ALLON - SIHIRI Littafi na Biyar (5) Part A Ku ziyarci Shafin www.rumbunlabarai.com domin samun littattafai masu daɗi da debe kewa __LOKACIN DA Yarima Mangul da Barde Ruhaisu suka ruguntsume da azabbaben yaki mai tsananin muni,sai wani abin mamaki ya afku domin kuwa gashi a zahiri Yarima Mangul yafi barde Ruhaisu karfin damtse da iya yaki,domin da kyar ma barde Ruhaisun ke iya kare saransa saboda nauyin saran,amma da yake Barde Ruhaisu nada matukar zafin nama gami da juriya da mugun naci sai Yarima Mangul ya kasa cutar dashi.Saida suka shafe sa'a guda cur suna wannan mugun artabu amma dayansu bai sami nasarar koda lakutar jikin dayan ba.Al'amarin daya fusata su kenan kowa yaja da baya suka tsaya suna kallon kallo suna haki kamar zakaru.Koda Yarima Mangul ya karewa Barde Ruhaisu kallo ya fahimci cewar ba sa'ansa bane a kallah Barde Ruhaisu zai iya girmarsa da tazarar shekaru kusan goma sai takaici ya kamashi yaga cewa ai yakamata yayi ace tuni ya gama da wannan JARUMI tunda yafishi kuruciya,idan kuwa kafi mutum kuruciya zaka iya finsa kuzari,saidai kawai ya nuna maka tsohon kashi.Gama aiyana hakan keda wuya sai Yarima Mangul ya daga hannunsa sama yana mai baiwa dakarunsa inkiyar su afkawa su barde Ruhaisu.Ai kuwa shima Barde Ruhaisu sai ya baiwa nasa dakarun umarnin su taresu.Nan fa kowacce RUNDUNA ta ruga da rugu izuwa kan dayar ana haduwa a tsakiya aka ruguntsume da azababben yaki.Karar karafa gami da ihun mazaje ya cika dajin gaba daya.Jini ya rinka fallatsi da fantsama sai gashi al'amarin ya rinciba a tsakanin dakaru dubu da guda dari.Kodaga nesa ne mutum ya zuba ido yana ganin abinda ke faruwa bazai iya gane bangaren mutum zai zuba ido da kyai a cikin lura zai gane cewa anfi ragargazar dakarun Yarima Mangul.Lokacin da aka fara wannan gumurzun ne Yarima Mangul ya sami damar matsawa kusa da inda Yazarina ke tsugunne saboda duk Badakaren Barde Ruhaisu da yazo gabansa kwaf daya yakeyi masa.A lokacin Barde Ruhaisu ya shiga cikin tsakiyar dakarun Yarima Mangul yana ta ragargazarsu yana yi musu sarki ya hana dawa tsayuwa.Hakan ne yasa ya sha'afa ya bar daidai wajen da Yazarina ke tsaye.A wannan lokaci da yakin yai tsamari ne Yazarina ta dimauce kuma ta firgice saboda wannan ne karon farko a rayuwarta da akayi yaki a gabanta.Koda taga an sare wani Badakaren ya fado a gabanta jininsa yai feshi akan fuskarta bata san sa'adda ta kurma uban ihu ba ta daka tsalle sama.Faruwar hakan keda wuya sai rawanin fuskarta ya subuce ya fadi kasa.Kyakkyawan dogon gashin kanta ya tarwatse a sama ya zubo kasan kafadunta.Koda Yarima Mangul yayi arba da fuskar Yazarina yaga itace sai ya kamu da tsananin mamaki ya daka tsalle sama ya dira a bayanta yasa takobinsa a wuyanta ya ritsata kuma ya daka tsawa.Take aka daina yakin kowa ya juya ya dubeshi.Take aka daina yakin kowa ya juya ya dubeshi.A sannan ne Barde Ruhaisu ya hango abindake faruwa sai hankalinsa ya dugunzuma ainun.Yarima Mangul ya bushe da dariyar farinciki a lokacin daya dora yankakken hannunsa akan kafadar Yazarina ya sumbaci wuyanta yace,marhaban da ganinki ya abar kaunata.Tabbas nayi matukar farin cikin sake saduwa dake a wannan lokaci da ban taba zata ba.A tsammani sai na karbi karagar mulkin ubana sannan zan sami damar sake ganinki na kashe mijinki Lubainu koda yana raye domin na mallakeki amma sai gashi yanzu na sameki a banza ba tare da wata matsala ba.Ki sani cewa yanzu ina gama kashe wadannan abokan tafiya naki zan tafi dake can sansani na a daura mana aure bisa dole..Kafin Yarima Mangul ya gama rufe bakinsa tuni Yazarina ta tofa masa yawu a fuska sannan tace karyarka tasha karya saidai ka auri gawata amma bani ba.Yaza'a yi na auri azzalumin daya lalata rayuwar wani saboda son zuciyarsa?Ka sani cewa ni yanzu bana tsoron mutuwa tunda kasa mijina ya tafi izuwa inda zai iya rasa rayuwarsa gaba daya.Idan kuwa har Lubainu ya mutu to nima banga amfanin tawa rayuwar ba saidai na bishi.Koda Yazarina tazo nan a zancenta a lokacin da jikin su Barde Ruhaisu duk yayi sanyi sun sauke makamansu kawai suna kallon abin da ke faruwa tsakanin Yarima Mangul da Yazarina cikin alamun tsananin tsoro da fargaba.Har izuwa wannan lokaci Yarima Mangul bai cire kaifin takobinsa daga kan wuyan Yazarina ba don haka sai ya sake bushewa da dariya,kuma yayi amfani da dan yatsansa guda daya ya lakuci yawun bakin Yazarina data tofa masa akan fuskarsa ya lashe a bakinsa yace,ban taba jin abu mai zakin yawun bakinki ba yake MASOYIYATA.Yana gama fadin hakan sai ya dubi Barde Ruhaisu ya daka masa tsawa yace maza ku bude fuskokinku kaida yaranka kuma ku zubar da makamanku ko yanzu nan na shaftare makogwaron yazarina.Har su Barde Ruhaisu zasubi wannan umarni sai Yazarina ta daka musu tsawa tace,kada ku yarda ku aikata hakan domin bazai kasheni ba saboda bashi da burin dayafi ya mallakeni a rayuwarsa.So yaje kawai ya yaudareku ku zubar da makamanku yasa a kasheku a banza.Koda ma ya kasheni din bani da asara ko nadama,domin babban bakin cikina shine ya mallakeni din.Ku ci gaba da yaki har sai idan karfinku ya kare,domin ku zamto masubin umarnin sarki.Zaku iya bude fuskokinku domin ko baku bude ba su ba yanzu yasan cewa ku dakarun sarki Sailur ne.Koda Yazarina tazo nan a jawabinta sai Barde Ruhaisu da dukkan sauran yaransa kimanin mutum saba'in suka bude fuskokinsu kuma suka daga takubbansu sama suna masu niyyar cigaba da yaki.Koda Yarima Mangul yayi arba da fuskar Barde Ruhaisu sai ya jinjin kai yace,tabbas babu mamaki domin banda sarki yakin garinku da Yarima Lubainu babu wanda zai iya tarata muyi GUMURZU na tsawon wannan lokaci ba tare dana sami nasarar hallakashi ba face kai.Ai kuwa dayanmu bazai bar wannan wuri ba a raye saidai a dauki gawarsa!Yarima Mangul na gama fadin hakan sai ya wurga Yazarina izuwa hannun sarkin yakinsa ya cafketa ya dubeshi yace,mazaka ka tafi da ita izuwa sansaninmu a tsareta kuma ka dawo nan tare da dakari dubu goma.Koda jin wannan batu sai Barde Ruhaisu ya falfalo da azababben gudu izuwa inda Yazarina take ya kutsa ta tsakiyar dakarun Yarima Mangul yana karkadesu da karfin sara da suka domin ya isa inda sarkin yakin Yarima Mangul yake a lokacin daya ja Yazarina da karfin tsiya izuwa kan wani doki.Koda ganin haka sai shima Yarima Mangul ya falfalo da gudun tsiya da nufin yasha gaban Barde Ruhaisu ya hanashi isa inda su Yazarina suke.Koda ya rage saura baifi taku goma ba tsakanin Barde Ruhaisu da Yarima Mangul sai Ruhaisu ya daka wawan tsalle a sama ya tsallake Yarima Mangul ya doki gadon bayan sarkin yakin nasa.Ba shiri sarkin yakin ya saki Yazarina ya fadi can gefe daya.Kafin Yarima Mangul ya juyo baya da gudu yazo ya riskesu tuni Barde Ruhaisu ya daka tsalle