[1/25, 7:57 AM] ‪+234 706 774 5996‬: 👫 *HA'DI DAGA ALLAH*👫 ********************** ⬇ ************************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** *WRITTEN BY* KHADIJAH AL'EEMAN " _Da Sunan Allah mai Rahma mai jin 'kai_" Wanan littafin "true life story" ne ban kwafa na wani ko wata ba, kuma banyi dan cin zarrafin wani ko wata ba. ********** 1 - 10 ✍🏻 Wani tangamemen gida na hango mai girman gaske, gida ne Wanda ya amsa sunan sa gida, _na bude get din gidan a hankali na shiga_, gabanah sai da ya fad'i saboda gidan ya bala'in haduwa daga gani anarka kud'i a cikinsa, kuma duk Wanda ke zaune a gidan nan ba kara min attajiri bane, juyawan da zanyi sai na hango mutane nata kaiwa da komowa sai kace gidan sarkin Katsina.. Lol, ina karawa gaba sai na ga ashe ma'aikatan gidan ke kaiwa da komowa, kuma na fahimci cewan duka ma'aikatan kowa da bangaren da yake aiki, both of Maza da Matan. Masu gadin gidan mutum biyu ne, Masu bama flowers ruwa da ban, masu kula da tsaftan tsakar gidan daban, haka zalika masu kula da fanin cikin gidan daban, _na kara shigewa ciki don in bama idona abinci_, na kalla cikin fallon da kyau naga ya hadu sossai colour din fallon red and white nace _woow_ na juya naga dining area shima ya bala'in haduwa, çan kuma sai na hango wata yarinya tana gyara dining din, ta jera wasu had'add'un kuloli, daga gani ba abinci kala daya bane aka dafa ba. Sai kuma naji taku daga bayana, ina juyawa naga wata kyakyawar mata ta d'an manyanta, fara ce sol, kayan jikinta kadai ya isa ka gane cewa Matar gidan ce, ta karasa saukowa daga stairs din, tace *Nasrin* kin kammala hada break fast din ne?, tace eh Hajiya na gama komai, toh Ma shaa Allah, Jeki ki kira min *Na'im* amma fa idan baki Gandhi a falonsa ba karki shiga ciki ko ki kwankwasa ki juyo kawai ki dawo abinki, tace toh Hajiya, ta juya tana cewa a cikin ranta _ni mai zai kaini shiga ko kuma in kwankwasa mai kofa wanan mai shegen bakar zuciyar tsiya, shi kamar ba d'an gidan nan ba_ da wanan tuna nin ta karasa cikin fallon, colour Fallon kuwa gaba daya white ne, ta shiga da sallama yana yana zaune yana danne danne a Laptop,yasa three quartern wando da rigarsa short slip kayan white gaba daya *Na'im*(white man) kenan first born a gidan *Alhaji Harris Saif* amma su yan biyu ne dayan macece, ko dagowa beyiba sai dai ya amsa sallaman da tayi ciki ciki fuska a murtuke, tace Hajiya tace kazo angama hada komai, yi yayi kamar be jita ba, sai da ta maimaita maganarta sau uku tukunna ya Daka mata tsawa Wanda yasa ta firgita sossai yace ance miki banji bane ke mayya ce wai?, nan da nan sai hawaye a fuskanta tace kayi hakuri naga baka amsa bane shiyasa na maimaita. Yace sai anyi magana ki wanni sadda kai kasa mtsw *poor girl* kawai, inda sabo ta saba da bala'in sa kullum sai ya zageta koh ya dakka mata tsawa, ta juya da nufin tafiya yace kice bantashi ba, tace toh cikin sarkewan murya. Sai sukaji ance kai Yaya Na'im karya bata dace da kai ba wlh, kuma ni na rasa mai Nasrin ta tsare maka a gidan nan, kaita hantaranta kamar ba mutum ba, kuma nidai naga da arziki da talauci duk dayane a wajen Allah, domin shine mai badawa, *NA'IMA* kenan 'yar uwar haihuwan Na'im, dukansu zasu kai shekara ishirin da takwas, Nasrin na jin abinda ta fada ta juya da Saudi ta bar wurin, shi kuma Na'im ya tashi yana nunata da yatsa yace ni wai tsaran wasanki ne?, ya bita zai duketa ta ruga da gudu a haka suka kai har dining area ta tsaya kusa da *HAJIYA NABILA* tace mommy kinga _white man_ koh, yace me wayace ki kira sunan nan, ni sa'anki ne wai, Dady kana jin abinda Na'ima take min amma kayi shiru sai Mommy tace kai dai wlh anyi baban banza, Dady yace a'a karkice haka, ki bincika kiji meya had'asu. Na'ima zatayi magana kenan sai *SHUREM* dake zaune ya tab'e fuska yace, _I am Hungary_ na gaji da jiranku ni zan fara cin nawa gaskiya, sai Labiba tace kullum sai fada kamar wash Tom and Jerry, sai Na'im ya kallesu ya galla musu harara, yace shiyasa nake son *SAFIYYA* ita ba ruwanta da surutu, Ku kuma kullum sai cacacaca like parrot, Dady yace toh anji Ku zauna muci abinci, suka zauna sukayi adu'a suka fara cin Abinci.. Iyalan gidan Alhaji Harris Saif kenan, shahararen mai kud'ine mai fada aji, ya mallaki manyan kamfanoni, da gidan biredi, yana da gidan ruwa, ga kaddarori da yake da su, yana da gidajen da yake bada haya, yana kuma business tsakanin Nigeria, Ghana,India da kuma Dubai. Matarshi daya Hajiya Nabila, mata mai mutunci da karamci ga son mutane ga tausayin talakawa, Allah ya azurtasu da yara Biyar, Na'im da Na'ima (twins) ne sunyi karatu a Malaysia, inda Na'im ya karanta business admin, Na'ima kuma Doctor CE a bangaren mata,Sai mai bi musu mai suna Labiba,tana karanta micro biology a B.U.K Kano wanan shekaran zata gama, sai mai bin ta Safiyya,tana karanta mass com a A.B.U zariya,tana Three hundred level, sai Autansu Shurem,yana Hampos international scul, s.s 3, sun taso cikin gata da kulawa,ga tarbiya Ilimin boko da na Islamiyya dai dai gwargwado sun samu,sai dai Na'im yana da wasu d'abi'u , toh koma mene ne d'abi'unsa zakuji. *EDITING BY* NUSNIM (twin sis) *DEDICATED TO* Anka,Maman shakur,Munay,Mamu,Afrah and Rash kadam.. Luv u all😘 [1/25, 7:57 AM] ‪+234 706 774 5996‬: 👫 *HA'DI DAGA ALLAH* 👫 *WRITTEN BY* KHADIJAH AL'EEMAN *11 - 15* ************* ✍🏻Alhaji Haris Saif suna zaune a u/rimi lowcost ne, 'yayyansa ba masu son fita bane akwai su da son mutane,amma in ka cire mutum daya wato Na'im, shi a rayuwarsa baya son talaka, kuma duk kudinku idan ya ganka sai ya rainaka,burinshi befi ace kullum yafi kowa ba, abokanasa ma hakuri sukeyi dashi, kuma halinsa ne yasa sauran abokanan sa suka gujesa, don baza su iya da wulakancinsa ba... Wanan dalilin ne yasa baida budurwa kwata kwata, gani yakeyi har yanzun be samu daidai dashiba, abokanansa kuwa yanxun biyu ne kwata kwata daga Ahmda sai Lukman, suma ayi fad'a a shirya, yawan zuwa gidan da sukeyi ne yasa Ahmad yaga Na'ima ya 'kyasa, a yanxun kowa yasan cewa Ahmad da Na'ima na son junansu.... Shiko Na'im anyi anyi ya fito da mata ya'ki waishi bega wadda yake so ba har yanxun, iyayensa kuwa nason suka sun had'a su da Na'ima amma har yanxun shiru..... Na'im ba wance ya tsana a cikin gidansu, sai mai aikin 'bangaren abincinsu, wato Nasrin,ya dauka tsanan duniya ya d'aura mata ba daman ta sake indai Na'im na wurin, al'amuran dake faruwa kenan a cikin gidan Alhaji Haris Saif. *WACECE NASRIN* Nasrin yar gidan *Mallam 'kasim* ce, suna zaune suma a u/rimi a layin rafin dad'i, sunan mahaifiyarta *Fatima*,tanada 'Kanne uku, *Habib* ke binta,sai *Salim*,sai autansu me suna *Nadra* , su talakawa ne sossai, sai sai mahaifinsu ya fita ya samo da kyar, tukunna zasu samu abin sawa a baki.... *Dalilin da yasa ta fara aiki a gidan Alhaji Haris Said* Shine Mahaifinta yazo ya fara rashin lafiya,ba mai fita yaje ya nemo,sai 'kanwar mahaifiyarta *Aisha* wadda dama tun farko ita ke aikin irrin abincin gargajiya a gidan Alhaji Harris Saif, itace ke kawo musu abinci...... Ita ta dauki Nasrin ta kaita makarantar Primary, ta gama ta sata a secondary, daga nan ta kaita makarantar koyon abinci, Nasrin yarinya