Mutum Da Aljan Littafi Na Hudu (4) Part A. yan suka taho izuwa kan sarki Alkasim suka tsaya suka yi cirko cirko suna kallonsa kawai . Al amarin da yayi matukar bashi mamaki kenan ya dubesu a fusace ya daka musu tsawa yace menene zaku tsaya a kanmu haka kuna kallonmu kawai ba zaku taimaka mana ba mu mike tsaye mu koma can sansani ba ! . Koda jin wannan batu sai ramjis da hatyan sukayi girgiza suka juye izuwa kamannin jarumi zaihas da jaruma namrita, cikin kaduwa sarki Alkasim ya mike tsaye zumbur jiri na dibarsa sakamakon jinin dake zuba a sassan jikinsa yayi wuf ya zare takobinsa ya fuskancesu yana mai gyara tsayuwarsa kawai sai yaga namrita ta kyalkyale da dariya . Lokaci guda kuma saita turbune fuskarta ta dubeshi a fusace tace ya za ayi mu yakeka kana cikin wannan mugun hali ba zamu dauki fansa ba a kanka sai kana cikin koshin lafiyarka gami da jin izzarka . Ka sani cewa bamu shiga wannan gasa ba domin mu samu damar da zamu hallaka ka ba sai domin mu nuna maka cewa dan hakin da ka raina shike tsone maka idanu ka sani komai karfinka komai mulkinka zaka iya faduwa kasa a ko yaushe saboda ita wannan duniyar fadi gareta kuma abin cikinta yawa gareshi . Babuwanda yasan iyakarsa ka tsaya kayi tunani wannan fa dabbace kawai ta galabaitar da kai haka in ba don mun kawo maka dauki ba da sai dai kuyi ragas kai da ita ka tuna fa cewa ko birnin sarki masarul anjana bamu isa ba inda za a tara gaba dayan jarumai da matsafan duniya . Kanka ka sani kawai amma baka san sauran mutanen duniya ba babu mamaki akwai wadanda suka fika da yawa amma kace idan muka sake kawo maka hari zaka kashemu to mu ma mun dauki alkawarin cewa ba zamu sake kawo maka hari ba har sai mun isa can birnin sarki masarul anjana ina mai tabbatar maka da cewa har abada ba zamu taba durkushewa ba a gabanka mu nemi gafararka ba face mun cika burinmu na kashe ka ka kashe mana mahaifinmu kuma mahaifiyarmu ta mutu a sanadiyyar ciwon zuciyar da ka dasa mata na ganin gawar mijinta . Ta yaya kake tsammanin zamu iya yafe maka har abada babu yafiya a tsakaninmu dakai ga wannan dabbar sai ka dauka ka koma da ita can sansanin a matsayin kai ne ka lashe wannan gasa sai ranar da zamu cika burinmu akanka sannan zamu sake haduwa koda gama fadin hakan sai jaruma namrita da dan uwanta jarumi zaihas suka bace bat daga wajen tamkar basu taba wanzuwa ba a wannan lokaci zuciyar sarki alkasim ta kama tafarfasa kamar zata kone saboda tsananin bakin ciki don haka bai san sa adda ya takarkare ba ya kurma uban ihu mai tsananin firgitarwa wanda yasa gaba dayan halittun dake cikin dajin darul samjul suka firgice suka dimauce babu shiri tsuntsaye suka kama tashi suna sauya sheka dabbobi kuwa da sauran kananan kwari suka rinka shigewa cikin ramukansu suna buya kai hatta halittun dake karkashin ruwa lambo sukayi suka ki tasowa izuwa saman ruwa ashe duk wannan abu dake faruwa tun a farkon fara gumurzun da wannan katuwar dabba sai dabbar ta make sarkin yaki ya fadi kasa kansa ya gwaru da wani dutse take kan nasa ya dare jini yayi ta tsartuwa ya baje a kasa sumamme a wannan lokacine da sarki ya kurma uban ihu sarkin yaki ya farfado daga dogon suman da yayi a firgice ya mike zaune ya dubi gabas da yamma kudu da arewa sannan ya lura da sarki wanda ke tsaye a gabansa ruke da takobi jikinsa na kyarma ga jini na yoyo a sassan jikinsa kuma ga gawar wannan dabba a gefe guda, shi kuma yarima yana kwance a kas a gabansa ya kasa tashi , kawai sai yaji sarki ya daka masa tsawa yace maza ka dauki yarima ka goyashi a bayanka ka ruga dashi izuwa can sansaninmu domin likitoci su dubaku cikin hanzari sarkin yaki ya suri yarima ya goyashi a bayansa har ya juya zai tafi sai ya dubi sarki yace ya shugabana tunda dao ka samu nasarar kashe wannan dabba ai saika daukota mu tafi tare domin jama a su tabbatar da cewa kaine ka lashe wannan gasa Al amin Ahmed Misau guyson sunana kenan daga page na 'zauran labarai' sarki Alkasim ya gyada kai yace bani ne na kashe wannan dabba ba makiyanane suka kasheta zaihas da yar uwarsa namrita kuma sun juye kamannin ramjis da hatyanne suka shigo wannan gasa maza kayi sauri ka kai yarima tantinsa zan jira isowarku a can koda jin haka sai mamaki ya kama sarkin yaki amma sai yayi shiru bai kara cewa uffan ba ya runtuma da gudu izuwa hanyar da zata kaishi sansanin goye da