sama ya haye dokin dake gabansa.Kawai sai ya mikawa Yazarina hannunsa ta kama ya dagota sama cak ya dorata a bayan dokin kuma ya zaburi dokin da gudu izuwa cikin daji.Koda ganin haka sai shima Yarima Mangul ya ruga izuwa inda nasa dokin yake ya daneshi kuma ya zabureshi da gudu yana mai bin bayan dokin su Ruhaisu.Nanfa filin yakin ya watse kowacce runduna hankalinta ya tafi izuwa tafiya neman shugabanta tamkar ma an manta mummunan yaki da ake fafatawa.Lokacin da Barde Ruhaisu ya sami nasarar gudu da Yazarina akan doki suna tsala gudu a cikin daji ba tare da sanin inda suka dosa ba sai suka jiyo sukuwar doki a bayansa.Cikin firgici Yazarina ta waigo baya kawai sai taga ashe Yarima Mangul ne ya biyosu kuma tazarar dake tsakaninsu bata wuce taku ashirin da biyar ba,kuma dokin nasa gudun bala'i yake yi yana rike da linzaminsa da lafiyayyen hannin nasa sai dada zungurar dokin yake da kafafunsa yana kara masa kaimi ga zabgegiyar takobinsa rataye a bayansa.Cikin tsananin firgici Yazarina ta juya tace,yakai Ruhaisu kayi sani cewa wannan azzalumin makiyi makiyin namu yana daf da riskarmu.Koda jin haka sai shima Barde Ruhaisu ya karawa nasa dokin kaimi.Nanfa dawakan suka cigaba da kasa mugun gudu,tseren gudu na ban al'ajabi.Koda karfin gudun dokin Ruhaisu ya karu sai Yazarina taji tana neman fadowa kasa don haka ba shiri tasa hannayenta biyu a zagayen cikin barde Ruhaisu ta rukeshi gam gam da kyau ta kwantar da kanta akan gadon bayansa.Haka dai aka cigaba da wannan tseren gudu na tashin hankali har izuwa tsawon sa'a guda.Kwatsam sai dokin Barde Ruhaisu dana Yarima Mangul din suka iso wani wuri mai tudu wanda basu ankara dashi sukayi tuntube suka zube kasa gaba dayansu har su Barde Ruhaisu.Cikin gaggawa Barde Ruhaisu ya mike tsaye zumbur ya kama hannun Yazarina ya tasheta tsaye suka sake ruguntsumawa da gudu izuwa cikin daji.Shima Yarima Mangul a dimauce ya mike tsayen da sauri yabi su a guje suka kasa sabon tseren gudu kafafunsu tamkar zasu tashi sama saboda karfin gudu.Faruwar hakan keda wuya sai Yazarina ta sare ta fadi kasa kuma a lokacin tazarar dake tsakaninsu da Yarima Mangul bata wuce taku ashirin ba.Koda Yarima Mangul yaga Yazarina ta fadi kuma gashi babu makami a jikin Barde Ruhaisu sai yayi wuf ya zaro sharbebiyar takobinsa yayi kansu da nufin ya riskesu kafin Barde Ruhaisu ya tasheta tsaye ya sare masa kai.Amma sai yaga Barde Ruhaisu yayi wuf cikin wani bakin zafin nama da bajinta ya suri Yazarina tamkar sillan karah ya daga ya goyata a bayansa.Ita kuma ta rukunkumeshi ya cigaba da falfala azababben gudu.Sai gashi sun ci gaba da tseren gudun nasu tamkar mai kaya ya biyo barawo.Yarima Mangul ya dage iya karfinsa domin ya cimmusu amma sai abu ya gagara.Al'amarin daya daurewa Yarima Mangul kai kenan ya cika da tsananin mamakin yadda akayi ya kasa cimma Barde Ruhaisu duk da cewa yana fama da nauyin Yazarina wacce ke goye a bayansa.Barde Ruhaisu na cikin wannan gudu ne ya riski wani katon tsauni mai fadi,girma da tsawon tsiya a gabansa,kuma babu wata hanya da zai iya ratsewa tsaunin dole ne yabi ta kansa in ba haka ba kuwa saida ya tsaya ya jira isowar Yarima Mangul ayi wacce za'ayi.Ta yaya zan fuskanci Yarima Mangul alhalin babu makami a hannuna?Tabbas bani da wani zabi wanda yafi na hau kan wannan tsauni.Ya bawa kansa amsa a cikin zuciyarsa.Yaba gama aiyana hakan sai ya hau kan tsaunin goye da Yazarina a bayansa yana cigaba da gudun.Shima Yarima Mangul yana isowa bai tsaya jiran komai ba sai yabi shi izuwa kan tsaunin a guje yana ruri da kururuwa mai ban tsoro,cikin murna domin gani yake kamar ma ya gama samun nasarar kashe Barde Ruhaisu gami da mallakar Yazarina.Nanfa duka cigaba da gudu akan tsaunin tun sunayi da karfinsu da guzarinsu har saida suka sare suka fara faduwa kasa suna mikewa da kyar suna haki.Saida suka shafe sa'a daya da rabi suna gudu gudu,tafiya tafiya akan tsaunin sannan suka iso can kokoluwar karshensa.Koda Yazarina Da Barde Ruhaisu suka leko kasan tsaunin wanda saboda tsananin nisan zurfinsa mutum baya iya hangi abinda ke xan kasan nasa sai hankalinsa ya dugunzuma ainun,a lokacin da suke ta fama haki saboda tsananin gajiya tamkar ransu zai fita.A daidai wannan lokaci ne shima Yarima Mangul ya iso kusa dasu da kyar yana haki da layi rike da takobinsa.Koda yaga cewa ai sun iso karsshen tsaunin sai ta dubesu ya bushe da dariyar farin ciki duk da cewa makogwaronsa a bushe yake saboda muguwar kishirwa gashi babu ruwa a kusa.Suma su Yazarina haka suke jin tsananin kishirwa tamkar zata kashesu domin yawun bakinsu ma daukewa yake kamar babu shi.Yarima Mangul ya gyara tsayuwarsa irin ta wadanda suka sami nasara ya dora zabgegiyar takobin tasa kan kafadarsa ya dubesu cikin izaa yace,yanzu kuma ta yaya zaku iya guje mini tunda gashi kunzo makura?Tabbas yanzu zan kasheka yakai Barde Ruhaisu,amma fa ka burgeni domin kayi jarumtakar da ban taba zaton kana da ita ba,kuma dole ne na rubutaka a cikin KUNDIN TARIHIN rayuwata,saidai kash,jarumtakarka taka ta zama ta banza tunda baka cika aikin sarki Sailur ya baka na kare Yazarina kuma gashi zaka mutu a banza.Koda Yarima Mangul yazo yazo nan a zancensa sai Barde Ruhaisu ya tari numfashinsa yace,kaicinka yakai wannan azzalumin dan sarki wanda rayuwarsa ta gama tarwatsewa.Ka tuna cewa ka rasa masoyiyarka yazarina kuma ka rasa abokinka amininka YARIMA LUBAINU,Kuma ka cutar dashi bisa son zuciyarka don kawai ka rabashi da wacce ya riga ka SO da KAUNA kun zama ABOKAN GABA!Yanzu gashi ka rabu da mahaifinka ka rabu da matsayinka na Yarima tunda Mahaifin ya zama abokin gabarka,kana hada runduna ta YAN TAWAYE domin kaje ka kashe shi,kaga kenan kai yanzu abin tausayi ne tunda baka ga tsuntsu ba bakaga tarko ba.Baka da komai bakada kowa sai mafarkin zuciya wanda ina tabbatar maka da cewa har abanda ba zai taba tabbata gaskiya ba.Da wannan furuci nake yi maka bankwana domin ko zaka sami nasarar mallakar Yazarina saidai ka mallaki gawarta.Nima saidai ka tusa gawata amma ba dai ka kasheni da hannunka ba!!!Barde Ruhaisu na gama fadin haka sai ya juya da sauri ya daka tsalle ya fado kasan wannan tsauni mai zurfi shi da Yazarina suka kurma ihu saboda sun san cewa mutuwarsu ce tazo. Just now · PublicALLON-SIHIRI Littafi na Biyar (5) Part B Suka kurma ihu saboda sun san cewa mutuwarsu tazo.Shi kuwa Yarima Mangul sai bakin ciki ya turnukeshi ya durkuse kasa bisa guiwoyinsa sannan ya wangame baki shima ya kwarara uban ihu kuma ya fashe da matsanancin kuka saboda yasan cewa shike nan har abada bazai sake ganin Yazarina a raye ba.Kafin Yazarina da Barde Ruhaisu su kai rabin nisan tsaunin tuni sun sume saboda karfin iskar dake kadasu da kuma jirin daya kwashesu