*_Typing📲_* ********************** ? ************************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************? ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ? ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ? ************************** *_MAKAUNIYAR ƘADDARA😭_* *_Bilyn Abdukk ce🤙🏻_* *_Da sunan ALLAH mai rahama mai jinƙai. Ya UBANGIJIN al'arshi ka bani ikon rubuta abin zai amfani al'ummar MANZON ALLAH. Ka tsare harshena da alƙalamina rubuta abinda zai cutar da ni da duk wanda zai karanta littafin nan. Ka bani ikon rubuta abinda zai amfaneni duniya da lahira ni da masu karatun._* *_Ina mai farin cikin sake dawowa a wannan karon tare da ƴan uwana, yanda muka fara lafiya ALLAH ya sa mu gama lafiya, UBANGIJI ya bamu kariya yay riƙo da hannayenmu baki ɗaya._* *_Ya rabbi ka gafartama Mahaifina da sauran al'umma da suka rigamu gidan gaskiya. Idan tamu tazo ALLAH yasa mucika da imani. ALLAH ka wajabta mana tsoranka da soyayyar MANZON ALLAH😭🙏🏻._* _Zafafa Next level_ *Page 1* ..............“Inada tabbacin wannan itace tashar da zaki iya samun motar duk wani gari da kike buƙatar zuwa”. Mai napep ya faɗa dai-dai yana samun wajen fakin, da ɗan karkato kansa yana duban yarinyar dake a baya zaune.       Batace da shi komaiba. Sai ƙoƙarin kwance haɓar zaninta da takeyi jikinta na rawa. Ta miƙa masa ɗari biyar ɗin dake a ƙudundune saboda uban ƙullin da tasha a cikin zani. Baki ya buɗe kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa. Ya ɗan fisgi ƙudundunanniyar ɗari biyar ɗin daga hannunta yana ƙunƙuni ƙasa-ƙasa.       A yanzu ɗinma batace da shi komaiba, sai hawayen dake famar zarya daga idanunta zuwa kumatu. Tsohuwar ɗari biyu guda biyu da naira talatin a sama ya miƙa mata fuska a tsuke.     “Nagode”. Ta faɗa a karo na farko tana amsar kuɗin. Batare da ta jira amsarsaba ta fito daga Napep ɗin tana kalle-kalle da ƙoƙarin sake maida kuɗin daya bata a haɓar zani ta ƙulle kamar ɗari biyar ɗin ɗazun.      A kallo ɗaya zaka iya fahimtar ƙarancin shekarunta. Dan kuwa bazata wuce shekaru sha huɗu ba. A tsarin halitta batai kama da mai taɓin hankaliba, amma a yanayi zaka iya kiranta da mai ƙarancin hankalin. Duk da kuwa babu wani datti ko makamancin hakan a kaf illahirin jikinta.       Ƙara kai hannu tayi ta share hawayenta a karo na babu adadi, cikin rauni da alamun tsoron dake tattare da ita ta furta, “ALLAH gani gareka. Da kai na dogara, a gareka kuma nake buƙatar taimak......”      “Ƙanwata ina zakije?”. Karaɗin wani kwandasta ya katseta batare da takai ƙarshen addu'arta ba. Kallonsa tai da jajayen idanunta dake a kumbure saboda kuka tace, “Danya”.        “Danya? Ƙanwata sai kinyi ƙarin bayani, dan nikam bamma taɓajin sunan wannan garin ba”.     Shiru tai alamar nazari, ‘Gaskiyar kwandasta ɗin nan. Danya dai garinsu motama bata shiga sosai. To amma idan bata mantaba lokacin da zasu taho da Hajji Lanti bayan sun fito daga Danya a mashin, a Gozarki suka kwana, washe gari kuma daga Gozarki sukazo kusada, anan suka sami motar Katsina’.        “Wai kodai bakisan ina kika dosa bane ƴammata?”.      Kwandasta ɗin nan ya sake katseta. Da sauri tace, “Kusada zanje”.      “......Kusa da kano, nesa da birnin katsina” kwandasta ya faɗa cike da barkwanci. ita dai batace da shi uffanba, sai ma faman waige-waige da takeyi, har yanzu akwai tsoron ko wani zai iya biyo bayanta tattare da ita.      “Kinga ga motar da zaki hau can ta kaiki Gidan mutum ɗaya. Inada tabbacin daga can zaki samu motar kusada ƴar ƙyaƙyƙyawa”.      “Nagode sosai” ta faɗa tana ɗan risinawa. Daga haka tai gaba da sassafa batare data sake bi takansa ba.       Tana isowa motar daya nuna mata ko jiran ba'asi bata tsaya yiba saboda jin kwandasta ɗin motar nata faman faɗin, “Charanci, kankia, Gidan mutum ɗaya, Tsanyawa, Bichi, har kano.     Can baya ta shige inda wata mata ke zaune ita da yaranta biyu da bazasu wuce sa'annintaba. Ta sauke nannauyar ajiyar zuciya dasa hannu ta gyara ɗan labulen jikin gilashin yanda take fatan ko su Hajiya biyota sukayi bama zasu iya ganinta ba. Duk da hakan kuma roƙon ALLAH take a ranta ALLAH yasa motar ta cika da wuri su tafi.      Addu'ar tata kuwa ta amsu. Dan ko cikin ƙanƙanin lokaci motar ta cika. Ita dai tana duƙunƙune cikin hijjab har kanta. Ko wanda ya shigo ya zauna a gefenta bata kallaba sanda ya shigo. Ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya jin motar ta ɗaga alamar zasu bar cikin tashar.       Sunyi tafiya mai ɗan tsayi data tabbatar sunbar cikin birnin katsina ta tsinkayi maganar kwandasta na ambaton kowa ya bada kuɗin mota. Ciro kanta tai daga hijjab ɗin bayan ta kunto kuɗin data ɗaure a haɓar zaninta na canjin mai napep. Jin matarnan mai ƴaƴa na tambayar “Nawane gidan mutum ɗaya” ya sata tsaida hankalinta tana jiran amsar kwandasta ɗin itama.     “Ɗari huɗu ne kuɗinki hajiya”. Ya bata amsa yana amsar kuɗin na kusa da shi.     Matar tace, “Haba ɗana adai duba. Wlhy jiya a ɗari uku-uku mukazo. Yaran nanma ɗari bibbiyu na biya musu”.      “Ai jiya kikace hajiya. Jiya kuma ba yau bace. Dan haka kuɗinki keda yaranki dubu da ɗari biyu ne”.       Zatai magana wani dake can gaba yay saurin amshewa. “A'a fa gaskiya ɗari uku ne, ni kaina ɗazun nan da safe nazo a haka”.      A take rigima ta kaure tsakanin kwandasta da matarnan da mutumin da yay maganar da safe yazo a ɗari uku. Da ƙyar dai aka tsaya akan ɗari uku da hamsin.      Ita dai yarinyarnan dama bata tanka ba. Ta miƙa masa ɗari huɗun da mai napep ya bata canji.       “Ƙanwata ina zakije?”. A taƙaice tace, “Gidan mutum ɗaya”.      Canjin hamsin ya miƙo mata. Batare datace komaiba ta amsa ta maida a haɓar zaninta. Sai dai bata koma cikin hijjabinba tabi ayarin masu kallon hanya. Kasancewar motar mai lafiya ce bayan sallar la'asar kaɗan suka iso gidan mutum ɗaya. Danma sun ɗanyi tsaye-tsaye a hanya na sauke mutane.           A gidan mutum ɗayarma dai a rikicen take. Dan ba taɓa yin tafiya irin haka ba sai wannan karon. Sanda zasu tafi kuwa hajji Lanti ce tai musu komai. Da ƙyar ta samu ta tambayi wani yaro mai saida biredi inda zata sami motar kusada. Shine ya nuna mata. Tai masa godiya.        Ta iske ƙananun motoci kusan huɗu dake jere a kan hanyar da yaron yace mata itace hanyar kusada. Lokacin da suka tafi su tun daga cikin kusada suka shigo motar katsina.      “Ƴammata kusada ne?”. Wani tsamurmurin saurayi ya faɗa yana nufota. Saurin ɗaga masa kanta tayi alamar eh. Cike da jin daɗi yace, “Yauwa taho muje, dama mutum ɗaya muke nema”.     Har cikin ranta taji daɗin hakan. Ya nuna mata jar motar data gama fita hayyacinta. “Yauwa shiga nan. Bayin ALLAH a matsa mata mu kama hanya ko”.       Cike da mita fasinjojin suka shiga muskutawa dan sama mata waje. badan wajen zai wadacetaba ta shiga ta zauna. Sai dai kasancewar ta mai ƙaramin jiki yasa bata takuraba matuƙa. Sai dai waɗanda ta tarar a ciki sunata faman mita sukam an takura musu. Direban ya cika haɗama da son kuɗi. Yanda direba bai tanka musuba itama bata tanka ba. Sai dai acan ƙasan ranta daɗi takeji zata koma gida taga Babanta da su Yaya Tinene, duk da su ba son ganinta sukeba.       Tsabar rashin isashshiyar lafiyar motar basu iso ba sai gab da magriba, dan sun kwashe kusan awa ɗaya da rabi a hanya. Ga tsaye-tsaye da suka dingayi ana sauke wasu da ɗauka a ƙananun ƙauyika har kusan sau uku.     Hankalinta bai tashiba sai da suka iso taga kowa na miƙawa direba ɗari da hamsin kuɗin mota. Cike da tashin hankali da fargaba ta miƙa masa naira tamanin ɗin da suka rage mata. Wani banzan kallo yay mata sheƙeƙe yana nuna kuɗin.     “Naga kina miƙamin murtala huɗu (80n), bakiga abinda kowa ke badawa bane?”.       Cikin rawar murya da cikowar ƙwalla a idanunta tace, “Wlhy su kaɗaine suka ragemani, dama ɗari biyar ce na taho da ita da ga katsina, to sai naba mai ƴar ƙurƙura......”       “K! dakata. Wannan damuwarkice ba tawaba. Inda kinsan baki da kuɗin mota da baki bari nayi jigilar ɗakkoki ba ai. Dan haka ni kuɗina kawai na sani ba wai yanda kika taho daga katsina ba”.        Sharr hawaye suka shiga sakko mata. Ta durƙusa a ƙasa zata fara roƙonsa, hayayyaƙo mata yayi da masifa. A take hankalin mutane ya fara dawowa kansu. Ita dai duƙe take tana kuka da roƙonsa.          A mutanen da suka taru wajen duk basu bata goyon bayaba. Acewarsu miyyasa bata faɗa masaba kafin ta shigo. Idan data faɗa in yaso saiya taimaketa. Suma ɗin haƙuri take ta basu ita dai, dan harga ALLAH batasan adadin kuɗin motar ba. Hakama direba da zugar mutane ke sake harzuƙawa yana mata tujara.         Tun tana roƙonsu a duƙe harta koma gurfane abin tausayi. A haka wani saurayi da tausayinta ya kamashi ya ciri naira ɗari ya bama mai motar. Daga haka suka sama mata lafiya. Har ƙasa ta duka taima saurayin godiya. Yace karta damu, tadai daina shiga mota babu kuɗi. Gara ma idan bata da shi ɗin ta dinga faɗa kafin ta shiga zaifi sauƙi. Godiya nanma tai masa ta miƙe riƙe da naira talatin ɗin daya sake rage mata tunada an biya mata ɗari.        A kusada ɗinma ba sanin ina zata gano hanyar garinsu tai ba. Dan tunda tasan kanta bata taɓa zuwa cikin Kusada ba. Iyakarta ƙananun ƙauyukan dake gefen ƙauyensu kawai.       Tana son tambaya tanajin tsoro, ga wani azababben ciwon ciki da takeji yana taso mata kaɗan-kaɗan. Duk yanda taso cigaba da tafiya sai ya gagara. Da ƙyar taja ƙafafunta zuwa wata runfa ta zauna. Da alama runfar mai yin faci ne. Kasancewar magriba tayi harya tashi.      Zama tai ta duƙunƙune kanta cikin kafafu jikinta na rawa. Ga wata irin zufa na keto mata ta ko ina saboda azabar ciwon ciki. Tun tana zaune har sai da takai kwance a wajen tana juye-juye. Bata damu da cinnakun daketa galla mata cizo ba a jiki, dan ciwon da cikin nata ke mata ya danne komai.       Tsahon lokacin data ɗauka a yanayin ciwone yasa har dare ya rufa bata saniba. Sai jin garin tai ya rage hayaniyar jama'a. Ba ciwon cikin bane kaɗai matsalarta harda Yunwa da ƙishi. Dan rabonta da abincin kirki tun jiya a gidan Hajiya. Abincin da aka bata a gidan da aka kaita ƙinci tayi sosai, dan tana tsoron taci su yanke mata kanta kamar yanda zuciyarta ke bata danshi suka kaita gidan.     Tashi tayi zaune a hankali tana ɗan waige-waige. Titin babu haske. hakama jama'a duk sun nufi gidajensu sai ɗai-ɗaiku. Duk yawan motoci da mashinan ɗazun yanzu babusu. Sai wasu da basu wuce uku ba. Mashinanma bazasu gaza haka ba. Sai fitilar mai shayi da take hangowa can a wajen da motocin ke tsayawa (Tasha).      Komawa tai ta kwanta. Dan haka kawai taji wani shegen tsoro ya turniƙeta. Ta rufe idanunta gam tana karanto abinda ta sani na addu'a. Cikin amincin ALLAH kuwa sai ga barci ya kwasheta. Da alama hakan nada nasaba da gajiyar dake tare da ita ta wahalar tafiya da gudun da taci kafin samun Napep.. ★★★★★        Tun kiran sallar farko na asubahi ta farka da wani irin ciwon ciki. Murkususu ta dingayi tana kuka. Ta jima tana shan azaba kafin ya lafa mata. Zuwa lokacin anata ƙoƙarin shiga sallar asuba. Tashi tai a jikkace, dan yunwa takeji sosai. Ta taka a hankali zuwa inda massallacin tashar nan yake. Butocin da akai alwala ta dinga taɓawa harta sami mai ruwa. Ɗakkowa tai ta dawo wajen rumfarnan. Ta zagaya bayanta tai fitsari da yin alwala. Sauran ruwan kuma ta shanye. Sai a yanzune ta tuna ko sallar La'asar ɗin jiya batayiba. Rabonta da salla tun ta azhar da bayan idarwarta ta gudo.        A take ta fara maka sallolin nan batare da tabi tsarin daya dace na mai ramuwaba. Sai da ta gama jerosu har asubahi. Zuwa lokacin mutane nata fitowa, hakama masu mashina da motoci.      Da farko zaman kallonsu tayi. Daga baya kuma saita mike bisa shawarar zuciyarta. Ƙarasawa tai wajen mai  shayin nan daketa ƙoƙarin ɗora tukunyar garwar shayinsa yana raira waƙar shata. bayan ta masa sallama ya amsa ta gaishesa da girmamawa dan babbane ba laifi.       “Baba dan ALLAH tambaya nake?”. Ɗago kansa yay ya kalleta a karon farko. “ALLAH yasa na sani ɗiyata”. Ya faɗa da kafeta da kallon ƙurilla.    Kanta a ƙasa tana ɗan juya yatsun hannunta cikin juna tace, “Baba dan ALLAH inane hanyar Danya?”.       “Danya! Danya!?. To indai Danya dana sanice ta kusa da Gozarki hanyarta na nan gabas da mu”.       Jin sunan Gozarki ya sata kallonsa cike da jin daɗi. Ta kaɗa kanta fuskarta na sauyawa alamar farin ciki tace, “Eh itace baba”.          Yace, “To zaki zauna ki jira masu mashina dake shiga kenan. Idan kuma bazaki iya jiraba ki samu mai mashin anan ki biyasa talatin ya kaiki ainahin Gozarki ɗin anan zaki samu ƴan mashinan Danya”.       Taji daɗin shawararsa. Hakan yasata masa godiya. Duk da talatin din ta rage mata a jiki, kuma yunwa takeji gara tabi shawararsa. Babu wani jimawa kuwa ta samu mai mashin. Kamar yanda mai shayi ya faɗa talatin mai-mashin din yace zata bashi. Sai da ta bashima sannan ta hau.      Cikin mintuna ƙalilan suka iso Gozarki. Amma sai da ya kaita har hanyar ƙauyensu Danya. A take farin cikinta ya ƙara bayyana. Harta zauna da nufin jiran masu mashin dan babu wanda ya fito saboda akwai sauran safiya, sai kuma ta mike. Ba komai ta tunaba sai nasihar saurayin jiya daya cika mata naira ɗari. Bata da ko sile. Mizaisata zaman jiran mashin? Gara ta taka da ƙafa, duk da kuwa tasan akwai nisa. Amma ɗokin gata a kusa da gida sai ya gusar mata da komai har yunwar da takeji da rashin daɗin jiki.        Tafiya ta fara a doguwar hanyar jan birjin da batasan iyakar lokacin ƙarewarsa ba. Ga ɗan sanyin safiya na busawa kaɗan-kaɗan.       Tayi tafiya mai nisa ciwon cikin nan da batasan dalilinsaba a kwana biyun nan ya ƙara turniketa. Ƙarƙashin bishiyar dalbejiya ta samu ta zauna. Taci murƙususnta da kuka na wani lokaci kafin ta tashi ta cigaba da tafiya. Zuwa lokacin ƴan mashinan garinsu nata fitowa ɗai-ɗai da fasinjoji akai.        Kafin ta gama ankara rana ta ƙwalle. Ga yunwa na cigaba da ragaɗar hanjin cikinta. Haka ta cigaba da jurewa tana jan ƙafafu tamkar mai tsohon ciki. A lokacin da dukkan wani ƙarfinta ke gab da ƙarewa ne ta hango rufin ginin makarantarsu dake da matuƙar tsaho fiye da duk gine-ginen gidajen garin. Ta saki murmushin yaƙe idanunta dake ganin duhu-duhu na lumshewa. Sai faman sauke ajiyar zuciya takeyi da sauri-sauri. A hankali hajijiya ta fara juya mata hanyar, saiko gata ƙasa yaraf babu numfashi..........✍ *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_Typing📲_* *_😭MAKAUNIYAR ƘADDARA!!😭_* *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* _ZAFAFA 5 NEXT LEVEL_ Page 2 ............Saukar ruwa mai bala'in sanyi a jikinta ne ya sakata farkawa a firgice. Ta zabura zata ƙwalla ihu taji an riƙeta.        Kafin ta gama tantance abinda ke faruwa muryar da bata gama sanin ta wacece ba ta tsinkaya yana faɗin, “Haba innar Karima, yanzu yarinyar da aka tsinto cikin wannan halin akema wannan izayar haka? A ganina kamata yayi musan halin da take ciki ai k.......”         A fusace, cikin katseshi tace, “Sallau! Ince dai kai ka gama naka?. Kokuwa bayan taimakon kawota gida akwai wata a ƙasa ne a tsakaninku?”.        Da sauri Sallau ya dubi tsirarun mutane da tarin yara da suka biyo bayanshi saboda ganin a yanda ya shigo da yarinyar cikin garin tamkar mara numfashi.       Yace, “Haba! Haba! Innar Karima. Da ga taimakon yarinya kuma sai ki fassarani da neman laƙamani laihi. Naga dai na maki bayanin komai ban ɓoye maki a yanda na tsintota bisa hanyar shigowa gari a yashe ƙasa bata lunhwashi ba, kuma agaban kowa na hiɗi”.        Baki ta ƙyaɓe tana wani juya idanunta abin tsoro, ta nuna masa hanyar ƙofa, “To ga hanya kama gabanka. Taimakonka kuma angode ince dai shikenan daɗa”.      Cike da takaici Sallau ya buga ƙafarsa ya fito a gidan yana huci. A ransa kuwa sai tsinar Inna ya keyi akan mugun halinta da kowa ya sani a ƙauyen nasu.       Duk mahawarar dake faruwa a tsakanin Inna da Sallau tana kwance a gefe cikin laimar ruwan da inna ta jiƙeta tana murƙususun azabar ciwon ciki. Yayinda yara da waɗanda suka shigo a manyan ke tsaye cirko-cirko na kallonsu. Matan makwafta nason taimakon yarinyar amma tsoron Inna ya hanasu iya yin komai, dan ba ƙaramar jarababbiya baceba kowa ya sani.      A wannan halin wani dattijo ya shigo gidan ɗauke da icce saman kansa, sai gatari dake rataye bisa kafaɗarsa ta haggu. Tun a ƙofar gida yaci karo da tsirarun mutane, hakanne ya sakashi shigowa gidan da matuƙar sassafa. Ya jefar da iccen gefe guda saboda ruɗewar sake ganin wasu mutanen da sukafi waɗanda ke a waje yawa. Kafin yace wani abu nishin kukan yarinyar ya sashi saurin kai dubansa gareta.       “Subahanallahi Zinneerah!!” ya faɗa a firgice yana nufar inda yarinyar take. Duk da yanda jikinta ya ɓaci a laimar ruwan daya gauraya da jar ƙasar garin bai fasa saka hannu ya kamota ya ɗago ba. Cike da firgicin da yafi na farko yake sake faɗin, “Zinneerah! K Zinneerah mike hwaruwa dake haka? Daga ina kika hito ne?”.        Ina Zinneerah batasan yanayi ba, sai faman cigaba da murƙususunta takeyi a jikinsa. Duk ta naɗe masa ƙwaɓaɓɓiyar ƙasar jikinta akan matacciyar rigar yadinsa.      Duk yanda yaso Zinneerah tayi magana bai samu hakanba. Su kuma waɗanda ke tsaitsaye a gidan tsoron Inna ya hanasu cewa komai. Yayinda ita kuma taketa sakin ɗanwakenta a tukunya tamkar batasan da shigowar mai-gidan ba ma.      Tsahon lokaci suna a wajen har ciwon ciki ya lafama Zinneerah tai luf a jikin dattijon tana sauke tagwayen ajiyar zuciya. Da tsananin damuwa tattare da muryarsa yace, “Sannu Zinneerah, sannu kinji”.        Kanta ta ɗago a karon farko ta dubesa, sai kuma ta yunƙura da ƙyar ta tashi zaune tana faɗin, “Baba!” kafin ya bata amsa ta maida dubanta ga sauran mutanen dake a gidan har zuwa kan Inna dake gyara wutar ɗan-wakenta. Ta duba jikinta matsanancin tsoro na bayyana mata a kan fuska.      Kafin wani ya samu damar cewa komai Inna ta miƙe a hasale, dan takai matuƙar cika da haushi. Bakin wuta ta ɗauka tana miƙewa. Kafinma tace wani abu an fara rige-rigen fita a gidan da gudu dan kowa yasan hali.     Da sauri Zinneerah ta kalli dattijon dake mata kallo irin na tsananin damuwa. “Baba yunwa nakeji”. Ta faɗa tana mai raba hankalinta biyu a kallonsa da kallon Inna dake masifa tana bin mutane da bakin wuta.        Duk da tsoron Inna dake cike fal da ransa bai ƙi amsa ɗiyar tashi ba. Ya miƙe da rawar jiki yana faɗin, “To Zinneerah jirani”.        Buta ya ɗauka ya nufi bayinsu, yana shiga ya ajiye butar yana waige-waige. ta inda katangarsu ta faɗi akai dannin itacen geza yay dabarar ficewa a gidan, yasan mutum ɗaya ce zata iya zuwa gidan ta taimaki Zinneerah daga halin Asabe. Duk da yunwar dake cin hanjin cikinsa shima bai fasa ɗaukar hanya ba zuwa ƙauyen Sanni inda babbar ɗiyarsa ke aure. Da yake babu nisa sosai, rafi ne ma kawai ya rabasu.       A ƙasan ransa yana matuƙar jin ƙuna da zafin halin da ɗiyarsa Zinneerah ke a ciki, sai dai tsoron matarsa Asabe bazai barsa yay maganaba. Shi kansa yaga ƙarfin halinsa ainun a yau da har ya iya fuskantar Zinneerah kai tsaye, sai dai yasan shirun da Asabe tayi bana alkairi bane dan cike take da shi.      Da wannan tunanin Baba ya iso ƙauyen Sanni.        Ƙauyen Sanni ƙaramin garine da ko rabin rabin Ƙauyen Danya bai kaiba. Gaba ɗaya gidajen garin basufi goma sha biyarba. Sai dai a kowanne gida zaka samu family house ne mai tarin iyalai.  Kasancewar irin wannan lokacin na rani babu yawan maza duk sun tafi neman kuɗi birni sai mata kawai a gari da yara. Tun daga ƙofar gidansu Gajeje dake jerin gidaje uku da sukafi kowa yawan iyalai a ƙauyen ake jiyo arerewar mata da ihun yara da luguden daga.     Baba yaɗan matsa ga yaran dake a gindin bishiyar ƙatuwar ceɗiya suna wasan langa. Ɗaya daga cikinsu ya taɓa yana faɗin, “Ɗana ko Gajeje na ciki?”.        Wanda aka taɓa ɗin ya sauke ƙafarsa dake a ɗane yana kallon dattijon. “Eh baba tana nan, yanzuma suka gama sussukar maiwa anan”.      “Yauwa dan ALLAH sanar mata ana sallama”.         Kamar yaron bazaijeba sai kuma ya kwasa da gudu yana faɗin, “Kai Garzali ku jirani indawo”.       Ba'a wani ja lokaciba wata mata ta fito, a yanayinta zaka ɗauka wani shekarune da ita masu yawa. Sai dai a kallon idanu zaka samu amsar ƙarancin shekarunta. Wahalar rayuwace kawai ta maidata tamkar mai shekaru arba'in a duniya. Ta gyara gyautan zanen data yafo a kanta tana washe baki da fadin, “A'a lale-lale. Baba kaine tahe a tsakkiyar ranarnan haka?”.        Baba dake duban ɗiyar tashi daso da kauna ya murmusa yana jinjina mata kansa, “Nine kuwa tahe Gajeje”.       “To sannu da zuwa Baba. Bara na kawo maka tabarma da ruwa ko...”     Saurin dakatar da ita yayi ganin zata juya. “A'a Gajeje dakata, tahiyarnan tawa bata lahiya bace. Dan haka zama bai ganni anan ba”.      Cike da tsoro tace, “Wani abune ya faru kuma? Ko Innace tsiyar tata ta motsa yau?”.       “To ba'ace ba dai Gajeje. Ƴar uwarkice ta dawo cikin wani yanayin da sam ban gane masaba. Yanzu haka na barota a gida tana maɗoɗowar yunwa. Gashi kuma naga ran Asabe a ɓace yake, dan ko uffan taƙi hiɗi mani, kinsan kuma bata barin kowa ya hiɗi yanda akai ko?”.        “Wai Baba kana nihin Zinni ce ta dawo gida?”.     Da damuwa ƙarara a fuskarsa ya ɗaga mata kai.        Zanen kanta ta gyara kawai rai ɓace tace, “Muje baba. Dan inna zumace sai da wuta. Karta sake bi ta hanyar da tabi a baya ta maidata wani gun kuma”.       Sosai yaji daɗin hakan. Dan haka suka kamo hanyar komawa Danya suna tattaunawa akan matsalar Inna Asabe da halin da Zinneerah ke ciki a dalilinta. ★★★          Baba da Gajeje sun iske ƙofar gidan a yamutse da hayaniyar Inna da wasu a mazan maƙwafta da suka kasa haƙuri suka tanka mata akan dukan Zinneerah da tahau yi tun bayan barin Baba gidan. Yayinda Zinneerah ke gefe tana murƙususun ciwon ciki.      Ran Gajeje a ɓace da halin mahaifiyar tasu ta shiga cikin rikicin da ƙyar ta lafar da kowa. Kusan minti talatin aka samu wajen ya nutsa. Inna ta shiga gida mutanen dake a ƙofar gidan kuma kowa ya kama gabansa ana zagi da ALLAH wadai da halin Inna Asabe na rashin tausayi.       Sai a lokacin Gajeje ta samu damar kama Zinneerah dake kwance gefe buɗu-buɗu da ƙasa tamkar an tonita a rami. Gidan ta shiga da ita, Inna zata fara sabuwar jaraba Gajeje ta haɗe fuska tana faɗin, “Innarmu! Innarmu!”.      Shiru tayi saboda sanin halin babbar ƴar tata itama. Sannan duk yanda takai ga hawa akan masifarta da Gajeje tayi magana bata iya cigaba saboda wani dalilinta daba kowa ya gama saninsa ba.        Itama Gajejen bata sake cewa komaiba sai kallon Tinene ƙanwarta tayi. “Ke Tinene ɗaukamin karauni a ɗakinku”.      Baki Tinene ta cika da iska tana ƙunƙuni, sai dai kuma babu damar ƙinyi. Fuuu ta shige ɗakin kwanansu da ada can shine ɗakin mahaifiyar Zinneerah kafin tabar gidan. Wata tsohuwar tabarmar karauni ta ɗakko zuwa gindin bishiyar mangwaro dake a kusan tsakkiyar gidan. Zinneerah na zaune an jinginata da bishiyar, Baba na daga tsaye gefenta kaɗan yana kallonta dayin hawayen zuci. Sai Gajeje dake can kusa da Inna a gaban murhu taɗan kara ruwa jikin wutar ɗan waken Inna na saidawa dan yay ɗumi.             Gidan yay tsit babu mai cewa uffan duk da kuwa kowa nada abin cewa a bakinsa. Musamman ma Baba, sai dai tsoron matarsa Inna bazai barsa iya furtawaba duk da tsantsar tausayin ƴarsa dake ransa.       Gajeje ta juye ruwan ɗumin a wani roban wankansu ta sirka takai banɗaki tazo ta kama Zinneerah ta miƙar. Har banɗaki ta kaita da kanta. Bata wani tsaya jan zance ba ta ɗaurayema Zinneerah jiki da kanta duk da kuwa tanata mammaƙewa dan nauyin yayar tasu da suke kallo tamkar uwa a garesu. Tinene ta ƙwalama kira ta kawo mata zani da riga.             Sosai Zinneerah taji daɗin jikinta da wannan wanka. sai faman sauke ajiyar zuciya takeyi da lumshe idanu. Baba dake tsaye har yanzu da kansa ya gyara mata tabarmar ta kwantar da ita.       Inna na kallonsu a kaikaice, watsama Baba wata uwar harara tayi tana yin ƙwafa. Sai dai kuma batace komaiba ta cigaba da tsame ɗanwaken ta.         Duk da Gajeje taga harar da Innar tasu taima mahaifinsu bata tankaba. Sai ma kwance gefen zaninta tayi tana ciro nera hamsin data sha ƙudindina. “K Tinene zokije nan wajen Dijen kamaye ki sayo mani kunu da suga”.      “Yaya Gajeje tallafa zan ɗauka, kina ganin Inna harta gama kwashe ɗanwake, gahi Sa'a bata dawo ba, Karima kuma na rimaye”.       Wani mugun kallo gajeje ta watsamata, a hasale tace, “Ni kike hiɗima haka Tinene?”.       Kafin Tinene ta bata amsa Inna ta dubesu a hasale. “Wai Gajeje miyasa ke baƙya son zaman lahiyane? Ai gaskiya Tinenen ta hiɗi, inke idonki bai gane miki na kwashe ɗanwakenba”.        “To amma Innarmu koda shirin ɗaukar ɗanwaken take nanda gidan Dije ne zai gagareta zuwa ta sayo mani kunu? Kenan iya shegen da sukema kowa nima ya hwara zuwa bisa kaina?”.        Yanda Gajeje ke magana a hasalene ya saka Inna cewa, “K Tinene amshi ki sayo mata, ni bansan wani kace-nace”.       Tinene na faman tunzura baki da ƙunƙuni tazo ta amshi hamsin ɗin ta fice bayan ta ɗauki wani tsohon kofi. Babu jimawa sai gata da kunun kuwa. Kusan tare suka shigo da Sa'a ɗauke da ƙaton botiki mai ɗauke da sauran gyaɗa da riɗi da taje talla.       Da sauri ta ƙarasa shigowa tana fadin, “Kai, Kai, Zinni! Yaushe kika dawo?”.        Murmushin ƙarfin hali Zinneerah taima Yayar tata da itama ke ƙaunarta a gidan, sai dai kuma ta kasa bata amsa sai Yaya Gajeje ce dake zuba suga a kunun da Tinene ta sayo ta bata amsar.     Kafin Sa'a da hawaye suka cikama ido tace wani abu Gajeje ta maida hankalinta ga Tinene. “K samo mani lidde”.       “Mu bamu da lidde nan gidan”. Cewar Tinene tana murguɗa baki.     Jikake bamm! A goshin Tinene, Gajeje ta jefa mata murfin kwano dake kusa da su.      A take ta zube ƙasa ta fara kururuwar ihu kamar wandda aka kashe. Inna ta saki kwanon yaji a ƙasa ta nufi ƴar tata da sauri. “Gajeje kashemin yarinya zakiyi akan wannan sheɗaniyar yarinyar data gudu yawon tambaɗarta?”.       “Kaɗanma na mata Innarmu”. Gajeje ta bata amsa rai ɓace.       Cikin raɗa-raɗa Sa'a data je ta ɗakko mata ludayin tace, “Yaya Gajeje ki ƙyalesu dan ALLAH, karki tahi gida a huce kan Zinni. Kindai san halin Innarmu ai”.      Shiru Gajeje tayi bata tankaba. Baba ma dake tsaye har yanzu bai tanka musunba, hasalima hankalinsa na kan Zinneerah da ke shan kunun cike da zalamar yunwar da takeji.       Zuwan Gajeje gidan ya matuƙar taimakawa wajen bama Zinneerah kulawa. Inda kuma ya katange duk wani bala'i da masifar dake cin Inna a rai. Dan bayanma ta kammala saida ɗanwakenta su Tinene sun ɗauka wani sun wuce talla zani ta ɗauka ta fice gidan wai taje barka wani ƙauye dake can gefensu shima.      Hakan yama baba daɗi sosai. Dan koba komai sa samu damar jin yaya akai Zinneerah tabar gida a kwanaki ashirin da shida da suka shuɗe, da kuma yanda akai ta dawo musu yau a wannan halin?.           Suna zaune shi da Gajeje suna tattaunawa akan hakan Zinneerah dake barci tun ɗazun ta farka a firgice da ciwon ciki. Duk kanta sukayo suna tambayar ko lafiya?. Bata iya amsasuba sai da ya lafa mata.     Ta share hawayen dake sauka a kumatunta. “Yaya Gajeje cikina kemin ciwo”.      Basu kawo komai a ransuba sai yunwa. Dan haka Gajeje tace, “Zinni yunwace nasani. Sannu kinji. Idan zaki iya tashi kiyo alwala kiyi sallar azahar da la'asar sai kizo ga abinci kici”.            “Zan iya yaya Gajeje”  Ta faɗa tana maida kallonta ga baba dake kallonta cike da raunin zuciya dana idanu.    “Baba ina wuni”. Murmushin ƙarfin hali yay mata da shafa kanta. “Lafiya lau Uwata yaya jikin?”.       “Da sauƙi baba”. “To madalla. tashi kiyi sallar maraice na ƙara yi”.       Bata musaba ta miƙe. Jin gidan shiru ya sata sanin Inna da su Tinene duk sun fice. Hakan ya mata daɗi. Alwala tayo tazo ta wucesu zuwa ɗakin kwanansu. Babu abinda ya canja a ɗakin nasu sai ma shirgin kayan dauɗar su Yaya Sa'a. Dama itace mai kimtsa ɗakin dayi musu wanki. Kayan taɗan ture gefe ta tayar da salla cike da ƙarfin hali dan batajin daɗin jikinta gaba ɗaya. Duk da sallar ba'a cikin tsari akayitaba tadai gabatar ta sake komawa wajen baba da yaya gajeje.           Abinci yaya Gajeje ta fara bata taci. duk da yunwar da take ji har yanzu taci abincin a nutse dan sam dama ita bata da garaje ko gaggawa. Bayan ta kammala ta wanke hannu ne Yaya Gajeje ta ce, “Zinni kinga marece yayi inason na koma gida nabar su Rabi'u. Munason ki nutsu ki faɗa mana yaya akai kika bar gida ne batare da sanin kowaba? Ina kuma kikaje?”.           Duk da ƙarancin shekarunta hakan bai hanata jin ɗaci ba a ranta. Ta share hawayen dake rige-rigen zubo mata tana gyara zama. “Baba wlhy ban gudu ba. Bayan tafiyarka kasuwa sai I.......        Jin tayi shiru tana kallon hanyar shigowa yasa Baba da Gajeje saurin kallon wajen suma. Inna ce ke shigowa cikin gidan tamkar wadda aja jeho.      Ganin yanda duk suka watso mata idanu ya sata fara magana a harzuƙe. “Halan cin nama na akeyi kuka watso mani idanu haka?. Wani annamimancin kike hiɗi masu a kaina ko?”.      Ta ƙare maganar tana watsama Zinneerah mugun kallo.         Gajeje ta dubi Baba da yay ƙasa da kansa. ta dubi Zinneerah da itama kan nata ke a ƙasa tana hawaye. Wani irin tausayinsu da jin zafin mahaifiyar tasune ya ɗarsu a ranta, musamman yanda take ƙasƙantar musu da mahaifi a gabansu duk da tsufansa. taɗan girgiza kanta tana dubanta. “Amma Inna miya kawo wannan zancen daga shigowarki? Yarinyar da ke cikin halin ciwo wane kuma munahincinki zatayi?. Ni a ganina kamata yayi kema ki shiga jerin masu murna da dawowar Zinni gida kodan tashin hankalin da muka shiga na rashin sanin inda take a kwanaki ashirin da shida ɗin nan”.        “Tunda uwatace ta ɓata ko? Kune kuke ɗauka ɓata tayi dama ai, yarinyar da ta tafi yawan taɓaɗanta data saba har kuke damuwa da inda taje. Inda ba guduwa taiba wane shege ne ya dawo da ita yanzu da ƙahwarta?. adai jura zuwa rafi, wataran muna zaune za'a shigo mamu da ɗan dakan kuka na tabbacin yawon tazubar....”     Tsam baba ya miƙe batare da cewa uffanba ya fice gidan. Itama Gajeje rai ɓace ta miƙe tana magana cike da rawar murya. “Innarmu wannan hurucin naki dai kau sam bai dace ba. Dan koba komai itama Zinni ɗiya take garegi, yanda kuwa take mace haka Sa'a da Tinene da Karima suke mata. Baƙya tsoron mugun alkaba'in da kike hiɗi gareta ya dawo bisa kanmu ne”.       Wani mugun kallo Inna taima Gajeje. Kamar zatai magana sai kuma tai shiru. Itama Gajejen bata sake tankawaba sai miƙar da Zinneerah da ke kuka tayi suka shige ɗaki. Sai da taga ta kwanta sanann ta fara magana. “Zinni bara naje gida, insha ALLAHU gobe da hwarar sahiya zan dawo, dan akwai raɗin suna gidan malam mato dama da zamu shigo. To daga can nan zan wuto na yini. Ki ƙara haƙuri da halin Innarmu watarana sai labari kinji”.        Kai Zinneerah ta ɗaga mata tana share hawaye. Muryarta na rawa tace, “Nagode Yaya Gajeje”.     Murmushi kawai Gajeje tayi da shafa kanta ta fito a ɗakin. kai tsaye ɗakin Inna ta nufa dan tanaso suyi magana.............✍       *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_Typing📲_* *_😭MAKAUNIYAR ƘADDARA!!😭_* *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* _________________________ Duk wacce batayi anfani da sabulunnan ba anbarta abaya acan karshen bayama kuwa duk Mai tantama akan sabulai nagyaranjiki cewa basa Aiki toh yacire mg's domin kankat ne insha Allah babu Wanda yayi anfani dasabulunmu yace baiyi ba koyaushe mg's sai sanbarka amare da uwargidaye hardama yanmata kuhanzarta kusamu naku ba karya domin bama cika Baki kugwada kubada labari da bakunanku sabulu daya tamkar dubu wadandama basasan using cream sabulun mg's herbal whitening black soap yawadacemuku jikinku zaiyi kyau koyaushe kukasance clean cikin kamshi Kuna glowing koda bakusa turare ba🤗 Kayanmu bana bleaching bn organic ne sunagyarajiki fiye da tsammaninku zaifiddomuku da ainihin natural beauty dinkine Wanda yagwada shi zaitabbar amare kuyi kokari kumallaki mg's domin baruwanku da zuwa adirjemuku jiki zakuga yanda fatarku zata dinga walwali Ina masu pimples Tabo(spot) Sunburn dama dukwani matsalar fata kuyi kokari kunemi soap dinnan before 2weeks zaisharemuku hawaye kuzama abun kwatance Sister's masu nankarwa kuma kunemi soap dinnan Yana rage nankarwa sosai🧖🏻‍♀️duk me shakku tayi kokari tagwada mg's insha Allah bazakiso rabuwa dashi ba Akwai maisa haske Amma kayanmu nafada bana bleaching bn zaifiddomiki d ainihin halittarkine yagoge dukkan dattin jiki Akwai Kuma Wanda zaimiki maintaining skin dinki yasaki fresh fatanki tazama kalar hutu Pls bamacika Baki you HV to try it and see for yourself 100%tested nd trusted Soap price:3k Location:kaduna buh munaturawa ko Ina Amma delivery is not free Maiso kindly message 08062991549 Call 08064532391 Note:Babu inda zakusami mg's herbal whitening black soap sai a number dinnan bairiga yakai market b inyakai we will let you know buh as for now wnn numbern ne kawai🙏 Maiso yahanzarta before yaji sold out akwaisu available now insunkare you HV to wait akawo so maiso yahanzarta🙏adade anayi sai gsky🤭🤝 Mg's skincare Mg's bakery You can still order ur birthday cake, cupcake,slice cake,meat pie,shawarma,samosa nd spring rolls for ur event @mg's bakery Kindly call or chat 07046881166 07067210195 08062991549 Masu bukatar abayas,takalma da jakunkuna,ashobe,laces d atamfofi, materials nd the rest 07046881166 👏🤝 _________________________ _ZAFAFA 5 NEXT LEVEL_ *Page 3* ............Gajeje bata wani jima ba a ɗakin Inna tafito rai ɓace alamar dai wani rikicin suka sake tafkawa. Tana fita a gidan kuwa Inna ta fito a matuƙar hasale itama.     Ɗakin su Zinneerah ta shiga. Zinneerah dake zaune tana hawaye har yanzun sai jin saukar lafiyayyen mari tayi. Zabura tayi zata ƙwalla ihu Inna ta daka mata tsawa.       “Munahika yimani shiru kona lallasaki. Dan uban daya haiheki sheri da kikai shirin ƙullamani ashe? Wa billahillazi koda wasa kika sanarma wani a yanda kika bar gidanga sai na lahira ya hiki jin daɗi. Idan kuma kiji ƙarya don ALLAH ki hiɗi masu yanda akayi. Aradun ALLAH ubanki ma sai na ci masa bura-uba bamake kadaiba dan buhun ubanki. Lalatacciya kawai mai shegen nunkuhurci irin na uwarta”.        Ita dai Zinneerah kuka kawai take jikinta na rawa dan tsoron Inna da takeyi. Sai da ta gama zazzage mata ruwan bala'i iri-iri sannan ta fice a ɗakin.     Kuka kam Zinneerah ta shashi matuƙa. Ga ciwon da cikinta kanyi lokaci zuwa lokaci. Dawowar Sa'a gidan da kayan ɗanwake ta samu tsagaitawar kukan saboda lallashinta da Sa'a ta zauna yi. Ganin yanda Sa'a ta nuna matuƙar damuwarta yasata shanye sauran kukan nata dan ba yaune farauba a gareta ga halin Inna matar ubanta. WASHE GARI.        Da safe kamar yanda ta saba kafin tayi tafiya tanayin sallar asubahi ta fito tsakar gida ta hau shara. Duk da sanyin dake busawa na sanyin safiya haka taima tsakar gidan ƙwal da shara, ta gyara turken dabbobin Inna ta zuba musu sabon abincinsu. Sannan tazo ta fara haɗa wuta. Cikin dauriya take komai, dan wani irin zazzaɓine ke ratsa dukkan ɓargon jikinta a hankali. Haka ta cigaba da daurewa harta kammala dukkan ayyukanta wajibabbu a gidan.      Babu wanda ya fito a mutanen gidan sai can gyallowar rana. Sa'a ce ta fara fitowa tana mata sannu, sai ga Tinene ta fito itama tana mika da hamma dan sai yanzu zatai sallar asuba. Can sai ga baba ya shigo gidan, da alama tunda ya fita salla masallaci bai shigoba sai yanzun.      Dukawa sukai har ƙasa ita da Sa'a suna gaishesa. Ya amsa idanunsa aka Zinneerah da ya kwana da damuwarta a cikin ransa. Murya ƙasa-ƙada dan kar Inna taji yace, “Zinneerah yaya jikin naki?”.       “Da sauƙi Baba”. Ta amsa kanta a ƙasa.     Kafin ya ƙara cewa wani abu Inna ta fito wuff. Da sauri yabar wajen saboda wani shegen kallo mai kama da harara data watso masa. Taja tsaki tana duban Zinneerah dake durƙushe har yanzu.         “Ki tashi ki ɗebo mani ruwan rahi dan randunan gidanga duk babu ruwa. Kuma na rahin yamma nakeso dan ruwansa yahi garɗi da haske”.      “To inna. Ina kwana?”. A takaice ta amsa mata tana karasowa wajen murhun inda wutar da Zinneerah ta haɗa ta kama sosai.       Fuskar Sa'a babu walwala tace, “Inna dakin barta sai anjima rana ta ƙara dagawa sama, kinga akwai sanyi garin sosai”.          “To uwata, yanda kikace ai haka zanyi”. Inna ta faɗa a hasale..       Shiru Sa'a tayi, dan tasan gatse Inna tai mata.      Zinneerah dama bata tsayaba, tuni ta ɗauki botikin fenti da hijjab ta nufi ƙofar fita cike da dauriya. Hakan ba sabon abu bane a gareta, shiyyasa fita ɗibar ruwan a yanzu bai dametaba. Kawai yanda takejin jikinta babu daɗine matsalarta. Amma haka ta nausa kanta hanyar jeji domin ɗebo ruwa. Harta isa babban rafinsu da su kansu basusan iyakar inda ya tsayaba bata haɗu dako kare ba. Ta ajiye botikin a gaban rijiyar da aka gina a tsakkiyar yashi wadda bawani zurfine da itaba. Hasalima a gabanta ake duƙawa asa kwano a kwarfo ruwan dake kwance. Bismillah ta ambata tana saka kwanon cikin ruwan, sai da ta kwashe na ciki tas ta watsar waje sannan ta jira ya sake taruwa ta diba a botikin nata. Bayan ta cikashi taf ta miƙe da ƙyar ta ɗora bisa kanta.          Koda tai sallama Sa'a ce kawai dake wankin baki da gawayi ta amsa mata. Inna ko dake bakin murhu tana yanka tuwon dare daya rage tana jefawa a ruwan data saka a wuta ko kallonta bataiba. Hakama Tinene dake gefen Innar tana shan koko.       Sai da ta wanke duk randunan gidan guda huɗu sannan ta juye ruwan ta Sake komawa. Haka ta dinga kai kawo tsakanin gida da rafi ɗibar ruwa. Tun bata haɗuwa da kowa har mutane suka fara fitowa. harma da irinta masu zuwa sakkon ɗibar ruwan na rafi. Duk wanda ta haɗu dashi gaisuwar mutunci ce tsakaninsu. Har ALLAH yasa ta kammala gaba ɗaya.         Zuwa yanzu Inna ce kawai a gidan, Baba ya fice wajen sana'arsa. Sa'a da Tinene kuwa sun ɗauki tallar gyaɗa da Riɗi da itama tasan tata tallan na jiranta ne.      Sai da ta gama ɗauraye ƙafafunta da sukai futu-futu da ƙura tazo inda Inna ke tankaɗen garin ɗan-wakenta.      “Inna na gama ɗibar ruwan”. Yanda tai maganar murya na rawa yasa Innar kallonta. Duk da yanayinta ya nuna bata jin daɗi hakan baisa Inna tambayarta ba. Sai ma sake tsuke fuska tayi da faɗin, “Zauna inason magana dake”.      Babu musu Zinneerah ta zauna duk da ranta fal tsoro.          Ƙare haɗe fuska Inna tai tana dubanta da ƙyau. A tsawace tace, “Miya maidoki garinga?”.        Sosai gaban Zinneerah ya ƙara tsananta faɗuwa. Murya na rawa tace, “Inna sune suka koroni. Sunce basa buƙatar baƙauya irina. Kuma saida suka shinhiɗa mani uban bugu da aibantani kahin su bani jikka biyu da rabi su sani a mota....”       “Munahika, halan wata tsiyar kika ƙulla masu acan? Saboda kina buƙulu da abunda zan samu na hassahi daga kuɗin aikin naki?”.       “Wlhy Inna ba haka bane. Matar gidance bata sona dai na rantse”.        “Ruhwa mani baki dan bantan ubanki. Ai hajji Lanti zatazo ne, zanji gaskiyar zance a gareta. Wa billahillazi naji saɓanin abinda kika hiɗi yanzu ina halakaki na halaka banza wohi babu mai sanin yanda akai. Ƴar banza, kinhi son mu zanna ga ƙugunki ga nawa a gida. Sabidda kina kishi dani tunda uwarki bata gida? To mu zanna ga hili ga mai doki ai. Dan uban mutum yayi idan yana iyawa dani ko. Tashi ɓacemin a ido kahin naita tsinarki har se zaman Danya ya gagari ubanki ma bake kaɗai ba”.        Mikewa Zinneerah tai tana shartar hawaye. Duk da cin zarafi ga inna ba yaune farauba a gareta. Sai na yau ɗin yay mata zafi ainun. Karon farko taji tana kwaɗayin son sanin inda mahaifiyarta ke rayuwa a yanzu.     Ɗakin kwanansu ta shige, ta faɗa akan yamusashshiyar katifar da Yaya Sa'a da Tinene ke kwana. Dan ita bisa tabarmar karauni take kwana kamar yanda Inna take buƙata. Dauɗaɗɗun kayan dake gefe ta jawo ta shiga rufawa a jikinta saboda sanyi da takeji.      Sosau ta ringa rawar sanyi tana sambatun zazzaɓi. Har tsahon lokaci babu wanda ya shigo ɗakin. ba kuma ta ƙarajin motsin Inna ba. A haka barci yay gaba da ita mai nauyi.       “Zinni!! Zinni!!. Wai dan buhun ubanki baki jina inata kware baki?”.      A firgice ta tashi zaune jin irin kiran da Inna ke ƙwalla mata tamkar ana yaƙi. Ta amsa a kasalance tana ƙoƙari janye kayan data nausama kanta gefe dan ta samu damar mikewa.        Fitowar tata yay dai-dai da shigowar Yaya Gajeje gidan da sallama. Inna ta sake tsuke fuska tana kallonta. sai kuma ta ɗauke kai ta maida ga Zinneerah dake fitowa tana rawar sanyi da yamutse fuska alamar bata da lafiya.       “Oh sannu ƴar gata! Ina nan tsaye ke kina can kina jan nashari a ɗaki? To kizo ki haɗa mani wutar ɗan wake kar rana tayi..”       Da sauri Yaya Gajeje tai saurin tare numfashin Inna, “Haba Inna, wane haɗa wutar ɗanwake kuma kike magana haka? Diba kiga yanda take rawar ɗari da alama bata da lahiya”.        “Mtsoww!!” Inna taja tsaki. Kafin ta cigaba da magana a hasale. “To ina ruwana da ciwon nata. A yanzu ma wagga duniya waye ke da lahiyar. Gajeje ki hita idanuna, karki kaini maƙurar randa zan maki bankaɗa wallahi”.       Murmushi Gajeje tai tana kaiwa zaune. Cikin kwantar da murya tace, “To inna idanma kin mani bankaɗa ai kin isane tunda kece kika haiheni. Ni dai kin sanni ban ganin gaskiya na riheta ai. Amma dai kiyi haƙuri ni bara na haɗa miki wutar tunda ita batajin daɗi. Harma sakin danwaken yau nice zan miki Innarmu kwantar da hankalinki”.     Baki taɗan taɓe. sai dai batace komaiba. Hakan yasa Gajeje fahimtar taci nasara. Tai murmushi da tura hannu a zaninta ta ciro leda dake a lalitarta ta bujen ciki. Goro ne da alawa da biscuits guda biyu ƴan goma-goma. “Innarmu ga kayan suna”. Tai maganar tana miƙa mata.       Ɗan sakin fuskarta tayi da miƙa hannu ta amsa. “Yo kuma ƙya bani duka. Su su Rabi'u fa?”.       “Karki damu na ba Salame ta kai musu nasu suma. Wannan nakine. Nima Agali ya bani shi bayan mun hito”.       “To, to maddala. Ni bamma sami leƙawaba yau na tashi da ƴar mashashshara ne. Sai zuwa anjima zanje nai masu an raɗa suna. Miye sunan ɗiyar ne?”.        “Ai Hadiza aka samu, sunan Innar Bilkin aka saka”.      “Tofa ɗigifi. Shi yanzu duk yawan gidansu ya rasa wazai saka sai sunan uwar matarsa?”.       Ƴar dariya Gajeje tayi tana yafito Zinneerah dake tsaye rakuɓe jikin bango da hannu. “Inna kenan, ashe babu daɗi Lawal ya sakama Ummita sunanki shima”.      Shiru tai bata tankaba. Dan an ƙure tsoguminta kenan.     Zinneerah ta zauna tana gaida Gajeje. Cike da kulawa ta amsa mata da kai hannu a jikinta. Jin uban zafin ya sata ambaton, “Ya subahana. Zinni ai masassara ce a jikinki sosai. Kin karya dai ko?”.       Ƙasa Zinneerah tai da kanta tana haɗiye hawayen dake neman zubo mata. Dan harga ALLAH yunwarma tanajinta mai tsananima kuwa. Saboda Inna batai mata tayin abinciba yasa ta haƙura.      Shirunta yasa Yaya Gajeje fahimtar bataciba ɗin. Tasan za'a rina. Dan innarsu lamarinta sai du'ai. Bata sake cewa komaiba kamar yanda itama Innar bata tanka musu ba. ta dai miƙe zuwa gindin murhun inda tukunya ke aje saman duwatsun murhun. Tuwone a ciki na dawa da aka yanka aka ɗumama. Duk ma ya zama gutsatstsari alamar masu gidan sunci. Yaya Gajeje da ranta ke mata ƙuna ta ɗauka kwano ta zubama Zinneerah, tare da koriyar miyar kukar dake gefe. Har gabanta takai ta dire tana fadin, “Maza ci na samu mai sayo miki magani nan gidan Rahine idan bata fita tallar kayan koli ba”.       Jan kwanon Zinneerah tayi gabanta, babu musu ta hau ci dan yunwa takeji sosai..      Inna dai bata sake tankawaba har Zinneerah ta gama cin tuwon nan. Yayinda Yaya Gajeje ta koma can wajen murhu tana haɗama Inna wutar ɗanwake da ƙoƙarin saka ƙatuwar tukunyar da take amfani da shi.                  Kasancewar Yaya Gajeje a gidan yau sai ta samu ƴar salama. Dan har Baba daya shigo shima ya ɗan samu sakewar bata kulawa, harda siya mata awara.      Washe gari kam Inna bata saurareta ba. Duk da ta fahimci har yanzun bata da lafiya, dan ba'a ƙulla awa biyu Zinneerah bata raɓe gefe tana riƙe cika ba alamar dai cikin na mata ciwo.       Sai dai tsabar rashin tausayi ko'a fuska Inna bata nuna ta fahimtaba, daga ƙarshema tallar riɗi da gyaɗa ta sakata ɗauka. Da Sa'a tayi magana kuwa ta hayayyaƙo mata da masifa kamar zata daketa. Dole tai shiru tana maijin babu daɗi da halin mahaifiyar tasu. ★★★             Yau satin Zinneerah ɗaya kenan da dawowa da ga Katsina. Tun Inna na zuba idon ganin Hajji Lanti ta biyo bayan Zinneerah harta fara sarewa. Dan har ranta ta ɗauki alwashin sai Zinneerah ta koma, bazata taɓa yarda kuɗin data ƙwallafa ran samu su wuceta a banza ba.        A ɓangaren Zinneerah kam a kwanakin nan daka kalleta kasan bata da lafiya. Musamman yanda ta wani rame sosai. Gashi sam bata da kuzari a jikinta. Yanda ta saba aiki ada da kazar-kazar yanzu sam bata iya hakan. Komai zakaga tana yinsane da sanyin jiki kamar mara ƙashi. Inna tayi masifar harta gaji ta barta, sai dai zagi da tsina ne tana shansa, dan ranar har marinta tayi.        Yau ma kamar kullum tana gama ɗibar ruwa da dukkan aikinta na gidan tai shirin ɗaukar tallar riɗi da gyaɗa. Tinene kaɗai ta samu a tsakar gida tana suyar wainar fulawa. Inna kuwa ta fice barka wai.       Ɗakin Inna ta shiga ta ɗakko ƙaton farin botikin da aka cika da gyaɗa da riɗi, ta sake fitowa tsakar gidan. Cike da sanyin murya tace, “Tinene idan Inna ta dawo ki hiɗi mata na wuce”.       Kallon banza Tinene tai mata ta ɗauke kanta. Cike da rashin mutunci tace, “Inma wannan allagiran kike mawa kima cire rai yarinya, dan aradu baki cin ko ranyo anan”.      Murmushi Zinneerah tayi kawai ta fice, dan tasan inhar ta biyema Tinene zama su iya faɗa, itako bata da wannan ƙarfin yanzu kam.          Dai-dai fitowarta ƙofar gidan nasu gabanta ya faɗi. Tai ƙasa da kanta saboda cin karo da fiska mafi daraja a zuciyarta bayan ta iyayenta. Ba kowa bane face saurayinta Babawo wanda a yanzu ya maida akalar neman auren nasa kan yayarta Karima da yaya Sa'a ke bimawa. Babawo ya sota tun bata san kantaba. Da farko matsin rayuwar data tsinci kanta a hannun Inna dalilin rashin mahaifiyarta a gidansu Babawo yake tausaya mata. Shine silar cigaba da karatunta bayan gama firamare , shine ya tsaya tsayin daka harta shiga makarantar gaba da firamare (Secondary), tana aji ɗaya wani kawunsa ya zo ya tafi da shi kaduna. Bai dawo ba sai da ya shekara. Kamar yanda ta ɗokantu da zuwansa haka shima ya ɗokantu da ganinta. Yazo mata da tarin tsaraba, tare da burin iyaye su shiga akan maganar aurensu, a cewarsa data kammala aji uku na sakandire zasuyi aure. zai wuce da ita can kaduna sai ta cigaba a gidansa har sai taga ƙarshen biro. Hakan yama Zinneerah daɗi a zuciya da ruhi, sai dai kuma a kwana biyu da zuwan Babawo labarin ya canja alƙibla. Dan kuwa bai komaba sai da tsuntsun soyayyarsa ya tashi daga kanta ya koma kan yayarta Karima yar wajen Inna ta uku. Ƙiri-ƙiri ta gaza gane kan Babawon ta, ya canja mata gaba ɗaya. Kosan ganinta bayayi. Taci kuka sosai, ta kuma shiga ruɗani, dan har ciwo tayi. Mutane sunta kace nace akan wannan al'amari, wasu na faɗin asiri Inna taima Babawo ɗin, wasu suce kuma shine dai yake ganin Karima ta fiye masa tunda ita babbar budurwace wadda akema surutu akan rashin samun miji. Dan Karima shekararta sha takwas da wasu watanni, a ƙauyen kuma sa'annin su Zinneerah sune dai-dai aure ƴan sha biyu. Amma sai dai ita ƴaƴan Inna dama sukanyi jinkirin samun miji a ƙauyen saboda mugun halinta, shiyyasa ma har yau babu wacce ta taɓa aure a nan cikin Danya. Gajeje na kauyen Sanni, Atine na can Rimaye. Sai yanzu ga Karima da Sa'a waɗanda duk sun zama manyan ƴammata. Karima nada sha takwas Sa'a na sha shida. Sai Tinene sa'ar Zinneerah itace auta.          Bayan wucewar ruɗanin canjawar Babawo da shekara ɗaya da wasu wattani, dan har manya sun shiga maganarsa da Karima sai kuma Inna ta haɗata da hajji Lanti da tai sanadin kaita birnin Katsina da niyyar aikatau, inda ita kuma ta gudo ta dawo gida........          “K! Wai baƙyaji ana miki magana”.    Tsawar da Babawo ya daka matace ta dawo da ita daga dogon tunanin da ta tafi batare data farga ba. Saurin haɗiye hawayen da suke neman zubo mata tayi tana girgiza masa kanta.          Ta ɗan risina kaɗan tana faɗin, “Kayi haƙuri Ya Babawo banji bane wlhy”.       Tsaki yaja yana taɓe baki da jifanta da wani irin mummunan kallo na tsana, wanda a da idan wani yay kuskuren yimata irin wannan kallon sai inda ƙarfinsa ya ƙare. A gadarance yace, “Kiramin Karima nace”.         Idonta ƙasa-ƙasa tana mai satar kallon yanda ya ƙara ƙyau da cikar zati tace, “Yaya Kareema bata nan, tana Rimaye wajen Yaya Atine, nima ban dawo na sameta ba”.        Tsaki yaja yay gaba batare da ya sake tanka mataba. Ta bisa da kallo cike da tsananin so da ƙaunar da take masa har yanzun. yayinda ƙamshinsa daya bar mata take jinsa mafi daraja da tsada a cikin iskar da take shaƙa. Duk da ƙarancin shekarunta zuwa yanzu tasan minene soyayya, dan shine ya rene ta akan bigirenta, tun bata fahimta harta fara ganewa da banbancewa, sai gashi rana tsaka rabuwa tazo musu bisa tafarkin MAKAUNIYAR ƘADDARAR da batasan sila ko mafarinta ba, tunda har yanzu bazata iya faɗin dalilin rabuwar tasuba balle dalilin komawar Babawonta kan yayarta.      Hannu tasa ta sharce hawayenta tana gyara riƙon botikin gyaɗa da riɗinta ta cigaba da tafiya ranta na mata zafi da ƙuna.............✍ *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_Typing📲_* *_😭MAKAUNIYAR ƘADDARA!!😭_* *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* _ZAFAFA 5 NEXT LEVEL_ Page 4 ...............Ƙarfe kusan biyu na rana Zinneerah ta dawo gidan a gajiye. Duk uban riɗi da gyadan data fita da shi kaɗanne ya rage a botikin. Tun a sallamar farko na shigowa gidan dukkanin ɗan guntun farin cikinta ya gushe. Ba komai ya kawo hakanba kuwa sai cin karo da Yaya Kareema datai, wadda ta dawo daga Rimaye wajen yayarsu ta biyu dake bima yaya Gajeje dan ita acan take aure.         Zaune suke a ƙarƙashin bishiyar tsakar gidan nasu sun baje kaya ita da Sa'a da Tinene. Inna na daga bakin murhu tana talgen tuwon dare. Dariyarsu suke sha cike da nishaɗi dajin daɗi.      Sa'a ce kawai ta amsa sallamar Zinneerah tare da mata sannu. Ta amsa a ɗarare tana duban Karima data haɗe girar sama data ƙasa. “Yaya Karima ashe kin dawo, sannu da zuwa, yaya kika baro su Yaya Atinen?”.         “To uwar iya, halan kin aikenine da kike lissaho mani wannan tambayoyin? Kai wagga ɗiya hi'ilinki yayi yawa wallahi, k.......”         “Haba Yaya Karima, minene laihinta anan kuma? Danta maki barka da dawowa da tambayar su Yaya Atine?”. Sa'a ta faɗa cikin katse ƴar uwar tata rai ɓace.      A fusace itama karimar ta katseta da fadin, “To kema waya saki a ciki, ALLAH ina ci maki uwa yanzun nan Sa'a. Ita ɗin uwarki ce ko mi?”.        “Ba uwata bace, amma ƴar uwatace kamar yanda take ƴar uwarku kema. Daga hiɗin gaskiya sai laihi. Ni banga abinda Zinni ta tarema wani a gidan nanba da kuke tsangwama mata, itama fa ɗiyace kamar yanda muke ɗiyan gidan. Duk da baba baya magana akan abinda ake mata na tabbatar yanajin ciwo a rans........”           Timmm!! Kake jin saukar dundu a bayan Sa'a. Ta gyantsare saboda azabar zafi tana sosawa. Inna dake tsaye a kanta tana huci tace, “Kaɗanma nai miki dan ubanki. Wa kike hiɗima waɗanan maganar banzar to? Sheɗaniya munahika. Anya kuwa nice uwarki Sa'a? Kodai kema Hauwar ce ta haiheki taimin mucanje ban saniba?”.          Baki cike da iska Sa'a tace, “Amma inna dan na hiɗi gaskiya sai kimin wannan uban ƙullin a baya?”.        “Kaɗanma nai miki shegiya ƴal bura'uba bai baki kamar na reza, hita kibar gidan nan kona sauya miki wannan shegiyar huskar da maruka”.       Fita Sa'a tai tana ƙunƙuni da cigaba da shafa bayanta inda yasha dundun.      Sum-sum Zinneerah ta wuce ɗakin Inna zata kai botikin tallar tata Karima ta daka mata tsawa. “Munahika dawo a lissahwa sannan”.        Dawowa Zinneerah tayi jikinta na rawa ta  mikama Karima kuɗin da botikin. Fisgar botikin Tinene tayi, Karima kuma kuɗin ta ƙwata tana buge mata hannu.       “Innarmu na nawa kika aza mata?”.     Karima ta faɗa tana fara irga kuɗin.            Daga inda Inna take ta bata amsa da, “Na jikka sha huɗu ne cir gaba daya, dan na rantse da ALLAH kona hicika ya ɓata ina miki ɓatanci da shegen bugu a gidan nan. Kuma sai ubanki ya biyani kuɗina babu ɗagin ƙahwa”.      Zinneerah dai batace komaiba. Sai su Tinene ne suka kwashe da dariya. Karima ta gama irga kuɗin tana jijjigasu da faɗin, “ALLAH ya sota Inna sun cika. Kuɗin anan jikka goma sha ɗaya da murtala uku, sai kayan daya rage na jikka uku ba murtala uku”.       “Ta taimaki kanta. Ga tuwo can kije ki ci idan kina so, dan nasan dai abokan iskancinki sun gama cika maki ciki da shinkahwar tasha”.       “To” kawai Zinneerah ta ce ta nufi hanyar ɗakinsu. Dan wani irin jiri takeji yana neman kwasarta. Tana shiga ɗakinsu ta zube a katifar su Tinene tana sauke numfashi. A hankali barci ya fara rinjayar idanunta mai daɗi.        “Baƙo na sallama da Zinneerah a waje”.      Ta tsinkayo muryar yaro sama-sama da ga tsakar gida. Tsawar da inna ta dakama yaron ce ta sakata buɗe idanunta gaba ɗaya babu shiri. Sai kuma ta jiyo Sa'a na faɗin,          “Inna bafa wani bane ba, malam badamasi ne malaminsu”.      Tsaki Inna taja batare data tankaba. Yayinda Sa'a ta ɗaga labulen ɗakin tana kiran sunanta. “Zinni ki tashi ga Malam Bade yazo nemanki”.       Yinƙurawa tai ta tashi zaune tana gyara hijjab ɗin jikinta. Cikin sanyinta dana barcin data fara tace, “To Yaya Sa'a”. Daga haka ta miƙe ta fiti cike da dauriya.             Matashin saurayine, dan gaba ɗaya shekarun nasa bazasu wuce talatin da ɗoriya ba. Zinneerah data fito a ɗarare saboda tsoron Inna ta rissina tana murmushi. “Sannu da zuwa malam. Ina yini?”.      Shima tashi fuskar faɗaɗe da murmushi ya amsa yana kallonta. “Zinneerah Sulaiman ashe kin dawo gida babu labari? Sai ɗazu ina bisa mashin na hangeki da botikin gyaɗa da riɗi a bakin yara”.       Har yanzu tana a duƙe kai a ƙasa tana murmushi, cikin ƴar muryarta tace, “Na dawo Malam, dama naje wajen mamana ne gaisheta”.        Yanzu kam da mamaki yake dubanta. Cikin kasa haɗiye abinda ke a ransa yace, “Amma a gari aketa hiɗin guduwa kikai bama asan ina kika nuhwaba? Kai mutane sai dai a barsu da halinsu. ALLAH ya ƙyauta to, kin baro maman naki lahiya ko?”.        “Lahiya lau suke Malam”. “To Alhmdllh, Yanzu ni bama wannan ba, nazone dama akan jarabawarku ta jsce. Ina hwata dai baki manta nanda kwanaki takwas zaku hwara ba ko?”.       Karan farko ta ɗago taɗan kallesa ta sake maida kanta ƙasa. Kafin tace wani abu Inna ta banko ƙyauran langa-langar ƙofar gidan nasu ta fito.             “Uhyimm! Kaji farkar taka ta dawo kazo kenan? To billahillazi bari kaji yanzu bazan ɗauki wannan sheɗancinba. Kaji da ƙyau karna sake ganinka ƙohwar gidan nan. Idan son ganinta kake ta bika can mahaɗar taku man......”       “K dalla malama saurara, tsohuwar banza da bakinta bai hiɗin alkairi sai sheri wa ɗiyan mutane. Na rantse da ALLAH kika ƙara hiɗin wani kalmar ɓatanci garemu yau sai kin kwana ofishin ƴan sanda. Ni nazo ne akan maganar jarabawa da zasu yi ta koma makaranta....”         “Anƙi ta koma ɗin munahiki algungumi. Dama can niya nai na barta take zuwa. da ga yau da ga yanzu kuma na hwasa. Bata sake zuwa talla zataimani”.       “Ashe kuwa zaki gurfana gaban mai-gari......”        “Kaini gaban sarkin katsina ma ƙarewar mai-gari mana. Ke kuma munahika dan ubanki tashi ki shige ciki, ƴal bura'uban yarinya kulin bata iya komaiba sai janyoma mutane jidali da yaye-yaye a ƙwar gida. Zanyi maganin rawar kanki ne ai...”        Yanda ta kaima Zinneerah duka ya sata miƙewa da gudu ta shige gidan. Shima Malam Badamasi bai sake tanka mataba ya bar ƙofar gidan rai ɓace. Inna kuwa masifa ta cigaba da zazzagawa har sai da Sa'a da Karima suka fito suka shiga da ita gida.      Tana shiga ta hau dukan Zinneerah babu ji babu gani. Sai da tai mata lilis ta barta kwance tana numfashi da ƙyar. Zinneerah akwai taurin zuciyar tsiya da kafiya wani lokacin. Duk wahalar da take sha wajen Inna akan jima ba'aga kukanta ba idan ba ita taso ba. Idan kuwa kaga ta cika yawan kuka to lallai abin ya kai babba gareta sosai.       Inna na tsaka da cigaba da jarabarta aka buga sallama. Sa'a ce ta amsa tare da nufar zauren gidan nasu dan taga wanene. (Sanƙira) mai shela idan abu ya faru a garinne tsaye yana baza babbar riga. Ta rissina tana gaidashi dan dattijo ne sosai, amma Baba zai iya girmarsa.      “Tsohuwar taki na nan ko?”. “Eh baba tana nan”. “To maza sanar mata mai-gari na biɗar ganinta. inko bata zuwa cikin salama ƴan doka zasuzo su kaita da kansu. Tazo tare da ƴar uwarki zinneerah”.       Sosai gaban Sa'a ya faɗi, amma ta daure cikin girmamawa ta amsa masa tare da juyawa cikin gidan.        Inna ta dubi Sa'a cikin haushin Zinneerah da bai gama sakintaba tace, “Ke kuma minene kika shigo ma mutane haka? Halan shegen nanne bai tahi ba?”.      Kan Sa'a a ƙasa tace, “A'a Inna. Baba Lado sanƙira ne fa, wai ana kiranki gidan mai-gari ke da Zinni....”        “Ki koma ki hiɗi masa ba'a zuwa. Ba'a kamar ana zuwa ɗin...”     “Inna wlhy cayay fa idan baki zuwa ƴan sanda zasuzo su tahi da ke”.        Shiru Innar tayi ƙirjinta na bugawa. Ta tsani harkar ƴan sanda, dan tun sanda sukai faɗa da Lamunde aka adashi ta kaita kusada ofishin ƴan sanda akazo har gida aka kamata sai da tai kwana biyu a kusada hannunsu take shakkarsu. Ba ƙaramin wuya taciyo a kwana biyun datai wajensu ba. Amma a fili sai ta ƙyaɓe baki zata fara masifa kuma.......        “Shin wai Asabe saƙon mai-gari bai iso gareki bane?”.     Karaɗin Sanƙira daga ƙofar gida ya katse mata masifar datai nufin farawa. A tsorace Karima tace, “Innarmu dan ALLAH kije, tunda kinga harda ita akace kuje. Kinsanfa mai-garin nan ba mutuncine da shi ba wlhy yana iya kira maki ƴan dokar”.       Kamar zatai magana sai kuma ta fasa. Ta kai dubanta ga Zinneerah dake kwance barci ya fara ɗaukarta. Tsawa ta daka mata wadda ta sakata tashi a firgice babu shiri.       Ran Inna fal masifa ta tasa Zinneerah gaba Sanƙira na biye dasu suka tafi gidan mai-gari. Acan suka iske malam badamasi. Tun daga nesa Inna ta dinga antaya masa uwar harara kai kace idonta zasu zubo ƙasa ne. Shiko baima san tanaiba. Dan hankalinsa dana mai-garin da fadawa duk yana kan Zinneerah ne dake ɗingishi.        “Ranka ya daɗe ka ga abinda nake hidi maka ko! Da alama bayan barowata gidan bugunta tai”.       Ran mai-gari a ɓace ya wurgawa Inna mugun kallo. “Ke dai Asabe baki gamawa da duniya lahiya inhar baki canja halinki. Ace mutum shi dai baisan komaiba sai mugunta, ke shikenan zicciyarki tamkar ta kahiran hwarkon ƙarni! Kai ALLAH ya wadaran halinki wlhy Asabe. shi dai malam Sule bai sa'ar mace irinki ba. Ya auri ta arziƙin kin koreta a gidan kina kuma gallazama abunda ta haihwa. Wlhy ina mai tabbatar maki wata rana sai kinyi nadama, dan wanga ɗiya sai ta zame miki ɗan hakkin faka raina, RAINA KAMA kuma mara mutuncin mata”.         Kan Inna a ƙasa tanata faman kumurya da kumatu babu damar magana, sai da mai-gari ya ƙare mata zagi tas da gorin asalinta kafin ya ɗora da gargaɗi.       “To naji kince baki sake barin yarinyar nan taje makaranta. Kece kika sata ne?”.      Kan Inna a ƙasa har yanzu tace, “ALLAH shi sawwaƙa ranka ya daɗe. Niko miya ja mani kai ɗiyana boko. Ubana bai saniba bani kai ɗiyana su tabaɗe. Can abokan cin mushenta ne suka kaita......”         “E, ai shi abokin cin mushen nata da kike magana shine kika asirce ya koma kan ɗiyanki, kinga ashe kema abikiyar cin mushen tashi ce ko?”.      Malam badamasi ya faɗa a harzuƙe cikin katse Inna. Babu wanda ya dakatar da shi, dan kowa yasan Babawo take nufi, tunda shine yay tsaye tsayin daka har Zinneerah ta shiga makaranta saboda tana so. Amma yaran gidansu daga firamari basa cigaba. Sa'a ce ma taɗan fara sakandire ɗin itama zango ɗaya tayi ta gudo saboda wani malami ya daketa Inna taje tai masa tijara tace Sa'ar bata sake zuwa. Daga nan kuma bata sake zuwan ba.        Mai-gari ya cigaba da faɗin, “To bara na gaya miki a gaban kowa ki riƙe a ranki yarinyarnan zata cigaba da karatunta har sai ta gama. Ni nan mai-gari zan ɗauki nauyin ɗawainiyar karatun natama daga yau, tunda ance dama yaron daya kaita ya janye dama daga yi saboda sherin da kikayo ta ƙarƙashin ƙasa. Wlhy kinji na rantse, dai-dai da rana ɗaya yarinyarnan kika hanata zuwa makaranta sai kin kwana a kusada ofishin ƴan sanda. Kowa dake nan ya shaida”.        A take duk suka amsa masa da cewar sun shaida. Banda Inna dakeji tamkar zata haɗiye zuciyarta ta mace. Zinneerah kam a ranta wani irin daɗi ne ya lulluɓeta.         Sai da mai-gari ya ƙarama Inna dogon gargaɗi sannan ya sallameta banda Zinneerah.        Bayan wucewar Inna Mai-gari ya shiga yima Zinneerah tambayoyi tana bashi amsa kanta a ƙasa. Sosai tausayinta ya sake mamayesu, suka shiga mata nasiha akan muhimmancin haƙuri da ribar da mai yinsa kanci a duniya ko a lahira. Sannan ya damƙa amanarta hannun malam Badamasi. Tare da tabbatar masa duk abinda za'a buƙata na ɓangaren makaranta na Zinneerah yazo gunsa ya amsa. Daga haka aka sallamesu bayan mai garin ya bata ƙyauta jikka biyu da rabi (500).        Godiya tai musu sosai cike da girmamawa itama, tare da addu'oin fatan alkairi sannan suka taso ita da malam badamasi daya rakota har gida yana ƙara mata nasiha.       Koda Zinneerah ta dawo gida tayi tunanin inna zata hukuntata akan abinda ya faru a gidan mai-gari. Amma sai taji shiru batace da ita ƙala ba. sai dai tana ɗaure mata fuska fiye da yanda ta saba. Sannan komai ƙanƙantar aiki ita ake kira tayi koda su Sa'a na zaune a kusa da ita. ★★''★★"★★"★★            Akwana a tashi babu wahala wajen UBANGIJI, haka rayuwa ta cigaba da shuɗawa. Yau fari gobe tsumma a gidan su Zinneerah. Ita dai batasan minene farin ciki ba ko jin daɗi a gidansu.        Tun randa sukaje gidan mai-gari da inna sai ta sake ninka gallazawar da take mata fiye da da. Makaranta dai ta barta tana cigaba da zuwa. Amma kafin ta wuce ƙa'ida saita kammala ayyukanta. Idan kuma ta dawo ta iske wasu na jiranta him. Ga tallar riɗi da gyaɗa babu fashi gareta. Tsangwama wajen Karima da Tinene sai abinda yay gaba. Idan kaga taji daɗi sai wajen Sa'a da Yaya Gajeje idan tazo gidan. Shi dama Baba ba'a sakashi a lissafi. Dan tamkar bashi da wanima amfani a gidan. Idanma baiso ba sai ya yini a gona tun safe sai yamma zai dawo. Duk abinda Inna zatai a gidan ƙala bai iya cewa saboda tsoron da yake mata.        A haka su Zinneerah suka fara jarabawar junior waec ɗinsu. Zinneerah ba wani ƙoƙari ne da ita sosai ba. Sai dai tanada naci akan abu sosai. Duk abinda takeso takan dage a kansa domin ganin ta cimma nasara. Hakan yasa sam bata da wasa, musamman ma daya kasance itaɗin miskilace ta gaske. Ga halin gidansu ya sake maidata shiru-shiru da rashin son sakewa da mutane.      Zuwa yanzu ta daina jin ciwon cikin nan da kasala. Sai wani irin ƙiba take mai ban mamaki da haske. Ɗan matashin ƙirjinta na ƙara fitowa fili sosai fiye da da.       Kowa ya ganta sai ya tanka canjawar tata na ƙanƙanin lokaci, dan abun na bama mutane mamaki sosai. Musamman da aka san bawani daɗi takeji a gidan nasu ba. Ita kanta Innar bata gajiya da kallon Zinneerah ɗin a ƴan kwanakin nan. Sai dai tanayi tana jan tsaki da ƙyaɓe fuska.             A yau ma data kasance juma'a bayan tasowarta makaranta gida tayo. dan jarabawa ɗaya kacal sukayi, wadda daga ita sai ta ƙarshe da zasu zana. Cike ta iske gidan nasu da ƴan kawo lefen yaya Karima, wanda aka kawo da ga gidan su Babawonta. akwatina uku zuƙa-zuƙa ƴan yayine. Itace kuma budurwar farko da akaima akwati uku a garin, dan ɗaya sukeyi kacal su haɗa rio irin na saka kayan yara ɗin nan babba. Wasuma basayin Rio ɗin. Amma sai ga Babawo shi yayi har uku, ga kaya fal.            Sosai hankalin Zinneerah ya tashi, dan zuwa yanzu dai ta tabbatar Babawo kam ya barta har abada. Sum-sum ta lallaɓa ta shige ɗakinsu tunda babu wanda ya ganta hankalinsu nakan ganin kayan. Hijjab kawai ta cire ta zauna tana haɗiyar zuciya da ƙoƙarin ganin hawayenta basu zuba ba. Tsawon lokaci tana zaune hayaniyar mata da yara na daɗa ƙaruwa harda guɗe-guɗe. Ganin abin nasu bana ƙare bane ta zame ta kwanta hawayen da taketa ƙoƙarin dannewa suka shiga silalowa a kumatunta. Daga haka ta lula duniyar tunani mai zurfi har barci yay gaba da ita bata farga ba.        Timmmm!!! Kakejin ƙarar saukar dundu. A firgice Zinneerah ta farka tana sosa gadon bayanta inda Karima ta daketa.        “Munahika ƴar buƙulu. Ashe nan kikazo kika ɓuya kina baƙin ciki da abun hwarin cikin daya sameni ko? To bara ki ji sai dai ki mutu wlhy. Ni Karima kamar na zama matar Babawo na gama. Dan nan da sati biyu za'a ɗaura mana aure ma”. Ta ƙare maganar da ƙyalƙyalewa da dariyar rashin mutunci.      Ita dai Zinneerah ko ɗaga kai ta kalleta batayiba. Ta kuma ƙi yarda tai kuka. Dan dama wani lokacin haka take da shegen taurin zuciya. Musamman akan abinda ta tabbatar da natane akai mata fin ƙarfi. Haka Karima ta cigaba da mata tujara har sai da Yaya Gajeje da bata tafi ba ta shigo tana zaginta sannan tabar Zinneerah.              Karan farko da baba ya nuna tsananin ɓacin ransa akan abinda akema Zinneerah har takaisa da yima Karima faɗa. Dan duk abinda tayi ya farune a kunnensa kasancewar ya shigo gidan.       Babu wanda ya iya magana har Inna. Dan ita kanta yau sai taji wani shakkar Baban a cikin ranta. Dama ance mai haƙuri bai iya faɗa ba.       Ɗan Murmushi Zinneerah dake a ɗaki zaune har yanzu tayi. A ranta kuwa tana mai tsananin jin tausayin mahaifin nasu da ta tabbatar anfi ƙarfinsa ne dama game da al'amarin gidan nasa, bawai dan Inna ta gagaresa bane ba. ★★★          Tun daga wannan rana su Inna suka hau shirin biki. Dama can a shirye suke tsaf dan sun daɗe suna jiran wannan ranar dan dai kawai Babawon nata musu yawo da hankaline kamar ma zai suɓuce. Sai kuma gashi cikin lokaci ƙanƙani hankalin nasa ya sake dawowa ga Karimar a bazata.............✍                      *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_Typing📲_* *_😭MAKAUNIYAR ƘADDARA!!😭_* *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_HAPPY HAUSA DAY!!🎈🎉🎊🪄_* _Inama ɗaukacin al'ummar HAUSAWA na duniya baki ɗaya murnar zagayowar wannan rana ta HAUSA ta duniya. Alkairin ALLAH yakai gareku a duk inda kuke, ALLAH ya ƙara ɗaga darajar HAUSA da ɗaukacin HAUSAWA baki ɗaya. Harma da sauran yarukanmu🥰🥰_🤗 *Page 5* ..........Lallai da gaske shirin biki ake na ƴar gata. Dan bama Inna kawai ba hatta da Atine dake aure Rimaye ta shiryama bikin. Ko kayan ɗakin Karima daga can akayosu. Ita dai Yaya Gajeje bata biye musu. Sai ma nuna musu illar ƙulla wannan aure takeyi. Dan ta tabbatar an cuci Zinneerah. Tun abin bai kai hakaba take ma Inna magana amma bata saurarenta. Sai ɓacin rai dake biyo baya a tsakaninsu akan hakan. Zuwa yanzu kuma data tabbatar sunyi nisa saita zuba musu ido. Dan akwai ranar ƙin dillanci ai. Kuma nasihar baba ta shigeta. Dan shima da kansa yace ta barsu karta sake cewa komai akan auren. Inhar an cutama Zinneerah ne akan hakan ALLAH na nan baya barci.          Tun ra da aka kawo lefe lafiya taima Zinneerah ƙaranci, a haka ta daure take komai na rayuwarta data saba. Harma ta ida zana jarabawarta ɗaya data rage ranar litinin. Sun kammala junior secondary school kenan suna jiran result kuma ya fito aga abinda ALLAH zaiyi.          Biki kam dai shiryashi ake sosai kamar yaune aka fara aurar da ƴa a gidan. Ita dai Zinneerah nata ido ne kawai, sai idan ta keɓe ne takan sha kukan zuci. A randa aka saka Karima a lalle jikinta yay tsanani, har takaita da kaiwa kwance dole.       Cike da damuwa Yaya Gajeje ta takura mata taci alala da suka girka a gidan saboda baƙi da sukazo daga marabar musawa dangin Inna. Da ƙyar Zinneerah ta iya cinye guda ɗaya sai amai. Kowa ya tausaya mata anata mata sannu. Harma wata ƙanwar Inna na cewa shawara ce a nemamata sassaƙe tasha. Itadai bata iya magana sai amsawa da kai harta samu ta koma ɗaki ta kwanta.      Cikin tsoffin da sukazo daga maraba ne ɗaya ta dubi Yaya Atine dake gefenta tana shayar da ƴarta da take goyo. “Niko nace Atine”.       “Na'am Gwaggo ladi”. Yaya Atine ta amsa tana kallonta tana maido hankalinta gareta. Wadda aka kira da Gwaggo Ladi tace, “Wanan ƴar uwar taku tayi aure ne dama bamu da labari?”.       Da mamaki a fuskar Yaya Atine tace, “Gwaggo wai kina nufin Zinneerah? Indai itace batai aureba. Yaya zatai aure baku jiba”.      Cikin waro idanu na alamar gulma tace, “Kanjakar ubancan kayyasa. To lallai idon Asabe a rufe yake a gidan nan bata bahimtar komai daɗa”.       “Gwaggo miyasa kika hiɗi haka”. Yaya Atine ta sake faɗa tana duban Gwaggon nasu da ƙyau.      “Uhm-uhm babu komai Atine. Kawai dai naga abinda yafi ƙarhin ganina ne. Dan wannan ɗiyar ciki ke ga jikinta, harma ya tasa gashi nan”.       A razane Atine ta saki ƴarta ƙasa da dukan ƙirjinta tace, “Gwaggo ciki?!! Zinni ɗince ke da ciki!!?”.      Yanda tai maganarne ya jawo hankalin sauran mutanen dake a gidan kansu. Ga ƴarta data saki ƙasa ta tsage da kuka saboda zafin faɗuwar da taji..             Yaya Gajeje ma a ruɗe ta saki kwanon data ɗakko zata saka a sayoma Zinneerah kunu ko zata iya sha. Ta ƙaraso gasu Atine da sassarfa tana faɗin, “Atine wannan wane irin mugun alkaba'ine kike hiɗi dan ALLAH?”.         Da sauri Atine tace, “A'a yaya Gajeje bafa ni na hiɗi ba....”      “To waya hiɗi?”. Gajeje ta katse ƴar uwar tata.          “Kunga bafa zancen hayaniya bane ba Gajeje. Ku kira yarinyar tazo nan”. Gwaggo Ladi duk ta katsesu.        Zinneerah na ɗaki kwance tana sauke numfashin wahalar amai da tayi wata cikin ƴan bikin ta shigo ɗakin tana ƙwala mata kira. Miƙewa tai daga kwancen da take a razane tana dubanta batare data amsaba.     Matar tace, “Kinga taso ana kiranki a waje”.          Batare da tunanin komaiba Zinneerah ta miƙe ta biyo bayanta cike da dauriya. Tana fitowa gabanta ya faɗi ganin kowa na gidan ya zubo mata idanu, har waɗanda ke a cikin ɗakin Inna duk sun fito tsaye cirko-cirko. Rasa ina zata dosa tayi dan ruɗiya. Sai da yaya Gajeje tai ƙarfin halin kiran sunanta cike da tashin hankali. Dan ita kanta kam zuciyarta ta fara gaskata zancan tsohuwar saboda wani irin canjawar da Zinneerah tayi, wanda ada sam hankalinta bai taɓa bata abu makamancin ciki ba akan canjin....      Ƙarasowar Zinneerah inda suke ne ya katse tunaninta. Tsohuwa Gwaggo Ladi ta kamo hannun Zinneerah ta buɗe tafin tana kallo, ta kuma ɗago fuskarta ta gwale mata idanu nanma. Sai kuma tace ta buɗe bakinta ta turo harshenta waje. Ita dai Zinneerah babu musu komai yi take cike da tunanin ko wani ciwone ya kamata. dan a watani uku ɗin nan data dawo gida ƙwarai da gaske tanajin canji sosai a jikinta wanda batasan kansa ba.....        “Wlhy wannan yarinyar ciki ne da ita Asabe. idanma baku yarda ba ku kaita ayi gwaji wajen likita”.      Zancen Gwaggo Ladi ya katse tunanin Zinneerah. Yayinda a take gidan ya harmutse da salllami da gulma. Sam Zinneerah bata fahimci komai a zancen Gwaggo Ladi ɗinba, duk da yanayin mutanen dake gidan ya sake sakata a tashin hankali.      A haukace Inna tazo ta kai hannu zata kai mata maguza wata ƙanwarta ta tare tana janye Zinneerah ɗin. “Haba Asabe, ita dake cikin wannan halin zaki kaima wannan bugun? Kamata yayi a bita a sannu asan inda al'amarin ya hito ai ko?”.          “A ina ya hito banda wajen yawonta na tazubar Haule. Idan na hiɗi ya rinyarnan nabin maza sai ace sheri nake mata dan ban haiheta ba. Kwanan nan fa tahiya tai babu wanda yasan ina taje kusan mako huɗu sannan ta dawo. Amma da yake ubanta shashasha ne bai ɗauki wani mataki a kantaba. Wace irin makauniyar rayuwace wannan? Na rantse da ALLAH bata zaunamin gida da cikin rariya. Sai dai ta koma can gidan wanda ya ƙunsa mata masihwar su ƙarata tambaɗaɗɗiyar yarinya”.       Yanda Inna ke masifa kamar zata haɗiye harshentane ya saka gidan yin tsit kowa yana saurarenta. Yayinda hajijiya take juyama Zinneerah garin a hankali. Babu zato sai ganinta kawai akai ƙasa ta zube.      Babu wanda yay yunƙurin taimaka mata sai Sa'a dake kuka tun farkon fara maganar, ta taho da gudu ta durƙusa gabanta tare da ɗagota jikinta tana jijjigata. Tsawa inna ta daka mata akan ta tashi a wajen kota tsine mata.      Cikin kukan Sa'a ke girgizama Inna kanta. “Haba Innarmu! Haba Innarmu!. Wlhy Innarmu Zinni ba ƴar iska bace. Wlhy Zinni bata iskanc......”     Ta kasa ƙarasawa saboda kukan daya sarƙeta. Yaya Gajeje ce ta tako inda suke itama tana share hawaye da bakin zaninta. Ta durƙusa ta kamo kan Zinneerah dake a jikin Sa'a ta maido kan cinyarta tana fashewa da kuka maiban tausayi.....          Bayyana irin tashin hankalin da Zinneerah ta tsinci kanta a cikin wannan rana da duk wani masoyinta ma ɓata lokacine. Hatta da maƙiyan nata jimami suke nunawa a zahiri, a baɗini kam ransu fari tas musamman ma Inna da ke ganin fatanta ya tabbata.        Kamar yanda Zinneerah ta yanke jiki ta faɗi sai da aka zuba mata ruwa haka Baba ma da labarin ya riskesa tamkar saukar aradu ya zube babu numfashi sai da aka zuba masa ruwa ya farfaɗo da ƙyar.       Kafin wani dogon lokaci garin ya ɗauki zance Zinneerah tayi cikin shege. Tofa abin nema ya samu ga masu ƴancin faɗin albarkacin baki. Wasu suce mugun alkaba'in Inna ne ya kamata, wasu suce wahalar da Innar ke batace ta kaita da fara bin mazan ai. Wasu suce babu wani dama halintane. Dan kawai tana shan wahala a gidansu sai ta bi maza.      Kowa dai da inda nasa furucin ke sauka. Duk da ba yaune ainahin ɗaurin aure ba sai ga mutane na tururuwar shigowa gidan gulma da son ganin ƙwaƙwaf. Ƴammata kam harda waɗanda Karima ma bata gayyata zaman ƙunshin ba sai gasu.       Inna kam tanata zabga bala'i sai Zinneerah ta bar mata gida ƴan uwanta na tausarta. Yayinda Zinneerah ke a ɗakinsu tare da Baba da Yaya Gajeje da Sa'a. Sai wasu ƙanen Baban maza su uku da mace ɗaya sun turketa akan saita faɗa musu a ina ta samo wannan jidalin?…       Kuka Zinneerah keyi tamkar numfashinta zai rabu da gangar jikinta. A karo na babu adadi ta sake faɗin, “Wlhy! Ta-kwaran-kwatsa Kawu ban taɓa aikata iskanci ba. Wlhy ni banda ciki.”        Cikin daka mata tsawa Kawu haruna yace, “Kinci uwarki Zinni. Su waɗanda sukace kinada cikin zasu maki ƙarya kenan? Bayan duk ga alamomin mai juna biyu tattare da ke. Idanfa baki hiɗi mamu wanda kukai wannan lalatar to kuwa kina barin garinga kije can ki nema wasu iyayen bamuba. Dan bamu zama da mai halin banza cikin zuri'armu kau...”         “Ai bama barin gariba ni nan da kake gani rami zansa amani na bizneta da ranta har sai ta mutu idan bata hiɗi mamu gaskiya”.      Tirƙashi. Tunfa su kawu nabin Zinneerah da lallami akan sanin gaskiyar magana har takai Kawu Sabi'u da fara bugunta amma ta kafe akan itafa bata taɓa aikata abinda ake tuhumarta ba. Tsabar tashin hankali kowa kansa ya ɗauki zafi. Baba ma ya kasa magana sam.      Ganin suna neman halaka yarinya wata a cikin ƴan uwan Inna dake aure a kankia tace, “Kunga karkuce ta wannan hanyar zaku tuhumi yarinyarnan. Sannan har yanzu babu tabbacin cikinne a jikinta ko saɓanin haka. Kamata yayi ku sami likita yay mata gwaji, idan an tabbatar cikinne sai a bita ta hanya mai sauƙi a binciketa bawai ta kwakwazo da azabtarwaba. Dan yanzu idan cikinne ai sai kuyi mata lahani ita da shi k.......”        “K Halima bamu son tsarin banza da wohi. Kinason hiɗin ita Yaya Ladi ƙarya tayi kenan da tace akwai cikin? Bayan duk wanda ya kalla wannan sheɗaniyar yarinyar zai tabbatar da alamomin mai ciki tattare da ita...”        “Ba haka nake nihi ba yaya Asabe. Tayaya zan ƙaryata Yaya Ladi ni kuwa. Ni dai ina nuna maku muhimmancin bin komai a sannune. Yanzu wannan ruɗama yarinyar tunani da bugun nata da akeyine zaisa ta hiɗi gaskiya? A ganina idan anbi komai a sannu sai a kamo gaskiyar al'amarin da mahwarinsa basai anbi hanyar ilatata ba a dawo kuma ana dana sani”.     Inna zata sake magana Yaya Gajeje ta katseta. “Maganar Gwaggo Halima gaskiyane. Ya kamata mubi komai a sannu kawu. Dan kowa yasan halin Zinni bazata aikata wannan al'amari da ganganba inma har ya tabbata hakane. Ba muba ko jama'ar gari idan zasu hiɗi gaskiya sunsan Zinni yarinyace mai nutsuwa da haƙuri. Wlhy inaji a raina inhar da gaske ciki ne a jikin Zinni sai dai ɗayan biyu ne ya hwaru. Kodai wani la'ananne ne yay mata wayo ya ɓata mata rayuwa. Ko kuma acan inda ta baro wani yay mata hin ƙarhi ya aikata mata wannan zaluncin. Ku tunafa yarinyarnan nemarta akai aka rasa rana tsaka. sai kuma gata ta dawo babu zato. Abin mamaki kuma tamkar an rihe mana bakuna har yanzu bamu sake bi takanta muji yaya akai tabar garinga ba ta kuma dawo? Miya hwaru da ita data tahi? Ina taje? Waye silar hitar tata? Duk bamu binciketa b..........”        “Gajeje!!!”   Inna ta faɗa da wata irin mahaukaciyar tsawa tana nunata. Ta cigaba da faɗin, “Na rantse da ALLAH idan baki hita batun wannan ƴar iskar yarinyar ba daga yau sai na tsine maki a gidan nan ke da Sa'a. Har uban waye zai hiddata a gida da gari banda abokan iskancinta wanda ga sakamakon abibda takeyi ɗin nan ya bayyana kowa ya gansa”.       Dubanta Gajeje tayi zatai magana. Sai kuma mita tuna oho tai shiru kawai tai ƙasa da kanta tana sharce hawayen dake sakko mata.         Har dare gidan ya gagara komawa dai-dai. Zinneerah kam tana can ƙuryar ɗakinsu ta ɓuya tana cigaba da kukanta. amma duk da haka bata kasa jiyo yanda ake aibantata a tsakar gidanba ita da mahaifiyarta a bakunan wasu a cikin dangin Inna. Yayinda ƴammata masu zaman ƙunshin Karima suka fara raira mata waƙa cikin habaici da izgili kamar yanda Karima ta sakasu.      Babu wanda ya hanasu, dan Yaya Gajeje tabar gidan tun ɗazun. Baba kuwa yana zaune daga can bayan runbunsu shiba mai rai ba shiba gunki ba. Sam zuciyarsa da ƙwaƙwalwarsa basa aiki irin na mutane.         Duk da ƙarancin shekarunta yinin yau ya sake tabbatar mata da rayuwa ta sake kaita wani ajin jarabawar da yafi zaman gidansu ƙunci da tashin hankali. Ita dai ko Al-qur'ani aka bata zata iya rantsewa da shi akan bata taɓa aikata iskanci ba, amma sai gashi yau an wayi gari ita ake kira da suna mai ciki, cikinma cikin shege. Ta sake fashewa da kuka mai cin rai. ★★★         Zamu iya cewa a wannan dare barci ɓarawo ne kawai ya saci Zinneerah kasancewarsa gwanin iya sata. Amma badan taji sha'awar yinsaba ko buƙata.       A kiran sallar farko ta tashi, taji daɗin jin gidan shiru alamar kowa bai tashiba. Ta lallaɓa ta fito zuwa bayi. Bayan ta kammala lalurarta tai alwala ta sake shigewa ɗakinsu. Daga haka bata sake fitowa ba har sai da rana ta haska. Zuwa lokacin gidan ya cika da hayaniyar baƙi da yaransu. Kamar jiya dai kowa da zancen cikin nata ya tashi a baki, hakan yasa ta sake maƙurewa a ɗaki taƙi fitowa.     Tana zaune kanta cikin gwiwarta taji muryar Gwaggo Laritu ƙanwar su baba na kiran sunanta. Kanta ta ɗago muryarta data sha kuka a dusashe tana amsawa. Fuskar Gwaggo Laritu a haɗe tace, “Taso ki hito”.        Sosai gabanta ya faɗi, sai dai babu damar musu dole ta miƙe tana rangajin yunwa da damuwa. Kamar jira ake ta fito tsakar gidan yay tsit idanu caahh a kanta. Tai ƙasa da kai zuciyarta na tsitstsinkewa dan tashin hankali...       “Munahika, ƴar iskar yarinya. Ƙyahwa ta duƙar da kai kamar balamar tunkiya tunda kin kwaso mamu abin kunya”.     Inna ta faɗa tana jan tsaki. Ita dai Zinneerah kanta a duƙe bata yarda ta kalli kowaba. Ta kuma kasa ɗaga ƙafarta dan batasan ina zata dosaba.         Sa'a ce ta taso daga inda take zaune tazo ta kama hannunta, itama muryar tata a dasashe alamar tasha kuka tace, “Muje Zinni, su baba na jiranki a zaure”.      Da ƙyar ta iya ɗaga ƙafafunta tabi Sa'a har zauren. Baba na zaune shi da su Kawu Haruna. Ƙasa ta zube cikin rawar murya tana gaishesu. Babu wanda ya karɓa mata, sai Gwaggo Laritu ce tace, “Ya kamata mutahi kar rana tai tsaka tunda ta hito”.      Nanma babu wanda ya iya cewa komai, sai miƙewa da su kawun sukai amma banda Baba da kansa ke ƙasa. tunda Zinneerah ta fito ko motsi baimayiba. Koda sukai masa sallama zasu tafinma bai motsa ba. Bai kuma ce uffanba har suka tasa Zinneerah gaba suka fice.       Mashina biyu dake jiransu suka taras a ƙofar gida. Kawu Sabi'u da Kawu Haruna suka hau ɗaya. Ita kuma da Gwaggo Laritu suka hau ɗaya batare da tasan ina suka nufa ba.          Ƙasa zinneerah tai da kanta har suka baro cikin garin Danya. Wanda tasan tunda kasancewar safiyane kowa yaga tahowar tasu, waɗandama basu ganiba zasu samu labari ga waɗanda suka gani ɗin.                 Har cikin Kusada masu mashinan nan suka kaisu babban asibitin Kusada. Kasancewar ɗan mashin ɗin daya goyo su Kawu babban ɗan Kawu Sabi'u ne shine yay musu shige da ficin komai har suka sami ganin likita kusan sha ɗaya na rana. Duk da a matuƙar tsorace Zinneerah take bataƙi amsa tambayar da duk likitan yay mata ba. Bayan ya gama mata tambayoyin yasa aka kira masa wata matashiyar budurwa. Zinneerah ya nuna mata yana faɗin, “Maryam kuje da ita tai hitsari akaima Bashir”.       Budurwa daya kira da Maryam ta amsa da to a girmame tana duban Zinneerah. Tashi Zinneerah tayi ta bita zuciyarta na ƙara shiga damuwa da firgici. Bayan ta kaita wani banɗaki tayi fitsari a wata roba suka fito. Zinneerah wajensu Gwaggo Laritu ta dawo. ita kuma Maryam ta tafi cika umarnin likita.      Sunyi zaman kusan mintuna arba'in Maryam tazo ta wucesu zuwa ofishin likita. Dansu tuni sun dawo waje sunba sauran marasa lafiyar damar shiga suma.. Kusan mintuna goma Maryam tazo tai kiransu.      Kamar ɗazu daga ita sai Gwaggo Laritu suka shiga. bayan sun zauna likita ya dubesu da murmushi yana faɗin, “Masha ALLAH mamana ga sakamakon gwajin hitsarin da mukai mata ya hito. Duk da dama dai kafinma hakan na fahimci ciwon na ƙanwata abin so ne. Amma duk da haka dai nafi yarda da'a gwada ɗin......”        Cikin ƙosawa Gwaggo Laritu tace, “To madallah, mike damunta?”.        Sake faɗaɗa murmushi likita yay yana duban Zinneerah da kanta ke a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta. “A'a Inna ba wani abu baneba face ƙaruwa muka samu. Tanada ciki na kusan watanni huɗu. Kuma Alhmdllh yana cikin ƙoshin lafiya kamar yanda itama alamomi suka nuna tana cikin ƙoshin lafiya, sai dai kuma ya kamata a ringa kula da abincin da zataci saboda shima yaron cikin nata ya samu nagartaccen raino.......”      Sam Gwaggo Laritu da Zinneerah ba fahimtar bayanin likitan sukeba tunda ya ambaci ciki. Dan Zinneerah ma wani irin hajijiya take gani. Tun ofishin na juya mata har ta koma ganin duhu a cikin idanunta. Sai kawai ganinta sukai a ƙasa daga ita har kujerar robar da take zaune a kai.        “Ya subahana”. Doctor ya faɗa yana zabura saboda faɗuwar Zinneerah. Hakan kuma yay dai-dai da dawowar Gwaggo Laritu datai suman wucin gadi itama hayyacinta. Yayinda su Kawu Rabilu suka shigo da gudu saboda jin sallalamin da likita da budurwar nan Maryam keyi akan Zinneerah da alamomi suka tabbatar da suma tayi............✍ “Hummmm!!!! Turƙashi, masu karatu wannanfa shi ake kira da ANA DARA GA DARE YAYI. shin yaya akai hakane? Yaya kuma za'ai? Mi kuma zai faru?. Gadai likita ya tabbatar da ciki a jikin Zinneerah baiwar ALLAH. yayinda Zinneerah ta tabbatar mana kuma bata taɓa iskanci da kowa ba. Shin tayaya aka samu ciki idan babu mahaɗi? Shin wanene uban wannan cikin? Ta yaya aka samar dashi? Da sanin Zinneerah ko fyaɗe ne? Mi Inna ta sani akan barin Zinneerah gida? Anya kuwa babu lauje cikin naɗi masu karatu? Ina mahaifiyar Zinneerah? Yaya Baba zai kasance da tabbatuwar wannan cikin dake jikin ƴarsa dake a matsanancin rayuwa a gidansa? Yaya jama'ar garin Danya zasu cigaba da ɗaukar Zinneerah yanzu? Yaya rayuwar Zinneerah zata cigaba da kasancewa a gidansu da garinsu?. Wannan amsoshin duk suna ƙumshe a cikin littafin MAKAUNIYAR ƘADDARA da zai zo muku akan naira 300 kacal insha ALLAH. Dan girman ALLAH ina roƙonki ƴar uwata. Kibi ta hanyar data dace domin mallakar naki cikin kwanciyar hankali. Idan kin zama mai shigewa gaba wajen girmama sana'armu kema sai ALLAH ya ɗaga darajar taki komai kanƙantarta. Idan kin zama jagora ko mai burin ruguzamu UBANGIJI ya fimu sanin ke wacece.. Fatanmu kowa ALLAH yay riƙo da hannunsa akan neman halak ɗinsa. Dan ALLAH kuzo ku saya kafin ku karanta. Dan ALLAH idan kin saya karki zama ɗaya daga cikin masu fitar mana dan kawai ganin mun koma baya ko kuntata mana. Ku tuna da tarin alkairinmu na baya gareku, koda bazaku rama manaba karku cutar damu dan girman ALLAH mun roƙeku dan shine kaɗai zamu iya haɗaku da shi🤓🙏🏻. ALLAH kai mana jagora. Yanda zamu fara lafiya ALLAH ya bamu ikon gamawa lafiya. Masoyanmu da basu gajiyawa wajen sayen hajarmu da mun fitar muna sake godiya a gareku, ALLAH yabar zuminci. Masoyanmu da basu taɓa sayaba kuma ku garzayo dan bana Zafafa shiri sukai na musamman domin farin cikinku. Masu jira a fiddo ku karanta kuma dan ALLAH kuzo ku biya ku mallaki naku a wannan karon kuma sai ALLAH ya kawo muku Customers akan naku kasuwancin. Mun gode. Mun gode irin trillions ɗin nan😘😍😘😍🤗😊😉. *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* *Page 6* _________________________ Duk wacce batayi anfani da sabulunnan ba anbarta abaya acan karshen bayama kuwa duk Mai tantama akan sabulai nagyaranjiki cewa basa Aiki toh yacire mg's domin kankat ne insha Allah babu Wanda yayi anfani dasabulunmu yace baiyi ba koyaushe mg's sai sanbarka amare da uwargidaye hardama yanmata kuhanzarta kusamu naku ba karya domin bama cika Baki kugwada kubada labari da bakunanku sabulu daya tamkar dubu wadandama basasan using cream sabulun mg's herbal whitening black soap yawadacemuku jikinku zaiyi kyau koyaushe kukasance clean cikin kamshi Kuna glowing koda bakusa turare ba🤗 Kayanmu bana bleaching bn organic ne sunagyarajiki fiye da tsammaninku zaifiddomuku da ainihin natural beauty dinkine Wanda yagwada shi zaitabbar amare kuyi kokari kumallaki mg's domin baruwanku da zuwa adirjemuku jiki zakuga yanda fatarku zata dinga walwali Ina masu pimples Tabo(spot) Sunburn dama dukwani matsalar fata kuyi kokari kunemi soap dinnan before 2weeks zaisharemuku hawaye kuzama abun kwatance Sister's masu nankarwa kuma kunemi soap dinnan Yana rage nankarwa sosai🧖🏻‍♀️duk me shakku tayi kokari tagwada mg's insha Allah bazakiso rabuwa dashi ba Akwai maisa haske Amma kayanmu nafada bana bleaching bn zaifiddomiki d ainihin halittarkine yagoge dukkan dattin jiki Akwai Kuma Wanda zaimiki maintaining skin dinki yasaki fresh fatanki tazama kalar hutu Pls bamacika Baki you HV to try it and see for yourself 100%tested nd trusted Soap price:3k Location:kaduna buh munaturawa ko Ina Amma delivery is not free Maiso kindly message 08062991549 Call 08064532391 Note:Babu inda zakusami mg's herbal whitening black soap sai a number dinnan bairiga yakai market b inyakai we will let you know buh as for now wnn numbern ne kawai🙏 Maiso yahanzarta before yaji sold out akwaisu available now insunkare you HV to wait akawo so maiso yahanzarta🙏adade anayi sai gsky🤭🤝 Mg's skincare Mg's bakery You can still order ur birthday cake, cupcake,slice cake,meat pie,shawarma,samosa nd spring rolls for ur event @mg's bakery Kindly call or chat 07046881166 07067210195 08062991549 Masu bukatar abayas,takalma da jakunkuna,ashobe,laces d atamfofi, materials nd the rest 07046881166 👏🤝 Page 6 .........Tun bayan wucewar su Zinneerah kusada Inna ta kasa zaune ta kasa tsaye. Ba komai ke mata kai kawo a rai ba sai maganar Gajeje da take cewa babu wanda ya binciki Zinneerah yaji ina taje. Idan har bata ɗauki matakiba to lallai abinda bata buƙatar ya fito da ga bakin Zinni shine zai fito, dan suna dawowa gida kowa zaiso jin ina taje ɗin? Yaya akai kuma ta dawo?.      Tsulum ta miƙe da ga zaman da tayi a bakin gado, ta rarumo yamutsatstsen gyalenta daketa tsamin dauɗa. Tana ƙoƙarin warwaresa ta yafa Magajiya ta shigo ɗakin...         “A'a, Asabe ina zuwa kuma?”. Ɗan duru-duru tayi na alamun rashin gaskiya. Sai kuma tai saurin faɗin, “Uhm Magajiya zanje nan ƙauyen kwangi ne na amso kuɓewar dana bada a daka saboda miya. Na sha'ahwa gaba ɗaya sai yanzu na tuna. Gashi Atine tace tuwo aka ɗora yanzu da za'aci da rana. Kinga kuma dole ne miyar ɗaurin aure ma na gobe a haɗa da miyar yauƙi dan taushe ɗin nan ba isa zataiba”.       Kai Magajiya ta ɗan kaɗa mata, sai kuma tace, “Amma nikau da dai kin aiki ko Tinene ko Sa'a mana. Ke da mutane keta shigowa kuma ace kinje wani waje ai babu daɗi. Sannan waɗanan masu tahiya asibitin ya kamata ki jira kiga dawowarsu ko”.      Nannauyan numfashi Inna ta sauke tana ƙyaɓe fuska. Tace, “Kinga Magajiya hita batun waccan watsatstsiyar yarinyar. Dan babu mai ɓata mani taro aradu. Maganar amso kuɓewa kuwa gara naje da kaina. Dan daga Tinene har Sa'a mashiririta ne da kike ganinsu”.        Magajiya tace, “To ni haɗani da Tinenen muje. Ai in dani dai batacewa bata zuwa ko?”.             Sosai wani irin tuƙuƙin baƙin ciki ya turniƙe zuciyar Inna. Ji take kamar ta kaima Magajiya duka. Da ƙyar ta shanye abinda ya tokare maƙoshinta ta ƙaƙaro murmushi dan tasan nacin Magajiya batun yanzu ba. Tace, “To nahi yarda da wagga shawarar kau. Bara naga giccin Tinenen saina hiɗi maki ku tahi”.       Da to Magajiya ta amsa, tare da ɗaukar buhun da garin masara ke ciki wanda dama shita shigo ɗauka ta fita. Da wata muguwar harara Inna ta raka bayanta tana jan tsaki. Ta sauke gyalen nata tana ƙudundunesa ta cusa cikin lalitar bujenta na ciki. Ganin ya kwanta babu mai ganewa ta fito a ranta tana ayyana. (Ai idan kinsan wata bakisan wataba magajiya).      Shigewa tai cikin masu hidimar aikin abinci ta cigaba da harkokinta. Sai da taga kowa hankalinsa baya kanta tai wuff zuwa bayinsu tabi ta cikin dannin geza da akai musu sakamakon zubewar katangar bayin lokacin damuna daya wuce. Har yanzu kuma ALLAH baiba baba damar gyarawa ba.        Saurin zaro gyalenta tai ta warware ta aza bisa kai. Cike da sauri da sassarfa ta dinga ratsawa ta cikin gonaki dan kar wani ya ganta........ ★★★★                      A asbiti kam bayan tabbatar da Zinneerah ba suma tayi ba ruɗanin maganar likitace kawai ta haifar mata da hajijiya sai suka saka mata ƙarin ruwa. Hankalin su Gwaggo Laritu bai kwanta ba sai da likita yay musu bayani.      “Ku kwantar da hankalinku tana cikin ƙoshin lafiya. Kuma Alhmdllhi bama suma tayiba. Yanayin da take cikine ya kawo hakan, da alama kuma ko karin kumallo bataibama kuka fito”.       A kusan tare suka sauke ajiyar zuciya. Rabilu yaron Kawu Haruna daya kawosu yay saurin faɗin, “Likita to ko za'a samo mata wani abune taci?”.          “Eh za'a iya. Amma a yanzu dai mun saka mata ƙarin ruwa ta samu barci. a cikinsa kuma akwai abinda zai taimaka mata akan yunwar, da alama dai kai ne mai-gidan nata ko?”.       Murmushi kawai Rabilu yayi batare da ya amsawa likitan maganarsa ba. Sai dai Cikin ƙarfin hali duk sukai masa godiya. Amma a ƙasan ransu su kaɗai sukasan irin tashin hankalin da suke ciki game da wannan ciki na jikin Zinneerah. Suna tsananin tausayin yarinyar saboda halin data tsinci kanta a ciki a gidansu na rashin mahaifiya. Ga yayansu shi da babu duk ɗaya a gidansa saboda makircin matarsa Asabe. Sunyi iya ƙoƙarinsu dan ganin sun maidosa hayyacinsa tun tuni amma Asabe ta sake shiga ta fita ta raba tsakaninsu da shi. A yanzu haka ko mu'amula bayayi da kowa a cikinsu, ko maganar auren Karima bai sakasuba sai ji sukai a gari. Abin bai ɓata musu rai ba sosai saboda sunsan baya a cikin hayyacinsa ne sam. Yanzu haka maganar cikin nan Sa'a ce taje ta sanarma Gwaggo Laritu tana kuka, kuma da'ace ba Zinneerah abin ya shafaba cikin ƴaƴan Inna ne ko takansu bazasubi ba. Lallai lokaci yayi da zasuyi wani abu game da gidan yayan nasu kam a wannan karon. Dolene kuma susan wanda ya shiga mutuncin Zinneerah kar rayuwarta ta ƙarasa shigewa cikin garari sunaji suna gani.         Kusan su dukansu haka suka dinga tanani a cikin zukatansu har ruwan da aka sakama Zinneerah ya ƙare, sai dai barci takeyi sosai. Sallar azhar su Kawu suka tafi yi massallaci. Itama Gwaggo Laritu saita fito dan neman inda zata gabatar da tata. Bayan duk sun idan da sallarne Rabilu yaje ya samo musu abinci dan su ɗanci, dan su kansu akwai waɗanda basu karya ɗinba a cikinsu.......... ★★★★            Sauri sosai Inna ta dinga zabgawa harta iso ƙauyen mahuta dake can yamma da su. Ƙauyene sosai dan gidajen garin bazasu gaza biyarba ma gaba ɗaya. A farkon shiga garin ta gamu da yara sun dawo ɗibar ruwa rafi. Tsaidasu tai ta ɗiba ruwan tasha sosai tana sauke numfashi a jajjere. Dan ba ƙaramin sauri ta zabgaba a tafiyar tata.      Daga haka ta isa gidan dake ƙarshe a jerin gidajen ƙauyen. Tun a ƙofar shiga zauren gidan ta zabga sallama. Daga ciki akai gyaran murya tare da amsawa, sannan aka bata iznin shigowa. Babu kowa a soron, sai dai akwai ƙofar dake nuna alamun ɗakine, dan akwai labule da takalma a ajiye, sai wata a gefe ta shiga ainahin gidan kuma.       “Gahwaranku dai”. Inna ta sake faɗa tana matsawa ga ƙofar ɗakin. Daga ciki muryar namiji dattijo ta sake amsa mata da “ALLAH yay mana aikin gahwara shigo”.        Labulen ta ɗaga ta shiga ɗakin dake cike da shirgin da zama lissafasu ma ɓata lokacine, sai Dattijon dake zaune yana rubutu a allo da tawwada da alƙalami. Kallonta yay cike da fara'a kamar yanda itama take faman washe haƙwara.       “A'a Asabe ce a garin yau?”. “Wlhy nice malam kallamu. Kasan gobe ne ɗaurin auren ƴar wajen tawa, gashi kuma banzo na amshi abinda ka ce ba tun kwanaki idan auren yazo. Bayan nan kuma ga watama matsalar datake neman sake taso mani kuma”.       “Tofa babbar magana. Ai dama inata tsumayen zuwan naki, dan kwanaki hudu da suka shige na shigo Danya ɗin nakejin auren yarinyar wajen naki ya tashi. Harma naita mamakin banji daga garekiba”.        “Ayya, ka gahwarceni malam. Abubuwane sukaima kaina yawa a tsakanin nan wlhy. Amma zuwa nanɗin yana raina kodan a shiryamin yarinyar tunda kaima kasan dai yanda abubuwan suke ai”.      Murmushi yayi yana ajiye allon da yake rubutun da gyara zamansa. Ya jawo wani ƙwarya yana tura mata gabanta. “Kinga komai ma na haɗa. dama ko bakizoba ni zanje ɗaurin auren gobe, to niyyata dama naje miki dasu ai”.         “Kai madallah madallah malam kallamu, nagode nagode sosai da wannan karamci naka. ALLAH ya saka maka kaima da alkairinsa”.      “Amin. Yanzu minene gudar matsalar kuma?”.       Nannauyan nishi Inna ta sauke tana gyara zama. Cike da takaici da baƙin ciki tace yarinyarnan da uwarta ta bar mani ciki ya bayyana ga jikinta jiya. Tofa shine shaggun dangin uban nata sukazo sukai tsaye akan lamarin har suna iƙirarin sonjin ina taje kwanaki. Kasan kuma munyi aiki kwanaki akan rihe bakin kowa bai sake tambayarta ina taje. Itama kuma karta hwaɗi ma kowa ɗin. To wlhy yau malam kallamu suna neman ɓalloman aiki musamman ɗiyar wajena dake aure Sanni. Kasan nayi-nayi na rabata da yarinyar abun ya hwaskara”.        Kai malam kallamu yaketa girgizawa yana saurarenta. sai da taje har ƙarshen zancenta ya fara magana. “Kamar yanda na hiɗi maki tun kwanaki uwar yarinyarnan shu'umace ta gaske. Dan duk da kin hiddata a gidan nan bawai ta barki bane, sannan tana aikoma yarinyar da wasu ayyuka, shiyyasa da munyi aiki akan yarinyar baya wani nisa yake warwarewa. To amma ke kin tabbatar akwai cikin kuma?”.         Cikin wata lalatacciyar dariya Inna tace, “Ciki kau akwaishi malam kallamu, dan ƙuru-ƙuru ya bayyana kansa ga mutane”.          “Tohwa babbar magana. Amma yanzu kunsan wanene yay cikin?”.     “Inaaaa! Babu wanda ya sani, inada tabbacin acan inda nasa ƙawata ta kaita aikataune wani ya ɗura mata shi. Kasan yaran birnin nan akwai basira. Balle ƴar banzar yarinyar tanada ƙyau irin na uwarta. Yanzu haka jiran Hajji Lanti nake tazo naji miya hwaru. Amma itama bullum kakeji kamar an aiki bawa garinsu”.         “Shikenan, yanzu dai ayau ɗinnan zanyi wani aiki. Kamar dai yanda na hwahinta ke dai bakiso yarinyar ta hiɗi ta sanadinki tabar gari ko?”.        “Kwarai ko Malam Kallamu wannan shine hwatana. Dan nahi son kowa ya dinga kallonta da hita tai yawon tazubar ɗinta harta samo wannan cikin. Nihwa idan san samunane tabarma garin baki ɗaya yanda mutane zasu sake yarda komawa tai wajen farkan nata. Bazan ɓoye makaba zaman yarinyarnan a gidan na baƙantan rai, dan ji nake kamar har yanzu uwarta na tare damu, duk da na nisantata da garin tuni, to itama ɗiyar sonake na nisantata da Danya har abada, nahison na rayu gidan mijina dagani sai ɗiyana aradu”.         Kai Malam Kallamu ya jin jina yana murmushi saboda shima mugunne na haƙiƙa, shiyyasa tasu tazo ɗaya da Inna. Kuma wai a haka shiɗin malamine, harda almajirai a ƙarƙashinsa yana basu ilimi🤦🏻.       Ya sake haɗa mata abubuwa da yawa. Tare da tabbatar mata a daren yau zaiyi wani aiki akan Zinneerah. Ta ajiye masa kuɗi tana masa godiya ta taho akan sai gobe yazo ɗaurin aure zai tahoma da Karima wani haɗin neman sa'a a gidan Babawo. (Humm ALLAH ya shirya mana zukatanmu. Babu wani banza daya isa baki ƙyaƙyƙyawar rayuwa a duniya sai UBANGIJI. Domin shima idan kura na maganin zawo yayma kansa mana. Idanma asirin kikayi akan wani kikaga yacisa dama can ƙaddararsa kenan koda bakiyi komaiba tunda ALLAH yay alƙawarin shigarsa wannan halin saiya shiga ɗin. Abindama jahilai suka gaza ganewa shine. Da yawan jarabawa tsanice na kaiwa ga nasarorin rayuwa ga bawa. Dan da wahala kaga mutum yaci wahala a rayuwarsa daɗi da farin ciki basu biyo bayansaba. Bawai dole sai a duniyaba. dan UBANGIJI yay mana alƙawarin samun babban tagomashi a lahira da yafi na duniyar komai. Dan kaci wahala a rayuwarka ba dolene sai kayi arziƙiba a ƙarshe. Ba dolene saika zama mai ɗaukakaba a ƙarshe. ba dolene saika zama tauraron al'umma ba a ƙarshe. UBANGIJI zai iya sakanka makane ta hanyar da kaima bakai zatoba. Amma fa saika zama mai juriya da haƙuri wajen karɓar jarabawarka da ƙaddararka. ALLAH kai riƙo da hannayenmu a komanmu😭🙏🏻). ★★★★            Bayan farkawar Zinneerah a barci kusan ƙarfe huɗu suka baro Kusada zuwa danya. Kallo ɗaya zaka fahimci ransu a dagule yake su duka. Zinneerah kam bama a iya tantance halin tashin hankali da ruɗanin da take a ciki. Sam zuciyarta da ƙwaƙwalwar kanta basa aiki irin na kowanne mutum. Abubuwa da yawa ke zuwa mata a rai game da wannan ciki, har kashe kanta ta ayyana yi amma wani ɓangare na zuciyarta ya ƙwaɓe akan wannan ba mafita bace.       Tunda mashinansu suka shigo garin idanu caa a kansu. A take ƙananun magana suka fara tashi akan wai ankai Zinneerah kusada ne an zubar da ciki. Su dai basu san sunayi bama. Wani matsanancin tsoro ne ya shiga zuciyar Zinneerah ganin sun iso gida. da ga ita sai Gwaggo Laritu suka iya shiga gidan. Su kawu juyawa nasu gidajen sukai abinsu dan basusan yanda zasu tunkari yayansu da wannan magana ba. Gashi likita yace abar Zinneerah ta huta na kwana biyu kamar yanda jikinta ke buƙata.      Mata ne cike da gidan danƙam anata arerewa da guɗa. Dan masu kiɗan ƙwarya Inna ta kira suke wasa a gidan wai yau take nata yinin bikin. Da farko har suka shigo gidan sukama kusa kaiwa ɗakin kwanan su Zinneerah babu wanda ya kula da su. Suna gab da shigewarne Inna ta hango Zinneerah. A tsawace tace, “K! K! K! Dakata mani. Masu kiɗa ku saurara kaɗan ina zuwa”.       Kamar wadda tai busa da sarewa a kunnuwan jama'a a take gidan yay tsit, hankalin kowa ya dawo kan Zinneerah da Yaya Gajeje yasata saurin nufosu itama. Kusan a tare suka iso gaban Zinneerah ɗin, inna ta kalla Gwaggo Laritu datai kamar batajiba tana neman shigewa ɗakin su Zinneerah ɗin.          “Lallai ko ba'a faɗaba yanayin da kuka shigo mani gida kawai ya tabbatar da zancen ciki......”       Da sauri Gajeje ta katseta da faɗin, “Haba Inna wacce irin maganace haka? Wannan ai zancene na cikin gida ko”.      Harara Inna ta watsama Gajeje, ta kai hannu ta finciko hannun Zinneerah da kanta ke a ƙasa hawaye masu zafi na ziraro mata a saman kumatu. Hannu tasa ta yaye hijjab ɗin jikinta ta jefar. Ta kama rigarta zata cire Gwaggo Laritu ta riƙeta a fusace. “Wlhy! Wlhy wlhy kinji na rantse sau uku, inhar kika hiddama yarinyar nan riga yau saina nuna miki ni jinin gidan baduku ce Asabe. Wai kina tunanin ana tsoronkine ko me? Mi yarinyarnan ta tsare maki a gidan nan ne wai shin? Idan ma cikkinne da gaske a jikinta ai kece silarsa. Dan kece kika hana mata rayuwa zaman lahiya kamar yanda kika hana ubanta. Ya auro mahaifiyarta dan yaji sauƙi kika shiga kika hita sai da kikaga tabar gidan saboda son zuciyarki. Wama yasani yanzunma ko kece kika biya aka lalatama yarinya rayuwa, dan wlhy duk abinda akace kinyi Asabe nasan zaki iya mahiyinsa saboda son duniyarki”.       Tofa babbar magana. Waɗan nan zantuka na Gwaggo Laritu a take ya hargitse gidan, kafin kace mi taron biki ya zama taron faɗa da bala'i. Tun anayi a cikin gida har aka koma ƙofar gida, abu kamar wasa sai ga ƙaramar magana ta zama babba. Dan kuwa dai faɗa ya juye tsakanin dangin Baba dana Inna. Yayinda jama'ar gari suka rabu gida biyu, wasu na goyon bayan Inna wasu na goyen bayan dangin Baba da Zinneerah. Abu yay tsamari har magriba babu alamar zasu sarara, daga ƙarshe dai sai da zance ya kaisu ga gidan mai-gari daya aiko aka tattaresu zuwa can.          Sosai zancen ciki a jikin Zinneerah ya tayarma mai-gari hankali. dan har ransa yakejin ƙaunar yarinyar da tausayinta. Tun a randa sukazo shari'arnan shi kaɗai yasan abinda ke ransa game da Zinneerah. Dan ya ɗaukama kansa alƙawarin zai tsaya mata tai karatu, kuma ɗansa dake karatu yanzu haka a Katsina shi yake burin zama mijinta. Sai kuma gashi yau wannan magana maiban tashin hankali ta ɓullo rana tsaka.      A yau ma tambayar duniya anma Zinneerah akan wanene mai ciki tace ita bata taɓa aikata iskanciba, dan haka batasan ina ta samo ciki ba. Lallai wannan al'amari ya kai a kirasa MAKAUNIYAR ƘADDARA, ita da ciki ke jikinta batasan yanda samuwarsa ta wanzuba, su kuma dake tuhumarta ina zasu kama?.       Ganin dare yana neman rufawa mai-gari yace suje gida gobe idan ALLAH ya kaimu zai nemesu, dan wannan magana babbar maganace dolene sai sunje ga hakimin kusada ko a samo bakin zaren a can. Wannan magana ta tadama Inna da Zinneerah hankali matuƙa. Ita Inna tsoronta ALLAH tsoronta a gano gaskiyar da sa hannunta Zinneerah ta tafi Katsina. Saukinta ma Hajji Lanti bata dawo garinba ai tun tafiyar da tai dasu Zinneerah ɗin. To amma tasan akaje gaban hakimi ai ca za'ai sai wajen ƴan doka (Police) da ga haka kuma sai wajen alƙali. Lallai tsugunne bata ƙare ba kenan, ba burinta kenanba, babban burinta kawai Zinneerah tabar mata garin baki ɗaya dan bata ƙaunar ganinta a cikinsu kamar yanda ta tsani mahaifiyarta sanda tana tare da su.        Sanin halin inna yasa Gwaggo Laritu tafiya da Zinneerah gidanta, bayan ta saka Sa'a ta tattaro mata duk kayan Zinneerah dake a can gidansu dan dolene ta dawo zama a gidajen ɗaya daga cikinsu har ALLAH ya sauketa lafiya.           Tunda suka shigo gidan sam hankalin Zinneerah baya a jikinta. A hankali wani irin tsanar garin Danya da komai nasa ke shiga jikinta. Koda Sa'a ta kawo mata kayanta tana zaune can rakuɓe kanta cikin ƙafafu, ba kuka takeba ba kuma tunani ba. baƙon al'amarin dake shiga cikin jikinta ne kawai ke ratsata. Ta ɗago ta kalli Sa'a data dafa ta, ganin yanda Sa'a ke hawaye ya sata sakin wani murmushi maiban mamaki, batare da tace komaiba ta maida kanta yanda yake.         Hankalin Sa'a ne ya ƙara tashi, dan a duk sanda taga irin wannan murmushin a fuskar Zinneerah to takai ƙololuwa a shiga tashin hankalin rayuwa kenan. Dan duk lokacin da takurawa da matsawar Inna yaymata yawa bata kuka. Ko nuna tausayinta sukai kuma sai dai tai musu wannan murmushin bazata taɓa ta tanka ba.           Zuciyar Gwaggo Laritu a kusa take ainun da baƙin cikin halin da suke ganin Zinneerahn ta jefa kanta. Da kuma haushin Inna dana Baba da ya koma tamkar mara amfani agaresu, yanzu haka a kaf ruguntsumin nan da akeyi yaƙi cewa ƙala. Wanan takaicin da sukai mata yawane ya sata shigewa ɗaki tabar Zinneerah waje zaune batare da tace taje ta kwanta ba. Sauƙinta ma itama su kaɗaine a gidan sai matan ƴaƴanta biyu, suma kuma an katangema kowa sashensa babu mai ganin wani.        Abinka da ƙauye ahankali garin ya fara ɗaukar shiru. Har takai Zinneerah dake zaune a ƙofar ɗakin Gwaggo Laritu barci ɓarawo ya saceta har takai ga zamewa ƙasa ta kwanta akan sumintin wajen tai filo da jikkar kayanta da Sa'a ta kawo da yake ba wata babba bace, dan kayan nata basu wuce a ƙirga ba.         Barci ne sosai mai nauyi yay gaba da ita, yayinda itama acan Gwaggo Laritu datai tunanin idan Zinneerah ta gaji da zaman wajen zata shigo ɗaki ta kwanta barcin yay gaba da ita dan gajiya.          Tamkar wadda akace ta tashi Zinneerah ta miƙe zumbur, babu wani tunani ta ɗauki jikkar kayanta ta nufi hanyar ƙofar gidan nasu Gwaggo Laritu. A hankali ta zare sakatar murfin gidan ta fice kamar tana tsoron wani ya jita koya ganta. Kallon gabas da yamma kudu da arewa tayi, garin tsit babu alamar akwai wani rai mai numfashi, ga wata yayi nisa babu wani hasken kirki, ga sanyi kasancewar lokacinsane sai dai farko-farko dan baiyi ƙarfi ba. Ta sauke wani nannauyar ajiyar zuciya ta fara tafiya babu alamar tsoro ko fargabar jin garin shiru tattare da ita sam.            A cikin daren nan Zinneerah ta nausa kanta cikin daji batare da alamun akwai hankali a jikintaba, dan yanda take matsoraciya ko fitsari ya kamata da dare sai ta tada Yaya Sa'a ta rakata. Amma yau sai gata a hanyar daji cikin tsakkiyar dare babu ko gezau.............✍ Hasbinallahu wani'imal wakil. Ya rabbu ka iya mana da abinda yafi ƙarfinmu, harma da wanda mukafi ƙarfinsa.😭🙏🏻        *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 https://youtu.be/NgqdCTVKOF8 Channel name Abdul-rahmaan. He's a very young boy who's passionate about becoming one among the huffaz, he loves reciting the Holy Qur'an even at his younger age. He has memorized so many surahs within juz ammah. please help him grow his channel fisabilillah and also pray for him to be come a Hafiz in future in sha Allah. Jazakumullah khair ________________________ *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* *Page 7* ...........Tafiya take batare da tasan ina take dosaba. Gashi babu alamar gajiyawa tattare da ita, duk da mai kallo a kallo ɗaya zai iya fahimtar lallai tana tare da gajiyar, amma ita kasancewar bata cikin hayyacinta bata saniba. Babban burinta kawai tai nesa da garin Danya baki ɗayansa. Bata damu da yunwa da ƙishirwar dake damunta ba, balle ta tuna bayan ita akwai wata halitta a jikinta dake buƙata idan ita bata buƙata.             Kusan dai-dai ketowar alfijir ta iso bakin titin da batasan kona wane gari bane. Batai kuma tunanin son ta sani ɗinba ta zube a ƙofar wani shago ta kwanta cike da gushewar hankali dana tunani. Wani irin nannauyan barcine ya ƙwasheta kuwa, kafin wani dogon lokaci ta fara sauke numfashi...... ★★★★          Tsabar gajiyar da suka kwasone a yinin yau ya saka Gwaggo Laritu barci mai nauyi sosai, har takai da sai da babban ɗanta ya leƙo sashen domin tada ita da asuba. Dan da kullum itace mai tashinsu, amma sai gashi yau sun rigata su. Rashin jin motsinta kuma ya tabbatar masa da makara tayi kenan.        Tashi tai da ƙyar tana mamakin barcin da tai haka mai nauyi. ga ƙofartata buɗe alamar Zinneerah bata rufe musu ba. Kallon saman gado tayi inda ta bar mata ta kwanta dan ita dama bata iya kwanciya a gado sai ƙasa. Ganin babu kowa a gadon tai tunanin ko Zinneerah bayi ta shiga ita ta tashi ne.      Bata damuba ta fito gabatar da alwala. Saboda tunanin Zinneerah na bayin ya sata zuwa can wajen dabbobinsu tayo fitsari tazo tai alwala kar makarar tai yawa. Hankalin Gwaggo Laritu bai sake tashi ba sai da taga harta idar da salla gari yay ɗan shaaaa babu motsin Zinneerah. Ajiye carbin da take ja tayi ta fito tsakar gidan. Ganin babu alamarta ya sata nufar ƙofar bayi tai gyaran murya. Shiru. ta sakeyi, nanma shiru. Sai kawai ta danna kai. Gabanta ya faɗi ganin babu alamar anyi amfani da bayin ma. A rikice ta fito, hakan yay dai-dai da dawowar Awwal babban ɗanta daga masallaci, shi Safiyanu yana Lagos neman kuɗi.       “Mama lafiya kuwa? Mi kike nema?.”        A rikice tace, “Zinneerah wannan yaron (bata faɗar sunansa saboda ɗan fari). Ban gantaba”.       Da mamaki shima yace, “Dama anan ta kwana? Ko zuwa tai yanzu da sahe?”.         “Anan ta kwana mana. tare da ita muka taho nan saboda gidan nasu kasan akwai mutane bazai yuwu zama gareta ba ai ko?”.       “Hakane Mama”. Ya faɗa yana cigaba da lalleƙa ko'ina na sashen nata. Har takaisa ga fita nasu sasssan. Har sashen ƙaninsa Safiyanu ya tambayi matar tace bataga Zinneerah ba itakam. Bama tasan anan ta kwanaba, dan sanda su Gwaggo Laritu suka dawo gidan tayi barci kasancewar tanada tsohon ciki dama.      Wani tunani ne yazoma Awwal a rai, dan idan bai mantaba dazai fita salla a buɗe yaba ƙofar zaure. Ya dawo sashen Gwaggo yana faɗin, “Lallai Mama akwai matsala. ALLAH yasa yarinyar-nan ba guduwa tai ba, dan wlhy a buɗe naga ƙofar soro yau, kuma na tabbatar bazaki kwanta baki rihe ba”.         “Hazbunallah! Wlhy na rihe wannan yaron, ni kuma takaici da damuwar da suka haɗu sukaimin yawa ya sani shigewa na barta anan zaune akan idan ta gaji da zaman zata shigo ɗaki ta kwanta. Aiko zama bai ganniba bara muga ko tana gidan nasu”.        “A'a mama yi zamanki ni bara inje”.       “Kai dai barsa naje. Ai ba fasa zancen za'aiba cikin hikina za'a dubata. Dan dama dole naje gidan saboda aiki tunda yau ne ɗaurin auren Karima ”.       Badan hakan ya masaba ya haƙura. Dan har ransa yana son Zinneerah da tausayinta matsayinsa na ɗan-uwanta.        Koda Inna taje gidan bata shigaba. Dan dama batazo danta shiga ɗinba. Tayi alƙawarin har agama wannan bikin bazata leƙa gidanba. Sunbar Inna da ƴaƴanta kamar yanda tafi buƙata. Yaro ta samu ta aika ya kira mata Sa'a anan maƙauftansu da yace sun kwana ita da su Karima.. Babu jimawa kuwa sai gata ta fito tana mutstsukar ido alamar yanzu ta tashi. Ko gaisuwarta Gwaggo Laritu bata tsaya amsawaba tace, “Sa'a shiga gidan nan naku cikin hikima ki dubamin Zinneerah ”.         “Gwaggo Zinni kuma? Ba'a gidanki ta kwanaba dama?”.       “Nidai ba surutu na tambayeki ba, jeki fara dubawa”.       Kai Sa'a ta kaɗa tana nufar cikin gidan da ƴar hayaniyar waɗanda suka tashi ta fara kaurewa. Babu wanda ta tambaya ta shiga neman Zinneerah a gidan. Sai dai babu mai ko alamarta. A rikice ta dawo ta sanarma Gwaggo Laritu. Itama sai ta sake ruɗewa...... ★★★★          A ɓangaren Zinneerah kuwa barci tasha sosai a ƙofar wannan shago har fitowar rana. Sai da mai shagon ya fitone ya tadata domin buɗewa. Tashi tai kawai ta matsa gefe batare data tanka masa ba. Shima ɗin bai tanka ba dan kallon mahaukaciya kawai yake mata duk da babu alamar datti a jikinta. Saɓanin kwanciyar yanzu kam zama tai tana kallon motsin mutane dana wucewar motoci. Babu abinda take fahimta dan ƙwalwarta ba aiki take irin na mutane ba. Ga yunwa mai tsanani na cinta. Dan haka ta ƙurama mutane dake a runfar mai-shayi dake acan tsallaken titi idanu sunasha suna kwasar hira da dariya da gaddamar siyasa. A hirar tasunema takejin sunan garin da take a yanzu mai suna Tsanyawa.        Mai shagon ne ya lura hankalinta na ga masu shan shayi, haka kawai yaji tausayinta, dan haka ya fito zuwa tsallaken ya siyo mata shayin da biredi harda indomie.        Wajenta ya dawo yana murmushi, “Baiwar ALLAH kina son kici ko?”. Ya faɗa yana kallonta. Batace komaiba tai ƙasa da kanta kawai tana wasa da yatsun hannunta. Murmushi ya sakeyi shima ya ajiye mata filet ɗin indomie ɗin da kofin shayin da aka ɗora biredi a sama. “Gashi to kici”. Kanta ta rausaya masa kawai taja filet ɗin nanma batai magana ba. Batai ko tunani wanke hannu ba balle yin sallar asuba. Tasa hannu ta hau cin abincin a nutse kamar yanda nutsuwa ta kasance jinin jikinta dama can. Citai ta ƙoshi tai gyatsa. Batare da wanke hannunba ma a yanzu ta zame ta sake kwanciya sai barci.        Sosai tausayinta ya sake cika zuciyar mai-shagon nan. Yazo ya kwashe kayan data gama cin abincin batare da yayi magana ba.        Yanzu ma barci sosai Zinneerah tasha a wajen, dan bata farkaba sai gabanin la'asar. Zama tai tana kallon mutanen garin daketa faman kaiwa da komawa, dan wajen ya sake cika fiye da ɗazu da safe. Ga titin motoci nata kai kawo suma. Mai-shagon nan ne dai ya fito salar la'asar ya ganta zaune ta tashi. Cike da tausayinta yace, “Baiwar ALLAH kin tashi ashe?”.      Bata tanka masaba yanzu ma. Tadai ɗago kai tai masa kallo guda ta maida kanta ƙasa. Yanzuma kamar ɗazun murmushi yayi, ya nufi inda masu abinci suke ya siya mata yazo ya bata. Kamar ɗazu bata tankaba bakuma ta wanke hannu ba tahau ci, tare da ɗaukar ledan ruwan ta fasa tasha ta ƙoshi tana lumshe idanu. Tamkar ɗazun sai ta sake zamewa a wajen ta kwanta sai barci.      Mai shagon ya dawo sallar la'asar ya ganta ta koma barci, mamaki ya kamashi sosai ganin barci bai mata wahala. Yama fahimci yunwarce ke tadata kenan. Barcin kuma shine salon nata lalurar.      Har lokacin tashinsa yayi kusan ƙarfe takwas na dare bata tashiba. Ya sai abinci ya ajiye mata bayan ya rufe shagon ya wuce gida.          Zinneerah bata farka ba sai kusan sha biyun dare. Yanda ta tashi tana riƙe ciki da matse fuska zai baka tabbacin yunwace. Idonta na sauka akan roba rufe da leda tai saurin jawowa kuwa. Ganin abinci jikinta har rawa yake ta hau ci. Sai da ta cinye tas tasha ruwa sannan ta miƙe tamkar an tsikareta. Jakkar kayanta ta ɗauka ta fara tafiya tamkar daren jiya dan jitai gaba ɗaya nanma ta tsanesa. Burinta kawai ta ƙara gaba tai nesa da garin na Tsanyawa.         Tafiya take cikin gushewar hankali da tunani tamkar daren jiya. Gashi abin tashin hankalin yau a kan titi ne. Sauƙinma darene babu yawan mitoci sai jefi-jefi. Haka dai ta cigaba da nausa kanta cikin kariyar UBANGIJI a wannan dare ma..... ★★★            Hankalin kowa ya tashi na rashin ganin Zinneerah ɗin, dan Gwaggo Laritu kasa haƙurin ɓoye rashin ganin nata tai sai da ta fasa. A take aka shiga nemanta lungu da saƙo na garin, sai dai ganin har wani daren ya sake rufawa kowa ya fahimci dai da gaske Zinneerah ta sake guduwa kamar yanda Inna ke faɗi cike da gadarar tabbatarwa tana dariya kuma.         Kuma duk da tashin hankalin rashin ganin Zinneerah ɗin a haka aka ɗaura auren Babawo da Karima. Aka kuma kaita gidan mijinta a wanann daren. Dan zasu fara zama anan Danya kafin su wuce Kaduna kamar yanda ya faɗa.        Washe gari an sake tashi da neman Zinneerah a ƙauyikan kusa da su har zuwa kusada ko za'aji labarin tahau mota zuwa wani waje. Babu wani labari makamancin an ganta da suka jiyo. Haka suka dawo gida cike da damuwa da tashin hankalin wannan al'amari.         Ran Inna ya ɓaci dan ba haka tasoba. Sotai ace kowa ya dinga zagi da faɗin Zinneerah guwa ta sakeyi wajen karuwancinta. Amma sai taga saɓanin hakan kowama sai tausayinta yakeyi da damuwa da halin da zata shiga bayan wanda ta tashi a ciki. Sa'a kuwa kuka taci na tashin hankali ita da Yaya Gajeje, har takai Sa'ar da kwanciya zazzaɓi mai zafi. Duk da Atine ba damuwa tai da Zinneerah ba ita kanta saita wuni sukuku da ita, dan jini ya wuce wasa ai. Wannan yasa duk bikin na Karima yaƙi armashi kamar yanda Inna taci buri. An ɗaura aurene kawai hankalin mutane ba'a kwance ba.        Kamar ko yaushe yanzunma Baba baice ƙalaba akan al'amarin, sai dai a kallo ɗaya zaka fahimci tsantsar tashin hankali da damuwar dake a tattare da shi. Yana tsananin so da ƙaunar Zinneerah, musamman daya zam soyayyar da yakewa mahaifiyarta bayan barinta gidan nasa duk sai ya tattarata akan Zinneerah bayan itama wadda yake mata. Dan wannan tsantsar soyayyar Inna ta hango tattare da shi ai ta shiga ta fita ta raba tsakaninsa da ƴar tasa har bai iya cewa uffan akan al'amarinta a gidan.       Haka wannan dare ya kasancewa duk wani masoyin Zinneerah a cikin tashin hankali da damuwa da tausayinta. Inda washe gari kuma suka sake tashi da wani sabon tashin hankali na barin baba shima garin.     Wannan tashin hankalinne ya sake ruɗasu suka sake ƙare yinin ranar da neman Zinneerah da Baba a dukkan garuruwan dake da maƙwaftaka da su. Sai dai babu koda labarin ɗayansu. Yau kam saɓanin jiya harda Inna a wannan tashin hankalin. Dan bata taɓa tunanin Baba zai iya bin bayan Zinneerah ba. Duk haukanta da rashin tausayi tana bala'i-bala'in son mijinta uban ƴaƴanta. Dan badanma soyayyar da take masanba bazata taɓa  zuwa wannan ƙauyen ta zauna ba da sunan aure. Saboda garinsu Marabar musawa yayi ashirin din Danya yawa da komai na kayan more rayuwa. ★★★         Tamkar jiya yau ɗinma sai gabannin asuba Zinneerah ta yada zango a wani ƙaramin ƙauye da ke a bakin titi. Yau kam a ƙarƙashin wata bishiya ta samu ta kwanta sai barci. A haka mutanen ƙauyen suka wayi gari suka ganta. Da farko ma su tsoronta suka farayi, dan a fuska da jikinta babu mai ɗaukarta mara hankali kasancewar komanta fes yake. Haka yara suka zagayeta harma da manyan kowa ya kasa zuwa inda take. To duniyarce babu gaskiya ai.        Barcinta tasha sosai sai wajen sha biyu ta farka da yunwa kamar jiya. Ta shiga bin mutanen dake zagaye da ita da kallo ɗaya bayan ɗaya. Batare da tayi magana ba ta maida kanta ƙasa ta duƙar tana yamutsa fuska da dafe cikinta dan yunwa takeji sosai.          A ɗan tsorace wani dattijo a cikinsu yace, “Mutum ce ko aljana?”. Banza Zinneerah tai bata amsaba, sai faman riƙe ciki take ita dai. Kusan min tuna biyar ta ɗago tana kallonsu hawaye na zirara mata. Cikin rawar murya tace, “Dan ALLAH ku bani abinci”.       Kallan kallo suka shigayi a junansu batare da wani ya amsa mata ba. Cikin fisgar numfashi ta kuma faɗin, “Abinci dan ALLAH zan mutu”.          Tausayintane ya kama wani matashin saurayi dake tsaye gefe da jikka a hannu alamar abin hawa yake jira. Ya matso kusa da ita yana faɗin, “Komi aka baki zakici dai ko?”.      Da sauri ta kaɗa masa kanta. Fuskarsa cike da tausayinta ya zaro hamsin a aljihu ya bama mai wainar ƴar tsala ta gero a gefe yana faɗin, “Bata ta duka”.        Amsar kuɗin mai ƴar tsala tayi ta zuba mata wainar a roba, tasa yaji a gefe ta miƙawa saurayin. shine ya ajema Zinneerah gabanta, zata saka hannu ya dakatar da ita akan ta bari ta wanke hannun. Ina bata sauraresaba ta hau cin kayanta hannu baka hannu ƙwarya. Sai gashi cikin ɗan ƙanƙanin lokaci ta cinye tas. Ruwan da ya ajiye mata dan wanke hannu ta raruma ta kafa kai tasha sosai. Sai gata tana lumshe idanu da sakin murmushi, a fisge tace masa “Nagode”. Daga haka ta zame ta kwanta a wajen sai barci.         Yanda tai din ya bama kowa mamaki, sai dai bayanin wani tsoho ya sakasu maida kallonsa garesu.        “Wannan yarinyar ba mahaukaciya bace, da alama kurciya akai mata ko makamancin hakan”.       “Baba lado miye kurciya?”. Saurayin da ya sai mata ƴar tsala ya tambayi tsohon. Kamar tsohon bazai sake magana ba, sai kuma ya ɗan girgiza kansa yana mamular goron dake bakinsa. “Kurciya asirine mana shamsu. Akan yima mutum idan ba'a son ya zauna a waje. Akanyi asirin a jikin tsuntsuwar kurciya. Duk inda kurciyar ta nufa can mutum zai nufa shima”.          A take jikin mutanen wajen yay sanyi, tausayin Zinneerah da batasan sunayiba ya shigesu sosai, suka shiga ambaton ALLAH ya saka mata.          Yauma kamar jiya yunwa ce kawai ke farkar da ita. Data samu taci saita koma barci, da daddare tsohon nan ya saka aka kama masa ita zuwa gidansa da nufin zai taimaketa. Babu musu kuwa matarsa ta amsheta hannu bibbiyu dan dama ya mata bayani akan Zinneerah ɗin hasalima itace ta bada shawarar su taimaketa.      Sai dai kuma yauma cikin daren ta farka a firgice kusan ƙarfe ɗaya. Cikin sanɗa ta silale tabar gidan dan ko katangar kirki tsoffin basu da ita. Haka ta ɗauki hanyar titi taita tafiya cikin ficewar hayyaci. Sai dai wayar gari sukai babu ita. Sun tausaya mata matuƙa. Dan basusan inda ta nufaba kuma. gashi ko jikkarta bata ɗaukaba nan ta barta a gidan nasu.        Haka al'amari ya cigaba da kasancewa akan Zinneerah. Duk inda asuba tayi takan tsaya ta yada zango, a wani garin ta samu tallafin abinci, wani garin kuwa babu mai kallonta. Dan zuwa yanzu kamanninta sun fara canjawa saboda rashin wanka da sauran buƙatu. Ba kullum take samun damar yada zango a gariba. Watarana a daji take yada zangon, haka zata yini kuka da juye-juyen yunwa har barcin nata na ƙa'ida ya ɗauketa.        A randa ta cika kwanaki goma sha ɗaya da baro gida ALLAH ya iso da ita cikin garin kano, inda ita batasan inane ɗinba. Sai dai taga yawan jama'a da gine-ginen nan yafi na duk garuruwan data baro a baya. Anan ɗinma ba a hayyacinta takeba. Dan kamar yanda ta saba kwanciya da tashi taita tafiya haka ta cigaba dayi, hakanne yasa taita nausa kanta cikin ƙwaryar kano sosai har batasan tanayiba.      Zuwa yanzu har takai kowa kallon mahaukaciya yake mata, dan yaran kan tsokaneta. Harma manyan sukan koreta idan ta ɗan laɓaɓa wani gurin zata huta ko tana neman abinci. A haka ta sake share kusan sati biyu cikin ƙwaryar kano, indan kuma an haɗa da barowarta gida tana neman ƙulla wata ɗaya. Ɗan cikinta ya fara fitowa fili kowa yana gani, duk da ba wani uban girma yayiba na azo a gani.            Duk da yanayin da take ciki haka take kasancewa cikin laulayi, dan kusan kullum da zazzaɓi take kwana, wani abin kuma idan taci takanyi amansa dan baya zama.      Yau data kasance juma'a mutane nata kai kawo na zuwa masallatan juma'a a cikin garin na kano, wanda a yanzu haka Zinneerah na gab da barin garin tana neman ɗaukar hanyar jigawa dutse. Tafiya take a hankali cike da kasala saboda rashin samun inda zata raɓa ta kwanta tun ɗazun, dan tun barcin gabannin asuba data kwanta a ƙofar wata maƙaranta gari na wayewa aka korota. Shine har yanzu bata samu ta sake samun wajen kwanciyarba kuma. Ga yunwa na cin hanjinta da zazzaɓi. Tun tana tafiya tana kallon inda take saka ƙafarta har takai idanunta sun lulluɓe da duhu.              Gudu motar takeyi sosai daga hanyar jigawa tana nufo cikin Kano. Yanda passengers ɗin cikin motar basu damu da gudun da direban keyiba zai tabbatar maka da suma son ai gudun suke dansu sami sallar juma'a cikin jam'i.          Sam idonsa bai kula da abinda ke gabansaba sai da yazo gab. Yay ƙoƙarin taka birki yana salati kamar yanda suma fasinjoji keyi cike da tashin hankali da ruɗani, sai hakan ya gagara dan sun riga sunzo gab da ita. Gashi ita kuma sam batajin uban horn ɗin da drivern ke zabga mata da iyakar ƙarfinsa ba.      Ji kake wani ƙuuuuuuuu!!!!!! Motar ta bada sauti mai ban tsoro, yayinda razananniyar ƙarar da zinneerah ta ƙwalla saboda azaba ta danne ƙarar ƙugin da motar tayi.. Cikin tsananin tashin hankali kowa dake a cikin motar yake ƙoƙarin fitowa. Dan cikin amincin ALLAH babu abinda ya faru da kowa a cikinsu. Gaba ɗayansu kan Zinneerah dake kwance wanwar a ƙasa sukayi kowa na salati a rikice.............✍             *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* *_Page 8_* ________________________ *ZAUREN GIRKI* Abinci na *gargajiya* ...Kuka,Taushe,Danbu, Sinasir,Waina Abinci na *zamani* ...Afang,Edikaikong, Coconut Rice, Ofada Rice *Garabasa* ...Salads,Pancakes, Plantain mosa, Gyaran nama/kifi kafin girki,Shirin/shinfida abinci kan table. • A kowane sati,in shaa ALLAAH, za a koyi miya/abinci daya da kuma wani abu ta karkashin *Garabasa* . • Duk ranar *Lahadi* za fito da sabobin *videos* guda biyu na miya/abinci da na wani abu daga karkashin *Garabasa* . • Kowacce daga cikin masu koya zasu bibiya video su kwaykwaya su gwada yin abincin bisa ga umurnin *video* • Kowane ranar *Asabar* za a yi *Q&A* a inda kowa zai samu yin tambayoyi akan *videos* din satin daya gabata, da inda suke neman karin bayani/gyara akan kokarinsu na gwada abincin *video* da kawunansu • Ga wace taga dama,daga ranar *Talata* za a iya fara turowan *video* ta kokarin da aka yi na kwoyon abincin da aka kwoyar ta *video* na ranar *Lahadi* . • Inda akwai me bukatan wani fanni na abinci,ana iya hada *aji(Special Personal Video Classes)* musamman domin wannan bukatan.Anan za a shirya live *video* sessions domin cimma wannan burin • Za a biya dubu biyu *(#2,000)* na watan farko,sannan za dinga biyan dari biyar *(#500)* ta kowane sati ga masu bukatan shiga group dinnan namu mai albarka • *Zen Commute,account number 0119343451 Union Bank* ,asusunmu • Duka lokacin da aka biya sai a turomana da hoton teller ko bank confirmation akan wannan number ta *WhatsApp 0817-541-7533* • Ana iya tuntubammu akan wannan number domin karin bayani; **0817-541-7533(WhatsApp kawai)*                                   ZA MU FARA ZAUREN GIRKI LAHADIN SATIN FARKO TA WATAR SEPTEMBER,IN SHAA ALLAAH! *MU TSARE MUTUNCINMU,MU KARE MAZAJENMU...MU KOYI GIRKI!!!* __________________ *Page 8* ..........Ko tsayawa fahimtar a ina taji ciwon direban baiyiba. Kasancewarsa mutum tamkar ruɗaɗɗe, abu kaɗan ke gigitashi. A yanzu hakanma jikinsa sai rawa yakeyi.      “Dan ALLAH ku taimaka a sata a mota muje asibiti karta rasa ranta”. Ya faɗa a gigice da rawar jiki saboda jinin dake zuba a jikinta da basusan ko daga ina bane.       Suma kansu yanda ya rikice ɗin sai hankalinsu ya ƙara tashi, ga yarinyar tunda tai ƙarar farko bata sake ko motsiba alamar numfashinta ya rabu da gangar jikinsa. Ga jinin dake fita a jikin natama tashin hankaline mai zaman kansa.      Wani abokinsa driver ne daya tsaya  a wajen kamar yanda yaga motoci nata tsayawane ya nufesu a rikice. “Ya ilahi, Naziru Accident kukayi haka?”. Cike da tashin hankali ya bashi amsa. “Wlhy bugeta nayi Malam Abubakar, sam banga yarinyarnan ba sai da mukazo gab da ita. Nayi ƙoƙarin kauce mata kuma hakan ya gagara”.         “Hasbinallahu wani'imal wakil. Inaga to kusata a mota, wasu ƴan motar taka saisu dawo nan wajena tunda ba mutane sosai”.      Kowa yayi na'am da wannan shawaran, dan haka a take sukayi hakan kuwa. Cikin kano suka ƙarasa shiga, inda kai tsaye suka nufi wani asibin kuɗi kamar yanda wani a motar ya bada shawran, dan sunsan yanzu idan sunje na gwamnati wani sabon turancine zai tashi na maganar ƴan sanda da sauransu. Cikin amincin ALLAH suna zuwa kuwa aka amshesu kasancewar ansan shi wanda ya bada shawaran. Ashema yana taɓa aiki a asibitin. Da taimakon wannan bawan ALLAH aka shiga bama Zinneerah da batasan ina kanta yakeba taimakon gaggawa.            Alhmdllh kusan awa ɗaya da rabi saurayin nan da likitan da suka taimaketa suka fito, fuskar saurayin da murmushi yace, “Alhmdllhi kowa ya kwantar da hankalinsa komai yazo da sauƙi, cikin ikon ALLAH ma bataji wasu ciwuka masu tsauriba, sai dai cikin jikinta da ƙyar aka samu ya tsaya, saboda shi ne ma zamu riƙeta dan tana buƙatar kasancewa a ƙarƙashin kulawar likita na kamar sati biyu zuwa uku haka”.          Ajiyar zuciya drivern ya sauke. Hakama sauran fasinjojin da sukai karar biyosu duk suka shiga ambaton Alhmdllhi. Sai dai kuma hankalin drivern a wani fanin a tashe yake. Da damuwa yace, “Amma zamanta sati uku a asibitin nan zan iya shiga wani hali ɗan uwa. Kuɗin gado kansu aikine babba a gareni”.         Murmushi saurayin yayi yana dafa kafaɗarsa, yace, “Karka damu za'asan yanda za'ai insha ALLAH. Idan kuma yarinyar ta farka ai dolene musan daga ina take? A nema iyayenta da mijinta ko”.         Ajiyar zuciya ya sauke yana gyaɗa kansa. Daga haka suka fita zuwa massallacin da basu tayar da sallaba su har yanzun.           Bayan an idar da salla daga can sauran fasinjojin kowa ya kama gabansa. Da ga shi Naziru direba sai abokinsa Abubakar da saurayin nan da ya faɗa musu sunansa Khalipha suka dawo asibitin. Sun sami damar shiga dubata yanzu kam. Tana kwance an saka mata ruwa. Sai hanunta dake ɗaure da bandage alamar taji ciwo a wajen, sai gefen kanta shima da sauran gurare jefi-jefi. Kasancewar an cire mata kayan dauɗar jikinta an saka mata na asibitin kalar green sai taɗan canja kamanni kaɗan. Duk da idanunta a rufe suke sun fahimci dai ta farfaɗo barci takeyi yanzun, dan haka sukaji daɗi har cikin ransu, a fili kuwa suna ambaton Alhmdllh tare da mata fatan samun lafiya. daga haka suka fita domin biyan kuɗi suma suɗanje gida kuma. *BAYAN KWANA UKU*          Kwana uku Zinneerah na samun kulawa a asibitin da taimakon Khalipha dake tsaye akan komai. Dan koda direba Naziru ya bada iya kuɗin da ALLAH ya hore masa Khalipha ɗinne ya ƙara wasu aka biya kuɗin gado harna kwana goma, yace idan da buƙatar tafi waɗanan kwanakin sai asan abinyi. Alhmdllh jikin nata da sauƙi, dan ƙananun ciwukan harsun fara nuna alamar warkewa saboda bata da ƙan jiki, sai dai hannun natane take kuka da shi dan ta samu tsagewar ƙashi ne. Amma shima Alhmdllh yau ta tashi da sauƙi.        Abu ɗaya ke tadama su Khalipha hankali, shine da zaran dare yayi babu zaman lafiya. Tata zabura kenan akan saita fita a asibitin. A daren farko sun ɗaukama tanada taɓin hankaline, hakan yasa suka danna mata allurar barci mai ƙarfi sosai, wadda ta jata har washe gari da rana tana barci. Sai da likita yay bincike kamar yanda Khalipha ya buƙata sannan suka fahimci lafiyar ƙwaƙwalwarta ƙalau sai dai kuma wani abu daban da basu saniba.       A dare na biyu kam tana farawa wani tunani yazoma Khalipha. Kafin azo ai mata allura ya shiga tofa mata addu'oi, tun tana ɗan fisge-fisgen kaɗan da faɗin ita a barta ta tafi har ta fara lafawa, sai kuma gashi kafinma ayi allurar barci mai nauyi yay gaba da ita. A ranar haka Khalipha ya kwana da abin nan a rai, dan ji yake a ransa tamkar ya santa ko yanada alaƙa da ita. Dare na uku ma tana farawa ya fara mata addu'oin nanma sai gashi ta lafa. To a yau Alhmdllh bayan an cire mata ruwan da aka saka mata Khalipha ya saka wata Nurse ta taimaka mata aka goge mata jiki da duk abinda zai taimaka mata.      Kusan ƙarfe bakwai sai ga Naziru direba da abincin karyawa kamar yanda ya jura kawowa kullum, da rana kuma almajiri yake kawo mata. Idan kuma ya dawo aiki yakan zo asibiti yay kamar awa guda sanann ya wuce gida. Hakan da yake yi nama Khalipha daɗi, shiyyasa baijin ƙyashin taimaka masa akan jinyar yarinyar dako sunanta har yanzun basu sani ba.         Sai da aka gama kimtsata sannan suka shigo ɗakin. Fuskar Naziru washe da fara'ar jin daɗin ganin jikin nata yaketa ambaton, “Alhmdllhi, Alhmdllhi. Kai naji daɗin ganinta haka Malam Khalipha, ALLAH ya saka maka da alkairi, nagode-nagode”.       Murmushi Khalipha yayi idanunsa akan Zinneerah shima yace, “Ai ƙoƙarin ka ne da adalcinka ya kaimu ga wannan nasarar Malam Naziru. Da ace guduwa kayi bayan kawota nan muma bazamu sami ƙwarin gwiwar taimakonta ba, dan direbobi da yawa idan irin haka ta faru guduwa suke subar majinyaci a asibiti koda kuwa ya zama gawa. Yanzu inaga jikin nata Alhmdllh gaskiya, ya kamata musan sunanta da inda ta fito dan mu nema iyayenta da mijinta kodan abinda ke a cikinta”.      Cikin washe haƙora Naziru yace, “Wannan gaskiya ne Malam Khalipha”.        Duk wannan magana dake fita tsakanin Khalipha da Naziru Zinneerah na zaune ne a gadon kanta a ƙasa tana saurarensu. amma ko sau ɗaya bata ɗago ta kallesu ba tanata faman wasa da yatsun hannunta ne kawai kamar bata a wajen ma.        Nurse ɗin dake a gefenta ta ƙarasa gyara mata abinda ya rage ta fice ta barsu. Sai a lokacin su Khalipha suka ƙarasa inda take suna mata sannu. Yanzunma bata ɗago ta kallesu ba. Sai dai cikin rawar murya tace, “Ina yini”. Daga haka tai tsit.      Wannan shine karon farko da sukaji muryarta tana cikin hayyacinta, dan haka sukaji daɗi har cikin ransu. Khalipha yace, “Masha ALLAH, yau dai naji muryar ƙanwata”.        Batace komaiba, kamar yanda bata ɗagoba. Bai damuba, dan ya fahimci akwai damuwa tattare da ita. Zama yay a bakin gadon daga can ƙarshe, dan haka tai saurin janye ƙafafunta data miƙe ta naɗesu. Baice komaiba, sai ma Naziru ne yaja kujerar roba shima ya zauna a kusa da shi. Su dukansu idanunsu a kanta suna kallonta cike da tausayi, dan shekarunta sunyi ƙanƙanta da fuskantar lalurar ciki irin haka a ganinsu.       “Ƙanwata!”. Khalipha ya kirata cike da kulawa..       A karon farko ta ɗago taɗan kallesu, sai kuma tai azamar maida kanta ta duƙar batare data amsa masaba. Ya ɗan murmusa da sake faɗin, “Ki saki jikinki munan duk yayunkine kinji, munason miki wasu tambayoyine, ko zaki taimakemu da amsa?”.       Kanta a ƙasa har yanzu ta gyaɗa masa kanta. Shima kan nasa ya gyaɗa cike dajin daɗin tana fahimtarsu. Ya cigaba da faɗin, “Minene sunanki?”. Shiru bata amsaba. Fahimtar bazata faɗaba ya sashi sake cewa, “A wane anguwa kike anan kano?”. Yanzu kam kanta ta girgiza masa.       Cikin rashin fahimta yace, “baki san anguwarba ko ba'a nan kikeba?”.     Kanta ta ɗaga masa. Naziru ya amshe da sake faɗin, “Ba'a nan kike ba?”.       Kanta yanzu ma ta kaɗa musu. Kallon junansu sukai da mamaki, kafin Khalipha yace, “A wane gari kike to?”.        “Nima ban saniba, na manta komai”.     Ta basu amsa a fisge tana ƙara ƙasa da kanta alamar gajiyawa. Nanma kallon juna sukai cike da mamaki da fargaba. Naziru zai sake magana Khalipha ya girgiza masa kai alamar su barta kawai.       Badan Naziru yasoba yay shiru, Khalipha ya miƙe yana faɗin, “Yauwa to bara na turo sister Salima ta baki abincin kici, dan nasan kina bukatarsa”. Daga haka ya kama hannun Naziru suka fice batare da ya jira amsawarta ba.          Bayansu tabi da kallo har suka fice, ta sauke nannauyan ajiyar zuciya tana lumshe ido. haka kawai take shiga takura da shiga wani yanayin da batasan dalilinsa ba a duk sanda Khalipha ya kasance a ɗakin.         “Malam Khalipha akwai matsala kenanfa idan yarinyarnan batasan wacece ita ba, gata da ciki”  Naziru ya faɗa cike da damuwa sanda suke fitowa.      Ajiyar zuciya Khalipha ya sauke yana furzar da iska. Yace, “Tabbas akwai matsala, amma ni tun daren farko da aka kawota na fahimci akwai wani ɓoyayyen al'amari tattare da ita. Dan yanda take zabura cikin dare da faɗin abarta ta tafi, da safe kuma taita barci yasa nake ganin kamar tana a wani hali. So yanzu dai sai munyi haƙuri munbi a hankali zamu kamo bakin zaren insha ALLAH”.         Numfashi Naziru ya sauke shima. ransa da damuwa yace, “Ni kuma yarinyar kama ma takemin da amaryar Yayana wlhy, sannan maganar ɗawainiyar asibin wani abune mai zaman kansa Khalipha, badan ka taimaka min ba ai bansan yaya zanyiba nikam”.      Murmushi kawai Khalipha yayi, cikin kauda maganar ƙarshe yace, “Kana nufin tana kamani da wadda kasani?”.      “Sosaima kuwa, tun jiya da aka ɗan goge mata jiki naga kamaninta da Maman Sadiq sosai wlhy. Amma dai yau zan kawo matata da yamma dan ina komawa gida da wuri irin yau ɗin, kasan mata sun fimu lura. Kaga sai muji abinda zatace itama”.       “Wannan shawaran yayi Malam Naziru, ALLAH ya jishemu alkairi”.      “Amin ya rabbi, bara nazo na wuce dan na samu damar dawowa da wuri, yau katsina zan nufa insha ALLAH. Kuma sahu ɗaya zanyi na dawo gida”.      “ALLAH ya bada nasara. Ya kuma maido mana daku lafiya”.     Godiya Naziru yayma Khalipha ya wuce. Shima Khalipha sai ya wuce nasa uzirin acikin asibitin. ★★★        Misalin ƙarfe huɗu na yamma Zinneerah na zaune a gadon jinyarta, idanunta tsaye ƙyam akan matashin cikinta, wanda yau ne karan farko data iya zaman masa wannan kallon. A duba guda da zakai mata zaka iya fahimtar ta lula duniyar tunanine. Dan har Naziru direba da matarsa sukai sallama biyu a ɗakin babu amsa.       Kallon juna sukai shi da matarsa, kafin su sake maida idanunsu ga Zinneerah wadda da'alama har yanzu batasan da shigowar tasu ba. Takowa matar Naziru tayi har inda take, ta kai hannu akan kafaɗarta tana sake rangaɗa wata sallamar. Zabura Zinneerah tayi dan kamar daga sama taji sallamar tata. Ganin Naziru tsaye a ƙofa ya saka sauke ajiyar zuciya. Ta janye hanunta data ɗora saman cikin nata tana maida dubanta ga matar Nazirun da tai tsaye ƙyam tana duban Zinneerah ɗin da alamun mamaki a fuskarta.       Kafin Zinneerah tai magana tai saurin faɗin, “Ikon ALLAH, Abban Nasiba kaga kuwa abinda nake gani?”.      Cikin nuna tamkar bai fahimceta ba yace, “Mi kika gani?”.      Ganin kallon da Zinneerah ke musu ne na alamar tsoro ya sakata wayancewa ta zauna kusa da Zinneerah ɗin tana faɗin, “Gani nai ƙanwar tawa ta lula tunani batama san da zuwan namu ba”.      A hankali Zinneerah ta sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya da sake maida kanta ta duƙar a ƙasa.     Yayinda shi kuma Nasiru ya kasa ko motsi dan yayi zaton abinda ransa ke raya masa na kamannin yarinyar da Maman Sadiq matar tasa zata faɗa. Sai kuma yaji saɓanin hakan. Jin Zinneerah da matar tasa na gaisawa ne ya sakashi shima ƙarasowa gaban gadon ya ajiye ledan hannunsa yana dubanta da kulawa.         Itama batare data sake ɗagowa ta kallesaba ta shiga gaishesa kamar yanda ta saba. Da kulawa ya amsa mata da sake tambayarta ƙarfin jikinta. Tace taji sauƙi.      Sun jima a ɗakin tare da ita, sai dai su kaɗai suke ƴar hirarsu jefi-jefi. Zinneerah na zaune shiru tana saurarensu kanta a ƙasa. Sai da Naziru ya tambayeta ko Khalipha ya shigo? Ne ta girgiza masa akai alamar a'a kawai batare da tayi magana ba.       Fara kiraye-kirayen sallar magriba da akai ne yasa sukai mata sallama suka fito.       Suna fita ta sauke ajiyar zuciya, tare da zamewa a gadon ta kwanta ta lumshe idanunta da sake maida hannunta akan cikinta kamar ɗazun. Batasan wane tunani zatai akan wannan cikinba a rayuwarta. Dan yazo mata a yanayin MAKAUNIYAR ƘADDARA. shin tayaya wai aka samar da shi ne? Wanene ubansa? Kodai dama cikin basai mutum yayi aure ko ya aikata iskanci ba yake samunsa?.       Wannan tunanin shine a ranta. Dan harga ALLAH ita dai tasan duk masu haihuwar garinsu sai sunyi aure. sannan idan akaga wadda batai aureba da ciki akance mata ƴar iskace mai bin maza. A yanda kuma takejin ma'anar kalmar mai-bin maza a abaki manya shine mace mai zuwa ta aikata abu mara ƙyau da namiji. To amma ita yau gashi bata a cikin duk waɗancan kason mutanen amma gata da ciki. Bata taɓa aure ba. Bakuma ta taɓa iskanci irin na waɗancan matanba. To kenan bayan waɗanan dalilan mace zata iya samun ciki ta wata sigar kenan kamar yanda itama a yanzu take tsamanin ta hakan ta sameshi?.         Lokacin da Zinneerah ke wancan tunani a waje tsakanin Naziru da natarsa kam tattaunawa sukeyi suma akan abin al'ajabin da suka gani. Dan suna fitowa Matar tasa ke faɗin, “Abban Nasiba wlhy ɗazunfa waskewa nayi dan naga yarinyar nan ta tsorata. Kasan kuwa mina gani tattare da yarinyar nan?”.        Kansa ya girgiza mata kawai batare da yace komaiba. Itama batare data damu da hakan da yayinba tace, “Wai shin kai bakaga kamarta da Maman Sadiq ɗin gidan babban yaya bane?”.         A yanzu kam gaba ɗaya ya tattara hankakinsa gareta. Cike da zumuɗi yace, “Wannan dalilin yasa na kawoki nan Faɗima. Dan inata kokwanto, kinsan akan hakan jiya har gidan Yaya naje na sake ganin Maman Sadiq kuwa?”.        “Ikon ALLAH, to amma ita yanzu ai kaga yan uwanta ko?”.        “Inafa, bata iya faɗa mana komai akantaba wlhy, da alama akwai saka hannu a al'amarinta gaskiya, dan kamar bata da isashshiyar kafiya, kamar kuma mai tare da sammu ko jinnu. Amma ni yanzu kinsan wane tunani nayi?”.      Kanta ta girgiza masa. Ya sauke numfashi yana bin Khalipha dake fitowa daga wata baƙar mota data faka a kusa dasu da ido. Tinted glass ɗin motar yasa basuga wanda ke zaune matsayin driver ba. Sai Khalipha ɗin daketa faman ɗaga masa hannu yana murmushi har motar ta sake ficewa a harabar asibitin.       Inda su Nazirun suke ya ƙaraso yana faɗin, “A'a malam Naziru kune anan haka?”.          Cike da kallon alamar tambaya da Nazirun ke masa ya gyaɗa kansa. Dan mamakin wannan babbar motar da aka saukesa a ciki yakeyi. fahimtar hakan da Khalipha yasoyi ya sakashi yin murmushi da juyawa yana kallon motar da har ta gama ficewa a gate ɗin asibitin ta hau titi. Sake maido dubansa yay ga Naziru da shima motar ya koma kallo yanzun cike da basarwa.          “Yaya dai malam Nazir?”. Murmushi Naziru yayi a karon farko ƙasan zuciyarsa fal saƙe-sake akan tunanin da alama Khalipha ɗan masu da shi ne. Dan shi tunma randa suka ɗakkosa a Jigawa yaso fahimtar hakan. Amma shi Khalipha kamar bayason nuna shiɗin wanine.......        Gyaran muryar da Khalipha yayine ya katse tunaninsa. Shi kuma Khalipha ya maida dubansa ga matar Nazirun suka fara gaisawa. Bayan sun gama gaisawarne Naziru yay masa bayanin itama abinda matar tasa ta faɗa game da kamannin yarinyar da matar yayan nasa.        Khalipha yace, “To inaga mafita ɗayace damu kamar akan wannan tunain naku, mizai hana kubi hanyar data dace ita matar yayan naka tazo asibitin nan ko zamu sami wani bakin zaren, idan kuma babu damar yin hakan mu haƙura har yarinyar ta samu sauƙi sosai sai mu kaita gidan yayan naka mu da kanmu”.         “Lallai wannan shawaran taka yayi Khalipha, kuma na gamsu da shi. Insha ALLAH zanyi iya duk ƙoƙarina zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu Maman Sadiq tazo asibitin nan kafin yarinyar nan ta kammala kwanakinta inaga kamar zaifi sauƙi”.        Daga Khalipha har matarsa sun gamsu da hakan, dan haka sukai sallama yay cikin asibitin su kuma suka fito don tafiya gida. __________________★          A haka kwanaki suka cigaba da tafiya, Zinneerah na cigaba da jiyya da samun kulawa ga Khalipha, Naziru ma yana iya bakin ƙoƙarinsa ganin yazo dubata koda hidimar Khalipha ɗin da baya gajiyawa.      Sosai ta samu sauƙi, dan yanzu Alhmdllh ko zaburan daren nan nason a barta ta fita batayi saboda Khalipha bai barin asibitin da wuri saboda ita kawai. Kasancewar suna sakata barci da wuri dan ta sami hutu sosai yakan zauna yayta mata addu'oi yana tofa mata, itako bama tasan yanayiba dan tuni tayi barcinta.      Yawan kulawa da samun abinci mai inganci da takeyi yanzu ya sakata canjawa a zaman asibitin tamkar bamai zaman jinyaba. Tayi wani fresh da ita ga cikin nata nata sake nuna kansa. A duk sanda ta dubi cikin takan zauna taita kuka maiban tausayi. Dan takan rasa wane irin kalar tunani zatayi akan wannan MAKAUNIYAR ƘADDARA data riski rayuwarta?. Gaka da ciki amma bakasan ta hanyar daka samosaba balle ai tunanin wanene ubansa kuma. Ita yanzu ma da'an sallameta daga asibitin nan batasan indama ta dosaba kuma. Dan koda sha'awa bata son tunawa da Danya a ranta ma balle ai tunanin komawarta can.      Har yanzu su Khalipha basusan sunantaba, tun kuma waccan ranar basu sake neman jin wacece itaba. Tamaƙi yarda ta saki jiki dasu gaba ɗaya.        Yauma kamar kullum tana zaune a ɗakin da tab ɗin Khalipha dakan bata wai tayi game ko kallo haka danta rage kaɗaici. Game ɗin takeyi fuskarta na fidda murmushi mai ƙayatarwa, a kallo ɗaya zaka fahimci tana cikin nishaɗi, shiyyasa shi kansa Khaliphan yake ɗaukar Tab ɗin ya bata dazaran ya shigo cikin asibitin. Shekaran jiyama a wajenta ta kwana.       Ɗan harbawar da zuciyarta yayi yasata dakatawa dayin game ɗin, haka yau ta tashi da wannan tsinkewar zuciya da batasan dalili ba, jin abin na ƙara ƙarfi ne ya sakata ajiye tab ɗin ta Khalipha gefe ta zame ta kwanta tana ambaton ‘hazbunallahu wani'imal wakil’ a ranta ko zataji ɗan daɗi............✍ *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* *Page 9* ________________________ *_Hummmmm!!. Wai wai wai, wani aiki sai: GIDAN ƘAMSHI💃🏻💃🏻💃🏻🥺_* *_INA MATA ƳAN ƘWALISA MA'ABOTA SON ƘAMSHIN GIDA DANA JIKI?_* *_INA MATAN DAKAN SO DUK INDA SUKA DOSA KO SUKA BARI SAI SUN BAR MUSU TARIHIN ƘAMSHINSU_* *_TO MATAN ƘWARAI KUZO GA WANI SIRRI DAZAN BAKU DAGA FITACCEN GIDAN ƘAMSHIN NAN DA BAIDA NA BIYU A KANON DABO😁_* _Ina magana ne akan GIDAN ƘAMSHI da ke a Jihar KANON DABO MAIDUGURI ROAD MARIRI_. *MUNA SIYAR DA TURARURRUKAN WUTA SET NA AMARE, MUNA KUMA BADA SARI.* *AKWAI KUMA SABULUN GYARAN JIKI MAIDA TSOHUWA YARINYA, BUDURWA TAURARUWA, MATAN ƘWARAI ANNURIN HASKAKA GIDA. SHIMA DAI AKAN SARI, DOZIN KO KATON* *AKWAI KUMA ZUMAR ƘARA ƘIBA GA MATAN DA KESON SU GANSU DUMURMUR SUNA JUYAMA OGA KAYAN...😉🙈💃🏻 kundai gane*. *_Mata ku garzaya GIDAN ƘAMSHI domin ƙamsasa kanku kuma kar aci kasuwar sama babu ku😁_* *ZAKU IYA SAMUN MU TA WANNAN LAMBAR WAYAR: 07033778564 DOMIN JIN ƘARIN BAYANI*. *KO A KANO MAIDUGIRI ROAD MARIRI*.💃🏻💃🏻👍🏻 _______________________ *Page 9* ..........Jin kamar ana nufo ɗakin ya sata miƙewa zumbur taja hijjab ɗinta da Khaliphan ya kawo mata saboda salla ta saka da sauri. Ƙirjinta ne ya sake ƙarfin bugawa fiye da ko yaushe lokacin da Khalipha yay sallama a ƙofar ɗakin. Haka yakeyi mata a duk sanda zai shigo sai yayi sallama ta amsa sannan yake shigowa.      Yanzu ma bai shigo ɗinba sai da ta amsa ya turo ƙofar ya shigo. Kallo guda tai masa tai saurin maida idanunta ƙasa saboda kwarjinin da yake mata da cika ido. Sai dai kuma luguden dakan da ƙirjinta ke mata ne ya tilastata sake ɗago kanta badan ta shirya ba. Naziru ne biye da bayansa. Sai matarsa. Sai wasu mata biyu da batasan daga inaba. Sai dai shigowar ta ƙarshen ya sakata wani irin zabura tana binta da kallon ƙurilla maiban mamaki.        Yanda take kallon matar da yanda itama matar take kallonta tana tafiya da ƴar sassarfa ne yaja hankalin su Khalipha garesu baki ɗaya. Kusan mini ɗaya matarnan da Zinneerah na kallon juna batare da sun saniba, sai can Zinneerah ta fara janye nata tana sauke wata irin nannauyar ajiyar zuciya a ɓoye. Kanta ta maida ƙasa tana ƙoƙarin haɗiye hawayen da suka cika mata ido da batasan na minene ba.          Jin yanda ɗakin yay shiru ɗayar matar da suke tare da itama al'ajabi ke neman halakawa ta katse shirun da faɗin, “Baiwar ALLAH sannu kinji, ALLAH ya kiyaye gaba, ya ƙara lafiya”.         Kusan a tare duk sukace amin, banda matarnan mai kama da Zinneerah da gaba ɗaya hankalinta bayama tare da ita. har yanzu kuma idonta nakan Zinneerahn. Sun ƙara jajanta mata da mata addu'ar samun lafiya mai ɗorewa sukai musu sallama suka fita bayan matan nan biyu sun ajema Zinneerah kuɗi. Koda zasu fitanma matarnan tana tafiya tana waigen Zinneerah har suka fice. Shi dai Khalipha yana tsayene yana kallonsu da nazari tun shigowarsu har suka fice.         Wayarsa da ke ring a aljihu ta sashi sauke numfashi da warware hannayensa daya harɗe a ƙirji ya cirota a aljihu. Wani lallausan murmushi ya saki wanda yay dai-dai da ɗagowar Zinneerah. Sai ko ga idanunsu cikin na juna. Tai azamar maida kanta ƙasa ƙirjinta na wani irin harbawa, dan ba ƙaramin dukan zuciyarta wannan murmushi nashi yayiba.         Shikam wayar ya kai a kunne yana ɗan lumshe idonu, cikin wata murya mai ɗunbin ladabi da girmamawa yace, “Assalamu alaika Yayanmu”.      Batajin mi ake faɗa acan ɗin, sai Khalipha ne taji ya wani sake narke murya da shagwaɓa yana faɗin, “Oh Yayanmu Please ka jirani gani nan zuwa, nifa nace zan kaika da kaina yau, nanda mintuna goma insha ALLAH ina gida”.          Bataji mi nacan ya sake cewaba. Sai Khalipha ne ya matso gaban gadon yaɗan bubbuga yana cigaba da sauraren abinda ake faɗa ɗin daga can. Ɗago kanta tayi ta kallesa dai-dai ya sake narke fuskar tamkar wani yaro ƙarami, kokuma yana a gaban wanda yake wayar. “ALLAH Yayanmu bazanyi gudu ba, kasan mashin bakamar motaba ai, kuma zanbi ta hanyan dazan samu sauƙine fa Please ”.         Ita dai Zinneerah ganin yana neman zauta mata kwanya taso sake maida kanta ƙasa sai yay saurin mata alama da hannu wai yana zuwa. Bai jira cewartaba ya fice da hanzari. Bin bayansa tai da kallo harya fice, tsigar jikinta na wani tashi batare da tasan daliliba. Sai kawai ta fashe da kuka.        Kuka sosai Zinneerah taci wanda yana alaƙa da wasu baƙin al'amura a gareta, sai dai ƙuruciya ta hanata fahimtar komai. Ta zame a hankali ta kwanta tana lumshe idanunta badan barciba, sai don son samun damar tunani da wassafo matar ɗazun da takesonyi harma da tuno halin data shiga a dalilin ganin nata da wanda ta lura itama matar ta shiga saboda ganinta.      A ɓangaren Maman Sadiq kam itama tunda suka fito daga asibitin tafiya kawai take tamkar bata cikin hayyacinta, jitake kamar ta dawo ta sake ganin Zinneerah ɗin saboda abinda takeji a ranta da dukkan magudanar jinin jikinta a dalilin tozali da yarinyar. Duk da wani ɓangare na zuciyarta na ƙwaɓarta da cewar ba haka bane ta kasa yarda sam.        Daga Naziru har matarsa hankulansu nakanta ne suna nazarin halin da take a ciki, sai dai basuce komaiba har ya maidasu gida shima ya wuce nasa gidan da matarsa. Inda sai anan suka sami damar tattaunawa akan yanayin maman Sadiq ɗin.         Tunda suka shiga cikin gida ta buɗe ɗakinta ta shige saita kasa zaune ta kasa tsaye, kaikawo taketa famanyi a ciki, duk da masifar kishiyarsu Saude da take jiyowa akan taƙi fita ta ɗora girkin rana ga lokacin kaima yara abincin rana makaranta ya kusa bata fito ɗinba. Sai Uwargidansu da sukaje asibiti tare ce ta jiyo tana bama Sauden amsa da “Haba dai Maman Sakina, kodan himma irinta Maman Sadiq ai yakamata ki fara tunanin anya lafiya kuwa? Amma sai ki ɓige da neman fitina daga shigowarmu gidan dai”.          A harzuƙe da masifar da dama Sauden jira take ta hayayyaƙoma Uwargidan nasu.....        “Yaya! Yaya! Ƴar ayi jikan nasaba”. Muryar mai-gidan dake shigowa ta katse masifar Sauden ta koma ƙunƙuni ciki-ciki. Baibi takantaba sai uwargidan tashi dake masa sannu ya duba. “Mike faruwa kuma daga dawowarku Binta?”.       “Babufa komai Alhaji, fitinace irin ta Saude da baƙarewa take a gidan nan ba. Kawai dan Maman Sadiq bata fito ba shine take tsogumin batazo ta ɗora abinciba wai lokacin kaima yara makaranta ya kusa”.        Ɗan tsaki yayi yana girgiza kansa. Yace, “Ina ita Hauwa'un take?”.       “Tana ɗakinta, inaga dai akwai abinda ke damuntane, dan tunda muka baro asibitin naga yanayinta ya canja, na bartane muzo gida taɗan huta dama ko wani abune ya tada hankalinta acan ɗin tunda wajene bana daɗin rai ba”.      Baice komaiba ya nufi ɗakin Maman Sadiq ɗin, wadda duk tanajin mi'ake a tsakar gidan amma taƙi yin ko tari dan abinda ya isheta ya girmi fitinar Saude. Labulen ya ɗaga yana dubanta daga bakin ƙofar, yitai kamar bata gansaba, hakanne yasa ya shigo ciki yana faɗin, “Hauwa'u lafiyarki kuwa”.        Juyowa tai ta kallesa tamkar yanzune tasan da zuwansa. Tace, “Ashe ka shigo? ALLAH yasa dai lafiya?”.         “Ai ke za'a tambaya ko lafiya Hauwa'u? Mike faruwa ne?”.     Tamkar jira take ya tambayeta sai ga hawaye sharrr. Zumbur ya miƙe daga ɗan zaman da yay a hannun kujera yace, “Subahanallahi, wai mike faruwa ne? Ko wani abun ya faru acan inda kukaje dubiyan?”.       Hawayen ta share, tace, “Lallai Alhaji akwai matsala wlhy, dan ALLAH inason na sake komawa asibitin nan yanzun”.       “Ki koma asibiti kuma? Akan wane dalili to?. Kimin bayanin dazan gane mana”.       Wasu hawayen ta sake sharewa. Muryarta na rawar tahowar sabon kuka tace, “Alhaji yarinyarnan da mukaje dubawa wadda Nazirun ya kaɗe wlhy kamar Zinneerah, kai inamji a jikina itace duk da kuwa rabon dana ganta tun tana ƙarama”.         Shima kansa da mamaki yace, “Zinneerah dai tamu dake a Danya?”.       Cike da ɗanjin nauyinsa ta gyaɗa kanta, dan shi mutumne mai kara, duk da ɗan uwantane dama can, auren zumincine akai musu bayan aurenta ya mutu, ya sota tun tana budurwa ALLAH baiyi zata zama matarsaba a lokacin sai da ta fito yace shifa yana sota har yanzun. Da farko taso ta tirje dangi sukai mata caa akan rashin dacewar hakan. Dan kowa yasan irin son da ya nuna mata. Haka dole ta haƙura akayi aka kawota nan Kano gidansa dan dama can anan yake zaune shi shekara da shekaru, to gashi yanzun har ALLAH ya azurtasu da ƴaƴa uku duk maza. Tana kuma samun kulawa da soyayyar mijinta mai tsafta da saka kwanciyar hankali, ga Uwargidanta mutuniyar kirki, Saude ce dai sai a hankali, dan dama tun farko fitinar Sauden tasata son zamewa daga auren nasa.....        “Wai tunanin mi kuma kika tafi haka ne?”.       Kallonsa tai da sauri tana sauke ajiyar zuciya. Ya ɗan girgiza kansa kawai yana miƙewa. “Kinga ki kwantar da hankalinki tunda dai tana asibitin babu inda zataje, bara na kira Nazirun anjima yazo sai mu koma insha ALLAH dan wannan ba al'amarin da za'ai wasa bane”.      Cikin jin daɗi tace, “To Yaya ALLAH ya saka da alkairi”.        “Saboda ƴarki ce ke kaɗai kikemin godiya kenan?”.        Ƙasa tai da kanta tana murmushi. “A'a kayi haƙuri bankai canba”.         