_typing🖌️_ *🔘JEEDDATOU🔘* *************************⬇********************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************* NA MARUBUCIYAR:-👇 SAMHA ƳAR MACE KISHIYACE SURUKAR ZAMANI GIDAN SADIƘ MATAR BAHAUSHE TAHEER LAILAH A GIDAN MU SUKE NOOR JAHAN JAHAN KHATOON ND NOW AWANI GARI MALLAKIN:- *Khadeejour Muhammadou(THE CAT LOVER😸😹)* *(🌲S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE🌲)* https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo WHATSAPP NUMBER:- *08167151176* WHATPADD:- *MRS BASAKKWACE* GMAIL:- *MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM* IG ACCOUNT:- *KHADDEJATOU BASAKKWACE* TWITTER:- *@MRSBASAKKWACE* SNAPCHART:- *KHADEEJATOU BASAKKWACE* SADAUKARWA GA-:- *MOMYNA HAFSAT ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA UWAR MARAYU* *PAGE 1&5* *BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* ___________📖Ƙauyen Lafani wani ƙauye ne a ƙarƙashin ƙaramar hukumar Illela local govment yamma da ƙauyen ciwake,sanaan mutanan garin noma,mazan garin kusan mafi aka sarin su suna fita hausa(lagos ibadan etc) shi ake nufi da hausa. _WANNAN KENAN_ "Jiddah-Jidda,wai Jiddah dan uwarki bakiji ina kiran kine,ko so kike muryata ta dashe?,shegiya dangin mayu masu ƙashin tsiya,yanda uban naki yake kwance ba cas sai an juyar tayaya in baki fita kinyo talla ba zan ciyar dake dashi,su Atiƙha dai da Sa'ina wa ƴanda suka kawo dukiyar auran su,sun hana su tallah,ke ko basu hana su bama baza suyi b,tunda gaki ƙatuwar banza duk kin tsofe musu shekara sha huɗu ba mashin shini duk ƙauyen nan babu sa'ar ki,ni wallahi da babban budurwa gwamma ƙaraman bazawara". Wata ƴar matashiyar dattijuwa,bazama akirata dattijuwa ba ,kasancewar ƴaƴan ƙauye ana musu auran wuri,ga wahala da rashin gyara ke sa su su tsofe,fara ce gajera mai faɗeɗen baki da gajeran hanci,daja-daja take da ƙazanta. Daga wani ɗan ɗaki Jidda share hawayen da ya zubo mata gyara ma mahaifinta kwanciya tayi bayan ta goge masa jiki ta cire masa kayan da yayi fitsari ta aje a gefe,"Gwaggo ina zuwa,na gyara ma Abba jikine bari in ɗauko hijjabi". Fyace majina tayi da saleɓen zanin ta daga bisani tace,"dan uwarki ma karki fito,in rana tayi kyasan yanda zakiyi da kayan nan nide kuɗi nake buƙata". Fitowa tayi da sanye da hijjab ɗinta duƙun-duƙun ta cukuykuye shi don matuƙar kunya takeji yanda take fita,yau inshaAllahu sai taje ƙauyen ɗan boka wajan yayar mahaifiyarta ta samo ɗan sabulu na wanka dana wanki tazo har kayan kashi da fitsarin Abbanta ta wanke,don duk tallan nan da take ma Gwaggo iyakan ta ta bata abinci ba suturan balle tokan wanka dana wanki. Ɗaukan bokitin wainar tayi ta ɗaura akai ta fita,bayan gwaggo ta gaya mata na nawa tayi. Zahra kenan ,bata aje komi ba face gulma,ba ruwan ta da sallah tun ƙarfe uku na dare take tashi ta hasa wutan ta ɗaura masa,ba ruwan ta da sallah ko wanke ido,neman kuɗi ne kawai a gaban ta. "Zarah ki wanke min kayana gaskiya duk sunyi dauɗa". Faɗan wata ƴar yarinya ɓai kama da zarah kallo ɗaya zakai mata zaka tabbatar da ƴarta ce ,yarinyar bazata gaza shekara sha ɗaya ba,ɗaure take da ɗaurin ƙirji kan nan daga-daga ba kitso hamma take tana miƙa. "Kajimin ƴar kaza-kazan uwa,in ankai ki gidan Hallirun hakanan ubanki zai rinƙa zuwa miki aiki". "Wallahi Zarah kwasowa zanyi in rinƙa kawo miki,ai baki koya min ba". "Gafaran kudai mai kuke tattaunawa ne hayani har killa tunda safen nan? Wata yarinya ƴar kimanin shekara sha uku tana sanye da riga da zani, ta ɗauke da baƙar leda. "Ke kuma daga gidan uban wa kika kwana?. Ya tsina fuska tayi tace,"ke zarah ansa wannan Alhaji Sa'idu ne ya ce inkawo miki kaji ne ki goge wiya". Lokaci ɗaya Zarah ta washe hauru ta amshi ledan tana dubawa. "Alhaji Sa'idu ɗan albarka,kinsan de gidam sarkin aska sun kawo kayan auren ki koh?,tou ki iya takun ki a hankali,karki bari ki kawo min ciki gida". "Kinga Zarah innayi cikin ma uban shi yafi kowa kuɗi a wannan ƙauyen namu,ko zubar wa bazan yi ba don inci gado". *😲😲😲😲😲😲OHH NI JIKAN HAJJA TALA,WA YA GAYA MA BALLAGAZAN GA ƊAN SHEGE NA GADO???* *WANNAN WATA IRIN UWACE,MAI KASHE ƳAƳANTA???* Jidda ko tana fita tayi sa'an saida masar ta,daganan ta wuce ɗan boka inda yar mahaifiyata ta amso sabulu da omo,a gaggauce bata zauna ba ta juyo don tana tsoro kar Gwaggo ta casa ta,don don yau tana da cin kasuwar gada kuma tana so ta tsamtsame kayan su. "Assalamualaikum gwaggo n dawo". Tana aje bokitin. "Tou ina ruwa na,da dwowar ki,bani kuɗina in biyar ya ɓace wallahi sai na naɗa miki na jaki". Cike da masifa take maganan. Miƙa mata tayi daidai lokacin ledan sabulun ya faɗo. Da kallo Zarah tabi leda kafin ta ɗago,tace,"kuɗina kike ɓoye wa ki kashe,shegiyar ɓarauniya". Girgiza kai tayi jikin ta ma rawa tace,"...........! *SAI NAGA COMMENTS ƊIN KU* *DEDICATED TO ALL MY FANS,luv u oll kamar saman alala🥰😘* _typing🖌️_ *🔘JEEDDATOU🔘* NA MARUBUCIYAR:-👇 SAMHA ƳAR MACE KISHIYACE SURUKAR ZAMANI GIDAN SADIƘ MATAR BAHAUSHE TAHEER LAILAH A GIDAN MU SUKE NOOR JAHAN JAHAN KHATOON ND NOW AWANI GARI MALLAKIN:- *Khadeejour Muhammadou(THE CAT LOVER😸😹)* *(🌲S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE🌲)* https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo WHATSAPP NUMBER:- *08167151176* WHATPADD:- *MRS BASAKKWACE* GMAIL:- *MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM* IG ACCOUNT:- *KHADDEJATOU BASAKKWACE* TWITTER:- *@MRSBASAKKWACE* SNAPCHART:- *KHADEEJATOU BASAKKWACE* SADAUKARWA GA-:- *MOMYNA HAFSAT ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA UWAR MARAYU* *PaGe 6&10* *BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* ___________📖Girgiza kai tayi jikin ta na ɓari yana rawa tace,"Gwaggo ban taɓa miki kuɗi ba wallahi". Ahasale tace,"in baki taɓa min kuɗi ba kanti sani kikaje kikai sata koko yawon ta zubar ɗin da kike zuwa yi anan kika samo,dole ma yau in duba ki,don karki kwaso min abin kunya duniya ta zageni baccin ina iyakan ƙoƙarina akan ki". "Gwaggo wallahi Inna Mairamu ta tabbani,naje ɗan boka ne kayana duk sunyi dauɗa". Cikin muryan kuka take maganan,yayinda hawaye ya saukko kan farar fatan fuskan ta da ta koɗe da datti. Gwafar uban can,har can kika je don kija min zagi,in banda kin rainani,in ɗaura miki talla ki wuce ɗan boka wajan munafukar Inna ki,tou uban mai kika ce mata, wani sharri kika laƙaba min,ko kinje tabaki sabon maitan ne?. Cike da masifa take maganan,ta ƙarashe maganan da sigar tambaya. Girgiza kai take yayinda hawaye ke cigaba da wanke mata fuska. Sa hannu Zahra tayi ta wufce ledan sabulun. "Bazaki wanki da wankan ba,saide ki mutu cikin dauɗa,harni zaki gaya ma kayanki sunyi dauɗa". Tana magana tana dukan ƙirjinta. Gwagg......! "Zanci uwarki kika ƙara kiran sunana kurwata kur la'ilafi ƙafa dubu,in wani sidda barun maitan aka ƙara baki tou namana ɗaci". "Zarah wai miyasa baki karkashe ƴar iska da mari,bata san ban bancin ɗiyar bora da ɗiyan mowa ba,da kin bari ta fara wanka da wanki,wannan mai ƙwalaƙwalan idanuwan sai tace tafi ƙarfin miki talla". Faɗar Atiƙa dake zaune kan gadon kara ƙarƙashin bishiyar dalbejiya tana kallo a wayarta sha kiɗanka baƙauye. "Ke Atiƙa ina zanyi sake ,ai wallahi a ƙauyen nan na lafani JIDDAH sai ta zama abin kwatance ba boka ba mallam,amma sai ta zama mafi ƙatuwar budurwan da ta tsufa ba aure,inko kinga tafara tsafta ta samu wanda zai aureta sai bayan raina". *😲😲😲😲😲😲NIKO DA NAKE GEFE NACE TA ALLAH BATAKI BA ZARAH DAKE DA ƳAƳANKI* Sum-sum Jiddah ta wuce tana sharan ƙwalla ta nufi ɗakin da mahaifin ta yake kwance,da sallama ta shiga ɗakin duk da tasan bazai iya amsawa ba. Ƙarasawa tayi kan gadon karan da ko tabarma babu akai da yake kwance. Hawaye tagani nabin fuskan shi,jikin ta na rawa ta duƙa daidai kan fuskan shi duk tabi ta ruɗe jikinta har yafi ɗazun rawa,don sam bataso taga mahaifinta cikin damuwa,da da dama ta ɗauke mai ciwon da ta cire mai ajikin shi tace,"subuhanallah Abba hawayen kuma na miye?,dan Allah Abba kadena damuwa cuta aiba mutuwa bace,zaka warke inshaAllahu kaji Abba". Cikin muryan lallashi take maganan,tana haɗiye kukan dake ƙoƙarin ƙwace mata. *********** "Dady-Dady katashi kamin wanka natafi school,Momy tace in tasoka ai ita ba ƴar aiki bace,kuma kar in ƙara tashinta in tana bacci". Faɗan wata ƴar cute girl da bata wuce shekara biyar ba da take tsaye bakin gadon mahaifinta tana bubbuga ƙafafuwan sa. Girgiza kai yayi lallai Abeeda bata da ranan shiryuwa,ace ka haifi ƴa bazaka iya kula da ita ba,taɓa baki yayi ya miƙe yana kallon agogon da ke manne jikin ginar ɗakin lokaci guda yace,"muje bedroom ɗinki,inyi miki wanka kinji Little cute". Ko alaman damuwa babu atattare dashi don inda sabo ya saba da halin Abeeda,kamar ba auran soyayya sukayi ba,burinta guda tahau motor tasa manyan kaya sam bata damu da gyaran gida ba,balle kula da ƴar da ta haifa,gashi mugun halinta baisa ta zauna da ƴan aiki. Daf da zasu shiga bedroom ɗinta ta tace,"Dady ka samo min Nany gaskiya". Shafa kanta yayi yana murmushi yace,"inshaAllahu Little Cute ɗina ,zansa Hajiya Mama ta samo miki new nany". Tsalle tayi cike da murna tace,"thank you Dady i love you",tare da manna masa kiss a hannu. Tare suka sake ma juna murmushi. Wanka yayi mata ya shiryata kafin yaje kitchen ya dafa musu indomie da ƙwai ,abaki ya bata kafin taje ta ɗauko jakan ta ya kira driver ta ya tafi da ita makaranta. Nufan ɗakin matan shi Abeeda yayi,tana kwance kan gado ga uban tulin kaya ba ninki,ranshi yaji yayi matuƙar ƙara ɓaci da halin Abeeda ƙwafa yayi ,sai lokacin tasan ma anbuɗo ƙofa anshigo sam bata sani ba. Ɗan gajeran tsaki taja ta gyara kwanciyar ta taci gaba da danna wayarta alaman chart take a hasale yayo kanta yasa hannu.........! *THANK YOU FOR UR COMMENTS FANS LUV YOU LODI-LODI* *DON JIN YANDA ZAA KWASHE SAI NAGA RUWAN COMMEMTS KAMAR MUNA WATAN TAKWAS🤗* _typing🖌️_ *🔘JEEDDATOU🔘* NA MARUBUCIYAR:-👇 SAMHA ƳAR MACE KISHIYACE SURUKAR ZAMANI GIDAN SADIƘ MATAR BAHAUSHE TAHEER LAILAH A GIDAN MU SUKE NOOR JAHAN JAHAN KHATOON ND NOW AWANI GARI MALLAKIN:- *Khadeejour Muhammadou(THE CAT LOVER😸😹)* *(🌲S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE🌲)* https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo WHATSAPP NUMBER:- *08167151176* WHATPADD:- *MRS BASAKKWACE* GMAIL:- *MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM* IG ACCOUNT:- *KHADDEJATOU BASAKKWACE* TWITTER:- *@MRSBASAKKWACE* SNAPCHART:- *KHADEEJATOU BASAKKWACE* SADAUKARWA GA-:- *MOMYNA HAFSAT ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA UWAR MARAYU* *PaGe 11&15* *BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* ___________📖Ɗan gajeran tsaki taja ta gyara kwanciyarta taci gaba da danna wayarta alamun chart take a a hasale yayo kanta yasa hannu ya fisge wayar ya bugata da bango ta fashe ta watse. Buɗe baki tayi da hanci ta kalle shi ta kalle inda wayar ta fashe. Azuciye yake kallonta,kallon raini da ƙasƙanci ya kumbura yayi fam. "Wai dan Aliyu wannan wani irin wulaƙanci ne,har yakai yau da ka fasa min wayata". Cikin ƙunan rai take magana,don chart ɗin da suke da ƙawayen ta awani group ya ɗau daɗi gashi ya fasa wayar. Murza ƴan yatsu yakama yi yana nuna ta da ɗaya,yace,"Abeeda wallahi tallahi sai nayi mum-munanan saɓa miki,ke wata irin sakarya ce ƙazamar gida,wacce bata san ciwon kanta ba,wallahi Abeeda baki san inda yake miki ciwo ba,ji ɗakin ki,inda kike kwana kamar juji bola,anjima kifita ko ɗan kamar matan gwamna". Nau yayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin yaci gaba da faɗin ɗakin ki kenan inaga falo,toilet kitchen tirrr da auran ƙazama irinki,bedroom ɗina dana ƴarki sai in ni na gyara,tou wallahi daga yau nazo na ƙara ganin kina chart baki aikin da matan gida maana matan aure sukeyi ba wallahi sai na mummunan saɓa miki,mtsewww. Ya ƙarashe maganan dajan tsaki. "Aliyu ni ba ƴar aiki bane inko kanaso kaga waje tass kanemo ƴar aiki,kuma wallahi ba abinda zan gyara". Cike da rashin kunya take maganan kana,ta miƙe ta faɗa toilet kai ko ɗan kwali babu tabarshi tsaye. Girgiza kai kawai yayi yafita ranshi na ƙuna. *NIKO NACE DAMA DUK WANDA BAIJI BARI BA,YAJI YEHO,YANZUN ALIYU TAURIN KANKA WA GARI YA WAYA* ************* Abba na inshaAllahu zakaji sauƙi ka taka kamar yanda kowa ke.....! "Kina fitowa ki ɗau lalamen ga ki bashi abinda ya rage kisha kizo ki ɗebo ruwa kafin lokacin gada yayi koko sai nazo na lallasa miki jiki". Maganan Zarah ne ya katse mata maganan da take wa mahaifinta,miƙewa tayi jiki a saɓule tacire hijjab ɗinta tasa akan ƙofa tafito ta ta ɗau ƙwaryan dake buɗe duk ƙuda nabi kana,ta ɗauke ludayin dake gefe kan wani fayfay tasa acikin lalamen ta nufi ɗaki. Aje ƙwaryan tayi ta gyara masa kwanciya ta yanda zata bashi baibiyo ta hanci ba ta ɗeba takai mai baki taga ya kauda kai,murmushi tayo don tasan mai kauda kan yake nufi. Zama tayi ta lanƙwashe ƙafarta ta fara sha ,ganin ta fara sha yafara murmushi,don wani lokaci bai fara shan fura ko lalame sai yaga tasha ta ƙwoshi kafin yake karɓan wanda taba shi,hakan ko akayi sai da ta ɗansha,duk da lalamen baida wani yawa,kafin tabashi yasha. Tana gama bashi ya goge mai baki ta gyara mai kwanciya kafin ta kwashe kayan tafita ta ɗau bokati tafita rijiyan dake jikin gidan su ta baya ta ɗebo ruwan ta cika ko ina. Fakan idon Zarah tayi ta kamfata ruwan taje tayi wanka,duk da babu kayan da zata sauya,wannan masu warin datti da dauɗa ta kuma sawa tafito ta anshi sautun zuwa cin kasuwar gada. ********* "Wallahi Salman nagaji da zama da Abeeda,ƙazantar ta tayi yawa". Aliyu ne cike da takaici yake gayama Salman damuwar shi. "Ni wallahi Aliyu da kaji maganan Ummie game da aure da baka shiga halin damuwan nan ba,jiyanda ka susuce kazama kaima wani ƙazami dakai". "Wallahi ko Salman nabiye wa son zuciya,nayi zaɓen ƙyale-ƙyalen banza,zaɓen tumin dare". "Wallahi fushin Ummie ne kaje ka lallaɓatw kabata haƙuri Allah bashi kwana biyu kanuna mata kana son waccan yarinyar". "Hakane ko aboki koko amini zance,duk da bata nuna mani komi game da auran Abeeda banbi wasiyar mahaifina ba,ɓacin ran da nasa mata a lokacin shi kaɗai ya isa yabibiye ni". Tattaunawa suka rinƙa yi yanda zasu ɓullo ma wannan alamarin. ********* Dafda magariba ta dawo niƙi-niƙi da kayan da suka fi ƙarfinta. "A'a Hauwa Jidda kindawo gadan ne,wai bakijin kunya goɗai-goɗai dake kina zuwa cin kasuwa?. Haɗa rai Jidda tayi tamm kamar zata fashe ta haɗa giran sama dana ƙasa,a hasale tace,"Maa'u ina ruwanki,banjin kunyar ke da kike da kunyar ai baki zuwa". Maa'u ƙawar shashancin Atiƙa ce duk sa'ani suke da Atiƙa bata da kunya sosai. Riƙe ƙugu Maa'u tayi,kana tace,"ke mayya bora kawai harkinyi bakin da zaki zageni yau keda Zarah ne,sai naja an lakaɗa miki