Compilied By Abubakar Saleh AlQuyraemey Whatsapp Number 08138873799 Visit www.rumbunlabarai.com For More Complete Documents Mutum Da Aljan Littafi Na Biyar (5) Part A. . Marubucin littafin :- Abdul aziz sani madakin gini typing by :- Al amin Ahmed Misau nickanme ; Guyson sunana kenan call:- 08064594218 For more doka ;- Itace ban yarje ba a yi edit na post dina ba tare da sani na ba ehem . Labari ya isowa guyson cewa. JARUMAR TA MIKE TSAYE DAGA KAN KARAGAR MULKIN, ta tako kafafunta tazo har daf da alkasim ta tsugunna fuskarrta na kallon tasa yadda har suna iya jin numfashin juna sannan ta dubeshi fuskarta a daure tace wnene kai kuma me kake takama dashi har da zakayi kokarin zaluntata ka rabani da abinda na farauto a daji alhalin hannuna ya riga naka kaiwa kan dabbar? Sa adda yarima alkasim yaji wannan tambaya sai yayi murmushi yace bazan baki amsar wannan tambaya ba sai kin fara gabatar da kanki tukunna nasan ko ke wacece. Koda jin haka sai jarumar ta fusata ta mike tsaye zumbur ta koma da sauri zuwa kan karagarta ta zauna zamanta keda wuya sai ta yi nuni da hannunta zuwa kan alkasim take wannan murtukekiyar macijiya data kanannadeshi ta sauka daga jikinsa amma sai wadansu sarkokin karfe suka fito daka cikin bango kimanin guda dubu suka kanannadeshi har kansa suka janyeshi zuwa jikin bangon suka shiga matseshi yarima alkasim bai san sa adda ya fara kurma ihu da kururuwa ba sakamakon tsananin zafi da zugin da yake ji koda ganin haka sai jarumar ta fara kyalkyala dariyar mugunta tana cikin yin dariyar ne kwatsam taji alkasim ya daina yin ihu da kururuwan kuma nan take sarkokin suka karkatse suka zube kasa gutsungutsun sai gani tayi Alkasim ya baro jikin bangon ya durfafota yana tafiya da karfinsa tamkar wani abu bai taba samunsa ba Manya gatan wasa kenan sarki Alkasim. Cikin tsananin kaduwa da mamaki jarumar ta mike tsaye tana kallonsa kawai alkasim ya iso har daf da ita yadda suna iya jin numfashin juna kamar yadda tayi masa dazu ya dubeta cikin murmushi yace duk abinda kike takama dashi nima ina da irinsa ko ma wanda ya fishi akan wane dalili zaki dauki girman kai a gareni alhalin nine yakamata na zamo mai girman kai a gareki tun da na kasance da ga sarkin dake mulkin wannan kasa da kike cikinta. Koda jin wannan batu sai jarumar tayi murmushi sannan tace dama saboda kai nazo wannan kasa abinda yasa banje fada kai tsaye ba shine ina son na gabatar da abinda nazo yi a sirrance ya kasance a tsakaninmu ne kawai mu biyu sunana LUSLAIYA YA GA SARKIN MAFARAUTA NA BIRNIN TEHERAN tun ban fi shekara takwas ba a duniya mahaifina ya bani horon yaki wanda ina iya fuskantar zaratan mayaka guda dubu sannan ya bani horon gumurzu da manyan dabbobin daji baya ga hakan ya bani horon rayuwa a cikin daji gami da yin gudu na tsawon kwanaki tara ba tare da tsayawa ba sama da dakika arba in ba bugu da kari mahaifina ya tsumani a cikin tsumin tsafi irin wanda samun mai irinsa sai an tona lokacinda na samu shekaru goma sha takwas ina samun wannan horo ya zamana cewa na zama budurwa cikakkiya sai na kawai da dukkan yan fashin dake cikin dazuzzukan kasarmu ni kadai hakanne yasa yan fashin suka fusata suka nemo taimakon yan uwansu dake cikin kasashen ketare amma duk da hakan sai na zame musu alakakai na zamo tamkar shaidaniya a cikin bil adama akwai wata ranar da wadannnan yan fashi suka ritsani a daji adadinsu yakai miliyan shida amma ni kadai na kashe mutum miliyan uku da rabi daga cikinsu sauran suka tsere daga wannan rana ne na dinga jin kamar babu wani mayaki ko sadaukin da yafi ni jarumtaka amma sai mahaifina ya dubeni yace yake yata kada ki kuskura ki dorawa kanki girman kai bisa wannan jarumtaka da kika ga kin samu a halin yanzu ina mai tabbatar miki da cewa akwai wani dan sarki wanda karfinsa da jarumtakarsa har da karfin sihirinsa zasu iya zuwa dai dai da naki koma yafiki koda jin wannan batu saina kamu da tsananin mamaki na tuna irin karfiin da nake dashi amma ace wai har akwai wanda ya kaini koma ya fini bisa wannan daliline na yanke hukuncin nazo na hadu dakai domin muyi gasa guda mu banbance tsakanin aya da tsakuwa gasa ta farko itace gudun tseren da zamuyi tsawon kwana tara ba tare da tsayawa ba ta sama da dakika arba in ba gasa ta biyu itace akwai wani babban gari na arnan daji dake can kudancinmu na taheran ina son mu je mu sato gunkin da suke bautawa domin mu tsokano yaki dasu wadannan arnan daji suna da mugun yawanda ba asan iyakar adadinsuba ni dakai dai zamu yakesu domin mu tantance iyakar jarumtakarmu gasa ta uku wacce itace ta karshe zamu shiga daji kowannanmu yayi farautar dabbar da babu kamarta ya kasheta yazo da gawarta idan har dabbar da na kashe tafi taka hadari ka tabbata cewa nafika karfi da jarumtaka kenan Al amin Ahmed Misau Guyson sunana kenan daga zauran labarai page nake typing nan take zamu rabu na koma kasata cikin farin cikin cewa nafi ka komai yayinda jaruma luslaiiya tazo nan a zancenta sai hankalin alkasim ya dugunzuma ainun saboda zuciyarsa ta karaya akan wannan abu guda uku amma daya tuna cewa shifa mutum ne mai sa a da nasara bisa duk abinda yasa a gabansa sai yaji dukkan tsoro ya kau daga cikin ransa don haka bai san sa adda ya dubi jaruma luslaiya ba yace na yarda da duk wannan sharadi na gasar da kika shirya mana kuma saina tabbatar miki da cewa nafiki karfi da jarum taka wow nima Guyson saina tabbatar muku da cewa jarumi ne ni. Yanzu idan na lashe wannan gasa menene sakamakona? Koda jin wannan tambaya sai mamaki ya kama luslaiya tace inda dai ace kai ba dan sarki bane toda saina baka dukiyar da har ka mutu kai da danginka ba zaka yi talauci ba amma ai mahaifinka yafi mahaifina dukiya yanzu ban san dame zan iya biyanka ba koda jin wannan batu sai alkasim yayi murmushi yace ai kuwa kece kike da abin da zaki iya biyana yake jarumar jarumai kuma tauraruwar taurari ba komai nake so a wajanki ba face soyayyarki da aurenki idan har na lashe wannan gasa akanki to na siyi soyayyata kenan kuma babu abinda zai hana aurenmu koda jin wannan batu sai jaruma luslaiya taji zuciyarta tayi baki kirin kuma nan take taji ta tsani yarima alkasim fiye da komai a duniya saboda tunanin cewa ya na so yayi mata dole ta soshi kuma ta aureshi cikin tsananin fushi ta dubeshi tace nayi maka alkawari zaka sha bakar wahala da baka taba sha ba a rayuwarka a cikin wannan gasa wacce zata kaika ga rasa lafiyarka ko rayuwarka gaba daya kuma ina tabbatar maka da cewa baka da jarumtakar da zata iya burgeni har zuciyata ta kamu da sonka don haka duk yadda zanyi naga ka fadi wannan gasa sai nayi ya kasance ne ne na lashe gasar ka sani cewa babu hada kai a cikin wannan gasa ni dakai sai dai kowa tasa ta fishsheshi kuma kowannanmu zai iya shiryawa dan uwansa tarkon mugunta domin ya hallaka iana son mu zamo tamkar abokan gaba masu farautar rayukan juna lokacin da sarki alkasim yazo dai dai nan a labarin da yake baiwa yarima kamsus sai yaga idanun yarima sun ciko da kwalla kuma hankalinsa ya dugunzuma ainun ya tari numfashinsa yaana mai cewa daka ta yakai abbana yanzu kana bani labarin wata jaruma a matsayin itace mahaifiyata to ita kuma junaina wadda na taso nake ganinta a matsayin uwata wacece ita?? Koda jin wannan tambaya sai hawaye ya zubowa sarki Alkasim yayi shiru kamar ba zaice komai ba daga can ya dago kai ya dubeshi cikin rawar murya yace yakai dana kayi hakuri zakaji amsawar wannan tambaya da kayi min a karshen wannan labari da nake baka kafin mu isa birnin masarul anjana Tabbas zaka tantance a tsakanin mahaifiyarka junaina da kuma mahaifiyarka jaruma luslaiya zaka san matsayin kowacce a wajenka koda sarki alkasim yazo nan a zancensa sai zuciyarsa ta karaya ya fashe da matsanancin kuka al amarin da ya dugunzuma hankalin yarima kamsus kenan ya shiga rarrashin sarki a lokacin da yaji ya kamu da tsananin tausayin mahaifin nasa sarki Alkasim da kyar ya shawo kansa ya daina kukan sannan yarima kamsus ya dubeshi cikin zakuwa yace na rokeka dakaci gaba da bani wannan labari domin naji yadda karshen