*GOJE!*🏹 🐕‍🦺🐕‍🦺🐕‍🦺 _(SADAUKI OMAR RETURN👑💫_) *BINTA UMAR ABBALE🍒* *_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION🖊️📚_* _____________________ ********************** ? ************************** ********** Ai Hausa Novels **************** *************************? ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ? ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ? ************************** FREE PEGE *1&2* "A zahiri kamar cikkaken namiji amma abun kunya kamar ka shekara talatin da uku ba aure ace namiji kamarka mara tsoro mafarauci a dajika! amma a gida malalaci gauro tuzuru wanda ya gaza samawa kansa nutsuwa wannan jarumtar taka a banza tunda baka da aure har yanzu baka cika cikakken namiji ba." Wata 'yar tsohuwa ce take wannan maganar, idona na kai kan wanda takewa surutun ya juya baya jikinsa sanye da kayan farauta ba'kin yadi mai kaurin gaske rigar mai fadi ce iya kafadarsa, ta tsaya iya kacin gwiwarsa sai yayi amfani da wandon jens kafarsa sanye da takalmi mai igiyoyi, bayansa kawai na kalla na gazgata maganar tsohowar, hakika duk inda cikakken namiji yake mai zati da kirar mazantaka to za a sanya guy a ciki dogo ne mai fadin kirji jikinsa a cike a murde babu rama ko ta kwabo a tare dashi, har yanzu be juyo ba da alama akwai abinda yake. Tsaki taja tace." *UMARU* ina magana amma dai yau a gida zaka kwana ko."? Ba tare da ya juyo ba yace." A'a bah! zan kwana a gida ba"!! yanayin yanda yake magana a ciccije sai dana tsorata!. sake 'buya nayi ina gyara biro da takardar dake hannuna. Tace."To koda naji ai gwara dana tambayeka saboda ana magariba zan rufe kofata kaje ka 'karata." Uffan bece mata ba, na hangoshi yana d'aura wasu tafka-tafkan layu a damtsan hannunsa. Ya dauki wata hula mai kunnuwa ya kwafa akansa kafin ya juyo, saurin sunkuyar da kaina nayi gabana na dukan uku-uku! yana da manyan idanuwa sosai amma sunyi wani mugun jaa! lebansa bakikirin, alamu sun nuna farin mutum ne amma tsabar busa hayaki gami da shaye-shayen magungunan tauri! fatarshi tayi wata irin dabbara-dabbara! Kafin nayi aune! naji ya kurma uban ihu! ya dunkule! hannu kafin ya kalli gabas yamma kudu arewa ya fara yiwa kansa kirari kamar haka. "Nine *Umaru!* Namijin duniya! mai tarwatsa namun daji! Na d'aya 'kwal! a gurin uwa da uba! dubu jiran mutum dubu!! naci uwar d'an iska! naci uwar duk wani dan tauri! Ihuuuu!!! Nine Umaru! wanda wuka komai kaifinta bata ratsani! Nine dai Umaru! mai karnuka dari ba d'aya, mai masoya gabas! yamma! kudu! arewa! An buga an barni! naci dubu sai ceto! nayi tawa nayi ta wasu!! Umaru nake d'aga Tanimu jika gurin Uwale! Idan da wanda yake da yaja ya fito don uwarsa."!!! Yana maganar yana zazzare ido da ciccije baki sai rarume-rarume yake a dakin. Uwale na ganin ya zaro labceceyar wukar dake rataye a kafadarsa taje gurin tana rirrikeshi, ya tureta gefe, fito da wukar yayi sai sheki take ya fara gurzawa a jikinsa. Gabadaya jikina in banda kyarma babu abunda yake, yau garin neman labarai na kawo kaina mahallaka, da gudu! na fito daga bayan kyauren nayi waje! ba zan iya ganin wannnan tashin hankalin ba😂 A maimakon na kama hanya na gudu,sai na b'uya a bayan wata bishiya ina jiran fitowarsa, kimanin mintina goma ya fito, kallo guda nai masa na sunkuyar da kaina, gabadaya jikinsa kayan farauta ne, kwari da baka, wukake a soke a kowane sassa na jikinsa. Tirkashi ashirye yake na sheda cewa babana Umaru jarumi ne. Wani irin fito yayi fit-fit! kawai sai ganin karnunka nayi suna fitowa ta bayan gidan, kafin wasu zaratan matasa kamarsa suka biyo bayan karnukan suna sanye da kwatankwacin kayan dake jikinsa. Sun kai su goma suka zageyeshi kafin su farayi masa kirari! kamar haka, *GOJE!* jarumi a gida jarumi a waje! *UMARUL-FARUK!* ba ka san wargi ba, baka san tsoro ba! baka san wasa ba! kayi taka kayi ta wasu! Namijin duniya tarwatsa namun daji! *Zaki!* uban mafarauta! kaine jagora *GOJE!* Ja muje! Mudubi mai nuna mana hanya." Kallonsu kawai yake yana tattauna lebensa kafin ya gyada kansa, A ciccije yace." Zamu kai sati muna gwagwarmaya ina fatan kowa ya sallami iyalinsa." Suka bashi amsa da fadin "Eh ranka ya dade munyi yanda ka umarcemu." Hanya kawai ya kama suka rufa masa baya tare da karnukansu dake faman haushi!! duk sun cika unguwar. sawun tafiyarsu kawai kake ji da sautin kukan karnukansu. A daddaure suka shiga da ita motar suka sanyata a tsakiyarsu, kafin direban ya shiga ya zauna, a gaggauce ya figi motar suka fita daga masarautar, yau suna cikin farin ciki bukatarsu ta biya gurin kidnaping din yarinyar da suke sanya ran samun makudan kudi daga gurin iyayenta. Wani irin nishi! take gumi duk ya jika mata jiki sun daure mata fuska da kyar take jan numfashi, kawai sai ta shiga nanata kalmar shahada watakila ajalinta ne ya sauka a cikin wannan dare. Da yake dare ya tsala shiyasa motar ta samu sararin sharara gudu yanda ranta yake so, Wani irin wawan burki motar taci! ji kake kuuuuuuu!! kafin ta gangara can gefe guda tana watangaririya! Da azama! ya isa gurin jama'arsa na tare dashi, yayin da gurin ya cika da kukan karnuka abunka da dare! Motar dake watangaririya ya durfafa! babu tsoro a tare dashi yasa kafarsa ya daki murfin motar, cikin ikon Allah ta bude, a take suka fara rige-rigen fitowa, lokacin da sukayi arba dashi suka tabbatar *Makashinsu* ne sai gudu! radada! direban kuwa kafin ma ya samu nasarar fitowa motar ta kama da wuta! Tana kwance! magashiyan! ko ina na jikinta a daure! wucin wutar ya kama gefen zaninta! ta rasa yanda za tayi sai ta fara jan jiki tana gurnani! Allah yayi masa ji! da sauri ya juyo yana haska gurin da wata katuwar fitila, da sauri ya mikawa daya daga cikin yaranshi fitilar ya sunkuya ya dauketa, a kafada ya sa'bata, wutar na cin gefen zaninta cinyoyinta wasu guraran duk sun kone! sai da sukayi nisa da wutar ya kwantar da ita kan ciyayi, gabadaya yaran sukayi masa rumfa karnuka sai ihu! suke a gurin suna zagaye. Ya dago jajayen idanuwansa da fadin." Ku matsa a gurun." Da sauri suka watse! Da hannu ya bubbuge sauran wutar dake jikin zanin. Ya janye idonsa daga kan cinyoyinta da suka fito waje, tsigar jikansa ta dinga tashi, ya jima kafin ya sake kallonta, hannu yasa ya kwance zanin ya jefar ya fizge siket din da duk ya manne da fatar jikinta, Ido ta runtse! tana jin wani irin azabar zafi har tsakiyar kwakwalwarta. Yayi saura daga ita sai wando, (pant) Fuskar nan babu walwala ya fara kwance mata daurin fuskarta, suka had'a ido, kuri! tayi masa yana gama kwance mata daurin bakinta, ta samu sararin d'aga hannu a zafafe! ta nufi fuskarsa zata gaura masa mari! Da azama! ya rike! hannun murdeshi yayi da karfin gaske! yatsun suke bada sautin qararas!! lokaci guda ta shiga nutsuwarta, ya saki hannun ya dinga jale-jale! da alama wasu yatsun sun samu Matsala. Zafafan hawaye suka dinga karakaina a saman fuskarta, tana kallonsa tana kallon cinyoyinta da suke waje muraran! Ihu! ta kurma! ta nunashi da hannu da fadin." Ni *Gimbiya Zinat* zaku wulakanta me kuke bukata? wanda masarauta ta gaza yi muku! wallahi sai kun gane kuskuranku."! Jajayen idanuwansa ya zuba mata, kafin yaja dogon tsaki! ya mike tsaye yana gyara kayan farautar dake jikinsa! da azama tayi nufin mikewa! azabar quna yasa ta koma ta zauna hawaye na cigaba da gudana a fuskarta. Fito yayi alamun yana kiran yaransa, aikuwa kafin kiftawa da bisimillah sun kewayeshi har karnukan, ba tare da yace komai ba yayi gaba, suka rufa masa baya. Hannu ta d'aga da fadin." Kada ku tafi ku barni a wannan dajin ku mayar dani gaban iyayena."!! Babu wanda ya saurareta a cikinsu sai sauri suke suna taka ciyayi tare da ratsa itacuwa. Cikin dauriya ta mike tsaye! tasa hannu ta lalubi tsommokaran da suka daure mata fuska, ta daura a jikinta hanyar da suka bi ta kama tana tafiya tana waiwayen bayanta, bata iya addua ba ballanatana tayi domin ta kare kanta ita a inda tafi kauri rashin kunya girman kai izzah! isa! jiji da kai maganar abinda ya shafi addini bata san komai ba tafi karfi bangaran boko gami dabin dabi'ar 'ya'yan nasara. *#500 via 0543282124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....* *22796074090* *GOJE!*🏹 🐕‍🦺🐕‍🦺🐕‍🦺 _(SADAUKI OMAR RETURN👑💫_) *BINTA UMAR ABBALE🍒* *_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION🖊️📚_* _____________________ FREE PEGE *3&4* Tuntun'be tayi da wani girkakken icce tayi mummunar faduwa kanta ya bugu da tsinin iccen, lokaci guda jini ya fara tsartuwa, hannu tasa ta dafe gurin, murya ta bud'e sosai ta kwarma ihu! wanda ya tashi dabbobin dake dajin. lokaci guda suka fara koke-koke, wasu daga ciki har sun fara fitowa daga ramukansu. Hakan ya sanyasu tsayawa a gurin kwakkwaran motsi babu wanda yayi a cikinsu, da ido yayi musu magana cewa suyi lamfu a kada wanda yayi motsi wanda zai dauki hankalin dabbobin da suka fara fitowa, hakan sukayi, dajin! yayi tsit! sai kukan dabbobin ne kawai ke tashi. Wani irin juwa da hajijiya ta dinga yi a gurin kafin ta yanke jiki ta fad'i kan ciyayi, jini kuwa duk ya jika mata fuska da gaban rigarta. Cike da jarumta ya daidaita kwari da bakar dake hannunsa, yanayi yana waiwayen bayansa yana hasashen ta inda wata dabbar zata fito, da baya da baya ya dinga tafiya har ya cimma inda take kwance, yana yunk'urin d'aukarta yaji hucin wucewarsa zurrrrrrr! cikin zafin nama yayi wani irin tsalle ya zaro kaifaffar wukar dake rataye a bayansa ya fille masa kai! tsayin macijin ya kai in taha.! Fitilar dake hannunsa ya kunna ya haske mata fuska yana kallonta, yayi mamakin yanda akayi ma har ya dawo da baya domin taimaka mata, wai kamarshi, *GOJE!* yarinya 'kank'anuwa irin wannan tayi yunkurin marin fuskarsa. Tsaki! yaja yana gyada kanshi, da alama hakan ya zame masa jiki, tsumman dake d'aure a k'ugunta ya fizge, ya yagi rabi ya daure mata kan dashi, tsam ya matse jinin ya daina zuba, ya dauketa kacokan ya goya a bayansa yasa tsumman ya daureta, yanayin tafiyarsa sam be sanja ba cike da jarumta yake taka itacuwan gurin tunda ya fahimci a sume take burinshi ya samu inda ruwa yake domin ceton rayuwarta. Yaran ya kira suka fito, daga mab'oyarsu da yawa daga cikinsu sun farauci k'ananun dabbobi irin wanda suka firfito, ya basu umarnin zuwa su nannad'o macijin da ya sare masa kai, yana gama basu umarni yayi gaba bai tsaya ba har sai da ya cimma inda ruwa yake, Kwantar da ita yayi kan rairaiyi, yasa hannunsa cikin ruwan yana debowa yana watsa mata a ko'ina na jikinta. Sai da jikinta ya jike jagab da ruwa sannan Allah ya bata ikon sauke ajiyar zuciya, gashin idonta ya fara motsi tana so ta bude idon amma sunyi mata nauyi ga wani irin ciwo da kanta yake mata, hannu ta dora saman kanta bakinta sai motsi yake, Tashi yayi ya bar gurin. Ta jima tana ganin dishi-dishi a idonta kafin su bude sosai, da yake garin ya soma haske can nesa ta hangoshi tsaye amma bayanshi kawai take gani, cikin mugun tsamin jiki da azabar qunar data tashi tai jawur! ta mike zaune tana bin ilahirin jikinta da kallo, wasu zafafan hawaye suka kwace mata, lebe ta ciza tana furzar da wani irin huci! wai kamar ita Gimbiya gaba da baya itace a wulakance a yashe a bakin kogi, wani kazami bagidaje yana ganin sassan jikinta, wannan abun yayi mata mugun ciwo a rai. Yana daga inda yake tsaye ya dinga jin shashshekar kukanta na tashi. Ya juyo tare da da zuba mata jajayen idanuwansa. Itama shi take kallo tana kisma irin hukuncin da za tayi masa mutukar ya kusanto inda take. Be saurareta ba, bakin kogin ya nufa ya tsuguna yana daura alwala. Jin sawun tafiya da haushin karnuka yasa da sauri ta waiwaya, yaran shi ne tare da karnukansu da kuma abunda suka farauto. Suka samu wani fili suka zube kayansu da yake duk inda zasu shiga sukan tafi da guzurinsu, wata katuwar dadduma suka shimfida, kafin su hura wuta, sannan suka nufi bakin kogin domin daura alwala kamar yanda suka ga ogansu yayi Shine ya jasu jam'i, duk tana zaune tana kallonsu, suka idar ya daga hannu sama yana addua suna amsawa mamaki sosai ya lullubeta ganin yanda yake azkar masu zafi da adduoin da takasa tantance mai yake fada tunda wasu da labarci yake, tayi mamakin hakan daga gurinsa a ganinta rikakken *d'an daba* *d'an ta'addah!* irinsa bai kamata a samu ilimin addini a tare dashi ba. A nutse ya juyo yayi wani irin zama tamkar basarake! ya kashingida tare da tankwashe kafa daya ya dogare dayar tare da dora hannunsa akai. A maimakon musabaha kamar yanda Annabi ya koyar sai kawai suka dinga dukan hannunwasu da sunan gaisuwa a gareshi, wasu daga cikinsu suka fara bushe-bushe irin nasu suka hada baki gurin fadin." *A lafiya Goje!* *Cauuu!!* Uban mafarauta! *Sa'a dai* mai maganin *wuka da kaho* *Dawa dai!! Umarul-Faruku* muna mika gaisuwa a gareka." Ya dinga girgiza kansa yana jin tsigar jikinsa na wani irin tashi, numfashi ya shiga saukewa yana furzar da wani irin huci, Shisha ya kaiwa raruma yasa a baki ya fara tada hayaki a gurin. Ganin haka sai suka tashi suka bar gurin, rabuwa sukayi wasu suka fara aikin gashe-gashen irin dabbobin da suke farauto, wasu kuma suka kutsa cikin dajika domin samun abun da zasu ci. Tana nan zaune a inda take k'aik'ayi duk ya isheta, rana ta kwalle a gurin, so take ta tashi ta sauya guri kunya da tarin takaici sunyi mata dabaibayi, yanda Allah ya taimake ta ma ta lura sam ita din bata gaba gabansu, domin dik wanda yazo wucewa ta kusa da ita ba yayi mata kyakykyawan kallo. Kafafunta ta motsa, domin mikewa tsaye, aikuwa qunar ta kwaile ta fara fitar da ruwa da jini, tsananin azabar zafi ya sanyata tayi saurin mikar da kafar cikin tsautsayi ta danne kunama! lokacin ta d'ana! wani irin 'kara tayi jikinta ya dinga rawa! da rarrafe ta matsa daga gurin, idonta kan kunamar tana kokarin bin gefen kogin domin shiga wani rami...........Kafarsa yasa ya murjeta! yana cire kafar taga yanda tabi kasa tayi daga-daga a gurin!! Inuwarsa ta dinga kallo yayi mata rumfa gata tayi goho tamkar mai shirin haihuwa, gabadaya duwawunta a waje wando ne kawai ya taimaketa. Duk da tana jin tsoron sake zama a gurin hakan nan ta hakura ta zauna jikinta har yanzu rawa yake ga zufa sai ketowa take da sassan jikinta. Tsugunawa yayi kusa da ita har tana jin hucin numfashinsa, ta kalleshi, beyi aune ba yaji saukar kakkauran yawun bakinta a fuskarsa, yasa hannu ya sharce yawun yana me cigaba da watsa mata kwala-kwalan idanuwansa, Cikin zafin nama ta ciko hannunta da kasar gurin zata watsa masa ya kautar da fuskarsa, kasar ta zube a jikinsa, hannu yasa ya buge, ya kalleta fuskarsa a murtuke yace." Meye sunanki a wane gari kike."? Tana kuka me cike da azabar data rasa wace iri ce tace." Ni kake tambaya garinmu kaje ka daukoni a gaban iyayenta amma saboda rainin hankali kazo kana tambayata." Ya girgiza kai da fadin." Ni taimaka miki zanyi amma ban san abinda ya shafeki b.........."Karya kake."! ta katse shi da karfin gaske sai huci take! tana jira ya sake wata magana ta kaiwa fuskarsa mari! Ya jima yana kallonta da mamakin furucinta, tunda ya taso a lokacin yarinta da girma babu wanda ya ta'ba karyatashi cikin abokai da sauran jama'ar gari sai wannan karamar yarinyar, Sa'arta ta sameshi mai tsananin tausayin mace amma ba don hakaba da yau ta gane kuranta a hannunsa. Cinyoyinta ya zubawa ido yana kallon yanda qunar ta ruruce! tana ruwa da jini gashi har ta fara cin jikinta, ba tare da tayi aune ba taji saukar hannunsa, fittt ya d'aye fatar data qone! jiki na karkarwa ta rike hannunsa, tana aika masa da Allah ya isa. Be saurareta ba ya hade duka hannuwanta ya rike da hannunsa daya, ya sake bin d'aya cinyar ya d'aye fatar qunar! kawai sai ta zube a gurin tana makyarkyata. Tsallaketa yayi yaje ya dauko wata 'yar roba cike da gishiri yazo ya tsuguna yana kokarin bude robar gishirin. Ta dinga girgiza masa kai tana kokarin tashi zaune, ya mayar da ita ya kwantar, cikin rashin tausayi, ya barbade qunar da gishiri! ya tashi ya bata gurin..........Sandarewa tayi a gurin kamar matacciya yanzu kukan zucci take mai mutukar zafi, tsabar azaba hawaye ya bushe a idonta, yana daga inda yake ya hango yanda ta wargaje a gurin ta daina boye komai, ya bude wata jaka wani yadi mai kauri ya dauko, ya nufeta dashi, bata iya ce masa komai ba tana kallo ya cicibeta ya dora kan zanin ya nannade mata jiki, can inda shimfidar daddumar take ya nufa da ita ya samu gefe guda ya kwantar da ita. Sannan ya tashi daga gurin, ido kawai ta rufe tana sakin wani irin nishi irin na wahala.... *Ga wa 'yanda basu samu damar karanta Sadauki Omar ba, zasu tura 1k domin samun damar karanta littafi biyu, wato Sadauki Omar tare da Goje! Sadauki Omar return* *#500 via......0542382124....Binta Umar gtbank, idan kati zaki turo #600 ne sai kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262......Mutanan Nijar ku tuntubi wannan number...... 22796074090* *GOJE!*🏹 🐕‍🦺🐕‍🦺🐕‍🦺 _(SADAUKI OMAR RETURN👑💫_) *BINTA UMAR ABBALE🍒* *_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION🖊️📚_* _____________________ FREE PEGE *5&6* Kwanciyarta da kamar mintina goma bacci ya kwasheta sai dai baccin beje ko'ina ba dafin kunamar ya fara yawo a sassan jikinta, a gigice ta tashi zaune gabadaya jikinta ya dauki rawa ga wani irin gumi da yake karyo mata! rikicewa tayi ta rasa inda zata sanya ranta taji dadi. Gurin ya karaso, yana tambayarta, abunda ke damunta, da kyar ta iya bude baki tayi magana. Bece komai ba ya bar gurin, halin da take ciki besa ta bishi da kallo ba, har ya dawo kanta yana kasa wannan karan kuka ya samu ta nayi, ta dan bashi tausayi kadan, amma bai nuna a fuska ba. Ya bude gwangwanin Milo din dake hannunsa, wani abune mai duhu a ciki, da alama magani ne aka kwaba da mai, ya kalleta da fadin." Zaki iya nuna min gurin da kunamar ta cijeki."? Wani irin kallo ta tsawa masa, ta dauke kanta, ranshi ya baci ya daka mata tsawa da fadin" Taimakonki fa zanyi kike min kallon banza kin san wanene a gabanki kuwa."? Hannu tasa ta goge fuskarta ta daure zugin dake damunta, cikin rashin tsoro tace." Sanin wanene kai bai dameni ba, na dai san ka amsa suna biyu wato *barawo* kuma dan *ta'addah."!* Ya tsira mata idanuwansa masu kaifi! yana mamakin maganarta, *'barawo kuma d'an ta'addah!* tunda yake a duniya babu wanda ya ta'ba kiransa da sunan *barawo* sai ita, kalmar *d'an ta'addah* kuwa yana ji tana yawo a gari a kansa. Ya girgiza kansa cikin yanayin maganarsa yace." Wannan shine karon farko da aka ta'ba kirana da wannan kalmomin a gaban idona, kiyi kokarin kiyaye harshenki kafin ki bar hannuna, *GOJE!* nake ba'a kawo min wargi duk tsagerancinki ni zan daidaitaki. Ta kalleshi a wulakance kafin tace."A hakan? babu tarbiyar! ka fara daidai ta kan............'Barin makauniya yayi ya fuskarta, a take hancinta ya tsinke da jini, tasa hannu ta dafe, jiki na kyarma! take kallonsa, fuskarsa ta rikide da zallan bacin rai! "Zaki janyo nai miki mugun rauni a gurin nan, babu ruwana da kowace masarauta kika fito, ki sani ba'a nuna ni da yatsa ban karya ba! sannan ba'a jayayya dani, kuma bana magana biyu, *Billahil-lazi hurramanu!* duk sanda kika kara fadin wata mummunar magana akaina sai na illataki."! Shuru tayi jikinta yayi bala'in mutuwa ganin yanda hancinta ke zubar da uban jini shine abinda yafi zaburar da ita. Ta kalleshi, yana safa da marwa a gurin, tace." A kan me ba zan kira ka da wannan suna ba? ka sato ni a gaban iyayena domin su baka kudi. akan me ba zan kiraka da *'Barawo* ba me kake bukata? da ka kawoni daji ka ajiye kana azbtar dani, kamar ni *Zinatu* wacce ta gaji sarauta gabada da baya ina rayuwa a wannan kazantaccen gurin, tare da kai makaskanci to saurara kaji da kyau! wannan jinin da ya zuba, be zuba a banza ba, wallahi sai kayi daka sanin zubar dashi."! Hannu d'aya yasa cikin aljihun jins din dake jikinsa, ya dan sunkuya tare da dogare gwiwarsa, fuskarta ya dago da hannunsa, yana kallonta tana kallonsa, yace."Daga wace masarauta kika fito naga kina girmama kanki kina mutunta kanki, duk wanda ya gaji saurata baya kambaba kanshi kamar yanda ke kike, ina so ki sani zargin da kike a kaina kar ki gazgata, Allah ya kawoni ne tareda jama'ata domin na taimakeki, kuma zan taimakaki bakin kokarina, amma ni zan koya miki tarbiya. Magana za tayi ya sanya yatsunsa biyu ya murje fatar bakin...........tsam! ya rike lebunan yana ligwigiwitawa, kukan zucci kawai take, jikinta yayi mugun sanyi, yana sakin bakin ta silale a gurin, yaja tsaki da furta "kalankasa kawai."! Zanin dake nannad'e a jikinta ya janye duk tana jin abinda yake amma tsabar yanda jikinta yayi tubus, ta kasa hanashi sarrafata. Bai damu da kallon wasu sassan na jikinta ba, domin gabad'aya babu wani feelings a tare dashi, tunda yake sai yace babu ranar da wata mace ta ta'ba tayar masa da hankali duk zubi da kirar dake gareta, Asalima yakan jima bai shiga yanayi na bukata ba, shiyasa auran baya gabanshi, wanda uwar rikonshi wato kakarsa Uwale keyi masa surutu akan hakan. Da kanshi ya lalubi inda kunamar! ta harbeta ya shefe gurin da magani, ganin duk yaran nashi sun bar gurin yasa ya bude mata jikin domin qunar tasha iska. Har ya gama abinda yake a gurin bata daina zubar da hawayen takaici ba, tayi turr! da wannan rayuwar da take ciki, a tunaninta hanya ba zata iya had'awa dashi ba, sai gashi w *Kazami- Bagidaje!* irin sa yana ganin sirrin jikinta. tana ganin wannan ko hadimanta (masu yi mata bauta) sun fishi kyawun gani sai gashi a banza yana yin yanda yake so a kanta ya tatta'ba jikinta babu tsoro ko shakka a tare dashi hawaye masu zafi ta goge tana jimanta al'amarin. Taji dadin maganin sosai domin tana tsaka da tunanin hanyar da zata bi domin kubutar da rayuwarta bacci mai nauyi ya dauketa. ***** Kana ganinta kaga bafulatana, doguwa ce sambal kyakykyawa a fuska, gata fara tas! ta tara duk wasu abubuwa da da namiji ke bukata amma hausawa sukace wai Dan Adam tara yake be cika goma ba, Hamra'u bata da cikkar kirji hakanan kuma babu baya a tsaye take kamar muciya da zani, sai dai akwai tarbiya da kunya irin ta fulani. A nutse tayi sallama a gidan, Uwale dake uwar daki ta amsa, da fadin.'' 'Yar halak yanzu nake maganarki a zuciyata. Murmushi tayi ta cire takalminta, ta shiga dakin, Uwale na kurbar kunu ta mika mata kofin da fadin " Bisimillah." Girgiza kai tayi tana murmushi tace." Ai daga gida nake kuma sai dana karya kafin na fito. Dariya tayi irin ta tsoffi tace." Hamra'u kenan wai me yasa duk sanda zan baki abu sai kice daga gida kike ko dai kankyamina kike ne."? Da sauri tace."Aa Wallahi ba haka bane Uwale na koshi." Tace."To ai shikkenan duk ya mutan gidan."? Tace."Suna nan lafiya lou alhamdullhi babanmu yace a gaisheki da kyau.'' Tace."Ina amsawa ai a cikin satin nan nake so nazo gidanku mu gaisa sai kuma *UMARU* Yayi tafiya gashi zai dauki sati guda bai dawo ba. A sanyaye tace."Yanzu fa nake shirin tambayarki ina yake shine zakice yayi tafiya kuma sai yayi sati zai dawo." Tace."Eh haka yace min da zai tafi kin san dai yanayin al'amuranshi, wani sa'in ma har wata guda ya kanyi yana gwagwarmaya a daji" A raunane tace." Ni wallahi ba naso yana irin wannan yawace-yawacen tsoro nake kada 'yan fashi su kasheshi ko kuma namun daji su cinyeshi." 'Yar dariya tayi tana sud'e kofin kunun data gama sha tace."Sai dai kiyi hakuri Hamra'u wannan mijin naki yayi nisa addua kawai zaki dinga yi masa. Tace."Kullum inayi masa addua tare da sauran jama'a." Tace."yawwa hakan yana da kyau, sannan ki cigaba da hakuri insha Allahu, hankalinsa zai karkato kanki." Idonta ya cika da ruwan hawaye, tace."Uwale sai nake ganin kamar baya sona tausayina kawai nake gani a kwayoyin idonshi. Tace." To in banda abinki Hamara'u ai sai da so ake tausayi, da baya sonki ba zai tausaya miki ba." Shuru tayi tana nazarin maganar, itafa tunda take dashi babu wata kalmar so daya taba furta mata, asalima yana kiranta da kanwata, amma bai taba cewa Hamra'u ina sonki ba, sai dai yana tsananin bata kulawa komai take bukata idan tayi masa magana kai tsaye yake mata, wannan dalilin yasa iyayenta da ita Uwalen suke ganin kamar sonta yake, ajiyar zuciya ta sauke ta kudire a ranta cewa idan ya dawo zata cire kunya ta tambayeshi matsayinta a zuciyarsa. Hamra'u 'yar kanin Uwale ce, tun tana yarinya Allah yasa mata so dakaunar Goje tun be fahinta ba har Allah ya fahintar dashi, be ajiyeta a wani matsayi na daban ba face wanda take dashi a zuciyarsa, gabadaya tunda ya taso baya da ra'ayin soyayya, shiyasa baya fahimtar tarin 'yan matan dake k'aunarsa, Samari da yawa a karkarar tasu suna kishi dashi, a cewarsu sai kace shi kadai ne namiji ko wacce budurwa bata da magana sai tasa, ransu yana baci mutuka, suna kuma bala'in kishi a kan haka, ita kanta Hamra'un akwai wanda yake mutuwar sonta amma fafur taki amince masa ita dai Umaru takeso wanda bata da tabbas a kansa.............. Uwale, kayan dillacinta ta dauko ta nada gammo ta dora aka, tana gyara yafan mayafi take fadin."Hamra'u ni zan fita dama a irin wannan lokacin nake samu na nemi halalina idan kin gama gyara min gidan ga kwado ( dan mukulli) akan taga ki kulle gidan ki bawa Tasallah ta ajiye min." Tace."Uwale inace Yayana ya hanaki yawon dillaci nan kuma kin san Babana ma baya so me kike bukata ne a duniyar nan." Tsaki taja da fadin." Sai kiyi kuma kinga tafiya ni babu wanda zai hanani neman kudi." tana gama maganarta tasa kai ta fita daga gidan. Hamra'u girgiza kanta kawai tayi idan da sabo ta saba da hakan , a nutse ta mike ta fara ayyukan dake gabanta.... *********** *WAIWAYE* K'allo d'aya nayi masa na fahimci wanene a gabana, ko da yake koda zanyi shekara d'ari ba tare da na sanyashi a idona ba to ba zan mance kammaninsa ba, *Sadauki Omar* kenan Sarkin dake kan karagar mulki a jahar *Kano* Adalin sarki wanda al'ummarsa ke jin dadin mulkinsa. Yana nan a yanda kuka san shi tsayayye! kuma jarumin namiji! kamanninsa suna nan sai dai alamun girma da ya baibayeshi amma a tsaye yake da jarumta babu abunda ya samu nakasu a cikin halayensa da d'abi'unsa. Yana tsaye a tsakiyar babban falonshi hannuwansa goye a banyanshi yana kai kawo a gurin, kallo daya kayi masa zaka fahimci yana cikin damuwa. Cikin nutsuwa da kamala tayi sallama be juyo ba ballantana ya amsa sallamarta, kai tsaye inda yake ta nufa, sai na bita da kallo, ina hasashen a inda na san fuskarta, Gimbiya *Aysha ce fa* zuciya tayi saurin tuna min ita Cike da dumbun mamaki nake kallonta tana sanye cikin laffaya milk color da adon zaiba kafarta sanye da takalmi rufaffe irin na sarauta, ban hango wata tawaya a tare da ita ba domin kuwa jikinta ya nuna alamun hutu da jin dadi sai dai alamun shekaru sun tura hakan ma sai ka 'kura ido a kanta sannan zaka fahimci cewa ta kwana biyu a duniya. Hannunta ta d'ora kan kafadarsa, a nutse ta kira sunanshi *"Jarumi."* be juyo ba ballantana ya kalleta, sai ta dora kanta kan kafad'arsa, hawayen da take boyewa suka kufce, wai shin ya za suyi da wannan ibtila'in da yake kokarin ruguza musu farin cikin da suke ciki na tsayin shekaru masu yawa................ *Ga wanda bai samu damar karanta Sadauki Omar ba, zai tura 1k domin samun damar karanta littafi biyu tare da Goje! Sadauki Omar return* *#500 via 0543282124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....* *22796074090* Mutanan Nijar zaku turo min katin Mov ko airtal na Dala dari. *GOJE!*🏹 🐕‍🦺🐕‍🦺🐕‍🦺 _(SADAUKI OMAR RETURN👑💫_) *BINTA UMAR ABBALE🍒* *_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION🖊️📚_* _____________________ FREE PEGE *7&8* _*Banyi tsammanin rubuta wannan littafin a kusa ba, asali ma nayi wa kaina alkawari cewa na daina sakin littafi sai na kammala, amma cikin ikon Allah ya nufe ni da fara rubuta wannan littafin ba tare da nayi tunanin hakan ba, ina rokon Allah ya bani hakuri da juriyar rubuta abinda za'a amfana dashi, sannan ina mika godiya ga dubbanin masoyana wanda na sani da wanda ban sani, hakika duk wanda Allah yayiwa baiwa ta jama'a dole ya gode masa, babu abunda zance da masoya sai godiya da fatan alkairi, sannan a cigaba da hakuri da yanayi na rayuwa, koda zanyi wa wani laifi a bisa rashin sani to ina neman afuwa🙏🏻 d'an adam ajizi ne, ina fatan zaku bibiye ni a wannan littafin nawa mai suna a sama, ku bani hadin kai sannan ku bini a sannu a hankali domin isar da sakon dana dauko, #500 kacal zaku biya domin karanta cikakken labarin.*_ *WANNAN NAKI NE* _(AUTAR MANYA)_ *A cikin marubuta ke ta dabban ce a gurina🤝🏻🥰* Jin kukanta yake har tsakiyar kansa, koda can baya son ganin tana zubar da hawaye ballanatana yanzu da ta riga ta zama garkuwa a tare dashi. Ajiyar zuciya ya sauke ya juyo tare da rike kafad'unta, hannu yasa ya share mata hawayen dake zuba a saman fuskarta, ta rike hannunsa da fadin.'' Ka bari nayi kukan domin shi kadai zanyi na samu sassaucin abinda nake ji a cikin zuciyata." Ya girgiza kansa da fadin." Ke kin san bana son zubar hawayenki Aysha me zai sanya ki kara tayar min da hankali bayan wanda nake ciki." Ta tsira masa idanuwanta wanda suke cike da ruwan hawaye " Me yasa ka kasa fahimta ta? me yasa ka dauki laifi kacokan ka dora a kaina bayan idan adalci a za'ayi kaine babban mai laifi dangane da faruwar wannan al'amarin." Girgiza kansa yayi zuciyarsa nayi masa wani irin zafi da k'yar ya iya magana." Bani da laifi Aysha ba zan haifi d'a a cikina na lalata shi ba, ba zan gaji da fadi miki cewa tarihi ne yake maimaita kansa." Ranta ya 'baci da jin furucinsa, a duk sanda zai fadi wannan kalmar akan wannan al'amarin sai taga kamar akwai rashin adalci a cikin maganarsa. Tana kokarin magana, Safa ta shigo da sallama a bakinta, suka amsa tare da bin ta da kallo har ta karasa inda suke tsaye. fuskarta kadai zai nuna maka cewa akwai rashin kwanciyar hankali a tare da ita, ba ita ta haifi Yarinyar ba amma tafi kowa shiga tashin hankali da rashinta. A raunane ta kalleshi da fadin.'' Ranka shi dade har yanzu babu wani labari ko."? Kanshi ya daga da fadin." Babu wani labari Safa watakila ma yarinyar nan bata raye domin duk iya binkice anyi amma ba'a samu wani labari mai dadi ba." Kuka ta fashe dashi, ta nemi guri ta zauna tare da rufe fuskarta da tafikan hannayenta. Ganin tana kuka yasa Aysha da sauri ta kama hanya domun fita bata so duk su lalace a gurin koke-koke domin mutukar tana kallon kukan Safa to itama zata iya taya ta. Karo sukayi da juna, Aysha kanta a kasa yake shiyasa bata ga shigowarta ba, Maijidda ce matar mijinsu, da ya aureta bayan shekara masu yawa da suka wuce. Kasancewar basa shiri da juna yasa tayi saurin kauda kanta ta wuce, ita kuma hamshakiyar ta bita da wani irin kallo kafin ta ta'be bakinta cikin wata irin tafiya ta isa da ta'kama tayi sallama a falon. Shi kad'ai ne ya amsa sallamar Safa har yanzu kuka take yana tsaye ya gaza rarrashinta shima da zai samu yayi kukan da yaji sassauci a zuciyarsa. Wawan kallo takewa Safa kafin tace."Ke a ganinki hakan kauna ce? kullum baki da aiki sai kuka uwar data haifi yarinyar ma har ta fiki dauriya Safara'u kuka bashi ne mafita ba." Safa ta dago kanta tana kallonta da mamakin furucinta, za tayi magana kenan, Yace." Abinda nake ta so su fahinta kenan yanzu ita kanta Ayshan ta gama nata ta fita, na fada masu cewa addua itace abinda ya cancanta. A tausashe tace."Hakane ranka ya dade shiyasa ko kadan ban zubar da hawaye na akan wannan al'amari ba, abinda nayi shi ya cancanta, ya kuma kamata, tun ranar da al'amarin ya faru na sanya almajiran mahaifina suyi saukar al'kur'ani na tsayin sati guda, da izinin Allah yarinyar nan tana hannu nagari za kuma ta dawo gida cikin aminci." Safa ta watsa mata wani irin kallo na zargi kafin ta tashi tare da kama hanyar fita. Sunanta ya kira ta juyo tana kallonsa babu walwala ko ta kwabo a fuskarta. Yace."Kada ki cigaba da wannan kukan bashi da fa'ida ko kadan addu'a zakiyi kinji ko." Ba tace masa komai ba ta fita ta basu guri, kai tsaye sashen Aysha ta nufa, ta sameta tare da babban yaron su wanda suke kiransa da magajin Sarki. Tana shiga ya mike tsaye yana mata barka da zuwa, ta zauna kusa da 'yar uwata kafin ta bashi umarin zama. Ya zauna kasan kafafunsu, a nutse yace." Mommah don Allah ku kwantar da hankalinku bana so naga daya daga cikinku na zubar da hawaye ni nayi imani da Allah da manzon Allah yarinyar nan tana hannu nagari da yardar Allah zata dawo gida cikin koshin lafiya. Aysha bata iya magana ba, Safa tace."Babana ina mamaki idan naji kai da mahaifinka kana maganar mu kwantar da hankalinmu, ta ina hankalinmu zai kwanta? a cikin wannan yanayin yarinyar nan sace ta akayi kuma akwai sanya hannun makusanta bana shakka a cikin maganata." Yace."Hakan tana iya kasancewa amma Mommah kada ki manta fa yarinyar *Zinatu* bata jin maganar kowa kuma a daran da al'amarin nan zai faru gabadaya sai da kuka hanata fita amma saboda rashin tarbiya ta tsallake maganarku to me zai sanya hakkinku be bibiyeta ba." Shuru sukayi domin kuwa babu mai bakin magana a cikinsu, abinda ya fada gaskiya ne, yarinyar ta fita zakkah a cikin zuriarsu, sai kuma Allah ya jarabcesu da tsananin sonta, shi kansa maimartaba wato mahaifinta baya son laifinta, ko kad'an duk da ya san abubuwan da take na rashin kyautawa a masarautar duk zafinsa baya iya tsawatar mata, sai 'yan uwanta mata dake gidajen auransu suke tsaye a kanta, wani sa'in su din ma bata saurara musu rashin kunya take musu kuma ta kwana lafiya, babu wanda take shakka sai shi Magajin sarkin, shima a bayan idonsa zaginsa take tana fadin be isa ya hana rayuwar jin dadi tun bayan dawowarta daga kasar waje bayan ta kammala karatunta ta dawo da mugayen dabi'u irin na turawa, duk wanda ya nuna mata kuskure akan abinda take cewa zai shafi masarauta da martabar mahaifinta sai ta d'aura gaba dashi, halin da ake ciki shi kansa Magajin sarkin ba tayi masa magana saboda yana tsawatar mata akan abubuwan da take na rashin tarbiya, jin kade - kade sanya matsatsun kaya bayan baiwar da Allah yayi mata na qira, yawace-yawacen pary cloub club babu inda bata shiga tayi b'arna da kudi da famkama da manya motoci ta fito babu abunda ya dameta. Da yawa mutane ba sayi mata kallon cikakkiyar mace saboda mummunan dabi'unta. Don akwai lokacin da wani babban malami ya nemi ganawa da maimartaba akanta, suka tattauna sosai maimairtaba ya fahimceshi ya san me kaunarsa shine zai zo har gabanshi ya fahimtar dashi abunda ya shige masa duhu, a lokacin ya tashi tsaye a kanta, kuma ya gargadeta kan cewa mutukar bata sanja hali ba to zaiyi mata aure duk wanda yayi ra'ayi, hakan ya tsorarta da ita, tayi sanyi na kwana biyu amma kwanaki suna turawa ta cigaba da abinda take, Gabadaya sai ya dauki al'amarin ya jinginashi a matsayin jarabta, abin na damunsa mutuka amma ya rasa me yasa baya son bacin ran yarinyar, Dan uwanshi, Abbas wanda yake Waziri a gareshi ya bashi shawara kan cewa aurene kadai abinda zai daidaita nutsuwar yarinyar saboda haka shi zai umarci babban yaron sa domin yazo su fahimci juna, maimartaba yaji dadin shawarar dan uwansa. Koda Taufiq ya sameta domin bin umarnin mahaifinsa rufe ido tayi taci masa mutunci harda zagi kamar ba jininta ba, aikuwa ya fusata! ya gaggaura mata mari hade da farfada mata mumunan magana, "Bani da ra'ayi auran mace mara tarbiya irinki umarnin mahaifina nabi har nazo neman auranki saboda haka wallahi ko ba dazi rasa mijin aure ba zan aureki ba shashaha mara hankali kawai " Bata saduda ba tana kuka tana zaginsa, Magajin sarki ya samu labarin abinda tayi wa abokinsa ya shiga har dakinta ya zaneta da belt ya fito yana huci! Gimbiya Aysha na zaune a falo yazo ya wuce ba tace masa komai ba. Washe gari ta hada kayanta kaf ta koma sashen Safa, itama anan din bude mata wuta tayi ta nuna mata kuskuranta, kafin ta bar sashen sai da tayi mata rashin kunya tasa wata baiwa ta daukar mata akwatin kayanta ta nufi sashen Maijidda, a maimakon ta nuna mata kuskuranta, sai ta hau rarrashinta ta nuna mata cewa itake da gaskiya kuma ba zata bari ayi mata auran dole ba, a takaice dai da sanya hannun Maijidda komai ya lalace! itace kuma ke daure mata gindi tana iskanci iya son ranta. To wannan dalilin yasa ita Ayshan take ganin harda sa hannunsa dana matarsa gurin lalacewar yarinyar, amma tun sanda al'amarin ya faru ya dauki laifi ya dora mata, kullum idan zai budi baki magana daya yake fada *(Tarihi ne zai maimata kansa)* tana jin bala'in haushin wannan magana, ta san a lokotan baya tayi sharafi amma abinda tayi be kai wanda ita yarinyar keyi ba, dalili iyayenta da tayi rashinsu a halin yanzu a tsaye suke a kanta, abunda tayi be kai wanda 'yar cikinta keyi a yanzu ba, ita dashi suka san hakan, amma idan ya tashi magana saboda rashin gaskiya a gaban kowa fadi yake abinda yarinyar take gado ne don haka itace sila akan faruwar al'amarin. Ta kalli Safa bayan fitar yaron nasu, tace."Duk ranar da Maijidda ta sake magana al'amarin nan sai tayi data sani domin duk irin abinda take aikatawa ina fahinta na gane itace ke zugashi yana daukar laifin yana dorawa a kaina." Safa ta girgiza kai da fadin." Eh ba zan hana ki ba ni kaina zan tayaki cin mutuncinta domin ta kai ni bango abin mamaki kuma har yanzu laifinmu yake gani, akan hakan ta shigo ta sameni cikin halin damuwa tana min maganar banza ya goya mata baya, ta kaini karshe duk sanda ta sake min katsalandan a gabanshi zan taka mata burki sai dai duk abinda zai faru ya faru." Tace."Safa ba zaki iya dasu ba, ki kyaleni ita dashi duk zanyi maganinsu, nagaji da wannan abun zanyi magani." Zuciyarta tayi sanyi da jin furucinta, ba tun yau ba, ta san halin Aysha ba kanwar lasa bace da sannu za tayi maganinsu gabad'aya. ********* Lokacin data farka garin yayi duhu, kuma bai kunna fitila ba tun bayan daya gabatar da sallahr isha'i sai ya kishingida a gefenta, saboda ita ya sanya bai jagoranci yaran sa farauta ba, sai kawai ya turasu daga shi sai ita ya rage a gurin, sai kuma kukan 'kananun dabbobin dake tashi. Cike da tsananin tsoro! da firgici! ta mike zaune tana lalube a gurun, masifaffan tsoro ne da ita, rarrafe ta fara ko'ina zata oho! yana kokarin tashi zaune ta afko kansa, fuskokinsu suka hadu, bakinta ya hadu da nasa, lokaci guda numfashinsu ya had'u! da sauri ta kautar da fuskarta, ta danne kirjinsa da hannu tana kokarin barin jikinsa, ba tare da wata manufa ba ya zuba dukka hannuwansa kan kwankwansonta, gefe guda ya ajiyeta, ta sake yunk'urin barin gurin domin kan ciyayi a ajiyeta tana kuma jin tsoron wani mugun k'waron ya cijeta, kafarta daya ya rike, can kasan makoshi yace." Ki samu nutsuwa."