ce mai Haza'ka gata da farin jini mutane na sonta sossai..... Ta gama makarantar koyon abincin, ba abinda bata iya dafawa ba, ciwon mahaifinta yayi tsanani sossai, Ashe ciwon ajaline sunyi kuka ita da mahaifiyarta da 'kanenta sossai, haka sukaci gaba da rayuwa,'kanwar mahaifinta ke samowa ta basu suci, mahaifiyarta ta fara sana'ar d'anwake ita ma,kuma Alhamdulillah suna samu sossai, ana haka Innarta Aisha wato 'kanwar mahaifinta ta fara ciwon 'kafa,har ta kai ga bata iya fita taje wurin aikinta..... Hajiya Nabila kuwa ta shirya taje har gida ta gaisheta, anan ne Inna Aisha ta roketa akan Nasrin ta maye gurbinta, ta bata labarin karatun da Nasrin tayi, tace ba matsala,aka kira Nasrin ta ganta, ta dauketa suka tafi, Hajiya Nabila ta lura Nasrin akwai natsuwa ga tarbiya, tana da hankali sossai, Hajiya Nabila na matu'kar son Nasrin, har mamakin son da Hajiya take nuna mata takeyi.... Da haka Nasrin ke samu suci abinci, kuma take biya ma 'kanenta kud'in makaranta, ta na Neman ma Inna Aisha maganin ciwon kafa, kar wai kuce mahaifinta beda wasu 'kanen, a'a yanada wasu 'yan uwan, mallam barde da mallam shu'aibu kuma sunada rifin asiri daidai gwargwado, amma basu damu da iyalan d'an uwansu ba,wanan kenan..... Alhaji Harris Saif na kishin gid'e a falonshi na sama Hajiya Nabila ta shigo ta zauna tace Daddyn yara kana nemana gani,yayi murmushi yace Hajiya wai bakya ma yaronki magana ne akan aure ?, tace wlh Ina masa amma haryanxun shiru,amma ka d'an kara masa lokaci In shaa Allah zeyi, yace toh ba damuwa, Allah yasa mu dace,ameen.... Yau ta kama Monday Alhaji ya fita haka Hajiya taje wani meeting na Ummul-khair foundation, yaran kuma kowa ya koma school, daga Na'im,Na'ima sai masu aikin gidan,Nasrin ta gama abinci ta had'a komai a dining ta gayawa Na'ima ta fito zata shiga bangaren Na'im kenan taji ance mayya dawo nan ya daka mata tsawa,ta juyo da sauri tana kallonsa, yace uban me zakiyi min a 'bangare, jiki na rawa tace abinci ne daman na gama zan kiraka, yace zonan, ta juyo ta bishi har dining d'in, lokacin kuma Na'ima ta sauko ta zauna a dining d'in, Na'im yace me kika dafa?, tace fried rice ne da farfesun kayan ciki, yaja tsaki yace kije ki dafa min _jalouf rice with cabbage da farfesun hanta_ Na'ima zatayi magana yace wlh I will deal with u stupid kawai, will u get out of here, ya daka ma Nasrin tsawa, da sauri ta bar wurin, ya juya ya kalli na'ima yace idan ina magana kina sa min Baki sai na karyaki, tace mommy ma ta karyaka wlh, yaja kula ya fara zuba abincin, tace Yaya Na'im abincin da kasa ayi maka fa wa zaici?, ya ce ina ruwanki, tayi shiru ta fara cin abincinta..... ********** After one hour Na'ima ta gama cin abincin ta koma ta zauna ta kunna kallo shi kuma ya d'auki wayan shi yana Dane dane , haryanxun yana kan dining din be tashi ba, ta dauko kulan ta fito daga kitchen d'in.... Tana kaiwa dining d'in yasa mata kafa ta fad'i abincin ya zube, ya tashi ya ce sai ki kwashe ki juye a Leda ki tafi dashi gida, dama babu... Ya harareta ya wuce, Na'ima ta taso tazo ta d'agata tace bakiji ciwo ba koh, ta gyada kanta, tace ki daina jin tsoron shi , inya miki ki rama, mommy na nan ba abinda zai miki... *EDITED BY* 🍒Nusnim ( *TWIN SIS*)🍒 📝 *DEDICATED TO*📝 Nafee Anka,Mm Shakur,Munay,Mamu,Afra and Rash Kadam Love u All😘 [1/25, 7:57 AM] ‪+234 706 774 5996‬: 👫 *HA'DI DAGA ALLAHH*👫 *WRITTEN BY* KHADIJAH AL'EEMAN *16-20* ************* ✍🏻Nasrin tace haba Ni'ima ta Yaya kike tunanin idan ya min abu zan rama, ai a 'kar'kashin shi nake, komai zaiyi min sai nayi hakuri, nasan komai lokaci ne,zai daina watarana, kuma ko ance watarana ma ya ganni ya min bazai min ba...... Na'ima tayi dariya, tace Nasrin wanan haka yake,shima d'abi'a ce ya d'aukota lokacin da muke Malaysia, baya tarayya da 'ya'yan talakawa sai na masu kud'i, kuma ya wulakanta mutum a wurinsa ba komai bane,kinga nima kaina ba wai ya barni bane, idan ya tashi muguntashi yi yakeyi har akaina, sai dai wani abunda ke birgeni shine,nice kad'ai abokiyar shawaran Yaya Na'im, kuma yana matukar sona..... Kiyi hakuri da halinsa mu dai muna sonki,kuma In shaa Allah baza mu wulakantaki ba, ki cigaba da aikin ki Allah ya taimaka, tace Ameen Na'ima nagode...... Sai sukaji gyaran murya suna juyawa Mommy suka gani a tsaye tayi murmushi, tace halan ya mata wani abun ne?, Nasrin tace a'a bakomai...... Mommy tace haba Nasrin ai a tunanina babu abinda zaki 'boye min, tsakanina dake ba wani 'boye 'boye, ta juya ta kalli Na'ima tace meya faru ne?, a nan ta 'kwashe komai ta fad'a mata, tace babbar magana, Na'im bazai taba canjawa ba, amma komai lokacine,nasan wata rana zai bari,Allah ya shirya suka amsa da Ameen, tace je ki had'a abinci, tace toh ta juya ta wuce... Na'ima tace ni tausayi ma take bani wlh, duk ya bi ya takura ma rayuwarta, ba daman yaga tana walwala, Mommy gaskiya kiyi wani abu akai idan ba haka ba wata rana zai mata abinda yafi haka wlh, ga yarinyan akwai hakuri, kuma tana bala'in tsoron shi..... Mommy tayi murmushi tace na samo mafitan yadda zai daina tsanan mata bama Nasrin kad'ai ba, rayuwarsa ta dawo sabuwa,dan nagaji da hali irin na Na'im wlh, kullum abinda yake tsurowa dashi da ban.... Na'ima tace Mommy menene shi tace karki damu zakiji kome nene idan na gama shawara da Daddyn Ku, Allah yasa mu dace, tace ameen mommy... Na'im tunda ya shiga d'aki be fito ba sai bayan sallah la'asar, ya sauko yazo ya zauna kusa da Shurem, shi kuma shurem ya na buga game da wayan mommy, ya daka mai tsawa yace ban hanaka buga game ba, ba gobe ne zaku fara waec ba?, ina tanbayanka kayi shiru, yace to Yaya Na'im ai ina karatu kuma ban taba zuwa ko na biyu ba, na d'aya nake zuwa, aikuwa ya sa hannu ya kama kunnensa yace daga yau sai yau na'kara ganin zakayi exam kazo kana game sai ba 'ba'bbalaka stupid kawai, Shurem kuwa ya tsala wani irin ihu.... Sai ga Mommy da Daddy sun sauko da sauri, Na'ima da ke kitchen Nasrin na koya mata dambun nama suka fito da gudu tare da Nasrin din, kowa na tanbayan lfy, Na'im yace yaron nan bazaiyi karatu ba sai ya kwaso muku f9 tukunna, wai game yakeyi... Daddy yace to kai Shurem me yasa kake game tunda gobe zaka fara waec ai natsuwa zakayi kayi karatu domin ka fito da good result, ko ba kason kaje wajene kayi karatu?, Shurem yace Daddy ni irin nasu Aunty Labiba da Aunty Safiyya nakeso, nima bani da ra'ayin fita waje gaskiya, nan Kadsu ma ya isheni, Na'im yace ji baki a wurin, wai kai Auntah koh, Mommy tace ka barmin yaro dan Allah, haba kai haka akayi maka ne wai?, yace mommy kekike 'bata yaron nan wlh.... Na'ima tayi carab tace kai Yaya Na'im kai wa ya takura maka ne wai?, komai fa kakeso kayi kanayi, shima ka barshi yayi yadda yake so, kasan yaron akwai brain ai........ Lokacin ya juya yana kallon wurin da take, kawai ya hango Nasrin a wurin yace ke..... Lallai ma uban wa ya baki izinin zuwa nan wurin, Family na magana kin wani kutso kanki didn't I tell u dat idan muna magana ki daina zama a wurin, kalleki kazama kawai bar nan kafin yanxun nan in bibbigeki wlh..... Dady ya tsaya galala yana kallon shi, yace Na'im wai kai bazaka canja halinka bane?, tarbiyan dana baka kenan?, ashe Na'im bazaka ma kanka fad'a ba?, ni ina son talakawa kuma ina tausayinsu, haka mahaifiyarka, haka 'kanenka amma kace kai talaka ba abakin komai yake a wurinka ba, ka wulakanta mutum ba komai bane, to Allah ya shiryeka.... Ya juya ya bar wurin yana mamakin hali irin na d'ansa, abin na damunsa, ya rasa menene mafita, da tunanin ya koma d'akinsa...... Itako Mommy cewa tayi kai dai wlh Allah shi zai shiryeka ba kowa ba, ka canja halinka tunda wuri, ta juya ta Mara ma Alhaji baya..... Ita kuma Na'ima tace kagani ko Yaya Na'im kullum ina baka shawara bakaji Allah ya ganar da kai, ta juya ta wuce ta koma kitchen d'in...... Ta ce Nasrin kiyi hakuri kinji, Nasrin tayi murmushi tace ai in da sabo na saba, karki damu, mu cigaba da abinda mukeyi..... Shiko gogan naku kad'a kai yayi ya tafi Garden abinsa.... Mommy ta shiga d'akin Dady, tace Dadyn yara, niko ina da wata shawara in da zaka amince, yace menene shawaranki tace mai zai hana a had'a auren tsakanin Na'im da Nasrin, ya d'ago kai da sauri ya kalleta, yace mommyn Yara kina ganin idan mukayi haka bamu cutar da ita ba?, tace Nasrin ce kad'ai nayi imanin zata sa Na'im ya canja halinsa, domin tana da tarbiya, kuma na tabbata in na samu iyayenta zasu fahimce ni, zakuma su yarda da abinda zan fad'a musu.... Dady yaja dogon numfashi yace toh idan kuma shi yana da wadda yake so fa?, Mommy tayi murmushi tace Na'im d'in lallai kam, beda wata wadda yake so, idan kuma yana da ita kace ya fito da ita, ni kuma in dai da ita toh wlh zan janye maganata...... Yace to bari nasan yadda za'ayi, miko min wayata, ta mika mai, ya danna Number Na'im saida tayi kamar zata tsinke sannan ya d'auka, yayi sallama, ya amsa yace kasa meni a fallona yanxun nan, bai jira mai zaice ba ya kashe wayan..... Na'im gaban shi ne ya fad'i, yace toh fa lpy irin wanan kiran, bari inje inji.... Ya fito zai shiga Main fallo kenan ya hango abokanansa wato Ahmad da Lukman suka gaisa, yace musu Ku shiga, ni bari inga Dady, Ahmad yace Na'ima na nan dai koh, yace baka da kirki ina suruminka baka jin kunyanah?, yace kunyan me zanji, a haka suka shiga daga ciki shi ya wuce wurin dady..... Ahmad kuma ya kira Na'ima tazo suka Lula duniyan soyayya Lukman kuma na zolayansu.... Nasrin ta kawo musu abin mosa baki, Lukman yace woow wanan kyakya wan fa, Ahmad yace itace wadda take shan wahala a hannun Na'im wlh..... Yace da za'abani ai da na aura,Na'ima tayi dariya, tace kai Lukman, ai kai kana da kud'i da kyar in iyayyenta zasu baka, yace saboda me?, tace irin wulakancin da Yaya Na'im yake mata, ai dole tace a'a..... Yayi murmushi yace Yayanan naki bazai canja ba, ko yaushe zai daina abinda yakeyi oho, Allah ya sawake, sukace Ameen ya rabbi.... Na'im ya shiga Fallon Daddy da sallama, ya zauna, yace Daddy gani kayi kirana, yace Na'im, ya amsa da Na'am, ina son ka bani hakalinka anan, ya maganar da mukayi dakai kwanakin baya?,ya dukar da kai yayi shiru, yace toh na baka wata biyu idan har baka fito da mata ba zan aura maka Duk wadda naga dama.... Hankalinsa ne ya tashi, yace Daddy pls, ya dakatar da shi da hannu yace tashi ka tafi na gama magana..... Ya fito zufa na keto masa ya shiga Fallon shi, ya zauna ya dafe kai, Na'ima ta taso da sauri tace Yayanah lpy?, meya faru?,.... Yace Na'ima Dady ya bani two months in fito da matar Aure idan ba haka ba zai bani wadda yaga dama, ni wlh banda Wanda nakeso kuma duk fad'in k.d banga wadda ta mun ba, inaga barin garin kawai zanyi ko kuma 'kasar ma gaba d'aya.... Tace a'a Yaya iyaye daban suke,kayi hakuri komai zai wuce In shaa Allah, zaka samu wadda kakeso, kaga before lokacin anyi bikin mu nida Ahmad, kila a friends d'ina kasamu wadda tayi maka, kayi hakuri.... Ahmad yace karka damu, zamu fara searching In shaa Allah zaka samu.... Lukman yace wanan gaskiya ne karka damu, kawai canja halinka zakayi ka koma normal kamar kowa, yace to dama ni abnormal ne?, yace kai wlh baza ka canja ba, Allah ya shiryeka.... Sai ga Nasrin ta shigo kwashe kayan da ta kawo ma su Ahmad abin motsa baki, ta dauka mistakely sai Cup ya fad'i a kasa ya fallatsa a kayan Na'im gasu white, yana tashi ya wanka mata wani lafiyayyen mari.... Yace ke jahillace, ko kuma makauniya, da bazaki iya d'aukar abu a hankali ba, dama halin yaran talakawan nan kenan wlh, jiki na rawa an'kosa aje a shanye sauran, banza kawai.... Na'ima tace haba Yaya Na'im dan ya fad'i bata Sani ba, gaskiya ka daina irin wanan... Lukman baki bud'e yake kallonsa, Ahmad kuwa cewa yayi bansan randa zaka canja ba wlh, meye abin wulakantawa a talaka, da mai kud'i da talaka duk d'aya suke a wurin Allah..... Ya juya yayi tsakiya shige d'aki ya bugo kofa... *EDITED BY* 🍒Nusnim ( *TWIN SIS)🍒 📝 *DEDICATED TO*📝 Nafee Anker,Mm Shakur, Munay,Mamu,Afra and Rash kadam Love u All😘 [1/25, 7:57 AM] ‪+234 706 774 5996‬: 👫 *HA'DI DAGA ALLAH*👫 *WRITTEN BY* KHADIJAH AL'EEMAN *21-25* *********** ✍🏻 Na'ima ta girgiza kai tazo ta kama Nasrin tace dan girman Allah kiyi hakuri, nasan zakice saboda anga baki da gata ne shiyasa, ba haka bane kina da gata, tunda Allah ya baki rai da lafiya, ki cigaba da hakurin da kikeyi nasan dole watarana Yaya Na'im zai nemeki, kuma zai baki hakuri, kiyi hakuri kinji, bata ce komai ba ta juya ta fita abinta.... "Lukman yace ma Ahmad ni wlh halinsa na bani mamaki, yarinyan da kwata kwata abin duniya be dameta ba, na tabbata da tanada inda zataje tayi aiki abiyata ta samu su rinka cin abinci zataje wlh.... Ahmad yace danma su mommy da sauran yaran gidan basa wulakantata, da wlh "she will run away" na tabbata, Allah ya kyauta ya shirya Na'im, sukace Ameen.... Yace mu zamu koma, Swt berry sai munyi waya koh, tace alright baby, "thanks for coming", ta rakasu har wajen mota suka kama hanya suka fita.... Yau ya kama Thursday, da daddare suna zaune dukan su a fallo, sai ga kiran Labiba ya shigo phone d'in mommy, ta dauka tace yakike ya school?, ta amsa lafiya lau, nan take fad'a ma mommy cewa next week Friday ne zasuyi send forth, mommy tace Ma shaa Allah zamuzo da izinin Allah, Allah yasa Albarka ta amsa, sukayi sallama ta kashe, ta juya wurin Dady, tace dadyn yara wai next week Friday send forth d'in su Nabila, yace toh fa na manta d'azun na je makarantan su shurem shima ranan Friday graduation d'in su..... Mommy tace Shurem shine baka fad'a ba?, yace Allah mommy na manta ne,Na'im yace wawa kawai wata rana ma zaka manta da kanka ai, Na'ima kuma cewa tayi in an fad'a muku Abu a school kana dawowa ka fad'i kaji, yace toh Aunty Na'ima shiyasa nake sonki wlh amma shi Yaya Na'im d'inan sai masifa kawai ya sa ni, Dady yace a'a Shurem banda rashin kunya kajikoh, ya gyada kai, sai mommy tace to yanxun ya za'ayi Daddyn yara?, wa zaije ma Nabila?, ..... Yayi murmushi yace ina ganin Alhaji Tofiq da matarsa sai kuma Na'im, ya d'ago kai da sauri ya kalli Dady kamar zeyi magana sai kuma ya fasa, Alhaji Tofiq 'kanin Mahaifin Na'im ne su biyu ne kad'ai mahaifiyarsu ta haifa, daga kansu bata kara haihuwa ba har Allah ya mata rasuwa, ta rasu da shekara biyu Mahifinsu shima ya rasu, dangin mahaifinsu suna Libiya, mahaifiyarsu kuma danginta na kano, amma saboda basa son Auren shiyasa basu damu da a ina suke rayuwa ba, gashi mahaiginsu nada kud'i dai dai gwargwado, ya basu ilimi sossai kafin ya rasu, kuma dukansu suna da kud'i sossai, sai dai shi Alhaji Tofiq bai ta'ba haihuwa ba, wanan kenan.... Na'im ko aransa yace ni banzanje ba amma nasan Dady in har nace bazanje ba, zaisa ni zuwan dole, nasan abinda zanyi ai...... Haka rayuwa keta tafiya, kullum da muguntar da Na'im kema Nasrin, itako jar ta saba, da idan ya mata sai dai ta koma gefe tayita kuka Na'ima ke bata hakuri, amma yanxun ta daina, sai dai tsoron shi datakeyi haryanxun..... 