Fita yay yana murmushin shima. Saude dake laɓe a jikin Window ɗinta tana irga mintunan shigarsa ɗakin taja tsaki ganin ya fito yana murmushi. Afili tace, “Shegiya munafika, zanyi maganinki a gidannan wlhy. Oho ita dai maman sadiq bama tasan tanaiba, dan bayar fitar maigidan fitowatai ta ƙara gawayi a wuta ta ɗora ruwan abinci, dan dama tunkan su fita tayi miya shiyyasa bata damu da tsegumin Sauden ba ashe. ★★★★           A asibiti kam shiru-shiru Khalipha bai dawoba har lokacin yin barcin ranar Zinneerah yayi tasha magani ta kwanta. Bata tashiq farkawaba sai bayan sallar la'asar. Ganin lokaci yaja ya sata miƙewa aɗan harzance ta shiga toilet ɗin dake a ɗakin. Alwala tayo ta fito, bayan idar da sallar ne Salima ta shigo dan bata abinci kamar yanda Khalipha ya rataya mata alhakin yin hakan ga Zinneerah. Itako bala'in son da takema Khalipha yasa bata iya ƙetare buƙatarsa a rayuwarta, shiyyasa take bama Zinneerah kulawa sosai dan duk zatonta yanada alaƙa da zinneerah ɗinne musamman dataga an kawo zinneerah ɗin ɗaki na musamman ita kaɗai an ajiye.         Zinneerah na tsaka dacin abincinne Salima na mata hira tana ɗan murmushi sukaji sallamar Khalipha bayan yayi ɗan knocking. Saurin jan hijjab Zinneerah tai ta saka, Salima ma ta gyara zamanta dana ƙaramin hijjab ɗinta tana amsawa.        Shine ya fara shigowa ɗakin tamkar ɗazun, sai Naziru biye da shi, wani da suke tsananin kama da Nazirun na bayansu, sai dai a kallo ɗaya zaka fahimci ya girmi Nasiru ɗin dan ba yaro bane.        Sai matan ɗazun biye da su a baya, amma banda matar Naziru. Matar ɗazun da taji suna kira da Maman Sadiq ta ƙaraso gaban gadon sosai batare da tama saniba. Hannu takai bisa kumatun Zinneerah jikinta na wata irin tsuma da karkarwa. Ko shekara dubu tai bataga wannan halittarba tayi imani da ALLAH randa suka haɗu saita gane abarta. Tunda tabar ƙauyen Danya cikin gushewar hankali dana tunani har zuwa yau ɗinnan bata daina kwana da mafarkintaba da tashi da tunaninta kuma. Ta kai ƙasa durƙushe hawaye na silalo mata a kumatu. Tabar ƴarta da ƙarancin shekaru hannun kishiya mai ƙarancin imani dana tausayi badan ranta yasoba, sai dan anfi ƙarfinta kawai. Yau kuma sai gata a inda bata taɓa zatoba ko tsammani a shekarun girma....        “Zinneerah!”. Ta ambata da wani irin rawar murya dana harshe.      Ganin Zinneerah ta kasa magana sai kallonta kawai da takeyine kamar ɗazun ya saka Naziru faɗin, “Maman Sadiq ki kwantar da hankalinki, insha ALLAHU itace ma”.          Idanunta da hawaye ke kwarara ta ɗago ta kallesa, taɗan saki murmushin ƙafin hali tana miƙewa tsaye sosai. “Nasiru indai har yanzu ba ƙwaƙwalwata ce bata gama dai-daitaba to wannan kam Zinneerah ce, dan naji hakan a jikina duk da kuwa bata amsa sunan dana kirata da shi ba”.         Maman Halima da sukazo tare yanzunma ta matso gaban gadon itama ta zauna kusa da Zinneerah da alamu suka nuna tamkar bata a cikin hayyacinta. Sai da ta riƙe mata hannune tai firgigit alamun ta dawo cikin hayyacinta. Ƙasa tai da kanta saboda wani irin bugu da ƙirjinta ke mata ainun, Maman Halima ta katse shirun ɗakin da faɗin, “Ƴammata minene sunanki?”.      Babu wanda yay tsammanin zata amsa. Sai ji sukai a bazata tace, “Zinneerah”.       Wata irin nannauyar ajiyar zuciya maman Sadiq ta sauke, yayinda ɗunbin mamaki ya kashe Khalipha da  Naziru, musamman da suka tuna randa sukaita ƙwaƙwar jin sunan nata amma tai musu shiru..      “Masha ALLAH Zinneerah daga ina kike? Ina nufin a wane anguwa iyayenki suke?”.      Shiru kamar bazata amsa ba yanzu. Sai kuma zuwa can tace, “Ba'anan nake ba”.         Cike da zumuɗi maman Sadiq tace, “Daga wane gari kike?”.       Ɗagowa tai tana kallonta na tsawon kusan mintuna biyu, sai kuma ta maida kanta ƙasa tana sauke ajiyar zuciya. Cikin suɓutar bakin da bata shiryaba tace, “Danya”.       Gani kawai sukai maman sadiq ta zube kan kujerar roban dake a gaban gadon ta fashe da kuka tana faɗin, “Wlhy itace, Zinneerah tace”.      A yanda tai maganarne ya sakasu jin wani irin tausayinta ya ɗarsu a rayukansu, cike da son jin ƙarin bayani Naziru yace, “Zinneerah kekam miya kawoki hanyar jigawa keda ke a jihar katsina?”.        Hawayen dake sakko mata ta share tana girgiza kanta. “Nima ban saniba, na samu kaina ne kawai a haka”.          Sai yanzu ne Alhaji yay magana. “Lallai da alama kamar bata cikin hayyacintane ta baro gida fa kenan”.       “Tabbas hakane Alhaji, kenan har yanzu Asabe bata canjaba ko kuma Zinneerah ma tayi gamo da abokiyar zama irin Asabe a gidan aure.” Maman Halima ta faɗa saboda ganin ciki a jikin Zinneerah duk da kuwa ta saka hijjab.       A karon farko shima Khalipha da tun ɗazun baice komaiba sai kallonsu ya sauke numfashi. Gyara tsaiwarsa yayi a jikin bangon daya jingina yana kallon Zinneerah da keta satar kallon maman Sadiq da suke tsananin kamanni. janye idanunsa yay ya maida ga Naziru yana faɗin, “Inaga tunda har an fahimci bakin zaren ayi haƙuri haka har zuwa lokacin da za'a sallameta daga nan ɗin insha ALLAH. Sai dai ya kamata ku sanar mata wacece ita a gareta dan na kula ba fahimtarku takeba kamar”.      Sosai duk suka gamsu da bayaninsa, suka zazzauna aka shiga gaisuwa da tambayar jikin Zinneerah ɗin, wanda Khalipha ya ƙara musu bayani game da matsalar dake tare da ita akan buƙatar hutu bisa ga lalurar cikin jikinta. Sun shiga mata addu'ar fatan sauka lafiya.       Maman Halima dai ce da har yanzu ke zaune a kusa da ita tana riƙe da hannunta ta nuna mata wadda aka kira maman Sadiq. “Zinneerah wannan ɗin mahaifiyarki ce, duk da nasan baki santaba kamanin dake a tsakaninku da duk bayan da mukeyi a wajennan zai tabbatar miki hakan, kai namasan zakiji a jikinki koda ba'a faɗaba dan mahaifiya tafi gaban wasa ai.”          Kafeta da kallo kawai Zinneerah tayi tamkar wadda ta suma a zaune. Sai da Maman Halima ɗin taɗan taɓatane ta kawo numfashi, sai kuma ga hawaye sharr. Batare datace komaiba tai ƙasa da kanta, daga haka bata sake ɗagowa ta kalli kowa a cikinsuba.      Sosai hakan da Zinneerah tayi ya taba zuciyar Maman Sadiq. Dan ta fahimci kamar Zinneerah ɗin fushi take da itane kokuma kalar nata murnar kenan oho. Kowa ma dake wajen da irin fahimtar da yayma shirun na Zinneerah. Murmushi Alhaji yayi, cike da sanin yakamata da hangen nesa irin na manya yace, “Kubata lokaci kamar yanda likitan nata ya faɗa ko”. Sai kuma ya juya ga Khalipha batare da ya jira amsarsuba. “Likita yaushene zaku sallameta?”.        Murmushi Khalipha yayi yanaɗan sosa gefen goshinsa. “Alhaji banine likitanba dai, amma insha ALLAH zuwa nan da kwana biyar haka akoda yaushe za'a iya bata sallama tunda jikin nata yana ƙyau, dama matsalar kamar daga cikin jikintane yasa aka riƙeta”.       “To masha ALLAH, ALLAH ya kaimu, ya kuma bata lafiya”.     A tare suka amsa da amin. Daga haka sukai musu sallama domin tafiya badan Maman Sadiq tasoba. Sai dai taji daɗin abinda Maman Halima ta faɗa akan cewar itace zata dawo ta cigaba da jinyar Zinneerah ɗin har a sallameta. Kowama yaji daɗin hakan har Khalipha.               ★★★        Tun daga wannan ranar jiyyar Zinneerah ya dawo hannun Maman Halima, Khalipha ma bai janye daga mata hidimaba, hakama Naziru, ga Alhaji ma ya ƙaru. Sai ga Zinneerah ta sake zama ƴar gata, sai dai abinda kebama kowa mamaki har yanzu taƙi barin damar da zasu fahimceta game da komanta. Hatta haɗuwarta da mahaifiyarta sun kasa gane mike a ranta. Dan taƙi cewa komai, ta kumaƙi nuna murnarta a fili ko damuwarta. A duk yanda Maman Halima ke janta a jiki dan son jin wani abu gameda rayuwarta da Inna taƙi sakin jiki da ita, duk da kuwa ta fahimci babu wata mummunar manufa ga Maman Halima ɗin. Sanin yakamatane kawai irin na matar.       Tun daga ranar Maman Sadiq bata sake zuwa asibitinba, sai dai ranta fal yake da damuwar yanayin Zinneerah a kanta. Tadai danne ne kamar yanda mijin nasu ya bata shawara akan ai haƙuri da komai har Zinneerah ɗin ta dawo gida.         Itakam Zinneerah bawai farin cikine batai da ganin Mahaifiyartaba. Har ranta ita kaɗai tasan daɗi da take a ciki, sai dai wani ɓangare na zuciyarta ya sakata jin ciwo da zargin mahaifiyar tata ta watsar da itane akan sani kenan. Dan duk wanda zai kalli Maman Sadiq ɗin yasan tana a cikin kwanciyar hankali a gidan aurenta na yanzu.        A ganinta idan ba tana saneba yaya za'ai ta watsar da ita tsahon shekaru batare data taɓa waiwayar inda take ba, hakama danginta. Wannan dalilinne ya saka yin kamar batai farin cikiba. Sai dai a randa abin ya faru tasha kuka a ɓoye, still rashin ganin kuma Maman Sadiq bata sake zuwa asibitinba ma ya ƙara taɓa mata zuciya.        Ana gobe za'a sallamesu Khalipha yazo mata da zancen da yasata tasha kuka sosai, dan har saida ta kaita da zazzaɓi mai zafin gaske. Ba komai yaja hakanba sai jin Khalipha ɗin zaiyi tafiya. Ashe dama yana karatune a wata ƙasa can daban, hutu yazoyi gida shine yake ɗan zuwa nan asibitin yana rage zaman banza saboda asibitin nada alaƙa da shi. Yanzu kuma hutunsa ya ƙare, yaso ace sai an sallami Zinneerah yaji cikakken labarinta sannan. Amma sai Yayansu yaƙi saurarensa da ɗaga masa ƙafar ƙarin kwana ukun daya buƙata. Ya tabbatar masa da dole-dole saiya koma makaranta gobe idan ALLAH ya kaimu. Shiko a duniya baya taɓa iya ƙetare maganar Yayan nasu saboda ƙauna da girmamansan da sukeyi akaf gidansu koma yace family ɗinsu.       Kuɗaɗe masu yawa da sayayya yayma Zinneerah ya kawo mata cike da damuwa. Bayan ya mata nasiha akan yanda zata kula da kanta yace ta bashi lambar mijinta koda ya tafine zai nemsa suyi magana ta waya. Shiru Zinneerah bata iya cemasa komaiba akan wannan magana. Ya sake mainaita mata, nanma shiru tai sai hawaye dake gudu a kumatunta.          Ƙyaleta Khalipha yayi, dan a tashi fahimtar kawai ta bashi cewar Zinneerah kodai rabuwa tai da mijin nata kokuma bata buƙatar ana alaƙantata da shi bisa wani dalili na ɓacin rai. Dan haka ya ƙyaleta kawai saboda ya amsa lambar Naziru. koma miye zai dinga ji daga garesa kawai.       Haka dai Khalipha yay mata sallama ya wuce ya batta da kukan zuci. Dan hatta Maman Halima da bata daɗe da saninsaba yaron da halayensa sun sakashi shiga ranta sosai.       Dalilin tafiyar Khalipha gaba ɗaya yinin ranar a rashin daɗin rai Zinneerah tayisa a asibitin, harma tanaji ta ƙagara a sallamesu gobe idan ALLAH ya kaimun, gara taje gidan maman tata taji nata dalilin itama na guje mata datai ta barta cikin wahalar rayuwa..          Haka dai a daddafe suka kai washe gari, inda ALLAH ya taimakesu aka basu sallama tunda safe. Dan haka Nasiru yazo ya kwashesu dan yakai gidan yayan nasa inda mahaifiyar Zinneerah ke rayuwa a yanzu matsayin gidan aurenta..............✍          *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* *_Page 10_* ________________________ *_Hummmmm!!. Wai wai wai, wani aiki sai: GIDAN ƘAMSHI💃🏻💃🏻💃🏻🥺_* *_INA MATA ƳAN ƘWALISA MA'ABOTA SON ƘAMSHIN GIDA DANA JIKI?_* *_INA MATAN DAKAN SO DUK INDA SUKA DOSA KO SUKA BARI SAI SUN BAR MUSU TARIHIN ƘAMSHINSU_* *_TO MATAN ƘWARAI KUZO GA WANI SIRRI DAZAN BAKU DAGA FITACCEN GIDAN ƘAMSHIN NAN DA BAIDA NA BIYU A KANON DABO😁_* _Ina magana ne akan GIDAN ƘAMSHI da ke a Jihar KANON DABO MAIDUGURI ROAD MARIRI_. *MUNA SIYAR DA TURARURRUKAN WUTA SET NA AMARE, MUNA KUMA BADA SARI.* *AKWAI KUMA SABULUN GYARAN JIKI MAIDA TSOHUWA YARINYA, BUDURWA TAURARUWA, MATAN ƘWARAI ANNURIN HASKAKA GIDA. SHIMA DAI AKAN SARI, DOZIN KO KATON* *AKWAI KUMA ZUMAR ƘARA ƘIBA GA MATAN DA KESON SU GANSU DUMURMUR SUNA JUYAMA OGA KAYAN...😉🙈💃🏻 kundai gane*. *_Mata ku garzaya GIDAN ƘAMSHI domin ƙamsasa kanku kuma kar aci kasuwar sama babu ku😁_* *ZAKU IYA SAMUN MU TA WANNAN LAMBAR WAYAR: 07033778564 DOMIN JIN ƘARIN BAYANI*. *KO A KANO MAIDUGIRI ROAD MARIRI*.💃🏻💃🏻👍🏻 ______________________ *Page 10* ............Tunda suka iso gidan Zinneerah keta kalle-kalle. Basai an faɗaba a ganin gidanma kasan mahaifiyar tata yanzu kam tai gaba, kuma tana cikin jin daɗi da kwanciyar hankali. Bawai ƙaton gida baneba irin na masu kuɗi, babbane dai kam amma gini irin na mai rufin asirin ALLAH. Dan da Alhaji Bashir Ɗanmusa kam yayi kuɗi sosai, sai dai daga baya ya fuskanci ƙalubalen karayar arziƙi, tun daga nan ne dai har yanzu bai koma yanda yake daba, amma ko a hakan Alhmdllh dan yana iya ɗaukar nauyin komai na gidansa harma ya taimakawa ƴan uwa da maƙwafta. Hatta da motar da Nasiru keja a yanzu haka shine ya siya masa ita. Sannan duka ƴaƴansa suna karatu gwargwadon ƙarfinsa danshi mutumne maison ganin zuri'arsa ta samu ilimin addini dana zamani.         Zinneerah ta samu tarba maiba mamaki a gidan na kawunta, kuma mijin mamanta. Hakama yaran gidan duk da ba saninsu tayiba suma basu santaba sunzo sun zagayeta sunata kallo. Bata wani sake da kowa ba dan har yanzun damuwar tafiyar Khalipha bata saketa ba. Tanajin raɗaɗi da zafi a ranta wanda ita kanta batasan dalili ba.       Duk da a yanayin da take na rashin sakin jiki hakan bai hana Mama Sadiq nuna zumuɗin ganintaba, danma tana ɗan kawaicine wa Maman Halima kasancewar Zinneerah ƴar fari ce, sannan kuma yanda Maman Haliman ke nuna kara ma ta cancanci a ɗaga mata ƙafa ai. A yanzu hakama duk da tare suka dawo a ɗakinta ta sauketa. Sai dai an kawo kayan Zinneerah ɗakin Maman Sadiq ɗin alamar anan zata zauna.        Da ƙyar Maman Halima ta lallaɓa Zinneerah taci abincin da Maman Sadiq ɗin ta tarbesu da shi, bayan ta ɗan tsatstsakura aka kaita tai wanka, tare da bata kaya sabbi fil da Maman Sadiq ɗin ta ɗiɗɗinka mata a ƴan kwanakin nan gudun kar'a sallamosu tazo babu sitirar da zata saka, dan a yanzu haka gidan nasu ƴammatan dake sa'annin Zinneerah duk ƴaƴan Saude ne, Saude kam ba bari zatai su bama Zinneerah kayaba, ballema yaran suma sun rigada sun haddace karatun uwarsu suma kishi suke da su, danma sunajin tsoron ubanne, suma kansu su Maman Sadiq ɗin kuma basu basu fuskar rainiba suna ɗan shakkarsu.          A zahiri Maman Sadiq cike take da murnar kusantowar ɗiyar tata kusa da ita duk da batasan dalilin barowarta gidaba har yanzun. sai dai ƙasan ranta cike yake da fargabar yanda Zinneerah taƙi sakin jikinta ita. Haka dai ta daure ta danne damuwarta a ƙasan zuciyarta bayan sallar isha'i da Zinneerah ta dawo ɗakin nata bisa rakkiyar Maman Halima. Alhaji yayi tafiya, hakama Saude bata gidan, tana can gidansu bikin ƙanwarta akeyi, yaran natama suna dawowa Islamiyya da yamma yau suka bita can. Dan haka gidan ya kasance daga ita Maman Sadiq sai Maman Halima. Sai yaran Maman Sadiq uku duk maza ƙannen Zinneerah data haifa anan. Abubakar Sadiq, Abdul-Salam, sai Aliyu auta. Itako Maman Halima yaranta duk matane, huɗu sunyi aure ma, sai biyu yanzu a gabanta ƴan biyune sa'annin Sadiq. Sai itama Saude nada biyar, yanzu haka akwai ƴammata biyu da suka isa aure, sai ɗaya zasuyi kusan sa'a da Zinneerah, da ƙannensu biyu ƙanana suma kusan sa'annin su Sadiq ɗin dai.       Sosai Saude take kishi da Maman Sadiq saboda tazo gidan ta haifi ƴaƴa maza su basu haifaba, taso su haɗe kai da Uwargidan da suke kira maman Halima amma taƙi, dan dama itama ɗin can ba zaman lafiyarne a tsakaninsuba, to mizaisa ta yarda su haɗe su cuci wani bayan ALLAH shine mai badawa. Kuma koda Maman Sadiq tazo gidan batazo musu da raini ba, su duka girmamasu takeyi dan mace ce mai sanyin hali, sai dai idan ka ƙureta kam zaku kwasa da ita. Shiyyasa duk haukan da Saude zatai a gidan ko kallonta batayi, sai idan ta kaita maƙurane ta yaɓa mata maganar da zatai kwana da kwanaki tana damunta a rai.....          Numfashi Maman Sadiq taɗan sauke da duban Zinneerah dake a takure gefe tana magana dasu Sadiq  dake zagaye da ita a hankali. Tanajin misu Sadiq ɗin ke faɗa, amma batajin na ita Zinneerah ɗin. Gashi kuma ta duƙar da kai bata ko kallon sashen da take.       “Abdul!”. Ta kira sunan yaron nata na tsakkiya da yafi kowa ƙiriniya a yaran, dan a yanzu haka kusan rabin jikinsa na manne da na Zinneerah ne, gashi dama suna kamanni sosai da ita.      Kansa ya ɗago ya dubeta, “Na'am Mama”.       “Ku tashi aje ai shirin barci hakanan, duk kabi ka katantaneta bakaga halin da take ciki bane”.     Baki yaron yaɗan tura gaba da faɗin, “Ayya mama ki barmu muyi barci tare da ita, muna sonta sosai”.       A karon farko Maman Sadiq taga Zinneerah ta saki murmushi tana shafa kan yaron, sai dai bataji mita faɗaba sai da yaran suka haɗa baki wajen cewa, “Muma ai muna sonki sosai” ne ta gane cewa tai tana sonsu itama.       Murmushi tayi tana maijin daɗi da farin ciki a ranta, ta sake faɗin, “Karku damu ai tana nan tare da ku babu inda zata, kuje ku kwanta akwai islamiyya gobe idan ALLAH ya kaimu”.      Badan sunso ba sukaima Zinneerah sallama suka nufi ɗakin barcinsu. Shiru falon yayi na tsahon mintuna. Ita dai Maman Sadiq kallon Zinneerah ɗin takeyi cike da nazari, itako kanta a ƙasa tana wasa da zanen carpet ɗin dake shimfiɗe a falon.       “Zinneerah.” Ta kira sunanta cike da rauni.      Karon farko Zinneerah ta ɗago ta dubeta, sai kuma taɗan risinar da idonta. Murmushi mai ciwo Mama tayi, ta sake faɗin, “Taso ki dawo nan”.     Babu Musu Zinneerah ta miƙe zuwa gareta. Sai dai kamar bazata zauna inda ta nuna mata ɗinba, sai kuma mita tuna oho ta zauna a hankali gab da Maman nata. Mama dake cigaba da kallonta ta riƙo hannunta cikin nata tana gyara zama da fuskantarta sosai. Hakanne ya saka Zinneerah maida kanta ƙasa idanunta na cika da ƙwalla.       Itama Mama idanun nata cike suke da ƙwallan, cikin rawar murya tace, “Kiyi haƙuri Zinneerah, kiyi haƙuri kiyi haƙuri. Na fara da baki haƙuri ne saboda dalilai masu yawa. Nasan har ranki kina kallona ne matsayin uwa gareki mara adalci. wadda ta wofantar da ke ta manta da rayuwarki. Wlhy Zinneerah ba hakan baneba. Ni mahaifiyarki ban taɓa mantawa dakeba koda na daƙiƙa guda. A kowane sakanni kina maƙale a raina da zuciyata. Hawayena basu taɓa jinkirin fitowa ba a duk sanda na tunaki. Duk wanda ke tare dani yasan hakan Zinneerah. Nisantarki da nai itace babbar jarawar da har yanzu na kasa cimmawa wajen cinyeta, sai dai Alhmdllh, tunda yau gani gaki a yanda ban taɓa tsammataba ko tunani. Inason ki daure ki cire komai a ranki ki saki jiki dani ko hakan zai ragemin raɗaɗin ciwon gyanbon dake maƙale a zuciyata kinji”.         Hannu Zinneerah tasa ta share hawayen dake sakko mata daga idanu zuwa kumatu, cikin rawar harshe tace, “Amma miyasa baki taɓa zuwa gareniba mama”.      Murmushi Mama tayi itama tana sharar nata hawayen. “Zinneerah bana cikin hayyacinane, koda na baro ƙauyen Danya a yanayin ciwon hauka na barosa, sai dai Alhmdllh ALLAH ya taƙaitamin wahala maimakon na nufi wani waje saina nufi gida. Bayan isowata gida ƴan uwana sunje har Danya danjin miya faru dani amma mahaifinki yaƙi saurarensu, yama nuna bai sansuba baisan daga ina suka fitoba. Asabe kuma taci musu zarafi da musu korar kare. Duk da sunji zafin abinda akai musu sun buƙaci tahowa dake dan a gida na barki ni. amma mahaifinki ya hanasu, yama ɗora musu da cin zarafin dayafi na farko. Wannan shine dalilin yin fishinsu, amma basu haƙura akan wataran zasu amsoki ba. Ansha fama wajen nemamin magani sosai,  har takai mai gidannan dake a matsayin yayana yaje Ɗanmusa yaga halin da nake a ciki, shine ya fahimci sihiri ne tattare dani. Shine yasa aka kawoni nan kano wajen wani mutumi mai bada magungunan musulinci. Ya kashe kuɗi bana wasaba wajen ganin hankalina ya dawo tare dani, bayan wani tsahon lokaci aka dace na samu lafiya. Daga nanne ya nema aurena. Duk da banso hakanba aka tirsasani harna amince. Sosai kina maƙale a raina tunda na dawo hayyacina Zinneerah, sai dai bansan miyasaba ko sha'awar nufar hanyar Danya banayi, kai hasalima duk sanda nai yunƙurin son naje sai ciwona ya motsa min. Ƴan uwana kam bansan daliliba kowa ya bar zancen amsoki ko zuwama inda kike. Hakan na damuna a cikin rai, amma inajin kunyar yima wani magana ace na zaƙe da yawa, amma kiyi haƙuri Zinneerah ki yahe mani kinji”.         Kuka sosai Zinneerah keyi fiye da farko. tausayi da ƙaunar mahaifiyarta na sake shigarta cikin jiki da ɓargo. sun daɗe a haka kafin Mama ta koma lallashinta da tambayarta abubuwa game da rayuwarta da Inna Asabe.       Wani takan bata amsa, wani kuma takanyi murmushi ne kawai, hakan yasa Mama sake fahimtar ɗiyar tata tasha wahalar rayuwa kamar yanda tasani Asabe zama tayi fiye da haka. Dan ko ita ba daɗin zama taji da itaba a tsahon shekarun da sukayi tare na zaman kishi.       Yanda Mama bataima Zinneerah zancen ciki ba itama Zinneerah batace komai game da cikinba. Ganin dare yayi Maman tace ta taso taje ta kwanta haka nan.          Yau kam Mama da Zinneerah sunyi barci ne a gado ɗaya, hakan ba ƙaramin farin ciki da jin daɗi ya saka Zinneerah ba, har takaita da shagala dogon tunani akan abinda ke a cikinta itama. Mace ne ko namiji bata saniba. Wanene mahaifinsa yaya aka samar dashi bata saniba, wace amsa zata bashi taba mutane da mahaifiyarta game dashi bata saniba. Ta shafa cikin tana sakin wani murmushi mai ciwo da saka ƙunar zuciya, daga haka barci yay awon gaba da ita mai cike da mafarkin Khalipha. *WASHE GARI*           A yau kam Zinneerah ta sake tabbatarwa ashe itama mutum ce mai daraja kamar kowa, dan yanda ƴan uwanta da Mamanta suka kasance da ita ya jefa zuciyarta cikin matsanancin farin ciki. Kowa burinsa yaga dariyarta a gidan, ko yaya tai ɗan shiru sai ance mata mike damunta?. Abinci kam saita zaɓa wanda ranta keso ake bata taci.         Dawowar maigidan kuma aka sake ninka tattalin da ake mata, dan shima da aka kaita ta gaidashi bayan yaci abinci ya huta janta yay tayi da hira cikin kulawa, tun tana ɗan noƙewa bata iya amsawa harta saki jiki dashi ta fara amsa masa. Ta jima a wajensa tare da sauran ƙannenta kafin ta dawo sashen Maman Sadiq suka cigaba da shirmensu ita da ƙanen nata.       Haka rayuwa ta cigaba da yima Zinneerah daɗi a gidan mijin mamanta kuma kawunta, a hankali tana sakin jiki da kowa da komai nagidan. Har zuwa yau kuma da zata cika kwanaki uku babu wanda yay mata tambaya akan cikin jikinta balle jin ba'asin sanin inda ubansa yake. Itakuma bataima kowa maganaba dan addu'arta bai wucema ace kowa yaƙi tambayar tataba tunda batasan wace amsa zata basunba.         Yau ma duk suna zaune tsakar gida gab da magriba, tunda yaran suka dawo daga islamiyya anan suka yada zango inda suka sameta tana gurzama Maman Halima kuɓewa da zatai miyar tuwon dare. Anan suka shiririce bata labari tana musu dariya da biye musu kamar yanda ta saba.       Ƴammata ne biyu suka shigo gidan da sallama a bakinsu ciki-ciki. Sai ƙananu biyu dake biye dasu da ledoji a hannu. Idanu Zinneerah ta zuba musu kawai dan bata sansuba, hakama sauran yaran kallonsu kawai suke babu wanda yay magana. Sai Aliyu ne cikin tsalle yake faɗin, “Gasu Zainab gasu Luba”.           Ko kallon inda Aliyun yake basuyiba suka nufi ƙofar ɗakin uwarsu, dai-dai Maman Sadiq na fitowa ne uwar tasu ta shigo itama da ɗayar yarinyar da zasuyi sa'anni da Zinneerah. Cike da fara'a a fuskar Maman Sadiq ta shiga faɗin, “A'a ƴan bikine tafe. Sannunku da zuwa”.       A ɗan yatsine Saude da suke kira Maman Sakina ta amsa idanunta akan Zinneerah ko ƙyaftawa batayi. Ganin kallon ƙurillar da take matane ya saka Zinneerah faɗin, “Sannu da zuwa ina yini”.      “Lafiya” tace kawai tana nufar ƙofar ɗakin nata itama.      (Ashe tsugunne bata ƙareba kenan) Zinneerah ta ayyana a ranta zuciyarta fal tunanin waɗannan kuma daga ina?. Bata da mai bata amsa, dan haka ta miƙe dan ganin lokacin sallama yayi gashi wasu masallatan har an fara kira.        Alwala tace su Sadiq suje suyi su tafi massallaci, ita kuma suka shige sashen Maman Halima ita dasu ƴan biyu domin gabatar da tasu sallar. Daga haka bata sake jin ɗuriyar Saude da ƴaƴanta ba a gidan, bakuma ta tambayaba har suka gama hira ta miƙe ita dasu Abdul suka nufi sashen mahaifiarsu dansu kwanta.      Washe gari da safe bayan sallar asuba gari yay ɗan sha suka tafi gaida mutanen gidan kamar yanda Maman ta horesu. Sashen Alhaji suka fara zuwa wanda yaran gidan ke kira da Abba. Yana zaune a falonsa madaidaici da redio a hannunsa da alama kunnawa zaiyi, shigowar tasu ya sakashi ajewa yana dubansu da kulawa. Aliyu yaje jikinsa ya zauna, suko duk suka durƙusa a ƙasa suna gaidashi. Da fara'a yake amsa musu yana shafa kan Aliyu, ya ɗan duba Zinneerah da kanta ke a ƙasa, “Ɗiyata ya jiki-jikin?”.        Takanji kunya idan sukai mata tambaya akan jikinta, ta ƙara ƙasa da kanta da cemasa “Alhmdllh Abba”. “Masha ALLAH ai haka akeso, ALLAH ya saukeki lafiya”. Daga haka ya maida hankalinsa kan Aliyu.        Itace ta fara miƙewa, sauran yaranma duk suka miƙe suka fito a tare. Suna gab da shiga sashen Maman Halima Aliyu ma ya iso garesu da gudu yana faɗin, “Aunty! Kinga kuɗin makarantana Abba ya bani”. Juyowa Zinneerah tai tana murmushi, tace, “kace ka gode ko?”. Kansa ya kaɗa mata yana riƙo hannunta suka ƙarasa shiga sashen Maman Halima itama.          A falo suka isketa tanama Hussaina faɗa akan zubar da suga da tai ƙasa, ganinsu ya sata dubansu tana murmushi. Itama har ƙasa suka durƙusa gaisheta, ta amsa musu da fara'a da kulawa tana tambayar Zinneerah yaya jikinta. Nanma dai cike da kunya ta amsa kanta a ƙasa. Sunɗan jima anan fiye da sashen Abba. Daga haka suka shiga na Maman Sakina..         Suma dai a falon suka samesu sunata hayaniya, dan ɗakinta yafi na kowa yawan yara a gidan. Yanda suka wani watsoma Zinneerah idanu gaba ɗayansu har uwar sai duk taji ta muzanta. amma haka ta daure takai ƙasa tana gaida Maman Sakina ɗin. A ɗan yatsine ta amsa mata. Carab Luba dake kwance a kujera ta miƙe idonta akan Zinneerah. “Tab ɗi jan, jama'a wai kuna ganin abinda nake gani kuwa? Wai wannan ƴar yarinyarce da ciki”. Kusan a tare suka sheƙe da dariya, Sakina tace, “Kinsan ƴan ƙauyen nan sai a hankali, amma dubetafa sa'a tace, koma na girmeta kamar”. Cikin taɓe baki uwar tace inako sukaga hankali, ai kamar dabbobi suke basu banbance komai sai shirme. Nanma dariyar suka kwashe dashi su duka harsu Zainab ƙananu.        Tsam Zinneerah ta miƙe daga durƙuson da tai batare da tace komaiba ta kama hannun Aliyu suka fito zuwa sashen uwarsu.        Suna shigowa Abdul ke faɗama Mamansu abinda akaima Auntynsu a sashen Maman Sakina. Wai su Sakinar ne ke dariyar Zinneerah ƴar ƙarama da ita tanada ciki. Shine mamansu tace wai ai kusan mutanen ƙauye ba hankaline dasuba kamar tumaki suke. Ran maman Sadiq ya ɓaci, amma saita shanye bata nunaba. Hasalina batace komaiba ta cigaba da haɗa musu abin karin da takeyi. Itama Zinneerah komai bataceba tamayi kamar ba a gabanta akai abinba.      Bayan sun kammala karyawan ne Zinneerah tahau gyaran ɓangaren kamar yanda ta saba tun zuwanta gidan, su Sadiq kuma suka shiga shirin tafiya Islamiyya dan suna hutun boko. Tsaf ta gyara ko ina ta saka musu ƙamshi, ganin komai ya mata tsaf yanda takeso sai taje itama tayi wanka. Ta fito tana cikin shiryawa Mama ta shigo ɗakin.         Sai da ta ƙarasa abinda takeyine Mama tace, “Zauna magana nazo muyi”. Zama Zinneerah tayi inda Mama ta nuna mata babu musu, Mama taɗan sauke numfashi tana dubanta, itako kanta a ƙasa tamkar ko yaushe.        “Zinneerah!”. Maman ta kirayi sunanta a karo na farko. Batare data ɗagoba tace, “Na'am mama”..          “Zinneerah tun zuwanki gidannan nake jiran naji miya baroki da gida? Amma shiru bakice dani komaiba. Ya kamata nasani ai, sannan nasan kuma  ta yanda zamu nema mijinki shima dan yasan inda kike ko hankalinsa zai kwanta, tunda nasan duk inda yake kodan cikin dake jikinki basai samu nutsuwar zuciyaba”.        Yawu Zinneerah ta haɗiye da ƙyar wani abu na tattarowa a ƙirjinta. Ganin taƙi magana Mama tace, “Ke nake saurare”.        Maimakon amsa sai kawai Zinneerah ta saka mata kuka. Idanu kawai Mama ta zuba mata kamar yau ta fara ganinta, bata kawo komai a rantaba sai tunanin harda matsalar mijin ƙila ta barota da gidan.        “Abinda ya faru ya riga ya faru, dan haka kuka baida wani amfani a yanzu. Ki sanarmin nasan madafar kamawa wajen samo mafita”.        Yanda Mama tai maganar babu wasa ya saka Zinneerah bata amsa cikin dauriya da matsanancin tsoro. “Nima bansan ya akai na baro gida ba, nawayi garine kawai naga kaina a asibiti”            “Nikam ban fahimceki ba, sai kimin bayani dalla-dalla”. Mama ta faɗa tana tsareta da idanu.      Maimakon amsa sai hawaye Zinneerah ke faman sharewa. Shigowar Alhaji ya hana Mama sake cewa komai...........✍      *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍   *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* *page 11* ________________________ *_Hummmmm!!. Wai wai wai, wani aiki sai: GIDAN ƘAMSHI💃🏻💃🏻💃🏻🥺_* *_INA MATA ƳAN ƘWALISA MA'ABOTA SON ƘAMSHIN GIDA DANA JIKI?_* *_INA MATAN DAKAN SO DUK INDA SUKA DOSA KO SUKA BARI SAI SUN BAR MUSU TARIHIN ƘAMSHINSU_* *_TO MATAN ƘWARAI KUZO GA WANI SIRRI DAZAN BAKU DAGA FITACCEN GIDAN ƘAMSHIN NAN DA BAIDA NA BIYU A KANON DABO😁_* _Ina magana ne akan GIDAN ƘAMSHI da ke a Jihar KANON DABO MAIDUGURI ROAD MARIRI_. *MUNA SIYAR DA TURARURRUKAN WUTA SET NA AMARE, MUNA KUMA BADA SARI.* *AKWAI KUMA SABULUN GYARAN JIKI MAIDA TSOHUWA YARINYA, BUDURWA TAURARUWA, MATAN ƘWARAI ANNURIN HASKAKA GIDA. SHIMA DAI AKAN SARI, DOZIN KO KATON* *AKWAI KUMA ZUMAR ƘARA ƘIBA GA MATAN DA KESON SU GANSU DUMURMUR SUNA JUYAMA OGA KAYAN...😉🙈💃🏻 kundai gane*. *_Mata ku garzaya GIDAN ƘAMSHI domin ƙamsasa kanku kuma kar aci kasuwar sama babu ku😁_* *ZAKU IYA SAMUN MU TA WANNAN LAMBAR WAYAR: 07033778564 DOMIN JIN ƘARIN BAYANI*. *KO A KANO MAIDUGIRI ROAD MARIRI*.💃🏻💃🏻👍🏻 _______________________ *Page 11* ............Alhaji dake dubansu yace, “Lafiya kuwa naga tana kuka?”.        “Humm lafiya ƙalau wlhy, daga tambaya fa shine sai kukan nan. Gani nai ya kamata musan matsalar data barota daga gida. Idan ya dace mu nema mijinta saimu nemesa kuma”.        Murmushi Alhaji yayi yana zama a kujera, cike da nazarin Zinneerah yace, “Uhm inaga bata wannan hanyar ya kama mu saniba Hauwa'u, ki barta kawai ta huta dan yanzun farin ciki da kulawarmu tafi buƙata. Sauran maganar idan na dawo zamuyi ni da ke”. Bai jira amsar Maman Sadiq ba ya maida dubansa ga Zinneerah dake kuka har yanzu.      “Ɗiyata kinga share hawayenki kinji, banason na sake ganin kinyi kuka a gidan nan dan ALLAH. Ki fahimci mamanki kuma, batai miki wannan tambayar bane danta ƙuntataki. Wannan shine halin girma daya kamata kowacce uwa ta nuna ga matsala irin wanna. Ina fatan kin fahimceta”.      Kai Zinneerah ta ɗaga masa alamar eh.       Yace, “Alhmdllh, to share hawayenki kinji, ki kuma saki ranki a gidan nan dan baki da maraba da sauran yaran gidan, ALLAH yay miki albarka ya saukeku lafiya. Mikikeso na sayo miki idan zan dawo?”.      Ƙasa Zinneerah ta karayi da kanta cike da girmamawa da ƙaunar wannan bawan ALLAH.      Shima sai ya miƙe yana murmushi, “Shikenan tunda kin kasa faɗa, kafin dai na taso ki faɗama mamanki saita kirani a saya miki komi kikeso ɗin”.       “Nagode Abba, ALLAH ya tsare ya bada sa'a”.      Murmushi ya sakeyi cike dajin son yarinyar a ransa. Ya amsa idonsa akan matarsa. ___________________★          Tun daga wannan ranar babu wanda ya sakema Zinneerah magana akan sanin uban cikin jikinta da dalilin barowarta gida. saima kulawa ta musamman da Maman Sadiq, Abba, Maman Halima suka sake ninka mata. Koyaya aka ganta a damuwa sai anbi ba'asinta domin son kauda mata. Duk da Maman Sadiq na kawaici a kanta cikin hikima take jan abarta a jiki idan sun shige ɗaki, hakan yasa shaƙuwa mai ƙarfu ke sake shiga tsakaninsu, tana sake sakin jikinta sosai kuma. hakama ƙannenta idan ka gansu saika ɗauka dama can tare suka tashi.       A wajen ƴaƴan Maman Sakina (Saude) ne kawai Zinneerah batajin daɗi da ita kanta Sauden. Dan ko ranar girkinta bacin Maman Sadiq nakai zuciya nesa da sun dinga tafka rigima akan abincin da ake zubama Zinneerah ɗin. Amma sai bata cewa komai ta barta da halinta. Tadai gargaɗi Zinneerah ɗin akan koda wasa karta shiga hurimin Maman Sakina da ƴaƴanta inhar ya wuce gaisuwa da girmamawa. Sannan duk wanda zai sakata aiki a gidan tai masa indai ya girmeta.      Dayake Zinneerah ɗinma bamai kwaramniya bace sai tabi huɗubar mahaifiyarta aka zauna lafiya. Dan duk da cikin dake tare da ita da gadara Maman Sakina ke sakata aiki a gidan, itako babu musu takeyi koda batajin daɗin jikinta. Saima idan Maman Halima taga abin yayi yawane takanyi magana kota hana Zinneerah ɗin. Haka yakan saka Maman Sakina taita masifa a gidan da gori tana kiran Zinneerah da suna agola kinfi masu gida.           Maman Sadiq bata taɓa tankawaba, bakuma ta taɓa gayama mai gidanba. Ta kuma roƙi Maman Halima akan karta faɗa itama, dan tasan duk dai iya zaman Zinneerah a gidan naɗan lokacine kafin ta koma gidan mijinta.      Haka kwanaki suka cigaba da shuɗawa Zinneerah na rainon cikinta dake bata wahala. dan bata taɓa ƙulla kwana biyu babu ciwo. Sai dai yanda cikin ya fito ɗas a jikinta ba ƙaramin ƙyau yasa tayi ba. Gashi tana samun kulawa sosai yanzun.        Dan hatta da zuwanta asibiti Naziru ke zuwa ya kaita kamar yanda Khalipha ya bar masa sallaho. A ranar farko da suka fara komawa asibitin domin ganin likita Zinneerah ta samu damar ƙare masa kallon tsaf bayan ta karanta sunan asibitin tun daga waje. *_SHIRA HOSPITAL_*.        Sosai take jinjina ƙoƙarin maginin wannan asibiti, dan yayi ƙyau sosai kuma an zuba masa kayan aiki bana ƙaramin kuɗiba. Ga likitoci ƙwararru da basa wasa da aikinsu kuma babu wulaƙanci. Sai dai abinda ke matuƙar bata mamaki yanda asibitin yay matuƙar haɗuwa zaka ɗauka sai wane da wane ne masu iya shigarsa neman lafiya, amma saika shigo ciki kai gamo da masu karamin ƙarfi bila-adadin suna amsar magani hankalinsu kwance.      Samun damar ganin likita akan lokacine ya katse mata dukkanin tunaninta. Sai dai yanda aka karɓesunne ya sake bata mamaki, amma jin zancen Khalipha a bakin likitan kuma sai ta fahimci a dalilin shine ake mata wannan tattalin da kulawar. An bata magungunan da suka dace da ita, tare da sake gargaɗinta akan daina duk wani aiki dan cikin jikin nata yana buƙatar hakan saboda ƴar matsalar da suka hanga tattare da shi.     Ƙuruciya tasa batako damuba suka dawo gida. Sai dai bayanin da Naziru yayi na maganar kula da hutun nata a gaban Yayansa da bai kai ga fitaba yasa Abba gargaɗin kowa na gidan akan yasa ido kar Zinneerah ta sake wani aiki. Baki maman Sakina ta taɓe cikin ƙunƙuni take fadin, ‘Wayaga agola kinfi ƴaƴan gida’.         Babu wanda ya tanka sai shi Alhajin ne ya dubeta rai ɓace, “Saude mikike faɗa?”.        A zabure ta mike tana yarfar da hannaye da tafasu, “A'a kaga Alhaji bance komaiba nikam, karkuma a bugamin gangar ɗan bazakuɗa babu gaira babu sabar”.      Daga haka tabar wajen fuuu. Ƙwafa yay kawai batare da yace komaiba.        Tun daga wannan zuwan sai yazam Naziru kanzo ya kaita asibitin ganin likita kamar yanda akan rubuta musu.        A kwana a tashi babu wahala wajen UBANGIJI sai ga cikin Zinneerah ya shiga watanni na takwas. Zuwa yanzu ta saki jikinta sosai a gidan, musamman ma da mahifiyarta da kannenta dake faɗaɗa farin cikinta a koda yaushe. Idan ka ganta bazaka taɓa dauka ita bace, bakinta ya buɗe sosai alamar dama can rashin samun ƴancin kai ke sakata zama mai sanyi. Ita kanta maman Sadiq har mamaki take a ranta dama Zinneerah nada surutu haka? Ta tabbatar nan gaba idan ta sake warwarewa sai tafima haka kauɗi. Danma lalurar cikin kanɗan taƙaita mata wasu abubuwan.          Duk da waɗanan sauye-sauye da Zinneerah ta samu a rayuwarta hakan baisa ta manta da Khalipha a rantaba. Koda yaushe yana nan maƙale a ranta, wani lokacin har mafarkinsa takeyi, kota zauna zugum tana tunanin yaushene zai sake dawowa gareta ne ko dan ta masa godiya akan ɗawainiyar da yayi da ita?. Idan kuma Naziru yazo gidan har ALLAH ALLAH take taji yace Khalipha na gaisheta, dan yana kiransa lokaci-lokaci idan ya samu dama. Sai dai bai taɓa cewa a haɗasuba dan shi duk zatonsa tanada aure ne.        Yauma kamar kullum suna baje a falon Mamansu suna cin gyaɗa dafaffe da Zinneerah ta ƙwallafa rai sai da aka sayo aka dafa mata, kallo suke suna kwasar dariya. Maman Sadiq dake ciki tana shirin tafiya sashe Alhaji ta fito falon da kwalliyarta. Kallon yanda suke cikin nishaɗi tayi daɗi da farin ciki na ratsa ranta itama. Ta ɗauki tiren data shirya abincin Alhajin tana faɗin, “Zinneerah tashi ki tura muku ƙofar ni zanje na kaima Abbanku abinci, idan kunji barci kafin na dawo kimasu Aliyu addu'a karsu kwanta babu addu'a. Wannan sarkin fitsarin Abdull ki tabbatar ledan katifan bata zameba a inda zai kwanta. Ga kuma magungunanki nan kisha kema kafin ki kwanta”.        “To mama sai kin dawo”. Ta faɗa fuskarta washe da murmushi. Suma sauran yaran duk adawo lafiyar sukai mata ta ɗauki tiren ta fice. Yayinda Zinneerah ta saka Sadiq zuwa ya tura ƙofar suka cigaba da kallonsu.      A can ɓangaren maman Sadiq ko bayan Alhaji yaci abincinsa ya ƙoshi take dubansa da damuwa. “Yaya dan ALLAH karkace na takura, baka ganin kuwa ya dace mijin yarinyarnan yasan wani abu game da ita”.       Murmushi Alhaji yayi na manya. Ya gyara zamansa da cewa, “Eh kina kan gaskiyarki Hauwa'u, nima bawai hakan baya raina bane. Dama inason dai ta gama sakin jikintane sosai ta manta da duk wani ɓacin ran da yabarota daga gidan sannan. A yanda kuma nake tunani bata wajenta ya kamata muji komaiba. Nine zan shirya da kaina naje Danya ɗin domin ganawa da Baban nata da Mijinta. Kinga idan mun samu bakin zaren saimu yanke hukuncin daya dace. Dan indai ba rabuwa tai da mijin nataba tofa sai dai yasan mai yuwuwa”.         Murmushi kawai taɗanyi, “To duk hukuncin daka yanke ai shine dai-dai Yaya. ALLAH yay mana jagora”.      “Amin” ya faɗa yana maijin daɗi a ransa na yanda duk ta sakar masa ragamar rayuwarta batare da jin ko ɗarba garesa.        ★★★ Bayan sati ɗaya dayin wannan magana Alhaji ya shirya zuwa Kusada ƙauyen Danya batare da sanin Zinneerah ba.         Kasancewar a ranar yaje ya dawo kuma bata san komai akaiba tunda tasan yana fita kasuwa dama. Abinda dai kawai ta fahimta ranar Mamansu ta kwana cikin wani irin yanayi na tsantsar baƙin ciki. Dan harta kai washe gari ma sai da aka kwantar da ita asibiti. Kwananta ɗaya aka sallamota ta dawo gida. Zinneerah ta shiga damuwa da ganin yanayin na mamansu daya kaita ga kwanciya asibitin. Amma sai rashin wayo ya hanata tambaya koda suka dawo. Kallo ɗaya zakai mata itama dai ka fahimci tana cikin damuwar.       Kusan kwanaki goma tana ganin Maman tasu a wannan bahagon yanayin, kafin kuma taga ta warware ta cigaba da harkokinta a gidan cike da ƙarfin hali.         Abinda Zinneerah bata saniba shine mummunan labarin da Alhaji yaje ya samo a garinsune yakai ga mahaifiyarta kwantawa asibiti saboda motsawar hawan jininta. Sai dai kamar yanda Alhaji ya gargaɗeta yin gum da bakinta kar Zinneerah da abokan zamanta susan wani abu game da cikin Zinneerah ɗin yasata shanye komai a rai ta fawwalama UBANGIJI ikonsa da amsar ƙaddara. Musamman daya kasance duk wanda Alhaji ya jiyo labarin cikin Zinneerah a bakinsa saida ya yabi kyawawan halayyarta da wahalar data dinga sha ga matar ubanta. Harma takai wasu na ganin Inna ce silar komai akan cikin na Zinneerahn.            Hakan yaɗan sake girmama danganarta ta shanye komai ko a fuska basu taɓa nuna Zinneerah sunsan komaiba daga ita har Alhaji. matan gidan kuma sun sanar musu cewar ashe mijin Zinneerah ɗinne ya mutu kawai, ruɗanin rasuwarne ya sata baro gida cikin gushewar hankali. Maman halima ta tausaya mata, Maman Sakina kuwa ko'a jikinta. saima ƙorafi data dingayi akan kenan an ƙara ma mijin nasu nauyi tunda dai nan Zinneerah zata cigaba da zama ita da abinda zata haifa.      Babu wanda yabi takanta dan idan da sabo kowa ya rigada ya saba da halinta a gidan ai.          Zinneerah ta cigaba da rainon cikinta aɗan tsakanin nan cikin rashin jin daɗin jiki, dan tunda ya shiga wata na tara komai ya sake mata wahala. Harma takai randa suka koma asibiti dole Doctor ɗin ya riƙeta akan zata cigaba da zama anan har saita haihu.      Hakan baima Zinneerah daɗiba. Amma yaya zatiyi tunda ance wannan ne samun sauƙi a gareta. Yanzunma dai Maman Halima ce tare da ita, sai Mamanta dakanzo duk bayan kwana biyu ta amsheta ita kuma taje gida ta huta. Abba kam babu fashi kullum sai yazo safe da dare dubata. Ko'a fuska bai taɓa nuna ƙyamar cikin jikintaba balle bakinsa ya suɓuta wajen faɗama matansa dalilin samuwarsa.        A randa ta cika kwana tara a sibitinne da Naziru yazo dubata yake faɗa mata kwana biyu bayajin Khalipha kwata-kwata. Yayi ƙuru ya gwada kiransa ranar kuma bata shigaba. ya tura masa saƙo babu reply har yanzun.        Murmushi kawai Zinneerah tai na ƙarfin hali batare da tace komaiba. Hakan yasa shima bai sake cewa komaiba akan batun.         Washe gari data cika kwana goma cif a asibitin jikinta ya ƙwaɓe ta fara zubar jini (bleeding). Hankalin likitocin ya tashi harma da su Maman Sadiq dan sun fahimci naƙudace tazo mata a bahagon yanayi. Tun suna ganin zata iya haihuwa da kanta har al'amarin yasoyin tsamari suka yanke shawarar mata cs kawai.      Babu wani ja'inja Abba ya saka hannu matsayinsa na uba gareta. Daga haka suka shiga da ita ɗakin theatre su kuma suka koma gefe suna mata addu'ar rabuwa lafiya da abinda ke a cikin nata.         Awa kusan uku Doctor Mansura ta fito fuskarta da murmushi. Duk miƙewa sukai suna mai sauke ajiyar zuciya ganinta a yanayi mai daɗi. Ta sake faɗaɗa murmushin da faɗin, “Alhmdllhi, an ciro baby boy ƙyaƙyƙyawan gaske, mai kuma lafiya insha ALLAH”.         Basu gaza wajen ambaton Alhmdllh ɗinba suma, dan sunyi imani akan duk abinda kaga UBANGIJI ya jarabceka da samu ta hanyar da kai baka buƙatarsa ya fika sanin dalilin yin hakan. Basu isa canja ƙaddarar Zinneerah ba komai son hakan da zasuyi, sai dai su tayata da addu'ar ALLAH yasa haka shine mafi alkairi. Duk da har cikin ransu suna tsananin tausayin uwar da ɗan.        Abbane yace, “Yaya jikin ita Zinneerah ɗin kuma?”        “A Alhmdllh Alhaji. Itama dai insha ALLAH komai zai dai-daita zuwa nan gaba kaɗan. Kuyi haƙuri sai zuwa anjima zaku samu ganinsu koma da safe”.        Godiya sukai mata. Ta wuce su kuma suka koma suka zauna kowa da abinda yake saƙawa a ransa.     ★★★      Kamar yanda likita Mansura ta faɗa basu sami ganin Zinneerah ba a ranar dai kam, sai dai zuwa yamma an fiddo musu da jariri ƙaton gaske kuma ƙyaƙyƙyawa kamar yanda Dr Mansura ta faɗa ɗazun.      Abba ne ya fara amsarsa yana mai yin godiya ga ALLAH tare da jin tausayin yaron da baisan wanene shiba. Bayan ya masa addu'a ya miƙama Maman Halima daketa faman washe baki. Tace, “Masha ALLAHU mijin nawa kam dai-dai ni. ALLAH ya rayaka ya albarkaci rayuwarka. Ya jiƙan mahaifinka kaji”.         Da amin suka amsa. Kafin ta miƙama Maman Sadiq dake kukan zuci. Bata musaba ta amsa itama ranta fal tausayin yaron dabaijiba bai ganiba. Ta ƙura masa idanu na tsahon lokaci zuciyarta na suya akan samuwarsa ta hanyar da ba ita sukai fataba. Sai dai a gefen zuciyarta na gargaɗinta da ambaton Alhmdllh. Dan babu maima UBANGIJI dole akan abinda yaso. Babu kuma mai sakashi saɓanin hakan.      Itama dai addu'ar tai masa tamkar kowa ta sake miƙama Maman Halima dake kusa da ita. Ita kuma ta miƙama Matar Naziru. Bayan sun gama ganinsa da masa addu'a Nurse Salima tazo ta amshesa tana faɗin, “To waye zai zauna a wajenta? Dan an kaita ɗakin hutu yanzu haka. Sai dai likita tace wadda zata zauna da ita kawai za'a kai sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu zaku ganta”.         Dukansu sun gamsu da hakan, kafinma kowa yay magana Maman Halima tace ai bama sai anja zanceba itace zata cigaba da zama da ɗiyarta.     Wannan karamcin na Maman Halima kesa Maman Sadiq jin daɗi sosai da sake ganin girmanta da kimarta a koda yaushe, dan mace ce data cancanci girmamawa kodan ƙyawawan halayenta.          Sallama tai musu tabi bayan Nurse Salima. Su kuma suka fito domin komawa gida. ★★         Koda suka shigo gidan Maman Sakina batako leƙoba balle ta tambayesu yaya jikin Zinneerah ɗin tunda batabisu asibitinba. Duk da kuwa sanda Matar Nasiru tazo ta sanar musu ruɗewar jikin Zinneerah ɗin itama tana zaune a tsakar gidan. Amma taƙi bin Maman Sadiq. Bayan tafiyarta kuma bata kira waya taji halin da ake cikiba. Gashi yanzu sun dawo bataleƙo tajinba kuma.       Hakan bai dami Maman Sadiq ba. Dan halin da take ciki ya wuce na matsalar Saude a yanzun. Tana shiga ɗaki fashewa tai da kuka, kamar Alhaji yasan za'ai haka ya biyo bayanta kuwa. Ganinta tsaye gaban mirror kanta a ƙasa tana shashshekar kuka ya sashi ƙarasowa cikin ɗakin sosai.        “Haba Hauwa'u, minene kuma abin kuka anan dan ALLAH? Kenan bazaki iya karɓar ƙaddaraba? Ki tuna UBANGIJI ya fimu sanin abinda ke a ɓoye. Sannan yarinyar-nan mutane da yawa sun shaideta akan ba yarinyar banza bace. Kowa na ƙyautata mata zaton cewar tsautsayine kawai da ƙaddara da babu wanda ya isa kankaresu a rayuwarta. A ganina yanzu kamata yayi mu sake nutsuwa da janta a jiki wajen samun gaskiyar zance game da samuwar cikin, dan a yanda na fahimci zantukan jama'a a inda taje kwana da kwanaki ba'a saniba acan koma minene ya faru. Ina son ki kwantar da hankalinki ki karɓi komai a mashayin ƙaddara da jarabawa. Karki bari yarinyarnan ko wani a gidan nan yasan gaskiyar zance gameda yaron nan saboda gudun matsala, kokuma ita mu sakata  a wani halin da har zata iya tunanin sake sulalewa ta gudu daga nan kamar yanda ta baro can”.      Cike da gamsuwa da bayanin mijin nata ta share hawayenta. “Nagode Yaya, nagode sosai da rufa asirina dana yarinyarnan. Lallai kaiɗin masoyine na gaskiya abin alfaharin kowacce mace. Insha ALLAH zanyi kamar yanda kace, sai dai ka tayani addu'ar jurewa wannan al'amari”.        “Insha ALLAHU zan tayaki Hauwa'u. kema kuma kisa a ranki zaki iya ɗaukar komai kamar yanda kika ɗauki na baya da suka shuɗe. Kuma in ALLAH ya yarda inhar yarinyar nan bata da hakki duk inda uban yaron nan yake sai ya bayyana kansa watarana. ALLAH kuma zai wanketa ga idon kowa da izininsa”.       “ALLAH ya tabbatar da hakan Yaya”.       “Amin” ya amsa yana juyawa ya fita. Itama saita sake share hawayen da ke sake zubo mata. Zuwa tai ta leƙa yaranta taga harsun kwanta. Dama tasan Sadiq akwai ƙoƙarin kulawa kamar yanda ta horesa. Ɗan gyara musu abinda baiyiba tayi ta fito. Bayan tayi wanka itam ta kimtsa zuwa ɗakin maigidan dan girkintane.      Sosai ya sake mata nasiha da tausarta akan komai, ya kuma sakata sukai salla da mikama UBANGIJI kukansu da bukatunsu. Sai gashi Alhmdllh ta wayi gari zuciyarta sakayau. Harma da jin zumuɗin komawa a sibitin taga halin da ƴarta ke ciki da baƙon duniya da baisan wanene shi ba.             A asibiti kam da daddare ansha rikici, dan ɗan jinjiri dai kuka ya dinga tsula musu na yunwa gabannin asuba. Haka dai Maman Halima taita ƙoƙarin bashi ruwan zam-zam da aka haɗa da zuma a ciki. Zinneerah kam tanata faman barci batare da tasan wace wainar ake toyawaba.        Koda suka tashi aɗan barcin daya figesu bayan lafawa da kukan jaririn sai maman Halima ta samu sun makara. Lallaɓawa tayi domin gabatar da alwala. Tana kabbara salla tamkar jira yake ya fara raira kukansa da muryarsa dake cauy-cauy masha ALLAH.       Sosai maman halima ta rikice, tana a raka'ar ƙarshe taji shigowar mutum cikin ɗakin, ba'ayi maganaba dai, sai wani irin ƙamshin turare mai shegen daɗi daya gauraye ko ina na ɗakin. Tana ƙoƙarin sallamewa taji an fice da jaririn da har yanzu kukan yakeyi. Saurin sallamewa tai ta miƙe zaram ta biyo bayansu. Wayam babu kowa a wajen, sannan babu kukan yaron kuma. Hankalintane yay masifar tashi sanin duniyarnan fa babu gaskiya a cikinta. A cikin matuƙar ruɗani ta shiga leƙe-leƙe na neman inda aka nufa da yaron..............✍             *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* *_Page 12_* ________________________ *_Hummmmm!!. Wai wai wai, wani aiki sai: GIDAN ƘAMSHI💃🏻💃🏻💃🏻🥺_* *_INA MATA ƳAN ƘWALISA MA'ABOTA SON ƘAMSHIN GIDA DANA JIKI?_* *_INA MATAN DAKAN SO DUK INDA SUKA DOSA KO SUKA BARI SAI SUN BAR MUSU TARIHIN ƘAMSHINSU_* *_TO MATAN ƘWARAI KUZO GA WANI SIRRI DAZAN BAKU DAGA FITACCEN GIDAN ƘAMSHIN NAN DA BAIDA NA BIYU A KANON DABO😁_* _Ina magana ne akan GIDAN ƘAMSHI da ke a Jihar KANON DABO MAIDUGURI ROAD MARIRI_. *MUNA SIYAR DA TURARURRUKAN WUTA SET NA AMARE, MUNA KUMA BADA SARI.* *AKWAI KUMA SABULUN GYARAN JIKI MAIDA TSOHUWA YARINYA, BUDURWA TAURARUWA, MATAN ƘWARAI ANNURIN HASKAKA GIDA. SHIMA DAI AKAN SARI, DOZIN KO KATON* *AKWAI KUMA ZUMAR ƘARA ƘIBA GA MATAN DA KESON SU GANSU DUMURMUR SUNA JUYAMA OGA KAYAN...😉🙈💃🏻 kundai gane*. *_Mata ku garzaya GIDAN ƘAMSHI domin ƙamsasa kanku kuma kar aci kasuwar sama babu ku😁_* *ZAKU IYA SAMUN MU TA WANNAN LAMBAR WAYAR: 07033778564 DOMIN JIN ƘARIN BAYANI*. *KO A KANO MAIDUGIRI ROAD MARIRI*.💃🏻💃🏻👍🏻 ________________________ *Page 12* .........Iya ruɗewa Maman Halima ta ruɗe. Tun tana leƙe-leƙe ita kaɗai harta nufi reception ta sanarma wanda ke zaune a wajen shi da wata budurwa. Ganin yanda take a rikice suka shiga tambayarta ko lafiya?.       “Inafa lafiya bayin ALLAH, ina salla wani ya shigo ya ɗauke jaririnmu. Dan ALLAH ku taimakeni na shiga uku”.         “Kinga mama kwantar da hankalinki, mu anan ba'a wannan dan asibitine dake tare da tsaro ta ko ina da kike gani” saurayin ya faɗa da sauri yana mikewa.        Katsesa Maman Halima tai, “Wane tsarofa anan yaro, inda da tsaro a shigo a ɗauki Jariri har cikin ɗaki? Ku taimakeni yaron nan ko uwarsa da tasha wahalar haihuwarsa bata dawo hayyacintaba, balle tasan mita haifa”.       Ganin bata cikin hayyacinta budurwar ta fito a inda suke a killace tana faɗin, “Mama dan ALLAH ki taimakemu ki nutsu, boss yana cikin asibitin nan karki ja mana matsala dan girman ALLAH”.      Sam Maman Halima ba saurarensu takeba, saima hankalin mutane data fara jawowa kansu saboda kwakwazonta. A wannan yanayi Maman Sadiq da Alhaji da Maman Sakina data biyosu yau saboda cin mutuncin da Alhajin ya mata suka iso. Jin abinda ya farune ya saka hankalinsu suma tashi, sai dai kafin suce wani abu sai ga Nurse Salima ɗauke da jaririn a hannu tana faɗin, “Wannan taron lafiya kuwa?”.      Yanda taɗanyi maganar da ƙarfine ya saka yawancin mutanen wajen juyawa suna dubanta. Kafinma wani ya bata amsa idon maman Halima ya sauka akan jinjirin, hakan yasata kwasa da gudu gaban Salima tana faɗin, “Ya ilahi, to aiga yaron ma anan”.        Kusan duk saida jama'ar wajen suka sauke numfashi. Saurayi da budurwar nan dake a reception sukace, “Mama abinda muke sanar miki kenan, amma kika gaza fahimta. Mudai munsan babu yanda za'ai mutum ya bata a asibitin nan”.       Salima data ɗan fahimci zancen tai ƙaramar dariya tana faɗin, “Kai mama wai kin ɗauka sacesa akai?. Asibitin nan yanada matuƙar tsaro fiye da yanda kike zato. Oga ne da kansa yazo gittawa zaije office ɗin Dr Mahmud yaji kukansa, shinefa ya shiga ɗakin danya duba. Sai ya samu kina salla shine ya ɗaukesa ya fita da shi. Yanzu na shiga wajen Dr Mahmud shine ya bani shi da faɗamin lambar ɗakin daya ɗakkosa. gashi ma yace a bashi wannan”. Ta ƙare maganar da miƙa ma mama wata ƴar takarda dake a linke da alamu suka nuna cheque ne na kuɗi.         Takardar Mama ta amsa batare data fahimci ta minene ba, yayinda su kuma mutanen wajen suka sami damar yin dariyar yanda ta ruɗe musu ɗazun.        Mama ma dasu Alhaji duk dariyar sukeyi, daga haka suka ɗunguma ɗakin da aka kwantar da Zinneerah. Mamaki ya kama Mama ganin ashema ta farka har likitan daya shigo ɗakin dubata yana ɗan musu faɗa akan fita su barta ita kaɗai haka.      Haƙuri mama ta bashi, tare da masa bayanin dalilin fitar tata. Ya ɗan murmusa yana faɗin, “A mama ai asibitin nan akwai tsaro sosai, motsin kowa dake ciki ana ganinsa ta cctv, dan haka ku kwantar da hankalinku babu abinda zai faru harku tafi insha ALLAH”.        “ALLAH yasa hakan” suka faɗa kusan a tare.        “Amin ya rabbi. Yanzu ga wannan, shine list ɗin komai na kuɗaɗen da zaku biya, sai kuma jini da zaku samo yanzu dan za'a ƙara mata. Dama jiran farkowarta muke mugani koda yuwuwar hakan, to yanzu kam naga alamar tana buƙatar jini leda ɗaya”.      Amsar takardar Alhaji yayi yana masa godiya, daga haka Doctor ya fice. Gaban gadon suma duk suka ƙarasa sunama Zinneerah sannu, da kai kawai take iya amsa musu batare data iya kallonsu ba. Sai faman haɗiyar zuciya take dan ita kaɗai tasan mitakeji a ranta. Ganin kamar batason hayaniyar ne ya saka Nurse Salima dake ɗauke da ɗan jinjirin daya gama shige mata rai har yanzu faɗin, “Inaga batason yawan hayaniya yanzu, idan kun gama dubata sai muɗan fita waje a bata waje”.      Gamsuwa da bayaninta ya sakasu amsa mata. Mama ta kalli Salimar tana faɗin, “Yauwa ƴarnan kinma sa na tuna. Ina dabinon da kika bada shawarar a tauna a bashi? Kinga yanzu tunda ga Alhaji sai ya bashi ɗin ko”.        Cikin ɗan nuna shakku Salima tace, “Aiko mama na muku laifi ko nace shishshigi, nazo da dabinon danna kawo mikine na biya office ɗin Dr Mahmud ɗin inda na sami Oga acan. To daya sanar min ɗakin da zan kawo yaron sai nake cewa dama can zani nakai dabino a bashi ko zai rage kukan yunwar da yakeyi. Jin hakan da kuma kukan da yaron keyi har lokacinne ya saka Oga ya amshi dabinon da kansa ya tauna ya bashi, har yana faɗin ALLAH yasa ya gaji sunansa”.        Alhaji dake saurarensu yace, “To masha ALLAH, ALLAH ya saka masa da alkairi duk da mu bamusan shi wanene ba”.       Salima tace, “Baba ai shine mai asibitin nan”.         Dukansu sai da suka ɗan ƙwalalo idanu waje. Mama tace, “Babbar magana, shima likitanne kenan?”.       “A'a mama, shi ba likita baneba, ɗan kasuwane. Nasan dai bazaku gaza sani kojin sunan *_AK SHIRA_* ba a garin nan ai”.          “Lallai kam sani bana wasaba, duk da dai ba sani na zahiri bane, amma wannan sunan ba ɓoyayyen suna bane, dan a Shira Family kowa yasan *AK SHIRA* ba ɓoyayye bane, kodan gidajen mansa kawai ai sun isa ka sanshi, balle kuma hidimar da yake ga bayin ALLAH mara iyaka”.        “To aiko Baba shine da kansa ya bama jaririn nan dabino yau, tare da wannan takarda da nake kautata zaton kuɗine rubuce a ciki”.      Sosai maganar ta sake girgizasu, mama ta mikama Alhaji takardar cheque ɗin. Amsa yay ya duba yana jinjina kansa. “Uhm lallai wani aiki kam sai manya. ALLAH ya saka masa da alkairi. ya azurtashi da duk alkairan duniya da lahira, ya kuma cigaba da karesa a duk inda ya saka ƙafa. Kuɗine zunzurutu harna dubu ɗari biyu ya rubuta anan”.      Sosai suka ƙara jin mamakinsa, ace lokaci guda mutum yay ƙyautar dubu ɗari biyu wa jariri kawai. Alhaji ya katse zantukan nasu da faɗin, “To lallai kam abokina dole kaci sunan AK Shira ai”.      Dariya duk sukayi banda Maman Sadiq datai ɗan murmushin kawaici. Hakama Zinneerah dake saurarensu kawai tana share hawayenta a ɓoye.      Alhaji ya buƙaci Salima ta rakashi yaymasa godiya, daga nan yaje wajen neman jinin da biyan kuɗaɗen da sukace. Bata musaba ta miƙama Mama jaririn suka fita. Office ɗin Dr Mahmud sukaje. Bayan Salima tai knocking ya basu izinin shiga suka shigo.          Shi kaɗaine a ciki, sai dai mayen ƙamshinsa na nan manne da office ɗin duk da babu shi a ciki. Dr Mahmud yace, “Salima lafiya dai?”.      “Laya ƙalau Doctor, dama Baba ne yace na rakosa yayma Oga godiya. Sune masu jinjirin nan na ɗazun”.       “Oh ALLAH sarki, Baba ina yini”. “Lafiya lau likita, ya aikin naku?”.      “Alhmdllh baba. Sai dai gashi kuma shi harya tafi, kasan shi uziri ba ƙaremasa yakeba. Dama yakan zo duk irin wannan ranar a tsakkiyar shekara da ƙarshenta ne ya bada jini inhar yana kano, yanzu hakama zaije Lagos ne ya biyo tanan ya bayar, ina ƙyautata zaton yanzu haka ya isa airport”.       Alhaji yace, “Ashsha. Naso kam na gansa nai masa godiya wlhy, sannan ya cika ladansa nama yaron nan huɗuba ya kuma saka masa sunan nasa dan ya cancanta”.        Cikin jin daɗin wannan karamci Mahmud yace masha ALLAH, shi da ya faɗa da wasa ashe ALLAH ya amsa mai sunan nasa aka samu, duk da nasan yanzu yayi nisan kiwo, amma bara na taɓasa a waya muji ko zamu samu ya ɗaga baba ka zauna”.       Zama Alhaji yayi yana murmushi. Dr Mahmud ya ɗauka wayarsa shima fuska ɗauke da murmushi ya shiga kiransa. Tana gab da tsinkewa aka ɗaga. Harma Mahmud ya fidda ran hakan. Cike da zumuɗi Mahmud yace, “Afuwan ranka ya daɗe kaga na kiraka”.      Basusan amsar da aka bashi daga canba. Cikin ƴar dariya yace, “Tona gode ranka ya daɗe. Dama masu jaririn daka ɗakko ɗin nan ne sukazo maka godiya, tare da sake kawosa ka cika ladanja ta masa huɗuba da saka masa sunan naka”.     Nanma basuji miya faɗaba, sai dai yanda fuskar Dr Mahmud ta ƙara washewa da fara'a zaka tabbatar da magana mai daɗi yake masa. Sai kuma ya saka wayar a amsa kuwwa (Hansfree) ya ajiye gaban Alhaji.          Wata tattausar murya mai cike da tarin nutsuwa kamar ta rowa sukaji tace, “Assalamu alaikum, baba barka da rana”.        Da sauri Alhaji yace, “Wa'alaikissalam, barka dai ranka ya daɗe, yaya ƙoƙari?”.      “Alhmdllhi baba. Yanzun nakejin daddaɗan albishir na samun takwara, gashi kuma nayi gaggawar tafiya”.      Yanda yake maganar cike da nutsuwa kamar bayasone ya saka Alhaji yin murmushi mai faɗi. “Alhaji ai kowa zaiso samun mai sunanka a gidansa kodan tarin alkairan dake tattare dakai. Munga hidima ALLAH ya saka da alkairi ya ƙara buɗi. Amma naso ace kaine da kanka kaima yaron nan huɗuba da sunan daka zaɓa masa”.       Kaɗan sukajiyo sautin murmushinsa daga can, cikin sake nutsar da muryar tasa mai sauti a tausashe yace. “Nima naso hakan Baba, dan kun bani abu mai daraja da bazan mantaba a tarihin rayuwata, amma duk da haka na bama Mahmud wakilcin yima takwarana huɗuba. ALLAH ya rayasa ya albarkaci rayuwarsa, ALLAH yasa ya zama mai tausayinmu da jin ƙanmu anan gaba”.           Atare suka amsa da amin kowa cikin jin daɗi. Musamman ma Alhaji dake mamakin yau shine ke magana da AK Shira baki da baki ta waya. Wata hikima sai UBANGIJI. Shikam dai har abada bazai taɓa mantawa da haihuwar wannan yaro ba a rayuwarsa.       Kamar yanda ya bada wakilci ga Dr Mahmud hakance ta faru, dan har ɗakin da aka kwantar da Zinneerah Dr Mahmud yaje yayma yaro huɗuba. Ya kuma ajiye kuɗi dubu hamsin shima yace asai rago a yankama takwaran abokinsa, kuma ogansa ranar suna.       Shima sun masa godiya sosai, kowa na jinjinawa a ransa yaro yazo da farin jini. yayinda Maman Sakina keta taɓe baki a kaikaice, a ranta kuwa tana ganin tsabar iya asirine na ƴan ƙauye kuma Katsinawa da kullum take ambata ga maman Sadiq.           Tare Alhaji suka fita da Dr Mahmud. Sai bayan kusan mintuna talatin ya dawo ɗauke da madaidaicin kwali da aka zubo masa magungunan da Doctor yace su sayo da drips, sai jini leda ɗaya. Kwalin Maman Sadiq ta amsa takai ɗakin dan sun fito waje. Tana fitowane yake faɗin, “Wani iko sai ALLAH, kunga jininma da naje nema a lab ɗin nasu saina samu bawan ALLAHn nan ya bada nasa a ajiye idan masu bukata sunzo nema. Cikin ikon ALLAH sai gashi ni na fara zuwa kuma. Gashi sun bada ƙyauta babu ko sule”.       Cikin riƙe haɓa Maman Sakina da hassada kecin ranta tace, “Oh har jini yake zuwa ya badar a asibitin kuma? Dan tsabar jin daɗi irin na masu arziƙi”.      Alhaji ya bata amsa da cewar, “Wlhy kin gani dai, dama likitan daya kira mani shi a waya yace jinin yazo badawa kawai shiyyasa bai jimaba ya tafi”.         Sudai su Maman Sadiq godiya suka sakeyi da jera masa addu'oin gamawa da rayuwa lafiya. ★★★          Sai yamma Zinneerah ta farka sosai cikin hayyacinta, bayan an cire mata jinin da aka gama ƙara mata. Bayan likita ya shigo ya fita suma su Maman Sadiq suka shiga. Zaune suka isketa jingine da filo ta zubama yaron dake gefenta yana barci ido. A zahiri shi take kallo, amma idan ka nutsu kaima a kallonta zaka fahimci sam batama tare da duniyar mutane gaba ɗaya. Dan yaron kuka yake iya iyawarsa amma da alama ba jinsa takeba.      Matar Naziru ce tasa hannu ta ɗauki yaron tana faɗin, “Haba Zinneerah, yaro na kuka ke kuma kin tsaya kallonsa kawai”.      Nan ɗinma ba jinta tai ba. Sai da Maman Halima ta taɓata sannan ta kawo numfashi. “Oh ni Binta, mi kike tunani haka Zinneerah?”.     Maman Halima ta faɗa tana tsatstsareta da idanu. Ƙasa kawai Zinneerah tai da kanta tana ƙoƙarin haɗiye kukan daya tokare mata ƙirji tun ɗazun. Matar Naziru dake jijjiga yaron dai yay shiru tace, “Haba Zinneerah ai yanzu ba lokacin kuka bane, lokacibe da zamu taru mugodema ALLAH ne. Jiya iyanzu muna nan cikin tsananin tashin hankali da fargabar rasaki, amma cikin amincin UBANGIJI yau gaki zaune da ƙyauta mai girma da wasu kecan suna bulayin nema da kuɗi amma ALLAH bai ƙaddara samuwarta garesuba. Kiyi haƙuri kibar kukan nan, mu yanzu babban fatanmu kuma ALLAH ya baki lafiya mu koma gida”.        “Maganarki kam gaskiyace Maman Abu. Zinneerah yanzu lokacine na godiya ga ALLAH kinji. ALLAH ya ƙara miki lafiya. Kinga yaron nanma ya kamata a bashi abincinsa dan wannan kukan bana komai bane sai na yunwa, tunda likita yace zaki iya ɗan gwada bashi yanzu sai a gwada ɗin ai ko”.        Sake fashewa da kuka Zinneerah tayi, dan ita kaɗai tasan yanda takeji a ranta akan wannan al'amari mai rikitarwa da matuƙar ruɗani. Tunda take bata taɓajin labari irin nataba. Tayaya zaka haifi ɗa na mutum batare da kasan yanda ka samu cikinsa ba. Anya kuwa yaron nan baɗan wani aljanin baneba?......       Shigowar Alhaji da Maman Sadiq da gayyar yaran gidan gaba ɗaya har da ƴaƴan Maman Sakina ya katse mata tunani. A take kuma ɗakin ya kaure da hayaniyar yaran. Dan bayan sun mata yaya jiki gaba ɗaya hankalinsu suka maida ga ɗan jinjirin suna yaba ƙyawun da ALLAH yay masa. Sai da Maman Halima taga kukansa na ƙara ƙarfine ta amsheshi cikin tilastawa suka saka Zinneerah bashi abincinsa tanata kuka.       Alhaji da Maman Sadiq ne kawai suka iya fahimtar kukan Zinneerah saboda sune sukasan labarin tushen samuwar yaron. Dan ita kanta maman Sadiq konawarsu gida tasha kuka, a yanzu hakanma kukan zuci takeyi. Su Maman Halima kuwa da basusan dawan garinba sai tunaninsu ke basu Zinneerah tana kukane saboda tunawa da mahaifin yaron da akace rasuwa yayi.      Da ƙyar aka samu ta bari yaɗan kama na wasu mintuna. Dan kuka take sosai tana yarfa hannu wai zafi. Maman Halima ta ɗaukesa tana mata faɗa akan karta sakama ranta fargabar tsotso dan yaron nan daga gani ba wasa zaiyi da cikinsaba. Ita dai Zinneerah zamewa ma tai ta kwanta a hankali tana matse baki dan inda aka yankata na mata ciwo sosai har yanzun.       Sun daɗe a asibitin yaran na cigaba da jagwalgwala yaron da aka samu yay shiru, yayinda Zinneerah ke kwance shiru bata sake kula kowa ba. Idonta a lumshe suke tana zirar da hawaye ta gefensu, yayinda hancinta ke shaƙar daddaɗan ƙamshin turaren dake manne da jikin showal ɗin yaron da batan a ina ya kwasoshi ba.        Ƴar hayaniyar yarance ta saka Doctor shigowa ɗakin yace suyi haƙuri a barta ta huta hakanan, ya kuma bada damar a bata abu mara nauyi tasha, kamar shayi ko kunu haka. Godiya sukai masa ya fice. Alhaji kuma ya tattara iyalansa shima sukai musu sai da safe suka tafi. Aka barta daga ita sai Maman Halina dake haɗa mata kunun da akace zata iya sha ɗin. _____________★         Haka Zinneerah ta cigaba da jiyya a asibiti. yayinda abokan arziƙin Maman Sadiq na anguwa da dangi ɗai-ɗai dake anan suke ɗan shigowa dubata. Kulawa da take samu na abinci ya saka komai yake tafiya kan tsari Alhmdllh. Dan jikinta yayi ƙyau sosai a kwanki shidan data ɗauka a asibitin. Idanma ba'a faɗa makaba bazaka taɓa ɗauka cs akai mataba. Sai dai sam babu mai ganin walwalarta, sannan ko kallo yaron bai ishetaba sai Maman Halima ta mata jan ido.      Matsalar da suke fuskanta da yaron kawai shine idan yasha nono cikinsa sai ya kumbura yayta kuka. Da farko basu fahimci hakanba sai suke ɗauka cibiyarsa ne ke ciwon. Sai daga baya Doctor ya gane inda matsalar take. Dan haka ya dakatar da Zinneerah daga bama yaron nonon gudun kar a cutar da yaron kuma. Sai dai sun ɗorata akan magani zuwa wani lokaci sai ta cigaba da shayar da shi. shi kuma yaron suka bada shawarar a ringa bashi madara.       Hakan yama Zinneerah daɗi, dan a shirementa ayyanawa take a ranta ta huta da ciyar da ɗan aljanu, dan har cikin ranta ta yarda aljanune sukai mata ajiyar yaron kawai a cikinta.      Babu wanda yasan da wannan shirmen nata, sai dai ranar tsabar jin daɗi har ɗan sakin jikinta tai sukai hira da Maman halima da ada take danganta rashin walwalar Zinneerah ɗin da rashin ƙarfin jiki.        Washe gari Alhaji ya sayi raguna biyu aka raɗama yaro suna Abdul-Mutallaf a masallaci, wato dai takwaran AK Shira kenan kamar yanda akai masa huɗuba. Ba ayi wani shagaliba kasancewar mai jego na asibiti, sai dai maman Sadiq tayi abinci ta bada sadaka ko zata samu sassauci a ranta da nutsuwar rugumar wannan ƙaddara a garesu.         Da yamma da sukazo dubasu a asibiti Alhaji yake sanarma Maman Halima cewar yaro yaci suna Abdul-Mutallaf.      Cike da murnarta da farinciki taita jera addu'a ga jariri tana tsokanarsa. Zinneerah kam ko motsi bataiba balle ta nuna taji sunan da yaron yaci. Sai dai tausayinsu da takeyi akan sunatama ɗan aljanu hidima batare da sun saniba. Ta tabbata wataran sai aljanin daya ajiye mata ɗan yazo ya ɗauke ɗansa batarema dasun saniba zasu gane wahalar banza sukayi. Babu wanda ya damu da rashin tankawar tata. Garama maman halima taɗan mata faɗa kamar yanda ta saba idan taga tana share yaron. Shiru dai tai batace komaiba kamar kullum, sai hawayen data share a ɓoye duk da ita Maman Sadiq na lure da ita.          Ganin komai normal ta samu lafiya Alhmdllh washe gari aka basu sallama. tare da basu ranakun da zasu dawo domin duba lafiyarta. Daɗi sosai Zinneerah taji da wannan sallama. dama ba ƙaramin gundura tayi da zaman asibitinba.         Koda suka dawo gida sun sami ƙyaƙyƙyawar tarba daga yaran gidan, dan harda ƴaƴan Maman Halima na ma'auri duk sunzo gidan tarbarsu, dama duk sai da sukaje asibiti anan nema Zinneerah ta fara saninsu. Amma yanda suka karɓeta saika ɗauka a cikinsu ta tashi itama.      Yau ɗinma tararwa sukai sun haɗa wata ƴar ƙwarya-ƙwaryar liyafa iya su kawai ƴan cikin gidan, sai ƴaƴan Naziru da matarsa da maƙwafta na kusa da ake gaiswar mutunci. Kowa yayi mamaki dan babu wanda yasan da wannan shirin nasu. Maman Sadiq zata hana Alhaji ya hanata akan kartace komai, dan sudai basusan komaiba akan wannan haihuwa ba. Sannan kosu ɗin da suka sani ai Zinneerah batasan sun saniba. Su daure su ƙarfafa farincikinta har lokacin da za'aje gaɓar da tuhumarta zatai musu amfani, kuma dalilin hanyar samuwar ɗan bazaisa su toshe hanyoyin karɓar ƙaddarar da yazo a cikintaba, da har zasu ƙi farinciki ko nuna godiyarsu ga ALLAH.       Badan tasoba ta haƙura ta zuba idanu itama.      Ita dai Zinneerah bata nuna wani alamun damuwa da hakanba, dan tunda suka shigo gidan Maman Halima tai mata gashi na musamman a jikinta sai ta samu nutsuwa sosai, aka kawo mata abinci kuma taci ta ƙoshi tasha magani sai barci. Sai gashi har suka gama walinarsu ita bama tasan wace waina suke toyawaba, sai bayan ta tashine su Aunty Halima suka shigo sukai mata sallama zasy wuce gida dan lokacin anyi sallar isha'i.        Yanda suke nuna mata so da ƙauna su da mahaifiyarsu yasa itama take sakin jiki dasu sosai, kuma tanajinsu tamkar yayunta, dansun maye mata gurbin su Yaya Gajejen ta.............✍       *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* *Page 13* ________________________ *_Hummmmm!!. Wai wai wai, wani aiki sai: GIDAN ƘAMSHI💃🏻💃🏻💃🏻🥺_* *_INA MATA ƳAN ƘWALISA MA'ABOTA SON ƘAMSHIN GIDA DANA JIKI?_* *_INA MATAN DAKAN SO DUK INDA SUKA DOSA KO SUKA BARI SAI SUN BAR MUSU TARIHIN ƘAMSHINSU_* *_TO MATAN ƘWARAI KUZO GA WANI SIRRI DAZAN BAKU DAGA FITACCEN GIDAN ƘAMSHIN NAN DA BAIDA NA BIYU A KANON DABO😁_* _Ina magana ne akan GIDAN ƘAMSHI da ke a Jihar KANON DABO MAIDUGURI ROAD MARIRI_. *MUNA SIYAR DA TURARURRUKAN WUTA SET NA AMARE, MUNA KUMA BADA SARI.* *AKWAI KUMA SABULUN GYARAN JIKI MAIDA TSOHUWA YARINYA, BUDURWA TAURARUWA, MATAN ƘWARAI ANNURIN HASKAKA GIDA. SHIMA DAI AKAN SARI, DOZIN KO KATON* *AKWAI KUMA ZUMAR ƘARA ƘIBA GA MATAN DA KESON SU GANSU DUMURMUR SUNA JUYAMA OGA KAYAN...😉🙈💃🏻 kundai gane*. *_Mata ku garzaya GIDAN ƘAMSHI domin ƙamsasa kanku kuma kar aci kasuwar sama babu ku😁_* *ZAKU IYA SAMUN MU TA WANNAN LAMBAR WAYAR: 07033778564 DOMIN JIN ƘARIN BAYANI*. *KO A KANO MAIDUGIRI ROAD MARIRI*.💃🏻💃🏻👍🏻 _______________________ *Page 13* ............A zahiri dai Zinneerah ce ta haifi Abdul-Mutallaf. Amma dukkanin abinda ya shafi yaron ƙiri da muzu ta sakarma Maman Sadiq. Musamman daya kasance ba abincinsa yake sha ba yanzu sai madara. Idan ka gansa a hannunta ko tana masa wata hidima to Mama Sadiq na wajen Abba ne ko tana aiki, yaran kuma basa gida.       Wanda bai saniba ma idan yazo gidan saiya ɗauka Maman Sadiq ɗince ta haifi yaron. Tsabar ƙwarewa a shahara wani lokacin idan tace Zinneerah tai masa wani abu tata kumbura baki kenan. Ita maman Sadiq ma abin har dariya yake bata.         Itako Zinneerah ba komai ke ɗawainiya da itaba sai tsabar shirme da ƙuruciya, sannan har cikin ranta ta rigada ta saka cewar yaron ɗan aljanune suka ajiye mata. Bawai bata sonsa bane, sosai take son abinta kasancewarta mai son yara dama can, dan a hankanma wani lokacin haka zata zauna taita satar kallonsa, idan kuma Mama ta fita a ɗakin takan ɗaukesa kota zauna tana kallonsa tana murmushi da shafar kansa, kai har kiss idan ALLAH ya cidashi yimasa akeyi ko rawa.       A yau kusan shine ma ya tadasu da asubahi da kukansa, dan a daren jiya tsautsayi ya saka Maman Sadiq tsare Zinneerah ta shayar dashi akan ko za'a dace yanzun tunda tana shan maganin. Sai gashi a cikin rashin dacewar cikin yaron ya kumbura kamar yanda ya ringayi a asibiti. Abba daya dawo daga masallaci ya shigo yana faɗin, “Yaya dai wai nikam?. Mi akaima abokina ne yau a gidan nan?”.       Maman Sadiq dake bashi maganin da aka dinga bashi sanda suna asibiti idan hakan ta faru ta ɗago tana dubansa. “Wlhy Yaya tsautsayi yasa na sakata ta shayar da shi jiya da daddare dan tausayi yake bani, ace jinjiri kamar wannan babu abincinsa sai madarar banzar nan. Tofa shine kaga cikin dai ya kumbura kamar yanda yakeyi”.       Amsarsa yayi a hannunta bayan ta goge masa maganin daya ɗan ɗisa masa a wuya. Ya sakashi a kafaɗa yana hura masa kunne da shafar bayansa. sassauta kukan ya farayi kaɗan-kaɗan, kafin ya koma ajiyar zuciya. Kusan mintuna biyar suna a haka yaron ya saki gyatsa mai ƙarfi. Su dukansu sai da suka sauke numfashi. Su Sadiq dake zaune duk cikin damuwa Abdul yace, “Abba Little yaji sauƙi (dan haka suke kiransa saboda Abdul ɗin).        Fuskar Abba da murmushi yace, “Insha ALLAH yaji sauƙi gashi yayi gyatsa. Da alama kuma barci ma zaiyi, sai a goyashi”. Ya ƙare maganar da kallon Maman Sadiq.        Miƙewa tai tana faɗin, “Tazo ta goyashi ɗakinka zanje na gyara, dan sakarci duk wannan ihun da yaron nan keyi tana ciki tana jinmu amma ko leƙe, tun a ɗakinma luf tayi ita a dole barci take bata jimuba”.      Dariya kawai Abba yayi batare da yace komaiba. Maman Sadiq kuma ta shiga kwalama Zinneerah da duk tana jiyosu daga ɗakin kira. Fitowa tai sum-sum-sum kamar wata munafuka. Abba yace, “Koma ki ɗakko zani kizo ki goyashi akwai sanyin safiya”.        Cike da kunya ta juya ta koma. babu jimawa ta dawo da zanin goyon a hannu. Maman Sadiq ce ta amshesa ta saka mata a baya dan har yanzu ba wani iya goyon tayi da ƙyauba. Kusanma wannan shine karo na uku kacal da zata goyashi. Dan mafi yawancin lokuta su ƴan biyune ke goyashi ko Maman Halima ko ita Maman Sadiq ɗin. Har Sadiq da Abdull goyamusu akeyi, ƴaƴan maman sakina ma sukan faki ido suzo su ɗaukesa saboda kusan shine ɗan ƙaramin yaro yanzu a gidan, sai yazan abin sha'awa ga kowa banda maman sakina da ko sau ɗaya bata taɓa ɗaukarsaba ma ita.      Da ƙyar Maman Sadiq ta samu goyon yayi dai-dai tanata ma Zinneerah ɗin faɗa. Ita dai batace komaiba sai dariya takema a ranta wai mama ta dage da masifa akan ɗan aljanu, sai randa sukazo suka ɗauke abinsu taga yanda kowa zaiyi a gidan ai.           Bayan fitar Abba da Maman Sadiq Zinneerah ta hau gyaran ɓangaren nasu kamar yanda ta saba, Sadiq kuma suka shige suna shirin makaranta dan an koma hutu. ★★★★        Haka rainon Little Abdull ya cigaba da gudana kusan kaso biyu a hannun Maman Sadiq da maman Halima ne. Kaso ɗaya kuwa Zinneerah na rabawa dasu Sadiq. A haka sukai arba'in yaron yay ɓulɓul masha ALLAH, ga ƙyawunsa na sake fitowa. Yaro gaba ɗaya bai ɗakko kamannin Zinneerah ba ta fuska sai halittar yatsunsa na ƙafa da hannu da abinda ba'a rasaba. Amma daga basuba kamanninsa daban da nata. Takan zauna ta dinga kallonsa da shiga dogon nazarin ko zata iya gano da wanda yake kamar. Amma sam bata iya hasaso komai ga kamannin nasa.         Sosai jikinta ya warke, idanma baka saniba bazaka taɓa ɗauka cs akai mataba. Musamman da yazam bayan dawowarsu gida maman Sadiq da Maman Halima kulawa da gyara na musamman suke mata wanda ita bawani gane inda suka dosa take ba. Abinda kawai ta sani tanajin daɗin jikinta sosai balle yanzu barci take sosai tamkar kasa. Ga lafiyayyen abinci da take samu kuma ga kwanciyar hankali. Sam bata wani tunawa da Inna. Garama Babanta da Yaya Sa'a da Yaya Gajeje. Takanyi kuka a duk sanda sukazo mata ranta koda a boyene. Sai ko Khalipha da har yanzu yake maƙale a zuciyarta. Gashi yanzu Naziru ko gidan yazo baya mata maganarsa ma. Itako kunya ta hanata sake tambayarsa ko yanzu yana samunsa.       Bayan tayi arba'in da kusan wata ɗaya Maman Sadiq taga zaman nata baida wani amfani. sai dai taci ta ɗanyi aikin gida ta kwanta barci. Samun Abba tai da shawara akan Zinneerah ɗin ta shiga wata islamiyya dake anan kusa da su ta ƴanmata, inda su Sakina ke zuwa da yamma. To sunayi da safe kuma zuwa ƙarfe ɗaya ga yaran da basa zuwa boko.       “Eh shawaranki mai ƙyau ce Hauwa'u, nima kuma maganar fara karatunta dama yana raina. Na bartane kawai Abdul-Mutallaf ɗin ya ƙara ƙwari sannan. To amma tunda dai naga bama itace ke rainonsa ba gara ta fara islamiyyar kawai itama bokon sai a nema mata inda zai dace da ita dan nasan da wuya ace acan tayi karatunma”.        Cikin gamsuwa da bayaninsa Maman Sadiq tace, “ALLAH ya saka da alkairi yaya, sai dai duk da bamu taɓa maganar karatu da itaba sai naga kamar taɗanyi acan, dan naga wasu lokutan idan su Abdull na Assignment haka takan saka musu baki harma tayi gyara a wani wajen”.      “A'a ikon ALLAH, to kinga kiramin ita dai muji ta bakinta, kinga ai sai mu sami madafar kamawa ko”.      Miƙewa tai tana amasa masa da to. Babu jimawa kuwa sai gasu sun dawo tare da Zinneerah. Bayan ta gaida Abba sai yake tambayarta ajinta nawa a makaranta?.        Duk da a bazata tambayar tazo mata sai gashi ta saki murmushin da ya basu mamaki. Kanta tsaye cike da zumuɗi tace, “Abba nayi jsce ma ai”.       “Ikon ALLAH, to to Alhmdllh. Ashe ɗiyar tawama ƴar boko ce bamu da labari. Amma gaskiya naji daɗin hakan sosai, kuma na yaba ƙoƙarin babanki anan....”      Cikin suɓutar baki tace, “Lah Abba ai bama shine ya sakaniba. Inagama Baba fa baisan ina zuwa makarantaba, dan shifa babu ruwansa dani a gidan. Ni saima nayi kwana hudu biyar ban gansaba wani lokacin”.       Duk idanu suka zuba mata, a ransu kuma cike suke da zumudi da jin daɗin yanda ta fara sakin jiki da faɗa musu abinda ke ranta.      Maman Sadiq ce tace, “To wani guri yake zuwa da har kike kwanaki baki gansaba?”.       “A'a mama, yana nan a gidan, kawai dai bansan miyasaba shi bayason ganina ne wani lokacin, wani lokacin kuma daga sallar asuba idan ya fita bai dawowa sai munyi barci”.         Babu wanda ya iya magana tsakanin Maman Sadiq da Alhaji. Maman Sadiq dai rayawa take a ranta yaushe al'amarin baban ya taɓarɓare haka kuma?. Dan tasanshi a da mutumne tsayayye akan iyalansa da gidansa. Dan ko talla wannan bai yarda yaronsa ya fita ba. Duk inda akai sallar isha'i kuwa yana gidansa, bazai sake fitaba sai asuba. Da an idar da salla zai dawo gida ya karya sai rana ta haska zai fita kasuwa wajen sana'ar sai da dankalinsa ɗanye da makani.......          Tambayar da Alhaji ya jefama zinneerah ce ta katse tunanin Maman Sadiq ɗin ta maida hankalinta garesu.        “Karki damu yarinyata, haka rayuwa take kullum cikin tsere-tsere da jarabawa. To amma wanene ya kaiki makarantar?”.        Kunyar wanda zata ambata ɗin ya sakata jan lokaci kafin ta bashi amsa. “Abba Babawo ne ya kaini kafin ya koma yace Yaya Karima yake so”.        Duk da a dunƙule tai maganar kasancewarsu manya masu hangen nesa sai duk suka gano inda ta dosa kai tsaye.      “ALLAH ya saka masa da alkairi”. Abba ya faɗa dajin daɗi. Amin sukace ita da maman Sadiq. Daga haka Abba ya sallameta suka cigaba da tattaunawa shi da matarsa.        “Hauwa'u kinga fa'idar shiru da mukai mata akan son sanin bayanta ko? Ina mai tabbatar miki inhar zamu cigaba da binta a haka harma abinda bamuyi zatoba sai munji daga gareta wataran. Kinsan shi yaro tamkar dabba yake, mai kula dashi da mai sake masa shi yake sakewa da shi shima. Dan haka ki sake nutsuwa wajen fahimtarta a hankaki komai da muke buƙata zai fito. Domin a fahimtar danai mata rashin samun sake a inda ta baro ya sakata kasancewa shiru-shiru kamar mara wayo. Amma ras take kuma tanada kwaramniya, sai a hankali zakiga ta hau bisa hanya da ƙyau”.      Murmushi maman Sadiq tayi har haƙoranta na bayyana. “Maganarka haka yake Yaya. Dan yanda ma zakaji tana faman shagali dasu Sadiq idan na barsu su kaɗai ya isa tabbatarwa. Idan kaji bakinta cauy-cauy baka taɓa cewa itace ke zuba zance”.      Dariya shima Abban ya sakeyi. “Ahaf kaɗanma kenan. Bayan takurar data taso a can harda cikin yaron nan ya sake dankwafe dukkannin kuzarinta da karsashi. Amma zata ware tsaf ta bama kowa mamaki. Naga alamar kuma tanason karatu ma sosai, dan jin daɗinsa ya sakata bamu labarin abinda bamu tambayetaba ma”.       Haka suka cigaba da hirarsu cike da fahimta dajin daɗi. Yayinda Zinneerah kecan tana tsallen murna zata koma makaranta. Harda ɗaukar Little dake barcinsa ta hau masa rawa. Aiko ya farka ya birkuce mata kuma. Da ƙyar ta lallashesa tana dungure kansa da goyasa wai karya tona mata asiri Mama tazo tai mata faɗa ta tada ɗan aljanu kuma.        Kwana uku dayin maganarnan aka saka Zinneerah islamiyyar safe zuwa 2 sun taso. Kusan dai-dai da yaran gidan kenan amma ƴammatan kawai dake shirin gama secondary. Su Sadiq kam sai shidda suke tasowa makarantarsu haɗe take da islamiyya.       Faɗa muku irin kalar farinciki da Zinneerah tayi ɓata lokacine. Sai da akaje makarantar kuma ta raina kanta dan batasan komaiba. Amma tayi alwashin nutsuwa sosai ta fahimci komai ɗin kodan ta ribantu a duniya da lahirarta                         _________________★        A kwana a tashi babu wahala wajen UBANGIJI. Yau ga Abdul-Mutallaf (Little) da wattani bakwai a duniya. Yaro ƙyawunsa nata ƙara fitowa fili da lafiya ingantacciya. Bazaka taɓa cewa ba abincinsa yake samu daga mahaifiyarsa ba. Dan ma zazzaɓin haƙora kan girgiza kuzarin nasa wasu lokutan.         Amma da yake zuwa yanzun cin abubuwa yake sosai, dan su Aliyu komai suka yayo kimsa masa suke shiko ya cinye abunsa sai hakan ya ƙara taimaka masa aynun. Rarrafe yake ko ina ga ɓarna, inda yana waje kowa kaye-kayen kayansa yake inba hakaba yazo ya tarar an canja musu sabon tsari.       Babu ruwansa da Zinneerah, hasalima ƙyuya yake mata wani lokacin. ba komai ya jawo hakanba sai itama rashin kulashin da takeyi sosai. Dan komansa Maman Sadiq ce sai kace itace uwarsa. Shi da su Sadiq kuwa ai da kuka ake rabuwa idan zasu makaranta. Dasun dawo kuwa zakaga walwalarsa ta daɗu.        Zinneerah nata karatun islamiyyarta wanda a yanzu tayi matuƙar yin nisa dai-dai gwargwado, dan ko a Alkur'ani ta kusa kai izifi biyu, ta saka himma sosai. Hakama sauran littatafai bata wasa. Bokon dai ce ba'a kai ga sakataba har yanzu saboda wasu ƴan dalilai da suka riƙe Abba. Amma yanata shirin hakan batarema da sanintaba.          ★★★★★★    Little nada shekara ɗaya cif a duniya da ƴan kwanaki ALLAH ya bashi ikon fara takawa. Ranar zokaga murna wajen su Aliyu. Zinneerah na zaune a falon ita da Mama suka dinga ihunsu na murna mama na tayasu da dariya. Zinneerah dai ta murmusa ta kauda kanta ga abinda takeyi, sai dai a kallo ɗaya zakai mata ka fahimci kawaicine kawai takema mahaifiyarta, amma har cikin ranta tanason ɗanta da jin daɗin duk cigaban da zaizo masa a rayuwa. Duk da kuwa har yanzu tunaninta na nan akan aljanu suka saka matashi a ciki ta haifa musu. Wataran kuma zasuzo su sace abinsu.     Maman Halima dake tsakar gida tana girki ta leƙo tana tambayar lafiya su Sadiq ke ihu haka?. Cike da murna Abdull yace, “Mama little ya fara tafiya”.      Dariyar itama tayi, tare da shigowa ɗakin sosai ta ɗauka Little tana juyi dashi. Dariya su Sadiq suka sake sakawa. Amma banda Little da kowa ya fahimci miskilancin yaron tunda ya fara wayo. Sam baida yawan fara'a, akan daɗe ba'aga yana dariya ba. Garama idan su Aliyu ke masa wasa zakaji har ƙyalƙyalewa yanayi abunsa. Zinneerah ma catai ita daya rainama ko dariyar yake idan ya ganta dainawa yakeyi.    Duk sanda ta faɗi haka mama kan girgiza kai kawai da faɗin, “ALLAH ya kaimu randa zakiyi hankali dai, harshi Abdul-Mutallaf ɗin miya sani da sai ya zaɓa wanda zaima dariyar? Kawai dai zuciya nason mai ƙyautata mata, keko ko wasa bayimasa kikeba”.       Idan mama ta faɗi hakan Zinneerah bata ƙara cewa komai kuma, dan dai kam da gaskiyar mama. Idan kaga tama yaron wasa sai inba idon Mama a wajen. To kafin hakan ta faru kuwa akan jima musamman daya kasance yanzu itama ta fara makarantar boko a sukul ɗin su Sakina.     Duk da Sakina nashan zubar mata da mutunci ga abokan karatunsu na cewar ai bazawarace ta taɓa aure harda ɗa. Da farko ƴan ajinsu kan ƙaryata ta sukeyi, dan a ganinsu nawa Zinneerah ɗin take da za'ace ta haihu, a yanzunefa suke shekaru sha biyar suna farkon shiga sha shida. Tsabar son ƙara wulaƙanta Zinneerah saita ƙirƙiri dinga gayyatarsu gidansu dan aga little. Wasu ko sunje sun gansa basa yarda, amma yau da gobe sai suka fara amincewa da Sakina ɗin har suna tsokanar Zinneerah.      A farko takansha kuka. Amma zuwa yanzu da take neman watanni kusan biyar a makarantar sai hakan ya bar ɓata mata rai. Tama sake ɗammarar maida hankali akan karatunta kamar yanda a kullum Mama ke jaddada mata ta dage wannan karatun sai ya zame mata ado mai ƙawata tarihinta watarana.      Ba fahimtar Mama takeba kai tsaye akan furucin, dan ita a shirmenta har yanzu Mama batasan yaya aka samu Little ba. Bayan sun gama darerakunsu akan fara tafiyar little ɗin Mama ta fice. Su kuma suka cigaba da hidimarsu a ɗakin kasancewar lahadice yau islamiyya kawai yaran zasuje da yamma.      Ganin Little ya ɓingire ƙasa alamar barci zaiyi yasa Zinneerah ajiye buk ɗin hannunta da take Assignment ta ɗaukesa ta goyashi, dan Mama ma ta shige ciki kanta na ciwo. Fita tai tsakar gida dan ta taya Maman Halima aiki kasancewar yau ranar girkintace.         Maman Sakina kawai ta samu zaune dasu Luba dake wanki a bakin rijiya. Ba wani shiga sabgarta suke a gidanba shiyyasa itama bata matsawa kanta na shiga tasu. Dan wasa-wasa Zinneerah ma akwai miskilanci da tsiwa idan taso. Sai dai yanayin rayuwar data tashi a cikine ya sakata komawa sanyi-sanyi.      Yanzu ɗinma Maman kawai ta gaida taja kujera ta zauna a bakin rijiyar itama inda aka tara wanke-wanke. Cikin neman tsokana Luba ta dubeta taɗan taɓe baki, sai kuma a bazata ta bushe da dariya. Kallonta Aliya tayi, hakama Mamansu. “Luba lafiyarki kuwa da wannan dariya kamar wata mara hankali?”.      Cikin dariyar tace, “Mama bazaki ganeba. Wlhy wannan agolance take bani dariya. Idan ta fita waje samarin anguwarnan suyita wani rawan kai a kanta su sun sami budurwa, shashashun basusan harda surƙumemen ɗa gareta a gidaba. Jiyafa Faisal ɗin gidan Alhaji Zubair bakiga yanda ya nacemin da tambaya akan wacece ita ba? Niko na ce masa bazawarar agolan gidanmuce”.        Dariya suka bushe dashi su duka har Maman. Maman Halima dake kicin ta fito a fusace tana kallon Luba mai zancen. “Haba Luba wane shirmene haka da girmanki. Zinneerah ba ƙanwarki bace amma kike wannan sakarcin?”.      Da kunƙunin rashin tarbiyya Luban tace, “A'a Umma nikam ba ƙanwata bace, dan bamu haɗa komaiba banda agolanci datazo gidanmu cin arziƙi”.        “To sannu mara kunya, yanda kikejin nan gidankune itama haka gidansu ne. Dakike aibantata wajen mutane cewar bazawara kuma agola kina tunanin hakan zai hana wanda ALLAH yasa ya zama mijinta zuwa har gidan nan neman aurenta. Kubar wannan banzan halin dan baida ƙyau, ku matane gidan wani zakuje wataran kuma.......”      A fusace Maman Sakina ta tare zancen. “A'a Maman Halima kinga, miye na wannan dogon alkaba'in bayan gaskiya yarinyar ta faɗa. Daga ni har ke kowa yasan ai ita agolarce a gidan. Kuma bazawara. Luban ai taimakonta takeyi wajan faɗar gaskiya dan kar bayin ALLAH suzo a rufesu a basu budurwa bayan gata harda ƙurmusheshen ɗa a baya”.        Maman halima zata sake magana Maman Sadiq da hayaniyarsu ta sakata fitowa dole tai saurin faɗin, “Yaya dan ALLAH abar maganar dan bata da amfani. K kuma Luba ki kwantar da hankalinki ko baki faɗa musu ba dama idan sunzo ɗin zasu sani ai. Cin arziƙi kuma da tazoyi gidanku naɗan lokacine insha ALLAH ”. Daga haka ta juya ta koma ɗaki idanunta na cika da ƙwallar tausayin ɗiyar tata da babu ranar da zata fito ta koma ga ALLAH Saude da ɗiyanta basu yadda habaici akanta ba a gidan. Sai dai suna musu shirune daga ita har Zinneerah ɗin saboda tana ƙwaɓarta akan karta kulasu komai mai wucewane. Sai dai na yau ya mata zafi har tanajin kamar tasa Zinneerah tabar gidan ko itama ta huta da wannan gorin.        Maganar Maman Sadiq sai gashi tabar baya da hazo. dan dama irin wannan damar Maman Sakina ke jira ta dirje Maman Sadiq ɗin akan haushin zaman Zinneerah da ɗanta a gidan. Aiko ta zauna ta fara zuba tijara har su Luba na iƙirarin dukan Zinneerah wai.      Shiru Zinneerah dai bata kulaba, tamkarma batasan anaiba tanata wanke-wankenta. Sai da cikin suɓutar baki Aliya ta zagi Maman Sadiq ne Zinneerah ta miƙe batare da kowa ya luraba. Sai saukar sautin mari kawai sukaji akan fuskar Aliya a bazata..........✍ *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* *Page 14* ____________________ *_INA MATA ƳAN ƘWALISA BA'ABOTA SON GYARA JIKI DA FATA SUYI ƘWANAS TAMKAR WATA ƊAN DAREN SHABIYAR?!_* _Ku marmatso kusa maza na kaiku kantin sauƙi na UMMU DUFAIL gidan sauƙi da biyan buƙatar MATA SARAKAN ado harma da MAZA ƴan ƘWALISA._ *_MATA da yawa kanso su koma Taurari ababen kallo da burgewa ga ma'abota kallo sai dai basusan ina zasu sami sinadarin kankaro wannan ƙyawu da mutuncinba._* _To maza kuzo kusa dan Bilyn Abdull ta lalubo muku kantin sauƙi na Umm Dufail dakeda kaya masu sauƙi da gamsar da maison afani dasu_. *_UMMU DUFAIL nada kayan gyaran jiki masu rahusa da inganci da gamsar da mai saya cikin ƙanƙanin lokaci kamar haka👇🏻😁_* *Customers price list By Ummu Dufail FACE AND BODY* SCRUB=2500(300ml) Face and body mango butter=3k (250ml) Face cream= 1800 Corretor oil/vitamin C oil=2k Fairness skin lotion= 2500 Hot chocolate skin lotion 2500 Serum (for Nuckles )2k Nuckles cream (stubborn)3500 Mix fruits Arabian black =soap 1800 Mix fruit glycerine soap =1900 Beetroot=1900 Coconut, milk,egg..face soap=1200 Lavender mix fruit soap =1800 Body wash =1500 cleanser=1600 Hair spray =700 Hair oil =1500 Hair relaxer =700 Hair butter 1700 Shampoo =1500 Breast=oil 2k powder 2k Strech marks cream= 2k Beetroot pink lips =700 Baby care soap glycerine=1k Baby care butter =1500 Shea butter baby soap =700 Tsumin tula =2200 Tsumin zinariya =1200 Sliming tea =1500 Amarya set =25k Liquid Arabian black soap =1900 Cleansing water =1500 *_Zaku iya bibiyarta domin gani da ido ta Handle ɗinta na istagram da facebook kamar haka_* Ummu Dufail @ Facebook Ummu Dufail @ instagram Phone no: 07067943479. _Ƴammata harma da masu auren karku bari ayi babuku. Dan gyara shine mace a wannan ƙarnin😉👍🏻_. _____________________ *Page 14* ............Tsitt gidan yay na wucin gadi kowa na duban Zinneerah da mamaki. Cikin fushin da basusan ta iyaba ta nuna Aliya idonta na cikowa da ƙwalla. “Ki kama harshenki a duk lokacin da zuciya ke ingizaki wajen kuskuren suɓucewarsa. Zaki iya mani ni baki isheni ko kalloba. Amma idan kikace ƙarancin tarbiyyarki zai cigaba da rufe idanunki wajen raina waɗannan lallai zan maidaki cikin hayyacinki!!”.            A yanda tai maganar babu tsoro ko alama a cikin idanunta ne yay matuƙar saka shakkarta a zuciyar Aliya. Dan haka ta kasa komai sai kallonta da take hannunta riƙe da kuncinta.      A fusace Luba tayo kan Zinneerah, wani wawuyan cakuma tai mata wadda tai sanadin suɓucewar zanin goyon datake goye da little. A take yaron yay baya gaba dayansa. Ita kuma Luba ta cakumi Zinneerah ɗin sukai gaba.     Kusan a tare Maman Sadiq da Maman Halima suka iso wajen daf da Little daya tsage da wani gigitaccen kuka zai kai ƙasa. Cikin amincin ALLAH ya faɗa cikin hannunsu da suka tara a tare.         A can kuwa tsakanin Luba da Zinneerah dambe ne sosai ya harƙume. A tunanin Luba zata iya dukan Zinneerah ne dan tana ganin ta fita girman jiki. Sai gashi Zinneerah ɗin na tumurmusar hancinta a ƙasan sumintin gidan. Ganin irin dukan da Zinneerah kema Luba yasa Aliya da Maman Sakina rufe Zinneerah da duka suma.     Masu iya magana sunce sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi, da wannan damar suka sami galaba akan Zinneerah duk da dai ta more sosai itama akan Luba ai. Ganinfa abin zai zama hauka Maman Halima ta sakarma Maman Sadiq Little dake kuka saboda tsoratan da yayi ta nufesu tana ƙoƙarin janye Maman Sakina da Aliya amma ta kasa. Sai faman kaima Zinneerah duka suke suna ɗura mata zagi, har takai Maman Halima ɗinma na samun rabonta.         Ana cikin wannan rikici ALLAH ya kawo sallamar wata baƙuwa mai tsananin kama da Maman Sadiq. Ganin abinda ke faruwa duk da batasan wa suke duka ba ta ajiye jakka itama ta shiga cikin masu rabo. Da ƙyar suka iya yakice Zinneerah a tsakkiyar su Maman Sakina daketa zage-zage tamkar dangin maguzawan farkon ƙarni.        “Innalillahi, mike faruwa kukuwa haka a gidan naku Yaya Hauwa? Maman Halima miya kaiki shiga wannan shirmen?”. Baƙuwar ta faɗa tana duban Maman Sadiq dake jijjiga Little, sai kuma ta maida kan maman halima. Kafin ta dubi Zinneerah data nufi ɗaki abinta kamar bada ita aka gama kicimilliba yanzun.          Cikin baƙin ciki Maman Halima tace, “Sannu da zuwa Maryama. Dolene ta kaini ga hakan ai, taya zasu tararma yarinya haka bayan ta fisu gaskiya. Sam Saude batason a zauna lafiya a gidan nan wlhy Maryama”.       Ganin yanda su Maman Sakina ke ƙara hayayyaƙowa yasa baƙuwa Maryama cewa, “Kunga naga wata sabuwar fitinar ke neman tashi kuma. Maman Luba dan ALLAH kuyi haƙuri haka ya isa. Yaya shige muje, Maman Halima dan ALLAH kema shiga ɗaki kawai”.      Shawarar Maryama Maman Halima da Maman Sadiq sukabi kowa ya shige aka barsu sunata haushi kamar karnuka. Sai da suka shiga ne Maryama taga Zinneerah da ƙyau. Cikin ɗaurewar kai tace, “Wai nikam wa nake gani anan haka Yaya?”.        “Hummm Maryama bar wannan batun zauna ki huta. Sannu da zuwa kinsha hanya. Bansan kina tafeba ai”.         “Tafiyar bata shiri bace ba ai Yaya. Kuma nama nema wayarki amma sam bana samu, shiyyasa kawai nai ƙuru nace bara na biyo ɗin dai kar nai rashin hankali”.       “Tofa, ALLAH yasa badai wani abune ya faruba kuma?”. Mama ta faɗa tana mikama Zinneerah da kanta ke duƙe a ƙasa alamar kuka take little. “Ki tashi ki masa wanka a bashi abinci tunda yayi shiru”.        Sai lokacin Zinneerah ta ɗago tana share hawayenta. Ta amshi little ɗin kafin ta gaida Maryama. Amsa mata tai tana binta da kallo, hakan yasa Zinneerah miƙewa ta shige ɗaki da Little a hannu. Ajiyar zuciya Maryama ta sauke bayan shigewar Zinneerah ɗin, duk maman sadiq dake ƙoƙarin kawo mata ruwa na kallonsu. Sai da ta ajiye ruwanne ta sake maimaita mata tambayar ɗazun.        Maryama tace, “Lafiya ƙalau, sai dai lafiyar mai rauni. Inno ce jikin nata babu daɗi, dan sunce shekaran jiya da daddare kamarma bazata kwana duniya ba”.        “Innalillahi wa'inna ilairraji'un. Yanzu nan har jikin Inno yakai tsanani haka amma baza'a sanarminba Maryama, har ke dake a Minna kiji”.       “Kiyi haƙuri Yaya Hauwa, wlhy ba laifinsu bane. Buba yace tunda ciwonta ya fara motsawa a cikin satin nan suke neman wayarki data Yaya amma basa samunku. Ni kaina Baban su Atiku suka samu tunda kinsan dai ba wani muhimmanci wayata kedashi ba”.         “Eh kuma sun fini gaskiya, dan layin nawane ya samu matsala wlhy, Yaya kuwa bansan yaya akai suka gaza samun nasaba, kokuma matsalar network ne. UBANGIJI ALLAH ya ƙara mata lafiya. Jikine na tsufa sai dai Alhmdllh”.        “Wlhy jiki kam na tsufa. Dama na biyo ne idan babu matsala sai mu wuce Baucin tare mu dubata, to saima ina shirin tahowa danai waya da Buba yake sanarmin ai Hajiya Iya taje garin taga halin da take ciki ta ɗakkota suna anan kano wajenta”.          “Tofa, ita Hajiya Iya ɗin dama suna anan kano ɗin har yanzu?”.      “A'a yaya yakike wannan magana haka. Handa Hajiya Iya da iyalanta sukai ƙarfi a garin nan kina ganin zasu iya barinsa kuwa? Kenan baki cikama Inno alƙawarin da kikai mata na neman inda suke ɗinba?”.          “Humm Maryama bazaki ganeba. Ni wlhy kin ganni nan harka da masu kuɗin nan ba sonta nakeba sam. Bani ƙaunar shiga inda akafi ƙarfina a wulaƙantani”.       “Kai Yaya kenan har kin sani dariya. Aiko kinga Hajiya Iya bata da wannan, mace ce maison zuminci sosai. Danni kinga mun taɓa haɗuwa da ita kusan sau biyu kuma duk banga wani nuna ƙyama daga garetaba. Saima jana da taitayi a jiki tana min faɗa da cewar Baba ya rabamu da dangi bamusan kowaba sai Inno”.          “To kinsan abinne da wuya wlhy Maryama. ALLAH ya ƙaddara bazanje ɗinba sai ta silar zuwan Inno ɗin. Dan yanzu hakama ni nama manta yanda adireshin gidan yake”.        “Wannan mai sauƙine ai Yaya sai a kira Baban su Atiku ya kira Buba muji. Nidai na kasa haƙuri, dan ALLAH wai wacece wannan mai kamanni damu haka? Inaji a raina jininmuce yarinyarnan”.      Murmushi Maman Sadiq tai tana mata harar wasa. “Rashin haƙurinki na nan dai Maryama. to ƴarki ce ta Danya ƙaddarar rayuwa ta kawota nan”.      Da matuƙar mamaki Maryama tace, “Wai Yaya kina nufin Zinneerah?”.      Kai kawai Mama ta gyaɗa mata tana amsa sallanar Maman Halima.       Shigowar Maman Haliman ta saka Maryama yin shiru, Maman Halima ta ajiye mata kular abinci tare da zama suka gaisa cikin mutunta juna da tambayar lafiyar iyalai. ta mike zata fita Maman Sadiq ke sanar mata dalilin zuwan Maryama ɗin.           Jajanta musu Maman Halima tai cike da alhini, tare da addu'ar samun lafiya ga Inno ɗin kakarsu data haifi mahaifiyarsu. Bayan sun mata godiya ta fice. Maman sadiq kuma ta ƙwalama Zinneerah kira.      Koda Zinneerah ta fito sai Maryama dake sharar hawaye ta miƙa mata hannu tana faɗin, “Zonan ɗiyata dan ALLAH, zo naji ɗuminki”.     Babu musu Zinneerah ta nufeta duk da batasan wacece itaɗin ba. Sai dai kamaninta da mahaifiyarta ya tabbatar mata jininta ce. Haɗata tai ita da Little da yasha wanka duk ta rungume kukanta na ƙara ƙarfi. Maman sadiq ta miƙe tana ƴar dariyar ƙarfin hali da faɗin. “Oh halin naki dai bai canzuwa kenan har sai ƴar taki ta ganoki itama. Nikam bara kiga na miƙe, kema idan kin gama kukan kizo kiyi sallar la'asar kiɗan watsa ruwa sai ki zaman cin abincin ƙyafi jin daɗi”.        “Yaya dole nai kuka kodan kunya da takaicin kammu akan yarinyarnan. Zinneerah ki gafarcemu dan ALLAH, munsan bamu ƙyauta mikiba, bamuyi miki adalciba a rayuwa. Dan ALLAH ki mana afuwa”.        Zinneerah bata iya cewa komaiba. Sai murmushi kawai da take famanyi da ƙoƙarin danne nata kukan dake neman kufcewa. Sai da Maman Sadiq data sake fitowa mata maganar tazo tai wankan ne ta lallaɓeta da ƙyar ta share hawayenta da sakin Zinneerah da itama zuwa yanzun hawayen take sharewa. ★★★       Bayan Gwaggo Maryama tayi wanka da salla sukai zaman cin abincin zuminci da ƴar uwarta. Yayinda little kenan tare dasu a falo nata wasansa konace ɓarna. Zinneerah kam tuni ta shige ɗaki dan zazzaɓi nema ke neman rufe mata jiki.       Gwaggo Maryama ƙanwa ce ga Maman Sadiq. Uwarsu ɗaya ubansu ɗaya. Sukaɗai mahaifiyarsu ta haifa a duniya ALLAH yay mata rasuwa, dan haka akwai shaƙuwa mai ƙarfi da ƙaunar juna tsakaninta da ƴar uwartata wadda ƙaddarar aure takai can Minna jihar Niger. A yanzu haka itama ta zuba iyalai acan Alhmdllh.          Kaf labarin Zinneerah da dalilin zuwanta nan wajensu da samuwar Little Maman Sadiq sai da ta zayyanema ƴar uwarta dakeshan kukan tausayin Zinneerah har cikin ranta. Tare da ɗaukar dukan laifi ta ɗora akansu suda sukai wasarere da lamarin Zinneerah ɗin bayan sunsan rashin imani irin na Asabe. Tunda har ta iya rabo Maman Sadiq da mijinta itama Zinneerah ɗin ba barinta zataiba.         Murmushi mama tayi, cikin son kwantarma da ƴar uwarta hankali ta shiga nuna mata komai ƙaddara ne. Tunda UBANGIJI ya hukunta sai Zinneerah tai irin wannan rayuwar babu wani daya isa hana hakan a cikinsu ai. Sai dai su cigaba da mata fatan alkairi kuma a rayiwarta ta gaba. Wannan kam ta rigada ta faru kuma.          “Hakane Yaya Hauwa. Amma wannan tabon bazai taɓa goguwa a zuciyar yarinyarnanba dangane da watsi da mukai da ita bayan duk munsan a inda take”.       “To yadai wuce yanzu dan ALLAH. Muci abinci koma kimtsa kafin Yaya ya shigo gidan muji yanda za'ai tafiya inda Inno take. Dan da san samune mu tafi yau duk da naga garinma dai yana haɗe fuska alamar hadari”.         Da wannan maganar ta Maman Sadiq bakin Gwaggo Maryama yayi shiru. Suka ƙarasa cin abincin da saida ta matsa mata. Daga haka suka zauna zaman hirar zuminci da jiran dawowar Abba gidan.      Kamar yanda su Maman Sadiq ke jiran dawowar Abba iyalan Maman Sakina ma zaman jiran dawowar tasa gidan suke cike da alwashin sai Zinneerah tabar gidan yau ɗin nan. Duk da sun shige ɗaki basubar zage-zage ba da aibanta Maman Sadiq da Maman Halima. Dan ko abincin rana yau sunƙi zuwa su ɗakko na ɗakinsu har yamma tayi yara suka dawo daga makarantar islamiyya.          Tunda su Abdull sukaga Gwaggo Maryama suka rikice da murna sosai. Itama taji daɗin ganinsu. Ta haɗasu a jikinta ta rungume harda Little daketa walwalar ganinsu.         Bayan an idar da Sallar Magriba Sadiq yazo yana sanarma Mama Auntynsu bata da lafiya. Kafin tace wani abu sallamar Abba ta shigo kunnuwansu alamar ya dawo gidan kenan.        Duk da suna a cikin ɗaki ba kuma nan ya shigoba kai tsaye sai da suka amsa. Su Sadiq duk suka fice yima Abban sannu da zuwa kamar yanda suka saba idan ya shigo suna gida.      Wuff Maman Sakina ta fito daga ɗakinta tunda taji sallamar mijin nasu. Kusan a tare suka shiga falonsa da ita da yaran. Sama-sama ta gaidashi, zata fara kumfar baki ya ɗaga mata hannu dan dama tun a yanayin data shigo yasan gidan babu lafiya. Ga kuma Aliyu na faɗa masa Auntynsu bata da lafiya tana ɗaki kwance.       “Salla zanyi, sannan kinsan dokata a gidan nan bana buƙatar yin maganar da duk bata shafi alkairiba a gaban yarana. Dan haka ki koma sai anjima idan na nutsu kizo miyi magana ba yanzu ba”.      Wani irin baƙin cikine ya turnuƙe zuciyar Maman Sakina. Ta fito fuuu kamar zata tashi sama. Da kallo kawai ya iya binta yana mai girgiza kansa.      A ɗaki kuma Gwaggo Maryama ce da kanta ta miƙe zuwa wajen Zinneerah da Sadiq yace bata da lafiya. Ƙudundune ta sameta cikin bargo tana rawar sanyi. Saurin ƙarasawa tai gareta tana faɗin “Subahanalillahi Zinneerah dama baki da lafiya amma kikayi shiru?”.     Kafin Zinneerah ta bata amsa Maman Sadiq ta shigo ɗakin itama. Duban inda take kwancan tayi tana bama Gwaggo Maryama amsar zancenta. “Tunda ta iya cin dambe ba dole tai zazzaɓi ba. Ki tashi kiyi wanka da ruwan zafi kici abinci kisha magani, dan wannan dai zazzaɓin bai wuce sanadin hayaniyar nan ba”.     Cike da takaici Gwaggo Maryama tai tsaki. “Shi dai yaya ya auroma kansa masifa wlhy. Ayi mace bata son zaman lafiya kamar dangin yahudawa”.       “Humm ai kaɗanma kenan Maryama, dan wannan fitinar ba mutuwa taiba rufa tai, na tabbata jiran dawowar maigidan take, bara kuma kiji zakice nina faɗa miki”.       “Fitinanniyar banza. Gashi nan duk tabi ta koyama ƴaƴa hali mara amfani, aini Zinneerah ta birgeni sosai data nuna musu ƙyalesu dama kawai take ba tsoro bane. Shi kuma yayan tunda yasan halinta dama ai kinga sai yay musu iyaka yanzun”.       “To ALLAH yasa. Dan da kike ganinta a haka son matarsa yakeyi”.        Kiran sallar magriba da aka kirane ya katse hirar tasu. Zinneerah kam dama harta shige bayi tuni.        Bayan idar da sallar magriba Gwaggo Maryama ta tsare Zinneerah taci abinci tasha magani sannan ta kwanta. Maman Halima ma ta kawoma Gwaggo Maryama nata abincin yaɗan zauna sukai hira bayan ta shiga ta duba Zinneerah data sanu barci. Kiran sallar isha'i yasata komawa nata sashen.         Alhaji da yara kam basu shigo gidanba sai da aka idar da sallar isha'i. Harda Little da yay barci. Gwaggo Maryama ta amshesa ta goya tana maijin tausayin yaron a ranta.         Sai da Maman Sadiq ta tabbatar Alhaji yaci abinci ya huta sannan suka fita ta raka ƴar uwarta danta gaidashi. Sai da sukai sallama ya amsa shi da Maman Halima dake tare da shi  sannan suka shiga. Sosai fara'ar fuskarsa ta daɗu yanama Gwaggo Maryama lale da zuwa dan dama yara sun sanar masa zuwanta.        Suna kaiwa zaune sai ga Maman Sakina tamkar an jehota falon dan ko sallama basa tunanin tayi. Kallonta Alhaji yayi kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya maida hankalinsa ga Gwaggo Maryama. Hakan da yayine ya saka Maman Halima da Maman Sadiq suma yin kamar basusan da shigowar tataba.        “An haɗa kai an shigo dan a ƙulla mana sheri ni da ƴaƴana. To ta ALLAH bata mutumba”.      Babu wanda ya tanka mata. Sai da Alhaji ya gama gaisuwarsa ta zuminci da Gwaggo Maryama sannan ya dubeta fuska a tsuke. “Saude yaushe ne zakisan inda ke miki ciwo ne wai kekam?”.         “Taya kuwa zansan ciwon kaina agola ta haɗani da ƴayana ta doka saboda an gina mata jiki da tuwon gero dana dawa Abban Luba”.       Kallonta kawai yake batare daya tankaba. sanin baya son jan rai a magana ya sata fara zayyane masa abinda ya faru, sai dai tanayi tana haɗowa da ƙarya da sheri. Tsam Gwaggo Maryam ta miƙe zata fice ya dakatar da ita. “Maryam kina gidan duk akai wannan?”.       “A'a gaskiya Yaya kafin nazone. Nadai iske kawai suna rikicin faɗa nashiga na taya Maman Halima rabawa”.       Komai baiceba sai kallonsa daya maida ga Maman Sadiq. “Ina Zinneerah ɗin take?”.      “Tana can kwance babu lafiya”. “A dalilin shi wannan rikicin kenan?”. Ya tambaya yana cigaba da dubanta.     Kafin ta amsa masa Maman Sakina ta karɓe da faɗin, “Andai shirya munafunci kawai za'ace, yo inba munafun........”      “Saude!”. Ya katseta a tsawace. Badan tasoba dole tai shiru. Yaja tsaki da faɗin, “Da safe inason ganinku dukanku har yaran”. Ya faɗa yana miƙewa ya fice.     Ganin haka ya saka su Maman Sadiq miƙewa suma duk suka fito. Sai dai a mamakinsu sai hangarsa sukai ya nufi sashenta da alama duba Zinneerah zaijeyi.      Hakan yama Gwaggo Maryama daɗi sosai, duk da dama tasan halin ɗan uwan nasu baya wasa sam da lamarin gidansa. Amma batai tunanin Zinneerah ta samu matsayi na musamman haka a garesaba.       Bayan ya shiga ya dubata tana barci dan haka ya fito falo. Batare da dubansuba ya nufi hanyar fita yana faɗin, “A tada ita muje ko nan kyamis ɗin Umar ne tunda dare yayi”.      Halinsa da Maman Sadiq ta sani yasa bataja zancenba taje ta tado Zinneerah suka tafi kyamis ɗin. Itako Saude nacan tana tijara a sashenta kamar zata haɗiye haƙoranta, musamman ma dataga Alhajin ya fita tare da Zinneerah da Sadiq. WASHE GARI         Washe gari da safe Zinneerah ta tashi Alhmdllh babu zazzaɓin dan tasha allura jiya. Bayan idar da salla suka zauna zaman hira ita da Gwaggo Maryama dake janta a jiki cikin hikima. Sai da gari yay ɗan haske suna shirin fita gaida Alhaji sai gashima ya shigo duba Zinneerah ɗin. Kanta a ƙasa ta gaidashi. Ya amsa mata da kulawa kamar yanda ya saba da tambayarta kuma jikinta.      “Alhmdllh Abba naji sauki”.. “Haka akeso ai, ALLAH ya ƙara lafiya”.     “Amin” suka amsa gaba ɗaya. Sai da ya koma sashensa da kusan mintuna biyar sai ga Hussaina tazo kiransu. Maman Sadiq tasan Maman Sakina ce zata matsa da fitinar sai an zauna. Dan haka ta mike ita da Zinneerah ɗin suka tafi, aka bar Gwaggo Maryama na ƙarasa aikin da Zinneerah ta fara.        Kowa ya hallara su kaɗai ake jira, dan haka suka sami wajen zama suma su Luba nata harar Zinneerah. Alhaji daya gama nazarin kowa a ƴan sakanni ya basu damar bayani ɗaya bayan ɗaya.     Ya ɗan murmusa yana girgiza kansa. Sai kuma ya haɗe fuska ya balbalesu da bala'i su duka. Kafin ya dawo kan Aliya da Luba da sukaima su Maman Sadiq rashin kunya harda zagi. Ganinfa reshe zai juye da mujiya Maman Sakina ta miƙe da bala'i zata taresa ya daka nata tsawa itama. Cikin jan dogon gargaɗi yace, “Wlhy daga yau ya sakejin makamancin haka akan matansa saiya musu dukan mutuwa a gidan”. Ya kuma sakasu bama su Maman Sadiq haƙuri da ita kanta Zinneerah ɗin. Sannan itama yay mata faɗa akan marin Aliya da tayi tunda yayartace. Yayi hakanne dan kawai kar ace yayi son kai dan yasan dai Zinneerah ta fisu gaskiya. Daga haka ya sallami kowa suka fito Maman Sakina da ƴaƴanta ransu fal baƙin ciki da alwashin hana Zinneerah zaman lafiya a gidan cikin hanya mai sauƙi da Abban bazai gane komaiba.            Maman Sadiq kam ko a jikinta dan bataji komai ga abinda Abban yayiba. Sai ma shirin zuwa inda Inno take suka farayi dan Abban yace su shirya sai ya kaisu da kansa idan zai wuce kasuwa shima ya dubba Innon daga nan. Hakan yasa Maman Sadiq amso wayarsa suka kira mijin Gwaggo Maryama ya turo musu lambar Buba dazai kwatanta musu gidan Hajiya Iya ɗin ko asibitin da Inno ke kwance.............✍ *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* *Page 15* ____________________ *_INA MATA ƳAN ƘWALISA BA'ABOTA SON GYARA JIKI DA FATA SUYI ƘWANAS TAMKAR WATA ƊAN DAREN SHABIYAR?!_* _Ku marmatso kusa maza na kaiku kantin sauƙi na UMMU DUFAIL gidan sauƙi da biyan buƙatar MATA SARAKAN ado harma da MAZA ƴan ƘWALISA._ *_MATA da yawa kanso su koma Taurari ababen kallo da burgewa ga ma'abota kallo sai dai basusan ina zasu sami sinadarin kankaro wannan ƙyawu da mutuncinba._* _To maza kuzo kusa dan Bilyn Abdull ta lalubo muku kantin sauƙi na Umm Dufail dakeda kaya masu sauƙi da gamsar da maison afani dasu_. *_UMMU DUFAIL nada kayan gyaran jiki masu rahusa da inganci da gamsar da mai saya cikin ƙanƙanin lokaci kamar haka👇🏻😁_* *Customers price list By Ummu Dufail FACE AND BODY* SCRUB=2500(300ml) Face and body mango butter=3k (250ml) Face cream= 1800 Corretor oil/vitamin C oil=2k Fairness skin lotion= 2500 Hot chocolate skin lotion 2500 Serum (for Nuckles )2k Nuckles cream (stubborn)3500 Mix fruits Arabian black =soap 1800 Mix fruit glycerine soap =1900 Beetroot=1900 Coconut, milk,egg..face soap=1200 Lavender mix fruit soap =1800 Body wash =1500 cleanser=1600 Hair spray =700 Hair oil =1500 Hair relaxer =700 Hair butter 1700 Shampoo =1500 Breast=oil 2k powder 2k Strech marks cream= 2k Beetroot pink lips =700 Baby care soap glycerine=1k Baby care butter =1500 Shea butter baby soap =700 Tsumin tula =2200 Tsumin zinariya =1200 Sliming tea =1500 Amarya set =25k Liquid Arabian black soap =1900 Cleansing water =1500 *_Zaku iya bibiyarta domin gani da ido ta Handle ɗinta na istagram da facebook kamar haka_* Ummu Dufail @ Facebook Ummu Dufail @ instagram Phone no: 07067943479. _Ƴammata harma da masu auren karku bari ayi babuku. Dan gyara shine mace a wannan ƙarnin😉👍🏻_. ___________________ *Page 15* ...........Tunanin basusan mi zasu tarar a inda zasujeba Maman Sadiq ta yanke shawarar barma Zinneerah little a gida tunda yau bazataje Islamiyya ba, Alhaji yace saita warke. Su Abdul kam duk sun wuce makaranta dama. Sai da Mama ta jama Zinneerah dogon gargaɗi akan su Maman sakina sannan sukai mata sallama suka tafi. A tsakar gidanma sallama sukaima Maman Halima harma da Maman Sakinar duk da ba kulasu tai da ƙyau ba.       Sai da Alhaji ya ɗauka hanyar barin anguwar tasu sannan ya kira wayar buba dazai musu kwatancen asibitin da Inno ke kwance a yanzu haka. Bayan sun gama wayarne ya ɗan duba Maman Sadiq dake a gefensa yana ajiye wayar. “To ashema asibitin da aka kwantar da ƴata Innon take”.           Batare da kawo komai a raiba Maman Sadiq tai murmushi da bashi amsa, “Oh to abin yazo da sauƙi Alhmdllh. Dama inata tunanin karmu baka wahala musaka makarar zuwa kasuwa”.       “Kenan saboda Inno takuce ku kaɗai?”.      Yanda yay maganar cikin raha ya sakasu suma fara dariya suna faɗin, “A'a Yaya harda kai ai mana afuwa”.        Sun iso *_SHIRA HOSPITAL_*. Alhaji ya kira Buba ya fito ya shiga dasu har ɗakin da aka kwantar da Inno ɗin. Wajene na musamman a cikin asibitin da iyalan family ɗin Shira ne kawai keda hurumin shigarsa koyin jiyya a wajen idan hakan ta kama. Wajen tsitt yake sosai babu wata hayaniyar komai. Gashi a gare tsaf duk da kuwa sun tadda mutane kusan shidda tare da Inno ɗin.      Ɗakin da take ɗakine babba da komai na kulawar marasa lafiya wanda ko ƙasar ka bari iya abinda zaka iya zuwa ka tarar kenan acan ɗinma.        Inno ta tsufa sosai, sai dai ba irin tsufan nan da za'ace ta fita hayyacintaba. Dan tana gani ras tana kuma magana. Matsalarta kawai ciwon ƙafa dake damunta kasancewar ta mace mai jiki a da can. A yanzu hakanma bawai ramammiya baceba.         Tunda sukai sallama a ɗakin kusan duk waɗanda ke a ciki suka zubo musu idanu suna mai amsa musu sallamar tasu. Tsohuwa mai ɗan yanayin kamanni da Inno, sai dai bata kaita tsufaba, sannan alamar jin daɗi fiye dana Inno ɗin ya bayyana a gareta ta tsaresu da idanu tamkar maison gano wani abu.     Ganin duk sun tsargu da kallon da take musunne ya sata sakin murmushi da faɗin, “Wannan dai kamar Maryama idan idanun nawa na gani da ƙyau?”.      Murmushi Gwaggo Maryama tayi a karo na farko, dan sai yanzune ta gane Hajiya Iya. Cike da girmamawa tace, “Nice Gwaggo. Tare da Yaya Hauwa da mijinta”.            “Eh to naganki dai ke da na sani, sai kuma mijin nata zan masa na baƙunta, amma ita kam idona bai gantaba tunda itama nasan bason ganin nawa takeba kamar yanda bana tunanin tama sanni. Mutuniyar da aka sanarmin an bata adireshin inda nake a garin nan kusan shekara huɗu kenan amma bata nemeniba sai yau dalilin zuwan Inno, ai nikam banace nama santaba tunda dama canɗin ba sanin nata nayiba”.         Sanin halin Hajiya Iya ya saka sauran mutanen ɗakin kowa yin murmushi harda Alhaji da Gwaggo Maryama. Maman Sadiq ma kanta a ƙasa take murmushin. Inda Hajiya Iya ke zaune kusa da Inno ta ƙara ta durƙusa akan gwiwoyinta tana faɗin, “A gafarceni Gwaggo. Nasan ni mai laifice amma dan ALLAH ina mai neman afuwarki”.        “To zanɗan haƙura kaɗan idan mijinki ya sanarmin bashi da laifi wajen hanaki neman inda nake. Shi zuminci ai daɗine dashi koda na zaman anguwane balle ace na ɗan uwanka na jini. Uwa ɗaya uba ɗaya fa mahaifiyata suke da Inno, hasalima itace ta riƙe mahaifiyar tawa harta aurar da ita, dan itace ƴar zaman ɗakinta. Da hannunta ta raini mahaifiyarku har tsahon shekara huɗu kafin a aurar da ita. Amma ace yau ƴaƴan Hafsat na gudunmu saboda mahaifinku ya nisantamu daku a dalilin Hafsat bata raye a duniya”.     Yanda ta ƙare maganar tana sharar hawaye ya saka ɗakin yin tsitt, itama Maman Sadiq sai hawayen suka shiga silalo mata saboda tinawa da mahifiyarsu da ALLAH yayma rasuwa tun suna yara.       “Kiyi haƙuri Gwaggo munyi kuskure. amma insha ALLAH zamu gyara, na tabbatar miki zamu gyara”. Alhaji ya faɗa cike da girmamawa.      Gyalenta tasa ta sake share hawayen nata, sai kuma ta kalli Alhajin tana murmushi. “Shike nan ɗana ALLAH ya tabbatar da hakan. Tunda harkun gane kunyi kuskure na haƙura. Amma dan ALLAH ku gyara dan shi zuminci babban abune mai girma da ta silarsama za'a iya zuwa aljanna. Mu daina biyema sharrin sheɗan dana zamani zukatanmu nayin nisa da juna. Ina daɗi ace ƴaƴan Hafsat basusan inda nakeba saboda iyayenmu basa raye. Wajen gwaggo kawai kuke zuwa”.         “Tabbas ba'a ƙyautaba Gwaggo. Amma dan ALLAH ayi haƙuri. Kamar yanda ya faɗa insha ALLAH zamu gyara. Wlhy zuwanma da kikaga banyiba nima rasa takardar da aka rubutamin adireshin da lambar wayar nayi. ALLAH kuma bai ƙaddara duk sanda na shigo bauchi na sake amsar wani adireshin ba a wajen Buba”.         Hannu Hajiya Iya tasa ta kamo na Mman sadiq mai maganar, sai kuma ta kamo na Gwaggo Maryama duk ta haɗa cikin nata tana murmushi. “Ya wuce insha ALLAH, nima namuku hakane danku ƙara sanin muhimmancin zuminci, mu kuma sake dunƙulewa tsintsiya naɗaurinki ɗaya. ALLAH yayi muku albarka kuda zuri'arku damu baki ɗaya”.      Cikin jin daɗi su mmn Sadiq suka amsa mata. Daga haka aka koma gaishe-gaishe kamar ba yanzu Hajiya Iya ta gama sharar ƙwalla ba.      Sai da aka gama gaishe-gaishe da tambayar jikin Inno daketa kallonsu kawai dan ko magana bata iyayi amma tana jinsu. Hajiya Iya ta koma nuna musu sauran jama'ar ɗakin.        “To ga ƴan uwanku nan nasan duk baku sansuba. Waɗan nan biyun matan yayanku ne. Waɗan nan kuma ƴaƴanku ne dukansu gasu nan. Badai zaku gane lissafinba anan sai munje gida”.        Su mmn Sadiq dai murmushi sukeyi cike dajin ƙaunar ƴar tsohuwar, suka sake gaisawa da waɗanda ta nuna musun. Yanda suma babu alamun wulaƙanci a garesu yasaka jin farin ciki a zukatansu Mmn sadiq ɗin.     Hajiya Iya ta nuna su mmn sadiq kuma garesu suma tana faɗin, “Ku kuma waɗannan ƙannenku za'ace kenan ko. Dan ƴaƴan Yaya Hafsat ne da ALLAH yayma rasuwa babbar ƴar Gwaggo da aure ya kai can Katsina, nasan dai bazaku gaza jin sunantaba a hirata ma. mahaifinsu ne bai barsu sakewa a cikinmuba tun suna kananu shiyyasa baku sansuba basu sankuba kuma. Amma insha ALLAH daga yau kowama zai sansu ɗin”.      Duk suma amsa mata sukai da girmamawa dan babu mai jayayya da ita a kaf family ɗin harsu matan ƴaƴan nata. Sallama Alhaji yay musu ya tafi saboda ganin lokaci zai ƙure masa na kasuwa. ya wuce akan zai dawo anjima ya ɗaukesu idan ya taso.       Sosai su Mmn Sadiq suka tsinci kansu cikin farin cikin kasancewa da dangin mahaifiyar tasu da suka gaza samun kusanta a lokacin ƙuruciya yanda ya kamata. Dan mahaifinsu baison kaisu su sake a cikinsu gudun karsu ƙwace masa su. Sukan dai je suga Inno naƴan kwanaki su dawo. Hakan yasa ko lokacin aurensu dangin mahaifiyarsu ba kowa yazoba dan haushin babansu. Su kuma bayan duk sunyi aure rashin sabon tun farko ya hanasu sakewa dasu, dan Inno kawai suka sani da wasu tsuraru a ciki.         Babban abinda ya basu mamaki bai wuce yanda zuri'ar Hajiya Iya ke tururuwar zuwa asibitin duba jikin Inno ba. Saika rantse Hajiya Iya ɗince kwance ke jiyya. duk wanda yazo kuma saita masa bayaninsu suma sai ta musu bayaninsa. Alhmdllh kuma basuga raini ko wulaƙanci ga kowaba dukda kuwa sun shaida akwai kuɗi a wannan zuri'a kodan manya-manyan kulolin abincin da ake shigowa dasu na dubiya.      Har dare suna a asibitin Inno bata wani san da zuwansuba saboda zafin ciwo, sai dai binsu da take da ido da kuma surarensu. Gashi kuma ɗiyar ƴar uwarta nata kaf-kaf da abunta gwanin sha'awa.        Rigimar Hajiya Iya bata basu mamakiba sai da Alhaji ya dawo ɗaukarsu bayan ya taso kasuwa. Ta tubure akan babu inda zasuje gidanta zata wuce dasu su kwana dan asibitin Nurses ke kwana da Inno. Ana cikin wannan kicimilli babban ɗan Hajiya Iyan ya iso asibitin. Dawowarsa kenan daga tafiya ko gida bai shigaba ya wuto nan dan duba Gwaggo mahaifiyar tashi, shi kuma kakarsa.        Tunda yay sallama cikin ɗakin Alhaji yay suman zaune. Akan laɓɓansa ya ambaci *_“Alhaji Kabir Abdul-Mutallab Shira_* babbar magana”.      Alhaji Kabir Shira da baisan da zancen zucin Alhaji ba ya ƙarasa gaban mahaifiyarsa duk da shekarunsa na girma ya kai har ƙasa duƙe yana gaisheta da tambayar mai jiki.       Amsa masa take da kulawa tare da tambayarsa yaya hanya?.       “Alhamdulillahi innata. Ina fatan ana samun cigaban sauƙi a jikin Inno ɗin?. Dan tunda kika sanarmin halin da kuka sameta jiya da ƙyar nai barci. Inagama zuwa Laraba insha ALLAH kawai za'a wuce da ita India”.       Cike dajin daɗi Hajiya iya ke jinjina kanta. “Wannan tunanin shine dai-dai Babangida. ALLAH yay maka albarka. jikin kam Alhmdllh dan bakamar jiya da muka baro Bauchi da ita ba. Amma dai nima nafi yarda da maganar zuwa india ɗinma a duba wannan ƙafar tata da ƙyau”.        “Karki damu Innata, insha ALLAHU harma nayi magana da Bashir zai fara shirye-shiyen tafiyar daga daren yau ɗin nan”.      Sai da ta jero masa addu'a sosai, sannan ta nuna masa su maman Sadiq dake gaisheshi. Bayan ya gama amsa gaisuwar yaransa da suma ke cike da ɗakin mazansu da matansu. Dan dolene kazo duba Inno saboda muhimmancinta ga Hajiya Iya.        Da kulawa ya amsa musu yana sauraren bayanin mahaifiyar tasa. bayan ta gama ya miƙe tsaye yana bama Alhaji hannu da faɗin, “Lallai yau ina cike da farin ciki gani ga ƙannena da ban saniba suma basu sanniba kuma. Idonku kenan a gabanmu?”.        Cike dajin kunya da mamakin sauƙin kansa tamkar mahaifiyarsa suka shiga bashi amsa. shiko kasancewarsa mutum ɗan boko kansa tsaye yake masu magana har Alhajin dake mamaki da al'ajabin dama Alhaji Kabir Shiran haka yake da sauƙin kai ashe? Bazaka taɓa cewa shahararren ɗan kasuwar nan bane mai faɗa aji a cikin kano da wajenta a gabansu haka ba. Dan ya saki jiki dasu sosai babu wani alamun girman kai ko raini duk da ya gansu talakawa kuma yaune ya fara sanin nasu.       Sai da suka fito zasu tafi ne dan itama ashe isowarsa take jira su tafi gida tare yakejin zancen cewar ta hana su maman sadiq bin alhaji gida.      Murmushi yayi mai ƙayatarwa yana duban mahaifiyar tasa da jinjina rigimarta dason zuminci.        “Innata ai ba'ayi hakaba. Nasan dai ƙannena bazasu rasa yara a gidaba. Dan haka kiyi haƙuri suje yau ɗaya su shiryo kamar zaifi”.         “Uhm-uhm Babangida banyardaba. Salon suje suƙi dawowa tunda dama gudunmu sukeyi”.       “A'a Inna baza'ayi hakaba insha ALLAH”. Mmn Sadiq ta faɗa da sauri.      Sudai sauran jikokinta da suke asibitin dariya suketa kwasa a gefe sanin halin kakar tasu. Itafa indai akan zumincine bata da wasa. Shiyyasa su kansu suka tashi da wanan trianing ɗin nata kansu ke a haɗe bakajin wani fitina sai wadda ke a ɓoye dan ba'a rasataba musamman a tsakanin iyayensu mata.      Da ƙyar dai Alhaji Kabir ya lallaɓa Hajiya Iya ta yarda akan su mmn sadiq su taho da shirinsu gobe idan ALLAH ya kaimu. Daga haka Alhaji Kabir ya buɗe mata motar da aka kawosa da kansa ta shiga, shima ƴaƴansu suka buɗe masa yana ma su Alhaji sallama da jaddada ma su mmn sadiq su taho da ƙatuwar jakka dan sai Iya tasha ziyararsu ta more zasu koma gidajensu.        d sukai masa dajin daɗin wannan karamci da suka samu daga manyan mutane da ada basu taɓa tunanin ganiba ido da ido sai gashi sun kasance jininsune ma ashe. _______★★          Sai da suka ɗauki hanyar gida ne cikin mamakin daya kasa sakin Abba har yanzun yace, “Nifa kaina a ɗaure yake har yanzu Hauwa'u. Wai dama kunsan familyn Alhaji Kabir Abdul-Mutallab Shira sune ƴan uwanku ɗinnan da kika taɓa bani labari?”.         Saurin kallonsa Mmn sadiq tai da mamaki itama tace, “Kabir Shira kuma yaya? Muko a ina zamu san Shira? Bashi baneba”.        Ƙaramar dariya yayi saboda fahimtar itama dai da gaske batasan hakanba, ya kalli Maryama ta mirror “Maryama kema baki saniba kenan?”.      “Wlhy Yaya ban saniba. Nadai san Gwaggo Aminan na anan cikin kano da iyalanta, kuma sunda arziƙi suma, sai dai bansan sune ake kira Shira ba koda wasa”.        “Ikon ALLAH kenan. To aiko waɗanan dai sune Shira Family da ake faɗa a cikin kano da wajenta. Kuma kenan wanda yayma Abdull-Mutallab alkairi har yaci sunansa shima jininsu ne. Wata hikima sai UBANGIJI kenan”.       “Gaskiya kam Yaya. Dan wannan UBANGIJI ne kawai mai kusanta abinda suka kasance makusanta batare da su kansu sun saniba. Amma wlhy ni harma na tsorata. Sai dai sun bani mamaki yanda sukasan darajar mutane”.        “Ai babu wani abin tsoro Hauwa'u, sanin darajar mutane kam tarbiyyarsuce hakan daga mahaifiyarsu. ALLAH ya ƙara mana zuminci da sanin darajarsa”.     Sun amsa da “Amin ya rabbi” dai-dai suna isowa gida. Bayan Alhaji yayi fakin a inda yake ajiye motarsa anan ƙofar gidan duk suka fito suka shiga dan ba'akai ga rufe gidanba da alama su ake jira.     Ilai kuwa a tsakar gida suka iske Maman Halima zaune baiwar ALLAH. Ta tarbesu da sannu da zuwa tare da tambayar mai jikin?. Saida suka tsaya wajenta suma suka gaisa da sakejin lafiyar gidan sannan suka shige dan duk a gajiye suke.      Yaran duk sunyi barci kamar yanda Maman Halima dama ta sanar musu. Sai Little ne kawai kecan wajenta shima bayan tafiyar tasu zazzaɓi ya rufesa ashe. Itama dai Zinneerah wuni tayi kwance sai yamma zazzaɓin ya saketa harta ɗan fita tsakar gida ta zauna dan Maman Sakina da yaranta basu yini a gidanba.       Wanka kawai sukai suka nema makwanci tunda a ƙoshe suke.         Washe gari tunda safe Alhaji ya samu kira daga Alhaji Kabir Shira daya amsa lambar hannun Buba. Da farkoma bai gane mai maganaba sai da yay masa bayani. Cikin ɗan rikicewa Abban ya shiga gaishesa dan zai iya girmarsa ma ko'a shekaru. Sai kuma yanda yaji muryarsa ya sake rikitashi.       Daga can Alhaji Kabir ya sanarma Abba ALLAH yayma Inno rasuwa tun asubahin yau, yanzu haka ga gawarta zasu ɗauka zuwa can gidan, sai suyi ƙoƙari suzo ayi jana'izarta dasu.       “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un” Abba keta faman ambata dukkan gaɓɓansa na saki lokaci guda. Da ƙyar ya iya fitowa zuwa sashen Mmn Sadiq ɗin yace musu su shirya zasuje asibiti. Sosai hakan ya basu mamaki, sai dai ganin bai basu fuskar da zasu tambaya ba ya sakasu yin shiru gabansu na faɗuwa. Dan sunaji a jikinsu lallai babu lafiya.      Yau ɗinma dai haka suka shirya suka tafi su biyu kawai ko little ba'aje da shiba sabboda baijin daɗi. Zinneerah dai gara ita da sauƙi jikinta ba kamar jiyaba.     Kasancewar gidan Alhaji Kabir Abdul-Mutallab Shira ba ɓoyayye bane a birnin na kano kai tsaye Abba ya nufi can dasu bayan ya kira Buba kawai ya tambayi anguwar.      Gidane katafare sosai, duk da kuwa gidajen anguwar ma babu ƙaramin gida. Kasancewar Buba ya fito gate ya saka suka samu damar shiga babu wani gargada dan mutane basu kai ga fara isowaba. Ruɗanin mutuwar da suka samu ya hanasu damuwa ko tsayawa duban yaya gidan yake, balle tsarinsa.       Kukan Hajiya Iya ya matuƙar sake tada hankalin kowa dake a gidan matuƙa. Su Mmn Sadiq kam ai ba'a magana dan suna tsananin so da ƙaunar kakar tasu, musamman daya kasance ita suka tashi suke gani tamkar mahaifiya a garesu tunda sun rasa tasu tun basusan kansuba.        Cikin ƙanƙanin lokaci gidan ya cika da ƴan uwa da abokan arziƙi, dan ba'a binne Inno ba sai da tawagar ƴan bauchi ta iso. Inno uwace kuma kaka da wannan family bazasu taɓa mantawa da alkairan data ginasu a kaiba. To yau dai gashi ta tafi ta barsu da kewa da kuma alkairin data bari baya garesu. Dama ita kaɗai ta rage musu cikin iyaye. To ya rage nasu subi bayan nata da addu'a batare da gazawa ko ƙosawaba.      (Ya rabbi kasa mu kasance cikin bayinka masu barinma bayanmu tarin alkairi ba sharriba. ALLAH yasa ranar barinmu duniya ta zama ranar farin ciki a garemu😭🙏🏻, ALLAH ka gafartama iyayenmu da bayin ALLAHn da suka rigamu tafiya badan sunyi gaggawaba🙏🏻😭).     A ranar dai dole su Maman Sadiq anan gidan suka kwana. Yanda manyan mutane keta shigowa gaisuwa sai kasha mamaki da tabbatar da lallai Inno nada matuƙar daraja ga Hajiya Iya. Dan dukkan ahalinta suna ɗaukartane kakarsune uwa ga Hajaiya Iya, hakan yasa dukan harkokinsu suka tsaya cak harna tsahon kwanaki uku da aka amshi gaisuwa. Sai a ranar cikon ta huɗu ne ƴan Bauchi da suka rage suka koma gida, hakama sauran dangi dake wasu garuruwa kowa ya kama gabansa.     Suma su mmn sadiq shirin komawa gidan sukeyi yau dan harma sunyi waya da Abba akan zuwa anjima zaizo ya ɗaukesu insha ALLAH. Shima dai kwanakin nan uku kullum sai yazo gidan wajen amsar gaisuwa, hakama mijin Gwaggo Maryama yazo harda ƴaƴanta biyu maza duk da ƙananune, amma a ranar suka koma.       Da ƙyar Hajiya Iya ta aminta da komawar tasu, sai dai ta musu dogon sharaɗi da gargaɗin wannan karon bazata yarda da sakaci da zuminciba. dan su kaɗaine jinin inno mafi kusanci da suka rage a yanzu. Dama Inno bata wani haihu da yawaba. Yaranta biyune kacal a duniya, mahaifiyarsu sai mahaifin Buba. Kuma duk ALLAH yay musu rasuwa, shima Buba shi kaɗaine namiji a wajen mahaifinsa sai ƙannensa mata biyu duk sunyi aure anan Bauchi. Suma kuma sai da Hajiya Iya taja musu dogon gargaɗin kafin su wuce da safe. Sai su kuma su Mmn Sadiq ɗin da suka kasance suma su biyu kawai.      Sun mata alƙawarin kulawa insha ALLAH a wannan karon. Da wannan yasa ta amince su koma gida ɗin dan Gwaggo Maryama ma da anyi bakwai zata wuce duk da ba taro zasuyiba, amma tace zata sake dawowa nan gidan taima Hajiya Iya sallama.      Sai kusan biyar na yamma Abba ya iso tare da su Sadiq da Mama batasan dasu zaizo ba. Amma hakan da yay ya sakata jin daɗi matuƙa kamar yanda Hajiya Iya ma ta nuna jin daɗinta sosai.      Har ƙasa su Zinneerah suka kai suna gaisheta da mata gaisuwa. Cikin jin daɗi ta kamo hannun Zinneerah ta zaunar kusa da ita tare da Aliyu. Suma su Sadiq tace su matso gareta.       “Ikon ALLAH, nan ai Inno ce kamar an tsaga kara an karya”. Hajiya Iya tai maganar tana nuna Zinneerah da kanta ke a ƙasa.      Sauran dake ɗakin suma suka shiga faɗin albarkacin bakinsu akan tsananin kamanni da Zinneerah ɗin keyi da marigayiya Inno. Dan duk wanda yasan Inno yaga Zinneerah yasan jinintace. Gashima ita Zinneerah ɗin ba saninta tayiba.      Hajiya Iya ta ƙara damƙe hannun Zinneerah dake cikin nata tana faɗin, “Lallai akwaiki da karambani, duk iyayenki damu kakanni kika tsallake sai kammanin Inno kika kwaso. Inno ta tafi ta barni ga ALLAH ya sake bani Inno a kusa dani dan na ƙwace”.       Kusan kowa dake falon sai da murmushi ya suɓuce masa. Yayinda kuma duk suka fahimci Hajiya Iya na nufin zata amshe Zinneerah kenan ta dawo hannunta. Hakan yasaka gaban Mmn Sadiq faɗuwa, amma sai ta dake dan ba wajen da zata iya jayayya bane balle musu............✍ 🤣😂Tofa, yau naga ƙarfin hali wajen wagga tsohuwa.      *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* *Page 16* ____________________ *_INA MATA ƳAN ƘWALISA BA'ABOTA SON GYARA JIKI DA FATA SUYI ƘWANAS TAMKAR WATA ƊAN DAREN SHABIYAR?!_* _Ku marmatso kusa maza na kaiku kantin sauƙi na UMMU DUFAIL gidan sauƙi da biyan buƙatar MATA SARAKAN ado harma da MAZA ƴan ƘWALISA._ *_MATA da yawa kanso su koma Taurari ababen kallo da burgewa ga ma'abota kallo sai dai basusan ina zasu sami sinadarin kankaro wannan ƙyawu da mutuncinba._* _To maza kuzo kusa dan Bilyn Abdull ta lalubo muku kantin sauƙi na Umm Dufail dakeda kaya masu sauƙi da gamsar da maison afani dasu_. *_UMMU DUFAIL nada kayan gyaran jiki masu rahusa da inganci da gamsar da mai saya cikin ƙanƙanin lokaci kamar haka👇🏻😁_* *Customers price list By Ummu Dufail FACE AND BODY* SCRUB=2500(300ml) Face and body mango butter=3k (250ml) Face cream= 1800 Corretor oil/vitamin C oil=2k Fairness skin lotion= 2500 Hot chocolate skin lotion 2500 Serum (for Nuckles )2k Nuckles cream (stubborn)3500 Mix fruits Arabian black =soap 1800 Mix fruit glycerine soap =1900 Beetroot=1900 Coconut, milk,egg..face soap=1200 Lavender mix fruit soap =1800 Body wash =1500 cleanser=1600 Hair spray =700 Hair oil =1500 Hair relaxer =700 Hair butter 1700 Shampoo =1500 Breast=oil 2k powder 2k Strech marks cream= 2k Beetroot pink lips =700 Baby care soap glycerine=1k Baby care butter =1500 Shea butter baby soap =700 Tsumin tula =2200 Tsumin zinariya =1200 Sliming tea =1500 Amarya set =25k Liquid Arabian black soap =1900 Cleansing water =1500 *_Zaku iya bibiyarta domin gani da ido ta Handle ɗinta na istagram da facebook kamar haka_* Ummu Dufail @ Facebook Ummu Dufail @ instagram Phone no: 07067943479. _Ƴammata harma da masu auren karku bari ayi babuku. Dan gyara shine mace a wannan ƙarnin😉👍🏻_. ______________________ *Page 16* ............Kamar da wasa sai ga ƙaramar magana ta zama babba. Dan kuwa dai Hajiya Iya da gaske take akan amshe Zinneerah daga hannun su Mama. Dan take a wajen ta ɗaga waya tai kiran Alhaji Kabir da dukkan ahalin gidan ke kira da suna Baffah.      A rayuwa Alhaji Kabir bai haɗa uzirin mahaifiyarsa dana kowaba. Kai bama shi kaɗaiba har sauran ƴan uwansa da jikokin familyn babu mai sakaci da buƙatar Hajiya Iya. Dan ita ko wasan jika da kaka sai taso takeyinsa.     A cikin ƙanƙanin lokaci sai gashi a sashen nata. Hannu ya bama Abba suka gaisa yana faɗin, “Ai bansan ka shigo gidanba Alhaji Isma'il, dana fito mun gaisa”.        Abba yace, “Wlhy yanzuma na shigo Yayanmu, nazo wucewa da ƙannenka ne, sai kuma ƴayanka dana kawo suma suyi gaisuwa su kuma gaida Gwaggo”.        “Kai kai masha ALLAHU, lallai yau ka farantamin sosai sosai. Kuzo-kuzo ƴaƴan albarka ga babanku da baku saniba ko”.      A nutse su Sadiq duk suka nufesa harda Zinneerah. Sai dai ita ta durƙusane daga gefensa kaɗan. Saɓanin su Abdul daya jawo jikinsa ya rungime. Sai da su Sadiq suka gama haishesa ya amsa da kulawa da tambayarsu sunyaensu da ajinsu nawa a makaranta kafin ya maida dubansa ga Zinneerah itama.      “Ikon ALLAH, Inna wannan ai saikace Inno ta haifeta dan kamanninsu. Ɗiyata yaya sunanki?”.        Zinneerah da kanta ke duƙe tana wasa da yatsun hannuna tace, “Zinneerah”. “Masha ALLAHU suna mai daɗi kamar yanda kike ƙyaƙyƙyawa ɗiyata. ALLAH yay muku albarka. Ke ajinki nawa a makarantan?”.      A take murmushi ya subucema Zinneerah tace, “Abba ss1”.       “Kai-kai, kice Maman nawa bata wasa bace ƴar boko ce”.       Barkwancin nasa ya saka dariya suɓucema Zinneerah. Yayinda hakan kuma ya sake saka ƙaunarta a zuciyar Alhaji Kabir dan nutsuwar yaran da tarbiyyarsu ya matuƙar birgesa, musamman Zinneerah ɗin da take mace.     Kallonsa ya maida gasu Mmn Sadiq yana fadin, “You see. Gashi kun fara tara zuri'a amma basusan kowaba suma. Sai dai ko a hanya naci karo da Zinneerah ai nasan jini nace. Idan akaimin gaddama kuma har kotu zan kai dole a bani abata”.       Sosai maganar tasa ta saka kowa dariya. Hajiya Iya tace, “Aini kiranma danai maka kenan. Dan nikam dai babu mai rabani da mai kama da Inno tazo gida kenan”.       “Ina bayanki Innata. Dan haka Alhaji Isma'il dan ALLAH a taimakemu badan halinmuba a bamu Zinneerah, bamason a kalli hakan kuma fin ƙarfi roƙo muke gwiwoyinmu a ƙasa. Ƙila hakan ya zama sanadin gyaruwar zumincin dake neman kufce mana. Amma kuje dai kuyi shawara. Idan kuma akwai matsala dan ALLAH karkuji kunya ku sanar mana kanku tsaye zamu fahimceku insha ALLAH. Kunga ko ba'a bamuba sai take zuwa mana hutu ita da sauran ƴan uwanta lokaci-lokaci”.         Cike da jin kunyar wannan roƙo nasa Abba yace, “Ai kunfi ƙarfin hakan a garemu”. Yay maganar yana duban Mmn Sadiq data duƙar da kai.        Daga Hajiya Iya har Alhaji Kabir suma idonsu na kanta. Dan haka Alhaji Kabir yay saurin fadin. “To Alhmdllh, yanzu dai kuje kuyi shawaran nan da kwana uku sai muji yaya ake ciki kamar zaifi”.       Sam Hajiya Iya bataso jin hakan daga bakin ɗan nata ba, dan sotai take yanke su tafi su barta da Zinneerah, saboda wata irin ƙaunar yarinyarce ta musamman ta shigeta lokaci guda. Amma sai tai shiru dan itama taga cancantar barinsu suje su shawarta ɗin. Amma kuma komai zasuyi tasa a ranta sai Zinneerah ta dawo hannunta da zama dan yarinyar ba karamin shiga mata rai tayiba lokaci guda. shi kansa Alhaji Kabir wani irin kaunar yarinyar yaji a ransa batare da yasan dalilin hakanba.       Alkairi mai tsoka Alhaji Kabir yayma su Aliyu. kamar yadda aka koyar dasu tarbiyyar godiya haka suka shiga masa godiya da addu'ar fatan alkairi a rayuwa. Sosai hakan yay masa daɗi har cikin rai. Ya kuma kara jin girma da darajar su mmn sadiq sosai. Dan a wannan zamanin bama yaro tarbiyya shine mai matuƙar wahala ga iyaye aynun. ★★★★        Tunda suka baro gidan babu wanda ya iya yin magana, sai da suna gab da shiga anguwarsune ma Gwaggo Maryama tai ƙarfin halin tambayarsu ina suka baro little kuma?.       “Gwaggo ai baida lafiya an kwantar dasu a asibiti shida Umma”. Abdull ya bata amsa da damuwa a fuskarsa.       Saurin juyowa Mmn Sadiq tai ta kalli yaron, kamar zatai magana sai kuma tai shiru ta maida kanta. Fahimtar hakan da Abba yayi ya sakashi faɗin, “Ban faɗa muku bane dan banason raba muku hankali biyu, amma jikin nasama Alhmdllh dan yanzu haka sun koma gida ta kirani cewar an sallamesu ga Naziru yaje zai maidasu gida. Bakomai ke damunsaba kuma sai zazzaɓin haƙora”.      Addu'ar samun ingattacciyar lafiya sukai masa ita da Gwaggo Maryama. Daga haka suka ƙarasa gidan.         Sai da sukayi sallar magriba suka huta Maman Halima ta shigo gaishesu ɗauke da Little daya rame sosai saboda yasha jiki. danma ALLAH yayisa mai kwaramniya ga karfin hali da akasan duk yaro da shi.     Ƙiri-ƙiri sai gashi yana musu ƙyuya. Yaƙi yarda da kowa sai Zinneerah da kunya ta rufe kamar ƙasa ta tsage ta shige. Badan tasoba dole ta amshesa. Aiko ya wani lafe a jikinta yana kallon su Gwaggo Maryama dake jan kafarsa cikin tsokana tana fadin, “Aiko yaro nama fasa auren. Na maka saki goma sha biyu ni da kai baram-baram”.      Dariya Mman halima tai tana tare masa. Ana cikin haka Maman Sakina ta shigo da yaranta wai zatai musu gaisuwa. duk da bataje can gidanba sai mmn sadiq bata nuna mata komaiba ta amsheta hannu bibbiyu suka gaisa tai musu godiya.    ______________,★       Har washe gari babu wanda ya sake tada maganar komawar Zinneerah gidan hajiya Iya. Dan shi Abba ma ya fice kasuwa abinsa tun safe.        Sai bayan sallar la'asar ne Mmn Sadiq da abin keta cin ranta dai ta tunkari ƴar uwarta da maganar. “Maryama nifa inaga kodan matsalar gidan nan zanbar yarinyarnan ta koma wajen Gwaggo, sai dai kuma idan na tuna kar ace dansu masu arziƙi ne mukai haka abin na damuna. Sannan shi kansa Yaya na fahimci baison maganarnan”.      Murmushi Gwaggo Maryama tayi tana gyara zamanta sosai. “Yaya Hauwa nifa kin ganninan babu abinda ya dameni da cewa ta mutane. Abinda duk ra'ayina ya bani na kuma ji raina ya aminta da shi kuma bai saɓama addinina ko al'adata ba to tabbas yinsa nake dan bama kaina farin ciki. Shi ɗan adam babu wani abu da zakayi a rayuwa ƙyaƙyƙyawa ko mummuna da zai iya gani bakinsa bai tankaba koda kuwa shi a tare dashi akwai abinda yafi naka muni ɗin da ƙyau. Dan haka ajiye batun cewa na mutane muyi abinda ya cancanta. Tun jiya nima cikin nazarin maganar nakeyi da shi Yaya kansa. Shi kawai abinda na fahimta da shi gani yake kamar za'a nuna gazawarsa akan riƙon Zinneerah tunda ba shine ya haifetaba. To amma abinda bai tunaba kuma shine sufa mutanen nan bawai sunsan bama shine ya haifitaba. Sai dai ni har cikin raina na yarda da komawar Zinneerah can gidan kodan wannan fitinanniyar matar tasa dake ganin Yayan ne kawai keda arziƙin da ake zuwa a ci”.         “Maganganunki duk suna a kan hanya Maryama. Harga ALLAH inason basu ita domin ALLAH da suka roƙa da kuma darajar zumincin da suma sukayi dan shi. sai dai inason tai nesa da su Saude kodan ɓata mata suna da suke a anguwatnan miji zaima Zinneerah wahalar samu. Dan damafa ni ko wannan bata tasoba nayi niyyar ta biki can ku zauna har muga abinda ALLAH zaiyi”.       “A to tunda hakane a bani abata mu tafi”. Gwaggo Maryama tai saurin faɗa tana dariya. Itama Mmn sadiq dariyar tayi. Haka suka cigaba da tattaunawa har tsawon wani lokaci kafin subar maganar da nufin jiran dawowar Abba yau su tunkaresa da batun.        Zinneerah da batasan mike faruwaba tana can ɗaki da Little wanda a yanzu yake maƙale mata baya yarda da kowa a gidan sai ita da Gwaggo Halima. Sai su Sadiq idan yaso. Makarantama yau da zata tafi kuka yayta zabgawa sai daga baya ya haƙura bayan yayi barci ya tashi. Wauta da ƙuruciyar dake tattare da ita kuma yasa bata ɗauki hakan komaiba saima tausayin yaron da ƙaunarsa dake ƙara ratsata. Maganar komawa gidan Hajiya Iya kuwa bata damuba ba kuma ta mantaba. Sai dai bata wani ɗaukesa da muhimmanci ba balle taji wani abu a ranta game da hakan. _________________★         Koda Abba ya dawo gidan sai da Mmn Sadiq ta bari yaci ya ƙoshi ya nutsu sosai sannan ta tunkaresa da zancen kasancewar yau itace dashi dama. Shiru yay mata tamkar baijitaba. Ita kuma tunanin baiji ɗin bane ya sata sake maimaitawa kai tsaye. Sai dai yanda ya sake tsuke fuska ya saka tasha jinin jikinta kuma.         Bai kulataba sai da ya mula dan kansa sannan ya fara magana a ƙufule. “Hauwa'u kun shirya hakanne dama saboda abinda ya faru a gidan nan kwanaki shida da suka wuce komi? Shin halin Saude ne baki saniba a gidan nan ne? Da har zaki yanke hukuncin rabani da Zinneerah bayan ni har cikin raina ɗaya na ɗauketa da duk wani yaro dake a gidan nan”.       “Yaya kayi haƙuri dan ALLAH, sam ba yanda kake tunani baneba. Ni abinda yasama kaji namaka magana saboda mu toshe ɓarakar da dangin mahaifiyarmu ke ganin mahaifinmu ne ya assasata. Su daina ganin tamkar muna gudunsune. Sannan baiwar ALLAHn nan ka duba yanda suka ɗauka Inno, wandama bai saniba zai ɗauka itace ta haifi Hajiya Iyan ai. Wlhy na tabbata da ace banan ta kawo Inno har ALLAH ya ƙaddara rasuwarta ananba da sai munyi kuka bana wasaba akan wannan rasuwar. Yanda zuminci ya taɓarɓare kowa zagayewa zaiyi yabar Buba da gawar Inno, da kuma sun bizneta su kama gabansu su barmu. Amma yanzu kaga yanda suke tururuwar zuwa nan hardama waɗanda bakai zaton ganiban. Amma kayi haƙuri nayi kuskure, dan babu yanda za'ai Zinneerah ta koma can bada yardarkaba”.       Numfashi Abba ya sauke yana ɗan jinjina kansa. “Maganarki akan hanya take Hauwa'u, ni kaina naji daɗin wannan karamci da suka nuna akan marigayiyar, dan sun nunama sauran dagi su basu manta alkairin Inno ɗinba garesu har yanzun. Badanma ALLAH bai ƙaddaraba kinjifa maganar kaita india da suka fara. Da ace masu kuɗi haka suke daraja zuminci fiye da dukiyarsu dake tsone idonsu lallai da bamu lalace hakaba. Ace dan ALLAH ya baka wani abin jin daɗin duniya kakoma ƙyamar ɗan uwanka baka ƙaunar ya raɓeka. shiko yana gudun raɓar takane saboda karka wulakantashi. Kaiconmu da fifita abinda zai halakamu sama da abinda zai kaimu aljanna”.        “Amin ya rabbi Yaya. Al'amuran kam sai dai addu'a. Ni kaina halayyar mutanen nan ta zaburar dani wani muhimmin abu insha ALLAH”.       “Ai haka akeso dama. idan kaga wani ya aikata alkairi kayi ƙoƙarin koyi da shi, ka kuma nisanta kanka ga mai aikata mummuna. Dan masu iya magana kance zama da maɗaukin kanwa shike kawo farin kai”.          “Sosai kuwa Yaya, ALLAH kai riƙo da hannayenmu”.     “Amin. To amma nima kuma sai a duba ni dan har cikin raina inason zaman Zinneerah tare damu kodan kansu ya haɗu da sauran ƴan uwanta. Gashi kuma inajin matuƙar kunyar mutanen nan wlhy, yanzu hakamafa ɗazun sai da Alhaji Kabir ɗin ya kirani da kansa akan suna nan dai suna jira”.        Cike da mamaki Mama tace, “Wai kirafa Yaya?”.        “Wlhy kuwa, mutanen nanfa mutanen kirkine masu ban mamaki. Toni banda dalilinki ta inama zan ishesu kallo koda a haɗuwar hanyane. Amma ki duba yanda suke da sauƙin kai. Yanzu da wani zaiji nace Alhaji Kabir Shira na kirana a waya ai cazai na zuga ƙarya ko”..      Dariya ta kufcewa Mmn Sadiq, shima Abban ya shiga tayata. “ALLAH kuwa Hauwa'u koni kallon abun nake tamkar mafarki. Ku riƙe bayin ALLAHn da ƙyau bawai dan arziƙin da ALLAH yay musuba, sai don sanin darajar ɗan adam da zuminci da ALLAH ya azurta zukatansu da shi”.      “Insha ALLAHU Yaya. ALLAH ya bamu ikon gina zuri'armu bisa ƙyaƙyƙyawar tarbiyya muma. Koda sun zama wanu abu a rayuwa sukasance masu sanin mutunci da darajar ɗan adam”.       “Amin ya rabbi Hauwa'u. To ammafa zan basu Zinneerah ne kawai banda Abdul-Mutallab. Tunda ba wani shayar dashi takeba tabar mana abummu anan. Itama dai su tausaya mana ta dinga ziyararmu akai-akai. dan ɗazun namasa maganar karatunta dan shine babban burina a gareta. Inason rayuwarta ta inganta sosai kodan kaddarar data ziyarci rayuwarta tun tana ƙanƙanuwarta. To shine yake cewa indai karatune sai Zinneerah tace ya isheta da kanta insha ALLAH”.        “Yaya ALLAH ya saka da alkairi. Dama nima damuwata akan Abdul ɗinne. To amma kana ganin mu sanar dasu gaskiyar al'amari game da haihuwar tata kenan?”.       “Eh to, bazance miki a'a ba, bakuma zance e ba. amma inaga muɗan bada lokaci taje gidan muga yanayin zaman nata tukunna, duk da har cikin raina bana tunanin wani abu saɓanin ƙyaƙyƙyawa”.        Cike da gamsuwa Mmn Sadiq ta gyaɗa masa kai. ___________________★         Washe gari Gwaggo Maryama ta shirya taje yoma Hajiya Iya sallama dan zata wuce itama. Shatara ta arziƙi aka haɗota dashi, tare da driver na ɗaukar Zinneerah, dan Hajiya Iya tace ta gaji da gafarasa bataga ƙaho ba. Da tarema zasu zo da kanta ta ɗauka Zinneerah ɗin sai akai rashin sa'a tai baƙi. Hakan yasa ta haɗo Gwaggo Maryama da driver tace kafin itama tazo, dan tayi alƙawarin dukkan zuri'arta sai sun tako har gidajensu suma insha ALLAH.        Wannan al'amari ya bama su Mmn Sadiq Mamaki da dariya. Babu shiri tai kiran Abba ta sanar masa. Dole ya baro kasuwa yazo sukai magana. Gashi su kofa Zinneerah basu zaunar akan batunba dan sun yanke da saita samu hutun makarantane.        Ganin kar Hajiya Iya taga kamar suna mata yawo da hankali suka yanke shawarar barin Zinneerah taje kamar da nufin yin kwana biyu haka. Dan karsu mata gatsau takuma shiga wani hali musamman akan Little.       Ilai kuwa da suka kirata aka sanar mata zataje wajen Hajiya Iya ta zauna da ita na kwana biyu saboda batajin daɗi sai bata wani damuba. Hasalima taɗanji daɗin tafiyar kodan taje ta huta daga izgili da ƴaƴan mmn sakina da ita kanta maman sakinar kemata a kwanakin nan musamman a makaranta. Shiru kawai takeyi dan karta tada hankalin mahaifiyarta. Amma abin na damunta, dan takai yau har ihu Sakina ta saka akai mata a aji ana kiranta agola ƴar cin arziƙi. Damuwarta ɗaya karatunta da kuma Little dake nane da ita a kwanakin nan duk da ya ƙara samun sauƙi bakamar daba.      Bayan Mama da Abba sun mata nasiha akan ta kula da kanta da kuma girmama kowa yanda zasuyi alfahari da ita ta ɗauka kaya kala uku kawai abinta tai musu salama cikin dabara ta fito saboda little. Su Sadiq kuwa suna makaranta sai dai su dawo suga wayam bata nan.       Motane lafiyayya kuma ƙosashshiya. Dan ƙamshin dake a cikintama kansa na musamman ne. (Abinda bata saniba wannan mota ta mai gayyace mai aiki ce. dan Alhaji Kabir motarsa ya bada musamman domin ɗakkota. Haka kawai yarinyar ta shiga ransa yakejinta tamkar ƴaƴansa daya haifa. Ga kuma son daya fahimci mahaifiyarsa na mata itama). Tana a baya driver na gaba yana tuƙinsa a nutse, tai tagumi kawai tana kallon waje da zurfafa a tunanin yanda rayuwarta keta walagigi. Anya kuwa ita tanada farin jini ga mutane? Duk inda zata rayu bata taɓa samun salama hundred percent sai da matsaloli. A Danya matsalarta Inna, Yaya Karima, Tinene. Bayan ƙaddara ta haɗata da mahaifiyarta gakuma su Maman Sakina da ƴaƴanta yanzu suna neman hanata shan ruwa a gidan data samu gata da kulawa. Anya kuwa idan ta dawo daga inda zata yanzu bazata shawarci mamansu akan a maidata boarding school ba ko zata samu nutsuwar yin karatunta cikin salama?.       Wannan tunanin yasata jin nutsuwa a ranta taketa sakin murmushi batare data saniba har suka iso gaban katafaren milk color ɗin gate ɗin gidan. Sai da driver yay horn maigadi ya wangale gate ɗin ta dawo hayyacinta. Nannauyan numfashi ta sauke zuciyarta na wani irin tsargawa tamkar waccan ranar da Abba ya kawosu. Addu'a ta shiga karantowa a ranta har driver ya buɗe mata ta fito. Godiya tai masa cikin risinawa. Hakan ya sakashi jin daɗi har cikin ransa. Ya miƙa hannu zai amshi jakkar hannunta amma sai ta hanashi. “Haba Yayana, jakkarma kai zan ba ka ɗauka min, ai babu dacewa a cikin hakan, kaine zan ganka da kaya na amsa bakai zaka ganni dasu ka amsa ba”.      Murmushi ya mata cike da jin ta kuma birgeshi. Shine da kansa yay mata rakkiya har sashen Hajiya Iya. Inda a tafiyar tasu take samun damar yima gidan mai sassa da yawa kallon tsaf. A ranta kuwa raya irin jin daɗi ta masu hannu da manda takeyi. Shiyyasa akace wasu tun a duniya suke cinye rabonsu na lahira. Wasu kuma sai kaga ALLAH ya haɗa musu duniyar da lahirar duka. Ya ALLAH kasa muna cikin masu samun dukan gaba ɗaya.............✍                            *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* *Page 17* ____________________ *_INA MATA ƳAN ƘWALISA BA'ABOTA SON GYARA JIKI DA FATA SUYI ƘWANAS TAMKAR WATA ƊAN DAREN SHABIYAR?!_* _Ku marmatso kusa maza na kaiku kantin sauƙi na UMMU DUFAIL gidan sauƙi da biyan buƙatar MATA SARAKAN ado harma da MAZA ƴan ƘWALISA._ *_MATA da yawa kanso su koma Taurari ababen kallo da burgewa ga ma'abota kallo sai dai basusan ina zasu sami sinadarin kankaro wannan ƙyawu da mutuncinba._* _To maza kuzo kusa dan Bilyn Abdull ta lalubo muku kantin sauƙi na Umm Dufail dakeda kaya masu sauƙi da gamsar da maison afani dasu_. *_UMMU DUFAIL nada kayan gyaran jiki masu rahusa da inganci da gamsar da mai saya cikin ƙanƙanin lokaci kamar haka👇🏻😁_* *Customers price list By Ummu Dufail FACE AND BODY* SCRUB=2500(300ml) Face and body mango butter=3k (250ml) Face cream= 1800 Corretor oil/vitamin C oil=2k Fairness skin lotion= 2500 Hot chocolate skin lotion 2500 Serum (for Nuckles )2k Nuckles cream (stubborn)3500 Mix fruits Arabian black =soap 1800 Mix fruit glycerine soap =1900 Beetroot=1900 Coconut, milk,egg..face soap=1200 Lavender mix fruit soap =1800 Body wash =1500 cleanser=1600 Hair spray =700 Hair oil =1500 Hair relaxer =700 Hair butter 1700 Shampoo =1500 Breast=oil 2k powder 2k Strech marks cream= 2k Beetroot pink lips =700 Baby care soap glycerine=1k Baby care butter =1500 Shea butter baby soap =700 Tsumin tula =2200 Tsumin zinariya =1200 Sliming tea =1500 Amarya set =25k Liquid Arabian black soap =1900 Cleansing water =1500 *_Zaku iya bibiyarta domin gani da ido ta Handle ɗinta na istagram da facebook kamar haka_* Ummu Dufail @ Facebook Ummu Dufail @ instagram Phone no: 07067943479. _Ƴammata harma da masu auren karku bari ayi babuku. Dan gyara shine mace a wannan ƙarnin😉👍🏻_. ________________________ *Page 17* ...........Tarba mai ban mamaki da tu'ajjibi Zinneerah ta samu daga hajiya iya, harma da wasu daga cikin jikokinta dake gida ta iske a sashen. Duk yanda taso ta takura kanta saboda baƙunta da rashin sabo sunƙi bata damar hakan. Dan sai faman jera mata tambayoyi suke tamkar ƴan jaridu.       Dolenta ta saki jiki dasu dan su biyun duk sa'anninta ne. Biyu mata, Bahijja da Meenal wadda taci sunan Hajiya Iya kenan. Sai ɗaya Namiji mai suna Jamal.     Harga ALLAH Zinneerah taji daɗin kasancewa dasu, dan ta fahimci sunada tarbiyya da sauƙin kai sosai, sannan son ɗan uwansu ko yaya yake wannan trianing da akai musu ne tun asali.       Cikin katsesu Hajiya Iya dake shafa man zafi a ƙafarta tace, “Niko kun isheni da subaɗi Bahijja. Kuma barni nai hira da Innon tawa kunbi kun hana. Sai ku tashi ku kaita wancan ɗakin kuɗan ƙara gyarawa duk da dai ko jiya Rahi ta garasa ta samu taɗan watsa ruwa ta huta dan shine zai zama ɗakinta”.        Wani irin waro idanu Jamal yayi tare da zabura. Haka Meenal da Bahijja ma duk sai da suka zaro idanun. Jamal yace, “Granny kina nufin ɗakin Yayanmu fa kenan?”.       Harara sosai Hajiya iya ta watso musu tana ƙyaɓe fuska. “Eh shi dinfa nake nufi ba waniba. Zuwa yake ƙasar ne da har za'a wani cigaba da faman barin ɗaki haka aljanu na dubulwa a cikinsa? Ubansama dana haifa bai tuna inda nakeba shekara guda balleshi da ke neman haɗa kusan uku”.        Yanda ta ƙare maganar cikin ɗacin rai ya saka jikinsu duk yay sanyi. A sanyaye Meenal tace, “Kiyi haƙuri Granny, mu dama zaki yarda sai mu tafi da ita sashenmu, kinga saita zauna a ɗakinmu dan ALLAH”.         “Hakan zaifimin daɗi kuwa Amina. Sai dai kuyi haƙuri nafison zamanta kusa dani akoda yaushe. Koba komai zanga fuskar Innota naji sanyi”.       Kansu kawai suka iya kaɗa mata, dan tunda ta faɗi haka basu isa jayayya da ita ba. Ko min roƙon da zasu mata kuma bazata canja ra'ayintaba. Zinneerah dai najinsu kanta a ƙasa, sai dai babu abinda ta fahimta a zancen nasu kuma. Amma ganin yanda fara'ar fuskar Hajiya iyan ta ɓace tun daga maganar ne ya saka jikinta yin sanyi itama......       “Taso muje kiga ɗakinki Sister”. Bahijja ta katse tunanin Zinneerah tana kama hannunta cikin nata. Babu musu ta miƙe tabi bayanta, Meenal da Jamal ma suka mike suka biyosu.      Kallo Hajiya Iya ta bisu dashi idanunta na cika da ƙwalla. Dan maganar nan ta tado mata da wani babban miki dake zuciyarta tsahon shekaru, wanda a shekarin can da suka shuɗe kusan biyar sun fara ganin haske, amma a wannan karon al'amarin na neman komawa baya. Dan inhar lissafinta bai ƙwace mataba kusan shekararsa ɗaya kenan rabonsa da Nigeria. A take wasu hawaye masu zafi suka fara gangaro mata. Saurin saka hannu tai ta sharesu tare da miƙewa ta nufi hanyar ɗakinta tana ɗan ɗingisa ƙafarta dake mata ciwo tinda safe.         “Sister Zinneerah lallai keɗin mai sa'a ce”. Meenal ta faɗa tana tura ƙofar ɗakin da suka iso a ɗan lungun corridor ɗin dake facing jikin ɗakin Hajiya Iya. Kafin Zinneerah ta iya cewa wani abu Jamal ya karɓe da cewa “Mai sa'a kuwa ta gasken gaske. Dan kece ta farko a tarihin gidannan kaf da zaki rayu a wannan ɗakin na Yayanmu bayan shi kaɗai dake rayuwa a cikin kayansa idan yazo ƙasar”.       Haka kawai gaban Zinneerah ya faɗi batare da tasan daliliba. Har suka shige ɗakin ita tama kasa motsawa balle ɗaga ƙafarta. Ganin hakan yasa Jamal dawowa da baya yaja hannunta suka shige ciki, duk da taso ƙoƙarin ƙwace hannun nata amma yaƙi bata dama sai da suka shigo tsakkiyar ƙaton ɗakin da batamasan yanda zata fasaltashi ba a fahimceta.            Sakin hannunta da Jamal yayi ya bata damar ɗago idanu tanabin ɗakin da kallo. Yayinda hancinta ke shaƙar mata wani irin mayataccen ƙamshi mai sanya zuciya salama. Wani irin saki gaɓɓanta sukai a lokaci ɗaya, ta zubama su Bahijja daketa yaye fararan ƙyallayen da aka lulluɓe komai na cikin ɗakin dasu saboda gudun ƙura ta hausu.          Sai da suka gama yaye komai ya bayyana Meenal ke faɗin, “Bara na ɗakko kayan shara mu tayaki ɗan ƙara gyarawan baƙunta. Kuma mufa kibar mana wannan ɗari-ɗarin Madam”.      Cikin tsokana Jamal yace, “Barta sotake mu kirata baƙauya maybe. Gwarama ki sake damu kafin su Yah Haneef su dawo gidannan gobe idan ALLAH ya kaimu, dan zasu cinyeki da bakine”.        “Kaji munafiki, saina faɗa musu yasin”. Bahijja dake hararsa ta faɗa.     Yanda Jamal yay da fuskane ya saka dariya kufcema Zinneerah batare data shiryaba. Hakan yay dai-dai da dawowar Meenal ɗauke da kayan shara ɗakin. “Oh ALLAH, kokefa ƴar uwa. Ni kuwa an taɓa faɗa miki keɗin ƙyaƙyƙyawa ce musamman idan kina dariya?”.           Kasa bata amsa Zinneerah tayi, sai dariyar tatace ta koma murmushi kawai. Hakan datai ya saka su Jamal kwashewa da dariya a tare. Bahijja tace, “Kinga kinsatama ta haɗiye abinta da wannan bakin naki da bai gani ya ƙyale”.......        “Wai nikan sharar zakuyi ko damuna da shegen surutu?”. Suka jiyo muryar Hajiya Iya dake tunkaro ɗakin.        A take kowa ya nutsu suka fara ƙoƙarin sharar. Shigowa tai har yanzu fuskarta a dagule da ɓacin ran ɗazun. Tabi ɗakin da kallo da ƙyau kamar mai nazari. A ƙarshe ta sauke idonta akan Zinneerah dake ƙoƙarin tayasu itama. Haka kawai kuma sai taji ɓacin ran nata ya sassauta. Ta sauke ajiyar zuciya da juyawa ta fice a ɗakin.       Tsaf suka gyara komai dan an horar dasu aiki tuni. Cikin kanƙanin lokaci ƙyawu da tsaruwar ɗakin ya ƙara bayyana a idon mai kallo. Musamman da suka cire labulayen ɗakin duk suka sake canja wasu fararen tas dan dama fararen suka cire. Kaso mafi yawa dake a ɗakin kalar blue and white ne. Sai wasu colors ɗin ɗai-ɗai da ba'a rasaba. Da yawansu kuma an ɓaɓɓoyesu ma.       