffen mari ta bayanta kuma kan kunneta. Wani irin dummmm taji ya biyo bayan kauuu ɗin cikin gigita ta juyo... Dai-dai lokacin kuma Barrister Kabir ke tsaye gaban Dijat dake mishi bayanin abinda yasa Jannart ta tafi. Ta kara da cewa. "Ɗan Allah Abban Hafiz ka bita, kaga meke faruwa kada Junaidu ya mata wani abu”. Cikin sauri Barrister Kabir yace. "Zai matama maza ku koma ciki bari inje”. Ya faɗi mgnar yana komawa cikin motarsa. Ita kuma taja hannun Hafiza tayi gaba Hafiz na biye dasu a baya. Shi kuwa Barrister Kabir cikin gudu yake tuƙib ya nufi gidan yayan nasa. A gidansu Jannart kuwa. A falon Daddy cikin wani irin masifeffen hatsala Dr Rayyern Mai-nasara ya juya zai fita. Har yaje bakin ƙofar sai kuma ya tsaya tare da juyowa ya kallesu kana yace. "Wallahi Ni nan Muhammad Rayyern wargine dai-dai da ƙugun ko wanne mugun tsohon ɗan riba”. Yana faɗin haka ya sako kai ya fito. Dai-dai lokacin kuma Junaid yayiwa Jannart wani irin shaƙa mai ƙarfi kana ya wurgata ƙasa. Hakan yasa ta saki wani irin raunataccen kuka mai masifar wahala tare da yunƙurawa ta kuma tasowa. Tana mai yarfa hannun tare da ja baya gaba ɗaya jikinta rawa yakeyi. Wani irin gigitaccen mari ya kuma zuba mata kan kunneta wanda yasa ta buga wani irin tsalle tare da ihun wahala a tare. Dai-dai lokacin kuma Rayyern ya iso parking lot ɗin. Da sauri ya juyo ya kalli gefen da yaji ihun sabida karadin ihun ya cika masa kunne da ƙarfi har saida yaji kansa ya sara. Siraran idanunshi ya zubawa fuskar yarinyar tabbas ya ganeta. Kai ya rausayar ya juya tare da taɓe bakinsa alamun. Oho yama kasheki in yaso kunfi kusa ai. Barrister Kabir kuwa gudu yakeyi sosai sabida kiran Jannart da yayi har sau uku bata amsaba ya tabbatar masa ba lfy ba. Shi kuwa Junaidu cikin tsananin mugunta da son huce haushinsa ya kuma shaƙo wuyanta. Wanda yasata yin wani irin kakari tare da zazzaro idanunta woje. *Dan girman Allah da Manzonsa da darajar iyayenki kada ki fitar min da littafina dan kin biya kudin karantawa bawai yana nufin kin mallakeshi bane, na roƙeki da isar zatin ubangiji daya bamu rai da lfy, don soyayyar manzon tsira dan mutuncin iyayenki kasa ki karantamin littafina in baki biyaba, tun forko kunsa littafina na kuɗine, kada ku tauye hakkina kuji tausayin maraicina* Wanda kuma su Baba Ado da Ashiru mai gadi kab suka rumtse idanunsu da ƙarfi sabida ganin yana son kashe baiwar Allah. Wani irin kallo Rayyern yayiwa Usman P.A dake cewa. “Innalillahi zai kashe tafa". “Toh me ruwanka ba gidansu ɗaya ba”. Dr Rayyern ɗin ya fad’a, Waɗannan ƙattin samudawan kuwa suma cirko-cirko sukayi to ya zasuyi. Ɗan uwanta ne wa zai hanashi in ba mahaifinsu ba. Su kuwa su Alhaji Abdu suna jin ihunta amman basu fitoba hakama Daddy. Mom kuwa dake wonka sauri-sauri takeyi dan ta samu ta fito. Abdul kuwa gefe ya tsaya yana zubda hawaye. Wani irin gigitaccen duka fa Junaid ya fara yi mata tamkar zai ɗauke ranta. P.A kam tuni shima hawayen tausayin yarinyar ya cika masa idanu. Shi kuwa Dr Rayyern Mai-nasara cikin yanayin halinsa na babu ruwansa da shiga harkar da bata shafeshi ba, yayiwa motar key kana ya tada ya juya akalarta zuwa bakin gate. Hon ya danna amman ina Ashiru mai gadi baima san yanayi ba. Cikin jan tsaki ya kuma danna horn still Ashiru baima san yanayi ba. Shi kuwa Junaid cikin huce haushinsa ya daddage ya yarfa mata wani irin marin. Da yasa ta saki ihu da ƙarfi. "Wayyo wayyo Allah na Wayyo Mom Wayyo Abba Yah Junaid zai kasheni Daddy”. Bata ida rufe bakinta ba ya kuma zabga mata wani marin azabebben mari. Wanda yasa jinin haɓo ɓallo mata ta hancinta. Da k’arfi Dr Rayyern ya rumtse ƙwayar idanunsa, kana ya bud’esu a hankali. Dai-dai lokacin kuma Abba ya iso bakin gate ɗin, ganin yanata dannan hon ba'a buɗe mishi bane yasashi. Buɗe mota ya fito.yana fitowa yana jin ihunta. Haka yasa ya kutsa kanshi da gudu cikin gidan ta ƙaramar kofar. Dr Rayyern kuwa kashe motar yayi ganin ba'a buɗe mishi gate ba. A hankali ya meda bayanshi ya jingina da jikin kujerar kana yasa hannunshi ya dafe saman marfin motar sabida yayi ƙasa da glasss ɗin. Tallabe kanshi yayi da tafin hannunsa kana a hankali yace. "Bari muga ƙarshen Game ɗinnan ko P.A”. Cikin tausayi P.A yace. "Sir zai kasheta fa”. Ganin kallon da ya mishi da idanunsa da suka time zuwa launi jane ne kuma yasa yayi shiru. Kana ya zuba musu ido ta cikin mirror motarsan sabida zuwa yanzu sun dawo bayanshi kusa da motarshi ƙanƙance idanunsa yayi tare da zubasu kan madubin yana kallon duk yadda Junaid ke mata. Isowarsu bakin motar tasa ne kuma, yasa Junaid damk’o tarin sumar kanta, wanda gaba ki daya ya watse akan gadon bayanta, saboda tsananin wahalan daya bata, irin damk’an da yayiwa fashion nata ne kuma yasa ta sakin wani irin azababben ihu, batare da ko gama rufe bakinta tayi ba, ya bugata da jikin motar. Wanda hakan yasa Ta fad’a kan motar, atake kuwa jinin dake zuba daga hanci da bakinta ya tsananta ya fara zurarowa har kan motarsa. Da ƙarfi ya rumtse idanunshi tare da kame jikinsa. Da yaji zuciyarshi tana wani irin masifeffen harbawa da wani irin masifeffen tsalle kamar zata fito woje. Dai-dai lokacinne kuma Abba Kabir ya shigo cikin gidan hankalinsa amatukar ta she. Ashe kuwa baimaga komai ba a tashin hankali ba, saida yaga yanda Junaid din ya buga Jannart ajikin mota. Wanda hakan yasa ko ihu mai karfi ta kasa fitarwa, ga kuma jinin dake ci gaba da fita ta hancinta ba ƙaƙƙautawa. Cikin wani irin tashin hankali kiɗima maitsanani Abba Kabir ya nufosu a guje. Shi kuwa Dr Rayyern Mai-nasara wani irin masifeffen tsuma yaji naman jikinshi nayi gaba ɗaya babbar yatsarshi da Jannart ta fasa mishi had’uwarsu ta forko sai wani irin karkarwa takeyi. Abba kuwa yana gudun nufosu yana. "Innalillahi wa innailaihi rajiun. Junaid! Junaid!! Junaid!!! Baka da hankali ne kasheta zakayi ne. Kai wanne irin azzalumi ne!?”. Ya ida mgnar yana isa inda suke. Batare da wani jinkiri ba kuwa ya d’auke Junaid da wani irin gigitaccen Marin da yasa Junaid yayi tagal-tagal ya koma baya, Cikin tsananin fusata da makatar ido da zuciya yasa hannunshi duka biyu, ya hankaɗeshi, saida ya faɗi ƙasa. Abu da ɗan giya dama ba ƙarfi ba. Jikinsa na rawa kana kuma Ransa amatukar bace yace. “Baka da hankali ne Junaid wannan wani irin dabbanci ne, ko kasheta kakeson yi?” Abba din ya fada amatuk’ar tsawace. Tare kuma da sunkuyowa kan Jannart dake kwance akan motar Dr Rayyern jini na ci gaba da fita ta hanci da bakinta. “Jannart! Jannart!! Jannart!!!”. Ya kirata da azaban ƙarfi cikin tarin ruɗani. Wanda sautin kiranta da yayine yasa Dr Rayyern Mai-nasara buɗe kwayar idanunshi da suka sauya launi daga fari zuwa jazir. Idon ya zuba musu ta cikin madubin yana ganin yadda Barrister Kabir yake jijjigata a gigice yana mai cewa. “Jannart Bud’e idanunki nine Abbanki ne yazo bud’e idanunki Jannart!!!” Barrister Kabir din ya fada da muryarsa wacce tayi rauni sosai, kana kuma yana me dan jijjigata tuni ya gama gigicewa gaba ɗaya jikinshi rawa yakeyi rauni mai tarin yawa ya rufeshi. Duk wanda ya ganshi yasan yana cikin tashin hankali. A dai-dai lokacin ne kuma Rayyern ya bud’e murfin motar tasa ya fito, wanda ya fito ne kuma saboda yiwa Junaid warning, akan jinin daya shafa masa ajikin sabuwar motar sa. Kana kuma ya sashi ya wonke mishi jinin daya zuba mishi jikin motarsa, in ba wani salon sharri bane yake neman sa dashi. Barrister Kabir kuwa dake dukufe akan Jannart jin motsin mutum da yayi abayansa ne yasashi saurin juyawa, inda idanunsa suka sauka akan Dr Rayyern Bashi Muhammad Mai Nasara din koda yana cikin gigita ya gane waye ne shi. Aikuwa azabure ya mike tsaye, batare kuma da wani dogon tunani ba ya kamo hannun Rayyern d’in, cikin muyarsa dake rawa yace. “Dan Allah Dr. Rayyern ka taimakamin, kalli Jannart jini take ta zubarwa, Dan Allah Kataimaka kada ta rasa rayuwarta. Dan Allah ka ceceta ka ceci tsohuwar gsky itace hujja ɗaya gareni...” Yanayin yanda yaji maganar mutumin dake rik’e da hannunsa ne, yasa akaron farko yakai dubansa, ga Jannart d’in dake kwance, kan motarsa jini na zuba mata ta hanci da baki. Idanunsa ya d’an k’ank’ance saboda, yanda yaga numfashinta na sama da k’asa. Lallai Tabbas yasan cewa Idan bai taimaka mata ba, To zata iya fad’awa cikin wata matsalar daban kana ya lura wannan mutumin mutum ne mai daraja da Kekkyawar zuciya, a hankali ya kuma kalli yadda hancinta keta zubda jinin haɓo. Da sauri ya Juya. tare da kutsa kansa acikin motarsa, cikin sauri ya d’auki wannan bottle water din nasa mai matukar sanyi. Sabida muryar Barrister Kabir da yaji yana kuka da kiranta. Da sauri ya juyo ya K’arasowa kan Jannart din wacce. Yanzu Barrister Kabir ya ɗagota daga kan motar ya tallabeta a jikinsa yana kiran Daddy. “Yaya! Yayah Idi !!!”. Da sauri ya ƙara so gabansa tare da murɗa marfin gorar faron mai masifar sanyin nan. Kanta da Abba ke tallabe dashi ya saita tare da d’an sunkuyowa ya soma zirara mata ruwa mai bala’in sanyi a tsakiyar akanta. Yayi hakanne kuma saboda bata taimakon gaggawa sabida yasan idan ya zuba mata ruwan sanyi akanta, Lallai jinin dake fita a hancin nata zai tsaya. A dai-dai lokacin da yake tsaka da zuba mata ruwanne kuma, Alhaji Idi Sale Dakata, da kuma aminansa da suke cikin babban falonsa suka fito zuwa tsakar gidan, ganin abunda ke faruwane kuma yasa suka nufo kansu gadan-gadan. Jannart dake kwance akasa kanta bisa cinyar ƙanin mahaifin nata kuwa sanyin ruwan da Rayyern din ke zuba mata ne yasa ta, jan wani irin dogon numfashi, lokacin ɗaya kuma jinin dake zuban ya tsaya. *Kiyiwa Allah da Manzonsa kada ki fitar min da littafina, in kin San kin sayane dan ki fitarmin da littafina ki gaya min in meda miki kuɗin dan girman Ubangiji ɗayae haliccemu, kada ki karantamin littafina in baki biyaba ganan account na 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU, sai ki turo shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276 ko kuma ki sayi katin MTN ki copy number's din ki turo min ta WhatsApp* Ganin jinin ya tsaya ne kuma yasa. Dr Rayyern Mai-nasara juyawa sauran ruwan ya zuba a jikin motarsa inda junin yake ya gangara yayi ƙasa. Kana ya juya ya shiga motarsa tare dayi mata key da danna horn. Cikin sa'a kuwa Mai gadin ya fara kiciniyar buɗe mishi gate yanayi yana sharce hawayen tausayin Jannart. Ita kuwa Jannart Lokaci ɗaya kuma gaba daya jikinta ya d’auki karkarwa, take ta soma fitar da wani irin numfashi mai kaman sheshshek’a alamun kuma athsman ɗinta yana tasowa. Idanu duk suka zuba mata, Yayinda Abba kuwa ya tsaida idanunshi kan ƙirjinta. Inda yake Kallon yanda bugun zuciyarta ke tayin k’asa. Adai-dai lokacin da bugun zuciyar nata ya tsaya cak ne, kuma Idanunta suka soma kakkafewa, lokaci d’aya ta saki wani irin nishi’n daya saka Abba firgici. Dai-dai lokacin kuma k’irjin Dr Rayyern Mai-nasara yayi wani irin masifeffen harbawa. Take kuwa numfashinta ya d’auke D’ibbbbbb..... _Dan Allah ba danniba dan Allah da Manzonsa da darajar iyayenku nace kada ku fitarmin da littafina in kin sayane don ki fitar kiyiwa girman Allah ki gaya min in meda miki kuɗinki, dan Allah kada ki karantamin. In baki biya kuyiwa Allah kada ku watsa min littafina baku san wahalar da nake sha kan rubutun nanba._ BY *GARKUWAN FULANI* 11/15/21, 7:20 PM - Auntyna: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *TUBALI* PAGE 16 NA *AYSHA ALIYU GARKUWA* *FREE PAGE NE* *FREE PAGE sunzo karshe, daga gobe zamu gama FREE PAGE, ki biya ki karanta. 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU sai ki turo min shaidar biyanki ta whatsApp number 09097853276, ko kuma ki sayi katin MTN ki copy number's din ki turo min ta WhatsApp na. Special people group 1k ne karamin group kuma 500 ne, wanda bonus ne wa fan's na, asalin kudin littafin 1k ne saukine ga masoyana in an gama kuwa document 1k ne* Cikin tsananin tashin hankali, da kuma tsananin rud’ewa, Barrister Kabir ya sanya hannayensa duka biyu ya tallafo Jannart d’in. “Jannart! Jannart!! dan Allah bud’e idanunki Jannart!!! innalillahi wa inna Ilaihirraju’un! Yaya Idi Jannart ta suma, bata numfashi!!!” Barrister Kabir din ya fad’a yana me. Kallon Yayan nasa, wato Alhaji Idi Saleh dakata, cikin matsanancin tashin hankali. Shima kuwa Alhaji Idi Saleh Dakata'n tashin hankali ne, kwance akan fuskarsa, cikin yanayin rud’ewan da yayi, ya kalli Dr Lukman dake tsaye, tare da cewa. “Dr. Lukman ka duba mana ita dan Allah.” Jin hakanne kuwa yasa Dr Lukman dake tsaye, d’an matsowa kusa dasu, dan duba Jannart din, wacce ita yanzu bata masan duk wata Waina da ake toyawa acikin gidanba. Idanu Barrister Kabir ya d’ago tare da watsawa, Dr Lukman din muguwar harara, cikin kuma yanayin fushi da tsananin b’acin rai yace. “Kada kayi kuskuren tab’a min y’a. Domin kuwa na jima da sanin muguwar cutar da kakeyi mata ta karkashin k’asa.” Cak Dr.Lukman din ya tsaya, tare da matsawa gefe batare kuma daya karaso wajen ba, saboda jin abunda Barrister Kabir din ya fad’a. Barrister kuwa sungumar Jannart din yayi, kaitsaye kuma cikin sauri ya nufi hanyar fita daga cikin gidan. Da hanzari kuwa maigadi ya bud’e masa dan madaidicin kofar dake jikin gate din gidan ya fice. Koda ya fito kuwa murfin motarsa na gidan baya ya bude, tare da tura Jannart din ciki ya kwantar da ita. Batare kuma daya jira komai ba, ya zagaya ya shiga b’angaren driver, ahanzarce ya tada motar, tare kuma da cillata kan titi, kaitsaye yabi bayan motar Dr Rayyern Mai-nasara dake ta sharara gudu, akan shumfud’add’en titin kofar gidan daya mike santa yana mai jin jijiyoyin kansa na tsananta harbawa sabida ihu da hayaniyar da akayi tayi a kanshi . Shi kuwa Barrister biye dashi yake a hamzarce. Wanda kuma yayi hakanne saboda sanin matsayin Rayyern da yayi, na likita zai iya taimaka musu. Yayinda ab’angaren Rayyern kuwa tuk’in motar yake, yana maijin wani irin b’acin rai acikin ransa, badan komai ba kuwa saidan b’ata masa rai da lokaci da akayi agidan Alhaji Idi Salte Dakata, Tabbas yasan cewar. Koda ace yaje asibitin nasa yanzu, babu wani abu da zai iya aikatawa, Domin yafi kowa sanin kansa Idan ransa na b’ace baya tab’a iyayin komai, koda ma kuma ace yayi din bisa dole, to abun bazai zama hundred percent yanda yake so ba ga kuma alamun ciwon kansa da yake ji. Y’ar k’aramar tsuka yaja, tare kuma da d’an buga kan steering motar tasa, kaitsaye ya sanja akalar tafiyar tasa, inda ya saki hanyar asibitin nasu daya kama, direct ya shari kwana tare da hawa kan titin da zai sa dashi da gidansu. Ganin hakanne kuma yasa P.A d’agowa ya kalleshi, kamar zaice wani abu kuma saiya fasa, saboda yasan halin maigidan nasa, da yawan lokuta bayason adameshi da yawan magana. Barrister Kabir dake bayan su Rayyern din kuwa, shima gudu yake shararawa, still kuma har yanzu yana mebin ba yansu, sai-dai duk bayan mintuna kad’an yana juyawa ya kalli Jannart dake kwance flat agidan baya, babu alaman numfashi ko d’igo ajikinta. Wanda hakan kuwa shi yake k’ara sanya Barrister Kabir din acikin tashin hankali. Tafiyar da bata wuce ta 30mn ba sukayi, isowarsu wajen wani jection ne kuma yasa, Usman P.A d’an d’ago kai ya kalli Rayyern din. Sake Kallon bayansu Usman P.A din yayi, still kuma ganin motar da tun d’azu yake ankare da ita, na binsu abayane , yasa shi d’an muskutawa cikin kuma yanayin mamaki yace. “Sir kaman fa binmu wannan motar dake bayanmu takeyi.” Idanu Rayyern din ya d’aga, tare da maida kallonsa ga madubin motar wanda yake haska musu duk abunda ke bayansu. Tabbas shima ya lura da motar, saidai kuma bai d’auki hakan amatsayin wani serious abuba, batare kuma daya tankawa Usman P.A ba, kaitsaye ya hau kan titin daya shigar dasu layin gidansu. Suna isa bakin gate din tamfatsetsen gidan nasu ne kuma, barrister Kabir ya taka wani irin birki. Wanda kuma hakan yayi dai-dai da tsayawar motar Rayyern din shima, cikin kuma zafin nama da zafin ciwon kan sa yakeji ya bud’e murfin motar ya fito, saboda duk atunaninsa Alhaji Idi Sale Dakata ne, bai daddara da gargadin daya yi masa ba, ya sake turo masa wasu mutanen dan su bibiyeshi. Fitowarsa daga cikin tasa motar ne, kuma yasa Barrister Kabir fitowa shima cikin hanzari, kuma ya nufo Dr. Rayyern d’in. Muryarsa na rawa yace. “Dan Allah Dr. Rayyern ka taimakamin, kada Jannart ta rasa ranta, Dan Allah ka taimakawa rayuwarta, wlh itace kaɗai babbar *HUJJATA,* ita kad’ai ce Hujjar da zan nuna anan gaba, please ka taimaka min!!” Barrister Kabir din ya fad’i haka cikin tsananin tashin hankali, da kuma muryarsa wacce take fitar da sautin kuka. Dr. Rayyern din kuwa Jin amo da kuma sautin, muryar Barrister Kabir din dake fita cikin kuka ne, da kuma amo mai shiga kunne, yasa shi rumtse I danunsa, tare dasa hannunsa na dama ya dafe kansa, dake wani irin sarawa, dan lokaci daya yaji kaman ana buga masa gudu ma a tsakiyar kannasa, abu na farko da bayaso arayuwarsa shine, yi masa magana cikin sigar kuka da kuma d’aga murya, sannan kuma aduk sanda wani ya buk’aci taimako afujajan awajensa, ya kanji zuciyarsa ta karye. Balle kuma Barrister Kabir din da yake ta had’ashi da sunan Allah. *Inama ace makaranta zasu kasance kamar Dr Rayyern in an had’asu da Allah zasuyi abu ko zasu bari, dan Allah da Manzonsa da darajar iyayenku idan Free PAGE ya kare kada ku fitarmin da littafina, in kinsan kin sayane dan ki fitar dan Allah ki gaya min in meda miki kuɗinki Dan girman Allah da tsarki littafinmu akwai karami. Group 500 ne kacal 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU sai ki turo min shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276 ko ki sayi katin MTN ki copy edin ki turo min ta WhatsApp* “Usman!” Rayyern din ya kira sunan Usman P.A da wata irin murya. Jin amo da kuma sautin muryar Rayyern din cikin wani irin yanayi na dabanne kuma yasa, cikin sauri Usman ya fito, tare da k’arasowa yana Kallon Ogan nasa. “Ka kaishi hospital Usman kacewa Sulaiman ya duba patient din, please kuje Usman kutafi daga nan please.....” Rayyern din ya fad’i hakan, cikin wani irin yanayi marar dadi dayakejin kansa aciki, tare kuma dasa hannayensa duka biyu ya kama kansa. Usman kuwa fahimtar halin da Ogan nasa ke cike ne yasa shi, saurin kallon Barrister Kabir. Ahanzarce yace. “Muje na rakaku hospital dinsa akwai Doctor's zasu dubata in sha Allah zata samu lfy.” Ko jiran abunda Barrister Kabir din zaice kuwa baiyi ba, ya bud’e murfin motar barrister din, nan b’angaren mai zaman banza ya zauna. Ganin hakanne kuma yasa Abba Kabir din shima komawa cikin motar, a 360 ya murzawa motar key tare da cillata kan titi, kaitsaye suka nufi asibitin Mai-nasara Hospital, saboda dama Barrister Kabir din yasan asibitin. Ganin sun miki hanyar asibitinne kuma yasa Usman P.A ciro wayarsa ya dannawa Dr Sulaiman Kira. Bugu biyu kuwa Sulaiman ya dauki wayar, bayan sun gaisa ne kuma Usman P.A ke fad’awa Sulaiman din cewa. “Gamunan a hanyan Mai-nasara Hospital zamu kawo emergency patient, bisa umarnin Dr Rayyern.” Da “to.” Kawai Dr. Sulaiman ya amsa, Yayinda shi kuwa Usman P.A ya katse kiran. Rayyern kuwa da har yanzu ke tsaye abakin, motar tasa hannayensa duka biyu yasa ya cigaba da rike kansa dake sarawa. Jin da yayi cewar bazai iya jurewa tsayuwar bane, yasa shi nufar gate din gidannasu, koda ya isa jikin gate din, hannunsa ya daura akan y’ar karamar kofar dake jikin gate din, tare da tura ta ciki. Baba Maud’o dake zaune abakin kofar dan Part ɗin sa, yana me sauraran radio ne ya d’ago kansa, saboda ji da yayi an tab’a kofar shigowa gate din. Aikuwa yana d’aga kansa ya sauke idanunsa akan Rayyern, da har yanzu yake dafe da kansa da hannuwansa duka biyu. “Rayyern!!!” Baba Maud’o ya kira sunansa, cikin yanayi na mamaki da kuma zallar damuwa. Batare kuma daya bari Rayyern din ya amsa masa ba, ya d’aura da cewa. “Subahanallah Rayyern maiya sameka? Lafiya kuwa? Meke damunka? Bugewa kayi akan naka ne? Ko kuwa wani abune ya same ka?” Baba Maud’o yayi masa duka tambayoyin cikin bayyana tsananin damuwarsa. Shikuwa Rayyern da ayanzu, yakejin idanunsa sun fara yi masa nauyi, kai kawai ya iya girgizawa Baba Maud’on, batare kuma daya iya cewa komai ba, kaitsaye ya wuce cikin gidannasu. Hakan da yayi dinne kuwa yasa Baba Maud’o, Jin wani iri acikin zuciyarsa, take kuma damuwa maitsananin yawa ta bayyana akan fuskarsa, saboda ya sani ba karamin abubane zai sa Rayyern din dawowa acikin irin wannan yanayin, Lallai akwai abunda yake damunshi. “To kodai awajen aikin nasa ne aka bata masa rai? Kodai kuma ciwon kansa ne?” Baba Maud’o yayiwa kansa tambayar da bashi da mai amsa masa ita, sai Rayyern din. Ganin da yayi zancen zuciya bazai kaishi bane kuma, yasa shi dan bud’e kofar gidan ya lek’a waje, ganin motar Rayyern din da yayi fake akofar gate dinne kuma yasashi saurin fitowa, tare da leka cikin motar, ganin akwai key ajikin motar ne kuma yasa, da kansa ya wangale makeken gate din, tare da dawowa ya shiga cikin motar, da kansa ya shigo da motar ciki, saboda a lokacin shi kad’aine ya rage agidan, Hadi driver da kuma sauran masu bawa flowers ruwa duk basanan. *Dan Allah da Manzonsa idan free PAGE sun kare kada ku fitar min da littafi, ina rokon nanne da yakinin duk Musulmin kirki mai cikar imani da sanin darajar Allah da Manzonsa da darajar iyayensa nasan bazai fitarmin da shi ba, ko ya karanta na watan* Rayyern kuwa Ahankali yake tafiya, yana me d’an jujjuya kai tare kuma da rumtse idanunsa, da yakejin sunyi masa matukar nauyi. Isowarshi jikin kofar da zata sadashi da babban falon gidanne kuma, yasa shi d’aura hannunsa akan handle din kofar. Dai-dai lokacin kuwa Abba da Mamy ne ke zaune acikin falon da alamun tattauna abu mai mahimmanci sukeyi. Inda Abba ya d’ago kansa ya kalli Mamy, cikin yanayin yin ƙasa da murya da alamun tsawatarwa yace. “Kinsan abunda yake bunne, wanda kuma har yanzu bamu shirya tono shi ba. Meyasa kikeson ki bada kofa da abubuwa da yawa zasu iya wakana ba tare da mun shirya musuba. Wannan sirrin mai karfi ne da cikar rauni, Tono shi kuma dai-dai yake da tsayawar bugun zuciyar wasu mutanen, musamman Rayye......” Sauran maganan dake bakin Abban ne kuwa, suka mak’ale, asakamakon jin motsin bud’e kofar falon da akayi, Wanda hakan yasa cikin sauri duk suka maida kallonsu ga bakin k’ofar. Ganin Rayyern din da sukayi dafe da kai ne kuma, yasa duk suka mimmik’e, “Rayyern lafiya kuwa?” Abba ya tambaya hankalinsa atashe. Kai Rayyern din ya d’an girgiza musu, batare daya ce komai ba, kuma ya k’arasa shigowa cikin falon, tare da nufan kan 3 seater, din leather cushion dake Cikin falon ya kwanta. Still kuma hannayensa ya sake maidawa duka biyu ya rik’e kansa. Al’amarin daya sanya hankalin su Abba da Mamy matukar tashi kenan. Da sauri Abba ya k’arasa inda Rayyern din ke kwance, hannunsa ya d’aura akan Rayyern din, cikin muryar dake bayyana zallan damuwarsa da farga yace. “Rayyern me yake damunka, kodai ciwon kanka ne ya tashi!?” Kai Rayyern din ya jinjina alaman “Eh.” Saboda ayanzu yakai wani stage da bayajin zai iyayin wata magana. Zazzafan numfashi Abba da Mamyn suka sauƙe, cike kuma da alhinin tashin ciwon kannasa, Abba ya zaro waya dan kiran Ramadan. Yayinda Mamy kuwa ta matso kusa da Rayyern d’in, anutse ta zauna tare da soma shafa masa tarin sumar dake kansa. A dai-dai wannan lokacin kuwa, Ramadan ne ke zaune acikin wani had’add’en lambu, dake cikin wani katafaren gida, yayinda ya k’urawa wata fara kyakkyawar matashiyar budurwar dake zaune agefensa idanu. duk da cewar kuma ak’alla budurwar dake zaune agefen nashi, ba zata wuce 20 years ba, amma tana da cikar halitta mai kyau, da ganinta kuma kasan cewa yar manyan mutane ne, Rayhanna kenan kyakkyawar matashiyar budurwar mai alkunya. Yayinda ad’an gefe da Rayhannan kuwa Riyyam-nsra ne zaune, yanata yiwa Hamman nasa tsiya. Cikin kuma ya bawa da zab’in Ramadan d’in yace. “Gaskiya Hamma Ramadan ka iya zab’en kyakkyawar budurwa, tamkar daga saudiya aka sassak’ota.” Murmushin Jin dadi Ramadan yayi, tare da sanya hannunsa na dama ya dafa kafad’an Riyyam din, again kuma cikin kasa dauke idanunsa daga kan Rayhanna’n nasan yace. “Angaya maka cewar ni na wasa ne, ai kwata kwata bana sanya, ko da ka d’auka cewar ni irin suma Hamma Rayyern ne waliyai.” Dariya Riyyam nsra ya saka, Yayinda ita kuma Rayhanna ta sanya mayafinta ta rufe fuskarta, wanda tayi hakanne kuma saboda Sam bazata iya jurewa, irin Kallon da Ramadan din keyi mata ba, Domin kallone da yake bayyana tsananin kauna da soyayyarsa agareta. Baki Ramadan din ya bud’e da niyar cewa wani abu, amma kuma sai k’aran wayansa dake tashi, acikin aljihun rigarsa, ya hanashi furta komai. Zaro wayartasa yayi, ganin sunan Abba na yawo akan screen din wayar ne, kuma yasa shi d’agawa da sauri. Daga can b’angaren kuwa Abba dake tsaye agefen Rayyern ne yace. “Ramadan, Rayyern! Rayyern ciwon kansa ya tashi!” Idanu Ramadan din ya dan zazzaro tare kuma da, mik’ewa tsaye cikin tashin hankalin daya samu kansa aciki yace. “Innalillahi Wa’inna Ilaihirraju’un, Abba maiya samu Hamma Rayyern din, yaushe kuma ciwon kan nasa ya tashi?” Ya tambayi Abban cikin tashin hankali, gami da tsananin damuwa. “Bansani ba Ramadan, Domin yanzu dawowanshi gida, yanzu haka gashinan a kwance sai faman rike kan na yakeyi. Maza Ramadan kabar duk abunda kakeyi ka dawo gida, sannan ka biya ta pharmacy ka had’o masa magunguna.” Abban ya fad’i hakan, cikin muryar dake bayyana cewa, kwarai yana cikin damuwa. Ramadan kuwa idanunsa da suka ciko da k’walla, saboda tausayin dan uwannasa yad’an lumshe, kana cikin muryarsa da tayi rauni sosai yace. “Shikenan Abba ganinan zuwa.” Yana gama fadan hakanne kuma Abba ya katse kiran. Riyyam-nsra da tun d’azun shima ya mik’e tsaye hankalinsa atashe matuka, yace. “Hamma Ramadan mai yasamu Hamma Rayyern? Dan Allah karkacemin wani abu na cutarwa ne ya sameshi.” Idanu Ramadan din ya bud’e, cikin yanayin sanyi yace. “Ba abunda ya sameshi Riyyam, kawai dai ciwon kansa ne ya tashi, wanda dama kuma yana dashi, saidai bai cika tashi ba, harsai da dalili, Idan ciwon kannan ya tashi Riyyam, Hamma Rayyern yana shan wahala, saidai duk da haka gwara ciwon kan, akan matsanancin ciwon cikin da yake tashi mishi, awasu mabanbanta lokuta.” D’an rank’wafowa yayi ya kalli Rayhanna, da itama gaba daya damuwa ta bayyana akan fuskarta, saboda tasan matsayin Dr Rayyern din awajen Ramadan, tasan yanda Ramadan ya dauki Rayyern, da kuma yanda yake girmama duk wani abu daya shafesa, haka kuma tasan yanda Ramadan din ke daukan duk wata matsala ko damuwar yayansa, Domin sauda yawan lokaci Ramadan din, kan fad’a mata cewar Hamma Rayyern dinshi, shine duk wani Garkuwa’rsa, shine kuma wanda ya tsaya masa akan jindadi da farincikinsa. “Hanna zantafi, Hamma Rayyern bashi da lafiya, zamuyi waya later.” Ramadan din ya fada murya asanyaye. Mik’ewa tsaye Rayhanan tayi, tare da cewa. “Shikenan badamuwa, Allah Ubangiji ya bashi lafiya, yasa zakkan jikine.” Da “Ameen.” Ya amsa, har wajen da motarsa kirar Benz ke fake kuma Rayhanan ta rakosu, inda tayiwa Riyyam-nsra sallama. Saida taga ficewarsu daga cikin compound d’in gidan nasu, kuwa kafun ta koma ciki. Duk zuciyarta babu dadi, saboda duk wata damuwa da tagani akan fuskar Ramadan to ta shafeta. Ramadan kuwa suna ficewa daga cikin gidansu Rayhannan, wani irin gudu ya soma shararawa akan titi, wanda hakan yasa cikin mintuna kadan suka iso, babban pharmacy dinsu. Ko gama dai-dai-ta parking din motar baiyi ba, haka ya fito ya shiga cikin pharmacy din, duk wasu magunguna da yasan Rayyern din zai buk’ata ya had’a, tare da fitowa agurguje yaja motar suka nufo gida kaitsaye. Isowarsu bakin gate din gidanne kuma yasa, Ramadan soma danna horn. Wannan yasa cikin sauri Baba Maud’o dake zaune abakin gate din, yayi jigum, yazo ya bud’e musu, gaba d’aya bayajin dadi acikin zuciyarsa, saboda sai ayanzunne ma yake tunawa da cewar, halan ciwon kai din Rayyern dinne ya tashi, saboda aduk cikin gidan babu wanda baisan da cewar, Rayyern na fama da ciwon kai dana ciki ba. Ramadan kuwa yana shigowa cikin gidan yayi parking motar, cikin sauri kuma shida Riyyam suka fito, kowannensu fuskarsa dauke da matsanancin damuwa suka shige cikin gidan. Tunkafun su karasa shiga cikin babban falon gidan kuma, Ramadan ya soma b’abb’alle magungunan da zai bawa Rayyern din. Wanda hakan yasa suna shiga cikin falon, direct Riyyam-nsra ya k’arasa gaban deep freezer, tare da dauko bottle water marar sanyi kasan cewar ba'a jima da sasuba. Koda ya dawo goran ruwan ya mik’awa, Ramadan wanda zuwa lokacin harya gama b’are magungunan, inda da kansa ya tallafo Hamman nasa, tare da zuba masa magungunan, kana ya had’a masa da ruwan faro. Atake kuwa Rayyern ya had’iye magungunan, saidai kuma cikin radadin ciwon kan nasa da yakeji, ya sake komawa ya kwanta, Yayinda sannu Ahankali yake ci gaba da d’an jujjuyawa kan nasa. Idanu duk suka zuba masa, kana cike da tsananin tausayawa sukeyi mishi sannu, Riyyam-nsra kuwa zama yayi dab’as ak’asa, idanunsa da suka cicciko da hawaye ya zubawa Hamma Rayyern d’in, acikin ransa kuwa yana me addu’a, da fatan Allah Ya bawa hamma Rayyern dinnasu lafiya. Rayyern kuwa dake kwance kannasa ya sake rikewa, tare da lumshe idanunsa, wanda sukayi jazur, saboda tsabar wahalan da yakeji kuwa, hatta jijiyoyin dake kwance akan goshinsa saida suka fito rud’u rud’u. *Dan girman Allah masu sayan littattafai dan su fitar su watsashi kuyi hakuri kada ku saya littafina dan Allah nace in kin saya kuma ki gaya min in meda miki kuɗinki* Bayan kaman mintuna 15 dashan maganin nasa ne kuma, ya soma sauke wani irin wahalalliyar ajiyar zuciya. Yayinda sannu ahankali yakejin relief nad’an saukar masa. In a 20mn kuwa batare da zato ko tsammani ba, bacci mai nauyi ya daukesa. Jin yanda numfashinsa ke fita da d’an fusga ne kuma, yasa su Abba gane cewar yayi bacci, ajiyar zuciya suka sauk’e dukansu, Yayinda Abba kuwa ya d’an rankwafa tare da gyarawa Rayyern din kwanciya. Bayan ya koma ya zauna akan kujera ne kuma yasa hannunshi duka biyu yayi tagumi cikin alamun tarin fargaba, tashin hankali, so, da tarin tausayin d’an nasa . Ido Ramadan ya ɗan zuba mishi kana a hankali yace. “Abba ba komai fa in sha Allah zai samu lfy”. Numfashi ya ɗan sauƙe a hankali kana murya asanyaye yace. “Hakika yanzu aduniya babu wani abu da yake, damuna da kuma matuk’ar d’agamin hankali sama da ciwon Rayyern. Ciwon Rayyern yana damuna, musamman ciwon cikinsa da Idan ya tashi masa, yakeyin kamar zai rabamu dashi, Tabbas Ina matuk’ar tsoron ranan da ciwon nasa zai tashi, Ina fargaban hakan akoda yaushe, Ina mai kuma addu’a da fatan, Allah ya yayemishi wannan ciwon kai da ciwon cikin, Domin kuwa aduk sanda d’aya daga cikinsu ya tashi, shi kad’ai yasan wani irin zafi da yakeji tunda har yake fidda shi hayyacinsa.” Abban ya kai k’arshen maganan nasa, cikin raunatacciyar murya, Yayinda idanunsa kuma suka cicciko da hawaye. Ganin hawaye a idanun Abban ne kuma, yasa Mamy, Ramadan, Riyyam duk sukaji jikinsu yayi sanyi, take kuma idanun Mamayn ma duk suka cicciko da hawaye, kasancewar ta Mace ne kuma, yasa ta kasa controlling hawayen nata, harsaida suka sauk’o kan fuskarta, batare kuma da ta bari kowa yaga hawayen nata ba, ta share da sauri. Dai-dai lokacin kuwa Baba Maud’o dake tsaye abakin k’ofar shigowa falon, ya d’an d’aga muryarsa wajen yin sallama. Jin muryar Baba Maud’o dinne kuma yasa, Ramadan mikewa ya k’arasa tare da bud’e kofar, Cikin kulawa yace. “Baba Maud’o bismillah ka shigo mana.” Kai Baba Maud’on ya girgiza, tare da cewa. “A’a basai na shigo ba Ramadan, dama nazo ne na tambaya naji ya jikin Rayyanu.” Ajiyar zuciya Ramadan ya sauk’e, cikin kuma son kwantarwa da Baba Maud’on hankali yace. “Jikinsa da sauki sosai Baba Maud’o, yasha magani kuma yanzu haka ma bacci yake, Insha Allah kuma Idan ya tashi daga baccin, zai ji saukin ciwon kan.” Kai Baba Maud’on ya jinjina, cike kuma da gamsuwa yace. “Masha Allah! Allah Ubangiji ya k’ara masa lafiya da Nisan kwana mai amfani.” Da “Ameen.” Ramadan ya amsa, ganin Baba Maud’on ya juya ya tafi ne kuma, yasa shima komawa cikin falon. Baba Maud’o kuwa Koda ya nufi dakinsa dake cikin gidan, hannayensa yasanya ahankali ya share hawayen da suka gangaro daga Cikin idanunsa, wanda kuma yayi imani cewa, da ace bai bar wajen Ramadan din da wuri ba, To da akan idanun Ramadan hawayen nasa zasu zubo. _Littafin TUBALI na kuɗine ki biya ki karanta cikin salama special Group 1k ƙaramin group 500 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU sai ki turo min shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276 ko ki sayi katin MTN ki copy number's din ki turo min ta WhatsApp_ Acan b’angaren su Barrister Kabir kuwa, da wani irin speed suka shiga cikin asibitin. Wanda kuma suna shiga ko gama parking ba suyiba, aka turo wasu nurses da gado irin maitayannan, su dakansu nurses din suka d’aura Jannart akan gadon, tare da kutsawa da ita cikin asibitin, kaitsaye zuwa emergency. Suna shigar da ita emergency din kuwa, Dr. Sulaiman, da kuma Dr. Imran, kana da Dr. Fatymah, suka shiga emergency din, tare da duk’ufa akanta, cikin sauri suka soma bata taimakon gaggawa. Yayinda acan waje kuwa, hankali atashe Barrister Kabir ya karasa receiption na, Hospital din dan bud’ewa Jannart din folder. Koda yaje kuwa baiwani dau lokaci ba layi ya iso kanshi. Mai bud’e folder dinne ya dago kansa ya kalli Barrister Kabir tare da cewa. “Sir me sunan patient din?.” D’anjim Barrister Kabir yayi, natsawon wasu mintuna, kafun ya dago kai, cikin aminta da abunda zuciyarsa ta yanke yace. “Sunanta *Jannart Abdulkarim Saleh Dakata.”* Kai mai bud’e folder’n ya jinjina, tare da maida kansa k’asa ya rubuta abunda yaji mutumin ya fad’a masa. Yan cike cike yayi cikin abunda bai wuce 5mn ba kuwa, ya bud’ewa Jannart folder acikin Hospital din. Barrister Kabir kuwa ganin komai ya kammala ne, yasa shi komawa bakin emergency room din ya zauna, tare da sanya hannayensa akan fuskarsa ya zuba tagumi, Tabbas a yanzun abubuwa da yawa ne ke damunsa, amma babban burinsa shine farfadowar Jannart da kuma dawowa cikin hayyacinta. Acan cikin Emergency room din kuwa, sosai su Dr. Sulaiman suka duk’ufa akan Jannart don ceto rayuwarta, saidai kuma duk yanda suka dauki abun ya wuce nan. Dr. Sulaiman daya shaida fuskar yarinyar ne ya sharce gumin dake goshinsa, tare da d’auko wani abu mai kaman dutsin guga guda biyu ya manna akan kirjin Jannart din, ganin da yayi batayi motsi bane kuma, yasa shi jin wani irin fad’uwar gaba, saboda sanin da yayiwa abun, sau uku kawai ake dannashi ak’irjin mutum, Idan aka dannawa mutum sau daya, ya farfado ya koma, aka kuma na biyu still bayan ya farfado ya sake komawa, To Idan akayi na uku mutum baiko motsa ba, Lallai alamace dake nuna cewar bashi da rai. Sake danna mata abun Dr. Sulaiman yayi akan kirjinta, cikin sa’a kuwa yaji taja wani irin numfashi, saidai kuma kafun su ankara numfashin harya koma. Kallon-kallo sukayiwa junansu, kafun Dr. Sulaiman ya sakeyin shahadan danna mata abun da karfi akan kirjinta. Wani irin dogon numfashi maikama da shak’uwa taja, tare da mimmik’e jikinta, lokaci daya kuma bugun zuciyarta ya...! *littafin TUBALI na kuɗine, 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU* *Albishirinku! Ma'aurata, GA GARKUWAR KU nan tafe muku da tsarabobi na musamman gareku ma'aurata daga cibiyar mgnin mata mai taken GARKUWAR MA'AURATA* NI DAI AYSHA ALIYU GARKUWA. Ina matukar mamakin wani irin lokaci da ya riske mu mai wahalallan fassara. Kullum dai magana daya ce, akan ma’aurata, fada, rashin jituwa, mutuwar aure, akan kuskure kalilan, rashin kula, rashin yi wa juna uziri. Toh wai duk me ya janyo hakan? Na zurfafa a tsananin tunani hakan ya tilasta min bincike mai tarin yawa wanda ya kai ni ga gano inda matsalar take? Shin yar’uwa ke macece amma kin san wacece mace ku? Kin san me ake kira mace kuwa? Mace ita ce matar da take zama iyali a wajan namiji ta zame masa bango, sanyin idaniyarsa, ta zame masa gata da farin cikin rayuwarsa ta zame masa ruwa abar kore ƙishinsa ta zame masa mayafi mai karesa daga gigitar kadaice, ta kuma dorar da mijinta kan turbar gaskiya, ta kashe masa jiki da salonta ta rikita shi da baiwa da ni’imar da Allah ya bata idan har ta san hanyar mayar da kanta sabuwa dal awajanta, wato kullun takasance masa tamkar amarya har ya kasa tantance daren amarcinsu da sauran dararen rakun rayuwar su. Wannan ita ce mace. Ina da wata saukakkar hanyar da zaki zama abar so da kulawa da soyayya a wajan mijinki ta hanya mafi sauki, 09097853276 hanyar ita ce ki gwada amfani da kayana na gyara ki gani, ina mai tabbatar miki da in sha Allahu sai kin dara da murna sai kuma kin gode min. Kayana kaya ne da aka yi shi da zallan itacanmu na gado marasa illa a cikin jikin dan adam musamman mace, kaya ne da suke taimakawa (sex hormones 😍) dinki. Misali kina kallon India😘, hollywood, Asian film🥰 kina ganin yanda mazansu ke nunawa matansu tsananin soyayya kamar su ba su kyautar ransu!? Saboda me hakan? Saboda suna sadaukar da lokacinsu wajan gyara jikinsu da kayan da ke tsattsafo da ni’ima cike da tsukewa, kayan nan kuma ana yinsu ne zallar magungunan gargajiya wanda ba su da illa domin haɗine na ingantattun itatuwa da yayansu. Ina baiwar Allahn da miji ke daure mata fuska babu hirar arziki? Zo ki ji yar’uwa zan baki gumbata da zallar gari wanda aka yi su da nagartattun itacen da ke da matukar amfani a jikin mace. Gubar ciko, gumbar tsalle dole, gubar da ba'a baiwa mai kishiya, garin maɗi, garin mallaka, tsumin goron tula, tsumin tsartai, tsumin maratsi, pala-pala butar sirri, kwanon k’asaitacciyar mace, furar mata madararta gareki Hajia takenta sha yanzu mgni yanzu, Ina mata masu fama da sanyi? Sanyin mara ki zo na hadaki da magani na na sanyi wanda yake wanke mara ya fitar da duk wata cuta da ke samun mazauni a wajan. Ina da ciccibi mai kyau. Ina da hadin amare mai kyau wanda zai gyara yarinya ya kankaro mata kimarta akwai hadin mai jego wanda muke yinsa na asali inada kekkyawan Hadi maida tsohuwa yarinya. Akwai daya bangaren wato *KAMSHI* Kimarki gyaranki da kamshinki. Matan da suka gane suka san yanda za su kankaro da mutunci su ne masu amfani da kayan gyara da kuma sanyaya jikinsu da kamshi, ina da turaren wanka da na bandaki na daki na jiki da na kaya dana tsuguno kamshin turarena na dabam ne mai sanyaya zuciyar wanda ya shaka ina da kayan kamshi na amarya da na maijego da na uwargida da dukkan macen da take kokarin mayar da kanta mai daraja a idon kowa ta zamo sarauni a idon mijinta, akwai shu'umar humra, sayan na gari maida kuɗi gida, banda karanta yayin gyara Hajia. Zaku iya samun kayyakina a duk garin da kike, zakiyi min mgn ta whatsApp number na 09097853276 domin yin zaɓinki, ko karin bayani, zaki tura kuɗin ta account na 0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU in mun gama mgna zan sa miki kaya a mota yazo duk garin da kike, duk ƙasar da kike kayana zaije gareki ta karkashi D.H.L. in dai kin cika jakarki baki shirya saya yanzuba Please kada mu wahal da juna ki bari sai kin shirya kafin kiyi min mgn. 🤝🏻🥰😘 Daga taku AYSHA ALIYU GARKUWA *(GARKUWAR MA'AURATA)* By *GARKUWAR FULANI* 11/15/21, 7:20 PM - Auntyna: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *TUBALI* PAGE 17 NA *AYSHA ALIYU GARKUWA* *FREE PAGE NE* *LITTAFIN TUBALI NA KUƊI NE, KI SAYA KI KARANTA BA TARE DA HAKKIN WAHALATA A KANKIBA, SPECIAL GROUP 1K AKWAI KUMA KARAMIN GROUP 500 KACAL A YAWAN POSTING NE BABBANCINSU YAKE, 0661110170 GTBank AYSHA GARKUWA ALIYU, sai ki turo min shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276, in Kuma baki da halin turawa ta banki to ki sayi katin MTN! MTN!! Mtn!!! Ki copy number's din sai ki turo min ta whatsApp 09097853276. 🙏🏻🙏🏻🙏🏻😭😭😭 Na rokeku da girman Allah da Manzonsa da darajar iyayenku tsarkin al'ƙur'ani mai girma, kada ki karan littafina in baki SAYABA! In kuma kin saya dan soyyarki da Nabiyi rahamati kada ki rink’a fitarmin da littafina, mutanen dake karanta Audio books da masu posting a wasu wuraren kamar Facebook wattpad da kuyiwa girman Allah da isar mulkinsa da soyeyyarku da manzo mu Muhammad Rasulullah, kada ku taɓa min book har sai da izinina ga number wayata 09097853276, ka/kiyi min mgn ta whatsApp in mun dai-dai ta na lamunce miki/ka sai ka karanta ko ka saka domin wannan littafin dama kab sauran littattafai na hakkin mallakarsa nawane ɗan Allah kiyiwa Allah ba danniba sabida bana ɗin tashin hankali da fitina bare akai ga babin hatsaniya🤗🤝🏻🙏🏻😭😭😭* _Special Group 1k ƙaramin group 500 ne kacal 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU_ Ya harba ya fara aiki. Ajiyar zuciya Dr. Sulaiman Dr Fatymah, da kuma Dr. Imran suka sauk’e, tare kuma dajin wani irin farinciki saboda, taimakon da Allah ya basu iko da dama wajen iya ceto rayuwar Jannart d’in. Dr. fatymah ce ta soma treating duk inda Jannart din taji ciwo, bayan ta kammala ne kuma, Dr. Imran yayiwa Jannart din wasu allurai, wanda zasu taimaka mata wajen samun ingantaccen bacci, da kuma k’warin jiki idan ta farka. Bayan sun kammala yi mata duk wani abunda ya dace ne kuma, Dr. Sulaiman da kansa ya turo gadon da Jannart din ke kwance, zuwa wani d’aki dake gefen Emergency’n na musamman. Fitowarsu daga Cikin Emergency room dinne kuma, yasa Barrister Kabir ta sowa, cikin sauri ya nufesu, hankalinsa amatukar tashe yace. “Dr. Yaya ya jikin Jannart din? Dan Allah ku fadamin halin da take ciki, kada ku b’oyemin.” Ya kare maganan yana me hade hannayensa biyu, waje daya alaman roko. Dr. Sulaiman ne ya dan matso tare da cewa. “Calm down jikinta da sauki sosai, Domin da taimakon Allah munyi nasaran samo numfashinta, yanzu dai haka tana dakin hutu.” Wani irin kakkarfan ajiyar zuciya Barrister ya sauk’e, tare da d’aga hannunsa sama cikin matsanancin farinciki yace. “Alhamdulillah Allah Nagode ma, Yah Allah ina rokonka da ka cigaba da bawa Jannart kariyarka akoda yaushe.” Dr. sulaiman kuwa kallon Barrister din yayi, cikin kuma tausasa murya yace. “Idan babu damuwa zan iya ganinka a office dina, saboda akwai maganar da nakeso muyi.” Kai Barrister Kabir din ya jinjina, tare da cewa babu wata damuwa. “Dr muje.” Hakan kuwa akayi inda Dr. Sulaiman ya shige gaba, shi kuwa Barrister Kabir ya take masa baya. *Alhaji Idi Saleh Dakata House.* Dr. Lukman ne ya d’ago da kansa ya kalli Alhaji Idi Sale Dakata dake tsaye, fuskarsa dauke da bacin rai da kuma zallan rashin jin dadin abunda ya faru yace. “Alhaji Idi Saleh Dakata, kana ga abunda k’aninka yayimin yau, ya hanani duba Jannart, bayan yafi kowa sanin cewar nine likitan da yake dubata tun tana yarinya, kana ga fa har tsawa yayimin wai kada nayi kuskuren tab’a ta, har yana cewa wai yasan abunda nake shiryawa takarkashin k’asa. To Meya sani kenan? Yanaso yace ban iya aikina bane?” Dr. Lukman din ya tambaya yana sakin hucin iska. Shikuwa Daddy hannu ya d’agawa Dr. Lukman di, Domin ayanzu kwata kwata baya bukatar jin korafin kowa, abun dake cikin zuciyarsa kawai ya ishesa. Wani irin numfashi mai zafi ya fesar, tare da d’agowa ya kalli Alhaji Abdu Tababa, da kuma Dr Lukman din. “Kuje zan ne meku daga baya.” Yana gama fad’in haka ya juya, zuciyarsa amatukar hasale ya nufi cikin falonsa. Ganin hakanne kuma yasa Alhaji Abdu Tababa kama hannun Dr Lukman suka shiga mota, bayan maigadi ya wangale musu gate ne kuma, kaitsaye suka fice daga cikin gidan. Daddy kuwa Koda ya karasa cikin falon nasa, Sam kasa zama yayi, shi d’ayansa yake ta safa da marwa atsakiyan falon, Yayinda ya had’e hannayensa duka biyu awaje d’aya. Lallai Tabbas akwai aiki babba a gabansa, wanda kuma dole saiya tashi tsaye. Babban abunda yake tambayar kansa kuma shine, Tayaya akayi Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara yagane cewar, shine wanda yasa ake bibiyansa?. Ya akayi ma yasan gidansa, har tsaurin ido irin na yaron ya kawosa? Tayaya akayi ya yi wannan saken? “Wani irin shegen yaro ne wannan? Mai tsaurin ido da taurin kai da rashin tsoro?” Yayiwa kansa tambayar, yana me sharce gumin daya keto masa. Dai-dai lokacinne kuma Mom ta shigo, cikin falon, hankalinta amatuk’ar tashe, batare kuma da fahimci din da Daddyn yake ciki ba tace. “Alhaji Ina Jannart d’in, Ina aka kaita wanni hali take ciki dan Allah ku fadamin.” Amatuk’ar fusace Daddyn ya juyo, cikin tafasan zuciya ya dann wani tsawan daya saka hanjin cikin Momn kad’awa yace. “Waya baki izinin shigomin falo kai tsaye? Kifita daga harkata fa Maryam, da kike tambayan Jannart kinfini sonta ne? Ba’ayata bace, Ina ruwanki da inda aka kaita? Ko kece kika haifa min ita? Fice min daga falo, tunkafun na aikata abunda zai bata miki rai!!!” Daddy’n ya fad’a fuskarsa babu alaman annuri asamanta. Hakan kuwa shiya sanya, gaba d’aya jikin Mom yayi sanyi, kamar kuma yanda ya buk’ata cikin sauri ta juya ta fice daga cikin falon. Abdull dake tsaye awaje kuwa ganin Mom nasu tafi to jiki asanyaye ne yasashi rufa mata baya. Bayan sun isa nasu falonne ya kalli mahaifiyar tasa cikin sharce hawaye yace cewa. “Ki kwantar da hankalinki Mom, Insha Allah Aunty Jannart ako Ina take Allah zai kula da ita, kuma naga Abba Kabir nema da kansa ya d’auketa, nasan kuma asibiti zai kaita.” Jin abunda Abdull din ya fad’ane kuwa yasa Mom sauke ajiyar zuciya, lokaci guda kuma taji hankalinta ya d’an kwanta. Wayarta ta dauka tare da lalub’o lamban Barrister Kabir din, saidai kuma amma kwata kwata wayartasa bata shiga, hakanne kuma yasa ta hakura tare da ajiyewa akan anjima zata sake kira. *Mainasara hospital* Cikin yanayin tashin hankali Barrister Kabir ya zauna bisa kujerar dake gaban babban table ɗin dake gaba Dr Sulaiman. Gyara zama Dr Sulaiman yayi tare da d’an sauk’e numfashi, kana ya fuskanci Barrister Kabir, murya a tausashe yace. “Babanta ne kai?”. Cikin sauri Barrister Kabir ya gyaɗa mishi kai alamun eh kawai. Shi kuwa Dr Sulaiman, kai ya jinjina tare da ci gaba da cewa. “Kuna sane da cewa tana ɗauke da chronic Asthma, wanda yayi worst sosai ajikinta ko kunsan hakan?” Kai Barrister Kabir ya jinjina, kana cikin bada tabbaci yace. “K’warai Dr. munsan da hakan.” Ajiyar zuciya Dr. Sulaiman din yayi, kamar kuma zaice wani abu saiya fasa, rubutu ya danyi ajikin wata takarda. Bayan ya mikowa Barrister Kabir din takardar ne kuma yace. “Way’annan sune magungunan da zata sha idan ta farka, sannan kuma Dan Allah ana kiyaye yawan bacin ranta please dan abubuwan sunyiwa zuciyarta yawa, har ta fara samun raunin harbawar jini.” Kai Barrister Kabir din ya jinjina, tare da cewa. “Insha Allah Dr. Nagode sosai, amma ya kake gani shin zan iya zuwa na Ganta kuwa.” “K’warai kuwa saidai kada kayi wata magana mai karfi da zai disturbing nata, saboda akwai alluran da mukayi mata, wanda akwai buk’atar dole saita huta.” Kai Barrister Kabir din ya jinjina, tare da mikewa tsaye musabaha suka sakeyi da Dr. Sulaiman din. Bayan kuma ya gaya masa numbern dakin da Jannart din ke ciki ne ya juya yafice daga cikin office din. _Dan girman Allah da isarsa masu fitar da littafina da masu karanta na sata da masu karanta Audio books da masu sawa a YouTube da masu posting nashi a wani wurin kuyiwa girman zatin ubangiji daya haliccemu kada ku taɓamin. Littafina sai kunmin mgn kun saya na lamunce muku ku, dan kin biya 1k ko 500 bawai kuɗin mallakarsa kika biyaba, kudin samun damar karantawa ne 09097853276, ga number' ta, in Kuma zaki sayane ga ac no dina 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU_ Kaitsaye dakin da aka kwantar da Jannart din ya nufa, Koda ya shiga tura kofar dakin yayi, inda ya Sameta kwance tana bacci, an daura mata drip ajikinta. Karasowa Cikin dakin Abba Kabir din yayi, cikin tsananin kulawa hadi da tausayawa ya sa hannu ya shafi goshin Jannart din dake bacci Cikin kwanciyar hankali. “Insha Allah Jannart farinciki yana nan zuwa acikin rayuwarki, Domin ba zaki tabbata acikin kunci ba har abada, Tabbas watarana makiyanki sai sunji kunya, kunya irin Wanda ba zasu taba iya daga Ido su kalleki ba, Insha Allah watarana zaki zama y’antacciya nan bada jimawa ba.” Abba Kabir din ya fad’a, cikin tabbaci da kuma sanin lokacin hakan na k’aratowa sabida yasan dole watan-wata rana gsky zatayi halinta. Sanin da yayi kuma cewar Dr yace abarta tasamu ishashshen hutu ne yasa shi matsawa can gefe, tare da zaro wayarsa kaitsaye ya dannawa lamban Dr Sajo Kira. Cikin sa’a kuwa bugu uku kacal Dr Sajo ya d’aga wayan. Bayan sun gaisane kuma Abba Kabir din ya gyara zamansa tare da cewa. “Yaya Sajo jikin d’iyarku Jannart ne ya tashi, yanzu haka muna cikin Mai-nasara Hospital an bata gado, saidai kuma ba Dr. Rayyern ne ya duba ta.” Daga can b’angaren Dr. Sajo yace. “Subahanallah yanzu Ina fata jikin natan da sauki.” “Eh.” Abba ya bashi amsa. Dr. Sajon kuwa cewa yayi. “Karka damu Barrister Kabir Indai kuna Cikin Mai-nasara Hospital, koba Dr. Rayyern bane ya duba ta, To Ina tabbatar maka da zata samu isashshen kulawa, Domin gaba d’aya likitotin dake cikin asibitin sunsan aikinsu, kuma dukansu k’wararrune kamar yadda suke da lafiyayyun kayan aiki, sannan maganar Dr. Rayyern dinma zaku samu ganinsa Idan kukayi booking Insha Allah. Cikin samun karfin guiwa yace. "In Sha Allah kuwa zamuyi booking”. “Yauwa sai munzo”. To yace kana sukayi sallama da juna. Yana katse kiran ne kuma ya kira Matarsa Aunty Dijat ya Sanar da ita halin da ake ciki, nanfa tace gatanan zuwa ta k’are mgnar da cewa. “Yanzu ya jikin nata?”. Juyowa yayi ya d’an ya kalleta. a hankali take fesar da numfashi alamin baccinta yayi zurfi. “Da sauki.” Ya bata amsa, Domin kuwa harzuwa lokacin Jannart din bacci take bata farka ba. “Allah ya ƙara sauki”. Amin yace kana sukayi sallama. K’arfe 5 dai-dai ne kuma yana nan zaune, kiran Yayan nasa, wato Alhaji Idi Sale Dakata ya shigo cikin wayarsa. Bayan ya d’aga wayarne kuma Daddy da hankalinsa ke tashe yace. “Wai Kabir ina kuka shiga ne? Wani asibiti ne ka kai Jannart, duk na karad’e asibitoci mafi kusa damu amma babuku babu alaman ku, kuna Ina sannan ya jikin Jannart din?” Daddyn ya had’ewa Barrister Kabir duka tambayoyin awaje d’aya. Barrister Kabir kuwa ajiyar zuciya ya sauk’e, tare da cewa. “Kayi hakuri Yayah, gaba daya sha’anin ciwon Jannart dinne ya rudar dani, shi yasa bankira na sanar dakai komai ba, yanzu dai haka muna Cikin Mai-nasara Hospital, kuma jikin nata da sauki sosai Dan tun da doctors suka duba ta take bacci har yanzu kuma bata farka ba.” Shima Daddyn ajiyar zuciya ya sauk’e, nan take kuwa yace. “Okay ganinan zuwa Mai-nasara Hospital din” Yana gama fadin hakan kuwa ya kashe wayan. Mom dake kallonsa ne kuma tace. “Bari na dauko mayafi na muje, Domin dama na gama abinci, Idan yaso saina tafi musu dashi.” Kai kawai Daddyn ya jinjina mata, Domin kuwa hardai yanzu, Jin zuciyarsa yake a Jagule. Koda Mom ta d’auko mayafin nata, kitchin ta wuce tare da daukan basket din da ta shirya food flask acikinsa. Kaitsaye waje ta nufa, saboda tuni Daddyn ya fice. Tana fita compound din gidan kuwa ta sameshi zaune acikin motarsa, bayan ta shiga kana driver yaja suka fice daga cikin gidan. 