gasarku da jaruma luslaiya zata kasance sannan kuna na gane banbancin dake tsakanin luslaiya da mahaifiyata junaina Al amin Ahmed Dan misau Guyson sunana kenan daga zauran labarai nake magana tayaya zan karbi luslaiya a matsayin uwa ta alhalin ban san wata uwa ba face junaina gama fadin haka keda wuya sai hawaye ya kwararo bisa kumatun yarima kamsus take shima sarki alkasim yaji ya kamu da matukar tausayinsa don haka sai ya rungumeshi akan kirjinsa sannan yaci gaba da bashi labari yana mai cewa..... . LOKACIN DA NAJI ABINDA LUSLAIYA ta fadi cewar a cikin wannan gasa zamu zamo tamkar abokan gaba kuma zamu rinka shiryawa juna tarkon muguntar da zan iya hallaka sai hankalina ya tashi saboda dalilai guda biyu. Dalili na farko shine na kamu da tsananin sonta dalilina biyu kuwa bazan iya shirya mata mugunta da zata hallaka ba nan take zuciyata ta gamsu cewar lallai zan sha bakar wahala a cikin wannan gasa musamman da na tuna cewa inda zamu je mu gabatar da wannan gasa acanne nahiyar su jaruma luslaiya don haka ban san sirrikan dazuzzukan dake can ba. Yayin da luslaiya taga na sunkuyar da kaina kasa ina tunani da nazari saita kyalkyale da dariyar mugunta sannan ta hade fuska tace yaro bai san wuta ba saiya taka ta yanzu saika tashi ka koma gida ka sanar da iyayenka duk abinda ya faru a tsakaninmu domin kayi musu sallama ka dawo mu tafi ka sani cewa tun daga nan gasar mu zata fara don haka kayi amfani da damarka ta kowa a gidansa sarkine duk yadda zakayi ka tabbatar kaga bayana kafin mu bar nahiyarku dajin wannan batu sai yarima Alkasim yayi murmushi ya mike tsaye ya juya mata baya har yayi taku uku gaba zai yi tafiyarsa sai ta kira sunansa ya waigo ya dubeta cikin mamaki ita kuma sai tace da sassafe zaka fito gobe ka sameni anan wurin idan ka baata min lokacin zanyi tafiyata sai kayi da gaske zaka riskeni alkasim yayi murmushi yace babu matsala zanzo akan lokaci yana gama fadin hakan sai ya juya yayi tafiyarsa har yarima alkasim ya isa gida jikinsa a sanyaye yake kuma hankalinsa a tashe yake domin guiwarsa tayi sanyi ainun bisa wannan gagarumar gasa dake gabansa da isar yarima Alkasim a lokacin da magariba ta gabato sai ya nufi kai Tsaye bisa mamaki sai ya hango kofar dakinsa a bude al amarin da yayi matukar bashi mamaki kenan domin babu wanda yake da ikon shiga dakinsa ba tare da izininsa ba face mutum biyu daga sarki sai mahaifiyarsa a fusace yarima Alkasim ya kunna kai da sauri cikin turakar tasa da nufin yaci mutuncin wanda ya bude ya shiga koda yayi arba da wanda ke zaune a cikin dakin sai zuciyarsa ta buga da karfi ba wani bane ba face mahaifiyarsa tana zaune bisa shimfidarsa kanta a sunkuye hawaye na diga daga idanunta cikin firgici ya karasa gareta da sauri ya durkusa a gabanta ya rike hannayanta biyu yana dubanta cikin tsananin damuwa yace yake ummina ina dalilin zubar wannan hawaye daga cikin idanunki sa adda taji wannan tambaya sai tasa hannunta na dama ta share hawayan nata sannan ta janyo yarima izuwa jikinta ta rungumeshi akan kirjinta tace ya kai dana yau shekara talatin da kadan kenan ina tare dakai bamu taba rabuwa ba amma yau sarki ya tabbatar min da cewa a wannan karon zaka nisanta dani kuma zaka yi wata tafiya mai hadari wacce zama ka iya rasa rayuwarka koda jin haka sai yarima alkasim yayi murmushi cikin nutsuwa yace haba yake ummina akan wane dalili zaki damu kanki alhalin kin san duk ahalin gidan nan yana da sa a da nasara bisa duk abinda yasa a gabansa ke da bakinki kin sha bani labarin irin gwagwarmayar da sarki yayi a rayuwarsa tamkar ba zai tsira da rayuwarsa ba wai shin ma me yasa kika shigo cikin turakata kika zauna kina ta kuka? Shin yanzu kina nufin ki ce dake za ayi wannan muguwar tafiya ne? Nayi murna da ganinki a yanzu domin dama akwai wani abu daya shige min duhu ina son kiyi min cikakken bayani kada ki boye min komai taji zuciyarta ta buga da karfi tsoro ya shigeta ta fara zargin anya kuwa sarki bai sanar dani sirrin da suka boye ba tsawon shekaru cikin karfin hali na budi baki nace yake umma ina sonki sanar dani matsayina kafin yarima alkasim ya karasa fadin abin dake bakinsa sai yaji motsi a bayansa don haka sai ya waigo da sauri sarkine tsaye a bayansa fuskarsa a murtuke yana mai kada kansa wato yana yi masa nuni da kada ya fada mata abindake bakinsa.... ALLON-SIHIRI, Littafi na Shida (6) Part A Lokacin da aka ruguntsume da Azabebben yaki tsakanin suhailat da wadannan samudawan maridai su sarauniyya Akisatul sauwara suka fice daga tsakiyar da'irar da'akeyin gumurzun suna masuyin rarrafe tamkar kananun yara saboda tsananin razana dasukayi,. Nanfa jaruma suhailat tazamawa samudawan Alakakai yazamana cewa Anrasa Wanda zaisamu daman koda lakutan jikinta, haka itama takasa samun koda Kai guda daya kasa acikinsu, alokacin dasu sarauniya akisatul sauwara suka koma gefe duksu su ukun suka takura jinkinsu suka zama 'yan kallo, banda muzurai da rawar jiki babu abunda sukeyi, kamar Ace kyat!! Su fita da gudu. Saida akashafe kusan sa'a biyu Ana wannan mummunan dauki ba dadi ba tare da wani yasamu nasara ba Atsakanin jaruma suhailat da wadannan samudawan maridan. Al'amarin daya fusata samudawan maridan Kenan, bashiri sukaja da baya sunamai kurawa suhailat idanu suna huci da numfarfashi kamar do Dodonni. Hakika wadannan halittar sunyi matukar mamakin yadda wannan karamar halitta ta gagaresu Alhali Tana yakarsune da tsagoron KARFIN DAMTSENTA da iya takinta batare da nau'in wani sihiri tsafi ba. Itakuwa jaruma suhailat Ashe wannan ja da baya da samudawan maridan sukayi, dama suka bata takaranta Addu'ointa na neman tsari da sa'a. Duk da cewa jaruma sulailat batasamu wata nasara akansuba, Amma Sam zuciyarta bata karaya ba, saboda ta dogara ga Allah, kuma tasan cewa babu abunda zai gagareshi, nanfa suhailat tafarayiwa Allah kirari acikin zuciyarta Tana kiran sunsyensa tsarkaka guda Dari ba daya. Tana cikin wannan Addu'o inne taga samudawan sun hada kawunansu waje guda suna kus kus! Kawai Sai suka rugo da guda gaba dayansu izuwakan suhailat acikin sabon SALON YAKI na musamman. Komai jarumtar mutum da iya yakinsa idan yaga salon yakin da samudawan sukazo dashi dole ya firgita, domin arike sukeda hannunsu sunayin KAWANYA, sauran hannayennasu na rike da makamai. Koda jaruma suhailat taga sun durfafota acikin wannan salon yakin sai nantake tagane nufinsu wato sosuke lalle suyimata kuri a tsakiya yadda bazata taba samun daman motsawa ba izuwa duk inda taga dama, saidai sutakure awaje daya har yazamana cewa tagaji sannan su samu lagonta. Koda yarage saura baifi taku biyarba samudawan maridan su cimmata sai tadaka tsalle sama ta tsallakesu, kafin ta dira Achan bayansu saita dako daya daga cikinsu. Take yarinjayi sauran suka kife kasa. Al'amarin dayi matukar baiwa maridan dasu sarauniya Akisatul sauwara mamaki kenan bisa ganin yadda jaruma suhailat tasami wannan gagarumin wannan karfin. Cikin tsananin fushi samudawan maridan suka miki zumbur! Suka juyo da baya a fusace. Maimakon susake rike hannun juna su rugo gareta sai suka tarwatse kuma kowannensu yadako tsalle daga inda yake, saigasu a sama tamkar tsuntsaye masu fuka_fukai. Asamanne ko wannensu yazaro makaminsa da nufin suyiwa jaruma suhailat rubdugun SARA DA SUKA. Kafin kowannesu yasamu daman Kai makaminsa jikinta tuni jaruma suhailat tayi Dan tsalle sama tayi wata irin katantanwa Sama tamkar An murza mazari ta tarwatsasuTana Mai naushin fuskokinsu da kafafunta dakuma hannayenta duk alokaci guda. Kawai saigani akayi samudawan maridan suna zuzzubewa kasa itakuma saitacigaba da katantanwa Asaman kaman Anmurza mazari ta tarwatsu Tana Mai naushin fuskokinsu da kafafunta dakuma hannayenta duk a lokaci guda.kawai saigani akayi suna zuzzubewa kasa, itakuma tacigaba da katantanwa Asama har izuwa 'yan wasu dakiku ba tare da tafado kasaba harsaida gaba daya samudawan maridan sukaje Kasa sannan taduro kasa da kafafunta. Saboda tsananin mamaki bisa ganin gagarumar wannan jarumta da jaruma suhailat tayi Akisatul sauwara, jarumi lubainu, sarki