dukan tsiya". Tsaki Jidda taja,tare da cewa kije ki faɗa mata inyaso karta barni da rai". "Kam bala'i haka kikace?. Ko tanka ta Jidda bata kuma yiba. Wucewa tayi kai tsaye gidan su Jidda tana kuka ta kwashe ƙarya da gaskiya ta faɗa ma Zarah da ƴaƴanta,zarah tacika tai fam jiran jidda take ta ɗau mummunan mataki akanta. Jidda ko da ƙyar tasamu yaron da ya temaka mata ya ɗauko mata kayan. Assalam.......,batakai da ƙarasa sallaman ba ko sai dai taji sauka abu akanta wanda yayi sanadiyar ...........! *YAUWA FANS DA COMMENTS ƊINKU NAKE ƘARA JIN ƘARFIN GUYWAR TYPING KUCI GABA DA SAMBAƊO COMMENTS,INA GANIN COMMENTS ƊINKU SOSAI NAKE GODIYA LODI-LODI👌🤗* _typing🖌️_ *🔘JEEDDATOU🔘* NA MARUBUCIYAR:-👇 SAMHA ƳAR MACE KISHIYACE SURUKAR ZAMANI GIDAN SADIƘ MATAR BAHAUSHE TAHEER LAILAH A GIDAN MU SUKE NOOR JAHAN JAHAN KHATOON ND NOW AWANI GARI MALLAKIN:- *Khadeejour Muhammadou(THE CAT LOVER😸😹)* *(🌲S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE🌲)* https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo WHATSAPP NUMBER:- *08167151176* WHATPADD:- *MRS BASAKKWACE* GMAIL:- *MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM* IG ACCOUNT:- *KHADDEJATOU BASAKKWACE* TWITTER:- *@MRSBASAKKWACE* SNAPCHART:- *KHADEEJATOU BASAKKWACE* SADAUKARWA GA-:- *MOMYNA HAFSAT ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA UWAR MARAYU* *PaGe17&20* *BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* ______📖Assalam....,bata kai da ƙarasa sallaman ba ko,sai dai taji saukan abu akanta,wanda yayi sanadiyar zubewar ta ƙasa wanwar babu motsi. Duk da haka Zarah bata kula da aika-aikan da tayi ba,ta bita ta hau ruwan cikin ta tana ta bugu bata ji bata gani. Hansai ce tazo wucewa taga tana dukan ta,amma ko motsawa batayi,tazo a zuciye ta ja Zarah gefe ta wurgar,kan Jiddah ta nufa tana girgiza ta. "Ke Hansai kina shiga min hanci da duƙunƙune akan lamuran gidana,in banda iskanci ƴarki ko ƴata". Cike da masifa take hayayyaƙo ma Hansai. "Tou sakaryar mace sha-sha-sha samna,kin kashe masu ƴa kin huta". Kuru-ruwa Zarah ta sake take mutane suka fif-fito,ga Jidda kwance bata ko motsi. "Na shiga uku na lalace ni Zarah". Cike da tashin hankali duk ta ruɗe take magana. "Aiko baki shiga uku ba tukunan,yanzun zan ruga gidam mai gari inkai ƙaranki,Allah bashi a turo da ƴan sanda daga birni atafi dake ki bayani". Faɗan wani ɗan matashin yaro da jiya yadawo daga cirani. Hansai tace,"wallahi ko hanzarta Zarah bata da mutunci bata da imani". "Dan Allah kuyi haƙuri kuyi min rai". Atiƙa da Sa'inah ko duk sunyi ƙulu-ƙulu da ido ,sun rakuɓe a gefe. *********** "Ummie na tuba". Faɗan Aliyu dake duƙe gaban mahaifiyar sa ya haɗa hannuwan shi biyu tare da maraice murya. Murmushi tayi tare da gyara zama,tace,"mai kayi kuma da kake neman tuba?. Ta tambaya cike da mamaki. "Ummie kinfa sani,Ummie na tuba zan zauna da ita". Riƙe baki tayi da mamaki,kafin ta kuma cewa,"wai kai lafiyan ka kuwa?,wa zaka zauna da ita?,ina Abeedah?. Lokaci ɗaya ta jero masa wa ƴannan tambayoyin. "Ummie ɗiyar baba Ibrahim nake nufi,na gaji da auran Abeeda Ummie,ƙazantat-ta yayi yawa,Ummie harfa Cutie bata kula da ita". Taɓa fuskan tayi,ta kauda kai gefe kafin tace. ********* "Wai ke Aisha kina tunanin zan maida kaina ƴar aiki ne?,wallahi bai isa ba. Faɗan Abeedah dake zaune rashe-rashe a ɗakin ƙawarta Aisha. Aisha murmushi tayi kafin tace,"kar ki saki jiki kiyi aikin gida ,wallahi ƙawata jikin ki ɓaci yakeyi,ni kin gani kafin ya fita sai yayi komi,tunda yace bai son ƴan aiki". "Ai ke kin huta,kin samu mijin marainiya,kin dace miji,ba kalan nawa ba sai girman kai kamar fir'auna". Dariya suka sheƙe dashi suka tafa. *SHIN WANI HALI JIDDAH TAKE* *SHIN MAI UMMIE ZATA CE MA ALIYU???* *ANYA KUWA AISHA BA RAINA MA ABEEDA HANKALI TAKE BA??* MORE COMMENTS MORE TYPING🤗 *MASOYA COMMENTS ƊINKU YANA ISKE NI,INA GODIYA INA FARIN CIKI SOSAI,LUV U LODI-LODI🥰😘* _typing🖌️_ *🔘JEEDDATOU🔘* NA MARUBUCIYAR:-👇 SAMHA ƳAR MACE KISHIYACE SURUKAR ZAMANI GIDAN SADIƘ MATAR BAHAUSHE TAHEER LAILAH A GIDAN MU SUKE NOOR JAHAN JAHAN KHATOON ND NOW AWANI GARI MALLAKIN:- *Khadeejour Muhammadou(THE CAT LOVER😸😹)* *(🌲S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE🌲)* https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo WHATSAPP NUMBER:- *08167151176* WHATPADD:- *MRS BASAKKWACE* GMAIL:- *MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM* IG ACCOUNT:- *KHADDEJATOU BASAKKWACE* TWITTER:- *@MRSBASAKKWACE* SNAPCHART:- *KHADEEJATOU BASAKKWACE* SADAUKARWA GA-:- *MOMYNA HAFSAT ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA UWAR MARAYU* *PaGe 21&25* *BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* ___________📖Dariya suka sheƙe dashi suka tafa,Aisha wani shu'umin kallo tabita dashi. ********* Aliyu bazan taɓa yarda dakai ba yanda kakeson matar nan naka,in ɗauko ƴar mutane abaka,ƙilama kun haɗa bakine kai da ita a ɗauko ta ku azabtar da ita,ku maidata bora,abinda nasani kawai zaka iya rubuta ta kaddan saki,inkai wa mahaifinta ya samu wani ya bata,don bazatai ta zaman jiran gawon shanu ba". Cikin haɗa rai take magana,babu alamun dariya ko wasa a tattare da ita. Subuhanallah,ni Aliyu naga ta kaina,komai zance ma Ummie da wiya ta fahimce ni,don na ɓata rawana da tsalle,dana amince da wasiyar mahaifina da duk haka bai faruba,da yanzun gida biyu maganin gobara. A ƙasan zuciyar shi yake wannan maganan. Miƙewa Ummie tayi tana ƙoƙarin shigewa cikin gida,yai saurin ruƙo saleɓen zanin ta,tsayawa tayi cak batare da ta kalle shi ba. "Ummie pls forgive me". "Aliyu ka kiyayeni,kabani takaddan saki kawai,kaje ka zauna da wacce ka zaɓi farin cikin ta fiye da nawa". Cikin fushi take maganan. Gaban shi tsananta bugu yake,yaune rana na uku da ya taɓa ganin mugun ɓacin rai fuskan mahaifiyar shi,gaskiya na tafka babban kuskure ya faɗa a ƙasan zuciyar shi. Azahiri ƙara marairaice murya yayi yace,"Ummie na kiyi haƙuri". Hmmmm Aliyu ɓace min daga gani inka ƙara zuwa min da maganan nan ranka sai yayi mugun ɓaci". "Tou Ummie inshaAllahu". Miƙewa yayi jiki a saɓule yai mata sallama,ya tafi yana tunanin mafita,lokaci ɗaya kuma yayi murmushi. ********* Kan kuce mai har ankai ma mai gari labari,take ya buga waya zuwa birni akaturo masa ƴan doka. Ɓangare guda ko Tani ta rinƙa ƴaban ruwa Hansai na watsa ma JIDDA amma ko kaɗan bata dawo ba,alama dai rai kamar ya fita. Zarah tayi yunƙuri guduwa mata suka riƙe ta masu jin haushin ta suka naɗa mata bugu tsiya,sai da ta kasa tashi,ana haka ƴan doka sukazo suka tafi da ita ,yayinda suka ɗau JIDDA,zasu kaita asbiti,su Atiƙah sai kuka suke. Sai da suka fara kai Jidda asbitin UDUTH kafin suka wuce da Zarah police station bayan sun bar Jidda da police mace guda da Hansai da Tani. A&E aka shiga da ita likitoci da nursing suka rufu akanta. ********** "Dady wai ina zamuje ne?. Cutie take magana ta naɗe hannuwan ta cikin riga da wando yellow purple ɗin ɗan ƙaramin hijjab yasa mata da takalmi purple,akwatin ta yake sa mata kaya. "Weekend zamuje,ran sunday zamu dawo sabida school". Ya faɗa batare da ya kalle ta ba yaci gaba da sa mata kayan a ɗan akwatinta. Tsalle tayi da murna,ta hau bayan shi tana dariya. Dariya yayi shima daidai lokacin yana rufe akwatin. Ɗauka yayi suka fito riƙe da hannun juna. Daidai lokacin tafito taci uban ado kamar bazata mutu ba,kallon-kallo sukai ma juna,yawani murtuke fusa,yayin da ita harara ta galla masa. "Good morning momy". Faɗan Cutie da ta tsare Abeeda da ido. Batare da ta kalle inda take ba taja dogon tsaki ta wuce ta fita ba tare da ta ko gaisheshi ba. Murmushin takai ci yayi tare da shafa kan Cutie. Cutie ko jikin ta duk yayi sanyi. Koda suka fito harta banka ma motor ta wuta ta wuce. Aliyu ko matuƙar mamakin halin Abeedah yake. ********** ALIYU INA ZUWA HAKA???? SHIN WANI HALI JIDDA TAKE,TA MUTU KO TANA RAYE. WANI HALI ZARAH TAKE DAMA ASHE ALIYU BA AURAN ABEEDA KAWAI YAKE DASHI BA????. *INA GODIYA DA COMMENTS ALLAH YABAR ƘAUNA* _typing🖌️_ *🔘JEEDDATOU🔘* NA MARUBUCIYAR:-👇 SAMHA ƳAR MACE KISHIYACE SURUKAR ZAMANI GIDAN SADIƘ MATAR BAHAUSHE TAHEER LAILAH A GIDAN MU SUKE NOOR JAHAN JAHAN KHATOON ND NOW AWANI GARI MALLAKIN:- *Khadeejour Muhammadou(THE CAT LOVER😸😹)* *(🌲S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE🌲)* https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo WHATSAPP NUMBER:- *08167151176* WHATPADD:- *MRS BASAKKWACE* GMAIL:- *MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM* IG ACCOUNT:- *KHADDEJATOU BASAKKWACE* TWITTER:- *@MRSBASAKKWACE* SNAPCHART:- *KHADEEJATOU BASAKKWACE* SADAUKARWA GA-:- *MOMYNA HAFSAT ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA UWAR MARAYU* *PaGe 26&30* *BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* ___________📖Aliyu ko matuƙar mamakin halin Abeeda yake,da kafin suyi aure ba ƙaramin biyayya take masa ba kamar zata maida shi ciki,ko kaɗan bata son ganin ɓacin ransa,amma yanzun dattin ɗakin ta yafishi daraja a idon Abeeda. ********* Mahaifin Abeedah ko duk hayaniyar da ake yanaji,bai iya kukan zahiri sai na fili,jikin sa ya tsanan ta da zafi,gashi babu mai temako akusa,don har ya cire rai da ita,jin ana faɗin ta mutu. Addua yake a zuciyar sa Allah ya saka ma Jidda,shi kuma Allah yakawo masa ɗauki a rayuwar shi,in kuma lokacin sa yayi Allah yasa ya cika da kalman shahada. *********** Zarah ko nacan police station tana amsan azaba kala-kala ,duk marasa imanin police ɗinnan sun gama ƙara canja mata kama gaba ɗaya. *********** Saida likitici suka kwashe awa uku akan ta kafin sukayi nasaran dawo da numfashin ta,don dogon suma tayi lokacin da Zarah ta buga mata sandan. Don ko su kansu likitocin har suncire rai da zata shi,duk da akwai alaman rai atattare da ita. Hansai ko hankalin su duk a tashe yake tunda sukaji shiru ba wanda yafito balle suji tana raye ko ta mutu. *********** Tafiyan awa biyu da rabi yayi daga shi sai ƴarshi komi ta gani a hanya sai tace Dady saya min,ko kuma ta tambaya miye wannan,wani yabata amsa wani yai murmushi yaja mata hanci,hartai bacci ta tashi tace,"Dady bamu iso ba?. Murmushi yayi ya shafo kanta da ɗanyan hannun shi yace,"mun zo mana yanzun zamu ƙarasa". Gyaɗa kai tayi ta kwanta taci gaba da wasa da yatsun ta kamar wata babban mace. Cutie kenan akwai manyan ce kamar wata ruƙon tsofaffi. Parking yayi a dai-dai killan gidan su mahaifin shi ba kowa a a wajan sai bisashe da suke ta kiwo,yara ne daga can nesa suke wasan su,kulle motor dayayi ta hanyar danna key yasa motor tai kuka,take yaran hankalin su ya dawo kan su. Zuba musu ido sukayi,shiko ɗaukan Cutie yayi suka fara tafiya,yaran ko zuba musu ido sukai kamar sunga tv. "Assalamualaiku",sallama ya rinƙa kwaɗawa,amma ba kowa shiru,har ya juya zai fita,ya lura da Sa'ina dake zaune ƙarƙashin dalbejiya tana damɓara kwalliya kamar wata jaka yasa ran shi ya ɓaci. Cutie ko tana arba da ita dawani saki ƙara ta ƙanƙame Aliyu,tana faɗin Dady dodo". Lokacin Sa'ina ta ɗago ta kalle su tawani saki baki da hanci. Shafa kan Cutie yayi yace,"ba dodo bane,ƴar iska ce". "A'a Dady". Aliyu ko wani mugun kallo ya watsa ma Sa'ina kafin yace,"ke mahaukciya baki iya amsa sallama bane?. Washe haƙora tayi da sukai ja kamar ma aikatan cokula tace,"Ali banji bane". Ɗan tsaki yaja yace,"dalla ina Abba". Taɓa baki tayi tace,"yana ɗaki". "Ni kike taɓa ma baki,shegiya mai suffan buranya,inna ƙaraso sai na karya ki". Ranshi ɓace yake maganan. Shiru tayi tai muƙus don tasan shi da rashin imani yanzun sai ya nema ya karyata,gashi tana shirin zuwa wajan saurayin ta. Dogon tsaki yaja ya nufi ɗakin Abba,kwance yake jikin sa ne kaɗai ke rawa gashi yai fitsari da kashi ɗakin duk ya ɗume da wari,ga yunwa naci cikin sa. Har Aliyu ya tusa kai yai saurin dawowa baya yana toshe hanci. "Ke da mutum a ɗakinnan ?ya tambayeta cikin tsawa. Jiki na rawa tace "eh baida lafiya ne Jiddah ne ke kula dashi". Ina Jiddah take da bata gyara shiba?,maike damun shi?. Lokaci ɗaya ya jero mata wa ƴannan tambayoyin. "Jidda an tafi da ita asbiti tun jiya baa dawo ba". "Miya faru da ita?. Dama-dama tawani fara kame-kame. "Zaki min magana ko sai na taka ki mai suffan burai". Dama Zarah ne,nan ta kwashe abinda ya faru ta gaya masa,ransa yai mugun ɓaci sai huci yake kamar ya daki babu. "Ke tou uban miye amfanin ki da bazaki dubashi ba banza ballagaza wanda tasha a mama,dalla tashi kije ki gyara shi tas". Yanda yake ihu yake tada jijiyoyin wiya ba ƙaramin razana tayi ba,jiki na rawa ta miƙe ta nufi ɗakin Abba yaune rana ta farko kenan da tunda ya fara ciwo shekara huɗu kenan bata ko leƙa shiba ta ga yayake. Azuciyar ta kuwa tsine ma Aliyu kawai take,toshe hanci tayi tana tsoron ta fita ya kileta,gashi saida tayi wanka taci kwalliya zaisa ta aikin kashi tou ita ta yaya ma zata fara. Ƙwafa yayi ya samu turmi ya zauna ya ɗaura Cutie kan cinyarshi da tuntuni tawani ƙanƙame shi,a zuciyar shi ko ganin rashin kyautawan shi yayi da har ƙanin mahaifin sa ɗaya tilo da ya rage masa a duniya yana ciwo bai san ma yanayi ba,gashi yana da halin temakon sa,rabon sa dashi tun ɗaurin auran sa da Abeeda ko ban gajiya bai samu zuwa yayi masa ba,sabida kunyar da abinda yai masa. Tana kuka wi-wi-wi tana sharan majina,kwalliyan ta ƙara dame fuskan tazama kaman buranya ta ɗebi ruwa ta gyara shi ta canja mai kaya,duk da sunyi dauɗa acikin su ta samu wasu ta sauya masa ta fita da kayan can. Fitowa tayi tace mai ta gama,sauke Cutie yayi ya miƙa mata wayar shi yace tayi game. Ɗakin ya nufa,ba ƙaramin tausayawa Abban nasu yayi ba ɗaukan shi yayi ya fito dashi yakai sa motor Cutie na biye dashi ,abaya ya kwantar dashi yana hawaye yayinda suka shiga gaba shida Cutie. Cutie tsura masa ido tayi na seconds kafin ta kai duban ta kan Aliyu tace,"Dady waye shi". "Cutie Baba nane,sunan shi Abba,ke kuma Kakan ki ne". Yana juya motor yana mata magana. Cikin mintina ƙalilan ya harba motor kan titi sai cikin gari. *NAGODE SOSAI DA COMMENTS ƊINKU ALLAH YABAR ZUMUNCI🥰🥰💖❤️* _typing🖌️_ *🔘JEEDDATOU🔘* NA MARUBUCIYAR:-👇 SAMHA ƳAR MACE KISHIYACE SURUKAR ZAMANI GIDAN SADIƘ MATAR BAHAUSHE TAHEER LAILAH A GIDAN MU SUKE NOOR JAHAN JAHAN KHATOON ND NOW AWANI GARI MALLAKIN:- *Khadeejour Muhammadou(THE CAT LOVER😸😹)* *(🌲S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE🌲)* https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo WHATSAPP NUMBER:- *08167151176* WHATPADD:- *MRS BASAKKWACE* GMAIL:- *MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM* IG ACCOUNT:- *KHADDEJATOU BASAKKWACE* TWITTER:- *@MRSBASAKKWACE* SNAPCHART:- *KHADEEJATOU BASAKKWACE* SADAUKARWA GA-:- *MOMYNA HAFSAT ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA UWAR MARAYU* *PAGE31&35* *BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* ___________📖Cikin