6:12 pm dai dai suka iso cikin asibitin, wanda kuma zuwannasu yayi dai dai da zuwan Aunty Dijat. Domin kusan atare ma suka shiga cikin d’akin da Jannart din ke kwance bisa jagorancin Barrister Kabir. Bayan sun gaggaisa da junansu ne kuma, Aunty Dijat ta zubawa Barrister Kabir din kunun data dama musu ya sha kasancewar itama tayi girki na musamman ta taho dashi. A lokacin da aka soma kiraye kirayen Sallah magriba ne kuma, Daddy da Abba suka fice dan zuwa masallaci. Yayinda su Aunty Dijat da Momy kuwa anan cikin d’akin asibitin sukayi nasu sallan. Dawowar dasu Barrister Kabir din sukayi a masallaci kuwa, yayi dai-dai da shigowan wasu nurses guda biyu. Ledan ruwan dake jikin Jannart din, wanda ya k’are nurses din suka cire, tare kuma da sake yi mata wasu y’an gwaje gwaje. Bayan sun kammala duba lafiyar Jannart d’inne kuma, suka juyo inda d’aya daga cikin nurses din tace. “Kuyi hakuri patient din batason hayaniya sosai, kuma ak’a’idar aikinmu Idan dare yayi, bama barin kowa acikin Hospital din sai masu kula da majinyata, saboda haka dole duk zaku tafi, saidai za a bar mutum guda d’aya kawai da zaina kulawa da ita, ma’ana wanda zai kwana da ita.” Kai Duk suka jinjina, cikin gamsuwa da bayanan Nurse din Aunty Dijat tace. “Shikenan To Abban Hafeez kuje, Idan yaso ni zan kwana da ita” Saurin girgiza Kai Mom tayi tare da cewa. “A’a Dijat baza’ayi haka ba, duk kuje ni zan kwana da ita, Domin ba wani d’awainiya ne akaina sosai ba, ke kuwa nasan dole su Hafeeza zasu nemeki.” Murmushi Aunty Dijat din tayi kawai, saboda tasan maganan da Mom'n ta fad’a gaskiya ne. Hakan kuwa akayi kamar yanda Momy tace, ita dince ta zauna awajen Jannart din , yayinda Barrister Kabir, Daddy, da kuma Aunty Dijat suka koma gida. Mom na zaune kuwa har wajajen k’arfe 11 zuwa 12 amma Jannart bata farka daga nannauyan baccin da takeyi ba, wanda kuma hakan ya samo asaline saboda, k’arfin alluran dasu Dr. Sulaiman sukayi mata. *Littafin TUBALI na kuɗine ki biya kafin ki karanta cikin salama special Group 1k ne karamin group 500 kacal kuɗin karantawa ne bawai kuɗin mallakan littafin bane, 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU sai ki turo min shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276 in ba halin turawa ta ac no kuwa ki sayi katin MTN ki copy number's din ki turo min ta WhatsApp* Acan gidansu Rayyern kuwa, gaba d’aya babu wani wanda zaka kalla kace yana cikin farinciki, musamman ma da ayanzun suka ga, Rayyern din ya kwashe sama da awanni bakwai bai farka daga baccin daya daukeshi ba. *11:30 pm* Dai-dai ahankali ya soma bud’e idanunsa da sukayi masa nauyi. Inda yana gama waresu kuwa ya sauk’esu, tarwal akan Abbansa dake zaune agefe, ya k’ura masa ido, da dukkan alama kuma jiran farkawan nasa yake. Idanun nasa ya sake bud’ewa da kyau, cikin kuma dan kuzarin da ya saura masa, ya soma yunkurin tashi zaune. Ganin hakanne kuwa yasa Abba sakin numfashi, tare da cewa. “Alhamdulillah Rayyern ka tashi ko, sannu ya jikin naka? Ya kakeji yanzu?” Idanunsa ya d’an lumshe tare da k’ak’alo murmushin karfin hali, kana murya asanyaye yace. “Alhamdulillah Abba, yanzu banajin komai naji sauki.” Murmushin Jin dadi dukansu sukayi, Yayinda Riyyam da har yanzu yake cikin gidan, ya matso kusa da Rayyern din da sauri. Hannun Rayyern din ya kamo, tare da d’an langwab’ar da kansa gefe, kana cike da soyayya hadi da kulawa yace. “Masha Allah Hamma Rayyern, Naji dadi daka ji sauki, sannu ya jikin naka?” Kansa yad’an jinjinawa Riyyam din, tare da dan gyara zamansa, Ahankali yace. “Da sauki.” “Hamma Rayyern sannu ya jikin naka?.” Cewar Ramadan daya taso ya matso kusa da Hamman nasa. Kai Rayyern din ya jinjina alaman da sauki, dai-dai lokacinne kuma idanunsa suka sauka akan agogo. Ganin lokaci ne kuma yasashi dan fiddo idanunsa, tare da Kallon Abba da Mamynsa cikin marairaice fuska yace. “Abba 11:30 pm, narasa sallan magriba, da Isha, Ayyah Abba mai yasa baka tasheni ba.” Kai Abban ya girgiza tare da cewa. “Tayaya zan tasheka Rayyern? Ai rashin lafiya ya kauda komai, yanzu ba gashi ka tashi ba, kuma Alhamdulillah ciwon naka da sauki, sai kaje ka rama sallolin da ake binka, tun kafun 12 am ya cika. Kansa ya jinjina alaman “To.” Inda Kaitsaye Ramadan ya wuce sama ya had’a masa ruwan wanka acikin bathtub. Da taimakon Ramadan din kuma ya haura sama yayi wanka. Koda ya fito daga wankan, wani brown din jallabiya ya saka, tare da shumfud’a sallaya ya tada sallah. 30mn kuwa cas ya dauka yana sallan, bayan ya gama biyan duka sallolin nasa ne kuma ya sauk’o k’asa. Inda har yanzu suna zaune a falon. Gefen Abbansa ya zauna ya d’an kallon mamynsa dake cewa. “Sam Rayyern, baka kula da kanka saboda kwata kwata bakacin abinci, d’azu ma haka kafita bakasa komai acikinka ba sai kayan zak’i.” Kaitsaye kitchine Mamyn ta wuce, batare kuma da taji ta cewarsa ba, ta hado masa ferfesun kaza, da kuma gasashshen kifi, hadi da ruwan tea mai kauri. Ganin kuma yanda iyayen nasa suka sakashi agaba ne yasa shi dagewa yaci, duk da cewar bayajin dadin bakinsa, amma haka yaci sosai. Koda ya kammala cin abincin sama ya haura, saboda still wani sabon bacci yakeji a idanunsa. Haurawansa sama dinne kuma yasa, Riyyam-nsra mik’ewa tsaye. Cikin alamun bacci da kuma gajiya yace. “Abba Mamy Yah Ramadan ni zan tafi, dama na zaunane kawai saboda inason naga tashin Hamma Rayyern.” Kai Ramadan ya dago tare da Kallon Riyyam din, Cikin nuna damuwarsa ga Riyyam din kuma yace. “Gaskiya ba zaka tafi yanzu ba Riyyam, ka ko san k’arfe nawa? Yau kam dai ka kwana anan kabari gobe da safe Idan mukayi breakfast saika tafi.” “K’warai kuwa Riyyam dare yayi yanzu shabiyu fa, Ina zaka samu abun hawa ma, ka kwana anan kawai, yanzu ai duk munzama daya” Cewar Mamy da ta cab’i zancen. Abba dake zaune, kuwa baice musu komai ba. Ganin hakanne kuma yasa Ramadan kama hannun Riyyam din suka haura sama. Koda suka isa saman direct dakin Ramadan din suka nufa *Mainasara hospital* Abba ne da Aunty Dijat suka turo kofar d’akin da Jannart take, a nitse suka kutsa kai ciki. Dai-dai lokacin kuma Jannart ta ɗan fara motsa kwayar idanunta. Wanda kuma ganin hakan yasa dukansu cikin sauri suka k’arasa shigowa cikin dakin. Barrister Kabir da farin cikinsa ya kasa buya ne yace. “Alhamdulillah Masha Allah Jannart ta farfad’o, Alhamdulillah.” Jannart kuwa jin sautin Abban nata acikin kunnuwanta ne, yasaka ta kara Ware idanunta tare da yunkura ta tashi zaune. Kallon Abban nata tayi tare kuma da sakin sassayan ajiyan zuciya mai cike da burbushi kuka, kana Ahankali tace. “Abbana.” “Na’am Jannart ya jikinki? Ina da Ina keyi miki ciwo?.” Abba Kabir din ya amsa mata yana me shafa kanta. “Babu inda yakemin ciwo Abba saidai banajin karfi ajikina.” Jannart din ta fada tana me Zuro kafafunta k’asa. Dai-dai wannan lokacinne kuma Daddy ya turo kofar dakin ya shigo. Yana Ganin Jannart din azaune ya saki murmushi, tare da karasowa cikin dakin, kaitsaye wajen Jannart din ya nufo, cikin nuna so da kauna hadi da tsantsar kulawa yace. “Allah abun godiya Jannart ya jikin naki?.” Murmushi Jannart din tayi tare da langwabar dakai cikin sanyi tace. “Daddy jikina da sauki sosai.” Kanta Daddyn ya ci gaba da shafawa, cikin kuma muryar dake bayyana rararrashi yace. “Kiyi hakuri kinji Jannart, kwata-kwata bansan me yake damun Yayanki Junaid ba, Sam Junaid baida wadataccen hankali, duk lokacin daya shawo giyarsa akanki yake huce duk wani haushinsa, bansan ya zanyi dashi ba Jannart, amma na d’auki samunsa amatsayin k’addarata wacce bazan taba iya sauya taba.” Ya kare maganar yana mai matsan k’walla daga cikin idanunsa. Wanda hakanne kuma yasa Jannart girgiza masa, Kai kana cikin sanyi tace. “Karkayi kuka Daddy kaifa mahaifinmu ne, kuma zubda hawayenka asanadiyar Yah Junaid ba karamin masifa zai haifar masa ba.” Shiru gaba daya dakin ya dauka, inda hakanne kuma yasa Momy zubawa Jannart din abinci. Saidai kuma bataci abincin ba saida taje tayi brush tare dayin wanka kana ta kimtsa kanta da kayan da Aunty Dijat ta kawo mata wanda harda pand. Anan cikin toilet din dake cikin dakin ta gama kimtsawanta. Bayan ta fito ne kuma ta zauna taci abincin, Duk da cewar batajin dadin bakinta kuma haka ta daure taci sabida yadda iyayen nata suka matsanta. Kafun ta gama cin abincinne kuma Momy, tayi shirin komawa gida, acewarta zata je ta dawo. To shima dai Daddyn kasancewar ba jimawa zaiyi bane yasa Mom'n na tafiya shima ya tafi ba jimawa, acewarsa akawai wani aiki da zaiyi. Hakan yasa dakin ya rage daga Jannart sai Abba Kabir da Aunty Dijat da kuma Hafeeza. Wanda Hafeezan ne kuma ta kamo hannun Dijat, tare da cewa “Momy taso muje kiga waje.” Yadda take tajan hannun tane tana d’aga sautin cewa su fitane yasa Dijat din ta mike kasancewar tasan ba'a son cika hayaniya kan mara lfy. Koda suka fito harabar wajen kuwa, akan wani kekkyawan kujeran silver Dijat din ta zauna. Ko mintuna 3 ba ayiba da fitar tasuba. Barrister Kabir ya gyara zamanshi tare da jawo kujerar da yake kai ya ƙara matsowa kusa da Janbart Zama yayi agefen Jannart din. Wanda hakan yasa ta d’ago Idanunta dake cike tab da hawaye ta kalleshi. Kai ya fara jujjuya mata yana mai jin rauni. Gaba daya fuskarta ne ya sauya, Yayinda rauni da kuma matsanancin damuwa ya bayyana akan fuskarta. Cikin kuna da kuma ciwon da takeji acikin zuciyarta ta ɗan gyara konciyar da tayi murya a sanyaye tace. “Abba”. Cikin tarin kulawa yace. “Na'am Jannart”. Ɗan yunƙurowa tayi ta ɗan tashi ta jingina da jikin gini. Murya can ƙasa hawaye na kwaranya tace. “Abba Yah Junaid ya tsaneni. Yah Junaid shine babban matsalata aduniya, Yah Junaid baya k’aunata Koda kad’an, Abba sai yaushe ne nima zan zama y’a kamar kowa? Sai yaushe ne zan samu ingantaccen farinciki? Sai yaushe zuciyata zata huta da kuncin rayuwa? Yaushe Daddy zai fara daukan mataki akan abubuwan da Yah Junaid keyi min Abba ka rabani da gidan Daddy mana dan Allah ka medani gidanka...” Dan tsagaitawa da maganan tayi tare da dafe saitin kirjinta dakeyi mata zafi. Cikin kuma muryar kuka tace. “Abba zuciyata tana gab da bugawa, matukar rayuwata taci gaba da tafiya ahaka,Abba mutuwa zanyi, Domin wata kilan hakan shine zai zamo silar farincikina.” Saurin rufe mata baki Barrister Kabir yayi, cikin kuma muryar dake bayyana tsananin takaicinsa da tausayawa da son fara fahimtar da ita wani abun da bata saniba sabida fara shirin kawo mata sauyi a rayuwarta yace. “Bazaki tabbata ahaka ba Jannart Insha Allah haske yana nan zuwa, sannan ki rabu da maganan Junaid dana Daddynki. Domin kuwa Dadynki *HANKAKA NE*...!!!” Littafin TUBALI na kuɗine ki biya kafin ki karanta cikin salama special Group 1k ne karamin group 500 kacal 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU sai ki turo min shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276. *GARKUWAR taku ce dai MA'AURATA, da masu shirin aure, da masu jego, da yan gayu masu son k’amshi kece raini, da gyaran da zaike maimaita muku dararen forkon kuruciya* Ko kunsan Jikinmu na da sinadaran hormones da suke taimakawa dan’adam akan komai musamman lokacin da mace take mu’amalar aure da mijinta. Mafi akasari wannan hormones din ne ke samun matsala ko su yi sanyi koma su daina aiki kwata-kwata shi ne dalilin da zai sa mace tace bata jin sha’awa ko bata san dadin aure ba. Albishirinku ina da kayan da ke taimakawa wannan sinadaran du dawo aiki tukuru don karkato miki da kimarki wajan mai gida sannan su taimakawa wannan sinadaran hormones dinki su dinka secreting din ni’ima wadatacciya da zata taimaka miki ki gamsu mijinki ya gamsu fiye da tunaninki. Note: Kayana ba sa tsinka ruwan ni’ima suna dai taimakawa hormones dinki ne su tsattsafo da ni’imar musamman wacca cutar sanyi ko dattin mahaifa ya dankarar da su ya hana su yin aikinsu yanda ya kamata. Haka zalika idan kina da kyau ki kara da wanka. Zaki iya amfani da magani na na gargajiya wanda zai gyara miki sex hormones din kullum ki kasance cikin humidify wato cikin damshi mai albarka kamar yanda ake son mace. Yana gyara miki mara. Sai kamshi. Hajiyata daure ki fara amfani da turarena ki ji irin salon kamshin sa salo ne da zai daidaita ki da mijinki ya kankaro miki da kimarki a wajansa. Siyan na gari mayar da kudi gida. Ga masu buƙata ga number' wayata wanda nake whatsApp dashi 09097853276 kimin mgn ta whatsApp in har kin tabbatar kin shirya saya mu dai-dai ta, kayana ba ƙanana bane, shiyasa bana harkan karanta, muddin kinsan baki shirya sayaba Please kada kiyi min mgn ki bari sai kin shirya kuɗinki a hannu, ba ina nufin kayana bana talaka bane, no akwai ƙananan set na masu karamin karfi, banson aimin mgn a ɓatamin lokacin aiyukana a shirme baki shiryaba. Shine karantan da bana so. 0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU. In kin shirya ga number ta ga kuma account number ta wanda in mun gama mgn zaki turo kudin ki, kana insa miki kaya a mota, duk ƙasar da kike kayana zaije gareki, amman fa in kinada dalilin zuwan nasune🤝🏻sayan na gari meda kudi gida. GARKUWAR MA'AURATA By *GARKUWAR FULANI* 11/15/21, 7:21 PM - Auntyna: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *TUBALI* PAGE 18 NA *AYSHA ALIYU GARKUWA* *WANNAN PAGE D’IN SHINE K’ARSHEN FREE PAGE, DAGASHI BABU WANI FREE PAGE IN KIN GANSHI A WOJEMA TO SATA PAGE NE daga wannan PAGE 18 na gama free PAGE, dan sonku da Allah da Manzonsa kada ku fitarmin da littafina 1k ko 500 da kika bada bawai yana nufin kin biya kin mallakeshi bane kuɗin karantawa ne, dan Allah nace ba don niba, in Zaki saya ga ac no 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU sai ki turo min shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276, in baki da damar tura ta account ki sayi katin MTN ki copy number's din ki turo minshi ta WhatsApp 09097853276.* _Masu karanta Audio books kuyiwa girman Allah ku kiyaye min littafina domin zama lafiya yafi zama ɗan sarki, ga number birjik a pages idan ki/kana so ki/kayi min mgn mu dai-dai ta masu posting a wasu shafukan kuyi girman Allah ku barmin books na, 09097853276_ Shiru Jannart tayi tare da zuba mishi idanu, tana mai nanata kalmar daya suffanta Daddy'nta dashi. “Hankaka!!!?”. Ta faɗa can ƙasan zuciyarta tana mai son nazartar ma'ana da tushen kalmar a hausan ce. Gyara zama Abba yayi tare da fuskantar ta da kyau cikin tsananin kulawa, tausayi ƙauna, jinƙai. Murya a sanyaye yaci gaba da cewa. “Bazaki fahimta ba Jannart kada ki tsauwalawa kanki tafiya nazari ko tunanin sarƙaƙiyar dake cikin rayuwarki. Bazaki ganeba sai an ganar dake, ina cikin matuƙar damuwa mai tarin yawa. Na yadda zan samu in zama GARKUWAR ki, ina tunanin kamar yarda da kikayi min tana da rauni bazan samu amincin da nake buƙata daga garekiba. Na amsar umarni na sawa ko hanawa!!!”. Hawayen dake kwaranya bisa fuskarta tasa hannun ta ta share kana a take wasu suka kwaranyo. Hakan kuma baya rasa nasaba ne da yadda taga idanun ƙanin mahaifin nata yana kwaranyo da hawaye. Tana hango tsananin tausayinta cikin kwayar idanunshi. Numfashi ta fesar a hankali tare da danne shessheƙan kukan dake son kumbce mata cikin aminci da dukkan yarda da yaƙini murya na rawa tace. “Abba kana da ƙarfin iko a kaina. Ni ɗiyace a gareka, kuma zan zamo mai biyayya akan dukkan umarninka, zan kuma nitsu in fahimci abun da kakeso in fahimta bani da wani katanga jigo majingini sai kai, Abba inada kekkyawan yaƙini kaine TUBALIN farin cikina”. Wani zazzafan numfashi Barrister Kabir ya fesar kana ya ƙara jawo kujerar ta matso kusa da ita, cikin sanyi ya kama tafin hannunta murya can ƙasa yace. "Yadda na riƙe hannunki haka. Ana haifoki mahaifiyarki ta damƙa min amanarki. Tana mai jaddada min cewa in zama Garkuwanki inyi miki zaɓi mijin na gari wanda naga ya dace dake, in gaya miki ke marainiyace tace in faɗawa duk wanda zan bawa aureki cewa ke marainiyace dan ya duba maraicinki.” Ina shessheƙan kuka wanda yake tafe da zazzafan tsohon dafi mai ciwo a zuciyarsa ya danne mgnar. Itama kukan ta farayi. Wanda Har Aunty Dijat dake woje ta fara jiyo sautinsu. Cikin tsananin rauni ya kalleta murya na rawa yace. “Jannart in nayi miki zaɓi da miji kamar yadda mahaifiyarki ta roƙa, zaki amince dashi, zaki yarda da duk tsarin da zan zo miki dashi dan mu cika fatan mahaifiyarki!!! In Kuma samar miki ƴanci!?”. Cikin kukan ta gyaɗa mishi kai. Hannunshi yasa ya sharce hawayen sa kana ya tsareta da ido tare da cewa. “Zaki iya amincewa in ɓoyeki, in bada ajiyarki a killataccen wurin da zaki tsira da ranki da lfyarki tun kafin wa'adin da suka tsara a kanki ya cika”. Zuwa yanzu kanta ya ƙara ɗaurewa, duk da ta saba jin waɗannan zantukan a bakin ƙanin mahaifin nata, amman har yau ta gaza samar musu muhallin ajiyewa. Cikin rashin fahimta tace. “Abba na amince”. Kai ya gyaɗa kana yayi ƙasa da murya yace. “Har Daddynki fa zaki bari bazaki kuma sanar mishi komaiba, bazai san inda kikeba”. Hannu tasa ta dafe ƙirjinta tare da zaro ido kana tace. “Abba in na dawo Yah Junaid zai kasheni, kuma Daddy na zai shiga tashin hankali!”. Numfashi ya fesar kana a hankali yace. “Lokacin da zaki dawo, zaki dawo da encinki mai ƙarfi, Junaid ko farcenki bazai taɓa ba, Daddy kuwa kunya zata makantar da idanunshi sabida ya gaza zama uba kuma Garkuwa a kanki. Sai dai hakan bazai faruba sai da amincewarki da sahalewarki. Kuma sai haka ta faru zaki gane kurman baƙin dake cikin rayuwarki. Shin kin amince!!!?”. Cikin zulimi tace. “Abba har na tsawon wani lokacin zaka ɓoyeni? Kuma ina zaka ɓoyenin?”. Da sauri yace. “Bana tantance lokacin ba, amman zan ƙiyasta wata takwas zuwa shekara ɗaya. Sannan inda zan ɓoye ki kuma shine ban gama tantancewa ba, amman ki aminta dani GARKUWA zan nema miki”. Ajiyan zuciya mai nauyi ta sauƙe kana a hankali tace. “Abba na aminta da kai nasan baza cutar dani ba”. Da sauri yace. “Toh ki adana wannan mgnar amanace tsakaninmu kada ki gayawa kowa, duk faɗin duniyar nan. Nan kusa kuma zan samu wurin adanaki mai inƙanci”. Cikin sauƙe numfashi tace. “Toh Abba”. Shigowar Aunty Dijat ce yasa suka katse zancen. *Wannan shine PAGE na karshe a FREE PAGE in ki. Kuma ganin ci gabama to na satane baiwar Allah in kinaso ki saya, in bazaki iyaba babu dole ga littatafai da dama na kyauta, special Group 1 karamin group 500 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU* A nan gidan nasu kuwa. Mom na komawa ta shiga Kitchen aikin ta farayi yayinda Abdul ke gefenta yana tayata kana yana mgna, da Yah Azeez ɗinshi wanda. Kwanan ya koma Macsow kasan cewar acan yake aiki. “A jikin da sauƙin Yah Azeez yanzuma Mom ta dawo anjima in munje zan haɗaku a waya”. Abdul ya bawa Azeez amsa. Cikin tausayawa Azeez yace. "Toh shi kuma wawan ina yake”. Mom ce ta ɗan ja tsaki tare da cewa. “Yoh waya sani tun jiya da abin ya faru daya fita bai dawo ba”. Kwaffa yayi tare da cewa. “Allah zai saka mata”. Daga nan dai sukaci gaba da mgnar suna aikinsu. Saida suka gama aikin ta shiga Bathroom Dan yin wonka. _Dan Allah daga wannan PAGE din kada a fidda wani_ A can Gidansu Dr Rayyern Mai-nasara kuwa kasan cewar yau jumma'a. Basu dawo masallaci da wuriba, Sai kusan ƙarfe takwas suka shigo A jere da ma'aikatan gidan baki ɗayansu. Yayinda suka gaggaisawa suna tambayar jikin Rayyern. A hankali ya kalli Baba Mauɗo tare da cewa. "Alhamdulillah Baba Mauɗo na saumu sauƙi banjin komai sai baccin da nake ji bai isheni ba”. Cikin jin daɗi Baba Mauɗo yace. "Alhamdulillah Allah ya ƙara mana lfy”. Amin Amin sukace baki ɗayansu. Abba ne ya ɗan kalli Ramadan dake cewa. “Eh kasan mgnin ne zai ɗan saka jin bacci”. Kai suka gyaɗa alamun gamsuwa. Dai-dai lokacin da suka shiga falon ne Riyyam-nsra ya lumshe idonshi sabuda sabida ƙamshin masar da Mamy ke toyawa wanda duk ranar jumma'a take yinshi bisa umarnin Rayyern za'a cika manya-manyan kuloli kana ta dama kunun gyaɗa suna kaiwa tsangayar al'majirai”. Da sauri ya nufi Kitchen din yana cewa. “Mamy Barka da safiya”. Murmushi tayi tare da sauƙe kaskon tuyan dan tun ƙarfe huɗu take farawa in lokacin salla yayi sai taje tayi kana tazo taci gaba. So yanzu ta gama. “Barka dai Riyyam-nsra kun dawo ko”. Kai ya gyaɗa mata yana kallon tukunyar ferfesun data sauƙe. Shaƙan zazzafan ƙamshi yayi tare da cewa. "Wow special Mamy girkinki da daɗi”. Juyowa tayi ta da sauri jin ƙamshin turaren Rayyern. Ƙarasowa yayi cikin Kitchen din. Gefenta ya ɗan tsaya, tare da buɗe manyan kulolin. Ita kuwa foodflask ɗin da ta zuba musu breakfast ɗinsu a ciki ta nunawa Riyyam-nsra tare da cewa. “Kai manasu Dinning”. Da sauri yace to kana ya ɗauka ya fita. Juyowa tayi ta kalleshi tare da cewa. “Rayyern ya jikin naka?”. Kai ya jinjina tare da cewa. “Na worke”. Cikin jin daɗi tace. “Alhamdulillah, Allah ya ƙara mana lfy”. Amin Amin suka amsa shida Riyyam-nsra. Ramadan kuwa da Abba suna can falo, da alamu mgnar aure Ramadan keyiwa Abba duk ya marairaice. Cikin haɗe fuska Abba yace. "Kai da Allah tafi daga nan, Yayanka ma baiyi aureba sai kai ai dole dai ka jira sai yayi ko”. Fuska ya kwaɓe tare da longobar da kai kana cikin girmamawa yace. “Toh Abba”. Yana faɗin hakan kuma ya miƙe ya nufi Kitchen ɗin. Da ido ya bishi yana mai jin zafin tsawar daya daka mishin a ransa Allah ya sani baya son yin abinda zai b’atawa yaranshi rai more especially Rayyern. ```Special people group 1k ne karamin group kuma 500 BABBANCINSU a yawan posting ne``` Rayyern kuwa dake gefen Mamy cikin nitsuwa yace. “Mamy kada Ramadan ya kai masar tsangayar malam Babayo. Ya bari yau tsanƙayar Malam Mai-nasara zan kaishi, in Abba ya amince”. Juyowa tayi ta ɗan kalleshi tare da cewa. “Toh Allah yasa ya amincen”. Amin yace yana mai bin bayanta suka fito. A Dinning area Suka haɗu da Ramadan da yayi fuskar tausayi, Ɗan zuba mishi ido yayi kana ya kauda kanshi ya nufi tsakiyar falon. Mamy kuwa gefen Ramadan da Riyyam-nsra da suka zauna bisa Dinning table tayi kana ta kalli Riyyam-nsra tare da cewa. “Baka kaiwa su Baba Mauɗo nasuba”. Da sauri Riyyam-nsra ya miƙe tare da cewa. “Toh”. Kana ya ɗauko kulolin da plate cups and spoons. Ya wuce. Shi kuwa Rayyern a nitse ya zauna gefen Abban nasa, cikin sanyi yace. “Abba”. Numfashi ya ɗan fesar kana yace. “Na'am Rayyern, ya akayi”. Yayi mgnar cikin tsananin kulawa. Cikin yanayin neman al'farma yace. “Abba sadakan nane nace, dan Allah yau ka amince mu kaishi tsangayar Mai-nasara”. Ga mmkinsa sai yaji Abba yace. “Toh Allah ya bada ladan”. Cike da mmki yake kallonsa yana kuma muƙewa, Numfashi ya fesar fahimtar Abba yana cikin zurfin tunanine shiyasa ya amsa a sauƙaƙe. Hakan yasa da sauri ya dawo Dinning area. Cikin bada umarni ya kalli Ramadan da Riyyam-nsra da ya shigo yanzu yace. “Yauwa taso maza ku ɗauki womas ɗinan ku kai min cikin mota”. To sukace kana suka fara ɗauƙa. Shi kuwa da sauri ya haura sama ya ɗauko car key ɗin nasa. Koda ya sauƙo a hankali yace. “Toh Abba na tafi”. “Sai ka dawo”. Ya bashi amsa da alamun har yanzu yana cikin nazari ne. Yana fita su Ramadan na fita da kulolin ƙarshe. Riyyam-nsra ne ya buɗe mishi gate ya fita. Kana ya rufe sannan suka dawo cikin gida. Bayan duk sun zauna kan table. Mamy ta kalli Ramadan tare da cewa. "Kira Abbanku”. To yace kana ya miƙe ya sauƙo steps ukun tare da cewa. “Abba breakfast is ready”. Wani dogon numfashi mai nauyi yaja ya sauƙe a hankali kana yace. “Toh”. Sannan yazo saida ya zauna ya kallesu cikin kulawa yace. “Rayyern fa!?”. Cikin nitsuwa Riyyam-nsra yace. “Abba ba yanzu ya fita kai abincin al'majirai ba”. Kai ya jinjinawa Riyyam-nsra. Ita kuwa Mamy cikin fahimtar halin da yake ciki ta zuzzuba musu breakfast ɗin kana suka fara ci. Mai-nasara Hospital. Suna cikin hirar Jannart ta ɗan gyara konciyarta tare da lumshe idonta lokaci ɗaya bacci yayi awon gaba da ita. Hakanne yasa Abba koma gida. Aka bar Aunty Dijat. Abba na tafiya ba dadewa Mom da Abdul suka iso. Kasan cewar tana baccine yasa suka koma gefe suka zauna suna ɗan taɓa hira sama-sama gudun kada su tasheta. Yayinda Abdul yake riƙe da wayarta. Yana mgna da Salman. Nan ya gaya mishi suna asibiti. Koda Dr Sulaiman yazo ya dubata. Ganin tana bacci ya shaida musu jikin da sauƙi sosai. Shi kuwa Dr Rayyern Mai-nasara. A hankali yayi parking a gaban tsangayar malam Mai-nasara. Kana ya fito, Cike da Mamiki Uncle Mustapha da shima yanzu ya iso da abincin al'majirai da yake kawowa daga gidansan. Dan al'majiran malam Mai-nasara basa yin Bara shi da yaransa suke ciyar dasu. Da sauri ya nufi Dr Rayyern cike da mamaki yake cewa. “Ikon Allah wa nake gani kamar Dr Rayyern Mai-nasara?”. Da sauri ya juyo suka fuskanci juna, musabiha sukayi cikin jin daɗi yace. “Ya Malam da jiki?”. Cikin jin daɗi yace. “Masha Allah mu isa ciki, malam na nan jiki yayi lfy sosai fa!.” Ya ƙare mgnar yana miƙawa wani Gardi key ɗin motarsa tare da cewa. “Yauwa Yayana gashi fito muku da abincinku”. Da sauri Dr Rayyern Mai-nasara shima ya miƙa masa key ɗin motarsa tare da cewa. “Ga wannan ma ka duba baya ka fito muku da abincin”. Cikin jin daɗi Wanda Uncle Mustapha ya kira da yaya ya amshi key ɗin. Tare dayi musu godiya. Shi kuwa Uncle Mustapha jagora yayiwa Dr Rayyern Mai-nasara, har cikin gidan Malam Mai-nasara. Kana suka nufi wannan falon. Yana mai cewa. "Duk ranar jumma'a Malam bai fiye amsar baƙiba, amman nasan kai na musamman ne, mu shiga”. Ɗan guntun Murmushin yayi kana suka kutsa kai tare da sallama a baki. Can Dr Rayyern Mai-nasara ya hango Malam Mai-nasara, zaune tsakiyar falon. Yayinda wata kekkyawar tsohuwa ke gefenshi, da alamun abin karin kumallo take zuba mishi. Ganin Dr Rayyern Mai-nasara ne yasa Malam yunƙurawa ya tashi zaune. Cikin yalwataccen murmushi ya miƙo mishi hannu tare da cewa. “Masha Allah. Wa nake gani kamar Dactana mai Nasara”. Hannunshi ya miƙa mishi ya jawoshi ya zaunar dashi kusa dashi. Yayinda ya kalli Uncle Mustapha dake cewa. “Ai kuwa shine dai Malam”. Hannunshi ya ɗaura tsakiyar kan Dr Rayyern Mai-nasara tare da cewa. “Lallai.kuwa yau ka amsa sunanka Mai-nasara dunda kayi nasarar ganina da safiyar jumma'a.” Cikin son dattijon yace. "Alhamdulillah Nasara ta haɗu da nasara kenan”. Murmushi sukayi baki ɗayansu. Yayinda tsohuwar nan kuma ta zuba mishi ido tana mai mishi wani irin kallo. Kai ya juyo ya kalleta tare da cewa. “Barka da safiya”. Gyara zamanta tayi tare da sauƙe numfashi kana cikin kulawa tace. “Barka dai Mai-sa'a. Yau dai da Malam zakayi karin kumallo”. “Sosai ma kuwa”. Malam Mai-nasara yace yana mai gyara zamanshi. Ita kuwa tsohuwar kekkyawan akoshin dake tururin danderun naman ragon ne, ta turo tsakiyarsu. Kana ta jawo ɗayan kuma tuƙeƙen tuwon alkmana ne mai kyau. Da miya a kanshi miyar ɗanyar kuɓewa mai kyau tana ƙamshin man shanu, da ƙamshin ɗumamen. Sai kuma bread mai kyau na masu ciwon sugar sai flask. Da cups biyu. Misa alamu dai da basu zoba da tare zasuci abinci da tsohuwar. Kai Rayyern ya ɗan jinjina tare da cewa. “Alhamdulillah fa malam kaci kawai”. Cikin kula Malam yace. “Ina muci dai, ai dole kaci, tunda ba giya bace, ko kyamar tsoho kakeyi ne?”. Da sauri ya jujjuya kanshi alamun a a. Ita kuwa tsohuwar nan ɗan ƙaramin kwaryar dake gabanta da ruwa a ciki ta tura masa tare da cewa. “Toh wonke hannunka kuci”. Abu kamar wasafa dole suka matsa mishi. Allah ya sani yana son tsohon haka yasa ya ɗan gyara zamanshi, cikin nitsuwa yace. "To a bani tea”. Da sauri ta haɗa mishi tea. tare da amsar akoshin danderun da Malam ke miƙo mishi. Dole yasa hannunshi cikin kwaryar ya wonke. Kana ya gyara zamanshi tare da kallon Malam yace. “Malam ya jikin naka kuma?”. Loman tuwon daya sa a baki ya haɗiye kana yace. “Alhamdulillah Rayyanu naji sauƙin jikina sosai sai yawan ci”. Juyowa yayi ya kalli Uncle Mustapha dake cewa. “Dan Allah Dacta kaci girkin Innayinmu, zaka jishi da banne dana sauran matan duniya”. Ya ƙare mgnar yana miƙewa tsaye. Yayinda ita kuwa Innayi tayi murmushi tare da cewa. “Kwarai kuwa har matarsa ma”. Murmushi yayi tare da cewa. “Toh ki bari a yaba miki mana”. Dariya sukayi duka. Kana su suka fita. Ya rage dagashi sai Malam Mai-nasara. Wanda ya maida hankali kan cin abinci. Shi kuwa tea ɗin ya ɗan zuƙa a hankali. Idanunsa ya lumshe tare da buɗe su. Tabbas Mamynshi ƙarshece a girki amman daga shayin tsohuwar nan yaji da ban. A hankali ya ɗago kanshi ya kalli Malam dake cewa. “Dan Allah Rayyanu kaci naman nan zakaji dadinshi”. Kai ya jinjina kana yasa hannunshi cikin akoshin. A nitse ya ɗan yagi tattausan tsokar kana ya kai bakinshi. Wani irin tsinkewa yaji yawunsa yayi tare da amsar saƙon ɗanɗanon naman nan mai cike da ƙamshi. “Ya Salam”. shine abinda ya faɗa a zuciyarshi. Tea ya kurɓa kana ya ɗan kalli Malam cikin hikima yace. “Ni ko Malam sunan kakanka ne Mai-nasaran ko?”. Kai malam ya jujjuya mishi alamun a'a. Cikin jin daɗi ya gyara zamanshi tare da ɗan ture akoshin gefe. Sosai naman ya mishi daɗi to amman matsalar bazai iya cin abincin nama da sassafe hakaba. In yasha tea ɗin kawai ya gamsu sai irin 11-12 haka zai iya cin wani abu kuma. “Kaci mana”. Malam yace. Kai ya gyaɗa kana ya kafe kofin a baki ya zuƙe team ɗin kana ya ajiyeshu gefe, tare da cewa. “Toh Alhamdulillah na ƙoshi”. Murmushi kawai malam yayi tare da wonke hannunshi. Shi kuwa a hankali yace. “Toh Malam menene Tubalin sunan naka”. Toro mishi kwaryar malam yayi tare da yin dariya sosai. Hannunshi yasa yana wonkewa yana kuma kallon tsohon yana murmushi ganin yadda yake dari. Cikin tsagaita dariyar Malam yace. “Lallai kam ka nemi jin tsohon lbri”. Sai kuma ya ɗan kishingiɗa. Da sauri Dr Rayyern Mai-nasara yace. “A'a Malam tashi zaune, ba'ason mutun ya kwanta bayan cin abinci a take, anfi son ka ɗan zauna koma motsa jiki, ko ga masu lfy kwanciya da zaran an gama cin abinci yana haifar da cutar sugar.” Da sauri Malam yace to kana ya zauna tare da cewa. “Tubalin sunana ya samo asaline tun ina yaro ɗan shekaru tara a duniya, da aka kaini al'majiranci. Anan na samu sunan Mai-nasara nawane na kaina bana Babana bane ko kakana”. Sai kuma ya ɗanyi shiru ganin hakane yasa Dr Rayyern cewa. “Tah yaya aka sama sunan?”. Numfashi ya ɗan fidda kana yace. “Asalina ɗan jihar Adamawa state ne, yankin Jada al'majiranci iyayena suka kawoni jihar Kano. Nazo kano bani da kowa sai Allah sai malamina, wanda a ƙalla yakeda ɗalibai sun kai ɗari biyu,200 baya shayar damu bare ci damu. Mafi akasari ranaku ɗalibai kaso 100 cikin 200 da yunwa suke kwana da wuni. Wasu kan shiga gidaje 7 ba'a kirasu ba, cikin ikon Allah ni kuma duk gidan dana shiga sai an kirani kuma sai an bani abinci. Haka yasa abincin da nake samu yafi ƙarfin cikina, sai nake rabawa yara kamata. Yayinda wasu manyan ma ke zuwa suna roƙata inje musu Bara, duk wanda ya bani akoshinsa sai na cika mai nake dawowa. Toh fa daga nan ɗalibai suka samin Mai-nasara. Cikin ikon Allah kuma nasarar ta bini. Nayi karatu na tsawon shekaru goma sha biyu na haddaci al'ƙur'ani mai girma da tarin littattafai. Daga nan kano ta zamemin uwa goya marayu, malam ya bani yarsa itace wannan data tafi yanzu na aura. Kana na fara kasuwanci Allah cikin ikonsa ya samin al'barka a harkar kasuwanci na. Na ƙara mata biyu ƙannena suka dawo gareni da iyayena. Allah ya azutani da yara sama da 37. Kaga ai nasara ta yiwu, duk da bayan nasarar na fuskanci ƙalubale akan d’a mafi soyuwa a gareni”. Cikin gamsuwa Dr Rayyern Mai-nasara yace. “Allah sarki”. Da sauri ya katse shi da cewa. “Kai kuma menene TUBALIn sunan naka”. Murmushi yayi tare da cewa. “Nima ɗalibai ƴan uwanane suka samin shi. Sabida duk jarranawar da zanyi bana faɗunwa. Kuma duk abinda nasa gaba sai na cimmasa”. Shigowar Uncle Mustapha ne yasa suka tsagaita da hirar, kana akaci gaba da hirar dashi. Har sai tara dai-dai suka sallami Malam suka tafi A bakin gate suka samu wannan gardin ya basu keys ɗin su suka tafi. Daga nan kai tsaye gida ya koma. ~0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU sai ki turo min shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276 special Group 1k karami kuma 500~ A can MAI-NASARA Hospital kuwa. Ma'aikatan Arewa 24 TV ne, kusan su shida ke cikin ɗakin da Jannart ke konce. A hankali ta kalli Aisha Lawal dake ta gyara mata gashin kanta dake kan kafaɗunta. Salman ta ɗan kalla cikin nitsuwa tace. “Yah kiraka kuwa?”. Cikin yanayin tausayawa yace. “Keda baki da lfy me ruwanki da kiran wani”. Hajia Rabi'ah ce ta ɗan yi murmushi tare da cewa. “Yoh keda ma gaki a asibitinsa”. Aunty Fauziyya D Sulaiman kuwa cikin kula da nagarta ta ɗan shafa goshinta tare da cewa. “Ai dukkan uzuri bayan lfy yake, kada ki damu kinjiko Jannart MD da kansa yace a gaidaki da jiki”. Cikin jin daɗi ta kalli Fauziyya D Sulaiman tare da cewa. “Ngd matuƙa My Aunty”. Mom kam dake gefe sai godiya takeyi musu. Sun jima anan kana suka ajiye ledodin Fruits da suka kawo mata, Kana suka fita. Har sunje bakin ƙofar fita Salman ya juyo jin tana cewa. “Salman kada ka manta fa saura kwana biyar kacal”. Murmushi yayi tare da cewa. “In dai ina raye to kisa a ranki kinada GARKUWA”. Yana faɗin haka suka fita. Kasan cewar yau jumma'a haji babbar ranace yasa, dukkan Al'ummar musulmai suke cikin yanayi na musamman duk kan maza nata shirin zuwa sallan jumma'a tako ina. Sha biyu da rabi dai-dai haka take a gidansu Dr Rayyern Mai-nasara ma. Yayinda hakama Barrister Kabir kasan cewar duk a Nassarawa G.R.A suke yasa gaba ɗaya masallacin Al'furƙan suke da niyar zuwa. A hankali ya kalli Mamy dake ce mishi. “Toh Rayyern me kake so in dafa maka ne? Ni bana son zamanka da yunwar nan fa”?. Yana mai haurawa saman yace. “Mamy yanzu lokacin jumma'a ya ƙara to, bari inje inyi shirin salla in na dawo zanci abincin”. Da ido kawai ta bishi ganin tuni ma ya haura sama. A hankali ya ɗan juyo ya kalli ƙofar Bedroom din Ramadan jiyo muryarsa shida Riyyam-nsra alamun suma shirin tafiya jumma'a sukeyi. Dan yana jiyo muryar Riyyam-nsra na cewa. "Nima fa mai gare zaka bani in saka Hamma Ramadan”. Kai kawai ya jinjina ya wuce Bedroom ɗinsa. Kai tsaye Bathroom ya wuce. Bayan 15mn ya fito ɗaure da towel. Gaban dreesing mirror'nsa ya nufa cikin yanayin sauri-sauri ya busar da sumar kanshi tare da shafa mai kana ya miƙe ya nufi gaban ƴar ƙaramar Driver'n'shi na glass dake gefen babban durowar. A hankali ya buɗe, ido ya ɗan zubawa ƙananan kayanshi dake kimtse a ciki. Wata tattausan boxer and single ya zaro masu ɗan karen taushi. A hankali ya meda marfin ya rufe, sauri-sauri yasasu kana ya zare towel din ya cilla gefe ganin ɗaya ta kusa cika. Babbar durowar ya buɗe, Wasu kayan ya zaro Getzner fara ƙal mai masifar kyau da sheƙin maiƙo. Riga da wondo. Sauri-sauri ya saka su. Kana ya koma gaban Driver'n'shi na glass din hula damanga ya zaro Royal blue kalan zaren surfanin da akayi wa Getzner aikin rigar. Sunkuyowa ya ɗanyi toms masu masifar kyau samfarin Italy ya zaro suma Royal blue. Kana ya dawo gaban dreesing mirror'nsa. Kafa hular yayi irin kafin nan da matasa ke cewa. Babu ruwanka da duniya. Wato ya ɗan ture hular ta koma baya kaɗan hakan yasa tattausar sumarshi ta fito tana zuba sheƙi sajenshi ya kwanta lib sai sheƙi yake siraran lips dinsa suma suna sheƙin taushi. Sai kuma ya sunkuyo yasa fararen sawunsa cikin takalman. Agogon Daimond dake kan mirror'n ya saka. Turarensa Oud Zauji mai masifar daɗin shaƙa ya fesa. Kana ya zari car key ɗinsa Dan lokacin ya ɗan so ƙure mishi. Da sassarfa ya sauƙo kan steps din har yana takawa bibbiyu. Ba kowa a falon yasa da sauri yasa kai ya fita, ko su Baba Mauɗo duk sun tafi sai Ari. Haka yasa ya buɗe mishi gate kana Suka tafi tare haka nan yake ta jin tsinkewan zuciya da faduwan gaba. Numfashi ya ɗan fesar lokacin daya shiga cikin masalacin sabida har yanzu huduba akeyi. Inda ake hudubar akan illar cin riba. Sosai aka nitsu, bayan an ida hudubar ne kuma aka kabbarta sallan... Bayan sunyi raka'a biyun, an zauna zaman tahita. Sun ida zasuyi sallama sunyi gefen dama sun juyo hagu. Kenan Barrister Kabir ne dake gefen daman Rayyern ɗin ne ya ɗan leƙo fuskar Dr Rayyern bayan ya sallame. Wata iriyar sassayar ajiyar zuciya mai nauyi ya sauƙe tare da ɗaga hannunshi sama ya fara yiwa ubangiji kirari cikin zuciyarsa yana ƙara neman zaɓin Allah kan manufarsa da addu'a in al'khairi ne Allah ya nufeshi da ida nufinsa a wannan lokacin. Yayinda shima Rayyern da mafi akasarin mutane hakan sukeyi. Bayan an idar da salla ne, Dr Rayyern na fita yaji an riƙo hannunsa tare da ce masa. “Assalamu alaikum”. Da sauri ya juyo tare da cewa. “Wa alaikassalam”. Fuskarshi ya ɗan yamutsa alamun tunani kana a hankali yace. “Lfy”. “Lfy lau Alhamdulillah Dakta”. Barrister Kabir ya faɗa yana mai jawo hannun Dr Rayyern ya nufi can kan titi wurin motarsa. Ba tare da ya ƙara mgna ba yabi bayansh. Suna zuwa ya buɗe suka shiga....! Anan asibitin kuwa, da Yamma Dr Sulaiman ya bawa Barrister Kabir takardar sallama, sabida sosai jikin Jannart yayi sauƙin. Ya ƙara da cewa. “Idan an barku kun ƙara kwana tofa sai ranar Monday za'a sallameku. Toh kuma tunda jikin da sauƙi gwara kuje gida zaifi”. Dr Sulaiman yayi mgnar bisa bin umarnin da Dr Rayyern ya kidanya mishi a waya. Cikin jin daɗin samun lafiyar nata Barrister Kabir yace. “Toh Alhamdulillah Dr Sulaiman mun gode matuƙa Allah ya bar zumunci”. Amin Amin yace tare da juyawa ya fita. Su kuwa biyar dai-dai Barrister Kabir ɗin ya ɗauki Jannart da Mom ya nufi gida dasu. Suna kan hanya ne Daddy ya kirasu yazo bai samezu ba. Nan yake ce mishi ai an sallamesu gasu a hanyar gida. Nan dai suka koma gida Barrister Kabir ya bawa Mom magungunan tare da cewa ta kula da Jannart da shan mgnin. Ba tare da yayiwa yayan nasa mgnar Junaid ba ya sallamesu ya tafi. Toh a hankali dai abubuwa ke juyawa suna wakana. Yau Monday kwana biyu kenan da sallamo Jannart Alhamdulillah kuma jiki yayi sauƙi sosai. Junaid kuma har yau bai zo gidaba. Barrister Kabir kuwa duk cikin kwanakin nan bashi da zama yana yawan zirga-zirgan da Aunty Dijat ta gaza gane na menene. Yau Monday misalin biyar na yamma. Dr Rayyern Mai-nasara ne dake zaune a yar barandarsa balcony dake sama can jikin Bedroom ɗin sa. Sanye yake da wasu tattausan riga da wondon iya guiwa rigar kuma irin mara hannun nance. System ɗinshi ne bisa stoll ɗin dake gabansa sai plate da chocolate sai Bootle water a gefenshi. Sosai ya dugufa kan aikin da yakeyi. A hankali ya ɗago kansa cikin tarin gajiya ya juyo ya kalli farfajiyar gidan nasu can bakin gate. Wani irin juyowa yaye tare da tashi tsaye da masifar fargaba ya zubawa fuskar Barr....! *TUBALI na kuɗine ki biya kafin ki karanta cikin salama Da Allah.* *Albishirinku! Ma'aurata, GA GARKUWAR KU nan tafe muku da tsarabobi na musamman gareku ma'aurata daga cibiyar mgnin mata mai taken GARKUWAR MA'AURATA* NI DAI AYSHA ALIYU GARKUWA. Ina matukar mamakin wani irin lokaci da ya riske mu mai wahalallan fassara. Kullum dai magana daya ce, akan ma’aurata, fada, rashin jituwa, mutuwar aure, akan kuskure kalilan, rashin kula, rashin yi wa juna uziri. Toh wai duk me ya janyo hakan? Na zurfafa a tsananin tunani hakan ya tilasta min bincike mai tarin yawa wanda ya kai ni ga gano inda matsalar take? Shin yar’uwa ke macece amma kin san wacece mace ku? Kin san me ake kira mace kuwa? Mace ita ce matar da take zama iyali a wajan namiji ta zame masa bango, sanyin idaniyarsa, ta zame masa gata da farin cikin rayuwarsa ta zame masa ruwa abar kore ƙishinsa ta zame masa mayafi mai karesa daga gigitar kadaice, ta kuma dorar da mijinta kan turbar gaskiya, ta kashe masa jiki da salonta ta rikita shi da baiwa da ni’imar da Allah ya bata idan har ta san hanyar mayar da kanta sabuwa dal awajanta, wato kullun takasance masa tamkar amarya har ya kasa tantance daren amarcinsu da sauran dararen rakun rayuwar su. Wannan ita ce mace. Ina da wata saukakkar hanyar da zaki zama abar so da kulawa da soyayya a wajan mijinki ta hanya mafi sauki, 09097853276 hanyar ita ce ki gwada amfani da kayana na gyara ki gani, ina mai tabbatar miki da in sha Allahu sai kin dara da murna sai kuma kin gode min. Kayana kaya ne da aka yi shi da zallan itacanmu na gado marasa illa a cikin jikin dan adam musamman mace, kaya ne da suke taimakawa (sex hormones 😍) dinki. Misali kina kallon India😘, hollywood, Asian film🥰 kina ganin yanda mazansu ke nunawa matansu tsananin soyayya kamar su ba su kyautar ransu!? Saboda me hakan? Saboda suna sadaukar da lokacinsu wajan gyara jikinsu da kayan da ke tsattsafo da ni’ima cike da tsukewa, kayan nan kuma ana yinsu ne zallar magungunan gargajiya wanda ba su da illa domin haɗine na ingantattun itatuwa da yayansu. Ina baiwar Allahn da miji ke daure mata fuska babu hirar arziki? Zo ki ji yar’uwa zan baki gumbata da zallar gari wanda aka yi su da nagartattun itacen da ke da matukar amfani a jikin mace. Gubar ciko, gumbar tsalle dole, gubar da ba'a baiwa mai kishiya, garin maɗi, garin mallaka, tsumin goron tula, tsumin tsartai, tsumin maratsi, pala-pala butar sirri, kwanon k’asaitacciyar mace, furar mata madararta gareki Hajia takenta sha yanzu mgni yanzu, Ina mata masu fama da sanyi? Sanyin mara ki zo na hadaki da magani na na sanyi wanda yake wanke mara ya fitar da duk wata cuta da ke samun mazauni a wajan. Ina da ciccibi mai kyau. Ina da hadin amare mai kyau wanda zai gyara yarinya ya kankaro mata kimarta akwai hadin mai jego wanda muke yinsa na asali inada kekkyawan Hadi maida tsohuwa yarinya. Akwai daya bangaren wato *KAMSHI* Kimarki gyaranki da kamshinki. Matan da suka gane suka san yanda za su kankaro da mutunci su ne masu amfani da kayan gyara da kuma sanyaya jikinsu da kamshi, ina da turaren wanka da na bandaki na daki na jiki da na kaya dana tsuguno kamshin turarena na dabam ne mai sanyaya zuciyar wanda ya shaka ina da kayan kamshi na amarya da na maijego da na uwargida da dukkan macen da take kokarin mayar da kanta mai daraja a idon kowa ta zamo sarauni a idon mijinta, akwai shu'umar humra, sayan na gari maida kuɗi gida, banda karanta yayin gyara Hajia. Zaku iya samun kayyakina a duk garin da kike, zakiyi min mgn ta whatsApp number na 09097853276 domin yin zaɓinki, ko karin bayani, zaki tura kuɗin ta account na 0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU in mun gama mgna zan sa miki kaya a mota yazo duk garin da kike, in baki shirya saya yanzuba Please kada mu wahal da juna ki bari sai kin shirya kafin kiyi min mgn. 🤝🏻🥰😘 Daga taku AYSHA ALIYU GARKUWA *(GARKUWAR MA'AURATA)* By *GARKUWAR FULANI* 11/15/21, 7:21 PM - Auntyna: Da sauri ya miƙe. Idanunsa ya d’an zazzaro tare da sanya hannu ya dafe forehead d’insa, bakomai ne ya sashi yin hakan ba kuma, face ganin Barrister Kabir da ya shigo cikin gidan. “Wannan mutumin Again? to me yazoyi? Kardai akan wancan magananne mai kama da tatsuniya ya biyoni har gida? gaskiya Indai hakane bazan iyaba, gwara ma tunda wuri naje na dakatar dashi.” Ya fad’i maganar cikin sauri, batare kuma daya tsaya wani jinkiri ba kaitsaye ya juya, ya nufi asalin cikin sashinsa, Domin dole saiya sauko kasa, kafun zai iya dakatar da Barrister Kabir din. Barrister Kabir kuwa Koda ya gama dai-dai-ta parking din motar, budewa yayi ya fito. Ahankali ya juyo tare da nufo inda Baba Maud’o ke tsaye, idanu Baba Maud’o ya zubawa, fuskar mutumin da yaga yana tunkarosa, babu ko kyaftawa, Yayinda ajikinsa yakejin wani irin yanayi na girgizar kwanya. “Assalamu Alaikum Barka da aiki.” Barrister Kabir ya fad’a yana me mik’awa Baba Maud’o hannu, alaman suyi musabaha. Hakan kuwa shi ya katsewa Baba Maud’o d’an guntun tunanin da yakeyi, hannu ya mik’awa Barrister Kabir din suka gaisa. Saidai kuma duk yanda Baba Maud’on yaso dauke idanunsa daga Kallon, mutumin dake tsaye agaban nasa ya kasa. Barrister Kabir kuwa Dan gyara tsayuwarsa yayi, kana cikin sakin fuska yace. “Ni bak’one kuma nasan baka shaidani ba, amma Dan Allah ko zaka iya yimin sallama da maigidan?” Still idanu Baba Maud’o ya zuba masa, saidai kuma jin yace Yayi masa sallama da mai gidanne, yasa shi d’an sauk’e ajiyar zuciya. Kai Baba Maud’on ya jinjina, cikin kuma gamsuwa da yaji acikin zuciyarsa yace. “To Kajirani anan, ba matsala bari nayi masa magana.” “To Masha Allah nagode sosai.” Barrister Kabir ya fad’i hakan, yana murmushi. Yayinda shi kuwa Baba Maud’o kaitsaye ya nufi cikin gidan. Aikuwa yana fara tafiyanne hankalin Barrister Kabir gaba d’aya ya tattare ya tafi kanshi, inda ya zubawa bayansa idanu baya ko k’yaftawa. Musamman tafiyan mutumin, yaso tuna masa da wasu abubuwa. Saurin girgiza kansa yayi, tare kuma da ture duk wani tunani da yazo cikin k’wak’walwarsa, saboda yasan ma ba hakan bane, maybe yanayi ne kawai yazo d’aya. Sannan babban abunda yake gabansa ayanzu ma yafi karfin wannan tunanin. Shikuwa Baba Maud’o Koda ya k’arasa jikin k’ofar babban falon gidan, tsayawa yayi tare da soma dan k’wank’wasa kofar. Abba kuwa dake zaune acikin falon, Jin ana buga kofarne yasashi, d’an d’ago da kansa, tare kuma da bada izinin shigowa. Jin anbada izinin shiga ne kuma yasa Baba Maud’o d’an tura k’ofar, ahankali ya saka kansa acikin falon bakinsa d’auke da sallama. Ganin Baba Maud’o ne kuma yasa Abba dake zaune saurin mik’ewa, lokaci daya kuma ya saki fuskarsa tare da cewa. “A’a Baba Maud’o yau kaine da kanka, shigo daga ciki.” Murmushi Baba Maud’o yayi, tare kuma da d’an girgiza kansa, kana murya asake yace. “A'a ai bama sai na shigo ba, yanzuma daliline ya kawoni, wani mutumi ne yazo yananan awaje, ya kuma ce Kai yakeson gani.” Kai Abban ya d’an jinjina, tare kuma da danyin shiru na. Dan wasu sakanni, saboda duk a iya saninsa baiyi da wani akan cewar za’azo nemansa ba. Watsar da tunanin dake zuciyar tasa yayi, cikin kuma sakin fuska yace. “To Baba Maud’o ace masa ganinan zuwa.” Abban ya fad’a yana me gyara zaman babbar rigar dake jikinsa. Kai Baba Maud’o ya jinjina, batare da yace komai ba kuma, ya juya ya fice daga cikin falon. Dai-dai lokacinne kuma Rayyern ya gama sauk’owa cikin falon. Ganin da yayi kuma Abban nasa na shirin fita ne yasashi, dan Sosa k’eyansa, cikin yanayin inda-inda yace. “Abba fita zakayi ne?” Juyowa Abba yayi ya d’an kalleshi tare da cewa. “Eh yanzun nan Baba Maud’o yake cemin wai wani mutumi awaje yana son ganina.” Kansa yad’an shafa still, kana cikin yin k’asa da murya yace. “No Abba basai kajeba ai, ba bak’on ka bane bak’onane, kuma nasan ni yake nema.” Idanu Abban yad’an tsura masa, cikin rashin gamsuwa da hakan yace. “To kuma Idan ba bakona bane yace kuma yana nema na? Bari dai naje naji ko menene.” Saurin d’ago da kansa yayi ya kalli Abban nasa, lokaci daya kuma ya marairaice fuskarsa tamkar karamin yaro. “Abba dan Allah ka zauna, Zanje naji ko menene.” Ya fad’a yana me kokarin fita wajen. Kallonsa Abba yayi kana cikin rashin bai yarda da hakan ba yace. “Anya kuwa Rayyern To waye ne, lafiya dai kam ko?” “Eh Abba Lafiya kalau, bari naje na sameshi.” Rayyern din ya fad’a cikin d’an sauri, tare da gudun kada Abban nasa yace Lallai shi da kansa zaije. “Da kata Rayyern, koma dai wajen waye yazo, ai dai yanzu kam ni ya buk’aci gani ko, To barni naje na sameshi.” Abban ya fad’a cikin serious, wanda hakanne kuma yasa duk jikin Rayyern din yin lak’was, kansa yad’an langwabar gefe, cikin kuma yanayin sanyi yace. “Shikenan To Abba Dan Allah muje tare.” Kai Abban ya jinjina masa alaman to. Inda Abban yayi gaba shi kuma Rayyern ya biyoshi abaya, Yayinda acikin zuciyarsa yakejin babu dadi, saboda baisan da wacce maganan Barrister Kabir din ya kuma zuwa yau ba. Saidai koma meye yana fatan ace sab’anin waccan magananne da sukayi last Friday acikin mota. Koda suka fito compound din gidan, Barrister Kabir dake tsaye ajikin motarsa, yana hangosu ya fadada murmushi da kuma fara’ar dake kwance akan fuskarsa. Bayan sun k’arasone kuma Abba’n ya mik’a masa hannu sukayi musabaha, kana Rayyern ma ya bashi hannu suka gaisa. D’an Kallon Barrister Kabir din Abba yayi, cikin yanayin sakin fuska yace. “Sannu bawan Allah saidai kuma gaskiya ban shaida fuskar taka ba.” Murmushi Barrister Kabir din yayi, tare da gyara tsayuwarsa, still kuma fara’a fad’ad’e akan fuskarsa yace. “Eh gaskiya bazaka shaidani ba, Domin wannan zuwan nawa, shine zuwana na farko cikin gidanka, sunana *Barrister Kabir Saleh Dakata!!”