don haka sa'adda suka iso can karshen tsaunin sun zama tamkar gawarwaki sai ji kake tunjum...!sun fado cikin kogi.Lokaci guda suka nutse kasa amma sai suka taso sama igiyar ruwa ta rinka kadasu cikin tsananin sa'a da rabon sauran rayuwa ta kaisu can gefe kogin ta watsar.Saida suka shafe kusan rabin sa'aa kwance a gefen kogin a sume basu farfado ba,iska mai sanyi ce ta rinka kadawa a wajen ta yadda utace ta zamo sanadin farfadowarsu daga dogon suman da sukayi.Koda suka bude idanunsu suka kalli juna suka tabbatar da cewa suna raye basu mutu ba sai suka kamu da tsananin mamaki suka kama kyalkyala dariya.Saboda tsananin farin ciki Yazarina batasan lokacin data rungume Barde Ruhaisu ba.Faruwar hakan keda wuya ta tuna cewa ita fa matar Yarima Lubainu ce,kawai sai tayi saurin janye jikinta daga cikin na Barde Ruhaisu ta sunkui da kanta kasa ta budi baki cikin rawar murya da kunya tace ka gafarceni.Take shima Barde Ruhaisu yaji kunya ta lullubeshi yama rasa abinda zaice da ita.Kawai saiya juya mata baya ya fada kogin tunanin abubuwan da suka faru a baya tsakaninta dashi yana mamakin al'amarin da ya kasance hakan.Wannan shine abinda ya faru tsakanin Barde Ruhaisu Da Yazarina a lokacin da suka baro Birnin Zamrul domin neman Yarima Lubainu. 쇼쇼쇼 쇼쇼쇼 쇼쇼쇼 AL'AMARIN SU Bakon Jarumi kuwa lafiya sumul suka kwana a cikin fadar Boka Darbusa kuma dukkaninsu suka wayi gari cikin koshin lafiya ba tare da fuskantar wata matsala ba.Da sassafe bakon jarumi da bawansa Dazyan suka shiga daji suka farauto wani katon tsuntsu suka zo suka fisgeshi sannan suka gasashi.Da naman wannan tsuntsun kowa yayi kalaci.Bayan an gama kalacin ne bakon jarumi ya dubi Dazyan yayi masa inkiya shi kuwa sai ya dubi Sarauniya Akisatul Sauwara,Yarima Lubainu da Sarki Darmanu yace,yaku abokan tafiya,maigidana yace na gaya muku cewa zamu cigaba da tafiya gaba dayanmu izuwa kogin BAHAR IMFALkamar yadda akayi alkawari da farko domin ya nuna muku karfi da iko na ubangijin musulunci amma badon ya yarda da tsafinku ba.Zai baku dama ku tsirar da rayuwarku da karfin ababan bautarku da karfin sihirigami da karfin damtsen ku har sai yaga kun kasa kare kan naku sannan zai taimakeku da taimakon ubangijinsa.Yace na dada jaddada muku cewa idan fa har aka isa can kogon Bahar Imfal aka samo abinda akaje nema da taimakonsa to dole ne ku karbi addininsa ko kuna so ko bakwa so,in ba haka na kuwa zaku zamo abokan gabarsa babu abinda zai rabaku face yaki!Daga yanzu zai ci gaba da ajiye ALLON SIHIRI a wajensa har izuwa wannan lokaci don haka tun yanzu kuna da sauran damar da zakuyi shawara bisa abinda kuke ganin cewa shine zai fissheku.Koda Dazyan yazo nan a zancensa sai su Yarima Lubainu suka dubi junansu suka rasa abinda zasu ce kawai sai Yarima Lubainu yajasu gefe daya ya dubesu cikin nutsuwa yace,abinda nake so daku shine,kada dayanku ya bigire sharadin wannan bakon jarumi domin yanzu a hannunsa muke sai yadda yayi damu,idan muka ce zamuyi masa tawaye dayanmu bazai tsira da rayuwarsa ba bare ya cika burin rayuwarsa.Ko kuwa akwai mai korafi a cikinku akan wannan shawara dana kawo? Koda jin wannan batu sai Sarauniya Akisatul Sauwara da sarki Darmanu suka budi baki a lokaci guda sukace bamu da wani korafi face bin sharadinsa.Dajin haka sai farin ciki ya lullube Yarima Lubainu yaja su suka koma wajen bakon jarumi ya sanar dashi cewa sun amince da dukkan sharadinsa kuma basu da wani korafi.Da jin haka sai bakon jarumi ya mike tsaye ya dubi Dazyan yayi masa zancen kurame shi kuma ya dubi su Yarima Lubaiun yace,shugabana yace kowa ya debo kayansa zamu cigaba da tafiya yanzu.Dajin haka sai kowa ya ruga izuwa cikin fadar Boka Darbusa ya dauko jakar guzurinsa ya dora akan dokinsa kuma ya hau kan dokin nasa ya zauna.Saida kowa ya gama kimtsawa sannan bakon jarumi ya hau nasa dokin ya wuce gaba,Dazyan ya jere dashi.Sarauniya Akisatul Sauwara ce ke biye dasu sannan Yarima Lubainu,Sarki Darmani ne na karshe.A wannan lokaci bakon jarumi ya lullube ALLON SIHIRI a cikin wani babban mayafi ya dora akan wuyan dokinsa ya daureshi tamau.Ana fara yin wannan tafiya ne sarauniya Akisatul Sauwara ta waigo ta dubi Yarima Lubainu sai taga ya sunkui da kansa kasa yana tunani mai zurfi.Koda ganinsa a wannan hali sai ta tsayar da dokinta har saida taga ya iso daf da ita sannan suka cigaba da tafiya a tare a jere,a sannan ne ta dubeshi cikin alamin tausayawa tace,yakai Yarima menene yake damunka ne?Tun jiya na lura da kai baka yin magana sosai,kuma baka cin abinci kamar yadda ka saba,sannan ko yaushe sai naga kayi shiru kana tunani mai zurfi ina dalilin hakan? Koda Yarima Lubainu yaji wannan tambaya daga bakin sarauniya Akisatul Sauwara sai ya kawo gwauron numfashi ya ajiye sannan ya dubeta yace,yake wannan sarauniya mai daraja,kiyi sani cewa tun jiya ne naji zuciyata tana yawa bugawa da karfi haka kawai ba tare da nasan dalili na,sannan kuma a daren jiyan nayi wani mafarki mai ban tsoro.A cikin mafarkin an nuna mini katon bakin kumurcin maciji yana bin inuwata da gudu a cikin daji har inuwar rawa tana yin tuntube tana faduwa amma a karshe sai inuwar tawa ta yanke jiki ta fadi kasa ta kasa cigaba da gudu har macijin yazo daf da ita ya fasa kai.Yana shirn saranta ne na farka daga barci a cikin daren naji jikina na kyarma saboda firgita danayi kuma gaba daya jikina a sannan ya jike sharkaf da gumi tamkar abinda na gami a mafarki ya faru ne a gaske.Lokacin da Yarima Lubainu yazo nan a zancensa sai Sarauniya Akisatul Sauwara tayi ajiyar zuciya sannan tace,indazaka tuntubi bakon jarumi akan wannan mafarki naka da zai iya gaya maka fassararsa.Koda jin haka sai mamaki ya kama Yarima Lubainu yace yaya akayi kika san cewa ya iya fassara mafarki alhalin bashi da bakin yin magana?Akisatul Sauwara tayi murmushi tace,ji nayi wancan bawan nasa dan wada Dazyan ya bashi labarin wani mafarki dayayi shi kuma ua fassara masa mafarkin a cikin yaren kurame,al'amarin daya bani sha'awa kenan na tambayi Dazyan nace yakai Dazyan naji kana gayawa shugabanka cewa kayi mafarkin wata kaza wacce tayi kwaikwaye biyu kala daban daban.Kwan farko data sako FARI ne fat na biyu kuma JA ne,kawai sai tayi kwanci akan farin ta kyankyashe UNGULU da kuma tayi kwanci akan jan saita kyankyashe ZABUWA.To waishin menene fassarar dayayi maka akan wannan mafarki naka? Lokacin da Dazyan yaji wannan tambata dana yi masa sai yace,fassarar da maigidana yayi mini itace,Allah ne yakeyi mini nuni dana nutsu nayi hankali da duniya.Wannan kasa itace duniya,kwan farko ya kasance FARI shine hali nagari idan mutum ya rikeshi zuciyarsa zata zama fara mara mugunta da kyakkyawan nufi.Kwai na biyu data kyankyashe wanda shine JA alama ce ta mugun