ALLON SIHIRI Littafi na Hudu (4) LOKACIN da Yarima Lubainu ya gama aiyana haka a zuciyarsa sai ya daga kai ya dubi Aljana Badi'atul Sarira yace,yake wannan ma'abociyar kyau da siffa ta ban al'ajabi,kiyi sani cewa hakika kin zo mini da babban al'amaro wanda bazan iya yin saurin yanke hukunci a kansa ba,saboda haka ina so ki bani lokaci zuwa gobe da safe nayi tunani,sannan na yanke shawara bisa abinda nake ganin zai fissheni.Koda jin wannan batu sai Aljana Badi'atul Sarira taja dogon numfashi cikin alamun takaici ta dubi Yarima Lubainu tace,kaiconka ya kai wannan dan sarki,kayi sani cewa tabbas saikayi babbar nadama idan kaki amfani da wannan dama dana baka yanzu,domin kuwa har abada bukatarka bazata taba biya ba.Ina mai tabbatar maka da cewa Sarauniya Akisatul Sauwara da Sarki Darmanu yaudararka zasuyi su gudu da wannan ALLON SIHIRI,Shi kuwa wannan Bakon Jarumi indai ka yi kuskuren karbar ADDININSA to har abada bazaka warke ba daga wannan lalura taka,saidai ka rungumi kaddara.Lokacin da Aljana Badia'atul Sarira tazo nan a zancenta sai hankalin Yarima Lubainu ya sake dugunzuma fiye da koyaushe.Nanfa ya kama duru duru ya rasa abinda zaiyi,kawai sai ya dubi Badi'atul Sarira yace,kiyi hakuri ni bana aiki da gaggawa,dole ne ki bari zuwa gobe da safe.Nayi miki alkawarin zan dawo gareki da duku dukun safiya kafin sauran abokan tafiya su fito domin na sanar dake hukuncin dana yanke.Yarima Lubainu na gama fadin hakan sai ya juya da nufin ya fice daga cikin lambun,amma sai Badi'atul Sarira ta kira sunansa ya waigo da sauri suka dubi juna a lokacin dayaga hawaye na cigaba da tsartuwa akan kumatunta.Badi'atul Sarira ta budi baki tace,shikke na tunda ka kasa yanke hukunci yanzu,ina son kayi min alkawarin cewa bazaka sanar da abokan tafiyarka labarina ba koda kuwa ka yanke hukuncin bazaka kwanceni ba daga cikin wannan dauri daka riskeni a ciki?Sa'adda Yarima Lubainu yaji wannan batu sai ya sake yin shiru yayi dan guntun tunani sannan yace shike nan babu matsala nayi alkawarin zan rufe sirrinki.Yana gama fadin hakan ya juya ya fice daga cikin lambun ya nufi wani dakin dabam ya fada cikinsa.Yana shiga yaga ashe falo ne guda daya,wato falle daya babu dakin barci a cikinsa,kuma babu komai a cikin falon face shimfida ta wani jan kilishi da kuma manyan dogayen kujeru masu taushi guda biyu.A tsakiyar kujerun kuma an ajiye wani farin tebur na azurfa.Koda ganin wannan tsari sai Yarima Lubainu ya aiyana a cikin ransa cewa"duk yadda akayi wannan daki ne inda Boka Darbusa ke Hutawa".Take Yarima Lubainu ya tafi izuwa kan daya daga cikin kujerun ya kwanta.Kwanciyarsa keda wuya sai barci mai karfi ya saceshi saboda tsananin gajiya da tsamin jiki sakamakon gumurzun da suka sha.Wannan shine abinda ya garu gasu Yarima Lubainu bayan sun sami nasarar dauko ALLON SIHIRI a gidan Boka Darbusa. ¤¤¤ ¤¤¤ ¤¤¤ AMMA abinda basu sani ba shine,karbar wannan ALLON SIHIRI na Boka Darbusa daidai yake da ALLURA TA TONO GARMA!Domin duk halin da suke ciki Boka Darbusa ya gani a cikin MADUBIN TSAFINSA a cikin wani kogon dutse dake wani bangare dabam na wannan daji da suke ciki.Shidai wannan kogon dutse babu yadda za'ayi a gane cewa akwai mutum a cikinsa,saboda dutse ne lailayayye kuma fafaffe mai siffar kwai,amma sai Boka Darbusa yasa Aljanu suka fafe cikinsa suka gina masa dakuna a ciki wadanda aka shiryawa kayan kawa a cikinsu tamkar aljannar duniya.A cikin wannan gida akwai hadima sama da guda dubu na jinsin mutane da aljanu,kuma suna rayuwa a cikinsa tamkar ba a cikin dutse suke ba saboda tsananin karfin sihirin tsafi irin na Boka Darbusa.Bayan Boka Darbusa yaga yadda Bakon Jarumi ya sami nasarar tarwatsa wannan bakaken aljanu daya turo su dauko ALLON SIHIRI sai ya takarkare ya bushe da dariyar mugunta yayita kyakyatawa kamar bazai daina ba.Al'amarin dayai matukar baiwa babban wazirinsa mamaki kenan wanda ake kira da suna YAUHAN.Ya dubeshi a cikin alamun damuwa yace,haba ya shugabana yaya kake ta faman yin dariya haka alhalin makiyanmu ne suke samun galaba akanmu?Shin ka manta ne cewa sun koremu daga cikin ainihin fadarmu kuma sun rabamu da Allonmu na Sihiri? Koda jin wannan tambaya sai Boka Darbusa yayi murmushi mai nuna jin kai gami da izza yace,ai duk wannan nasara dasu Bakon Jarumi suka samu ta banza ce domin yanzu aka fara wannan mugun wasa.Ka sani cewa ina da tarkuna guda arba'in da zan dana musu a cikin hanyoyinsu wadanda basu isa su shallakesu ba har su iso KOGIN BAHAR IMFAL ba tare da sun hallaka ba gaba dayansu.Abinda ya bakanta mini rai a yanzu shine Yarima Lubainu ya san cewa shi dasu Akisatul Sauwara bazasu iya karanta dalasiman tsafin dake jikin Allon Sihirin ba,Badi'atul Sarira ce kawai zata iya.To amma abin tambaya game da Yarima Lubainu a yanzu shine,shin zai iya taimakon Badi'atul Sarira har ya kwanceta,kuma idan ya taimaketan itama zata taimakeshi ne bazata ci amanarsa ba?Koda jin wadannan tambayoyi sai hankalin Waziri Yauhan ya dugunzuma ainun ya dubi Boka Darbusa cikin alamun damuwa yace,ya shugabana yanzu yaya zamuyi kenan?Tabbas idan Yarima Lubainu da Badi'atul Sarira suka hada kai suka taimaki junansu bada yaudara ko cin amana ba tamu ta kare.Koda jin wannan batu sai Boka Darbusa ya kyalkyale da dariya sannan ya daga kafadar waziri Yauhan yace,ai abinda ba zai taba yiyuwa bane Badi'atul Sarira da Yarima Lubainu su hada kai ba tare da dayansu ya yaudari dayan ba.Shin ka manta cewa dukkan wani MATSAFI mayaudari ne,kuma makaryaci?Ka zuba ido kawai kasha kallo kawai,zakaga yadda zata wakana a tsakaninsu.Shi kansa wannan Bakon Jarumi sai yayi nadamar kulla alaka dasu Sarauniya Akisatul Sauwara domin yaudararsa zasuyi a karshe ba zasu taba karbar wannan bakon Addini nasa ba. ¤¤¤ ¤¤¤ ¤¤¤ A CAN BIRNIN ZAMRUL kuwa tun daga ranar da Yarima Lubainu ya bar kasar domin tafiya neman maganin lalurar da Yarima Mangul ya saka masa sai Amarya Yazarina ta kasance kullum cikin kuka da bakin ciki dare da rana,har ya zamana cewa ta fara shiga wani mugun hali na rashin lafiya sakamakon yawan tunani da rashin cin isasshen abinci.Al'amarin dayai matukar dugunzuma hankalin Sarki Sailur kenan da kuma mahaifinta Attajiri Abu Yazarina suka rasa yadda zasu bullowa al'amarin saboda babu irin matakan da basu dauka ba wajen ganin ta daina kukan da bakin ciki gami da yawan tunani amma abun ya gagara.Lokacin da Tura takai Bango ya zamana cewa rashin lafiyar Yazarina tayi tsamarin da takai ga kwanciya sai likitan sarki Sailur ya bashi shawarar lallai a hanzarta yiwa Yazarina maganin abinda yake damunta,idan ba haka ba kuwa za'a iya rasa rayuwarta ma gaba daya.Koda jin wannan batu sai hankalin sarki sailur ya tashi,take ya tura aka kirawo Attajiri Abul Yazarina suka kadaita a cikin turakarsa.Sarki Sailur ya dubi Abul Yazarina cikin alamun tsananin damuwa yace,yakai abokina na sani cewa a duniya kaf babu abinda kakeso sama da wannan 'ya taka Yazarina wato matar 'dana Yarima Lubainu.Kuma nayi imamin kasan dukkan wani hali da yanayi da take ciki dangane da rashin lafiyarta,to ka sani cewa a yau abin yayi tsamari fiye da koyaushe wanda sanadin hakan ne ma yasaka likitana ya tabbatar mini da cewa idan har ba'a sadata da mijinta ba da gaggawa wannan ciwo nata zai iya zama sanadin ajalinta.Koda jin wannan batu sai nan take idanun attajiri Abul Yazarina suka ciko da kwallah.Sarki Sailur ya cigaba da cewa,nidai yanzu na kirawoka ne domin mu yanke shawara bisa abinda nake gani zai kawo karshen wannan matsala.Ka sani cewa ni kaina ina cikin mugun tashin hankali tun daga ranar da dana Yarima Lubainu yasa kafarsa yabar garin nan saboda bani da tabbacin cewa zai sami nasarar samo abinda ya fita nema ba