* Dammmmm dammmmm haka zuciyar Baba Maud’o tayi wani irin bugawa, a lokacin da yaji sunan mutumin dake tsaye agaban nasa. A hankali ya lumshe idanunsa sabida jin zuciyarsa na wani irin harbawa da karfi, tamkar zata faso kirjinsa ta fito. Abba kuma kai ya jinjina nawa Barrister Kabir alamun gamsuwa. Rayyern dake tsaye agefensu kuwa, Dan lumshe idanunsa yayi, cikin kuma yanayin kosawa yace. “To Barrister mungode k’warai da ziyara.” Ya k’arasa maganar tasa atak’aice Domin Sam bayason daga haka mutumin ya sake fad’an wani abu kuma. Barrister Kabir kuwa fahimtar hakanne yasa shi, sakin murmushi, batare kuma daya lura da shock din da suke ciki ba yace. “Alhaji wajenka nazo Idan babu damuwa kozan iya samun lokacinka muyi magana.” Saurin girgiza Kai Rayyern yayi, lokaci daya kuma gaba daya mood d’insa ya sanja. Kallon Barrister Kabir din yayi, kana cikin dagiya yace. “Mun gama magana dakai tun a wancan ranan. To yanzu kuma ai inaganin babu buk’atar kace lallai saika yi magana da Abbana, Dan Allah kaje kawai.” Dr. Rayyern din ya k’arasa maganan, cikin son kin bawa Barrister Kabir din dama. Shikuwa Barrister Kabir murmushi yayi, batare kuma daya ce komai ba, ya sake gyara tsayuwarsa. Abba kuwa wani irin boyayyar ajiyar zuciya ya sauk’e, tare da d’an juyawa ya kalli Rayyern dake bayansa, wanda yayi kicin kicin da fuska. Tabbas zuciyar Abban ta raya masa wani abu. Hakanne kuma yasa shi dawo da kallonsa ga Barrister Kabir d’in. “Shikenan badamuwa Barrister Kabir Saleh Dakata mushiga daga ciki.” Abban ya fad’a yana me juyawa, kaitsaye, Barrister Kabir kuma ya rufa masa baya. Rayyern kuwa idanunsa ya rumtse, cikin haushi da takaici ya d’an ciji Labb’an bakinsa, sam kwata kwata ba haka yaso ba, yaso ace Barristern bai samu attention din Abban nasu ba. Juyawa yayi shima asukwane yabi bayansu. Yayinda Baba Maud’o dake zaune akan d’an bencinsa kuwa duk yabisu da idanu. Acan cikin falon kuwa, suna shiga Abba ya nunawa Barrister Kabir din wajen zama. Bayan duk sun zaunane kuma, Abban ya kalli Rayyern, da yake shigowa yanzu. Kuma shidinma waje ya samu acikin falon ya zauna, saboda ya fiso duk wani abu da Barrister din zai fada ya jita acikin kunnensa. Abba da Barrister Kabir din kuwa sake gaisawa sukayi, kafun duk sukayi shiru na d’an wasu sakanni. Still Abban ne kuma da har yanzu zuciyarsa bata daina bugawa da karfi ba, ya kalli Barrister Kabir din, tare da cewa. “Barrister inajinka meke tafe dakai?” K’akk’afar ajiyar zuciya Barrister Kabir ya sauk’e, lokaci daya kuma duk wani mood d’insa ya sanja, tsananin rauni da kuma karyewar zuciya ne suka bayyana akan fuskarsa, Yayinda zallan damuwa ta fito tayiwa fuskarsa kawanya. Gyara zamansa yayi ahankali, cikin kuma sanyin murya dake bayyana tarin fargaba hadi da damuwarsa yace. “Tabbas ni mabuk’aci ne awajenku, sannan kuma banzo dan komai ba, saidan saka rai da kuma fatan cewa watakila zaku dubeni..” Dan Jim yayi kana cikin k’ank’an dakai yace. “Taimakon had’i da Alfarma nazo nema awajenku, Dan isar Allah da Manzonsa idan zaku iya.” Shiru gaba d’aya falon ya d’auka, Yayinda kuma har yanzu zuciyar Abba keci gaba da bugawa, saidai kuma jin abunda Barrister Kabir din ya fad’ane yasa shi, sauk’e ajiyar zuciya, tare da kallon Barrister Kabir din cikin, kuma rashin gane inda kalamansa suka dosa yace. “Inajinka Barrister wacce irin taimako kake nema awajenmu, Allah Dai yasa zamu iya sabida yadda ka haɗamu dashi da fiyayyan halitta in ban iya maka shiba zanji ciwo a raina.” Idanunsa da suka d’an ciko da hawaye lokaci daya ya lumshe, cikin sanyin da jikinsa yayi ne kuma ya d’an zamo jikinsa daga kan kujeran, batare kuma dasu Abban sun farga ba, sai ganinsa sukayi ya durk’usa guiwowinsa biyu agaban Abban. Cikin wata irin muryar dake bayyana karyewar zuciya da kuma tsananin damuwarsa yace. “Dan Allah Dan Annabi Sallallahu alaihi Wasallam. kuyimin taimako, da kuma alfarma kamar yanda na buk’ata a farko, saboda tseratar da rai da kuma lafiyar y’ar Adam.” Again gaba d’aya falon shiru ya dauka, babu abunda ke tashi acikinsa kuwa face bugawan zuciyoyi, Yayinda kwakwalwar kowanne daga cikinsu ke kawo masa tunani na daban. Bama kamar Abba da gaba d’aya kalaman Barrister Kabir din suka d'aure masa Kai, tare da juya masa tunaninsa izuwa wani waje na daban. Yayinda shikuwa Rayyern gaba daya ya dauke kansa gefe, tare da hade fuskarsa. Kallon Barrister Kabir din Abba yayi, cikin kuma rashin fahimta da kasa sanin makaman kalaman nasa, hadi da rudun daya samu kansa aciki yace. “Barrister har yanzu dai ban fahimci inda kalaman naka suka dosa ba, bamusan me kake nufi ba? Rayuwar waye zamu tseratar, sannan me hakikanin zancen naka yake nufi?” Idanu Barrister Kabir ya d’an lumshe, sannan kuma murya araunace yace. “Tana tsananin buk’atar taimako, Tabbas Jannart tana buk’atar Garkuwa, had’i da ingantaccen mafaka, tana buk’atar haske acikin rayuwarta, wanda yake dauke da sarkakiya maitarin yawa, gaba daya duhu da bakinciki sunyi tasiri acikin rayuwarta, hakika tana buk’atar taimako, da kuma samun ceto daga irin azabar da d’an uwanta yake gana mata, Dan Allah ku taimaka ku bata mafaka, ku taimaka ku tayani inganta rayuwar marainiyar da Allah kejin kanta akoda yaushe.” D’an tsagaitawa da maganan nasa yayi, tare da d’ago kansa akaro na barkatai ya kalli Abba daya zuba masa ido. Saidai kuma awannan karon irin Kallon da yakeyiwa Abban ya banbanta dana sauran lokutan. Bakinsa ya bud’e Ahankali cikin kuma fata da addu’an cikar burinsa yace. *”Dan Allah Ina meneman alfarma agareku, Ina nemawa y’ata auren d’anka Dr. Rayyern Mai-nasara!!” zan bashi ɗiyata bisa yarda da gamsuwa da tarbiyarshi da gskyarsa da amanarsa* Wani irin bugawa maitsananin karfi zuciyar Abba tayi, wanda kuma harsaida rud’u da kuma mamakin daya shiga ya kasa b’uya akan fuskarsa. Idanunsa ya d’an zazzaro waje, da tsananin mamaki al’ajabi hadi da tu’ajjudi, yake Kallon Barrister Kabir din, saboda zai iya yin rantsuwa cewar maganan da Barrister Kabir din ya fad’a, ta daki zuciyarsa sosai, Yayinda kuma ta rarraba masa tunaninsa zuwa wani waje na daban. Rayyern dake zaune kuwa idanunsa ya rumtse da k’arfi, adai-dai lokacin da maganan Barrister Kabir din ta daki dodon kunnensa. “Aure! Aure!! Aure kuma!!!” Abba ya fad’a cikin bayyana tsananin mamakinsa, saboda shidai zaice tunda yake bai tab’ajin anyi irin hakan ba, sai awasu k’asashen kamar India, koda ma kuwa anan din anayi to ya sani ba acikin zuriyar Hausa Fulani ba gidan mata suje nemawa yarsu auren gidan maza. Barrister Kabir kuwa Kai ya jinjina, fahimtar da yayi kuma cewar sun yiwa maganan nasa wata kalar fahimta ne yasa asanyaye yace. “Kuyi hakuri banzo da maganar dan yin kaina, ko kuma wani abu na daban ba, saidai halin matsalar da nake ciki da kuma wanda nake shirin fuskanta yasa nazo muku da wannan buk’atar, nasan bakusanni ba baku kuma San komai akaina ba, amma Idan har buk’ata ta bazata samu ba, Dan Allah kuyi mini alfarma na kawo Jannart gidanku, ku b’oyemin ita, ku bata kariya kuma ku zame mata Garkuwa, ta yanda baza’a tab’a sanin cewa tana nan ba, kamar yanda na fad’a muku a farko, Jannart Marainiyace, marainiya kuma wacce take tsananin buk’atar taimako, amatsayinku na y’an uwa musulmai Dan Allah kuyi min wannan taimakon, ku zama kariya ga Jannart!!” Barrister Kabir ya kare maganar yana me had’e hannayensa duka biyu waje d’aya, alaman rok’o. Wani irin doguwar ajiyar zuciya Abba ya sauk’e, tare dasa hannunsa ya dafe zuciyarsa, da ayanzu ta rage yawan harbawan da takeyi tun lokacin da yaji sunan Barrister Kabir, maida bayansa yayi ya jingina da jikin kujerar da yake Kai. Idanunsa ya lumshe, Yayinda yake amsar duk wani tunani da ke yawo acikin k’wak’walwarsa, wanda kuma har yakeji tamkar zasu hautsuna masa k’wak’walwa. Tabbas ayanzu duk wani nazarinsa ya tsaya cak. Yayinda Rayyern kuwa dake can gefe, idanu ya tsurawa Abban nasa zuciyarsa na bugawa, saboda sam bayason Abban nasa ya aminta da maganar Barrister Kabir din. Domin shi agaba daya rayuwarsa babu maganan wata Mace acikin tsarinsa, ba kuma yajin zai iya auren wata, balle kuma ya karb’i wani ajiya ji rainin hankali wai ajiya!? Kamar a garin gaɓa-gaɓa. Abba kuwa kusan mintuna 5 kenan yanzu da ya nutsa acikin duniyar tunanin da yake. “Lallai Wannan shine k’arin dama, abubuwa nata kusantowa, nesa na matsowa kusa, Yayinda haske ke shirin bayyana ya mamaye duhun duhuwan daya danne kekkyawan Tubalin da yake gine tun da dadewa.” Abban ya fad’i hakan acikin zuciyarsa, adai-dai lokacinne kuma ya dawo daga duniyar tunanin daya tafi. Ajiyar zuciya mai karfi ya sauk’e, tare kuma da dawo da kallonsa ga Barrister Kabir dake zaune agabansa. Kwarai ya aminta da shawarar da zuciyarsa ke basa, ya kuma yi Na’am da hakan domin akwai wani ƙulli a tsakani. Numfashi me zafi ya fesar, cikin kuma yarda da kai hadi da gamsuwa yace. *Littafin TUBALI na kuɗine dan girman Allah da Manzonsa da darajar iyayenku kada ku karanta min littafina in baku biyaba, 1k ko 500 da kika biya ko zaki biya kuma bawai kuɗin mallakan littafin bane, kuɗin samun damar karanta Littafin ne, kiya girman zatin ubangijin daya bamu rai da lfy, kada ku fitarmin da littafin, dan darajar Allah kada kuyi ta posting na littafina. Special Group 1k ƙaramin group kuma 500 yawan posting ne babbancinsu, 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU sai ki turo min shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276, in ba halin turowa ta account ki sayi katin MTN ki copy number's ɗin katin ki turo min ta whatsApp number na* *”Ni Alhaji Bashir Abban Rayyern na amince da buk’atar da kazomin dashi Barrister Kabir, saboda haka na amincewa d’ana Auren Jannart!!” bisa tsarin Musulunci mu zamu nemi aurenta* Tamkar rugugin tsawa asararin samaniya haka Rayyern yaji fitan kalaman Abban nasa, hakanne kuma yasa shi mik’ewa tsaye agigice, hankalinsa amatukar tashe yake Kallon Abban nasa baya ko k’yafta idanunsa, wanda lokaci daya sukayi jajur. Barrister Kabir kuwa idanunsa ya lumshe, zuciyarsa cike da matsanancin farinciki, hadi da jin dadi marar misaltuwa, saboda tsabar farincikin da yaji acikin zuciyarsa ne kuma, yasa wasu irin hawaye suka gangaro kan fuskarsa. Hannayensa ya had’e waje guda, tare dayin shiru Dan yama kasa sanin da wacce irin kalmace zai godewa Abban. Rayyern kuwa da gaba d’aya jikinsa ya d’auki rawa, kansa ya soma girgizawa cikin, wata irin murya dake bayyana gaskiyar abunda ke cikin zuciyarsa yace. “A’a Abba Dan Allah kada.....” Saurin dakatar dashi Abban yayi, ta hanyar d’aga masa hannu, mai dauke da alamun dakatarwa, wanda kuma hakan shiya tilastawa Rayyern din yin shiru tare da haɗiye ragowar mgnarsa. Idanunsa ya rumtse da karfi, tare da taune jajayen labb’ansa, haka yakejin kansa na wani irin juyawa, arayuwarsa kwata kwata bayason jin wata magana da ta shafi mata, Babu mata atsarin rayuwarsa, saboda ya aminta cewa, zai iya rayuwa ko babu Mace a kusa da shi, Domin ko a addinance Aure bai zama dolen dole ba, matuk’ar zaka iya kare kanka daga aikata Zina da fasikanci toh shi bai kawo mace a rayuwarsa ma bare wani abu ya kwashesa. “Kabamu wuri!!” Abban ya fad’a atak’aice fuskarsa babu alaman wasa ko wargi. Idanunsa da sukayi ja sosai ya bud’e ya kalli Abban nasa, saidai kuma yanayin da ya gani akan fuskar Abban nasa, yasa shi juyawa cikin sauri ya nufi stairs din dazai sadashi da part d’insa, ransa amatukar jagule. Barrister Kabir kuwa ganin Rayyern din ya tafi ne, ya sashi juyowa ga Abba. Kansa ya d’an sunkuyar fuskarsa dauke da tsananin farinciki yace. “Tabbas Alhaji Bashir kayimin halacci, kayi min abunda bakowane zaiyi minshi ba, nagode matuka na gode sosai da sosai, nagode Alhaji Allah Ubangiji ya biyaka ya sanya farinciki mai dorewa acikin ahalinka.” Kai Abban ya d’an girgiza Barrister Kabir din, tare da cewa. “Bakomai Barrister Kabir ai duk yiwa kaine, Fatana da kuma burina shine Allah yasa hakan shine sanadiyar kawo haske acikin rayuwar da gaba da bayanta ke dauke da duhu da kuma rashin sani.” Kai Barrister Kabir din ya jinjina, batare kuma daya zurfafa tunaninsa akan maganan da Abban ya fad’a ba ya ci gaba da yi masa godiya. Haka dai suka dauki kusan 30mn suna maganganu irin tasu ta manya. Kafun daga bisani Barrister Kabir ya mik’e da niyar tafiya. Har bakin kofar falon kuwa Abba ya rakosa, ba tare kuma daya tsaya yaga tafiyarsa ba, ya maida kansa cikin falon. Juyowarsa cikin falon kuwa yayi dai-dai da fitowar Mamy dake cikin kitchine, wanda kuma tun d’azu take tsaye tana sauraran maganganun da suke fad’a. Kallon Mamyn Abban yayi, Yayinda ita kuwa Mamy keyi mishi Kallon mamaki. Fuskarta d’auke da damuwa sosai tace. “Duk naji abunda kuka tattauna Alhaji, amma kwata-kwata banajin hakan dai-dai ne, tayaya zaka amincewa mutanen da baka sansu ba? Tayaya zaka dauk’o wasu daban ka sakosu acikin rayuwar mu? Wayesu mene hadinmu dasu, da har ka amince akan Rayyern ya auri y’arsu?” Ajiyar zuciya mai k’arfi Abban ya sauk’e, kana Ahankali ya shiga takowa har zuwa inda take. Batare kuma daya amsa mata duka tarin tambayoyin nata ba, ya kama hannunta kaitsaye suka nufi falonsa dake cikin main parlor din. Koda suka karasa falon nasa kaitsaye bedroom d’insa suka wuce, still kuma har yanzu yana rik’e da hannunta. Suna karasawa cikin dakin kuwa, ya maida kofar ya rufe tare da murzawa kofar key. Numfashi ya d’an fesar, kana Ahankali ya d’ago Kai ya kalli Mamyn, wacce har yanzu takeyi masa Kallon mamaki. K’asa-k’asa yayi da muryarsa, yadda yasan koda akwai wani adakin To bazai tab’a iya juyo abunda yake fad’a ba, sai ita d’in kawai. “Kiyi k’asa-k’asa da muryarki Ruk’ayya, kinsan komai babu wani abunda baki sani ba, Dama ce ta samu, hakika naji ajikina cewar komai yana gab da had’uwa waje d’aya, da yardar Allah abubuwa suna ta had’uwa waje d’aya.” Idanu Mamyn ta zuba masa cike da d’an d’aurewar kai, cikin kuma muryarta da yayi sanyi sosai tace. “Har yanzu bangane abunda kake nufi ba, meke shirin faruwa ne?” Ajiyar zuciya Abban ya sauk’e tare da sake rik’o hannunta da kyau. Again kuma Cikin yin k’asa da murya yace. “Kintuna Barrister Abdulkarim Saleh Dakata?” Kai Mamyn ta jinjina, cikin sauri kuma tace. “Natuna shi mana, har abada kuma bazan manta shiba.” Kai Abban ya jinjina cike da gamsuwa, yace. “To wannan bak’on da yazo wajena k’aninsa ne, shima kuma Barrister ne, sunansa Barrister Kabir Saleh Dakata.” Idanu Mamyn tad’an zaro cike da tsananin mamaki, tace. “Ikon Allah, Allah mai iko, mai kumayin duk yanda yaso, Lallai Tabbas kuwa na amincewa maganarka, Nesa na matsowa kusa, kuma haske zai bayyana Insha Allah.” “Insha Allah kuwa.” Abba ya maimaita cike da k’warin guiwa. Acan b’angaren Rayyern kuwa...! *GARKUWAR taku ce dai MA'AURATA, da masu shirin aure, da masu jego, da yan gayu masu son k’amshi kece raini, da gyaran da zaike maimaita muku dararen forkon kuruciya* Ko kunsan Jikinmu na da sinadaran hormones da suke taimakawa dan’adam akan komai musamman lokacin da mace take mu’amalar aure da mijinta. Mafi akasari wannan hormones din ne ke samun matsala ko su yi sanyi koma su daina aiki kwata-kwata shi ne dalilin da zai sa mace tace bata jin sha’awa ko bata san dadin aure ba. Albishirinku ina da kayan da ke taimakawa wannan sinadaran du dawo aiki tukuru don karkato miki da kimarki wajan mai gida sannan su taimakawa wannan sinadaran hormones dinki su dinka secreting din ni’ima wadatacciya da zata taimaka miki ki gamsu mijinki ya gamsu fiye da tunaninki. Note: Kayana ba sa tsinka ruwan ni’ima suna dai taimakawa hormones dinki ne su tsattsafo da ni’imar musamman wacca cutar sanyi ko dattin mahaifa ya dankarar da su ya hana su yin aikinsu yanda ya kamata. Haka zalika idan kina da kyau ki kara da wanka. Zaki iya amfani da magani na na gargajiya wanda zai gyara miki sex hormones din kullum ki kasance cikin humidify wato cikin damshi mai albarka kamar yanda ake son mace. Yana gyara miki mara. Sai kamshi. Hajiyata daure ki fara amfani da turarena ki ji irin salon kamshin sa salo ne da zai daidaita ki da mijinki ya kankaro miki da kimarki a wajansa. Siyan na gari mayar da kudi gida. Ga masu buƙata ga number' wayata wanda nake whatsApp dashi 09097853276 kimin mgn ta whatsApp in har kin tabbatar kin shirya saya mu dai-dai ta, kayana ba ƙanana bane, shiyasa bana harkan karanta, muddin kinsan baki shirya sayaba Please kada kiyi min mgn ki bari sai kin shirya kuɗinki a hannu, ba ina nufin kayana bana talaka bane, no akwai ƙananan set na masu karamin karfi, banson aimin mgn a ɓatamin lokacin aiyukana a shirme baki shiryaba. Shine karantan da bana so. 0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU. In kin shirya ga number ta ga kuma account number ta wanda in mun gama mgn zaki turo kudin ki, kana insa miki kaya a mota, duk ƙasar da kike kayana zaije gareki, amman fa in kinada dalilin zuwan nasune🤝🏻sayan na gari meda kudi gida. GARKUWAR MA'AURATA By *GARKUWAR FULANI* 11/15/21, 7:21 PM - Auntyna: In Sha Allah kuwa. Abban ya maimaita cike da k’warin guiwa. Acan b’angaren Rayyern kuwa, koda ya koma part d’insa, gaba daya kasa zaune yayi, Domin kuwa abubuwa da yawa ne keyi masa yawo acikin tunaninsa. Direct kuma saman balcony d’insa ya koma, yana nan tsaye ne kuma yaga Barrister Kabir din ya fito. Hakan yasa cikin sauri ya juya, tare da nufan falon k’asan nasu kaitsaye. Koda ya fito falon, rashin Ganin Abba acikin falon Yayi masa dadi, wanda kuma hakanne ya bashi daman nufan waje kaitsaye. Fitowarsa compound din gidan, kuwa yayi dai-dai da mik’awa Baba Maud’o hannu da Barrister Kabir din yayi. Cikin aminci suka sake gaisawa, inda Baba Maud’o yace. “Masha Allah har kafito zaka tafi, To mungode sosai a gaida gida.” Murmushi Barrister Kabir din yayi, tare da cewa. “Nima Nagode Baba.” Dai-dai ya juya zai shiga cikin motarsa ne kuma, Rayyern ya k’araso wajen. Kallon-kallo suka danyi da Barrister Kabir din, Yayinda Barrister Kabir din ke kallonsa cikin sakin fuska. Shikuwa Rayyern yaken dole yayi, kana anutse yace. “Har zaka tafi?” Kai Barrister Kabir din ya jinjina masa alaman. “Eh.” Shikuwa Rayyern kaitsaye bud’e murfin motar yayi, b’angaren mai zaman banza ya shiga ya zauna. Ganin hakanne kuma yasa Barrister Kabir yin murmushi, tare da bud’e murfin motar shima ya shiga ya zauna. saboda Lallai yasan cewa akwai magana. Yana zama kuwa Rayyern ya fuskancesa. Cikin muryar dake bayyana gaskiyar abunda ke cikin zuciyarsa yace. “Bansan me kake nufi ba, Bansan me kake nema da rayuwata ba, Bansan wani k’ulline kuke nufina dashi, kaida y’an uwanka da kuma abokan kasuwancinka akaina ba, inayiwa fuskarka kyakkyawan gani , da kuma kyakkyawan zato, amma why zakayi min haka? kayi min bayanin yarinyar, kuma na saka baki anbata taimakon daya kama ta a Hospital dina? To yanzu kuma me kuke nema awaje na? Meyasa dole saini zaku zab’a mainayi muku? Ina da yakinin Akwai dubbannin mutanen, da zasu iya taimaka muku akan matsalarku, bawai dole sai lallai niba, To Meyasa kuke son takuramin? Meyasa kuke bibiyata? Meyasa zaka zo da wannan maganan mai kama da tatsuniya? Wanda ko’a labarai ko a fina finai babu irin wannan al’amarin, ni nakan cire kaina acikin duk wani abu danasan babu ruwana, Meyasa kukeson sakani acikin abunda baidace dani ba??”. Juyowa Barrister Kabir din yayi, ya kalli Rayyern d’in. Domin kuwa acikin kalaman da yaji sun fito daga bakinsa babu wanda bai fahimta ba ya fahimci Rayyern yanayi musu kuɗin goro shi dasu Alhaji Idi Saleh Dakata dasu Dr Lukman da Abdu Tababa. Ajiyar zuciya mai karfi ya sauke tare kuma da kamo hannun Rayyern d’in, cikin fuskantar juna yace. “Rayyern! Rayyern ka yarda dani, Rayyern ka aminta dani, bazan tab’a cutar dakai ba har abada, wallahi babu cutarwa tsakanina da kai, saidai ina tsananin neman taimakon ka, Ina neman taimakonka. Dan tsiratar da ran Jannart, Jannart marainiya ce, Dr. Rayyern ba zaka gane halin da nake ciki ba, ba ni kuma da isashshen lokacin da zanyi maka bayanin da zaka fahimceni, fatana ayanzu shine Jannart ta kasance ak’ark’ashin inuwarka, ba naso asan ma tana tare dakai, Domin Kuwa auren da zakayi da ita, Aurene na sirri, haka kuma aure ne da zai zamo auren manufa, Dan Allah Rayyern ka amincewa buk’atata, ko badan niba Kodan maraicin Jannart..” *”Manufa? Auren manufa Wanne irin manufa kenan?”* Rayyern din ya tambaya, yana me tsare Barrister Kabir da ido. “Manufa saboda ceto Rayuwarta, da kuma manufar fidda gaskiyar da take b’oye tsawon shekaru ashirin da biyu.” Idanu Rayyern din ya lumshe, akaron farko cikin kuma halin ko inkula yace. “To ni meye had’ina da wannan? Meya shafeni da hakan?” Ajiyar zuciya Barrister Kabir ya sauk’e. Kana cikin sanyi yace. “Baka da had’i dashi, amma kuma abad’inance kana da had’i dashi, Domin idan kataimaketa Allah Zaibaka lada, kuma kayi taimakon musulunci.” Barrister Kabir din ya fada idanunsa na ciko da k’walla. Lips d’insa ya cije, tare da sake rumtse idanunsa, cikin yanayin dake nuna Kosawa da da maganan yace. “Har dai yanzu bangane inda komai suka dosa ba.” Still ajiyar zuciya Barrister Kabir din ya sake saukewa, kana ahankali yace. “Nidai fatana shine ka amince, Idan ka amince ninasan yanda zan gudanar da komai.” Kai Rayyern din ya girgiza Cikin kuma rashin gamsuwa, da abunda Barrister Kabir din ke fad’a yace. “Wannan tatsuniya ne, ko kuma nace mafarkin da bazai kammala ba har gaban abadan, well yanzu me kaje ka fad’awa mahaifina mai kuka tattauna dashi?.” Murmushi Barrister Kabir din yayi. Kana yace. “Idan ka tambayeshi duk zai gaya maka na tabbatar da hakan.” Kafad’ansa yad’an d’age, batare kuma daya sake yiwa Barrister Kabir din wata, tambaya ba ya bud’e murfin motar ya fice. Hakanne kuma yasa Barrister Kabir sakin murmushi, tare da dan juyawa yana kallonsa. Harsaida Rayyern din ya b’a cewa ganinsa, kafun ya yiwa motar key kaitsaye ya fice daga cikin gidan. Rayyern kuwa kaitsaye part d’insa ya koma, gudun kada wasu banzayen tunanin abunda basu da muhimmanci arayuwarsa su dameshi ne kuma yasa shi, daukan laptop d’insa ya soma shigar da wasu bayanai. Acan b’angaren Barrister Kabir kuwa, zuciyarsa cike da tsananin farinciki ya Baro gidan su Rayyern din. Koda ya isa inda zaije kuwa ansoma kiraye kirayen sallan la’asar, bayan yayi sallan ne kuma ya ci gaba da sabgoginsa. Yayinda acan b’angaren Jannart kuwa, yau din kusan wuni tayi tana bacci, kasancewar acikin magungunan da aka bata a asibitin Mai-nasara’n, akwai way’anda suke sa bacci sosai, babu laifi kuma tana samun kulawa mai kyau, daga wajen Momy da kuma k’aninta Abdull. 10:00 pm Aunty Dijat ne wacce Tasha wanka cikin night gown, ta turo kofar dakin mijinnata, Ahankali Yayinda bakinta ke dauke da sallama. Saidai kuma ganin abunda mijin nata keyi ne, yasa taja ta tsaya tare da kura masa ido. Domin kuwa shigowarta cikin dakin, yayi dai-dai da dirowar Barrister Kabir din k’asa, wanda kuma fitowarsa daga cikin silin kenan. Idanu Aunty Dijat din ta d’an zaro, cikin kuma yanayin mamaki tace. “Barrister, yana ganka haka cikin silin fa ka shiga?” Kansa ya jinjina mata alaman Eh. Batare kuma daya motsa bakinsa ba, ya koma ya zauna, tare da baje tarin takardun dake hannunsa ak’asa, wanda duk sukayi kura ya soma kad’ewa. Ganin hakanne kuma yasa Aunty Dijat din cewa. “Barrister lafiya kuwa, way’annan tarin tsofin takardun duk na meye?” Juyowa yayi ya kalleta, cikin kuma son samun nutsuwa yace. “Dijat dan Allah kid’an hakurtamin, Domin ayanzu bani da amsar da zan baki, bincikene akan abunda ya shafi aikina, please kije anjima zanne meki, yanzu Idan kika tsaya zaki iya disturbing dina.” Ya fad’i hakan yana me Dan tausasa muryarsa. Aunty Dijat kuwa sanin irin yanayin aikin nasa ne yasa batare da ta musa masa ba, ta juya ta fice daga cikin dakin, saboda tasan watarana Idan tension din aiki Yayi masa yawa, To kwata kwata bayason damuwa. Shikuwa Barrister Kabir Ganin Dijat din tatafi ne, yasa shi soma bubbud’e takardun dake zube agabansa. Yayinda kowacce takarda Idan ya bud’e, sunan Barrister Abdulkarim Saleh Dakata ne ke bayyana, da kuma sa hannunsa. Yayinda acan gefe guda kuwa, kan wani file me kaman document aka yi rubutu da manyan bak’i. *”Bashir Muhammad Mai-Gaskiya”* shine abunda ke rubuce ajikin file din. Ajiyar zuciya Barrister Kabir din ya shiga saukewa akai akai, Yayinda kuma yake ci gaba da kimtsa takardun awaje daya. Saida hakan kuwa ya d’aukesa kaman tsawon 30mn kafun ya kammala. Kana anutse yasake maida takardun inda ya d’auko su, ma’ana cikin mab’oyansu na musamman. Acikin zuciyarsa kuwa wani irin k’warain guiwa yakeji, tare da sake yiwa Allah Godiya, saboda ayanzu yasan kowanni shaida yana hannunsa. Bayan kuma ya kimtsa wajenne, ya shige toilet kaitsaye alwala ya dauro, bayan ya fito ne kuma ya shumfud’a sallaya, tare da tada sallah ya d’anyi nafilfilu, hade da sake godemawa Allah. Koda ya idar da sallan hannayensa ya d’aga sama. Kana cikin aminci yace. “Alhamdulillah Allah Nagode ma, daka bani Aron raida lafiya, har kuma ka kawoni tsawon wannan lokacin, da ake gab da samun nasara akan Jannart, da kuma ida bunne duk wata hujja, kuma ya Allah kataimakeni kabani sa’a, in tono duk wata hujja na bayyanata, gaskiya tayi halin ta..” Shafa addu’ar tasa yayi, bayan wasu yan mintuna ne kuma ya tashi kaitsaye ya nufi dakin Dijat d’insa. *Washegari* Tuesday. Jannart 8 am dai-dai ta bud’e Idanunta Ahankali, tare kuma da tashi ta mike zaune. Tabbas taji karfin jikinta sosai yau din, tasan kuma hakan bai rasa nasaba da magungunan da Tasha. Cikin kuzarin data dan samune kuma ta mik’e tare da fad’awa bathroom tayi wanka. Koda ta fito, mai kawai ta shafa, batare da ko powder ta kuma mutstsukawa fuskarta ba, ta bud’e drawer dinta, hade da zaro wata Brown din jallabiya na mata, mai kyau da Tsushi ta zura ajikinta. Sosai kuwa rigar tayi mata d’as ajikinta. Normal perfume din da ta saba shafawa, ta shafa ajikinta, batare kuma da ta tsaya wani jikiri ba, ta d’auki wayarta kaitsaye ta fice daga cikin dakin. Direct falon k’asa ta nufa. Koda ta karasa cikin falon, Momy da Abdull kawai ta samu akan dining table suna breakfast. Ganinta ne kuma yasa dukansu sakin murmushi. Inda Cikin tsananin kulawa Momy tace. “Masha Allah Jannart tayi sauk’i, Alhamdulillah hinyau Lallai kinji karfin jikinki.” Murmushi Jannart din tayi, adai-dai lokacin da ta karaso dining table dinne kuma tace. “Good morning Momy, Alhamdulillah naji sauki sosai.” “Alhamdulillah ai haka akeso, dazu na shiga ai naga kina bacci shiyasa kawai ban tasheki ba, amma tunda kintashi yanzu zoki zauna kici abinci.” Momyn ta fad’a cikin kulawa. Abdull kuwa Kallon yayartasa yayi, kana fuskarsa dauke da murmushi yace. “Sannu Aunty Jannart ya jikin naki, Ina fatan ace yanzu kin gama warkewa har tsere zaki iyayi.” Dariya duk sukayi Yayinda Jannart din tace. “Momy Daddy fa?.” Ajiyar zuciya Momyn ta sauke, kafun daga bisani tace. “Yau ai Daddynku tun sassafe ya fita, yace yana da ayyuka sosai.” Kai kawai Jannart din ta jinjina, batare kuma da ta sake cewa komai ba, ta soma cin soyayyen chips and ketchup din da Momy ta saka mata, hadi kuma da fruit salad. Bayan sun dan tab’a hira ne kuma, Abdull ya mik’e ya tafi makaranta, saboda yau din yana da lecture 10 am. Itakuwa Jannart falo ta dawo ta zauna, tana falonne kuma Aisha Lawal da kuma Salman suka zo duba ta. Har cikin falon kuwa ta shigo dasu, sosai kuma zuwan nasu ya debe Mata kewa, Yayinda Momy kuwa tayi musu tarba ta mutumci. Ita dai Jannart kam yau tana cikin farinciki, saboda har yau Junaid enemy dinta baidawo gidan ba. Acikin hirar tasu dasu Aisha Lawal dinne kuma, take tambayar Salman, ko wannan mutumin ya kirasa. Numfashi Salman din yadan fesar, kana Cikin son kwantar mata da hankali yace. “Har yanzun dai baikirani ba, amma nasan zai kira Insha Allah, karki damu ai daganinsa yasan muhimmancin alkawari, kuma ko yanzu ma da zamu taho saida muka biya wajen wasan polo’n, nayi tunanin zan hadu dashi kamar wancan ranan, amma kuma saidai ko mai kama dashi bangani ba.” Ajiyar zuciya ta d’an sauk’e, tare da karyar da wuya cikin, sanyi tace. “To Allah Yasa ya Kira.” Da “Ameen.” Suka amsa dukansu. Ganin yanda Jannart din ta damu ne kuma yasa, Aysha Lawal dafa kafad’anta, cike da son bata kwarin guiwa tace. “Please Jannart karki damu kanki, Insha Allah komai zai tafi dai dai, kuma Koda ma ace baku samu ganinsa yanzu ba, ai ba matsala saboda MD yace ya k’ara miki one week, saboda rashin lafiyarki, kinga before nan ma kin sake warwarewa.” Jin abunda Aishan ta fad’ane yasa, Jannart sauke Ajiyar zuciya mai karfi. Cikin Jin dadi tace. “Alhamdulillah, amma duk da haka nafison naganshi nan kusa, saboda muyi hira dashi asatinnan,kinga hakanne kad’ai zai karamin nutsuwa.” Kansu suka jinjina dukansu, tare da sake bata kwarin guiwa akan cewar Lallai zata ga DR. Rayyern Bashir Muhammad Mainasara. Haka dai suka ci gaba da hira, saidai kuma basu wani jima sosai ba, sukayiwa Jannart din sallama suka tafi. Bayan tafiyar tasu ne kuma Jannart din tabi Momy kitchine Dan Tayata aiki. Ganin Jannart din acikin kitchine ne kuma yasa Momy cewa. “A’a Jannart bazaki fara aiki daga yanzu ba, kwata kwata ma yaushe ne kika samu sauki, ki koma ki zauna ni zan karasa komai.” Jin abunda Momyn ta fad’ane yasa ta k’wab’e, fuska cikin sigar shagwab’a tace. “Dan Allah Momy kibari nayi aikin ko kad’anne Allah naji sauki sosai.” D’an Jim Mamyn tayi, saidai kuma ganin yanda Jannart din ta matsa yasa, ta bata bleending na pineapple. Haka kuwa suka shiga yin aikin suna hira. Bayan sun kammala ne kuma Jannart ta koma daki koda tayi sallahn Isha kwanciya kawai tayi. *Littafin TUBALI na kuɗine special Group 1k ne kacal karamin group kuma 500 ne kacal 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU sai ki turo min shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276, in kuma babu halin turawa ta banki ki sayi katin MTN ki copy number's ɗin katin ki turo min ta whatsApp number na. Babbancinsu a yawan posting ne, dan girman Allah da Manzonsa kada ki karanta min littafina in baki biya, in kin biya kuma kiyiwa Allah kada ki fitarmin da littafina domin ba kuɗin mallakansa kika biyaba kuɗin samun damar karanta littafin kika bada* Acan b’angaren Dr. Rayyern kuwa gaba daya sabgogin gabansa yake, musamman ma yau din da duk baisamu zama ba, Domin gaba ɗaya wuninsa acikin Hospital yayi sa, saboda wasu patients da aka kawo masa, masu heart attack yayi musu operation. Adangane da batun Barrister Kabir kuwa, tuni ya watsar da duk wasu maganganun da sukayi da Barrister din acikin kwandon shara, impact ma shiya manta da wani batun maganan aure da aka fara. Domin ko yanzu daya dawo gida, bayan yayi sallan isha ko dinner bai tsaya yiba, kaitsaye ya wuce bedroom d’insa. Bayan ya sake wankane kuma ya dauro alwala, tare da kimtsa kansa cikin wasu tausassun fararen kaya. Chocolates d’insa masu dadi yaci har kusan Leda uku dake ledan ƙananane, kafun ya daura da ruwa. Ko takan laptop d’insa bai kuma biba, baccin gajiya ya daukesa. Ahakama Acan b’angaren Riyyam-nsra, duk wunininsa na yau acikin dakin hotel din Tahir Guest Palace yayi sa. Yayinda yake manne da wayarsa tsawon awanni kenan yanzu daya ke bad chat da wata sabuwar babe yar k’asar Morocco daya samu. Kwata kwata yarinyar bata da kunya, da kamun Kai. Wanda hakanne kuma yasa gaba daya Riyyam nsra ya susuce akanta, tare da b’ata duk wasu lokutansa na yau din akan yarinyar. Domin kuwa Koda Ramadan ya kirasa akan yazo suyi dinner, cewa yayi sai Gobe da safe zaizo suyi breakfast, saboda yau din bacci yakeji sosai. Akasin hakan kuwa saida yakai 2 am a online inda suke vedio chat da yarinyar ta Instagram. Wanda ko kaya babu ajikinta. Haka take zaune agaban wayarta single, Yayinda shi kuwa Riyyam keta susucewa akanta, Koda suka fara video sex chat, kusan gigicewa yayi, saboda yarinyar ta fisa tsaurin ido da iya iskanci sosai. Saboda zaucewar da Riyyam din yayi kuwa, harji yayi inama da ace yayi tsuntsuwa ya gansa a Morocco, manne ajikin abokiyar tab’ewar tasa. Haka dai ya hana idanunsa bacci. Har sai 3am kafun bacci ya daukesa ba kuma ibada yakeyi ba. *Washegari.* Kamar kullum kuma kamar Koda yaushe. 8 am dai-dai gaba ki dayansu zaune suke akan babban dining table din. Abba, Mamy, Rayyern, Ramadan da kuma Riyyam nsra wanda kallo daya zakayi mishi kafahimci cewar bacci bai ishesa ba, saboda yanda idanun nasa sukayi luhu-luhu. Rayyern kuwa da tun zamansu awajen yake lure da yaron, tass ya fahimci cewar yaron baya bacci da wuri, saboda wani dalili dayayi imani cewa ba dalili mai kyau bane. Abinci sukeci cike da nutsuwa. Yayinda Abba kuwa ya dago kansa ahankali ya kalli Riyyam-nsra. Cikin kuma son sake sanin da wanda suke tare. Ya ɗan gyara zamanshi tare da cewa. “Riyyam”. Da sauri ya amsa tare da kallon Abban. Shi kuwa Abba cikin tsareshi da ido yace. "Mahaifinka yana raye? shima Acan ethopian yake da zama ne?.” Abban ya kare maganar yana me kafe yaron da ido. Riyyam kuwa daya Kai loman abinci bakinsa, Jin abunda Abban ya tambayeshi ne yasa shi d’ago kansa Ahankali. spoon din dake hannunsa ya ajiye, lokaci d’aya kuma idanunsa suka cicciko da hawaye. Labb’an bakinsa ya motsa ahankali, cikin sanyi yace. “Mahaifina ya rasu.” Gaba daya dagowa sukayi duk suka kalleshi. Tare dajin wani irin matsanancin tausayin sa, musamman ma Rayyern da hakanan yaji wani iri acikin jikinsa. Riyyam-nsra kuwa da gaba daya zuciyarsa tayi rauni, hawaye ne suka gangaro daga cikin idanunsa. Wanda hakan yasa Ramadan share masa hawayen, cike da tausayawa yace. “Kayi hakuri kaji Riyyam, Allah yajikansa da Rahama, amma kadaina kuka, addu’a zaka nayi kaji.” Kai Riyyam-nsra din ya jinjina, kana cikin sanyi yace. “Insha Allah.” Ad’an fakaice kuma ya kalli wayarsa da tun dazu take aiki, saboda kiransa da Mammy d’insa tayi, sai kuma ya d’aga ab’oye batare daya fad’awa kowa ba. Daga can cikin wayar kuwa Mammy duk taji abunda yake faruwa. Wanda hakan yasa hawayen dake cikin idanunta gangarowa kan fuskarta, haka ma Zaiton dake gefenta, hawayene kwance akan fuskar ta, saboda itama taji abunda akace, Dan Mammyn nasu a hands free ta saka wayar. Shikuwa Abba har yanzu idanunsa akan Riyyam din yake. Sake gyara zamansa yayi, tare kuma da duban Riyyam din. Cikin sanyi da kuma dan bugun zuciyar da yakeji yace. “Allah ya jiƙanshi da rahma?” Idanu Riyyam din yadan lumshe, still cikin zubar da hawaye yace. “Amin Amin. Ameeeeeeen ya rabbil izzati ngd matuƙa da addu'arga.” Ayanzu kam gaba daya tsananin tausayi da kuma raunin yaronne ya rufe musu zuciya. Hatta Abba kuwa saida yaji zuciyarsa ta raunana. Nandai sukayiwa Baban Riyyam din addu’a, bayan sun kammala cin abincinne kuma kowannesu ya watse zuciyarsa cike da tausayin Riyyam-nsra. To ayau din dai kam gaba daya Riyyam din tare da Ramadan suka wuni har dare kuma suna tare. Inda washegari laraba ne kuma, Jannart taji saukin jikinta yasa ta shirya zuwa aiki, bayan ta gaya wa Daddyn nata cewa zata biya ta gidan Abba Kabeer. Daddy kuwa Ganin cewa Jannart din bata da wani ishashshen lafiya sosai ne, yasa bai hana ta zuwa gidan Abba Kabeer dinba. Jannart din kuwa Koda ta fito daga gidan nasu, kaitsaye gidan Abba Kabir ta nufa. Koda ta isa gidan tarba maikyau ta samu daga wajen Aunty Dijat, bayan sun gaisa ne kuma. Aunty Dijat din ta sanar mata cewa. Abba Kabir din na kiranta. Akaron farko kenan a iya tsawon rayuwarta, da taji wani abu mai kama da faduwar gaba, saboda Abba Kabir din ya kirata. Sunan Allah ta soma ambato acikin zuciyarta. Lokacin da ta isa bakin kofar bedroom din nasa ne kuma tayi knocking daga ciki aka bata izinin shigowa. Ahankali ta tura kofar dakin ta shiga bakinta dauke da sallama. Bayan Abba Kabir din ya amsa mata sallaman ne kuma yayi mata alama akan tazo ta zauna. Babu musu kuwa ta karaso ta zauna agabansa, Yayinda shikuwa yake zaune akan gado. Koda suka gaisa kuwa Almost 5 minutes haka suka zauna shiru. Ahankali kuma Barrister Kabir din ya gyara zamansa. Cikin kuma muryar dake bayyana iya gaskiyarsa, da kuma abunda ke cikin zuciyarsa da alamun umarni yace. *”Jannart Aurenki ya kusa fa zanyi miki Aure!”* Ya fadi mgnar cikin serious Wanda hakan yasa Jannart cikin wani irin yanayi mai rauni. Da harbawar zuciya cikin sauri Jannart din ta D....... By *GARKUWAR FULANI* 11/15/21, 7:21 PM - Auntyna: D'ago kanta ta kalleshi, da Idanunta wanda lokaci daya yanayin cikinsu ya sauya, musamman yadda maganar da taji ya fito daga bakin Abban ya daki zuciyarta matuka gaya. Abba Kabir kuwa ganin ta d'ago kanta ne yasa shima ya zuba mata ido, fuskarsa sam babu alaman wasa. Hakannne kuma yasa ta maida kanta k'asa, tare da d'an lumshe Idanunta, a hankali ta soma wasa da y'an yatsun hannunta. Yayinda takejin zuciyarta na dan bugawa. Dai-dai lokacinne kuma Aunty Dijat ta bud'e kofar d'akin ta shigo. Yanayin yanda tagansuda dinne kuma ya sakata sakin murmushi, tare da karasowa ta zauna  akusa da Jannart din. Kallon Jannart din Aunty Dijat tayi, tare kuma da bud’e bakinta da niyar yin magana. Ganin hakanne kuma yasa Abba Kabir saurin d’aga mata hannu alamun dakatarwa. Kallonsa Aunty Dijat din tayi, lokaci guda kuma itama ta sauke kanta k’asa. Hakanne kuma yasa gaba ki d’aya d’akin ya dauki shiru, babu abunda ke tashi sai sautin fitan numfashi, da kuma ajiyar zuciya da suke ta saukewa dukansu akai akai. Almost 10mn kafun Abba Kabir din ya sake d’ago Kai ya kalli Jannart, cikin tausayawa da kuma danne abundake cikin zuciyarsa yace. “Jannart kinji abunda nace, Ina fatan bazaki bijirewa umarnina ba kamar yadda kika al'ƙ’warta min.” Kai Jannart din ta d’ago Ahankali ta kalli Abban nata. Domin sai takejin maganganun nasa tamkar wani abu na daban, wanda bata tab’aji ko sanin akwai shiba. Ita dai tasan kalmar Aure, amma batasan haka kalmar kan zuwarwa mace cikin zuciyarta ba, batasan ya rayuwar cikinsa yake ba. Saidai koma meye ta sani bazata tab’a bijerewa umarnin Abban nata ba. Idanunta tasake mayarwa k’asa, kana kuma Cikin sanyi ta jinjina masa Kai, alaman “Eh.” Ajiyar zuciya mai k’arfi Abba Kabir din ya sauk’e, cikin kuma son sake tabbatarwa kansa amincewarta yace. “Jannart duk da cewar bani nahaifeki ba, amma matsayin uba nake awajenki, haka kuma Kallon y’ata ta cikina nake miki, wannan yasa bazan tab’a yi miki dole ba, shin kin amince da hukuncin dana yanke akanki?” Kanta ta sake jinjina masa, tare da bud’e Labb’an bakinta da takejin sun danyi mata nauyi a hankali tace. “Eh Na amince Abba, duk hukuncin daka yanke akaina dai-dai ne.” Numfashi Abba Kabir din ya fesar, tare da sake gyara zamansa. Kana yace. “Alhamdulillah naji dadi kwarai, Insha Allahu kuma yanzu akwai shirye shiryen da zamu fara, Domin banason lokaci ya ja da yawa.” Kanta ta d’an langwabar gefe, kana cikin yanayin sanyi tace. “To Abba, amma akwai abunda nake shiryawa, saboda ranan alhamis dinnan, zanyi wani program, Dan Allah Abba kabani dama, nasamu nayi shirin nan, Idan yaso daga baya komai ma sai ayi.” D’an murmushi Abba Kabir din yayi, tare da cewa. “Karki damu Jannart, shirin da nakeyi akannaki ma zaikai har bayan alhamis din, saboda haka kina da ishashshen dama na y’an wasu kwanaki.” Ajiyar zuciya ta sauk’e, tare da d’an sakin murmushi, saboda yanzu ta danji sanyi acikin ranta, Yayinda ta kuma k’ara samun hope akan cewar Lallai lailai bazata rasa aikinta ba. Aunty Dijat kuwa Kallon Jannart din tayi, Yayinda takejin tasananin tausayin yarinyar na ratsa zuciyarta. Lallai Tabbas tasan cewa, Jannart din bata san komai ba, aharkar auratayya sai abunda ta karanta a musulunce, wanda hakan yasa dole tana buk’atar mai taimaka mata. Sanin wasu abun a zahiriyar rayuwar duniya more Especially aure. Tasan Jannart cikekkiyar janitalauce, sabida kan haka aka reneta aka bata tarbiya, bin umarnin na gaba da ita, ya zama komai na rayuwarta bata da zabin kanta ko ra'ayinta sai abinda manyan ta suka faɗa, shiyasa suke sarrafa ƙwaƙwalwarta sun hanata yancinta sun dakufeta bata da wani abu sai amsar umarni daga garesu. Shiyasa ta kasance mai sauƙin kai da rauni kana ga tarin haƙuri. Wanda suke tasirin hanata tsayuwa kan ra'ayinta. Hannunta Aunty Dijat din ta rik’o, kana cikin tausasawa tace. “Naji dadi da kika amincewa maganan auren nan Jannart, Domin kuwa aure shine cikar farinciki dajin dadin rayuwa, acikin aure akwai abubuwa da yawa, farinciki da kuma akasin haka, amma ni naji ajikina cewar auren da zakiyi shine zai zame miki Tubalin farin cikin ki, Rayuwa zata sauya miki Jannart, zaki zamanto Mace mai y’anci, k’uncinki zai gushe, Yayinda haske zai bayyana acikin rayuwarki Insha Allah, sannan kuma ako da yaushe kiyi riko da addu’a, Domin abubuwa sukanyiwa bawa tsanani ne Idan yana wasa da addu’a, Addu’a makamin mumini ne Jannart, musamman gake, da ace bakya sakaci da addu’o’i da ko Junaid da yake yawan musgana miki, bazai tab’a samun daman fuskantar ki ba, saboda Allah zaina baki kariyarsa akoda yaushe.” Kai Jannart din ta jinjina, cike da gamsuwa da maganganun Aunty Dijat din kuma tace. “Insha Allah zanna rik’o da addu’o’i, Nagode sosai Aunty Dijat.” Murmushi Aunty Dijat din tayi, tare kuma da cewa. “Ba komai Jannart, Allah Ubangiji ya kawo mana saukin damuwarmu.” Da Ameen suka amsa dukansu, Yayinda Jannart din kuwa ta d’an kalli agogon dake daure a tsintsiyar hannunta, ganin lokaci yaja sosai ne kuma yasata, d’an mikewa tsaye. Tare da Kallon Abban nata tace. “Abba zan tafi wajen aiki kada nayi latti.” Kai Abba Kabir din ya jinjina, had’e kuma da mik’ewa tsaye yace. “Allah ya kiyaye hanya Jannart ya kuma Kareki aduk inda kike.” Da Ameen ta amsa, tare kuma da daukar jakarta, ta juya ta fice daga cikin dakin. Sam bata damu da maganan auren da Abban yace zaiyi mata ba, saboda batasan menene zata tsinta acikinsa ba, wannan yasa ko tambayan wanda sa’a aura mata din da kuma sunansa batayi ba, Ita dai ahar kullum tamkar rak’umi da akala take, duk inda aka jata zuwa zatayi. Saidai kuma tana da tabbaci cewa Abban nata bazai yi abunda zai cutar da ita ba. Koda ta fito compound din gidan, kaitsaye wajen motarta ta nufa. Tana shiga cikin motar kuwa Drivern yaja suka tafi, Yayinda kattin guard dinta suka rufa musu baya. Kaitsaye hanyar tashar tasu ta Arewa24 suka nufa. Jin yanda suka mik’i titi ne kuma yasa ta, jingina bayanta da jikin kujerar motar, tare da lumshe Idanunta. Ahankali ta sauk’e wani irin ajiyar zuciya, Yayinda kalaman Aunty Dijat kuwa suka shiga dawowa cikin kanta filla filla. “Aure shine cikar farinciki dajin dadin rayuwa, Aure shi zai zame miki tubalin ginuwar farincikin ki.” Abunda kwakwalwarta ke maimaita mata kenan, wanda kuma har yanzu ta kasa warware kalaman. Meyasa Aunty Dijat din tace aure zai zame mata tubalin farin ciki? Menene acikinsa? Wacce kalan rayuwa ce zatayi, har kuma ta samu farinciki bayan zata zaune akarkashin wani ne wanda bata saniba bai santaba. Ya yake irin Yah Junaid da Daddy ne ne ko irin Yah Azeez da Abba? Wai shin menene ma manufar auren nata da Abba bai gaya mataba? Tayiwa kanta duka way’annan tambayoyin da ko kusa bata da amsarsu, ba kuma ta da mai amsa mata su yanzu. Batasan komai akan hakan ba, ba ta kuma tab’a tunanin hakan acikin kwakwalwarta ba, shiyasa takejin duk wata kalma da ta shafi aure, amatsayin bak’on abu. D’an numfasawa tayi, tare da watsar da duk wani tunani dake cikin ranta, dai-dai lokacin kuwa suka iso babban parking space dake cikin tv station din. Bayan Baba Ado ya gama dai-dai-ta parking din motar ne kuma ta fito, kaitsaye ta nufi cikin gidan tv’ nasu. Ahankali take taka k’afafunta, Yayinda kowanni taku da zatayi yake dauke da jan hankalin mai Kallon ta. Azahirin gaskiya kuma awajenta tafiya takeyi normal, Yayinda duk wani mai Kallon ta kuwa, ke ganin tafiyar tata tamkar tafiyar hawainiya, saboda komai nata na dabanne, tana da wani irin tsarin halitta mai matukar burgewa, wanda kuma ko ita kanta batasan cewar tana dashi ba. Tura kofar babban office dinnasu tayi ta shiga bakinta dauke da sallama. Jin Sauti da amon zazzakar muryar nata ne kuma yasa, duk mutanen dake cikin office din juyowa suka kalleta. Wani dogon tsaki Asiya taja tare da kauda kanta daga kallonta. Ita kuwa Jannart Sam hankalinta ba a kanta yake ba, duk da irin Kallon da taga tanayi mata kuwa Amma bata damu ba. Fuskarta d’auke da murmushi ta k’arasa wajen, Aysha Lawal da kuma Salman wanda suke zaune awaje daya suna duba wasu takardu. Murmushi Aisha Lawal din ta sakar mata, tare da cewa. “Jannart Idi Saleh Dakata yau kinyi lattin zuwa wajen aiki, saboda haka sai munciki tara.” Murmushi mai kama da dariya Jannart din tayi, har saida fararen hak’waranta suka bayyana, hakan kuwa shiyasa dimples dinta duk suka lotsa. Kafad’an Aysha’n ta d’an buga, kana cikin muryata da babu hayaniya sosai tace. “Kai Aysha kwata-kwata fa mintuna 10, na kara akan yanda nake zuwa kullum.” “Eh duk da haka dai.” Ayshan ta fad’a tana murmushi. Jannart kuwa zama ta d’anyi agefe dasu, tare da dawo da Kallon ta ga Salman Wanda ya saki idanu da baki yana Kallon ta. Had’a idanu da sukayi ne kuma yasa shi saurin janye idanunsa daga kanta. Itakuwa Jannart batare da ta fahimci komai na daga Kallon da Salman din keyi mata ba tace. “Good morning colleague.” Gashin kansa ya d’an Sosa kana awayance yace. “Morning Colleague, fatan kin tashi lafiya ya jikin naki.” “Da sauki sosai, Domin nama warke yanzu babu wani abu dake damuna.” Jannart din ta fad’a tana me ajiye Jakarta, Adai-dai lokacinne kuma Hajia Rabi'ah da Aunty Fauziya D Sulaiman suka shigo, cikin sashin su Jannart din. Ganin Jannart din da sukayi acikin office dinne kuma yasa, Aunty Fauziya D Sulaiman sakin murmushi, kana cikin jin dadi da kamala da mutuntaka tace. “Masha Allah gaskiya Jannart ansamu lafiya, tunda har an fara fitowa office.” Murmushi Jannart din tayi, cikin kuma jin dadin kulawan da yan office din nasu ke bata tace. “Alhamdulillah my Aunty Fauziya naji sauki, kuma Ina saka rai da fatan cewa Insha Allah Gobe ma zan gudanar da program dina.” Kai Aunty Fauziyan ta jinjina, tare kuma da matsowa kusa da Jannart din sosai. Cikin yin k’asa da murya irin ta maganan sirri tace. “Masha Allah, amma Jannart kinaga kuwa Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara din zaizo.” Kanta tad’an langwabar tare kuma da juyawa, ta kalli Salman wanda shidinma kuma Kallon ta yake. Kai Salman din ya jinjina mata, cike dason bata karfin guiwa yace. “Karku damu Insha Allah Zaizo.” Ajiyar zuciya Aunty Fauziyan ta sauke, tare da daura hannayenta akan kafad’an Jannart din. Murya atausashe tace. “Karki damu Jannart, ko da ma ace bai samu zuwa goben ba, ai kina da sauran chance harna tsawon one week, Insha Allah kuma muna saka ran dacewa.” Kai kawai Jannart din tad’an jinjina, tare da komawa ma zauninta ta zauna, lokaci daya kuma duk jikinta yayi sanyi, domin tasan gobenne kawai last hope dinta, kasancewar bata da tabbacin cewa, wani satin zata kasance available, musamman ayanzu da Abba Kabir yake kokarin fara shirye shiryen b’oyeta. “Yah Allah Kabani sa’a.” Tafad’a k’asa-k’asa, tare da maida idanunta ta lumshe, saboda gaba daya yanzun ta karaya da komai. Salman kuwa daya karanci tarin damuwa akan fuskar Jannart din, ji yayi komai na Office din baya yi mishi dadi, duk yanda yaso ya daure zuciyarsa akanta kuwa baya tab’a iyawa. Haka yake d’agowa time to time yana satan Kallon ta. Itakuwa Jannart samma batasan yanayi ba. Aysha Lawal ce kawai take lure dashi, fahimtar abunda ke ran Salman din agame da Jannart dinne kuma ya sakata sakin murmushi. Batare kuma da tace komai ba taci gaba da ayyukanta. Haka dai Jannart ta kare gaba d’aya wuninta a office din, duk yanda kuma taso kawar da fargaban dake ranta ta kasa. K’arfe 5 dai-dai tayiwa su Salman da Aysha Sallama,kaitsaye ta wuce gida. Koda suka iso gidan nasu, haka ta fito daga cikin mota gaba daya duk jikinta asanyaye. Direct falonsu ta nufa, inda tana shiga cikin falon kuma wayarta dake rik’e a hannunta ta soma kara. Kallon ta ta mayar kan screen din wayar. Lokaci daya kuma murmushi ya bayyana akan fuskarta, saboda sunan Yah Azeez da ta gani. Picking call din tayi, tare da kara wayar akan kunnenta. Sallaman da tayi dinne kuma yasa Daga can b’angaren Yah Azeez ya amsa mata, tare da cewa. “My y’ar k’anwa Jannatuwa, bari na fara bada hakuri kafun ki shigo da korafin rashin kiranki da wuri da banyi ba.” Murmushi Jannart din tayi, tare kuma da dan shagwab’e fuska, tamkar Yah Azeez din yana ganinta. Tace. “ai saura kad’an nayi maka fushi Yah Azeez, kuma da baka kirani yau ba ko hmmm, ko kakira bazanji rarrashi ba.” Murmushi Yah Azeez din yayi, cikin tsananin so da Kaunar yar uwartasa yace. “I’m sorry Jannart wallahi aikine yayimin yawa kuma na kira sau biyu Mom ke ɗagawa tace kina bacci, yanzu ya jikin naki, Ina fata kinji sauki sosai.” Kanta ta jinjina had’e da cewa. “Naji sauki sosai Yah Aziz, Domin yau har wajen aiki naje, yanzu shigowa ta ma gida.” “Masha Allah Lallai jiki yayi kyau, To Allah ya kara afuwa, sannan kuma ki kara hakuri kinji Jannart, Insha Allah watarana sai labari, komai da Junaid keyi miki zaizo ya wuce, kuma Allah zai saka miki akan duk wani cutarwa da Junaid keyi miki, shima kuma zai ga sakamakon abunda ya aikata.” Idanunta ta d’an lumshe, saboda har acikin zuciyara taji sanyi da dadin kalaman Yayan nata, inama da ace shine akusa da ita ba Junaid ba, Lallai da taji dadin duniya, Domin ko ayanzu da baya kasar, yana iyaka kokarinsa wajen bata kulawa, da nuna tausayawansa agareta. Numfashi ta d’an fesar kana Asanyaye tace. “Nagode Sosai Yah Azeez, kuma Insha Allah zan kara hakuri akan wanda nakeyi.” Murmushin Jin dadi Yaya Azeez din yayi, Domin dama yasan tuncan k’anwartasu mai biyayyace, akan duk wani abu daka umurceta. Still cikin nuna kulawa yace. “Yauwa y’ar k’anwata, yanzu fad’Amin akwai wani abun da kike buk’ata ne, ko kud’i sai na tura miki ta account, ki saya duk wani abu da kikeso.” Murmushi tayi, hadi da cewa. “A’a Yah Azeez bana buk’atar komai. Domin last week Abba Kabir yayimin shopping, sannan kasan akwai kudi da yawa a account dina, ko salary na Idan anturomin bana sayan komai dasu.” Ajiyar zuciya Yah Azeez din dake kan wayan ya sauk’e. Nandai suka d’an tab’a hira kafun daga bisani sukayi sallama. Bayan ta kashe wayar nata ne kuma ta lek’a kitchine ko zata ga Momy, saboda tunda ta shigo babu motsin kowa agidan. Ganin kitchine din bakowane kuma yasa kaitsaye ta wuce bedroom dinta, saboda tanason yin wanka Tsarkin data samu. Akwai kuma wasu bayanai da zata had’a acikin system dinta. Acan B’angaren Dr. Rayyern Muhammad Mai-nasara kuwa zaune yake akan wata had’add’iyar royal chair, Yayinda yake sanye da wani had’add’en suit mai kalan ruwan k’wai ajikinsa. Daga gefe guda kuwa drinks da kuma Chocolate d’insa ne, sai kuma sabuwar wayarsa Iphone daya k’ara saya, dake rik’e ahannunsa. Inda kaitsaye ya shiga cikin contact d’insa, yana neman wani numbern tsohon abokinsa, Salisu, saboda yanason yiwa Salisu din ta’aziyya kasancewar yaji labarin rasuwar Baban shi. Yana cikin tsaka da duba contact dinne kuma, idanunsa suka sauk’a akan numbern Salman. Numbern da Idan bazai manta ba, sune wanda suke son ganinsa, ya kuma yi musu alk’awari zuwa. Saurin sanya hannunsa yayi ya dafe kansa, saboda sai ayanzu ne ma abun ya fad’o masa, gaba daya kwata kwata ya manta ma dasu. Sassanyar ajiyar zuciya ya sauk’e, tare da dan cije Labb’an bakinsa. Acikin zuciyarsa kuwa cewa yayi. “Allah Nagode ma daka tunatar dani, Allah kada ka bani ikon daukan al'k’awarin da bazan iya cika shi ba.” Jawo wayarsa yayi ya duba date da kuma rana. “Today is Wednesday, gobe ne al'k’awarin dana d’auka kenan zai cika, Insha Allah zanyi kokari naje, kodan yaronnan ya tsira da aikinsa, ya kuma samu abunda zai ciyar da iyalansa. Tabbas zanyi cancelling duk wani schedule dina na Gobe, har sai na samu naje tv station dinnan, bazan tab’a zama mai karya alk’awari ba Insha Allah bazan zama sanadin rasa aikinsa ba.” Ya fad’i hakan, yana me mik’ewa tsaye, tare kuma da d’aukan laptop d’insa. Kaitsaye ya koma wajen zamansa da yake na musamman, acikin katafaren office din da yake new company’n’ sa. Tahir Quest Palace. Riyyam nsra ne kwance akan makeken gadon dake dakin hotel din, wanda kuma yanzun gama wayarsa da Mammy da kuma Zaiton. Idanunsa ya d’an lumshe tare kuma da juyowa ya kalli, matashiyar budurwar dake kwance agefensa. Almost 1hour kenan yanzu da zuwan ta wajensa, wanda kuma itama sun had’u ne da ita anan Tiktok, Yayinda itama take cikakkiyar celebrity ce a Tiktok din, sannan kuma yar asalin Nigeria ce cikin Kano tayi shuhura a iya tiƙa rawa da bin waƙa, ga iya sa fitinennun suturu masu bayyana tsiraici hakan yasa kasuwarta ke ci. Idanu