Idanu ta lumshe a hankali tana maijin wani abu mai nauyi dake a ƙirjinta yana narkewa sannu-sannu zuwa cikinta. Nannauyar ajiyar zuciyar da bata shirya fitartaba ta kufce mata a karon farko. Kusan a tare Meenal, Bahijja, Jamal suka dubeta. Sai dai babu wanda ya iya cewa komai a cikinsu, dan sun fahimci Zinneerah bata da sakewa da mutane, gata kuma da alama akwai miskilanci tattare da ita. ★★        Ƙarfe bakwai da wasu mintuna Alhaji Kabir ya iso katafaren family House ɗin nasu. Bayan samun wajen fakin da direba yayi ya tsaya aka buɗe masa ya fito riƙe da leda a hannunsa wadda kowa yasan mai ita. Dan babu fashi kullum sai ya shigo da irin wannan ledar domin mahaifiyarsa koda iyalansa basu samu hakanba. Sanin baya bama kowa dakon ɗaukarta, shi yasa babu wanda ya tunkaresa domin karɓa. Sai dai sauran kayansa da ɗallami driver ya kwasa zuwa sashensa shi da iyalansa. Shi kuma ya nufi sashen Hajiya Iya kansa tsaye.         Ɗauke da cikkakkiyar sallama a bakinsa ya shigo falon duk da yasan a irin wannan lokacin Hajiya iya na ƙuryar ɗakinta. dan idan tai sallar magriba bata fitowa sai isha'i. Amma yanada tabbacin baza'a rasa wasu daga cikin ƴaƴansaba da basa rabo da sashen a koda yaushe.     Ilai kuwa yana shiga da fuskar Zinneerah da Meenal ya fara tozali dan sune ke facing ƙofa. A take falon yay tsit kowa ya ƙara nutsuwa. Sai Meenal ce datai saurin miƙewa ta nufesa domin amsar ledar hannun nasa. “Baffah sannu da zuwa?”.       “Yauwa uwata kune anan?”. “Eh Baffah, munzo tarbar Sister Zinneerah ne tun ɗazun”.      Murmushi Alhaji Kabir yayi yana maida kallonsa ga Zinneerah data risinar da kanta ƙasa tun bayan amsa sallamarsa. Ya ƙaraso cikin falon sosai su Bahijja ma na masa barka da dawowa. A hankali Zinneerah ta zamo ƙasa tana faɗin, “Sannu da zuwa Baffah. Ina wuni”.      Murmushinsa ya sake faɗaɗawa da faɗin, “Yauwa ɗiyata. Welcome to Shira's family”.        “Thanks you Baffah”. Ta faɗa a hankali cike dajin kunya.        Ya cigaba da faɗin, “Yaya kika barmin ƙanwata da ƙannanki da Abbanki?”.       “Lafiya lau Baffah, sunce suna gaisheka”.      “Ina amsawa. Alkairin ALLAH yakai garesu. Tashi ki zauna”.     Babu musu Zinneerah ta miƙe ta koma kusa da Meenal data kaima Hajiya Iya leda ta dawo ta zauna. Shikuma ya wuce bedroom ɗin Hajiya iyan domin gaisheta.        Tunda yay sallama a yanda ta amsa masa ya saka gabansa faɗuwa. Cikin ƴar ruɗewa ya ƙaraso ƙaton ɗakin nata itama da sassarfa. Gabanta ya zube jikinsa na rawa. “Innata mike faruwa naji muryarki tamkar baƙyajin daɗi?”.        Ɗago kyawawan idanunta da mafi yawan ƴaƴa da jikokin gidan suka gada a wajenta tai tana kallonsa. A take hawayen da taketa maƙalewa tun ɗazun suka silalo mata tare da murmushi a lokaci guda. Sake ruɗewa Alhaji Kabir yayi idanunsa shima na kawo ruwan hawaye.      Kanta ta girgiza masa a hankali tana share nata. “Hawayena basu zuba domin kai ba Kabir. Dan kai ɗa ne tamkar da dubu ga kowaɗanne irin iyaye. Nagodema ALLAH domin yayimin ni'imomi masu yawa a rayuwa da har wanda ke a nesa dani bazai ɗauka inada wata damuwa ko jarabawa nima tattare dani ba, kuma har da samunka matsayin ɗa a cikin ni'imomin. Kabir tabbas ɗan uwanka shine jarabawata. Dan ALLAH ka tayani addu'a ALLAH ya bani ikon cinyewa. A lissafin danai yau shekarar Ahmad ɗaya da watanni biyu kenan rabonsa da ƙasarnan. Yanzu ace Kabir har Inno ta rasu Ahmad ya gagara ɗakko iyalansa suzo sumin ta'aziyya. Idanma ita data nisantani dashi bazatazo ba shi bazai iya zuwaba koda shi da Modibbo ne?. Moddibo fa kansa shekararsa uku kenan rabonsa da ƙasarnan. Tunda nai maganar yay auren nan bai sake zuwaba, uwarsa kuma ta hana wannan ƙoɗaɗɗiyar yarinyar zuwa nan ɗin koda ta haihunma. To kosai na mutune zata barsu suzo su raɓi gawata......”       Ta kasa ƙarasa maganarta saboda kuka daya kufce mata.       “Innata dan girman ALLAH ki daina kuka. Kiyi haƙuri dan ALLAH, addu'arki da tamu Ahmad yafi buƙata. Kuma insha ALLAH namiki alƙawarin a wannan karon zanbi duk hanyar data dace domin maido ɗan uwana gida. Har ita ɗin da shaiɗancinta dole ta biyosa. inko taƙi wlhy sai dai ta kama gabanta inda ta fito. Amma dan ALLAH kibar kuka Inna”.       “Kayya Kabir. A baya fa kayi irin wannan namijin ƙoƙarin amma kaga ta sake sabon shiri, harshi Moddibo ɗinma da ada bayabin ra'ayinta yanzu ta sake janyesa. A zatonmu kusancin da Khalipha ya samu dasu zai kawo wani canjin sai gashi ba hakaba”.        “Insha ALLAH Inna komai zai wuce. Ai duk abinda ya saka kuka wataran zai saka dariya. Duk kuma abinda ya saka dariya wataran sai ya saka kuka. Itama ai gasunan ta haifa indai ƴaƴane ko. kuma Alhmdllh sai ya bata mafi rinjayensu maza. Itama kukan da zatayi akansu sai ya ninka naki sau dubu. Amma dan ALLAH ki daina masa kuka Inna dan shima ba laifinsa bane, anfi ƙarfinsa ne kawai”.       “Humm ko anfi ƙarfinsa kam da halima. Dan shima kaidin macen yana iske haline. Kai miyasa matan naka basu rabani da kai ba”.      Kasa cemata komai yayi sai ban haƙuri dai. Sai da yaga hankalinta ya kwanta sanann ya miƙe ya fice domin zuwa gabatar da sallar isha'i tunda ya cinye lokacin zuwa yay wankan anan.      Bai iske su Zinneerah a falonba yanzu. Da alama sun shige gabatar da sallar suma. ______________★       Duk yanda Alhaji Kabir yaso rintsawa a daren yau hakan ya gagara. Ba komai ke masa kai kawoba a rai sai tattanawarsa da Mahaifiyarsu akan ɗan uwansa.        Su uku kacal mahaifiyarsu Hajiya Iya ta haifa a duniya. Shine babba, sai ƙaninsa Ahmad, sai autarsu Bilkisu da ayanzu haka tana Lagos tana aure. Rana ɗaya aka ɗaura masa aure da ɗan uwansa Ahmad, wanda mafi yawan mutane sukafi sani da suna AK Shira. Ba komai yasa ake kiransa da suna AK ba sai tsanain soyayyar da sukema juna tun ƙuruciya. Kasancewar boarding school sukayi acan ake kiransa da suna Ahmad ɗin Kabir. A hankali kuma sai abokai suka koma kiransa a takaice da suna AK Shira. Mai makon Ahmad Abdul-Mutallab Shira kamar yanda shi ake kiransa Kabir Abdul-Mutallab Shira. Bayan sun kammala secondary tare suka wuce ƙasar Turkey ƙaro karatu. Cikin amincin ALLAH suka haɗa digiri ɗinsu na farko dana biyu duk a tare. Tun suna farkon fara digiri na biyu Ahmad ya haɗu da matarsa ta yanzu mai suna Hindatu. Asalin Hindatu ƴar ƙasan Nigeria yace. dan mahaifinta ɗan nanne. Sai dai mahaifiyarta ƴar asalin ƙasar Morocco ce. Amma suna zaune a ƙasar Turkey tun tanada ƙuruciya, acan ta girma tamafi sanin can matsayin ƙasarta fiye da Nigeria dan sukan jima basuzoba. Ƙyaƙyƙyawa ce itaɗin sosai kasancewarta halfcast ce. Sai ALLAH ya bata wani irin usilin ƙyau mai ɗaukar hankalin mai kallonta.      Duk da yasan ba wannan ƙyawun bane ya ruɗi ɗan uwansa ga sonta, amma shima ya taka rawar gani wajen jan hankalinsa gareta. Bayan sun kammala digirinsu na biyu suka dawo Nigeria kamar yanda mahaifinsu ya buƙata. Dan yana bukatar suzo suyi aure. Koda suka iso suka huta babu wani jan rai iyayensu suka gabatar musu da matan aure. Shi Alhaji Kabir ya amsa da hannu biyu yay godiya dan dama baida ko budurwar. Amma Ahmad ƙiri-ƙiri yace shifa yanada matar aure. Hajiya iya ce ta fara nuna rashin yardarta akan hakan amma ya nuna bamai rabasa da Hindatu dan yana mata so mai zafin gaske. Gudun samun ɓaraka yasa Marigayi Alhaji Abdul-Mutallab zaunar da Hajiya Iya yaymata nasiha harta amince badan ranta yasoba.        A take aka hau shirin biki, cikin kanƙanin lokaci komai ya kammala dan ana zuwa nemawa Ahmad auren Haindatu babu wani ja'inja aka bashi. Ansha biki na nunawa sa'a lokacin, dan Alhaji Abdul-Mutallab ya tara musu. Bayan biki duk aka kai amare garin Bauchi, harda Hindatu. Ƙyawawan halin Hindatu yasa Hajiya Iya ta fara sonta, sai kuma akazo dandanan ta samu ciki. Duk da Hindatu na karatu a jami'ar Turkey bata taɓa nuna ƙorafinta nason komawa makarantaba. Tai shiru abinta har ALLAH ya sauketa lafiya ta haihu ɗanta namiji da yaci suna Abdul-Mutallab. Amma saboda alkunya suke masa laƙani da suna Adnan, Hajiya Iya kuma na kiransa Moddibo.      Bayan haihuwarsa da kusan  watanni huɗu Ahmad ya buƙaci sake komawa ƙasar Turkey dan cigaba da karatunsa. Sai dai a baɗini wannan shirin Hindatu ne. Basu kawo komai a ransuba suka amince Ahmad ya ɗauka Hindatu da dansu suka tafi Turkey saboda kowa yasanshi da matuƙar son zurfi a karatu, shi kuma a lokacin matar Kabir ta fara laulayin nata cikin ita.         Kamar wasa tun daga wannan tafiyar ganin Ahmad ya fara musu wahala. Dan ya samu aiki acanma ta dalilin mahaifin Hindatu. Sannu-sannu ƴaƴa suka fara yawaita a wannan family, yayinda ALLAH yayma Alhaji Abdul-Mutallab rasuwa. Akan wannan rasuwa kuwa saida sukai yaƙi na gaske Ahmad yazo Nigeria. Inda a wannan zuwan nasane Hajiya Iya ta amshe Moddibo ko hakan zaisa Ahmad ya ringa tunawa dasu.       Hakan kuwa yaso fara tasiri akan Ahmad ɗin, saboda tsananin so da sukema Moddibo daga shi har Hindatu. Sai dai kuma yana kammala secondary daga tafiya karatu ƙasar London aka sake samun matsala suka sake ƙwace abinsu. Ɗan dawowa da Ahmad ɗin ya farayi garesu ta ƙara lalacewa. Sai dai Alhmdllh duk hutun duniya a Nigeria Moddibo keyinsa. Wannan ne ya ɗan sanyaya ran Hajiya Iya. Amma duk da haka basu daina yaƙin son maido Ahmad jikinsu ba. A dalilin Adnan da shima rashin zuwan mahaifin nasa gida ke cin ransa suka sake dawo dashi cikinsu a shekarun nan, sai dai kuma suna murna an samu waraka shima sai Adnan ɗin ya ɗauke tasa ƙafar gaba ɗaya a dalilin aure da Hajiya iya ta matsa masayi.......          Nannauyan numfashi Baffah ya sauke mai haɗe da ajiyar zuciya saboda fahimtar da yay tunaninsa yayi zurfi. A yanzu haka kuma ba tunanin abinda ya shuɗe bane mai muhimmanci garesa, a'a abinda zaizo shi ya kamata yay tunanin gyarawa kodan farin cikin mahaifiyarsa ma dasu kansu shi da ƴar uwarsa da zuri'arsu. Dan haka ya sake zurfafa a wani dogon tunanin da bai dawo hayyacinsaba sai a wani tsahon lokaci daya samo mafitar da yaji har a cikin ransa ya gamsu da ita sannan.          ★★★★    Washe gari daga sallar asuba ya zarto sashen Hajiya iya. Bayan ya zauna sun gaisa ya zayyane mata shawarar da ya yanke a wannan karon. Cikin jimami tace, “Amma Kabiru baka gani wannan shawarar tana kamanceceniya data baya kuwa?”.         “Eh to Inna tana kama da ita. Sai dai akwai ɗan banbanci da waccan ɗin. Ki dai tayani addu'a, kuma ki ƙara nazari kema akan hakan mugani”.       “To shilenan. Ai ba'aƙi ta mutumba inji masu iya magana. ALLAH ya shige mana gaba”.       “Amin ya rabbi Inna nagode. Ina mutuniyar takine banji motsintaba?”.       “Oh kana maganar Zinneerah ne? Tana ɗakin Moddibo tunda ba zuwa yakeba ita ai saita zauna. Dan nace ja'iran nan suzo su rinƙa tayata kwana harta saba wai tsoro sukeji sudai. taya zasu iya kwana ɗakin Yayansu bayan kowa yasan dokarsa ba'a shigar masa ɗaki sai da dalili mai ƙarfi”.        Dariya Baffah yayi yana faɗin, “Inna sunsan halinsa ba wasa yake dasuba ai Babana. Itama Zinneerah ɗin dai gara a gyara mata wani karki haɗa rikici Inna”.        “Oh to nima tsoron nasa nakeji kenanma ashe?. To yaci ƙaniyarsa shida dokar tasa babu inda zataje. Idan yazo ni basai ya dakeniba mai bauɗaɗɗen halin tsiya irin na uwarsa”.       Dariya Baffah ya mike yanayi shidai da faɗin, “Ai kunfi kusa Innata.  Wazai yarda ya shiga tsakaninki da Adnan da Khalipha a gidan nan”.        “Aikam ni yanzu bana yayin wani Moddibo can. Garama Khalipha ɗin duk da shima ja'irin kansane, daka ɗakko laifin takwaran nasa zai fara karewa da yayansu kaza-kaza, saikace akansa aka fara ɗan uwa”.      Shi dai Baffah dariyarsa yaketa sha harya samu ya gudu domin zuwa yay shirin fita kasuwa.        Lokacin da Hajiya iya kenan suna maganarsu da Baffah Zinneerah datai kwanan baƙunta a ɗakin data fahinci mai shi mutum ne mai matuƙar daraja da girma ga jama'ar gidan, dan su Meenal ƙiri-ƙiri sunƙi zaman ko mintuna goma a ciki, nacan ta shige cikin masu aikin Hajiya Iya tana tayasu aikin gyaran sashen. Lokacin da Baffah ya fito ya fice suna Kitchen domin haɗa breakfast kasancewar kullum anan Baffah ke karin kumallon safe tare da mahaifiyar tasa.     Masu aikin sunso hanatayi amma taƙi. Dole suka barta saboda sunsan yaran gidan dama kan shiga ai aiki dasu suma bisa dokar Hajiya Iya. Amma da dan ta iyayensu matane kam da ba hakaba. Itako Hajiya Iya ta tsaya tsayin dakane domin taimakonsu tunda tasan gidan wani zasuje.      Bayan sun kammala komai tsaf Baba Rahi tace taje tai wanka kafin Hajiya Iya ta fito dan batason ƙazanta ko kaɗan. Shiyyasa kosu kansu idan baka saniba bazaka taɓa ɗauka ƴan aiki bane a gidanma sai an faɗa.............✍       *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* *Page 18* ____________________ *_INA MATA ƳAN ƘWALISA BA'ABOTA SON GYARA JIKI DA FATA SUYI ƘWANAS TAMKAR WATA ƊAN DAREN SHABIYAR?!_* _Ku marmatso kusa maza na kaiku kantin sauƙi na UMMU DUFAIL gidan sauƙi da biyan buƙatar MATA SARAKAN ado harma da MAZA ƴan ƘWALISA._ *_MATA da yawa kanso su koma Taurari ababen kallo da burgewa ga ma'abota kallo sai dai basusan ina zasu sami sinadarin kankaro wannan ƙyawu da mutuncinba._* _To maza kuzo kusa dan Bilyn Abdull ta lalubo muku kantin sauƙi na Umm Dufail dakeda kaya masu sauƙi da gamsar da maison afani dasu_. *_UMMU DUFAIL nada kayan gyaran jiki masu rahusa da inganci da gamsar da mai saya cikin ƙanƙanin lokaci kamar haka👇🏻😁_* *Customers price list By Ummu Dufail FACE AND BODY* SCRUB=2500(300ml) Face and body mango butter=3k (250ml) Face cream= 1800 Corretor oil/vitamin C oil=2k Fairness skin lotion= 2500 Hot chocolate skin lotion 2500 Serum (for Nuckles )2k Nuckles cream (stubborn)3500 Mix fruits Arabian black =soap 1800 Mix fruit glycerine soap =1900 Beetroot=1900 Coconut, milk,egg..face soap=1200 Lavender mix fruit soap =1800 Body wash =1500 cleanser=1600 Hair spray =700 Hair oil =1500 Hair relaxer =700 Hair butter 1700 Shampoo =1500 Breast=oil 2k powder 2k Strech marks cream= 2k Beetroot pink lips =700 Baby care soap glycerine=1k Baby care butter =1500 Shea butter baby soap =700 Tsumin tula =2200 Tsumin zinariya =1200 Sliming tea =1500 Amarya set =25k Liquid Arabian black soap =1900 Cleansing water =1500 *_Zaku iya bibiyarta domin gani da ido ta Handle ɗinta na istagram da facebook kamar haka_* Ummu Dufail @ Facebook Ummu Dufail @ instagram Phone no: 07067943479. _Ƴammata harma da masu auren karku bari ayi babuku. Dan gyara shine mace a wannan ƙarnin😉👍🏻_. ______________________ *Page 18* ...........Washe gari daga sallar asuba Baffah ya zarto sashen Hajiya iya. Bayan ya zauna sun gaisa ya zayyane mata shawarar da ya yanke a wannan karon. Cikin jimami tace, “Amma Kabiru baka gani wannan shawarar tana kamanceceniya data baya kuwa?”.         “Eh to Inna tana kama da ita. Sai dai akwai ɗan banbanci da waccan ɗin. Ki dai tayani addu'a, kuma ki ƙara nazari kema akan hakan mugani”.       “To shilenan. Ai ba'aƙi ta mutumba inji masu iya magana. ALLAH ya shige mana gaba”.       “Amin ya rabbi Inna nagode. Ina mutuniyar takine banji motsintaba?”.       “Oh kana maganar Zinneerah ne? Tana ɗakin Moddibo tunda ba zuwa yakeba ita ai saita zauna. Dan nace ja'iran nan suzo su rinƙa tayata kwana harta saba wai tsoro sukeji sudai. taya zasu iya kwana ɗakin Yayansu bayan kowa yasan dokarsa ba'a shigar masa ɗaki sai da dalili mai ƙarfi”.        Dariya Baffah yayi yana faɗin, “Inna sunsan halinsa ba wasa yake dasuba ai. Itama Zinneerah ɗin dai gara a gyara mata wani karki haɗa rikici Inna”.        “Oh to nima tsoron nasa nakeji kenanma ashe?. To yaci ƙaniyarsa shida dokar tasa babu inda zataje. Idan yazo ni basai ya dakeniba mai bauɗaɗɗen halin tsiya irin na uwarsa”.       Dariya Baffah ya mike yanayi shidai da faɗin, “Ai kunfi kusa Innata.  Wazai yarda ya shiga tsakaninki da Adnan da Khalipha a gidan nan”.        “Aikam ni yanzu bana yayin wani Moddibo can. Garama Khalipha ɗin duk da shima ja'irin kansane, daka ɗakko laifin takwaran nasa zai fara karewa da yayansu kaza-kaza, saikace akansa aka fara ɗan uwa”.      Shi dai Baffah dariyarsa yaketa sha harya samu ya gudu domin zuwa yay shirin fita kasuwa.        Lokacin da Hajiya iya kenan suna maganarsu da Baffah Zinneerah datai kwanan baƙunta a ɗakin data fahinci mai shi mutum ne mai matuƙar daraja da girma ga jama'ar gidan, dan su Meenal ƙiri-ƙiri sunƙi zaman ko mintuna goma a ciki, tana can ta shige cikin masu aikin Hajiya Iya tana tayasu aikin gyaran sashen. Lokacin da Baffah ya fito ya fice suna Kitchen domin haɗa breakfast kasancewar kullum anan Baffah ke karin kumallon safe tare da mahaifiyar tasa, weekend ne kawai bayayi anan.     Masu aikin sunso hanatayi amma taƙi. Dole suka barta saboda sunsan yaran gidan dama kan shiga ai aiki dasu suma bisa dokar Hajiya Iya. Amma da dan ta iyayensu matane kam da ba hakaba. Itako Hajiya Iya ta tsaya tsayin dakane domin taimakonsu tunda tasan gidan wani zasuje.      Bayan sun kammala komai tsaf Baba Rahi tace taje tai wanka kafin Hajiya Iya ta fito dan batason ƙazanta ko kaɗan. Shiyyasa kosu kansu idan baka saniba bazaka taɓa ɗauka ƴan aiki bane a gidan ma, sai an faɗa.          Babu musu ta nufi komawa ɗakin data kwana. Ɗakin da kallonsa kawai saka mata wani shakkar zama a cikinsa take shiga. Dan har cikin ranta tanaji cewar matsayinta bai kai na ta zauna wannan ɗakinba da take ƙyautata zaton na musamman ne.        Kamar yanda ta kasance a ɗarare daren jiya yanzunma a ɗararen tai komai. ALLAH ya taimaketa ma hatta da soson wanka da kayan shafarta ta taho da abinta. Komai na ɗakin bata yarda tai amfani da shiba bayan ruwa, sai bargo data saka a ƙasa ta kwanta a daren jiya.      Tsaf ta kammala shirinta cikin riga da skirt na atanfa ruwan bula da ratsin fari, sai ɗan baƙi-baƙi kaɗan. Hijjab ƙarami data taho dashi saboda zaman gida ta ɗauka ta saka sannan ta fita. karo suka kusanci da Jamal tai baya da sauri.      “Oh sorry Sister, dama Granny tace ki fito ke kaɗai ake jira cin abinci”.  Kallonsa tai kamar zatai magana sai kuma tai shiru saboda tinawa da nasihar mahaifiyarta data tuno akan zaman gidan. Tai ɗan murmushi da faɗin, “Ina kwana”.       Dariya yayi yana susan kai. “Uhm su Jamal an girma. Wai ni kike gaidawa ma kowa?”.      Karon farko tai dariya da fara tafiya, har cikin rai yanda suke da barkwanci na birgeta. Shima sai ya biyota yana rawa wai an gaishesa, bayan kaf gidan shike gaida kowa. Koda suka iso ƙaton dining ɗin karaɗinsane ya saka kowa maido hankalinsa kansu. Ya ƙaraso garesu yana basu labarin yau an gaisheshi shima ya tashi daga autan gidan nan yanada ƙanwa.         Babu wandama yaji miya faɗa dan duk hankalinsu nakan Zinneerah da duk ta daburce saboda idanunsu. Ƙasa takai tsugunne dai-dai tana isowa gabansu tace, “Hajiya ina kwana?”.        Fuskar Hajiya Iya ɗauke da fara'a da kulawa ta amsa mata, tare da tambayarta baƙunta. Kan Zinneerah a ƙasa take amsawa. kafin ta juya ga Baffah shima ta gaidashi da girmamawa. Amsa mata yay shima cikin kulawa da faɗin, “Kinga taso ga abinci, ga kuma ƴan uwanki nan dake gida duka”.        Kanta ta jinjina masa jikinta na ƙara saki saboda jin idanunsu duk a kanta. batare data miƙe ɗinba tace, “Ina kwanan ku?”.      Moos'ab ne ya fara sauke numfashi da amsa mata. “Lafiya lau ƴar ƙyaƙyƙyawa, Granny ina kika samo mai kama da Inno haka?”.       Kafin Hajiya Iya ta bashi amsa Haneef ya amshe da cewa, “Masha ALLAH ko itace ƙanwar tamune?”. Saifudden zaiyi magana shima Baffah da ke shirin fara cin abincin da Abidah ta haɗa masa yace, “Wai ni gidan nan halan duk ƴan jarida muka tarane? Indai kune yanzu sai kowa yace sai ya mata tambaya anan. Ɗiyata taso kinji”.        Cikin jin kunya ta taso ta zauna kujerar da Ni'ima ta gyara mata. Kallonsu Baffah yayi su duka, danya fahimci har yanzu duk hankulansu naga Zinneerah musamman ƴan samarin ƴaƴan nasa. Yay ɗan murmushin manya yana lumshe ido da buɗewa. “Wannan itace Zinneerah ƙanwarku. Wadda tun kafin zuwanta an sanarma kowa dake gidan nan. Muna fatan zaku karɓeta da hannu biyu ku kuma ɗauke babu wani banbanci daku”.       Insha ALLAHU Baffah. Suka haɗa baki wajen faɗa su duka.     Kansa ya jinjina cike da gamsuwa yana maida dubansa ga Zinneerah da kanta ke ƙasa. “Ɗiyata Zinneerah ɗago ki kalli kowa danki haddace fuskokinsu da sunayensu”.        Duk da tana cikin yanayin jin nauyi bin umarnin Baffah dolene a gareta. Hakan yasa ta ɗago a hankali. Da wanda ke kusa da Hajiya Iya ya fara. “Wannan sunansa Mas'ood, ƴan biyu ne shi da Moos'ab gashinan. Wannan kuma Saifudden, wannan Haneef, wannan Abidah, wannan Safiyya, wannan Ni'ima. Sai Jamal, Meenal, Bahijja. Akwai yayunki kusan goma da babusu anan. Koda yake ba duka bane yayun naki a cikinsu dan kin girma wasu. Insha ALLAH duk zaki sansu su sanki suma a hankali. Waɗan nan dai sune yanzu tare dake anan gida, zaki kuma kasance da kusan dukansu yanzu a gida insha ALLAH”.         Fuskarta daɗan murmushi tace, “Nagode Baffah”.       Murmushin shima yay mata yana jinjina kansa. Yayinda su Haneef suka haɗa baki wajen, “Welcome to Shira's family ƙanwarmu”.        “Na gode Yayuna”. Ta faɗa ita cikin son aro jarumtar son sakewa da su. Dan taji daɗin yanda duk suka nuna jin daɗin kasancewarta a cikinsu.     Ƴar gajeruwar nasiha Hajiya iya tai musu akan zuminci kafin su fara cin abincinsu a tsanake. Wajen yayi shiru bakajin ko ƙwaƙwƙwaran tarin wani saboda dokace a garesu ba'acin abinci ana magana musamman idan Hajiya Iya da Baffah na waje. Uwa uba kuma Babban Yaya mai gayya mai aiki dashi ko ƙara cokalinka ya cikayi sai kasha uwar harara.          Koda duk suka kammala duk ficewa sukai, dan dukansu karatu sukeyi a mabanbanta makarantu jami'oi. Wasunsu na gab da kammalawa, wasu kuma yanzu suka fara musamman ƴammatan. Wasu kuma na tsakkiya. Sai su Bahijja dake secondary sun wuce Zinneerah da aji daya, dan suna ss2. Sai dai yau bazasujeba dan suna wani ɗan hutun kwana biyu a gida.       Bayan wucewar kowa ita dasu Meenal ɗin ne suka gyara dining ɗin. Hajiya Iya kuma ta nufi ɗaki gabatar da sallarta ta walha tana bar musu saƙon raka Zinneerah wajen iyayensu ta gaishesu.      Suna kuwa kammala gyara wajen suka jata. Meenal ce taja birki lokacin da suke gab da kaiwa tsakkiyar ƙaton harabar gidan nasu. “Kunga ku tsaya a fara da nunama sister kowanne sashe first”.        “To uwar tsari”. Cewar Jamal da shaƙiyanci.      Hararsa Meenal tayi sai dai batace komaiba. Bahijja tace, “Da gaskiyar sister ai, a fara da waje”.       “Naji karku cinyeni da baki malamai. Sister Zinneerah nan inda muka fito shine sashen Granny nasan kin sani ai?”.     Jamal ya faɗa idonsa a kanta. Batare da jiran amsarta ba ya cigaba. “Wannan na kusa da shi shine sashen Daddy Ahmad ne. Sai dai basa nan suna ƙasar Turkey lokaci-lokaci suke zuwa. Yaransa biyar shima. Yah Ibrahim, Yah Sadiq, Yah Hafeez. Aunty Zuhrah. Sai Aneesa dan bazance mata Aunty ba, kwana tara kawai ta bani a duniya kamar wannan yarinyar”. Ya nuna Meenal.       “Shashasha ai dai na girmekan ko?”.         “Oho a banza dai tunda kammu ɗaya”. Ya bata amsa yana mata gwalo.     Dariya abin nasu keba Zinneerah. Dan haka yanzuma tai murmushi mai faɗi.        “Yauwa sai nan kuma Sashen Gwaggo Bilkisu ne idan tazo nan take sauka itama. Tana Lagos da yaranta huɗu itama, kada lissafin yay miki yawa zakisan sunayensu suma nan gaba. Sai nan shine sashen su Yah Saifudden. Nan kuma sashen baƙine. Wannan da zamu shiga shine sashenmu, iyalan Baffah kenan”.     Murmushi Zinneerah tai cike da gamsuwa dajin birgewar tsarin nasu. Batare da tayi maganaba suka nufi sashen Baffah ɗin da yafi na kowa girma a gidan kasancewar yafi kowa yawan iyalai.       Sun fara shiga katafaren falo da yaji kayan more rayuwa da ƙawa, wanda har suka fice daga cikinsa Zinneerah bata gama kammala kallon daular dake shimfiɗe a cikinsaba. Basu tsaya anan ba suka isa falo na biyu wanda shima ƙatone na gaske harma zai iya ɗara na farko kayan alatu. A tunaninta an gama kenan, sai taga sun shigo wani falon a hannunsu na dama, sai dai shikam madaidaicine bakai na baya girmaba amma ya fisu tsaruwa.       Hamshaƙiyar mace ƙyaƙyƙyawa dake zaune da waya a kunne ta ɗago tana kallonsu. Fuskarta a sake take sai dai ba murmushi takeba. Zama su Bahijja sukai a kujera suna faɗin, “Barka da safiya Momie”.       Kasancewar waya take bata amsa musu ba. Tadai ɗaga musu hannu kawai idonta akan Zinneerah data kai zaune ƙasa zuciyarta na harbawa da ganin kamanin matar da Khalipha sosai. Bayan ta kammala ta ajiye wayar tana faɗin, “Masha ALLAH ɗiyata sai yanzu muke ganinki?”.        “Kuyi haƙuri Momie”. Zinneerah ta faɗa kamar yanda taji su Meenal na kiranta.       Cikin ƴar dariya tace, “A'a aiba laifi kikaiba ƴata. muna miki maraba da shigowa cikinmu”.        Gaba ɗaya kan Zinneerah a kulle yake. Tadai daure ta amsa mata da godiya tana gaisheta cikin girmamawa. Hakan yasaka Hajiya Nafisa jin daɗi har ranta dajin ƙaunar Zinneerah. Sun ɗanja lokaci a sashen Hajiya Nafisa da suke kira Momie nata mata ƴan tambayiyi jefi-jefi da janta da hira.        Hajiya Nafisa itace Baffah ya aura bayan rabuwarsa da Hindatu. Itace mahaifiyar Khadija da a yanzu haka tayi aure itada ƴar uwarta Hafsat. Sai Khalifa, Saifudden, da auta Bahijja. Sunɗan jima Kafin su miƙe su fito dan itama wajen aiki zata fita.     Daga nan sai sashen Hajiya Halima mahaifiyar su Meenal. Wadda suke kira Ummi. Itace ta haifi Mas'ood, Moos'ab, Ni'ima, Meenal auta. Itama ɗin dai ta tarbesu da kulawa da sakewa. Dan tamafi Momie fara'a gata da barkwanci. Yanda Zinneerah ta lura su Jamal sunfi sakewa sosai anan. Nanma sun jima sosai kafin su fito zuwa sashen Hajiya Ai'sha amaryar Baffan da suke kira da suna Ammi. Itace mahaifiyar su Haneef Safiyya, Abidah Jamal auta.        Mahaifiyar su Jamal ba mace bace mai yawan fara'a. Amma tanada son mutane itama. Dan ta tarbi Zinneerah ɗin da kulawa sosai, harma takai hirarsu tafiyin tsaho anan fiye da kowanne sashe. Basu fitoba sai da akai kiran sallar zuhur suka koma sashen Hajiya Iya data gaji da zuba idon dawowar tasu ma. ★★★         Lallai da gaske Shira's Family yayma Zinneerah daɗi. A cikin kwanaki huɗu kacal sai gashi ta saki jikinta da kowa, musamman ma su Bahijja dake ɗorata a hanya waɗanda bata da aminai sama dasu a gidan. Zata iya cewa shine gidan zama na farko data shigo bata fuskanci ƙiyayyar waniba a zahiri. Dan inma akwai masu ƙin nata sun danne a zukatansu basu taɓa nuna mataba.        Daɗin zama cikinsu ya matar da ita batun kwana biyu da akace zatayi ta koma. Abinda kawai ta kasa sakewa da shi shine kwana ɗakin da aka bata matsayin nata. Komai take a cikinsa a ɗararene. Gashi su Meenal basa shiga ɗakin sam. Ko zuwa sukai tana ciki sunfi yarda su jirata a falo harta fito..          A randa ta cika kwana na biyar suka koma makaranta. Ranar duk sai taji kuma babu daɗi. Amma janta a jiki da Hajiya iya keyi yay matuƙar ɗebe mata kewar su Little da ke damunta a rai tun zuwanta gidan. Tamkar kuma Hajiya iya ta shiga ranta sai gashima ta kira mata Mama a waya suka gaisa. sai dai su Sadiq duk sun wuce makaranta. Gwarancin Little dake wasa kawai take jiyowa. Tanason tambayar lafiyarsa tanajin kunyar maman Sadiq. Dan haka tai shiru tunda dai ALLAH yasa ta jisa ɗin.          Zinneerah na zuba ido taji ance ta shirya ta koma gida kodan karatunta sai taji tsit. A ranada ta cika kwanaki tara a gidanma Baffah yasa ta shirya Yah Saifudden ya kaita makarantar su Meenal da sunan sabuwar ɗaliba. Hakan ya bata mamaki dan babu wanda yay mata bayanin za'a canja mata makarantane. Garama Hajiya iya ta mata nasiha akan ta dage sosai karta bari su maidata baya. Tafi son karatunta da nasu Bahijja ya tafi dai-dai.      Zinneerah ba ƙoƙarine da itaba. Sai dai tanada naci akan abinda takeso. wannan ne ya taimaka mata matuƙa wajen amsa interview da akai mata duk da dai karatun da tayi a gidan Abba ya matuƙar taimaka mata. Da ace sanda ta baro Danya ne to lallai wannan haɗaɗɗiyar makarantar babu fashi aji ɗaya zasu maidata kuwa.       A yanzunma sunyi batun sai da ta koma js3. Saifudden ne ya roƙa alfarmar barinta a ss2 ɗin da alƙawarin zata dage insha ALLAH. Da yake maganace ta kuɗi kuma su ɗin sunada babban matsayi a makarantar yasa suka bar Zinneerah ɗin Ss2. cikin amincin ALLAH kuma aka kaita ajinsu Meenal. Zokaga farin ciki da murna lokacin da aka rakata ajin a zuwan sabuwar ɗaliba. Malamin na fita Jamal ya fita gaban aji ya sake gabatar musu da Zinneerah matsayin sister ɗinsu ce. Hakan yasa ta samu tarba mai ƙyau daga ƴan ajin dansu Jamal ƙurayene sosai akan ƙoƙari.       A ranar kam dai babu abinda Zinneerah ta fahimta a wannan aji. Sai ma neman ruɗewa da tsorata da tayi ganin yanda tsarin karatun nasu yake. Sam babu maganar hausa a ajin ma balle ga malami. Turancine da larabci kawai ke tashi.     Fahimtar yanda ta shiga ruɗanine ya saka su Bahijja kwantar mata da hankali akan karta damu zata iya itama ai wataran. Badan ta yarda da hakanba tai shiru, amma har cikin ranta a tsorace take kam. Sai dai kuma tana fatan iyawar kodan wasu abubuwa masu yawa dake cimata rai da zuciya a tarihin rayuwarta. Itama tanason ta zama wani abu kodan wani dalili nata dake ɓoye mata a cikin rai game da samuwar ɗan da batasan wanene ubansa ko yanda aka samar da shi ba.      Bayan tasowarsu ne Hajiya iya ta kira mata Mama a waya suka gaisa. A take ta labartama Maman komai har tana hawayen farin ciki dana kewarsu. Dan tasan dai tunda har aka sakata a makaranta da wahala ace zata koma zama wajen Mamanta sai dai idan anyi hutu. To koba komai dai ai tamayi nesa dasu Sakina iyayen gorin gida dana arziƙi. Kuma karatunta zaifi inganci anan fiye dacan duk da shima Abba bazata taɓa gajiya da yaba masaba a rayuwarta har ƙarahen numfashinta kuwa. ★★★      Kamar da wasa sai ga rayuwa ta fara canjama Zinneerah alƙibla. Dan kuwa dai da alama *_MAKAUNIYAR ƘADDARA_* data barota da Danya na neman zame mata ƙyaƙyƙyawar nasara mai abubuwan fata ga duk wanda ya tsinci kansa koda a makamancin irin tata rayuwarne. Yau ita Zinneerah mai tallar riɗi da gyaɗa da ɗanwake ce a wanann matsayin. Ita da kashin gidansu ma ya fita matsayi da daraja wajen Inna dasu Yaya Karima. Lallai ta yarda da yawan ƙaddara tsanine na nasara gamai haƙuri insha ALLAH. Sai dai ya danganta ga yanda ƙaddarar tazo maka da kuma yanda kai ka amsheta kai haƙuri da ita.      Sosai a kallo ɗaya zakaga ɗumbin canjin data samu. Jikinta ya murje matuƙa, ƙyawunta da nutsuwarta na sake fitowa gareta. Yayinda cikakken budurci ke sake huda gaɓɓanta da surarta. Ta kuma dage da naci akan karatu da taimakon su Bahijja duk da sukan sha wahala wani lokacin kafin ta gane abu daƙyau.      Zuwa yanzu a hankali su Meenal na jan ra'ayinta kwana sashensu fiye da ɗakinta. Wani lokacin kuma wajen Hajiya Iyama take kwana musamman idan ta tashi batajin daɗin ƙafarta haka ko jikinta. Tsakaninta da ɗakin nata bai wuce shiga tai wanka sai kuma gyarawa. Sai randa ALLAH kuma ya ƙaddara zata kwana a cikinsa.                 A kwana a tashi babu wahala wajen UBANGIJI sai gasu Zinneerah an cinye hutun zangon farko a tsadajjiyar majaranta. Kwanansu biyar dayin hutu Baffah ya haɗa mata shatara ta arziƙi Yaya Haneef ya kaita gida wajen mahaifiyarta. Da dasu Jamal zasu tafi Baffah yace su bari sai ta tashi dawowa sai suje su ɗakkota tunta dai kwanaki goma zatai kacal ai.      Haneef ya shiga sun gaisa. Sai dai bai jimaba ya fito ya tafi, dan makaranta zaije kuma yace yanada jarabawane. Amma daɗin tarbar daya samu ga Mama yace zai dawo. Bai iske su Sadiq gidaba suna islamiyya. Little kuma yana barci abinsa.        Kwatanta irin farin cikin da Zinneerah ta tsinci kanta a ciki ɓata lokacine. Amma tsabar kewar Mama da tayi harda rungumeta. Little kuwa data shiga ta samu yana barci yasha kisses, harda hawayenta ganin yanda ya ƙara girma a watanni uku kacal data ɗauka bata ganshiba. Wani irin son yaron da ƙaunarsa na ƙara tasiri a ranta alamun hankali ya fara game jikinta a yanzun fiye da da.      Lokacin kuwa data shiga gaida Maman Sakina ai baki ta saki tana kallonta tamkar sokuwa. Hakama dasu Luban suka dawo gidan daga makaranta dan suna jarabawa sai da ƴaƴan cikinsu suka hautsina da ganin canjawar Zinneerah ɗin a ƙanƙanin lokaci. Duk da sunsan dama ƙyaƙyƙyawa ce a yanzu kam ƙyan nata yafi fitowa da armashin gani gamai kallonta.      Itako sosai ta nuna murnar ganinsu cike da sakewa alamar yanzu akwai banbanci da da kenan. Dan babu wannan yawan duƙar dakan da ɗari-ɗari tattare da ita. Miskilancin nedai kam akwaishi saima abinda yay gaba.      Sai da suka shiga ɗaki sukaita gulma da zaginta wai dan taje gidan masu kuɗi kanta ke rawa tana musu shan ƙamshi. Duk da har yanzu basusan taka maimain a inda takeba. Har uwarsu ba sani taiba duk bin ƙwaƙwƙaafinta. Koda ta tambayi Abba cayay mata dangin mahaifanta ne suka ɗauketa dama basusan ta baro gida baneba zuwa nan shiyyasa. Daga haka kota masa maganar sai yace taje ta tambayi maman sadiq ɗin mana. Daga haka yake kashe bakin son gulma da tsugudidi.       Maman halima kuwa taji matuƙar daɗi da canjin da Zinneerah ta samu. Koba komai itama ta samu ingantacciyar rayuwa bisa ga zaluncin Asabe ai.      Dawowar su Sadiq aka sake kafa sabuwar murna da bidiri har takai ga tashin Little. Sosai girman nasa ya sake bama Zinneerah mamaki dan bakace ɗan shekara ɗaya da rabi bane. Da alama akwaishi da garin jiki kam. Yanda yaga su Aliyu nane da ita shima sai ya nane natan yana gwarancinsa dan maganar tasa bawani ganewa sosai akeba garama maman sadiq.      Ganin ƴan uwanta yay mata daɗi duk da bata mance dasu Jamal ba suma. Kullum ma babu fashi sai tayi waya dasu ta wayar Hajiya Iya ko cikin wayar ƴammatan gidan............✍       *_1~UBAYD MALEEK_* _By MamuhGee_ *_2~ MAKAUNIYAR QADDARA_* _By Billyn Abdul_ *_3~ DALAAL_* _By Miss Xoxo_ *_4~ MABUDIN ZUCIYA_* _By Hafsat Rano_ *_5~ ALKIBLA_* _By Safiyya Huguma_ Zaku samu wainnan duka biyar din akan farashin 700, Guda 5👉700 Guda 4👉500 Guda 3👉450 Guda 2👉400 Guda 1👉300 Zakiyi payment dinku cikin account dinmu dake rubuce na👇👇👇👇 *_0225878823 HAFSAT KABIR UMAR GTBANK_* Saika tura shedar biyanka ta wannan numbern👇👇 *08085405215* Idan kuma katin wayane zaka turo da MTN card ta  wannan numbern👇👇👇 *09032345899* Mungode *_TM ZAFAFABIYAR🔥_* *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* *Page 19* _________________________ *Assalamu alaikum warahmatullah, shin kinaba amfani da turaren gashi a matsayinki na mace data amsa sunanta idan amsarki aa toga dama tasamu *awwaba scent* *tazomaku* *da turaren fesawa a gashi natural 100% organic *wanda akahada rose water da essential oils tripped action gashi yy kamshi yay kyali kuma moisturiser at *the same time ba anan abun yatsayaba duk wanda yy order zaahada masa da freshener kala hudu ta daki *ta bandaki ta Mopping da turaren wanka a kan kudi 3,000 kacal indai q cikin watan September dinnna ne daganan kuma zasukoma *normal price dinsu, hakanan turarukqn wuta da humra dinmu anyi masu ragi duk me bukata se nememu a 08034236800 ta what's app kokuma ya ziyarci shafinmu a instagram* @turare_by_awwaba mungode* ______________________ *Page 19* ...........Sosai zaman hutun nan yayama Zinneerah daɗi. Dan koba komai shaƙuwa sosai ta sake shiga tsakaninta da Little, dan yanzun taɗan rage yin kawaici akansa. Hakama ƙannenta koda yaushe suna nane da ita.       A randa ta cika kwanaki goma sai ga su Jamal babu zato wajen sha ɗaya na safe. Lokacin suna shirin fita gidan sunan ƙanwar Maman Halima. Duk da taso taje gidan sunan sai zuwan nasu ya kauda son fitar, ta shiga murnar ganinsu. Su maman Halima kam dake goye da Little suka tafi bayan sun gaisa dasu Bahijja iyayen rawar kai.     Sukam babu ruwansu da wata baƙunta. Dan sakin jikinsu sukai tamkar a gidansu. Sai hakan yayma maman sadiq daɗi sosai, dan koba komai hakan girmamawace suka nuna mata. Maman Sakina da yaranta kam sai suka shige ɗaki suna leƙensu ta Window da gulmar a ina su mmn sadiq ɗin suka samo yaran ƴan gayu haka?. Basu da mai basu amsa, dan haka suka cigaba da habaice-habaice da sukar mmn sadiq ɗin harma dasu Meenal da basusan da zamansu a gidanba. Harda cewa kodai a gidansu Zinneerah ke zaune aikin wanke-wanke yanzun?. Sai suka yarda a haka duk da suma sun san faɗane kawai danjin daɗi. Dan Zinneerah batai kama da wadda taje aikatauba. Su Jamal ma sun sami rabon nasu zagin sosai, dan koda sukazo suka iske Maman sakina a tsakar gida dasu Luba ko kallo basu ishesuba. Sai mmn halima data tarbesu da fara'a suka gaida cike da girmamawa. Hakanne ya sake baƙanta ran mmn sakina taja ƴaƴanta suka shige ɗaki.       Wainar filawa Zinneerah tai musu kamar yanda sukace suna buƙata, sai da sukaci suka ƙoshi Abba ya dawo gidan bayan la'asar suka gaisa sanan driver yazo ya kwashesu harda Zinneerah da taso yin sallama da Little da sauran yaran, dan sanda maman halima ta wucene da shi yana barci, ko ganinsu su Bahijja ma bayi sukaiba. To da yakema ba sanin labarinsa sukaiba basu kawo komai a ransuba sun zatama ɗan mmn halima ɗinne duk da dai basuga fuskarsaba.        Sosai Hajiya iya dasu Yah Moos'ab suka nuna farin cikinsu na dawowarta. Tare da faɗi mata sunyi kewarta kowa a gidan. Cikin ƴar dariyarta tace, “Nima nayi kewarku ai, wani lokacin har mafarkinku nakeyi”.        Sunji daɗin maganarta har cikin ransu, dan itama suna mata kallone na ɗaya daga cikinsu bawai wadda tazo cin arziƙi gidansu ba. Moos'ab da bai cika yawan maganaba shi dama yaɗan ɗage gira yana gyara kishingiɗar da yay a kujera da faɗin, “Ni ba yarda nai dakeba fa yarinya”.      A hankali Zinneerah ta ɗago manyan idanunta farare tas ta zuba a kansa, irin kallon da yake matane ya sakata saurin maida nata ƙasa tsigar jikinta na tashi, ba yaune karan farko da Yah Moos'ab ɗin ke mata irin wannan kallonba, shiyyasa a mafi yawan lokuta bata wani cika sakewa da shiba sosai. Kasa bashi amsa tayi, hakan yasa Saifudden kwashewa da dariya yana faɗin, “Wataran dai zata fashe”.        “Minene zai fashe?”. Cewar Haneef dake a kusa dashi yana latsa waya.      Saifudden yace, “No jaridar mai tsadace, duk maiso ya tanaji kuɗi akwai ranar da zan saida muku”.      Abidah ce tai dariya tanama Saifudden alamar jinjina. “Ai Yah Saif nima na daɗe da harbo jirgin, kasanfa idanuna sun iya gane-gane nima, duk randa suka tashi saya ka nemoni zan ƙara da nawa rahoton”.      Tsam Zinneerah ta miƙe zata bar wajen, dan haka kawai ta tsargu da zancen nasu, tanaji a ranta kenan suma duk suna sane da Yah Moos'ab ɗin komi?.       “A'a, auta ina zuwa?”. Cewar Safiyya da sauri.       “Im ihm Aunty Safiyya zanje cikine nayi wanka”.      Da sauri Ni'ima tace, “Wankafa? Ba shigowata Granny ke faɗin kina ciki kina wankaba Auta (Mafi yawan lokaci haka suke kiranta auta).       Kasa magana tai, hakan yasa Saifudden kwashewa da dariya yana raira waƙa. Duka Moos'ab ya kai masa. Yay saurin wuntsilowa a kujerar yana cigaba da dariyarsa. Da sauri Zinneerah tabar wajen ranta fal tsoro. Ɗakin da har yanzu ta kasa sakin jiki da zamansa ta shige tare da faɗawa saman gadon a karo na farko. Tai ɗan murmushi dajan filo ta cusa kanta a ciki. A ranta kuwa rayawa take itakam karsu Yah Saifudden su jawo mata rigima. Ina ita ina soyayya da waninsu bayanma duk kallon yayu take musu itakam. Wannan zance ai da girma yake idan har yazo a yanda zuciyarta ke hankaltar da ita game da take-taken Yah Moos'ab ɗin.       Haka ta kasance cikin dogon tunanin da har barci mai nauyi yay awon gaba da ita batare data saniba. Harsuka gama hiratsu kowa ya miƙe zuwa makwancinsa basu sake ganintaba. Hajiya Iya kam dama ta kwanta tuni saboda maganin mura da tasha, kuma dama ita ba'a doguwar hira da ita, tanada saurin barci. Wani lokacinma sai jikokin nata suzo su ƙaraci shirmensu a sashen bata saniba. Dan kullum nanne wajen hiratsu sai dai idan yayansu na gari kam babu sakewa, duk da suna zuwa a hakan.              Sosai Zinneerah taji daɗi barci akan wannan gado da yau ya zame mata na farko, dan ko fitsari bata farka yiba yau saboda daɗin barci. Sai kiran sallar farko na asuba ta buɗe idanunta da ƙyar tana karanto ɗaya daga cikin addu'ar tashi daga barci. "الحَمْدُ لله الذِي أَحْيَانَا بَعْدَ مَا أَمَاتَنَا وَإِلَيْهِ النُّشُور" Alhamdu lillahil-lazee ahyana ba'ada ma amatana wa-ilayhin-nushoor.        Sai da ta bada ratar kusan mintuna uku bata motsaba dan idanunta su ƙara saki sosai sannan ta tashi zaune tare da zuro ƙafarta ta sauka a gadon. Tayi mamakin ganin an kashe mata wuta da lulluɓa mata bargo, sai dai tasan bazai wuce ɗaya daga cikin su Aunty Safiyya ba. Wanka ta farayi da ɗauro alwala ta fito. Bayan ta gabatar da nafila raka'a biyu ta ɗakko AL-QUR'ANI ta fara duba inda akai mata ƙari jiya a islamiyyasu data koma zuwa ta anguwar su mmn sadiq.     Tana zaune a wajen har akai salla. Bayan an idar tai Azkar kamar yanda Hajiya Iya ke maimaita mata muhimmancin yinta a kowacce safiya da maraicen duniya. Sai da ta kammala gari yay haske ta miƙe ta gyara ɗakin tsaf kamar yanda ta saba, ta saka kayan ƙamshi ta fice zuwa taya su baba Rahi aiki. Amma sai da ta fara shiga ta gaida Hajiya Iya da mura sannan.         Sai da suka kammala komai tsaf suka shirya tebir sannan ta koma ɗakin domin yin wanka.        Sanin ba kowa ke shigowa ɗakinba sai Hajiya iya yasata fitowa kanta tsaye da towel. Sai ƙarami da take ƙoƙarin naɗe kanta data wanke a ciki. Wani irin mugun tsargawa zuciyarta tayi dai-dai lokacin da take fitowa daga ɗan lungun da toilet ɗin yake. Tsabar ruɗani da firgici batama san ta saki towel ɗin da take ƙoƙarin ɗaurawa kantaba a ƙasa....      Ƙyaƙyƙyawan matashin dake zaune hakimce a bakin gadon ƙafa ɗaya kan ɗaya waya manne da kunnensa ya ɗago dara-daran idanunsa masu cikar gashi da haske yana kallonta da alamun tsantsar mamaki a cikinsu. Hannunsa yakai bisa kwantaccen sajen fuskarsa da babu yawan fara'a a kanta ya shafa ɗan guntun sakewar dake kanta na ƙoƙarin gushewa gaba ɗaya. Sauke hannun daya shafa fuskar yay yana gyara ɗayan dake riƙe da wayar da yakeyi har yanzun yana janye idanun nasa daga kanta yana furzar da wani irin huci daya saka Zinneerah dawowa hayyacinta ta ƙwalla ƙara dan duk zatonta aljanine kawai ya shigo mata, shiyyasa tai sumar wicin gadi.       Gaba ɗaya ya saki wayar a ƙasa, yay saurin saka tattausan hannunsa ya toshe kunnuwansa yana runtse idanunsa da ƙarfi.            Kusan rige-rigen shigowa ɗakin akai tsakanin Hajiya Iya da Baba Rahi.  Su duka kan Zinneerah sukayi dan babu wanda ma hankalinsa ya kai kansa. Hajiya Iya ta kamo Zinneerah da alamu suka nuna bata cikin hayyacinta jikinta. “Ya ALLAHU, Zinneerah! Zinneerah kinga buɗe idonki gani tare dake. Miya faru? Ko wani abune ya tsorataki?. Rahi kawo ruwa a bata dan ALLAH da sauri”.        Fita Baba Rahi tayi da sauri sai gata da ruwa ta dawo. Amsa Hajiya iya tai ta bama Zinneerah daketa faman ɓoye fuskarta a jikin Hajiya Iya nata jikin na rawa dan ta tsora sosai musamman data sake kallon fuskarsa yanzu hankalinta ya sake tashi. Kaɗan ta sha dan bata tare da nutsuwar shansa. Hannunta na karkarwa ta sake ƙanƙame Hajiya Iya  ta nuna inda yake zaune kunnensa toshe, hakama idanunsa a rufe har yanzu.        “Aljani, wlhy Aljanine Granny”. Tana maganar hawaye na ziraro mata kamar an buɗe fanfo.        Daga Hajiya iya har Baba Rahi turus sukayi suna kallonsa suma fuskokinsu ɗauke da mamaki musamman Baba Rahi da sam bataga shigowarsaba duk da tana kitchen tana wanke-wanke. Sai dai tabbas taji baƙon ƙamshin turare datai tunanin ko cikin samarin gidanne suka fara shigowa yin breakfast.          Fuska hajiya iya ta haɗe da kamo hannun Zinneerah dake nunashi har yanzun ta riƙe, ta sake kwantar da ita a jikinta tana shafa mata baya da sauke ajiyar zuciya. “Kinga Zinneerah kwantar da hankalinki ba aljani bane mutumne”.      “Wlhy ba mutum bane Granny, aljanine, dan aljanine kawai zai iya buɗe ɗakin dana rufe kuma na cire key ɗin kingansa acan na ajiye......”        “Shiii, ya isa kiyi shiru, Yayankune ba aljaniba, yanada key a hannunsa shiyyasa ya shigo”.        Kafin Zinneerah ta samu damar cewa wani abu Baffah ya shigo ɗakin saboda jiyo muryar Zinneerah ɗin dake magana tana kuka, sai kuma ya jiyo hajiya Iya itama.       “Lafiya kuw....” ya kasa ƙarasawa saboda sauka da idanunsa sukayi akansa shima. A take fara'ar fuskar Baffah ta ɓace ɓat. Saurin duƙawa Baba Rahi tai tana gaishesa. Bai iya amsa mataba sai hannu kawai ya ɗaga mata. hakanne ya sakata tashi da ta fice a ɗakin.            Hijjabin Zinneerah na salla hajiya iya ta jawo ta saka mata, batare da tace komaiba ta kama hannunta suka fice daga ɗakin. Bayansu Baffah yabi shima batare da yace uffanba.         Kansa dake a duƙe tun haɗa ido da sukai da baffa ya ɗago a hankali yabisu da kallo har suka fice gaba ɗaya. Sake lumahe idanun yay da furzar da huci mai ƙarfi tare da kai hannunsa ya dafe kansa.               Tsaye cirko-cirko suka iske yaran gidan da suka fara shigowa sashen. Dan har sunji labarin zuwan Yayan nasu gidan a bakin Yaya Khalipha da sukazo tare.       Wucesu Hajiya Iya tayi riƙe da hannun Zinneerah dake sharar hawaye ɗakinta. Baffah kuma ya nifi dining shima fuska a ɗaure.      Baffa mutum ne mai barkwanci ga yaransa, amma idan ransa ya ɓaci dolene kowa ya shiga hankalinsa. Da sauri Safiyya ta taso inda yake ta fara ƙoƙarin haɗa masa abincin gabansa. Hakan yasa suma sauran yaran nufo dining ɗin duk suka zauna. Hajiya Iya ce ta fito daga ɗakinta tana ƙwalama Jamal kira. Dai-dai yana ƙoƙarin zama danshi shigowarsa ma kenan sashen baisan mike faruwa ba.       “Na'am Granny ”. Ya amsa yana maida kujerar daya jawo tare da juyawa gareta.      “Ka shiga ɗakin can ka ɗakkoma Zinneerah Uniform ɗinta da jikkarta”.       Cikin rashin damuwa da abinda tace ɗin, yace, “Okay maa”.      Yanda ya nufi ɗakin kansa tsayene ya saka sauran ƴan uwansa binsa da kallo. Bahijja ta saka hannun ta rufe bakinta jin dariya na neman kufce mata. Meenal kam ƙasa tai ƙarƙashin tebir tamkar zata gyara wani abu tayi tata.        “Oh ni Jamal ni za'a saka na ɗakkoma ƙanwata abu. yau yarinyarnan zatasha ƙwanƙwashe a kai kuwa a class na rantse”. Yay maganar yana tura ƙofar ɗakin da shiga kansa tsaye.      Wani wawan birki yaja yana waro idanu waje ganin wanda baiyi zatoba tsaye yana ƙoƙarin zame rigar saman suit ɗinsa. Cikin rawar baki yace, “Bar... Ba.. Barka da zuwa Yayanmu. Kazo lafiya? An barosu lafiya? Ya hanya?”.      Yanda ya jero gaisuwar kawai zaka fahimci a kiɗime yake. Shiko da ake gaidawar kallo ɗaya yay masa ya janye idanunsa batare daya amsa ko ɗayaba a ciki, dan gaba ɗaya ransa a dagule yake. Yasan shiɗin mai laifine ga mahaifinsa da kakarsa. Amma yayi zaton Baffa ya yafe masa kamar yanda ya roƙesa tun a waya kafin ya taho....      Da sauri Jamal ya juya zai fice a ɗakin....           “Mi kake buƙata?”.    Nutsatstsiyar muryarsa mai kama data rowa ta bayyana cikin kunnuwan Jamal. Tamkar zai fasa kuka ya juyo garesa. “Yayanmu Granny tace nazo na ɗaukama Zinneerah Uniform ɗinta zamu wuce school”.       Uffan baice da shi ba, sai ma towel daya ɗauka a akwatin da yazo dashi ya nufi toilet abinsa. Jamal na ganin ya shige ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, tare da nufar Uniform ɗin Zinneerah dake ajiye a bakin gado ya ɗauka sauri-sauri tare da schoolbag ɗinta da takalma ya fita da gudu.         Shikam koda ya shiga toilet ɗin kallon tsaf ya shiga masa, dan a rayuwa ya tsani ƙazanta. Jin ƙamshin toilet ɗin gaba ɗaya ya canja daga nashi ya sakashi cije baki a ransa yana raya hukunci da zaima yarinyar nan da har idonta yay tsaurin shigo masa ɗaki tai wanka. Gamsuwa da tsaftar bayin ya sakashi ƙoƙarin ajiye towel ɗin hannunsa a bazata idonsa ya sauka akan B&P ɗin Zinneerah data shanya. Kauda ido yay yana wani cizar baki da rinmtse idanu da ƙarfi, a fusace ya rataye towel ɗin ya fito yana ƙwala kiran sunan Jamal.        Wayam babu Jamal a ɗakin alamar ya gudu, ya riƙe ƙugunsa da hannaye duka biyu idanunsa na canja launi saboda haushi. Ƙofa ya nufa kamar zai fita sai kuma ya fasa ya dawo da baya yanayin ƙwafa. Haka ya haƙura ya gudanar da dukan uzirinsa, sai dai sau goma idonsa yakai ga kayan sai sun sami tsarabar harara talatin da tsaki. Sai wani faman yamutsa fuska yake tamkar yau ya fara ganin irinsu.      Oho ita mai kayanma batasan yanayiba. Dan tanacan tayi shirin makaranta bisa umarnin Hajiya iya. Sai dai ranta cike yake da ruɗani. a kuma matuƙar kiɗime take da ganin wannan fuskar. Tasata gaba Hajiya Iya tai suka fito dining domin karyawa. Baffa ta fara gaidawa sannan su Haneef dasu Ni'ima. Ta bama Meenal da bahijja hannu sukai musabaha sannan ta zauna.      Hajiya iya kam da suka fito tare abinci ta fara shiryawa. wanda kowa yasan na yayan nasune, shiyyasa duk suke addu'a a ransu kar mutum yazam shi za'a aika yakai masa.     Ganin Hajiya iya ta zauna bayan tagama yasa kowa ke ƙoƙarin ganin ya gama ya fita, Jamal ne ya fara miƙewa yana kallonsu Zinneerah. Guys kutashi muje kunsan yau Sir Mansur ne damu a period ɗin farko”.       Daga Meenal har Bahijja sun ramfo saurin nasa. Dan haka suka miƙe da hanzarinsu suna faɗin, “Hakanefa ka tuna mana”.       Miƙewa Baffah yayi yana goge bakinsa da tissue. Ya ɗan kallesu ya kauda kansa. “Kumuje sai mu saukeku dan zan shiga makarantar taku ne”.       Sosai daɗi ya kamasu. Duk suka washe bakuna suna kashema juna ido najin daɗi yau tare da Baffahnsu zasuje school. Duk da dama yakan musu haka lokaci zuwa lokaci dan kawai ya sakasu farin ciki.        Zinneerah dai duk jikinta a sanyaye yake har yanzu. Babu abinda ke mata gizo a zuciya sai ƙyaƙyƙyawar fuskarsa mai cike da kwarjini da kamalar cikar haiba. Sallama sukaima Hajiya iya sukai waje suna ɗagama sauran yayyensu hannu.              Cikin raɗa-raɗa Saifudden yake cema Moos'ab mumafa mu tashi mu fece dan yau gidanan akwai ƙura tsakanin Granny da Yayanmu. Wannan faɗan kuwa yafi ƙarfin ganinmu koda ta bayan katanga ne”.     Miƙewar kuwa duk sukayi sunama Hajiya Iya dake kicin-kicin da rai sallama. A dai-dai wannan lokacin Khalipha ya shigo falon da sallama. Kansa ƴammatan sukai cike da ihun murna ƙasa-ƙasa dan gudun kar Yayansu yajiyosu. Fuskarsa washe da murmushi kuwa ya buɗe musu hannayensa. Sai dai harar da Hajiya iya ta balla masa ce ta sakashi maida hannun ya naɗe a ƙirjinsa yana dariya. Duk da haka sai da sukaje suka ɗan fabu da jikinsa suna jera masa kalaman kewarsa da sukayi.      Gudun samun matsala yasa sukai masa sallama suka fice su dukansu. Shi kuma ya ƙarasa ga Hajiya iya. Ɗan rungumeta yayi ta gefe yana faɗin, “Oh my sweetheart, i miss you so much”.        “Oh ai nazata kaima ka koyo halin turawanne ka fara ƙyama da gudun danginka”.        “Kai! Granny ni na isa. Babu wani ɗaukaka da ALLAH zai mana a duniya mu kyamaceku ai. Dan kune kuka nunamu ga duniyar harta san da zamanmu”.      Cikin taɓe baki tace, “Kai kasan wannan ai. Banda wasu bauɗaɗɗu masu bahaguwar rayuwa”. Ta ƙare maganar da harar gefenta tana ƙara ɗaure fuska.       Juyawa Khalipha yay da sauri saboda jin ƙamshinsa, ya kuma tabbatar da shi Hajiya iya ke wannan zancen. Ilai kuwa shine ke takowa inda suke, kuma komai da Hajiya Iyan ta faɗa ya shiga cikin kunnuwansa. Amma yay tamkar bai jiba sai ma kujerar daya ja ta dining ɗin ya zauna.      Murmushi Khalipha yay yana dubansa. “Barka da fitowa Yayanmu. Yanzu nake batun zuwa na fiddoka kayi breakfast dan nasan kana jin yunwa sosai”.        Wani ɗan murmushi yayma Khalipha ɗin yana lumshe idanunsa masu yalwar gashi da cikar gira. Khalipha yasan halin kayansa. Dan haka cike da rashin damuwa yace, “Mi za'a haɗa maka?”.      Kafin ya bashi amsa Hajiya iya ta amshe da faɗin, “Ni ban girka abincina da shi ba. Sai yayi waya su ƴan can London ɗin ko Morocco su kawo masa yaci”.        Ƙaramar dariya Khalipha yayi da kai hannu ya fara buɗe kwanikan dake shirye akan tray wanda ya tabbatar nasu ne. Shiko gogan hannayensa kawai ya harɗe a ƙirji yana kafe Hajiya iya da kallo.       “Bar kallona malam karka cinyeni da waɗanan shu'uman idanun naka  lokacin mutuwata baiyiba”.        A karo na biyu ya sake sakin lallausan murmushi yana kauda kansa gefe. Cikin magana ƙasa-ƙasa yace, “Bazata canjaba kullum”.       “Anƙi canjawar dan ubanka”. Hajiya iya ta faɗa tana zabga masa harara da masa daƙuwa.      Bakinsa yaɗan taɓe da ɗaukar wayarsa ya hau latsawa kamar bashine ya takalo rigimarba. Khalipha dai abinci yake haɗa masa yana dariya, dan inhar Yayansu na gidan nan irin wannan rigimar shi da kakar tasu ba sabon abu bane. Sai suyi sau goma a rana su shirya. Hakan kuma bazai hana gobe su ɗora daga inda suka tsayaba.      Masifa Hajiya Iya ta cigaba dayi, inda take shiga ba nan take fitaba. Shi dai yay mata shiru yanata cin abincinsa hankali kwance. Danshi mutum ne da baya wasa da abinci. Cinsa yake bil haƙƙi da gaskiya a duk lokacin daya samesa. Musamman daya kasance mutum mai tsananin son abincin Nigeria ma.        Hajiya iya dai batai shiruba sai da tayi mai isarta sanann ta mike tabar wajen. Dan Khalipha ne keta faman bata haƙuri, shiko yayi kamar babu shi a wajen sai cin abinsa yakeyi.      Bayanta yabi da kallo harta shige. Ya maido idonsa kan Khalipha, “Besty matarnan bazata taɓa canjawaba da wannan faɗan nata?”.         Dariya Khalipha yake sosai. “Yayanmu kaimafa mai laifine, bai kamata kai mata shiruba, amma ka barni da bada haƙuri”.       “Bazaka gane bane, itafa idan kana bata haƙuri kamar tunzurata kakeyi. Bakinta ko gajiya bayayi”.        “Munafiki, ai inajinka”. Suka jiyo muryar Hajiya Iya da basuji fitowartaba a bayansu.       Dariyace taso kufce masa. Dan haka ya miƙe da sauri yana goge bakinsa da tissue yabar falon gaba ɗaya. Da alama gaida matan gidan zaijeyi.           Harya gama ficewa bai daina jiyo masifar Hajiya iya da dariyar Khalipha ba. Ya ɗan dafe kansa yana furzar da huci da faɗin, “Madam Problem”............✍        *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* *Page 20* ______________________ *Mg's herbal whitening black soap* Duk wacce batayi anfani da sabulunnan ba anbarta abaya acan karshen bayama kuwa duk Mai tantama akan sabulai nagyaranjiki cewa basa Aiki toh yacire mg's domin kankat ne insha Allah babu Wanda yayi anfani dasabulunmu yace baiyi ba koyaushe mg's sai sanbarka amare da uwargidaye hardama yanmata kuhanzarta kusamu naku ba karya domin bama cika Baki kugwada kubada labari da bakunanku sabulu daya tamkar dubu wadandama basasan using cream sabulun mg's herbal whitening black soap yawadacemuku jikinku zaiyi kyau koyaushe kukasance clean cikin kamshi Kuna glowing koda bakusa turare ba🤗 Kayanmu bana bleaching bn organic ne sunagyarajiki fiye da tsammaninku zaifiddomuku da ainihin natural beauty dinkine Wanda yagwada shi zaitabbar amare kuyi kokari kumallaki mg's domin baruwanku da zuwa adirjemuku jiki zakuga yanda fatarku zata dinga walwali Ina masu pimples Tabo(spot) Sunburn dama dukwani matsalar fata kuyi kokari kunemi soap dinnan before 2weeks zaisharemuku hawaye kuzama abun kwatance Sister's masu nankarwa kuma kunemi soap dinnan Yana rage nankarwa sosai🧖🏻‍♀️duk me shakku tayi kokari tagwada mg's insha Allah bazakiso rabuwa dashi ba Akwai maisa haske Amma kayanmu nafada bana bleaching bn zaifiddomiki d ainihin halittarkine yagoge dukkan dattin jiki Akwai Kuma Wanda zaimiki maintaining skin dinki yasaki fresh fatanki tazama kalar hutu Pls bamacika Baki you HV to try it and see for yourself 100%tested nd trusted Soap price:3k Location:kaduna buh munaturawa ko Ina Amma delivery is not free Maiso kindly message 08062991549 Call 08064532391 Note:Babu inda zakusami mg's herbal whitening black soap sai a number dinnan bairiga yakai market b inyakai we will let you know buh as for now wnn numbern ne kawai🙏 Maiso yahanzarta before yaji sold out akwaisu available now insunkare you HV to wait akawo so maiso yahanzarta🙏adade anayi sai gsky🤭🤝 Mg's skincare _____________________ *Page 20* ..........Ƙarfe biyar da rabi motar dake ɗakko su Zinneerah makaranta ta shigo harabar gidan. Kamar yanda ta fita gidan da damuwar baƙon dasu Jamal ke kira Yayansu haka ta dawo da ita a rai. Babban damuwarta ya ganta daga ita sai guntun towel a jiki. Gashi yanda taga fuskarsa da yanda su Meenal ke labarinsa tasan ba kirki zaiyiba sam, sai kuma wani abu mai kama da almara da take hangowa, wanda ƙwaƙwalwarta sam ta kasa ɗauka.         Kamar kazar da ƙwai ya fashema a ciki haka ta nufi sashen Hajiya iya tana mai addu'a a ranta ALLAH yasa baya nan. Koda tazo ƙofar falon sai da ta tsaya tai addu'a sannan ta shigo bakinta da sallama. Da sauri taja birki a taku huɗu, dan tun sakko ƙafarta ciki hancinta ya shaƙo mata mayataccen ƙamshin turare. Bata kawo a ranta falon yakeba idanma shine, sai da ta ƙarasa shigowa sosai idanunta sukai gamo maiban ruɗani, dan a yanzune ta sake samun damar yimasa kallo mai ƙyau.       Zaune yake bisa kujera 1seater dake facing kofar, ƙafarsa ɗaya kan ɗaya. Hajiya Iya na zaune kujerar gefensa tana dama fura. Sai wanda bataga fuskarba saboda juya mata baya da yayi. Har cikin ranta taji daɗin samunsa bashi kaɗaiba duk da bataso ganin nasaba ma gaba ɗaya.        Sallamarta Hajiya iya ta amsa fuska ɗauke da murmushi take faɗin, “Ƴan makaranta an dawo?”.        Cike da ƙarfin hali Zinneerah ta sakima Hajiya Iya murmushi da faɗin, “Eh Granny barka da yamma”.        “Barka dai Inno na, da alama yau kam an dawo da yunwa naga kinyi zuru-zuru?”.        Murmushi tayi batare da tace komaiba. Ta ɗan saci kallon inda yake zaune idonsa a wayarsa dake hannunsa yana latsawa tamkar baisan da shigowartaba. Sai dai abinda bata saniba cikin abinda baifi sakkani ashirinba ya gama ƙarema shigar Uniform ɗin jikinta kallo. Skirt ne iyakar ƙwauri pink color. Sai farar shirt dataji guga da baby hijjab fari daya tsaya mata iya ƙirjinta shima dai a gogen yake. Sai farar safa data rufe ƙwaurin nata da farin takalmi. Bayanta goye da school bag ɗinta data saki hannunta guda. Babu mai cewa Zinneerahn danya ce data taɓa rainon ciki harta haifesa yake gudu ko ina da kafarsa a halin yanzun. Baka iya hango komai tattare da ita sai zallar ƙuruciya da jin daɗin rayuwa na canjin data samu cikin ƙanƙanin lokaci.          “Yayanmu barka da yamma”. Ta faɗa ciki-ciki tsabar fargaba da tsoron dake mamaye da ita. Harta fidda rai zai amsa sai taga ya ɗaga mata hannu alamar amsawar kenan.      Gaba tai zata wuce, batare da ta gaida ɗayan wanda bata ganin fuskar tasa ba. A tunaninta ko shi baisan da shigowarta ba. Sai da taɗan gitta su taji ashe waya yake amsawa. Numfashi ta sauke da nufar ɗakin Hajiya Iya da saurinta, dan bata fatan abinda zai sake tsaidata a wajen. Ajiyar zuciya ta sauke a hankali dai-dai tana saɓule school bag ɗinta da zubewa akan sofar ɗakin. Zamewa tai ta kwanta ko jininta daya ɗauke na wucin gadi zai dawo aiki jikinta yanda ya kamata.         “Kina lafiya kuwa Zinneerah?”. Hajiya iya data shigo ta faɗa tana kai hannunta saman goshin Zinneerah dake kwance rigingine. Buɗe idanu tai a hankali tana kallon Hajiya Iyan, ta yunƙura zata tashi Hajiya iya tace, “Kinga yi kwanciyarki abunki. Amma kina lafiya dai ko?”.        “Lafiyata ƙalau Granny, na gajine sosai yau shiyyasa”.      “Tofa, halan tsalle-tsallen wofin nan naku kukayi a makarantar ko?”.     Ƙaramar dariya Zinneerah tayi tana tashi zaune saboda ganin a yanda Hajiya Iya tai magana fuska a yatsine. “Granny yanzu yaya zanyi kayana nacan ɗakin fa. Ni kuma wlhy wannan mutumun tsoro fuskarsama take bani. ALLAH yasa dai baiyi faɗan ganina a ɗakinsaba”.        “Idan yayi tsoronsa zanjine Zinneerah? Indai Moddibo ne ma bar wahalar da kanki wajen tsoron wani faɗansa na wofi. Shi haka yake baida fara'a dason hayaniya. Harkar kowa kuma ba shiga yakeba sai idan yaso hakan dan kansa. Tashi kije ki ɗakko kayan da zaki saka, zuwa weekend idan ALLAH ya kaimu sai ki tattaro kayan da zakiyi amfani dasu harya tafi kafin ki koma”.      Cikin waro idanu Zinneerah tace, “Granny kina nufin sake koma masa ɗaki zanyi da zama?”.        “Oh to kajimin ja'ira bakison ɗakinne?”.       “Nidai zan zauna dake anan. Ɗazu ɗinnan da ace babu kowa a gidannan da yazo ya sameni a ɗakinsa ai kakkaryani zaiyi yasin”.      Yanda take maganar da iya gaskiyarta yasa Hajiya Iya yin dariya. “Idan bazaki takuraba anan ɗin nima zanfi jin daɗin ganinki kusa dani. Dama danki sake yasa nace kije ɗakinsa ki zauna a binki ai. Yanzu tashi ki watsa ruwa sai kizo kici abinci duk kinmin zuru-zuru a idanuna”.        Miƙewa Zinneerah tai tana ƙoƙarin cire baby hijjab ɗinta. Hajiya iya kuma ta fice a ɗakin.        “Granny wai keda wa naji kuna magana ɗazun ina waya?”.     Khalipha ya faɗa dai-dai Hajiya iya data fito tana kaiwa zaune. Sai da ta zauna ta bashi amsa da, “Ƙanwarku ce mai kama da Inno. Yanzu zata fito sai ku gaisa”. Cikin rashin damuwa da sonjin daga ina yace, “Okay. Bara naje nan waje ga Sadam yana jirana zamu ɗan fita. Yayanmu baka buƙatar komai?”.          Har yanzu idanunsa nakan wayarsa tun yanda Zinneerah ta barshi. Ya ɗan ɗago kansa ya duba Khalipha ɗin ya maida. “No jeka abunka. Nima zuwa 6:30 Mahmud zai shigo muɗanyi magana”.      “Okay bye, insha ALLAH zan dawo nima kafin ya tafi. Dan nasan yau tare zakuci abincin dare. Granny bye”.        “A dawo lafiya”. Ta faɗa dai-dai yana ɗaga mata hannu zai fice.      Koda Zinneerah tai wankan ƙin yarda ta fito ɗaukar kayan tayi, duk da tanajin yunwa ta gwammaci ɗaukar sauran biscuit ɗinta dake cikin jakka taci, a ranta addu'a take ALLAH ya kawo wani acikin su Jamal ya taimaketa ya ɗakko mata kayan. Sai dai addu'arta bataciba. Dan muryar Hajiya Iya ta tsinkayo tana ƙwala mata kira. Hijjab ta ɗauka ta fito badan tasoba. Hajiya iya dake kallonta tunda ta fito tace, “Wai nikam bazakizo kici abinciba kika maƙale a ɗaki kamar wata sabuwar amarya?”.         “A'a Granny dama yanzu zan fito”. Ta faɗa tana satar kallonsa ta gefen ido. Yanzu kam waya yake a kishingiɗe saɓanin ɗazun. Saurin nufar kitchen tayi ɗebo abincin a bazata ta tsinkayi nutsatstsiyar muryarsa mai kama data rowa cikin kunnenta a karon farko. “Ki kwashe tarkacen da kika barmin a toilet”.        Duk da ba ita yake kalloba ta tabbatar da ita yake. Tuna abinda ta bari ɗinne ya saka kunya mai tsanani lulluɓeta. da sauri tabar wajen.      Gaba ɗaya turarensa mai ƙarfi ya danne nata daya fara zama a ɗakin cikin wuni ɗaya. Toilet ta wuce sum-sum tamkar yana a cikin ɗaki. Ganin alamar yayi amfani da toilet ya ƙara saka zuciyarya shiga cikin wani irin matsananciyar kunya. Ta kwaso kayan tana rintse ido kamar ta fasa ihu. shikenan ya gama gane mata sirrinta wayyo ita Zinne. Koda ta fito sum-sum ta wuce bata yarda ko sashen da suke ta kallaba.               Fitar da yay da daddaren saboda zuwan abokinsa Dr Mahmud ta bama yaran gidan damar shan sharafin hirarsu yanda suka saba. Sai dai anayi ana leƙen waje wai karya shigo. Sai ma ALLAH ya taimakesu har suka tashi bai shigo ɗinba.      Washe gari da safe ma har suka gama breakfast kowa ya fice yana ɗaki bai fitoba. Kasancewar juma'a ce da wuri su Zinneerah suka dawo gidan.               A bedroom ta iske hajiya iya zaune tana karatun AL-QUR'ANI. Bata zaunaba ta ajiye school bag ɗinta da cire hijjab ɗinta ta fice zuwa kitchen dan yunwa takeji, yau bata wani zauna tayi karin kirkiba suka fita makaranta. Gaba ɗaya ta shafa'a da kasancewar sa a gidan. dan haka ta fito kanta tsaye ko ɗan kwali babu akan nata. Sai gashinta data wanke dan zuwa kitso dake ɗaure a tsakkiya. Tanada gashi duk da bamai wani uban tsaho bane, dan yakanzo mata dai har kafaɗa musamman idan ta wankosa a saloon.         A yanda take tafiyar yasa sam bataga mutum dake tahowa a gabantaba. Gab sukai karo da juna. Ta ɗago a firgice tana murza goshinta zatai magana, amma sai maganar tata ta maƙale a maƙoshi ta tsaya kawai tana kallomsa. Shima ɗin dai kallo yake mata irin na sani, sai dai ya kasa tunano a inda yasan fuskar.         Baki ta buɗe da nufin ambaton sunansa ya katseta yana murmushi. “Sorry Beauty. Ko kece Sister ɗin tamune?”.         Saurin haɗiye maganar tata tai itama mamaki na neman kasheta a tsaye. Kenan bai ganetaba komi? Kokuwa basarwace irinta masu hannu da manda. Aiko inhar hakane itama ta iya ai, musamman a yanzu da take ƙara samun wayewar rayuwa da zamantakewa wajen malamta su Jamal.        Kanta ta kaɗa masa tana ƙaƙaro murmushi. Tace, “Eh nice Yayanmu, kunzo kafiya?”.         “Alhmdllh, amma kinma sanni kenan?”.       “Eh mana. Na sanka a bakinsu Bahijja”.       “Kai-kai a bakin magulmatan gidannan kenan. to ALLAH yasa dai basu koyama ƙanwar tawa gulma ba?”.          Ƙayataccen murmushi ta saki har haƙoranta na bayyana fili. Hakan yayi dai-dai da isowarsa wajen. Ta buɗe baki da nufin bama Khalipha amsa idanunta suka faɗa cikin nashi. Wani irin yarrr tsigar jikinta ta tashi, tai azamar maida kanta ta duƙar ƙirjinta na bugawa saboda abinda zuciyarta ta hasko mata a yanzunma kamar jiya data fara ganinsa, koma wanda yafi na jiyan, idanunsu iri daya hatta da kwayoyin ciki.       Juyawa Khalipha yayi domin son ganin abinda ya hanata maganar, yay murmushi a dai-dai sanda yayan nasu ke ƙoƙarin gittasu tamkar baima gansuba. Da sauri Khalipha yace, “Barka Yayanmu”.      Hannu ya ɗaga masa kawai yawuce abinsa. Hakan yasa Khalipha ƙara matsawa gaban Zinneerah da kanta ke a ƙasa. Cikin raɗa-raɗan magana yace, Beauty bara muje massallaci, idan na dawo zakizo ki tayani hira”. Daga haka yabi bayan Yayan nasu ɗakin Hajiya Iya daya shiga.         Nannauyan numfashi Zinneerah ta sauke tare da lumshe idanu ta dafe kirjinta. Zuciyarta na gargaɗinta akan abinda ƙwaƙwalwata ke hasko mata maiban tsoro da ruɗani. jiki a saɓule ta wuce kitchen dan neman abinda zata sakama cikinta ko taji dama.       Sosai ran Zinneerah yake a jagule da tunani mai tarin ruɗani kala-kala. Ba komai ya janyo hakanba sai ganin da taima Khalipha. Wanda zuciyarta taƙi aminece mata cewar bai ganetaba. Amma har a ranta tana shiga ruɗani da al'ajabin yanda ya nuna ɗin. Itako tayi imani da ALLAH ko shekaru fiye da haka sukai bata gansaba duk randa suka haɗu saita ganesa. Kenan itace keta shirmenta shi baimasan tanayiba, koda yake alkairinsa garetane yasa ta kasa mantawa dashi bawai wani abuba. A take ƙwalla suka cika mata idanu, sai dai tai ƙoƙarin hanasu su zubo dan ba wannan matsalar kaɗai bace matsalarta, hadda wadda take tsoron bayyanar tabbatuwarta saboda ɗimuwa.      Duk yunwar da take iƙirarin ji sai gashi ba wani abincin kirki taciba  bakuma ta yarda ta fitoba har saida ta tabbatar a ranta sunbar gidan.     Koda ta koma ɗakin Hajiya iya wanka ta farayi itama tai salla sannan tai zaman karanta suratul kahfi. Bayan ta kammala suka gaisa da Hajiya iya take sanar mata “Af Inno na kinga ina neman shafa'a. Idan kin idar da addu'arnan jeki ki gyara Moddibo ɗakinsa”.       Cikin dauriya da danne damuwoyinta tace, “To Granny”. Daga haka ta miƙe zuwa ɗakin nasa datai zaman watanni kusan uku a ciki. Cikin ƙanƙanin lokaci ta gyara komai ta baza ƙamshi. dan ita bama taga wani datti da ɗakin yayiba. Rufo ɗakin tai ta fito. Hakan yayi dai-dai da fara shigowar samarin gidan falon alamar yanzu suke dawowa daga massallaci. A ƙa'ida kuma duk irin wannan ranar anan suke lunch saɓanin breakfast kawai da sukeyi anan kowacce safiya.        Ƙasa tai da kanta cike da jin kunyar kallon da Moos'ab ke mata tunda suka haɗa ido. Batare da tayi tunanin hardasu Khalipha ɗin suke tareba itama ta zauna a falon saboda harda Jamal daya ja hannunta suka zauna a centre table ɗin falon yana miƙa mata ledar hannunsa da faɗin, “Surprise sweet sisi”..          Murmushi tayi tana ƙoƙarin buɗe ledar. Ganin abinda ke a ciki ya sata waro manyan idanu waje ta ɗago da niyyar yin magana taja birki wajen ganin ta haɗiye abinda ke a bakin nata saboda idanunta da suka sauka akan wanda batai fatan ganiba....       Ledar hannun nata Khalipha ya zare yana faɗin, “Ƙanwata mi muka samu haka?”.       Kasa amsa masa tai saboda wani kallo data kasa fassara inda ya dosa da Yah Adnan ya watso mata. Sai dai zata iya fassarashi da kamanni dana gargaɗi ko takaici.     Tsam ta miƙe batare data iya amsa Khalipha daya fiddo agwaluma ɗaya dake a ledarba yana faɗin, “Lallai kayan daɗin nan dani za'a shashi ƙanwata”.       Tana ƙoƙarin gittashi tace, “Na bakama Yah Khalipha kasha ma duka kawai”.         Saurin bin bayanta yay dan shima yaga kallon da Yayan nasu yay mata, wanda ya tabbatar shine ya hanata zama wajen. “No. Kinga tsaya Beauty guda ɗaya ma ya isheni karɓa kayanki”. Badan tasoba dole ta tsaya ta amsa. Shi kuma yace, “Thanks” cike da wani salo daya sanya Moos'ab dake binsu da kallo cike da kishi yay azamar kauda kansa garesu.       Koda ta samu ta shige bataso sake fitowaba Hajiya Iya ta korota domin zaman yin Lunch. Badan tasoba dole ta biyota, dan ko tace taci ba barinta zataiba sai dai ma tai mata faɗa. Duk sun hallara a dining har Baffa dasu aunty Ni'ima. Baffah ta fara gaidawa da juma'a, sannan ta zauna a kujerar data rage kusa da Khalipha da Meenal. Hajiya Iya kuma ta zauna a mazauninta da kowa ya sani.           Sai da Ni'ima ta fara miƙewa ta zubama Hajiya iya abincin sannan Baffah. Sanin halin Yayansu itama Safiyya ta miƙe ta zuba masa dukkan abinda tasan yana buƙata a wajen. Daga haka kowa ya fara ƙoƙarin zubama kansa abinda yafi buƙata.        Zinneerah dai duk jinta take a matuƙar takure. Kaɗan ta zuba dambun cus-cus a filet ɗin gabanta. Tana ƙoƙarin ɗaukar Mango juice ta zuba Khalipha ya rigata azamar ɗauka jug ɗin ya zuba mata a ƙaramin cup yana murmushi. “Thanks you Yaya” ta faɗa a hankali tana ƙoƙarin kai hannu ta ɗauka aka rigata..        Da azama ta ɗago fararen idanunta tana tsuke baki dan duk zatonta Jamal ne, kasancewar sun saba irin wannan wasan. “Malami kafa raina min....” ta haɗiye sauran maganar tata da sauri har tana sarƙewa saboda a hannun data hango juice ɗin.        Kowa dake wajen sai da ya ɗago ya dubeta tare da kallon abinda taima kallo guda ɗin ta duƙar da kanta. Jamal ya ɗan harareta batare da yace komaiba.        Duk kansu suka maida ƙasa kowa na mamaki a ransa ganin Yayansune da aikin, harma ya kai juice ɗin bakinsa tamkar bashi ya aikataba. Baffah da Hajiya iya kam da basu fahimci ainahin abinda ya faruba har haɗa baki suke wajen faɗin, “Kubata ruwa mana kuna ganin ta sarƙe”.      Saurin miƙa mata ruwan Meenal tayi a baki. Babu musu Zinneerah ta buɗe baki ta hau sha. Hajiya iya tace, “Maganin mai cin abinci yana magana ai kenan”.        Shiru Zinneerah tayi, dan bata da bakin yin bayanin gaskiyar zance. Khalipha dai mamakin abinda Yayan nasu yayi yake a zuciyarsa. Dan shi da kansa yasan baya shan mango juice. Hasalima daga shi sai Baffah suke matuƙar sonsa. Zinneerah ɗinma dan yaga ta nuna tanaso ne ya zuba mata. kauda tunanin yayi a ransa ganin yanda Yayan nasu ya sake cin mur tamkar bai aikata komaiba, sannan kuma yafi kowa sannin halinsa, shiyyasama bai kawo komai a ransa ba.          Kowa nama Zinneerah sannu shi banda shi, abincinsa ma yaketa faman ci hankali kwance tamkar baya jinsu.        Tsakurar abincin kawai Zinneerah keyi a takure matuƙa. Sosai zamnsa a wajen yay masifar cika mata ido. Hakama idanun Yah Moos'ab suma sun takura mata. Ga kuma wani irin yanayi mai kama da shauƙi da takeji game da ganin Khalipha, duk da yanda ya nuna bai ganetaba yana damunta cikin rai. Ganin batacin abincin sai juya cokali yasa Baffah yimata magana.          “Baffah na ƙoshine”. “Ƙoshi kuma ɗiyata? Haba yaushema kika fara cin abincin, bayanma kaɗan dama naga kin zuba. Kodai baki da lafiyane?”.      Kai ta girgiza masa da sauri. “A'a Baffah lafiyata ƙalau, barci nakeji”.         “Barci kuma? A to tashi kije ki kwanta kafin la'asar tayi dan yau lokacin gudu yake ga mai yawan rai...”      Zaram ta miƙe kafinma Baffah ya rufe baki. Ta nufi ɗakin Hajiya iya tanaji kamar ta runtse ido ta ganta a kwance ko zataji sassauci daga abinda takeji na ruɗani akan mutanen nan uku da sukazo mata da mabanbanta tunani.        Washe gari weekend suka tashi kowa yana a gida. Sai sune zasu fita islamiyya zuwa yamma. Tunda Zinneerah ta gama taya su Baba Rahi aikin safe ta gudu ɗaki ta sake kwanciya. Har Hajiya iya na mata ƙorafin anya wannan yawan kwanciyar tata ba shawara bace ke damunta?.       Luf tayi tamkar tai barcin, dan batason Hajiya iya tace yau saita fita dining yin breakfast. Batare da tunanin komaiba hajiya iya tace, “Oh harma kinyi barcin kenan? Dolene nazo na nema miki maganin shawara kuwa”. Daga haka ta cigaba da duba littafin hannunta, Zinneerah kuwa ta ƙara lafewa a bargo.       Tun tana barcin ƙarya harma na gaskiyar yay gaba da ita. Kasancewar weekend basu zauna breakfast ba sai wajen tara. Iya su yaranne kawai babu Baffah.       Shine ƙarshen fitowa sanye cikin wando 3quarter fari da yellow ɗin t-shirt. Gaishesa ƴammatan suka farayi yana ɗaga musu hannu saboda waya dake manne a kunnensa yana magana. Ni'ima ta fara haɗa masa abinci gabansa. Kamar an tsikari Moos'ab ya ɗan wawwaiga yana faɗin. “Wai ina Zinneerah ne?”.        Saurin ɗagowa Khalipha dake zuba kunu a kofi yay yana kallon Moos'ud saboda jin sunan daya ambata. “Dama sunanta kenan?”. Yay tambayar ga Moos'ab ɗin kansa tsaye. Wani ɗan murmushi Moos'ab yay yana sosa gefen wuyansa alamar dai akwai wata a ƙasa. “Sunanta kenan Yah Khalipha, ya haɗu ko?”. Ya ƙare maganar da ɗage gira.      Dariya su Haneef sukayi suna masa daƙƙuwa.          Ɗan jimm Khalipha yayi yana tunani a ransa. sai dai kafin yace wani abu Moos'ab ɗin ya sake faɗin, “Bahijja dubata a ɗakin Granny tazo ta karya”.       “To Yaya”. Bahijja ta faɗa tana miƙewa. Sai dai babu shiri ta koma ta sake zama saboda wani malalacin kallo da Yayansu ya watso mata a kaikaice, ya kuma ɗauke kansa tamkar bashi yayiba.        “A'a yaya kika koma kika zauna kuma? Nace kije ki duba Zinneerah ne fa”. Fuska ta narke tamkar zata fasa kuka tana duban sashen Yayan nasu da yay tamkar baisan abinda akeba a wajen. Dan dama dai duk a hankali suke magana gudun yin laifi a garesa.      Kallonsa shima Moos'ub ɗin yayi, mamaki ya kamashi ganin hankalinsa bama a garesu yake ba. Cikin faɗa yace, “Bazakije bane komi?”.        Da sauri ta girgizama Moos'ab ɗin kanta, da idanu ta nuna masa Yayan nasu tana ɗan noƙe kafaɗa. Baki ya sake buɗewa zaiyi magana suka tsinkayi fitar siririn tsakinsa. yaɗan watsama sashin da Moos'ab ɗin yake  kallo. A yanayin maganarsa na rashin son sakewa yace, “Kun isheni da surutu fa”.         Tsit wajen yay suna satar kallonsa ta ƙasan idanu da mamakin ganin yanda yay maganar tamkar a hasale..........✍ *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 *_★ MADUBIN ZUCIYA_*💖 *_★ DALAAL_*💝 *_★ UBAYD MALEEK_*💓 *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafarma iyayenmu🙏🏻😭_*    *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* ________________________ *_OUMMAHMAD COLLECTIONS_* _(WE’VE GOT YOU&YOUR HOME COVERED)_ _MUNA SAYAR DA KAYAYYAKI MASU KYAU, INGANCI, DA KUMA RAHUSA👏🏻KAYAYYAKIN MU TUNDAGA NAHIYAR KETARE AKE KAWO MANA SU, DAGA RASSA DA DAMA._ _KAMAR SU: Kitchen utensils_ _Fabrics_ _Shoes nd bag_ _Phones_ _Veils_ _Children's wears_ _Furnitures_ _Dubai, china, India, turkey, Malaysia_ _MUNA GARIN: Kano, Unguwar hotoro_ _Facebook handle d’inmu: Maryam muhd_ _Lambar tarhon mu: 07014488636_ _________________ *Page 21* ...........Khalipha kam da zuciyarsa tayi matuƙar nisa a cikin tunani sam baiji mi yayan nasuma ya faɗaba. Yaɗan ɗago ya dubi Moos'ab ɗin kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru yana binsu da kallon mamaki su duka ganin yanda duk suka sake nutsuwa. Sashen da yayansu yake ya maida kallonsa, sai yaga hankalinsama baya kan kowannensu.       Maida kansa kawai yayi ga abincinsa shima, sai dai gaba ɗaya hankalinsa ya tafine ga tunanin sake son ganin yarinyar ɗazu da sukace sunanta Zinneerah.       Har aka kammala breakfast ɗin babu wanda ya ƙara ƙwaƙwaran motsi. Shine ya fara tashi a dining ɗin, suka bishi da kallo harya shige ɗakinsa. Tamkar jira suke yabar wajen suka fara ƙus-ƙus na gulma.         “ALLAH ya baku sa'a ya fito ya jiku”. Khalipha ya faɗa yana miƙewa shima ɗauke da kofin shayi ya nufi ɗakin Hajiya Iya. Zaune take a gaban gadon saman carpet ɗin dake a malale, ta mimmiƙe ƙafafunta dake mata zugi, dan ciwon da suke matannema ya hanata zama cin abinci a dining ɗin yau.        Fuska ɗauke da murmushi take duban Khalipha. Ya zauna a kusa da ita yana ajiye kofin ya amshi man zafin ya fara shafa mata. “Moddibo fa?”. Hajiya iya ta tambaya tana kallon Khalipha.     Ya buɗe baki zai bata amsa sallamarsa ta katsesa. Duk suka kalli ƙofar dai-dai yana ziro ƙafarsa ciki. Kallonsu yay ya kauda kai, sai da ya shigo ciki sosai yakai zaune a bakin gadon dai-dai ƙafafun Zinneerah dake ƙudindine a bargo sannan yace, “Ciwo ƙafan yake ne?”.         “Ba wani da yawa bane ai. Yanzuma zakaga ta saki tunda Khalipha ya daddana min ita”.       Kansa ya maida ga wayarsa dake haske alamar kira ake batare da yace komaiba.      “Fita zakayine Yayanmu?”. Khalipha ya faɗa yana kallonsa.          Kansa ya girgiza masa da faɗin, “No, Phones ɗin yaran nan ne”.        “Woow, autoci an shigo gari kenan”. Khalipha yay maganar yana jawo ƙyaƙyƙyawar ledar gabansa. Kwalayen wayoyi masu ƙyau da tsada guda shidda ya fiddo a ciki. Ya miƙama Hajiya Iya. “Granny ga wayoyin jikokinki Yayanmu ya cika alƙawari”.       Murmushi tayi a karan farko da miƙa hannu ta amsa ɗaya tana kallo. “A to lallai munyi rabin shiri da ja'irin nan yau. ALLAH ya saka da alkairi ya bada ladan zuminci”.      Da amin suka amsa shi da Khalipha. Hajiya iya tace, “To ga kuma Zinneerah ta ƙaru, sai itama kasan yanda zakai da ita, dan ba'a basu wayoyiba ita batada ita”.       Kamar bazai tankaba sai kuma ya ɗan dubi Hajiya Iyan. “Tunda bansan tana a gidanba sai tai haƙuri sai wani karon”.       “A'a bazai yuwuba gaskiya Moddibo. A duba mata dai ko anan ita sai a saya mata”.      Shiru yay bai sake tankawaba duk da sarai yaji mi Hajiya iyan ta faɗa. Sanin halinsa yasa Khalipha saurin faɗin, “A'a Granny a bar Yayanmu ya huta. insha ALLAH ni saina saya mata kawai”.         Hajiya Iya tace, “To shikenan hakanma yayi ALLAH ya saka muku da alkairi. ya ƙara haɗemin kanku”.       Khalipha ne kawai ya amsa da amin. Shiko laɓɓansa kawai yaɗan motsa kaɗan alamar ya amsa ɗin.         Daga Haka Khalipha da Hajiya Iya suka cigaba da hira, shiko yana saurarensune kawai amma baya saka baki sai yaso, yama maida hankalinsa gaba ɗaya akan latsa waya.                Zinneerah da tun shigowar Khalipha ɗakin ta farka taɗan motsa kafarta, jin ta dunguri abu yasata saurin matsarwa baya tana rintse ido. Hakanne ya sakashi ɗan juyawa ya kalli abinda ke bayan nasa duk da tun shigowarsa yaga alamar mutumne kwance. Kamar zaiyi magana sai kuma ya miƙe yana tura wayarsa a aljihun wandon 3quarter ɗinsa. “Ni bara naje zanyi magana da Baffah, zuwa anjima inason zuwa Jigawa”.       “Jigawa kuma? Yin me?”. Duban Hajiya iya mai maganar yayi, yaɗan kai yatsa gefen idonsa ya sosa kaɗan da cewar, “Akwai wani gona ne da nakeson yin noman shinkafa. So mun gama magana da Mahmud shine nakeson dubawa”.        “Tofa, bana kuma nan aka tsallaka kenan? Kai dai duk hanyar neman kuɗi kasanta Moddibo. Kana gudunmu kuma kana son zuwa kaci arziƙin ƙasarmu”.       “Tunda ni ba ƙasata baceba ko. Idan wannan mai barcin ta tashi taje ta gyaramin ɗaki”. Ya faɗa yana ficewa daga ɗakin abinsa.        Harara Hajiya iya ta raka bayansa da shi tana yamutsa fuska. “Bauɗaɗen banza jikan ƴan Morocco”.     A yanda tai maganarne ya tilasta Khalipha ƙyalƙyalewa da dariya shima yana miƙewar. “Granny rigima. show ɗinki da Yayanmu nada matuƙar ƙayatarwa ga mai kallo. ALLAH ya ƙara miki lafiya da tsahon rai mai amfani uwargida kuma amaryar Abdul-Mutallab Shira”.          “Oh to, ko kanamin baƙin cikine ba'a taɓamin kishiyaba?”.     “Wah? Ni?  Rufamin asiri Granny karkisa Baffah yaji ya zagemin uwa. Kinga nayinan raba tsaraba na samo tukuyci. Itama  ya kamata ta tashi ta karya”. Ya nuna Zinneerah da duk tana jinsu amma ta lafe.        “Eh nima yanzu nake tunanin nan a raina. Barama naji jikin nata kodai batajin daɗine, dan bata saba irin wannan barcinba sam”.        “Okay to bara naje na dawo sai naji wane hali take ciki”. Daga haka ya fice a ɗakin.        Ihun murnar waya da su Meenal suka shigo ɗakin sunayi ya tilasta Zinneerah tashi. A take suka kaure ɗakin da sabon ihu. Koda Hajiya iya data shiga bayi ta fito tana musu maganar su fice sun dameta a guje suka fita kuwa suna cigaba da ihunsu. Acan harabar gidan suka iske su Abidah suma suna nasu tsallen murnar dan da gaske yayan nasu ya shigo dasu gari da masu zafi kam.         Duk da babu Zinneerah a cikin masu wayar babu damuwa ko ɗigon sisi tattare da ita, hasalima itace mai farke wayoyin su Bahijja daga cikin kwalinsun. Da ƙyar hajiya iya ta tilastata zama cin abinci. tana gamawa kuma taje tai gyaran ɗakin nasa daya faɗa kamar yanda Hajiya iya ta sanar mata saƙon duk da itama taji da kunnenta.     Koda ta kammala taje tai wanka fitowa tai suka ɗora shirmensu daga inda suka tsaya ita da su Jamal. A haka Khalipha ya shigo ya samesu, daga asibiti yake yin bincike akan Zinneerah da suka haɗu wancan karon, dan gaba ɗaya zuciyarsa ta kasa yarda cewa wannan ɗin itace waccan Zinneerah ɗin. Gadai satar kammani sunayi da juna. Amma kuma wayewar kai da wasu abubuwa da yawa ya banbantasu. Babbar matsalar daya samu na rasa Number Naziru da yayi sakamakon wani tsautsayi daya samesa acan London. Yanzu kuma yaje asibitinma a iya binciken da yayi bai samu wani bakin zaren da zai iya nemansu ba. Amma an tabbatar masa ta haihu baby boy.            Gida ya dawo da sabon tunani akan tunkarar wannan Zinneerah ɗin yaji daga gareta ita kuma, dan a tunaninsa da ace waccan ɗince data ganesa. To waccanma ai matar aurece miyasa zaiyi tunanin itace anan?.       Ruwa Meenal ta kawo masa ya sha. Ya kumace ta haɗa masa abinci a dining zaije yay wanka ya dawo. Binsa Zinneerah tai da kallo a cikin wani irin bahagon yanayi. Cikin dabara takai hannu ta share ƙwallar da suka ciko mata idanu. A yanzu haka babu abinda kecin ranta da damuwarta sai yanda Khalipha ya nuna tamkar baima taɓa sanintaba. Bayan ita tunda ya barta bata taɓa hutawa da tunaninsaba a ranta. har mafarkinsa tasha yi ma. Amma insha ALLAH zata daure itama ta kama kanta gareshi, idan ya ganota fine. idan ya cigaba da pretending ɗin rashin sanin nata itama saita samawa kanta lafiya ai. Da wannan tunani ta cigaba da hidimarta har lokacin Islamiyya yayi suka fita. *_DANYA_*             Tafe take buguzun-buguzin cikin uwar ranar dake ƙwalle ga zafi da take da shi. Ga wanda baisan halin ruɗanin da take ciki a ƴan watannin nan ba sai ya ɗauka ko mahaukaciya ce. Duk ta fige ta fita hayyacinta tun barin Baba garin Danya. Duk dukiyar datake taƙama ta tara ta dabbobi da buhunan kayan masarufi sun ƙare tas wajen bin gidajen malamai dake mata aiki akan yima Baba kiranye ya dawo gida duk inda yake.        Aikin ake kamar ba gobe amma babu alamar yanaci dan har yau ko inda Baba yake babu wanda yazo yace yaji. Gashi kullum malam nata ƙarya suke mata Zinneerah nacan tama zama karuwa a binnin ikko. Sosai wannan labarin ke mata daɗi akan Zinneerah. dan bata da burin daya wuce taga yarinyar ta tagayyara ta wulaƙanta a duniya, saboda kawai tazo matsayin ƴar kishiyarta.      (Ƴan uwana mata dan ALLAH mu canja, mu daina saka yara a kishinmu. sannan kishinma mu dinga sassautama zukatanmu. Nasan kishi dolene domin kamar jininmune. To amma suma mazan idan suka fahimci kana musu kishi na hauka duk da sonsu ne yake jawo hakan saisu maidaka wawa mahaukaci. ka kuma fita a cikin ransu ma baki ɗaya su koma ganin baƙinka maimakon hasken da kake dashi a garesu. Babu amfani kai burin lalacewar ɗan wani ko shigarsa wani bala'in rayuwa. Dan kaima ba tsira naka zaiyiba wlhy. dan ba'a taɓa shuka dawa a girbi shinkafa. Sai ka ƙyautata zato da addu'a ga ɗan wani kaima ALLAH zaiji ƙanka ya ƙyautata rayuwar naka ƴaƴan insha ALLAH. ALLAH yasa mufi ƙarfin zukatanmu😭🙏🏻).        Yanzunma wani ƙauye can nesa dasu sosai akai mata kwatancen wani malami shine taje. A yanzu haka dai ya mata alƙawarin dawowar Baba nanda kwanaki bakwai, idan har bai dawo ɗinba zai biyata kuɗin daya karɓa a wajenta. Hakkane ya sata tahowa gida cike da ƙwarin Gwiwa ko ranar dake dukanta da azabar tafi bataji.         Shiru ta iske gidan babu kowa. ta zube ƙarƙashin bishiyar tsakar gidan nasu tana maida numfashi da ƙyar. Ta kusa mintuna biyar a haka kafin ta miƙe zuwa randunansu dan tasha ruwa. Wayam ta samu tabbacin dai Tinene data barma sallahon ɗebo musu ruwan bata ɗebo ɗinba kenan. A take ranta ya ɓaci taja ƙafafunta da ƙyar ta koma ta zauna dan har juwa takeji saboda yunwa. Ko karyawa bataiba ta fita, ɗan hatsin da baba ya bari a rumbu duk sun cinye ta salwantar da wani kuma wajen bin malamanta na tsiya. Hakan yasa abincima sau uku a gidan wataran gagararsu yakeyi. sai idan Yaya Gajeje taji tausayinsu ta ɗakko ta kawo musu. Koda yake mafi yawancin lokacima itace ke zama da yunwar, dan Tinene sai dai ta ganta da kayan ciye-ciye ta shigo. bata isa tambayarta kuma ina ta samosuba saita hayayyaƙo mata da rashin kunya. Wani lokacinma bata tambayar tata amsa take itama taci saboda wahala. Sa'a kuwa yanzu takan jera kwana huɗu biyar bata kwana a gidanba. Tuni ta koma gidan Baba Rabilu abinta, dan ɗansa ya maidata makaranta tana zuwa. da Inna ta nuna bata yarda bane yasa Sa'a tattara inata-inata ta kona can gidan. Sai randa ta bushi iska take zuwa ta kwana anan tunda yanzu babu talla Malamai sun cinye jarin Inna Asaben.        Miƙewa Inna tai tana tsinar Tinene a cikin ranta, dan yunwa da wahalar tafiya tasa koma magana mai ƙarfi bata iyayi. Ɗakinta ta shige ta faɗa saman gado da fatan ALLAH ya kawo wani a cikinsu Sa'a ɗin ya taimaketa da ko kunu ne taɗan kurɓama cikinta ko taji dama-damar tashi ta bizne aykin malam.        ALLAH kuwa ya taimaketa babu jimawa ta farajin motsi a tsakar gidan da ƙarar taunar chewing gum. ko ba'a faɗaba tasan dai Tinene ce. Dan itace mai ɗabi'ar cin cingam ɗin a koda yaushe. Idan tai mata magana tace mata ƙoshi ya sakata ci danta rage nauyin cikinta. Dole Innar keyin shiru dan Tinene kam ta fara fin ƙarfinta. Gashi kuma wani lokacin tana ɗan samun mai daɗi a wajenta taci.      Bankaɗa labilen da akaine ya sakata ɗago idonta ta kalli ƙofar. Tinene dake tsaye a bakin ƙofa tana cakal-cakal da cingam a baki cikin rashin ladabi tace, “Oh oh, wai se yanzu kike dawowa gida Innarmu? Ke dai baki gajiya da mikama maluma kuɗi suna cinyewa mu baki anhwana mana da ko taro ba a ciki. Naga dai Baban da ƙahwarsa yabar gidan ba saceshi akaiba halan”.      Kasa cemata uffan Inna tai, sai kanta data girgiza kawai. Hakan datai ya bana Tinene haushi, harta saki labulen da niyyar barin wajen Inna ta ƙwala mata kira cikin ƙarfin hali. “Tinene wai nikan yaushene zaki natsune? Ni yanzu duk bama wanga ba. Dan ALLAH idan da goma hannunki ko murtala kije nan gidan dije ki sayo mani kunu koba suga nasha”.     Baki Tinene ta zunɓura gaba. kanar zatai magana sai kuma taja tsaki fuuu ta fice tana ƙunƙuni. “K kuɗinki na wajen bokaye da malamai ni kuma kin sakama nawa ido mu ramtsesu tare. Bayan duk kece kika jehwamu a wagga rayuwa ta yunwa da talauci wajen neman baƙin asirinki mtsoww”.       Da wanan mitar taje ta sayo kunun na goma ta kawo mata dukda ba wani na kirki bane. Da rawar jiki kuwa Inna ta amsa tahau sha duk da zafin da yake da shi. Ta saki gyatsa tana ajiye kofin duk da bata ƙoshi bane yanda take buƙata. Daga haka ta zame ta koma kwance tana zufa. Tinene ta taɓe baki da nufar hanyar ficewa gidan tanama Innar tasu baƙar magana. (Hhhh yanzu aka fara wasan Hajja Asabe😂😂😜). ________________________★★            Washe gari lahadi ma duk suna a gidan, sai dai banga Khalipha da Yah Adnan da suka tafi jigawa. Dan jiya bai samu damar zuwanba saboda wani uziri. Bayan sallar la'asar duk suna zaune a falo suna ɗan hira iyasu ƴammatan sai ga Safiyya da ita kaɗaice bata gidan. Momie ta aiketa can wajen yayarta kai saƙo.         A yanda ta shigo falon kamar wadda aka koro ya sakasu duk suka zuba mata ido. “Ke lafiyarki kuwa?”. Hajiya iya data kasa haƙuri ta faɗa tana duban Safiyyan.           “Humm Granny inafa lafiya, wlhy wani abun al'ajabi da ruɗani nai gamo dashi a yanzun nan hanyata ta dawowa daga gidan Umma”.        Duka falon maida hankalinsu sukai a kanta, kowa nason jin dami tai gamon?. Wayarta ta lalubo a jakka tai ƴan danne-danne sannan ta miƙama Hajiya iya. “Granny dan ALLAH kikalli yaron nan dawa yay miki kama?”.       Cikin rashin damuwa Hajiya Iya ta amshi wayar. Yanda tai kasare tana kallon wayar ya saka su Meenal duk suka zuba mata ido suma. Itama da alamun makamancin irin ruɗanin da Safiyyar ta shigo da shi tace, “Keko Safiyya a ina kikaga wannan yaron haka?”.         “Wlhy Granny a Napep. Mun taho da driver motar ta mutu a hanya. Shinefa nace masa bara na tare napep na ƙaraso gida. Mun daɗe tsaye yanason taremin ba'a samuba sai da ƙyar ya tsaida wanda ke ɗauke da maman yaron nan.      Hajiya iya daketa faman jinjina kanta tace, “Amma wannan kamanni da mamaki a cikinsa. Koda yake hakan kan faru koda baka haɗa komai da mutumba. Amma ita matar a ina take?”.        “Wlhy ban tambayetaba Granny, amma da alama wani waje zatajema. Bama tasan na ɗauki hoton yaronba dan cikin dabara nayi”.       Wani irin nannauyan numfashi hajiya iya ta sauƙe. Sai kuma ta miƙama Abidah wayar ganin duk sun zaƙu su gani. A haka samarin gidan dake shigowa a tare sukazo suka samesu. Ganin yanda aketa ƴar bayayya da waya ya sakasu tambayar ko lafiya?. Safiyya ce tai musu bayani. Amsar wayar suma sukai duk suka gani. Duk wanda ya kalli hoton sai ga mamaki ya bayyana a fuskarsa da ruɗani.         Duk wannan al'amari dake faruwa Zinneerah nacan ɗaki tana shirya kayanta data kwaso a ɗakin Yah Adnan cikin wadrobe ɗin Hajiya iya. Hakan yasa batasan hidimar da akeyiba. Dan so take ta gama shiryasu a daren yau tunda gobe idan ALLAH ya kaimu monday akwai makaranta.         Kasancewar dama bata fara aikin da wuriba sai gashi har Hajiya iya ta shigo domin sallar magrib bata kammalaba. Sai kusan sha ɗaya ta gama lokacin hajiya iya ta jima dayin barci mai cike da mafarkin yaron da Safiyya ta kawo musu a hoto, takan dai tashi tai salla idan lokaci yayi. Su meenal kuma sunɗan lekota, sanin hajiya iya idan ta kwanta batason surutu yasa suka fice suka barta ita kaɗai ta cigaba da aikinta.           A falo kuwa hirarsu suka cigaba dayi bayan tasowar hajiya iya. Dan duk sun barma kansu cewar kamannine kawai da akan samu a rayuwa tsakanin wani da wani koda babu alaƙar jini saboda hikimar UBANGIJI. Basu wani jimaba suka fice duk da Moos'ab yaso ganin Zinneerah kafin ya wuce ɗin. Rashin samuwar hakan ya sakashi haƙura kawai.         Tun daga wannan ranar babu wanda ya sake tada zance akan hoton yaro, sai dai abin na nan maƙale a zuciyar Hajiya Iya ta kasa mantawa. Tanason yin maganar kuma wata zuciya na kwaɓarta akan kamannine kawai. Idan kuma tace zata kawoma zuciyarta wani tunani daban ya zata alaƙanta al'amarin ma to. Hakan yasata tsuke bakinta ta barma ranta komai kawai.      kwanaki sun cigaba da shurawa a hankali sai ga Khalipha da Adnan na cika kwanaki goma da zuwa. Ko kaɗan Zinneerah ta kasa sabawa da kasancewar sa a gidan duk da a kwanakin nan bai cika zamaba kullum suna hanyar Jigawa gonar da zaiyi noman shinkafa. Sukan fitama kafin su su fito, wani lokacin kuma sai sunyi barci suke dawowa. Wannan dalilin yasa takanyi kwanaki uku biyu ma bata sakashi a idontaba har Khalipha ɗin da take marmarin gani a ko yaushe.       A kwanakin nan daya ɗauka gaba ɗaya hidimar gyaran ɗakinsa ta dawo kan Zinneerah. Kullum ita yake cewa taje ta gyara masa ɗaki. Bata damuba dan dama ta rigada ta saba. Idan ta ganshi tsoro na matuƙar kamata, dan kullum abubuwan daya dangancesa suna sake danganta kansu da abinda sam ta kasa gaskatawa.         A randa suka cika kwanaki goma sha uku a gidan basuje gona ba, amma duk da haka babu wanda ya sakashi a ido sai yamma. Yana ɗakinsa yana harkokinsa na business a lap-top.         Zinneerah, Meenal, Bahijja sai Jamal na zaune a falon hajiya iya Yah Khalipha ya shigo. duk sannu sukai masa ya amsa yana zama kujerar dake facing ɗin Zinneerah da Bahijja. Cikin kafe Zinneerah ɗin da idanu ya miƙa mata ledar hannunsa yana murmushi.         “Ƙanwata yau dai ga wayarki na cika alƙawari”. Kafinma ta kai ga yunƙurawa amsar wayar Jamal yay azamar zuwa ya amsa yana washe baki. A take suka rufi akan wayar suna tayata murna duk da ba irin tasu Meenal ɗin bace ba, amma itama ta haɗu. Tasowa Zinneerah tai tsam inda yake takai tsigunne kanta a ƙasa tana faɗin, “Nagode sosai Yah Khalipha, ALLAH ya ƙara buɗi mai albarka”.       Kansa ya jinjina mata yana sake faɗaɗa murmushinsa. Sai kuma ya miƙe ya fice zuciyarsa na bashi ƙwarin gwiwa akan yau ya tunkareta da zancen nan. Dan yauɗin kawai ke garesa Yah Adnan yace nanda kwanaki huɗu idan ALLAH ya kaimu maybe zasu wuce Abuja. Daga can kuma bazasu dawo Kano ba London zasu koma zaiyi wasu uzirinsa kafin ya dawo akan zancen auren su Ni'ima da ayanzu haka an tsaida rana da kuma maganar Company da yake tunanin buɗew na shinkafa.      Binsa da Kallo Zinneerah tayi ƙwalla na cika mata idanu, sai kuma ta miƙe tsaye tana murmushi saboda wani abu data tuna. Idanuntane suka sauka akan Yah Adnan dake tsaye bakin ƙofarsa da waya a kunne yayi wani kicin-kicin da fuska............✍ *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 *_★ MADUBIN ZUCIYA_*💖 *_★ DALAAL_*💝 *_★ UBAYD MALEEK_*💓 *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafarma iyayenmu🙏🏻😭_* *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* __________________________ *_ina 'yan uwa musulmai masu kishin addinin islama???_* *_maza ku matso ga wani aikin lada ya samu_* *_Ɗanku kuma dan uwanku kuma qaninku wato ABDURRAHMAN, yaro mai hazaqa, ƙwazo da tarin baiwa, gami da kwadayin haddace littafin Allah mai tsarki, ya bude YOUTUBE CHANNEL nashi na qashin kansa, ku tallafa masa ta hanyar shiga wannan shudin rubutun ku danna masa subscribe, ba abunda xai rageku dashi saima samun dimbin lada dalilin KARFAFA MASA GWIWA, MUN GODE 🙏🏽🙏🏽🙏🏽_* 👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽 https://youtu.be/WWIGq5Jbtb0 _______________________ *Page 22* .........Cikin sauri ta haɗe murmushinta dayin diri-diri na alamar rikicewa. Dan wani irin kallo da take kasa fassarawa a duk sanda yay matashi ya watso mata yanzuma ya ɗauke kansa fuskarsa na ƙara tsukewa fiye da yanda ya fito. Sum-sum ta juya gasu Bahijja da suma sukai tsitt daga ihun da sukeyi na murnar wayarta zata zauna yace, “Haɗomin black tea yanzun nan”. Daga haka ya juya ya koma ɗakinsa.        Da sauri duk suka kalli Zinneerah da itama kallonsu take. Meenal tace, “Wlhy ki tashi kafin yace kin ɓata masa lokaci”. A take idon Zinneerah ya fara tara ƙwalla. Dan wannan shine karo na farko da ya sakata irin wannan aikin bayan gyaran ɗakinsa.      Bahijja tace, “Kinsan mi zakiyi?” Zinneerah ta girgiza mata kai da sauri. “Kije kima Baba Rahi magana ta haɗa miki, dan tafi kowa sanin abinda yakeso a nan gidan bayan Granny. ALLAH yasa basu tafi ba, tunda ba gani yayba ki fiske abinki ki kai masa kawai a rabu lafiya. Dan shi inhar ya sakaka abu bakayi dai-dai yanda ya buƙataba ka shiga uku”.        Jin abinda Bahijjan ta faɗa ɗinne ya sake tsurar mata da ciki, amma shawarar saka Baba Rahi ta haɗa matan ya sata jin sassauci. Da sauri ta miƙe zuwa kitchen, sai dai wayam babu baba Rahi a ciki. Tai saurin kallon agogon dake a kitchen ɗin wanda ya bata tabbacin Baba Rahi ta wuce gida dan ba'a nan take kwanaba daman.      A take ƙwallan da take maƙalewa suka silalo mata. Jiki a sanyaye ta ɗiba kayan ƙamshi tasa a turmin ƙarfensu ɗan ƙarami ta hau dakawa. Cikin ƙanƙanin lokaci ta gama dafa shayin daketa uban ƙamshi a kicin ɗin, sai dai duk wannan ƙamshin nasa dazai iya saka mai kallo buƙatar sha ita a tsorace take. Ƙaramin flask ta samu ta juye tare da ɗorawa a tire ta saka kofuna biyu da mitsilin bowl data zuba suga a ciki ta ɗakko ta fito tana karanto addu'ar nasara a cikin ranta.        Bata iske kowa a falonba su Jamal sun gudu, hakanne ya sake ɗarsa mata tsoro a cikin rai ta nufi ɗakin tamkar an daddoke mata gwiyawu. Sai da tai sallama kusan sau huɗu sannan ya amsa mata da bata izinin shiga. Ta tura ƙofar ta shigo ƙamshinsa na rige-rigen shiga mata hanci. Tsaye yake a gaban mirror sanye cikin farar jallabiya ruwan madara yana ƙoƙarin ɗaukar wayarsa dake vibration.      Tai saurin kauda kanta ƙasa murya na ɗan rawa tace, “Yayanmu ga tea ɗin”.         Juyowa yay dai-dai yana ɗora wayar tasa a kunne ya kalleta da fararen idanunsa da suka nema ruɗata. Dan itama yayi dai-dai da ɗago nata zata saci kallonsa. Ƙasa tai da kanta shima ya janye nasa yana zama kan sofa. Ƙafa ɗaya ya ɗora kan ɗaya yana kai bayansa ya jingina da kujerar ya sake dubanta ya ɗauke kai. “Zaki cigaba da tsayamin a kaine?”.          A sanyaye Zinneerah ta ƙaraso ta ajiye tiren saman table ɗin gabansa, dai-dai yana faɗin, “Ina ruwanki da ko wacece. Ki cigaba da maganarki kona kashe wayata”. Ya ƙare maganar dajan guntun tsaki.         Zinneerah dai dake saurarensa haka kawai ranta ya bata matarsace. maganar su Meenal data tuna yasata kaiwa tsuggunne ta fara ƙoƙarin zuba masa a kofin. Sai dai jin kamar ana kallonta ya sata ɗan daburcewa, kamar zata ɗago sai kuma ta fasa.      Kamar ya fahimci ta gane kallonta yake sai ya miƙe gaba ɗaya yana bama matarsa dake tambayar ya bata hajiya iya amsar da cewar “Bama tare”.            Tabbas Zinneerah taji kalmar “Bama tare” daya faɗa, sai dai batajin mi matar tasa ke faɗa dagacan, a bazata taji saukar wata gigitacciyar tsawarsa cikin kunnuwanta. Ai batama san sanda ta zube ƙasa daɓar ba tana cusa kanta a ƙafafunta jikinta na rawa. Shiko da baisan tanayiba ya cigaba dayin magana a hasale matuƙa.         “Farah! Ki shiga hankalinki, ke miyasa a kullum tunaninki baya a layin na masu hankali? To kije hakaɗinne ma, ai dai nima namijine ko? Wawuya kawai mtsoww”. Ya ƙare maganar dajan wawan tsaki yana yanke wayar ya jefa saman gado. Wadrobe ya nufa ya finciki murfin da ƙarfi ransa na nasa suya, ya rasa wane irin hukunci zai fara yima Farah akan yawan furta kalmar zargi gareshi a duk lokacin da yay nesa da ita zuwa wani waje. Inhar zaiyi tafiya ta dinga bin ƙwaƙwƙwafinsa kenan tamkar wani ɗanta saboda shegen kishinta na tsiya.           “Zan koya miki hankali” Ya fada zuciyarsa na sake kumbura. Ɓacin ran da yake a ciki ya sakashi mantawa da Zinneerah a ɗakin ya fara ƙoƙarin fara shiryawa.         Shirun da tajine ya sakata ɗago kanta a tunaninta fita yayi. Babu shiri ta miƙe ta fita da gudu ganin ya fiddo kaya alamar sanyawa zaiyi.        Shikam baimasan tanayiba, Sai da ya gama saka kayan ya nufo mirror dan saka turare idonsa ya sauka a kan kayan data ajiye, sai dai babu ita a wajen. Wani sabon takaicine ya sake lulluɓesa tuna abinda Farah ta faɗa akanta. Ya cije baki da rumtse idanunsa da ƙarfi yana raya wannan karon sai tasan shi take dangantawa da Zina wlhy.....        Yana ƙoƙarin zaman shan shayin da Zinneerah ta zuba kira ya shigo masa. Sanin mai wannan ringtone ɗin yasashi miƙewa ya ɗauka wayar yana ƙoƙarin sassauta fushinsa.        “Barka Mammah”. Ya faɗa cikin nuna girmamawa a gareta. A take zuciyarsa ta kara rinewa da ɓacin rai dan dama yasan bai wuce Farah takai ƙararsa wajentaba kamar yanda ta saba. Uffan baiceba har Mammah dake zuba faɗa daga can tayi ta gama. Sai daga ƙarshe da tace Farah ɗin zata biyowa Nigeria itama sannan yay magana.        “Mammah abinda nazoyi nanfa important ne, karki biyema shirmen.......”     “Saurara min Abdul-Mutallab!!” Ta katsesa a tsawace. “Kana nufin bansan abinda ubanka da kakarka suke shiryawa a kanka bane?, to wlhy su sani ƙwatarka a hannuna wannan karon sunyi kaɗan. Idan har bakaso Farah ta biyoka ka dawo London yau yau ɗin nan tunda kasan tanada lalura a jikinta. Inba hakaba bayan itama tazo nima zanzo dan ina dai-dai da kowa cikinku”.        “No, Mammah Please, nafa faɗa miki abinda zanzoyi tukan na taho”.       “Amma baka sanarmin zaka daɗe haka a nanba, dama an manna maka harkar noman ne saboda munafunci ai. Sannan wannan munafikin yaron dake nane da kai ko yaushe idan kun dawo ya wuce hostel da zama, inba hakaba Abdul-Mutallab sainayi bala'i bala'in ɓata ranka, wlhy ubanka ma sai yayi dan.........”        “Mammah Pleaseeee!”. Ya faɗa cikin zafin rai, dan ya mugun tsanar yaji tana zagar masa mahaifinsa da ƴan uwansa.          Ƙitt ta yanke wayar batare data sauraresa ba.        Kansa ya dafe saboda wani jiri-jiri dake neman kwasarsa. Shin wai wace irin rayuwace wannan mahaifiyarsu kesan taga sunyi? Gaba ɗaya ta tsani taga sun raɓi mahaifinsu da ƴan uwansu. Ta yaya kuwa hakan zata kasance bayan hausawa sunce da uba ake ado. Duk ƙoƙarin da yake wajen fuskantar da ita muhimmancin family ɗinsa bata fahimta. nata ƴan uwan kawai takeso su girmama su raɓa. Anya kuwa idan ya cigaba da biye mata bazai halaka ba. Tunda suke da Baffah bai taɓa nuna masa matsanancin ɓacin ransa akan abinda Mammah takeyi na katangesu daga garesaba irin wannan karon. Har a yanzu haka ya kasa tarosa gaba ɗaya. A da kam idan yayi masa faɗan yakan sakko ya koma nasiha. Amma wannan karon yaƙi sakkowa. Ya dage akan sai yabi umarnin hajiya iya ya ƙara aure yabar matar anan Nigeria idan ita waccan tafi ƙarfin dawowa cikin family ɗinsa ta zauna.      Zazzafan huci ya furzar yana zamewa ya kwanta a sofar da dafe kansa kawai ya lumshe idanunsa.        Lokaci mai tsaho ya ɗauka a haka batare da ya saniba. Dan har saida Hajiya Iya ta shigo ɗakin dubashi dan taga har anyi magrib bai gitoba.        “Moddibo kana lafiya kuwa?”. Ta faɗa tana kai hannu ta cire nasa daya dafe kansa. Idanunsa ya buɗe a hankali yana kallonta, ta sake maimaita tambayar tana taɓa goshinsa.      “Lafiya kuwa kake yau har anyi salla baka fito kaje massallaci ba Moddibo?”.        Zaune ya tashi sosai, Sai kuma ya girgiza mata kansa, “Kaina ke ciwo kawai Granny, bamma san anyi sallanba ai”.      Tsura masa idanunta tai cike da nazarinsa. Dan ta riga ta gama karance halayyarsa tun ƙuruciya. Duk da ta hango damuwa tattare da shi sai batace komai a kai ba. ta nufi hanyar fita kawai tana cemasa ya tashi to yay sallar”.       Goshinsa ya murza yana cige laɓensa na ƙasa, har yanzu yana takaicin da mamakin yanda Mammah ke biyema Farah a kowanne lokaci. Duk da yasan akwai nata halin itama ya fahimci akwai zuga mai ƙarfi da akai mata a yau ɗin, a bazata wani guntun murmushi ya suɓuce masa, ya miƙe yana abinsa harya shiga toilet dan shi kaɗan yasan muguntar daya shiryama Farah da mai zuga Mammah ɗin dan ya tabbatar itace taje London ɗin kokuma sunyi waya akan tahowar tata.      Alwala yayo yazo ya gabatar da sallar magrib data wucesa. Daga haka ya fito zuwa massallaci samun jam'in isha'i. Koda aka idar tare da samarin ƙannensa suka shigo gidan abin sha'awa, su sukai sashensu shi kuma yanufo sashen Hajiya iya. Kamar yanda ya fita bai samu kowa a falonba yanzuma haka ya dawo bai samu kowaba.      Ɗakin Hajiya iya ya shiga da sallama. Tana zaune a inda tai salla Zinneerah dake fashin salla na kan kujera kwance tana latsa waya, lokaci-lokaci takan matse idanu da baki saboda mararta dake ɗan mata ciwo can ƙasa. Saurin miƙewa tai zaune saboda jin sallamarsa. Sai dai kafin tace zata tashi harya rigada ya shigo. Akanta ya fara sauke idanunsa ya janye. Batare da damuwar ganinta zaune a Sofa ɗinba yakai zaune yana cema hajiya iya “Barka da dare”.       Zaram Zinneerah ta miƙe a sofar har tana neman faɗuwa. “A hankali mana Zinneerah. Koma saman gado ki kwanta, jira nake wani ya shigo cikin su Mas'ood su nema miki magani”.      Da sauri Zinneerah tace, “Granny yama daina ai, bara naje wajensu Bahijja”     Kafin Hajiya Iya tace wani abu harta nufi hanya da sauri. Tana gab da fita yace, “Zonan”.         Tamkar ta fasa ihu taji. babu yanda ta iya dole ta dawo kanta a ƙasa. Batare da shima ya ɗago daga latsa wayar da yakeba yace, “Ki ɗauka min lap-top a ɗaki da abinda kika kai ɗazun”.          Amsa masa tai da to tana fita cika umarninsa. Harga ALLAH yana burgeta saboda baida hargowa. Banda ɗazun bata taɓa ganin yayi faɗaba ko tsawa ma wani a gidan. Shi dai kawai baida sakewane, idan kaga fuskarsa a sake yana tare da Yah Khalipha ne ko Hajiya Iya. A zatonta yanda yasan ita ba komai bace a gidan face mai cin arziƙinsu zaita karta mata wulaƙancine. Amma sai taga saɓanin hakan.      Da wannan tunanin ta ɗakko duk abinda ya sakata ta dawo ɗakin. Magana ta samu yanayi da Hajiya iya. Amma ko a cikin ɗakin kake da wahala ka jisa.        Wani shayin ta sake zuba masa zata saka suga uku yace, “two is ok”.     Maida ɗaya tay ta saka masa biyun, daga haka ta ɗauki ƙaramin hijjab ɗinta da waya ta fice ta barsu       koda taje sashensu Bahijja da suka tambayeta labarin yanda ta ƙare da kai shayi catai musu ai babu abinda ya faru, dama takai masa shayin yana wanka ajiyewa kawai tayi ta fito abinta. Mararta ke mata ciwo kaɗan-kaɗan shiyyasa taje ɗaki ta kwanta ganin sun fito.        Meenal tace, “Yo tsoro mukaji kar wani abu ya faru yazo ya haɗa damu. dan laifinmu sai yafi naki. cazaiyi mune bamu nuna mikiba yasin”.      Ƙaramar dariya kawai Zinneerah tai ta zame ta kwanta. Daga haka suka cigaba da hirarsu. Daga ƙarshe ranar anan ta kwana abinta. _____________________★     *DANYA*      Ta daɗe kwance tana maida numfashin gajiya dana yunwa daya jigatata. Kafin ta miƙe dan ɗan kunun da tasha ya taimaketa. Ledar data shigo da ita ta jawo, ta buɗe tana fiddo kayan da malam ya haɗa mata da ƙara bitarsu yanda bazata mantaba. Baki ta washe na farin ciki tunawa da baba ya kusa dawowa gareta. Ta ɗaga wata ƴar kwalbar turare tana jujjuyawa.         “Yanda ka bani wahala akan ƴarka Sule, sai na sakaka mantawa da ita na har abada acikin jerin ƴaƴanka. Duk dukiyata data salwanta dan ganin ka dawo saina fansheta a jikinka ko sisi bazanyi asaraba. Ƴan uwanka kuwa dake aibantani a gari cewar ta sanadina kabar Danya zan koyar dasu hankali a sannu, duk sai kunsan kunyi da Asabe wlhy”. Ta ajiye kwalbar tana cigana da dariyarta. Maida komai tai a ledar bayan ta ɗauka wasu layu guda biyu ta fice a ɗakin.         Inda murhun girkinsu yake ta nufo. kasancewar jiyama ba girki sukai a gidanba yasa ta turbuɗa hannunta tsakkiyar tokar hankali kwance ta fara tonawa. Sai da ta ƙwakule tokar duka tasa icce ta fara tona ƙasar sannan ta saka layun nan guda biyu ta maida ƙasar da tokar ta rufesu ruf tamkar komai bai faruba. Duk da basu da isashen hatsin yin tuwon dare a gidan haka ta tattare ɗan wanda Yaya gajeje ta kawo musu daya rage ta wanke ta fita kai niƙa da kanta. Tasan ko jiran Tinene tace zatayi tayi a banza, baizama lallaima ta sake ganinta gidan a yanzuba kuma.        Da ƙyar ta samu Malam Mati yay mata niƙan akan bashi zata kawo masa kuɗin. Rai ɓace ta baro injin saboda yarfin da malam mati ɗin yay mata a gaban yara. Tai ƙwafa kawai da ayyana rashin mutuncin da zatai masa shima.          Sa'a ta iske a gidan tana shara, da alama ganin gidan datai kaca-kaca yasata takaici tana shigowa tahau aikinsa. “Sannu innarmu. Tun ɗazu nazo ai gida babu kowa ga ko ina kaca-kaca kamar ba mutane ke rayuwaba. Shiyyasa na hau aikin nan”.         Baki innar ta taɓe tana ajiye ƙwaryar da tayo niƙan dawa a ciki. “Kin san dai Tinene ba moriya takesoba, ke kuma tunda kin zaɓi dangin ubanki sama dani wazai gyara mani”.         “Kiyi haƙuri dan ALLAH Innarmu”.      Banza tai mata. saima ƙoƙarin fara haɗa wuta a murhun data saka layun nan ta farayi, itama Sa'a sai ta cigaba da sharar tsakar gidan ranta duk babu daɗin. Bayan ta gama sharar ta tattara duka kwanika ta hau wanke-wanke da ruwan data fita ta roƙo a maƙwaftansu dan gidan ko ruwa babu. Itama Inna shita samu ta ɗiba tasa ruwan tuwo. Tsaf ta gama wanke-wanken shima ta ɗauki botiki ta fita dan dama ta gyaro ɗakunan.        Sa'a na fita Inna ta miƙe ta ɗakko sauran kayan da malam ya bata ta ƙarasa yin yadda yace, sannan ta cigaba da hidimar girka tuwonta.        Haka Sa'a taita kai kawon ɗibar ruwa har sai da ta cika ko ina na gidan sannan tai zaman hutawa. Sai a lokacin Tinene ta dawo gidan niƙi-niƙi da ledar kayan ƙwalam da maƙulashe. Yanda tayi tamkar bataga Sa'a bane ya bata haushi tahau zaginta, a take suka harƙume faɗa. Inna najinsu da kallonsu taƙi ta tanka sai da ta gaji da hayaniyarsu ta kora Sa'a wai ta tashi ta koma inda ta fito ita batason fitina.        Da haushi Sa'a taja hijjabinta ta fice a gidan tana sharar hawaye...... __________________________★ *_SHIRA'S FAMILY_*          Washe gari a bazata suka tashi da baƙuncin matar Yah Adnan. Lokacin duk suna dining suna karyawa saboda masu fita makaranta. Sai dai shi bandashi, amma yana zaune a falon shi da Khalipha suna magana akan wasu takardu dake baje a centre table ɗin falon, shi yanata danna lap-top Khalipha na gefensa yana masa magana da takarda ɗaya a hannunsa.      Kasancewarsa a falon yasa babu yawan hayaniyarsu, dan Baffah ma bayanan yayi tafiya tun shekaran jiya. Iyakar sune kawai a falon suna taya Zinneerah murnar wayarta kowa na ƙoƙarin saka mata Number ɗinsa.        Hajiya iya ce ta fito daga kitchen ɗin ita da baba Rahi tana faɗin, “Oh ALLAHU ni Amina. Yanzu dan ALLAH zaman latsa wayoyi zakuyi ko karin kuyi ku tafi makaranta. Sai kuma kun makara ku ishi mutane da mitar an saku makara”.       Alamar roƙon tayi shiru suke mata wai dan kar Yayansu yaji. Basu sanma duk abinda suke tun ɗazun yana jiyosun ba. Ya sharesune kawai saboda aikin dake gabansa mai matuƙar muhimmanci ne. Suna fidda kuɗaɗen da zasuyi ginin company shinkafa ne da waken suya. Shiyyasa tun jiya yake busy. Da niyyar yin noman shinkafar kawai yazo Nigeria, sai dai Dr Mahmud da Khalipha sun canja masa tunani da shawarar mizai hana ya buɗe company kawai tunda dai yanzu Alhmdllh noma ya fara farfaɗowa a arewan. Ya yarda da Dr Mahmud sosai, dan ya jima yana bashi shawara tai masa amfani kuma, Shiyyasa ya amince babu wani ja'inja ya fara shirye-shiye. hakama Khalipha na hannun damarsane, akwai shaƙuwa mai ƙarfi a tsakaninsu kasancewarsa mutum maison ƴan uwansa. Kosu sauran yaran gidan gama fahimtarsane kawai basu yiba, shiyyasa suke nuna tsoronsa da ganin tsaurinsa a garesu, dan da shima Khalipha hakanne a tsakaninsu, sai a ɗan zaman da yake tare da shi yanzu London ya fahimci yayansu mutumne mai sauƙin kai da haƙuri, sakewace dai kawai baida ita ga mutane sai wanda yaso. A yanzu haka suna kan yin cinikin wani fili ne da za'a fara ginin company ɗin.        A fusace Hajiya Iya tace, “Anƙi ai shirun dan ubanku”.      Bakuna suka shiga turawa gaba, dan duk ɗinsu sukanji haushi idan ta zagar musu iyaye. Yanda sukayinne ya sata hararsu ta koma kitchen.       Baki Ni'ima ta buɗe baki zatai magana ƙarar takun takalma masu azabar tsini suka katseta. Su dukansu ƙofar suka zubama idanu banda shi da yayma wajen kallo guda ya maida kansa ga aikinsa duk da baisan wanene ba.        “Hii Guys!!”. Ta faɗa dai-dai tana shigowa cikin falon.       Duk idanu suka waro waje na mamakin ganinta matuƙa, dan badan ma akwai hotunan bikinta da Yayansu a gidanba, babu yanda za'ai su iya ganeta. Cikin ƙarfin hali Khalipha ya miƙe yana murmushi da faɗin, “Woow Aunty Farah Surprise Kece tafe haka?”.          Ɗan yatsine fuska tai tana wani yarfar da hannu gefe da juya idanunta manya masha ALLAH, “Oh ko bakuyi murnar ganinaba na koma?”. Tai maganar tana kafe Khalipha daya nufeta da ido. Amsar handbag ɗinta yayi da cewa, “No. no auntynmu, taya zamu ƙiyin murnar ganinki bayan duk gidanan ƙishirwar ganinki sukeyi daman”.       “Oh nice”.   Ta faɗa cike da yanga tana sauke idanunta kan mai gayya mai aiki da yay mata kallo guda tun shigowarta ya maida kansa. Inda yake ta nufa cikin takunta na izza da tsantsar gayu da yanga mai gauraye da wayewa. “I miss you my hero”. Ta faɗa tana kaiwa duƙe ta sumbaci gefen fuskarsa na dama. Tare da nufar bakinsa da ware duka hannayenta zata rungumesa............✍ *_Wa yaga ƙawar su aunty Shahudah ƴar turawa😜😂😂_* *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 *_★ MADUBIN ZUCIYA_*💖 *_★ DALAAL_*💝 *_★ UBAYD MALEEK_*💓 *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafarma iyayenmu🙏🏻😭_*        *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* *Page 23* ______________________ _*YERWA INCENSE & MORE**_ _(The scents with diff essence for YOU& your HOME)_ _(MASARAUTAR KAMSHI)_ _Ina masu neman kayayyakin kamshi yan nahiyar ketaran chadi da Senegal? Kai harma da ingataccen had’i yan bornu? To ku matso domin nesa tazo kusa..._ _YERWA INCENSE & MORE: Sun zo muku da kayayyakin turaruka kamar haka:_ _Khumra kowacce Iri._ _Turarukan Wuta_ _Mopping khumrah_ _Washing khumrah_ _Bathing khumrah_ _body mist_ _kullaccam_ _scented hair cream/spray_ _wardrobe balls_ _carpet spray_ _air-fresheners_ _scented pebbles_ _body sprays_ _oil perfumes_ _Perfumes_ _kabbasa_ _burners_ _coal igniter_ _tong_ _kasko_ _kujerar tsugunno_ _english coal_ _dilke&halwa set_ _scented body mist_ _kai dama sauran kayayyakin da bamu ambata ba, YERWA INCENSE AND MORE, Na tura kayayyakin su ko’ina a fadin Nigeria da ketare. Domin tuntubar su. Suna instagram: _@yerwaincense_and_more. Ko _Facebook site:YERWA _COLLECTIONs. Ko a duba su ta number su: ___08095215215/09044191709! _ _suna bada kayan su kan sari ko sayi dai-‘dai_ _______________________ *Page 23* ...........Mamakinta ya sakashi ɗago manyan idanunsa ya zubasu cikin nata. Ɗunbin al'ajabin sabon salon nata na bayyaya ƙuru-ƙuru a cikinsu. Dan wannan salon iskancin tabbas ba nata bane aroshi tayi saboda wani dalilinta.          Itama ganin yanda ya zuba mata idanunne yasa gwuyawunta yin sanyi, ta sakar masa Murmushin ƙarfin hali da cije leɓenta na ƙasa tana janye jikinta baya.           Duk da yaji ɓacin ran ganin nata bayan ya gargaɗeta jiya da daddare akan kar tazo amma tay watsi da maganar tasa tazo, ga kuma salon isanci data shigo dashi gidan alhalin hakan ba ɗabi'arta baceba sai ya basar ya sakar mata wani lallausan murmushi daya sata sauke ajiyar zuciya babu shiri.      Su Saifudden kam dake dining jin shiru ya sakasu ɗagowa daga duƙar da kawunansu da sukayi, ganin  abinda sukai tunanin zatayi bashi ya faruba duk sai suka saki numfashi. Musamman da suka hangota zaune a gefensa suna kallon juna da murmushi kamar ba yayansu ba. Itama kuma kamar ba itace ta shigo da salon rawar kai ba yanzun. Ta koma Farah ɗinta da suka sani mai tsanin miskilanci a garesu da jan aji.        Cikin magana ƙasa-ƙasa da babu wanda yake iya jiyosa. Dan saima ka ɗauka wani magana mai daɗin gaske yake faɗa mata, yace, “Wannan salon bai dace da ke ba, kowaye ya baki shawarar shigowa cikin shirawa dashi ya ɗoraki a kan keken ɓera da ta zubewar mutuncikine, da sakaki a layin masu ƙarancin tarbiyya”.            Shiru kawai tai tana kallosa cikin ido, tabbas gaskiya ya faɗa mata, dan ita kanta yanda ƙannensa duk suka zubo mata ido sanda ta shigo sai taji kamar ta muzanta a cikin idanunsu.. Dama da ƙyar ta iya dauriyar hawa kan shawarar auntynta da tace ta shigo musu gidan a salon gatse-gatse zasuji shakkarta fiye da da da take musu isa da shariya kawai. Kamar zatai magana sai kuma ta fasa ta ɗago tana kallon sashen dining ɗin.        Ganin duk yanda sukai ƙasa da kawunansu yasa ta wani yatsine fuska tana taɓe baki, dubanta ta maida ga Yah Adnan daya sake maida hankalinsa ga aikinsa. “Baby ku baku iya tarbar baƙo bane da masauki a gidan naku?”. Tai maganar a Farah ɗinta daya sani mai tsananin son nuna isa da miskilanci.       Cak ya tsaya daga danna keyboard ɗin da yakeyi. Sai dai bai ɗago ya kalletaba. Kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa yay wani guntun murmushi na takaici ya cigaba da abinda yakeyi batare daya tanka mataba.        Ganin zata ƙara magana Khalipha yay saurin tareta da faɗin, “Sorry Aunty. muko muka iya tarar baƙi. Amma muje ki gaisa da Granny first”.       “Oh no Khalipha, zan fara wanka kafin na iya gaisuwa-gaisuwa ɗin nan naku da baya ƙarewa”.            Saurin girgiza mata kai Khalipha yay yana nuna mata Yayansu da ido, dan yasan hakan da zatai ba ƙaramin kuskure bane duk da yasan itama ta sani, tunda tafi kowa sanin halin Yayan nasu ai.......        “Kai lafiya na ganku cirko-cirko?”. Hajiya iya dake fitowa daga ɗakinta ta faɗa batare da hankalinta yakai ga Farah ba. Kafin wani ya samu damar bata amsa Farah ta miƙe tsam cikin komawa ainahin takunta ta nufi hajiya iyan. Idanu Hajiya iya ta zuba mata harta ƙaraso gareta dan ta ganeta sarai duk da zuwanta gidan uku ne kacal, kuma duk kwananta bibbiyu ta koma         “Granny barka da safiya” ta faɗa tana ɗan kai jikinta ga hajiya iyan ta rungumota kamar yanda larabawa keyi. Duk da abun yazo banbarakwai Hajiya Iya bata damuba. Dan tasan akwai banbancin al'adu da yanki a tsakaninsu, kuma ko wancan zuwan da tayiyyi haka ta dinga mata gaisuwa, shiyyasa takemata uziri idan tayi wani abun. Hannu biyu ta karɓeta tana sake faɗaɗa murmushinta. Kafin ta ɗagota tana faɗin, “Uhm lallai yau munada manyan baƙi ashe”.        Murmushi Farah tayi cikin  basarwa, dan tanajin hausa ras yine saita gadama take, tafi yin larabcin ƴan Morocco da turanci.            Sai a yanzu suma yaran gidan suka fara gaidata, duk da mamakin a yanda ta shigo gidan ɗazun ya kasa barinsu. Binsu kawai take da kallo tana amsa musu a yatsine. Kowa ta gane a cikinsu tunda tanada hotunansu na biki, duk da sanda akai auren nasu su Meenal basu da wayo sosai, amma tana jin hirarsu bakin Khalipha koshi uban gayyar idan yaso, musamman idan ƙanwarsa tana tare dashi.        Kafe Zinneerah dake can ƙarshe tai da idanu, kamar zatai magana sai kuma ta basar abinta ta maida kallonta ga Khalipha da Hajiya Iya ke masa magana ya rakata ɗakin Moddibo ta huta.         Da to ya amsama hajiya iyan. Shi dai oga na zaune har yanzu yana aikinsa kamarma ya manta dasu a falon, sai da Hajiya iya ta zauna a kusa dashi sannan ya ɗago ya kalleta. Ganin yanda launin idonsa ya canjane ya sata sakin murmushi ta shafa fuskarsa.        “Babba da haƙuri aka sanshi, tunda ta kawo kanta karka wani saka damuwar hakan a ranka. Mu dama ai burinmu ta dinga shiga cikinmu a koda yaushe. Ba daɗin nisantarmu da kuke mukejiba”.         “Amma Granny sau nawa nake cemata tazo domin gaisheku tace batason zuwa. Sai yanzu dan son fitina. Wai kinmaga a yanda ta shigo gidannan da farko ma kuwa?.......”         “Shiii! ya isa, koma dai a wane dalili tazo ko ta shigo kai ka ɗaukesa ƙyaƙyƙyawa a ranka, ka kuma ɗauki ɗamarar canjata yanda kakeso duk da kayi sakaci tun farko, amma lokaci bai ƙure makaba”.      Huci ya ɗan furzar kawai yana jingina da kujera da lumshe idanunsa.          Sudai su Zinneerah da bajin mi su Hajiya iyan ke faɗaba sauri-sauri duk suka kammala cin abincinsu suka miƙe dan suna neman makara. Ɗakin hajiya iya ta nufa ɗakko school bag ɗinta, lokacin data fito su Yah Moos'ab duk sun fice, harsu Jamal ma. Da alama ita kaɗaice ta rage. Sau ɗaya ta kalli sashen da yake zaune har yanzu yanata faman aiki a lap-top, shi kaɗai ne a falon yanzun. Hajiya iya ta tashi zuwa kitchen saka su Baba Rahi haɗama Farah breakfast tare da Khalipha dake nuna musu yanda zasuyi.     Sum-sum ta wucesa a tunaninta baya ganinta saboda aikin da yake kamar ya kwashe dukan hankalinsa.       “Zonan”. Ta tsinkayi muryarsa cikin kunnenta a bazata. A lokaci guda ƴan cikinta da jinin jikinta suka yamutsa na tsoro, tuna maganar su Jamal da sukace baya maimaita magana idan yay maka yasata nufosa. Zinneerah yarinyace mai tarin nutsuwa, sam bata da garaje akan komai, hakan yasa ko tafiya takeyi saika ɗauka yangace. sai dai sam ba haka bane, halittartace hakan. Komai nata cikin sanyi da nutsuwa bana sakarciba ko rawar kai.        Gabansa takai tsugunne kanta a ƙasa tana faɗin, “Yayanmu gani”.        Batare daya ɗago daga abinda yakeba, a daƙile yace, “Ɗiba tissue ki kwashe wannan jambakin”.         Ɗagowa tai babu shiri ta kallesa tare da waro manyan idanunta masu tsananin haske, cikin suɓucewar baki tace, “Iyeee Yayanmu miye laifinsa? Malaman basa faɗa f.....”        Sai kuma tai saurin ɗora hannunta a baki saboda tuna a ida take.       A karan farko yaɗan ɗago ya dubeta, hararar data saka kayan cikinta sake hautsunawa ya wulla mata tare da maida kansa ga aikinsa. Da sauri takai hannu ta cira tissue ɗin dake a centre table ta kaisa kan bakinta ta kwashe pink lipstick ɗin da yay mata ƙyau sosai tana ƙoƙarin haɗiye ƙwallarta. Cikin ɗan rawar murya tace, “Na kwashe”. Yanzun ma batare daya ɗagoba yay mata nuni da hannu alamar taje.      Tana miƙewa Hajiya iya na fitowa da ga kitchen, tabi Zinneerah ɗin da kallo. “Inno lafiya baku tafi bane?”.       Ɗan juyowa Zinneerah tayi kanta a ƙasa tace, “Eh Granny yanzu zamu tafi”. Daga haka ta fice da sauri kafin hajiya iya ta sake cewa wani abu. Duban inda yake zaune Hajiya iya da zuciyarta ke ayyana mata ba lafiyaba tayi, “Moddibo mike faruwane da Inno, ko wani abu akai mata?”.         “Waye haka?”. Ya faɗa yana ɗan ɗagowa ya dubeta. Harara ta zabga masa tana kaiwa zaune. “Kaifa wulaƙancinka yawane dashi Moddibo, ita Zinneerah ɗince baka saniba ko yau na fara kiranta Inno a gabanka?”.       Ɗan murmushi yayi hankalinsa a aikinsa, a taƙaice yace, “ALLAH ya baki haƙuri”. Daga haka yaja bakinsa ya tsuke batare daya amsa mata maganar farko ba.        Ƙwafa tayi ta miƙe da sauri ta nufito ƙofar fita danta leƙa. tana fitowa maigadi na rufe gate alamar su Zinneerah sun wuce. Dawowa tai ranta daɗan damuwar ALLAH yasa ba wanine yayma Zinneerah ɗin wani abuba mara daɗi. Koda ta dawo falon bata kulashi ba saima harar inda yake da tayi ta shige ɗakinta abinta.        Murmushi yayi a karo na biyu yana girgiza kansa. dan yaga hararar da Hajiya iyan tai masa. Ajiye lap-top ɗin yayi zai miƙe Khalipha ya fito ɗauke da tire. Yaɗan bisa da kallo harya ƙaraso inda yake. “Yayanmu ga abincin Aunty”.      Kauda kansa yayi yana ƙarasa miƙewa. Sai da ya raɓa Khaliphan zai wuce sannan ya bashi amsa da, “Ka ajiye mata anan mana ta fito taci inma zatacin”.        Sanin abinda Yayan nasu ke nufi ya sakashi yin ƙaramar dariya, ganin zai shige yace, “To kaima ai baka karya ba”.        “Karka damu Besty yau ina azumine”. Ya bama Khalipha amsa yana shigewa corridor ɗin ɗakin nasa.          Zaune a bakin gado ya iske Farah ɗaure da towel nashi ajiki alamar wanka tayo. Sallamarsa ta sakata saurin zare wayar dake a kunnenta ta ajiye alamar magana takeyi da wani, kuma bataso yaji. Wayar yaɗan kalla tamkar zaiyi magana sai kuma ya fasa.         Cike da basarwa itama ta miƙe duk da tasan ya fahimci waya take ya basar dan shi mutum ne mai lura. Sai dai bai zama lallai ya nuna makan ya fahimtaba sai yaso.            Ganin yanda ta ciskule fuska cike da isar tata shima sai ya basar da ita ya nufi wadrobe zai dauka abu. Bayansa ta harara da miƙewa sanin idan miskilancine ya fita iyawa. Rungumesa tai ta baya tana jero masa kalaman kewarsa da tayi a kwanakin nan da basa tare. Komai bai ceba sai janyeta a jikinsa da yayi. Tabbas yana son Farah fiye da hasashen mai tunani. Dan duk inda mace takai ƙyaƙyƙyawar Farah takai, a zaman takewarsu tana ƙoƙarin ganin ta ƙyautata masa da faranta masa. matsala ɗaya ce ke cimasa tuwo a ƙwarya game da ita zuwa uku. Na farko shine ƙin danginsa. Sai dai yasan wannan training ɗin su Mammah ne, dan mafi yawan rayuwarta a hannunta tayi. Shiyyasa yakan mata uziri da hakan da ƙoƙarin ganin ya canjata. Sai kuma shegen kishinta da sam ta tsani taga wata mace ta raɓesa koda a wayane, ga ɗan banzan zargi daya tabbatar duk kishinne yake kawo matashi. Na uku son isa da nuna gadara a dole ita isashshiyace ƴar masu mulki.       Zaune yakai saman sofa yana lumshe idanu. Da wannan damar tazo ta zauna a cinyarsa tana ɓata fuska da faɗin, “Wai kana nufin fushi kake dani? Bayan nice ya kamata nai fushi da kai Yah Mutallab”.       Banza yay mata kamar bazai tankaba, sai da yaji ta fara masa murje-murje a jiki cike da salo ya buɗe idanunsa da sauri. “Kinga tasarmin a jiki azumi nakeyi”.       “Azumi kuma? Nami to?”. “Ina ruwanki da ko namiye?”. Ya faɗa yana tureta.        Kallonsa tayi da ƙyau idanunta na kawo ruwan hawaye dan tanada saurin kuka dama. Muryarta na rawa tace, “Dan nazo gidanku zakaimin wulaƙanci?”.          “Anmiki wulaƙancin, ni bance karkiyi abuba amma kikayi saboda kin rainani yanzu kina ganina dai-dai dake ko? Sannan tsabar iskanci wai gidanmu zaki shigo da wani salon sakarci, yanzu da Hajiya iya ko Baffah wani na falon kika shigo ɗin nan mi zasuyi tunanin kin koma kuma?”.        A take jikinta yayi sanyi, hawaye na rige-rige sake zubowa. Kamar baza tayi maganaba sai kuma mita tuna oho mata ta kallesa da sakin ƙaramin murmushi tana share hawayenta. “Kayi haƙuri nayi kuskure, kuma daka tabbatar min hakan sai naji ban ƙyautaba, nima kuma salon bai dace dani ba sam. Amma maganar tahowa ba laifina bane har da su Mammah”.        “Tunda su Mammah ɗin ke aurenki saiki kirasu ki sanar musu kin iso su nema miki wajen zama. dan ba zaki zauna a gidan nan ba. Lokacin da nake lallaɓaki kizo domin gaishesu matsayinsu na iyayena kai tsaye kike cemin bakison zuwa inda suke. To suma yanzu basa buƙatarki”.         Ya ƙare maganar da miƙewa ya fice a ɗakin batare da ko waiwayenta ya sakeyiba.        Bayansa ta raka da kallo idanunta na wani ƙankancewar bacin rai, ta cije baki zuciyarta na mata zugi da sakejin zargin jiya na dawo mata a rai sabo. Tabbas huɗubar aunty data hauce taso jamata wannan wulaƙancin nasa. Duk da dama bata isa tanƙwarashi ko juyasa yanda takeso ba tunda shima bauɗaɗɗen ne, dan ya fita zafin kai da shegen taurin kai tamkar shine jinin mulkin ma ba itamba.         Tayi alƙawarin bazata ƙara kamanta irin kuskuren dataso tafkawa a yau ba nason kwatanta zubar da kimarta. Dan wani raɗaɗi takeji a zuciyarta idan ta tuna a yanda ta shogo gidan a dole ita wayayya. Bandama shirmen aunty data bata shawarar ba ita kuma ta hau ai ko ba'a faɗaba duk wanda ya ganta yasan wayayyace ita, bawai saita nunama duniyaba kodan jinin mulki dake yawo cikin jikinta da tarihinta.            Taja ƙaramin tsaki da ɗauka waya ta kira Mammah, labarta mata duk yanda sukai yanzun tayi. Faɗa sosai Mammah keyi kafin ta yanke wayar domin nemansa.        Itakuma sai ta juya akalar kiran ga auntynta. dan dama da ita suke waya ɗazun daya shigo, itama ta labarta mata komai daya faru da nuna mata gaskiya shawaran data bata na shigowa gidan a yanayin gatse-gatse baiyiba. Dan gashi hakan da tayi yaso taɓa mata kima har a idanunsa, balle ƙannensa da tasan suma kowa ya gumtsi gulma ne dan babu damar yi a gabanta ne ko shi Abdul-Mutallab ɗin dan tasan yanda suke shakkarsa a gidan.        Itama dai auntyn tata kamar Mammah faɗan ta kamayi kamar Adnan ɗin ne a gabanta. Ta kumace ita ai batace tayi gatse-gatse a gabansu kamar wata sashasha ba ko mara tarbiyya, tadaice ta nuna musu banbancin da da yanzun kawai, daga haka ta yanke wayar itama ta koma neman Yah Adnan ɗin.       Su dukansu daga can nemansa a waya suka shigayi, sai dai babu wanda ya iya samunsa dan cama ake musu switch off. Mammah tai ƙwafa dan tasan kashe wayar yayi tunda yasan tsiyar daya shuka.          A falo kam a yanda ya fito ɗakin a fusace ya fice abinsa yasa Khalipha dake zaune yana karyawa fahimtar babu lafiya. Duk da dama dai ba wannan ne karon farkon daya fara ganin rikicin yayan nasu da matarsa ba. Duk da shi yayan nasu kan kauce faruwar hakan a gaban idonsa, amma da yake Farah mace ce mai nacin masifa da mita saita kaisa ƙarshe ya yaɓa mata maganar da zata koma rusar kuka. Dama kuma da yawan faɗan nasu ana yinsane akan zamansa gidansu nacan london ɗin, dan kullum zancenta baya wuce sai ya barmata gidanta ya koma hostel da zama.       Hajiya iya na ɗaki tana gabatar da walha dan haka batasan wainar da ake toyawaba. Sai da ta idar ta fito ne ta iske shi da Khalipha ɗin duk basu a falon. Baba Rahi ma ta sake gyara falon tsaf sai tashin ƙamshi yake. A tunaninta yana ɗaki tare da matarsa yasa bata damuba ta koma ɗakin danta ɗan kwanta itama ta huta.    ________________________ *_DANYA_*             Yau a lissafi kwanaki bakwai kenan da bizne aikin Malam da Inna tayi, hakan yasa tun a daren jiya take zuba ido akan dawowar baba. Sai dai har garin ALLAH ya waye babu shi babu labarinsa. Bata damuba dan tasan akwai yau.     Aiko yau ɗinma dai tunda gari ya waye idanunta basu huta da kallon ƙofa ba. Da taji an motsa ƙyauren gidan sai ta hau washe baki, sai kuma taga bashi ya shigoba saita haɗe fuska dajan tsaki. Kamar wasa tana zaune a bishiyar tsakar gidan har aka kira azhar. Maimakon ta tashi tai sallar sai ta cigaba da zama wai idan ya shigo ta haɗa duka tayo ai.      Duk wannan zaman zuba ido da Inna keyi na dawowar Baba Tinene na a gidan tana wanki, ta ƙure waƙa a wayarta da inna bata taɓa tambayarta daga ina ta samotaba. Koda ta tambayi Innar zaman mi take ta sanar mata sai kawai ta hau dariyar shaƙiyanci tana faɗin, “Oh kice tsohon tsimin soyayya ne ya motsa Innarmu”.      Banza Inna tai mata tunda tasan ba kunyace da Tinenen ba, yanzu saita yaɓa mata wata maganar. Haka ta cigaba da zama a wajen har akai sallar la'asar. Tinene data gama wankinta har tayi wanka tana kwashe kayan da alama fita zatayi a gidan. Buga ƙyauren gidan da akai da masifar ƙarfi ya sakasu dubar hanyar zauren a firgice su duka.        A bazata Karima ta shigo gidan jaye da akwati buju-buju da ita tamkar wadda aka ƙwato daga bakin kura. Babu shiri Tinene ta watsar da kayan hannunta ƙasa. Innama ta zabura kan Karimar dake tafiya kamar ma da tangaɗi.       “Mi nake gani haka ni Asabe. Karima daga ina kike tahe da maraicen nan?”.      Ina babu bakin amsawa daga Karima, sai ma zubewa datai a ƙasa cikin hakki tace, “Innarmu ku bani abinci yunwa nakeji”.        Tinene dake tsaye tana kallonsu har yanzun tace, “Tab abu mai wahala anan gidan yanzu Yaya Karima, amma bara naga inada wazobia ko awarar gidan Rashida a samo miki idan bata ƙareba dan maraice yayi”.      “Nagode auta. Inna bani ruwa”. Ta sake faɗa tana kaiwa kwance da zare hijjabin jikinta gaba ɗaya ta jefar. Ruwan Inna ta ɗebo mata da sauri ta kawo mata, ta ɗagota daga kwancen da take danta bata sai a lokacin idanunta suka sauka akan sayin duka dake a wuyan Karima da damtsen hannunta ruɗu-ruɗu ga tsohon ciki. Duk da kasancewarta baƙa hakan bai hana fitar sayinba da ƙyau.       “Na shiga uku ni Asabe waya maki wanga bugun haka ga ciki Karima? Badai sheɗanin yaron nanbane Babawo?”.       Karima ta sake zamewa ta kwanta cikin tirɓayar jar ƙasar batare data bama Inna amsaba. Ganin Innar zata takura mata tace, “Inna ki barni dan ALLAH, ku bani abinci nide karna matu”.       Kafin Inna ta samu bakin sake cewa wani abu Tinene ta shigo gidan ɗauke da farar leda da awara a ciki. Kwano ta dauka a wanke-wanke ta juye mata takai gabanta. Cikin rawar jiki Karima ta tashi zaune taja kwanon. Bibbiyu ta dinga haɗa awaran tana turawa a baki. Ganin tana neman shaƙewa Inna tai azamar bata ruwa ta sha. Koda ta cinye saita kuma zubewa tana sauke numfashi wani irin zufa na karyo mata ta ko ina duk da kuwa awaran bamai zafi baceba.      Sudai suna tsaye shiru cirko-cirko kowanne da kalar tunaninsa akan wannan al'amari..........✍                      *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_* *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* *Page 24* _________________________ _RANO NET! RANO NET! RANO NET!_ _WHO NO LIKE BETA AWUUF THINGS?_ _IDAN KAJI GANGAMI DA LABARI....! INA MASU ZUBIN ADASHEN DA BA RANAR DAUKA NA DATA?_ _TO KU MARMATSO KUJI, KU KUMA SHARE HAWAYEN KU, MUNZO MUKU DA SABBIN TSARE TSARE NA DATA, WADDA KOWA ZAI IYA SAYA DAI DAI KARFIN SA. A FARASHI MAI RAHUSA_ _RANO NET! RANO NET! RANO NET!__ _(Afford data at chikini price)_ _MALLAKI DATA A KUDI KALILAN DA RANO NET_ _TSAYA KUJI, A RANO NET ZAKA IYA ZAMA RESELLER KO WHOLESALER KAI MA, EH ZAKA/KI IYA ZAMA MA SAYAR DA DATA A FARASHIN SARI MUKE BAYARWA, KAI/KI KAFA KASUWANCIN KU KUMA. DA KUDI KALILAN._ _MUNA KUMA SAYARWA AKAN ‘DAI DAYA, KOWANE NETWORK MUNA SAYARDA DATA PLAN DINSA AKAN KUDI KALILAN, MASU FARASHIN SARA KUWA MA KU KUDIN BAI KAI HAKA BAMA_ _AIRTEL_ _9MOBILE/ETISALAT_ _MTN_ _GLO_ _DUK MUNA SAYARDA TSARIN DATA DINSU. KAMAR MISALI MTN MUNA SAYARDA 1GB.24MB AKAN FARASHIN NERA 300 KUMA YANA KAIWA WATA DAYA, GWARGWADON YADDA KAKE AMFANI DA DATA, 2GB 600, 3GB 900!!_ _DUKA WADANNAN TSARIN DATA DAMA NA SAURAN LAYIKA MUNA SAYRWA AKAN FARASHI MAI RAHUSA, WANDA KOWA ZAI IYA YIN TSARIN DAI DAI ALJIHUN SA_ _Ranonet.com.ng_ _GA SITE DINMU NAN DAKE YANAR GIZO, KAI TSAYE ZAKI/KA IYA SIYAN NAKA TA NAN. _ _KO A TUNTUBE MU TA NAMBAR TARHON MU: +234 803 081 1300/+234 808 540 5215_ _KYAU, INGANCI, RAHUSA, ADADE ANA YAWO A YANAR GIZO SAI RANO NET._ _RANO NET..!!!!_ ________________________ *Page 24* ...........Koda Farah ta gama surutan haushinta gado ta faɗa daga ita sai towel ɗin da tai wanka tai kwanciyarta batare data tuna ya kamata taje ta gaida matan gidanba. Barcinta tasha sosai kafin ta miƙe saboda shigar kiran salla a kunnenta dan bata da sakaci da ibada. Ruwa ta ƙara watsowa tayo alwalar salla.       Koda ta fito ta gabatar da sallar kwalliya tayi dai-dai misali ta shirya cikin baƙar doguwar rigar jallabiya mai ƙyau, ɗan kwalin rigar ta naɗa a kanta yanda larabawa keyi dai.        Farah ƙyaƙyƙyawa ce kamar yanda mijinta ya faɗa. Tanada jiki mai ƙyau ga kuma ilimi, matsalarta kawai itaɗin ƴar gatace ta gani kasheni, ƴar shagwaɓace bugun farko kuma jinin mulki. Dan itace auta a gidansu shiyyasa kowa sonta yake. Sannan ta girmane a Morocco hanun kakarsu dan a wajen haihuwarta mahaifiyarta ta rasu, daga bayane bayan rasuwar kakar tasu itama riƙonta ya dawo hannun Mammah duk da babbar yayarsu taso ita ta zauna a hannunta. Tana da son girman tsiya da miskilanci, dan koshi kansa oga kwata-kwatan yimasa isarta da taƙama takeyi. Sai dai shima da yake gwanine wajen iyawa duk da baɗan masu mulkin bane sai sukeyin dai-dai da juna harma ya kaita ƙasa ta risina tana mitar ya cika baƙin hali.         Tana son Yah Abdull-Mutallab kamar yanda kowama yasan shima yana sonta. Sai dai tanada matsalar tsananin kishi, wanda da alama ta gadane wajen su Mammah. Dan ita kanta Mammah ɗin ta rabu da Baffah ne saboda kalmar ƙara auren nan daya furta gareta duk da ɗunbin son da take masa har yanzu. Dan ko aure taƙi sakeyi.       Bayan ta shirya ta feshe jikinta da turarenta masu shegen ƙamshi da ɗaukar hankalin mai shaƙa ta fito. A falo ta sami Khalipha daya shigo zaune yana lunch. Ta ƙarasa inda yake taja kujerar dining ɗin ta zauna itama. Duk da ya girmeta shine ya fara gaidata dan yasanta da son girman tsiya. Babuko kunya ta amsa masa kuwa tana buɗe kulolin dake dining ɗin.        Yanda take yatsina fuskarta ne ya tabbatarma Khalipha komai bai mataba a wajen. Dan haka yay ɗan murmushi da fadin, “Ki faɗa abinda kike son ci sai a sayo miki idan duk nanan basu mikiba”.      Kanta tsaye kuwa ta shiga zayyano masa duk abinda takeson ci ɗin. Batare da damuwar komaiba kuwa ya miƙe ya fita dan dama ya kammala nasa cin abincin.      Khalipha na fita babu jimawa su Zinneerah suka shigo gidan. Ita kaɗai ta shigo sashen na Granny cike da ƙarfin hali dan mararta ciwo take mata. Batare data lura da Farah dake zaune a dining tana latsa wayaba ta nufi ɗakin Hajiya iya.     Farah da tun shigowar Zinneerah ita idanunta suka sauka gareta ta wani bita da kallo a yatsine tanajin rashin son yarinyar a ranta haka kawai. Sai dai kuma mamaki take ita wacece a gidan ma? Dan bata santaba a tarihi da labari. (To anya kuwa ƴar gidan nan ce?) ta ayyana a ranta gabanta na faɗuwa. Yunƙurawa tai ta miƙe zata bita ɗakin Hajiya iyan dan yanda Zinneerah ta wuce bata gaidataba sai abin yay mata zafi taga kamar rainine dan ta lura da yarinyar itama akwaita da nuna isa tun kallon datai mata ɗazun, sai kuma mita tuna oho mata ta koma ta zauna tana yin ƙwafa.        Zinneerah kam da batasan tanayiba tana shiga suka gaisa da Hajiya Iya wanka ta shiga. Bayan fitowarta ta shirya cikin doguwar rigar boyal less da yay mata ƙyau ɗas a jiki, dan ɗinkin ya zauna da ƙyau masha ALLAH. Tayin abinci hajiya iya tai mata. Amma sai tace ta ƙoshi sai anjima. Basu jima da cin abinciba a makaranta. Daga haka ta kwanta a sofa sai barci.        Barci tayi sosai, dan bata farkaba sai bayan sallar la'asar da Hajiya Iya ta tadata. Toilet ta shiga ta ɗan gyara jikinta ta fita zuwa falo cin abinci. Yanzu kam mafi yawan yaran gidan sun dawo. duk suna ma a falo zaune suna hira har Granny. Sai matar yayansu baƙuwar ɗazun dake zaune gefe ta haɗe fuska tamau kamar tanajin warinsu.     Cikin ƙarfin hali tai mata barka da yamma. Batare da sauraren amsartaba ta gitta zata wuce saita dakatar da ita. Juyowa Zinneerah tai gareta fuskarta ɗauke daɗan murmushi. A ɗage sosai Farah dake ƙarema Zinneerah kallon sama da ƙasa tace, “Kema anan gidan kike?”.       Kai Zinneerah ta ɗan jinjina mata kawai batare datace kimaiba.     “Uhyim! Amma ban sankiba ni”. Kallonta Zinneerah tai cikin ido kamar zatai magana sai kuma tai shiru fara'ar fuskarta na raguwa. Dan tsaf ta fahimci dizgata matar Yayan nasu da taji suna kira da Aunty Farah ke neman yi. Itama Farah ɗin da har yanzu ke mata kallon wulaƙanci da isa duk da kuwa babu wani abin kushewa tattare da Zinneerah ɗin, dan duk da take ƙyaƙyƙyawa babbar yarinya babu abinda zata nunama Zinneerah, itama idan dirin jikinne ALLAH ya bata, musamman ma yanzu da take a kan ganiyarta na kammaluwar sirrikan budurci, sannan jikinta a mulmule yake dan ba siririya bace bakamar Farah ɗin. Ga fatarta kalar ɗaukar hankali gamai kallo. ta buɗe baki zatai magana Hajiya iya ta katseta dan dama ta saka musu idone taga mi Farah ɗin zatayi.        “Tunda ba zuwa cikinmu kikeba ta yaya zakisan kowa. Ke Zinneerah wuce kici abinci”.      Sum-sum Zinneerah ta wuce dining tana ƙoƙarin maida duk wani ɓacin ran Aunty Farah ɗin daya fara yunƙuro mata. Dan a rayuwa ta tsani wulaƙanci da raini da disgi a rayuwarta. Zata iya jure komai banda waɗannan abubuwan.      Sosai su Jamal sukaji daɗin abinda Hajiya tayi, itako Farah a fusace ta miƙe tabar falon zuwa ɗakin mijinta. Yi hajiya iya tai kamarma bata ganiba. Ta kuma haɗe fuska dan karma wani a cikin yaran yace wani abu. Daga hakama hirar ta watse. Dan barin falon itama Hajiya iya tayi.          Kusan 6 Zinneerah da tuni suka fice suna can harabar gidan anata hira ta shigo sashen hajiya iya saboda matsa mata da mararta tayi. Bedroom ta nufa inda ta iske hajiya iya na waya. Sai da ta kammala ta dubeta tana ajiye wayar data gama ɗin.  “Fitinar Moddibo dabance wlhy. Inno dubamin ko su Rahi sun wuce?”.        “Lah Granny ai sun tafi, bakuyi sallama bane?”.      “Munyi sallama. Na zata basukai ga tafiyar banebam wannan fitinatunne yay kirana yanzu, wai ashe azumi yakeyi amma bai faɗaba tun ɗazu ba sai yanzu. Kuma wai abinci yakeson a haɗa masa. Gashi su Rahi ba tuwo sukaiba yau”.       Cikin ƙarfin hali Zinneerah tace, “Granny yaya za'ai yanzu to?”.          “Nima ban saniba to Zinneerah, sai dai ko ke zaki shiga kitchen ɗin ki haɗa masa tunda waccan malalaciyar matar tasa na tabbata ƙila ko shayi bata iya dafawaba balle wani tuwo”.      Idanu Zinneerah taɗan waro waje da faɗin, “Kai Granny nikuma? Ta ina zai iya cin jagwalgwalona”.       “Ci kuwa zaiyi harda santi Inno na. Kinga tashima kije kar ya dawo ya samu ba'ayiba ya fara baƙar zuciya danshi baya wasa da cikinsa. Tuwon zaki masa da ɗan wani abun mai sauƙi tunda azumi yakeyi”.        Zata ƙara magana Hajiya Iya ta girgiza mata kanta. “Kinga babu abinda zai faru, lafiya lau zakiyi insha ALLAH kinji ƴar albarka. nina ai dana idar da sallar magrib zanzo nama tayaki muyi tare”.     Jin abinda Hajiya Iyan ta faɗa ya sata miƙewa tana fadin to ta fice zuwa kitchen da kwarin gwiwarta. Sai da ta fara karanto addu'ar nasara kafin ta ɗauraye tukunya tasa ruwan tuwo dai-dai misali, dan itama dai tana ganin tuwon zataɗanci ko zataji sassaucin ciwon marar nan da taketa dannewa dan karta tadama hajiya Iya hankali.       Cikin ƙanƙanin lokaci ta kammala tuwon semo.. data bama nutsuwa sosai gudun yimasa kuskure, sai da ta kammala kwashewa zuciyarta keta ƙara ƙarfafata akan miyar da taketa tunanin masa tunda ta fara tuwon. Ɗanyen kifi ta cira ta gyara tasashi a wuta da kayan ƙamshi da albasa dan rage masa ƙarni. Kafin ta koma ta ɗiba kayan miya zallar attarigu da tattasai sai albasa da tumatur guda biyu kacal ta wankesu suma tasa a blender da ɗan ruwa bamai yawaba can tai musu markaɗe ɗaya da yay kamar jajjage amma yaɗara jajjagen laushi kaɗan. Kifin ta sauke ta tsamesa a ruwan ta buɗesa ta cire ƙayarsa duka ta farfasashi, ta ƙara ɗora tukunya tasa manja a wuta ta zuba wannan fasashshen kifin da albasa da magi ƙwara ɗaya ta rage wutar can ƙasa. Sallamar hajiya iyace ta sakata juyawa tana kallonta. Ta ƙaraso cikin kitchen ɗin tana magana cike da tsokana. “Wai wai, anya kuwa yau kunnen moddibo bazai kai ƙasaba Inno. Irin wannan ƙamshi haka da aka cika mana gida”.      Dariya Zinneerah tai tana faɗin. “Kai Granny bammafa fara miyanba”.        “Amma kuma ga ƙamshi ya cika ko ina”  Hajiya iya ta faɗa tana buɗe tukunyar data saka kifin nan dake fidda ƙamshi mai daɗi a cikin manja. “Masha ALLAH miyar mi zakiyi?”.        “Granny ɗanyen kalkashin nan dana gani da zanyi”.        “Eh lallai kinyi tunani mai ƙyau, dama ɗazun Rahi tazo dashi wai ko zamuyi amfani dashi a gidanta suke ɗan shukashi”.      “Aiko gashi yayi ƙyan fita Granny. shiyyasama ya birgeni. Kuma ta taimaka ta tsinkesa tun daga can yankawa kawai zanyi yanzu nasa a wuta”.       “To bara na tayaki yankawa saiki haɗa miyar”.     Babu musu ta bama Hajiya iyan, tunda dama tanason ɗan haɗa masa ko fruit salad ne haka da ɗan coconut juice idan zata iya. Ganin kifin ya mata yanda takeso ta zuba kayan miyarta a ciki da daddawa ta ƙara rufewa. Inda suke ajiye kayan fruit taje ta ɗauka komai dai-dai misali ta ajiye gefe, ta ɗauka kwakwa ta fasata itama ta ajiye gefe. Komawa tai ga miyarta taga kayan miyan yaɗan soyu, saita zuba ruwa ɗan kaɗan da kayan ƙamshi da magi amma ba star ba dan yana hana miya yauƙi. Da duk abinda take buƙata na saka miya ƙamshi ta saka ta maida ta rufe a binta da sake maida wutar can ƙasa. Dai-dai Granny ta gama yanka mata ɗanyen kalkashin. Amsa tai tana mata sannu da godiya. Granny ta bita da kallo tana murmushi. Madaidaiciyar tukunya ta samu ta saka kalkashin nan dan babu zancen wankesa shi. Tasa ruwa kaɗan da kanwa ta barsa a buɗe wutar naci daidai misali.     Fita Granny tai dan an kira sallar isha'i, ita kuma tahau gyaran fruit salad ɗinta dan ɗan kaɗan zatayi ba yanda aikin zai mata yawaba. Saiko gashi ta gama a ƙanƙanin lokaci, tasa flavor na gwaba dana strawberry ta motsa. Kaɗan ta ɗan-ɗana, jin zaƙin ya mata dai-dai ta ɗaukesa tasa a fridge ta dawo wajen miyarta da dudduba. Komai yayi, kalkashinma ya dahu, kashe gas ɗin tayi ta koma wajen gyara kwakwar da zatayi juice itama, tabar kalkashinta dayay kauri sosai yana hucewa. Hakama miyar kayan miyanta tayi kauri yanda ko an haɗata da kalkashin bazata tsinkashiba. Sai da ta kammala haɗa coconut juice ɗinta ta saka a fridge shima sannan ta tattara kayan data ɓata ta wanke tsaf sannan tazo ta juye kalkashin cikin soyayyun kayan miyarnan ta motsa da kyau suka haɗe. Ɗanɗanawa tai taji komai dai-dai yanda take fata duk da dai akwai fargaba tare da ita har yanzun.       “Inno an gama ko?”. Hajiya iya data sake dawowa ta faɗa tana shigiwa. “Eh Granny duk an kammala, amma dan ALLAH ki ɗanɗana wlhy inajin tsoro”.       “Haba ɗiyar albarka nasanma komai yayi daɗi. ALLAH ya saka miki da kairan ya baki miji nagari dazai riƙemin ke gam, bar wani jin tsoro”. Kanta kawai ta duƙar tana ɗan murmushi. Sai dai a ƙasan ranta tana tunanin ita data haihu a waje ina ita ina yin aure. tafi ganema ta dage taita karatunta har itama ALLAH ya kaita lokacin da zata taimaki kanta da iyayenta......        “Inno kinga ga naman kai nan da Rahi tai farfesu kafin ta tafi a haɗa masa dashi, sai akai masa gashi can ya dawo har yay wanka yana jira”. Hajiya iya ta katse mata tunaninta. Amsa mata tai da to tana haɗiye ƙwallar dake neman ciko mata idanu.       Kular tuwon ta ɗauka tasa kan tire, ta zuba miyar a wani bowl mai murfi na tangaran mai haske, hakama farfesun tasa a ƙaraminsa duk ta ɗora a tiren. Fruit salad ɗin da lemon kwakwar ta fiddo a fridge duk da basuyi sanyi mai tsananiba sunyi dai-dai gamai sha. Fruit ɗin ta saka a bowl fruit salad, juice ɗin kuma tasa a jug da ruwa a wani tiren. Ta kuma gyara ɗan kwalinta cike da ƙarfin halin danne ciwon dake cinta ta ɗauka ta fito ranta fal fargaba.      Zaune ta samesu shi da matarsa a dining ɗin. Tai sallama ya amsa batare daya ɗago daga latsa tab da yakeba. Farah kuwa bata amsaba saima harara data galla mata na tsananin kishin babu gaira babu dalili da haushin abinda hajiya iya tai mata akanta ɗazun. Ita dai Zinneerah gaishesu tai da masa barka da shan ruwa ta ajiye tiren ta koma ɗakko sauran kayan ba tare data damu da ƙin amsawar tataba.       Harta gama shirya komai a dining ɗin bai ɗago ya kalletaba. Ta juya zata bar wajen ganin ta gama aikinta taji yace, “Zoki zuba”.         Dawowa tai da baya cike da ƙarfin hali dan mararta ƙullewa takeyi. Sama-sama take jin tsawar Farah na faɗin, “Kinga dalla kama gabanki zan zuba masa ni tunda inada hannu”. Juyawa Zinneerah tai zata wuce dan taimakontama ita Farah ɗin tayi, amma saita tsinkayi muryarsa a karo na biyu. “Malama ki zubamin abinci nace ko”.      Jitai kamar ta fasa ihu dan takaicinsu, ta kalli yanda Farah ɗin ke watsa mata harara kamar idanunta zasu faɗo. Shima ta dubesa har yanzu kansa a ƙasa yanata danna tab. Dawowa tayi da baya tunda tasan dai itama matar tasa ai ƙarkashinsa take duk da wannan isar tata da rainin wayo. Batare data sake kallon sashen Farah ɗinba ta fara zuba masa komai tana ajewa gabansa.        Tana cikin zuba masa lemon kwakwar mararta tai matuƙar ƙullewa. Dole ta ajiye jug ɗin tai saurin zama a kujera tana kifa kanta a teble ɗin dan azaba.        Karan farko ya ɗago kai ya dubeta. Farah kuma da kishi keci ta daka mata tsawa, “Kujimin ƴar barikin yarinya. bakin gama aikin da aka sakiba miye kuma na zama?”.      Bata samu amsa daga Zinneerah ba dan bama jinta da ƙyau takeyiba. Shiko tab ɗin ya ajiye da maida hankalinsa gareta cike da nazari, ganin kusan sakan talatin bata ɗagoba yaɗan lumshe idanu ya buɗe akanta. A karon farko na rayuwarsa ya ambaci sunanta cikin muryarsa mai taushi da tarin nutsuwa da rashin sakewa. “Zinneerah are you ok?”.        Har cikin rai da jini sai da Zinneerah taji fitar sautin sunanta akan harshensa. Ta ɗan ɗago hawaye shaɓe-shaɓe a fuskarsa ta. “Ba komai Yayanmu kaina ke ciwo”. Ta faɗa tana miƙewa tabar wajen.      Da kallo ya bita kawai, Farah kuma ta rakata da harara tanajan tsaki da faɗin, “Lallai yarinyarnan idan kikace zakishiga gonata zanko juya fuskarki daga gaba ta koma baya a gidan nan wlhy”.          Goshinsa ya murza kaɗan, dai-dai yana maida kansa ga abincin. Ya ɗan furzar da huci yana ɗaukar juice ɗin data zuba masa kaɗan a ƙaramin kofi ya kai baki. Duk jarabar da Farah keyi akan Zinneerah ɗin bai ma nuna yasan tanayiba balle ya tanka mata. Sai dai a ransa haka kawai yakejin dariya nazo masa.           Zinneerah kam tunda takai ɗaki kwanciya tai a sofa tana riƙe mara dan Hajiya iya na bayi tana wanka. Taja kusan mintuna goma a wajen tana murƙususu harta faɗo a kujerar dan azaba kafin Hajiya iya ta fito.       “Subahanallahi, Inno lafiya kuwa?”.       Cikin kuka ta nunama hajiya iya saitin mararta. “Ikon ALLAH, nikam dai wannan ciwon mara daga ina? Keda baƙya ciwon mara mai ƙarfi irin haka amma wannan karon da alama ta canja miki sallo. Kinga tashi kije kiyi wanka da ruwan zafi sosai bara na leƙa su Haneef ko sun dawo, bansan ina Khalipha ya kwashesu suka tafiba tun ɗazun.        Da ƙyar ta amsama hajiya iyan. Sai dama ta taimaka mata zuwa bayin, ta kuma haɗa mata ruwa mai zafi tace tai wankan tana zuwa.       Ganin yanda Hajiya iyan ta fito da hanzari daga ɗaki Yah Adnan dake cin abinsa hankali kwance matarsa na gefe tana masa hira bayan ta gama bala'in Zinneerah ya ɗago ya dubeta. Tana gab da fita yace, “Granny lafiya kuwa?”.       Juyowa tai ta dubesu dan ita hankalinta baima kai garesuba. Cike da damuwa tace, “Moddibo Zinneerah ce bata da lafiya. Inason na duba cikin su Moos'ab ne wani yazo ya kaita asibiti kar abin ya ƙara mata tsanani”.        Shiru yay yana kallonta kamar bazaice komaiba. Ganin Hajiya Iya ta juya zata fita yace, “Granny su da basa nan ki jira na kammala dan zanje wajen Mahmud dama”.       Dawowa Hajiya iya ta sakeyi tana faɗin, “To Alhmdllh shikenan ma, bara naje ta shirya kafin ka kammala”. Kansa kawai ya jinjina mata yana lumshe idanu da buɗewa alamar amsawar kenan.          Wani irin kallo Farah ta zuba masa na tsananin takaici da kishi. Muryarta har rawa yake wajen faɗin, “Wai ban ganeba. kaine zaka kaita asibitin kuma?”.        Idanunsa ya ɗago ya dubeta ya maida ga abincinsa batare daya bata amsaba. A ƙufule ta miƙe tana cewa, “Wlhy to sai dai mutafi tare. Dan bazan yarda ka tafi da wannan shegiyar yarinyar mai kama da aljanu kai kaɗaiba. Ni wlhy bazan iyaba ka shirya mukoma gaskiya”.      Da kallo ya bita harta shige lungun da ɗakinsa yake. A bazata murmushi ya suɓuce masa ya girgiza kansa da ɗan taɓe baki ya ɗauke kai.         Harya kammala abinda yake ya miƙe zuwa ɗakin bata fitoba, koda ya shigo isketa yay tana waya. Yasan dai bazai wuce Mammah ko cikin yayuntaba. Dan haka bai tsaya sanin dawa takeyiɗin ba ya shiga toilet. Cikin abinda baifi mintuna uku ba ya fito. Key ɗin mota da ke a bed side drawer ya ɗauka ya nufi hanyar fita ya barta tana wayar har yanzun.        Yana fita itama ta miƙe ta ɗauka ɗan kwalin abayarta ta bisa tanayin sallama da yayanta da shigowarta ɗakin kiransa ya shigo mata a waya. Shine ta zauna amsawa. Sai da yay sallama a ƙofar ɗakin Hajiya iya ta amsa masa da bashi izinin shigowa sannan ya shiga. Zinneerah data fito wanka ta gama shiryawa cikin baƙar doguwar riga tana kwance a bakin gadon idanunta a lumshe hawaye na zirara. Kallo guda yay mata ya ɗauke kai ya maida ga hajiya iya data ɗakko mata hula da ɗan kwalin rigar.           “Haka take ciwon kai?”.   Ya tambaya kansa tsaye kamar yanda ta sanar musu ɗazun. Kallonsa hajiya iya tayi, “Ciwon kai kuma Moddibo? Zinneerah ce zata zauna yima ciwon kai raki kamar haka?. Ita jarumace ai da kake ganinta, tunda ka ganta haka ai abinda yafi ƙarfin ciwon kanne mararta ke ciwo, kuma da ba haka take mataba”.        Jin abinda Hajiya iya tace ya sashi janye idanunsa daga kallonta ya maida kan Zinneerah data zumɓuro baki alamar bataso Granny ta faɗa abinda ke damun nataba. Baki yaɗan taɓe da nufar hanyar fita yana faɗin, “ta sameni waje”. Daga haka ya fice abinsa ya barsu da ƙamshinsa........