yarima kamsus a bayansa nan dai yayi ta gudu ba tsayawa kuma babu waiwaye yana isowa sansanin ya hango sarki zaune a kofar tantinsa bisa kujera likitansa na dinke raunukan jikinsa' hm kunji aikin tsafi fa wai Guyson nake magana a guje wadansu dakaru hudu suka taryi sarkin yaki suka karbi yarima suka shigar dashi cikin tantinsa suka kwantar dashi nan da nan shima nasa likitan ya dukufa a kansa aka shafa masa wani irin magani na musamman a gadon bayan nasa sauran jaruman gasa dai Tuntuni daya bayan daya suka rinka dawowa sansanin tun sa adda suka sare sakamakon azababben gudun tseren da akayi na kece raini ramjis da hatyan ne kadai ba a ga dawowarsu ba abinda ya kara daurewa jama a kai shine sarki ya dawo dauke da raunuka a jikinsa kuma babu wata dabba a hannunsa shi kuma yarima an kawoshi a matukar galabaice to wai shin menene yake faruwa ne haka amsar da aka rasa wanda zai iya bayar da ita kenan shi dai sarki alkasim tunda ya dawo daga dajin darul samjul baice uffan ba kuma baiyi magana da kowa ba har aka gama dinke raunukan jikinsa aka shafa masa magani kawai sai akaga ya shige cikin tantinsa yaje ya kwanta gaba dayan hadiman ma korarsu yayi daga cikin tantinsa kuma yaki ci da shan komai saboda bakin ciki abu na farko da ya fara tunowa shine maganganun da jaruma namrita ta gaya masa na batun ya kashe mahaifinsu kuma mahaifiyarsu ta mutu a sanadiyyar bakin cikin mutuwar mijinta abu na biyu kuma shine batun cewa ya daina tunanin cewa yafi kowa karfi isa da iko domin za a iya samun wadanda suka fishi a cikin wannan duniya mai fadi idan kuwa hakane ashe ya dade a cikin jahilci irin na iyayensa da kakanninsa wadanda suka tabbatar masa da cewa zai iya ja da kowa a wannan duniya walau mutum ko Aljan idan maganarsu gaskiyace to ya ya akayi dabbba ma ta gagareshi har ya zamana cewa ta yi kusan hallakashi yanzu a haka ne zai iya zuwa ya tari sarki masarul anjana sarkin da dukkan aljanu da mutanen duniya ke tsoronsa da shakkarsa koda sarki alkasim yazo nan a zancensa sai wata zuciyar kuma ta ce dashi kai ai ka da mage ba yanka bane yau shekararka talatin da uku kenan akan mulki ba a taba samun bacin rana ba irin ta yau kuma yau din ma ai ba a kaika kas ba inda ma zaka je kasan saidai ayi ragas duk maganganun wannan yarinya namrita zancen banza ne idan ka kuskura ka sasu a ranka har sukayi tasiri a cikin zuciyarka shi kenan ka samu raunin da darajarka zata zube a idon duniya kada ka manta cewa duk inda kake kuma a duk halin da kake ciki kana tare da rahamar ruhin iyayenka da kakanninka don haka ba zasu taba barinka kaji kunya ba yayinda sarki alkasim yazo nan a zancensa sai zuciyarsa tayi fari dukkan wata fargaba ta yaye daga cikin ransa bai san sa adda ya kwalawa wata kuyangarsa kira ba tashigo cikin tantin da sauri kawai saiya dubeta yace maza kije ki shirya min giya kuma a shirya min makada da masu rawa . Nishadi nake bukata , hm kunji karfin hali' guyson sunana' kuyangar ta risina tana murmushi tace an gama ya shugabana lokacinda jama ar wannan sansani sukaga an kama yiwa sarki kida da raye raye yana ta nishadi gami da shan giya sai kowa ya cika da mamaki har ni kaina Al amin Guyson kuwa ba komai ne ya baiwa jama a mamaki ba face ganin cewar ai yanzu lokaci ne na bakin ciki bana farin ciki ba tunda an dawo daga gasar farauta babu nasara yarima ma an dawo dashi ba lafiya shi kansa sarki ya dawo dauke da raunuka masu yawa amma kamar babu abinda ya dameshi sai sharholiya yakeyi yarima kamsusu dai bai dawo cikin hayyacinsa ba kuma baiji kwarin jikinsa ba sai da dare ya raba a wannan lokacine ya farka daga dogon barcin da yayi sakamakon maganin da likita ya bashi yasha zumbur ya mike zaune akan shimfidarsa cikin kuzari tamkar wani abu bai sameshi ba bisa mamaki sai yaji ko kadan bayan nasa ya daina zugi da radadi tamkar an zare masa ciwon da yake ji tun daga lokacin da wannan katuwar bakuwar dabba tayi masa mugun duka abu na farko daya fara fado masa a rai shine abubuwan da suka faru a can dajin darul samjul duk da cewa ya tsinci kansa a cikin wani irin mugun hali mai kama da wani irin mugun hali mai kama da jirkitar hankali ko rabin suma sai yaji yana iya tunowa da duk abubuwan da suka fara tun daga lokacin da suka fara yin bakin artabu da wannan muguwar dabba kawo izuwa lokacin da namrita da dan uwanta suka