Riyyam din ya zuba mata, Domin kuwa Wannan shine Karonsa na farko daya fara mu’amala da wata mace y’ar Nigeria. Yarinyar dake kwance agefen nasa, kuwa ganin irin Kallon daya ke mata ne, yasa ta kashe masa Ido, tare da turo masa kirjinta gaba, wanda ko kaya babu ajikinta. Hakan ya faru ne kuma saboda sheke ayarsu da sukayi ita da Riyyam nsra din. Wani irin nishadi takeji acikin zuciyarta, kasancewar Riyyam din yayi mata hundred percent. Shikuwa Riyyam da baya gajiya da tab’ewa, hannunsa yasa ya shafo kirjinta, cikin kuma yin k’asa da murya hadi da kashe mata idanunsa yace. “Are you ready?.” Idanu ita dinma ta kashe masa, hade da jinjina masa Kai alaman she’s ready. Batare kuma da ta bari ya kawo kansa ba, ta hade bakinsu waje daya. Akaro na biyu kenan yanzun da suka sake shigewa duniyar Mazinata, duniyar da muninta ya wuce misali, kyamatacciyar duniya marar kyaun gani mai cike da masifu wanda duniyar TIKTOK ya zamo kawali'unsu. Bayan Riyyam din ya fito awankane kuma, ya shirya kansa cikin shigar daya saba yi ta kananan kaya. Wayarsa dake aje kan table ya d’auka tare da Kallon yarinyar da take kokarin saka kayanta. Bandir din fararen y’an one one k dake hannunsa ya cilla mata. Tare da d’alewa saman table din ya zauna, hakanan yakejin wani irin haushi, takaici, da kuma kunci acikin zuciyarsa, Yayinda yaji ko ganin yarinyar baya mason sake yi. Sometimes kuma baisan Meyasa yakejin hakan ba, aduk lokacin da yayi sex da mace, bayan ya samu biyan bukatarsa sai yaji duk duniyar ma batayi masa dadi. Itakuwa Yarinyar ganin da tayi mood d’insa ya sanja ne, yasa ta tattare kudin daya watso matan ta zuba acikin Jakarta. Bayan ta gama kimtsa kanta ne kuma tayi masa sallama ta tafi. Kamar kuwa dama jiran tafiyan nata yake, Domin tana tafiya shima ya rufe dakin. Bayan ya bada key din a reception ne kuma, kaitsaye ya fito daga cikin hotel din. Taxi ya tara, tare da fad’awa mai taxi din ya kaisa can cikin Nassarawa G.R.A din. Acan b’angaren Rayyern kuwa bai baro Companyn nasu ba, har saida ya kammala duk wani abu da yakeyi. Koda ya fito daga cikin company din kuma, kaitsaye motarsa ya shiga. Inda suka nufo gida. Isowarsu bakin gate din gidan kuwa, yayi dai-dai da fitowar Riyyam nsra din acikin taxi. Ganin motar Rayyern dinne kuma yasa Riyyam sakin murmushi, Bayan ya biya mai taxi din kudinsa ne kuma kaitsaye ya nufi cikin gidan. Kasancewar tuni motar Rayyern din ta shige ciki. “Baba Maud’o barka da gida.” Riyyam din ya fad’a alokacin daya bud’e karamar kofar gate din ya shigo. Baba Maud’o dake zaune kuwa, ganin Riyyam dinne yasa kashi sakin murmushi. Cikin kulawa kuma yace. “Yauwa barka dai Riyyam, tun safe yau baka zoba sai yanzu ka samu zuwa kenan.” Kai Riyyam din ya jinjina tare da cewa. “Eh, yau din nayi bacci sosai, kuma abokai na sun kawomin ziyara shiyasa Banzo da wuri ba.” Kai kawai Baba Maud’on ya jinjina, Yayinda shikuwa Riyyam kaitsaye ya nufi inda motar Rayyern yake. Yana zuwa wajen kuwa Rayyern na fitowa daga cikin motar. K’arasowa Riyyam din yayi, cikin sauri yace. “Oyoyo Hamma Rayyern sannu da dawowa.” Ya k’are maganan yana me rungume Rayyern din. Rayyern kuwa zame jikinsa ya d’anyi, tare da jinjina kansa alaman yauwa. Kamar zaice wani abu kuma sai ya fasa, kaitsaye duk suka nufi babban falon gidan. Yayinda afakaice kuma Rayyern ke Kallon Riyyam din, Domin hakanan yaji zuciyarsa na raya masa wani abu na daban, dangane da Riyyam din musamman kamshin turaren jikinsa da yaji wanda ya tabbatar turaren matane. Shigowarsu cikin falonne kuma yasa. Hankalin Mamy dana Ramadan harma da Abba ya dawo kansu. Ganin Rayyern dinne kuma yasa Abba sakin murmushi. Yayinda Riyyam kuwa ke biye dashi abaya. Karasowa cikin falon sukayi suka zauna. Inda Riyyam ya durkusa har kasa ya gaishe da Abba da Mamy, fuska asake duk suka amsa masa. Rayyern kuwa da ya Zauna akan kujeran dake gefen na Mamy. Kallon Abban nasu yayi tare da cewa. “Abba Mamy barka da gida.” “yauwa Rayyern barka dai ya company’n.” Abba ya tambaya. “Alhamdulillah Abba komai yana tafiya dai-dai an kusa gama haɗa komai.” Rayyern din ya fad’a yana me d’an gyara zamansa, tare kuma da sauk’e idanunsa akan, Riyyam wanda yaje ya manne da jikin Ramadan. “Masha Allah Allah ya taimaka.” Abba da Mamy suka hada baki wajen fad’an hakan. “Ameen.” Ya amsa still yana mai Kallon Riyyam. Kwarai so yake ya fahimci yaron, saboda yarda da abunda zuciyarsa ke gaya masa, yanaji ajikinsa cewar yaron kamar yana bin mata, musamman Idan akayi duba da irin rawar kan da yake dashi, ya cika rawar Kai da yawa. Janye kansa daga Kallon Riyyam din yayi, saboda bayason yana shiga abunda bai shafesa ba. Ramadan kuwa dake rik’e da wayarsa d’ago kansa yayi ya kalli Rayyern din. Cikin sigar lallashi hadi da roko kuma yace. “Yauwa Hamma Rayyern dama kai nake jira ka dawo, please Hamma Rayyern Dan Allah ka fito da mata kasamu kayi aure, kaga Abba yace bazanyi aure ba harsai kayi, ni kuma Allah yanzu aure nakeso nayi, bana son na rasa Rayhanna please Hamma na.” ya k’are maganan yana me d’an langwab’ar da kansa gefe. Shikuwa Rayyern d’ago kansa yayi, da kuma fuskarsa wacce ta sanja kala zuwa yanayin bacin rai. Wani irin kallo ya watsawa Ramadan din, cikin hade fuska yace. “Rufe min baki Ramadan kada fa ka tunzura min zuciya Kaine zaka tsaramin yanda zan tafiyar da rayuwata? Ko ka fini sanin abunda nakeyi ne, da har zaka zo kana cewa wai nayi aure! Kai ubana ne!? ko yayana!? kama fini sanin abinda ya dace kenan?.” Rayyern din ya k’are maganan cikin fad’a. Wanda hakan yasa Ramadan Dan sunkuyar da kansa, cikin yanayin sanyi kuma yace. “Ayyah Hamma Rayyern kayi hakuri Insha Allah bazan sake ba kaji kayi haƙuri.” Kai Rayyern din ya kawar, Yayinda Abba da Mamy kuwa suka kalli junansu. Ramadan kuma mik’ewa tsaye yayi, tare da kama hannun Riyyam-nsra suka fice daga cikin falon. Fitansu daga cikin falonne kuma yasa Abba d’ago Kai ya kalli Rayyern din. Yayinda su Ramadan kuwa suna fita, kaitsaye wajen Baba Maud’o dake zaune abakin gate suka nufa. Ganin su dinne kuma yasa Baba Maud’o sakin murmushi. Bayan sun zauna akan dogon bencin da Baba Maud’on ke kaine kuma. Baba Maud’on Ya kalli Riyyam-nsra tare cewa. “Riyyam ya mutanen can k’asar taku, da su Mammyn ka da Zaiton.” Murmushi Riyyam-nsra yayi, tare da gyara zamansa ya kalli Baba Maud’on cikin kuma jin dadi yace. “Munyi waya dasu dazu kowa da kowa yana nan lafiya, sunma ce na gaishe da kai, saboda na tura musu hotonka, har Zaiton tana cewa wai itama zata zo ka nad’a mata irin abunda kake sawa afuskarka, wai zatana boye fuskarta saboda Samarin dake damunta.” Yar dariya Baba Maud’o yayi, tare da jinjina kansa. Cikin jin dadi yace. “To shikenan Idan tazo zan koya mata yanda ake na dawa, ai rawani ne ba komai ba, nadashi kuma ba wahala.” “To Baba Maud’o nima dai ai watarana zaka koya min ko, sai naje na koya mata.” Kai Baba Maud’on ya jinjina alaman. “Eh.” Daga haka kuma suka ci gaba da hiransu. Ethiopian. Adai-dai lokacin ne kuma Mammy dake zaune akan sallaya ta kurawa, hoton dake kan screen din wayar nata idanu, wanda kuma hoton Baba Maud’o ne da Riyyam ya turo mata. Azahirin gaskia ba kuma tana Kallon hoton da wata manufa ko tunani bane. Kawai dai tana mamamkin irin shigar da taga mutumin yayi ne, saboda su anan basu tab’a Ganin irin shigar ba. Ajiye wayar nata tayi tare kuma da watsar da duk wani tunani dake ranta, kaitsaye ta mike daga kan sallayan ta shige kitchine. Acan falo kuwa Abba dake Kallon Rayyern d’an gyara zamansa yayi. Tare da fuskantar shi kana cikin yanayi masifa faɗa da kuma umarni yace. “Uhmmm RAYYERN kenan. Saboda kawai yace maka kayi aure shine kake daka masa irin wannan tsawan? Da ɗaga jijiyoyin wuya. To shi meyene laifinsa, saboda kawai yace ka cika martabarka, ka kuma raya sunnar Annabi Muhammad SAW shine, yayi laifi?”. Ya ƙare mgnar tare da tsareshi da idanun Da dole yasa RAYYERN yayi ƙasa da kansa. Shi kuwa Abba kwaffa yayi tare daci gaba da cewa. “Yoh wai kai azatonka da tunaninka haka zaka ta zama babu aure ne, saboda kawai kaga na zuba maka ido tsawon shekaru, kayi tunani da hankalin ka fa Rayyern, ayanzu Kai ba yaro bane, Domin kuwa kabawa shekaru 30 baya, shin kana tunanin banason yin aurenka ne? Ko atunaninka bana da buk’atar Ganin aurenka ne? To kasani duk da cewar nasan tabbas na sakar maka ragaamar komai, na tara maka ayyukan da sukafi karfinka, bawai Ina nufin ka zauna haka babu aure bane ba wurin aiki kawai nake son ganin kamalarka ba harda aure, Tabbas banajin dadi aduk sanda ka nuna cewar babu maganar aure kwata-kwata agabanka, kaine babba akan Ramadan, ya kuma zama dole kayi aure, Domin duk wani Namiji mutumcinsa da Darajarsa bata cika ko a idanun mutane, har sai in yana da aure, komin dukiya da mulkinsa kuwa, aure shine abunda ke maida Rabi ya dawo Guda, ka d’aga mutumci da darajarka ta hanyar yin aure, Allah dakansa zai dubi al’amuranka, amma ace akoda yaushe Kai baka da zance sai na cewar bakason aure...” *Albishirinku! Ma'aurata, GA GARKUWAR KU nan tafe muku da tsarabobi na musamman gareku ma'aurata daga cibiyar mgnin mata mai taken GARKUWAR MA'AURATA* NI DAI AYSHA ALIYU GARKUWA. Ina matukar mamakin wani irin lokaci da ya riske mu mai wahalallan fassara. Kullum dai magana daya ce, akan ma’aurata, fada, rashin jituwa, mutuwar aure, akan kuskure kalilan, rashin kula, rashin yi wa juna uziri. Toh wai duk me ya janyo hakan? Na zurfafa a tsananin tunani hakan ya tilasta min bincike mai tarin yawa wanda ya kai ni ga gano inda matsalar take? Shin yar’uwa ke macece amma kin san wacece mace ku? Kin san me ake kira mace kuwa? Mace ita ce matar da take zama iyali a wajan namiji ta zame masa bango, sanyin idaniyarsa, ta zame masa gata da farin cikin rayuwarsa ta zame masa ruwa abar kore ƙishinsa ta zame masa mayafi mai karesa daga gigitar kadaice, ta kuma dorar da mijinta kan turbar gaskiya, ta kashe masa jiki da salonta ta rikita shi da baiwa da ni’imar da Allah ya bata idan har ta san hanyar mayar da kanta sabuwa dal awajanta, wato kullun takasance masa tamkar amarya har ya kasa tantance daren amarcinsu da sauran dararen rakun rayuwar su. Wannan ita ce mace. Ina da wata saukakkar hanyar da zaki zama abar so da kulawa da soyayya a wajan mijinki ta hanya mafi sauki, 09097853276 hanyar ita ce ki gwada amfani da kayana na gyara ki gani, ina mai tabbatar miki da in sha Allahu sai kin dara da murna sai kuma kin gode min. Kayana kaya ne da aka yi shi da zallan itacanmu na gado marasa illa a cikin jikin dan adam musamman mace, kaya ne da suke taimakawa (sex hormones 😍) dinki. Misali kina kallon India😘, hollywood, Asian film🥰 kina ganin yanda mazansu ke nunawa matansu tsananin soyayya kamar su ba su kyautar ransu!? Saboda me hakan? Saboda suna sadaukar da lokacinsu wajan gyara jikinsu da kayan da ke tsattsafo da ni’ima cike da tsukewa, kayan nan kuma ana yinsu ne zallar magungunan gargajiya wanda ba su da illa domin haɗine na ingantattun itatuwa da yayansu. Ina baiwar Allahn da miji ke daure mata fuska babu hirar arziki? Zo ki ji yar’uwa zan baki gumbata da zallar gari wanda aka yi su da nagartattun itacen da ke da matukar amfani a jikin mace. Gubar ciko, gumbar tsalle dole, gubar da ba'a baiwa mai kishiya, garin maɗi, garin mallaka, tsumin goron tula, tsumin tsartai, tsumin maratsi, pala-pala butar sirri, kwanon k’asaitacciyar mace, furar mata madararta gareki Hajia takenta sha yanzu mgni yanzu, Ina mata masu fama da sanyi? Sanyin mara ki zo na hadaki da magani na na sanyi wanda yake wanke mara ya fitar da duk wata cuta da ke samun mazauni a wajan. Ina da ciccibi mai kyau. Ina da hadin amare mai kyau wanda zai gyara yarinya ya kankaro mata kimarta akwai hadin mai jego wanda muke yinsa na asali inada kekkyawan Hadi maida tsohuwa yarinya. Akwai daya bangaren wato *KAMSHI* Kimarki gyaranki da kamshinki. Matan da suka gane suka san yanda za su kankaro da mutunci su ne masu amfani da kayan gyara da kuma sanyaya jikinsu da kamshi, ina da turaren wanka da na bandaki na daki na jiki da na kaya dana tsuguno kamshin turarena na dabam ne mai sanyaya zuciyar wanda ya shaka ina da kayan kamshi na amarya da na maijego da na uwargida da dukkan macen da take kokarin mayar da kanta mai daraja a idon kowa ta zamo sarauni a idon mijinta, akwai shu'umar humra, sayan na gari maida kuɗi gida, banda karanta yayin gyara Hajia. Zaku iya samun kayyakina a duk garin da kike, zakiyi min mgn ta whatsApp number na 09097853276 domin yin zaɓinki, ko karin bayani, zaki tura kuɗin ta account na 0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU in mun gama mgna zan sa miki kaya a mota yazo duk garin da kike, in baki shirya saya yanzuba Please kada mu wahal da juna ki bari sai kin shirya kafin kiyi min mgn. 🤝🏻🥰😘 Daga taku AYSHA ALIYU GARKUWA *(GARKUWAR MA'AURATA)* By *GARKUWAR FULANI* 11/15/21, 7:21 PM - Auntyna: TUBALI 23 D’an gyara zamanta tayi, tare da sake fuskantar cameras din dake shooting fuskarta. Ajiyar zuciya ta d’an sauke tare da nemo jarumtarta dake suɓuce mata, cikin Taushi da kuma amon muryanta zakin tace. “Assalamu Alaikum Masu kallonmu, sannunmu da arzikin sake saduwa, acikin shirinmu mai farinjini wanda mukeyi Domin farincikin ku, wato Bak’onmu na Mako, To ayau dai shirin namu ya gam da katar yayi babban kamun gayyato muku wani babban bak’o, wanda nasan idanuwanku suna cike da dokin ganinsa. Wannan bako kuwa ba kowa bane face. Dr...!”. Sai ta kuma datse sunan tare da sakin murmushi. Wanda hakan yasa kab masu kallo suka ɗokanta da son jinnwayene baƙon makon. Mayafin kanta ta ɗan gyara tana mai jin harshen ta bazai iya furta sunansa ba, cikin nitsuwa ta tare da lumshe taci gaba da cewa. “Sanannen mutumin da sunansa yayi shuhura acikin kasarmu Nigeria dama wajenta baki daya, nasan da yawan masu kallo basu tab’a Ganin wannan bak’on namu ba. Dan yauce rana ta farko daya amsa gayyatar wata kafar sadarwa ta jarida, da TV. Alhamdulillah sai namu a yau. Kasancewarsa Babban Doctor kuma babban d’ankasuwa da duniya ke damawa dashi, saboda haka yau dai gamu gashi, zakuma mu haska mukushi, inda zai fayyace mana koshi din waye.” D’an tsagaitawa da maganan nata, tayi tare da juyowa Ahankali ta fuska ce sa. Cikin muryarta mai taushi tace. “Doctor barkanka da zuwa, barkanka kuma da shigowa cikin wannan tasha tamu mai Al'barka, da fari dai munaso ka gabatar da kanka ga masu kallonmu.” Numfashi ya d’an sauk’e, batare kuma da wani sakin fuska ba, ya dago da kansa ya d’an kalli cameran a fakaice, cikin muryarsa da ako yaushe yake kara bayyana asalin wanene shi yace. “Dr.Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara.” Ya k’are maganan atak’aice, Cikin kuma halin nitsuwa. Kai Jannart din ta jinjina, tare da hade yatsunta awaje daya, cikin tsananin kwarewa da sanin makamar aikinta tace. “Masha Allah to Dacta, yanzu dai ka gabatar da kanka awajen al’umma, saura kuma mu shiga cikin shirin namu ka'in da na'in,. Dai-dai lokacin kuma aka ɗan ɗauke fuskokinsu aka sa ɗan sautin tambarin tashar Arewa 24 din. Kana aka dawo dasu. Cikin nitsuwa ta ɗan kalleshi a fakaice kana a hankali tace. “Shin amatsayinka na cikakken Likita, wanda kasa keji dashi, wacce irin shawara zaka bawa al’umma dan kula da lafiyarsu da matakan kariyar riga-kafi?. Sannan kuma ya kake Ganin irin yanda al’amarin k’asarnan yake, ma’ana irin halin da al’ummar k’asar take ciki, da kuma irin k’alubalen da muke fuskanta more Especially wurin kiwon lafiyar kananan yara da mutanen karkara da tsofaffinmu, Sannan wani irin hanya da kuma mataki zamu bi, Domin mu samu nasara akan yaƙar cututtukan dake addabar al'ummar ƙasar mu? Then menene matsalarmu aharkar malaman kiwon lafiya?”. Kanshi ya ɗan kauda gefe tare da yamutsa fuska, ɗan gajeren tsaki yaja. Ji yadda yarinyar nan take zuba babu ƙaƙƙautawa kamar carbi ya tsinke ko numfashin bata ja. Ta wani jero min tambaya kusan goma, a dungule. Ni Radio ne ko ni parrot ne da zan iya haka. Duk yayi tunanin cikin second 5. Numfashi ya ɗan fesar kana cikin haiba da dakewar murya yace. “Privet Hospital!!! Sune matsalan kiwon lafiyar kasarmu. Domin sune suke dak’ushe asibitocin gwamnati, har suke zama ba masu inganci ba.” Ya fad’i maganan kai tsaye, batare kuma da wani dar ko shakka ba. Jannart kuwa Kai ta d’an jinjina, tare da sake rik’on wani farin card dake hannunta, saboda acikine duk wani tsare tsaren tambayoyin da zatayi masa suke. Kanta ta d’ago daga Kallon takardar da takeyi, still kuma Cikin muryarta da akoda yaushe take fitar da daddad’an sauti tace. “To Dakta. munji abunda kace. Kuma al'umma zata iya gamsuwa da hakan. Toh amma kamar wani mataki za’abi, Domin asamar da ingancin asibitocin Gwamnati da kiyaye lfy?.” Numfashi ya ɗan fesar a hankali kana yace. “Dole gwamnati ta tsaya ta gyara asibitotin ta, ta ingantasu hade da kawo nagartattun kayan aiki, da kuma kwararrun ma’aikata, baya ga haka kuma ta rika biyan likitotin isassun kudaden da zasu iya biya musu bukatunsu, saboda mafi akasari acikin kasar bawai Nagartattun Doctor’s dinne bamu da suba, kawai dai basa samun yanda suke sone, hakanne kuma yasa suke fita wasu k’asashwn suje su fara aiki Acan, ko kuma kowannensu saiya zaga gefe yaje ya bud’e asibitin kanshi, saboda baisamu yanda yake so a gwamnati ba, wannan dalilin yasa ayanzu asibitocin gwamnati suka lalace suka zama kara zube,, Domin anriga da ancire Tubalin abunda aka gina asibitin akai haka yasa duk mai ƙarfi da yar wadata bazaibi ta kan asibitin gwamnatin ba, wanda kuma da al'ummar ƙasa aka ginasu. Sannan yana da matukar muhimmanci ga iyayen yara suke kula da tsabtar jikin raya da muhalli da abinda zasuci domin shine babban rigakafi.” Ya k’are maganan yana me gyara zaman necktie din dake wuyansa. Sosai yayi masifar kyau yadda yake dan jujjuya fararen yatsunshi Inda Jannart kuwa ta ci gaba da cewa. “To Doctor yaya za’ayi agyara matsalar Government Hospitals din domin in ƙantasu ta yadda al'ummar ƙasa zasuje garesu da kekkyawan yaƙini!?.” Dan muskutawa yayi still kuma cikin rashin tsoro ko fargaba cikin yaƙinin da Kekkyawar manufa yace. “To Da farko dai asibitotin gwamnati abunda zai gyarasu abu maisauki ne!?”. Da sauri ta ɗan fuskanceshi tare da cewa. “Duk da lalacewar da sukayi gyaran mai sauƙin ne? Ta yaya ko kuma ta ina gyaran zai fito da sauki!?”. Cameras din ya ɗan kalla kana ya gyara zamanshi tare ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya cikin masakaicin amo yace. “Idan har gyara akeso ta yadda zasu in ƙanta tofa dole daga kan, Shugaban k’asa, Governors, Ministers, senator's har zuwa kan ciyamomin kana kama daga Sarki, Waziri, Galadima, Wambai, Chiroma, Durbi, Garkuwa, Ɗan buram, Majidadi, Ma'aji, dama duk wasu masu fad’a aji, na siyasa da masarautun gargajiya. suyi kokarin daina zuwa asibitotin kudi, ko fita kasashen waje Dan duba lafiyarsu, su tsaya su ingata asibitotin Gwamnati, ta hanyar dasu kansu asibitotin zasuna basu Kekkyawar kulawa, Ya zama asibitin da Sarki zaije. To shi fadawan sarki zasuje. Kana asibitin da shugaban kasa zaije ya zama shine na talakawa, ta hakane zai sa shugabanni su san halin da asibitocinsu suke ciki, da inƙancin likitocin da kayan aikin. Haka zai sa a kula da in ƙancin asibitocin. Domin duk wani asibitin gwamnati matukar akwai ingantattun Doctor’s da kayan aiki da watar tsabtacewa. Toh dai-dai yake da duk wani asibitin kudi, hakanne kuma zaisa asibitotin kudin su dakushe, su durkushe. saboda yawnacinsu bawai anginasu Dan taimakon al’umma bane, anginasu ne kawai saboda neman kudi irin na yaki haram yaki halal, tayanda talaka bazai tab’a amfana dasu ba sai dai su cika aljihunsu.” Da sauri Jannart ta juyo ta kalleshi. Ido cikin ido sukayi da juna, Bakinshi ya taɓe tare da yimata wani irin munafukin harara, hakane yasa tayi saurin yin ƙasa da kanta Kai ta jinjina, cike kuma da gamsuwa da kalaman nasa tace. “Tabbas maganarka tatafi Kan hanya mai kyau, sai-dai kuma amma baka ganin yin hakan zai dakushe mutane da dama, musamman ga masu privet hospital kamar yanda ka fad’a!!!.” Kansa ya d’an girgiza, sannan kuma akaro na farko da tun zamansa awajen ya dago kansa da nufin ya kalleta da kyau dan tambayar da tayi masa. Saidai ko secan daya bai dauka yana kallontan ba yakau da kansa gefe. In don’t care manner yace. “Hakan ba wata matsala bace ai, Domin bani da yakinin cewa yin hakan zai tauye musu hakkinsu”. Da sauri ta kuma cewa. “Toh kuma kake bada shawara a rushe asibitocin?”. Wani irin kallo ya ɗan watsa mata. Sabida ta mishi tambayar cikin gajin haƙuri irin nasu na ƴan jaridu. Dan bata tsaya taji ya dasa Ayaba. Koda yake haka suke. Yan jaridun suna jin daɗin jefowa mutun tambaya kamar sauƙawar aradu ko kuma titsiye. Cikin tsare fuska yace. “Dama meyake sawa su bude nasu asibitotin?”. Ya mata tayarma tare da tsareta da ido. Yar-yar haka taji tsikar jikinta na tashi. Haka yasa da sauri ta kauda kanta gefe. Shi kuwa kai ya jin jina tare da cewa. “Baki sani bako? To bari in gaya miki...” Ya kare mgnar yana mata hararan ƙasan ido kana yaci gaba da cewa. “Dama rashin samun isasshen abunda zasu rufawa kawunansu asirine, saboda sometimes acikin asibitotin Gwamnatin, gwamnati bata biyansu al'bashi akan kari, baya ga haka kuma bata basu isassun al'bashin da zasu dauki nauyin iyalansu sabida gwamnatin tayiwa malaman jinya dana makarantu riƙon sakainar kashi Alhamdulillah gwarama wannan gwamnati da muke ciki. Duk da haka ana buƙatar ƙari. Domin duk lokacin da Gwamnati ta fara biyansu isassun al'bashi, To ba wani abu da zaisa suje su bude privet Hospital toh ko sunje sun buɗewama wa zai je musu in dai asibitocin gwamnatin nada inkanci , Domin ak’asarnan ba yawan asibiti muke da bukata ba, ingancinsu kawai shine abun buk’atar mu, tayanda talaka da maikudi da fulanin daji zasu samu gamsashshiyar kulawa, batare da nuna wani banbanci ba!!!.” Ajiyar zuciya Jannart ta sauk’e, kana kuma cikin yanayin nutsuwa tace. “Mungode sosai Dr. inafatan kuma Gwamnati zataji shawarar daka bada kuma tayi aiki dashi, yanzu kuma zamu shiga babi na biyu. wanda ya shafi b’angaren kasuwanci kafin mu dawo nan a likitance. Yah Salam shine abinda ya faɗa a ransa. Sabida ya lura yau bakinshi sai yayi tsami sabida magantuwa da wannan fitinenneyar yarinyar take sashi. Kamar a tsakiyar kanshi yaji ta kuma cillo mushi tambaya. “Shin Dakta wacce irin shawara zaka bayar, agame da yanda sha’anin saye da sayarwa ya zama acikin k’asarnan, misali ta yanda ayanzu kayan abinci yayi tsada sosai, akullum wasu daga cikin yan kasuwa k’ara farashin kayansu suke, rayuwa tayiwa talaka tsada, manyan y’an kasuwa da kamfanoni sun had’e kai da baki waje daya, Koda yaushe farashin kaya hauhawa yake, tayaya ne za’a samawa al’umma sauk’i, musamman manoma, wanda sune ma suke noma abincin amma kuma Idan ya shigo kasuwa sai yazo yafi karfinsu, shin wacce shawara zaka iya bawa manoma?.” Numfashi ya dan fesar ta bakinsa, saboda yanda yaji labbansa sun soma gajiya da yawan motsasu da yake. Hakanne kuma yasa batare daya dago ya kalli ko cameran ba, saidai atausashe yace. “Shawarar da zan iya bawa Manoma itace, duk wani manomi Idan har ya noma abunda zaici, To kada yayi gangancin saidawa, har sai ya tabbatar daya ware ishashshen abincin da zai isheshi, har na tsawon wata shekarar da zai sake noma wani abincin, kafun nan sai yazo ya saida wanda zai sayar, saboda gudun kada ayi gaban mai haƙar rijiya. kai ka noma ka gama shan wahala, sannan kuma ka tattara ka sai dashi lokacin da yake araha, bayan y’an wasu watanni sai yayi tsada, ga kuma wanda kake dashi ya riga ya k’are ga damuna ta sako sama ruwa ƙasa ruwa, fita nemowar ma wata rana sai ya gagara, kaga kenan nakan daka saida shi zaka sake zuwa ka saya, akan farashi mai masifar tsada, kenan Kai Manomi kaine ka wahala a banza. Sannan kuma ya kamata manyan kamfanoni su dinga tausayawa talakawa, su daina yi musu irin wannan hawan k’awaran, zuwa su sai abincin manoma tun yana gona basu shigo dashi gari ba su kuma manoma ku farga da wannan sagegeduwar da akeyi muku. Sannan kuma su manoman kansu, su daina sayarwa masu manyan kamfanoni abincinsu tun yana gona, saboda wasu tun abunda suka noma yana yabanya suke saida shi, atunaninsu ko da ace abun da suka noma din baiyi kyau ba ko sanadin fari ko tsuntsaye ko kwari ko tsutsa, su dai sun samu kudi, da yawan mutane basu san al'barkar dake cikin kayan gonansu ba, saboda haka yana da kyau, ka dinga girbe abunka kana gyarawa da kanka, ka kididdige abinda ka samu ka ware na buƙatunka kafun ka mik’ashi ga wasu, sannan kuma duk wani manomi yayi kokarin saida abincin daya noma, akan farashi mai kyau, saboda ko yaya guminsa ya keci. Domin shi kadai yasan wahalar daya sha wajen noma ta, sannan yanzu Idan akayi dubi, gaba daya manoma da talakawa su suke shan wahala, musamman Idan aka shiga cikin damuna, haka komin ruwa da iska zasu tsaya neman abunda zasu rufawa kansu asiri suyi noma dan ciyar da al'umma duk kudinka fa, in manomi baiyi noma koda kuɗin ka bazaka samu abincin ba, shin zakaci kuɗin naka ne!!!?. Sannan ku kuma y’an kasuwa da kamfanoni masu karawa kayan abincinsu kudi, ba komai kuke ciba face *RIBA* haramtacciya, wanda kuma kowa yasan hakan ba abubane mai kyau bane, ga wanda suke sayan abinci su b’oye sai yayi tsada su fito dashi, suma duk Allah naganinku, kuma Allah da kansa baya tausayawa wanda baya tausayin na kasa dashi.” Kai gaba daya mutanen dake boye abayan cameras din suka jinjina, hatta MD da kansa shima ya samu cikakkiyar gamsuwa da bayanan da suka fito daga bakin Dr. Rayyern din. Ba kuma a iya cikin tv station din ba, har acikin gaba daya k’asar tamu, mutane da yawa dake Kallon Live Program din sun samu cikakkiyar gamsuwa, Yayinda kalaman Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara din ya ratsa zuk’atansu, ciki kuwa harda mafiya yawan manoma da suke kallon shirin, sabida Tashar Arewa 24 TV tayi zarran birni da ƙaune suna kallonta maza da mata manya da yara. Adai-dai lokacin kuma Abba Kabir zaune yake agaban tv yana Kallon shirin, shi kansa ya gamsu da kalaman Dr. Rayyern din, saidai kuma sosai zuciyarsa ta cika da tsananin mamakin, ganin da wanda Jannart din ke hira yau. Acan babban falon gidansu Jannart din kuwa, Alhaji Idi Sale Dakata, Dr. Lukman da kuma Alhaji Abdu Tababa ne, zaune sun zubawa babban TV plasma din dake cikin falon idanu. Wanda kuma yanzun akayi musu kira na musamman, akan su kunna tashar Arewa24 Dan Ganin hirar da akeyi da Dr.Rayyern din. Hakance kuma ta kasan a wurare da dama yadda wasu ke kiran wasu manyan ƙasar suna shaida musu su kunna tv tashar Arewa 24 TV suga program ɗin da akeyi da Dr Rayyern Mai-nasara. Jin abubuwan da Rayyern din ya fad’ane kuma, yasa Alhaji Abdu Tababa yin k’wafa, kana cikin takaici yace. “Amma dai wannan yaron anyi d’an iska, mai tsaurin ido, kujifa abunda yake fad’a, wai gwamnati ta rushe asibotin kudi ta inganta nata, Lallai yaron nan bashi da tsoro.” “To shi nashi asibitin na uban meyene, shegen yaro mai jajayen kunnuwa.” Cewar Dr. Lukman da yakejin kansa kamar ya kurma ihu yayi fiffige yaje ya shaƙo wannan yaron. Yayinda Alhaji Idi Sale Dakata kuwa ya rumste idanunsa, saboda shi ayanzu ko son Ganin yaron bayayi, hasalima gaba daya tunaninsa ya tafi ne akan yanda zai ga bayan Rayyern din, saboda al'ƙawari ne da yayiwa kansa cewar saiya b’atar da yaron daga Doron k’asa. Acan cikin tashar ta Arewa24 kuwa, Jannart ce ta sake gyara zamanta, batare kuma da ita ma ta d’ago kanta ta kalli Dr. Rayyern MAI-NASARA dinba tace. “Toh Doctor mu dan koma baya. Kaba da shawara akan cewar aduk’ar da asibitotin kudi, a tada na Gwamnati, ta hanyar zuba ingantattun likitoti da kuma kayan aiki, To irinku fa masu asibitotin kudi yaya zakuyi kaida ire-iren ka masu privet Hospital's, kodai kuma zaku dawo aiki a asibitotin Gwamnati ne! Ku watsar da naku asibitocin!!?.” Cikin gamsuwa da yarda da kai yace. “Kwarai kuwa, saboda ai hakan bawai gazawa bace, Indai muka had’e hannu da Gwamnati dan musamar da ingantaccen kulawa ga al’umma, To mu hakan kamar alkhairi ne agaremu, ba kuma najin hakan zai tauyemu ko ya ragemu da wani abu.” Ya fad’a atak’aice saboda ya fara gajiya da amsa tambayoyin yarinyar mai shegen baki cai-cai surutu tuni yawun bakinsa sun kafe. Hannunshi yasa ya ɗan shafa sajenshi har zuwa kan lips ɗinshi sabida ji yayi kamar bakinshin yayi tsawo ne da surutu. Jannart kuwa, again cikin sanin makamar aikinta tace. “Amma kamar baka goyon bayan duk wani privet hospital, in na fahimceka. Kuma naga kaima kana da naka hospital din, wanda kuma bana gwamnati bane, ya akayi to hakan ta kasance? meyasa baka had’a hannu da Gwamnatinba!? kun ingata Koda asibiti daya ne!!!?”. Wannan Tambayar ta saka duk magautan Dr. Rayyern Mai-nasara dake Kallon tv suka saki Murmushin mugunta, saboda atunaninsu yarinyar ta kawosa makura inda bazai iya amsa tambayoyin nata ba Alhaji Idi Saleh Dakata kuwa. Saida yaji tamkar ya shiga TV ya goya ɗiyar tasa Jannart, sai yakeji kamar dan su tayi mishi wanna tambayar dan ta kure musushi. Dr Lukman kuwa hannunshi ya dunƙule tare da jinjinawa Jannart harda yimata alamar kiss dan masifar daɗi. Ita kuwa Jannart batama san sunayi ba, kuma bada wata manufa tayi tambayarba sai dan dacewar hakan tunda tasan yanada asibitin. Shikuwa Rayyern ko ajikinsa baiji wani abu ajikinsa dangane da tambayar da Jannart din tayi masa ba, hasalima Dan gyara zamansa yayi, cikin kuma kwarin guiwan da ako yaushe yake tare dashi yace. “Banyi karatun likita Dan yin aiki akarkashin wani ba, asali Tubalin karatuna shine Idan na kammala na raya asibitin, dake gine tun kan zuwata duniya. saboda amfanar al’umma, bawai iya mai kudi ba kawai harda talakawa, saboda babu wani wanda, asibitin Mai-nasara Hospital yafi karfin zuwansa, koda kuwa bashi da karfi, Mai-nasara Hospital muna da foundation na taimakawa marassa karfi dashi mukeyin dukkan taimakon daya dace, sannan kuma Mai-nasara Hospital bawai irin asibitotin nan ne da kowa ya sani ba, Ina da confidence akan Hospital dina, ako ina kuma zan fada batare dajin na fadi ba daidai ba!!!.” Kai Jannart ta jinjina, saboda ayanzu kam amatsayinta na y’ar jarida ta gamsu da duk kalaman mutumin, musamman da ta fahimci with full confidence yake magana, ba irin na wasu mutanen ba, da mafi yawancin maganansu Kame kame da kuma k’aryane. Domin sometimes ma suna fad’an karyane Dan su kare kawunansu daga titsen yan jarida. Daga can gefe kuwa, Asiya ce dake tsaye take ta aikin bankawa Jannart d’in Harara. Yayinda takejin wani irin kuna da radadi acikin zuciyarta, Lallai Tabbas taso ace itace ta samu wannan damar, taso ace yau itace akan stage din tare da mutumin da kyau, nutsuwa da kuma haibarsa suka matuk’ar tafiya da hankalin ta, kana kuma mutumin da take ganin cewa, samun daman magana dashi ma wani matakin nasara ne. Kamar kuwa yanda Asiya ke jin tukukin bakinciki acikin zuciyarta, haka ma Dr Lukman, yakejin kamar ya shiga cikin tv’n ya shak’o wuyar Dr Rayyern. Abunda yasan bazai taba samun daman aikatashi ba a gaske kenan. Kallonsa ya mayar gasu Alhaji Idi Sale Dakata, cikin takaici yace. “Lallai wannan Dr Rayyern din shege ne, ko ta Ina so yake ya tauyeni, bakinsa baya tab’a mutuwa, kowacce tambaya akwai amsarta acikin kansa.” Murmushin daya fi kuka ciwo Alhaji Idi Sale Dakata’n yayi, cikin takaicin daya lullub’e zuciyarsa yace. “Nan kusa wannan bakin nasa bazai sake motsawa ba, wannan alk’awari ne na daukawa kaina.” Murmushin Jin dadi Dr Lukman da kuma Alhaji Abdu Tababa sukayi, saboda sanin hali irin na Alhaji Idi Sale Dakata da sukayi, Domin sunsan duk abunda yace zai aikata saiya aikata Tabbas. Ab’angaren Gidansu Rayyern kuwa, Abba Mamy, Ramadan da kuma Riyyam-nsra ne zaune afalo suna kallon shirin, gaba daya sun bada hankalinsu akan shirin, musamman ma Abba, da tunaninsa ya rabu izuwa wani waje na daban. Kallon Rayyern da kuma yarinyar da takeyiwa Rayyern din tambayoyi yake baya ko k’yaftawa, Yayinda acikin zuciyarsa yakejin wani irin abu na daban. Su Ramadan kuwa Hamman nasu suka tsurawa ido,suna mai jinjina kawunansu saboda irin amsoshin da Hamman nasu ke bayarwa, yana matukar ratsa zuciyarsu, acikin zuciyarsu kuwa babu wanda bai yaba da irin kyawun yarinyar da takeyiwa Rayyern din tambayoyi ba. Jannart kuwa, akaro na barkatai ta d’ago ta kalli camera’s din dake haska su, mike din dake gefenta ta gyara, tare da cewa. “Kamar dai yanda kuka sani, ayanzu zamu bud’e layukan wayoyinmu saboda, masu kira. Dan fadar ra’ayoyinsu da tambaya, ga numbar layin namu kamar haka... Tana gama fad’an numbers dinne kuma ta kunna wata waya mai kaman telephone dake aje agabansu, kan wani had’add’en table. Aikuwa kaman jira ake sukunna layin saiga kiraye-kiraye suna shigowa. Wanda manyan mutane-ne suke kiran. Numfashi ta ɗan fesar tare da gyara zamanta. Kana ta ɗan kalli wayar da wani kiran ya kuma shigowa tun kan ta ajiyeta. Picking call din Jannart tayi, tare kuma da latsawa tasa wayar a hands free. Cikin zazzakar muryarta tace. “Assalamu Alaekum.” Daga can b’angaren aka amsa mata, da murya irin ta manyan mutane. Jin hakanne kuma yasa ta cewa. “Barka da shigowa filin bakon mako.” “Yauwa Barka dai”. Aka faɗa daga daya sashin cikin girma. Ita kuwa Jannart lumshe idonta tayi tare da cewa. “Ko zamu iya sanin waye akan layi?.” “Sunana Alhaji Abubakar Ginsau S.A protocol na gwamna, nakira ne kuma Domin na jinjinawa babban Bak’o DR. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara, agame da maganganu masu amfani daya fad’a, Insha Allahu kuma maganan zata isa ga kunnen way’anda ya kamata suji, sannan muna godiya k’warai matuk’a, da irin shawarwarin daya bayar.” Kai Jannart ta jinjina, tare da dan satan Kallon Dr Rayyern din, wanda ya kauda kansa gefe, kamar baiji ana yabonsa ba. “Girman kai rawanin tsiya.” Tafad’a acikin zuciyarta, Yayinda afili kuwa cewa tayi. “To S.A protocol muma godiya muke sosai, sannan bakon mu Dakta shima yana godiya.” Daga haka kuwa kiran S.A din ya katse, wani kiran kuma ya sake shigowa. Cikin tashin hankali Dr Lukman ya mik’e tsaye, tare dasa hannunsa ya dafe kansa, zuciyarsa cike da takaici yace. “Lallai wannan yaron ya shallake duk wani tunani na, ba a banza ba ake kiransa da Mai-nasara ba, tunda gashi yayi sara akan gab’a, daga maganansa har S.A da kansa ya kira, ya kuma shaida cewa maganar zata tafi har wajen governor, wannan wanne irin Dan iskan yaro ne? Mai sa'a”. Cikin tsananin takaici tsana Alhaji Idi Saleh Dakata ya fesar da numfashi tare da cewa. “Ai yamafi Dan iska wannan yaron da kake gani Dr Lukman, shegen yaro ne kwance-kwance yake mana, da sannu Idan bamu tashi ba, duk sai yabi ya sare mana duk wani reshen mu, b’arna babba yake aikata mana, batare da ko damuwa da hakan yayi ba, Tabbas kuma ya kafu iya kafuwa, da wayannan kalaman nasa masu ratsa zuciya yake yaudarar mutane, waishi ala dole mai tausayin talakawa, yana abu tamkar Dan siyasan da yake barar neman kujerar takara, hmmmm Lallai zanyi maganin wannan yaron, zan kawar dashi kamar yanda na kawar da way’anda suka fishi tsauri a baya.” Alhaji Idi Sale Dakata ya ƙare mgnar yana me sakin zazzafan numfashin takaici. Yayinda Alhaji Abdu Tababa kuwa yace. “Lallai kawar dashi daga doron k’asa shine hanya mafi a’ala, Idan ba haka ba kuwa duk sai ya fito damu waje cikin rana daga gidajenmu.” “Hakan bazaiyi wuba kuwa.” Alhaji Idi Sale’n ya fad’a yana me mikewa tsaye. Yayinda acan gidan su Rayyern kuwa, har yanzu su Abba basu matsa daga gun tv’n ba. Sunanan zaune kowannensu dauke da farincikin, irin nasaran da Rayyern din ke samu. Haka ma agidan Barrister Kabir har yanzu shima yana zaune agaban tv’nsa. Dai-dai lokacin da ake cigaba da haska shirinne kuma, Aunty Dijat ta fito daga daki. Zama tayi akusa da mijinnata tare da soma kokarin had’a masa coffee. Kallon ta Barrister Kabir din yayi, kana cikin tausasa murya yace. “Dijat kalli tv kiga, Jannart da matashin saurayin nan dake zaune agefenta”. Da sauri ta miƙa mishi cup ɗin tare da zubawa tv ido tare da cewa. “Masha Allah”. Kurban coffee'n yayi tare da cewa. “Sundace ko?.” Ware ido Aunty Dijat din tayi ta kalli tv’n, dai-dai lokacin kuwa aka sake matso da fuskokin Jannart dana Rayyern din kusa. “Masha Allah, ai kuwa Abban Hafeez matukar dacewa ma sukayi, kyau da kyau kenan.” Murmushi Barrister Kabir din yayi, tare da gyara zamansa a takaice yace. “Shine mijin dana zab’a mata, kuma shine wanda zata aura amma batare da ta sani ba.” Ya fad’a yana me karb’an coffee din da aka had’asa masa. Idanu Aunty Dijat ta d’an zaro waje, cike da tsananin mamaki hadi da zallar farinciki tace. “Allahu Akhbar, Lallai girman Allah iko da buwayarsa tana da yawa, Masha Allah Lallai Jannart ta dace da hazik’in Namiji kuma jarumi, mai dauke da nagarta, Tabbas ka cika Uba nagari, ai kuwa zamusha biki yaushe ne Auren?” Murmushi Abban yayi, tare da girgiza mata Kai, Ahankali kuma yace. “A’a bayanzu zan gaya miki ba, abun namu sirrine.” *GARKUWAR taku ce dai MA'AURATA, da masu shirin aure, da masu jego, da yan gayu masu son k’amshi kece raini, da gyaran da zaike maimaita muku dararen forkon kuruciya* Ko kunsan Jikinmu na da sinadaran hormones da suke taimakawa dan’adam akan komai musamman lokacin da mace take mu’amalar aure da mijinta. Mafi akasari wannan hormones din ne ke samun matsala ko su yi sanyi koma su daina aiki kwata-kwata shi ne dalilin da zai sa mace tace bata jin sha’awa ko bata san dadin aure ba. Albishirinku ina da kayan da ke taimakawa wannan sinadaran du dawo aiki tukuru don karkato miki da kimarki wajan mai gida sannan su taimakawa wannan sinadaran hormones dinki su dinka secreting din ni’ima wadatacciya da zata taimaka miki ki gamsu mijinki ya gamsu fiye da tunaninki. Note: Kayana ba sa tsinka ruwan ni’ima suna dai taimakawa hormones dinki ne su tsattsafo da ni’imar musamman wacca cutar sanyi ko dattin mahaifa ya dankarar da su ya hana su yin aikinsu yanda ya kamata. Haka zalika idan kina da kyau ki kara da wanka. Zaki iya amfani da magani na na gargajiya wanda zai gyara miki sex hormones din kullum ki kasance cikin humidify wato cikin damshi mai albarka kamar yanda ake son mace. Yana gyara miki mara. Sai kamshi. Hajiyata daure ki fara amfani da turarena ki ji irin salon kamshin sa salo ne da zai daidaita ki da mijinki ya kankaro miki da kimarki a wajansa. Siyan na gari mayar da kudi gida. Ga masu buƙata ga number' wayata wanda nake whatsApp dashi 09097853276 kimin mgn ta whatsApp in har kin tabbatar kin shirya saya mu dai-dai ta, kayana ba ƙanana bane, shiyasa bana harkan karanta, muddin kinsan baki shirya sayaba Please kada kiyi min mgn ki bari sai kin shirya kuɗinki a hannu, ba ina nufin kayana bana talaka bane, no akwai ƙananan set na masu karamin karfi, banson aimin mgn a ɓatamin lokacin aiyukana a shirme baki shiryaba. Shine karantan da bana so. 0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU. In kin shirya ga number ta ga kuma account number ta wanda in mun gama mgn zaki turo kudin ki, kana insa miki kaya a mota, duk ƙasar da kike kayana zaije gareki, amman fa in kinada dalilin zuwan nasune🤝🏻sayan na gari meda kudi gida. GARKUWAR MA'AURATA By *GARKUWAR FULANI* 11/15/21, 7:21 PM - Auntyna: Murmushin Jin dadi Aunty Dijat din tayi, kana cikin sakin fuska tace. “Alhamdulillah nidai ko yaushene ma ina jira.” Barrister Kabir dinma murmushi yayi, batare kuma daya sake cewa komai ba, ya cigaba da shan coffee d’insa. Acan cikin tashar kuwa, zuwa yanzu kira na 15 kenan Jannart din ta amsa, wanda kuma daga kan kira na 15 dinne ta katse layin gaba d’aya, tare da d’agowa ta kalli cameras din dake jere agabansu. “To masu kallonmu laifin dadi dai ance karewa, Domin naga lokaci yana daga mana hannu, saboda haka duka duka anan muka kawo k’arshen shirin namu Na Bak’on Mako, sai kuma wani sati Idan mai kowa mai komai ya kaimu, Insha Allah zamu sake zuwar muku da wani bak’on na musamman.” Dan Juyowa tayi ta kalli Rayyern dake zaune, Cikin kuma sakin fuska kamar yanda ta sabayiwa kowa tace. “Doctor ayiwa masu kallo da sauraronmu sallama.” “Assalamu Alaikum.” Dr Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara din ya fad’a atausashe, saboda yasan izuwa yanzu duk su Abbansa suna kallonsa. Jannart kuwa juyowa tayi ta fuskanci Camera hadi da cewa. “To masu kallonmu duka duka anan muka kawo k’arshen shirin namu, tare da babban bak’onmu”. Ta ƙare mgnar da juyowa tana kallon Dr Rayyern. Numfashi ya ɗan fesar tare da cewa. “Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara”. Gyara zamanta tayi tare da cewa. “Sai kuma ni dana shirya na kuma gabatar JANNART IDI SALE DAKATA. Nake, mana fatan mu hade awani sati Idan Allah ya kaimu a huta gajiya.” Cuttt haka masu d’aukan shirin suka katse tare da kashe cameras dinsu. Dai-dai lokacin ne Kuma anan gidansu Rayyern din Zuciyar Abba tayi wani irin bugawa, saboda sunan Yarinyar da yaji acikin kunnuwansa. “Jannart Idi Sale Dakata!!”. Abba ya maimaita sunan acikin zuciyarsa, cikin sauri kuma ya d’ago da kansa ya kalli Mamy, wacce ita dinma shi take kallo, fuskarta dauke da tsananin mamaki. Atare kuma suka sake maida kallonsu ga tv,n. “Idan har sunan da yarinyar ta fad’a shine sunanta na gaskiya, To Lallai kuwa, wannan itace yarinyar da Barrister Kabir yazo musu da maganarta.” Abban ya fad’i haka azuciyarsa, fuskarsa cike da tsananin mamaki, hadi da tu’ajjudin faruwar hakan. Tuno wani abu da yayi ne kuma yasa Lokaci daya ya saki wani irin murmushi, mai dauke da tsananin jin dadi, hadi da cin nasara. Tabbas ayanzu ya sake gaskatawa, cewar Nesa tazo ta kusa. Acan TV station din kuwa Zumbur haka Dr Rayyern din ya mik’e tsaye, wanda hakan yasa cikin sauri MD da kuma sauran assistance managing director hadi da manyan masu muk’amai na tashan suka nufo wajen Rayyern din kaitsaye, hannayensu suka dinga mik’a masa daya bayan daya suna gaisawa cikin mutuntaka. Inda MD da farinciki yasa bakinsa kasa rufuwa yace. “Mungode Kwarai Dr. Rayyern, Allah Ubangiji yasa kafi haka, nida sauran ma’aikatan wannan tasha, muna godiya agareka, daka samu daman zuwa wannan tasha. Tabbas zuwanka ya sake daga darajar tasharmu.” Yar sauk’ak’ekk’iyar Murmushi kawai yayiwa MD’n, Yayinda MD kuwa yasa a daukowa Dr. Rayyern din kyauta ta musamman, wanda sukayi dan nuna godiyarsu agaresa. Salman, Aysha Lawal da kuma Aunty Fauziy D Sulaiman dake gefe kuwa, hannayensu suka d’agawa Jannart alaman jinjina, kowannensu fuskarsa cike da farincikin, irin nasaran da Jannart din ta samu, Domin kuwa ta kafa tarihin da akab gidan television’s din dake Nigeria babu wanda ya tab’a kafawa. Ta kawo musu babban hazikin Dan kasuwa kuma Doctor, mutumin da kowa yake fatan ganinsa, yau gashi Jannart din ta kawosa ta kuma bayyanawa duniya fuskarsa, daya jima yana b’oyeta. Murmushi Jannart din tayi musu, tare kuma da k’arasowa ta kalli Salman, wanda azahirance yana cikin tsananin farinciki, akasin hakan kuwa, shine Sam bayajin dadin zuciyarsa, saboda tun zaman Jannart da kuma Dr. Rayyern din daya gani awaje daya, yaji zuciyarsa ta karye, badan komai ba kuwa saidan tsananin matching din da yaga sunyi, sosai suka haska tamkar wasu taurari, sai kuma ayanzun ya sake tabbatarwa da kansa, cewar kwata-kwata ma Jannart Dakata ba sa’ar sa bace, Jannart matar manyan mutane ce. Kana kuma Jannart zara ce acikin taurari, furta wani abu daya shafi so agareta, kuwa tamkar karambani ne, saboda ya sani bashi da wannan matsayin. Haka dai jikinsa adan sanyaye ya juya suka rufawa su MD din baya, wanda tuni sun nufi hanyar waje, Dan raka Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara mota. Cikin masu rakiyan kuwa harda Asiya, wacce takejin kamar ta fashe da kuka, ko tasa ihu. Badan komai ba kuwa, saidan ta samu ko kallo daya ne Dr. Rayyern din yayi mata. Jannart kuwa kaitsaye Office dinsu ta wuce, batare da tabi yan rakiyar ba, Sam ita rakasa ma baya gabanta, hasalima mamaki take akan yanda taga, y’an Office din nasu suna karramasa, Tabbas Koda ga wahalan da tasha wajen nemansa, tasan cewar shidin babban mutum ne. D’an tab’e bakinta tayi alokaci da ta samu waje ta zauna. Hakanan takejin zuciyarta wasai, tamkar an zare mata wani mashi dake sukanta. “Alhamdulillah Allah, Kai katsaramin komai, yanzu bazan rasa aikina ba, bana kuma da wata fargaba, Thanks for everything Allah.” Ta fad’i hakan abayyane Cikin kuma tsananin farinciki, dajin dadi. Saboda duk wata fargabanta yanzu ya yaye. Acan compound din tv station din kuwa, har wajen mota su MD suka rako Dr. Rayyern, bayan sun bashi kyautar karramawa. Kasancewar kuma tun kafun su isa, Hadi'nsa ya bud’e masa murfin motar tasa ne, hakan yasa yana zuwa batare da wani b’ata lokaci ba ya shiga ya zauna. Still harya rufe murfin motar kuma godiya su MD sukeyi masa, tare dayi masa fatan sauk’a lafiya. Anutse kuwa Hadi yaja motar suka fice daga cikin gidan tv’n. Fuska Asiya ta had’e tamkar zata had’iyi zuciyarta haka takeji. Lallai tayi takaicin wannan ranan, saboda ko kallo daya bata samu daga wajen Dr. Rayyern din ba, hasali mai irin halittarta ma baisan tana wajen ba. Dan Kallon kanta tayi, can cikin zuciyarta kuma taja tsaki, tare da cewa. “Tayaya ma zai kalleni, tunda akwai irin waccar mayyar aduniya, natsaneki wallahi Jannart natsani ma Koda ganinki, saboda ke ne zaman office dinnan ya fara yimin kunci, kinzo kin hanani sakat, wai kawai saboda kina da kyau, mcheewww.” Tak’are maganar nata da jan tsaki tare da juyawa ta koma Cikin office din, dan zuwa yanzu ita kad’ai aka bari awajen. Acan cikin Office din kuwa, MD dakansa ya shigo cikin Office din su Jannart din, tare da bud’e hannayensa ya soma tafa mata. Aikuwa Ganin haka yasa duk sauran ma’aikatan suma bud’e hannayensu suka soma tafa mata. Cike da jinjina hadi da yaba k’wazonta MD yace. “Congratulation Jannart, Lallai kin cika hazikar yar jarida, na kuma jinjinawa kwazonki, Tabbas samun irinki acikin aikin jarida abune mai kyau, ayau ta sanadiyarki tasharmu ta sake daukaka, kin shammace mu Kwarai, dole ne mu baki lambar yabo, zaku ma muyi miki karramawa ta musamman.” “Kwarai kuwa Jannart hakika kinyi Namijin kokari, Tabbas kin cika hazikar Mace mai kishi da kuma son aikinta congratulations.” Cewar Aunty Fauziya D Sulaiman. Jannart din kuwa murmushin daya bayyana kyawawan hakwaranta tayi, cikin tsananin jin dadi tace. “Congratulations to you all my colleagues, Domin duk wannan nasaran nasa meta ne da k’arfafawar guiwanku, musamman Salman, Thank you so much Salman.” Murmushin Jin dadi duk sukayi, Yayinda Salman kuwa ya sunkuyar da kansa kasa yana murmushi. Asiya dake gefe kuwa ji take kaman tayi hauka, tsabar k’unci takaici da kuma bak’in Cikin daya cika zuciyarta. Haka dai suka ci gaba da tattaunawa atsakaninsu, Yayinda fuskar kowannensu ke dauke da tsananin farin ciki. Amma banda na Asiya da har hawayen takaici saida suka tara. MD kuwa yau din da kansa yasa akayi musu order’n delicious food, tare da kayan drinks. Anan cikin babban falon da suke ajiye baki, suka gudanar da d’an kwarya kwaryan party. Inda kuma sukayiwa Jannart din tanadin Karin matsa yi na musamman. Bayan sun gama yar kwarya kwaryan Partyn nasu ne kuma ta dau Jakarta Kai tsaye ta wuce, gida zuciyarta cike da tsananin farinciki. Yayinda daga can b’angaren Dr Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara kuwa, daga tv station din kaitsaye gidansu ya nufa. Suna isa bakin gate din kuwa Baba Hadi ya danna horn, cikin sauri da kuma azama Baba Maud’o ya karaso ya bude musu gate din, direct Baba Hadi ya tura motar cikin gida, tare da dai-dai-ta parking dinta a parking space. Ahankali Rayyern din ya bud’e motar ya fito, Kana ya juya ya nufi wurin da Baba Maud’o yake tare da ɗan longoɓar da kai alaman gaisuwa. Murmushi Baba Mauɗo yayi tare da mishi sannu. kafun kaitsaye ya nufi babban falon gidan. Inda Mamy da Abba dasu Ramadan ke zaune. Shigowarsa cikin falonne kuma yasa duk suka d’ago Kai suka kalleshi, Riyyam-nsra ne ya taso da d’an hanzari ya rungumeshi, tare da cewa. “Gaskiya ko Hamma Rayyern kaina musamman ne, ka iya amsa duk wata tambaya da akayi Ma.” Kansa kawai ya Dan jinjina saboda duk ji yakeyi kansa a gajiye, karasa shigowa cikin falon yayi, tare da yiwa Abba da Mamy sannu da gida. “Yauwa Rayyern sannu da dawowa.” Mamy ta amsa masa, Yayinda Abba kuwa Da Kai ya amsa masa. “Hamma Rayyern congratulation.” Ramadan ya fad’a k’asa k’asa yayinda yake Dan danne dariyarsa, badon komai ba kuma saidan sanin halin Yayan nasa da yayi, kwata-kwata baya son yawan magana amma kuma yau gashi wata tasashi yayi ta magantuwa. Da kai kawai Rayyern din ya amsa masa, batare daya zauna acikinsu ba kuma kaitsaye ya wuce part d’insa. Wanka yayi tare da dauro alwalan sallan magriba, bayan ya kimtsa kansa acikin wasu kaya marar nauyi ne kuma, ya fito inda dukansu suka had’a hanya wajen zuwa masallaci. Koda sukaje masallacin kuwa kamar Koda yaushe basu dawo ba saida aka Sallame sallan Isha. Suna dawowa gidan kuwa suka samu Mamy ta had’e musu lafiyayyen dinner, hakan yasa duk suka k’arasa kan dining table din suka zazzauna. Yau din kuma Riyyam-nsra ne da kansa ya amshi Mamy wajen yin saving dinsu, shida kansa ya zubawa kowa abincin banda Abba da Mamy ta zuba mishi nashi, sannan da kansa ya had’awa Hamma Rayyern din tea. Bayan ya kammala had’a musu ne kuma, kowa ya soma cin abincinsa, anutse Abba ya d’ago da kansa ya kalli Rayyern cikin jinjina da kuma ya bawa yace. “Tabbas hirar da akayi da kai yau, tayi armashi da kuma ma’ana, sannan shawarwarin daka bayar shawara ne masu kyau, gaskiya na jinjina maka,”. Sai kuma ya ɗan tsagaita kana ya ɗan kalleshi tare daci gaba da cewa. “Amma da kashawarce ni kafun hakan, To fa da bazakaje ba.” Zazzafan tea din dake bakinsa ya had’iya, kana cikin yin kasa dakai yace. “Kayi hakuri Abba nima banaje Dan son raina bane, naje ne kawai saboda nayi musu alk’awari, sannan banason wanda aka bawa kwangilar nema na din ya rasa aikinsa, kamar yanda manyansa suka bashi zab’i.” Kai Abban ya jinjina, batare kuma daya ja zancen yayi tsawo ba yace. “Shikenan To Rayyern Allah ya taimaka ya tsare min kai.” Da Ameen duk suka amsa. Bayan sun kammala cin abincinne kuma, kaitsaye Rayyern din ya wuce daki’n sa. Yayinda Ramadan da Riyyam kuwa suka dawo Cikin falon suka ci gaba da hirararsu, daga karshe ma game suka had’a, suka soma yi. Ganin hakanne kuma yasa Abba da Mamy wucewa sashinsu. Rayyern kuwa yana shiga dakinnasa kwanciya yayi, Cikin mintuna kad’an bacci yayi nasaran daukarsa. Acan falon kasa kuwa Ramadan da Riyyam, duk kowannensu saman kujera ya d’ale