hali.Ai bakaji karshen mafarkin nawa ba saboda a cikin yaren kurame na karasa bashi labari.Cigaban labarin kuwa shine,bayan kazar ta kyankyashe kwaikwayen biyu sai unguku taka jewa.Koda tazo giftawa ta gaban zabuwar sai zabuwar ta cafko kanta ta gutsure mata kai,kuma ta hau bayanta ta zauna.Wannan alama ce ta cewar mutane a yanzu sunayin UNGULU da KAN ZABO!Ma'ana idan sukaga yan'uwansu masu kyawawan halaye sai su jasu a jiki kamar suna koyi dasu,amma a karshe sai suyi amfani da wannan dama su turmushesu su hallakasu.Sa'adda maigidana yazo nan a jawabinsa saina dubeshi cikin alamun mamaki nace,to yanzu menene matakin daya kamata na dauka don kada irin haka ta sameni?Maigidana sai yace,kayi gaskiya,amana da rikon alkawari.Idan kayi hakan Allah zai kareka daga sharrin dukkan mai son cutar dakai.Koda Sarauniya Akisatul Sauwara yazo nan a jawabinta sai Yarima Lubainu yaji gaba dayan tsigar jikinsa ta tashi,take yaji a cikin ransa cewa lallai akwai alamun gaskiya a cikin wannan addina na bakon Jarumi saboda jin irn wannan hikima da aka zuba a cikin mafarkin dan wada Dazyan.Kawai sai Yarima Lubainu ya dubi Sarauniya Akisatul Sauwara yace,ai kuwa duk sa'adda muka yada zango zanje na sami bako jarumi na sanar dashi nawa mafarkin don naji irin fassarar da zaiyi.Waishin ke bakiji wani abu a ranki ba ko a jikinki sakamakon labarin wannan mafarki mai dauke da dumbin hikima da basira.Sarauniya Akisatul Sauwara ta numfasa tace,tabbas naji gaba dayan tsigar jikina ta tashi kuma zuciyata ta daskare tamkar na tsomata a cikin ruwan kankara.Koda kin wannan batu sai mamaki ya turnuke Yarima Lubainu yace,ai nima irin abinda naji kenan sak da naki.Anya kuwa wannan addini na bakon Jarumi bashi ne ADDININ GASKIYA BA?Koda jin wannan tambaya sai sarauniya Akisatul Sauwara ta gyada kai tace,ai kuwa ita gaskiya bata buya har abada,idan har shine ADDININ GASKIYAR to da sanni zamuga babbar shaida dazata tabbatar mana da hakan.koda jin wannan batu sai Yarima Lubainu ya girgiza kai yayi shiru bai kara cewa komai ba aka cigaba da tafiya ba sassauci.Ba'a tsaya ba har saida bakon Jarumi ya fuskanci cewa lokacin sallar Azahar yayi sannan ya bayar da umarnin a tsaya a yada zango,kuma sai akayi sa'a a wannan lokaci an iso wani wuri mai magudanar ruwa.Koda su Yarima Lubainu sukaga wannan ruwa sai suka kamu da matukar sha'awarsa suka ruga izuwa cikin ruwan suka kama shansa suna wanke fuskarsu suna zubashi a kansu.Koda bakon Jarumi yaga duk hankalinsu ya tafi izuwa cikin wannan ruwa hardashi kansa Dazyan ya tafi cikin ruwan ya tsugunna yana alwala.Nan take bakon jarumin ya sulale daga wajen ba tare da dayansu ya ganshi ba ya zagaya bayan duwatsun da wannan ruwa ke fitowa ta cikinsa inda babu mai ganinsa.Da zuwansa sai ya tsaye cak ya dubi gabas da yamma,kudu da arewa yaga babu wani mahaluki mai ganinsa,kawai sai ya tsugunna a gaban ruwan yasa hannayensa biyu ya cire rawanin dake kansa,wanda ya rufe fuskarsa.Dogon bakin gashi ne mai tsananin haske da kyalkyalu ya zubo kasa bisa kafadunsa,a lokacin da kyakkyawar fuskar 'YA MACE ta gaban kwantace ta bayyana.Idan mutum ya kwatanta kyawun wannan mace dana sarauniya Akisatul Sauwara sai yaga ashe sarauniya Akisatul Sauwara ma mummuna ce akan wannan BAKUWAR JARUMA saboda bambancin a bayyana yake babu gami!"Ni kaina a matsayina na marubicin wannan littafi an shammaceni a cikin labarin,domin ban taba zaton cewa bakon jarumi MACE ce ba NAMIJI ba musamman da nayi la'akari da irin abubuwan dayayi na jarumtaka".Nan take kyakkawar jarumar ta ajiye rawanin nata daf da ita sannan ta sanya zara zaran yan yatsun hannayenta guda biyu a cikin ruwan ta kwarfoshi tana mai yin bismillah.Ina jin sautin muryarta zuciyata ta buga da karfi naji kamar kirjina zai tsage saboda tsananin zakin muryar,domin kamai dacin ran mutum idan kunnuwansa suka ji wannan murya mai zaki da taushi sai yaji kamar ruwan sukari aka watsa masa ya gauraye da dukkan JININ JIKINsa.Nan take ma'abociyar kyawun ta fara alwala a nutse cikin ilmi da kwanciyar hankali saida tazo kan wanke kafar hagu a karshen alwalar sai kawai taji takun sawu a bayanta.Cikin bakin zafin nama ta suri rawaninta ta kifa a kanta,take ya rufe gashinta da fuskarta kamar yadda ya saba rufeshi koda yaushe,sannan ta yunkura da nufin ta waiga don taga ko waye ke tahowa ta bayan nata,kawai sai taji ansamata tsinin takobi akan tsakiyar wuyanta ta baya ana bata umarnin kada ta kuskura ta motsa.Sautin muryar data bata umarni ne ta firgitata ainun fiye da tsinin takobin dake kan wuyan nata ba don komai ba sai saboda ta shaida cewa ba wani bane mai wannan murya face YARIMA LUBAINU.Yarima Lubainu ya kurawa kyakyawar jarumar idanu ta bayanta a lokacin da gaba dayan jikinsa ya kama kyarma saboda dimauta dayayi tun farko hango kyakkyawar fuskarta.Ko a mafarki Yarima Lubainu idanunsa basu taba siffanta masa mace mai irin kyawun ta ba.Inda za'a dauki matarsa Yazarina a ajiyeta kusa da bakuwar Jarumar da kyawunta disashewa zaiyi ta koma mummuna saboda kwarjini da haibar bakuwar jaruma.Yarima Lubainu ya sake budar baki da kyar muryarsa na rawa yace,saboda me zaki yaudaremu tun farko ki boye wannan kyakkyawar fuskar taki da kuma siffarki ta 'ya mace da wannan murya taki mai tsananin zaki da naushi tamkar sarewa?Koda jin wannan tambaya sai Jarumar ta mike tsaye ta juyo ta fuskanceshi tace,Kamar yadda bawana Dazyan ya gaya muku tun farko ina da hujjar da tasa na boye fuskata,muryata da jikina wacce ba lallai bane na sanar dakai a yanzu,amma kadan daga cikin hujjar ka gani yanzu da idanunka,kuma kaji ta a jikinka,domin naga yadda jikinka ya kama tsuma a lokacin dakayi arba da kyakkyawar fuskata.Ina mai tabbatar maka da cewa in da kuma gaba daya surata ka gani zaka iya fita daga hayyacinka.Har izuwa wannan lokaci da jarumar ke magan zuciyar Yarima Lubainu bata daina daka ba kuma jikinsa bai daina kyarma ba.Abinda zuciyar tasa ke raya masa shine,wannan ma'abociyar kyau dazata kasance sarauniya to zai iya yarda tsafanceshi ya zamo gadonta na barci don kawai ya kasance kullum yana tare da iya yana ganinta kuma yana jinta a jikinsa.Ai kuwa nan take ya fada cikin kogin tunanin yiyuwar hakan tamkar a mafarki.Koda jarumar ta lura da cewa Yarima Lubainu baya tare da ita ya tafi izuwa wata duniyar ta tunani sai tayi murmushi ta tafa hannyenta a daidai kunnuwansa.Yarima Lubainu yai firgit tamkar wanda ya farka daga barci mai nauyi ya kura mata idanu.Ita kuma sai ta dubeshi cikin nutsuwa tace,yakai wannan dan Sarki ka yi sani cewa tun a farkon danaji labarinka na kamu da tausayinka kuma a cikin zuciyata sai na yanke hukuncin taimakonka koda kuwa ba zaka karbi addinina ba saboda ina kishin halin da