ceci rayuwar sarki suka murdewa dabbar wuyanta ta fadi kasa matacciya da kuma lokacin dasu namrita suka rikida izuwa ainihin kamanninsu nan take yarima kamsus ya kamu da tsananin mamakin yadda wadannan al amura suka kasance haka a dai dai wannan lokaci ne kuma yaji ya kara kamuwa da tsananin son jaruma namrita fiye da ko yaushe ma tunda gashi sun ceci rayuwar mahaifinsa ita da dan uwanta duk da cewa suna son ganin bayansa daga can kuma sai yaji zuciyarsa ta buga da karfi tsoro ya baibayeshi ba komai ne ya haddasa hakan ba face ganin yadda dabba ta kusan hallakasu a yaki to wai shin kuma idan suka isa birnin sarki masarul anjana inda za a tara gaba dayan jaruman duniya ya matsayinsu zai kasance ? Koda yazo nan a tunaninsa sai fuskar namrita ta fado masa a rai lokacin da tayi masa wani duba tana murmushi nan take yarima kamsus yaji dukkan fargaba ta kau daga cikin zuciyarsa kuma yaji babu abinda yake so a duniya a wannan lokaci sama da ganin jaruma namrita kawai sai yarima kamsus ya mike tsaye daga kan shimfidarsa ya fito daga cikin tantin ya kama kai kawo a cikin sansanin inda ya iske dakarun tsaro akan aikinsu sauran jama ar sansanin kuwa duk suna cikin tantunansu a kwance suna ta Ta faman shara barci abinsu kai tsaye yarima kamsus ya nufi tantin sarki tun kafin ya karasa bakin tantin da tazarar taku biyar ya jiyo munsharin sarki koda ya gane cewa sarki barci yake yi sai ya juya ya nufi kofar fita daga sansanin da isarsa kofar sai dakarun dake gadin kofar suka dubeshi cikin alamun firgici shugaban dakarun yace ya shugabana ina kuma zakaje a cikin wannan tsohondare kayi sani cewa akwai hadarin gaske ka fita daga cikin sansanin nan kuma sarki ya kafa dokar cewa in dai dare yayi to babu wanda zai fita daga cikin wannan sansani kafin shugaban dakarun ya gama rufe bakinsa tuni yarima kamsus ya zaro takobinsa daga cikin kufe kawai saiya dubi badakaren a fusace cikin harara yace na rantse da darajar sarki duk wanda yace zai hanani fita yanzu daga cikinku saina sare masa kai ''.......... . Topha nima jin wannan zance na sare kai yasa na dan dakata a nan sbd nakasance jarumi bana son fada ehem , Mutum Da Aljan Littafi Na Hudu (4) Part B. . Author' madakin Gini typing by' Al amin Ahmed Misau Guyson sunana kenan . Ku bani aron lokacinku.... Marubucin littafin yaci gaba da cewa.... - koda jin wannan batu sai gaba dayan dakarun suka tarwatse suka baiwa yarima hanya ya bude kofar ya fita yana fita sai suka janyo kofar suka sake rufeta ba tare da tsoron komai ba sai yarima kamsus ya nausa cikin daji yana tafe abinsa yana kallon bishiyoyi da ganyayensu yana jin nishadi tamkar ba a cikin daji yake ba kuma ba dare bane sa ar da yayi ma shine babu duhu a dajin sakamakon hasken farin wata amma kuma tsananin shirum dake dajin ya isa ya firgita mutum komai jarumtakarsa tsulum ba zato ba tsammani sai yarima kamsus ya hango jaruma namrita ta nufoshi tana sanye da wata doguwar shudiyar riga fuskarta cike da annuri da farko sai yarima kamsus ya mari kansa domin a zatonsa mafarki yakeyi abinda idonsa suke nuna masa ba zahiri bane' bisa mamaki sai yaga har yanzu yana iya ganin namrita tana ci gaba da durfafarshi hakane ya tabbatar masa da cewa lallai ba mafarki yake yi ba don haka shima sai ya kara sauri ya tunkareta a wannan lokaci kowannansu mamakine ya kamashi da yaga dan uwansa saboda abin ya zo dai dai tamkar hadin baki. Ashe kamar yadda yarima kamsus ya tsinci kansa a cikin tunani da begegn namrita haka itama ta tsinci kanta kuma taji ta kasa yin barci kuma babu abinda zuciyar tata ke so sama da ganin fuskar yarima kamsus hm Lallaifa wannan shine so gamon jini Al amin guyson sunana daga zauran labarai. A lokacin data tsinci kanta a cikin wannan hali dan uwanta jarumi zaihas na ta faman shara barci abinsa baima san halin da take ciki ba kawai sai namrita ta mike tsaye ta kama tafiya ta nufi sansaninsu sarki Alkasim tana mai ayyanawa a ranta cewa komai rintsi sai taga yarima kamsus a wannan dare koda namrita ta hango yarima kamsus a cikin daji saita kamu da tsananin farin ciki saboda tasan cewa ba zata sha wata wahala ba wajen ganinsa cikin hanzari suka karaso suka riski juna suka tsaya daf da daf yadda suna iya jin numfashin junansu kuma kowannansu na murmushi kawai sai yarima kamsus ya dubeta yace mene ne dalilin da yasa