! kafarta ta fizge, da rarrafen ta lalubi daddumar ta zauna tana ya mutse fuskarta, gabadaya cinyoyinta sun dauki kaikaiyi da azabar zafi. Fitila ya kunna yana kallonta, sai yamutse ya mutse take, mikewa yayi ta kalleshi, yana kokarin barin gurin, da sauri tace." Ina zakaje."? Bai juyo ba domun ji yayi tambayar tayi kama data rainin hankali sai kace uwarsa tana masa magana gatse-gatse! Ya cigaba da tafiyarsa ba tare da ya amsa maganarta ba, kallonsa ta dinga yi tana mamakin girman jikinsa dogo mai garin jiki yana yanayi da jarumin kasar hindu *( Parbahs bahubali)* idonta a hanyar da yabi gabanta sai faduwa yake, can taji wani irin kukan dabbah! a bayanta, a zabure! ta juya tana zare ido! jin kukan na kara kusanto inda take yasa ta kurma ihu! sai ta fara jan gwiwa tana waiwayenta bayanta. Jin ihunta ya tashi hankalinsa da saurin gaske yasa bakin kokon dake hannunsa ya kamfaci ruwan dake gudana ya juyo da saurin gaske, me zai gani ita ya hango a gigice! tana rarrafe tare da d'aga masa hannu, haushi ta bashi, bega abun gudu a gurin ba, tuntuni sun saba yada zango a gurin, babu wata dabbah mai cutarwa da ke zuwa gurin. saboda su kansu dabbobin sun gane gurin, basa tunkarar zuwa sun san idan sun shiga basa fitowa cikin dadin rai. Koda ya k'arasa inda take sai kawai ta rike masa kafafu tana karkwarar jiki, "Allah yasa tsakanina daku azzalimai macuta." Kalmomin da suka futo daga bakinta kenan ta nayi tana dukan gwiwarsa harda cizo. Gabadaya ta kanainayeshi, tana dukansa, kuka take sosai! bece mata komai ba har sai da ta gaji da kukan ta cikashi, ta daga kai tana kallonsa, ya cije baki kamar yanda ya saba idan zaiyi magana "Na fahimci duk gidan da ki kaka fito babu tarbiya, bana shiri da mara kunya ba kuma na san raini! meye laifina anan? ina iya kokarina akanki kina zagina saboda kina takama da mulki da sarauta ko."? Hannu ta daga masa da fadin." Kaga malam ya isa haka kawai ni ka daukeni ka bar gurin nan dani." Ya girgiza kansa kamar koda yaushe idan zaiyi magana yace."Ba zaki samu hakan ba, yanda kika rarrafo da gwiwarki hakanan zaki biyo bayana." yana gama maganarsa ya fizge kafafunsa ya barta a gurin. Da kyar tayi yunkurin tashi tsaye, ta daga masa hannu da fadin." Don Allah kada ka tafi kayi hakuri ka dawo kafafuna sunyi tsami ba zan iya tafiya mai tsayi dasu ba." Yana jin maganarta be juyo ba ya cigaba da tafiyarsa, yana so ya fara koya mata hankali tunda ya fuskanci bata da mutunci. Takawa take tana ciccije baki, hawaye kuwa sai karakaina yake a fuskata, abubuwa da yawa sunyi mata dabaibayi, ciwo! tsananin fargaba da tashin hankali bakar azaba da yunwa ta rasa da wane bala'i za taji. Tun tana hangensa har ta daina, ta dinga tafiya cikin ciyayi tana jin saukar kwarika a kafafunta, ta riga ta saduda ta barwa Allah da wannan masifar da take ciki gwara wata dabbar ta cinyeta. Ya kai minti ashirin da isa amma shuru babu labarinta, a jikinsa yaji akwai wani abu tunda babu wata tazara mai tsayi tsakaninsu da bakin kogin. Bayanta yabi yana haske fitilar hannunsa, yaci tuntube da ita, kwance kafafunta sun rufta cikin wani rami da alama na wasu dabbobin ne, sai kici-kici take tana kuka, hannunsa ya mika mata, ta rike da kyau! yasa karfi ya fizgota! Ajiyar zuciya suka sauke a tare, be jira komai ba, ya sunkuya tare da juya mata baya, kafira!😂 bakin rashin kunya ya mutu, tana zazzare ido ta haye bayansa ya mike tsaye da ita, hannunta tasa sosai ta matseshi, sai ajiyar zuciya take, shi kam cakumar da take masa ta sanyashi shiga tashin hankali wanda sai yayi shekaru be shiga irinsa ba, huci kawai yake yana cizan lips dinsa, cikin mawuyacin hali suka isa gurin, Yayi gaggawar sauketa, tayi kwance a gurin tana fitar da numfashin wahala, shi kam can gefe ya matsa tare da juya mata baya, matsalarshi guda a yanzu halin da ya shiga, shigarsa a wahala amma fitarsa nada wuya yakan yi kwana da kwanaki kafin yanayin ya bar jikinshi. *Ga wa'inda basu samu damar karanta Sadauki Omar ba, zasu biya 1k domin samun damar karanta littafi biyu* *#500 via 0543282124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....* *22796074090* katin Mov ko airtal *GOJE!*🏹 🐕‍🦺🐕‍🦺🐕‍🦺 _(SADAUKI OMAR RETURN👑💫_) *BINTA UMAR ABBALE🍒* *_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION🖊️📚_* _____________________ _*INA MAFITA?*_ _*Matsalar dai guda daya ce data addabi tsakanin ma'aurata rashin hakuri da juna, wanda shike haddasa fitintinu masu yawa, ma'aurata shifa aure gabad'ayansa ibadah ne, jin dadinsa kadan ne, to mai yasa ba za'ayi hakuri da juna a mayar da hankali gurin ribatar ladan dake cikin auran ba*_ *WA YAFI LAIFI*? _*Shin wa yafi laifi a tsakanin ma'aurata biyu wato mace da namiji? ni dai ba zance ga wanda yafi laifi a tsakanin ma'aurata ba, saboda i dan akayi duba na tsanaki za'a fahimci cewa kowanne bangare da nasa laifin. a matsayina na mace bana goyon bayan 'yan uwana mata akan matsalar data shafi zamantakewar aure wanda kullum ta Allah sai na samu sakon da ya danganci wannan maganar da nake a yanzu, hankalina ya kan tashi idan naji yarinya karama auran fari haihuwa daya biyu kai wata ma auran beyi shekara ba zata kira waya ko ta turo sako tana kuka a taimaka mata da shawarwari yanda zata zauna lafiya a gidan auranta, haka zalika daga b'angaran mazan ma ina samun irin wannan sakkonin cewa baiwar Allah matata tana karanta littatafai na hausa amma bata daukar darasin komai karshe ma tarbiyar tace take lalacewa sakamakon karance-karance littafan da kuke rubutawa. ire-iren wannan sakkonin ba zasu lissafu ba, shin wai ta yaya marubuci zai lalata tarbiya? a ganina marubuci har in dai ya san abinda yake bai cancanta da a kirashi da mai aikata 'barna ba."*_ FREE PEGE *11&12* Tun bayan tafiyarsa farauta, Uwale ta samu 'kafar yawo, wanda idan yana gari ko nan da can baya bari taje a cewarsa ta tsufa abinda yafi cancanta a gareta ta zauna a gida ta huta, tunda shi yana iyakacin bakin kokarinsa gurin daukar dawaniyarta da duk wani abu da take bukata na yau da gobe. Ita kuma a nata bangaran haushin abinda yake mata take, ta dingi mita da surutai tana fadin ba zata zauna zuciyarta ta mutu ba sai ta fita ta nemi kudi kodan bada gudumawa idan sabga dangi ta tashi, Hakan ya sanyashi yanke hukunci a duk sanda zai fita sai ya sakar mata kare a gidan ya rufe kofar daga waje yayi tafiyarsa. A ranar yini take d'aki bata fitowa saboda yanda Allah ya zuba mata tsoron kare a rayuwarta, idan ya dawo gidan sai ta fashe da kuka tana fadin." *UMARU* saboda bani na haifeka shine kake azabtar dani, ka san sarai bana san kare amma saboda mugunta zaka sa min kare sannan ka rufe kofa ka tafi yawo to babu shakka wata rana zaka dawo ka samu gawata." Sai yace."Uwale idan kina so mu shirya dake ki daina dillanci domin kuwa kina zubar min da mutunci a gari, ni mutum ne mai zuciya da gudun magana bana son jama'a na ganin gazawata a kanki." *"UMARU* Ba zan daina dillaci ba saboda itace sana'ar data ci da kai ta shayar da kai har ka kai munzali, sannan kuma kana maganar zagin jama'a kai yanzu *UMARU* wane irin zagi ne jama'ar gari ba suyi maka irinshi ba, babu fa wanda yake maka kallon mutumin kwarai mai daraja, kowa yana maka kallon banza tare da kiranka da sunaye masu muni! *B'arawo* *'Dan ta'addah!* duk saboda wannan harkar daka jefa kanka a cikinta, Mahaifinka da bakin cikin hakan ya mutu dalili irin zagi da habaice-habaicen da mutanan gari ke masa, bana rana dayan biyu bakin cikinka ne ya kasheshi." Duk sanda zata fad'i wannan maganar hankalinsa yana tashi mutu'ka, shi fa har yanzu bai ga illar abinda yake aikatawa ba, na farko bai ta'ba tare wani a hanya ya k'waci abunsa ba, na biyu tunda yake ba'a ta'ba kamashi ya haura wani gida yayi sata ba, na uku bai ta'ba yiwa yarinyar wani fyade ba, abu na karshe shine baya muggan! shaye-shayen da zai janyo masa zubewar kima da mutunci, abunda ya sani shine yana busa Sigari sa'i da lokaci sai shan Shisha da ya zame masa masifa, wannan abu biyun sune abunda ya san yanayi bayan haka azimi sallah akan lokaci basa wuceshi, a ganinsa zagin da jama'ar gari ke masa k'in gaskiya ne, babban abin mamaki kuma duk sanda yayi nisan kiwo dashi da jama'arsa ma'ana suka fita farauta, to duk sanda ya dawo gari da yawa masu zagin nasa sune suke zuwa su gurfana a gabansa domin kar'bar maganin sanyin da yake guzurin zuwa dashi. Ita kanta Uwalen matan da suke zuwa gurinta kar'bar magani suna da yawa, wani sa'in yana kallo zata zabga kudi masu yawan gaske sai sun nemi alfarma a gurinsa sannan take sassauta musu, amma shi anasa b'angaran 'karamar sadaka yake kar'ba wani sa'in ma kyauta yake bayarwa yace sadaka ayi wa Annabi Salati dubu, Uwale tayi ta jin haushin hakan, idan ya fita sai ta samu buhu mai zurfi ta shiga dakinsa ta kwashe rabin maganin ta boye a karkashin gadonta, idan ta samu sarari ta fita cikin gari ta siyar akan kudi masu yawan gaske. Wannan dabi'ar ta kakar tashi tana b'ata masa rai, mutuka idan yana so ya tsoratar da ita akan ta daina abinda take sai yace." Uwale shifa aljani ba'a wasa dashi kuma wannan magungunan da nake zuwa dasu ba a banza nake samu ba, musulman aljanu ne suka lamunce min da hakan domin kin san kowane bawa da hanyar abincinsa to nima bani sukayi domin na taimaki jama'a idan kika wuce gona da iri zan barki dasu." Sai ta tsorata ta dinga rokansa kan cewa ya basu hakuri ta daina abinda take, yace shi babu ruwansa taje ta nemi inda suke ta basu hakuri ba maganarsa bace, kuka irin na tsofaffi take sawa ta rikeshi ta hanashi fita tace lallai sai ya basu hakuri sannan zai futa. sai ya fahimci tayi laushi sannan sai yace tayi shuru ya basu hakuri sun hakura amma kada ta sake aikatawa, Zata amsa da cewa ba zata sake ba, amma cikin ikon Allah idan aka kwana biyu zata manta ta cigaba da sayar da magani da tsada tana boye kudin a cikin adaka a cewarta da kudin zata hada masa lefen auransa. *********** Kishingide suka sameshi a gurin hutawarsa, ya mike zaune tare dan gyara zama ido ya tsira musu har suka samu guri suka zauna kafin su gaisheshi, ya amsa still idonshi na tsaye a kansu mussaman mutuniyar tashi da yake hango rashin walwala a tare da ita, koda yake tunda al'amarin ya faru gabadaya walwala da farin cikinsu ya gushe duk abinda suke karfin hali ne. Gyaran murya yayi kafin yace." Idan kaga wata to za kaga zarah Aysha Safara'u wannan tafiyar taku tana burgeni." Babu wacce ta saki fuska a cikinsu, domin kuwa suna ciki dashi sakamakon hade kai da yayi da matarsa suna daukarsu a matsayin marasa tawakkali. D'aya daga cikin hadimanta ne yaje ya sheda mata cewa yanzu - yanzu ya gansu sun nufi gurin hutawar Maimartaba Da saurin gaske ta shiga daki ta shiryo ta fito kai tsaye can ta nufa, tana sauri taje ta riski abinda ya kai su bayan itace da girki. Tunda ta doshi gurin take hangoshi gabadaya hankalinsa yana kan wacce ta tsana a cikin matan nasa fuskarsa akwai alamun sassauci da rarrashi, gabadaya ma kamar ita kadai ce a gurin babu Safah. Ta isa gurin da sallama wacce bata fito sosai ba. Ya amsa yana kallonta kafin ya kallesu da fadin." Kuna ji 'yar uwarku na muku sallama kunyi shuru." Safah ta amsa a ciki Aysha kam ko kallonsa ba tayi ba ballanatana 'yar koran nasa. Ta samu guri ta zauna tana ya mutse fuska da fadin." Ranka shi dade barka da dare." Ya amsa "Barka dai Maijidda ya hidima." Ta amsa "Alhamdullhi." Gurin yayi shuru na 'yan mintina kafin gimbiyar ta kalleshi babu fara'a tace."Ranka ya dade wannan magana iyakacin nida kai da 'yar uwata muka tattauna bana son wani yaji abinda ya shafeni da zuriata." Ya 'bata rai da fadin." Aysha wannan wace irin magana ce? shin ita Maijiddan bare ce a cikinmu."? Ta d'aga masa hannu da fadin." Allah shi gafarta maka tunda na fara maganata kaji sunan Maijidda a bakina."? Ransa ya baci mutuka, yace." Ki sauke hannunki idan ba hakana ranki ya b'aci zaki nuna min abinda zanyi ne? ko kuma zaki hanani iko da abinda na haifa? dake da ita Zinat din da ita Safa da Maijiddan duk ikona ne to ke baki isa ki tsara min yanda zanyi ba." Maijidda ta fashe da kuka da fadin." Ranka ya dade na rasa me yasa har yanzu matarka bata kaunata, meye laifina ? me kuma nayi mata? haihuwa dai Allah ke bayarwa ba wani ba, nima ban cire rai ba." Tausayinta ya rufeshi, sassauta murya yayi yace." Maijidda kada ki sanya damuwa a ranki nida na aureki nafi kowa sanin halinki babu wanda zai kawo min jita-jita a kanki na dauki maganarsa, maganar haihuwa kuma kada ki cire tsammani, zaki haihuwa da izinin Allah, bayan haka kuma baki da shamaki da zuriata zaki iya yanke hukunci akansu ba tare da na daga kai na kalleki ba." Gabad'aya suka kalleshi a lokacin da yake wannan maganar, Aysha gaza hakuri tayi tace." Ba zai yuwu ba ranka ya dade ana duba nagarta da cancanta kafin a yanke hukunci babu wani d'a da zan haifa na amince ya dauki wannan matarka taka a matsayin me kaunarsa duk mutumin da ya fito da kiyayyarsa a sarari a kanka be kamata kayi rayuwa dashi ba. Gabadaya sai suka rasa inda maganarta ta dosa, ta mike tsaye tana gyara lifayar dake nade a jikinta, sunkuyawa tayi da fadin." A tashi lafiya." Bakinsa ne ya mutu kawai ya bisu da kallo a lokacin da suka kama hanyar fita, Ya girgiza kai yana jimanta al'amarin wato dai har yanzu Safa taki zama cikkakiyar mai 'yanci a gidan auranta, tana biyewa Aysha suna zuwa har gabanshi suna masa rashin kunya, to babu shakka zai sa kafar wando guda dasu. *********** Washe garin ranar da ciwon ciki ya tashi, yaransa suka kewayeshi suna masa sannu, yana kwance idanuwansa a lumshe yake amsawa, daya daga cikin rayan nashi, yace." Allah ya taimaki *Mai dawa!* ga magani na had'a maka." A hankali ya bude idonshi ya dora kan 'kwaryar maganin dake hannunsa, ya mutse fuska yayi ya mayar da idonsa ya rufe da fadin." Alba ka ajiye wannan maganin ka matsa min lemon tsami guda shida." Da sauri yace." An gama ranka ya dade. Ya dan sauke numfashi tare da sake rintse idonsa shi kadai yasan irin ciwon da marar shi ke masa. Alba ya k'araso gurin cike da bin umarni yace." Allah yaja zamaninka ga abinda ka bukata. Ba tare da ya bude ido ba yace." Nagode Alba kuna iya tafiya Allah ya bada sa'a." Suka amsa da ameen kafin su bar gurin sai da sukayi yi masa kirari kamar yanda suka saba. Kimanin minti biyar da tafiyarsu ya tashi da kyar, ya jima yana yamutse-yamutse kafin ya dauki matsatstsan lemon tsamin ya shanye tas, ya ajiye ya koma ya kwanta, yana danne saman cikinsa. Tayi mamaki da gari ya waye be zo ya dubata kamar koda yaushe ba, kawai tashi tayi a bacci ta samu ruwa cikin kwarya da asuwaki sai manya manya ayaba da mangwaro a gabanta. Ta wanke bakinta da fuskarta, dama can ibadah bata dameta ba domin data dameta da duk yanda za tayi sai tayi ta gabatar da sallolin da suke kanta. Yunwar da takeji bata tsammanin Ayaba da mangwaro zasu kawar da ita, taja tsaki tana harare-harare a gurin da babu motsin kowa sai ikon Allah. Jikinta ta duba tayi fututu! fatar jikinta duk ta bushe tayi datti! ta dubi qunar da duk ta bushe tana mata kaikayi, ruwan hawaye ta goge tana tunanin jin dadi da irin rayuwar da take ciki amma lokaci kankanki rayuwa ta juya mata baya. Kullum idan za ta kirashi da *'Barawo* zai kalubanceta kan cewa shi ba *'Barawo!* bane to idan ba haka ba waye silar zuwanta wannan kasurgumin dajin."? Ta girgiza kai cikin qunar zuciya ta kudiri aniyar irin rashin mutuncin da za tayi mata huce takaicinta. Ayaban kadai ta iya ci ta dauki kwaryar ruwan ta shiga tsakanin bishiyu kayanta jikinta ta cire tas ta wanke jikinta, gurin wankan ta jike rigar data zame mata garkuwa, bata damu ba kawai tasa breziyya ta mayar da wandonta ta fito a haka, taja ta tsaya tana dube-dube a gurin. Babu motsin mutum sai kukan tsintsaye da alama yau ma sun fita sun barta a dajin ita kad'ai. Ajiyar zuciya mai zafi ta sauke taja tsumman zanin ta dan daure tsakain cinyoyinta kafin ta nemi saman wani kuttuturun icce ta zauna tana tunanin halin da iyayenta ke ciki na rashinta, ta san mahaifinta sai yafi kowa shiga tashin hankali rashinta a kusa dashi. Ya kai minti arba'in cikin halin ni 'yasu kafin Allah ya sassauta masa, ya mike zaune da kyar! duk da halin da yake ciki hankalinsa na kanta burinshi ya tashi yaje ya duba halin da take ciki. Ya mike babu kuzari a jikinsa, kai tsaye gurin da take ya nufa...................Rintse idonsa yayi da karfi yana Auziya a fili sakamakon ganin da yayi mata ita ba tsirara ba ita mai tufafi domin breziyar dake jikinta bata hanashi ganin kamai ba........"Subahanallah ! Ya jima a tsaye a gurun yana kiran sunan Allah! kafin yayi namijin kokarin bude idonsa yayi ya'ki da shaid'an da kuma zuciyarsa ya durfafeta babu alamun wasa a tare dashi............ *Don Allah idan ba sayan littafin nan zaki ba kada ki dauki number ta kiyi min magana abubuwan da yawa Nagode🙏🏻🤝🏻* *Ga masu bukatar sadauki Omar 1k za'a tura domin samun damar karantawa littafin tare da Goje! sadauki Omar return* *#500 via 0543282124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....* *22796074090* katin mov ko airtal. *GOJE!*🏹 🐕‍🦺🐕‍🦺🐕‍🦺 _(SADAUKI OMAR RETURN👑💫_) *BINTA UMAR ABBALE🍒* *_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION🖊️📚_* _____________________ FREE PEGE _Ina mika sa'kon ta'aziyya ta ga al'ummar musulman duniya baki daya, Na babban rashin da mukayi, hakika ba zuri'ar Malam kadai ne sukayi rashi ba duk duniya ne, muna rokon Allah ya jikin Malam Ahamad B.u.k (Bamba) Ya sanyashi cikin Aljanna madawwamiya Allah ya kyauta namu zuwan bayan tasu🙏_ *9&10* Ya jima yana kokarin kawar da yanayin daya yake ciki amma abun ya gagara! yakan zama sakarai mara dubara a duk sanda irin wannan yanayin zai shiga jikinsa, gabadaya wayo da dubararsa nemarsu yake ya rasa, jikinsa ya takure guri daya, yana jin wani irin sanyi tare da tashin tsigar jiki. Ba da son rasa ba ya juya kanta, yaga tana wanke fuskarta da ruwan daya ajiye, Asuwaki ya mika mata tabi asuwakin da kallon banza kafin tasa hannu a wulakance ta karba, duk da asuwakin sabo ne sai da ta wankeshi sannan tasa a bakinta, dauke kansa yayi yana girgiza kai ya lura da yarinyar kyankyaminsa take, a tunaninta ko yasa asuwakin a bakinsa. Wani buhu ya janyo ya dauko wasu mangwaro masu nuna manya guda uku, ya wanke tas karamar wuka ya zaro daga jikinsa ya mika mata mangwaron da hade da wukar. Hannu na rawa ta kar'ba yawunta na tsinkewa, bala'in yunwa takeji dama. Kafin tayi amfani da wukar sai data tasa ruwa ta wanke duk da tana ganin acikin gidanta ya fito da ita amma bata yarda da tsabtar duk wani abu da zai fito daga jikinsa ba. Inda Allah ya taimkashi, kayan dake jikinsa masu kauri ne wannan dalilin ya hana girmanshi fitowa amma a zahiri gabanshi yana tsaye kyam! sama da awa daya da rabi yaki kwanciya duk da 'yan dabarun da yayi abun yaci tura, sa'i da lokaci yana shiga irin halin amma na yau yafi muni. Itacuwa ya had'a ya kunna wuta ya zauna yana gasa jikinsa duk a kokarinsa na ganin ya kawar da abunda ke damunsa. Ita da take zaune ba tsirara ba ba kuma mai suttura ba, ta yun'kura ta mike da kyar take tafiya har ta cimma inda yake jin zaune. Zata zauna ya daga mata hannu, ba tare da ya kalleta ba yace."Ki koma ki zauna a inda kike ko kina bukatar wani abu ne."? Hararsa tayi tana murguda baki kafin tace."Naga kana shan dumi kai kadai shiyasa nazo nima ina bukata. Tana maganar tana kokarin zama kusa dashi. Tun daga sama har kasa yake bin ta da kallo, har ta samu guri ta zauna tana kara hannuwanta a jikin wutar, yanayin zaman da tayi yayi masifar jefashi cikin tashin hankali, inda ita kuma a wautar ta bata kawo komai ba tana ganin ai da tun farko yayi niyyar lalata da ita to da yayi amma ta lura sam ba wannan ne a gabanshi ba. Ya dinga kokarin dauke kansa da kanta amma Shaidan yana kara 'kawata masa suffarta, gaza dauke idanuwansa yayi daga kanta, ya cigaba da satar kallon wasu guraran da suka bashi sha'awa a jikinta, amma be yarda ta fahimci halin da yake ciki ba. Sun jima a haka babu wanda yayi magana a cikinsu, kafin suji bushe-bushe na kusanto inda suke da alama yaranshi ne suka dawo daga farauta. Ta kalleshi a lokacin da ya tsirawa shara'ban kafarta ido. Tayi saurin gyara kafafunta tana watsa masa harara. Ya sauke ajiyar zuciya tare da sake tamke fuskarsa cike da bada umarni yace."Ki tashi ki bar gurin nan." Yanda yayi maganar babu wasa yasa ta tashi tsaye, yayi saurin dauke kansa, kawai sai taja masa tsaki ta wuce! Abin ya bashi mamaki mutuka! ya girgiza kai tare da nazari da tunanin matakin da zai dauka a kanta Gurin gabad'aya ya rikice da gangi da bushe-bushe duk a sakamakon dawowarsu, hannu tasa ta toshe kunnuwanta takaici kamar ya kasheta, da yake da akwai hasken wutar daya kunna tana kallo suka dinga firfito da matattun macizai da mesa tare da sauran dabbobin da suka farauto, Abun ya dinga bata mamaki ganin sun daga wani lafcecan maciji sun sanya wuka mai kaifi sun rabashi gida biyu, suka tsire shi a jikin wani itace kafin su barbada masa gishiri da wani abu ja da alamar manja ne sannan suka sanyashi a wuta suna gasawa. Hankalinta yayi bala'in tashi, karni da wari duk ya cika gurin zuciyarta ta dinga hantsilawa saboda tsabar kyankyamin abunda suke. Tana nan zaune tana kallon ikon Allah suka gama gasa maciji nan wanda bai sani ba sai yace bushashshan kifi ne suka fara yankarsa da wuka suna ci hankalinsu a kwance. A gurin ta dinga kyalaya amai duk sai da ta amayo mangwaron data sha, taja gefe guda tare da toshe hancinta. Sai da dare ya tsala sosai sannan kowa ya nemi makwanci, yana sanya kafarsa yaji ya taka abu cabal! yayi saurin kunna fitilar hannunsa yana dubawa, aman da tayi ne duk ya bata kan shimfidar, tana rakube a gefe guda bacci ya dauketa. Yaji takaicin bata mai shinfida da tayi yaja tsaki tare da samun ruwa ya wanke kafarsa ya dawo yana tunanin inda zai sanya hakarkarinsa ya kwanta ba don bacci ba. Kusa da ita ne kadai babu kazanta kuma baya so ya kusanceta gudun abinda ka iya zuwa ya dawo, domin har yanzu yanayin be bar jikinsa ba. Kawai sai ya yanke shawarar zuwa gurin yaranshi domin samun matsuguni, tsakaninsu babu wata tazara mai tsayi kuma yana da tabbacin babu abunda zai sameta, rigar jikinsa ya cire ya rufa mata a jikinta sannan ya bar gurin. Da yake baccin ya dauketa a cikin tsoro da fargaba yasa ta dinga munanan mafarkai da namun daji sun biyo ta zasu cinyeta sai ta farka a gigice! tana kwalla ihu! da fadin." Kura ce! kana inaaaa! *GOJE!!* zata cinyeni."! Gabadaya suka tashi tsaye da shirin ko ta kwana, amma ba subi bayansa ba, shine ya cimma inda take tsaye sai rawar dari take a tsaye. Yana zuwa ta rungumeshi, tsam! tsam! tana wani irin kuka da fadin." Kura ce ta biyo ni."!!! Ya dinga nanata mata addua a kunnuwanta har ta samu nutsuwa, ya zaunar da ita, amma fafur taki zama wai dole sai sun zauna tare. ta rike masa hannu katamau! Shi kam taushin hannunta da dumin da yake shine yayi masifar sanyayyar masa da jiki, Babu zato babu tsammani ta janyoshi duk karfinsa, sai ya tsinci kansa a zaune a kusa da ita, yayi mamakin hakan mutuka A maimakon ta saki hannunsa, tunda yana kusa da ita, sai ma ta sake shigewa jikinsa, tana boye fuskarta a kirjinsa dake waje babu riga sai singlet. Tsigar jikinsa ta tashi gabadaya ya rasa nutsuwarsa, so yake yafi karfin zuciyarsa amma ta kanainaiyeshi, ta hana shi tsira da mutuncinsa. Haka suka wanzu har asubah! tana makale a jikinsa, ta hanashi sakat daga yayi motsi zata zabura! ta matseshi, tana goga masa sassan jikinta. Da kyar ya iya furta magana." Sai ki sakeni haka asubah tayi babu wata dabba da zata zo ta cutar dake." Kanta ta cire daga kafardarsa tana kallonsa da jajayen idanuwanta tace."Kayi wa Allah da Annabi ka hada tawagarka mu bar dajin nan! duk abunda kuke bukata mahaifina zai baku kada ka cutar dani ko kuma wata dabbar tayi sanadiyar rayuwata. Ya jima yana mamakin furucinta ashe tana da hankali irin haka. Sai shi ma yayi mata magana irin ta samu hankali yace."Bana bukatar komai a gurin mahaifinki, kuma ki daina dora zarginki akaina ni ba 'barawo bane Allah ya nufeni ne da na taimaka miki." Yana kare maganarsa ya nufi bakin kogi da asuwaki a hannunsa, kallo ta bishi dashi har kurewa ganinta kafin ta girgiza kai tana tunanin wani abu akansa. Sai da gari yayi haske sosai sannan ya dawo gurin dunga nesa yake hangota a kwance rigingine, ta dogare kafafunta a kasa cinyoyinta a waje amma ta suturta gabanta, saurin dauke kansa yayi har ya karasa gurin be sake kuskuran kallonta Ya dauki rigarshi data cillar masa ya rufa mata a jiki, baya so yana ganin abinda zai tayar masa da hankali. Ai da sauri ta cire rigar ta cillar da ita can tana ya mutse fuska, zaune ta tashi tace."Idan zaka kwana kana rantsuwa cewa kai ba dan ta addah bane ba zan yarda ba wallahi." "Ke baki isa nayi rantsuwa a kanki ba, kuma idan kika sake kirana da wannan sunan zan nuna miki ta'addanci na."! Yanda yayi maganar shi ya tsorata sai tayi shuru amma bata fasa yi masa kallon banza. Ya dauki rigarsa data jefar yana girgiza kansa ya rasa wace irin yarinya ce me manta alkairi ina laifin wanda ya suturta ka. Rigar ya sanya a jikinsa, can kasan makoshi tace." Kazami kawai." Yaji abinda tace amma be tanka mata ba, ya juyo, tayi saurin dauke kanta, janyeta yayi kan daddumar ta fadi kasan gurin, ba tare da ya saurareta ba ya bar gurin da daddumar a hannunsa. Ta ciji yatsa tana bin bayansa da mummunan kallo. Daya daga cikin yaransa ne ya karbi daddumar ya wanke tas ya shanya kan wata bishiya. Ya umarcesu da suyi shirin fita shima tare zasuje don baya tsammanin zai zauna da yarinyar tana 'bata masa rai bayan masifar data jefashi a ciki. Be saurareta ba ya hada kan tawagarsa suka fice ba tare data sani ba, hankalinta ya kai kololowa gurin tashi, lokacin data fahimci ita kadaice a cikin dajin sai ta raina kanta da wayonta, tana kuka ta kama hanya ta cire tsoro da fargaba kokarinta ya za'ayi ta fitar daga kanta daga cikin masifa. Aikuwa kanta ne ya juye! a maimakon tayi baya sai ta dinga gaba, tana kutsawa cikin dogwayen bishiyu na kuka da tsamiya nan ta dinga arba da manya manyan birai iyaye da 'ya'yansu, hankalinta ya tashi, abinda ta tsana kenan a rayuwarta, gwagwgwan biri! ido sukayi da wani kato ya tsufa sosai! yana zaune duguzun-duzugun jikin wata narkekiyar bishiyar kuka! Da baya da baya ta farayi kafin ta juya a sukwane tana falfala gudu hade da kiran sunansa *GOJE!!* shi kuwa Gwaggon birin nan dariya yayi da ya fahimci tsoronsa take sai ya kudiri aniyar tsokanarta, ya fara bin jikin bishiyu yana tsalle yana mata dariya har ya dura a gabanta. Zubewa tayi tana daga masa hannu yawun bakinta ya bushe "Don Allah kayi hakuri! wayyo Allah na wayyo na shiga uku kuka ta dinga yi hawaye da majina sunyi kaca kaca da fuskarta. Daya bayan daya suka kewayeta iyaye da kakanni! da alama sassaninsu ta shigo bata sani ba. Kanta ne ya dinga juyawa a gurin kafin ta fadi, suma tayi, ba tare da bata lokaci ba wannan dattijon birin ya dauketa yasa a kafada, kataf-kataf ya fara tafiya da ita iyalinsa suka rufa masa baya. Dabaru irin nasu sukayi mata ta dawo hayyacinta koda ta bude ido ta ganta a tsakiyarsu, sai ta mayar da idonta ta rufe jikinta sai karkarwa yake, su kuwa suna zazzaune sai cin manya manya ayaba sukeyi suna gurnani da alama zantuka suke a tsakaninsu. Sai gefin magariba suka dawo, hankalinsa ya tashi lokacin daya duba sama da kasa be ganta ba, Dajin ya shiga yana yana sasssare mattatun itatuwan da suka cika gurin, ya fito da sarewa yana busawa tare da cigaba da ratsa cikin dajin. Zumbur! ta tashi zaune jin busar sarewar na kusanto gurin da suke, daga can nesa ya tsaya yana hango tawagarsu tana tsakiyarsu sai kace 'yar tsana saboda kankanta. Kai tsaye gurin ya nufa yana cigaba da busa sarewar dake bakinsa, tsakiyarsu ya shiga yayi wani irin tsugo gaban dattijon birin nan yana me cigaba da busa abinda ke bakinsa, Murmushi yayi ya dora hannunsa me cike da gashi da farata zako-zako a hannunsa a saman kansa, kafin ya cire ya nuna masa ita, yana gurnani! Kansa kawai ya girgiza ya nufi inda take, hannu ya mika mata ta mike tsaye kafafunta sai kyarma! suke a haka suka bar gurin. Saboda fargaba da mutuwar jiki yasa gabadaya kafafunta sukayi sanyi da kyar take iya jansu, bakinta ya mutu murus! tsabar tashin hankali binsa kawai take duk inda yaja ta, b'angaransa kuwa yana sane yaki goya ta saboda tayi bala'in bashi haushi, ya tabbata idan wata dabbar ce sai yasha mutukar wahala kafin ya samu damar fito da ita daga cikinsu idan sun barta da rai kenan. Wannan Gwaggon birin sun saba dashi sosai duk sanda zasu shigo farauta dajin basu da matsala dashi da iyalinsa, wani sa'in ma har kyautar ayaba mai yawa suke basu. Cikin mawuyacin hali suka karasa gurin da suka yada zangon ya jefar da ita ta fadi kasan gurin, zaune ta mike tana kallonsa ya juya mata baya gabadaya jikinta yayi sanyi domin ba tayi tsammanin zata cigaba da rayuwa ba. Cikin wani irin amo! taji maganarsa. "Kada ki kuskura ki sake barin gurin nan dana ajiye ki domin kuwa yin hakan na barazana da rayuwarki, babu inda yake da tsaro a cikin dajin nan fiye dana nan gurin, idan kika sake fita yawo to ba zan sake yunkurin ceto rayuwarki ba, yau kwananmu biyu sai kuma munyi sati guda kafin mu koma gida don haka ki kiyaye rayuwarki kibi umarnina kuma mutukar kina bukatar cigaba da rayuwa.'' Kuka ta fashe! dashi ra rarrafa ra rike kafafunsa, " Kada kace haka mana! ka tausaya min a matsayina na mace mai rauni ka fitar dani daga wannan dajin ni ba zan iya sati a guda a cikin wannan tashin hankalina ba, wallahi komai kake bukata mahaifina zai maka ka taimakawa rayuwata." Yanda take kuka tana rokonsa sai ku dauka mutuniyar kirki ce, haka take dama a duk lokacin da zata ganta cikin wata ukubar takan gigice ta saduda amma daga an kwana biyu sai ta koma baya. Kafafunsa ya cire ba tare daya ce mata komai ba ya bar gurin, Hakan da yayi ya 'bata mata rai! sai kawai ta kullaceshi a ranta, ta kuma kudiri aniyar wani abu a ranta zata tayar masa da hankali wanda zai daga Masa hankali dole ya kaita gaban iyayenta........ *#500 via 0543282124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....* *22796074090* Katin Mov ko airtal *GOJE!*🏹 🐕‍🦺🐕‍🦺🐕‍🦺 _(SADAUKI OMAR RETURN👑💫_) *BINTA UMAR ABBALE🍒* *_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION🖊️📚_* _____________________ *Mijina mazinaci ne* _________ _Mazinacin namiji daban yake a cikin maza, duk irin kokarin da za kiyi a kanshi to hakan ba zai hanashi neman matan banza ba, da yawa daga cikinsu jarabtace daga Allah! amma kuma son zuciya yafi yawa a ciki, 'Yar uwa idan Allah ya jarrabeki da auran mai irin wannan dabi'ar, ba zama zakiyi ba addua zaki tsananta akan Allah ya kawo miki mafita, Allah kuma ya shiryeshi ya gane hanya mai kyau. amma mafi alkairi a rayuwarki rabuwa da auransa domin samun zaman lafiyarki, koda kuwa akwai zuria a tsakaninku rabuwar ita tafi alkairi._ *Ubangiji Allah ka shirya mana mazajenmu ka dauke hankalinsu daga kan haram ka mayar da hankalinsu kan halalinsu, mu kuma Allah ka bamu hakuri da juriar dawainiya da bukatunsu.