matarka zata shiga sakamakon rabuwarku.Abinda nakeso dakai shine ka cigaba da rufe sirrina kada ka kuskura ka nuna wata alama da zata nuna cewa ka gane cewa ni mace ce.In dai ka ruke wannan al'amari ni kuma zan cigaba da taimakonka harka rabu da wannan lalura.Amma inason nayi maka wata tambaya guda daya,kuma lallai ka bani amsarta bisa gaskiya idan kayi mini karya ka sani cewa anan gaba zakaji kunya.Koda jin wannan batu sai Yarima Lubainu yayi ajiyar zuciya sannan yace,babu yadda za'ayi nayi miki karya saboda kafin na baro gida mahaifiyata ta bani guzurin abubuwa uku wadanda tace dani in dai na rikesu sai na sami nasarar abinda na fita nema.Abu na farko shine lallai duk abinda zan fadi ko zanyi nayi shi bisa gaskiya.Abu na biyu shine,na zamo mai cika alkawari.Abu na karshe shine na zamo mai rike amana idan har an bani na karba.Tace idan na rike wadannan abubuwa dukkan wani burina na duniya zan cikasu,kuma makiyana tasirinsu kalilan ne akaina na dan lokaci kankani.Yake wannan ma'abociyar kyawu na ban al'ajabi ki yi mini tambayarki ni kuma na rantse da darajar uwata da ubana zan baki amsa iyakar gaskiya.Koda jin wannan batu sai murna ta kama jarumar tace,daga lokacin dana hadu daku kawo iyanzu me kaji a zuciyarka dangane da addinina? Koda jin wannan tambaya sai Yarima Lubainu yayi murmushi yace,ai tun a ranar farko da muka kusan hallaka a cikin fadar Boka Darbusa naga kin baiyana tsulum,kin cecemu naga irin gagarumin karfinki na ban al'ajabi na gane cewa al'amari ne wanda yafi karfin tsafi ko na Aljan.Lallai karfi ne na wani ubangiki da babu kamarsa.Koda Yarima Mangul yazo nan a zancensa sai farin ciki ya lullube jarumar tace,shin hakan yana nufin cewa zaka iya karbar addinina.?Yarima Lubainu yace,kwarai kuwa ko a yanzu ina muradin karbarsa,amma na fuskanci cewa sauran abokan tafiyar tawa basuyi imani dashi ba kuma akwai alamin cewa in suka sami dama zasu iya yaudararmu su sace ALLON SIHIRI su gudu.Koda Yarima Lubainu yazo nan a zancensa sai farin ciki ya lullube bakuwar jarumar saboda ganin cewa ko ba komai yanzu ta sami nasarar jawo hankalin mutum daya ga ADDININ GASKIYA.Jarumar ta dubi Yarima Lubainu cikin nutsuwa tace banaso yan'uwanka su san cewa ka karbi addina a yanzu saboda in hakan ta faru bazan sami damar jayo nasu ra'ayin ba.Ba komai ne yasa na amince na biku har izuwa kogin Bahar Imfal ba face saboda inason na nunawa sarakanku na wannan nahiya cewa nayi abinda su bazasu iya ba da taimakon ubangijina,saboda hakan ne kadai zaisa zuciyoyinsu su karaya su bada gaskiya ga Addinin nawa,saboda na fuskanci cewa ba karamin aiki bane a rabasu da addininsu da suka gada tun iyaye da kakanni.Koda Jaruma tazo nan a zancenta sai Yarima Lubainu yayi ajiyar numfashi yace tabbas zancenki dutse ne kuma nima nayi miki alkawari zan taimaka miki iyakar kokarina wajen ganin mun shawo kan jama'a sun fuskanci gaskiya sun karbeta. 1 hr · PublicALLON-SIHIRI Littafi na Biyar (5) Part C Mun shawo kan jama'a sun fuskanci gaskiya sun karbeta.Ina da wata alfarama guda daya danake so na nema a wajenki.Cikin mamaki bakuwar jarumar ta dubi Yarima Lubainu tace,kai kuwa wacce irin alfarma kake son nayi maka?Yarima Lubainu ya numfasa yace,sarauniya Akisatul Sauwara ta gaya mini cewa kina da.ilmin fassarar mafarki,kuma nayi wani mafarki ne wanda ya razanani ainun wanda nake son ki fassara mini shi.Nan take Yarima Lubainu ya kwashe labarin mafarkinsa ya zaiyana mata.Koda jin labarin wannan mafarki na Yarima Lubainu sai nan da nan fuskar bakuwar jarumar ta sauya izuwa alamun damuwa tayi shiru tana mai sunkui da kanta kas.Al'amarin dayai matukar dugunzuma hankalin Yarima Lubainu kenan ya budi baki da nufi yace wani abu,sai kawai suka hango Dan wada Dazyan ya rugo izuwa garesu.Da zuwansa gaban bakuwar jaruma sai ya zube kasa cikin girmamawa yace,ya shugabana tun dazu nayi alwala nake jiranka kazo muyi sallah amma sai naji shiru ban ganka ba shi yasa na taho nema.Koda jin haka sai bakuwar jaruma ta mike tsaye suka nufi wani waje mai rairayi suka tsaya.Dan wada Dazyan ya tsaya a gaban bakon jarumi ya tayar da sallah ita kuma ta tsaya a bayansa tana binsa.A daidai wannan lokaci ne Yarima Lubainu yaji kamar daga sama an kirawo sunansa.Yana waigowa bayansa yaga ashe sarauniya Akisatul Sauwara ce ta nufoshi fuskarta cike da annuri.Saida tazo daf dashi sannan ta tsaya suka fuskanci su Dazyan dakeyin sallah.Sarauniy a Akisatul Sauwara ta dubi Yarima Lubainu tace,nifa wani abu yana daure min kai duk sa'adda Dazyan da maigidansa suka zo yin wannan ibada tasu sai naga Dazyan ya wuce kan gaba,shi kuma maigidan nasa ya koma baya.Ai kamata yayi ace maigidan nasa ne yake jagorantarsa a komai.Abu na biyu kuma shine a duk sa'adda na kalli idanun wannan bakon jarumi sai naga kamar mace ce ba namiji ba!zuciyata zata dade tanayi mini zargi da wasi wasi akan hakan.Inda ina da iko danaje na tuje rawanin dake kansa munga gaskiyar al'amari.Koda jin wannan batu sai Yarima Lubainu ya turbune fuskarsa ya dubi Sarauniya Akisatul Sauwara cikin alamun fishi yace,kada ki kuskura kiyi irin wannan tabargaza domin idan muka sami matsala da wannan bakon jarumi nine zanfi kowa kwaruwa.Keda Sarki Darmanu kun fito ne domin neman duniya,ni kuma neman lafiya ne ya fito dani.Koda jin wannan batu sai jikin sarauniya akisatul Sauwara yayi sanyi tace,shike nan nayi maka alkawari bazanyi duk wani abu dazai kawo matsala a tsakaninmu da wannan bakon jarumi ba.Shin yayi maka bayani kuwa akan mafarkinka? Na san cewa saboda hake ne ka biyoshi izuwa nan bayan wannan dutse?Koda jin wannan tambaya sai Yarima Lubainu yai caraf yace,to banda abinki ta yaya kurma zaiyi mini wani bayani na fahimta alhali ni ban iya zancen kurame ba,kuma babu Dazyan a lokacin danazo wajensa.Sarauniya Akisatul Sauwara ta jinjina kai ta dubi Yarima Lubainu cikin alamun rashin yadda tace,amma kuma ai naga ka dade anan tare dashi,hirar me kuke tayi ne?Cikin fishi Yarima Lubainu ya mike tsaye yace,ai wannan tambaya ce ta rainin hankali to gaki nan gashi sai ki bari ya gama ibadar tasa ki tambayeshi irin hirar da nayi dashi.Kinsa ance waka a bakin mai ita ta fi dadi.Sarauniya Akisatul Sauwara ta mike zumbur tasha gaban Yarima Lubainu tace,ka gafarceni yakai Lubainu tabbas nayi kuskure bisa wannan tambaya danayi maka.Kodajin haka sai Yarima Lubainu yai shiru baice da ita komai ba,ya tafi ya barta tsaye a wajentana mai binsa da kallo sannan ta juya ta kurawa bakon jarumi idanu wanda keyin sallah tare da Dazyan tace a cikin ranta."Komai naka irin na mata ne,ta yaya zuciyata zata gamsu cewa kai namiji ne?Tunda muka hadu dakai ban taba ganin lokacin daka cire kayan jikinka ba bare naga zahirin jikinka,kaki