Darmaz da Dazyan basusan sa'adda suka wangame bakinsuba sukazama kamar gumaka domin ko giftawa basayi. Mutara kokuma Anjima idan nasamu time gobe Naku Khamis Idris Muhammad Allon sihiri littafi na 6 shida Part B Koda samudawan maridan sukaga abunda jaruma suhailat tayi musu yazamana cewa duk ta farfasamusu baki da hanci, sai suka fusata Ainun suka taso mata da nufin su tarwatsata. Koda ganin haka sai itama jaruma suhailat ta fusata ta maida takobinta cikin kufenta ta taresu Tana Mai karanta wasu Addu'a ta musamman acikin ranta. Aikuwa suna riskarta sai sukaci gaba da kaimata Sara da suka da manyan miyagun makamansu, ita kuwa sai tawanzu Tana Mai Kare duk hare harensu Tana Kama hannayensu da kafafunsu Tana kakkaryasu. Nanfa ihun samudawan maridan da kururuwarsu tacika dajin gaba daya. Karar karyewan kasusuwannasu kuwa tamkar karyewar bishiyoyine Manya ke faduwa Kasa. Kafin cikan dakika Dari bakwai da sittin gaba daya samudawan naridan sun zube kasa sunzama naka sassu sai koke-koke da ruri sukeyi sakamakon tsananin zafi da zogin da sukeji. A daidai wannan lokacin ne sarki Darmaz yadubi sarauniya Akisatul sauwara yace, Tabbas wannan jarumin ba mutum bane, Aljanine yazo garemu domin ya yaudaremu. Saboda idan ba Aljani ba banga wani mahaluki da zaizo yayi wannan gagarumin jarumtakar ba. Koda jin wannan Batu sai sarauniya Akisatul sauwara tayi murmushi tace, Tabbas mutum ne ba Aljan ba, domin inda Aljanine tun farkon haduwarsu za'agane, saboda dukkan matsafi yana gane Aljani adukkan shigar da yazomasa, kawai kace hatsabibine kuma takadarin BIL'adama Mai abubuwan Al'ajabi na gaban kwatance, Saidai Akwai wani Abu guda Dana kasa fahimta akansa, har yanzu nakasa ganewa shin namiji ne kokuma mace ne?? Koda jin haka sai Dan wada Dazyan yadubi sarauniya Akisatul sauwara afusace yace, wannan wace irin maganan banza kikeyi yake wannan sarauniya? Ina Mai tabbatar miki da cewa maigidana namiji ne ba mace ba, saboda meye kike tantama akan haka? Koda jin haka sai itama sarauniya akisatul sauwara ta dubi wada Dazyan afusace ta dakamar tsawa tace, idan hard Mai gidan naka namiji ne meyasa yakejin kunyan ya rube agabana?? Tunda muka Fara wannan tafiyar babu Wanda ya taba ganin gashin kansa bare cinyarsa. Akan wane dalili yake boye komai na jikinsa? Koda jin haka sai Dan wada Dazyan yayi tsaki yamiki daga cikinsu yatafi inda jaruma suhailat take. Shukuwa yarima Lubainu daman yana gefe daya yana ganin ikon Allah. Lokacin da Dan wada Dazyan yace wajen jaruma suhailat sai ya sanar mata da duk abunda suke fada akanta, sai hankalinta ya dugun zuma ainun, tayi mamakin yadda har sarauniya akisatul sauwara take kokarin gano haka. Kawai sai ta dubi Dan wada Dazyan acikin YAREN KURAME. Karka damu da ita akan Hakan zargi takeyi batada yakini akan hakan. Gama fadin haka keda wuya sai jauma suhailat ta juya gefen inda yarima lubainu yake tsaye. Awannan lokaci samu dawan maridan da jaruma suhailat ta bazar akasa sun Fara Jan jikinsu akasa dakyar tamkar macijiyar da tayi babban hadiya. Kwatsam bazato ba tsammani sai sukaji wata gagarumar iska a samansu. Kafin daya daga cikinsu yayi wani yunkuri tun An mammakesu. Saboda karfin bugun da akayiwa kowannensu a fuska, take suka zube kasa sumammu. Lokacin da jaruma suhailat da yarima lubainu suka farfado daga suman da sukayi sai suka tsinci kansu a daddaure da wata murtukekiyar sarka ajikin wata bishiya kuma duk gabobin jikinsu a sanyaye suke ta yadda ko daga hannunsu bazasu iyaba saboda rashin karfi da kuzahari. Acan gefe guda kuma sarauniya akisatul sauwara, sarki Darmaz, Dan wada Dazyan ne suma acikin mummunan Hali suyi darsham akasa kamar yadda su jaruma suhailat suke na dauri. Har izuwa wannan lokaci wannan iska bata daina ba ta gabar da yamma kudu da Arewa. Nanfa jaruma suhailat da Dan wada dazyan suke kokarin bude bakinsu suyi Addu'oi Amma abun ya gagara. Al'amarin dayayi matukar dugun zuma hankalinsu kenan suka rasa abunda keyimusu dadi, sabida tamkar sunayin yakine da abunda basa ganinsa! Kawai sai sukaji An bushe da wata mahaukaciyar dariya wacce sautinta yacika dajin gava daya karfinta yasa tantuna sukafara jijjiga kamar zasu tumfuke sufadi Kasa. Bazato ba tsammani sai halittar ta baiyana tsulum! Agaban yarima lubainu ta yadda har sunajin nunfashin junansu. Bakowa bace wannan halittar face Aljana badi'atul sauwara. Cikin razana da mamaki yarima lubainu yaja da baya yadubeta yace, Kekuma waye ya kunceki acikin daurin Dana baroki? Koda jin haka sai Aljana badi'atul sauwara tasake bushewa da dariya a Karo na biyu sannan ta tsuke bakinta Tana Mai turfune fuska tace, Kai a iya tunaninka ka dauren kana tunanin vazan taba kubuta ba ko? To kayi babban kuskure da kayi zaton haka, saboda Mai RAI baya fidda tsammanin RABO face yaba nunfashi a doron Kasa. ALLON SIHIRI LITTAFI NA SHIDA 6 PARTC Tabbas yanzu ne zakayi babban nadama akan rashin bani hadin Kai domin mugudu tare mu tsira tare da Kai. Aljana Badi'atul sauwara takauda kanta wajen jaruma suhailat race, Angaisheki BABBAR JARUMA! Hakika kin yaimakeni kin gajarcemun duk wahalan da zansha ta hada wannan ALLON SIHIRI guda uku, tunda gashi yanzu gaba dayansu a Hannunki. Kisani cewa wadanchan samudawan maridan da kika yakesu bakowa bane ya turosu face Boka darbusa, kuma har ynz baituromuku kaso goma ba daga cikin dubun irin mugayen abubuwan da yayi tanadi domin ku Akan wannan ALLON SIHIRI''. Lokacin da Aljana badi'atul sauwara tazo daidai nan a zancenta sai Sarauniya Akisatul sauwara ta wunkura cikin karfin Hali ta bushe da dariyar farinciki sannan tace, yake wannan Aljana Mai tsananin SA'A da RABO! Ina Mai godia a gareki da kika fitar damu faga cikin duhun daya baibayemu game da Abokanan tafiyarmu. Tun a farkon tafiyar mu da wannan bakuwar jarumar idanuna suka nunamin cewa wannan MACE ce ita Name MIJI ba kamar yadda take ikirari. Shin yanzu ke mecece ribarki idan kika tafi kika barmu awannan mawuyacin halin makiya sukazo suka hallakamu tunda dai kinsami abunda kike nema? Sa'adda Aljana badi'atul sauwara taji wannan Batu saita bushe da dariya tace, Ai shi makiyi ba'a bashi dama komai kankantarta. Ni banida makiyin da yawuce boka Darbusa a duniya, shikuma awajensa kune manyan makiyansa tunda kunzo har gidansa kurrabashi da abunda yashafe shekara da shekaru yana gadinsa Dan yacika burinsa na duniya. Kusani cewa bayan na dauke Allunan sihiri da suke wajenku yanzu, ina tafiya da tsawon dakiku sarkokin Dana daureku zasu bace bat! Daga cikin jikinku, kuma kuzaharinku zai dawo kamar yadda kuke a da, Amma fa kusani boka darbusa bazai taba barin kokarin hallakakuba tunda shi azatonsa kuna tare da ALLON SIHIRI. Nikuma daman zanyi Amfani da wannan ALLON SIHIRIN Wanda daman asalinsa nawane tunda mahaifinane yakerashi, kafin ku fita daga cikin masifun da kuke ciki tuni nagama dukkanin shirye shiryena na zama SARAUNIYAR DUNIYA acikin kwanciyar hankali batare da na fuskanci wata matsalaba. Gama fadin haka keda wuya sai tajuwo ta dubi yarima lubainu tadubeshi cikin wani irin murmushi na mugunta tace, tabbas kasaki reshe ka Kama ganye! Yanzu inda ace ka taimakeni ka kunceni acikin daurin da boka darbusa yamin da yanzu take Zan daukeka na doraka akan gadon bayana natafi dakai Chan fadata. Achanne zan karanta wannan ALLON SIHIRI nagano inda KOGIN IMFAL yake nakaika Chan kaciro saiwar da bishiyar da ake bukata wacce zakasha ka warke daga lalurar da yarima mangul ya sakamaka. Yanzu gashi kayi biyu babu, domin bazaka warke ba, kuma bazaka sake saduwa da matarkaba GIMBIYA YAZIRINA har Abada, dimin a halin yanzu suna Chan wani waje Mai mugun Nisa acikin daji acikin mugun yanayi na rashin sanin inda suke dama inda zasu dosa. Kuma yarima mangul bazai daina farautarsuba har saiya riskesu ya kashe SADAUKI RUHAISU sannan ya dauke gimbiya yazarina''. koda Aljana Badi'atul sauwara tazo nan a zancenta saitakara Bushewa da dariya akaro na biyu sannan tadubi yarima lubainu tace, shin kanada wata wasiyya ne ga mahaifinka!? tabbas zanyi maka wannan Alfarmar