* FREE PEGE *17&18* *UBAN DABA!* Ya gagara! yayi shura! a harkar ta'addanci! ya addabi 'kasa da jama'ar dake cikinta, ran mutum abun banza ne a gurinsa, da yawa jami'an tsaro suka shiga sassaninsa, basa fitowa da rai! idan anyi sa'a wasu su fito a raye to za'a samu muggan raunika a jikinsu, shekaru bakwai kenan daya kafa sansani a cikin dajin dashi da jama'arsa, manya manyan bishiyun kuka ciki suka fafake ya zama makwancinsu, duk abunda yake faruwa a cikin gari yana samun labari akwai redio a tare dashi, bayan haka kuma yakan tura yaran sa suyi badda kama su dauko masa rahoton abinda kasa take ciki. Masana sunyi hasashen cewa Gurin da ya kafa sansani akwai albarkar kasa a gurin, irinsu gold da man fetur da sauransu, wannan dalilin yasa shima ya tsaurara matakan tsaro a gurin, babu wanda yake amfana da albarkar dake gurin sai shi da jama'arsa, duk sanda suka haqo gold din akwai wani hamshakin dan kasuwa dake zuwa ya saya. cikin dare ya kan shiga dajin kar'ba! ya basu kudi da kayan masarufi, sannan a duk sanda sukayi ra'ayi zasu badda kama su shiga cikin gari suyi siye-siyen abunda suke bukata. *Mashekin daji!* Hatsabibin mutum ne wanda yake da suddubaru! duk sanda hukuma ta tura jami'anta binkice a dajin, basa nasarar ganin sansaninsa amma kuma shi da jama'arsa suna ganin duk irin d'auki ba dadin da jami'an tsaron keyi a kok'arinsu na ganin sun ga mafakarsu, wannan damar suke samu su karkashe wanda sukayi ra'ayi, sai dai a fito da gawarsu. *GOJE!* Ya jima da jin labarin hatsabibancinsa, kullum tunaninsa ya za'ayi ya kawo karshen ta'addancin daya ke a kasa. Kafin ya yanke shawarar tunkarar inda yake sai da ya zauna da yaransa domin yaji ra'ayinsu, da yawa daga cikinsu jikinsu ne yayi sanyi domin dai sun san tunkarar mutumin babban al'amari ne! dalili shi akwai kayan aiki a tare dashi da jama'arsa, duk da suma suna da dabaru amma a ganinsu tunda sojoji da 'yan sanda suka kasa samun nasara a kansa to waye zai iya . Ganin jikinsu yayi sanyi yasa ya karfafa musu gwiwa da fadin." Su cire tsoro a cikin ransu, kada su sanya a ransu cewa *masheki* da jama'arsa zasu samu nasara a kansu, idan sun yarda da kansu cewa sunfi karfi wuka da bindiga to tunkarar inda yake abune mai sauki bayan haka kuma su dauka cewa wannan aikin da za suyi kamar jahadi idan ma Allah ya kaddara mutuwarsu a gurin aljanna ce makomarsu. Wannan maganar da yayi ya sanya suka samu karfin gwiwa, suka kwanta da shirin tunkarar *masheki* ba tare da k'asa ta san abinda suke shirin aikatawa ba. Tafiya suke tsakankanin bishiyu da manyan tsaunika, gami da kwazazzabe, gabadayansu, babu alamun gajiya a tattare dasu, tafiyar suke suna bushe-bushe tare da farautar duk wata dabbar data gilma a gurin, ita dashi ne a gaba, yayin da jama'arsa ke take masu baya, tayi masifar galabaita! bakinta ya bushe cikinta in banda qugi! babu abinda yake, ba komai ke damunta sai yunwa, kallonshi tayi kamar tunda aka halliceshi be taba dariya ba, tunda ya rike hannunta da zasu tafi be sake kallonta ba ballantana magana ta had'asu, Magana takeso tayi masa amma tana jin shakka! don yanayin sa kadai dole ya baka tsoro! sai taja ta tsaya cakk! tana sauke wani irin numfashi! Kallonta yayi na minti biyu, kafin ya juya yayi masu magana da ido, sun gane abinda yake nufi, sai suka samu guri suka zazzauna wasu kuma suka fara hawa kan bishiyu suna kad'o 'ya'yan itace. Kan wani ice ta zauna tana kallonsa sai kai kawo yake a gurun.........."Ina bukatar ruwa da abinci." tafada tana dam hararar bayansa. Yana jin maganarta amma be juyo ba. "Ina magana fa."! tafada kamar zata fashe da kuka. " Alba." sunan d'aya daga cikin yaransa kenan. Yayi saurin zuwa gurin, yace."Ka bata ruwa da abinci." Yace." An gama maigida. Gabanta ya k'araso da wata 'yar jarka ruwane a ciki, ya mika mata da fadin." Kisha yanda kike so" Cike da k'yan'kyami take bin jarkar da kallo, 'ya'yan wasa sun tashi a cikin ruwan. Tsaki! taje cikin tsawa! tace."Wuce ka ban guri waye zai sha wannan kazantaccen ruwan." Maganar ta dauki hankalinsa ya juyo yana kallonta, shi kansa Alba d'in ransa ya baci da jin irin tsawar data buga masa. Ya kalleshi da fadin." Jeka kawai." Ya girgiza kai, da fadin" Angama." Gurin ya bari. Shi kuma ya juya mata baya, tunda ba zata sha ruwan da kowa yake sha ba sai ta zauna a haka. Ranta ya baci ganin ya juya mata baya tace." Wai me ake nufi ne."? Ba tare da juyo ba yace." Ya kike so ayi miki? an baki kince bakya so akwai wanda kike so ya zama ruwa a cikinmu kisha."? Tace." Ruwan fa bashi da kyau, bayan haka ya za'ayi na hada bakina dana wannan 'kazamin." Ya girgiza kai da fadin." Sai ki zauna da ishirwarki ." Kuka! ta fashe dashi! da fadin" Allah ya isa tsakanina da kai mugu azzalimi."!! Ya juyo da fuskar bacin rai yana kallonta.....Alba dake kokarin zuwa gurin yace."Oga wannan yarinyar fa tana da matsala wallahi! da zaka bani dama sau daya dana koya mata hankali ." Ya kalleshi na minti biyu kafin yace." Ko bana guri ban amince da hakan ba amana ce a gurina." da sauri yace."Allah ya huci zuciyarka." Ya gyada kai da fadin ." Wanke lemon ka bata." Da sauri yayi abinda aka umarceshi, ta kar'ba tana yatsine fuska. Yana kokarin barin gurin yace."Bani wannan jakar ruwan ta hannunka." Ya mika masa, a gabansa ya bude murfin ya zubar da ruwan ciki. Ya bar gurin da ita a hannunsa. Ita dashi duk suka bishi da kallo yana tsallake manya duwatsu kafin su daina ganinsa, gabanta ya tsananta fad'uwa ganin baya gurin, ta dora idonta kan Alba dake tsaye yana zazzare mata jajayen idanuwansa, saurin sunkuyar da kanta tayi, tsoro takeji kada yayi mata wani abun, sai da ya gama cije-cije kafin ya bar gurin. Ya kasance sai ita kadai a gurin, sai motsi da maganarsu da takeji a saman bishiyu, ta daga kai tana so ta hangesu, amma ta kasa ganinsu, Dajin ta dinga bi da kallo, kanta yana juyawa, manya dutsina da tafka-tafkan bishiyun dake gurin sun juyar mata da kai. Da sauri ta kama hanyar da taga yabi, tana tafiya tana waiwayen bayanta. Sai da yayi tafiya mai tsayi sannan ya cimma ruwa yana gudana daga kasan wani tsabtataccan dutse gare-gare dashi.........Ya haura wasu manya duwatsu kafin ya samu nasarar d'ibar ruwan. Yana juyowa kibiyar ta gilma ta gefan fuskarsa, da alama saita shi akayi Allah be bada nasara ba.......Da mugun sauri ya daga kanshi sama, can ya hango su saman wani dutse sun kai su biyar, yayi gaggawar fitowa daga tsakanin ruwan. Suma basu fasa harbinsa da kibiya ba. A gaggauce ya fara kurd'awa inda jama'arsa suke baya su cimma inda suke ba tare da shiri ba. sai dai me! biyoshi sukayi suna sakar masa harbi ta ko'ina!! K'aro sukayi da juna!! ya rike hannunta tamau! bayan wata bishiya suka 'buya, suka 'karaso gurin suna sassare matattatun itacuwan da suke gurin. Hannunsa dake cikin nata yake kokarin cirewa ta rike da kyau! tana girgiza masa kai! wai kada ya fita, ya sake yunkurin cire hannunsa ta rike! hawaye masu tsananin zafi suka wanke mata fuska, bakinta tasa a kunnansa, a hankali tayi magana "Kada kaje." Jajayen idonsa ya tsira mata! ta marairaice fuska, tana ro'konshi da idanuwanta. Tausayi ta bashi ganin yanda jikinta ke wani irin karkarwa, cikin zuciyarsa yace."Ba yanda za'ayi yana ji yana gani nasara ta kufce mai wannan ce hanya mafi sauki da zai tunzura zuciyar abokin gabarsa. Kafin ta ankara, ya fuzge! hannunsa, ya fice! ta leqa kanta tana hango artabun da suke a tsakaninsu, su biyar ne shi d'aya, amma cikin ikon Allah ya samu nasara a kan mutum biyu ukun kuma suka gudu!. Ya k'wace wukaken dake jikinsu, da sauran kayan ta addanci, kana ya d'aure musu hannuwa, gaba ya tisa su har inda suka yada zango shida jama'arsa. *#500 via 0542382124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....* *22796074090* dala dari katin Airtal ko mov *GOJE!*🏹 🐕‍🦺🐕‍🦺🐕‍🦺 _(SADAUKI OMAR RETURN👑💫_) *BINTA UMAR ABBALE🍒* *_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION🖊️📚_* _____________________ FREE PEGE *15&16* Sosai ta kwanta jinya sakamakon artabun da sukayi ita dashi, jikinta yayi mugun tsami! ta shar'be! a guri guda da kyar take iya motsa hannu saboda tsabar sanyi da jikinta yayi, al'amarin bai tashi tsananta ba sai da dare ya tsala tukkuna, ta kasa rintsawa gabadaya jikinta ya dauki ciwo! ga wani irin kaikayi da ciwukan jikinta keyi. Kuka ta dinga yi tana jan hanci! ita kam wannan bala'i bata san ina zata kai shi ba. Can cikin baccin daya dan fizgeshi ya dinga jin shashshekar kukanta, zumbur ya mike zaune, dama babu wata tazara a tsakaninsu, ya d'auki fitilar dake gefansa ya kunna yana daga inda yake zaune yake haska gurin da take. Hannu tasa ta kare fuskarta ta sake takure jikinta tana cigaba da zubar da hawayen azabah!. Ya karaso gurin da fitilar a hannunsa, ya dudduba ko'ina babu wani abu. tsugunawa yayi a gabanta yana duba fuskarta, hannu tasa ta doke fitilar ta fadi. a take ta mutu gurin yayi duhu! ya lalubi fitilar yana kokarin gyara batir din, amma ina ta rikice! yayi-yayi ta kama taki, haka ya hakura ya ajiyeta kafin yace." Kukan me kikeyi ko wani guri yana miki ciwo a jikinki."? Shuru tayi masa, ya sake maimaita maganarsa, uffan ba tace masa ba. Sai ya yun'kura da niyyar barin gurin tayi saurin rike gefan rigarsa, a rikice tace."Jikina ne duk yake ciwo ko'ina babu dadi." Yanda yaji tana magana a rikice da alamun kuka ya sanya ya gazgata maganarta, bece komai ba ya sake yunk'urin tashi. Ta rike gefan rigarsa da kyau! yaja! taja! sai ya juyo yana kallonta, da k'yar ta mike zaune kafin tace."Kada ka tafi kayi wani abu wallahi zan iya mutuwa." Yana da tsananin tsausayi mussaman akan 'ya mace! sai duk jikinsa ya mutu, ya koma ya tsugana yana dan ganin shatin fuskarta duk tayi wani iri idonta yayi jajawur! fuskar duk ta kumbura!. Be iya tausasa murya ba, amma sai ya tsinci kansa da sassaita muryasa yace."Yi hakuri ki sake min rigar na samo miki magani."! Hanci taja kafin ta sakar mai rigar ya tashi, tabi inuwarsa da kallo tana sauke ajiyar zuciyar wahala. 'Daya daga cikin yaranshi ya umarta daya had'a masa maganin ciwon jiki, da yake duk suna tafe da guzurinsu, ba tare da anja dogon lokaci ba, ya harhad'a komai ya nufi inda take dashi a hannunsa. Samun ta yayi tana rawar d'ari, domin lokacin sanyi asubah ya fara sai zazzabi yake kokarin rufeta, sai datse hakoran bakinta take. Cikin wani irin yanayi ya mika mata maganin da fadin." Kar'bi kisha wannan za kiji sasaauci sannan zaki samu bacci." Kasa kar'ba tayi saboda halin da take ciki kawai ido ta tsirawa fuskarsa hawaye na sharara! jikinta gabadaya yaki tsayuwa a guri daya saboda karkarwa!. Ya ajiye maganin hannunta ya lalubo ya rike a cikin nasa, nan yaji zafi rau!! ya sake shiga damuwa da ya fahimci zazzabi ne a jikinta. Sosai ya zauna a gurun ya kama dukkanin hannunta cikin kokarin sassaita muryarsa da sigar rarrashi yace."Zazzabi ne ko."? Sai ta fashe da kuka! mai karfi! kamar me jiran kiris! da sauri yasa hannu ya rufe mata baki yana girgiza mata kai! Hannunsa ta cire tana me cigaba da janyo kukan dake cin zuciyarta. Kawai sai ya tsinci kansa da janyota jikinsa, ya sata cikin katuwar rigar dake jikinsa, ya san nauyin rigar zai zame mata garkuwa gurin karkarwar da take. Da yake taimako take nema ba tayi wani turjiya ba mussaman da taji ta kan faffadan kirjinsa dake cike da gargasa ga wani irin dumi da ya fara ratsa jikinta, luf tayi ta kwanta sosai tare da sanya hannu a bayansa ta rikeshi kam! tana sauke ajiyar zuciya daki-daki. Sai da ya fara jin saukar numfashinta a hankali sannan ya dan gyara zaman shi, cikin wannan muryar daya aro yace." *GIMBIYA!* Yanda ya kira sunan yayi masifar kassara mata gabobin jikinta. Taji shi sarai! tayi shuru motsin kirki ta kasa mamakin ma take yanda akayi ta saki jikinta a kirjinsa ba tayi tsammanin zata yarda numfashinta da nasa ya hadu ba sai gata a kwance a kirjinsa male-male maimakon taji wari! ko wani abu makamancin haka na fita a jikinsa sai taji akasin haka, jikinshi baya fitar da wari! ko kad'an sai ma wani irin dumi! da takeji na ratsa ta, nutsuwa da kwanciyar hankali na sauka a sassan jikinta. *"GIMBIYA."* Ya sake kiran sunan daya sanya mata a lokacin, koda yake daman Gimbiyar ce shiyasa shima ya ara ya yafa. Dan motsi tayi amma bata amsa ba, kuma bata sakeshi ba, ya dan ja numfashi, jin yanayinsa yana sauyawa, ya fara kokarin cireta daga jikinsa. Ta dage! harda gyara kwanciya kamar wacce take kan katifa. Mamaki sosai ya rufeshi, tunda yaji tayi shuru kuma numfashinta ya daidaita ya san ta samu sassauci bayan haka kuma jikinta ya daina karkarwa da alamar zazzabin yayi nasa a guri, amma meye amfanin abinda take. Namijin kokari yayi ya cireta daga jikinsa, babu kunya ta zuba masa ido kamar wanda yayi mata laifi. Ya saisaita yanayinsa kafin yace."Sannu kina bukatar magani ko."? Shuru tai na minti biyu kafin ta kalli hannunsa, maganin ne yake kokarin sanya mata a baki. Tasa hannu ta buge kwaryar maganin gabadaya ya zube kasan gurin da jikinsa Cike da takaici da bacin rai yake kallonta, ta 'bata rai da fadin.'' Wane irin magani ne wannan me wari zaka sa min a baki." Ya hadiye b'acin ransa wannan karan bai sassauta murya ba da yanayin maganarsa yace." Ke ki kace jikinki na ciwo maganin karfin jiki ne." Ta'be baki tayi da fadin." Bana bukata." Bece komai ba ya tashi daga gurin tare da jin takaicin abinda tayi. Ta kalleshi da fadin." Ka bani aron wannan rigar ta jikinka na rufe jikina da ita tana da d'umi." Uffan bece mata ba ya bar gurin, minti uku ya dawo da irin rigar a hannunsa. Ya mika mata, ta kalleshi da fadin." Ta jikinka nake so."? Yace."Duk daya ce da wannan din." A yamutse tasa hannu ta kar'ba tana kokarin sawa a jikinta ya bar gurin . Sai kace suddabaru! hankalinta ya gaza kwanciya koda tasa rigar ta kwanta domin jin d'umi kasa nutsuwa tayi ta tashi zaune tana rawar jiki.......Me yasa ta kasa samun abunda takeso a jikin rigar! ita a tunanin kaurin rigar ne ya saukar mata da nutsuwa sai taga akasin haka. "Ba rigar bace mai rigar ne yasa miki nutsuwa da kwanciyar hankali." zuciyarta ce take mata wannan maganar. Da sauri ta k'aryata zuciyarta ta sake rurrufe jikinta da rigar tana korar abinda zuciyarta ke raya mata, babu yanda za'ayi ta amince da cewa wannan gantallalan ne zai zama garkuwa a gareta. Daya daga cikin yaranshi ne ya kawo mata ruwa da asuwaki da abin kari. ganin yanda maigidansu yake bata kulawa ya sanyashi gaisheta, bata amsa ba sai wukalantaccan kallon da take masa shida tarkacen da ya ajiye a gabanta. Girgiza kansa yayi baki a cije! ya bar gurun ba don kar ya dauki mataki akan yarinyar ya samu matsala da maigidansa ba, da sai ya fasa mata baki domin yaji ciwon kallon banza da tayi masa. Har gari yayi haske sosai tana takure cikin rigar har yanzu ta kasa tantance a wane iri yanayi take, Can ta hangoshi yana zuwa inda take, ido kawai ta tsira masa babu kiftawa sosai take mamakin tsananin kamar da yake da jarumi(Barbahs) tana bala'in son jarumin saboda jarumtarsa da iya soyayyarsa idan yana abu a film kamar gaske, zazzafar ajiyar zuciya ta sauke tana kokarin karyata abinda zuciyarta ke raya mata a kansa. Tsaf yake cikin shirin fita, ya sauya rigar jikinsa doguwar jallabiya ce browan mai gajeran hannu sai ya sanya dogon wadon jens kanshi nannad'e da bakin yadi yayi gammo sosai! idanuwan nan rad'au! da bakin kwalli! kafad'unshi rakwacam! da tarin kayan farauta, har da irin doguwar bindigar nan, hakanan wuyanshi da damtsan hannuwansa wasu irin abubuwa ne a d'aure.! kafafunsa sanye suke da wani irin takalmi mai tarin igiyoyi a jikinsa. Tunda ya tsaya a kanta take kallon kafarshi, mamakin kyawun kafar take, bata ta'ba kallon kafarsa ba sai yau, faratanshi tas babu kazanta sai kananun gashi dake kwance saman yatsun kafar. A tsorace ta dinga sauke ajiyar zuciya tana kokarin kawar da idonta daga kan kafar. taji muryarsa cike da wani irin amo!! "Tashi zaune." Yanda ya fadi maganar babu wasa yasa ta tashi tana kallon fuskarsa, babu fara'a yace." Zanja ragamar yara na wani aiki a cikin dajin nan, ina so ki kula da kyau! kada kiyi kuskuran barin gurin nan! ki kiyaye! mutukar kina so ki cigaba da rayuwa a duniya. Kuka tasa tana kallonsa da fadin." Me yasa ba zaka tafi dani ba, saboda tsabar mugunta shine zaka had'a kan yaranka ku tafi ku barni ni kad'ai! bayan ka san dajin bashi da kyau komai yana iya faruwa da rayuwata." Yace." Nan gurin yana da tsaro bayan haka kuma gurin da zamu shiga yana da had'ari shiyasa na yanke shawarar barin ki anan sai yafi miki kwanciyar hankali." Ta girgiza kai tana shakar hanci tace."Aa nifa ba zan zauna ba wallahi ko kun tafi sai na biyo bayanku." Yanda tayi maganar babu alamun wasa a tare da iya yasa yaji shakkar tafiya ya barta. Ya kalleta a lokacin da take kokarin mi'kewa. "Na fad'a miki abinda yake da akwai kina kuka ko."? Hannu ta d'aga masa da fadin." Nifa ba zan zauna ni kadai a wannan gurin ba." Tana gama maganarta ta kama tana tafiya babu takalmi a kafarta, ga kanta babu dankwali." "Ki tsaya nan nace."! Cikin tsawa yayi maganar. taja ta tsaya ba tare da ta juyo ba. Yaja tsaki tare da komawa baya, takalmi ya lalobo mata tare da wani farin yadi. Ya karasa inda take da fadin." Kar'bi wannan ki rufe jikinki dashi." ba tayi musu ba ta kar'ba, ta lullube jikinta har kasa. Ya bata takalmi ta tsuguna tana kokarin sawa, ganin tana 'bata masa lokaci yasa ya tsuguna da kansa ya d'aura mata takalmin sosai yanda duk wuya ba zai fita a kafar ba. Hannunta ya rike a cikin nasa suka nufi inda ayarin jama'arsa suke tsayuwar jiransa, ganinsa tare da ita ya basu mamaki! amma babu wanda yayi magana a cikinsu, yayi gaba suka rufa masa baya. karnuka wasu a gaba wasu a baya, sai kuma bushe-bushe da gangi! da ya cika dajin! *Free pege ya kusa 'karewa a hanzarta biyan kudin karatu.* *0542382124...Binta umar gtbank* a tura sheda ta wannan number...... 07084653262 *Ayi kokari a duba wannan👇🏻* _Mijina baya bani_ kulawa bayan kafin muyi aure yana bani kulawa da duk wata soyayya ___________ *Watakila kece kika janyo faruwar hakan, na farko dai namiji yana da bukatar kulawa, ta kowane fanni, watakila kafin kuyi aure ke din 'yar gayu ce mai tsafta, bakya rabo da kwalliya kamshin turare ako da yaushe, sai bayan auranki kuma ki mayar da kanki jakar mata, da kuruciyar da komai ki shiririce wanka ma sai kiyi kwana biyu ko uku ba kiyi ba mussaman a cikin wannan lokacin, sai kiyi kwaskwarima ki shafa mai akan dauda kina tsamin hammata! to me zai hana namiji bai kyamace ki ba, babu mummunar mace, kuma komai shekarunki mutukar kina da miji to kada ki zauna a lalace domin hakan zai janyo miki bacin rai mai tsanani mussaman idan kina da abokiyar zama to zaki zama koma baya ta kowane fanni, tsafta jigo ne a cikin zamantakewar aure don haka ki kula da wannan abubuwan.* *1- Wanka sau biyu a rana* *-2 yawan aske sassan dake fitar da gashi a jikinki* *4-Zama cikin kamshin turare mai sanyi da sanyaya zuciya* *3-Kitso duk bayan sati ko kwana goma kuma kafin ayi kitson a wanke kan* *5-Wanke baki sau biyu ko uku mussaman idan zaki kwanta* *6- Taraiyaya da iya kalami mai dadi a lokacin da kike tare da mijinki* *7-Sauya kalolin abinci masu inganci* *8- Sanya kaya na mussaman domin zuwa turaka* *9- Shagwaba wata abace mai muhimmanci* *10- Banda yawan dariya mara ma'ana a gaban miji murmushi zaki yawaita yi masa kina sarrafa kwayar idonki a kansa kina bashi labarai masu dadi.* _Mutukar kin kula da wannan to zaki kama mijinki a hannu kuma zai baki kulawa ta mussaman_ *#500 via 0542382124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....* *22796074090* Dala dari Katin Airtal ko Mov *GOJE!*🏹 🐕‍🦺🐕‍🦺🐕‍🦺 _(SADAUKI OMAR RETURN👑💫_) *BINTA UMAR ABBALE🍒* *_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION🖊️📚_* _____________________ *MIJINA BAYA IYA GAMSAR DANI* ________________ *_Wannan ba sabon abu bane, da yawa mata suna kuka da hakan cewa duk sanda za suyi rayuwar aure da mijinsu basa samun gamsuwa, matsalar daga shi mijin ne daga zarar ya biya bukatarsa zai tashi, bai damu da damuwar matasa ba, wannan kuskure ne babba! idan kasan baka da cikakkiyar lafiya to kayi hanzarin neman magani domin kana aikata kuskure! mata suna da kawaici da hakuri mussaman a wannan bangaran, duk macan data bud'e baki tafadi wannan maganar to ka tabbata tura ta kai bango! shi aure na mutum biyu ne to kai d'an uwa bai kamata ka ajiye mace a gida don kana ta'kama kana ci da ita ka tauye mata hakkin aure ba, wannan abun shine ginshikin aure domin daga ranar da akace babu shi to matsala ta dinga afkuwa kenan, saboda haka d'an uwa kayi hattara daga ranar daka fahimci cewa ka gaza gurin sauke hakkin matarka, to ka tashi tsaye ka nemi magani, idan kuma kasa taurin kai kace kai lafiyarka lau ba zaka sha magani ba to babu shakka! komai yana iya faruwa..... ke kuma 'yar uwata, kada ki yarda shaid'an ya rimbaceki ki aikata wani mummunan aiki ta sanadiyar wannan matsalar, domin da yawa daga ciki akwai matan da suka famtsama kansu harkar banza, saboda rashin samun kulawa daga mazajensu, akan ki aikata hakan gwara ki rabu da auran ki roki Allah ya baki daidai da rayuwarki_* FREE PEGE *21&22* Hakika baka sanin amfanin mutum a rayuwarka sai ranar da wata musiba ta sameka, ya taimakawa rayuwarta, ita kuma ta daukeshi a matsayin abokin gabarta! tayi masa mummunar fahinta duk da irin taimakon da yake akanta, ni a ganina idan shi din macuci kamar yanda kullum take kiransa ba zata kai labari ba, domin da tuni ya keta mata haddi ya yasar da gawarta a dajin. koda yake kowane dan adam da irin tunaninsa, har yanzu ita tana shakku akansa cewa bashi ne ya sato ta daga gaban iyayenta ba. Kwanciyarta da kamar minti goma mugun k'aikaiyi ya tasheta, ashe tsutsar data sauka kan kafad'arta tana da dafi! kuma ta cijeta a gurin har ya kumbura sai tsuko! yake mata, yatsunta biyar tasa a gurin tana aikin sosawa amma kamar 'kara angiza kaikaiyin take, fatar gurin tayi jajawur! saboda susa duk ta kwaile. Hawaye kawai take tana jan hanci! daga wannan sai wannan! ciwuka a jikinta iri-iri! sosai take kuka tana kiran innalillahi-wa'ina ilaihi raji'un! Ya rage shi kadai a waje yana kai kawo a gurin, har yanzu zuciyarsa taki aminta da gurin, yana ganin kamar idan yaje ya kwanta wata matsalar zata faru! zagaya gurin yake karnukansa na binsa duk inda ya nufa sai koke-koke suke.........Alba ya cimma inda yake tsaye cikin girmamawa yace."Maigida yarinyar nan fa tun dazu ta ishi mutane da kuka." Yace."Me kukayi mata."? Da sauri yace."Wallahi maigida babu abunda mukayi mata kawai dai munji tana kuka shine nace bari na sheda maka." Ya girgiza kansa da fadin." Jeka gani nan zuwa." da sauri ya juya ya tafi. D'azu ta 'bata masa rai! ya hakura ya shanye amma baya tsammanin yanzu zata kawo masa shiririta ya saurara mata. Ya sameta sai gursheken kuka take gabad'aya ta cire rigar dake jikinta sai breziya sai soshe-soshe take. Ganinta a haka ya 'bata masa rai! rashin kamun kanta yana bashi haushi, idan ba hakaba ta san da cewa ita kadai ce mace a cikinsu mai yasa ba zata suturta kanta ba, kullum shike k'okarin ganin ya suturta ta a matsayinsa na namiji amma ita a cikin maza! saboda rashin sanin darajar kai take bude tsaraicinta. Tsaki mai karfi yaja ya juya yana kallon gurin da ya yaransa ke zazzaune! akwai tazara a tsakanin inda take, baya kuma tsammanin zasu hangeta saboda kafin ya fita sai da ya katangeta. Murya a sama! yace."Mayar da rigarki." ido gaja-gaja da hawaye! ta kalleshi, ya murtuke fuska! ko alama bata bashi tausayi ba, ya bude mata dukkanin idanuwansa! umarni ya sake bata, a dashe tace." Ka daina yi min tsawa! ko ka san abinda yake damuna."? Yace"Babu abunda ke damunki sai hauka! da gidadanci! idan ba haka mai zai sanya ki cire riga cikin maza." Wani abu mai nauyi ya tsaya mata a wuya! wai ace wannan gantalallan ne yake kiranta da mahaukaciya. Nauyin abunda ya tsaya mata a wuya ya hana ta magana sai uban hawayen dake tsere a saman fuskarta, abu biyu ne suka dameta a halin yanzu. "Mtswwww! tsaki mai tsayi yaja kafin ya fita da gurin, ya dawo da fitila a hannunsa sai da ya rage karfinta sannan ya tunkari inda take. Ta sake takure jikinta tana kallonsa yana dube-dube a gurin, rigar ya mika mata da fadin." Kar'bi kisa ko kuma yanzu nayi abinda ba kiyi tsammaninsa ba." Ta tsira masa ido! da jin shakkar maganarsa, ganin babu alamun wasa a fuskarsa yasa tasa hannu ta kar'bi rigar amma bata sanya ba, ta rike kawai a hannunta tana cigaba da sosa gurin dake mata ciwo. Ya haskata da fadin." Cire hannuki a gurin! da sauri ta cire! tsigar jikinsa ta tashi! ganin yanda gurin yayi jawur! har da kumburi! zuciyar musulunci, duk sai jikinsa yayi sanyi haka kawai baya so wani abu ya cutar da ita, burinsa bai wuce ya kaita gaban iyayenta lafiya lou ba. Sassauta murya yayi yace."Sannu yaushe hakan ya faru."? a maimakon ta bashi amsar tambayarsa sai kawai ta sake rurucewa da kuka!! Yatsansa yasa saman bakinsa da fadin." Shiiiiii." kukan bashi da amfani kiyi shuru zan taimaka miki." Ba tayi shuru ba kuma bata daina kallonsa ba, yace."Kina bukatar hakan ko."? Kamar wata sakarai ta daga mai kai! Yace."To ki zama jaruma! ki daina yawan kuka bashi da fa'idah."! Taji kamar ta kai masa duka! ta'ina zata iya daure wannan azabar! Fita yayi da kamar minti biyar ya dawo da magani a hannunsa. yayi zaman ra'kuma a gabanta cikin muryar da ya saba rarrashinta ya mi'ka mata maganin da fadin." Jarumata! kar'bi maganin ki shafa a gurun zai daina miki ciwo." Maganin ta kar'ba ta lakato a yatsanta, can bayan kafad'arta gurin ciwon yake ta daga hannu sosai tana kokarin shafawa hannunta ya gaza kaiwa! Ganin haka yasa ya kar'bi maganin daga hannunta ya lakato kan yatsansa, ya kalleta da fadin." Kin bani izini."? Shuru tai masa. Ya sassauta murya yayi da sake maimaita maganarsa. Kai kawai ta iya daga wa gabadaya jikinta ya mutu! ya lalubi gurin yana shafa maganin a hankali yana sake kwantar mata da hankali da cewa gurin zai daina ciwo insha Allah! Ido kawai ta lumshe tana jin maganganunsa sama-sama a cikin kunnanta, har ya gama shafa maganin fuskarta ya dan kalla sai yayi sauri ya janye idonsa jin yanayinsa na neman sauyawa, gefe ya matsa tare da sassauta murya ya kirayi sunanta............ *GIMBIYA!* a kasalance ta bude idonta! tana kallonshi , tana masifar son taji ya kira ta da wannan sunan. yace."Sannu ki kwanta ki huta na shafa miki maganin." Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta zame ta kwanta tana tattakure guri daya, Shima ajiyar zuciya ya sauke kafin ya lalubi wani zani mai kauri ta fara k'okarin rufa mata a jiki akayi rashin sa'a gwiwarsa ta zame ya fad'i kanta! fuskarsu ta hadu! da sauri yayi gaggawar rabuwa da jikinta yana bata hakuri! uffan ba tace ba asalima lokacin da hakan ya faru idonta a rufe yake. Ganin tayi shuru ba tace masa komai ba yasa a gaggauce ya fita yana auziyya a zuciyarsa, be san me yasa ba kullum zuciyarsa take kwadaita masa wasu gurare na jikinta, a duk sanda zasu kasance a guri daya yakan rasa nutsuwarsa. Itama anata bangaran hakane, har yanxu idonta a rufe yake ta rasa abinda yake mata dadi! yanda yake sassauta murya yana rarrashinta yakan karya mata garkuwar jiki, tana jin dadin hakan sosai, a rayuwarta tana masifar son namiji wanda ya iya soyayya, bayan haka kuma bata san lusarin namiji tafi son tsayayye shiyasa wasu lokatan yake birgeta domin dik ya tara abubuwan da take bukata. Ajiyar zuciya ta sauke tare da jan zanin daya rufa mata ta rufe gabadaya jikinta harda fuskarta, addua take a zuciyarta Allah ya sa bacci ya dauketa. Cikin ikon Allah kuwa bacci mai nauyi ya dauketa................ Kamar a mafarki! ta dinga jin ihu!!! da hayaniya tare da kukan karnika! da karar wu'ka'ke! a firgice ta tashi tsaye! tana bin gurin da kallo, babu kowa duk sun fice! yanda 'kura! da guguwa! take shigowa har gurin da take shi tabbatar mata da cewa babu lafiya! Fitowarta daga gurin yayi daidai da tashin bomb! gabadaya gurin ya kacame! ya hargitse! da hayaki! da rarrafe ta koma katangaggen gurin ta takure guri daya tana kiran sunan Allah. Ta jima a haka kafin ta dago kanta, still tana jiyo hayaniya da kuwwa! tare da kukan karnika! ga wani irin b'akin hayak'i! da ya turnuke! a gurin! Hannu tasa ta toshe hancinta tare da sake takurewa a guri daya jikinta in banda rawa babu abunda yake, bakinta sai motsi yake adduar yaye masifa takeso tayi amma bata iya ba, sai kawai ta dingi nanata innalillahi da karfin gaske! Hakan ya janyo hankali d'aya d'aga cikin yaran *uban daba* wanda yake shawagi a gurin...........Gurin ya shiga yana zazzare ido! ita kuma ganin b'akuwar fuska yasa ta sake rikicewa! shi kuwa murmushin farin ciki yayi ya nufeta da saurin gaske! Hannunta ya fizgo! ta turje! tana rirrike itaccen dake katange da gurin, kuka take tana rokonsa yayi hakuri, ya d'auke fuskarta da mari! da tafkeken hannunsa!! a take hancin ya fashe! ya dinga tsiyayar da jini! Janta yake tana turjewa da bashi hakuri cewa bata da laifi itama sato ta sukayi, ya sanya kan k'otar lafceciyar wu'kar dake hannunsa ya dinga bubbuga mata a gwiwa, lokaci guda ta galabaita! ta zube a gurin! d'aukarta yayi ya sa'ba a kafad'a ya fito da ita. kai tsaye mafarkarsu ya nufa da ita a kafad'arsa............. Tashin hankali kenan! lokacin daya hangeta sa'be a kafardar gardi! sai da wukar hannunsa ta subce! ta kusa fad'uwa amma yayi muzzakaracin riketa da kyau a hannunsa!! Wani uban ihu! ya kurma! wanda ya razana! abokan fad'an nasa suka ranta ana kare, amma ina! basu samu nasara ba, sai da ya kama su, ya sanya wata narkekiyar igiya ya daure musu hannuwa da kafafu! Gabad'aya gurin ya hargitse! sakamakon bomb din da ya tashi, yayi sanadiyar kona biyu daga cikin yaran shi, suna kwance magashiyan! rai a hannun Allah...... Duk da cewa sune suka samu nasara amma beso wata matsala ta afku da yaran sa ba.. Ya kallesu gabad'aya kammaninsu ya sauya hatta da fuskokinsu sun rine! da baki! sakamakon tashin bomb din, wannan ce hanya mafi sauki da abokin hamayyar ya samu nasara a kansa! Ya kallesu da fadin." Yayi imani! da cewa idan ya tunkari inda muke da wu'ka ko wani abu makamancin haka ba zai samu nasara akanmu ba, wannan shine dalilin daya sanya shi jefo mana bomb! ba tare da munyi tsammanin hakan ba, to Alhamdullhi duk da hakan be samu nasarar da yake bukata akanmu ba, yanzu kalubalan dake gabanmu tunkarar sansaninsa domin gwabzawa a tsakanimu, babu yanda za'ayi mu tafi mu bar masa wannan yarinyar da yayi nasarar dauke mana ita, duk da cewa tsintar ta mukayi akan hanya bamu san daga ina take ba, hakan ba zai sanya mu bar masa ita ba, duk yanda za'ayi sai mun samu nasara a kansa." Da yawa daga cikinsu sun tausaya mata, amma wasu sun kalubalanci maganarsa! bai ta'ba sanya kara sun tsallake ba, amma da alama akwai wa'inda za suyi masa tawaye a cikinsu. Ya dinga kallonsu yana nazarin yanayinsu, yace." Babu wanda zan tursasa! cewa ya take min baya! a cikunku. zan iya tunkarar sansanin ni kadai! ba tare da kowa ba! saboda haka wanda yake ganin zai bi bayana bisimillah." Yana gama maganarsa sai yayi gaba, wasu suka bi bayan shi da sauran karnukan! dake raye, wasu kuma suka tsaya suna surutai da mai da magana a tsakaninsu! *Free pege ya kusa karewa a daure a biya kudin karatu🙏🏻 don Allah idan kin san ba siyan littafin nan zaki ba kada ki dauki number ta kiyi min magana* *#500 via 0542382124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....* *22796074090* dala dari. katin airtal ko mov. *GOJE!*🏹 🐕‍🦺🐕‍🦺🐕‍🦺 _(SADAUKI OMAR RETURN👑💫_) *BINTA UMAR ABBALE🍒* *_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION🖊️📚_* _____________________ *_KADAN DAGA CIKIN IRIN SAKKONIN DA NAKE CIN KARO AKO DA YAUSHE_* _*1-* Mijina baya bani kulawa bayan kafin muyi aure yana masifar sona_ _*2-* Mijina baya iya biya min bukatata._ _*3-* Mijina baya hira dani kullum idan ya dawo daga aiki ko kasuwa wayarsa ce abokiyar hirarsa_ _*4-* Mijina kazami ne sai yayi sati ko kwana goma beyi wanka ya wanke bakinsa ba._ _*5-* Dangijin mijina sun matsa min basa kaunata saboda bana haihuwa._ _*7-* Bana jin dadi a duk sanda mijina zai kusanceni da kyar nake amincewa saboda zafi._ _*8-* Mijina yana cutar dani baya sauke hakkina dake kansa bayan Allah ya hore masa._ _*9-* Mijina mazinaci ne yana neman mata bayan ina iyakacin bakin kokarina gurin ganin na dauke masa bukata._ _*10* Mu biyu ko uku ko hudu ne a gurin mijinmu amma baya adalci a tsakaninmu._ _*11-* Mijina yana da taurin kai da wani irin hali baya sarrafuwa._ _*12-* Mijina Miskili ne kullum babu mu'amular arziki a tsakaninmu sai muyi kwana da kwanaki babu magana._ _*13-* Ina fama da rashin nutsuwa da kwanciyar hankali a gidan aurena bayan ta kowane bangare bani da matsala._ _*14-* Mijina shaye-shaye yake nayi - nayi ya daina yaki baya sallah a kan lokaci sannan idan mukayi mu'amula ta aure baya wankan tsarki._ _*15-* Mijina baya dogon zango yake release kuma bai damu dani ba, haka zai tashi ya barni cikin halin damuwa._ FREE PEGE *13&14* Sosai yayi namijin kokarin tunkarar inda take kafin ya karasa ya cire duk wani kawazucin dake cikin zuciyarsa yana isa ya bude mata wuta sosai yana mata fada tare da nuna mata illar abinda ta aikata. Tsaye ta mike tana masa wani irin kallo kafin tace."Wai shin ubana ne kai da zaka zo kana min tsawa ina ruwanka da rayuwata, idan har baka san ganina a haka to kayi gaggawar mayar dani inda ka daukoni." Ya nuna ta da yatsa kamar zai tsole mata ido Yace." Banyi ra'ayin haka ba kuma ke baki isa kisa na tafi ba tare dana shirya tafiya ba, idan kina san kanki da arziki ki dauki rigarki kasa a jikinki." Ta nuna masa jikakkiyar rigar dake yashe a gefe, ya kalleta da fadin." Meye manufarki na jika rigarki da ruwa ko kinyi hakane don kija ra'ayina akanki.? Wulakantaccen kallo tayi masa kafin tace."Allah ya kiyaye meye abin sha'awa a tattare da kai da har kake wannan maganar." Ya zuba mata jajayen idanuwansa yana kallo, ta gyada kanta idonta a soye a kansa tana kara tabbatar masa da maganarta. Yace."Idan babu abin sha'awa a tattare dani to ni naga abinda ya burgeni a jikinki kuma ke zaki janyo na aikata abinda ba shikkenan ba." Gabanta ya fadi da jin furucinsa, amma bata saduda ba, ta ya mutsa fuska da fadin.'' Da kuwa nayi maka illah! domin ka kuskura ka keta min haddi wallahi sai ka dawwama a daure. a kurkuku." Leb'ansa yasa a bakinsa ya dan ciza kafin ya furzar da wani irin huci! yace."Baki san ni bana d'auruwa ba? ko ba kiji sunana ba *GOJE!* nake ko kuma ki kira ni da *MAI DAWA!