tare daya rasa rayuwarsa ba.Sannan kuma idan har ya dawo ya iske Yazarina ta mutu zai iya kashe kansa koya susuce yadda bazai iya gadar karagata ba,yanzu menene abinda kake ganin ya kamata muyi domin ceton rayuwar wadannan 'ya'ya namu.Sa'adda sarki Sailur yazo nan a zancensa sai Attajiri Abu Yazarina ya kawo gwauron numfashi ya ajiye kuma yayi shiru yana tunani har izuwa tsawon yan dakiku daga can kuma sai ya dago kai ya dubi sarki Sailur yace yakai abokina kayi sani cewa hanya daya ce damu wacce zamu iya bi mu magance wannan matsala.Dole ne mu hakura da zaman 'yata anan kasar mu hadata da amintattun dakarunmu su tafi neman Yarima Lubainu.Ina mai tabbatar maka da cewa ko a yanzu muka yiwa Yazarina bushara da hakan take zata sami lafiyar jikinta ta mike tsaye.Yayin da sarki Sailur yai wannan shawara sai ya gyada kai cikin alamun murna yana murmushi,sannan can kuma sai ya hade rai ya dubi Abu Yazarina cikin alamun matukar damuwa yace,na yarda da wannan shawara taka,amma fa kasani cewa akwai mugun hadari a cikinta.Hadari na farko shine zamu iya baiwa Yazarina cikakkiyar kariya ne kadai idan tana cikin wannan birni namu,amma idan har tasa kafarta ta fita koda mun hadata da dukkan dakarun yakin kasar nan ba zasu iya kareta daga harin mai son ta ba,wato YARIMA MANGUL.Saidai idan baisan cewa ta fito ba domin kuwa dole ya tura a satota a kaita gareshi.Hadari na biyu shine wannan tafiya da zatayi izuwa inda Yarima Lubainu ya nufa tafi komai hadari domin takadiran mutane da aljanu da matsafa suka kwallafa ransu akan wannan ALLONSIHIRI kuma suna da yawa,kuma zasu iya kawar da duk wanda ya shigo cikin al'amarin.Bisa wannan dalili da hujjoji kaga kenan 'yata zata iya rasa rayuwarta tun kafin ma ta sadu da masoyin nata Yarima Lubainu.Lokacin da attajiri Abul Yazarina yazo nan a zancensa sai Sarki Sailur yayi ajiyar numfashi yace,tabbas duk abinda ka fada gaskiya ne amma kuma akwai wani hanzari akan haka.Da farko dai inaso ka sani cewa zamu iya fitar da 'yarka daga cikin garin nan a sirrance ba tare da kowa ya sani ba bare har labarin hakan ya kai izuwa kunnen Yarima Mangul.Kuma koda ace ma yaji din kuma ya sami nasarar saceta ai garinsu zai kaita,kasan kuwa indai Sarki ALKAS na raye,bazai taba barin shi ya aureta ba bisa dole,kuma zai karbeta ne ya dawo da ita garemu.Dangane da batun hadarin dake cikin tafiyar zatayi kuwa,ina son na tambayeka.Shin da zamanta a gabanmu cikin mayuwacin halin rashin lafiyar da zata iya zama sanadin ajalinta a ko yaushe da kuma tafiyarta cikin koshin lafiya bisa burin saduwa da masoyinta wanne ne yafi mana sauki?Koda jin wanna batu sai Attajiri Abul Yazarina ya sunkui da kansa kas yayi shiru yana tunani sannan ya dago kai ya dubi sarki Sailur yace,hakika shawararka itace mafi kyau,don haka inason ka zabo BABBAN JARUMI daga cikin mayakanka wanda ka aminta dashi ainun ka hadashi da wadannan AMINTATTUN DAKARUNKA suyiwa 'yata rakiya a cikin wannan tafiya.Amma abinda danake so dakai shine,dasu da ita zasuyi bad-da- kama ne ma'ana suyi shiga kawai irin ta FATAKE su fice daga cikin garin nan a sirrance ba tare da wani ya shaidasu ba.Koda jin wannan batu sai farinciki ya lullibe sarki Sailur yace,nima na karbi wannan shawara dakazo da ita,kuma na umarceka daka tafi izuwa bangaren da yarka take a cikin wannan gidan sarauta nawa kayi mata wannan kyakyawan ALBISHIR da duk wani abu da muka shirya yanzu.Kuma ka gaya mata cewa a yau dinnan zan kammala dukkan wani shirye shirye na wannan tafiya tasu,kuma a tsakiyar dare zasu fita daga cikin garin nan.Koda jin wannan batu sai farinciki ya lullube Attajiri Abu Yazarina ya zube lasa a gaba sarki Sailur ya kama godiya.Koda ganin haka sai Sarki Sailur yayi sauri ya sunkuya ya kama kafadunsa ya tasheshi tsaye,ya sallameshi ya tafi izuwa bangaren da turakar Yazarina take.Fitar Attajiri Abul Yazarina keda wuya daga cikin turarkar sarki Sailur ya nufi cikin gidan Sarautar bangaren 'yarsa Yazarina,sai sarki Sailur ya tura aka kirawo masa mataimakin sarkin yakin kasar wanda ake kira da suna BARDE RUHAISU.Barde Ruhaisu ya kasance saurayi kyakyawa dan kimanin shekaru ashirin da takwas,amma kuma GWARZON JARUMI NE mai TARWATSA MAZA a FILIN DAGA.Sau bakwai Barde Ruhaisu yana jagorantar rundunar yaki a birnin Zamrul ana samin nasara na tare da anyi wata mummunar asara ba ta rayukan DAKARUN YAKI.Allah ya horewa Ruhaisu baiwar sanin YAKI da TUGGUNSA kuma yana da matukar TUNANI mai kyau gami da HANGEN NESA.Duk da cewa sarkin yakin kasar yafi barde Ruhaisu KARFIN DAMTSE da iya yaki da kuma kwarewa akan sanin tuggun yaki amma sarki sailur yafi aminta da Barde Ruhaisu dari bisa dari saboda ya jarraba amanarsa ya gani.Shi kuwa sarkin yaki mutum ne mai tsananin son abin duniya gami da MULKI,don haka sarki Sailur yana tsoron cewa wata rana zai iya cin amanarsa don cika burin rayuwarsa.Bisa wannan dalili ne sarki Sailur yake shirya komai nasa na sirri da Barde Ruhaisu,shi kuwa sarkin yaki sai ya bar masa abubuwan da basa bukatar sirri na cigaban kasa da kuma kare kasar daga yan hari ko ABOKAN GABA.Sarki Sailur yana zaune a cikin falon turakarsa yayi tagumi yana tunani da nazarin abinda ke gabansa,sai ga Barde Ruhaisu ya shigo.Tun daga nesa kadan Barde Ruhaisu ya cire takalminsa saboda biyayya,yana kara matsowa kusa da sarki Sailur sai ya zube kasa wanwar ya kwashi gaisuwa.Cikin hanzari sarki Sailur ya mike daga kan kujerar dayake zaune ya kama kafadunsa ya tasheshi tsaye kuma ya rike hannunsa yajashi izuwa kan kujerar da yake zaune suka zauna tare.Sarki Sailur ya gyara zama ya dubi Barde Ruhaisu cikin nutsuwa yace,yakai JARUMIN JARUMAI kuma BABBAR DIRKA ta birnin Zamrul,ka sani cewa ban kirawoka nan ba sai domin na baka wani gagarumin aiki mai mugun hadari wanda nakeson ka gabatar dashi a cikin sirri.Kafin na sanar dakai yanayin wannan aiki inason nayi maka wadansu tambayoyi guda biyu.ALLON SIHIRI Littafi na Hudu (4) Part B Kafin na sanar dakai yanayin wannan aiki inason nayi maka wadansu tambayoyi guda biyu.Tambaya ta farko itace shin zaka iya sadaukar da rayuwarka don ceton ta wanda nake kauna fiye da komai a duniya?Koda jin wannan tambaya sai nan take idanun Barde Ruhaisu suka ciko da kwalla ya dubi Sarki Sailur yace tayaya zan kasa fansar da raina ga wanda ya raineni ya rikeni tamkar dan cikinsa alhalin na kasance tsintaccen bawa da baisan iyayensa ba kuma bai san asalinsa ba?Koda jin wannan batu sai shima Sarki Sailur yaji hawaye ya subuto masa amma sai yai sauri ya sunkui da kansa kas yace,yakai Barde Ruhaisu shin zaka iya rabuwa da amaryarka wacce ke dauke da juna biyu na tsawon wata takwas tana shirin haife maka 'da ko 'ya don zuwa cika aikina alhalin ganin 'danka ko 'yarka a yanzu shine babban burinka a rayuwa?Da jin wannan tambaya sai hawaye ya zubowa Barde Ruhaisu yace,ya shugabana kasani cewa dani da duk abinda na mallaka zan iya bayar dashi FANSA akan halaccin da kayi mini a rayuwa,kuma a kaso dari ban saka maka da kaso goma ba.Koda jin wannan batu sai sarki Sailur ya rungume Barde Ruhaisu duk su biyun suka fashe da kuka.Tsakanin Sarki Sailur da Barde Ruhaisu akwai tsananin kauna da shakuwa domin kafin Allah ya baiwa Matar Sarki Sailur haihuwar Yarima Lubainu saida suka shekara goma sha shida da aure ko batan wata bata bata yiba.A wannan lokaci babu irin kokarin da Sarki Sailur da matarsa basuyi ba akan su sami haihuwa har saida suka hakura suka rungumi kaddara.Wata rana sarki Sailur ya fita wani gagarumin yaki a wata kasa da ake kira DARNIS,wadanda tun iyaye da kakanni akeyin mummunar gaba a tsakanin kasashen biyu,sai Allah ya basu nasara suka kashe gaba dayan dakarun yakin birnin Darnis,kuma