kika fito a cikin wannan daren alhalin bamu dade da rabuwa ba acan dajin darul samjul? Sa adda namrita taji wannan tambayar sai ta yi yar karamar dariya sannan ta dubeshi cikin nutsuwa tace ta yaya zan iya zama banzo naga halin da kake ciki ba tunda na barka a cikin mugun yanayi bisa dukan da wannan dabbar tayi maka a gadon bayanka ka sani cewa dan halak ne yake maida martanin halacci ga wanda yayi masa guyson ke magana har abada bazan taba mancewa da halaccin da kayi min ba na ceton rayuwata dakayi daga hannun mahaifinka yau zan sanar dakai wani babban sirri wanda baka san dashi ba yakai wannan tauraro abin haskakawa kayi sani cewa tun muna kanana sa adda ka nuna tausayinka a garemu bisa kisan da mahaifinka ya yiwa mahaifinmu naji ka shiga raina. Tun daga wannan lokaci a kullum rana ba zata fito ta fadi ba ba tare dana tuna kyakkyawar fuskarka ba wacce a lokacin da take zubar da hawayen tausayi ba. Ka gaya min iyakar gaskiyarka kada ka boye min komai shin abinda nake ji a kanka a cikin zuciyata kaima kana jin irinsa?? Koda jin wannan tambaya sai yarima kamsus yaji wani irin farin ciki ya baibayeshi irin wanda bai taba jin kamar saba nan take yaji kamar ya kamo namrita ya rungumeta akan kirjinsa amma saiya dake ya dubeta cikin murmushi sannan mai taushi yace yake sarauniyar matan duniya kiyi sani cewa ni dake zanice ta tarar da mujemu, ina mai tabbatar miki da cewar duk abinda kikeji a cikin zuciyarki dangane dani bai kai rabin wanda nakeji ba a kanki saboda jina da ganina sun zama naki ne dukkan bugun zuciyata yana ambaton sunanki ko a kwance ko a zaune a tsaye ko a tafe ke nake tunani dare da rana amma duk sa adda na tuno da gabar dake tsakaninku da mahaifina sai naji zuciyata na daka kafin yarima kamsus ya gama fadin abindake bakinsa tuni jaruma namrita tasa tafin hannunta a karon farko tun haduwarsu ta toshe masa baki kawai saita dubeshi a lokacin da hawaye ya zubo mata tace daga yau kada ka sake yadda gabata da mahaifinka ta shafi soyayyarmu. Hm wannan itace bakar soyayyah ko nace makauniya Guyson sunana muje zuwa kawai. Ka sani cewa koda zaka kasheni bayan na samu nasarar kashe mahaifinka ruhina zai bar gangar jikina yana begenka da ambatonka ni yau na cire sartsen da ya makale a cikin makoshin zuciyata tun da nasan matsayina a wajanka shawarara da zan baka itace kayi duk iya kokarinka wajan kare mahaifinka daga sharrinmu ni da dan uwana domin ba zaka taba sanin dadin mahaifi ba sai a ranar daka rasashi da wannan kalami nake yi maka sallama sai mun hadu a cikin birnin sarki masarul Anjana amma ina son kayi min alkawarin guda daya idan har soyayyarka a gareni gaskiyace koda jin wannan batu sai yarima kamsus ya dubi namrita cikin tsananin mamaki yace ke kuwa wane irin alkawari ne haka kike so nayi miki ? Guyson nake magana Namrita tayi ajiyar zuciya tace kayi min alkawari cewar ba zaka hada soyayyata da ta wata 'ya mace ba walau MUTUM KO ALJAN'' Koda jin wannan tambaya sai yarima kamsus yaji zuciyarsa ta buga da karfin gaske kuma ya rasa dalilin faruwar hakan saida ya shafe kimanin dakika biyar baice komai ba sannan ya dago kai yadubi namrita cikin murmushi yace na yi miki alkawari kece kadai zaki mallakeni a matsayin abokiyar rayuwata hm wai tarar Aradu ba gammo kenan yaji dadin zance fa guyson nake magana ki sani akan ki na fara yin soyayya don haka taya ya wata zata iya zuwa daga baya ta karbo miki abinda kika rigada mallaka? Yayinda namrita taji wannan batu sai farin ciki ya kamata ta sake yiwa kamsus sallama sannan ta bace bat tamkar bata taba wanzuwa ba a wajen -- gari na wayewa sai yarima kamsus ya farka daga barcin da yake yi mai nauyi yana bude idansa ya yi arba da mahaifinsa sarki Alkasim a zaune gefensa ya kura masa idanu yana yi masa murmushi yarima ya mike zaune zumbur ya dubeshi cikin kaduwa yace ya kai abbana yaushe ka shigo cikin tantin nawa ban sani ba? Koda jin wannan tambaya sai sarki alkasim ya bushe da dariya sannan yace ya za ayi kasan lokacin dana shigo alhalin jiya ka bata dare a wajen kulla soyayyarka. Koda jin haka sai mamaki gami da tsoro suka kama yarima zuciyarsa ta buga shi kuwa sarki sai yaci gaba da kalllonsa yana murmushi kawai yace bazan taba hanaka yin soyayya ba tunda ka riga ka kamuda son namrita amma ka sani cewa babu abinda yake janyowa jarumi rashin nasara