mintina ƙalilan ya harba motor kan titi sai cikin gari,asbitin daji yakai shi wajan wani abokin shi Dr Munir inda aka anshe shi aka shiga dashi A&E don bashi temakon gaggawa. ************* Ɓanagaran Jidda ko likitoci bayan sunyi nasaran cetou rayuwarta suka fito inda suka kira Hansai da Tani sukayi masu bayanin ta farfaɗo,amma basu san lafiyan kanta tana cikin hayyacin ta ko ta samu taɓin ƙwaƙwalwa sai ta farka daga bacci tukunan zasu iya gane haka,da ta farka su tabbatar da sunzo sun gayama likita,don a ƙara dubata,su ci gaba da addu'a,godiya sukayi suka tashi suka nufi ɗakin da aka kwantar da ita. ************** Zarah ata ko ina jin jiki takeyi,tun balle da akace ƴar kishiyan ta ta kashe,hatta wa ƴanda aka haɗa su cell ɗaya gana mata azaba sukeyi. Duk ƙiban nan ta zaizaye ta rame tayi zuru-zuru kamar wata jaɓa. *********** Hajiya Abeeda ko bata damu da tasan inda mijinta da ƴarta suka je ba,ta shiga cikin gari abinta,taje gidan wannan ƙawa taje na wancan,su kwashi jiki su bi can ta saki baki tana ta basu labarin mijinta. *********** "Ke mai bakin surutu tsiya daga ina?,ina Abeeda?,ko Aliyun ne ya kawo ki". Ummie ce kema Cutie magana da ganin ta kawai tayi agabanta batare da tasan sanda ta shigo ba don harta bata tsoro. Turo baki tayi ta yamutsa fuska kamar zatayi kuka ta hau kujera tare da kalmashe ƙafa tace,"Ummie yunwa". A taƙaice tayi maganan. Buɗe baki Ummie tayi kafin tace,"kaji min ƴar jakan uwa,ni zaki turo ma baki kice min yunwa". "Ummie yunwa",ta ƙara maimaitawa a taƙaice. "Zo cinye ni,tunda ninayi miki magana baki ban amsa ba kin shigo kamar wata aljana wai Ummie yunwa". "Dadyne fa ya kawo ni,yace ince miki banci abinci ba". "Ina Aliyun?. "Ya wuce". "Tashi kije kitchen kice Sadiya tabaki abinci". Tashi tayi da gudu ta nufi hanyar kitchen. ********** Aliyu ko bazama yayi police station neman Zarah tanan ne zai iya gane inda yarinyar take. Saida yaje police station uku ana huɗu ne ya samu nasaran ganinta. Sanda aka fito da ita zuwa bayan kanta inda zasuyi magana. Zarah ƙasa tayi da idonta tana hawaye dama can shakkan Aliyu take don baida mutunci ko kaɗan tsaye-tsaye yake mata magana babu ko kara. "Gwaggo nazo ja miki kunne ne wallahi,matuƙar yarinyan nan ta mutu ko wani abu ya sameta wallahi tallahi billahillazi ko duka arzikina zai ƙare,sai na ƙarar don inga an hukunta ki,baruwana da ke ƴar kakana ne,sannan mijinki kawunane mafi soyuwa a gareni zan rufe ido a wulaƙanta min ke,police kuci gaba da hukuntata". Cikin kakkausar murya yake mata maganan yanayi yana murza yatsun sa suna ƙara,iya abinda ya faɗan kenan ya ciro rafar ɗari biyar ya aje musu akan tebur ya juya yabar wajan. Duk wani dake tsaye a wajan saida yayi mamakin maganganun shi,sannan ya aje uban kuɗi ya tafi. Zarah ko duk ta rikice tasan halin Aliyu saide bai furta ba sai ya aikata,tayaya asirin da tayi mai na bazai ƙara waiwayan ƙauye ba ya karye har yazo,dole takoma wajan mallam,don maganin ɗan iskan yaron nan. Acikin zuciyarta take wannan maganan,duk da ana dukan ta amma saƙa mugunta take a ƙasan ranta. Nan ko police sun samu abin nema take suka ɗauke kuɗin suka tasa ƙeyarta ana bugu har cikin cell. *********** Kai tsaye uduth ya nufa,da kwatancen da police sukayi masa ya isa ward ɗin da take. Tura ƙofar yayi ya shiga da sallama. Hansai da Tani ansawa sukai suna duban mai shigowa. "Sannun ku babaa, ya mai jikin?. Yai maganan yana kallon gadon da take kwance ɗaure da roban ruwa,tana bacci gwanin ban tausayi,ga kayan jikinta duƙun-duƙun,lokaci ɗaya yaji tausayin ta ya shiga jikin sa da jijiyar sa. "Mai akace damuwar ta?. Yatambaya akaro na biyu. Nan Hansai tamai bayani,bai wani gamsu ba,yafita ya nemi likita ya ƙara yi masa bayani,kafin ya fito yaje chicken republic yayo take away yakai musu,har lokacin bata farka ba. Inda Abba yake ya koma,lokacin har an gama dubashi an kwantar dashi shima sai bacci yakeyi,wajan likita yaje yamai bayanin hawan jinine yai sanadiyar kawo mai mutuwar jiki,rashin kulawa da zuwa asbiti yasa jikin sa ya mutu gaba ɗaya. Dr Munir yabashi tabbacin zai iya tashi,inde aka dage masa da gashi. Sallama sukayi ma juna bayan an samu mai kula da Abba namiji,zai biyashi. *MrS BaSaKkWaCe* _typing🖌️_ *🔘JEEDDATOU🔘* NA MARUBUCIYAR:-👇 SAMHA ƳAR MACE KISHIYACE SURUKAR ZAMANI GIDAN SADIƘ MATAR BAHAUSHE TAHEER LAILAH A GIDAN MU SUKE NOOR JAHAN JAHAN KHATOON ND NOW AWANI GARI MALLAKIN:- *Khadeejour Muhammadou(THE CAT LOVER😸😹)* *(🌲S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE🌲)* https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo WHATSAPP NUMBER:- *08167151176* WHATPADD:- *MRS BASAKKWACE* GMAIL:- *MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM* IG ACCOUNT:- *KHADDEJATOU BASAKKWACE* TWITTER:- *@MRSBASAKKWACE* SNAPCHART:- *KHADEEJATOU BASAKKWACE* SADAUKARWA GA-:- *MOMYNA HAFSAT ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA UWAR MARAYU* *PAGE 36&40* *BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* ___________📖Sallama sukayi ma juna bayan an samu mai kula da Abba namiji,zai biyashi. Kai tsaye gida ya wuce daga farfajiyan gidan ya gane hajiyar gidan bata dawo ba,taɓa baki yayi da girgiza kai cike da takaici. Ɗakin shi ya wuce kai tsaye,bayan ya aje key da wayoyin shi ya cire kaya,ya shiga toilet ya watso ruwa tare da ɗauro alwala,yai shafa'i da wutiri,kayan baccin sa ya saka ya hau gado ya ɗau wayar shi yafara dannawa. Sai 10:30pm yajiyo shigowan ta ta ƙure waƙa a motor kamar club. Girgiza kai yayi cike da takaici,watou a tinanin tafiyar kwana yayi shiyasa taje tai dare,ƙwafa yayi. Itako sam bata kula da motor shiba tafito ta wuce ciki riƙe da takeaway ɗin da tayi order. Ɗakin kaca-kaca da kaya gefe ta aje ta cire kayan ta watsar a gefe ,tura kayan da ke kan gadon tayi gefe ta hau ta zauna bata damu da tayi wanka ta canja kaya ba,buɗe takeaway ɗin tayi tafara cin abinta tana danna waya hankalin ta kwance. Washagari tunda sassafe ya tashi nufi gidan Ummien sa,basu tashi ba ya zauna a falo suna ta hira da Iya mai ma Ummie girki,tun yana yaro suke tare da Iya ke gidan ,tana da kirki ga tsafta tare da halin dattako,sam bata nuna kwaɗayi a abinda ba abata ba. Umurni yabata tamai girki yana da marasa lafiya a asbiti baban wai course mate ɗin shi,aiko a mintina ƙalilan ta haɗa musu breakfast,harta gama ya ɗauka ya tafi dashi, su Cutie basu tashi ba. Abba yafara kai mawa,ya farka amma yana kwance sai bin Aliyu da ido yake ,yana mamaki,yana so ya motsa bakin shi ya tambaye shi ina Jidda amma ba dama sau hawaye. Aliyu aje kwandon yayi jiki na rawa ya ƙarasa jikin gadon yana faɗin,"subhanallah Abba hawaye kuma mai yafaru?. Kallo wanda ya kwana da Abba yayi,yace,"ya jikin nasa?. Ɗan dattijon gyara zama yayi yace,"alhamdulillah,daya farka na kira Likita ya duba shi,an ƙara mai allura". "MashaAllah ubangiji ya ƙara masa lafiya". "Ameen ya Allah". "Ga abinci nan na kawo ma,zanje in duba ƙanwata da take Uduth". "Tou ɗannan Allah yayi albarka". Amin ya amsa dashi,kafin yakai duban shi ga Abba dashi yake kallo,har yanzun amma hawayen ya tsaya yace,"Jiddah itama tana ƙarƙashin kulawan likitoci,jikinta taji sauƙi,yanzun haka zanje wajan sune,Allah ya baka lafiya zanje indawo". Cikin murya ƙasa-ƙasa mai cike da tarin ladabi yake maganan,yana gamawa yai ma mai kula da Abban sallama ya wuce. ********** Jidda ko ɓangaren ta ƙarfe uku da wasu mintoci ta wani farka a razane tana kira Abba-Abba-Abba",can cikin bacci Tani ta jiyo ta ta tashi a razane take Hansai da tayine yai sanadiyan tashin ta. Idon ta arufe yake tana kiran Abba. "Tani riƙe mata hannuwa tayi tana faɗin sannu Jiddah kin farka". Cike da kulawa take maganan. Muryan da tajine yasata waye manyan idanuwan ta da sukayi mata nauyi. Ganin su Hansai yasa take mamakin,kallo tafara bin ɗakin dashi,daga gani nan ba ƙauyen su bane,ya akayi tazo nan waya kawo ta. Hansai tace,"sannu Jidda Kulu bari akira Likita". Da mamaki take kallon Hansai nan asbiti ne tou mi ya faru waya kawota nan. Hansai jiki na rawa taje ta kira Likita suka dawo tare. Dudduba ta yayi,kafin yai mata tambayoyi yace,"ya sunan ki?. Ahankali ta buɗe baki tace,"Jiddah". Good yace,yana gyaɗa kai,ya nuna Hansai yace yasunan wannan?. Kallonta takai gareta tsawon minti ɗaya,tace," Hansai,wancan kuma Tani duk ƴan ƙauyen mune ,ina Abba na?,wake kula dashi ,mai ya kawo ni nan?. Aruɗe take magana tana kallon Dr. Gyara murya yayi yana murmishi yace,"........! *NAGAJI DA TYPING😢WALLE BAKU COMMENTS😌SHIYASA KUKAJINI NAYI LAUSHI NAYI LUƘUS KWANA BIYU BANA TYPING🌝 TAYPING ƊINKU SHINE ƘWARIN GUYWAN MARUBUTA🥰* _typing🖌️_ *🔘JEEDDATOU🔘* NA MARUBUCIYAR:-👇 SAMHA ƳAR MACE KISHIYACE SURUKAR ZAMANI GIDAN SADIƘ MATAR BAHAUSHE TAHEER LAILAH A GIDAN MU SUKE NOOR JAHAN JAHAN KHATOON ND NOW AWANI GARI MALLAKIN:- *Khadeejour Muhammadou(THE CAT LOVER😸😹)* *(🌲S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE🌲)* https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo WHATSAPP NUMBER:- *08167151176* WHATPADD:- *MRS BASAKKWACE* GMAIL:- *MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM* IG ACCOUNT:- *KHADDEJATOU BASAKKWACE* TWITTER:- *@MRSBASAKKWACE* SNAPCHART:- *KHADEEJATOU BASAKKWACE* SADAUKARWA GA-:- *MOMYNA HAFSAT ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA UWAR MARAYU* *PaGe41&45* *BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* ___________📖Gyara murya yayi yana murmushi yace," Alhamdulillah,ta maganganun ta nagano bata da matsalan ƙwaƙwalwa,nan asbiti ne,Hauwa,Abban ki na gida". Cikin tattausan murya yake mata magana. Hansai ta amsa da cewa,"Ali ɗan gidan Abban ki Aminu,ya ɗauko Abban ki ya kaishi asbiti shima". Sauke nauyayyam ajiyar zuciya tayi kafin ta ɗuƙar dakai tace,"Alhamdulillah".,duk da ambaton Aliyu saida ya faɗar mata da gaba. Dr tambayoyi yai mata cike da ƙwarewa irin nasu na Likitoci tana bashi amsa,daga bisani yasa aka kawo mai allura yai mata take bacci ya ƙara ɗaukan ta. *********** Ƙarfe bakwai da ƴan mintoci ta kuma farkawa,da salati bayan nan tayi addu'an tashi daga bacci,kana ta miƙe ta zauna,tanabin ruwan da ke tafiya cikin hannun ta da kallo. Tani ta taso da hanzari tace,"sannu JIDDA, ya jikin?. "Alhamdulillah",ta amsa dashi murya ƙasa-ƙasa. "Tou-tou Allah ya ƙaro dama". "Amin",ta amsa dashi a taƙaice. "Ko akira likitane?. Tani ta ƙara tambaya. "A'a temaka min zaki in rama sallolin da ake biyata". Da mamaki Hansai ta riƙe baki ganin ƙarfin hali wai sallah zatayi,ita in tana ciwo ai bata rama sallah,lafiya ƙalau ma bata dameta ba,sai taga idon mutane takeyi,taɓa baki tayi kana daga bisani tace,"tou bari intemaka miki,baki bari ƴarnan jikin ki har ya ƙara ƙarfi?. Ta ƙarashe maganan da sigar tambaya. Ahankali ta girgiza kanta,kana tace,"ke Tani inna mutu fa?,inje ince ma Allah maine?ince banji sauƙi ba?. Lokaci ɗaya ta jero mata wa ƴannan tambayoyin. Mamaki Tani take ƴar ƙaraman yarinya da magana babba,yarinyar nan dai wuni take talla,ya akayi tasan karatun islamiya. Abinda ko ke faruwa,inde Jidda ta ɗau tallan goro da yamma,can gidan fura take tafiya,su suna da yawan islamiyoyi da boko,jikin wata islamiya take zama tana sauraran karatun su,anan duk ta iya abu-buwa da yawa,tana sha'awan karatun addini,amma ita talla bazai bari tayi ba,kullum tana ti-ti yawon talla. "Temaka min manaTani". Ta ƙara magana,muryanta ciki-ciki. Tani sa hannu tayi ta tallafo haɓanta,suka taka ahankali harcikin banɗakin ta barta tafito don ta kama ruwa tayo alwala,tace mata inta ida ta kirata,hakan ko akayi tana idawa ta buɗo ƙofa ta kirata,kamata tayi takaita kan kallabin ta da ta shimfiɗa ta zaunar da ita tabata hijjab ɗinta ta saka. Rama salloli tafarayi tun na jiya har yau. ************* Zarah jiki yayi tsami yayi laushi,bata ƙara tabbatar da ƴan sanda basu da imani basu d mutunci ba,saida Aliyu yazo ya basu kuɗi ,suka ƙara ƙaimi amata rashin mutunci. Duk tayi laushi,dana sanin abinda tayi takeyi yanzun da yanzun tana gida tana juya biyar ta zama goma. Da tabari ta shigo ta same ta da icen dalbejiya ta jibga babu mai ce mata kanzil,Allah ya tsine ma Hansai take faɗa a zuciyarta. Duk da haka bata saduda ba,jira take ta fita,duk wahalar da aka bata anan sai ta fanshe ajikin JIDDAH. ************ Uban dame suke tiƙawa a tsakanin su,mutane sun taru ana raba su amma sam basa ji,har yakai da mutane sun koma kallon su. "Shegiya karuwa,karuwan cina yamin rana tunda ni ina iya sayan sabulu kizo ki ɗauke kina wanka". Faɗan Atiƙa datake ta huci kamar maciji. "Karuwa gakinan ƙatotuwar ashawo ciki nawa kika zubar". Faɗar Sa'ina da take ƙoƙarin cakumo Atiƙa,dakyar aka shiga tsakanin su,amma basu dena cin mutuncin juna ba da ɓacin su. _NIKO NACE ALLAH YA WADARAN RAƘUMIN DAWA YAƘI ƳAƳA🤦‍♀️_ "Shegiya ƴar iska ke Saminu da ya kawo dukiyar auren ki,ina ce har ubanshi kike lalata dashi". Faɗan Atiƙah da har yanzun huci take tana zare ƙananun ido irin na uwarta Mutanan wajan salati suka ɗauka cike da mamaki. Take dambe ya ƙara kaurewa tsakanin sun suna yaga ma juna kaya. Daƙyar aka raba su,akaja Sa'ina akayi waje da ita. Asafiyar ranan ko,ƙauyen nan labarin su ake lungu da saƙo. ********** Turo ƙofar da akayine yasa dukan su suka ɗago kai.............! MORE COMMENTS MORE TYPING🤗 *MASOYA NAGODE DA ADDUOIN KU,ALLAH YABAR ZUMUNCI🥰* _typing🖌️_ *🔘JEEDDATOU🔘* NA MARUBUCIYAR:-👇 SAMHA ƳAR MACE KISHIYACE SURUKAR ZAMANI GIDAN SADIƘ MATAR BAHAUSHE TAHEER LAILAH A GIDAN MU SUKE NOOR JAHAN JAHAN KHATOON ND NOW AWANI GARI MALLAKIN:- *Khadeejour Muhammadou(THE CAT LOVER😸😹)* *(🌲S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE🌲)* https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo WHATSAPP NUMBER:- *08167151176* WHATPADD:- *MRS BASAKKWACE* GMAIL:- *MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM* IG ACCOUNT:- *KHADDEJATOU BASAKKWACE* TWITTER:- *@MRSBASAKKWACE* SNAPCHART:- *KHADEEJATOU BASAKKWACE* SADAUKARWA GA-:- *MOMYNA HAFSAT ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA UWAR MARAYU* *PAGE51&56* *BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* ___________📖Kafin ya wuce da ita gidan Ummie gaban shi na faɗi,yan a tunanin draman da zasu kwahe da Ummie sa. Ko da suka isa yace,"mata ta fara shiga ciki,fita tayi jiki a sanyayye ta nufi cikin gidan,don rabon da tazo gidan tun bikin Aliyu da sukazo da Abban ta da zai ɗaura ma Aliyu aure,ana gama ɗaurin auran suka koma ƙauye tun da suka koma Abban ta ya faɗi tun daganan ya kama ciwo. Ahankali ta tura ƙofar tashiga da" asallamualaikum". Cikin sanyin murya tayi maganan can ƙasa-ƙasa. "Waalaikumusalam",Ummie dake ɗaura ma Cutie ɗan kwali,ba tare da ta ɗago ba. Jin