✍ *_Sauran inji wani yace kaɗanne gobe na rage mudu😂🤒🤒._* *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_* *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* *Page 25* ________________________ *ZAUREN GIRKI* Abinci na *gargajiya* ...Kuka,Taushe,Danbu, Sinasir,Waina Abinci na *zamani* ...Afang,Edikaikong, Coconut Rice, Ofada Rice *Garabasa* ...Salads,Pancakes, Plantain mosa, Gyaran nama/kifi kafin girki,Shirin/shinfida abinci kan table. • A kowane sati,in shaa ALLAAH, za a koyi miya/abinci daya da kuma wani abu ta karkashin *Garabasa* . • Duk ranar *Lahadi* za fito da sabobin *videos* guda biyu na miya/abinci da na wani abu daga karkashin *Garabasa* . • Kowacce daga cikin masu koya zasu bibiya video su kwaykwaya su gwada yin abincin bisa ga umurnin *video* • Kowane ranar *Asabar* za a yi *Q&A* a inda kowa zai samu yin tambayoyi akan *videos* din satin daya gabata, da inda suke neman karin bayani/gyara akan kokarinsu na gwada abincin *video* da kawunansu • Ga wace taga dama,daga ranar *Talata* za a iya fara turowan *video* ta kokarin da aka yi na kwoyon abincin da aka kwoyar ta *video* na ranar *Lahadi* . • Inda akwai me bukatan wani fanni na abinci,ana iya hada *aji(Special Personal Video Classes)* musamman domin wannan bukatan.Anan za a shirya live *video* sessions domin cimma wannan burin • Za a biya dubu biyu *(#2,000)* na watan farko,sannan za dinga biyan dari biyar *(#500)* ta kowane sati ga masu bukatan shiga group dinnan namu mai albarka • *Zen Commute,account number 0119343451 Union Bank* ,asusunmu • Duka lokacin da aka biya sai a turomana da hoton teller ko bank confirmation akan wannan number ta *WhatsApp 0817-541-7533* • Ana iya tuntubammu akan wannan number domin karin bayani; **0817-541-7533(WhatsApp kawai)*                                   ZA MU FARA ZAUREN GIRKI LAHADIN SATIN FARKO TA WATAR SEPTEMBER,IN SHAA ALLAAH! *MU TSARE MUTUNCINMU,MU KARE MAZAJENMU...MU KOYI GIRKI!!!* _________________________ *Page 25* ............“Kajimin ja'iri, basai ka tsaya ka kamata ba kuma? Kinga Inno na tashi muje ni na rakaki”.         Zinneerah da tonon sililin Granny yasata fahimtar shine zai kaita asibitin tace, “Granny dan ALLAH muje da wani cikinsu aunty Abidah ko su Meenal basai shiba”.        “Keda kike a wannan halin sai kin zaɓi mai tafiya. Kinga maza miƙe karma ya tafi dan shi ba saiti ne da shi ba wani lokacin”.       Dole ta miƙe Granny ta kamata badan taso ba. Tsaye suka samesu su duka a jikin mota, shi yana waya Farah na tsaye jingine tana danna tata wayar. Batare da hajiya iya ta damu da ganinsu su biyunba ta buɗe gaban motar ta saka Zinneerah shiga. Sai lokacin suka lura da zuwanta. Farah tabi Hajiya iya dake duban inda Yah Adnan ɗin yake da kallo. “Moddibo kuje dan ALLAH, kasan shi mai ciwo ƙosawa ne da shi”.        Kansa ya jinjina mata kawai batare daya bar wayarba ya buɗe murfin zai shiga Farah da haushi ya kume tace, “Granny ai sai dai ta dawo baya dan tare zamuje”.       “Asibitin? A'a idan kin bisu ni motsinwa zanji kuma tunda su Jamal basa nan. Kinga muje ciki muyi hira mai sunan ƴan gayu”. Ta ƙare naganar dajan hannun Farah batare data jira abinda tai niyyar faɗaba.       Ta cikin mirror Yah Adnan ke kallonsu. Ya danne murmushin dake neman suɓuce masa a fuska saboda rigimar Granny. Daga haka yay horn yana harba motar zuwa gate.          Tunda suka hau hanya baiyi ko tari ba duk da yana jin shashshekar kukan Zinneerah daka ƙudundune kanta cikin ƙafafunta data naɗe sama gaba ɗayanta ta dunƙule a kujera. Sai dai duk kiran wayarsa da akeyi tunda ya gama ta farko bai sake ɗagawaba har suka iso Shira hospital.      Duk da darene ko ina cikin haske yake kamar ka yarda allura kaga abunka. Sai da ya gama dai-daita fakin yaɗan dubeta ya ɗauke kansa. Wayoyinsa biyu ya ɗauka batare daya mata magana ba ya buɗe ɓangarensa ya fito. Sai da ya rufo murfin ta fahimci ya fita dan haka ta ɗago cike da ƙarfin hali fuska shaɓe-shaɓe da hawaye.     Tana ɗaura hannunta akan handle ɗin ƙofar da niyyar buɗewa ta fita tunda tasan bacewa zai ta fito ɗinba sai taji ƙofar ta buɗe. Akansa idanunta suka sauka da mamaki, sai dai ganin yanda yaci toka yasata saurin maidawa ƙasa. Gudun kartai laifi ya sata ziro ƙafa ɗaya zata fito ɗayar kuma ta riƙe. Tsareta da ido da yayi ga kuma azabar da takeci yasata sakar masa kuka.         A ransa yace (sai shagwaɓan tsiya). a fili kam sai ya girgiza kai kawai ya ɗauke kai yana miƙa mata handkerchief. “Malama goge waɗanan hawayen tunda ba satoki naiba”.          Duk da halin da take a ciki saida tace (bama gara wanda ya satoni da kai ba) amma a zuciya😂. A zahiri kuwa baki ta tura gaba da amsar handky ɗin nasa da keta uban ƙamshin turarensa tahau share hawayen. Shi kuma yay gaba abinsa cikin asibitin batare daya jirataba duk da ya fahimci bazata iya taka ƙafarba dan tun'a gida ya lura dama da ɗingishi ta fito sanda Granny ta kamota.           Kanta ta ƙara maidawa cikin ƙafafu ta dasa sabon kukan takaicinsa dana ciwo. A haka Nurse ɗin daya turo tazo ta sameta. Itace ta taimaka mata ta fiddota a motar suka fito. Da ƙyar ta taka ƙafar data ƙara riƙewa zuwa cikin asibitin. Suna shigowa a bazata sukaci karo da Khalipha.        “Kai! Beauty lafiya kuwa? Ke da wa haka?”.         Bata iya bashi amsaba sai dai ganinsa yasata jin sanyi har cikin rai. Shima bai damu da rashin amsawar tataba ya maida dubansa ga Nurse ɗin. “Sister Sadiya ita da waye sukazo?”.       Cike da girmamawa tace, “Ogane nidai yace naje na shigo da ita sir”.     Yasan Yayansu suke cema oga a asibitin. Dan haka cike da mamaki yace, “Yana ina shi ɗin?”.      “Dr Mahmud office sir”. “Okay kuje ina zuwa nima”. Ya faɗa yana nufar wani hanya alamar akwai abinda zaiyi.         Sai da Nurse Sadiya tai sallama aka basu izinin shiga sannan ta shigo riƙe da Zinneerah da ganin Khalipha yasaka kukan nata tsagaitawa. Miƙewa Dr Mahmud yayi yana mata sannu, shiko kansa yana duba wani file bai ɗagoba balle ya nuna yasan sun shigo office ɗin. A kujerar dake kallon wadda yake zaune Dr Mahmud yasa Nurse ɗin ta zaunar da ita.          “Sorry ƙanwarmu kukan ya isa ko?”. Dr Mahmud ya faɗa yana murmushi da kallon Zinneerah ɗin a zuciyarsa yanaji kamar yasan fuskarnan.        Kanta taɗan jinjina masa tana ƙara takure kanta waje ɗaya a cikin kujerar dan kusancinsu ya sakata jin ta takura, duk ya cika wajen da kwarjininsa. Kallonsa taɗan sata taga har yanzu yana a yanda suka samesa. ta janye tana maidawa ga Dr Mahmud daya jeho mata tambaya.        “Ƙanwarmu mike damunki ne?”. Ɗan jimm tai kamar bazatace komaiba dan har sai d Yah Adnan dake saurarensu ya ɗan ɗago ya dubeta ya maida kansa. Fahimtar da Dr Mahmud yay kamar tanajin nauyin maganar saboda AK ya sashi faɗin “To ko dai zamu tada boss a wajen nan ne? Ranka ya daɗe kamarfa........”      Saurin katsesa tai da cewa, “Cikina ke ciwo”.      AK daya ɗan ɗago ya dubeta a karo na biyu saiya girgiza kansa kwai kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya sake maida kansa ga takardun hannunsa. Takarda da pen Dr Mahmud ya tura mata, “Idan babu damuwa rubuta anan kawai”.         Har cikin ranta taji daɗin hakan, babu musu taja takardar ta fara rubutawa tana cije baki. Koda ya amshi takardar ya duba yaga mita rubuta sai baice komaiba ya jin jina kansa yana nuna mata ɗan gadon duba marasa lafiya dake can gefe. “jeki kwanta acan ina zuwa”.          Miƙewa tai cike da ƙarfin hali ta nufi gadon ta kwanta. Shima sai ya miƙe ya bita da wani ɗan dogon roba a hannu da syringe. Tambayoyi ya ɗan ƙara mata tana bashi amsa cike da jin nauyinsa. Daga haka ya ɗiba jininta.      A dai-dai nan Khalipha yay sallama ya shigo office ɗin. Ɗagowa Yah Adnan yay ya dubesa da ɗan mamaki. Amma baice komaiba. Khalipha da hankalinsa duk yana ga yanda yaga Zinneerah ɗin ya ƙaraso yana faɗin, “Yayanmu barka da dare”.         “Dama kana nan?”.   “Eh wlhy ban jima da zuwaba. Dr Muneer ne ya kirani mukai wani aiki. Miya samu Beauty ɗin ne?”.        Wani ɗan luu da idanu yayi da tsatstsare Khaliphan da idanu tamkar baiji miya faɗa ba. Shima Khaliphan sai yanzu ya fahimci katoɓarar da yay na cema Zinneerah beauty ɗin. Ya ɗan sosa gefen wuyansa yana murmushi. “I'm sorry yayanmu”.         “For what?”. Ya faɗa cike da salon basarwar tasa yana maida kansa ga file ɗin hannunsa.       Dariya Khalipha ya ƙyalƙyale dashi yana barin wajen ya nufi can inda Zinneerah da Dr Mahmud suke. “Oh oh sweet sister sorry, dama haka kike ragguwa ashe?”.         Dr Mahmud ne ya bashi amsa cikin dariya. “A'a Khalipha karfa ka cika baki, dan sai na bata labarin naka rakin kaima”.        “Lalala Yah Mahmud yi haƙuri kar kaja ta rainani, mike damunta ne? Naga kamar sun shigo tana ɗingishi”.      Kai tsaye Dr Mahmud yace, “Tana complain ne na mara, inaga zamuyi mata text mugani, duk da ina zargin dai bazai wuce....” Sai kuma yay shiru yana ɗan duban sashen da AK yake zaune. Addu'ar samun lafiya Khalipha yay mata yana ɗan murmushi da kauda zancen ta hanyar cewa, “Bara naje da jinin lab to”. Daga haka ya fita. Duk abinda suke tattaunawa Yah Adnan na jinsu. Amma saika rantse ma baya office ɗin, daga ƙarshema waya ya kira har Khalipha ya dawo bai gamaba.        Drip Dr Mahmud ya sakama Zinneerah ya dawo inda AK yake ya zauna suka cigaba da tattauna abinda ya shafesu har Khalipha ya dawo da result ɗin da magunguna daya sayo. Bayan Dr Mahmud ya amsa ya duba yace, “Dama abinda nai zargi kenan, bazai wuce harda Imfection ɗin ba, zamuyi treating ɗinsa insha ALLAH zai barta tunda baiyi ƙarfi ba. Tunda ma ka haɗo maganin inaga kai mata allurar nan kawai”. Miƙewa Khalipha yay yana faɗin, “Okay ALLAH yasa dai bata tsoron allura to”. Dariya kawai Dr Mahmud yayi, shima bayan ya mata allurar duk da barci naɗan figarta sai ya fita ƙarasa uzirinsa. Yabar Dr Mahmud suna cigaba da tattaunawa da Yayan nasu da ya koma kamar baya office ɗin. ★★★         A gida kuwa Farah tamkar zatai ƙaramin hauka a cikin ranta. Tanada kishi sosai wanda ita kanta wani lokacin abun har tsoro yake bata, dan Adnan dai ba taɓa mata alƙawarin bazai ƙara aure yayi ba. Ko lokacin da su Hajiya Iya suka takura masa saiya ƙara aure badan tsayawar Mammah a kansa ba da babu abinda zai hanashi ƙarawar duk da ba nuna mata yanada buƙatar hakan yayiba.        Tsaf hajiya iya tana lure da ita. Kuma dama da biyu ta hanata bin nasu. Dan haka ta shige ɗaki abunta tai shirin barci ta kwanta tunda tasan dai ba binsu Farah ɗin zataiba a yanzu.                Kamar yanda ta ƙware akai ƙara wajen Mammah yanzu ɗinma sai da ta faɗa mata tana kuka. Ran Mammah ya ɓaci sosai jin yarinyarma ba'a cikin ƙannensa takeba kamar yanda ita Farah ɗin tace tana tunani. Koda Mammah ta kirasa ashe wayar a nan gida ya barta, bai fita da ita ba, na hannunsa na alaƙar business ɗinsa ne kawai.      Wannan abinne ya ƙara ƙular da Farah ta dinga kai kawo tsakanin ɗakinsa da falo ita kaɗai dan hajiya iya dai ta shige. yaran kuma da suka dawo basu shigo nanba dan a gajiye suke.          ★★ Sai kusan sha ɗaya ruwan da aka sakama Zinneerah ya ƙare suka nufo gida. Tana a baya ita kaɗai, Khalipha ne yanzu ya amshi driving ɗin, shi kuma yana a gefensa zaune. Babu mai magana a motar dan duk sun gaji kwanciya duk suke buƙata, sai sanyin ac daya takurama Zinneerah, hakan ya sata dunƙulewa waje guda barci sama-sama nason figarta.          Koda suka iso gidan Khalipha ne ya buɗe mata ta fito, ganin yanda take ɗan tangaɗin barci dana rashin ƙwarin jiki yace, “Ƙanwata kodai na kamaki ne?”.     Kanta ta girgiza masa a hankali cikin yanayin kasala tana dafe jikin motar dan ji take tamkar zata faɗi. Ɗan matsawa Khalipha yay da ita gab yana ƙoƙarin kai hannunsa zai kamo nata. Yah Adnan dake kallonsu ta gefen ido, amma saika ɗauka gaba ɗaya hankalinsa baya tare da su ya katse hanzarin Khalipha ɗin dake neman kamo hanun Zinnerah, “Besty kaje da takardun nan ɗakinga zuwa safiya idan ALLAH ya kaimu saika dubasu zamuyi magana daga baya”.      Dole Khalipha ya haƙura daga son taimakon Zinneerah ya juya garesa ya amshi takardun.      “Kaje kawai sai da safe muma bara mu shige dare yayi. Ke kuma muje”. Ya sake faɗa ciki-ciki yana duban Zinneerah da duk tana saurarensu.         Dole Khalipha yay musu sai da safe yana nufar sashen samarin gidan. Shikuma ya tasa Zinneerah dake tafiya da ɗan layi na barci suka nufi sashen hajiya Iya. Abin tsautsayi tana tura ƙofar falon da niyyar shiga hannunta ya gota akan handle ɗin saboda tuntuɓe da takalmi da tai.      Saurin tarota yay ganin zata faɗi, saboda ya rigada ya kawo jiki ita kuma tayo baya. Sai kuma ya ɗagata da hanzari yana miƙar da ita tsaye sosai akan ƙafafunta. Ɓoyayyen numfashi ta sauke da saurin yin gaba har ƙafafunta na neman harɗewa. Ya ɗan bita da kallo ƙasa-ƙasa harta shige bedroom ɗin hajiya iya. Janye idanunsa yay da zummar nufar nasa ɗakin shima yaci karo da gimbiya Farah mai zamani hakimce cikin kujera tacika tayi fam. yanda tai mugun tsatstsaresa da idanu ya bashi tabbacin tunda suka shigo tana a falon kenan.. Sanin halinta yasa bai tanka mataba ya ɗauke kansa yay gaba.         Sai da yay kusan mintuna biyar da shigowa sannan ta biyosa. Tana shigowa yana shiga bayi. Duk da tsahon lokacin daya ɗauka bai fitoba a tsaye ya sake isketa ta kuma cika fam fiye da farko.         Hidimar shiryawarsa ya shigayi yanzunma bai kulataba. Sai da ya gama tsaf cikin kayan barci ruwan sararin samaniya sannan. Kamar zai shareta dan takaici sai kuma ya ɗan dubeta ya ɗauke idanunsa. Inda take ya matsa sosai tare da dafe bangon da hannayensa biyu ya sakata a tsakkiya yana zuba mata fararen idanunsa da alamun barci ya bayyana a cikinsu.        A take dukkan fushinta ya fara rauni dan waɗanan idanun nasa suna ladabtar da ita idan tai laifi. Suna kuma tabbatar mata da ɗunbin soyayyarta a cikinsu idan yaso lallashi. Suna kuma mata kwarjini da girmama kimarsa a gareta a duk sanda shi ɗin yazam mai laifi a gareta.        A karan farko ya saki murmushi ganin yanda ta lumshe nata hawaye na silalowa. Fuskarsa yakai gab da tata suna musayar shaƙa da zuƙar ƙamshin juna. Kafin ya cire hannunsa guda dake dafe da bango ya saƙalo ƙugunta ya sake mannata da jikinsa sosai yana wani sakar mata numfashinsa da ƙarfi akan fuskarta. A take ta saki nannauyar ajiyar zuya da saka duka hannayenta ta zagayoshi ta ƙanƙame itama.       Murmushin ya sake saki, batare daya ce komaiba ya ɗauketa cak ya nufi gadon da ita. Yana sauketa bargo yaja ya lulluɓa musu, zatai magana ya rufe mata bakin da nashi. Daga haka ɗakin yay tsit kamar ba ita ta gama cin alwashin karta masa shika shikan rashin mutunci cassa'in da tara ba. ______________________________★        *_DANYA_* Duk yanda Inna tasoji daga Karima hakan ya gagara. Dan ciwo ta kwanta kashirɓan tun randa ta dawo. Abin kamar wasa sai ga ƙaramar magana na neman zama babba. Tuni Inna ta manta da wani zancen kiranyen dataima Baba saboda ruɗanin halin da Karima ke ciki.       A rana ta uku duk yanda taso ɓoyewa hakan ya gagara. Dan dole ta nufi gidansu Babawo ta sanarma innarsa. Sunyi mamaki matuƙa. Dan shi dai baice dasu Karima tana Danya ba, kuma koda safe sai da sukai waya da shi. Dole Innar Babawo ta ɗakko gyale ta biyo Inna gidanta. Itama hankalinta ya tashi ganin yanda jikin Karimar yay kaca-kaca da sayin duka ga ciki tsoho haihuwa ko yau ko gobe.        A ruɗe tace ma Inna ta shirya karimar suje asibitin kusada. Bara taje ta nemo ƙanin Babawo ɗin tunda yanada mashin. Daga haka ta fice ita kuma Inna daketa tsinar Babawo ɗin ta shiga kimtsa Karima......... _____________________★               Hajiya iya batasan su Zinneerah sun dawo gidanba sai da asuba ta ganta kwance a bayanta. Hannu tasa ta shafa mata fuska tare da gyara mata bargo. Itama cike da ƙarfin hali ta nufi bayi yin alwala dan ƙafarta ciwo take mata tun da daddare dama. Da ƙyarma ta iya kai kanta bayin. hakama da tayo alwalar da gyar ta fito. Duk yanda taso gabatar da salla a tsaye hakan ya gagara sai a zaune tayita. Bayan ta idar kuwa ko azkar yau batayiba ta zame ta kwanta a wajan.        Itama Zinneerah farkawa tai, sai dai koda taga Hajiya Iya kwance a ƙasa bata kawo komai a rantaba ta shige bayi kimtsa jikinta. Ganin harta fito Hajiya Iya na kwance a wajen sai abin ya ɗan bata mamaki amma batai magana ba ta hau shiryawa dan wanka tayo. Batajin ciwon komai yau sai rashin ƙwarin jiki. Ta shirya cikin siket da riga na baƙin Material mai adon firanni golden. Ganin Hajiya Iya taɗan motsa ya sata zuwa gabanta ta tsugunna tana gaisheta.      Hajiya Iya ta buɗe idanu da ƙyar tana duban Zinneerah ɗin. Murmushin ƙarfin hali tayi da miƙa mata hannu ta kamo nata. “Inno na yaya jikin?”.      Kasa amsawa Zinneerah tayi saboda jin zafi jikin na Hajiya Iya. aɗan rikice ta sake damƙe hannun cikin nata tana faɗin, “Granny baki da lafiya ne?”.         Kamshinsa ne ya katse Hajiya iya dake ƙoƙarin bama Zinneerah amsa. Zinneerah ma sai ta ɗan dubi ƙofar dai-dai ya shigo idanunsa suka shige cikin nata. Saurin janye natan tayi tana maida kai ƙasa dan wani irin matsananciyar kunyarsa taji saboda tunowa da faɗa masa a jiki datai jiya da dare. Ga sirrinta daya gamaji a bakin hajiya iya kafin su wuce da kuma tabbacin ya sakejin wani wajen Dr Mahmud.       Shima nasa idanun ya janye yana duban Hajiya iya dake kallonsa a kwance. A take ya gano babu lafiya dan yasan hajiya iya sosai a rayuwarsa. Duk da kuwa zaman da yay a wajenta na shekaru tara ne kacal, sai hutun da yake zuwa mata kuma bayan ya koma London karatunsa.        Ta inda Zinneerah ke tsugunne ya ƙaraso ya ɗan ranƙwafo kansu yana kai hannu goshin Hajiya Iyan. “Granny lafiya kuwa?”.         “Wlhy ƙafafun nan ne ke neman takuramin kwana biyun nan Moddibo ”.       Idon Zinneerah na cikowa da ƙwalla tace, “Amma Granny shine baki faɗaba? Wlhy jikinki zafi dan ALLAH ki tashi muje asibiti”.      Yanda ta ƙare maganar hawaye na silalowa ga rawar murya ya sakashi ɗan dubanta, kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa. Ɗayan hannun Hajiya iya ya kama shima ya tadata zaune sosai dan tanada jiki itama masha ALLAH.         Gaban Hajiya Iyan yay wani ɗan tsuggunne idanunsa na sauya launi zuwa damuwa. Dole Zinneerah ta miƙe saboda kusancin da suka samu yayi yawa. Cikin wayancewa tace, “Bara na haɗo miki kunu kiɗansha sai kisha maganinki”.      Murmushi Hajiya Iya tai tana binta da kallo harta fice, kafin kuma ta sake maido idonta kan Yah Adnan dake mata tambaya muryarsa a ƙasa.       Al'amarin kamar almara sai ga jikin hajiya iya na neman rikicewa a wannan yini, dole Dr Mahmud da Khalipha suka rufu a kanta duk da shi bai kammala nasa karatunba ma. Amma kwazon da yake nunawa yasa ko ƙasar yazo yakanje Shira hospital yay wasu ƴan ayyuka dai-dai saninsa.         Tashin hankalin ruɗewar jikin ya saka Yah Adnan cewa zai wuce da Hajiya Iyan london a yau. Amma sai Baffah da ake saran zai dawo ƙasar yau ya taushesa akan yay haƙuri yana zuwa shima.     Badan yasoba dole yabi umarnin mahaifinsa da yake zuwa yamma jikin Alhmdllh ya ɗan ɗaga mata. Duk wanda ya kalli Zinneerah yau yasan tasha kuka. tayi wuni firgai-firgai da ita na damuwa. tabi ta nane a ɗakin wajen Hajiya iya ita dasu Jamal. Ko yayansu ya shigo su su Jamal tsoro na sakasu fita da shakkarsa. Itako duk da tanajin shakkar tasa da kwarjin da yake mata saita fiske abinta taƙi fita.          Dama tun lokacin da jikin ya rikice tai kiran Maman Sadiq ta sanar mata. Itama hankalinta ya tashi matuƙa dan haka tace zuwa yamma zata shigo tare da yara su dubata dan yanzu duk sun wuce makaranta Little ne kawai a gidan.     Aiko kamar yanda Mman Sadiq tai alƙawari bayan sallar la'asar sai gata tare da Sadiq, Abdull, Aliyu sai Little. A napep sukazo kasancewar Abba baya nan yaje ɗanmusa duba yayansa da baida lafiya shima.         A gate ya saukesu mmn sadiq tai kiran Zinneerah a waya dan tazo ta shiga dasu. Duk da tana tare da damuwar ciwon hajiya iya cike da ɗokin ganin ƙannen nata da gudan jininta ta fito zuwa hanyar gate. Sai da suka gaisa da maigadi ta sanar masa baƙine zasu shigo.       “To Hajiya bara a buɗe musu”. Ya faɗa yana ajiye butar hannunsa daya ɗauka alamar zaiyi wani abu. Da gudu su Abdull sukayo kanta lokacin da suka shigo. ganin yanda Little ya biyo rububi a guje shima ya bata dariya. Tsugunne yakai da buɗe musu hannayenta duk suka shige su huɗun. Mmn Sadiq dake binsu da kallon sha'awa taɗan murmusa tana ɗauke kanta. Da ƙyar Zinneerah ta samu ta miƙe tsaye hannunta riƙe dana Aliyu tana ɗauke da Little a ɗayan ta dubi mmn sadiq da faɗin, “Mama sannunku da zuwa kumuje ciki”.        Kai kawai Mmn sadiq ɗin ta jinjina mata tana mamakin yanda ɗiyar tata ta ƙara canjawa a ƴan kwanakin data dawo gidan. Zuwansu tsakkiyar harabar gidan yay dai-dai da fitowar AK daga sashen Hajiya iya kunen sa manne da waya alamar magana yakeyi, sanye yake cikin ƙananun kaya da suka sakko fiddo zallar ƙuruciyarsa da hutu dajin daɗi, ya cigaba da takowa a hankali garesu suma suna nufarsa duk da Zinneerah jitake tamkar zata faɗi dan har haɗewa ƙafafunta keɗanyi..........✍            *_Harda na gobe😫😫🤧_*        *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_* *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* *Page 26* ___________________________ 💫💥💫💥💫💥💫💥💫💥💫 *_ALBISHIRINKU MATAN AFRICA DA KEWAYE , SHAHARARRAR KUMA KASAITACCIYAR MAI SAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI MAMAN YUSUF YAR SOKOTO TANA YI MAKU ALBISHIR DA CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE CIKIN FADIN NIGERIA DA NIGER KARKU MANTA MACE MAI GYARA KANTA BATA BORANCI_* 💃💃💃💃💃💃💃 07069711327 _Akwai zafafan kayan Mata masu kyau da arha cikin sauki da rahusa Kuma duk inda kike zamu aika maki kayanki cikin aminci da yardar Allah ba cuta ba cutarwa don a Dade anayi sai gaskiya uwargida da amarya ku garzayo Kar abaku labari_ Munada kalolin Kaya kamar haka💥💫💥💫💥💫👇🏻👇🏻 Maganin sanyi sahihi Mai fatattakar sanyi cikin kankanin lokaci na maza Dana Mata Maganin gyaran nono domin dawo da martaban nononki hadin gargajiya da bashida illah ajiki Maganin hips Mai tado da hips cikin kankanin lokaci Maganin kiba Wanda zaisa ki ciko dai dai misali kiyi kyau kema ki shigo cikin jerin Mata masu aji Maganin rage kiba da tumbi Wanda zaisa ki sace ki koma Yar dai dai abin alfaharin kowane namiji, Akwai kalolin gumbuna masu kyau da saukar da ni'ima Maganin matsi masu ciko da gaba da matseki Kamar Yar budurwa uwa uba zasu Baki dandano Mai gamasar da maigida Kalolin garrika masu bawa mace niima da jimawa ajiki Kalolin tsumi Sha yanzu magani yanzu dasa Mai gida ihun Dadi Zumar mallaka Zumar goron Tula Zumar ridi Zumar Mai rubutu Hadin mallaka Turaren mallaka Shu'umar humra Turaren AL'AJABI Matan gaske Ak 49 Sirrin tafin k'afa Turaren fuska Hatsabibin turare Kwallin mallaka Zoben mallaka Jigidar maida tsohuwa yarinya Maltinar Mata Karya gado Yajin Mata (yajin Mai ciko da mace) Yajin maza (domin Karin k'arfi) Muna dahuwar Kaya kamar haka💫💥💫💥👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 Dahuwar zabo (mallaka) Kazar Yar gata Yan shila Ciccibi Dambu Zuciya Yan ciki Kwai ukku Tsoka Tara Kifi Da sauransu Akwai sirrika sosai da muke hadawa ga wacce kishiya ta addabeta ko wadda take fama da butsarin namiji ko mafadacin namiji ko namiji Mai yawon dare ko Wanda yake bin Mata insha Allah duk zaku samesu Kuma da yardar Allah za'asamu biyan bukata Muna bada magani ga yarinyar da tsautsayi ya fad'a Mata ta rasa budurcinta ta hanyar fyade ko yaudarar da namiji Kuma insha Allah zaadace da yardar Allah Abubuwan da yawa gsky Wanda in nace Zan lissafasu sai nakwashi tsawon lokaci maiso tabini PC don ganin kalolin kayan da muke dasu , Karku manta mace Mai gyara kanta Bata boranci taku ce maman yusuf Yar mutan sokoto 07069711327 . Don Allah wadda Bata shirya ba tabari sai ta shirya sannan tayimun magana🙌🏼🙌🏼🙌🏼🙌🏼🙌🏼ngd 07069711327 __________________________ *page 26* ...........Baki ya buɗe zai bama wanda suke maganar amsa dai-dai da isowarsa gab dasu hakan ya gagara. Dan a take harshensa ya sarƙe saboda sauka da idanunsa sukai akan fuskar Little dake ɗauke a kafaɗar Zinneerah ya wani lafe jikinta hannunsa na wasa da jelar kitsonta ta bayanta. Ita kanta sake shiga ruɗani zuciyarta tayi kasancewar kusancinsu sosai yau da little ɗin ya ƙara fiddo mata da kamanninsu ainun.        Sannan ganin yanda yake kallon little ɗin shima sai da hanjin cikinta suka motsa. Ba ita da shi bane kawai a ruɗanin hatta da mmn sadiq sai da tayi kamar zata kifa daga bayansu. Ƙirjinta kuwa yay wani mummunar bugawa tanabin AK ɗin da kallo. Duk da ƙarancin shekarun Sadiq da Abdull suma dai su kalli little su kalli AK ɗin da ayanzu yay ƙarfin halin ɗauke idanunsa yana maida hankalinsa ga wanda suke wayar duk da a baɗini sam hankalin nasa baya tare da shi.       A haka suka wuce juna su Sadiq na waiwayensa, hakama mmn sadiq sau kusan uku tana waiwayowa ta kallesa, kamar yanda shima ɗin ya kasa daina binsu da kallo. Zinneerah kam da ƙar ta cigaba dajan ƙafafunta ta ƙarasa dasu sashen hajiya iya. Inda acanma kallo ya koma sama. Dan tun sallamar da sukayi kowa ya amsa su Meenal suka taso da gudu suka rungume Mmn sadiq suna mata sannu. Sun juyo da nufin ma su Sadiq sannu da zuwa idanunsu ya sauka akan little.       “What!”. Jamal ya faɗa a hankali yana tsare little ɗin dake lafe a kafaɗar Zinneerah har yanzu da ido. Sam hankalin Zinneerah baya tare dasu a yanzu, dan yau tafi kowacce irin rana shiga ruɗani akan kamannin little da Yah Adnan. Shiyyasa harta sauke little ɗin ƙasa bama tasan tayi ba. Hakan kuma dataine ya bama duk sauran yaran gidan ganinsa sosai. A take sannu da zuwan da suke Mmn sadiq ya shiga maƙalewa a maƙosansu. Dan yau harsu Momie suna a sashen suma.          Cikin ƙarfin hali Khalipha da yay mutuwar tsaye shima ya nuna musu hanyar ɗakin hajiya iya yana faɗin, “Mama ku shiga tana ciki”.      Kai Mmn sadiq ta ɗaga masa tana murmushin yaƙe dabin Khalipha ɗin da idanu itama dan ta ganesa duk da ya ƙara buɗewa fiye da wancan sanin datai masa.     Duk wannan al'amari dake faruwa Farah na ɗaki kwance dan taƙi sakewa a cikinsu kamar yanda takeyi dama idan tazo gidan. Saboda karma Adnan ɗin ya zargeta catai masa bata da lafiya. Yarda yay tunda yasan tana laulayin ƙaramin ciki kamar yanda Mammah ta sanar masa.         Hajiya iya na kwance suka shigo. amma tunda idonta ya sauka akan little itama babu shiri sai gata zaune. Ta haɗiye yawu da ƙyar tana miƙa masa hannu shi dasu Aliyun. Babu musu duk suka nufeta. Sai da suka gaisheta da jiki sannan suka zazzauna inda ta nuna musu a kusa da ita kan gadon. Little kuwa matsawa yay jikinta ya kwanta dan shi dama akwai son jiki. Su Sadiq sun shagwaɓa shi, harma dasu Mmn Sadiq ɗin.          Hajiya iya takai hannu kan little ta shafa zuciyarta na wani irin harbawa. A ranta ko rayawa take tamkar Moddibo na ƙarami. A fili kuma saita maida hankalinta ga Mmn sadiq dake gaisheta cike da kulawa.         Tunda suka shige aka shiga ƴar kallon kallo a falon, dan bakin kowa ya kasa furta komai. Sai can kamar a fisge Saffiya tace, “Wannan ai yaron dana ɗakko muku hotonsa ne. Amma kuma ba maman bace wannan”.       Shigowar Baffah da AK ne ya hana kowa amsa zancen Safiyya ɗin. Sai ma zubama Yayan nasu ido sukai zukatansu fal ruɗani. Shima kansa a ruɗanin yake. Amma kasancewarsa gwanin kamewa yasa babu mai iya fahimtar halin da yake a ciki akan fuskarsa. Sannu da zuwa duk suka shiga yima Baffah. Ya amsa musu sama-sama yana nufar ɗakin mahaifiyarsa dan ba'a cikin hayyacinsa ya dawo ba.      Da sallama ya shigo, AK biye dashi a baya. Ganin Mmn sadiq ya saka Baffah nuna jin daɗinsa. Suka gaisa cikkn girmama juna. Suma su Sadiq suka gaishesu ya amsa musu da kulawa. Sai da ya maida hankalinsa ga Hajiya Iya data kafe AK da kallo sannan shima idanunsa suka sauka akan little da barci ya fara ɗauka a jikin hajiya iya.      Wani irin muƙut, Baffah ya haɗiye yawu da ƙyar yana kallon little da ƙyau. Kasa jurewa yay sai da ya juyo ya kalli AK da gaba ɗaya hankalinsa ke akan little shima. Ya sake maidawa ya kalli little again zuciyarsa na wani irin rawa. Dan ƙarara zakaga shi ruɗaninsama akan fuska. Kasa jurewa yay sai da yace, “Ikon ALLAH innata kunga wani kamanni yau dake neman hargitsa tunanina anan, ɗan wanene wannan?”.         “Bakai kaɗaiba Babangida. Ni kaina bakaga na kasa daina kallon yaron da Moddibo ba. Ai wani hikima sai UBANGIJI. Wlhy sai kace Moddibo na ƙarami. Hauwa'u wannan yaro nikam idan a wani guri na gansa ai sai nace namune ma. Ina kika samosa?”.      Duk da faɗuwa da gaban mmn Sadiq yayi cikin juriya tai murmushi zata bata amsa Aliyu yay saurin faɗin, “Mama ƙaninmu ne”.         Shiru ɗakin yayi, Mmn Sadiq ta sauke wani ɓoyayyar ajiyar zuciya. Dan a ganinta ba'a wannan halin da hajiya iya ke a ciki yakamata tasan matsayin little ba. Amma insha ALLAHU tayi alƙawarin tana samun lafiya zasuzo ita da Abba sumasu bayanin komai. Shiyyasa taso tunma kan Zinneerah ta taho su faɗa musu. Amma batasan dalilin Abban na hanawaba.        Baffah ne ya katse tunanin na maman sadiq da faɗin, “Kai masha ALLAH, ALLAH ya albarkaceku, hikimar UBANGIJI ai tafi ƙarfin mamaki. Hakan na ƙara nuna mana muhimmancin zuminci da ƙarfin jini dake tsakaninmu Hauwa'u. ALLAH ya sake ƙara mana ƙarfi da kusanci, ya kuma sa muci amfanin hakan duniya da lahira”.      Da amin duk suka amsa. Baffa ya shafa kan yaran duka har little daya ɗan buɗe ido ya dubesa na kusan sakan goma sannan ya maida ya rufe. Daga haka aka koma gaishe-gaishe duk da zuciyar kowa dai ba adaidai takeba.                    Bayan Baffah ya fita aka kawoma su mmn sadiq abinci da ruwa. Ruwanma kawai suka sha dan a ƙoshe duk suke dama. Suna nan zaune tare da hajiya iya har akai kiran sallar magriba Khalipha yaja su Sadiq suka tafi massallaci. Bayan an idar ne sun dawo suka iske Little ya tashi. Sai dai suna toilet Zinneerah ta kaisa zaiyi fitsari. Sannu suka sakema Hajiya iya dake zaune ta idar da salla duk suka fita.          Zinneerah ta fito riƙe da little dake mata maganar da ba wani fahimta takeba sosai saboda bawani ya iya bane da ƙyau. Murmushin ƙarfin hali take masa itama tana magana ƙasa-ƙasa. Hakan yayi dai-dai da shigowar AK ɗakin da sallama. Amsa masa duk sukayi idanunsa na sauka akan Zinneerah da little ɗin. Ita dai bata yarda ta kalli sashen da yakeba, sai da a bazata suka ji little yace, “Abbah ruwa zan ca”.          Gaba ɗaya suka kalli yaron da mamaki dan AK yake kallo, kuma shine ya shigo hannunsa riƙe da goran ruwa.        Murmushi AK ɗin ya saki wanda ya sake fidda kamanninsa da little ɗin ainun yana nufosu. Ƙirjin Zinneerah ya harba da ƙarfi lokacin da yazo gab da su ya miƙama little ɗin hannu alamun yazo gareshi yana faɗin, “Oh my Sweetheart zo, zo”.       Saurin sakar masa shi tayi tana ja baya, shiko little cike da farin cikin daya bawa kowa mamaki musamman ma su su Zinneerah da suka san miskilancin yaron ya wani maƙalƙale Yah AK ɗin yana sauke ajiyar zuciya. Shi kansa AK ajiyar zuciyar ya sauke a ɓoye da sake manne yaron a jikinsa jininsa na tsinkewa. A hankali ya sumbaci goshin yaron sannan ya zauna a bakin gado ya saka masa ruwan a baki yana shafa kansa.        Baki little ya janye yana faɗin, “Ƙoshi Abbah”.       A bazata sukaga AK ɗin yayi dariya da jan hancin yaron yana faɗin, “Wannan hausan naka bai cikaba little Handsome”.       Ƙaramar dariya hajiya iya da zuciyarta ke ƙara raunana da shiga ruɗanin wannan al'amari tayi. hakama Mmn sadiq tai murmushin yaƙe kawai. Kallon Zinneerah hajiya iya tayi. “Inno na a bashi abinci ko”.        Kai ta kaɗama Hajiya iyan da nufar kulolin da aka kawoma su mmn sadiq ɗin basu ciba. Ta buɗe ta zubo abincin kaɗan a filet. Kallo ɗaya tayima little ɗin dake jikin Yah AK yana masa firar da baya fahimta dan maganar tasa ba nuna taiba ta ɗauke kai. “Malami sakko ga abincin”. Tai magana tana dubansu.      Kafaɗa ya noƙe alamar bai zuwa. Hakan yasa Zinneerah hararsa ta ɗauke kanta ta maida gasu Aliyu. “Kuma zakucine Abdull na saka muku?”.        Kai suka girgiza mata alamar a'a. Dan haka ta sake duban inda little yake ganin ko motsi baiyiba har yanzun. Zata sake magana AK ya harareta kaɗan da miƙa mata hannu alamar ta bashi abincin. Baki ta ɗan tura gaba da miƙewa takai masa. Harta juya little yace, “Aunty!”.    Juyowa tai ta kallesa, ganin ya maida kansa kamar bashi ya kiraba yasata hararsa, sai ko a cikin idon AK daya ɗago. Da sauri ta ɗauke kanta ta nufi hanyar ƙofa tana ƙunƙuni a cikin ranta.            Baya taɗan ja saboda Khalipha da zai shigo. Ya dubeta da murmushi dan zuwa yanzu kam ya yarda wannan Zinneerah ce daya sani a Shira hospital. Sai dai little ya saka zuciyarsa a tsananin ruɗani da firgici, dan inhar zai auna da ma'aunin hankali shekarun little zasu iya kaiwa dai-dai da hasashen haihuwar Zinneerah. Amma yaƙi ya yarda da cewar shine ɗan data haifa ɗin.          “Kanwata sai ina kuma?”. Murmushi tai masa daɗan shafar wuya. “Yah Khalipha zan fitane kawai”. Murmushin ya sake sakar mata shima, da matsawa ya bata hanya ta fice shikuma ya ƙarasa shigowa idanunsa na sauka akan Yayansu dake bama Little abinci a baki. Ji yay sun wani bala'in birgesa. Har yana ayyanawa a ransa inama ace yaron nan jinin yayan nasune da gaske.        Takawa Khalipha yay ya zauna kusa da yayan nasu yana mai shafa kan little ɗin. Juyowa little yay ya kallesa sai kuma ya juya ya cigaba da karɓar abincin. Kaɗan yaci abincin yace ya ƙoshi, badan AK ya gaji da bashiba ya haƙura ya barsa. Haka ya cigaba da zama a jikinsa har ya sake komawa barci.       Su Mmn Sadiq basubar gidanba sai wajen tara saura na dare. Da ƙyar aka raba little da jikin Yayah Adnan, dan lokacin da Khalipha dazai kaisu yazo amsarsa sai gashi ya farka a bazata. ya ƙanƙame AK ɗin yaƙi zuwa wajen Khalipha. Murmushi AK yay da lumshe idanun yana sunbatar little ɗin a goshi da shafar bayansa. Shi kansa ƙarfin hali kawai yakeyi, amma ji yake kamar karya rabu da yaron dan yayi bala'in shiga ransa.       Daga ƙarshe dai da ƙyar ya yarda Khalipha ya ɗaukesa dan sai da aka haɗa da masa wayo. Motar na ficewa ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya hawayen da baisan kona minene ba suna ciko masa idanu. Ƙoƙarin maidasu yay yana furzar da huci mai zafi da nufa garden ya zauna dan babu abinda yafi buƙata a yanzu kamar kaɗaici.               Yanda AK ya kaɗaice kansa Zinneerah ma harabar gidan ta fito can wajen motoci ta hau bayan ɗaya daga ciki ta zauna tare da faɗawa duniyar tunani. Gaba ɗaya zuciyarta a ruɗani da ɗimuwar kiɗima take. Shin a ina aka faɗi a ragaya ne? Wane darasi rayuwa keson karantar da ita a wannan gaɓarne bayan darasissikan data baro a shekarun baya?. Ko mahaukaci ya kalli little ya kalli Yah AK dolene ya danganta alaƙar jini a tsakaninsu. Dan abinda zai matuƙar baka mamaki ba kammaninne kawaiba. Hatta da wasu a cikin halayen Yah Adnan akwai alamunsu ga little. Kenan to.......      “Kai ina”. Ta faɗa a fili tana girgiza kanta dake matuƙar sara mata. Kamar ance ta ɗaga kai can ta hango Baffah a barandar sama yana kaikawo alamar shima akwai abinda ke damunsa, wanda bata raba ɗayan biyu zancen kamanin little ne da Yayan nasu.        “Ya ALLAH kai ne gagara misali, ka buɗemin tunani, ka yalwatamin fahimtata. Ka gafarta mini zunubaina”. Ta faɗa hawaye na silalo mata akan kumatunta masu zafi. Zurfi sosai ta ƙarayi a tunani har motar Khalipha daya kaisu mmn sadiq ta shigo gidan bata saniba. haskatan da yayne shima ya sakashi ganinta. yana gama fakin ya nufo inda take. Sau biyu yanayin sallama babu amsa, har dai ta kaisa ga ɗan bugar motar ta gefen kunnenta sannan ta kawo nannauyan numfashi tana dubansa.        “Wane irin tafiya tunanine haka da zurfi ƙanwata?”.       Murmushin yaƙe tai masa tana duƙar da kanta ƙasa. Hakan datai sai ya ƙara fiddo masa da kamanninta na baya sosai. Yay murmushi yana gyara tsaiwarsa da faɗin, “Zinneerah na tambayeki mana?.”          Gabantane ya faɗi, amma sai cikin dauriya tace, “Ina jinka Yah Khalipha”.       Kansa ya kaɗa mata yana ajiye keys ɗin hannunsa da wayarsa alamar maganar mai muhimmanci ce. “Dan ALLAH ki faɗamin gaskiya kin manta dani ko?”.        Duk da tambayar tasa tazo mata a bazata dan ba ita tai zaton jiba sai da taji dumm. Ganin ya kafeta da idanu ya sata yin murmushin yaƙe tace, “Ban gane mi kake nufi ba Yah Khalipha”.          “Nasan kin gane Zinneerah, amma tunda hakane bara na miki dallah-dallah”.          “Tun randa na ganki a gidan nan nasan nasan fuskarki, amma na rasa ina na sanki dan kin banbanta da waccan ɗin dana sani a yanzu. Nasha gwadaki naga ko zaki nuna ke kin sani amma baki nunaba, sai yau da naga mama na tabbatar da cewa kece. Shiyyasa mamaki ya kamani na rashin nuna kin sanni da kikai kafin yau”.         Tabbas taji kunya. amma sai ta dake, ta buɗe baki da zummar bashi amsa sukaji ƙamshin turarensa da takun tahowarsa. Duk kallon waje. sukai Zinneerah na haɗiye maganar da tai niyyar yi. Ganin yanda yake kallonsu ya sata jin wani iri, babu shiri ta diro akan motar tai cikin gida sum-sum duk da alamar ta zauna da Khalipha ke mata da hannunsa.             Khalipha da shi kansa kallon da Yayan nasu ke musu ya bashi mamaki, cikin dauriya yace, “Yayanmu na zata ka kwanta ma ai”.         “Shiyyasa kazo nan kake taɗi?”. Ya faɗa yana wucesa. Saurin waro idanu Khalipha yay waje da biyo bayansa. “Ni Abdul-Mutallab, jikan Abdul-Mutallab, ƙanin Abdul-Mutallab wane ni Yayanmu”.     Ɗan juyowa yay ya dubesa. Hakan yasa kunya kama Khalipha yakai hannu yana shafa wuya da risinar da nasa idanunsa ƙasa.          Wani irin juya idanunsa da suka ɗan fara sauya kala yayi yay gaba batare da ya sake cema Khalipha ɗin komaiba, dan harga ALLAH baya cikin hankalinshi da nutsuwar. Binsa da kallo Khalipha yay harya shige sashen Hajiya Iya. Kasa binsa yayi, sai kawai shima ya nufi sashensu zuciyarsa na ƙoƙarin karkato masa wani abu daban.         ★★★★     Washe gari da safe suka tashi da tashin hankalin ruɗewar jikin Hajiya Iya. Dan tunanin data kwana yi jiya game da kamanin little da AK ya ja jininta sake hawa sama matuƙa. Ita Zinneerah bata fahimtaba dan duk zatonta Hajiya Iya barci takeyi, dan itama kanta barcin nata rabi da rabi ya kasance. Sai da ta farka da asuba taji hajiya iya na wani irin wahallen nishine hankalinta ya tashi. Ruɗani ya sata fita da gudu zuwa ɗakin AK ta hau bugawa tana kiran sunansa.      Zaune yake saman sallaya yana karatun Al-Qur'ani dan shi ko sau ɗayama bai rintsa ɗinba. Yanda yaga rana haka yaga dare, a daren na jiya. Tunda yaji bugun ƙofar yasan ba lafiyaba. Ya ajiye Qur'anin tare da miƙewa a nutse ya nufi ƙofar ya buɗe ko sauraren Farah data farka da jan tsaki baiyiba.      A rikice Zinneerah ta damƙo hannunsa jikinta na rawa ga hawaye na kwarara. “Yayanmu Granny, Granny Yayanmu, dan ALLAH kazo Granny karta mutu”.       A take shima ya rikice. Ya shiga binta a baya tana riƙe da hannunsa har sannan tana jansa. Tunda suka shigo yaga halin da Hajiya Iyan ke a ciki sai hankalinsa yafi nata tashi, a take yay kanta yana kiran sunanta da ƙarfi.       Zinneerah daketa yarfe hannu kukanta na ƙara tsananta ya duba cikin sarƙewar harshe yace, “Ɗakkomin waya a ɗakina, m....”     Batama bari yakai ƙarsheba ta kwasa da gudu ta fice. A guje ta shigo ɗakin har tana bangaje Farah data sakko daga gadon tana mitar an tasheta tana barcinta. Wanwar Farah ta zube a ƙasan tiles ɗin amma ko kallonta Zinneerah bataiba ta nufi wayar data hango a drawer gefen gado duk da bata da tabbacin nasane. Sai dai tana kaiwa garesu ƙamshinsa dake manne dasu suma ya tabbatar mata nasanne. Duka ukun ta kwasa ta sake tsallake Farah dake nishi a ƙasa ta fito.          Da ƙyar ya iya saita kansa ya lalubo Number Baffah, shima Baffah da yake ba wani barcin kirki yayiba akan idanunsa kiran ya shigo. Mamaki da tsoro ya sakashi ɗagawa ganin sunan Adnan.      Cikin ƙanƙanin lokaci dukkan ƴan gidan suka gama taruwa sashen hajiya Iya dake cikin mawuyacin hali. Khalipha ne keta ƙoƙarin bata taimakon gaggawa kasancewar ɗalibin likitanci dake gab da kammalawa insha ALLAH. Da ƙyar ya samu yaɗan saita wasu abubuwa. sai dai ya basu tabbacin dolene a wuce asibiti da ita tunda nan gida ba kayan aikine da shi ba.      Suna idar da sallar asubahi ko Shira Hospital suka wuce. A canne likitocin da sukai duty ɗin dare suka rufu kanta. Yayinda AK kuma ya shiga bige-bigen waya na shirin wucewa da Hajiya Iya London kamar yanda dama yaci buri tun da, sai dai tace bata zuwa Nigeria ma akwai likitoci ƙwararru. A yanzun kam tunda bata a hayyacinta yaci alwashin sai ya kaita insha ALLAH an duba wannan ciwon ƙafartata mai kama dana gado. Dan mafi yawan ƴan family ɗinsu na ɓangaren mahaifiyarta duk sanadin ciwon ƙafa suke barin duniya kamar dai Inno. Ga su duk ALLAH ya basu jikin ƙiba dama masha ALLAH............✍         *_Kuyi haƙuri naji kunata cewa bana bana yayinku naƙi muku surprise. Wannan karon abin ya haɗa da wasu uzurorine wlhy. Amma insha ALLAH zan baku mamaki indai pages ne, ina kuma sake baku haƙuri wannan karon akan tafiyar hawainiyarmu ta Typing gaba ɗaya. Ku ɗauki hakan matsayin yau da gobe sai ALLAH. Sannan wasunmu sunada lalurorin yau da kullum tattare da su, da kuma uzirorin rayuwa da duk sukazo mana tamkar an saita. Mukammu bama jin daɗin hakan, dan babban burinmu shine muga mun taru gaba ɗayanmu mun faranta muku tamkar yanda kuka faranta mana kuma kuke zuwa kuna sayen buks ɗinmu a koda yaushe. ZAFAFA TEAM na godiya gaba ɗayansu tare da fatan alkairi a gareku da ban haƙuri. da babban albishirɗin ganin gyara daga garemu baki ɗaya insha ALLAH_* *_Masu karantawa a waje kuma dan ALLAH ku daure kuzo ku saya naku copy ɗin da halalinku kuma ALLAH zai sakama kasuwancinku albarka ta inda bakuyi zato ko tsammaniba insha ALLAHU. Dan duk wanda ya kare mutuncin wani da fita haƙƙinsa kaima ALLAH zai fita naka ya kuma kare mutuncinka da izininsa._* *Muna godiya da zaɓin zafafa a koda yaushe😍😍😘😍😋🤗🙏🏻*. *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_* *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* *Page 27* _______________________ *_WANI KAYA SAI AMALE💃🏻💃🏻💃🏻._* *_INA MATA ƳAN ƘWALISA MA'ABOTA SON KALOLIN GIRKE-GIRKEN ZAMANI. KU GARZAYO GA DAMA TA SAMU A TAFIN HANNUNKU CIKIN SAUƘI💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻😋😋😋😋_* Nigeria @ 61 COOKING COMPETITION!!! from lavender Catering ina masu son koyon girki ga dama zaku shiga gasarmu ta girki bayan kunyi register damu akan 10k,wanda yazo na 1zai shiga ajin mu free hade da wasu prize din na 2 da na 3 kuma zasu bayar da rabin kudine da wasu prize suma saura kuwa zasu ayi musu ragin 5% da wasu prize wannan gasa zamu yita ranar lahadi ne 3/10/21 zamu rufe registration na gasar ranar asabar. Lavender catering school zamuyi practical class. zamuyi 30 dishes continental, snack & desserts, traditional dishes, drink. Fee din 40k phone number WhatsApp and call 09080299283 akwai discount na 5% ga mutum uku farko wadanda sukai register aranakun independence 1/10/2021 to 3/10/2021 Nigeria @ 61 Shi class zamu fara on 14/10/21. *_KU GARZAYO KAR ACI KASUWAR SAMA BABUKU, DAN NAMU BA IRIN NASU BANE💃🏻💃🏻💃🏻😋😋_* ________________________ *Page 27* ...........Alhmdllh an samu daidaituwar jikin hajiya iya, amma bawai tana a cikin hayyacinta yanda ya kamata baneba. Shiyyasa shima AK ya kammala dukan shirinsa akan tafiyar da ita. A wannan karon Baffah baiyi yunƙurin hanashiba. Sai ma taimaka masa da yay da wasu abubuwan kasancewar tafiyar ta zama ta gaggawa.         Duk wanda ya kalla shirawa a yinin yau yasan lallai an taɓa musu wani babban jigonsu, dan kowa idanu jajur. Daga masu kukan zuci har masuyin na zahiri irinsu Zinneerah. Dan ita dasu Bahijja haɗe kawuna sukai sukaita rusar uban kuka sai da Yah Haneef yayta lallashinsu da ƙyar da nuna musu sumata addu'a sannan suka ɗan nutsu.         Haka suka kasance yau yini guda a asibiti likitoci nata ƙoƙarin su, yayinda AK keta shigi da fici na ganin sunbar Nigeria a yau insha ALLAH. Yau ko ƙwaƙwaran abinci babu wanda ya samu yaci a cikinsu, sai ruwa da ƴan kame-kame. Salla kawai ke tashinsu.      Yah Adnan bai farga da babu matarsa a asibitinba sai da zasu koma gida domin shiryawa. Ransa ya ɓaci matuƙa amma ya daure ya shanye har suka isa gidan. Kamar yanda yay hasashe kuwa a gidan ya isketa wai taji ciwo a ƙafa saboda turewar da Zinneerah tai mata da asuba, ga kuma zazzaɓi tanaji. Duk da ya lura da yanda take alamar kuka ta zauna tasha baibi takantaba ya hau shirya musu kaya da kansa batare daya mata bayaniba. Yana gamawa kuma fiwowa yay zuwa ɗakin hajiya iya. Inda ya iske Zinneerah zaune tanashan sabon kuka.      Tsaye yay kawai shiru yana kallonta batare dayayi maganaba tsahon lokaci. ita kuma batasan da shigowar tasaba kanta na a cikin ƙafafunta ne. Yaɗan furzar da huci da cije lip ɗinsa yana ƙarasa takawa cikin ɗakin da ƙyau. Gyaran muryar daya saka Zinneerah ɗagowa yayi. Kallon cikin ido sukaima juna sai kawai ta fashe masa da kuka. Idanunsa ya lumshe yana ɗan kauda kansa gefe.          “Dan ALLAH Yayanmu kaje dani duk inda zaku kaita”. Ta faɗa kukanta na kuma tsananta. Baice mata komaiba ya nufi bathroom ɗin ɗakin dake gyare tsaf duk da yau babu wanda yabi takansa. Ruwa mai ɗumi ya tara a botiki ya fito, inda ya barta anan ya isketa tana cigaba da kukan nata. “Tashi kije kiyi wanka”. Ya faɗa yana nufar inda littatafan hajiya iya suke na addini batare daya sake kallontaba.      Jin abinda yacene ya saka Zinneerah miƙewa da saurinta duk zatonta ƙorafinta ya karɓune. Littatafan ya gama ɗauka da wasu ƴan abubuwa na Hajiya Iyan yasa a ƙaramar jikka. a saman gado ya barta ya fice domin zuwa shima yayi wankan.      Sauri-sauri Zinneerah tahau shiri bayan fitowarta wanka kasancewar ba salla takeba. Tana gamawa ganin jikkar daya ajiye akan gado itama ta jawo akwati tahau haɗa nata kayan. Tana tsaka da neman wayarta da tun jiya bayan ta kira mmn sadiq bata sake ganin wayarba, har so tai ta kirata yau ma ta sanar mata halin da ake ciki amma sai bataga wayarba.        Shigowar AK ɗakin da sallama ciki-ciki, Baba Rahi biye da bayansa ɗauke da tire ya sata dakatawa da leƙe-leƙen neman wayar da takeyi.  Juyowa tai tana kallonsu, yanzu kam shima yayi wankan dan yana sanyane cikin ƙananun kaya sai uban ƙamshinsa ke tashi dan yama danne nata turaren data saka. Shiko kallo ɗaya yay mata ya ɗauke yana maidawa kan akwatin data haɗa kaya. Baiyi maganaba sai zama da yay  cikin sofa ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya yana sauraren Baba Rahi dake lallaɓata ta zauna taci abinci.       “Baba Rahi na ƙoshi, ALLAH bana jin yunwa”.        Manyan idanunsa da launinsu ya canja gaba ɗaya a yunin yau ya ɗago ya zuba mata cike da gargaɗi, babu shiri ta amshi kofin shayin da Baba Rahi ke miƙo mata tai ƙasa da kanta tana kaiwa baki badan yana mata daɗi ba, dan bakintama ji take yana wani ɗaci-ɗaci. Ɗauke idanun nasa yay ya jingina da kujerar yana mai lumshe su. Sai dai kuma yana kallonta ta ƙasan idon.        Baba Rahi ce ta cigaba da lallashinta har taɗanci abincin shima kaɗan ta ture idanunta cike da kwalla tace ta ƙoshi, Batare da Baba Rahi tace komaiba tahau tattare kwanikan zata fita da su ya dakatar da ita. “Baba barsu anan jeki abinki”.        Amsa masa Baba Rahi tai tana maido tiren ta ajiye, Zinneerah kuwa kallon inda yake ta ɗanyi kamar zatai magana sai kuma ta maida kanta ta duƙar. Shi kuma batare daya tashi koya buɗe idanunba yace, “Tashi ki ɗauka maganinki da abincin kizo nan”.        Ita tama manta wai bata da lafiyane. Shakkarsa yasata miƙewa ta ɗakko din tayi yanda yace batare data musa bin umarninsa ba. Ɗagowa yay daga yanda yake a zaune ya buɗe abincin da kansa ya sake tura mata gabanta. “Na baki 10minutes kawai ki cinyesa”. Daga haka ya koma a yanda yake kamar ɗazun. Cika idanun Zinneerah sukai da ƙwalla. Taja abincin gabanta tana ƙoƙarin haɗiye ƙwallar tata dan bataga wajen yin wargi ba. ALLAH ma ya sota abincin ba wani mai yawan tsiya bane dan baba Rahi dama ta santa bawani cin abincin take sosai ba. Sai da ta gama tasha maganin sannan ya sauke ƙafarsa da gyara zamansa yana faɗin, “Zonan”.      Babu musu ta miƙe zuwa garesa. Sai dai inda ya nuna matan ta zauna ne yasata jin shakku tatsaya tana duban gefen nasa. Harar daya balla mata ce ta sata zaman babu shiri daga can ƙarshen kujerar duk da tazarar ba wata mai tsaho bace a tsakaninsu.         Ƙasa tai da kanta tana wasa da yatsun hannunta, ji take ba'a taɓa saka rayuwarta a takuraba irin ta yau ba, dan kwarjininsa da ƙamshinsa gaba ɗaya sun sakata jin ɗakin ya musu kaɗan. Shiko ko a jikainsa kallon hanunta da taketa faman cuɗawa a juna kawai yakeyi cike da nazari. Mikuma ya tuna oho masa sai yay saurin kauda kansa. Kusan mintuna uku suna a haka shiru kafin ya sake dubanta.         “Kikace zaki bimu?”. Ya faɗa ciki-ciki idanunsa ƙyam akan fuskarta.      “Eh Yayanmu dan ALLAH”.   Ta bashi amsa itama murya na rawa. Kwarjininsa na sake tsumata dan ta kasa ɗagowa ta dubesa. Tamkar bazai sake cewa komaiba sai kuma yaɗan girgiza kansa. “Idan kin bimu karatunki fa? Ko kin jinginesa kenan?”.      Idanunta da suka ciko da ruwan hawaye ta ɗago a karo na farko ta kallesa, sai gasu a cikin nasa dan shima ita ɗin yake kallo. Yanda ya tsatstsareta dasu ne ya tilastata maida nata ƙasa hawayen cikinsu da batasan na miyeba na gangarowa. Sai dai tana danganta zubar tasu da takurar da tayi na kasancewar su zaune a waje ɗaya yanda mafalkinta bai taɓa kaiwaba.     Ya sake maimaita mata cewar, “Nace karatunki fa idan kin bimu?”.       Muryarta na rawar kuka tace, “Yayanmu nidai kaje dani dan ALLAH, idan na dawo naje makarantar, inason na kasance da Granny kawai”.         “Saboda karatun baida muhimmanci a wajenki ko?”.      Kasa cewa komai tayi a wannan gaɓar, hakan ne ya sakashi sauke murya ƙasa da alamun lallashi a ciki yace, “Bazaki bimu yanzuba, dan shi ilimi abune mai muhimmanci ga mai nemansa, adalci ɗaya zan miki shine idan kunyi hutu zakizo ki ganta ok”.       Sharrr hawaye suka sake ɓalle mata. Ta ɗago zatai magana ya miƙe abinsa yana faɗin, “Na gama magana ki tashi ki saka mata kaya kala biyu a wancan jikkan dana ajiye, sai abubuwan da kika sani masu muhimmanci da take amfani dasu yau da kullum. Wannan kayan naki da kika haɗa kuma ki kaisu sashen Momie dan zaki koma da zama can wajenta”.        Daga haka ya fice abinsa ko waiwayenta baiyiba duk da yaji kukan data fashe dashi. Kansa kawai ya girgiza yana ƙara jinjina ƙuruciyarta da shagwaɓa a ransa.        Karo ya kusanci da Farah wadda ke ƙoƙarin shigowa ɗakin alamar biyosa tayi, ya ɗan bita da kallon mamaki kamar zaiyi magana sai kuma ya ɗauke kansa da raɓata ya wuce abinsa. Har tayi kamar ta shiga ɗakin Hajiya iyar taga mi yayo a ciki tun ɗazun sai kuma ta fasa tabi bayansa da sauri. Yana shiga ɗakin itama tana shigowa. Zama yay cikin kujera ya hau haɗa shayin daya saka Baba Rahi dafa masa shima. Sai da ya kammala zai fara sha sannan ya kalli Farah data zauna kusa da shi ta wani tsatstsaresa da idanunta manya.       “K kina ganin abinda kikayi yau shine dai-dai? Kowa yana asibiti ke kina gida kwance?”.        Cike da isarta tace, “Amma dai kasan nima banda lafiya ne ai. Sannan wannan shegiyar yarinyar sanda ta shigo ɗakinan ta ɗauka wayoyinka turenifa tayi a ƙasa amma ko waiwayena batayiba. Jiba kaga yanda ƙafata ta kumbura”. Tai maganar tana nuna masa ƙafar da cigaba da faɗin, “Wlhy yanda ta sani jin azabarnan itama sai na sakata taji wadda ta fita dan saina karyata kafin nabar gidan nan”.        Ɗauke idanunsa yayi daga kan ƙafar kamar baiji mita faɗaba. Duk da masifar data cigaba dayi akan Zinneerah ɗin bai tanka mataba harya gama shan tea ɗinsa sannan ya miƙe. Hakan da yay ya ƙona ran Farah, sai dai ganin ya ɗakko man zafi ya dawo ya zauna da kama ƙafar tata ya ɗora a jikinsa ya sakata sauke ajiyar zuciya.      Duk da ya jita baice uffanba ya hau shafa mata maganin a wajen yana ɗan dannawa kaɗan-kaɗan itako tana zuba shagwaɓa. Sai da ya tabbatar maganin ya shigeta sannan ya ajiye ƙafar yana dubanta cikin ido. “Yau zamu wuce”.      Mamaki ƙarara a fuskarta tace, “Ina?”.        Kansa tsaye yace, “London, Granny zataga Doctor acan”.      Jitai kamar an daɓa mata mashi a ƙirji. ta tattaro yawun takaici ta haɗiye muƙut tana dubansa, “Amma my Hero duk likitocin ƙasarnan har sai an kwashi kamar Granny dake fama da jikin tsufa an wahal da ita zuwa wani waje”.        “Ke kika kallesa a fuskar wahala. mu neman sauƙi zamu insha ALLAH ”.        Harara ta zuba masa a kaikaice zuciyarta nayi mata zafi, cikin ɗan rawan murya tace, “To sai dai kuje ni kasan dai babu inda naje. Bazai yuwu na shigo ƙasarnan ba kuma ban ziyarci kowaba”.         Juyiwa yay ya kalleta cikin ido fuska a tsuke ainun, cike da gargaɗi da barazanarsa yace, “Da zaki taho ai nan aka turoki, dan haka iya nan ɗin zaki tsaya. Nan da awanni shida jirginmu zai tashi”.        Yanda ya tsareta da idanun ya hanata iya cewa ƙala, dan tasan mi wannan kallon nasa ke nufi a gareta. Dole ta tsuke bakinta hawaye na rige-rigen sakko mata. Batare dayabi takantaba ya miƙe ya fice dan yanason yin magana da Baffah.      Miƙewa tai a harmutse itama ganin ya fice tana masifar bazata yarda hajiya iya ta bisuba. Dan babu yanda za'ai a jajubar musu gayya a takurawa rayuwarsu. Khalipha ɗinma ta ɗauki alwashin wannan karon bazai koma mata da zama a gidaba. Sai dai ya koma hostel kamar yanda Mammah ta faɗa. Haka taita masifa tana kuka da neman wayar Mammah amma taƙi shiga. daga ƙarshe sai auntynta ta samu ta kira sukaita masifar tare, Auntyn ta ta katse wayar ta kirashi. Yana ganin kiran sanda yake tare da Baffah yaƙi ya ɗaga dan yasan zancen dai bai wuce mai hali tayi halin nataba...........✍ ★★★          *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_* *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* *Page 28* ___________________________ *MG’s SKIN CARE* (With us, your skin is elegant..) Are you guys  looking for where to buy ur skincare product @ mg's skincare is the best plug for you🤗 Do you wish to have that flawless skin that's free of all skin prblm Do you wnt to achieve that milky skin that turn heads wherever you go😉 Try mg's product nd I assure you you'll never use any other product except mg's product✅ Mg's will gv you the best out of all With mg's product ur skin is 💯 clear,fresh,smooth nd ur skin will absolutely glow all day💃 We have herbal whitening black soap now nd beauty set available Nd both the soap nd the beauty set is for all skin type everyone can use it🤗 Just gv it a try now nd see wonders✅ Chat:08062991549 Call:08064532391 Soap price:3k set:11k Follow us on Instagram@glow_with_mgs Facebook:mg's skincare Nd guess wht🦻 Duk Wanda zesiya Kaya daga yau Alhamis  30-9-21 zuwa Nanda 5days that is ranar talata there will be 20% off discount a soap nd the set😍so what are you guys waiting for hurry nd grab urs💃 now is  the time to glow🧖‍♀️ Pamper ur skin🦵 Shine like a bride 👰 be part of the glow team karkubari abaku lbr Just chat 08062991549 to plc ur orders😘 Do not forget to follow us👆 Like nd comment pls dearies😘 Patronize us🙏 mg's always serve you the best✅❤️ KAYAN MG’s SKIN CARE, GANGARIYA NE, SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI, KU GARZAYA KU SAYI NAKU KAYAN A KULI KALILAN DOMIN DAGA YAU TAFARA BONANZA. IDAN ANJE ACE DAGA ZAFAFA NE, AKWAI RANGWAMEN KUDI SOSAI, KYAU, INGANCI, RAHUSA.. SAI KAYAN MG’s SKIN CARE. ___________________________ *Page 28* ............Ƙarfe takwas da kwata dai-dai jirginsu ya tashi zuwa ƙasar London. Farah nata ƙunci akan ita batai shirin komawaba yau. Sai dai shi uban gayyar yasan haushinta bai wuce na tafiya da Hajiya iya ban. Har cikin ransa mamakinta ke ƙara faɗaɗa a ransa. Yanaji kuma lokaci yayi dazai maidota cikin hayyacinta akan danginsa.      Ita kanta Mammah wannan karon ya shirya mata tsaf, dan yasan ba ƙaramin rikici zadu kwasaba akan wannan tahowa da Hajiya iyan da yay, shiyyasama ko faɗa matai biyiba sai sun isa ta gansu. Ita kanta Farah sai da suka isa airport hankalinta ya ƙara tashi.           Tun bayar wucewarsu zazzaɓi mai zafi ya rufe Zinneerah. Ta kuma maƙale a sashen hajiya iya taƙi tafiya wajen Momie da yace mata. Sai da su Meenal da suma suka gama shan nasu kukan suka biyota sannan. Ganin halin da take ciki suka koma suka sanarma Momie. Da kanta tazo har sashen hajiya iya ta lallaɓata da lallashinta sannan suka kashe komai na sashen ta ɗauki duk abinda take buƙata na amfaninta da kuɗin da Yah Adnan ya bata, dana Khalipha suka wuce. Sai dai fa wayarta ce sunsha nema yanzun ma amma basu ganiba. Ta rasa inda ta jefata tun jiya da rana bayan tayi waya da Mmn sadiq. Momie ce tace subar wayar da safe azo a sake dubawa tunda an kira ma a kashe take. Haka ta haƙura suka tafi can sashen duk da dama ta saba kwana wani lokacin.    Tun daga wannan ranar rayuwar Zinneerah ta koma sashensu Jamal, tanajin daɗin zama da kowa dan babu mai tsangwamarta ko nuna mata banbanci, sai ma wani al'amari mai ƙarfi dake neman saƙuwa tsakaninta da Yah Moos'ab duk da har yanzu bai firta mata cewar yana sonta ba. Yabarma ransa har sai ta kammala secondary kamar yanda yaci buri.          Amma sai kaf-kaf yake da ita musamman da yaga tafiyar Granny ta sakata shiga wani hali. Itako tsaf ta fahimci inda ya dosa amma take nuna masa bata gane komai, ɗaukarsa take kamar sauran samarin gidan kawai, dan ita bata saka soyayya a lissafin rayuwarta duk da tanajin Yah Khalipha a ranta shikam. Amma sai take ɗaukar hakan matsayin ganin girmansa akan taimakon da yay mata wancan karon da bata da gata.        Kullum takanyi waya da Khaliphan a wayar su Jamal, anan ne takejin cigaban da ake samu game da jikin hajiya iya da Yayansu keta kashe kuɗi akan ganin ta samu lafiya. Bata taɓa waya da shi ba. Sai dai duk santa ta buɗe akwati zata ɗauka abu takanci karo da kuɗin da ya bata bandir guda na ɗari biyar, sai turarensa shima daya bata tare duk a ranar da zasu tafin, duk da ko sau ɗaya bata taɓa shafashiba ya gauraye mata kayan cikin akwatin da ƙamshinsa.            Sai da suka cika sati uku cif da tafiya Zinneerah taji muryar Hajiya iya. ALLAH sarki zokaga murna da farin ciki ita dasu Bahijja. Bama suba duk wanda yake a gidan ranar saika fahimci yana a cikin farin ciki, dan duk sai da ta gaisa dasu. Kwana biyu dayin haka kuma Baffah ya dawo daga can ya ƙara sanar musu da cigaban da aka samu.         Hajiya iya na cikin sati na bakwai a london su Zinneerah suka sami hutun makaranta. Kai tsaye ta sanarma Momie tanason taje gida hutu, duk da tana waya dasu kullum ta wayar su Bahijja dan ita dai tata wayar an rasa inda ta faɗa har yanzun, harma ta haƙura dan tasu Meenal ma ta wadatar da ita tunda dama daga amsa waya da kiran su mama sai games suke da wayoyin, sauko abinda ya shafi karatu idan ta kama. Yah Khalipha kuma ya mata alƙawarin zuwa mata da wata idan zaizo.        Shiri Momie tai mata na zuwa gida ita da Baffah duk da kuwa anan cikin garine. Ranar da suka cika kwana biyu da samun hutu Moos'ab da kansa ya kaita gida tare dasu Jamal. Ganin little ɗinta daya ƙara girma da ƙannenta da mama ya mantar da ita kewar su Bahijja da suka wuce. Tuni suka shiga hira tana ƙara bama mama labarin yanda jikin hajiya iya keta ƙara ƙyau. Amma Yayansu yace bazata dawoba sai bikin su Aunty Safiyya.      Mmn sadiq taji daɗi sosai, dan tana ƙaunar hajiya iya da zuri'arta kodan karamcinta garesu. Sai dai kuma a wannan karon ta shirya binciken Zinneerah akan samuwar little. Dan tun ganin AK datai hankalinta bai sake kwanciya ba. Ita harma zargi take itama Hajiya Iya dalilin little ɗinne ciwonta ya motsa.       Ba ƙaramin girgiza zukatansu Sakina wannan zuwan ma Zinneerah tayiba. Dan su kansu sunsan ta wuce da ajinsu yanzun, samarin anguwar kuwa da suka nuna suna sonta a baya suka dingi ɓata Zinneerah a wajensu ganinta ya sake dawo dasu gareta. Sai dai taƙi bama kowa fiska dan burinta bana aure bane yanzu karatu ne.       Tana kwana huɗu da zuwa sai ga Yah Haneef da Yah Mas'ood sunzo wai zasu kaita ai mata passport inji yayansu. Bata fahimci inda zancen ya dosaba amma saita shirya suka tafi harda Little da tun zuwansu gidan suka janyesa. Shiko duk da rashin son mutanensa sai gashi ya saki jiki dasu kamar yanda yayi randa su Jamal sukazo.         Wajaje sukaje kusan uku kuma duk sun jima. basu dawoba sai yamma lis tare da siyayyar kayan ciye-ciye fal leda da suka yima little. Bayan wucewarsu ne Mmn Sadiq dakema little shirin barci ta duba Zinneerah ɗin.        “Niko nace dama tunkan kizo nan kinsan wannan Yayan naku ne Zinneerah?”.      Zinneerah dake cin gyaɗa ta ɗago tana kallon mama. “Mama wane Yayan a ciki?”.        Kai tsaye Mama tace “Adnan”. Shiru Zinneerah tai tana kallon Mama na wani ƴan sakkani, a ranta tambayar na bata mamaki. “Wai badake nake maganaba ne kika tsaya kallona?”.        Numfashi Zinneerah ta sauke dan itama ta tafi wani tunani ne kuma daban. “Yi haƙuri Mama, tambayarce wlhy ban ganeba”.       “Basai kin fahimceniba dama ai. Amsa zaki bani”.       Da ƴar dariyarta tace, “A'a wlhy mama ban sanshiba sai a wannan karon da yazo gidan, bamma taɓa ganinsa ba nikam. To shi dama akace baya zuwa ma ƙasar a ina zan sanshi Mama?”.       Idanu Mmn sadiq ta zuba mata cike da nazari, kamar zatayi magana sai kuma tai shiru ta barta kawai. “Tashi ki kai Wannan ɗaki tunda barcin nasa yayi nisa”. Miƙewa tai ta ɗauka little da yay barci tunkan su dawo, sai da maman zatai masa wanka ya farka. Ana gamawa kuma ya sake komawa dan ya gaji matuƙa sunsha yawo.     Da kallo kawai mmn sadiq ta bita harta shige ɗauke da little ɗin. Harga ALLAH ranta cike yake fal da fargabar abinda zuciyarta ke ayyana mata a koda yaushe tun ganinta da Adnan ɗin. Shi kansa Abba data bashi labari zancen ya girgizashi, har yau kuma sun kasa daina tattauna maganar a duk sanda take tare da shi. Sai dai sun kasa fahimtar komai akan al'amarin sam. To gashi wadda ma suke da hope ɗin samun wani bakin zare a gareta tace bama tasanshiba itama. Duk da ta fahimci Zinneerah bata iya ƙarya ba wannan karon ta gagara gaskatata akan batun rashin sanin Adnan.     Washe gari da taci burin sake zaunar da ita akan batun sai ga Moos'ab wai yazo ɗaukarta dan zasu wuce da sassafe gobe idan ALLAH ya kaimu wajen hajiya iya. A take farin ciki ya bayyana ga Zinneerah tahau shiri, mmn sadiq kuma suka hau gaisuwa da Hajiya iya ta wayar Moos'ab ɗin itama. Sai da suka gama wayarne ta miƙe ta shiga haɗama hajiya iya ƴar tsarabar data san zataji daɗinta idan an kai mata. Cikin ƙan ƙanin lokaci Zinneerah ta gama shirinta tsaf suka wuce bayan sunyi sallama da Abba ta waya duk da dama jiya mama ta sanar masa fitar su Zinneerah ɗin, shine ya ɗanyi zargin ko wajen hajiya iya zasuje dama. To amma baiyi tunanin tafiyar haka gab ba.          Tunda suka iso gidan suka haɗu dasu Jamal suketa murnar tafiyar musamman ma ita da ko jirgin ƙasa bata taɓa ganiba😹, dan su huɗu kawai zasuje ashe. Ita, Jamal, Meenal, Bahijja. Anan ma koda ta dawo ba zaman sukaiba, fita suka sakeyi ita da Moos'ab ta ƙarasa abinda ya rage mata tunda wannan ne karon farko da zata ƙetare 9ja. Abinka da maganar kuɗi kuwa sai gashi a tsakanin fitarsu ta jiya data yau ɗin komai ya kammala, tunda dama ƙasar tamu waka sani ya sanka akeyi.     Suna dawowa sashen hajiya iya taje ta ɗakko abinda zata buƙata suka shirya kayansu tsaf duk da bawasu uban kaya suka ɗauka ba. Gara itama ta haɗama Hajiya iya da saƙonta na wajen mama da kuma abinda tace ta ɗakko mata. ________________★★         Abin mamaki yau sai ga Zinne ta danya mai tallar riɗi da gyaɗa a airport za'a ƙasar burtaniya. Babu wani ɓoye-ɓoye murnarta take nunawa a fili musamman da suka iso airport ɗin. Aiko su Jamal suka tasata gaba da tsokana suna dariya. Ko'a jikinta dan iya gaskiyarta ta faɗa. Bayan kammala tsarabe-tsaraben airport jirginsu ya ɗaga zuwa ƙasar burtaniya zuciyar Zinneerah cike taf da tsoro lokacin da jirgi zai tashi. Dan sai da ta ƙanƙame hannun Bahijja dake kusa da ita hanjin cikinta na wulƙitawa tamkar zata amayosa ta baki. Sai da jirgin ya gama dai-daita a gajimare ta buɗe idanunta tana sauke tagwayen ajiyar zuciya.        Tun Zinneerah na marmarin tafiyar da ɗoki harta fara ƙosawa, dan bata da jimirin dogon zama dama ita. Lokacin da jirgin ya samu kaiwa ga ƙasa jitai kamar tamafi kowa farin ciki tsabar gajiyar datai da ƙaguwar son ganin Hajiya Iya. A wannan gaɓar ba itace kaɗai baƙauya ba hatta dasu Jamal ɗin ƙauyawa suka koma. Dan shine karonsu na farko zuwa ƙasar london.        A yayin sakkowar tasu Jamal ne gaba. Ita a bayansa sai Bahijja da Meenal biye dasu. Kowanne yana jaye da trolly ɗinsa ƙarami a hannu. A kallo guda dolene su birge ka musamman da suka kasance a ganiyar shekarunsu na ƙuruciya..............✍ *_Masha ALLAH. Guys asha hutun weekend lfy ko😋😉😘😍😘😍🤗._* *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_* *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* *Page 29* _________________________ *MG’s SKIN CARE* (With us, your skin is elegant..) Are you guys  looking for where to buy ur skincare product @ mg's skincare is the best plug for you🤗 Do you wish to have that flawless skin that's free of all skin prblm Do you wnt to achieve that milky skin that turn heads wherever you go😉 Try mg's product nd I assure you you'll never use any other product except mg's product✅ Mg's will gv you the best out of all With mg's product ur skin is 💯 clear,fresh,smooth nd ur skin will absolutely glow all day💃 We have herbal whitening black soap now nd beauty set available Nd both the soap nd the beauty set is for all skin type everyone can use it🤗 Just gv it a try now nd see wonders✅ Chat:08062991549 Call:08064532391 Soap price:3k set:11k Follow us on Instagram@glow_with_mgs Facebook:mg's skincare Nd guess wht🦻 Duk Wanda zesiya Kaya daga yau Alhamis  30-9-21 zuwa Nanda 5days that is ranar talata there will be 20% off discount a soap nd the set😍so what are you guys waiting for hurry nd grab urs💃 now is  the time to glow🧖‍♀️ Pamper ur skin🦵 Shine like a bride 👰 be part of the glow team karkubari abaku lbr Just chat 08062991549 to plc ur orders😘 Do not forget to follow us👆 Like nd comment pls dearies😘 Patronize us🙏 mg's always serve you the best✅❤️ KAYAN MG’s SKIN CARE, GANGARIYA NE, SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI, KU GARZAYA KU SAYI NAKU KAYAN A KULI KALILAN DOMIN DAGA YAU TAFARA BONANZA. IDAN ANJE ACE DAGA ZAFAFA NE, AKWAI RANGWAMEN KUDI SOSAI, KYAU, INGANCI, RAHUSA.. SAI KAYAN MG’s SKIN CARE. _________________________ *Page 29* .............Meenal da ke ƙarshensu ce ALLAH ya bata ikon hango Yah Khalipha. Cike da jin daɗi da zumuɗi tace, “Guys ga Yah Khalipha can”.      Kusan duk a tare suka kalli inda ta nuna ɗin, hakan yayi dai-dai da ɗagowar Khalipha ɗin kuwa shima idanunsa suka hango masa su. A tare suka nufi juna cike da zumuɗi da farin ciki. Jamal ya shige jikinsa suma su Bahijja haka. Hannu ya miƙama Zinneerah alamar tazo itama sai ta noƙe kafaɗa tana murmushi. Sosai hakan da tai yay bala'in birgesa. Ya saki ƙannensa yana nufowa inda take fuska ɗauke da murmushi.       “Uhm Gimbiyar mata ke ta dabance fa”.      A bazata kalmar tazoma Zinneerah daga bakin nasa. Kamar yanda shima tazo masa a suɓutar baki. Ta ɗago manyan idanunta cikin nasa tana wani warosu irin alamar dai mamaki. Kansa ya girgiza mata shima yana waro nasa idanun dariyarsa na ƙara faɗaɗa. Babu shiri Zinneerah tai dariya da saka tafin hannunta ta rufe fuskarta dan taji kunya kuma.         Su Jamal dake musu dariya suma suka shiga gaishesa. Da kulawa ya amsa musu har ita Zinneerah data samu ta gaishesa a ƙarshe. Daga haka suka nufi taxi suka shiga yana faɗin, “Kuyi haƙuri fa nan kunsan ajiye mota ga talaka sai yayi nishi, motar gidan Yayanmu ya fita wajen aiki da ita”.           Cikin rashin damuwa da wannan suka shiga dariyar maganarsa. Sai ma suka koma tambayarsa Hajiya iya. A take ya fara basu labarin tana nan suna zuba tsiya da Aunty Farah. Yana basu labarin rikicin da akeyi a gidan suna kwasar dariya. Sai dai ko sau ɗaya Zinneerah bata saka baki a hirar tasuba. Murmushi kawai takeyi tana dai saurarensu da kallon hanya, zuciyarta na yaba ƙyawun ƙasar burtaniya da tsarinta. Tare da godiya ga UBANGIJI da ya bata damar ƙetare ƙasarta zuwa wata ƙasa batare da ko a mafarkinta hakan ya taɓa zuwa mata a cikin ranta ba.         Sai da suka iso inda ya dace ta kawo numfashi, waje ne daya samu tsararrun gine-gine da burgewa ga mai kallo. Babu wani hayaniya a wajen dan saima ka ɗauka ba gidaje baneba wata ma'aikatace. Su kansu sai bayan shigarsu ainahin cikin estate ɗin suka fahimci nannefa inda gidan Yayan nasu yake kenan. Sun haɗu da mutane ɗai-ɗai dake kai kawo, kamar masu fita da masu shigowa. Duk da kasancewar ginin estate ɗin a dunƙule yake waje ɗaya idan ka shiga baka da alaƙa dana kowanne, abinda kawai zakai nufar hanyar da zata kaika ainahin number naka building ɗin. Abinda kuma zai birgeka a rayuwar wajen babu ruwan wani da wani. Iyakarka da kowa hello hii idan an gamu.         Zinneerah daketa tunani a ranta taketa ayyana dolene turawannan su dinga ganinmu a banza. Dan duk wani jin daɗin duniya tamkar an tattarashine garesu. Basusan wani tashin hankalin rayuwaba sukam sam. A African kashe-kashen nan kawai ya ishi bawa da yunwa. Mu baga neman lahirarba duniyar da mukeso kuma kullum cikin wahal damu take. Gamu nan dai babu fasali ko wasu abubuwan birgewa duk mun fita a hayyacinmu.....     Nannauyan numfashi ta sauke saboda taɓatan da Bahijja tayi, “Haba Baby ina kika tafi haka ne?”.      Ɗan murmushi Zinneerah tayi da duƙar da kanta saboda kallon da Khalipha ya kafeta da shi. A hankali tajawo trolly ɗinta ta fito a cikin taxi ɗin tana gyara bag ɗinta. Jamal sarkin tsokana yace, “Ashe ni ƙauyancina ma kaɗanne ga wadda ta fini”.      Harara ta zuba masa da kai masa duka ya goce yana dariya. Khalipha ya girgiza kansa yana nufar ƙofar da zata sadasu da gidan na yayansu yana faɗin, “Uhm kudai tuna a ina kuke yanzun, kokuma ku koma Nigeria ba'a yanda kuka zo Burtaniya ba”.         Dukansu sun fahimci inda zancen nasa ya dosa. Dan haka duk sukai ƙaramar dariya kowa na faɗin albarkacin bakinsa.          Tunda suka shigo man kan kowa ya tsiyaye tas suka koma santin zuciya, sunaji a ransu dolene Aunty Farah da take hura musu hanci ashe tasan abinda ta taka. A ɗan corridor ɗin kafin ka shiga ainahin falon duk suka cire takalmansu suka saka cikin drawer dake a wajen alamar ba'a buƙatar ganinsu a waje. Sabbin Slippers na zaman gida Khalipha ya ciro daga cikin drawer ɗin ya miƙa musu. Kowa cira yay ya saka sannan suka shigo ainahin falon daya tsaru harya gaji. Sai ka rantse ma ba'a amfani dashi tsabar yanda yake fes. Tozali da Hajiya iya dake hakimce zaune ta ƙara ƙyau ya mantar dasu a ina suke da kuma santin. Tuni suka yadda bags suka nufeda da gudu cike da ihun farin ciki duk suka ɗaneta.     Itama dai cike da farin cikin ta tarbesu tana dariya dajin ƙaunar ƴan jikokin nata da kewarsu.         Cikin ɓacin rai Farah ta fito daga wani lungu danjin hayaniya na neman halaka mata kunnuwa, sanye take cikin wando dogo da riga da sukai mata ƙyau ainun, taku take cike da isa da ƙasaita fuska a yatsine. Taja ta tsaya turus tana dubansu alamar batama san da zuwansuba, dan sosai mamakin ganin nasu ke bayyana mata kan fuska ƙuru-ƙuru. Gashi kuma babu damar magana saboda hajiya iya. Sai dai wani kallon tsantsar takaici takema Khalipha da shima kai tsaye ita ɗin yake duba.      Kamar zatayi magana sai kuma ta fasa ta janye idanunta daga kansa ta maida kansu Meenal da sai a yanzu nasu idanun suka ganta. Duk da sunsan halinta na wulaƙanci sai sukai ƙoƙarin nuna murnar ganinta suna gaisheta cike da girmamawa kodan darajar wanda ya ajiyeta a gidan. A yatsine ta amsa musu ɓacin ranta na kasa ɓoyuwa, ta kafe Zinneerah da ko kallon inda take bataiba balle gaisheta da ido. Zinneerah da batasan tanaiba gaba ɗayama hankalinta nakan Hajiya iya batasan da zuwanta wajenba. Lura da kallon da Farah kema Zinneerah ɗinne yasa Khalipha kiran sunanta.     Ta juyo fuskarta ɗauke da murmushin da takema Hajiya iya ta dubesa. batare da yayi maganaba ya nuna mata Farah.      Da iya gaskiyarta tace, “Ayyah Aunty kiyi haƙuri bansan kin fito bane. Mun sameku lafiya? Yaya jikin Granny”.       (Buhun bura uban nan kayyasa) Farah ta ambata a zuciyarta tana kafe Zinneerah da wani shegen kallo, dan babu abinda ta hango a zancenta sai tsantsar rainin wayo a gareta. Batare data amsama Zinneerah ɗimba tabar wajen cike da takunta na ƙasaita da izza kai kace wata sarauniya ce.      Gaba ɗayansu da kallo suka bita. Hajiya iya ta girgiza kanta kawai tana mai nema mata shiriyar UBANGIJI a ranta. Yayinda su Jamal duk jikinsu yayi sanyi. Zinneerah kam ko'a jikinta, dan itako a masu mugun hali taga waɗanda suka taka Farah suka shanye mizaisa na Farah ya dameta. A bazata dariya ta siɓicema Khalipha ya kauda kansa gefe yanayi. Dan haka kawai ta bashi dariyar. Ita dake takaicin zamansa shi kaɗai ga wasu huɗun nan an kuma kwaso mata bayan Hajiya Iya. Sai dai kuma shi duk zatonsa tasan da zuwan nasune tun farko, amma a yanda tayi yanzu kam ya tabbatar Yayansu ya ɓallo ruwa yau.        Hajiya iya ce tai masa daƙƙuwa, ya ɗauke kansa yana haɗiye dariyar badan yaso ba. Itama maida hankalinta ta sakeyi gasu Bahijja dake gaisheta da tambayar lafiyarta, itama tana tambayarsu mutanen gida da hanya.         Sai da Khalipha yace, “Ashe ƙaryar gajiya kukeyi daman”.         “Yah Khalipha ganin Granny yasa gajiyarma ta gudu ALLAH”. Bahijja ta faɗa tana dariya. Murmushi yayi da kallon Granny dake magana da Zinneerah fuskarta a washe itama alamar tana cikin farin ciki yau fiye da kullum, sai yaji daɗi a ransa. Koba komai sa huta da mitarta na a maidata gida ita ta gaji da zaman kurkuku.       “Assalamu alaikum”.    Suka tsinkayi muryar Yayansu dake ƙoƙarin shigowa a bazata. A take duk sukai tsit da maida dubansu ga ƙofar. Khalipha ya miƙe ya nufesa ganinsa ɗauke da ledoji a hannu. Suma ɗin duk tsaye suka miƙe domin bashi girmamawa. Ledojin ya miƙama Khaliphan yana faɗin, “Thanks besty” ba tare dasu sunji miya faɗa ɗinba. Sai motsawar laɓɓansa kawai suka hanga.       Cikin haɗa baki sukace “Barka da dawowa yayanmu;       Sai yanzune ya kallesu fuskarsa da ɗan sakewa amma ba murmushi yakeba. Ya zame rigar sanyin saman suit ɗinsa yana hanging ɗinta a hanger ɗin dake gefensa, sannan ya ƙaraso cikin falon. Gaba ɗayansu gani sukai ya ƙara musu ƙyau da cikar haiba a idanu, kamar yanda Hajiya Iya da Yah Khalipha suka ƙara musu. Sai da yakai zaune ya harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya sannan yay magana. “Kun iso kenan?”.      Nanma a tare sukace, “Eh Yayanmu”. Batare daya kalli kowansuba ya jinjina kansa yana musu nuni dasu zauna. Babu musu suka zauna suna gaisheshi da tambayar jikin Granny.        “Ta warke ai, tunda gashi tana mana boren sai kunzo”.       Duk da ba cikin raha yay maganarba sai da sukai ƴan ƙananun dariya suna gumtse bakuna. banda Zinneerah da tun shigowarsa kanta ke a ƙasa murmushi yanzunma kawai tayi.     Granny dake hararsa tace, “Ai ni ba irin wasu bane da basa son mutane. Na saba jina cikin hayaniya da karaɗin ƴan jikokina ina jin daɗi”.      Karan farko ya saki lallausan murmushi yana miƙewa da ɗan taɓe baki, duban Khalipha daya kai ledojin abincin kitchen ya dawo yayi. “Besty ina zuwa”. Ya faɗa yana nufar hanyar da Farah ta fito ɗazun.        “A fito lafiya Yayanmu” Khalipha ya faɗa yana wata shaƙiyyar dariyar tsokana ƙasa-ƙasa da kaiwa zaune. Hajiya Iya data fahimci mi yakema dariyar tace, “Halan zargina ya zama gaskiya akan ƴar tutsun tasa? Tunda yanzu dai ba lokacin dawowarsa gida bane ba”.         “Ai da alama itace tai kiransa a waya ko kuma ta kira Mammah ita kuma ta kirashi, dan a yanda ta nuna mamakin ganin su Jamal na tabbata bai sanar mata zuwan nasuba. Kinsan wannan jikan naki shine dai-dai dasu ai, ya manna musu rashin m ya noƙe da barinsu suyita masifa”. Khalipha ya bata amsa magana ƙasa-ƙasa kamar wani munafiki yana ɗan dariyar ƙeta.        Dariya Hajiya iya tayi itama, “Kaɗanma ta gani indai nice Amina, ita Hindatun idan ta isa tazo gidan mana ta sameni ja'ira kawai. Nima nan saina saitasu a layi da ƙyau ai kafin nabar wannan garin da ba daɗin zamane da shiba”.       Sudai su Zinneerah da ba sanin ina zancen ya dosaba saurarensu kawai sukeyi, ita babban burintama azo a basu masauki ta kwanta dan kanta ciwo yake mata.        Shiko Khalipha dariyarsa ya cigaba da sha dan show ɗin na Granny na birgesa. Sosai a zaman nan nata take ƙara cusama Yayansu son ƴan uwansa a ransa da sanin muhimmancin su da girman zuminci. Shiko da alama yana haddace karatunta tsaf kuma yana aiki dashi. Dan rana ɗaya babu zato ya sanar masa ya kira cikinsu Haneef akan tahowarsu Meenal nan ɗin. Bashi ba hatta Granny tayi mamaki dan duk tsogumin da take masa nason zuwan su Zinneerah ɗin batai zaton zai saka suzo ɗinba. Aiko ranar yasha addu'a a wajenta da albarka.     To yanzu dai gasu sunzo, shi dai yasan akwai ƙura akan wannan zuwa nasu gidan, musamman daya kasance uwargida gimbiya Farah batasan da maganar zuwan ba, amma bara su zuba ido suga yanda wasan zai kasance dai, tunda shima yayan nasu ba kanwar lasa baneba.............✍        *_Masha ALLAH Guys, ina fatan asha hutun weekend lfy ko😋😉😘😍😘😍🤗._* *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_* *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* *Page 30* ________________________ *MG’s SKIN CARE* (With us, your skin is elegant..) Are you guys  looking for where to buy ur skincare product @ mg's skincare is the best plug for you🤗 Do you wish to have that flawless skin that's free of all skin prblm Do you wnt to achieve that milky skin that turn heads wherever you go😉 Try mg's product nd I assure you you'll never use any other product except mg's product✅ Mg's will gv you the best out of all With mg's product ur skin is 💯 clear,fresh,smooth nd ur skin will absolutely glow all day💃 We have herbal whitening black soap now nd beauty set available Nd both the soap nd the beauty set is for all skin type everyone can use it🤗 Just gv it a try now nd see wonders✅ Chat:08062991549 Call:08064532391 Soap price:3k set:11k Follow us on Instagram@glow_with_mgs Facebook:mg's skincare Nd guess wht🦻 Duk Wanda zesiya Kaya daga yau Alhamis  30-9-21 zuwa Nanda 5days that is ranar talata there will be 20% off discount a soap nd the set😍so what are you guys waiting for hurry nd grab urs💃 now is  the time to glow🧖‍♀️ Pamper ur skin🦵 Shine like a bride 👰 be part of the glow team karkubari abaku lbr Just chat 08062991549 to plc ur orders😘 Do not forget to follow us👆 Like nd comment pls dearies😘 Patronize us🙏 mg's always serve you the best✅❤️ KAYAN MG’s SKIN CARE, GANGARIYA NE, SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI, KU GARZAYA KU SAYI NAKU KAYAN A KULI KALILAN DOMIN DAGA YAU TAFARA BONANZA. IDAN ANJE ACE DAGA ZAFAFA NE, AKWAI RANGWAMEN KUDI SOSAI, KYAU, INGANCI, RAHUSA.. SAI KAYAN MG’s SKIN CARE. __________________________ *Page 30* ............Tunda ya turo ƙofar tsararren bedroom ɗin ya shigo da shashshekar kukanta ya faracin karo cikin kunnuwansa. Batare da damuwa da rashin amsa sallamarsa ba ya ƙaraso cikin ɗakin yana kallonta.       Zama yay a kujerar dake ɗakin tamkar bai damu da kukan nataba, a dakile yace, “Kinsa an tasoni daga office, gani to, mike faruwa?”.      A fusace Farah da ke a kwance tana kukan ta tashi duk da tun farko tasan da shigowar tasa dama. Hawayenta ta share tana kallonsa, sai dai yanda ya tsatstsare ta da idanunsa dake rikitata yasa ta janye nata danta samu damar faɗar abinda ke a bakinta.      “Babu abindama bai faruba. Ni wlhy bazan iyaba, tayaya wannan gidan zai ɗauki wannan gayyar dan ALLAH? Hidimar nawa zasuci ta kuɗaɗe tun daga kan abinci, ruwa da wasu wahalhalunsu?. Kawai sai dai muga yara batare da an sanar mana ba daga ni har kai. Ita bata tunani zamanta ma a takure muke bare tasa an ƙaro mana wannan yaran harda mara kunyar yarinyarnan data kusa min sanadin karayar ƙugu. Ko an faɗa musu rayuwar Nigeria da babu tsari da tanan iri ɗaya ce? Nasan duk Khalipha ne munafukin nan dan dashi zata haɗa bak......”         “K ya isa haka malama!!”. Ya faɗa a kausashe cike da nutsuwarsa. Dan inma baka saniba sai kace ba shine yay maganarba. Babu shiri Farah tai baya dan firgita tana kallonsa dan ya fito mata a zakinsa. Ya tsatstsare ta da birkitattun idanunsa yana nunata da ɗan yatsa. “Farah! Farah! Wlhy daga yau, daga yanzu, bakinki ya ƙara kuskure akan Granny saina zubar miki da haƙora a wannan gidan. Da kike cewa ta takura miki, mizai hana bazaki tafi inda zaki shaƙata ɗinba ke?. Ki kiyayeni Farah, ina ɗaga miki ƙafane kawai saboda ra'ayina badan kai ƙarata da kikeyi wajen mahaifiyata ba. Yara kuma nine na kawosu, idan kin isa dan ALLAH ki maidasu Nigeria yau ɗin nan stupid kawai”. Ya ƙare maganar yana karkaɗa mata yatsansa alamar gargaɗi na ƙarshe ya mike ya shiga toilet.        Da wani banzan kallo ta bisa, ji take tamkar ƙirjinta zai buɗe dan tsananin zafin da takeji na cika mata gida da akayi. Ta tsani takura a rayuwarta. Dama Mammah ta faɗa, zuwan Khalipha tamkar buɗe hanyar banbarowar danginsa ne garesa, dan sun sami ƙofar da suka kasa samu tuni. To ita kam sai dai ayi duk ma abinda za'ai waɗanan yaran bazasu zauna a gidan nanba, kai itama makirar tsohuwarnan mai ƙulla komai saita tafi.........          Fitowarsa ta katse tunaninta. Tasa hannu ta share hawayenta tana dubansa duk da kallon fuskar tasa kawai tsoro take bata ma. Zatai magana ya katseta dan yasanta da shegen naci da mita akan abu,  “Ki kwaso duk kayanki na ɗakincan tunda ba amfani kike da shi ba su zauna. Jamal ya zauna wajen Khalipha”.       A zabure ta miƙe tsaye tana dubansa hawaye na rige-rigen sakko mata. “Haba Yah Abdul-Mutallab, ɗakin nawa zan basu?”.       “Zama ɗakin kikeyi ne?”. “To amma dan ALLAH kodai bana zama a ciki ai dai sunansa ɗakina.  Suje ɗakin Granny su zauna mana”.      Wani banzan kallo ya mata idanunsa na sake canja kala. “Wlhy Farah idan kikace zaki bani ciwon kai akan zuwan yarannan tabbas zan baki ciwon zuciya ni kuma. Garama tun muna mu biyu kije ki kwaso abinda yake naki a can ki basu ɗakin, idan kuma kinƙi zakisha mamakina dan ina nan Abdul-Mutallab ɗin ɗin da kika sani”. Yana gama faɗa ya fice abinsa.          Khalipha kawai ya samu a falon, Granny taja su Zinneerah zuwa ɗakinta. Jamal kuma Khalipha ya kaisa nasa ɗakin. Duk ƙoƙarin ɓoye fushinsa da yake sai da Khalipha ya gane. Har cikin ransa baiji daɗiba. Shiyyasa yaso Yayan nasu ya haƙura da batun zuwan yaran tunda ba dole bane. Dan yasan Farah ba zataso suzo ɗinba. Tunda shima a yaya yake zaune gidan ma. Ita kanta Granny ɗan hali Farah ke nuna mata duk da tsufanta.....        “Ina suke?”. Ya katse Khalipha muryarsa cike da ɗaci. Cike da son kauda masa damuwarsa Khalipha ya miƙe yana dariya. “Ai Yayanmu kasan waɗanan yaran ƴan gatan Granny ne. Ta jasu ɗaki wai suyi wanka da barci. Shima Jamal yana wajena”.      Goshinsa yaɗan murza da furzar da huci yana lumshe ido. Batare da ya samu yanda yake so na daidaiton muryar tasaba ya nufi ɗakin yana cewa, “Taya zasu zauna a wannan ɗakin harsu huɗu zasu takura mata ai”.               Bin bayansa Khalipha yay yana magana cike da lallashi. “Yayanmu daka barsu isarsu zaiyi ALLAH, kaga munma huta da mitar Granny akan kaɗaici ko”.         “Bazai yuwuba Khalipha ɗakin Farah zasu koma”.      Dama abinda Khalipha kema gudun kenan. Ya ƙara buɗe baki zaiyi magana a dai-dai isowarsu ƙofar ɗakin AK ya ɗaga masa hannu alamar ya isa. Kai Khalipha ya dafe dan harga ALLAH baya buƙatar wata fitina akan zuwan yaran nan tsakanin yayan nasu da matarsa. Idan ta gaskiya za'abi sune da laifi, gashi kuma dama ba'a sanar mata ba tun farko. To amma yasan halin Yayan nasu tunda yace haka za'ayi dole a yarda ayi hakan”.            Daga can Granny tace, “Khalipha shigo mana”. Dan batai zaton AK ɗin baneba. Batare daya nuna shi ɗin baneba kuma ya murɗa ƙofar ya shiga da sallama ciki-ciki. Akan Zinneerah data fara wanka harta kwanta ya fara sauke idanunsa. Ya janye yana maidawa ga Granny dake gyarama Meenal kwalar riga. Bahijja kuma na toilet tana wanka.       “A'a wai dama baka komaba?”. Hajiya iya ta faɗa idanunta akan AK. Kansa kawai ya kaɗa mata yana kaiwa zaune. “Yanzu zan koma Granny, akan waɗannan dama na shigo, su koma can ɗakin ba'anan zasu zauna ba”.        Shiru tai tana kallonsa cike da nazari, sai kuma ta saki murmushi tana girgiza kanta. “Moddibo bazai yuwuba. Ka barsu anan muyi zamanmu zai ishemu”.        A karon farko ya kalleta shima. Ta kaɗa masa kanta da iya gaskiyarta tace, “Idan akai hakan ba'a ƙyautaba Moddibo. Inda itace taso su zauna mata a ɗaki dan kanta hakan ba damuwa bane. Amma ko nice miji yayma ƙarfa-ƙarfa akan danginsa su zauna min ɗaki zanga kamar an ƙasƙantar da nine. Ka barsu kawai suyi zamansu nan zai ishemu duka zaman kwana nawane ma”.       Bai iya yace mata komaiba, sai idanunsa dake ƙara canja launi ɓacin ransa na bayyana a fili, miƙewa yay a hankali batare da ya sake kallon kowansuba yace, “Saina dawo”. Daga haka ya fice yabar ɗakin..         Da ga hajiya iya har Khalipha da su Meenal da kallo suka bisa suma damuwa fal ransu. Suna son Yayansu dan shima yana son su. Ko rashin sakewarsa a garesu kowa yasan wannan halinsane da kuma yanayin rayuwar daya tashi a hannun Mahaifiyarsa. Amma sunsan badan ƙuntatawa a garesu yake musu hakaba.         Afusace Meenal tace, “Wlhy na tsani matarnan, danma taga ta samu Yayanmu mai haƙuri dajin maganar iyayensa shiyyasa takema mutane wani iskancin”.       “Barta hankali zamu koyama shegiya ai a wannan karon, tunda ta yarda mukazo gidan nan wlhy tayi gamo da gamonta kuwa”. Cewar Bahijja itama muryarta har zuga take.      Rai ɓace Hajiya iya ta kallesu tana musu daƙƙuwa. “Duk kunci iyayenku, ina ruwanku a cikin wannan zancen? Kunsan ALLAH duk wanda ya aikata wani abu a gidannan saina ɓata masa rai kuma ya koma gida. Ina kuma sake gargaɗinku shiga abinda ba'a sakakuba. Wannan ma ai rainine. Koyaya take ai matar Yayankuce taci albarkacinsa a wajenku marasa kunya”.       Duk ƙasa sukai da kawunansu alamar nadama. Dan dama sunsan wannan ba tarbiyyarsu bace. Hasalima Hajiya iya bata yarda da irin wannan maganar a gabansu, yau ma dai akasi aka samu. Haƙuri suka bata. Shima Khalipha ya ƙara musu faɗa sannan yace suzo suci abinci shima zai wuce school ne.      Duk wannan abin da sukeyi Zinneerah najinsu sarai, amma tai shiru kamar barci takeyi. da Khalipha ma yace a tadata taje cin abincin Hajiya iya hanawa tai. Catai su barta idan ta tashi sai taci nata tunda ta riga tayi barci.       A ɓangaren AK kuwa koda ya fito daga ɗakin hajiya iya ɗakinsa ya sake komawa. Zaune ya tarar da Farah da waya a hannu kamar ba ita ta gama kukaba yanzun. Ko'a jikinsa dan ya shirya mata tsaf, ya kuma san Mammah bazatazo gidanba dan yunda Hajiya Iya ta dawo daga asibiti taƙi zuwa, dama kuma ko asibitin bataje ta dubataba. Yanzu hakama tana China batare da sanin Farah ɗin ba, dan shekaran jiya ta wuce da daddare.         “Ki tashi ki tattara komanki dake a ɗakin nan ki maidashi ɗakinki. Karna dawo na taddaki anan ko wani abu naki”. Daga haka ya juya ya fice abinsa bai jira cewartaba.        Fuskarta bayyane da tsantsar mamakinsa ta bisa da kallo. Yana fita ta miƙe a fusace dayin wurgi da wayar hannunta. ‘Ni zaka wulaƙanta akan waɗanan banzayen ƴan uwan naka Abdul-Mutallab? Saboda nace bazasu zaunamin ɗakiba kaima zakace na bar maka ɗakinka bayan kasan nafi son zama a cikinsa. Na rantse da ALLAH sai yaran nan da tsohuwarnan sunbar gidannan zan baka mamaki kai dasu. Bazan sake zubar da hawayena akansu a banzaba mu zuba mu gani’.      Yanda take surutai ita kaɗai a kuma matuƙar fusace sai ta baka dariya. Ta koma tamkar wata zararriya. Sanin halinsa yasa bata ƙetare maganarsaba ta shiga tattare duk wani abu nata tana saka mai aikinta tana kaiwa ɗakinta. Sai dai kuma alwashin ƙuntata su Hajiya iya a gidan tacisa yafi sau shurin masaƙi.          Bayan ta gama tattare komai nata tsaf ta saka mai aikin nata sake gyara masa sannan ta jawo masa ɗakin ta rufo harda saka key. Su dai duk wannan abu dake faruwa su Hajiya iya basu saniba suna ɗaki abinsu tana hira da jikokinta. Abincin ma anan sukaci kusa da ita har Jamal da yana gama kimtsawa ya tafi can. Shiko Khalipha ya wuce school kamar yanda ya faɗa. ________________★          *_DANYA_*    Su inna sun kai Karima asibitin kusada. Likitocin nata faɗa ganin yanda jikinta ko ina sayin duka ga tsohon ciki da a yau ma yaketa nuna alamun zai fito duniya. Dan tunkan su wuce ashe naƙuda take shiyyasa jikin nata ya nema rikicewa.        Ɗakin haihuwa suka kaita dan shine yafi cancanta da ita a wannan halin. Daga haka suka shiga bata taimakon gaggawa. Suka bar su Inna a waje da zaman jigum-jigum. Tun suna zuba idanun jiran kukan jariri da wuri har al'amarin ya fara fin ƙarfinsu. Dan ihun Karima kawai suke jiyowa babu na jariri. A haka suka cinye wannan yinin suka shiga marece. mahaifiyar Babawo sai kiransa take a waya yaƙi ɗauka. dan tunda ta sanar masa abinda ke faruwa kafin su baro Danya bai sake yarda ya ɗaga mata wayaba. Dole sai ƙaninsa keta kaiwa da kawo akan komai har ALLAH ya sauki Karima wajen ƙarfe goma na dare.      Tsabar wahalar data sha daga ita har jaririyar sun fita hayyacinsu ko kukan kirki batayiba. Koda aka buƙaci kayan haihuwa babu abinda sukazo dashi asibitin. Aiko Nurse ta balbalesu da masifa dan haushi. Inna ta miƙe itama a fusace tana danƙarama Nurse zagi abu ya nema zame musu faɗa sai da aka lallashi Nurse ɗin da ƙyar. Dan sun fahimci Inna ma ba kanwar lasa baceba.       Wannan abin daya faru yasa gari na wayewa aka basu sallama suka dawo gida duk da Karima na buƙatar zama ƙarƙashin kulawar likita. To amma jarabar Inna bazaisa su iya cigaba da kulawa da Karima ɗin cikin kwanciyar hankaliba dan haka suka sallamesu..........✍            *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_* *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* *Page 31* _________________________ _*LAVENDER RESTAURANT..*_ _(Palace of mouthwatering food/delicacies)_ _IDAN KUKAJI GANGAMI DA LABARI, INA MASU SON INDA ZASU SAMU INGATACCEN ABINCI MAI DADI DA LAGWADA? KAI BA ANAN MUKA TSAYA BA, INA SABBIN AMARE? MAMAs, YAYYU? DA KANNEN MU MASU SON KOYAN GIRKUNAN YAN GAYU NA KASAR NIJERIYA DA KETARE?_ _*TO KU MATSO...! AT LAVENDER RESTAURANT GOTS YOU COVERED. ABINCIN KASASHE DA DAMA MUKE KOYARWA,,COME LETS UPGRADE YOUR FOOD TIME TABLE, MATSO KUSA YAR UWA GA DAMA DA ZAKI CANZA YANAYIN ABINCIN GIDAN KI, KOWA YASAN IYA SARRAFA ABINCI NA TAKA RAWAR GANI A GIDAJEN AURE. KAI KO BUDURWA CE INDE KIN IYA GIRKI ZAKIGA KOWA YANA HABA HABE DAKE.._* _*UNCLES, DADDIES, BROTHERS., NEWLYWED HUBBYS..! KU ZO KU YIWA ‘YAYAN KU, MATAN KU DA KANNEN KU RAJISTAR WANNAN HARKA TA KOYAN GIRKI.._* _*Lavender catering school zamuyi practical class. zamuyi 30 dishes continental,snack & desserts, traditional dishes, drink. Fee din 40k NE. phone number WhatsApp and call 09080299283 akwai discount na 5% ga mutum uku farko wadanda sukai register aranakun independence 1/10/2021 to 3/10/2021 Nigeria @ 61_* _*ZA’A FARA CLASSES RANAR 14/10/2021. WATO SHA HUDU GA WATAN OKTOBAR DA MUKA SHIGA YAU._* _*GIRKE GIRKE GUDA 30😫😨AKAN DUBU 40 KAWAI, HARDA BONUS NA SNACKS, DESSERTS, TRADITIONAL AND MODERN DRINK, GARGALIYA DA ZAMANI🥂WATA DAYA CHAS ZA’AYI ANA KOYAN GIRKE GIRKEN. _* _*KU SAKE KARANTA WANNAN BONUS DIN👇🏾RIGIJI GABJI_* _*Nigeria @ 61 _* _*COOKING COMPETITION!!!_* _*from lavender Catering ina masu son koyon girki ga dama zaku shiga gasarmu ta girki bayan kunyi register damu akan 10k,wanda yazo na 1zai shiga ajin mu free hade da wasu prize din na 2 da na 3 kuma zasu bayar da rabin kudine da wasu prize suma saura kuwa zasu ayi musu ragin 5% da wasu prize wannan gasa zamu yita ranar lahadi ne 3/10/21 zamu rufe registration na gasar ranar asabar_* _*LAVENDER RESTAURANT: NA GARIN KANO, CLASSES DIN AKWAI PRACTICAL AND ONLINE CLASS GA WANDA KE NESA_* ____________________ *Page 31* ..............Farah na kammala bin dokar AK na komawa ɗakinta shiri tai ta fita zuwa gidan Mammah, a garin suke amma ba'a street ɗaya suke ba. Su Hajiya iya basusan bata a gidanba sunata hidimarsu. Sai dai su duba lokacin salla su tashi suyi su koma tebirin hira. Sai da Khalipha ya dawo shima ya zauna suka ɗora cike da farin ciki.        Sunata zuba idon ganin dawowar AK gidan amma shiru, dan har lokacin dawowarsa aiki ya wuce babu shi. itama kuma Farah ɗin dawowar Khalipha gidan ya fahimtar dasu ta fita. Dan mai aikinta ta gama duk wani aikinta na wannan ranar ta tafi itama. Sai ya kasance sai su kaɗai ne a gidan kawai. Gajiya ta saka su Zinneerah kwantawa da wuri suka bar Yah Khalipha da Hajiya iya zaman jiran shigowarsa amma shiru.      Hankalin Khalipha ne ya fara tashi, duk da yasan bawai wani abune ya samu yayan nasu ba, bazai wuce dai ɓacin rai ya hanashi shigowa gidan ba. Miƙewa yay ya fita domin zuwa can ma'aikatar tasu ya dubashi ko yanacan idan bai tafi gidan Mammah ba, tunda yaga gimbiyar gidan da alama itama tana can. Zuwanta canɗin kuma bawai zai haifar da ɗa mai ido ba ga Yayansu, dan sai ta masa haɗin da sai Mammah ta ɓata masa rai musamman daya kasance itama akan abinda bata farin ciki da shine tunda itama Farah ɗin ai karatunta take bi. Tun farko an nuna mata su ɗin basu da muhimmanci da mutunci shiyyasa take kallonsu a hakan        Kusan a lokaci guda AK da Khalipha suka ɗora hannyensu akan handles ɗin ƙofar, shi da nufi fita, shi kuma da nufi shingowa. Sai dai AK dake ƙoƙarin shigowar ya samu nasarar turo ƙofar. Baya Khalipha yaja yana sauke ajiyar zuciya. Hakan yasa Yayan nasu binsa da kallon mamaki.       “Lafiya kuwa? Ina zakaje?”. Yay maganar yana kallon agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa da duban Khalipha ɗin.      Cikin damuwar ganin yanayinsa Khalipha yace, “Yayanmu dama kai zanbi hankalin Granny duk ya tashi da rashin dawowarka akan lokaci.       Duk da damuwar dake tattare da fuskarsa da zuciyarsa sai ya saki guntun murmushi kawai yana miƙama Khalipha ɗin kayan hannunsa. Shi kuma ya hau zame coat ɗin saman sult ɗinya yay hanging ɗinta. Takalman ma ya zame ya ajiyesu a ma'ajiyarsu ya saka Slippers ɗin shiga cikin gidan. Batare da yanzuma yay maganaba ya nunama Khalipha hanya alamar suje.        Tunda suka shigo falon idon Hajiya iya na a kansa. Shima inda take ya nufa kai tsaye, batare da yayi maganaba ya zauna kusa da ita yana sauke numfashin gajiya da lumshe idanunsa. Hannunsa hajiya iya ta kamo cikin nata tausayinsa da ƙaunarsa na ratsata. Batare da ta damu da sanin matsalarsaba ta fara magana cikin lallashi.         “Bansan yaushe ka fara zama mai rauni hakaba Moddibo? Dan nidai moddibo dana sani ada mai yawan haƙurine da juriya da kawaici akan al'amuran rayuwa. Sannan ba komai yakema zafi ba sai yayi nazari akansa”.        Lumsassun idanunsa dake cike da gajiya dason yin barci ya buɗe yana ɗagowa zaune sosai, ɗayan hannunsa ya ɗora kan nata yana dubanta cike da sonta da ƙaunarta. cikin muryarnan tasa mai tarin kamala da rashin sakewa yace, “Har yanzu Moddibonki na a yanda kika sanshi Granny. Abinda kike tunanin ba shine damuwarsa ba”.        “Miye damuwarka idan ba matsalar matarkaba to Moddibo?”.        “Haba Granny, ni yanzu har akwai wata matsala ta Farah da zata sakani a matsala? Wlhy sam ba itace tushen damuwataba. Ɗazunma ta taka sahun ɓarawone kawai shiyyasa kika ganni kamar a cikin zafi. Wani ɗan matsalane akan business insha ALLAH kuma komai zai dai-daita ki tayani addu'a”.       Sosai Hajiya iya ta gamsu da maganarsa. Dan tasan shi mutumn kai tsaye da bai iya ɓoye-ɓoye ba ko ƙarya akan abinda ba haka yakeba. Tunda yace ba Farah bace matsalar da gaske ba itaɗin baceba. Ajiyar zuciya ta sauke tana sake kammo hannun nasa cikin nata. Da kulawa tace, “Muna muku addu'a a koda yaushe Moddibo, kuma zamu ƙara insha ALLAH. Duk wanda ya manta da ALLAH shike ambato yaya zaiyi”.         Murmushi yayi dake bayyanar da gajiyarsa mai sanyi, ya jinjinama Hajiya iya kai yana duban Khalipha dake murmushi shima, “Hakane Granny, shiyyasa a koda yaushe nakeson kasancewa a tare dake. ALLAH ya ƙara miki lafiya da tsahon rai mai amfani”.         “Amin ya rabbi”. Ta faɗa tana murmushin itama da shafa kwantaccen sajensa.       Mikewa yay yana faɗin, “A gajiye nake Granny, bara naɗanje na kwanta ina baƙin naki ne?”.        Khalipha ne ya bashi amsa da cewar, “Tab Yayanmu ai duk sunyi barci. dan Beauty ma da tafi kowa ragantaka tariga kowa kwanciya”.        Kallon Khalipha yay gira a ɗage kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa. Gaba yay a binsa murya a cinkushe yace, “Sai da safenku nidai nayi ciki”.       Da ALLAH ya tashemu lafiya suka amsa Hajiya iya na nufar ɗaki, shima Khalipha sai ya miƙe ya nufi nasa ɗakin bayan ya kashe komai na falon. *WASHE GARI*        Hajiya iya ce ta tashi su Bahijja da ƙyar domin yin sallar asuba. Dan har yanzu akwai tarin gajiya tattare dasu. Suna idar da sallar ma tsaresu tai sukai zaman yin azkar. Kowa yana tura baki gaba yayi sannan suka koma suka sake kwanciya. Bata hanasuba dan tasan akwai su dason barci dama.        Barcinsu suka sake kwasa sosai, dan basu farkaba sai kusan tara shima hajiya iya ce ta tadasu. Bayan duk sunyi wankan haɗuwa sukai suka gyara ɗakin sannan suka fito falo inda hajiya iya take. Fitowarsu dai-dai da shigowar mai aikin Farah. Cikin girmamawa ta gaida Hajiya Iya. suma su Zinneerah ta dubesu tana musu sannu da zuwa dan jiya tsoron uwar ɗakinta ya hanata musu.        ★★ A ɓangaren Farah kuwa. Koda ta fita gidan a jiya kai tsaye gidan Mammah ta tafi, sai dai tayi rashin sa'ar iske Mammah ta wuce ƙasar China jiya akan harkokin business ɗinta. Hakan baisa ta damuba ta shige tsohon ɗakinsu da Adilah tai kwanciyarta. Dan ita tana ƙasar U.S yin wani course na shekara ɗaya da rabi.       Mama Zaliha da suke kira da Mahma ce kaɗai a gidan, itama Yayace gasu Mammah anan gidan take zaune tun bayan rasuwar mijinta acan Morocco. Takaicin halin Farah yasa taƙi tambayarta miya kawota gidan har sai safiyar yau. Bayan ta idar da sallar asuba ta sami Farah a ɗakin nasu itama ta idar da sallan tana karatun Al-Qur'ani. Zama tai a bakin gado tana kallon ɗiyar ƙanwar tasu da gata ya maidata kamar wata shashasha. Tabbas ta yarda da maganar hausawa da sukance gata mugun ciwo. Dan kuwa shine yayma Farah katutu har bata banbance fari da baƙi a cikin al'amuranta.          Sai da Farah takai aya sannan ta rufe Al-Qur'anin tana duban Mahma. Cike da girmamawa da shagwaɓanta ta gaidata kamar yanda ta saba. Mahma dake dubanta da kulawa itama tace, “Miya faru kikazo nan kika kwana auta?”.       Baki Farah ta tura gaba idanunta na cika da ƙwalla. Kanta tsaye cike da gadaranta tace, “Mahma na baro masa gidanne su zauna shi da dangin nasa”.       “Kimin magana a warware zanfi fahimta fiye da bani ita a dunƙule. Ko kina nufin har yanzu matsalar zuwan Kakar tasane bai kareba kuma?”.        “Ni bashi bane Mahma, ai nace dai na haƙura wannan, amma yanzu dan tsabar wulaƙanci shine ya ƙara kwaso min ƙannensa da wata yarinya da bansanma miye alaƙarsuba aka kawo batare da ya sanar min zuwansuba”.       “Humm” Mahma ta faɗa tana murmushi da girgiza kanta. Sai da ta gama yima Farah kallon nazari na kusan sakkani arba'in kafin ta gyara zamanta da ƙyau. “Farah anya kuwa kinsan mikikeyi? Gaki dai mace mai tarin ilimin addini dana boko, wayayya wadda ALLAH yayma baiwa kala-kala da ni'imomi, sai dai kuma shashasha ce. Wai sai yaushe zaki daina biyema Hindatu da Zakiyya ne? Farah kinsan ko muhimmancin nuna darajar dangin miji da mutuntasu ga miji kuwa? Kodan kina ganin kullum Hindatu na aibanta dangin Abdul-Mutallab shiyyasa kike ganinsu kamar marasa daraja a idanunki? Bara na faɗa miki gaskiya idan zaki ɗauka. Hindatu mahaifiyarsa ce, zai iya jurewa ya shanye yakumayi haƙuri akan duk wani tarkace da zata jingina danginsa da shi koda yanajin zafin hakan. Keko matarsace duk da kina ganinku jini ɗaya da kuma fawar da kike samu ga mahaifiyarsa zai iya ajiyeku akansu wlhy. Shin bazaki godema ALLAH da ni'inar da yay miki na samun miji irin Abdul-Mutallab mai kawaici da haƙuri ba. Dan wlhy na tabbatar badan soyayyar da yake miki ko tirsasawar hindatu a garesaba yake ƙyaleki. Haƙurinsa da sanin ya kamatansane kawai ke rinjayarsa wajen baki uziri kafin ki kaisa bangon da bazai iya jurewaba. Idan kuma kikai wasa zakiyi nadama a lokacin da guri ya ƙure miki ki kuma rasa samu damar gyara komai. Saboda zuwan wannan yaran kawai ya isa nuna miki gudin halinki yasa ya guji ya faɗa miki ki sanarma mahaifiyarsa ta hanashi, kinga kuwa sai ki dawo hankalinki da irin masu halinki dan mata da yawa sunada wannan bazan halin shiyyasa da yawa duk son da mazansu ke musu sai kiga yana raguwa harsu fara tunanin ƙaro musu abokiyar zama koda kuwa babu haka a tsarinsu. Ni nasan babu wani ilimin zama da miji da baki dashi Farah. Dan kuwa idan da dama ma sai dai ki koyar da wasu. Amma tun zuwan ƙaninsa gidanku kin watsar da komai na ingatacciyar rayuwar aurenku. Kin maida hankalinki wajen kawo ƙararsa kullum da kushe danginsa da nuna ƙyamatar su kusancesa. Anya baƙya tunanin cewa akwai matsala? Baƙya tunanin hankalinsa zai iya fara karkata bisaga ƙudirin dangin nasa nason ƙara aurensa. Yanzufa cikine dake, amma ki duba ko'a jikinsa. Yanda ya nuna murnarsa da farin cikinsa akan wancan cikin da kika samu ya zube bai nunaba akan wannan. Banama tunanin ya sanar da kowa a cikin dangin nasa, tunda dama wancan karon hanashi faɗa musu kukayi wai sai dai suji kin haihu. Sai gashi baki haihunba kuma sabida ALLAH ya rubuta cikin ba zaunanne baneba. Wlhy ki dawo hayyacinki, ki dawo da ingattacciyar rayuwar aurenki kamar farko domin cigaba da damƙe zuciyar mijinki. Duk wannan gantali da shirmen naki babu inda zai kaiki sai komawa baya a garesa. Dan kullum sabbin halayyarki dusashe taurarenki yakeyi a wajensa. Ki dinga daurewa wajen danne wannan zafin kishin naki da kika gada kodan tsare martabarki. Wlhy duk yanda kuke zaton kunada kishi na damaku na shanye. Amma tunda nai haƙurin zama da kishiyoyi har biyu a lokacin rayuwar aurena ya kamata kuma ku saduda. Dan rayuwarma nawa takene baki ɗaya. Daga randa UBANGIJI ya bukaci ganinka dole ka amsa kiransa koka shirya kobaka shiryaba. Duk wata dukiyarka da suna da ilimi da mulki da nasaba da koma miye da kake takama dasu bazasu amfanar dakai da komaiba sai ƙyawawan halayenka da ibadarka. Dan haka sai kisan inda ke miki ƙaiƙayi kibar wannan shirman da kika ɗakko mara hanyar ɓillewa ki koma Farah ɗinki dana sani ada mai hankali da sanin yakamata akan rayuwar aurenta. Ki kuma tashi ki shirya ki koma gidan mijinki tunkan ya fahimci kinbar gidan. Ki kuma kama kanki akan zaman dangin nasa. Ki kiyayi yawan kawo kararsa dan kina zubar masa da kimarsa a idanunmu alhalinsa dan kece sheɗaniyar. Dan wlhy idan Hindatu ta dawo naji kin kira wayarta akan wata matsalar danginsa da kaina zan saka Abdul-Mutallab ya ƙara aure......”       Da sauri Farah ta ɗago ta duba Mahma idanunta na kawo hawaye. Mahma tace, “Kalleni da ƙyau da gaske nakeyi, dan ko ita Hindatun sai dai tazama ƴar kallo bareke da kike matsayin ƴa. Idan zakije ki kama kanki kije ki kamasa kafin na saitaki a layin daya dace da ke tunda ke shashash ce. shin gata haukane ma kenan?”.          Cikin kuka Farah tace, “To amma Mahma shima idan yazo kimasa faɗa ya daina min ihu banaso. Sannan ya daina nunamin kamar danginsa sun fini a wajensa tunda nima dai ƴar uwarsace kuma jininsa mafi kusanci”.        “Naji zan masa. Amma sai naga gyara daga gareki sannan.”        “Insha ALLAH zan gyara, kuma zanyi duk yanda kikace”. A karan farko Mahma tai murmushi da kamo hanunta jikinta. Tace, “Yauwa kokefa ƴar albarka. Amma duk kin wani susuata kanki tamkar wata shashasha wadda batasan ciwon kantaba da mutuncinta. Karki sake kiyi saken da Abdul-Mutallab zai kufcemiki dan zaki dawwama a dana sani har ƙarshen rayuwarki kuwa”.      Kanta ta jinjinama Mahma cike dajin daɗin nasiharta tana kwantar da kanta a bisa cinyarta. Sake kwantar da murya Mahma tayi ta lallasheta sosai da ƙara mata shawarwari sannan ta sakata tai wanka ta shirya, ko breakfast batai zamanyiba ta kamo hanyar dawowa gida zuciyarta fal tsare-tsaren dawowa da martabar aurenta daga yau kamar yanda take ada kafin zuwan Khalipha daya susutata saboda rashin son ganin dangin AK raɓe dashi bisa huɗubar Mammah............✍               *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_* *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* *Page 32* ___________________ _*LAVENDER RESTAURANT..*_ _(Palace of mouthwatering food/delicacies)_ _IDAN KUKAJI GANGAMI DA LABARI, INA MASU SON INDA ZASU SAMU INGATACCEN ABINCI MAI DADI DA LAGWADA? KAI BA ANAN MUKA TSAYA BA, INA SABBIN AMARE? MAMAs, YAYYU? DA KANNEN MU MASU SON KOYAN GIRKUNAN YAN GAYU NA KASAR NIJERIYA DA KETARE?_ _*TO KU MATSO...! AT LAVENDER RESTAURANT GOTS YOU COVERED. ABINCIN KASASHE DA DAMA MUKE KOYARWA,,COME LETS UPGRADE YOUR FOOD TIME TABLE, MATSO KUSA YAR UWA GA DAMA DA ZAKI CANZA YANAYIN ABINCIN GIDAN KI, KOWA YASAN IYA SARRAFA ABINCI NA TAKA RAWAR GANI A GIDAJEN AURE. KAI KO BUDURWA CE INDE KIN IYA GIRKI ZAKIGA KOWA YANA HABA HABE DAKE.._* _*UNCLES, DADDIES, BROTHERS., NEWLYWED HUBBYS..! KU ZO KU YIWA ‘YAYAN KU, MATAN KU DA KANNEN KU RAJISTAR WANNAN HARKA TA KOYAN GIRKI.._* _*Lavender catering school zamuyi practical class. zamuyi 30 dishes continental,snack & desserts, traditional dishes, drink. Fee din 40k NE. phone number WhatsApp and call 09080299283 akwai discount na 5% ga mutum uku farko wadanda sukai register aranakun independence 1/10/2021 to 3/10/2021 Nigeria @ 61_* _*ZA’A FARA CLASSES RANAR 14/10/2021. WATO SHA HUDU GA WATAN OKTOBAR DA MUKA SHIGA YAU._* _*GIRKE GIRKE GUDA 30😫😨AKAN DUBU 40 KAWAI, HARDA BONUS NA SNACKS, DESSERTS, TRADITIONAL AND MODERN DRINK, GARGALIYA DA ZAMANI🥂WATA DAYA CHAS ZA’AYI ANA KOYAN GIRKE GIRKEN. _* _*KU SAKE KARANTA WANNAN BONUS DIN👇🏾RIGIJI GABJI_* _*Nigeria @ 61 _* _*COOKING COMPETITION!!!_* _*from lavender Catering ina masu son koyon girki ga dama zaku shiga gasarmu ta girki bayan kunyi register damu akan 10k,wanda yazo na 1zai shiga ajin mu free hade da wasu prize din na 2 da na 3 kuma zasu bayar da rabin kudine da wasu prize suma saura kuwa zasu ayi musu ragin 5% da wasu prize wannan gasa zamu yita ranar lahadi ne 3/10/21 zamu rufe registration na gasar ranar asabar_* _*LAVENDER RESTAURANT: NA GARIN KANO, CLASSES DIN AKWAI PRACTICAL AND ONLINE CLASS GA WANDA KE NESA_* ____________________ *Page 32* ............Shigowarta gidan yayi dai-dai da dawowar Khalipha daga yo musu takeaway daya fitayi. Kamar koda yaushe shine ya gaisheta sabida halinta nason nuna isa. Koda ta shigo gidan ta kalli ko'ina sai taga yamata yanda takeson tsaftarsa duk da an cika matashi, dan Farah mace ce mai tsafta, sannan duk wani abu da mace keyi dan ganin ta faranta ran miji Farah ta iyashi. Matsalarta kawai zafin kishi da hawa kan karatun su Mammah naƙin danginsa, dan tunda Khalipha yazo gidan ta dainama Adnan mafi yawan abubuwan da take masa na kulawa, ita burinta kawai Khalipha yabar mata gida. Shiko ya fita taurin kai yay kunnen uwar shegu da ita.          Samun komai yanda takeso yasata batayi ƙorafi ba ta shigo cikin kame kai da tsare gida ta gaida hajiya iya. Yanda take cika da batsewa yasa suma su Jamal gaisheta suna ƙoƙarin kama kansu.      Ko kaɗan hajiya iya bata nuna mata komaiba ta karɓa mata gaisuwarta hardasu tsokana. Batare data kula tsokanar da Hajiya iyan kemataba ta nufi ɗakin AK tana harar Zinneerah da ƙudirta abubuwa masu yawa akanta. Dan har cikin ranta tanajin kishin zamanta a gidan fiye dasu Bahijja. Bakomai yasata jin sassauci akan su Bahijjan ba sai sanin uba ɗaya suke da AK babu wani maganar aure a tsakaninsu. Sai dai kishin cika mata gida da sukayi. Zinneerah kuwa tasan babu uwar da suka haɗa na shaƙiƙanci shiyyasa takejin zafinta. Itafa sabida shegen kishinta ko ƙawayenta bata yarda su raɓeta balle suzo mata gida. Tafi ganewa ayi catin ko waya yafi sauƙi ƴar nesa-nesa. Suma fahintarta yasasu janye jikinsu gareta suka bita yanda takeso duk da wasunsu ma sunyi aure. Tsaron nata kuma baisa wasu a cikinsu gagarar bibiyar mijin nataba acan waje batare da sanintaba. Danma shi AK ɗin na ƙoƙarin taka musu burki dan ba ɗaukar wargi ko shirme yake ba shima ɗin aƙidarsa tayi yawa.      Tsaye ta samesa gaban Mirror yana fesa turare. Ta bishi da kallo cike da so da ƙauna da kishinsa mai yawan gaske, wanda ita kanta batasan adadinsaba. Sosai yayi ƙyau cikin pitch suit ɗin nasa da suka dace da kalar fatarsa mai sheƙi da ɗaukar idon mai kallo. Ga abu mafi soyuwa a gareta tare dashi shine kwantaccen sajensa da sumar kansa dake dai-dai misali dan ba tarata yayba da yawan tsiya. Tana nan dai-dai misali.     Duk da yaji shigowar tata bai fasa abinda yakeyiba. Sai da ya ajiye gwangwanin turaren ya gyara zaman tie ɗinsa sosai da ƙara kwantar da sajensa sannan ya juyo gareta yana zuba mata manyan idanunsa masu cikar gashi da haske. Gasu da kwarjini masha ALLAH tamkar ba namiji ba. Haddace kowanne kalar kallonsa da ma'anarsa ya sakata risinar da kanta ƙasa. Kafinma yay magana tace, “I'm very sorry, bada niyyar kwana najeba zazzaɓine ya rufeni acan ka tambayi Mahma ma”.          Janye idanun nasa yayi kawai yana girgiza kansa. Ya ɗauka agogonsa ya hau ɗaurawa batare da yace mata komaiba. A hankali ta tako garesa tana kama hanun da ɗage wanda yake ƙoƙarin ɗaura agogon dashi. Sakar mata yayi babu musu ta ƙarasa saka masa. ta sake ɗaukar wasu kalolin gwangwanayen turaren ta fesa masa tana ɗan murmushi, kafin kuma ta rungumesa cike da so da ƙaunarsa.        Ajiyar zuciya suka sauke a kusan tare. Ya lumshe idanunsa da zagayeta da hannayensa shima yana lumshe idanunsa. Dan da gaske shima yayi kewar tata. Tunda suka dawo daga 9ja taƙi kwantar da hankalinta waje guda ta nutsu kullum da shirmen da take tashi musu dashi a gidan. danma wani abun tana shakkarsa shiyyasa take tsoron aikatawa. Fatan da addu'arsa shidai dama a kullum ALLAH ya gyarata ta koma Farah ɗinta daya sani ta baya mai tattalinsa da son farin cikinsa akoda yaushe.       Ɗagota yayi yana mai tsare ƙyaƙyƙyawar fuskarta da kallo mai cike da ma'anoni masu yawa. “K baki gajiya dakai ƙarar mutane kullum wajen iyayenki?”.        Cikin marairaice murya da shagwaɓa duk da ranta fal yake da tsantsar takaicin zaman su Hajiya iya gidan ta sake narke masa. “Ai dai nace kayi haƙuri, kuma kaima kasan a yanayin da nake shiyyasa nake shiga saurin fushi”.         Kansa kawai yaɗan rausayar yana sauke idanunsa akan cikinta. Sai kuma ya ɗaura hannunsa saman cikin  tare da ranƙwafawa ya sumbacesa sannan ya ɗago. “Dolene inzo naima babyn nan gargaɗi ya bar rikitamin ke kina bani ciwon kai”.       Karan farko tai ƴar dariya da sake rungumesa tana maijin tsananin daɗi. Dan tunda ta samu cikin nan bai taɓa nuna kulawarsa kamar ta yau ba. Kodan ta kasa kwantar masa da hankaline oho, dan wancan cikin daya zube lokacin da aka sanar masa da samuwarsa tamkar zaiyi hauka dan daɗi, yabi ya rinƙa tattalinsa da nuna zaƙuwar ganin ya fito duniya. Daya zube ɗin kuwa hardasu ƙwalla yayi, yabi ya shiga damuwa sosai, sai zuwan Khalipha gidan ne ya sakashi komawa normal life ɗinsa. yayinda ita kuma suka fara samun matsala daga nan.         Shima ƙaramar dariyar yayi yana ɗagota. “Uhm kinga barni naje mu gaisa dasu Granny inada meeting 11am”.      Duk da zuciyarta ta sosu da zancensa sai ta daure ta kanne, koba komai anci mata lokaci ai tunda gashi lokacinta sai ta raba dasu. Da basa gidan kuwa itace zata kasance da shi har lokacin fitar tasa ta cika. A tare suka fito dan tayi alƙawarin sai dai suci lokacin nasu tare itama dan bazata barmusu ba.          A dining suka iske su Hajiya iyan zasuyi zaman karyawa da abincin da Khalipha yaje ya sayo. Mai aikin Farah kuma ta shirya musu shi a dining tamkar a gidan aka girka shi. Khalipha na daga tsaye bayan Granny suna magana dan shi fita zaiyi. Juyowa yay saboda jin ƙamshin turaren yayan nasu da takun sa da baya ɓoyuwa ga duk wanda ya sanshi. “Barka da asuba Yayanmu”. Ya faɗa dai-dai suna ƙarasowa wajen.         Hannunsa AK ya kamo cikin nasa yana faɗin, “Halan yanzu ka tashi kake kiran asuba likita?”.       Fuskar Khalipha da murmushi yace, “Ai ni harma fita nayi naga gari Yayanmu, kai nedai nake tunanin yanzun ka tashi shiyyasa na faɗa”.         Kafin AK ɗin yace wani abu Granny dake kallonsu cike dajin daɗi da sha'awar yanda shaƙuwarsu take wanzuwa cikin ƙanƙanin lokaci tace, “Ni nama zata yau bazai fitaba ganin har wannan lokacin bai fitoba. Bayan kuma nasansa shi baya saɓa lokaci”.         Kallonsa ya maida ga Hajiya Iyan tare da jan kujerar kusa da ita ya zauna. “Yau meeting kawai nake da shi Granny shiyyasa na koma barci bayan sallar asuba. Ina fatan kin tashi lafiya?”.         “Lafiya lau na tashi, sai dai waɗanan akkunayen da suka cikani da surutu jiya”.       “Ai kece kika gayyatosu”. Ya bata amsa idonsa na sauka akan Zinneerah dake facing kujerar daya zauna. Tun zuwansa wajen tai ƙasa da kanta tana juya cokalin hannunta cikin abincin da sam ba daɗi yake mataba, wai a hakanma sai da Khalipha ya zaɓo musu wanda yasan zasu iyaci suji daɗinsa tunda ba sabawa sukai da abincin nan ba.        Janye idanun yayi cike da basarwa yana ɗaukar tea ɗin Hajiya iya ya fara sha. Hakanne ya bama Jamal damar fara gaidashi. Sai Meenal ma ta gaisheshi. Itama Bahijja haka. Zinneerah ce ƙarshen gaishesan batare data yarda ta kalli inda yakeba.      Dukansu amsa musu yay kamar yanda ya saba cike da rashin sakewa. Hakan da yayi yayma Farah dake bayansa tsaye daɗi, tai wani ƙasaitaccan murmushi da ɗora hannunta kan kafaɗarsa tana sake matsowa jikinsa. Cike da yanga da ƙasaita tace, “Za kaci wani abune anan ɗin?”.       “No, shayin Granny kawai ya isheni”. Daga haka ya maida hankalinsa kan hajiya iya ya fara magana ƙasa-ƙasa batare da kowansu yaji mi yake faɗa ba. Hakan kuma sai ya soki zuciyar Farah tabar wajen fuska a haɗe. Khalipha ya danne dariyarsa da ƙyar yana binta da kallo, tana gab da shigewa yace, “Kunga nikam bara na wuce school zanyi latti”.       Ɗagowa AK yayi ya dubesa. “No ka jira na kammala mu wuce tare kusa da school ɗinku zanje nima”. “Okay thanks you Yayanmu”. Khalipha ya faɗa yana jan kujerar data rage ta dining ɗin ya zauna.       Farah ko dake ƙoƙarin shigewa ɗakin jin zancen nasu ya sakata dakatawa. Kamar zata juyo sai kuma mita tuna oho mata ta cigaba da tafiya harta shige ɗakinta tana taunar lip ɗinta na ƙasa da ƙarfi.     Sosai zamansa shi da Khalipha a wajen ya saka Zinneerah shiga takura, garama Khalipha tana ɗan sakewa da shi. Amma wannan shugaban tsare gidan da ƙasaitar gaba ɗaya tare mata iska yake idan yana a waje. Sai dai kuma takan tsinci kanta cikin jin daɗi dan tana kallon little ɗinta tattare da shi. Yanzunma murmushi ta sake a bazata saboda faɗo mata a rai da Little yayi, dan hutun nan na kwanaki huɗu da tayi ba ƙaramin shaƙuwace ta sake shiga tsakaninta da yaron ba. Har takai tanajin kamar ta ɗakkosa su taho tare.     AK da sarai yaga murmushin nata ya ɗan kafeta da kallon sakanni a kaikaice ya ɗauke kansa, a ransa kuwa tambaya yake komi ya bata suga?. Baida mai bashi amsa dan haka ya miƙe dayin ɗan hugging Hajiya iya ta gefe ya sumbaci hannunta daya kamo. “Kimin addu'ar cin nasara, dan zamane mai muhimmanci zanje Granny”. Ya ƙare maganar idanunsa na faɗawa cikin na Zinneerah data ɗago a bazata. Yanda ya juya idanun da wani salo ya sakata saurin maida nata ƙasa ta risinar zuciyarta na matuƙar harbawa.       Kasancewar babu wanda ya lura da abinda ya faru suka rakashi da addu'ar samun nasara harsu Jamal. Zinneerah dai akan laɓɓa ta fisgo tata addu'ar da ƙyar ta furta. Hayanr fita ya nufa yana saka rigar sanyinsa a saman suit ɗinsa fuska ɗauke da wani ɓoyayyan munafikin murmushi.      Suna ficewa Zinneerah ta saki ajiyar zuciya. A take su Jamal duk suka kalleta. Hajiya iya kuwa ta saki wata ƴar dariyar data basu mamaki itama, sai dai koda suka maida dubansu gareta sai ta basar. Babu wanda ya sake magana dan dokace hakan ga Granny indai anacin abinci. Sai da suka gama ita dasu Bahijja suka gyara wajen domin taimakawa mai aikin da suke ganin kamar aikin gidan ya mata yawa saboda ƙaruwarsu.      Yau ma dai hirarsu suka sha tare da kakarsu. Daga ƙarshe Zinneerah ta bama Hajiya iya tsarabar mmn sadiq tare da saƙon zungureriyar wasiƙa da batasan ta micece ba itama. Hasalima sai yanzu da ake buɗe kayan duk suka gani. Jamal ya ɗauka zai buɗe Hajiya iya ta girgiza masa kai da amsa.      Babu musu ya bata. Koda ta amsa itama sai ta miƙe taje ta adanata dan tanaji a ranta abune mai muhimmanci a ciki mmn sadiq ɗin ta rubuto, dan dama ɗazun da sukai waya da Baffah yake sanar mata Abbansu Sadiq ya sanar masa yanason ya bashi lokaci zaije har gida suyi wata magana mai muhimmanci. Amma shi yanata juya abin a ransa da tunanin wace maganace haka? Shiyyasama ya sanar mata.    To a yanzu ganin wannan wasiƙar ya sakata jin maganar da Abban zai faɗama Baffah lallai tanada alaƙa da takardar kenan. Wannan hasashen ya sakata adana takardar sai ta nutsu sannan ta duba dan itama tayi karatun boko duk da bamai tsaho bane a wancan lokacin iyakartama firamare aji biyar aka aurar da ita...............✍           *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_*              *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* *Page 33* ___________________ _*LAVENDER RESTAURANT..*_ _(Palace of mouthwatering food/delicacies)_ _IDAN KUKAJI GANGAMI DA LABARI, INA MASU SON INDA ZASU SAMU INGATACCEN ABINCI MAI DADI DA LAGWADA? KAI BA ANAN MUKA TSAYA BA, INA SABBIN AMARE? MAMAs, YAYYU? DA KANNEN MU MASU SON KOYAN GIRKUNAN YAN GAYU NA KASAR NIJERIYA DA KETARE?_ _*TO KU MATSO...! AT LAVENDER RESTAURANT GOTS YOU COVERED. ABINCIN KASASHE DA DAMA MUKE KOYARWA,,COME LETS UPGRADE YOUR FOOD TIME TABLE, MATSO KUSA YAR UWA GA DAMA DA ZAKI CANZA YANAYIN ABINCIN GIDAN KI, KOWA YASAN IYA SARRAFA ABINCI NA TAKA RAWAR GANI A GIDAJEN AURE. KAI KO BUDURWA CE INDE KIN IYA GIRKI ZAKIGA KOWA YANA HABA HABE DAKE.._* _*UNCLES, DADDIES, BROTHERS., NEWLYWED HUBBYS..! KU ZO KU YIWA ‘YAYAN KU, MATAN KU DA KANNEN KU RAJISTAR WANNAN HARKA TA KOYAN GIRKI.._* _*Lavender catering school zamuyi practical class. zamuyi 30 dishes continental,snack & desserts, traditional dishes, drink. Fee din 40k NE. phone number WhatsApp and call 09080299283 akwai discount na 5% ga mutum uku farko wadanda sukai register aranakun independence 1/10/2021 to 3/10/2021 Nigeria @ 61_* _*ZA’A FARA CLASSES RANAR 14/10/2021. WATO SHA HUDU GA WATAN OKTOBAR DA MUKA SHIGA YAU._* _*GIRKE GIRKE GUDA 30😫😨AKAN DUBU 40 KAWAI, HARDA BONUS NA SNACKS, DESSERTS, TRADITIONAL AND MODERN DRINK, GARGALIYA DA ZAMANI🥂WATA DAYA CHAS ZA’AYI ANA KOYAN GIRKE GIRKEN. _* _*KU SAKE KARANTA WANNAN BONUS DIN👇🏾RIGIJI GABJI_* _*Nigeria @ 61 _* _*COOKING COMPETITION!!!_* _*from lavender Catering ina masu son koyon girki ga dama zaku shiga gasarmu ta girki bayan kunyi register damu akan 10k,wanda yazo na 1zai shiga ajin mu free hade da wasu prize din na 2 da na 3 kuma zasu bayar da rabin kudine da wasu prize suma saura kuwa zasu ayi musu ragin 5% da wasu prize wannan gasa zamu yita ranar lahadi ne 3/10/21 zamu rufe registration na gasar ranar asabar_* _*LAVENDER RESTAURANT: NA GARIN KANO, CLASSES DIN AKWAI PRACTICAL AND ONLINE CLASS GA WANDA KE NESA_* ____________________ *Page 33* ............A ɓangaren Farah kuwa tabbas a cikin tsananin tashin hankali take. Tana ƙoƙarin dannewa ne kar a samu matsala. Amma lallai zuwan waɗannan yaran gidan nan bazai haifar da ɗa mai ido a gareta ba, dan bawai zuwan nasu bane kaɗai matsalarta. Wannan itace dai-dai gaɓar da zata nisanci gidan nata da mijin ma ta koma zaman Morocco saboda killace ɓoyayyen sirrinsu, dama shirin yanda zasu saka AK maida Hajiya iya Nigeria sukeyi da zaran Mammah ta dawo daga China, sai gashi kuma wasu sun ƙaru. Gashi batama san iya adadin kwanakin da zasuyi ba. bata kuma san randa itama Mammah zata dawo ba.     A take hawaye masu zafi suka silalo mata. Ta jawo wayarta domin ƙara gwada kiran Aunty Zakiyya. Tun jiya take nemanta amma wayan yaƙi tafiya. Ta tura mata saƙo babu reply. Yanzunma dai switch off.      ‘Na shiga uku ni Farah, aunty ina kika shigane dan ALLAH?’. Ta faɗa a fili hankalinta na sake tashi. Har zatai wurgi da wayar sai wani tunani yazo mata. Cikin hanzari ta shiga fara neman babbar ɗiyar aunty Zakiyya. Cikin sa'a kuwa sai ga tata ta shiga. A take bakinta ya washe da murmushi, taja wani dogon numfashi ta fesar da ƙarfi.          Ana ɗaga wayar ko amsa sallamar yarinyar batayiba tace, “Ameera ina aunty?”.        Cike da shagwaɓa Ameera tace, “Aunty tana ɗaki, yanzu suka dawo daga Niger ita da Daddy”.         “Niger kuma? Kinga kaimata wayar”.         Ameera ta nufi ɗakin mamanta tana cigaba dama Farah surutun da ba fahimta takeba sam, burinta kawai taji muryar Aunty......      “Assalamu alaiki auta”. Muryan Aunty Zakiyya ta katse mata tunaninta. Batare data amsa sallamarba ta fara magana, “Aunty ina kika shiga kwana biyu, damuwa na nan zata kasheni lokacin mutuwata baiyiba. Wlhy akwai matsala babba aunt, muna kukan targaɗe ga kuma karaya ta samu”.        Babu shiri aunty dake kwance tana hutun gajiyar da suka kwaso a hanyar Niger ta miƙe zumbur tanama Ameera nuni data je. Koda Ameera ta fita ƙofar ɗakin ta murzama key kafin tace, “Auta miya faru?, kinsa zuciyata na neman bugawa wlhy”.       “Wlhy aunty ni tawama saura ƙiris ta buga. Muda muke burin tafiyar tsohuwarnan jiya sai ga wasu huɗun sun ƙaru, harda shegiyar yarinyarnan data tureni naji ciwo, aunty kinsanfa wannan watanne ya kamata na taho nan ko naje Morocco.......”         “Kinga nutsu kimin bayani yanda zan fahimta Farah, wai ƴan gidansu ne suka sake zuwa nan london ɗin?”.       “Eh”. Ta bata amsa tana jan numfashin kuka. Kafin ta faɗa mata duk yanda sukai dashi akan zuwan su Zinneerah.          Itama kanta Auntyn hankali tashe tace, “Aiko bazai yuwuba Farah, kinsan dai wannan shine wata na biyar da samuwar cikinki, ya kuma zama dole kibar London dan Abdul-Mutallab ba mahaukaci bane ba. Yanzu babbar matsalarmu da Mammah bata nan, amma na tabbata itama ai lissafin cikin naki na'a ranta bazata wuce satin nanba zata komo nan london ɗin, ki kwantar da hankalinki karki ja ya fahimci wani abu. ko ita tsohuwar ta fahimta”.         “Aunty taya zan kwantar da hankalina. Wlhy na mugun tsanar yarinyarnan da har yanzu bansan alaƙarsu ba. Dan inaji a jikina akwai aure a tsakaninta da shi, n.......”        “K dalla rufama mutane baki, wai ke Farah wace irin banzar yarinyace. Ana ga yaƙi kina ga ƙura. Ki fuskanci abinda keda muhimmanci a gareki kin wani zauna tunanin kishin banza da wofi akan yarinyar da ƙilama bata ishesa kallo ba, cayay miki yana sonta ne? Haba dan ALLAH, kishin nan duk muna dashi muma dan ya zame mana tamkar gado, amma ke kam naki ya fara zama na hauka dan kina gaurayashi da zargi. Inda Abdul-Mutallab zai ƙara aure na tabbatar da tun sanda ake dabin ya ƙara tunda baƙya haihuwa daya ƙara ai. Amma yanzu ki maida hankali wajen abinda zai kawo miki mafita kinama mutane shirme bayan ke da bakinki kince yarinyar bama ta wuce shekara sha bakwai ba. Ubanmi zaiyi da sa'ar Ameera shida ke da ke mtsoww, ni kinma bani haushi wlhy sai anjima”. Ta ƙare maganar da yanke wayar.         A fusace itama Farah tai wurgi da wayar tata zuciyarta na mata zafi da maganganun auntyn ta. Miye laifinta idan tayi kishin mijinta? Ta yaya zata kasa fahimtarta bayan tasan ƙudirin waɗan nan mutanen akanta, ƙilama da biyu suka ɗakko yarinyar suka ajiye saboda mijin nata. Su dan basusan halin wannan munafukar tsohuwar dake nuna kamar bata gane komai amma tsaf idonta buɗe yake. Ita zama ta iya cewa a wajenta AK ya gado nuna halin ko in kula akan abu koda kuwa yana sane.      Haka ta cigaba da kai kawo a ɗakin har tsahon lokaci duk da tana jiyo motsinsu da hirarsu a falo taƙi fita.     ★    A ɓangaren su Hajiya iya kuwa babu wanda ya damu da rashin sake ganin Farah a gidan. Hirarsu suka sha yau ma, salla kawai ke tashinsu har Khalipha ya dawo musu da abinci shima ya zauna aka ɗaura hirar da shi. Babu jimawa shima AK ya dawo gidan. Koda ya shiga yayo wanka shima dawowa yay cikinsu ya zauna ransa fes da farin cikin ganinsu cike da gidansa, abinda yayta fata da mafarkin gani a shekarun baya amma hakan bata kasanceba sai yanzun, duk da ba saka baki yake a hirarba sai ya gadama zaka fahimci yana tare da jin daɗin zaman. Hasalima aikinsa yaketa famanyi a lap-top kamar baya a wajen. Dan shima rashin ganin gilmawar Farah a gidan yasashi tunanin ko bata nan.          Sai kusan gab da magriba sai gata ta fito da alamun barci ta tashi. Sosai yake binta da kallon mamaki. Itako tayi kicin-kicin da fuska cike da takaicinsa. Kenan har takai ya dawo gidan bazai nemetaba saboda yana tare da ƴan uwansa. Batare da tayi magana ko kula gaisuwar dasu Meenal ke mataba ta juya ta koma ɗakinta hawayen takaici na zubo mata. Da kallo duk suka bita harta shige.       Fuskarsa na nuna alamun ɓacin rai yace, “Dama tana gidan?”.      Babu wanda ya iya bashi amsa a cikin su Jamal. Sai Hajiya iya ce tace, “Nima duk zatona ta fice ai, dan tunda kuka bar gidannan wani cikinmu baiji ko motsinta ba. Lafiya kuwa take Moddibo? Ya kanata kaje kaji”.        Maida kansa yayi ga aikinsa yana gyaɗama Hajiya Iya kai kawai, dan shi bazaiso ɗan sauran mutuncinta ya ƙarasa zubewa a idonsu ba. cikin son danne takaicinsa dason rufa asirinta,  Ya miƙe yana faɗin, “Inaga to jikin natane babu daɗi. Granny wannan babyn naku na bama matata wahala ya kamata ku tsawatar masa”.       “Kai kai Moddibo kana nufin ciki ne da ita?”. Hajiya iya ta faɗa cike da zumuɗi saboda jin firucinsa.     Ƙayataccen murmushi ya saki yana kallonta. Hakan da yayi ya saka su Bahijja miƙewa suka hau murna da rawa. Yanda sukai ɗin sai ya sakashi jin ƙarin daɗi a cikin rai, a bazata suka haɗa ido da Zinneerah da take murmushi har haƙoranta na bayyana, ita dai tana daga zaune bata tashiba. Saurin maida nata idanun tai ƙasa tsigar jikinta na tashi, dan yanda yay murmushin ba ƙaramin sake fiddo kamanninsa da Little yayiba. A hankali shima ya janye nasa da raɓasu ya wuce zuwa ɗakin Farah ya barsu hajiya iya na jero godiya ga ALLAH da kirarin farin ciki Khalipha da Zinneerah na amsa mata da amin. Dan su Bahijja shirmen da suke na murna yasa bajin mi hajiya iya take faɗa sukeba.         Sai da suka bari yaja wasu ƴan mintuna da shiga sannan suka miƙe suma domin zuwa dubata. Sallama suka farayi ya amsa musu da cewar su shigo sannan suka shiga. kusan Zinneerah ce ƙarshen shigowa.      Farah na kwance a gadon. shi kuma yana zaune kusa da ita gab hannunta cikin nasa. Dan tunda ya shigo zuciyarta ta bata shawaran cewar tai amfani da wannan damar kawai tace bata da lafiya. Hakanne kawai mafitarta gudun samun matsala. Sai kuma akai sa'a shima ya shiga tambayarta mike damunta? Shine ta sanar masa da zazzaɓi ta yini da ciwon kai. amma tasha maganin da Doctor ya bata.        Kukan da tasha yasa idanunta kumbura dama gata fara. Ta ɗagosu da ƙyar tana ɗan dubansu da amsa sannu da addu'ar da suke mata. Koda idanunta suka sauka akan Zinneerah dake can ƙarshe bayan Khalipha sai da taji wani tuƙuƙin baƙin ciki. Ta janye idanunta dake sake cikowa da ƙwallar jin kishin kasancewar yarinyar a garesu, tanajin tsoron ganin wata mace da aure zai iya shiga tsakaninta da mijinta ta raɓesu, shiyyasa zaman Zinneerah a gidan yafi na kowa damunta a yanzu........       “Da alama ma dai yinin yau bakici komaiba?. ko kina da buƙatar wani abune a nema miki ƴar albarka?”. Maganar hajiya iya dake shafa mata kanta ta dawo da ita hankalinta. Kafin tace wani abu AK dake jin daɗin kulawar da Hajiya iyan ke nunawa akan matar tasa yace, “Nima abinda nake mata magana kenan kafin ku shigo, ya kamata ko tea tasha”.       “Banajin cin komai ne ALLAH”. Ta faɗa a hankali cike da shagwaɓa tana kallon AK ɗin da shima ita yake kallo har yanzu hannunsa cikin nata.        “A'a bazai yuwuba Farah. Zinneerah jeki ki haɗo mata ko tea ne da wani abin dan kinfi waɗanan nutsiwar yin abu”.      Kai Zinneerah ta jinjinama Hajiya iya da nufar ƙofa. Duk da tanajin Farah na cema Hajiya Iyan ta ƙoshi bata dakataba ta fice. Dan ita dai har cikin ranta tausayin Aunty Farah taji ya shigeta. Ta ɗanɗana wahalar ciki tasan mi akeji, shiyyasa da ance ciki na wahalar da mace sai taji tsananin tausayinta.      Bata wani zaman ɓata lokaci ba ta haɗa tea mai daɗi dan komai akwai, har kayan abinci akwai duk da ba irin wanda suka sani bane, dan mafi yawansu na gwangwanine da sauransu, taɗan ɗiba mata cake da Khalipha ya kawo musu ɗazun ta haɗa dashi ta koma ɗakin.        Duk suna tsaye har yanzun, batare data yarda ta kalli kowa ba ta nufi gaban gadon, tana niyyar ajiye tiren a ƙasa ya riƙosa batare da yayi magana ba. Ita kuma batai tunanin shiɗin bane dan haka ta ɗago, saurin sakar masa tiren tayi saboda shigewar idonta cikin nasa. cikin ɗan daburcewa ta miƙe daga ranƙwafowar da tayi a gabansu taja jikinta baya.         Da wani irin tashin hankali Farah ta tashi zaune tana duban Zinneerah ɗin dan komai akan idonta ya faru, zatai magana AK daya gama karantarta yay azamar katseta. Ganin yanda yay da fuska yasata haɗiye abinda tai niyyar faɗa akan Zinneerah ɗin, da wannan damar ya kalleta cikin ido yana jefa mata gargaɗin ki kama kanki.        Tare da ɗaukar kofin shayin ya miƙa mata. A cinkushe tace, “Ni nace na ƙoshi”.      “Ni kuma nace sai kinsha”. Ya katseta a kausashe.      “Haba-haba Moddibo minene abin faɗa kuma anan, kaga bani ni na bata da kaina. Kai sam baka iya lallaɓa mutumba wlhy”. Hajiya iya da batasan dalilin kaushin nasaba ta faɗa. babu musu ya miƙa mata kofin shayin.         Akan dole Farah tasha shayin da cake ɗin badan tasoba. Dan har wani ɗaci-ɗaci suke mata a maƙoshi. Musamman da idanunta suka sake gano mata AK na kallon Zinneerah da kanta ke a ƙasa tana latsa wayar Jamal hankalinta kwance. Ita kanta da take mace sai da taga annurin fuskar Zinneerah ɗin musamman yanda hasken wayar ya haskata ga kuma wani ɗan murmushi bisa fuskar tata dake da nasaba da abinda take gani a wayar. Itako Zinneerah ba komai yasata murmushin ba sai hoton Little da take gani a wayar Jamal ɗin.           Khalipha daya fahimci inda Farah ɗin ke duba rai ɓace ya sakashi cewa suje falo, duk da shi baiga kallon da Yayan nasu kema Zinneerah ɗinba sam. Bama shiba kowama ba lura da AK na kallon Zinneerah ɗin yayiba, dan itama ɗin dai shegen zargi dabin ƙwaf-ƙwaf ɗintane ya kaita ga hango abinda yake neman saka zuciyarta bugawa.      Fita sukai suka barta da hajiya iya da Yayan nasu. Koda suka dawo falonma Zinneerah shigewarta tai ɗaki acewarta lokacin salla yayi. Tanason kuma tayi tilawar karatu yau dan ta kwana biyu batayiba.       Suma ganin lokacin sallar yayi sai duk basu zaunaba suka nufi ɗaki, har Meenal dake fashi binsu tayi kawai...........✍      *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_* *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* *Page 34* _______________________ *Assalamualaikum warahamatullah taala wabarakatuhu* 08121491609 *Aisha s bayero traditional medicine and herbal reaserch center* 08121491609 08121491609 1_maganin sanyi 2_maganin niima set 3_maganin nankarwa 4_maganin kiba babba 8kkkarami 5_maganin hips 6_maganin gyaran nono 7_maganin rage kiba 8_maganin saka feeling 9_maganin cida kwai 10_zuma yar asali 11_maganin basir kowanne iri 12_hodar niiama 13_maganin mallaka 14_gumbar nonon rakumi 10k boket😨 15_gumbar madara 10k boket😨 16_turaren farin jini 17_kaza Mara kwai 18-turaren mallaka 3step 19_hadin matar minister 20_ kaza me kwai Step 2 1.Turaren mallaka me kwalba 2. Me kunama Dan matsi 3k 3.tuaren goshi 4.turaren girji 5.tauwadar Mata 6.memory 7.kahon mallaka 8.yajin maza tea din maza 9. Dambun matsi 10. Man ayu 11.man damo pure daga zuwa sama 12. Kwallin idonka idona 13 garin Sha daka me kyau 14. Kubewar Mata gasunan dai da yawa bazan iya lisaafawaba harda na kyakkayin cinyoyin da matse matsi kina shafawa zakiji wasai 08121491609 dadai sauransu serious buyer yabiyoni private me shawara ta bari saita gama karki batamun lokaci plx **08121491609 _________________________ *Page 34* ............WASHE GARI ta kasance babu inda AK zaije. Khalipha ma sai yamma zaije school bakuma zai daɗeba zai dawo. duk sai da suka shiga sukaima Farah sannu da jiki, sai dai kuma hajiya iya yanda taga Farah ragal yau sai abin yaso bata mamaki, gashi ita dai idonta bai gano mata wani alamun mai ciki tattare da Farah din ba, saurin kaudashi tai a ranta da danganta hakan da kowa yanada irin salon laulayin cikinsane. To maybe itama Farah nata salon kenan tunda gashi duk zamanta gidan bata taɓa fahintar Farah na laulayiba sai a jiya. Koda yake bama tasan dai cikin wata nawa bane. Amma da alama dai kamar yanda take hasashe ƙila bazai wuce ɗaya zuwa biyuba.       Haka taita saƙawa da kwancewa har AK ya fito ya tuna mata yau fa zai kaita taga likita, yama zata zai iske ta shirya. Lallai ta shafa'a da cewar zataje ganin Doctor yau, amma da yake tsaf take dama sai kawai ta saka Bahijja ta ɗakko mata mayafinta a ɗaki. Dan Zinneerah da Meenal suna ɗaki su basu fitoba, dama ita kaɗaice a falon sai Bahijja da Jamal. Khalipha ma duk yau babu wanda ya gansa. Garama su Zinneerah sun fito sun gaida Farah da jiki sun kuma taya mai aikin gidan da aiki.            Duk da baiga su Zinneerah ɗinba baiyi maganaba, saima kama hannun Hajiya iya da yay suka fice. ★★      Bayan tafiyar su Hajiya iya da kusan awa ɗaya da rabi su Zinneerah suka fito, zamansu babu jimawa a falon sai ga Khalipha ya fito riƙe da waya yana magana alamar video call yakeyi. A bayan Jamal yaɗan ranƙwafo yana kanga masa wayar yanda zaiga mai magana. Cike da farin ciki Jamal ya ɗagama Moos'ab hannu yana faɗin, “Hy Yah Moos'ab”.     Jin haka yasa Bahijja da Meenal tasowa duk suka dawo kusa dashi, suka sakashi tsakkiya Khalipha na bayansu. Duk da Zinneerah na falon ƙin tasowa tai, sai dai yanda suketa surutu da ihu yasata kallonsu tana murmushi, jin kuma suna ambatar sunan little ya sata jin ɗokin ganinshi amma ta kasa tashi taje garesu duk da Meenal nata kiranta. Daga ƙarshe ma saita miƙe ta nufi kitchen da ake hango komansa ta falon saboda da glass kawai aka rabashi da falon, duk abinda kakeyi acan zakaga na falo shima zai ganka. Shayi ta fara haɗama kanta dan yunwa takeji ko karyawa batayiba yau, sam abincin da ake kawo musu gidan baya mata daɗi, balle yau ma mai aikin gida ta haɗa musu breakfast ɗin tunda babu wanda ya fita tsakanin Yayansu da Khalipha masu sayo musun.       “Gata nan na biyota da wayar ai Yah Moos'ab, kasan mutunuyar taka da miskilancin tsiya”. Ta tsinkayi maganar Bahijja a bayanta. Tana juyowa Bahijja ta kamo hannunta ta ɗora mata wayar ta juya tabar kitchen ɗin tana dariyar shakiyanci. Dansu tuni suka fara harbo jigin Yah Moos'ab ɗin akan Zinneerah, sai dai suna tsoron faɗa ya ci musu kaniya.        Wayar Zinneerah ta ajiye jikin wani ɗan maƙali dake a basket ɗin da kayan shayin ke ciki, fuskarta ɗauke da murmushin jin kunya ta dubi Moos'ab ɗin dake faɗin, “Gimbiya a rage wannan jan ajin mana Please”.      “Kai Yah Moos'ab wane irin jan aji ana zaune ƙalau, ina fatan kuna nan lafiya?”.         “Lafiya lau muke, dan ganima tare da Little Handsome tun safe na ɗakkosa daga wajen Gwaggo yau a gidanmu zai kwana insha ALLAH”.      Idanu ta ɗan waro na mamaki, “Baka tsorin yay muku kuka Ya Moos'ab?”.      Maimakon ya bata amsa sai ya karo mata fuskar little ɗin yana dariya. “Hy Gentleman kalla Aunty a waya tana maka magana”. Ya faɗa yana sunama little wayan. Ɗagowa kuwa Little dake kokawa da chocolate yayi ya duba wayar, sarai ya gane Zinneerah dan haka ya washe baki cike da ɗoki yake faɗin, “Aunty! Aunty”.      Dariya sosai ta kama Zinneerah cike da jin daɗin ganinsa mai tsanani, idonta na tara ƙwalla tace, “Uhm su malami an ƙara wayo ashe?”.      A dai-dai nan Farah ta shigo kitchen ɗin cike da tafiyarta ta ƙasaita da isa. Dama kuma hango Zinneerah a kitchen yasata shigowa dan tanason jamata winning akan shigo mata kitchen. Wani irin mahaukacin bugawa ƙirjinta yayi lokaci guda har takalmin ƙafarta na neman kadata a ƙasa. Tai azamar dafe kitchen cabinet jikinta na rawa.     Harga ALLAH da farko ta zata AK ne akan waya saboda yanda Moos'ab ya sakama little wayar kusa da fuska sosai, sai dai data ƙara matsowa taga wannan yarone. Amma duk da haka wani irin jiri-jiri taji yana neman kwasarta saboda ganin matsanancin kamannin. Babu wani neman excuse ta ɗauka wayar cikin hannunta tana faɗin, “Wannan yaron wanene haka?”.        A yanda tai maganar, da tsoratar da Zinneerah tayi dan batasan da shigowarta kitchen ɗinba yasa Moos'ab maido da wayar kansa yana ɗaukar little ɗin yasa bisa cinyarsa tana ganinsu su biyu. Batare da tunanin abinda zai faɗa zai iya zama matsalaba yace, “Hy Auntynmu yaronmu ne. Bakiga yana kama da Yayanmu ba, shi ya haifa muna baku sani ba”.      Harga ALLAH cike da barkwanci Moos'ab yay wannan furuci, sai dai ya zoma Farah a bahagon tunani, dan babu shiri ta nema sakin wayar a ƙasa sai da Zinneerah ta tarota ALLAH yasa bata kai ƙasaba. Itako a take takai ƙasan saboda santain tiles dana takalmin ƙafarta. Wata irin gigitacciyar ƙara ta saki wadda ta saka su Khalipha da sam hankalinsu baya kansu maido dubansu wajen, kusan a tare suka kwaso da gudu zuwa kitchen ɗin duk da su basajin mi suke faɗa. Ihun Fara ɗinma dan tayi da ƙarfi ne yasa sukajita, gashi kuma tana ta wajen saitin ƙofa ne ma.       Shigowarsu tayi dai-dai da kaiwar Zinneerah durƙushe kanta, a kuma dai-dai lokacin numfashin Farah ya bar gangar jikinta alamar dai suma tayi. Ƙara ruɗewa Zinneerah tayi ta shiga jijjiga ta tana shafa fuskarta da kiran sunanta. Suma su Meenal duk ƙasa suka kai durƙushe suka shiga taya Zinneerah jijjigata ta.      Khalipha da shi kansa yake a rikice duk da ya fahinci suma tayi yama rasa taimakon da zai bata, sai da Jamal yay hikimar ciro ruwa a fridge shima a ruɗe ya mika masa sannan.      Yana ƙoƙarin ɓalle murfin gorar ruwan Hajiya Iya da AK suka shigo. Kuka da ihun su Meenal ya sakasu nufo hanyar kitchen ɗin cike da sassarfa.      “Ya ilahi, kuko yaran nan miya faru kuka cika gida da ihu haka dan ALLAH?”.  Hajiya iya ta faɗa tana isowa inda suke.     Khalipha ne dake ƙoƙarin ɓalle murfin goran ruwan har yanzu ya kasa dan tsabar ruɗewa yace, “Granny Aunty Farah ce ta suma wlhy”.       “Suma?”. Cewar AK da shima ya karaso inda suke. Ganinta kwance a jikin Zinneerah da har yau take jijjigata tana kuka ita dasu Bahijja ya sakashi tabbatar da e da gaske suman kuwa tayi, amsar ruwan hannun Khalipha ɗin yayi ya zuba a hannu ya ranƙwafo ta bayan Meenal ya shafa mata ruwan akan fuska har bisa hannun Zinneerah dake shafa fuskar tata.      A take ta kawo wani irin nannauyan numfashi. Ganinsu a kanta ta miƙe a zabure jikinta na rawa. Babu zato babu tsammani sukaga ta cakumi wuyan Zinneerah ta shaƙe. “Tsinanniya matsiyaciya. Dan ubanki yau sai kin faɗamin wacece ke? Ta gidan ubanwa wancan yaron ya zama ɗan mijina kuma?”.          Wani irin kakari Zinneerah ta shigayi dan ba ƙaramin shaƙa Farah tai mataba, ga Hajiya Iya na ƙoƙarin janye hannunta dasu Bahijja amma sun kasa. Cikin rufewar idanu AK ya sauke mata mari dan ganin tana neman masa kisan kai a gida, bayan yanzu ya gama ganin yarinyar na kuka iya iyawa saboda shigarta wani hali.      Azabar zafin mari ya saka Farah sakin Zinneerah babu shiri ta ƙwalla wata irin gigitacciyar ƙara da ta sakasu toshe kunnuwansu babu shiri. Banda Zinneerah datai baya ta zube riƙe da wuyanta tana ƙoƙarin jawo numfashi da ƙyar.      Saurin riƙota Khalipha yayi, yayinda Hajiya iya kuma ta riƙo Farah da take neman fita hayyacinta saboda gigitar mari da abinda kunnuwanta suka jiye mata yanzu a bakin Moos'ab.       “Wai nikam mike faruwane haka? Farah ki nutsu ki mana bayani, ya mun tafi mun barku lafiya kuma mu iskeku a wannan harmutsatstsen yanayin abin ban tsoro”.      Kasa magana Farah tayi, sai jikinta ke wani irin rawa ga hawaye na rige-rigen sauka, yanda ta tsire AK da kallo tana sake hango tsananin kamanninsa da yaron ya sake harmutsa tunaninta, sai kawai ganinta sukai a ƙasa ta sake sumewa.      Sake rikicewa sukai gaba ɗaya, dan shi kanshi yanzu al'amarin nata ya fara bashi tsoro. Duk da yasan halinta ta iya ɗaukar abu da girma amma na yau ɗin kamar yafi na kullum. Hajiya iya ce tace ya ɗauketa suje ɗaki kafin a ƙara saka mata wani ruwan. Baiyi musuba ya ɗauuta gaba ɗayanta zuwa bedroom ɗinta. Hajiya iya da Khalipha ne kawai sukabi bayansu, su kuma su Meenal suka kama Zinneerah suka tayar zuwa falo.   Jamal kuma ya ɗauka mata ruwa a fridge yabi bayansu zuciyarsa fal mamakin miya kawo wannan tashin hankali haka?. Baida mai bashi amsa, bai kuma zaton samun amsar ga Zinneerah a halin yanzun ba.       A can ɗaki kuwa ruwa aka ƙara shafama Farah ta farfaɗo, sai dai tambayar duniya sunyi mata taƙi cewa komai sai uban kuka take dirza. Data kalli fuskar AK kuma ta hasaso ta little sai ta sake fashewa da wani kukan.        Sanin halin Farah da AK yayi ne ya sashi jan tsaki tare da daka matsa tsawar data sakata shanye gumjin kukan da take ɗin. “Ki nutsu karki maidamu wasu ƴan iska mana, ya ana taroki kina zillewa sai kace wata karamar yarinya?”.         “Wlhy bazanyi shiru ba, har sai an faɗamin ƴar iskar data haifi wancan shegen yaron da Moos'ab ya kira da naka, har wannan matsiyaciyar yarinyar ke magana dashi ta waya.....”        A fusace ya zuba mata wani shegen kallo daya sakata haɗiye maganarta babu shiri ta ƙanƙame hannun Hajiya iya dake riƙe da nata. duk da bai fahimci inda zancenta ya dosaba sai da gabansa ya faɗi, juyawa yay ya sauke idonsa akan Khalipha.       “Mike faruwa?”. Kai Khalipha ya girgiza masa. kansa tsaye yace, “Wlhy ban saniba Yayanmu, nidai Moos'ab ya kirani ina ɗaki kwance yace na bama su Meenal waya su gaisa. na kawo musu ya gaisa dasu Jamal sai aka kaima Zinneerah wayar kitchen dan tana can kuma tare yake da little. Daga haka bamusan miya faruba sai ihun Aunty Farah mukaji kawai dan ko wucewarta kitchen ma ni wlhy ban ganiba”.        Batare da yace komaiba ya maida dubansa ga Farah dake kuka har yanzu kamar zata shiɗe. “Meya faru ke da kika shiga kitchen ɗin?”.         Wani irin kuka ta kuma fashewa da shi, tace, “Miya faru kuwa bayan ganin shegen ɗanka da nayi wanda kake ɓoyemin karna sani, a duk sanda nai maganar kanacin amanata da wasu matan a waje ka balbaleni da bala'in ina zarginka. Sai gashi ALLAH ya tona maku asiri ɗan uwanka yau ya fallasamin, ALLAH ya nunamin shege ɗan ƴar iskar yarinyarnan na waya dashi. Wlhy bansan haka kakeba Abdul-Mutallab, dana gwammaci dawwama banyi aure ba akan ganin wannan baƙar ranar........”        “Haba kekuwa ƴarnan wane irin kalaman rashin ɗa'a ne haka kike jefar mijinki dasu? Ni wlhy saima yanzu na fahimci daga ina matsalar take, halan yaron nan na wajen Hauwa'u ta gani?”.           Khalipha ne ya bata amsar cewa, “Eh shine kuwa Granny, dan Moos'ab ne yake can gidan ya ɗakkosa. To inaga sanda suke magana da Zinneerah ita kuma ta shiga kitchen ɗin ta gansu. Amma aunty Farah ya kamata kiyi haƙuri ai miki bayani, yaron nan baida wata alaƙa da Yayanmu sai ta zuminci, kamannine kawai da ga ALLAH b........”        “Ƙarya kakeyi munafukin ALLAH ta'ala, idan kai kaƙi faɗar gaskiya ai shi Moos'ab ɗin da bakinsa yace ɗansa ne”.        Hajiya iya da mamakin Farah ke neman kasheta tace, “Shi Moos'ab ɗin ya faɗa miki yaron na Moddibo ne?”.       A gadarance tace, “Ƙwarai kuwa”.    Yanda tai maganarne ya saka AK kaima bakinta bugu. sai dai da sauri Hajiya iya ta kare tana faɗin, “Kull da wannan ɗabi'ar, karka sake ka aro halin da ba nakaba kayi haƙuri abi komai a sannu harta fahimta. Kai Khalipha kiramin Moos'ab a waya yanzun nan”.        Amsa mata Khalipha yayi yana fita falo domin amso wayarsa a wajen su Zinneerah.       Dai-dai lokacin da Khalipha ke ƙoƙarin kiran Number Moos'ab kiran Baffah ya shigo wayar AK. Cike da ƙarfin hali ya ɗaga, sallama yay yana mai ƙoƙarin dai-daita muryarsa dake a cinkushe. Sai dai kuma yanda yaji muryan Baffah sai ya bashi mamaki.         “Kaga Babana haɗani da Inna”. “Baffah lafiya kuwa?”.      “Karka damu lafiya lau, haɗani da ita”.       Cikin sanyin jiki ya mikama Hajiya iya wayar yana faɗin, “Baffah ne”. Amsar wayar tayi takai kunnenta. Batare da sunsan mi Baffah ya faɗa mataba ta miƙe ta fito daga ɗakin. Hakanne yasa AK miƙewa shima ya fito domin jin ko Khalipha ya samu Moos'ab. Dan shi kaɗai yasan irin hukunci dazai masa idan har yaji gaskiyar zancen.        Kamar jira suna fita kira na shigowa wayar Farah. Kamar zata share sai kuma ta duba wayar tana sharce hawaye. Wani irin zabura tayi saboda cin karo da sunan Mammah akan fuskar wayar alamar ta dawo kenan..............✍ ********************** ? ************************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************? ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ? ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ? ************************** *_Hummmm, tofa masu karatu ga wuri fa ga waina. Yanzu aka fara wasan kumuje zuwa😉🐥🐥._*              _Kar kuma naji wani yacema aunty Farah wani abu, kokuma na rage mudu ehe_🤒🤕😒☹️😖 *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_*              *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* *Page 35* ________________________ *ZAUREN GIRKI* Abinci na *gargajiya* ...Kuka,Taushe,Danbu, Sinasir,Waina Abinci na *zamani* ...Afang,Edikaikong, Coconut Rice, Ofada Rice *Garabasa* ...Salads,Pancakes, Plantain mosa, Gyaran nama/kifi kafin girki,Shirin/shinfida abinci kan table. • A kowane sati,in shaa ALLAAH, za a koyi miya/abinci daya da kuma wani abu ta karkashin *Garabasa* . • Duk ranar *Lahadi* za fito da sabobin *videos* guda biyu na miya/abinci da na wani abu daga karkashin *Garabasa* . • Kowacce daga cikin masu koya zasu bibiya video su kwaykwaya su gwada yin abincin bisa ga umurnin *video* • Kowane ranar *Asabar* za a yi *Q&A* a inda kowa zai samu yin tambayoyi akan *videos* din satin daya gabata, da inda suke neman karin bayani/gyara akan kokarinsu na gwada abincin *video* da kawunansu • Ga wace taga dama,daga ranar *Talata* za a iya fara turowan *video* ta kokarin da aka yi na kwoyon abincin da aka kwoyar ta *video* na ranar *Lahadi* . • Inda akwai me bukatan wani fanni na abinci,ana iya hada *aji(Special Personal Video Classes)* musamman domin wannan bukatan.Anan za a shirya live *video* sessions domin cimma wannan burin • Za a biya dubu biyu *(#2,000)* na watan farko,sannan za dinga biyan dari biyar *(#500)* ta kowane sati ga masu bukatan shiga group dinnan namu mai albarka • *Zen Commute,account number 0119343451 Union Bank* ,asusunmu • Duka lokacin da aka biya sai a turomana da hoton teller ko bank confirmation akan wannan number ta *WhatsApp 0817-541-7533* • Ana iya tuntubammu akan wannan number domin karin bayani; **0817-541-7533(WhatsApp kawai)*                                   ZA MU FARA ZAUREN GIRKI LAHADIN SATIN FARKO TA WATAR SEPTEMBER,IN SHAA ALLAAH! *MU TSARE MUTUNCINMU,MU KARE MAZAJENMU...MU KOYI GIRKI!!!* _______________________ *Page 35* ............“Babangida duk ka rikitar dani wlhy, gani na dawo ɗaki ni kaɗaice yanzu mike faruwa ne?”. Hajiya iya dake zama a bakin gado ta faɗa.          Numfashi Baffah ya furzar daga can. Cikin nutsuwa yace, “Inna yanzu muka rabu da mijin Hauwa'u, kamar yanda na sanar miki dama munyi dashi yau zaizo yanada muhimmiyar magana”.        “Eh ƙwarai anyi haka”. “Yauwa to Inna, maganar zancen yaron nan ne dai daya tsayamin arai mukayi dashi, ashe yaron ɗan wajen Zinneerah ne”.       “Uhm ban fahimcekaba dai babangida. Wace Zinneerah kake magana? Inno wai?”.      “Tabbas ita kuwa”. Sosai zancen ya daki zuciyar Inno. Har sai da ta janye wayar daga kunnenta ta kalla, ta dai tabbatar da ɗan nata take waya ba wani dabanba dan haka ta mayar. “Babangida tayaya hakan ta faru? Dama Zinneerah ta taɓa aure ne?”.       “Bata taɓaba Inna. Ƙaddarar rayuwa ce takaita ga haihuwarsa.......   (Anutse ya shiga yimata bayani dalla-dalla kamar yanda Abba ya sanar masa). Sai ga hajiya iya na hawaye shaɓe-shaɓe na tausayi. Dan har cikin ranta tanaji Zinneerah bazata aikata hakan da ganganci ba, dole akwai abinda ya faru dai......        Baffah ya katse tunaninta da cewar, “Inna harga ALLAH ta ɓoye-ɓoye ya ƙare, shin baƙya wani tunani game da kamannin yaron nan da Adnan kuwa? Adnan ba kama yake da yaran gidannan ba mahaifiyarsa ya biyo komai a kamanni balle muce ƙarfin jini yakai yaron Zinneerah da ɗakko kamannin yaran gidan nan. Shin kodai akwai abinda Adnan ke ɓoye mana ne?. Dan kwanaki sau biyu ana sanarmin shigowarsa Nigeria baizo inda mukeba. Nayi shirune kawai na ƙyalesa dan karna tayar miki da hankali”.      Babu shiri Hajiya iya ta miƙe tsaye tana ambaton, “Shi Moddibon da kansa?”.      “Wlhy kuwa Inna, ko lokacin da Khalipha yazo hutu tare sukazo”.     A take kan hajiya iya ya sake kullewa. Kamar yanda shima Baffah kan nasa yake a kulle. Dan sudai sunyi imani da cewar yanda yaron ya shiga ran kowa a gidan akwai wata a ƙasa. Sannan kamannin kam sunyi yawa, sai dai idan acan kuma dangin hindatu tushen matsalar take ba abinda zukatansu ke karkatar dasu akai bane.          Hajiya iya da takardar wajen mmn sadiq ta faɗo mata a rai tai masa sallama akan zuwa anjima zasuyi waya bara ta kashe wata wutar.       Tana katse kiran takardar ta ɗakko a inda ta ɓoyeta, ta sake komawa inda take zaune da ta warware.      *_Assalamu alaiki_*     *Alkairin ALLAH da samuwar lafiya mai ɗorewa su tabbata a gareki Gwaggo. ALLAH ya dawo mana dake gida lafiya*        _Gwaggo zan fara da baki haƙuri akan wani abu da muka ɓoye miki game da Zinneerah, munyi hakanne saboda ba abune mai daɗi ba ko farin ciki. Duk da dama dai munyi niyyar sanar daku ɗin harga ALLAH. Akwai ƙaddarar data faɗama Zinneerah wadda itace tai sanadin dawowarta zama a wajena, dan da tana can wajen mahaifinta da muka rabu...................._       _(Ta bada labarin tun aurenta da baban Zinneerah har bayyanarta da ciki a garesu da haihuwarsa kaf bata rage komaiba. Daga karshe ta ɗora da faɗin___). Yaro da mukazo dashi ranar da yara sukace ƙaninsune shine yaron, sunansa Abdul-Mutallab. Dan ALLAH ku gafarcemu da rashin sanar muku wannan labarin tun farko, bamun ɓoye bane dan bamu yarda dakuba. ALLAH ya hukunta sai yanzune zaku sani kawai. ALLAH ya ƙara miki lafiya da tsahon rai mai albarka da amfani._         Sosai Hajiya iya taja wani irin dogon numfashi mai tafiya a sarƙe. Ko kaɗan bataga laifin mmn sadiq akan ɓoyewarba. Domin ko itace zata iya ɓoyewar bisa dalilai masu yawan gaske. Abinda kawai yake neman jefa zuciyarta a ruɗani irin wanda Baffaah ya shiga anan uku ne zuwa biyu. Shigowar sunan Khalipha a labarin da taimakon da yay ma Zinneerah a Shira hospital, Kamanin yaron da Abdul-Mutallab, dan wannan kamanni yakai ai zaman dogon nazari akansa.        Sannan har cikin ranta kuma tausayin Zinneerah da ƙarajin ƙaunar yarinyar ya ƙara faɗi a zuciyarta. Yarinya ƙarama kamar wannan ta fuskanci irin waɗan nan manya-manyan jarabawoyi na rayuwa. Amma abin mamaki ko'a labari bata taɓa nunama waniba, hakan na nufin itaɗin yarinyace mai yawan kamun kai da riƙe sirri, insha ALLAH kuwa zatayi wani abu, sai ta ƙwato mata haƙƙinta, dan har cikin ranta son yarinyar takeyi tamkar nata jikokin........ ★   Daga ɓangaren Farah da kiran Mammah ya shigoma a waya. Wani ɗan karan daɗine ya tsarga mata. Tai saurin ɗagawa tana kai wayar kunnenta, dan har cikin ranta tana son Mammah kamar yanda itama take nuna mata soyayya.        Tana ɗagawa ta fashe mata da kuka, a rikice Mammah tace. “Auta lafiya kuwa? Miya faru da kuka haka ni hindatu?”.       “Babu lafiya Mammah, ina cikin damuwa da tashin hankali. Naje gidan jiya kawai na tarar bakyanan sai Mahma kaɗai, yau kuma sai ga tashin hankalin da yafi na jiyan ya riskeni”.        Hankali tashe Mammah tace, “Am so sorry baby na. Ai bazan jimaba zan dawo kodan saboda halin da ake ciki. dan yanzu hakama na kammala tura kaya Morocco. Na Nigeria suka rage kawai insha ALLAH. Amma mi kikajeyi gida? Wane kuma irin tashin hankali kike a ciki?”.        “Ƙannen Yah Abdull ne suka zo jiya, harda yarinyarnan mara kunya data jimin ciwo a ƙafa. Mammah duk bama wannan ba. Wlhy Yah Mutallab ya haifi yaro da wata a waje kokuma yayi aure a ɓoye bada saninmuba”. Ta ƙare maganar da fashewa da kuka.         “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un. Farah wane irin maganane wannan? Ya haifi ɗa da watafa? Ke waya faɗa miki? Wacece ita wadda ta haifi ɗan kuma?” Mammah ta faɗa itama cikin tashin hankali.       “Mammah wlhy nima ban sanba. Yanzun nan naga yarinyarnan tana waya da yaron da Moos'ab, shine Moos'ab ɗin ya sanarmin yaron na Abdul-Mutallab ne, kinga kuwa indai ba'a waje wata ta haifa masa shiba wlhy aure yayi a ɓoye bamu saniba. Indai hakan ta faru mutuwa zanyi Mammah          “Kai ina!! Duk rintsi bazan bari hakan ta faruba Farah, dan wlhy har abada bazanyi sakacin da Kabeer zai ƙwacemin Abdul-Mutallab ba. Nayi alƙawarin tarkon da suke ganin zasu ɗana masa ya faɗa bazan bari yayi tasiri ba, dan haihuwarki itace kawai raba gardama a tsakaninmu. Kinga kuwa hakan na nufin babu wata mace data isa zuwa ta haihu da Abdul-Mutallab a ɓoyema ban saniba. ki kwantar da hankalinki yau ɗin nan zan baro china kuwa, dan bani da wata nutsuwar zaman yin abinda nazo yi ɗin”. daga haka ta yanke wayar.          Faɗawa Farah tai saman gadonta tare da fashewa da kuka mai cin rai, ji take tamkar numfashinta zai rabu da gangar jikinta, dan inhar wannan ɗan ya tabbata na Abdul-Mutallab tasan ita kam rayuwarta tazo ƙarshe. Kenan bayan ita ya taɓa sanin wata mace a duniya? Ya taɓa dai-daita farin cikin da yake bata da wata mace? ‘Kai ina wlhy hakan bazai yuwuba’ ta faɗa a fili tana fashewa da matsanancin kuka ta miƙe ta fito daga ɗakin.         Ficewa tai daga gidan dan ta rantse bazata sake kwana ba sai Mammah ta dawo sunji daga ina aka samo little. Ko kallon su Zinneerah dake falo zaune Farah batayiba ta nufi hanyar fita abinta.         Da kallo suka bita a tsorace. Cikin damuwa Jamal yace, “Gaskiya Yah Moos'ab baiyi tunaniba, miyasa shima ya faɗi cewar ɗan Yayanmu ne bayan yasan halin Aunty Farah da kishi. Gashi nan wannan maganar dashi yake gani yayi akan wasa gashi tana neman zama babba”.         Wasu hawaye ne masu zafi suka sake silaloma Zinneerah, dan ita a yanzu damuwarta daban da tasu, bataga laifin Farah ba, dan ko ita data haifi little har yanzu ta kasa fita daga ruɗanin kamannin da yakeyi da Yah Adnan. Balle ita dataga komai sama taka yau, ai komi tayi bai kamata aga laifinta ba.     Tunda ta haifi little yau shine karon farko data tsinci kanta a matsanancin tashin hankali tun bayan barowarta Danya.      Acan kuwa wajen su Hajiya iya an kira Moos'ab dan yayma Farah bayani akan wasa yake mata, Hajiya iya da Khalipha sun fito dan a bata wayar amma suka samu ta fice. Cikin damuwa suka sake shiga, dan ba ita kaɗaiba harsu Hajiya iya ganin kamannin yaron da AK ɗin sukai sosai fiye da kullum a yau.        Hajiya iya ta dubi Khalipha daya yanke kiran tace, “Ina Moddibon yake harya bari ta fita?”.     Kansa ya girgiza mata alamar bai sani ba. Sai su Bahijja ne suka sanar mata sungafa kamar ya fita.       “Fita kuma? To lafiya?”. Hajiya iya ta faɗa. Khalipha da zuciyarsa ta bashi inda Yayan nasu yake yace, “Granny ina zuwa. Inaga yana baya, kinsan shi idan ransa ya ɓaci yafi bukatar ya killace kansa inda babu hayaniyar komai.     Batare da ya jira amsartaba ya fita shima. Kamar yanda yayi hasashe acan bayan ya samesa yanata kaikawo hannayensa goye a baya.       Harya karaso gab dashi baisan da zuwan Khaliphan ba, dan harga ALLAH kamanin yaron da shi ƙara gigitashi sukeyi, zai iya rantsewa tunda yaga yaron nan bai ƙara barci mai daɗi babu mafarkinsa ba. Dauriya kawai yake aɗan tsakanin nan har Hajiya iya ta samu lafiya. Amma da tuni ya koma Nigeria dan kawai yaga asalin mahaifin yaron nan shikam. Sai dai kuma abinda ya faru a yau ya ƙara tada masa tsumin ƙwaɗayin son zuwa Nigeria. Ko ita Farah jin gaskiyar zancen ya sakashi yimata uziri, dan inhar shi da yaron ke kama dashi zai iya rikicewa dolene ita yaga fiye da haka a gareta. Musamman daya santa da shegen zafin kishin tsiya, a yanzu babuma abinda zuciyarta bazata hasaso mataba game da yaron kamar yanda shi kansa duk da ance yaron ɗan Gwaggonsu ne zuciyarsa taƙi samun nutsuwa.       “Yayanmu”. Khalipha ya kirashi cike da damuwa. Juyowa yay ya kallesa sai dai baiyi magana ba. Khalipha ya ƙarasa takowa garesa, kansa ya ɗan risinar ƙasa saboda abinda zai faɗa.          “Yayanmu kayi haƙuri, kar abinda aunty Farah keyi ya dameka. Dan ALLAH kumata uziri dolone ta shiga ruɗani kamar yanda muma ɗin muke a cikinsa tun ganin yaron da mukai a Nigeria, kawai dai ita matsalarta bata da nutsuwar zama ta fahimci abune”.       Karon farko AK ya saki murmushin ƙarfin hali, hannunsa ya ɗora bisa kafaɗar Khalipha ɗin. “Hakane bestie, Farah ta cancanci uziri a wajenmu, sai dai minene dalilin Moos'ab na cewa yaron nawane?”.       “Wlhy tsokanarta kawai yake Yayanmu, kasanshi duk da baida yawan magana yanada son wasa. Kuma inaga ya manta bataga yaronba a waccan ranar”.       Kai AK ya shiga jinjinawa yana sauke nannauyan numfashi, ya sauke hannunsa daga kafaɗar Khalipha yana maidasu bayansa ya harɗe. Taku biyu yayi batare daya juyo ya kalli Khalipha ba yace, “Bestie mi zuciyarka ke baka akan kamannina da yaron nan?”.        Babu shiri Khalipha ya kalli bayan nasa da sauri, haka kawai yaji gabansa ya faɗi, dan inhar gaskiya zai fito ya faɗa to komaima zuciyarsa na bashi musamman idan tunanin Zinneerah ce mahaifiyar yaron yazo masa arai kamar yanda yake zargi. Baki ya buɗe da ƙyar zaiyi magana Hajiya iya data biyo bayansu ta katsesa.......       “Wai tsayuwar mi kukeyi anan? Yarinyarnan fa bata gidan nan”.     Atare suka juyo suna kallonta. Takowa AK yay cikin tafiyarsa da babu gareje zuwa inda take, bai kawo wa take nufi ba dan haka yace, “Wace yarinya Granny?”.       “Matarka mana”. Ɓoyayyen numfashi yaɗan sauke, a ransa yace ‘da sauƙi’ tunda yasan dai Farah ƴar garice bazata je wani wajeba sai gidan Mammah.       “Karki damu Granny babu inda zataje sai wajen su Mammah. Ya kamata mujema kisha maganinki”.      Daga haka ya kama hannunta suka nufi ciki Khalipha biye dasu. Basu sami su Zinneerah a falonba, sai mai aikinsu dake ƙara gyarawa. Har ɗaki ya raka Hajiya iya, ganin Zinneerah kwance a gado su Bahijja zaune jigum-jigum yasa Hajiya iya tambayarsu ko lafiya?.............✍         *_Masha ALLAH. Guys asha hutun weekend lfy ko😋😉😘😍😘😍🤗._* *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_* *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* *Page 36* _________________________ _*YERWA INCENSE & MORE**_ _(The scents with diff essence for YOU& your HOME)_ _(MASARAUTAR KAMSHI)_ _Ina masu neman kayayyakin kamshi yan nahiyar ketaran chadi da Senegal? Kai harma da ingataccen had’i yan bornu? To ku matso domin nesa tazo kusa..._ _YERWA INCENSE & MORE: Sun zo muku da kayayyakin turaruka kamar haka:_ _Khumra kowacce Iri._ _Turarukan Wuta_ _Mopping khumrah_ _Washing khumrah_ _Bathing khumrah_ _body mist_ _kullaccam_ _scented hair cream/spray_ _wardrobe balls_ _carpet spray_ _air-fresheners_ _scented pebbles_ _body sprays_ _oil perfumes_ _Perfumes_ _kabbasa_ _burners_ _coal igniter_ _tong_ _kasko_ _kujerar tsugunno_ _english coal_ _dilke&halwa set_ _scented body mist_ _kai dama sauran kayayyakin da bamu ambata ba, YERWA INCENSE AND MORE, Na tura kayayyakin su ko’ina a fadin Nigeria da ketare. Domin tuntubar su. Suna instagram: _@yerwaincense_and_more. Ko _Facebook site:YERWA _COLLECTIONs. Ko a duba su ta number su: ___08095215215/09044191709! _ _suna bada kayan su kan sari ko sayi dai-‘dai_ _________________________ *Page 36* ..............Meenal ce tai ƙarfin halin faɗin, “Granny zazzaɓi ne a jikin Zinneerah”.       “Ya salam, zazzaɓi kuma?”. Granny ta faɗa tana zagayowa inda Zinneerah take. Hannu ta saka a goshinta da wuyanta da sukai zafi rau. “Kai aiko jikin da zafi Inno, sannu kinji”.     Zinneerah da bacci-bacci ya fara figa ta ɗaga mata kai tana maida idanunta ta lumshe.        AK na tsaye yana kallonsu kamar baiji mi Hajiya iyan ke faɗaba. Sai da ta dubesa ne ya ɗan tako inda suke shima, kanta ya ranƙwafo yasa hannu yana cire bargon data lulluɓa. “Tashi zaune”. Ya faɗa ciki-ciki.      Tun matsota da yayi ƙamshinsa ya cika mata hanci, daƙyar taja numfashi lokacin daya ranƙwafota, duk da yanda taji maganar tasa gab da ita bata miƙe zaunen ba sai idanunta data rumtse da sauri.       “Baƙyaji ne?”. Ya sake faɗa kamar bayaso.      Idanunta ta buɗe a hankali tare daja baya kaɗan daga kusa dashi, kafin ta yunƙura da ƙyar ta tashi zaune. Shima tsaye ya miƙe da ƙyau idanunsa a kanta. “Mike damunki?”.      Wani irin haushi tambayar tasa ta bata. Sai kace ba'a gabansa matarsa ta shaƙeta zata kashe ba yake wani mata wannan tambayar. Batare data yarda ta kalli sashen da yakeba ta nuna masa wuyanta.         Ɗan luu yay da idanunsa da gaba ɗaya suka canja kalarsu yana ɗaukesu daga kallonta. Batare da yayi maganaba ya fice a ɗakin su Bahijja na binsa da kallo.      Zama Hajiya iya tayi kusa da Zinneerah ta kamota jikinta tana mata sannu da duba wuyan nata. Duk da bata kasance fara tas ba ana ganin shatin hannun Farah a wuyan, saboda ba shaƙar wasa tai mataba. Gashi wajan kiciniyar ƙwaceta kuma duk an jijji mata ciwo da farce.     Shigowarsa shi da Khalipha ta sakasu kallonsu, Khalipha ya ƙaraso inda suke ya zauna a bakin gadon shima yana mata sannu. “Tashi ga magani kisha zai saki insha ALLAH”.     Babu musu ta tashi zaune ta amshi ruwa da maganin hannun Khalipha ɗin tasha. Tana gama sha kwanciya ta koma tayi jikin Granny. Hakan yasa ɗakin ɗaukar shiru na wani lokaci kowa da abinda yake saƙawa da kwancewa a cikin ransa game da al'amarin....... *_DANYA_*         Koda su Inna suka iso Danya mahaifiyar babawo ta buƙaci wucewa da Karima gidanta amma sai Inna taƙi fir. Acewarta sai sunsan miya faru tsakanin Karima da Babawo koda hakan zata kasance. Badan innar babawo tasoba dole ta haƙura aka wuce da Karima gidan su Inna. Ita kuma tace zataje gida taɗan kimtsa saboda kwanan asibiti da sukai zata samesu daga baya dan tana son taɗan haɗoma karimar kayan kunu kafin babawon ya gadama yazo.       Baki amare Inna ta amsa mata tana jan hannun Karima suka shige cikin gidan.          Tun'a farkon shigowa gidan idanun Inna suka sauka akan Hajja lanti. Sosai ta waro idanu waje tana kallon hajja lanti da itama ita take kallo.      “Ni Asabe mi nake gani haka kamar hajja lanti? Idan mahwalki nake karku tadani dan ALLAH jama'a”.      Cikin dariyar yaƙe hajja lanti tace, “Ba mahwalki kike ba Asabe. Ni ce dai aminiyarki a zahirance walle”.     Jikin Inna na ɓari ta kwanto jaririyar Karima dake goye a bayanta ta mikama Sa'a data fito daga ɗaki dan yau anan ta kwana. “Ku shiga ciki, Sa'a kizo ki haɗa murhu asama ƴar uwarki ruwan wanka”.     Cikin ɗokin ganin baby Sa'a ta amsa tana ƙwalama Tinene dake barci a ɗaki ko sallar asuba batayiba kira dan tazo taga Baby. Karima kuwa ko gaida hajja lanti bataiba ta shige ɗakin Inna dan burinta kawai ta kwanta ta hutama ranta.           “Hajja lanti dama rai kanga rai?”. Inna ta faɗa tana zama a kusa da ita cike da jimami.      A raunane Hajja lanti tace, “Ba lafiya bace ta ɓoyeni ai Asabe, bayan ALLAH ma ya ƙaddara da sauran shan ruwana a duniya da ba wannan zancen mukeba anan”.      “Munga boni, mikuma ya hwaru hajja lanti? Dan ko baki hiɗi ba duk wanda ya dubeki yasan akwai damuwa, duk ƙibarkin nan ta zube kinyi baƙi”.       Hannu Hajja lanti tasa ta sharce hawayen da suka cika mata ido. “Asabe ai tun tahiyar danai da ɗiyar gidan nan abin ƙaddara ina baro garin katsina ashe ƴan doka na biye dani wlhy sukai ram dani aka sake maidani cikin garin katsina. Ashe wata matace dana ɗauka ɗiyanta a carachi tai shune na garesu”.       “Kai mun ɓitire. Hajja lanti kice kin auna arziƙi ke kau”.      “Bama ƙaramiba asabe, dan nahi wata biyu a wajen ƴan doka kahin su gaji da zamana wajensu babu mai belina suka mikani gidan yari wai zasu kaini kotu. Zancen da nake miki daga ranar babu wanda ya sake bi ta kaina ina gidan yari duk tsahon zaman nan. Sai shekaran jiya wani bawan ALLAH yaje ya fiddamu mu ɗari biyu”.      Sosai Inna keta faman tafa hannu tana sallallami da jajantama Hajja lanti dake matsar hawayen tuna azabar datasha a gidan yari. Sai da ta gama ƴan hawayenta sannan ta sake duban Inna. “Asabe yanzu abinda ya kawoni garin nan akan yaran dana ɗiba ne a tahiyar da nayi, dan nasan iyayensu hankalinsu a tashe yake. Nafara zuwa nan wajenki dan naji ko yarinyar gidan nan ta dawo ita kafin naje sauran gidajen suma naji yaya ake ciki? Dan naje can gidan hajiyar da nake kaima yaran a katsina na iske wai ta tahi saudia shekara biyu kenan”.          Ɗan waige-waige Inna ta fara, ganin su Sa'a har yanzu suna ɗaki tare da Karima dan Tinene ma ta fito tuni ta samesu. Ƙasa-ƙasa ta maida muryarta tace, “Ta dawo tun bayan mako uku da tahiyarku ai”.     Cikin zumuɗin dajin daɗi Hajja lanti ta ce, “Kai ALLAH na gode maka”.     Baki Inna ta taɓe tana gyara zama. “To ai baki saniba da ɗan ƙunshi ta dawo mana, nikuma a sanadinsa na kaɗa kanta tabi duniya yanzu haka ance tana birnin ikko ta kama ɗaki”.       “Kina nihin ciki tazo dashi Asabe”. “Ƙwarai da gaske hajja lanti, dan ciki ma ya giyata ya hito duniya ta sani kahin nasata barin garin nan bayan na rihe bakin tambaɗaɗɗiyar gudun karta tona mani asiri dan na hiɗima duniya cewar yawan tazubar dama ta tahi tunda dagani sai ke mukasan yanda akai”.       “Amma asabe.....” “Karkice komai hajja Lanti, dan kema kinsan komai akan tsanar ɗiyar nan danai, kinga can wajen” tai nuni da ƙasan turminsu na daka. “Acan na binne tsiyar, kinsan malam kallamu, shine yay mani aikin nan na rihe bakin kowane shege har abada kuma babu maiji, kema na hiɗi maki ne dan nasan abikiyar cin mushe ce. Kema kuma baki rihemani komai na rayuwarki”.      “Hakane Asabe. Amma ni abinda yaban mamaki ma a ina yarinyarnan ta samu ciki to? Kodai dashi ta tahi daman? Dan inda na kaita bawata harkar banza akeba, inbadai bayan barina ta samu wajen aiki ba acan komai ya hwaru”.      “Sudai suka sani lanti, ni dai tunda na kaɗata kuma bakin kowa ya rihe miye damuwata. matsalata kawai tahiyar malam adalilin barinta gida, amma inaji a jikina shima ya kusa dawowa gareni”.     “Ban ganeba yimani karin. bayani”. Babu musi Inna ta shiga bata labarin komai tana matsar hawaye, dan tana son baba so mai yawa da itama batasan adadi ba a rayuwarta.       Sa'a dake laɓe a bayansu tanajin komai ta sharce hawaye da fitowa kamar batajiba ta fara haɗa wutar ɗorama Karima ruwan wanka kamar yanda innar tace. tana ƙoƙarin aza garwar wankan maƙwafta suka fara shigowa ƴan barka da ganin ƙwaƙwaf dan sai yanzu labarin dawowar karima gidan ya fara zuwa kunnuwansu.       Daga haka hirarta da hajja lanti ta watse. tashi hajja Lantin tai ma ta tafi bayan taje taga baby itama. dan mutane sai kallonta suke tunda ita ba ɓoyayya bace a garin dama tayi dillanci kafin fara ɗaukar yara tana kaiwa aikatau birni.    Ta tafine ranta makale da zancen Inna akan cikin Zinneerah. Itakam wahalar da taci a rayuwa yasa tayi nadama. Ta nunama Inna tana tare da itane kawai danta samu bakin zaren da zata taimaki Zinneerah. dolene saita koma katsina ta binciko ainahin gaskiyar abinda ya faru da ƴar mutane kozata samu kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya. Yanzu hakama zataje sauran ƙauyikan data ɗakko waɗancan yaran ne dan taji sukuma yaya suke ne? Ta kuma nema gafarar iyayensu.      Firar Inna da Hajja Lanti tasa Sa'a kuka sosai a yinin yau, saboda ƴan barka daketa shigowa yasa taketa ƙoƙarin dannewa har dare ya rufa. Saboda ƙudirin dake ranta yasa yau tai shirin kwana a gidan nasu. Bata kwantaba kuwa har wajen sha ɗaya da ƴan barka suka gama shigowa Tinene ta dawo gidan. Kallonta kawai Sa'a tai ta watsar, dan ko uffan batace mataba akan ina ta fito ko taje. Tunda dama zance nata yawo a gari Tinene na yawon dare, amma ko an faɗama Inna saita karyata tace anama Tinene sharrine dan ba'a ƙaunarta.     Sai da taga Tinene ta kwanta sannan ta fito kamar zata bayi, ta Window ta leƙa ɗakin Inna taga duk sunyi barci ita da Karima da jaririya.       Kanta tsaye wajen turmin sissikar hatsinsu da inna ta nunama hajja lanti ta nufa. dana tunda rana ta jiƙa wajen da ruwa dan ƙasar tayi laushi. Aiko an dace, dan tana ture turmin ta fara tona da fatanya a hankaki tana addu'a. Cikin sa'a ALLAH ya bata damar tone ƙasar sosai har takai ga abinda take buƙata. Wata ƙaramar kwanon tasa ta tono, jikinta har rawa yake ta ajiyesa gefe ta maida ƙasar wajen da ruwa ta rufe, ta ɗebo busashen ƙasa ta zuba sannan ta mauda turmin ta ɗauka tasar taje ta ɓoye akan sai da safe zatayi abinda ya dace. Daga haka ta koma ɗaki cike da danuwa da tashin hankali ta kwanta. Barci barawo shine kawai ya sace Sa'a a wannan dare amma bawai dan taji zata iya yinsaba.      Kuka tasha sosai na tausayin ƴar uwarta Zinneerah da taji Inna tace wai tana Lagos yanzu tana zaman kanta. Wannan kalma ta tsaya mata a rai, itace kuma take ƙara rura wutar tashin hankalinta akan zancen fiye da komai.......... _________________★      *_LONDON_* Halin da Zinneerah take ciki na zazzaɓi ya hana sake tada wata magana a gidan. Duk da kuwa Hajiya Iya da taji komai akan ƙaddarar Zinneerah ita da Baffah dake anan Nigeria zukatansu basu hutaba da saƙawa da kwancewa akan little.          Hakama AK duk da baisan komai game da Zinneerah ba shi nashi tunanin akan kamanninsa da little ɗin suka tsaya da kuma damuwar Farah. Dan yanason matarsa bai kuma son shigarta tashin hankali. Yaje can gidan domin lallashinta ya kuma fahimtar da ita gaskiyar zancen taƙi yarda su haɗu, saima kulle kanta datai a ɗaki.      Duk lallaɓata da sukai shi da Mahma danya sanar mata komai itama amma fir Farah daketa kwasar kuka taƙi buɗewa. Sai ma jiyota sukai tanata fashe-fashen abubuwa tana tabbatar masa cewar ta tsanesa. bakuma zata sake zaman aure dashi ba yaje ya zauna da karuwar data haifa masa ɗan ita ta haƙura.       Duk da kalamanta na masa zafi a rai haka ya dannesu yana cigaba da lallashinta daga inda suke tsaye a bakin ƙofa dan yasan tanada hujjar yin hakan. Sai dai matsalarta data kasa kwantar da hankalinta taji ta bakinsa sam saboda rashin man kanta.       Duk yanda sukaso ta sauraresu taƙi, hakanne ya bama Mahma haushi tace yay tafiyarsa kawai. Idan ta gadama ta fasa gidan tunda ita batasan lallashi ba. Badan yaso ba ya baro gidan ya dawo gida. Koda ya shigo bai nema kowaba ɗakinsa ya shige kansa na sara masa na azabar ciwon da yake masa.       Wanka yayo kozaiji sassauci, yana niyyar kwanciya kiran Baffah ya shigo masa. Batare da tunanin komaiba ya ɗaga suka gaisa. “Mike faruwa naji muryarka haka?”. Baffah ya faɗa daga can jin yanda AK ɗin ke magana da ƙyar.       “Baffah kaina ke ciwo”. Ya bashi amsa murya a raunane.     “ALLAH ya ƙara afuwa, sai ka daure kasha magani dan zama da ciwo babu daɗi. dama na kirakane muyi wata magana, amma tunda naji baka da lafiya mayi daga baya kasha magani ka kwanta”.       “Babu damuwa Baffah muyi maganar kawai, dan sai anjima nakeson shan maganin yanzu lokacin salla ya kusa anan”.     Ɗan jimm Baffah yayi daga can, dan shima dai maganar cin ransa take yafi buƙatar suyita yanzu ɗin ko zai samu sassauci a ransa. Ya sauke numfashi da cewa, “To shikenan hakanma yayi. Abdul-Mutallab!”.    Baffah ya kirayi ainahin sunansa. Hakan yasa AK ƙara nutsuwa gabansa na faɗuwa. Dan ya tabbatar maganar mai girmace tunda har Baffah ya kira sunansa na ainahi. Cikin sake bayyanar nutsuwarsa ya amsa masa.       Baffah ya cigaba da faɗin, “Abdul-Mutallab maganace mai muhimmanci ta sa na kiraka. Kuma inason ka faɗamin gaskiya kamar yanda na sanka, gaskiyar da zaka faɗamince zatasa na fahimceka kuma nai maka uziri”.      “Insha ALLAH Baffah zaka samu kowace irin gaskiyace daga gareni inhar na sani”.      “To Alhmdllh. Akwai yaro da ranar Gwaggonka tazo dashi, wanda na tabbatar bazai yuwu ka manta da shi ba, tunda yanzu Inna ke sanarmin matarka ta gama rikici akansa saboda ganinsa?”.      “Eh Baffah ban mantaba”.. Ya amsa masa gabansa na faɗuwa batare da yasan dalili ba.       Baffah da shima cikin ƙarfin hali yake maganar ya cigaba da faɗin, “Abdul-Mutallab kafin yau zuciyatace kawai kemin kaikawo akan kamaninka da yaron, amma zuwa yau da naji wanene yaron yasani cikin tashin hankali da damuwar abinda raina ke rayamin. Da farko ɗaukarmu hauwa'u ce ta haifesa, sai dai a yau suka tabbatar min da Zinneerah ce ta haifesa”.       “Z.. Zi... Zinneerah!?”. AK ya haɗa sunan Zinneerah da ƙyar zuciyarsa na wani ƙara kamar zata faso ƙirji ta fito dan kaɗuwar jin zancen............✍ *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_* *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* *Page 37* ________________________ _RANO NET! RANO NET! RANO NET!_ _WHO NO LIKE BETA AWUUF THINGS?_ _IDAN KAJI GANGAMI DA LABARI....! INA MASU ZUBIN ADASHEN DA BA RANAR DAUKA NA DATA?_ _TO KU MARMATSO KUJI, KU KUMA SHARE HAWAYEN KU, MUNZO MUKU DA SABBIN TSARE TSARE NA DATA, WADDA KOWA ZAI IYA SAYA DAI DAI KARFIN SA. A FARASHI MAI RAHUSA_ _RANO NET! RANO NET! RANO NET!__ _(Afford data at chikini price)_ _MALLAKI DATA A KUDI KALILAN DA RANO NET_ _TSAYA KUJI, A RANO NET ZAKA IYA ZAMA RESELLER KO WHOLESALER KAI MA, EH ZAKA/KI IYA ZAMA MA SAYAR DA DATA A FARASHIN SARI MUKE BAYARWA, KAI/KI KAFA KASUWANCIN KU KUMA. DA KUDI KALILAN._ _MUNA KUMA SAYARWA AKAN ‘DAI DAYA, KOWANE NETWORK MUNA SAYARDA DATA PLAN DINSA AKAN KUDI KALILAN, MASU FARASHIN SARA KUWA MA KU KUDIN BAI KAI HAKA BAMA_ _AIRTEL_ _9MOBILE/ETISALAT_ _MTN_ _GLO_ _DUK MUNA SAYARDA TSARIN DATA DINSU. KAMAR MISALI MTN MUNA SAYARDA 1GB.24MB AKAN FARASHIN NERA 300 KUMA YANA KAIWA WATA DAYA, GWARGWADON YADDA KAKE AMFANI DA DATA, 2GB 600, 3GB 900!!_ _DUKA WADANNAN TSARIN DATA DAMA NA SAURAN LAYIKA MUNA SAYRWA AKAN FARASHI MAI RAHUSA, WANDA KOWA ZAI IYA YIN TSARIN DAI DAI ALJIHUN SA_ _Ranonet.com.ng_ _GA SITE DINMU NAN DAKE YANAR GIZO, KAI TSAYE ZAKI/KA IYA SIYAN NAKA TA NAN. _ _KO A TUNTUBE MU TA NAMBAR TARHON MU: +234 803 081 1300/+234 808 540 5215_ _KYAU, INGANCI, RAHUSA, ADADE ANA YAWO A YANAR GIZO SAI RANO NET._ _RANO NET..!!!!_ _________________________ *Page 37* .............“Tabbas Zinneerah Abdul-Mutallab, sai dai itama bayin kanta bane ƙaddarartace hakan. Zan baka ainahin tarihin rayuwar yarinyar domin ka fahimci ainahin yanda zancen yake kafin mukai inda ni nake buƙata”.     Tamkar AK na gaban Baffah ya shiga gyaɗa masa kansa dake ƙara ƙarfin sarawa tamkar zai buɗe.       Baffah da duk yake jiyo yanda yake sauke ajiyar zuciya a jajjere ya fara bashi labarin rayuwar Zinneerah tun daga zaman mmn sadiq a gidansu har haihuwarta da barota datai, zuwa maganar cikin little da har yanzu babu wanda yasan wa yayma Zinneerah shi, itama kuma tambayar duniya tace batasan komaiba akai. Abdul-Mutallab ban taɓa zarginka da aikata ɓarna makamancin haka ba, sai dai zuciyata ta gagara nutsuwa akan kamanin yaron nan da kai musamman a yau da naji ainahin tarihin samuwarsa. Dan haka a matsayina na mahaifinka dan ALLAH ina roƙonka ka faɗamin gaskiyar abinda ka sani, koda ace da ganganci ka aikata zan fahimceka. Kaji tsoron ALLAH mu tausayama rayuwar yarinyarnan, dan kaima kanada ƙanne gasunan cike da gidan nan, sannan uba zaka zama watarana, na tabbata bazakaso hakan ta kasance akansu ba. Na baka dama kaje kayi tunani daganan zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu, na barka lafiya”.    Baffah ya katse wayar batare da ya jira cewar AK da gaba ɗaya yakejin duniyar na juya masaba.......         Barowar AK gidan su Mammah baifi da mintuna ashirin ba ta iso daga ƙasar China. Dan harga ALLAH zancen Farah ya matuƙar gigitata akan wai Abdul-Mutallab ya haihu da wata a waje harma taga ɗan. Tsabar tashin hankalin data shiga ko gama abinda ya kaita bataiba ta dawo dan zancen waya bazai gamsar da itaba gara azo ayi ƙuru-ƙuru.      Maganarta da Farah taji yasa ta buɗe ɗakin data maida kaca-kaca da fashe-fashe. Rungumeta Mammah tayi tana lallashi. itako kuka take kamar zata shiɗe duk ta fita a hayyacinta.      Ko tsayawa taji ta bakin Mahma dake son mata bayani bataiba ta kama hannun Farah suka fito. Sanin halinta yasa Mahma itama biyosu dan batason ƴar uwarta taje ta ida zubar da sauran mutuncinta a idon mahaifiyar Kabeer (Hajiya iya) kodan darajar ƴaƴan dake a tsakani.              Su Hajiya Iya duk suna a ɗaki suka dinga jin ƙwala kiran sunan Abdul-Mutallab da Mammah takeyi kamar zata fasa gidan. Babu shiri duk suka fito har Zinneerah dake barcin wahala dan zazzaɓin nata bai gama sakintaba duk da jikin babu zafi sosai yanzun.      Cikin ɗan barcin daya fara figarsa na kiɗimar kalaman Baffah da yaketa bita a zuciya da ƙwaƙwalwa yake jiyo muryar Mammah na ƙwala masa kira. Ahankali ya buɗe idanunsa da sukai masa matuƙar nauyi ya yunƙura da ƙyar ya tsashi zaune, jin kamar muryar tata na kusanto ɗakinsa ya sakashi zira ƙafafunsa ƙasa ya sauka a gadon gaba ɗaya domin neman riga yasa, dan daga shi sai boxer a jiki.            Jallabiya ya samu ya saka sannan ya nufi ƙofar ya buɗe hannunsa dafe da kansa dake sara masa. Mammah da Farah na neman danna kai a ɗakin Mahma data ƙaraso gurin kusan tare da Hajiya Iya ta riƙo mata hannu tana girgiza kanta, tana mata magana da idanu akan ta kama kanta.       Mahma tamkar uwa ce a garesu, dan itace babbar yayarsu, ta kuma riƙe girmanta agaresun. Sai dai a yau Mammah batajin zata iya controling kanta wajen mata biyayyar. Zatai magana Hajiya Iya datai kicin-kicin da fuska dan al'amarin Farah ya fara bata haushi ta katseta.       “Lafiya kuwa Hindatu irin wannan ƙwala kira haka?”. Tai maganar da mata kallo ɗaya ta maida ga AK dake dafe da kansa yana kallonsu kawai.        Mahma ce tai saurin cewa “lafiya lau Hajiya, mun sameku lafiya ya ƙarfin jiki?”.       “Bafa lafiya ba Adda, nifa kin sanni ba ɓoye-ɓoye na iyaba”. Mammah ta faɗa kafin Hajiya iya ta amsa gaisuwar Mahma.      Kai Hajiya iya ta ɗan girgiza, danta fahimci halin Farah dana Mammah suna kamanceceniya. “To ALLAH ya ƙyauta” Hajiya iya ta faɗa tana nufar AK.         A harzuƙe Mammah tace, “Hajiya zai ƙyauta ne idan naji a inda wannan mara mutuncin ya samo ɗa? Auren da kuke iƙirarin masane akai masa a ɓoye ban saniba? kokuwa a waje ya samar da ɗan ga wata?”.     Cikin sauri Mahma ta riƙe hannun Mammah ranta a ɓace tace, “Hindatu! Wai nikam yaushe zakisan kin girmane? Wane irin kalamaine haka masu tsauri akan yaro?”.       Hawayene suka ɓallema Mammah, “Addah yaya kikeson nayi? Kema kinsan halin Abdul-Mutallab, idan ba tauri nai masaba yanzu zai maidani sakara tunda huɗubar ubansa ta fara sakashi ganina a banza, yo inba a banza yake ganinaba yanzu a ina ya samo ɗa saboda ALLAH?. Na rantse da ALLAH a wannan karon sai inda ƙarfina ya ƙare, bazan taɓa yarda a rabani da yarona ba, ance ba'a ƙaunata, to basai a barni da ƴaƴana ba tunda ni na haifi abuna. Amma sai bita da ƙulli akemin akan Abdul-Mutallab”.      Karan farko Hajiya iya tai murmushi tana jinjina kanta, danta fahimci da biyu Hindatu tazo gidan kenan, to lallai tana dai-dai da haukarta kuwa. Juyawa tai ta kamo hannun AK da shi bama fahimtar Mammah yakeba da ƙyau, sam a rayuwarsa baison hayaniya, tada masa da hankali takeyi matuƙa gaya, shiyyasa duk irin waɗanan abubuwan yakan so kauce musu gudun shigarsa wani hali, amma a wannan gaɓar yaya zaiyi? Uwa uwace, tanada mutunci mai nauyin gaske a gareshi da baki bazai musaltaba. Sannan ya mata uzuri daga ita har Farah ɗin dan yasansu mutane ne masu wahalar fahimtar abu a lokaci ɗaya, musamman abinda basa so.         “Zamu iya zama”. Hajiya iya ta faɗa tana jan hannun AK. Mammah zatai magana Mahma ta dakatar da ita, hannunta taja itama da watsama Farah dake kuka har yanzu wani shegen kallon ina tafe kanki kema..        Duk zama sukai badan Mammah taso hakanba, Hajiya iya da har yanzu take riƙe da hannun AK ta fara musu bayani akan su basuma Moddibo aure da ƴar kowa ba........       “Mammah kinji ko, wlhy ɗan shege ne?”.     Fara ta katse Hajiya iya dake bayani cikin fashewa da matsanancin kuka.      A fusace itama Hajiya iya ta dubeta zatai magana sukaji fasa ihun Zinneerah data yanke jiki ta faɗi. A zabure Hajiya iya da AK suka miƙe, hakama Mahma duk da batasan wacece ba babu shiri ta miƙe. Farah da Mammah ko ƙin tashi sukai, dansu jin daga ina ɗa ya fito shine babbar damuwarsu.         Tuni hajiya iya ta mance da jikinta na tsufa, cike da sassarfa ta nufi ɗakin dan tun zamansu a wajen Khalipha ya janye su Zinneerah suka koma ciki. Saurin rufama Hajiya Iya baya AK yayi. Hakan yasa Mammah son tsaidashi amma bai saurareta ba. A ƙufule Farah tace, “Kingani ko Mammah, a cikin ƴan iskan yaran nan nefa, na tabbatar shegen Khalipha ɗin nan ne ya haɗa drama ɗin nan, yanzu hakama harda ita tsohuwar nan kafin ta fito”.       Miƙewa Mammah tayi tana faɗin, “Aiko sunyi ta banza, tashi muje, ni zanyi maganin kowansu, yanda sukace basa ƙaunata nima bazan taɓa son kowaba a cikisu”.        Lokacin da suka shigo ana ƙoƙarin shafama Zinneerah data suma ruwa. Wani irin nannauyan numfashi ta kawo, sai kuma ta ƙanƙame Meenal dake riƙe da ita jikinta na wani irin rawa. Kuka ta fashe da shi tana faɗin kanta zai fashe, su taimaketa kanta kanta.       Hankalin Hajiya Iya ya tashi matuƙa, da ƙyar ta iya janyo Zinneerah daga jikin Meenal ta maidata jikinta. Akwai sani sosai tattare Mahma game da irin waɗanan abubuwan na sammu da aljanu da sauransu, dan mijinsu da ALLAH yayma rasuwa babban malami ne akan wannan harkar, shiyyasa suka koyi abubuwa da dama agaresa musamman ita data kasance matarsa ta farko tun tanada ƙuruciya, dan ita dama ba'a nan London ta tashiba a Morocco ne hannun kakarsu, sai dai tazo yawo ta koma harma aka aurar da ita, sai dai dayake ALLAH ya ƙaddara zamanta anan bayan rasuwar mijin ta dawo da zama nan ɗin duk da mahaifiyarsu ta jima da komawa Morocco itama acanma ALLAH yay mata rasuwa, dan ko sanda Hiddatu ta kashe aurenta ta koma London mamansu tana Morocco, kuma wani daliline mai ƙarfi ya maidata zamancan ɗin dole.        Zama tai kusa da Zinneerah itama ta ruƙo hannunta tana magana a hankali jin Hajiya Iya na cewa azo akai Zinneerah ɗin asibiti a kiɗime..         “Wannan ba ciwo bane na asibiti Hajiya, addu'a take buƙata dan al'amarine kamar na sammu ko jinnu”.     Kallonta hajiya iya tai da mamaki, tace, “Sammu kuma Zaliha?”.       “Tabbas haka nake hasashe”. Ta faɗa kanta tsaye tana ɗora hannunta akan Zinneerah daketa jujjuyashi tana kukan zai fashe.      Sam AK baya son wannan abun, dan kusanma shine maƙasudin ɗakko Mahma da yay daga Morocco ya maido London, a wani zuwa da yay can ya samu harkokin mijin nata na neman dawowa kanta shiyyasa ya tattarota ya maido nan. Cikin ƙarfin hali dan shima kan nasa ciwo yake masa har yanzun kamar zai tarwatse ya matso kusa da su. “Mahma da ga faɗuwa kuma sai ace sammu, ita wannan ƴar yarinyar wama zai damu da lamarinta balle ya ɓata lokacinsa wajen aikata mata wani sihiri?”.        Kallonsa Hajiya iya tai taɗan girgiza kai, muryarta cike da damuwa tace, “Modibbo tunaninka kenan, shi magauci ina ruwansa da ƙanƙantar shekarunka, sannanma hakan zai iya faruwa dan kishiyar mahaifiyar yarinyarnan atsabibiyace komai zata iya aikatawa. Kinga Zaliha nidai dubamin ita, shi ba komai ya saniba sai zama cikin masu jajayen kunne”.      Mahma dama ita ba tsayawa tai saurarensuba, hannunta riƙe da kan Zinneerah take tofa mata addu'oi, a hankali ta fara rage kukan da takeyi tana juya kan a hankali. Cikin abinda bai fice mintuna a shirinba sai ga wani irin nannauyan barci yayi awon gaba da ita sai ajiyar zuciya take saki a jajjere.       Khalipha da kamar shima zaiyi kuka ya kalli su Jamal, “To kukan ya isa haka ko, kuyi mata addu'ar”. Hawayensu suka shiga sharewa.     Godiya Hajiya iya ta shiga yima Mahma bayan ta godema ALLAH. Mahma dake murmushi ta miƙe tana faɗin, “Babu komai Hajiya ai muma ƴarmu ce. Insha ALLAH idan ta farka mukaga yanda jikin yayi sai asan abinyi, ALLAH ya bata lafiya. Amma bara na baku addu'oin da zakuyi abata taita sha kafin gobe idan ALLAH ya kaimu, suma zame mata sune ruwa”.       “Aiko mun gode sosai Zaliha. ALLAH ya jiƙan magabata kinji, ya raya miki zuri'arki da namu baki ɗaya”.      Baki Mammah ta taɓe tana ɗauke kanta, dan itafa ko'a jikinta ma, tama ƙagara su gama ƙaƙale-ƙaƙalensu azo a gaya mata abinda ya kawota. Mahma data gama karantarta tsaf tana gama rubuta addu'oin da za'aima Zinneerah ta dubeta tana faɗin, “Hindatu muje gida”.       “Adda muje gidafa kikace? Kina tunanin zanbar gidan nan banji miya kawoni ba?”.      “Sosaima kuwa zaki barshi, tunda ita maganar ai ba guduwa zatai ta barmuba, idan yarinyarnan ta samu lafiya saimu dawo a yita a tsanake dan a yanzuma babu nutsuwar da zaki fahimta tattare dake”.        Baki ta buɗe a hasale zatai magana Mahma taja hannunta suka fice. Farah zata bisu Mahma ta dakatar da ita. “Wlhy idan kika biyomu ko Abdul-Mutallab naso ko baya so sai na sakashi ya sakeki tunda ke hankalinki a gwiwa yake, idan zaki zauna gidan mijinki ki zauna. Idan kuma zaki biyomune ki tabbatar kin fito kenan wawuya kawai”.      Saurin ja baya Farah tayi dan Mahma ta fito musu ne a ainahinta shiyyasa itama Mammah ɗin ta gagara cewa uffan, sai masifa take a zuciyarta kamar zata haɗiye harshenta cikin ciki.       Daɗi sosai AK yaji akan hukuncin Mahma, danshi kanshi a yanzu filin yin nazari yake buƙatar samu akan wannan al'amarin, ALLAH shine shaidarsa bai taɓa aikata zina da ƴar kowa ba, shi baima taɓa ganin Zinneerah ba sai a gidansu wannan zuwan. Amma gashi Baffah kansa zargin yaron nasane yake. Kai shi kansa da kansa zargin kansa yake dan kamaninsa da yaron abun a dubane akumayi nazari. A yanzu kawai yana ganin shawarar da zuciyarsa ke bashi ya kamata yabi kozai fita daga ruɗanin da yake ciki daga shi har ƴan uwansa. Miƙewa yay batare da yacema kowa komaiba ya fice a ɗakin. Hakan yasa itama Farah dafa masa baya sai dai ɗakinta ta nufa tana kuka ba nashiba.      Hajiya iya da gaba ɗaya take jin komai yana mata nauyi a zuciya ta duba Khalipha a sanyaye tace, “Ka bisa Khalipha, kasan Moddibo bai iya ɗaukar damuwa da sauƙi ba”..         A raunane Khalipha ya jinjina mata kansa, dan shima a ruɗan yake da komai, saboda Hajiya Iya ta bashi takardar wajen mmn sadiq ya karanta ɗazun saboda fitowar sunansa a ciki. Ya kuma sanar mata gaskiyar abinda ya sani game da haɗuwarsa da Zinneerah.............✍ *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_* *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* _________________________ *Page 38* ............Sai da Khalipha yay sallama a ƙofar ɗakin aka bashi izinin shiga sanna ya shigo, zaune ya sameshi cikin kujerar dake a ɗakin kansa jingine ya lumshe ido da makarinta. Bai motsaba daga yanda yake har Khalipha ya zauna a ɗayar kujerar dake kallonsa cike da tausayin ɗan uwan nasa. ɗan jimm yayi na wasu sakanni kafin yay ƙasa da kansa cikin lallashi yace, “Yayanmu dan ALLAH ka kwantar da hankalinka, insha ALLAH bin komai a sannu zai warware dukan aninda zuciya ke hasashe duk rintsi”.        Wani ɗan murmushi AK ya saki yana buɗe idanunsa da gaba ɗaya launinsu ya canja, sai da ya yima Khalipha kallon wasu sakanni kafin ya tashi zaune sosai yana furzar da abinda ya tokare maƙoshinsa mai ɗaci. Cikin son danne duk damuwarsa yace, “Bestie dama kasanta?”.     Ɗan kallonsa Khalipha yay alamar wa?.      Idanunsa ya lumhe ya buɗe akansa, kamar bazai sake tankawaba sai kuma ya furta, “Zinneerah!”. A saman laɓɓansa.       A bazata Khalipha ya saki murmushi, a ransa ko gulma yake (kai yayanmu kako iya faɗar sunan). A fili kam sai ya gyaɗa masa kai tare da ƙara nutsuwa sosai. “Nasanta Yayanmu, amma sanin na kwanaki goma zuwa sha ɗaya ne kacal idan ban mantaba. (A take ya fara bashi labarin haɗuwarsu a randa aka bigeta, wanda a dalilin aiken da yay masanema yaje jigawan, suna hanyar dawowa motar ta samu matsala. ya baro wanda sukaje taren da motar shiko yabi ta haya dan zuwa ya isar da saƙon karsu makara tunda yasan jira yakeyi).          “Wannan shine dalilin dayasa na santa Yayanmu, ni duk zatona ma tanada aure wlhy, shiyyasa ban wani taɓa maida hankali akanta ba, inma baka mantaba na baka labarin accident ɗin ai a wancan lokacin. kuma ni a zuwan nan da mukaima sai ban ganetaba saboda duk ta canja, sai randa naga Gwaggo (Mmn sadiq) sannan na ƙara tabbatar da itace, inataso muyi maganama hakan bai faruba saboda ciwon Granny”.        Ɗari bisa ɗari AK ya yarda da Khalipha, dan yason bai iya ƙaryaba, tunda suke dashi bai taɓa kamashi da wani abu na rashin gaskiya ba, zamansa ya gyara da ƙyau yana furzar da numfashi, cikin tsatstsare Khalipha da idanu yace, “Miye amsata ta ɗazun game da kamannina da yaro?”.         Ƙasa Khalipha yay da kansa cike dajin nauyin gaskiyar abinda ke a ransa. Muryarsa a dakushe yace, “Yayanmu al'amarin akwai rikitarwa, harga ALLAH banida takamaimai amsa, dan bayan matarka nine mutum na biyu da zan iya bada shaida akanka, hakan yasa duk abinda zuciyata zata iya hasasomin ƙwaƙwalwata bazata iya ɗaukaba, shawara ɗayace shine ai gwaji kawai, maybe hakan ya kawo hasken da kowa zai iya fahimtar bakin zaren. Ka gafarceni idan nayi kuskure”.        Murmushi AK ya sake saki mai sanyi yana gyaɗa kansa. Cikin nuna gamsuwar zantukan Khalipha yace, “Shiyyasa nake kiranka Bestie, dan mafi yawan tunaninka irin nawane, inason mutum mai gaskiya da ƙyaƙyƙyawan nazari akan komai Khalipha. ALLAH yay maka albarka, nima a raina shawarar zuwa Nigeria nake domin gwada ƙwayoyin halitarmu ni da yaron, maybe hakan zaisa na iya tuna wani abu dana manta ko samun ƙwarin gwiwar bakin zaren”.       Khalipha dake murmushi yana jinjina masa kai yace, “Nagode Yayanmu”.        “Nizan gode maka ai, dan ka zama ɗan uwa ɗaya tamkar da dubu. Yanzu kaje ka huta kaima, sai dai banason ka sanarma Granny tafiyata, sai na gama shiri zan sanar mata, insha ALLAH nanda awanni biyar zan wuce”.          Cikin waro idanu Khalipha yace, “Yayanmu ince sai nan da kamar kwana biyu?”.      Kai kawai ya girgizama Khalipha yana miƙewa da murmushi akan fuskarsa. Ganin ya nufi toilet shima sai Khalipha ya miƙe ya fita cike da tausayin Yayan nasu, ya tabbatar jarumtarsa da ƙoƙarin iya shanye damuwane kawai ya danne dukkan halin da yake ciki, amma duk wanda ya sanshi ya kalli ƙwayar idonsa yasan baya cikin kwanciyar hankali. (Ya ALLAH ka kawo mana mafita, ka haska mana duhun da muke ciki domin rahamarka ya UBANGIJI). Khalipha ya faɗa yana nufar ɗakinsa zuciyarsa cike da rauni da ɗaci. Har ransa kuma yanajin zai iya auren Zinneerah koda ace ƴaƴa goma ta haifa, amma yanason jin ta bakinta itama harga ALLAH. ★★      Tun bayan fitar Khalipha a ɗakin babu wanda ya sake jin ɗuriyar AK a gidan sai bayan awannin daya ambata ma Khalipha na wucewa 9ja. Duk da halin da yake ciki na tsananin ciwon kai dana zuciya jarumtarsa ta shanye kaso mafi yawa. Sam bazaka iya hasaso damuwarsa a saman fuskaba, sai dai idan ka masa sanin ƙwarai a kallo ɗaya zaka gano damuwar cikin ƙwayoyin idanunsa da rauninsu ya bayyana ƙuru-ƙuru.         A falo ya samu su Jamal nacin abinci su uku. Yay musu kallon nazari ganin yanda suke kowa fuska da damuwa ya ɗauke kansa. Sai da yazo dab dasu suka farga da shi saboda motsin takunsa da yawaitar ƙamshin turarensa. Gaishesa sukayi, ya amsa musu yana wucewa ɗakin hajiya iya.         Koda ya shigo bayan sallamar da yayi baiji an amsaba bai samu kowa a ɗakinba sai Zinneerah dake kwance tana barci har yanzun. Hanyar toilet ya ɗan duba saboda jin motsin ruwa, da alama Granny ce a ciki. Ya ɗauke kansa yana maidawa ga Zinneerah. Bayanta kawai yake iya gani, dan haka ya taka a hankali zuwa inda ta juya fuskarta, kansa tsaye ya zuba mata fitinannun idanunsa dake cike da abubuwa masu yawa a wannan yinin, kallo yake mata irin na ƙurulla da bai taɓa matashiba, ya kai tsahon minti ɗaya da wasu sakanni a haka kafin ya matso dab da ita, ahankali yaɗan ranƙwafo kanta, tare da kai hannusa a fuskarta ya janye mata jelar gashinta daya zubo biyu da akai mata kalba da ɗan yatsansa manuniya.     Motsawa tayi alamar zatai juyi. Kauda kansa yayi yanaja da baya kamar bashi ya aikataba. A dai-dai nan Granny ta fito.        “Lafiya kuwa na ganka da jikka moddibo?”.     Juyiwa yay ya dubeta, kansa tsaye yace, “Zanje Nigeria ne Granny”.         “Nigeria kuma? Akanmi to?”. “Akan abubuwa da yawa. Kimin addu'a ke dai”.        “To addu'a kam kullum cikin yimuku ita muke Moddibo, amma daka sanar dani nikam da tare muka wuce, dan zaman garin nan fa ya isheni”.       Guntun murmushi yayi yana matsawa inda take. Ya kamo hannunta, cike da lallashi yace, “Kiyi haƙuri kinsan baki gama ganin likitaba, nima bawani jimawa zanyiba inagama 2days zanyi insha ALLAH”.      “To ALLAH yasa haka. Amma wannan birkitacciyar matar taka tare zaku tafi? Dan bazaka barmana ita nanba”.         Maganar tata ta bashi dariya. sai dai baiyiba. hannunta ya saki da faɗin, “Matar tawace birkitacciya Granny? To ai duk birkicewarta kin iya da ita na sani. Karki damu babu abinda zai faru insha ALLAH”. Ya ƙare maganar yana ɗan duban inda Zinneerah take ya ɗauke kansa.      Duk da hajiya iya batasan manufar tafiyar tasaba bataso ya tafi ya barta ananba. Amma duk da haka sai tai masa fatan alkairi da gargaɗin karfa yaje yay zamansa.      Shidai fita yay kawai yana ɗan murmushi. Yasan ko mi zaiyi Farah bazata sauraresaba a yanzun, dan haka baibi takantaba dan ya bar mata saƙo a ɗakinsa. A falo ya tsaya ya aika Jamal kiran Khalipha. Babu jimawa kuwa sai gashi ya fito cikin shiri.     Tare suka fita shi da Jamal da Khalipha ɗin da zasu masa rakkiya airport. _____________★      Zinneerah batasan da tafiyar AK ba, koda ta tashi kuma su Khalipha sun dawo gida. Kowa yaji daɗin yanda ta farka normal, sai dai jikinta duk a sanyaye, komai yinsa take kamar mara ƙashi a jiki, gashi sam bata da walwala. Abinci ma sai da Hajiya iya ta takura mata sannan tacisa tasha ruwan addu'oin da tai mata tun ɗazun kamar yanda Mahma ta faɗa.      Ta farka da abubuwa masu yawa a cikin rai. sai dai miskilancinta da rashin son nuna damuwa akan abu ya shanye kaso mafi yawa, dan haka yanayin ya rikiɗe mata kawai zuwa sanyin jiki da rashin son hayaniya.       A ɓangaren Farah kam kamar yanda bata fito ta nema kowa ba babu wanda ya nemeta. Sai dai mai aikinta dake ɗan shiga da fita zuwa ɗakinta lokaci-lokaci tana kai mata abunda ta buƙata, itama batasan AK yabar gidanba sai a bakin mai aikin nata daya barma saƙon cewa ta sanar mata yabar abu a ɗakinsa. Sosai hakan yayma Farah ciwo, badan tana tsoron hukuncin Mahma ba da wlhy saita bar masa gidansa. Bata kira Mammah ba sai aunty Zakiyya. Mammah kuma saita tura mata text message akan tafiyar AK ɗin. Ta kuma tabbatar mata wani ƙullin AK ya tafi yowa a Nigeria danya binne abinda ya shuka akan yaron. Itama kanta Mammah ranta yay matuƙar ɓaci da tafiyarsa bai sanar mataba. Hakan yasa ta shiga gayama Mahma rai a ɓace.     Murmushi kawai Mahma tayi, a nutse tace, “Duk ke kikaso hakan Hindatu, na daɗe da nuna miki tsaurinki akan Abdul-Mutallab bashike nufin zaki iya rabasa da mahaifinsa ba. Adilah mace ce zaki iya tanƙwarata ko bataso tamiki biyayya. Amma Abdul-Mutallab namiji ne, su kuma maza da kike gani kullum tunaninsu dabanne da namu, suna da saurin hango kuskure idan sun so hakan, sai dai su ɗauki mataki kosu bari wannan zaɓinsu ne, dan hakan a jininsu yake. Ni banga dalilin da zaisa kicigaba da damuwa da alaƙar da ALLAH ya haɗaba, tun ran ginifa tun ran zane, kuma da uba ake ado kema kin sani. Inba hakaba miyasa sanda Mama ta koma Morocco kika dawo london kika zauna da Daddy? Ai da saiki bita can kota hanaki zama anan ɗin wajen Daddyn. Yakamata ki dawo da hankalinki jikinki, dan amatsalarki da Kabeer daban ki daina ƙoƙarin saka yaranku a ciki, hakan bazai haifar miki da ɗa mai ido ba. Da yawan labarai a tarihi maza ke nuna ƙarfa-ƙarfa wajen amshe ƴaƴa a hannun uwa idan ƙaddarar rabuwa ta ratsa, sai dai abinda mutane basu saniba ko suke gaza tunawa idan mu mata muka sami damar nasarar karɓe yara a hannun ubansu bisa irin wannan ƙaddarar munfi mazan atsabibancin cusama yaran aƙidar ƙin uban koda ace mune da kaifi a wajen haifar da rabuwar auren. Ya kamata ki dawo cikin hankalinki, ki daina azabartar da Abdul-Mutallab da laifin Kabeer. Dan na fahimci haushin Kabeer kike saukewa akan Abdul-Mutallab akowane lokaci, wannan itace kawai gaskiyar dazan iya gaya miki dan karkiyi biyu babu. Daga lokacin da zuciyar Abdul-Mutallab ta fara raya masa tsaurinki yayi masa yawa to tabbas zaki rasashi ki kuma rasa Adilah itama dan zatabi ɗan uwanta kodan so da shaƙuwar dake a tsakaninsu mai ƙarfi”.        Mahma ta miƙe tabar mata wajen tana gama faɗa. Da kallo kawai Mammah ta bita batare data iya cewa komaiba. Tabbas gaskiya Yayar tata ta sanar mata. Sai dai bataji a ranta zata ɗauka dan itafa bazatabarma Kabeer da uwarsa ƴaƴanta ba. Dan ita tasha wahala akansu bawani shege ba. Zata riƙe ƴaƴanta shima ya riƙe nashi daya tara da shegen aure-aurensa da idan ta tuna sukafi baƙanta ranta fiye da komai. Taɗau alwashin zatayi yaƙi mai girma akan tabbatar da cigaban wanzuwar ƴaƴanta tare da ita duk wuya duk rintsi. *_NIGERIA_*        Koda AK ya iso Nigeria Baffah yayi mami matuƙa, amma da yake shima a yunwace yake da son ganinsa sai hakan yay masa daɗi. Ko gaisuwar kirki basuyi zaman yiba AK ya sanarma Baffah abinda ya kawosa. hundred percent Baffah ya gamsu da hakan, shiyyasa ya shiga saka masa albarka. a take kuma ya kira Mmn Sadiq. Bayan sun gaisa itama kamar yanda suka saba cike da girmama juna, ya sanar mata hukuncin da suka yanke.       Sosai mamakin hakan ya kama mmn sadiq. Cikin sanyin jiki tace, “Ya ilahi, Yaya mufa bamun faɗa muku labarin nan bane domin zargin Adnan akan kamanninsa da Little”.      Murmushi Baffa yayi mai faɗi, ya gyara zamansa yana faɗin, “Nasani Hauwa'u, muma kuma ba hakan bane a ranmu wlhy, sai dai ki sani tun randa kukazo da yaron nan gidannan babu wanda zuciyarsa ta huta akan kamaninsa da Adnan a gidan nan. Jin gaskiyar samuwarsa tasa muke kwaɗayin yin gwajin ko hakan zai sama mana kwanciyar hankali, dan nayi alƙawarin saina ƙwatoma Zinneerah haƙƙinta awajen koma wanene. Yanzuma bayan anyi gwajin insha ALLAH gobe idan ALLAH ya kaimu zamuje can asalin ƙauyen nasune. Dan haka banason zuciyarki ta ƙara miki wani hasashe daban bayan ƙyaƙyƙyawa”.       Sosai raunin mmn sadiq ya bayyana, tace, “Shikenan yaya, ALLAH ya saka da alkairi yabar zuminci. Bara nama Yaya magana to dan yana gida sai mu kawosa kawai”.      “Hakan shine dai-dai, mu haɗu a shira hospital daku”. Daga haka Baffah ya yanke wayar.       Wanka kawai AK ya samu yayi bayan Safiyya sunje sun gyara masa ɗakinsa da falon ɓangaren hajiya iya, abincima bai iya ciba sai tea yasa Ni'ima ta haɗa masa. daga haka ya fito ya sami Baffah dake zaman jiransa yana waya rai ɓace.     Shiru yay yana nazarin wayar ta Baffah, inda kai tsaye ya gane da Mammah suke waya, runtse idanunsa yayi da ƙarfi jin yanda Baffah ke dasama Mammah baƙaƙen maganganu, wanda ya tabbatar itace ta fara masa, shiko yake maida mata murtani.     Juyawa yay a hankali zai fita ya jiyo kalaman Baffah da suka sakashi dakatawa a kausashe.       “Komi zakice kice Hindatu, wlhy da banma kawo hakan a rainaba game da Adnan. Amma wlhy kinji na rantse a wannan gaɓar zan tabbatar miki da cewa ni Kabeer Abdul-Mutallab Shira nine mahaifin Adnan, ba kuma tsoronkine yasa na barmiki shiba daga shi har ƴar uwarsa. Dan haka muzuba mu gani ni dake ɗan hakal ka fasa”.    Daga haka Baffah ya yanke wayar yama kasheta gaba ɗaya dan baya buƙatar ta sake kiransa..............✍ *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_*  *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* _________________________ *Page 39* ..........Da sauri AK ya ƙarasa ficewa ransa na masa ƙuna da wannan halayya na Mammah, bashi da burin daya wuce ganin iyayensa sun sasanta kansu sun koma rayuwar aurensu, sai dai ya gwada ƙoƙarin yin haka yafi sau a ƙirga abin ya gagara. Kuma Mammah ce ke bada matsala a koda yaushe. Tunma Baffah na nuna masa zai amince shi, har takai yanzu idan yay masa maganar Mammah saiya ja masa warning.          A mota ɗaya suka tafi ran kowa babu daɗi, dan haka motar ta ɗauki shiru sai driver daketa aikin tuƙi har suka isa Shira Hospital.     Tuni AK ya tanadi likitocin da zasu aikin harsu uku domin samun gamsuwa akan abinda zai fito, dan haka suna isowa suma su Mmn Sadiq suka iso ɗauke da Little.       Yanako ganin AK ya maƙale masa, duk da ɓacin ran da AK ke ciki sai da yay murmushi yana mai rungume little a jikinsa. Ganin yaronma da yayi sai yakeji a ransa ALLAH ma yasa ya kasance nashi ɗin, dan har cikin ransa wata irin ƙauna yake masa mai ƙarfi da saka zuciya nutsuwa.      Cikin mutunta juna suka gaisa, inda mamaki ya cika Dr Mahmud saboda ganin Abba. Shima Abba daya ganesa sai wani tunani yazo masa. Cikin kasa jure abinda ke ransa yake tambayarsa ko ina bawan ALLAHn nan daya sakama little sunansa?.     Kai tsaye Dr Mahmud dake dariya ya nuna AK, “Baba ai gashima zaune, ina takwaran nasa kuwa? Nasan ya girma yanzun ko?”.        Da sauri Abba ya kalli AK da Little ke a jikinsa zuciyarsa na bugawa. Cikin ɗan rawar murya yace ai ga yaron nan a hannunsa”.       Ba Dr Mahmud ba, hatta AK sai da zuciyarsa ta harba. Yay saurin duban Abba da faɗin, “Uncle kana nufin kaine wanda ya bani damar zaɓama yaro suna shekara uku data shuɗe?”.      “Tabbas nine kuwa. Kuma wannan shine yaron”.      Sosai maganar Abba ta sakasu jin shock su duka. Baffah dake saurarensu ya nemi jin ƙarin bayani. Dr Mahmud ne yay masa bayanin komai har yanzu firgici da al'ajabin kamannin little da AK na bayyane a fuskarsa.       Murmushi baffa yayi yana jinjina kansa. Sai dai komai baiceba yabarma zuciyarsa. Dan yama gama yarda AK na ɓoye masa wani abune game da yaron kenan, inba hakaba yaya akai hakan ta faru? Tunda a wannan zuwan basusan yazoba sai a shanun ƴan talla yaji. To lallai kam zaiyima tufƙar hanci, dan yama gama yanke hukunci saura zartarwa.        Baffah ne ya dakatar da wannan hasashen su Dr Mahmud suka shiga aikinsu. Duk wani gwaje-gwajen daya dace akan ƙwayoyin haluttar little da AK akai musu. Abinka da masu abu, ba'a wani zauna wasaba suka shiga ganin sun tantance komai dan Baffah yace bazasubar asibitinba sai da result....... _________________________★        *DANYA*   A lokacin da gwajin ƙwayoyin halitta ke gudana acan Shira Hospital tsakanin AK da Little anan danya kuma baƙuncin Baba su Inna suka samu da farar safiya babu zato babu tsammani.         Duk suna zaune a tsakar gida ƴan barka na shigowa jefi-jefi da ƴan gulma. Karima na ɗaki kwance ita da ƴar jinjirarta tana kwasar kuka akan abinda ya barota da Kaduna, dan wahalar ciki tasa bata samu damar nazari akan komaiba sai yau da take jinta sakayau.      Tinene na kwance a ƙofar ɗakinsu wai ƙirjinta da kanta na ciwo, tun safe data tashi da abinda ta wayi gari kenan. Sai Sa'a daketa kaikawon yin aiki ita da Yaya Gajeje. Inna kuma na zaune kusa da Tinene tana gyaran gyaɗa da Yaya Gajeje tazo da ita gidan domin yin miya.           Sallamar mace da sukaji ya sakasu ɗan juyowa kusan su dukansu dan duk zatonsu ƴan barka ne ko cikin dangin Babawo dakan zo jefi-jefi, dan innarsa ma da tace zata dawo tun jiya har yau basuga ƙeyartaba. Sai dai ta aiko musu da kayan kunun da tace dana barka kuma kamar yanda uwar miji keyi a al'adar ƙauyen.         Ƙyaƙyƙyawar mace mai tarin kamala da ƙwarjini ta sake maimaita sallamar datai musu ganin duk sun zubo mata idanu basu amsaba. Yaya Gajeje ce tai ƙarfin halin amsawa da cewa, “Maraba, bismillah shigo baiwar ALLAH duk da dai bamu wayekiba”.         Murmushi matar tayi tana ɗan juyawa bayanta jin motsin takowar abokin tafiyar tata. Kafin ta samu damar bama Yaya Gajeje amsa Baba ya shigo shima da sallama a bakinsa. Duk da ƙyawun da yayi cikin ɗanyar shadda fara tas da ƙiba daya ƙara da haske hakan bai hana iyalan nasa shaida shi ba.      A take fara'ar fuskar Inna ta ɓace ɓat sai gabantane ke wani irin bugawa da sauri-sauri kamar zai buɗe. Cikin rawar murya tace, “Malam?!”.       “Na'am Asabe”. Ya amsa kansa tsaye yana kallon cikin ƙwayar idanunta.     Baya tai a tsorace zata zube dan ruɗani, a dai-dai sansa du Yaya Gajeje ke haɗa baki ita da Sa'a da Tinene data tashi zaune da ƙyar wajen kiran “Baba!”.      Nanma kai tsaye ya amsa musu da “Na'am ƴaƴana”.       Ai tuni Sa'a ta kwasa da wani irin gudu tayo kansa batare data saniba. Ta faɗa jikinsa tana fashewa da wani irin kuka maiban tausayi. Hannu biyu yasa wajen riƙe abarsa yana murmushi, ya miƙama Tinene hannu itama. Da sauri tayo kansa duk da halin ciwo da take a ciki itama ta shige jikinsa.     Hayaniyarsu tasa Karima fitowa itama. Ganin Babansu yasata kware baki cike da firgici ta kwala ihun daya jawo hankalin maƙwafta suka fara leƙe ta kantaga. Sai gashi cikin ƙanƙanin lokaci gida ya ɗauki harama. dan tuni ashe jama'ar gari sunga baba sanda yake shigowa garin tare da matarsa.          A take gida ya ɗauki murna, dan tuni dangin baba su Gwaggo Laritu harsun iso jin labarin dawowar ɗan uwansu. Sai koke-koke akeyi na farin ciki. Da ƙyar aka samu gidan yaɗan natsa aka kawoma Baba da baƙuwarsa ruwa. Babu musu suka amsa suka sha dan sunada buƙatarsa.     Baba Rabilu cikin kasa haƙuri yace, “Yaya gaka da baƙuwa kuma bamusan wacece ba?”.      Murmushi baba yayi yana mai kallon ƙyaƙyƙyawar matar, zuciyarsa fes da farincikin daya bayyana a saman fuskarsa yace, “Itama yayarku ce. Dan tazama ɗaya daga cikin zuri'armu tunda ta kasance Matata harma da tsohon ciki gashi nan”.        Cikin mamaki da nuna bayyanannen farin cikinsu suka shiga sake mata gaisuwar girmamawa. itako cike da fara'a da mutuntawa a garesu take amsawa. Babu wanda ya lura a cikinsu sai jin faɗuwar Inna sukai timmm a ƙasa. Dan hatta da Tinene sai da ta gaida matar da baba ya kira da matarsa. Karima ce kawai ta wani gwalalo idanu tana kallonta.       Kusan su duka kan Inna sukayi, banda Baba da ko motsi baiyiba sai dai ya kalli wajen. Ruwa Sa'a ta ɗebo da sauri ta kawo, Gwaggo Laritu dake riƙe da Inna ta amsa ta shafa mata a fuska. A take ta kawo numfashi tana binsu da kallo. idonta ta sauke akan baba da Amaryarsa. Babu zato sukaji ta fashe da kuka kawai ta fara sambatu       “Dan girman ALLAH na roƙeku ku taimakeni ku hwaɗa mani gaskiya, kuce dani mahwalki nake ba gaske baneba, na shiga uku ni Asabe. Yanzu malam irin sakayyar da zakaimin kenan akan wahalar ganin ka dawo gida da nakeyi tsahon shekaru? Yanzu malam duk hwaɗi tashin da nake akanka karasa da abinda zaka dawo gareni sai kishiya? Na shiga uku na lalace ni Asabe. Shikenan watan lalacewata ya tsaya kuma sai abinda ALLAH yayi. Ku dubetahwa jama'a kamar aljana. Wlhy tahi Hauwa kyau da ƙuruciya.....”     Ta ƙare maganar da ƙara jan wani nannauyan numfashi alamar ta sake suma......... ____________________________★          *_KANO_*     Bayan dogon zaman jira dasu AK sukasha sakamakon gwajin DNA ya fito daga likitocin guda uku, Batare da ko su Dr Mahmud sun dubaba aka mikama Baffah. Shima ɗin bai buɗeba ya sake miƙama Dr Mahmud dan yasan amintaccen AK ne. Kuma shina ya yarda dashi ɗari bisa ɗari.              Dr Mahmud da duk al'amarin yake neman rikita masa kai ya amsa ya buɗe takardun ɗaya bayan ɗaya zuciyarsa na wani irin harbawa da sauri-sauri. Sai da yayma takardun kallon kusan sakan biyar kafin ya ɗago ya ɗan dubi sashen da AK ke zaune rungume da Little dake barci yanzun. Cikin wani irin rawar murya da firgicin abinda ya gani ya maida kallonsa ga takardun yana magana da rawar harshe.        “Ba lallai ku fahinci duka bayanan cikin takardun ba saboda wani abun daga bincike likitocine kawai. sai dai ina mai sanar muku cewar zan faɗi gaskiyar abinda na gani kamar yanda baffa ya bukata tsakanina da ALLAH”. Ya ɗan sharce gumin daya taru masa a goshi da cigaba da faɗin, “B...Baffah sakamakon duka takardun ya nuna ya..ron... Na na na AK ne, dan duk ƙwayoyin halitarsa babu banbanci da yaron kamar yanda ya biyosa a kammani”. Ya ƙare zancen da tsananin raunin harshe dana zuciya.      Kusan a tare suma su Baffah zukatansu suka buga. AK dakejin kansa na neman tarwatsewa ya ƙanƙame little a jikinsa yana rumtse idanunsa da matuƙar ƙarfi, har takai yaron ya farka daga barci yana ƙoƙarin fara kuka saboda jin matsar da akai masa.      Yanda yayi ɗinne yay matuƙar tada hankalin Dr Mahmud da gaba ɗaya hankalinsa ke akansa. Da sauri ya miƙe zuwa garesa yana ambaton sunnsa. Hakanne ya fargar dasu Baffa ruɗani da ɗimuwar da suka shiga suma duk sukai kansa.        Da ƙyar suka iya ɓanɓare little daga jikinsa, Baffah da Abba suka riƙe AK ganin jikinsa na wani irin rawa maiban mamaki da tsoro, cikin ƙanƙanin lokaci kuma duk sai gaɓoɓinsa suka saki alamar ya suma.       Wannan shine tashin hankali wanda ba'a saka masa rana, dan kuwa dai Baffah ji yay tamkar ya fasa ihu dan tashin hankali goma da ashirin, yana matuƙar ƙaunar AK a ransa. Dan yana ɗaya daga cikin ɗa mafi soyuwa a garesa, sai dai yana dannewa ne gudun rarraba kan ƴaƴansa.      Da ƙyar suka iya ɗagasa zuwa gadon duba mara lafiya dake a office ɗin Dr Mahmud. Mmn Sadiq kam kuka take sosai dan gaba ɗaya ta gagara fahimtar wannan al'amari maiban ruɗani da al'ajabi........ *_BAYAN WASU AWOYI_*        Bayan wasu taƙaitattun awoyi aka samu nasarar farkawar AK da tun ɗazun ya farfaɗo daga sumar da yayi. A hankali ya buɗe rinannun idanunsa ya saukesu akan Baffah dake zaune riƙe da hannunsa. Sai Abba dake ta wajen ƙafafunsa shima a zaune. Mmn sadiq kam ta wuce gida tuni tare da little dan taje ta huta itama gudun kar taje ƙasa. Dan kallo ɗaya zakai mata ga gano tsananin tashin hankali da ruɗaninta.        Kallonsu yayi ya maida idanun ya lumshe a hankali yana wani irin murmushi da baida maraba da kukan ƙunar zuciya. Idanunsa a lumshe yace, “Baffah nasan ba lallai ku yarda daniba akan bansan yaya akai na samar da Abdul-Mutallab ba. Domin ni kaina na kasa yarda da kaina balle ku da zan faɗamawa. Sai dai ku sani lallai ina cikin *_MAKAUNIYAR ƘADDARA_* babu wani haske da zai haska min idanun ganinta kuma sai UBANGIJINA da haƙurin fahimtata da zakuyi na ɗan wanu lokaci dazanyi ƙoƙarin ganin bakin zaren, b.........”      Saurin katsesa Abba yay ta hanyar faɗin, “Ya isa Adnan. A yanzu halin da kake ciki baya buƙatar duk waɗanan maganganun. Dan Mahmud ya tabbatar mana da jininka yayi ƙololuwar hawa sama. idan kuma ka matsa da yawa za'a iya samun matsala. Mu dukanmu nan musulmai ne, muna kuma iya fahimtar yaran ƙaddara ko jarabawa, suk da dai ita wannan tazo mana a makance. Dan kai da Zinneerah ne ya kamata muji amsar tambayoyinmu a gareku, sai kuma gashi kuma neman amsoshin kukeyi a karan kanku. A ganina mafita ɗaya ce da shawara ta rage mana Alhaji”. Ya faɗa yana duban Baffah.      Kai tsaye Baffah yace, “Karka damu Alhaji Abubakar, kai maganarka kai tsaye dan kaima ubane mai cikakken iko akan su Adnan da wannan matsalar tasu da ni ta sakani a babban ɗakin duhu bama na makanta kawai ba”.     Murmushi Abba yayi, cikin son tausasa fushin Baffah da yake hangowa yace, “Nagode Alhaji Kabeer, abinda nakeson faɗa kai tsaye shine, mu koma ainahin ƙauyen Danya ko zamu samo bakin zaran inda matsalar take, dan a binciken da nayi wancan karan bazai gamsar damu ba saboda rashin samun mahaifin Zinneerah da nayi, sannan ƴan uwansa duk sunƙi bani haɗin kai akan wani dalilinsu da ban saniba. To amma sai nake dangantashi da fushi, sai dai ina fata da tsamanin insha ALLAHU zuwa yanzun sun huce. Maybe mu samu wani bakin zare da zaisa shima Adnan ya fahimci daga inda matsalar take ko zai tunano wani abu tunda dai babu wata hanyar samuwar ɗa sai da nasaba mai ƙarfi. Amma yaya kuka gani, dan yanzu ni wannan hasashena ne kawai”.        “Maganarka nakan hanya Alhaji Abubakar, kumani wlhy na gamsu da ita ɗari bisa ɗari”. Baffah ya faɗa yana miƙewa tsaye.        Zaune AK ya tashi da ƙyar, cikin son danne damuwarsa yace, “Uncle wannan shawaran naka yayi dai-dai, nima na gamsu da ita. Sai dai dan ALLAH ku gafarceni idan na ɓata ranku”.       Da sauri Abba ya girgiza kansa. “Ka kwantar da hankalinka Adnan kaji, ALLAH zai warware mana komai cikin sauƙi”.     Kai kawai AK ya ɗaga masa, dan yasan Baffah a ƙullace yake da shi. Duk yanda Dr Mahmud yaso riƙesa a asibitin yaƙi yarda, dole ya barsa suka tafi gida shi da Baffah Abba ma ya nufi nasa gidan. Bin bayansu Dr Mahmud yayi da drip da magunguna dan yasan AK na buƙatar hutawa na wasu awoyi ko hankalinsa zai dawo jikinsa.          Tunda suka taho ko sau ɗaya Baffah bai yarda sunyi maganaba. Shima bai iya cewa dashi komaiba saboda ciwon kai dake damunsa har yanzun.       Da suka shigo gidanma baffah cayay AK yaje shi yana buƙatar hutu. Ganin Dr Mahmud biye dasu yasa baiyi musu ba ya nufi sashen Hajiya iya shima. Acan Dr Mahmud ya samesa. duk yanda yaso ƙin yarda ya saka masa drip ɗin haka Dr Mahmud ya dage sai da ya saka masa tare da allurar barci mai ƙarfi. Aiko cikin amincin ALLAH sai gashi a ƙanƙanin lokaci barcin yay awan gaba dashi.............✍ *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_*            *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* ________________________ *Page 40* ...........Da farko Baffah yaso kira ya sanarma Hajiya iya komai, sai dai a bisa wani tunaninsa kuma sai yace bara ya bari har zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu da yake da burin yanke hukuncin daya dace ya kuma san Hajiya iya zataji daɗi sosai. Bai sanarma kowa mike faruwaba a cikin matan nasa, ya dai nema ƙanwarsa Bilkisu a waya sunyi magana, anan nema take sanar masa itama gobe idan ALLAH ya kaimu takeson sake zuwa london ɗin domin duba jikin hajiya iya, tanata neman wayar AK ma bata samuba ashe ya shigo 9ja ne. Tace amma tunda wannan ta taso bara ta dakata harsu dawo daga danya, dan dama tanason su tattauna akan ɓoyema Ahmad rashin lafiyar Hajiya iyan da sukayi.       Cike da so da ƙaunar ƴar uwarsa Baffah yace, “Babu damuwa Bilkisu, kiyi haƙuri na kashe wannan ƙurar duk da nasan tawuce kasuwar gobe, dan yanda Adnan ya dage cewar bai aikata wani abu akan samuwar yaron nanba hankalina na tashi, inaji a raina kuma kamar akwai wani abu ɓoyayye da bamu saniba”.      “Gaskiya kam Yaya al'amarin yana buƙatar bincike, baka shaidar ɗan yau amma koni dai inaji a raina Adnan bazai aikataba, to amma jin cewar gwajin DNA ya tabbatar da ɗan nasane yasaka jikina duk yayi sanyi gaskiya. Amma inaga zan shigo zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu nan ɗin kawai”.       “To ALLAH ya kaimu da rai, kizo ɗin kozanji sanyi a raina na samu abokin shawara nima”.    Daga haka sukai sallama. Idan barci ya figi baffa a wannan dare sai dai ɓarawo. Hakama mmn Sadiq acan barci ya gagareta. Danma Abba nata mata nasiha da lallashi harya samu taɗan saki jikinta saboda kar matan gidan su fahimci akwai matsala. *WASHE GARI*.       Washe gari Alhmdllh AK ya tashi garau a zahiri. a cikin zuciyarsa kuwa shi kaɗai yasan mi yakeji gameda son tunano ko ya taɓa aikata wani abu makamancin wanda yake tuhumar kansa akan samuwar little. Sam bai iya tuna komaiba balle ya gano, dan haka ya ajiye komai a ransa yay shiri kamar yanda baffa yace.       Yayi ƙyau matuƙa cikin ɗanyar shadda fara tas da taji ɗinki mai ƙyatarwa da ɗaukar hankalin mai kallo, ya murza hula a kansa wadda ta sake ƙawata tsarin adon nasa da bayyanarsa cikakken bahaushe. Turare ya saka ya fito yana baza ƙamshinsa mai sanyi da daɗin shaƙa. Yayi mamakin cin karo da matasan ƙannensa suma cikin shiri, sai dai baice komaiba ya shiga amsa gaisuwar da suke masa cikin girmamawa.       Baffa ne ƙarshen fitowa sanye shima cikin tashi ɗanyar shaddar, fuskarsa a sake tamkar babu damuwar komai tattare da shi, har hakanma ya bama AK mamaki da tsoro, dan tun yana yaronsa ya gama karantar irin wannan yanayin na Baffa. Idan kai masa laifi ya nuna kamar bai damuba to lallai akwai abinda yake shirya maka kuwa.      Motoci suka shiga, Baffa shi kaɗai sai drivern sa, dan acewarsa zasu ɗauki Alhaji Mansur babban amininsa a gidansa. Sai yazam su Moos'ab sun taru a mota ɗaya su huɗu. AK na shirin shiga wata motar shi kaɗai sai ga Dr Mahmud ya iso. Hakan yasa ya shiga motar Dr Mahmud ɗin kawai da shima dai da alamar shirin tafiyar yazo gidan dama.         Duk da AK cike yake da mamakin wannan gayya sai baice komaiba. Sun dai gaisa da Dr Mahmud ya tambayi yaya ƙarfin jikinsa daga haka sukai shiru, Dr Mahmud nata juya abinda yakeso su tattauna a ransa ya kasa furtawa, dan duk da AK abokinsane yana girmamashi akan wasu dalilai masu yawan gaske.       Sai da suna gab da fita cikin garin kano zasu kama hanyar katsina AK ya sake fahimtar bayan motocinsu uku akwai wasuma biye dasu kusan guda uku. Cikin kasa jurewa yace, “Wai nikam wannan gayyar ta minene Baffah yayi?”.       Ɗan dubansa Dr Mahmud yayi, cikin rashin fahimtar inda zancen nasa ya nufa yace, “Gayya kuma ranka ya daɗe?”.      “Uhm, ko bakaga motocin dake biye damuba?”.     Ta mirror Dr Mahmud ya duba bayansu, a nazarce yace, “To inaga dai ba tafiyarmu ɗayaba gaskiya”.      Shiru AK yayi duk da bai gamsu da hakanba, sai ma ya jawo wayarsa kawai ya shiga daddanawa.      Tafiyar da bata gaza awa ɗaya ba suka iso gidan mutum ɗaya, kai tsaye hanyar kusada suka shiga, a lokacin kuma AK ya sake tabbatar da tafiyarsu ɗaya da motocin nan, amma sai yay shiru bai sake magana ba. Abinka da lafiyayyun motoci ga kuma lafiyayyar hanya cikin ƙanƙanin lokaci suka iso cikin kusada. Basu wani tsayaba suka ɗauki hanyar Danya.          Haka kawai AK ya samu kansa da nutsuwa a kallon hanyar zuciyarsa na masa wasu tunani daban akan rayuwar Zinneerah a ƙauyen, rashin ƙyawun hanya ya ɗan jasu lokaci mai tsaho kafin su shigo cikin ainahin ƙauyen Danya. Duk da ba safiya bace garin akwai mutane sosai, dan lokacine na shigowar farkon damuna mazan garin nata dawowa gida domin haramar noma.     Sosai idanu suka dawo caa akan dalla-dallan motocin kowa na tunanin daga ina haka?. Wasu suce ƴan siyasa wasu suce daga fadar sarkin katsina ne. to basu dai da tabbas, duk da kuwa kai tsaye Abba gidan maigari ya nufa dasu, dan shine jagoran tafiyar tasu. A ganinsa kuma hakan shine yafi cancanta da wannan tawagar tasu dan bayaso ai musu irin wulaƙancin da akai masa a wancan zuwan.          Su maigari suna zaune a bishiyar ƙofar gidansa shi da fadawansa sukaga motoci galla-galla na tsayuwa. Ba karamin kaɗawa hantar cikin maigari da ƴan fadarsa tayiba. Dan duk zatonsa samame aka kawo masa daga fadar sarikin katsina. Duk da yasan baya aikata wani mummunan al'amari ga ƴan garinsa sai da yaji tashin hankali. Bai ƙara rikicewaba sai da su AK suka fara firfitowa.      Daka gansu kaga manyan ƙasa masu ci da tsinin allura, dan duk sun jiƙu cikin shaddoji masu maiƙo da ɗaukar idanun mai kallo. Abba ne ya matsa inda suke yaɗanja maigari dake a ruɗe gefe sukai ƴar magana. a take bakin maigari ya washe ya shiga sakin tagwayen ajiyar zuciya. Bai tsaya jan jikiba yasa ƴan fadar tasa shiga cikin gida suka fara fitowa da tabarmi sabbi ƙal tare da manyan dardumai aka shishshimfiɗa a babban zauren maigari dake share ƙal ga sanyi mai saka nutsuwa gaduk wanda zai zauna.        Duk ciki suka shiga, akabar Baffah da Abba da Alhaji Mansur da Alhaji Yusif a waje suna son yin magana da maigari, dan Alhaji Yusif Mande da Alhaji Mansur Tofa manyan aminan Baffah ne da kowa yasani, tun kuma a daren jiya ya sanar musu abinda zasuzo yi anan ɗin.        Abba ne yayma maigari bayanin nason ganin dangin Malam Sule baduku. Da kuma abinda ke tafe dasu. Jin sunan Zinneerah ya saka maigari jin dunbin daɗi a ransa, dan shi wlhy yama manta da yarinyarnan sam a rayuwarsa. sai dai yau dalilin ambatonta yasakashi farin ciki musamman da yaji dalilin zuwa waɗanan manyan mutane. Bakinsa a washe yace, “Ai Alhmdllh ma kun yanka akan gaɓa Alhaji, dan Malam Sule ɗinma ya dawo garin jiya-jiya, zanma iya cemuku yanzu da safen nan sukabar gabana shi da fitinanniyar matarsa akan rikici data tada dan yazo da sabuwar amarya daga Niger. Inaga yanzu bara na aika a kirashi shi dasu Rabilun ku zauna ku huta”.      Sosai su Baffah sukaji daɗin jin cewar mahaifin Zinneerah ya dawo gida. Dan Abba ya sanarma Baffah cewar wancan zuwan da yayi ya iske bayanan ya bar gari ba'asan inda yakeba.         A take maigari ya aika kiran Baba da su Kawu Rabilu, shi kuma ya shiga gida yasa aka fara haɗa fura da sauran cimar ƙauye domin fitoma baƙi. Bayan ya aika a siyo musu ruwan leda da lemo acan kusada dan musamman ya tada mai mashin. ★★       Baba na ƙofar gida tare da ƴan uwansa yana basu labarin tun barinsa gida ashe Niger ya dosa, acan yayi gamo da wani bawan ALLAH daya taimakesa saboda fahimtar baya cikin hayyacinsa da yayi. Shine ya dage masa da addu'a da neman magani harya samu lafiya acikin watanni shida. Koda yaga ya warke duk da ya tuna komai daya faru sai yace bazai dawo gidaba zaiyi zamansa can neman arziƙinsa. Aiko wannan mutumi yaji daɗin haka. a take ya ɗaurasa akan hanyar sana'a, cikin ƙanƙanin lokaci ALLAH ya amince masa abubuwa suka canja ya fara juya kuɗaɗe duk da bawai masu ɗunbin yawaba. Nadai rufin asirin ALLAH dai-dai gwargwado. Ganin zaman nasa bana ƙare bane mutumin daya taimakesa ya bashi auren ƙanwarsa da mijinta ya rasu bakuma ta taɓa haihuwaba, hasalima shekarunta biyar kacal dayin aure. Ya amsa hannu biyu yayma ALLAH godiya da wannan bawan ALLAHn nan, ya kumayi sa'a Zainaba nasonsa itama. cikin amincin ALLAH basu rufa wata uku ba sai gata da ciki, sunyi murna sunyi farin ciki mara musaltuwa. Da cikin ya tsufane yaga ya dace yazo gida da ita ta haihu a cikin danginsa, shine dalilinsa na ɗakkota suka taho yanzun.       Cikin jin daɗi Kawu Sabi'u yace, “Yaya to yanzu kadawo garemu baki ɗaya kokuwa haihuwa kawai aka kawo yayarmu tayi ka sake gudu ka barmu?”.      Kafin Baba ya bashi amsane ɗan aiken maigari ya iso. Tun anan ya gumtsa musu zancen baƙi. Cike da mamaki suka tashi suka bisa dan su dukansu fes suke cikin shiga ta kamala babu wani damuwa.      Lokacin dasu baba suka iso sun iske an cikama su AK gaba da kayan abinci, duk da dai fura ce da ruwa da lemo, sai zabi da maigari yasa aketa yankawa ana shiga dasu cikin gida dan yacema matansa dan ALLAH suyi maza a gyara a gasasu gashi mai ƙyau.      Fahimtar muhimmancin baƙin ya sakasu miƙewa suma babu sanya suka haɗu da ƴaƴansu suka fara aikin babu wasa. Koda su Baba suka iso Baffah ya buƙaci su zauna a waje suyi magana iyakarsu manyan. Sanin maganace mai muhimci tafe dasu maigari yasa aka sake saka musu tabarma ƙatuwa a zaurensa na biyu dake ƙarami bai kai na farko girmaba.        Bayan duk sun zauna sukai gaisuwa ta mutunta juna. Inda Abba ya bama baba sani. Baba da dama tuni yake masa kallon sani yace, “Haba koda naji, tun ɗazun naketa tunanin wannan fuskar kamar na santa amma na kasa. Kai sannunku da zuwa, sannunku”.       Fuskar Abba da murmushi yace, “Yauwa mun gode sosai Malam Sulaiman. Nasan zakai mamakin wannan zuwa namu, sai dai ba abin mamaki baneba. Kwanaki nazo garin nan amma ban samekaba. Zuwan nawa kuma yanada nasabane da Zinneerah ”.      Da sauri baba ya dubesa jin sunan gudan jininsa abar begensa a koda yaushe. Murya a raunane yace, “Zinneerah kuma Alhaji Abubakar? Ai ina mai baƙin cikin sanar dakai muma nemanta mukeyi tun bayan wani babban al'amari na ƙaddara daya giftama rayuwarta”.        “Eh nasan duk wannan Malam Sulaiman, dan akansama nazo kwanaki, sai dai rashin samunka ya sani komawa. Yanzu dai a taƙaice Zinneerah tana tare damu, dan waɗanan bayin ALLAH daka ganni tare dasu ma a dalilinta sukazo nan. Wannan” ya nuna Baffah. “Shima kawuntane, dan yayane ga hauwa'u, nasan dai bazaka gaza jin labarin dangin mahaifiyarta dake a bauchi ba sanda kuna tare? To Alhaji Kabir Shira yana ɗaya daga cikinsu, sannan kuma yaron wajensa ne ke son auren ita Zinneerah shiyyasa mukazo nan”.       Wani irin daɗi da al'ajabine ya bayyana a fuskokin su Baba da maigari da su Kawu Rabilu. Baba da ƙwalla suka cikama ido yace, “Ashe dama Zinneerah na tare daku? Kai ALLAH na gode maka da wannan ni'ima taka. Nagode maka ALLAH daka bama yarinyata kariya ta hanyar sadata da mahaifiyarta. Sannan kuma nagode muku da kuka zama masu karamci daƙin riƙe baya a ranku kuka jiƙan gudan jinina duk da hanaku ita danai a lokacin da kuka buƙata. Kuyi haƙuri, bansan da wane irin yare ko harshe zan muku bayaniba, amma tunda ba wannan ya taramu yanzuba mu fara maganar da kukazo da ita, waccan zata biyo baya danni na cancanci naje inda kuke muyita. Batun auren Zinneerah kuwa wlhy koda bakuzo inda nakeba kunada iko da damar aurar da ita ga duk wanda zuciyarku ta baku yarda akan ingancinsa da mutuncinsa. Dan haka ni dai a ɓangarena babu matsala na bama wannan yaro Zinneerah halak malak. Ga kuma ƴan uwana nan inada tabbacin bakinmu ɗaya dasu”.      Cikin jin daɗi da farin cikin kalaman baba su Baffah suketa ambaton Alhmdllh bakunansu a washe. Alhaji Yusif yace, “Masha ALLAH, gaskiya munji daɗin wannan karamci, sai dai kuma muna roƙon alfarma ta biyu idan bamu takura muku ba”.       Kawu Sabi'u dake kusa dashi yace, “Alhaji ku ɗauka mudaku duk ɗayane, dan koba komai kuma kunada ƙarfin iko akan Zinneerah, dan haka ba zancen alfarma a tsakaninmu”.       Nanma kowa ya nuna jin daɗinsa. dan haka kai tsaye Alhaji Yusif ya sake faɗin, “To Alhmdllh, dama alfarmar tamu dai bata wuce cewar mufa da shirinmu mukazo nan ba, ma'ana da shirin ɗaura aurenma baki ɗaya muka iso bawai tambaya ba. Muna buƙatar ɗaurin auren ne a gaggauce bisa wani dalili da insha ALLAH daga baya za'a tattaunashi. Fatanmu dai a ɗaura auren kawai”.        Duk da baba yaji daɗin wannan zance sai da yay ɗan jimmm, kafin ya gyara zamansa murya a sanyaye yace, “Amma Alhaji dakun bari dai a fara magana ta fahimta, dan yadace ace kunsan ƙaddarar data afkama yarinyar nan harta kai ga barin gida ta iskeku”.     Da sauri Baffah yace, “Karka damu ɗan uwa, duk abinda kake ƙoƙarin son sanar mana mun sanshi, dalilin sanin nema yasamu cewa a gaggauta ɗaura auren yau, daga baya dukma abinda zai biyo baya sai ya biyo”.        Daɗine sosai ya ƙara kama baba, cikin share ƙwalla yace, “Shikenan mun amince, dan haka ga ƴan uwana nan suke da sauran magana”.        Kowa ya nuna farin cikinsa ananma. Dan haka maigari ya fita cike da farin ciki ya sanarma sanƙira a sanar da ɗaurin aure yanzu idan anyi salla a masallacin juma'a.       Cikin ƙanƙanin lokaci sanarwar sanƙira ta gauraye ƙauyen danya. Kasancewar dama azhar ta taho nan mutane suka fara haramar nufar massalacin juma'a domin yin salla duk da ba juma'ar baceba. Suma su AK da duk basusan mi ake cikiba fitowa sukai sukayi alwala. Mutane sai kallonsu suke tamkar sun sami television. Yara kuwa nata kaima mata labari a cikin gida.          Koda suka shiga cikin massallacin liman sai yaja baya, a mamakin kowa sai gani sukai ya kamo hannun AK ya tsayar a mazaunin liamami.        Kasa magana AK yayi ya tsaresa da idanu, ganin yanda yayi ɗin sai Liman yay murmushi, kansa tsaye yace, “Kai kafi cancanta da ka jamu salla badan nasan kaiɗin wanene ba. Haka kawai zuciyata ta rayamin baka wannan damar, dan haka dan ALLAH karkai musu ko jayayya”.       Baki AK ya buɗe zaiyi magana Baffah ya girgiza masa kai alamar yabi umarni kawai. Dole ya ɓame bakinsa yana wani lumshe idanu da buɗewa a lokaci ɗaya. Dolensa ya juya yana gyara taiwarsa, a ransa rayawa yake da ace baida ilimin addini lallai yau da yaji kunya mai tsanani ashe. (hummm, jama'a ni kaina sai da na sauke numfashi saboda jin muryar Abdul-Mutallab Kabir Abdul-Mutallab shira dake raira karatu a nutse a cikin salla, dan yanda yake cikin masu jajayen kunne banyi zaton yanada ilimin addini haka ba).     Kasancewar ƙaramin gari jin baƙuwar murya da salon karatun yasaka mata cece kucen anyi baƙon balarabe mai jan salla yau a babban masallaci, a cikin wannan zantuka kuwa hardasu yaya Gajeje dake zagaye da Inna dake kwance rijib babu lafiya tun faɗuwar jiya, da alama dai hawan jini ne ke neman bigeta.       A masallaci kam bayan an idar da salla aka tsaida mutane duk da kuwa dama sunsan da zancen ɗaurin aure da aka sanar dan shine maƙasudin taruwarsu da yawa haka a massallacin tunda akwai kananun masallatai.      Mamakine ya kama su AK jin alinahin liman na sake sanar da maganar ɗaurin aure. AK ya kalli Baffah cike da alamomin tambaya, wani murmushin manya Baffa ya sakarma AK ɗin yana ɗauke kansa ya maida ga Haneef. Magana ya faɗa masa a kunne. A take Haneef ya tashi yana jan hanun Mas'ood suka fita. Cikin mintuna ƙalilan suka dawo da yara ɗauke da kwalayen sweets da huhunan goro da biscuits. Bayan an ajiyesu Alhaji Mansur ya ciro kuɗi ƴan dubu-dubu sabbi ƙal ɗauri biyu ya ajiye a tsakkiyarsu alamar dai kuɗin sadaki ne.       Kai Kawu Sabi'u ya girgiza da faɗin, “Alhaji sunyi yawa, dubu ashirin sun isa matsayin sadaki”.       Baffah ne yay murmushi shima yana girgiza nasa kan. yace, “Darajar ɗiyata ta wuce dubu ashirin, idan tanima za'abi sai sun ƙara mana sadaki wannan yayi kaɗan”.      Kusan waɗanda ke a kusa dasu sai da suka zaro idanun mamaki, Baba yay saurin faɗin, “A'a dan ALLAH ayi haƙuri alhaji, waɗanan ɗinma sunyi yawa kamar yanda Sabi'u ya faɗa”.      “Basuyiba malam Sulaiman”. Cewar Alhaji Yusif. Abba ma yay murmushi da kallon Baba. “Kamar yanda Alhaji Kabeer ya faɗa a barsa haka ɗin kawai ALLAH ya sanya albarka ya basu zaman lafiya da zuri'a ɗayyaba”.     A take aka amsa da amin, tare da shiga hidinar ɗaurin aure kai tsaye.  Bayan tsarebe-tsaraben ɗaurin aure da addu'a. Sanƙira ya miƙe ya fara shelantawa ga jama'a an ɗaura auren *_“Alhaji Abdul-Mutallab shira da amaryarsa Zinneerah Sule baduku akan sadaki naira na gugar naira, wuri na dukan wuri dubu ɗari biyu”_*...............✍ *_Tofa, yaufa ake ƙuru-ƙuru, jama'a yaya wannan labari zai kasance a kunnen hajiya aunty mandiya gimbiya Farah uwargida ran gida a gidan Abdul-Mutallab shira. Yaya kuma Mammah zataji? Sai kuma uwar gayya Zinneerah da batasan hawaba batasan saukaba. Shin yaya takene a zuciyar mai gayya mai aiki Abdul-Mutallab Kabir Shira? Moos'ab, Khalipha yaya zasuji da wannan juyin mulki?. Inna dake iƙirarin Zinneerah na birnin ikko yaya zataji?. Amsarku duk tana acigaban MAKAUNIYAR ƘADDARA da nakeda tabbacin yazo muku da sabon salo na musamman 🤏🏻🤓, kumuje zuwa yanzu aka fara wasan_*       _Asha hutun weekend lafiya😍😘😍😋💃🏻💃_. *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_* *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* *Page 41* _________________________ *MG'S SKINCARE* Hi my peole🙋‍♀️ Are you tired of using different skincare product that won't work on ur skin no matter what❓then trust me @mg's skincare is the right plug for you💯 Are you guys battling with pimples,dark spot, sunburn, acne, stretch mark,knuckle,dark armpit,damaged/bleached skin Have you getting dark due to childbirth or sun exposure🥺worry no more@mg's skincare gat you covered✅ Want ur skin to glow buh you don't like using cream/lotion try *mg's herbal whitening black soap* nd you'll achieve that free/shiny skin🧚🏻‍♀️ For those that wanna achieve that milky flawless skin that turns head wherever you go🧚🏻‍♀️ try mg's *beauty kit* that's the secret to beautiful skin😎you'll get an amazing magic result😘 you can also buy the soap nd combine it with any of our product to get more result😀 Glow gang What are you waiting for Shop urs now before we get sold out again😍 Mg's product is 1in town😃if you know you know kawai😜 Nd mg's products are organic they dnt bleach they are made with natural ingredients that will make ur skin lk brighter nd tone ur skin😘 it just bring out that hidden beauty in you😘we HV everything available now so is time to glow dearies Pamper ur skin🧖‍♀️ Shine like a bride💯 Make ur skin brighter🤗 Glow🦵 Soap price:3k Beauty kit:11k Chat 08062991549 Call 08064532391 Instagram: glow_with_mgs Facebook:mg's skincare DNT forget to follow us😇like/comment😍 Team glow🤝 _________________________ *Page 41* ............Tun farkon fara ƙulla auren da yaji sunansa a ciki yay mutuwar zaune, bai dawo hayyasa ba sai da sanƙira ya ƙara tabbatarwa da babbar murya. A hankali AK ya lumshe idanunsa dake ɗauke da nauye-nauye kala-kala a cikinsu yana sauke wata ɓoyayyar ajiyar zuciya.       Haɗa ido sukai da Baffah dake masa kallon nazari, kansa ya maida ƙasa yana ƙoƙarin danne ɓoyayyan al'amarin dake neman bayyana kansa a saman fuskarsa. Shima Baffa sai kawai ya ɗauke kansa zuciyarsa na masa wasiwasi.         Koda aka mimmƙe domin fita a masallacin da ƙyar Saifudden ya iya kama Moos'ab da yay suman zaune, dan tun farkon fara ƙulla auren da yaji an ambaci Yayan nasu sai da gabansa ya faɗi, jin zancen sanƙira kuwa tamkar saukar guduma ne a bisa tsakkiyar kansa. Gefe Saifudden ya maida shi tare bashi ruwa dan yasha. Babu musu Moos'ab dake hawaye kamar wani mace ya amsa ya sha ruwan yana sauke tagwayen ajiyar zuciya.       “Wannan shine abinda na gudar maka tun farko Moos'ab, shiyyasa nace ka bayyanama Zinneerah kana sonta, ka kuma sanarma Baffah da Granny amma kaƙi wai saita gama secondary school, gashi nan to shi Yayanmu yayi wuff da ita”.      Murmushi mai ciwo Moos'ab yayi, cikin raunin murya yace, “Saifudden ALLAH ya ƙaddara dama shine mijinta, kuma ni wlhy na haƙura na bar masa har abada. Yayanmu yanada daraja da mutuncin da zamu iya sadaukar masa da komai, komai muhimmancin abinnan kuwa. Dan shima yayi mana abubuwa masu ɗunbin yawa da bazasu ƙirguba. Sannan nasan Zinneerah zata samu dukan farin ciki daga garesa insha ALLAH. Kuma anyi maganin wannan mahaukaciyar matar tasa da kishi ya maida zararriya, wlhy kodan kiran dataimin jiya da dare wai saina faɗa mata uwar little yasa naji daɗin ƙulla wannan auren, tunda tana kukan targaɗe ga karayanan ta samu, sai tai zaman jinya kuma”.       Rungumesa Saifudden yayi yana share ƙwalla shima. Ya ɗagosa yana share masa hawaye da faɗin, “Naji daɗin kalamanka Moos'ab, hakan kuma ya tabbatar min yaƙin da Granny da Baffa keyi akan sanin darajar zumincinmu ba abanza sukeyiba. Tabbas Yayanmu ya cancanci sadaukarwar da tafi haka ma, inaji a jikina kuma maganar shekaran jiyace ta kawo wannan ƙulla auren, amma tabbas sun dace wlhy”.       “Tabbas na yarda da zancenka Saifu. Da alama hauka tai musu na haƙiƙa shiyyasa Yayanmu da Baffah suka yanke wannan hukuncin, na taya Yayanmu murnar samun nutsatstsiyar yarinya mai kunya da tarbiyya ga haƙuri, sannan itama na tayata murnar samun gwarzon namiji mai haƙuri da mutunci, uwa uba ya tara qualities masu yawa da duk mace take buƙata ga mijin aure, duk da nasan akwai ta inda shima yake da rauni kodan kasancewarsa ɗan adam kamar kowa. ALLAH ya basu zaman lafiya, yasa ta zama sanadin farin cikinsa da kwaranyewar hawayensa akan rashin haihuwa”.      “Amin ya rabbi” Saifudden ya faɗa yana sake rungumesa.      A hankali AK dake a bayansu basu saniba ya ɗanja da baya yana lumshe idanu, tun sanda Saifudden ya kamo Moos'ab suka fito ya biyosu, dan ya jima yana zargin akwai wani abu tsakanin Moos'ab da yarinyar, ashe kuwa da gaskene. Hannu yakai bisa sajensa ya ɗan shafa, kafin ya bar wajen batare da ya bari sun gansaba.       Moos'ab ne ya farga da ƙamshin turarensa. Yaɗan janye Saifudden yana faɗin, “Bro ƙamshin turaren Yayanmu fa kamar nakeji”.     Saurin ja baya Saifudden yayi shima yana waige-waige, sai dai basuga kowaba a wajen, “Inaga hancin kane kawai, kaga zomuje karma a nememu”.       Koda AK yabar wajensu nufar inda su Dr Mahmud suke yayi, inda ya samu wani maroƙi yanata zabgama masa kirari duk zatonsa shine angon. Yana ganin AK ya iso ko yay saurin kamo hannunsa da nuna musu shi, “Yauwa to ga angon nan bayin ALLAH”. Ya faɗa yana ciro kuɗi ya miƙa musu yana tura AK gabansu yana dariya.        Idanu sosai AK ya waro waje ganin sun zagayesa suna masa ihu akai, ai gudun hayaniyar tasu ya sashi babu shiri ciro kuɗi ya miƙa musu yana harar Dr Mahmud daya koma gefe yana kwasar dariyar mugunta, su Mas'ood na tayashi ƙasa-ƙasa.           Jama'ar gari kuwa ganin ango yasa suketa sake tofa albarkacin bakinsu. Wasu suce ita cikin shege ya mata riba, wasu suce koma shine abokin tsiyar tata, wasu su tayata murna, wasu suce sakkayar ALLAH ce ga zalincin da Inna tai mata, wasu suce baisan ta taɓa yin cikiba ƙila data bar garin ta zubar ne. Wasu ko hassadace kawai, kasancewar sunso zinneerah ɗin basu samuba. Magana dai iri-iri. Har takai wani ya samu AK gefe yana masa gulmar wai kuwa yasan waya aura?.        AK dake jingine jikin mota yana latsa waya ya ɗago ya dubi mutumin ƴar walwalar fuskarsa na ɓacewa ɓat. Amma duk da haka mutumin nan sai yay ƙasa da kai yana wani soshe-soshe. “Ayi haƙuri Alhaji, ganinka mutum mai tarin kamala da mutunci yasa naji bara na faɗa maka gaskiya, dan na tabbatar an rufekane akan yarinyarnan. Duk da kafin faruwar komai kowa yasan yarinyar kirki ce a garin nan dan har kwatance akema yara akanta. Amma daga ƙarshe ta ɓata rawarta da taalle. Dan kuwa cikin shege tayi, Katsina tabi saurayi sukayo kusan mako biyar sannan suka dawo, a dalilin cikinne ma ta gudu a ƙauyen nan babu wanda ya sake jin labarinta sai yau da kukazo wai aurenta. Nifa k........”      Wani shegen kallo da AK ya dasa masa dai-dai ya ɗago ya sashi saurin haɗiye sauran zancen yana zazzare ido. AK ya gyara tsaiwarsa idanunsa na canja launin ɓacin rai, cikin nutsuwarsa da rashin sakewa yace, “To dakazo kana faɗamin idan kuma nine nayi cikin fa?”.      A razane mutumin ya waro idanu waje. Sai kuma yay saurin yin ƙasa da kansa yana girgizawa. “Haba-haba Alhaji ni nasan hakanma bazata faruba. Ai daga ganinka anga mutum mai mutunci da kamun kai, kawai dai an rufekane, amma dan ALLAH karka bari so ya rufe maka ido ka ɗaukama ƴaƴanka uwar banza”.       “Ai kaine banzan sha-sha-sha” AK ya faɗa a fusace, cikin kaushin murya yace, “Mutumin banza kawai, saboda tsabar rashin mutunci ko kunya bakajiba kai kazo kana aibantamin mata? To bara na sanar maka kaima kaje ka sanar tunda naga shine aikinka. Shi wannan cikin da kuka ganta dashi nawane. Nine nai mata kuma ta haifamin, daɗin hakannema yasa na aureta yanzu stupid ɓacemin anan”.      Da sauri mutum yabar wajen kuwa tamkar zai kifa, AK ya rakashi da wani irin kallon tsana da takaici, tsabar takaici dole ya buɗe motar da yake a jingine ya shiga batare daya rufe murfinba ƙafafunsa a waje. Sosai launin idanunsa suka sake canjawa, badan kar ace yayi ƙarantaba da lallai saiya nunama shegen mutumin nan kuskurensa yau wlhy. Tsaki yaja da dafe kansa dahar ya fara masa ciwo ƙasa-ƙasa zuciyarsa na masa zugi. Tabbas yanada buƙatar dawowa ƙauyen nan domin wanke yarinyarnan duk da har yanzu baisan yaya ya samar da Abdul-Mutallab ba.....          “Yayanmu!” Moos'ab ya sake kiran sunansa a karo na uku.      Sai yanzu kunnensa ya ji, ɗago idanunsa yay ya dubesa, Moos'ab yay ƙasa da kansa cikin girmamawa yace, “Baffah ke kiranka”.      Komai baicema Moos'ab ɗinba ya fito a motar ya nufi cikin zauren maigari inda su Baffah suke tattaunawa da Baba akan abinda suka sani game da ƙaddarar data afkama Zinneerah da har yau basusan mafarintaba.      Waje ya samu ya zauna yana ƙoƙarin ɓoye ɓacin rai da takaicin da mutumin can ya cusa masa. Cikin girmamawa ya sake gaida su Baba dan yanzu dai a matsayin suruki yake. Sosai baba yaji daɗin wannan girmamawa. yakumaji a ransa AK ya kwanta masa, yana taya ƴarsa murna dajin insha ALLAH ta samu mijin marainiya.       A nutse baba ya sake maimaita masa bayanin da yayma su Baffah game da Zinneerah, sannan a ƙarshe ya roƙesa alfarmar dawowar Zinneerah danya domin shirya mata biki nanda wata ɗaya.     Ɗan murmushi AK yayi kansa a sunkuye yace, “Baba karka damu, duk yanda kukaso muyi mu masu biyayyane a gareku, sai dai kayi haƙuri a yanzu bata ƙasar tana can London, insha ALLAH nan da sati biyu zata dawo”.       Cikin ɗan waro ido Kawu Rabilu yace, “Landan kuma? Ita Zinni ɗin?”.       Sosai yanda Kawu Rabilu yayi ya basu Saifudden dariya. duk sukai ƙasa dakai suna gumtse bakuna. Baffah ne ya amsama kawu Rabilu da cewar, “Eh suna can gidansa tare da mahaifiyata da taje ganin likita. Amma kamar yanda ya faɗa insha ALLAH nanda sati biyu zasu dawo, kuma insha ALLAH suna dawowa zata dawo nan ɗin itama a ɗauketa kamar kowace ƴa a kaita gidan aurenta”.       Jinjina kawuna suka shigayi na gamsuwa. Yayinda bakin Baba da nasu Kawu ya kasa rufuwa. Kasancewar yamma tayi sukai haramar tafiya. Naman zabi da basuciba haka maigari yasa aka saka musu a mota hardasu tsarabar mangwaro, gwaba, kashu da nono da ƙwan zabbi. dan su Baba suma sai gasu da nasu tsarabar harda Gwaggo Laritu da labari ya kaima ta bakin ƴaƴanta.      Lokacin da zasu wuce haka jama'a suka zagaye motocinsu anata ɗaga musu hannu. Sosai su Baffah sukaji daɗin wannan karamci, dan haka suka tafi zukatansu fes kowa na ALLAH ya sanya alkairi. ★★★       Tun kafin Baba ya shigo gida labari ya samu su Inna. Zaune ta tashi dangangan kamar ba itace kwance kashirɓan tana kukan ciwo da ɗan nishi ba. Cikin masifa take cema mai kawo labarin, “Kukam dai annamimanci bai muku kaɗan abaki Sahware. In banda shegen munahinci yaushe kikaga wata Zinni da har za'a ɗaurama aure. Dalla hice mani agida kahin nai miki bankaɗa wlhy”.         Baki Safare ta taɓe tana faɗin, “To oho ni dai Asabe. Koki yarda ko karki yarda yanzu na wuto ana ɗaura auren Zinni a masallacin juma'a. Banga dalilin da zaisa nazo na hiɗi abinda bashike nanba”.       “Kai kedai Sahwar ALLAH ya tsine maki albarka bankaɗaɗɗiyar mata watsatstsiya. Ki hitamin a gida wlhy kona nafka maki shegen duka naga mai ƙwatarki”.     Fita Safare tayi tana wata shegiyar dariya. Ana haka kuwa sai ga Tinene ta shigo gidan a guje tana hakki.      “Ke kuma lahiya kika shigoma mutane kamar wata korarra?”.     Yaya Gajeje ta faɗa dan shigowarta kenan gidan ko zancen Safare batajiba.      Cikin hakki Tinene ta dafe kanta dake mata ciwo dan dama sayan paracetamol ta fita yi, tace, “Inafa lahiya Yaya Gajeje. wlhy wani labari najiyo yanzun. ga baba can a babban massallaci an ɗaura auren Zinni da wasu mutane manyan ƴan gayu al-qur'an”.       Tsit gidan yayi na wucin gadi, sai da Sa'a tace, “Inna anya kuwa maganarnan bada gaske bane? Bara dai na hita nima na jiyo mana”.       Yaya gajeje da sai yanzu taji abinda ke faruwa cike da zumuɗi tace, “Jeki jeki maza Sa'a. Kai ALLAH ya tabbatar da wannan zance da nayi hwarin ciki mara misali wlhy”.       Amaryar Baba da duk ke saurarensu tun ɗazun bata tsoma bakiba ta kalli Yaya Gajeje da cewa, “Wacece wai ita Zinni ɗin?”.      Kai tsaye Yaya Gajeje dake murmushi tace, “Ƙanwarmuce itama mama........”       A fusace Inna ta zaburo tana watsama Yaya Gajeje harara, “Ƙanwarku a gidan ubanwa. Gajeje ki kiyayeni. Ke kuma munahika da kike tambaya bara a faɗa miki, itana ƴar kishiyace da zaman gidan nan ya gagareta kamar yanda kema zai gagareki. Dan wlhy na ɗau alwashin yanda na watseta kema saina watseki a gidan nan dama garin nan baki ɗaya”.      Murmushi amarya tayi tana ɗauke kanta batare datacema Inna komai ba. Hakan kuwa ba ƙaramin harzuƙa zuciyar Inna yayiba. Ta miƙe dingangan kamar ba ita ke ciwo ba tahau zazzaga bala'i tana zagin amarya da mmn sadiq da Zinneerah. A wannan bala'in baba ya shigo shi dasu kawu da yara ɗauke da kayan sweets dasu biscuits da huhunan goro cikin gidan. Suna shigowa Gwaggo Laritu ma na shigowa......... ★★★★          A ɓangaren su Baffah kam tunda suka bar Danya kowa ke tattauna karamcin da akai musu da abokin tafiyarsa. Motar su AK ce kawai ta kasance shiru dan tunda suka tafi ya jingina kansa da kujera ya lumshe idanu yana tariyo maganar mutumin nan ma ɗazu daki-daki cikin ransa. Lokaci-lokaci Dr Mahmud kan kallesa yayi murmushi. Sai da suka kusa shiga cikin kano ne ya ɗan sake dubansa da tsokana, “Haba ango duk daɗine ya saka zama kurman ƙarfi da yaji?”.      Shiru AK bai motsaba, sai da ya mula dan kansa ya ɗan buɗe ido ya harari Dr Mahmud ɗin, cikin rashin sakewarsa yace, “Dama haka kake da sa ido?”.        Dariya sosai ta kama Dr Mahmud har yana dukan sitiyari. Hakan ya saka AK ɗan sakin murmushi ya maida kansa ya sake kwantarwa da lumshe idanu. daga nan bai ƙara tankawa Dr Mahmud ɗinba daya cigaba da tsokanarsa har suka isa gida.      Sun iso suka iske hajiya Bilkisu da suke kira da Mommy ta iso tare da babban ɗanta Huzaifa. Huzaifa kusan sa'an AK ne, sai dai AK ya girmesa da kusan shekara biyu, amma ayanzu abokaine, dan saima suna tsokanar junane zaka iya sanin AK ɗin ya girmi Huzaifa.         Dr Mahmud na ajiyesa bai shigaba ya juya gida danya huta shima. Hakan yasa AK nufar sashen Hajiya Iya shi kaɗai, su Haneef kuwa duk sashen iyayensu sukai kai rahoton ɗaurin aure. Hakama Baffah ɗokin jin zuwan ƴar uwarsa yasashi nufar sashen nasa kai tsaye dan tanacan, tunda bada yara tazo ba duka bazata sauka a nata sashen ba.      Tunda AK ya shigo yaga Huzaifa zaune a falon Hajiya iya yanacin abinci sai ya ɓata rai cikin ɗan wasan da suka saba yace, “Oh oh yaushe wannan bawan yazo mana gida”  ya faɗa yana harar Huzaifa.     Dariya Huzaifa ya fashe da ita, saida yayi mai isarsa ya haɗe fuska yana harar AK ɗin shima. “Eh lallai ka nunamin kayi aure na biyu, ninema Bawan naka? Yaro jeka bincika ni dakai wanene bawa?”.      Hannu AK yasa ya tallare ƙeyar Huzaifan. Yay gaba da sauri yana faɗin, “Magananne jeka bincika kaidai”. Ya faɗa yana shigewa ɗakinsa murmushi ɗauke akan fuskarsa. Dan inhar yana tare da Huzaifa kobaiyi niyyar fara'a ba sai ya sakashi yinta dole saboda shi mutumne mai barkwanci dason wasa.        Cikin ihu Huzaifa yace, “Jeka fito ka sameni mijin mata biyu, indai maganace kuwa ka haɗu da ita yau ko barci bazan barka kayiba”.      AK na jiyosa daga ɗakin, dan haka ya girgiza kansa kawai yana murmushi. Kayan jikinsa ya cire ya nufi toilet dan watsa ruwa a gaggauce lokacin sallar magrib karya ƙure masa. ★★          Abba kam koda ya isa gida da albishir ɗin ɗaura auren Zinneerah da AK ga Mmn sadiq sai kawai ta fashe da kuka dan farin ciki, Abba dake mata dariya ya rungumeta yana lallashi.      “Tabbas mutanen nan sun cancanci yabo Hauwa'u. Dan halayyarsu na mana nuni da cewar har yanzu akwai mutanen ƙwari masu mutunci da sanin yakamata a cikin masu arziƙi bakamar yanda mu mutane muke zargiba. Inda ace ana samu mutane irinsu Alhaji Kabeer Shira koda a talakawanma wlhy da duniya ta zauna lafiya. Amma yanzu zakiga kowa ɗansa kawai da mutuncinsa yake karewa. Babu ruwansa dabin gaskiya koda ace yana ganinta ƙuru-ƙuru kuwa. Sau da yawa akan ɓata tarbiyyar yarinya amma kiji iyayen yaron na amabaton ɗansu bazai auri lalatacciya ba. Bayan kuma bata lalaceba sai da taimakon ɗan nasu. Tare suka aikatafa, amma sai a nuna tsangwamar macen fiye dashi namijin dan son zuciya. Bayan kuma shi namijin yafi macen hankali, ko ya girmeta, maybe ma shine yay amfani da wayonmu na maza ya lalata mata rayuwar tata. Hakan zaluncine dason zukata muke aikatawa wajen ƙasƙantar da mace akan zunubi koda kuwa tare ta aikatashi da abokin halittarta namiji.”          Hawaye mmn sadiq ta share tana duban mijin nata, “Yaya ai mutanen duniya haka suke tun na ƙarnin farko, suna amfani da raunin ɗiya mace akoda yaushe wajen sake raunanata, sun mance a ɓangaren zunubi da hukunci duk iri ɗaya UBANGIJI zai mana ga duk wanda ya saɓa masa. Wlhy bammasan yanda zan musalta maka daraja da kima ta mutanen nanba a zuciya ta, sukam waɗanne irin mutanene haka masu tarin adalci da sanin darajar ɗan adam?”.         Cikin dariyar farin ciki Abba yace, “Tabbas sun cika ƴan baiwa, dan samun irinsu a cikin al'ummarmu sai an tona. Amma akwaisufa. Yawaitar masu son zuciyarne ya lulluɓe irinsu saboda ƙarancinsu a cikin mutane. ALLAH ya bamu ikon koyi dasu”.       “Amin” mmn sadiq ta faɗa wani irin sanyi da nutsuwa na saukar mata lokaci guda.       Abba yace, “Yauwa inaga ki shirya Abdul-Mutallab zasu aiko a ɗaukesa daga can gidan wai ƙanwar Alhaji Kabeer ɗince zatazo daga Lagos yau, itama za'a kaimata shi ta gansa”.       Kai mmn sadiq ta jinjina masa tana faɗin, “To bara ka gani naje na tadashi a barci can kuwa sai nai masa wanka basai sunzo sunyi zaman jiraba”.      Cikin gamsuwa da bayaninta ya kaɗa mata kai..........✍ _Kuyi manage da wannan an mana rasuwane ban samu zaman nustuwar typing ba😊🙏🏻_. *_A page na ƙarshe na ranar Friday akwai inda nai kuskure, hakan ta farune dalilin rashin yin editin ranar, nayi typing na gaji. Inda nasa AK yayi limancin sallar zuhur nayi maganar yayi karatun salla har mutane na ambaton anyi baƙon balaraben limami. Please amin afuwa. Wannan ajizancine na ɗan adam sai daga baya na farga dalilin maganar da wata tayi na sake komawa na duba page ɗin. Ina ƙara bada haƙuri Please, mantuwa ce da rashin editin kamar yanda na faɗa tun farko😊🙏🏻_* *Barkanmu da dawowa hutun weekend😍😍😘😘😘💃🏻* *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_* *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* *Page 42* _________________________ *MG'S SKINCARE* Hi my peole🙋‍♀️ Are you tired of using different skincare product that won't work on ur skin no matter what❓then trust me @mg's skincare is the right plug for you💯 Are you guys battling with pimples,dark spot, sunburn, acne, stretch mark,knuckle,dark armpit,damaged/bleached skin Have you getting dark due to childbirth or sun exposure🥺worry no more@mg's skincare gat you covered✅ Want ur skin to glow buh you don't like using cream/lotion try *mg's herbal whitening black soap* nd you'll achieve that free/shiny skin🧚🏻‍♀️ For those that wanna achieve that milky flawless skin that turns head wherever you go🧚🏻‍♀️ try mg's *beauty kit* that's the secret to beautiful skin😎you'll get an amazing magic result😘 you can also buy the soap nd combine it with any of our product to get more result😀 Glow gang What are you waiting for Shop urs now before we get sold out again😍 Mg's product is 1in town😃if you know you know kawai😜 Nd mg's products are organic they dnt bleach they are made with natural ingredients that will make ur skin lk brighter nd tone ur skin😘 it just bring out that hidden beauty in you😘we HV everything available now so is time to glow dearies Pamper ur skin🧖‍♀️ Shine like a bride💯 Make ur skin brighter🤗 Glow🦵 Soap price:3k Beauty kit:11k Chat 08062991549 Call 08064532391 Instagram: glow_with_mgs Facebook:mg's skincare DNT forget to follow us😇like/comment😍 Team glow🤝 _________________________ *Page 42* ...........Cikin farin ciki Baffah da ƙanwarsa Mommy (Bilkisu) suka tari juna, duk da kuwa basu daɗe da rabuwa a london ba duba mahaifiyarsu Hajiya iya. Sama-sama suka gaisa ya shiga ciki watsa ruwa. Koda ya fito massallaci suka fice da matasan ƴaƴansa. Sai da aka idar da sallar isha'i sannan suka sake shigowa gidan.      Sai lokacin matan gidan suka sami damar zuwa masa sannu da zuwa da ALLAH ya sanya alkairin ɗaura aure da sukaji a bakin ƴaƴansu.     Hakama Mommy ta shigo har falonsa inda aka shirya musu abinci tare, cikin farin ciki sukaci abinci shi da ƴar uwarsa. Sai da suka kammala suka sami zaman yin hira sosai, inda a cikin hirar ne Baffah yay kiran Khalipha ya sakashi ya haɗasu da Hajiya iya.      Tsaf ya kwashe mata komai ya sanar mata game da ɗaurin aure. Duk da yasan zatai farin ciki dama dajin haka sai yaji murnar data nuna ma ta zarta wadda yay zato, dan albarka dai ya shata har babu adadin ƙididdiga. Suna tsaka da wayarne AK da Huzaifa suka shigo ɗakin. Kai tsaye wajen Mommy data ware masa hannu ya nufa. Ya zauna kusa da ita tare da ɗan hugging ɗinta ta gefe yana murmushi har haƙoransa na bayyana. Dan har ransa yana ƙaunar ƙanwar mahaifin nata saboda itama tana ƙaunarsa.         “Ina cewa zanje na gaisheki tunda wancan zuwan ban samu shigaba sai kuma gaki?”.     Murmushi Mommy tayi dakai hannu ta shafa kan AK mai maganar. Tace, “Ja'iri anya na yarda dakai kuwa? Yanda ka ƙwace mana Inna ka kai London bamma tsammaci zuwanka nan kusaba. Nazata sai bikin su Saffiya, ashe ma kai zaka fara angwancewa kafin su. To ALLAH ya sanya alkairi ya bada zaman lafiya na har abada”.       Kansa ya duƙar yana murmushi, akan laɓɓansa ya amsa da amin.     Cikin tsokana Huzaifa yace, “Aini Mommy soma nake naga wace mai sa'a ce ta shiga tsakkiyar lailah Majnoon ɗin nan haka? Dan naga alamar itama da ƙarfinta take dan tun ɗazun murmushi yaƙi barin fuskar ɗan naki”.     Dariya Mommy da Baffah suka sanya, AK kuma ya zubama Huzaifa harara da masa daƙƙuwa.       Cikin dariya Mommy tace, “To ai kaga ya nuna maka shi ba matsoraci bane, cikakken jarumine tunda gashi har yaje ta biyu, kai kota ɗayanma ka kasa”.        “Faɗa masa dai Mommy. Dan wlhy ban taɓa ganin matsoracin irin wannan yaron ba, maybe sai ya tsufa mu taimaka masa da wata yafendo a dangi”.       Filo Huzaifa ya ɗauka ya jefama AK mai maganar, saurin cafewa AK ɗin yay yana masa gwalo. Su Baffah dai nata musu dariya. Dan kowa yasan dama inhar Huzaifa da AK suka haɗu duk rashin son maganarsa sai ya takura masa yayi harma suyi faɗa.       Suna tsaka da wannan nishaɗin Moos'ab da Haneef suka shigo ɗauke da little daketa faman zuba musu surutun da ba fahinta sukeba sosai suna dariya.        Kusan a tare suka ɗago suna sauke idanunsu akan little. Yayinda Mommy ta sauke wata sassanyar ajiyar zuciya tana kallon yaron ko ƙyaftawa babu da tsarkake sunan ALLAH buwayi gagara misali daya sanya wannan kamar mai ƙarfi tsakaninsa da AK, Huzaifa kuwa hannu ya miƙa masa alamar yazo. Amma sai ya maƙalƙane Haneef yana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya.        Haneef ne dake ɗauke dashi ya ajiyesa a tsakkiyar falon yana faɗin, “Bara muga wajenwa zai je”.         Tsit falon yay sunason suga yaya za'a kwashe? Dan yanda little ɗin ke musu kallon ɗaya bayan ɗaya dolene ya baka dariya. Kamar wanda aka raɗamawa sai ya nufi inda Baffah yake, duk zatonsu wajen Baffah ya nufa, dan haka Baffah dake murmushi ya sake gyara zamansa. Yana zuwa gab da shi sai ya zagayeshi ya miƙa hannu zai tsinki appale ɗin dake a jikin flower ɗin kusa da baffan kamarma baiga kowa a falonba.        Hannu baffa ya kai ya dungure ƙeyar little ɗin yana faɗin, “Like father like son” fuskarsa ɗauke da murmushi.      A take duk suka kwashe da dariya, banda AK da yay ƙasa dakai kawai yana murmushi, dan shima dai yanda Little ɗin ya wanu basar da kowa ya bashi mamaki, dan sak halayyarsa na basarwa da mutane ke yawan faɗa masa ya iya.       Hannu Baffah yasa ya ɗaukesa ya ɗaura a cinya yana faɗin, “Ja'iri, saika mana yanga dan kaga muna son ɗaukarka?”.     Kamar little yasan mi baffan ke nufi ya wani ƙyalƙyale da dariyar data basu mamaki, dan sanda suka shigo duk da surutu yakema su Haneef dan zuwa yanzu ya saba dasu fuskarsa a turɓune take.     Suma dai duk dariyar sukayi kafin Baffah ya mikama Mommy shi. Zuciyarta cike da rauni ta amshesa tana murmushi, har cikin ranta jitayi so da ƙaunar yaron na shigarta. musamman yanda yake kamanni sosai da AK kamar yayi kaki ya aje.        Fita su Moos'ab sukayi dan son zuwa su huta. hakanne ya bama su Baffah damar tattaunawa akan zancen little dake lafe jikin Mommy. AK dai baice komaiba. Sai su uku suke maganarsu da juya al'amarin. Ganin sunata jefama AK tambaya a ɗan fakaice Huzaifa yace, “Niko dai zuciyata nason min wani hasashe, amma dai kubari zan sake bincike kafin kuji minene”.         Baffah dake kallonsa yace, “Son faɗa mana mana karka barmu a tunani”.        “A'a Baffah, banson inyi gaggawa ne, amma dai kuyi haƙuri na ƙara nazari akai”.        Haƙura sukai suka barshi akan yayi nazarin. AK da dai dama ba saka baki yake a zancenba sosai ya miƙe yana faɗin, “Bara naje na kwanta wlhy na gani Mommy”.          “Ai ya isa kam agaji Babana. jeka huta kaji”.      “Thanks you Mommy ”. AK ya faɗa yana murmushi da nufar ƙofa. Kamar an tsikari Little dake wasa jikin Huzaifa sai cayay “Abbah zanje”. Danshi kowa Abba ne a wajensa indai namijine babba.     Cak AK ya tsaya tare da juyowa yana kallonsa. shiko da gudu ya sauka a jikin Huzaifa ya nufesa. Babu musu ya  kama hannunsa suka fice.        Da kallo duk suka bisu cike da sha'awa, a ransu sunajin tausayin yaron da baijiba bai ganiba, amma yaya zasuyi da ƙaddara kowa da irin tasa. ALLAH ya rubuta cewar ta hanyar daya samar da yaron yaso azurtashi da shi, ya kuma fisu sanin dalilin yin hakan, fatansu kawai ALLAH ya rayashi ya albarkaci rayuwarsa data ƙannensa masu zuwa.         Huzaifa ne ya sake sauke numfashi, hakan yasa su Baffah dawo da kallonsu gareshi, cikin jinjina kai yace, “Ku daina zargin AK ya samar da yaron nan ta hanyar banza. Akwai wani voice recording dana taɓaji a wayar Adilah batare da itama tasan wayar ta naɗa ba, sai dai bai isa zama hujjaba sai nayi bincike”.       Da sauri Mommy tace, “Voice recording kuma akanmi?”.     “Kuyi haƙuri na bincika ɗin zaku sani, kudai ku tayani da addu'a ku kuma bani lokaci”.        Cikin jinjina kai Baffah yace, “Mun baka ɗan albarka. ALLAH yayi jagora muji alkairi”.      Da amin Huzaifa ya amsa yana miƙewa. dan shima so yake yaje ya kwanta ya huta. ________________________★         *_LONDON_*    Ganin yanda Hajiya iya ke murna ya saka Khalipha samun waje ya zauna danta gama ta gumtsa masa. Tana kuwa ajiye wayar ta ɗaga hannu sama tana ambaton Alhmdllh.     Katseta yayi da faɗin, “Niko Granny taƙaita addu'ar nan ki faɗamin minene?”.      Hannu ta sauke tana masa daƙuwa. Sai kuma ta ƙara washe baki da gyara zama. “Burina ne ya cika Abdul-Mutallab ƙarami, ALLAH ya tabbatar da tarkon dana ɗana. Na kuma daɗe ina mafarki da addu'a. Bazan ɓoye makaba yau dama saboda Moddibo nasa aka bani Zinneerah. Dan nasan duk daren daɗewa zaizo ya ganta, ko yasota ko karya sota dama na tanadar masa itane. Sai kuma cikin hukuncin ALLAH ga wani sarƙi ya ɓilla a tsakani........ (tsaf ta kwashe masa labari ta bashi).         Zuciyarsa ce ta shiga tsitstsinkewa, yay saurin yin ƙoƙarin dai-daita yanayin nasa yana haɗiye abinda ke neman toshe fitar numfashinsa. Cikin murmushi da ƴar dariyar yaƙe yace, “Kai kai kai Alhmdllh da wannan daddaɗar labari Granny. Wlhy wannan haɗi yayi kuwa, dan sun dace matuƙa, sannan hakan da baffa yayi shine maganin Aunty Farah da Mammah. Sai dai kuma abinda ya bani mamaki da al'ajabi wai little jinin Yayanmu ne. kainafa ya kulle”.        “Nima nawan a kulle yake Khalipha, amma dai ni yanzu burina jin ta bakin Inno, tunda dai ai ba'a shan ciki a ruwa ko? Sannan kuma babu ta wata hanyar da mace zata samu ciki sai da namiji, dan haka dan ubansu zasuma faɗi yanda akayine su dukansu”.         Ɗan jimm Khalipha yay yana wani nazari saboda maganar hajiya iya, yace, “Eh hakane Granny, amma dai yanzu akwai wasu hanyoyin da mace kan iya samun ciki koda babu alaƙar namiji a tsakaninsu”.      Cikin sauri hajiya iya tace, “Kai Khalipha kaji tsoron ALLAH ta wace hanyace kuwa? Ni dai ban taɓa jiba gaskiya”.      Murmushi Khalipha yayi, cike da rashin damuwa ko tunaninsa kaiwa nan ɗin da wata manufa yace, “Granny karki manta nifa Doctor ne. Doctor ɗinma dakeda alaƙa da matsaloli irin na mata. Akwai hanyoyi da dama kamar su yin dashen ciki da makamantansu”.        “Kamarya dashen ciki?”. Dariya yayi yana miƙewa. “Oh oh Granny wannan ai bayanine mai zaman kansa. Amma dai ki sani yanzu ana iya dasama mace ciki ta haihu wlhy”.        Baki hajiya iya ta taɓe da faɗin, “Ah kudai da shegen ƙaƙale-ƙaƙalenku na likitoci dalilin yin karatu cikin masu jajayen kunnuwa ba. Mudai ko anayin wannan sheɗancin baije manaba kaji, danni wannan ai badan karna yanke hukunciba sai nace kamar wuce wuri ne”.           “Tab Granny wlhy mutanenmu ma sunayi, duk da dai gaskiya turawa sukafiyi, amma yanzu kinga kamar a kudancin ƙasarmu sosai sukeyi, wasuma sana'a suka maidashi wlhy. A dasa musu cikin idan lokacin haihuwarsa yayi su haifa suba masu cikin ɗansu. ALLAH dai ya ƙyauta, dan wasu tsiraru a mutanenmu ma sun tsunduma wannan harkar sosai musamman ƴan gayun mata da basa son wahala, sai su bada a ɗaukar musu cikin idan ya isa haihuwa a haifa a basu abinsu. Wasuma a asibitin ake ajiye musu ba jikin kowaba. Idan ya isa haihuwa a ciresa a basu”.        “Kai wannan masifa dami tai kama. A lallai wannan duniya tazo ƙarahe kuwa”.      “Sosai ma” Khalipha ya faɗa yana ƙoƙarin ficewa dan bayaso halin da yake ciki yakai ga bayyana a fuskarsa har Hajiya iya ta fahimta.       A falo ya wuce su Zinneerah dake kallo, yanda ya wuce ko kallonsu baiyiba yasa Jamal cewa, “Tofa, inaga Granny da Yah Khalipha anɗan dambacebe naga kamar ya wuce a fusace”.        Dariya su Meenal sukayi. Zinneerah ko tayi kamar bata jiba dan tun ɗazun gabanta ke wani irin faduwa. zuciyarya na mata rauni kamar maijin tsoron faruwar wani abu a gareta. Sai dai ta daure bata sanarma kowaba tanata addu'a a zuciyarta. Dan kallonma yinsa kawai take ba fahimta takeba sam.        Duk wannn abu dake faruwa Farah na ɗakinta cike da damuwa. Dan tunda taji AK ya tafi Nigeria zuciyarya bata samu nutsuwaba. Wannan dalilin ya sata kiran Aunty Zakiyya ta sanar mata, ta kuma turama Mammah text message. Aunty Zakiyya ce ta kira Mammah suka tattauna, duk da ba'a kano takeba Mammah ta bata damar sakawa a mata binciken zancen yaron.       Daga haka ta kira baffa a gadarance tana tabbatar masa bai isa rabata da AK ba. Idan ma wani abu yake ƙullawa sunyi ta banza, dan ko aure suka saka AK yayi har aka samu wannan yaron ya tabbatar sai AK ya saki koma ƴar uban wacece. taji zafin maganganun da Baffah ya yaɓa mata, dan haka ta yanke shawarar Aunty Zakiyya na gama mata bincike zata tafi Nigeria ɗin da kanta, shiyyasa ta kira Farah ta kwantar mata da hankali da mata nasiha akan karta sake shiga harkar kowa a gidan harsu gama bincikensu.      To wannan nasiha ta Mammah tasa Aunty Farah nutsuwa waje guda ita a dole ta kama kanta.😹. Suma dai su Hajiya iya daba sanin miya faru sukaiba babu wanda ya shiga harkar tata. Dan yanda bata nema ganin kowaba tun bayan tafiyar mijinta, suma sai basu nemetaba. Dan a matsayinta na matar gida ita keda haƙƙin bin yanda suka tashi ko sukaci suka sha a gidan. Amma bata taba yiba tayaya suma zasu takura kansu ne akan damuwa da al'amarinta. Gara su rike mutuncinsu ko za'a zauna lafiya.       Su Zinneerah kam koda suka fahimci ɗunbin farin cikin da hajiya iya ke a ciki suka tambayeta catai babu komai. dan sunyi magana da Baffah akan zasubar zancen kar Zinneerah ta sani har sai sun dawo Nigeria saboda sheɗancin su Mammah. Baffah yace yana tsoron su sani subi ta wata hanyar su cutar da yarinyar mutane a ƙasar da batasan kantaba. Amma tunda nan da sati biyu zasu koma ayi haƙurin hakan kawai dan za'a haɗe bikinne da nasu Ni'ima. Hajiya iya kuwa ta gamsu da wannan shwarar ɗari bisa ɗari. Dan haka bayan Khalipha tai gum da bakinta...........✍ *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu😭🙏🏻_* *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* ___________________ *Page 43* ...........A Nigeria kuwa yau cikin farin ciki AK yay barci rungume da Little, haka kawai wata nutsuwa da farin ciki suka mamayesa. Dukan wani ƙunci da damuwa da tunani akan samuwarsa suka kwaranye, farin ciki da nutsuwa suka maye gurbinsa, jiyake tamkar ya haɗiye abinsa ya ƙara haifosa tsabar yanda yakejin abun kamar almara. wai shine da ɗa da rana tsaka, ɗan da baisan ta yanda ya samar da shi ba, ɗan da baisan a ina ya samar dashi ba. Shi tsabar ma nazari akan waɗanan tambayoyi. har ji yake ƙwalwar kansa na kuɗa, shiyyasa ya tattare komai ya ajiye gefe ya rungumi ɗansa tare da sumbatar goshinsa yana murmushi.       Ya jima barci bai ɗaukesaba yanata kallon little ɗin, sai can kusan ɗaya na dare barci yay awan gaba da shi. ALLAH ya soshi yaron baida fitina. Dan bai farkaba sai gabannin asuba ya tashi yana kiran “Mama ruwa, mama ruwa”.     A hankali AK ya buɗe idanunsa, ya miƙa hannu ta bayansa ya kunna fitila dake a bedside drawer dan da alama basu da wuta. Zaune ya tashi da ƙyau yana riƙo little dake neman yin kuka yana kiran ruwa. “Oh oh sweetheart i'm sorry ina zuwa”. Ya faɗa da ɗagashi gaba ɗayansa ya maida jikinsa. Kafin ya ɗakko ruwan daya ajiye gefensu dan shima yakan tashi shan ruwan dare shiyyasa baya kwanciya babu shi a kusa. Sosai little yasha ruwan. Yana gamawa ya lafe a jikinsa ya koma barci. Shiru yay yana kallon fuskar yaron mai tsananin kama da tashi, wani lallausan murmushi da ajiyar zuciya suka kufce masa a lokaci ɗaya. Kwantar dashi yay a hankali yaja bargo ya rufa masa shi kuma ya sauka dan yasan bazai iya sake komawa barcinba kuma.        Harya fita sallar asuba ya dawo little nata barcinsa, shima sake kwanciyar yayi dan barcin yake buƙata.        Kusan takwas na safe ya farka dole saboda tsalle-tsallen da little ya farka yana masa a jiki, dole ya buɗe idanunsa da sukai nauyi irin na wanda ya tashi a barci. Kamo hanunsa yay ya zaunar a jikinsa yana murmushi tare da kai hannu ya shafi fuskarsa. “Little Handsome ka hanani barci bayan kai kasha naka”.      Cikin rashin damuwa little yace, “Abba tea”. Dariya AK ya ƙyarƙyale da shi yana miƙewa zaune dashi a jikinsa. “Wato kai yaren abinda kakeso kawai kake ganewa ko? Inga bakin shan tea ɗin?”.      Babu musu little ya ko wage masa baki alamar gashi. Dariya nanma ya sakeyi da sumbatar goshin yaron wani farin ciki na saukar masa. Huzaifa dake tsaye a ƙofar ɗaki yana kallonsu yay murmushi tare da jin daɗin ganin ɗan uwansa na walwala maiban mamaki, dan ba abu ƙarami bane a rayuwa ke saka AK ƙyalƙyala dariya. Baiyi magabana ya juya abinsa. Shiko AK daba ganinsa yayiba little ya ɗauka zuwa toilet, da kansa yay masa wanka, ya naɗo abinsa a towel ya kawo ɗaki ya ajiye a kan gado. Wayar Haneef ya kira yana tambayarsa sunzoma little ɗin da kaya ne?. Daga can Haneef ya amsa masa da eh bara ya kawo.       “Okay” ya amsa yana yanke wayar, game ya sakama little a waya ya nufi toilet ɗin shima yin wankan. Shigarsa babu jimawa sai ga Haneef, sai da yayi sallama sau kusan uku, jin ba'a amsaba ya leƙo da kansa. Little kawai ya hango yana kokawa da waya, dan haka ya shigo yana dariya. “My Darling good morning ” ya faɗa yana kaiwa tsugunne gaban gadon. Little dayay busy abinsa ya ɗan ɗago ya dubesa ya sake maida kansa.      Yanda yayi ɗin sai ya bama Haneef dariya, ya fisge wayar yana faɗin, “Haba my man ni zakama jama aji danka samu phone?”.      Ɓata fuska little yay zaiyi kuka Haneef ya maida masa wayar yana dariya. Daga haka ya miƙe ya ɗakko man Yayansu daya hanga a kan mirror yazo ya yayema little towel ɗin da yake a ciki ya hau shafa masa. Sunayi ana kokawa dan little baison ajiye wayar hannunsa. Har dai aka gama. Yana saka masa kaya AK ya fito. Gaidashi Haneef yayi. Ya amsa shikam yana binsu da kallo, dan yanda suke kokawa wajen saka kayan kawai zai tabbatar maka akwai shaƙuwa a tsakaninsu sosai.       Haneef na gama shirya little ya ɗaukesa suka fice danya bama Yayansu damar shiryawa. A hankali AK ya sauke numfashi, zama yay a bakin gadon yana ɗan kai hannu ya murza goshinsa, hakan yayi dai-dai da shigowar kira a wayarsa.      Kamar zai share sai kuma ya ɗauka wayar dake a kife, duk da ganin Mammah da yayi ɓaro-ɓaro a jikin screen ɗin bai kawo komai a ransa ba ya ɗaga.       Sama-sama ta amsa masa sallanarsa, gaisuwa kuwama bata amsaba ta shiga masa magana cikin faɗa. “Yanzu Abdul-Mutallab danka maidani banza harka iya ɗaukar ƙafa ka tafi Nigeria bakako sanar minba!!?”.       Idanunsa yaɗan lumshe da raunan muryarsa gareta kodan daraja ta uwa da ALLAH ya bata, cikin girgiza kai kamar yana a gabanta yace, “Am so sorry Mammah, nima tafiyar ta dolece wlhy, ki gafarceni”.      “Dole kace ta dolece tunda ubanka ya gama gayamin magana jiya, aiko yayi da ƴar halak da bazata raga masaba. Dan insha ALLAH yau zan baro london nima zuwa Nigeria ɗin, sai naga munafurcin da kuke son biznewa”.      Babu shiri AK ya miƙe yana faɗin “Mammah Nigeria kuma?”.         “Ƙwarai da gaske, ko karnazo ne ubana?!”.      Bakinsa ya cije dakai hannu ya dafe kansa, zaiyi magana ta yanke wayar ƙitt Rasa abinyi AK yayi a ɗakin, ya shiga kai kawo kamar mai ɗawafi. Sam baiso Mammah tazo Nigeria a wannan gaɓar, dan yanda Baffah ya ɗauki zafi wlhy ba raga mata zaiyiba. Shiko baya buƙatar ganin suna shiga irin wannan rikicin dan ƙara nisantasu yakeyi.       Wayar Mahma ya kira da sauri dan yasan itace kawai zata iya takama Mammah birki. Harta tsinke ba'a ɗagaba, dan haka ya sake kira. Jin an ɗauka ya sauke ajiyar zuciya. Sai dai jin muryar Adilah na faɗin, “Sweet bro surprise”. Ya sakashi maida hannunsa a goshinsa yana murzawa. Ƙoƙarin dai-daita muryarsa yayi yace, “Uhmyim Darling badai kina london ba?”.       Ɓata fuska tayi daga can kamar tana gabansa. Cikin shagwaɓa tace, “Uhm ai dama nasan yanzu ka daina sona ALLAH, yau kwana biyu ina nemanka a waya saboda dawowana amma bana samunka, na dawo ɗazun nan, saina tarar wai kana 9ja, yanzu haka ina shirin tafiya can gidanka wajen Granny ne, ina jiran Khalipha yace zaizo mutafi idan ya fito school”.        “Oh parrot har yanzu dai baki canjaba. Ina Mahma ne?”.      Baki ta tura duk da kuwa bata kasance ƙaramar yarinyaba, dan tama girmi Khalipha da kusan shekara biyu. Cikin shagwaɓa tace, “Haka dai kakeson parrot ɗin nan taka. mahma gata can suna rikici da Mammah akan wai zatazo Nigeria ita da Farah. Wai mike faruwane na isketa sai faɗa faɗa, ni wlhy namaji dama ban dawo ba. Shiyyasa zan tafiyata gidanka dan banason faɗan nan na Mammah taita zagin mana Baffahn mu”.       Hankalin AK ne ya kuma tashi, atake raunin da yake ɓoyema ƴar uwarsa ya bayyana. Idanunsa suka sake kaɗawa sukai jajur. “Adilah akwai matsalane, amma yanzu sanin tushenta bashine abinyiba. Inason kije ki sace min passport ɗinta dana Farah ɗin duka”.         “Tab, wlhy Bro hakan dakamar wuya, dan inaga abinda Mahma tai niyyar yi kenan Mammah ɗin ta gani, yanzu hakama gata can harta fito da kayan tafiya shine Mammah ta kulle ƙofan ta canja security”.        “Thanks GOD”. Ya faɗa yana furzar da zazzafar iska. Hakan da yayine ya sake tayarda hankalin Adilah, dan ta tabbatar Yayanta na cikin damuwa, tambaya ta shiga masa amma bai iya bata amsa ko gudaba, sai ma yanke wayar yayi daga ƙarshe ya zame ya kwanta a gadon yana mai dafe kansa da yakejin ya fara sara masa da ƙarfi.                A cikin gida kuwa little nacan yanata hidimarsa a tsakanin su Baffah hankali kwance. Dan tare yay karin kumallo da Baffah da Mommy abinsa. Hakan harya dinga basu mamakin yanda ya saki jiki dasu sosai. Sai da suka kusa gamawa AK ya shigo falon. Gaidasu yayi sanan ya kai zaune kusa da Mommy. Ta shafa kansa cikin kulawa take faɗin, “Kana lafiya kuwa Son?”.      Ɗan ɗagowa yay daga kwanciyar da yay jikin kujerar yay mata murmushin yaƙe. “Lafiya lau Momy gajiyan jiyace kawai”.      “Aiko ya kamata ta sakeka haka. Kodai Daddy nane bai barka kayi barciba?”. Tai maganar tana kallon little dake wasansa hankali kwance. Shima kallon little ɗin yayi yaɗan ɗauke kansa da sakin guntun murmushi. “No Mommy, aishi wannan ko hidimarsa tasa idan ya kwanta bazai farkaba, kawai dai hajiyanne”.       “Ayya to sannu kaji, taso ka karya saika koma ka sake kwanciya ka huta”. Tai maganar tana faɗa haɗa masa abincin dake a tsakkiyar falon wanda basu jima da gama ciba suma. Baffah dai najinsu amma bai tankaba, sai dai yaji a ransa babu wata gajiya dake damun AK ɗin akwai dai dalili. Dan yanayinsa baiyi kama damai gajiyaba sai damuwa. *_DANYA_*      Ba ƙaramin sake rikicewa Inna tai ba da ganin kayan goron ɗaurin aure wai duk na Zinneerah, yarinyar da aka cemata tana can ta kama ɗaki. Kai ina akwai ƙarya a wannan al'amarin. Kawai dai ta fahimci Baba da wani sabon salo ya dawo danya. Kawai yayi hakane dan ace ƴarsa na cikin aminci. To itako zata tabbatar masa ras take kallonsa.      Da wannan banzan tunanin nata yasa ta wartsake kamar babu abinda ya dameta. Sai ma ƙoƙari sakama kanta wata walwalar dole takeyi musamman idan ƴar barka da gulma suka shigo, dan zuwa yanzu duk zancen ɗaurin auren Zinneerah ya shiga garin na Danya. Wasu kuma badan barkar suke zuwabama yanzu dan son gani da idone da son tabbatarwa da abinda ke faruwa a gidan. Dawowar baba da sabuwar amarya harda tsohon ciki, auren Zinneerah da dawowar Karima gida.      Aiko dai suna ganin abinda sukazo neman, dan haka duk wacce zata fita saita gumtsi gulma ta fita dashi a baki, duk yanda Inna ke ƙoƙarin nuna ita ta dake ranta kishinta da damuwarta sun kasa ɓoyuwa, sai zabga habaici take wasu Baba da gugar zana. Har takai Gwaggo Laritu na maida mata a kaikaice itama.      Sai da baba yaga abin zai zama fitina ya lallaɓa Gwaggo Laritu ta wuce gida aka bar Inna da takaici dan kukan zuci kawai take faman yi wanda yafi na zahiri ciwo da cin rai. ___________________★        Koda AK ya kammala karyawa fita sukai shi da Huzaifa da little, dan yanason rage damuwar Mammah dake cin ransa suk da yaji daɗin abinda Mahma tayi. Sai da suka fita ya samu damar yin waya da Hajiya Iya ta wayar Khalipha daketa ƙoƙarin danne damuwarsa.       Sun jima suna wayar da Hajiya iya harma da Huzaifa da little dataji daɗin gani tare dasu dan video call ne. A bakin Hajiya iyan ne ma yakejin wai Farah ta fita da akwati a gidan tun ɗazun, kuma su basusan ina ta nufaba dan bataima kowa maganaba.      Murmushi AK yayi, cikin rashin damuwa yace, “Karki damu Granny gidan Mammah ta tafi, kuma Mahma zatai maganinta ne ta dawo da ƙafafunta”.     Baki Hajiya iya ta taɓe da faɗin, “Kai nifa yanzu kam taitayi dan bata cikin lissafina. Tunda ALLAH ya baka ƴar mutunci da nakeda tabbacin zata share hawayenka in ALLAH ya yarda. Fatana dai ka riƙemin yarinya da ƙyau Moddibo, dan wlhy inhar Inno tai kuka akanka kaima sai kayi”.        Fiska ya ɓata yana wani ɗan yatsinata. Yace, “Oh kukuma naku salon kenan Granny?”.       “Ai mun wucema haka, dan wlhy bazan baka Inno ba saina shimfiɗa maka dokoki, ko ɗaya ka tsallaka kuwa saika haɗu da fushina”.       “To lallai naku babbane, nikam sai anjimanki”.        “Zakaci ubanka Kabirune yaro, bauɗaɗen banza jikan ƴan Morocco”.      “Ahaka dai kuka gani kuka nane”. Ya faɗa a hasale saboda zagar masa uba da tayi. Itako Hajiya iya dama tayine danta hasalashi ɗin dan haka ta hau dariya. Huzaifa fa ma dai dariyar yakeyi. Hajiya iya tace, “Kaima ai ina zuwa kanka dan uwarka Balkisu, tuzurun banza kana neman tsofewa a gida babu aure. Why bara dai na dawo ƴar kowa na samu aura maka zanyi a dangi, da wani shegen kansa uwa sheƙar angulu”.       A take shima ya shanye tasa dariyar yana ɓata fuska, “To kin kuma dawo kaina? Kefa ALLAH Granny kinada matsa kiyita zagema mutum iyaye babu laifin zaune babu na tsaye.  Sai ki nema wanda zaki samoma mata a ƙauye badai niba wlhy”.       “An zageka ɗin mai kama da zucbibin ƴan Lagos, bara dai na dawo kaga yanda zanyi maganinka wlhy, inba hakaba nasa Bashir ɗin yima uwarka kishiya itama wlhy. (Daddynsa take nufi😂) dan haka ya waro idanu waje da faɗin, “Kai! Wai ke Granny miyasa lamarin naki kullum gaba yakeyi?, sam bakison zaman lafiya?”.      “Oh bama kasan yana yin gaba ba saina dawo Nigeria”. Tai maganar tana yanke kiran.        “Tsohuwarnan akwai tarin matsaloli a kanta yasin”.     Cewar Huzaifa rai ɓace. Shi adole yaji haushi ance za'a saka aima Mommy kishiya😹.      “Ai indai Granny ce ta wuce duk yanda kake tunaninta”. Cewar AK yana wani ɓata fuska shima. Little da baisan anaiba wasansa kawai yake zabgawa.       Biyawa sukai ta gidan Dr Mahmud suka ɗaukesa dan gona zasuje duba masu aikin shinkafa, daga na su leƙa company da ayanzu haka an fara zuba aikinsa shima. Kasancewar sun tahoma Little da kayan ciye-ciye ko damuwa baiyiba, sai uban rashinji yake zubawa a gonar alamar yana cikin ƙoshin lafiya.         Huzaifa akwai son irin wannan wajajen, dan haka ya shiga cikin gonar sosai yana duba aikin da yaba ƙyawun da yayi. Da wannan damar AK da Dr Mahmud suka tattauna akan abinda ya shafesu game da ginin company nin shinkafa da kuma aikin shinkafar, dan a shirinsa so yake ya koma london zuwa jibi idan ALLAH ya kaimu, kuma da Little yake shirin komawar, baisan kuma yanda zasu kwashe da Baffah ba akan hakan.............✍                          *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_* *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* ________________________ *page 44* ...........A gajiye suka shigo gidan gab da magriba, dama sun ajiye Dr Mahmud a gidansa. Little kuwa yayi barci jikin Abbansa dan Huzaifa ne yay driving ɗin.         Koda Huzaifa yay fakin a inda ya dace AK fita yay ɗauke da little a kafaɗa, kai tsaye sashen Hajiya iya ya nufa batare da ya saurari maganar da Huzaifa ke masaba. Kasancewar bayan tafiyarsu Abidah ta shigo ta gyara masa sashen sai ko ina ya kasance ƙal ga kuma ƙamshi, sosai yakejin kewar rashin Granny a sashen. Dan haka baima son zama ya yini a gidan sam.       A hankali ya kwantar da little dake barcinsa. Duk da ya ɓata jikinsa sosai a can bai tadashiba, sai dai shi ya cire nasa kayan ya nufi bayi a gurguje saboda lokacin sallar magrib yayi.      Wankan ma a gaggauce ya yisa ya fito, jallabiya kawai ya zura ya ɗan saka turare ya fito yana addu'ar ALLAH yasa kar little ya farka harya dawo.      Bayan an idar da salla bai zaunaba ya nufo gida saboda tunanin barin little da yayi shi kaɗai. Koda ya leƙo yaga barcinsa yake har yanzu sai ya koma massallacin. Sai da akai sallar isha'i suka taho shi da ƴan uwansa da Baffah gwanin sha'awa.        A gajiye yake matuƙa, dan haka ya wuce sashen hajiya iya kai tsaye yana cema Mas'ood yasa cikinsu Safiyya wani ya kawo masa tea da abinci kaɗan saboda little karya farka ya nema. Da to Mas'ood ya amsa masa cikin girmamawa.       Harya nufi hanyar sashen hajiya iya baffah dake ƙoƙarin shigewa nasa sashe shima ya juyi ya dubi AK ɗin. “Karfa suga mun musu ƙarfa-ƙarfa akan yaron nan, daga zuwa ya gaida Bilkisu”.       Juyiwa AK yay zuciyarsa na harbawa, harga ALLAH baya fatan abinda zaisa Baffah yace ya sake rabuwa da little ɗin a yanzu, danshi yanzu haka yana shiryama zuciyarsa tafiya da yaron nema london. Amma yanzu sai ya ɗan murmusa, murya a sanyaye yace, “Baffah zai koma ai sonake saina tashi tafiya”.       “Sai da safe”. Baffah ya faɗa yana shigewarsa. Shima cigaba yay da tafiya zuciyarsa na masa rauni akan iya sake rabuwa da gudan jinin nasa gaskiya.       Washe gari da safe bayan idar da sallar asuba koda suka dawo sake kwanciya yayi, dan cikin dare Little ya farka da kuka, sai da yay masa wanka ya bashi abinci suka sami salama. Shiyyasa yau ya tashi kansa na masa ciwo. To ɗan barcin daya samu ya sake komawane kuma yana tsaka ya ringajin hayaniya na tashi sama-sama a cikin sashen nasu. Duk yanda yaso daurewa karya tashi hakan ya gagara. Dole ya miƙe da ƙyar yana jan tsaki. Mamaki ya kamashi ganin babu little a ɗakin, tashi yay ya zira doguwar riga bayan ya shiga toilet ya fito, yasa Slippers ya fita. Ganin babu little a ɗan corridor ɗin wajen nanma ya fita da sauri, abinda ya gani ya sakashi tsayawa cak. Ashe a falon hajiya iya ake hayaniyar shiyyasa yake jinta sosai. Ba kuma kowa keyiba sai Mammahn sa, Farah na gefenta tana kuka kamar zata shiɗe.      Yabi Baffah dake ɗauke da little da kallo, daga shi har Mommy suna zaune kawai sun zubama Mammah idanu tana ta zabga musu azabar masifa akan abinda shi yama kasa fahimta kai tsaye. A matan gidan Momie ce kawai, dan ita kaɗai Baffah ya bama damar zuwa lokacin da Saifudden yazo ya sanar masa da zuwan Farah da Mammah duk da sau ɗaya ya taɓa ganinta kuma suna yara sannan, amma tsananin kamarta da Yayansu yasa yaji a ransa lallai itace Mammah, hakama yaran babu ko ɗaya a waje sai Huzaifa kawai.      Ji AK yayi tamkar ya fasa kuka dan takaici, dan har cikin ransa yaji haushin wannan zuwa da sukai. A hankali ya fara takowa zuwa tsakkiyar falon cikin izzar da fushi ya haddasa masa, fuskarnan tai kicin-kicin kamar zata fashe dan ɓacin rai. Wani shegen tsawa data saka little fashewa da kuka yana ƙanƙame Baffah ya dakama Farah dake ƙoƙarin fara magana dan daga ita har Mammah basuga zuwansa wajenba. Ba Farah ba har Mammah sai da tai ɓam da bakinta ta juyo tana tana kallonsa ranta a matuƙar ɓace.        Yi yay kamar baiga Mammah ba ya fara saukema Farah duk fushin nasa. “Da izinin ubanwa kikazo Nigeria? Wai Farah kin maidani ɗan iskane da duk abinda ranki ya raya miki kikeyinsa komi?. Ki maida hankalinki fa.......”       A fusace Mammah ta katsesa da cewar, “Ubanka yace tazo, taƙi ta maida hankalin nata kuma, yanzu nan Abdul-Mutallab ko kunyar ALLAH bakaji a gabana kake cimata mutunci?”.          “Mammah!” ya faɗa ransa a ɓace, danya fahimci idan har ba nuna mata ɓacin ran nasa yayiba itama to zata cigaba da bauɗar masa da Farah da banzar aƙidarta. Cikin rufewar ido yace, “Please Mammah ba maganar wasa nakeba, wane kalar rashin mutuncine sai dai ta ɗauka ƙafa daga wata ƙasa ta taho bada izinina ba, kodan taga wancan karon na mata shirune? To wlhy ni bazan ɗauka wannan iskancin ba, na bata nanda awanni goma ta koma inda ta fito, inba hakaba wlhy saina tabbatar mata da ainahina na Abdul-Mutallab Kabeer Abdul-Mutallab Shira”.      Daga haka ya juya ya koma ɗakinsa. Wani ɗan murmushi Baffah yayi na manya ganin yanda Mammah tabi AK da kallo baki buɗe kamar sokuwa. Ƙara rungumesa little yayi da sumbatar goshinsa, shiko yaro ya ƙara lafe masa a jiki saboda tsorata da bala'in daddynsa.        Juyowa Mammah tayi tana kallon Baffah cike da tashin hankali. Idanu ya ɗan waro mata alamar minene? murmushi ɗauke a fuskarsa har yanzu.       Ƙara ƙufula tai da salon nasa, dan babu abinda ta gani sai Kabeer ɗinta masoyinta na da, muryarta har rawa take wajen faɗin, “Kabeer haka ka maidamin yaro?”.      “Dama haka kika haifi abinki”. Baffah ya bata amsa kansa tsaye yana sake sumbatar goshin little. Sai kuma ya kalleta yana ƴar dariya, “Hindatu ko iya haka muka tsaya kin sami amsarki akan Adnan, dan kinji dai abinda yace, sunansa Abdul-Mutallab Kabeer Abdul-Mutallab Shira. Ba Abdul-Mutallab Hindatu Umar Kaita ba. Ballantana yanzu muka fara wasan ni da ke wlhy, dan sai na tabbatar miki ke kaɗai kikazo gidan nan badasu ba”.       “Kabeer Shira!”. Ta faɗa a tsawace.      Shima Baffah a fusacen yace, “Yes! I am. Hindatu Kaita!”.        Ganin yanda Baffah da Mammah sukai ɗin ya tayarma Mommy da Momie hankali, shi kansa Huzaifa ƙarjinsa sai bugawa yake dan tamkar AK yake bayason hayaniya, barshi dai da shegen surutu shima yafiyi ga wanda ya sani sosai. Farah kuwa ai sake tsurewa tayi dan bata taɓa tunanin haka Baffah yakeba. Kallon mutum mai sauƙin kan tsiya take masa.       “Dan ALLAH kuyi haƙuri ni banga abin tashin hankali ananba Yaya”. Mommy ta faɗa hankalinta tashe tana dawowa kusa da Baffah. A fusace Mammah ta miƙe tare da kama hannun Farah da duk jikinta ke ɓari. Ta duba Baffah da manyan idanunta da har ƙwalla suke tarawa dan bala'i. “Banzo Nigeria da niyar yin fitina da kai ba Kabeer, amma tunda har kace ka shirya muje zuwa. Ina mai tabbatar maka bazan bar ƙasar nanba sai da yarona, sai kuma nasan uwar data haifa wannan ɗan da shi. In ko har aure ka ɗaura masa da ita aka samar da shi sai ya saketa, na haɗa da yaron kuma na wuce, dan yazama nawa shima”.        Wata ƴar dariya ce ta suɓucema Baffah babu zato, ya shafa kan Little yanayin kayarsa hankali kwance. Kafin ya ɗago yana nuna mata little. “Wannan shine tunani mafi gurɓata da kika taɓayi a rayuwarki Hindatu, kinsanfa ance abin cikin ƙwan yafi ƙwan daɗi. Dan haka ki sani wannan da kike gani zuciyata ne da duk ma wanda yake rayuwa a gidan nan. Kinsan kuwa raba zuciya da gangar jiki abune mai wahala ga ɓarawo. Amma tunda kema kin shirya wasan muzuba, ɗan halak ka fasa. Sai dai ki sani wasa zamuyi da basira bada hauka ba. Ki cire wannan shirmen a ranki ki nutsu waje guda wajen farautar dawo da Abdul-Mutallab gareki, nima zanyi farautar ganin ya dawo gareni daga shi har Maryam (Adilah) sannan kuma na haɗa da ɗan jikallena abin cikin ƙwan”. Ya ƙare da wani salon ɗage mata gira ɗaya.      Da ƙarfi ta rumtse ido da cije baki, harshenta har harɗewa yake wajen ambaton, “Muje zuwa mana, kaima kasan Hindatu, nama ƙwata ada da kake jin kanka Kabeer Shira balle yanzun. Wlhy saina tabbatar maka dani Hindatu bakatsiniyace ƴar asali”.       “Kika dai sata. Kamar yanda nima sai na ƙara tabbatar miki dani Kabeer jinin bauchi ne gaba da baya babu gauraye”.      Fuuuuu Mammah taja hannun Farah dake kuka dan duk a firgice take suka fice. Dama tun jiya da dare suka iso a hotel sukai masauki.      “Amma Yaya miyasa zaka biye mata? Kasan fa Hindatu dama can ƴar zafin kai ce. Dan ALLAH karku saka yaranku a rikicinku, gashi ma harda jiƙa da shi baima gama saninkuba da ƙyau har yanzun”.       Murmushi Baffah yayi yana kallon little. Hankalinsa kwance yace, “Zai sammu ne Bilkisu. Zafin kan Hindatu kuwa zan sauke mata shi a wannan karon dan na fita itama ta sani. Wasu dalilaine kawai yasa na barta ko a can baya ɗinma”.      Shiru falon yayi zuciyar kowa da fargaba. Musamman ma Momie da ayanzu ta gama sallama ma bala'i da gadarar Hindatu.        Silalewa Huzaifa yayi ya fice, dan abinda kawai zuciyarsa ke basa da wannan game ɗin kafin a farashi Hajiya iya ta dawo gidan nan. Inba hakaba Mammah zata iya bin ta wata hanyar ta sace koda little ne ta gudu dashi idan Ak ya gagareta a yanzun. Wayar Khalipha ya kira.      A lokacin yana kwance zazzaɓi ya rufesa, dan duk yanda yaketa ƙoƙarin danne damuwar rasa Zinneerah hakan na neman fallasa kansa. Amma dai yanata roƙon ALLAH ya rufa masa asiri ya cire masa ita a rai, dan baya buƙatar Yayansu dawowa ya gansa a wannan halin. Ɗagawa yay cikin dauriya, bayan sun gaisa Huzaifa ke tambayarsa ko lafiya?. Cikin dakewa yace masa a barci ya tashi.         Cikin gamsuwa Huzaifa yace ya haɗasa da Hajiya iya, shima kuma ya zauna a wajenta dan maganar ta shafesa. Amsa masa da to Khalipha yayi yana tashi ya fito. A falo ya samesu su duka zaune suna hira da kallo. Ya miƙama Hajiya iya wayar yana sanar mata Huzaifa ne.       Amsa tai cikin tsokana ta fara da faɗin, “Ɗan nema mun shirya kenan? Bandama abinka nima ai bazanso aima autata kishiya ba”.      Damuwar da Huzaifa ke a ciki ta tashin hankalin daya gani ya sakashi cewa “Granny magana zamuyi ni dake da Khalipha ”.      “Lafiya dai ko?”. “Da sauƙi dai”. Tsaye hajiya iya ta miƙe tabar wajen zuwa ɗaki Khalipha ya bita. Daga haka Huzaifa ya yanke kiran shi kuma ya kirasu a video call. Bai ɓoyema Hajiya iya da Khalipha komaiba daya gama faruwa yanzun nan. Cikin matsanancin mamaki Khalipha yace, “Dama Nigeria wai su aunty Farah ɗin suka taho?”..         “Gasu harma suna ƙulla game da Baffah. Granny inaga ki dawo gaskiya dan wannan al'amarin ba wasa bane. Na tabbata Mammah zata iya sace little shima, dan nidai yanda ta nuna ɗin na tsorata. Ni kuma wlhy yanda na fahimci Yayanmu nason Abdul-Mutallab banason ta rabashi da shi. Bama shiba koni yaron ya shiga raina. Hakama yaran gidan nan wlhy suna tsananin ƙaunarsa, dan yanda suka shaƙu da shi aduk da ba gidan yake ba ya isa amsa gamai kallo. Khalipha zan turo kuɗi a shiyama Granny tahowa, idan lokacin ganin likitan yayi saita koma”.      Cikin gamsuwa Khalipha ya gyaɗa masa kai kawai. Dan shima ya gamsu da hakan, shi kansa zai bisu dan yasan Yayansu nacan cikin damuwa da tashin hankaki dama gashi ya tafi a birkice.        A ɓangaren AK kam koda ya koma ɗakinsa duk abinda ke faruwa tsakanin Baffah da Mammah yana jiyosa, har game ɗin da suka ƙulla tsaf yaji, mamakin Mammah ya sake kamashi jin kuma little ɗinma ya zama abin harinta bayan ita ta gama bala'i ranar a london.       Safa da marwa ya shigayi a ɗakin yana tunani da nazarin matakin dazai ɗauka akan Farah dan harga ALLAH yana tsoron Mammah ta cigaba da busar masa da idonta akan wannan halayen da sam basa birgesa. Dolene yayi wani abu kafin wankin hula ya kaisa dare.     Ciwon da kansa ke masane ya sakashi tattara komai ya ajiye ya koma gado ya kwanta. Duk da tarin ayyukan dake garesa a yinin yau dan yanason komawa london gobe idan ALLAH ya kaimu baijin zai iya fita a gidan. Maganar komawama babu ita tunda su Mammah sukazo nan ɗin. Dan dole ya haƙura har sai yaga sun koma. _________________★      Babu wanda yasan mi Huzaifa ya ƙulla. Cikin dare sai ga baƙin london. AK na zaune bisa sallaya yana karatun Al-qur'ani bayan kammala nafilfilinsa ya ɗanji maganganu sama-sama. Mamaki ya kamashi duk tunaninsa Farah da Mammah ne suka kwana a gidan, dan shi da wuri yay barci jiya saboda allura da Dr Mahmud yazo yay masa kasancewar jininsa ya hau sama sosai dalilin ɓacin ran safiyar jiyan. Little ma yau a wajen su Momie ya kwana, tunma fitar da Baffah yay dashi bai sake ganisa ba sai da yamma Huzaifa ya shigo tare dashi duba jikinsa. Da Abidah kuma ta shigo kawo musu abinci ya maƙale mata.       Bai tashi ba sai da yakai inda ya dace, Al-qur'anin ya rufe ya tashi ya fita a ɗakin. Turus ya tsaya yana kallonsu Meenal dake shigowa da kaya, ga Hajiya iya zaune cikin kujera tana shan ruwan da Zinneerah ta ɗakko mata a kitchen. Murmushin kwantar da hankali Hajiya Iya tai masa. Yayinda su Jamal suka shiga gaishesa murya ƙasa-ƙasa dan darene sosai kusan ƙarfe uku ma.       Da ƙyar ya iya ɗaga ƙafarsa ya tako garesu, Zinneerah da sai yanzu hankalintama yakai garesa dan ta juya baya a yanda take tsaye ta ɗan matsa ta bashi hanya murya ƙasa-ƙasa tace, “Barka da dare Yayanmu”............✍                       *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_* *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* _________________________ *Page 45* ...........Sai da ya kai zaune sannan ya ɗan dubeta ya kauda kansa yana maidawa ga Hajiya iya mamaki har yanzu shimfiɗe a fuskarsa. Kansa ta shafa tana murmushi. “Mamaki ko?”. Ta faɗa tana kamo hannunsa cikin nata.       Cikin ɗacin murya yace, “Amma Granny yanz......”      “Shiii” ta faɗa tana girgiza masa kanta alamar kar yace komai. Badan yasoba dole yay shiru yana binta da kallo. Barin wajen Zinneerah tayi dan kasancewarsa a wajen yasa taji ya cika mata fili kamar yanda takeji a duk sanda yana a waje. Handbag ɗin Hajiya iya ta ɗauka tabi bayan su Bahijja da har sun shige, barci da gajiyar da take ciki ya haddasama tafiyar tata sanyi sosai fiye da ko yaushe.      Shigowar Khalipha ya sanya Ak dake binta da kallo juyawa ya dubesa. Murmushin ƙarfin hali Khalipha yayi da matsowa ya rungumesa yana jera masa kalmar “I'm sorry yayanmu”.     Komai baice masaba, sai kansa kawai daya ɗan kaɗa yana miƙewa. “Dare yariga yayi nisa, yakamata ku kwanta ku rage gajiya”. Daga haka ya nufi ɗakinsa ransa duk babu daɗi da dawowar tasu, dan shi ba haka yaso ba.          Ƴan gidan babu wanda yasan da dawowar ƴan london sai washe gari, a take suka rikice da murnar dawowar Granny, yayinda Baffah kuma keta mamaki, sai dai dariyar da yaga Huzaifa nayi suna magana da Khalipha ƙasa-ƙasa ya sashi fahimtar sune suka ƙulla komai. Uffan baiceba ya shiga layin ƴan murnar ganin hajiya iya shima.     Sai da duk suka lafa da gaishe-gaishe da tambayar jiki sannan su Zinneerah suka fito suka gaida Baffah suma. Cike da jin daɗi da kulawa yake amsa, dan ƴan kwanakin da sukai acan harsun ƙara canja kala.          Sai da kowa ya nutsa sannan Baffah ya samu zama da Granny shi da Mommy da hajiya iya keta murnar ganinta da kiranta autarta. Yanda Mommy ke nane da hajiya iya sai hakan ya birge Zinneerah har little ɗinta ya faɗo mata a rai da mamanta itama da baba. Murmushi tayi a zuciyarta tana mai begen ganinsu.       Kamo hannunta Mommy tayi ta zaunar kusa da ita tana faɗin, “Masha ALLAHU, lallai yarona ya iya zaɓe, dan ɗiyar tawa kam badaga nanba”.     Kunyace ta kama Zinneerah duk da bata fahimci inda zancen na Mommy ya dosaba. Sai kuma can gefen zuciyarta ke raya mata ko dai Moos'ab ya faɗa musu wani abune?. Sosai gabanta ya faɗi, taɗan saci kallon Khalipha dake ƙoƙarin fita zuciyarta na bugawa da sauri-sauri. Bata gama kammala tunanintaba ta miƙe ganin kowa ya fice a yaran sai ita kaɗai. Itama ficewa tai tabar su Granny dan taga alamar magana zasuyi.         Kayan barcine wando da riga a jikinta, sai dai ta ɗora hijjab mai hannu a sama kalar pink mai haske daya kai mata har gwiwa, gashi ya ɗau guga dan da zatai salla ta cirosa ta saka.       Fitowarta dai-dai da shigowar AK ɗauke da little a hannu, kamar daga sama taji muryar gudan jininta na ambaton, “Aunty! Aunty!”.     Da sauri ta ɗago ta kalli hanyar shigowar duk da zuciyarta bata yarda da abinda tajin ba. Cikin sa'a kuwa sai a kan little daketa zillo daga jikin AK alamar zaizo wajenta. Shiko yaƙi sakinsa sai ma kafeta yay da idanu kai tsaye hankalinsa kwance.         A hankali ta motsa laɓɓanta wajen ambaton “Little” da mamaki shimfiɗe a saman fuskarta. Ga wani bugawa da ƙirjinta keyi saboda matsanancin kamannin yaron nata da Yayansu da suke ƙara bayyana kansu a koda yaushe. Musamman yau da fuskarsu ke gab da juna kuma little ɗin tamkar ya ƙara girma da wayo.       Duk yanda taso ɗaga ƙafarta zuwa garesu ta amshi little ɗin ta kasa, haka ta cigaba da tsayuwa harshi ya fara takowa a hankali yana nufota. Tsitt falon yayi kowa ya zuba musu idanu ƙasa-ƙasa, musamman su Mas'ood da sukasan mike tsakani yanzun. Su Jamal dai yanda Yayan nasu ke kallon Zinneerah ɗinne da yanda tayi itama ya basu kala suka tsaya kallo dan son ganin mike shirin faruwa.        Gab da ita ya tsaya, batare da yayi maganaba ya kamo hannunta ɗaya ya ɗaura na little akai. Kafin ya saki yaron gaba ɗaya gareta yana motsa laɓɓansa a hankali yanda ita kaɗai zata iya jinsa, itama ɗin sai da taimakon motsin laɓɓansa. “Sai na tsone wannan idanun”.      Sosai taji wani irin shock saboda jin hannayensa da nata na neman sarƙewa waje guda lokacin da yake sake mata little, magarsa da yanayin da ta ji ya sata tura baki da ɗan juya kwayoyin idon dazai tsokale batare da tasan tayiba.         Leɓensa na ƙasa ya wani cije ganin yanda ta tura baki ga idanunta sun fara tara ƙwalla suna wani farfar. Ya saki wani munafikin murmushi da ya nema sakata sakin little ɗin ƙasa yana ja da baya. Da wani irin slow tafiya ya raɓata ya wuce ƙamshin turarensa na sake bugun hancinta.     Babu shiri ta ƙanƙame little jin zai suɓuce mata. Suko su Saifudden suka shiga sunne kawuna ƙasa suna dariyar shaƙiyanci ƙasa-ƙasa. Su Bahijja kuma da basusan dawan garinba bakuna suka saki cike da mamaki da al'ajabin abinda Yayan nasu yayi yanzun, amma ya fiske ya wucesu tamkar baisan da zamansu a wajen ba.        Yana shigewa ɗakin Hajiya iya su Mas'ood suka shiga tafawa da juna. Khalipha yay ƙasa da kansa yana sakin murmushi da ƙoƙarin kauda komai dake ransa dan yasan dai ta ƙare. Koda ace ya furtama Zinneerah so Yayansu ya nuna yanaso wlhy zai iya sadaukar masa. Ballema ALLAH ya soshi bai taɓa koda nuna mataba duk da kuwa tun sanda ya haɗu da ita a gidan tai caraf da zuciyarsa. Dan bazai saka haɗuwarsu ta farko a lissafi ba, saboda kallon matar aure yake mata. Duk abinda yay mata kuma tausayine a wancan lokacin ba so ba.       Moos'ab ma dai daurewa yake matuƙa wajen danne komai, dan yayi alƙawarin koda yaƙi sai ya cire Zinneerah a ransa ta koma matsayin matar Yaya da ƙanwarsa har cikin zuciya.       Zinneerah kam ƙanƙame little tayi a jikinta da sauri mamakin abinda Yayansu yayi na neman kasheta da ranta. Ta bisa da kallo harya shige ɗakin hajiya iya ko waiwayosu baiyiba. “Aunty!!” little ya faɗa da ƙarfi cikin kunnenta yana bubbuga mata kafaɗa. Babu shiri ta juyo garesa tana sauke tagwayen ajiyar zuciya. Sai kuma ta saki murmushi da lakace hancin little ɗin tana faɗin, “Haba bawan ALLAH kashemin dodon kune zakayi ne? Waya kawoka nan?”.       Bata da mai bata amsa. Danshi little ma dariyarsa ya saki maiban sha'awa saboda lakace masa hanci da tayi, ya kwanta a kafaɗarta yana zagayo hannunsa ɗaya a wuyanta zuwa ɗayar kafaɗarta. Hannunta ta ɗora akan gadon bayansa tana shafawa a hankali da murmushi, murya ƙasa-ƙasa tace, “I miss you my heart, ALLAH ya albarkaci rayuwarka, ya baka kariya a kowanne sakan na agogo”.                     A ɗakin hajiya iya kuwa koda AK ya shiga tararwa yay su Baffah na magana. Baffah na zayyanema Hajiya iyan yanda sukai da Mammah. Gaishesu yayi, duk suka amsa masa da kulawa. ya yunƙura da nufin fitowa ya basu waje Hajiya iya ta dakatar dashi ranta a ɓace dajin abinda Mammah tazo tayi.      Komawa yayi ya zauna kansa a ƙasa dan yaƙi yarda ya kalli kowansu,  bayason suga damuwar dake kwance a cikin idanunsa.          Cikin kaushin murya Hajiya iya tace, “Ina maka murna da samun yarinyar ƙwarai kamar Zinneerah moddibo, itama kuma ina tayata murna da samunka matsayin miji. duk da har yanzu zuciyata ta gaza hasaso ko tunanin ta yanda kuka samar da Abdul-Mutallab. Amma a dalilin wani bayani da Khalipha yaymin yasani shiga wasuwasi, zuciyata kuma ta ƙara shiga ruɗani da bayanin mahaifinka akan abinda ya faru randa aka sanar maka yaron jininka ne. Sai dai hakan dakai ba shike nuna zan yarda dakai ɗari bisa ɗari ba Moddibo har saina san gaskiyar al'amarin nan. Amma zan cigaba da roƙon ALLAH ya bayyanamin gaskiyar kafin nabar duniya. Ada nayi tunanin barin tarewar Zinneerah harta kammala karatunta na sakandire. Yanzu kuma na canja shawara saboda dalilai masu yawa. Ciki kuwa harda gadaran da mahaifiyarka keson nuna mana akanka da ƴar uwarka, tunda dai ita na fahimci batasan kawaiciba. Kaje daga yau ka fara gyaran gidanka, ka kuma shirya haɗama Inno lefe dan nan da kwanaki goma zata tare”.      Ba AK kawai ba hatta Baffah da Mommy sai da suka ɗago suka kalli Hajiya iya. Cinkin ɗan rawar baki Baffah yace, “Amma Inna karatunta fa?”.       “Tayi a gidansa”. Ta bama Baffah amsa kai tsaye babu alamar wasa ko sassauci a saman fuskarta. Ɗan ajiyar zuciya Baffah ya sauke duk da shima bawai yana nufin wani dogon zango Zinneerah zata kaiba. Dama dai tunaninsa bai wuce ta gama zana jarabawarta ta ssce da zasu fara kwanan nanba. Amma kuma tunda hajiya iya ta yanke hukunci shi hakan ya masa kodan ya sake tabbatarma Hindatu shine boss.       Mommy ce tai ɗan murmushi tana kallon hajiya iyan, cikin kwantar da murya tace, “Innarmu baƙya ganin anyi gaggawa. Mu bashi damar shiryawa a tsanake sai a haɗa danasu Ni'ima tunda wata biyu ne kawai ya rage”.         “Na riga na gama yanke hukunci Bilkisu, ba kuma zan canjaba saboda shine dai-dai. Anjima kaɗan za'a kaini gidan Hauwa'u itama”.        Dole Baffah da Mommy suka amsa da to, AK kuwa uffan baice mataba. Dan shi yanzuma hankalinsa ba'a kansu yakeba. Tunanin wace magana? Khalipha ya sanarma Hajiya iyan yakeyi.         Ganin yanda yayi ɗinne yasa hajiya iya kallonsa a ƙufule. “Saboda an manna maka abinda ka ɓata yasa kaimin shiru Abdul-Mutallab?”.       Yanda ta faɗi real name nashi ya tabbatar masa da har zuciyarta ne. Dan haka ya ɗago ya kalleta, wani ɗan murmushi ya sakar mata yana miƙewa, “Indai nine kamar ki ɓata ranki, duk yanda kikeso haka za'ayi”.     Daga haka ya nufi ƙofar fita abinsa. Su duka da kallo suka bisa. Hajiya iya dake masa kallon harara tace, “Munafuki kama fito ka faɗa kowa ya sani”.        Babu shiri dariya ta suɓucema Baffah da Mommy, dan yanda Granny tai maganar dolene ta baka dariya. Itako tai kicin-kicin da fuska kamar ba ita ta faɗa ba.        Koda AK ya fita baiko kalli kowa a falonba ya fice, garden ya nufa kai tsaye, yana shiga ya ciro wayarsa a aljihu ya dannama Khalipha kira. Cikin sa'a kuwa ta shiga. Ring ɗaya ana biyu Khalipha ya ɗaga dan yaga sanda Yayan nasu ya fita daga falon kamar a fusace.      “Ka sameni a garden”. Ya faɗa kawai yana yankewa.      Miƙewa Khalipha yayi da sauri ya fice shima sauran yaran na binsa da kallo. Tun kafin ya ƙaraso cikin garden ɗin ya hango AK daketa safa da narwa hannayensa duka biyu goye a bayansa. Sai da ya iso daf da shi sannan yay sallama. Juyowa AK yayi ya zuba masa birkitattun idanunsa da suka gama tsorata Khaliphan a take. Duk yanda yaso daurewa sai ya kasa dole ya risinar da kansa ƙasa. Cikin harɗewar harshe yace, “Yayanmu gani”.        “Na ganka ai”. AK ya faɗa yana nufar kujera ya zauna. Fahimtar da Khalipha yayi yau a yaya yake ba besty ba sai ya nufesa shima ya zauna kusa da shi cikin rauni.       “Yayanmu wani abu ya faru ne?”. “Zai dai faru Khalipha”.     Ƙara daurewa Khalipha yayi, dan shi duk tunaninsa ko Yayansu bayason auren Zinneerah ne, duk da yanajin zafin rasata bazai so Yayansu rabuwa da itaba dan sun dace. Duk da kuma yanada mata ya fisu buƙatar Zinneerah a yanzu.          Cikin nuna damuwarsa a bayyane yace, “Yayanmu dan ALLAH miya faru? Wlhy tsoratani kake sakeyi”.        Kamar AK bazai tankaba sai kuma ya gyara zamansa yana duban Khalipha ɗin da ƙyau. Zazzafar iska ya furzar idanunsa na sake rinewa. Kai tsaye yace, “Wace magana kukai da Granny?”.       “Granny kuma? Ni?”. Khalipha ya faɗa cikin jinjinawa da son tunanowa.       Shiru AK yayi baice komaiba. Hakan ya bama Khalipha damar shiga kundin tunani na tsahon mintuna huɗu. Sai kuma ya duba AK yana ɗan jinjina kansa. “A sanina dai gaskiya babu wata magana da nayi da ita. In badai akan maganar IV......”.      Sai kuma ya kasa ƙarasawa. Da idanu AK yay masa alamar cigaba. Dole Khalipha ya ɗan haɗiye yawu yana maida kansa kasa. Maganar da suka tattauna da Hajiya iya akan hanyoyin iya samuwar ciki ya sanar masa. Har yakai aya AK baice komaiba, dan tun a fara bayanin ya raba hankalinsa biyu, ɗaya ga Khalipha ɗaya ga nazari da fashin baƙin dukkan kalma ɗaya dake fita a zancen Khalipha ɗin.        “Amma kai miyasa kayi wannan hasashen?”. AK yay tambayar yana duban Khalipha cikin ido.       “Ba hasashe nayiba Yayanmu, kawai dai yanda ita Granny tai maganar hanyoyin iya samuwar cikine sai ta dalili ɗaya yasa nai mata fashin baƙi akai cewar yanzu akwai wasu hanyoyi da suka ɓullo a likitance. Ni wlhy bamma ɗauka zata riƙi maganar serious ba sam”.      Karan farko AK ya saki wani lallausan murmushi da ɗaura hannunsa akan kafaɗar Khalipha ya dan bubbuga tare da miƙewa. Daga haka baice komaiba ya nufi barin garden ɗin yabar Khalipha binsa da kallo.      Sai da ya ɓacema ganinsa sannan ya sauke numfashi shima da ɗaura hannunsa akan kumatu yayi tagumi. A fili ya furta, ‘Anya kuwa nima ban cancanci yin nazari akan wannan batunba. Gashi dai na faɗama Granny ne kawai bada wani daliliba. Amma yanda Yayanmu yay serious a maganar da yanda ya dage akan shi bai aikata komai akan samuwar Abdul-Mutallab ba kamar akwai ruɗani’.       ‘Tabbas akwai ruɗani’. Khalipha ya sake faɗa yana miƙewa zaram tamkar wanda aka tsikara. Domin shikam dai akwai abinda dama ya tsaya masa a rai game da cikin da akace aunty Farah na dashi ranar, shi likitane, likitan ma dayake karatu akan matsalolin mata. Amma sam baiga wani alamomin mai ciki tattare da Aunty Farah ɗinba. Anya kuwa Yayanmu da Aunty Farah babu wani abu da suke ayanzu yake ƙoƙarin bayyana kansa da kansa?...........✍        _Sannu-sannu bata hana zuwa, sai dai a daɗe ba'ajeba. Naga wasu sun ƙagara susan yanda aka samu little da zuwan Zinneerah aikatau, karku damu zaku sani, dan kowane al'amari da muhallinsa yake tafiya, idan kuma gaggawa ta shigo sai ya koma ba'akan tsarin dazai birgeba, wata ranama labarin zamu gama baki ɗaya insha ALLAH. Kudaiyi tattalin man kanku karya tsiyaye, al'amarin mai saukine😂. Ina gaisuwa irin trillions ɗin nan.☺️🤝🏻._ *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* _______________________ *Page 46* .........Koda akazo yin breakfast yau gaba ɗaya gidan aka haɗu harsu Momie domin nuna murnar dawowar Hajiya iya. Aiko taji matuƙar jin daɗi dan bakinta yaƙi rufuwa. Little na jikinta tana bashi da kanta. Ita Zinneerah ma har mamakin yanda ya saki jiki da kowa takeyi, gashi yanzu ta fahimci dai yana neman zama ɗan gidan. Har ranta tanajin daɗin yanda kowa bai taɓa gano alaƙarta da little ɗinba. Amma idan ta tuna randa zasu iya sanin abin na damunta da sakata a fargaba.         Tunda ta zauna bata yarda ta kalli inda AK yake ba, dan ta samu ta ɗan maƙale ne jikin aunty Safiyya ba sosai ake iya ganinta kamar kowa ba. Garama Huzaifa da yazo zai zauna sai da ya tsokaneta. Murmushi kawai tayi dan ita kam ba iya irin wannan wasan tayiba saboda miskilancin ta. Shima dai ya fahimci miskilarce, hakan ya sashi faɗin, “Like Husband like wife”.      