suka balle kofar birnin suka cigaba da kashe dukkan mazajen garin manya da kanana banda yan kasa da shekara goma saida ya zamana cewa sun gama da dukkan wani namiji mai karfi a jika wanda zai iya tabuka wani abin arziki.Ba komai ne yasa su sarki Sailur sukayi wannan rashin imani ba face akwai lokacin da gaba daya mazajen garin suka kai musu harin sumame suka kashe sama da mutane miliyan uku,da kyar da sidin goshi aka koresu daga cikin birnin Zamrul bayan sunyi mummunar barna sun kama bayi kuma sun kwashe dukiya mai yawan gaske sun kone kusan rabin birnin.Da gaiya Su Sarki Sailur su kayi ta ragargazarsu baji ba gani,kuma ba sassauci sannan suka yi ta kama matayensu a matsayin bayi,yara da tsofaffi ne kadai suka kai labari.Lokacin da Sarki Sailur ya shiga cikin gidan sarautar birnin Darnis ya sami nasarar kashe sarkinsu,ya kama matayensa a matsayin bayi da 'ya'yansa kanana saiya kunna kai izuwa cikin turakarsa.Yana shiga cikin turakar ne ya iske wani yaro dan kimanin shekaru goma kwance a kas an dora masa wani katon dutse a ciki yana ta numfarfashi kamar ransa zai fita.Koda ganin wannan yaro a cikin wannan halo sai Sarki Sailur ya ruga da gudu izuwa ga yaron yai sauri ya dauke dutsen daga kan cikin yaron sannan ya tasheshi zaune.Koda ya kalli fuskar yaron yaga yadda lebensa ya bushe saboda tsabar kishirwa da kuma yadda ya galabaita ainun sai ya kamu da tsananin tausayinsa.Nan take yai sauri yaje ya nemo ruwa ya baiwa yaron yasha.Saida yaron ya dawo cikin hayyacinsa sannan sarki Sailur ya dubeshi cikin nutsuwa yace,yakai wannan yaro waye yayi maka wannan muguwar azaba haka yake neman hallaka ka?Koda jin wannan tambaya sai yaron ya budi baki da kyar yace,sarki ne yayi mini wannan azaba saboda bani da lafiya na kasa aiwatar da aikin dana sabayi a kullum.Cikin mamaki sarki Sailur ya sake duban yaron yace,aikin ne kakeyi masa na bauta?Yaron yace nine mai wanke masa kwanukan abinci da kofuna.Sarki Sailur ya girgiza kai yace,shin kai haifaffen nan garin ne? Yaron ya girgiza kai yace NI BAWA ne bansan ASALINA ba,bansan IYAYENA ba,kawai na taso ne na tsinci kaina a cikin wannan gidan sarauta tun banyi wayo haka ba ina aikin bauta.Koda jin wannan batu sai sarki Sailur yaji ya kamu da tsananin tausayin yaron fiye da koyaushe ya dafa kafadarsa yace mene ne sunanka?Yaeon yace Sunana RUHAISU.Cikin murna da murmushi sarki Sailur ya dubi Ruhaisu kayi sani cewa daga yau ka zama dana,kuma nayi maka alkawarin cewar zan rikeka tamkar dan dana haifa a cikina,kuma zan duba abinda kafi cancanta dashi a rayuwa na doraka a kansa.Koda Yaron Ruhaisu yaji wannan batu sai fuskarsa ta fadada da murmushi ya kamu da tsananin farin ciki ya dubi Sailur yace,wane ne kai,kuma menene dalilin da yasa kukazo garin nan kuka afka mana da yaki?Shin kun kashe sarki ne ko kuwa kun kamashi a raye.Koda jin wannan tambaya sai sarki Sailur yayi murmushi yace Sunana SARKI SAILUR nai mulkin BIRNIN ZAMRUL.Ya kai Ruhaisu kayi sani cewa tsakanin kasata da wannan birni na azzalumin sarkinku akwai TSOHUWAR GABA tun iyaye da kakanni,kuma kimanin shekaru uku baya sarkinka da mayankansa sunje birnina sunyi mini mummunar barna shine mu ma yanzu mukazo mukayi RAMUWAR GAYYA.Tuni sarkinka ya dade da shekawa BARZAHU.Daga yau na yantaka kashi daga matsayin bawa ka zama cikakken da kuma dan sarki ba wai talakan gari ba.Koda gama fadin hakan sai sarki Sailur ya kama hannun yaro Ruhaisu yajashi suka fice daga cikin turakar.Ai kuwa suna fitowa kofar turakar ne yaro Ruhaisu yayi tuntube da gawar azzalumin sarkinsa.Kawai saiya tofawa gawar yawu yace,tur dakai azzalumi,azaba ninkin wadda ka yimini sau dubu ta tabbata a gareka a cikin kabarinka.Koda jin wannan batu sai sarki sailur ya fahimci cewar tabbas yaro Ruhaisu yasha bakar wahala ta gaske a hannun wannan sarki. Tun daga wannan rana kasar Darnis ta dawo karkashin mulkin birnin Zamrul,aka mayar da ita bbabar jaha kuma babbar cibiya ta kasuwanci. ¤¤¤ ¤¤¤ ¤¤¤ LOKACIN da Sarki Sailur yazo da yaro Ruhaisu gida sai ya tara gaba dayan yan majalisarsa da fadawansa ya gabatar da yaro Ruhaisu a garesu kuma yace dasu daga yau sunan wannan yaro Yarima Ruhaisu.Bawa ne amma na yantashi na maishe dashi tamkar dan cikina.Koda jin wannan batu sai mamaki ya turnuke kowa fadawa suka kama kace nace.Wasu suce yama za'ayi sarki ya dauko bawan da bashi da asali yace ya maishe dashi dansa,harma ya kirashi a matsayin yarima mai jiran gado!Au wannan abin kunyane abin gori a gareshi dama masarauatar birnin gaba daya!!!Wasu kuwa sai suka rinka cewa ai bazata sabi ba BINDIGA A RUWA a kawo bare wanda ba an kasa ba ace nan gaba shine zai mulkesu.Koda sarki Sailur yaji irin surutun da yan majalisarsu da fadawansa sukeyi sai ransa ya baci,zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone bai san sa'adda ya mike tsaye ba zumbur daga kan KARAGAR MULKINsa ya daka kakkafar TSAWA wadda tasa hantar cikin kowa ta kada saboda tsananin tsoronsa da akeji.Nan ake fadar tayi tsit kowa ya sunkui da kansa kasa kamar ruwa yaci su.A sannan ne sarki Sailur yace,nine sarki a wannan birni na Zamrul,babu wani mai matsayin dayafini don haka idan har na gabatar da HUKUNCI babu wanda ya isa ya sauya mini shi.Wannan Yaro Ruhaisu shine Yarima na,wanda duk ya kara magana akan haka da hannuna zan cisge masa kansa!!!Koda jin wannan batu sai gaba dayan mutanen dake cikin fadar suka sake shiga taitayinsu aka rasa wanda ma zai iya daga kansa sama ya dubi sarki Sailur.Koda Yaro Ruhaisu yaga abinda ya faru tsakanin sarki Sailur da mutanensa sai ya fashe da kuka ya durkusa bisa gwiwoyinsa a gaban sarki saiur.Al'marin daya baiwa kowa mamaki kenan a fadar aka kurawa sarki Sailur da Yaro Ruhaisu idanu.Shi kuwa sarki sailur sai hankalinsa ya DUGUNZUMA shima ya durkusa a gaban Ruhaisu ya kama kafadarsa ya rike kuma ya dubeshi cikin alamun tsananin damuwa da fargaba ya ce yakai dana ina dalilin wannan kuka naka? Yaro Ruhaisu ya dubi sarki Sailur cikin nutsuwa yace,yakai wannan sarki mai daraja,kayi sani cewa babu wani jin dadi ko kwanciyar hankali ga kowanne sarki komai arzikinsa da daukakarsa face ya sami soyayya da kaunarsa a cikin zukatan jama'arsa sannan ya cika sarki mai kima da daraja,domin a sannan ne jama'ar tasa zasu iya siyar da rayukansu domin tsare lafiyarsa da mutuncinsa.Ya kai wannan sarki mai daraja,mai adalci,bana son ka rasa wannan babbar dama saboda ni don haka na roke ka don darajar karagarka daka janye wannan matsayi daka bani na Yarimanka,ni kuma nayi alkawarin cewar zan cigaba da nuna maka SO da KAUNA kamar yadda kowanne da ke nunawa ubansa.Koda Yaro Ruhaisu yazo nan a zancensa sai gaba dayan jama'ar dake fadar suka cika da tsananin mamakin hankalinsa da basirarsa ta iya magana da sanin yakamata da kuma hangen nesa.Kawai sai jama'a suka kama yiwa yaro Ruhaisu tafi.Al'amarin daya aurewa sarki Sailur kai kenan,kuma yaji ya kara kamuwa da tsananin son yaro Ruhaisu fiye da koyaushe a rayuwarsa,don haka sai ya tashe shi tsaye ya rungumeshi yana mai cewa tabbas ka cika da na gari abin alfahari.Lallai na yarda da wanan shawara taka kuma zanyi aiki da ita.Koda jama'a suka ji haka sai suka rude da shewa,suka kama yiwa sarki Sailur jinjina da kirari suna masu nuna soyayyarsu a gareshi.Tun daga wannan rana Ruhaisu ya tunawa sarki Sailur cewa babu abinda yakeso a rayuwarsa sama da ya koyi YAKI.Ai kuwa ba tare da wata gardamar komai ba sarki Sailur ya shiga koya masa yaki da kansa,ya zamana cewa a kullum sarki sailur yana shafe kimanin sa'a guda yana koyawa Ruhaisu yaki.Da safe suyi sa'a biyu,haka ma da rana da kuma daddare.A cikin kwanaki goma sha hudu Kacal Ruhaisu ya iya sarrafa takobi