a rayuwarsa face soyayya kaje ka nemi tarihin manyan mazajen duniya wadanda sukayi shuhurar da har yanzu ba a sami kamarsu ba irinsu HANTARU NA BIRNIN MISRA MAI TAKOBIN SAIFUL LUJARA soyayyace ta kai su izuwa ga hallaka dakuma SADAUKI SHADDADU DA HULKAS NA BIRNIN KUFAAA... duk sun mutune ta sanadiyar soyayyah na sani cewa duk abinda ya faru jiya a tsakanina da wannan muguwar dabba a lokacin damuka je gasar farauta a dajin darul samjul da kuma su namrita duk ka gani duk da cewa baka cikin hayyacinka sosai. To ka da zuciyarka ta karaya akan karfina da daukakata saboda ita wannan muguwar dabba data gagareni ba dabba bace aljanine kuma ya kasance daya daga cikin manyan zakwakuran jaruman sarki masarul Anjana kawai an turo shine domin a jarraba iyakar karfina . Aljanin yayi amfani da karfin sihirinsa ni kuma karfin damtsena kawai nayi amfani dashi saboda a dokar wannan gasa tamu ba aikin sihiri ko tsafi su kansu su namrita sun samu nasarar kashe aljanin ne da karfin sihiri ba wai da karfin damtesnsu ba na tabbata cewa yanzu shi kansa sarki masarul anjana ya tsorata da lamarina tunda ya gani da idanunsa yadda babban jaruminsa ya kasa hallakani da iya tsagwaron karfin damtsensa duk wannan lamari na gano shine bayan nayi bincike mai zurfi a cikin mudubin tsafina lokacin da sarki alkasim yazo nan a zancensa sai yarima kamsus ya kamu da matukar farin ciki don haka sai ya rungume sarki alkasim yana mai cewa ina alfahari dakai ya kai abbana hakika nasan cewa ruwa baya tsami banza domin nayi matukar mamakin yadda akayi dabba ta gagareka sarki alkasim ya janye jikinsa daga cikin na yarima yana murmushi yace ai na gaya maka tuntuni ko mutum ko aljan a cikin wannan duniya bana shakkarsa bare wata dabba in dai a fagen yakine ko gumurzu ba za a iya kaini kas ba sai dai da yaudara da ma sukayi amfani da ita da suka ga na ajiye sihirin tsafina a gefe daya amma daga yau bazan sake yin irin wannan kuskuren ba har yarima ya budi baki zaice wani abu sai ga kuyangi su biyu dauke da farantin abincinsa na kalaci Al amin Ahmed Misau Guyson Sunana kenan daga zauran labarai page nake magana bisa mamaki sai yaga yau abincin mai yawa ne ba yadda aka saba kawo masa ba koda kuyangin suka ajiye farantin abincin biyu a gabansu yarima sai suka juya suka fice daga cikintantin fitarsu keda wuya sarki ya dubeshi yace tashi da sauri kaje ka wanke bakinka muyi kalaci domin yanzun nan zamuyi shirin ci gaba da tafiya da jin haka sai yarima ya tashi da sauri ya bude akwatinsa ya dauki asuwakinsa kuma ya dauki battar ruwa ya fice da fitowarsa wajan tantin sai yaga ashe kowa ya dade da tashima an gama kimtsawa shine kadai ya makara ai kuwa sai yayi sauri ya goge bakinsa ya kuskure da tafin hannayansa ya koma cikin tantin da sauri ya zauna suka kama cin abincin shi da sarki rabon da yarima yaci abinci da sarki anfi shekara guda don haka sai ya kamu da mamaki dalilin da yasa sarki yazo har tantinsa domin suci abinci tare nan dai suka ci gaba da cin abincin cikin nishadi da nutsuwa. Tsawon yan dakiku dayansu baice uffanba sannan yarima yayi gyaran murya yace yakai abbana menene dalilin da yasa yau kayi sha awar cin abinci tare dani koda jin wannan tambaya sai sarki alkasim ya tsame hannayansa daga cikin abincin yayi shiru kansa na sunkuye kamar ba zaice komai ba daga can kuma sai ya dago kai ya dubi yarima a lokacin da idanunsa suka ciko da kwalla sannan yace kafin mahaifiyarka ta rasu ta bar min wasiyya akanka guda uku wasiyya ta farko itace kada na kuskura na hanaka duk abin Da kake so a cikin wannan duniya bisa wannan daliline na kasa hanaka yin soyayya da abokiyar gabata namrita guyson nake magana wasiyyata ta biyu itace lallai na baka horo na tarbiyya mai kyau domin kasan gaskiya da karya bisa wannan daliline nake yi maka horo idan ka aikata laifi ko da kuwa ni ka yiwa laifin ba wani ba wasiyyata ta karshe itace naja ka a jikina na nuna maka soyayya irin ta da da mahaifi bisa wannan daliline nake cin abinci tare dakai a cikin kwana guda ka sani cewa akan mahaifiyarka na fara yin soyayyah kuma a kanta na kulle soyayya daga ranar da mutuwa ta rabamu kawo i yanzu ban sake sha awar naso wata ya mace ba bare na sake yin aure ba komaine ya janyo hakan ba face nayi imani a cikin zuciyata cewar idan mutum ya rasa masoyiya ta farko ba zai taba samun kamarta ba mahaifiyarka ta fara kaunata tun bata san cewa ni dan sarkine ba a daji na hadu da ita kuma da kiyayya muka fara muka zamo abokan gaba wannan al amari ya farune kimanin shekaru talatin da biyu da suka shude.