* Babu wani mahalukin da ya isa ya tunkari inda nake ban ci Uwarsa ba!" Sai ta tsargu! ta nuna kirjinta da hannu da fadin." Ni kake zagi ko? shin ka san su waye iyayena a fadin kasar nan kuwa"? Ya gyda kansa da fadin" Babu ruwana da ko su waye iyayenki ni na fada miki wanene ni! babu wanda ya isa ya daureni ba tare dana rikirkita masa al'amuraba." Ta dinga kallonsa tana mamakin furuncinsa, babu wanda ya isa ya daureshi ba tare da ya rikirkita masa al'amuraba ba." "Kana nufin kafi karfin hukuma kenan."? tafada idonta a tsaye a kansa. Tsaki! yaja mai karfi kafin ya nuna kirjinsa da fadin." Ni nan! ni ne hukuma! duk wani mai bukatar kwanciyar hankali a kasar nan to kada ya ta'boni."! Cike da Izzah! da jin kai ya fadi maganar, kai daga jin yanda yake magana kasan akwai abinda da ya taka. Ta sunkuyar da kanta tana mamakin furucinsa wato shi bai yarda ma akwai hukuma ba! to bari ta ta'bashi taga abinda zai yi. Yanke shawarar zaginsa tayi, ta dago kai suka hada ido, yana tsaye kikam! a kanta, tsoro ta cire Cikin turanci ta fara zazzzaginsa tana kiransa da sunayen dabbobi........ Iyakacinsa secondary skull turancin nata yayi tsayi sosai da kyar ya fahimci wasu kalmomin mussaman sunayen dabbobin da take kiransa dashi. Bahagon mari! ya kifa mata a fuska a take taurari masu haske suka gilma, ta rintse idonta hawayen azaba na zuba! Tana cire hannunta daga gurin shatin yatsunsa suka fito radau! Ta tsira masa ido gabanta sai faduwa yake, tunda take a duniya babu wanda ya taba fitar da hannu ya tsinka mata mari sai shi. Ta dinga bin sassan jikinsa da kallo, shi kuma yana dogare a kanta yana tsuma! da alama tsumin ne ya tashi. Kafin kiftawa da bismillah tayi wani tsalle sai kace aljanna ta fizge kaifaffar wukar dake soke a gaban rigarsa. Ta rike da kyau! tana kallonsa da fadin" Sai na zubar maka da jini yau! *GOJE!* kake ko? har kana Ikirarin cewa wuka bata huda ka, bayan haka yaranka suna kumbura maka kai kana d'aukar kanka wata tsiya! to yau ni zanyi ajalinka."!! Da gaske take domin hannu bibbiyu ta ri'ke wukar da kyau sai huci take! tana mazari! kanshi tayi da wukar zata yankeshi, ya kauce! tabi iska! a sukwane ta sake kai masa sarah! ya kauce ta sake bin iska! dariya ta kusa kufce masa ganin yanda ta dage! wai dole sai ta yankeshi da wukar wanda duk kokarin da take a banza bata samu damar saka wukar a jikinsa bama ballanatana ta fitar mai da jini. Haka suka dinga bugawa ya dinga watangaririya da ita yana bata wahala! ta galabaita mutuka gumi duk ya jika mata jiki shi kanshi tsumman data daure cinyoyinta dashi ya kwance,ribbon din data d'aure gashinta dashi ya cire ya fadi kasan gurin, kafafunta sunyi bududu! amma saboda tsabar karfin hali taki saduda!. Yana sane ya dinga bata wahala sai da ya tabbatar data galabaita sannan ya murde hannunta ya kwace wukar! faduwa tayi a gurin tana wani irin kukan bakin ciki! Tausayi ta bashi! wannan artabun da sukayi koda namiji ne zai ji jiki ballantana mace irinta da bata saba da wahala ba, yayi mamakin karfin halinta mutuka. Kusa da ita ya tsuguna yana duba kafafunta duk ta taka k'ananun k'ayoyi, hannu yasa domin cire mata k'ayoyin ta harbeshi da kafa daya, kallonta yayi cikin zafin nama! ta ciko hannu da kasa zata watsa masa ya kautar da fuskarsa, ta watsawa iska. tana daga kwance tana nishi ta cigaba da cin mutuncinsa da turanci, hakan be dameshi ba tunda ya kaita kasa bukatarsa ta biya. Duk buge-bugen da take bai hanashi ciccire mata kayoyin da suka huda kafafunta ba, ya cire rigar jikinsa ya rufa mata a jiki. Da sauri ta cire ta jefar da ita. Yace." Ni zan iya kawar da kwadayina akanki amma kika yarda wata dabbar ta gilma ta hangi tsaraicinki ba zaki kai labari ba, bayan dabbobi akwai aljanu a gurin nan kiyi hattara." Jin maganar aljanu yasa jikinta mutuwa idan akwai abinda take tsoro a duniya aljan ne! hakura tayi kan dole ta karbi rigar sa tasa. Tana share hawaye ta mike tsaye, ya kalleta yana jimanta karfin halinta, wai dashi za tayi fada, dariya yayi wacce ta dauki hankalinta ta kalleshi tsantsar kyawunshi ne ya bayyana a lokacin, ganin tana kallonsa yasa ya gimtse fuska yaje ya dauki rigarta da tsumman ya bar gurin dasu a hannunsa, ********* Yau ma da wuri ta isa gidan, ta sameta ta shirya tsaf domin fita! A gabanta sabbin atampopi ne irinsu nicham hartget da makamantasu, cike da ladabi suka gaisa, tace."Kinga sabbin atampopi ne Rakiya ta kawo min na saya wai itama a cikin gari ne aka bata su shine nakeso nayi musu kudi a ganinki duk daya za tayi nawa."? Hamra'u ta kalli atampopin kafin tace."Uwale ke kin kasa yi musu kudi ballanatani ni da ba sana'ata ba." 'Yar dariya tayi kafin tace."Don kar nace da ita dubu uku taga kamar wulakanci ne abun amma iyakacin abinda zan iya siya kenan.'' Cike da mamaki tace."Uwale dubu uku a tamfa turmi hudu haba Uwale kiyi adalci mana shiyasa jama'a suke zaginki har suna kiranki da mummunan suna." Ta 'bata rai da fadin." Sun jima basu zageni ba! ai Hamra'u a wannan duniyar idan zaka dauki maganar mutane to wallahi babu abunda zaka tsinana, amma meye laifina don na saya dubu uku, itama ai kyautarsu a ka bata. Tace."Duk da haka dai sunyi arha da yawa duka cotton ne babu leda a ciki maimakon ki saya dubu biyar gabadaya." Tace."Aa ba zan iya saya dubu biyar duka ba, dubu uku zan saya kuma ke da kike surutu ai idan na saya to tanadi nake miki kayan lefanki ne." Murmushi tayi kafin tace."Uwale nifa jikina yayi sanyi sai nake ganin kamar burina ba zai cika ba." Murya na rawa ta karashe maganar. Tace."Aa ki daina sanya damuwa a ranki insha Allahu ba zakiyi zaman banza ba UMARU zai aureki koda baya sonki to ni zan umarceshi ya aureki. Tace."Aa Uwale ni nafi so ya aureni dan yana sona bana so muyi irin wannan auran da iyaye suke hadawa daga baya a samu matsala." Tace."Insha Allahu ba za'a samu matsala ba, domin ni kaina na gaji da ganinsa a haka babu aure sa'anninsa sun jima da aure da 'ya'yansu amma shi yana zaune a haka, idan za'a biye masa to zai kare rayuwarsa a haka wannan dalilin yasa zan tilasta masa auranki." Hawaye ta share tana girgiza kai, itafa kwata-kwata bata son irin wannan auran tafi so da bakinsa ya furta mata kalmar so, amma dole haka zata hakura tunda yaki gane irin son da take masa. watakila idan Allah ya kaddara auran nasu Allah ya sanya masa kaunarta a cikin zuciyarsa. Tace."Ki goge hawayenki ki daina kuka mutukar ina raye to kamar kin auri UMARU kin gama, shiyasa duk tsumi da tanadina ya kare akanki gashi cikin ikon Allah na kusa kammala hada miki lefe, kinga sai komai yazo da sauki." Tace."Nagode Uwale Allah ya tabbatar mana da alkairi" Ta amsa da "ameen" tana kokarin tashi, Rakiya tayi sallama, gabadaya suka amsa, Uwale tayi saurin fadin." Yanzu nake maganarki a cikin raina nace har gida zanje na kai miki kudinki." Tace."To ai baki fada min nawa kika sayi atampopin ba." Ta ya mutse fuska da fadin." Gabadaya dubu uku na saya domin dai kema kin san atampopin naki an daina yayin irinsu bayan hakan haka kuma sun jima a ajiye sai warin ajiya suke." Rakiya ta mika hannu da fadin." Ban siyar a hakaba bani na kai inda za'a saya da mutunci." Baki ta bude da fadin." Rakiya ina zaki kai a siya da mutunci bayan nan, kin san dai idan kika kaiwa Delu siyan banza za tayi miki gwara ki tsaya mu sassanta." Taja tsaki da fadin." Ai har gwara Delu a kanki Uwale sai kace kayan sata zaki saya dubu uku duk daya a kasuwa dubu biyu da dari biyar ce, idan sayan mutunci zakiyi ina laifi ki saya dubu biyar gabadaya." Tace." Oh!oh zan dai saya dubu hudu idan kin sallama min a haka." Jim tayi kafin tace."Na siyar miki amma kada ki tsinka min kudi ki bani kudiba cif." Tace."Maganar kike so Rakiya ai a inda ba kasa anan ake gardamar kokawa da ban shirya ba ai ba zan karbi kayanki ba." Rigar jikinta ta daga ta zuge zif din lalitar dake daure a jikinta kudi ta fito dasu, a dukunkune yawanci duk 'yan dari biyu ne, duk sun ya mutse, Hamra'u tasa hannu suka lissafa dubu hudu kudin me kayan ta mika mata da fadin." Gashi maganin karya hallara ki lissafa a gabana na san halinki kada ki dawo kice min basu cika ba." Rakiya ta dangwali yawun bakinta ta fara lissafa kudin ta kalleta da fadin "Sun cika." Tace."To masha Allah idan an samu wasu kayan ina bukata." Tana kokarin fita tace." To shikkenan idan an samu zaki jini." Bayan fitar Rakiya daga gidan itama Uwale kayan dillancinta ta dauka ta fita, ya rage saura ita kadai a gidan, ta jima tana sakawa da kwancewa kafin ta tashi cikin sanyi jiki ta gyara gidan tsaf ta kulle da kwado, gidan Tasallah ta shiga ta bayar da mukkulin kafin ta kama hanyar gidansu, salo-salo take tafiya kamar wacce kwai ya fashewa a ciki........."Hamra'u." da sauri ta juya jin muryar kawarta Zabbah, taja ta tsaya tana wasa da karan dake hannunta har ta karaso gurin da faratin goro da lemon tsami a kanta. Zabbah ta karaso inda take da fadin." Daga ina kike haka naga duk jikin a sanyaye."? Ajiyar zuciya ta sauke kafin tace." Daga gidan yayar mahaifina nake kullum ina zuwa nayi mata aiki kafin ta fita. Zabbah ta fashe da dariya irin ta shakiyanci kafin tace."Hamrau kenan wai kenan kina kamun kafa ko? wallahi kina wahalar da rayuwarki domin kaf cikar karkarar nan banga wata mace da zata ja ra'ayin *GOJE! ba* Tace." To ke Zabbah waye ya fada miki ina kamun kafa da Uwale a matsayin uwa take a gurina laifi ne don naje gidanta." Zabbah ta tabe baki da fadin." Hamra'u bari na fada miki abunda baki sani ba, kaf 'yan matan garinan babu wacce bata san halin da kike ciki akan *GOJE!* ba kowa ya san kece kike sonsa baya sonki kullum sai kinji kinyiwa kakarsa aikace-aikace sai kace baiwa bayan haka ance idan yana gari kece kike masa wankin kayansa ki goge ki wanke masa takalma saboda rashin hankali irin naki kin mayar da kanki yar aiki bayan baki da tabbacin zai aureki. Tace."Zabbah! duk abinda kika fada hakane babu karya ina san UMARU kuma ina rokon Allah yasa ya zama uban 'ya'ya na, bayan haka kuma duk wata bauta da nake masa ra'ayi na duk surutun da jama'a za suyi akan hakan bai dameni ba." Ta girgiza kai da fadin." Shikkenan ai tunda kinyi nisa duk abinda zan fada miki a yanzu ba zaki fahimta ba, saboda haka muna zuba ido muga yanda za'ayi wannan auran. Shuru kawai tayi bata sake magana ba, ita Zabbah ce keta surutu tana bata labarin saurayinta wanda zata aura uffan bata ce ba har suka rabu da juna. Cikin kunci da damuwa ta shiga gidansu, nan ma ta iske wani bacin ran don mahaifiyarta fada ta rufeta dashi sosai tace."Ina ji ina gani kinfi karfina Hamra'u! saboda kulafucin namiji kullum da gari ya waye hankalinki na wani guri kisa kafa ki fita ki barni da aikin gida, kina can kina bauta a wani gurin, to wallahi nagaji ba zan hanaki ba tunda ke ki kasa kanki amma ba zaki kara fita ba sai kin gama min aikin gida." Daki kawai ta shige tana kokarin danne kukan dake kokarin kufce mata, wai shin da wane bala'in za taji? ko'ina babu sassauci, bata samun nutsuwa da kwanciyar hankali sai a gurin Uwale ita kadai ce ke kwantar mata da hankali, amma ita kanta wacce ta haifeta kullum habaici take mata akan wanda ta kwallafawa rai! kowa yana ganin laifinta bayan itama ba ita tayi kanta ba, Allah ne ya halliceta ya sanya mata soyayyar wanda bai san ta nayi ba, dole idan ya dawo ta cire kunya ta sameshi da maganar ko ta san matsayinta.. *Don Allah idan ba sayan littafi zaki ba kada ki dauki number ta Nagode🙏🏻* *Ga mai bukatar Sadauki Omar 1k zai tura domin samun damar karanta littafi biyu Goje sadauki Omar return* *#500 via 0542382124......Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....* *22796074090* dala dari Katin airtal ko Mov Aa *GOJE!*🏹 🐕‍🦺🐕‍🦺🐕‍🦺 _(SADAUKI OMAR RETURN👑💫_) *BINTA UMAR ABBALE🍒* *_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION🖊️📚_* _____________________ FREE PEGE *29&30* Kusan a tare suka d'auke idonsu daga barin kallonta, Asp din yayi magana amma shi uffan bece ba har ta gama harare-harare! ta fita daga ofis din. Ya d'an ja k'aramin tsaki da fadin." Yarinya nan babu tarbiya a tattare da ita duk kuwa da cewa ta fito daga tsatso mai kyau, ba ta gaji dattako da karamci irin na mahaifinta ba, duk da ba a garin kano muke zaune ba muna da labarin dattakon mahaifinta mutum ne mai karamci da mutunci yana aiki da hankali da ilimi yana kuma gudanar da mulki a bisa tsari na isalama." Beso ya tanka a cikin al'amarin yarinyar ba amma ganin yanda Asp din yake jaddada maganar yasa yace." Akwai irinsu da yawa wa'inda suka dauki mulki wata tsiya idan akace mahaifinsu nada sarauta ko wani muk'ami sai su dauki girman kai su dora a kansu suna ganin babu wanda ya isa dasu, hakane maganarka mutumin kwarai yana iya haifar baragurbi acikin al'umma jarabtace kawai daga Allah.'' Yace." Kwarai kuwa wannan haka yake sai dai kawai mu roki Allah ya shirya mana zuria baki d'aya." Ya amsa da ameeen ya Allah. Shuru na minti biyu ya ratsa gurin, cikin 'yar tsokana Asp din yace." Akwai abinda na manta ban tambayi *MAI DAWA!* ba."? Murmushi yayi da fadin." Akwai sauran tambayoyi kenan."? Girgiza kai yayi da fadin." Tambaya daya ce shin kana da iyali kuwa.''? Girgiza kai yayi gami da dan ta'be bakinsa.........Asp ya dan zare ido da fadin." Kana nufin babu iyali kenan." Kai ya daga masa still da murmushi a fuskarsa. Sai kawai ya shiga girgiza kansa da fadin." Gaskiyar magana yanda kake jarumin namiji mata hudu suka cancanta da kai amma ace ma ko daya babu." cike da alhini ya kare maganar. Sai abun ya bashi dariya ya dan dara kafin yace." Asp matsalar mata nada yawa shiyasa nayi zamana a haka ba wai don bani da bukata ba, kawai nafi bukatar kwanciyar hankalina nayi duk abinda nake so ba tare da wani ya caza min kai ba.'' Yace." To ai hakan nan ake hakuri dasu da matsalarsu Umaru kowane maigida yana da matsalar iyali mussaman idan mace fiye da d'aya yake da ita, dole ba zaka rasa shi da matsala ba, nima matana biyu sai dai kowacce da gidanta kuma yanzu haka ina shirin yin ta uku da yardar Allah sai na cike domin ina da ra'ayin hakan." Ya girgiza kai da fadin." Kayi kokari sosai kuma ka aikata sunnah Allah ya baka ikon yim adalci a tsakaninsu." Ya amsa da "Ameen ya Allah ina fatan kai ma kayi koyi dani." Girgiza kai kawai yai baya tsammanin hakan domin baya san damuwa ba lallai sai ka tara mata a gidanka za'a tabbatar da jarumtarka ba, shi a ra'ayinsa zai iya 'kare rayuwarsa da mace daya, sai dai kuma duk yanda Allah ya shirya masa rayuwa to zai kar'ba hannu biyu tare da godiya a gareshi. **** Ke'bantacen guri aka ajiyeshi shi kad'ai ba tare da da sauran yaran sa ba, sai dai su an tattarasu guri guda da sauran masu laifi gama gari. wannan karamcin da Asp din yayi masa ya tsaya masa mutuka a rai yayi ta tunanin irin alkairin da zai saka masa. *** Uwale duk atamfofin da take k'uzu tana tarawa a cikin adaka fito dasu tayi ta siyar. ta dinga bin tsangaya-tsangaya tana bayar da sadaka domin almajiran suyi mata saukar al'kur'ani akan bukatarta, Allah maji rokon bawansa addua ta kar'bu. Washe garin ranar da ita da Mahaifin Hamra'u da ita Hamra'un suka yanke shawarar zuwa headquarter 'yan sandan domin samun cikkenan bayani. Sun jima a tsaye kafin wani jami'i ya sauraresu, Malam Hafi'i mahaifin Hamra'u shine yayi masa bayanin abinda yake tafe dasu. Yayi jim! yana kallonsu kafin yaja tsaki ya barsu a gurin......Uwale da sauri taje tari gabansa kuka ta fashe dashi ta zube gwiwa biyu a gabansa tana rokonsa, hakan ya janyo hankalin ma'aikatan dake gurin suka fara tambayar ba'asi. Cikin kuka tace." Me yasa dukkaninku baku da imani ne? tunda muka zo gurin nan babu wanda yayi mana kallon mutunci Allah da Annabi sunfi karfin wasa amma gabadayanku bakwa tsoron Allah."! Daya daga cikin musulman dake tsaye gurin ne yace." Tayi masa bayani abinda yake tafe da ita. Hanci ta fyace kafin." Tace "Mun zo gurin UMARU wanda ku ka d'aure kuna zarginsa da ta'addanci bayan ba haka gaskiya take ba." Yace." Yi shuru ki kwantar da hankalinki ki daina kuka zanyi miki kokari yanzu." Ta mike tsaye tana gyara yafan mayafinta, tace."Nagode sosai Allah yayi maka albarka." Ya amsa da 'ameen kafin ya umarcesu da suje su zauna a wata rumfa. Sai da yaga zamansu sannan ya bar gurin, kai tsaye ofis din Asp ya nufa domin sheda masa abinda ke faruwa. Ya k'ame da sarawa kafin ya sheda masa abinda ke da akwai, kai tsaye ya bashi umarnin shigowa dasu. Da kanshi ya nuna musu gurin zama yana musu sannu, Malam Shafi'i da 'yarsa suka zauna kamar yanda ya umarcesu Uwale kuwa kai tsaye kujerarsa ta nufa, ya dinga kallonta har ta iso inda yake ta zube gabansa kawai sai ta fashe da kuka tare da rirrike masa kafafu! kuka take sosai tana bashi hakuri. Tausayi ya rufeshi da kyar ya iya mik'ewa tsaye sakamakon rikon da tayi masa, ya sunkuya tare da sanya hannu ya dago ta ta mike tsaye, rungumeta yayi yana rarrashin gami da bata hakuri. Ita kuma fadi take." Ku za'a bawa hakuri ku dubi girman Allah kuyi adalci kada ku yanke hukunci akan wanda bashi laifi bashi ne wanda kuke zargi ba. Hankici ya ciro daga jikinshi, ya goge mata hawaye yana sake kwantar mata da hankali, sai da ya tabbatar da cewa ta samu nutsuwa sannan ya umarcesu da cewa subi bayan shi. Kai tsaye ke'bantaccan gurin da aka ajiye shi suka nufa...........Aps din a gaba suna bayansa, yana shiga sai ya basu hanya. gabadaya suka hada ido dashi yana zaune kasan kafet da tire din abinci a gabansa tsaf dashi da nutuswa a tare dashi bashi da wata matsala bayan sararin! dake daure da kafafunsa Hamra'u da gudu ta iske inda yake, kawai sai ta fad'a kansa tana wani irin kuka! wanda yake nuna tsantsar tashin hankalinta, itama Uwalen da kuka ta karasa gurin duk da ganin da sukayi masa cikin nutsuwa hakan be gamsar dasu ba. Asp ya juya ya fita yana jimamin al'amarin. Tun bayan data fad'i jikinsa yasa hannu a bayanta yana dan bubbugawa, a Hankali cikin taushin murya yake rarrashinta, ta dago kai tana kallonsa hawaye sai ambaliya yake a saman fuskarta, kai yake girgizawa alamun ta daina kukan, yasa hannu ya goge mata fuskar sosai yake mamakin irin k'aunar da yarinyar take masa, shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya sai dai har yanzu bata saki hannunsa ba ta rike tsam a hannunta. Ya d'ora idonshi kan Uwale da ta dage tana kuka sai kace wacce aka nuna mata gawarsa. Murmushi yayi tare da mika hannunshi kan fuskarta hawayen ya share mata da fad'in." Kukan bashi da Fa'idah Uwale addua zaki min." Tace."UMARU kukan shi yake kansa yin kuma shine samun salama, amma a zahirin gaskiya muna cikin tashin hankali bamu da kowa sai Allah shine kuma zai fitar damu." Yace."Kin gama magana tunda ki kace Allah, kuma gaskiya tayi halinta tun kafin tafiya tai nisa gaskiya ta bayyana cewa wanda suke zargi bani bane nima kuma na san da hakan saboda haka ku kwantar da hankalinku insha Allah zan fito lafiya na cigaba da rayuwa da ikon Allah." Tace."Idan hakane mai yasa basu kwance maka wannan d'aurin ba, duba fa yanda kafafunka suke daure. Yace."Akwai dalilin da ya sanya hakan wannan ba matsala bace kada hakan ya daga muku hankali." Kusan a tare suka sauke zuciya da jin furucinsa suka shiga godewa Allah da abinda yayi musu. Har yamma suna tare ya saki jikinsa sosai yana basu labarin irin gwagwarmar suka sha a dajin! tace."Kaga Umaru shiyasa kwata-kwata hankalina bai kwanta da wannan harkar ba mahaifinka har ya mutu da abun a cikin ransa saboda haka idan Allah yasa ka kubta to dole ka ajiye wannan sana'ar ka nemi wata domin hakan shine samun nutsuwarmu baki daya. Domin ya kwantar mata da hankali sai ya amsa mata akan abinda take so, taji dadin hakan kuwa tay tai masa addua da fatan samun nasara akan dukkan abinda ya sanya a gaba. ***** Ta jima a toilet din tana durje jikinta da sabulai iri-iri kafin ta dauro towel ta fito. idonta ya sauka kan tufafi wanda aka ajiye mata su kan gado komai sabo underwears sai riga da siket na wani material mai taushi, goge jikinta tayi kafin ta zauna gaban mudubi tana kokarin duba man da zata shafa a jikinta, tsaki taja tana hararar tarin kayan kwalliyan dake dressing mirror din duk ciki babu kalar man da yayi mata ballantana ta shafa a jikinta........wani lotoin ta dauka tana jujjuyashi a hannunta sai ya mutse fuska. Ta turo kofar dakin ta shigo da sallama a bakinta kallo guda kayi mata zaka fahimci cewa tana daga cikin jerin mutane masu sauki kai da daukar rayuwa a sannu, tana da fara'a sosai domin da wuya kaga bacin ranta sai in tura ta kai bango. Fuskarta yalwace da fara'a ta 'karasa shiga dakin da fadin." Yawwa kin fito ko ga kaya nan na ajiye miki na san za suyi miki dadin sawa.'' Shuru tayi bata tanka ba. Ta kalleta da fadin." Ko dai na sauya miki wasu wannan ba suyi miki ba."? Tsaki taja da fadin." Don Allah kin cikani da surutu haka na duba na gani okey nagode." Ranta ya 'baci da abinda tayi mata amma sai ta danne ko alama bata nuna a fuska ba tace." Okey to shikkenan idan kin shirya sai ki fito muci abinci ." Ta'be bakinta tayi ba tace komai ba ta cigaba da jujjuya abinda ke hannunta. Juyawa tayi da niyyar fita daga dakin. sai ta dakatar da ita, ta tsaya tana sauraranta. A yatsine tace." Wannan tarkacen mayukan shafawar taki ba zan iya shafawa ko daya a jikina ba domin ni ba irinsu nake shafawa ba. Cike da mamaki take kallonta tana mamakin furucinta, tarkace!!! duk man da take shafawa babu na kasa da dubu biyar sai sama amma shine har take magana cewa ita tafi karfin ta shafa a jikinta. Jinjina al'amarin tayi kafin tayi 'yar dariya da fadin." Lallai 'kawata kina ji da gayu amma idan ba haka ba meye laifin mayuka na ko wannan na hannunki kika shafa ya isheki." Cike da wasa ta karashe maganar..........Sai ta fusata! ta mike tsaye tare da buga mata tsawa! da fadin." Ke kin san wacece ni kuwa? da har kike min wannan banzar maganar."? Ta'be bakinta tayi tace." Ina zan sani hajiya ni dai Daddy ya kira ni a waya ya sheda min cewa zanyi b'akuwa shiyasa nake karramaki bahaushe yace." bakon ka Annabin ka." Dogon tsaki! taja kafin ta koma ta zauna..........Ita kuma da sauri ta bude kofar dakin ta fita tana mamakin al'amarin. Zama tayi tare da sauke ajiyar zuciya, ta kalleta da fadin.'' Ya akayi ne? bata gama shiryawa bane."? Baki ta dan ta'be kafin tayi 'yar dariya da fadin." Na isketa ta fito daga wanka tana nazari man da zata shafa." Cike da mamaki tace." Kamar yaya nazari duk cikin mayukan shafawar taki babu wanda yayi mata."? Tace."Hakan take nufi." Tana kokarin magana motsin fitowarta ya katseta duk sai suka juya suna kallonta tayi kyau sosai a cikin material din sai dai siket din ya matseta dalili tana da kwankwaso mai fadi da cika sakamakon mai kayan da nata bai kai hakan ba. Da murmushi a fuskar matar gidan tace." Kin fito."? "Umm." tace kawai ta nemi kujera ta zauna sai wani basarwa take. Ta kalleta da fadin." Nabila mai yasa ki ka bata wannan kayan kamar sun matseta ki tashi ki dauko mata wasu." Tace."Mommy kin san duk kayana riga da siket ne kuma bai zama dole suyi mata yanda takeso ba tunda ta fini kiba." Ta kalleta da fadin." Zinatu baki takura ba dai ko."? Girgiza kai tayi da fadin." Kada ki damu hakan yayi min daidai domin yawancin kayana haka suke." Tace." To masha Allah ku tashi muje muci abinci." kusan a tare suka mike kai tsaye gurin cin abincin suka nufa. To duk wasu bayanai da ya kamata ace gwamnati ta san dasu Asp ya harhad'a komai ya turawa maigirma governor domin ya saurara dashi da wa'inda da ke da alhakin hakan, sai dai ya sheda masa cewa ranar asabar shi da wanda ake zargi da aikata ta'addancin zasu shiga sansanin domin binkice akan sassan sannun da zai tabbatar da gaskiyar magana. maigirma governor yayi na'am da maganar ya kuma bada goyon baya akan tafiyar. *'Yan jarida mane ma labarai suka samu abun yayatawa a gari! gidajen redio da television gami da jaridu labarin abinda suke nunawa kenan cewa ashe wanda ake zargi da *UBAN DABA!* *bashi da ala'ka da zargin da ake masa asali ma shine mutum na farko wanda ya fara karya alkadarin d'an ta'addan da ya addabi kasa da al'ummar dake cikinta, domin tabbatar da gaskiyar magana kakakin rundunar 'yan sanda wato Asp Musa Baharu zai jagoranci shi wanda ake zargi domin gudanar da binkicen sassan hannun wanda ake nema ruwa a jallo...........Sannan kakakin rundunar 'yan sandan ya shedawa mane ma labarai cewa yanzu haka akwai d'iyar Sarkin Kano mai suna Zinatu wanda ake zargin cewa wasu 'bata gari sunyi kidnapping d'inta domin samun kudi daga gurin mahaifinta, amma ha'kan su bai cimma ruwa ba sakamakon zuwan shi wanda ake zargi da ta'addanci mai suna UMARU wanda jama'a suka fi sanin sa da GOJE!* *shine wanda ya zama garkuwa a gareta har yayi nasarar tallafar rayuwarta bayan ya samu nasara akan wa'inda sukayi garkuwa da ita............Wannan shine cikakken rahoton da ya cika garin Katsina dama kewayanta.* Duk wanda ya danganci masarautar yana cikin farin ciki sakamakon samun cikkaken labarin bayyanuwar ta............Fada ta cika da jama'a masu zuwa taya murna da fatan alkairi maimarta da 'yan uwansa fuskokinsu tamkar gonar auduga saboda tsantsar farin cikin da suke ciki a ranar yini cir masarautar babu masaka tsinke mata da maza wannan ya fita wannan ya shiga. Gimbiya Aysha da 'yar uwata tare da 'ya'yansu su ka kasance cikin farin ciki mara misaltuwa, Maijidda ma tayi nata murnar daidai gwargwado amma ta ciki na ciki domin kasa zama tayi cikin 'yan uwanta ta nufi b'angaranta jikinta duk a sanyaye yanzu babbar damuwarta kada asiri ya tonu sunanta ya fito shine abinda yafi tsaya mata a rai.... *Hello my fans A hanzarta biyan kudi domin yanzu zamu shiga cikin labarin akwai kuraa!! 😄 kada ki sake ayi bbu ke 'yar uwata kada ganin k'yashi ya hanaki biya ki zauna jiran na sata wallahi tallahi! hakkin wani masifa ne!! mai girman gaske!! yi kokarin gudun haram! komai kankantarta!!!* *#500 via 0542382124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....* *22796074090* dala dari katin mov ko airtal *GOJE!*🏹 🐕‍🦺🐕‍🦺🐕‍🦺 _(SADAUKI OMAR RETURN👑💫_) *BINTA UMAR ABBALE🍒* *_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION🖊️📚_* _____________________ FREE PEGE *23&24* *Biyu da rabi na sulusin dare!* Cikin firgitaccan yanayi ta tashi zaune tana kiran sunan Allah! hakan ya janyo farkawarsa dama can bashi da nauyin bacci, zaune ya tashi kafin ya rike hannunta dake wani irin rawa, yace."Menene Aysha."? Sai kawai ta fashe da wani irin kuka ta rungumeshi tana girgiza kai da fadin." Zinat ce ranka ya dade yarinyar nan na cikin mugun yanayi Allah ya nunan hakan a mafarkina." Sake rungumeta yayi a jikinsa cikin sigar rarrashi yace."Aysha mafarki ba gaskiya bane kada ki gazgata abinda ki ka gani, bana tsammanin cewa mafarkinki zai tabbata, jikina yafi bani cewa yarinyar nan tana a raye kuma daf take da ta dawo garemu da ikon Allah." Kallonshi tayi hawaye na tsere a saman fuskarta tace.''Ranka ya dade koda Allah ya nufa yarinyar nan ta dawo gida bai zama lallai a sameta da cikakkiyar lafiya ba ka san dai yanda duniyar nan ta lalace da rashin gaskiya wannan shine babban tashin hankalina." Ya sauke ajiyar zuciya da fadin." Kada ki fadi haka Aysha! zuciyarki ta dinga halarto miki alkairi akan yarinyar nan! adduarki a gareta karbabbiya ce a gurin Allah, kada ki yarda zuciyarki ta yarda da wannan mafarki ki dauka cewa k'anzon kurege ne, a yanzu abinda zakiyi ki faranta min shine ki tashi kije ki dauro alwala ki gabatar da nafila a gaban ubangiji kana ki mika masa kukanki." Ta sauke ajiyar zuciya da jin sassauci acikin zuciyarta, a hankali ta zame jikinta daga nasa ta sauka daga gadon ta nufi toilet domin daura alwala. Tana fitowa shima ya tashi ya shiga ya daura alwalar ya fito, lokacin har ta tayar da sallar, jallabiya da gajeran wando ya sanja kana ya gyara dadduma shima ya tayar da tashi sallar. ****** Tun bayan daya sa'ba ta a kafad'a suke buga artabu a tsakanisu, rikon tsauri! yayi mata yana gudu tare da tsallake manya-manyan dutsina da ita a kafadarsa! tayi duk wani kokari gurin ganin ta ceci kanta abun yaci tura! domin mutumin mugun basamude! ne wanda cizo da yakushi basa shigarsa! dukansa take tana cizo duk ta dauke masa fata amma ko ajikinsa, ya riketa katamau! yana gudu! burinsa kawai ya kaita gaban ogansa ya san hakan zai faranta masa rai. Hakan ne ya kasance kuwa, Ogan nasu yana cikin bacin rai! mai tsanani sakamakon rashin samun nasara! bai ta'ba fuskantar irin hakan ba sai a wannan lokacin, kai kawo kawai yake gurin ya rasa abinda yake masa dadi! ............Amma zuwan babban yaron sa da yarinyar ya faranta masa rai! mutuka, sai kawai ya kwashe da wata 'yar iskar dariya kafin yayi wani irin tsalle! da juyi na jin dadi, ya zuba mata kwala-kwalan idanuwansa! Bakinsa kawai yake lasa, jikinsa na wani irin tsuma! komai na yarinyar yayi cif da cif! bata da makusa, cikakkiyar mace irin wacce ya jima bai kwanta da irinta ba! Gurin ya tsit! gabad'aya yaransa sun zagayeta motsin kirki ta kasa, kanta ne ma yake juyawa a gurin, dishi-dishi! take kallonsa har ya karaso inda take zube! Ya tsugana kusa da ita, sai tayi saurin janye jikinta, ya sha kunu; tare da matsawa jikinta, ta sake janyewa tana watsa masa mugun kallo! Mahaukaciyar dariya yayi! ya cigaba da lasar lebansa, yana bin sassan jikinta da wani irin kallo na tsantsar sha'awa! Hannu ya kai jikinta, a zabure! ta fitar da hannu ta bashi kyakykyawan mari a fuskarsa! ko gezau! beyi ba sai dai yaransa da suka zabura! sukayi kanta! Ya daga musu hannu da basu umarnin matsawa baya. Suka matsa can nesa suka bar shi da ita, zaman dirshan yayi a gabanta ya mika mata tafkekiyar fuskarsa dake cike da kasumba! yace. " Idan hakan yana miki dadi ki sake aikatawa." Ya fada yana sake tura mata fuskar. Tsaki mai tsayi taja! ta matsa nesa dashi! ya rarrafa kan gwiwarsa ya cimma inda take! kafafunta dake daure da takalmi ya tsirawa ido, babu abunda yafi tafiya dashi irin shara'ban kafafunta, ya kai hannunsa gurin yana shafawa da lumshe ido, janye kafarta tayi da fadin." Allah ya isa!! Ya bude idanuwansa da suka rikice! da zazzafar sha'awarta! "Ni kikewa Allah ya isa."? yafada yana nuna kirjinsa. Ba ta amsa ba, wani irin kallon banza take mai, ya lumshe idonsa ya bude da fadin." Ina sonki saboda kinyi min, ban ta'ba amfani da mace na maimaita ba, amma gani guda da nayi miki naji cewa kece zaki zama mahadin rayuwarta, shekaru sun ja ya kamata ace nima na ajiye k'wai a duniya kece zaki zama uwar 'ya'yana, kinzo hannuna babu wani mahalukin daya isa ya rabani dake." Maganganunsa suka dinga amsa kuwwa! a kunnanta, ta tsira masa ido tana mamakin furucinsa, kallonsa kawai take ta rasa yanda zata fasaltashi, shi ba mutum ba ba aljan ba. Ya mike tsaye a kanta! saurin kauda kanta tayi gabanta na lugudan duka! Blet din dake daure a kugunsa ya fara kokarin kwancewa, tayi saurin tashi tsaye! dariya ya fashe da ita, kafin ya cire blet din ya jefar dashi ya zame wandon............"Innalillahi- wa'ina ilahi raji'un! abinda ta ambata kenan, ta rintse idonta da karfi! tunda take bata ta'ba ganin tsaraicin namiji ba sai a kansa, yanda yake mara fasali to hakama gabanshi yake tamkar na mahaukacin doki!! Wandon ya mayar jikinsa, yana kyalkyala dariyar hauka kafin ya fizgo kafadarta! fuskarta ya rike a cikin tafin hannunsa, ta rufe idonta gam! bata son kallon mummunar fuskarsa. "Ina fatan kin shirya zama tare dani! masoyiyata nayi miki alkawarin baki dukkan wani jin dadi na duniya! gwarzo ne ni akowane fanni! na tabbata cewa ba za kiyi nadama da kasancewarki a tare dani ba." Zuciyarta ta dinga tashi sakamakon warin bakinsa, fuskarta ta fizge! da karfi ta matsa can gefe tana numfarfashi! yawu ya cika mata baki! yana zuwa gurin da take ta fesa masa yawun a fuskarsa! Ya sanya hannu ya shafo yawun yana lashewa! amma kuma fuskarsa ta rikide da alama yaji haushin abinda tayi masa. Sai da ya lashe yawun tsaf! sannan ya kalleta, ta tsorata da yanayinsa, sai ta sunkuyar da kanta, a kausashe! yace." Wannan shine na farko kuma shine na karshe kada ki sake maimatawa idan ba hakaba zan ladabtar dake. Ta cire tsorosa da fadin." Wawa!! kafara ladaftar da kanka kafin ka ladaftar da wani." "Wawa!! kalmar tayi mai ciwo! sosai a ransa sai kawai ya dingi maimaita kalmar a fili yana zagayeta, ta dinga binsa da kallo duk inda yayi, ya shammaceta yasa mata kafarsa ta fadi a kasan a gurin! turmusheta yayi ya danneta iyakacin karfinsa! bakinta yake kokarin sumbata tana kautar da kai yana bin duk inda ta nufa, be fasa maimaimata maganar ba! suka dunga bugawa! domin duk yanda yaso hada baki da ita ya gagara! ta gumtse bakinta gam!!! sai ya zama kamar mahaukaci sai rawar jiki yake babban burinsa yaji yana shan bakinta.................Ba zato! ba tsammani! yaji saukar kibiya a gadon bayansa!! Ya gantsare! tare da zabga ihu!! a zabure! ya mike tsaye! ya fizge! kibiyar ya jefar jini ya fara tsiyaya! tashin hankali kenan! waige-waige yake a gurin yana mamakin yanda akayi hakan ta faru. Cikin zafin nama! ya mikar da ita tsaye sai numfarfashin wahala take, ya rike hannunta katamau! yana sake dudduba gurin!..................! Wani abu dake daure a hannunsa ya murza! kafin ya kirayi yaran sa! kaf! suka kewayeshi! sai dai ganin jini na tsiyaya a bayanshi ya firgitasu! a garin ya akayi hakan ta faru! Ya akayi ogansu ya bari aka cimmasa irin haka? a tarihin rayuwarsa kaf babu wani mahalukin da ya ta'ba fitar masa da jini sai zuwan wannan matashin saurayin lallai akwai wani abu da yake shirin faruwa! Wani irin nishi! yake yana zazzare idonsa! shi kansa yayi mamakin al'amarin, yana da suddabaru! iri-iri! ya akayi har yaron ya samu damar ganin inda yake tare da samun damar harbinsa da kibiya!! Sai kawai ya fasa ihu!!! ya dubi abunda ke daure hannunsa yana wasu irin surutai! ya sake murza abun! yana sambatu! gurun yayi tsit! babu mai kwakwkwaran motsi a cikinsu, domin sun shiga rud'ani da faruwan wannan al'amarin!! Sautin muryarsa ne kawai yake tashi a gurin, yana wasu irin maganganu!..............Can kuma sai haushin karnkuna! ya maye gurbin maganarsa, Tsit! yayi gabansa na wani irin fad'uwa!! Hankalinsu ya kai kololowa gurin tashi!! duk suna tsaye sun kasa tabuka! komai ya zabura! da karfi yace."Tsayuwar me kuke ba zaku ba zama ba har sai ya cimma na." Da sauri suka rarrabu a cikin dajin suna neman inda yake.. Yana tsaye! a gurin sai kace dasashe! har yanzu kuma hannuta yana rike a hannunsa ya rike tamau!! Haushin karnukan! suka cigaba da kusantowa inda yake! da saurin gaske ya fara kokarin janta tana turjewa! kawai sai ya dauketa ya sa a kafad'a, ya riketa da kyau! da niyyar neman mafaka! taku daya yayi yaji saukar wata kibiyar! ya gantsare! tare da sakin ihu!! amma duk da haka bai sauketa ba. *"Ni ne GOJE!!! mugun! makangari sai kuree! Ni cinkun! naci garina kuma ni ke zuwa garin wasu yaki!! kandagarki kurmar dutse! mugun makangari sai kureee!