nakai wannan wasiyyarka tunda nima Kayimin Alfarma guda daya ta rufamin Asari baka sanar da wannan BAKUWAR JARUMA Mai Rufe fuskarta da jikinta labarina sa'adda ka ganni acikin gidan boka darbusa da bansamu wannan damar yanzu ba Dana shammaceku Dana sumar daku, kuma nasanya muku wannan tsananin mutuwar jikin. koda jin haka sai Aljana Bari'atul sauwara tasake tuntsurewa da dariyar mugunta taita kyalkyalewa kamar bazata dainaba ba. daga can kuma saita tsuke bakinta tace, Ai shi kenan nida Kai zanga Wanda zancensa zai tabbata. Tana Gama fadin haka sai ta bude fuka fukanta saiga ALLON SIHIRI guda uku amakale a hammatarta. harta yunkura zata tashi sai yarima lubainu yace yake wannan Aljana, waishin wanene ya kunceki daga wannan daurin da boka darbusa yamiki? Koda jin wannan tambaya sai Aljana badi'atul sauwara tayi murmushi tace, babu Wanda ya kunceni face ni kaina. Kasan Ance Mai rai baya kasa motsi! Bayan kaki kunceni katafi kabarni acikin wannan mawuyacin Hali ina zubar da hawaye sainarinka buga kaina ajikin bango saboda bakin ciki kuma narinka buga kafafuwana a kasa. Adalilin hakanne kafafuwan nawa suka rinka fasa malalen kasan har suka haddasa rami Mai zurfi, Ashe acikin kasan dakin danake aciki yake ajiye Littatafai dayawa na sirrikan tsafin boka darbusa. Dayake sarkar dayake daure Dani Mai tsawo ce sosai, take nakarasa Burma ramin da kafafuna sukayi nafada kasan dakin nashiga karanta littatafan. Acikin littatafanne naga sirrin yadda zan kwance kaina daga sarkokin da boka darbusa ya daureni. Nantake nakamu da tsananin farinciki dakuma takaici ganin cewa sai a sannan ne nasan da wannan damar bayan na shafe shekaru da dama acikin kurkukun bakin ciki. Da wannan furuci nakeyi muku bankwana na karshe. Koda Gama fadin haka sai Aljana badi'atul sauwara tasake bude fukafukanta ta tashi sama. kafin giftawar ido ta luluka acikin gajimare ta bace bat!! Tamkar bata taba wanzuwa ba awajen. Bayan shudewan wasu 'yan dakiku ne su jaruma suhailat sukaga sarkokin da aka dauresu dashi sun bace bat!! Tamkar basu taba wanzuwa ba Sannan sukaji karfin jikinsu yadawo dakuma kuzaharinsu yadawo tamkar wani Abu bai taba samunsuba. Cikin hanzari jaruma suhailat mike tsaye zumbur! Tacire rawanin dayake kanta tayi jifa dashi. Alokacinne dogon gashin kanta ya zubu izuwa gadon bayanta yana sheki da walwali. Jaruma suhailat ta cire babban rigan da ke jikinta doguwa ta tsargeta da hannayenta biyu tayi jifa da ita saiga gaba daya surorin jikinta sun fito. Koda sarauniya Akisatul sauwara da sarki darmaz sukayi Arba da wannan baiwa ta kyau wacce Allah yayiwa jaruma suhailat saisuka dimauce suka fita a haiyacinsu alokacin idanuwansu suka kafe, jikinsu ya Kame suka kuramata idanu kawai. Ita kuwa sai ta durfafosu saida tazo dafda su sannan ta tsaya fusakrta a murtuke. Susana SUHAILAT BINTU AFUWAN, kuma nafitone daga wata nahiya Mai Nisa, daban da taku ba, Acikin wata kasa da ake Kira DARUL ILMUN. Bakokai ne yakawoni nayiyarku ba face jaddada ADDINiNA Wanda shine Addinin gaskia a bautawa Allah shikadai Wanda bashida Abokin tarayya, wato ADDININ MUSULUNCI! Lallai saina tabbatarwa da sarakunanku da kuma Bokayenku cewa bautar gumaka da tsafin da kukeyi duk karyace, kuma hanyace ta bata mabaiyani. idan har na'isa login bahar imfal da taimakon ubangijina nayi nutso acikinsa na tsunto Dan itatuwar da yarima lubainu zaisha ya warke daga asirin da yarima mangul Yamar dolene su yarda da Addinin tunda sun tabbar babu Wanda yataba yin hakan, kuma babu Wanda zai iya. Kosani cewa koda Allon sihiri na wajenmu ko bayanan zamu isa kogin bahar imfal nabiyawa yarima Lubainu bukatarsa Da izinin ubangijin musulunci. Sa'adda jaruma suhailat tazo nan azancenta sai sarauniya akisatul sauwara da sarki darmaz suka dawo haiyacinsu sunamasuyin doguwar ajiyan nunfashi, sannan sai sarki darmaz yadubi jaruma suhailat cikin fushi yace, to mu meye Amfanin mu cigaba da binku acikin wannan tafiyan tunda Arrabaki da Allunan na sihiri? tayaya zaki iya dauko wannan makarun maganin da akayiwa trains lubainu Alhalin babu ALLON SIHIRI awajenki? koda jin wannan Batu sai jaruma suhailat tace, tunda imaninku ya karkata akan sai da ALLON SIHIRI?! Za'a aiwatar dashi, to shiekenan zan karbo muku ALLON SIHIRIN daga hannun wannan Aljana da tazo tasaceshi. ALLON SIHIRI Littafi na shida (6) Part D Kusani cewa sakaci ne yasa har tasamu dama ta shammaceni kuma bansan da batuntaba, Amma a yanzu Dana Dani duk inda take saina bita na karbo ALLON SIHIRIN naku da iznin ubangijina. Kusani cewa wannan buri na banza da kuke son MALLAKAN DUNIYA da abun cikinta shirme ne kuma nadaukeshi tamkar tatsuniya, wato Abunda bazai taba faruwa ba, Saboda shi tsafi karyane kuma batane. Da idanunku kunga dai Abubuwa da dama danayi na Al'ajabi cikin jarumtaka cikin taimakon ubangijin gaskiya kokuwa har yanzu zukatanku suna yaudarar ku?? Sa'adda jaruma suhailat tazo daidai nan a zancenta sai dadin muryanta yasake dimauta Sarki darmaz, yadubi sarauniya Akisatul sauwara sai sukakamayin in'ina suka kasacewa komai. Koda ganin haka sai jaruma suhailat ta yafito yarima lubainu da hannunta tajashi can gefe daya inda baza'aji abunda suke tattaunawa ba, suka kamayin maganganu. Koda ganin haka sai KISHI yakama Sarki darmaz da Dan wada dazyan, domin kowannensu jiyayi inama shine yakadaita da jaruma sulailat haka yana kallon kyakkyawar fuskarta kuma Yana ka sauraron naganarta Mai zaki wacce ita kadai zatasa mutum yayi bacci kokuma ta kwantar masa da hankali a lokacin da yasamu kansa cikin bakin ciki ko damuwa. Ita kuwa Akisatul sauwara wani tunanine yafado mata nan take Wanda ya dugunzuma hankalinta tarasa Abinda yake mata dadi. Dafarko dai sa'adda taga yarima lubainu da jaruma suhailat sun koma gefe sun tsaya dabda juna suna magana saita kuramusu idanu Tana Lura da irin kallon da sujeyiwa junansu, kawai so take ta gano shin Akwai soyayyane a tsakaninsu? To idanma Akwai soyayya ai saidai idan ayanzu take aka farata tunda dai shi baitaba ganin fuskartaba sai a yanzu. Tun a ranan da Sarauniya akisatul sauwara tafara ganin yarima lubainu taji ya kwanta mata aria domin yanada duk abunda takeso ga namijin da zaizamo abokin rayuwarta. Abu nafarko dai shine, yanada tsananin kyau, kuma gashi basarake ne, sannan jarumin maza. Wadannan abubuwa uku sune samarin da suke nemanta suka kasa hadawa duk, kuma shine dalilin dayasa itama taki karbar soyayyarsu. Daga ranan da tahadu da yarima lubainu taga Ashe Allah yakawo mata karshen laluben da takeyi. A yanzu kuma dataga jaruma suhailat tare da yarima lubainu, saitaji wani irin BAKIN KISHI ya turnuketa, saboda.... KUYI HAKURI BABU PAGE DAYA missing 27 page. Sarauniya akisatul sauwara sai taji kamar Tasa kafarta tayi tamaula dashi, tunda tsawonsa gaba daya baiyuce tsayin guiwartaba. Dan wada dazyan yayi shiru ga barin yin dariyan sannan yadubi sarauniya akisatul sauwara yace, dafarko dai kisani cewa ban isa na fadi komai akan shugabata face sai da izninta saboda bin umarninta. Abu na biyu danakeso na tunamiki shine, yarima lubainu yanada mata wacce tunima Andaura musu Aureda ita, kuma saboda itane yafito neman maganin lalurarsa. Shin tayaya kike tsammanin zaibada soyayyarta take tsawon shekaru izuwa wata macen daya hadu da ita acikin kankanin lokaci? Idan kema kinji kinfara kamuwane da soyyar yarima lubainu inamai shawartarki da ki gaggauta ki shafeshi acikin Kundin rayuwarki don kada yabada miki kasa..... Kafin Dan wada dazyan yagama fadin abunda ke bakinsa tuni sarauniya akisatul sauwara ta daka masa tsawa. Al'amarin dayasa yarazanane har hantar cikinsa ta kada yadan ja da baya a firgice. Sarauniya Akisatul sauwara ta dubeshi a fusace tace, waccer Shugaba taka babu wani Abu da da namiji bazata iya saye zuciyarshiba saboda kyawunta, koda kuwa shine Wanda ya kirkiri soyayya a duniya. Ni kaina danake 'ya mace kuma kyakkyawa abar kwatance ayanzu Dana ganta saida na Raya a Raina cewa imani ni namiji ne Dana mallaketa Amatsayin Matata. Kasani shi SO ba karya bane gaskiyane