Murmushi su Baffah duk sukayi, yaran kuwa kowa yay ƙasa da kai yana gumtse dariya. Ita dai Zinneerah ba sanin inda ya dosa tai ba. AK kuwa yi yayi kamarma baiji mi Huzaifa ya faɗaba, ya maida hankali gacin abincinsa kawai dan hajiya iya ta riga tai musu sabon idan suka zauna gaban abinci shi kaɗai suke bama dukan nutsuwarsu har sai sun kammala.       Shine farkon tashi, kamar an tsikari little shima ya miƙe daga jikin hajiya iya yana faɗin, “Abbana zanje”.       Yanda yay zaram ɗin ya miƙe da maganar tasa data fita raɗam ya saka kowa yin dariya, banda Zinneerah da aranta take raya (kajimin yaro da shegen ɗafa, wai Abbana).      AK kam dawowa yay da baya yasa hannu ya ɗaukesa yana murmushi, ba komai kesa little na ƙara manne masaba sai yawon da yake fita da shi, shiko yaro dama akwai son yawo shiyyasa duk inda sukaga maza koda basu da wayo suke maƙale musu. Balle little dake da wayo masha ALLAH.        “Sweetheart kaima fa ka iya yawo na lura”. AK ya faɗa lokacin da suke nufar ɗakinsa shi da little.       Mommy dake binsu da kallo ita da Baffah tace, “Ƙuruciyar little tamkar Adnan, har wayon tsiyar ya kwaso bai rageba. Wani irin bugawa ƙirjin Zinneerah yayi a take, har takai ta ɗago ta kalli Mommy batare data saniba. Haɗa ido sukai da Hajiya iya dake kallonta cike da nazari ita, tai saurin maida kanta ƙasa. Harga ALLAH maganar ta daketa shiyyasa duk abincinma ya fita mata a rai.        Ganin yanda taketa faman juya cokali a cikin abincin Hajiya iya tace, “Inno kin ƙoshi ko?”. Da sauri tako ɗaga kanta jin ta samu mafita, kafinma Hajiya iya ta sake cewa wani abu ta miƙe da sauri. Sauran da duk basu san mike faruwaba basu fahimci komaiba. Da wannan damar Zinneerah ta samu ta silale daga wajen ta koma ɗaki.      Tayi zurfi a tunani sosai Hajiya iya ta shigo, harta zauna Zinneerah batasan da zuwantaba, sai da ta gama mata kallon nazari tsaf sannan ta taɓata. Nufashi Zinneerah ta kawo a zabure, sai dai ganin hajiya iya ya sakata sauke ajiyar zuciya da ɗan ƙaƙaro murmushi.       “Granny ashe kin shigo? Bara na ɗauka miki maganinki kisha”. Tai maganar tana ƙoƙarin tashi. Kamo hannunta Granny tayi ta maida ta ta zaunar. Hakan yasa Zinneerah ɗan kallonta. Amma ganin itama kallonta Granny keyi saita maida kanta ƙasa dan kallon ya banbanta da wanda ta sani. “Kamannin Abdul-Mutallab da Moddibo na ruɗaki ko? Muma haka suke ruɗamu a koda yaushe. Sai dai nasan jinine kawai yasa Hauwa'u haifo mai kama da Moddibo”.      Ɗan murmushin yaƙe kawai Zinneerah tayi kanta a ƙasa har yanzu, Hajiya iya taci gaba da magana batare da ta damu da yanayin Zinneerah ɗin ba. “Ki shirya zuwa anjima da yamma hajiya Zulai zatazo ku wuce katsina akwai wani aike da zaku kaimin amma ke da ita kawai zakuje”.       Saurin ɗagowa Zinneerah tai ta kalli Hajiya iyan a karo na farko, dan itafa tama kanta alƙawarin bazata ƙara taka ƙafarta katsina ba saboda tsoron karsu Hajiya su ganta. Duk da a yanzu tafi ƙarfin a ƙara kaita inda aka kaitan, kuma tasan ba gidan yankan kai baneba kamar yanda ƙuruciya ta sata kiran wajen a baya.     Cike da basarwa Hajiya iya tai ɗan dariya, “Oh wai kokin taɓa zuwa Katsina ne Inno?”.       Murya a raunane Zinneerah tace, “Sau ɗaya Granny”.       “Kai, duk da kasancewarki bakatsina? A to karma ki faɗa gaban su Jamal sumiki dariyar Danya kawai kika sani”.      Ƴar dariya tayi saboda yanda hajiya iya tai maganar cike da raha. Batare da tunanin komaiba tace, “Granny ai shima aiki Inna tasa wata mata taje dani nayi bama yawo naje ba”.        “Aiki kuma? Kina nufin aikatau fa kenan?”.       A take damuwa ta bayyana akan fuskar Zinneerah, ƙwalla suka ciko mata idanu, murya a raunane tace, “Eh aikatau Granny, ni bansan miyasa Inna bata sonaba. Dagafa wata ƙawarta tazo ta bata labarin kuɗin da ake samu shikenan tasa na bita ko baba bai saniba. Amma tsabar sharri dana dawo sai tace wai yawon banza naje, wlhy kuma ba yawo najeba”.         “Toke miyasa baki faɗama Babanki gaskiyar abinda ya faruba?”.      “Haka kawai naji inajin tsoro Granny, koma nayi niyyar faɗa masa saina kasa dan Baba tsoron Inna yakeji saboda masifarta wlhy, bama shi kaɗaiba ƴan garinmu da yawa tsoronta sukeji dan jarababbiyace sosai”.       “Kai wannan mata ALLAH ya wadaran halinta, ina daɗi ace miji na tsoronka. To amma ke miya faru har tasa aka tafi dake aikatau babu wanda ya sani, harma ta samu damar miki sharri kinje yawo?”.     Hannu Zinneerah tasa ta share hawayenta daketa sakkowa saboda tuna a yanda tabar Danya wancan lokacin, babu wani tunanin wayon manya Hajiya iya ke mata ta fara zayyana mata yanda abin ya kasance.       “Hajja lanti ƙawar inna ce sosai, dan nidai tare na sansu tunda na fara wayo, dan Hajja Lanti dillaliyace a garinmu, tana kuma saida abubuwa iri-iri. Daga baya kuma ta koma ɗaukar yara tana kaiwa aikatau a birni. Hajja lanti ba sona takeba itama, shiyyasa bana murna da zuwanta gidanmu, dan duk randa tazo da wahala kaga harta tafi Inna bata dakeniba saboda tsaban iya haɗa gulmanta. A wata ranar asabar na dawo daga tallan gyaɗa da riɗi a gajiye na iskesu zaune a tsakar gidanmu suna magana da ban san kota micece ba. Ni dai na gaidasu na bama Inna kuɗin tallar na shige ɗaki dan tace karna sake zama a tsakar gida idan tayi baƙi. Ban jima da shiga ba ta ƙwalamin kira. Koda na fito sai da suka gama min kallo na wani lokaci ne naji hajja Lantin na cewa “Ai wannan ma itace dai-dai a yanzu. Dan za'a jima ana samu tattare da ita”. Bansan ina zancen nasu ya dosaba. Ni dai Inna tacemin naje na canja kaya nawuce can bakin ɗorawar kan hanya na jira Hajja Lanti zamuje anguwa. Ban musa mataba naje na canja kayana na fito, saita sake korani da cewar naje na saka kayan sallata. Zuwa nai na sake canjo kayan na fito, a gabansu na tafi inda tace naje na jira hajja Lanti ɗin. Na jima a bakin ɗorawa zaune sannan hajja lanti tazo ita da wasu yara da ban sansu ba. Batare da itama tamin bayaniba ta bani hijjabi da nikab wai na saka. Nidai ban musa mataba na saka. bayan na sakane ta kira masu mashin su uku suka daukemu zuwa Gozarki. A Gozarki muka kwana dan maraice ya rufa lokacin. Washe gari tunda farar safiya muka tafi inda ake hawa mota muka shiga motar Katsina da naji ana faɗi a wajen. Nasha mamaki amma a raina ina ɗoki zanje katsina da nakeji a labari. Koda muka isa Katsina an saukemu a wani waje mai tarin jama'a, mudai muka shiɗa a motar kamar yanda tace mana. Daga nan an ɗibemu a napep zuwa wani waje da naji hajja Lanti ta kira da suna anguwar yari.           Kamar yanda ƴan uwan tafiyata basa gane komai a wannan tafiya nima dai ba ganewa nakeba. Sai dai ina lure da komai da akeyi. Kamar sunayen wajajen da muka sauka da inda muke tafiya. Mun isa anguwar yari da tace a kaimu. Inda aka saukemu a wani gida mai matsakaicin ƙyau da girma.         Koda muka shiga cikin gidan mun samu kusan mutane goma a cikinsa, Sai wata dattijuwar mata da tafi hajja Lanti shekaru dajin daɗi. Yanda ta tarbemu ne yasa naji ɗan dadi ga raina. Sai dai yanda maza da mata ke shiga da fita gidan baiminba a rai. Mun jima zaune suna hira kafin a kawo mana abinci muci, bayan mun koshi aka haɗamu da wata a gidan mai suna Sadiya. Itace ta kaimu wani ɗaki wai anan zamu zauna. Nidai kallon kowa nake da mamaki da tunanin mi mukazoyi nan? Miyasa Inna tace na biyo wannan matar nan batare da Baba ma ya sani ba?. Banda mai bani amsa, shiyyasa naja bakina na tsuke. Daga wannan lokaci ban sake ganin hajja Lanti ba a gidan, ban kawo komai a rainaba sai tunanin ko taje wani wajene ta dawo tazo mu dawo gida. Amma sai naji shiru har tsayin kwana biyu. Duk da ana bamu abinci muci mu ƙoshi, ga television muna kallo hakan baisa hankalina ya kwantaba, sai dai inajin tsoron na tambayi wani ina hajja Lanti take?. A randa muka cika kwanaki uku a gidan naga an kwashi abokan tafiyata su uku aka fita dasu a gidan, daga haka ban sake ganinsuba suma. Hankalina ya tashi na shiga yi musu kuka akan nidai su maidani garinmu, danni na ɗauka kodai ƴan yankan kai ne ma. Ranar naga ruwan masifa wajen matar nan, dan kamar zata dakani a turmi saboda masufar data dinga min. Dolena shanye kukana saboda tsoronta. Da maraice aka sake kwashe sauran abokan tafiyata su biyu da suka rage aka barni ni kaɗai sai waɗanda na samu a gidan. Ranarma nayi kuka har takaini gayin masassara.           Magani kawai suka bani nasha, daga haka babu wanda ya sake bi takaina, sai ma da daddare kusan ƙarfe takwas hajiyar tace a tasoni zamu fita. Ina jinta daga ɗaki danba barci nakeba, tunanin asibiti zata kaini yasa ban kawo komai a rainaba na tashi na fito bayan na saka hijjab ɗina. Tsaye na sameta a tsakar gida cikin gayu, na gaisheta jikina duk a sanyaye saboda zazzaɓi dake cina. Gaba tai na bita baya batare damin maganaba. Muna fitowa ƙofar gida muka iske mota mai ƙyau.        Motarnan muka shiga, gabana nata faɗuwa nidai inata tunanin lokacin yanke nawa kan yayi. Dan haka naita addu'a kala-kala ina sharar hawaye a ɓoye da roƙon gafarar babana a zuciya, a haka muka iso wata babbar anguwa dabansan sunantaba, sai dai yanda ko'ina ke ƙwanyar da hasken lantarki zai tabbatar maka da anguwar masu kuɗice. Katafaren gida mai blue gate aka buɗe mana muka shiga, kasancewar darene bazan iya banbance tsarin gidanba, sai dai lallai ya haɗu matuƙa. Koda muka fito a motar hajiya ce ta kama hannuna muka shiga ciki. Anan ne na sake tabbatar da gidan ya haɗu, masu shi kuma sunada kuɗi.      Waɗanda muka samu a falon ne sukai mana iso zuwa ciki bayan mun gaisa, an sake kaimu wani falon, inda muka zauna zaman jiran matar gidan. Munfi ƙarfin awa ɗaya zaune kafin ta fito, ƙyaƙyƙyawa ce sosai baƙa, daka ganta kaga bafulatanar bakatsiniya, dan ƙyawun nata ya fita sosai masha ALLAH. Sai da ta gama mana kallon tsaf kafin ta amsa mana gaisuwa tana sake ƙaremin kallo, cikin maganar daban ganeba hajiya tace, “Ranki ya daɗe ga wata ki duba ko zata iya, yau kwana uku da kawomin su daga wani ƙauye”.       Kallona ta sakeyi sama da ƙasa tana ɗan yamutsa fusaka. Ta ɗage kafaɗunta cike da isa tana faɗin, “Uhm babu laifi kam, dan tafi waccan komai, girma kawai waccan zata fita. Amma ina zuwa”. Tai maganar tana miƙewa, fita tai, babu jimawa sai gata ta dawo ɗauke da waya, batare da tayimana maganaba ta shiga haskani da hasken wayarta daban fahimci ma'anarsaba a wancan karon, sai dai a yanzu inaji a raina camara ne. Bayan ta gama kuma ta fara waya, da turanci take magana shiyyasa banji komaiba, bansan dai ga hajiya ba. Ta ɗauki lokaci mai tsaho tanayi kafin ta ajiye ta dubi hajiyar, “Ba damuwa zamu gwada mu gani, bara na ɗakko miki sauran saƙonki ko, idan akwai wani matsala zan nemiki daga baya kafin ki wuce, namafison sai mun kammala komai mun fara wucewa kafin taki tafiya”.      Baki a washe Hajiya tace, “Ato babu damuwa ranki ya daɗe, ni bani da matsala duk yanda kukeso sai ayi, fatana dai ALLAH yasa a dace akumayi nasara”.      Cike da yanga ta amsa da amin. Daga haka taje ta kawo mata saƙon da tace. Inaji ina gani hajiya ta miƙe tana faɗamin aini nan zata barni, nanne zanyi nawa aikin, dan haka sai nayi biyayya, yi nayi bari na bari.       Sosai na fara hawayen fili saɓanin na zuci, yanda zuciyata kemin zugi da zafi ya hanani yin magana harta fice ta tafi bayan ta bani ɗari biyar a kuɗin danaga an bata masu yawa, itama haijiyar gidan ta shige batare damin maganaba. Da wannan damar nai zaman kuka na kusan awa ɗaya kafin wata tazo cikin wanda muka fara tararwa a falon farko ta kama hannuna muka fice.         In taƙaita miki Granny tun daga ranar zazzaɓina ya ƙaru, inaga ganin yanda nake galabaita yasa Hajiyarnan ɗaukata a washe gari takaini wani asibiti mai ƙyau da alama na kuɗine. Anan aka bani gado. Sosai likitan yaytamin tambayoyi harnaji nama ƙosa dashi, amma na daure dan lafiyata nake nema ai. Kwanana shidda a asibitin nan na warke sarai aka sallamoni, sai dai kuma hajiya ta kaini wani gida ba nata da aka fara kainiba, naji tsoro sosai, dan can babu kowa sai wata dattijiwar mata mai suna Harirah.      Ɗaki guda aka bani a gidan, wanda yaji duka kayan more rayuwa, ni harma abin ya ban mamaki amma sai ban tambayaba tunda dai ance aiki nazoyi. Komai na nema ina samu a gidan, amma sai dai a tsorace nake, dan haka kawai na kasa yarda da sakin jiki da baba harirah, sai dai kullum sai ta shigo ɗakina ita ta sakani shan magungunana na asibiti da aka bani. Hajiyar kuma ban sake ganintaba sai bayan kwanaki sai gata. Cataimin na shirya muje asibiti likita ya sake dubani, ban kawo komai a raiba na shirya na bita zuciyata fal fargaba. Munje likita ya sakemin gwaje-gwaje, sai yace wai akwai wani ciwo dake damuna zasu ban magani. Daga wannan maganar aka kaini wani ɗaki, tunda akaimin wata allura ban sake sanin inda nakeba sai a gida. Ni kuma tunda na farka sai tsoro ya kamani ganin ko baba harirah ɗinma yanzu babu, sai wani gardi abin tsoro dake a waje. Hankalina ya tashi, da ƙyar na samu nai wanka nayi salla. ina idarwa na saka kayan danazo dasu daga gidan hajiyar farko da aka kaini, ALLAH ya taimakeni na silalo na fito daga gidan, ɗari biyar ɗin da hajiyar ta bani da zata tafi lokacin data kaini can gidan itace ta taimaka mani na koma Danya. Koda na koma kuma saina kasa bama kowa labarin abinda ya faru har Babana, duk da inason na faɗa masa kodan kalmar iskanci da Inna ke dangantani da shi sai dai inajin tsorone”.            Shiru hajiya iya kawai tai tana kallon Zinneerah kamar mai karanto komai akan fuskarta, sai dai wani irin tausayin yarinyar da ƙaunarta na sake shigarta. Dan yanda take bata labarin a nutse sai take ƙara godema ALLAH da samunta matsayin matar jikanta mafi soyuwa a ranta. Ta ɗan murmusa cike da basarwa tana faɗin, “Uhmm lallai dole ki kasa mantawa da birnin katsina. To amma ita hajiyar data kaiki gidan baki koma gidantaba bayan kin baro can?”.      “Wai Granny sokike na koma ta sake maidani, nifa wlhy haka kawai naji banason hajiyarnan data kaini asibiti, ta cika tsare gida da mulkin tsiya kamar sarki”.       A karon farko Hajiya iya tai dariya da juyawa tana kallon AK datun fara maganarta da Zinneerah ya shigo ɗakin, sai dai jin labarin da Zinneerah ta fara badawa ya sakashi dakatawa batare daya shigoba. Yanda ya kafe Zinneerah da idanu yana ma labarin nata fashin baƙi da nazartarsa yasa hajiya iya faɗin, “Amma baki taɓa gamo da maikama da wancan mutumin a katsina ɗinba?”.      Sai a lokacin Zinneerah ta farga da AK, duk da ta jima tanajin ƙamshinsa a hancinta bata kawo shi baneba. Kallo ɗaya tai masa tai saurin maida kanta ƙasa saboda yanda kwarjininsa ke cika mata idanu da zuciya. Cikin girgiza kai tace, “A'a Granny, anan na fara ganinsa nikam”.      “Inno bafa wasa nakeba”. Da iya gaskiyarta tace, “Wlhy kuwa Granny”.      Hajiya iya zata sake magana AK ya katseta da faɗin, “Kin shirya ne na kaiki gidan Gwaggon?”. (mmn sadiq).       Tsaf hajiya iya ta fahimci dalilinsa na katseta, dan haka tai guntun murmushi da cewa, “Eh bara na kimtsa, ai hada Inno ma zamuje saimu barta acan dan da safe idan ALLAH ya kaimu zata dawo akwai inda zan turata”.     Baice komaiba sai duban Zinneerah ɗin datai ƙasa da kanta yaɗanyi, ya ɗauke idanunsa ya juya ya fice.     Binsa da kallo Zinneerah tayi, tana ganin ya fice ta sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya da har sai da hajiya iya tai murmushi.............✍ *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* _________________________ *Page 47* ...........Cike da ɗokin zuwa ganin mmn sadiq dasu Aliyu Zinneerah ta shirya cikin wando da riga na parkistan red and white, sai gyale red data naɗa a kanta wanda ya fiddo mata ƙyawun da fuskrta ta ƙara. Kayan sun zauna mata ɗas a jiki kasancewarta mace mai mulmulallan jiki da ƙyawun surarta ta ƙuruciya. Babu wani kwalliya a fuskarta, amma ta saka lipstick kaɗan da yayma lips ɗinta ƙyau, dan tanada lips masu ƙyau da tsarinsu ya fita sosai yanda suke ɗaukar jambaki kamar wata babyn roba. Takalmi tasa mai ɗan tudu da igiya, sai side bag ɗinta ƙarama. A yanda tai ƙyau dolene ka kalleta ka sake kallo, ga ƙamshi tana bazawa dan Zinneerah gwanace wajen ɓarnar turare, idan ta samu batai masa da sauƙi. Ƴar jikkar data zuba kayanta kala biyu da tsarabar chocolates ɗin su Abdul ta ɗauka, dama hajiya iya ta fice ita tana falo tuni.        Hajiya iya kawai ta samu a falon itama tana ƙoƙarin fita, samarin gidan tun bayan breakfast suka fice, hakama ƴammatan, su Jamal kuwa batasan ina suka dosaba. Hajiya iya dake ƙoƙarin fita tace, “Inno kashe tvn nan ki taho nasan Moddibo nacan ya cika da hasahinmu”.      Da to Zinneerah ta amsa tana ɗaukar remote, bayan ta kashe tvn ta gyara labulolin sannan ta fito, ƙofar ta rufe dan masu aikin Hajiya iya basu dawoba, maybe sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu. Tafiya ta fara cikin nutauwarta tana ƙoƙarin ɗaura agogo data ɗakko a tsintsiyar hannunta da dosar inda ta hango Hajiya iya da Mommy tsaye da alama harda ita zasuje. Idonta bai lura da AK ba sai da tazo dab dasu tana ɗagowa da shi ta fara tozali yana ɓullowa daga ta gaban motar waya a kunnensa alamar magana yakeyi.      Kallon nata yayi dai-dai da saukar nasa idanun a kanta. A take ƴar sakewar data hango akan fuskar tasa ta ɓace ɓat, ya tsuke fuska yana mata kallon data nema kifawa saboda harɗewa da ƙafafunta suka shigayi. Saurin maida kanta tai ƙasa tana cigaba da takowa ranta fal nauyinsa da kwarjini, sai mita take a ranta kuwa. (Haka kawai bakama mutum komaiba yayta hararka, shi wai baya ganin waɗanan idanun nasa manya da ƙarfinsu yay yawa suna tsorata mutane).......      Da wannan tunanin ta ƙaraso Mommy dake kallonta tana ambaton, “Masha ALLAH ɗiyata irin wannan ƙyau haka”.     Ƙasa Zinneerah ta ƙarayi da kanta tana murmushi, hakama Hajiya iya murmushi take tana kallonta itama. A bazata sukaji AK ya saki tsaki, cikin faɗa-faɗa yace, “K! Koma kisa hijjab”.    Ba Zinneerah ba hatta su Mommy sai da suka dubesa, shiko ya fuske ya buɗe murfin motar ma a fusace ya shige abinsa. A sanyaye Zinneerah ta juya zata koma dan shi ba abin wasanta bane, waɗandama suka girmeta da shekaru masu yawa a gidan sunabin dukkan dokarsa balle ita ƴar jiya. Dakatar da ita Hajiya iya tayi ganin yanda tai ƙwalƙwal da idanu kamar zatai kuka, ta kamo hanunta tana matsawa saitin driver da yake zaune. “Haba Moddibo aimata haƙuri tunda ta rigada ta fito, ai kaga gyalen ya rufe mata jiki, kuma naga daga mota sai gida”.        Shiru yay kamar baiji mi Granny ta fadaba, sai da ta ƙara leƙasa tana faɗin, “Oh nima yarfin daka iya zakamin?”.     Idanunsa da suka canja launi ya ɗago ya dubi Hajiya iyan, “Amma Granny .......”       “Dan ALLAH ai nace”. Tai saurin katsesa dan tasan shegen taurin kansa da dagiya akan abinda duk ya kafama sharaɗi. Badan yasoba ya ɗauke kai daga kallonta yan yima motar key. Murmushi Hajiya iya tayi da duban Zinneerah. “Kinga zagaya can kusa dashi ki zauna Inno, mu saimu zauna baya da Mommynku”.       Kamar Zinneerah ta fasa ihu taji, dan yanda taga fuskarsa batai zaton ya haƙuraba, kawai dai yayi shirune dan Granny ɗin. Amma yata iya, dole ta zagaya tabi umarni. Zama tai maƙure jikin murfin mota, zuciyarta na mata hasashen ko ina little yake? Dan tayi tsammanin dashi zasuje itakam. Yanda AK ya figa motar da ɗan ƙarfi yasata saurin dubansa, sai dai da sauri ta ɗauke idonta ganin wani shegen harara daya watso mata laɓɓansa na motsawa tamkar mai magana komai son cewa wani abu amma ya gagara furtawa.         “Kai malam wlhy karka zubar damu, dan idan ka kasheni banga sake ganin ɗan inno ba ALLAH ya isa mai kishin tsiya”. Hajiya iya ta faɗa da iya gaskiyarta tana zazzagama AK masifa. Dariya Mommy ta sanya ganin yanda AK ɗin ya hararo Hajiya iya ta mirror.     Zinneerah kanta sai da zancen hajiya iya ya bata dariya, amma sai tai murmushi kawai tana kauda kanta gefe, dan zuwa yanzu ta fahimci Yayansu da Granny ba'a haɗuwa ba'ai faɗa ba. Kuma itace mai takalar faɗan shi kuma yayta mazurai, idan kuma ya magantu ya rama sau ɗaya yay mata banza.       A nutse yake tuƙin cike da ƙwarewa da bin dokoki, sai da suka hau titi sosai ya fara amsama Mommy maganar da take masa daga can baya, hajiya iya na tayata. Zinneerah dai bakinta gum, sai strawberry sweet ɗin dake bakinta take ta faman juyawa tana kallon hanya, tana jiran taji ya tambayeta ina suka dosa taga ya ɗau hanyar anguwar kai tsaye. Mamakine ya kamata sai dai babu damar magana, sunyi kusan rabin tafiya taga ya gangara dasu wani super market, sai da ya samu waje yay fakin sannan yay magana batare da ya kalli kowa a cikinsu ba. “Mommy muna zuwa Please”.         Cike dajin daɗi tace, “A fito lafiya”.     Hajiya iya kam baki ta taɓe da ɗauke kai tana maganar da su dake gaba ba jinta sukeba. “Muje”. Ya faɗa yana buɗe murfin ya fice. Zinneerah bata fahimci da ita yakeba sai da Mommy tace, “Ɗiyata fita kuje ku dawo kinji”.      Sai da Zinni taɗan waro idanunta waje, tace, “Mommy amma.....”       “Maza kije karyayi faɗa”. Mommy ta katseta kafinma tace komai. Dole Zinneerah ta yunƙura ta fita zuciyarta na dukan goma-goma. Idanunta kuwa harsun tara ruwa. Ina ita ina shiga irin wannan wajen da Yayansu, itakam yau tana cikin abba-tuwa, shikenan ya samu damar dazai cimata uwa akan ƙin bin maganarsa na saka hijjab duk da Granny ce tai bell nata dai.       Koda ta fito da birkitattun idanunsa ta fara cin karo, ga fuskarnan kamar zatai aman abinda kecin ransa. Ƙasa tai da kanta tana ƙoƙarin haɗiye rauninta dake son bayyana. Ta fiske abinta da takowa inda yake a hankali batare data sake yarda sun haɗa ido ba. Tana isowa wajen ya miƙa mata handkerchief ɗin hannunsa, “Kwashe wannan abun na bakinki”.     Idanunta dake tara ruwan hawaye ta ɗago ta kallesa. ya zuba mata hararar data sakata amsar handky ɗin babu shiri, cikin ɗan tura baki ta fara kwashe ɗan janbakin dabai taka kara ya karya ba. Handky ɗin ta miƙa masa tana ƙoƙarin haɗiye kukanta. Batare daya amsaba ya raɓata zai wuce da faɗin, “Idan baki shiga hankalinki da saka wannan janbakin ba saina tsinke waɗanan lips ɗin da haƙori mtsoww”.         Duk yanda Zinneerah taso daurewa kasawa tai sai da ta bisa da kallo mamaki ƙarara akan fuskarta. Ganin bata biyosaba ya sakashi tsayawa cak. Da sauri ta nufesa saboda fahimtar dan ita ɗin ya dakata. Jerawa sukai a tare gwanin sha'awa, dan yanda yake tafiya babu garaje haka itama take tafiyar, amma kasancewar abinda ya faru tana tsoron sake laifi ya ƙara hanzarta tata tafiyar, sai suka samu daidaito dashi dan ya fita kuzari da tsaho.       Shigarsu wajen ya sake bayyana ɓacin ransa a saman fuska ganin yanda mutane ke ɗan kallonsu jefi-jefi, a bazata kawai taji ya ruƙo hannunta cikin nasa mai taushi da ƙamshi tamkar nata ɗinma, dan zuwa yanzu ta fahimci jin daɗi ke kawo irin wannan baiwar ga fata bawai shafe-shafe ba. A kusan tare ita da shi suka lumshe idanu saboda jin sabon al'amarin dake saukar musu a gangar jiki da magudanar jini, ya sake damƙe hannun da ƙyau yana ƙoƙarin dai-daita kansa gudun kar ayi abin kunya.     Zinneerah kam ai murus bakinta ya ƙara mutuwa sai sama da ƙasa da numfashinta keyi tana ƙoƙarin fisgosa da ƙyar. Haka tanaji tana gani ya shiga zagayawa dasu yana ɗaukar abubuwa da sakawa a basket ɗin da ɗaya a ma'aikatan wajen ke biye dasu da shi. Itama kuma sai yanda budurwar ke kwarkwasa da wani iyayi a gaban Yayan nasu ya bama Zinneerah haushi ta shiga hararta ta gefen ido tana faman yamutse fuska.       AK bai fahimci halin da take ciki ba sai da sukazo wajen biyan kuɗi, har lokacin yana riƙe da hannunta tamkar ance za'a ƙwace. ATM ya ciro a aljihun wandon getzner shaddarsa ash zai miƙa budurwar data tayasu takai hannu zata amsa cike da yauƙi, caraf Zinneerah ta kawo hannu ta amsa daga hannunsa tana wani juya ido da sake miskile fuska.     Yanda tai ɗin ya saka wata dake kusa dasu kwashewa da dariya ita da ƙawarta. A fili tace, “Wlhy yarinya kin birgeni, adana abinki kar ƴan shishshigi suyi miki wuff da shi”.      Sarai Zinneerah ta jita, amma sai ko kallon inda suke bataiba tama ɗauke kai gefe. AK ma da sarai yajisu bai nuna yajiba, sai dai ya ɗan dubi Zinneerah ta gefen ido maganar ƴammatan na masa kaikawo a zuciya da ƙwaƙwalwa.      Koda aka gama saka musu a leda budurwar bata daddaraba duk da yarfatan da ƙawayenta sukayi da Zinneerah ta sake kai hannu zata ɗauka ledar Zinneerah ta rigata ɗauka da faɗin, “Don't worry, thanks”.      Kasa haƙuri AK yayi yanzu kam sai da ya ɗan dubeta, mi zuciyarsa ta ayyana masa oho sai gashi da sakin wani malalacin murmushi yana sake damƙe hannunta dake cikin nasa, daga haka ya jata suka fito yana mamakin miskilancinta da kame kai tamkar ba ƙaramar yarinya ba.          Zinneerah na ganin sun fito ta fara ƙoƙarin zame hannunta a nasa, shima babu musu ya saki tare dayin gaba abinsa. Sai dai kuma abinda sukema gudun su Granny, kuma sun gani. Dan Granny dake bama Mommy labarin da Zinneerah ta bata akan zuwanta katsina aikatau tun bayan fitarsuce ta fara hangosu. Ta taɓa Mommy tana faɗin, “Auta kalla mutanenki”.        Ɗago kan Mommy yayi dai-dai da sakin hannun juna da sukayi, dan haka ta murmushi kawai da faɗin, “Inna tarkon nan naki fa mai ƙarfine, dan na ƙaramin damƙa yayma ɗana ba, yana dai ƙoƙarin nuna halin nasa na basarwa ne”.       Baki Hajiya ita ta taɓe da cewa, “Ai sai yayma ubanda baisan halinsaba. Ni tuni na harbosa ai. Itace dai na kasa gane kanta dan itama gidan miskilancince, bansan yanda gidan nasu zai kasanceba an tara masu shegen baƙin rai da miskilanci. Shiyyasa banason a faɗa mata har sai ta tare suje can su ƙarata”.      Dariya Mommy ta sanya har su Zinneerah suka iso wajen, sai da suka shigo mota ta haɗiye abinta tana musu sannu. Duk amsawa sukai yana tada motar, daga haka sai gidan mmn sadiq da Zinneerah taita mamakin tayaya ya sani?.     ★★   Tarba suka samu maiban mamaki daga mmn sadiq da maman halima. ashe hajiya iya ta sanar musu da zuwan nasu, shiyyasa mmn sadiq datai niyyar zuwa dubata yau dole ta haƙura. Zinneerah kam ai tuni ta faɗa jikin mmn sadig tana murnar ganinta ita da mmn halima. hakan datai har sai da ya bama AK mamaki dan baiyi zatonta hakaba. Kasancewar Abba na gida yana jiransu a falonsa aka sauke AK, su Hajiya iya kuwa da mmn sadiq keji kamar ta goya suna a sashenta.         Duk yanda mmn sakina taso nuna halin nata garesu saita kasa. Dan wani cika mata ido sukai dole ta kama kanta harda zuwa ɗakin mmn sadiq gaishesu. Ai kam sun amsa mata da fara'a da mutuntawa, hakan da sukai kuma sai ya ƙara musu kima a idonta da shakka. Mmn halima ma cike da girmamawa tazo ta gaidasu, Hajiya iya nata sanya mata albarka dan bata manta da fuskartaba taje mata gaiauwar Inno.         Saboda zuwa nan hajiya iya dama taƙi cin abinci, dan ta taho da shirin cin abincin gidan ɗiyar tata. Aiko taji daɗin samun masa da mmn sadiq tai musu, sai gashi daga ita har Mommy sunci sosai suna godiya. hakan yasa Mmn sadiq ƙara jin daɗi da nutsuwa. Dan koba komai ai sun bata kimarta. Zinneerah kam tuni tana sashen mmn halima ta barsu dan su sake da kuma kasancewarsu manya a gareta.     Da wannan damar mmn sadiq da baƙinta sukai hirar zuminci da tattaunawa game da labarin da Zinneerah ta bama hajiya iya da kuma abinda ya faru akan zancen little da maganar ɗaurin aurenta. Harma da shirye-shiryen tariya da a take mommy ta tabatar musu ita ta gama shirya komai rana kawai suke jira insha ALLAHU.     Hawaye sosai mmn sadiq keyi har sai da hajiya iya ta shiga lallashinta.      Sai da akai sallar la'asar Abba ya shigo gaida su hajiya iya tare da AK da shima yaci masa sosai dan yana sonta, ya kuma sha zoɓo shima. Sun gaisa cikin mutunta juna, suka ɗan ƙara tattaunawa har zuwa kusan biyar da rabi sannan sukai haramar tafiya.     Sai kuma ga Zinneerah tai ƙwalkwal da idanu na kewar hajiya iya da zatayi duk da dai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu zata koma. Sau biyu suna haɗa ido da AK da tuni ya shige mota ta mirror ɗin waje, daga ƙarshe dai ta matsa daga saitinsa tana ɗaga musu hannu.     Tafiyarsu da mintuna basufi talatinba su Sadiq suka dawo gida. Ganin Zinneerah suka haukace da murna suna tambayarya ina little ɗinsu?, su dai sunyi kewarsa dan ALLAH a dawo musu da abinsu. Dariya kawai take musu dan ita dai wannan ba huruminta baneba ai. Tunda batasan yaje canba itama ganinsa tayi.      Bata samu zama da mahaifiyartaba sai dare bayan yaran sunyi barci, kasancewar ɗakin mmn sadiq ɗin zata kwana suka sami damar yin hira, yayinda mmn sadiq ketama ƴar tata nasiha a kaikaice akan aure da muhimmancinsa da darajojinsa. Ita dai Zinneerah saurarenta kawai takeyi bawai fahimtar dalilin yinsuba. Sai dai suna shiga kwakwalwarta tana kuma ƙoƙarin adanawa da fatan yin aiki dasu a duk sanda ƙaddara ta tilasta mata yin aure dan bata kawosa a lissafinta sam. ita kullum lissafi da budget ɗinta akan karatune mai zurfi kawai.      Washe gari ma bayan tafiyar su Abdul skull sake zaman hira tayi da mamanta. A yau ɗinma hirar ta kasance kusan duk nasiha da dabarun zaman gidan aure koda da kishiya. Harma dai takai abin ya fara bama Zinneerah mamaki amma saita danne a ranta kawai.      Karfe huɗu dai-dai sai ga Ni'ima da driver sunzo ɗaukarta, jitai kamar ta fasa kuka. Amma jin mmn sadiq tace zasuje taron biki Danya kuma harda ita nanda kwanaki tara yasa taɗanji daɗi a ranta har fuskarta ta nuna. Bayan ta gama matse-matsen hawayenta ta shirya suka wuce ɗauke da madaidaicin botikin gullisuwa da mmn sadiq ɗin tai musu.           Koda suka iso gidan cike da murna suka tari juna dasu Bahijja daketa mata ƙorafin basusan zataje wajen mama ba da sun bita. dan sai da su Mommy suka dawo suka sani. Haƙuri ta basu kawai, daga haka suka shiga hidimar cin gwullisuwa kuma.          Ana idar da sallar magrib hajiya iya tai baƙuwa. Bayan sun shiga ɗaki kusan awa ɗaya aka kira Zinneerah, kai tsaye hajiya iya tace mata ta shirya zasu tafi da baƙuwar gidanta. Mamaki ya kama Zinneerah, amma ganin yanda hajiya iya ta fiske dole itama ta shanye mamakin nata.      Bayan ta shirya Hajiya iya ta jata gefe tai mata ƴar nasiha da gargaɗin duk abinda akai mata a inda zataje kartai jayayya, karkuma tai wasa wajen koyon komai ɗin. Ta amsama hajiya iya da girmamawa ita dai tana matsar ƙwalla, dan hankalinta ya tashi jin wai sati ɗaya zatai acan, a hakanma hajiya fadi take waje ya ƙure ba haka tasoba.       Zinneerah naji na gani ta tafi tabar su Meenal tana hawaye suma sunayi tamkar masu rabuwa har abada. Hajiya iya kanta sai da taji kewarta, to amma wannan shine kawai gatan da zatai mata ta miƙata wajen kwararrun mata ta fannin sanin gyaran jiki da wasu sirrika irin su hajiya Falmata su gyara mata ƴar jikallen tata. Dan idan tai dubi da abinda ya faru da kuma kishiya irin Farah saita ƙara jin wannan shine gatan.       Koda suka iso gidan hajiya falmata bata tsaya sanyaba saboda gargaɗi da sharuɗɗan hajiya iya akan irin salon gyaran da take buƙata aima Zinneerah ɗin, itako hajiya falmata dama aikinta kawai ta sani batasan wasaba. Musamman ma aiki irin wannan na manyan mutane kamar su hajiya iya da suke alaƙa tun zamanin ƙuruciya ba abinda zatai sanya bane. Dan haka tun a ranar ta fara gyara Zinneerah daga isowarsu gidan ko hutawa batama bari sunyi zaman yiba. Tun Zinneerah na kallon abin wani iri hardai ta fara jin yana shiga jikinta da sha'awarsa ganin yanda ta fara canjawa da ƙamshi mai kama jiki da gogewar fata a cikin kwana biyu.        Babu abinda ke damunta sai kewarsu Jamal da hajiya iya dan ko abinci da ake bata na musamman ne. Hajiya Falmata kuwa nata aikinta da koya mata abubuwa kai tsaye har kunya na neman kashe Zinneerah da ganin hajiya falmata zata iskantar da ita shekarunta basu kai ba. A ranta kuma tana mamaki yanda ake mata magana mai kama da harshen damo akan aure da zamantakewarsa. Ta rasa wannan dalili itakam, takumayi alwashin bazata tambayaba zata cigaba dabi da ido da kuma saurare.       A Ɓangaren su Hajiya iya kuwa Zinneerah na barin gidan aka ware fara tsare-tsaren biki da maganar invitations dan hajiya iya da Baffah fa shiri suke gagarumi kodan ƙular dasu Mammah dake can hotel suna jiran tsammani daga mai bincike, AK kuwa daketa ƙoƙari akan aikin shinkafarsa yana sane dasu, dan tuni yasa aka bincika masa inda suke, ya kuma shirya ɗaukar mataki akan Farah data bijirema maganarsa.      Akan gyaran gidansa kuwa Dr Mahmud da Huzaifa ne tsaye akai duk da gidan bama taɓa zamansa Farah tayiba. Garamashi yankan zauna lokacin da yake shigowa ƙasar a munafunce.      Ranar da Zinneerah ta cika kwanaki huɗu wajen Hajiya falmata lefen da Momie ta haɗa gudunmawarta ya iso, sai kuma ga Adilah da Mahma daga london suma sun iso da nasu kayan lefen, dan AK na sanar da ita komai bai ɓoyeba, takuma bashi goyon baya ɗari bisa ɗari.      Zokaga yanda Adilah ke murna da farin cikin kasancewarta cikin ƴan uwa. mahma kuwa abinci kawai taci anan taɗan huta ta nema inda su Mammah suke, dan bata son ita kanta su san da maganar auren har sai ranar tariyar insha ALLAHU..............✍ *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_* *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* *Page 48* __________________________ Duk wacce batayi anfani da sabulunnan ba anbarta abaya acan karshen bayama kuwa duk Mai tantama akan sabulai nagyaranjiki cewa basa Aiki toh yacire mg's domin kankat ne insha Allah babu Wanda yayi anfani dasabulunmu yace baiyi ba koyaushe mg's sai sanbarka amare da uwargidaye hardama yanmata kuhanzarta kusamu naku ba karya domin bama cika Baki kugwada kubada labari da bakunanku sabulu daya tamkar dubu wadandama basasan using cream sabulun mg's herbal whitening black soap yawadacemuku jikinku zaiyi kyau koyaushe kukasance clean cikin kamshi Kuna glowing koda bakusa turare ba🤗 Kayanmu bana bleaching bn organic ne sunagyarajiki fiye da tsammaninku zaifiddomuku da ainihin natural beauty dinkine Wanda yagwada shi zaitabbar amare kuyi kokari kumallaki mg's domin baruwanku da zuwa adirjemuku jiki zakuga yanda fatarku zata dinga walwali Ina masu pimples Tabo(spot) Sunburn dama dukwani matsalar fata kuyi kokari kunemi soap dinnan before 2weeks zaisharemuku hawaye kuzama abun kwatance Sister's masu nankarwa kuma kunemi soap dinnan Yana rage nankarwa sosai🧖🏻‍♀️duk me shakku tayi kokari tagwada mg's insha Allah bazakiso rabuwa dashi ba Akwai maisa haske Amma kayanmu nafada bana bleaching bn zaifiddomiki d ainihin halittarkine yagoge dukkan dattin jiki Akwai Kuma Wanda zaimiki maintaining skin dinki yasaki fresh fatanki tazama kalar hutu Sannan munada beauty kit🤗duk me bukatan (flawless skin/perfect glow) toh yy kokari yamallaki set dinnan wn zncn baa mgn🧚🏻‍♀️cuz duk inda kayi se ankalleka😀 Buh gsky wnd besan yy haske karyayi using set din cuz gsky yn sa haske buh bn bleaching ne b zaidai murje fatane nd bring out that hidden beauty in you😍 Pls bamacika Baki you HV to try it and see for yourself 100%tested nd trusted Beauty kit:11k Soap price:3k Location:kaduna buh munaturawa ko Ina Amma delivery is not free Maiso kindly message 08062991549 Call 08064532391 Note:Babu inda zakusami mg's herbal whitening black soap sai a number dinnan bairiga yakai market b inyakai we will let you know buh as for now wnn numbern ne kawai🙏 Maiso yahanzarta before yaji sold out akwaisu available now insunkare you HV to wait akawo so maiso yahanzarta🙏adade anayi sai gsky🤭🤝 Mg's skincare _________________________ *Page 48* ...........Lefe kam yayi sai dai makiyi ya kushe, dan daga na Momie harna Mahma sai dai ace ALLAH ya saka musu da alkairi, da AK yace sunyi yawa akai ɗaya Baffah cayay duka za'a kai, idan yay wasama shima sai ya haɗa nashi dole an haɗa an kai. Dole AK yay gum da bakinsa dan yaga waɗanan iyayen amaryar sai da lallaɓa.             Kamar yanda ake shiri gagarumi a shira's family da gayyatar dangi lungu da saƙo hakama su mmn sadiq suke nasu shirin, dan tuni Gwaggo Maryam ta iso kano sun ɗinke itada ƴar uwarta suna shawararsu, hakama Abba ba'a barsa a bayaba wajen gayyatar dangi da shirya yima Zinneerah kayan ɗaki duk da AK yace basai sunyi komaiba, dan koba shine ya auri zinneerah ba dole shine mai mata kayan ɗaki matsayinsa na babban yaya.          Lokacin daya ambata hakan murmushi kawai Abba yay da sanya masa albarka, a zuciyarsa yana mai jin daɗi da taya Zinneerah samun miji irinsa.    A danya ma baba shirinsa yake da ƴan uwansa batare da sanin Inna ba, dan Baffah da kansa ya kira Baban a waya ya sanar masa hukuncin da hajiya iya ta yanke akan tarewar, baba baiji komaiba yace ALLAH ya kaimu. Daga haka suka fara shirye-shirye.      Akan zuwan su mmn sadiq can kuwa har agama biki sun gama magana da Abba. Dan ana gobe tariya can zataje, danginsu na ɗanmusa ma acan zasu sameta, idan za'a ɗakko amarya washe gari su biyota zuwa kano insha ALLAH.      Zinneerah dai nacam nashan gyaran wajen hajiya falmata lungu da saƙo, ita kanta tasan ta gyaru sai dai Alhmdllh, har tsara yanda zataima su meenal yanga take a ranta tana murmushi. Sai dai kuma iya hasashenta ta rasa dalilin wannan gyara haka, duk da yanda hajiya falmata kan zauna tana mata lectures akan abinda ya shafi aure kan tsunduma zuciyarta a dogon tunani da nazari. Har takan tambayi kanta anya ba aure akai mataba kuwa?. Rashin samun amsa ke sakata jefar da tunanin ta kama wani daban.     A randa Zinneerah ke cika kwanaki shidda gidan hajiya Falmata aka kwashi akwatinan lefenta zuwa gidan Abba. kasancewar ansan da zuwansu sun sami tarba mai ƙyau duk da dai daga nan Danya zasu wuce. Sai da aka buɗe kaya Abba dasu Mmn halima suka gani. Su mmn sakina ma dai sun shiga layin ƴan kallo suna haɗiyar zuciya, daga ƙarshe suna shiga ɗaki Sakina harda kukanta rurus. Ita kanta maman tasu kukan zucin take wanda yafi na fili ciwo dacin rai.          Maƙwafta sun shishshigo suma suka sanya albarka kafin masu binsu Danya su kammala shiri su sake ɗunguma domin kaiwa can. Dole badan mmn sakina tasoba akai tafiyar da ita, itako mmn halima da yaranta biyu ai sune ƴan gaba-gaba, sai maƙwafta da ake gaisawar mutunci da matar Nazifi da suma za'aje dasu.      A ƴan gidansu AK kuwa Mommy ce, sai Adilah data maƙale, sai Momie da Ummi, da su Aunty Khadija yaran Momie na farko su biyu. Sai matar Alhaji Yusif. Sai kuma mahaifiyar Dr Mahmud. Gaba ɗayansu dai mota huɗu sukayi harda ta kaya, suka tafi a jere gwanin sha'awa dan su Khalipha ne masu kaisun, karan farko da zaije tushen Zinneerah.        Anan ɗinma dai ansan da zuwansu, dan sai da safe baba yake sanarma Inna, amaryarsa kuwa tasani kusan kwana biyu, da itama akai aikin abincin baƙin a gidan Gwaggo Laritu harda Yaya Gajeje ma.      Ƙarfe ɗaya da wasu mintuna motocin su Khalipha suka shiga cikin garin Danya. Gidan maigari suka fara isa dan can su Haneef suka sani, daga can aka saka yaro musu rakkiya dan babu wanda yako fito a motama a cikin matan.       Cike gidan yake da ƴan uwa domin amsar lefe, dawowar su Gwaggo Laritu gidan kenan su Mommy suka iso, an musu tarba ta mutuntawa da girmamawa, inna dai shigowar waɗan nan ƴan gayun matama neman birkitata yayi. dan duk iya jarabarta sai gata tai muƙus sai kallo da idanu.         Gidan baba yasha gyara aƴan kwanakin nan, dan ɗakuna ya sake zubawa sabbi aka kuma siminte tsakar gidan tsaf, ga amaryar baba akwai tsafta dan tunda tazo gidan ya ƙara ɗaukar saiti. Musamman yau ma datai masa gyara na musamman ita da Sa'a. Dan jiya akai taron sunan Karima duk da dai baimayi wani armashiba. Sai uwar rigima da aka kwasa tsakanin dangin Babawo dana Inna. Saboda Babawo har yau baizoba yakumaƙi cewa komai, ita kuma idan an tambayeta sai tace bata masa komaiba.        A ƙarƙashin bishiyar gidan aka shimfiɗa musu tabarmi dansu sha iska, aka kawo musu lemuka da ruwan leda da su baba suka tanada domin su kawai. Ba ƙaramin daɗi su Mommy sukaji ba a yanda aka tarbesu da girmamawa da mutunci. Bayan anyi gaisuwa da tanbayar iyalan juna aka shigo da akwatunan da suka saka ƴan uwa fara callara guɗe-guɗen da suka nema jefa Inna a hauka. Dan duk yanda taso ta daure ta kasa sai gata ta shiga zage-zage.     Cikin mamaki da ɗaukarta mahaukaciya su Momie ke kallonta, yayinda su Gwaggo Laritu da sukasan hali basubi takantaba, sai maida hankali a murna da farin cikin Zinni tayi goshi da sukai, suna kuma yaddama Inna habaici akaikaice. Cikin ƙanƙanin lokaci gidan ya sake haukacewa da makwafta da yara ƴan kallo, dole aka maida su Mommy ɗaki dan suma su samu suyi salla. Su dai yanda mutan garin keta arerewa akan wannan lefe nasu sai abin ya ƙayatar dasu ainun, Adilah harda yin video dan ita kam wani ƙayatar da ita suke da sakata nishaɗi, sai washe baki take ranta fes.       A waje ma dai yanda mata ke gudun shigowa gidan da yara sai abin ya dinga saka su Khalipha dariya, da birgesu. Dan suma suna zaune ne a ƙofar gidan a ƙarƙashin bishiya ni'imtacciyar iska na kaɗasu.      Haka suka kasance a ƙauyen danya suna kallon yanda ake kai kawo akan ganin lefe. Sai da sukai sallar la'asar sukai haramar baro garin cike da alkairi da tukuyci, duk da sunƙi amsa Baba yace indai basu rainaba su amsa dan ALLAH. Jin furucinsa yasa dole suka amsa suna mai yaba ƙoƙarinsa da dattako. Daga haka akai musu rakkiya suka shiga motoci suka ɗauka hanyar tafiya kano akan sai kuma ranar juma'a sunzo ɗaukar amaryarsu da zata iso zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu itama.          Koda suka taho a hanya labarin yanda al'amarin ya faru suketayi, dan sun baro Inna ta birkicema jama'a kamar sabuwar kamu a hauka. Duk da dai Yaya Gajeje da Karima na ƙoƙarin tausarta. Gida su mmn halima suka wuce, suma suka wuce nasu gidan inda suka kaima hajiya iya labarin farin ciki. AK na zaune a dining yana cin abinci shi da little yana jinsu, sai dai uffan bai tofaba bayan sannu da zuwa da yay musu.     Adilah ce tazo inda yake bakinta a washe ta sumbaci little da tunda tazo take maƙalle da yaron, cikin sabawa daya farayi da ita ta bashi nata kumatun shima yay mata kiss suna dariya. AK dake kallonsu yay ɗan murmushi kawai batare da yace komaiba.      Zama tayi tana fara bashi labari, tare da nuna masa video ɗin da tayo a waya. Shi kansa abin ya burgesa da bashi dariya. amma sai baiyiba yaɗan murmusa kawai yana ajiye wayar da dubanta cike da kulawa.       “Yaushe zakije ki gaida su Mammah?”.     A take fara'ar fuskarta ya ɓace, ta shagwaɓe fuska idanunta na cika da ƙwalla. “Bro ka barni Please basai najeba, kuma bama kace tana katsina ba tunda mukazo da Mahma?”.      “Kema ai katsinan zakije, gobe idan ALLAH ya kaimu zanje sai muje tare na baroki can ki biyo Mahma ranar biki”.            Hawayen da suka cika mata ido suka gangaro, sai kawai ta miƙe tabar dining ɗin ta shige ɗakin Hajiya iya. Binta yay da kallo kawai yana dariya a ransa. Dama tsokanarta kawai yakeyi, shima yaso zuwan amma Mahma ta hana, tace ya bari ai zata ɗakko su Mammah suzo wajen bikin dan dole suma dangin mahaifiyarsa su kasance ai tunda aure abin farin cikine ga kowacce zuri'a. Yanzu kuma Mammah ɗin kanta a zafi yake zuwansa bazai haifar da ɗa mai ido ba. _________________________________         A washe garin da aka kai lefe hajiya iya ta samu Zinneerah a gidan Hajiya Falmata ita da Adilah. Yanda Zinneerah ta ƙara canjawa a cikin sati ɗaya ya saka hajiya iya jin daɗi matuƙa, hakama Adilah da sau ɗaya kawai suka taɓa ganin juna a london rungume tayi dan tunda ta ga yarinyar dama ta shiga mata rai, da Hajiya iya ta bata labarin komai kuma shima AK ya bata sai ta ƙarajin tausayi da ƙaunar Zinneerah, tare da ƙara taya ɗan uwanta murnar samun mata dai-dai da shi da zata kawo ma rayuwarsa farin ciki tunda Farah taƙi kwantar da hankalinta ta daina biyema Mammah ta riƙe mijinta kamar yanda ta fara a farkon aurensu.      Daɗin yanda Zinneerah tai ƙyau mai ɗaukar hankali yasa hajiya iya harda ƙarama hajiya falmata kuɗi tana jera mata tagwayen godiya. Cike dajin daɗi itama hajiya falmata tace, “Ai hajiya namaso ace daga gidan nan sai gidan mijinta za'a kaita, amma hakanma babu laifi tare dani zata tafi can ƙauyen muɗan ƙarasa abubuwan da suka rage”.          Hajiya iya taji daɗin wannan karamci na hajiya falmata, dan duk da yanda Zinneerah ta canja kogi bayaƙin ƙari. Da wannan damar hajiya iya ta zauna ta sakema Zinneerah nasiha, a yau kuma ta sanar mata an ɗaura mata aure amma bata sanar mata da waye ba. Share-share sai ga Zinni na kuka da hawaye tana kallon haijiya tamkar wata sokuwa.      Cike da kulawa hajiya iya ta kamo hannunta cikin nata da sigar lallashi tace, “Nasan bamu ƙyauta mikiba Inno, amma insha ALLAH wannan shine gatan da zamuyi miki na har abada. Ki saka a ranki wannan itace taki nasarar cin jarabawar, insha ALLAH nasan bazakiyi kuka ba a wajen wanda muka baki, inamiki fatan alkairi da tarin farin ciki mai ɗorewa a rayuwarki da rayuwar aurenki”.      Kasa magana Zinneerah tayi sai kuka, ta faɗa jikin hajiya iya tana abinta. Itace kuma aka ɗaurama aure bayan taci alwashin bazata taɓa aureba. Gaskiya da anyi shawara da ita da haka bata kasanceba, batason tai aure a gorantama little, batason tai aure a aibantata akan ta taɓa haihuwa a waje. Bata da burin daya wuce yin karatu mai zurfi a rayuwarta, sai dai kuma duk waɗanan burikan nata da farga basu kai daraja da kimar hajiya iya ba a wajenta. Ta cancanci sadaukar mata da komai kodan alkairinta a gareta. Takumayi imani hajiya iya bazata badata ga wanda zata cutuba insha ALLAH, dan haka zatai haƙuri tayi biyayya a gareta insha ALLAHU. Ashe shiyyasa mmn sadiq keta mata nasiha mai harshen damo ita da hajiya falmata.      Lallashinta sosai hajiya iya tayi da sake mata nasiha itama tana hawayen, dan dauriya dama kawai takeyi, amma harga ALLAH tana tsananin ƙaunar yarinyar, wannan kuma hukuncine na ALLAH mai saka soyayyar wani a zuciyar waninsa dominsa badan wani abu dake garesaba. Sannan ta sanar mata yau za'a kaita danya wajen babanta, daga can za'a ɗakkota insha ALLAH zuwa gidan mijinta.       Nanma dai Zinni tayi kuka dajin fargabar tunkarar garin nasu data baro bisa ga dalili mai ƙarfi, takumaji ɗokin zuwa taga babanta da akace ya dawo da ƴan uwanta kuma.        Hajiya iya na gidan har Zinneerah da hajiya falmata suka kammala shirinsu na tafiya, sai Saifudden da zai kaisu wanda ya iso gidan hajiya Falmatan daga baya ya samesu. ★★★★★        Koda suka baro gidan hajiya Falmata gidan mmn sadiq suka nufa domin ɗaukar Gwaggo Maryama, ai ko Zinneerah nayin arba da ita ta faɗa jikinta tana kukaama. Ta basu tausayi daga ita har maman sadiq, to amma wannan shine kawai gatan da zasuyima rayuwarta koda ace babu ransu ta dinga tunawa sun mata gata. Dan little ga mahaifinsa kawai zai kasance itama ta samu kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya. Lallashinta suka sake zamanyi da mata nasiha, kafin Gwaggo Maryama ta shirya su fito dan da ita zasu wuce danya kafin su Mmn sadiq su biyosu suma daga baya.        Tunda suka ɗauki hanya Saifudden ne kawai ke hira da hajiya falmata da Gwaggo Maryama, itako tayi shiru lafe cikin kujera idanunta a lumshe. Kasancewar tafiyar ba ita kaɗai bace sai taji fargabar tunkarar danyan ta ragu mata a zuciya. Har suka iso gidan mutun ɗaya suka ɗauka hanyar kusada bata buɗe idoba. Sai da taji sun hau hanyar Danya ta buɗe idanu da kallon hanya cike da kewar garinta da tunano abubuwa masu yawan gaske da suka gudana. Isowarsu cikin garin yasa zuciyarta karyewa, sai gata tana hawaye shaɓe-shaɓe.      Zuwa yanzu kam ƴan Danya sun saba ganin yawan shigowar waɗanan manyan motoci, dan haka kai tsaye aka fara ƴan ƙananun maganar cewar angon Zinneerah ne yazo.               Su Zinneerah dai basusan anaiba, dan motar na tsayawa a ƙofar gidansu daya sha gyaran biki da aketa shirye-shiye sai zuciyarta ta ƙara karyewa. Itace ƙarshen fitowa jiki a sanyaye, sai da ta ƙarema anguwar tasu kallo da yara da suka baibaye motar waɗanda takeda tabbacin babu wanda ya shaidata, wasuma basu santaba. Murmushi tayi a karo na farko da ambaton Alhmdllhi cikin matuƙar rauni.        Da sauri ta buɗe idanun nata saboda jin maganar baba dake fitowa yanama Saifudden sannu da zuwa. Juyawa tai a hankali ƙirjinta na harbawa da sauri-sauri. Shima baban tunda idanunsa suka sauka akanta dukkan maganar bakinsa ta gagara fita. Yay tsai yana kallonta zuciyarsa fal wasiwasi. Tabbas fuskarnan dai ta ɗiyarsace, kuma irinta tsohuwar matarsa mafi soyuwa a garesa. Sai dai kuma yana tantama ace Zinneerah ɗinsa ce ta zama budurwa haka tamkar wata jinin larabawa. (Dan gyaran datasha ya sake ƙawatata da ƙyawu mai ɗaukar hankali)      A wani irin slowly Zinneerah ta nufi baba, batama san ta faɗa masa a jikiba ta fashe da kuka ba. Hakan yayi dai-dai da isowar Tinene ƙofar gidan wadda tun ɗazun aka aiketa amma sai yanzu take dawowa gidan, dan yanzu bata samun damar fita yawonta saita hanyar aikan.        Da mamaki take kallon wadda ke runme musu da baba, dan haka cikin sassarfa ta nufi cikin gidan kai rahoto. A zabure Inna data gama yima yarinyar karima wanka ta miƙe, hakama Sa'a dake wanke-wanke. Karima ma madai da Yaya Atine dake a cikin ɗaki sai gasu waje wuff babu shiri. Yaya Gajeje dake can gaban murhu ita da ɗiyar Baba Sabi'u suna suyar naman ragon sunan Karima suma dai duk duban Tinenen sukai, amaryar baba dai datasan ina zancen ya dosa tana ƙofar ɗaki zaune tana gyaran ƙumba da tsohon cikinta, murmushi kawai tayi hankali kwance. Kafin bakin wani ya samu damar furta kanzil sai ga baba ya shigo baki washe yana sharar ƙwalla, hannunsa riƙe da Zinneerah dake kuka rurus. Hajiya Falmata da Gwaggo Maryama biye dasu suna faman murmushin jin daɗi.             Yaya Gajeje ce ALLAH ya bama ikon gane Zinneerah, a take ta saki ludayin hannunta tana ƙwalalo idanu waje da faɗin, “Zinneerah!!”.       Da gudu Zinneerah ta saki hannun Baba tai kan Yaya Gajeje. Bata damu da a yanda yaya Gajejen takeba ta faɗa jikinta suka saki kuka tare. Tuni Sa'a ta saki soson wanke-wanke itama tayo kansu. Su kansu su Yaya Atine da ba ƙaunar Zinneerah ɗin sukeba, kuma tunda aka kawo kayan lefen nan nata ƙiri-ƙiri suka nuna hassadarsu suda Inna basu san sanda suka nufo ƴar uwar tasuba suka haɗu wajen rungumeta.      Hakan da sukai ya matuƙar saka baba jin daɗi, yayinda Inna ta daka musu wata irin gigitacciyar tsawa. Sai dai ina su bama susan tanaiba. Amaryar baba kuwa tashi tai da ƙyar tanama su Gwaggo Maryama barka da zuwa, waɗanda sai yanzu Inna tama gansu. Gabanta ne yay matuƙar faɗuwa datai tozali da fuskar Gwaggo Maryama, dan sarai ta ganeta. A kiɗime tace, “Dangin Hauwa a gidana?”. Karaf kuwa sai a kunnen baba. Kansa tsaye yace, “Hauwarma tana nan tafe a gidan naki”. Ya raɓata ya wuce abinsa dan tabarma zai amsa ya kaima Saifudden.        Ba ƙaramin dukan ƙirjinta furucinsa yayba. Tai baya tana neman faɗuwa ALLAH ya taimaketa ta dafe bango. Babu wanda ya lura da halin da take ciki dansu ta murnar ganin ƴar uwarsu sukeyi.      “Zinneerah kece kika koma haka kamar wata ƴar ƙasar waje?”. Yaya Gajeje ta faɗa tana sharema Zinneerah hawayenta, itako murmushi kawai take ga hawaye shaɓe-shaɓe.       Sa'a dake riƙe da hannunta tace, “ALLAH na gode maka daka nunamin wannan rana da naketa mahwalki da fatan gani, nagodema UBANGIJI daya maido ƴar uwata gida cikin kamala da mutunci harda igiyar aure akanta”.     Yanda take maganar da kuka ya sake raunana zuciyar Zinneerah dasu Gwaggo Maryama da amaryar baba ta sama tabarma a ɗakinta, dan suna jiyosu. Sake faɗawa jikin Sa'a Zinneerah tayi tana sakin wani sabon kukan.     Sai a lokacin baba daya dawo ɗaukama Saifudden buta zaiyi alwala yay sallar la'asar ya ɗauka hanyar komawa ya lura da halin suma da Inna ke ciki. Sallallami ya fara da nufarta, a take suma hankalinsu ya dawo kanta duk suka juya. Ita Zinneerah ma sai yanzu idanunta sukaga Innar.      Ruwa aka yayyafa mata ta farfaɗo, tana buɗe idanu sai akan Zinneerah, ai sai kawai ta fashe da kukan daya bama kowa mamaki da tsoro a wajen. Tashi Baba yay abinsa ya ɗauka butar data kawosa ya fice.         Zinneerah ta matsa jikin Inna tana hawaye da nufin rungumarta, hankaɗeta Inna tai cikin kuka da faɗa. “Munahika karki taɓeni, kinje kin gama yawon tazubar ɗinki zakizo ki goga mana ƙanjamau. To idan uwarki tayo asiri da rufe ido da bakin kowa akan hakan ni na gagareta, asirinta bazai ciniba. Nasan komai kina ikko kina karuwanci, shima shegen da aka ɗaura muku auren ƙaryar abokin cin mushenki ne. ALLAH ya wadatanki tambaɗaɗɗiyar yarinya gantalalla”.      “Kece gantalalliya, ni Sulaiman ban haifi gantalalliya ba”.     Baba ya bata amsa a fusace yana nunata da ɗan yatsa. Ya cigaba da faɗin, “Wlhy kika ƙara aibantamin ɗiya koda da furucin bakine saikin bar gidan nan, bari kuma nahar abada tunda ke bakisan ANNABI ya fakuba mara mutunci kawai.       Wani irin waro idanu Inna tai tana kallon baba, cikin rawar baki tace, “Malam ni kake cewa zan bar maka gida akan Zinni?”.      “Da giduma kuwa, harda jan kati”. Da sauri Zinneerah ta shiga girgiza kanta tana hawaye. “Baba dan ALLAH kayi haƙuri ka daina faɗi, Inna uwace a gareni, komai ta faɗa a kaina ba laifi bane”.          Baba ya buɗe baki zai bama Zinneerah amsa Gwaggo Laritu da Tinene taje kaima rahoto ta shigo gidan. Zinneerah na ganinta ta miƙe da gudu tai kanta. Sai kuma gasu baba Rabilu suma harda ƴaƴansu. Cikin ƙanƙanin lokaci gidafa ya haukace da sabon murna. Makwafta nata shigowa  ganin Zinni. Kafin kace mi zance ya fara yawo amarya Zinneerah tazo kamar an sata a injin gyara mutane ta koma balarabiya.       Haramin da gidan ya ɗauka yasaka kowa mantawa da wata Inna. Har Saifudden ma ya wuce su Gwaggo Maryam basu saniba. Aiko dai a wannan rana Zinneerah bata iya ta samu kantaba har dare, sai can kusan goma yaya Gajeje ta janyeta ɗaki ta bata abinci taɗanci. Daga haka aka zaman sake kafa sabuwar hira dan har zu baba Sabi'u suna gidan har lokacin basu tafiba. Zinneerah ta basu labarin daya sakasu kuka sosai dan tausayi.       Suka shiga godema ALLAH daya saka Zinneerah faɗawa a hannun nagari har ya sadata da mahaifiyarta. Wannan rahamarsace da jin ƙansa ba wayo ko dabarar waninsu ba. Sun kuma tabbatar a katsina aka lalatama Zinneerah rayuwa itama bada sanintaba, saboda a yanda ta basu labarin zuwanta. Inna nata zaginta da tsinarta akan ta mata sharri ita ƙarya Zinneerah tai mata akan cewar itace tasa tabi hajji lanti. Babu wanda yace da ita uffan akan hakan kaf ɗinsu.       Itama Zinneerah tayi kuka jin labarin yanda baba ya kasance, amma tayi farin cikin ƙara aurensa wanda yasa Inna ji kamar ta kasheta, sai dai babu damar yin magana baba ya kafa sharaɗi. Yanda kuwa yayin ta tabbatar zai iya sakin nata akan Zinneerah. Shiyyasa tai gum da bakinta tana binsu da ido, lokaci-lokaci takan fakaici ido ta share hawaye. Dan ga abin faɗa fal a bakinta amma babu damar faɗin sai tsinar Zinneerah dai take kawai.      Murnar dawowar Zinneerah yasa yaya Gajeje kwana a gidan, acewartama sai biki ya tashi kuma kenan. Aiko kusan kwana sukai hira da Zinneerah dan ɗaki ɗaya suka kwana. Hajiya Falmata nason cigaba da aikinta dole ta haƙura, sai dai ta bata abubuwan sha da abinda yake mai sauƙi da bazai takura Zinneerah zaman hira da ƴan uwantaba............✍       *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_*            *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* *Page 49* _________________________ Duk wacce batayi anfani da sabulunnan ba anbarta abaya acan karshen bayama kuwa duk Mai tantama akan sabulai nagyaranjiki cewa basa Aiki toh yacire mg's domin kankat ne insha Allah babu Wanda yayi anfani dasabulunmu yace baiyi ba koyaushe mg's sai sanbarka amare da uwargidaye hardama yanmata kuhanzarta kusamu naku ba karya domin bama cika Baki kugwada kubada labari da bakunanku sabulu daya tamkar dubu wadandama basasan using cream sabulun mg's herbal whitening black soap yawadacemuku jikinku zaiyi kyau koyaushe kukasance clean cikin kamshi Kuna glowing koda bakusa turare ba🤗 Kayanmu bana bleaching bn organic ne sunagyarajiki fiye da tsammaninku zaifiddomuku da ainihin natural beauty dinkine Wanda yagwada shi zaitabbar amare kuyi kokari kumallaki mg's domin baruwanku da zuwa adirjemuku jiki zakuga yanda fatarku zata dinga walwali Ina masu pimples Tabo(spot) Sunburn dama dukwani matsalar fata kuyi kokari kunemi soap dinnan before 2weeks zaisharemuku hawaye kuzama abun kwatance Sister's masu nankarwa kuma kunemi soap dinnan Yana rage nankarwa sosai🧖🏻‍♀️duk me shakku tayi kokari tagwada mg's insha Allah bazakiso rabuwa dashi ba Akwai maisa haske Amma kayanmu nafada bana bleaching bn zaifiddomiki d ainihin halittarkine yagoge dukkan dattin jiki Akwai Kuma Wanda zaimiki maintaining skin dinki yasaki fresh fatanki tazama kalar hutu Sannan munada beauty kit🤗duk me bukatan (flawless skin/perfect glow) toh yy kokari yamallaki set dinnan wn zncn baa mgn🧚🏻‍♀️cuz duk inda kayi se ankalleka😀 Buh gsky wnd besan yy haske karyayi using set din cuz gsky yn sa haske buh bn bleaching ne b zaidai murje fatane nd bring out that hidden beauty in you😍 Pls bamacika Baki you HV to try it and see for yourself 100%tested nd trusted Beauty kit:11k Soap price:3k Location:kaduna buh munaturawa ko Ina Amma delivery is not free Maiso kindly message 08062991549 Call 08064532391 Note:Babu inda zakusami mg's herbal whitening black soap sai a number dinnan bairiga yakai market b inyakai we will let you know buh as for now wnn numbern ne kawai🙏 Maiso yahanzarta before yaji sold out akwaisu available now insunkare you HV to wait akawo so maiso yahanzarta🙏adade anayi sai gsky🤭🤝 Mg's skincare _________________________ *Page 49* ...........Koda suka wayi gari lafiya ma da ƴan zuwa tabbatar da dawowar Zinneerah suka tashi, dan babu kunya mata keta shigowa da ƴammata da yara. Duk da abinda ya faru a baya yana a zukatansu kwarjini da cikar kamalar Zinneerah a yanzu ya hana bakinsu aibantata, dan dama wasu suna zuwane dalilin wancan abun daya faru bawai dan Zinneerah ta kasance zinari ba.       Itako duk da kasancewar ta miskila haka taita dauriyar musu murmushi da nuna kulawarta garesu babu wani wulaƙanci ko yarfi. A ranarma dai duk yanda taso samun kanta bai yuwuba, haka suka yini amsar baƙi da ƴan tsirku har yamma.      A ɓangaren Inna kuwa a ranar taso bazama wajen malamanta baba daya gama karantarta tsaf ya hanata fita, yama kafa mata sharaɗin har Zinneerah tabar Danya idan ta leƙa waje a bakin aurenta. Wannan al'amari ya mata ciwo, ta dinga zazzaga masifa da jidali masu shigowa na mata dariya. Yaran nata da su Gwaggo Maryama kuwa babu wanda yabi takanta. Garama Zinneerah takance “Kiyi haƙuri Inna”. Aiko wannan kalmar haƙuri na mata zafi a rai fiye da masu mata shiru. Itako Zinneerah har cikin ranta batajin daɗin ganin yanda Innar ta koma kamar wata zararriya.      Da daddare aka buɗe mata kayan lefenta ta gani ita dasu Gwaggo Maryama, abin ya bata mamaki sosai, ta kuma jinjina ƙoƙarin su hajiya iya. Suna gama ganin kaya Hajiya Falmata ta jata ɗakin da tasa aka ware musu ta ɗora aikinta daga inda ta tsaya gudun karsu cigaba da cinye lokacin a banza.      Washe gari tun kusan gabannin azhar aka fara karɓar baƙuncin dangin Mmn Sadiq na ɗan-musa a danya. Hakan ya ƙara tabbatarma Inna lallai bikin na gaskene ba wasa ba. Sai kawai ta zauna ta fara kuka rirus ƴaƴanta na lallashinta. Tinene kuwa dariya taita kwasa dan itako ko'a jikinta. Tama nanema Zinneerah ne kamar basuke zuba faɗaba a baya.          Bayan la'asar itama mmn sadiq ɗin sai gata da tawagar ƴan kano. Gida ko ya sake haukacewa da murna. Ita da Inna suka shiga kallon kallo. Mmn sadiq na ganin tsufan inna da komawarta kamar wata zararriya. Inna na kallon komawar mmn sadiq ɗanya shataf ga ƙyau dajin daɗi da kwanciyar hankali tattare da ita.     Cikin rashin damuwa da yanda Innar ta tarbesu Mmn sadiq tashiga gaisheta. Banza Inna tai mata dan idan tai magana to lallai bazata zama mai daɗiba. Fitar mara daɗin kuma shine zai zama tabbatar sharaɗin baba a gareta. Haka kawai yasata zaɓar yin shiru, amma tana ƙullama zuciyarta abinda zata aikata musu wanda sai sunyi nadamar dawowa cikin rayuwarta su dukansu.       Duk wani abinda mmn sadiq zata iya buƙata na abincin da ƴan uwanta zasuci da abinta tazo, hakan yasa suna isowa babu jimawa ta bada aka saya mata icce mai yawa, ta kuma ware kuɗin ruwa. Duk da abin yama baba ciwo baice mata komaiba, dan ganinta kawai sai da ya sakashi share ƙwalla, yanason Hauwa'u matuƙa, ƙaddarar iyakar zamace kawai ta shiga tsakanin su da sharrin Inna.       Tuni Zinneerah ta shige cikin dangin mahaifiyarta da suka nuna damuwarsu akanyi watsi da lamarinta sunata neman afuwarta. Ita dai nata murmushi ne da tabbatar musu babu damuwa. Daga haka aka shiga shagalin biki.          Batare da Zinneerah tasan da zuwan su Bahijja ba sai gasu suma kusan biyar na yamma driver ya kawosu, taji daɗi matuƙa dan sune dai ƙawayen dama. Garama isowar ƴan ɗan musa da sakina yasa taɗan samu ƙawaye, Tinene nata ɗari-ɗarin shiga cikinsu Zinneerah ta jawota tare da gabatar musu da ita.     Sukam babu ruwansu basusan wulakanta mutaneba, hankali kwance suka amsheta babu wani nuna ƙyama gareta ko makamancin hakan. *KANO*         A kano ma dai gidan hajiya iya ya ɗauki haramar dangi da abokan arziƙi, dan dole AK yabar gidanma gaba ɗaya ya koma nashi dayasha gyara inda za'a saka amarya dama Uwargidan kanta. Dan ya ƙullama Farah batare data san dawan garinba tanacan katsina suna jiran tsammani ita dasu Mammah.        Ƙiri-ƙiri AK yace bai yarda da wata dinner da shirme ba. Hajiya iya tasan kishinsa na tsiya, amma batai zaton zai nuna akan Zinneerah da aka aura masa babu neman shawara ba, dan duk da bikin Farah Mammah ta nuna musu iko akansa haka ya hana yin kowacce bidi'a. Ba kuma komai yasa hakaba sai kishi, dan AK nada matuƙar kishi gaskiya abin a jininsu yake kam da gaske.       Amma duk da haka dai an shirya walima da liyafar cin abincin rana, dan Baffah yace bazasuyi biki lami ba, Khalipha kuma da su Huzaifa suka shirya fati iyakar su mazan kawai dan gayyato abokan AK na kasuwa dana makaranta sukai sosai batare daya sani ba.         Abin mamaki kuma sai ga Uncle Ahmad da iyalansa babu zato babu tsammani, sai baffah da AK ne kawai suka san da zuwansu. A take gidan ya ƙara harmutsewa da farin ciki, babu wanda yabi takan matarsa daketa faman yatsine-yatsine, ƴaƴanshi kuwa dake a ɗarare saboda rashin sanin dangi AK ya musu jan ido tunda shi ba baƙonsu bane. Aiko sai gasu sun saki jiki a cikin su Saifudden.        Hajiya iya kuwa duk da haushin uncle Ahmad ɗin da takeji saita daure ta danne komai dake ranta ta tarbesu da farin ciki da ƙewa. Uncle Ahmad ya rungumeta yana hawaye itama tanayin nata. Daga ƙarshe dai su Mommy suka lallashesu akan suyi haƙuri.            *KATSINA*        Ta wajen su Mammah kuwa yau Farah ta haɗa kayanta tunda safe tace zata wuce kano sabida cimata ƙaniya da Mahma tayi a ɓoye a daren jiya, ta kuma nusar da ita inhar bata daina biyema Mammah da aunty Zakiyya ba to wlhy ƙwaɓarta na gab dayin ruwa. Dan AK zai iya ɗagama mahaifiyarsa ƙafa kodan kasancewarta uwa a garesa amma ita wahala zatasha, ƙarshema ta ƙare da saki idan bata maida hankalinta jikintaba.      Kalmar sakin nan itace ta rikitata tun a daren ta shiga kiran AK amma yaƙi yin picking call ɗinta, daga ƙarshema ya kashe wayan duka. Wannan ruɗanin ya sata shiryawa da farar safiya tace itafa sai kano.     Masifa Mammah da Aunty Zakiyya suka shiga mata akan hakan amma taƙi saurarensu tace suyi haƙuri itadai zataje ƙilama ta samo amsoshin da suke zaman jiran nema ga wanda ke musu bincike. Ba ƙaramin haushi abin ya basuba, musamman ma aunty Zakiyya data nuna har a fuskarta, sai dai tai shiru bata faɗi abinda ke bakintaba saboda wani dalilinta.      Lallaɓa Farah Mammah tasoyi. Ta kamota jikinta cikin lallashi take faɗin, “Haba Farah, kinsan dai komi muke akanki mukeyinsa, bakuma zamuyi abinda zai cuta miki ba. Indai Abdul-Mutallab ne zaiyi fushinsane ya gama ma ya dawo lallaɓaki da kansa. Ni banason ne dangin ubansa su maidaki kamar wata mara gata shiyyasa kikega ina haƙilon nan. Dagani harke taimakon juna mukeyi, banason rasa Abdul-Mutallab a rayuwata, kema kuma nasan bazakiso ki rasashi ba ai. Kuma wannan sakacin namu shi zaisa ya suɓuce mana ɗin dan wannan kakar tasu da Kabeer kansu kawai suka sani, sosuke su rabani da shi”.       Cikin rashin damuwa Farah tace, “Amma Mammah sai nake ganin kamar bata hanyar da mukebi zamu iya maidoshi garemuba. Kinsan dai yanada taurin kai, garama ki bari na kasance a kusa da shi maybe naji komai dake faruwa sai mu magance cikin sauƙi”.       Wani alama Mahma taima Farah da ido tana sakin murmushi da ɗauke kanta gefe kamar batasan sunayi ba.      Cike da masifa Aunty Zakiyya tace, “Mammah dan ALLAH barta taje, itace zatasha wahala a hannunsu ai bawani shege ba, su dangin miji har wani abin kwantarwa kai ne. Wlhy banason dangin miji bakuma zan taɓa sonsuba musamman irin naki. Kina dai ganin duk sadaukarwa da Mammah tayi ta bar karatunta da ƙasar data tashi a ciki ta biyo Abbansa daga ƙarshe mata har uku ya aure sai kace wani bazazzage (zazzagawa😂😜🙏🏻), mi ake da namiji mai shegen aure-aure. Kema idan kikai wasa haka kakarsu zatasa Abdul-Mutallab ɗin yayta aure-aure shiyyasa mukeson baki kariya tunkan faruwar hakan amma kina neman watsa mana ƙasa a ido”.       Wani irin tuƙukin bakin cikine da kishi ya tasoma Farah, a take tsanar da Mahma ta fara rage mata nasu Hajiya Iya ta ƙara dawo mata sabo, ganin yanda ta fara nutsuwa da maganar aunty Zakiyya yasa Mahma saurin tsoma musu baki.       Nikuwa da zakuji dakun barta ta tafi ɗin, ta hakanne kawai zamusan mike faruwa? Sannan muji ta tushiyar da aka samar da yaro, tun farkoma da haka kukayi da an wuce wajen, dan irinsu Abdul-Mutallab kwantar da kai sukafi so ga matansu ba shirme da hayaniya ba. Yanda yakeson Farah data lallami kuka bisa ko kuka sakata tabisa ita da kun kamo bakin zaren. Su kuma danginsa wannan kauɗin da kuke sakata tana musu shi zaisa su sakashi ƙara auren dan zasuga tanada ƙarancin tarbiya, tun farko data bisu a yanda sukeso da bahaka ba, kudaiyi tunani gaskiya”.         Zaram Farah ta miƙe tana faɗin, “Mahma maganarki gaskiyace wlhy, ni dai kuyi haƙuri Mammah bara naje, duk halin da ake ciki zakunaji ta waya insha ALLAH ”.     Daga haka bata saurari cewarsuba ta fice abinta dan Mahma ma tama driver dazai kaita magana.     Daga aunty Zakiyya har Mammah sun shaƙa, sai dai yanda Mahma ta haɗe gabas da yamma yasasu kasa cewa komai. Sunaji motar data ɗauka Farah ta wuce badan sunso ba.      Tafiyar Farah kano da kusan awa shidda wanda suka saka ya musu bincike ya iso gidan. Ko gaisuwar kirki basu bari sunyi dashi ba suka fara jera masa tambayoyi akan aikin da suka bashi. Sanin halin aunty Zakiyya yasa baice komaiba ya miƙa musu takardun hannunsa.       Mahma data fahimci komai zai iya faruwa ta dakatar da Mahma daga bude envelope ɗin, “Nikam da kun sallamesa ya wuce sannan zaifi”.     Babu musu Mammah ta miƙe ta ɗakko masa sauran kuɗin aikinsa ta bashi, yaji daɗin haka kuwa ya tafi yana musu godiya, dan ya tabbatar da ace sai da suka duba babu abinda zai samu.          Aunty Zakiyya ce ta fara cin karo da invitation ɗin walima da za'ai jibi idan ALLAH ya kaimu da liyafar cin abinci, jikinta har rawa yake wajen miƙama Mammah. Itama da taci karo da hoton Zinneerah da AK a take ta miƙe cikin rawar jiki tana kallon invitation ɗin. Wani shegen ashar ta kwaso ta dire akan Baffah.      Mahma da dariya ke neman kufce mata tai saurin riƙo hannunta tana girgiza mata kai ganin ta doshi ƙofar fita. “Hindatu ki nutsu mana, faɗamin mike faruwa?”.      “Ai komaima ya faru Addah, ni Kabeer zai rainama hankali, yasan mi yake ƙullawa akan Abdul-Mutallab shiyyasa yace muyi game. Na rantse da ALLAH sai na nunama guy ɗin nan asalin color ɗina. Na shiga uku shikenan ya ƙwacemin yarana. Wlhy bazan bashiba ko sama da ƙasa zai haɗe......”       “A'a bama sai sama da ƙasa ya haɗeba kwantar da hankalinki”. Mahma ta faɗa tana zaunar da ita a kujera. Amma ina Mammah zillewa take tana botsewa hawaye fal fuskarta wasu na korar wasu. Sai masifa take tamkar zata haɗe harshenta. Tana ta rantsuwar saita maka Baffah kotu akan ƴaƴanta dan bazata yarda ya rabata dasuba. Kuma auren AK ta rantse saita rabashi da Farah kawai zai rayu.     Aunty Zakiyya ma masifa take iyakar iyawa. Sai dai ita Mahma batabi takantaba dan nata mai sauƙine. Da ƙyar Mahma ta samu ta taushi Mammah akan ta bari sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu suje Kano ɗin suyi nagana da Baffah. Sanin Baffah na matuƙar ganin girma dajin maganar Mahma yasa ta haƙura akan sai zuwa goben, sai dai tanata neman no ɗin AK a kashe, dan dama Mahma ta sakashi ya kashe wayar, baƙon na zuwa ta turama AK text message. ___________★       A kano kam lafiya lau Farah suka isa. Kasancewar dama shirine tsakanin AK da Mahma kai tsaye gidansa aka wuce da Farah ɗin. Taji daɗin hakan dan bata ƙaunar zuwa family house ɗinsu dama. Ta gwammaci suyi zamansu nan su biyu hartaji gaskiyar zance akan little. Dan ba ƙaramin yaƙi zatai da zuciyartaba wajen bin shawarar Mahma akan ta kwantar da hankalinta wajen AK.       Shiko AK duk da abinda tai masa naƙin bin umarninsa datai ta koma haka ya danne yay mata tarba data bata mamaki. Daga ƙarshema suka shiga duniyar soyayya. Biye masa tayi da ƙoƙarin danne damuwarta, amma duk da haka sai da ta tambayesa ina ya samu gida?.      Murmushi kawai yay mata da kissing goshinta, a AK ɗinsa data sani mai tattalinta da bata kulawa ya amsa mata da cewar, “Gidanki ne da baƙyason zuwa, ina fata dai komai ya miki?”.        Fuska taɗan ɓata tana gyara kwanciya a jikinsa, “My hero ko yamin miye amfaninsa tunda ba zama cikinsa zanyiba, dama ka sayar kayi wani hidimar da kuɗinka danni nanda sati gudama zan koma london”.      Wani shegen murmushi ya sakar mata da kashe mata ido ɗaya, yace, “Yayi Mrs Shira, nifa shiyyasa kike matuƙar birgeni”.      Yanda yay mata ɗin ya sakata nishaɗi ta ƙara ƙanƙamesa tana dariya. Da ga haka suka sake komawa duniyar masoya ƙasan ran kowa da abinda ya damesa, sai dai sunata ƙoƙarin ɓoyema junansu bisa mabanbanta dalilai.          Washe gari tunda safe AK yabar gidan bayan Khalipha da kansa yazo ya kawo musu breakfast, lokacin ma Farah nashan barcin gajiyar murzar juna da sukai jiya, shima sai note ya bar mata suka fice tare da Khalipha. *_DANYA_*       A Danya shagalin biki ake na gaske, dan dangin mmn sadiq har safiyar yau zuwa sukeyi, hakama abokan arziƙinta na nan danya sunta zuwa mata baici duk da zuwa yanzu ta wuce da saninsu. Kusan goma na safe sai ga dj da kayan kiɗa dasu Haneef, dama sun haɗa ɗan meeting nasu zasuzo Danya su cashe tunda Yayansu ya hanasu a kano, su dukansu suka taho har Adilah da ƴaƴan Uncle Ahmad da zuwa yau dai sun zama ƴan gari kodan halin su Haneef na barkwanci.     Sosai isowarsu da dj ya karama bikin armashi, dan a take suka warware sauti biki ya ɗau harama ƴan danya suka ƙara shaidawa. Dan su Meenal da ƴan ɗan musa filin rawa suka shi su Moos'ab suka dinga zazzaga musu liƙi. Yaran gari dana dj na daka wawa. Al'amarin kamar wasa saiga biki yayi armashi, dan ita Zinneerah harma ta faraji a ranta ko Moos'ab ɗin aka aura matane.     Tayi ƙyau cikin less lemon green da ratsin orange, Meenal ta tsara mata kwalliya ta fito ɗas a amaryarta abin shawa da birgewa. Gyaran da tasha yana nuna kansa a fartarta da ƙamshinta da duk inda ta zauna sai ya cika waje. Ga lalle tasha a daren jiya da yay matuƙar mata ƙyau. Badan tasoba Jamal ya jata har tsakkiyar fili inda su Saifudden suka rufeta da liƙin ƴan ɗari bibbiyu sabbi ƙal. Ai sai bama tasan lokacin data fashe da kuka ba bisa dalilai masu yawa. Hakan da sukai yasa yaya gajeje ma zuwa ta farama Zinneerah liƙin ƴan hamsin-hamsin tana hawayen daɗi, sai ga Sa'a da chewing gum da sweet itama data siya ta fara zazzagesu akan Zinneerah. Aifa sai guri yaɗau ihu da sowa dan sun burge. Gwaggo maryama ma shigowa tai tayi nata liƙin, suma sai ga ƴan ɗan musa suna nuna tasu bajintar kowa dai-dai karfinsa. Wanima naira 100 zaizo ya liƙa mata ya fita.       Wannan al'amari ya ƙuntata zuciyar Inna matuƙa, har takai ta yanke jiki ta faɗi sai da akai kama-kama wajen kaita ɗakinta. Sai Karima da Atine da Tinene da nunkufurci kecin ransu suka zauna da ita a ɗaki suna zage-zage wai da biyu su maman sadiq sukazo suka kafa bikin ai dama a danya. Duk da wasu a ƴan uwan mmn sadiq ɗin sunji sai basu kulasuba. Dan tunkan su taho an roƙesu kosunzo dan ALLAH karsu shiga sabgar Inna Asabe komi zatayi, dan su dai farin cikine ya kaisu suje ayi a tashi lafiya a miƙa amarya ɗakinta. Da wannan yasa suka sharesu.     Su Yaya Gajeje kuwa basusan mike faruwaba suna can anashan dj dasu a waje hankali kwance.      Shagali kam dai an shasa sai dai ace Alhamdulillahi, Zinneerah tayi kukan daɗi, tayi na damuwa, tayi na godiya ga ALLAH, ansha hotuna kuma da mai hoto dasu Mas'ood sukazo dashi, zuwa ƙarfe huɗu kuma sai ga motsocin ɗaukar amarya sunzo.      Kasancewar Zinneerah tasha faɗa wajen iyaye da kakanni tun a daren jiya sai yazam yau sallama kawai aka kaita taima su baba da danginsa. har ɗakin Inna da sai yanzu kowa yasan da faɗuwarta, amma kasancewar ta farfaɗo hakan bai hana su Yaya Gajeje shirin raka ƙanwarsu ɗakintaba. Hardasu Karima mai jego kuwa dan sunce sai sunje sunga uwar da ake nusu fariyya da ita sukam.     Inna bata hanasuba, dan itama daga ƙarshe catai zataje duk da halin da take a ciki na alamar ciwo. Dan ko gani batayi daƙyau saboda jininta da ya hau sama ƙololuwa dan damuwa da ruɗanin tashin hankalin da take a ciki. Baba zai hanata Gwaggo Laritu tace ya barta. Ai gara taje ta gano komai da idanunta zaifi. Amma yace sam bazatajeba sai daga baya saje da amaryarsa idan ALLAH ya sauketa lafiya. Tamaji da kanta. Badan tasoba dole ta haƙura dan da gaske tana a cikin wani hali dannewa kawai takesonyi dan zuwa taga ƙwaƙwaf. Amma tunawa ga ƴaƴanta nan yasa ta haƙura ta shige ɗaki tana kukan da bataso kowa ya gani.        Tunda aka saka Zinneerah ta shirya bayan an ɗanƙara mata nasiha take rusar kuka da shiga tashin hankalin tunanin wanene mijin nata. Dan yanda Moos'ab ya nuna mata baiyi kama da miji a garetaba. Sai dai idan suna ɓoyewane har sai taje can ta gani. Kasancewar an turo motoci babu laifi kowa sai da ya samu wajen zama duk da wasu a matse suka tafi, ga kuma motocin ƴan ɗan musa suma sun sake taimakawa. dan a danya har ƴan gayyar soɗi dason ɗakko rahoto sai da sukabi.      Motar da baba ya kama amarya Zinneerah kuwa ya saka da hannunsa sabuwace dal a ledarta Baffah ya bada a ɗakkota ciki, ita da Gwaggo Laritu da wata Gwaggo Aisha ƴar ɗan musa suka shiga tana tsakkiya, Adilah na gaba kusa da Huzaifa da zai ja motar. Wasu a cikin baƙin ɗan musa zasu wucene gidan mmn sadiq sai zuwa gobe suje suga ɗakin amarya kafin su koma gida. Dan haka motocin ɗaukar amarya sun riga su mmn sadiq tafiya dan su sai da sukai zaman yin sallama da mutane da godiya ga baba sannan suka taho gab da magriba. Zuwa lokacin motocin ɗaukar amarya tuni sun isa cikin kano har Shira's house, inda Zinneerah keta kwasar kuka har suka iso gidan. Gidan da take zaune a cikinsa matsayin ƴa gata ta dawo a matsayin amarya.      Hajiya iya da kanta ta fito ta tarbi Innon ta bakinta kamar zai yage dan fara'a. Zinneerah ta faɗa jikinta tana sakin wani sabon kukan. Itama rungumeta tayi cike da farin ciki.       Ƴan kawo amaryama sun sami tarba ta mutunci da girmamawa. Inda aka saukesu a sashen Mommy dan sassan gidan duk cike suke da baƙi, hatta sashen Uncle Ahmad da matarsa keta baƙin rai sai da hajiya iya ta tura baƙi idanma mutuwa zatai ta mutu matsalartace cewar hajiya iya.      Zinneerah kuwa direct sashen hajiya iya aka nufa da ita. Baƙi kuwa aka sake karramasu da lafiyayyen abinci mai rai da lafiya. Aikam su kam warshan, dan babu wanda yayma kansa mugunta ci sukai sukai nak banda Tinene da ta faraci tahau amai.      Wannan abu ya bama kowa mamaki har aka shiga kallan kallo, amma gudun tada zaune tsaye Gwaggo Laritu da ke kallon tinene gabanta na faɗuwa ta janyeta gefe tana sanarmusu shawarace taima Tinene mugun kamu. Shiru dai kowa yayi badan baida abin faɗaba. Musamman ma su yaya Gajeje da tsoronsu ya fito ƙarara a fuskokinsu suna bin Tinenen da kallo.         Bikin mata ya cigaba da gudana a cikin gidan, dan sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu za'ai walima and liyafar cin abinci, su AK kuma bayan isha'i zasuyi fatin da su Huzaifa suka shirya wanda sai a yammacin yau yasan dashi. Faɗa yaytayi su Dr Mahmud na lallaɓashi, sai da yaji iyakar su mazane kawai ya sami nutsuwa ya sassauta masifar yana maida numfashi.          Dole badan yasoba yay shirin cikin ɗanyar shadda bayan sallar isha suka tafi hall ɗin da fatin zai gudana. bayan yama Farah dabara irin na maza akan zaije bikin wani abokinsa ne. Sanin baya zuwa irin waɗan nan abubuwan da ita saboda kishi yasa batako damuba...............✍ *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_*             *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* *Page 50* _________________________ _*MS TREATS*_ _(PALACE OF PERFUMERY & TRADITIONAL VARIETIES)_ _COME & EXPERIENCE EXCEPTIONAL SCENTS’  AND DELICACIES, YES WE ALSO CARTER TO SMALL & LARGE EVENTS._ _Turaren wuta irinsu_ _Smal halut_ _Sandal coconut _ _Janal banal _ _Arabian oud sandal bakhuor _ _Special kajiji _ _Sandal flake_ _Vip hawi _ _Sudanes sandal rose _ _Humra _ _White humra_ _Black humra _ _kulaccam _ _Dilka soap_ _Whitening soap _ _SPICES_ _Curry powder _ _Corriander powder _ _Tumeric powder _ _Mix spices _ _Ginger powder _ _Black pepper _ _White pepper _ _SNACKS_ _ _Samosa_ _Spring rolls _ _Meatpie _ _Cupcake _ _Birthday cake _ _Doughnut _ _Contact 07061106161 or 08099990056_ _address: bayan northwest university layin gidan ruwan dish_ _KANO, NIGERIA_ _________________________ *Page 50* ..........Soaai AK yayi mamaki matuƙa da ganin abokansa waɗandama shi kobi takansu bayayi yanzun, hakama abokan harkar business ɗinsa dake anan Nigeria. Dole dai ya ware ya shanye mamakinsa ya shiga basu hannu suna gaisawa da tayashi murna, tare da masa ƙorafin ba'a gayyacesu ɗaurin aureba sa fatin da babu amarya babu ƴammatan amarya balle Uwargida. Murmushi kawai yakeyi bai iya cewa komai dan baida abin faɗar.     Daga haka komai ya kasance a nutse cike kuma da birgewa. Dan abune na masu aji sam babu wata hayaniya. Anci ansha an sake taya ango da amarya murna da musu fatan alkairi, zuwa goma taro ya tashi lafiya kowa yana sam barka. Baƙi suka koma masaukinsu masu gidaje anan kano suka kama gabansu.      Sosai AK yaji daɗin fatin nasu kuwa. Dan koba komai ya haɗu da tsoffin abokansa da uzurorin rayuwa ya sashi mantawa dasu. Koda ya ɗan leƙa gidan nasu bayan sun tashi kasa zama yayi saboda hayaniyar ƴan biki, wai a hakanma wasu sunyi barci saboda gajiya, dole yayma su Baffah da Uncle Ahmad da suke nane da juna sallama ya gudo gida.        Lokacin daya shigo gidan Farah tayi barci, dan haka shima kayan jikinsa kawai ya zare yay wanka da neman makwanci saƙe-saƙe fal ransa. Musamman fargabar zuwan su Mammah gobe idan ALLAH ya kaimu da Mahma ta sanar masa. Sam bayason Mammah tazo ta tada hankalinta a cikin wannan taron mutanen ƴan biki, shiyyasa tun ɗazun abin ke damunsa da ƙyar yaketa faman tausar kansa.     Yau sukai niyyar tahowa Mahma ta sake lallaɓasu akan su zauna zaman shirya abubuwa yanda zasu iya tunkarar Baffah. Dan  sunyi aniyar tahowa su shiga garin danya da akace musu amarya take kafin su wuce kano. Hakan yasa Mahma kautar da hankalinsu har amarya ta isa ɗakinta lafiya sannan. Tasan dai idanma sunzo a gobe insha ALLAH aikin gama ya gama kuma.      _______________________★     Washe gari aka tashi da shirin gagarumar walima wadda daga ita kuma sai miƙa amarya Zinneerah ɗakin mijinta. Zinneerah data kwana a ɗakin AK ita da Adilah kuwa da zazzaɓi ta tashi, amma tanata daurewa dan har wasu ƴan sauran gyara da suka rage hajiya Falmata tai mata a daren. Tsabar gyaran data sha maranta har wani ciwo yakeyi mata. Haka dai ta cigaba da daurewa har hajiya Iya ta shigo ɗakin domin dubata. Dan Adilah dake fashin salla ma ko tashi a barci batayiba.        Sun gaisa da hajiya iya take tattaɓata ganin duk tayi wani iri, “Kai Inno ai zazzaɓi ne a jikin nan naki, haka kika kwana da shi ma ko?”.       Cikin ƴar shagwaɓar da suka sabama hajiya iyan ita dasu Jamal ta ɗaga mata kai idanunta na cika da ƙwalla. Sannu hajiya iya ta shiga jera mata, kafin ta taimaka mata shiga bayi dan ta samu tayi wanka. Koda tayo wankan ta samu ta shirya cikin atanfa sabuwa ƙal data amshi jikinta ɗas ta fito a amaryarta, Adilah kanta data farka sai yaba ƙyan datai takeyi, murmushi kawai Zinneerah keyi dan sosai take ganin girman Adilah ɗin kasancewarta ba ƙarama ba, sai dai kawai ALLAH ya bata ƙaramin jiki ga kuma yanayin inda ta tashi rayuwar turai, dan ita hausarma ba iyawa taiba tunda ba zuwa Nigeria ɗin Mammah take bari tayiba. Iya kacinta dasu magana da turanci, saiko AK dake iya jin yaren Mammah na larabci sukanyi, shiyyasa basa shiri da hajiya iya sosai saboda takaicin Adilah ɗin bata iya hausaba.      Tea hajiya iya ta kawo mata a sha da magani ta sake kwanciya kafin lokacin walimar. ★★★       A katsina kam ko breakfast ɗin arziƙi basuyi zaman yiba suka kamo hanyar kano, lokacin da suka iso gidan anata kwasar mutane zuwa ƙaton hall ɗin da za'a gudanar da walimar. Yanda anguwar ta rikice da kai kawon motoci masu kwasar mutane yasa dole su Mammah suka fakin tun a waje, Mahma ce kawai ke dauriyar gaisawa da mutane, amma Mammah da Aunty Zakiyya sunata shan ƙamshi.     Koda suka iso cikin gidan sun sami Baffah tare da baƙi, yana ko ganinsu yabar baƙin da uncle Ahmad ya nufosu fuskarsa ɗauke da murmushin daya sake fusata Mammah, aiko tayi kicin-kicin da rai tamkar zata fasa ihu. Sai dai batace komaiba bisa ga gargaɗin Mahma da sukasha.       Duk yanda Aunty Zakiyya taso nuna halin nata ga Baffah kasawa tai, dan wani irin kwarjini yay mata da cikar kamala. Dole tai ƙasa da kanta tana gaisheshi da girmamawa. Shima cike da fara'a ya amsa mata harda tsokanarta.      Yanda Mammah ta ɗauke kanta daga garesa haka shima yayi tamkar bai gantaba, cikin girmamawa yacema Mahma su shiga ciki. Murmushi tai masa, yay gaba suna binsa a baya har sashensa tacan baya da ƙofar falonsa ta ainahin bedroom ɗinsa take. Dan yasan acanne kawai babu wani hayaniyar mutane da hankalinsu zai kai kansu saboda wutar bala'i daya hanga a idanun Mammah.      Kafin su shige ya aika Jamal da sukaci karo ya sanarma hajiya iya zuwansu, daga nan ya wuce a haɗo abinci a kawo musu. Mammah zatai magana cikin masifa Mahma ta dakatar da ita da idanu, dole taja bakinta tai shiru tana haɗiyar zuciya.           Cikin ƙanƙanin lokaci hajiya iya ta ƙaraso tareda su Bahijja dake ɗauke da abinci, suna ajiyewa suka gaishesu suka fice. Mahma da aunty Zakiyya ne kawai suka gaida hajiya iya, Mammah kuwa sai da Mahma ta harareta sannan ta gaisheta da ƙyar. Hajiya iya bata damuba kam, dan ba yaune farauba.          Yanda hajiya iyan ta nuna rashin damuwarta ya ƙara zafar Mammah ta fara magana a ƙufule, “Kabeer  miye wannan ke nufi?”. Tai maganar tana ajiye masa invitation card a tsakkiyar centre table. Uncle Ahmad daya shigo falon ne ya ɗauka ya duba ya maida ya ajiye. Kasancewar shima ɗan zafin kan ne a gadarance yace mata “katin gayyatar walimar liyafar cin abincin auren gudan jininmu mana”.      Kallonsa tai rai a ɓace tana juya idanu, “Kai kuma bansa da kaiba mijin tace, kaji da taka matsalar kafin ka tsoma baki a ta wasu”.         “Hakan na nuna miki cewar wadda ta maidani mijin tace ɗin tafiki komai, tunda ke kin kasa maida Yayana mijin tace ɗin saboda ƙarancin ƙyaƙyƙyawan nazari da kishin hauka dake damunki. In banda abinki Hindatu tayaya kike tunanin raba ƴaƴa da mahaifinsu ta ƙarfin tsiya? Ke waya rabaki da naki har suka bar duniya”.          “Wlhy Ahmad ka kiyayeni, kasan na fika zafin kai”.     “Anƙi kiyayar taki, kiyi duk abinda zakiyi”.        “Zako kaga mizanyi ɗin, dan wlhy wannan auren kun ɗaura banza saina rabashi, in banda son zuciya taya yaro yana zamansa lafiya da matarsa zaku ƙaƙaba masa auren yarinya baƙauya mara galihu.........”        A fusace hajiya iya ta katseta da faɗin, “A rashin galihun nata shi ɗan naki ya gani yakeso, tunda har ya iyama yarinya ciki a waje ta haihu ita ƴar son naki bata haifaba. Hindatu ki kiyayeni wlhy, ina ɗaga miki ƙafa saboda ɗanki, amma inaga wannan karon saina fito miki a Amina ta, moddibo ne dai ya dawo gidansu kenan daga shi har ƴar uwarsa babu kuma yanda kika iya. idan buƙatar kasancewa kike dasu kema saiki dawo gidan ubansu ki zauna cikin kishiyoyin da kike gudu. Dan daga yau na yanke shawarar moddibo ya dawo ƙasarnan da zama kenan da iyalansa idan kin gansa a wata ƙasa sai dai yaje harkokinsa ko gaisheki ya dawo wlhy”.        Tsabar yanda zuciyar Mammah takai maƙura a hasala sai kawai ta fashe musu da kuka. “Wlhy bazan yardaba, bazan yarda a rabani da ƴaƴana ba tunda nice na haifi abuna bayan wahalar rainon cikinsu dana sha. Ita matar Ahmad data kwace miki shi miyasa kika kasa komai sai ni zakibi ki sama ido akan nawa ƴaƴ.......”       “Hindatu!!”. Baffah ya daka mata tsawa jikinsa har rawa yake na ɓacin rai. Murmushi hajiya iya tayi da ɗaga masa hannu. ta duba Mammah da ƙyau tana faɗin, “Itama ba ƙarfina tafi ba, kamar yanda kika ɗauke su moddibo muka barki yanzu kuma lokacin dawowarsu cikinmu yayi, itama lokacin da zan nuna mata nina haifi Ahmad ɗin yayi ai”.         “Wlhy ni kuma nayi alƙawarin yin amfani da ƙarfina na uwa wajen raba wannan auren, ɗa kuma da suka haifa a waje zaimin bayanine dalla-dalla dan ubansa”.       Ran Mahma da yay matuƙar ɓaci da abinda Mammah keyi bayan sai da ta ƙwaɓeta kafin su taho ta kama hannunta ta maidata ta zaunar a fusace. “Hindatu wai mike damun kanki? A ganina kamata yay ki nutsu ayi magana ta fahimta amma kinzo kinama mutane shirme. Kifa sani yanda kike da haƙƙi akansu Adilah haka shima mahaifinsu keda haƙƙi a kansu, yakumayi iya bakin ƙoƙarin sa wajen yimiki kawaici akansu, ai idan kinason yaranki su kasance dake basai ta hanyar ƙarfi da iko ba tunda suma sunsan ke uwa ce a garesu. maimakon ki damu dajin ta yanda akai Abdul-Mutallab ya samar da yarog yarinya a waje ke damuwarki kawai ƴaƴanki zasu suɓuce miki, haba wane kalar son kai ne wannan?”.     Kuka sosai Mammah keyi, tace, “Haba Addah kinajinfa yanda suka haɗa kai zasumin taron dangi, taya zasu ma yaro aure bada saninaba haka ake rayuwa?......”       “Ke sanda kikai masa aure bada saninmu ba wace gadarace baki manaba”.  Baffah ya katseta a fusace. Ransa a ƙololuwar ɓace ya cigaba da faɗin, “Hindatu idan kin manta bara na tuna miki, matar da Adnan ke aure karki manta sai ana gobe ɗaurin aurensa da ita kika faɗa mana, amma duk da rannmu ya ɓaci Inna ta tilasta mana haƙuri mu barki tunda aurene, yarinyar kuma ƴar uwarki ce. Haka muka danne zukatanmu muka amsheta a cikinmu da hannu bibbiyu amma ki ka ɗorata akan keken ɓera wajen nuna mata muɗin mutanen banza ne bama sonki da ƙaunarki, sai kuma a yanzu dan mun maimaita abinda kika aikata zakiji zafi? Ai dama na faɗa miki ƴaƴana sai sun dawo gareni tunda ke bakisan mutunciba, burinki kawai ki nisantasu dani da ƴan uwana to muzuba mu gani ɗan halak ka fasa ni da ke a garin nan”.      Mammah zata sake magana Mahma ta dakatar da ita da sauri. “Kuyi haƙuri Kabeer, tabbas Hindatu ta aikata laifi, amma inason ku fahimceta itama, kunsan a duk sanda mace ta rabu da uban ƴaƴanta babbar fargabarta shine barin masa ƴaƴanta wata tazo ta cuta musu koshi uban ya nisantasu da ita. Na tabbata wannan shine fargabar Hindatu tun a wancan lokaci da yanzu haka. Amma bawai hakan na nufin ina goya mata baya akan abinda takeyi nason ganin ita ta nisantasu da ku ba duk da kawaicin da kukai mata na tsayin shekaru. Ina son dan ALLAH a wannan gaɓar mu haɗu wajen yafema juna, mukuma fahimci juna dan mu duka munada ƙarfin iko akan Adilah da Abdul-Mutallab. Sai dai hakan ba yana nufin mu cigaba da raba hankalinsu ba da ƙarfin ikon da ALLAH ya bamu akansuba na iyaye”.      Tsit falon yayi dan maganar Mahma tayi tasiri a zukatansu sunkuma san gaskiya ta faɗa. Hakan yasa AK dake tsaye tun ɗazun daga bakin ƙofa ya ƙarasa shigiwa. Zama yay ya gaidasu batare da ya yarda ya haɗa ido da kowaba dan ransa a jagule yake babu daɗi.      Mahma ce ta dubesa da kulawa, “Abdul-Mutallab nasan duk kaji mike faruwa. Sai dai jin naka bashine mai muhimmanci ba, a yanzu mu munfi buƙatar son sanin a ina aka haihu a ragaya game da haihuwar yaro mai sunanka?”.         Iska yaɗan furzar kansa a ƙasa. “Mahma wlhy nima ban saniba”.     “Kamarya baka saniba, a ruwa ake shan ciki balle kace mana itama acan tasha?”. Aunty Zakiyya tai magana karon farko tun shigowarsu a hasale          “Tabbas ba'a sha, amma inaga itakam dai acan ta shashi. Dan ni dai ban taɓa tarayya da wata mace bayan matata ba ALLAH shine shaidata. Sannan ban taɓa ganin yarinyarnan da idanuna ba sai a gidan nan. Amma kuma tabbas na yarda Abdul-Mutallab ɗa nane, ina kuma kan binciken ta yadda aka samar dashi insha ALLAH”.       Shiru falon yayi tsahon lokaci, sai Uncle Ahmad da wani tunani yazo masa a zuciya dan shidai shedane akan AK bai iya ƙaryaba yace, “Abdul-Mutallab maganar nan ba wadda mutane zasu ɗauka bace balle su fahimceka. Amma sai nake tunanin ko kun taɓa yunƙurin yin wannan dashen na zamani da aketa nusar al'ummar musulmi rashin anfaninsa?”.       A karon farko AK ya ɗago ya duba Uncle ɗin nasa da rinannun idanunsa. Hakama Mammah da aunty Zakiyya a razane suka dubi Uncle Ahmad har hakan ya bama Mahma da Hajiya iya mamaki. Da sauri AK ya girgiza masa kansa. “Wlhy Uncle ni ban taɓa son hakanba dan bayama birgeni, na tabbatar idan ALLAH yaso zai bani, da bai baniba kuma ƙila haka shine mafi alkairi a gareni”.        Cikin jinjina kai Uncle Ahmad yace, “Na yarda da kai Adnan dan baka taɓa min ƙaryaba, sai dai wannan al'amarin na buƙatar bincike, musamman ga matarka kota taɓa wannan yunƙurin aka samu kuskuren ɗaukar sparm ɗinka aka saka ga ita yarinyar bada sanin ku ba ku duka tunda wannan matsalar kan faru saboda son zuciyar wasu likitocin, kokuma daga likitocin matsalar take baki ɗaya”.        Wani irin mugun tarine ya sarƙe aunty Zakiyya har sai da aka bata ruwa. Ita kanta Mammah sai zufa take gogewa a kaikaice. Cikin rawar murya tace, “Hakan bamai yuwuwa bane, tayaya za'ai yunƙurin hakan shi bada saninsa ba, kuma shi da ke a london yarinyar na ƙauyen katsina taya ya hakan zai faru, yadai zauna yayi tunani ko wani akasi ya taɓa faruwa”.        Hajiya iya da zuciyarta keta kaikawo da nazarin kowa a wajen tace, “Inaga to wannan maganar babbace gaskiya, mu ajiyeta a yanzu idan an gama biki lafiya saimu yita a tsanake, dan yanzu haka ga Huzaifa nata kirana kunsan ana jiranmu a wajen walimar can”.        Baffah da shi kansa tunanin zuciyarsa ya fara canjawa daga akalar zargin Ak da yake har yanzu zuwa zancen ɗan uwansa cikin gamsuwa yace, “Hakan shine dai-dai Inna”.       Tabbas a wannan gaɓar suma su Mammah sunfi buƙatar tsayawar zancen su sami dama da sararin yin nazari, dan haka duk suka amince. Sai dai basuso zuwa wajen walimarba Mahma ta takura musu akan saifa sunjeta dole ko shima AK ɗin zaiji sanyi a ransa ai.       Gudun zargin wani abu daban daga AK yasasu yarda zasuje. Dan ya tsatstsare su da idanunsa da gaba ɗaya suke a birkuce da abubuwa kala-kala da shima baisan adadinsu ba. ★★       Sun isa ƙaton hall ɗin da za'a gudanar da walima and liyafar cin abinci rana daya ƙawatu matuƙa. Ya kuma cika taf da al'ummar MANZON ALLAH (S.A.W). Ga manya manyan malamai da zasu gabatar da lectures. Sashin mata daban na maza daban babu ruwan wani da wani, hakkane ya samama AK nutsuwar da yake buƙatar samu. Suna isowa aka gabatar da addu'oi da suka shafi komai na rayuwa bayan ma'auratan, kafin a fara abinda ya tara mutane.      Malamai sun ragargaza lectures masu ratsa jiki akan aure da zamantakewar rayuwa data saka jikin mutane da yawa yin sanyi, Zinneerah amarya da duk da basan waye mijin nataba tasha kuka itama, lectures ɗin kuma sun shigeta matuƙa. Lokacin salla nayi aka fita akai sallar zuhur sannan aka dawo aka ɗora dacin abinci, a hakanma dai malamai na cigaba da aikinsu har zuwa la'asar da aka rufe da addu'oin fatan alkairi ga ma'aurata damu da muke a gidan auren sannan aka tashi.       Da yawan mutane daga nan suka fara kama gabansu, wasu kuma suka koma gidansu AK domin rakiyar amarya ɗakinta da za'ayi da wuri, duk da dai hajiya iya tace ƴan danya bazasu koma a yau ba kamar yanda suka sanar, tace su bari sai ALLAH ya kaimu gobe su da ƴan ɗan musa saisu tafi.        Sunkiji daɗin haka dan sam garin ba isarsu yayiba. Musamman da kowa yake samun isashen abinci mai rai da lafiya nama har ba'a cewa komai.      Suna dawowa ba'a zaunaba Hajiya falmata ta hau yima amarya shiri na musamman wanda ya kaisu har bayan isha'i, ana idar da salla ta kammala naɗeta cikin haɗaɗɗiyar lifaya datai mata matuƙar ƙyau kamar ba an Zinnin danya mai tallar riɗi da gyaɗa ba. Daga haka aka miƙata wajen su Baffah da manyan iyaye ƴan bauchi sukai mata faɗa da nasiha matsayinsu na iyaye gareta, sai ga hajiya iya na sharar hawaye kuma, hakama su Meenal kuka rurus suke sha abin tausayi, Sa'a ma sai ta kama kuka dama tasha wani a danya. Tinene kuwa tana kwance rijib babu lafiya dan ko a wajen walima kasa sakewa tayi, danma Yaya Atine nata mata masifa wai harda langwai daga zazzaɓi.      Yaya Gajeje najinsu dai bata tankaba dan ita tasan mita hango tattare da Tinene ɗin, tanata ƙoƙarin dannewane harsu koma lafiya gida kawai.               Bayan an kwashi masu rakkiyar amarya a motoci aka fito da amarya daketa rusar kuka wadda Hajiya iya zatai mata rakkiya har ɗakin mijinta. Aiko Zinneerah na naɗe a jikinta tanata kuka ranta fal fargabar wanda zata tarar matsayin mijin nata har suka iso ƙyaƙyƙyawan gidan na AK da yaji kayan more rayuwa. Duk da yace kar iyayenta suyi komai sai da suka nuna bajintarsu suma gwargwadon ƙarfinsu. Dan kuɗin baba dana abba aka dunƙule waje ɗaya akai mata kaya ƴan ubansu da gara, hajiya iya kuwa dama itace tayi komai na kayan kitchen.       Ɓangaren ta daban na Farah daban, duk da dai babban falon farkon shigowa ya haɗa ɓangarorin gidan uku, dole ta cikinsa zaka doshi kowanne ɓangare harna mai gidan, amma kuma kowacce a sashenta tanada faluka guda biyu kuma da bedrooms har uku sai kitchen. Tun kafin fitowa mota sai da hajiya iya ta saka zinneerah dake lulluɓe har kanta tana kuka yin addu'a, hakama da zasu shiga babban falon da sashenta.       A lokacin da ƴan kawo amarya ke shigowa su Mammah suna sashen Farah cikin tashin hankalin sumar da tayi, dan tunda aka taso wajen walima su nan gidan suka nufo kai tsaye, tarbarau tayi da murnarta dan batasan mike faruwaba, kuma ko daɗewa dayin waya da AK bataiba. Sai dai halin da taga aunty Zakiyya da Mammah a ciki ya ɗaga mata hankali ta shiga tambayarsu lafiya? Duk yanda Mahma taso ƙwaɓar aunty Zakiyya da ido akan karta sanar mata sai da aunty Zakiyya da hankalinta ke tashe da zancen Uncle Ahmad na dashen ciki tai suɓutar baki wajen sanarma Farah zancen auren AK. Ko rufe baki batayiba Farah ta yanke jiki ta faɗi a sume.     ALLAH ya sosu hakan yay dai-dai da shigowar AK gidan a gajiye. Hankalin sane ya tashi matuƙa shima, babu shiri ya tsaida Dr Mahmud da ya kawosa gida. Tofa shine tun lokaci suka rufu akanta da ƙyar suka samu ta farfaɗo Dr Mahmud daya sa aka kawo masa kayan aiki daga asibiti yay mata allurar barci mai nauyi da har yanzu take kanyi bata farkaba.        Mammah sai masifa take akan wlhy idan Farah ta rasa ranta sai tayima Kabeer abinda bazai taɓa mantawa da ita a duniya ba. Tanayi tana sharar hawaye hakama aunty Zakiyya kuka take rurus dan tana tsananin ƙaunar autar tasu Farah da tausayinta ke damunsu saboda mahaifiyarsu na haihuwarta ta rasa ranta ko ganin Farah ɗin ma batayiba.      Koda sukaji an kawo amarya Mahma ce kawai tai ƙarfin halin fita tarbarsu kar ace babu kowa a cikinsu tunda ansan suna gidan kuma. Bata nunama hajiya iya komai na halin da ake cikiba ta rungume Zinneerah tana mata barka da zuwa cikinsu. Ita dai Zinneerah ba sanin wacece tayiba tunda kanta a rufe yake, tanata dai sharar hawayenta musamman da taji mutane nata sallama suna ficewa dan ance ba zama za'ai ba. Duk maison ganin ɗakin amarya yazo gobe idan ALLAH ya kaimu ya gani da ƙyau.      Wannan yasa Zinneerah batasan sanda hajiya iya ta sulale ta gudu ba ita dasu Yaya Gajeje. Kafinma ta farga sai jin hayaniyar tayi ta ɗauke ɗaf daga inda take sai acan harabar gidan take jiyosu.     Zamewa tai a gadon ta kwanta tare da sake fashewa da wani irin sabon kuka maiban tausayi dacin rai.............✍ *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_*        *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* *Page 50* _________________________ _*MS TREATS*_ _(PALACE OF PERFUMERY & TRADITIONAL VARIETIES)_ _COME & EXPERIENCE EXCEPTIONAL SCENTS’  AND DELICACIES, YES WE ALSO CARTER TO SMALL & LARGE EVENTS._ _Turaren wuta irinsu_ _Smal halut_ _Sandal coconut _ _Janal banal _ _Arabian oud sandal bakhuor _ _Special kajiji _ _Sandal flake_ _Vip hawi _ _Sudanes sandal rose _ _Humra _ _White humra_ _Black humra _ _kulaccam _ _Dilka soap_ _Whitening soap _ _SPICES_ _Curry powder _ _Corriander powder _ _Tumeric powder _ _Mix spices _ _Ginger powder _ _Black pepper _ _White pepper _ _SNACKS_ _ _Samosa_ _Spring rolls _ _Meatpie _ _Cupcake _ _Birthday cake _ _Doughnut _ _Contact 07061106161 or 08099990056_ _address: bayan northwest university layin gidan ruwan dish_ _KANO, NIGERIA_ _________________________ *Page 50* ..........Soaai AK yayi mamaki matuƙa da ganin abokansa waɗandama shi kobi takansu bayayi yanzun, hakama abokan harkar business ɗinsa dake anan Nigeria. Dole dai ya ware ya shanye mamakinsa ya shiga basu hannu suna gaisawa da tayashi murna, tare da masa ƙorafin ba'a gayyacesu ɗaurin aureba sa fatin da babu amarya babu ƴammatan amarya balle Uwargida. Murmushi kawai yakeyi bai iya cewa komai dan baida abin faɗar.     Daga haka komai ya kasance a nutse cike kuma da birgewa. Dan abune na masu aji sam babu wata hayaniya. Anci ansha an sake taya ango da amarya murna da musu fatan alkairi, zuwa goma taro ya tashi lafiya kowa yana sam barka. Baƙi suka koma masaukinsu masu gidaje anan kano suka kama gabansu.      Sosai AK yaji daɗin fatin nasu kuwa. Dan koba komai ya haɗu da tsoffin abokansa da uzurorin rayuwa ya sashi mantawa dasu. Koda ya ɗan leƙa gidan nasu bayan sun tashi kasa zama yayi saboda hayaniyar ƴan biki, wai a hakanma wasu sunyi barci saboda gajiya, dole yayma su Baffah da Uncle Ahmad da suke nane da juna sallama ya gudo gida.        Lokacin daya shigo gidan Farah tayi barci, dan haka shima kayan jikinsa kawai ya zare yay wanka da neman makwanci saƙe-saƙe fal ransa. Musamman fargabar zuwan su Mammah gobe idan ALLAH ya kaimu da Mahma ta sanar masa. Sam bayason Mammah tazo ta tada hankalinta a cikin wannan taron mutanen ƴan biki, shiyyasa tun ɗazun abin ke damunsa da ƙyar yaketa faman tausar kansa.     Yau sukai niyyar tahowa Mahma ta sake lallaɓasu akan su zauna zaman shirya abubuwa yanda zasu iya tunkarar Baffah. Dan  sunyi aniyar tahowa su shiga garin danya da akace musu amarya take kafin su wuce kano. Hakan yasa Mahma kautar da hankalinsu har amarya ta isa ɗakinta lafiya sannan. Tasan dai idanma sunzo a gobe insha ALLAH aikin gama ya gama kuma.      _______________________★     Washe gari aka tashi da shirin gagarumar walima wadda daga ita kuma sai miƙa amarya Zinneerah ɗakin mijinta. Zinneerah data kwana a ɗakin AK ita da Adilah kuwa da zazzaɓi ta tashi, amma tanata daurewa dan har wasu ƴan sauran gyara da suka rage hajiya Falmata tai mata a daren. Tsabar gyaran data sha maranta har wani ciwo yakeyi mata. Haka dai ta cigaba da daurewa har hajiya Iya ta shigo ɗakin domin dubata. Dan Adilah dake fashin salla ma ko tashi a barci batayiba.        Sun gaisa da hajiya iya take tattaɓata ganin duk tayi wani iri, “Kai Inno ai zazzaɓi ne a jikin nan naki, haka kika kwana da shi ma ko?”.       Cikin ƴar shagwaɓar da suka sabama hajiya iyan ita dasu Jamal ta ɗaga mata kai idanunta na cika da ƙwalla. Sannu hajiya iya ta shiga jera mata, kafin ta taimaka mata shiga bayi dan ta samu tayi wanka. Koda tayo wankan ta samu ta shirya cikin atanfa sabuwa ƙal data amshi jikinta ɗas ta fito a amaryarta, Adilah kanta data farka sai yaba ƙyan datai takeyi, murmushi kawai Zinneerah keyi dan sosai take ganin girman Adilah ɗin kasancewarta ba ƙarama ba, sai dai kawai ALLAH ya bata ƙaramin jiki ga kuma yanayin inda ta tashi rayuwar turai, dan ita hausarma ba iyawa taiba tunda ba zuwa Nigeria ɗin Mammah take bari tayiba. Iya kacinta dasu magana da turanci, saiko AK dake iya jin yaren Mammah na larabci sukanyi, shiyyasa basa shiri da hajiya iya sosai saboda takaicin Adilah ɗin bata iya hausaba.      Tea hajiya iya ta kawo mata a sha da magani ta sake kwanciya kafin lokacin walimar. ★★★       A katsina kam ko breakfast ɗin arziƙi basuyi zaman yiba suka kamo hanyar kano, lokacin da suka iso gidan anata kwasar mutane zuwa ƙaton hall ɗin da za'a gudanar da walimar. Yanda anguwar ta rikice da kai kawon motoci masu kwasar mutane yasa dole su Mammah suka fakin tun a waje, Mahma ce kawai ke dauriyar gaisawa da mutane, amma Mammah da Aunty Zakiyya sunata shan ƙamshi.     Koda suka iso cikin gidan sun sami Baffah tare da baƙi, yana ko ganinsu yabar baƙin da uncle Ahmad ya nufosu fuskarsa ɗauke da murmushin daya sake fusata Mammah, aiko tayi kicin-kicin da rai tamkar zata fasa ihu. Sai dai batace komaiba bisa ga gargaɗin Mahma da sukasha.       Duk yanda Aunty Zakiyya taso nuna halin nata ga Baffah kasawa tai, dan wani irin kwarjini yay mata da cikar kamala. Dole tai ƙasa da kanta tana gaisheshi da girmamawa. Shima cike da fara'a ya amsa mata harda tsokanarta.      Yanda Mammah ta ɗauke kanta daga garesa haka shima yayi tamkar bai gantaba, cikin girmamawa yacema Mahma su shiga ciki. Murmushi tai masa, yay gaba suna binsa a baya har sashensa tacan baya da ƙofar falonsa ta ainahin bedroom ɗinsa take. Dan yasan acanne kawai babu wani hayaniyar mutane da hankalinsu zai kai kansu saboda wutar bala'i daya hanga a idanun Mammah.      Kafin su shige ya aika Jamal da sukaci karo ya sanarma hajiya iya zuwansu, daga nan ya wuce a haɗo abinci a kawo musu. Mammah zatai magana cikin masifa Mahma ta dakatar da ita da idanu, dole taja bakinta tai shiru tana haɗiyar zuciya.           Cikin ƙanƙanin lokaci hajiya iya ta ƙaraso tareda su Bahijja dake ɗauke da abinci, suna ajiyewa suka gaishesu suka fice. Mahma da aunty Zakiyya ne kawai suka gaida hajiya iya, Mammah kuwa sai da Mahma ta harareta sannan ta gaisheta da ƙyar. Hajiya iya bata damuba kam, dan ba yaune farauba.          Yanda hajiya iyan ta nuna rashin damuwarta ya ƙara zafar Mammah ta fara magana a ƙufule, “Kabeer  miye wannan ke nufi?”. Tai maganar tana ajiye masa invitation card a tsakkiyar centre table. Uncle Ahmad daya shigo falon ne ya ɗauka ya duba ya maida ya ajiye. Kasancewar shima ɗan zafin kan ne a gadarance yace mata “katin gayyatar walimar liyafar cin abincin auren gudan jininmu mana”.      Kallonsa tai rai a ɓace tana juya idanu, “Kai kuma bansa da kaiba mijin tace, kaji da taka matsalar kafin ka tsoma baki a ta wasu”.         “Hakan na nuna miki cewar wadda ta maidani mijin tace ɗin tafiki komai, tunda ke kin kasa maida Yayana mijin tace ɗin saboda ƙarancin ƙyaƙyƙyawan nazari da kishin hauka dake damunki. In banda abinki Hindatu tayaya kike tunanin raba ƴaƴa da mahaifinsu ta ƙarfin tsiya? Ke waya rabaki da naki har suka bar duniya”.          “Wlhy Ahmad ka kiyayeni, kasan na fika zafin kai”.     “Anƙi kiyayar taki, kiyi duk abinda zakiyi”.        “Zako kaga mizanyi ɗin, dan wlhy wannan auren kun ɗaura banza saina rabashi, in banda son zuciya taya yaro yana zamansa lafiya da matarsa zaku ƙaƙaba masa auren yarinya baƙauya mara galihu.........”        A fusace hajiya iya ta katseta da faɗin, “A rashin galihun nata shi ɗan naki ya gani yakeso, tunda har ya iyama yarinya ciki a waje ta haihu ita ƴar son naki bata haifaba. Hindatu ki kiyayeni wlhy, ina ɗaga miki ƙafa saboda ɗanki, amma inaga wannan karon saina fito miki a Amina ta, moddibo ne dai ya dawo gidansu kenan daga shi har ƴar uwarsa babu kuma yanda kika iya. idan buƙatar kasancewa kike dasu kema saiki dawo gidan ubansu ki zauna cikin kishiyoyin da kike gudu. Dan daga yau na yanke shawarar moddibo ya dawo ƙasarnan da zama kenan da iyalansa idan kin gansa a wata ƙasa sai dai yaje harkokinsa ko gaisheki ya dawo wlhy”.        Tsabar yanda zuciyar Mammah takai maƙura a hasala sai kawai ta fashe musu da kuka. “Wlhy bazan yardaba, bazan yarda a rabani da ƴaƴana ba tunda nice na haifi abuna bayan wahalar rainon cikinsu dana sha. Ita matar Ahmad data kwace miki shi miyasa kika kasa komai sai ni zakibi ki sama ido akan nawa ƴaƴ.......”       “Hindatu!!”. Baffah ya daka mata tsawa jikinsa har rawa yake na ɓacin rai. Murmushi hajiya iya tayi da ɗaga masa hannu. ta duba Mammah da ƙyau tana faɗin, “Itama ba ƙarfina tafi ba, kamar yanda kika ɗauke su moddibo muka barki yanzu kuma lokacin dawowarsu cikinmu yayi, itama lokacin da zan nuna mata nina haifi Ahmad ɗin yayi ai”.         “Wlhy ni kuma nayi alƙawarin yin amfani da ƙarfina na uwa wajen raba wannan auren, ɗa kuma da suka haifa a waje zaimin bayanine dalla-dalla dan ubansa”.       Ran Mahma da yay matuƙar ɓaci da abinda Mammah keyi bayan sai da ta ƙwaɓeta kafin su taho ta kama hannunta ta maidata ta zaunar a fusace. “Hindatu wai mike damun kanki? A ganina kamata yay ki nutsu ayi magana ta fahimta amma kinzo kinama mutane shirme. Kifa sani yanda kike da haƙƙi akansu Adilah haka shima mahaifinsu keda haƙƙi a kansu, yakumayi iya bakin ƙoƙarin sa wajen yimiki kawaici akansu, ai idan kinason yaranki su kasance dake basai ta hanyar ƙarfi da iko ba tunda suma sunsan ke uwa ce a garesu. maimakon ki damu dajin ta yanda akai Abdul-Mutallab ya samar da yarog yarinya a waje ke damuwarki kawai ƴaƴanki zasu suɓuce miki, haba wane kalar son kai ne wannan?”.     Kuka sosai Mammah keyi, tace, “Haba Addah kinajinfa yanda suka haɗa kai zasumin taron dangi, taya zasu ma yaro aure bada saninaba haka ake rayuwa?......”       “Ke sanda kikai masa aure bada saninmu ba wace gadarace baki manaba”.  Baffah ya katseta a fusace. Ransa a ƙololuwar ɓace ya cigaba da faɗin, “Hindatu idan kin manta bara na tuna miki, matar da Adnan ke aure karki manta sai ana gobe ɗaurin aurensa da ita kika faɗa mana, amma duk da rannmu ya ɓaci Inna ta tilasta mana haƙuri mu barki tunda aurene, yarinyar kuma ƴar uwarki ce. Haka muka danne zukatanmu muka amsheta a cikinmu da hannu bibbiyu amma ki ka ɗorata akan keken ɓera wajen nuna mata muɗin mutanen banza ne bama sonki da ƙaunarki, sai kuma a yanzu dan mun maimaita abinda kika aikata zakiji zafi? Ai dama na faɗa miki ƴaƴana sai sun dawo gareni tunda ke bakisan mutunciba, burinki kawai ki nisantasu dani da ƴan uwana to muzuba mu gani ɗan halak ka fasa ni da ke a garin nan”.      Mammah zata sake magana Mahma ta dakatar da ita da sauri. “Kuyi haƙuri Kabeer, tabbas Hindatu ta aikata laifi, amma inason ku fahimceta itama, kunsan a duk sanda mace ta rabu da uban ƴaƴanta babbar fargabarta shine barin masa ƴaƴanta wata tazo ta cuta musu koshi uban ya nisantasu da ita. Na tabbata wannan shine fargabar Hindatu tun a wancan lokaci da yanzu haka. Amma bawai hakan na nufin ina goya mata baya akan abinda takeyi nason ganin ita ta nisantasu da ku ba duk da kawaicin da kukai mata na tsayin shekaru. Ina son dan ALLAH a wannan gaɓar mu haɗu wajen yafema juna, mukuma fahimci juna dan mu duka munada ƙarfin iko akan Adilah da Abdul-Mutallab. Sai dai hakan ba yana nufin mu cigaba da raba hankalinsu ba da ƙarfin ikon da ALLAH ya bamu akansuba na iyaye”.      Tsit falon yayi dan maganar Mahma tayi tasiri a zukatansu sunkuma san gaskiya ta faɗa. Hakan yasa AK dake tsaye tun ɗazun daga bakin ƙofa ya ƙarasa shigiwa. Zama yay ya gaidasu batare da ya yarda ya haɗa ido da kowaba dan ransa a jagule yake babu daɗi.      Mahma ce ta dubesa da kulawa, “Abdul-Mutallab nasan duk kaji mike faruwa. Sai dai jin naka bashine mai muhimmanci ba, a yanzu mu munfi buƙatar son sanin a ina aka haihu a ragaya game da haihuwar yaro mai sunanka?”.         Iska yaɗan furzar kansa a ƙasa. “Mahma wlhy nima ban saniba”.     “Kamarya baka saniba, a ruwa ake shan ciki balle kace mana itama acan tasha?”. Aunty Zakiyya tai magana karon farko tun shigowarsu a hasale          “Tabbas ba'a sha, amma inaga itakam dai acan ta shashi. Dan ni dai ban taɓa tarayya da wata mace bayan matata ba ALLAH shine shaidata. Sannan ban taɓa ganin yarinyarnan da idanuna ba sai a gidan nan. Amma kuma tabbas na yarda Abdul-Mutallab ɗa nane, ina kuma kan binciken ta yadda aka samar dashi insha ALLAH”.       Shiru falon yayi tsahon lokaci, sai Uncle Ahmad da wani tunani yazo masa a zuciya dan shidai shedane akan AK bai iya ƙaryaba yace, “Abdul-Mutallab maganar nan ba wadda mutane zasu ɗauka bace balle su fahimceka. Amma sai nake tunanin ko kun taɓa yunƙurin yin wannan dashen na zamani da aketa nusar al'ummar musulmi rashin anfaninsa?”.       A karon farko AK ya ɗago ya duba Uncle ɗin nasa da rinannun idanunsa. Hakama Mammah da aunty Zakiyya a razane suka dubi Uncle Ahmad har hakan ya bama Mahma da Hajiya iya mamaki. Da sauri AK ya girgiza masa kansa. “Wlhy Uncle ni ban taɓa son hakanba dan bayama birgeni, na tabbatar idan ALLAH yaso zai bani, da bai baniba kuma ƙila haka shine mafi alkairi a gareni”.        Cikin jinjina kai Uncle Ahmad yace, “Na yarda da kai Adnan dan baka taɓa min ƙaryaba, sai dai wannan al'amarin na buƙatar bincike, musamman ga matarka kota taɓa wannan yunƙurin aka samu kuskuren ɗaukar sparm ɗinka aka saka ga ita yarinyar bada sanin ku ba ku duka tunda wannan matsalar kan faru saboda son zuciyar wasu likitocin, kokuma daga likitocin matsalar take baki ɗaya”.        Wani irin mugun tarine ya sarƙe aunty Zakiyya har sai da aka bata ruwa. Ita kanta Mammah sai zufa take gogewa a kaikaice. Cikin rawar murya tace, “Hakan bamai yuwuwa bane, tayaya za'ai yunƙurin hakan shi bada saninsa ba, kuma shi da ke a london yarinyar na ƙauyen katsina taya ya hakan zai faru, yadai zauna yayi tunani ko wani akasi ya taɓa faruwa”.        Hajiya iya da zuciyarta keta kaikawo da nazarin kowa a wajen tace, “Inaga to wannan maganar babbace gaskiya, mu ajiyeta a yanzu idan an gama biki lafiya saimu yita a tsanake, dan yanzu haka ga Huzaifa nata kirana kunsan ana jiranmu a wajen walimar can”.        Baffah da shi kansa tunanin zuciyarsa ya fara canjawa daga akalar zargin Ak da yake har yanzu zuwa zancen ɗan uwansa cikin gamsuwa yace, “Hakan shine dai-dai Inna”.       Tabbas a wannan gaɓar suma su Mammah sunfi buƙatar tsayawar zancen su sami dama da sararin yin nazari, dan haka duk suka amince. Sai dai basuso zuwa wajen walimarba Mahma ta takura musu akan saifa sunjeta dole ko shima AK ɗin zaiji sanyi a ransa ai.       Gudun zargin wani abu daban daga AK yasasu yarda zasuje. Dan ya tsatstsare su da idanunsa da gaba ɗaya suke a birkuce da abubuwa kala-kala da shima baisan adadinsu ba. ★★       Sun isa ƙaton hall ɗin da za'a gudanar da walima and liyafar cin abinci rana daya ƙawatu matuƙa. Ya kuma cika taf da al'ummar MANZON ALLAH (S.A.W). Ga manya manyan malamai da zasu gabatar da lectures. Sashin mata daban na maza daban babu ruwan wani da wani, hakkane ya samama AK nutsuwar da yake buƙatar samu. Suna isowa aka gabatar da addu'oi da suka shafi komai na rayuwa bayan ma'auratan, kafin a fara abinda ya tara mutane.      Malamai sun ragargaza lectures masu ratsa jiki akan aure da zamantakewar rayuwa data saka jikin mutane da yawa yin sanyi, Zinneerah amarya da duk da basan waye mijin nataba tasha kuka itama, lectures ɗin kuma sun shigeta matuƙa. Lokacin salla nayi aka fita akai sallar zuhur sannan aka dawo aka ɗora dacin abinci, a hakanma dai malamai na cigaba da aikinsu har zuwa la'asar da aka rufe da addu'oin fatan alkairi ga ma'aurata damu da muke a gidan auren sannan aka tashi.       Da yawan mutane daga nan suka fara kama gabansu, wasu kuma suka koma gidansu AK domin rakiyar amarya ɗakinta da za'ayi da wuri, duk da dai hajiya iya tace ƴan danya bazasu koma a yau ba kamar yanda suka sanar, tace su bari sai ALLAH ya kaimu gobe su da ƴan ɗan musa saisu tafi.        Sunkiji daɗin haka dan sam garin ba isarsu yayiba. Musamman da kowa yake samun isashen abinci mai rai da lafiya nama har ba'a cewa komai.      Suna dawowa ba'a zaunaba Hajiya falmata ta hau yima amarya shiri na musamman wanda ya kaisu har bayan isha'i, ana idar da salla ta kammala naɗeta cikin haɗaɗɗiyar lifaya datai mata matuƙar ƙyau kamar ba an Zinnin danya mai tallar riɗi da gyaɗa ba. Daga haka aka miƙata wajen su Baffah da manyan iyaye ƴan bauchi sukai mata faɗa da nasiha matsayinsu na iyaye gareta, sai ga hajiya iya na sharar hawaye kuma, hakama su Meenal kuka rurus suke sha abin tausayi, Sa'a ma sai ta kama kuka dama tasha wani a danya. Tinene kuwa tana kwance rijib babu lafiya dan ko a wajen walima kasa sakewa tayi, danma Yaya Atine nata mata masifa wai harda langwai daga zazzaɓi.      Yaya Gajeje najinsu dai bata tankaba dan ita tasan mita hango tattare da Tinene ɗin, tanata ƙoƙarin dannewane harsu koma lafiya gida kawai.               Bayan an kwashi masu rakkiyar amarya a motoci aka fito da amarya daketa rusar kuka wadda Hajiya iya zatai mata rakkiya har ɗakin mijinta. Aiko Zinneerah na naɗe a jikinta tanata kuka ranta fal fargabar wanda zata tarar matsayin mijin nata har suka iso ƙyaƙyƙyawan gidan na AK da yaji kayan more rayuwa. Duk da yace kar iyayenta suyi komai sai da suka nuna bajintarsu suma gwargwadon ƙarfinsu. Dan kuɗin baba dana abba aka dunƙule waje ɗaya akai mata kaya ƴan ubansu da gara, hajiya iya kuwa dama itace tayi komai na kayan kitchen.       Ɓangaren ta daban na Farah daban, duk da dai babban falon farkon shigowa ya haɗa ɓangarorin gidan uku, dole ta cikinsa zaka doshi kowanne ɓangare harna mai gidan, amma kuma kowacce a sashenta tanada faluka guda biyu kuma da bedrooms har uku sai kitchen. Tun kafin fitowa mota sai da hajiya iya ta saka zinneerah dake lulluɓe har kanta tana kuka yin addu'a, hakama da zasu shiga babban falon da sashenta.       A lokacin da ƴan kawo amarya ke shigowa su Mammah suna sashen Farah cikin tashin hankalin sumar da tayi, dan tunda aka taso wajen walima su nan gidan suka nufo kai tsaye, tarbarau tayi da murnarta dan batasan mike faruwaba, kuma ko daɗewa dayin waya da AK bataiba. Sai dai halin da taga aunty Zakiyya da Mammah a ciki ya ɗaga mata hankali ta shiga tambayarsu lafiya? Duk yanda Mahma taso ƙwaɓar aunty Zakiyya da ido akan karta sanar mata sai da aunty Zakiyya da hankalinta ke tashe da zancen Uncle Ahmad na dashen ciki tai suɓutar baki wajen sanarma Farah zancen auren AK. Ko rufe baki batayiba Farah ta yanke jiki ta faɗi a sume.     ALLAH ya sosu hakan yay dai-dai da shigowar AK gidan a gajiye. Hankalin sane ya tashi matuƙa shima, babu shiri ya tsaida Dr Mahmud da ya kawosa gida. Tofa shine tun lokaci suka rufu akanta da ƙyar suka samu ta farfaɗo Dr Mahmud daya sa aka kawo masa kayan aiki daga asibiti yay mata allurar barci mai nauyi da har yanzu take kanyi bata farkaba.        Mammah sai masifa take akan wlhy idan Farah ta rasa ranta sai tayima Kabeer abinda bazai taɓa mantawa da ita a duniya ba. Tanayi tana sharar hawaye hakama aunty Zakiyya kuka take rurus dan tana tsananin ƙaunar autar tasu Farah da tausayinta ke damunsu saboda mahaifiyarsu na haihuwarta ta rasa ranta ko ganin Farah ɗin ma batayiba.      Koda sukaji an kawo amarya Mahma ce kawai tai ƙarfin halin fita tarbarsu kar ace babu kowa a cikinsu tunda ansan suna gidan kuma. Bata nunama hajiya iya komai na halin da ake cikiba ta rungume Zinneerah tana mata barka da zuwa cikinsu. Ita dai Zinneerah ba sanin wacece tayiba tunda kanta a rufe yake, tanata dai sharar hawayenta musamman da taji mutane nata sallama suna ficewa dan ance ba zama za'ai ba. Duk maison ganin ɗakin amarya yazo gobe idan ALLAH ya kaimu ya gani da ƙyau.      Wannan yasa Zinneerah batasan sanda hajiya iya ta sulale ta gudu ba ita dasu Yaya Gajeje. Kafinma ta farga sai jin hayaniyar tayi ta ɗauke ɗaf daga inda take sai acan harabar gidan take jiyosu.     Zamewa tai a gadon ta kwanta tare da sake fashewa da wani irin sabon kuka maiban tausayi dacin rai.............✍ *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_* *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* *_Ashe yau monday😂🤣🙏🏻_* _______________________ *page 51* ...........Kamar jira ƴan kawo amarya na wucewa Farah ta farka, sai dai a yanayin data farka ɗin yay matuƙar tada hankalin su Mammah, AK daya tuna cewar tana tare da ciki ya cema Dr Mahmud suje asibiti kawai kar a rasa abinda ke cikinta. Mammah ce tai azamar son dakatarwa Mahma ta tsaidata itama ta hanyar faɗin, “Maganar Abdul-Mutallab nakan hanya, hakan shine yafi dacewa kar azo ana dana sani kuma daga baya”.         Cikin tashin hankali aunty Zakiyya tace, “Mahma kubarta-fa komai zai dai-daita, inaga ya ƙara mata allurar barcin sai mu wuce can gidan da ita dan Abban Ameera ya kirani cewar wanda zai kawo mana key ɗin ya iso yana can yana jiranmu”.       “Addah abi shawarar Zakiyya ɗin na tabbatar shock ne zata dawo dai-dai idan ta ɗanyi nesa da nan ɗin kamar”.       Ak dake binsu da kallon mamaki ya dafe kansa dake neman fara masa ciwo, dan shikam dai abubuwan na neman masa yawa gsky. Mahma da wani tunani yazo mata a zuciya tace, “To babu damuwa kai mata allurar kawai sai mu wuce”.       Kallon AK Dr Mahmud yayi, “Amma ranka ya daɗe karfa allurar tai mata illa, ni bansan ma tana tare da ciki ba da ban mata ita ba, tanada ƙarfi, nayi mamakin ma data farka a yanzu dan allurar mai ƙarfice”.        Karan farko AK ya saki ɗan murmushi, dan shikam dai zuciyarsa ta fara raya masa wani abu game da yanayin Mammah da Aunty Zakiyya, ya ɗan lumshe idanunsa ya buɗe da gyara tsaiwarsa. Cikin rashin sakewarsa yace, “Kaga yimata ɗin kamar yanda sukace, dan a ganina zamanta a farken yafi allurar zama matsala ga lafiyar tata”.        Kai kawai Dr Mahmud ya gyaɗa masa, dan shikam dai baimaga wani alamun ciki a jikin Farah ɗin ba. Yana ƙoƙarin haɗa allurar yace, “Amma cikin nata yakai wata nawane?”.       Shiru Mammah da aunty Zakiyya sukayi, sai Mahma ce tace, “Kamar dai biyar ko”.      “Biyar fa?”. Dr Mahmud ya ambata mamaki ƙarara a fuskarsa. Ɗan duban Farah ɗin dake riƙe jikin Mammah tana kuka da wani ɗan fisge-fisge yayi ya ɗauke kansa. Batare da yace komaiba yay mata allurar kawai ransa fal wasiwasi.      Yana gama mata allurar ko mintuna biyar ba'a ƙullaba barci ya ƙara ɗaukarsa. Kallon AK Mahma tayi da cewa, “Taimaka ka kai mana ita mota Abdul-Mutallab, ku kuma kumuje shima ya samu ya huta”.        Babu shiri Mammah tace, “Addah ai shine zai kaimu, taya matarsa na wannan halin yaga wani ta hutu?”.      Murmushi Mahma tayi na takaici, muryarta aɗan hasale tace, “Duk mu da muke tare da ita bai wadatarba sai shi ya kasance a wajen?. Ai ya kamata a tausaya masa ya huta ga kuma yarinya an kawo zai barta ita kaɗai kenan komi?”.       A take Mammah ta sake tamke fuska matuƙa. Ta kalli AK da yay tamkar bayama jinsu yanata latsa waya. Sai kuma ta maida kan Mahma, “Addah to in hakane muyi kwanciyarmu anan ɗin kawai basai yayi wahalar da kike gudar masanba..”      “Bazai yuwuba, tunda dai ga gida can da zamu zauna mu kaɗai bamu takura kowa ba, ba'a takuramu ba, can zamuje. Abdul-Mutallab ɗauketa”.      Yanda Mahma tayi maganar babu wasa a ciki ya sakashi zura wayarsa aljihu ya tako a hankali inda Mammah ke rungume da Farah. Ɗaukarta yay cak ya fita da ita duk da nauyin datai masa saboda yanda jikinta ya saki sosai. Duk yanda Mammah keta kumbure-kumbure Mahma batabi takantaba ta tasasu gaba suka fice suma. Dan ita aunty Zakiyya ma ta ƙagu subar nanɗin dama suje inda takeson amayar da abinda ke a bakinta.       Aunty Zakiyya ce ta jasu. Suna ficewa daga gidan AK yaɗan lumshe idanunsa da murza goshinsa yana furzar da huci. Sai kuma yay murmushi da girgiza kansa saboda harar da Mammah keta faman antaya masa da gargaɗi da idanu.         Juyawa yay zuwa cikin gidan dan shima wani ma zazzaɓi-zazzaɓi ke neman rufesa, sashen Farah ya koma ya kashe komai da maida ƙofar ya rufe, koda ya fito sashensa ya nufa dan yafi buƙatar watsa ruwa a yanzu.        ★★★     A ɓangaren Zinneerah kam kuka taci sosai, sai da Mahma ta leƙo tai mata sallama akan suma zasu wuce, ta kuma ɗan lallasheta da ƴar nasiha sannan ta sassauta. Fitsarin da takejine ya sakata tashi dole ta shiga toilet ɗin ɗakin tayo, tana fitowa ta sake komawa saman gadon ta kwanta dan zazzaɓi takeji yana neman rufeta ga ciwon kai. Ba tare data damu da cire komai ba ta kwanta a haka dajan bargo ta lulluɓa har kanta saboda sanyi da takeji yana ratsata. Ga kuma ac a ɗakin dake aiki ta kasa kashewa.         Batafi mintuna goma da kwanciyarba barci ya kwasheta sama-sama. A ɗan firgice ta farka saboda ƙarar buɗe ƙofa da taji, ta ƙanƙame jikinta waje guda jin tabbas mutum ne ya shigo. Sai dai ta kasa ko motsi saboda yanda zuciyarta ke wani harbawa da sauri sauri na tsananin tsoron wanda zataci karo da shi a matsayin mijin nata.       AK da tun shigowarsa ɗakin idanunsa suka fara sauka akanta ya cigaba da takowa cikin ɗakin a hankali sassanyan ƙamshin turaren wutar da ɗakin yaji, da ƙamshin sabbin furnitures dana fenti na rige-rigen shiga masa hanci, a hankali ya sauke ajiyar zuciya yana ƙarasawa gaban gadon sosai. Hannayensa ya tura duka biyu cikin aljihun wandon blue pyjamas ɗinsa har lokacin idanunsa akan Zinneerah dake ƙudun-dune cikin bargo zuciyarta na nemam faso ƙirjinta ta fito.        “Assalamu alaiki”. Sassanyar muryarsa ta daki cikin kunnuwanta. Sosai ƙirjin Zinneerah ya buga fiye da farko, dan idan har babu kuskure ai muryar Yayansu taji kam. ‘Kai ina ganganne’ ta ayyana a zuciyarta dake raunana.        “Nasan ba barci kike ba”. Ta ƙara tsinkayar muryar tasa a karo na biyu, a yanzu kam kasa jurewa tayi dole tai ƙasa da bargon a hankali daga saman fuskarta. A hankali ta buɗe idanunta zuciyarta na gudu dai-dai da jinin jikinta dake tsinkewa daga cikin jijiyoyinta. A wani irin firgice ta yaye bargon babu shiri tana miƙewa zaune jikinta na rawa. “Y...y....Yayanmu!”.       Ta faɗa da wani irin kiɗimammiyar murya dake nuna tsantsar tashin hankalinta a fili. Sosai yanda tayi ɗin ta bashi dariya, amma sai ya daure ko ɗigon fara'a babu a fuskarsa, sai dai idanunsa kafe suke a kanta ko ƙyaftawa bayayi yana ƙarema ƙwalliyar tata kallo, dan zaburar da tayi ta saka lafayar warwarewa daga saman kanta zuwa jikinta. Sai baƙar rigar jikinta mai dogon hannu data lafe da bayyana ainahin surarta da gyaran da fatarta ta samu wajen hajiya Falmata.            Janye idanunsa dake binta da kallon yayi yana maidawa akan fuskarta, ganin yanda take ɗan ja baya da rawar jiki laɓɓanta na rawa alamar sonyin magana ya sakashi lumshe idanu ya sake buɗewa a kanta yana zare hannayensa daga aljihun wandon barcin nasa. Cikin nuna rashin damuwa da yanayin nata ya kai zaune a bakin gadon yana facing ɗinta. Hannunsa ɗaya yakai akan goshinsa yaɗan shiga murzawa. Sai kuma ya ɗago ya dubeta da birkitattun idanunsa dake rikitata, batare da yace uffanba ya miƙa mata hannunsa ɗaya alamar tazo.      Kanta ta shiga jujjuyawa tana ƙara nanema fuskar gadon, hawaye na gudu a saman fuskarta kamar an buɗe fanfo. “Yayanmu dan ALLAH kace bakai bane ba”. Ta faɗa cikin tsananin rauni da rawar harshe.       A karan farko ya ɗanyi luuu da idanunsa da sakin guntun murmushin da ita ko alamarsama bata ganiba, ya ɗan ƙara ware idanunsa a kanta da kai hannunsa ya shafi sajensa dake a kwance luf duk da ba gyaransa yay ba, dan koda yay wankan ma turare kawai yasa da kayan barci ya fito domin dubata. Cikin muryarsa ta rashin sakewa yace, “Bani bane mi?”.        Cijin suɓucewar baki Zinneerah tace, “Miji!, mijin da aka kawoni gidansa matsayin matars.......”      Ta kasa ƙarasawa saboda yanda yay bala'in kafeta da idanunsa masu cikar gashi da kwarjini. “Ban cancanta bane?”. Ya faɗa yana cigaba da tsatstsareta da idanu.     Babu shiri tai ƙasa da kanta kuka na sake kufce mata. Kansa ya ɗauke daga kanta jin wayarsa na vibration, hannu yasa ya cirota daga aljihun wandon barcinsa yana jan guntun tsaki alamar baiso shigiwar kiranba dai. Sai dai ganin Number aunty Zakiyya ya sakashi yi kamar bazai ɗagaba sai kuma ya ɗaga ɗin batare da yayi magana ba.       Cikin sake fusata daga can Mammah tace, “Abdul-Mutallab nasan kana jina”.      Runtse idanunsa yay da cije lip ɗinsa na ƙasa. yay ƙoƙarin daidaita kansa wajen faɗin, “Am sorry, bansan ke bace ba”.        “Ai yanzu ka sani, na kiraka ne na gargaɗeka, wlhy ka taɓa musu yarinya sai ranka yay mummunan ɓaci, dan nayi alƙawarin wannan auren sai na tsinkashi wlhy, saboda haka karma ka ƙwaɗaitama kanka abinda zai dameka daga baya na faɗa maka”.          A bazata ya saki murmushi mai sanyi da kai hannu ya shafi kansa, dan tana gama faɗa ta yanke kiran bata jira amsarsa ba. Ajiye wayar yayi yana miƙewa gaba ɗayansa idonsa akan Zinneerah dake cuɗa yatsunta cikin juna tana cigaba da kukanta  harda shashsheka.       Batare da tunanin kanta ya nufoba sai ganinsa tai ya hawo gadon sosai, filo ƙarami ya jawo daga gefenta ya kishin giɗa, dan ɗaura gwiwar hannunsa ɗaya yay ya tallafe kansa da tafin hannun yanda yake iya kallonta da ƙyau, sai kuma ya saka yatsunsa biyu na ɗayan hannunsa ya tallafo haɓarta yanda zasu haɗa ido.       Suna haɗa idanun kuwa tai saurin son maida nata dake kwarar da hawaye amma ya hanata wannan damar. Sai kawai ta shiga sake matso hawayen. Dan irin kallon ƙurullar da yake yima fuskar tata ne yake ƙara ƙarya mata zuciya ga kwarjininsa daya cika mata idanu.            “Shi wannan kukan ba'a gajiya dashi?”. Yay maganar da muryar lallashi data sakata ɗago idanu ta sake kallonsa, yanda yay ɗan yi luuu da idanun nasane ya saka tsigar jikinta tashi, cikin harɗewar harshe tace, “Yayanmu!”.        “Uhmyim ƙanwata”. Ya faɗa yana sakin haɓar tata da janye hannunsa daya tallafe kansa shima yana gyara kishingiɗar tasa da matsowa daf da ita yanda takejin har saukar numfashinsa shima yanajin nata.      Ganin yanda ta kasa ci gaba da maganar sai juya yatsun hannunta take a cikin na juna ya sashi ɗaura hannunsa akansu yana kallon zanen baƙin lallen da ja dayay matuƙar ƙyau a kansu, “Kuka ga amarya a ranar da aka kawota gidan miji cikar kamalace da bayyana adon mutuncinta, sannan kuma tarbiyyace da nuna tsantsar soyayya ga iyaye, sai dai idan yayi yawa yana gundurata. Karki damu da neman amsar duka tambayoyinki, a hankali zaki samu amsarsu. Inason mutum mai biyayya akan umarnina, banason hayaniya, banason taurin kai, banason ƙarya. Duk wanda zan rayu dashi inhar zai kiyaye waɗannan zaiji daɗin zama dani fiye da yanda yake zato. Bana yanke hukunci ga mai laifi da sauri ko cikin fushi har sai na bisa mataki-mataki wajen fahimtarsa da dalilinsa. Mun sami juna a yanayin da banso ba, sai dai ba hakan na nufin zanyi sakaci da damata bane, komu samu tsaurin idon bijirema hukuncin ALLAH dana iyayenmu, dan sun cancanci sadaukarwa koda ace mu zukatanmu basa buƙatar hakan, ina ƙyautata miki zato bisa ga wasu dalilaina, dan haka sai kiyi ƙoƙarin tabbatar mini da hakan”.        Hannunta ɗaya ta zare daga cikin nasa a hankali ta share hawayen da suka jiƙe mata fuska.      “Good” ya faɗa yana tashi zaune daga kishingiɗar da yayi. Sauka yayi gaba ɗaya a gadon Zinneerah na binsa da kallo ta ƙasan ido da ƙoƙarin ganin ta shanye hawayen dake shirin sake zubo mata. Akwatin daya gani a gefe ya ɗakko, ya ɗaurashi a gadon tare da buɗewa. Da kayan barci dake sama ya fara cin karo, batare da damuwaba ya ɗakko na saman kawai ya maida ya rufe. Takowa yay ya ajiyesu gabanta fuskarsa a tsuke kamar yanda ta santa, cikin rashin sakewarsa yace, “Ki tashi ki sauya kayanki ki kwanta”.      Daga haka ya juya ya nufi ƙofa. Da kallo ta sake binsa tana share hawayen da suka ziraro mata. Yana fita ta ɗaura hannu duka a kai tana sake fashewa da kuka. A fili tace, “Na shiga uku ni Zinneerah ina ni ina zaman aure da Yayanmu? Wlhy yafi ƙarfina, matarsa tafi ƙarfina bazan iya da bala'inta dana Mammah ba”.     Sai kuma ta zame ta kwanta tana jan numfashi dake sarƙe mata a ƙirji da ƙyar. Tabbas bazatace batason Yaya Abdul-Mutallab ba, dan ya cancanci zama abinso ga kowacce irin mace ciki harda ita da a yau zata iya kiran kanta mai sa'a ma, amma tasan yafi ƙarfinta ta kowanne fanni na rayuwar duniya, duk da tasan zata iya finsa a lahira itama wannan hukuncin ALLAH ne. Miyasa MAKAUNIYAR ƘADDARA zata rasa a inda zata jefata sai cikin rayuwarsa?. Ta inama zata fara kwatanta zaman aure dashi itako?.              “Idan nace bana son abu sau ɗaya to a kiyaye mini, inba hakaba zan ɓata ran mutum kamar yanda ya shirya ɓata nawa”.      Ta tsinkayi muryarsa a bazata batare data san ya sake dawowa ɗakin ba. Zumbur ta miƙe zaune da kwasar kayan barcin daya ajiye mata tana sauka a gadon batare data yarda ta kalli ko sashen da yake ba. Kamar ƙyaftawar ido ta afka toilet ɗin ɗakin.         Tea cup ɗin hannunsa ya ajiye a bedside drawer yana ƙoƙarin zaro wayarsa datai alamar shigowar saƙo. Ganin no ɗin aunty Zakiyya ta sakashi buɗe saƙon dan yasan Mammah ce.        _Ina ƙara tabbatar maka karka taɓa yarinyarnan Abdul-Mutallab, dan zaka gamu da ɓacin raina da baka taɓa ganiba a tsahon shekarun rayuwarka talatin da huɗu_.        Murmushi ne ya suɓuce masa, yaɗan girgiza kansa da faɗin, “Mammah problem”. Akan laɓɓansa. sai ma ya kashe wayar baki ɗayanta ya ajiye ya ɗauka lap-top ɗinsa daya shigo da ita ya shiga hidimar kunnawa dan akwai abinda yake son yi daya shafi business ɗinsa da wani abokin harkarsa mai turo masa kaya daga dubai...............✍     *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_* *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* _________________________ *Page 52* ...........Gargaɗinsa yasa Zinneerah tana canja kayan tayo alwala da sake naɗe jikinta da lifaya ɗin ta fito duk da kayan barcin wandone har ƙasa da riga, kasancewar rigar guntuwa mara hannu yasa taji bazata iya fitowa da itaba gabansa. Gashi ta cire bra ɗinta dan bata iya barci da ita ciwon ƙirji take sanya mata. Buɗe ƙofar tai a hankali ta fito cike da sanɗa kamar wadda ta aikata wani abu. Ganinsa zaune a saman sofa hasken system ɗin da yake sarrafawa ta haska kamilalliyar fuskarta ya sata satar kallonsa.          Duk da yaji motsin fitowar tata bai ɗagoba yanata aikin gabansa, ganin ta cigaba da tsiwa yace, “Ɗakko tea gashi can kizo nan”.          Cike da dauriyar yanda kanta ke mata tsananin ciwo ta wuce ta gabansa ta ɗakko kofin tea ɗin daya ajiye a bedside drawer ɗin, gabansa tazo tana niyyar kaiwa tsuggune dan duk zatonta shine zaisha abinsa sai taji yace, “Zauna anan”. Ya nuna mata gefensa yana cigaba da aikinsa.       Taji ko tamkar ta kurma ihu, dan duk da kujerar doguwace yazo kusan tsakkiyane ya zauna, hakan yasa inda ya nuna mata ɗin dolene zai basu kusanci matuƙa idan ta zauna. Shiɗin ba abin wasanta bane a kafin yau ma ballantana kuma a yau ɗin da take jinsa a sama ƙololuwa da girma, a can ƙarshe takai zaune tana ɗan gyara lafayar dake neman zamowa.        Ɗan dubanta yay a karo na farko ya ɗauke kansa ya maida ga abinda yakeyi, “Maza shanye ki bani kofin”. A yanda yay maganar ya sake tabbatar mata da umarninsa, sannan ko banza ma dai tanajin kunyar, dan dama dawowarsu daga wajen walima ne Hajiya iya ta tilasta mata shan tea ganin bataci komaiba a can sam. Kusan rabi tasha tace ta ƙoshi, bai tanka mataba bai kuma kalletaba yanata aikinsa. Tsahon minta ɗaya ta fahimci baima da lokacinta sai ta cigaba da shan shayin hawaye na ziraro mata, cikin dabara take saka bakin lafaya ɗin tata tana sharewa harta kammala shanyewa ta miƙe da kofin a hannu.      Tunanin ina zata kai ya sata duƙar da kai ƙasa, muya na rawa tace, “Ina ne kitchen?”. A yanda tai maganar ya tilasta masa ɗagowa ya dubeta na kusan sakan huɗu, ajiye lap-top ɗin yayi gefe ya kamo hannunta ya sake zaunar da ita kusa da shi, kansa tsaye ya janye lafayan data sa har a saman kai da ɗaura hannunsa a saman wuyanta. Sosai jikinta yay zafi. Kansa ya ɗan girgiza batare da yace komaiba ya miƙe tare da ɗaukar cup ɗin ya fice, zamewa tai a hankali ta jingina da kujerar tana lumshe ido da jan ajiyar zuciya, acan ƙasan ranta kuwa fal mamakinsa take da gulmarsa akan ashe yana da ɗan sauƙin kai.         Tashi tai zaune jin ya sake dawowa, kanta a ƙasa harya ƙaraso ya sake zama a inda ya tashi yana miƙa mata magani da ruwa daya zubo a glass cup, babu musu ta amsa dan tana buƙatar maganin kodan ciwon da kanta ke mata.         “Tashi ki cire wannan abun da kika naɗe jiki kamar magani kije ki kwanta”. Ya faɗa kansa tsaye yana ɗaukar lap-top ɗinsa ya cigaba da aikinsa. Miƙewa tai cikin bin umarninsa, sai dai gaba ɗaya tama rasa ta ina zata fara warware lafayar saboda tsananin kunya da shakkarsa. Ta saci kallonsa yafi sau goma, ganin shi hankalinsa ma nakan aikinsa yasata juya masa baya da fara warwarewa da sauri-sauri, ko batun linkewa bataiba ta ajiyeta gefenta ta haye gadon taja bargo har wuyanta tana sauke ajiyar zuciya dajan numfashi a gwame.        AK daba kallonta yake ba, burinsa kawai ya kammala aikin shima ya kwanta dan kansa ya fara ƙarfafa ciwo ya ɗan dubeta jin ajiyar zuciyar data ja da ƙarfi. Ita kam runtse idanunta tayi da fatan barci ya ɗauketa ko zataji sassauci da nutsuwar halin da take ciki a yau. Har yanzu ta kasa daina imagine cewar Yayansu ne mijinta. Ta rasa miyasa su Granny sukai tunanin yin wannan kwamacalar? Inama laifin a bata Khalipha ko Moos'ab, amma maganar ta girmama Yah Abdul-Mutallab matsayin mijinta na aure.      Da wannan tunane-tunanen barci ya ɗauketa, harya kammala abinda yake ya fita a ɗakin kusan mintuna talatin sannan ya dawo, fitilar ɗakin ya kashe zuwa ta barci, ya nufi gadon ya hau yana ɗan yamitsa fuska saboda kansa dake masa ciwo. Sai da ya zauna yaɗan jingina da gadon yana furzar da huci da lumshe idanu, kusan minti ɗaya sannan ya buɗe da waiwayawa yana kallonta ‘Komanta mai sanyi dai-dai da yanayinta’ ya ayyana a ransa dakai hannu ya gyara mata bargon dake neman toshe mata hanci. Ya mata kallon kusan mintuna uku kafin ya janye idanun nasa da sauke ajiyar zuciya.         Cikin barci Zinneerah taji kamar an sakata cikin wani abu mai ɗumi da yafi bargon bata kariya daga sanyin da takeji, taja numfashi da iskarsa ta haɗa da daddaɗan ƙamshin turarensa wajen shige mata hanci, gabantane ya faɗi dan tabbas ɗumin yayi kama dana jikin mutum, babu shiri ta buɗe idanu duk da ɗakin babu wadataccen haske kuma kanta na'a ƙirjinsa ne. Ba ƙaramin harbawa zuciyarta tayiba na tsoro, sai dai can wani shashi na gargaɗinta akan karta nuna ta farka zaifi taimakawa tsananin kunya da fargabar dake tare da ita.      Dole ta ƙarajin zuciyarta da jinin nikinta na cigaba da tsitsinkewa da tsananta sauri wajen gudu. Sarai ya fahimci ta farka, amma sai ya shareta saboda taimakama zuciyarta dake harbawar da har yake iya jiyowa bata salama. Su dukansu sun jima basuyi barciba kowa yana saƙa mai fisheshi, yayinda ɗumin jikinta ke raguwa saboda taimakon daya bata da jikinsa.  Daga ƙarshe dai su duka barcin ya ɗaukesu saboda maganin da suka sha. _________________★           A ɓangaren su Mammah kuwa ita da aunty Zakiyya barci sai dai ɓarawo ne ya figesu, sunason zaman tattauna abinda ke musu kaikawo hakan ya gagara saboda Mahma, daga ƙarshema Mahma hukunci ta yanke ita zasu kwana ɗaki ɗaya da Mammah, aunty Zakiyya kuna ta kwanta wajen Farah.      Wannan abu ya musu ciwo su duka amma babu damar magana. Itako tayi hakane saboda fahimtar take-taken Mammah akan son hana AK nuna kulawarsa ga amaryarsa. Rashin mafita yasa Mammah amsar wayar aunty Zakiyya ta sake turama AK saƙo bayan ta kirasa a wayar ta masa gargaɗin farko. sarai Mahma na lure da ita amma sai batai maganaba ta girgiza kai kawai tana nemawa ƴar uwar tata shiriyar UBANGIJI danshi tafi buƙata a yanzun.        ★★★★    Kiran sallar farko ya buɗe idanu kamar yanda ya zame masa jiki, dan ko a london yake a irin wannan lokacin yake farkawa duk asubahi saboda alarm da yake saitawa. Sam barcin bai isheshiba, hakan ya saka idanunsa yi masa nauyi matuƙa amma ciwon kan ya sauka. Akan Zinneerah dake nannaɗe a jikinsa ya saukesu, yanda fuskarta tai wani fayau a barcin ya sakashi nutsuwa wajen ƙare mata kallon kusan mintuna uku, hannunsa dake a saman cikinta ya ɗaga a hankali yakai ga fuskarta yaɗan tallafi kuncinta ta gefe da ɗaura babban yatsansa akan laɓɓanta da suka daɗe suna tsole masa idanu. Yatsan ya shiga zagayawa a kansu taushinsu da santsinsu na masa daɗi, duk dama aɗan bushe suke a yanzu.           Cikin barci ta dingajin kamar ana shafa mata lips, ga kuma hannunsa da kusan nauyinsa ke a ƙirjinta, ɗan motsawa ta shigayi alamar zata farka, sai kawai ya janye hannun nasa ya tashi zaune tamkar bashi ya aikata ba, buɗe idanunta yayi dai-dai da saukarsa a gadon yana faɗin, “Ki tashi kiɗan watsa ruwan ɗumi zakiji jikin ya saki gaba ɗaya”. Cikin muryar barci yay maganar dan haka ta fita a sanyaye da ɗan kauri kuma.       Bata iya motsawaba harya fice dan wata irin matsananciyar kunya ke cinta, wai yau itace kwance a gado ɗaya da Yayansu. Jikinsu manne da juna, kai itako ina zata kai wannan abun kunya yau. Da wannan tunanin ta miƙe da ƙyar ta nufi toilet domin yin amfani da shawrsa nayin wanka.         Tako ji daɗin wankan, dan jinta take fayau saboda zazzaɓin ya saketa, tana fitowa jikinta kawai ta tsane ta ciri doguwar rigar jallabiya a akwatin daya cirar mata kayan barci jiya ta saka, ta ɗauka turare a handbag ɗinta ta fesa sannan ta saka hijjab domin yin salla.                      Bayan ta idar da ƙyar ta iya zaman yin azkar, tanayi tana gyangaɗi harta samu ta kammala da ƙyar ta sake komawa gadon ta kwanta dan wani irin barci takeji bana wasaba.      Shima koda ya dawo daga massallaci sashensa ya wuce ya sake kwanciya koma azkar ɗin shi bai iya zaman yiba.           ★★★          A gidansu Hajiya iya kusan baƙi duk sun tashi da haramar wucewa yau, musamman ma ƴan danya da jikin Tinene ya rikice, dan kwana tai tana sheƙa amai a daren jiya, sai gabannin asuba tai barci. Da safe basu tadataba har suka kammala shirinsu, kusan ƙarfe takwas aka kawo musu abincin kari suda ƴan ɗanmusa da suma suke shirin fitama da wuri dan zasu biya ta gidan mmn sadiq su.          Zuwa ƙarfe goma duk suka kammala abinda sukeyi, har Tinene ma an tadata ta shirya sai dai ta kasa cin komai duk ƙaunar abinci da takeji a ranta. Hajiya iya data shigo suka gaisa ganin sunta shiri take tambayar badai tafiya da sassafen nanba kamar korarru?.        Cikin jin nauyinta da girmanta sukace tayi haƙuri zasu tafi haka nan ai anci biki Alhmdllh. Da yawansu sunbar yara a gida kuma.       Godiya tai musu da addu'oin fatan alkairi, tace su ƙarasa shirin to a fara kaisu gidan amarya. Gwaggo Laritu ce tace, “Hajiya ai dama an barshi kawai tunda jiya munje”.         “A'a ya kamata kuje gaskiya itama zataji daɗi, jiya duka zuwan minti nawa akai, ku ƙarasa shirin kawai bara naje na shirya abincinsu suma”. Daga haka tai sallama da su ta fice.     ★★★     Kusan tara da rabi Zinneerah ta farka, yanda ta ƙarajin ko ina na jikinta ya ƙara saki taji daɗi, gadon ta gyara tsaf, duk da ɗakin ba wani datti yay ba ta fito neman kayan shara. Sosai falon yay mata ƙyau, komai na cikinsa ya kasance ash color da ɗan ratsin pitch kaɗan-kaɗan, sai ƙamshi ke tashi mai daɗi na turaren wuta. Sake fitowa tai inda nanma falo ne da yafi na ciki girma sosai mai ɗauke da bedrooms biyu sai ƙofar kitchen da zakabi ta dining, kalar komai dake a falon ta kasance lemon green and light orange. Fallon babbane dan yafi wanda ta baro, samun kanta tai da leƙa bedrooms ɗin suma ta gani, ɗaya akwai gado a ciki da komai na kayan ɗaki brown da sukai matuƙar ƙyau, dan shima ya burgeta sosai, tana kuma ƙyautata zaton sune ƙoƙarin iyayenta. Har bathroom sai da ta leƙa tana maijin ƙaunar Abba da Baba har cikin ƙoƙon ranta. Daga haka ta fito ta leƙa ɗayan ma. Shikam katifa ce kawai aciki babba sai ƙaramar drawer da mirror. Shima dai ya mata ƙyau ɗin. Ta dining tabi zuwa kitchen, shi kansa dining ɗin abin kallone. Data shiga kitchen kam ai bama tasan sanda hawaye suka silalo mata ba, tasa hannu ta share da jama iyayenta da Granny ƙyawawan addu'oin gamawa da duniya lafiya. Anan ta samu kayan sharar datazo nema ta ɗakko ta fito. Iya bedroom ɗinta kawai ta share ta goge dan shine kawai tama fahimci yana buƙatar hakan, sauran kuwa ta bisu da fresheners masu daɗin ƙamshi da turaren wuta kasancewar akwai nepa. Gaba ɗaya sashen ya ɗauki ƙamshin dake sake tabbatar da ita a amarya, daga haka ta koma ta sake kintsa jikinta ta shirya cikin shadda less skirt da riga kalar light pink. Sosai kayan sukai mata ƙyau, tana tsaka da ɗaura ɗan kwali take jiyo ƙarar door bell. Da sauri ta ƙarasa da ɗaukar turare ta ƙarama jikinta taja mayafi ta rataya a kafaɗarta tunda bata da tabbacin wanene. Tana tafiya tana ƙoƙarin saka abin hannunta da suka rage bata sakaba.         Tana isowa babban falon gidan daya haɗa duka sassan nasu shima yana fitowa daga nasa sashen cikin ɗanyar shadda daketa maiƙo da ɗaukar idanu, ɗinkin heif jamfa data sake fidda ƙuruciyarsa da kwarjini honey color. Dabircewa Zinneerah ta nema yi, babu shiri taja birki da saurin duƙar da kanta ƙasa.        Shikam kansa tsaye yake dubanta daga sama har ƙasa yana cigaba da takowa. Ta gabanta ya wuce zuwa ƙofa da aka ƙara dannawa ya buɗe yana ƙoƙarin dai-daita yanayinsa.        Babu shiri Jamal da Nawaff ɗan Uncle Ahmad suka sake nutsuwa da fara gaishesa. Batare da ya amsa musu ba ya matsa baya ya basu hanya alamar su shigo. Shigowar sukai kowanne ɗauke da basket da aka lulluɓe da farin ƙyalle. Sake gaishe da yayan nasu sukai sannan suka dubi Zinneerah fuskokinsu washe da murmushi kamar yanda itama nata murmushin yaƙi ɓoyuwa duk da batasan Nawaf ɗin ba ita.      Jamal nason ya tsokaneta babu dama. Dan haka murya ƙasa-ƙasa yace, “Good morning auta”.        Sai da ta ɗan saci kallon AK daya wucesu sannan ta amsa masa da, “Morning small bro”.      Ƙaramar dariya Nawaf yayi shima yana gaisheta. Duk da bata sanshiba ta amsa da kulawa dan kamanninsa da Jamal ɗin ya tabbatar mata shima jininsu ne, sai tayi tunanin ko cikin ƴaƴan Mommy ne tunda Huzaifa kaɗai ta sani har yanzun.        Sanin halin yayansu yasa Jamal haɗiye duk wani surutunsa yace, “Ga abinci inji Momie mu bara mu wuce tunda boss na gida, amma daya fita zamu dawo yasin”.        Murmushi kawai Zinneerah tayi da girgiza kanta. Ta amshi baskets ɗin hannayen nasu biyu tana godiya da tambayar Granny dasu Meenal?.       “Granny na gaisheki, su Meenal kuma anjima zamu dawo, ki kuma shirya baƙi na nan tafe inji Granny. Bara muje sai mun dawo”.      Daga haka yaja hannun Nawaf suka fice. Jitai kamar karsu tafi, badan tasoba ta nufi hanyar sashenta dan can AK ya shiga. Zaune ta samesa a falon farko yana waya, da alama da Mammah yakeyi saboda ambatar sunanta da taji yayi. Saɗaf-saɗaf ta wuce dining da kayan shiko ya bita da kallo.      Duk da bata da buƙatar cin abinci tasan ya kamata shi ta bashi, dan haka ta nufi kitchen ɗakko plate da abinda duk ya kamata bayan ta ɗaurayosu. Har lokacin wayarsa yakeyi, sai kawai ta shiga ƙoƙarin duba abincin kafin ya gama taji mizaici a ciki?.        Tana ƙoƙarin buɗe kular farko ta kasa kawai taji ƙamshin turarensa ya sake kusantota. Batai yunƙurin juyawaba ta cigaba da abinda takeyi. A hankali AK ya sake matsota, ta bayanta shima ya ziro hannayensa da ɗaura kansa bisa kafaɗarta har gashin sajensa na tsikarar mata fatar kafaɗa zuwa gefen wuya, numfashinsa na sauka a dokin wuyan nata, ya manna ƙirjinsa da bayanta sai kawai ta saki kulan da take ƙoƙarin buɗewar babu shiri jikinta na rawa...............✍ 🚶🏻mudai dangin aunty Farah muna kishi😒😒😕🤧😏😏. *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_* *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* _________________________ *Page 53* ............Bai nuna yama fahimci yanda ta firgitan ba ya fara magana a hankali da ƙoƙarin buɗe kular tana a jikinsa. “Wannan ba aikin amarya bane, koda yake amaryan marowaciya ce”.       Yanda yay maganar a saitin kunnenta yasa tsigar jikinta tashi, ga ɗunbin mamakinsa dan batai zaton sa hakaba sam. ta ɗan ƙanƙame jikinta daya fara rawa dan wannan shine karon farko a rayuwarta data kasance da namiji a irin wannan kusanci. Abin tashin hankalin ma da ɗunbin kunya namijin ya kasance Yayansu, abinda bata taɓa kawowa a mafarkintaba balle hasashe.         Ƙamshin naman kazar da akaima gyara na musamman dake kular daya buɗe ɗin taɗan kalla jin yace, “Uhm-uhm Momie ta hutar dani sayen kazan amarya kenan”.         Ba ƙaramin mamakinsa ke ƙara dasuwa a rantaba, ta haɗiye yawu da ƙyar dan bata da burin daya wuce ya matsa daga manneta da yayi. Harta fara murna ganin ya maida kular ya rufe, ya ɗan matsa baya kaɗan yana raba jikinsa da nata. Sai kuma taji ya kamo hannunta cikin nasa ya juyo da ita suna facing juna.       Sake dulmiyewa cikin matsananciyar kunya tayi, tai azamar duƙar da kanta zuciyarta na harbawa da sauri-sauri. Shiko tsaywa ya gyara da ƙyau yana tura hannayensa cikin aljihun wandonsa. Duk da kanta a duƙe yake tanajin yanda idanunsa masu kaifi da ƙarfi suke yawo a jikinta. Tsahon mintuna biyu suna a haka har takaita ga daburcewa takai tsugunne tana cemasa ina kwana.       Dariya ta bashi sosai, musamman daya san dama da biyu yay mata hakan, amma ya gimtse baiyiba. Sai ma ɗan ranƙwafowa yay ya kamo kafaɗunta ya miƙar da ita tsaye tare da jawo kujerar dining ɗin ya zaunar da ita. Shima sai yaja ta kusa da ita ya zauna.         Yana ƙoƙarin buɗe kular dake kusa da shi cikin ɗan rawar muryar da jin nauyinsa ya haifar mata tace, “Kabari zan zuba maka Yayanmu”.       Komai baice mataba ya janye hannunsa. Hakan yasata miƙewa tsaye ta jawo plates ɗin data ajiye sannan ta bubbuɗe kukolin.          “Miza'a zuba a ciki”. Tai tambayar batare data yarda ta kallesaba.          “Duk wanda yay miki” ya bata amsa yana ƙoƙarin ɗaukar wayarsa da kira ya shigo.       Cike da fargabar karta zuba abinda bayaso ta haɗa komai a gabansa, harda kunun gyaɗa dake cikin flask madaidaici, daga haka ta ɗanja kujerar baya da nufin barin wajen ya riƙo hannunta. Juyiwa tai ta ɗan kallesa dan ta zata wani abun yake buƙata. Da idanunsa dake lumshewa da buɗewa kamar maijin barci yay mata nuni data zauna. Babu zance musu a tsakaninsu dan haka ta koma ta zauna.        Wayarsa ya cigaba da yi da ɗaukar wani cokalin bayan wanda ta saka masa ya ajiye a gabanta, ya ja kofi ya fara haɗa kayan tea dake a dining ɗin a ciki. Ita dai bata motsaba tanata satar kallonsa da tunanin ko bazaisha kunun bane?, harya kammala komai ya buɗe ɗayan flask ɗin da ruwan zafi ke ciki ya tsiyaya. Motsawa ya farayi dai-dai suna sallama da Huzaifa dake faman masa sheri, ya ajiye wayar gefe da ɗaukar kofin ya ajiye gabanta muryarsa ƙasa-ƙasa yace, “Bismillah”.       Dole ta ɗago kai ta dubesa. A lokacin shi kuma yana ƙoƙarin kai Irish daya ɗebo bakinsa. Kai ta ɗan girgiza tana marmar da idanu tace, “Yayanmu na ƙoshi ni sai anjima zanci”.        Bai fasa cin abincinsaba bai kuma tanka mataba. Hakan da yay ta tabbatar bata da amsa kenan, dan haka ta ɗauka kofin tea ɗin ta fara sha badan yana mata daɗi a bakiba saboda zazzaɓin da take fama a kwana biyun nan.       Ko'a can gidan tasan baya wasa da abinci, cinsa yake bil haƙƙi idan ya samu musamman zaɓinsa. Dan haka ta dinga satar kallonsa zuciyarta na tuno mata ko ina little yake yanzun?.      Ganin batacin abincin ya ɗago ya dubeta, karaf ya kamata tana satar kallonsa. Janyewa tai cike da basarwa. Yanda tayi ɗin ya sakashi sakin wani munafikin murmushin daya tsaya masa iya maƙoshi yana mai jinjina miskilancinta a ransa.        A fili kam sai yace, “Gulma dai ajaline. Kisa hannu kici abinci kona ɗura miki shi dan na gaji da wannan jan ajin.”        Wani irin waro idanu Zinneerah tayi a kansa babu shiri, har cikin ranta mamakine ke neman kasheta dan batasan bakinsa ya iya zaro zanceba kamar haka. Ganin yanda shima ya waro mata nasa manyan idanun masu kwarjini da faɗin, “Zancen nawa akwai gyara ne?” ya sata saurin janye nata zuciyarta na wani irin harbawa da sauri.         Dolene ta ɗauka cokalin ganin ya cigaba da tsareta da idanu, gashi duk wannan zaro maganar da yakeyi fuskarsa a ɗinke take kamar yanda ta sanshi. Tsakurar abincin ta farayi. Shima daga haka ya ɗauke kansa ya maida ga cin abincin.     Shine ya fara kammalawa saboda yangar da ita takema cin abincin ko nace kunya, ya cira tissue yana goge bakinsa da faɗin Alhmdllhi. Harta fara murnar zai tashi ya barta sai gani tai ya ɗaura hannunsa akan nata da take cin Irish ɗin da shi ya zare cokalin. Ɗebowa yay ya nufi bakinta yana ambaton “Haaah”.       Itakam yau taga idi, ta ayyana a ranta tana buɗe bakin domin bin umarninsa. Feeding ɗinta ya cigaba dayi har sai da ya tabbatar taci da yawa ta shanye tea ɗin daya haɗa mata rabin cup, dan tun acan gidan ya gama karanceta akan rashin son cin abinci.          Batare da yace mata uffanba ya miƙe ɗauke da wayarsa ya nufi bedroom ɗinta. Da kallo ta bisa tana sauke ɓoyayyun tagwayen ajiyar zuciya. Duk yanda taso tashi ta fara tattare kayan hakan ya gagara harya fito yazo ya wuce hannunsa ɗauke da ɗayar wayarsa, yanzunma baiyi magana ba.      Miƙewa tai ta shiga tattare dining ɗin tana ɗaukar kwanin da sukai amfani dasu takai kitchen. Zaman wankesu tayi, tana kammalawa kamar jira ta jiyo ƙarar door bell. Hannunta ta goge da ɗaukar mayafinta data ajiye ta yafa ta fito daga sashen nata gaba ɗaya zuwa general parlor. Ƙofarma ba wani a rufe yakeba, turawa kawai yayi, amma sai ta buɗe da tunanin ko bamai hurumin shigowa bane sai da izini.       Wani irin ɗan karen daɗine ya tsarga mata saboda ganin Bahijja da Meenal da tawagar su Yaya Gajeje da ƴan ɗan-musa. Suka rungume juna dasu Meenal, sannan ta sakesu ta koma gasu Gwaggo Laritu. har Tinene dake nishi da ƙyar na ciwo dasu Yaya Atine da suka saki baki suna kallon ikon ALLAH. Wai wannan shine gidan Zinneerah? Yarinyar da suke kallo a wulaƙance a ƙasƙance a cikinsu?......        Da wannan tunanin a zukatan mafi yawan ƴan Danya suka shigo ciki, inda anan nefa kallo ya koma sama. Bata barsu anan ba tai sashenta dasu, inda suka zube a falon farko su Meenal na mata magana ƙasa-ƙasa suna waige-waige.        “Madam naji ƙamshin turaren Yayanmu. ko yana ciki ne?”.       Hararsu Zinneerah tayi cikin gatse tace, “Eh kunada matsala da shi ne?”.    “Mu mun isa mu faɗa”. Cewar Bahijja tana sheƙewa da dariya da nufar ɗayan falon cikin sanɗa zata leƙa. Ɗauke hankalinta Zinneerah tai daga garesu ta maida kan ƴan uwanta daketa kalle-kalle kowa da kalar tunaninsa. Har ƙasa ta durƙusa ta gaida Gwaggoninta da yayunta, suka amsa mata suna jera mata addu'ar fatan alkairi da samun zaman lafiya a gidan aurenta. Ita dai bata iya ta amsa a fili ba dan kunya. sai su Meenal ke amsawa. Ita kuma ta kamo hannun Tinene dake kwance a ƙasa tana faɗin, “Tinene lafiya kike kuwa?”.       Da ƙyar tace, “Zazzaɓi nake tunda mukazo”.       “Ya salam amma shine ba'aje asibitiba? Anya Granny ta sani?”.      Meenal ce tace, “Gaskiya babu wanda ya sani, muma sai yanzuma mukeji”.       Sosai Zinneerah ta nuna tausayin ƴar uwar tata tanata faman jera mata sannu-sannu.        Tana kitchen tana haɗo musu abin sha Bahijja ta kawo mata waya zasuyi magana da Granny. Cike da ɗoki da kewarta ta amsa tana mata sallama a shagwaɓe. Daga can Hajiya iya tai ƴar dariya da faɗin, “Inno na kinfa girma”.     Sake marairaicewa Zinneerah tayi idanunta na tara ƙwalla tace, “Nidai a'a Granny. Ina kwana”. Hajiya iya na dariya ta amsa mata da tambayar lafiyarsu, sai kuma ta ɗora da tambayar “Baƙi sun sami Moddibo a gidan ko?”