shiru ba'a ƙara magana ba ba'a shigo ba yasata ɗago kai,karaf idon su ya sarƙe da juna,da mamaki Ummie ke kallon ta,yau ne rana na farko da taganta cikin shiga mai kyau, don kullum zata ganta cikin duƙu-duƙun kaya,taso ta temaka mata amma masifar ZARAH ya hana ta temake ta,tunda ALIYU ya watsa mata ƙasa a ido,cikin ma wuyacin halin da take ganin ta bai mata daɗi yana ɗaga mata hankali yasa tadena zuwa Lafani. Lokaci ɗaya ta faɗaɗa murmushin ta mai nuna alamun tsan-tsan farin ciki ganin ta tace,"a'a Hauwa Jidda ce agidan namu yau lale marhaban,ina Ibrahim ɗin?,ki shigo ma kin coge jikin ƙofa kamar baƙuwa". Murmushi tayi tana sunkuyar da kai ta ƙaraso cikin falon ta zauna a ƙasa. "Keko Jidda wannan halin naki na ƙauyawan fulani nanan,sai wani noƙe jiki kikeyi kamar wata kifi". "Kwallahiya Ummie?. "Lafiya lau ya kike,kitashi ki zauna kan kujera". Girgiza kai,Jidda tayi tana tura shi cikin hijjab. Hmmm" ni wallahi ban san wannan hali,ina Abban naku nagan ki ke kaɗai?. "Ni da Yayane bada Abba ba,Yaya bai gaya miki mun kwanta asbiti ba,yanzun haka Abba na shi baa sallame shi ba". Gwalalo ido Ummie tayi cike da mamaki,ranta lokaci guda ran Ummie ya ɓaci,ohh dama Maman abokin nashi da ba ta da lafiya yake amsan abinci yana kaiwa,ashe Abba ne da Jiddah. "Mi ya sameki keda Ibrahim ɗin?. Nan ta kwashe ciwon Abba tun daga randa suka koma bikin Aliyu ta gaya mata,da kalan azaban da tasha,da sanadin kwantawan ta asbiti,ta gaya mata batasan yanda Aliyu yasan Abba baida lafiya ba har ya kawo shi asbiti,amma yanzun jikin sa alhamdulillah. Ummie tun kafin ta gama ta fara sharan ƙwalla,lallai bata kyauta ba,ta yada zumun ci,da Abdullahi na raye da bata kwashe shekarun nan ba bataje ba nan lafani ga baki ga hanci ko motor haya zata hau ɗari shidda ne,balle ga motocin gidan birjit sai wanda ta zaɓa zata hau. Share ƙwalla tayi kafin cikin dasha-sh-shiyar murya tace,"ina Aliyun ya tsaya?. "Yana waje yace," zai shigo",ta bata ansa a taƙaice. Aliyu ko yana jikin ƙofa yanajin komai dake wakana,ya turo ƙofar ahankali ya shigo,jikin sa a sanyaye ,ko kafin ya ƙaraso tsakiyan falon Ummie ta ture Cutie dake kwance ajikin ta ta rai ɓace tayo kansa,yana ɗago fuska yaji saukan mari tassss-tasssaa ke ratsa falon hagu da dama take marin sa. Jikin Cutie na rawa ta ƙara haye wa cikin lallausan kujeran falon ta tura kanta saƙon kujeran a firgie JIDDA ta miƙe tana zaro ido. Bata taɓa gani an doke babba ba a ƙauyen su,gani take in yaro ya girma ya wuce duka,koda ko wani irin laifi yayi,haka take ganin ƴaƴan ƙauyen su suyi ta ma iyayen su raini amma ba mai dukan su,ashe ba haka abin yake ba. Iyah dake haɗa masu Ummie breakfast da sauri ta aje ta fito falon tana faɗin subuhanallah,lafiya wa ake ma.......! Turus tayi ta haɗiye maganan dake fitowa daga bakin ta ganin Ali zaki ake mari. Ƙasa yayi da kan sa,gaban sa na tsanan ta faɗi yana jira kawai tasamu bulala ta fara dukan shi,inde haka zaisa ta huce daga fushin da hau,don ko bijire mata da yayi akan auran Abeeda da wasiyar mahaifin shi da yayi batayi fushi haka ba,ta kauda komi don ta faranta masa ya rabbbb sa'iduni ya furta a zuciyar shi. "Aliyu,ni kake rainawa,ka ɗauke ni ako da yaushe ba abakin komi ba,banda mahimmanci awajan ka ko,tou wallahi Aliyu ko ban maka baki ba,duniya zata gaya ma,akoda yaushe ba burin ka ka faranta min ba,saide ka ɓata min ko,nagode Allag yasaka maka da alkhairi Allah yama albarka,Allah yabaka abinda kake nema duniya da lahira". Cikin mummunan ɓacin ran da bai taɓa sani zata iya ba take maganan,tana kai ƙarshe batare da tabi takan kowa ba dake falon fuuuuu ta wuce hanyar birthroom ɗin ta. Daga Iyah har JIDDA suna tsaye cirko-cirko,JIDDA cike take da dana sanin da bata gaya ma Ummie ba da tasan ranta zai ɓaci har ta mare shi ta gaya munanan kalamai akan shi. Iyah ko mamaki take mai Aliyu yayi haka da haryasa Hajiya tayi wannan mugun fushin akan sa. Cutie ko tana maƙure waje ɗaya jikin ta har rawa yakeyi. Jidda jiki a sanyaye ta ƙarasa inda yake tsaye dafe da kumatuka da sukayi ja ta duƙa ta ruƙo guywowin sa,wani abu yaji ya ziyar ce shi mai kama da shocking ɗin wutam lantar ki da sauri ya ja baya ƙirjin sa na tsanan ta bugu. Jikin ta sanyi yayi ahankali ta ta buɗe baki tace........! MORE COMMENTS MORE TYPING *ƘILA ZAKUJINI SHIRU KWANA BIYU SABIDA WANI UZIRI DAKE GABANA LOVE U OLL MY FANS💙❤️😘🥰* _typing🖌️_ *🔘JEEDDATOU🔘* NA MARUBUCIYAR:-👇 SAMHA ƳAR MACE KISHIYACE SURUKAR ZAMANI GIDAN SADIƘ MATAR BAHAUSHE TAHEER LAILAH A GIDAN MU SUKE NOOR JAHAN JAHAN KHATOON ND NOW AWANI GARI MALLAKIN:- *Khadeejour Muhammadou(THE CAT LOVER😸😹)* *(🌲S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE🌲)* https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo WHATSAPP NUMBER:- *08167151176* WHATPADD:- *MRS BASAKKWACE* GMAIL:- *MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM* IG ACCOUNT:- *KHADDEJATOU BASAKKWACE* TWITTER:- *@MRSBASAKKWACE* SNAPCHART:- *KHADEEJATOU BASAKKWACE* SADAUKARWA GA-:- *MOMYNA HAFSAT ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA UWAR MARAYU* *PAGE 56&60* *BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* ___________📖Jikin ta a sanyaye a hankali ta buɗe baki tace,"Yaya kayi haƙuri wallahi ban san ranta zai ɓaci ba harta yanke ɗanyen hukunci haka akan ka,don girman Allah kayi haƙuri ka yafe min". Ta ƙara she maganan da muryan kuka,ji yayi duk ba daɗi lokaci ɗaya a zuciyar shi,tayi matuƙar bashi tausayi yanda take maganan. Duƙawa yayi yana fuskan tan fuskan ta,sa hannun shi yayi a hankali kan lallausan fuskan ta ya share mata hawayen da suka zubo yana murmushi kamar bashi aka gama kashe da mari ba yace,"ƙanwata karki damu Ummie zata sakko zanje in bata haƙuri ". Yauwa abinda yakamata kayi kenan gadanga,fushin mahaifiya,bala'i ne da masifa akan ɗanta,hatta Allah fushi yake dakai in kasa mahaifiyar ka cikin ƙunci tashi kaje kabata haƙuri,don gujewa fushin ubangiji. Faɗan Iya da take tsaye ta bayan su tun ɗazun da sai yanzun tayi magana. Murmushi yayi yace,"zan bata haƙuri Iya,Ummie ta mai fahimta ce da haƙuri,nasan zata haƙura". "Yauwa tashi kaje". Faɗar Iya akaro na biyu. Miƙewa yayi yana fasha fuska,tare da riƙo haɓan ta yamiƙar da ita. Cutie da gudu ta taho wajan sa ta ƙan-ƙame shi,duƙawa yayi ya ɗagota ya shillata sama,sukayi hanyar bedroom ɗin Ummie,yana raɗa mata magana akunne tana gyaɗa kai tana murmushi. ************ "Abeeda wai ke bazaki bikin ƙanwar Najaatu bane a katsina,ki tambaye mijinki,in zai barki". Faɗar Aisha da suke zaune wajan shaƙatawa,suna ciye-ciye,duk sunci ado kamar bazasu mutu ba. "Kam bala'i da yasani da kar ya sani uwar su ɗaya uban su ɗaya,kayan ankon ma na wajan ɗinki,tafiyata zanyi,aini aduk fitata ban jiran umurnin Aliyu inde zan jira umurnin sa tou bazani ba,kulle yake min kamar matan mallam,ban ɗauka ba kuma bazan ɗauka ba yasani ,banda lokacin sa". Taɓa baki Aisha tayi cike da mamaki take kallonta ita ta isa tafita gaba gaɗi batare da sanin Abubakar ba da ta kwana gidan su,bikin nan ma ya tubure yace baiga uban da zataje yi ba biki katsina bikin ƙanwar ƙawan ƙawa cabɗi. "Azahiri ko tace,"ai da yaganki sakwa-sakwa rainaki zai rinƙa yi,mazan nan in baka nuna musu kaima jan wiya ne kana da taurin kai ai sai sharan gidan ka yafika walwala". "Kide bari ƙawata,ni wallahi ko ƴa mantawa nakeyi ina da ita,don shike mata komi,kwana biyu ma ban ganta ba ko tana gidan uwarsa ne oho,duk inda yakaita shi ya jiyo bani da asara". Lallai lamarin Abeeda yana matuƙar ba Aisha mamaki itade duniya kawai tasa agaban ta ,wani kallo Aisha ta watsa mata a zuciyarta tace ƴar wahala,kibiye ma matan bariƙi sunan ki bazawara wata rana,bakina ganin yana ƙaunar ki bazai iya turaki gidan ubanki ba,ni naiman haihuwar ma muke ido rufe bamu samu ba keda yake jaka ce kin samu kina wulaƙantawa,azahiri ko haƙori ta washe tace. "Ƙawata aikin ki nakyau wallahi,karki yarda ko ƙara haihuwa balle harki tsufa,atara miki ƴaƴa ,shikuma yaje ya ƙara aure". Kaɗa manyan idanuwan ta Abeeda tayi kamar zasu faɗo ƙasa tace,"aure ai wallahi Aliyu bai isa ya auro wata ƴar iska ba,yamin alƙawari dagani babu ƙari,ke in taƙai ce miki Aliyu bai iya haɗani da kowa a zuciyar shi balle har yaji shaawan yimin kishiya,haihuwa ko bazan iya buɗe mai ƙafa ba kullum yaci kamar yasamu shinkafa,ke in taƙaice miki ancire min mahaifa,yanda bazan haihu ba kwata-kwata,inci duniyata datsinke da kyau,ba wanda yasani sai ke da yau na faɗa miki don kema ƙawar arziki ce baki bani shawaran banza ". Ɓoye mamakin ta Aisha tayi da yacika zuciyarta lallai Abeeda ba Allah sam a gabanta,sheɗan yayi mugun buga mata gangar mu'azu tayi nisa banta jin kira a zahiri ko tace. "Shegiya ƙawata aikin ki na kyau sosai". Dariya suka fashe dashi tare da tafawa. Aisha na mata kallon sakarya. ************* "Atiƙa-Atiƙa ke Atiƙa tashi ki ɗaukan min tallan kokon nan rana nayi". Faɗan Zarah dakw tsaye kan Abeeda da tayi ɗaiɗaya kan gadon kara kannan tugu-tugu ba kitso,miƙa tayi ta miƙe tana gantsaro ƴan matasan nonon ta da suka ɓullo kamar kan gero,suma azaban taɓawan maza ne yasa suka fito,turo baki tayi tana bin Zarah da wani mugun kallo tace. Zara kin raina min wayo da yawa,ina bacci zaki wani tasheni akan banzar kunun ki ni bazani ba ki ɗauka da kanki kije ko kijira ƴar iskan can Sa'ina tazo ta je miki don wallahi bazani ba". Riƙe baki tayi tanabin Atiƙa da ido harta dasa aza tace,"kaji min shegiya ƴar iska nizaki gayama bazakije min tallan koko ba lallai wiyan ki ya isa yanka". Wallahi Zarah ko shure-shuren mutuwa kike bazani ba,zaki zubar min da aji talla Allah ya kiyaye wallahi in zaki jira Jidda ta dawo taci gaba miki ita ce bautantar ki amma bani ba,in kin matsy kije da kanki". Tana kai aya ta miƙe ta shige bayi batare da ta ɗauko buta ba. ********** Tura ƙofar suka tura a hankali suka shiga tana zaune bakin gado tayi tagumi lokaci ɗaya ya ɗuƙa guywowin sa a ƙasa ko ɗagowa ba tayi balle ta kalle su,lokaci ɗaya suka...............! MORE COMMENTS MORE TYPING🤗 _typing🖌️_ *🔘JEEDDATOU🔘* NA MARUBUCIYAR:-👇 SAMHA ƳAR MACE KISHIYACE SURUKAR ZAMANI GIDAN SADIƘ MATAR BAHAUSHE TAHEER LAILAH A GIDAN MU SUKE NOOR JAHAN JAHAN KHATOON ND NOW AWANI GARI JIDDATOU MALLAKIN:- *Khadeejour Muhammadou(THE CAT LOVER😸😹)* *(🌲S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE🌲)* https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo WHATSAPP NUMBER:- *08167151176* WHATPADD:- *MRS BASAKKWACE* GMAIL:- *MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM* IG ACCOUNT:- *KHADDEJATOU BASAKKWACE* TWITTER:- *@MRSBASAKKWACE* SNAPCHART:- *KHADEEJATOU BASAKKWACE* SADAUKARWA GA-:- *MOMYNA HAFSAT ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA UWAR MARAYU* *PAGE61&65* *BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* ___________📖Tura ƙofar suka tura a hankali suka shiga tana zaune bakin gado tayi tagumi lokaci ɗaya ya ɗuƙa guywowin sa a ƙasa ko ɗagowa ba tayi balle ta kalle su,lokaci ɗaya suka fashe da kuka lokaci ɗaya a tare,don Aliyu yasan tun yana ƙarami Ummie ta tsani kukan shi hankalin ta yanzun zai tashi ta shiga damuwa. Runtsa idon ta-tayi tana jin wani abu yazo ya tokare ƙirjin ta sam batason jin sautin kukan Aliyu,lokaci ɗaya ta maida kallonta kan Aliyu da Cutie da suke kuka duk sun zuba mata ido. "Ya isa haka Aliyu" ta faɗa da ƙarfi cikin ɗaga murya. Lokaci ɗaya suka haɗe kukan su kamar haɗin baki. ~*NIKO NACE LALLAI UBA DA ƳAR NAN TASHI ƳAN DRAMA NE,DAMA RAƊAN DAYAI MATA A KUNNE KENAN SUNA DARIYA ASHE DRAMA SUKA HAƊA*~ "Kasan bansan ganin hawayen ka a ƙasa shine zaka zo ka tasa ni gaba dakai da mai kama da kyanwar ~MRS BASAKKWACE~ da baƙaƙen idon ta kamar na ~ZEE YERO~ kuna min kuka ,kutashi kuban waje in kuka zakuyi min kuma ka tafi da ƴarka can ku ƙarata". Cikin ɗaga murya take maganan. Cikin marai-raicewa murya suka haɗa hannuwa suka ce," sorry Ummie". a taƙaice. Shiru tayi bata kalle su ba,bata kuma basu amsa ba. Cutie sauka tayi a jikin Aliyu tasa guywowin ta a ƙasa ta kamo ƙafar Ummie ɗaya da yake ƙasa tace,"Ummie Dadyna bazai ƙara ba wallahi,kiyi haƙuri,kinga Dady ma yayi kuka". Maganan taso taba Ummie dariya amma ta danne dariya tace,"tashi kiban waje ko inyi ball dake mai bakin tsuntsu kawai,nayafe masa na haƙura haɗa kayan ki kukoma gidan ku,maza tashi kikira Iya ta haɗa miki kayanki don banson takura". Kumburo baki Cutie tayi kumatun ta suka ƙara cikowa kamar na ~LIPTON GIRK~ tacw,"ni anan zan zauna Momyta bata son". Saurin toshe mata baki Aliyu yayi yace,"mata kull yana girgiza kai,kar na ƙara ji yanada nake son ki haka Abeeda kinji". Gyaɗa kanta tayi. Ummie ko tausayi ƴar jikan tata ɗaya tunƙwal take bata ace ka haifi ɗa kamar ka haifi ɗan shegw baka iya kula dashi balle kanuna masa so wannan wata irin ballagazan uwa ce. Ummie kinyi haƙuri ko?,,faɗan Cutie davta kafeta da ido. "Eh nayi badon halin ki ba da ubanki,tashi kije ki ce Iya ta baku abinci keda Auntyki JIDDA". Tashi tayi cike da farin ciki tai ma Ummie kiss a gefan kumatun ta ta fita da gudu cike da murna. Harara ta galla ma Aliyu da kan shi ke ƙasa tace," watou ka raina ni baka ɗauke ni da mutunci ba ko da matsayi shiyasa zan maka magana kasa takalmi ka shure maganata katafi lafani don baka da kunya kaje kace ma Ibrahim maine yayi haƙuri yabaka JIDDA koko tou wallahi sai kabani takaddan sakin ta don ko Ibrahim bai isa ya hanani ansan takaddan sakin JIDDA a hannun kaba,don haka ka gaggauta katashi ka kawo min takaddan sakin ƴata JIDDA don amana uwarta tabani ita don kawai anfi ƙarfinane na haƙura". _NIKO CIKE DA MAMAKIN MAGANAN UMMIE NAKE DAMA JIDDA MATAN ALIYU NE?,TOU TAYA HAKA TAFARU BAI ZAUNA DA ITA BA YA AURE ABEEDA BISA DUKKAN ALAMU ABIDA BATA SAN DA WANNAN JIƘAƘƘAN A ƘASA BA,RANDA TAJI KO AKWAU ƘURA A ƘASA🤔_ Tunda Ummie tafara maganan saki yaji kamar tana buga masa guduma akai a razane yake kallonta yana girgiza kai. "Wallahi Aliyu ko mi zai faru sai ka saki JIDDA wato kun haɗo baki da matar ka abaka ita kuje ku maidata boyi-boyi ku bautar da ita,tou bazan yarda ba aci amanar baiwar Allah ba marainiya". Cikin kakkausar murya take maganan tanayi tana murza ƴan yatsu. Aliyu ko sam a zuciyar shi bai ji zai iya sakin ta,don zaman da sukayi da ita a asbiti ta shiga ransa,zai lallaɓa Ummie ta barshi da ita ko bazasu tare ba. Sosa ƙeyan shi yayi yace,"Ummie itama ya kamata a samo mata malami da zai rinƙa mata lesson ta iya karatu da rubutu kafin akaita makaranta na boko dana islamiya". Buɗe baki Ummie tayi lallai Aliyu ya raina ta watou tana gabas yana yamma duk maganan da tayi masa bai ma shiga kunnesa ba ,wani magana ya kawo mata,ƙwafa tayi ta tashi ta shiga ban ɗaki,don bama tasan mai zata