kuma nasani cewa yarima lubainu yanada matar da yakeso, Amma shin mainene tabbacin zaisake saduwa da ita Alhalin rayuwarta nacan acikin mugun hadari? Kai! Ni tuni ma nayi bincike acikin tsafina nagano cewa gimbiya yazirina da yarima lubainu baza su tabayin zaman mata da miji ba, Dan haka babu abunda zaisa nadaina sonsa. kuma kasani cewa nice nafara haduwa da yarima lubainu har nabaro kasata, mulkina da jama'ata domin na taimakeshi. kaikanka kasan cewa idan babu SO da KAUNA babu yadda za'ayi Nabaro wadannan Abubuwa uku, na sallama rayuwata kawai Dan biyan bukatarsa. Caraf! Sai dazyan yatari mumfashin Akisatul sauwara yace Ai badon bukatarsa kadai kema kika fitoba sai domin kema ki samu daman hada Allunan sihiri guda uku. sarauniya Akisatul sauwara tayi murmushi tace, maiyasa tuntuni banyi wukurin Nemo wadannan Allunan sihiri ba guda biyu tunda nasan A inda suke sai ayanzu da yarima lubainu yazo gareni? Kai! Dakata nagaya maka gaskia, karfin soyayya yafi dukkan karfi, domin so yana iya sakawa mutum yadaina tsoron abunda yake tsoro, Saboda soyayya ta mantar dashi baya ganinsa. SO yana sakawa mutum ya fansar da rayuwarsa, kuma duk Wanda yayi yunkurin rabani da Abunda nake kauna shima zarrabashi da rayuwarsa!!! Ko ka sanar da shugabarka wannan ko baka sanar ba wannan ba matsalata bace, Amma zaifi kyau kagaya mata, domin ta nisanta kanta da yarima lubainu domin nawane ni kadai."" koda fadin haka sai Sarauniya akisatul sauwara tajuya da nufin ta koma inda tabaro sarki darmas,Amma sai Dan wada dazyan yayi saurin kiran sunanta sai tajuyo ta dubeshi sannan yace, Babu yadda za'ayi ta nisanta da yarima lubaino saboda ahalin yanzu yazama tamkar Dan uwanta najini tunda yakarbi Addininta, wato Addinin musulunci. koda jin haka sai habkalin sarauniya Akisatul sauwara ya dugunzuma fiye da ko yaushe, tayi shiru Tana Mai sunkuyadda kanta kasa, inda tafada cikin kogin tunani Mai zurfi. Tana cikin tunanin ne taga yarima lubainu ya baru inda jaruna suhailat take ya durfafo inda suke, Dan haka saita kura masa idanu Tana Mai murmushi.. Compilied By Abubakar Saleh AlQuyraemey Whatsapp Number 08138873799 Visit www.rumbunlabarai.com For More Complete Documents da isawarsa inda suke yadubeta sannan yadubi sarki darmaz yace, jagorar tafiyarmu tace nasanar daku cewa anan zamu kwana tunda Rana ta fadi sai gobe mucigaba da tafiya. Kodajin wannan Batu sai Sarauniya Akisatul sauwara tadubi yarima lubainu cikin fushi tace, waishin akan wane dalili zamucigaba da bin jagorancinta Alhalin tanaji Tana gani akazo aka kwace mana ababan dogaranmu aka tafi dasu?? Ai wannan alamune na gazawa, waishin yanzu tasan inda zamuga Aljana badi'atul sauwara ne bare har muje mu risketa a fafata KAZAMIN YAKI Don kwato kayanmu. to kasani Aljana badi'atul sauwara bakamar hatsabibiya bace, Sarkin wannan Birni na Istanbul saurayine kyakkyawan gaske, kuma sadauki Mai TARWATSA MAZA a FILIN DAGA!! A duniya kaf! Awannan lokaci babu Wanda yafishi tarun dukiya, girman sarauta da kwarjini. wannan daliline kowace kasa ke shakkarsa, domin yatara mayaka 'yan gaban gani kasheni masu tsananin karfi da horon yaki na ban Al'ajabi. Ana kiran wannan sarki na Birnin Istanbul da suna SHA'AFARAN IBN AUHID. ALLON SIHIRI Littafi na shida (6) Part E Babu wani jindadi Wanda Allah baibawa sarki Lubainu ba face Abu guda daya jal!! Bakomai bane face Rashin lafiyar maza kuta!!! Tundaga balagar sarki lubainu har yacika shekara talatin da uku baisan wani Abu waishi Sha'awa ba akan 'ya mace, baitaba yin wata mu'amala dawata mace ba hasalima ko kuyangi basa masa yidima saboda sanin baya bukatarsu a rayuwarsa. Duk wata hidima tasa maza ne ke masa, dafarko boye matsalarsa yayi Sai akafara zargin ko yana harkan banzane da maza Amma da'aka gano baya wannan harkan Sai akagano bashida lapia ne, saboda tunda yake arayuwarsa baitaba yin soyayya ba, kuma baitaba tunanin koda yin Aure ba. Akaf duniya babu abunda Allah yajarrabi sarki lubainu yakeso sama da kananan yara 'yan shekara hudu zuwa kasa. A kullim yanasa adebomasa kananan da yammaci acikin lambunsa azauna acikinsu yaita wasa dasu har magariba tayi sannan za'araba musu kayan wasanni iri iri da kayan zaki sannan ya sallamesu. Duk sa'ilin da sarki lubainu ya kurawa wa'yannan yaran idanu ASA ilin da suke wannan wasa Sai yafara zubda kwalla saboda takaicin sanin bashida haiwuwa bare yasamu magaji na har Abada! Babban abun bakinciki ma agareshi shine, shine zuri'a na karshe a wannan gidan sarauta, dazarar ya mutu shikenan sarautar tabar Ahalin gidansu takoma kan wata zuri'a sannu ahankali za'amanta da zuri'arsu ma gaba daya a doron kasa. Bisa wannan daliline yabaza yaransa afadin duniya suna ziyartar bokaye da manyan likitoci har tsawon shekara uku domin asamo masa magani Amma ba'adaceba,kuma Duk wajen bokan da akaje saiyace indai sarki Lubainu yanso yasamu lafiya irinta da namiji toko saidai yaje birnin Hindu yayi tsirata a gaban sarauniya Mauzuratul shardila ya fadi bukatarsa bayan yayimata yanka sannan ne bukatarsa zata biya shikuwa sarki Lubainu yace bazai taba kaskantar da Kansa irin haka ba ace har mutane suga tsiraicinsa don kawai biyan bukata Lallai daya Aikata haka gwara yamutu babu haihuwa. Dukkanin samoyan sarki Lubainu da makusantanshi da Aminansa babu Wanda baibashi shawari akan yaje gaban sarauniya mauzuratul shardila baya Aikata abunda aka uwarceshi domin yasamu Haihuwa, Amma Sai yaki. Duk Wanda yamatsamar akan yaje karshenta batawa sukeyi da shi yadaina kulashi, dukkuwa kusancin dake tsakaninsu dashi. Haka dai sarki Lubainu yaci gaba da tayuwa haryacika shekara sha biyar akan mulki bayatare dayasamu da ba bare jika. Kwatsam! Sarki Lubainu wata rana yayi sha'awar yafita daji yayi farauta, don haka saiyadibi dakarunsa mutum shida kacal! Domin suyi masa rakiya, sukayi shiri irin na mafarauta suka shiga daji.s A farkon yammaci sarki Lubainu yafito wannan farutan, alokacin da rana tayi sanyi launin garin sunyi shudi, alokacin anayin wata iska mai sanyi atakaice dai yanayin da akeciki yanayine mai dadi, uanayin da yakesa mutum nishadi da farinciki. Duk da sarki Lubainu ya kasance sadauki, kuma GORZON MAYAKI mai TATWATSA MAZA a FILIN DAGA Amma Sau uku kacal yataba fita farauta a rayuwarsa, don haka baisan sirrin dajiba sosai, kuma baisan sirrin dabbobin daji ba. Sai da sarki Lubainu suka shafe kusan sa'a biyu da rabi a daji suna yawon farauta Amma ko zomo basu kamoba. Hatta ysuntsayen da suke Yawo asararin samaniya sunkasa hatbo ko guda daya. Al'amarin da ya fusata sarki Lubainu kenan yadubi wa'yannan dakaru guda shida a fusace ya daka musu tsawa sannan yace, Amma tur! Da Ku! Tabbas kunji kunya!! Nazaboku ne saboda dukkanku kunkasance 'ya'yan manyan mafarauta, Amma kunkasa farauto koda Kwaro ballantana dabbar daji ko tsuntsayen da suke giftawa ta saman knmu. Towai shin sokuke mukoma gida cikin Abun kunya agammu babu komai a hannunmu ko yaya ?? Koda jin haka Sai babban cikinsu Wanda shine Dan sarkin mafarauta na garin yarisina Ga sarki Lubainu yace, agaskia Akwai matsalar da tafaru akan wannan lamarin. Yau kusan sati uku kenan dazuzzukan dake yankin birnnan namu sun zama wayam! Duk dabbobin dake cikinsa sun face bat! Tamkar Anyi ruwan sama Andauke. Amma mahaifina yace yanaganin wasu bakin mafarautane suka gifta ta wannan dajin kuma suna da yawan gaske, Ayari ne guda, yana zaton sune suka kwashe mana komai."" Kodajij wannan batu Sai ran sarki Lubainu ya baci, zuciyarsa tayi bakikkirin sayake dakawa Dan sarki mafarauta tsawa har said a hantarsa ta kada yace, yanzu daman Ansan da wannan matsalar ba'azo an sanar daniba?? Dan sarki mafarautan yasake risinawa yace, ya shigabana mahaifina ya sanar da waziri, kuma waziri yasa Ana bincike akan lamarin, nayi tsammanin Sai abun yafi karfinsa ne zai sanar dakai"". Koda sarki Lubainu yaji haka Sai yayi kwafa yacije lebe sannan yace, aikuwa idan nakama wa'yannan bakin mafarauta Sai sun biya duk abunda akarasa acikin dazuzzukanmu kokuma su fanshi laifin su da rayukansu,,,,,"" Kafin