.        Cikin rashin tabbas Zinneerah tace, “Eh, amma dai basuga juna ba”.      “Oh to ai dama abinda nakeson ji kenan. Ki kira musu shi su gaisa ya sansu su sanshi. Ki nuna masa Gwaggonninki da ƴan uwanki su Gajeje”.       A ɗan tsorace Zinneerah tace, “Amma Granny......”        “Amma mi? Inno idan bai sansuba a yanzu yaushe zai sansu? Suma kuma ai ya kamata su sanshi. Banason shashanci maza jeki kira musu shi su gaisa karya fice wannan sarkin sabgogin”.       A sanyaye tace, “To Granny”. Dole badan taso ba ta nufi cika umarnin Granny bayan ta kawoma baƙin ruwa da lemon da aka tanada dansu ita da su Bahijja, tana ɗan sissinne kai tacema Gwaggo Laritu “Bara na kira Yayanmu ku gaisa”.        Cikin fara'a Gwaggo Laritu tace, “Eh to ai haka shine dai-dai, ya kamata muga ɗan namu kar ai shirme shima ya gammu kuma”.     Ita dai Zinneerah kai kawai ta kaɗa mata, ranta fal fargaba ta fito daga sashen nata, dan ko nashi sashen ba sani tai ba. Tsaye tai a general falo tana ƙarema kowacce kusurwa kallo cike da fargaba. Ita yanzu ina ita ina shigar masa ɗaki banda dai rigimar Granny da bata ƙarewa dan ALLAH?.        Ƙofar dake facing sashenta ta fara zuwa ta taɓa. jinta a kulle sai zuciyarta ta bata maybe sashen matarsa ne. Ta kalli wadda take a tsakkiyarsu ranta na biya mata nan ne nashi. Mayafinta ta gyara da ƙyau ta nufi ƙofar zuciyarta na rawa na shakku da ganin kamar ta zaƙe. Sai dai tasan bata da mafitar daya wuce bin umarni. Koda ta buɗe ƙofar tana rumtse ido da corridor ta fara cin karo saɓanin nasu da falo ne. Ta ɗan ƙarema corridor ɗin daya sha ado da kallo kafin ta ɗaga ƙafa daƙyar zuwa ƙofar data gani ita kaɗai. Anan kam batai gigin tafiya kai tsaye ba sai tai knocking a hankali kamar mai tsoron a jita. Shiru babu alamar akwai motsin mutum sai ta ƙara da ɗan ƙarfi fiye dana farko. Nanma dai shiru, ta ɗaga hannu zata ƙara na biyu aka buɗe ƙofar. Baya taɗan ja tana mar-mar da idanu.        Jin ƙamshin turarensa yasata ɗan dubansa zatai magana ya juya ciki da barin mata ƙofar buɗe alamar dai ta shigo. Sai da ta cije leɓe da dafe goshi irin (mutum nan ko) sannan ta bi bayansa.       Masha ALLAH ta ambata a zuciyarta saboda yin tozali da ni'imtaccen falon nasa dayaji kayan kuɗi. Komai na cikinsa lemon green and milk color ne. Sai ƙamshi ke tashi ga uban sanyin ac da tsigar jikinta har tashi takeyi. Bata da zaɓin daya wuce ƙarasawa inda yake dan tuni ya koma inda ya taso zaune cikin kujera 1seater takardu barbaje a kan centre table ɗin daya maida gab da kujerar alamar aiki yakeyi. Sai dai yanzu ya zauna ne ƙafa ɗaya kan ɗaya yana kallonta harta ƙaraso tana harhaɗewa saboda idanunsa masu kaifi gareta.        Idanunsa ya ɗan lumshe yana ɗauke kansa daga kanta zuciyarsa na jinjina rashin saurin sabonta, ganin zata kai tsugunne ya sake maido dubansa gareta, “Banason wannan durƙuson zauna a kujera”.     Bata musa masaba ta zaune a kujerar dake gab da ita. Kanta a ƙasa tace, “Dama baƙine su Gwaggo sukazo, sh.... Shine Granny tace na faɗa maka ku gaisa”.        Kallon yanda take cuɗa yatsun hannunta dake cikin jan lalle da baƙi kawai yake, ya ɗan ɗauke kansa yana girgizawa. “Taso nan ki sake maimaitawa banjiba”.        Ɗagowa tai ta ɗan kallesa. Ganin yanda ya ɗauke kai gefe yana ƙoƙarin rage sautin tv ya sata ɗan tura baki, dan ita dai tasan babu yanda za'ai ace ba'a jitaba. Miƙewa tai ta nufesa. Zuwanta gab da shi dai-dai da ajiye remote ɗin hannunsa. jitai kawai ya riƙo mata hannu sai gata a saman cinyarsa.      Ba firgitaba kaɗan ya rage tayo aman zuciyarta a tafin hannu dan razana da ɗunbin mamakinsa. Ganin yanda ta daburce ya riƙo haɓarta yana juyo da fuskarta saitin tashi, ƙoƙarin ganin sun haɗa ido yake amma taƙi. Sai jikinta dake tsuma. “Maimaita”. Ya faɗa yana ƙara ɗago haɓarta.       “Granny ce dama tace na kiraka ku gaisa da baƙi”. Ta faɗa da in ina.      Idanunsa akan laɓɓanta yace, “Inda bataceba fa?”.. Shiru tai dan batasan amsar da zata bashiba. Cikin matso da fuskarsa daf da tata yace, “Uhmyim”.     Sosai tsigar jikinta ya tashi ta fara marmar da idanu dake neman fara tara ƙwalla.      “Oh, inada hanyoyin da zaki magantu ai”. Ya faɗa yana sake matso da fuskarsa daf da tatan har hancinsu na gogar na juna. Ba ƙaramin wantsalawa hanjin cikin Zinneerah sukaiba, mamakin Yayan nasu na neman kasheta. A bazata taji saukar laɓɓansa saman nata. Bama tasan ta zazzaro idanuba. da wannan damar ya samu saka nashi idanun cikin nata suna kallon juna. Duk yanda taso ta kauce nata hakan ya gagara sai jikintane ya hau ɓari jin yanda yake sarrafa lips ɗinta cikin bakinsa.        Tsabar ruɗewa bama tasan ta faɗa jikinsa ta ƙanƙamesaba saboda neman hanyar kuɓuta. Hakan datai ya masa dai-dai shikam, sai kawai ya lumshe idanunsa yana ƙara adanata a jikinsa.         Sai da ya tabbatar ta ruɗu sannan ya sarara mata. Jin ta ƙubta ta cusa kanta a ƙirjinsa jikinta na wata irin tsuma. rungumeta yayi shima da ƙyau yana murmushi da lumshe idanunsa wani irin kasala na neman saukar masa. Bakinsa ya kai saitin kunnenta muryarsa a ƙasan maƙoshi sosai yace, “A ƙara ne?”.       Duk da yanda jikinta yay laushi bata san tama zabura ta miƙe ba. Karan farko a rayuwarta dataga yayi murmushi har haƙoransa na bayyana. Baya ta juya masa tana rumtse idanunta itama murmushin na suɓuce mata da sabuwar matsananciyar kunyarsa.          Batare da ya sake ce mata komaiba ya miƙe shima yana gyara rigarsa data ɗan yamutse saboda zama da tai a cinyarsa. Raɓata yay ya wuce. Sai da yaje fita ya ɗan juyo ya kalleta har yanzu fuskarsa da sauran murmushin ɗazun. Saurin jan mayafinta tai ta rufe fuska............✍ *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_* *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* _________________________ *Page 54* ...........Duk yanda taso dojewa a baya doleneta ta yarda suka shigo sashen nata a tare, kusan duk sai da suka ɗago suka kallesu jin sassanyar muryarsa na sallama. Bayansa ta koma ta maƙale saboda kunya da taji na iyayenta da ƴan uwanta. Gani take kamar kowa zai gane abinda ya faru kafin su shigo, Aunty Salima ce ta bashi kujerar da take zaune. Babu musu ya zauna yana musu sannu da zuwa fuskarsa a ɗan sake.     Cikin mutunta juna sukai gaisa. Yana musu godiya suna masa, tare da jera musu addu'oin zaman lafiya mai ɗorewa na har abada da zuri'a mai albarka da nagarta. Gwaggo Maryama ce tai masa bayanin kowa a wajen da matsayinsa wajen Zinneerah, ya ƙara musu godiya yana ambaton masha ALLAH. Kafin ya miƙe bayan suma su Meenal sun gaishesa.      Sai da yazo saitin Zinneerah dake tsaye yay magana ƙasa-ƙasa yana raɓata ya wuce. “Ki sameni idan sun tashi tafiya”.       Binsa da kallo kawai tai ta gefen ido dan ya riga ya shige bai bata damar amsa masaba. Hankalinta ta maida akan ƴan uwanta dake yabonsa da sake jera masa addu'an fatan alkairi. Ita dai uffan bataceba sai zama data sakeyi. Sun ɗan ƙara taɓa hira kafin su mike domin ganin ɗaki. Lungu da saƙo babu inda basu shigaba, Sa'a nata santi da ƙarajin daɗin sauyin rayuwa da ƴar uwarta ta samu. Hakama Yaya Gajeje bakinta yaƙi rufuwa dan farin ciki. Karima da Atine kam dai anata naɗar rahoton da za'a kaima Inna fuska a taɓe.      Babu wanda ya damu dasu, dan ƴan ɗan-musan ma dasu Gwaggo Laritu sai faman yabawa sukeyi abinsu. Bayan sun gama zagayensu sukai haramar tafiya, maganar cewa ta sameshi yasata cewa su jirata tana zuwa. Duk da ranta cike yake da fargabar abinda ya faru ɗazun ga kunyarsa haka dole ta nufi sashen nasa again.        Yanzu kam bata tsaya knocking ba sallama kawai tayi da murɗa kofar ta shiga, yana tsaye alamar shirin fita yake ta shigo bayan ya amsa mata sallamarta da bata izini. Kanta a ƙasa saɓanin shi da yake kallonta kai tsaye, yanda batai magana ba shima baiyiba, sai ma ya ɗauke kansa daga kallon nata yana ƙoƙarin tattare takardun daya baza a falon. Ganin haka yasata faɗin, “Yayanmu zasu wuce”.       Bai amsataba sai da ya gama abinda yakeyi, ƙananun ledoji guda biyu dake a saman kujera ya nuna mata, “Ki bama Gwaggo Maryam ɗaya taba ƴan ɗan-musa, ɗayan ki bama Gwaggo ta danya nasune suma”.        Ɗaukata tai tana kaiwa tsuggune. “ALLAH ya saka da alkairi ya ƙara arziƙi mai albarka da amfani, ya cigaba da baka kariya a dukan al'amuranka”.       Har cikin ransa yaji daɗi da farin cikin wannan addu'a tata, dan haka yay ɗan murmushi yana amsa mata da “Amin, nagode”.              Kamar yanda ya bata umarni haka ta aikata, aiki suka shiga godiya da masa addu'a harta rakosu harabar gidan ita da su Meenal. Kasancewar motocin da zasu wuce dasu suna ta waje yasata jan birki iya nan tana hawaye. Rungumeta Sa'a tayi itama tana hawayen, dan harga ALLAH tanason Zinneerah. jitake kamar karsu rabu a yanzu, amma yaya zasuyi da ƙaddarar aure sai haƙuri.       Tanaji tana gani suka wuce su Bahijja suka tafi rakasu har waje. Jikin bango ta lafe hawaye na cigaba da sakko mata, ɗan kwana ukun can da taje tayi a Danya sam ba isarta sukai ba, musamman da ayanzu baba ya samu ƴancin kansa daga hannun Inna, sai taji inama tana a zaman gidan ne har yanzu.           Dawowar su Bahijja ya sata share hawayenta suka koma ciki suna mata tsiya ƙasa-ƙasa gudun kar Yayansu yaji. Ita dai hararsu kawai tayi dan basusan yaya takejinta bane. Da taimakonsu ta gyara falon, suna ƙoƙarin dasa zaman hira AK ya shigo. Tsit sukai daga dariyar zancen Meenal dake basu labarin abinda wata innarsu datazo daga bauchi tayi a sashen Granny yau da safe.        “Ku baku wuce ba?”. Ya faɗa idonsa akan Zinneerah. Meenal ce tai ƙarfin halin bashi amsa. “Yayanmu muna nan sai anjima, dan ƴan bauchi ma zasu zo suyi muku sallama”.      Baice komaiba sai kallon agogon hannunsa da yayi ya sake duban Zinneerah. “Ni zan fita, Khalipha zaizo da mai gyaran ruwa dake fita ta baya, idan sun gama ki ɗauka masa kuɗi a ɗaki saman bedside drawer”.        Kanta ta gyaɗa masa da cewa “to” idanunta a ƙasa. Daga haka shima ya juya ya fita a binsa suna masa a dawo lafiya.      Sai da suka tabbatar da fitar motarsa a gidan sannan bakin su Meenal ya buɗe. Suka sheƙe da dariya suna tafawa da faɗin, “Soyayya ruwan zuma. Abin mamaki Yayanmu da auta a gado ɗaya”.         Hararsu kawai Zinneerah tayi ta ɗauke kanta. Bahijja ta kamo hannunta murya ƙasa tace, “Tawan dan ALLAH da gaske ɗaki ɗaya kuka kwana da Yayanmu a gidan nan?”.       “Ya ilahi”. Zinneerah ta faɗa tana zaro idanu, sai kuma ta rankwashi kan Bahijjan da faɗin, “Kirasa a waya ki tambayesa mana, wai yaushe kuka lalace haka ne?”.         “Karkiga laifinmu, tunda kema jiya Yayanmu ya lalataki a gado muma gara dai ku guntsa mana kafin a kaimu dan wlhy nima aure nakeso”. Cewar Meenal tana wani karya jiki.      Bahijja tai zaram tana faɗin, “Haɗa dani ƴar uwa”.     Kallonsu kawai Zinneerah take baki buɗe, suko ko'a jikinsu. A haka su Jamal suka shigo suka samesu ɗauke da abincin rana, yanzu kam a sake suka shigo dan sunsan sun baro boss a can gidan. ___________________★         A ɓangaren su Farah kam lafiya lau ta farka yau, sai dai tunda ta tashi hawaye basubar sauka mata a idanu ba, sai faman sambatu take akan dan ALLAH suce mata mafarki take bada gaske AK yayi aure ba.      Da farko daga Mammah har Mahma lallashinta sukeyi, ganin abun nata bana ƙare bane yasa Mahma fara mata masifa.      “Ke dan ALLAH kin ishemu haka nan, ba'irin wannan ranar ake hanngo mikiba ana nuna miki hanya kina kaucewa. Ni bansan wane irin rashin hankali ke damunku ku yaran yanzu da bakwa aiki da tunaninku ba. Abinda kawai kuka ɗauka idan namiji na sonku dolene ya cigaba da sonku, kun manta ita soyayya ado ce a cikin aure, a duk lokacin da ɗiya mace ta kasa toshe ƙofofi da ramukan ginshiƙan aurenta adon soyayya zai disashe. Duk yanda zakiso miji ki nuna ƙin danginsa rayuwar aurenki na cikin matsala koda kuwa su suna nuna miki basa son nakine ƙiri-ƙiri a gabansa. Koda shike kawo miki sukar danginsa ki faɗi alkairi da tausar zuciyarsa karki yarda ki tofa mara daɗi. Kiyi haƙuri da halayensa ku kashe ku rufe a ɗakinku dan kai ƙarar miji ga iyayenki ko nashi na zubar miki da kima, ke hatta ƙawayenki kikace ke kullum ƴar fallasa asirin gidankice da niyyar neman shawara to kina cikin kwan gaba kwan baya kuwa a garesa da zubar muku da kimar aurenku. Domin shi aure ibada ne ba komai ake samu hundred percent a cikinsa ba. Dole yau ayi dariya gobe kuka, jibi rabi da rabi tsakanin ɓacin rai da farin ciki. Sannan duk son da namiji ke miki kika nuna zaƙewa da yawa akan kishinsa har zargi na zuwa miki a harshe da tunani to lallai ki tabbata zaki koma 0 a ziciyarsa. Matan yanzu da yawa ba kishin mazansune kaɗai matsalarsu ba, harda zargi. Idan miji ya fita zuciyarki na miki kaikawo yanacan tare da wasu matan, idan ya shigo gida ya ɗauki waya bazakiyi masa zaton alkairi ba sai kice yana cheating da wasu matan. Idan yana huɗɗa da mata a ikinsa ko kasuwanci zuciyarki taita kitsa miki karuwansa ne, idan mai yawan sakewa ne da mutane ki zargesa da yawan son mata. To dama kin taɓa ganin namijin daya rayu babu mace a ransa? Komin tsanani da tsantsenin ki baki isa hana namiji ɗabi'ar son mata ba dan haka ALLAH ya haliccesu, ba kamar ke bace da akai miki iyaka dakinyi aure shikenan. Daga lokacin da kishi ya sakaki yawan zargin miji koda hankalinsa baya kan matan ma to zai fara nutsuwa wajen fuskantarsu, daga ƙarshe kodai ya ƙaro auren da kike tsoro, ko ya fara bin matan a waje su halakashi kema ya halakaki, waya janyo?. Ki nutsu ki zama jaruma ta kowanne fanni, nasan yaƙine ba ƙaramiba amma inhar kinsa kanki zaki iya, koda kina kishin mijinki ki dinga dannewa kinayin mai aji wanda shi kansa zaisa yaji shakkarki akan wata macen, da kuma shiga damuwar anya ma kina sonsa? Ya dingaji ƙaimi wajen kafa soyayyarsa a gareki dan yaga wannan kishin naki amma hakan ya gagaresa, sai kiga yafi lalacewa a wajenki fiye da wadda yake hange a wajen. Duk da nasan maza kala-kala ne kuma kowanne da irin nashi salon, ki nutsu ki karanci nakin, ki daina kuma tilastama kanki sai kin samesa ɗari bisa ɗari yanda kike buƙata. wannan bamai yuwuwa bane a gareki, dan kema baki cika hundred percent ɗin ba a garesa. Mijinki na sonki Farah, yana kuma miki kawaici darajar mahaigiyarsa da na zuminci, amma kinata ƙara sakaci da damarki, wadda idan har kikai wasa anzo gaɓar da zaki iya rasashi ma baki ɗaya wlhy, dan Abdul-Mutallab yana tarakine kawai, ina jimiki tsoron randa zai kai ƙarshe a al'amuranki, duk yanda kike tunanin Hindatu na tsaya miki bazai sauraretaba itama, sai kuma kin fita kwana a ciki dan ita uwa ce babu yanda zai mata. Aurensa bashi ke nufin ƙarshen rayuwarki yazo ba, yanzune ma ya dace ki zage damtse wajen dawo da kimarki da martabarki a wajensa, inba hakaba kuka yanzu kika fara dan zaibi ta hanyar ƙara auren nasa ya rama dukkan ƙuntatawar da kike masa ke da Hindatu, hakama danginsa zasuyi amfani da ita wajen ganin sun rusaku ke da ita ɗin tunda kin shiga makarantarta babu gaira babu dalili, itama ɗin da take hura hanci sun mata laifi banga ta inda sukai matanba balle ke da kikai taka haye akan abinda bakisan yaya yake ba. Ƙiri-ƙiri tana amfani dake akan wani shashanci nata mara tushe balle makama. Sai ki shiga hankalinki idan zaki shiga, dan daga ita har Zakiyyar ba hanyar da zata ɓille dake suke ɗauraki ba”.       Tana kaiwa nan ta miƙe ta barta da sharɓar kuka tana nazarin maganar Mahma ɗin dalla-dalla. Dan tabbas sanda bata zama haka ba dukkan kulawa da tattalin rayuwa Yah Abdul-Mutallab yana batasu, danshi mutum ne mai kawaici, idan kuma ya ɓalle bayajin bari. Yasha nusar da ita illar kai ƙararsa da takeyi ga Mammah da Aunty Zakiyya amma ta kasa fahimta, dan a ganinta Mammah da Aunty Zakiyyar ne kawai zasu iya saita mata bauɗaɗɗen halinsa na tsiya koda yanaso ko bayaso. Ashe ba haka bane, sake kangarar masa da zuciya kawai sukeyi da kusantashi da dangin nasa da suka tsana. Itakam ta shiga uku, wlhy bazata iya zama da wata ɗiya mace a matsayin kishiya ba koda kuwa ƴar waye.        A lokacin da Mahma da Farah ke wannan maganar Zakiyya da Mammah nacan sun kulle kansu a garden suna maganar da suka gagara samun sararin yi tun ɗazun.       “Mammah inajin tsoro wlhy, anya mutanen nan basu fahimci wani abu daga garemuba suketa ambaton zancen dashen ciki? Gashi munyi sakaci wannan harmutsin na neman kaimu ga tonon silili, lokaci yayi da Farah zata koma Morocco da zama harta haihu amma hakan ya gagara. Kigafa yanda abokinsa yayi jiya da akace tanada ciki”.        “Hakane Zakiyya, nima kaina da abin nan na kwana a raina jiya, babban tashin hankalina kuma yaƙin da mukeyi ɗinma baiyi amfaniba, tunda gashi dai Kabeer na neman cin galaba a kaina tunda sun aura masa wadda suke so ɗin, amma na ɗau alwashin sai Abdul-Mutallab ya saketa wlhy. Babban tashin hankalina a yanzu zancen yaron nan da Abdul-Mutallab ya haifa da yarinyarnan. Nasanshi sarai akan faɗar gaskiya, da ace ya aikata wani abu a gareta har aka samu cikin ko zamu kashesa sai ya faɗi yanda akayi, amma ki dubafa yace shima baisan yarinyarba sai a gidansu, kuma ma idan mukai aiki da hankalinmu muma ta ina zai santa? ita da akace a wani ƙauyen ƙayau take da ko kwalta basu da. Wlhy na rasa ina tunanina zai shiga, yarinyar dai dana san anyima aikin farko a gabanmu tai ɓari balle muce ko ƙarya tai mana taje ta haihu a wani waje. Kuma bama ita bace wannan dan waccan babbace ma ai, wannan kuwa yarinyace ƙarama fa sweet 17”.      Gumi aunty Zakiyya ta share wani bahagon tunani nason mata kutse a ƙwaƙwalwa, ta haɗiye yawu da ƙyar tana gyara tsaiwa, “Mammah inason ganin ita wannan yarinyar dan kinsan ni bamma santaba”.      “To Zakiyya miye amfanin ganinta tunda tunda ba wani abu muka haɗa da itaba. Ko akwai wani abu da kike tunani wanda ni ban sanshiba?”.      “A'a wlhy Mammah ”. Tai saurin faɗa tana girgiza kanta da ƙara share gumi.       “To kin gani. ai ganin nata baida amfani dan jira nake yazo gidan ma yanzun nan ya rubuta mata takardar saki ta kama gabanta. A yau kuma nakeson mubar ƙasarnan da Farah kafin ita kanta Addah da farga da halin da muke ciki, dole kuma mu sake neman wanda zai mana bincike sosai akan yarinyarnan, dan na kula wancan da yay mana shirme kawai ya tafka yaci kuɗi shegen, dan binciken nasa akan auren Abdul-Mutallab da yarinyar kawai ya tsaya. Ni kuma ta inda yarinyarnan ta samu ciki nakeson sani, dan ta wannan hanyar ne kawai zamu fahimci inda matsalar ta faro mukumayi maganinta kafin su Kabeer su kaimi ƙasa. Duk da yaron na tsananin kama da Abdul-Mutallab ban yarda da gwajin da akace an musu ba, gani nake kawai haɗin bakine dasu Kabeer dan a tabbatar da ɗan nasane a kaini ƙasa wajen aura masa yarinyar da maidosa zama cikinsu”.         Nanma kai kawai Zakiyya ta gyaɗama Mammah dan tunaninta ya fara ƙarfi akan abinda zuciyarta keta mata kai kawo....       AK dake tsaye a ƙofar garden ɗin tun fara maganarsu ya dinga jan ƙafafunsa da sukai masa nauyi da baya-baya zuciyarsa na wani irin harbawa, idan har lissafinsa da abinda yaji zasu iya zama a muhalli dai-dai kamar akwai lauje cikin naɗi a maganar Mammah da aunty Zakiyya. Dan tun fara maganarsu akan kunnuwansa suka shiga kaf. Kasancewar a can wajen gate ya ajiye motarsa ya shigo shi kaɗai. Hango a yanda su Mammah suka nufi garden ɗin lokacin da yake shigo gidan ya sashi tunanin ko wani abune ya faru shine yabiyo bayansu. Furicin Zakiyya na farko ya sakashi dakatawa daga yunƙurin shiga cikin garden ɗin da yayi ya tsaya saurarensu.............✍      *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_*      *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* _________________________ *Page 55* .............Motarsa ya buɗe ya shiga badan son tafiya ba sai dan son samun sararin yin tunani. Dan abinda ƙwaƙwalwarsa ke neman ayyana masa game da zantukansu sosai yake figitar da ziciyarsa. Lallai yana buƙatar haɗuwar Aunty Zakiyya da Zinneerah akan wasu dalilan da yake auna labarin data bama Granny da nasu zantukan, sannan yana son sanin mi zasu tura Farah yi Morocco?, dan idan bai mantaba tunkan tahowarsa Nigeria a wancan karon Mammah ta sanar masa Farah zataje Morocco tayi rainon cikinta kamar na farko har sai ta haihu. A lokacin bai amsa mataba yace ta bari ya dawo daga Nigeria zasuyi maganar, shine kuma komawar tasa ya koma da Hajiya Iya. Kenan tafiyar tata nada alaƙa da wani abu dake ɓoye kenan?.           Ya jima yana tarawa da kwashewa, daga ƙarshe ya yanke shawarar komawa cikin gidan bayan ya kira Khalipha yace idan yaje gidan ya jirasa karya tafi. duk da Khalipha nada nashi uzirin shima sai ya amsa masa da to saboda girmamawa. Dan komai girman uzirin nasa zai iya ajiyewa domin amsa kiran Yayan nasu.       Sai da ya gyara yanayinsa sannan ya tada motar ya ƙarasa gaban gate ɗin da ita. Yayi horn kusan sau huɗu sannan aka buɗe masa. aunty Zakiyya ce da kanta dan gidan babu maigadi tazo ta buɗe masa, hasalima mijinta ya sayesane kawai saboda harkokin siyasarsa idan ta kawosa kano yakan sauka.      Yana gama fakin tana ƙarasowa inda yake, yanda tai wani kicin-kicin da fuska sai ya ƙara ɗaure tasa shima. A ɗage yace mata, “Barka da safiya” yay gaba abinsa batare daya jira amsarta ba. Bayansa ta raka da harara zuciyarta na ƙara mata zafi akan rainin wayonsa. Dama can ita bawani shiri take dashi ba sosai. Ta girmesa sosai amma sam baya bata irin girma ɗin nan yanda take buƙata, wani lokacinma idan yana mata faɗa akan abu sai ka ɗauka shine babba, dan akwai lokacin da mijinta ya taɓa sanar masa wata rigimarsu, daya bincika yaga itace bata da gaskiya ya dinga mata masifa harda cewa zai iya mata dukan tsiya har sai fatar jikinta ta fashe.     Suna gab da shiga falon tace, “Kai yanzu Abdul-Mutallab ka ƙyautama kanka kenan?”.      Batare daya juyo ya kalletaba a daƙile yace, “Da nai mi?”.      Cikin hasala tace, “Aure!. Mi kake buƙata ga mace wanda matarka bata da shi? Wane irin rayuwane wannan mutum yayta tara mata a gidansa kamar wani binsuru.....”       Cak ya tsaya tare da waiwayowa gareta tamkar mai ciwon wuya, ya zuba hannayensa duka cikin aljihu yana jifanta da wani irin shegen kallo da har cikin ranta sai da razani ya kamata, “Masu mata huɗu da ƙwarƙwara su kuma wane matsayi kika basu?”.        “What!?” Ta faɗa a razane tana kallonsa dan tasan da ubanta yake. Gira ɗaya ya ɗage mata yana ƙara kicin-kicin da fuska. Cikin hayayyaƙo masa itama tace, “Mikake nufi Abdul-Mutallab?”.       “Na baki gundarin baƙin ai, sai ki masa fassarar data dace”. Ya bata amsa da juyawa ya cigaba da tafiya abinsa kamar bashi ya aikata tsiyarba.      Wani irin ƙululun baƙin ciki ya saka idanun Aunty Zakiyya cikowa da ƙwalla, cikin ƙunar rai ta fara zazzaga masa masifa. Ko waiwayenta bai sakeyiba harya shigo falon gidan da sallama.      A kusan tare Mammah da Mahma da Farah suka ɗago suna kallonsu, musamman Zakiyya dake masifa iya iyawarta.       “Ku lafiya kuwa?”. Mahma ta faɗa tana tsare Abdul-Mutallab da idanu. Zama yay kusa da ita cike da basarwar da ya iya yace, “Mikika gani Mahma?”.       Sosai ta sake zuba masa idanu dan tasan halin Abdul-Mutallab ɗin ya iya manni ya kuma fika tsare gida, sai kuma ta maida ga Zakiyya dake masifa iya iyawa har hawaye na sauka mata a fuska. Kafin ta sake cewa dasu wani abu Mammah tace, “Wai miya faru Zakiyya kike wannan zantukan?”.       Hawayenta ta share da nuna AK dake zaune ƙafa ɗaya kan ɗaya ya jingina da kujera ya lumshe idanunsa, yayinda Farah ta kafesa da ido zuciyarta na harbawa da sauri-sauri akan yanayinsa. “Mammah waini Abdul-Mutallab zai jefa ubana da kalmar suna bunsuru!”.      A kusan tare Mammah da Mahma sukace, “Bunsuru kuma?”.     “Ai gashi nan ku tambayesa mana”. Ta sake faɗa tana fashewa da kuka.        Ganin ko motsi baiyiba yasa Mahma kallonsa da ƙyau tace, “Abdul-Mutallab!”.      Idanunsa ya buɗe a hankali ya kalleta batare daya motsa ba. “Miya kaika wannan zance haka babu daɗin ji? Zakiyya ba yayarka bace?”.         Murmushi ya saki mai ƙayatarwa a karon farko da ɗan yamutsa fuska, kansa tsaye yace, “Mahma ni ƙarya takemin, ita da bakinta ta kirashi hakan”.     Ba mahma ba har Farah sai da ta maida kallonta ga Aunty Zakiyyan da tace, “Kaji munafiki, dagafa na masa magana akan ƙara aurensa nace miyasa zaita tara mata kamar wani bunsuru shine yace wai masu mata huɗu da ƙwarƙwara fa? Kenan yana nufin Abbanmu ko?”.         “To ke miya kaiki faɗa masa haka Zakiyya da girmanki? Aure ba ALLAH ya halasta ayisa ba? Taya za'a danganta wanda yay koyi da MANZON ALLAH (S.A.W) da wannan mummunar kalmar domin ALLAH idan ba neman tada zaune tsaye ba? Dan ALLAH ku ringa sassautama kanku, rayuwarma duka nawa take ALLAH natuba. Kai kuma Abdul-Mutallab baka ƙyautaba daka bata wannan amsar, saika fahimtar da ita kuskurenta ko kai mata shiru”.       “Am sorry Mahma” ya fa ɗa batare da nuna nadamar abinda yay ma aunty Zakiyya ba. Mammah kuwa kasa cewa uffan tayi. Zakiyya ma ƙin cema Mahma komai tayi, dan kai tsaye ta fassara abinda Mahma tayi da son kai. Duk da Mahma ta fahimceta batabi dakantaba ta fara musu nasiha su duka. Sai da ta gama AK ya samu damar gaishesu.     Rai ɓace Mammah tace, “Sai yanzu muke ganinka a gidan? Bayan kasan matarka na cikin halin rashin lafiya, Abdul-Mutallab! Abdul-Mutallab! kana shigarmin hanci fa da yawa”.       Murmushi yayi yana gyara zamansa. Cike da girmamawar da yake bata yace, “To yi haƙuri karki fyatoni Mammah, ba gani nazoba yanzu kuma nama ganta ragal”.     Harara Mammah ta zuba masa kawai dan takaici, zata ƙara magana Mahma tai saurin katseta da faɗin, “Tunda ya nema afuwa basai a sarara masaba a kama wata tashar kuma”.      Dole Mammah ta haɗiye maganar tana marairaice fuska. “Ke kam Addah bakison ace yayi abu saiki fara karesa,  to naji yanzu sai ya nema mana ticket ɗin tafiya Morocco”.        “Morocco kuma Mammah? Mizakuyi acan a irin wannan lokacin daba komai akeyi ba?”.       “Eh to lallai ubanmu, sai ana wani abu zamuje tushen uwarmu kenan? To Farah zamu kai ta ƙarasa rainon cikinta acan har sai ta haihu.”        “Kaji kuma wani abu, to banda abinki Mammah sai kace mai cikin fari? sannan wancan karonma bacan tajeba har ya zama sanadin fitar cikin? Ni wannan karonma na yanke shawarar a Nigeria zata haihu babu inda zataj......”        Tassss!!! kakejin sautin fashewar kofin hannun Farah da take shan tea tun shigowarsa. aunty Zakiyya kam a bazata tace, “What!”. Mammah kuma ta ɗan zabura jikin kujera da faɗin, “Baka isaba ko!”.       Yanda sukai ɗin ba ƙaramin mamaki ya bama Mahma ba, shiko sai yay wani shegen murmushi da komawa ya lafe jikin kujera yana zuƙar sassanyan numfashi da iskar ac ke busowa.      Mahma tace,  “To minenen abin razana anan? Dan kawai yace a Nigeria matarsa zata haihu? Ai hakan da yay shine dai-dai, kuma shine zai ƙara kawo dai-daito tsakaninta Farah da ƴan uwansa ko?”.        “Adda bazai yuwuba wlhy, karma ki goya bayansa a wannan gaɓar dan tafiya da Farah kamar nayi na gama ne, sannan maganar yarinyar dake gidanka yaya muke ciki?”.      “Ki tayamu addu'a kawai Mammah”. Ya faɗa kansa tsaye.       “Uban addu'a zan tayaku ba addu'a ba Abdul-Mutallab, ni kake gayama na tayaka addu'a akan wannan figaggiyar yarinyar da'a haihuwar kaji ka isa haifarta, to wlhy tunma muna shaida juna ka sakar musu yarinya ko na ɓata maka ranka”..         “To amma Mammah baƙya ganin idan na aikata hakan shima Baffah zai ɓata ran nawa? Kiyi haƙuri kawai kamar yanda nai biyya a zaɓinki shima nayi biyayya anasa. sannan kuma idan ina sonta kuma fa....”       Kafinma ya rufe baki Farah ta fashe da wani irin razanannen kuka sai da Mahma ta daka mata tsawa tasa hannu ta toshe bakinta tana faɗawa kan Mammah.     A zafafe aunty Zakiyya tace, “Wlhy inma baka saketaba da ƙafarta saita bar gidan”.     Banza yay kamar bai jitaba, zata sake magana Mahma ta harareta dole tai shiru tana ƙunƙuni. Cikin rawar murya na alamar jin zafi Mammah tace, “Abdul-Mutallab na rantse zan iya tsine maka akan auren yarinyarnan. Dan haka na baka kwanaki bakwai kacal ka sallameta. Idan kuma ka kuskura ko ɗan yatsanta ka taɓa ALLAH ya is......”      Da sauri yace, “Oh Mammah Please!.....”     Yanda yay maganar cike da ƙosawa ya sata dakatawa tana kallonsa. Cikin ƙunar da zuciyarsa ke masa yace, “Bama sai kinyi wani ALLAH ya isaba haba sweetheart, nifa wasa nake miki kawai dan naga yaya ƴarki zatayi? Tana sona har yanzu kokuwa?, indai nine ki bani wata ɗaya kacal zanyi komai a tsare yanda shima Baffah bazaiga na masa tsageranci ba harya canja wata hanyar da ni dake zamu gaza ganewa kuma ok?”.        A yanda yay maganar seriously yasata yarda dashi, dan tasan halinsa bayason dukkan abinda zai ɓata mata rai, cikin gamsuwa tace, “Idan ka saɓamin alƙawari Abdul-Mutallab bazan maka da sauƙiba fa”.       “Karki wani damu kanki Noorunnisa, sai dai ga shawara, dan akwai abinda naɗan hango idan akace na saketa yanzun, kiɗan sassauta kinsan shima Baffah akwai taurin kai, idan wata ɗaya bataiba zan iya kaiwa biyu ko uku haka, dan dole na haɗa da Granny, kinga hakan na nufin kenan gara ayi sakin cikin hikima yanda zan ɗaura laifin akan wani abu taimin ita yarinyar bawai kece kika saniba. Dan wlhy yanda Baffah ya fusata nace zan saki yarinyarnan yanzu to kuwa zai auramin mata uku rana ɗaya, ya kuma kafamin sharuɗɗan masu tsauri da bazan iya yin wani abuba, kinga kema yaci galaba a kanki kenan, amma idan cikin hikima mukai komai sai a rabu lafiya. Taɓa yarinya kuwa ki ɗauka ko kallo bata ishi Abdul-Mutallab ɗinki ba, na Farah ɗinkine kawai har a aljanna”.      Karan farko ta saki tattausan murmushi da cewa, “To ALLAH yay maka albarka, naɗan gamsu da bayaninka danni shaidace akan Kabeer da halayensa, amma kamar yanda ka faɗa ta wannan hanyarne kawai zamuyi maganinsa da wannan kakar taku sarkin iko wa ƴaƴan wasu”.       “Amin sweet Mammah”. Ya faɗa yana wani shegen murmushi daya zafafa zuciyar aunty Zakiyya ta miƙe fuuu ta shige. dan itakam tsaf ta fahimci shirya rainama uwar tasa hankali yayi kawai.      Mahma kuwa murmushi tayi itama da cewar “Nasan zaka iya Abdul-Mutallab, kamar yanda Hindatu ta faɗa haka mukeson kayi, abinda yasa zan goya bayanka kamar nan da wata ukun saboda dalilan daka faɗa suna akan hanya”.         “Nagode Mahma” ya faɗa yana wani lumshe idanu da komawa jikin kujera ya lafe abinsa.       Sosai dariya kecin zuciyar Mahma tanata ƙoƙarin danneta, a ransa kuwa tanata saka masa albarka da ƙarajin ƙaunar AK ɗin har cikin ranta. A kullum ƙoƙarin sa yaga ya kauce ɓacin ran mahaifiyarsa koda ace ya fita gaskiya, irin wannan ƴaƴan sune abin buƙatar kowa, dan suna ƙoƙarin kiyayewa daga fushin mahaifiya, su kuma kautar da ita faɗawa halaka itama dake zuwa akan dokin fushi kona son zuciya.           Farah ma tashi tai ta shige ɗaki tana rusar kuka. Hakan yasa AK miƙewa yabi bayanta. Mammah zata bisu Mahma ta dakatar da ita.      “Kinga barsu ya lallashi abarsa da kansa. Babu ruwanki a wannan sabgar tunda kinji daɗi yace zai miki abinda kika buƙata saboda ƴar so ɗin taki”.     Ƙaramar dariya kawai Mammah tayi da komawa ta zauna. “Oh Addah kemafa kina bayanmu wannan karon bare kimana wa'azi”.       “Ai nabi bayankunne kawai saboda farin cikinki, sannan nima matar tasa bataminba tayi ƙarama da yawa”.      “To kema dai ƙya faɗa Addah, bandama namiji baida kunya ba, ta ina zai fara nuna wannan ƴar ficilar yarinya matsayin matarsa”.     Dariya sosai Mahma tayi abinta.      AK da Farah kam kusan tare suka shiga ɗakin, ta faɗa saman gado tana sake fashewa da kuka mai cin rai. Shiko yana shigowa ya ɗaure fuskarsa tamau da murzawa ƙofar key sannan ya ƙaraso gaban gadon cikin takun izza da bayyanar ɗacin da zuciyarsa ke masa ƙuru-ƙuru akan fuskarsa. Cikin tsananin kaushin murya yace, “K tashi zaune!”.       Sosai yanda taji muryarsa ya ƙara razanata. Dole ta miƙe zaunen dayace tana kallonsa idanunta cike da tsoronsa. Ƙafarsa ɗaya ya ɗora saman gadon ɗayar na ƙasa yana binta da wani shegen kallo daya saka jikinta fara tsuma tana girgiza masa kanta hawaye na rige-rigen fitowa.       “Share waɗan nan hawayen, kuma ki nutsumin wlhy kona karyaki a ɗakin nan na karya banza”. yay maganar yana matsar da fuskarsa gab da tata da nunata da ɗan yatsansa cikin gargaɗi. Hannu tasa da sauri ta goge hawayen tana magana cikin rawar murya, “Yah Abdul-Mutallab wlhy ba laifina bane, ni bani nace zanzo nan ba, tashi kawai nayi na ganni anan gidan”.      “Bashi na tambayekiba, dan matdalarkice ba tawaba wannan”. Ya katseta a kausashe.        “Dan ALLAH kayi haƙuri, wlhy banason kishiya, zan iya mutuwa ka taimakeni ka barni ni kaɗai, na rantse da ALLAH zan dinga maka duk abinda kake so daga yanzun”.       “Daga baya kenan yarinya. ai kin makaro kuma, dan na baki damammaki bama damaba amma kika cigaba da ɗaukata ɗan iska ko maijin tsoronki ma. Dama na tabbatar miki a randa yaran nan sukaje London inhar kika sakamin ciwon kai sai na baki na zuciya. Koda yake wannan duk bashine a gabanaba yanzu, dan idan na tafi kema kinsan bana waiwaye. Gargaɗi zan miki idan kinbi kin huta, idan kinmin taurin kai da shirya samun ciwon kai wlhy sai na saka miki na jini bayan na zuciyar da kika samu yanzun, kindai sanni sarai. Koda ban miki gargaɗin nanba nasan baki da wata dama ta sake barin ƙasar nan yanzu, amma dole zan miki. Kiyi duk yanda zakiyi ki tabbatarma da Mammah zaki haihu a Nigeria, inba hakaba wlhy ki kuka da kanki, dan inhar ta ɓata ranta a kaina toke zuciyarki da kamanninki zan ɓata gaba ɗaya a rasa ganeki. Ki kuma nutsu akan wannan haukar sumar da kuka da kikema mutane, bake kika jawa kanki kishiyar ba, saurama biyu zan ƙaro bayan wannan shashasha kawai”.      Ya ƙare maganar da sauke ƙafarsa ƙasa yana binta da wasu shegun looks masu riƙe maƙoshi da ƙahon zuciya.       Sai da yaje gab da ƙofa ya juyo cikin wani gargaɗin yace, daga nan zuwa kwana biyu ki dawo inda na ajiyeki, na baki kwana biyunne ma dan banason takurar kowa a cikinsu, idan kuma kin fita yanzu ki sanar musu duk abinda mukai a ɗakin nan, ni kuma na tabbatar miki sunana Abdul-Mutallab Kabeer Shira”. Daga haka yay ficewarsa. Koda ya fito falon babu wata alamar akan fuskarsa dazai nuna ba lallashin Farah yayba da gaske. Bai zaunaba yay musu sallama akan yana son yin wani uziri ƙilama ya wuce Jigawa duba masu aiki.         Mammah ce ta kallesa cikin harara, “Ban gane zaka wuce Jigawa ba tickets ɗinmu fa?”.       “Oh GOD, Mammah Please kibar maganar zuwa Morocco ɗin nan dan babu ita, idan haihuwarta a london ne baƙyaso nace miki zata haihu anan ne. Zaku iya barmata Mahma su zauna tare kokuma a samo tsohuwa daga Morocco ɗin ta zauna da ita, ke kanki akwai maganar business da nakeson nayi dake wani abokina yanason kaya naga kuma kina dasu. Bye bye ana jirana nikam”.      Daga haka ya fice abinsa dan baiso ta ƙara tofa komai................✍            *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_* *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* _________________________ *Page 56* ..........Sai da ya tsaya yay sallar azhar a hanya sannan ya ƙarasa gidan. Tun daga falon farko yake jiyo dariyar su Meenal da Jamal. Ya ɗanyi shiru na wasu sakanni a wajen amma baiji muryar Zinneerah ba ko sau ɗaya, firar tasu kuma dukta makaranta ce Nawaf na basu labarin makarantarsu ta Turkey shima. Kamar zai nufi can sai kuma ya fasa ya ɗauka hanyar sashensa.          Khalipha dake zaune yana kallon television a falon nasa ya ɗago yana amsa masa sallamar da yayi. Cikin falon ya ƙaraso yana faɗin, “Am sorry besty na barka jira ko?”.      “No babu damuwa Yayanmu, nima ban wani jima da zuwanba sai da na biya ta asibiti”.       “Thanks”. Yace masa kawai yana nufar hanyar bedroom ɗinsa. Kusan mintuna goma sai gashi ya fito sanye da ƙananun kaya da alama waɗan can ɗin sun damesa. Yana zama Khalipha ya miƙe ya buɗe fridge ya ɗakko masa ruwa.     “Thanks Darling”. Murmushi Khalipha yay kawai ya koma wajen da yake ya sake zauma. Sai da AK yasha ruwan sosai dan ƙishirwar yakeji dama. Kofin ya ajiye yana gyara zamansa ƙafa ɗaya kan ɗaya ya ƙara komawa serious.       “Khalipha akan maganar da muka farone ranar, inason ka amsa min wasu tambayoyi”.       “Okay Yayanmu kaimin, inhar na sani zan baka amsa insha ALLAH ”.     Kansa ya jinjina masa da kai hannu yaɗan shafo sajensa zuwa gemu. “Yanzu idan nace kamin bayani akan dashen cikin gaba ɗayansa zaka iya?”.       “Zan iya Yayanmu, sai dai zai cimana lokaci matuƙa, kai kuma nasan bakason a cinye maka lokutanka”.      Sassanyan murmushi yayi yana ɗauke kansa daga Khalipha ɗin. “Ai wannan nine na bashi lokacin da kaina, sai dai kuma barsa kawai muje ga tambayoyin zasu wadatar dani insha ALLAH ”.       “Okay Yayanmu ina saurarenka to”.       Ɗan jimm yayi na wani ɗan lokaci kamar mai nazari, kafin ya duba Khalipha da ƙyau, “Bani bayani a taƙaice ta yanda za'a iya dashen cikin?”.       Zama sosai Khalipha ya gyara da nutsuwa. “Abunda kake magana ana ce mishi artificial insemination Yayanmu. Ana daukar maniyyi namiji (semen) a tace, a ɗauki sperms sai a haɗa da Kwan mace (ovum). Shi Kwan mace sai an shirya ake ɗaukan shi shima, anabada magunguna kafin ayi hakan, sannan ba haka kawai ake ɗauka ba sai an duba lokacin da matar take ovulation, ma'ana Kwan yayi girma sai ayi amfani da na'urar scanning a ɗauka. Ta Mara ake ɗauka bata al'aura ba, sai a haɗa a Laboratory (invitro fertilization). Idan anyi sa'a an samu fertilization sai a ɗauki abunda ake cewa fertilized ovum kamar guda biyu a sa a mahaifar matar wannan ta vagina ɗinta za'a saka sai a jira a gani idan dashen ya kama. Idan ban mantaba kuma na fahimci tambayarka wannan itace amsar”.         Sosai AK ke ɗan jinjina kansa yana taunar lip ɗinsa na ƙasa a hankali da haƙiri. “Okay Thanks. Next, za'a iya ɗaukar sperm daga wani ƙasa a kawo wani ƙasa batare daya lalace ba?. Misali kamar daga london zuwa Nigeria?”..       “Eh to Yayanmu za'a iya ɗaukar semen akai wani wuri, amma gaskiya yanada matuƙar wahala saboda sai an sashi a ma'adani na musamman  (Google: transport sperm from one place to another). ba kowanne likita banema zai iya maka wannan juriyar kai tsaye”.        “Lallai kam. To amma za'a iya ɗaukar sperm ɗin namiji bada saninsaba aje a aikata dashen?”.        “Yayanmu idan na fahimceka kamar ace matarsa ta ɗauka a ɓoye bada saninsa ba? Dan ko likita sai dai ya saka a kawo, bawai ya ɗiba kai tsaye ba tunda ba kamar jini bane ko fitsari da sauransu”.       “Good, haka nake nufi?”.                “Gaskiya Yayanmu kamar ba zai yiwu ba, saboda idan za'ayi irin wannan abun shi namijin shine zai bada maniyyi asa a kwalba na musamman a tace sannan ayi, ba zai yiyu ayi irin wannna kuskuren ba, kamar yanda na faɗa maka sai an shirya ake ɗaukan Kwan mace, sannan akwalba ake haɗawa sai ya haɗu sannan za'a ɗauka a dasa a mahaifar macen. Sai dai a sakashi ya bada da kansa ta wata sigar batare da shima ya san mi za'ai da shi ba nakega”.      Ɗan jimmm AK yay yana wani tunani da ƙiyasta shekarun Zinneerah a ransa. Kafin ya duba Khalipha ɗin,      “Okay, kenan za'a iyama yarinya ƴar 14years dashen cikin?”.       “Eh Yayanmu za'a iya yi, sai dai kamar yanda na faɗa maka kafin ayi sai an shirya, ma'ana akwai lokacin da akeyinshi sai an duba menstrual cycle ɗin matar, sabida haka idan bata fara al'ada ba, ba zaiyi wuya ba, idanko ta fara zai iya yuwuwa”.         “Akwai ta hanyar da ku likitoci kuke iya gane ɗan na dashe ne?”.      “A iya sanina babu yanda za'a iya gane dashe ne, bandai saniba ko ga wasu manyan likitoci da suka fini ƙwarewa kasan har yanzu ni ɗalibin ilimi ne”.        Ɗan murmushi AK yayi yana sake gyara zamansa. “A nawa tunanin idan har dashen ciki akai ma yarinya, ya kuma kasance cs akai mata bata haihu da kanta ba, kenan zata iya cigaba da kasancewarta cikkakkiyar mace dazai iya bada dukkan amsoshin ko hujja akanta tunda babu wani dalili dazai iya gusar mata da budurci”.        Murmushi ne ya ɗan suɓucema Khalipha, dan sai yanzu ya fahimci dai Yayansu yana magana ne kamar akan Zinneerah, ya dai ƙi fitowa fili ne, zama ya ƙara gyarawa da ƙyau yana faɗin. “Eh to Yayanmu idan dai mace ta haihu ai babu zancen virginity ya kare nake gani ko kuwa?. Sai dai kuma da kace idan ya kasance an mata cs ne. Abunda mutane ke cewa budurci abun ba haka bane, virginity shine idan bata taba saduwa da namiji ba ko an zura wani abu a vagina babu yanda ake ganewa saboda mata da yawa wannan abun mai kama da yaɗi da yake ɗan rufe bakin vagina ba kowa keda shi ba, hasalima idan mace tana manyanta abun yana raguwa, sannan tsallle-tsalle da irinsu hawan doki ko Keke duk yana sawa a rasa shi, haka kuma Koda mace tana dashi ba kowa ke zubar da jini lokacin saduwar farko da ɗa namiji ba. Shi yasa yanzu duk ake hana abubuwa kamarsu vaginity testing. Kaga nauyin ciki zai iya sa ta rasa wannan yaɗin kenan itama inhar tanada, amma ba haka na nufin ta rasa budurci ba, dan dole a kirata virgin inhar bata taɓa sanin ɗa namiji ba, ko kuma wani abu makamancin haka kamar haihuwa bai ratsata ba”.        AK ya ɗan sauke numfashi, “Sannu da ƙoƙari Khalipha. to amma za'a iya yin dashen batare da ta saniba kuwa? Kamar a bugar da ita ko something hakan?”.        “Tabbas za'a iya bata maganin bacci ayi, amma bazai yuwu ayi a gida ba ko ɗakin likita ba, a ɗakin theater akeyi, bai kuma zama lallai a samu nasara ba a yin farko, wasuma sai kaga sunyi sama da sau hudu biyar goma ma basu daceba, ƙwayayen sukan mutu kafinma a dasa ko bayan an dasa cikin yaƙi zama. Idan kana buƙata zan iya baka number wani likita ƙwararre akan wannan fanin kawai dazai maka ƙarin bayani sosai, zaima iya nuna maka yanda akeyin komai insha ALLAHU”.       Murmushi AK yayi da ɗaukar ruwa yasha. “Ai ko haka aka tsaya ma na gamsu Khalipha, na kumaji a raina baka wasa da karatunka, tunda gashi tun a yanzu mun faracin tagomashinsa, inaga nan gaba kuma ka zama cikakke. ALLAH yay maka albarka ya ƙara ƙwaƙwalwa. Akwai wasu bayanai da nakeson sake tattarawa, dana kammala zan baka wani aiki insha ALLAHU”.        “To yayanmu ngd sosai. ALLAH ya ƙara girma da nasarorin rayuwa”.     Murmushi kawai AK yayi da amsawa da amin akan laɓɓansa. Daga haka suka koma wata hirar kuma. _______★      Sam su Zinneerah basusan da dawowar AK gidanba, tunda su Jamal suka ƙaru sai sukai zaman sake babin sabuwar shafta, sun dai san Khalipha na nan, tunda bayan mai gyaran ya kammala ya sanar mata zai jira dawowar Yayan nasu.          Kiran sallar la'asar ya saka Jamal da Nawaf fitowa massallaci, shine suka haɗu da Khalipha da yayan nasu. Sunata faman sinne kawuna da tunanin zai musu faɗa sai sukaji tsit, tundama ya amsa gaisuwarsu yay gaba bai sake cewa dasu uffanba har aka idar da salla suka fito.     Khalipha ne ya dubesu lokacin da suke shigowa harabar gidan. “Guys kuje ku tattaro waɗan can sauran yan-yan ɗin muwuce gida haka nan”.       Cikin marairaicewa Jamal yace, “Wayyo Yaya Khalipha Please sai anyi magriba zamu dawo fa, can gidan duk mutane, ni wlhy suna takuramin”.      “Ƙaniyarkace mutanen, dalla jeka kirasu mu wuce. Mutanen da kake magana ba duk sun kama gabansu ba, ga aiki can a gida kunzo nan kun zauna”.       Baki cike da iska Jamal ya wuce ciki kiransu Meenal. Duk wannan abin dake faruwa AK na ɗan gefensu kaɗan yana waya, sarai kuma yanajinsu amma sai baima nuna kunnensa na akansun ba. Ba'afi mintuna uku ba sai gasu sun fito harda Zinneerah da fuskarta ke a ƙwaɓe.      Sam bata lura da AK ba, dan haka kai tsaye ta isa gaban Khalipha. “Wayyo Yah Khalipha dan ALLAH ka barsu, hirafa suke tayani”. Ta ƙare maganar hawaye na sakko mata a kumatu.      Tausayi ta bashi dan yasan shaƙuwa da sabon dake a tsakaninsu, sannan kuma akwai rashin sabon nan ɗin tattare da ita. Balle Yayan nasu daba sakewa ya iya da jama'a ba sai yaso dan kansa.         Murya ya kwantar sosai cikin lallashi yace, “Haba auta ai abun sai ya zama rashin hankali kuma. Kiyi haƙuri gobe idan ALLAH ya kaimu sai su dawo ku ɗora daga inda kuka tsaya tunda ku shiririta bata ƙare muku. Kinga yanzu aikine a gidan can sosai, su kuma da zasu taimaka sunzo nan sun zauna aikin yama su Ni'ima yawa.”        “Amma Yah Khalipha zasu koma ai, kaga yanzu suna tayani hira”.       “Indai hirace karki damu ga Yayanmu nan a gida ai zai tayaki”.      Batare da tunanin yana a wajanba tace, “Tab, Yayanmu ne zaiyi hira? Wanda ko dariya yana shekara baiyita ba ma......”       Karaf Bahijja ta katseta da faɗin, “Baya hira, amma ya iya soyayya, nifa nan gidan zanma dawo da zama yasin nasha kallo, dan na taɓa ganin wata zazzafan soyayyar Yayanmu da aunty Farah wani zuwa da sukayi na rakasu gidan Uncle Yusif, ku kunga abu, wlhy Zinneerah zaki sh.......”     “K!”.   Khalipha da abin ya ishesa yay saurin katseta. tun fara sakin zancen nata yake mata alamar tai shiri amma taƙi fahimta. Suko su Jamal hannu suka ɗora bisa kawunansu suna zaro ido da bubbuga bakinsu na mata alamar tai shiru, amma ina yarinyarnan kamar an kunna mata batir. Tsawan da Khalipha yay mata kuwa baki ta turo, cikin ƙunƙuni tace, “Yah Khalipha labarifa nake baku dan kuma ku koya irin ƙwarewan Yayanmu kuma ku dinga yi”.      Kai kawai Khalipha ya girgiza yana ƙoƙarin danne dariyar dake neman kufce masa ganin Yayan nasu ya nufo inda suke yana saka wayarsa aljihu alamar ya gama.      Gyaran murya ya ɗanyi, ba Bahijja mai bada lecture ba hatta Zinneerah sai da hanjin cikinta ya wantsala suka juyo a firgice su uku harda meenal dan sune dai suka juyama inda yake baya.       Kafinma yace dasu wani abu Bahijja da Meenal sun kwasa da gudu hanyar gate, Jamal da Nawaf duk da sunsan dashi a wajen suma dai rufa musu baya sukayi dan hanyar lafiya a bita da shekara.       A bazata dariya ta suɓucema Zinneerah duk da itama fa a tsoracen take. Amma yanda su Jamal suka dafe ƙeya dasu Bahijja ya bata matuƙar dariya. Khalipha da shima dariyar yake dannewa tana kufcewa ya afka mota yana faɗin, “Mu kwana lafiya Yayanmu”.        Kai kawai ya jinjina masa tashi fuskar babu ko ɗigon murmushi ammafa a ransa dariya yake ɗan rainin wayon😂. Dan duk dauriyarka dolene abinda su Meenal sukai ya baka dariya. Maigadi kansa dariya yakeyi dan har bangajesa sukai wajen gudu.       Ganin Khalipha zai wuce Zinneerah ta shirya nata gudun itama amma tana ɗaga ƙafa zata fece taji an cafko mata hannu. Gaba ɗaya ta rikice, dariyar data rage a saman fuskarta ta ɓace ɓat. Baya ya dawo da ita gabansa yana kallonta da birkitattun idanunsa dake neman sakata sakin fitsari dan fuskar ta kuma tsukewa tamau. Shi dai Khalipha motarsa ya harba yana dariyar ƙeta, dan yasan dai Bahijja ta kunno wuta. Kuma gaskiya ta faɗa indai soyayya ce kam Yah Abdul-Mutallab ba'a magana, shi da yake rayuwa a gidansu yake shan kallo.              Cikin tsagwaron marairaicewa Zinneerah da idanunta ke tara ƙwalla tace, “Yayanmu wlhy bance komaiba, ALLAH Bahijja ce ka tambayi Yah Khalipha kuma. Uffan baice mataba, sai jawota da yay a hankali ta faɗa saman jikinsa, rawa jikinta ya fara, batare da yabi takanta ba ya ɗauketa cak a bazata. Babu shiri ta cusa kanta a ƙirjinsa dason sauka amma tama kasa motsawa. Koda suka iso ƙofar falon da ƙafa ya tura, hakama da sukaje ta sashensa da ƙafa ya tura, duk yanda take zame-zame bai direta a ko inaba sai falonsa.     Tanajin ya ajiyeta ta ɗago fuskarta daga jikinsa dajan jikinta dake ɓarin tsoro baya dan catake ko duka zataci, duk da dai bata taɓaji a tarihi ko labarinsa ya taɓa dukan kowaba a gidan nasu, barsa dai da barazana da mazurai, hana rantsuwa marin da yayma matarsa a london sanda ta shaƙeta, shima ba wani lura tai da ƙyauba ranar dan a firgice take sai da su Meenal suka bata labari.       Baya ta dinga ja tana girgiza kanta. “Yayanmu ALLAH bance komaiba, ka tambayi Yah Khalipha”.     Hannayensa ya zuba a aljihu duka biyu yana binta a baya fuska a tamke, sai wani lumshe idanu da buɗewa yakeyi akan lips ɗinda dake motsawa a hankali da yanayin tsoron daya bayyana ƙarara a fuskarta. Tana tafiya yana binta sai ji tai ta dangane da bango, juyawa tai a firgice ta kalli bayanta, ganin dai da gaske tazo ƙarshe hankalinta ya ƙara tashi, ta dubesa da saurin yin ƙasa zata durƙushe ya riƙo hannunta.      “Yayanmu wl.....” “Shiiii!!!..”      Ya faɗa a hankali yana saka idanunsa da suka canja launi cikin nata, tare da saka duka hannayensa a bangon ya dogareta yanda babu damar kuɓuta kenan. Gashi ya hana kuka dole kuma ta haɗiyesa, sai dai zuciyarta kamar zata faso ƙirjinta ta fito.          A wani irin ƙasa da murya sosai ya fara magana idanunsa cikin nata da takeson janyewa ya hana. “Dama idan kuka zauna gulman mutane kawai kuka iya ko?”.        “Wlhy a'a Yayanmu, bama gulmar kowa ka tambayi Granny”.     “Ni yanzu danaji ana tawa fa?”. “Y...y...Yayanmu ba gulm...ma bane fa?”.       “To miye sunansa?” Shiru tai dan batasan mi kuma zatace ba itakam. Hakan datai ya sashi juya idanunsa yana sauke hannunsa ɗaya dake dafe da bango ya maida cikin aljihu. Yace, “Anyhow zan fara hukuntaki kafin ita mai baku lecture ɗin na kamata da sauran ɗaliban nata”.       “Wayyo Yayanmu, wayyo Yayanmu”. Zinneerah ta faɗada iyakar marairaicewar data saka AK cije lip ɗinsa, yana binta da wani irin ƙasalallen kallon daya saka hawayen ƙaryarta ɗaukewa ɗaf ta shiga mar mar da idanu zuciyarta na harbawa da sauri-sauri..........✍     *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_*       *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* _________________________ *Page 57* ...........“Nine kuma bana dariya sai shekara-shekara ko?”.       “A'a wlhy Yayanmu bakai nake nufi ba, wani ne acan Danya”. Zinneerah ta faɗa tana duban gefen daya janye hannunsa. Hakan yayi dai-dai da wayarsa ta fara tsuwwa. Aljihunsa ya kalla da ƙoƙarin zira hannunsa zai ɗakko, ‘Alhmdllh’. Zinneerah ta faɗa a zuciyarta tana kwasa da gudu.            Duk yanda AK yaso danne dariya a yanzu kam ya kasa, dole yay murmushi har haƙoransa na fitowa tare da girgiza kansa kawai.       yace, ‘Zan kamaki har inda zakije ɗin ai” daga haka ya kai wayarsa kunnensa dan Hajiya iya ce.       Zinneerah kam bata tsaya a ko inaba sai bedroom ɗinta nacan ciki, ta murzawa ƙofar key tana sauke numfashi da faɗin, ‘ALLAH na godema daka kuɓutar dani, Bahijja taso jamin salalan tsiya yau, dan ƙila zaneni yay niyyar yi ma’.        Sai kuma ta kwashe da dariya saboda tuno su Bahijja, inama tanada waya yau data kirasu taji yanda aka kwashe. Bata taɓajin takaicin rashin wayarta irin yau ba, harta kaita da zama tunanin yanda wayar ta ɓata abin kamar almara      ★★★   Tun abinda ya faru Zinneerah da AK basu sake ganin junaba har akai sallar magriba. Sai lokacin ta fito daga ɗakinta ta duba dining ɗin. Tasha mamaki ganin anci abinci data ajiye. Aranta take tunanin ashe ya shigo yaci abincin. Wajen ta tattara tare da falon, ta saka turaren wuta sannan ta koma ɗaki tai wanka. Tana fitowa sallar isha'i ta gabatar, bayan ta idar tai zamar gyara jikinta ranta fal tunanin mmn sadiq dasu Abdull, harma da Little da rabota dashi tun randa zata wuce danya. Tana kewarsa sosai harma da ƴan danya ɗin, yanzu da tanada waya ai da ta kira taji yanda suka sauka lafiya da jikin Tinene kuma. Tsaki ta ɗan ja ranta duk babu daɗi. Doguwar riga kawai ta saka yanda zata sake, tana ɗaure gashinta data taje taji an turo ƙofar ɗakin.         Juyowa tai a hankali tana duban ƙofar aɗan rikice, wanda tayi zaton dai shine, yana sanye cikin wando jeans baƙi da baƙar t-shirt, sosai kayan sukai masa ƙyau duk da alamu sun nuna badan kwalliya ya sakaba.          Ganin yanda idanunsa ke a kanta yasata yin ƙasa da nata, ya ƙaraso cikin ɗakin kansa tsaye da tafiyarnan tasa daba garaje, ga fuskar kuma babu alamar fara'a kamar ko yaushe, amma hakan bai hana ƙyawunsa da kwarjininsa fita ba a bayyane.       “Barka da dare”. Ta faɗa kanta a ƙasa da ƙoƙarin jan gyalen jallabiyar zata yane kanta duk da bata kamla ɗaure gashin ba. AK da tunda ya shigo idanun nasa ke akan gashin nata ya janyesu yana zama bakin gadon. Batare da yayi mata magana ba ya miƙa mata wayarsa.          Amsa tayi duk da bata fahimci mi yake nufi ba, sai dai ganin sunan Granny da alamar tana online yasata kai wayar kunnenta tai sallama murya a marairaice.     Dariya Granny tayi daga can da cewar, “Inno irin wannan marairaicewa haka?”.      “Granny nayi kewarki ne”. “Nima haka Inno, shiyyasa nace Moddibo ya banike na karajin muryarki kafin na kwanta”.       A take hawaye suka ziraro a kumatun Zinneerah, muryarta ta fara rawa alamun kuka. Kai kawai AK ya ɗan girgiza da mikewa tsaye, batare da yace komaiba ya zare wayar daka kunnenta....      Da sauri ta kallesa dai-dai yana maida wayar kunnensa. Idanun nasa ya ɗan juya mata da faɗin, “Daga gaisuwa kuma sai ki samin ita kuka Granny? To an fasa gaisuwar dake sai da safe”.       Da alama wata baƙar maganar ta faɗa masa daga can, dan janye wayar yay yana murmushi. Batare da yacema Zinneerah dake sharar ƙwalla uffanba ya raɓata ya wuce inda ta ajiye masa system ɗinsa daya bari a ɗakin jiya. Ɗauka yay tare da nufar ƙofa yana faɗin, “Ki kawomin lipton”.         Baki ta kuma tunzurawa tana matso hawaye da bin bayansa da kallo harya fice, babu yanda ta iya dole bayan ta gama kukanta ta share hawayen da ɗaukar turare ta ƙara a jikinta, hardasu fesa much freshener kamar yanda Hajiya Falmata ta koya mata, ta ɗauka wani ɗan kwalban turare da batasan kona minene ba ta shafa a bayan kinnenta da wuyanta, kamar yanda Hajiya falmatan ta sanar mata ta ringa shafa shi duk dare idan tai wanka, ta kuma ƙara da khumra mai shegen daɗi da narkar da mai shaƙa.      Daga haka ta ɗau hijjab mai hannu jaa ta saka sannan ta fito. Kitchen ta nufa ta ɗaura masa lipton ɗin da ganyen shayin da hajiya Falmata ta bata shima, rashin wayonta yasa batai tunanin ko ganyen shayin na wani abu baneba daban. A wani butar shayi mai azabar ƙyau daya ɗauka hankalinta ta juye tare da kananun kofunansa tasa biyu, sai ɗan bowl ɗin data zuba suger shima ta ɗora da tea spoon guda ɗaya ta ɗauka tray ɗin tana addu'ar ALLAH yasa tayi komai dai-dai.          Yana zaune a doguwar kujera ƙafarsa a miƙe yasa filo da ɗaura lap-top ɗinsa saman filon. Koda tai sallama bai dagoba amma ya amsa mata a saman laɓɓa yana cigaba da aikinsa.        Kallo ɗaya tai masa ta ɗauke idanunta, a centre table ɗin tsakkiyar falon ta ɗaura ƙaramin tray ɗin da jawosa kusa da shi tace, “Yayanmu gashi”.      Ɗan ɗagowa yay yayi mata kallo ɗaya ya ɗauke kansa, a taƙaice yace, “Zuba”.         Kanta ta jinjina masa kawai ta tsugunna gaban table ɗin tana ƙoƙarin fara zubawar, yanda hijjab ɗinta yay ɗan bula lokacin da take kaiwa tsugunne ya bama hancinsa damar shaƙo fitinannun ƙamshin turarurrukan data sakama jikinta, duk da tun shigowarta ya jisu, sai haka datai ya ƙara ƙarfinsu fiye da farko a cikin hancinsa.      Wani irin harbawa zuciyarsa tayi, har baisan yatsunsa sun kauce wajen tafa saƙon shirme ba a system ɗin. Ya lumshe idanu ya sake buɗewa a kanta yana ɗan cizar lip dinsa na ƙasa.      Zinneerah da batasan mi yake cikiba ta miƙo masa ɗan mitsilin tea cup ɗin irin na larabawa bayan tasa suga ɗaya dan tasan yanda yake so tunda yasha sata aikin sanda suna gida, tsaf ta gama haddace adadin da yake so.        Idanunsa da suka canja launi lokaci guda ya zuba mata, dai-dai yana amsar shayin muryarsa a ƙasan maƙoshi yace, “Cire wannan hijjab ɗin banaso”.        Mamakin maganar tasa yasata ware idanu sosai tana kallonsa. Sai dai yanda fuskarsa ke a ɗinke ya sata yin ƙasa da kanta ta hau ƙoƙarin cirewa tana haɗiye abinda ya tokare mata maƙoshi, dan duk da doguwar riga ce a jikinta tsananin kunyar zama take a gabansa a haka saboda santsin rigar yasa ta kwanta mata a jiki ta lafe, musamman da yazam ita da kanta ta rage faɗin rigar tun suna gida ita dasu Bahijja.    Hannu ya miƙa mata alamar ta bashi, dole ta miƙa masa, kusa dashi ya ajiye hijjab ɗin dan son tabbatar da shike ƙamshin ko ita?.       “Zauna”. Ya faɗa yana matsar da ƙafafunsa. Yanzun kam kasa haƙuri tayi sai da tace, “Yayanmu zanje na kwanta inajin barci”.       “Nima ba gadin gidan zanyiba ai”. Ya bata amsa a daƙile.      Tashi tai tsam ta zauna inda ya nuna matan har jikinta na neman hayemasa ƙafafu, tai saurin muskutawa kanta a ƙasa.        Idanu ya tsira mata yana kurɓar shayin kaɗan-kaɗan saboda zafinsa. Amma dai haka yafi bukatarsa musamman wannan da yay masa matuƙar daɗi, ga wani irin ƙamshi mai daɗi dake fita a cikinsa.        Ya fahimci ta matuƙar ƙwarewa da iya cuɗa hannunta cikin na juna idan tana waje a takure ko makamancin hakan. Ya danyi gyaran murya nason gusar da shirun nasu. Ɗagowa tai ta kallesa.         Idanunsa a cikin nata yace, “Kin kira su baba ne? Kinji yanda su gwaggo sukaje gida lafiya”.       Ya sosa mata inda ke mata ƙaiƙayi, atake idanunta suka ciko da ƙwalla ta girgiza masa kai. “A'a ai bani da waya ta ɓata”.       “Ɓata fa? A ina kenan?”.    Da damuwa sosai a fuskarta tace, “A can gida, tun lokacin da Granny bata da lafiya zaku wuce london”.        Cikin ɗan taɓe baki yace, “Kin dai jefashi wani waje”.      “A'a wlhy Yayanmu, nifa ina gama waya da Mama a ranar daga ajiyewa naje na tarosu na nemeta na rasa. har yanzu kuma ban ganshiba, kuma ko ina su Meenal sun tayani na duba”.        “Uhm to wani ya sace kenan”. Ya bata amsa cike da basarwa.      Itako tace, “Amma kuma a gidan nan wazai saci waya?”.             Wani ɗan murmushin daya bata mamaki taga yayi yana lunshe idanunsa. Cikin basar da maganar yace, “Ganyen shayin nan yanada daɗi waya baki?”.       Badan taso barin waccan maganarba tace, “Hajiya Falmata”.     “Wacece ita?”. “Nima sai kwanan nan na santa suna mutuncine da Granny”.        “Uhm! Itace ta baki wannan turaren mai ƙamshi haka?”. Ya faɗa murya a shaƙe dan shayin da yasha ya fara aikinsa.      Rasa amsar da zata bashi tayi, sai ta ɗan jinjina kanta kawai.     “Baki da baki ne?”. “A'a kayi haƙuri itace ta haɗa, khumrah ne”.        Komai bai sake faɗaba ya sauke lap-top ɗin dan aikin kam bazai iya cigabuwaba, ƙafafunsa ya zaro daga kusa da ita ya ajiye ɗaya a ƙasa ya tanƙwashe ɗayar, sake ɗaukar butan shayin yayi ya tsiyaya dasa suga ɗaya a ciki ya motsa. Cigaba da shan abinsa yayi da maida hankalinsa ga television. Itama gyara zamansa da yayi ya sakata jin ɗan sanyi ta koma kallon television ɗin da satar kallonsa. dan ya dage sai ɗora shayin yake hankali kwance. Daya shanye yake karawa, tanata lissafi sai da yasha kusa cups bakwai duk da dai ɗan mitsitsine kofin.        Sai da aka kammala labaran da suke kallo ya miƙe, batare da yayi mata magana ba ya fice gaba ɗaya a sashen har tana mamakin ina zaije? Bata da mai bata amsa dan haka ta ƙudiri aniyar zaman jiransa ya dawo ita dai taje ta kwanta ta farajin barci.      Shiko daya fita kai tsaye sashenta ya nufa, kitchen ya fara shiga ya kaso wutar can ya rufosa. ta Dining ma ya kashe tare da leƙa bedrooms ɗin dake a falon duk yaga akashe sannan ya nufi nacan ciki da take amfani da shi.       Akwatin kayanta ya buɗe, duk da shi ba mutum bane mai buƙatar matarsa tasa kayan barci idan zasu kwanta tare ba, yafi buƙatar tazo masa a natural ɗinta, hakan bai hanashi ɗauka mata suba. Sai dai yau ba kamar jiyaba sai da ya zaɓo dai-dai da ra'ayinsa. Gaban Mirror ɗinta yaje nanma ya shiga shinshina turarurrukan wajen kamar mai neman wani daban. Sai dai abin mamaki ya kasa tantance wanda yake buƙatar jin, har takai ya fara buɗe kwalaben khumra dake wajen kusan kala shidda dan bama a kawo mata sauranba tukunna. Ya ɗan samu wasu a ciki, harya ɗauka biyu sai idonsa ya sauka akan kananun ƙwalabe dake cikin wani haɗaɗɗen kwandon saƙa na kaba da aka zubasu ciki kusan kala goma nanma. Murmushi ya danyi dan shi mutum ne mai son ƙamshi, ƙamshi yana ɗaya daga cikin abinda Farah tai galaba a kansa kenan dan itama gwanace wajen baza turare. Nanma shinshinawa ya ringayi ɗaya bayan ɗaya, sai dai ya kasa tantance wanda yafi daɗi da wanda yaji a jikinta. Sai ma neman rikita masa lissafi sukeyi. Nanma biyu ya zaɓa a ciki ya fice bayan ya kashe komai. falukanma duk kashe komai yayi ya rufe sashen baki ɗaya ya nufi nasa.        Zinneerah da har ta gaji da jiran dawowarsa ta jingina da makarin kujera tana lumshe idanu ta buɗesu a hankali jin sallamarsa. Bataga mike hannunsaba dan kai tsaye bedroom ɗinsa ya nufa. Zamanta ta gyara da ɗaukar hijjab ɗinta ta riƙe a hannu gudun kar tai laifi.     Babu jimawa kuwa sai gashi ya fito, batare da yay mata magana ba ya ɗauka remote ɗin tv ya kashe tare da nufar fridge, yana juyowa ɗauke da fura a hannu tana miƙewa. Fuskarta a marairaice tace, “Yayanmu zanje na kwanta barci nakeji”.        Baiyi maganaba sai da ya karaso, ya ajiye roban furan da kamo hannunta ya zaunar. “Zauna kisha wannan sai kije ki kwanta”.       Cikin langaɓe kai tace, “ALLAH yayanmu na ƙoshi barci nakeji kawai”.         Harar daya zuba mata tasata ɗauka dan harya buɗe mata robar, cokalin dake haɗe da robar furan ta ɗauka ta fara sha a hankali tana lumshe ido dan barci takeji, sosai furan na mata dadi sai dai barci na neman kwafsa mata. Shiko lap-top ɗinsa ya ɗauka yana ƙarasa aikin nasa.       “Yayanmu ALLAH ta isheni barci”. Ɗan ɗagowa yay ya kalleta, yaɗan jinjina mata kai kawai yana ajiye lap-top din daya kashe gaba ɗaya. Miƙewa yay hannunsa ɗauke da remote na ac ya kashe. Sannan ya tattara wayoyinsa da nuna mata hanyar ɗakinsa.       Sosai ta ɗan waro masa manyan idanunta dake cike da barci waje. Sai dai yanda ya tsuke fuska dole ta haɗiye abinda ke bakinta ta maida kanta ƙasa. Sum-sum ta fara tafiya hanyar ɗakin da bata taɓa shigaba. Kasancewar ya tsaya kashe fitila ta rigasa shiga ɗakin. Da wani ni'imtaccen ƙamshi tafara cin karo, ta ware idanunta sosai tanabin bedroom ɗin da kallo baki sake. Komai yaji masha ALLAH, white and golden kamar kaci dan ɗaukar idon mai kallo. Ga uban sanyin ac.      Tana tsaye a wajen harya shigo bata saniba. Sai jitai kawai anyi sama da ita gaba dayanta. Sosai ta firgita sai dai babu damar yin magana. Bai direta ko inaba sai toilet ɗinsa da komai yake a tsare kuma a tsaftace. Dan shi kansa kamshi yake na musamman.        “Kiyi alwala”. Ya faɗa kansa tsaye. Sabo da alwalar kwanciya barci yasa bataji komai a rantaba, gashi dama ko shafa'i da wutiri ma bataiba. Alwalar ta ɗaura yana kallonta cike da nazari, da alama yana tabbatar da ingancinta a fannin addinine ne. Sai da ta kammala shima ya ɗaura tasa suka fito tare kamar yanda yay mata alama da ido.      Da kansa ya sa musu abin salla. Ganin yayi tsayuwar alamar jansu salla yasata kallonsa da mamaki. “Yayanmu nayi sallar isha'i”.      “Nima nayi ai”. Shiru tai bata ƙara maganaba harya tada sallar, itama tayarwar tayi dan bin umarni shine masalaha a gareta. Sunyi salla raka'a biyu suka ɗora da shafa'i da wutiri, sannan ya juyi ya dafa goshinta da ambaton. *اَللَّهُمَّ  إِنِّي أَسْأَلُكَ خَيْرَهَا، وَخَيْرَ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّهَا، وَشَرِّ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ* *_Allahumma innee as-aluka khayraha wakhayra ma jabaltaha 'alayh, wa-a'oothu bika min sharriha washarri ma jabaltaha 'alayh._*         _Ya ALLAH ina rokon Ka laherinta da alhrin da Ka dabi'antar da ita a kansa, kuma ina neman sarinka daga sharrinta da shaarrin Da ka dabi'antar da ita a kansa._       Lumshe idanunta tayi tana sauraren daddaɗan muryarsa mai cike da kamun kai da nutsuwa. Bayan ya kammala ya juya da ɗaga hannayensa sama ya cigaba da kwararo addu'oi kala-kala da harshen larabci.        Sai da suka kammala addu'ar ya juyo yana fuskantarta da ƙyau. Tambayoyin ya fara mata a fannoni daban-daban daya shafi addini, wasu ta amsa wasu tace bata saniba dan a yanzu take kan neman ilimi, danma Alhmdllh batai wasaba akan hakan tunda ta dawo da zama kano.      Ya gamsu da yanda tayi ɗin, ya kuma karba uzirinta, daga haka ya miƙe yana magana batare daya kalletaba. “Ga kayan barci nan ki canja”.     Yana fa ɗaya yana nufi hanyar toilet. Kaɗan ya rage Zinneerah ta saki kuka amma ta dake ranta fal tsoro. Kenan anan zata kwana tare da shi yau ma?. Ta ayyana a ranta. Sanin bata da mafita kuma baya maimaita magana, gashi batason ya fito ya sameta batai abinda yaceba yasata ƙoƙarin canja kayan. Ganin turarrukanta tare da kayan ta mulke jikinta dasu duk da kuwa ƙamshin take dama. Tana gamawa yana fitowa ɗaure da towel jikinsa nata raɓar ruwa. Ƙasa tai saurin yi da kanta tana gyara zaman hijjab ɗinta data ɗora saman kayan barcin. Komai baice mataba ya hau tsane jikinsa da towel ɗin daya ratayo a wuya.     Da wannan damar ta wuce toilet ɗin nasa sumi-sumi danyin brush tunda taga sabbi a toilet ɗin, dan ta tuna Hajiya Falmata tace duk rintsi karta kwanta batai brush ba, idan da dama ma ta haɗa da much freshener, sannan ta tabbatar duk sanda zata kwanta barci tayi tsarki da ruwan ɗumi koda ace ta yini amfani da shine.       Brush ɗin ta farayi, sannan tai fitsari dayin tsarki da ruwan ɗumi. Much fresheners ɗinsa data gani ajiye a ɗan drawer ɗin glass ɗin toilet ɗin ta ɗauka, dan gasunan kala-kala, banana, cucumber, kai kala-kala ta fannin fruit duk gasu nan. Son da takema S...barry ya sata ɗaukarsa shi da banana ta saka sannan ta fito cikin sanɗa, a ranta tana addu'ar ALLAH yasa ya gama shiryawa dan shiyyasama ta daɗe danta bashi dama.      Tsaye ta iskesa gaban mirror sanye da wando 3quarter iya cinya da riga mai buɗaɗen ƙirji farare tas. Yana fesa turare. Ta madubi yake kallonta harya kammala sannan ya juyo...........✍ *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_*   *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* *Page 58* ________________________ *_KAƊAN YA RAGE SU ƘARE_* *_MATA ƴan ƙwalisa kuna ina za'aci kasuwar sama babu ku?. Mg's skincare ɗin fa na gab da ƙarewar kaya kuna nan sake da baki baku mallaki naku ba_* _Mg's SKINCARE nagartattun kayan ne dake gyara jiki da fata cikin sauƙi, sunada inganci da rahusa dai-dai da aljihunku._ *Da kin fito a ringa ga tauraruwar taurarin nan mai fatar da babu kamarta tamkar dinare abin haske da walwali.* *_Sabulunsu kawai kika ɗana sai kinsan kin kai kuɗinki inda babu asara balle dana sani_* _A yanzu haka muna jerin kayayyaki da suka rage kamar haka_👇🏻 Available _Akwai: herbal whitening black soap 3k_ Akwai: beauty kit 11k shi set ne yakunshi Abu 6 Soap Body cream Face cream Body nd face scrub Cleanser Glow oil Location kaduna buh mn tura Kaya ko Ina saidai inmutum ya amshi kayanshi zebada kudin delivery WhatsApp 08062991549 Call 08064532391 Instagram:glow_with_mgs Facebook:mg's skincare *_Karku bari ayi babu ku guys, siyan nagari maida kuɗi gida._* ________________________ *Page 58* ...........Gabanta ya tako a hankali, ya tsaya tamkar zai shige mata jiki. Baice komaiba sai kama hijjab ɗin jikin nata yay ya zare. Ganin yanda ta duƙar da kai ya sashi saka yatsunsa biyu ya ɗago haɓarta. Ba karamin firgita tai ba da ganin yanda ƙwayoyin idanunsa suka canja launi tamkar wani bugagge. Muryarsa a shaƙe matuƙa tamkar mai mura yace, “Turaren nan naki zai kashe ni kairunnisaa”.        Sosai jikin Zinneerah ya hau rawa saboda kusanto da fuskarsa da yay gab da tata, ya ɗaura hannayensa duka a kafaɗarta ya fara tafiya dasu a hankali zuwa gaban gadon, gwiwar ƙafarsa ɗaya ya ɗaura a bakin gadon, hakan da yay ya daidaita tsahonsu. Ya cusa fuskarsa akan dokin wuyanta yana wani jan numfashi a fisge dan neman ƙwace masa yake.        Yanda ƙamshin turaren ke neman zauta masa ƙwaƙwalwa baima san bakinsa ya suɓuce wajen fallasa asirin zuciyarsaba yace, “Ina ƙaunarki da komanki Neerat”.     Yay maganar da in ina jikinsa na wani ɗan tsumar da shi kaɗai yake jinsa a jininsa. Dan ita Zinneerah ma ruɗewar datai da salon nasa batasan ta fashe masa da kuka ba. Babu alamar ya jita, dan luuuu yayi dasu suka faɗa saman gadon. Babu shiri ta kanƙamesa jikinta na ɗaukar rawa jin harshensa akan kunnenta.       “Na shiga uku Yayanmu Please ”. Ta faɗa cikin muryar kuka tana ƙoƙarin ture fuskarsa dan neman sakata yin fitsari yake.     Al'amarinne yazo mata a bazata, gashi farko, gashi da mutum mai matukar girma da daraja a idonta, gashi ta sha gyara na musamman da ita kanta ko yaya akai mata wani salo sai jininta ya motsa.        “Shiiiiii!!!” Ya faɗa a cikin kunnen nata yana zagaya yatsansa saman bakinta. Tsit tai shiru tana haɗiyar zuciya. A nutse ya ɗago fuskarsa yana kallon tata cikin ɗan hasken fitilar ɗakin green.       Kasancewar idanunta a lumshe suke batasan kallonta yakeba, murmushi yayi mai sanyi ganin yanda take rawar jiki da ƙanƙame hannayenta a ƙirji. Kwanciyarsa ya gayara da kife fuskarsa akan tata, ya sumbaci haɓarta da matsar da lips dinsa kan nata da yatsansa ke kai har yanzun. A bazata taji saukar tausasan lips ɗin nasa akan natan. Sosai ta zabura da neman jan fuskarta sai dai babu damar hakan, dan ya tsare ko ina da ina babu wata damar kuɓuta yau sai alƙawarin ALLAH ya cika da izinin mai hukunci da rahama akan bayinsa masu haƙuri da juriyar karɓar ƙaddara da hannaye bibbiyu batare da raki ko ƙosawa ba.          Duk da ya haɗa bayanai masu yawa akanta lokacin da yazo babbar gaɓar mallakarta da iyakar jarumtarsa yaje, sai dai samun hanyarsa ɓam ta sakashi jin wani irin zazzafan tausayinta da ƙaunarta mai tarin yawa da tsanani na shigar gaɓɓansa. Ba tare da tuna son binta a matakin tausayawaba ya ji saukar ƙarar kukanta cikin kunnensa, dan a gigice ta ƙwala kiran hajiya iya da Maman Sadiq tana ƙanƙamesa jikinta na wani irin mahaukacin rawa data sakashi ƙanƙameta shima ya manne bakinsa da nata...........          Da ƙyar take fitar da numfashi hawaye masu matuƙar zafi da tausayin kanta na sakko mata. Bata taɓa sanin Yayansu mugu bane sai yau, ita kanta batasan adadin kuka da roƙon datai masaba, zata iya rantsewa har suma tayi na wucin gadi ta farfaɗo amma bai shirya barintaba sai da yakai inda yake buƙatar zuwa. Hannunsa dake damƙe da nata ya ɗan matsa da mirginowa ya rungumeta gaba ɗayanta a cikin jikinsa yana bata wasu irin hort kissis da ita kanta tasan na tsantsar ƙauna ne a gareta.       “Thanks you, thanks you, thanks you” kawai yake jera mata hawayen tausayinta na taruwar masa a idanunsa. Dan duk da kasancewarsa mutum mai tsananin jarumta da kakan daɗe bakaga kuka daga idaniyarsaba yau yaji tausayi mai tsanani akan Zinneerah, saboda abubuwa masu yawan gaske dake zuwa masa arai game da haihuwa da rainon cikin Little da tayi. Sunanta ya ɓaci ta yanda ba lallai kowa ya yarda da ita ɗari bisa ɗariba koda yayi ƙoƙarin fallasama duniya gaskiyarta. Tayi kuka, tayi wahala, tayi ciwo, ta rabu da garinta, ta rabu da mahaifinta, ta rabu da ƴan uwanta, ta rabu da farin cikinta duk a dalilin cikin ɗansa da batasan mafarinsaba. Dolene ya godema ALLAH daya ƙaddara yarinyarnan kasancewa matarsa ba wani daban can ta auraba. Yayi alƙawarin zai jiyar da ita daɗin duniya gwargwadon ƙwazonsa har sai ta san itaɗin ta musamman ce a garesa kuma mutum mai daraja. Dolene ya sanarma duniya wacece ita? Dolene ya wanketa ga mutane koda bazasu yardaba ya tabbatar musu da *_MAKAUNIYAR ƘADDARAR_* data jefa rayuwarta cikin hajijiyar rayuwa badan ta shiryama zuwanta ko karɓartaba itama. “I'm so sorry Neerat”.      Ya sake faɗa a cikin kunnenta hawayenta na sauka har bisa fuskarsa suna gaurayuwa da nasa na tsananin tausayin da yake mata dajin zafin zalunci mafi muni da akaima rayuwarta.         Cikin kuka tace, “Yayanmu ruwa. Ruwa zansha”.      A hankali ya ɗago kansa yana kallon fuskarta data kacame da hawaye, idanun sunyi luhu-luhu yana kallonta. Goshinta ya sumbata a hankali yace, “Ruwa kike so?”.      Kanta ta ɗan juya masa a hankali itama tana matso wasu sabbin hawayen. Hannu yasa ya share mata su. “Tom ya isa haka kinji, banason kukannan zai saki ciwon kai. ALLAH yay miki albarka uhmyim”.         Kanta ta maida gefe tana ƙoƙarin haɗiye kukan amma ta kasa. Raba jikinsa yay da nata da ƙyar ya jawo rigarsa ya saka, sakkowa yay daga gadon ya fita ɗakko mata ruwa dan yau ko shigowa dashi baiyiba ya manta.       A yanda ya barta haka ya sameta. Zama yay ya jingina da gadon sannan ya ɗagota jikinsa, ta saki karamar ƙarar azabar da wajen ke mata. Ruwan ya saka mata a baki yana ambaton, “Sorry sha ruwan muje ki shiga ruwan zafi”.       Sosai tasha ruwan wata sabuwar zufa na keto mata. Ta lafe a jikinsa tana lumshe idanu da sauke numfarfashin wahala. Idan zata iya tunawa bayan rainon cikin little da naƙudarsa data sha kafin ai mata cs bata taɓa jin abu mai azaba makamancin wanda taji yau a hannun Yah Abdul-Mutallab ba. Ta jigatu matuƙa irin jigatuwar da mantata gareta abune mai wahalar gaske. Tana tausayin mace a rayuwarta, da ace mata zasu nutsu su ajiye duk wani shirme da ruɗanin huɗubar sheɗan da tabbas wasu abubuwa ƙalilian dake zama wajib a rayuwarsu kawai sun isa zama sanadin kaisu aljannah. Yanzu da irin wannan daren kawai aka barka ai ba ƙaramin abin tashin hankali bane, balle akwai rainon ciki, uwa uba naƙuda da babu abinda za'a iya misaltata da shi. Ga fitar rai, Raino, hidimar gidan aure da ƙalubalensa.         (Kai jama'a mata masu duniya, mata sarakan duniya, mata na gaisheku, na gaisheku gaisuwa irin ta girma da mutuntawa dan kun cancanci a yaba muku, ku ƙara haƙuri jaruman duniya, ku cigaba da haƙuri taurarin duniya, kuzama masu haƙuri ALLAH zai sakanka muku da aljannarsa😍😘).         Ruwa AK ya shiga da kansa ya haɗa mata a toilet, sannan ya fito da kansa ya taimaka mata ta sauka a gadon hawaye na rige-rigen sauka mata, ganin tafiyar tasu babu sauri yasashi ɗaukarta kawai. Ajiyar zuciya ta sauke mai haɗe da kuka, dan hakan da yay mata ba ƙaramin taimakonta yayi ba.          Koda suka shiga ba kai tsaye ya tsundumata a ruwanba, cikin dabara da lallashi yay mata. Zinneerah nada dauriya sosai, koshi ya shaida hakan dan ta nuna masa jarumta yau duk da taci kuka, amma tun ihun farko datai lokacin isarsa gareta bata ƙara buɗe baki domin yin kwakwazo ba, sai dai hawayene kam da suna ƙarewa yau da sun ƙare gareta. A yanzunma hawayenne kawai sai ƙanƙamesa da tayi amma ko uhum batace ba.         Hakan ya masa daɗi, dan ya tsani kwakwazo a rayuwarsa da hayaniya, yafison komai a silent kuma da nutsuwa, wannan yana ɗaya daga cikin hallayarta data fara jan hankalinsa gareta batare da ita ta sani ba. Kanta dake kwance a ƙirjinsa ya rinƙa shafawa yana hura mata iskar bakinsa cikin kunne. Hakan ya matuƙar shagaltar da ita har ruwan ya ratsata yanda ya kamata ya ƙara mata wani kuma. Sai da ya tabbatar taji daɗin duka jikintama ba wajen kawai ba sannan yace mata tayi wankan.          Duk da tanajin nauyinsa ga zazzaɓi dake neman rufeta haka tabi umarninsa tayi, dan tsaye yay a kanta da alama yana son tabbatar da ingancin abinda zatayin. Yaji daɗin ganin yanda tayi komai dai-dai, sai kawai ya ɗauka mata bathrobe ya saka mata. Zai ƙara ɗaukarta cikin dasashshiyar muryarta tace,      “Zan iya”    Baice komaiba ya matsa ya bata hanya, cikin dauriya ta fice a toilet ɗin, saida ta fita gaba ɗaya ta cije bakinta da jingina jikin bango tana maida numfashi, tayi hutun kusan minti ɗaya sannan ta ƙarasa kaiwa gadon dake a hargitse. A ranta tace, ‘Dole ka hargitse gado dan nima an hargitsani’.        (😂🤣wayaga mai cikuykuya an zinni😆😝).        Ƙarasawa tai ta fara ƙoƙarin ganin ta gyara don buƙatarta kawai takai kwance. A dai-dai nan boss ya fito yana tsane jikinsa. Ƙarasowa yay inda take yana murmushi tausayinta fal ransa. Batare da sanin fitowar tasa ba taji an rungumeta ta baya da amshe bedsheet ɗin hannunta. “Uhm-uhm waya saki wannan aikin?”.      Sosai tsigar jikinta ta tashi saboda yanda yay maganar a cikin kunnenta. Bai damu da amsawarta ba ya ɗauketa ya dire a saman sofa. Shi kuma ya juya gaban gadon ya kimtsa musu shi, gabanta ya dawo ya durƙusa, tai saurin yin ƙasa da kanta saboda matsananciyar kunyarsa dake neman halakata, gashi yanzu babu riga a jikinsa sai towel daya ɗan yafa a wuyansa ƙarami bayan wanda yake ɗaure da shi. Lallausan murmushi ya saki yana lumshe idanu da sake buɗewa akanta lokacin da yake warware towel ɗin data naɗo gashinta dan ya tsane. Towel ɗin ya warware yana ƙara tsane mata gashin da ƙyau gudun kamuwa da mura.      “Duk zafinsa naƙuda tafisa ko?”. Ya faɗa yana zame towel ɗin daga cikin kanta.        Rashin fahimtar tanbayar tata ya sata ɗago kumburarrun idanunta ta kallesa. Ya sakar mata lallausan murmushi da ɗan jinjina kansa. Kanta ta maida ƙasa kawai gabanta na ɗan faɗuwa da tunanin koya san itace ta haifa little ne?.          Hannunsa ya ziro ta ƙugunta, ɗayan ya ɗago haɓarta sosai suna kallon juna. Duk yanda taso janye idanunta da suka shige cikin nasa hakan ya gagara, dan shu'umin kallon da yake mata tamkar yana zuba mata wasu sinadaraine masu matuƙar daraja da tsada, ta ɗan fara mar-mar da idanunta dake cikowa da ƙwalla.      Kansa ya girgiza mata alamar kartayi, kafin ya saki fuskar tata da matsota jikinsa ya rungumeta a haka suna sauke ajiyar zuciya a tare. “Aure jarabawane kuma ibadace, haƙuri a cikinsa nasarace kuma daraja ce. Riƙe mutunci da kame kai martaba ce, mutuntawace ga iyaye da tarbiyyarsu. Dan duk namijin daya sami mace a yanda yay hasashe ba ita kaɗaice ke samun kima a garesaba har iyayenta ma mutunci da kima suke ƙarawa. Kinsha wahalhalun rayuwa amma hakan baisaki yin gaggawa ba wajen ƴanta kanki har sai da ALLAH ya iyakance miki. Daga yau ke sarauniyace a fadar Abdul-Mutallab, ki ɗauka kin mallakesa shi da komansa. Kin bashi ƙyauta mafi daraja guda biyu da bazai manta da itaba. Kin haifamin Abdul-Mutallab, kin daɗamin da tukiycin budurci. ALLAH yayi miki albarka. ya yalwata rayuwarki da tarin farin ciki, ya share hawayenki ya yaye damuwarki, ya ɗaga darajarki ya cigaba da kare mutuncinki fiye da yanda kika kare nawa”.         Sosai tsoro ya kama Zinneerah jin ya ambaci haihuwar little, sai dai daɗaɗan kalamansa da batasan zai iya kwantar da kai wajen furtasu ga mace ba suna ratsata. Ya ɗago fuskarta yana kallonta. Lumshe nata idanun tayi saboda nauyinsa da kwarninsa.         Ɗan murmusawa yay da miƙewa tsaye, ya kamo hannunta suka nufi gaban mirror batare datasan mi zaiyiba. Dan barci takeji sosai tanada tabbacin kuma asuba ta gabato, ga zazzaɓi jikinta zau, tasan kuma yanajin zafin. Baice mata komaiba ya zaunar da ita a kujerar mirror ɗin, kanta a ƙasa harya jona handryer dake ajiye, gashinta ya fara busar mata sannu a hankali, sannan ya tufƙe matashi da ƙyau yanda bazai takura mataba. Rigarsa ya juya ya ɗakko cikin Wadrobe yazo ya fesheta da turare sannan ya saka mata bayan ya zame bathrobe ɗin tanata noƙe-noƙe dan kunya. Rigan ya kai mata har cinya dan haka ta saki ajiyar zuciya. Sake kamata yay ya kai bakin gado ya zaunar, ya buɗe drawer gefen gadon ya ciro magani dan yaji zazzaɓi a jikinta. Bata yay, babu musu tasha saboda bukatarsa da takeyi. Tana sha yana shafa kanta harta shanye ta miƙa masa ruwan.      “Good girl.” Ya faɗa yana kamata ya kwantar, tare da ja mata bargo ya lulluɓa mata iya rabi sannan ya sumbaci goshinta da cewa “Good night”.       Kanta kawai taɗan jinjina masa tana lumshe idanu. Wahala tasa barcin ɗaukarta cikin ƙanƙanin lokaci, sai saukar numfashinta ya rinƙaji a hankali. Lip ɗinsa ya cije yana firzar da wani irin huci mai ɗaci dan tabbas bazai bar duk mai hannu a al'amarin nanba. Matakin farko zai fara ajiye hujja ga iyayensu a safiyar gobe idan ALLAH ya kaimu, zai kuma saka bincike na kwanaki biyu zuwa uku domin tabbatarwa da kama masu hannu a ciki dumu-dumu.     Duk da shima barcin yakeji bai kwantaba, alwala yayo da saka jallabiya ya fara nafilfili dan asuba ta gabato ma, yasan idan ya kwanta zasu makarane kawai. Zinneerah kam tasha tarin addu'oi harma da iyayenta, yana a wajen har akai sallar asuba dan bai fita massallaci ba yau bayajin ƙarfin jikinsa sam.      Badan yaso ba ya tada ita da ƙyar domin yin salla. Aiko yasha langaɓe dan sai faman lumshe idanu take, sai da ya taimaka mata zuwa toilet ɗinma tayo alwala sannan. Tanako idar da salar yau babu zancen azkar ta ɓingire a wajen. Ɗagata yay cak ya maida a gadon ya kwantar shima yabi sahunta dan kansa ya fara masa ciwo saboda barci. Cikin so da ƙauna ya rungume matarsa cikin jikinsa suka lula duniyar barci.        *_12:5pm_*     Sai ƙarfe sha biyu da mintuna biyar AK ya farka saboda kiran wayarsa da akayi, ƙaramin tsaki yaja dan barcin sam bai ishesaba. Da ƙyar ya lalubo wayar ya buɗe ido yana kallon mai kiran. Ganin Granny ya sashi gyara kwanciya sannan yakai kunne.         “Assalamu alaiki, Granny barka da asuba”.       “Ai dama barka da dare kacemin, kujimin iya shege da ranar ALLAH kake kiramin barka da asuba. Kai ko moddibo kana lafiya yau kuwa kai da inno? An aiko muku da abinci kusan mutum uku suna zuwa amma an ƙwanƙwasa ƙofa ko motsinku babu”.        “Oh God! Granny sai kin mana kwakwazo duniya tasan bamu tashi ba? To barci mukeyi”.       “Eh lallai ai nafaji barci kukeyi ja'iri, sai ka tashi ka buɗe ƙofa ka amsa ka koma ku cigaba da barcin”.      Murmushi ya saki da ajiye wayar yana faɗin, ‘Hajiyar matsala’. Daga haka ya ɗan leƙa fuskar Zinneerah dake barcinta hankali kwance sannan ya zare jikinsa a hankali ya sauka a gadon. Jallabiya ya ɗauka ya ɗaura saman boxer ɗinsa ya fito.        Haneef ya samu zaune a saman motar da yazo, yana ganinsa ya duro ya nufosa ɗauke da basket. “Yayanmu barka da hantsi?”. Ya faɗa cike da girmamawa.        Amsa masa yay da kulawa yana tambayarsa jama'ar gidan.     “Kowa lafiya yake yayanmu”. “Alhmdllh, yanzu daga nan ina zaka?”.       “Ba ko'ina zan koma gidane”. “Okay to kabar zuwa gidan, gidan Abba zan aikeka kaje ka ɗakko min Gwaggo Maryama, sai ka biya ta gidan dasu Mammah suka sauka ka ɗakkomin Mahma. Kafin kaje duk zan kirasu”.          Kai Haneef ya jinjina ransa fal wasiwasin lafiya kuwa?. Rashin mai basa amsa ya sashi miƙa masa basket ɗin kawai ya juya domin cika umarninsa..      Shima ciki ya koma kai tsaye sashensa. a dining ɗin falon nasa ya ajiye basket ɗin ya koma ciki. Wayarsa ya ɗauka yay zaman kiran Hajiya iya, sun ɗanyi magana ya maida kiran ga Mahma kuma sannan ya kira Abba na gidan mmn sadiq...............✍ *_Aunty Farah kina can wagaga da baki za'a mallake mana AK😖😖😬😬😒😒😏😏😏😾😾🙄🙄😑._* *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_*   *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* *Page 59* ________________________ *_KAƊAN YA RAGE SU ƘARE_* *_MATA ƴan ƙwalisa kuna ina za'aci kasuwar sama babu ku?. Mg's skincare ɗin fa na gab da ƙarewar kaya kuna nan sake da baki baku mallaki naku ba_* _Mg's SKINCARE nagartattun kayan ne dake gyara jiki da fata cikin sauƙi, sunada inganci da rahusa dai-dai da aljihunku._ *Da kin fito a ringa ga tauraruwar taurarin nan mai fatar da babu kamarta tamkar dinare abin haske da walwali.* *_Sabulunsu kawai kika ɗana sai kinsan kin kai kuɗinki inda babu asara balle dana sani_* _A yanzu haka muna jerin kayayyaki da suka rage kamar haka_👇🏻 Available _Akwai: herbal whitening black soap 3k_ Akwai: beauty kit 11k shi set ne yakunshi Abu 6 Soap Body cream Face cream Body nd face scrub Cleanser Glow oil Location kaduna buh mn tura Kaya ko Ina saidai inmutum ya amshi kayanshi zebada kudin delivery WhatsApp 08062991549 Call 08064532391 Instagram:glow_with_mgs Facebook:mg's skincare *_Karku bari ayi babu ku guys, siyan nagari maida kuɗi gida._* ________________________ *Page 59* ............Koda ya dawo bedroom ɗin wanka kawai ya shiga batare daya tada Zinneerah ba. Harko ya fito ya kammala shirinsa tsaf cikin ƙananun kayan da sukai masa matuƙar ƙyau da ƙara fidda kwarjininsa da ƙuruciya bata farkaba. Yana tsaka da saka turare ya jiyo ana danna door bell, ajiye turaren yayi ya ɗauka wayarsa da ƙarasowa gaban gadon saitin da take kwance. Wani lallausan murmushi yake saki yana ƙarema fuskarta kallo musamman bakin daya tsuƙe. A hankali ya ranƙwafo ya sumbaci bakin da hancinta da goshinta, yana motsa laɓɓansa a hankali wajen ambaton, “ALLAH ya albarkaci rayuwarki”.      Daga haka ya fice abinsa. Yana buɗe ƙofar da Hajiya iya da Moos'ab ya kawo yaci karo. Ta zuba masa harara da faɗin, “Shegen gida kamar na ƴan yankan kai, sai ka danna ƙararrawa an gama yarfaka za'a buɗe maka”.      “Oh-oh daga zuwanki sai neman faɗa, yi haƙuri ni yau bana faɗa”.        “A lallai ai naga alama a goshin ka ma ja'iri mara kunya”. Hajiya iya ta faɗa tana turesa da shigowa cikin falon abinta.     Murmushi ya ɗanyi dakai hannu ya murza goshinsa. A ransa yana faɗin ‘Mi matarnan ke nufi dani?’. Bashi da mai bashi amsa dan haka yay ƙoƙarin bin bayanta. hannunta ya riƙo ganin ta nufi sashen Zinneerah. “Kinga inda zakiyi nan madam”.        “Kai ni sakeni naje na fara ganin Inno tukunna, haka kawai ka wani tattaromu sai kace ƴaƴanka”.        “Uhm ke dama ba'ayi miki dai-dai, ai Innon taki na inda zan kaikin ko”.      “Ato muje naga abuta dan nikam ban yarda da wannan munafurcin nakaba yau Moddibo”.     Murmushi kawai yayi batare da yace mata komaiba suka nufi sashensa. Kamar jira suna isa falon saiga sallamar Haneef. Zaunar da hajiya iya yayi sannan ya amsa da cewa “Shigo da su”.      Kasancewar dama Haneef na tare da Mahma da  Gwaggo Maryama da duk hankalinsu ke tashe da wannan kira na AK ɗin sai ya matsa musu alamar su shiga. Shi kuma ya juya.                Cikin girmamawa AK yay zaman gaishesu su duka. Cikin rashin haƙuri Hajiya Iya tace, “Mukam dai duk ka tada hankalinmu Moddibo, mike faruwa ne? Ina Inno kuma?”.         Ɗan dubanta AK yay yana maida kansa gefe da faɗin, “Ku kwantar da hankalinku ba wani abu bane, na saku zuwa nanne domin ku zama na farko dazan fara tabbatarmawa kafin kowama ya sani”.         Hajiya iya dake cikin jimamai tace, “To muna saurarenka, ALLAH ya jishemu alkairi”.     Da amin Mahma da Gwaggo Maryama suka amsa. AK ya gyara zamansa kansa a ƙasa dan nauyin maganar da zaiyi. “Kuyi haƙuri duk da ba magana bace wadda ya kamata kusani, amma saboda wasu dalilai naga ya dace ku sani ku kuma zama hujja akan binciken da zan ƙarasa. Mu dukanmu nan munsan cewar Zinneerah ta haihu a shekarun baya, kuma koda yaushe maganarta shine batasan a inda ta samo ciki ba. Wasu kan ɗauketa mara hankali, wasu na ganin tana wasa da hankalin mutanene kawai ko rainin wayo da makamantan haka. Wasu kuma kan mata uziri da cewar ƙaddara ce ta afka mata. Tabbas ƙaddara ce, da a zahirance zamu iya kiranta *_MAKAUNIYAR ƘADDARA_*. ALLAH shine shaidata ban taɓa taɓa ƴar kowa ba da nufin fasiƙanci. hakkane ya tada hankalina matuƙa akan Zinneerah har takai bana iya barci, a ƴan kwanakin nan gaba ɗaya cikin shan maganin hawan jini nake saboda tashin hankali da tunanin ta hanyar da aka samar da Abdul-Mutallab, sai da Granny ta kawo wani zance da Khalipha yayi akan dashen ciki sannan ALLAH ya haskamin hanya. A dalilin haka na cigaba da bibiyar abubuwa da dama a ɓoye batare da sanin kowaba, har ALLAH ya tabbatar a yau nakai gaɓar da nine na farko da zan fara tabbatarma duniya lallai dashen cikin Abdul-Mutallab akaima Zinneerah bata hanyar banza ta samoshi ba. Dan bata taɓa tarayya da namiji ba sai daren jiya. Inaji a raina ALLAH ya keɓance tane daga haihuwa da kanta sai cs akai mata domin irin wannan ranar dazai wanketa ga kowa”.        Kallon kallo aka shigayi tsakani Mahma da Granny da Gwaggo Maryama, shi dai AK tunda ya fara bayaninsa harya ƙare bai yarda ya kallesu ba idanunsa a ƙasa.       Cikin karfin hali Mahma ta katse tararrabin su ta hanyar kallon AK da faɗin, “Abdul-Mutallab ka sakamu a duhu nikam, kenan tayaya aka dasama baiwar ALLAH nan gudan jininka?”.        “Wannan ne nakeson sani yanzun, amma Mahma kiyi haƙuri, inaga wannan abin ba kowa bane ya ƙullasa sai Zakiyya, Farah da Mammah, dan naji wasu zantuka nasu da suka rikitani jiya da rana sanda nazo gidan nan, to kafin na shigo na fara samunsu a garden ne amma su basu san na jiba. Sannan idan kin lura duk sanda akai maganar dashen cikin nan sai sun razana. Dalilina na biyu Dr Mahmud ya tabbatar min shi baiga wani alamun mai ciki tattare da Farah ba. Sannan ni kaina idan zanyi aiki da hankalina ai ciki girma yakeyi a jikin mace, amma ace kusan 5months babu wani alamarsa a jikin Farah. Idan baki mantaba cikin farko data samu tun yana wata uku suka matsa sai da ta tafi Morocco, bata dawo London ba sai da tai ɓari kamar yanda suka faɗa. To wannan ma a ƙiyasina tun yana wattani ukun ta shiga damuna zataje, amma zuwan danai da Granny ya sani taka mata birki. Hujja ta biyu a labarin da Zinneerah ta bamu na zuwanta katsina aikatau yayi kama da wadda aka yaudara saboda ƙuruciyarta, bayan an cutar da itane ta gudo batare da saninsu ba. Abinda kawai ban fahimtaba anan shine Mammah tasan hakan kokuwa ita Zakiyya da Farah ne kawai suka sani ko itama Farah bata sani ba? Hujjata ta ƙarshe samun Zinneerah da martabarta ta ƴa mace”.       “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un” Mahma dasu Granny keta ambata, hawaye suka shiga sakkoma Mahma, tasa hannu ta sharesu da faɗin, “Lallai biri zai iyayin kama da mutum Abdul-Mutallab, dan nima kaina ina mamakin rashin tasawar cikin Farah. Sannan akwai wasu abubuwa na rashin gaskiya da zakaga suna shan aikatawa a wani lokaci kuma, lokacin cikin farko na taɓajin wata wayarta da Adilah lokacin tana hostel a makaranta, sai dai ina shiga ta yanke wayar. Indai kuwa hakane sun cutar da yarinyar nan matuƙa, sun ɓata mata suna, sun sakata wahala da ƙarancin shekaru. Wane irin son zuciya ne wannan? Kai kanka damu sun cutar ai”.     Ta kare maganar tana kuka sosai. Gwaggo Maryama ma hawaye takeyi, Granny dai idanunta sunyi matuƙar yin jajur alamar shiga ƙololuwar ɓacin rai. taja numfashi mai zafi da faɗin, “Lallai kayi haƙuri Moddibo, idan har ta kasance wannan zancen ya zama gaskiya sai nayi shari'a da uwarka da matarka. Dan wlhy sai na bima inno kadin haƙƙinta. Yanzu abinda nakeso da kai kar kai musu maganar komai, kuma tabbas inaga Zakiyya itace hajiyar da aka kai Inno gidanta. To karka yarda su haɗu anan gidan yanzun, dan idan suka gane itace zasu iya bin wata hanyar suga sun rufe asirinsu. Abinda nakeso dakai yanzu daganan zuwa safiyar gobe idan ALLAH ya kaimu ka aika hukuma a kama matar data kai Zinneerah aikatau katsina, itace zata kaimu ga hajiyar farko, ita kuma ta kaimu wajen wadda Zinneerah ta faɗa mana tata jerangiya da ita asibiti, na tabbatar zamu kamo bakin zaren insha ALLAHU.”          Duk da kalaman cewar sai tayi shari'a dasu Mammah ya bashi tsoro dan yasan Granny akan tsayawa wanda aka zalinta hakan bai hanashi ɗaga mata kai ba cikin girmamawa yace, “An gama insha ALLAH, dan yanzu hakama zancen da nake miki tana police station tare da Khalipha. Tun da safe yaje Dayan akanta, ya tatar tana katsina, shine ya zarce can har inda take bisa taimakon wani bawan ALLAH ɗan nan Danya ɗin. Dan da nace a fara kamamin matar baba sai Khalipha ya bani haƙuri akan a barta kodan darajarsa dan yama tarar itama bata da lafiya. Mu kama matar dai kawai tunda ta hanyartane kawai za'a iya bin diddigin abun”.        Mahma tace, “Alhmdllh hakan da kukai shine dai-dai, yanzu yaya akai mi matar tace?”.      “Mahma ba'akai ga tambayarta komai ba, dan inaga ko mintuna goma basuyi da isowaba ma, ina gama waya daku ya kirani yake sanarmin ya dawo harda matarma tana station yanzu haka”.          Gwaggo Maryama dai ta kasa tofa komai, sai hawaye taketa faman zirararwa. Hajiya iya tace, “Kabeer ya san duk wannan?”.       “A'a ban faɗa masa ba”. “To ya kamata ya sani dagashi har Ahmad da Abubakar (Abba mijin maman sadiq) da baban ita Zinneerah, dan babbar maganace wannan data wuce yinta iya mu kaɗai”.        “Babu damuwa Granny, dama ai dole zasu sani, dama munason mu kammala gano inda mutanen suke tukkuna sai na sanar dasu. Amma tunda kinga ya dace su sani tun yanzu shikenan”.          Mammah ta buɗe baki zatai magana kenan sai ga Zinneerah ta fito tana tafiya a hankali batare da tasan da zamansu a falonba. Ita cama take AK ɗin baya gidan, dan tun ɗazu ta tashi, cikin ƙarfin hali ta gyara masa ɗakin da wanke toilet, yanzuma ta fito ɗaukar kayan sharane.        Tun fitowarta ƙamshin turarenta ya isar masa hanci, dan haka ya waiwayo domin tabbatarwa. sai dai yayi dai-dai da suma duk suka ganta ɗin.      Sai dai babu wanda ya iya cewa komai a cikinsu harta iso kusan tsakkiyar falon, turus taja ta tsaya gabanta na faɗuwa ganin yanda suke mata kallon ƙurulla su duka. Sai duk ta daburce dan gani take kamar duk sun san miya faru da ita a daren jiya. Da sauri ta juya zata koma inda ta fito Hajiya Iya tace, “Inno ba gaisuwa?”.       Matse idanunta tai da cije lips ɗinta waje guda tamkar zata nutse dan kunya. Musamman daya kasance cike da tsokana hajiya iya tai maganar.       AK dake binta da kallo ƙasa-ƙasa yace, “Granny ke baki iya gani ki ƙyale?”.          Dariya duk suka ɗanyi, dai-dai Zinneerah na isowa inda suken kanta a ƙasa. Can jikin kujera ta lafe tana gaishesu, saika rantse wasu baƙin tane da bata saniba ko take matuƙar jin kunyar haɗuwa dasu. Yanda tayi ɗin ya bama AK dariya matuƙa amma ya gimtse baiyiba.       “Oh kajimin ja'ira wa kikema wannan lafe-lafen anan to? Koda yake sai dai idan surukarki Zaliha”. hajiya iya ta faɗa tana nuna Mahma dake kallon Zinneerah ɗin da murmushi a fuskarta tanajin tausayi da ƙaunar yarinyar har cikin bargonta. Itace ta tashi tsam ta kamo hannun Zinneerah data kasa tasowa duk da maganar da Granny tayi.       “Haba ɗiyata minene najin kunya, mufa nan duk iyayenki ne, ga kuma kaka nan. ALLAH yay miki albarka kinji, ya sakanka miki da alkairi mai yawa ta inda bakiyi zatoba. ALLAH ya tsare gabanki da bayanki ya ƙara ɗaga darajarki a wajen mijinki”.       Babu kunya AK yabi sahun ƴan amsawa da amin, sai dai shi a saman laɓɓa yayi saɓanin su hajiya iya da sukai a fili. Ita dai Zinneerah ta kasa kallonsu koda sau ɗaya dan jitake kamar ƙasa ta tsage ta shige ciki. Dama kuma ga miskilanci data ƙware kuma ta haddace duk da bataima Hajiya iya yau dai itama ta shafeta kam.      Duk yanda sukaso ta sake hakan ya gagara, hakan yasa hajiya iya cewar, “Tunda yanzu baƙya yayina Inno tashi kije abinki, ai gobema rana ce”.      Tsam ta mike a tunaninsu tafiyar zatai, sai sukaga ta nufi hajiya iya. Tana zuwa a jiki ta faɗa mata hawaye na gangaro mata.       “Oh ashe moddibo ne ya fara koya miki gulmarsa ta basarwa kina yina”. Hajiya iya ta faɗa tana shafa kan Zinneerah ranta fes da so da kaunarta data kara ninkuwa a ranta, ga ɗunbin tausayinta kuma.     Albarka suka dinga saka mata AK na tayata da amsawa. Daga ƙarshe hajiya iya ta sata sake basu labarin abinda ya faru a zuwanta katsina. Suka kuma dora mata da ƴan tambayoyin abinda ya shige musu duhu musamman Mahma da hausar tata ba cika yay ba.          Sallamar Zinneerah sukai su kuma suka cigaba da tattarawa, da wannan damar ta samu kuɓuta ta koma ɗakinsa. Barin batun shara tai ta shige toilet tai wanka da sake gasa jikinta da ƙyau, yunwa takeji sosai ga jikinta da takeji fayau, sai bakinta dake ɗaci amma babu zazzaɓin. Sai dai illahirin gaɓɓanta babu inda baya mata ciwo. Taji daɗin ruwan zafin sosai. Dan sai da ta tabbatar ko wace gaɓa tata ta gamsu kafin tai wanka ta fito ɗaure da towel ɗinsa daya tsaya mata iya cinya. Batai tunanin samunsa a ɗakinba tunda tasan yana tare da baƙi, sai dai kuma tana fitowa tai turus saboda cin karo datai dashi zaune a bakin gado yana waya.        Da baya-baya ta dinga jan ƙafarta zata koma AK ya miƙe yana binta da wani shu'umin kallo daya nema harmutsa hanjin cikinta dan tsoro, dan ita dai harga ALLAH wani irin tsoronsane ya sake tasiri a ranta bayan matsananciyar kunyarsa da bata taɓa ji ga wani ba. Ganin ya taso ɗin ya sata kara sauri, sai dai babu nasara dan taku baifi huɗu yayba ya cafkota. Gaba ɗayanta ya jawo jikinsa yana faɗin, “Okay Baffah sai nazo gidan zuwa anjima ɗin”.     Daga haka ya ajiye wayar a ƴar drawer ɗin wajen da suke gab da ita.        “Anya wannan jikan na Granny zatai jarumta?”.     Ya faɗa cikin wani irin kasalalliyar murya dai-dai yana sa kansa a wuyanta. Duk da wanka tayo hakan bai hana tasirin fitar kamshin mayun khurah ɗinta ba. Ya ƙara tura hancinsa cikin wuyan duk da laimar ruwan dake naso a jikinta. Tare da zagayo duka hannayensa akan cikinta.       Cikin rawar murya kamar mai shirin fasa kuka tace, “Yayanmu su Granny”.          “Su Granny mi? Ba suna falo ba muko muna nan abunmu a ɗakin sirrinmu”.          “Amma zasu ce.....” Ta kasa ƙarawa saboda nauyin maganar.        Yana cigaba da shin-shinar wuyan nata dake tada mata tsigar jiki yace, “Zasuce ina lalube amaryana?. To ai suma sunsan tunda suka bani komaima zanyi baby girl”.        Zinneerah da kunya ke neman kasheta da mamakinsa, tai saurin cewa “Nifa ba hakaba Yayanmu”.       “To yaya ne?”. Ya faɗa yana ɗagowa da birkitota suna fuskantar juna. Kafafu ta shiga matsewa saboda kunyar cinyoyinta dake waje. Yanda take ɗinne ya sashi kallon cinyoyin, idanu ya ɗan lumshe da sake buɗesu a kansu, kafin ya cije lip ɗinsa muryarsa na canja amo yace, “Karfa kisa nai miki wani sabon aika-aikan ALLAH. Muje ki shirya ga abinci har 2 tana neman yi. Kinyi salla ko?”.           Kanta a ƙasa ta daga masa kawai.       “Magana da baki”. Dole ta buɗe baki tace, “Eh nayi tunma dana tashi naga lokaci yayi”.      “Good. kije ki shirya to, ko na shiryaki ne?”.        Babu shiri ta waro masa idanunta da har yau ke a ɗan kumbure. Shima waro mata nasa yayi sosai. Hakan sai ya sata jin kunya tai saurin saka tafukan hannaunta ta rufe fuska murmushi na suɓuce mata.         Wannan salon nata na nuna yawan jin kunya na kayatar dashi, dan haka ya rungumeta gaba ɗaya a jikinsa yana faɗin, “Ina son wannan salon naki baby. Da gaske fa kina neman shigama Farah hanci, idan kuma ta tashi fyatoki zakiji jiki”.      Gaban Zinneerah ne ya faɗi dan itakam sai an amfaci sunan aunty Farah take tunawa da ita, tare da tuna cewa Yay Abdull-Mutallab bafa nata bane ita kaɗai, akwai wadda ta fita tsananin sonsa da kishinsa, komai kuma zata iya aikatawa akansa. lallai tana cikin lukutin yanayi duk randa aunty Farah tazo Nigeria (dan itafa batasan suna nan ba har Mammah).       Ganin yanda ta koma saboda ambaton Farah da yayi sai ya ɗauketa cak domin gusar mata da tunanin, saman gadon ya ɗorata yana ƙoƙarin kwance towel ɗin jikin nata ta riƙe gam idanunta na firfitowa waje da jera masa roƙon haƙuri jikinta har rawa yake.      Duk yanda yaso ya danne sai ya kasa sai da ya dara. Ya ɗan dungure mata kai da faɗin, “Matsoraciya kawai. Tashi ki shirya kici abinci inason fita”.      Yana gama faɗa ya nufi hanyar fita dan ya bata damar da zata kimtsa tunda ya fahimci a takure take matuƙa.      Koda ya fita ɗakinta ya nufa, babu jimawa sai gashi da kayanta ya ɗakko mata. Less ne zani da riga kalar milk da kwalliyar coffee. Sai B&F ɗinta daya tuno masa randa ya far ganinta a gidan Granny. Haka kawai ya shiga sakin murmushi shi kaɗai tun a ɗakinta. Tana gyar gashinta ya shigo, ganin duk ta daburce sai baiyi magana ba ya ajiye mata kayan kawai a gado ya fice abinsa zuwa falo.         Ajiyar zuciya ta sauke tare da juyowa ta kalla kayan nata. Har cikin ranta tanajin daɗin wannan kulawar tasa na yimata hidima batare da duba cewar ya girme mataba. Sannan inda wani ya bata labarin zata iya samunsa haka da sauƙin kai bazata yardaba. Musamman idan tai dubi da halayyarsa da kowa ke kallonsa da ita na rashin sakewa da barazana da rashin ɗaukar raini. Shiyyasa akace karka yankema mutum hukunci har sai ka zauna da shi sannan. Dan wani ɗan adam ɗin ba'a taɓa karantar shi wanene sai an rayu da shi. Ashe wannan damar Farah ta samu daga garesa take yanda ta gadama. A binda kuma ta fahinta da shi adalcine kawai da sanin darajar mace da son mutuntata ya sashi zama mai sauƙi ga iyalansa badan anfi karginsa bane ko bazai iya motsa ƙwanji ba. Jitai wani natsuwa da kaunarsa na sake saukar mata a rai da bargo, har tana jerama UBANGIJI kalaman godiya da samunsa matsayin abokin rayuwarta batare da yayi shawara da itaba ko dubi da cewar AK ɗin ya ɗarata a komai na darajojin duniya, a lahiran kuma tana fata da addu'ar su kasance a muhalli ɗaya a gurbin gidan aljanna insha ALLAHU rabbi..      Da wannan tunanin ta kammala shiryawa a gurgurguje duk tunaninta su Granny na'a gidan basu tafi ba.............✍ *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_* *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* *Page 60* ________________________ *_KAƊAN YA RAGE SU ƘARE_* *_MATA ƴan ƙwalisa kuna ina za'aci kasuwar sama babu ku?. Mg's skincare ɗin fa na gab da ƙarewar kaya kuna nan sake da baki baku mallaki naku ba_* _Mg's SKINCARE nagartattun kayan ne dake gyara jiki da fata cikin sauƙi, sunada inganci da rahusa dai-dai da aljihunku._ *Da kin fito a ringa ga tauraruwar taurarin nan mai fatar da babu kamarta tamkar dinare abin haske da walwali.* *_Sabulunsu kawai kika ɗana sai kinsan kin kai kuɗinki inda babu asara balle dana sani_* _A yanzu haka muna jerin kayayyaki da suka rage kamar haka_👇🏻 Available _Akwai: herbal whitening black soap 3k_ Akwai: beauty kit 11k shi set ne yakunshi Abu 6 Soap Body cream Face cream Body nd face scrub Cleanser Glow oil Location kaduna buh mn tura Kaya ko Ina saidai inmutum ya amshi kayanshi zebada kudin delivery WhatsApp 08062991549 Call 08064532391 Instagram:glow_with_mgs Facebook:mg's skincare *_Karku bari ayi babu ku guys, siyan nagari maida kuɗi gida._* ________________________ *Page 60* ...........Fitowa tai da sanɗa kanta a ƙasa saboda tunani da kunyar su Granny da take zaton har yanzu suna gidan. Yayinda AK dake zaune a falon shi kaɗai yana latsa waya mayataccen ƙamshin haɗin khumrah ɗinta ya samu nasarar kaiwa ga hancinsa. A hankali ya ɗago yana kallon sashen ƙofar bedroom ɗin nasa zuciyarsa na wani motsawa a cikin ƙirji.        A kan laɓɓansa ya ambaci kalmar “Mash ALLAH” yana wani lumshe idanunsa. Ganin tana nufar hanyar fita da sanɗar da takeyi ya ɗan murmusa, sai da ta ɗan gotashi yace, “Nan zaki zo ai”.          Ina ƙasa Zinneerah ta shige dan kunya, har mamakinsa take ganin shi ko'a jikinsa tamkar bai aikata wani aika-aika ba.       “Kona taso?”. Taji ya sake ambata. Kafinma ya gama rufe baki ta nufosa dan shi ba abin wasanta bane, abinda ya shiga tsakaninsu kuma bai rage masa kimarsa da girmansa a idanuntaba sai ma ƙaruwa da yayi. Ta ɗanji sanyin ganin babu su Granny, dan haka taso kaiwa tsugunne gabansa.           Bai motsa daga kishin giɗar da yay a kujera yana mata kallon ƙasan ido ba, ya kamo hannunta ganin zata tsugunna. A saman cinyarsa yay mata masauki. Hakan ya sata saurin kallonsa. Da wannan damar yay amfani wajen riƙe idanunta cikin nasa. Duk yanda taso ta janye ta gagara. Sai neman kashe mata jiki yake da wani sakaltaccen kalo dake tada mata tsigar jiki. Babu shiri idanunta suka fara tara hawaye.        Karan farko tun shigowarta falon guntun murmushi ya bayyana a fuskarsa, ya lumshe ido ya buɗe a kanta yana kamo fuskarta cikin tafukan hannunsa. “Miyasa ke raguwane?.”       Cikin suɓutar baki tace, “Tsoro kallon yake bani”.       Harga ALLAH ta bashi dariya, duk yanda yaso danneta kar yayi kuma hakan bai yuwuba, sai gashi da sakin murmushin da har haƙwaransa na bayyana. Shagala tai da kallonsa dan tabbas murmushi na masa ƙyau musamman wanda ke bayyana haƙwaransa irin wannan. Nisan da tai a nazari yasa harya iso da fuskarsa gab da tata bama ta saniba. Sai jin saukar laɓɓansa kawai tayi akan nata. Duk yanda taso ta nuna zamewa hakan ya gagara. Dan wani irin sallo da tunda uwarta ta haifeta ba'a taɓa mata shiba yake sarrafa lips ɗinta.         Luf tayi tana amsar rikitaccen karatun na babban yaya data fara haddacewa daga safiyar jiya zuwa yau. Sai da ya tabbatar ya ida zubar da ɗan sauran ƙarfin data samu sannan ya barta yana rungumeta a jikinsa gaba ɗayanta. Yanda yaken sauke numfashinsa mai sanyi da nutsuwa a cikin kunnenta yasata sake lafe masa a jiki tana rumtse idanu. A ranata ko rayawa take, ‘Yayanmu zaka kasheni da wannan salon naka da yafi ƙarfin shekaruna’.        Sun kai kusan mintuna uku a haka kafin ya ɗagota yana kallon fuskarta, duk yanda yaso su haɗa ido yanzun kam taƙi yarda. Yatsunsa biyu ya sa ya ɗago haɓarta, bai damu daƙin yarda su haɗa ido da taiba.         Tana bashi dariya da ƙara birgesa da wannan sanyin nata, dan haka yay wani munafukin murmushi da kamata ya miƙar.         Dining suka nufa yana riƙe da hannunta, sai da ya zaunar da ita sannan shima ya zauna. Da kanta ta miƙe ta haɗa masa abincin yanata faman binta da fitinannen kallon nan nasa dake sakata dabircewa komin jarumtar da taso nunawa.      Shiko fahimtar da yay kallon nasa na mata tasiri tunma suna can gidan yake sakashi kasheta da su. Bata zuba nataba, bai kumayi maganaba, sai da ta gama ta koma ta zauna ta ɗan dubesa. Ganin shima dai kallon nata yake ya sata janye nata idanun gefe.        Komai baice mataba ya fara cin abincin, sai da yay nisa da ci sannan yay magana batare daya kalletaba. “Juyo nan”.       Juyowar tai tana fuskantarsa, sai kawai yay mata alamar ta buɗe bakinta. Ganin yanda fuskar tasa take ya sata buɗewar. Daga haka ya cigaba da ciyar da ita yana ci shima har suka cinye. Godiya yayma UBANGIJI yana miƙewa ya barta a wajen. Hakan ya sata miƙewa itama ta tattare kayan a basket ɗin da aka kawo, sam batajin daɗin jikinta, a yanzu haka tafi buƙatar ta samu waje ta kwanta. Sashen ta bari baki ɗaya zuwa nata, tana shiga ta sauke ajiyar zuciya da nufar kitchen.       Tana cikin wanke kwanikan ya shigo kitchen ɗin, waiwayowa tai ta dubesa. Ya canja kayansa zuwa shadda fara tas da tai masa tsananin ƙyau, ga mayataccen ƙamshinsa mai cika hancin mai shaƙa da bashi nutsuwa. Ya ɗan janye idanunsa daga kanta yana kallon agogon hannunsa. “Bara na gaishe da su Mammah kina buƙatar wani abu ne?”.           Duk da tayi mamakin jin zancen Mammah sai batace komaiba taɗan girgiza masa kanta.      Takowa yay gabanta yana ɗago fuskarta suka kalli juna. “Baza'amin addu'a ba?.” ya faɗa a wani irin sanyin murya.         Tana mamakin a yanda ya iya sarrafa yanayinsa a salo daban-daban, kuma duk cikin kame kansa babu wani rawan kai ko gaggawa tattare da shi. Idan badan ita da take ganin true color ɗinsa a tsakanin jiya zuwa yau ba babu wanda za'a faɗama haka yake ya yarda, dan ko'ita idan yay abu ya basar sai take ganin tamkar ba shine ya aikataba. Ya barta da kunya shiko ko'a jikinsa.......        “ALLAH ya tsare ya dawo da kai lafiya Yayanmu”.      Haɓarta ya saki da tura duka hannayensa a aljihunsa yana kallonta,  “Har yanzu matsayin Yayan kawai gareni?”. Ya faɗa yana tsatstsare ta da idanunsa masu kaifi a gareta.         Ɗan ɗago idanu tai ta kallesa, ya wani juya mata nasa manyan idanun yana ƙara tsuke fuska.       “Yanzu ni waye a wajenki?”   Ya faɗa cikin muryarnan tasa ta rashin sakewa.      Mamaki tambayar tasa ta bata, da ɗan rawar murya da kunyarsa ta haifar mata tace, “Yayanmu!”.       “Daga nan fa?”.     Duk da ta fahimci abinda yake son jin sai ta noƙe dan itama ɗin dai gwanace a miskilancin.       “Zaki magantune”. Ya faɗa yana sake kallon agogonsa da juyawa zai fita. Jitai duk babu daɗi,       “Kayi haƙuri idan na ɓata maka rai Yayanmu”.         “Ba haka matata ke bani haƙuri ba, dan haka sai ki shirya ta yanda nafi buƙata kafin na dawo”. Ya faɗa yana ficewa batare da ya waiwayota ba.          Kallo ta bisa da shi zuciyarta na maimaito mata karatun hajiya Falmata daki-daki. Ganin tunanin bazai kaita ko inaba ta cigaba da aikinta cikin dauriya dan wani sabon zazzaɓi ke neman saukar mata, ga wajen itakam har yanzu zafi yake mata kaɗan-kaɗan. Duk da yanda take jin nata haka tai juriyar gyara gidan har sashensa, sauƙintama ba wani datti bane. Turaren wuta ta saka har General falo da ƴar barandar waje. Ta bi kuma da fresheners masu daɗi. Sosai nutsuwa ta ƙara saukar mata jin ko'ina ya ɗauka ƙamshi kamar yanda take buƙata. Daga haka ta taƙarƙara ta koma bedroom ta kwanta kozata samu barci ya ɗauketa kafin sallar la'asar.       Tana kwanciya ana fara knocking, dole ta miƙe kamar zatai kuka. Hijjab ta saka sannan ta fito ta buɗe. Ganin su maman halima yasa fara'arta bayyana tana jera musu sannu da zuwa. Suma cike da kulawa suke amsa mata suna shiga da kayayyakin da sukazo dashi. Akwatinanta ne na lefe da tarkacen ƴan kayayyaki. Sai kayan gara da suka bata mamaki.       Naziru daya kawosu ne yace ta buɗe ƙofar kitchen ta baya a saka tacan zaifi sauƙi. Dan yasan hanyar tunda da shi aka kawo furnitures ɗinta. Cike da girmamawa ta karɓa masa. Taje ta buɗe ƙofar shi da maigadi suka dinga jigilar shiga dasu su Sakina na tayasu da wanda zasu iya. Hardasu kayan cin-cin. Jitai ƙwalla ya cika mata ido najin daɗi da tausayin su baba. Iyaye dabanne, duk da sunsan babu abin AK ɗin ya rasa a rayuwarsa sunyi hoɓɓasa ɗin ganin sun cika mata darajarta akan abinda al'ada ta tanadar. Dan dai gara al'adace da ƙyautatawar iyaye ga miji bawai wajib bace kamar yanda samarin yanzu suke kallo, harma suke samun damar yarfa mace in ba'ai mataba saboda son zuciya.        Sai da aka gama shiga da komai sannan ta kawo musu ruwa da lemo sukai zaman gaisawa. Sakina sai kalle-kalle take da jinjina wannan gida a ranta, duk da da ita aka kawo amarya yau dai tafi kallon komai yanda ya kamata dan shiyyasama ta nace sai tazo. Aiko sai gashi ƙiri-ƙiri tana nuna hassadanta a fili dan sai wani yamutse-yamutsen fuska take ita da uwarta dake ji kamar ta fidda Zinneerah ɗin ta kawo sakina ciki.       Ita dai Zinneerah bama bi takansu taiba, dan akwai sauran ƴan ɗan musa da sukazo tare su uku sai maƙwaftansu mmn sadiq ɗin abokan arziƙinta suma su uku, sai ƴaƴan mmn halima da ita, da matar Naziru.        Kasancewar su mmn halima tsaffin mata ya sasu fahimtar yanayin Zinneerah ɗin, sai mamaki ya kama irinsu mmn sakina da matar Naziru da ita kanta mmn Haliman dan sudai sunsan Zinneerah ba wannan ne aurenta na farko ba, tunda gata harda little. To amma yanayin nata yayi kama da na wadda namiji ya fara taɓawa. Sauran kam dai har ransu gani suke Zinneerah ta kawo mutuncinta, musamman ma ƴan dan musa da babu wanda yasan ƙaddarar data afku ga Zinneerah ɗin har yanzu. Duk da kuwa Inna Asabe ta saki maganganu da sukaje danya sai duk suka kallesu matsayin hassada kawai da sharrin baƙin kishinta da bai ɓoyuwa harga ƴaƴa. Sai da suka shiga ko ina suna mai yabawa da jera addu'oin fatan alkairi. ★★★        Koda Mahma ta koma gida bata yarda ta nunama su Mammah komaiba, hasalima dama basusan inda tajeba. Da sukace zasuzo gidan AK ɗin kuma cikin dabara ta hanasu akan su bari sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu sai a maida Farah baki ɗaya dan ya kamata takoma ɗakin mijinta tunda ta samu sauƙi.      Da farko Zakiyya ta tubure akan Farah bazata komaba har sai AK ya saki Zinneerah, zuwa lokacin Farahn ta haihu. Kallonta kawai Mahma tai tana gitgiza kai da sake yarda da zancen AK. Kamar zatai magana akan cikin Farah ɗin sai tai musu shiru kawai. Dan ita Farah ɗince da kanta tace zata koma gidanta saboda tunowa da zafafan gargaɗin AK. Ba aunty Zakiyya da Mammah ba hatta Mahma sai da tai mamakin furicin na Farah, amma sai batace komaiba tai murmushi kawai.      Aunty Zakiyya kuwa wani shegen harara ta watsa mata da faɗin “Saiki koma ballagaza kawai mayyar miji”.      Kaucewa dukan nata tayi tana kumbura baki, dan ita dai wlhy shawarar Adilah da sukai waya jiya da daddare zatabi, gara ta koma koma mi za'ayi ayisa acan. ★★★      Hajiya iya kuwa data koma duk da tana fushi da Uncle Ahmad har yanzu taƙi saurarensa dan ta dage sai ya ƙara aure ya ajiye matar a Nigeria koda zata barsa ya koma. Kokuma ya bar iyalansa anan. Wannan shine zaɓin data bashi kawai ta tsuke bakinta.       Zaunar dasu tai shida Baffah da Mommy ta sanar musu komai daya faru. Baffah dai yasha mamaki wannan al'amari, Uncle Ahmad kuwa da dama gaba ɗaya hasashensa da nazarinsa ya tafi kacokan a wajen ne tunda Baffah ya bashi labarin abinda ya faru da tarihin Zinneerah sai baiji komai ba sai takaici da tausayin Zinneerah ɗin.         Cikin zafinsa yace, “Aiko indai ta tabbata sune suka aikata yanda sukai wasa da rayuwar yarinyarnan suma tasu saita shiga garari wlhy, dan bazamu barsuba sai inda ƙarfinmu ya ƙare. Gatan da suka kalleta da tashinsa a farko har suka aikata mata wannan ta'asar zasu tabbatar da tunaninau gurɓatacce ne kuwa”.        Ɗari bisa ɗari duk suka bashi goyon baya. Suna cikin tattauna yanda zasu ɓulloma al'amarin Khalipha ya shigo gidan, shine ya musu ƙarin bayani akan kamo hajiya lanti da sukai a yanzu haka kuma tana hannun hukuma, Alhmdllh kuma ta bada haɗin kai akan cewar zata sadasu da hajiyar data kaima su Zinneerah dan itama saboda ita taje katsina. Amma sai ta tarar tana saudia dan can ta koma da zama. dama can sana'arta kai yara saudia aikatau, duniyace tai mata gwatson ƙyanwa tunda aka cimimiyota ta dawo kuɗin komawa ya gagareta. To yanzu dai Alhmdllh akwai bikin yaronta da akai a wannan satin rana ɗayama da nasu Zinneerah, itama jira take a gama bikin dama ta sameta dan tazo Nigeria.        Sunji daɗin jin hakan, a take suka yanke zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu itama a damƙota kawai kafin ta sake tafiya, suma kuma su Mammah karsu bar ƙasar.         A wannan tattaunawar AK da yazo gidan gaishesu ya samesu. Zama yay suka ɗan ƙara tattauna zancen sannan ya shiga ya gaida matan gidan. Daga haka ya ɗauka little daya maƙale masa suka wuce gida dan sai da ya fara zuwa ya gaishe dasu Mammah. Acan ɗinma bai nuna musu komaiba, dan koda Farah tace zata koma gida gobe a taƙaice yace mata, “Ƙofa abuɗe take”  daga haka yaja bakinsa ya tsuke. Bai kuma bi takantaba harya baro gidan. Aunty Zakiyya kam bata tanka masaba shima bai tanka mataba dan idan taurin kai ne gidan ta taras. ______________________       *_DANYA_*     Ƴan biki sun dawo gida lafiya, yayinda kowa ya fara ƙoƙarin fesar da maganar daya gumtso akan auren na Zinneerah da daular duniyar da ALLAH ya kaita ciki. Ga miji ɗan gaske acewarsu (🤣ba bily ba😂). Wasuma da biyu suke ƙara kambama zancen dan baƙanta ran Inna data haukace musu da bala'in su fice mata a gida.            Ko'a jikinsu, dan da suka fitanma gaba suka ƙara wajen isar da labarai kala-kala harda waɗanda ba'ayiba ma. Gasu Yaya Gajeje kuwa ga labarin a ransu ga tsoron tunkarar Inna da batun abinda suke hasashe tattare da Tinene, dan tunda suka shigo gidan ɗaki ta shige ta ƙudundune a zani tana rawar sanyi.       Da ƙyar Yaya Gajeje taja ƙafafunta ta nufi gidan saboda yara data bari, gashi yamma nayi tunda tana ƙauyen gaba dasune duk da babu nisa.      Duk da takaici da zafin da inna keji a ranta da labarin ɗaukakar da Zinneerah ta samu hakan bai hanata zaman jin labari a bakinsu Atine dakeyi suna gatsine-gatsine ba kishi fal ransu. Abinda kuma sukazo dashi sai faman ci suke har Inna ɗin dan tace raba mugu da makami ibada ne..   (😂🤣gaskiya kam aunty Asabe)       Shi Baba ma da amaryarsa dake jiyosu daga ƙofar ɗaki dariya suka basu, musamman Inna da baba yasan shegen kwaɗayinta bazai barta ta kasa cin abinda akazo da shi dinba koda kuwa tanaci tana kuka ne.      Washe gari da safe jikin Tinene ya ƙara tsananta, tun dare taketa kwara amai har safiya ta tashi a galabaice. Baba ya ce ta shirya suje asibi maybe dai typhoid ne ke damunta, dan itace kesa zazzaɓi mai zafi haka da naci. Amaryar baba ba sanin ciki tai ba sosai, Inna kuma idanunta ya rufe da damuwar ɗaukakar Zinneerah sam taƙi fahimtar halin da Tinene ke ciki. Su kuma su Karima tsoron faɗar abinda ransu ke raya musu inna ta hau tsinarsu sukeyi.      Ana haka sai ga Gwaggo Laritu tazo domin ai zaman raba alkairin da AK ya basu, bata jima da zama ba Yaya Gajeje ta iso itama. Cikinsu babu wanda yay magana akan shirin kai Tinene asibiti da baba ke shirin yi. Sai da Gwaggo Laritu tai wani tunani sannan tai magana.        “Niko Yaya nakega kai Tinene asibiti bazai jawo komai a garin nanba sai kace nace. Musamman ma daya kasance asibitin garin nan zakuje”.      Da mamaki baba yace, “Kace nace kuma Laritu, akan ciwon?”.      “Tabbas kuwa Yaya, dan banga amfanin aita ɓoye-ɓoye ba akan abinda kowa yasan dama wajib ne. Dan shi dai sharri ɗan aike ne dama shiyyasa ake nusar damu illarsa ga aikama kowa. Asabe tama Zinneerah fata kuma ALLAH ya karɓa mata, sai dai kuma ga sakamakon nan ya dawo ga Tinene. Dan babu wani taifot dake damunta ciki ne jikin wannan yarinyar wlhy”.     Ba baba da amaryarsaba hatta da Inna dake jiran Gwaggo Laritu takai ƙarshe ta sauke mata kwandunan bala'in da take Tattarowa a take ta saki robar ruwan wankan ƴar Karima data ɗauka zata sako ruwan zafi, ALLAH yasotama bata kai ga zubawarba.       Wani irin shuuu taji abu ya gitta mata cikin idanu da ƙwaƙwalwa saboda tsabar razani. Cikin rawar baki tace, “Munahika annamimiya, Laritu kirasa wanda zakima wannan sherin sai ɗiyar zumunki. To wlhy sai dai kiga ciki a jikin jikokinki, ALLAH ya isa kuma sherin da kikaima yarinyata”.      Murmushi kawai Gwaggo Laritu tayi. amma uffan bata sake cewa ba. sai Yaya Gajeje ce tace, “Inna ya kamata ki fahimci zancen Gwaggo, ku kuma nutsu wajen karantar Tinene wlhy cikine da yarinyar nan da gaske”.         Baki sake tabi Gajeje da kallo, sai jitai Atine tace, “Wlhy Inna da gaske ne, ki kalla Tinene da ƙyau zaki tabbatar”.          Tsitt gidan yayi saboda kakarin aman Tinene, Inna ta fashe da kuka jikinta na wani irin rawa lokacin da idonta ya sauka akan Tinene da har ciki ya fara tasawa sama kaɗan, da alama ma ya wuce watannin da suke hasashensa. Baba kansa baya yay sai da amaryarsa ta riƙosa jikinta na rawa itama dan batason damuwa sam, musamman ma yanzu data samu cikin nan. Kafin wani ya samu damar sake cewa uffan sukaji ana rangaɗa sallama daga waje. Da ƙyar baba ya iya amsawa da nufar hanyar ƙofar gidan domin duba wanene. Da Laminu ƙanin Babawo yaci karo, Laminu ya gaishesa da girmamawa yana miƙa masa takardar hannunsa da nuna masa kayan daya sauke a mashin ƙasa. “Baba Sule gashi inji Yayana Babawo, yace a bama Karima tare da waɗan nan kayan. Yace a sanar mata ta tuna yau saura sati biyu wa'adin da kotu ta bata na kai kuɗin sarƙar hajiyar data satamawa ya cika”.      Cikin rashin fahimta baba yace, “Laminu ban fahimcekaba nikam sam, amma kaga shigo daga ciki kai bayani agaban Karimar”.     Babu musu kuwa yabi baba ciki, bayanin daya zayyana masa shiya sake maimaitawa Karima.     Gani kawai sukai ta saki ƴar sai da Atine tai azamar tarota tana ambaton, “Na shiga uku Karima baki da hankaline?”.     Ina Karima ba saurarenta takeba, dan atakema gani sukai ta yanke jiki ta faɗi, Inna ma da tun fara bayanin garin ke juya mata da wata irin hajijiya sai tabi bayan Karima ta zube ƙasa.      Ƙarar da Atine da Sa'a suka ƙwalla na firgici ya saka amaryar baba dafe bango saboda wani irin murɗawa da mararta tayi alamar tahowar naƙuda......... ____________________     *_KANO_*   Bayan wucewar su mmn Halima salla kawai Zinneerah ta samu tayi ta la'asar. Duk yanda taso daurewa da zazzaɓin daya rufeta kasawa tai, dole ta rrrafa saman gado ta kwanta dajan bargo ta lulluɓe tana rawar ɗari.       Cikin barcin daya ɗan fara figarta little ya faɗo mata a jiki yana faɗin, “Aunty!” cike da farin cikin ganinta. Buɗe idanu tayi da ƙyar tana kallon ƙyaƙyƙyawar fuskar yaron mai tsananin kama da mahaifinsa. Ta ɗan lumshe ta buɗe da ciro hannunta a bargon da ƙyar ta shafa kansa.         “Kaga ka tadani daga ɗan barcin dana fara sweetheart, waye ya kawoka?”.        “Abbana”. Ya bata amsa kansa tsaye yana ƙara daka tsalle akanta.        “Wai ALLAH little karka ƙarasani dan ALLAH, ka tausaya mani”. Ta faɗa tana yunƙurin miƙewa zaune. Idontane suka sauka akan AK dake bakin ƙifa tsaye kawai yana binsu da kallo tamkar ya samu television.       “Barka da dawowa” tai maganar da maida idonta ƙasa. Batare daya amsaba ya tako ciki sosai, a kusa da ita ya zauna da kamo little dake ɗane mata wuya...........✍                      *_Na gode da addu'oinku, na samu sauki Alhmdllh. Asha hutun weekend lafiya😘😍😍_* *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* *Page 61* ________________________ *_KAƊAN YA RAGE SU ƘARE_* *_MATA ƴan ƙwalisa kuna ina za'aci kasuwar sama babu ku?. Mg's skincare ɗin fa na gab da ƙarewar kaya kuna nan sake da baki baku mallaki naku ba_* _Mg's SKINCARE nagartattun kayan ne dake gyara jiki da fata cikin sauƙi, sunada inganci da rahusa dai-dai da aljihunku._ *Da kin fito a ringa ga tauraruwar taurarin nan mai fatar da babu kamarta tamkar dinare abin haske da walwali.* *_Sabulunsu kawai kika ɗana sai kinsan kin kai kuɗinki inda babu asara balle dana sani_* _A yanzu haka muna jerin kayayyaki da suka rage kamar haka_👇🏻 Available _Akwai: herbal whitening black soap 3k_ Akwai: beauty kit 11k shi set ne yakunshi Abu 6 Soap Body cream Face cream Body nd face scrub Cleanser Glow oil Location kaduna buh mn tura Kaya ko Ina saidai inmutum ya amshi kayanshi zebada kudin delivery WhatsApp 08062991549 Call 08064532391 Instagram:glow_with_mgs Facebook:mg's skincare *_Karku bari ayi babu ku guys, siyan nagari maida kuɗi gida._* ________________________ *Page 61* .............Hannunsa yasa a wuyanta bayan ya sauke little ɗin yana lallashi dan kuka yake nemanyi dan an saukesa a wuyan mamansa.        Tsatstsare ta da idanunsa masu tarin kwarjini yayi, cikin kulawa yace, “Zazzaɓin dai har yanzun?”.       Kanta taɗan jinjina masa batare data kallesaba. A mamakinsu sai gani sukai shima little dake jikinsa ya saka hannu a wuyanta kamar yanda AK yayi, yakuma kwaikwayi zancen daya faɗa. “Zazzaɓine har yanju?”.         Kallon juna sukai suka saki murmushi lokaci guda haƙoransu na bayyana a waje. dan yanda yaron yayi maganar cikin serious dolene kai dariya. Shiko da yayi ko'a jikinsa, dan saima ya miƙe saman gadon ya hau tsallensa.        AK daya samu ya danne dariyarsa da ƙyar sai murmushi ya kamo hannun Zinneerah daketa faman kare bakinta dan da gaske dariyar ke cinta itama amma dai taƙi yarda tayi sai murmushi. “Yaron nan wayonsa yayi yawa, minene sirrin?”.        Ƙoƙarin shanye dariyarta tai da faɗin, “Kawai dai danya tashi cikin yarane”.      “Uhmyim, su Sadiq sun iya raino kenan?”.       Ɗan kallonsa tai mamaki sosai a fuskarta, a tunaninta ina yasan su sadiq har haka. Murmushi yay mata cike da basarwa ya miƙe. Batare daya ƙara cewa komaiba ya fita a ɗakin, ajiyar zuciya kawai ta sauke da juyawa ta kalli little dake cigaba da tsalle-tsallensa hankali kwance. Sai kawai ta yaye bargon ta sauka baki ɗaya duk da kuwa dai tanajin zazzaɓin har yanzun.     Bata sake ganin AK ba sai da akai magriba, ta idar da salla kenan tana ninke sallaya, little na gefe zaune yana raira kukan makesa da tai saboda ɓarna da yake neman mata a mirror ta hanashi yaƙi hanuwa AK ya shigo. Kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa yana maidawa ga little ɗin. Wajensa ya nufa, ya kamashi ya ɗaga jikinsa yana murmushi, “Wai mi akaima sojan nan ne?”.       Zinneerah little ɗin dake cigaba da kukansa ya nuna. AK ya kalli Zinneerah ɗin shima, “Mami mi mukayi haka aka samu kuka?”.         Ɗan kallonsu tayi tana harar little ɗin, cikin muryarta datai sanyi saboda zazzaɓin da takeji tace, “Ɓarna zaimin nace ya bari yaƙiji shiyyasa na make hannun”.        Hannu yasa yana sharema little ɗin hawayen, “Handsome babu ƙyau a hana mutum abu ya ƙi bari, kaga Mami bata da lafiya ma uhmyim?. Ce mata sorry”. Yay maganar yana matsawa gabanta.       “Mami Shoyi”. Little ya faɗa jin AK ɗin ya kirata Mami.        Ɗan hararsa ta ƙarayi ta ɗauke kanta kawai. AK ya riƙo hannunta, dole ta sake ɗagowa ta dubesu. Sai dai narkakken kallon da yake mata yasata janye idanunta. Batare da ya damu da yanda tayinba yace, “Ai munce ayi haƙuri ko”.     “Nima na haƙura ai, zanje na kwantane sanyi nakeji Yayanmu”.       “A'a ba kwanciya zakiyiba, shirya asibiti zamuje”.     Kanta ta jinjina masa, dama jikinta doguwar riga ce da hijjab. Dan haka sai kawai taɗan ƙara turare a jikinta tabi bayansu dan shi harya fice ɗauke da little.         A general falo ta iskesu, batare da yayi maganaba ya nuna mata hanya alamar suje. Gaba tai ya bita a baya ɗauke da ɗansa. Shine ya rufe ƙofar sannan suka ƙarasa ga mota. Ganin little kamar zai takurasa a wajen tuƙin yasata miƙa masa hannu alamar yazo wajenta, amma sai ya noke.      Baki ta taɓe da hararsa ta ɗauke kanta. Sai da ya tada motar suka fice a gidan yay magana batare daya kalletaba. “Nikam wannan harar ɗan akemawa ko baban? Tunda shima mai laifine?”.        Gefe tai da kanta tana murmushi da faɗin, “Kai Yayanmu ni dai wlhy banceba”.     Shima murmushin yayi da sumbatar kan little dake cinyarsa suna tuƙin tare. Daga haka ya maida hankalinsa a tuƙinsa itako ta lafe cikin kujera ta lumshe idanu.       Sun isa Shira hospital inda suka samu ƙyaƙyƙyawar tarba ga ma'aikatan. Anata kallonsu cike da sha'awa da birgewa. Yayinda suke nuna son ɗaukar little amma sai yaƙi yana dai maƙale da babansa. A office ɗin Dr Mahmud suka yada zango, shima ya tarbesu cike da murna da girmamawa yanata tsokanar Zinneerah. Yayinda ya ɗauka little kuma da ƙyar.            “Ranka ya daɗe kune da dare haka? Lafiya dai ko?”.       “To da sauƙi dai madam ce babu lafiya”. AK ya faɗa yana duban Zinneerah da kanta ke ƙasa tana wasa da yatsun hannunta.        “ALLAH ya ƙara lafiya, Ko gajiyar biki ce ƙanwarmu?”.      Murmushi kawai tai batace komaiba. Shima sai ya murmusa da mikama AK little. Kafin ya maida hankali wajen mata tambayoyi. Magunguna kawai ya rubuta musu yay kiran wata Nurse a waya ya bata ta sayo. Ganin an kira isha'i suka fita salla suka barta a office ɗin. Suna dawowa ko zama basuyiba AK yace ta tashi suwuce kar dare yayi.         Har wajen motarsu Dr Mahmud yayo musu rakiya, sai da yaga tafiyarsu sannan ya koma ciki. Daga asibiti AK wani shagon sai da wayoyi ya kaisu, a mota ya barta suka shiga ciki shi da little. Babu jimawa kuwa sai gasu sun dawo ɗauke da leda. Daga haka gida suka nufa bayan ya sake tsayawa ya sai musu gasashshen kifi.           Sosai Zinneerah kejin barci lokacin da suka shigo gidan, fahimtar hakan da AK yayi ya sakashi dakatar da ita a falon farko na sashenta. Tsareta yay sukai zaman cin kifin tare, bama wani sosai taciba dan bakinta babu daɗi. Ya bata magungunanta ta sha taɗan tattare wajen ta shige. Shima sashensa ya nufa da little. Acan yay masa wanka, sai dai babu kayansa kuma balle na barci. Shaf yama manta da batun amso masa kaya. Pant dinsa kawai ya maida masa ya kwantar dashi a gadonsa dan sai hamma yake. Shima shirin barcin yayi sannan ya nufi sashen zinneerah. Isketa da yay har tayi barci ya sashi fitowa ya dawo sashensa. little ya ɗauka yaje can shima kawai suka saka yaronsu tsakkiya.     Zinneerah batasan da zamansu a ɗakin ba sai da asuba data farka, dan ta rigashi tashi. Ta jima tana kallonsa shi da little zuciyarta fal saƙe-saƙe iri-iri. daga ƙarshe dai ta mike ta shiga toilet. AK da shima ya jima da farkawa ya bata damar cigaba da kallon nasune tana shigewa ya miƙe. A bakin gadon ya zauna harta fito sanann. Ɗan kallonta yayi yana lumshe ido, muryarsa a dasashe irin ta wanda ya tashi barci yace, “Naje massallaci”.         Tace, “A dawo lafiya”. __________________        AK bai dawo gidan ba sai da rana tai ɗan haske. Ya shigo ya iske Zinneerah nata aikin kimtsa gidan kamar ba itace mara lafiyaba. Har ƙasa takai ta gaidashi. Ya amsa mata da kulawa yana tambayarta yaya jikinta. “Alhmdllh naji sauƙi ai”. Ta faɗa a hankali.       “Masha ALLAH”. Shima ya amsa mata kafin yace, “Ina little?”. “Bai tashiba har yanzun”. “Okay bara to na watsa ruwa dan inason fita da wuri”.     Kanta kawai ta jinjina masa. shi kuma ya juya zuwa sashen sa inda ta fara gyarowa duk da ba wani datti baneba.               Tana kammalawa bedroom ta koma tai wanka. Kammala shiryawarta kenan little ya farka. Wankan shima tai masa, ta shafa masa mai tana tunanin yanda za'ayi akan kayan da zaisa.. A dai-dai lokacin ta jiyo ƙarar doorbell. Little ɗin ta sauke daga kujerar mirror da yake a tsaye tana faɗin. “Ka jirani, idan wani abuna yay motsi anan kaima saina motsa maka jikinka da duka”. Daga haka ta ɗauka gyale ta fice.           Khalipha ne da kansa ɗauke da kayan little da breakfast ɗinsu. Ta matsa ta bashi hanya tana gaishesa. Cike da fara'a ya amsa mata idonsa akan little da batasan ya biyo bayantaba. “Uhm my boy ashe anan ka kwana?”. Ya faɗa yana mika mata basket ɗin ya ɗauka little daya nufosa baki a washe. Dan shi indai mazane to baya jimawa yake sabo dasu. Shiyyasa ko a gidan da wuri ya gama haddace samarin gidan. Kai tsaye sashen AK ya nufa abinsa. Itama sai tai ƙoƙarin juyawa nata sashen.     Kamar jira tana shiga aka sake danna doorbell ɗin. Sake dawowa tai zata buɗe taci karo da Khalipha ya fito shima. Barinsa tai ya ƙarasa ita kuma ta tsaya jiran ganin wanene?.      Farah ce ta fara shigowa idanunta jajur alamar tasha kuka. Sai Aunty Zakiyya a bayanta, Mammah na biye dasu. Ba karamin bugawa zuciyar Zinneerah tayiba da cin karo da Farah, tai wani diri-diri da ita dan koba komai dole taji hakan tunda ta aure mata miji. Jin muryar Mammah datai ya sata sake duban bayan Farah ɗin duk da kuwa sau ɗaya ta taɓa ganin Mammah ɗin.      Wani irin mahaukacin bugu ƙirjin Zinneerah yayi ta zabura baya batare data saniba. Wani irin duban aunty Zakiyya da itama ɗin dai ita take kallo takeyi baki a hangame.          Har abada bazata manta da wannan fuskarba. Koda shakara ashirin tai kuwa balle uku kacal. “H....h...hajiya?!”.        Zinneerah ta faɗa cikin rawar baki matuƙa. Wanda hakan yay dai-dai da fitowar AK da yasan da zuwan su Mammah ɗin a yanzu-yanzu da Mahma ta kirasa take sanar masa nan suka taho batare da sanintaba. Yayi duk yanda zaiyi karya bari Zinneerah ta haɗu dasu. Sai dai kuma hakan bai yuwuba tunda aikin gama ya gama.         Ba shi da Khalipha ba, hatta Mammah da Farah kallon Zakiyya suke da mamaki ganin yanda tai wani diri-diri tana kallon Zinneerah ɗin itama. Dan da hasashe kawai take, amma muryar Zinneerah ɗin ta tabbatar mata da eh lallai itace duk da ta ƙara girma ta kuma canja sosai.        “Kin santa ne?”. AK ya faɗa idonsa akan Zinneerah. Kanta ta shiga jinjina masa, kafin tace, “Itace Hajiyar nan ta katsina da aka kaini gidanta”.       “What!!” AK ya faɗa duk da kuwa dama aunty Zakiyya suke zargi.          Mammah da abun ya harzuƙata ta dakama Zinneerah tsawa. “K!! Shashasha daga ganinmu sai kice wani itace hajiyar da aka kaiki katsina wajenta. To aka kaiki kikai ubanmi acan?”.         Kafin Zinneerah tace wani abu AK yace, “Mammah kwantar da hankalinki Please. Inaga ai magana ta ƙare kawai. Khalipha kira Faisal kace ya kai matan nan gidan Baffah gamu nan zamu samesu acan”.           “Abdul-Mutallab banson iskanci, ya ana wata maganar kana ɗakko wata kuma?”.      “Nace ki kwantar da hankalinki Mammah, kumuje can gidan kawai, dan akan wannan sanin junan da sukai akwai magana”.       “Magana!?” Mammah ta faɗa tana kallon aunty Zakiyya da sai yanzu ta samu bakin cewa wani abu.           A firgice tace, “Magana! Dawa za'ai maganar?. Dan kawai ta kirani da hajiya sai kace wani akwai magana. Ke dan ubanki a inama kika sanni dazaki wani kirani da hajiya?”.       Mamaki ƙarara a fuskar Zinneerah tace, “Hajiya kin manta dani? Nicefa wadda wata hajiya Haule mai jiki ta taɓa kai miki har bani da lafiya kikaita kaini asibiti ana dubani, nikuma tsoro ya sani gudowa bayan na warke dan canake gidan yankan kai kika kaini”.     Zinneerah ta kara maganar kanta a ƙasa tana tuno komai a ranta tamkar yanzu yake faruwa.      Baki Zakiyya ta buɗe zata sake magana AK ya dakatar da ita. “Please kunga ya isa haka, kumuje can gidan tunda dama ai akwai maganar da akace za'ai bayan gama taron nan”.        Mammah ta kallesa, dan harga ALLAH ita tama kasa fahimtar ina suka dosa kai tsaye. Ta buɗe baki zatai magana sai ga Mahma data biyo bayansu, sallamar da tayi ya sakasu juyawa su duka suna kallonta.     Ganin yanda sukai cirko-cirko yasa Mahma faɗin, “Lafiya? Mike faruwa anan?”.          Mammah da dama magana ke bakinta tace, “Wlhy Addah nima da nake tare dasu anan na kasa fahimta, waifa muna shihowa gidan nan sai yarinyarnan mara kunya take kiran Zakiyya wai da hajiyar da aka kaita gidanta a katsina”. Tai maganar tana nuna Zinneerah da al'amarin masu ya ɗaurema kai itama. Dan harga ALLAH ita bataga wani abun tada jijiyar wuya anan ba. Daga ta nuna ta santa ai bai kai ya zama tashin hankaliba.....     Mahma data ɗauke kanta daga kallon Zinneerah da Mammah ke nuna mata ta maida ga AK, kai ya jinjina mata kawai. Hakan ya sata fara maganar data katsema Zinneerah tunanin da tatafi.       “Kunga duk a ajiye wannan shirmen nake ga. kuzo muje can gidan dama Kabeer ne ya kirani wai yanason magana damu akan Adilah”.        Tuni Mammah ta saki batun aunty Zakiyya da Zinneerah ta maida hankalinta ga Mahma wajen faɗin, “What!. Mi kuma yake nufi da zancen Adilah? To wlhy Addah wannan karon duk abinda zanyi karki tsayar dani, dan dama yau-yau ɗinnan nai niyyar zuwa har gidan na tarkatota itama gobe zamu wuce Morocco”.          Mahma ma nuna ɓacin ranta tai ta hanyar cewa, “Nima ai shiyyasa na biyoku nan ɗin, dan a wannan karon ba ɗagama Kabeer ƙafa zanyiba kuwa koda na mintuna ɗaya ne. Ku muje can, idan an gama mazo ayi wannan batun nasu Zakiyya ɗin”.      Kafinma Mahma ta rufe baki Mammah takai ƙofar fita, aunty Zakiyya da gaba ɗaya take a harmutse tai saurin fara magana cikin borin kunya. “Kuje, ni dai zan wuce katsina idan kun gama kwa sameni acan”.      AK daya saki wani murmushin mugunta yace, “Ai hardake za'aje hajjaju, dan maganace data shafi family, idan kuma kin fidda kanki a cikinmu sai muji”.          Wani shegen kallo ta bisa da shi mai kama da ruɗani da tsana, ta buɗe baki zatai magana Mahma ta katseta. “Kunga nifa banason wannan fitinar taku, ke Zakiyya wuce muje, da an gama maganar ai baki ɗaya zamu wuce komai dare”.       Badan Zakiyya taso ba tabisu, Farah dai ko motsi bataiba dan da ido AK yay mata gargaɗin tsayawa. Khalipha kuwa dama tuni ya fice shi da Little.        Sai da AK yaji fitar motarsu daga gidan sannan ya kalli Farah da Zinneerah ɗin. “Kuma kuje ku shirya zamu bisu”.        Jiki a sanyaye Zinneerah ta kaɗa masa kanta, sashenta ta nufa zuciyarta duk babu daɗi da abinda ya faru. Duk da dai tasan ita mai laifice kodan gudowar da tai bada sanin hajiya ba batai tunanin abin zaiyi girman haka ba tunda da ya wuce kusan shekara huɗu fa kenan.      Zinneerah na shigewa Farah tai saurin bin bayan AK, kusan a tare suka shiga falonsa. babu zaton tana biye da shi yaji ta rungumesa ta baya tana sakin kuka. Shiru yay kawai yana saurarenta dan yasan kukan mi takeyi, shi shaidane akan kishin Farah, amma yana ƙara hauhawane bisa karatun Mammah da Zakiyya.          Dalilin dayasa kuwa ta dawo gidan a yau Mahma ta sanar masa jiya ta zaunar da ita tai mata nasiha mai ratsa jiki, tare da tuna mata abubuwa masu yawan gaske waɗanda suka tada mata hankali, tun a daren tace zata taho nan gidan shine aunty Zakiyya ta rufeta da masifa. Ta ringa zaginta ta uwa ta uba daya kai har Farah kiran Abbansu ta sanar masa. Shine ya buƙaci ta haɗashi da Mahma suyi magana. Itako Mahma bata ɓoye masa komai dake faruwaba harma wanda su su Farah basu san ta saniba. Ya nuna matuƙar tashin hankali saboda shi mutumne nagartacce, ko zaman Farah a hannunsu dan anfi karfinsane kawai, amma duk sauran yayunta suna tare da shi sai dai irinsu Zakiyya da sukai aure. A yanzu hakama soyake yay murabus a ɗora babban yayansu Farah ɗin a karagar mulki. Zantukan da Mahma ta sanar masa ɗinne ya sashi sanar dasu yau zaizo kano, Farah kuma ta tabbatar ya sameta a gidan mijinta inba hakaba wlhy sai ya saka AK ya saketa saki uku, kuma ta dawo zaman Nigeria cikin masarauta.     Itako a duniya ta tsani zaman masarautarsu saboda yanda ake komai a takure, ga matan babansu sam basa ƙaunarsu saboda son da baban ke nuna musu a dalilin rashin mahaifiya. Dama can kuma yaso mahaifiyarsu sosai dan tunkan tabar duniya matan sun mugun tsanarta itama. Abu na biyu maganar sakin da yace zaisa AK ya mata. Tasan Abbansu sarai, wlhy zai iya sakawa AK ɗin ya saketa dan kaɗan daga aikinsa. Shima murɗaɗɗen mutumne mai tsayawa akan gaskiya duk ɗacinta.          A hankali AK ya janyeta daga jikinsa yana zagayo da ita gabansa. Ƙyawawan idanunsa masu cikar kamala da kwarjini ya zuba mata hannayenta duka biyu riƙe a cikin nasa. Sake fashe masa da kuka tayi kishinsa mai tsanani yana taso mata, amma tanata ƙoƙarin ganin ta danne dan duk runtsi bata iya rabuwa da shiba saboda tana sonshi.      Karan farko AK ya saki murmushi da kai hannu ya share mata hawayen dake sauka a fuskarta. “Nifa kinsan banason kuka ko?”. Ya faɗa yana rungumota jikinsa dan shima yanason kayarsa.         Ƙanƙamesa tai tana sake fashewa da wani kukan, “Dan ALLAH Yah Abdul-Mutallab kayi haƙuri wlhy Abbah zai iya rabamu, ka taimakeni karka faɗa masa na tuba”.           “Toni dama miya haɗamu da har zan sanar masa?”. Ya faɗa yana ɗago fuskarta. Cigaba yay da faɗin, “Kece kike biyema su Mammah ai dama, suna amfani dake wajen biyan buƙatunsu batare da kin fahimtaba. Sannan kina barin kishinki na rinjayar tunaninki bayan kinsan ina sonki. Sokike ne na dinga binki kamar wani sakarai dan kawai ki tabbatar ina sonki? Ko sokike nabar mahaifina da ƴan uwana dan kawai ina sonki Farah? Wannan abun shina dinga tsoratar miki dama. Randa zan iya ƙosawa da halayarki na fara tunanin ƙara aure. Iyayena da baki ragamawa suma su bani goyon bayan yin. Amma sai kika kasa fahimta, ke ga mai Mammah da aunty Zakiyya ko?. Gashi nan duk yanda nake ɓoyema Maimartaba halayyarki sai da takai kin tonama kanki asiri da kanki”.           “Na tuba wlhy, dan ALLAH ka taimaka karka faɗa masa yanzuma, dan wlhy yace yana hanyar zuwa kano. Na rantse yana tambayarka ka faɗa masa sai ya raba aurenmu kasan halinsa”.         “Idan kinmin alƙawarin zaki nutsu, ki komamin Farah dana sani a baya, mai tattalina da ƙaunata bazan faɗa masaba. Sannan duk abinda za'a tattauna a gidanmu yanzu zaki faɗi gaskiyar abinda kika sani bazan taɓa yarda a rabamuba koda kuwa zan hukuntaki da laifinki ne”.        Batare data nutsu ta tace zantukansa ba tace, “Na amince wlhy Yah Mutallab”.           Idanunsa ya ɗan lumshe ya buɗe a kanta, tare da sunbatar goshinta da laɓɓanta. A dai-dai lokacin da Zinneerah ta shigo falon da sallama, hannunta ɗauke da basket ɗin da Khalipha ya kawo musu breakfast. Dan harta fito saita tuna ko karyawa basuyiba. Shine tai tunanin kawo masa koshi zaici dan ita kam bazata iya shan ko shayi ba.      Wani irin bugawa ƙirjinta yayi, tai saurin ja da baya jikinta na rawa, dan shigowar tata yayi dai-dai da ɗaura lips ɗinsa akan na Farah, itako ta cafke tana kara rungumesa kamar yanda shima ya sake rungume abarsa.         Jin basket ɗin hannunta zai faɗi ya sakata saurin ajiyewa a ƙasa ta juya da sauri ta fita dama a farkon shigowa take.................✍             *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_* *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* *Page 62* ________________________ *_KAƊAN YA RAGE SU ƘARE_* *_MATA ƴan ƙwalisa kuna ina za'aci kasuwar sama babu ku?. Mg's skincare ɗin fa na gab da ƙarewar kaya kuna nan sake da baki baku mallaki naku ba_* _Mg's SKINCARE nagartattun kayan ne dake gyara jiki da fata cikin sauƙi, sunada inganci da rahusa dai-dai da aljihunku._ *Da kin fito a ringa ga tauraruwar taurarin nan mai fatar da babu kamarta tamkar dinare abin haske da walwali.* *_Sabulunsu kawai kika ɗana sai kinsan kin kai kuɗinki inda babu asara balle dana sani_* _A yanzu haka muna jerin kayayyaki da suka rage kamar haka_👇🏻 Available _Akwai: herbal whitening black soap 3k_ Akwai: beauty kit 11k shi set ne yakunshi Abu 6 Soap Body cream Face cream Body nd face scrub Cleanser Glow oil Location kaduna buh mn tura Kaya ko Ina saidai inmutum ya amshi kayanshi zebada kudin delivery WhatsApp 08062991549 Call 08064532391 Instagram:glow_with_mgs Facebook:mg's skincare *_Karku bari ayi babu ku guys, siyan nagari maida kuɗi gida._* ________________________ *Page 62* .........Kawai jitai hawaye sun ɓalle mata babu gaira babu dalili, ta zube a farkon kujerar shiga falonta na farko ta cigaba da zirarwa batare datayi yunƙurin sharesuba ko sau ɗaya. Har cikin ranta tanajin nadamar shigar masa ɗaki kai tsaye ba tare da jiran izini ba, sai dai ALLAH shine shaidarta batai tunanin matarsa na cikiba, dan duk tunaninta sashenta itama ta nufa.       Zumbur ta miƙe da saka bakin gyalenta tana share hawayenta saboda jin takun tahowarsa, tai saurin nufar ƙofar itama dan bata buƙatar ma ya shigo ya sameta. Kusan cin karo sukai yaja da baya itama taja tana ambaton, “Sorry bansan ka tahoba”.        Yanda yaji muryarta a shaƙene ya sakashi kallonta da ƙyau batare da ya amsaba. Abinda kawai zuciyarsa ta bashi akan maganarsu aunty Zakiyya ne, dan haka ƙarasa shigowa da jawota jikinsa kawai yay ya rungume. Wani irin sabon kuka ne taji ya taho mata dan haka ta sakeshi dan duk yanda taso riƙesa ta kasa. Ba komai ya sata gagara riƙewarba kuma sai ƙamshin turaren aunty Farah da taji jikinsa nayi. Ƙoƙarin janye jikinta tayi ba tare da shi ya ɗagotaba. Tai saurin nufar ƙofar fita tana share hawayen da mayafinta.         Da mamaki yaɗan bita da kallo zuciyarsa na raya masa ‘Anya kuwa zancen su aunty Zakiyyar ne kawai. Dan idan bai mantaba yaga basket a ƙofar falonsa da ƙamshin turarenta. Kafin ya shigo nan din yayi tunanin ko Khalipha ne daya shiga ɗazu ya ajiye dan lokacin da yazo a bedroom ya samesa, kamshin turarenta kuma ya barsa akan kawai dan ya shaƙane sanda suna tare a falon.      Kansa kawai ya ɗan girgiza dayin murmushi, a kan laɓɓansa ya furta, ‘Oh mata kenan’ dan yanzu ya gama da Farah itama, koda ya rakata mota ma ya bartane tana kukan.       Bayan Zinneerah ɗin ya bi, sai ya isketa a general falo tsaye. Tana ganin fitowarsa tai saurin ficewa baki ɗaya kuma. ‘Tofa babbar magana’  ya faɗa a fili murmushi na suɓuce masa.           Shi ya rufe ƙofar sannan ya iso wajen motar inda Zinneerah tai tsaye bata shigaba. Fuskarsa ya daidaita da ƙyau yana isowa, batare daya kalletaba yace, “Shiga muje”. Yay maganar yana buɗe mata baya. Ganin yanda yay kicin-kicin da fuska dama kuma ba wasan yake da itaba yasata shiga babu musu, sai da ta zauna ya gyara mata mayafinta daya fito sannan ya zagaya ya shiga shima mazaunin driver, Farah na gefensa itama ta cika tai fam.           Har zai sama motar key sai ya fasa, Kallon Farah yay sannan ya juya ya ɗan kalli Zinneerah. “Kun gaisa da juna?”. Ya faɗa a dake.         Kusan a tare sukace masa a'a. Sai Zinneerah kuma tace, “Aunty Ina kwana”. Kamar Farah zata share saita motsa laɓɓanta ciki-ciki tace, “Lafiya” saboda hararan da AK ya zubo mata.        Daga haka motar ta ɗauka shiru. Shima bai sake cewa komaiba yay mata key da harbata gaban gate. Ficewa yay kai tsaye dan dama maigadi ya buɗe masa tun ganin sun fito sun shiga.         Shaiɗan ɗin daya fahimci yana kai kawo a zukatan matan nasa ya sakashi saka karatun alkur'ani a motar, a ransa yana nema musu sassauci ga ALLAH dan shima yasan zafin kishi tunda yana dashi. Lokaci-lokaci yakan kalli Farah ya duba Zinneerah kuma ta mirror. Ganin yanda duk suka maida fuskoki gefe sai suka bashi dariya amma ya gimtse baiyi a fili ba sai a ransa. Harko suka iso gidan nasu daga Farah har Zinneerah babu wanda yayi ko tari. Bayan ya gaisa da maigadi ya ida shiga cikin gidan ransa fal mamakin ganin motoci da yawa a harabar gidan kamar har yanzu bikin sukeyi basu gamaba danma babbace.         Babu wacce ta motsa a cikinsu, dan haka shima sai bai tanka musuba ya buɗe motar ya fita. Ganin haka yasa suma duk suka fito kusan lokaci guda. Kallon juna sukai, sai kuma kowacce ta ɗauke kanta. Farah tazo ta gitta Zinneerah ɗin tanabin bayan AK da yay gaba abinsa ya barsu a wajen, dan harga ALLAH idan ya cigaba da zama yana kallonsu dariya zata iya kufce masa. Dan tsaf ya fahimci itama Zinneerah ɗin A ce a fannin kishi kenan. Koba komai kishin nata a karo na biyu ya tabbatar masa da shima ya samu karɓuwa a gareta, miskilancine kawai ya hana ta bayyana kamar yanda ya buƙata.        Sashen Hajiya iya suka nufa kai tsaye, inda sukaci karo da tarin takalma kala-kala ajiye, da alama baƙin da suka tara waɗan nan motocin duk sune anan ɗin.         Cikin nutsuwarsa da sallama ɗauke a bakinsa ya shiga, Farah na biye dashi Zinneerah a bayanta. Da sauri Farah ta nema komawa da baya saboda cin karo da fuskar mahaifinta da tai hakimce cikin kujera. AK yay saurin riƙo hannunta yana magana ƙasa-ƙasa. “Malama ki nutsu mana” Ya faɗa yana duban Zinneerah datai musu kallo ɗaya ta ɗauke idonta.          Kai Farah ta ɗaga masa idanunta cike da ƙwalla. Ya nuna musu hanya alamar su wuce. Babu musu suka nufi ƙarasawa cikin falon ran Farah fal mamakin zuwan Abban nata babu dogari ko ɗaya, sai ƙannensa biyu Matawalle da waziri, da babban amininsa da kowa ya sansu tare wanda ƙanine a wajensa shima amma kusan tare sukai rayuwarsu, sai dai ba mahaifinsu ɗaya ba. Sai da suka zo kusan tsakkiyar falon Zinneerah ma taci karo da Babanta da Abbah, harma da Maman Sadiq.      Ita kanta tsoro ne ya kamata, dan babu shiri ta fara satar kallon mutanen dake a falon, sai ga idonta akan Hajji lanti, da Hajiyar da aka kaita gidanta wadda ta kaita gidan aunty Zakiyya. Ai batama san lokacin da ƙafafunta dake rawa suka goceba ta durƙushe a wajen.       Hajiya iya ce tai murmushi da faɗin. “Haba Inno ya da zubewa haka ƙasa. Tashi kizo nan kinji, kema Farah taho”.        Miƙewa Zinneerah tai da ƙyar tabi bayan Farah da itama gaba ɗaya ganin Abbasu ya sata tsurewa, dan tsoronsa suke matuƙa saboda bai musu da sauƙi duk da yana tsananin sonsu kuwa. Shi dai AK tuni yakai zaune gaban Uncle Ahmad yana gaida iyayen nasa da surukansa cike da girmamawa. Ganin haka yasa Zinneerah da Farah suma suka shiga miƙa gaisuwa garesu duk da basusan iyayen juna ba, garama ita Zinneerah tasan su Mammah.     Bayan an gama gaishe-gaishe duk da su sun gaisa dama a tsakaninsu harma da gabatar da juna tunkan isowar su AK ɗin. Harma mai-martaba mahaifin su Farah ya shigar da ƙorafinsa na rashin sanar masa da auren AK ɗin na biyu. haƙuri Baffah ya bashi tare da masa bayanin a yanda abun ya kasance bada shiriba. Yasha mamaki matuƙa, amma cewar hajiya iya zaman nasu nada nasaba da auren yasa mai-martaban yin shiru bai nema ƙarin bayani akan zancen little ba da yana a falon jikin Abbah, dan tunda ya gansu shi da mmn Sadiq kuma ya maƙale musu cike da murna dan duk duniya su yafi sani fiye da kowa, tunda ko uwarsa batai wahalar da sukai a kansaba bayan ta haifesa.        Waziri ne ya gabatar musu da addu'a. Kafin hajiya iya ta fara magana.         “Zan fara da sunan ALLAH mai rahama mai jinƙai, dan shine yay sanadi da silar taramu anan ta dalilin wani saka mai sarƙaƙiya da duk ta sarƙe zukatanmu kafin shi wannan zaman. Anan mu dukanmu iyayene kuma kakannine, dan haka ina fatan zamu bada haɗin kai wajen nutsuwa mu fahimci abinda ya taramu, sannan duk wanda al'amarin ya shafa dan ALLAH ina mai roƙonsa dayaji tsoron ALLAH mai zartar ga hukunci a sanda yaso ga wanda yaso ya faɗi gaskiyar abinda ya sani. Mun cire hukuma ne a wannan zancen saboda wasu dalilai. Ba kuma hakan na nufin bazamu iya maida komai garesu bane duk da mun kasance a ƙarƙashin inuwar zumunta ta dalilin aure da sauransu. Wannan yarinya da kuke gani.....”      Ta nuna Zinneerah da kanta ke a durƙe tamkar Farah.       “Sunanta Zinneerah. Malam Sulaiman gashi nan zaune shine mahaifinta. Wannan kuma Hauwa'u ɗiyar ƙanwata itace mahaifiyarta. Waɗan nan iyaye sun rabu sanadin ƙaddara data saka Zinneerah zama a hannun matar uba bayan barin Hauwa'u gidansu. Inda ita wannan matar uba nata ta raineta cikin gallazawa da son zuciya, a ƙarshe kuma ta miƙata aikatau bada sanin mahaifintaba. Sanadin wannan aikatau ta dawo musu da ciki da suka rasa daga ina ta samosa. Aka turketa da tambayar duniya da barazana tace ita bata aikata komaiba kuma batasan mai ciki ba. An turza iya turzawa tace bata saniba. To a yanzu dai wannan yaro dake jikin Alhaji Abubakar shine ɗan data haifa. Nasan kuma duk wanda ya kallesa zaiyi mamaki da ruɗani akan kamanninsa da Moddibo. Kuma komi za'a faɗa bazai yardaba zai dangantashi da shi a matsayin mahaifinsa kamar yanda muma mukaitayi. Bazan kaiku da nisaba, ga dai wadda ta kai Zinneerah aikatau birni, zamu fara ji daga gareta yaya aka haihu a ragaya. Hajiya Lanti bismillah”.     Hajiya iya ta ƙare zancenta da kallon Hajji lanti dake zaune ita da hajiya Haule da kallo ɗaya zakai mata ka tabbatar a gigice take tun zuwansu gidan.         Zama hajji lanti ta gyara. Kanta tsaye ta fara magana da iya gaskiyarta. “Ni Lantana nayi alƙawarin faɗar gaskiya kamar yadda Hajiya mama ta buƙata, zanyi hakanne kuma domin na fita har a wajen UBANGIJI na. Wannan sunanta hajiya Haule. a garin katsina take zaune. Na santane dalilin wata ƙawata ƴar kankia da muke zuwa sarin kayan koli kano, itace ta haɗani da ita akan na dinga kai mata yara masu aikatau. Zuminci ya ƙullu a tsakaninmu mai ƙarfi saboda kai mata yara da nakeyi akai-akai. Har ALLAH yasa Zinneerah ta shiga sahunsu a dalilin matar mahaifinta Asabe. Labarin kuɗin da ake samu a dalilin aikatau yasa Asabe ɗaukar Zinni ta bani saboda ta mallake babanta ga shinan bai iya ce mata bai iya musata. Na ɗauka Zinni na kaita garin katsina aikatau tare da wasu yara, washe gari na juyo da nufin komawa gida ƴan doka suka kamani a tsaranci dalilin wata yarinya. Kusan shekarata biyu a gidan kaso, na fito shine naci karo da mummunan labarin Zinni ta dawo da ciki. Wlhy, wlhy, wlhy, wannan shine kawai abinda na sani, amma bansan komai game da cikin Zinni ba”.         Kowa ya gamsu da zancenta, dan haka suka maida dubansu ga Hajiya Haule dake sharar zufa.       “Nima nayi alƙawarin zan faɗi gaskiyata ni Hajiya Haule, dan faɗan da yafi ƙarfinka masu iya magana sunce ka maidashi wasa. Kamar yanda Hajiya lantana ta faɗa duk anyi haka. Ta kawomin yara ciki harda wannan yarinya Zinneerah saboda dama muna irin wannan huɗɗar. Inda ni kuma na danƙata hannun Hajiya Zakiyya. Amma kafin ita Zinneerah dama akwai wata yarinya da na taɓa bama ita Hajiya Zakiyya ɗin. Wadda ta sanarmin zasuyi mata aikine kuma zata bani maƙudan kuɗaɗe harda iyayen yarinyar. Babu wani ja'inja na yarda duk da kuwa bata fito ta sanarmin da ainahin aikinba, amma jin kuɗi ya sani ruɗewa na amince mata. A tashin farko ta diremin dubu ɗari biyar, hakan yasa a haukace na kai mata wata yarinya da aka kawomin dan sama mata aiki. Sai dai kuma bansan yaya akaiba bayan kusan sati ɗaya ta dawomin da yarinyar akan na sama musu wata ita bazata iya aikin da suke buƙataba. Nasha mamaki saboda yarinyar dana basu babba ce, nasan kowane irin aiki aka sakata zata iya. Dan haka na kasa daurewa na tambayeta duk da inajin tsoro saboda girmanta da kasancewar wadda ta fito daga masarauta. A lokacin bata kulani ba. ta daice naje idan an samu tana jira. Haka na baro gidanta cike da wasiwasi amma bani da mai bani sani sai ALLAH. Anyi haka da kusan wata ɗaya sai ga Hajji Lanti da yara. Da farko dai ƙyawun ita wannan yarinya yasani jin sha'awar kai mata ita, dan nasan masu kuɗinnan dason ƴar aiki mai tsafta da ɗan fasali haka. Cikin amincewar UBANGIJI kuma tana ganinta sai tace tayi, ta kuma ɗauka cikon kuɗina har naira miliyan ɗaya ta bani, duk da dubu ɗari biyar ya kamata ta cikamin. dan munyi da itane akan miliyon ɗayan, nawa dubu ɗari biyu na iyayen yarinya dubu ɗari uku, na yarinya ɗari biyar, amma ban saniba ko jin daɗin samo yarinyar yasata bani ƙarin dubu ɗari biyar, bakuma tamin bayanin ta karanba sai da naje gida na kirata dan duk zatona ko bata kulaba ta bani. Amma sai tace min tana sane. Samun yarinyar dai-dai da ra'ayinsu yasata ƙara mana waɗanan kuɗi mu da iyayen yarinyar. Ta kuma ɗora da faɗamin zasuma yarinyar dashe ne na ciki, idan yakai wata biyu zasu ɗauketa zuwa ƙasar waje har saita haihu musu su sallamota da tagomashin arziƙi, amma wannan sirrine tsakaninmu, ko iyayen yarinyar bataso su sani kawai nace dasu ta tafi turai ne da yarinyar inda take zama da mijinta. Iya abinda ta sanar min kenan ta yanke wayarta. Harga ALLAH na girgiza da zancen sai dai inda aka fi ƙarfi nane bani da damar cewa komai. Kamar yanda ta buƙaci karna bar Nigeria sai aikinsu ya kankama na amince, dan dama kuɗin data bani so nake na koma ƙasar saudia inda dama can nake zaune a da. An yayonine an maidoni rashin kuɗi yasa ban komaba. Gaba ɗaya na mallake kuɗi har na iyayen yarinya dana yarinya da tace, ko Hajji Lanti data kawomin yarinya ban nema ba. Dan na shirya kamfinma ta dawo amsar kuɗaɗen yaran data kawo nabar ƙasar insha ALLAHU. Bayan anyi haka da sati uku inata shirina sai ga wayar hajiya Zakiyya, ta tabbatarmin aiki yayi zan iya tafiyata cikin murnarta. Nima naji daɗi sosai dan dama kayana a shirye suke, hakan yasa kwana biyu dayin magana da ita na wuce saudi-arebia da yara guda biyu. Daga haka ban sake sanin komaiba sai jiya da ƴan sanda sukazo har gida batun kamani. Wallahi tallahi ALLAH shine shaidata wannan shine abinda nima na sani, dan ALLAH ku gafarceni na tuba”. Ta kare maganar tana share hawaye.         