ka bude fuskarka mu gani.Amma zan kafa naci da zuba ido har sai naga gaskiyar al'amari.Sarauniya Akisatul Sauwara na gama aiyana hakan a cikin ranta sai ta juya ta koma can inda aka yada zango.Bayan su bakuwar jaruma sun idar da sallah sai suka dawo wajen su Yarima Lubainu suka zauna akaci abincin rana.Daga nan aka mike kowa ya kimtsa aka cigaba da tafiya.Ba'a sake tsayawa a ko ina ba saida lokacin sallar La'asar yayi nan ma Dazyan da bakon jarumi suka gabatar da sallar aka sake cigaba da tafiya ba sassauci.Da yammaci ne sakaliya suka shigo cikin wani daji mai katon fili.Shidai wannan fili ana yi masa lakabi da sunan Dajin MUJALLUN HARBUN.Shidai wannan daji na Mujallin Harbun daji ne wanda sama da shekari dubu ba'ayin komai a cikinsa face yaki.Duk kasashen dake nahiyar idan zasu yaki juna a wannan fili suke haduwa a fafata.Da isowarsu Sarauniya Akisatul Sauwara farkon wannan fili,dama bakon jarumi ne akan gaba,sai kawai sukaga bakon jarumi yaja linzamin dokinsa ya tsaya cak,yana mai daga hannunsa sama alamar cewa kowa ya tsaya.Nan take kuwa Yarima Lubainu,Dazyan, Sarau­ niya Akisatul Sauwara da Sarki Darmanu sukabi umarnin bakon jarumi kowa yaja linzamin dokinsa suka tsaya cak,gaba dayansu,sai suka kama kalle kalle suna duban gabas da yamma kudu da arewa amma sai sukaji shiru basuga komai ba kuma basuji motsin komai ba.Kawai sar Sarki Darmanu ya bushe da dariya ya dubi bakon Jarumi ya sake bushewa da dariya tace,yazaka tsayar damu haka kawai muna cikintafiya?To idan ma kana zargin akwai wani mugun abu ne anan babu komai face tarin kwarangwal na bil'adama saboda wannan wuri fili ne na yaki asali kimanin shekaru dubu baya.Koda jin wannan batu sai bakon jarumi ya dubi Dazyan yayi masa magana a cikin yaren kurmanci.Dazyan ya dubi sarki Darmanu yace shugabana yace na gaya maka cewa,lallai akwai alamun wani mugun abun daya buya a cikin wannan duhowoyi ko a sama kan bishiyoyi saboda haka kowa ya zauna a cikin shirin yaki.Gama fadin hakan keda wuya sai bakon jarumi ya daga garkuwarsa sama kuma ya zare takobinsa.Nan take kowa ma yayi koyi dashi suka sakarwa dawakansu linzami suka cigaba da tafiya suna masu ratsawa ta cikin filin Mujallun Harbun suna waife waige don ganin ta inda za'a fara kawo musu hari.Saida suka iso tsakiyar filin sannan sukaga kasa na tsagewa da darewa.Kafin suyi wani yunkuri sai sukaga wadansu dodanni gabza gabza suna fasowa ta cikin karkashin kasa suna dira kan turba rike da MUGGAN MAKAMAI su da yawa ba adadi.Tun da Sarauniya Akisatul Sauwara tazo duniya bata taba ganin halitta mai tsananin muni da ban tsoro kamar wadannan dodanni ba.Saboda tsawonsi kuwa saisu Yarima Lubainu da dawakansu suka zamo 'yan kananu a gabansu bayan dodannin sun gama yi musu KAWANYA.Gurnanin da dodannin keyi ne ya fara firgita dukkan tsuntsaye da dabbobin dajin suka kama canja sheka.In banda bakon jarumi da dan wada Dazyan babu wanda jikinsa bai kama tsuma ba saboda razana sakamakon ganin wadannan dodanni.Kawai sai bakon jarumi ya mayar da takobinsa cikin kufe,shima Dazyan sai ya mayar da tasa takobin ya dubi Sarauniya Akisatul Sauwara,Sarki Darmanu da Yarima Lubainu yace,maigidana yace yanzu sai ku yaki wadannan dodanni da karfin damtsenku gami dana sihirinku,kuma ku hada da neman taimakon ababan bautarku domin ya gani ko zaku iya kubuta.Koda jin wannan batu sai tsoro ya kama su Sarauniya Akisatul Sauwara.Sarki Darmanu ya dubi dan wada Dazyan cikin alamun firgici yace,saboda me shugabanka zaiyi mana haka alhalin ko ba'a gwada ba linzami yafi karfin bakin kasa?Dan wada Dazyan yayi murmushi yace,ai idan baka manta ba haka ka'idar take,kafin mu fara wannan tafiya tare daku saida muka yi sharadin cewa duk masifae data taso kune zaku fara tunkararta da dukkan karfin damtsenku da karfin sihirinku,saidai idan mun ga kun gaza saimu kawo muku agaji.Koda gami fadin hakan sai bakon jarumi da Dazyan suka sauko daga kan dawakansu suka zauna a kasa dirshen suka rintse idanuwansu suka kama karanta wata addu'a ta musamman.Faruwar hakan keda wuya sai suka bace bat daga filin tamkar basu taba wanzuwa ba awajen.Al'amarin daya sake firgita su sarauniya Akisatul Sauwara kenan kuma ya girgiza hankalinsu.Su kuwa dodannin nan da suka ga mutum biyu sun bace musu da gani sai suka fusata sukayo caa!izuwa kansu Yarima Lubainu suna masu yin wani irin ruri mai tsananin firgitarwa.Koda ganin haka sai sarauniya Akisatul Sauwara ta dubi Sarki Darmanu da Yarima Lubainu tace bamu da wani zabi wanda yafi mu kare kanmu muyi iya kokarinmu..Kafin ta gama rufe bakinta tuni wani dodo ya dako tsalle ya dira a gabanta ya kawo mata wawan sara da wata irin kakakifar adda mai cako cakon tsini kamar zarto.Cikin bakin zafin nama ta sunkuya addar ta sari iska amma saita fille kan dokin sarki Darmanu fit,dokin da sarki Darmanu suka zube kasa.Nanfa wuri ya hargitse aka rincabe da mugun azababben yaki mai tsananin muni da tayar da hankali.Ai kuwa ana fara wannan yaki su sarauniya Akisatul Sauwara suka raina kansu suka gane cewa yau sun gamu da gamonsu,domin dai wadannan dodanni basa jin SARA DA SUKA da zarar an saresu saidai kaji kara kal!tamkar karfe da karfe ne suka hadu,kuma a fuska ne kadai suke jin naushi,kuma saboda zafin namansu su sarauniya Akisatul Sauwara basa iya naushin nasu ko saransu a fuskar.In badin ma suma suna da nasu zafin naman ba da tuni dodannin sun hallakasu farat daya.Haka dai su Yarima Lubainu suka cigaba da yin iya kokarinsu waje kare kansu gami da maida martani.koda aka shafe sa'a guda anayin wannan BAKIN GUMURZU sai yaki ya sauya salo,ya zamana cewa su Yarima Lubainu sun fara gajiya,ai kuwa a sannan ne dodannin suka fara samun nasarar gabza musu naushi suka rinka hada musu JINI DA MAJINA har ma ka yanki kowannensu sau daidai jini yayi tsartuwa a jikinsu.Su ukun suka kurma ihu a lokaci guda sakamakon jin tsananin zafi da zogi,suka durkushe a kasa yayin da jiri ya kwashesu.Ai kuwa sai dodannin sukai caaa!izuwa kansu da nufi su dasa musu wawa su daddatsa su.Kwatsam ba zato ba tsammani sai su sarauniya Akisatul Sauwara sukaga bakon jarumi da danwada Dazyan sun faso karkashin kasa a tsakiyar dodannin suna masu kwalla KABBARA sun tarwatsasu da karfin tsiya kuma suka hausu da SARA DA SUKA ba sassauci.Nanfa jinin dodannin ya kama fallatsi a sama sassan jikinsu ya rinka shawagi a sararin sama yana zubowa kasa suna ruri da kururuwa suna zubewa kasa mattatu.Koda su Sarauniya Akisatul Sauwara suka ga dan wada Dazyan yana yaki da wadannan dodanni cikin gagarumar jarumtaka ta ban al'ajabi sai suka sake kamuwa da tsananin mamakinsu,saboda su dai a saninsu rago ne bashi da wata jarumta tunda a baya ma da suka shuga rintsin yaki kan bishiya