sarki Lubainu yagama rufe bakinsa Sai sukaga giftawar wani mutum cikin wani azabebben gudu tamkar tauraruwa mai wutsiya ya wuce fit! Tagabansu ya bausa cikin daji , kafin giftawar ido yabace bat! Aikuwa Sai sarki Lubainu ya sakatwa dokinsa linzami yabi wannan mutum, cikin hanzari suma dakarun suka rufa masa baya. Sarki Lubainu uacigaba da baiwa dokinsa kaimi yanamai irin wani azabebben gudu tamkar zai tashi sama, Amma Dakar ya iya hango mutumin daya gotasu a can gaba nesa dashi. Ashe ma macece acikin shigar kayan fatar damisa. Koda sarki Lubainu ya hango wannan mace tana faman wannan azabebben gudu na ban Al'ajabi kuma yaga Ashe dawata damisa suke tsere. Damisar gudu take iya karfinta domin ta ceci ranta Amma tazarar dake tsakaninsu da wannan macen baiwuce taku biyar ba, Ako yaushe za'aiya cimma damisar, Nan take sarki Lubainu yacika da tsananin mamaki kuma ya dimauce sakamokon dalilai biyu. Dalili na farko shine, Duk da cewa bayan wannan macen yake hangowa mai kyan kira da siffa kamar ta ba. Gashin kanta kadai ya isa mutum yasa ya dimauce saboda ya zubo harkan kasan kugunta saboda tsawonsa. Duk da cewa an tartare gashinne a gadon bayanta Sai tarwatsewa yakeyi acikin iska saboda yawansa ya kasance yanada tsananin baki gami da kyalkyali da hasken da mutum zai iya gamin fuskarsa akansa tamkar madubi. Dalili na biyu kuwa shine, sarki Lubainu baitaba ganin bil'adama ba mai karfin gudun wannan mace ba wacce take kokarin kurewa damisa gudu. Nan da nan zuciyarsa ta Aiyyana masa tambayoyi. KUMA WAI SHIN ITA WANNAN JARUMA MACE WACE IRIN SHAIDANIYACE ITA HAR DA WANNAN KATUWAR DAMISAR ZATA GUJE MATA. KOKUWA TA KASANCE ALJANA BA MUTUM BA.?? Sarki Lubainu yabaiwa kansa Amsar da yayiwa kansa wannan tambaya kawai saiyaga wannan mace ma'abociyar kyau tayi sufa tafadi cahn gefe ta chapo wuyan namisar suka kama kokawa a kasa. Kawai Sai jarumar ta miki tsaye ta rike makoshin damisar da hannu daya tayiwa damisar hajijiya Asama say uku ta fyadata da kasa ta takemata wuya da kafarta guda. Nan fa damisar tafara kakakin Mutuwa inbanda jelarta da kafarta babu abunda take iya motsawa kafin sarki shahran ya iso garesu tuni damisar tazama gawa. Koda wannan jarumar taji sukuwar dawakai abayanta sai tajuyo saita kurawa sarki Lubainu idanu batare da tayi wani motsiba ko taji wani tsoro ba. Sarki Lubainu yadira a gabanta yajuyo yana mai yimata nuni da tabashi wannan damisar. Jarumar ta wunkura kamar zata mikamasa wannan damisar. Amma Sai itama ta daka tsalle sama cikin shammata takaimasa duka da kafarta a girjinsa. Duk da tsananin karfi irin na sarki Lubainu said a yayi baya taga taga kamar zai fadi, yzamana suna kaiwa junansu naushi da bugu da hannu da kafa acikin tsananin zafin nama. Juriya da bajinta. Ai kuwa Anafara wannan gumurzu ne Sai sarki Lubainu yacika da tsananin mamaki domin a iya rayuwar gwagwarmayarsa baitaba haduwa da jarumin da karfinsu na damtse yazo daya ba irin wannan jaruma. Komai karfin kato da iya fadansa akaron farko yake gamawa da shi Amma gashi wai 'ya mace ya shafe 'yan dakiku da ita. PAGE 46 IS MISSING. Wannan bakuwar jaruma kasa, kuma ya kwace wannan damisa dake hannunta ta kowane hali, Idan ba hakaba kuwa ta karya Alkadarin jarumtakarsa kuma ta bashi kunya agaban dakarunsa. TUNDA DAI TA'IYA FADA DA HANNU GASHI HARMUNYI KUNNEN DOKI , BARIN GWADA IYA YAKINTA DA MAKAMI NAGANI. Koda Aiyana hakan acikin ransa Sai sarki Lubainu yadubi jarumar a fusace yace, yake wannan budurwa INA gargadinki da ki mika wuya agareni na kamaki amatsayin mai laifi, kuma ki bani wannan damisar dake hannunki inbahaka ba kuwa zaki tilastani nayi Amfani da takobina akanki, kuma banaso naragewa wannan kyakkyawar sura naki kyawu. Koda jin wannan batu Sai jarumar tayi wani dan guntun murmushi Ga sarki Lubainu kuma tasake murtuke fuskarta tace. Ai ba'a sanin maci tuwo Sai miya takare! Idan har kana ganin zaka iya samun nasara akaina da karfin takobinta saika jarraba!!. A India babu kasa Anan ake gardamar kokawa!!! GA FILI GA MAI DOKI Mu zuba mugani!!! Tana gama fadin haka tasa hannu ta zare takobinta, Al'amarin dayayi matukar girgiza dakarun sarki Lubainu kenan suka kamu da tsananin mamaki kuma suka tausayawa wannan jarumar domin inda tsan tsananin iya yakin sarki Lubainu da batayi wannan ganaganciba duk da cewa sums basusan iya NATA yakinba. Koda yake makaho bayacewa ayi wasan jifa saiyaga hoge, Amma kuma ai bakin rijiya bawajen wasan makaho bane!!! Koda sarki Lubainu yaga irin dakewar wannan jarumar budurwa harms ta rigashi zare takobi Sai ya sake cika da mamakinta, kuma yaji ta Dada burgeshi Ainun,domin yanason mace mai zuciyar maza wacce yakeganin itace kadai zata iya dacewa da shi , Nan take sarki Lubainu ya sake ja da baya kamar taku biyar sannan yatsaya tsaf yazare tasa takobin yanamai bude hannayensa suka kurawa juna idanu shida ita har izuwa wani Dan lokaci. Kamar hadin Baku Sai duk su biyun suka Togo da gudu izuwa kan junansu sunamasu kartan kasa da takubbansu kaida gani kasan cewa idanu akayiwa wannan haduwar komai zai iya faruwa. Muhadu gobe in Allah yakaim . ALLON SIHIRI Littafi na shida (6) Part F Koda yarage saura taku uku su hadu Sai suka daka tsalle sama suka kaiwa jujansu mugun hari. Shidai sarki Lubainu a wuya ya kaimata saran da nufin ya tsizge mata kai, ita kuma Sai takaimasa Sara a kafada da nufin ta zaftaremasa hannunsa na hagu. Cikin zafin nama kowannensu yakaucewa harin da aka kawomasa Amma Sai wani abun Al'ajabi yafaru a lokacin da suka duro a kasa a bayan junansu a tare. Abunda ya faru shine, sakaomakon da saran da sarki Lubainu yakaiwa jarumar wuya ko shafar jikinta baiyiba Amma Sai kaifin takofinsa ya tumke wani Jan kyalle da ta daure gashin kanta da shi, ya tsargeshi gida biyu ya fado kasa. Ita kuwa kwalar rigar da ke jikinsa ta yanke ta yanke tafadi kasa. Ita dai wannan rigar ta sarki Lubainu mai muguwar tsada domin ta zallar rigar Alhariri akayita gami da zaren danyen zinare, musamman yasa akaje birnin farisa aka dinkota. Koda sarki Lubainu yaga An lalata masa wannan Riga mai Daraja Sai ranshi ya baci Ainun. Itama jarumar dataga An yanke mata wannan Jan kyalle nata Sai tajuyo a fusace Ainun. Ashe wannan kyalle shine matsayinta na sarauniyar mafarauta a cikin gabilarsu. Cikin tsananin bakin zafin nama sarki Lubainu da wannan jarumar suka juyo a cikin fushi Sai suka juyo izuwa kan junansu suka ruguntsume da sabon masifeffen yaki yazamana cewa suna kaiwa junansu mugayen harehare. Nan fa karar haduwar takubbansu yacika dajin gaba daya, motsinsu da hare harensu ya haifar da tashin kura, kuma ya dugunzuma hankalin duk wani Abu dayake kusa. Domin hatta yaran sarki Lubainu Sai suka rinka ja da baya, wani lokacimma har buya sukeyi a bayan bishiyoyi kar tsautsayi ya hausu,Dan wata 'Yar karamar bishiya ma sarki Lubainu da jarumar Sara daya sukeyi mata ta fadi kasa,a lokacin da suke kaucewa harin junansu. Nanfa dajin gaba daya ya hautsine, tsuntsaye ma dake kan bishiyoyi babu shiri suka farayin yijira dole suna sauya sheka. Wannan tashin hankalin ne gami da karafkakiyar yakuba na sarki Lubainu da jarumar ne yakai izuwa kunnen 'yan uwan jarumar dake can gefe nesa kadan awani bangare a dajin, inda suke yada sansani. Adadin wadannan Ayari yakai na mutum dubu uku da sittin da biyu, kuma dukkajinsu suna karkashin wani mutum ne ma'abocin kwarjini da kamala gami da kira Da SADAUKANTAKA Amma girma yafara kamashi, domin ya haura shekara sittin a duniya, Ana kiransa da suna ZAHAR BIN AUDASI. Sadauki zahar shine mahaifin waccer yarinyar da take fafatawa da sarki Lubainu. Koda sadauki zahar yajuyo karar takuban 'yarsa saiya zabura yafito ya fito da sauri daga cikin tantinsa ya dubi gaba dayan dakarunsa wadanda suka kasance maza da mata, kuma dukkaninsu acikin shigar yaki suke irinta mafarauta yace, Ga Sarauniyarmu can tana gunurzu, kuzo muje mukai mata dauki tunda bamusan Adadin mutanen da take yaki dasuba, kunsani cewa 'yata daga nesa da sarki Lubainu yaga wannan gagarumar jarumtaka da jarumar tayi kuma ya