--- ---- YAMMACI NE MAI KYAN YANAYI DOMIN DAJIN YA KASANCE A CIKIN WATA IRIN NI'IMA ta wata irin iska mai dadin bugawa wacce bata haddasa sanyi ba kuma ta kore zafi bishiyoyi da koramai sai rangaji suke yi abin gwanin ban sha awa a dai dai wannan lokaci ne jarumi alkasim ya shigo cikin dajin rataye da kwari da baka a gadon bayansa a kuibin cinyarsa ta hagu kuwa wata sharbebiyar addarsa ce a daure ko riga babu a jikinsa sai gajeran wando iya guiwar kafafu wanda akayi shi da fatar damisa kyakkyawar surar jikinsa ta sadaukai duk ta bayyana a fili karara. Tun safe jarumi alkasim ya shiga cikin wannan daji da niyyar yin farauta amma baiga wata babbar dabba ba ko guda daya face kanana irinsu zomo da sauransu a tunanin yarima Alkasim a matsayinsa na babban jarumi kuma dan sarki guda daya jal tilo abin kunyane a gareshi ya shigo daji farauta ya koma gari a ganshi da karamar dabba. Bisa wannan daliline ya ci gaba da kutsawa ta cikin wannan daji har yamma ta riskeshi yana ta sanda gami da dube dube kwatsam ba zato ! Ba tsammani sai ya jiyo wani irin gurnani gami da sauti wanda ke nuna alamun cewa ana fafata gumurzu acan cikin wata sarkakiya mai duhuwa dake can gabansa nesa kadan nan take farin ciki ya kamashi ya ayyana a ransa cewa lallai wadansu manyan dabbobin dajin ne guda biyu suke yin gumurzu a tsakaninsu don haka ya samu damar da zai jefi tsuntsaye biyu da hoge guda kai tsaye alkasim ya ci gaba da durfafar wannan duhuwa yana mai ci gaba da yin sanda koda ya isa daf da wajen yaga abin dake faruwa sai ya kamu da tsananin al ajabi ba wani abu bane ya gani ba face wata zukekiyar santaleliyar kyakkyawar jarumar mace tana kokwawa da wani murtukeken zaki..... . Wow ni kaina guyson da nake typing ganin wannan kyakkyawar yarinya yasa na kasa ci gaba da typing kuma nake cewa mu tara a gobe idan Allah ya kaimu zaku jini da ci gaban wannan labari . Al Amin Misau ke magana Mutum Da Aljan Littafi Na Hudu (4) Part C. . Author- Abdul madakin gini AA Misau ke Magana . Labarin ya isowa Guyson cewa.. Lokacin da zukekiyar jarumar macen nan mai kyawun gaske ta ci gaba da gumurzu da wannan zakin sai ya zamana cewa idan zakin ya danne ta yana kokarin turmusheta ya kafa mata hakoransa sai ta juye dashi itama ta turmusheshi tana kokarin shake masa wuya duk da cewa zakin na karta faratan hannayansa a sassan jikinta amma ko kwarzane ya kasa yi mata saboda karfin sihirin tsafinta. Tun da sarki Alkasim yake yawo a duniya bai taba ganin mace mai karfin damtse kamar wannan ba don haka bai san sa adda yaci gaba da kallon taba kawai yana ganin ikon Allah sai da wannan jaruma da murgujejen zakin suka shafe kusan rabin sa a suna bakin artabu amma dayansu ya kasa samun nasarar hallaka daya ga dukkan alamu dai karfi yazo daya har jarumar ta yunkura ta zaro wata sharbebiyar wuka ta daga sama zata kirbawa zakin a makoshinsa sai kawai taga kibiya ta taho da gudu ta soke zakin a goshinsa ta faso keyansa maimakon zakin ya fadi kasa sai ya juya yayi arba da wanda ya harbo kibiyar ba wani bane ba face ALKASIM kawai sai zakin ya daaka tsalle saama izuwa kan Alkasim da nufin ya raromeshi su yi mutuwar kasko amma kafin zakin ya fada kansa tuni ya sake dana kibiya a cikin bakarsa ya sakar masa wani harbin ai kuwa sai kibiyar ta huda idon hagu na zakin ta sake bullowa a bayan kansa take zakin yayi sama yana ruri da kururuwa sannan ya fado kasa tim yana shure-shure. Ba a jima ba sai zakin ya zama gawa a sannan ne aka fara kallon kallo tsakanin sarki Alkasim da wannan bakuwar jaruma wacce bai santa ba kuma bai san daga inda tazo ba. Fuskarta a murtuke take sai daka masa harara take tamkar tana tsaye a gaban babban makiyinta na duniya kai kace ubanta ya kashe ba zaki ba yayin da alkasim yaga wannan tsaleliyar budurwa tana harararsa kuma tana yi masa wani irin kallo tamkar daga taga bakin kumurci sai kawai yayi murmushi ya mayar da takobinsa izuwa gadon bayansa ya sakaleta sannan ya nufi inda gawar zakin take ya sunkuya da nufin ya dauki zakin ya sabashi a kafadarsa kawai sai ji yayi anyi masa wani irin wawan naushi a gadon bayansa saboda karfin