kuma ce masa ba. Murmushi yayi ya tashi ya fuce. Ba kowa falon sai ƙaran AC da TV ga daining nan alaman anci abinci an tashi. Suna gama cin abinci Cutie taja hanun Jidda wai suje ɗakin ta suyi wasa,hakan ko akayi JIDDA tabita bedroom ɗinta ta kwaso kayam wasan da Ummie ta sayo mata ta baje a tsakar ɗakin suka kama wasa JIDDA ko kamar saanta ta biye mata Cutie sai farin ciki take. Har ya shigo basu sani ba hankalin su ya ɗauku wajan wasa,ya jima tsaye yana kallon su yana jin wani nishaɗi daɓa Abeeda ce da bazai taɓa tinanin ƙara zama da wata mace ba. Nima nazo ayi dani faɗan Aliyu,dukkan atre suka ɗago suka zuba masa ido cike.......... ! *************************⬇********************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************* MORE COMMENTS MORE TYPING _typing🖌️_ *🔘JEEDDATOU🔘* NA MARUBUCIYAR:-👇 SAMHA ƳAR MACE KISHIYACE SURUKAR ZAMANI GIDAN SADIƘ MATAR BAHAUSHE TAHEER LAILAH A GIDAN MU SUKE NOOR JAHAN JAHAN KHATOON ND NOW AWANI GARI JEEDATOU MALLAKIN:- *AMMIEY CAT WOMAN(THE CAT LOVER😸😹)* *(🌲S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE🌲)* https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo WHATSAPP NUMBER:- *08167151176* WHATPADD:- *MRS BASAKKWACE* GMAIL:- *MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM* IG ACCOUNT:- *KHADDEJATOU BASAKKWACE* TWITTER:- *@MRSBASAKKWACE* SNAPCHART:- *KHADEEJATOU BASAKKWACE* SADAUKARWA GA-:- *MOMYNA HAFSAT ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA UWAR MARAYU* *PaGe66&70* *BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* ______📖Nima nazo ayi dani faɗan Aliyu,dukkan su a tare suka ɗago suka zuba masa ido,cike da mamakin yaushe ya shigo sam basuji takowar sa balan tana buɗe ƙofar sa. Idon shi cakkkkk akan JEEDAH da itama shi take kallo ido cikin ido kallon kallo suke mai juna,a hankali ta jaye idanuwan ta don lokaci ɗaya taga wasu kibiyoyi daga ƙwayan idanuwan shi suna fitowa suna shiga nata. Murmushi Cutie ta sake tare da haɗa hannayen ta-tafa su waje ɗaya tace,"perfect match,Dady ka ɗauke ta mukoma gidan mu wallahi kunyi matuƙar dacewa". Ɗan sosa ƙeyan shi yayi yana murmushi ya sa guywowin sa ƙasa yana shafa lallausan gashin kanta yace,"Cutie kin cika magana babu wani perfect match,kuci gaba da wasan ku,bari inje gida in dawo". "Dady Momy fa,kace mata nayi missing ɗinta over one billion". Shafo kanta yayi lokacin ɗaya takaici da haushin Abeeda ya sauka a zuciyar shi,ɗan gajeran tsaki yaja can ƙasan maƙoshin sa yace," zan faɗa mata,ki kula da kanki". "Ummie dai ta kula dani,ni mai zan iya ɓa kaina". Ta faɗa tana wani ƙyafta manyan idanuwan ta. Murmushi yayi tare da sake mata peak kiss a goshi,tare da miƙewa yana satan kallon JEDDATOU da kanta ke ƙasa kamar ruwa ya shanye ta-tawutsiyar ido ya ke kallonta har yafice,sai da ya tabbatar ya fice ya kulle ƙofar ya wani jingina da jikin ƙofar ya sauke wani nauyayyan ajiyar zuciya yana runtsa idon kallon ta yake cikin ido da ɗazun suke kallon juna,murmushi ya sauke harsai da kumatun shi suka lotsa a zahiri ya furta "gaskiyan kine CUTIE mun dace sosai". Jin motsi kamar wani na fitowa yasa yai saurin bin hanyar waje. Da mamaki Ummie take kallon bayan shi dama bai fita ba,mi ya tsaya yi,lallai sai ta tsaya tsayin daka akan Aliyu game da Jiddatou sai tayi bake-bake taga yanda zai ganta har ya hure mata kunne ta soshi. ********** Zai shiga kenan tana danno hancin motor ta waje,da baya yaja motor sa ya buga tagumi yana bin motor ta da kallo har ta ɓace ma unguwan kafin ya samu daman shigewa da tashi motor. Halin Abeeda yadena bashi mamaki tsoro kawai yake bashi ta rikiɗe ta sauya kamar ba Abeedan da suka soyayya ba kamar zasu lashe junan su,ko kaɗan a da bata son ɓacin ransa yanzun ko saide ya mutu ba ruwan ta da damuwar shi. Cike da tinani kala-kala yai packing ya shiga ciki. ********* Ɓangaran Abeeda koda tagan shi ko ɗarrr bata ji ba don bala'in haushi Aliyu ke bata,duk yabi ya takura ma rayuwar ta,gwamma da tabi shawaran AISHA da yanzun kanta yayi murfi yabarta a baƙauyiya bagida jiya,dayanzun ya ɗinkira mata ciki ya barta dareno,thank God da tacire mahaifan gaba ɗaya ta huta da ɗaukan ciki,in yaso in tama son wani haihuwar taje asa mata wani. _🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔OHHHHHH NI MATAR DATTIJO WACCE MIKI ANA CIRE MAHAIFA A MAYAR,LALLAI KINA RUWA GAKI GA KADA_ ********** "Yauwa ƴar halak irin albarka ƴaƴar da aka haifa tsiya na bacci,zo ki ɗau min tallan ku......! Sa'ina da yanzun shigowan ta ɗauke da jaka a kafaɗa,da alaman kwanan waje tayi,tawani katse Zarah da ganin ta yasa ta washe jajayen haƙoranta take mata maganan ɗauka talla. Kambala'i injiwa Zahra ɗaukan talla,ko kaɗan ba ajina bane,ke kika jama kanki da yanzun Jiddah na nan da ita zatayi miki,wa a birnin ma a ina take,kiyi yanda zakiyi ta dawo kici gaba da ɗaura mata tallan,amma ga dubu uku ki raba ma almajirai,amma wallahi bazan ɗau talla ba". Tana magana tana girgiza jiki tana ya mutsa fuska. Sa hannu tayi a acikin jaka ta ɗebo dubu uku ta watsa ma Zarah dake tsaye buɗe da baki. Zarah a hasale tace,"kaji min ƴan jaka da lalainta ƴaƴa ,tallan ce bakuyi min kun gwammace kuyi ta yawo kwararo,lungu-lungu,amma dai zanyi manaji,duƙawa tayi ta kwashe kuɗin ta kalmashe shi tasa a lalita,ɗaukan roban kunun tayi ta ɗaura akai tafita. *NIKO NACE YAFI MIKI,GA RANAN JIDDA DE KIN GANI,ƳAƳAN DA KIKA HAIFA SUN GAGARE YI MIKI WACCE KIKAI MA RIƘON SAKAINAN KASHI TAFI MIKI AMFANI DASU* ~ASALIN LABARI~ Malam Muhammad mai gemu,shine asalin kakan su Jiddatou,haifaffan ƙauyen........! MORE COMMENTS MORE TYPING _typing🖌️_ *🔘JEEDDATOU🔘* NA MARUBUCIYAR:-👇 SAMHA ƳAR MACE KISHIYACE SURUKAR ZAMANI GIDAN SADIƘ MATAR BAHAUSHE TAHEER LAILAH A GIDAN MU SUKE NOOR JAHAN JAHAN KHATOON ND NOW AWANI GARI JIDDATOU MALLAKIN:- *(THE CAT LOVER😸😹)* *(🌲S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE🌲)* https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo WHATSAPP NUMBER:- *08167151176* WHATPADD:- *MRS BASAKKWACE* GMAIL:- *MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM* IG ACCOUNT:- *KHADDEJATOU BASAKKWACE* TWITTER:- *@MRSBASAKKWACE* SNAPCHART:- *KHADEEJATOU BASAKKWACE* SADAUKARWA GA-:- *MOMYNA HAFSAT ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA UWAR MARAYU* *PAGE71&75* *BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* ___________📖 ~vASALIN LABARIN~ Mallam Ibrahim Muhammad mai Gemu shine sunan cikakken sunan mahaifin su JIDDATOU,su biyune awajan iyayen su,shida wan shi Abdullahi,sun taso wajan maƙwafcin su Mallam Ibrahim,kasancewar tun suna ƙanana ,Allah ya ɗauki ran iyayen su ta sanadiyan gobaran wutan da baa san dalilin tashin sa ba,kasan cewar maƙwaftakan da,da amin takan da,tafi na yanzun,ada maƙwafcin ka zaiyi yanda ya gadama da ƴaƴanka,saɓanin wannan lokaci da kowa nashi ɗan yasani. ~TO WANNAN KENAN~ Mallam Ibrahim yana da mata ɗaya Zarah wacce take ɗiya ga ƙanwar mahaifiyar sa,auren ladan noma akai musu,watou na jeka ga ɗakin ka. Shekaran su shabiyar basu taɓa koda ɓatan wata ba,hakan yasa shi zuwa maƙwaftan garin su ya auro wata yarinya mai suna Aisha. Zarah tayi bala'i tayi bore ba,amma hakan bai hana Ibrahim aure ba. Aisha tasha tsagwama da kyara a wajan Zarah,bata da sakewa sai in Ibrahim na gida,inko bayanan bautan duk duniyan nan sai tayi shi. Shekaran ta guda,sai ga ciki ya bayyana a jikinta. Zarah kamar tai hauka,ta kasa zaune ta kasa tsaye,alokacin ta fantama zuwa gidan bokaye,duk inda taje saide aci mata kuɗi ace cikin zai zube,amma shiru,maye yaci shirwa. Wahal-halun duniyan nan ta ɗauko ta ɗaura mata. Inda ko ɓangaran Ibrahim tarai-raiya kawai takesha kamar ƙwai acikin cokali,komi yasamo Aisha,komi Aisha,ran Zarah ɓaci yakeyi kamar zata mutu,tai ta zage-zage da habaice-habaice. Bayan wata tara ta haifo ɗiyarta mace,mai kama da ita,buɗan bakin Zarah ko cewa tayi taga haihuwa zataga yanda yarinya zata rayu a doran ƙasa. Aisha ko addua kawai take ma ƴarta Allah ya tsareta,Ibrahim ko komi lodowa yakeyi,jikin sa na rawa,da wanda zaiyi amfani da wanda bazaiyi amfani ba siyowa yakeyi. Ranan suna yarinya taci sunan mahaifiyar su Hauwa'u,suke kiranta da JIDDATOU,kulawan duniya Ibrahim ya ɗowa ma wannan ƴa,har matan ɗan uwan shi sunzo daga birni da ɗan uwan nashi da ɗansu ɗaya Aliyu mai shekara goma,Aliyu ko yarinyar nan wuni take awajan sa,har Aisha kece masa kana son ta nabaka ita,sai yace eh Ummie na zamu tafi da ita ko?,Ummie ta gyaɗa kai suyita dariyan yarintar sa. Zarah ko kamar ta kashe su don haushi da takaici,ta tsani matan Abdullahi,basa zama inuwa guda. Haka rayuwa taci gaba da tafiya da daɗi ba daɗi,Aisha nata rainon ƴarta cikin kulawa haka mahaifinta ta,bata fito da ƴarta tsakar gida matuƙar Zarah na nan,don cin zalinta take da gan-gan. Sai da Jiddatou tashekara biyu da rabi lokacin Aisha ta yayeta,tana yawo ko ina,sai ga Zarah tafara laulayin ciki. Murna wajan Aisha kamar itace keda cikin,Ibrahim yanuna farin cikin sa,amma ba kamar cikin Jidda ba. Zarah ko andena sa riga sai ɗaurin ƙirji,tun kafin ciki yafito ake turo ciki,tsurfa kala-kala,kilibi-bi iri-iri,kitifi ba wanda batayi. Watan ta tara da kwanaki ta haifo ƴarta mace itama mai kama da ita,Ibrahim yayi hidima amma bakamar haihuwar Jidda ba,hakan ya ƙulal da Zarah,a tsakanin ne Aisha ta fara sabon laulayin ciki,ran Zarah yayi matuƙar baƙi. Tunda Aisha ta ɗau cikin nan yau lafiya gobe ciwo,ba mai kula da ita gashi ƴarta batavda wayon yin abubuwa haka take cijewa ta daure tayi ayukan gida harda na Zarah. Watarana ciki dare naƙuda ya taso mata,gashi Ibrahim baa ɗakinta yake ba,gashi bata isa ta je ta buga musu ba tasha zagi,tayi matuƙar galaibaita tafita hayyacinta. Jidda ko baccinta kawai take batasan maike faruwa ba. Tun Aisha na iya motsi har tazo bata iyawa. Ko da safe tayi Zarah sai ƙwala mata kira takeyi tajita shiru ban kaɗo ƙofar da zatayi ta iske ta kwance male-male cikin jini ga ɗa yafito babu mai motsi cikin su,ga Jidda nacan na bacci. Wani mugun ƙara ta sake wanda yai sanadiyan tada Jidda daga bacci a firgice,Ibrahim ya fito daga make wayi ya yarda buta yana tambaya lafiya. Zarah ko komawa tayi ta zauna daɓas tana kurma ihu,kan kuce mi gida ya cika sa mutane. Hankalin Ibrahim yayi ƙololuwar tashi,take aka kaita asbiti aka tabbatar musu da rai yayi halin sa. Dawowa akayi da ita aka kai mata sutura aka kaita gidan ta na gaskiya,bayan share zaman bakwai ƙanwar Aisha taso ta ɗauketa Ibrahim ya hana,haka Ummie taso ta ɗauketa Ibrahim da suke kira da Abba ya hana,alokacin ne suka yanke shawara da ɗan uwan shi Abdullahi da matan shi Ummie na haɗa auran Jidda da Aliyu,basu ko bar garin nan ba saida aka ɗaura aure,bada sanin Zarah ba,daga dangin Aisha sai Abba a ɗan shagon ƙofar gida sukayi cikin sirri . Ummie taso ta tafi da ita tasata makaranta amma ina Abba ya hana,yace sai in zata tare yasata anan gaba,ai bokoko a wuta ne,miye amfanin bokon mace. Ahaka suka tafi suka barta,bada son ran Ummie ba,lokacin Aliyu yana india yana karantun shi,bai san wani wainar ake toyawa ba. Haka rayuwa taci gaba da tafiya ba daɗi ɓangaran Jidda don tun tana ƙarama ta ke amsan gasashiyar gyaɗa a hannun Zarah ,bayab haihuwar Atiƙa zarah ta ƙara haihuwar Sa'ina. Ta sangarta su sosai bata son mai zai taɓa su,gashi sun rainata tun suna ƙanana suke zaginta,basa ganin girman kowa. Jiddatou ko wuni takeyi yawon talla na safe daban na rana daban na yamma daban. Uƙuban rayuwa ba wanda bata ganshi ba. Lokacin da takai minzilin girma,ana ta tururuwan nema auran ta,amma zarah ta hana,tace ita da aure sai bayan ranta,rayuwar JIDDATU a tallatan zai ƙare. Kwatsam aka kira Abba aka sanar dashi mutuwan ɗan uwan shi tunƙwal guda ɗaya,sanadiyar haɗarin motor zuwa kaduna,wajan ɗaurin auran ɗan abokin sa,ya shiga tashin hankali,sosai na rashin ɗan uwan sa,da ƙyar ya dawo hayyacin sa,don Hajiya Asma'u tafishi jarumta da take,haka aka share zaman bakwai, Lokacin Aliyu har yagama bautan ƙasan sa yasamu aikin bank UBA,kuma sun haɗu da wata yarinya Abeeda ɗiyar ɗan babban kasuwa Manmadu Sharif mai goro,suna soyayya sosai da son junan su kamar su lashe junan su sabida ƙauna. Ko kaɗan bata son ɓacin ran Aliyu. Dayazo ma Ummie da buƙatan auran Abeeda,tatuna masa da yana da wani aure fa a ƙauye in ya matanta ya tuna. Aliyu shafa ma idon shi toka yayi yanuna baisan da wannan labarin ba,kamar sa ace yazauna da ƴar ƙauye,shi yama Abida alƙawarin bazai mata kishiya ba,kuma bai son ɓacin ran ta. Ummie taji matuƙar baƙin cikin maganan Aliyu,amma ta danne zuciyarta tanuna mai ba komi,taje ta samu Ibrahim a ƙauye,yaji takaici,amma sanin halin ɗan yau yasa ya daure ma zuciyar sa,shiyaje yanemo ma Aliyu auran Abeeda kuma ya amso masa auranta. Ko sati baayi ba suka fara samun matsala da Abeeda Abeeda kwalliyan wajene amma bata iya komi ba,bata iya ladabin kula da miji ba,shigo-shigo ba zurfi tayi masa sam bai gane waye ita ba sai bayan aure,satin su uku tafara laulayin ciki,ta tada rashin mutunci sai de acire ita haihuwa ba yanzun ba,bata son ta tsufa da wuri,ga Aliyu nason haihuwa da siɗin goshi ya shawo kanta ta bar ciki,da tatashi haihuwa ko aiki ta sa akayi mata,wai ita batason wahalan naƙuda ta mutu bata gama cin duniyarta da tsinke ba ba,anko ciro mata ƴa mace,in Aliyu farin ciki kamar ya zuba ruwa a ƙasa yasha,haka Ummie ranan suna taci sunan Ummie watao Nanah Asma'u,Nany aka ɗauka don kula da Nanah wanda Aliyu ke kiranta da Cutie ,bata samun kulawa sam wajan mahaifiya,ko arzikin nono bata samu abata saide tasha madaran yara,Nany ko sabida wulaƙancin Abeeda basa ko daɗewa suke guduwa kawo wasu da haka har Cutie ta girma tayi wayo yakaita school sam bata samun kulawa wajan Abeeda. Abubuwan Abeeda kullum ƙara yawa yakeyi,Aliyu ganin ta yakeyi kamar mai aljanu wani lokaci,sam bata waiwayen bayanta. Tun daga lokacin da Aliyu ko yayi aure Abba yasa maka sa damuwa harta kai shi da rasa ɓarin jikin sa,jinin sa kullum hawa yakeyi ,gashi babu mai temakon sa ZARAH ce ta zama mijin inko Jidda batayi talla ba baza suci ita da baban taba saide su zauna da yunwa,ZARAH da ƴaƴanta ba mai zuwa duba Abba Jidda ke hidima dashi Ƴaƴanta ko ba wanda yanzun ba'a kawo kayan nagani ina son shiba,duk da suna yawo ba ma maza haɗin kai acikin gonaki ba komi bane a wajan su,basa ganin mutuncin kowa harda na uwar tasu,bata isa tasa a ayi ba kuma bata ta hana ba su hanu ba *WANNAN KENAN,ATAƘAICE,A GURGUJE* Ɓangaran Abeeda shirin zuwa katsina biki kawai akeyi. MORE COMMENTS MORE TYPING _typing🖌️_ *🔘JEEDDATOU🔘* NA MARUBUCIYAR:-👇 SAMHA ƳAR MACE KISHIYACE SURUKAR ZAMANI GIDAN SADIƘ MATAR BAHAUSHE TAHEER LAILAH A GIDAN MU SUKE NOOR JAHAN JAHAN KHATOON