ainun,kuma ya iya kare dukkan irin harin da sarki Sailur ke kawo masa.Koda aka shiga sati na uku kuwa sai gashi yana iya maidawa sarki sailur martanin kai hari,har ma akwai lokacin da saura kiris ya yiwa sarki Sailur rauni a lokacin daya kawo masa wani wawan sara aka,ya matsa baya cikin zafin nama,amma duk da haka sai da kaifin takobin tasa ta zabtare wani bangare kadan na rawaninsa.Shi kansa sarki sailur bai san sa'adda ya kama yiwa yiwa Yaro Ruhaisu tafi ba.Daga wannan rana ne sarki Sailur yakai Ruhaisu cikin manyan dakarun yakin kasar ya cigaba da daukar HORON YAKI a cikinsu.Abi dai kamar wasa sai gashi Ruhaisu yana iya jure duk irin wahalar da manya ke jurewa a matsayinsa na yaro karami dan shekara goma.Ashe wannan juriya tasa ta samo asalo ne tun daga azabar da sarkin birnin Darmis ya rinka yi amsa shi kuma yana shanyeta.Kai saida takai cewa barde Ruhaisu yana iya yin yaki da karti hudu yana yaro amma duk sai ya kaisu kasa.Lokacin daya cika shekara goma sha takwas a duniya kuwa sai gashi shi kadai yana iya tarwatsa mutum arba'in.A wannan shekarar ne aka jarraba iya yakin Ruhaisu inda aka shirya wata gagarumar GASA ta JARUMAI akan akarfin damtsensu da iya Yakinsu.Jaruman gasar su dari da goma sha hudu ne,amma RUHAISU ne ya karbi KAMBUN GASAR.Daga wannan lokaci ne sarki sarki ya sake jan barde Ruhaisu a jikinsa ainun ya zamana cewa duk wani abu da zaiyi na sirri tare dashi yakeyi.Al'amarin dayasa sarkin yaki ya fara kyashi da hassada dashi kenan,kuma ya tsaneshi ainun,amma sai Ruhaisu ya zame masa kadangaren bakin Tulu.Babu irin tuggu da makircin da sarkin yaki bai shiryawa Barde Ruhaisu ba amma sai sarki sailur ya rinka kareshi a boye ba tare da ya sani ba.Kai sau tari ma akwai mugayen tarkuna da Ruhaisu yake fadawa ya kasa fitar da kansa,amma sai yaga wani yazo tsulum ya ceceshi,kuma wanda ya ceceshin ya rufe fuskarsa da bakin rawani idanunsa kadai ake gani gaba dayan kayan jikinsa ma bakake ne.Saida akayi hakan kusan sau hudu.Abinda ya faru a karo na hudun shine. pls Like and comments 15 hrs · PublicALLON SIHIRI Littafi na Hudu (4) Part C A BINDA YA Faru a karo na hudun shine,wata rana da magriba Ruhaisu ya dawo daga FARAUTA a daji kawai sai yaga wadansu dakarun sumame kimanin su arba'in sanye da jajayen tufafi sun dako tsalle a sama sun kewayeshi.Su duka sai suka zare takubbansu suka ja tunga cikin shirin afka masa.Tunda Barde Ruhaisu yazo duniya bai taba ganin ZARATAN DAKARU masu kwarjini da kirar SADAUKAI ba irin wadannan.Nan take jikinsa ya bashi cewa yau fa ya gamu da gamonsa,amma da yake shima jarumi ne mai DAKAKKIYAR ZUCIYA ko kadan baiji tsoron yayi kokarin ceton kansa ba.Abinda ya aiyana aransa shine ko ba komai sai yayi iya bakin kokarinsa yaga cewa bai mutu shi kadai ba.A kalla yana son ya sami nasarar kashe koda mutum goma ne daga cikin wadannan zaratan jarumai da suka kawo masa MAMAYAR BAZATO.Lokacin da dakarun suka ga Ruhaisu ya gyara tsayuwarsa yana dafe kufen takobinsa ba tare daya nuna alamun tsoro ba ko tunanin guduwa,sai su ma suka sha jinin jikinsu,suka fahimci cewa lallai shima JAN IDO ne,kuma zai iya yin barna kafin a gama dashi.Hakan ne yasa dakarun basuyi saurin afka masa ba suka tsaya daga baya baya suna nazarinsa tukunna.Shi dai wannan wuri inda DAKARUN SUMAMEN suka ritsa Ruhaisu wajen gari ne sosai a tsakiyar daji inda babu gida gaba ko baya,kuma babu wani mahaluki dazai tsaya a wajen tsawon dakika goma batare daya firgita ba saboda waje ne mai yanayi na ban tsoro.Akwai dogayen bishiyoyi masu duhuwoyi gami da manyan tsaunika wanda dole ne baza a rasa mugayen dabbobin daji ba akansu.Ko yaushe wajen tsit yake tamkar babu wata halitta mai rai a wajen,kai da gani kasan cewa ba za'a rasa mugayen MUTANEN BOYE ba a wajen.Ana cikin wannan hali ne sai tsulum dakarun sumamen sukaga wani Badakaren a cikin shigar bakaken kaya rike da takobi ya duro tsakiyarsu daga can sama daga kan wata doguwar bishiya ya tsaya daf da Ruhaisu suka hada baya alamar ce Ruhaisu ya kawowa dauki.Koda ganin haka sai shugaban dakarun sumamen yabaiwa sauran yan uwansa inkiya suka afkawa su Ruhaisu.Nanfa aka ruguntsume da azababben masifaffen yaki mai matukar tayar da hankali da muni.Ana fara yin wannan gumurzu ne kowa ya san cewa KARO DA KARO sai RAGO!Kamar yadda dakarun sumamen suke da KARFIN DAMTSE da iya yaki,zafin nama da bakin naci,haka Ruhaisu ma da mai bakaken kayan nan suke dashi,don haka saida aka shafe sa'a biyu da rabi ana dauki ba dadi,in banda karar haduwar takubba gami da sautin naushin jiki babu abinda kunne yakeji.Gashi dai an kasa koda lakutar jikin mutum daya a GUMURZUN bare a fitar masa da JINI mai yawa,amma kuma ana naushin juna yadda yakamata kuma ana shanye naushin sai kace jikin kowa bana jini da tsoka bane.Duk wanda ka duba saidai kaga hancinsa da bakinsa na yoyon jini.Koda shugaban sakarun sumamen yaga an bata wannan lokaci mai tsawo haka ba tare da sun sami wata nasara ba saiya fusata ainun ya bayar da wata inkiya.Take dakarun sumamen suka ja da baya su duka alokaci guda suka zaro wadansu adduna guda dai dai wato ya zamana cewa kowannasu na rike da makamai biyu a jikinsa ga TAKOBI ga kuma ADDA.Koda ganin haka sai wannan badakare mai bakaken tufafi yai wuf ya zaro wadansu Wukake guda biyu a cikin jikinsa ya mikawa Ruhaisu guda ya karba,suma suka dubi juna sukayi wata inkiya iri daya.Koda Ruhaisu yaga sunyi inkiya iri daya shi da wannan badakare mai bakaken kaya sai zuciyarsa ta buga da karfi kuma tsoro ya shigeshi.Ba komai ne yasa masa wannan tsoro ba face ya gane cewa ba wani bane wannan badakare mai bakaken kaya face SARKI SAILUR.Take Ruhaisu ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa yace,saboda ne sarki yake siyar da rayuwarsa don ceton tawa rayuwar?Ai wannan ba karamin ganganci bane a matsayinsa na sarki yayi haka kuma idan wani abu ya sameshi nima na shiga wani bala'in.Yana cikin wannan tunani ne dakarun sumamen suka sake afko musu aka sake ruguntsumewa da sabon masifaffen yaki a karo na biyu wanda yafi na farko tashin hankali da bala'i domin wannan karon wani irin sabon salon yaki dakarun sukazo dashi ya zamana cewa sun hada da tsalle tsalle da kwance kwance suna yawo a saman su Ruhaisu da kasansu suna kai musu hari ta ko ina.Faruwar hakan keda wuya kuwa sai suka fara ruda sarki Sailur da Ruhaisu nan take suka sami nasarar yankar kowannansu sau uku uku,jini yai tsartuwa daga jikinsu suka kurma ihu sakamakon tsananin zafi da zogin da suka ji.Nan take jiri ya kwashi Ruhaisu ya durkushe kasa yana mai cake takobinsa cikin kasa don kare kansa daga faduwa.Koda ganin haka sai shugaban dakarun sumamen ya dako tsalle sama cikin shammace da zafin nama ya daga makaman nasa biyu sama da nufin ya fille masa kai.Koda Sarki Sailur yaga abinda ke shirin afkuwa gashi yana yaki da sauran dakarun sumamen shi kadai ya hanasu kusantar Ruhaisu sai ya daka tsalle sama yayi wata irin katantanwa da kafafunsa a tsakiya dakarun sumamen ya tarwatsa su kuma ya kare saran da shugaban dakarun sumamen ya kawowa Ruhaisu a gadon bayansa.Taka takobin da Addar suka datsa bayan sarki Sailur jini yai feshi a lokacin da sarki sailur ya kurma uban ihu kuma ya fadi kasa tim a sume.Koda Ruhaisu yaga abinda ya faru ga Sarki sai ya kurma ihun daya ninka na sarki Sailur sau goma kamar MAHAUKACIN ZAKI ya faso gari.Take gaba dayan dakarun sumamen suka firgita suka ja da baya.Shi kuwa Ruhaisu zuciyarsa ce ta kekashe ga barin jin dukkan tsoro da kasala saboda tafarfasa data kamayi kamar zata kone saboda fishi bisa ganin halin da sarki ya shiga,kawai sai gani akayi Ruhaisu ya daka tsalle sama tamkar daga cikin BAKA aka harboshi ya sare kan