ya haye ya buya saida aka gama yakin sannan ya sauko.Haka dai bakon jarumi da dan wada Dazyan suka cigaba da ragargazar dodannin nan suna cigaba da kwallah Kabbara har saida suka karar dasu gaba dayansu,ya zamana cewa babu dayansu daya tsira da rayuwarsa.A sannan ne Dazyan ya ruga wajen su Yarima Lubaimu ya kama duba raunikan dake jikinsu.Sa'ar da sukayi ma shine babu wanda rauninsa yayi zurfi saidai darewa kawai da yayi.Nan da nan cikin gaggawa dan wada Dazyan ya dinke musu raunikan aka saka musu magani.Bakon jarumi ya taho garesu ya bisu da kallo daya bayan daya yana maiyi musu sannu da hannu.Koda yazo kan sarauniya Akisatul Sauwara da nufin yayi mata sannu sai ta murtuke fuska ta daka mata harara kuma ta tari numfashinsa ta dubeshi cikin fishi tace,yanzu a haka kake nufin zamu cigaba da wannan tafiya duk sa'adda muka hadu da masifa saidai ku barmu da ita?Ai kafin mu isa ma can duk jikinmu ya lalace da raunika kuma raunikan ma zasu iya zama sanadin ajalinmu.Koda jin wannan batu sai shima bakon jarumi ya fusata ya dubi Dazyan yayi masa zancen kurame.Dazyan ya dubi sarauniya Akisatul Sauwara yace,idan bakwason jikinku ya lalace ko kuma ku rasa rayuwarku to ku karbi Addininmu.Idan kuka karbeshi munyi muku alkawarin zamu roki ubangijinmu akan ya biya muk dukkan bukatunku muddin bukatun bazasu cutar da wani ba!Koda Dazyan yazo nan a zancensa sai jikin sarauniya Akisatul Sauwara yayi sanyi sai kuma kunya ta kamata ta rasa abinda zatace.Shi kuwa Yarima Lubainu kansa na sunkuye ko kallon bakon jarumi baiyi ba.Sarki Darmanu kuwa ya bata rai sai muzurai yakeyi kawai.Nan dai aka samu aka huta har izuwa lokaci mai dan tsawo,sannan aka kafa sansani aka kwanta domin a kwana a wajen in yaso gobe da safe a cigaba da tafiya.Har dare ya raba Yarima Lubainu bai iya yin barci ba a cikin tantinsa shi kadai.Gashi dai ya kishingida amma zuciyarsa cike take da tunani da wasi wasi gami da fargaba.Yana cikin wannan hali ne yaga bakon jarumi tsulum ya shigo cikin tantin nasa.Cikin kaduwa da alamun tsananin mamaki Yarima Lubainu ya mike tsaye zumbur ya kurawa bakon jarumi idanu amma alamomin tsoro duk sun bayyana akan fuskarsa.Koda gin haka sai bakuwar jaruma ta dubeshi tace,kwantar da hankalinka yakai Yarima Lubainu,kayi sani cewa babu wanda zai ganmu ko yaji zancen da zamuyi a yanzu saboda nayi wata addu'a barcin kowa yayi nauyi hatta na Dazyan kuwa.Ba komai ne yasa ba kowa maka ziyara a cikin wannan dare ba face saboda na fahimci kana cikin damuwa da tashin hankali wadanda bazasu barka kayi barci ba.Ta gama fadin hakan sai ta cire rawaninta ta ajiye gefe daya kuma ta zauna nesa kadan dashi inda suka fuskanci juna.Koda yai arba da kyakyawar fuskarta sai yaji cewa inda zai rinka ganin wannan fuska to bazai sake yin bakin ciki ba a rayuwarsa har abada,kuma yunwa da kishirwa bazasu taba damunsa ba.Saboda kallonta ne zai hanashi jinsu ya sanyashi cikin farinciki mara misaltuwa.Har bakuwar jaruma ta budi baki zata ce wani abu sai Yarima Lubainu ya tari numfashinta yace,kafin kice komai ina rokonki da girman ubangijin musulunci daki fara sanar dani sunanki.Koda jin haka sai bakuwar Jarumar tayi murmushi tace,gaskiya banso na sanar dakai sunana ba yanzu sai a karshen tafiyarmu,a lokacin dazan bude fuskata da jikina kowa ya ganni,to amma tunda ka hadani da girman Allah dole ne na sanar dakai.Da farko sunana SUHAILAT IBINI AFUWAN,kuma na fito ne daga can wata nahiya dabam a wata kasa da ake kira DARUL ILMUN.Yanzu sai ka nutsu ka saurari fassarar mafarkinka.A takaice wannan mafarki naka yanayi maka nuni da cewar matarka Yazarina ta baro kasarku ta fito nemanka amma kuma ta fada hannun wani babban abokin gabarka wanda ke kokarin rabaka da ita.Saidai mafarkin bashi da karshe bare musan halin data shiga,walau abokin gabar taka ya kamata ko kuma ta tsira daga sharrinsa.Koda Suhailat tazo nan a zancensa sai hankalin Yarima Lubainu ya dugunzuma ainun fiye da koyaushe ya rasa abinda ke masa dadi a duniya,ya mike tsaye zumbur da nufin ya ruga waje ya hau dokinsa ya tafi neman Yazarina,amma sai Sulailat tayi wuf ta ruko hannunsa a karon farko da hannunta ya fara taba wani 'da namiji ba muharramin ta ba.Cikin sauri ta saki hannun nasa tana mai istigifari a cikin zuciyarta sannan ta sha gaban Yarima Lubainu tace,ka kwantar da hankalinka yakai Angon Yazarina,kayi sani cewa da izinin ubangijina babu abinda zai sami matarka domin zan cigaba da rokonsa akan ya bata kariya kuma ya kareta daga sharrin wannan makiyi naka.A yau din nan zanyi istihara domin na ga halin da take ciki,kuma kafin mu cigaba da tafiya zan sanar dakai duk halin da take ciki.Abinda nakeso dakai kawai shine ka cigaba da rike alkawari na boye sirrina ya zamo amana a tsakaninmu.Koda gama fadin hakan sai Suhailta ta juya ta fice daga cikin tantin sai Lubainu ya kira sunanta ta waigo ta dubeshi cikin mamaki tace,mene ne?Nan fa Yarima Lubainu ya rasa abinda zaice da ita,dama bashi da abin fadar,kawai ji yayi baison rabu da ganin fuskarta gami dajin muryarta.Ashe Suhailat ta fahimci hakan,sai kawai ta dubeshi tayi masa murmushi mai dauke da alamar tambaya(?)tace saida safe.Take ta sake juyawa ta fice daga cikin tantin ba tare data sake waigowa ba.Kashe gari kuwa da sassafe jaruma Suhailat ta fito daga cikin tantinta ta iske Dazyan kwance a filin Allah bisa shimfida ya lulluba da bargo.Kawai sai tasa hannunta guda ta yaye bargon,take Dazyan ya farka yai firgigit.Koda yaga itace sai ya dukar da kansa kasa ya gaisheta cikin girmamawa.Kawai sai Jaruma Suhailat ta sunkuyo tayi masa rada a kunne sannan ta ruga izuwa cikin jeji domin farauto naman daza'ayi kalacin safe.Tafiyarta keda wuya sai Dazyan ya zaga bayan tantin Yarima Lubainu yayi kamar bawali zaije yayi domin a lokacin tuni sarauniya Akisatul Sauwara ta fito daga cikin tantinta ta tsaya tana mika da kallon yanayin dajin,kuma taga sa'adda Suhailat ta dashi Dazyan daga barci.Koda Dazyan ya zagaya bayan Tantin Yarima Lubainu sai ya kira sunansa a cikin karamar murya mai kama da rada.Yarima Lubainu ya amsa kiran,shi kuma yace dashi shugabata tace kayi sauri ka sameta a daji bangaren gabas domin ku tattauna ta tafi farauta.Koda jin wannan batu sai Yarima Lubainu ya mike tsaye zumbur,dama a tube yake ko riga babu a jikinsa sai wani gajeren wando.ALLON-SIHIRI, Littafi na Biyar (5) Part D Dama a tube yake ko riga babu a jikinsa sai wani gajeren wando.Cikin hanzari ya sanya kayansa ya dauki KWARI DA BAKA sannan ya leko da kansa waje kadan sai ya gano Sarauniya Akisatul Sauwara a tsaye a bakin tantinta tana yin asuwaki.Cikin hanzari ya maida kansa cikin tantin don kada ta hangoshi a lokacin da zuciyarsa ta cika da damuwa saboda yasan