'Bangaren gidansu Nasrin kuwa in ka cire ummanta ba Wanda yasan halin da take ciki, idan Inna Aisha ta tambayeta sai tace komai na tafiya daidai, mahaifiyarta kuwa kullum tana 'kara bata hakuri, tana ce mata ta rinka hakuri, takanyi murmushi tace Umma wlh baya damuna tunda dai ina samun abinda zamu rufama juna asiri, 'kannena na zuwa makaranta, muna samin abinda zamuci, kinga kome zemin ina 'karuwa dasu, kuma kowa na gidan na sona, Dan shi kad'ai yana hantarata bazai damena, ummanta ta ce Allah ya miki Albarka, tayi murmushi tace nagode ummanah..... Yau ta kama an tashi anata girke girke da abubuwan da za'a kai makarantansu Nabila da kuma shurem, shiko goganaku ya kudundune a cikin blanket, Mommy ce taga har karfe takwas be fito ba kowa ya shirya har Alhaji Tofiq da matarsa sun zo, amma shi ko lekowa beyiba, ta shiga d'akinsa ta Ganshi a kwance tace Na'im lafiyanka kuwa naganka haryanxun baka fito ba, yace Mommy cikina ke ciwo sossai, tace subhanllah kasha magani kuwa?, yace eh nasha, kodai za'a kira Doctor ne, yace ai nasha magani zai sauka, tace toh Allah ya sawa'ke, ta fita ta fad'a musu, suka shigo suka mai sannu, suna fita ya fara tsalle yana murna, haka kawai a sa mutum zuwa wani B.U.K banzuwa.... Sai dai Na'ima ta bisu suka tafi, shikuma Shurem su mommy suka je mai.... Gidan yayi shiru ba kowa sai ma'aikatan gidan, Nasrin ta kammala komai ta shirya zata tafi, Na'im ya kirata yace mata farfesun Kaza yake son ci yanxun nan, haka ta shiga kitchen d'in tayi mai, rabin kaza ta sa mai, tunda shi kad'ai ne a gidan, ta gama ta juye a bowl ta kaimai, yana bud'ewa yace yana ga kamar be kai kaza daya ba, ko kin sata ne zaki kai gidanku, zuciyanta na tafasa tace a'a rabi nasa saboda naga kai kad'ai ne...... Aikuwa ya d'aga ya watsa mata a jiki yace ki wuce kije ki yi wani, nan gidan ubanane kuma muna da komai enough, "dan haka sai kiyi min na kaza d'aya nake so, wawiya kazama kawai, 'bace min da gani karnayi 'kasa 'kasa dake a nan wurin,.... Ta juya ta tafi kitchen d'in ta had'a mishi wani ta kawo mai, ko kallonta beyiba, ta juya zata tafi yace ke, zonan, ta dawo tazo ta tsaya yace d'auka kije kisa a fridge na fasa ci, ko kuma ki zuba a leda ki kai gida, Dan na San kafin Ku samu irinshi sai anyi albashi ko kuma in daddy ya fitar da zakka, bata ce mishi komai ba, ta d'auka ta fita, ta kaiwa masu gadi, ta juya ta fita abinta..... Angama su mommy sun dawo inda Labiba tazo da kyaututtuka, shi kuma Shurem shi a kaba "the best student" a school d'in..... Akwana a tashi yau wata d'aya ya shud'e a cikin wata biyun da aka d'iban ma Na'im kuma yau ne aka d'aura Auren Ahmad da Na'ima, biki ne Wanda ya amsa sunansa, manyan masu kud'i sun halarcin d'aurin auren, Haka kuma amarya tayi kyau sossai, kawayenta sunzo har wa'inda sukayi school d'aya, An shirya dinner bayan ankai amarya, Lukman da Ahmad sunata nuna ma Na'im 'yan mata amma sai ya ta'be baki yace basu yi ba,a haka har a ka gama, washe gari kuma dangin ango suka had'a walima, can na hango Hauwa Usman da Hauwa Nuhu Shehu sunata kwasar girki Lol😂.... A haka a ka kare amma fir Na'im yace bega wadda ta mishi ba, Ahmad yace mun maka Wanda zamu iya, Dady ya nema maka wadda ya ke so mu ba abinda ya damemu, da fad'a suka rabu ko rakiyan ango ma beje ba..... Anyi sati biyu da bikin Na'ima, Dady ya kira Na'im yace masa kadai San yau saura kwanaki wata biyun dana d'iba maka ya cika koh, to wlh bazan sarara maka ba tunda kai ba kara min yaro bane, tashi kabani wuri..... Yaje ya samu mommy a d'aki yana mata magiya, tace kaga Na'im ka fita a idona in rufe, aure ne sai kayi shi wlh, so kake mu zuba maka ido muyita kallonka ko menene, toh wlh baka isa ba dolenka kayi aure, shasha sha kawai, ta tashi ta fita ta barmai d'akin..... *EDITED BY* 🍒Nusnim ( *TWIN SIS*)🍒 📝 *DEDICATED TO*📝 Nafee Anker, Mm Shakur, Munay, Mamu, Afra and Rash Kardam Love u all😘 [1/25, 7:57 AM] ‪+234 706 774 5996‬: 👫 *HA'DI DAGA ALLAH*👫 *WRITTEN BY* KHADIJAH AL'EEMAN *26 27* *********** ✍🏻 Mommy na fita ya ri'ke kai yana salati, toh wai auren nan dole ne, a ina zan samu matar da zan aura daidai ni, ya Allah ka sa kada Dady yayi abinda yace zeyi, wlh bana son yin aure yanxu.... *BAYAN WATA 'DAYA* Dady ne zaune shida mommy, Na'im yayi sallama ya shigo cikin fallon, suka amsa tare da kalonsa, ya nemi wuri a kan carpet ya zauna, yace Daddy ka kirani gani.... Yayi ajiyan zuciya yace Na'im ban ta'ba tunanin in nasa maka doka bazaka biba sai a wanan lokacin, na baka ilimi, tarbiya, soyayya ta d'a da mahaifi, kome zanyi sai na fara tuntu'banka kafin nakeyinsa, amma kai baka gani, Ashe ban isa ince ina son wani abuba kayi shi cikin gaggawa har sai raina ya 'baci, toh shikenan tunda na lala'baka, na nuna maka, na nuna 'bacin raina, amma still baka canja ba, ka 'ki bin dokata, kwata kwata, toh ka sani na 'baka za'bi ka'ki bi, this time around ni zan aura maka duk wadda naga dama.... Yace daddy pls ka saurareni, "Daddy yace Na'im bana magana biyu" tashi ka bani wuri, ya juya wurin mommy yace yanxun mommy kina kallo za'amin haka, ta daka mai tsawa tace Na'im you are very stupid, kana tunanin zamu zauna da kai a haka ne ba aure, toh ina son ka Sani kaima ta dalilin aure kazo duniya, don haka u most do it, tashi ka fita ka ba mutane wuri..... Yana fita ta juya ta kalla Daddy tace toh yanxun ta ina zamu fara, yace bari Tofiq yazo muji yadda za'ayi, kinsan shi shawara yana da dad'i ko ya kika gani, tace wanan gaskiya ne, ya d'aga waya ya kirashi, yace gashinan a hanya dama gidan zaizo.... Ba afi minti talatin ba sai gashi, nan daddy ya fad'a masa duk halin da ake ciki, Alhaji Tofiq yace Yaya da an d'an kara bashi lokaci, Daddy yace kasan na bashi lokuta sossai, tun yaushe nake mai magana ya'ki saurarata yaushe zan zauna ina kallon shi, Na'im yafi so ayi mai duk abinda yake so, toh kuma ni abinda nake so ya gane mu muka haifeshi, mune iyayen shi, dole ya bimu..... Alhaji Tofiq yace wanan haka yake, sai dai wani hanzari ba guduba kuna ganin haka ze yiwu tunda fa kowa yasan irin tsanar da yake ma Nasrin, Mommy tace In shaa Allah babu wata damuwa, kubar min komai a hannu na, ya kuma cewa toh iyayenta fa?, Mommy tayi murmushi tace abu mai sau'ki gobe In shaa Allah zanje in samesu kuma da izinin Allah komai zai daidaita, yace toh shikenan Allah yasa Albarka, suka ce ameen.... 