shugaban na su kuma ya soka masa wuka a tsakiyar kirjinsa ta fullo ta gadon bayansa.Take gangar jikin shugaban dakarun sumamen ta sulale kasa matacciya.Shi kansa Jarumi Ruhaisu yayi matukar mamakin yadda akayiyayi wannan gagarumar BAJINTA da JARUMTAKA.Koda sauran dakarun sumamen suka ga yadda Ruhaisu yayi da abin dogaronsu,wato shugaban nasu sai suka firgice suka zubar da makamansu suka cika wandunansu da iska.Kafin kace wani abu babu dayansu a kusa.A sannan ne Ruhaisu ya fashe da kuka ya fara dinke raunikan dake gadon bayansarki sailur cikin razana da dimauta yana ta fama rusa kuka domin a lokacin ma gani yake kamar tuni sarki ya dade da mutuwa.Bayan ya gama dinke masa raunikan ne yaga har a sannan jini bai daina zuba daga cikin raunikan,al'amarin daya dugunzuma hankalinsa kenan ya ruga da gudu izuwa cikin daji ya samo wadansu saiwoyin bishiyoyi yazo ya dakesu ya shafe raunin dasu.A sannan ne jinin ya daina zuba,har izuwa wannan lokaci Ruhaisu bai daina kuka ba saboda ko kadan babu alamar numfashi akan kirjin sarki Sailur,kuma babu inda yake motsi a jikinsa.A daidai wannan lokaci ne Ruhaisu ya fara sakar zuci wata zuciyar tace dashi menene amfanin rayuwarka a duniya tunda ka rasa wannan BABBAN MASOYI wanda baka da kamarsa a duniya.Ai gwara kaima ka kashe kanka tunda idan ma ka dauki gawarsa ka kaita cikin gari babu yadda za'ayi ka tsira daga zargin cewa kaine ka kasheshi.Koda gama aiyana hakan sai Ruhaisu ya sake fashewa da matsanancin kuka na bakin ciki har izuwa lokaci mai dan tsawo.Daga can kuma saiya daga takobinsa sama da nufin ya cakata a cikinsa ya kashe kansa.Kwatsam ba zato ba tsammani sai yaga sarki sailur yayi wuf ya taso zaune ya rike hannunsa kuma ya budi baki da kyar cikin matukar karfin hali yace,dakai ka mutu gwara ni na mutu kai ka rayu saboda indai ban samu haihuwa ba kai nakeso ka gajeni.Har yau har gobe wannan shine babban BURIN ZUCIYATA.Koda sarki Sailur yazo nan a zancensa sai Ruhaisu ya rungumeshi cikin tsananin farin ciki bisa ganin cewa bai mutu ba.Kafin sarki Sailur ya sake budar baki yace da Ruhaisu wani abu sai Ruhaisu yayi wuf ya goyashi a bayansa ya falfala da azababben gudu izuwa hanyar dazata kaisu cikin gari.Nanfa ya rinka yin wani irin gudu na ban al'ajabi yana gifta bishiyoyi tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya.Cikin kankanin lokaci suka iso cikin gari suka karasa fada,tun a kofar gidan sarautar Ruhaisu ya kwallawa likitan sarki Sailur kira don haka kafin su karasa turakar sarki sailur tuni anje an kirawo likitan ya karaso da gudu izuwa cikin turakar.Nandai Likitan ya shiga aikinsa ya baiwa sarki sailur wadansu magunguna wajen kala uku yasha kuma ya shafa wani maganin akan rauninsa.Faruwar hakan keda wuya sai barci ya sace sarki.Saida sarki Sailur ya shafe sati uku a kwance yana jinyar wannan rauni na gadon bayansa sannan ya warke sumul,tamkar bai taba samun wani rauni ba ma.Sa'ar dayayi itace saran da akayi masa bai taba kashi ba,tsokar nama ce kawai ta dare.Wannan shine takaitaccen tarihin Barde Ruhaisu. ¤¤¤ ¤¤¤ ¤¤¤ BAYAN SARKI SAILUR da Barde Ruhaisu sun dan jima a tsaye rungume da junansu suna kuka sai sarki sailur ya janye jikinsa daga cikin na Ruhaisu ya dubeshi a nutse yace,yakai dana kayi sani cewa ba komai nake so kayi mini ba face ka yiwa surukata Yazarina rakiya izuwa tafiya neman mijinta dan'uwanka Yarima Lubainu.Ka sani cewa tuni mun gama shirya komai ni da mahaifinta Abu Yazarina saboda haka a cikin wannan dare nake so kayi wannan tafiya kuma zan hada ka da wadansu amintattun zakwakuran dakaru nawa kamar mutum dari kacal wadanda zasu taimaka maka.Ina son kuyi bad-da-kama a cikin daren yau zaku bar garin nan domin a samu cikakken sirri.Koda Sarki Sailur yazo nan a zancensa sai farinciki ya lullube barde Ruhaisu ya dubi sarki sailur fuskarsa cike da annuri yace,yakai Abbana kayi sani cewa a iya tsawon rayuwata ban taba jin farin ciki ba a raina irin na yau saboda yaune ranar farko daka taba neman wata alfarma a wajena.Tun daga kuruciyata kawo izuwa girmana bantaba saka maka ba da abin alherin daka ke yi mini tsawon shekaru,amma yau gashi ka bani damar dazan iya kwatantawa.Na rantse da darajar kauna da soyayyar dake tsakaninmu dakai zan sallama rayuwata don kare ta surukarka,kuma duk inda dan'uwa na Yarima Lubainu yake a cikin duniya sai na damka Yazarina a hannunsa cikin koshin lafiya kuma a raye.Koda jin wannan batu sai farin ciki ya sake baibaye sarki sailur ya rungume barde Ruhaisu a karo na biyu yace,ina alfahari dakai yakai yayan Lubainu,kuma nasan cewa saika cika wannan aiki dana baka bisa amana.Ni yanzu babbar masifar dazan fuskanta itace ta kewarka a yayin daka yi wannan tafiya.Ka tuna cewa tun daga ranar dana daukoka a gidan sarautar Birnin Darnis kawo izuwa yau bamu taba rabuwa daidai da rana daya ba,yanzu gashi zakayi wannan tafiya mai mugun hadari wacce bansan ranar dawowarka ba.Koda sarki sailur yazo nan a zancensa sai ya sake kankame barde Ruhaisu a kirjinsa ya fashe da matsanancin kuka.Al'amarin daya karya zuciyar barde Ruhaisu kenan,shima ya fara yin sabon kukan.Tabbas irin son da sarki Sailur yake yiwa Barde Ruhaisu har yafi wanda yake yiwa Yarima Lubainu duk da ya san cewa barde Ruhaisu ba dansa bane na cikinsa,'da ne na TSUNTUWA wanda ma baisan asalinsa ba.Tsananun tausayin barde Ruhaisu da yakeyi be yasa yake kaunarsa fiye da Yarima Lubainu.Sarki Sailur bai taba fifitashi ba kan Ruhaisu,kuma kowanne taro sarki zai tura wakilci bai taba tura Yarima Lubainu ba saidai ya tura barde Ruhaisu.Kai saida takai cewa Yarima Lubainu ya fara nuna kishinsa a fili akan Barde Ruhaisu saboda ganin yadda sarki ke fifitashi akansa.Daga ranar da sarki sailur ya baiwa Yarima Lubainu labarin haduwarsu tun yana dan shekara goma kawo izuwa girmansa shike nan sai Yarima Lubainu ya kaunaci barde Ruhaisu fiye da yadda ma sarki ke sonsa,kuma suka zamo manyan abokai yan'uwa kuma aminan da basa son rabuwa.A ranar da Yarima Lubainu zaiyi wannan tafiya saida suka shafe rabin sa'a cif a tsaye rungume da junansu suna kuka na bakin cikin rabuwa,da kyar suka saki juna Yarima Lubainu ya tafi,domin a cikin zukatansu ji suke kamar dama can sun kasance yan'uwan juna na jini.Bayan bardw Ruhaisu da sarki Sailur sun dan sake jimawa a kankame da juna sai Ruhaisu ya janye jikinsa daga cikin nasa suka fuskanci juna yana mai share hawayensa yace,yakai Abbana kayi sani cewa akwai bukatar naje na kammala dukkan shirye shiryena yanzu tunda bani da isasshen lokaci kuma nayi bankwana da matata.Sarki sailur ya gyada kai a lokacin da hawaye ya subuto masa yace wannan gaskiya ne,kuma ka nema mini gafara a wajen surukata matar taka tunda na rabata dakai a lokacin datafi koyaushe kewarka.Na sani cewa bata da burin dayafi ta haihu kana nan ku raini abinda kuka haifa tare domin babu takaicin dayafi na rabuwa da IYAYE tun mutum yana karami.Gashi kai ka rabu da iyayenka a lokacin ma baka sansu ba,amma na sani kuma naji a jikina cewa tarihi bazai maimaita kansa akanka ba,lallai kai zaka dawo gida a raye cikin koshin lafiya tun kafin 'danka ko 'yarka tayi wayo.Koda jin haka sai fuskar Barde Ruhaisu ta fadada da murmushi ya yiwa sarki Sailur godiya sannan ya juya da sauri ya fice daga cikin turakar ba tare daya yarda ya sake waigowa ba.Take Barde Ruhaisu ya nufi izuwa gidansa. 