Gaba ɗaya falon ya ɗauka salati ana duban Zakiyya da tai ƙasa da kanta, daka ganta kasan a firgice take matuƙa. Hakama Mammah a ruɗan take amma duk tasan itama akwai sunanta a ciki so take taji ta bakin Zakiyya game da cikin Zinneerah da ita dai harga UBANGIJI batasan da zamansaba.       Zinneerah kam mutuwar zaune tayi tanabin kowa da kallo kawai tamkar butun-butumi, dan harga ALLAH suna neman rikitar mata da tunani. Ita kanta burinta kawai aunty Zakiyya tayi magana.      Mai martaba da zuciyarsa har wani tafasa take ya kafe Zakiyya da kallo yana kuma duban Farah dake kuka itama wiwi. A zafafe yace, “To dan uban daya haiheki sai kimana bayani muji lalatacciyar yarinya kawai. Wannan wane irin kafurcine kuma daga ina kika samosa ko kuka samosa tunda dai babu yanda za'ai dashe masu ƙwai basu saniba. Shi ƙwan na wanene? Kuma yaya akai?”.          Ƙasa ta zamo ta dirƙushe jikinta na rawa, dan tafi kowa sanin wanene mahaifinsu. Inhar kuma tai gigin faɗar abinda ba haka bane lallai zai mata abinda gwamma ta faɗi gaskiyar.       Kafin tace komai Farah da tsoro ke neman gigitata na tsawar mahaifin nasu ta fara rawar jiki da faɗin, “Wlhy Abbah babu ruwana nidai, duk aunty Zakiyya ce ta tsara komai, itace tasa muyi wlhy badan inaso ba......”        Hankali tashe itama Zakiyyan ta fara magana, “Dan girman ALLAH Abbah ka gafarceni. dan ALLAH kar kayi fushi dani, Baba wambai ka bashi haƙuri dan ALLAH”.         Aminin mai martaba da suke kira da baba Wambai ya gyara zamansa cikin kasaitar mulki da dattako yace, “Zakiyya kafin azo ga neman gafara ai nakega ya dace musan yaya akai ko? Kinsan mai martaba bayason jayayya, dan haka ki buɗe baki kiyi bayani tamkar yanda suma waɗanan mata sukayi, inaga shine zaifi sauƙi kamar kafin muzo ga gaɓar da kike so”.       Kanta ta jinjina masa tana sharce hawaye.          “Kowa yasan Farah dai autarmu ce da tausayinta yasa duk muka ɗauka son duniya muka aza mata, musamman ma ni daya kasance itace kawai ƴar uwata mace, sauran ukun duk maza ne. Farah a Morocco ta rayu hannun kakarmu data baro london, bayan rasuwarta Mammah yayar mahaifiyarmu ta amsheta ta koma da ita london. Tausayin da kowa yakema Farah a cikin dangi shi Abdul-Mutallab ke mata shima. Hakan yasa yafi kowa nuna jin daɗinsa da komawar Farah garesu. Kamar yanda take samun gata daga Mammah haka shima take samu a garesa, ta sanadin hakan shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakaninsu, daga karshema ta juye soyayya. Kowa yaji daɗin hakan a dangi, dan babu wani ja'inja aka yanke zancen aurensu. Bayan bikin su da kusan shekar biyu babu wani labari koda na ɓatan wata daga wajensu, babu kuma wanda ya damu da hakan sai ni dana farajin damuwa. A wani zuwa da tayi Nigeria na takura mata mukaje Doctor ya dubata, inda mukaci karo da mummunan labarin daya nema zautani, dan ita koma a jikinta saboda ƙuruciya na ɗawainiya da ita a lokacin. Doctor ya tabbatar mana akwai wani tsiro daya toshe bakin mahaifar Farah gaba ɗayanta. Yanda da wahala ace ciki ya shiga, kodama ya shigan bazai zaunaba. Na bukaci ai mata aiki a ciresa idan zai yuwu, sai ya tabbatar mana taɓashi babbar matsalace, dan zata iya rasa ranta, sannan basu da wani maganin da zai iya gusar da shi a yanzu haka dai. Naci kuka sosai na kuma shiga damuwa da tunanin neman mafita ma yar uwata. Da farko dai son ganin jinin autarmu yasani damuwar, amma dalilin shigowar wasu maƙudan kuɗi ga Abdul-Mutallab da zantukan danginsa na ya ƙara aure ya far canja alkiblar tunanina, zuciyata ta fara rayamin idanfa ƴar uwata ta haihu da shi komi ya tara mallakintane ita da ɗiyanta. Idan kuma nayi sakacin hakan suka aura masa wata akwai matsala tunda likita ya tabbatar mana akwai matsala game da mahaifarta ita. Wannan tunanin ya sani ɗaukarta a wani zuwa london da nayi muka fara bin likitoci ba tare da sanin Abdul-Mutallab kosu Mammah ba. Sai dai duk inda mukaje amsar dayace mahaifarta nada matsala, kuma irin bayanin wancan likitan suma suke mana dai. Hankalina ya ƙara tashi haka itama nata, dan haushin rashin damuwarta yasani zama na fahimtar da ita. Nasha takaici ganin daga baya ta nuna ita fa ba komai bane, tunda Abdul-Mutallab na sonta tana sonshi ko bata haihuba babu damuwa, ballema bata fidda ran a gaba su samuba dan bata yarda da maganar likitocinba ALLAH ne maiyi. Duk da gatan da mukema Farah na tsiya nasan tanada zurfin tunani da aiki da hankalinta matuƙa, sai dai banyi zaton zata kasa fahimtataba musamman dana san tanada kishi mai zafi irin namu musamman akan Abdul-Mutallab. Lokacin da suke cika shekaru uku da aure kakarsa ta ƙara bijiro masa da zancen aure a time ɗin sunzo Nigeria tare, hankalin Fara ya tashi matuƙa, dan tanada tsananin kishi”...........✍        *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_*         *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* _________________________ *Page 63* ............“A wannan gaɓar saboda yanda ta nuna tashin hankalinta matuƙa sai nayi amfani da damar wajen sake zaunar da ita na nuna mata muhimmanci haihuwarta. Tare da kawo mata zancen dashen ciki. Ta razana matuƙa, ta kuma ce ita dai gaskiya tanajin tsoro, dan tasan Abdul-Mutallab ma ba yarda zaiba. Dan haka kawai mubar zancen na tayata da addu'a dan bazata iya zama da kishiya ba zata iya halaka kanta. Wannan furuci nata ya kuma ɗagan hankali matuƙa, dan nasan zata iya aikata abinda ta faɗan, na kuma tabbatar auren Abdul-Mutallab bazai fasu ba inba danginsa sunga ta haihu ba. Ta kuma nunamin su Mammah ma ba yarda zasuyiba dan abune da kowa yasan malamai na nuna illarsa a addinance dama lafiya ta wani fannin. Ban gusaba wajen zaman cigaba da nusar da ita, tare da kawo mata dabarun da zamuyi maganin kowacce matsala. Na farko karmu bari AK ya sani, ayi komai a ɓoye harta wadda za'a sama cikin ta haihu ace itace ta haihu. Ta tambayeni taya za'ai hakan ta kasance bayan koyaushe tana tare da AK. Na ce mata ta bari zanyi tunani. Bayan kwana biyu dayin maganar na samo mafita a wajen Doctor ɗin da zaiyi aikin, idan an dasama wadda zata raini ciki ita zata fara pretending like pregnant, bayan yakai kamar 3months zata koma zama a Morocco ta hanyar wasu dabaru namu na mata har mai ciki ta haihu a bata ɗanta ta shayar ita da kanta. Cikin tsoro tace amma tayaya hakan zata faru bada yardar su Mammah ba. Niko nace mata Mahma ce kawai za'a ɓoyema gaskiyar zance, amma Mammah da ita za'ai komai. Tacemin ta yaya Mammah zata yarda da hakan?. Nace mata ta hanyar yin amfani da ita akan so da kishin da takema mahaifin Abdul-Mutallab da ganin laifin danginsa da take na rabuwarsu, da kuma ƙin son rabata da ƴaƴanta da shine babbar barazanarta a rayuwa. A lokacin Farah bata bani goyon bayaba, dan tace bata yarda a cutar da kowa ba, musamman ma Mammah da ta ɗauketa daidai da nata ƴaƴan saboda ƙaunar da takema mahaifiyarmu. Sosai na mata masifa ni da Muktar a lokacin, dan shine ya taimaka mana da likutan da zaiyi aikin ma. Da dai mukaga taƙi tanƙwaruwa ta sauki sai itama nabi da ita ta hanyar razanarwa da kshiya har tai laushi ta amince. Tun daga lokacin itama Mammah na fara aiki a kanta, sannan Doctor ya tsarama Farah yanda zamu sami sparm ɗin Abdul-Mutallab cikin sauƙi”.                Babu wanda mamaki bai nema kashewa a falonba, musamman ma Mammah datai mutuwar zaune akan wannan labari na Zakiyya. Zakiyya ta cigaba da faɗin,         “Bayan wani lokaci na tunkari Mammah da batun ya kamata musan halin da Farah da Abdul-Mutallab ke a ciki game da haihuwa, kar muyi sakacin da dangin mahaifinsa zasu aura masa wata zasu rabamu da shine kawai ya koma hannunsu. Na tabbata wannan kalma ta tada hankalinta matuƙa, dan babu abinda tafi tsana arayuwa kamar ace yaranta zasu koma hannun mahaifinsu. Bayan munyi wannan maganar washe gari taima Abdul-Mutallab maganar a gabana, amma sai ya nuna ɗan ɓacin ransa akan duka shekararsu nawa da auren da har za'a fara nuna damuwa basu haihuba, shi wannn maganar dan ALLAH a barta ALLAH ne mai badawa kuma zai basu lokacin da yaso. Da wannan furucin yabar gidan a zuciye. Hankalina ya tashi, dan gashi saura kwana biyu na baro london ɗin, dan haka na sake sabon zaman fanfa Mammah da kawo mata dalilai kala-kala da suka dinga ruɗa mata tunani itama tana ruɗashi. Tashin hankalin data nema sakashi a ciki ya sashi tattaro Farah suka gudo Nigeria a lokacin bamu sani ba. Sai da sukaje ta kira take sanar mini. Naji daɗin hakan, dan nima a gareni wata dama ce. Dan haka na sake buɗe wutar data harzuƙa Mammah harta kirasa ta tabbatar masa da inhar bai yarda da batuntaba wlhy zata iya tsine masa. Sosai Abdul-Mutallab na gudun ɓacin ran mahaifiyarsa. Dan haka furucinta ya tada masa hankali yace ya amince zasuje idan sun koma london. Still nice dai na sake bama Mammah shawarar suga Doctor Hannafi dake nan Nigeria shima kwararrene a wanna fanin kuma a can london ɗinma yay karatunsa da aiki harna tsahon shekara bakwai. Batare da wani jayayyaba ta kirasa da tura masa address da phone Number ɗin Doctor Hannafi dana bata nima kuma na tattaro na dawo Nigeria neman yarinyar da za'aima dashen. Ta farko bataiminba, dan tanada wayo kuma idonta a buɗe yake, hakan yasa nasa hajiya haule canjamin ita.”          “Biyayyar da Abdul-Mutallab yake ma Mammah ya sashi ɗaukar ƙafa sukaje ga Doctor Hannafi, wanda dama mun gama tsara komai. Dan haka kawai abinda ya buƙata a garesu shine sparm ɗin sa, ita kuma Farah yay mata wasu gwaje-gwaje kamar gaske. Domin kawai bin umarni Abdul-Mutallab ya yarda ya bama Dr Hannafi Sparm ɗin nan, wanda da shine aka haɗa da ƙwan Farah akaima ita Zinneerah dashen bayan mun tabbatar zata iya. Dan ita bata kai waccan girma da wayo ba, amma yanayinta kawai zaka kalla bama zaka ɗauka a ƙauye ta fitoba dan ƙyakyawa ce. Da wannan karancin shekarun nata mukai amfani wajen yin komai na dashen batare da ita ta fahimci komaiba, dan ALLAH ya taimakemu sanda aka kawo min ita tana cikin halin zazzaɓi sai komai ya ƙara zuwa mana dai-dai muka tafiyar da ita akan treating ɗin zazzaɓin nata. Sai dai kuma bayan dashen muna fata da addu'ar ALLAH yasa ya zauna da kwana uku muka nemeta muka rasa. Hankalina ya tashi matuƙa a wannan lokacin, nama kasa sanarma Farah yanda akai sam. Sai dai munta tararrabin mu da neman yarinya ni da Muktar da Dr Hannafi. Gashi Hajiya Haule ta wuce saudia kuma bani da contact ɗinta nacan balle mu binciki garin da ta ɗakkota. Dr Hannafi ne ya kwantar min da hankali ta hanyar sanar min da wahalama cikin ya zauna, dan bai kai kwanakin da ake buƙatar nutsuwarta a waje guda ba, kawai yanzu dabarar da zamuyi a karasa AK ya bada sparm ɗin nasa kafin su wuce sai a sake yima wata dashen, wannan kuma mu ɗaukama bazai zauna ba kawai, musamman da ko magungunan daya kamata tasha sau daya ta shasu. Na ɗanji sanyi da wannan shawarar tasa, akanta kuma na yanke hukuncin tun karar Mammah da batun dashen cikin. A ranar na kirata, na sanar mata Dr Hannafi ya tabbatar mana AK nada matsalar bama mace ciki, amma za'a iya yin amfani da sparm ɗinsa ai dashe, sai dai matsalar itama Farah nada tata matsalar a mahaifa kuma”.           “Hankalinta ya tashi, harta buƙaci na haɗata da Dr Hannafi ɗin, na kuma haɗata dashi ya sake mata bayanin daya kamata akan dashen da tsarin da za'ayi. Ta tabbatar masa da zata iya yarda ayin kodan a samu ɗan danginsa su daina harar mata yaro dason mallakesa. sai dai babbar matsalarta shine Abdul-Mutallab, tasan bazai taɓa yarda da hakanba koda zata tursasashi a wannan gaɓar. Cikin dabara Dr Hannafi ya shigar mata da shawararmu na yanda tsarin zai kasance batare da Abdul-Mutallab da kowama sun fahimci hakanba bayan mu. Tace ya bata dama zatai tunani da shawara. Cikin amincin ALLAH sai tai shawara dani, dan a tunaninta bansan komaiba game da dabaran. Babu wani ja'inja na nuna mata hakan shine dai-dai, tare da sake kawo mata dalilaina nima. Sai ko aka dace ta yarda dan nayi amfani da inda ke mata ƙaiƙayi. Amincewar tatace ta zama ginshiƙin tushen aikinmu na biyu, sai dai a wannan karon cikin bayin gidanmu na ɗakko, kuma da amincewarta dana iyayenta, ana kuma gamawa na maidota gidana ina kula da duk motsinta har ALLAH tasa ciki ya zauna ya kai wata biyu da wasu kwanaki sannan Mammah tazo da kanta ta tafi da ita Morocco. Zuwa sannan kuma Abdul-Mutallab da wasu a cikin danginmu sunsan Farah nada ciki, sai dai mun gargaɗi Abdul-Mutallab da sanarma danginsa zancen ciki har sai Farah ta haihu saji hakan zaisa sufi murna ya kuma musu surprise. Ya amince da hakan kuwa sai dai bamusan dalilinsaba. Sai dai ashe kana nakane ALLAH na nashi, dan randa Farah ta baro london da nufin zuwa tai goyon ciki a Morocco wanda tursasawar Mammah yasa Abdul-Mutallab yarda washe gari yarinyar tayi barinsa. Ranar ba Farah kawai ba hatta ni da Mammah sai da mukai kuka wlhy, Abdul-Mutallab kuwa a ranar ya baro london zuwa Morocco hankali a tashe. Shima har kukan yayi saboda ya ƙwallafama cikin nan rai kamar mi. Bayan gama wannan taraddadin bawai na haƙura bane akan ƙudirina. Na cigaba da zungurar Farah da Mammah suna zillewa. Dan kai tsaye Farah tace min alhakin Abdul-Mutallab ne yasa cikinma ya zube. Faɗa mukaita mata a lokacin, amma taƙi saurarenmu. Mun tattara mun ƙyaleta a lokacin danta huta dan naga itama Mammah na neman fara zamemin. Taimakon da ALLAH ya sakemin shine takurawar Abdul-Mutallab ya ƙara aure daga hajiya iya, wanda har takai ga ya ɗauke kafarsa da Nigeria, sukuma suka tura masa ƙaninsa. Tun daga nan na fahimci hankalin Farah baya tare da ita, dan duk wani abinda ya faru tsakaninta da Abdul-Mutallab sai ta kira ta sanarmina lokacin. Abinda na fahimta shine kishin zancen ƙara aurensa na cinta har take ganin kasancewar wani nasa tare da shi zai sa danginsa suci galaba a kansa. Na biyu kuma tashin hankalin Mammah itama na kada Abdul-Mutallab ya komawa danginsa yasa take goyama Farah baya.”       Takai ƙarshen zancenta tana share hawayen da tun ɗazun basu gajiya wajen kwaranya ba daga kumatunta, dan muryarta har dashewa takeyi dan kuka.       Tsitt falon yayi motsima kowa ya kasa dan al'ajabi, wane irin masifa ne wannan da haɗa boom. dan wannan al'amari na Zakiyya yayi kama da haɗa boom. Dan kawai kinason ƴar uwarki sai ki ƙulla abinda zaki cutama rayuwar wasu.        Kallonta kawai AK yace cike da tsana da takaici. idanunsa sun kaɗa sunyi jajur, hakama jijiyoyin kansa sunyi ruɗu-ruɗu. Hakama Farah kuka take tamkar ranta zai fita, dan tasan dai komai Zakiyya tayine dominta, gashi tun ba'aje ko'ina ba komai ya ƙwaɓe. Kishiyar da take tsoro kuma an mata ta sanadinsu.          Mammah ma kanta duƙe a ƙasa dan tama rasa mi zatace dan tashin hankali da baƙin cikin kanta da kanta, tayaya ta zurma haka da yawa yarinya ƙarama ta ɗana boom ɗin da a ƙarshe yake neman tashi da ita? Tayaya idonta ya rufe haka da yawa ne akan abinda yana a hannunta amma gashi sakacinta ya ta miƙashi ga mai shi?.......          Cikin ƙunar Zuciya AK ya katse tunanin kowannensu ta hanyar faɗin, “Shima cikin da take dashi yanzu na ƙaryane kenan? Randa mukaje asibiti da nufin sake duba lafiyata kune kuka ƙulla?.”           Kasa magana Farah da Zakiyya sukayi. sai Mammah ce cikin kuka tace, “Kayi haƙuri Abdul-Mutallab, tabbas wannan duk laifinane, da ace ban bata goyen bayaba babu yanda za'ai hakan ta kasance. Nayi nadamar saninki Zakiyya, wannan wane irin haline haka da kika nema jefamu a ciki. Har takai na saka hannu wajen cutama gudan jinina ta hanyar makircinki”.         “Dama shi son zuciya ai ɓacin zuciya ne, daga lokacin da kake ganin wayonka ko dabararka zai baka abu to lallai a lokacin ka ɗaura ɗammara da ɗambar rasashi, dan koka samu sai ya suɓuce maka. Kin biyema yara ƙanana saboda wani shirmen banza da wofi Hindatu, yanzu da ALLAH bai ƙaddara yarinyarnan ta faɗo cikinmu ba yaya kenan? Duk da dai sanda sukayi na farko basu sanar miki ba, amma na biyun da'an haifesa fa? Shikam kinada kamasho a ciki ai”. Uncle Ahmad ne ke magana cikin ƙunar zuciya.        Kauda kai AK yayi yana rumtse idanunsa saboda zafi da ƙirjinsa ke masa. ga kansa sai juya masa yakeyi alamar hawan jininsa na neman motsawa. Cikin harɗewar harshe yace, “Uncle idan wancan ya salwanta aiga waninan ma sun sake dasawa. Tunda sunce tanada ciki kuma likitoci sun tabbatarmin babu wani ciki tare da Farah”.      Yanzu kam duk yanda mai martaba da mukarrabansa sukaso daurewa sun ƙasa. Cikin kaushin murya yace, “ALLAH zai sakamin ɓatamin suna da kukayi. musamman ke Zakiyya dan kece kika ƙulla komai, kece kika ɗora ƴar uwarki akan abinda sam babu shi a ranta, ni yanzu bamma san mizance mukuba wlhy, dan yanda nakejin raina zanma iya tsine muku. Amma inason sanin gaskiyar zancen shi cikin da akace tana dashi yanzu, dan nikam kotun musulinci zan kaiku a yanke muku hukunci dai-dai da laifinku”.       Sosai Farah ta fashe da kuka. Ta rarrafo gaban mai martaba ta kama ƙafafunsa da fashewa da kuka. “Dan ALLAH Abba kayi haƙuri, nidai wlhy bazan sakeba, wannan ma kota haufa banaso zanyi haƙuri ALLAH ya bani nawa. Na tuba Abbah dan ALLAH na tuba”.      Banza yay mata yama ɗauke kansa ya maida ga Zakiyya da itama kukan take. “Wai bada Zakiyya nake maganarnan ba?!”      Zabura ta ɗanyi saboda yanda yay maganar a tsawace, ta shiga jinjina kanta da faɗin, “Abba hakane, shima dasawar akai, amma wannan ƴar Morocco ce, kuma da amincewarta itama wlhy”.      Sake ɗaukar sallalamu falon yay gaba ɗaya, hajiya iya dake sharar ƙwalla tace, “Gaskiya baku ƙyautaba, wannan zaluncine wlhy dason zuciya. A barshima mutum shi ya yarda yay muku wannan aikin da sauƙi ai, amma kamar yarinyarnan aikun zalunceta. Inda ALLAH bai ƙaddara tamu bace kamar yanda Ahmad ya faɗa harta mutu baza'a daina mata kallon wannan tabon ba. Yaya zakuyi da alhakin wannan yarinyar kawai ma balle na sauran suma, sai dai idan da yardarsu kukayi sukam. Nikam dai ina bayan mahaifinku a kaiku kotun musulinci a bin kadin jikata na rainon cikin da tayi. kuma wlhy ko sama da ƙas zata haɗe ɗannan ya zama nata har gaban abada marasa mutunci”.           A take su waziri suka shiga goyama hajiya iya baya, kowa na tofa albarkacin bakinsa. Mmn sadiq, Abba, baba sune dai basuce komaiba, sai dai duk sai da sukai ƙwallar tausayin Zinneerah harma da AK da little. Sai da ƙyar Baba ya fara magana ganin kowa ya yarda da zuwa kotin.       “Ranka ya daɗe nikam kuyi haƙuri zance wani abu”.     Duk hankalinsu suka maida garesa. Ya ɗan muskuta zamansa yana gyarama little dake a jikinsa kwanciya, dan shi yaune karon farko daya ga jikan nasa, “Kuyi haƙuri nasan tabbas basu ƙyautaba, kuma zaluncine abinda sukayi dan yarinyarnan taga rayuwa mai zafi kala-kala a dalilin cikin nan. To amma Alhmdllh ta wani gaɓar ya zamar mata alkairi. Dan a sanadin samunsa ta sadu da mahaifiyarta, ƙaddara ta ɗakkota ta kawota cikinku da har a yau ya zama sillar bayyanar komai, bugu da ƙari yay mata ƙyauta da miji uban ɗan kuma saboda hikimarsa. Sannan a sanadinsa nima kaina nabar gida harna samu waraka daga kaidin matata, na kuma ƙara aure a yanzu haka matata ta haifamin yara maza ƴan biyu guda biyu tun washe garin da suka koma gida. Waɗanan kaɗanne daga ni'imomin UBANGIJI gagara misali daya lulluɓe Zinneerah dasu a sanadin cikin yaron nan da batajiba bata ganiba. Tabbas duk mai haƙuri zai dafa dutse harma yasha romonsa. Su dai duk sun aikatane akan dalilai biyu zuwa uku. Mahaifiyarsa dalilinta kawai kar ya dawo hanun ubansa ne da rayuwa, sai kuma gashi ya dawo cikin sauƙi. Ita wannan yarinya saboda kar mijinta ya ƙara aure ne, kuma gashi ya ƙara ɗin harma suna zaune a inuwa ɗaya. Ita wannan ƴar uwa tata kar wata tazo ta haihu ba ƙanwartaba. Gashi kuma watan ta haihu ba kanwar tata ba. To idan mukai tsam a nazari zamu fahimci UBANGIJI ya bama kowa sakamako nan duniya dai-dai da shi da tabbatar musu cewar wayo ko dabarar bawa bata kaisa da nasara. duk saurinka kuma saika jirayi zartar da ƙaddarar UBANGIJI gamai ita. Tunda su duk sunyine a ɓoye domin bama kayinsu kariya akan abinda yake gaibu kuma dauɗar duniya amma daga ƙarshe gashi duk sun rasa, kuma wanda sokaso ƙwata daga wajensu ALLAH ya maido musu. A ganina kuma miya rage banda mu barma UBANGIJI ikonsa ya ƙarasa zartar da hukuncinsa. Basai anje kotuba, dan mu dukanmu ALLAH ya haɗamune a ƙarƙashin inuwar zumunci sai muyi haƙuri wajen haɗiye duk wani saɓani da zaizo a garemu duk da kuwa wannan ya banbanta ba abune mai saukiba. Amma idan mun sauƙaƙashi a ranmu sai ya zame mana alkairi kamar yanda ya zamewa Zinneerah. Sai dai kuma su sauran yarenne bamuda hurumi a kansu inhar suma tirsasu sukai ko yaudararsu. Abin na gaba shi annamimin likitan dake wannan aikin ya kamata a dakatar dashi, dan gwara ace ma'auratan dake buƙatar hakan da kansu suka amince suka kai kansu bawai ta irin wannan hanyar dabita wagga ɗiya Zakiyya tabi ba. Wannan al'amarima malamai sunata nasiha akansa. barinsa yafi alfanu fiye da yinsa. Dan UBANGIJI shine yasan miya gani har bai bakaba, zata iya yuwuwa rashin haihuwar sai yafi zame maka alkairi fiye da yinta. To mizai hana bazaka dogara ga UBANGIJIN talikai harya baka ba kuma?. Sai kuma ina roƙon alfarmar ku taimaka kuje can garinmu ku wanke wannan yarinya agaban al'ummarmu, dan inba hakaba harta mutu wannan tabon na biye da ita. Haka shima wannan yaron bazasu taɓa kallonsa da darajaba dan ɗan shege zasuke kallonsa bayan ba haka bane. Ayi haƙuri da juna ayi sulhu dan ALLAH shine mafi alkairi a garemu fiye da mu tonama kammu asiri kodan kasancewar ku manyan mutane danmu namu mai sauƙine iya garine kawai, idan yazu kuma mukace mun barsa zance ya ƙare. Kuko magauta sun sami abin faɗa a gareku kenan har takai shi yaron ana goranta masa duk da kuwa ba alfasha aka aikata wajan samuwarsa ba kai tsaye”.      Harga ALLAH kowa maganar baba ta sanyaya masa ransa. Kuma kimarsa da darajarsa ta ƙaru a cikin idanunsu, hajiya iya ta shiga jera masa tagwayen addu'oi shi da zuri'arsa kowa na amsawa da amin.      Sai da kowa ya natsa sannan mai martaba ya fara magana bayan yayi gyaran murya. “Ni a nawa hukuncin to Abdul-Mutallab da Sageer (mijin aunty Zakiyya) duk ku saki waɗanan marasa mutuncin, kowacce ta koma masarauta sai sunyi zaman shekaru bibbiyu kafin na barsu su dawo gareku idanma kuna sha'awa kenan, kokuma su sake auran wasu mazan suji, dan masu iya magana sunce idan kai nada tsoka taɓa naka kaji. hukunci na biyu koda na faɗa ko ban faɗaba musilinci ma ya bama wannan yarinya yaro duk da dai malamai sunyi bayani kala-kala akan hakan, dan haka ko da wasa idan kuka ɗauka yaron nan kuka bama Farah matsayin uwarsa ALLAH ya isa ban yafe mata ba idan ta amsa. Yaro na Zinneerah ne har abadan kuma itace zata cigaba da iko da shi matsayin mahaifiyarsa har ƙarshen rayuwarta, kai bamma yarda koda wasa wani ya dangantashi da Farah ba zan ɗauka mataki mai tsauri koda kuwa Abdul-Mutallab ne yayi hakan. Koda alaƙa zata shiga tsakaninta da shi sai dai ta zumunci ko matsar ubansa amma ba uwa ba. Hukunci na ƙarshe idan waɗancan da sukaima wannan ƙullalliyar yazam suma bada saninsu bane to lallai zan kaisu kotu a bi musu kadin haƙƙinsu. Wannan shine hukuncina a matsayina na maihaifinsu”.     Kuka wiwi Farah da Zakiyya keyi musamman akan zancen sakin da mazajenau zasu musu dana haramta mata Little. Dan Farah a yau karo na farko ƙara ganin little yasa ya shiga ranta dan kamar an ɗakko ƙaunrasa mai tsanani an dasa mata a ƙirji takeji.       Babu wanda ya iya jayayya da wanan hukuncin na mai martaba dan shine kawai zai iya zama darasi garesu. Sai dai yanda suke kuka dolene su baka matuƙar tausayi..............✍   *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* ________________________ *Page 64* ............Cikin dakiya Baffah yace, “Wannan hukunci naka yayi dai-dai kuma na gamsu dashi nima wlhy, dan haka nima ga nawa hukuncin akan ƴaƴana da Hindatu. Duk da ni bazan rabaki dasu ba amma tabbas zan nesanta rayuwarsu da taki. Daga yau Abdul-Mutallab zai dawo rayuwa a Nigeria, idan har kikaga ƙafarsa a london sai dai harkar kasuwarsa amma bada rayuwaba. Hukunci na biyu anan gurin nakeson a ɗaura auren Huzaifa da Adilah itama ta baro can har abada sai dai taje domin gaisheki ita da mijinta. Hukunci na ƙarshe karna sake ganin ƙafar Hindatu a gidana har abada, idan kuma ta sake shigowa nima zanyi ƙararta........”          Katsesa Abba yayi (mijin mmn sadiq) “A'a dan ALLAH ayi haƙuri Alhaji Kabeer, ai ko babu komai ALLAH ya haɗa tunda gashi har an fara ajiye jikoki bama ƴaƴa ba. Hukuncin dawowar yara dai yayi amma ita kar ace bazata zo nan ba dan ba'asan mi rayuwa zatai nan gaba ba”.          Wambai yace, “Maganarka gaskiyane Alhaji Abubakar, a daiyi haƙuri Alhaji kabeer a tsaya kan yaran kawai domin ALLAH. Babu yanda za'ai tunda zuminci ya sarƙa a tsakani, koba komai darajar shi Abdul-Mutallab ɗin da biyayyarsa a ɗagama Hindatu ƙafa. Mai afkuwa ta afku, kamar yanda kuma Malam Sulaiman yay bayani ALLAH ya bama kowa sakamakonsa tun a duniya tunda mainakon nasara duk faɗuwa sukai batare da sun ci nasarar burinsu ba. Koba komai ita wannan yarinya MAKAUNIYAR ƘADDARA ta zame mata BUƊAƊƊEN HASKE, ta mallaki ɗa, ta mallaki uban ɗa, sarƙin dake tsakanin iyayenta ya buɗe, sai muyita mata fatan gamawa da rayuwa mai albarka har ƙarshen numfashinta. Su kuma nema gafararta dan alhakinta bazai barsu cigaba da rayuwa cikin salamaba. Suma kuma waɗanda suka sakema ta'asar a nemesu aji ta bakinsu, idan kuma da amincewarsu ne shikenan ai. Sai a tattara a barma UBANGIJI ikonsa. Koda hukuncin mai martaba aka barsu ya ishi rayuwarsu izina. Masu shirin aikata wanan taɓargazar ko ma suka aikata suma sufa sani sakamakonsu naga ALLAH, dan shine kaɗai yasan hukuncin daya dace ga mutane irinsu. Ina amfanin abinda yahudu da nasara suka ƙirƙira da har zai birgeku wajen aikatawa bayan kuna al'ummar musulmai? Koba komai ka nuna rauninka kenan ga jarabawar da UBANGIJI yay maka domin gwada imaninka. Sannan zata iya yuwa shi wannan ɗan ya girma ma ya gallabi rayuwarka, ƙilama yay sanadin hallakaka ko shigarka wuta. Dan ƴaƴa da yawa sune zasu kai iyayensu wuta. Dan haka ya kamata mu kiyaye, dan kana neman haihuwa bai kamata kabi ta kowacce hanya domin samu ba. Hakan son zuciyace da rashin godiyar ALLAH. Domin idan zaka nutsu ga ni'imominsa ya maka ta hanyoyi da dama ba sai ta haihuwa ba, ko musulinci da yayika aciki da soyayyar MANZON ALLAH (S.A.W) daya dasa maka a zuciya kawai aka barka ya maka babban ɗaukaka da rahama. Balle wanima zakaga bayan wannan akwai wasu tanade-tanade da UBANGIJIN yayma rayuwarsa waɗanda shi kansa baima san yawan adadinsu ba. Amma saboda kawai ya jarabcesa da rashin samun ƴaƴa sai ya ruɗe ya fita hayyacinsa. Kaiconmu da wannan shiriritar, nasan rashi ƴaƴa nada zafi a rai da damuwa. Amma duk abinda ka ɗaukesa mai sauƙi sai UBANGIJI ya sake sauƙaƙa makashi kai ma a zuciyarka da ayyukanka. Idan kuma ka dage sai ka samu to lallai San zuciya kuwa ai ɓacintane ga duk mai sha'awa ko buri. Duk wanda basu haihu ba ya ALLAH ka azurtasu da zuri'a masu albarka a garesu, idan ba alkairi bane ALLAH ka sakanka musu da abinda yafi alkairi, ka yalwatasu da tarin haƙuri da juriya a zukatansu”.         Da amin duk suka shiga amsawa, kuma kowa ya gansu da bayanin waziri, saurama suka shiga tofa albarkacin bakinsu. Sai da duk mazan suka gama kace nace Mahma da tun ɗazun al'ajabin su Zakiyya ya hanata tofa komai ta duba su Zakiyyan. “Wannan shine abinda naketa nusar daku amma kuka kasa fahimta, bansan miyasa a mafi yawan lokuta gatan rayuwa da tagomashin arziƙi dake zuwa cikin hannayenmu ke dulmiyar da zukatajen jin muna sama da kowa ba. Zamu iya zartar da hukunci ga kowa, zamu iya taka kowa dan ko anje an dawo babu yanda zaiyi damu. Duk da dai anata maimaita magana ɗaya amma dolene a faɗa. Kun zalunci yarinya saboda kuna mata kallon mai ƙarancin gata, sai gashi UBANGIJI ya biyo muku ta inda bakuyi zatoba ya ruftaku a ramin da kuka tanadi sakata ku kuka afka. Shi kansa Abdul-Mutallab kun cutar dashi ai, gara ace fitowa kukai kuka shaida masa ƙudurinku, idan ya amince fine, idan bai aminceba sai ku bi duk hanyar data dace wajen ganin kun lallaɓasa ya yardan koku haƙura har ALLAH ya kawo mata iyakar da zata samu. To yanzu dai dukma abinda zai faru ya faru. kun aikata a ɓoye ALLAH ya buɗa kowa ya gani, kunyi danku tsare mutuncinku gashi ya zube a idanun kowa. Kunyi don samun haihuwa, gashi an haihu ɗan yafi ƙarfinku dan nima ina bada goyon bayan hukuncin Abdul-Hakim (Mai martaba), kunyi dan gudun kishiya, ga kishiyar nan mai daraja ma kuwa da inhar Abdul-Mutallab ya wulaƙantata koda na second guda bazamu yafe masaba, dan ta cancanci a kula da ita a riritata. Kunyi dan kar Abdul-Mutallab ya suɓuce muku, gashi ya suɓuce mukun ya dawo inda baƙwaso ya rayu dagashi har ƴar uwarsa. Da wannan kawai aka barku ya isheku, dan nidai banga ribar da kukaciba anan sai asarar kuɗaɗenku dana lokacinku da kukayi a banza a wofi, idan kuma wannan baiwa da waɗan can ma basu yafe mukuba to yanzu aka fara wasan. Koda sun yafe muku sai kuma ku jira hukuncin UBANGIJI a gareku dan shi ne yafimu sanin abinda ya cancanta da mutane masu hali irin naku. Hindatu kinfi kowa ganganci matsayinki na uwa, duk da kuwa Zakiyya ce tai amfani da abinda ke damuwarki ta sarrafaki cikin sauƙi kika afka, amma ba komai ya jawo hakanba sai gurɓataccen tunaninki da son zuciyarki. Wanda inada tabbacin son Kabeer ne ɗawainiya dake ba komaiba, girman kai ya hanaki nutsuwa ki nema sulhu da shi sai kike huce komai akan yaronsa da baijiba bai gani ba. Gashi nan ai kin rasa Kabeer ɗin da Abdul-Mutallab ɗin duka harma da Adilah. ALLAH UBANGIJI ya rabamu da son zuciyoyinmu, ya yalwatamu da haƙurin ibadarka. Daga ƙarshe dan ALLAH ina roƙama ƴan uwana gafara a gareku iyayen Zinneerah, ku yafe musu, karkuyi dubi da halayensu da cutar da sukaima ƴarku. Dan tunkan aje ko ina ALLAH ya saka mata. Dan ALLAH ku gafarcesu ko zasu sami sassauci daga raɗaɗin da za'a bar rayuwarsu da shi. Keko Zinneerah bazance ki yafe musu ba, idan zaki iya yafe musu Alhmdllh, idan kinga bazaki iyaba ki barsu da ALLAH zai cigaba da saka miki ta hanyoyi daban-daban kamar yanda ya fara tun yanzu anan duniya. Kabeer da Hajiya Mama (Hajiya iya) kuma dan ALLAH ku yafe musu badan halinsu ba, kodan darajar Abdul-Mutallab dake a tsakani, dan ya can-can-cin yabo yaron nan ta fannoni daban-daban. Duk da kun sakashi a tsakiya game da wannan al'amari a koda yaushe burinsa yaga ya saka farin ciki a zukatan kowannenku koda kuwa shi zai ƙuntata tashi zuciyar. Dan ALLAH muyi haƙuri mu yafi juna kodan shima yay farin cikin da yaketa fata akan kwanciyar hankalinmu”.         Baba ne ya fara jinjina kansa bayan kammalawar Mahma. Yace, “Kinyi bayani mai ƙyau hajiya, kuma nidai ta ɓangarena na yafe musu wlhy, dan koba komai abinda suka aikata ɗin ya zama tsanin nasara ga gudan jinina. Shiyyasa akace idan kaga UBANGIJI ya jarabceka da wani al'amari ka nutsu wajen kwatanta haƙuri dan zata iya yuwuwa wani tsanin zuwa ga nasara ne. Na yafe musu. ALLAH ya yafe mana baki ɗaya”.      A take aka shiga amsawa da amin duk cikin farin ciki. Maman sadiq da batace komaiba tun zamanta a wajen, tace, “Tabbas abubuwa da yawa sun faru an maimaita wasu anan amma wasu bazasu maimaituba. Ni shaidace daga wahalhalun cikin nan da yarinyarnan tasha wanda da da ƙarar kwana ranar haihuwarsa da ta bar duniya. Amma Alhmdllh, nagodama UBANGIJIN daya rayata, ya kuma kaimu ga ganin wannan ranar tunda gata a ɗakin mijinta cikin mutinci, kuma gaskiya ta buɗe a garemu ALLAH ya wanketa tun anan dunuya. Da yaso sai ya barmu muyita kallonta da laifin har ranar tashin alƙiyama. Nima na yafe muku domin ALLAH da wasu dalilai da Gwaggo ce silarsu (Hajiya iya) ALLAH ya yafe mana baki ɗaya ya kuma kiyaye na gaba”.       Itama godiya suka shiga mata da amsawa da amin. Kafin Hajiya iya ta fara magana.     “Tabbas dolene nima nace a yafemin ɗin bisa wani dalili, dan ƙila daban matsama Moddibo da ƙara aure ba da tunaninsu bai karkata ga hakan ba. Ni kuma ba komaine ya sani damuwarba sai ganin yanda matarsa bata ɗaukemi da darajaba. Hakama Hindatu. dan duk da Kabeer ya fita ƙarfin faɗa aji akan yarannan tana nuna masa iko a kansu, ko zancen auren yarinyarnan bamusan komai ba saida yazo gab. Koda yake duk ta wani tone-tone ya wuce, Moddibo ka yafemin kai da matarka dan zan iya saka kaina matsayin silar faruwar komai”.         “Bake bace sila Granny, dan koda kikace na ƙara aure baki tursasaniba, sannan tsarin da sukazo muku dashi ya sakaki wannan tunanin kema. Dan haka nikam kima daina neman gafarata bakimin komaiba why”. AK ne ya faɗa cikin dauriyar abinda yakeji game da jikinsa.        Mammah ta karɓe da faɗin, “Tabbar Inna ba laifinki bane, nice da wannan laifin, dan daban zurfafa da yawaba akan yaran nan da Zakiyya bataci galaba a kainaba har nakai ga bata goyon bayaba, dan ALLAH Adnan ka yafe min kaji, ajizancine na ɗan adam da son zuciya da tsoron rasaku tamkar yanda gangancina ya kaini ga rasa kabeer. Kishi ba hauka bane, kuma halas ne. Amma irin namu yayi muni da yawa dan muna zafafawa, da nayi haƙuri da hukuncinsa a wancan lokacin da duk haka bata faruba na tabbata. Dan ALLAH ku gafarceni baki ɗaya. Ɗiyata Zinneerah kema dan ALLAH ki yafemin kinji, wlhy bazan ɓoye mukuba tun randa na diro ƙasarnan naga yaron nan da kika haifa ƙaunarki data yaron ta kamani, duk abinda kukaga inayi borin kunyane kawai, amma har cikin raina son ɗanki dake kanki ya shigeni, koda nake cewa kar Adnan ya taɓaki ya sakeki inason na gwada yanda yake sonkine kawai ba wani abuba, kuma koda ya gama tsarani bawai ban fahimci tsaranin yayba. Sarai na san bazai iya sakinkiba wlhy, nima kuma bama zan yarda yay wannan taɓargazarba. Ki yafemin na ƙara roƙonki......”      Da sauri Zinneerah ta shiga girgiza mata kai, “Mammah dan ALLAH ki daina roƙona. Wlhy ni bakimin komaiba sai tarin alkairi kodan zama mahaifiya ga Yayanmu da kikayi. Kuma ni kallon uwa nake miki daman, har abada kuma zan cigaba da kallonki da wannan kimar da darajar. Dan haka ki ɗauka bakimin komaiba. Idanma kinmin na yafe miki wlhy”.      Tasowa Mammah tayi ta rungume zinneerah tana saka mata albarka. Kamar yanda zancen nata ya saka kowa dake falon murmushi, duk da ƙarancin shekarunta ALLAH ya bata baiwar shirya lafuza masu taushi ga nagaba da ita duk da kuwa ko ba'a faɗa da gaske an tauye mata haƙinta.        Farah da Zakiyya dai babu wanda ya roƙa gafarar Zinneerah, babu kuma wanda yace dasu ƙala akan hakan, kai kowama basu roƙaba sai kuka da sukeyi kawai. Dan haka mai martaba ya umarci AK da mijin Aunty Zakiyya da shima yana a wajen akan su basu saki. Babu wanda yace komai a falon, sai AK ne ya miƙa hannu ya amshi takarda da biro daga hanun Baba Wambai. Haka shima mijin aunty Zakiyya.      Gani kawai sukai Zinneerah ta tashi da sauri taje gaban AK ta durƙusa. Biron daya dasa akan takardar ta riƙe da fashe masa da kuka tana girgiza kai. Jajayen idanunsa ya ɗago yana kallonta. “Yayanmu dan ALLAH karka aikata, na roƙeka karka saketa. Kuma koba hakaba ka tausaya mata ba laifinta bane itama tursata akayi”. Tai saurin juyawa ga mai martaba dake mata kallon mamaki hakama sauran jama'ar falon. “Abbah dan girmana ALLAH kayi haƙuri ka janye wannan hukuncin naka koda kuwa sauran zasu tabbata. Gara komi za'a musu ai musu da igiyar aurensu kar'a rabasu da iyalansu na roƙeka Abbah. Dan ALLAH kodan maraicinsu ai musu afuwa, wlhy na tsani naga an saki mace inajin ciwo. Granny, Baffah, Mahma, Babana dan ALLAH kusa baki, Abba dan ALLAH ku bama Abbah haƙuri dasu Yayanmu karsu aikata”.         Yanda take kuka kamar ranta zai fita sai duk hankulansu suka tashi. Dan har suƙewa takeyi, ƙoƙarin son fisge pen ɗin AK yayi yana harararta ta sake damƙesa da fashe masa da kuka. “Yayanmu dan ALLAH, kodan ƙyautar little da ALLAH ya azurtaka da shi ka taimaka karkayi, idan ka saketa ALLAH nima bazan zauna da kai ba, zan ɗauke little na tafi inda bazaka sake ganinmuba wlhy”.         Kansa dake sara masa ya dafe, da wannan damar ta samu amshe takardar da biron, ta koma gaban Mai martaba ta gurfana tana cigaba da roƙonsa shi da su baba wambai da su waziri. Sosai ta basu tausayi ta kuma sake birge kowa. dan haka hajiya iya tai ɗan murmushi da duban mai martaba ɗin da shi kansa yakejin wani irin ƙaunar Zinneerah na shigarsa. Dan koda ƴaƴansa suka kasance masu laifi bazaiso mutuwar aurensuba ai. Sai dai kuma dolene ya yanke musu hukunci domin yin gargaɗi.         “Inaga a amsa kukan Zinneerah dan ALLAH, za'a iyama su Farah hukunci bawai sai an katsa igiyoyin aurensu ba, dan koda abinda duk ya faru aka barsu ya ishesu tunawa da ishara har ƙarshen rayuwa. Ayi haƙuri dan ALLAH”.      Ƙasa kawai mai martaba yayi da kansa dan yana ganin girman tsohuwar ainun, yanda yayi ɗin ne ya saka sauran ƴan falonma fara roƙonsa harma dasu AK kansu. Ganin sun masa taron dangi ya sashi jan numfashi da dafa kan Zinneerah ya shiga jera mata addu'oi masu daraja da ake jifan mutum mai daraja dasu. Sai da ya gama ana amsawa da amin sannan yace, “Shikenan zan janye maganar saki, amma kuma dolene sai sunje masarauta sunyi wancan zaman wlhy, sauran hukuncin kuma tsakanina da sune. ALLAH yay miki albarka ke kuma, daga yau kema kin zama cikin jerin ƴaƴana”.       Kabbara aka ɗauka a take. Kowa na nuna jin daɗinsa da farin ciki. Daga haka Hajiya iya tai musu nasiha. Hakama baba wambai yayi musu sannan shima maimartaba ya ɗaura tashi, daga ƙarshe aka rufe taro da addu'a saboda lokacin sallar zuhur yayi. ★★★      Ana idar da sallar azhar aka gabatar da ɗaurin auren Huzaifa da Adilah bisa alƙawarin Baffah, dan dama sun gama magana da mahaifin Huzaifa tun daren jiya, ya kumace ya bashi wuƙa da nama dan zaman Huzaifa hakan ya ishesa dama. Shima dan baya Nigeria ne da dashi za'ai komai a yau.    Koda suka dawo cikin gida tuni labari yaje kunen kowa. Zokaga murna wajen ango da amarya dan dama sun folama juna tuni. Daga haka sukai zaman cin abincin da matan Baffah suka shirya musu, suka kuma sake tattaunawa a tsakaninsu na maza. Kamar yanda anan cikin gida suma su Granny basu gaji da sake tattauna zantukanba a tsakaninsu. Mahma taja su Zakiyya gefe tana musu faɗa akan ƙin neman gafarar kowa da sukayi. Ta zazzagesu tas tai gaba ta barsu batare da kowa ya sani ba.       AK kam bayajin daɗin jikinsa, dauriya kawai yakeyi, hakama Zinneerah tana gadon Granny ƙudunsune dan zazzaɓi na neman dawo mata sabo ga ciwon kai na kukan data sha. Tanason zuwa ta gaisa da Baba ma ta kasa.    Zuwa la'asar su maimartaba suka fara tafiya bayan ya tasa su Farah dake faman kuka gaba ya wuce dasu masarauta, harda Baba dan yanason ya shiga har ƙauyen Danya yayma baba rakkiya ya kuma gana da dagacin garin danya ta silar baba. Hakan yama Zinneerah data fito suka gaisa da ƙyar daɗi, yau ga babanta ga maimartaba wata hikima sai UBANGIJI. Shima kansa AK hakan da maimartaba yayi ya masa daɗi sosai.     Bayan wucewarsu suma su mmn sadiq suka wuce, suma hajji Lanti tafiya sukai bayan sun sake gurfana neman gafara ga Zinneerah da AK dama su Hajiya iya baki ɗaya.         Da wannan damar Mammah ta samu suka sake zama ita da Mahma dasu Baffah ta ƙara neman gafararsu da sake tattauna duk abinda ya faru. AK dai bai zaunaba ɗakinsa ma ya shige yay kwanciyarsa dan bayajin daɗi, ya tabbatar yau jininsa yayi ƙololuwar hawa tabbas.      Hajiya iya ce ta hana su Mammah komawa gidan mijin Zakiyya. Tace Khalipha zaije ya ɗakko musu kayansu suyi zamansu anan har randa za'aje ga yarinyar datake rainon cikin a Morocco.     Zinneerah ma dai magani Granny ta bata tasha ta kwanta. ________________________       *_DANYA_*   Su baba sun iso danya da tawagar maimartaba. Inda tsabar ruɗewar da maigari yayi kai kace zai kife ƙasa. Maimartaba da kansa yau a ƙauyensa, bayan ko'a labari bai taɓa jin ko kusada wajen hakimi yaje ba sai dai ya aiko wakili idanma wani abune ya taso. Ai baima san ya gurfana yana kwasar gaisuwa ba. Hakama garin danya cikin ƙanƙanin lokaci labarin zuwan maimartaba da baba a tare ya shiga kunnen kowa harsu Inna da ke kwance rijib cikin ciwo. Dan tun zancen cikin Tinene dajin uwar sata da Karima ta kima na sarƙar zinarin wata hajiya da har yay silar Babawo yimata dukan mutuwa ya korota gida ta yanke jiki ta faɗi aketa fama har yanzun. Dan saki uku Babawo yayma Karima. Ga kuma aike daga kotu cewar Karima zata biya naira dubu ɗari huɗu na sarƙar mata bayan tara kuma da zaman kaso na wata shidda bayan ta yaye ɗiyarta. Ga zancen cikin Tinene ya baje ko ina na garin danya da kewaye har ƴammata sun dasa mata waƙar dandali. Matan aure kuwa da biyu suke zuwa barkar ƴan biyun amaryar baba dansu sake tabbatar da zancen ciki da halin da Inna ke ciki na samun ciwon ɓarin jiki a silar faɗuwar da tayi.        Ga ƴan uwan amaryar baba sun cika gida daga jiya zuwa yau dan ana haihuwa baba ya kirasu ya sanar musu. A safiyar jiya saiga kusan mutane shidda sunzo, sauran kuwa sai daren suna. Duk abinda ke faruwa kuwa akan idonsune sai mamaki sukeyi kamar almara ko hikayoyin marubuta.               Cikin ƙanƙanin lokaci ƙofar gidan maigari ya cika taf da jama'ar gari saboda kiranye da aka saka sanƙira yayi musu. Ciki kuwa har dasu Sa'a a ƴan kallon zuwa ganin maimartaba. Sai da guri ya nutsa sannan maimartaba ya fito. A take waje ya ruɗe yau gasu ga maimartaba. Farin ciki duk ya bayyana a fuskokinsu kamar shima yanda yaji daɗin yanda suka amshesa duk da basu da wani cigaban kirki a garin, zaima iya cewa baisan da zamansuba saita wannan silar. Sai yaji zuciyarsa ta ƙara rauni da karaya akan nauyin al'umma dake kansa.           Bayan Matawalle ya isar da saƙon gaisuwar sarki a garesu ya gabatar da hajji lanti a gabansu tai bayani akan silar ɗaukar Zinneerah zuwa birnin katsina. Itama Hajiya Haule tayi bayani kamar yanda tayi a kano. Kafin Zakiyya ma da takejin tamjar ranta zai fashe tai nata bayanin akan gaskiyar dasama Zinneerah ciki da sukai ba ta hanyar iskanci ta samosa ba.         Take gurin ya ƙara ruɗewa da al'ajab da mamaki. Ɗunbin tausayi da nadamar cin kashin da suka dinga ma yarinya ya ringa dawo musu a rai harda masu kuka. Kafin wani dogon lokaci labari ya ƙara kaiwa ga mata dake cikin gida da jama'ar sauran ƙauyukan gefensu da duk sukasan da labarin cikin na Zinneerah. Abinka kuma da ƙananun gari babu wanda ya manta musamman daya kasance ba'a jima da zuwa akai bikin Zinneerah ɗin ba. Bakajin komai sai ALLAH wadarai ga Inna asabe dasu Zakiyya. Dan su maimartaba kan sun tafi sunbar abin faɗa ga mutane. Musamman daya kasance yanzu ALLAH ya bama Zinneerah cigaban rayuwa. Ga kuma samakon nan a jikin Tinene da ita kanta Innar dake kwance rijif ita ba gawaba ba kuma rayayya ba.      Ita kanta da labarin yaje mata sai gata tana hawaye zuciyarta na ƙara hauhawar zafi. Daga ƙarshe jikintane ya ruɗe sai da aka kwasheta zuwa asibitin cikin kusada..............✍        *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* _________________________ *Page 65* ............Ganin dare ya fara yasa Hajiya Iya tada Zinneerah, shima AK taje ta tasoshi akan suzo su wuce gida haka nan. Badan Zinneerah taso hakanba ta miƙe, shima AK ɗin ya fito yana faman dafe kai. Kowa bai kallaba a falon yay ficewarsa duk da yasan akwai su Mammah zaune. A waje ya samu su Haneef da little a hannu, aiko ya maƙale masa. Amsarsa yay suka shiga motar da Khalipha zai jasu dan shi bazai iya tuƙinba. Zinneerah ma da Hajiya iya ta rakota dasu Meenal ta shiga baya.                      Koda suka iso Khalipha ne ya buɗe musu ƙofar falon, daga haka ya juya yana musu sai da safe. AK ya ɗauka Little suka wuce sashensa batare daya kula Zinneerah ba. Itama ɗin ba kulashi taiba ta shige nata sashen. (Faɗan masoya hutu😂😝).         Ko wanka kasa zamanyi Zinneerah tayi, tana shiga gado ta faɗa tai kwanciyarta dan barcin tafi bukata. Musamman daya kasance maganin da Granny ta bata yana saka barci.     Shima a ɓangaren AK kwantar da little dayay barci tun a mota yayi, ya samu yaɗan watsa ruwan yasha tea dan yanajin yunwa, duk yinin yau ya gagara sakama cikinsa abinci, basket ɗin abincin da suka bari a gidan tunna safe ya ɗauka ya bubbuɗe. jin babu abinda abincin yayi ya sashi ɗauka ya fita dashi ya kaima maigadi yace ya badashi kar ai asararsa. Daga haka ya dawo shima yay kwanciyarsa bayan yaɗan leƙa Zinneerah yaga harma ta kwanta. *_WASHE GARI_*       Da safe sun tashi Alhmdllh, musamman Zinneerah batajin ciwon komai a jikinta. garama AK dai jikin nasa sam baya masa daɗi. dan ko sallar asuba a gida yayi abunsa ya koma ya kwanta. Sai kusan ƙarfe bakwai da little ya farka yana damunsa ya miƙe da ƙyar ya ɗakkosa gaba ɗaya yayo sashen Zinneerah da shi. A lokacin tana cikin saka turaren wuta dan ta gama gyaran ko ina.       Sanye take cikin wando da riga na kayan barci farare tas, yanda suke da santsi yasa suka manne mata a jiki sosai, gashi ko bra babu a jikinta. Kallo ɗaya yay mata ya kauda idanunsa, itama cike dajin kunyar yanda ya sameta dan batai zaton shigowarsaba takai ƙasa tana gaidashi cikin girmamawa batare da ta yarda sun haɗa ido ba.      Amsa mata yay a daƙile yana dire little kusa da ita dan haushinta yakeji, har itace zata buɗe baki tace zata barsa saboda wasu. Wannan magana tai masa ciwo, tanama cikin masa ciwon. Juyawarsa yay ya fice ta bishi da kallo zuciyarta na raya mata yana fushine saboda matarsa da aka wuce da ita. Haka kawai sai taji ranta ya sosu. Ta ɗan taɓe baki tana miƙewa da ɗaukar little ɗin dake mata ƙorafin shi tea zaisha.       “Dalla yima mutane shiru abinda ka iya kenan sai cin tsiya kamar ubanka”.         Kuka ya sanya mata saboda dungure kansa da tayi. “Malam yimin shiru ALLAH kona huce a kanka”. Daga haka ta ɗaukesa suka nufi ciki dan ta masa wanka sannan tazo tanadar musu abinda zasuci dan tacema Granny abar kawo musu abinci zata fara girki.        Wanka tayi masa itama tayi sannan, tura little tayi wajen AK ya amso kayansa, ita kuma tai ƙoƙarin shiryawa a gurguje ta fito. Sai da ta haɗa ma little tea ta fara nema musu abinda zasuci yanda bazata takura ba. Harta gama bataji ɗuriyar little mai kukan yunwaba, hakan bai dametaba dan tasan wani abun ya samu acan.       Kamarko ta sani dan AK na gama saka masa kaya tea ɗin ya haɗa masa da ruwan dispencer, ya haɗa masa da biscuits. Shima wankan yayi dan yanason yaje asibiti kar abin yay masa nisa. Koda ya fito wankan rashin ƙarfin jikin ya sakashi sake komawa ya kwanta har takai barcin ya sake figarsa.        Lokacin da Zinneerah ta shigo falon da kayan abincin little kawai ta samu a falon ya barbaza filos ɗin kujera yayma falon kaca-kaca. “ALLAH ya shiryeka” kawai ta iya cewa ta ajiye abincin a dining. Kayan shara ta ɗakko ta fara a tunaninta AK yana wani abunne a ciki. Waje ɗaya ta saka little zama harta kammala kimtsa falon tasa turare. Ganin har lokacin shiru babu motsin dadynsa ga goma harta gota ya sata nufar bedroom ɗin a ɗarare danta sanar masa ga abinci. Kusan sau uku tai sallama babu amsa. hakan ya sata tura ƙofar ta ɗan leƙa kanta a tunaninta koma dai baya gidan ne.        Zaune ta hangosa a bakin gado dan dai-dai ya tashi kenan saboda sallamarta. Hannunsa dafe da kansa dake masa tsananin ciwo. Jitai tamkar ta juya da baya dan da ga shi sai boxer ne, amma ganin yanda ya dafe kansa yasata tunanin ba lafiya ba. tunda jiya dai ga a yanda suka dawo su duka, kuma tanaji sanda yake sanarma Khalipha kansa na masa ciwo a jiyan.         Kanta a ƙasa ta ƙaraso cikin ɗakin, sai da tazo kusa da shi sannan ta rissina tana gaishesa batare data sake yarda ta kallesa ba. A yanda ya amsa ɗin kuma sai tsoro ya sake kamata, cikin damuwa tace, “Yayanmu baka da lafiya ne?”.       Shiru kamar bazai amsaba har kusan mintuna biyu sannan ya ɗago idanunsa da sukai jajur yana dubanta. Kwalliyar tata tayi masa ƙyau, dan haka yaɗan lumshe ido ya sake buɗewa a kanta da cewa, “Kaina ke ciwo. Haɗamin ruwan wanka inason naje asibiti”.            Sosai damuwa ta bayyana ƙarara a fuskarta. ta shiga jera masa sannu kamar zatai kuka. Shi dai kallonta kawai yake dan duk da yana cikin halin ciwo yanda takeyi ɗin tada masa tsigar jiki take. Ga mayatattun turarurrukan ta da ƙamshinsu ke ɗaga masa hankali zuwa ga buƙatarta.  Ya ɗan cije lips ɗinsa yana komawa da baya a saman gadon ya ɗan kwanta kafin ta kammala haɗa ruwan.      Sai da ta tsaftace masa toilet ɗin duk da ba wani uban datti yay ba sannan ta haɗa ruwan, ta fito hanunta da tissue data warwaro daga can tana gogewa. Da ƙyar ya iya yunƙurawa ya tashi zuwa bayin.        Ta ɗan sauke numfashi da fara ƙoƙarin gyara masa gadon, daga haka ta zarce da tsaftace ɗakin gaba ɗaya. Ɗan jimawa da yake a wanka yasa harta kammala kafin ya fito, tana fesa fresheners take jiyo little na ƙwala mata kira daga falo. “Aunty! Aunty!!”.        “Oh ALLAH! Na'am”. Ta faɗa tana ajiye gwangwanin freshener ɗin. hakan kuma sai yay dai-dai da fitowar AK daga bayi. Bata yarda ta dubesaba, sai sake amsama little kiran da yake mata tayi. Ta ɗaga ƙafa zata nufi hanyar fita taji an ruƙo mata hannu. cak ta tsaya dan tasan dai shine.         “Idan kin tafi wazai shiryani”. Ya faɗa a hankali yana jawota ta juyo tana fuskantarsa. Kasa kallonsa tai dan dagashi sai guntun towel. Ganin yanda taketa sinne kai ya ɗago fuskar tata da ƙoƙarin saka idanunsa cikin nata. “Nazama surukinki ne?”.        “A'a” ta faɗa a hankali tana ɗan murmushi.         “Hum” ya faɗa da kama hannunta yajata suka ƙarasa gaban mirror ɗin. Duk yanda taso zamewa dole tabi umarnin sa. dan dolenta ta shafa masa mai da kanta, ta kuma ɗakko masa kayan da zaisa wanda bazai takura ba. A gaɓar shiryawane dai kam ta kasa duk yanda yaso dole ya barta ya shirya da kansa.      Falo suka fito a tare suka sami little, baiyi tunanin ita tai girkinba, sai dai ya masa daɗi, kaɗan yaci yau kam dan da gaske bayajin daɗi, yana gamawa ya koma falo ya kwanta cikin kujera saboda jiri, wayarsa yace ta ɗakko tai kiran Doctor Mahmud yazo ya dubashi, dan bama zai iya driving ba. Cikin damuwa ta ɗakko ta lalubo masa no ɗin Dr Mahmud ɗin, yana ɗagawa ta miƙa masa wayar yay magana da shi.        Cikin ƙanƙanin lokaci sai ga Doctor Mahmud da Khalipha tare. Bayan ta gaisa dasu ta bar musu sashen saboda kallon da AK ke mata na gargaɗi dan ko mayafi babu a jikinta yau.         Koda ta koma a can tai zaman karyawa itama. Bata sake leƙo sashenba sai da little yazo ya kirata. Hijjab ta zunbula dan hanyar lafiya a bita da shekara. Khalipha kawai ta samu tare da shi sai Huzaifa da batasan da zuwansaba. Ta gaisa da Huzaifa daketa tsokanarta da amarya amarya. Ita dai murmushi ne nata kawai babu bakin ramawa.     Ta ɗan dubi AK da akema ƙarin ruwa idanunsa a lumshe. Sannu tai masa dan ta fahimci idonsa biyune, saboda riƙe yake da hannun little dake tsaye gaf da fuskarsa yana masa maganar da batasan kota micece ba. Khalipha ne ya sanar mata abinda zatayi, dan haka ta juya ta sake fita ta barsu.            ★*********★ Abu kamar wasa sai ga AK yasha zazzaɓi kwana biyu, dan sai da takai har Baffah da Uncle Ahmad sai da sukazo dubashi, hakama su Mammah dake shirin komawa gobe idan ALLAH ya kaimu sunzo sun dubata da sake neman gafarar Zinneerah. Yanda Mammah taketa tattalin Little sai ta baka tausayi, gashi shi saima wani ƙiwan wulaƙanci yaketa faman mata.      Shima AK ɗin sun ƙara masa nasiha da nuna masa muhimmancin yarda da ƙaddara. Mammah ta sake neman gafararsa duk da ta fahimci fushi yake da ita. Nuna mata yay shifa komai ya wuce, amma ita tasan bai wuce ba tunda ya kasa sakin jiki da kowa sai ɗansa da matarsa.         Yau Alhmdllh ya tashi jikin nasa da sauƙi sosai, dan har fita yay zuwa gidansu shi da little. Bayan sallar la'asar Zinneerah na falonta na biyu zaune tana cire ƙumba ya shigo da sallama. Gaidashi tai da masa sannu da dawowa. Ya amsa mata yana kaiwa zaune. Ita kuma ta miƙe dan kawo masa ruwa. Amma sai jitai ya ruƙota. Duk yanda taso zamewa ya hanata damar hakan. Cikin wani irin kasalalliyar murya yake mata magana a kunne. “Wace irin amaryace wannan mai rowan tsiya nikam?”.         Ɗan dubansa tai dan bata fahimci ina ya dosaba, ya ɗage giransa ɗaya yana kasheta da kallonsa mai sakata nutsuwa. Itama dai yau tayi dauriya da jarumtar kallon nasa cikin idon, da wannan damar yay amfani wajen ɗora lips ɗinsa kan tausasan nata. Sukaja numfashi a tare da lumshe idanunsu. Sai gata luff ta nutsu tana amsa saƙonsa. Sai da labarin ya fara canja salo kuma ta nema raina kanta. Ko saurarenta baiyiba ya ɗauketa cak yay cikin bedroom ɗinta da ita. Ganinfa irin na ranar yake son maimaitawa tuni ta fara tsuma da neman roƙomsa shikam baima jinta ya antaya duniyar kodumo.       Duk yanda taso daurewa yau ma dai kasawa tai, sai da ta kaita da masa kuka, dan wannan yayan nasu bana wasan yara bane, baisan sauƙi ko sassauci ba har sai ya kai boader.      Sai da ya ga ya samu kansa ya koma tsokanarta da suna ragguwa. Ita ko ta dinga tura baki har a wajen wanka da ya taimaka mata ta kuma gasa jikinta yanda zataji daɗi. Suna fitowa ya gudu sashensa dan kiran sallar magrib ake tayi.       Bata sake ganin ƙeyarsa ba sai bayan sallar isha'i, ta fito domin nema musu abinci shi kuma ya shigo hannunsa ɗauke da leda alamar ya biya ta ɗakinsa kafin yazo nan. Zama yay da kiran sunanta, dan haka ta nufosa zata zauna ƙasa ya nuna mata gefensa. Sai da takai zaune sannan ya miƙa mata ledar. Amsa tai tai godiya duk da batasan minene a cikiba, tana buɗewa taci karo da waya mai ƙyau. Ai tuni jin daɗi yasa ta manta da Yayansu ne fa. Ta miƙe ta ɗane masa jiki tana murna.            Murmushi yalwace da fuskarsa ya karɓe abinsa yana cusa kansa a wuyanta. “Yanzu kin ɗaneni, da an taɓaki kuma ki hau yima mutane raki”.      Kanta ta cusa a ƙirjinsa tana dariya da faɗin “ALLAH akwai wuya Yayanmu, kai dan baka sani bane”.      Dariya ta basa, amma sai baiyiba ya cigaba da murmushinsa yana cusa hannunsa cikin gashinta, “Ni kuma gashi ba wasa zan tsayaba ƙannen little nakeso da wuri, dan naga shikam ba barmana zasuyiba haka zai ringa yawo tsakanin danya, gidan Abba, gidan Baffah, london. Kinga saiki sama mana namu muma”.       Ƙwaɓe fuska tai cikin marairaicewa. “Yayanmu ba yanzuba akwai wahala wlhy”.      Kansa ya ɗan girgiza mata da sumbatar lips ɗinta. “Haba my Neerat ai ke jarumace tunda kika haifo Abdul-Mutallab tun kinada shekaru sha huɗu, yanzu kam ko ƴan huɗu ne zaki iya ai”.        “Sai dai in zaka tayani”. Ta faɗa tana ɓoye fuskarta a jikinsa. Sosai yanzu kam ya ƙyalƙyale da dariya. “Mizai hana na tayaki nikam Mrs Shira, ai tare zamuyi rainon cikin muyi naƙuda abunmu mukuma rainesa idan ya fito”.     Dariya sosai Zinneerah keyi itama mamaki fal ranta na Yayansu. Ashe haka yake da sauƙin kai da sakin jiki, amma yayta musu mazurai a gida.         Washe gari suna kammala breakfast yabar gidan zuwa jigawa. Da wannan damar ta samu zaman gyara gidan sannan tai zaman kiran ƴan uwa da abokan arziƙi data samu nombobin wasu a wajensa. Wanda bata da shi mmn sadiq ta tura mata da su hajiya iya. Ƴan danya ne ƙarshen kira. Inda tai farin ciki matuƙa dajin muryar babanta.       A wayar tasune yake sanar mata shagalin suna da za'ai gobe idan ALLAH ya kaimu. tare da abinda ke faruwa akan Karima na zancen sarƙa data sata acan Kaduna aka kaita kotu, a yanzu kuma babu sarƙar babu kuɗin ga Babawo ya saketa saki har uku. Ya ɗora da faɗa mata halin da Inna take a ciki da zancen cikin Tinene. Harma da wanketan da mai martaba yaje yayi har danya bayan sun bar kano tare.        Zinneerah tayi kukan daɗi tayi na damuwa tayi na baƙin ciki a wannan yinin. dan har AK ya dawo daga jigawa a jigace ya isketa. A kallo ɗaya ya fahimci damuwar dake tare da ita. Baice mata komaiba harta taimaka masa yay wanka yay zaman cin abinci, sai da ya kammala yaje sallar magrib da isha'i ya dawo sunyi zaman kallon labaran dare ya tambayeta. Da farko tata noƙewa akan ƙin faɗa ya nuna ɓacin ransa.        Kuka ta fashe masa da shi ta shiga basa labarin abinda duk ya faru. Shima yaji daɗin abinda maimartaba yayi. yakuma taya baba murnar samun ƙaruwa. Tare da jajanta abinda ke faruwa ga Inna da ƴaƴanta. Sannan ya ɗaura da lallashin matarsa ta hanyar daya dace.      Kwana biyu dayin wannan maganar Zinneerah ta kira taima Baba barka da tashin baƙi dajin yaya jikin Inna yake sanar mata ai jiya AK ya aika Khalipha danya. Yanzu haka Inna na asibitin katsina yau da safe aka wuce da ita. Ya kuma biya kuɗin sarƙar Karima ɗin.      Wannan zance ya saka Zinneerah matuƙar farin ciki dajin ƙaunar mijinta kuma Yayanta. Yana shigowa gidan tai masa ƙyaƙyƙyawar tarbar da bai taɓa samu daga garetaba. Dan yau fidda kunya tai abinta ta manne bakinta da nashi ta shiga masa salo akan karatun da yay mata. Wannan al'amari ya gigita AK musamman daya kasance ta cuɗe jikinta da turarukan dake neman zauta masa tunani. Yako zage wajen bata haɗin kai har sai da ta koma masa raki.      Sai da ya kai boader ya koma mata dariya da tambayarta wai minene sirrin?. Baki ta dinga tura masa tana zuba masa shagwaɓa. Sai da suka tsaftace jikinsu ta zaman masa godiya. Nuna mata yay shi baima san anyi hakaba. Maybe Khalipha ne yayi kawai.         Tasan sarai yayi hakane dan ya goce, bawai dan abinda ya faɗa gaskiya bane.       Haka rayuwar waɗanan ma'aurata ta cigaba da tafiya cikin aminci da kwanciyar hankali, duk da dai wataran saɓani kan gifta musu har rai ya ɓaci. Musamman daya zamto halinsu na kamanceceniya da juna wajen miskilancun tsiya. Little kan leƙosu kwana ɗaya biyu ya tafi, wani lokacin yana gidansu Granny wani lokacin yana gidansu mmn sadiq. Khalipha kuma kanje Danya shi da Dr Mahmud daya fola Sa'a tun a wajen biki batare da sanin su AK ba.          Sunata shirye-shiryen bikin ƴammatan gidan daketa gabatowa. Adilah ma na Nigeria bata komaba su Mammah ne kawai suka tafi.       Bukatar komawa ganin likitan Granny yasa AK shirya musu tafiya harda little. Dan yanason zuwa shima yaɗanyi wasu abubuwa acan kafin su dawo wajen biki kuma.       Zinneerah batasan da wannan shiri nasaba sai ana saura kwana biyu ya ɗauketa suka nufi Danya shi da ita da little. Wani irin farin cikine ya baibayeta ganin inda suka nufa. Ta kwanto jikin hannunsa da faɗin, “Oh oh thanks you so much Yayanmu”.      Murmushi ya ɗanyi yana sake maida hankalinsa ga tuƙi. Yace, “Yayansu dai, dan kekam kin gama gane Yaya ciki dabai yarinya”.      Kunyace ta kamata, ta maida kanta gefe tana ƙyalƙyala dariya. Little dake baya yanata harkokinsa da game da Khalipha ya saya masa shima jin dariyarta ya sashi ƙyalƙyalewa da tasa. Dariya suka shigayi saboda yanda yay dariyar abin dariya.       Tarbar data bama Zinneerah ɗunbin mamaki suka samu a garin Danya, dan bama ƴan gidansu ba hatta da maƙwafta shigowa suketayi. Itako cikin mutunci taketa gaida kowa. Suka dinga daukar little zukatansu fal mamakin yanda aka samar dashi. Tausayin Tinene ya kamata saboda itama ta ɗanɗana rainon cikin nan taji yanda yake musamman a irin wannan yanayin da mutane ke tsanarka da ƙinjin tausayinka. Dan Tinene dukta rame ta lalace cikin na bata wahala. Yayinda ta ɗauka ƴan biyun amaryar babansu kuwa sai daɗi ya kanainayeta ta dinga samusu albarka. Cikin tsokana amaryar Baba ke faɗin. “Ai saura ke ɗiyata, dan wannan ƙyawun da kika ƙara ai in kaji gangami da labari”.         “Kai Mama ni ALLAH bani da komai, kawai dai idanunki ne”.        Yaya Gajeje dake bama little abinci tace, “Haba Zinni ai duk wanda ya dubeki yasan kinada ciki, fatanmu dai ALLAH ya raba lafiya muje musha shagalin suna kamar na aure”.       Cikin shagwaɓa tace, “Kai Yaya Gajeje nifa banda komai”. Dariya suka sanya mata harda Karima da a yanzu take jin wani son Zinneerah ɗin, dan badan mijintaba lallai da yanzu tana birsin. Yanzu ɗinma a zuwansun nan sai da taje tai masa godiya ta musamman harda kukanta.       AK yace karta damu, shi komai zai iya musu akan Zinneerah. Fatansa dai ALLAH ya kiyaye na gaba kuma. Baba ma ya masa godiya sosai. Sukaje kuma har gidan maigari ya gaishesa tare da su Baba Sabi'u.        A firarta da Yaya Sa'a takejin batunta da Dr Mahmud. Taji daɗi tayi farin ciki. ta kuma taya Yaya Sa'a murna duk da Dr Mahmud nada mata da yara biyu. To amma tasan shi mutumin kirkine, dan haka ta taya ƴar uwarta farin ciki da wannan abun arziƙi.      Inna na asibiti har yanzu tare da wata kanwarta dake jinyarta. Suma sai lokaci-lokaci suke zuwa su dubata su dawo. Zinneerah taso lallaɓa AK suje ta dubata itama amma tanajin tsoro, dan dataje kai masa abinci take roƙonsa ko zasu ƙarasa katsina su gaida Aunty Farah wani shegen harara daya kaɗa hanjin cikinta yay mata. Dole ta fito sim-sim tana dana sanin yin maganar. Itako tayine saboda sanin har yanzu Yayan nasu na ƙaunar matarsa. Yana dannewane kawai saboda fushin laifin da suka aikata masa. Amma Sometimes idan suna fira zakaji yakan sakkota koyin misali da wani abunta yace Farah kaza Farah kaza. Tanajin zafin hakan sabida kishi, amma bata ganin laifinsa. dan tasan soyayyar da yake nunawa ga aunty Farah itama ko aure ya ƙara zai iya nunawa gareta bazai wulakantataba. Dan tunda suke bai taɓa kushe Farah a gabantaba, bai kuma taɓa yimata wani zancen halinta mara ƙyau ba indai kaji zancen Farah a bakinsa to alkairintane.          Yini guda sukai a Danya, dan basu tahoba sai gabannin magriba. Lokacin da suka shigo garin kano ana sallar isha'i.     Washe gari kuwa nan ma da kansa ya kaita gidan Mmn Sadiq danta yini. Sunyi farin cikin ganin juna itada mamanta da yan uwanta matuƙa. Duk da kuwa a yanzu tana waya dasu a koda yaushe. Hakama mmn halima da Abbah tare da ƴan biyun mmn Halima da suka fara zama ƴan mata. Dan jira kawai suke a kauda Sakina da miji ya gagara samuwa suma su ƙara zabgewa.     Nanma yini tai zur dan sai dare ya aika Khalipha ya ɗakkota saboda shi ya tafi wata sabgar shi da Dr Mahmud.      A ranar da daddare yake sanar mata gobe idan ALLAH ya kaimu zasu wuce london su da Granny. Bazasu dawoba sai bikin su Safiyya daya gabato gab danma ɗagashi da akayi saboda na Adilah daya shiga ai da wannan watanne za'ayisa.        Jin harda Granny za'a tafi yasata nuna jin daɗinta sosai. dan ita dai duk da Mammah ta nuna ƙaunarta daga baya tana shakkar matar har cikin ranta. Sai dai taso ace harda su Bahijja ma a wannan karon amma yaya zatai tunda aure take yanzu. Ga ssce exams ɗinsu zasu fara batasan yaya yake nufiba, amma dai bazatai maganaba tunda tasan ya fita sanin muhimmancin karatun ai. Suma kuma su Bahijjan zaman yaran Uncle Ahmad a gidan yanzu ya ɗebe musu kewarta sosai. Danfa Granny ta kafa ta tsare ta hanashi komawa. Dan kuwa dai bai shirya kara aure ba. Matarsa taci kuka harta gode ALLAH ta haƙura. Dan harma yaje ya tattaro musu duk abubuwansu masu muhimmanci da yoma yaransa transfer ɗin makaranta zuwa Nigeria. Manyan ne kawai dake jami'a zasu koma su ƙarasa.............✍ *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_* *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* _______________________ *Page 66* ............Washe gari da yammaci jirginsu ya ɗaga zuwa Birtaniya. Inda al'amari yaso ƙwaɓema Zinneerah. Dan tamkar jira jirginsu na ɗagawa amai ya ringa taso mata. Ganin yanda taketa rintse ido da yamutse fuska yasa AK taɓata. Ido ta buɗe da ƙyar tana dubansa. “Lafiya dai?”. Ya tambaya cikin kulawa.       “Yayanmu amai nakeji wlhy”. Ta faɗa da ƙyar tana danne bakinta da hannu. Cikin mamaki yace, “Amai kuma?”. Kanta ta ɗaga masa tana miƙewa da sauri domin zuwa toilet. Dole shima ya miƙe yabi bayanta, Hajiya Iya na tambayarsu ko lafiya ma basu jitaba.        Sosai ta jigatu wajen yin aman, sai da ya taimaka matama sannan suka fito. Ganin yanda duk ta jigata hajiya iya ta shiga salati. “Inno baki da lafiyane dama aka ƙirƙiri wannan tafiyar dake haka?”.        Kanta taɗan jujjuya mata da ƙyar, murya a sanyaye tace, “A'a Granny lafiyata lau, kawai yanzu ne dai na dinga jin aman”.         Khalipha dake mata kallon tsaf ya ɗauke kansa yana murmushi da gyarama little dake jikinsa yana barci zama. Hajiya iyama kallon tsaf takema Zinneerah ɗin har wasu mintuna. Kafin tai murmushi da faɗin, “To ALLAH ya rabaku lafiya, ya inganta kuma”.        “Amin” Khalipha ya amsa mata. AK da duk bai fahimcesu ba ya kalli hajiya iyan sai dai baice komaiba. Harara ta zuba masa tana mita. “Ka wani tsareni da ido minaci ban bakaba to?”.       Ƙara tsuke fuskarsa yay yana ɗauke kai gefe batare daya tanka mataba. Sai dai har cikin ransa waswasin maganar tata yakeyi. Ya kwantar da Zinneerah jikin kafaɗarsa yana gyara mata mayafinta. Cikin ƙanƙanin lokaci sai ga barci yay awan gaba da ita. Itace bata farkaba sai gab da zasu sauka.      Abin mamaki sai ga Mammah tazo da kanta ɗaukarsu. Cikin girmamawa kuma ta gaida Hajiya iya tare da rungume Zinneerah da duk alamun rashin lafiya ya bayyana gareta. Khalipha ma cike da kulawa ta amsa masa gaisuwarsa tana dungure kan little da yaƙi zuwa wajenta ya maƙale Khalipha ɗin.         Har cikin rai AK yaji daɗin canjawar mahaifiyar tasa. Sai dai bai nunaba ko'a fuska. Tunda ya gaishetama sai ya ɗauke kansa ya maida ga waya.         Sun iso gidansu da suka samu ƙal an gyara, ya kuma san aikin Mammah ne da Mahma. Nanma yaji daɗi. Hajiya iya ɗakin data zauna wancan karon ta sauka. Khalipha ɗakinsa. AK da Zinneerah ɗakinsa. Dan ɗakin Farah ma a rufe yake bai kuma nuna alamun son a buɗeba.        Wanka ya taimakawa Zinneerah tayi ta kwanta dan zazzaɓi ne rijif a jikinta. Ga yunwa na cinta dan bataci komai a jirgi ba. Hakan yasa AK tsareta taci abincin da Mammah ɗin ta kawo musu. Da ƙyar tai lauma uku, sai gata hanyar toilet da gudu. Duk binta sukai da kallon tausayi, AK idonsa ya kaɗa yay jajur, dan shi ya rasa wannan amai na minene?. Bayan ya taimaka mata ta fito ya kwantar da ita sannan yazo falo yana cema Khalipha yazo suje asibiti dan shi wannan amai ya rasa na miye ko wani abu taci ya bata mata ciki.          Dariya ta kusa suɓucema Khalipha akan wannan zance, a ranaa yace, (Waken daka batane Yayanmu ya bayyana kansa) a fili kam sai yace, “Uhm ai Yayanmu bara dai na duba mata wani magani kozai taimaketa, amma wannan amai ai na farin cikine bana ɓacin ciki ba”.        Fuska ya ɗaure tamau yana hararsa, “Shi aman har abin sone?”.        Mammah da itama dariya ke cinta tace, “Barma yarona mazurai malam, ai gaskiya ya faɗa wannan amai abin so ne, dan kuwa dai na rabone sai dai muyi fatan ALLAH ya sauketa kafiya”.        Karon farko AK ya ƙwalalo idanu waje yana kallon Hajiya Iya da Mammah dake dariya, ya maida ga Khalipha daketa ƙoƙarin ɓoye tashi. “Nikam ku fiddani a duhu, kuna nufin ciki ne da ita komi?”.        “Tabbas hakane Yayanmu, Congratulations”.     Kasa motsi AK yayi dan alja'ab ko ruɗani zai ce. Sai gani kawai sukai yakai gwiyawunsa ƙasa yay sujuda ga UBANGIJIN talikai mai badawa ga wanda yaso a kuma lokacin da yaso, kafin ya koma gaban Hajiya iya ya rungumeta, ya saketa itama Mammah ya rungumeta, kafin ya koma kan Khalipha.      Yana sakinsa ɗakinsa ya nufa cikin sassarfa, cikin barci Zinneerah taji an mata wata lafiyayyar runguma ana sakar mata kissis tako ina a jikinta. Ta buɗe idanu da ƙyar tana kallonsa. Jin godiya da kirarin da yake jerama UBANGIJI tare da addu'ar ALLAH ya sauketa lafiya ya sata fahimtar lallai zancem su Yaya gajeje ya tabbata cikine da ita, hawayene suka silalo mata na jin daɗi da tausayin kai. Tayi farin ciki dan tasan koba komai mutane da yawa zasuyi farin ciki ta silar wannan cikin, sannan ta tausayama kanta dan tasan da wahala karatunta bai salwantaba.        Aman daya taso matane ya sakata samu AK ya saketa ta nufi toilet da gudu. Wani irin tausayinta da ƙaunartane ya kamashi ya dafe kansa yana mai jin kamar inama ace zai iya rage mata wani yanki na raɗaɗin da takeji.              Khalipha ne ya fita dole ya samoma Zinneerah maganin dazai taimaketa ta ɗan huta da aman duk da dai yasan baizama lallai ta daina duka ba. Cikin amincin ALLAH kuwa tana sha sai barci. Daga haka suka cigaba da farin cikinsu, yayinda labari har ya kaima ƴan Nigeria.         Zo kaga murna wajensu Meenal da dariyar mugunta wai su Zinneerah an cika zalama, daga shiga harta ƙumso. Sunji inama zasu iya samun wayarta su baɗaɗeta da sheri.     Mammah ma cikin farin ciki ta komawa Mahma da wannan daddaɗan labari. Sosai itama tai farin ciki da shiga jerama Zinneerah addu'ar lafiya mai inganci. ta sake ɗorawa da yima Mammah nasiha kamar yanda takeyi kullum yanzu tunda suka dawo. Hakkanne ma ya ƙara sakama Mammah nutsuwar zuciya da sake duƙufa neman gafarar ALLAH.              Sabon tattali Zinneerah ta fara gani a london hannun AK da mahaifiyarsa da Mahma. Hajiya iyama duk da tana ƙarƙashin kulawar likita tana binta da addu'a da dabarunsu na tsoffi. Dama little tun kwana biyu da zuwansu ya koma gidansu Mammah ɗan gata. Hakan yasa AK samun damar baje sharafin soyayyarsa a cikin gidannan. Dan Khalipha na musu kawaici da basu fili yaje yay zamansa wajen Hajiya iya susha hira.      Ita kanta Zinneerah ɗin shegen ƙwaɗayin da cikin yazo mata da shi yasata sake nanuƙema AK, dan babu abinda tafi ƙauna daso kamar ƙamshin turarensa da kasancewa dashi. Randa tai waya dasu Bahijja tasha Sheri, hakama su Sa'a nata tsokanarta.     Ita dai babu baki dan ya mutu murus. Suna cikin sati na uku da zuwa jikinta yay ɗan mata ƙarfi irin na mai ciki, yau lafiya gobe jangal. Gyaran ɗakin nasa ko nace nasu tai ƙoƙarin yi, tanayi tana ɗan hutawa harta ga yay mata ƙal. Tana cikin gyaran ne sai ga idonta takai kan tsohuwar wayarta da aka sace a ɗakin hajiya iya. Mamaki yasata jujjuya wayar tana kallo dason tunani yanda akai tazo London, london ɗinma ɗakin Yayansu.        “Malama miya kai idonki nan?”. Taji an faɗa a bayanta cikin dakakkiyar murya. Tasan Yayansu ne, dan haka ta juya fuska a ƙwaɓe tana kallonsa da cigaba da juya wayar a hannunta. Takowa ya ƙarasa yi cikin ɗakin yasa hannu ya amshe wayar fuska a tamke. Ya ɗaga ƙafa zai juya ta riƙo hannunsa da faɗin, “Wai Yayanmu dama kaine ka sacemin waya?”.      Harga ALLAH yanda tai maganarne yay matuƙar bashi dariya, duk yanda yaso cigaba da pretending ɗin mazuran nasa sai gashi ya saki murmushi da hararta. Ya dungure mata kai yana cije lip ɗinsa na ƙasa.       “Yarinyarnan kin fara rainani ALLAH. Ni nema ɓarawo ko?”.        Hannu tasa ta rufe fuskarta tana murmushi. “Nidai bance dakai barawo ba. Amma idan ta gaskiya za' sace wayarnan akai na nemeta na rasa”.      Cak ya ɗagata da ƙasa yay saman gado da ita yana faɗin, “To bara na nuna miki ba satar waya kaɗai na iyaba yarinya”. Ya ƙare maganar da tura hannu cikin ƴar fingilar rigar jikinta da iyakarta cinya. dama ta sakatane dantayi aikin a sake babu takura. Dariya ta shiga ƙyalƙyalewa tana faɗin, “Na tuba wasa nakeyi ALLAH”.     Kobi takanta baiyiba ya lula da ita duniyar kodumo, dama ita kam duk sanda ya taya tana maraba, inma bai kawo kansaba ita zataje.     Sai da suka samu nutsuwa aka koma firar waya. Babu kunya yake sanar mata ai tun randa Farah taje Nigeria lokacin da take bama su Mas'ood Number ta yay ƙudirin rabata da wayar, sai dai bayaso yayi gatse-gatse su Granny su saka masa ido ko Khalipha ya fassara abun da wani abu daban. Shiyyasa yabi dare ya sace batare da sanintaba. Dan tana gama waya dasu maman sadiq ta fita tarbosu ya ɗauke wayar yasa a aljihu, ya fito da nufin barin gidan yaci karo da fuskar little.       Jikinsa ta faɗa ta rungumesa tana dariya. “Kai Yayanmu amma ranar harda tambayata ina take? Sannan duk yanda kaga ina zaune babu waya bakaji tausayina ba”.     Hancinta yaja yana murmushi, “Uhmyim, salon na barki ki riƙe wani yaymin fashi da makami. Na tabbata Khalipha nema zai fara shiyyasa nai azamar yin maganinku, dan bana haɗa takara da kowa nikam. Duk abinda zuciyata taji tana muradi nawane ni kaɗai insha ALLAH. Dan tun randa kikaimin ihu a ɗaki da kirana aljani kikai wuff da tunanina da zuciyata, shiyyasa duk motsinki yazama akan idona”.       Ƙarara mamakin maganganinsa suka bayyana a fuskar Zinneerah, sai ga hawaye na cika mata ido, batama san ta ɗane jikinsa da haɗe bakinsu waje gudaba dan daɗi.         Soyayyar Zinneerah da AK abin sha'awa. Gwargwadon iko yana bata kulawa. kuma yana so da kaunarta. Sai dai soyayyarta sam bata rufe idonsa ya manta da Farah ba. Tana nan maƙale a ransa yana kuma son kayarsa. Babban fatansa ALLAH ya shiryeta ta gane gaskiya a duk sanda zata sake dawowa rayuwarsa ta dawo a Farah dinta da suka shinfiɗa ƙyaƙyƙyawar rayuwa a baya. Ya kuma yafe mata daga ita har Mammah da Zakiyya, dan koba komai sun zama silar mallakar Zinneerah a rayuwarsa, tare da kusantashi da ahalinsa. Da kuma samun dai-daito tsakanin Mahaifinsa guda biyu, abinda tayta fata a tsahon shekaru amma ya gagara. ______________       Haka rayuwar London ta cigaba da tafiya cikin jin daɗi da farin ciki, sai dai wataran saɓani da ɓacin rai kanɗan gitta tamkar yanda akasan kowanne gidan ma'aurata. Amma lallai bazasu taɓa iya mantawa da rayuwar london ba dan rayuwace mai tsayawa azuciya garesu. Anci soyayya kamar babu gobe.       Sunada wata ɗaya a london matar dake ɗauke da cikin da aka dasa mata ta Morocco ta haihu, sai dai abin ƙaddara ta haifi yarinya mace babu rai, abinda yasa zancenta baiyi tsaho ba ta tabbatar ma su Baffah cewar da amincewarta su Zakiyya sukai komai, ko yanzu suka shirya kuma zata ƙara ɗauka musu wani cikin tunda wannan batazo da rai ba. Godiya kawai sukai mata da bata wasu kuɗaɗe suka barota.         Duk da kuwa AK yaji baƙin cikin ta yanda aka samar da ɗiyar itama sai da yay hawayen rasuwarta lokacin da aka turo masa hotonta a waya abin sha'awa. Ya sunbaci wayar da jerama UBANGIJI kirari da addu'a a gareta da sauran al'ummar musulmi baki ɗaya. Zinneerah kanta sai taji yarinyar ta shiga ranta. Hakama Hajiya iya dasu Mammah. To amma yaya za'ai da hukuncin ALLAH sai haƙuri.       Watansu biyu cif suka dawo gida Nigeria domin halartar bikin ƴaƴa bakwai daga zuri'ar Abdul-Mutallab Shira. A lokacin cikin Zinneerah nada watanni huɗu cif. Ya ɗan turo abinsa duk mai lura zai iya ganinsa.          Aiko sai ta dinga ƙunshe-ƙunshe musamman da taje gidan mmn Sadiq. aiko su Meenal suka dinga mata dariya. Taso zuwa duba Inna kafin a shiga hidimar bikin amma AK ya hana, acewarsa ta bari a gama biki sai suje dan akwai maganar Dr Mahmud ma da Sa'a a ƙasa.        Kamar yanda ya umarceta da haƙurin haka ta haƙura aka shiga shagalin bikin su Abidah da aka shiryama bidi'oi kala-kala, danma AK ya zaftare wasu a ciki yanata faɗa.     Ranar ɗaurin aure a bazata sai ga sunan Khalipha a cikin anguna. An zarga masa igiya uku da ɗiyar Uncle Ahmad Raheenat (Noor). Kowa kam yayi farin ciki da wannan haɗi musamman ma Uncle Ahmad. Shima dai ango da gaske yanaso dan ƙiri-ƙiri ya nuna farin cikinsa. Abin sauƙin ma shima yanada gidansa dama da yake gini, ƴan abubuwane kawai suka rage a ƙarasa dan haka aka hau sauran aiki babuji babu gani. Matar Uncle Ahmad tayi baƙin cikin wannan haɗi itakam, sai dai babu yanda zatai dole ta haƙura. Dan dama taƙi sakin jiki da matan gidan sam. Suko da yake ba kanwar lasa bane duk sai suka watsar da ita suma suka cigaba da sabgogin gabansu.        A bikin nan dauriya kawai Zinneerah keyi dan batajin daɗin jikinta, hayaniyarma sam bataso, shiyyasa lokuta da dama zaka sameta can gefe a killace. Hakan sai yayma AK daɗi dan bata halarci bidi'a ko daya ba da akai garama kamu da akayi anan cikin gidan. Ana saka kiɗa kuwa sai da tabar gidan saboda ciwon kai mai tsanani. Can gidansu ta koma tai kwanciyarta ta hutama ranta.        Ansha shagalin biki harna kwanaki uku aka miƙa amare ɗakinsu. Adilah lagos, Safiyya Abuja. Sauran kuma Ni'ima da Abidah duk anan kano ne, sai Noor da aka bari sai nan da kwanaki uku an kammala aikin gidan Khalipha.      (To amare da angwaye ALLAH ya sanya albarka ya kawo ƴan dugwi-dugwi iyalan baba).          Washe garin da aka shashshare daga bikin nan kuma aka kai kuɗin auren Sa'a danya. Inda baƙi suka sami tarba ta mutunci da girmamawa. Inna ga dama ta samu amma babu halin damawa, sai hawayen zuci takeyi.    Dan tuni aka maidota gida. Sai dai a duk sanda ta kalli Tinene da tsohon ciki ranar sai ciwonta ya rikice. Hakan yasa suka yanke shawarar maida Tinene gidan Gwaggo laritu harta haihu, dan an ajiye magana randa ta haihu za'a ɗaura mata aure damai cikin tunda ya amsa nasane.      Daga kai kuɗi baba yace shikam dai baimaga wani abun jeka ka dawo ba a ɗaura aure kawai a huta. Zuwa wani satin ta tare ɗakinta taje tai haƙuri tamkar kowa. Hakan yama Dr Mahmud daɗi, hakama su Baffah da suka kai kuɗin. Nanko take aka zarge igiya uku tsakanin Sa'adatu Sulaiman Danya da Dr Mahmud Dawood. Zokaga baki wajen ango. Aiko AK ya dinga masa sherin kurame yana ramawa shima kamar yanda yay masa. Dan bazai fito kai tsaye yay maganaba sai dai yayi a fisge ya tsuke baki cikin basarwa tamkar bashine yayi ba.     Cike da farin ciki suka dawo kano da wannan labari, Zinneerah kam tafi kowa murnar wannan al'amari dan har kukan daɗi tayi.        Cikin amincin ALLAH sati na zagayowa akai tariyar Sa'a. sai dai Zinneerah bataje Danya ba dan batajin daɗin jikinta kam, Khalipha ma tasa amaryar ta tare a nasa gida da aka kammala. Yanzu kam sai dai mu cigaba dabin kowa da fatan alkairi.           Tun bayan tariyar Sa'a komai ya sake lafawa, Khalipha ya koma London shi kaɗai domin karasa karatunsa. Zinneerah ma cikin ƙarfin hali AK ya sata zana exam na November/December. Tasha wahala saboda laulayin dake damunta, amma babu laifi tayi ƙoƙari Alhmdllh, sai fata da addu'ar fitowar ƙyaƙyƙyawan result.        Haka rayuwa ta cigaba da tafiya Zinneerah na rainon cikinta dake ƙara fitowa yana wahal da ita, duk ta rame sai haske data ƙara kam masha ALLAH. Yanda wahalar tai mata yawa ne ga aikin gida ga little ya fara makaranta, dan yanzu yafi zama anan fiye da ko ina, yawonsa sai weekend, ga gida shiru ita kaɗai yasa Hajiya iya cemasa ya maidota nan gidan sai ta haihu.      Babu wani ɓoye-ɓoye ya ɓata ransa. Dan shi dai yafison su cigaba da lallaɓawa a hakan har ALLAH ya sauketa lafiya. Tunda dai bawai kwance take rijif ba. Aikin gida da lalurarsa girki da sauransu duk tanayi. Fitace kawai bata cika sonyi ba dan wahala take sha sosai koda kuwa zuwa gidan su Granny ne kawai tayi ko gidan mmn sadiq. Shiyyasama ta tattara kowanne yawo ta ajiye.        “Ikon ALLAH, wai ka cika baki da iska! Bazaka maidotan bane komi kake nufi moddibo?”.        Shiru yay mata kamar bazai tanka ba, sai da yaja wasu sakanni ya dubeta yana ajiye wayar hannunsa. “Granny ki fahimta mana dan ALLAH, taya yarinya na gidan mijinta ace ta taso ta baro. Wazai kula damu ni da Abdul-Mutallab to?”.         “Owoo, sai ta zauna zaman kula da ku ita kuma ta kashe kanta. Kana ganin yanda duk jikinta ya koma ko abincin kirki bataci sai yame-yame”.        “Granny duk nasan da waɗanan matsalolin kuma suna damuna wlhy nima, ina kuma yin iya bakin ƙoƙarina na ganin na bata kulawa nima, kuma Alhmdllh jikin natama ya fara sauƙi. Kawai dai idan kin yarda a samo wata ta zauna da ita ni ko nawane zan biya. Kokuma ke ki koma can dan ALLAH ”.       “Wa? Kama kanka. Kawai sai naje ƙososo na zauna muku a gida raba kanka malam”.        Murmushi yayi a ransa yana faɗin, ‘Ai wlhy ke zan lallaɓa kije madam, nasan maganinki ai’. A fili kam sai yay mata shiru, daga ƙarshe ma ya miƙe yana faɗin, “Bara naje na ɗauka Abdul-Mutallab a makaranta”.       “ALLAH ya kiyaye ka gaishesu”.    Zinneerah na falon farko na sashenta a kwance cikin kujera barci ya ɗan fara figarta daga charting dasu Meenal suka shigo. Kamar yanda Little ya saba duk da kuwa yanzu ya ƙara girma da wayo ga shegen miskilanci kamar sunyi kaki sun ajiye ya nufeta da gudu. Yana ƙoƙarin faɗa mata a jiki AK ya ɗagashi sama dan yanayinta ya nuna masa batajin daɗin jikin. Kuma lafiya lau ya fita ya barta.      Itama ajiyar zuciya ta sauke ganin ya hana little ɗin faɗa mata a jiki. Ta yunƙura ta tashi zaune tana musu sannu da zuwa. Amsawa yay idonsa a kanta yana kaiwa zaune kusa da ita little a jikinsa.       “Jikin ne kuma?”.   Fuska Zinneerah taɗan yamutse tana kamo hannun little ɗin. “Kawai dai banajin ƙarfi ne amma babu inda kemin ciwo, garama tashin zuciya daketa damuna tun cin kifin nan na jiya da naci”.       Tausayintane ya sake kamashi, musamman daya tuna yanda taita damunsa da maganar kifin. harma ya dawo gida jiya da nufin bazai sake fitaba ta takura sai da ya fita kusan goma na dare ya nemo mata kifin, gashi kuma taci ta kasa zaman lafiya.          “Sannu ALLAH yay miki albarka ya saukeki lafiya. Bara na taɓa Mahmud naji kozaki iya shan wani abu dazai baki nutsuwa”.        “Yayanmu kama barshi zai bari dan kansa. Dan nayi waya da Yaya gajeje tace na samu ɗan kanwa kaɗan nasa a ruwa na sha zai faɗa min”.         Kafin yace wani abu little da yay kamar ba saurarensu yakeba yace, “Aunty sorry, idan kika haifa mana babynmu zan kaiki makka”.        Dariya zancen nasa ya basu, dan haka suka murmusa AK na shafa kansa. “ALLAH ya tabbatar ɗan albarka. Yanzu ka muje na maka wanka kaga aunty yau babu kanta”.     Kansa ya ɗaga masa. Zinneerah tace, “Kama barshi zan iya masa. Bara kaima na haɗama ruwan wankan ga abinci nan na shirya”.         “Kina fama da kanki kika wani kama abinci? Nace miki duk randa baƙyajin daɗi basai kinyi ba tunda ga gidan Granny sai a kawo daga can”.     Murmushi ta ɗanyi da kama hannunsa dan ta tura little ɗaki ya kai kayan sa. Ta kwanto jikin hannunsa tana duban ƙyaƙyƙyawan fuskarsa. “Yayanmu nace makafa bawani ciwo nakejiba ALLAH. Kuma idan ban motsa jikin ai sai wani kuma ciwon ya taso”.     Kanta ya shafa yana rungumota da ƙyau jikinsa. Ya sumbaci laɓɓanta da goshinta yana jera mata addu'a. Itama hannunsa ta sumbata ranta fes ƙaunarsa na ƙara shigarta jini da ɓargo.         Kwana biyu dayin haka sai ga Mahma daga london. AK yaji matuƙar daɗin wannan zuwa nata, dan dama lokacin bikin su Adilah ta tabbatar masa da cikin Zinneerah ya shiga watanni bakwai insha ALLAH zatazo Nigeria. To shikam ya ƙudiri tunda tazo riƙeta zaiyi har sai matarsa ta haihu.       Sosai Zinneerah ma ta nuna farin cikinta sosai na zuwan Mahma. Dan-danan ta gyara mata ɗayan ɗakinta na falon farko duk da dama fes yake. Bakuma wani amfani take da shiba garama da ƴan Danya sukazo tariyarar Yaya Sa'a sun kwana a ciki.      Itama Mahma taji daɗin yanda suka tarbetan, tare da ɗunbin tausayin Zinneerah daketa fama, dan ga cikin nata yayi girma sosai Alhmdllh kamar ba ɗan wata bakwai ba. Kasama haƙuri tayi sai da tace, “Anya cikin nan ba ƴan biyu bane kuwa a cikinsa?”.      Cike da kunya Zinneerah tai ƙasa da kai tana murmushi kawai. Sai AK dake saurarensune yace, “Ƴan biyu kuma Mahma?”.        “Eh mana Abdul-Mutallab, ai girman cikin ne masha ALLAH kamar ba wata bakwai ba”.        Kallon Zinneerah ɗin yayi shima da ƙyau zuciyarsa na fata da tabbatar wannan zance na Mahma. Yace, “To Mahma bamu saniba dai, amma ALLAH ya tabbatar”.        “Amin to, amma baku dubaba kenan?”.       “Wlhy Mahma banason wannan bin ƙwaƙwƙwafin, komai ya fito a cikin nan ina maraba dashi da so da ƙaunarsa”.        “Alhmdllh aihaka akeso musulmi ya kasance Abdul-Mutallab, ALLAH ya rabasu lafiya”.     Da “Amin” ya amsa mata. Zinneerah kuwa tayi a zuciyarta kawai.............✍ *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_* *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* _______________________ *Page 67* .............Alhmdllhi sosai zuwan Mahma ya taimakawa Zinneerah, dan tana ɗebe mata kewa da rage wasu abubuwan. Tana kwana na huɗu ma da zuwa sai ga wata dattijuwa Hajiya iya data sa aka kawo mata daga bauchi ta iso. Nanma ya haɗu ya ƙara taimakawa Zinneerah ɗin sosai. Dan Mama A'i mace ce mai ƙoƙari da haƙuri. Gashi bata da yawan hayaniya itama ga kuma tsafta. Hakan yasa tasu tazo ɗaya da AK. Duk da dai iyakacinta ɗan taya aikin gida Mahma ke musu girki, wani lokacin kuma Zinneerah ɗin kan shiga da kanta tayi. Hidimar Little kuwa dama ta koma hannun Mahma. Yanzu ma a ɗakinta yake kwana abinsa.      Haka aka cigaba da turawa har ALLAH ya sauka Tinene lafiya daga danya. Ta samu ƴarta mace mai kama da ubanta sak. A randa ta haihu a ranar aka ɗaura aurenta da Lado. Bayan arba'in zata ta tare. Baba bai gayama Sa'a da Zinneerah ba sai kusan kwanaki biyar da haihuwar ma. Dukansu sun mata addu'a da fatan alkairi, suka kuma aika musu da abinda ALLAH ya hore musu tunda duk ba sana'a sukeba. Dan Sa'a ma makaranta ta koma Dr Mahmud nason ta haɗa kwalinta na secondary da shirirta da halin Inna yasata kasa haɗawa. Tunda koda ta koma bayan baro Zinneerah Danya bata kammalaba tunda komawa tai ta fara daga js1.        Ranar tarewar ma da ƙyar AK ya yarda suka tafi ita da Sa'a. Amma ya tabbatar mata banda kwana ranar zasu dawo. dan ko little ma bai bitaba ita kaɗai ta tafi Haneef ya tafi kaisu ita da Sa'a dasu Bahijja.        Sun sami tarba mai ƙyau, dan kowa sai ji dasu yake sun zama tamkar wasu taurari a dangi baki ɗaya. Kowa nata tausayin Zinneerah da fatan ALLAH ya sauketa kafiya. itama Sa'a ALLAH ya bata nata dan har yanzu dai babu ciki.      Ganin yanda jikin Inna ya ƙara rincaɓewa yasa hankalin Zinneerah da Sa'a ƙara tashi, dan Karima dake gidan tana kula da ita tata ƙorafi kenan da mita. Wani lokacinma sai yaya Gajeje ta yunƙuro tazo ko matar baba tai mata wani abun Karimar na zaune taƙiyi. Kiran AK tai ta sanar masa. Bai wani ja zancenba yace ta haɗashi da Haneef dan tunma ɗazu yake nemansa ya gaza samu, itama ɗin ya nemetan yaji yaya suka sauka amma bai samuba sai yanzu data kirasa.      Umarni ya bama Haneef ɗin akan su taho da Inna kano. Batare da Zinneerah tasani ba sai da aka idar da sallar la'asar Baba ya tunkaresu da zancen. Murmushi kawai tayi bata nuna bata saniba. A ranta kuwa tana mamakin Yayansu.        Kowa yaji daɗin abinda AK ɗin yayi, dan haka ana gama shagali basu zauna akai amarya ɗakintaba suka tattaro zasu taho, wai kuma Karima zata biyosu Baba yace bata isa ba. Yaya gajeje zata bisu daga baya. Itako ta zauna Danya.           Sa'a ma da nufin kwana tazo, amma jin Zinneerah bazata kwana ba kuma za'a tafi da Inna sai kawai ta shirya ta biyosu. A shira hospital suka sauke Inna, inda Dr Mahmud yasan da zuwan nasu dan sunyi nagana da AK. Anan suka bar masa Sa'a bayan sunga komai ya dai-daita na kula da Inna. Haneef ya wuce da Zinneerah gida ya fara ajiyeta sannan suka wuce gida suma dasu Meenal.          Tun daga ranar jinyar Inna ya dawo ƙarƙashin kulawar su AK, amma Yaya Gajeje tazo daga danya tana tare da ita a asibitin. Kullum sai Zinneerah taje ta dubata kamar yanda Sa'a ma haka. Alhmdllh kuma jikin nata na ƙyau ba kamar sanda tana Danya ba. Dan magunguna masu ƙyau da tsada ake mata amfani dasu, ga kulawa ta musamman da take samu daga mazan ƴaƴan nata. Baba ma lokaci-lokaci yakanzo dubata shi da yan uwansa da amaryarsa da Karima.                  A haka Zinneerah ta cigaba da turawa har aka shiga kwanakin jiran tsammani na haihuwarta. Zuwa yanzu kam sosai bata da lafiya tamkar cikin little, dan dolema aka koma da ita zaman asibiti. Kwanakinta shidda a asibitin a wata safiya ta wayi gari da naƙuda. Sai dai fa tamkar cikin little jini ya ɓalle mata ga haihuwar shiru. Hankalin AK da kowama ya tashi, hakan yasa Dr Mahmud ya bada shawarar kawai ai mata cs kafin ta jigata ƙarfinta ya ƙare.     Babu wani jayayya AK ya amince. Zuciyarsa fal tausayin halin da take ciki. Yayinda yake rayawa a ransa ko wannan tashin hankali da ta shiga a wancan karon na haihuwar little ya isa hana su Farah zaman lafiya da jin daɗi. Shikam sai yanzuma yake ganin matsalar da sukaita fuskanta na rashin jin daɗin rayuwar aurensu kullum faɗa da fitina shi da Farah ko wannan halin da suka zama sanadin jefa yarinyarnan ya isa su rasa farin cikin rayuwar aurensu ai. Dan Dr Mahmud ya tabbatar masa da haka tasha irin wannan wahalar a wancan karon ma.       Alhmdllh an yi mata cs aka ciro ƴaƴa biyu mace da namiji. Zokaga murna wajen kowa. Shikam AK duk da yana murna da samuwar tasu hankalinsa nakan matarsa. sai da yaji tabbacin kasancewarta cikin ƙoshin lafiya sannan hankalinsa ya ɗan kwanta harya amshi jariransa ƙyawawa masu lafiya yana mai jerama UBANGIJI godiya daya bashi ƙyautarsu ta silar da ALLAH ya halatta masa bayan ya cire tsammani daga hakan.          Inna daketa samun sauƙi tana zaune dan yanzu takan ɗan motsa jikin aka sanar mata da haihuwar Zinneerah. Hawaye kawai su Sa'a sukaga tanayi amma batace komaiba. Hakan yasa suka gagara fahintar na minene? Na daɗine kona nadama? Kona baƙin cikin har yanzu?.      Oho masu karfin ajin ma basusan tanai ba. Dan cikin ƙanƙanin lokaci Shirawa suka cika asibitin domin taya Yayansu murna da samun wannan ƙaruwa. Waɗanda basa kusa kam irinsu Khalipha da Adilah tuni hotunan babes ya isa ga wayoyunsu.        Addu'a dai kam sun shata kamar yanda Zinneerah ma keshan tata na fatan samun lafiya. dan kowa bai gantaba itakam har AK ɗin sai da daddare. Shima ya samu tanata barci. Ya ƙureta da ido cike da tausayi da ƙauna dan dukta rame sosai fiyema da lokacin da cikin na jikinta. Sumbatar goshinta yayi da hannunta yana mai jera mata addu'ar samun lafiya.     Sauran ƴan uwa kuwa da abokan arziƙi basu sami ganintaba sai washe gari, zuwa sannan ta farka Alhmdllhi. Kuma tana gane kowa da amsama kowa gaisuwarsa.      Lokacin da taga ƴan jinjirayenta da farin cikin dake shinfiɗe a fuskar AK murmushi ta dinga zubawa itama. a ranta tana musu addu'a. A fili kuwa sai ta dinga nuna alkunya su Hajiya iya na mata dariya. Sai dai har cikin ransu hakan da tai ya musu daɗi, dan yaran yanzu daba kawaici garemu akan ƴaƴaba koda na farine balle na biyu.       Sai dai kuma wata sabuwa. wannan karonma tamkar haihuwar little ruwan nono ya zamarwa yaran damuwa. Dan da sun sha cikinsu duk sai yake kumbura suyita kuka. Ga namijin da son abinci tamkar ubansa. Hankalin AK ya tashi matuƙa da hakan. Amma da Dr Mahmud ya sanar masa haka dama sukasha fama akan little sai yaɗan sami nutsuwa. Yanzuma magunguna suka haɗa mata. Amma sai Mahma tace wanann al'amari kamar bana asibiti ba. Yanada nasaba da jinnu sai an dage sosai ma Zinneerah ɗin.     Kowa yasha mamaki, amma sanin wacece ita a wannan fanin yasa duk suka amince. Itace da kanta ta fara harhaɗama Zinneerah magungunan gargajiya ta fara amfani dasu, tace insha ALLAH komai zai daidaita.       Kwananta takwas a asibitin aka sallameta, Alhmdllhi zuwa yau kuma yara sunsha nono kuma babu wani matsala data biyo baya. Hakan ya saka kowa farin ciki dajin daɗi. AK yaga amfanin wannan sani na Mahma da yaketa ƙorafi akansa tunda gashi ta bama matarsa magani an kuma dace.       A randa aka sallamesun ranar Mammah ta iso Nigeria, zokaga murna wajenta datai tozali da ƴan jikokinta. Su Adilah ma an iso daga Lagos suda tawagar Mommy. hakama Gwaggo Maryama. Inna ma da aka sallamota nan AK yace a kawo ta huta sosai kafin a maidata Danya.      Kai tsaye gidan hajiya iya aka wuce da Zinneerah, za'ai suna acan sannan su koma gidansu su cigaba da jego kuma.      Yara sunci sunayen Hajiya Iya da Baffah. *_Ameenatu & Kabeer_* za'ake kiransu (Amaan & Anam). AK ya zata Mammah zatai fushi, sai yaji batace komaiba. Yaji daɗin hakan, dan koba komai ya yarda ta dawo hankalinta yanzu kam.       (An zinni sai muce ALLAH ya raya keda yayanmu angon jego).         AK dai bason bidi'a yakeba. Dan haka aka shirya ƙwarya-ƙwaryar liyafa anan harabar gidan akaci akasha kowa ya godema ALLAH. Ƴan Danya, ƴan ɗanmusa ƴan bauchi sun cika gida dam domin taya murna. Hakama mai jego da jarirai sunsha ƙyau harsun gaji masha ALLAH.     Kowa ka gani sai son barka. Amare ma da yawansu suna maƙale da cikkuna kanana sai fatan suma ALLAH ya saukesu lafiya.         Kwana biyu da suna AK ya takura dole su Zinneerah suka tattaro suka dawo gidansu, aranar kuma ƴan danya da ƴan ɗanmusa suka koma. Suma ƴan bauchi washe gari suka kama gabansu sai kuna wata ta taso.       Zinneerah tayi farin cikin kasancewar gidan cike da jama'a. Dan kuwa Ga mahma ga Mammah da suka koma sashen Farah suka zauna. Ga kuma Mama Ai, ga Yaya Gajeje da Inna. karima ma maƙalewa tai taƙi bin ƴan suna. Sai Tinene da Atine ne suka koma da amaryar baba.       Ganin al'amura komai ya daidaita jikinta yayi sauƙi kamar ba yankata akaiba Alhmdllh yasata ƙudirin tunkarar AK da batun dawowar Farah gida. Dan itako tama fi son ta dawo hakanan tunda dai tasan zuwa yanzu ta horu. Dan su Meenal suna bata labari da sukaje da Granny kwanaki duba Farah ɗin abin gwanin ban tausayi. Duk sun fita hayyacinsu ita da Zakiyyan dan horo mai tsanani maimartaba yasa aketa musu batare da sanin kowa ba. Idan ka gansu bazaka taɓa ɗauka su din bane ƴan gayu ƴan ƙwalisa masuji da naira a bankuna.           Suna zaune a falonta na farko ita da Yaya Gajeje da Karima, Yaya Gajeje tana shirya ƴan biyu da akaima wankan safe. Zinneerah ma tayi nata dan tana cikin kwalliyarta tamkar ba jego takeba. Har Karima na tsokanarta da tacigaba da kashe ɗauri baban ƴan biyu ya lallaɓo a samo gambo kafin arba'i.         “Ya ilahi, dan ALLAH Yaya Karima barmin baki, ina ni ina wani gambo ana zaune ƙalau”.      Dariya suka sanya mata, suna cikin dariyarne Mama A'i ta shigo riƙe da hannun Little dake kuka wai ya faɗi. Dubansu duk suka maida garesu, Karima na kamo hannun little ɗin da faɗin, “Yaya akaine Abdul?”.        “Faɗuwa yayi, ya shigo da gudu yaci karo da kujera”. Mama A'i ta bama Karima amsa.        Baki Zinneerah ta taɓe tana miƙama Yaya Gajeje pampas da za'a sakama Anam. Tace, “Maganinsa kenan, shidai a rayuwarsa yayi gudu, bansan daɗin mi yakeji ba sai kace wani ɗan ƙwallo”.       Yaya gajeje ta katseta da faɗin, “Ai tsautsayi dai baya wuce ranarsa, sannu kaji Abdul ka daina gudu wannan gidan naku dake cike da kayan santsinnan, ni kaina babba idan ina tafiya wlhy a hankali nakeyi dan ji nake kamar zan faɗi”.      Dariya Karima da A'i sukayi, Zinneerah taɗan murmusa da zancen Yaya Gajejen tana maida hankalinta ga little. “To gudun mi kakeyi?”.       Baki ya tura gaba yana makalewa bayan Karima. “Daddyna yace nakiraki zaije anguwa”.        “Naji to, kace ina zuwa”.   Sai da little ɗin ya fita ta duba Mama A'i. “Mama an gama haɗa abinda ya rage ɗinne?”.        “Eh an gama maman Abdul, harma na miki karanbani na shirya a tray ”.       “Kai aiko ngd aiba karanbani bane”. Zinneerah ta faɗa tana mikewa. Fita tayi domin kai masa kayan breakfast ɗinsa.          A falo ta samesa zaune yaci gayu cikin ɗanyar shadda ash, yana zaune a dogon kujera little a kusa dashi yana duba masa ƙafarsa da yaji ciwo. Koda tai sallama bai ɗagoba har ta karaso inda suke ɗauke da tray ɗin. “Barka da hutawa”.      “Barka” ya amsa mata yana ɗan dagowa ya dubeta. Duk yanda yaso maida idonsa ga ƙafar little ɗin kuma sai ya kasa. tai ɗan murmushi da ɗauke kanta ganin kallon da yake mata. “A ajiye nan ko dining?”.       Lumshe idanun yayi ya ɗan buɗe a kanta, cikin kasalar data samesa yanzu yace, “Ajiye anan kawai”.     Saman centre table ta ɗaura tray ɗin da duban ƙafar little dake cikin hannunsa. “Shi kuma wannan miya samu ƙafar tasa?”.     Iska AK ya ɗan furzar. “Yace faɗuwa yayi ga waje harya fashe, taimakemu da man zafi ma a ɗaki”.        Bedroom ɗin nasa ta nufa tana faɗin, “Maganin mai gudu kenan idan yana tafiya”.       Murmushi kawai AK dake binta da kallo yayi, dan a kwankin nan data haihu duk ramar nan ta ciki da tayi nan ɓacewa take, sai wani irin buɗewama takeyi alamar lafiya ta samu. Miƙewa yay yabi bayanta yanama Little gargaɗin ya jirasa ya dawo.       Zinneerah na ƙoƙarin fitowa sukaci karo, baya ta koma tana faɗin, “Ouch Yayanmu zaka fasamin kai”.          “Kokuma ni zaki fasamin ba”. Ya faɗa yana matsota. Kallonsa take da mamaki, ganin dai da gaske kanta yayo tai saurin faɗin, “Yayanmu wani abu ya farune?”.        “Faffaruwa ma madam” Yay maganar yana kamo hannunta da jawota jikinsa. Hancinsa ya cusa cikin wuyanta yana magana raɗa-raɗa. “Ko tausayinama baƙyaji kin barni da kwana da little ke kinacan kina morewarki ko?”.      Dariya zancen nasa ya bata, amma sai batayiba tai murmushi da ƙoƙarin ƙwace kanta. “Yayanmu ai amfanin mata biyu kenan, ni ina fama da wannan fiɗan inani ina ɗaukarka. Kawai aunty Farah ta dawo kaga ni sai nayi arba'in”.         Gani tai ya saketa baki ɗaya yana tsuke fusaka. Ya watsa mata harara yana jan guntun tsaki, batare da ƙara cewa komaiba ya juya ya fita a ɗakin. Bayansa tabi da kallo tana murmushi, a fili tace, ‘Uhm ka gama mazuranka ne dan nasan kana son kayarka’.              Iskeshi tai yana zuba abincin da kansa. Batai maganaba ta matsar da little kusa da shi ta zauna, “Ina waje. ciwon Alhaji?”. Ta faɗa tana kamo ƙafar little. Nuna mata yayi, ta buɗe man zafin ta shafa masa yana wani shii da baki da yarfar da hannu. “Daddy kace tayi a hankali zafi”.        “Oh ALLAH, ALLAH yaron nan saika kashe auren da babu soyayya, yanzu shafa maganinne da zafi?”.           Zancen nata ya bama AK dariya amma sai ya gimtse bai yiba. Yadai kamo hannun little ɗin yana bata amsa a daƙile. “Dama can babu soyayyar ne ai”.      Tasan da biyu ya faɗa, dan haka taja bakinta tai shiru. Sai dai ta cigaba da kallonsu yanacin abincin yana bama yaronsa har suka kammala.       Bai wani jima da gamawarba ya mike yana kallon agogo. “Saifudden zai kawo muku cefane. Dan bazan dawo ba sai dare”.      Mikewa itama Zinneerah tayi da faɗin, “ALLAH ya saka da alkairi ya kara buɗi, miza'a dafa maka da daren”.       Kallonta yay cikin ido sonta da buƙatarta na ɗawainiya da shi, yaja numfashi da duban inda little yake. Ganin hankalinsama ba'a kansu yakeba sai ya sake kallonta. “Abinda nakeso a dafamin kam ai ba bani za'aiba. Sai dai nayi manage da tuwo”.      Murmushi tayi tana maida kanta gefe dan tasan ina ya dosa, ta hau tattara kwanikan, “Uhm ni Yayanmu ALLAH fitina kake ƙarowa kullum, na kawo mafita kuma kaji haushina”.        “Ke dai kika sani” ya faɗa yana nufar ƙofa.       Murmushi kawai tayi ta cigaba da abinda take. Sai da ta kammala ta tisa ƙeyar little da baima lura da fitar Daddyn nasaba ta rufo sashen. A sashenta ta samesa zaune suna gaisawa dasu Yaya Gajeje ƴan biyu duka na'a jikinsa yana kallonsu zuciyarsa fes da farin ciki. Inda yake little ya nufa ita kuma ta nema waje ta zauna. Ya ɗan jima a falon suna maganar jikin Inna daya fara lekawa tana barci dasu Yaya Gajeje kafin ya basu yaran da musu sallama ya fice, bayan ya jefeta da wani kallon duk randa na kamaki. Murmushi mai sanyi kawai tai masa da rakashi da addu'a.       Shima daga nan sashen Farah ya shiga inda ya samu su Mammah na karyawa. Sun gaisa nanma yaɗan zauna suka taɓa hira sannan yay musu sallama yabar little anan ya fice.        ★★★ Daga ranar Zinneerah bata sake masa zancen Farah ba har ALLAH yasa sukai arba'in. A randa tai arba'in ɗin kuma su Mammah ke shirin tafiya katsina duba su Farah daga can su wuce london.          Gaba ɗaya Zinneerah sai ta shiga damuwa. Dan zamansu a gidan ba ƙaramar shaƙuwace ta shiga tsakaninsu ba. Ganin shine zai kaisu katsinar ta sake daurewar masa zancen dawowar Farah sai ya balbaleta da faɗa, duk da tasan bayason wargi bata taɓa ganin fushinsa irin yau ba. Ita kuma yanda yake mata ihu akai yasata fara kuka.       Suna haka Mammah ta shigo falon. Saurin share hawaye Zinneerah tayi tana ƙaƙaro murmushi da yima Mammah ɗin dake binsu da kallo sannu. Daga haka ta zame ta gudu ta barsu, dan tasan tunda Mammah din ta shigo nan da kanta magana zatayi da shi.       Da kallo tabi Zinneerah harta fice kafin ta maida ga AK dake ta wani bata fuska. “Abdul-Mutallab mi kaima yarinyarnan?”.        Guntun tsaki yaja yana murza goshinsa. “Mizan mata kuwa Mammah, itace da neman fitina kawai”.      Shiru Mammah tai tana kallonsa cike da nazari, sai kuma taɗan girgiza kanta da cewa, “Fitina kamar ya? Ai kowa Yasan Zinneerah bata da kwaramniya, dan nidai a zamanmu gidan nan banga wani abun ashsha daga garetaba sai dai ajizanci irin na ɗan adama kawai. Amma yarinya mai kawaici da kunya ga haƙuri. Sai dai idan kai ne da laifin tunda sarai na san halinka bawai baƙona bane. Miya haɗaku?”..          “Nifa Mammah babu abinda nai mata. Kawai ta isheni da zancen Farah ne”.       Kallonsa kawai Mammah keyi dan maganar yanayintane da faɗa sosai. Ta sauke numfashi da gyara zamanta. “Abdul-Mutallab nasan Farah mai laifine tabbas, amma karka manta harda gudunmawarmu, kuma maganarta da yarinyarnan take maka tasan kantane. Dan wannan haline irin na mutanen ƙwarai da sake tabbatar maka ita mai tarbiyyace da hangen nesa. Ni bazance dole ka dawo da Farah gidankaba, amma zan baka shawarar ka daina ƙuntata yarinyarnan akan abinda ba laifinta bane saima alkairi da takeson ɗoraka akai. Ita rayuwa komai ɗan haƙuri ne ai. idan akai haƙurin sai komai ya zama labari wataran”.        Shi dai kansa na ƙasa baice mata komaiba harta gama zancen Farah da Zinneerah ta ɗakko abinda ya shafesu sannan ya tsoma baki.     Duk da Zinneerah tasan su Mahma basu rasa komai na rayuwaba sai da ta shirya musu tsaraba domin girmamawa. Musamman turarurrukan khumrah dana wuta da a koda yaushe suke yaba kamshin a jikinta da gidanta. Hakan yasa tasa Hajiya Falmata ta haɗa musu na musamman akai musu packaging nashi.     Sai gata harda ƙwalla da zasu wuce. Bama ita ba hatta su Yaya Gajeje sunji babu daɗi. Inna ma da take ɗan magana yanzu kuma takan ɗan motsa jikinta tafiyace dai batayi sai da ta nuna alhinin tafiyar tasu, dan kullum sai sun shiga sun gaidata sau uku a rana babu fashi.        Duk yanda Zinneerah ke share hawaye AK na kallonta ta mirror. Yay ɗan murmushi yana cizar lip ɗinsa dan yau kam yasan ango yake tunda Mahma ta ɗaure mata ƙugu sai da tai arba'in duk da ba haihuwa tayi da kanta ba.       Baisan Mahma ta masa wayo bane tanata gyare masa Zinneerah ɗin a ɓoye. Ga gyaran Hajiya Falmata datake ɗorata a layi, hakama Hajiya Iya kullum cikin faɗa mata dabaru takeyi. Ita kanta tasan idan taje hannun boss din nata sai ta yabama aya zaƙinta. Shiyyasa yau duk take a tsure.    Kasancewar da little ya tafi suna wucewa mai ƙunshin da zatai mata tana isowa. Ƙunshi akai mata na gani na faɗa na jan lalle da baƙi, Yaya Karima ta yarfa mata kitso kananu da ya fiddo mata ƙyawunta sosai musamman yanzu data yi wani bulɓul da ita tamkar ba itace tasha fama da rama lokacin cikin ƴan biyu ba.         Kasancewar basu zauna wasaba kamar wasa kafin la'asar suka kammala komai tai fes da ita. Dama tunda ta fara zaman jegon nan take dilke jikinta da kayan gyaran fata na musamman da Hajiya Falmata ta haɗa mata ga kuma na Mahma. A gurguje ta shiga gyaran sashe. AK duk da bawani ƙura yayi ba. Sai da ta tsaftace komai yay mata yanda takeso ta baje kalolin ƙamshinta masu rikitashi. Sanda ta dawo sashenta ma su Mama A'i sun gyare ko ina sai ƙamshi yake.        Waya tai zamanyi da AK ɗin taji kosun taho. amma yace mata yana dai shirin tahowar. Taji daɗin haka dan ta samu damar shiga kitchen kenan ta haɗa abinci da kanta. Dan tunda ta fara zaman jegon nan kullum cikin ƙorafi yake akan abinci, idan kaji baiyi maganaba Mahma ce tai girki da kanta saboda shi.      Lafiyayyen abinci ta shirya masa da tasan zai gamsar dashi. Tare da haɗaɗen shayin barnawa daga Hajiya Falmata da kalolin kayan sha na zoɓo da kunun aya. Suna kammalawa dan da taimakon Mama A'i tayi ta bar mata idawa bayan ta ɗiba na AK takai sashensa.       Wanka takeson shiga Amaan ya wani saka kuka shi a dole yunwa yakeji. Ɗaukarsa tai tana dungurinsa da kiransa acici like Daddynsa. Tana gama bashi a tsaitsaye itama Anam ta saka tata rigimar. Kanta ta dafe da amsarta Yaya Gajeje na dariya. “Wai yaran nan mi kuke son maidani ne halan? Ku gama naku shima yazo ya isheni da tasa rigimar”.         “Ai daidai kenan”. Cewar Yaya Gajeje tana dariya. Murmushin jin kunya Zinneerah tayi da ajiye Anam din ta shige cikin dan watsa ruwa...........✍ *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_* *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* _______________________ *Page 68* ..........Sai da Zinneerah ta fara gabatar da sallar magrib bayan fitowarta wanka sannan ta zauna ta tsara kwalliya ƴar gaske, tare da baje lungu da saƙo na jikinta da ƙamshin mayun turarurrukan ta sabbin haɗi daga Hajiya Falmata. Ta ɗakko less da yaji ɗinki mai ƙyau da tsari ta saka tare da kashe kan ɗauri. Awarwaraye da sarƙa ta zuba kai kace wani biki zata. Ta sake ɗorawa da wasu turarurrukan sannan tai zaman sallar isha'i. ALLAH ya sota ƴan biyu suna goye a bayan Yaya Gajeje da Mama A'i.        Sauri-sauri ta kammala ganin har isha'i su AK basu shigoba. Koda ta fito su Yaya Gajeje wani ihun dariya suka ɗauka da yaba wannan wanka nata. Kunya tasata jan mayafi ya rufe fuskarta.       Mama A'i da yake itama a ce, babu yawan magana sai lalata tace, “A'a wannan gayun bai kamata ki kaisa turaka ke kaɗai ba. Bara na ɗakkoma su Alhaji ƙarami kaya a canja musu suma dasu za'a”.        “Wannan zance nakan hanaya Mma A'i”. Yaya Karima ta faɗa tana dariya. Zinneerah ta tura baki kaɗan tana faɗin, “Gaskiya nai dai a'a, salon su batamin gayu”.       “Iyee, lallai Zinni binni ta buɗe miki ido da baki, a gabana babu kunya”. Cewar Yaya gajeje tana riƙe haɓa.      Dariya Zinneerah ta shiga kwasa. Ta faɗa ɗaki tanayi da faɗin, “Yi haƙuri Yaya gajeje na tuba”.    Suma dai dariyar suke tayata harta ɗakko kayan da za'a canjama ƴan biyu. Su Mama A'i suka shiryasu tsaf sannan Zinneerah ta kwashesu. Dan Yaya Gajeje korata tai wai ta tafi can yazo ya sameta zaifi jin dadi. Su Yaya Gajeje tsoffin masoyane da sukasan takan maza da muhimmancin irin wannan ranar. Aiko shawararsu Zinneerah ta bi. Dan dama itama akwai nata shirin a ƙasa.           AK bai shigo gidan ba sai wajen tara da rabi na dare. A gajiye yake matuƙa. Dan haka kai tsaye ya nufi sashem Zinneerah ɗauke da little dayay barci. A falon farko ya samesu dan sunfi zama nan, kai shi baima taɓa samunsu a falon ciki ba dan daga shi sai Zinneerah ɗin ke shigarsa da bedroom dinta na ciki, saiko little.      Mama A'i ta mike tana amsar little ɗin da masa sannu da zuwa. Suma su Yaya Gajeje sannun suke masa. Cike da mutuntawa yake amsa su yana baza idon ganin ta inda Zinneerah zata ɓullo da twins nashi. Ganin dai babu alamarta ya sashi leƙa Inna sannan ya fice.     Gulmarsa su Yaya Karima suka shigayi suna dariya. Dan yanda yaketa kalle-kalle sunsan matarsa yake son gani, gashi su kuma sun yi gum bama su nuna sun fahimcesaba.      Shiko harya ɗan shaƙa dan ya zata abinda ya faru tsakaninsu ɗazun da safe ne ya sata fushi. Sai da ya shigo sashensa ya shaki wani mayataccen ƙamshi daya nema karar masa da man kai lokaci ɗaya sannan ya sauke ajiyar zuciya. Taku yake tamkar mara laka a jiki yana bin falon data sakama hasken wuta kaɗan da kallo. Bukatar fara wanka ta sashi nufar bedroom ɗinsa ransa fal waswasin ina ta shiga.       A bedroom ɗinma ƙamshin da yafi na falo ɗaga masa hankali ya shaƙa. Kasancewar wutar ɗakin a kashe dindim ta sashi fara lalauben makunnar fitilar. Ɗan zabura baya yayi lokacin da haske ya gauraye ko ina a ɗakin. Kyawawan idanunsa kuma sukai masa gani na musamman daya sakashi hangame baki. Zinneerah ce zaune a tsakkiyar gadon lulluɓe tamkar sabuwar amaryar da aka kawo ɗakin miji yau. gefe da gefenta Amaan da Anam ne cikin showals suna barcinsu hankali kwance suma cikin gayu.       Jiyay gaba ɗaya yana neman daburcewa da salon nata. Ya shiga takawa a hankali zuwa gaban gadon jininsa na tsinkewa tamkar manjan da yaji zafin wuta.           الْحَمْدُ للهِ الَّذِي بِنِعْمَتِهِ تَتِمُّ الصَّالِحَاتِ . *_Alhamdu lillahil-lazee bini’imatihi tatimmus-salihat._*       _Godiya ta tabbata ga ALLAH wanda saboda ni'imarsa ce kyawawan ayyuka suke cika._ اَلْحَمْدُ ِللهِ عَلَى كُلِّ حَالٍ. *_Alhamdu lillahi ala kulli halin_*      _Godiya ta tabbata ga ALLAH a cikin kowane hali._        Ya faɗa lokacin da yake kaiwa zaune bakin gadon. “Dan ALLAH ki zauna a haka karki motsa harna fito a wanka, dan wannan sirrin ya wuce na gani da ido kawai ko fatar baki”.      Zinneerah da duk take jinsa tai murmushi batare datayi ko tari ba balle ta motsa. Bai damuba shima dan mikewa kawai yay ya nufi toilet.       A yanda ya barta ɗin kuwa haka yazo ya sameta. Tsane jikinsa yake amma ya kasa daina kallonta ita da yaran daga inda yake. Turarurruka ya cuɗe jikinsa da shi da ɗaukar wando fari ƙal iya cinya ya saka da ƙaramar riga armless ya haura gadon     Zama yay a gabanta ya tanƙwashe kafafunsa suna fuskantar juna. Yasa hannayensa biyu ya kamo bakin mayafinta ya ɗaga sama ƙyaƙyƙyawan fuskarta na bayyana garesa tana neman zautashi da wani sassanyan murmushi.      Da ƙyar ya iya fisgar numfashin dake neman ƙwace masa yana wani mar-mar da idanunsa dake neman zubowa jikinta. Luuu ta ɗanyi da idanun tasa tafukan hannunta ta rufe fuskarta. Hakan da tai ya bashi damar yin tozali da ƙyaƙyƙyawan ƙunshinta.         “My Neerat zaki halakani wlhy”. Ya faɗa a wani irin sassanyan sauti da ita kanta sai da tsigar jikinta ta tashi. Hannayensa duka ya ɗaura akan nata yana janyewa daga fuskarta. Cikin idanunta ya zuba birkitattun nasa yana faɗin, “Ina ƙaunarki da yawan yawa My Neerat, zaki zautan ɗan Shira da salonki”.          Zinneerah dake amsar saƙwanninsa ta cikin idanunsa itama da wata irin muryar da batasan tanada shi bace, “أَحَبَّكَ الَّذِي أَحْبَبْتَنِي لَهُ.    *_Ahabbakal lazi ahbabtani lahu._* _Wanda ka so ni saboda Shi, kai ma Ya so ka Yayanmu. Kuma nima ina ƙaunarka”_.         Gaba dayanta ya cacumo jikinsa ya rungumeta tamkar zai cusata a fata da ɓargon jikin nasa gaba ɗaya. Cikin fisgar numfashi ya shiga laluben bakinta ya manne a cikin nashi jikinsa na wani irin tsuma na zalamar son kasancewa da ita. Bata iya ta hanashi ba. Sai ma haɗin kai data shiga bashi.     Sai da labarin ya nema yin nisa kuma tsoro ya kamata, dan gasu Anam a gadon karsu taushesu. cikin taimakon da ALLAH yay mata sai Amaan ya farka da kuka. Da ƙyar AK ya iya sakinta yana cizar lip. Itama ta mike da ƙyar daga jikinsa dan tunaninta kar hayesa sukai. Ganin babu abinda ya samesa ya sakata sauke ajiyar zuciya da hararsa. “Ɗan ɗagwai na zatama hayeka akai”.        Idanu Ak ya buɗe da ƙyar yana duban inda Amaan ɗin yake. Kafin ya yunƙura da ƙyar ya matsa garesa yana dungure masa kai. “Haka kawai ka ɓatamin wasa. Shiyyasama bana Baffan da kai yaro”.     Murmushi Zinneerah dake kallonsu tayi, ta sauka ƙasa gaba ɗaya tana kai hannu ta ɗaukesa dan tasan yunwa yakeji. Komawa AK yayi ya kwanta dan cikinsa ya ƙulle tamau. Har Zinneerah ta gama shayar da Amaan ta maidashi ta kwantar sannan ta dubesa.      “Yayanmu ga abinci fa a falo kar dare ya ƙara zurfi”.     Lumsassun idanunsa ya buɗe a kanta. Akan laɓɓansa da ƙyar ya furta, “Ke kaɗai kin wadatar dani”.     Dariya zancen nasa ya bata dan tasan dai shi da abinci sai ta ALLAH. Ta miƙe tana fadin, “Nidai daka daure kaci bara na kai su Anam ai musu shirin barci. Uffan bai iya ce mataba harta fice a ɗakin. Bai kuma iya motsawa ba yana a inda ta barsa har kusan mintuna talatin sai gata ta shigo ɗauke da tea. Ajiye masa tai tana faɗin, “Ga tea nanto Yayanmu bara na ɗakkosu.”     Bai motsaba bai kumayi magana ba harta sake ficewa yanzu ma. Bata jimaba yanzu ta dawo ɗauke da ɗan gadon su Amaan. Ta ajiye ta koma falonsa inda Mama A'i ta rakota da yaran ta amso su sannan tai mata sai da safe dan tama su Yaya Karima sallama.        Jin ta dawo tana kwantar dasu ya sashi miƙewa da ƙyar zaune. Kofin tea ɗin ya ɗauka ya hau sha dan da gaske yanajin yunwar ma. Sai dai duk inda tai yana binta da kallo harta gama hidimar yaran tai musu addu'a. Dan ma sanye take da zumbulelen hijjabi a saman kayan barcinta.     Sai da ya kammala yaje yay brush itama taje tayo dan ta kimtso kanta daga can, alwala kawai tayo da brush ɗin ta fito. Tsugunne gaban gadon su Anam ta samesa yana musu addu'a fuskarsa ɗauke da murmushi yana faman shafa kawunan yaran. Ta zare hijjab ɗin nata tana nufar falo ɗakko ruwa duk da ta tabbatar sai yaci abincin nan ko zuwa anjima ne.     Da kallo ya bita harta fice. Ya sauke ajiyar zuciya yana mikewa daga wajen su Amaan ɗin.     Tsaye ta samesa gaban mirror yana saka turare. Tana ajiye ruwan ta juyo da nufin masa magana taji anyi cak da ita sai gado. A tare ya faɗa da su yana magana cikin kuneneta. “Wai sokike dai sai na miki kuka yarinyarnan. Sai wani ƙwalele kikemin ni da kayana”.     Siririyar dariyar data nema zautashi ta saki tana cusa kanta a wuyansa da shaƙar ƙamshinsa itama. Babu shiri ya lalubo bakinta dake ƙamshin strawberry freshener ya manna nasa a ciki. A zalame yake, dan haka cikin zalamar ya shiga sarrafata shima, itama kuma tana amsarsa da zalamar dan koba komai tayi kewa.      Sai da tafiya tai nisa sosai ta gama shagala a hannunsa da salonsa sai ga idon madam ya raina fata ta koma raki daga karshe. Inama AK ke wani jinta shi a wannan yanayin. Sai da ya more duk ƙwalelen kwanakin da akai masa shima sannan ya koma lallashi yana mata dariyan mugunta.     Kamar yanda tai hasashe kuwa suna kimtsa jikinsu sai da yaci abinci waishi duk ta sakashi jin yunwa. Murmushi kawai ta dingayi dan dai al'amarin nasa yakanfi ƙarfinta wani lokacin, babu abinda ya damesa ɓaro mata zance yake kansa tsaye kamar ba yayansun nan sarkin mazurai da tsare gida ba. A yanzu haka idan su Jamal na tsogumi akansa sai taita dariya kawai dan tasan dai mazuran iya na waje ne. Itama dai sai da tacin danya tsiyayeta tas ga yaransa a gefe da nasu suma.       A tsakanin dare zuwa safiya dai sai da Zinneerah ta raina kanta a hannun AK, dan babu kunya ya hanata komawa sashenta yinin ranar shima kuma bai fita ko inaba sai massallaci. Sai dai taje ta ɗauka abu a sashenta ta dawo, su ƴan biyu kam ko ƙofar ɗaki basu jeba suna nane da shi harda little da tunda gari ya waye shima ya taho nan ya tare. Sai da zai wuce islamiyya.        Babu abinda suke zubawa sai zallar soyayya da nunama juna tsantsar ƙauna a wannan yini. Duk wani motsinta idonsa na kanta. kamar yanda itama dai ta murje nata idon take masa komai dai-dai da buƙatarsa. Sai ta gama ta koma sinne kai wai ita kunya. Hakan na birgesa da sakashi a nishaɗi, dan ji yake tamkar yayi gamo da sabuwar budurwa a haɗuwar farko.      Washe gari ma duk da ayyukan dake a gabansa tari-tari haka ya lalace wajenta sai bayan azhar ya shirya ya fita. Magribar fari sai gashi ya dawo. Sakawa yay ta shirya ita da yara ya fita dasu wani haɗaɗen joint ɗin cin ƙwalam da maƙulashe, suka shawo ice-creem. Yana ɗauke da Anam tana ɗauke da Amaan. Little na riƙe da ɗayan hannunsa abin sha'awa. Mutane sai kallonsu suke abin birgewa, dan shi kam rashin zamansa a ƙasar sosai yasa bawani saninsa akai a fuskaba da yawa. Sunansa yafi fuskarsa fita ga kunnuwan jama'a. Ganin yanda ake kallon nasu sai kishi ya kamasa ya kuma dinga ɓata fuska. Itama kuma madam ɗin nasa sai kishin ya rufeta ruf saboda yanda ƴan matan wajen ke rawar kai gaban samari dama irinsu AK ɗin duk da suna ganinsu tare da iyalansu (Ƴammata a yi haƙuri inaji daku😂😹😹🙏🏻). Haka dai suka kasance a daddafe a wajen danma vip suke zaune. Daga nan wajen wasan yara suka kai Little dan duk akwai a wajen duk da dare ne. Ya ɗan hau abubuwa yana maijin nishaɗi harda rigimarsa ta aɗora su Anam. Zinneerah tace wlhy bata yardaba. Bata gama dawowa daga maganin naƙudaba ba'a sata kuka. Maganarnan ta bama AK dariya. Ya dubeta fuska ɗauke da murmushi har haƙwaransa na bayyana yace, “Haba karki bada mata mana madam, ni har ina murna na sake jefa ƙwallo tsakanin jiya da yau”. Cikin ƙwaɓe fuska tace, “Wayyo ALLAH Yayanmu dan ALLAH daina min fatan nan ka tausaya min”. Nanma ƴar dariya yayi da sumbatar goshin Anam dake a hannunsa. “My Sweetheart kinji Mamin ku zata mana buƙulun gambo ko? Ku faɗa mata ku kuna son ƙani da wuri Mammah da Mahma, badan kar ace na cika son kai ba sai nace a haɗo da Uncle Ahmad duk lokaci ɗaya, daga baya sai a bani Mommy na da Gwaggo da Baba suma, sai Abbah kuma ya zama auta”. Yanda tai sagade tana kallonsa baki a hangame ya sashi dungure mata kai. “Kallon fa?”. Kai tsaye tace, “Na tsoro da al'ajabi ne ai. Ƴaƴa bakwai fa kake lissafi daga gama arba'in Daddyn Little”. “Oh kinma ɗauka ni na wasane kenan. Yarinya shirya da ƙyau Shirawa yawa suke son ƙarawa, mu babu ruwanmu da wani tsarin iyali”. “Aiko na rantse yaji zanzo nayi, danya zan tafi sai nayi wata uku acan”. Dariya sosai yakeyi yanzu kam. Yace, “Ai wlhy Baba koromin ke zaiyi, kije wajen Granny kuma kin kai kanki, dan ba ɗaga ƙafa zanba harcan zan biki, gara-garama wajen gwaggo, zanji kunya. Amm nasan itama koroki zatai”. A ranta tace, (Zaka iya wlhy Yayanmu) a fili kam cewa tai, “Wannan zance yafi ƙarfina karka lalatani da ƙarancin shekaruna gaskiya”. “Lalacewa kuma ta yaushe yarinya, tunda ga ƴan biyuna a hannu ina kallonsu inajin daɗin raina su da babban Yaya takwaran Daddynsa. Zaki gane kuranki bara mu koma gida”. Jin haka ya sata yin ɓam da bakinta. Shiko ya samu na tsokana har suka bar wajen bayan yama su Yaya Gajeje takeaway ɗin tasu tsaraban na kayan ƙwaɗayi...........✍ *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_*  *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* _______________________ *Page 69* ...........Rayuwa ta cigaba da tafiya cikin farin ciki gasu Zinneerah, babu abinda zatacema ALLAH dasu Hajiya iya sai godiya, dan itakam sun bata ƙyauta da har abadan bazata daina alfahari da tutuiya dasu ba. Kwananta goma dayin arba'i su yaya Gajeje suka shirya komawa Danya, duk da dai Inna bata warke bane sarai Alhmdllh jikinta yayi sauƙi sosai, dan kullum sai Dr Mahmud yazo safe da dare ya sake dubata. Tana ɗan magana da motsa jikinta, tafiya ce dai babu kam kafafun zuwa gidan malamai sun mutu.      A ɗan zaman nan gidan Zinneerah babu fashi kullum sai tayi kuka. Musamman idan AK ya shiga ya gaisheta ko aka kawo wani lafiyayyen abinci aka bata, ko Zinneerah ta shiga da yaranta abin sha'awa gaisheta. Balle ta zauna dan su ɗanyi hira ta dinga haɗiyar zuciya kenan kamar budiddigin ƙwaɗo. Little kam baya minti goma bai shiga ɗakin ba inhar yana gida. Dole kuma take kulashi saboda shi babu ruwansa haye mata jiki yake, sai ma idan Zinneerah ta ganine taita masa faɗan karya ƙarisa mata uwa, daya faki ido kuma zai sake komawa, ko ganinta a zaunen ne shike ɗaukar masa hankali oho😂..            A dalilin zaman Inna maman sadiq kuma tazo gidan sau kusan uku dubata ita da mmn halima. Na kusan ƙarshene sukazo harda mmn sakina da matar naziru da ayanzu suketa zuminci da Khalipha, dan sun zama abokai tunda ba wani girman Khalipha ɗin yayba shima auren gata ne Abba dama yay masa.     Shatara ta arziƙi AK da Dr Mahmud suka haɗa musu, sannan kuma suka tafi gaba ɗayansu musu rakkiya harda AK da Dr Mahmud dan sunason zuwa su gaida Baba duk da baima jima da zuwa ya dubata ba shi da ƴan uwansa, sai su Meenal da suka maƙale. Tarba suka samu mai ban mamaki daga amaryar baba da dangi, kowa yana sambarka da ƴan biyun Zinneerah dan hada yawon arba'in duk ta haɗa tazo. Ga Sa'a ma na fama da nata laulayin cikin sai fatan sauka lafiya.       Anan su AK suka barsu zasu kwana biyu, ya juya shi dasu Jamal da Dr Mahmud kowa na kewar matarsa. Da farko little ya maƙale binsu zaiyi, mi kuma ya gani harya shiga motar tama ɗakko masa kayansa sai cayay kuma zai zauna wajan su Anam indai badasu za'a koma Kano ba.               Kwanansu huɗu a Danya Zinneerah da Sa'a suka shiga lungu da saƙo gaida ƴan uwa da abokan arziƙi, duk inda suka gitta sha'awarsu ake ana san barka dan sun zama abin kwatance ga kowa. Alkairi kam duk inda suka shiga sukan ajiye gwargwadon ƙarfinsu su wuce ana saka musu albarka. Baba kansa yana cikin farin ciki da kasancewar ƴaƴansa cikin kwanciyar hankali. Mutane nata zuwa ganin Inna ana yadda mata habaici akan ga wadda ta tsana da gallazamawa nan ta zama silar samun lafiyarta ai.       Babu bakin magana ga Inna Asabe danya musu murus, sai kukan zuci da haɗiyar zuciya kawai.     Randa suka cika kwanaki huɗu babu daɗi babu ƙari sai ga Moos'ab yazo kwasarsu. Zinneerah bataso hakaba dan catake zaiyi haƙuri sukai 1week ɗin data roƙa. Amma hakanma sun gode dan batai zaton zai bari ba. Aiko data dawo tasha mitar shi an barsa shi kaɗai a gida kamar mara gata.          Dariya ta dinga masa da bashi haƙuri. daga ƙarshe tabi hanyar data dace wajen lallashin abinta. Gaba ɗaya gidan yanzu sai take jinsa wani iri da duk suka tafi, sauƙinma ta taho da ɗiyar Yaya gajeje zata ɗan mata hutu mai suna Saliha. Yarinya ce ƙyaƙyƙyawa kuma nutsatstsiya, shekaranta goma kwata-kwata. Tarbiyan yarinyar yasa ta shiga ran AK yace makaranta zai nema mata dan tazo kenan bazata komaba. Sosai Zinneerah taji daɗin hakan kuwa taita masa godiya.          Bayan sati uku da dawowarsu daga Danya da ƙyar ya barta taje Minna wajen Gwaggo Maryama. Aiko taji daɗin wannan zuwa harda ƴar ƙwallarta. Kwanansu biyu acan suka dawo, Hajiya iya ta sake jajubarta suka tafi bauchi. AK nata fushi batabi takansaba tace yawan arba'in Zinneerah keyi dana aure daya hanata yi.                 Yama zai yi da tsohuwarnan inba yay gum da bakinsaba. Dan yana tankawa zatama iya ƙwaƙulo wasu dangin a wani garin tace Zinneerah taje. Satinsu ɗaya a can suka dawo. Shima kuma sai ya fara musu shirin zuwa Morocco daga can zasu wuce London su ɗan huta tunda little sun sami hutu. Fatansa kuma ya tarkato su Mammah su dawo a maida aurenta da baffah tunda yaga sun sakko an daina faɗan masoya saita waya idan sun kira juna da nufin gaisuwa. Mahma kuwa gida zai saya mata tai zamanta kusa dasu.   *_MOROCCO_*    Wannan shine karon farko na zuwan Zinneerah dangin kakarsu AK, tako sami tarba ta mutunci ga mutanen har taita mamaki, yaranta kowa yana nuna musu so da ƙauna abin birgewa. Yaran Mahma kuwa kamar sun santa dama can, dan janta suka dingayi a jiki ita dasu little. Magana kuwa sai da turanci, waɗanda basaji sai larabci sai dai ake musu tafinta da Zinneerah dan ita dai ba iyawa taiba sai abinda ba'a rasaba na islamiyya, wanda bai wuce gaisuwa ba da kalmomi.      Satinsu ɗaya cif suka wuce london cike da kewarsu, inda acanma suka sami tarba ga Mahma da Mammah. Kwanansu biyu da isowa Adilah da Huzaifa suka iso suma. Ai fa sai gida ya kacame da farin ciki bakin Mammah tamkar zai yage dan farin ciki. dan itama Adilah fama take da ciki harya fito abinsa.     Sunsha hutu da soyayyarsu a london kafin su tattaro kuma su dawo gida dansu little sun koma school. Satinsu biyu da dawowa aka maida auren Mammah da Baffah.         Zo kaga farin ciki wajen yaran gidan, dan koba komai AK ya cancanci su girmama mahaifiyarsa su kuma sota dan shima yana girmama nasu. Ba'a wani tsaya ja'inja ba Mammah ta tarkato kayanta ta dawo Nigeria gidan masoyinta bisa rakkiyar dangin mahaifinsu.             Aiko sai ga baffah da mammah an ƙara shimfiɗa sabuwar soyayya, ita da abokan zamanta kuwa sai dai sambarka. Dan tana ƙoƙarin danne kishinta kamar yanda suma suke danne nasu kodan yara da nasihar da hajiya iya ke musu kullum babu gajiyawa. Dan babu abinda zatace da UBANGIJI sai godiya na sake haɗe mata kan family ɗinta da yayi, bayan gwagarmaya da jarabawar data sha a shekarun baya wajen ganin ta haɗesu waje guda hakan bai samuba sai da iyaka tazo.     Mahma kuma AK ya saya mata gida anan kusa dasu, da yake mutumce maison jama'a saita tarkato ƴaƴan dangi daga kaita dansu tayata zama. ★★★         Daga haka rayuwa ta cigaba da turawa Zinneerah na cigaba dama AK naci akan dawowar Farah. Duk da yana ɓata mata rai haka take sake dawowa ta ƙara masa maganar.      Sai gashi a wasa-wasa dai sai da Farah da Zakiyya suka cika shekaru biyu cif da maimartaba ya basu. Zuwa lokacin ƴan biyu babu inda basa zuwa da kafafunsu, yara sunyi ɓul dasu masha ALLAH ga wayo dan sun hau karatun little.      Naci Zinneerah ta cigaba da masa akan dawowar Farah ɗin yana basar da ita har sai da ta ƙara wata uku akan shekara biyun mai martaba sannan yace mata zaije. Amma babu rana.     Wannan maganar tasata tunkarar hajiya iya da batun da Baffah a karo na farko. Albarka suka dinga saka mata. Uncle Ahmad yace insha ALLAH da kansa zaije ya ɗakko Farah ɗin. ★__________★      Aiko kamar yanda Uncle Ahmad yay alƙawari bayan sati guda da wannan zance batare da sanin AK ba sai gashi tare da Farah. Lokacin suna a barandar gidan su duka da yammaci iskar la'asar na kaɗasu. Boss na zaune yana harkar business ɗinsa a lap-top duk da ma su Anam na hanashi, dan sai hawa masa jiki suke suna ƙirniya. Zinneerah na gefensa tana koyama Little homework.         Duban Zinneerah yay yana nuna mata Anam data haye masa dokin wuya. “Mami kizo ki ɗauke kakarnan taki kona jehota ƙasa ta isheni ALLAH, ta hanani aiki”.      Dariya Zinneerah tai saboda yanda yay maganar a marairaice tana kallon uban da ƴar. Tace, “Idan ka jeho Granny ƙasa aiko ka koma Morocco da ƙafa dan takwararta ba ɗaga maka ƙafa zatai ba”.      Murmushi yay yana sauke Anam ɗin da faɗin, “Madam rikici ba, ai saita saukemin Nigeria a kaina wlhy. Inaga dai bara na haƙura da aikin nan kawai dan ba barina zasuyi ba, shi baffah ma neman rikitamin system ɗin yake”.      Little daketa tunzura baki gaba ya gaji da homework ɗin yace, “Daddy na ɗakko ball muyi?”.        “Kokuma kakan ball ɗin ba”. Zinneerah ta faɗa tana nuna masa littafin gabansa. sake tunzura bakin yay yana kallon AK kamar zai kuka. Yanda yay ɗin ya bama AK dariya. Shima sai ya duba zinneerah yana marairaicewa kamar yanda little yayi. “Mami a tausaya mana a barmu mu huta. Itafa bokon nan iyakarta duniya, kuma mu ba dangin mango park ba”.           Ta buɗe baki zata bashi amsa motar Uncle Ahmad dake tare da Khalipha da Farah ta shigo gidan. Shi AK da farko ma ya zata ko Suhail ne babban ɗan Uncle Ahmad ɗin dan nan ɗin gidan zuwansa ne sosai tunda ya baro Turkey. Dan haka yayma Zinneerah nuni da hijjab ɗinta dake gefe dama ajiye. Sai da yaga Khalipha ya fito da Uncle Ahmad ɗin ya sashi miƙewa tsaye babu shiri. Yana ƙoƙarin nufarsu Farah ta fito a motar. Ta rame sosai ta canja tamkar ba itaba. A take fara'ar fuskar AK ta ɓace ɓat. Sai dai babu damar magana saboda Uncle Ahmad.         Sannu da zuwa Zinneerah taketa musu fuskarta ɗauke da murmushi. Uncle Ahmad ya ɗauka little yana faɗin, “Uhm babana zoka samin albarka”.     Shima Khalipha sai ya ɗauka Amaan yace, “Nima taho samin tawa albarkar babana tunda abin hakane”. Dariya aka sanya musamman da Anam taje jikin AK itama ta maƙale. Shi dai ko murmushi baiyiba.      Ita dai Zinneerah nufar Farah dake kallonsu tamkar tana hawayema tayi tana mata sannu da zuwa cikin fara'a. Yanda ta amsa mata kamar a kunyace sai ta bata mamaki, ta kama hannunta sukabi bayan su AK ɗin da har sun shige ciki.      Sashen AK suka nufa, sai da ta raka Farah sannan ta dawo ta koma sashenta tasa Saliha haɗa abin sha da motsa baki takai musu, ita kuma ta ɗauka abincinsu na dare da aka girka gaba ɗaya ta nufi sashen nasa. Ta iske Khalipha nata tsokanar Saliha dan mutuniyarsa ce sosai. Bayan ta gama zata wuce ta kirata tazo ta tattara yaran suje. Ɗaukar Anam tayi da tisa ƙeyar little da Amaan suka fita. Itama ta gama shirya abincin a dining zata fita Uncle Ahmad ya dakatar da ita.        “Dawo ki zauna Inno ai maganar ta shafeki kema”. Dawowa tai babu musu ta zauna.          Bayan Uncle Ahmad ya buɗe taron da addu'a ya fara musu da nasiha mai ratsa jiki, kafin ya duba AK da yay kicin-kicin da rai. “Abdul-Mutallab ayi haƙuri, a cigaba da haƙuri a ƙara haƙuri. Ita ƙaddara haka take babu abinda ya isa tsaidata ga bawa. UBANGIJI ya riga ya hukunta faruwar hakan a garemu tilas. Hakan jarabawa ce. Maganar tone-tone bama ta tasoba tunda anyi komai ya wuce sai ayi haƙuri kuma a sake kafa sabuwar rayuwa. Ga Farah nan ta dawo cikin iyalinka. Ina fatan zaku manta da komai ku ringumi junanku kuyi haƙuri. Darajar haƙurin da zakuyi sai ALLAH ya ƙara muku kwanciyar hankali da farin ciki kaji”.        Kan AK a ƙasa yace, “Dady taya zan zauna da wadda bata amshi laifinta ba, girman kai ya hanata neman yafiya ga wadda suka zalunta duk da rawar gani data taka wajen hana katsewar igiyar aurenta”.      Shashshekar kukan Farah ne ya fito, tace, “Wlhy ba girman kai ya hanani neman gafarar Zinneerah ba kunya ce kawai da nauyin girman laifin da aka aikata mata, duk da ALLAH shine shaidata ban sanma wadda aka sakama ciki ba. Amma inajin nadama da kaico da kawunanmu saboda son zuciya. Zinneerah ki yafe mana domin ALLAH badan halinmu ba. Duk da nasan munzo a makare ga neman gafarar taki. Amma dan girman ALLAH ki gafarcemu, gwiyawunmu bisa ƙasa........”       Sauron katseta Zinneerah tai da faɗin, “Haba aunty Farah, wlhy ni ban rikeku ba tun a waccan ranar komai ya wuce a gareni. Sai dai muyi fatan ALLAH ya yafe mana baki ɗaya. Ya kuma bamu zaman lafiya da haƙuri da juna”.       Da amin duk suka amsa. Yayin da AK ya ballama Zinneerah harara. Murmushi kawai tayi ta ɗauke kanta. Shima AK ɗin gafararsa Farah ta nema, duk da dai bai kulataba bai kumace uffanba. Uncle Ahmad dai ya ɗora musu da sabuwar nasiha data ƙara sanyaya jikinsu.     Da ga ƙarshe ya rufe taron da addu'a suka tattara suka tafi aka bar Farah anan.        Tashi Zinneerah tai zata barsu AK ya dakatar da ita wai ta haɗa masa ruwan wanka. Kafinma ta nufi ɗakin shi ya shige. sai taji duk babu daɗi ga Farah zaune ko kallonta baiyiba.       Tayi tunanin Farah zata ɓata rai, sai taga kawai ta bisa da kallo tana murmushi da share hawaye a kaikaice. Ta maido dubanta ga Zinneerah datai shiru kanta a ƙasa ta kasa tashi. “Mamin Abdul kije karya ga kin ɓata masa lokaci, sai dai ki sake roƙamin shi gafara dan ALLAH, da kuma keys ɗin sashena”.        “Kiyi haƙuri dan ALLAH aunty Farah komai zai wuce. Kinsan dai halinsa kinma fini sani. Keys kuma suna wajena ma bara na ɗauka miki”. Tai maganar tana nufar hanyar ƙofar fita. Da sauri Farah ta dakatar da ita tana miƙewa. “A'a kinga jeki ki cika umarninsa zanje na jiraki a general falo”.         Kai Zinneerah ta kaɗa mata kawai cike dajin nauyi ta nufi ɗakin nasa. A cike fam ta iske AK da haushi. Kamar jira yake tana shigowa ya balbaleta da masifa wai ta wulakantasa bayan ya faɗa mata bukatarsa. Hankalintane ya tashi dan faɗa sosai yakeyi.        Ganin abin karya juye mata yasata faɗawa jikinsa ta manne bakinsu waje guda ta shiga lallashi ta hanyar da yafi buƙata. Ai ko saigashi yay bulum harma yana neman zurmawa. Da ƙyar ta ƙwace kanta ta na masa dariya. Ƙwafa yay da fadin, “Zan kamaki ne ai, zakimin bayani dalla-dalla tunda na fara zama abokin wasanki”.     Ita dai shigewa toilet tai tana masa dariya.      Da taimakon su Saliha Farah ta gyara sashenta, Zinneerah takai mata abinci da kanta tana sake mata sannu da zuwa. Dan harda yara taje mata. Jawosu Farah tai jikinta ta rungume ƙwalla na cika mata ido. Little kam daga jikin Zinneerah ya makale yana gaisheta. Duk yanda taso yazo gareta yaƙi dole ta haƙura. Anan ta bar mata Amaan da Anam suka fita ita da little tana masa faɗa.         Buɗar bakin yaron nan sai cewa yay, “Mami ni bana sonta...”.  Baima rufe bakiba ta make bakin har yana fashewa. Ta shiga masa masifar da ta kai har AK dake falonsa fitowa dan suna a general falo ne tsaye.        Kallon yanda bakin little din ke jini yana kuka yayi. “Lafiya? miya miki haka harda fasa baki?”.        Ranta a ɓace tace, “Idanma ya sake maimaita abinda ya faɗa wlhy haƙwaran zan zubar ƙasa. Dalla matsamin na wuce mara mutunci”. Ta faɗa tana turesa tai shigewarta sashenta.       Da kallo AK ya bita ransa a ɓace, dan ya tsani ana dukar masa yara itama kuma ta sani, yakance ko laifi sukai ta zaunar dasu ta musu nasiha bawai dukaba dan baya magani. Hannun little ɗin ya kama suka shige sashensa yana tambayarsa miyayi mata?.      Abinka ga yaro saiya maimaita abinda ya fadama Farah ɗin. Faɗa shima yay masa da nasiha akan karya sake itama Momy ce. Yaron sai yace bazai sakeba ya kuma bashi haƙuri. Tare da cewa bara yaje itama Mami ya bata haƙuri.      Cayay ya barta idan sun dawo salla saiya rakashi ya bata. Haka kuwa akai bayan sun dawo salla sashen Zinneerah ɗin suka shiga shi da little. Acan ɗakinta na ƙurya suka sameta ita da Saliha suna magana. Saliha ta gaishesa ta fice. Zama yay bakin gado little kuma yaje gabanta ya durƙusa. “Mami kiyi haƙuri bazan sakeba dan ALLAH”.     Shiru tai masa tamkar batajiba sai da AK ɗin yace tunda ya baki haƙuri ba kuma sai ya wuce ba.       “Yayanmu so kake na haƙura gobe ya sake kenan? Shi ɗan karamin nan dashi har yasan wani cewa baya son mutum?”.       Kuka little yasa mata yana ƙara bata haƙuri hannayensa riƙe da kunnuwansa. Nanma dai baki AK ɗin yasa harta haƙura. Little ya fita ya barsu a ɗakin saboda aikansa da tayi wajen Saliha.       Mikewa tai tana ninke abin sallar da take kai zaune, AK dake binta da kallo yace, “Kemafa masifanki yayi yawa”.      Baki ta kumbura gaba amma batace komai ba. Hakan yasa AK kamota ta faɗo jikinsa. Lips ɗinta ya ɗalla da yatsunsa yana faɗin, “Dan wulakancin kin fasamin bakin yaro harda jini”.     Murmushi tayi tana cusa kanta a ƙirjinsa da faɗin, “Kaga gobe idan zaima wani rashin kunya sai ya tuna da wannan ai”.       “Uhmyim, to ai ba ƙyaleki zanyiba sai na rama masa”. Yay maganar yana ɗaura lips ɗinsa kan nata. Daga hukunci aka zarce soyayya. Daga karshe dai sai da aka kai gayin wanka...........✍      *_Dan ALLAH ku saka ɗan uwana addu'oinki na yinin yau, ya ɓata an rasa inda yake kuma babu labarinsa. ALLAH ya bayyanashi, ya karama mahaifiyarsa damu nutsuwa. Ya kuma tsaresa a duk inda yake. Ya bashi kariya daga abokan banza ko miyagun mutane. Tare da sauran al'ummar musulmi baki ɗaya_*😭🙏🏻 *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_* *_TYPING📲_* *_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* _______________________ *Page 70 End😭🙏🏻* ...........Iya ƙokari Zinneerah yi take akan ganin zaman AK da Farah ya dai-daita, dan sai faman fushi yake har yanzu. Itama idan tai maganar sai ya hau fushin da ita. Ya hana taje ɗakinsa balle ta amshi girki. Gudun shiga haƙƙinta yasa Zinneerah riƙa ƙin zuwa ɗakinsa duk bayan kwana biyu, zatai girki ta kuma gyara masa sashinsa amma bata yarda ta kwana ba duk iya masifar da zaiyi. Dan har cikin ransa haushin Farah da yakeji akan al'amarin nan yaƙi barinsa.       Randa ya fahimci take-taken Zinneerah yayi mata faɗa kamar zai cinyeta, uffa batace da shiba saima kuka da taci. Washe gari sai ya tsiri tafiya Lagos. Kwanansa biyu ya dawo ran girkinta.       Duk da taji haushin hakan da yayi saita sharesa ta amshesa kamar yanda ta saba daya dawo. Takumabi hanyoyin daya dace ta bashi haƙuri da ƙara roƙonsa akan ya mance komai. A lokacin tana lafe jikinsa.       Cikin lallashi tace, “Yayanmu nasan daga ni har kai duk an mana laifi, amma idan mukai haƙuri muka mance da komai sai ALLAH muma ya yafe mana kurakuranmu. Shi riƙo baida amfani, sai dai ya dinga zafafa zuciyar mutun da ƙuntata ta. Dan ALLAH kayi haƙuri, wlhy nasan itama tayi nadama. Ka duba fa yanda aunty Farah ta canja tamkar ba itaba, tayi laushi fiye da zaton duk wanda ya santa”.         Guntun tsaki yaja da yunƙurawa zai tashi tai saurin riƙosa ta sake naɗe masa a jiki. “Yayanmu Please mana, i beg you”. Ta faɗa cikin tsananin raunin murya.      Dafe kansa yay da ɗan cije baki yana wani luu da idanu, aɗan hasale yace, “Wai ke miyasa bakison kiga mutum yana hutawarsa ne? Sai kin takura masa da silly zantukanki?. Idan ke zaki iya haƙura kamar bakisan ciwon kanki ba, ni bazan haƙuraba. Ban kasance mazinaci ba amma kullum ana haɗa kai da matata ana min rarraba da sperm a jikin wasu matan dama bansan su ba. Wannan wane irin son zuciya ne da yahudanci?”.          “Duk nasan ba'a ƙyautaba My Heartbeat, amma Please kayi haƙuri tunda sun amsa laifinsu kuma sunyi nadama. Kodan rahamomi da UBANGIJI yay maka kashi-kashi ciki harda yinka musulmi mai imani daya yarda da ƙaddara da jarabawa. Ya azurtaka da dukiya badan kafi saura ba, ya kuma baka ƙyaƙyƙyawar zuciya da damar sarrafa dukiyar daya baka ta tsaftatattun hanyoyi da babu saɓon UBANGIJI a ciki, wannan ma ba dabaranka bace. Ya baka lafiya a jikinka baka kasance gurgu ba, makaho, kurma ko wani abu daban ba. Zakaji sautin kiran salla, kaji na karatun alkur'ani, kaga ayoyin alkur'anin, ka taka kafarka kaje massallaci, ka daga hannayenka ka roƙa UBANGIJI bukatunka ya ɗauka ya baka babu gajiyawa. Ya cika ƙwaƙwalwar ka da ilimin addini dana zamani danka iya shiga ko'ina cikin duniya babu fargaba. Ya baka nutsuwa da tarin hankali da mutunci ga duk wanda zai mu'amulanceka koda ya fika a shekaru. Ya azurtaka da mata har biyu da ƴaƴa a lokacin da bakai zato ko tsammani ba. Ya bama Baffah da Mammah da Granny tsahon rai kanata ganinsu kanajin farin ciki. Yayanmu duk waɗanan tarin ni'imomin basu isa susa ka yafema duk wanda yay maka kuskure ba koda yakai girman duniya? Haba Yayanmu kaifa shugabane a garemu kuma uba, duk abinda kayi dashi zamuyi koyi muda ƴaƴanmu. Wlhy aunty Farah tanada ƙyawawan halaye kawai anyi amfani da wani raunintane wajen ɗaurata akan hakan. Kai mata afuwa muma sai ALLAH yayi mana. Ka haɗamu ka runguma domin gidanka ya zama tsintsiya ɗaya maɗauri ɗaya. Kagafa yanda take jan su Anam jikinta da soyayya irin ta uwa da ƴaƴa batare da nuna damuwa ba. Ina kishinta dan nima mace ce kuma inason mijina, amma wlhy ina sonta tunda har taso jinina”.     Ta ƙare maganar hawaye na silalo mata. Sake matseta yay a jikinsa yana bata wasu hot kissis data ƙara tabbatar da yes itama takai mace kuma abinso ga mijinta kuma ɗan uwanta uban ƴaƴanta. Cikin jin daɗin hakan ta sake bashi haɗin kai ya kuma tabbatar mata da ita ɗin mai darajace ta gaske a garesa.      Koda suka kimtsa jikinsu baice da ita komaiba itama batace da shi ba. Dan tasan idan miskilancin yay miskilanci toshi baya magana da baki sai dai a aikace. Murzar da yay mata yanzu kuma itace amsar komai da furucin bakinsa gareta. Itama hakan ya wadatar da ita dan maimaita maganar bashi da wani amfani ko alfanu sai maida hannun agogo baya.         Tun daga ranar ta tattara zancen shirinsa da Farah ta watsar da su gefe kamar bata fahimtar komai. Daga ƙarshe ma cemasa tai ita Danya ma take son zuwa sake duba jikin inna dan duk ƙarshen wata sai sunje dama har da shi da yaran.     Banza yay mata akan hakan tamkar baijiba har tsahon kwanaki da sukai ɗanyi shariya da juna ita da shi itama. Sai kuma suka koma dai-dai.     Bata sake masa maganar Farah ba ta zuba musu na mujiya. Tun suna fishe-fishesu har dai takai sun shirya batare dama ta saniba. Sai ganinsu tai ana shimfiɗa shika-shikan soyayya ko kunya babu. Duk da tanajin kishi a ranta haka ta danne ta kauda ido dan karatunta na islamiyya data koma cinye mata kaso mafi yawa na zaman gidan da rana yanzu, ga kuma su Saliha da mama A'i na ɗebe mata kewa sosai.. Dama tunda Farah ta dawo gidan ta canja salon girkin gidan kwana bibbiyu, randa taƙi zuwa garesa yay masifar yay faɗan sai dai ta bashi haƙuri kawai tace ga aunty Farah nan.         Sai gashi tsakanin miji da mata sai ALLAH sun ɗinke abinsu batare data saniba. Duk da tanajin kishin mijinta haka ta cigaba da ƙoƙarin ganin ta danne kamar yanda itama Farah ke ƙoƙarin dannewa a yanzu, suna kuma girmamawa da mutunta junansu duk da ta girmeta nesa ba kusaba.         Ya zaunar dasu ya musu nasiha sosai da shimfiɗa sabbin dokoki masu tsauri a garesu. Dukansu sun amsa masa da alƙawarin kiyayewa insha ALLAH.          Tun daga nan zaman gidan ya canja salo, duk da sunajin kishin junansu haka suketa dannewa kowacce tana nuna bajintarta akan kulawa da shi da saka shaƙuwa tsakaninsu. Ashe Farah har girki ta iya iskanci ke hanata yi ko a baya. Sai gashi yanzu ta zage tanayi, tarema suke haɗuwa suyi dan haka baka iya banbance girkin wance ne inba ka ganta a turaka ba.          AK ya ɗaukesu zuwa Family house Farah ta ƙara neman gafarar su Hajiya iya. Inda acanma dai nasihar aka sake musu daɗi kamar ya halaka Mammah. Gata ta dawo gidan aurenta ga ƴaƴanta duk suna cikin kwanciyar hankali a gidan nasu auren, ga kuma ƴan jikokinta dan Adilah ma ta haihu. Itama har nasiha tai musu mai ratsa jiki da roƙonsu su haɗa kansu kar taji karta gani, su duka ƴaƴantane bazata fifita wata akan wataba.       Sunji daɗin hakan sun kuma mata godiya.      Ya kuma kaisu gidan mmn sadiq data nuna jin daɗinta sosai itama da dawowar Farah ɗin. Dan dama kullum itace ke ƙara ɗora Zinneerah a kan taita lallaɓasa har matarsa ta dawo su haɗa kai su zauna lafiya. Karta yarda ya guji matarsa akan laifinta itama wataran idan tai masa kuskure koda ba irin wannan ba zai iya gudarta. Dan duk abinda namiji ya ƙware wajen yima matarsa ta farko ke amarya kikaji daɗi har kika zuga ya ƙara fusata kema wataran sai ya aikata miki fiyema da wanda yay mata. Itama kuma ta musu nasiha ta kuma karɓi Farah hannu biyu kamar komai bai faru ba, Farah ɗinma kuma ta mutuntata da gurfana a gabanta ta nema gafararta.       Mmn sadiq tace karta damu komai ya wuce wlhy ALLAH dai ya kiyaye na gaba ya ƙara musu zaman lafiya da haƙuri da juna. Dan shi kishi tamkar jinin jiki ne ga mace, sai dai idan ta iya sararafashi zataci riba a duniya da lahira. Zafafa kishi a zuciya babu abinda yake haddasawa sai ƙunci da tarin baƙin ciki da kaucema dokokin UBANGIJI batare daka fargaba. Kaɗan daga aikin kishi ya ɗoraka a hanyar zuwa wuta ya sakeka a ciki ya kama wani kuma. Amma daka iya sarrafasa sai gaka ka tsira da mutuncinka da farin cikinka. Ka kuma zama tauraro ga mijin ga kowama, duk mai son ganin bayanka sai dai shi ya wahala kaiko ALLAH yayta ɗaga darajar ka.      Sunji daɗin nasiharta sosai sun kuma mata godiya su duka. Dan shi kansa AK daya dawo ɗaukarsu yanda ya samesu sunata wasa da dariya sai hakan ya ƙara masa farin ciki dajin ƙaunarsu. Ya dinga kashesu da salon looks nashi da duk yake rikita manyan mata sujisu suna sake dulmiya a tarin sonsa da ƙaunarsa.       Daga haka rayuwa ta cigaba da turzawa. AK na ƙoƙarin gina adalci a tsakanin matan nasa. Duk ƙwaƙwƙwafinka baka isa banbance wayafi so ba. Ya bar wannan sirrin a ransa da ga shi sa UBANGIJIN daya haliccesa. Idan saɓani ya shiga tsakaninki da shi bazai taɓa yarda ya wulaƙantaki gaban ƴar uwarkiba sai dai kuyi abunku ku kashe ku rufe ke da shi a ɗaki. Ku kuma shirya batare da kowa ya sani ba.       Idan a tsakanin saune saɓanin ya shiga tunda yau da gobe sai ALLAH sukanyi ƙoƙarin ganin sunyi saurin fahimtar juna kafin abin yay musu zurfi.       Su Anam gaba ɗaya saboginsu ya koma sashen Farah saboda jansu da take a jikinta. Little ne dai duk yanda taso ya sake da ita yaƙi. Komai zakaga yana yinsa a ɗarare indai tana a waje. Kuma babu abinda take masa mara ƙyau sai ma sakin fuska da ganin ya saki jikin da ita, amma hakan ya gagara. Takansha kukanta a ɗaki da godema ALLAH. Wani lokacin idan AK ya gani ya lallasheta da nuna mata ƙuruciyace kawai ke damun little ɗin zai daina wataran.        Takance ita badan wani dalili take kukanba dan har ranta ta cire kallon little daga wani sashe na jikinta. Hundred percent kallon jinin Zinneerah kawai take masa. Amma koyaya tanason ya dinga sakewa da ita kamar su Anam.     Itama Zinneerah abun na damunta dan kulum cikin yima little ɗin nasiha take amma abu ya kasa ƙarewa duk da dai yana ragewa Alhmdllh.       Yaye su Amaan Zinneerah tayi dan zata fara karatunta da AK yay alƙawari. Sai dai kuma ya fara mata zancen samun ciki tana zillewa dan ita tasan wahalar data sha. Ganin yanda take zame-zamen ma ya fara faɗa ko wani abu tasha akan hakan.       Rantsuwa ta dinga masa ita batasha komaiba wlhy ALLAH ne dai bai kawo ba, tunda yanzune ma fa ta yaye su Anam ai. Badan ya yardaba ya barta. Amma dai yace zai ƙara himma yaga ƙaryar zame-zame.     Ita dai dariyace kawai tata dan bata da abin faɗa kuma.       Rayuwa ta shuɗa abubuwa da yawa sun faru wasu sun canja. Su Sa'a dasu Adilah, Raheena matar Khalipha tuni sun hahhaihu. Hakama ansha bikin su Bahijja dasu Moos'ab.        Zinneerah ta dage da ƙyar ta ƙara santaloma AK ƙyaƙyƙyawar budurwa data ci sunan Mammah. Sai dai yasha mita suna mata dariya shi da Farah akan saura shidda ya rage ta ciko musu tunda bakwai ne a lissafi. Baki ta dinga kumbura musu da cewar ita wajen Granny zata koma tunda basa sonta. Aiko suka sami abun tsokanarta daga shi har Farahn da itama a yanzu ake shirin mata aikin mahaifarta saboda cigaba da aka samu akan masu matsalarsu. Fatansu kuma ALLAH yasa a dace.      Dan yanda takema su Anam saita baka tausayi. Gaba ɗayama yaran yanzu sun koma hanunta. An barma Zinneerah Little da mai sunan Mammah da suke kira Nu'aymah.     Anyi aiki kuma Alhmdllh an dace. Dan ƴan watannin da Farah ta ɗauka na jinya sai gata ta warke sarai kamar ba'ai mata komaiba, ta koma normal rayuwarta da fatan ALLAH ya kawo rabo mai albarka. Dan AK ya dage ba wasa. Addu'arsa kullum ALLAH yasa su harbu su duka dan shi fa ƴaƴannan basu gama isarsa ba.     Bayan kusan watanni takwas da aikin saiko gashi andace Farah da ciki. Zokaga murna wajen ƴan uwa da abokan arziƙi tare da uban gayya AK. Nanfa suka shiga bata kulawa da tattali dan cikin nata mai laulayine sosai tana shan wahala. Da yawan nauyinta sai ya dawo kan Zinneerah. Ga karatu ga yara dan ma akwai mama A'i da Saliha a gidan.      Haka a ka dinga cuɗawa cikin amincin ALLAH har ciki ya shiga watan haihuwa ta haihu lafiya ƴarta mace ƙyaƙyƙyawa mai kama da sauran ƴan uwanta. Zokaga murna wajen su Amaan anyi ƙanwa, har iyayi sukema little da suke kira da big bro waisu an musu ƙanwa. AK da Zinneerah kanyi dariya, yakance, “Mami to gaskiya kema ki dage ki cikoma big bro sauran shidansa, dan nima su naketa jira fa”.      Duk sanda ya faɗi haka sai tace, “Ka rufamin asiri Yayanmu ga Momy nan tayo ɗaya ita zata cika mana sauran biyar ɗin ai”.          Farah kuwa ta karɓe da “Uhm-Uhm Mami ƙarasa biyar ɗin nan wlhy akwai wuya kece da biyu, ni nawa ukun nan sun isheni. Amaan, Anam, Manha”.       Baƙaramar dariya suke mataba akan hakan, dan gaskiya tasha wahalar cikin nan sosai, musamman ma a wajen haihuwarsa kamar bazata kai ba.       Ƴan uwa da abokan arziƙi nata tururuwar zuwa har ranar suna.     Ƴan katsina dasu Mammah sun cika gida fam ansha shagali, itama dangin Zinneerah sunzo Alhmdllh dan zuwa yanzu kam an zama ɗaya sai haƙurin yau da gobe. Dan itama Farah ɗin tasha zuwa Danya musamman akan duba Inna da har yanzu aketa ibadar ALLAH na jinya. Yarinya taci sunan Mahma Zaliha. Za'ake kiranta Manha.     Tunda abin nan ya faru sai a sunan nan Zinneerah ta ƙara ganin Aunty Zakiyya. Tanata ɓoye-ɓoyen karsu haɗu dan kunya. Ita Zinneerah ma saita bata dariya. Ta shirya da kanta ita taje ta sameta aka gaisa.        Ansha suna an shashshare dan walima kawai akayi tamkar sauran ƴaƴansa. Aka bar su Zinneerah da zaman gyaran gida da barcin gajiya.       AK na jera kalmar Alhmdllhi da wannan ni'imomi na samun haɗin kan zuri'arsa da yayi. Fatansa kawai ƙarewa da rayuwa lafiya tare da samun ƙwarin gwiwar bama ƴaƴansa tarbiya har lokacin data ALLAH zata kasance akan kowannensu.✍😭🙏🏻 *_TAMMAT BI HAMDULLAH_* _To nima dai bara na dakata da alƙalamina a nan, kuma ku huta dan ansha fama. Abinda na rubuta dai-dai ALLAH ka haɗamu a ladansa. wanda nayi kuskure ALLAH ka yafe min daku masu karatu baki ɗaya_. *_LITTAFI nishaɗi ne, faɗakarwa ne, tunatarwa ne, ilimantarwa ne. Idan kayi gamo da faɗakarwa ɗauki ka amfana gwargwadon iyawarka, idan kaci karo da tunatarwa ɗauki ka amfana gwargwadon fahimtarka, idan kaci karo da ilimi a ciki, ɗauka ka amfana gwargwadon nazarinka. Idan kaci karo da nishaɗi, tabbatar ka tace shi ka rairaye koda ace zaka iya kwatantashi a zahiriyyarka. Idan nazarinka ya baka mai cutarwane barsa a nan inda ka-gansa nishaɗine kawai ba lallai saika sakama zuciyarka ba. dan babbar matsalar masu karatu. kunfi ɗaukar nishaɗi ku fifitashi a littafi ko ku ƙalubalanci marubuci da shi, ko aiki dashi. Sannan ku kuma kunmafi kowa son ganin nishaɗin a littafin fiye da duk sauran abubuwa masu ma'anar. Ƙalilanne a cikinku sukafi yarda da ilimi, faɗakarwa, tunatarwa da makamantansu, amma ƴammatan nan namu (kuyi haƙuri) ku daina sakama ranku tunanin rayuwar novels da wasu abubuwan nishaɗin cikinsa a zukatanku da tunanin samun irin rayuwar. Kisa a ranki ALLAH ya baki miji nagari mai addini dazai kwatanta miki rayuwa mai albarka agidan aurenki ba nishaɗin hikayoyin marubutaba. Sai dai kamar yanda kuke tunanin babu rayuwar novels ko yanayin jin daɗin cikinsa a zahiri wlhy akwai, akwaima wanda suka ninka rayuwar novels jin daɗi da nishaɗi a cikin gidajenmu, sai dai basu da yawa. Masu shan wahalhalun gidan aure sun rinjayesu. Mata ku ƙara haƙuri, kuyi haƙuri kuyita haƙuri. Idan baki samu hakanba karki damu, ki nutsu wajen ibadar ALLAH dan aure ibadane. Wata rana sai ALLAH yay miki sakamako da abinda yafi duk wannan jin daɗin da kika rasa. Dan duniya zaman wucin gadine. Kowa burinsa samun aljanna maɗaukakiya. (ALLAH ka sadamu da aljannarsa musami farin ciki mai ɗorewa na har abadan acan😭🙏🏻)._* *_YA rabbi ka gafartama mahaifina, ka yafe masa da dukkan ƴan uwa musulmi da suka rigamu tafiya. ALLAH yasa ranar mutuwarmu ta zama ranar farin cikinmu, ALLAH ya ƙara mana tsoronsa a zukatanmu da soyayyar MANZON ALLAH (S.A.W)😭🙏🏻_* _Duk wanda naima kuskure a yayin rubuta littafin nan ya gafarce ni, dan ban saniba ko shine littafi na ƙarshe da zan rubuta a rayuwata. Nima na yafema kowa waɗanda suka saya, muka kasance tare dasu a inuwa ɗaya, kuma suka cika alƙawarin ƙyautata mana basu cutar damu tako wata hanyaba. ALLAH ka ƙara mana haƙuri da juriyar zaman tare. mun gode, mun gode, mun gode ƙwarai da gaske da ƙoƙarin haƙurin bibiyarmu da kukayi. Zafafa biyar basu da bakin nuna muku farin cikinsu sai dai muyitama juna fatan alkairi har ƙarshen rayuwa🙏🏻😭_. *_ZAFAFA biyar na sake muku bankwana a karo na ƙarshe, tare da bangajiya sai mun haɗu a ZAFAFA BIYAR 2K22 insha ALLAHU_*. Ƙauna irain trillions ɗin nan. Dan kuɗin na dabanne, idan nace na daban ina nufin nadaban har acan ƙasan zukatan ZAFAFA BIYAR😉🤗🤗😁😁😍😘😍😘😍🤗🤗🤗🚶🏻.       _Idan kunga kuskure a rubutunmu Please kubi ta ƙyaƙyƙyawan hanyar nusar damu, insha ALLAH zamu duba, zakuma mu gyara, hakan da zaku mana shine ƙauna🤗._    *_ZAFAFA BIYAR  NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_* Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻. *_★ AL-ƘIBLA_*💘 _Na Safiyya Huguma_ *_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖 _Hafsat Rano_ *_★ DALAAL_*💝 _Na Miss xoxo_ *_★ UBAYD MALEEK_*💓 _Na Mamu gee_ *_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔 _Na Bilyn Abdull_ Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻. Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske. Kamar haka👇🏻💃🏻 Ɗaya___300 Biyu____400 Uku_____450 Huɗu____500 Biyar_____700 Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇 0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇 *_08085405215_* IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇   0903 234 5899 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍 *_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_*         ********************** ? ************************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************? ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ? ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ? **************************