ya kwanta, su kansu ba zasu iya sanin tayaya nema bacci ya kwashesu ba, kowannensu da abun buga game din ahannunsa, haka sukayi bacci kasancewar dare ya nisa. A sashin Jannart kuwa yau tun 9 tayi baccinta mai cike da nutsuwa, Yayinda takejin zuciyarta wasai babu sauran wani fargaba. Washegari. Friday. Tun tashinsa karfe 7 ya gama shirya kansa, saidai shigarsa ta yaudin ta banbanta dana kullum. saboda wani riga da wando mai Taushin gaske ya saka ajikinsa, sabanin suit daya saba sakawa akowacce rana. Sosai kayan Yayi masa kyau, musamman daya daura boyfriend jacket mai kyau akan kayan. Wasu bakaken shoe masu tsada da watch ya daura a tsintsiyar hannunsa . Bayan ya gama kimtsa kannasa ne kuma, ya dauki wayarsa tare da duba sakonnin da suke ta shigo masa ta Twitter, saboda yanda duniyat Twitter din ta Dinke da hotunansa, gaba daya shi kawai ake watsawa, da kuma bayani akan hirar da akayi dashi. Kashe data dinnasa yayi, tare da juyawa ya nufi k’asa kaitsaye. Anan cikin falon ya samu su Abba, harma da Riyyam nsra wanda yake ta hamma da alama bacci bai ishesa ba. Dan Koda asuba ma Abba ne daya fito yagansu kwance afalo, shi ya tashesu tare da saka su agaba suka wuce masallaci. Karasowa yayi ya zauna akan dining table din, bayan kuma Mom tayi saving dinsa ne, ya soma cin abincin atsanake, saidai kuma bai wani ci sosai ba, ya mik’e tsaye. Yaudin ma dai atare suka fita shida Ramadan, saidai kuma Riyyam-nsra ya dage kan cewar, tare zasu tafi Hospital shida Ramadan. Hakan kuwa akayi inda Ramadan din ya dauki Riyyam din suka wuce Hospital, shikuwa Rayyern dama yau ba Hospital din zaije kaitsaye ba. Bayan anwangale musu gate din gidan sun fito da tsalatsalan motocinsu ne, kaitsaye su Riyyam suka wuce Hospital, shikuwa Company’n sa ya nufa. Koda ya isa company din kuwa ya samu, ma aikata madasa in juna suna ta aikinsu, Domin yau din injunan da zasuna had’a kwalaye da buhuna ake kafawa amazauninsu. Sosai ya jinjina kansa ganin yanda aikin nasu ke tafiya yanda ya kamata. Kasancewar kuma akwai aikin da zaiyi ne yasa, kaitsaye ya haura sama inda Office d’insa yake. Acan gida kuwa Baba Maud’o na zaune yaji karan horn din mota, atunaninsa ko su Rayyern dinne suka dawo, hakan yasa ya wangale gate din gidan. Barrister Kabir kuwa dake cikin motar, kaitsaye ya shigo da motar tasa cikin gidan. Bayan ya gama dai-dai-ta parking din motar tasa ne kuma, ya bud’e ya fito, saidai kuma ayau din bashi kad’ai yazo ba, atare dashi akwai Dr.Sajo. Karasowa wajen Baba Maud’on sukayi tare da bashi hannu sukayi musabaha. Baba Maud’o kuwa fuska asake ya amsa musu, sannan kuma da kansa yayi musu iso zuwa cikin gidan, har cikin babban falon kuma ya kaisu. Ganinsu ne kuma yasa Abba fadada fara’arsa, tare da sawa Mamy tayi musu tarba maikyau. Bayan sun gaggaisa ne kuma, Barrister Kabir ya gyara zama, tare da Kallon Abban ya gabatar masa da Dr. Sajo. Haka dai suka Dan tattauna, agame da abunda suke shirin had’awa. Bayan kuma sunyi tattaunawa mai tsawo ne, suka yanke shawara akan cewar yau Idan an sauk’o daga sallan Jumm’a za’a daura auren. Da wannan batun sukayi sallama. Inda Abban ya rakosu har waje, bayan sun tafi ne kuma ya zauna anan awajen Baba Maud’o suka d’an soma tattauna wasu batu. Acan Office din Rayyern kuwa. Ganin 11:30 am ne yasa shi mik’ewa. Tare da barin duk wani abu da yakeyi. Kaitsaye kasa ya sauko, saboda yanason sake komawa gida saboda yin shirin zuwa masallaci. Koda ya shiga motar tasa kuwa cewa Hadi yayi su wuce gida. Take kuwa kaitsaye suka nufo gida. Koda ya dawo gidan, wanka ya sakeyi inda ya shirya kansa cikin riga da wando da kuma babbar riga, ta hadaddiyar getzner’n da ak’alla kudinta ya haura sama da 100k, sosai kayan sukayi masa kyau kasan cewar kalarsu lemon green ne kana zaren da aka watsawa garen su kuma shudi ne da fari da baƙi sosai sukayi mishi kyau, musamman daya kafa hulan zanna bukar blue color Kansa, ga kuma wani tsadadden takalmin toms suma blue da agogo daya saka, Tabbas yayi kyau kwarai. Domin shigar tasa bawai gama gari bace, shigace ta musamman, wacce ta kara bayyana kyau da kwarjininsa. Bayan ya gama kimtsawa ne kuma, ya feshe jikinsa da turare tare da sauk’owa k’asa, saboda jiyo hayaniyar Ramadan da kuma Riyyam da yayi, wanda suma sun shirya ne tsab, Cikin sabin getzners dinsu, masu kyau. Kallonsu Riyyam din kawai yayi kana a takaice yace. “Ka kwaso kayanka ka dawo nan, ka dena kwana a hotel”. Ya ƙare mgnar cikin bada umarni. Cikin yanayin ba zata jin mgnar Riyyam-nsra ya kalleshi da alamun zaiyi mgn sai kuma yayi shiru. Ganin tuni ya fice batare kuma daya ƙara ce musu komai ba. kaitsaye ya fice daga cikin falon. cikin sauri-sauri kuma ya nufi motarsa saboda bayason rasa hud’uba. Bayan ya fita daga gidanne kuma suma suka fito inda suka shiga motar Ramadan daketa murna da farin cikin mgnar Hamma Rayyern ɗin nasu. kaitsaye masallacin Alfruq’an suma suka wuce. Acan gidansu Jannart kuwa hakanan tun tashinta yau din takejin zuciyarta na yawan tsinkewa, ga kuma wani irin faduwar gaba da takeji akai akai. Sai-dai rashin sanin takamaimai abun yi, yasa ta fara ambaton sunan Allah a cikin zuciyarta. Barrister Kabir kuwa, bayan yayi shirin zuwa masallaci, yau din ko motarsa bai dauka ba, da kafansa ya fito inda ya tako har bakin titi, taxi ya tara, tare kuma da yiwa mai taxi din bayanin inda zai kaishi. Wanda kuma bako Ina bane face masallacin dake gefen gidan Dr. Sajo. Koda mai taxi din ya saukesa a masallacin, kaitsaye wajen Dr. Sajo ya nufa, atare sukayi sallan Jumma’a, bayan sun idar da sallan ne kuma, Dr. Sajo ya fito musu da mota. Kaitsaye suka nufi unguwar Nassarawa GRA. Yayinda acan masallacin alfurq’an kuwa, bayan an sallame sallan jumma’an, Ramadan da Riyyam-nsra suka sulale, kaitsaye basu zame ko inaba kuwa sai kasuwa, saboda kafun su fita Abban ya basu kudi yace su sayo masa huhun goro da kuma katton katton na mintuna. Sudai haka suka je suka sayo batare da sanin na meye bane. Koda suka dawo gida, anan cikin falon Abban suka jibge huhun goron da kuma mintunan da suka sayo. Dawowarsu kuwa yayi dai-dai da isowan su Barrister Kabir da kuma Dr. Sajo. Inda Abba da kansa yazo yayi musu iso zuwa babban falon k’asa. Bayan sun zazzauna ne kuma ya fita ya kira Baba Maud’o, inda yace. “Baba Maud’o ka shigo, yau abun na musamman za’ayi acikin gidannan, Insha Allah yanzu za’a daura auren Rayyern.” Idanu Baba Maud’o ya d’an fitar, lokaci daya kuma yaji wani irin farinciki ya lullub’e sa, wanda hakan yasa Cikin matuk’ar jin dadi yace. “Masha Allah lokaci yayi kenan, yau dai Ranar Rayyernu ta tsaya, To Allah yasa hakan shine mafi alkhairi.” Da “Ameen.” Abba ya amsa. Dai-dai lokacin kuma suka shigo cikin falon shida Baba Maud’o. Acan waje kuwa yanzu motar Rayyern din ke isowa, Jin sunyi horn ba a bud’e musu bane kuma, yasa Hadi fitowa da kansa ya bud’e musu gate din suka shiga ciki. Da mamaki Rayyern yake Kallon bakuwar motar dake fake afarfajiar gidan nasu, yayinda daga gefenta kuma motar Usman PA ne wanda yazo babu jimawa, kuma shima ya shigo yana can cikin falon Abban. Ahankali ya bud’e murfin motar ya fito, Yana fitowa dinne kuma, Abba ma ya fito daga cikin falo, Kallon Rayyern din yayi, lokaci guda kuma ya hade fuskarsa, cikin tsare gida, ta yanda yasan Rayyern din bazai samu daman tambayarsa wani abuba yace. “Hadi ka shigo daga ciki, kaima Rayyern ka biyoni.” To Hadi yace tare da rufawa Abban baya, shima Rayyern din haka cikin daurewar Kai yabi bayan Abban nasa. Suna shiga cikin falon kuwa, yaji zuciyarsa tayi wani irin harbawa, saboda yanda yaga mutane atare. Daya bayan daya yake bin kowannesu da kallo, Koda ya sauke idanunsa akan Barrister Kabir, ji yayi wani irin abu ya tsarga mai. “Oh My God meye kuma wannan mutumin ya sake zuwa yi agidan mu? Waishi bazai tab’a fahimta bane, nace masa ban shiryawa auren yartasa ba banasonta wai ko ana dole ne ai gaggawa dai bata da kyau.” Yayi maganan azuciyarsa, tare da yin kicin kicin da fuskarsa. Gudun kada yaji wata magana ta taso ne kuma yasa, cikin nitsuwa. Ya ɗan motso ya gaidasu a mutunce. Kana sauri-sauri ya soma kokarin haurawa sama. “Rayyern zo zauna.” Muryar Abba ta katse shi daga tafiyan da yakeyi, wanda kuma hakan yasa dolensa ya dawo cikin falon. Zama yayi akusa da Abban nasa, tare da dago kansa ahankali yace. “Abba Lafiya kuwa, meke faruwa?” “Lafiya kalau sai alkhairi.” Abban ya fad’a yana me d’an gyara zamansa, tare da fuskantar Baba Maud’o, cikin mutumtawa Hadi da karramawa yace. “To Baba Maud’o kaine babba amatsayinka na babba kuma Kai ya kamata ka fada mana wanda zai zama waliyin Rayyern.” Murmushi Baba Maud’o yayi, cikin muryar tausasawa yace. “Kai ne zaka waliyancesa Alhaji, ai babu damuwa Dan uba ya waliyanci dansa.” Baki Abban ya bud’e daniyar cewa wani abu, amma kuma saiya fasa saboda wani tunani daya fado cikin zuciyarsa. Ajiyar zuciya yadan sauke tare da gyara zamansa yace . “To shikenan ba matsala, wanene waliyin amarya?.” “Gashi nan.” Barrister Kabir ya fad’a yana mai nuna Dr Sajo, yana me fuskantar sauran mutanen dake cikin falon kuma da kyau. Kai Abba yajinjina tare da juyawa ya kalli Rayyern. Cikin yanayin dake nuna babu alaman wasa acikin magana ko fuskarsa yace. “Rayyern kawo sadaki.” Wani irin karya wuya Rayyern yayi, lokaci daya kuma ya narke fuska cike da tsananin mamaki yace. “Sadaki kuma Abba? Sadakin menene, nifa...” Ganin wani kallon da Abban ya watsa masa ne yasa shi yin shiru, tare da sunkuyar da kansa k’asa, asanyaye yace. “Abba yanzu ba kudi ajikina, a daga auren sai na samu kudin.” Cike da mmkin mgnar tasa Abba yace. “Eh munsani fa baka da kuɗi. Amman kada ka damu ko transfer ne kayi mana.” Saurin dagowa yayi ya kalli Abban nasa, lokaci daya kuma ya kwab’e fuska, Murya araunace yace. “Ni wayata ba charge, amma muje sama da Ramadan dakina in bashi kuɗin ya kawo muku.” Ya ƙare mgnar yana yunƙurin tashi. Alamun guduwa da yake son yi. Murmushi ɓoye Abba yayi tare da danne kafaɗarsa kana yace. “Zauna”. Cikin kwaɓe fuska yace. “Abba Kudin zan bashi”. Ya k’are maganar tamkar zai zubda hawaye. Cikin tsare fuska yace. “Ina kuɗin suke?”. A sanyaye yace. “Cikin bed side drower”. Kallon Ramadan Abba yayi kana cikin, bada umarni yace. “Ramadan jeka ɗebo kudin koma nawane kawosu.” “To“ Ramadan din yace, tare da mikewa cikin sauri ya haura sama. Inda Rayyern kuwa ya bishi da Harara kasa kasa. Mintuna biyu kacal kuma saiga Ramadan ya dawo da bandir din yan dubu dubu, na dubu dari biyu, Dan kowani bandir dubu dari ne. Mik’awa Abban nasu yayi. Tare da komawa ya zauna. Abba kuwa duka dubu dari biyun din ya mik’awa, Dr Sajo tare da cewa. “Ni Alhaji Bashir Muhammad ina nemawa, d’ana Dr Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara auren yar wajenka Jannart Idi Sale Dakata, akan sadaki naira dubu dari biyu.” Karb’an kudin Dr Sajo yayi, tare da gyara zamansa cikin mutumtawa yace. “Ni Dr Sajo Umar, na bawa danka Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara auren yata Jannart Abdulkarim Saleh Dakata akan sadaki naira dubu d’ari biyu.” Daga nan kuma sukayi duk abinda ya dace na tsarin daurin aure bisa koyarwar musulunci. “Alhamdulillah! Alhamdoulillah!! AURE Ya D’auru jama’a muyi salati goma ga Annabi.” Cewar Baba Maud’o, cikin tsananin farinciki. Adai-dai lokacin kuwa Rayyern ya rumtse idanunsa da karfi, tare da dafe dai-dai saitin zuciyarsa cikin rudu hadi da bugawar zuciya Ya......! *Dan Allah ki saya ki karanta littafina na kuɗine special Group 1k ƙaramin group 500 yawan posting ne banbancinsu, 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU sai ki turo min shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276, in ba halin turawa ta account ki sayi katin MTN ki kofi number's ɗin katin ki turo min ta whatsApp.* By *GARKUWAR FULANI* 11/15/21, 7:21 PM - Auntyna: Danne jajayen labb’ansa. “Innalillah wa innailaihi rajiun. Oh ni Rayyern wannan wacce irin rayuwace? Wannan wanne irin ƙaddara ne mai tafe da jarababbe .ayataccen kuma lik’akk’en aure ne, shikenan dai ni. Bani da freedom din kaina, dolen-dole sai an sako min wata acikin rayuwata!!!.” Yayi maganar azuciyarsa, yana mejin tamkar ya mike tsaye, yace sam shi baiyarda da wannan auren ba. Su Abba, Ramadan, da kuma Riyyam-nsra, kuwa gaba d’aya farinciki ne ya lullub’e zuciyoyinsu, more especially Ramadan da ayanzu yake Ganin shima ya samu chance na auren Rayhanna’n sa. Baya ga haka kuma abun farinciki ne awajensu ace yau Hamma Rayyern din nasu yayi aure. Barrister Kabir kuwa idanunsa ya lumshe tare da soma sauke ajiyar zuciya akai akai, Lallai yasan cewa yau din ya bawa Jannart Garkuwa, da kuma mafakar da babu wani mahaluki daya isa ketare ta, Allah Sarki Jannart marainiyar Allah, akullum Allah shike zama gatanta. Dr. Sajo ne ya gyara zama, tare da somayin addu’a, bayan ya kammala addu’an ne kuma yace. “Ina rokon Allah madaukakin sarki daya sanya al'barka da kuma al'khairi mai tarin yawa acikin wannan auren, Allah ya kade duk wata fitina da zata kunno Kai, Kai kuma Rayyern Allah Ubangiji ya baka ikon sauke nauyi da kuma hakkin dake kanka.” Da “Ameen.” Duk suka amsa amma banda Rayyern wanda yakejin kamar yasa musu kuka, Dan takaici, Yayinda acikin zuciyarsa kuwa yace. “Ni babu wani nauyi daya hau kaina.” Barrister Kabir ne kuma ya d’an kallesu, kana. Cikin taushin murya yace. “Nagode Kwarai da irin karamcin da kukayi mana, kun amince damu, sannan kuma kun karb’i auren y’armu da daraja, nagode Kwarai abu na karshe kuma da zan rokeku dukanku shine, Dan Allah wannan magana ta daurin auren ya zama sirri atsakaninmu, Domin nima dole ce ta sani yin hakan.” Kai duk suka jinjina, Yayinda Abba Kuwa ya gyara zamansa tare da fuskantar Barrister Kabir din yace. “Karka damu Barrister, nayi maka al'k’awarin bayan mu babu wani wanda zaisan da batun auren, haka kuma babu wanda zaisan da zaman Jannart acikin gidannan.” Kai Barrister’n ya jinjina cike da gamsuwa, Yayinda Abban kuwa ya dawo da kallonsa gasu Ramadan din, cikin tsare gida yace. “Dukanku ku tashi ku bamu waje.” Aikuwa Rayyern kam dama kaman jiran hakan yakeyi, Domin bakin Abban ko gama rufewa baiyi ba ya mik’e zumbur, Da sauri Abba ya kalleshi har ya buɗe baki zaice banda kai. Sai kuma kawai yayi shiru ya bishi da ido har ya haura sama. Ramadan kuwa hannun Riyyam-nsra ya kama, suka nufi side d’insa, Tabbas suna cikin farinciki, amma daga wani b’angare tsananin mamakin yanda auren Hamman nasu ya kasance sukeyi, auren bazata, auren da ba tsammani kuma auren sirri auren shaidu goma. Suna shiga cikin side din Ramadan din ne kuma, Riyyam-nsra ya zaro wayarsa, Yayinda shi kuwa Ramadan kaitsaye ya wuce toilet. Riyyam kuwa numbern Mammynsa ya kira, bugu biyu kuwa ta d’auka, bayan sun gaisa ne kuma Riyyam din, ya dan jujjuya ya kalli kofar shigowa data Bathroom, tare da karyar da wuyansa gefe, bakinsa cike da tarin maganganu kala-kala yace. “Mammy kinsan me yake faruwa?”. Da sauri Mammy ta jujjuya mishi kai tare da cewa. “A'a sai ka faɗa!”. Numfashi ya ɗan fesar kana a hankali yace. “Yau ɗinnan a yanzun nan aka d’aurawa Hamma Rayyern aure.” Idanu Mammyn ta d’an zaro cike da tarin mamaki, tace. “Aure kuma Riyyam, wanne irin aure haka?.” Gyara zamanshi yayi tare da sauke nannauyan numfashin yace. “Aure dai da kika sani Mammy irin dai wanda ake daurwa tsakanin mata da miji”. Lumshe ido tayi cike da al'hini tace. “Ikon Allah”. Shi kuwa Riyyam-nsra ci gaba da cewa yayi. “Mammy kinsan meye ma kuwa? acikin falo fa aka daura auren, kuma kwata-kwata bamu wuce mu goma ba, wa y’anda aka daura auren agabanmu”. Da sauri tace. “Toh wannan wanne irin aurene meke ɓoye a ƙasa, tabbas akwai manufar auren!”. Da sauri yace. “Uhumm ai baki sani, bama Mammy Hamma Rayyern fa bayason auren wallahi Mammy, karki ga yanda ya had’e fuska, kamar zai daki babu. Domin shi kanshi baisan cewa za’a d’aura masa aure yau ba.” Ajiyar zuciya Mammy’n ta sauke, cikin yanayin mamaki kuma tace. “To Riyyam Allah Ubangiji yasan hakan shine mafi al'khairi, ya kuma basu zaman lafiya yasa kuma wani matakin nasara ne.” “Ameen.” Ya fad’a, Ganin fitowar Ramadan daga cikin toilet ne kuma, yasa shi katse kiran, inda yacewa Mammyn nasa zai kirata anjima. Acan falon Abba kuwa tafiyar su Rayyern dinne, yasa Usman P.A, Hadi da kuma Ari mikewa duk suka fice daga cikin falon, suna mai fadin Allah ya sanya alkhairi acikin auren. Baba Maud’o kuwa Kallon su Barrister Kabir yayi, cikin muryar dake bayyana farin cikinsa, yace. “Barrister mun gode da kyauta mai daraja. Yanzu yaushe ne za’a je d’auko mana diyar tamu.” Gyara zama Barrister Kabir din yayi, kana cikin mutumtawa yace. “Insha Allah ni dakaina zan kawo muku diyar ku, bama sai kunje d’auko ta ba. Domin kamar yanda aka daura auren nan, asirrance haka kawo amaryar ma zai kasance asirrance, saboda nima acikin hikima zan samu na fita da ita daga cikin gidan da yake gab da zame mata kabari, bisa taimakon maigadin gidan, da kuma driver’nta, saboda mun shirya akan da misalin k’arfe sha d’aya zata fito daga gidan, Idan ta fito ni kuma zan dauketa na kawota.” Kai duk suka jinjina, Yayinda Baba Maud’o kuwa yayi murmushi, tare da cewa. “Masha Allah hakan ma yayi, Allah Ubangiji ya taimaka.” Da “Ameen” duk suka amsa. Batare daya sake cewa komai ba, kuma ya tashi ya tafi. Acan b’angaren Rayyern kuwa, yana haurawa sama, babbar rigar dake jikinsa ya zare, tare da hayewa saman gadonsa ya kwanta. Idanunsa da sukayi ja, ya rumtse da karfi tare kuma da soma fitar da wani irin numfashi mai zafi ta bakinsa. Shikam acikin rai da zuciyarsa ya rasa wannan wanni irin fitinannen aure ne da aka lik’a masa, gaba daya suna neman dagula masa rayuwarsa, wanda bai kuma San dalilin yin hakan ba, dududu acikin kwanaki goma da dawowarsa daga Ethiopia, acikin kwanaki takwas na cikin gomanne kuma, abubuwa mabanbanta suka faru dashi, aciki kuwa harda babban abu daya kasance Aure. Auren da bai shirya masa ba, auren da yazo da wani irin k’ulli. Sam arayuwarsa shi bai tab’a kawo tunani ko maganar aure cikin k’wak’walwarsa ba. Fact Shi baima tab’aji ajikinsa cewar zaiyi aure ba. But why yanzu suke son sanja masa rayuwa? Yar karamar tsuka yaja, tare da gyara kwanciyarsa, cikin takaici kuma abayyane yace. “Koma meye nidai bazan sanja tsarin rayuwata daga yanda na saba ba, babu wata mace agabana, haka kuma babu wata wanda zan tsaya kulawa da ita ehe inji da kaina ma mana.” Ya kare maganan yana me jawo murfin bedside drawer’nsa, inda ya d’auko ledan chocolate d’insa na kinder bueno, bayan ya bare ledanne kuma yasa chocolate din abakinsa yana sha. Acan falon kasa kuwa, su Abban suna gama tattaunawa ne, Barrister Kabir da kuma Dr. Sajo suka mik’e Daniyar tafiya, har bakin mota kuwa Abba ya rakasu. Bayan yaga tafiyarsu ne kuma ya dawo gida, kaitsaye kuma dakin Mamy ya nufa, Dan sanar da ita abunda ke wakana. *Jannart* Zaune take akan lallausan carpet dake, cikin falon nasu, Yayinda ta duk’ar da kanta k’asa, nail cutter ne hannunta, tana gyara yan fara tun yatsun kafarta, Yayinda Momy da kuma Abdull ke zaune agefe. Azahirance Idan ka kalleta zakayi tunanin, cewa hankalinta ya tafi ne Izuwa kan nails dinta da take gyarawa, saidai kuma awajenta sam ba hakan bane. Domin tunaninta ya tafine izuwa wani waje na daban, wani abu takeji na musamman yau din, Domin kuwa abubuwa uku ne suka hade acikin rai da zuciyarta, Wanda kuma batasan dalilin jin hakan da takeyi ba. Idanunta tad’an lumshe ahankali, saboda yanda takejin kirjinta na bugawa time to time, kuma zuciyarta na tsinkewa, Yayinda wani abu mai kama da fargaba ke yawan tasan mata. Acan kasan zuciyarta kuwa, ji take tamkar ana zare mata wani babban kaso na daga cikin damuwarta. Jin kanta take tamkar awata duniya sabuwa. Bud’e kofar falon da akayi ne kuma yasa ta saurin d’ago kanta. Inda idanunta sukayi mata tozali da Daddy. Har zata dauke Idanunta daga kan Daddy’n ne kuma, Idanunta suka sauka akan Junaid dake bayan Dadyn, wani irin matsanancin fad’uwar gaba taji, lokaci daya kuma duk jikinta ya d’auki tsuma. Wani irin matsanancin tsoro ne ya shigeta, wanda hakan yasa tayi saurin mik’ewa tsaye. Ido biyu da sukayi da Junaid dinne kuma, yasa ta soma girgiza kanta, tare da jan jikinta baya baya. Kamar wanda aka tsikara kuma, haka ta juya Cikin sauri, har k’afafunta na hard’ewa ta nufi sama. Idanu Junaid ya zazzaro cike da haushi hadi da takaici. Yace. “Ke Jannart, Ki dawo nan dan Uwarki mahaukaci kika ganine da zaki gudu, ki dawo nan na fad’a miki.” Ya k’are maganan cikin d’aga murya da tsananin b’acin rai. Jannart kuwa duk da taji kiran da yakeyi mata din, amma Sam batajin zata tsaya ko ta juyo ta sauraresa. Domin sosai ganin nasa ya haifar mata da tsoro, hadi da kuma tsananin fargaba, kasancewar. Ganin nasa da tayi ayanzu, ya dawo mata da duk wata bakar izaya daya gana mata. Daddy dake tsaye kuwa, Ganin hakan bai wani dameshi ba, hasali ko damuwa baiyi ba, saima juyawa da yayi ya fice daga cikin falon, yana me amsa kiran wayan da akayi masa. Momy da Abdull kuwa tsit sukayi, domin sunsan suna magana zai sauke abunda ke tsakiyar kanshi anasu kan. Kwata kwata Junaid ba mutumci ne dashi ba, baya ganin darajar kowa acikin gidan, musamman ma Momy da ko kadan baya mutumtata, amatsayinta na matar Babansa. K’wafa yaja tare da fesar da hucin sauran hayakin taban dake bakinsa, cikin haushi da kufula kuma ya zaro wayarsa tare da dannawa numbern Jannart din kira. Jannart kuwa da bata zame ko ina ba sai cikin dakinta, tana shiga kuma ta dannawa kofar key. Numfarfashi ta soma fitarwa, tare dasa hannunta ta dafe kirjinta dake bugawa, dai-dai lokacinne kuma kiran Junaid din ya shigo cikin wayarta. Arazane takai dubanta ga screen din wayar, ganin sunan Junaid din dake yawo akan screen din wayar nata ne kuma, yasa tayi saurin karasawa jikin gadonta, ayunkurinta na rejecting call dinne kuma, tayi picking batare da ta sani ba, still batare kuma da ta. Ankara da hakan ba, ta cilla wayartata kan gado, tare da daura pillow akanta ta kwanta. Junaid dake tsaye afalo kuwa jin Jannart din ta d’aga wayarne yasa, amatukar hasale yace. “Yau zakici uwarki wallahi, wancan karon Sumar dake kawai nayi, amma yanzu kasheki ma zanyi kawai kowa ya huta, wallahil azim kuma nayi rantsuwa, adaren yau basai gobe ba saina cika burina akanki, yar iskar yarinya kawai me zubin munafukai.” Yana gama fad’an hakan ya kashe kiran, sai faman zuba huci yake tamkar mayunwacin zaki. Dab da zaifita ne kuma ya juyo, ya bankawa Mom da kuma Abdull Harara, cikin halinsa na y’an shaye shaye daya saba yace. “Mchewww munafukai kawai.” Yana gama fadin haka yasa kai ya fice daga cikin falon. Momy kuwa Kai ta girgiza, cike da takaicin halin Junaid din kuma tace. “Insha Allah babu wani burinka dazai cika akan Jannart, bazaka tab’a samun nasara akants ba kowanni mugun nufinka, in banda ma halin dabbanci da hauka, ace yarinya uwarku daya ubanku daya amma baka da aiki sai musgunawa, da son b’ata rayuwarta, hmmm Allah Ya kyauta.” Abdull dai dake zaune shiru yayi, saidai kuma har acikin zuciyarsa yana matuk’ar takaicin irin rayuwar da akeyi acikin gidan nasu, wanda kwata-kwata babu girmamawa ko tarbiya acikinsa, kiri-kiri ana zalunci amma babu wani wanda zaiyi magana. Acan b’angaren su Abba Kabir kuwa, Koda suka baro gidansu Dr. Rayyern, abakin titi Dr Sajo ya sauk’e Abba Kabir, inda kaitsaye Abban ya Tari taxi ya nufo gidansu Jannart. Koda ya iso cikin unguwar daga nesa, yasa mai taxi din ya sauk’eshi, bayan ya biyasa kudinsa ne kuma kaitsaye ya nufi katafaren gidan Yayan nasa. Tura k’aramar k’ofar dake jikin gate din yayi ya shiga, bayan sun gaisa dasu Ashiru dake bakin gate dinne kuma kaitsaye, ya nufi cikin gidan. Koda ya shigo ya samu su Momyn, bayan sun gaisa ne kuma Momyn tasa Abdull ya cika masa Dan table din dake gabansa da kayan drinks hadi da fruits. Lemun exotic ya dan kurb’a, tare da duban Momyn. “Yaya Baya nan ne?” Ya tambaya da kulawa. “Eh dazun nan ya fita babu jimawa, amma munyi waya dashi, wai wani meeting ne aka kirasa na gaggawa.” Momyn ta bashi amsa. Shikuwa kansa ya jinjina, alaman gamsuwa, kamar zaiyi shiru kuma sai ya sake duban Mamy, tare da cewa. “Jannart fa, kodai ta tafi wajen aiki ne? Duk da shigowa na ma naga guard dinta awaje.” Ajiyar zuciya Momy ta sauke, cikin Dan yanayin sanyi kuma tace. “A’a Jannart tana sama, batama jima da haurawa ba, dazu dukanmu mu nan azaune, dawowan Junaid ne yasa duk ta tsorita.” D’an Jim Barrister Kabir din yayi, na y’an wasu daƙiƙu kafun daga bisani, ya mik’e tsaye, yana me cewa. “Badamuwa To bari na haura saman na duba ta.” Da “To.” Momyn ta amsa, Yayinda shikuwa kaitsaye ya wuce saman. Koda ya karasa jikin kofar nata tsayawa yayi, tare da kwankwasawa. Jannart dake kwance akan gadonta, Jin ana knocking kofar nata ne yasa ta zaro Idanunta da sauri tare da tashi zaune. Kana cikin yanayi na tsoro, saboda duk atunaninta Ya Junaid dinne ya biyota. “Jannart! Jannart ki bude nine Abba ne.” Barrister Kabir ya fad’a, cikin dan daga murya yanda zata jiyosa. Jin muryar Abba Kabir dinne kuma ya sata, sauke Wata irin wawiyar Ajiyar zuciya, tare da tashi cikin sauri ta nufi kofar. Murza key din tayi ta bud’e k’ofar, wanda hakan ya bashi daman shigowa, murmushi tayi kana cikin jin wani abu na daban, acikin zuciyarta da ganin nasa ya haifar mata tace. “Good morning Abba.” “Morning Jannart, fatan kina lafiya.” “Lafiya na kalau Abba.” Ta fad’a tana me komawa kan gado ta zauna. Shikuwa Abba Kabir din karasawa cikin dakin yayi, tare da zama akan daya daga cikin bedside carbinate dinta. Bayan ya zauna dinne kuma, ya zura Hannunsa acikin aljihun rigarsa, tare da zaro rapper’n kud’i. “Jannart.” Ya kira sunanta cikin tausasawa. “Na’am Abba.” Jannart din ta amsa tana me juyowa izuwa gareshi. Shikuwa Abban Ajiyar zuciya mai nauyi ya sauk’e, tare da d’an muskutawa ya kamo hannayenta, rappern kudin dake hannunsa ya dank’a mata acikin nata hannun. Cikin muryar da yake fatan zata gamsar da ita yace. “Ga sadakin ki Jannart, an d’aura miki Aure yau, bayan an idar da sallan Jumma’a.” Amatuk’ar razane da kuma wani irin bugun zuciya ta d’ago Idanunta da suka firfito ta kalleshi, hakanan taji maganan Abban nata wata iri, duk da kuwa tasan da plan d’insa nayi mata aure, amma sam kwata-kwata bata tab’a kawowa aranta cewar, arana irin tayau za’a daura mata aure ba kana taji kalmar tayi mata nauyi. Ganin Abba Kabir din na kallonta ne kuma yasa Ahankali ta janye Idanunta kasa, tare da kama y’an yatsun hannunta ta soma motsawa. “Jannart.” Again Barrister Kabir din ya sake kiran sunanta. Idanunta da sukayi raurau ta d’ago ta kallesa, dai-dai lokacin kuwa hawayen dake cikin idanun nata suka gangaro zuwa kan k’uncinta. Cikin sanyi da kuma raunin dake kwance acikin zuciyarta tace. “Abba Karik’e su awajenka.” Kai Abba Kabir din ya girgiza, tare kuma da dan gyara zamansa yace. “Bazan karb’a ba Jannart, sadakin kine kuma halal dinki, sabida haka ki rik’e awajenki.” Yana gama fad’in haka ya kuma saka hannayensa acikin aljihun rigarsa, sweets da kuma chewing gums ya fito dashi, tare da Mika mata Cikin kulawa yace. “Ga goro da kuma sweets din daurin aurenki. Alhamdulillah kin tabbata matar aure yanzu Jannart, babu wani wanda zai sake kokarin keta haddinki, ayanzu kin tabbata mai y’anci, zan kaiki inda zaki samu kariya, zan kaiki wajen way’anda nake da tabbacin cewa ko bayan ba raina, zasu zame miki Garkuwa, har abada ina al'fahari da wannan Auren naki Jannart, kuma Insha Allah yau da dare zan kaiki d’akinki, na dank’aki ga Mijinki, sannan karki damu da batun su Baba Ado da Baba Ashiru maigadi, akoda yaushe Idan kika fito zaki samesu abakin gate, sannan na sashi yasa maganin bacci acikin abincin bodyguard dinki, ta yanda za ki fita ba tare da sunsan da hakan ba, Baba Ashiru ma yasan duk wani shirin mu, sannan ki tabbatar idan zaki fita babu wanda ya ganki, ciki kuwa harda Momyn ki, Abdull da Junaid, meyene Junaid din ya miki dazu har yasa kika hawo sama.” Ya jero mata jawabin a tare. Idanunta ta d’an marairaice, kana asanyaye tace. “Ni tsoronsa nakeji Abba, daya shigo nagansa shine na gudu, amma kuma ina shigo daki saida ya kirani awaya.” Kai Abban Ya jinjina, cikin gamsuwa da samun wata sabuwar dama yace. “Alhamdulillah dama me kyau, to kidai kiyaye idan zaki fita, Idan ba Baba Ashiru da Baba Ado ba, banason kowa ya ganki Jannart, sannan kina fita kibi layin bayan kunnan, ki tsallake layi uku ana gefe zaki sameni Ina tsaye ina jiranki, please Jannart kiyi komai da takatsantsan. Dan inason na mikaki ga mijinki cikin aminci, wanda nake da yakini akan zamanki acan zai kawar da duk wani damuwarki.” Kanta ta d’an jinjina, kana cikin muryarta dake rawa tace. “Insha Allah zanyi abunda kace Abba, amma inajin wani irin acikin zuciya da gangar jikina, inajin cewa zanyi kewar Daddy Momy, da kuma Abdull, yanzu idan na tafi kuma sai yaushe zanzo na gansu?” Tak’are maganan Idanunta suna zubda da k’walla. Ajiyar zuciya Abban ya sauke, tare da kamo hannunta Cikin kulawa yace. “Kada ki damu Jannart, Insha Allah Watan-warana zaki zo ki gansu, komai zai dai-dai-ta.” Kai ta d’an jinjina, still kuma da muryar kuka tace. “Abba kayi hakuri kawai dai inajin ba dadi ne, Ina son gidanmu sosai, inajin banason barinsa, matsalata kawai. Yah Junaid ne, shine wanda ako da yaushe baya son farinciki na, asanadinsa ne kuma yau gashi, zan bar gidan zantafi wajen way’anda, basu sanni ba.” Hannayenta Abban ya kama, tare da girgiza mata Kai. “Kada kiyi kuka Jannart, gidan da zan kaiki zai samar miki da ingantaccen farinciki, mutanen cikinsa masu karamci ne kuma zasu zame miki yan uwa da yardar Allah, kinsani Jannart bazan tab’a cutar dake ko na kaiki inda za’a cutar dake ba.” Kai Jannart din ta jinjina, alaman gamsuwa da kalamansa. “Yauwa Jannart, Allah ya sanyawa rayuwar aurenki al'barka, sannan idan zaki fita, ki tattare duk wani abu naki mai amfani, kama daga kan laptop da kuma certificates, and duk wasu takardunki masu amfani, ki sasu ajaka ki kuma taho dasu, wayoyinki kuma ki barsu a nan a tsakiyar gadonki. Maganan kaya kuma banda kayan jikinki kada ki d’auki kaya ko kala d’aya, ni da kaina zanje na saya miki kayayyakin da zakina sawa.” Kanta ta jinjina tana mai son tsaida hawayenta, Yayinda shi kuwa Abba Kabir din, ya mik’e ya fice daga cikin dakin. Yana fita kuwa Jannart din ta mik’e, jiki asanyaye ta soma harhad’a takardun ta dama yan kananan abubuwan ta masu amfani. Ab’angaren Abba Kabir kuwa yana fita daga cikin gidan, kaitsaye gidansa ya nufa. Koda yaje ya samu Aunty Dijat zaune afalo, anan yake shaida mata cewar yau an daura Auren Jannart. Farinciki ne ya lullub’e zuciyar Aunty Dijat, cikin jin dadi tace. “Masha Allah, gaskiya naji dadi Allah Ya basu zaman lafiya, yaushe za’a kaita gidan Mijin?” “Adaren yau zan kaita, amma Dijat karki manta, wannan maganan sirrine atsakaninmu, muddin ta fita daga bakinki, kada kiyi tunanin soyayyar dake tsakaninmu, da kuma irin zaman lafiyar da mukeyi, hadi da al’amarin yaya, zan watsar da ita, zan gurfanar dake agaban hukuma, ke kanki zan iya daura ayar zargi akanki.” Kai Aunty Dijat din ta jinjina, cikin yin imani da abunda zata fad’a tace. “Insha Allah Abban Hafeez, zaka sameni me matuk’ar sirrinta sirrinka, da izinin Ubangiji, wannan magana ba zata tab’a fita daga bakina ba.” Kansa ya jinjina, alaman gamsuwa da bayanan nata. By *GARKUWAR FULANI* 11/15/21, 7:21 PM - Auntyna: https://chat.whatsapp.com/K6m92SSD10n24Jc3FDLxMp Samun zafafan saukakan kayayyakin zamani na mata tun daga kan leshi, shadda, atamfa, material, jaka da takalmi, hijab..... da dai sauransu akan farashi mai sauki da rahusa sai a kamfanin Garkuwa collection. Bama wannan kadai ba akwai kayan order da muke yi shi ma duk a cikin rahusan da saukin kudi. Ba mu tsaya nan ba ina kuke yan kasar *NIGER* albishirinku kuma kuna iya siyan kayanmu ya isa gareku cikin aminci ba tare da bata lokaci ba. maza yan’uwa ku garzayo ku gane wa kanku wannan rahusar da kuke jin labari. Kayanmu ko a kasuwa ba zaka samu farashinsu ba. gidanmu gidan duniyar leshi, atamfa shadda, material da sauransu. Sai kun zo. Muna maraba da kai a kowanne gari kake. GARKUWA COLLECTION! Siyan nagari mayar da kudi gida! Acan B’angaren Daddy kuwa, shida Dr Lukman, da kuma Alhaji Abdu Tababa ne ke zaune, ad’aya daga cikin hall, na Tababa Company. Wanda kuma gama meeting dinsu kenan, bayan kowa ya watse ne kuma suka d’auko zance akan Rayyern. K’wafa Alhaji Idi Sale Dakata’n. Yayi, tare da d’agowa ya kalli abokanan makircin nasa. “Yaron nan Dr. Rayyern ya tsayamin aka, kullum da zancen kawar dashi nake kwana nake tashi, amma Dan iskan yaro har yau ko gidansu na kasa ganewa, yaron yana nan kamar Maye, duk wani motsin da kayi yakan zama tamkar a tsakiyar tafin hannunsa yake, narasa wanni irin yaro ne, nasa abibiyeshi amma ya gane, binciken da yayi akaina kuma saida ya ninka wanda nayi akansa, yanzu shi babu abunda bai sani ha akaina, yasan gidana yasan komai akan al’amurana, ni kuma har yau bansan inane, gidansu ba, nadaisan acikin Nassarawa G.R.A suke, amma bansan Ina ne taka maimai gidansu ba acikin unguwar, duk iya bincikena na gaza ganewa, karfi da yaji. D’an karamin tsako yana nema ya zamarmin ciwon ido, ya kuma zama dole na kawar dashi dole na b’atar dashi adoron kasa, dole yabar numfasawa nan bada jimawa ba, Domin Idan ba haka ba zai jawo babban b’arakar da dinketa zaiyi mana matuk’ar wahala.” Gyara zama Alhaji Abdu Tababa yayi, cikin son kwantarwa da Alhaji Idi’n hankali yace. “Karka damu Insha Allah, duk yanda zamuyi sai munyi. Dan sanin duk wani abu daya shafesa, dole zamu kashe sa. Domin barinsa araye hadari ne.” “K’warai kuwa ai dole ne ma sai ya mutu, batun nemo gidansu kuwa, ku barshi a hannuna da kaina zanyi wannan, Domin ni na mafi bukatar mutuwarsa ayanzu fiye da komai, gaba daya duk ya tottosheni, acikin kaso 100 na daga mutanen da suke zuwa hospital dina, yanzu kaso 80 sun koma masa, kullum da bakin cikin abun nan nake kwana.” Cewar Dr Lukman. Dukansu kwafa sukayi, Yayinda kowannensu ya soma tsara irin bak’ar nufin dake cikin zuciyarsa. Acan gidan su Rayyern kuwa, da matsanancin farinciki, Mamy take Kallon Abba wanda ya gaya mata batun d’aurin auren Rayyern din. “Alhamdulillah, Alhamdulillah Allah mungode ma, Lallai Tabbas komai nada lokaci, Yau RAYYERN dina ya zama ango, Allah ya basu zaman lafiya, ya kuma saka al'khairi da al'barka acikin auren, ya kade musu duk wata fitina.” Da. “Ameen.” Abba ya amsa. Batare kuma daya jima awajen Mamyn ba, ya tashi kaitsaye ya tafi wajen Baba Maud’o. Mamy kuwa cikin tsananin farinciki ta fito falo ta zauna, dai-dai lokacinne kuma Ramadan da Riyyam-nsra suma suka sauk’o k’asa. Riyyam-nsra ne ya karaso wajen Mamyn da sauri, cikin farincikin da yake ciki ne kuma yace. “Mamy yaufa Auren Hamma Rayyern, gaskiya ya kamata ace mun d’an shashe, duk da ma auren sirrine amma ai dai mukam ya kamata, mu Dan shana ko Mamy.” Murmushi Mamyn tayi, tare da dan jinjina masa Kai alaman eh. Saboda tana cikin farin ciki itama yau din. Riyyam kuwa waka ya kunna awayarsa, tare dayi musu connecting da tv, nan take kuwa sautin wakan Davido Maisuna Jowo ya soma tashi. Nanfa Yayi starting video awayartasa, tare da soma rawa wayar na shooting d’insa, Mamy kuwa dake zaune gudun kada ya shooting da ita ne yasa ta tashi ta koma daki. Tana tafiya kuwa Ramadan shima ya mik’e yana taya Riyyam-nsra din dancewa dan shi farin cikinsa biyu ne auren Hammansa da kuma samun damar nasa. Adai-dai lokacinne kuma Rayyern ya bud’e murfin kofar dakinsa ya fito, jikinsa dauke da danshin ruwan alwala, kasancewar adai-dai lokacin ana ta kiraye kirayen sallan la’asar. Tun kafun ya gama saukowa akan steps din falon, kuwa yake jin kida na tashi. Da sauri ya dan karaso cikin falon. Abunda ya ganine kuma ya sashi tsayawa, tare da dakawa su Riyyam din tsawa, fuska a murtuke yace. “Mekukeyi haka, wannan wanni irin haukan banzane, ya zaku mayar mana da gida kaman filin gala ko club? Akan meye zaku cika mana gida da kide-kide, saboda meye akan wani dalili??” Cikin fada sosai ya kare maganar. Wanda hakan yasa Zakariyya Dan langwabar da kansa. “Eyyah Hamma Rayyern Dan Allah ka barmu, yau fa ranar farinciki ne ranar auren babban yaya.” Harara Rayyern din ya watsa masa, kana cikin takaici yace. “Nabaku nanda 1mn ku tsaida kidannan, sannan lokacin sallah yayi, kuje kuyi alwala ku wuce masallaci.” Baki Riyyam-nsra din ya dan turo gaba, dai-dai lokacin kuma Mamy ta fito daga cikin dakinta. Kallon Mamyn Rayyern yayi, tare da d’an narkar da fuska yace. “Mamy yaran nan basa ji, wai kida suke kunna mana acikin gida, kuma Mamy kinajinsu amma kika kyalesu.” Murmushi Mamyn tayi tare da cewa. “To Rayyern me kakeso nayi musu, na hanasu nishadi? Bayan ni kaina yau din farin cikin dake zuciyata bazai misaltu ba, yaufa aka daura maka aure, kaga Aikuwa ya zama dole muyi farinciki.” Fuskarsa yadan narke, kaman zaice wani abu kuma saiya fasa kaitsaye ya fita tare da wucewa zuwa masallaci. Yayinda su Riyyam-nsra da Ramadan kuwa suka haura sama dan gabatar da nasu alwalan. Rayyern kuwa Koda yaje masallacin, bayan an idar da sallah, kaitsaye company d’insa ya sake komawa, yayi hakanne kuma saboda kwata kwata bayason zama haka har wani tunani ya dameshi. Yayinda su Ramadan kuwa bayan sun idar da nasu sallan, suka shiga gari, musamman kuma suka yada zango a Green park, nanfa Riyyam-nsra ya shiga aikin yi musu Video, yana sending direct to Tiktok, daga karshe ma live ya fara yi. Daga nan masaukinsa Ramadan ya wuce dole yasa Riyyam-nsra kwatso kwamutsansa suka taho gida. Basu ne suka dawo gidan ba kuma, saida akayi sallan magriba. Bayan sun dawo dinne kuma suka shirya kayan Riyyam-nsra sukayi al'wala kana suka wuce masallaci. Rayyern kuwa har saida aka idar da sallan Isha kafun yake dawowa gida. Anan falo ya samesu dukansu suna dinner. Shigowarsa ne kuma yasa Mamy sakin murmushi, cike da kulawa tace. “Yauwa Babana ka dawo ko, yanzu nake zancenka araina, zo kaci abinci.” Kansa ya dan langwabar tare da Karasowa dining table din, “Na nakoshi.” Ya fad’a akasalance. Wanda hakan yasa duk suka tsura masa ido, musamman Abba. Shikuwa Rayyern still sake kwab’e Fuskarsa yayi, tare da dubansu yace. “Ni baccima nakeji saida safe.” Yana gama fadin hakan kuwa, baijirayi me waninsu zaice ba kaitsaye ya haura Sama. Da Kallo Abba ya bisa, Yayinda acikin ransa yake mamakin halin Rayyern din, daga daura masa aure kawai lokaci daya harya sanja, sai kace wani mai aljanu. Da haka dai suka ci gaba da cin abincinsu, bayan sun kammala ne kuma Abba ya koma dakinsa, Yayinda Ramadan Riyyam da Mamy kuwa suka zauna afalo, suna yar tab’a hira. 11:30 pm. Gaba d’aya ko ina dake Cikin gidan, yayi shiru babu wani alaman kwakkwaran motsi dake tashi, wanda kuma hakan alamace dake nuna cewar duk wasu mutannen dake zirga-zirga acikin gidan sunyi bacci. Haka ma compound din gidan babu kowa, ko ina shiru. Daga can gefe kuwa, gaba daya guards din da suke gadin Jannart ne kwance, kowannesu ya sake katon baki da ciki, suna bacci kamar matattu. Ind daga gefensu kuwa Baba Ado ne zaune, yana rik’e dayar radion sa. Sai kuma Ashiru dake bakin gate, yana ta faman lellek’awa tako ta Ina, gudun kada su aikata kifi na ganinka mai jarkoma. Acan cikin gidan kuwa, Momy ce ta fito daga cikin dakinta, cikin shirin kayan bacci, kaitsaye kuma dakin Daddy ta nufa. Jannart dake tsaye acikin dakinta kuwa, Idanunta dake zubar da hawaye ta lumshe. Wani iri takeji, Yayinda acikin ranta kuwa take cewa. Inama da zata iya bijirewa umarnin Abba Kabir din, da zatace itakam ta fasa, da zata zauna agidansu da dadi ko ba dadi, tayarda kaddarar ta ce tazo a haka. To amma ya zatayi? Bata da wani zabi ako da yaushe, tasani zatayi kewar gidansu sosai, zatayi kewar dakinta da kuma yan uwanta. “Zanyi kewarka Daddy na, zanyi kewar Momy da Abdull, nasani zanyi kewar duk wani abu daya shafeni, Daddyna baya tab’a takuramin, bayayimin komai, kawai dai baya daukan mataki akan duk wani cin zarafi da Yah Junaid zaimin.” Ta fadi hakan hawaye na ci gaba da zubowa akan fuskar ta. Cikin sanyi da mutuwar jiki kuma ta d’auki yar jakar da ya hade komai nata na amfani aciki. Drawernta ta bud’e tare da zaro, wani hijab mai kyau hadi da tsananin taushi ta zura akan, Daguwar rigar, Arabian gown dake jikinta. Juyawa tayi Ahankali ta nufi kofar fita daga dakin, Yayinda tabar wayarta da goro da kuma sweets din da Abba Kabir ya bata atsakiyar gadon dakin. Harta Kai bakin kofar fita ne kuma ta juyo, ta sake Kallon cikin dakin nata. Lokaci daya kuma hawaye ya cigaba da sauka akan fuskarta. Saidai kuma babu yanda ta iya, haka ta murda handle din kofar, cikin sand’a ta fice. Fitowar nata ne kuma yayi dai-dai da wulgawan Momy, wanda ta wuce dakin Daddy. Saurin komawa baya tayi ta labe. Harsaida ta tabbatar da wucewan Momyn kafun ta fito, cikin tsananin sand’a take tafiya. Harta karaso Cikin falon da Kwata Kwata babu yalwan haske acikinsa. Handle din kofar falon ta murda Ahankali, bayan ta fito ne kuma ta maida kofar ta rufe. Dai-dai lokacinne kuma Abdull wanda ya fito daukar ruwa, yaji kaman karan rufe kofa, saurin maida kallonsa ga kofar yayi, saidai ko alaman motsi baiga kofar tana yiba, gashi kuma babu kowa acikin falon, hakan yasa yayi tunanin ko kunnuwansa ne basu jiye masa dai-dai ba, kasancewar yana gigin bacci, bayan ya d’auki ruwanne kuma ya juya ya koma dakinsa. Jannart kuwa Koda ta fito compound din gidan, cikin sand’a take tafiya, wanda hakan yasa Baba Ado dake tsaye yi mata alama akan tayi sauri. Yayinda shikuwa Ashiru ya fita ya lellak’a musu waje, ganin babu kowa a arean wajenne kuma, yasa Ashirun daga mata hannu akan tazo ta wuce. Aikuwa cikin sauri, da kuma tarin fargaban da takeji ta zo ta fice daga cikin gidan. Yayinda Baba Ado shima ya rufa mata baya. Ganin ficewar nasu ne kuma yasa Baba Ashiru maida kofar ahankali ya rufe. Jannart kuwa tafiya suke ita da Baba Ado, wanda ya riga da yayi gaba, ita take biye dashi abaya. Tafiya kuwa sukayi mai dan tsawo. Kamar kuma yanda Abba Kabir din ya fad’a, kwana Uku suka shiga, ata ukunne kuma suka hango motarsa. K’arasawa sukayi da sauri, inda Baba Adon kuma da kansa, ya budewa Jannart din gidan baya ta shiga ta zauna. Kallon Abba Kabir din yayi, kana yace. “Barrister Allah Yatsare ya kuma, taimaka akan duk wani abu da kukasa gaba, Allah Ya tono gaskiyar da ake boyewa.” Da Ameen Barrister Kabir din ya amsa, Yayinda shi kuwa, Baba Ado ya juya Cikin sauri ya nufi hanyar komawa gidan, yana isa gidan kuwa, Baba Ashiru ya bud’e masa kofa. Sa d’ab sad’ab haka ya shiga cikin mayan guard dinnan ya kwanta. Barrister Kabir kuwa tada motar tasa yayi suka bar wajen. Kaitsaye kuma Nassarawa G.R.A suka nufa. Ita dai Jannart tunda ta shiga motar, ta kwantar da kanta ajikin kujera, hakanan takejin kanta wani iri. Tafiyar mintuna kadan sukayi, suka shigo Cikin unguwar. Adai-dai gaban babban gate din gidan, kuma Abba Kabir ya tsaya tare da dan danna horn. Ari dake zaune ne ya taso ya bude musu, kasancewar Baba Maud’o karatun Qur’ani yakeyi shiyasa, Arin bai katseshi ba kuma dama Abba da Rayyern sun hanashi ziryar buɗe gate. Ana bud’e gate din kuwa, Barrister Kabir ya tura hancin motar tasa ciki. Bayan ya gama dai-dai-ta parking din motar ne, kuma ya bud’e b’angaren da yake ya fito. Karasowa wajen su Baba Maud’on da yanzu ya shafa addu'a. Isa garesa yayi, cikin girmamawa da kuma sakin fuska, ya bawa Baba Maud’on hannu suka gaisa. kana yace. “Dan Allah Baba Maud’o ko zaka iya nemamin iso zuwa cikin gidan.” Murmushi Baba Maud’o yayi, tare da mikewa tsaye yace. “Babu komai, Barrister bari nayiwa Alhajin magana.” Kai Barrister Kabir ya jinjina, Yayinda shikuwa Baba Maud’o kaitsaye ya nufi cikin gidan, Koda ya karasa jikin kofar, kwankwasawa yayi tare dayin sallama. Abba dake zaune afalo kuwa, Jin muryar Baba Maud’o ne, yasashi mikewa tsaye. Tare da tasowa yazo ya bude kofar. “A’a Baba Maud’o kaine.” Abban ya fada. Inda Baba Maud’o kuwa gyara tsayuwarsa yayi, tare da cewa. ”Ni ne Alhaji dama Barrister Kabir ne yace na nemama masa iso.” Murmushi Abban ya fadada, tare da cewa. “Masha Allah kace masa ya shigo.” Da To Baba Maud’o ya amsa, kafun ya juya kaitsaye ya nufi wajen da Barrister din ke tsaye. “Yace ka isa.” “To To masha Allah Nagode sosai.” Barrister Kabir din ya fad’a, yana me bud’e murfin motar, nan b’angaren baya inda Jannart din take. Wanda kuma tad’an rufe gefen fuskarta, da tattausan hijabin dake jikinta. Hannunta Abba Kabir din ya kamo, tare da cewa. “Jannart fito, amma ki fito da kafar dama sannan ki rike addu’a a bakinki.” Kanta ta Dan jinjina, cikin kuma sheshshekan kukan da yaso kwace mata ta fito daga cikin motar. Sosai takejin kirjinta na wani irin bugawa, ga kuma wani nauyi da takeji acikin zuciyarta. Yayinda hawayen dake cikin idanunta kuwa har yanzu suka kasa tsayuwa, shin wanni irin kulline acikin rayuwarta da har yasa akayi mata irin wannan auren? “Masha Allah mu isa To.” Baba Maud’o ya fad’a, yana me shigewa gaba, shikuwa Abba dake rike da hannun Jannart ya rufa masa baya. Koda suka isa bakin kofar falon kuwa, Abba da kansa ya taso ya bud’e musu. Tare da yi musu iso, cikin tsananin farinciki da jin dadi. Karasowa cikin falon sukayi, Inda Abba Kabir din ya Zaunar da Jannart akan lallausan carfet din dake cikin falon. Kana ya zauna asaman kujeran dake gefenta. Abba kuwa Kallon Ramadan yayi, kana fuska asake yace. “Ramadan jeka kiramin Rayyern.” To Ramadan ya amsa, tare kuma da mikewa cikin sauri ya haura sama dan kiran Rayyern. Rayyern dake kwance yana latsa system d’insa, jin muryar Ramadan dake knocking yasashi bada izinin shigowa. Bud’e kofar Ramadan yayi ya shigo. Cikin girmamawa, yace. “Hamma Rayyern Abba na kiranka.” Kai Rayyern din ya jinjina, Yayinda Ramadan kuwa ya juya ya tafi. Koda ya dawo falon, cewa Abban yayi Rayyern din yana zuwa. Kai Abba Ya jinjina, tare da cewa. “Masha Allah to kaida Riyyam kudan bamu waje.” Babu musu kuwa, duk suka Mike suka nufi steps din sama. Suna haurawa kan steps din kuma Rayyern yana sauk’owa. Kallonsa Ramadan yayi, tare da d’an gumtse dariyar farin cikin dake cinsa na sanin yanzu shine a layi. Shikuwa Rayyern wani irin masifeffen kallon ya watsawa Ramadan, musamman alokacin daya sauke idanunsa akan Barrister Kabir da yake Zaune acikin falon. Hakan yaji wani irin takaici ya cika masa zuciya sabida anfa dameshi matuka an hanashi salama. Su kuwa Ramadan da Riyyam-nsra neman waje sukayi suka tsaya, Acan saman stairs din. Yayinda shikuwa Rayyern jiki asanyaye ya karasa saukowa cikin falon. Inda Barrister Kabir ke zaune agaban Abba, still kuma har yanzu yana rik’e da hannun Jannart wanda ta sunkuyar da kanta k’asa. Abba kuwa Kallon Barrister Kabir din yayi, cikin tausasa Murya yace. “Barrister daka koma sama ka zauna, Domin aduk sanda kazo gabana ka zauna akasa sai naji abun yamin nauyi.” Murmushi Barrister Kabir din yayi, kana cikin mutum tawa yace. “Babu komai Alhaji, zamana a k’asan bawai gazawa bace, kuma hakan yana da dalili.” Kai Abban ya jinjina. Tare kuma da kai dubansa ga Rayyern wanda ya karasa shigowa cikin falon. “Zoka zauna anan Rayyern.” Abban ya fada yana me nunawa Rayyern gefensa, kuma kusa da Mamy dake zaune. Yayinda Jannart kuwa hawayen Idanunta, kwata-kwata sun kasa tsayawa, saboda yanda kukan ke neman cin karfinta ne kuma yasa har shashshekan kukan nata ya Dan soma fitowa. Idanu duk suka zubawa Jannart din da kanta ke k’asa, Yayinda tsananin tausayin yarinyar ke sake lullub’e zuciyarsu, musamman ma Mamy da taji son yarinyar acikin zuciyarta, duk da cewar bata ga fuskar yarinyar ba, amma taji ta kwanta mata. Rayyern kuwa yanda ya dauke kansa gefe, tamkar ma baisan da wata mai sakin sheshshekan kuka acikin falon ba. Abba Kabir kuwa gyara zamansa yayi, tare da sake rike hannun Jannart kam, cikin muryarsa da tayi rauni sosai yace. “Alhamdulillahi. Yau gani na agabanka Alhaji Bashir, ga y’ata nan Jannart na kawota gareku”. Sai kuma ya ɗan numfasa kana a hankali yaci gaba da cewa. “Bansanku ba baku sanni ba, amma musulumci ya had’a mu kamar yanda manzon Allah yace, Almuslimu ak’ul muslim, musulmi d’an uwan musulmi ne, na nemi taimako kunyi mini, har lau kuma Ina sake neman taimakonku, akan kulawa da y’ata Jannart, da kuma rik’emin amanarta, Jannart amanace awajena numa kuma nima yau zan baku amana, arikemin Jannart Amana marainiya ce, Dan Allah ku rikemin amanarta, Jannart bata da laifi, jarrabawar rayuwace tazo mata ahaka. Kana bata da tashin hankali, Jannart yarinyace mai tsananin biyayya, haka kuma mai tausasshiyar zuciya, Jannart yarinyace mai rauni, yarinyar da maraici ya cika gaba daya rayuwarta, Ina da tabbaci akan biyayyar Jannart. Domin yarinya ce da take gudun bacin ran wanda ke kusa da ita, Idan tayi muku ba dai-dai ba ku hukuntata kamar yanda zaku hukunta y’ay’an cikinku.” Dan tsagaitawa da maganan nasa yayi, saboda yanda Hawaye ke sauka akan fuskarsa. Juyowa da kallonsa yayi ya kalli Mamy, cikin sanyin jiki yace. “Hajiya ga Jannart nan na kawo muku Amana, Dan Allah ki rikemin ita, ki dauketa tamkar yar da kika haifa acikin cikinki, Dan Allah ku killacemin Jannart, banason ko k’ofar gida ta l’eka, Idan kuma akwai buk’atar fitar ta wanda ya kama da dalili a gayamin, saboda banason idanun wasu su sauk’a akanta. Domin fataucin rayuwarta sukeyi, tamkar wanda yaje farauta yagaji bai samu komai ba, haka suke ayanzu, da zaran lokaci ya cika akanta zasu dire, suna son su kasheta, suna tsananin son ganin bayanta, Alhamdulillah yau inajin na sauke wani nauyi akaina...” Kasa karasa maganan nasa yayi, saboda kukan da yakeji na tasar masa. Yayinda Jannart kuwa tuni kuka yaci karfinta, ba abunda ke tashi kuwa face sautin kukan ta. Wanda hakan yasa gaba daya su Abba, Mamy, da Baba Maud’o duk jikinsu yayi sanyi. Shikuwa Rayyern zuwa yanzu ya tankwashe kafafunsa, tare kuma dayin shiru, ya sunkuyar da kansa k’asa. Haka kuma yakejin kansa na. Dan sarawa, Yayinda yakejin jijiyon dake cikin kannsa nayi masa ciwo. Badon komai ba kuma saidan saboda yanda yakejin kukan yarinyar na hawa kanshi. Barrister Kabir kuwa Hannun Rayyern din ya kamo. Da sauri Rayyern ya ɗago kansa ya kalleshi. Sai kuma yayi ƙasa da ida nunshi ganin yadda mutumin mai girma yana kuka. Shi kuwa Barrister Kabir. cikin sanyin da jikinsa yayi yace. “Rayyern ga amanar diyata matarka”. Ya ƙare mgnar yana mai ɗago hannun Jannart ya saka acikin tattausan tafin hannun Rayyern din tare dasa nashi hannun ya rumtse tafin hannun Rayyern dake riƙe