2 mins · PublicALLON SIHIRI Littafi na Hudu (4) Part D DA ISAR BARDE RUHAISU gidansa sai ya iske matarsa ZASMIN tsaye a falo dauke da tsohon juna biyu tana kai kawo cikin alamun damuwa.koda ta hango shigowar Barde Ruhaisu sai ta taho gareshi fuskarsa cike da annuri suka rungume,amma yayin data janye jikinta daga nasa taga idanunsa sunyi jajir alamar cewa yasha kuka sai zuciyarta ta buga da karfi ta dubeshi cikin alamun tsananin tashi hankali tace,gaya min gaskiya yakai mijina yau kuma menene ya faru a fada?Lallai ba ka taba dawowa gida a cikin irin wannan yanayin ba.Shin wani makusancinka ne ya mutu ko kuwa wani abu ne ya sami sarki?Tabbas yadda na sanka da DAKAKKIYAR ZUCIYA in ba wadannan abubuwa ba babu abinda zai saka kuka.Koda jin wannan tambaya sai Barde Ruhaisu ya suri Zasmin ya dagata sama yana mai rungumeta a kirjinsa yayi juyi da ita don haka bata san sa'adda ta kama kyalkyala dariya ba.A hankali Ruhaisu yaje ya shimfide Zasmin akan gado ya kama wasa da gashin kanta suna kallon juna cikin murmushi.A sannan ne ya kwashe labarin dukkan abinda ya faru tsakaninsa da sarki Sailur ya zayyane mata.Koda gama bata wannan labari sai yaga ta kyalkyale da dariya,amma kuma hawaye na zuba a cikin idanunta.Al'amarin dayai matukar bashi mamaki kenan kuma ya kadu,cikin mamaki yace,yake matata ina dalilin wannan dariya taki gami da kuka a lokaci guda.?Sa'adda Zasmin taji wannan tambaya sai ta nutsu ta dubeshi da kyau tace,ya kai mijina abin begena dare da rana,kayi sani cewa ba komai ne ya sakani wannan kuka ba face yau ne ranar farko da zan fara rabuwa dakai tun daga lokacin aurenmu.Alhinin rabuwar tamu ne kawai ya sakani kuka,amma ina ji a jikina cewa tabbas zaka dawo gareni.Abinda ya sani nake yin wannan dariya kuwa ba komai bane face tsananin tayaka farincikin samun damar dazaka iya sakawa sarki kadan daga cikin irin abubuwan alherin dayayi maka.Kash!In badon ina dauke da wannan TSOHON CIKI ba da lallai tare dani za'ayi wannan tafiya,sabida inason na haife maka danka a lokacin da kake cikin GWAGWARMAYA ko shima dan naka ya sami tabarraki irin naka.Koda Zasmin tazo nan a jawabinta sai farin ciki ya lullube Ruhaisu ya rungumeta ya kama sumbatarta yana sa mata albarka.Nan take Zasmin ta mike tsaye da kanta ta fara debo kayan Ruhaisu tana zuba su cikin jakar guzuri don kammala shirye shiryen tafiya.Al'amarin daya kara bashi mamaki kenan,kuma yaji ya kamu da tsananin sonta fiye da koyaushe.Cikin kankanin lokaci ta gama shirya masa dukkan kayansa sannan suka yi bankwana ya saba jakarsa a kafadarsa bayan yayi shigar bad-da-kama irin ta fatake sannan ya koma can kofar gidan sarautar.A wannan lokaco tuni Sarki Sailur ya gama shirya komai,domin a samu cikakken shiri dangane da wannan tafiya Tasu Ruhaisu saida aka sauya masu gadin kafor gidan sarautar gaba daya a cikin daren aka zuba wadanda ya tabbatar da cewa masoyansa ne na gani kasheni,kuma ya gargadesu akan cewa duk abinda suka gani ko sukaji a wannan dare su barshi a cikin zukatansu kada su kuskura su sanar da wani.D isowar Barde Ruhaisu bakin kofar gidan sarautar sai ya iske sarki Sailur tsaye a gaban wadansu dakaru guda dari suna bisa kan dawakai dauke da hajoji da makaman yaki alamar cewa su fatake ne.Tun daga nesa Barde Ruhaisu ya fara nazarin fuskokin wadannan dakaru,koda ya shaidasu sai ya kamu da tsananin farinciki da mamaki.Ba komai ne ya haddasa hakan ba face ganin cewa gaba daya sa'anninsa ne kuma manyan abokansa wadanda ya aminta dasu a cikin dakarun yakin kasar.Koda sarki Sailur ya hango tahowar Barde Ruhaisu sai ya tafi gareshi cikin murna yace,yakai dana an gama shirin komai dama kai kadai ake jira saboda haka sai kayi haramar tafiya.Koda jin haka sai Ruhaisu ya kama hannayen sarki guda biyu ya sumbacesu kawai sai ya sake rungume junansu suka dan jima a kankame da juna.Al'amarin daya karya zukatan sauran dakarin kenan suka kamu da tausayinsu saboda sunsan irin shakuwar dake tsakaninsu.Nandai Barde Ruhaisu da Sarki Sailur suka rabu bisa dole sunayin kwallah badon suna so ba,aka kawowa Barde Ruhaisu wani farin INGARMAN DOKI wanda ya fita dabam da dukkan dawakan abokan nasa ya kama ya hau.Take ya kada linzamin dokinsa ya fice daga cikin gidan sarautar ba tare daya yarda ya sake waigowa ba.Ai kuwa sai sauran dakarun guda dari suka rufa masa baya da sauri shi kuwa sarki Sailur sai ya bisu da kallo kawai,bai bar wajen ba har saida suka kule ya zamana cewa ko kurarsu baya iya hangowa,sannan ya juya ya koma izuwa cikin gidan sarautar yana mai zubar da hawaye. ¤¤¤ ¤¤¤ ¤¤¤ A CAN BIRNIN Sarki Alkasu kuwa tun da aka gama wannan gasa ta neman Auren YAZARINA tsakanin YARIMA LUBAINU da YARIMA MANGUL suka dawo gida sai sarki Alkas ya sanya hijabi tsakaninsa da Yarima Mangul.Suna dawowa gida yayi masa korar kare daga fada kuma ya gaya masa cewa idan ya sake sa kafarsa a cikin harabar gidan sarautarsa zai yanke masa hukuncin daurin rai da rai a gidan kurkuku.Koda jin wannan batu sai mamaki da bakin ciki ya turnuke Yarima Mangul ya dubi dungulmin hannunsa a lokacin da hawaye yake zubo masa sannan ya dubi Sarki Alkas yace saboda mezaka kyamaceni alokacin dana fi bukatarka?Ka dubi yadda na zamo musaki ka tuna cewa nine fa kadai danka guda wanda zai gaji karagarka?Ka tuno da irin tsananin son daka keyi min saboda me yau zaka bari zuciyarka ta rinjayi soyayyar danka?Kafin Yarima Mangul ya gama rufe bakinsa tuni sarki Alkas ya daka masa tsawa a lokacin da shima hawaye ya zubo masa ya dubeshi yace,karka sake kirana da matsayin ubanka domin tuni nasaka TAKOBI na datse wannan alaka dake tsakaninmu kamar yadda ka datse wacce ke tsakanina da Abokaina kuma manyan masoyana sarki Sailur da Attajiri Abu Yazarina.Ka sani cewa ka jefa wadannan masoya nawa a cikin bakin cikin da har abada babu abinda zai gusar dashi tunda ka rana Yarima Lubainu da lafiyarsa ka sanya masa cutar da bata da magani kuma a sanadiyyar hakan yayi rabuwar doke da masoyiyar tasa rabuwar da ba lallai bane su sake saduwa ba.Kaga keknan ka raba iyaye da 'ya'yansu kuma ka raba MASOYA.Ka sain cewa a yau idan na rasaka a gobe daya daga cikin matana zata iya sake haifa mini wani dan,amma aminaina daka rabamu dasu bazan taba samu kamarsu ba.Yarima ka cuceni cutar da har abada ba zan iya yafe maka ba.Koda jin wannan batu sai Yarima Mangul ya zube kasa a gaban sarki Alkas ya fashe da kuka kuma ya kama tuba yana rokon gafara.Maimakon sarki Alkas yaji tausayinsa sai ya dubi wadansu dakarunsa su shida dake tsaye a gefe daya yace dasu su kama Yarima Mangul su fitar dashi daga cikin gidan sarautar kuma a kulle kofar gidan.Nan take kuwa dakarun suka kama Yarima Mangul Suka fitar dashi daga cikin gidan Sarautar da karfin tsiya yana kuka da ihu gami da turjewa kuma yana kwallawa sarki Alkas kira mma sarki Alkas ko waigowa baiyi ba bare ya dubesi ya tausaya masa.Ana fitowa da Yarima Mangul daga cikin gidan sarautar sai akayi wurgi dashi a wulakance tamkar bai kasance dan sarki ba,aka janyo kofar gidan sarautar aka kulleta bam,aka zuba mata sakatu.Cikin tsananin bakin ciki da takaici Yarima Mangul ya mike tsaye yana kuma.Nan taje yaji ya tsani sarki Alkas yadda ya tsani mutuwarsa.Kawai sai ya takarkare ya bushe da dariyar mugunta iska ta dauki sautin dariyarsa takai har izuwa kunnen sarki Alkas gami da muryarsa yana mai cewa yakai Abbana ka saurari ranar da zan dawo gidan nan nine zan zama sanadin AJALINKA kuma saina hau kan KARAGARKA.Koda jin wannan batu sai bakin ciki ya turnuke sarki Alkas zuciyarsa ta kama tafarfasa.Har ya zare takobinsa da nufin ya juya da baya da gudu yaje ya kashe Yarima Mangul sai zuciyarsa ta daka masa tsawa tace dashi so kake kabarwa kanka abin gori a wannan masarauta?Ka kyale Yarima da Halinsa ai duniya makarantace zata koya masa darasi.Daga wannan rana Yarima Mangul ya bar cikin birninsu gaba daya ya koma daji da zama saboda bakin ciki.A sanadinyyar haka ne ya hada kai da 'yan TAWAYE gami da 'YAN FASHI suka fara shirye shiryen yadda zasu kawar da mulkin