'Bangaren Na'eem kuma hankalin shi ya tashi sossai, yaje har gida ya samu Na'ima ya fad'a mata komai, tace kaima Yaya Na'im nasha fad'a maka cewan ka daure ma xuciyarka ga 'yan mata nan kala kala a gari wasu har kawo Kansu sukeyi wajenka amma kwata kwata baka kulasu, kai ba Aljanu gareka ba kai ba wani matsala kake dashi ba, rayuwar nan da kake gani bata da tabbas, mutuwa akeyi, so kake idan ka rasu ya zama baka da gata, ba ka da mai cewa Allah ya ji'kan baban mu, ya kamata gaskiya kama kanka fad'a, ni dai a matsayina na 'yar uwarka na baka shawara..... Ya tashi tsaye yana kallonta idanuwansa sunyi ja sossai, yace gaskiya Na'ima bazan iyaba, barin 'kasar zanyi gaba d'aya, in na tafi sai inga wa za'a yiwa auren dole, Na'ima tace "haba Yayanah", iyaye daban suke komai zasu maka dole sai kayi hakuri, kuma kayi biyayya, sai kaga komai na tafiya dai dai yadda ya kamata..... Yaya Na'im komai kace daddy ya maka yana maka, haka mommy tana maka, toh meyasa wanan karan bazaka musu suma abinda suke so ba, Albarka yayita binka har karshen rayuwarka?,..... Gaskiya Yayanah ka zauna kayi tuna ni, kama Lanka fad'a, ni na rabu dasu lafiya, kai kuma d'an uwana ne rana d'aya, lokaci d'aya aka haife mu, sai dai kai ka rigani fito wa ne toh dan Allah kaima ka samu ka rabu dasu lafiya, ka roki Allah, Allah yasa shine mafi alkhairi a rayuwaka.... Jikin shi yayi sanyi, yace shikenan Na'ima zanyi yarda kika ce, kuma In shaa Allah bazan basu kunya ba, tace toh shikenan Allah ya bada Sa'a, yace "ameen" shiyasa nake sonki sis, akwai hankali, Allah ya baki masu miki yadda kike yima 'yan uwanki har iyayenki, sukaji ance Ameen, ba kowa bane illah Ahmad, ya karaso da murmushi a fuskansa ya d'aga ta, yana cewa lallai matanah yar aljannah ce, dukan su sukayi dariya, Na'im yace kunga tafiya ta nima na kusa auren nan in huta da abinda kukeyi min, Na'ima tace Yaya kazo kuci abinci, yace na 'koshi zanje gida inci, ya tafi abinsa... Mommy taje gidansu farko ta fara samun Inna Aisha da maganar, tace toh Hajiya ban'ki ta taki ba, kuma ba wai ban isa in baki ita ba, na fi son mu samu mahaifiyarta domin tana da hakki akanta, kar taga kamar an ma ta ba dai dai ba, har sauran 'yan uwan mahaifinta bama ita kad'ai ba, tace wanan haka yake, Inna Aisha ta d'aga waya ta kira Mallam Shu'aibu da Mallam Barde, tace suzo tana nemansu, saboda itace babba, duk ta girme musu, basu 'bata lokaci ba suka zo, aka kira itama umman Nasrin d'in tazo ta zauna,.... A nan Inna ta zayyane musu komai da ake ciki, hankalin Umma ya tashi tace Hajiya kina sane da irrin abubuwan da ke Shiga tsakanin Na'im da Nasrin, kinsan a duniya ba Wanda Na'im ya tsana kamar Nasrin koh, kuma sanan yanxun ace da shi za'a had'ata Aure, gaskiya bazai yuwu ba kiyi hakuri Hajiya, Mommy tace kiyi hakuri dan Allah, Fatima ki bani hankalinki a nan ki saurara da kyau kiji, Na'im nada wani d'abi'a na wulakanta mutane nida mahifinsa munyi munyi ya daina abu ya gagara, sai dai daga baya mun gane cewan aure ne kawai zaisa ya natsu, toh auren ma ya gagara, ya'ki fitowa da wadda yake so, munyi lallashin, abu ya gagara, toh ta wannan hanyan ne kawai za mu samu ya koma kamar kowa, kuma ta hanyan had'a shi aure da Nasrin ne kad'ai zaisa ya janja, domin Nasrin itace yarinyar da muka yarda da tarbiyanta, Fatimah, Nasrin na tabbata zata maida mana da gidan mu abin alfahari, zamuyi alfahari da ita, ki taimaka mana dan Allah..... Ummah tayi a jiyar zuciya, tace Hajiya na fahimce ki, kuma In shaa Allah zan 'karfafa ma Nasrin gwiwa, zan kuma fahimtar da ita yadda zata game, Allah yasa muce gwamma da akayi, kowa yace "Ameen".... Inna Aisha ta ce Alhamdulillah, naji dad'i sossai Fatima, Allah ya sa a dace, suka ce "Ameen".. Suko su mallam Shu'aibu da mallam barde a ransu dad'i sukeji, don sunsan Nasrin zata sha wuya, amma a filli sun nuna suna farin ciki da abin, Mommy ta musu godiya tayi musu sallama, tace sai anzo neman auren Nasrin, ta tafi abinta.... *EDITED BY* 🍒NUSNIM ( *TWIN SIS*)🍒 📝 *DEDICATED TO*📝 Nafee Anker, Mm Shakur, Munay, Mamu, Afra and Rash Kardam Love you all😘 [1/25, 7:57 AM] ‪+234 706 774 5996‬: 👫 *HA'DI DAGA ALLAH*👫 *WRITTEN BY* KHADIJAH AL'EEMAN *28 -30* ********** ✍🏻 Mommy ta isa gida lafiya, kuma ta fad'a ma Daddy yadda sukayi, Daddy yayi farin ciki kuma yaji dad'i sossai, yace Mommyn yara kira min Na'im d'in, ta d'aga waya ta kira shi, tace kazo ka samemu a Fallon 'kasa, bata jira abinda zaice ba ta katse wayan, cikin minti uku sai gashi yazo, yayi sallama ya shigo ya nemi wuri ya zauna....... Dady yace Na'im mun yake had'aka aure da Nasrin, ya d'ago da Saudi, cikin tashin hankali yace wata Nasrin d'in?, Mommy tace Nasrin dai ta nan gidan, yace mommy Nasrin d'in nan gidan kokuwa Nasrin mai aikin abinci?,..... Daddy yace ita,idon shi ya kad'a yayi ja sossai, yace "haba dan Allah a rasa wadda za'a had'a ni aure da ita sai 'yar aiki, 'yar talakawa, meyasa baza'a samu yarinyan mai kud'i a had'a ni da ita ba?, sai 'yar matsiyata haba dan Allah....... Mommy ta ce koma yar mecece aikin gama ya gama, auren ne ba fashi, in kaga dama ka mutu, aure ne kamar anyi an gama, ya tashi zai fita, Daddy yace kafara shiri nan da two weeks zaka zama ango, ya juya ya fita ya nufi sasan shi, tunda ya zauna ba abinda kemai yawo akai, sai maganganun mommy da Daddy, yace "wallahi indai yarinyar nan ta yarda ta aureni sai ta gudu da 'kafanta, sai ta zama baiwa a gareni, daga haka wani wahalallen bacci mai cike da matsanan cin ciwon kai ya d'aukeshi..... A 'bangaren gidan su Nasrin kuwa Ummah ta fad'a ma ta, hankalinta yayi mummunan tashi, Umma ta kira sunan ta tace "bawai na yarda da Auren bane saboda kud'insu ba, ban kuma amince ba saboda zaki aura mai kud'i ba, na yarda ne saboda hujojjin da Hajiya ta kawo min, Nasrin wannan Auren zakiyi shine saboda jahadi", kuma karki manta kina da lada har a wajen Allah, Nasrin ban yarda ko yaji kiyi ba bare kuma in ganki da takardan saki, ina son kimai biyayya yadda ya kamata, ki koya mai d'abi'a mai kyau, yanda zai rinka son mutane ya dinga tausayin talakawa, Nasrin na tabbata watarana zakizo kina murna kina dariya, kuma zakiji dad'in aurenki In shaa Allah, sanan karki yarda Hajiya ko Alhaji suyi kuka dake, domin sun yarda dakene sun kuma yarda da tarbiyanki, ina so kiba ma ma'kiyanki kunya, Dan Allah Nasrin...... Nasrin ta goge hawayenta tace ba komai, Ummah In shaa Allah sai kinyi alfahari dani, kuma na fahimce ki, na kuma ji dad'i sossai da Allah ya bani ke a matsayin mahaifiya, tayi murmushi tace Allah ya miki Albarka, Allah ya baki yara na gari, kuma Hajiya tace ki daina zuwa aiki, sannan zata turo mai gyaran jiki anjima, d'azun nima ta kirani take shaida min, tace Ummah Allah ya kaimu, tace ameen.... Yau aka kawo kayan sa rana, tare da akwatina set biyu, komai an saka a ciki sai kuma wani akwati daban shi kuma kayan event ne a Viki, tare da Invitation card na d'aurin auren dana event a ciki, kowanne an rubuta na randa zatasa, za'ayi kamar su "kamu (Indian Night), Dinner, arabian Night sai kuma walima" duk wanan aikin mommy ne da Na'ima su sukaje Dubai, suka had'o su, tare da furnitures da kayan kitchen da za'a zuba ma Nasrin a d'aki don sunce kar a kai mata komai, duk zasuyi..... A 'bangaren Na'im ko hankalin shi duk a tashe ne, ko a bokanan sa sai dai Ahmad da Lukman suka kai musu kati, kullum yana d'aki, Na'ima ce ta shigo tace haba Yayanah wlh sands Mommy ta kirani take fad'a min murna nayi sossa, domin ko ba komai nasan halin Nasrin, wallahi kayi dacen mata, ya kalleta yace shiyasa kika je Dubai siyo mata kaya koh, saboda bakya sona yanxun kema koh, tace ba haka bane ana maka gata ne amma bazaka Sani ba sai nan gaba.... Suna a haka Mommy ta shigo ta mika mai kaya tace yau da karfe shida za a fara Kamu (Indian night), su zaka sa, yace ni ba'inda zani, Mommy tace dole kaje kuma ka kuskura ka nuna ma mutane halin da ake ciki sai na 'bata maka rai wallahi, ta juya ta fita....... Na'ima tace daurewa zakayi dan Allah Yaya, yace ba komai Na'ima, zanyi kokari inga nayi yadda take so tace yauwa, toh yanxun ka fito Ku gaggaisa da mutane, yace toh muje, haka nan yake daurewa yana dariyan 'karfin hali, amma zuciyan shi ba'kin'kirin take........ Itako bangaren Inna Aisha tana ta tsuma Nasrin, ji'ka wancan, sarki da wancan, wanka da wancan, ga gyaran jikin da ake mata, sai tayi bala'in kyau, kamar ba ita ba, 'kawayenta na School sunzo sai tsiya suke mata......... Karfe shida naga kowa ya halarci Seventeen hotel, can na hango Ali jita a gefe yana jiran isowar ango da amarya, su bilkisu Ja'e da Aneelurv na hango a gaba gaba nace toh fa Lol...... Amarya da Ango na hango a tare sun shigo nace Ohmg wannan daga gani aikin Na'ima ne dan nasan halin Na'im sarai, Nasrin kuwa kanta a duke, shiko yana ta murmushi, hango mutanen da yayi ne yasa ya kamo hannun Nasrin ya rike, ita dai nata Ido, nan fa Ali jita ya fara wasa amarya da ango, can na hango tawagar gidan "Deejah's Kitchen" nata taka rawa nace lallai ma kowa ya gayyace su oho Lol😂..... *EDITED BY* 🍒NUSNIM ( *TWIN SIS*)🍒 📝 *DEDICATED TO*📝 Nafee Anker, Mm Shakur, Munay, Mamu, Afra and Rash Kardam Love you all😘 [1/25, 7:57 AM] ‪+234 706 774 5996‬: 👫 *HA'DI DAGA ALLAH*👫 *WRITTEN BY* KHADIJAH AL'EEMAN *31-35* *********** Assalamu Allaikum Masoyana ina mika godiya ta a gareku, na bada kulawa da kukeyi a gareni, na rashin lafiyan danakeyi, da wa'inda suka kirani da wa'inda suka min adu'a, nagode sossai Allah ya saka muku da aljannah, Allahumma Ameen👏 ✍🏻 Rana bata karya sai dai uwar d'iya ta ji kinya, a yau ne d'inbin Al'umma suka shaida d'aurin auren *Na'im Alhaji Haris Saif da Nasrin 'Kasim* wanda aka d'aura a masallacin dake unguwan sarki wato Sultan bello, d'aurin aure ne daya tara manyan masu kud'i, yan jaridu, sarakai da sauran su, 'kanin mahifin Nasrin wato mallam shu'aibu shine waliyin Nasrin a inda gwamnan jahar Kaduna shine waliyin Na'im a kan sadaki naira dubu d'ari biyar..... Anata d'aukan hoto da Na'im Wanda shikad'ai yasan abinda ke damun sa, amma a fili ya'ke kawai yakeyi, mahaifinsa yaji dad'in yadda ya sake, yana kuma rokon Allah yasa ya zarce a haka..... A 'bangaren Nasrin kuwa jikinta ya mutu ta koma gefe d'aya ta zauna, tana tunanin ko wani irin zama zasuyi da Na'im oho, amma tasa ma ranta duk zaman daya ce suyi shi zasuyi, Ummantah ne ta dafa ta tace lafiya kuwa?, tayi murmushi tace ba komai Ummah, tayi murmishi tace Nasrin ai kindai ji fad'an da nayi miki kuma da fatan kin d'auka tace "In sha Allah" Umma, sai ga Inna Aisha da 'kanwar mahaifiyanta Aunty Amina sun shigo suna cewa ina amarya ta fito, nan Ummah ta kama ganin Nasrin tace Allah yayi miki albarka, Allah yasa ki gama da duniya lafiya, suka amsa da "ameen", ta mika ma Inna Aisha ita, nan fa Nasrin ta fara kuka tana turjiya da kyar a ka samu ta tafi aka kaita gidan kakaninta na wurin Uwa sukayi mata fad'a, aka kaita gidan 'kanen babanta tunda kakaninta na wurin baba sun rasu, Mallam barde da Mallam Shu'aibu sukayi mata nasiha, matayensu ma suka mata, a gidan Mallam Shuaibu aka barta har aka kawo motoci, suka kama hanyan gidan su Na'im da ke low cost, anje ankaita wurin Mommy ankuma bata amanarta ta amsa kuma tayi godiya..... Aka kaita wani d'aki a gidan ita da 'kawayenta,kafin time d'in Arabian night yayi..... A 'bangaren ango kuwa ya nuna kamar ba abinda ke damun shi, har su Ahmad na mamakinsa, amma kuma sun ayyanah a ransu akwai abinda ya shirya, amma koma menene Allah yasa alkhairi ne..... 'Karfe hud'u aka shirya arebian Night, Na'ima bata a 'bangaren ango bata a 'bangaren amarya, sai da taga komai ya tafi daidai, sanan hakalinta ya kwanta..... Anyi arebian night lafiya, kowa yaci yasha, anyi hamdala, can na hango su *Fatima Malunfashi, Aneelurv, Stylish, Autar Hajiya, Fiddo Sodangi,JJ, Real Amani, Amra, Nafee Anka, sunci sun sha sunata selfie Lol😛....... Antashi lafiya kowa yana ta sa albarka, anfara shirin kai amarya, Matar Alhaji Tofiq ne Ta kama hanun Nasrin, ta kaita wurin daddy da Alhaji Tofiq, aka kira Na'im shima yaje, Mommy ta shiga itama, aka musu nasiha sossai, Mommy tace Na'im ba saki a tsakanin ka da Nasrin, ba duka, duk randa ka d'aga hannu ka duketa ban yafe maka ba, ya d'aga kai da sauri ya kalleta, Hajiya Hawwa matan Alhaji Tofiq tace haba Hajiya, don Allah ki janye wanan kudirin naki, tace a'a Hawwa nasan halin Na'im, gwara in mishi gargad'i tun yanxun, tace Allah yasa mu dace, Allah yayi muku Albarka, Hajiya hawwa ta maida Narin d'akin shi kuma ya tafi wurin abokanansa, a ka fara shirin dinner...... Happy Sallah to you all, may Allah continue to guide and protect Muslim Ummah Ameen... Takabalallahu minna wa minkum *EDITED BY* 🍒NUSNIM ( *TWIN SIS*)🍒 📝 *DEDICATED TO*📝 Nafee Anker, Mm Shakur, Munay, Mamu, Afra and Rash Kardam Love you all😘 [1/25, 7:57 AM] ‪+234 706 774 5996‬: 👫 *HA'DI DAGA ALLAH*👫 *WRITTEN BY* KHADIJAH AL'EEMAN *36 - 40* *********** ✍🏻Anje wurin dinner, nan ma anci ansha, kowa ya sha kaya white, can na hango 'yan Party, Fatima Malunfashi, BLG,Anee, stylish, Autar Hajiya sai shugaba kwatakwata Nafee Anka, ansha white gowns anata kai naman kaza baki Lol😂..... Akace Ango zai ciyar da Amaryarsa, haka ma Amarya zata ciyar da Angonta, Na'ima suka had'a ido da Na'im, ta nuna mai hannu alaman yayi yadda akeso, ya kad'a mata kai alamar bazai iyaba, ta kara rokonsa, ganin kar ya nuna ma mutane halin da ake ciki ya kama hanun ta suka yanka cake d'in, ya ciro yasa a bakinsa ya kamo ha'barta ya kai bakin shi kan nata, yasa mata cake d'in a bakinta yayi fuska abinsa, ita ko Nasrin kamar 'kasa ya tsage ta shiga don kunya, mutane kuwa sai shewa sukeyi suna ihu, aka ce saura Amarya ta rasa yarda zatayi tasa hannu ta d'auka ta kaimai baki ya bud'e ya amsa, wuri ya kaure da tafi, Na'ima tace ma Ahmad wallahi Yaya d'an duniya ne , ji shi kamar bashiba, Ahmad yace ke dai bari wallahi ni kaina mamaki yake bani, Allah yasa a d'aure a haka tace "ameen Hubby"......... Daga nan aka wuce da Amarya gidanta da ke malali kan titin Isa Kaita, gidan ya had'u sossai, a 'kasan akwai d'akuna hud'u ko wanne da toilet da bathroom a ciki, sai kitchen katon gaske a cikinsa akwai store komai da komai akwai, colour d'in Fallon blue and golden..... Sai in ka haura sama, saman 'bangare biyu ne d'ayan komai nasa white ne dayan kuma Orange and lemon green, wanan kad'ai ya isa mutum ya banbance 'bangaren Na'im da Nasrin, in ka shiga falonta akwai d'akuna guda uku kowanne an 'kaya tashi da kayan alfarma, daya colour d'insa pink ne, d'ayan kuma peach colour ne, na ukun kuma lemon green ne........ 