dana Jannart ya rumtse ya haɗe su...! *Littafin TUBALI na kuɗine special Group 1k ne ƙaramin group 500 yawan posting ne banbanci su, 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU sai ki turo min shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276, in baki da halin turawa ta banki to ki sayi katin MTN ki copy number's din ki turo min ta WhatsApp na* By *GARKUWAR FULANI* 11/15/21, 7:21 PM - Auntyna: Wani irin raunataccen kuka ne ya kwabcewa Jannart cike da rauni shessheƙan kukan yake fitowa, yana ratsa kunnuwansu. Banda kukan Jannart dake tashi, shiru gaba d’aya falon ya d’auka. Yayinda Rayyern kuwa ya sunkuyar da kansa k’asa, tare kuma da rumtse idanunsa gam dan jin fatan saman idonsa nata karkarwa. Domin kuwa adai-dai lokacin da hannun Jannart din ya sauk’a acikin nasa hannun, wani irin harbawa zuciyarshi tayi tare da buɗewa da azaban ƙarfi. Duk da cewar kuwa ba wannan bane first time nasa daya fara tab’a jikin mace, musamman Idan akayi duba da irin yanayin aikinsa, saidai kuma a iya tsawon rayuwarsa, bai tab’a rik’e jikin mace, da sunan wai dan yaji wani abu ajikinsa ba, yana rikewa ne kawai idan takama dole, enfact ma shi baicika son duba mata ba, sai idan abun yayi worst ya kuma zama lallai dole shidin ake da buk’atar ya duba su. Sam bai tab’ajin wani abu makamancin haka ba. Tamkar kuma yanda zuciyar tasa ke bugawa haka ma Jannart, da itama takejin wani irin bugun zuciya, badon komai ba kuwa saidan samun hannunta da tayi acikin nasa, haka kuma Wannan shine karo na farko a rayuwar ta, da wani d’a Namiji wanda bata sani ba kuma ba Muharraminta ba ya tab’a jikinta, domin kuwa Bayan Yah Junaid, Daddy, Abba Kabir, Abdull, sai kuma Dr Lukman wanda ya kasance Dr dinta ne, babu wani wanda ya tab’a kama Koda farcenta ne, sai wannan ayanzu da hannunta yake cikin nasa. Wanda kuma hakanne yasa taji zuciyarta tayi mata nauyi, Yayinda duk wani rauni dake narke acikin zuciyarta ya sake hauhuwa, lokaci daya taji tamkar wani mafakan kuka ta samu. Dan tsabar kukan dake cinta har wani seizing numfashinta keyi. Cikin muryarta da ta dashe sosai, ta saki Sabon kukan da sauti da amonsa ya zarce na baya mai cike da rauni. Domin ayanzun kuka take da duka zuciya da gangar jikinta, kukan dake bayyana tsananin tarin damuwa da maraicin rayuwarta, kukan dake bayyana rauninta, haka kuma kukan da yasawa kowannensu matsanancin tausayinta. Musamman Mamy da gaba daya k’walla ya cika mata idanu. Rayyern kuwa har yanzu idanunsa a rumtse suke, saboda yanda sautin kukan nata ke ratsa cikin kunnuwansa, yasa gaba d’aya yaji kansa na juyawa, Sam bayason wani hayaniya ko kuma yawan koke-koke, kwakwalwarsa bata iya jure hakan. Abba Kabir kuwa wasu irin hawaye masu zafi ne, suka gangaro daga kan fuskarsa, sake matse hannunsu awaje daya yayi, cikin kuma muryarsa da tayi rauni sosai yace. “Rayyern ga amanar y’ata Jannart na kawo maka, ayanzu kaine Mijinta majiɓamcin lamuran rayuwata, kaine kuma wanda nakesa ran zaka zame mata Garkuwa, Rayyern Jannart marainiyace, wacce tataso acikin kad’aici da tarin damuwa, Jannart batasan wani farinciki ba Rayyern. Domin ako da yaushe damuwa da kuma fargaba suke cika zuciyarta, Karikemin amanar Jannart Rayyern, Domin ayanzu duk wani motsinta yana karkashin kulawanka ne da ikonka, Jannart ta rayu akan wata turba ta daban, sannan an tarbiyantar da ita akan biyyya da kuma karb’an umarni akan duk wani abu da aka sata, ko kad’an bani da haufi akan Jannart, Domin kuwa Ina da tabbaci akanta, nasani Jannart bazata tab’a sab’amaka ba Rayyern idan kuma ta saɓa maka to ajizancin ne da yake halittar ɗan Adam. Dan Allah ka kula da ita, Koda ace bazaka dauketa awani matsa yi na musamman ba, To Ina fatan ka karb’eta amatsayin k’anwarka, Jannart tana buk’atar kulawa Rayyern, tana kuma buk’atar farinciki, saboda ita din Marainiya ce...” Ya Kai k’arshen maganan cikin muryarsa dake rawa, hadi da alhinin sark’ak’iyar dake cikin rayuwar Jannart din. Ahankali kuma ya dawo da kallonsa ga Jannart din, cikin matukar sanyin murya da kuma son kwantar mata da hankali yace. “Jannart ga Mijinki nan, kiyi masa biyayya kamar yanda kika saba, ki kuma gujewa duk wani abu dazai b’ata ransa, Dan Allah Jannart ki kiyaye kinji, Insha Allah watarana zaki samu ingantaccen farinciki, watarana duhu zaiyaye inda haske zai cika cikinsa, ako wani bayan kunci akwai farinciki,sannan ako wani bayan k’addara akwai sauki, komai da muke yi yanzu da kuma wanda zamuyi anan gaba, rubutacce kuma tsararrene, wanda Allah ya tsara mana, babu wata damuwa da zata Tabbata Jannart nasan kinyi imani da hakan.” D’an tsagaitawa Abba Kabir din yayi, cikin kuma hawaye dake zuba a idanunsa, ya zare hannunsa dake saman nasu, tare da tallafo fuskarta, ya sumbaceta akan goshinta. “Zan tafi Jannart, ki kula da kanki, kada ki sab’awa kowa dake cikin gidannan, Domin ayanzu sune y’an uwa kuma Garkuwarki.” Abba Kabir din ya fad’a yana me kokarin mik’ewa tsaye. Jannart da kuka ya riga daya ci karfinta, saurin rik’o k’afafunsa tayi, tare da sake fashewa da kuka. Domin hakanan takejin kamar Idan ya tafi bazai dawo ba, tayaya zata iya jure zama amatsayin matar aure? Hakan wani rayuwane da bata sanshi ba, batasan wacce irin kalubale ne zata fuskanta ba, Tabbas ta sani acikin rayuwarta gaba d’aya duhu ne, ita da batasan menene cikakken fari ciki ba, tayaya zata iya bawa wani? Rayyern kuwa cikin takaicin kukan nata dake shirin fasa masa kwakwalwa ya zare hannunsa, tare da kawar da kansa gefe, yana mejin tamkar yasa hannayensa ya toshe kunnuwansa ko bakinta. Abba Kabir kuwa kukan da Jannart din keyi ne ya matuk’ar karyar masa da zuciya. Ahankali ya d’an sunkuyo, tare da kama kafad’un Jannart din cikin tausasawa hadi da rarrashi yace. “Jannart din Abba ki daina kuka, tafiyar da zanyi ayanzu bawai yana nufin bazan dawo bane, Lallai Zan dawo Jannart, ki saki ranki ki dauka nan tamkar gidanku ne, kuma suma iyayenki ne, kamar yanda muke kulawa dake haka suma zasu kula dake, ako da yaushe Ina miki fatan al'khairi da nasara Jannart, Allah ya sanya al'barka acikin rayuwar aurenki.” Cikin matsanancin kukan dake addabarta, ta Dan soma jujjuya Kai. Ganin hakanne kuma yasa Mamy da ta kasa tsaida ruwan hawayen daya zubo daga cikin idanunta tace. “Zo Jannart kema y’atace kamar yanda su Rayyern suke yayana, ki daina kuka kinji, Insha Allah zan zame miki mahaifiyar dake share kukan yayanta, ki sa aranki kuma cewar kina tare da mahaifiyarki ce, ki kalleni amatsayin wacce ta haifeki, bawai matsayin suruka ba, ni kuma har abada zan rikeki amatsayin y’a, Domin dama Allah baibani y’a Mace ba,. To yanzu gashi ya turo min ke amatsayin kyauta biyu, y’ata kuma suruka ta, Insha Allah bazamu bari kiyi kuka ba.” Mamyn ta fad’a tana me jawo Jannart din jikinta, tare da kwantar da kan Jannart din akan cinyarta. Hakanne kuma yasa Jannart din, lafewa ajikin Mamyn tana sakin sheshshek’an kuka akai akai. Abba kuwa da Baba Maud’o duk mik’ewa tsaye sukayi, saboda Ganin Barrister Kabir din da sukayi ya mik’e. Koda ya soma tafiya, Mara masa baya sukayi, Dan yi masa rakiya. Suna fita daga cikin falon, kuwa Rayyern da yake jinsa tamkar akan k’aya ya mik’e tsaye, ko kallon inda Jannart din take kuwa baiyi ba, kaitsaye ya haura sama, yana Jin tamkar shi dinma ya fashe da kuka suyi tayi a tare tsabar takaici, haka kawai an takura yarinya. Tazo da wani shegen kukanta tazo ta saukar masa da ciwon Kai. Mamy kuwa, hannu tasa ta soma sharewa Jannart din hawayen dake kan fuskarta, wanda kuma saboda tsabar kukan da tayi, har saida idanunta suka zama jajur. “Kiyi hakuri Jannart, ki daina wannan kukan kinji, haka rayuwar kowacce ya mace yake, Aranar da aka rabata da gidan iyayen ta, saboda haka hakuri zakiyi, da sannu kuma zaki saba da zama damu, ba amatsayin surukata kawai kike ba, ke y’ata ce.” Mamyn ta fad’a tana me shafa bayan Jannart din alaman rarrashi. Saidai kuma duk da haka Jannart din ta kasa tsaida hawayen dake kwaranya daga cikin idanunta, kukan ya riga dayaci karfinta, duk yanda taso tsaida kukan nata ita kanta ta gaza, amma saidai jin kanta da tayi ajikin Mamyn, ya d’ansa zuciyarta tayi sanyi ko yanzu tasan ta samu madadin Mom. Yayinda Acan waje kuwa har bakin mota Abba da kuma Baba Maud’o suka rako Barrister Kabir. Ganin yanda shi kansa damuwa ke bayyane akan fuskarsa ne kuma yasa Abba da kansa yace. “Ka kwantar da hankalinka Barrister, Domin kamar yanda ka aminta damu, ka d’auko Jannart ka kawo mana ita cikin gidannan Insha Allah, bazamu bari hawayenta su zuba ak’asa ba, zamu zame mata iyaye na gari, idan tayi rayuwar maraici abaya Ina mai tabbatar maka da ayanzu Jannart bazata sakeyin rayuwar maraici ba, Zamu zame mata Garkuwa da yardar Allah, ka bamu amana kuma zamu rik’e, Jannart ba zata sakeyin kukan kadaici da maraici ba, zamu bata duk wani farinciki.” Kai Barrister Kabir din ya jinjina, tare da kamo hannun Abban yace. “Nagode kwarai Alhaji Bashir, Lallai Tabbas yanzu na sake gamsuwa da cewar, na kawo Jannart inda ya dace, na kawota inda za’a bata kulawa, inda bakuma za’a bari tayi kunci ba, Alhamdulillah Allah ya tayaku rik’o”. “Ameen.” Abba da Baba Maud’o suka amsa. Hannu Barrister Kabir din ya mik’awa, Abba da Baba Maud’o suka sakeyin musabaha. Bayan yayi musu sallama ne kuma ya bud’e motarsa ya shiga, Ari ne kuma ya bud’e masa gate din gidan ya fice. Har acikin ransa yana mejin gamsuwa na abunda ya aikata, Domin yasani acikin abunda ya aikatan Kwata-kwata babu kuskure, Allah yaga zuciyarsa da kuma kyakkyawan nufinsa. Burinsa shine fito da gaskiyar da azzalumai suka b’oye, wanda kuma yake da tabbacin Allah zai bashi sa’a, akan dukkan komai, Domin Allah ba azzalumin kowa ba ne, saidai wanda ya zalunci kansa. Su Abba kuwa ganin tafiyarsa ne, yasa Baba Maud’o wucewa makwancinsa kaitsaye, inda shi kuwa Abba juyawa yayi ya koma cikin gidan. Barrister Kabir kuwa kaitsaye gidansa ya nufa. Koda ya isa cikin gidannsa karfe 12:40 na dare. Kaitsaye dakinsa ya wuce, bayan yayi wanka ne kuma Aunty Dijat ta kawo masa Coffee. Sai-dai ganin yanda gaba daya jikin mijin nata ke sanyaye ne yasa, ta gyara zama tare da kamo hannunsa, cike dason basa kwarin guiwa tace. “Ka kwantar da hankalinka Abban Hafeez, Domin nasan duk wani abunda ke damunka, ayanzu bai wuce akan Jannart, meyasa zaka damu Abban Hafeez, bayan kasan cewar wannan auren shine abunda zai kawo sauyi da farinciki acikin rayuwar Jannart, wannan auren shi zaisa Jannart tasan wacece ita, shi ne kuma zai warware mata duk wani k’ulli dake cikin rayuwarta, Tabbas wannan auren al'khairi ne, kuma Insha Allah akwai lokacin da Jannart zatayi al'fahari da wannan Auren, musamman alokacin da ta gano cewar ka zab’a mata miji, mai nagarta irin wanda bashida saukin samu, sannan ka ceci rayuwarta daga sharrin mak’iyan dake kewaye da ita, way’anda take kwana acikinsu, take tashi batare da ta sani ba.” Kai Barrister Kabir din ya jinjina, Cikin samun karfin guiwa kuma yace. “Insha Allah Jannart zatayi farinciki, komai kuma zai yaye, ayanzu duniyarta zatayi sanyi, Domin tafita daga cikin magauta, hakika ko ayau na mutu, nasan na mik’a Jannart ga inda za’a tsaya mata, inda babu wani maitsaurin ido daya isa zuwa yaci mutumcin ta, saboda Rayyern ba kanwar lasa bane ba kuma mutum bane kamar kowaba, shi na musamman ne domin naga tsoronshi cikin idanun Magautan nasa da Jannart. Tun ran forko kuma dana ganshi ya tunomin wani ma irin zarrarsa a tsakiyar su Yaya idi wanda sukayi nasarar kaudashi a duniya. Sai naketa kamar Allah ya turo Rayyern garesune dan ya tono jiyansu ya tsaida yau ɗinsu ya birkita gobensu yadda yake musu mgna kamar ɗan fansa ne, Insha Allah kuma watarana Jannart sai ta zamo wani sashi na jikinsa.” Murmushi Aunty Dijat tayi, saboda ta fahimci kalaman da mijinnata ke nufi. Acan gidan su Rayyern kuwa, Koda Abba ya dawo cikin falon, anan ya sameta zaune ita da Jannart din, da har yanzu ta kasa daina zubda hawaye. Zama Abban yayi Tare da tausasa muryarsa cikin aminci yace. “Jannart”. Wani irin sanyi taji muryar Abba ya sakar mata. Shi kuwa a mutunce yace. “Jannart d’ago kanki ki kalleni.” Jannart dake sakin shesshekan kuka, sake Jin Muryar Babban mutum acikin kunnuwanta ne yasa ta d’ago kanta Ahankali, da kuma Idanunta wanda sukayi luhu-luhu ta kalleshi. Kai Abban ya girgiza, kana cikin lallashi da ban baki yace. “Kada kiyi mini wani kallo na daban Jannart, inaso ki kalleni amatsayin mahaifinki, ni Babanki ne, kada ki ajiyeni amatsayin suruki kawai, saboda na daukeki ne amatsayin y’a, wanda har abada kuma bazan tab’a bari kunci yayi tasiri acikin zuciyarki ba, wannan gidan kada ki daukeshi amatsayin gidan aurenki kawai, ki daukeshi amatsayin gidanku, kafun yanzu bamu sanki ba, amma ayanzu kedin tamuce, kin zama daya daga cikin iyalinmu, munzama iyayenki ke kuma kinzama y’armu, Ramadan ya zama shak’ik’in d’an uwa agareki, dama kuma duk wani wanda yake tare damu, duk wani damuwa da ya dameki kuwa ki sanar mana. Insha Allah zamu magance miki ita, saboda haka ki daina kuka kinji, kisa aranki cewa muna tare dake, kuma Allah Ma yana tare dake.” Kanta ta d’an jinjina, saboda yanda kalaman Abban sukayi tasiri a zuciyarta, duk da cewar ta kasa tsaida hawayen dake zuba acikin Idanunta. Cikin sanyi hadi da muryarta wacce bata fita sosai tace. “Nagode Abba, nagode da karamcin da kukayi min Allah ya kara girma.” Murmushi Abban yayi, kana cikin jin dadin biyayyar yarinyar yace. “Ba komai Jannart, Insha Allah zamu zame miki iyaye na gari, Mamyn Rayyern Ina Rayyern din kuma ya tafi.” Ya ƙare mgnar yana kallon Mamy. “Rayyern ya haura sama.” Mamy ta fad’a tana murmushi. Kai Abban ya jinjina, kana cikin kulawa yace. “To dare na tayi, ki Kai Jannart masaukinta ta kwanta.” Ya ƙare mgnar yana nuna mata side din da zata kai Jannart ɗin. To Mamyn tace, tare kuma da kama Hannun Jannart din suka nufi, wata had’add’Iyar k’ofa dake nan cikin falon, kusa da side din kitchine da kuma dining area. Ahankali Mamy ta tura k’ofar d’akin. “Ki shigo da bismillah.” Mamyn ta fad’awa Jannart Cikin kulawa, hakan kuwa akayi da bismillah Jannart ta jefa k’afarta ta dama acikin falon. Falo ne mai kyaun gaske wanda aka k’awata cikinsa, da wasu had’add’un royal cushions masu kyau, sai kuma labulayen da aka k’awata jikin window dana bedroom door dashi, atsakiyar falon kuwa, wani lallausan carpet ne maikyau da girma, sai kuma babban tv’ plasma’n da aka daurasa akan wani babban tv stand. Sosai falon yayi kyau, duk da cewar babu wasu tarkace masu yawa acikinsa, amma komai da komai mai tsada ne. Sanyin AC da kuma daddad’an kamshin room freshener dake tashi acikin falonne yasa Jannart lumshe Idanunta. Inda Mamy kuwa kaitsaye ta wuce jin wata kofa dake cikin falon, still kuma tana rik’e da hannun Jannart ta bud’e kofar suka kutsa ciki. Bedroom ne madaidaici wanda aka zuba masa furnitures na alfarma, bed, drawer, and dressing mirror with bedside drawer then shoe rug. Komai dake cikin d’akin kalan pink and white ne, shiyasa haduwarsa yake dajan hankali, kamar dai falon, Domin shima cushions da labulayen cikinsa duk pink and white ne. K’arasa shigowa cikin dakin sukayi, Yayinda Mamyn ta zaunar da ita bakin gadon daya sha bedsheet na alfarma. Kallonta Mamyn tayi, kana cikin tausasawa tace. “Jannart Nan shine masaukinki, zaki zauna ne kuma kafun agama gyara miki asalin inda zaki zauna. Dan Allah Jannart ki saki jikinki, babu wani wanda zai takura miki, akwai komai na amfani da zaki buk’ata, duk abunda kikeso kuma kiyi min magana, banason kiyi kuka kinji ko Jannart”. Cikin sharce hawayen ta gyaɗa kai alamun. Eh taji. Cikin jin daɗi Mamy tace. “Kinga ke amanace agaremu, zubar hawayenki kuma zai zamo damuwa azuciyoyin mu, duk wani abunda ya dameki ki sanar dani, kada kiji shakka ko kuma nauyi na. Domin bana daukanki amatsayin suruka, sannan kada ki bari damuwa tayi nasarar tank’wasar da zuciyarki, kowani bawa yana d’auke da irin salon k’addararsa, saboda haka ki kwantar da hankalinki, ke taki k’addarar ahaka tazo, Insha Allah kuma watarana komai zai wuce, babu wani damuwa dake tabbata, kiyi farinciki aduk wani yanayin da kika samu kanki kinji Jannart.” Kai Jannart din ta jinjina, tare kuma da kama y’an yatsun hannunta cikin sanyi tace. “Insha Allahu Mamy zanyi duk abinda kikace.” Murmushi Mamyn tayi, cikin tsananin jin dadi da farinciki tace. “Yauwa Jannart, Allah Yayi miki albarka, naji dadin biyayyarki. Domin duk wani wanda yake daukar maganan na sama dashi, har abada bazai tab’ayin dana sani ba.” Ta ƙare mgnar tana nufar Bathroom. Ruwan wanka mai dumi Mamyn ta had’awa Jannart acikin bath, tare kuma dasa mata turaren wanka mai dadin k’amshi. Koda ta fito daga toilet din, hannun Jannart din ta kamo ta miƙar da ita, tare da cewa. “Yauwa Jannart kije kiyi wanka ko nasan..” Sauran maganan Mamyn ne ya mak’ale, saboda yanda taji duk jikin Jannart din ya dau zafi. “Subahanallah Jannart gashi duk jikinki zafi, nasan kuma hakan bai rasa na saba, da kukan da kikayi, kije kiyi wanka, akwai sabin towels acikin toilet din saikiyi amfani dasu, akwai kuma ruwan dumi dana had’a miki a bathtub.” “Nagode Mamy.” Jannart din ta fad’a, Ahankali tare kuma da zare dogon hijab din dake jikinta. Mamy kuwa murmushi tayi, kana ta juya ta fice daga cikin d’akin. Koda ta fito nan cikin falon nasu, kaitsaye kitchine ta wuce. Yar ƙaramar tukunya tasa akan gas, cikin abunda baiwuce. 15mn ba kuwa ta kammala had’a indomie’n da ta dafawa Jannart din, wanda yaji kayan hadi da kifi, bayan ta juye indomie’n a plate ne kuma, ta had’a tea mai kauri acikin mug. Bayan ta gama kimtsa komai ne kuma, kaitsaye ta haura sama zuwa dakin Rayyern. Zaune yake akan gadonsa, inda ya sanja shigar jikinsa, zuwa kayan bacci masu taushi. Yanayin yanda yayi zaman duka k’afafunsa na k’asa, sannan kuma ya dafe kansa da hannayensa duka biyu. Idanunsa arumtse suke, kana kuma time to time yake fesar da wani irin numfashi mai kama da ajiyan zuciya. Mamy kuwa isowarta jikin kofar ne yasa ta d’an soma knocking. Sai-dai har tsawon mintuna 2 tana knocking amma bataji a bud’e k’ofar ko kuma bata izinin shigowa ba. Hakan kuwa shi yasa ta murd’a handle din kofar a zayonta ko yana bacci ne, ga mamakinta kuwa sai taga kofar ta bud’u. Ahankali ta tura kanta cikin dakin tare dayin sallama. Anan zaune ta hangosa, ya dafe Kai, da dukkan alama kuma yayi nisa acikin duniyar tunanin da yakeyi. Idanu Mamyn ta Dan tsura masa cike da mamaki, saboda wannan ne karo na farko da taga Rayyern din acikin yanayin zallar damuwa. Rayyen kuwa da yayi nisa acikin duniyar tunaninsa, Sam baisan cewa Mamyn ta shigo ba. Gaba daya hankalinsa ya tafi, izuwa sabuwar k’addarar daya samu kansa aciki. Yayinda har yanzu ya kasa tantance wani irin aure ne aka daura masa, Sam ya kasa tantance marabar auren dana dole, shi ya sani bayason lamarin mace acikin rayuwarsa, but why za’a takura masa? Yasan meye aure yasan manufarsa yasan hakkokin mata a kan mijinta. Yasan bashi da lokacin saukesu da reno da tattalin mace yadda ya kamata shiyasa bai kawo mace a rayuwarsa meyasa zasu liƙa mishi ita a dole su lika mata shi a dole. “Rayyern! Rayyern!!” https://chat.whatsapp.com/IM6PrgYNy9s6lP0aXmBkaN Samun zafafan saukakan kayayyakin zamani na mata tun daga kan leshi, shadda, atamfa, material, jaka da takalmi, hijab..... da dai sauransu akan farashi mai sauki da rahusa sai a kamfanin Garkuwa collection. Bama wannan kadai ba akwai kayan order da muke yi shi ma duk a cikin rahusan da saukin kudi. Ba mu tsaya nan ba ina kuke yan kasar *NIGER* albishirinku kuma kuna iya siyan kayanmu ya isa gareku cikin aminci ba tare da bata lokaci ba. maza yan’uwa ku garzayo ku gane wa kanku wannan rahusar da kuke jin labari. Kayanmu ko a kasuwa ba zaka samu farashinsu ba. gidanmu gidan duniyar leshi, atamfa shadda, material da sauransu. Sai kun zo. Muna maraba da kai a kowanne gari kake. GARKUWA COLLECTION! Siyan nagari mayar da kudi gida! By *GARKUWAR FULANI* 11/15/21, 7:21 PM - Auntyna: https://chat.whatsapp.com/IM6PrgYNy9s6lP0aXmBkaN Samun zafafan saukakan kayayyakin zamani na mata tun daga kan leshi, shadda, atamfa, material, jaka da takalmi, hijab..... da dai sauransu akan farashi mai sauki da rahusa sai a kamfanin Garkuwa collection. Bama wannan kadai ba akwai kayan order da muke yi shi ma duk a cikin rahusan da saukin kudi. Ba mu tsaya nan ba ina kuke yan kasar *NIGER* albishirinku kuma kuna iya siyan kayanmu ya isa gareku cikin aminci ba tare da bata lokaci ba. maza yan’uwa ku garzayo ku gane wa kanku wannan rahusar da kuke jin labari. Kayanmu ko a kasuwa ba zaka samu farashinsu ba. gidanmu gidan duniyar leshi, atamfa shadda, material da sauransu. Sai kun zo. Muna maraba da kai a kowanne gari kake. GARKUWA COLLECTION! Siyan nagari mayar da kudi gida! Mamy ta kira sunansa da d’an k’arfi, wanda hakan yasa shi dawowa daga duniyar tunanin daya fad’a. D’ago da kansa yayi Ahankali ya kalli Mamy’n, da ta tsare shi da ido. “Mamy yaushe kika shigo?” Ya tambaya da dan mamaki akan fuskarsa. “Tayaya zaka san lokacin dana shigo, bayan kanason takurawa rayuwarka, dason sawa kanka damuwa akan abunda kasan ya zama wajibi akanka.” Mamyn ta fad’a. Longoɓar da kansa yayi, kamar zaice wani abu kuma saiyayi shiru. Mamy kuwa Ajiyar zuciya ta sauk’e, had’e da cewa. “Idan akwai magananin zazzab’i awajenka, ko paracetamol ne ka bani, Jannart ce jikinta duk ya d’au zafi.” Jin abunda Mamyn ta fad’a ne kuma yasashi d’ago kansa ahankali ya kalleta, fuska ya kwab’e kana cikin muryarsa mai kama da shagwab’a yace. “Ni kam Mamy bani da wani magannin zazzab’i.” Harara Mamyn ta watsa mishi tare da gyara tsayuwarta tace. “Taya zaka cemin babu bayan bakaje ka duba ba.” Sake langwabar da kansa yayi, still yace. “Mamy nasan fa babunne, kuma yanzu ni bana ajiye magani, saidai ko ki tambayi Ramadan.” “Katashi Kai kaje ka karb’omin maganin awajen Ramadan.” Mamyn ta fad’a adake. Jin hakanne kuma yasa shi mik’ewa jiki asanyaye, ya nufi dakin su Ramadan. Yana zuwa kuwa ya samu Ramadan da Riyyam-nsra kowannensu na rike da waya ahannu. Ko Kallon kirki baiyi musu ba, ya tsaya tare da d’age kansa sama, kana yace. “Ramadan bani paracetamol.” Da mamaki Ramadan yake kallonsa, kamar zaiyi magana kuma saiya fasa, kaitsaye ya bud’e wani Dan box maganin zazzab’i ya ciro ya mik’awa Rayyern din. Yana karb’a kuwa ya fice, inda ya samu Mamy abakin k’ofa ya mik’a mata. Amsan maganin Mamy tayi, batare da tace masa komai ba kuma ta juya ta sauk’a k’asa. Shikuwa d’akinsa ya koma, zuciyarsa cike da takaici. Domin shi sai yanzu ne ma yakejin haushin yarinyar da aketa kira da Jannart din. Mamy kuwa kaitsaye kitchine ta nufa, bayan ta d’auki abincinne kuma ta wuce sashin Jannart. Jannart kuwa dai-dai lokacin ta fito daga wanka, bayan tayi wankanne kuma ta sake maida doguwar rigar da ta cire. Tana tsaka da maida hijab dinta ne kuma, Mamy ta shigo hannunta dauke da cup da kuma plate din indomei. Akan wani Dan stull Mamy ta ajiye cup da plate din, tare da duban Jannart din Cikin kulawa tace. “Yauwa Jannart kinfito ko, ga abinci nan kici, sai kisha magani saboda naji jikinki akwai zafin zazzab’i.” Kai Jannart din ta Dan sunkuyar kasa, kana aladabce tace. “Mamy nakoshi.” “A’a kam Jannart, saboda kefa na shiga kitchine na dafa abincin nan, saboda haka ki zauna kici, kada kiyimin gardama kinji, koso kikeyi na barki haka, Allah ya kama mu kefa amanace awajen mu, zo maza ki zauna kici.” Mamyn ta fad’i haka cikin matukar kulawa. Wanda hakanne kuma yasa Jannart din karasowa, ta zauna akan lallausan sofan dake malale agaban gadon. Abincin Mamy ta ajiye mata, Ahankali kuma ta soma tsakuran abincin tana kaiwa bakinta. Kasancewar kuma da gaske bata wani jin yunwa sosai ne, yasa bata wani ci abincin sosai ba, saidai tea din da Tasha har fiye da rabin kofin. Dan matsar da plate din abincin tayi gefe, tare da yiwa Mamy alama akan ta koshi. Hakanne ko yasa Mamy b’are maganin ta bata tasha. “Ki kwanta to ki huta, Dan Allah karki sakeyin kuka kinji Jannart, kinga shine ya haddasa miki wannan zazzab’in.” Mamy ta fadi haka tana me daukan plate da cup din abincin. “To Mamy.” Jannart din ta fad’a, tana me mikewa tsaye ta haura saman gadon ta kwanta. Murmushi Mamy tayi saboda a iya yaudin kawai ta yada da hankali,da kuma biyayyar da yarinyar take dashi. Cikin kula tace. “A'a Jannart tashi kiyi addu’a kinji, kada bacci ya daukeki batare da kinyi addu’a ba.” Aikuwa da d’an hanzari Jannart din ta tashi zaune, hannayenta ta hade waje guda, falaq,suratul nass, da kuma suratul Iqlas, k’afa uku uku, kursiyu da amarasulu sai kuma Hasbiyallahu la’ilaha illahuwa, alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azim, k’afa 7, sai kuma suratul Khafirun kafa uku shima. Bayan ta shafa ne kuma ta koma ta kwanta. Mamy kuwa cike da farincikin samun ya kuma surkuwa ta gari, ta ragewa Jannart gaba daya hasken wutan dake dakin. Bayan sunyiwa juna saida safe ne kuma Mamyn ta juya ta fita. Bayan ta maida plate and cup din kitchine ne kuma, kaitsaye Mamyn dakin Abba ta nufa. Koda taje Zaune ta sameshi akan gado. Zama ita dinma tayi agefensa, kana cikin tausasa murya tace. “Tabbas Rayyern ya samu mata, yayi dace da yarinyar arziki mai ladabi da biyayya”. Cikin jin daɗi Abba ya juyi ya fuskanceta yana mai jinjina kai alamun gamsuwa. Ita kuwa Mamy cikin girmamawa tace. “Toh amma Alhaji meyasa ka umarceni dana kaita wancan dakin, bayan ganan sashin Rayyern.” Murmushi Abba yayi, tare da maida kallonsa gareta yace. “Nace ki kaita wancan part dinne Saboda, sai anyi gyara a b’angaren Rayyern kafun ta koma can. Kadafa ki manta fa amaryace, Koda cewar auren ba dan shiri bane, amma yana da kyau a inganta mata komai nata”. Da sauri tace. “Eh gsky hakane kam”. Ɗan gyara zamanshi yayi tare da cewa. “Sannan kuma baki ga dan naki bahagon yaro bane, kwata-kwata na kasa gane inda ya dosa, Sam bai fahimci abunda muke nuna masa ba, atakaicema gani yake kamar takurasa mukeson yi. Bayan haka kuma ganan Ramadan shima yana saman. To dole yanzu zai dawo k’asa, kafun adai-dai-ta komai ta koma side din nasu.” Kai Mamy ta jinjina cike da gamsuwa. Kasancewar ta gaji ne kuma yasa ta zame ta kwanta gefensa. Acan b’angaren Rayyern kuwa, akwance kawai yake amma duk zuciyarsa babu dadi. Ak’alla saida ya kwashe sama da 50mn kafun bacci b’arawo ya iya satan shi. Jannart kuwa tun fitan Mamy ta lumshe idanunta. Yayinda tunani kala-kala ke yawo aciki kwakwalwarta, akaro na farko kenan tun tashinta izuwa yanzu, da zata kwana awani gida sab’anin nasu dan ko gidan Barrister Kabir Daddy bai taɓa barin ta ta kwana ba sai kuma asibiti. Tunani ne fal zuciyarta, saidai kuma kamar yanda tayiwa Mamy al'ƙawari, batayi kuka ba, da taimakon maganin zazzabin da tasha ne kuma bacci ya dauketa. Yayinda acan gidan Alhaji Idi Sale Dakata kuwa, kowa ya kwana sharbar bacci batare da tunanin Jannart bata cikin gidan ba, Domin wasu daga cikin mutanen gidan har da gwartin su, saidai banda Junaid Wanda ya taso sad’ab sad’ab ya nufi d’akin Jannart din, saboda gaba daya ya kasa bacci. Daya rufe idanunsa Surar Jannart dinne keyi masa gizo, shiyasa yazo domin rage zafin abunda ke damunsa. Koda ya karasa kofar dakin nata, kaitsaye ya tura kansa ciki. Saidai kuma rashin ganinta da baiyi acikin dakinba, yasa shi cije labbansa, lokaci daya kuma ya raya cewar ko tana toilet Murmushin mugunta yayi, tare da nufan toilet din kaitsaye. Tura kofar yayi batare daya jira komai ba kuma ya soma zare belt din wandonsa, saboda ya gama targetting yana ganinta zai Afka mata, amma kuma saidai meye? Wayam haka yaga toilet din, ba alaman ma anshigesa tsawon sama da 1hour. Tsuka yaja tare da fitowa, yana kwafa haka ya fice daga cikin dakin, cike da takaicin rasa damar da yayi. Badan ransa yaso ba haka ya koma sashinsa ya kwanta a tunaninsa ko tana dakin Mom. *Washegari* 8:00 am dai-dai Mom ta gama kammala musu breakfast, wanda kuma har zuwa tsawon wannan lokacin ba taga Jannart ta fito ba. Hakanne kuwa yasa bayan ta gama setting dining table, kaitsaye tatafi izuwa dakin Jannart din. Koda ta isa bakin kofar knocking ta fara yi, har na tsawon mintuna 2 kuwa bataji ko motsin za’a bud’e kofar ba, hakan yasa Ahankali ta tura kofar d’akin, tare da kutsa kanta ciki. “Jannart! Jannart!!” Momyn ta kira sunan Jannart din, saboda rashin ganinta da tayi adakin. Jin shiru ne kuma yasa Momyn juyawa ta fita, saboda atunaninta ko Jannart din tana cikin toilet ne. Kaitsaye dining table ta dawo, tana zuwa kuwa, Daddy da Abdull suma suka fito suka zauna. Momyn ce tayi saving dinsu, tana cikin saving dinnasu ne kuma, Junaid ya shigo cikin falon, yana fito, daga shi kuma sai t shirt da gajeren Wando. K’arasowa dining table din yayi, batare daya gaisar da kowanne daga cikinsu ba, cikin iskancinsa irin na wasu masifaffun sojoji yace. “Ina Jannart?” D’agowa duk sukayi suka kalleshi. Sanin halin rashin mutumcinsa ne kuma yasa Mom tace. “Yanzu na dawo daga dakinta banganta ba, tun safe kuma bata sauko ba, amma Ina tunanin ko tana toilet ne.” “Bawani bata gidan nanne ma gaba d’aya, y’ar iskar yarinya, jiya ma da dare ai naje dakinta amma bansa meta ba, wallahi Idan na kamata sainaci Uwarta.” Baki Momy ta tab’e, tare da kallonsa cikin yanayin mamaki tace. “To kai meya kaika dakinta da dare?.” “Oho bansani ba, munafurci kawai.” Junaid din ya fad’a kaitsaye, babu wani shakka ko shayi. Duk da Abba yana jinsa kuwa, haka yayi shiru bai tanka masa ba, saima Kallon Momyn da yayi, yace. “Kije ki duba toilet din, ko me ta keyi kice mata ta bari, injini tazo mu yi breakfast.” “To.” Momyn tace, tare da juyawa tasake nufan dakin Jannart din. Tana zuwa ta tura kofar, but still Jannart bata ciki, da d’an mamaki Momy ta karasa jikin kofar toilet din, tare da kasa kumnenta. Waiko zataji karar ruwa, saidai bataji komai ba, hakan yasa Momyn ta tura kofar tana me kiran sunan Jannart. Saidai meye, idanunta ba abunda suka gane mata, domin kuwa Jannart bata cikin toilet din. Mamaki ne ya kama Momyn, saboda Sam bata taba tunanin Jannart bata cikin toilet din ba. Juyawa tayi cikin sauri ya dawo falo. “Alhaji Jannart fa batanan, na duba bata dakinta kuma bata bayan gida.” Cak Alhaji Idi Sale Dakata yatsaida duk wani abu da yakeyi, cikin yanayin mamaki had’i da razana yace. “Bangane mekike cewa ba, wannan wani irin maganar banza ce, tayaya zakice bata dakinta kuma bata bayan gida, wannan gashi anan dinma batanan, To ko tana dakinki ne?” Kai Momy ta girgiza da sauri, tare da cewa. “A'a wallahi bata dakina, tun Safe ma banga sauk’owarta ba, zaiyi wahala ace ma tana dakina.” “Kije ki duba ta yanzu.” Dadyn ya fada cikin bacin rai. Hakan yasa da sauri Momyn ta juya zuwa dakinta, kamar yanda ta zata kuwa hakanne, domin Jannart bata cikin dakinta. Dawowa falon ta sakeyi, tare da Kallon Daddyn tace. “Alhaji Jannart fa bata dakina.” Idanu Daddyn ya zazzaro waje, Abdull kuwa da mamamki yace. “Ha’a To Ina Aunty Jannart ta shiga ita da yawo ma bayinsa takeyi ba, amma bari na duba compound ko Garden ko tafita shan iska.” Yana gama fadin hakan ya mik’e ya fita. Kaitsaye garden dinsu ya nufa amma baiganta ba, hakan yasa ya dawo, fuskarsa dauke da damuwa yace. “Daddy banganta ba.” Kwafa Junaid yayi, tare dasa hannayensa a aljihun wandonsa, cikin bakar muguntan dake cinsa yace. “Nifa Tunjiya na fada muku banganta ba, maybe yawon iskancinta ma ta tafi, dama ai ta saba tafiya kwanan gida. Rijiyace kowanni dan iska yana iya zuwa ya zira gugansa yaja ruwa son ransa.” Idanu Momy ta rumtse saboda har acikin zuciyarta bataji dadin bakar maganar da Junaid din ya fada akan Jannart d’in ba. Daddy kuwa Wayarsa ya zaro daga cikin aljihun rigarsa, tare da lalub’o numbern Jannart din ya danna mata kira. The first time akace masa wayan nata, is switch off, da Mamaki Daddy ya sake dialing airtel number dinta, still switch off, wani irin bugawa yaji kirjinsa yayi, cikin sauri yace. “Junaid je maza ka duba side dina, watakila ko taje gaisheni ne.” Juyawa Junaid din yayi, Inda kaitsaye ya nufi side din Daddyn, Koda ya karasa baiganta ba, har cikin bedroom na Dad din ya shiga amma babu ko alamarta. Dawowa yayi yana ta kwafa, yace baiganta ba. Mik’ewa tsaye Daddy yayi, cikin tsananin tashin hankali ya nufi kofar fita daga falon, batare kuma daya lura ba har tuntub’e yake. Kaitsaye compound din gidan ya fito, tun daga nesa kuma ya soma k’walla kira. “Ado! Ado!!” Baba Ado dake bakin gate wurin Ashiru ne, Jin irin kiran da Alhajin keyi masa ne kuma yasashi tahowa da sauri. Kallonsa Alhaji Idi Sale Dakata’n yayi, kana cikin dan daga murya yace. “Jannart ta fita ne?” Kai Baba Ado ya girgiza kana cikin girmamawa yace. “A’a Alhaji Jannart bata fita ba, kwata kwata tunsafe Ina zaune anan banga wani ma daya fita acikin gidan nan ba.” Shiru Daddyn yayi, na yan wasu mintuna, kamar kuma Wanda aka tsikara yasoma k’wala k’iran Guards. Su kuwa k’attin banzan ma sai yanzu suka tashi daga nannauyan baccin daya daukesu. Jin kiran da Ogan nasu keyi musu ne kuma, yasa cikin sauri duk suka k’araso. Kallonsu Daddyn yayi tsab cikin hade fuska yace. “Ina Jannart, dawa ta fita acikin ku?.” Kai suka girgiza dukansu, kana suka had’a baki wajen cewa. “A’a bamuga Jannart ba, mu yanzu ma tashinmu wata kila tana cikin gida.” “Wani irin cikin gida kuma, bayan babu Inda ban duba batanan, maza ku zagaye duka gidan nan ko zaku ganta.” Dadyn ya fada cikin bacin rai. Nan take kuwa guard din suka bazu ako ina dake cikin gidan, amma ko alamar Jannart basu gani ba. Hankalin Daddy yayi masifar tashi, musamman daya sake kiran wayanta yaji akashe. Haka ya dawo falon afujajan, Yayinda Momy kuwa ta kasa zaune ta kasa tsaye, saboda abune kaman wasa amma yana neman Zamowa gaskiya. Kallon Daddyn tayi, tare da Daukar wayarta tace. “Bari na kira Barrister Kabir.” Dialing number’n Barrister Kabir din tayi, bugu hudu kuwa Barrister Kabir ya dauka. Bayan sun gaisa da Momynne kuma, cikin tashin hankali tace. “Barrister bamuga Jannart bafa, munnemeta sama da kasa acikin gidan nan amma bamu sameta ba, munkira wayarta kuma akashe, Kodai tazo wajenka ne?” Daga can b’angaren Barrister Kabir ya mik’e tsaye tare da daga muryarsa cikin nuna tashin hankali yace. “What!! Wannan Wace irin magana ce, Ba’a ga Jannart ba, annemeta anrasa? Ita kudi ce da za’ace annemeta anratsa? Ko kuma ita din wayar hannu ce da za’ace an nemeta anrasa.” Ya k’are maganar cikin yanayin tsawan, dake nuni da bazai iya tolerating nonsense akan Jannart ba. Momy kuwa cikin tashin hankali tace. “Wallahi Barrister bamuganta ba, body guards dinta da masu gadi duk sunce basu ganta ba.” “Gani nan zuwa.” Barrister Kabir din ya fada agigice. Tare da kashe wayar. Bayan ya kashe wayartasa ne kuma ya saki wani irin murmushi tare da juyowa ya kalli Aunty Dijat dake zaune. “Sakarkaru sai yanzu suka lura da cewar Jannart bata gidan, hmmm da sannu munafukan boye zasu fito fili, kowa kuma zai girbi abunda ya Shuka.” Dariya Aunty Dijat tayi. Yayinda shikuwa ya dauki key din motarsa ya fice. Kaitsaye gidansu Jannart din ya nufa. Yana isa gidan kuwa ko gama dai-dai-ta parking baiyi ba, ya fito. Inda Daddy kuwa ke tsaye, gaba daya hankalinsa atashe yake sai safa da marwa yake, Yayinda kuma yake ta balbale guard din da fad’a, tankar zai hausu da duka, sai cewa yake, su je su nemo Jannart duk inda ta shiga ta fita. Barrister Kabir kuwa agigice ya karaso, hankalinsa amatuk’ar tashe yace. “Yaya ina Jannart? Waya dauke mana Jannart? Ina kuka kaita?.” Kai Alhaji Idi Sale Dakata ya girgiza, cikin tsananin damuwar da yake ciki yace. “Bansani ba Kabir, bansan Ina Jannart tayi ba, munduba ko ina amma babu ita babu alamanta.” Hannu Barrister Kabir ya daura akai, lokaci daya kuma ya jujjuya idanunsa sukayi jajur, ahaukace ya soma neman Jannart din, tare kuma da soma zagaye cikin gidan yana leka har cikin followers, sunan Jannart din kawai yake kira da iyaka karfinsa. Daddy kuwa bala’i da tashin hankali ne ke cinsa, cikin zafin nama kuma ya kalli Ashiru. Afusace yace. “Ashiru Ina Jannart waya bude mata kofa ta fita, ka fadamin nace ko kuma yanzu nasa bindiga na harbe kanka.” Yakare maganar atsawace tare dasa hannu kuma ya dauke Ashirun da lafiyayyen Mari. Kai Ashiru ya girgiza, cikin shanye zafin marin yace. “Alhaji banganta ba, tun jiya gidannan akulle yake, gaba daya jiyama kowa ya sani bataje aiki ba, tunjiya bata fito ba, ga guards dinta nan suma shaidane.” Sake hasala Daddyn yayi, Wanda hakan yasa ya sake gallawa Ashiru mari, tare da juyowa ya soma balbale Body guards din. Cikin fushi yake cewa. “Aikin banza k’attin banza kawai, angaya muku ahaka kawai na daukeku aiki ne, sokaye kun kwanta bacci sai kace matattu, yan iska kusan duk inda zaku ku nemomin y’ata.” Barrister Kabir kuwa, zuwa yanzu har muryarsa ta Dishe, saboda yanda yake ta k’wala kiran Jannart. Gaba daya lokaci daya jikinsa har karkarwa yakeyi, hankalinsa ya matukar tashi, inda yake reaction tankar da gasken gaske shima baisan inda Jannart din take ba. Cikin kuma tashin hankalin daya nuna yana ciki ne kaitsaye ya nufi dakin Jannart din. Yana shiga kuwa ya soma wargaza komai dake cikin d’akin, ananne fa kuma idanunsa suka sauka akan wayarta. Da sauri ya dauki wayar dake kashe ya kunna, batare ma daya jira wayar ta karasa kawowaba ya dawo cikin falon, inda dukansu ke tsaye, cikin kuwa harda Junaid dake zukan shisha. Wayar nata na kawowa Barrister Kabir ya shiga cikin dialing call dinta. Aikuwa last sunan wanda tayi waya dashi Ne ya bayyana. “Yah Junaid” Idanu Barrister Kabir din ya zazzaro cikin matukar hasala, kuwa ya karasa cikin falon, batare da wata wata ba, ya Ware yatsunsa biyar ya zabgawa Junaid zazzafan Mari. Tare kuma da juyawa afuce ya nunawa Dady screen din wayar Jannart din. Cikin tsananin fushi yace “Ba gashi ba, shine last mutum din da tayi magana dashi awaya, koma meye shi yasan inda take, Ina ya kaita? Yaya ka tambayeshi Ina ya kaita nace!!!!!!”. Barrister Kabir din ya fada amatuk’ar tsawa ce, tsawan kuma daya saka hantar cikinsu kadawa. Shi kuwa Barrister Kabir kuwa cikin fushi Ya...! *Albishirinku! Ma'aurata, GA GARKUWAR KU nan tafe muku da tsarabobi na musamman gareku ma'aurata daga cibiyar mgnin mata mai taken GARKUWAR MA'AURATA* NI DAI AYSHA ALIYU GARKUWA. Ina matukar mamakin wani irin lokaci da ya riske mu mai wahalallan fassara. Kullum dai magana daya ce, akan ma’aurata, fada, rashin jituwa, mutuwar aure, akan kuskure kalilan, rashin kula, rashin yi wa juna uziri. Toh wai duk me ya janyo hakan? Na zurfafa a tsananin tunani hakan ya tilasta min bincike mai tarin yawa wanda ya kai ni ga gano inda matsalar take? Shin yar’uwa ke macece amma kin san wacece mace ku? Kin san me ake kira mace kuwa? Mace ita ce matar da take zama iyali a wajan namiji ta zame masa bango, sanyin idaniyarsa, ta zame masa gata da farin cikin rayuwarsa ta zame masa ruwa abar kore ƙishinsa ta zame masa mayafi mai karesa daga gigitar kadaice, ta kuma dorar da mijinta kan turbar gaskiya, ta kashe masa jiki da salonta ta rikita shi da baiwa da ni’imar da Allah ya bata idan har ta san hanyar mayar da kanta sabuwa dal awajanta, wato kullun takasance masa tamkar amarya har ya kasa tantance daren amarcinsu da sauran dararen rakun rayuwar su. Wannan ita ce mace. Ina da wata saukakkar hanyar da zaki zama abar so da kulawa da soyayya a wajan mijinki ta hanya mafi sauki, 09097853276 hanyar ita ce ki gwada amfani da kayana na gyara ki gani, ina mai tabbatar miki da in sha Allahu sai kin dara da murna sai kuma kin gode min. Kayana kaya ne da aka yi shi da zallan itacanmu na gado marasa illa a cikin jikin dan adam musamman mace, kaya ne da suke taimakawa (sex hormones 😍) dinki. Misali kina kallon India😘, hollywood, Asian film🥰 kina ganin yanda mazansu ke nunawa matansu tsananin soyayya kamar su ba su kyautar ransu!? Saboda me hakan? Saboda suna sadaukar da lokacinsu wajan gyara jikinsu da kayan da ke tsattsafo da ni’ima cike da tsukewa, kayan nan kuma ana yinsu ne zallar magungunan gargajiya wanda ba su da illa domin haɗine na ingantattun itatuwa da yayansu. Ina baiwar Allahn da miji ke daure mata fuska babu hirar arziki? Zo ki ji yar’uwa zan baki gumbata da zallar gari wanda aka yi su da nagartattun itacen da ke da matukar amfani a jikin mace. Gubar ciko, gumbar tsalle dole, gubar da ba'a baiwa mai kishiya, garin maɗi, garin mallaka, tsumin goron tula, tsumin tsartai, tsumin maratsi, pala-pala butar sirri, kwanon k’asaitacciyar mace, furar mata madararta gareki Hajia takenta sha yanzu mgni yanzu, Ina mata masu fama da sanyi? Sanyin mara ki zo na hadaki da magani na na sanyi wanda yake wanke mara ya fitar da duk wata cuta da ke samun mazauni a wajan. Ina da ciccibi mai kyau. Ina da hadin amare mai kyau wanda zai gyara yarinya ya kankaro mata kimarta akwai hadin mai jego wanda muke yinsa na asali inada kekkyawan Hadi maida tsohuwa yarinya. Akwai daya bangaren wato *KAMSHI* Kimarki gyaranki da kamshinki. Matan da suka gane suka san yanda za su kankaro da mutunci su ne masu amfani da kayan gyara da kuma sanyaya jikinsu da kamshi, ina da turaren wanka da na bandaki na daki na jiki da na kaya dana tsuguno kamshin turarena na dabam ne mai sanyaya zuciyar wanda ya shaka ina da kayan kamshi na amarya da na maijego da na uwargida da dukkan macen da take kokarin mayar da kanta mai daraja a idon kowa ta zamo sarauni a idon mijinta, akwai shu'umar humra, sayan na gari maida kuɗi gida, banda karanta yayin gyara Hajia. Zaku iya samun kayyakina a duk garin da kike, zakiyi min mgn ta whatsApp number na 09097853276 domin yin zaɓinki, ko karin bayani, zaki tura kuɗin ta account na 0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU in mun gama mgna zan sa miki kaya a mota yazo duk garin da kike, in baki shirya saya yanzuba Please kada mu wahal da juna ki bari sai kin shirya kafin kiyi min mgn. 🤝🏻🥰😘 Daga taku AYSHA ALIYU GARKUWA *(GARKUWAR MA'AURATA)* By *GARKUWAR FULANI* 11/15/21, 7:21 PM - Auntyna: Ya shak’o wuyan Junaid din, ransa amatukar b’ace, cikin kuma son d’and’anawa Junaid din thesame azabar da yake ganawa Jannart yace. “Ina kakai Jannart! Kafadamin Ina kakaita, kasan inda take tabbas, ba kuma abunda bak’ar zuciyarka bazata iya sawa ka aikata ba, kafadamin Ina ka kai mana Jannart!!!?” Barrister Kabir din ya k’are maganan cikin tsawa sosai. Tare da sake makure wuyan Junaid. Junaid kuwa idanunsa ya Dan zaro cike da mamaki yace. “Wai Abba mekakeson fad’ane? Ni ban San inda Jannart take ba, ba kuma nina d’auketa ba, na d’auketa ma nakaita Ina, watakila tanacan ta tafi yawon banz......” Wani irin wawan mari Barrister Kabir din ya zabgawa Junaid din akan fuskar sa, cikin tsananin b’acin rai da hasala, ya kuma sake zabga masa wani marin, wanda har saida hakan yasa fuskarJunaid din tayi jajur mgnar da yake son fitarwa kan Jannart ta makale, idanunsa ya zazzaro lokaci daya tare da somayin huci. Barrister Kabir kuwa ji yake Kamar ya rufe Junaid din da duka, ransa yakai kololuwa wajen b’aci da irin mugayen furucin da Junaid din ka jefar Jannart dasu. Cikin fad’a sosai ya juyo ga Daddy dake tsaye yace. “Yaya ka fad’awa Junaid na bashi nanda anjima yaje duk inda ya kaita ya daukota, ni nasani shine ya sace ta, domin kuwa shine last mutumin daya kirata awaya. Uban meya gaya mata a wayan? sannan meye dalilinsa na kiranta awaya? Shi ya sace ta, saboda ya cika banzan burinsa na dabbanci akanta, komai zaiyi kuma bakayi masa magana, gashi nan kaga illar da hakan ya jawo ko Yaya?, gashi nan ya saceta ya rabamu da ita, ya kaita inda zai cutar da ita. Yaya kana mance Jannart marainiyace amma ya maida cutar da ita tamkar abinci da ruwan shansa, Allah ya wadaran hali irin naka Junaid.” Barrister Kabir din ya kare maganar cikin muryar kukan daya zo masa”. Momy da Abdull dake tsaye agefe kuwa, gaba dayansu kuka suka saka, saboda. Sunsan cewa tabbas Junaid din zai iya aikata hakan, ballema jiyan Momy da kunnuwanta taji yana cewa saiya cika burinsa akan Jannart din. Daddy kuwa ransa Idan yakai dubu to yayi masifar b’aci, akaron farko kuma cikin fushi, ya dawo da kallonsa ga Junaid, tare kuma da ta sowa ya nufi kan Junaid din. “Ina kakaita Junaid, Ina kakai min Jannart? Ka fad’amin Ina kakaita? Junaid me zakayi da ita.” Daddyn ya tambayesa atsawace. Abunda Bai tab’ayiwa Junaid din ba kenan, musamman akan Jannart. Ganin hakanne kuma yasa Junaid din soma girgiza kansa, cikin mamakin tuhuman da sukeyi Mishi yace. “Wallahi Allah Daddy bani na dauketa ba, bansan inda take ba, bani na sace ta ba.” Cikin nuna ɓacin rai a fili Barrister Kabir dake tsaye. Cikin rufe idaunsa da kuma mance alak’ae dake tsakaninsu yace. “Nabaka nan da awa 2 Junaid, Lallai-Lallai kanemomin Jannart, duk inda ka kaita, kaje ka daukota Idan kaki kuma nida kai bibbiyu, wallahi-wallahi saikayi dana sanin sace marainiyar Allah da kayi.” Sake dawo da kallonsa ga Daddy yayi, kana cikin tafasar zuciyar dake bayyana zai iya aikata komai akan b’atan Jannart din yace. “Yaya kasa baki kasake tuna masa, awa 2 na basa ya fito da ita daga inda ya b’oyeta, sannan yanzu zan. Kaiwa y’an sanda report, bayan haka kuma zan zagaya cikin duk wani asibiti da nasan yana cikin garin nan, dole ayau asamo inda Jannart take.” Yana gama fad’an haka ya juya kaitsaye ya nufi hanyar fita daga gidan. Koda yazo bakin gate harara ya watsawa Ashiru, kana cikin takaici yace. “Shashasha kana nan tsaye abakin gate Koda yaushe, amma ka kasa sanin fita da shigan mutane sakaran banza kawai.” Ya Kai karshen maganan nasa yana me bankad’e Ashiru’n, Cikin pretending yasakai ya fice daga Cikin gidan. Daddy kuwa zuwa yanzu saboda tsananin bakinciki, da takaici da kuma Tarin bacin rai, jikinsa har rawa ya somayi yayinda yake jin, tamkar yasaka hannayensa aka ya kurma ihu, saboda b’atan Jannart din. Sanin bashi da wata makamane kuma yasa shi, soma balbale guards din, Jannart din. Cikin fushi hadi da bala’in dake cinsa yace. “Bantab’a nadaman ajiyeku Acikin gidana ba sai yau, k’attin banza k’attin wofi kafuran arnan da basa sallah, tayaya ma za’ace yarinyar da nake biyanku mak’udan kud’i duk wata akanta, za’a nemeta a rasa, ashema k’attin wofi dana banza na tara, lusarai way’anda basu da aiki sai ci da kwanciya, ku fita ku barmin gidana yanzu basai anjima ba, dukka na sallameku, kada na sake. Ganin Koda mummunar fuskar daya daga cikinku ne, ku fitamin agida.” Daddyn ya kare maganan cikin bacin rai. Dan har yanajin tamkar ya rufe guards din da duka. Sukuwa k’attin banzan, sun matukar ji haushin zagin da Alhajin yayi musu, aso da niyarsu kuma shine su tanka masa, amma kuma saidai tuna cewar zai iyasa a dauresu ne, yasa basu tanka masa ba, sad’ab-sad’ab haka suka kwashe komatsansu suka fice daga cikin gidan. Junaid kuwa zaman dirshan yayi, yana Mejin wani irin tafasar zuciya, saboda alluran nasa ta motsa, sosai matukan da Barrister Kabir ya sharara masa suka tsaya masa arai. Lallai Barrister Kabir din yayi sa’a, kasancewar shi kanin mahaifinsa, domin yau da ace wanine daban Yayi masa hakan ba Barrister din ba, yayi rantsuwa bindiga zaisa ya harbe mutum. Acan b’angaren Barrister Kabir din kuwa, yana fita daga cikin gidan, motarsa da yayi parking awaje ya shiga, bayan yayiwa motar key ne kuma, ya saki wani irin Murmushi, mai kama da dariya. Hakika irin wannan firgicin ya jima yanaso ya gani, akan fuskar Yayan nasa akan Jannart dama shima Junaid, wannan tsoron shiyake matukar so yaga yayi tasiri acikin zuciyarsu “Tu kunnma Alhaji Idi Sale Dakata, wannan kadan daga cikin bangon littafin tashin hankalin da zaka fad’ane anan gaba.” Barrister Kabir din ya fad’a abayyane, kana zuciyarsa cike da nishadi ya nufi gidan Dr Sajo domin dama duk abunda yakeyi dazun, pretending ne kawai ba komai ba. Koda ya isa gidan Dr. Sajon kuwa, ya samu Doctorn na nan kasancewar yau din weekend babu aiki. Har cikin falon Dr Sajon kuwa ya shiga, bisa jagorancin wani Dan matashin saurayi wanda zai iya kai sa'an Rayyern. wanda kuma yake dan Dr Sajon ne. Yana shiga cikin falon ya durk’usa guiwowinsa ak’asa, tare da kai goshinsa k’asa, yayiwa Allah Sujjada, wani irin farinciki yakeji acikin zuciyarsa, bayan ya d’ago daga sujjadan ne kuma ya kalli Dr. Sajo dake kallonsa yana murmushi, cikin matukar farinciki yace. “Alhamdulillah Allah abun godiya, doctor shawararmu tayi, komai da muka tsara ya tafi yanda ya kamata, Insha Allahu yanzu kwata-kwata ma hankalinsu bazai tab’a zuwa kaina ba.” Murmushi Dr Sajon ya faɗada lokaci daya kuma farinciki ya bayyana akan fuskarsa. Barrister Kabir kuwa ci gaba yayi da cewa. “Junaid ya daure kansa da kansa, da zaluncin da yakeyi wa Jannart tsawon shekaru. yanzu shikansa Yaya Idi bai isa yayi wani tunani akan abunda ya shafeni ba, Alhamdulillah Allah.” Still murmushi mai kama da dariya Dr Sajon yayi, cikin kuma jin dadin labarin da Barrister Kabir din yazo masa dashi yace. “Masha Allah Barrister Kabir, wannan abu yayi dadi, haka mukeso yanzu kaga mun dauke hankalinsu daga kan komai, zasu tsaya wa abu daya ne kawai, inda kaikuma zaka ci gaba da bincike, da kuma kara Adana hujjojinka, sannan Jannart kuma tana killace a gidan mijinta, Alhamdulillah Wannan shine matakin nasara na farko da muka fara hawa.” Kai Barrister Kabir din ya jinjina, kana cikin gamsuwa yace. “Insha Allah, da sannu duk wani kulli zai warware, gaskiya kuma zatayi halinta, yanzu sunacan hankalinsu duk atashe, musamman shi Yaya.” Dariya Dr Sajo yayi, tare da gyara zamansa, cikin ya bawa shirin nasu yace. “Aikinmu yayi kyau gaskiya, Allah kuma ya dafa mana.” “Ameen summa Ameen.” Barrister Kabir din ya amsa, zuciyarsa wasai babu wani alaman damuwa. Hira suka d’an tab’a kad’n da Dr Sajon, kafun daga bisani Barrister Kabir din ya tashi ya tafi. Acan gidansu Rayyern kuwa, kusan atare suka jero wajen shigowa cikin gidan. Wanda kuma dawowarsu kenan daga sallan asuba. Abba, da kuma Dr. Rayyern ne agaba, sai Ramadan da Riyyam-nsra dake take musu baya. Ahaka suka k’araso cikin babban falon dake k’asa, tare da neman waje kowannensu ya zauna. Mamy kuwa sanin zaman shan coffee al’adar mazan gidanne, yasa tun kafun su dawo daga masallacin ta gama had’a musu coffee wanda yaji kayan k’amshi. Ganin shigowarsu Cikin falonne kuma yasa, Mamy daukan coffee din tare da tahowa cikin falon. Zama tayi a tsakiyarsu Kana ta fara tsiyayawa kowannensu a mug ta mik’a musu. Riyyam-nsra ne ya Karb’i Mug din coffee din da Mamyn ke mik’o masa, tare da tank’washe k’afafunsa, cikin yanayin jin dadi yace. “Mamy ngd. Da wannan al'farmar, da na samu. Wanda yake sawa nake ga kamar ina gaban Mammy na dan itama haka takeyi min da zaran nadawo amasallaci sai ta bamu abun tab’awa. wannan yana d’aya daga cikin abunda yasa naji zaman gidannan yafi min na hotel.” Dariya Mamy da Ramadan sukayi, domin hatta Abba ma saida ya dan murmusa. Shikuwa Rayyern gaba daya ma ya dauke wuta, Yayinda ya Kawar da kansa gefe, ahankali yake sipping coffee din, ko gefen dasu Riyyam din suke kuwa bai kalla ba. Mamy kuwa bayan ta kammala had’a musu komai ne, ta mike tare da komawa kitchine, mug din coffee din da ta had’ashi musamman dan Jannart ta d’auka, Koda ta fito daga cikin kitchine din, batare da ta tankawa su Ramadan da Riyyam dake hira ba. kaitsaye ta wuce dakin Jannart. Ahankali ta murd’a handle din kofar falon ta shiga, kamar kuma yanda ta tsammata hakanne ya kasance, saboda babu kowa acikin falon. Kaitsaye kofar bedroom din ta nufa, Koda taje tsayawa tayi abakin kofar tare, da d’an k’wank’wasawa kana cikin kulawa takira sunanta. “Jannart.” A can cikin Bedroom kuwa. Jannart dake zaune akan sallayan jin muryar Mamyn na kiran sunanta ne yasa ta, amsawa aladabce. Mamy kuwa dake tsaye, jin Jannart din ta amsa ne, yasa ta tura kofar dakin ahankali ta shiga, bakinta dauke da sallama.” Ganin Jannart din da tayi akan sallayane kuma, yasa kata sakin Murmushi, cikin kulawa tace. “Masha Allah Jannart kin tashi ashe.” Kai Jannart din ta jinjina alaman Eh, lokaci daya kuma tayi kasa da kanta, cikin sassanyar muryarta dake bayyana zallan ladabinta tace. “Mamy inakwana.” Yalwataccen murmushi Mamyn tayi, tare da cewa. “Lafiya lau Jannart, fatan kema kintashi lafiya ya jikinki?” Cikin jin daɗi tace. “Da sauki sosai.” Jannart din ta bata amsa tana medan wasa da yatsun hannunta. “Masha Allah, haka akeso Allah ya kara sauki”. “Amin Mamy ngd”. Jannart ta kuma faɗa. Ita kuwa Mamy murmushin jin daɗi tayi tare da cewa. “Ga coffee nan mai zafi maza ki shanye shi. zakiji d’umi cikinki zai ware.” Mamyn ta fad’a tana me ajiye mata mug din Coffee din. “Toh Mamy Nagode.” Still Jannart din ta fada tana mekokarin gyara zamanta. Mamy kuwa murmushi tayi tare da cewa. “Ba komai Jannart, ki saki jikinki, Idan kinsha coffee din kuma zaki iya komawa bacci, ki dai samu ki huta kinji ko.” Kai Jannart din ta jinjina, inda Mamyn kuwa cike da kauna, hadi da yaba hankalin yarinyar ta juya ta fita. Ganin fitar Mamyn ne kuma yasa, Jannart daukan coffee din ahankali ta soma sha, saboda dadin da coffee din yayi ne kuma yasa harta shanye feye da rabinshi, batare da ta farga ba cin cikinta yayi dumine kuma yasa aje sauran. Alhamdulillah kuma ta danji karfi ajikinta. Mamy kuwa tana fita daga dakin Jannart din, direct kitchine ta sake wucewa. Dan soma shirin aikin breakfast. Yayinda kuma har yanzu Ramadan da Riyyam ke zaune acikin falon suna tad’i. Kasancewar tuntuni Rayyern ya tashi ya haura sama, Koda yaje dakin nasa ma kuma kwanciyaya yayi, saboda gaba daya Daren jiya baiwani samu isashshen bacci ba. Cikin sa’a kuwa Yana kwanciya bacci ya d’aukesa. 