sarki Alkas ya dane KARAGAR MULKINSA,amma kullum idan ya dubi iya yawansu da iyakar makaman dasuka tanada sai takaici ya kamashi saboda yasan cewa ko kasa daya cikin kaso goma na shirin sarki Alkas basu kai ba don haka dole ne ya cigaba da hakurin jiran lokaci.A haka dai Yarima Mangul ya cigaba da jagorantar wannan runduna ta yan fashi da tawaye suka rinka kai harin SUMAME izuwa kauyukan dake sauran kasashen ketare suna kwaso mata,dukiya da kudi suna kamo bayi da karfin tsiya suna basu horon yaki domin kara yawan dakarunsu kuma suna siyan mugayen makaman yaki suna tarasu.Ana cikin wannan hali ne wata rana Yarima Mangul na zaune a cikin sansaninsu yana shan giya ga mata a gabansa suna ta fama tika rawa anayi musu kida saiga wani DAN LEKEN ASIRINSA ya rugo da gudu bisa kan doki.Da isowarsa kusa da Yarima Mangul sai ya tsaida dokinsa ya sauko kasa ya fadi a gaban Yarima Mangul yace ya shugabana ga wani AYARI can na BAKIN FATAKE kimanin su dari da doriya dauke da HAJAH mai tarin yawan gaske sun nufi hanyar dazata kaisu Birnin SARAUNIYA AKISATUL SAUWARA.Koda jin wannan batu sai Yarima Mangul yayi jifa da kwalbar giyar dake hannunsa ya mike tsaye zumbur cikin tsananin farin ciki yace,tabbas yau zamuyi babbar farauta mai inganci.Maza a kawo mini dokina da kayan yakina.Dakaru dubu daya kacal nakeson suyi min rakiya.Nan take kuwa cikin gaggawa aka kawowa Yarima Mangul kayan yakinsa ya sanya sannan ya hau dokinsa ya zabureshi da gudu dakaru dubu suka rufa masa baya."Ashe wannan AYARI na fatake ba wasu bane face su Barde Ruhaisu wadanda suka fito neman Yarima Lubainu a cikin shiga ta bad- da- kama domin a sada Yazarina da Mijinta Yarima Lubainu. kuyi hakuri yau Ansamu delay din post hakan yafarune sbd bansamu time bahALLON SIHIRI Littafi na Hudu (4) Part E TUNDA WANNAN Ayari nasu Barde Ruhaisu suka baro birnin Zamrul sukayi ta ratsa dazuzzuka,kauyaka da kananan Birane basu fuskanci matsalar komai ba har tsawon kwana tara.Kuma a duk tsawon wadannnan kwanaki Barde Ruhaisu bai taba yarda ya gusa ba daga kusa da Yazarina ba wacce koyaushe fukskarta a rufe take cikin mayafi idanunta kadai ake gani,kuma shigar datayi mutum bazai iya gane cewa ba macece ko namiji.Ko dare ne yayi har tayi bacci Barde Ruhaisu yana tsaye a kusa da ita kuma ya saka Dakaru sun kewaye yankin wajen da take.Kai ko wani kyakkyawan motsi yaji a kusa da wajen da suke sai ya duba ya tabbatar da cewar babu abu wanda zai kawo mata barazana.A tsawon wadannan kwanaki da suka shafe suna tafiya ko sannu babu wanda ya yiwa wania tsakanin Barde Ruhaisu da Yazarina ma'ana basuyi magana da junansu ba.A ranar kwana na taran ne da yammaci sakaliya suka yada zango a bakin wata korama domin su dan huta kuma dawakansu su sha ruwa.Bayan an tsaya kowa ya sauka daga kan Dokinsa,dakaru sun kewaye wajen don tabbatar da tsaro,Yazarina ta zauna a gefe daya ta bude jakar guzurinta ta dauko nama yana ci,shi kuma barde Ruhaisu yana tsaye a bayanta ya zare takobinsa yana wasata akan dutse sai kawai suka jiyo sukuwar dawakaia daga yamma,gabas,kudu da Arewa.Sannan kuma sai suka jiyo kururuwar mazaje mai ban tsoro amma saboda su Ruhaisu sun kasance ZARATAN JARUMAI masu dakakkiyar zuciya ko gezau basuyi ba,kawai sai sukayi sauri suka zaro wadansu manyan garkuwoyi daga kan dawakansu saboda tsoron kada a fara kawo musu hari da harbin kibiya.Take kowannen badakare yacake garkuwarsa a gabansa sannan ya zare takobinsa,kowa ya tsaya a inda yake ba tare da wata razana ba.Yazarina ce kadai ta firgita a lokacin data hango wadansu dakarun sumame su da yawa sun durfafosu a guje bisa dawakai rike da makamai tsirara suna ihu da kururuwa.Har ta yunkura zata mike tsaye a dimauce sai Barde Ruhaisu yayi wuf ya kamo hannunta ya zaunar da ita kasa.A karon farko ya dubeta yace,ki gafarceni ya shugabata idan kika matsa daga nan koda taku daya ne halaka zakiyi.Abinda nakeso dake shine komai RINTSI DA TSANANI kada ki gusa daga kusa dani,koda kuwa kinga an karar da dukkan dakaruna saura ni kadai jal na rage a raye!Lallai ki kiyaye wannan umarni dana baki muuddin kina son ki sake saduwa da masoyinki dan'uwana Yarima Lubainu.Koda Yazarina taji wannan batu sai ta gyada kai tana nuna masa alamun cewa lallai zata kiyaye wannan umarni nasa.Koda jin haka sai Ruhaisu yai sauri ya rufe fuskarsa da rawani suma sauan dakarun nasa sai sukayi koyi dashi.Abinda ya daurewa Ruhaisu kai shine har dakarun sumamen suka iso daf dasu ya zamana cewa tazarar dake tsakaninsu bata wuce taku ashirin ba amma basu harbo musu kibiyoyi ba.Da isowar dakarun sumamen sai sukayiwa su Ruhaisu KAWANYA suka yi cirko cirko bisa dawakansu.A sannan ne shugaban dakarun sumamen wanda dashi da dukkan yaran nasa sun rufe fuskokinsu sai ya sauko daga kan dokin sa ya karewa fataken kallo tsaf,sannan ya bushe da dariyar mugunta,lokaci guda kuma ya turbune fuskarsa ya dubesu yace,ni da yarana mu dubu daya ne da daya,ku kuwa bakufi ku dari ba,abin kunya ne mu yakeku ta hanyar farar harbo muku kibiyoyi.To waishin kuma menene amfanin rufe fuskokinmu damu daku mukayi?Ai kawai kowa ya bude fuskarsa muyi GABA DA GABA fada da buya ai tsoro ne.Koda gama fadin hakan sai shugaban dakarun sumamen ya kwaye rawanin dake kan fuskarsa su Barde Ruhaisu sukayi arba dashi.Ba wani bane face Yarima Mangul dan sarki Alkas!!! Hannunsa na dama na rike da zabgegiyar takobi,ya saki daya dungumin hannun nasa.Koda Barde Ruhaisu yayi arba da Yarima Mangul sai shida dukkan dakarunsa suka kamu da tsananin mamaki gami da tsananin tsoro.Koda ganin haka sai barde Ruhaisu ya kwaye fuskarsa shima ya mike ya matso gaba kadan ya dubi Yarima Mangul yace,sau tari Jarumi yakan rufe fuskarsa saboda wata BABBAR HUJJA da manufa saboda haka mu bazamu bude fuskokinmu ba saidai mu gwabza daku a hakan.Kafin sannan kuma muna son mu san dalilin dayasa kuka kawo mana wannan hari na MAMAYAR BAZATO.Koda jin wannan batu sai Yarima Mangul ya bushe da dariyar mugunta sannan yace,ai shi dan fashi bashi da wata hujja takai hari face don ya kashe rayuka kuma ya kwashe dukiya.Koda yake nasan ka san ko ni waye tunda ni fitacce ne a wannan nahiya kuma ada ni ba dan fashi bane,amma a yanzu ni UNGULU ne dakan ZABO!Har yanzu ina nan akan matsayina na Yarima Mangul dan Sarki Alkas mai jiran Gado.Yakai wannan jarumi ka sani cewa zan iya yi muku adalci guda daya kai da dukkan jama'arka naki kasheku na karbe dukiyarku,amma sai idan zaku bude fuskokinku naga ko ku su waye?Koda jin wannan batu sai Barde Ruhaisu ya tari numfashin Yarima Mangul yana mai daka masa tsawa yace,ba zamu taba bude fuskokinmu ba don cika umarninka kuma kaidin nan baka isa ka iya kashemu ba ko ka karbe dukiyarmu.Ina mai shawartarka daka janye jama'arka ku bar wannan wuri idan ba haka ba kuwa sai kayi nadamar kawo mana wannan hari.Idan ka kuskura ma sai na sake guntule maka daya lafiyayyan hannun naka!!Koda jin wannan batu sai Yarima Mangul ya fusata ainun ya zare takobinsa kuma ya daka tsalle daga inda yake ya dira a gaban Barde Ruhaisu ya kawo masa wawan sara aka.Cikin bakin zafin nama barde Ruhaisu ya kare saran.Nanfa suka ruguntsume da azababben yaki,ya zamana cewa suna kaiwa Junansu SARA DA SUKA cikin tsananin bakin zafin nama,juriya da bajinta,sauran dakarun kuwa na kowanne bangare sai suka zuba ido suka zama yan kallo tunda ba'a basu umarnin suyi yaki ba. WAYE ZAI SAMU NASARA A WANNAN AZABABBEN YAKI DA AKE KWABSAWA TSAKANIN YARIMA MANGUL DA BARDE RUHAISU? INA LABARIN YARIMA LUBAINU DA BAKON JARUMI DASU SARAUNIYA AKISATUL SAUWARA DAKE CIKIN GIDAN BOKA DARBUSA? SHIN YARIMA LUBAINU ZAI CIKAWA ALJANA BADI'ATUL SARIRA ALKAWARIN DAYA DAUKAR MATA NA KWANCETA DAGA DAURIN DA BOKA DARBUSA YAYI MATA ITA KUMA TA TAIMAKA MASA? WANE NE BAKON JARUMI DA TARIHINSA? YAUSHE BAKON JARUMIN ZAI SAMU NASARAR YADA ADDININSA NA MUSULUNCI A NAHIYAR? SHIN YARIMA LUBAINU YANA SAMU LAFIYA DAGA LALURAR DA YAKE CIKI? YAUSHE YAZARINA ZATA SADU DA MASOYINTA YARIMA LUBAINU? WAYE ZAI MALLAKI ALLON SIHIRI A TSAKANIN DUMBIN JAMA'AR DA SUKE NEMANSA? WANE IRIN MUGUN TANADI SU SARAUNIYA AKISATUL SAUWARA ZASU YIWA BAKON JARUMI?. Mu hadu a littafin ALLON SIHIRI littafi na Biyar (ALLON SIHIRI-5)don jin cigaban wannan kayataccen,kasaitaccen labari. 