ND NOW AWANI GARI JIDDATOU MALLAKIN:- *(THE CAT LOVER😸😹)* *(🌲S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE🌲)* https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo WHATSAPP NUMBER:- *08167151176* WHATPADD:- *MRS BASAKKWACE* GMAIL:- *MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM* IG ACCOUNT:- *KHADDEJATOU BASAKKWACE* TWITTER:- *@MRSBASAKKWACE* SNAPCHART:- *KHADEEJATOU BASAKKWACE* SADAUKARWA GA-:- *MOMYNA HAFSAT ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA UWAR MARAYU* *PAGE76&80* *BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* ___________📖Ɓangaran Abeeda shirin zuwa katsina biki kawai takeyi yayinda Aisha zugata kawai take tana cewa itama zataje. Bata damu da ta gaya ma Aliyu ba,ko ta kan shi bata bi ,in sun haɗu a get ne zai fita zata shigo ko zai shigo zata fita. ******* Ɓangaran Abba yana samun kulawa sosai daga wajan likitoci da Aliyu,alhamdulillahi sauƙi na samuwa,jikin shi na motsawa ta dalilin gashin ƙashin da yake samu daga ƙwararrun likitoci. ********* "Jidda zaki iya gane asbitin da Ibrahim ke kwance?. Faɗan Ummie da take zaune kan luntsa-ts-tsun kujeru falon ta. Tana sanye cikin riga da zani mai launin purple da pink ɗinkin dogon riga ta kashe ɗaurin Aisha baban gida,wani abun sai wanda ya gani. Cutie na zaune gefeta ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tana sanye da wando jeans blue da riga yellow an gyara mata gashin kanta. Jidda na zaune daga ƙasa can gefe daga ƙasa,Ummie tayi-tayi ta hau saman kujera taƙiya. Girgiza kai tayi alaman aa,kafin tace,"aa Ummie so ɗaya mukaje". Ummie ɗaukan wayarta tayi dake gefe,don rabon Aliyu da gidan watou fushi yake da ita daga mai faɗa. Lalubo number shi tayi ta buga masa kira,ringing biyu ya ɗaga,bata amsa sallaman da yake mata illa cewa datayi kazo gida yanzun nan ina son ganin ka. Bata jira mai zaice ba ta datse wayar. Ajiyan zuciya Aliyu ya sauke mai nauyi,gaban shi na faɗi, yana tunanin mai kuma yayi. Gama haɗa takaddun dake gaban shi yayi yasa laptop ɗinshi acikin breif case ɗin shi ya kulle ya kwashi wayar shi da key ɗin motor shi ya fito yana rataye breif case ɗin a kafaɗan shi. Biyawa yayi gidan abinci yasaya yanufi asbiti yakai ma Abba yasamu jikin nasa saide ace alhamdulillah. Gaisawa sukai Abba yana ta shi masa albarka yana amsawa cikin jin daɗi. "Ali,ina ƙanwar Jidda kace mata ina kewar tA". Faɗan Abba dake zaune tsakiyan gado ya jingina da bango. Wani nauyi da kunya Aliyu yaji ya rufe shi,yakamata ko ya kawo JIDDA gidan ma bai samu zuwa ba sabida abubuwa yayi mai yawa. Murmushi yayi a zahiri yace,"Abba suna gaisheka ifa da Ummie da Cutie,yau ma Ummie tace zan kawo su". Yagaya masa haka ne don bai sanmai zaice mata. Allah sarki Maa'u ina amsa faɗan Abba. Murmushi yayi Aliyu yamiƙe yai masa sallama yace zasu zo anjima. Kai tsaye gidan Ummie ya nufa ,a falo ya iske su suna kallo a tashan zeeworld. Bayan yayi sallama sun amsa,ya gaida Ummie,Cutie ta gaida shi kafin Jidda ta gaida shi,ya amsa cikin kulawa. Zama yayi agefe Cutie yana riƙo hannun ta,amma hankalin shi yana wajan Jidda yana wani satan kallon ta. Ummie kula da tayi da haka yasa ta tawani haɗa rai tace,"Jidda ,Cutie ku tashi ku shiga ciki mangariba ta ƙarato". Bako musu tatashi jikinta asanyaye ta matso inda suke zaune ta sa hannu zata Cutie na zare hannun ta jikin Aliyu ta miƙa ma Jidda hannun ta. Riƙe mata hannu tayi suka nufi hanyar bedroom ɗin su. Zazzare ido Aliyu yaketayi kamar yayi ƙarya. "Sannu Aliyu nikake fushi dani,don nayi ma faɗa". Faɗan Ummie da take kallon sa. Murmushi yayi ya kwanto kan kafaɗan ta cikin shagwaɓa yace,"Ummie ba haka bane,ayyuka suka min yawa,wa ƴanda kwana biyu banyi ba a office,wallahi kuna raina". Ƙwafa tayi kafin tace,"ni ɗaga ni karka karya ni ,ƴarka ta haumin jiki kaima kazo duk so kuke ku karya ni". Murmushi yayi tare da ƙara shigewa cikin jikin ta yana ƙyalƙyale dariya. Ran ƙwashi ta buga masa akai,da sauri ya saketa yana sosa inda ta buga masa ran ƙwashin. "Wani asbiti Ibrahim yake?. Ta tambaye shi tana kafe shi da ido. "Ummie Uduth yake fa". "Shine baka ji zaka iya gayamin ba?. "Ummie dama zan kaiku anjima ku shirya". "Tou Allah yakai mu,kaima Allah yama albarka". *********** In banda wulaƙanci taya bayan shekara goma da kuka kawo tsiyan auran ku zaku dawo kuce abaku abinku,gaskiya bazai saɓu ba bindiga a ruwa........! MORE COMMENT MORE TYPING _typing🖌️_ *🔘JEEDDATOU🔘* NA MARUBUCIYAR:-👇 SAMHA ƳAR MACE KISHIYACE SURUKAR ZAMANI GIDAN SADIƘ MATAR BAHAUSHE TAHEER LAILAH A GIDAN MU SUKE NOOR JAHAN JAHAN KHATOON ND NOW AWANI GARI JIDDATOU MALLAKIN:- *(THE CAT LOVER😸😹)* *(🌲S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE🌲)* https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo WHATSAPP NUMBER:- *08167151176* WHATPADD:- *MRS BASAKKWACE* GMAIL:- *MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM* IG ACCOUNT:- *KHADDEJATOU BASAKKWACE* TWITTER:- *@MRSBASAKKWACE* SNAPCHART:- *KHADEEJATOU BASAKKWACE* SADAUKARWA GA-:- *MOMYNA HAFSAT ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA UWAR MARAYU* *PAGE81&85* *BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* ___________📖In banda wulaƙanci taya bayan shekara goma da kuka kawo tsiyan auran ku zaku dawo kuce abaku abinku,gaskiya bazai saɓu ba bindiga a ruwa". Faɗan Zarah da take tsaye tana ta girgiza-girgize kamar bishiyan ceɗiya,tana wani fusgo masifa,masifa na fisgenta,kunga matan nan masu kamar goran bobo masifa a jinin su take. "Mtsewww ku at ciki,da hankalin mu baza mu ɗauka gurɓatacce fura musa a cikin muba,don haka mun baku sati ɗaya kudawo mana da dukiyan auren ɗanmu". Faɗan wata mace siririya doguwa,itama cike da masifa take maganan. "Ladi wallah bazamu dawo dasu ba,aure babu fashi,in kunga ko baayi auran nan ba sai bayan raina". "Tou matsiyaciya da ranki ko zaki ga mun rusa shi,ina zamu ɗau ƴar iska lalatatta mukai zuri'an mu,zuri'an muko ba lalatacce baragurbin ƙwai". "Ladi kika ƙara cema ƴata ƴar iska sai nayi ƙasa-ƙasa dake,ai ko ubanta bai isa ya hanata ba,don shima da gindinta ya ganta". "Ahhh Zarah dama nasan da ɗaurin gindin ki take aikata duk wata tsiya kwararo-kwararo,don haka baza'a kwaso ƙanjamau a ƙa-ƙaba mana ba". "La'ilafi ƙafa dubu,mai bakin karnuka,baa ce ɗanku keda ƙanjamau ba da suke zuwa hausa,duk ƴaƴan arna sun gama lalata dasu sai ƴata da ko sokoto bata taɓa zuwa,kenan illela bata sanshi ba,duk iskancin ta iyakan ta ƙauyen nan da gida fura,da ɗanboka,da su lakoda da iddirawa,da sagera". "Wallahi Zarah kinyi asaran rayuwar ki,kinzo duniya a banza haka zaki koma a banza keda ƴaƴanki,jakar gidan ki tafiki hankali da tunani,kina uwa amma kina alfahari kina gaya ma duniya ƴarki na yawon iskanci?. Faɗan Larai maƙwafciyan su,da tun ɗazun tana sauraran hayaniyan dake faruwa,duk maƙwafta suna ji,amma ba wanda zayi magana ko yabada haƙuri gudun cin mutuncin Zarah. Sheƙeƙe Zara ta kalleta tawani taɓa baki tafa hannu tayi tace,"tou maziga maƙwan gara masu zuwa lahira daƙoƙan dambu,munafukai kunan ku na gidan mutane kuna sauraran abinda ke wakana,ina ruwanki Larai,munafuka,kowa da guntun kashin shi a gindin shi amma ya take ya rinƙa hango na wani". "Gaskiya ko inzaki mutu sai na faɗa miki donni bani tsoronki bani munafurci". "Ki riƙe gaskiyan ki annami-miya,banso". "Dama bance kiso ba,matsitaciya mahaukaciya jakar da kike kiwo tafiki tinani". Nan fa faɗa ya koma kan Larai,sukai ta zuba ruwan masifa,su Ladi ƴan kallo suka koma,da ƙyar surukan Larai suka jata zuwa gida,don abin nanema yakai ga dambe. Ladi ko wucewa sukai ita da Sabuwa suna jaddada ma Zarah zasu dawo tanemo musu duk abinda ya kawo da abinda yakashe mata. Zarah wuni tayi tana zage-zage ranan a ƙauyen,daga ƙarshe shirya wa tayi ta nufi gidan aminiyarta Abu,don neman mafita da shawara. *************** Kamar yanda Aliyu yace ko bayan mangariba nayi ya,duk sun shirya,yanadawo wa sallah ya ya iske su afalo shi suke jira,dukkan su suna sanye cikin shigar abaya,don Aliyu abaya yasayo ma Jidda don yana matuƙar son abaya,duk yawanci in zai sai ma Abeeda kaya abaya yake saya mata,kafin yasai mata atamfa yana jimawa ko leshi,amma duk wani sabon style na abaya sai yasayo mata shi,yana son mace ƴargayu,amma kashe gayun Abeeda yayi yawa bata iya tsinana ma kanfa komi sai gantali,ɗan gajeran tsaki yaja a ƙasan zuciyar shi,a zahiri kuwa murmushi ya sake yana ɗaga Cutie sama da take sanye cikin blue abaya yayi matuƙar mata kyau Ummie ko nata baka ce tayafa gyalan akai,Jidda ko nata yellow ce duk da rashin wayewa da iya kwalliya ta ɗanyi kyau,itama gyalen tayafa akai. Cutie ƙyal-ƙyalewa tayi da dariya tace,"Dady nafara gilma kar ka yaddani". Dariya Aliyu ya sake yana dungurinta a goshi yace,"ina girman yake? Yai mata maganan da sigar tambaya. "Gashinan Ummie tashe in inacin abinci zan girma kamar ka". Dafe goshi Ummie tayi cikin ƙosawa da maganan Cutie tasan inta sake musu fuska sai sukai ishaai basu fita ba. Tace,"Aliyu ajeta,karku tasa mu a gaba da surutun ku na tsiya kaida mai bakin tsuntsu,dare nayi". Dariya suka ƙyalƙyale dashi,Jidda ko ɗan murmusawa tayi Ummiw ƙara haɗa giran sama dana ƙasa tayi ganin sun ɗau maganan ta wasa ai Aliyu naganin haka bai san sanda ya.............! *SHIN WAI YA ZATA KAYA TSAKANIN ZARAH DASU LADI,WANI SHAWARA ABU ZATA BA ZARAH?,SHIN SHAWARAN ZATA KAI SU GA ƁILLEWA KO ƘAƘA?* _COMMENTS ƊINKU SHI ZAI BANI ƘWARIN GUYWAR CIGABA DA TYPING GABA GAƊI 🤗👌🙅‍♀️_ MORE COMMENTS MORE TYPING🤗 _typing🖌️_ ~*Lokaci yayi da zaka daina mamaki akan butulcin mutum, kowa zai iya butulce maka, kowa zai iya cin amanarka, kowa zai iya zaluntarka.*~ ~*Tsakanin shimfiɗar fuska da labulen ɗaki basu da bambanci, labule idan babu shi za kaga komai na ɗaki, murmushi idan babu shi za kaga mummunan kuɗirinshi🤗👌*~ *🔘JEEDDATOU🔘* NA MARUBUCIYAR:-👇 SAMHA ƳAR MACE KISHIYACE SURUKAR ZAMANI GIDAN SADIƘ MATAR BAHAUSHE TAHEER LAILAH A GIDAN MU SUKE NOOR JAHAN JAHAN KHATOON ND NOW AWANI GARI JIDDATOU MALLAKIN:- *(THE CAT LOVER😸😹)* *(🌲S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE🌲)* https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo WHATSAPP NUMBER:- *08167151176* WHATPADD:- *MRS BASAKKWACE* GMAIL:- *MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM* IG ACCOUNT:- *KHADDEJATOU BASAKKWACE* TWITTER:- *@MRSBASAKKWACE* SNAPCHART:- *KHADEEJATOU BASAKKWACE* SADAUKARWA GA-:- *MOMYNA HAFSAT ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA UWAR MARAYU* *PAGE86&90* *BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* __________📖Dariya suka ƙyalƙyale dashi,Jidda ko ɗan murmusawa tayi Ummie ƙara haɗa giran sama dana ƙasa tayi ganin sun ɗau maganan ta wasa ai Aliyu naganin haka bai san sanda ya sauke Cutie ya ɗau basket ɗin da yagani gefen kujera,yasan abincin da zasu tafi ma Abba dashi ne yai hanyar fita Ummie harara tabishi dashi tana ƙwafa. Jin tayi ƙwafa yasa Aliyu sakin murmushi,bai san mai yasa ba yanzun ko kaɗan Ummie bata da wiyar hasala,da kuma ba haka take ba,tana da matuƙar kauda kai. Cutie sa hannun ta tayi ana JIDDA ,yayinda Jidda ta riƙe hannun ta suka bi bayan Ummie. Gida gaba Cutie ta shiga ita da Dadynta yayinda Ummie da Jidda suke gidan baya,hon yayi mai gadi ya wangale masa ƙatoton get ɗin gida ya fice. ************ Hajiya Abeeda ko ansha ƙunshi da saloon da kitson gashin doki har baya ba ita ta koma gida ba sai 09:30pm bayan ra amshe ɗinkunan ankon ta natafiya gobe *🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔ABEEDA KINA RUWA KUSA DA KADA TSUNDUM,KINA TA SHIRI BATARE DA SANIN MIJINKI KO IZININ SHI BA* ********* Saida suka biya super market ya loda musu chocolate kafin suka ƙarasa asbiti. Sun iske Abba na zaune kan dadduma aƙasa yana ta lazumi. Mai kula dashi yana zaune kan kujeran ƴan dubiya. Jidda ganin baban ta yaji sauƙi har yana sallah,bata san sanda ta ɗaga hannu ba tace,"(ALHAMDULILLA),Allah kaine abin godiya da kaba ma mahaifina lafiya Allah ya ƙara masa lafiya da nisan kwana". Duk ido suka zuba mata cike da mamaki,yayi da Abba ganin ta yasa shi washe baki kamar yau take sallah,kuma yau ne yafara ganin ta cikin kyakyanwan shiga da yake ta mata mafarki kullum yace. "JIDDATU NA ,Jiddatulkhair ki gode ma Allah ki ƙara gode masa,kuma ki gode ma Aliyu ta sanadiyan shi nasamu lafiya,dabadin shi ba da yanzun ban san wani hali nake ciki ba". Faɗawa tayi jikin sa tana kuka farin ciki yayin da ya rungumeta tsammm a ƙirjin sa. Aliyu wani irin tausayi suka bashi,lallai Jidda damahaifinta ba ƙaramin ƙauna ke tsakanin suba. "Ummie tace,"lallai Iro baka ganin kowa sai ƴarka ko?. Tai maganan cikin fara'a da sigar tambaya. Murmushi yayi yan dukan bayanta ahankali yace,"naganki mana Maa'u ai yanzun zamu gaisa". Aliyu aje kwandon dake hannun shi yayi ya jawo ɗayan kujera ya ajeta bayan Ummie. Ummie zama tayi tana faɗin sannu Ibrahim Allah ya ƙara lafiya,ai ɗannan naka bai faɗa min kai yake kawo ma abinci ba,sai da yakai Jidda". Abba murmushi yayi yana shafa bayan Jidda yace,"Jidda kuka ya isa haka". Kamar jira takeyi yai magana ta haɗiye kukan sai ajiyar zuciya takw saukewa. Gaisuwa sukai da Ummie Cutie ta gaisheshi haka Aliyu,take hiran yaushe gamo ya ɓarke a tsakanin su,basu sukabar asbitin ba sai 11:00pm saura,daƙyar Jidda ta yarda zata bisu,shima saida Abba yasa baki,ta tafi tana kewan baban ta dason kasancewa dashi. ********** Yana aje su yajuya kan motor yafita ya nufi gidan shi don wani mugun bacci yakeji. Bayan yayi parking ya nufi hanyar da zai sada shi da babban falon gidan,key yasa ya buɗe yashiga. Da mamakin sa ya ganta a falo ya wani ɗauke kai ya kauda mamakin sa kamar bai ganta ba ya wuce yanufi ƙofar da zai buɗe falon shi yashiga bedroom ɗin sa kamar daga sama yaji ance Aliyu tsayawa yayi cakkkkkk bai amsa ba kuma bai buɗw ƙofar ba balle ya shiga. Bata damu ba da ya amsa ko kar ya amsa taci gaba da magana kamar haka,"gobe tafiya zanyi zuwa katsina,bikin ƙanwar ƙawata,na faɗa maka don halin rayuwa ba wai izinin ka nake nema ba ko umurnin ka,tafiyata zanyi gaba gaɗi da kayarda da kar ka yarda". Cike da mamaki yake kallon Abeeda shi take gaya ma magana ba ladabi balle biyayya cabɗi dole ya gyara mata zama. Murmushin da yafi kuka ciwo,zuciyar shi tamai wani tuƙuƙi kamar an dasa dutse ya dannw kamar bai damu ba dawawa yayi inda take zaune yace ,"daga yau in kika saka ƙafa kika fita gidan nan wallah Abida abakin auran ki". Yana gama maganan bai jira mai zata ce ba ya juya da sassarfa ya buɗe ɗakin sa ya shige ya bugo ƙofa. Abeeda ko cike da rashin fahimta take binsa da kallo har ya shige taɓa baki tayi ta ɗaga kafaɗa alaman ba damuwa a tare da ita miƙewa tayi ta shige part ɗinta ita. ********* "Zarah ai cin kutumar uban su zakiyi ki shirya muje masallata aiki kamar yankan wuƙa sha yanzun magani yanzun". Zarah ce zaune ita da ƙawarta akan tabarman kaba da ta gama karanta mata halin da take ciki. Daga ganin itama Abun watsatstsiya ce kalar Zarah mara mutunci. *SHIN ABEEDA ZATA FITA KO ƘAƘA,INTA FITA INA MAKOMAR AURAN TA DA ALIYU?????