kare mata kallo yaga irin tsananin kyawun da Allah yayi mata Sai yasake dimaucewa kuma nan take akaron farko a rayuwarsa yaji yakamu da tsananin son 'YA MACE!! Lokacin da wannan jarumar taga sarki Lubainu ya kura mata idanu kuma ta kare masa kallo taga yanayin shigarsa Sai tagane cewa mai mulki ne Dom haka Sai ta turbine fuska tacigaba da kallonsa kawai har ya iso daf da ita. Dazuwansa Sai ya dubeta a fusace ya daka mata tsawa yace, yake wannan bakuwar mafarauciya wacece ke har da zaki shigu jejin kasata kiyi farauta ba tare da izininaba? Ina sauran 'yan uwanki suke wadan sukamin mummunar barna haka kuka kwashe mana duk Amfanin cikin dazuzzukanmu?? Kisani cewa tunda na kamaki dolene Ku dawomana da dukkanin abunda kuka kwashe kokuma Ku biya da rayukanku tunda kun karya doka. Hatta wannan damisa da kika kashe yanzu dolene ki bani ita. Koda sarki Lubainu yazo nan a zancensa Sai kyakkyawar jarumar ta kyalkyale da dariya, lokaci guda kuma ta turbune fuskarta tace, Ai isace takesawa akarya dokar sarki! Munan daka gammu babu bangaren da bamuje ba a duniya munyi FARAUTA, Kuma kasa ko birni ko Alkaryar da muka zuwa muka nemi izinin wani Wanda mukashiga yankinsa"". Koda gama fadin haka Sai jarumar ta sunkuya tadau wannan damisar ta saba ta kafadarta taruga inda 'yan uwanta suke, kawai Sai sarki Lubainu ya daka tsalle sama dagakan dokinsa ya shallaketa, sarki Lubainu yana gana Ayyana hakan a ransa saiyaja da baya yadaina yakar jarumar kamar zaiyi saran da Amma saiya shammaci jarumar yaruga da gudu izuwa inda damisar take. Koda ganin haka Sai ita jarumar ta falfala da wannan azabebben gudu nata tabi bayansa, saigashi har tashi sama takeyi saboda tsananin gudun, Amma duk da hakan dakyar ta riski sarki Lubainu sukayi kafada da kafada, ahaka sukaci gaba da kaiwa junansu naushi domin akai daya kasa Amma abun yaki yiwuwa. Koda sukaga saura baifi taku biyarba su isa inda damisar take.Sai duk su biyun suka daka tsalle suka kaiwa damisar cafka da Hannu daya. Bisa rashin sa'a Sai sarki Lubainu ya damki wuyan damisar, ita kuma Sai ta cafko kafadar damisar. Koda kowannensu ya yaja iya karfinsa Sai damisar ta rabe gida biyu duk su biyun suka fadi rike da tsagin damisar. Kawai Sai yaran sarki Lubainu suka farayimusu tafi sakamakon ganin gagarumar jarumtakar da sukayi. A daidai wannan lokaci ne zugar su sadauki zahar ta karaso wajen a guje bisa dawakai sukayiwa su sarki Lubainu KAWANYA. Koda jarumar taga mahaifinta shima yaganta kwance a kas rike da tsagin damisa kuma Ga jini a hancinta da bakinta kuma yana diga Sai ya dubi dakarunsa yamusu inkiya. Take tadarun suka zaro kibiyoyi suka tana suka ta6e zasu sakarwa sarki Lubainu da yaransa harbi, Amma Sai jarumar tayi sauri yace ae ba'abokin gaba bane, wannan shine sarkin wannan birni da muke ciki"". Koda jin haka Sai sadauki zahar ya dubeta a fusace yace, idan ba abikin gaba ba to menene yasa ya yakeki harya lalata naman farautarki?"" Koda jin wannan tambaya Sai tayi murmushi tace, "' saboda munyi masa babbar barna mun kore duk dabbobi da tsuntsayen dake cikin dazuzzukan birninsa.. Yanada gaskia akan wannan Al'amari duk da cewa shi daji na Allah ne bana kowa ba..yakai Abbana abunda nakeso dakai shine, mu biya wannan sarki duk abunda ya bukata dangane da wannan barnan da muka masa, Amma ayau dinnan nakeso mubar yankin kasar nan tasa mu kara gaba. Banason muyi yaki da wannan sarkin domin shine jarumi na farko dana taba ganin iyada jarumtaka irin taka"".. Koda jin wannan batu Sai mamaki Yakama sadauki zahar da sauran jama'arsa. Shi kuwa sarki Lubainu Sai hankalinsa ya dugun Zuma Ainun bisa jin ayau su jarumar sukeson subar kasarsa Alhalin ayanzu ma jiyake kamar bazai iyayin rayuwa ba in baya ganin wannan kyakkyawar sura tata. Nan take sarki Lubainu yashiga tunanin dabarar da zaiyi ya hana wadannan mafarauta barin kasarsa. Ita kanta jarumar ta gano abinda ke cikin ran sarki Lubainu domin ta lura da irin kallon da yakeyimata run farkon haduwarsu kuma itama jarumtakarsa ya burgeta. To Amma Sai ta tambayi kanta a cikin zuciyarta tace, MEYASA WANNAN SARKI YA YAKENI DA DUKKANIN KARFINSA DA NUFIN YA HALLAKANI IDAN HAR WANNAN KALLO DAYAKE YININI NA KAUNANE? WATA KILA DARAJARSA DA KIMARSA AWAJEN YARANSA KOKUMA DOMIN YA JARRABI JARUMTAKARSA AKAN TAWA"".. Shi kuwa sadauki zahar Sai ya sake doban 'Yar tasa yace, yake SUHAILAT, Nawa ne adadin kudin da wannan sarki yakeso mu biyashi bisa wannan barna da mukayimasa? Koda jin wannan magana Sai jaruma suhailat ta dubi sarki Lubainu tace, Ai waka abakin mai ita tafi dadi, don haka Sai yayi mana bayani da bakinsa muji. Koda jin wannan batu Sai sarki Lubainu ya kara fadawa kogin tunani. Abu na farko dayayi shine,ya karewa wadannan mafarauta kallo domin yaga ya Arzikinsu saboda yasamusu kudi mai yawa wadda baza su iya biya ba. Amma Sai wata zuciyar tace dashi, Aisu kudi basuda kama, kuma bisbisa ganin yadda wadannan mutane sukeyin wannan gagarumar farauta, Akwai alamun zasu iya Tara makudan kudaden da ba'a zato"". Koda jaruma suhaikat taga sarki Lubainu yayi shiru Sai ta matso kusa da shi ta katsenmar tunani tace Malam kana bata mana lokaci mu mata fiyane ba mazauna ba! Bamu gaba zama akowane gariba sama da tsawon kwana bakwai ba Sai a wannan gari naka"". Koda jin wannan tambaya Sai sarki Lubainu yayi murmushi yace, Ai wannan babbar barns da kukayimin baza Ku iya biyanta da kudi ba domin ni mawadacine na kudi, harma sunyi mini yawan da babu abunda zanyi dasu. Idan kunaso Ku biyani saidai mu shirya wata Gasa ta jarumta tsakanin zakurkuran mayakanku mutum Ashirin da nawa, kuma kullum mutum biyu ne kacal zasuyi wannan gasar. Abunda ake bukata a gasar kawai shine, akai mutum kasa ba tare ta an illatashiba, idan jama'atane suka lashe wannan gasa to dole Ku zauna a birnina tsawon wadansu kwanaki Ashirin din kunayimin Aikin bauta a cikin gidan sarautata. Idan kuma kune muka lashe gasar a cikin kwana ashirin din to shikenan kun biyani barnar da kukayinin saikuyi tafiyarku"". Koda jin wannan batu Sai sadauki zahar da jaruma suhailat Sai suka dubi junansu kawai Sai sukayi shiru suna tunani. Suma jama'ar tasu Sai suka kama kus kus suna tattauna Al'amarin a cikin fargaba da damuwa. Muhadu gobe in Allah yakaimu muji yadda wannan Al'amari zai kasance ALLON SIHIRI Littafi na shida 6 Part G Koda ganin haka Sai sadauki zahar Yakama hanjun jaruma suhailat ya jata gefe daya ya dubeta yace, ni Abunda na lura dashi shine, wannan sarki bayason tafiyar mu kuma laifin da muka masa mashine a gabansaba kece matsalarsa. Ga dukkan Alamu yafada irin tarkon da sauran sarakai dayawa suka fada akanki"". Sa'adda jaruma suhailat taji wannan batu Sai tayi ajiyar zuciya cikin alamun damuwa tace, yakai Abbana indai hakane kuwa bamuda wani zabi Wanda yafi muyi wannan gasa, domin idanma mukace zamu gudu nida kai ne kadai zamu iya gudun da barlza acimmana ba, yazamuyi da sauran jama'armu zamu barsu ne akamasu Amatsayin bayi? Duk da cewar bamusan irin jarumtakar dakarunsaba dolene muma a bangarenmu muma mu ware namu jaruman wadanda muka yarda dasu kuma dole ne muma mushiga cikin gasar domin karawa namu jaruman karfin gwuiwa"". Koda jin wannan batu Sai sadauki zahar ya jinjina kai yace, "" tabbas bamuda wata mafita da tahuce wannan"". Koda gama fadin haka Sai sadauki zahar ya matsa kusa da sarki Lubainu yadubeshi yace, "" mun yadda zamuyi wannan gasa ta kwana Ashirin a birninka, Amma bisa shatadi guda!! Sharadin kuwa shine, cimmu da shammu da masaukinmu yana hannunka Atsawon wannan kwanaki dakuma tsaron lafiyarmu dakuma rayukanmu tunda mu munfi kwarewa rayuwar daji yanzu kuma kai kanaso muzauna a birninka tare da jama'arka. Idan rayuwar daya daga cikinmu ta tabu ko lafiyarsa to zaka biya diyya mai darajar gaske, shin ka Amince da wannan sharadin??"". Lokacin da sarki Lubainu yaji wannan batu Sai zuciyarsa takamu da farin ciki tayi fari kal, kawai Sai yadubi sadauki zahar yace, "" Nima na Amince da duk wannan sharadin naku "". Batare da wani bata lokaci ba sarki Lubainu da