* Sautin maganarsa ya cika dajin gami da kunnuwansu. Ya juya gabas kudu yamma arewa! domin hasashen inda maganar ke fitowa, bashi da tabbacin gurin, kawai sai ya umarci sauran wa'inda ke tare dashi cewa su tashi bomb a kowanne sassa na gurin! Hakan ne kuwa ya faru tashin bomb! sukayi a gurin kowane sassa a dajin ya rikice! da hayaki! wannan damar ya samu yayi dirar mikiya! a gabansa! alokacin da yake kokarin neman mafaka. Kallon kallo aka fara! Zinat kam ganinsa ya sanyata sauke ajiyar zuciya ta shiga godewa Allah!!! Ido ya tsirawa! hannunta dake cikin nasa. wata kibiyar kishi ta sokeshi! cikin hargagi! yace."Sakar mata hannu ko na sheka da kai barzahu"!! ********************** ? ************************** ********** Ai Hausa Novels **************** *************************? ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ? ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ? ************************** Ya tsira masa jajayen idonsa kafin ya fashe! da dariya ya sake rike hannunta da kyau! Yace." Kai ne dan iskan da kake ganin ka isa kayi gogaggaya dani ko.! Yace" Eh ni ne UMARU! kuma ni zan kawo karshen ta'addancinka."!!! Kaifaffar wu'kar dake rataye a jikinsa ya cire ba tare da zato! ba ya datse! masa hannu wanda yake rike da nata! hannun tun daga kafada har kan yatsu ya fadi a gurin yana wutsil-wutsil, jini kuwa sai tsartuwa yake! ya durkushe! a gurin, yana wani irin ihu!!!!!! Kafin kice kwabo! kaf! kowa ya hallara a gurin, ganin ogansu a durkushe! babu hannu ga jini na zuba ya zaburar dasu! sukayi kansa! sai yayi gaggawar soka wu'ka a wuyan ogan nasu!!! *Uban daba!* ya sake rikicewa! domin bai shirya mutuwa ba, da hannu yayi wa yaran sa alama cewa su ajiye makaman dake hannunsa, sukayi yanda ya umarcesu! Ajiye makamansu keda wuya suka fara jin jiniya alamun jami'an tsaro sun shigo gurin!!!! *Uban daba!* hankalinsa ya sake tashi, babu shakka ya san ya shiga hannun hukuma k'aryarsa ta kare! sai kawai yayi kwance-kwance ya shammaceshi! wani wawan duka ya sakar masa a gwiwarsa!. dukan ya shigeshi! sosai yayi taga-taga! zai fadi wannan damar ya samu ya k'wace! daga hannunsa a sukwane! ya bar gurin cikin wani irin gudu na ceton rai! sauran yaransa suka rufa masa baya...........! Zubewa yayi k'asan gurin ransa a masifar bace! kwata-kwata bai so hakan ta faru ba, amma ba komai tunda har ya samu nasar raba shi da hannunsa guda, watarana zai samu babbar nasara a kansa! Tsinin bindiga! yaji a saman kansa! da sauri ya bude idonsa sai kawai yayi arba da zaratan! sojoji da 'yan sanda! sun zagaye shi kowanne ya saita shi da bindigar dake hannunsa.........."Babban cikinsu shine yayi magana ."You under arrest."! Hannuwansa ya daga sama cikin bin umarni, suka d'aura masa zabgegiyar tsar'ka! kafa da hannu suka sa key suka kulle, kafin su mikar dashi tsaye....! *#500 via 0542382124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....* *22796074090* dala dari katin airtal ko mov. *GOJE!*🏹 🐕‍🦺🐕‍🦺🐕‍🦺 _(SADAUKI OMAR RETURN👑💫_) *BINTA UMAR ABBALE🍒* *_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION🖊️📚_* _____________________ FREE PEGE *19&20* Cikin tsantsar tashin hankali! da gigita suka gurfana a gabansa kafin su sheda masa abinda yake faruwa.............."Ya wani mike a fusace! tare da mi'ka tafkaken hannunsa wanda yatsun ke cike da zabban zinare da azirfa! wani irin bahagon mari! ya dinga kifa musu kafin ya sanya kafarsa ya tunkudesu duka suka fadi wanwar! a gurin. gabadaya suka Sunkuyar da kansu, jikinsu in banda rawa babu abinda yake. Ya takarkare! da karfi! ya kurma uban ihu!!! lokaci k'ank'ani gabadaya kaf yaransa suka kewayeshi! ya goya hannu a baya yana kai kawo a gurun! Tsit! gurin yayi babu mai kwak'wk'waran motsi a cikinsu. Lokacin da yake kai kawo a gurin kallonshi nake ina mamakin muninsa! baki ne sosai gashi gajere dab da kasa, yana da katon kai da tafkekiyar fuska, gabadaya hallitunsa masu girma ne bayan gajartar da yake da ita, bakinsa kato haka nan hancinsa kwala-kwala idonsa kadai ya isa firgita yaro! jajawur! dasu, kasumba tayi kaca-kaca a fuskarsa babu kyawun gani! kallo guda za kayi masa ka tabbatar da rashin imaninsa.! Cikin kaushin murya! ya fara magana kamar haka." A jinin jikina naji cewar akwai ayarin da suka shirya min! Yau tsayin sati guda kenan idan na kwanta bacci nake ganinsu a idona! babu wani shirinsu da zai firgatani! na shiryawa zuwansu! na kuma yiwa kaina alkawari cewa duk yawansu sai naga bayansu! babu wani mahalukin daya isa ya tunkari inda nake ba tare da she'kashi barzahu ba! nafi karfin hukuma! ballanatana wani dan adam! saboda haka dukkunanin ku na umarceku da cewa ku zauna cikin shiri babu wanda zai fita da rai a cikinsu."! jiki na tsuma! yake maganar yana wani irin huci! gabadaya ya burkice sakamakon jin abin da yazo masa a bazata! ******** Saboda tsabar kwarjin da yayi musu sam sun kasa hada ido dashi, suna gurfane a gabansa, yayin da shi kuma ke kai kawo a tsakaninsu kafin yaja tunga ya tsaya a gabansu, hannuwansa ya goya a baya, babu wasa ya fara magana kamar haka." "Ya sunanku."? babu wanda yayi magana a cikinsu. Ya sake maimaita maganarsa! uffan basu ce ba. Ya juya baya yana kallon jama'arsa dake tsatstaye kowanne a cikin shiri. "Alba bani wannan dorinar." yafada yana kallonsa. Da saurin gaske ya ciro bulalar daga cikin gidanta, kaurinta ya isa! nayi imanin za ta iya dauke fatar mutum. Ya gyara rikonta a hannunsa, cikin wani irin hargagi! wanda yasa gurin amsawa! yace."Ba zaku bude baki kuyi magana ba ko."? Duk da sun tsorata da yanayinsa, amma hakan besa sun magantu ba. Ya zabura! ya juya tare da kiran Alba! yana zuwa ya umarceshi da ya cire musu kayan jikinsu kaf! Alba yabi umarni! Ya kai ya kawo ya gurin jikinsa na wani irin karkarwa! tsumin ne ya tashi! ganin haka ya sanya wasu daga cikin yaranshi suka bara buga gangi!!! da bushe-bushe? Ya sake rikicewa! wani irin tafka! yake musu! suna ihu! da birgima a gurin! Birgima suke a gurin suna gurnani! yana binsu da tafkekiyar dorinar dake hannunsa yana tafka musu, wanda ya janyo tsiyayewar idon daya daga cikinsu. Hankalinta a masifar tashi taje tana kokarin rike masa hannu kuka take kariris! tana bashi hakuri sunyi bala'in bata tausayi! bata san bashi da imani ba sai yau! Tureta yayi ta fad'i kasa ta rirrike kafafunsa "Kayi hakuri wannan rashin imani ne, ka zubar masa da ruwan ido ga jini yana fita a jikinsu kada kayi kisan kai." Wannan maganganun nata besa ya fasa abinda yake ba, ya sanya kafarsa ya taka gwiwar wanda yake kokarin gudu! ya murza da karfin gaske! wani marayan ihu! ya saki kafin ya zube a gurin yana karkarwa jiki yace." Yi hakuri kada ka kasheni zanyi ma bayani." Ba tare da cire kafarsa ba, ya buga musu tsawa! da fadin" Ya sunanka."? baki na rawa yace." sunana Yakubu ." Ya kalli dayan da yake matagugu a kwance "Kai fa."? Yace." Sunana Sulaiman." Kafarsa ya cire yana wani huci! ya barsu a gurin.......Saman wani icce! ya zauna! wasu daga cikin yaranshi suka bishi! da ruwa... Wasu na masa fifita wasu kuma na kara kambaba darajarsa! Nad'in kansa ya warware kafin ya sunkuya tare da bada umarnin a zuba masa ruwa a saman kan. Ya dago kan yana girgije ruwan sumarshi mai laushi tabi ta kwanta tana digar da ruwa. Alba yasa abu yana tsane masa ruwan. Har yanxu babu sassauci a tare dashi, idonshi na tsaye a inda suke. tana tsaye a gabansu, magana a suke a tsakaninsu amma basa iya jin abinda suke cewa. Ranshi ya baci da ganin abinda take, yarinyar ta nema ta lalata masa aiki. mikewa yayi da bulalar a hannunsa ya karasa gurin, kallon mara imani take masa, za tayi magana kenan, a zabure! yayi kanta da bulalar!! ta matsa gefe da sauri! gabanta na bugawa! jajayen idanuwansa ya tsira mata cikin mashahuriyar tsawar data kusa sanyata sakin fitsari yace." Wuce ki bani guri."! kafafunta na rawa ta bar gurin, bai ta'ba firgitata ba kamar yau. Ya kallesu kafin yace." Ku tashi tsaye! suka yunkura da kyar suka tashi! gabadaya jikinsu ya sauya kama saboda duka! yayi musu wani kallo kafin ya juya da basu umarnin bin bayansa. Ba tare da iya kallon fuskarsa ba ya fara yi magana kamar haka "Aikinmu shine ta'addanci! rai ba abakin komai yake ba a gurunmu, sannan muna tarewa jama'a hanya cikin dare mu farauci dukkanin guzirinsu, muna rabasu da matansu da 'ya'yansu, mu kwanta dasu, kamar matan auranmu daga 'karshe mu 'kona gawarwakinsu ko kuma mu fito dasu kan hanyar mu yasar! duk wanda ya shiga komarmu bama saurara masa muna da muggan makamai kuma muna da daurin gindi daga sama, kamar yanda ka sani cewa masana sunyi hasashen cewa gurin da muke rayuwa akwai albarkar kasa, to tabbas hakane akwai! amma maigidanmu yaci alwashin cewa babu wani mahalukin daya isa ya amfana da albarkar dake wannan guri sai shi da ayarinsa, yawancin mu musulmai ne magoya bayanshi, amma ya haramta mana ibadah! bama sallah bama salati da duk wani abu da ya cancanta, burin mu ako yaushe mu kashe duk wanda yayi yunkurin shiga gonarmu, maigidanmu yaci alwashi mai zafi! akan duk wanda yayi yu'kurin ganin bayan rayuwasa." Ya k'are maganar tare da sake risinar da kanshi kasa. Beyi mamakin da jin wannan jawabi ba, hausawa sukace da dan gari akan cin gari, a jawabin da sukayi masa ya fahimci cewa gabadayansu musulmai ne amma suka yarda suka bada goyon bayan ta'addanci a kasa. Ya girgiza kanshi da fadin." Yakubu-Sule daku aka hada baki wani wawa! zindiqi! mushiriki! ya addabi! kasa da al'ummar dake cikinta, shin me kuke nema a duniya da har kuka mayar da zubar da jini! abin banza? a matsayinku na Musulmai masu amsa sunayen annabawa! shin ya cancanta ku aikata wannan ta'addanci."! Gabadaya suka shiga girgiza, jikinsu yayi wani irin laushi, yaja numfashii ya fesar! kafin ya cigaba da cewa." Dukkaninku baku cancanta da cigaba da rayuwa a duniya ba domin barin irinku a ban 'kasa had'ari ne."! Jin abinda ke fitowa daga bakinsa ya firgitasu, a tsoroce! suka shiga bashi hakuri suna kiran sun tuba!! Wani mugun mari! ya kifa wa daya da jikinsu, 'yar hantsile yayi ya kifa yaci da kasa! tsaye ya mike! yana zagaye a kansu. gabadaya sun tsorata da yanayinsa, su kansu yaran shi basu taba ganinshi a cikin irin wannan yanayin ba, jikinsa in banda tsuma! babu abunda yake, Zinat kuwa addua take a zuciyarta kada Allah yasa ya aikata kisan kai! Da jan ido ya kallesu, da fadin." *Ni! ne zan kawo karshen ta'addancinsa! *GOJE!!* *Nake mai maganin wani takadiri! Nayi tawa! nayi ta wasu! wannan haka yake! ba'a zubawa dani a kwashe lafiya! *Billahil-lazi hurramanu!* *nayi wa kaina alkawarin ganin bayansah"!* Yanda yake maganar yana zazzare ido shi tabbatar da abinda yake cikin zuciyarsa hakan yake babu 'karya! Shar'bebiyar wukar dake rataye a kafad'arsa ya fizgo! daga gidanta, wani masifaffan ihu! ya kurma!!! kafin ya fara dadura! wukar a wuyansa!! Tashin hankali kenan! gabad'aya gurin ya kacame! dan yaran sa ma manyan wukake! suka fito dashi suna gurzawa a kowane sassa na jikinsu! . shi kuwa a wuyansa yasa wukar ya zage karfi sosai! yake gurzawa.! kuka wiwi! ta dinga yi tana kallon badakalar dake afkuwa, ita tsoronta kada su kashe kansu, ta rasa ya za tayi da rayuwarta a cikin wannan mashahurin dajin! Tana kuka na fitar hayyaci ta karasa inda yake gabanta na lugudan duka! hannu na karkarwa take kokarin rike damtsan hannunsa, "Ka bari don Allah! ka daina! ka umarci yaranka su daina kada ku kashe kanku."!! Ko sauraranta beyi ba ya cigaba da abinda yake, jikinta na wani irin rawa ta rumgumeshi tsam! tana kuka tare da dukan bayanshi. wannan ya janyo sadudarsa! ya cake! wukar! a gurin tare da danneta da tafin hannunsa! Numfarfashi kawai yake gumi na yankowa daga kowane sassa na jikinsa! Tsit! gurin yayi sakamakon umarnin da ya basu, suka mayar da wukaken jikin jikinsu. Har yanzu tana manne a kirjinsa ta kam'kamshi shi da yayi wani motsi zata kai masa duka! kuma bata fasan kukan ba. Hannu yasa ya d'ago fuskarta, suka tsirawa juna ido! ya jima yana kallonta kafin yasa hannu ya goge mata hawayen da suke ta zuba! yayi namijin kokarin cireta daga jikinsa! ta sake kokarin rungumeshi! duk a kokarinta na hanashi aikata wani abun. Hannu ya daga mata da ido! ya gargade ta, sai ta sunkuyar da kai! amma har yanzu bata dawo daidai ba. Ya kalli Alba da fadin." Bani abun rubutu." Da sauri ya fito da takarda da biro! ya mika masa. A takaice ya rubuta." _*(KA SHIRYA YAKI DA MAKASHINKA!!!)*_ Wanda yake da d'an sauran kuzari ya mikawa takardar da fadin." Sa'kona ne wannan kana isa ka bashi, cewa daga ni *MAKASHIN MAZA!* Da kyar! ya mike ya kama hanya yana tafiya tare da waiwayen d'an uwanshi dake kwance cikin halin rai da rayuwa! Koda ya karanta wasikar sai kawai ya fashe! da wata mahaukaciyar dariya! da mike tsaye tare da dukan! girkakken dutsen dake gabansa! Hannuwansa yasa ya tallefe 'keyarsa! tare da sunkuyar da kanshi kasa! Ya jima a haka kafin ya d'ago yana kallon yaranshi dake kewaye dashi, gabad'ayansu suma jikinsu yayi sanyi da wannan al'amarin. Ya kalli Nuhu dake rakube! gabadaya kammaninsa sun sauya saboda wuyar da yasha, ranshi ya sake 'baci! kawai ba tare da kowa ya ankara ba, ya fille wuka! tana! walwali a wuya ya burma masa! a take ya fara shure-shure a gurin jini sai tsartuwa yake, kafin wani lokaci rai yayi halinsa! Ya juyo kansu a sukwane! yana kallonsu da kwala-kwalan idanuwansa! Sun tsorata mutuka gaya da ganin tashin hankalin maigidansu. *"Cike da cin laya yace."Kamar yanda na soke! wuyan wannan shashashan! to haka zan soke! wuyan wannan marakunyar yaron daya tunkari inda nake! Ni! nayiwa kaina wannan alkawari!! saboda haka zamuyi kwankwance! kafin mu afka inda suke da yak'i."* Suka hada baki gurin fadin."Yanda kayi shine daidai maigida muna goyon bayanka ako wane yanayi." **** Tun bayan tafiyar Nuhu! babu wani abu daya gilma, hakan besa sun saki jikinsu a gurin ba, sai da duhun dare ya shiga sannan suka fara neman abinda za su ci. Ita dai 'ya'yan itacuwa kad'ai ta iyaci, tana zaune tana kallonsu sun tada wuta sai gashe-gashe sukeyi da kallon ikon Allah! da kudirarsa, ace wai mutum ya gasa majici gafiya da sauran dabbobi marasa kyau yana ci a cikinsa. K'auri da karni! duk ya cika gurin! dole ta tashi domin sauya gurin zama, domin mutukar tana shak'ar hayaki da kaurin dake tashi agurin zata iya amayar da abinda taci. Ido ya bita dashi! be dauke ba har sai da ta samu guri ta zauna can nesa dasu, inda Allah ya takaita akwai hasken farin wata a gurin. Ta jima a zaune a gurin tana sakawa da kwancewa! sai yanzu ta san ya rayuwa take, ta taso cikin kulawa da gata da komai na jin dadin rayuwa, tunda take bata ta'ba tsammanin cewa akwai ranar da za tayi rayuwa mai muni irin wannan ba! babban tashin hankalinta rayuwa da d'an ta'addah! irin wannan, duk abinda yake a kanta bai janyo masa 'kima da mutunci ba, domin kuwa shine mutum na farko wanda yayi sanadiyar tagayyara rayuwarta, hakika ta tsorota da rayuwa da duniyar ma gabad'aya, A yanzu babban burinta ta samu ku'bta daga cikin wannan dajin, sannan tayi wa kanta al'kawarin ganin ta jefa rayuwarsa cikin kunci da tashin hankali kwantankwacin yanda yayi mata. Saukar wani abu taji saman wuyanta, da sauri tasa hannu ta buge! ta mike tsaye! wata lafceciyar tsutsa ce ta fado daga saman bishiya. Rintse ido! tayi tana kiran sunan Allah! kafin taji zirrrrrr a kan kafarta, tayi tsalle ta matsa gefe tana kallon gurin, ashe gabadaya gurin tsutsutsine suke yawo. Jiki na wani irin rawa ta bar gurin, tana isa inda suke ta iske sunyi shimfida sun gatange gurin da itacuwa tare da rufe gurin da Net! Tsayawa tayi a gurin ta kasa shiga, domin gabad'ayansu mugun haushinsu takeji! daga nesa ta hangoshi ya nufo gurin, d'auke kanta tayi tare da jan tsaki a cikin zuciyarta. Koda ya iso gurin bece mata komai ba, ya kama hannunta! kallonshi tayi kamar za tayi magana sai dai tayi shuru, jan hannunta yayi suka shiga gurin. Guri guda ya zaunar da ita, muryar rarrashi da kwantar da hankali ya aro yace." Ki kwanta anan gurin nayi miki alkawai cewa babu abinda zan bari ya sami rayuwarki." A maimakon hakan ya faranta mata sai kawai taja masa tsaki! ta kawar da kanta tana zumbura baki! Hakan da tayi ya bata masa rai amma sai ya danne! be dauki mataki ba ya fara kokarin barin gurin, ta bude baki da fadin." Mamugunci! insha Allah sai naga karshenka." Maganar ta bashi mamaki mutuka! sai ya juyo da wani irin murmushi a fuskarsa ya nuna kirjinsa da fadin." Me yasa kike so ki kaga bayana."? Ta zabura! da fadin." Saboda kai din azzalimi ne macuci.!! Ya jima yana kallonta da mamakin furucinta" Saboda kai din azzalimi ne macuci."! to wai shin da take kiransa da wannan sunayen wane irin zalinci yayi mata tun farkon had'uwarsu? Still murmushin ya sake kafin ya furzar da iskar bakinshi, cikin gaggawa ya fita ya bata guri domin yana ji idan ya kara second a gurun zai iya nakastata. Ya jima yana fesar da hayaki kafin ya samu sassauci a zuciyarsa, zazzafar ajiyar zuciya ya sauke! yana me sake jin sautin muryarta na amsa kuwwa! a kunnanta a cikin kunnuwansa, tunda ya taso lokacin kuruciya da girma gwargwamaya yake da *Maza!* bai ta'ba sanya mata a cikin al'amuranshi ba, saboda sanin hallayarsu! yana da tausayi mussaman akansu amma baya yarda da raini daga garesu, mace daya ce yake jinta a cikin zuciyarsa, domin duk ta tara abinda yake da bukata, hankali nutsuwa ilimi tarbiya da sauransu, ita kad'ai! yake ji a zuciyarsa zai rayuwa mai tsayi da ita, ya kai ma'kura a gurin iskancin da yarinyar nan take masa, yana tausaya mata amma ya lura ita bata gani ta daukeshi a matsayin macuci! to yana ganin zai fita daga harkata domin ya samu zaman lafiya. tare da gudanar da aikin dake gabanshi. *#500 via 0542382124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....* *22796074090* dala dari katin Mov ko airtal *GOJE!*🏹 🐕‍🦺🐕‍🦺🐕‍🦺 _(SADAUKI OMAR RETURN👑💫_) *BINTA UMAR ABBALE🍒* *_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION🖊️📚_* _____________________ *RASHIN ADALCI A TSAKANIN MATA* ___________ _*Mata da yawa su kanyi kukan rashin adalci da mazajensu keyi a tsakaninsu. maza kuji tsoron Allah kuyi adalci a tsakanin matanku. lallai wajibi ne kuyi adalci tsakanin matayenku ga wanda yake auran mace sama da d'aya dole yayi adalci, ya sani cewa dukkan abinda yake gudana Allah yana sane kuma yana ganinsa, kuma wallahi sai Allah ya tambayeshi akan zaman da yayi dasu a goben kiyama.*_ *Manzon Allah SAW yana cewa." (Dukkan wanda yake da mata biyu sai ya karkata ga daya baya yiwa dayar adalci, to zai zo ranar alkiyama bangaran jikinsa guda a shanye)* *Malamai sunce karin aure ba wajibi bane, ba mustahabi bane ga wanda yake da ikon ya 'kara amma wajibi ne kayi adalci, idan har kasan ba za kayi adalci ba to kada ka fara neman k'ara auran ma domin k'arin zai iya kai ka zuwa ga halaka.* *Manzon Allah SAW yana cewa." (Dukkaninku masu kiwo ne kuma dukkan ku abin tambaye ne akan abinda aka baku kiwo a gobe kiyama)* *Allah a cikin alkur'ani yayi hani akan kada maigida ya karkata gabadaya zuwa ga wata daga cikin matansa ya kyale sauran matan saboda rashin adalci* *Allah ya baku ikon adalci a tsakanin matayenku🙏🏻* FREE PEGE *25&26* "Kada ku yarda ku bari ya kubce daga hannunku, mugu! ne macuci! ya jima yana ta'addanci a k'asa! kuyi masa hukunci mai tsauri! domun da bakinsa yake fadin cewa yafi karfin hukuma! yau tsayin kwana shida kenan daya raba ni da iyayena yayi kidnapping dina domin samun makudan kudi daga gurin mahaifina, " Sunana ZINATU ni 'yar asalin jahar kano ce mahaifina kuma shine sarki dake kan kujerar mulki a jahar." Bilhaki da gaskiya take maganar. Gabad'aya hankalinsu ya koma kanta a lokacin da take wannan maganar, da yawa daga cikinsu ba su lura da ita ba, maganarta ce ta janyo hankalinsu kanta. ganinta a firgice babu sutturar arziki yasa suka gazgata maganarta, babban cikinsu ya kwantar mata da hankali da cewa komai yazo karshe kuma sunyi alkawarin kaita gaban iyayenta idan sun gama gudanar da binkice. Beyi mamaki da jin furucinta akansa ba, ita kad'ai ce zata bada cikakkiyar sheda a kansa, amma ba tayi hakan ba, to ba zai tsananta ba, ba kuma zaiyi jayayya da hukuma ba, zai bi doka da odar amma ya san ita gaskiya d'aya ce kuma a kanta yake babu gudu babu ja da baya babu shakka! Allah za bayyana mai gaskiya. Da kansa ya haura ya shiga motar ya zauna, sojoji uku suka zauna hagu da damanshi, ya kalli na hannun damansa cikin nutsuwa yace." Akwai sauran yarana da suke n........ ya katseshi ta hanyar buga masa tsawa da fadin. "Rufe mana baki ko kai zaka nuna mana aikinmu."? Kansa ya girgiza, yace." To kabi umarnin mu domin shine samun zaman lafiyarka." Be sake cewa komai ba ya kauda kansa gefe yana hangensu suna ta binkice a gurin...........Can ya hango sun taso sauran yaransa a gaba! suna dukansu! bai dauke idonsa ba har sai da suka karaso gurin, gabadaya sun galabaita domin wasu harda rauni a jikinsu bayan wa'inda suka kone sakamakon bomb din daya tashi, ya tausaya musu sosai, domin ya san shine mujaza! domin da yawa daga cikinsu ba'a son ransu hakan ta faru ba. Suka dinga turasu cikin motar suna dukansu da wata murtukekiyar bulala irin ta karfe! To duk iya binkincensu a gurin Allah bai nuna musu dungulmin hannun *Uban daba!* da 'kasa ta turbudeshi a gurin ba, Yana kallonsu suka 'karaci dube-dubensu suka shishshiga mota da niyyar fita daga dajin. 'Bude baki yayi da niyyar magana kawai ya hangota tare da wani soja yana kokarin bude mata gaban mota domun shiga........Yaji wani irin ciwo a cikin ranshi! bakinsa ne yayi nauyi ya gaza furta maganar dake cikin cikinsa har suka fita daga cikin dajin bai dago kanshi ba! wani irin kuttun bakin ciki ya tsaya masa a wuya, tunda yake bai ta'ba ganin butulu irinta ba. Da yayi motsi zasu saita shi da bindiga! da fadin." Ya kiyaye idan kuma yayi wani yunk'uri na gudu to zasu harbe shi! murmushi kawai yake musu, wanda hakan ke 'kara tunzura musu zuciya. Labari kaf ya cika garin Katsina da kewayenta cewa A yau 11/3/2007 jami'an tsaro sunyi nasarar kama babban dan ta'addah nan wato *Mashekin daji!* wanda ya addabi k'asa da jama'ar dake cikinta. Headquarter 'yan sandan kuwa cike take da 'yan jarida da jama'ar gari masu ganin kwal uwar daka. Koda motocin jami'an tsaron suka shiga headquarter 'yan sandan sai gurin ya hargitse da hayaniya kowa burinsa yayi ido hudu dashi, Mussaman 'yan jarida masu daukar rahoto. Sai da suka rufe masa fuska sannan suka fito dashi a dadd'aure! Suka rirrikeshi da kyar yake cire k'afa sakamakon sark'ar da tayi masa dabaibayi! Duk da hakan sai da yan jaridan suka dinga daukar hotonsa tun daga sama har kasan Kafafunsa, da yawa daga cikin 'yan jaridar da jama'ar dake gurin sunyi mamakin ganinsa ingarmar namiji a labari dai sun san cewa ba haka kammaninsa yake ba gajere ne mara fasali ya akayi kuma a zahiri basu ga haka ba. Har sai da aka shiga dashi ofis din Asp sannan kowa ya watse, jama'ar gari suka tafi da zancan a bakunansu, su kuma 'yan jarida suka fara gudanar da ayyukansu. **** Cikin tsananin tashin hankali Saude matar Alba ta shiga gidan tana kuka hannunta rike da jarida. Uwale ta tare ta tana tambayarta abinda ke faruwa. Jaridar ta nuna mata da fadin." Uwale kin san abinda yake faruwa kuwa."? ta kar'bi jaridar tana dubawa tace." Saude kin san ban iya karatu ba me yake faruwa." Tace."Ki duba hoton jiki mana Mijina Alba ake tuhumarsu da ta'addanci." Gabanta ya fadi! tace." Ta'addanci kuma Saude! su da suka tafi farauta mai ya hadasu da ta'addanci inace gobe zasu dawo." Saude na kuka tace." Uwale kisa kunne da kyau ki saurari jawabin da zanyi miki." Jiki a sanyaye tace." Ina sauraranki." "Jami'an tsaro ne suka kama UMARU wato jikanki dashi da yaransa saboda zargin da ake musu na ta'addanci, a yanda na karanta rahoton cewa wai ana tunanin shi UMARU shine wannan d'an ta'addan da ya addabi kasa! yanzu haka dai gabad'ayansu suna hannun hukuma! jama'a da yawa sunyi imani da cewa hukuncin kisa za'ayi musu." Hankalinta ya tashi sosai sai ta fashe! da kuka ta tsirawa hotonsa ido duk da fuskarsa a rufe take hakan be hana ta ganeshi ba, ta tsirawa kafafunsa ido tana wani irin kuka tace." UMARU wannan ranar nake gudu a gareka, itace rana mafi muni da ba zan ta'ba mantawa da ita ba, ashe tsautsayi ne ya sanya ka tsunduma kanka wannan harkar, ni na san halinka UMARU kuma zan bada sheda a kanka, ka taka sawun 'barawo insha Allah sai Allah ya wanke ka daga zargin da ake maka." Kuka sosai takeyi hawayenta duk ya jika takardar dake hannunta. Hamra'u ta shigo gidan cikin kuka na fitar hayyaci! tana zuwa ta rugumeta da fadin."Uwale ya za muyi da wannan kaddara hukuma ta kama Yayana da laifin ta'addanci! bayan bashi da laifi Yayana bashi da mugunta baya cin hakkin wani burinsa kullum ya za'ayi k'asa ta samu cigaba, amma ya taka sawun barawo jami'an tsaro sun kamashi dumu-dumu a cikin sansanin da *Uban daba!* yake zaune da jama'arsa, Uwale ya za muyi bamu da kudi bamu da ikon da zamu tunkari hukuma! domin kalubantar zargin da sukeyi akan wanda bai ji bai gani ba." Tace."Hamrau bamu da komai wanda zamu tunkari hukuma dashi, amma muna da Allah shi kadai zai ne zai mana jagoranci Allah ba azzalimin sarki bane yana tare da masu gaskiya insha Allah cikin hikimarsa zai bayyana mai gaskiya." Asp Musa Baharu shine shugaban 'yan sandan jahar, kuma duk wani jami'in tsaro a karkashinsa yake, mutumin yana da hankali da nutsuwa gami da sanin makamar aiki, koda aka shigar masa dashi ofis din kallo daya yayi masa ya tabbatar da cewa bashi suke da bukata ba, amma be nuna hakan a zahiri ba, sai kawai ya bawa wa'inda suka shigo dashi umarnin fita, ya rage su biyu kacal a ofis din. Shi baya ganin komai saboda har yanzu fuskarsa a daure take, amma shi Asp din yana kallon duk wani motsinsa. K'ira ne ya shigo wayarsa, daga gidan gwamnati , cikin cikin girmawa ya daga da fadin." Ranka ya dade barka da wannan lokaci." Mai girma governor yace." Barka dai Asp barkanmu da samun nasara! wannan ranar ba zamu ta'ba mancewa da ita ba, yana kuma da kyau ayi rubutu na mussaman domin ajiyewa a kudin tarihi." Asp ya d'anyi murmushi da fadin." Hakane ranka ya dade, labarin samun nasara ya cika gari da sauran garuruwa jama'a da yawa sun kirayi waya suna yi mana murna! amma ban san me yasa ni nake shakku! akan hakan ba." Mai girma governor yace." Asp wannan wace irin magana ce? da farko kafin isowar rudunar da muka tura kaine ka kirayi wayata kake sheda min cewa an samu nasara ya za'ayi kuma yanzu kace na shakku akan hakan." Gilashin dake idonsa ya cire ya ajiye saman tevur din dake gabansa, ido! ya tsira masa yana sake nazartarsa, yace." Ranka ya dad'e ni da kai da sauran jama'ar gari bamu ta'ba ganin *Uban daba!* a zahiri ba, sai dai muna hasashe akansa cewa shi din wani irin mutum ne mara fasali sanin hakan ma ya samo asali ne daga bakin d'aya daga cikin yaransa da Allah ya bamu ikon kamawa a shekarun baya, shine yake sheda mana kammaninsa, a lokacin da al'amarin ya faru, banyi 'kasa a gwiwa ba na samu yaron daya haddace zane ya zana min kammaninsa domin samun sauki gurin binkice a kansa, amma abin mamaki! a yanzu wanda yake gabana a yanzu kuma muke hasashen cewa shine wanda muke nema ruwa a jallo kammaninsa yasha bambam! da wannan hoton zanen da nasa aka zana min a shekarun baya." Mai girma governor yace." Asp ya akayi hakan ta faru? kana so ka sheda min cewa bashi bane."? Ya mi'ke tsaye da wayar a kunnasa, kujerar ya janye ya fito daga tsakankanin kai tsaye inda yake zaune ya nufa!.......Yana wayar yana kokarin kwance masa fuska dake d'aure. Tsaf ya warware d"aurin fuskar, idanuwansu suka hadu guri guda, kujera yaja ya zauna suna fecing din juna. Ya cigaba da cewa." Gani gashi a halin yanzu kuma yanzu zan dauki hotonsa na turo maka dashi domin ka sheda maganata, amma duk wani binkice zanyi a kansa domin samun tartibiyar magana." Mai girma governor ya sauke ajiyar zuciya da fadin." Okey to babu damuwa ina tsumayinka." sallama sukayi kafin ya kashe wayar, ya tsira masa ido! shima nasa idon ya tsira masa suka dinga kallon kallo suna nazarta juna, shi Asp din shine ya fara janye idonsa daga kanshi, ya jima kanshi a kasa kafin ya dago ya sake mai da idonsa gareshi yace." Inaso naji cikakken sunanka gami da jin asalin tarihin rayuwarka."? *#500 via 0542382124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....* *22796074090* katin mov ko airtal. *GOJE!*🏹 🐕‍🦺🐕‍🦺🐕‍🦺 _(SADAUKI OMAR RETURN👑💫_) *BINTA UMAR ABBALE🍒* *_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION🖊️📚_* _____________________ *JAMILA MUHAMMAD-ALI* _(( (MMN BOBO💞) )_ Ina gaisuwa gami da fatan alkairi, Nagode sosai da kulawa da shawarwari Allah ya raya zuria, ya jikan MAMA yai mata rahama🙏🏻 FREE PEGE *27&28* Ya jima kansa a 'kasa tun bayan 'kare maganar Asp din yake cikin nazari da tunani, kafin ya d'ago kanshi ya fara magana kamar haka............Sunana *UMARUL-FARUKU* Ni d'an asalin wannan jaha ne wato jahar katsina.".........Asp din ya kalleshi na 'yan sakkwani kafin ya mayar da hankalinsa kan takarda da biron dake hannuna, yace."Ina sauraranka." numfashi ya fesar kafin ya cigaba da cewa." Kamar yanda na fada maka hakane an haifeni a karamar hukumar malumfashi cikin wani k'auye mai suna *'Kafur* ban taso na iske mahaifiyata a raye ba amma na taso da mahaifina da kakata wacce ta zama garkuwa a gare ni, mahaifina asalin sunansa Tanimu, amma da yawa jama'ar gari sunfi kiransa da *mai jakai!* dalilin sana'arsa ta jidon 'kasa akan jaki domin siyarwa da masu aikin gini da sauraransu. mahaifina ya bani dukkanin wata kulawar da ta cancanta ya ilimatar dani ilimin addini daidai gargwado yanzu haka ina da izifi sittin na al'kur'ani maigirma, duk da acikin k'auye muke sai da yayi k'okarin ganin na samu ilimin zamani (boko) hankalinsa bai kwanta ba sai da na kammala 'karamar makaranta wato secondary school............bayan hakan sai ya fara koya min sana'a domin dogoro da kai, a lokacin dana kai shekaru ashirin da biyar a duniya sai tunani na ya sauya wani guri, a zahiri dai kowa ya sanar sana'ar mahaifina wato *Jaki da mangala* ban gaji farauta ba, amma sa'i guda na tsinci kaina dumu-dumu a cikin harkar, mahaifina baya so ko kad'an saboda yayi wa harkar mummunan fahimta, dalili duk wata nutsuwa da nagarta ina da ita, amma daga ranar dana fara harkar farauta sai wasu daga cikin dabi'una suka sauya, ni zanyi shedar kaina cewa tunda na fara wannan harkar ban ta'ba haura gidan wani nayi sata ba, ban kuma ta'ba tarewa wani hanya nayi masa k'wace ba sannan kuma ba'a ta'ba kamani da laifin fyad'e ga yaran mutane ba, wannan sune munanan laifukan da zan aikata a kira ni da wani mummunan suna! busa hakin sigari ko Shakar Shisha wannan sanya kai ne ga wanda yayi ra'ayin hakan. wannan dabi'ar da nakeyi sai ta janyo cecekuce da surutai a gari cewa na zama d'an iska takai ta kawo babu irin sunan da mutane basa kirana dashi, mahaifina ya d'au damuwar hakan yasa a cikin ranshi har ciwo ya kama shi wanda shine ya zama ajali a gareshi, lokacin da ya fadi ya mutu jama'ar gari suka dauki mutuwarsa suka ala'kanta ta dani cewar b'acin raina ne ya kashe shi, a duk lokacin naji wannan maganar hankalina yana tashi mutu'ka! ni dai na san babu wanda ya isa ya kashe kuma babu wanda ya isa ya raya sai Allah! amma jama'a sun juya maganar domin wani sa'in ma ita kanta kakata Uwale takan jefeni da maganar a duk sanda ranta ya b'aci dani.........Da yawa yawan mutane suna ganin rasuwar mahaifina zata karyar min da gwiwa na janye kudirina sai abun ya basu mamaki! domin ana adduar bakwai na cigaba da harkoki na! idan na fita farauta na kanyi kwanaki ko satittika a daji! kuma da ikon Allah na kan farauci duk abinda nakeso kuma nayi guzurin magunguna iri-iri! ba zance maka ga iya adadin mutanan da suka samu lafiya ta dalilina ba, ina kar'bar 'karamar sadaka na bada magani daga cikin irin ilhamar da Allah yayi min, wannan hanyar itace ta zama hanyar abincina, domin ko bana gari kakata takan bada magani tayi d'awainiya da kanta bayan 'yan sana'o'in da take........Tafiya tana 'kara tafiya ta kowanne fanni ana samun cigaba da tarin masoya da kuma tarin ma'kiya domin duk abinda zaiyi ba zai rasa d'aya daga cikin abinda na fada a yanzu ba, shekara biyar da ta wuce ina fita farauta ni kad'ai! cikin ikon Allah sai na fara samun magoya baya a hankali a hankali na tara jama'a da yawa wanda muke tafiya tare dasu wannan harkar! jama'ar gari suka dauke mu mutanan banza saboda muna yawo da karnuka bayan haka kuma shaye-shayen magungunan tauri da sauransu, yanda jama'a suke kallonmu muma haka muke kallonsu a hangunce! domin mu mun san bama aikata wani mugun aikin da zai janyo mana zubewar mutumci wannan harkar ba *Daba!* bace, ba kuma *Ta'addanci* muke ba, muna neman halak dinmu ne domin mu tsira da mutuncin mu." Cike da karsashi da kwarin gwiwa ya 'kare maganar! Shuru ta ratsa gurin tun bayan 'kare maganarsa Asp din yake rubuce-rubuce yayi 'yan mintina a haka kafin ya d'ago kansa suka had'a ido! ya d'anyi murmushi da fadin." *UMARU-FARUK!* Maja ya'ki! ni Asp Musa Baharu! nayi imani da cewa babu *RAGO!* ga duk wanda ya amsa wannan suna domin Asali al'amarin ya dau'ko." Murmushi yayi wanda ya tsaya kan fatar bakinsa......Asp din ya cigaba da cewa." Yanda kayi min cikakken bayanin tarihin rayuwarka cikin nutsuwa babu inda-inda yasa naji bana shakka a kanka amma ina so yanzu ma kayi min cikakken bayanin yanda akayi har ka samu nasarar shiga sansanin mutumin da jami'an tsaro suke shakkar tunkarar inda yake, hukumar tsaro tayi mutukar mamakin! yanda akayi kai da yaran ka kuka samu hanyar shiga wannan gurin, bayan baku da manyan makaman kare kanku." Murmushi yayi wanda yake fito da zahirin kyawunsa ya tsira masa ido kafin yace." Me yasa kai ka yarda dani da sauri haka? me yasa har yanzu baka gazgata cewa Ni ne *UBAN DABA BA."?* Asp din yayi murmushi da fadin." Saboda sanin makamar aiki shiyasa kallo guda nayi maka na tabbatar da cewa ba kai ne wanda muke da bukata ba." Girgiza kansa yayi still da murmushi a fuskarsa, Asp ya cigaba da cewa." Kayi min cikakken bayanin yanda akayi kuka samu nasarar shiga wannan guri da kai da jama'arka ina sauraranka." Huci! mai zafi ya fesar! kafin yace." Na jima ina jin labarinsa na yawo a gari a duk sanda muka fita farauta sai mun ci karo da irin ta'addanci da yake, muna cin karo da gawarwarkin mutane bila adadin! mata da maza harda kananun yara! idan mun nausa mu ci karo da motoci irin na haya dana gida a k'one! wasu da rai wasu babu rai! mukan tsaya mu basu taimako daidai gwargwado kafin mu wuce! to wannan dalilin yasa ni d'aukar alkawarin ganin 'karshen ta'addancinsa duk da na san bani da alhakin hakan amma zuciyata bata karye ba, na zauna da yarana muka tattauna, da yawa daga cikinsu ba suyi na'am ba, sai dai kuma suka bi umarnina domin bana ajiye kara su tsallake! sannan kuma ba kai tsaye muka tunkari sansanin ba sai da muka bi matakan kariya kamar yanda yake da dabaru! da suddabaru iri-iri to muma muna dashi, domin sai da mukayi kwana biyar a dajin bai san da zaman mu ba! sai lokacin da naso ya san hakan, sosai yayi mamaki da faruwar al'amarin nayi masa bazata! kuma na fara karya alkadarinsa kenan tunda har na samu nasarar fitar masa da wani sassa na jikinsa to da ikon Ubangiji sai na gurfanar dashi a gaban hukuma."