naushin sai da yayi tsalle can gefe daya fuskarsa ta gwaru a jikin wata bishiya ya fado kasa da rub da ciki kawai sai ji yayi jini na yoyo akan hancinsa da bakinsa. Cikin fushi alkasim ya mike tsaye zumbur kafin jarumar ta tako kafafunta sau biyu ya daka tsalle sama izuwa kanta ya doki kirjinta da kafarsa guda jarumar tayi taga taga da baya har sau uku kamar zata fadi kasa amma sai ta tsaya kyam a tsaye tana karkade kurar da kafar Alkasim ta sanyawa rigarta. Al amarin da yayi matukar girgiza hankalin alkasim kenan domin ba wai ya mace ba komai girman kato idan yayi masa irin wannan duka a kirji take yake faduwa kasa ya kama aman jini amma yau gashi ya mace ta shanye wannan duka nashi anya kuwa wannan mutumce? Tambayar da alkasim ya yiwa kansa kenan kuma ya rasa amsarta kawai sai alkasim da wannan jaruma suka kama zagaya junansu suna yin kallon kallo a karo na biyu har izuwa tsawon yan dakiku kwatsam kuma sai suka ruguntsuma da masifaffen fada suka wanzu suna masu kaiwa junansu naushi da bugu hannu da kafa ba tare da dayansu yayi yunkurin zare makami ba wohoho idan karfi ya hadu da karfi dolene kowa yaji a jikinsa haka dai wadannan jarumai suka ci gaba da gabzar junansu suna hadawa kansu jini da majina gami da jigata da zarar dayansu ya samu nasarar naushin daya sai kaga shi ma dayan ya rama babban abinda ya firgita alkasim shine ganin yadda karfinsa dana wannan jaruma yake neman zuwa daya sai da suka shafe kusan rabin sa a suna wannan bakin artabu har ya zamana cewa sun galabaita ainun tun suna yin fadan da kuzarinsu har saida karfinsu ya kare suka durkushe kasa bisa gwiwowinsu suka ci gaba da fadan kamar zakaru masu magana sunyi gaskiya da sukace dole itace kanwar naki babu shiri alkasim da jarumar suka baje a kasa suna haki kamar ransu zai fita saboda tsananin jigata sai bayan wata rabin sa ar sannan sukayi zumbur a tare kamar hadin baki kowannansu ya kaiwa kofar mataccen zakin sura a lokaci guda koda taja shi ma yaja sai suka tsarge jikin zakin tamkar takobi aka sa aka datsashi kawai sai jarumar ta dubi sarki Alkasim tayi masa wani dan guntun murmushi na mugunta tace mun rabawa kanmu gardama yanzu tunda mun raba zakin biyu dai dai amma ka sani cewa daga yau nidakai mun zama abokan gaba tunda kaso ne kayi min kwace alhalin nice ta kamaci mallakar wannan zakin gaba dayansatana gama fadin hakan saita saba rabin zakin a kafadarta ta juya da sauri ta falfala da azababben gudu izuwa cikin wannan duhuwar daji cikin hanzari alkasin ya bita da gudun amma ko hangota baiyi ba domin ta bace bat tamkar walkiya sai da ya shafe yan dakiku masu yawa yana ta gudu a cikin dajin yana waige waige da dube dube ko zai ga wannan jaruma amma ko alamunta bai gani ba al amarin da Yayi matukar bashi mamaki kenan ya fara zancen zuci yana mai cewa anya kuwa wannan jarumar mutum ce? Idan har ta kasance mutum dole ne ya kasance tana da zuri:a Al amin Ahmed Misau Guyson sunana kenan nake magana daga zauran labarai page ina ne gidansu ko kuma ina ne garinsu ko kuwa a cikin wani ayari take na fatake? Amsar da alkasim ya kasa baiwa kansa kenan haka dai alkasim yayi ta wannan hasashe da zulumi a cikin zuciyarsa har ya dawo cikin birnin misra da shigarsa cikin gidan sarautar sai ya wuce kai tsaye izuwa fadar sarki inda ya zube gabansa ya kwashi gaisuwa guyson sunana ko kuce Al amin Ahmed Dan misau Daga zauran labarai shikuwa sarki sai ya dubeshi cikin alamun matukar mamaki yace yakai dana abin alfaharina ya kai dodon maza zaki uban dawa kuma guguwa mai baje birane yau kuma me ya faru naga ka dawo daga farauta babu komai a tare dakai shin babu sauran dabbobine a cikin dajin namu ko kuwa ka fasa yin farautar ne ka juyo da baya? Lokacin da yarima Alkasim yaji wadannan tambayoyi guda biyu sai yayi ajiyar numfashi cikin alamun karayar zuciya nan take ya kwashe labarin duk da ya faru tsakaninsa da wannan bakuwar jaruma ya zayyane masa koda jin wannan labari sai sarki ya takarkare ya bushe da mahaukaciyar dariya yana mai tsananin farin ciki tamkar wanda aka yiwa albishir babba Al amarin da yayi matukar baiwa kowa mamaki kenan daga can sai sarki ya tsuke bakinsa yayi shiru ga barin yin dariyar sannan ya dubi yarima alkasim cikin murmushi yace wannan bakuwar jaruma itace matar da zaka aura har ka samu haihuwa da ita toh Guyson nake magana