* *SHIN ZARAH ZATA AMINCE DA MAGANAN ABU AMINIYAR KO ƘAƘA?* MORE COMMENTA MORE TYPING ~*Lokaci yayi da zaka daina mamaki akan butulcin mutum, kowa zai iya butulce maka, kowa zai iya cin amanarka, kowa zai iya zaluntarka.*~ ~*Tsakanin shimfiɗar fuska da labulen ɗaki basu da bambanci, labule idan babu shi za kaga komai na ɗaki, murmushi idan babu shi za kaga mummunan kuɗirinshi🤗👌*~ *🔘JEEDDATOU🔘* NA MARUBUCIYAR:-👇 SAMHA ƳAR MACE KISHIYACE SURUKAR ZAMANI GIDAN SADIƘ MATAR BAHAUSHE TAHEER LAILAH A GIDAN MU SUKE NOOR JAHAN JAHAN KHATOON ND NOW AWANI GARI JIDDATOU MALLAKIN:- *(THE CAT LOVER😸😹)* *(🌲S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE🌲)* https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo WHATSAPP NUMBER:- *08167151176* WHATPADD:- *MRS BASAKKWACE* GMAIL:- *MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM* IG ACCOUNT:- *KHADDEJATOU BASAKKWACE* TWITTER:- *@MRSBASAKKWACE* SNAPCHART:- *KHADEEJATOU BASAKKWACE* SADAUKARWA GA-:- *MOMYNA HAFSAT ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA UWAR MARAYU* *PAGE91&95* *BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* *WANNAN SHAFIN TUKUYCINE GAREKU,:-AUNTY JAMILA ALIYU,MAMAN FARISA,DA MAMAN ABUBAKAR,INA JIN DAƊIN COMMENT ƊINKU SOAO ALLAH YABAR ZUMUNCI DA ƘAUNA🥰😘😍* ___________📖Daga ganin Abun watsa-ts-tsa ce kalar Zarah mara mutunci. Kyaɓe baki Zarah tayi tace," nifa bana son harkan bokaye nafi gane a watse a rashin mutunci ,ayi tsiya a dai-daita nafi gane wannan yaren". "Tsiyata dake fa sakaryace Zarah,ana nuna miki hanya ɓullalla kina bin lungun da bazai ɓulle dake ba,mtsewww,ni tashi kibar min gida tunda bazaki ɗau shawarata ba". Abu tai maganan cikin ɓacin rai tana turo kallabi gaba. Zarah washe jajayen hauru tace,"haba ƙawalliya,na amince gabe daka sammako zanyi inzo mutafi". Abu washe itama haƙora tayi tace,ko kefa ƙawalliya,sai an raba shi da har uwar shi,saide tsinannun su zama ƴan kallo,ki tabbata kina da kuɗi sosai don ke zaki min kuɗin mashin". "Ai ke daɗina dake son banza,kina da kuɗi kina ɓoye shegen wayo kamar bulbuli". Tana magana tana galla ma Abu hararan wasa. "Ina ruwana ai lalurat ki ta ba nauna ba,in bakiyi ai shikenan". "A'a aminiyata zanyi mana". Nan sukai ta shirya yanda zasu tafi daga ƙarshe tai ma Zarah rakiya tatafi. ************** Ɓangaran Abeeda kuwa tun da safe ta tashi tai wanka ta shirya,ta riga ta gama shirya a kwatin ta tsafff duk abubuwan da zata buƙata ta haɗa ta saka,shirya tayi cikin abaya blue tasa takalmi fari,tayafa ,ta kwashe wayoyinta da key ɗin motor ta taja akwati ta fita,ba tare da tinanin komi ba. Abayan motor tasa akwatin ta kafin tashiga motor ta fice a gidan ta harba motor ta kan titi takama hanyar katsina ba tare da fargaban komi ba. ************* Zara ko washa gari da sasaafe suka daka sammako,ba sallah ba salati,ba wanke ido balle ɗauraye ƙafa,mashin guda suka hau suka kama hanyar masallata. Koda suka isa sun iske layi waje suka kama suma kafin azo kansu. ************** Gudu take tsalawa sosai,kamar na miji,sai da ta isa gusau kafin ta tsaya tasai tsire da drinks taci kafin taci gaba da tafiya tana tsala gudu abinta,tana zuwa funtuwa ta ɗauke hanyar katsina ko tsoro babu atattare da ita. ************** 06:30am Jidda ta tashi Cutie tai mata alwala,tasa mata hijjab tayi sallah,bayan ta idar tai mata wanka ta ta gyara mata suman ta ta shafa masa mai har ƙyalli yake yi kama mata tayi acan ƙasan kai kafin ta shiryata cikin school uniform ɗinta,tasa mata safa da school shoe ɗinta. Cutie taɓa kanta tayi ta turo baki gaba kamar na *ZEE YERO*,tace,"Aunty a shushi maza ne zakimin kalan na senior ɗin school ɗin mu". Jidda zaro ido tayi tana murmushi tace," aa kibar shi haka kinfi kyau,minene senior Cutie?. Ta ƙarashe mata maganan da sigar tambaya. "Senior manya makarantar mu nake nufi ,zance Dad yasaki makarantan mu". Murmushi tayi tana jan hancin Cutie tare suka saka dariya. *********** Agaggauce yafito yana ɗaura agogo a tsintsiyar hannun shi,yana sanye cikin kaftan yadin mai launin blue,hulan kanshi baƙi haka takalmin ƙafar sa,kafaɗan sa rataye da brief case ɗin sa,sauri yake yaje ya ɗauko Cutie ya aje ta amakaranta don suna da meeting ƙarfe takwas dai-dai,yaga bakwai ta gota Da mamaki yake kallon parking space ɗin ganin babu motor Abeeda watou bataji maganan sa ba ta fitan kenan tatafi katsina take yaji ranshi ya ɓaci,ƙwafa yayi yashiga motor shi ya fice. Hon ya buga ,dama haka yakeyi bai shiga in yazo ɗaukan ta gudun ɓata lokaci saide yayi hon ta fito. Aiko yanayin hone ta ɗau lunching box ɗinta ta fice da gudu,ba tare da ta ɗau jaka ba. Jidda ɗaukan jakan tayi tabi bayanta,lokacin har yabuɗe mata motor ta shiga,ya ansa lunching box ɗin ya aje a gidan baya,kiss ta manna masa a goshi tana fara'a tace "morning dad". ataƙaice tayi maganan. "Morning too,ina school bag ɗinki?. Yai mata maganan yana kafe ta da ido. Ɗan zaro ido tayi tana dafe goshi tace," Dad i forget it,bari inje in ɗauko". Bata jira mai zaice ba ta buɗe murfin motor,daidai lokacin Jidda ta ƙaraso. Komawa tayi ta kwanta jikin kujeran tace,"yauwa nagode Aunty" . Jidda aje mata jakan tayi akan cinya,ta kai kallon ta kan Aliyu da shima ita yake kallo,idon su sarƙewa yayi ana juna,kallon ƙuda suke ma juna,yayinda wasu kibiyoyi ke fita daga idon junan su yana shiga na ɗaya. Ƙirjin Jidda matsanan cin bugu yakeyi kamar zai fita da sauri tace,"ina kwana",cikin sanyin murya. Da sauri ta juya ta rufe ƙofar motor tabar wajan don jitake ƙirjinta naneman fasowa tafito,bata san miyasa takejin wani yanayi ba da zaran ta ganshi. Sauke nauyayyan ajiyar zuciya yayi don take jikin sa ya mutu,yima motor key yayi suka fice,jikin sa a sanyaye,tafiya kaɗan ya ajeta a ƙofar school ɗinsu yatafi office,yaso yaje ya duba Abba amma yayi latti ,zai kira Ummie tasa driver yakai musu abinci. *********** Ta isa cikin garin katsina ƙarfe shaɗaya da ƴan mintoci,takira Na'ima ta hayo abin hawa tazo ta ƙarasa da ita unguwar su,duk ƙawayen su ƴan duniya suna wajan da wanda tasani da wa ƴanda bata sani ba,"Aisha bata ƙaraso bane?. Abeeda ke tambayar Na'ima "Eh bata ƙaraso ba,wayoyin ta duk kashe ko online yau banganta ba Allah yasa lafiya". *********** Aisha ko da gan-gan ta kashe wayarta don karsu dameta da kira,ta sami matsala da mijinta,don ko labari zuwa biki bata kawo masa ba,don tana mugun tsoran sa da shakkan sa,biki in ba na ƴan uwanta ko dangin ta ba,ƙawaye bakowa yake bari taje bikin shi ba,sai wanda ya gadama zataje, balle bikin ƙanwar ƙawa,har katsina,aibata isa ba. *********** Su Zarah sunga boka,tun kafin su faɗa mai yakawo su ya zayyana musu,kuɗin aiki ya buƙata su biya su tafi kawai zasu ga aiki ,aiko tabiya suka dawo gida. ********** Tun Abeeda nasa ran ganin Aisha harta cire rai,sai gwada number ta takeyi akashe daga ƙarshe haƙura tayi,don har anfara shirin zuwa mothers day,shiryawa sukai ,mai makeup tai musu makeup suka tafi duk sunci anko light pink,basu suka dawo ba sai shabiyu saura. Agida maƙwaftan su suka sami wajan kwana don gidan su Na'ima yacika sosai ba masaka tsinke. Ƙarfe ɗaya da wani abu unguwan ta karaɗe da harbe-harbe kota ina,hankalin mutanan unguwan yatashi sosai,sun san tabbas anzo ɗaukan wanine,unguwar masu garkuwa da mutane sun addabesu baa wata baazo musu ba,hakan yasa wasu suka tashi,Abeeda ko motsi batayi ƙwaƙwara don tashin hankali iya tashin hankali ta ganshi Gidan dasu Abeeda suka sauka nan suka fara shiga ko suka taso kan mutanan dake gidan tassssss sai wata mai ciki da sukai sukai ta tashi tace bata iyawa saide su kasheta awajan,bugun tsiya sukai mata suka barta awajan suka fita suka faɗa gidan su Na'ima nan ma ba wanda basu tarkata ba,sai wata tsohuwa,gida biyar suka kwashe mutane,basu sukabar unguwan ba sai asubah,suna bari police na zuwa,Abeeda kuka kawai takeyi...........! TO HWA KO ƘAƘA OHO😨 MORE COMMENTS MORE TAHIN🤗 _typing🖌️_ ~*Lokaci yayi da zaka daina mamaki akan butulcin mutum, kowa zai iya butulce maka, kowa zai iya cin amanarka, kowa zai iya v, labule idan babu shi za kaga komai na ɗaki, murmushi idan babu shi za kaga mummunan kuɗirinshi🤗👌*~ *🔘JEEDDATOU🔘* NA MARUBUCIYAR:-👇 SAMHA ƳAR MACE KISHIYACE SURUKAR ZAMANI GIDAN SADIƘ MATAR BAHAUSHE TAHEER LAILAH A GIDAN MU SUKE NOOR JAHAN JAHAN KHATOON ND NOW AWANI GARI JIDDATOU MALLAKIN:- *(THE CAT LOVER😸😹)* *(🌲S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE🌲)* https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo WHATSAPP NUMBER:- *08167151176* WHATPADD:- *MRS BASAKKWACE* GMAIL:- *MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM* IG ACCOUNT:- *KHADDEJATOU BASAKKWACE* TWITTER:- *@MRSBASAKKWACE* SNAPCHART:- *KHADEEJATOU BASAKKWACE* SADAUKARWA GA-:- *MOMYNA HAFSAT ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA UWAR MARAYU* *PAGE96&100* *BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* ___________📖Basu suka bar unguwar ba sai asubah,suna bari police na zuwa,Abeeda kuka kawai takeyi,tun baa kai ko ina ba ta fara tarin da ta sani,ɗaya daga cikin masu kama mutanan yasame ta ya buga mata gindin bindiga ,take ta faɗi ƙasa wanwar,aiko ruƙo hannun ta yayi ya fara janta a ƙasa kamar dabba. ************ Bayan sun fito daga meeting office ɗin sa ya koma yaje ya duba wasu files namasu sa hannun jari a company su na motor,daga bisani ya miƙe ya kwashe kayan sa ya nufi asbiti inda Abba ya duba jikin Abba alhamdulillah har ban ɗaki yake iya zuwa da kanshi,sun daɗe suna hira kafin yai musu sallama ya wuce. Kiran Jabeer abokin sa yayi ya tambaye sa ya samo masa lesson teacher yace masa eh yace tou yana gidan Ummie yazo dashi. Kusan atare suka ƙarasa gida Ummie da Jaafar,da Teacher da aka samoma JIDDA,sai da sukayi maganan kuɗin wata,ya rubuta masa takaddun da zai sai mata,kafin ya kira masa JIDDAN ya ganta,Jabeer tunda yaga Jidda yaji ya faɗa ƙaunar ta,kallo ɗaya bisa ƙa'ida yai mata yaji tatafi dashi kalan matan da yakeso tana da natsuwa sosai da kamun kai daga ganin yanayin ta. Bayan ta wuce ne Jabeer ya kalle Aliyu yace,"abokina,wannan ƙanwar tamu tayi min fa". Take ƙirjin Aliyu ya buga dummmdummm,yanayin shi na ƙoƙarin canjawa,amma yajawo jarumtar shi ya dake ya ƙaƙalo murmushi akan fuskan shi,ɗan sosa ƙeyan sa yayi yace,"kai fa Jabeer ɗan iska ne,duk inda kaga mace so kake,wannan tafi ƙarfin ka karatu zatayi". Dariya Jabeer ya sheƙe dashi kafin yace,"abokina wannan natsuwar ta tamin wlh auranta zanyi". Wani tuƙuƙun abu kamar dutsi ya tokare zuciyar Aliyu wani baƙin ciki yaji da Jabeer yace auranta zaiyi. Ɗan taɓa baki Aliyu yayi kafin yace,"sai kuma kayi". Yai maganan a taƙaice. Jabeer ganin Aliyu bai son maganan yasa ya watsar da alwashin sai ya sace zuciyar yarinyar da tashi salon batare da Aliyu yasani ba,kan ya farga ta faɗa ƙaunar shi dole ko abashi ita. Ɗan taɓa hira sukai kafi sukai ma Aliyu sallama,suka shiga motor Jabeer suka tafi,sun tsaida magana gobe mallamin zai fara zuwa. Ciki ya shiga ba kowa a falon sai ƙaran AC da ya ɗau sanyin da ya gauraye da wani daddaɗan ƙamshin turare da aka turara gidan dashi,lumshe ido yayi,kai tsaye bedroom ɗin Ummie ya nufa,tana zaune kan kushim tana waya,zama yayi gefenta,sai da ta ƙare ya gaisheta ta amsa. Bayani yai mata gobe zaa fara zuwa koya ma Jidda karatu,taji daɗi tayi murna sosai sai saka masa albarka takeyi. Zama sukayi jimmmm daga bisani yakauda zaman shiru yace,"Ummie na sake Abeeda sam bazan iya zama da ita ba". Arazane Ummie take duban sa tana salati da sallamewa tana tafa hannuwa. "Aliyu mai yai zafi haka?. Ta tambaye shi tana riƙe baki. Muskutawa yayi yace,"Ummie tun baya nazo nagaya miki damuwa ta,kika nuna halin ko in kula tou yaya kike so inyi,zan iya zama da ko wacce mace koda ɓarauniya ce,amma banson mace mai yawa,Ummie na ƙyaleta tana yawo cikin garinan bance mata komi,ban isa ma ta gaya min zata fita ba,sai lokacin da ta gada ta dawo Ummie,har yakai Abeeda da tafiya katsina bikin ƙanwar ƙawa". Cike da takaici yake maganan kamar zai fashe da kuka. Cike da mamaki Ummie tace,"bikin ƙanwar ƙawa kuma har katsina?. "Eh Ummie,bari in gaya miki yanda mukayi jiya",nan ya kwashe komi ya faɗa mata. Girgiza kai Ummie tayi tace,"Aliyu miyasa ka kulata,gaskiya banji daɗin al-amarin nan ba,Abeeda da kamar bazatayi ba". "Ummie ta fitar min arai kwata-kwata,Ummie don Allah ki tallafa min ki agaza min wallahi ina son Jidda tun ina ƙarami kibani matata Jiddah". Yai maganan yana wani fashewa da matsanan cin kuka. Daidai lokacin Jidda ta turo ƙofa hannun ta cikin da Cutie a sanyaye suka shigo,bayan sun gama jin duk maganan da Ummie da Aliyu sukeyi. Jidda duƙawa tayi gaban Ummie,Cutie ma haka. Jidda ƙasa tayi da kanta cikin sanyayyar murya tace,"Ummie kinga fa yana kuka,dama ni matar Yaya ce,Ummie in dagaske ne abinda naji Ummie ki temaka zan zauna dashi,koda kuwa baya sona,ni ina son shi. Daga Ummie har Aliyu da take kukan shi ya tsaya cakkk cike d mamaki suke kallon Jidda. JIDDA ko ɗago kai tayi taga duk sun zuba mata ido yasa tai ƙasa da idon ta da sauri,karde maganan dake zuciyarta tayi suɓul da baka yafito fili. "Ummie kinji ko tana sona zata zauna dani". Ummie ko mamakin yahanata magana. Da ƙyar ta iya cewa kutashi ku ɓace min daga gani,watou kafin ya shigo sai da ya zigo ki ko Jidda kizo gabana kimin rashin kunya". Yace wallahi Ummi ni ban........! *DAGA WANNAN SHAFIN NADENA POSTING AKO INA MASU MIN COMMENTS KAWAI ZAN SA SU A SABON GROUP ƊINA DANA BUƊE* _typing🖌️_ *🔘JEEDDATOU🔘* NA MARUBUCIYAR:-👇 SAMHA ƳAR MACE KISHIYACE SURUKAR ZAMANI GIDAN SADIƘ MATAR BAHAUSHE TAHEER LAILAH A GIDAN MU SUKE NOOR JAHAN JAHAN KHATOON ND NOW AWANI GARI JIDDATOU MALLAKIN:- *(THE CAT LOVER😸😹)* *(🌲S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE🌲)* https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo WHATSAPP NUMBER:- *08167151176* WHATPADD:- *MRS BASAKKWACE* GMAIL:- *MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM* IG ACCOUNT:- *KHADDEJATOU BASAKKWACE* TWITTER:- *@MRSBASAKKWACE* SNAPCHART:- *KHADEEJATOU BASAKKWACE* SADAUKARWA GA-:- *MOMYNA HAFSAT ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA UWAR MARAYU* *PAGE101&105* *BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* ___________📖Yajima yana tunani iriiri da tarin dana sani kafin bacci ɓarawo yai awan gaba dashi. ******** "Wai Aliyu lafiya