!! ya kare maganar cike da cin alwashi da cikawa kansa al'kawari! Asp yayi murmshi mai ma'ana kafin ya latsa wayarsa serving yayi na recoding din da dauka. yasa wayar gaban aljihun rigarsa, mai da hankalinsa yayi kan rubutun da yake, bayan ya kammala ya sauke ajiyar zuciya da fadin." *JAN GWARZO! MAJA YAKI!* Yanzu zamu d'an huta zuwa anjima zamu d'ora insha Allah, bari nasa nasa a kawo maka abinci da ruwa idan kuma akwai bukatar yin wani uzuri kana iya magana." Key yasa ya kwance masa hannu amma be kwance kafafun ba. Ya fito da waya ya kira wani jami'i minti uku ya shigo, ya bashi umarnin kawo abinci mai kyau da ruwa da lemo." Ya 'kame tare da sarawa kafin da sauri ya juya ya fita daga ofis din cikin bin umarni. Idonsa ya sauke kan agogon dake kafe a ofis din, daya da rabi na rana lokacin sallah yayi, sai ya mike tsaye Asp din ya kalleshi tare da tambayarsa, Uzurinsa ya fada masa, da kansa yaje ya bude masa kofar toilet din ya bashi hanya har ya k'araso bakin toilet wanda da kyar yake cire kafa sakamakon sasarin dake d'aure da kafafun! Alwala ya d'auro ya fito, shima Asp din ya shiga ya d'aura alwalar ya fito suka tada sallar a tare............... Tare sukaci abinci har suka kare babu wanda yayi magana a tsakaninsu sai dai nazartar junansu da suke. Asp wani jami'i ya k'ira ya umarceshi da ya shigo masa da yarinyar da suke maganarta. Tare suka shigo ofis din ya kame tare da sarawa kafin ya fita, Asp ya kalleta tare da nuna mata gurin zama, ta zauna kujerar dake kusa dashi sai ya kasance gabad'ayansu suna fecing Asp din. Tunda ta shigo kanshi yake k'asa sam baya so ya daga kai ya kalli fuskarta saboda tsabar yanda yake jin tsanarta a cikin zuciyarsa. Wani irin kallon k'askanci take masa! ranta ya 'baci sosai da ganinshi lafiya lau babu duka! ko mugun rauni! a jikinsa, ita a tunanin yanzu yana nan a galabaice! kammaninsa sun sauya saboda duka! sai taga akasin haka lafiyarsa lau da nutsuwa a tare dashi fuskarsa sai fitar da annuri take irin na musulunci bayan haka kuma an kwance masa sasarin dake hannunsa.........Sai duk jikinta yayi sanyi a fakaice take aika masa da mummunan kallo! wanda take a bayan duhu domin be san abinda take ba, sai shi Asp din dake hankalce da duk abinda yake faruwa. murmushi kawai yayi kafin yayi gyaran muryar da ta sanya shi dago kansa suka had'a ido, still da murmushin a fuskarsa Yace." *Jan wuya!! Goje kake mugun makangari sai kuree."!* Dariya yayi irin wacce bai ta'ba yin irinta ba, gabadaya suka shagala gurin kallonsa tabbas da ya san yanda dariya ke masa kyau to daya yawai ta ta, shima Asp din dariya yake yace."Na fahimci wannan kirarin yana maka dadi ganin yanda kake kyalkya dariya irin haka." Hannu yasa cikin suman kanshi ya d'an sosa kafin ya girgiza kai da fadin." Gaskiya ne ina mutukar jin dadin hakan! da yawa jama'ata na kambaba! daraja ta ina farin cikin hakan amma ban ta'ba dariya irin na yau ba, naji dadin hakan ranka ya dade nagode sosai." Yace." Ka cancanta da duk sunayen dana kira ka a halin yanzu, tun bayan shud'ewar zamanin maya'ki namijin duniya *ALI K'WARA* ban sake jin labari ko yin gaba da gaba da gwarzo irinka ba, *UMARU* muna sanya ran zaka maye mana gurbin wannan bawan Allah da mukayi rashi." Ya girgiza kansa da fadin." Insha Allahu a shirye nake dana bada gudumawata bakin rai bakin fama zan kare 'kasata cikin ko wane irin yanayi." Asp yace."Lallai kuwa idan hakan ta kasance 'kasa zata gyaru za kuma a samu sau'kin faruwar munanan ayyukan da sukayi wa kasa dabaibayi.'' Ofis din ya sake daukar shuru na 'yan mintina kafin ya kalleta tana zaune tsuru abin duniya yai mata zafi ganin yanda ma'kiyinta ya samu sake har yana kyalkaya dariya anya kuwa bukatarta zata biya a kansa........Asp ya katse mata tunani da fadin."Meye sunanki."? Banza tayi masa ta dauke kai domin shi din ma mugun haushinsa takeji...........Ya sake maimaita maganarsa, still bata tanka ba. Sai ya fusata! ya buga tevur din dake gabansa da karfi! yace." Ko da kurma nake magana."!? Kawai sai ta fashe da kuka! hawaye share-share! ta d'aga masa hannu da fadin." Kaga saurara Asp ka daina buga min tsawa haka ko ubane ne kai."!? Ya zuba mata idanuwansa da 'bacin rai a fuskarsa da maganarsa yace." Kina 'karkashin tsaro a halin yanzu duk abinda kike ta'kama dashi dole ki sauke kibi doka idan ba haka ba yanzu zaki fuskanci hukunci mai tsauri."! Shuru tayi ba tace uffan ba, ya koma ya zauna yana mayar da numfashi! ya kalleta tare da sake maimaita maganarsa. Cikin izzah! tace." ZINATU nake 'ya ga Saraki sarkin sarakuna arewa wato *SADAUKI OMAR!.* Asp yayi gaggawar kallonta, ta tsira masa ido cike da tsiwa tace." Ko kana mamaki ne."? duk da akwai hakan a tare dashi amma sai yayi sauri ya basar yasha kunu! da nuna mata shi da hannunsa....."Kin san wannan."? ta kalleshi a sheke kafin tace." Eh na sanshi." yace" meye alakarki dashi kuma wane dalili ne ya kai ki wannan gurun."? Tsaki! taja za tayi magana ya daga mata hannusa, ta kalleshi babu walwala ko ta kwabo a tare dashi, yace." Wannan shine last warning na k'arshe kada na sake miki magana kiyi tsaki ko abu makamanci haka kina k'ar'kashin hukuma! hukunci zai bi ta kanki duk matsayin ubanki dake kanki." ( Hausawa sukace dan kuka shike janyowa iyayensa zagi) ganin babu wargi yasa ta shiga taitayinta, ya sake maimaita maganarsa. Kai tsaye tace." *'Barawo* ne shine ya sato ni daga masarautarmu domin samun makudan kudi daga gurin mahaifina." Kallon mara hankali yayi mata kafin yace." Ya akayi kika gazgata hakan bayan kawai bude ido ki kayi ki ka tsince ki a gabansa a lokacin da wuta take kokarin cinye ki, ina tunaninki yake a lokacin? Shuru tayi tana tunani, zata iya tuna lokacin da ta fito da daddare domin zuwa partyn 'kawarta dake murnar karin shekara daga cikin shekarunta, tana kokarin bude motarta domin shiga al'amarin ya faru, daga lokacin bata sake sanin komai ba sai bude idonta tayi tai arba dashi a gabanta bayan ya bata taimakon daya dace, amma zuciyarta taki aminta dashi har yanzu tana zarginsa. Asp ya nuna mata shi da fadin." Wannan da ke zaune a gabanki bai cancanta da wannan sunan ba, domin kuwa ya taka muhimmiyar rawa a rayuwarki! kada ki sake kiransa da wannan sunan." Hannu ta d'aga da niyyar magana ya katseta da fadin." Duk abinda kike tsammanin faruwarsa ba zai faru ba da izinin Ubangiji muna da hankali kuma muna gudanar da aiki bisa hankali da nutsuwa saboda haka baki da hurumin magana a yanzu, binkice ya bar kanki a halin yanzu, insha Allah kuma zamu sadaki da iyayenki yau ko gobe." Bakinta ya mutu murus! ta rasa abin cewa tsabar yanda al'amarin yayi mata bazata! ta dinga zabga musu harara tana murguda baki babu wanda ya sake bi ta kanta maganarsu suke cikin fahimtar juna kafin ya kira wayar ma'aikaci guda, yana shigowa ya bashi umarnin kaita gidansa. Ya kalleta da fadin." Zaki zauna da iyalina na 'yan kwanaki kafin mu gama gudanar da binkice. " Kamar za tayi magana sai dai taja bakinta tayi shuru, mi'kewa tayi ta kama hanyar fita, direban yabi bayanta cike da bin umarni........... *#500 via 0542382124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....* *22796074090* dala dari katin airtal ko mov *GOJE!*🏹 🐕‍🦺🐕‍🦺🐕‍🦺 _(SADAUKI OMAR RETURN👑💫_) *BINTA UMAR ABBALE🍒* *_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION🖊️📚_* _____________________ FREE PEGE *29&30* Kusan a tare suka d'auke idonsu daga barin kallonta, Asp din yayi magana amma shi uffan bece ba har ta gama harare-harare! ta fita daga ofis din. Ya d'an ja k'aramin tsaki da fadin." Yarinya nan babu tarbiya a tattare da ita duk kuwa da cewa ta fito daga tsatso mai kyau, ba ta gaji dattako da karamci irin na mahaifinta ba, duk da ba a garin kano muke zaune ba muna da labarin dattakon mahaifinta mutum ne mai karamci da mutunci yana aiki da hankali da ilimi yana kuma gudanar da mulki a bisa tsari na isalama." Beso ya tanka a cikin al'amarin yarinyar ba amma ganin yanda Asp din yake jaddada maganar yasa yace." Akwai irinsu da yawa wa'inda suka dauki mulki wata tsiya idan akace mahaifinsu nada sarauta ko wani muk'ami sai su dauki girman kai su dora a kansu suna ganin babu wanda ya isa dasu, hakane maganarka mutumin kwarai yana iya haifar baragurbi acikin al'umma jarabtace kawai daga Allah.'' Yace." Kwarai kuwa wannan haka yake sai dai kawai mu roki Allah ya shirya mana zuria baki d'aya." Ya amsa da ameeen ya Allah. Shuru na minti biyu ya ratsa gurin, cikin 'yar tsokana Asp din yace." Akwai abinda na manta ban tambayi *MAI DAWA!* ba."? Murmushi yayi da fadin." Akwai sauran tambayoyi kenan."? Girgiza kai yayi da fadin." Tambaya daya ce shin kana da iyali kuwa.''? Girgiza kai yayi gami da dan ta'be bakinsa.........Asp ya dan zare ido da fadin." Kana nufin babu iyali kenan." Kai ya daga masa still da murmushi a fuskarsa. Sai kawai ya shiga girgiza kansa da fadin." Gaskiyar magana yanda kake jarumin namiji mata hudu suka cancanta da kai amma ace ma ko daya babu." cike da alhini ya kare maganar. Sai abun ya bashi dariya ya dan dara kafin yace." Asp matsalar mata nada yawa shiyasa nayi zamana a haka ba wai don bani da bukata ba, kawai nafi bukatar kwanciyar hankalina nayi duk abinda nake so ba tare da wani ya caza min kai ba.'' Yace." To ai hakan nan ake hakuri dasu da matsalarsu Umaru kowane maigida yana da matsalar iyali mussaman idan mace fiye da d'aya yake da ita, dole ba zaka rasa shi da matsala ba, nima matana biyu sai dai kowacce da gidanta kuma yanzu haka ina shirin yin ta uku da yardar Allah sai na cike domin ina da ra'ayin hakan." Ya girgiza kai da fadin." Kayi kokari sosai kuma ka aikata sunnah Allah ya baka ikon yim adalci a tsakaninsu." Ya amsa da "Ameen ya Allah ina fatan kai ma kayi koyi dani." Girgiza kai kawai yai baya tsammanin hakan domin baya san damuwa ba lallai sai ka tara mata a gidanka za'a tabbatar da jarumtarka ba, shi a ra'ayinsa zai iya 'kare rayuwarsa da mace daya, sai dai kuma duk yanda Allah ya shirya masa rayuwa to zai kar'ba hannu biyu tare da godiya a gareshi. **** Ke'bantacen guri aka ajiyeshi shi kad'ai ba tare da da sauran yaran sa ba, sai dai su an tattarasu guri guda da sauran masu laifi gama gari. wannan karamcin da Asp din yayi masa ya tsaya masa mutuka a rai yayi ta tunanin irin alkairin da zai saka masa. *** Uwale duk atamfofin da take k'uzu tana tarawa a cikin adaka fito dasu tayi ta siyar. ta dinga bin tsangaya-tsangaya tana bayar da sadaka domin almajiran suyi mata saukar al'kur'ani akan bukatarta, Allah maji rokon bawansa addua ta kar'bu. Washe garin ranar da ita da Mahaifin Hamra'u da ita Hamra'un suka yanke shawarar zuwa headquarter 'yan sandan domin samun cikkenan bayani. Sun jima a tsaye kafin wani jami'i ya sauraresu, Malam Hafi'i mahaifin Hamra'u shine yayi masa bayanin abinda yake tafe dasu. Yayi jim! yana kallonsu kafin yaja tsaki ya barsu a gurin......Uwale da sauri taje tari gabansa kuka ta fashe dashi ta zube gwiwa biyu a gabansa tana rokonsa, hakan ya janyo hankalin ma'aikatan dake gurin suka fara tambayar ba'asi. Cikin kuka tace." Me yasa dukkaninku baku da imani ne? tunda muka zo gurin nan babu wanda yayi mana kallon mutunci Allah da Annabi sunfi karfin wasa amma gabadayanku bakwa tsoron Allah."! Daya daga cikin musulman dake tsaye gurin ne yace." Tayi masa bayani abinda yake tafe da ita. Hanci ta fyace kafin." Tace "Mun zo gurin UMARU wanda ku ka d'aure kuna zarginsa da ta'addanci bayan ba haka gaskiya take ba." Yace." Yi shuru ki kwantar da hankalinki ki daina kuka zanyi miki kokari yanzu." Ta mike tsaye tana gyara yafan mayafinta, tace."Nagode sosai Allah yayi maka albarka." Ya amsa da 'ameen kafin ya umarcesu da suje su zauna a wata rumfa. Sai da yaga zamansu sannan ya bar gurin, kai tsaye ofis din Asp ya nufa domin sheda masa abinda ke faruwa. Ya k'ame da sarawa kafin ya sheda masa abinda ke da akwai, kai tsaye ya bashi umarnin shigowa dasu. Da kanshi ya nuna musu gurin zama yana musu sannu, Malam Shafi'i da 'yarsa suka zauna kamar yanda ya umarcesu Uwale kuwa kai tsaye kujerarsa ta nufa, ya dinga kallonta har ta iso inda yake ta zube gabansa kawai sai ta fashe da kuka tare da rirrike masa kafafu! kuka take sosai tana bashi hakuri. Tausayi ya rufeshi da kyar ya iya mik'ewa tsaye sakamakon rikon da tayi masa, ya sunkuya tare da sanya hannu ya dago ta ta mike tsaye, rungumeta yayi yana rarrashin gami da bata hakuri. Ita kuma fadi take." Ku za'a bawa hakuri ku dubi girman Allah kuyi adalci kada ku yanke hukunci akan wanda bashi laifi bashi ne wanda kuke zargi ba. Hankici ya ciro daga jikinshi, ya goge mata hawaye yana sake kwantar mata da hankali, sai da ya tabbatar da cewa ta samu nutsuwa sannan ya umarcesu da cewa subi bayan shi. Kai tsaye ke'bantaccan gurin da aka ajiye shi suka nufa...........Aps din a gaba suna bayansa, yana shiga sai ya basu hanya. gabadaya suka hada ido dashi yana zaune kasan kafet da tire din abinci a gabansa tsaf dashi da nutuswa a tare dashi bashi da wata matsala bayan sararin! dake daure da kafafunsa Hamra'u da gudu ta iske inda yake, kawai sai ta fad'a kansa tana wani irin kuka! wanda yake nuna tsantsar tashin hankalinta, itama Uwalen da kuka ta karasa gurin duk da ganin da sukayi masa cikin nutsuwa hakan be gamsar dasu ba. Asp ya juya ya fita yana jimamin al'amarin. Tun bayan data fad'i jikinsa yasa hannu a bayanta yana dan bubbugawa, a Hankali cikin taushin murya yake rarrashinta, ta dago kai tana kallonsa hawaye sai ambaliya yake a saman fuskarta, kai yake girgizawa alamun ta daina kukan, yasa hannu ya goge mata fuskar sosai yake mamakin irin k'aunar da yarinyar take masa, shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya sai dai har yanzu bata saki hannunsa ba ta rike tsam a hannunta. Ya d'ora idonshi kan Uwale da ta dage tana kuka sai kace wacce aka nuna mata gawarsa. Murmushi yayi tare da mika hannunshi kan fuskarta hawayen ya share mata da fad'in." Kukan bashi da Fa'idah Uwale addua zaki min." Tace."UMARU kukan shi yake kansa yin kuma shine samun salama, amma a zahirin gaskiya muna cikin tashin hankali bamu da kowa sai Allah shine kuma zai fitar damu." Yace."Kin gama magana tunda ki kace Allah, kuma gaskiya tayi halinta tun kafin tafiya tai nisa gaskiya ta bayyana cewa wanda suke zargi bani bane nima kuma na san da hakan saboda haka ku kwantar da hankalinku insha Allah zan fito lafiya na cigaba da rayuwa da ikon Allah." Tace."Idan hakane mai yasa basu kwance maka wannan d'aurin ba, duba fa yanda kafafunka suke daure. Yace."Akwai dalilin da ya sanya hakan wannan ba matsala bace kada hakan ya daga muku hankali." Kusan a tare suka sauke zuciya da jin furucinsa suka shiga godewa Allah da abinda yayi musu. Har yamma suna tare ya saki jikinsa sosai yana basu labarin irin gwagwarmar suka sha a dajin! tace."Kaga Umaru shiyasa kwata-kwata hankalina bai kwanta da wannan harkar ba mahaifinka har ya mutu da abun a cikin ransa saboda haka idan Allah yasa ka kubta to dole ka ajiye wannan sana'ar ka nemi wata domin hakan shine samun nutsuwarmu baki daya. Domin ya kwantar mata da hankali sai ya amsa mata akan abinda take so, taji dadin hakan kuwa tay tai masa addua da fatan samun nasara akan dukkan abinda ya sanya a gaba. ***** Ta jima a toilet din tana durje jikinta da sabulai iri-iri kafin ta dauro towel ta fito. idonta ya sauka kan tufafi wanda aka ajiye mata su kan gado komai sabo underwears sai riga da siket na wani material mai taushi, goge jikinta tayi kafin ta zauna gaban mudubi tana kokarin duba man da zata shafa a jikinta, tsaki taja tana hararar tarin kayan kwalliyan dake dressing mirror din duk ciki babu kalar man da yayi mata ballantana ta shafa a jikinta........wani lotoin ta dauka tana jujjuyashi a hannunta sai ya mutse fuska. Ta turo kofar dakin ta shigo da sallama a bakinta kallo guda kayi mata zaka fahimci cewa tana daga cikin jerin mutane masu sauki kai da daukar rayuwa a sannu, tana da fara'a sosai domin da wuya kaga bacin ranta sai in tura ta kai bango. Fuskarta yalwace da fara'a ta 'karasa shiga dakin da fadin." Yawwa kin fito ko ga kaya nan na ajiye miki na san za suyi miki dadin sawa.'' Shuru tayi bata tanka ba. Ta kalleta da fadin." Ko dai na sauya miki wasu wannan ba suyi miki ba."? Tsaki taja da fadin." Don Allah kin cikani da surutu haka na duba na gani okey nagode." Ranta ya 'baci da abinda tayi mata amma sai ta danne ko alama bata nuna a fuska ba tace." Okey to shikkenan idan kin shirya sai ki fito muci abinci ." Ta'be bakinta tayi ba tace komai ba ta cigaba da jujjuya abinda ke hannunta. Juyawa tayi da niyyar fita daga dakin. sai ta dakatar da ita, ta tsaya tana sauraranta. A yatsine tace." Wannan tarkacen mayukan shafawar taki ba zan iya shafawa ko daya a jikina ba domin ni ba irinsu nake shafawa ba. Cike da mamaki take kallonta tana mamakin furucinta, tarkace!!! duk man da take shafawa babu na kasa da dubu biyar sai sama amma shine har take magana cewa ita tafi karfin ta shafa a jikinta. Jinjina al'amarin tayi kafin tayi 'yar dariya da fadin." Lallai 'kawata kina ji da gayu amma idan ba haka ba meye laifin mayuka na ko wannan na hannunki kika shafa ya isheki." Cike da wasa ta karashe maganar..........Sai ta fusata! ta mike tsaye tare da buga mata tsawa! da fadin." Ke kin san wacece ni kuwa? da har kike min wannan banzar maganar."? Ta'be bakinta tayi tace." Ina zan sani hajiya ni dai Daddy ya kira ni a waya ya sheda min cewa zanyi b'akuwa shiyasa nake karramaki bahaushe yace." bakon ka Annabin ka." Dogon tsaki! taja kafin ta koma ta zauna..........Ita kuma da sauri ta bude kofar dakin ta fita tana mamakin al'amarin. Zama tayi tare da sauke ajiyar zuciya, ta kalleta da fadin.'' Ya akayi ne? bata gama shiryawa bane."? Baki ta dan ta'be kafin tayi 'yar dariya da fadin." Na isketa ta fito daga wanka tana nazari man da zata shafa." Cike da mamaki tace." Kamar yaya nazari duk cikin mayukan shafawar taki babu wanda yayi mata."? Tace."Hakan take nufi." Tana kokarin magana motsin fitowarta ya katseta duk sai suka juya suna kallonta tayi kyau sosai a cikin material din sai dai siket din ya matseta dalili tana da kwankwaso mai fadi da cika sakamakon mai kayan da nata bai kai hakan ba. Da murmushi a fuskar matar gidan tace." Kin fito."? "Umm." tace kawai ta nemi kujera ta zauna sai wani basarwa take. Ta kalleta da fadin." Nabila mai yasa ki ka bata wannan kayan kamar sun matseta ki tashi ki dauko mata wasu." Tace."Mommy kin san duk kayana riga da siket ne kuma bai zama dole suyi mata yanda takeso ba tunda ta fini kiba." Ta kalleta da fadin." Zinatu baki takura ba dai ko."? Girgiza kai tayi da fadin." Kada ki damu hakan yayi min daidai domin yawancin kayana haka suke." Tace." To masha Allah ku tashi muje muci abinci." kusan a tare suka mike kai tsaye gurin cin abincin suka nufa. To duk wasu bayanai da ya kamata ace gwamnati ta san dasu Asp ya harhad'a komai ya turawa maigirma governor domin ya saurara dashi da wa'inda da ke da alhakin hakan, sai dai ya sheda masa cewa ranar asabar shi da wanda ake zargi da aikata ta'addancin zasu shiga sansanin domin binkice akan sassan sannun da zai tabbatar da gaskiyar magana. maigirma governor yayi na'am da maganar ya kuma bada goyon baya akan tafiyar. *'Yan jarida mane ma labarai suka samu abun yayatawa a gari! gidajen redio da television gami da jaridu labarin abinda suke nunawa kenan cewa ashe wanda ake zargi da *UBAN DABA!* *bashi da ala'ka da zargin da ake masa asali ma shine mutum na farko wanda ya fara karya alkadarin d'an ta'addan da ya addabi kasa da al'ummar dake cikinta, domin tabbatar da gaskiyar magana kakakin rundunar 'yan sanda wato Asp Musa Baharu zai jagoranci shi wanda ake zargi domin gudanar da binkicen sassan hannun wanda ake nema ruwa a jallo...........Sannan kakakin rundunar 'yan sandan ya shedawa mane ma labarai cewa yanzu haka akwai d'iyar Sarkin Kano mai suna Zinatu wanda ake zargin cewa wasu 'bata gari sunyi kidnapping d'inta domin samun kudi daga gurin mahaifinta, amma ha'kan su bai cimma ruwa ba sakamakon zuwan shi wanda ake zargi da ta'addanci mai suna UMARU wanda jama'a suka fi sanin sa da GOJE!* *shine wanda ya zama garkuwa a gareta har yayi nasarar tallafar rayuwarta bayan ya samu nasara akan wa'inda sukayi garkuwa da ita............Wannan shine cikakken rahoton da ya cika garin Katsina dama kewayanta.* Duk wanda ya danganci masarautar yana cikin farin ciki sakamakon samun cikkaken labarin bayyanuwar ta............Fada ta cika da jama'a masu zuwa taya murna da fatan alkairi maimarta da 'yan uwansa fuskokinsu tamkar gonar auduga saboda tsantsar farin cikin da suke ciki a ranar yini cir masarautar babu masaka tsinke mata da maza wannan ya fita wannan ya shiga. Gimbiya Aysha da 'yar uwata tare da 'ya'yansu su ka kasance cikin farin ciki mara misaltuwa, Maijidda ma tayi nata murnar daidai gwargwado amma ta ciki na ciki domin kasa zama tayi cikin 'yan uwanta ta nufi b'angaranta jikinta duk a sanyaye yanzu babbar damuwarta kada asiri ya tonu sunanta ya fito shine abinda yafi tsaya mata a rai.... *Hello my fans A hanzarta biyan kudi domin yanzu zamu shiga cikin labarin akwai kuraa!! 😄 kada ki sake ayi bbu ke 'yar uwata kada ganin k'yashi ya hanaki biya ki zauna jiran na sata wallahi tallahi! hakkin wani masifa ne!! mai girman gaske!! yi kokarin gudun haram! komai kankantarta!!!* *#500 via 0542382124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....* *22796074090* dala dari katin mov ko airtal *GOJE!!🏹* 🐕‍🦺🐕‍🦺🐕‍🦺 _(SADAUKI OMAR RETURN💫👑)_ *BINTA UMAR ABBALE🍒* *MANAZARTA WRITER'S* *ASSOCIATION📚🖊️* ____________________ FREE PEGE *31&32* Jiki a mace! ta nemi kujera ta zauna tana laluben number k'aninta wanda suka shirya 'kula k'ulalliyar dashi. Yana d'aga wayar tayi kasa da muryata da fadin." Sadiq na san dai yanzu ka samu labarin abinda ke faruwa yarinyar nan fa ta bayyana ina tsoron kada asirinmu ya tonu.'' Yace."Aunty Maijidda kada ki damu babu yanda za'ayi asirinmu ya tonu tunda yarinyar ba zata iya sheda fuskokinmu ba, don haka ki saki jikinki kiyi mu'amula da kowa lafiya kada kiyi abinda zai sanya a gane cewa muna da hannu acikin al'amari! Ajiyar zuciya ta sauke mai zafi! kafin tace."Sadiq wallahi har yanzu na kasa samun nutsuwa gabadaya hankalina a tashe yake shiyasa na kasa zama a cikin jama'a na dawo gurina." Yace." hakan kuma da ki kayi shine zai janyo cewa a gane muna da hannu a cikin al'amarin ki saki jikinki kada ki kuskura ki tona masa asiri." Ta sassauta murya da fadin." Insha Allah zanyi kokarin ganin na boye fargabata." Yace."Yawwa hakan shine abinda ya dace dake. amma har yanzu akwai kurah fa."! Tace."Menene kuma."? 'Yar dariya yayi da fadin." Kudin da ki ka bayar domin gudanar da aikin nayi wata bukata dasu, yanzu zaki bada wasu a biya masu hakki." Tace."Yanzu Sadiq ina ka kai miliyan daya da rabi? cikin kwanaki bakwai kacal! fisabilillahi ba'a samu biyan bukata ba kuma sai ace sai na bada wasu kudin." Ya 'bata da rai da fadin." Kinga Aunty Maijidda duk wannan tambayoyin basu cancanta ba domin wannan aikin yafi karfin miliyan biyar amma don kin bada miliyan daya da rabi kike surutu haba kada ki bani kunya mana kawai ni ki tura min kudin ko kuma anjima kadan nayi miki dirar mikiya." Da sauri tace." Aa ba sai kazo ba bari zuwa anjima ko gobe da safe zan tura mak.....Katseta yayi da fadin." No! ni ban zarda a wayi gari ba, a yanzu mutanan suke bukatar kudinsu idan kuma kinfi so asiri ya tonu to." Da sauri ta girgiza kai da fadin." Aah! bana bukatar hakan ka saurari alert yanzu." Cike da farin ciki ya kashe wayar yana tsallan murna ya fad'i saman katifarsa yana kyalkyala dariyar biyan bukata, tunda ya fuskanci ta tsorata da al'amarin, cikin sauki ya samu hanyar samun kudi da ita. *** Jaridar Leader shirp ce a hannunsa yana dubawa, hausawa sukace labarin zuciya a tambayi fuska, annuri ne kadai yake fita a kyakykywar fuskarsa, hakan kuma shi yake nuna tsantsar farin cikin dake cikin zuciyarsa.......Shigowarta gurin yasa ya d'aga kansa yana kallonta bai janye ba har sai da ta isa inda yake zaune, ta zauna kusa dashi itama tata fuskar a sake, take gaisheshi, amsawa yayi tare da tsareta da wani irin kallo wanda ke nuna mata zahirin so da tsantsar kauna. 'Yar dariya tayi tare da lumshe ido, personality ta kirashi da suna na mussaman wanda take kiransa dashi tunfil-azal. Da murmushi a fuskarsa yace." Aysha Kinga Yaron da zaki kira da *JARUMI! NAN."* ya fad'a yana nuna mata hotonsa dake jikin jaridar. Ta tsirawa hoton ido tana girgiza kanta, ingarman namiji maji k'arfi kyakykwa tamkar *SADAUKINTA* murmushi tayi Ta kalleshi da fadin." Lallai ni Ayshatu na sheda cewa babu *RAGO!* ga duk wanda ya amsa wannan sunan, ha'kika wannan yaron ya cancanta ayi masa komai saboda jarumtarsa! da kuma sadaukarwarsa." Kansa ya girgiza da fadin." Sosai kuwa Aysha na jima ina nazari da tunanin irin alkairin da zanyi wa yaron, Munyi waya da Asp Musa Baharu mun tattauna muhimman maganganu dashi na fahimta, ya kuma bani tabbas a kansa cewa ZINATU ta samu dukkanin kulawar da ta dace a gurinsa, ya tabbatar min da cewa yarinyar tana cikin koshin lafiya babu wani mugun rauni! a jikinta bayan wanda ta samu kafin zuwan shi wannan yaron da ya taimaka mata, sannan bayan haka kuma ya sheda min cewa daga zarar sun gama gudanar da binkicen daya dace to dashi kansa da yaron zasu kawo min ZINATU har gida, sosai yaron ya taka muhimmiyar rawa akanta babban abinda yafi burge ni dashi yanda yayi namijin kokarin ganin ya karya alkadarin takadirin d'an ta'addan nan! da ya addabi! 'kasa da al'ummar dake cikinta, Aysha wannan yaron jarumtarsa! har ta zarce tawa." Murmushi tayi idonta cikin nashi tace."Ina shakku! akan maganarka ranka ya dade, domin kuwa ban yarda cewa akwai wanda yafi mijina jarumta ba, har yanzu kana nan yanda kake Jarumi! a gida kuma jajurtacce a waje."! Hannuwanta ya rike yana jifanta da wani irin kallo.........Har yanzu Tana nan mak'ale a zuciyarsa, sam bata tsufa a idonsa, duk kwanan duniya sonta nunkuwa yake a zuciyarsa, Aysha ta zame masa jinin jiki.......... Ganin irin kallon da yake mata ne yasa ta fahimci abinda yake da akwai, murmushi kawai tayi, tana mamakinsa, baya tsufa da soyayya, kullum da irin kalar soyayyar da yake nuna mata idan suka kad'aice, babu wani abu da ya samu tangard'a a zamantakewar auransu. kusan a tare suka mike tsaye, 'kugunta ya ratsa da hannunshi, ya riketa sosai a jikinsa, kai tsaye bedroom suka nufa domin mutunta junansu. ***** To Ranar da zasu cigaba da gudanar da binkice a sansanin *UBAN DABA!* Asp ya bada umarnin kwance masa sasarin! dake daure da k'afafunsa! 'yan jarida mane ma labarai suka cika harabar gurin, koda ganin fitowarsu sai sukayi caaa! a kansu sunayi musu tambayoyi. Asp a takaice yayi musu bayani, shi kam be iya ce musu komai ba, mota kawai ya shiga ya zauna jami'ai biyu suka sanya shi a tsakiya, Asp shima yayi saurin shiga mota domin ya san idan ya biye musu to su ba zasu gaji dayi masa tambayoyi ba. Tsit!! dajin babu alamun akwai wani dan adam dake rayuwa a gurin, kukan tsintsaye yafi yawa sai dai jefi-jefi suna jin kukan dabbobin dake can nesa!............binkice! suke sosai a gurin, sai dai kuma dukkaninsu a shirye suke domin Babu wanda ya saki jikinsa a cikinsu motsi kad'an zasu zabura! su juya gami da saita bindiga. Gurin da yake tsammanin faruwar badakalar! tasu ya nufa, ya jima yana duba gurin kafin yayi tunanin cire wu'kar dake rataye a jikinshi ya fara tona 'kasar gurin da tsinin wuk'ar. Cak! ya cire wu'kar ya ajiye a gefe ya tsuguna, hannu yasa yana tutture 'kasar data turbud'e abinda yake hasashen samunsa a gurin, lokacin da ya fito da sassan hannun yayi dai-dai da isowar Asp gurin! Ya tsuguna kusa dashi gabad'aya idanuwansa ya zuba kan dungulmin hannun! yana jimanta al'amarin! babu shakka! wannan shine hannun mutumin da ya sanya aka zana masa hotonsa shekaru biyar da suka wuce! abinda ya sanya ya gazgata hakan, zabban zinare da azurfan dake jikin wannan zane sune jere a jikin yatsun dake gabanshi a halin yanzu. Ya kalleshi da fadin." Yanzu na 'kara gazgata maganar ka, binkice ya k'are a kanka tunda ga sheda nan a hannunka wannan kad'ai ya isa a jinjina maka."!!! Bece komai ba, ya ajiye sassan hannun daya riga yayi wani irin kumburi! kwanaki biyu kacal! gefe ya matsa yana ya mutse fuskarsa, hannun har ya fara fitar da wari! Asp ya tattara ma'aikatan gabad'aya ya nuna musu sheda! gabad'ayansu mamaki ya rufesu, dukkaninsu zuwa sukeyi har inda da yake tsaye suna 'kamewa da sarawa!! alamun jinijina!! Asp abin ya burge shi, shima hularsa ya cire ya 'kame tare da sara masa! al'amarin ya bashi mamaki mutuka! Asp din yace." Wannan ba abun mamaki bane Cancanta ce ta janyo hakan. A takaice dai basu bar dajin ba sai da suka tabbatar da cewa babu wani mahaluki da yake rayuwa a gurin, iya binkicensu ya nuna musu cewa d'an ta'addan! ya canza she'ka, hakan be basu mamaki! ba domin dama gabad'aya sunyi hasashen cewa babu yanda za'ayi ya cigaba da rayuwa a gurin domin ya tsira da rayuwarsa, to har yanzu dai suna nan akan bakansu zasu cigaba da gudanar da binkice a kansa, ba zasu fasa ba har sai bukatarsu ta biya a kansa. Maigirma governor da kansa ya 'bukacin san ganin *GOJE!!* gani da ido domin tattauna wasu muhimman abubuwa. Asp ne ya jagoranci tafiyar........shigarsu government house din keda wuya Maigirma governor ya mike daga kan kujerarsa, Asp yayi mamakin hakan sosai! koda yake yaron ya kai kuma ya cancanta da girmamawa! Governor be zauna ba har sai da suka zauna sannan ya koma ya zauna kan kujerarsa. Cikin mutumci da girmama juna suka gaisa kafin su shiga tattauna abinda ya tarasu a gurin. Ya jima kanshi a sunkuye yana nazari da tunanin maganganun governor a kansa. ya sauke ajiyar zuciya, cikin nutsuwa ya kalleshi da fadin." Wannan shine burina a duniya cewar na tabbatu gurin hidimtawa addinin Allah da kuma hidimtawa k'asata Najeria da al'ummar dake cikinta, amma ranka ya dad'e ya za'ayi nayi gogayya da manya-manyan ma'aikatan tsaro! bayan bani da cikkaken ilimi a kan hakan, ba zan boye maka cewa iyakaci na secondary skull ba shin dama hakan tana iya faruwa."? Maigirma governor yayi dariya irin ta manya kafin yace." Malam bahaushe yace ta yaro kyau take bata k'arko! UMARU! ai bai cancata ka kira kanka da jahili ba, koda iyakacinka primary ka cancanta daka zauna a kujera irin ta Asp saboda jarumtarka, kayi abinda shi Asp din ya kasa dashi da wa'inda suke 'karkashinsa, sun buga! sun buga! sunyi-sunyi! Allah bai basu nasara ba, wannan dalilin ya sanya na d'auko hayar sojoji daga libiya domin su taimaka musu, sai gashi kai d'aya 'kwal kayi aikin mutum dubu! koda baka san (A) ba to ni na d'auke 'ka aiki a'kar'kashin mulki na, kuma zan biya ka albashi mai kyau! sannan kuma na baka kyautar gida da motar hawa, domin ka zauna da iyalinka a ciki." Sai ya rasa bakin magana kawai ya zubawa Asp ido yana jimanta al'amarin, ganin ya rasa bakin magana ne yasa Asp din ya ari bakinsa domin yaci masa albasa. Governor ya kalleshi da fadin." Asp babu batun godiya UMARU ya cancanci abinda yafi haka, godiyar ta isa haka, kai dashi duk kuna aiki kan gaskiya gami da kishin 'kasar ku, duka kun cancanci a baku lambar yabo." Asp ya mika masa sannu cike da farin ciki yace." Mungode sosai da wannan karamci ranka ya dade Allah yasa ayi a gama lafiya." Ya amsa da "ameen ya Allah, kuma Allah ya taimake ku akan aikinku." gabadaya suka amsa da "ameen." Hotona sukayi sosai suka sanya shi a tsakiya, sai kuma wasu da maigirman governor ya rungumeshi bayan ya bashi lambar yabo da girmamawa!! sosai ya samu kyaututtuka na mussaman daga gurin manya manyan 'yan siyasan dake gidan gwamnatin, su kansu sun jinjinawa kokarinsa, Cike da tsantsar farin ciki da annushuwa suka fita daga gidan gwamnatin. ****** A daran ranar da al'amarin ya faru ZINATU da kyar ta iya runtsawa saboda 'bakin ciki da takaicin ganin yanda lokaci guda Allah ya daukakashi, ganin hotonsa da governor a lokacin da ya bashi lambar yabo da girmamawa ya mugun daga mata hankali, haka kawai take so ta ganshi a tagaiyare! a wulakance! amma hakan bata samu ba, babban bakin cikinta yanda taga manya mutane na girmamshi tare da kambaba! darajarsa, bata damu da kyaututtukan da ya samu ba kamar yanda ta damu da taga ya k'askanta! Washe gari da 'kyar ta fito daga dakin domin breakfast, Asp din ya gidan be fita ba, ta gaisheshi kamar bata so, ya amsa yana nazarinta shi kansa d'abi'un yarinyar gabadaya basu bashi sha'awa, shiyasa yake so su shirya ranar da zasu kaita gaban mahaifinta kamar yanda yayi alkawari. Ya kalleta sai kumbure-kumbure take alhalin babu abunda akai mata, da kulawa a maganarsa yace."ZINATU Ina fatan dai kina jin dadin zama damu ko." Da 'kyar tace." Um ina jin dadin karamcinku a gareni nagode amma yaushe ne za'a sallame ni haka, tunda dai duk bukatunku sun biya." Ya kalleta da mamakin maganarta yace." Kamar akwai abunda yake cikin ranki duba da yanayin maganarki." Murmushi takaici tayi da fadin." Ranka shi dad'e wannan mutumin fa da kuka d'auki son duniya kuka d'ora masa bai da kirki ko kad'an! mugu! ne azzalimi! ni har yanzu ban yarda da gaskiyarsa ba." Asp ransa ya baci da jin maganarta sai kawai ya rufeta da fad'a ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, yace." Ban san wace irin kiyayya kike wa Umaru ba, shin me kike so muyi masa bayan wanda yafi haka? mutumin nan ya taimakeki a lokacin da kike bukatar taimako amma duk sanda za kiyi magana a kansa ba mai kyau bace! shin wai me yayi miki da zafi da kika tsaneshi haka."! Cikin 'Kunci da takaici tace." Ranka ya dade mu bar maganar kawai domin duk abinda zan fada maka a kansa ba zaka yarda ba duba da ganin yanda zuciyarka ta hasala! kawai saboda na kiraye shi da macuci alhalin sunan daya cancanta dashi kenan." Yace."Kin san Allah ba zan matsa daga gurin nan ba har sai kin sheda min irin cutar da yayi miki da har kike kiran sa da wannan sunan." Ganin yanda ya kafe ta da idanuwansa yasa jikinta mutuwa, me zata ce yayi mata bayan alkairi, ta san ya taka muhimmiyar rawa a kanta amma haka kawai take jin haushinsa! a yanzu duk abinda zata fada a kansa sharri ne! Ya katse tunaninta da fadin." Ke nake sauraro na fada miki ba zan bar gurin nan ba har sai naji dalilin da yasa kike tsaneshi." Bakinta ya sub'ce gurin fadin"Saboda ya keta min haddi sakamakon kad'aicewar mu a dajin." Ya zuba mata ido da so ya tabbatar da maganarta......."Ya keta miki haddi kamar yaya."