'Bangaren Na'im kuwa shima three bedroom ne, d'aya white and orange ne, na biyun white and peach, na ukun kuwa white and pink ne...... Gida kam ya had'u sai Sam barka, kowa ya musu fatan Alkhairi, an tafi an bar Nasrin da Na'ima kawai a gidan, bayan sun kimtsa Na'ima tasa Nasrin ta 'kara yin wanka, tayi kwaliya tasha gown d'inta white and orange........ Na'ima ta kama hanunta suka zauna, tace Anty Nasrin kinga yanxun kin zama matar aure,Ina son duk wani tsoron Yaya Na'im ki ajiyeshi a gefe, ki fuskanci auren kai tsaye, nasan kin fi kowa sanin halin Yaya Na'im daga 'bangaren good sight d'insa da kuma bad sight d'insa, yanxun ya'ki zakiyi ba d'an karami ba, canja Na'im Anty Nasrin ba abu bane mai wahala, sai kinyi hakuri, kin kuma daure, na yarda dake na kuma yarda da tarbiyanki, kiyi abinda dangin mijinki zasu 'kara sonki za kuma suyi alfahari dake...... Aunty Nasrin ina nan duk wani abinda zai shige miki duhu ki gaya minshi, ina son in zama abokiyar shawaranki, bana so ki rinka fad'a ma kowa sirrinki ki zama mai 'boye sirrin gidanki, Allah yama Auren nan naku albarka tace "ameen"..... A daidai lokacin sukaji an bud'e kofa, Na'im ne ya shigo da sallama suka amsa, yace Ku fito fallo, ya juya ya fita, suka rufa mai baya........ Sunje fallon sun sami Lukman, Ahmad sai Na'im, suka nemi wuri suka zauna, a nan Lukman yayi musu nasiha mai ratsa jiki, sukayi adu'a suka kama hanya Na'im ya raka su, itako Nasrin ta rike Na'ima tana cewa karki tafi dan Allah ki kwana a nan..... Tace Aunty Nasrin gobe zan dawo In shaa Allah, tace "to ina jiranki" ta juya ta tafi, Na'im ya dawo ya taradda bata a wurin ya d'auka ledar dasu Lukman suka sa ya siya, ya haura sama ya shiga 'bangaren ta, bata fallo ya shiga d'akinta, ya sameta a zaune ya wurga mata ledar a fuska, yace gashi nan mayya nasan abinda kika zo ci kenan, kin matsa dole sai kin aure ni toh wallahi sai kin gwammaci zama a gidan Ku akan wanan auren da kika yarda aka yishi, wawiya kwai, mtsw banza ya juya ya fita, ita ko bata ce mai komai ba har ya fita...... *EDITED BY* 🍒 *NUSNIM ( *TWIN SIS*)🍒 📝 *DEDICATED TO*📝 Nafee Anker, Mm Shakur, Munay, Mamu, Afra and Rash Kardam Love you all😘 [1/25, 7:57 AM] ‪+234 706 774 5996‬: 👫 *HA'DI DAGA ALLAH*👫 *WRITTEN BY* KHADIJAH AL'EEMAN *36 - 40* *********** ✍🏻Anje wurin dinner, nan ma anci ansha, kowa ya sha kaya white, can na hango 'yan Party, Fatima Malunfashi, BLG,Anee, stylish, Autar Hajiya sai shugaba kwatakwata Nafee Anka, ansha white gowns anata kai naman kaza baki Lol😂..... Akace Ango zai ciyar da Amaryarsa, haka ma Amarya zata ciyar da Angonta, Na'ima suka had'a ido da Na'im, ta nuna mai hannu alaman yayi yadda akeso, ya kad'a mata kai alamar bazai iyaba, ta kara rokonsa, ganin kar ya nuna ma mutane halin da ake ciki ya kama hanun ta suka yanka cake d'in, ya ciro yasa a bakinsa ya kamo ha'barta ya kai bakin shi kan nata, yasa mata cake d'in a bakinta yayi fuska abinsa, ita ko Nasrin kamar 'kasa ya tsage ta shiga don kunya, mutane kuwa sai shewa sukeyi suna ihu, aka ce saura Amarya ta rasa yarda zatayi tasa hannu ta d'auka ta kaimai baki ya bud'e ya amsa, wuri ya kaure da tafi, Na'ima tace ma Ahmad wallahi Yaya d'an duniya ne , ji shi kamar bashiba, Ahmad yace ke dai bari wallahi ni kaina mamaki yake bani, Allah yasa a d'aure a haka tace "ameen Hubby"......... Daga nan aka wuce da Amarya gidanta da ke malali kan titin Isa Kaita, gidan ya had'u sossai, a 'kasan akwai d'akuna hud'u ko wanne da toilet da bathroom a ciki, sai kitchen katon gaske a cikinsa akwai store komai da komai akwai, colour d'in Fallon blue and golden..... Sai in ka haura sama, saman 'bangare biyu ne d'ayan komai nasa white ne dayan kuma Orange and lemon green, wanan kad'ai ya isa mutum ya banbance 'bangaren Na'im da Nasrin, in ka shiga falonta akwai d'akuna guda uku kowanne an 'kaya tashi da kayan alfarma, daya colour d'insa pink ne, d'ayan kuma peach colour ne, na ukun kuma lemon green ne........ 'Bangaren Na'im kuwa shima three bedroom ne, d'aya white and orange ne, na biyun white and peach, na ukun kuwa white and pink ne...... Gida kam ya had'u sai Sam barka, kowa ya musu fatan Alkhairi, an tafi an bar Nasrin da Na'ima kawai a gidan, bayan sun kimtsa Na'ima tasa Nasrin ta 'kara yin wanka, tayi kwaliya tasha gown d'inta white and orange........ Na'ima ta kama hanunta suka zauna, tace Anty Nasrin kinga yanxun kin zama matar aure,Ina son duk wani tsoron Yaya Na'im ki ajiyeshi a gefe, ki fuskanci auren kai tsaye, nasan kin fi kowa sanin halin Yaya Na'im daga 'bangaren good sight d'insa da kuma bad sight d'insa, yanxun ya'ki zakiyi ba d'an karami ba, canja Na'im Anty Nasrin ba abu bane mai wahala, sai kinyi hakuri, kin kuma daure, na yarda dake na kuma yarda da tarbiyanki, kiyi abinda dangin mijinki zasu 'kara sonki za kuma suyi alfahari dake...... Aunty Nasrin ina nan duk wani abinda zai shige miki duhu ki gaya minshi, ina son in zama abokiyar shawaranki, bana so ki rinka fad'a ma kowa sirrinki ki zama mai 'boye sirrin gidanki, Allah yama Auren nan naku albarka tace "ameen"..... A daidai lokacin sukaji an bud'e kofa, Na'im ne ya shigo da sallama suka amsa, yace Ku fito fallo, ya juya ya fita, suka rufa mai baya........ Sunje fallon sun sami Lukman, Ahmad sai Na'im, suka nemi wuri suka zauna, a nan Lukman yayi musu nasiha mai ratsa jiki, sukayi adu'a suka kama hanya Na'im ya raka su, itako Nasrin ta rike Na'ima tana cewa karki tafi dan Allah ki kwana a nan..... Tace Aunty Nasrin gobe zan dawo In shaa Allah, tace "to ina jiranki" ta juya ta tafi, Na'im ya dawo ya taradda bata a wurin ya d'auka ledar dasu Lukman suka sa ya siya, ya haura sama ya shiga 'bangaren ta, bata fallo ya shiga d'akinta, ya sameta a zaune ya wurga mata ledar a fuska, yace gashi nan mayya nasan abinda kika zo ci kenan, kin matsa dole sai kin aure ni toh wallahi sai kin gwammaci zama a gidan Ku akan wanan auren da kika yarda aka yishi, wawiya kwai, mtsw banza ya juya ya fita, ita ko bata ce mai komai ba har ya fita...... *EDITED BY* 🍒 *NUSNIM ( *TWIN SIS*)🍒 📝 *DEDICATED TO*📝 Nafee Anker, Mm Shakur, Munay, Mamu, Afra and Rash Kardam Love you all😘 [1/25, 7:57 AM] ‪+234 706 774 5996‬: 👫 *HA'DI DAGA ALLAH*👫 *WRITTEN BY* KHADIJAH AL'EEMAN *41 - 50* *********** ✍🏻Nasrin tayi murmushi tace duk abinda ka min zan jure Na'im, amma wallahi sai ka durkusa kana rokona in soka, kuma wallahi zama a cikin gidan nan yanxun na fara, har sai na cika wa iyayenka burin su, kuma sai na canja maka halinka, sanan in koya maka sona duk da nasan nima ba sonka nakeyi ba amma zanyi hakuri, zan jure watarana zai zama labari, tayi kwafa ta tashi ta cire kayanta tasa night gown ta kwanta...... A 'bangaren Na'im kuwa tunda ya shiga 'bangarensa ya canja kaya ya kwanta, yana ta tuna nin yanxun haka zai cigaba da rayuwa da wanan 'yar talakawan, gaskiya Mommy ta cuceshi, shi wallahi ya tsaneta ko 'kaunar ganinta ma bayayi, mtsw ko da yake ma next week zai fara zuwa office, ya huta ta ganin ba'kin ciki ya kwanta....... *WASHE GARI* Nasrin ta tashi ta kimtsa ko ina, ta gyara gidan tas, ga wani turare da ta bad'e gidan dashi, ta yi wanka tayi kwalliya, tasa wani atampa red and white, yayi mata bala'in kyau, ta feshe jikinta da