7:30 pm dai-dai. Mamyn ta kammala had’a duk wani abu da takeyi. Ita da Riyyam ne kuma suka jere duk abincin akan dining table, Yayinda Abba da kuma Ramadan ke zaune acikin falon. “Bismillah komai ya zama ready, Ina Rayyern bai sauk’o ba ko.” Mamy ta fad’a adai-dai lokacin da take ajiye plate plates na cin abincin. Jin abunda ta fad’ane kuma yasa Abba dake zaune yana karatun Alqur'ani juyowa ya kalleta, cikin tausasa harshe yace. “Masha Allah, amma nikam daga yau na daina cin abinci acikin ku. ana shiryamin nawa Acan dining table dina” Murmushi Mamy tayi, cikin gamsuwa da kuma fahimta mijin nata tace. “To shikenan Ranka ya dad’e Insha Allah, naka shirin ma na musamman zanna maka.” Yar dariya sukayi, Yayinda Riyyam-nsra kuwa Kallon Abban yayi, cikin nishadi Yace. “Abba Kai bazakayi irin na turawa bane.” Murmushi Abban yayi, tare da girgiza kansa yace. “To ni ai ba bature bane Riyyam.” Kai Riyyam ya jinjina aransa yana mejin dadi, saboda akaron farko kenan da yaga Abban yayi masa murmushi, tabbas yaji dadin abun. Mamy kuwa cewa tayi, Ramadan da Riyyam duk su taso suzo suci abinci. Aikuwa dama kaman jira suke, zama sukayi akan dining table din, Yayinda Mamy da kanta tayi saving dinsu, kana Itama tayi saving din kanta. Abba kuwa har yanzu yana nan zaune acikin falon. Suna cikin cin abincinne kuma Mamy ta d’an d’ago Kai ta kalli Abban. Cikin tausasa muryarta irin na mata masu ladabi ga mazajensu tace. “Yauwa Alhaji, yarinyar nan Jannart kaga irin yanayin yanda tazo gidannan, komai anyisa ne asace a boye. Hakan yasa batazo da suturun sawa ba, sai nake ganin maizai hana, Indai babu matsala a fita aje asamomata suturun sawa.” Kai Abban ya jinjina cike da gamsuwar abunda Mamyn ta fad’a yace. “Tabbas ya kamata kam asamomata kayan sawa, tun dai ayanzu kam duk wani hakkinta ci da shanta da sutura jinya yana wuyan Mijinta ne, saboda haka ku tambayesa ya bada kudi, Idan yaso sai kije kiyi mata duk wata sayayya da ta dace.” Kai Mamy ta jinjina, cikin kuma yin kasa da murya da alaman ladabi tace. “Mijinta kuwa?” “K’warai kuwa shid’in dai, ai yanzu duk wani nauyinta ya rataya ne akan wuyansa ne. Hakkinsa ne dole kuma shi zai sauke dan haka ya fara da wurima.” Kai Mamyn ta jinjina, kana a gamsashe tace. “To shikenan Insha Allah zanyi masa magana.” Daga haka kuwa babu wanda ya sake cewa komai, suka ci gaba da cin abincinsu. Bayan sun kammala ne cin abincinnasu ne kuma suka dawo cikin falon. Mamy kuwa Ganin lokaci ya danja sosai ne, yasa ta kalli Ramadan, kana cikin kulawa tace. “Ramadan jeka kiramin Hammanku, gashi har kusan goma ko breakfast bai sauk’o yayi ba.” “To.” Ramadan yace tare kuma da mik’ewa ya haura sama, Koda ya k’arasa d’akin Rayyern d’in, samunsa yayi acikin blanket yana ta bacci. Batare daya tashesa ba kuma ya juyo, tare da dawowa falon. Tun kafun ya zauna kuma ya kalli Mamyn tare da cewa. “Mamy Hamma Rayyern fa bacci yakeyi, ni kuma gaskiya tsoron tashinsa nake kada na tashesa kuma ya hauni da fad’a.” D’an Jim Mamyn tayi, tare da mik’ewa tsaye tace. “Shikenan badamuwa bari na fad’awa Abban ku.” Kaitsaye falon Abban ta wuce. Koda taje zaune tasa meshi, zama tayi ad’an gefensa kana cikin tausasa Murya tace. “Natura Ramadan ya kira Rayyern, amma yace bacci yake har yanzu bai tashi ba, ka kumasan Rayyern kwata kwata baya so atashesa Idan yana bacci kasan matsalar ciwon kansa.” Kai Abban ya girgiza bayan ya tankwashe kafafunsa ne kuma ya d’ago da kansa ya kalli Mamyn, cikin bada umarni kuma yace. “Yau dai kam atashesa daga baccin da yakeyi, saboda yana da kyau yasan cewar yanzu bawai lokacin kansa kawai yake dashi ba. Yana da lokaci wata, maza ki tura Ramadan ya taso sa.” Kai Mamyn ta jinjina, cikin Dan ladabtar da murya tace. “Ramadan yace yana jin tsoron tashin sa, kada Yayi masa fad’a” “To ke kije ki tasosa.” Abban ya fad’a kaitsaye. Jin hakanne kuma yasa Mamy yin shiru, saboda tasani Sam Rayyern bayaso Idan yana bacci azo atashesa any how, musamman kuma kasancewar yana da matsalan ciwon Kai, shiyasa Mamyn ma take gudun yin duk wani abu dazai takurasa, domin tun yana karaminsa, Idan yana bacci bata cika son tashinsa, saidai idan ya gaji ya tashi dan kansa. Fahimtar hakanne kuma yasa Abba mik’ewa tsaye, tare da cewa. “To ni bari naje na tasosa da kaina.” Hakan kuwa akayi inda kaitsaye ya nufi sama, nan sashin Rayyern din. Yana zuwa kuwa ya tura kofar dakin ya shiga. Still Rayyern din bacci yake. Yayinda ya lullub’e duka jikinsa da blanket. Karasa shigowa dakin Abba yayi, Idanu ya ɗan zuwa fuskar Rayyern ɗin yana mai tuno wata kamanceceniya. Numfashi ya ɗan fesar tare kuma da matsowa ya daura hannunsa dai-dai kan wuyan Rayyern din, Jin da yayi jikin Rayyern d’in babu alaman zafi ne, yasa shi soma kiran sunansa a nitse. “Rayyern! Rayyern!! Rayyern!!!.” Abban ya kira sunansa sau uku cikin kuma yanayin Dan daga murya. Take kuma sauti da Amon muryar Abban ya ratsa kunnuwansa, wanda hakan ya sashi soma bud’e lumsasssun idanunsa ahankali, lokaci daya kuma jijiyoyin kansa suka amsa. Saidai Ganin Abban nasa da yayi atsaye ne yasashi karasa bude idanunsa. Abba kuwa gyara tsayuwarsa yayi, tare da cewa. “Katashi daga wannan baccin da kakeyi kaje kaci abinci, sam baka karya ba, sannan kuma ka kawo kudi za’aje a iyawa matarka sayayya.” Jin an ambaci mata ne kuma yasa shi shagwab’e fuska, tare da karyar da wuyansa gefe, cikin zallar yanayin shagwab’a yace. “Abba kudi kuma, ni fa banida kudi.” Tsareshi da ido Abban yayi, kana cikin tsare gida yace. “Ka kawo kudi za’ayiwa matarka sayayya nace, ko kamanta cewar yanzu duk wani ci da sha da tufatarwar ta yana wuyanka ne?” Bakinsa ya d’an tura gaba, kana cikin lumshe ido, ya mirgina gefe tare da saka hannunsa akan bedside drawer, ya d’auko Atm card d’insa, mikawa Abban atm card din yayi, still yana ta tura baki tamkar wani karamin yaro. Abba kuwa karb’an atm card din yayi, batare daya sake cewa Rayyern din komai ba ya juya ya fice sabida yasan Ramadan yasan pin number sa. Yana fita kuwa Rayyern ya sake langwab’ar da kansa, cikin wani irin takaicin yarinyar da aka tashesa daga baccin da yakeyi ta sanadiyarta, kwana daya kawai tak da tayi agidannasu, yau gashi har an fara takura rayuwarsa da shiga sabgar sa a kanta. Abba kuwa Koda ya sauko kasa, atm card din ya bawa Mamy tare da cewa. “Kisaya mata duk wani abu da kikasan zata buk’ata, maganan suturun sawa kuma ki saya mata isassu, komai da komai ahada a saya mata.” “To Insha Allah, zan saya mata duk wani abu daya dace.” Ramadan dake gefe ne kuma yace. “Mamy nida Riyyam zamuyi miki rakiya, ko Riyyam.” Ya ƙare mgnar yana kallon Riyyam-nsra. Kai Riyyam ya jinjina cikin sauri, hade da cewa. “Eh Mamy zamu rakaki, Ado Bayero Mall zamuje ko Jifatu, ko kuma Mudassir and Brothers?” Murmushi Mamy tayi, tare da cewa. “Shoprite dindai zamu fara zuwa, saboda nasan akwai komai da komai, Idan akazo b’angaren dogin riguna kuma, sai muje Jifatu, yanzu dai bari naje na shirya saina zo mutafi.” “To.” Suka amsa mata. Ramadan kuma juyowa yayi ya kalli Riyyam-nsra tare da cewa. “Wai ni kam yaushe kasan Kano haka!?.” Kai ya shafa tare da cewa. “Nida jihata ƙasata!”. Kiran wayarshi da akayi ne yasa baibi ta kan furucin Riyyam-nsra ba. Yayinda ita kuwa Mamy kaitsaye bedroom dinta ta wuce, bayan tayi wankane kuma ta shirya kanta acikin, wani tsadadden leshi, tare da yafa mayafinta cikin kamala ta fito. Kaitsaye kuma d’akin Jannart din ta nufa. Koda ta shiga falon, yanzun ma bata iske Jannart dinba shiyasa kaitsaye ta wuce cikin d’akin. A dai-dai lokacin kuwa Jannart din, zaune take abakin gado, hannunta rike da wani dan littafi na turanci tana karantawa, wanda kuma yana daya daga cikin, yan abubuwan da ta taho dashi. Ganin Mamy da tayi ne kuma, yasa tayi saurin sunkuyar da kanta k’asa, Mamy kuwa murmushi tayi, kana cikin kulawa tace. “Jannart nida Ramadan da Riyyam zamuje kasuwa, sannan Abbanku ma zasu fita yanzu saboda naji dazu suna magana da Baba Maud’o akan cewar zasuje wani waje.” Cikin girmama tace. “Toh Mamy sai kun dawo Allah ya kiyaye hanya”. Amin Mamy kana ta daura da cewa. “Yanzu ki fad’amin me dame kikeso asayo miki Idan munje.” Kai Jannart din ta dan sunkuyar k’asa, cikin sanyin murya, had’i da tsantsar ladabinta ga Mamyn tace. “Mamy duk abunda kika sayamin yayi.” Kai Mamyn ta jinjina cike da gamsuwa kuma tace. “Masha Allah! To bari muje saimun dawo ko. Idan zaman dakin ya isheki, zaki iya fitowa falonki kisha iska, ko kallo kiyi nasan zai d’ebe miki kewa kafin mu dawo”. “To Mamy, amman sai yaushe zaku dawo ne?”. Jannart din ta tambaya, cikin tausasa murya. Murmushi Mamyn tayi, again kuma itama cikin kulawa tace. “Jannart kinsan yanayin kasuwa, Idan ka shigesa sai abunda Allah yayi, kana lisssafin zaka dawo da wurwuri, kuma sai kaga ba haka abun yake ba.” Kai Jannart din ta jinjina, inda Mamy kuwa ta cigaba da cewa. “Ni kaina bansan yaushe zamu dawo ba, saboda iya yanayin cikowan jama’a,n da muka samu, iya jimawan mu, amma dai Ina da yakinin bazamu wuce azahar ba.” “Mamy har azahar.” Jannart din ta tambaya fuska a karye. “Eh mana Jannart, domin ya danganta da irin abubuwan da zamu saya, kuma kinga yanzu ma ana neman wajen karfe sha d’aya bamu tafiba.” Kai Jannart din ta jinjina tare da gyara zamanta, tace. “To Mamy saikun dawo Allah ya tsare.” Da “Ameen.” Mamyn ta amsa, harta juya zata fitane kuma idanunta suka Sauk’a, akan breakfast din da ta kawowa Jannart din, wanda ko tab’ashi batayi ba. Kallonta Mamyn tayi, kana cikin kulawa tace. “Jannart Meyasa baki ci abincin dana kawo miki ba?.” Kai Jannart din ta dan sunkuyar kasa, kana murya asanyaye tace. “Mamy banajin yunwa sosai ne, amma zanci zuwa anjima.” “A’akam, banyarda da hakan ba, sam ban lamunci zama da yunwa ba sauk’o maza kici abinci kinji.” Mamyn ta fad’a tana me kamo hannunta, ta zaunar da ita akan sofa, tare da matso mata kwanon abincin gabanta, cikin kulawa kuma tace. “Kici abinci kinji, kada ki zauna da yunwa, domin yunwa tana illatar da lafiya, ko ke dinma irin Mijin naki ne, baku damu da abinci ba sai kayan kwalama.” Shiru Jannart din tayi, kana Cikin matukar kunya, ta sadda kanta kasa, domin aduk sanda taji ance mijinta, wani irin abu ne takeji mai nauyi ya tsaya akan kirjinta to waye mijin? Ya yake? Me halinsa?. Wadanan sune tambayoyin da takewa kanta tun jiya. Mamy kuwa zuba mata abincin acikin plate tayi, tare da cewa. “Idan kina buk’atar wani abu kafun mudawo, akwai kitchine anan cikin falon mu. Taso ma muje na nuna miki.” Mamyn ta fad’a tana me kamo, hannunta babu musu kuwa Jannart din ta mik’e, tare dabin bayan Mamyn suka fito, har cikin babban falon. “Kinga wannan shine kitchine dinmu, wacccan kofan kuma anan part dina dana Abbansu Rayyern yake akwai kofar shiga da fita ta cikin falonmu wanda ba sai anbi ta nan ba.” Mamyn ta fad’a tana meyi mata nuni da kitchine da kuma sashin su ita da Abba. Kai Jannart din ta jinjina cike da gamsuwa. “Can kuma dakunan k’asane irin Part ɗin dake sama ne. sai kuma sama inda anan bedroom na Rayyern, da kuma Ramadan suke, sai kuma extra part guda d’aya da yake can ta woje. Sai nasu Baba Mauɗo, sai wanda kike ciki. A can saman Mai gidanki yake.” Mamyn ta k’are maganan tana meyi mata nuni da saman. Jannart kuwa, kanta tad’an sadda k’asa, tare kuma da soma wasa da y’an yatsun hannunta, kana cikin sanyin murya tace. “Mamy To meza’a girka yau d’in, kafun kudawo zan girka tunda dama ina zaune ne kawai babu abunda nakeyi.” Murmushi Mamy tayi, tare da girgiza Kanta, kana cikin tsananin kulawa tace. “A'a ki huta kinji Januart, bana son ki shiga kitchine daga yanzu. Idan na dawo, zan girka abincin karki damu, ai bazamu wani jima sosai ba” Dan juya kanta, tayi, saboda zuwan su Ramadan da kuma Riyyam kallonsu ta ɗanyi kana ta juyo ta kalli Mamy, atsanake cikin yanayin dake nuna biyayyarta tace. “Da gaske Allah Mamy zanyi girkin, kinga zaku dawo a gajiye.” Riyyam-nsra da yake karasowa wajennasu ne yayi saurin cab’e zancen da cewa. “Please mana Mamy kibar My Aunty tayi mana girki yau, nasan abincinta dole zaiyi dadi.” Jin muryar Riyyam-nsra dinne kuma yasa Jannart ɗin. Dan dago da kanta, ta kallesu dai dai lokacinne kuma Ramadan ma Ya karaso wajen. Fuskarsa dauke da murmushi kuma yake Kallon matar Hamman nasa. Cikin sakin fuska da kuma walwala yace. “Good morning my beautiful Aunty, ya kwanan bak’unta.” Murmushi ta ɗanyi kana ta ɗan kalleshi. Tare da cewa tace. “Morning.” Riyyam ne yayi saurin matsowa kusa da ita, tare da danyin kasa da muryarsa, cikin kulawa yace. “Aha My Aunty kin tunani ko?”. cikin ɗan sakin fuska ta gyaɗa mishi kai, alamun ta tunoshi haduwarsu a airport, Cikin yanayin rawan kansa yace. “Aunty Jannart ni sunana Riyyam-nsra, tiktokers nasan kinsani ko?”. Murmushi tayi tare da gyaɗa kai, ganin yadda ya tsareta da ido. Kuma tabbas ta tunoshi haɗuwarsu a airport. Shima murmushi yayi tare da cewa. “Yauwa shi kuma wannan Hamma Ramadan sunansa, kuma yaya nane, akwai kuma babban yayanmu Hamma Rayyern.” “Please kiyi mana abinci maidadi kinji, wanda zaisa kunnuwanmu su motsa.” Ba iya Mamy da Ramadan ba harta ita saida ta saki murmushi mai hade da dan dariya. Mamy kuwa Ganin lokaci na k’ure musu ne yasa, tace. “Jannart rabu da shirmen Riyyam, koma daki kije kici abincinki. Maganan girki kuma tunda kin dage sai kinyi, ki dafa mana abu mai sauki kawai.” Kai Jannart din ta jinjina, sannan cikin zazzakar muryarta tace. “Mamy ku dawo lafiya.” Da “Ameen” duk sauka amsa, inda Mamy ta had’a kan Ramadan da Riyyam sukayi waje. Itakuwa Jannart d’akinta ta koma, duk da cewar bata wani jin yunwa amma haka ta zauna ta d’an ci abincin, bayan ta kammala ne kuma ta d’aura da, lemon strawberry da Mamyn ta had’o mata dashi. Gyatsa mai sanyi tayi tare da cewa. “Alhamdulillah”. Kana ta yunƙura A nitse ta mik’e tsaye tare da d’aukan plates din da taci abincin ta fita dashi. A hankali ta buɗe ƙofar falon nata. Kana ta sako kanta. Cikin Babban falon. Numfashi ta dan fesar sabida wani irin masifeffen sanyin AC'n da suke busowa duka biyu. A hankali take takowa har ta iso tsakiyar falon. “Masha Allah, Mamy ba dai tsabta ba”. Ta faɗi haka tana jujjuya kai tana kallon komai doke cikin falon. Tsab-tsab sai ƙamshi da sanyi daya wadaci falon. A hankali ta juyo ta nufi Dinning area. Tray'n dake hannunta ta ajiye kam table ɗin. Kana ta juya a nitse. Ta dawo tsakiyar falon. Gaban tv ta nufa. Sabida shiru da gidan yayi sai taji kamar tana tsoron gidan. TV'n ta kunna cikin sa'a kuma kan tashar Sunnan TV yake. Inda aka saka sautin muryar Malam Sulaiman. Rage sautin tayi dai-dai misali. Kana a hankali ta juya ta nufi Dinning area. Tray'n data ajiye ta ɗauka a hankali ta nufi Kitchen kaitsaye. “Wow. Masha Allah”. Ta kuma faɗa tana mai bin tsarin Kitchen da kallo komai tsab-tsab. Kai tsabta rahmace. Ta kuma cewa tana mai nannad’e hannun rigarta. Tare kuma da k’arasawa gaban sink, plates din da taci abincin ta wanke, bayan ta kammala wanke wanken ne kuma. Ta ɗan tsaya jim a tsakiyar Kitchen din. Cikin sanyin murya tace. “Toh me zan dafa?”. Tayi mgnar alamun tambayar kai da kai. Kanta ta ɗan jinjina kana matso gaban Fridge guda biyu dake cikin Kitchen din. A hankali ta bud’e babban deep freezer Kai ta jinjina tare da ƙara matsowa. Gaba daya cikinsa shak’e yake da kayan Miya, hadi da kuma naman, Rago, Saniya, da kuma naman kaji, sai kifayen da tuni sun daskare ma acikin fridgen. Naman kaza ta d’ebo d’an da-dai. bayan ta wanke naman ne kuma ta zubashi acikin tukunya tare da kunna gas ta d’aurashi akai, al'basa ta ɗauka wanda ta gani a jere cikin wani da karfe. Mai yawa ta yanka kana ta watsa a cikin naman. Kana ta ɗan kalli gefenta inda wasu robobi farare masu marafe pink color ke jere, da kayan bukatu kamarsu. k’amshi, da dandano. garlic, kanumfari da kuma maggi Corry ta saka. Kana ta meda marfin ta rufe. Sai kuma taja kujera ɗaya dake gaban ɗan ƙaramin table ɗin dake tsakiyar Kitchen din ta zauna tana mai tunanin to me zata dafa musu. Lokaci ɗaya. Gidan ya cika da ƙamshin tafashen. A hankali ta ɗan juyo ta kalli tukunyar daketa fidda tururi mai masifar ƙamshi. Ganin naman na dahuwa ne kuma yasa ta mike ta sake bud’e fridge din, inda ta ibo. Pease, green beans, carrot, green pepper, red chilies, cabbage, cucumber, onion, and liver, tsayuwa tayi na musamman inda ta yanka kowannensu, awaje na musamman, saidai Banda carrot wanda tayi greeting d’insa. Bayan ta kammala duk wayannan dinne kuma, kazan na gama dahuwa. Ta sauƙeshi kana ta ɗauki kaskon suya ta doro tare da zuba mai. Kana ta fara soya shi sama sama. Tana gama ta ajiyeshi gefe. Kana ta ɗauko kayan miyanta duk abin buƙata tare fara aikinta a nitse ta hada masa pepper onion chicken soup. Gaba ɗaya kwamshin ya ƙara de ko ina. Tana kammala had’a kazartata kuwa ta d’aura shinkafa kasancewar, fried rice and coleslaw takeson yi. Da ɗan hanzarin taci gaba da aikinta yanayi tana ɗan jujjuyawa da waige-wauge na bakunta da kaɗaici. Cikin abunda bai wuce awa ɗaya da rabi ba kuwa ta kammala, had’a abincin acikin babban food flask. Bayan ta gama da abincinne kuma ta dawo b’angaren drinks. Shaka mai dadin gaske ta had’a musu, sai kuma pineapple and orange juice. Cikin abunda bai wuce 50mn ba ta gama haɗa abubuwan shan, gidansu Rayyern din gaba d’aya ya kacame da k’amshin daddad’an girkinta. Ganin akwai sauran lokaci ne kuma yasa ta, had’a fan cake ta somayi. Acan b’angaren Rayyern kuwa, sai yanzu yake tashi daga kwanciyar da yayi, ahankali ya zuro da k’afafunsa k’asa, tare kuma da mik’ewa, kaitsaye ya nufi bathroom saboda yanason sakarwa kansa ruwa. Ajiyar zuciya ya sauk’e a dai-dai lokacin da yaji saukar ruwan shower ajikinsa, lokaci daya kuma ya lumshe idanunsa, tare da soma gogawa jikinsa sabulu. Cikin nutsuwa yayi wankasa, tare da d’auro alwala. Yana fitowa daga cikin toilet din kuwa, k’arar fitar motar Abba, wanda suka fita da Baba Maud’o ya daki kunnensa. Wanda ya fita da Baba Mauɗo. D’an langawab’ar da kansa gefe yayi, tare dasa hannu ya shafa lafaffen cikinsa, kasancewar sai ayanzu ne ma yake tuna cewar rabonsa da abinci tun daren jiya, sosai kuma zuwa yanzu yakejin yunwa na k’wak’ulan cikinsa. Anutse ya shafawa jikinsa mai, bayan ya kammala shafa mai dinne kuma, ya karasa gaban Sif din kayansa. Wani had’add’en rika da wando, masu masifar taushi pink color masu digon fari-fari. ya ciro tare da sakawa ajikinsa, kasancewar kuma rigar irin mai aninaye a gaban nanne, yasa faffadan chest d’insa bayyana. Body spray ya shafa ajikinsa, tare kuma da d’aukan watch d’insa ya makala. Masha Allah bak’aramin kyau shigar riga da wandon tayi masa ba, musamman ma yanda kawataccen sajensa keta shining ya kwanta lib. Wayarsa ya d’auka, tare da k’arasawa, jikin dan karamin fridgen dake cikin dakin nasa ya bud’e, fuskarsa ya d’an ya mutsa, saboda yanda yaga fridge din babu komai naci acikinsa, chocolates dinsa duk sun kare, sai drinks kawai da sukayi saura. Maida murfin fridgen yayi ya rufe, kaitsaye kuma ya nufi cikin falon nasu dake sama, saidai still shima babu komai acikinsa, sai kayan shaye shaye. Kansa ya d’an girgiza saboda yunwa sosai yakeji. Batare da tunanin wani abu ba kuwa, ya nufi falon k’asa, inda ahankali yake sauk’owa daga kan matattakalan falon, Yayinda k’amshin sa ke dada mamaye ko ina. Saidai kuma jin da yayi ko ina shiru babu motsin mutanene yasashi soma rarraba idanunsa ba amun kowa a gidan. Sai wani ɗan karen kamshin da yake shige masa hanci. K’arasa sauk’owa daga kan steps din yayi, tare da k’arasowa tsakiyan falon ya tsaya, hannayensa duka biyu ya d’aura akan k’ugunsa, tare kuma da karyar da wuya ya d’an langwab’ar da kansa gefe, cike da alamun shagwab’a. Acan cikin kitchine kuwa Jannart ce tsaye, tana k’arasa had’a fan cake din da takeyi. Tana aikinta a sake. sabida doguwar rigarta ne ajikinta, sai kuma dan kwalin rigar da ta daura akanta, wanda hakanne kuma yasa dogon gashinta ya baje akan gadon bayanta kuma a zatonta babu kowa a gidan sai masu gadi. Aikinta take cike da nutsuwa, Yayinda karatun al’q’uranin da ta kunna acikin falon ke kawowa kunnuwanta ziyara har Cikin Kitchen din shiyasa tsoronta ya kau. Rayyern kuwa daya gama k’arewa falon kallo, Ganin babu motsin kowa acikinsa ne, yasa kaitsaye ya nufi dining table, inda yaga manyan food flask a ajiye. Acan b’angaren Barrister Kabir kuwa, Koda yabar gidan Dr. Sajo, kaitsaye wajen saida wayoyi ya nufa. Iphone 11promax ya saya, tare kuma da sabon SIM, wanda akayiwa register a matsayin nashi. Daga shagon sayan wayan kuma, kaitsaye gida ya nufa. Koda ya isa gidan nasa, anan falo ya samu Aunty Dijat zaune, yayinda Hafeeza ke kwance akan cinyarta tanayi mata tsifa. Hafeez kuwa yana can gefe, ya duk’ufa akan homework d’in da aka bashi a school. Shigowar Barrister dinne kuma yasa, duk yaran tashi Aguje sukaje suka rungume Babansu. Aunty Dijat kuwa murmushi ta sake, had’e da Kallon mijin nata cikin kulawa tace. “Sannu da dawowa Abban Hafeez.” Kai Barrister Kabir din ya jinjina mata, alaman amsawa, tare da neman waje agefenta ya zauna. Mintin daya kawowa su Hafeez ya basu, tare da zaro Sabuwar wayan daya sayo ya soma kokarin saka sim. Kallonsa Aunty Dijat tayi, cikin d’an yanayin mamaki kuma tace. “Abban Hafeez wannan Wayarfa ta waye?” Murmushi Barrister Kabir din yayi, tare da cewa. “Wayar Jannart ce dana sai mata, saboda yanzu babu waya a hannunta, bakuma zataji dadin zama ba waya ba gaskiya.” Murmushi Aunty Dijat din tayi, cikin yabawa da wayar tace. “Masha Allah gaskiya wayar tayi kyau.” Kansa ya jinjina alaman godiya, batare daya sake cewa komai ba kuma ya mike kaitsaye ya wuce dakinsa. Rayyern kuwa ahankali yake taka k’afafunsa, cike da shagwab’a, had’i kuma da yunwar dake k’wak’ulan cikinsa, ya nufi hanyar kitchine din. Hannunsa dafe da cikinsa, cikin kuma kasalalliyar murya ya fara kiran sunan Mamy. “Mamy! Mamy!!.” Sai kuma ya ɗan sa hannunsa ya shafa cikinsa murya can ƙasa yaci gaba da cewa. “Mamyna yunwa, please ki bani abinci..” Ya Kai karshen maganan nasa, yana me gab da saka kansa acikin kitchine din. Jannart dake tsaye cikin Kitchen din kuwa jin muryar mutum, akurkusa ne yasa ta saurin juyowa cike da tsoro. Dai-dai lokacinne kuma ya sako kansa cikin kitchine din. Ido hud’u da sukayi ne kuma yasa Zuciyar Jannart wani irin bugawa, take taji wani abu ya daki kirjinta, wanda har hakan yasa tayi saurin sadda kanta k’asa, tare da kama yatsunta ta had’esu waje d’aya. Cike da...! https://chat.whatsapp.com/IM6PrgYNy9s6lP0aXmBkaN Samun zafafan saukakan kayayyakin zamani na mata tun daga kan leshi, shadda, atamfa, material, jaka da takalmi, hijab..... da dai sauransu akan farashi mai sauki da rahusa sai a kamfanin Garkuwa collection. Bama wannan kadai ba akwai kayan order da muke yi shi ma duk a cikin rahusan da saukin kudi. Ba mu tsaya nan ba ina kuke yan kasar *NIGER* albishirinku kuma kuna iya siyan kayanmu ya isa gareku cikin aminci ba tare da bata lokaci ba. maza yan’uwa ku garzayo ku gane wa kanku wannan rahusar da kuke jin labari. Kayanmu ko a kasuwa ba zaka samu farashinsu ba. gidanmu gidan duniyar leshi, atamfa shadda, material da sauransu. Sai kun zo. Muna maraba da kai a kowanne gari kake. GARKUWA COLLECTION! Siyan nagari mayar da kudi gida! By *GARKUWAR FULANI* 11/16/21, 8:37 AM - Auntyna: *GARKUWAR taku ce dai MA'AURATA, da masu shirin aure, da masu jego, da yan gayu masu son k’amshi kece raini, da gyaran da zaike maimaita muku dararen forkon kuruciya* Ko kunsan Jikinmu na da sinadaran hormones da suke taimakawa dan’adam akan komai musamman lokacin da mace take mu’amalar aure da mijinta. Mafi akasari wannan hormones din ne ke samun matsala ko su yi sanyi koma su daina aiki kwata-kwata shi ne dalilin da zai sa mace tace bata jin sha’awa ko bata san dadin aure ba. Albishirinku ina da kayan da ke taimakawa wannan sinadaran du dawo aiki tukuru don karkato miki da kimarki wajan mai gida sannan su taimakawa wannan sinadaran hormones dinki su dinka secreting din ni’ima wadatacciya da zata taimaka miki ki gamsu mijinki ya gamsu fiye da tunaninki. Note: Kayana ba sa tsinka ruwan ni’ima suna dai taimakawa hormones dinki ne su tsattsafo da ni’imar musamman wacca cutar sanyi ko dattin mahaifa ya dankarar da su ya hana su yin aikinsu yanda ya kamata. Haka zalika idan kina da kyau ki kara da wanka. Zaki iya amfani da magani na na gargajiya wanda zai gyara miki sex hormones din kullum ki kasance cikin humidify wato cikin damshi mai albarka kamar yanda ake son mace. Yana gyara miki mara. Sai kamshi. Hajiyata daure ki fara amfani da turarena ki ji irin salon kamshin sa salo ne da zai daidaita ki da mijinki ya kankaro miki da kimarki a wajansa. Siyan na gari mayar da kudi gida. Ga masu buƙata ga number' wayata wanda nake whatsApp dashi 09097853276 kimin mgn ta whatsApp in har kin tabbatar kin shirya saya mu dai-dai ta, kayana ba ƙanana bane, shiyasa bana harkan karanta, muddin kinsan baki shirya sayaba Please kada kiyi min mgn ki bari sai kin shirya kuɗinki a hannu, ba ina nufin kayana bana talaka bane, no akwai ƙananan set na masu karamin karfi, banson aimin mgn a ɓatamin lokacin aiyukana a shirme baki shiryaba. Shine karantan da bana so. 0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU. In kin shirya ga number ta ga kuma account number ta wanda in mun gama mgn zaki turo kudin ki, kana insa miki kaya a mota, duk ƙasar da kike kayana zaije gareki, amman fa in kinada dalilin zuwan nasune🤝🏻sayan na gari meda kudi gida. GARKUWAR MA'AURATA Da al'hinin ganisa ya tsananta harbawa da ƙirjinta yakeyi. Shikuwa Rayyern a nitse ya kawar da kansa gefe, hade kuma da juyawa, kan Fridge. A hankali ya dan sunkuyo kan, fridge din dake cikin kitchine din ya bud’e, cikin sa’a kuwa ya samu chocolate aciki. Ba tare da ya kuma kallon inda takeba ya. D’aukan chocolate din nasa yayi mai, batare kuma dako juyowa ba, ya nufi hanyar fita Kitchen din cikin nitsuwa. Jannart kuwa zuciyarta ne ke harbawa da wani irin k’arfi, gaba daya ta kasa d’ago kanta kasan cewar kanta a sunkuye ne yasa idonta sauka kan tatrausan fararen sawunshi da in ya taka sai gefe da gefen yayi ja, kana in ya daga yayi fari, wani irin bugawa chest da kuma Heart dinta keyi. Cikin mgnar zuci tace. “Wannan mutumin kuma? To Meya kawosa cikin gidannan? Me yakeyi anan?”. Numfashi ta dan fesar a hankali kana taci gaba da nazari da zancen zuci. “Toh kenan shima d’an gidanne. Dr Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara.” Ta fad’i hakan acikin zuciyarta, lokaci daya kuma sunan wanda ake kira amatsayin Mijinta ya fad’o mata a rai. “Rayyern!” Ta maimaita sunan cikin zuciyarta domin har yau har yanzu bata taɓa iya furta sunanta kan harshen ta ba. Lokaci d’aya kuma tayi saurin girgiza kanta. Dan bataji ajikinta cewar shine Rayyern din da ake ta fadi ba, fact ma har yanzu batasan wayene mijinnata ba. cikin sauri kuma ta d’an d’ago Kai ta sake kalloshi. Dai-dai lokacinne kuma ya kusa kaiwa gab fita daga cikin kitchine din. Sunkuyar da kanta k’asa tayi, kana cikin sanyin muryar ta dake d’an rawa tace. “i...in Ina kwana.” ta fuzgo maganar a hankali. Idonshi ya ɗan lumshe jiyo sautin muryarta. Ido ta zuba mishi ganin yana tafe kamar bai ji taba. Ƙasa tayi da kanta, sai kuma ta ɗan ɗago idonta jin kamar yayi mgn amman bataji kamar “Lafiya.” Daya amsa mata atak’aice batare kuma dako ƙara ko second biyu ya fice daga cikin kitchine din. Fitar tasace kuma yasa Jannart sauke Ajiyar zuciya, tare dasa hannu ta dafe kirjinta da takejin yana Azabar bugu, bayansa tabi da kallo, har acikin zuciyarta tana me mamakin ganinsa da tayi a cikin gidan. Numfashi ta dan fesar tana mai yin rau-rau da idonta. Sabida bataji amsawar da yayiba dan larurar kunnuwanta. Yayinda a zuciyarta kuwa take fargabar baro Yah Junaid ta kuma samo irinsa a nan. A hankali tace. “Abba munyi gudun gara mun tadda zago!”. Shikuwa Rayyern yana fita falon, Wayarsa ya zaro tare da dannawa numbern Mamy kira. Bugu biyu kuwa Mamy ta d’aga wayar. Kasancewar daman jiran d’aga wayar nata yakeyi ne, yasa tana d’agawa ya kwaɓe fuska, tare da cewa. “Mamy ina kikajene gidan babu kowa.” Mamy kuwa da ke tsaka da sayan kayayyaki daka tawa tayi. Jin abunda ya fada dinne kuma yasa ta cewa. “Kamar ya gidan babu kowa Rayyern? baga Jannart ba.” Fuskarsa ya kwab’e batare daya nuna damuwarsa da zancen ba kuma yace. “Mamy yunwa nakeji.” “Yunwa kuma Rayyern? to kaje ka tambayi Jannart zata baka abinci.” Mamyn ta fad’a in a serious. Jin hakanne kuma yasashi Katse kiran, tare da turo bakinsa gaba, tamkar karamin yaro, cikin guna guni yace. “Ni meye hadina da wata Jannart, ce ko Jalila ce ma babu abunda ya shafeni da ita, I told you ai, I don’t love her, but kuka shareni kuka wani medani kamar karamin yaron da baisan abinda yake yiba.” Ya k’are maganan yana me karasa haurawa saman. Anan cikin falonnasu na sama ya zauna, bayan ya zuba. Wasu daga cikin Chocolate din cikin Fridge. Kana ya debi na cinsa a plate, sannan ya zo ya zauna yana latsa wayarsa tare da b’are chocolate dinsa yaci, bayan ya gama cine kuma ya d’aura da ruwa. Acan Shoprite kuwa, su Mamyn sayayya sukayi sosai, Yayinda kuma Rabin sayayyar tasu, kayan sawa ne, kama daga kan dogin riguna abayas, sai kuma yan kanti wandunan pallazo, da kuma skirts, sai atamfofi da lesuka, kama daga kan takalmi shoes, Hijabs, vails, bags, dama duk wasu abubuwan buk’atan Mace babu wanda basu saya ba. Haka dai suka dawo gida da kaya niki niki. Wanda zuwa lokacin kuma tuni Jannart ta kammala, had’a musu komai na lunch akan dining harma ta koma falon ta, bayan tayi sallan azahar ne kuma ta kwanta. Su Mamy kuwa Sai da karfe 1 ta gota, kafun suke dawowa. Ramadan nayin parking cikin gidan, Hadi ya matso da sauri ya budewa Mamy marfin motar. Bayan sun fito daga cikin motar ne kuma, Ramadan, Riyyam da kuma Hadi suka shiga jidon kayan da suka sayo din, suna shigarwa zuwa babban falon k’asa. Bayan sun gama shigo da kayanne kuma, Hadi ya koma waje. A tsakiyar falon suka ajiye kayyakin tare da kimtsasu wuri daya kayan masu yawane, domin duk wani abu na amfanin Mace babu wanda basu sayo ba hatta audugar mata Mamy ta saya mata, ga kuma wasu had’add’un akwatuna set masu kyau da suka sayo. Mamy kuwa wanda shigowarta cikin falon kenan, jakan dake hannunta ta ajiye, tare da wuce wa kaitsaye ta nufi bedroom dinta, saboda Ganin da tayi lokacin sallan azahar na kokarin gotawa. Ramadan da Riyyam kuwa, anan cikin bathroom din dake cikin falon, suka d’auro alwala, tare da jerawa atare suka wuce masallacin, dake jikin gidan nasu. Bayan sun idar da sallan azahar dinne kuma, suka sake dawowa cikin gidan, gaba ɗaya a sokane suke tafiya, wanda da dukkan alama kuma yunwa sukeji da tarin gajiya, saboda zagayen da suka sha a cikin Shoprite din, wai danma sun dan saya biscuit, sunci acikin Shoprite din. Dawowarsu cikin falonne kuma suka samu, Mamy zaune, wanda itama idar da sallanta kenan, ta dawo falon ta zauna. Akusa da Mamyn suka zauna. Yayinda Riyyam kuwa ya langwab’ar da kai, tare da karyar da wuyansa gefe, cikin yanayin shagwab’an wanda in yanayi, tsananin kamanninsu da Rayyern ke k’ara bayyana yace. “Wash Allah Mamy yunwa nakeji, har inaji kaman babu hanji acikina.” “To Riyyam, yanda naji gidannan gaba daya, ya gauraye da kamshi, ai nasan abinci na musamman Auntynku ta girka mana.” Mamyn ta fad’i haka tana murmushi, saboda sosai maganan Riyyam din ya bata dariya. Jannart dake kwance anan cikin falonta kuwa, cikin dan bacci Marar nauyin daya d’auketa ne, ta soma jin tashin hayaniyarsu, bud’e idanunta tayi, tare kuma da tashi ta zauna. Shiru tayi na y’an wasu mintuna, Jin da gaske maganan su Mamyn ne ke tashi acikin falon, yasa ta d’aukan mayafinta ta rufa, ahankali ta mike tsaye, kana cikin takunta na nutsuwa, ta nufi falon nasu kaitsaye. Ahankali ta murd’a handle din kofar falon nata ta fito, tozali dasu Mamyn da tayi ne kuma yasa ta sakin dan murmushi, tare da karasowa ta durkusa a gaban Mamyn.. “sannunku da dawowa Mamy.” Jannart din ta fad’a tana me duk’ar da kanta k’asa. “Yauwa sannunki dai Jannart, ya fama da kad’aici.” Mamy ta tambaya cike da nunawa Jannart din kulawa. Jannart kuwa Murmushi tayi tare da cewa. “Alhamdulillah amma da bakwa nan gidan ba daɗi Mamy”. Tayi mgnar cikin fito da gskyr zuciyarta. Mamy kuwa murmushi tayi tare da cewa. “Meyasa baki taso Rayyern yazo ya tayaki zamaba”. Tayi mgnar cikin son nuna kusancinsu. Ita kuwa Jannart da sauri tayi ƙasa da kanta. Kana cikin nutsuwa ta mike tsaye, direct gaban fridge ta nufa, inda ta bud’e ta dauko ruwa, da kuma tamarine juice maisanyi, bayan ta shiga kitchine ta dauko cups ne kuma, ta sake dawowa cikin falon, tare da ajiye juice da ruwan agaban Mamyn, cikin nuna tsantsar kulawa tace. “Mamy ga ruwa kusha, nasan kunsha hanya, sannan ga abinci ma, tun d’azu na gama.” Murmushin Jin dadi Mamyn tayi, tare da karb’an ruwan, da Jannart din ta tsiyaya a kofi Tasha, Zuciyarta kuma cike da annushuwa tace. “Masha Allah Jannart Allah ya miki albarka.” “Ameen.” Jannart din ta amsa cikin jin daɗi. Yayinda shikuwa Ramadan dake zaune, ya tankwashe k’afafu Kallon Jannart din yayi, cikin dan sigar gajiya yace. “Aunty Jannart wallahi yunwa nakeji, tun breakfast din safe, sai wani dan biscuit da naci, abamu abinci please.” Murmushi Jannart din tayi, kana cikin sakin fuska tace. “Sorry akwai abinci zakuje dining ko kuma akawo muku abincin nan.” “Kai Anya kuwa, gaskiya dai Jannart kawo mana shi nan muci, saboda dukanmu agajiye muke.” Mamy ta cab’i zancen domin itama kanta yunwa takeji. Jannart kuwa kaita jinjina tare da cewa. “To bari nakawo muku abincin nan.” Tana gama fad’an hakan kuwa, ta mik’e tsaye, tare da nufan dining table din, food flasks din da ta zuba abincin aciki ta d’auko, atsanake kuma ta shiga jere musu shi agabansu. Bayan ta kammala haka dinne kuma, ta d’auki plates tare da fara saving ko wannensu, had’add’iyar jollop rice and coleslaw din, ta zubawa Mamy, sai kuma pepper chicken onion soup din da ta zubashi acikin wani plate da ban. Kamar yanda ta zubawa Mamyn kuwa, haka ta sakawa su Ramadan da Riyyam ma, way’anda sukayi zaman dirshan. Saboda ma tunkafun su saka abincin abakinsu, kamshi duk ya cika musu hanci. Turawa kowannensu abincin agabansu tayi, yayinda na Mamy kuwa ta kai mata har gabanta. Tare da d’aukan cup ta zubawa kowannensu Shaka’n da ta had’a. Ramadan da Riyyam kuwa, tun a Loman farko da sukayi, duk suka lumshe idanunsu, saboda wani irin dadin abincin da sukaji, tun kafun su gama tauna abincin kuwa suka soma jijjiga kansu, cike da gamsuwa, Ramadan yace. “Masha Allah, nice taste gaskiya Aunty Jannart kin iya girki, ko daga aroma dinma kin biya.” “Sosai kuwa Aunty Jannart, gaskiya abincinki akwai dadi, wayyo Allah kaman kunnena zai tafi.” Cewar Riyyam-nsra daya cab’e zancen. Ba’iya Mamy dake dariya ba kuwa har Jannart saida tayi murmushi. Ahankali kuma ta mik’e tsaye, tare da sunkuyar da kanta k’asa cikin sanyi tace. “Mamy bari na koma d’aki.” Saurin Riko hannunta Mamy tayi, kana cikin kulawa tace. “A’a Jannart Ina kuma zaki, ki zauna mana muci abincin tare, ko wani abu zakiyi a dakin?” “A’a.” Jannart din ta fad’a ahankali, tare da soma wasa da y’an yatsun hannunta. “to zauna kinji, kada kice zakiji kunyan mu, duka munzama daya.” Mamyn ta fada mata cikin kulawa. Jin hakanne kuma yasa ta zama, tare da bud’e food flask din Fan cake din, ta soma kokarin saka Musu acikin plate. Ramadan da Riyyam kuwa tuni suke ta zuba santi akan abincin. Wanda hakan yasa, Mamy daukan pillow ta saka musu, amatsayin waiji, sabida yanda suka cikasu da surutu. Acan compound din gidan kuwa, Abba da Rayyern dinne suka shigo, atare kasancewar su sai yanzu ne suke dawowa daga masallaci, saboda Koda aka Idar da sallah basu bar masallacin da wuri ba. Dab da zasu k’arasa jikin kofar falonne kuma, Rayyern yaga Abba na kokarin wucewa gaba. “Abba Ina kuma zaka?” Rayyern ya tambaya, da dan mamaki. Hakan ne kuwa yasaka Abban sakin murmushi, kana cikin kulawa yace. “K’ofar baya zanbi Rayyern”. Da sauri yace. “Meyasa?”. Yana mai ci gaba da tafiya yace. “Sabida surkata daga yau ma tacan zanna shiga da fita.” Fuska Rayyern din ya kwab’e, kamar zaice wani abu kuma saiya fasa, Yayinda Abba kuwa kaitsaye ya nufi hanyar da zata sadashi da kofar falonsa na baya. Rayyern kuwa fuskarsa ad’an tsuke yake mgnar zuci. “Ba ga irin ta nanba kuma kanku takura zata zame muku”. Ya ƙare mgnar yana tura kofar falon ya shiga, bakinsa d’auke da sallama. Jin sautin muryarsa ne kuma, yasa Mamy dasu Ramadan d’agowa suka kalleshi, tare kuma da amsa masa sallaman nasa. Idanunsa ya d’an zuba musu, musamman Ramadan da Riyyam, wanda yaga sun maida gaba daya hankalinsu wajen cin abinci, musamman ma Ramadan wanda ya ritsa pepper chicken, babu abunda kakeji atsakaninsu sai kat-kat k’aran spoons. Idanunsa ya d’an lumshe, tare kuma dasa hannunsa ya dafe cikinsa, dan ƴar yunwar da yake ji. buɗe idanun nasa da zaiyine kuma ya sauk’e ganinsa akan Mamy, wacce ta d’an zuba masa ido. Idonshi ya kauda tare kuma da karyar da wuyansa gefe. yanayin yanda Mamyn taga yasa hannayensa akan lafaffen cikinsa ne, kuma yasa ta gyara zamanta, kana cikin tausasa murya tace. “Kwata kwata bakason cin abinci Rayyern, kana son barin kanka da yunwa bana son hakan Kai kullum rayuwarka ta ƙare a cimar zaki, duda kasan matsalar da ke damunta, da anyi mgn sai kace. Ba zaƙine matsalar ciwon kaba. Zo kaci abinci kaji, gashi nan da d’uminsa kaci tun kafun ya huce, saboda nasan bakason cin abinci mai sanyi.” D’an kwab’e fuskarsa yayi, had’e da kawar da kansa gefe. Yayinda Ramadan dake ta cin nama kuwa ya d’ago da kansa ya kalli Hamman nasa, kana cikin santin abincin yace. “Hamma Rayyern abinci yayi dadi, ka gwada ci kaji pepper chicken dinnan kuwa, badai dadi ba.” Ya k’are maganar yana me yagan cinyar Kazan yasa abakinsa. Riyyam-nsra kuwa, juyawa da kallonsa yayi ga Jannart, wanda take zubawa Mamy juice na pineapple and Orange din da tayi, kanta ak’asa yake, domin tun shigowar Rayyern din bata ma d’ago kanta ba. “Nasara miki Aunty Jannart, wallahi kin iya dafa abinci sosai, tunda na shigo Nigeria banci fancake mai dadin naki ba, please kullum kina yi manashi kinji..” ya k’are maganar yana me rausayar da kansa gefe, alaman rok’o. Jannart kuwa da har yanzu kanta ke k’asa murmushi tayi, batare kuma da tace komai ba, ta zuba musu shaka a cup shida Ramadan. Mamy kuwa Rayyern dake tsaye yana Kallon wani waje daban ta kalla, still kuma cikin kulawa tace. “Babana zokaci abinci kaji, ka daina zama da yunwa.” Kansa ya d’an girgiza alaman “A’a.” Batare kuma daya ce komai ba, ya zagaya ta gefensu, kaitsaye ya nufi hanyar steps din da zai kaishi zuwa sama, ko kusa kuwa bai kalli inda Jannart take ba, impact baisan da cewar tana acikin falon ba. Mamy kuwa da kallo ta bisa, harya soma haurawa saman stairs dinne kuma ya Dan tsaya, tare kuma da juyowa ya kalli Mamyn nasa yace. “Mamy Abba fa ya shigo, yana side d’insa.” Kai Mamyn ta jinjina, Yayinda shikuwa Rayyern din kaitsaye ya haura sama. Jannart kuwa har dai zuwa yanzu ta kasa d’ago kanta, saidai jin alaman tafiyarsa yasa ta sauk’e b’oyayyar Ajiyar zuciya. Mamy kuwa food flask din abincin ta d’auka, bayan ta mik’e tsaye ne kuma tace. “Barin kaiwa Abbanku nasa abincin.” Bayan ta wuce sashin Abban ne kuma, Jannart din ta d’an gyara zamanta, tare da d’ago kanta, ta kalli babban tv’n dake cikin falon, inda taga tv channel dinsu, wato Arewa24 suna haska film din, Nisan Kwana. D’an maida hankalinta ga tv’n tayi, Yayinda su Ramadan kuwa har yanzu cin abincin nasu yaki k’arewa, santi kawai sukeyi, shakan da ta had’a kuwa tas suka shanye shi. Acan b’angaren Rayyern kuwa yana shiga cikin falon nasu, jacket din dake saman rigarsa ya cire, tare kuma da karasawa gaban fridge dinsa, bud’e murfin fridge din yayi. Hade da d’auko babban kwalban chocolate d’insa, wanda saboda tsabar sanyi harya fara daskarewa. Murfin kwalban ya b’alle, tun kafun ya zauna kuwa ya saka spoon acikin kwalban, tare da d’ebo chocolate din ya soma sha. Idanunsa ya lumshe, alokacin da yaji zakin chocolate din na mamaye bakinsa. Cikin nutsuwa kuma ya zauna akan daya daga cikin kujerun falon, bayan ya daura kafafunsa akan rug ne kuma ya ci gaba da Shan chocolate d’insa. Yana girgiza k’afa alaman yana enjoying mood dinnasa. Mamy kuwa Koda ta isa part din Abban, zaune ta sameshi a falon, ganinta ne kuma yasa Abban sakin murmushi. Kana cikin sakin fuska yace. “Banyi tunanin zuwanki yanzu ba ai, naga kaman yaran naki sun rik’eki da zance saboda daga nanma inajin tashin maganganunku.” Murmushin Mamyn tayi, adaidai lokacin da take k’arasowa gabansa ta durk’usa, kana muryarta atausashe tace. “Barka da dawowa.” “Yauwa, kuma sannunku da dawowa, fatan kunyi sayyaya lafiya?” “Lafiya lau Alhamdulillah, munsayo duk wasu abu da suka dace gacan kayan ma acikin falo, ko kuncesu ba mu yi ba.” Mamy ta amsa tana me kokarin zuba masa fried rice acikin plate. Abban kuwa Kai ya jinjina cike da gamsuwa, kuma yace. “To Allah ya Amfana.” “Ameen.” Mamyn ta amsa tana me ajiye masa plate din abincin agabansa, hade kuma da zuba masa juice, and fancake. Juice din Abban ya d’auka ya d’an kurb’a, cikin rashin son tauyeta kuma yace. “Kije ki gama da yarannaki ko, ni Idan yaso kyaji dani anjima.” “To.” Mamy tace tana murmushi, kana kuma ta mik’e ta fice daga Cikin falon. Koda ta dawo falon,harsu Ramadan sun kammala cin abincin. Inda Riyyam da kansa ya tartare wajen,. Tare dakai plates din da suka b’ata kitchine. Mamy kuwa zama tayi tare da jawo kayyyakin da suka sayo. “Jannart zokiga kayayyakin da muka sayo.” Mamyn ta fad’a tana me bubbud’e kayan. Inda ta fara ciro wasu tsala tsalan laces, da kuma atamfofi masu kyau, Hadi da materials da shadda laces. Jannart kuwa ganin yanda kayan suke da kyau sosai ne yasakata sakin murmushi, tare da cigaba da Kallon kayayyakin da Mamyn ke fitowa dasu. Bayan Mamyn ta faka su laces din agefe ne kuma, ta soma ciro had’add’un Turkish, and Dubai abayas and kimonos, masu kyau da tsadar gaske, kasancewar kuma abayas din irin new design dinnan ne yasa suka dauki hankalin Jannart. Mamy kuwa sauran shoes bag and vails, da kuma sauran abubuwan da suka sayo duk ta nunawa Jannart, kana cikin kulawa kuma tace. “Jannart ga kayayyakin naki, Allah yasa sunyi miki.” Murmushi Jannart din tayi, tare da d’an sunkuyar da Kanta, tana kallon datsassun abayas masu masifar kyau da laces din cikin sanyin murya kuma tace. “Komai yayi, nagode sosai Mamy Allah Ya saka da al'khairi.” “Ameen Summa Ameen Jannart, ba komai ai yiwa kaine.” Mamy ta amsa, tana me zaro wayarta, inda ta dannawa number’n, tailor din da ta amince da k’warewar sa kira. Bugu biyu kuwa tailorn ya d’auka, bayan sun gaisane kuma Mamy ta shaida masa cewar tanason ganinsa. Kasancewar yasan inda Naira take ne kuma, yasa take yace. “Toh Hajjajo. Ganinan zuwa.” Kashe wayan Mamy tayi, tare da Kallon Jannart cikin kulawa tace. “Yauwa Jannart wani irin dinkuna kikeson ayi miki, kinsan ku y’an matan zamanin nan yanzu baku cika son riga da zani ba.” Sadd’a kai k’asa Jannart din tayi, ladabce tace. “Ni Mamy komai akayi ma inasawa.” Murmushin Mamyn tayi tare da cewa. “Shikenan To bari tailan yazo.” Nan dai suka shiga d’an tab’a hira, Yayinda Riyyam-nsra da Ramadan keta jan Jannart din da hira. Suna nan azaune kuwa, cikin abunda bai wuce 15mn ba saiga tailorn yazo. Bayan sun gaisane kuma Mamy ta basa, k’atuwar ledan da ta Ware kayayyakin dinkin aciki, kana cikin sakin fuska tace. “Fahad ga y’atanan dan Allah kayi mata dinkuna masu kyau, way’anda zasu sake fito da ita sosai, sannan kuma akan kari muke buk’atar kayan.” Murmushi Tailan da Mamyn ta kira da Fahad yayi, kana Cikin bata girma yace. “Insha Allahu Hajiya za’ayi mata dinki dai-dai da zamani, kafun nan da sati biyu kuma zaku samu dinkin Insha Allah.” “Yauwa to Allah yasa, yanzu za’a baka size dinta ne, ko zaka gwada ta?” Mamyn ta fad’a tana me Kallon Jannart da kanta ke sunkuye. Kanshi ya ɗago ya ɗan kalli Jannart kana yace. “A’a basai na gwada taba, ai naganta kuma Insha Allah zanyi mata komai yanda ya dace.” Fahad din ya kare mgnar yana sake harhad’a kayan waje daya. Mamy kuwa kaita jinjina cike da gamsuwa tace. “To nawa ne kudin dinkin naka.” D’anjim Fahad din yayi, saboda shi kansa baisan nawa zaice ba, kasancewar kayan suna da yawa, dole sai ya nutsu ayi total tukunna. Fahimtar hakanne kuma yasa Mamy mik’ewa tsaye, tare da cewa. “Kad’an jirani inazuwa.” Kaitsaye sama ta haura, tana shiga cikin falon saman kuwa ta hango Rayyern zaune, ya daura kafarsa daya kan d’aya, Yayinda idanunsa kuwa ke lumshe, sai kuma goran swan dake rike a hannunsa. “Rayyern.” Mamy ta kira sunansa. Jin sautin muryar Mamynnasa ne kuma yasashi bude idanunsa. Tare da gyara xamansa yace “Mamy.” “Na’am tunanin mekakeyi?” Mamyn ta tambaya cike da kulawa. Kansa ya dan juya, kana cikin sanyi yace. “Babu komai Mamy, kawai dai nagaji ne.” “Da kyau. dama kudin dinki nazo karb’a awajenka, yanzu na kira taila kuma yazo, zai tafi da kayayyakin da muka sayo zaije ya dinkosu.” Mamyn ta fad’a tana me tsaresa da idanu. Wanda hakanne kuma yasashi shagwab’e fuska, tare da karyar da wuyansa gefe, kana akasalance yace. “Eyyah Mamy ai duk kun kwashemin y’an kud’ad’ena, kuma fa bana da wani kudi sosai, sannan ba atm dina yana hannunku ba naga shima yadda kuka yasheni kamar ba gobe.” Murmushi Mamy tayi, saboda tasan maganar cewa ma bashi da kudi ba gaskiya bane. Sai dai al'adarsa ce bai cika son almobazaranci ba, yana fadin hakanne kawai saboda kaucewa mgnar da suke ta lika mishi “Cash mukeso yanzu ba wai transfer ko wani abuba, tailor ne yazo, ko atm card din kakeso mu bashi yaje ya cire?” Cewar Mamyn. Rayyern kuwa da sauri ya kalleta tare da cewa. “Atm card na din zaku bawa wani, uhumm lallai Mamy abun ya magaga”. shi bawai kudin bane bayason bayarwa, a'a kawai dai shi ayanda aka lika masa auren ne baiso ba, saboda dama yasan dolene sai antakurasa akan hakan. Ita kuwa Mamy ido kawai ta zuba mishi. Mik’ewa tsaye yayi, tare da nufan d’akinsa, kaitsaye gefen bedside drawernsa ya nufa, Koda ya ya karasa bud’e drawern yayi ya d’auko, bandir din kudi, Rafa daya inda kuma kowani Rafa daya 50k ne. Juyowa yayi ya dawo falon, tare da damk’awa Mamyn kudin. Cikin shagwab’a da kuma turo baki yace. “Mamy gashi yanzu a barni in huta ko. Kuma a kamo min ATM na kin san Ramadan ba mutuncine dashi ba, in ya samu kudi.” Karb’an kudin Mamy tayi, batare kuma da ta sake ce masa komai ba, ta juya ta fice daga cikin dakin. Koda ta sauko kasa, duka 50k din ta bawa Fahad. Da ya tashi tafiya ne kuma ta had’ashi da Hadi ya kaisa har zuwa babban shagonsa. Sauran kayan da suka rage din kuwa, Mamyn da kanta ta Taya Jannart suka shigar dashi, can cikin bedroom din Jannart din. Cikin kulawa kuma haka Mamyn ta Taya ta suka shirya duka sauran kayan acikin wardrobe, kayan shafa kuwa anan kan dressing mirror Jannart din ta jere su. Bayan sun kammala komai ne kuma, suka sake dawowa nan cikin main falon. Zama sukayi inda Riyyam da Ramadan kuwa suka shiga sana’arsu ta buga game, ganin yanda Game din ke dadi ne kuma yasa, Jannart maida gaba daya hankalinta garesu. Mamy kuwa kallonsu take fuskarta d’auke da yalwataccen murmushi, saidai kuma ganin yanda hankalinsu duk ya tafi akan game dinne yasa, ta mik’ewa. Anutse ta nufi sashin Abba. Ahankali ta tura kofar dakin ta shiga, bakinta dauke da sallama. Abba dake rike da wani littafi na Tafsir, ne ya amsa mata sallaman tare da d’ago kansa ya kalleta. Itakuwa Mamy fuskarta dauke da murmushi ta