cewa indai ta ganshi zai tafi daji farauta cewa zatayi saita bishi.Jim kadan sai Yarima Lubainu ya sake lekowa waje,saiya hango Sarauniya Akisatul Sauwara ta bar kofar tantin nata ta nufi inda tanti sarki Darmanu yake.Cikin hanzari yayi amfani da wannan dama ya fice daga cikin tantin nasa yana sanda da labiya ya nausa cikin daji ba tare da an ganshi ba.Da shigar Yarima Lubainu cikin daji ya nausa gabas yana duban sawun Jaruma Suhailat.Ai kuwa bai dade da fara duba sawun Suhailat ba ya ganshi don haka sai ya cigaba da binsa da sauri har dayayi tafiya mai dan tsawo.Kwatsam sai ya hango Jaruma Suhailat daga nesa kadan ta ratayo wata matacciyar barewa a kafadarta ta tunkaro inda yake.Tun daga nesa suka kurawa juna idanu suna murmushi har ta iso daf dashi.Kawai sai ta dubeshi tace,zo mu cigaba da tafiya muna hirar mu don kada abokan tafiya su ga mun dade bamu koma ba suyi zargin wani abu.Ba tare da wata gardama ba Yarima Lubainu ya jera da ita suka cigaba da tafiya don komawa can masaukin nasu.Suna cikin tafiyar ne ta dubeshi tace,yakai Yarima Lubainu,kamar yadda na yimaka alkawari jiya nayi istahara kafin na kwanta barci kuma ubangijina ya nuna mini halin da matarka ke ciki tun kafin ma ta baro kasarku Zamrul.Shin kasan wani mayakinku mai suna BARDE RUHAISU?Koda jin wannan tambaya sai Yarima Lubainu ya dubi Jaruma Suhailat cikin tsananin mamaki yace,kwarai kuwa na sanshi,abokina ne na amana,kuma na daukeshi tamkar dan uwa na jini,domin a hannun mahaifina ya girma.Ko na takaice miki labarin ma mahaifina yana kaunarsa fiye da yadda yake kaunata ni da ya haifa a cikinsa.Koda jin haka sai Suhailat ta jinjina kai sannan tace,hakika Barde Ruhaisu dan halak ne kuma ya cancanci mahaifinka ya so shi fiye da kai,saboda mutum ne mai karfin amana kuma yana kaunarku kai da mahaifinka fiye da yadda yake son kansa.In badin Barde Ruhaisu bada tuni yanzu makiyinka kuma abokinka Yarima Mangul ya mallaki Yazarina.Nan take Suhailat ta kwashe labarin duk abinda ya faru tsakanin Yazarina da Barde Ruhaisu tun daga lokacin da suka baro Birnin Zamrul tare da dakaru dari kawo izuwa sa'adda Yarima Mangul ya kawo musu harin bazato suka fafata kazamin yaki dashi,inda a karshe suka ruga izuwa cikin daji suka hau kan wannan dogon tsauni mai mugun nisa,Yarima Mangul ya bisu har izuwa karshensa suka fado kasan tsaunin don su tsira daga sharrin Mangul.Koda Suhailat tazo nan a labarinta sai ta dubi Yarima Lubainu tace,wannan shine iyakar abinda ubangijina ya nuna mini a mafarkina don haka daga lokacin da Yazarina da Barde Ruhaisu suka fado kasan wannan tsauni bansan abinda ya samesu ba.Wata kila sun hallaka wata kila kuma suna nan a raye,amma dai kayi hakuri izuwa wani daren zan sake yin istahara domin naga halin da suke ciki.Koda Suhailat tazo nan a zancenta sai Hawaye ya zubowa Yarima Lubainu yace,yanzu ni dame zan sakawa barde Ruhaisu bisa wannan gagarumin taimako dayayi mini?Ki dubi yadda ya sallama rayuwarsa don kare ta matata.Koda jin wannan tambaya sai Suhailat tayi murmushi tace,tabbas akwai abinda zaka iya saka masa dashi anan gaba,amma fa sai ka danne zuciyarka,domin wani abu ne mai daraja a wajenka zai bukaci ka sallama masa shi..Koda yake amma a wannan lokacin kaima ka sami wanda ya ninka wancan din daraja.Koda jin wannan batu sai Yarima Lubainu ya dimauce ya kasa fahimtar abinda Suhailat take nufi,don haka sai ya dubeta cikin alamun matukar mamaki yace,wane abu ne haka mai daraja a wajena wanda Ruhaisu zai bukaceshi kuma nima zan sami wanda yafishi daraja?Sa'adda Suhailat taji wannan tambaya sai ta hade fuska tace kasan komai yana da lokacinsa to ka yi hakuri lokacinka na sanin wannan al'amari baiyi ba.Idan kuwa ka matsa har ka sani din to tabbas zakayi nadamar sanin!!!Tana gama fadin hakan ne suka jiyo sautin haduwar takubba daga bangaren wajen da suka yada zango.Cikin firgici suka dubi junansu sannan suka falfala da azababben gudu suka nufi wajen.Ai kuwa suna isowa inda suka yada sansani sai suka hango sarauniya Akisatul Sauwara,Sarki Darmanu da dan wada Dazyan a tsakiyar wasu narka narkan SAMUDAWAN MARIDAI kimanin su saba'in suna yaki dasu.Kowanne maridi guda tsawonsa yakai kamu ashirin da biyar kuma fadin kirjinsa ya kai kamu ashirin.Suna rike da manyan sungumai guda bibbiyu.Sungumin dake hannunsu na dama da dutse akayi shi,don dunkulalle ne mai kauri da nauyi,duk abinda suka rotsawa shi sai ya dagargaje.Daya sungumin dake hannunsu na hagu da zallan kashin wata katuwar dabbar daji akayi shi mai KAIFI DA TSININ TSIYA!Komai kaurin bishiya idan suka caketa dashi sai ya hudata ya bullo ta karshenta.Su dai wadannan maridai sun kasance suna da tarin kwanji mai girman gaske gami da jijiyoyi tamkar jikin nasu ma na dutse ne bana tsoka ba.Ita kanta Jaruma Suhailta da ta jango wadannan samudawan maridai daga nesa saida ta firgita ta tabbatar da cewa karo dasu ba wasa bane,dole ne a sha BAKIN GUMURZU da wahalar gaske,don haka tun kafin ma su iso wajen su kawowa su Sarauniya Akisatul Sauwara dauki tuni maridan sun galabaitar dasu,sun kaisu kasa sun kasa koda mikewa tsaye saboda kowannensu ya sami rauni a jikinsa sama da guda uka sai zubar da jini suke,jiri na dibarsu. Koda ganin haka sai Suhailat ta dubi Yarima Lubainu ta gargadeshi da kada ya kuskura yace zai tayata yakar wadannan samudawan maridaiTana gama fadin hakan sai ta kara kardin gudun nata tana mai neman taimakon Allah a cikin zuciyarta.Ai kuwa sai karfin gudun nata ya zama tamkar na TAURARUWA MAI WUTSIYA!!!Nan da nan ta baiwa Yarima Lubainu tazara mai yawan gaske.Saura kiris samudawan maridansu hallakasu Sarauniya Akisatul Sauwara a lokacin da suka daga sungumayen hannayensu zasu mammaka musu sai kawai Suhailat ta daka tsalle sama tamkar an harbota daga cikin BAKA ta dira a tsakiyar samudawan maridan ta tarwatsasu da karfin naushin kafafunta biyu,sannan suka sake taso mata aka ruguntsume da sabon masifaffen yaki.. WAYE ZAI SAMI NASARA A WANNAN YAKI TSAKANIN JARUMA SUHAILAT DA WADANNAN SAMUDAWAN MARIDAI? A WANE HALI YAZARINA DA BARDE RUHAISU SUKE? SHIN YARIMA MANGUK ZAI SAKE TARFA SU BARDE RUHAIUS HAR YA MALLAKI YAZARINA? SHIN YARIMA MANGUL ZAI CIKA BURINSA NA KASHE MAHAIFINSA DON HAWA KARAGAR MULKIN BIRNINSU? WANE ABU NE MAI DARAJA WANDA BARDE RUHAISU ZAI NEMA NAN GABA A WAJEN YARIMA LUBAINU? YAUSHE NE YARIMA LUBAINU DA YAZARINA ZASU SAKE SADUWA KUMA YAUSHE NE ZA'A ISA KOGIN BAHAR IMFAL? Mu hadu a littafin ALLON SIHIRI(ALLON-SI HIRI-6)don jin cigaban wannan kayataccen labari. Alhamdulillah!!!Godiya ta tabbata ga Allah (SWT)daya bani ikon gama rubuta wannan littafi.Sai muyi jira littafi na shida(6).Allon-Sihiri 6 ya fito.Insha Allah yana nan tafe bada jimawa ba.