? Ko kunya ta sake lailayo wani sharrin......"Fyad'e yayi min." Tafad'a babu nadama a cikin maganarta. Ya jima yana kallonta da mamakin furucinta kafin ya girgiza kai da fadin." Wannan shaci fad'i ne ban yarda zai aikata hakan ba." Murmushin takaici tayi da fadin." Ai dama ba zaka yarda ba saboda jarumtarsa tana burgeka a matsayinka na babban mutumin mai rik'e da mu'kamin Asp bai kamata ace kana mubaya ga wannan k'azamin mutumin ba." Maganarta sai ta bashi dariya, ya tsaya ya dara kafin ya mike yana duba agogon dake daure a hannunsa yace." Lallai yarinyar nan da gaske kike amma babu damuwa, wannan maganar kuma ba zan barta ba sai mun tattaunata da mutumin naki." Shuru tayi ba tace komai ba, har ya bar gurin, tana zaune a gurin suka fito tare da madam d'inshi dirarriyar mace kyakykawa da kyawun jiki sam ba za kace ta haifi 'yar shekara ashirin ba, hannunta rike da 'yar jakarshi ta rakashi bakin mota ta nayi masa fatan alkairi. Koda ta dawo a falon ta zauna suna hira jefi-jefi ta d'an saki jikinta sakamakon mutunci da karamcin matar wanda ya janyo mata 'kima da mutunci a idonta......Sai dai kwata-kwata jininta bai had'u da Nabila ba, haka kawai ta tsani yarinyar alhalin babu wani abu da tayi mata na laifi........daidai gwargwado tana bata girma tunda ta fahimci cewa ta d'an girme mata sai take kiranta da Auntyna. hakan yana sake sanyawa kanta ya kara girma domin akwai ta da son girma, gata dai a gidan ubanta amma mulkar yarinyar take, da yake ita din mai saukin kai ce bata damuwa, domin bata mance ingantaccen hadisin nan da yake cewa "ka girmama bakon ka, wannan dalilin yasa take mata duk abinda take so, wanda ita kuma anata 'bangaran take ganin kamar ta isa ne! shiyasa take mata biyayya.....! *#500 via....0542382124.....Binta Umar gtbank, idan kati zaki tura kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.......07084653262....Mutanan Nijar ku tuntubi wannan number.... 22796074090....Dala dari katin airtal ko mov* *GOJE!!🏹* 🐕‍🦺🐕‍🦺🐕‍🦺 _(SADAUKI OMAR RETURN💫👑)_ *BINTA UMAR ABBALE🍒* *MANAZARTA WRITER'S* *ASSOCIATION📚🖊️* ____________________ _Mijina kazami! ne! to ni kam sai dai nace kiyi hakuri 'yar uwa domin akwai su a cikin maza amma ba duka ba, kuma bake kadai kike da matsala irin wannan ba, amma ki sani ke da kanki kina iya gyara abinki, da wayo da dabara, zahirin gaskiya kazamin namiji nada wuyar sha'ani! duk macan da take fuskantar wannan matsalar daga gurin mijinta akwai hanyoyi masu sauki da zata bi domin gyara masa dab'iu kamar yanda takeso ya kasance!_ FREE PEGE *33&34* Police barrack nan ne mafi akasarin ma'aikatan tsaro suke zaune da iyalansu, a nan gidan Asp yake, haka zalika ma anan ne mai girma Governor ya mallakawa UMARU gida tazarar su da Asp din babu yawa gida biyar ne a tsakaninsu, tsarin ginin gidan mai kyau ne, plate ne mai dauke da bangare uku, kowanne 'bangare a shirye yake tsaf da dukkan abinda za'a bukata na yau da gobe, abinda kawai ya rage a gidan mace, don a ranar da ya tare a gidan ma 'yan uwa da abokan arziki surutun da suke masa kenan, cewa a yanzu Allah yayi masa komai na rayuwa, abinda ya rage masa mace domin duk cikar mutum da kamalarsa mutukar bashi da aure to darajarsa dole tayi 'kasa..........'Kwarai hakane a yanzu ya san cewa cikar mutumcinsa shine aure, wannan dalilin ya sanya yaji sha'awar auran a cikin zuciyarsa, sai dai kuma babu wanda ya amsawa cewa zai auri 'yarsa a cikin wa'inda suke kawo masa tallan 'ya'yansu, da kansa zai duba wacce ta kwanta masa a ransa ya aura. B'angare d'aya ya dauka Uwale da Hamra'u sai suke amfani da daya, Uwale ganin ba zata iya zama a gidan ita kadai ba yasa tace Hamrau ta ta zauna domin ta taya ta zama, hakan yayi mata dadi mutuka domin dama tana neman hanyar da zata kusanta kanta dashi. Itace ta d'auki ragamar kula da gidan, ta tsaftacce ko'ina har sashensa idan zai fita take 'karbar key a gurinsa ta shiga ta gyara masa ko'ina tasa turare idan taga ya cire k'ananun kayanshi a toilet ta wanke masa tas ta shanya idan sun bushe ta ninnke tasa masa a wardrobe, kullum idan ya dawo daga gurin aiki tsaf-tsaf yake samun gurinsa yana kamshin turare na mussaman, kafin yayi wanka ya fito ta shirya masa abinci da duk wani abinda zai bukata, k'wazon yarinyar da yanda take kulawa dashi da kakarsa yana burgeshi! ba tun yau ba ya gane inda ta dosa a kansa, zai iya auranta saboda kyawawan dabi'unta dama wannan shine abin dubawa a cikin lamarin aure. 'Bangaranta kuwa shawarwari take da zuciyarta kan cewa ta sheda masa tana sonsa ko kuwa ta bari ya furta mata da bakinsa, a ganinta yanzu tunda yayi kudi yafi k'arfinta shiyasa kullum take jin tsoron tunkararsa da maganar gudun wulakanci, sai dai duk sanda masifar sonsa ta isheta daki take shiga taci kukanta ta koshi, kafin ta roki Allah ya za'ba mata abinda yafi alkairi a rayuwarta, amma tayi mamakin yanda akayi Uwale tayi shakulatun 'bangaro da maganar wanda ada can baya har kayan lefe take tarawa burinta bai wuce tabbatuwar auran ba, amma yanzu kwata-kwata bata maganar, ballanatana ta bashi umarnin auranta kamar yanda tayi alkawari a can baya. Kamar yanda gwamnati ta mutuntashi ta kuma karramashi, shima haka ya mutunta yaransa ya karramasu yayi musu alheri sosai, domin duk rabin alherin da ya samu ya sadaukar musu, a cewarsa suma suna da hakki duba da irin muhimmiyar rawar da suka taka, hakan ya sake janyo masa kwarjini da farin jini a gurinsu da sauran jama'ar gari. ******* Yau satin sa guda kenan da fara gudanar da aiki a ofis dinsa na mussaman, Uniform dinshi ma na mussaman ne, amma yayi kamanceceniya dana Asp amma kuma akwai bambanci sosai! Da yake yana da hikima da nazari babu wani abu da ya shige masa duhu, aikin yake kamar wanda ya shekara yana aikin tsaron lafiyar al'umma! Wasu takardu yake dubawa kira ya shigo wayarsa dake saman tevur din dake gabansa. Ya ajiye takardun cikin nutsuwa ya daga wayar da fadin.'' Ranka ya dade barka da aiki." Daga daya bangaran Asp ya amsa da "Barka dai *Jan wuya!* da yake sunan da yake kiransa dashi kenan, ya cigaba da cewa." Gobe ne fa tafiyar nan." Yayi jim! yana tunanin maganar kafin ya dan ja siririn tsaki! ya manta shaf da maganarsu ta zuwa garin kano domin kai marakunyar yarinyar nan gaban iyayenta........Yace."Ogah me zai hana ka sata a mota ta tafi ai ita din ba yarinya bace zata kai kanta gida." Ya girgiza kai da fadin." A'a mutumina ba za'ayi haka ba, ni nayi wa mahaifinta alkawarin cewa dani da kai zamu kai masa ita, sannan kuma ba haka dokar aikin take ba, dalilin da yasa ma tuntuni ban shirya tafiyar ba, saboda na fi bukatar yarinyar ta murmure na 'yan kwanaki hakan zai farantawa iyayenta rai su kuma ji dadin ganinta cikin koshin lafiya, to alhamdullihi yanzu naga tayi kyau sosai babu rama ko wani abu wanda ya danganci haka daga gareta." Ya sauke ajiyar zuciya da fadin.'' Ranka ya dade don dai kawai ka shirya tafiyar nan dani ne amma da sai dai nace kaje kai kad'ai kawai dalili bana bukatar abinda zai sake danganta ni da yarinyar nan wallahi.''! Cike da takaici ya 'karashe maganar. Asp na 'yar dariya yace." UMARU ban san me yasa kai da yarinyar nan bakwai jituwa ba, itama yanda kake jin haushinta haka take jin haushinka kullum bata da magana sai taka." Da sauri yace." Tana zagi! na ko."? Asp din yasa dariya da fadin." In kaji zagi! ma d'aya kenan! shin ka san kuwa maganar da mukayi da ita kwanaki a kanka."? Kai ya girgiza a k'untace yace." Sai ka fad'a." Jim yayi kafin yace." Na san sharri kawai tayi maka ba zaka aikata hakan ba, duk da dai zuciya bata da 'kashi kuma a lokacin hakan na iya faruwa saboda kusancinku da juna wanda dama shi shed'an burinsa kenan mace da namiji su kad'aice shi sai ya zama na ukunsu." Tsaf ya fahimci inda maganar ta dosa, murmushin takaici yayi kafin yace." Banyi mamakin jin wannan maganar ba domin duk mutumin da yake 'kin ka, to babu irin k'azafin da ba zai yi a kanka ba, Asp wallahi tallahi! da naso keta haddin yarinyar nan da ba zata kai labari a hannuna ba, saboda na samu dama iri-iri a kanta amma sam ba wannan ne a gabana ba, burina shine na kubtar da ita, sai kuma sharri! ya biyo bayan alkairi." Yace." Kwarai kuwa shiyasa a lokacin da take maganar na 'karyata ta domin na san ba za ka aikata hakan ba, kawai dai tana neman hanyar da zata tozartaka ne." Yace."Shiyasa ai nace kayi tafiyarka kawai Asp wallahi kaji rantsuwar musulmi ba naso na sake ganin fuskar yarinyar nan." Yace." A haba dai kada ka tsananta da yawa abu ne mai sauki wannan ki 'kiyayyar da kukewa junanku ta rikide ta zama soyayya irin wacce take da wuyar samu hakan na iya faruwa. Ranshi ya 'baci da jin haka tevur din dake gabansa ya buga! murya a sama yace." Allah ya kiyaye Asp bana fatan Allah ya jarrabeni da soyayyar wannan yarinyar, kawai kayi min fatan alkairi ba irin wannan ba." Asp din yayi mamakin yanda maganar ta fusata shi, sai ya sassauta murya da fadin." Colm dwon mana ka samu nutsuwa, wannan maganar dana nake maka a yanzu ba wai nace lallai hakan ya tabbata ba, kawai a jikina nake jin kamar akwai wani abu da zai ratsa tsakaninka da yarinyar domin anyi irin haka ba sau daya ba, ba kuma sau biyu ba, kiyayya ce ake wacce tafi wannan daga karshe kuma sai ta rikide ta juya matsananciyar soyayya." "Mtsssssw!!!! Yaja wani dogon tsaki kafin ya kashe wayar ya jefar saman tevur tunda ya had'u da Asp bai ta'ba 'bata masa rai irin yau ba........Shi kuwa Asp din sakin baki yayi da wayar a hannunsa yana mamakin al'amarin. Da takaicin maganganun Asp ya isa gida, takalmanshi kawai ya iya kwancewa ya kwanta saman kujera ba tare da ya cire inform din dake jikinsa ba, rungume hannunsa yayi a kirji ya rufe idanuwansa yana hasaso kammanin yarinyar............. 'baka ce ba sosai ba, idan be manta ba tana da tsayi gami da cikar kirji da fadin kwankwanso, 'kirar jikinta kenan, tana da manyan idanu da d'an k'arami hanci wanda ke tsatstsafo da gumi ako da yaushe, wannan sune kad'ai abunda zai iya tunawa a game da ita! Yaja tsaki! tare da gyara kwanciyarsa, har yanzu maganar ce take cin zuciyarsa! shi kam a rayuwarsa me zai yi da yarinyar da ta nuna masa tsantsar 'kiyayya irin haka, hanyar jirgi daban ta mota daban. Sallamarta ce ta katse tunaninsa, ya bude idonshi tare da tsareta dasu, be tashi zaune ba yana daga kwance ya amsa mata, still idonshi na tsaye kanta, sai tace tunda suke bai ta'ba yi mata kallon kurrullah irin haka ba, duk sai ta tsargu dama ta shigo ne domin ta duba taga ya dawo ta kawo masa abinci, jikinta duk sai ya mutu sakamakon kafe ta da yayi da kaifin idanuwansa. A sanyaye tace." Yayana sannu da zuwa ashe ka dawo."? Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya yun'kura ya tashi zaune yana kokarin b'alle botiran gaban rigarshi, yace." Na dawo my dear nagaji ne shiyasa ban leka gurinku ba, ina so nayi wanka na huta tukkuna." Cike da kulawa tace." Sannu ya aikin? bari na had'a ma ruwan wanka ko."? yana kokarin cire rigar daga jikinshi yace." Godiya nake Allah yayi miki albarka." Cike da jin dadi ta amsa, kafin da sauri ta kama hanyar dakinsa, ido ya bita dashi har ta shiga dakin ya girgiza kai a fili yace." Wannan itace matar aure mai cikakkiyar tarbiya nutsuwa sanin ya kamata yayi imani ko zuria ya had'a da wannan yarinyar ba zaiyi kaico ba. Ta fito falon ta sameshi daga shi sai vest wacce ta matse shi da gajeran wando domin ya cire gabadaya kayan jikinsa, da sauri ta sunkuyar da kanta kunyar had'a ido take dashi, ganin haka yasa yayi murmushi ya tashi ya bar gurin, da sauri ta dauki inform din ta kai masa daki ta rataye masa kafin ta bude wardrobe ta dauko masa 'kananun kayan shan iska, ta ajiye saman gado da sauri ta fita daga dakin. tana jin wata annushuwa a cikin ranta, yau ta d'an fara ganin alamun sonta acikin 'kwayar idanuwansa.... *Free pege zai 'kare a pege 40 ga masu bukatar wannan littafin suyi payment domin karanta littafin cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, kada mugunta!/hassada!/ ganin k'yashi! ya hana ku biya, ku jira na sata ku karanta, wallahi tallahi hakkin wani masifa ne! bala'i ne! muyi kokarin nesanta kanmu da haram! duk kankantarta!* *#500 via....0542382124.....Binta Umar gtbank, idan kati zaki tura kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.......07084653262....Mutanan Nijar ku tuntubi wannan number.... 22796074090....Dala dari katin airtal ko mov* *GOJE!!🏹* 🐕‍🦺🐕‍🦺🐕‍🦺 _(SADAUKI OMAR RETURN💫👑)_ *BINTA UMAR ABBALE🍒* *MANAZARTA WRITER'S* *ASSOCIATION📚🖊️* _______________ *35&36* Cikin 'kananun kayan data ajiye masa ya shirya jikinsa tsaf, ya fesa turaranshi mai sanyi da sanyayya rai, ya kimtsa tsaf dashi, kai tsaye b'angaran nasu ya nufa cikin yanayin tafiyarsa ta gwarazan maza! Uwale kawai ya samu a falon ta zubawa tv ido tana kallo, ya shiga da sallama a bakinsa tayi saurin kallon bakin kofar ganinsa yasa ta sauke ajiyar zuciya ta amsa sallamar tare da maida hankalinta kansa har ya k'araso inda take zaune. Tibin ya d'an kalla kafin ya zauna kusa da ita da fadin." Kallo kike ne."? Ta gyara zama da fadin." Gashinan dai Ina kallonsu da ido amma bana fahintar komai, yanzu nake cewa Hamra'u ta kai min tashar Arewa 24 nafi fahimtarsu duk da cewa su din ma wani sa'in suna da abun haushi." Ba tare da yace komai ba ya dauki romot ya canza tasha sunnah tv ya kai dai-dai lokacin da marigayi malam Ahmadu B.u.k yake tambihi akan hadisan Annabi Muhammad (SAW) tace." Allah ya jikan wannan malami yayi wa addinin Allah hidima." Yace."K'warai kuwa ba iyalinsa ne kadai sukayi rashi ba duk duniya ne muna rokon Allah ya jadadda rahama a gareshi." Cikin alhini ta amsa da ''ameen ya Allah." Gurin yayi shuru gabadaya hankalinsu na gurin sauraran malamin, har Hamrau ta 'karaso gurin kafin tace."Yayana na kawo maka abinci nan ne."? Hankalinsa na gurin malamin yace." Eh ki kawo min nan." Da sauri taje ta shiryo masa abincin a tire ta ajiye masa a gabansa, kasan kafet ya sauka ya tankwashe kafafunsa, yana kokarin bude kwanakun abincin tayi saurin zuwa ta bude cikin nutsuwa ta zuba masa towon farar shinkafa tas dashi lailaye a leda da miyar zogale wacce taji kayan hadi tayi kyau sosai sai kamshi ne yake tashi, ya kalleta da murmushi a fuskarsa yace."My dear wannan miyar wace kala ce.''? Tana kokarin magana Uwale tace."Miyar zogale ce, ni nayi sha'awarta nace a maimakon taushe tayi mana ko baka so ne."? Girgiza kai yayi da fadin." Ai ko bana so tilas naci domin farin cikin ku, na san kuma miyar za tayi min dadi kamar yanda nake bukata." Hamra'u farin ciki ya lullubeta, murmushi tayi ta tashi daga gurin taje ta samu kujera ta zauna. A nutse yake cin abincin yana yaba nutsuwa da nagartar yarinyar, duk inda ake tunanin mace ta kai, komai Allah yayi mata nutsuwa tarbiya uwa uba iya girki na zamani dana gargajiya, tunda yake cin abincinta bai taba cin karo da kuskure ba, komai yana masa dai-dai wannan dalilin yasa yake zagewa ya cika cikinsa ba tare da wata fargaba ba, ya cinye wanda tasa masa tas ya 'kara wani yaji dadin miyar sosai da sosai. Koda ya kammala cin abincin, sai ta kwashe kayan ta nufi kicin dasu domin wankewa........Ajiyar zuciya ya sauke bayan barin ta gurin, ya janye idonsa daga hanyar da tabi, Uwale ta kalleshi da fadin." UMARU ni kuwa ina labarin wannan yarinyar."? "Wace yarinya kenan."? Yafada idonshi a tsaye a kanta. Tace." Yarinyar da ka taimaka mata wacce ake maganar 'yar sarkin kano ce." 'Bata fuska yayi da fadin'' Tana nan Lafiya." daga haka sai yayi shuru da bakinsa. 'Yar dariya tayi irin ta tsaffi ta dauki goro ta gutsira kafin tace."Haka kawai nake maka sha'awar auranta" Ya kalleta da mamakin jin furuncinta, da kyar yace."Me yasa kike min sha'awar auranta bayan duk ga 'yan mata nan masu hankali da tarbiya'' Shuru tayi na minti biyu kafin tace."To UMARU kaine ai kamar mara lafiya duk macan da akayi magana maganarta sai ka 'bata ranka abinda yasa nayi maka maganar yarinyar domin naji abinda yake zuciyarka na d'auka ko akwai alakar soyayya a tsakaninku." Girgiza kansa yayi da fad'in" Babu kuma ki cire hakan a ranki, halin da ake ciki a yanzu shine ina binkice akan yarinyar da zan aura." Fuskarta a sake tace." To masha Allah, nayi farin cikin hakan, amma UMARU ya za kayi da wannan yarinyar Hamra'u ta jima tana sonka don Allah kada ka watsa mata 'kasa a ido" Murmushi yayi kafin yace."Ai ita zan aura da ikon Allah." sai ta wangale baki tana kyalkyala dariyar farin ciki ta dafa kansa da fadin." Kai masha Allah naji dadin wannan al'amari UMARU Allah ya tabbata da alkairi ya nuna min lokacin da zanga zuriarka, amma ina alfarma a gurina." Ya kalleta da fadin." Wace alfarma kuma"? tace." Bana so aja dogon lokaci ayi komai a gama a lokaci k'ankani." Yace."Kada ki damu insha Allahu daga na dawo daga training za'ayi komai a gama da yardar Allah." tace." to Allah ya tabbatar mana da alkairi" ya amsa da ameen ya Allah." ***** A daran ranar Asp ya umarce su ita da Nabila yace su shirya zasuje unguwa, ba a son ranta ta shirya ba, suka fito harabar gidan a tare sai cika take tana batsewa tana ya mutse- ya mutse, ita kuwa Nabila kamar koda yaushe fuskarta a sake kamar gonar audiga sa'i da lokaci ta kan yi mata magana, idan ta kama, sai taga dama take amsawa, a bayan motar suka zauna Asp din ya zauna kusa da direbansa. Babban super market suka nufa, ya kalleta da fadin." Duk abinda kike da bukata kina iya dauka." Uffan ba tace masa ba tayi gaba tana zagaye gurin, girgiza kansa kawai yayi ya matsa can gefe tare da fito da wayarshi. Abokin nashi ya kira, don yanzu UMARU ya zama abokinsa duk da ya girme masa, amma abota suke tamkar tare suka taso aiki yasa sun shak'u da junansu, Cike da girmamawa ya daga wayar suka gaisa kafin Asp din yace." Ka tsammaci zuwana gurinka yanzu." Cike da mamakin hakan yace." Ina fatan ba wata matsala bace." Yace." Alkairi ne zamu tattauna wasu batu masu muhimmanci" Yace." Okey to shikkenan sai ka shigo din" sallama sukayi kafin kowa ya kashe wayarsa. Turaruka kawai ta iya dauka sai kayan za'ki data jida sai kace shazumamu! haka take da shan zaqi kamar me a cikin hakoranta ma akwai wanda suka dan samu matsala duk ta dalilin shan zaqi. Tana gama tsintar abunda take bukata ta mi'kawa Nabila kwandon kayan, ita kuwa ta kar'ba ta had'a na da na hannunta, kai tsaye gurin total ta nufa da kayan, ita kuma ta fita daga gurin.......Tun kafin ta k'arasa bakin motar direban ya bude mata ta shiga ta zauna har yanzu babu sassauci a fuskarta. Ganin fitowarsu yasa tayi saurin dauke kanta babu wanda ya tanka mata, direban ya bude masa mota ya zauna, kafin ya kar'bi ledojin hannun Nabila ya bude boot ya zuba, ba ta jira ya bude mata motar ba, ta bude da kanta ta zauna tare da bisimillah a bakinta. Koda suka shiga barrack din direba na kokarin parking ya umarceshi da cewa ya zarce dasu gida mai lamba shida(number 6) kai tsaye can ya nufa yayi parking a inda aka ta nada kafin ya fito da sauri ya bude musu mota. Tun sa'ilin da Asp din ya kira wayarsa ya sheda masa zuwansa ya fito ya tsaya domin tsumayinsa sai dai ganinshi tare da yarinyar ya d'an sosa zuciyarsa, amma be nuna hakan a fuskarsa ba, cikin wani irin taku na gwaraza! ya isa bakin motar gabadaya hannuwansa goye a bayansa. Hannu ya mika masa sukayi musabaha ga juna, Nabila da saurin gaske ta gaisheshi har tana kiran shi da Uncle, ya dan saki fuskarsa ya amsa shima ya darajata kamar yanda tayi masa ya 'boye asalin sunanta ya maye gurbin sa da daughter ina godiya." Murmushi kawai tayi tana sunkuyar da kanta.............Kamar yanda ya watsar da lamarinta ita itama haka ta watsar dashi, ta dinga cika tana batsewa tana banka musu harara! tabbas da ta san gidansa ne da tuntuni ta sauka a hanya domin bata bukatar abinda zai had'ata dashi. Asp ya juyo cikin tsare gira ya kalleta da fadin." Ku shiga ciki ku gaisa da mutan gidan, sannan ke Zinatu sai kiyi mata bayanin kanki." Ta kalleshi da niyyar caccakarsa, yanda ya sha kunu! yasa ta d'an ji shakkarsa domin ta fahimci shima dan had'in takaici ne mybe tana iya magana ya buga mata tsawa! a gaban mak'iyinta wannan dalilin yasa tayi shuru amma a fuskarta zaka tabbatar da cewa ranta a b'ace yake, Nabila ce tayi gaba, kafin tabi bayanta tana d'acin rai! Barin su gurin yasa gabadaya suka sauke ajiyar zuciya, suna shakkarta tana shakkarsu, tana da wata baiwa wacce ita kanta bata san tana da ita ba, koda yake jinin saurata gaba da baya yana yawo a jikinta, dole takewa mutane kwarjini a ido, dan dai ta had'u da jajurtattu ne. A wasu kujeru suka zauna kafin su shiga tattauna abinda ya had'asu a gurin. Da yake ta sheda fuskarta a tv da jarida yasa suna shiga ta sheda ta, fuskarta a sake take musu lale marhabun tana nuna musu gurin zama, Uwale ba dai karrama mutane ba. Nabila ce kadai take amsawa, ita kuwa kamar kurma! uffan ba tace ba ta nemi kujera ta zauna tana bin falon da kallo, komai akwai tamkar falon shahararan mutumin daya amsa sunansa. hotonansa dake kafe falon sune suka dauki hankalinsa, uku ne d'aya yana sanye da inform wanda yayi masa bala'in kyau! biyun kuma kayan farauta ne rakwacam! a jikinsa hannunsa rike da wata gora mai lankwasa! kansa nannad'e da wani bakin yadi, gabad'aya jikinsa babu masaka tsinke damtsen hannuwansa daddaure da wasu igiyoyi! hoton ya dauki hankalinta mutuka sai kawai ta tsinci kanta da tunanin rayuwarsu a daji! tsigar jikinta gabadaya ta tashi sa'ilin data tuna sassanyar muryarsa a lokacin da yake rarrashinta idan wata masifa ta sameta, lumshe idonta tayi na minti biyu ta bude still hoton ta cigaba da kallo gabanta na wani irin fad'uwa!. Har Hamra'u ta shigo falon tana can gurin kallon hotonsa, gaisheta take amma inaa! hankalinta gabadaya na can wani guri, Hamra'u ranta ya b'aci wata kibiyar kishi mai mugun tsini tazo ta tsaya mata a wuya!! kusa da Uwale ta zauna tana jin takaicin abun a ranta. Maganar Uwale ce ta dawo da hankalinta, da sauri ta janye idonta daga kan hoton tana kokarin saisaita tunaninta ta kalleta da fadin" Kowa lafiya insha Allah gobe nake sa ran had'uwa dasu." Cikin kulawa tace."To masha Allah, don Allah idan kin isa gidan lafiya ki mika gaisuwarmu gare su, Allah ya kiyaye gaba." Ciki-ciki ta amsa da "Ameen." Ta dora idonta kan Hamra'u dake ciccin magani! kallon 'yar 'kauye tayi mata kafin taja tsaki a fili tace." Stupid girl!." Uwale ce kawai bata fahimci komai ba, Nabila da Hamra'u sunji lokacin da tayi zagin sai suka rasa da wanda take a cikinsu! Hamra'u tafi tsarguwa cewa da ita take, ba tace komai ba ta tashi domin barin gurin, ta kalleta a yatsine kafin tace." Ugly!!." (Mummuna!) da yake ta danyi karatu ta fahimci maganar, amma bata tanka ba, tayi saurin bude dakinta ta shige tana mugun mamakin al'amarin! Ita kuwa Nabila duk wannan abun dake faruwa ba sabon abu bane a gurinta ta riga ta san hali shiyasa uffan ba tace mata ba, har ta k'araci iskancinta ta gama, Uwale dai ba jin turanci take ballanatana ta fahinceta, tas taci musu mutunci cikin turanci ba tare da wata shakka ba! Yace."Kamar yanda muka tattauna maganar a kwanakin baya yanzu ma zan sake dawo mana da ita domin samun solution." Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya cigaba da cewa." Ka san da cewar duk abunda yake faruwa Commissioner of police baya gari yaje taron k'arawa juna sani dashi da ta kwarorinsa, sai dai duk abunda yake faruwa yana da labarinsa, ya san labarinka kuma yana da cikakken labarin irin muhimmiyar rawar da ka taka, sai dai kuma a lokacin da ya samu labarin cewa ka fara gudanar da aiki, sai ya nuna rashin goyon bayansa akan hakan, A cewarsa lallai sai kaje kayi training domin haka dokar aiki take, banyi masa gaddamar hakan ba saboda na san yana da hujjah mai kyau! amma na sheda masa cewa umarnin mai girma governor ne hakan, duk da hakan ya nuna rashin goyon bayansa da fadin shi zai zauna da governor din domin su tattauna maganar, shine nayi maka maganar a cikin kwana biyar da suka wuce, yanzu ma ina maimaita maka, gobe insha Allah muke sanya ran zai sauka, babu shakka na san cewa zai nemi zama da kai, ina so ka kula dashi da kyau!domin shi din wani irin bahagon mutum ne mai raina tunanin mutane, a tsarinsa bai yarda da cewa wani ya fishi ta kowanne fanni ba, kullum shine wanda ya iya, sannan baya kar'bar kuskure a tsarinsa, wannan kadan kenan daga cikin halinsa, ina so ka kiyayi mu'amula dashi." Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace." Asp tun lokacin da kayi min maganarsa ban ji wani tsoro! ko fargaba! ba (bahaushe yace fad'uwar gaba asarar namiji!!) Ni na fi so ma naje nayi training din domin nagoge! maganar halinsa kuma wannan bai dameni ba, abinda na sani shine ba zan yarda da rashin gaskiya ba! ba zan aminci a hada baki dani a cuci 'kasata ba! ba zan yarda a cutar da wani ba! ba kuma zan yarda da cin hanci da rashawa ba."! Cikin jaddada gaskiyarsa yake maganar. Asp yaji dadin furucinsa Yace."Naji dadi sosai da wannan alkawarin naka, ina rokon Allah ya tabbatar damu akan hanya ma daidaiciya." Ya amsa da "Ameeen ya Allah." Tare suka mike tsaye, Asp din yace." Idan babu damuwa inaso mu gaisa da Hajiyan." Cike da jin dadi yace." A haba babu damuwa mutumina muje kawai." Tare suka jera domin shiga gidan suna sake tattauna maganar. *Free pege zai kare a pege 40 kuyi payment domin karanta labarin cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, idan da akwai bukata Sadauki Omar 1k za'a tura domin samun damar karanta littafi biyu wato Goje (Sadauki Omar return) mu nesanta kanmu da haram! duk kankantarta! hakkin wani bala'i ne! kada ganin 'kyashi- hassada mugunta ya hanaki biyan kudin littafi ki jira na sata ki karanta! ki dauki nauyi kin dorawa kanki! abunda ba zai zama dole ba, idan baki da ikon biya babu lallai babu dole akan ki dauki hakkin wani gwara ki hakura!!!!* *Wa'inda zasu sayi littafin nake da bukata, idan kin san ba siya zaki ba don Allah kada ki dauki number ta kiyi min magana🙏🏻* *#500 via....0542382124.....Binta Umar gtbank, idan kati zaki tura kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.......07084653262....Mutanan Nijar ku tuntubi wannan number.... 22796074090....Dala dari katin airtal ko mov* *GOJE!!🏹* 🐕‍🦺🐕‍🦺🐕‍🦺 _(SADAUKI OMAR RETURN💫👑)_ *BINTA UMAR ABBALE🍒* *MANAZARTA WRITER'S* *ASSOCIATION📚🖊️* ____________________ *37&38* Da yake ta sheda fuskarsa suna shiga ta ganeshi, cike da farin ciki take masa barka da zuwa, ta nuna masa gurin zama da fadin." Ashe tare kake da yaran naka sannu da zuwa ga guri zo zauna." Asp ya zauna kusa da ita yana amsawa ya dora da fadin." Tare muke tafe dasu ai nace su zo su gaisheki sannan kuma ita ZINATU tayi miki bankwana domin gobe idan Allah ya nufa zamuje mu kaita gida da yardar Allah." Tace."Eh ta sheda min hakan har na bada sakon gaisuwata ga manyan nata, ina fatan Allah ya kai ku lafiya ya kuma dawo daku lafiya." Gabad'aya suka amsa da ameeen ya Allah. Falon yayi shuru na minti biyu kafin tace."Duk ya iyalin naka ina fatan kowa lafiya." ? Yace."Kowa lafiya lou insha Allah gabadaya zasu zo su gaisheki." Cike da jin dadi tace."To shikkenan ina nan jina jiran zuwansu." Tun shigowarsu shida Asp din yake a tsaye a gefen kujerar da take zaune, be kalleta ba ballantana ya fahimci yanayin da take ciki wanda tsayuwarsa a kanta ya janyo mata, k'amshin turaran jikinsa ne yake fizgarta take jin wani irin azababben feelings! ta rasa wace irin masifa ce wannan duk sanda zai kusanceta hankalinta ya kan tashi, gabadaya jikinta ya mutu ta dinga matse 'kafafunta wani irin sanyi ta keji a cikin jikinta, cikin zuciyarta take wasu irin tunane-tunane marasa kan gado............Gyaran murya yayi gabadaya suka kalleshi amma banda ita, Ya dubi Uwale da fadin.'' Ina Hamra'u ne."? Tace."Yanzu-yanzu ta shiga daki watakila ko tana wani uzuri ne." Ya kalli Asp da d'an murmushi a fuskarsa yace." Yana da kyau kafin ka wuce ku gaisa da matata da yardar Allah." Jin abinda yace yasa Asp din yin 'yar dariya ya bashi hannu suka tafa da fadin'' Gaskiya ne abokina hakan yayi ya kamata ta fito mu gaisa." Murmushi kawai yayi ba tare da yace komai ba ya nufi dakin nata. Cikin tsantsar fad'uwar gabada gami da jin wani abu mai bala'in d'aci a wuya ta bishi da kallo a lokacin da yake kokarin bude dakin, ba ta janye idonta daga kansa ba har sai daya shiga dakin, sannan ta sauke wata zazzafar ajiyar zuciya wacce ta janyo hankalinsu kanta, sunkuyar da kanta tayi 'kasa tana 'kokarin saisaita yanayin da take ciki, halin da ta shiga a lokacin da yake maganar ta kasa fassara shi shin wai me hakan yake nufi? Cikin yanayi na damuwa ya sameta, ya kira sunanta ta dago kai tana kallonsa , nan ya hango b'acin rai cikin 'kwayar idonta, cike da kulawa yace."Menene yake damunki."? da yake a kusa take kuma kishi yana cin zuciyarta, sai kawai ta fashe da kuka harda shashsheka! Hankalinsa ya tashi ya zauna kusa da ita yana rarrashinta, da kyar tayi shuru sai ajiyar zuciya take saukewa, ya rike hannunta da fadin." Waye ya ta'ba min ke."? shuru tayi ba tace komai ba, yace." Ba zaki fad'a min ba ko baki da lafiya."? Kai ta girgiza alamun a'a. Yace."Babu daya daga ciki amma kike kuka gaskiya ban yarda ba kada ki boye min abinda ke damunki kinji my dear." Zuciyarta ta sake karyewa kawai sai ta tsinci kanta da fadin." Yanana don Allah Menene tsakaninka da ita."? Yayi jim yana kallonta kafin yace." Wa kenan."? Ta kalleshi hawaye na karakaina a saman fuskarta, hannu yasa yana goge mata tare da girgiza kai alamun ta daina. Cikin shashshekar kuka tace." Kada ka gujeni na riga na makance akan sonka ba zan iya rayuwa da kowa ba idan ba kai ba, zuciyata tana wasiwahsi cewa zaka maye gurbina da wacce 'yar sarkin daka taimaka wannan shine dalilin daya sani zubar da hawaye." Da murmushi a fuskarsa yake girgiza kansa har yanzu hannunta na cikin nasa yace." Babu wata alaka da take tsakanina da ita, ki cire faruwar hakan a cikin ranki, bani da matar aure sai ke, domin duk kin tara abunda nake da bukata, insha Allahu kece uwar 'ya'yana." Wani sanyi ya ratsa zuciyarta, cikin tsantsar farin ciki ta kalleshi da fadin." Nagode masoyina ina fatan Allah ya tabbatar da alkairin da yake tsakaninmu." Ya amsa da "ameen ya Allah." A 'kalla ya kai minti ashirin da shiga dakin shiru bai fito ba, shi kansa Asp din ya 'kosa ballanatana ita da take jin kamar taje ta sha'ko wuyansa ko uwar me yake a dakin oho! A cunkushe! ta kalli Asp din da fadin " Ranka ya dade ya kamata mu tashi mu tafi wannan mutumin ya mayar damu shashashai! ya shige daki ya bar mu a zaune zaman jiransa." Ya kalli agogon dake daure a hannunsa da fadin." Hakane nima nayi mamakin jimawarsa amma bari na kira wayarsa naji." Uwale kuwa gyangyadi take bata ma san ma abunda ke faruwa ba. Yana kokarin kiran wayar tasa, suka fito a tare hannunta na cikin nasa. Har suka zauna bata kallesu ba, cika kawai take tana batsewa! wani mugun abu mai nauyi ya tsaya mata a wuya. Gwiwa a kasa Hamra'u ta gaishe da Asp, ya amsa da fuska a sake yana janta da wasa, murmushi kawai take ta kasa hada ido dashi, gabadaya farin ciki ya mamaye zuciyarta, tayi mamakin yanda akayi ya santa har yake kiranta da amarya hakan ya sanya ta sake gazgata maganarsa. Tashi tayi kawai ta kama hanyar fita ba tare da ta tankawa kowa ba, Nabilan ta kalli mahaifinta nata da fadin." Daddy bari muje kawai sai ka shigo." Ya mike da fadin.'' Aa ku jira ni mana saurin me kuke." duk da taji abunda yace hakan besa ta tsaya ba, ta bude kofa ta fita, ita Nabilan ita ta jira mahaifin nata har sukayi sallama cikin girma da mutunta juna. ***** Washe gari da wuri suka shirya tafiyar, bahaushe yace sabo turken wawa, 'yan kwanakin da tayi a tare dasu ya sanya duk jikinsu yayi sanyi har dashi Asp din kawai ya daure ne domin ya san dole watarana yarinyar zata bar hannunsa, Madam dai kasa hakuri tayi sai share hawaye take a fakaice. Al'amarin ya bata mamaki mutuka! ta rasa wane irin so matar take mata, gabadaya sai jikinta ya mutu ta rungumeta da fadin." Mommy kiyi hakuri ba mu rabu da juna ba insha Allah zan dinga ziyartar ki, bayan haka kuma zamu dinga gaisawa ta waya ki daina kuka." tana maganar tana share mata hawaye. Hannunta ta rike da fadin" Idan kin isa gida lafiya kice ina gaishe da mamanki kuma insha Allah idan an kwana biyu zamu kawo muku ziyara dani da Nabila." A sanyaye tace."To shikkenan in Allah ya yarda zan sheda mata sa'kon ki daga zarar na isa ." Nabila ta fito daga daki ta same su cikin damuwa, a sanyaye ta zauna kan kujera tana kokarin magana ya k'araso gurin yana duba agogon dake hannunsa, ya kalleta da fadin." Tashi muje ko." Ta mike tana gyara mayafin jikinta, Nabila ta kalleshi da fadin." Dady zan je nima." kai ya girgiza da fadin." Ki bari idan an kwana biyu zaku shirya zuwa keda Madam." Kamar za tayi kuka tace." Dady ni nafi so naje yau." be saurareta ba ya kama hanyar fita, itama da sauri tabi bayansa domin bata so ta tsaya dogowar magana zuciyarta ta karye, gabadaya suka bita da kallo cike da alhinin rabuwa da ita. Wayarsa ya kira ya sheda masa cewa sun fito suna jiransa. Da yake tuntuni ya shirya tafiya sai kawai ya fito daga gurinsa kai tsaye bangaran su Uwale ya nufa domin yi musu sallama. Fitowarsa ta dauki hankalinsu daga ita har Asp din......Yana sanye da kayan mu na hausawa shadda milk colour dinkin tazarce har kasa, sai yayi amfani da hula zannar bukar mai duhun zare, kafafunsa sanye da bakin takalimi mai gidan yatsa, agogon dake d'aure a hannunsa ma baki ne, yayi kyau sosai fuskarsa tayi kar! sai fitar da annuri take. Kasa janye idonta tayi daga kansa suna magana da Asp yana tsokanarsa cewa yayi kyau a cikin dogwayen kaya, murmushi kawai yayi kafin ya fara duba cikin motar, sai suka had'a ido da sauri ya janye nasa yana gyara yanayin fuskarsa, babu fara'a a fuskarsa ya kalleshi da fadin." Ya za'ayi tafiyar ne."? Asp din na 'ko'karin magana direban da zai jasu ya iso gurin, gaisuwa ya mi'ka kafin ya bude motar ya shiga Asp din yayi saurin zama a kusa dashi, ya kalleshi cike da mamakin abinda yayi wato yana nufin shine zai zauna kusa da yarinyar. Ba tare daya shiga motar ba ya kalleshi da fadin.'' Ni yafi kamata na zauna anan gurin." Ya kalleshi da murmushi a fuskarsa yace."Akwai dalilin da yasa nayi hakan kai dai kawai shiga mota mu, tafi." Ya jima yana kallonsa gami da hasaso dalilin da yasa zai ce dole ya kusanci yarinyar, ajiyar zuciya ya sauke bada son rai ba ya bud'e motar ya shiga da bisimillah a bakinsa. Duk maganganun da suke tana jinsu, itama taji haushin abinda Asp d'in yayi kome yake nufi oho! dalilin da yasa kenan yana shiga motar ta kawar da kanta tana ya mutse fuskarta. Shima bai ce mata komai ba ya mayar da hankalinshi gurin tasbihin da yake ja da carbin dake yatsan shi a ma'kale. Jefi-jefi suke hira a tsakaninsu kafin Asp din ya juyo ya kalleta da fadin." ZINATU yau sai kwanan gida ko."