1 hr · PublicTARWATSA MAZA-1 TYPE E »«« Nidai a iya yawon da nayi bantaba shiga daji mai kwarjini da ban tsoro ba, tamkar dajin shajaril maurud. Ba komai ne yabawa dajin kwarjiniba, face wasu irin dogayen bishi yoyi gami da tulun ganyaye a sama da suka cika gami gami da duhuwa mai yawan gaske, ga kuma tarin manyan duwatsu masu siffofin ababan tsoro da kuma jibga-jiggan tsaunika. Muggan dabbobin daji kuwa adadinsu ya wuce kima sai dai ka gansu suna ta gilmawa, in ba don a sama muke tafiya ba, da sai mu yita yaki da su sai da muka yi tafiyar sa'a hudu a sama cikin iska a dajin na shajaril maurud, sannan muka jiyo wani irin gagarumin gurnani na dodo gurmazu, koda jin gurnanin wanda ya cika djin gaba daya sai hantar cikina ta kada, duk da jarumtaka da dakakkiyar zuciya irin tawa. Shi kuwa aljani barzila gaba dayan jikinsa ne ya dume da zafi, tamkar an tsomasi a ruwan dumi mai tiriri, ya kama karkarwa bai san sa'adda ya saki fitsarin firgita ba. Duk da cewa a tsorace nake, sai da dariya ta kwace mini, na ce, "Haba namijin duniya, ai ka karya alkadarin jarumtakarka wadda kayi a baya, domin bai kamata ba ace tsoro har yasa ka saki fitsari saboda kawai ka ji gurnanin dodo gurmazu ba". Cikin karfin hali, da rawar murya barzila yace, "Haba ya shugabana, ai bama fitsari ba, ko kashi na saki bai kamata kayi mamaki ba, Katuna fa cewa shi fa dodo gurmazun nan a halin yanzu duk duniya babu wata halitta mai karfin damtsensa da karfin sihirinsa. An ce komai kaurin bishiya, idan ya nausheta da hannu daya, saita ratattake, ta fadi kasa idan kuwa ya kwarara ihu, girgizar kasa ake yi, tsawa da walkiya na amo daga cikin bakinsa. Komai yawan maza a cikin dakika biyar yake tarwatsasu, walau rundunar bil'adama ko ta aljanu". Kawai sai nayi ajiyar zuciya, nace "Lallai kuwa baka yi laifi ba, domin tsoro wajibine, amma fani bana tsoron bala'I dan babu Wanda banganiba, sai dai na firgita da shi. Ai kawai muci gaba da tafiya, ina so ka durfafi inda kake jiyo sautin wannan gurnani". Cikin matukar tsoro aljani barzila yace, "Banki tatakaba ya shugabana, amma dai katuna cewa, "Riga kafi yafi magani. Bai kamata mu tari dodo gurmazu gaba da gaba ba, zai fi kyau mu dunga yin sanda da labiya har mu isa inda yake, ai shi yaki dan zamba ne a duk sa'adda abokin gaba ya fara ankara da abokin gabarsa, to yana iya samun hikimar da zai iya samun nasara akansa da wurwuri". Batare da wata gardama ba, na amince da wannan shawara, saboda haka sai aljani barzila ya sauko kasa ya dira bisa turba, nima na sauko daga kansa muka fara tafiya sanda muna leke-leke, wani lokacin ma har kwanciya muke a kas muna tafiya da ruf da ciki. Kaico! Rashin sani yafi dare duhu, ashe duk wannan tafiyar dudduke da mukeyi dodo gurmazu ya hangomu tun daga can nesa, saboda kwarin idanunsa yana iya hango abin dake tafiyar sa'a shida a bayansa ko gabansa, sannan duk irin abin da ya jingina ajikinsa sai kalar jikinsa ta koma irin launin abin sak komai hasken da ke wajen, ido bazai iya shaidashi ba. A wannan lokaci da muke tafiyar ruf da ciki, dodo gurmazu na can sama bisa wata gabjejiyar bishiya mai tsananin girma da tsawo. Ni kam na tabbatar da cewa, wannan bishiya babu ta biyunta a duniya, domin ko a tarishi ban taba jin labarin bishiya irintaba. Haka dai muka ci gaba da tafiyar ruf da ciki har muka iso gaban wannan narkekiyar bishiya, amma bamu ga komai ba, kuma bamu sake jin gurnanin dodo gurmazu ba. Mun dade a kwance muna kasa kunne ko zamu ji wani motsi, amma ba muji ba. Daga can sai muka mike tsaye na dubi aljani barzila nace, "Abin da zamu yi kawai mu hau can saman wannan bishiya mu tsaya in dai muka yi haka zamu iya hango dodo gurmazu a duk inda yake domin zaton da nake ba a nan kusa yake ba. Yana nesa da mu ne". Koda jin wannan shawara tawa, sai barzila ya cika da murna, yace, "kwarai kuwa kayi tunani mai kyau, haka za a yi" nan take na sake hawa bayan barzila yai sama dani, sai da muka kure tsawon bishiyar sannan muka sauka a kan wani katon reshenta guda. Cikin hanzari aljani barzila ya zaro kwari ya dana akan wannan katuwar baka tashi ya tabe bakan ya shiga kalle-kalle ko zai hango dodo gurmazu ya sakar masa harbi. Ni da Nake bayan barzila sai na daga wani gatari nawa sama na tsaya cak! A waje daya ina kallon gabas da yamma, kudu da arewa, kuma ina leko kasan bishiyar. A binda bamu saniba shine, munyi aikin banza domin kuwa mun kulle kofar gida da barawo a ciki, domin kuwa tsakaninmu da dodo gurmazu bai wuce taku uku ba. Ashe shi ma yana kan bishiyar amma da yake kalar jikinsa ta saje da kalar jikin bishiyar ko kadan bamu ganshi ba. Kwatsam! Ba zato kuma ba tsammani, sai dodo gurmazu ya sauya kalar jikinsa izuwa ainashin tasa ta gaskiya, ya baiyana daf da aljani barzila. Koda barzila yai arba da dodo gurmazu yaga irin kwar jininsa da muninsa sai ya firgita kuma ya dimauce, bai san sa'adda ya saki kwari da bakan dake hannunsaba ya juya da nufin ya bude fuka- fukansa ya tashi sama, amma sai dodo gurmazu ya cabo jelarsa cikin zafin nama, sai ga barzila na reto a sama, tamkar dan biri na wasa. A dai-dai wannan lokaci ne na dako tsalle daga inda nake tsaye na taho a sama zan kirbawa gurmazu sara a tsakiyar kansa, amma sai gurmazu ya mangareni da daya hannun nasa, na rikito kasa, tun asama na fita daga haiyacina, naji kamar anyi mini kanshin mutuwa. Ai kuwa ina fadowa kasa na sume. Nidai ban san abin daya faruba daga sannan sai farkawa nayi na ganni a cikin katon keji tare da aljani barzila, da kuma wadansu aljanu kimanin su dubu biyu, duk suna ta faman rusa kuka shi ma aljani barzila sai ya tayasu kukan. Koda barzila yaga na farfado, sai ya dubeni a fusace, yace, "Kaga irinta ko, ai dama na gayamaka bamu isa mukawar da dodo gurmazu ba, ga shi yanzu ya kamamu. Wadannan aljanu duk fursunoninsa ne, kuma sun gaya mini cewa, sudubu arba'in ne ya kamosu, kullum yana diban biyar yana cinyewa, yanzu saura su dubu biyu kacal, kaga kenan muma mun zama abincin sa. Haka kuma sun tabbatar mini da cewa babu wani makami ko sihiri da zai iya karya wannan keji, har mu sami damar fita daga cikinsa. Abin da zance da kai kawai shine, ince koka bar wasiyya a gida kafin muyi wannan tafiya?". Yayinda naji wannan tambaya, sai na bushe da dariya, al'amarin daya baiwa dukkanin fursunonin aljanun mamaki kenan, domin gashi su a matsayinsu na aljanu, suna kuka saboda sun shiga bala'In da babu fita, amma ni a matsayina na bil'adama ina dariya. Ti me nake takama dashi? Shin ina zaton zan iya fita ne daga cikin wannan masifa? Amsar da basu sani ba kenan, amma dai ai tunda suna tare dani zasu zuba ido su ga iyakar gudun ruwana. sHIN HASANUL MAUZUR DA ALJANI BARZILA ZASU KUBUTA DAGA HANNUN DODO GURMAZU, HAR HASANUL MAUZUR YA KASHE WANNAN GIWA TA DODO GURMAZU, YA YANKO HARSHENTA? WADANNE SAMARI Ne ZASU SHIGA GASAR NEMAN AUREN GIMBIYA SHULAIRA, KUMA DAGA CIKINSU WAYE ZAI CI GASAR YA ZAMO MIJINTA. Muhadu a TARWATSA MAZA littafina biyu don jin cigaban wannan kasaitaccen labari. Daga mai debe maku kewa Khamis Idris yawan comment dinku shizai sa acigaba Dana biyu anjima if not sai jibi lolx