k’arasa shigowa cikin falon, cikin muryar dake nuna tautasawa tace. “Allah yasa bankatseka daga abunda kakeyi ba.” Murmushi Abban yayi, cikin fadada fara’ar dake kan fuskarsa kuwa yace. “Sam baki katseni ba, kamar kinsan cewar kuma dama ina nemanki.” Abban ya fad’a yana me jawo wata leda dake gefensa. Mamy kuwa k’arasowa inda yake zaunen tayi, tare da durkusawa ta zauna agabansa. Abba kuwa Ledan dake hannunsa ya mik’a mata, atausashe yace. “Waya ce wannan d’azu na sayowa Jannart ita, ki kai mata, duk na sha’afa shiyasa d’azu da kika shigo ban baki ba.” Murmushi ne ya bayyana akan fuskar Mamy, cikin farinciki kuma tace. “Kai Masha Allah, amma gaskiya Jannart zataji dadin hakan, Allah ya kara bud’i.” Mamy ta fad’a tana amsar ledan. “Ameen.” Abban ya amsa, Yayinda ita kuwa Mamy ta mik’e, tana fad’in. “Bari nakai mata wayar na dawo.” Abban kuwa Kai ya jinjina alaman “To.” Haka Mamy ta fito daga sashin Abban fuskarta d’auke da murmushi, ta karaso nasu sashin. Har yanzun kuwa su Jannart na zaune. Akusa da Jannart din Mamyn ta zauna, kana cikin tausasawa tace. “Jannart ga sak’o inji Abbanku.” Jin hakanne kuma yasa Jannart, d’ago Kai ta kalleta, tare kuma dasa hannayen ta bibbbiyu ta karb’i ledan, da Mamyn ke mik’o mata. Ahankali ta warware ledan, tare dasa hannunta ta zaro kwalin dake cikin ledan. Idanunta ta d’an zaro waje, saboda Ganin kwalin waya da tayi, kirar Samsung Galaxy S21 ultra. “Wow Samsung galaxy S21 ultra, gaskiya Abba yanaji dake Aunty Jannart.” Riyyam-nsra ya fad’a, Cikin nuna jin d’adinsa. Jannart din kuwa, itama tsananin farinciki ne ya bayyana akan fuskarta, wanda saboda jin dadin kyautan da tayi ne kuma yasa, har hakwaranta suka bayyana alokacin da take murmushi. Cikin tsananin jin dadi, da kuma nuna yaba kyautar da Abban yayi mata tace. “Nagode sosai Mamy Allah ya kara arziki, ya kuma kara rufa asiri, Allah ya jik’an magabata.” “Ameen Ameen Jannart, ba komai ai duk yiwa kaine, yanzu ke tamuce komai mukayi miki basai kinyi mana godiya ba.” Mamy ta fad’a ciki kulawa. Jannart kuwa rungume wayartata tayi, cikin jin dadi da kuma duk’ar dakai tace. “Mamy nagode sosai, kuma inason yiwa Abba godiya.” “Bakomai Jannart, taso muje to sainayi miki iso zuwa wajennasa ko.” Cewar Mamy tana me mik’ewa tsaye. Ganin hakanne kuma yasa Jannart itama mik’ewa tsaye, tabi bayan Mamyn, Yayinda tabar wayar nata awajen Ramadan, wanda tuni harya cirota ya kunna, domin shikansa wayar tayi masa kyau. Mamy kuwa ahankali ta murd’a handle din kofar falon Abban, tare dasa kanta ciki, hakanne kuma yasa Jannart dake biye da ita, itama ta shiga bakinta dauke da sallama. Abba dake zaune kuwa, ganinsu ne yasashi fad’ad’a fari’arsa, cikin sakin fuska yace. “A’a Jannart.” Murmushi Jannart din tayi, tare da k’arasowa dan nesa da Abban, ta durk’usa tare da zube guiwowinta ak’asa, kanta ta duk’ar k’asa, cikin muryar dake nuna girmamawarta agaresa tace. “Abba naga waya, nagode sosai, Allah ya kara budi da arziki, ya jikan magabata.” “Ameen summa Ameen Jannart, idan kina buk’atar wani abu ki sanarwa Mamynku, kinji kada kiji nauyi ko kunyarmu, muba iya surukanki bane kawai mu matsayin iyaye muke a gareku.” Abban ya amsa, yana murmushi. Itama Jannart din murmushi tayi, tare da mik’ewa cikin sakin fuska, ta fice daga cikin dakin. Direct falo ta dawo, zama tayi akan sofa, tare da karb’an wayan nata ta soma dud dubawa. Sosai wayar tayi mata kyau, musamman da colourn wayan ya kasance bak’i. Hira suka dan tab’a dasu Ramadan, din kafun daga bisani ta tashi ta shiga ciki. Kasancewar tana danjin gajiya ajikinta ne kuma yasa, kaitsaye toilet ta wuce tayi wanka. Bayan ta fito ne kuma ta shafa, daya daga cikin mayukan da Mamy ta seyo mata, tare da binjikinta da Body spray mai dadin kamshi. Direct wardrobe dinta ta bud’e, daya daga cikin dogin rigunan da Mamyn suka sayo mata ta saka ajikinta, kamar kuwa tun can dominta akayi rigar, saboda yanda rigar ta zauna mata d’as ajiki. Dai-dai lokacin kuwa aka soma kiraye kirayen sallan la’asar, kasancewar kuma tayi alwala tun acikin toilet shiyasa kawai hijab dinta ta zura tare da tada sallan, bayan ta idar ne kuma ta kwanta. Acan cikin gidan kuwa Rayyern tunda ya shiga daki baifito ba, sai yanzu da yaje yayi sallan la’asar, still kuma sake dawowa gidan yayi, tare da komawa daki yayi kwanciyarsa, kasancewar yau din weekend ne shiyasa yakeson morewa hutunsa. Su Ramadan kuwa Koda sukayi sallan la’asar, cikin gari suka kutsa shida Riyyam. Haka dai sukayi wunin wannan ranar. Mamy na mai jan Jannart a jiki sosai, ba laifi kuma ta ɗan sake. Washegari Acan gidan Alhaji Idi Sale Dakata kuwa, tashin hankali kam sun shigesa k’arara sun wuni sun kwana cikinsa, musamman awajen Alhaji Idi Sale Dakata, dako zaman kirki ya kasa yi, hankalinsa amatukar tashe yake, badon komai ba kuwa, face sanin da yayi cewar, b’acewar Jannart babban tashin hankalinsu ne, haka kuma kaman wani kalubale ne dake fuskantarsu, wanda ba zasu tab’a iya tsaidashi ba kwana yayi baiyi bacciba a wannan daren. Mom kuwa tayi hawaye har saida idanunta suka bushe, gaba daya ta shiga damuwar rashin Ganin Jannart din, Yayinda duk wani zarginta ta d’aurashi akan Junaid, saboda sanin da tayi cewa, ba k’aramin aikinsa bane sace Jannart din. Abdull ma gaba daya haka yayi wuni jiya ya kwana yau kuwa tun da safe ya gayawa Yah Azeez abin da ake ciki. Abinda yayi masifar tada hankalin Azeez kenan. saboda b’atan ƙanaartasa ya daki zuciyarsa sosai. Haka kuma yau ɗin ma gari na wayewa Alhaji Idi Sale Dakata ya fita, da kansa ya dinga zaga gari waiko zai samu wani labari amma Ina. Daga karshe dai haka ya dawo gida zuciyarsa duk ba dadi. Har dare kuwa babu wani labari akan Jannart din. Yayinda Barrister Kabir kuwa ya buwayesu da zurya da tashin hankali. Acan gidansu Rayyern kuwa ana idar da sallan isha'i Ramadan da Riyyam suke dawowa gida. Mamy kuwa bayan ta kammala dinner, har d’aki ta kaiwa Jannart nata zaune ta sameta bisa sallaya tasa hannunta duka biyu ta tallabe h...! By *GARKUWAR FULANI* 11/16/21, 9:10 PM - Auntyna: Habarta tana lallatsa wayarta. Cikin sauri ta ɗago kanta jin motsin Mamy. Ita kuwa Mamy ajiye mata tray'n tayi gefenta tare da cewa. “Ki ajeyi wayarnan haka, kizo kici abinci. Ga tea kisha da zafinsa mgnin wannan sanyin da akeyi mana”. Cikin girmamawa tace. “Toh Mamy sannu ngd”. Kai ta jinjina kana juya ta fita. Kasancewar kuma yanayin garin ana busa sanyi mai masifar ratsa jikine, yasa su Mamyn ma basu wani jima afalon ba, suna kammala diner din, kowannensu ya wuce dakinsa. Rayyern kuwa dama ko saukowa k’asan baiyi ba, abincinsa ma sai Mamy ne tasa Riyyam ya Kai masa daga nan ya zauna gefenshi yanata zuba mishi surutu. Nan ma baiwani ci sosai ba sabida ya rigada yaci Chocolate ɗinsa shi yasa Riyyam din ya fita dashi. Duk da cewar yanajin bacci kuwa, bai kwanta ba harsaida ya motsa jikinsa, na kusan tsaeon 1 hour kafun ya kwanta. Cikin yan mintuna kadan kuwa bacci ya daukesa, saboda duk garin ya dauki sanyi sosai. Acan b’angaren Jannart ma, da wuri ta kwanta, tare da shigewa cikin lallausan blanket dinta, tana rik’e da wayarta kuwa bacci ya dauke ta. Washegari. Kamar kullum kuma Koda yaushe, dukansu atare suka dawo daga sallan Asuba. Inda suna shigowa kuwa Mamy ta tarbesu da hadin Coffee dinta, mai dadi. Bayan sunsha ne kuma duk suka miƙe suka wuce sama dan sake kwanciya, Mamy kuwa kaitsaye kitchine ta wuce. Tare da soma shirye shiryen had’a musu breakfast. Tana cikin aikin nata ne kuma, Jannart ta fito zuwa main falon. Sanye take da Hijab ajikinta, Jin motsi acikin kitchine dinne kuma yasa ta, nufar kitchine din kaitsaye saboda tana da tabbacin cewa Mamy ne. Mamy kuwa dake tsaye, Jin alaman tafiyan mutum ne yasa ta Juyowa da sauri, dai-dai lokacin ne kuma Jannart din ta k’araso bakin kofar kitchine din riƙe da mug din coffee da Mamy ta kai mata. Murmushi Mamy tayi, tare da fadada fara’ar dake kan fuskarta, atausashe tace. “A'a Jannart da sanyin safiyar nan me kika fito yi?.” Kai Jannart din ta jinjina, cikin girmamawa kuwa tace. “Mamy aikin zamuyi.” “Da wannan sanyin, a jeki kwanta?” Mamyn ta fada tana murmushi. “A'a Mamy aiki da yawa ai bari na tayaki.” Jannart din ta fad’a tana me k’arasa shigowa cikin kitchine din. “A’a Jannart ki bar aikin nan ba damuwa, jekiyi kwanciyarki kinga ana sanyi, kuma yau dinma bawani aiki mai wahala zanyi ba, abinci mai sauki zan dafa.” Mamyn ta fada mata haka cikin kulawa. Hakanne kuma yasa Jannart din ta d’an langwabar da kai, murya asanyaye tace. “Dan Allah Mamy ki bari na tayaki, banajin bacci shiyasa.” Murmushi Mamyn tayi, Ganin kuma Jannart din ta dage ne yasa ta, matsawa gefe tare da cewa. “To ga Irish patatoes nan ki fere, ni bari na k’arasa had’a wannan farfesun, Idan kika gama saiki soya mana chips ko.” Kai Jannart din ta jinjina, alaman to, Cikin nutsuwa kuma ta d’auki abun fere dankalin ta somayi. Cikin abunda bai wuce mintuna kad’an ba kuwa ta kammala, da kanta ta kunna gas, tare da soma soya chips din, suna dan hira da Mamy harta gama. Wanda zuwa lokacin tuni Mamy ta gama had’a ferfesun, harta fara soya kidney sauce din da za’aci chips din dashi. Ganin hakane kuma yasa Jannart, had’a musu had’adden sandwich, sai kuma green apple juice wanda acikin mintuna 15 kwata kwata ta kammala had’a shi. Sosai Mamy taji wani irin farinciki ya cika mata zuciya, musamman saboda yanda taga Jannart din na taimaka mata da ayyuka batare da ganda ba, aikin da zatayi acikin 2hour sai gashi, da taimakon Jannart sunyi shi, acikin awa daya da yan mintuna. Bayan sun kammala had’a breakfast dinne kuma, Jannart da kanta ta kwashe abincin ta jeresu akan dining table, Yayinda Mamy kuwa ta kwashi food flask din da aka sawa Abba abincin aciki Ta kai masa zuwa sashinsa, sai kuma nasu Baba Maud’o, wanda sai gari yayi haske za’a Kai musu. Duk wani abu da suka b’ata kuwa saida Jannart din ta wanke, bayan ta gama kimtsa komai ne kuma Mamy ta kalleta, murya atausashe tace. “Allah Ya miki albarka Jannart, yanzu kije kiyi wanka saiki zo muyi breakfast ko.” “To Mamy.” Jannart din ta amsa, kana anutse ta juya ta nufi part dinta. Koda ta shiga cikin bedroom dinta, kayan dake jikinta ta cire, wani sabon towel ta daura, kaitsaye kuma ta shige Bathroom tayi wanka da ruwa mai ɗan karen ɗumi sabida yanayin ciwonta yafi tashi a irin lokutan sanyin haka. Koda ta fito feshe jikinta tayi da turare mai sanyin kamshi, bayan ta murzawa jikinta mai ne kuma, ta shafawa fuskarta powder, sai kuma wani brown lipstick da ta gogashi sama sama akan labb’anta, dama kuma ba al’adarta bane yawan kwalliya. Wani dogon riga mai kaman Kimono ta zaro, tare da sakawa ajikinta, d’as rigan ya mata ajiki, kasancewarsa Maroon color kuma shiya kara bayyana kyau da hasken fatarta. Dogon gashinta ta tubke atsakiyar kanta, tare kuma da d’aukan mayafin rigar ta yafa akanta, wanda ya sauko harzuwa kan kirjinta. Alokacin da ta kalli madubi kuwa, murmushi tayi saboda ita kanta tasan tayi kyau. Agogo ta kalla, wanda yake nuna mata karfe Takwas harda wasu mintuna. Wasu lallausan takalma flat ta saka ak’afafunta, cikin yanayinta na nutsuwa kuma ta bud’e kofar dakin ta fice wayarta na rik’e a hannunta. Kaitsaye Falon Mamyn ta fito, fitowar nata kuwa yayi dai-dai da fitowar su Ramadan da Riyyam. Riyyam ne ya kalleta tare da k’arasowa, inda take Cikin sakin fuska yace. “Barka da safiya my kyakkyawar Aunty na, gaskiya Hamma Rayyern yayi dace, Yah Allah Nima kabani kyakkyawa mata.” Lallausan murmushi ta sakar masa, tare da yin k’asa da kanta, cikin dakekkiyar murya tace. “Barka da safiya Tiktoker Riyyam.” Dariya Riyyam din yayi, Yayinda Ramadan da sai yanzu yake k’arasowa, shima fadada fara’ar dake kan fuskarsa yayi, cikin kulawa yace. “Barka da safiya Aunty Jannart fatan kin tashi lafiya.” D’agowa tayi fuskarta dauke da murmushi ta kalli Ramadan din, kamar yanda yayi mata magana a mutunce kuwa haka itama ta mayar masa. Dai-dai lokacin kuwa Mamy ta fito daga sashin Abba. Riyyam kuwa Wayarsa ya zaro, tare da Kallon Jannart din, cikin kulawa yace. “Hamma Ramadan Aunty Jannart kuzo na d’aga mana selfie, Mamy kema ki shigo.” Murmushi duk sukayi, Mamy kuwa Kanta ta girgiza, fuskarta dauke da dariya tace. “A’a nikam kudai kuyi selfien ku.” Tsayuwa sukayi inda suka saka, Jannart din atsakiyarsu, Riyyam din kuwa shiya d’aga musu wayar yayi musu selfie, har kala uku. Bayan sun gama ne kuma Mamy tace. “To saiku zo muyi breakfast ko.” Kai suka jinjina dukansu, tare da karasawa dining table din suka zazzauna, Jannart da kanta tayi saving nasu. Bayan sun fara cin abincinne kuma, Riyyam-nsra ya ciro Wayarsa tare, da turawa Mamynsa hotunansu da sukayi yanzun, Ganin Mammyn bata online ne kuma yasa shi danna voice, batare kuma daya gama cinye abincin dake bakinsa ba yace “Good morning Mammyna, ga amaryar Hamma Rayyern dina kiganta, she’s so cute Mammy kisa mata al'barka, kiyi musu addu'a'n zaman lafiya da samun yan tagwayen yara.” Yana gama fadin haka yayi sending voice din, tare da ajiye wayartasa ya cigaba da cin abinci. Mamy da Ramadan kuwa murmushi kawai sukayi, saboda sun San yanda Riyyam yake matukar kaunar mahaifiyarsa sun fahimci duk motsinshi sai ya sanar mata. Jannart kuwa jin abunda Riyyam din ya fad’ane yasa ta sunkuyar da Kanta k’asa, acikin zuciyarta kuwa ta maimaita abunda Riyyam din ya fad’a. “Amaryar Hamma Rayyern kiyi musu addu'a'n samun yan tagwaye.” Ya tabbata kenan cewa, Dr. Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara ne mijinta. Saboda shine kad’ai Rayyern din da tasani acikin gidan, shi dinne kuma wanda suke cewa Hamma Rayyern shine kuma mutumin da baimin mgn in na gaidashi ma bai amsawa ko yaushe fuskarshi kamar ta Yah Junaid. Share duk wani tunanin dake zuciyar nata tayi, tare da ci gaba da tsakalan abincinta tana ci. Mamy kuwa ganin Rayyern baisauko ba, yasa tayin tunanin ko bacci yakeyi, shiyasa bata tura ankirasa ba. Atsanake haka suka kammala breakfast din, dukansu kuma cikin falon suka dawo suka zauna. Inda Riyyam-nsra keta basu labarai kala-kala, wanda duk mafi yawansu akan TIKTOK ne. Acan b’angaren Abba kuwa yana kammala yin breakfast d’insa, ya kimtsa tare da bud’e kofar falon nasa ta bangaren baya ya fice, hannunsa rike da key din mota, saboda akwai inda zasuje da Baba Maud’o. Fitowarsa compound din gidan kuwa, yayi dai-dai da shigowar motar Barrister Kabir. Ganin motar Barrister Kabir dinne kuma, yasa Abba sakin murmushi, tare da dan tsayawa. Barrister Kabir kuwa yana gama dai-dai-ta parking din motar ya bud’e murfin ya fito, Fuskarsa dauke da murmushi. Karasowa yayi tare da bawa Abban Hannu suka gaisa. Cikin sakin fuska Abban yace. “Barrister ashe kana tafe, sannu da zuwa, mu isa daga ciki.” Kai Barrister Kabir ya jinjina, tare da cewa. “To bari na gaisa da Baba Maud’o.” Ya k’are maganan yana me mik’awa Baba Maud’o hannu sukayi musabaha. Bayan sun gaisa da Baba Maud’on ne kuma Abba Yayi masa jagora zuwa cikin gidan. Ta babban kofar falon kuwa suka shiga, wanda dai-dai lokacin kuwa su Jannart duk suna zaune akan sofa, ita dasu Ramadan. Da Sallama abakinsu suka kutsa Kai Cikin falon. Jin sautin muryar Barrister Kabir ne kuma yasa Jannart saurin d’ago kanta. Ganinsa dinne kuma yasa Murmushin jin dadi bayyana kan fuskarta. Shima Barrister Kabir din murmushi yayi, tare da karasowa cikin falon ya zauna. Mamy kuwa da murmushi akan Fuskarta tace. “Barrister sannu da zuwa”. Cikin jin daɗi ganin yadda Jannart ta dan sake a cikinsu yace. “Barka dai Hajia ya bakuwarku?". Murmushi Mamy ta ɗanyi tare da cewa. “A'a ai mu bamu da bakuwa, mu duk nan yan gidane”. Murmushi sukayi baki ɗayansu. Ita kuwa Mamy juyowa tayi ta kalli Jannart daketa murmushi tace. “Jannart kawo masa ruwa ko.” Mik’ewa Jannart din tayi, Tana murmushi, taje ta kawo masa ruwa da kuma ragowan drinks din da ta had’a, harma da sandwich din. “Abbana sannu da zuwa.” Ta fad’a cikin tsananin farin cikin da ta samu kanta aciki, tare kuma da ajiye masa dan tray din da ta Hado ruwan agabansa. “Yauwa Jannart sannu.” Barrister Kabir din ya amsa yana murmushi, tare da juyawa suka gaisa da Mamy. Ramadan da Riyyam ne kuma suka gaidashi, fuska asake ya amsa musu. Jannart kuwa sabida tsananin jin dadin ganinsa, dan matsowa kusa dashi tayi, tare da manna kanta jinin hannun kujerar da yake zaune a kai, cikin yanayin rauni tace. “Abba Ina kwana.” Murmushi Barrister Kabir din, yayi cikin jin dadin yanda ya ganta yace. “Lafiya k’alau Jannatuwa, ya kwanan bak’unta.” Kanta tad’an sunkuyar kasa, fuskarta dauke da dan murmushi tace. “Alhamdulillah Abba, yasu Aunty Dijat Hafeez,da Hafeeza”. “Alhamdulillah suna lfy”. Ya bata amsa yana kallonta. Cikin nitsuwa tace. “Ayya Abba da kazo min da Hafeeza.” Murmushi Barrister Kabir din yayi, tare da dubanta yace. “Uhummm Jannart kenan, waya gaya miki yanzu, bayanni akwai wanda zai na kawo miki ziyara.” Fuskarta ta dan shagwabe, cikin sanyi tace. “Ayya Abba yanzu har Aunty Dijat dasu Hafeez babu mai zuwa, ba wanda zaizo wajena kenan.” Kai Abbansu Rayyern ya jinjina tare da cewa. “Shima ai zamu hanashi zuwa sai naga kin saki jikinki kin dena zama kina tagumi da zubda hawaye”. Da sauri tace. “Abba na dena”. Yar dariya sukayi kana Barrister Kabir yace. “Ato kin dai ji kam ko”. Turo dan karamin bakinta gaba tayi, wanda hakan yasa Mamy, Ramadan da kuma Riyyam duk sukayi murmushi. Adai-dai lokacin kuwa Rayyern wanda fitowarsa daga part d’insa kenan, ya soma saukowa daga kan steps din, cikin shigar wani lallausan yadi mai kalan mobile blue mai masifar taushi da sheki wanda akayi masa dinkin half jamfa da kuma, wando pencil, sosai kayan sukayi masa masifar kyau yanayin kalarsu ya kara hasko farar fatarshi ta fito ras, Hular damanga farace a amsa mai ratsin Nobel blue ɗin. Yayinda kwantacciyar sajen dake kan fuskarsa ke zuba sheki har wani dauke ido yakeyi. Sai takalmin toms Noble blue dake kamarsa. Kamshi kawai yake zubawa, yanayin yanda yake takun nasa kuwa cikin dan sassarfa alamun sauri yakeyi. Yayi kyau matuk’a, Daddaɗan kamshi da kuma jin sautin takusa ne kuma yasa, duk suka kalli steps din. Dai-dai lokacin kuwa ya gama sauk’owa. Ganin Barriter Kabir da yayi ne kuma, yasa shi ɗan yamutsa muskarshi. “Kai wannan menne irin mutum ne mai masifar nacin tsiya mutun kamar maye!. Wannan jaraba har ina, toh yanzu kuma Meya kawoshi da sanyin safiyar nan, kamar mai binmu bashi.” Yayi mgnar zuci tare da kwaɓe fuska yana mai k’arasowa cikin falon. D’an rusunar da kanshi yayi, cikin naɗe murya can ƙasa yace. “Barka da zuwa Barrister.” “Yauwa Barka Dr. Rayyern.” Barrister Kabir din ya amsa masa, cikin sakin fuska. Rayyern din kuwa dan matsawa gefe yayi, tare da zama akan kujera dake gefen Ramadan. Ganin hakanne kuma yasa Abba kallonsa, cikin kulawa yace. “Rayyern fita zakayi ne.” “Eh Abba”. Ya bashi amsa a takaici. Cikin tsaresa da ido Abba yace. “Ina zakaje”. Ya ƙare tambayar da alamun son cikekken bayani ina zaije me kuma zaiyi. Hannunshi ya ɗan d’ago. Tare da saidashi kan wuyanshi. Ya ɗan shafa wuyanshi har zuwa kan ƙeyarsa kana a hankali yace. “Inason zanje company ne, saboda P.A yamin waya, wai akwai wani inji da ba’a gane kansa ba, like dai baya aikin daya dace kana Engineer bello yana can yana jirana shima.” Kai Abban ya jinjina, kana cikin gamsuwa yace. “To Allah Ya bada sa’a.” Da “Ameen.” Ya Amsa. Barrister Kabir kuwa, ledan dake hannunsa ya mik’awa Jannart dake zaune akasa, cikin kulawa yace. “Jannart ga waya nan na sayo miki, akwai new sim acikinsa, bayan number na kuma bansa miki numbern kowa ba, sannan kada ki fara amfani da laptop dinki yanzu, kina dai charging nasa amma kada ki yi using dashi,domin hakan zai taimaka wajen gujewa duk wani shaida.” Karb’an ledan da yake mik’o mata din tayi, cikin jin dadi tace. “Nagode sosai Abba Kabir Allah ya kara budi. Amma fa jiya Abba ma ya sayamin sabuwar waya.” Ta kare maganan tana meyi masa nuni, da Wayar dake hannunta. Barrister Kabir din kuwa murmushi, yayi cikin jin dadi yace. “Masha Allah waya tayi kyau sosai, Allah yasanya al'khairi ya kuma saka da alkhairin.” Da “Ameen.” Duk suka amsa, saidai banda Rayyern wanda ya kawar da kansa gefe yana kallon Riyyam-nsra daketa lallatsa woya ya kifa kai har kamar zai hade goshinsa da wayar haka yasa ya tsareshi da ido yana nazartarsa. Dan ko kasa inda take dinma bai kalla ba sai dai yana jin amon muryarta. Barrister Kabir kuwa Mikewa tsaye, yayi tare da Kallon Jannart din, cikin tausasa murya yace. “To Jannart ni zan wuce, dama sakon da nazo kawo miki kenan.” Murmushi Jannart din tayi, cikin sanyi tace. “Abba ka gaida gida, ka gaishemin da Aunty Dijat dasu Hafeeza.” “Zasuji Insha Allah.” Abban ya fad’a, tare da juyawa yayiwa Mamy sallama. A gaida gida Mamyn tayi masa, sannan suka fice shida Abba. Ganin hakanne kuma Yasa Rayyern ma mik’ewa tsaye. “Rayyern katsaya kayi breakfast tukun kafun ka fita, gacan abinci akan dining.” Cewar Mamy tana me kallonsa. Fuskarsa ya d’an ya mutsa, tare da Kallon agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa, adan kasalance yace. “Mamy banajin yunwa sosai, kuma Idan na tsaya break zan makara, saina dawo kawai ki ajiyemin lunch.” Ya k’are maganan yana me nufar hanyar fita daga falon. Wanda hakan yasa Mamy da Ramadan suka Bishi da kallo, Mamy kuwa har cikin ranta tana mamakin, yanda Rayyern din yake tafiyar da rayuwarsa, gaba daya sam cin abinci bai damesa ba sai dai wasu lokuta isasshen lokacin zaman cinnema yake rasawa, shiyasa idan ya tara yunwar tofa in ya samu ya ya zauna zaici da dama. Rayyern kuwa Koda ya fito compound din gidan, ya samu tuni harsu Abba da Baba Maud’o sun tafi, Yayinda shima Barrister Kabir Yayi nasa tafiyar. Motarsa ya shiga, Yayinda Hadi ya jasa suka fice daga Cikin gidan. Acan falo kuwa, har Rayyern din ya fice Jannart bata iya sake dago Kai ta kalleshi ba, saboda tun Kallon farko da tayi masa, taji zuciyarta na bugawa, wanda kuma batasan dalilin hakan ba. Bayan fitan nasa ne kuma ta d’ago kanta tare da Kallon Mamy, ad’an ladabce tace. “Mamy yau me zamu dafa da rana.” Murmushi Mamyn tayi, kana atausashe tace. “A’a Jannart yau kam kihuta, ina nan zanyi komai, basai kin wahalar da kanki ba wannan fa aiki nane!!!.” “Mamy ba wahalar da kai bane zanyi, na saba ko agida ma duk ranar da babu aiki Ina taya Momy duk wasu aikace-aikace gida, Dan Allah Mamy ki bari Ina tayaki ki dena cewa na bari.” Jannart din ta fad’a cikin tausasawa. Hakanne kuwa yasa Mamy jin sanyi acikin zuciyarta, saboda tasan Itakam tayi sa’ar suruka. “Shikenan Jannart babu damuwa, na baki wuk’a da nama ki dafa mana duk abunda kikeso.” Mamyn ta fad’a cikin sakin rai. Riyyam nsra kuwa, cikin dokin cin abincin Auntyn tasa yace. “Yauwa Aunty Jannart muje kitchine din, ni yau da kaina ma zantayaki aikin, amma mezaki dafa mana me dadi haka?” Murmushi Jannart din tayi, tare da cewa. “Muje zaka gani.” Yanayin yanda tayi maganan tana me mikewa tsaye ne, yasa Riyyam din rufa mata baya suka shiga kitchine. Shida kansa yayi mata wanke wanke, Yayinda ita kuwa tayi greetting kwawa, saboda abunda ta tsara zata dafa musu shine. Coconut rice, and onion sauce, sai kuma gas meat mai kayan kamshi, da salad cream, ab’angaren drinks kuma, Banana Milk shake zatayi musu. Anutse ta fara aikinta, Yayinda Riyyam keta yi mata hira, daga gefe guda kuwa yana tayata da y’an wasu ayyukan, kama daga kan yanke yanke zuwa yan kananun abubuwa masu sauk’i dai. Haka dai sukayi aikin cikin nutsuwa, almost 1hour kuwa ta kammala komai, tare da jeresu akan dining table. Gaba d’aya gidan kuwa haka ya gauraye da kamshin girkinta. Bayan sun kammala jere komai a dining table dinne kuma, ta kunna boner tare dasa turaren wuta mai dadin kamshi. Mamy kanta ta yaba da aikin Jannart din, bayan sunyi sallan azahar ne kuma, suka zo kan dining table din sukaci abincin. Saidai kuma Jannart din bata wani ci abincin sosai ba, ayanda Mamy ta fahimta kuwa shine, Jannart din irin Rayyern ce, kwata kwata basu dauki cin abinci serious ba sai dai tasan shi Rayyern in ya zaunawa abincin bai mishi da wasa ko dan yakan dade baici bane, ta lura ita kuma Jannart irin mutanen ne da zasuci kaɗan yanzu anjima su kuma cin kaɗan. Bayan sun kammala cin abincinne kuma suka dawo falo, hira suka Dan tab’a, lokacin da Ramadan da Riyyam suka fita yawo ne kuma, Jannart ta tashi ta koma side dinta, tana kwanciya afalonta kuwa bacci ya dauke ta. A can gidan Alhaji Idi Saleh Dakata kuwa. A gajiye ya dawo gida, daga Tashar Arewa 24 TV da yaje, yanzu ya samu MD da kansa ya mishi bayanin ɓacewar Jannart da kuma hukuma da suka shiga lamarin kana yasa gidajen Rediyo su cekinta su kuma ya bawa gidan tv nasu cekiyar gaggawa. Daga nan kuma asibitin Dr Lukman ya wuce inda anan sukayi tattaunawa mai yawa kana ya nufo gida. Da sauri Mom tabi bayanshi. Tana cewa. “Alhaji anji lbrin Jannart kuwa?”. Da sauri ta matsoshi ganin yadda ya dafe kanshi da hannaye bibbiyu yana mai jujjuya kanshi. Kana ya tafi lu alamun zai fadi. Cikin tsananin tashin hankali da kidima Mom ta saki ihu tare da isowa gareshi ta tallabeshi murya na rawa take kwarmawa Abdul kira. da gudu Abdul ya shigo cikin tashin hankali tace. “Abdul kira min Barrister Kabir Abbanku kace Daddynku ba lfy”. Kafin ta ƙare mgnar kuma Alhaji idi Saleh Dakata ya sake gaba ɗaya naushin ya jata suka tafi kasa bisa carpet. Ganin haka ne yasa Abdul gigicewa tare da zaro wayarsa ya kira Barrister Kabir. Wanda shi kuma lokacin ya fito daga gida shi kenan. Koda Abdul ya gaya masa abinda ke faruwa. A firgici ya dauko ya wuce asibitin Dr Sajo ya dauko shi. A gidan Alhaji Idi Saleh Dakata'n kuwa, suna cikin gigin suka jiyo muryar Dr Lukman yana sallama hakane yasa Mom sakin dogon numfashi tare da cewa. “Dr ka shigo, kayi sauri shigo ka taimaka mana Alhaji zai fadi”. Jin hakane yasa Dr Lukman kutsa kai cikin main falon nasu da hanzarin. Daga nan shida Abdul suka tallabeshi suka a mota suka wuce asibitin Dr Lukman din. Suna tafiya ba jimawa. Barrister Kabir da Dr Sajo suka iso. Bayan Ashiru ya musu bayanine suka nifi asibitin Dr Lukman ɗin. A nan gidansu Rayyern kuwa. Bacci Jannart tayi sosai dan Koda ta tashi tayi sallan la’asar sake komawa tayi ta kwanta. Ahaka dai har magriba. 9:30 pm dai-dai ya shigo gidan, wanda kuma tun fitan da yayi da safe sai yanzu yake shigowa. Da sallama abakinsa ya tura kofar main falon ya shigo. Jin da yayi ko ina shiru babu alaman motsin kowa ne, yasa kaitsaye ya wuce sama, saboda yasan zuwa yanzu su Mamyn nasa sunyi bacci. Yana haurawa saman kuwa, anan cikin falonsu ya samu Ramadan da Riyyam, ko wannensu rungume da waya ba abunda sukeyi sai chatting. Kana ga TV a kunne tashar Arewa 24 TV. Yayinda su basuma san me akeyi a TV'n ba. A hankali ya ɗan juyo ya kalli TV'n sabida ganin program ɗin da Jannart tayi dashi ake haskawa. Idanunshi ya zubawa rubutun dake tafiya kasan hotonsu mai motsin da yake fuskar TV'n. *Daya daga cikin ma'aikatan wannan ma'aikata Mai gabatar da shirin Baƙon mako mai suna Jannart idi Saleh Dakata ta bata tun daren jumma'a, kana har yau babu ita babu lbrin ta, a madadin tashar Arewa 24 TV muna cekinta Tata ga duk wanda Allah yasa ya ganta ko yaji lbrinta, ya taimaka ya nemi ɗaya daga cikin wadannan numbers din... akwai tukuici mai girma ga duk wanda ya kawo ta ko lbrinta kimanin Naira million 5. Muna addu'a Allah ya baiyana ta ya kuma bawa mahaifinta lfyar jikinsa wanda sanadin batanta ya tada masa ciwonsa* Wani irin numfashin ya fesar a hankali tare da mai-maita karanta rubutun a karo na barkatai. Can cikin zuciyarsa yake nazari. “Tabbas akwai gadar zaren da ake sakawa, wanda ake neman mai ruftawa a ciki. Dole suna da manufa a kaina. Amman manufar Barrister Kabir tafi ta kowa girmama a kaina, tabbas ba haka kawai ya zaɓeni ya lika min wannan mayataccen aurenba, nasani haƙƙun nasan akwai wata boyeyyiyar manufa da niyarsa ta liƙamin auren ya kawo diyarsu ya ajiye mana a cikin gida.” Idonshi ya lumshe tare da buɗe kana yaci gaba da nazari. “Wani wasane suke son bugawa dani, yarsu ta zamo yar leken asirinsu kenan itace zata basu duk wata damar cimma nasarar turani kan gadar zaren da suke saƙamin ko meye. Itace mai iya buɗe musu kofa ta su shigo rayuwata. Meyasa Abba na bai gane hakabanba ya akayi Abba na yayi saurin yarda dasu?”. Numfashi mai nauyi yaja ya sauƙe tare da yin kwaffa. Wanda sanadin hakane su Ramadan suka gane ya shigo. Kallonsu kawai yayi tare da amsa sannu da dawowan da sukeyi masa. Idonshi ya kuma maida kan TV inda ake haska fuskarsa data Jannart. Batare daya ce musu komai ba, ya wuce zuwa dakinsa. Yana shiga ya soma rage kayan jikinsa, tare ci gaba da nazari. “Me Barrister Kabir yake nufi dani? Alhaji idi Saleh Dakata dai ɗan uwansa ne uwa ɗaya uba ɗaya. Kana ita kuma wannan Jalila ne ko jalilu ne, yarsa ce ta cikinsa. Haƙƙun Barrister Kabir medani tsanin hawa yake son yi!.” A hankali ya tura ƙofar shiga toilet. A fili yace. “Me yasa Abbana ya yarda dashi, ya akayi yayi saurin gamsuwa dashi. Bayan kuma shine ya dauramu kan turbar kebanta kai da mutane da gudunsu da rashin yarda dasu. Sanadin haka muka taso ba abokai ba kawaye bama sakin jiki da kowa, daga ni har Ramadan, sabida horaswar Abbanmu ta gudun mu'amala da mutane, Yasha cemin. Rayyern ɗan adam abin tsorone kada ka yarda da kowa, mutun duhun darene Allah kadai ke saninsa! To ya akayi yayi saurin yarda da Barrister Kabir? Tabbas shima Abba na akwai manufar yardar sa”. A hankali ya ɗago ƙafarsa ta hagu ya sa cikin Bathroom din. Hannunshi duka biyu yasa ya matse kanshi da ƙarfi. Dan yadda yakejin kansa na jujjuyawa nazarurrukansu na hautsinewa suna haɗe zaren suna curkudeshi. Duk da azabebben sanyin da akeyi. Ruwan sanyin ya sakarwa kansa. Sabida jin kan nashi ya fara sarawar. Bayan ya fito ne kuma, ya shirya kansa cikin wasu tattausun kayan bacci. Wondon iya guiwa rigar irin mai hular nan. Fridge d’insa dake cike da kayan ciye ciye ya bud’e, Apple goran swan water da kuma ledan diary milk ya d’auko. Tare da komawa kan gadonsa ya zauna cikin sanyi yace. “Ta yaya zan yarda da ita, a wani sashin ma zan ajiyeta bayan nasan ita ɗin makamin magautanane sun turora cikin rayuwata ne dan cin nasarar kansu a kaina. Meyasa Abba na bai fahimci hakaba. Itama da mugun nufinta a ranta fa, iyayenta zatayiwa aiki”. Yayi mgnar yana mai ajiye Jannart a sashin da yake ajiye magautansa a cikin zuciyarsa da rayuwarsa da waɗanda yake zargi. A hankali ya jujjuya kansa. Kana ya ɗan gatsi apple din ya soma ci bayan ya gama ne kuma, ya daura chocolate d’insa da ruwa akai. Numfashi ya ɗan fesar Kana ya kwanta yana mai nazari. A nan asibitin Dr Lukman kuwa. Barrister Kabir ne da Mom ke zaune gaban table ɗin Dr Lukman. “BP'nsa ne ya hau sama sosai, sabida tashin hankali rashin yarsa. Kana kuma rashin baccin da baya samun yi, sai nazari da damuwa yasa zuciyarsa ta kumbura.” Dr Lukman ya ƙare mgnar yana mai yin ƙasa da idonshi sabida wani irin tsareshi da ido da Barrister Kabir yayi. Cikin zubda hawaye Mom tace. “Innallahi wa innailaihi rajiun, zuciyarsa kuma ta kumbura?”. Cikin murje ido yace. “Hakkun kuwa, sabida damuwa tayi mishi yawa, Jannart ta bata kana shima Junaid yana hannun hukuma, wanda kuma ƙaninsa uwa ɗaya uba ɗaya yasa aka kama ɗan nashi da wanne abu ɗaya zaiji?”. Cikin haɗe fuska Barrister Kabir yace. “Shine yace ma ni na kai Junaid hannun hukuma?”. Da sauri ya girgiza kai alamun a'a Miƙewa tsaye yayi tare da cewa. “Toh ka tsaya iya matsayinka, ka tabbatar da abu kafin kayi mgn”. Yana faɗin haka ya mike ya fita. Dakin da aka kwantar da Daddy ya nufa a bakin ƙofar shigowa yayi kiciɓis da Dr Sajo. Hannunshi Dr Sajo yaja kana suka juya suka nufi parking lot. Cikin motar Dr Sajo suka shiga. Wani dogon numfashi Dr Sajo ya sauƙe kana a nitse yace. “Dr Mina da Dr Lukman yayi aikin duba Alhaji tare da ita, ƙanwatace cousin sister na. Na samu duk bayanin komai a wurinta”. Da sauri Barrister Kabir yace. “Dan Allah menene gskyan abun dake damun Yayana?”. Kai Dr Sajo ya jinjina tare da yiwa Barrister Kabir duk abinda Dr Mina ta sanar masa... A nan Office din din Dr Lukman Kuma Barrister Kabir na fita, itama Mom ta fita. Ta koma wurin mijin nata. Ba ji mawa Barrister Kabir ya dawo akan dole a sallami yayanshi zasu sauya asibiti. Kuma dole haka akayi. Aka medashi asibitin Dr Sajo. Washegari. Kamar dai jiya yaudinma Jannart ce ta-taya Mamy duk wasu aikace-aikacen gida, bayan sun kammala ne kuma suka zauna suna dan tab’a hira. Kasan cewar yau Monday ne tushen aiki. Yasa tuni Ramadan ya tafi. Riyyam-nsra kuma Ahmad yazo sun tafi gidan Malam Mai-nasara. Takwas saura kwata. Ya sauko falon. Cikin shigar Suit red color masu masifar kyau. Hannunsa riƙe da wayarsa yana mgn. Cikin sauri ya kalli Mamy tare da cewa. “Mamy na tafi”. Kafin ma tace wani abu tuni ya nufi hanyar fita. Kawai sai ta bishi da ido. Har ya fita kuma sai ya juyo ya leƙe fuska ya kwaɓe tare da cewa. “Mamy na tafi”. Murmushi tayi dan dama tasan tabbas zai juyo muddin batace mishi. Allah ya bada sa'a yayi muku al'baka. Cikin sauri ya kuma cewa. “Mamy zan tafi”. Fuska ta tsuke tare da cewa. “Ka dawo kayi breakfast”. Cikin kwaɓe fuska yace. “Mamy sai na dawo, kinga Ramadan keta kirana, wai akwai matar da aka kawo haihuwa yaƙi kuma dole sai anyi mata CS, dan Allah Mamy ce Allah ya bani Sa'a yayi min al'barka Please Mamy say something". Ta sani in dai yace bazai ciba ko ta matsa mishi bazaici yadda take sonba. Hakane yasa tace. “Toh Babana Allah ya bada sa'a ayi aiki lfy rabbil yayi maka al'barka”. Da sauri ya juya yana mai cewa. “Yessss Mamy Amin Amin”. Da ido ta bishi tana murmushi tana tuno wasu abubuwa masu tarin yawa. Jannart kuwa dake cikin Kitchen tana wonke-wonke rumtse idanunta tayi tana mai jin yadda bugun zuciyarta ke harba a duk sanda sautin muryarshi ya sauka kan kunneta. Duk da bata hangoshi ba, ita robonta da shima tun jiya da safe zuwan Barrister Kabir nanma bataga fuskarsa ba, kuma haka yanzuma. Sai dai yanayin alaƙarsa da mahaifiyarsa yasata jin maraicin rashin tata mahaifiyar da jin bege. Domin a gidansu babu irin wannan tarbiyar shaukin mahaifa da Kekkyawar shaƙuwar. Haka dai taci gaba da aiki ita da Mammynsu. Alhamdulillah komai yana tafiya dai-dai, domin Jannart ta samu nutsuwa acikin gidan. Kasancewar yau tsawon kwananta biyar kenan da zuwan ta gidan. Akullum kuma sabonsu k’ara-k’arfi yake, da Mamy, Ramadan da kuma Riyyam, harma kuma Abba da take samun kulawa awajensa sosai ta kuma take jin daɗin zama dasu. Takan kalli Mamy matsayin Mom da Aunty Dijat dan duka biyu ta meye mata gurbinsu. Abba a matsayin Daddy kana Riyyam-nsra ya meye mata gurbin Abdul Ramadan kuma gurbin Yah Azeez yayinda tasa a ranta cewa wato duk inda kake a duniya sai ka samu kalubalen makiyin dan gashi nanma Rayyern ya zame mata gurbin Yah Junaid a cewarta kenan. Acikin kuma way’annan kwanki biyar din, sau biyu tak kawai Jannart da Rayyern din suka ga juna. Tun gaisuwar da tayi masa ranan farko kuwa, wata magana bata sake hadata dashi ba tunda bazai amsa mataba a zatonta bazata kara gaidashi ba Dan matsalar kunneta yasa bataji amsawar da yayinba. Rayyern kuwa kasancewar yau laraba, tun sassafe ya fita, saboda akwai wasu patients da suke da appointment din ganinsa. Bashi ne ya dawo gidan ba kuwa sai 2:00 pm, inda ya tsaya yayi sallan azahar d’insa a Darul Hadith Masque. Yanzun kuwa Shigowarsa Cikin gidan kenan, hannunsa rike da suit dinsa, ya murda handle din kofar falon ya shiga bakinsa dauke da sallama. Mamy dake zaune ne ta amsa masa. Ganin kuma yanda yake da'alaman gajiya atattare dashi ne yasa ta zuba masa ido. Shikuwa k’arasowa cikin falon yayi, tare da zama akan kujera, idanunsa ya lumshe, kana cikin sigar shagwab’a da bayyanar tarin gajiya da yunwar dake cinsa yace. “Mamy nagaji, kuma yunwa nakeji sosai.” Ya ƙare mgnar yana juya kwayar idanunshi da sukayi jazir. Ido Mamy ta dan zuba mishi cikin tausayawa tace. “Badole kaji yunwa ba Babana, kwata-kwata bakason cin abinci, saika wuni ka kwana batare da kasa abincin kirki acikin ka ba sai kayan zaki da Fruits.” Mamyn ta fad’i haka tana me K’are masa kallo, saboda har wani dan rama taga yayi, saboda rashin cin abincin da bayayi akai akai dan abin nashi ya karune tun zuwan Jannart gidan. “Kazo kaci abinci.” Mamyn ta fad’a cikin kulawa. Shikuwa Rayyern idanunsa ya d’an bud’e akasalance yace. “Mamy me aka dafa.” “Coconut rice, with onion sauce, gas meat, and salad cream, sai kuma milk shake, and plaintain da kuma fish.” Mamyn ta bashi amsa atakaice. Fuskarsa ya d’an kwab’e, tare da rausayar da kansa gefe, cikin sanyi yace. “Shike nan Mamy ku kullum abu ɗaya. Kwananfa naga shi kukayi kukayi taci ba sauki”. Da sauri tace. “Yoh ya mana daɗi Ramadan da Riyyam-nsra sukace a sake yinshi, nima kuma naji daɗinsa”. Cikin tarin gajiya yace. “Mutane ayi ta sasu tsatsagar shinkafa ba sauki kamar tsuntsaye. Gsky ni bazan ciba, abu mai dan ruwa ruwa nakeso, banason abinci mai nauyi.” Jujjuya kai Mamy tayi tare da cewa. “To Bari ayi maka.” ta fad’a tana me mikewa tsaye. Shikuwa mikewa yayi, tare da cewa. “Mamy bari naje nayi wanka, Please a gama da wuri.” “To.” Mamyn tace masa, Yayinda shikuwa kaitsaye ya haura sama. Mamy kuwa direct falon Jannart ta nufa. Cikin sa’a kuwa anan cikin falon ta sameta tana game a wayarta. Ganin Mamyn ne kuma yasa ta tsaida Game din, tare da sakin murmushi tace. “Mamy sannu da shigowa.” “Yauwa Jannart Sannu, game kikeyi ne.” Mamyn ta tambaya cikin kulawa. Jannart kuwa murmushi tayi, tare da ajiye wayan, cikin girmamwa tace. “Eh Mamy, akwai abunda zanyi miki ne?” “Kwarai kuwa Jannart, mijinki ne ya dawo wai, yunwa yakeji kuma abu mai dan romo-romo yakeso, Dan Allah ko zaki dan shiga kitchine kisama masa abu mai sauki.” Mamyn ta fad’i haka cikin tausasa murya. Jannart kuwa jin ance mijinta ne yasa ta sunkuyar da kanta k’asa, cikin wasa da y’an yatsun hannunta tace. “To Mamy bari na dafa masa.” “Yauwa Jannart Allah dai ya miki albarka.” Mamyn ta fad’i hakan, tare da juyawa ta fice daga cikin dakin. Ita kuwa Jannart a hankali ta miƙe cikin nitsuwa ta rufa mata baya. Koda suka fito falon kitchine Jannart din ta wuce, tare da soma kokarin had’a masa abunda xaici. Hearty Chicken Gnocchi soup ta had’a masa, wanda yaji kayan had’i da milk. Bayan ta kammala ne kuma ta juyesa, acikin wani Dan madaidaicin glass bowl maikyau. Tare kuma da had’a masa spearmint tea ta juyesa acikin wani cup mai kyau. Wani tray na glass ta dauka tare da jere masa abincin akansu. Anutse ta fito daga cikin kitchine. Din tare da ajiye tray din akan dining. Dai-dai Ta juya zata sauka akan dining table din ne, shi kuma sai gashi ya na sauk’owa, Inda ya sanja shigarsa cikin wani riga da wando masu masifar taushi farare kala-kala. Ganinsa ne kuma yasa Mamy dake zaune afalon tace. “Babana harka fito.” Kansa ya jinjina tare da shafa cikinsa, ashagwabe yace. “Eh Mamy abinci.” Murmushi Mamyn tayi, tare da cewa. “Abincinka is ready Jannart sa masa abinci yaci.” Dan tasan ba karamar yunwa ke azalzakarsaba tunda yaketa damunta da yunwa-yunwa. Ita kuwa Jannart dake kokarin komawa dakinta Jin abunda Mamyn ta fadane yasa ta tsaya. Shikuwa Rayyern batare ma daya kalli Inda Jannart din take ba, yaja daya daga cikin kujerun dining din ya zauna. Jannart kuwa Kanta ta sunkuyar, tare da juyowa a hankali ta fara ta kowa atsanake ta nufi dining table din. Isowarta kan dining dinne kuma yasa, tayi kasa da kanta kana cikin sanyin murya tace. “Sannu da dawowa.” “Uhum.” Ya amsa mata atakaice tare da kawar da kansa gefe, acikin zuciyarsa kuwa cewa yayi. “Kowa yayimin sannu da dawowa, amma ita sai yanzu zata wani yimin iyayi munafuka yar leken asiri.” Jannart kuwa plate ta d’auka, atsanake ta zuba masa. Hearty chicken Gnocchi soup din, wanda tana bude bowl din kamshin nama da milk din ya daki hancinsa. Zuba masa tayi tare da tura masa plate din gabansa, kana ta ajiye masa cup na Spearmint tea din agefensa. Juyawa tayi atsanake ta bar wajen. Shikuwa Rayyern numfashin ya ɗan shaƙar spoon ya dauka, ya ɗan jujjuya sabida yadda yake ta tururi alamun yanzu aka gamashi. Yasan da zafi amman yunwar dake zakularshi barata barshi ya kira ya huceba. Sa spoon din yayi tare dayin bismillah ya soma Kai gudan Tsokan Kazan bakinsa. aloman farko kuwa dadin abincin ya ratsa sa, wanda hakan yasa shi sauƙe numfashi tare da bude cikinsa ya fara ci duk loman da zaiyi kuwa saiya had’a da ruwan cikin hearty chicken din. Kana kuma time to time Yake zukan spearmint tea din, wanda yaji kayan kamshi, spearmint, and Lemongrass leaves, pinch of cloves and masoro, A piece of ginger, sai kuma sugar da ta saka mai dan dama aciki. Sosai spearmint Tea din yayi masa dadi. Hakan kuwa shiyasa yaci abincin sosai, irin cin daya jima baiyi ba, bayan ya kammala cin na plate din ne ya jawo yar kular da nufin ƙarawa sabida. Bai gama jin ya kai dai-dai gejiba. Wani ɗan guntun tsaki yaja tare da ture kular. Baki ya ɗan tura tare da cewa. “Mamy”. Dariyar dake son tsubuce matane ta danne tare da cewa. “Na'am”. Cikin hararan hanyar kofar dakin Jannart ɗin yace. “Mamy ni ban koshi ba”. Cikin dariyar yadda yake hararar hanyar da Jannart ɗin tabi Mamy tace. “To kaine ai Babana sai kayi ta tara yunwa in ka tashi ci in ba mutun yasan yadda kakeba sai yace kai ɗan boll ne ko pollo dan sune masu yawan cin abinci”. Fuska a kwaɓe ya mike ya tashi ya tafi wajen Abba. Cikin danne dariyar dai Mamy tace. “Yauwa to in kaje wurin Abbanku watakil ka samu wani abu dan na mishi gashi ɗazu”. Shi dai baice komaiba ya tafi yana tura baki har ga Allah bai koshin ba Koda yaje a falo ya samu Abba. Yana cin gashin gargajiya na jan nama. Zubawa a plate Abban yayi tare dasa mishi yajin. Kana ya miƙo mishi. Amsa yayi tare da gyara zamanshi. Da kallon flaks haka yasa Abba ya gane abin da yakeso. A cup din da yasha tea ya haɗa mishi. Sokan naman ya kai bakinshi kana a hankali ya tauna tare da kiransa da ruwan tea din. Shi kuwa Abba Qur'anin hannanshi yaci gaba da bita. Sabida yasan idan yana cin abinci muddin ya tara yunwa to bai mgn kuma baya son kallo, dan cine zaiyi sauri-sauri sai ya kauda yunwarsa. So haka yasa ya kauda kanshi daga gareshi. Shi kuwa cikin 13mnt ya cinye naman da Abban ya saka mishi tare da shanye shayin. A hankali yayi gyatsa tare da cewa. “Alhamdulillah Abba na koshi”. Kai Abban ya jinjina kana sai da yaje kan aya kana ya datse tare da shafa addu'a ya rufe Kur'ani. Sai lokacin yace. “Abba Barka da dare”. Murmushi Abba yayi kana yace. “Barka dai ka dawo lfy”. Bayan sun gaisane kuma ya gyara zamansa, tare da fuskantar Abban kana a nitse yace. “Abba daya daga cikin ingines dinmu fa yayi kadan, dole sai ansanja ankawo babba, To yanzu dai munyi magana, da wanda nasaya kayan awajensa, akwai wani babban ingine, amman dole zanje China na sayo". Cikin gamsuwa Abba ya jinjina kai. Dan shima da yaje Engineer Bello ya mishi bayanin komai. Shi kuwa Rayyern a nitse yaci gaba da cewa. “Ina tunanin zuwana China kwanan nan in sha Allah, dan shine babban abinda zai hana a fara aikin.” Kai Abba ya jinjina, kana cikin gamsuwa yace. “Masha Allah to yaushe ne zakaje china’n?” Sake gyara zamansa yayi tare da tankwashe kafafunsa, cikin nutsuwa yace. “Maybe next month Insha Allah, saboda Idan na tashi booking flight, kawai Zanyi kasancewar dama akwai sauran visa na.” Kai Abban ya jinjina kana cikin gamsuwa yace. “Masha Allah Allah Ya taimaka.” “Ameen.” Rayyern din ya amsa nan dai sukaci gaba da hiransu, kafun daga bisani ya tashi ya tafi. Alhamdulillah Alhaji idi Saleh Dakata kuwa jiki da dan sauki tuni ma an sallameshi ya dawo gida. Sai dai yana cikin tashin hankali. Junaid kuwa yana hannun hukuma. Akwana atashi ba wuya, domin yau satin Jannart biyu, agidansu Rayyern din. Abubuwa suna tafiya yadda ya kamata akan shirin kowa. Zuwa yanzu Jannart ta dan saki jiki sosai dasu Mamy da Riyyam-nsra da Ramadan. Yanzu ma zaune suke ita da Mamy acikin falon. Yayinda Jannart ɗin ke zaune akan kujera 3seater. Don lokacin ta gama sawa Mamy lallen gargajiya a ƙafarta. Mamy kuwa tana Dan nesa da ita kan 2 seater. Hira suke dan tab’awa kadan kadan. “Yau kuma har yanzu su Ramadan basu dawo ba. Su dai sun suka samu ba aiki to sai yawo kamar ababen hawa”. Kai ta dan dago ta kalli Mamy tare da yin ɗan murmushi kana tace. “Uhum ai dama tun jiya suke cewa yau jumma'a, tun daga masallaci kai tsaye min jibir zasu wuce”. Kwaffa Mamy tayi tare da buɗe baki zatayi mgn sai kuma tayi shiru tare da zubawa ƙofar shigowa falon ido. Ahankali ya turo k’ofar falon, tare da jefo k’afafunsa, dake wani irin b’ari. Ganin alamun bude kofar falonne kuma yasa, Mamy saurin juyawa da kai saboda bataji anyi sallama ba. Idanunta ta dan zazzaro waje, Cikin yanayin mamaki da kuma tsoron, yanayin da taga Rayyern din aciki wani irin yanayin dake nuna ba lfy ba. Rayyern kuwa, da gaba daya yakejiin duniyar na juya masa, Yayinda da hannunsa duka biyu ke dafe da mararsa. A hankali cikin tsananin wahala yake daga ƙafarsa. Gaba daya duk jikinsa rawa yake, ga kuma idanunsa da suka rufa, saboda tsabar azaban da yakesha duhu ya gama rufe ganin ko Kallon gabansa bayayi. Cikin wani irin yanayin da ke nuna baisan inda Kai da hayyacinsa yake ba, ya tunkaro cikin falon da salon tafiyarsa, Wacce ke nuna galabaitansa. Cikin tashin hankali Mamy ta miƙe tsaye. Jannart kuwa ido ta zubawa Mamy ganin yadda take kallon hanyar shigowa ne yasa ta juyo kanta itama. Shi kuwa Rayyern Isowarsa tsakiyan falonne kuma yasa, shi fad’a kan 3seater inda Jannart ke zaune wanda shine kusa da mashigar falon. Saboda yanda idanunsa suka daina ganine kuma yasa bai san cewa da Jannart din awajen baiyi ba sabida baya ganin komai sai duhu. Yanayin yanda ya fad’a kan kujeranne kuma yasa, kansa ya sauk’a akan cinyarta. Arazane ta shiga kallonsa, Yayinda Mamy ma cikin tashin hankali ta taso tayiyo Kansa tana kiransa a firgice. “Rayyern Rayyern!! Innalillahi wa inna Ilaihirraju’un, Yau kuma ciwon cikin kane ya tashi, Rayyern bud’e idanunka.” Mamy ta fad’a cikin tsananin tashin hankali da gigita gaba ɗaya jikinta tsuma yakeyi. Saidai Ganin da tayi kamar Rayyern din baya motsi ne yasa, cikin yanayin kidima da tsananin tashin hankali ta juya bayanta tare da fara kiran. “Ramadan!!!”. Gaba ɗaya tama mance baya gidan. Shi kuwa Rayyern wani irin azabebben numfashin yaja tare da cusa kanshi cikin j...!!! *Littafin TUBALI na kuɗine ki biya ki karanta cikin salama special Group 1k ne karamin group 500 kacal babancinsu yawan posting ne, 0661110170 GTBank AISHA GARKUWA ALIYU sai ki turo min shaidar biyanki ta whatsApp number na 09097853276, in baki da halin turawa ta banki to ki sayi katin MTN ki copy number's din ki turo minshi ta WhatsApp* *Albishirinku! Ma'aurata, GA GARKUWAR KU nan tafe muku da tsarabobi na musamman gareku ma'aurata daga cibiyar mgnin mata mai taken GARKUWAR MA'AURATA* NI DAI AYSHA ALIYU GARKUWA. Ina matukar mamakin wani irin lokaci da ya riske mu mai wahalallan fassara. Kullum dai magana daya ce, akan ma’aurata, fada, rashin jituwa, mutuwar aure, akan kuskure kalilan, rashin kula, rashin yi wa juna uziri. Toh wai duk me ya janyo hakan? Na zurfafa a tsananin tunani hakan ya tilasta min bincike mai tarin yawa wanda ya kai ni ga gano inda matsalar take? Shin yar’uwa ke macece amma kin san wacece mace ku? Kin san me ake kira mace kuwa? Mace ita ce matar da take zama iyali a wajan namiji ta zame masa bango, sanyin idaniyarsa, ta zame masa gata da farin cikin rayuwarsa ta zame masa ruwa abar kore ƙishinsa ta zame masa mayafi mai karesa daga gigitar kadaice, ta kuma dorar da mijinta kan turbar gaskiya, ta kashe masa jiki da salonta ta rikita shi da baiwa da ni’imar da Allah ya bata idan har ta san hanyar mayar da kanta sabuwa dal awajanta, wato kullun takasance masa tamkar amarya har ya kasa tantance daren amarcinsu da sauran dararen rakun rayuwar su. Wannan ita ce mace. Ina da wata saukakkar hanyar da zaki zama abar so da kulawa da soyayya a wajan mijinki ta hanya mafi sauki, 09097853276 hanyar ita ce ki gwada amfani da kayana na gyara ki gani, ina mai tabbatar miki da in sha Allahu sai kin dara da murna sai kuma kin gode min. Kayana kaya ne da aka yi shi da zallan itacanmu na gado marasa illa a cikin jikin dan adam musamman mace, kaya ne da suke taimakawa (sex hormones 😍) dinki. Misali kina kallon India😘, hollywood, Asian film🥰 kina ganin yanda mazansu ke nunawa matansu tsananin soyayya kamar su ba su kyautar ransu!? Saboda me hakan? Saboda suna sadaukar da lokacinsu wajan gyara jikinsu da kayan da ke tsattsafo da ni’ima cike da tsukewa, kayan nan kuma ana yinsu ne zallar magungunan gargajiya wanda ba su da illa domin haɗine na ingantattun itatuwa da yayansu. Ina baiwar Allahn da miji ke daure mata fuska babu hirar arziki? Zo ki ji yar’uwa zan baki gumbata da zallar gari wanda aka yi su da nagartattun itacen da ke da matukar amfani a jikin mace. Gubar ciko, gumbar tsalle dole, gubar da ba'a baiwa mai kishiya, garin maɗi, garin mallaka, tsumin goron tula, tsumin tsartai, tsumin maratsi, pala-pala butar sirri, kwanon k’asaitacciyar mace, furar mata madararta gareki Hajia takenta sha yanzu mgni yanzu, Ina mata masu fama da sanyi? Sanyin mara ki zo na hadaki da magani na na sanyi wanda yake wanke mara ya fitar da duk wata cuta da ke samun mazauni a wajan. Ina da ciccibi mai kyau. Ina da hadin amare mai kyau wanda zai gyara yarinya ya kankaro mata kimarta akwai hadin mai jego wanda muke yinsa na asali inada kekkyawan Hadi maida tsohuwa yarinya. Akwai daya bangaren wato *KAMSHI* Kimarki gyaranki da kamshinki. Matan da suka gane suka san yanda za su kankaro da mutunci su ne masu amfani da kayan gyara da kuma sanyaya jikinsu da kamshi, ina da turaren wanka da na bandaki na daki na jiki da na kaya dana tsuguno kamshin turarena na dabam ne mai sanyaya zuciyar wanda ya shaka ina da kayan kamshi na amarya da na maijego da na uwargida da dukkan macen da take kokarin mayar da kanta mai daraja a idon kowa ta zamo sarauni a idon mijinta, akwai shu'umar humra, sayan na gari maida kuɗi gida, banda karanta yayin gyara Hajia. Zaku iya samun kayyakina a duk garin da kike, zakiyi min mgn ta whatsApp number na 09097853276 domin yin zaɓinki, ko karin bayani, zaki tura kuɗin ta account na 0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU in mun gama mgna zan sa miki kaya a mota yazo duk garin da kike, in baki shirya saya yanzuba Please kada mu wahal da juna ki bari sai kin shirya kafin kiyi min mgn. 🤝🏻🥰😘 Daga taku AYSHA ALIYU GARKUWA *(GARKUWAR MA'AURATA)* By *GARKUWAR FULANI*