? Baki ta ta'be kafin tayi masa wani irin kallo mai kama da harara! kamar wanda yayi mata laifi, ta d'auke kanta uffan ba tace ba. A maimakon hakan da tayi masa ya 'bata masa rai sai kawai ya fashe da dariya yana kallonta da fadin." Ke kam kin zama hukuma! sai rarrashi abu kad'an ke tunzura zuciyarki kamar ba d'azu ki ka gama kuka ba okey mu yanzu dai ba za kiyi kukan rabuwa damu ba kenan." Ta kalleshi still dai bakin ta tabe kafin tace." Ranka ya dade meye had'a ni daku da zan zauna ina kukan rabuwa daku ni burina ma nayi nesa daku." Ya dinga girgiza kanshi yana mamakin furuncinta, yace." Ni dai na san a'iya zaman da mukayi dake banyi miki wani abu ba ballanatana ki k'ullaceni, meye duniyar ma da kuke gaba da junanku dalilin da yasa na shirya zamanku a kujera daya domin ku gaisa da junanku duka ku yafi junanku, duk da ba wani laifi kukayi wa junanku ba amma duk kun tsangwami kanku da kanku, ke ZINATU kece 'karama ya kama kiyi wa abokin zamanki sallama ki gashe shi sannan kiyi godiya akan alkairin da yayi miki wannan shine zaman duniya." Ta dinga kallon Asp din tana jin takaicin maganarsa, a maimakon tayi abinda ya umarceta kawai sai ta juya tana galla masa harara! wacce ta sanya shi juyowa yana kallonta ido suka hada hakan besa ta daina hararsa ba...........Yanayin fuskarsa kawai ya gyara ba tare da yace mata komai ba ya janye idonsa. Hakan da yayi ya 'bata mata rai sosai! wato ya ma mayar da ita mahaukaciya, tsaki taja mai tsayi ta kawar da fuskarta. Beyi niyyar kula taba amma tsakin da tayi masa yasa ya kalleta cikin shan mur! yace." Wa kikewa tsaki."? Kallon gefen ido tayi masa ta sake jan wani tsakin! ba zato! ya matseta jikin motar! lebunan ya kama ya shiga ligwigiwitasu! hawayen azaba! suka fara sauka saman fuskarta, Asp ya kalleshi da fadin." Ka kyaleta haka mana." Be kalleta shi ba ballanatana yaji maganarsa ya cigaba da ligwigwita leban! hannunta tasa kan nasa tana kokarin cirewa ya rike sosai! yace." Yau zanga karshen rashin kunyarki." Asp yace." Ka janye haka tayi kuskure tana neman afuwa." Yace."Da bakinta nakeso ta nemi afuwar idan ba hakaba to zamuje a haka ban damu ba." Asp din ya kalleta tayi wujiga-wujiga! ta shiga hannun maza! hawaye harda majina!! dariya ta kusa kubce masa ya danne ya kalleta da fadin ." Ni zan zama sheda idan zaki bada hakuri." Kanta ta d'aga alamun ta yarda. Ya kalleshi da fadin." Ta yarda zata bada hakurin ka saketa." Ba lokaci guda ya saketa ba sai da ya niyya tukkuna sannan ya saketa! kawai sai ta kifa kanta jikin motar tana wani irin kuka na tsantsar takaici da bakin ciki. Asp ya kalleshi da fadin." Baka kyauta ba, nida na had'a ku zama guri daya nayi hakan ne da kyakykyawar munufa dana san abunda za kayi kenan da ban zaunar da kai a kusa da ita ba. Ta'be baki yayi bece komai ba ya cigaba da jan carbin dake hannunsa. Motar tayi shuru na 'yan mintina 'kasa-'kasa sautin kukanta yake tashi tare da ajiyar zuciya. Asp yace." Kiyi hakuri kinji ki bar kukan kada mu sauka a haka wasu su dauka wani abu ne. Hannu ta dora saman lebanta da yayi tudu ya kumbura saboda ligwigiwatar daya sha ta kalleshi da fadin." Asp ni zaku yiwa haka ko? shikkenan yau zaku ga gatana." Asp yace."Aa ni meye laifi na babu ruwana wanda yayi laifi ai ya san kansa duk hukuncin da ya kamata kiyi masa daidai ne amma kema ki kiyaye ki dinga girmama na gaba dake." Bata iya ce masa komai ba taja mayafin jikinta ta rufe fuskarta dashi, gabad'aya jikinta laushi bakinta sai zafi yake, bata tsammanci rashin imaninsa ya kai hakaba ya ligwigwice mata le'be saboda tsabar mugunta har sai dai ya kumbura! wallahi ko za'a mutu ba zata bashi hakuri ba. Shima ganin yanda ta galabaita yasa beyi wata magana ba, yana dai jin yanda take sauke ajiyar zuciya dalilin kukan da taci, har suka isa masarautar bata sake magana ba, a maimakon tayi farin cikin dawowarta mahaifarta, kawai sai ta shiga kumbure-kumburen kiris take jira ta fashe da kuka. Maimartaba da kanshi ya fito domin yi musu barka da zuwa, direba yana parking ta bude motar ta fito, ba tabi ta kan kowa ba ta wani fashe da da kuka kamar wata kan'kanuwar yarinya taje ta rungumeshi tana shashshaka! shi kam fuskarta ya dago yana goge mata hawaye tare da rarrashinta, Aunty Maijidda ce ta jan hannunta suka nufi sashenta tare, hakan beyi wa Safah d'adi ba, ganin yanda yarinyar tayi kamar bata gansu a gurin ba, koda yake daman dole hakan ya faru tunda ita din ta kasance mai yi mata fada gami da nuna mata kuskuranta. Bata iya barin gurin ba sai da ta tabbatar da cewa an sauki bakin a guri mai kyau da kuma dukkan abun bukata. Gimbiya Aysha kuwa kunya da kawaici ya hana ta fitowa tarar su, amma tana zaune labarin abinda yarinyar tayi ya isa kunanta daga bakin 'yan uwanta Hassana da Husaina wanda su d'in ma ta nuna tamkar ba jininta koda yake inda sabo sun saba da halinta amma dai abunda tayi musu a yanzu ya 'bata musu rai mutu'ka! Sosai suka samu kulawa mai kyau kafin maimartaba ya bukaci zama dasu sai da sukaci abinci suka gabatar da sallar la'asar tukkuna sannan suka sameshi a fada shi kad'ai domin akwai maganar da yake so suyi a tsakaninsu. Gaisuwa suka sake mikawa a gareshi kafin shi da kansa ya mika godiya a garesu akan alkairin da sukayi masa. Asp yace."Ranka ya dade ai babu godiya a tsakaninmu da kai, domin kai uba ne a gurin mu, ka cancanta da abunda yafi haka, bayan hakan kuma kulawar da mukayi akan yarinyar nan hakkinmu ne tunda aikin mu ne kare rayukan al'umma." Ya girgiza kanshi da fadin." Tabbas maganarka haka take Asp amma dole nayi godiya domin samun irinku masu tsoron Allah da kishin 'kasa zaiyi mutukar wahala wannan dalilin yasa na jima ina nazari da tunanin irin alkairin da zanyi muku." Kafin Asp din yayi magana ya riga shi da fadin." Ranka ya dade kada ka damu kanka akan wannan al'amari wallahi ni abunda nayi akan yarinyar nan don Allah nayi bana bukatar komai a gurinka face addua." Murmushi yayi yana sake jin kaunar yaron a cikin zuciyarsa, yace." UMARU kenan addua kam zan cigaba dayi muku har karshen numfashina amma ba kaji bahaushe yana cewa (yaba kyauta tukwici ba) ba don kada nace na baka auran yarinyar nan ka dawo min da kyautata ba to dana baka ita sakamakon alkairin da kayi min." Fadar tayi shuru sakamakon maganar. Kasa d'ago kansa yayi ballanatana ya nuna rashin amincewarsa da kyautar da akayi masa..............Jin beyi magana ba yasa yace." UMARU kodai baka kar'bi wannan kyautar tawa bane."? Asp da sauri yace." Aa haba dai! ranka ya dad'e wane mutum! kyautar mutum ba karamin al'amari bane sosai ni naji dadin wannan al'amari kuma kayi kyautar akan ga'ba domin dama bashi da aure a halin yanzu mungode sosai da wannan karamcin." Fuskarsa cike da annuri yace." Asp ka ari bakinsa kaci masa albasa amma yanayinsa ya nuna kamar beyi na'am da wannan kyautatar tawa ba." Yayi namijin 'ko'karin kawar da damuwarsa kansa ya dago tare da kokarin aro walwala da farin ciki yace." Ranka ya dade farin ciki ne ya hana ni iya magana, tabbas abunda abokina ya fada hakane kayi min kyauta akan ga'ba kuma na kar'ba hannu biyu nagode kwarai da wannan karamcin." Ya sauke ajiyar zuciya a fili yace." Alhamdullihi Allah abin godiya, lallai babu shakka ZINATU tayi dace da miji irin wanda yake da wahalar samu ina rokon Allah ya tabbatar da alkairin dake cikin wannan al'amarin." Gabad'aya suka amsa da "ameen ya Allah." *Free pege zai 'kare a pege 40 masu payment kawai nake da bukata idan kin san na siyan littafin nan za kiyi ba kada kiyi min magana🙏🏻* *#500 via....0542382124.....Binta Umar gtbank, idan kati zaki tura kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.......07084653262....Mutanan Nijar ku tuntubi wannan number.... 22796074090....Dala dari katin airtal ko mov* *GOJE!!🏹* 🐕‍🦺🐕‍🦺🐕‍🦺 _(SADAUKI OMAR RETURN💫👑)_ *BINTA UMAR ABBALE🍒* *MANAZARTA WRITER'S* *ASSOCIATION📚🖊️* ____________________ *1-NANA KHADIJA* *2-YARO DA KUDI* *3-GIMBIYA BALARABA* *4-BABBAN YARO* *5- MASHAHURI* *6- LADIDI KWADAGA* *7-TSANTSAR BUTULCI* *8-SADAUKI OMAR* *9-NIDA YAYA SADAM* *10- 'YAR BANGAR SIYASA* *11-DA WATA A KASA* *12- MADADI* *13-KWARA TABI KWARYA* *14-GA RINTA NAN* *15- MATSALARMU A YAU!* *16-RUWAN DARE* *17-GOJE!!* _Littatafai na kenan ga duk mai bukatar karanta daya daga ciki zai samu damar karantawa cikin saukin farashi, wanda zai iya siya nake da bukata, don Allah idan ba siya za kiyi ba kada ki dauki number ta kiyi min magana NAGODE sosai masoya💞🙏🏻_ *SHAFIN NA YAU NAKU NE 'YA'YAN ALBARKA.* _DAUGHTER💞_ *ZEEY KUMURYA* _MARUBUCIYAR_ *(NEHAL)*💫 *DA* _MAMAN TEDDY💞_ *MARUBUCITAR* _LITTAFIN_ *WALI-JAM🐄* *BAFULATAN RUGA* _DA SAURANSU_ Allah ya kara muku basira da haza'ka, NAGODE 'kwarai! Allah yayi muku albarka.🙏🏻 ________ LAST FREE PEGE *39&40* A takaice dai basu bar masarautar ba sai da duk suka gaisa da duk wanda ya kamata, sun tafi da mamakin mutumci da dattakon mutanan, hakika kaf famliy din yarinyar nagartattun mutane ne masu hankali da sanin ya kamata, ita kadai ce ta fita zakka a cikinsu, koda yake dama haka Allah yake ikonsa, amma duk da hakan itama ba za'a rasa wani abu mai kyau daga cikin dabi'unta ba. Maimartaba ya basu kyautar dawakai lafiyyayu gami da kayan sarauta kwatankwacin irin wanda yake amfani dasu, mussaman yasa aka kawo masa kayan farauta daban-daban domin ya gwangwajeshi, aikuwa duk cikin kyautukan da yayi musu yafi farin ciki da kayan farautar domin dama yana da bukatarsu, a ganinsa koda zai cika d'aki guda da irinsu ba matsala bace a gurinsa. Wannan karon gabad'aya a kujerar baya suka zauna, sai da sukayi nisa da tafiya sannan Asp ya fara maganar da tuntuni take cin zuciyarsa. Ajiyar zuciya ya sauke ya kalleshi da fadin." Asp kwata-kwata fa ni wannan al'amari be kwanta min a rai ba, kawai dai na amsa masa ne amma bana jin zan kar'bi auran yarinyar nan." Asp ya 'bata fuska da fadin." Kada ka zama k'aramin mutum mana, ko dai har ka manta da wanda kayi magana, ba fa gurin wasan yara mukeje ba, ya za'ayi ka amsa masa cewa ka kar'bi kyautarsa daga baya kuma ka shigo da wata magana'' Kallonsa yayi babu farin ciki a fuskarsa yace." Kunyarsa ce ta sanya na amince na kar'bi kyautarsa amma kai kanka kasan tafiyarmu ba zata zo d'aya da yarinyar nan ba, naji takaici a lokaci da yayi maganar har kake cewa dashi bani da aure alhalin jiyan nan, na nuna maka yarinyar da zan aura a lokacin daka shigo gidana, tabbas ka shigo masa da maganarta ina ganin ba zai k'arfafa maganarsa ba." Yace."UMARU mace hudu Allah ya halasta maka mutu'kar za kayi adalci a tsakaninsu, wannan dalilin yasa lokacin daya fadi maganar na k'arfafa masa gwiwa, haba mutumina ai da kunya a gabansa ka nuna k'yamarka akan jininsa, kayi hakuri da katsalandan din da nayi maka domin ni kaina nasan da cewa yarinyar akwai matsala a tattare da ita, bata da tarbiya ko kadan, to amma hakan ba zai hana a aureta ba tunda wannan matsalar kawai gareta ina ganin idan ta hadu da jajurtacce namiji kamarka to cikin sauki rayuwarta zata sauya. Ya jima yana nazarin maganganun Asp din kafin yace." Kasan Allah a tsarina bani da ra'ayi tara mata amma ina ganin hakan ba zai samu ba, Asp ina jin tsoron auran yarinyar nan ta hana ni kwanciyar hankali, wannan dalilin yasa gabadaya al'amarin be kwanta min a raina ba. Ya dan doki kafadarsa da fadin." Haba mutumina kai da saba gwagwarmaya da maza mai zai sanya lamarin mata ya dinga baka tsoro! wallahi babu wani abun fargaba da tsoro a cikin al'amarinsu daga zarar ka gane hallayarsu shikkenan zaka zauna dasu lafiya saboda ka cire shakku akan hakan mutumina ba tun yau ba nasha fada maka cewa mace hud'u ce ta dace da kai haba *jan wuya* kada ka bani kunya mana." Dariya ya d'anyi ya bashi hannu suka tafa kafin ya girgiza kanshi da fadin." Asp ba zaka gane ba ne amma shikkenan kawai mu bar maganar Allah ya tabbatar da alkairi." Yace." Yauwa abunda nakeso naji kace kenan abokina insha Allahu za kayi fari ciki da wannan al'amari. To har bayan magariba ZINATU na tare da aunty Maijidda komai anan ta gabatar wanka cin abinci da sauransu, hankalinta da tunaninta gabadaya baya kan uwar da ta haifeta ba ballantana kuma wani, hakan yayiwa ita Maijiddan dadi dama babban burinta ta cusa bakin ciki a zuciyar Safah domin itace abokiyar gabarta tun sanda ta fahimci cewa gimbiya Ayshan tayi mata nisa, sai ta mayar bakin kishinta kan Safara'u wacce ita kuma ta mayar da ita shashasha domin duk abunda take na rashin hankali bata biye mata su taru su lalace gabadaya. Ta dinga bugar cikinta tana bata labarin abubuwan da suka faru, da rayuwar ta a dajin gami da irin wahalhalun da tasha, da labarin zamanta a gidan Asp babu abunda ta rage, sai dai koda wasa bata fada mata irin namijin kokari da kulawar da yayi akanta ba, duk abinda zata a fad'a a kansa sharri ne, har da k'azafin fyad'e kamar yanda tayi masa a gurin Asp, gabad'aya suka had'u suna zaginsa, Aunty Maijiddan ita ke fadin." Zata shedawa maimartaba komai domin abi mata hakkinta, hakan yayi mata dadi a ranta domin ta san mahaifin nata yana saurarar maganar auntyn nata. B'angaran Gimbiya Aysha kuwa ganin har bayan isha'i yarinyar bata shigo ba, sai ta kalli sauran yaran nata dake zaune a gabanta tace." Wannan zaman da kuke bashi da amfani domin dai kune kuka damu da yarinyar nan amma ita bata damu daku ba, da ta damu daku to da yanzu ta nemi inda kuke saboda haka ku tashi ku tafi gidajenku hakan shi yafi ku rabu da ita da mugun halinta, sannan kada wacce tayi yunkurin kiran wayarta ku 'kyaleta taje tayi rayuwa da wacce ta za'ba a madadi na da kuma ku." Cikin rashin jin dadin abinda 'yar uwar tasu tayi kowacce ta tafi gidanta da bacin ran abun a cikin ranta. Da yake aunty Maijiddan ce da girki a daran ta zauna tana shirya masa k'arya da gaskiya har da cewa ya dauki mataki mai tsauri a kan yaron domin yarinyar ta sheda mata cewa a yayin zamansu a dajin ya keta mata haddi." Duk cikin maganganunta wannan ce kadai ta dauki hankalinsa, hankalinsa ya tashi da jin maganar saboda ya san hakan na iya faruwa idan shad'en ya ratsa, to amma wannan maganar ba zata sanya ya janye manufarsa ta alkairi ba, kamar hakan ma shine rufin asirinsu, duk da hakan zai tuntubi yaran domin tabbatar da gaskiyar magana. Washe gari da safe kafin ya zauna a fada ya nufi b'angaran matayen nasa domin dubasu, gabadaya ya samesu ba yanda ya saba ganinsu ba, Safah dai tayi kokarin kawar da damuwarta har ya dan zauna sukayi hira, bangaran Gimbiya Aysha kam rigima suka tafka irin wacce sukayi shekara da shekaru ba suyi irinta ba. Cikin tsananin 'bacin rai yace."Aysha yau ni kike nunawa da yatsa akan wani dalili naki na banza da wofi shin wai me Maijidda tayi miki kika dauki karan tsana kika dora mata, baki da kawaici akan 'ya'ya Aysha baki tausaya mata cewa ita bata dashi meye laifinta anan don ta nuna kauna akan zuriarki." Ido jawur! tace." Bana bukatar ta a cikin al'amarina kuma ba tun yau ba na tabbatar da cewa kaine kake daure mata gindi take mana duk abunda takeso, shin itace ta haifar min 'yar da zata nuna min iko a kanta! na haifi 'yata ta lalata min ita duk hakan be isheta ba sai da ta san yanda tayi ta shiga tsakanina da ita da 'yan uwanta! bayan dawowarta har yanzu bata tako kafarta nan ba ballanatana taje gurin 'yar uwata, haka nan jiya 'yan uwanta suka gaji suka tafi gidan auransu bata shigo ba, shin kai a ganinka hakan shine dai-dai? duk abunda yarinyar nan take aikatawa da sanya hannun Matarka a ciki amma kullum sai ka dinga nuna cewa baka gane ba, to ni gaskiya na gaji da wannan al'amari zan kuma dauki mataki."! Ganin yanda take numfarfashi! ya sanya shi sauke nasa fushin, hannunta ya rike ya jata suka zauna gefen gado a tare. Cikin sigar rarrashi yace."Yi hakuri ki samu nutsuwa muyi magana da fahimta.'' ta kalleshi da fadin." Wane irin nutsuwa zan samu a cikin irin wannan yanayin."? hannun ya sake rikewa da fadin." Na yarda da gaskiyarki, Aysha amma kada b'acin rai ya sanya k'ima da mutuncinki ya zube kada fa ki manta kece babba a gidanan kowa yana ganin darajarki kada kuma kiyi wani abun da zai sanya mutuncin ki ya zube a idanun jama'ar dake cikin gidan nan, kibi komai a sannu a hankali." A raunane tace." To wai yanzu ya kake so nayi? kana so na bari Matarka ta samu nasara a kaina kenan." Ya girgiza kansa da fadin." Maijidda baza ta samu nasara a kanki ba Aysha kin zama murucin kan dutse a ko'ina kece a gaba." Ta girgiza kai da fadin." Ban da gurinka domin yanzu Maijidda ce ke tsara maka komai kuma idan ta fadi magana dai-dai ne a gurina." Murmushi yayi yana kallonta, ya san kawai ta fadi wannan maganar ne saboda kishi amma shi duk cikin matansa babu wacce ke tsara masa magana yayi amfani da ita gwanda ma ita takan bashi shawarwari yayi amfani dasu, amma don ya kwantar mata da hankali sai yace." Na amince da maganarki kuma zanyi wa tufkar hanci banji dad'in abunda suka aikata ba, kuma da kaina zan samesu na nuna musu kuskuransu." Ajiyar zuciya ta sauke da fadin." Shikkenan tunda kace haka amma dai duk da haka ina so kayi min tsakani da matarka babu abunda ya shafeta dani da kuma zuria'ta." Domin a zauna lafiya yace."Kada ki damu zanyi mata magana ta kiyaye shikkenan kowa ya zauna a matsayinsa." Ajiyar zuciya ta sauke da fadin.'' Hakan shine abinda ya dace. To atakaice dai bai samu damar zaman fada ba sai da ya tabbatar da cewa ya kashe wutar da take kokarin ruruwa, ya kuma yi namijin kokari gurin nunawa Maijidda kuskuranta duk irin hujjojin data kawo masa be saurareta ba, yace."Idan ita ZINATU tayi aikin kuruciya ke ya kamata ki nuna mata hanyar dai-dai, cewa taje gurin mahaifiyarta da 'yan uwanta da suka damu da rashinta, amma kema sai ki ka aikata aiki irin na k'ananun yara abunda ki kayi sam be dace ba." Kuka ta shiga yi tana fadin." An nuna mata iyakarta akan abinda take ganin tana da iko dashi, kuma ba tayi hakan da wata manufa ba amma tunda sun juya al'amarin da wata siga daban shikkenan zata cire hannunta daga kan 'ya'yansu." Maganganun da tayi besa yaji tausayinta ba domin idan da sabo ya riga ya saba da jin irinsu kawai dai shi ya nuna mata kuskuranta ne. Da kanshi kuma ya shiga dakin ZINAT din tana bacci ya tasheta sosai ya rufeta da fad'a irin wannan be ta'ba yi mata irinsa ba, a take a lokacin ya bata umarnin kan cewa tayi maza taje ta nemi afuwa a gurin mahaifiyarta. Tana share hawaye ta shirya, ya sanya ta a gaba sai da ya tabbatar da cewa ta shiga sashen sannan ya nufi fadarsa. Da sallama a bakinta ta shiga, ta amsa tare da tsira mata ido har ta 'karaso inda take ta zube k'asan kafet kawai sai ta rushe da kuka tana takure jikinta. Zuba mata ido kawai tayi tana mugun takaicin sangartar da take sai kace yarinya k'ankanuwa! Tsawa! ta buga mata da fadin." Za kiyi min shuru ko kuwa shashashar banza shashashar wofi."! Kokarin hana kanta kukan take amma hakan ya gagara yi take ita kanta takasa tantance me dalilin yin sa. Tace." To tunda haka ki ka za'ba bani da magana dake ki tashi ki koma inda kika fito."? Kasa tashi tayi sai dai tayi kokarin rage sautin kukan ya cigaba da fita kasa-kasa. Taja tsaki da fadin." Kullum kina girma amma kina cin 'kasa! Zinatu ban san lokacin da za kiyi hankali ba, ya kamata ace wannan abunda ya faru dake ya zama izina a gareki amma sai gashi kamar kin 'karo wani iskancin a inda ki kaje, to don baki mutun tani ba sai me? Allah dai yasa bake kad'ai na haifa ba ballanatana bakin cikinki ya kasheni! ina da wasu bayan ke kuma zan iya yafewa Maijidda ke babu abunda ya dameni." Cikin reshin kuka tace." Mammah don Allah kiyi hakuri wallahi duk abunda ya faru dani tsautsayi ne, kuma ina jin tsoron zuwa a gurinki kiyi min fada shiyasa na zauna gurin aunty Maijidda." Tace."Don Ubanki tsautsayi ko son zuciya? na dauka ranar da al'amarin zai faru sai da kowa ya hanaki fita amma ki ka fakaici idanuwanmu ki kama hanya ki ka fita ai naso wa'inda suka sace ki sun kasheki kowa ya huta." Ta dago kai tana kallon mahaifiyarta da mamakin jin furucinta. Tace."Eh ki kalleni da kyau! ni nayi wannan furucin saboda duk wani wanda zai zama annoba a cikin al'ummah to bashi da wani amfani a duniya rashinsa shi yafi alkairi." Yanzu take kukan gaske hawaye masu tsananin zafi suka shiga sharara a saman fuskarta! tunda take da mahaifiyarta bata ta'ba ganin bacin rainta ba irin na yau ba, har tana mummunan fata a kanta da rayuwarta gabadaya duk sai jikinta yayi sanyi. Numfashi ta sauke kafin ta cigaba da cewa." Shekarunki ashirin da hudu a duniya ya kyautu ace yanzu kin nutsu kinyi hankali kin fuskanci abunda yake gabanki amma kullum ke kina daukar kanki yarinya saboda mahaifinki yana sonki yana biye miki da dukkan abunda kike so, kin zauna shirme da shashanci 'yan uwanki na dakin mazajensu har da zuriarsu, 'kawayenki wasu daga ciki duk sunyi aure suna zaune lafiya da mazajensu, ke kuwa hakan baya burgeki kullum burinki ki sanya suttura masu tsada kiyi ado da gwalagwala ki shiga motar da kike so ki zaga duk inda kike so kina takamar cewa ke 'yar mulki ce duk mazan da suka zo da niyyar auranki ki sai ki kore su to me zai sanya mutane ba zasu d'ora ayar tambaya a kanki ba."? Shuru tayi tana auna maganar mahaifiyartata, tabbas duk abunda ta fada a kanta gaskiya ne babu abunda tayi mata kazafi a ciki, manya mutune masu kudi da muk'amai daban-daban sun zo da niyyar auranta amma duk ta koresu saboda ta ganin kamar auran zai tauye mata rayuwarta, a yanzu kuma maganganun mahaifiyar tata sun jefeta cikin rud'ani mai tsanani ashe kallon 'yar iska tantiriya jama'a suke mata. Ta katse mata tunani ta hanyar fadin." Daga yau sai yau babu ke babu Maijidda mutukar ni na haifeki na rabaki da ita ban hanaki gaisheta ba amma kada ki kuskura ki sake shiga sashenta ballanatana wata mu'amula ta had'aku, duk wani abu da kika sani naki ne to ki tura a dauko miki kada na sake ganin kafafunki a sashenta, bayan haka kuma ki tashi kije sashen 'yar uwata ki nemi afuwarta akan irin abubuwan da ki kayi mata, idan kin gama da wannan to d'aya bayan d'aya ki kira wayar 'yan uwanki ki gaisa dasu, har shi babban yayanku Magajin sarki wanda ki ka dauki karan tsana ki ka dora masa har kina gaba dashi saboda yana nuna miki hanya mai kyau, to shima ki nemi number sa don yanzu haka yana Egypt ki kirashi ki nemi gafararsa, wannan kadai za kiyi ki faranta min rai." Ajiyar zuciya ta sauke murya a dashe! tace."Shikkenan Mammah zanyi duk yanda ki kace amma don Allah kema kiyi hakuri ki gafarceni ki kuma dena yi min mugun baki." Girgiza kai tayi da fadin." Tunda kike shaid'ancinki na ta'ba jifanki da wata muguwar kalmar."? girgiza kai tayi da fadin " A'a." tace." To yanzu ma raina ne ya 'baci da al'amarinki, idan kina bukatar albarka to kiyi gaggawar gyara kuskuranki sai mu samu zaman lafiya da juna." A sanyaye tace."Insha Allahu zan kiyaye amma kice kin yafe mun." jim tayi na 'yan mintina kafin tace." Na yafe miki Allah ya shirya min ke shirin addinin islama Allah kuma ya baki miji nagari wanda zaiyi jimiri da hakuri dake da halayenki." A zuciyarta ta amsa da "Ameeen ta dan samu sassauci kad'an, da kyar ta yunkura ta tashi tace. "Zan shiga gurin Mommy kamar yanda kika bukata." Shuru tayi ba tace mata komai ta bita da ido har ta bude kofa ta fita. ***** Bayan kwana biyu da faruwar al'amarin, ta dan samu sassauci daga gurin mahaifiyarta, suna zaune lafiya wani sa'bani bai sake shiga tsakaninsu ba, kuma tana kokarin yi mata biyayya daidai gwargwado sai dai har yanzu mahaifiyar tata bata wani saki jikinta da ita sosai ba, A gurin Safah kawai ta samun walwala dan wani sa'in ma can take yini, wannan ce damar da ita Safah din ta samu take k'ara nusar da ita hanya mai kyau kuma take kwadaita mata son aure a cikin zuciyarta, sai dai kuma inda gizo ke sa'kar a yanzu bata da wani tsayayye a hannu lokacin da take kan ganiyarta take dasu rurutu amma duk ta koresu, a yanzu dai da zasu dawo da tantance nagartacce a cikinsu, ba kuma ta tunanin neman daya daga cikinsu a ganinta kamar hakan zubewar mutunci ne, ta san dai yanzu labarin dawowarta ya isa ace yaje kunnuwan masoyanta to tana zuba ido duk wanda ya damu da ita a cikinsu zai kawo kansa daga nan sai ta fitar da gwani. Sai dai kuma a ranar tunaninta ya rushe dalilin hukuncin da mahaifinta ya yanke mata, be fito fili ya sheda mata abunda ke zuciyarsa ba, amma yayi mata hannunka mai sanda cewa mutukar bata fitar da miji a cikin satikan daya bata ba, to lashakka shi zai aura mata wanda yayi ra'ayi. Tabbas mahaifinta yana tsananin sonta irin son da bayayi wa sauran 'ya'yansa amma ta sheda cewa shi din kaifi d'aya ne, a haka yake baya ta'ba yanke hukunci ya janye, ita a ganinta kamar hukuncin yayi tsauri da yawa, har yaushe ta dawo da za'a d'ibar mata sati biyu ace ta fito da mijin aure kamar akwai rashin adalci a cikin al'amarin. Ta samu mahaifiyarta da maganar cewa sati biyu yai mata kad'an tayi masa magana ya 'kara mata sati biyu ya zama wata daya, Gimbiya Aysha ta nuna sam babu ruwanta a cikin maganar dalili ta riga ta san abunda yake rufe wanda ita Zinat din bata san dashi ba..........da ta samu Safah da maganar itama cewa tayi babu ruwanta kawai dai tayi kokarin ganin ta fitar da miji kafin lokacin daka a bata ya cika, sosai ta shiga cikin wani irin hali mai wuyar fassaruwa tunani kaf ya ta'allaka a gurin neman mafita, babu yanda za'ayi tabi wani daga cikin samarinta nada tace yazo ya aureta wannan zubar da mutunci ne, tsintar kanta tayi da tashin tsakiyar dare domin neman zabin Allah, duk da bata da wani cikakken ilmin addini, a hakan take gabatar da nafila ta zauna saman dadduma tana salatin Annabi kafin ta mika kukanta ga mai kowa da komai. ***** To kamar yanda suka tattauna maganar commissioner of police da Asp abunda ya faru kenan, domin a daran ranar da ya dawo ya bukaci zama dashi..................Suka fara tattauna maganganu kamar gaske sai dai kuma tafiyar ba tayi tsayi ba suka samu sa'bani dalili bambacin ra'ayi, a take gurin ya nuna masa cewa shi din *Jan wuya!* ne tafiyar su ba zata zo daya ba, ya nusa masa cewa bashi yakewa aiki ba 'kasar sa yakewa aiki don haka bai isa ya gindaya masa wasu sharud'a wanda suka sa'bawa dokar aiki ba. mutukar yana bukatar tafiyarsu tazo dai-dai to kowa ya zauna a matsayinsa. Sosai commissioner din yayi mamakin yaron, koda yake tun yana can ya samu labarinsa da kuma irin alakar dake tsakaninsa da Asp Musa Baharu wanda ya zame masa kadangaran bakin tulu, babu shakka ya sake ya bar wannan ala'kar ta cigaba da gudana to akwai matsala, dole ya shiga ya fita ya raba tsakaninsu, domin samun cigaba da gudanar da al'amuransa hankali kwance. Ganin cewa ba zai samu yanda yake so ba yasa yayi saurin b'oye manufarsa yayi saurin gyara kuskuransa, kwantar da kansa yayi ya nemi maslaha dashi, sannan ya sheda masa cewa ya shirya tafiya training a sati a mai zuwa zai turashi can *Abeokuta* 'karo sani akan aikinsa." Cike da kwarin gwiwa ya amsa masa ba tare da wata fargaba ba. ******* Yau ne ya kasance cikar kwanakin da aka d'iba mata, kwance take sai juyi take ta rasa yanda za tayi da rayuwarta, tabbas da kuka yana magani da tuni yayi mata, babu yanda ba tayi da mahaifiyarta kan cewa ta sa baki a cikin al'amarin ba amma fafur! tace babu ruwanta ta dinga kuka tana rokonta amma taki sauranata, sai ta shiga kiran wayoyin 'yan uwanta tana sheda musu halin da take ciki, 'yan uwanta mata ne kawai suka saurareta amma Magajin sarki kashe wayarsa ma yayi yace hakan shine daidai idan bata fito da miji ba to duk wanda ya dace a daura mata aure dashi. Zazzafar ajiyar zuciya ta sauke ta mike zaune tare da sauke kafafunta k'asa! kawai ta tsirawa kasan kafet ido kamar me neman wani abu. Turo kofar dakin yaja hankalinta ta tsirawa kofar ido har sai da ta shigo tare da sallama a bakinta, ido kawai ta zuba mata har ta 'karaso kusa da ita, ta zauna gefenta tare da ajiye ajakar dake hannunta, wani irin kallo take mata kafin tace." Me zan gani haka ni Sakina 'kawata haka ki zama kamar wata zautacciya shin wai bayan kin dawo jinyya kika kwanta dubeki don Allah kin rame kinyi wujiga-wujiga dake."! Ajiyar zuciya mai zafi ta sauke kafin ta kalleta da fadin." Sakina baki da kirki wallahi ace wai don wulakanci sai yau ki kaga damar zuwa duba ni bayan ta dalilinki na samu matsala, yau satina uku da dawowa amma saboda baki da mutunci sai yau ki kazo." 'Yar dariya tayi da fadin." Ki bari kawai 'kawata wallahi abubuwa ne sukayi min yawa kin san dai harkar siyasa sai a hankali kullum cikin uzuri muke wannan dalilin ya hana ni zuwa duba ki amma wallahi kina cikin raina." Tace."Ban yarda ba Sakina ai na gane matsayina a gurinki kin nuna min kudi ya fini babu komai ai." Da sauri tace."Don Allah kada wannan ya janyo mana samun sa'bani 'kawata kiyi min uzuri ki kuma yafe min, kina nan a zuciyata." Ta'be bakinta kawai tayi ba tace komai ba. Tace." Zinat kina da damuwa gaskiya ba haka na san ki ba, ko dai mutanan nan sun samu nasara akanki ina nufin sunyi keta miki haddi"? Girgiza kai tayi da fadin." Ko d'aya Sakina kawai ina cikin wani lamari ne wanda na garara fita a cikinsa na rasa yanda zanyi." Tace."Menene yake damunki."? Kallonta tayi ta girgiza kai kafin ta sheda mata abunda ke faruwa. Taja tsaki da fadin." To yanzu ke ya za kiyi ? tunda kince ke ba zaki nemi tsoffafin samarinki ba, hakan yana nufin cewa kin amince da zabin mahaifinki." Hawaye ta share da fadin." Sakina kai tsaye ba zan saduda ba, na san tabbas yau zai kira ni domin jin ta bakina ni kuma anan zan sake rokar alfarma ya kara min kwanaki ina tunanin kafin lokacin na samu mafita." Ta'be bakinta tayi da fadin." Shikkenan ai amma wallahi da nice kai tsaye zan bijire na nuna rashin yarda ta, haba ai tuntuni an daina yayin auran dole." Girgiza kanta tayi da fadin." Sakina ni yanzu sulhu nake nema da iyayena farin cikinsu nake bukata dole nabi komai sannu a hankali amma ni kaina bana tsammanin zan amince da auran wanda bana ra'ayi." Tace."Wannan shine tunani mai kyau, ki zauna kiyi nazari da kyau domin ki taimaki rayuwarki." Haka suka wanzu a daki suna k'ulle-k'ullen yanda za'ayi su rusa hukuncin da yake da niyyar tabbata a ranar. Sai yamma likis tayi mata sallama ta tafi bayan ta bata shawarwarin da take ganin sune kwanciyar hankalinta. Lokacin da sakon maimartaba ya sameta sai da cikinta ya murd'a tsabar fargaba da tashin hankali, ta kai minti goma a zaune tana sa'kawa da kwancewa kafin tayi namijin kokarin amsa kiran. Tun kafin ma ya fara magana ta fara kuka, kawai sai ya zuba mata ido yana kallo, ta rarrafa har inda yake ta rirrike k'afafunsa tana wani kuka da fadin." Ranka ya dade kaji tausayina don Allah kada ka tarwatsa min farin cikin rayuwata bana so ka aura min wanda bana ra'ayi yanzu an dena auran dole idan kace za kayi min hakan zai janyo matsala babba. Numfashi ya sauke kafin ya tallafo fuskarta, ya sanya hannu yana share mata hawaye rarrashinta yayi da fadin tayi shuru suyi magana ta fahinta. Da 'kyar ta iya dakatar da hawayen dake zuba, ta zuba masa idanunta dake cike da fargaba burinta kawai taji abinda ke bakinsa. Babu alamun wasa a tattare dashi yace." Wannan shi ya nuna min da cewa baki da matsaya kin dauki maganata a banza ace duk a cikin mane ma auranki baki da gwani wanda kike ganin zai zama abokin rayuwarki, wannan karon ba zan tausaya miki ba, domin ni na haifeki amma na gaji da ganinki a haka babu aure, tunda har na baki dama kika watsar to ni ina da wanda nake ganin ya dace dake wanda kuma nake da tabbacin cewa idan na bashi auranki zai rike min ke da gaskiya da Amana, wannan hukuncin nawa babu wanda ya isa ya janye shi ZINATU mutukar ni na haifeki to baki da mijin aure wanda ya wuce takwarana UMARU ina nufin yaron nan daya cece rayuwarki a daji a kwanakin da suka wuce shine wanda na za'ba miki a matsayin mijin aure, kuma na sheda masa kyautar da nayi masa a ranar suka dawo dake gida, shi din ya kuma tabbatar min da cewa ya kar'ba kyautar da nayi masa saboda haka kada ki bani kunya ko kiyi jayayya da umarnina, insha Allahu nan da wata biyu auranku zai tabbata da ikon Allah."! Wani irin bugawa! gabanta yake kanta yana juyawa! tunda ya fara maganar ta nemi yawu ta rasa a bakinta! wani rikitaccen yanayi ta shiga wanda ta kasa fassarashi! kuka take ta gayyatowa amma fafur! yaki amsa gayyatarta idanuwan ma soyewa sukayi sai wani dan banzan zafi suke! jijiyar idon data kanta sun had'u sun d'aure guri daya wanda hakan ya janyo mata mugun ciwon kai irin na 'bari guda, sama-sama takejin maganarsa a lokacin da yake bata umarnin tafiya. Jiki a masifar sanyaye ta iya kai kanta dakinta, kawai ta zube kasan kafet tana janyo numfashi da kyar! ke kace ita din mai jinyya ce wacce ke fama da cutukan dake da ala'ka da numfashi. Wai ace kamar ita jinin saurata gaba da baya, sannan kuma bata rasa komai ba na matantaka ba, Matar manya manyan mutane masu kudi da mu'kamai! aka dauketa kacokan aka bawa wani ma'kaskanci kyauta! mutumin data riga ta raina masa hankali, bashi da komai na rayuwa! bak'auye dashi, wanda ko direbanta be kai matsayi ba amma wai yau shi mahafinta ke ikirarin bawa auranta, koda wasa ba tayi tsammanin hakan na iya faruwa ba! har yanzu ta kasa gano dalilin da yasa mutane suke k'aunarsa! a'iya nazari da tunaninta, ta fahimci cewa jarumtarsa ce take kawai ke burge mutane.......Wannan shine babban dalilin da sanya mahaifinta yin sha'awar bashi ita a matsayin matar aurensa, tabbas kuwa idan ya sake akayi auran nan to zai gane shayi ruwa ne a hannunta, domin sai ta nuna masa bakin rijiya ba gurin wasan makaho bane, sam-sam! ba zata yarda wannan karan ya samu nasara a kanta ba, babu ruwanta da jarumtarsa! tunda a zahiri ta fishi komai, to dole shi zai rusana mata!!!! *TURKASHI!!* ********************** ? ************************** ********** Ai Hausa Novels **************** *************************? ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ? ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ? ************************** *Tofah! yanzu za'a fara wasan😃 ko ya zaman auran nasu zai kasance oho? ni ban san ma me zance muku ba, amma dai muje zuwa..............!* *Wa'inda zasu sayi littafin nake da bukata, don darajar Allah da Annabi idan kin san ba siya za kiyi ba kada ki dauki number ta kiyi min magana🙏🏻* *#500 via....0542382124.....Binta Umar gtbank, idan kati zaki tura kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.......07084653262....Mutanan Nijar ku tuntubi wannan number.... 22796074090....Dala dari katin airtal ko mov*