gobe ka sake yin shiri ka tafi daji ba don kayi farautar dabba ba sai domin farautar wannan mata taka duk wahalar da zaka sha da duk irin wulakancin da zaka fuskanta ka juresa yayin da alkasim yaji wannan batu sai shima fuskarsa ta fadada da murmushi ya mike tsaye ya dafa kirjinsa da hannu guda ya dubi sarki cikin dakakkiyar zuciya yace yakai abbana idan har na cika jininka nayi maka alkawari cewar duk irin gabar da zamu yi da wannan jaruma sai na siye zuciyarta ta kaunaceni'' typing by me Al amin Ahmed Guyson daga zauran labarai koda jin haka sai sarki ya sake kamuwa da matukar farin ciki ya mike tsaye daga kan karagarsa ya rungume alkasim yana mai cewa ina alfahari dakai yakai dana nasan zaka iya har dare ya raba alkasim bai rintsa ba domin da zarar ya rufe idanunsa baya ganin komai face fuskar wannan bakuwar jaruma a yinin gaba daya ka kasa ci da shan komai ko a zaune ko a tsaye sai yayi ta tuno da abubuwan da suka faru a tsakaninsa da bakuwar jarumar a daji dakyar dai alkasim ya samu yayi dan barcin amma alfijir na ketowa ya farka nan take yasa kuyangi suka shirya masa ruwan wanka da abincinsa na kalaci ya kimtsa kafin gari ya soma haske tuni ya gama shirin tafiya farauta ba tare da bata wani lokaci ba yarima ya hau dokinsa ya fice daga cikin gidan sarautar ya nausa izuwa cikin wannan daji wanda ya hadu da bakuwar jaruma a cikinsa jiya alkasim yaci gaba da nausawa cikin dajin yana ta dube dube da waige waige kai wani lokacin har saukowa yake daga kan dokinsa yana duba kasa ko zaiga sahul bil adama amma ko alamarsa bai gani ba sai da ya shafe sa a biyu da rabi yana ta kai kawo a cikin dajin banda dabbobi da tsuntsayebabu abinda yake gani da yake wannan karon ba tasu yake ba sai dai su wuce ya wuce abinsa babu mai tankawa wani hakanne yasa alkasim yaji ya kosa kuma zuciyarsa ta fara karaya da saran cewa zai sake haduwa da wannan bakuwar jaruma duk da mahaifinsa ya gaya masa cewa itace matar da zata zamo abokiyar rayuwarsa lokacin da rana ta kwale sai alkasim ya nufi wata katuwar bishiya mai yawan ganyaye domin yaje ya zauna a karkashinta ya huta da isarsa bakin bishiyar sai ya sauka daga kan dokin ya daure dokin a jikin bishiyar sannan ya zauna a lokacin da wata irin iska mai dadin sanyi ta fara kadawa hakan ne yasa ya kishingida yana mai jingina gadon bayansa a jikin bishiyar saboda gajiyar dake jikinsa sai kawai ya fara yin gyangyadi faruwar hakan keda wuya sai yaji wani abu na yawo a jikinsa tun daga kan kafafunsa a firgice alkasim ya yunkura domin zare takobinsa amma sai yaji an kanannade jikinsa gaba daya kafin yayi wani yunkuri tuni wannan bishiya ta dare saiga wata kofa ta bayyana nan take wata iska mai karfi ta fito daga cikin kofar ta zuke alkasim a lokacin da yaji wata irin kasala ta shigeshi yadda ko hannunsa ba zai iya motsawa ba ashe wata murtukekiyar macijiyace ta kanannade shi gaba dayan jikinsa kawai sai gani yayi an fyadashi da kasa a tsakiyar wata kasaitacciyar fada. Fadar ta kawatu ainun da kayan kyale kyale kai kace fadar birnin misra, Al amin Ahmed Guyson sunana' koda alkasim ya dago kansa cikin matukar karfin hali sai yaga ashe babu kowa a cikin fadar face mutum daya jal kuma ba kowa bane face wannan bakuwar jaruma ita kadai zaune aakan wata katuwar karagar mulki taci ado irin na 'ya 'yan sarakai. Koda yarima Alkasim yaga jarumar a cikin wannan hali sai ya kidime yaji ya kara kamuwa da tsananin sonta fiye da ko yaushe.. Don haka sai ya kura mata idanu yana murmushi ita kuwa saita murtuke fuskarta ta dubeshi a fusace tace mazaka bani amsar tambayar da zanyi maka yanzu in ba haka ba kuwa zan gana maka azabar da ba a taba yi maka irin taba koda jin wannan batu sai alkasim yayi murmushi yace '' ina sauraronki me kike so kiji'' , kuma a nanne MUTUM DA ALJAN littafi na HUDU (4) Yazo karshe marubucin yace:- SHIN ME ZAI FARU A CIKIN TAFIYAR YARIMA ALKASIM DA JARUMA LUSLAIYA? . KAFIN SU KAMMALA GASARSU HAR TA KAMU DA SONSA SUYI AURE KUMA MENENE SANADIN AJALINTA? . IDAN AKA ISA GARIN SARKI MASARUL ANJANA ME ZAI FARU TSAKANIN GIMBIYA ZULFULAIFA DA YARIMA KAMSUS KUMA MAI ZAI FARU A TSAKANIN SARKI ALKASIM DA SARKI MASARUL ANJANA? . INA LABARIN JARUMI ZAIHAS DA YAR'UWARSA? . SHIN ZASU SAMU NASARAR DAUKAR FANSA A KAN SARKI ALKASIM? . mu hadu a littafi na Biyar domin jin cigaban wannan labari.