har 08:00am ta gauta bai zo ya ɗauki yarinyar nan ba ina ta kiran wayan shi tana ƙara baa ɗauka". Ummie ce ke magana tana ƙara danna kiran number Aliyu. Jidda na zaune daga can gefenta,yayinda Cutie ke kan cinyarta. Ummie ɗagowa tayi ta kalle Jidda tace," kaita wajan Adamu driver ya kaita". Tou Ummie Jidda ta amsa a taƙaice,yayinda ta sauke Cutie ta ɗau lunch box ɗinta da jakan ta suka fita. *********** Aliyu ko bashi ya farka ba,sai to 11:00am,daƙyar ya miƙe yai wanka kansa na sarawa,cike da mamakin baccin da yayi,sallah asubah ya gabatar a gurguje,yajima ya adduan Allah ya sassauta zuciyar Ummie akan sa,kafi ya tashi ya sauya kaya ya feshe jikin sa da turaruka,ya fara neman waya da key ɗin motor bai gani ba. Agurguje yafita waje ya duba ya hango motor shi a haraban gidan parking ɗinma gata ga kamar ta. Buɗe murfin motor yayi a kulle,tou ina ya aje key da wayoyin sa,yake tambayan kansa a cikin zuciyar sa. "Yallaɓai barka da kwana". Baba mai gadi ne duƙe a bayanshi yake biƙa gaisuwan sa wajan ubangidan sa. Dafa goshi Aliyu yayi,kafin yace,"Baba bana son duƙawar nan,dan Allah tashi". Baba mai gadi miƙewa yayi yana murmushi,tare da sa hannu agaban aljihun rigar sa yaciri key,ya miƙa ma Aliyu,yace,"Alhaji jiya kabar motor a kunne,naga baka ƙara fitowa balle ka kulle ba,nai karambani nasa Salim ɗan Alhaji Sada nan maƙwafcin mu da yake zuwa miyi hira ya kashe yaban key ɗin". "Allah sarki Baba aiko nagode",an san key yayi ya buɗe motor,har Baba zai juya yace,"tsaya Baba,Babako daga jin haka yasan kakan shi ta yanke saƙa,Aliyu akwai kyauta. Kuɗi ya ɗebo,da baisan yawan suba ya miƙa ma Baba,Baba amsa yayi yana ta zuba masa ruwan godiya da addua kala-kala. Ameen kawai Aliyu ya amsa dashi,yaja murfin motor shi ya rufe. Wayar shi ya ɗauko yaduba,miss call rutu-tu,musamman na Ummie,sai wa ƴanda ba suna dana ƴan office ɗin su. Wanda ba suna fara kira,don bai so ya kira Ummie tamai faɗa,gwamma yaje yabata haƙuri,ringing biyu aka ɗaga. Sallama yayi,amma baa amsa ba,saide akafara cewa,kaine mijin Abeeda da tazo biki katsina?. Jin muryan bafulati na masa magana yasa gaban shi faɗi amma ya danne yace............! MORE COMMENTS MORE TYPING🤗 ~*Lokaci yayi da zaka daina mamaki akan butulcin mutum, kowa zai iya butulce maka, kowa zai iya cin amanarka, kowa zai iya zaluntarka.*~ ~*Tsakanin shimfiɗar fuska da labulen ɗaki basu da bambanci, labule idan babu shi za kaga komai na ɗaki, murmushi idan babu shi za kaga mummunan kuɗirinshi🤗👌*~ *🔘JEEDDATOU🔘* NA MARUBUCIYAR:-👇 SAMHA ƳAR MACE KISHIYACE SURUKAR ZAMANI GIDAN SADIƘ MATAR BAHAUSHE TAHEER LAILAH A GIDAN MU SUKE NOOR JAHAN JAHAN KHATOON ND NOW AWANI GARI JIDDATOU MALLAKIN:- *(THE CAT LOVER😸😹)* *(🌲S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE🌲)* https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo WHATSAPP NUMBER:- *08167151176* WHATPADD:- *MRS BASAKKWACE* GMAIL:- *MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM* IG ACCOUNT:- *KHADDEJATOU BASAKKWACE* TWITTER:- *@MRSBASAKKWACE* SNAPCHART:- *KHADEEJATOU BASAKKWACE* SADAUKARWA GA-:- *MOMYNA HAFSAT ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA UWAR MARAYU* *PAGE106&120* *BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM* *LAST PAGE* ___________Jin muryan bafullaci na masa magana yasa gaban shi yai wani irin faɗi ya danne yace,"gaskiya ba matata bace,ni matana na gida bataje ko ina ba". Yana gama magana ya datse wayar sa ya kashe ta gaba ɗaya,gaban shi na faɗi,yana nanata innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Ya jima zaune cikin motor zuciyar shi ya rasa tinanin da zaiyi,ƙwaƙwalwan shi ta tsaya cakkkkkkk bata ko motsi,Abeeda wani kala hali ta jefa kan ta haka. ********** Mutumin ko yana jin abinda Aliyu yace,"yasamu kan bindiga ya kwaɗa ma Abeeda akai yace,"shege ni za kai wa ƙarya,kabani number da bashine ba,ɗan iska kawai". Abeeda ƙara tsurewa tayi gaba ɗaya,Aliyu ita zai ma haka,duk soyayyan dake tsakanin su,yau tana cikin wani hali ya nuna bai santa ba. "Dan ubanka kabani number ko in kashe ka yanzun" . Abeeda jiki na rawa taba shi number Dadynta. *********** Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un,Ummie ke nanatawa tana tafa hannu. Aliyu na zaune daga gefe ya rafka tagumi. "Hajiya Amina tasani kuwa?. "Ni ban kirata ba Ummie,can tabada number su a kira,biyar ɗina bazai yi ciwo ba,tunda bata ji maganana ba,sannan na tunkafin tatafi nagaya mata in ta tafi,abakin auran ta,kuma taƙi ji ,tou in mata yaya?. Ya ƙarashe maganan da sigar tambaya. *********** Dana sanin biye ma zugan ƙawaye Abeeda tayi ,gashi ita tana ɗakin mijinta,ita an saketa,so take taga Aliyu,ga Momyn ta tace in taje wajan Aliyu bata yafe ba,yasa taƙi zuwa,sabon ƙaunan Aliyu na bin jinin ta da jijiyar ta,gashi tana son ganin Cutie tana jin nauyin zuwa gidan Ummie. Aliyu yasama Jidda waya,samsung x5 yasa mata sim ta rinƙa game yace ma Ummie,yanzun alhamdulillah tana iya karatu tana iya rubutawa Ya samo mata addmision a nanah asmaa'u makarantan su Cutie school anyi mata primary certificate,yanzun tare suke zuwa duk week end a gidan Abba sukeyi. Abba yamanta da wata Zarah da ƴaƴanta,sabon rayuwa suke shimfiɗawa da amaryansa. ********* Iyayen Ila da kansu sukazo suka bada haƙuri akan cin mutuncin da sukai ma Zarah kwanaki,suka yanke randa zasu kawo taskiran Atiƙa asha biki. *********** Su Jidda sunyi exam sun samu hutu,suka shirya zuwa lafani da tsara mai tarin yawa. Kamar daga sama suka ga motoci sun dira a ƙofar gidan su, mutane suka firfito suna kallon su,da mamaki suka ga Abba ya fito yana takawa da ƙafar sa ,ganin Jidda yasa Tani buga tsalle tana murna ga Jidda ga Jidda mutane sai kallonta suke ta zama ƴar gayu gwanin ban sha'awa kamar su taɓata jini ya fito,ba wannan dauɗan ga kaya masu kyau na alfarma. Zarah saƙaiƙai tayi tana kallon Jidda cike da baƙin ciki dama Atiƙa ce ahaka. Atiƙa ko murna take tayi ganin Jidda da Abban su ,jitake dama itace,da gudu ta shiga gida ta ɗauko tabarmi ta shimfiɗa ta kamfato ruwan randa ta kawo ta aje agaban su don sun riga sun zauna. Zarah ko ta kasa zama. Atiƙa ta gaida su Ummie,Aliyu,Inna da basu taɓa ganin taba,suka amsa,Abba sai mamaki yake,Zarah ko ko gaisuwa sun kasa samu,sai taɓa baki takeyi tana girgije-girgije kamar kurna. Ummie ta gaisheta bata amsa ba illa tsaki da tayi ta wuce fuuuuuu. Atiƙa ina Sa'ima?. Abba ya tambaya. Atiƙa tafara matsan ƙwalla tabasu labarin abinda ya faru da Sa'ina. Abba yayi takaici sosai yai mata addua yayafe mata duk abubuwan da sukai masa,nan ta gaya masa an kawo taskiran auran ta sati mai zuwa za'ai bikin. Yayi mata adduan zaman lafiya. Sun jima suna hira,ya gabatar ma Abeeda da Inna amatsayin sabuwar matan shi,Atiƙa tayi murna, har suka tashi tafiya basu ƙara ganin Zarah ba ,suka sauke tsaraba suka tafi Atiƙa jitake kamar ta bisu,shaawar Jidda take. dana sanin biye ma zugan ƙawaye,gashi ita tana ɗakin mijinta,ita an saketa,so take taga Aliyu,ga Momyn ta tace in taje wajan Aliyu bata yafe ba,yasa taƙi zuwa,sabon ƙaunan Aliyu na bin jinin ta da jijiyar ta,gashi tana son ganin Cutie tana jin nauyin zuwa gidan Ummie. Aliyu yasama Jidda waya,samsung x5 yasa mata sim ta rinƙa game yace ma Ummie,yanzun alhamdulillah tana iya karatu tana iya rubutawa Ya samo mata addmision a nanah asmaa'u makarantan su Cutie school anyi mata primary certificate,yanzun tare suke zuwa duk week end a gidan Abba sukeyi. Abba yamanta da wata Zarah da ƴaƴanta,sabon rayuwa suke shimfiɗawa da amaryansa. ********* Iyayen Ila da kansu sukazo suka bada haƙuri akan cin mutuncin da sukai ma Zarah kwanaki,suka yanke randa zasu kawo taskiran Atiƙa asha biki. *********** Su Jidda sunyi exam sun samu hutu,suka shirya zuwa lafani da tsara mai tarin yawa. Kamar daga sama suka ga motoci sun dira a ƙofar gidan su, mutane suka firfito suna kallon su,da mamaki suka ga Abba ya fito yana takawa da ƙafar sa ,ganin Jidda yasa Tani buga tsalle tana murna ga Jidda ga Jidda mutane sai kallonta suke ta zama ƴar gayu gwanin ban sha'awa kamar su taɓata jini ya fito,ba wannan dauɗan ga kaya masu kyau na alfarma. Zarah saƙaiƙai tayi tana kallon Jidda cike da baƙin ciki dama Atiƙa ce ahaka. Atiƙa ko murna take tayi ganin Jidda da Abban su ,jitake dama itace,da gudu ta shiga gida ta ɗauko tabarmi ta shimfiɗa ta kamfato ruwan randa ta kawo ta aje agaban su don sun riga sun zauna. Zarah ko ta kasa zama. Atiƙa ta gaida su Ummie,Aliyu,Inna da basu taɓa ganin taba,suka amsa,Abba sai mamaki yake,Zarah ko ko gaisuwa sun kasa samu,sai taɓa baki takeyi tana girgije-girgije kamar kurna. Ummie ta gaisheta bata amsa ba illa tsaki da tayi ta wuce fuuuuuu. Atiƙa ina Sa'ima?. Abba ya tambaya. Atiƙa tafara matsan ƙwalla tabasu labarin abinda ya faru da Sa'ina. Abba yayi takaici sosai yai mata addua yayafe mata duk abubuwan da sukai masa,nan ta gaya masa an kawo taskiran auran ta sati mai zuwa za'ai bikin. Yayi mata adduan zaman lafiya. Sun jima suna hira,ya gabatar ma Abeeda da Inna amatsayin sabuwar matan shi,Atiƙa tayi murna, har suka tashi tafiya basu ƙara ganin Zarah ba ,suka sauke tsaraba suka tafi Atiƙa jitake kamar ta bisu,shaawar Jidda take. Ran Zarah bai mata daɗi ba,sanda taji Abba ya ƙara aure,tai alƙawari sai tako raba auran. Bayan sati ɗaya aka wanke Atiƙa aka kaita ɗakin miji,Aliyu ya aiko mata da kayan ɗaki na birni,Abba ya ziyarce ɗaurin auran Atiƙa tayi murna an mata kayan da baa taɓa ma wata ƴa a ƙauyen ba. Zagi da cin mutunci ba wanda Abba bai gani ba wajan Zarah bai ce mata komi ba,saida ya tashi tafiya ya dube ta cikin mutane ya danƙara mata saki ɗaiɗaya har uku,ya shige motor driver yajashi suka wuce,yabarta tana ihu tana hauka,da ƙyar mutane suka jata cikin gida. Abba ko ranshi fesss yatafi,ji yake kamar an sauke masa wani nauyi akan sa. Soyayya Jidda da Aliyu suke yi a ɓoye,Ummie sam bata sani ba,ta waya suke yi a fili ko halin ko in kula suke nuna ma juna. Duk a soyayyar da suke,bai hanata karatun taba. ********** Hajiya Abeeda ko har yanzun bata kula kowa gani take kamar Aliyu zai dawo ya maidata ,amma gashi shekara biyu shiru ko ahanya basu taɓa haɗuwa ba. Zarah ko shige da fice na bokaye akan Abba ya maida ta,amma duk ta gama saida tumakan ta,bokaye sun gama cinye kuɗin amma shiri,ko zanin ɗaurawa mai kyau bata dashi yanzun. Tayi-tayi tasa Atiƙa ta saida kayan ɗakin ta taje tabi mata mallamai ta mallake mijinta da dangin ta taƙiya tace ita lafiya take zaune da mijinta bazata bayar ba Abban ta yasai mata in ta ita ne saide ta kaita da gadon kara. *********** "Aliyu zama haka ya isa kane mi mata kayi aure". Faɗan Abba da Aliyu ya kawo su Jiddah gidan. Nan ya kwashe yanda sukai da Ummie ya faɗ ma Abba,Abba ko yace zaima Ummie magana. Aikam yai ma Ummie magama,da taso ya bijire ya nuna mata illan haka,don Jidda matan shi ce,sai ya saketa zata iya auran wani,badon taso ba ta amince. Sun tsada ranan biki tunda de matan shine. Ranan biki na zuwa,akai biki isu-isu babu wani bidi'a atiƙa tazo kamar karta tafi haka takeji,Abba da kansa yakai Jidda gidan Aliyu da ya tsaru. Satin su guda Ummie ta maida Cutie gida. Rayuwar gidan su Aliyu da Jidda gwanin ban shaawa,suna zuwa makaranta da Cutie,Aliyu bai yarda ta kula ko wacce ƙawa ba ,iyakan ta da ƙawa aji itama ƙawarta ɗaya Jamila. Watan ta uku tafara laulayin ciki taga gata d tarairaya wajan Aliyu da Ummie da Inna da Abba,kamar akan ta zaa fara musu haihu,aiki sai tayi da gaske Aliyu ke tafiya,cikin nada wata takwas tadena zuwa school,sabida girman da yayi jikin ta yamata nauyi sosai. Ummie zuwa tayi ta ɗauke ta da kanta ta maidata gidan ta,don tayi tayi Aliyu yadawo da ita gida yaƙiya,saide ya dawo yaga batanan ,aiko shima ya tattara yakoma gidan Ummie. Ranan wata talata ta tashi da ciwon naƙuda,a gaggauce aka kaita asbiti,zuwan su ba wiya ta haifo ƴan biyu duk maza. Aliyu murna kamar zai zuba ruwa a ƙasa haka Ummie da su Abba. Inna dawowa gidan tayi don ma Jidda wanka jego. Inda Abba ya bugama Atiƙa waya da ƴar wayan da yasai mata,jiki na rawa taje ta gayama Zarah,Zarah kamar ta mutu,tace sai taje taga uwar uban da akeci. Aiko ana gobe suna,suka taho,Zarah jikinta yayi sanyi sosai,yanda taga ana nan nan da ita kunya kamar ta nitse. Ranan suna yara suka ci sunan Abdullahi,da Muhammad,anci ansha an goge wiya,anyi rabon kaya kamar ba'a so. Zarah sakan baki tayi tana mamaki rabon kaya na kuɗi kamar baa so. Da suka tashi tafiya,akai musu shatara ta arziki,Zarah ta fashe da kuka ta nemi yafiyar Abba,da Jidda,nan suka yayyafe juna suka tafi. ********** Abeeda da taga ba sarki sai Allah harta samu labari auran Aliyu da yayi na ƴar uwansa,dole ƙanwar naƙi yasa ta fito da ɗaya cikin zaurawan ta tayi aure,yana da mata uku ga tarin ƴaƴa. *********** Jidda sai da tayi arba'in biyu kafin ta koma,bayan sunje ƙauye sun dawo,samo mata nany akayi,don rainon ƴan biyu ga school. Cutie nata girma tana zama ƴammata,tun tana ma Aliyu maganan Momynta harta bari. Jidda ce tabashi shawara yakamata akai Cutie gidan kakanin ta,aiko yabi shawaranta,tare yakaita da ƴanbiyu,iyayen Abeeda sunyi murna da farin ciki,kuma yai musu alƙawari zai rinƙa kawo ta in yasamu lokaci-lokaci inya samu. Haka rayuwa taci gaba da tafiya da daɗi ba daɗi,ya zaƙi gobe maɗaci,ko haƙori da halshe suna saɓawa balle mutum. Su Jidda suna zaman lafiya,burin su su faranta ran junan su basuso su ɓata ma junan su. Abeeda ko ta fuskanci matsi da takura ga kishiyoyi da ƴaƴansu,ga matsalan rashin haihuwa,ta koma asbiti don a maida mata mahaifa,Dr yace bazai yiwu ba,haka ta dawo ta haƙura taci gaba da bautan ƴaƴan miji,tunda ita bata haihuwa,dole yasa ta aje girman kai ta koyi girki,ga girkin gidan mai uban yawa. BAYAN SHEKARA BIYAR. Wata ƴar budurwan yarinya na hango mai shekara shabiyu tare da wasu ƴan matasan yara masu shekara shidda,ta zaune tsakiyan su tana koya musu karatu. Wata ƴar matashiyar dattijuwa ta sakko daga matattakalan bene ta dube su tace,"Cutie tashi in aike ki gida Ummie kisa driver ya kaiki". Tou Momy,momy nima zanje,ɗayan ɓa yace shima zaije tace tou taji. Saƙon ta basu suka tafi kaiwa. Aliyu da fitowan sa yanzun ya rungumo ta ta baya,yace,"gaskiya na gaji da ganin ki haka new baby nakeso,kan tai magana ya sun kuceta yayi bedroom ɗinsu na falo bai direta ko ina ba sai kan gado. Dagudu nafito don ba hurimina bane *************************⬇********************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************* ~ƘARSHE~ *SUBUHANAKALLAHUMMA WABIHAMDIK,ASH HADU ALLAH ILAH HA ILLALLAH WA ASH HADU ANNA MUHAMMADAN ABDUHU WA RASULAHU,KUSKUREN DANAYI ALLAH KAYAFEMIN,ABINDA NAYI DON ALUMMA SU AMFANA,ALLAH KABASU IKON AMFANI DASHI*