dakarunsa shida suka wuce gaba da dakarun su wannan tawagar su sadauki zahar suka rufa masa baya aka nufi cikin BIRNIN ISTAMBUL. Duk bayan kamar dakika goma Sai sarki Lubainu ya dubi jaruma suhailat. Koda taga kallon yayi yawa Sai ta dauko wani shudin rawani ta rufawa kanta yazamana cewa idanuntane kadai ake gani. Koda ganin haka Sai sadauki zahar ya bushe da dariya yace, dakyau 'yata kinyi maganin ido domin shi ido gubane! Ina mai shawartarki da kija ajinki awajen wannan sarki da dukkan jama'arsa, kuma ki kula da kanki don inatsaron wadannan mutane suyi wani Abu Wanda zai cutar da mu"", Koda jin wannan batu Sai jaruma suhailat tayi murmushi tace, " kwantar da hankalinka yakai Abbana, kayi sani Babu abunda zai samu dayanmu a wannan gari, lafiya lau zamu gama abummu acikinsu mutafi".. Lokacin da sarki Lubainu ya iso gidan sarautar akaganshi da wannan bakin mafarauta Sai aka cika da tsananin mamaki, Dafarko Sai dakarun suka taso danufin su tsare bakin masarautar domin su azatonsu kama sarkinsu Akayi, Amma Sai sarki ya musu inkiya suka koma suka tsaitsaya a inda suke. Nana take aka bude kofar masarautan take suka kunnakai ciki. Da zuwansu Sai akaga sarki Lubainu duk ya rude yanata haba haba da wadannan bakin mafarauta, domin da kansa yayi musu jagora izuwa masaukinsu, kuma masauki mai Daraja yakaisu inda ba'a saukar kananan mutane, daga manyan sarakai Sai shahararrun Attajirai. Nan take sarki Lubainu yabada umarnin Ashiryawa bakinsa abinci mai Daraja. Nana da nan kuwa akacika babban falon da aka kaisu da kayan ciye ciye da shaye shaye iri iri birjik! Wadanda ma sunyi musu yawa, baza su iya karar da su ba, duk da cewa adadinsu yahaura dubu uku. Dakin barcin da aka baiwa jaruma suhailat kuwa, koda matar sarki ce iya abunda za'a shirya mata Keenan acikin dakin, Dakin yana hade da makewayi acikinsa. Shikansa makewayin katone kuma bahon wankansama na zallan lu'u lu'u ne. Gadon da ke dakin kuwa Lumsheshene mai tarin shimfidu masu taushin gaske. Abinka da wadanda basusan komai ba Sai rayuwar daji, kuma basu da dakujan kwana Sai bukkoki da kogunan duwatsu da tanti, duk Sai suka zama cikakkun 'YAN KAUYE, don haka Sai suka kasa Amfani da kayan kyale kyalen cikin dakinnasu dole aka kawo kuyangi suka koyar dasu. Bayan jaruma suhailat taci abinci ta koshi Sai kuyangi uku su ka kamata suka shigar da ita kewaye domin suyi mata wanka. Koda suka kwabe mata kayan jikinta suka yi mata tum6ur! Sai suka rude suka dimauce sakamakon kyawun da dirin da Allah yabata dakuma kyawun da Allah yayiwa fatar jikinta dakuma laushi, domin ko a TARIHI basu tabajin An wassafa mace mai irin kyawun jikintaba. Hakadai kuyangin suka shigar da jaruma suhailat cikin bahon wankan suka shiga yi mata wanka hannunsu na kyarma, jikinsu nata makyarkyata saboda tsananin Al'ajabi. Bayan Angama yiwa jaruma suhailat wankan aka shafeta da mai dakuma turare Sai aka je Aka kwantar da ita bisa wannan lumsheshshen gadon. Koda taji laushin gadon kuma ta duba kayan kawan dake cikin dakin Sai fuskarta ta fadada da murmushi da Annuri gami da kurawa rufin dakin idanu tana mai cewa acikin ranta. WAI SHIN YAUSHENE NIDA MAHAIFINA DA JAMA'ARMU ZAMUSAMU NUTSUWA DA DAULA IRIN WANNAN? A IYA RAYUWAR DA NA TASO NA RAYU ACIKIN DAJI, YAKA MATA ACE YANZU NE ZAN HUTA NASAMU MIJIN DA ZAN AURA UBAN 'YA'YANA. BANIDA BURIN DAYAWUCE IDAN NAYI AURE NASAMU DA KO 'YA WACCE ZATA GADONI A JARUMTAKA DA KYAU, KUMA TACI GABA DA SHUGABANTAR KABILARMU!"" Koda jaruma suhailat tazo nan a zancen zucinta Sai hawaye ya zubo mata, saboda bataga ranar da wannan buri nata zaizo ba saboda amatsayinta na shugabar kabilarsu kafin abaya tashugabancin saida tayi rantsuwa akan har abada bazata taba nisantar jama'arsuba kuma zata ci gaba da shugabantarsu izuwa tafiye tafiye donyin farauta akowane bangare na duniya har izuwa karshen rayuwarta.haka Sai suhailat taci gaba dayin wannan tunani har bacci yasaceta bata sani ba. AL'AMARIN Sarki Lubainu kuwa, tunda yaga Anbaiwa su suhailat masauki da abinci mai kyau Sai yatafi izuwa turakarsa cikin tsananin farinciki. A wannan ranadai saida gaba dayan fadawansa da hafiman gidan sarautar sukasan cewa lallai yana cikin farinciki, domin saida halayensa suka sauya nan take, Kawai Sai Yakama yiwa mutane kyauta taban mamaki da bazato, sannan ya 'yanta bayi tamkar yasamu waraka daga lalurar da ta addabi rayuwarsa. Kai awannan ranadai sarki Lubainu kasa bacci yayi domin duk sa'inda ya runtse idanunsa domin yayi baccin saidai yaga fuskar jaruma suhailat na yi nasa murmushi. Atakaice Sai yadda sarki Lubainu yaga rana haka yaga dare a wannan ranar. Ita kuwa jaruma suhailat baccinta tayi ta more hadda munshari. Koda ta farka da safe saitaji zuciyarta na faman bugawa alamar cewa Akwai wani Abu dake shirin faruwa marar dadi agareta kokuma Ga jama'arta. Koda gama aiyana hakan acikin zuciyarta Sai hankalinta ya zugunzuma ainun. Bisa wannan daliline ta dauko madubin tsafinta ta shafashi da hannun hagu tashiga bincike. Nan take taga duk abunda yafaru Ga sarki Lubainu agaba dayan rayuwarsa da matsalar da ta Addabi rayuwar harda baccin da yakasayi sakamokon kamuwa da sonta da begenta. Koda ganin wannan Abu Sai nan take taji takamu da tsananin tausayin sarki Lubainu akaron farko dataji sonsa yadan digu cikin zuciyarta. Jaruma suhailat taci gaba da bincike akan rayuwarta da sarki Lubainu, Aikuwa Sai taga wani babban abin tashin hankali Wanda indai tana Raye da sarki Lubainu Sai ya faru. Ba komai ne wadannan abunba face mugayen yake yake Wanda za'ayi miliyoyin rayuka da dukiya dakuma tsananin wahala ta gaban kwatance. Koda ganin haka Sai jaruma suhailat ta Aiyana aranta cewa bazata taba baiwa sarki Lubainu fuskar da zasuyi soyayya ba. Abunda zatayi kokarin yi shine, ta tabbatar da cewa itada jarumansu sun sami nasara acikin wannan gasa da sarki Lubainu ya shirya. Bayan jaruma suhailat ta gama yanke wannan hukunci ne Sai ta mike da sauri taje tayi wanka da kanta domin wannan karon kuyangin basuzoba tunda sun koya mata yadda akeyin wankan. Koda tafito daga kewayenta tashiga dakin barcin domin tasanya tufafinta na fita farauta Sai tayi Arba da wasu tufafi masu kyawun gaske irin nasu na mata visa kan gadon nata wata kuyangan sarki na tsaye agefe daya. Koda kuyangar taga jaruma suhailat tashigo dakin saita zube kasa gabanta tayi gaisuwa sannan ta dago kanta ta dubeta tace, ya shugabata sarki ne ya turoni nasa miki wannan tufafi saboda ya gaiyaceku izuwa fadarsa keda mahaifinki, koma Akwai manyan bakin sarakuna da sukazo halattan wani biki da akasabayi a wannan gari namu arana irinta yau"". Koda jin wannan batu Sai jaruma tadubi wannan kuyanga da'alamun mamaki tace, Wane irin biki ne wannan haka?" Kuyangar tace, gasa ne na Raye Raye da kade kade gami da wake wake. Wanda duk yalashe gasar sarakuna nabashi kyaututtuka wani ma Sai yasamu sarkin dazai bashi kwangila ta daukemasa kewa har izuwa karshen rayuwarsa yana biyanshi Albashi mai tsoka." Koda jin wannan batu Sai suhailat takamu da murna saboda a rayuwarta tanson kallon abubuwan nishadi irin haka. Batare da wata matsalaba ta Amince akasanya mata wannan Riga mai Daraja akayimata kwalliya ta gani afada. Koda kuyangar takaita gaban madubi suka tsaya takalli kanta Sai tacika da tsananin mamaki, da farko razana tadanyi taja da baga don zato tayi wata Al'jana ce me kamarta a jikin madubin. Saida ta shafa hannunta ajikin madubin sannan ta tabbatar hotonta ne ajikin madubin ba Al'jana ba. Cikin murmushi suhailat tadubi kuyangar tace, "Kaini masaukin mahaifina", Nan take kuyangar tahuce gaba jaruma suhailat na biye da ita. MUHADU A LITTAFI NA GABA WATO NA BAKWAI (7) DON JIN CIGABAN WANNAN KAYATACCEN KASAITACCEN LABARI. DAGA MAI DEBE MUKE KEWA A KULLUM A KO YAUSHE. KING OF ADVENTURE STORY. ABDUL'AZEZ SANI MADAKIN GINI. NI NAKU HAR KULLUM KHAMIS IDRIS MUHAMMAD NAKE CEWA MUGANA A GABA NAN BADA JIMAWABA INSHA ALLAH Compilied By Abubakar Saleh AlQuyraemey Whatsapp Number 08138873799 Visit www.rumbunlabarai.com For More Complete Documents