turare ga d'an kwalin nan an nad'a shi kamar gwagwaro, ta na zaune a fallonta tana kallo..... Na'im kuwa ya tashi yayi wanka, yasa red polo da white jeans, ya bud'e kofar bedroom d'insa wani 'kamshi ya daki hancinsa, ya ja numfashi, yace "woow" irrin wanan 'kamshi haka, shi dai yana bala'in son 'kamshi ga son tsafta kamar ba namiji ba.... Ya fito ya shiga fallonta hankalinta na kan t.v bata ma lura dashi ba sa ji tayi ance daka mata tsawa "ke mayya, anzo an sami kallo an wani zauna kamar wata wawiya, gida ba a da irin shi, ba'a saba ganin irinshi ba, kin wani 'kura ma t.v ido sai kace wata doluwa,...... Ta tashi tazo ta d'an rusuna tace "ina kwana" ya hankad'eta saura kad'an ta fad'i yace da ban kwana ba zaki ganni, ya kalleta ya kalli kayan jikinsa yace toh fa, wato har kaya zaki rinka sawa iri d'aya da nawa, saboda kin raina min wayau to tashi kije ki cire shi ki canja wasu tun kafin na tattakaki a nan wurin, kuma ki dawo ina jiranki...... Ta tashi ta wuce d'aki ta d'auko wani material blue and white tasa ta 'kara feshe jikinta da turare ta fito, ya kalleta yayi tsaki zaiyi magana kenan aka kwankwasa kofa, ya juya yace ke 'yar aiki uban wa zaije ya duba miki, ta juya ta tafi ta bud'e 'kofan, Nafeesa mai girkin gidan su Na'im ce ta yanxun d'auke da basket, suka gaisa ta mika mata tace inji Hajiya, ta amsa tace ki gaisheta, ta juya ita kuma ta koma ciki.... Taje dining ta ajiye ta koma sama tace Nafeesa ce ta kawo abinci wai inji Mommy, yace muje dining d'in, suna zuwa ya daka mata tsawa yace "ni zanja kujeran"?, tayi Sauri taja mai kujeran ya zauna, zata zauna kenan yace "waye tsaran wasanki da zakici abinci tare dashi"?, sai a bari sai naci na rage tukunna.... Taja ta tsaya tana kallonsa, ya harareta, ta bud'e kulollin chips ne da egg, sai ferfesun kan rago, flask d'in kuma kunun gyad'a ne a ciki, ta zuzuba mai, ya fara ci, sai da ya 'koshi tukunna sanan ya tashi ya wuce, ko kallonta beyi ba..... Ta girgiza kanta, ta koma ta zauna tana tunani hali irin na Na'im, amma komai lokaci ne with time, taci ta 'koshi taje ta wanke kayan ta goge dining d'in ta koma sama, bata dad'e da zama ba ta fara jin bacci, ta tashi ta shiga cikin d'akinta ta kwanta sai bacci, tana bacci taji an watsa mata ruwa ta mike da sauri Na'im ne a tsaye yana huci, yace to atashi ayi sallah, daga ci sai bacci, ba'a saba cin irin wanan mai dad'i ba, kinzo kin kwanta, ni zan fita kafin na dawo a gyara min d'akina idan ba haka ba jiki yayi tsami, saura kuma a je ana ta'be ta'be yar aiki kawai, ya juya ya fita abinsa..... Nasrin ta girgiza kai tana murmushi, tace zanyi maganinka ne wallahi, daga yau ka daina min masifa, ta tashi ta Shiga toilet tayi alwala tayi sallah, ta fito ta shiga d'akinsa komai tsab, bata san mai zata gayara ba..... A haka dai ta 'kara gyarawa ta share tayi moping, ta sa turare, tabi ko ina na gidan ta gyara duk da bai 'baciba, ta zo wurin dining taga abinci , har ya zuba ya ci ta bud'e taga p Fried rice ne da ferfesun kifi, sai pineapple juice, taci ta 'koshi ta gyara wurin sanan ta shiga ciki tayi wanka, ta fito ta yi sallah tana idarwa ta d'auko wani dogon riga a cikin English wears d'inta, 'kasan shi ta baya da tsagu, saman shi a bud'e ana hango dukiyan fulaninta, rigan colour d'inta purple ne, ta matseta sossai, sannan rigan shara shara ce, ta dauko hula white tasa, ta zubo da gashinta ta baya, ta 'karshen gashin tasa d'an 'kara min ribbon white and purple, tayi simple make up, ta feshe jinkinta da turare gashi ta shafe jikinta da humra, ta dubi kanta a madubi, tace anya zan iya kuwa...... Wata zuciyar tace mata "karki manta ga lada, ga kuma burinki da kike so ki cimma, ki daure ki cire kunya, ki nemi lada, ki jawo hankalinshi, ki faranta ma mutanen da suke so su kyautata miki", tayi murmushi, ta d'auki cewing gum mai 'kamshin tom tom, tasa a bakinta, ta d'auko sim d'inta da Sabon wayar da aka sa mata a lefe dama ta riga da tayi charjinsa ta fita taje falon 'kasa ta zauna tasa, ta kira gida, sukayi waya da kowa..... Ta kira Mommy suka gaisa, tace mata komai lafiya koh?, tace "eh mommy ba komai tace yanxun zan aiko Nafeesa da abincin daren ku tace toh mommy, sukayi sallama, tana kashewa Na'im na shigowa.... Ya kalleta sama da 'kasa ya watsar, ta ce mai sannu da zuwa, ya juya yace "ke ni tsaran wasarki ne, dawa kike?, tayi murmushi "tace da Na'im nakeyi mana, idan banyi da kai ba dawa zanyi, ya tsaya yana kallonta da mamaki, yace "ke 'yar talakawa, wawiya, yaushe kika samu dama a gidan nan har kike kallon fuskana kike gaya min magana" ..... Ta d'aura 'kafa d'aya kan d'aya, tayi murmushi, tace daga ranan da aka d'aura mana aure, d'inbin al'umma suka shaida, ta mike tana taunar cingum ta kai dai dai kan step, tace Na'im inaso kasani daga yau Nasrin ta daina jin tsoronka, kuma wallahi duk zaman da zakayi dani I am ever ready for dat, ta juya ta haye sama ta barshin a nan yayi mutuwar tsaye..... *EDITED BY* 🍒NUSNIM ( *TWIN SIS*)🍒 📝 *DEDICATED TO*📝 Nafee Anker, Mm shakur, Munay, Mamu, Afra and Rash Kardam Love you all😘 [1/25, 7:57 AM] ‪+234 706 774 5996‬: 👫 *HA'DI DAGA ALLAH*👫 *WRITTEN BY* KHADIJAH AL'EEMAN *51 - 55* ********** ✍🏻Na'im yayi shiru yana mamakin Nasrin, yaushe yarinyar nan ta zama haka, dama tana da baki?, wallahi bazan yarda da wanan iskancin ba, yaushe ya bata dama har ta fara mishi rainin wayyon nan, yayi kwafa ya bi bayanta zuwa d'akinta..... A lokacin Nasrin ta cire kayanta ta d'aura towel, ko ciyanta towel d'in bai kai ba, ta danna handle d'in bathroom d'in kenan ya bud'e kofa ya shigo ya ce "ke 'yar aiki, ta tsaya bata juyo ba, yace bazan yarda da wannan iskancin naki ba, kina jina koh, nan ba gidanku bane bare kice zaki rinka shiga irin yadda kike so, kuma ma a gidan naku ina kika samu matsayin sa kaya irin wa'inan masu tsadar gaske?,..... Ta juya ta kalleshi zatayi magana kenan aka danna bell d'in fallon 'kasa, tace "heh relax" kwantar da hankalinka, menene na d'aga hankali da tada jijiyoyin wiya, ai ni banga abin fad'a an an ba, aure ne fa tsakanina da kai bawai zaman daduro mukeyi ba, duk abinda zansa halaliya tace don na tabbata da halal aka saye shi, tsada kuma da kake cewa akwai kwandalar ka aciki ne?, Iskanci kuma baka ga komai ba, nan gaba ma da ka fara son 'yar talakawa zan fara karuwanci, amma fa karuwanci mai lasisi, ga lada ga farin ciki, tace sorry sweet heart, kaje ka duba mana Nafeesa ce ke knocking kasan na fara jin yunwa, saboda abincin gidan su Na'im mai dad'i ne yanxun na fara cin irinsa, tayi mai blowing d'in kiss, ta shige bathroom ta rufe da 'karfi abinta....... Yace "ohh ya Allah wai meyasa kwata kwata Mommy ta hanani dukan yarinyar nan ne, ni kawai anja min masifa an aura min yarinyar matsiyata, mtsww, ya juya ya fita yaje ya bud'e kofar, ya amsa basket d'in ya juya ya shiga ciki,..... Ya kai dining ya a jiye, ya juya ya koma sama domin ya watsa ruwa, yana shiga d'aki wayarsa ce ta fara ringing, ya d'auka Ahmad ne yace "haba sirikina tunda ka agwance kwata kwata ko kira babu", Na'im yaja tsoki yace kai dai ka Sani wallahi ya gida, ina Na'ima?, daga d'aya 'bangaren yace gata nan laulayi ya sata a gaba, kasan na kusa zama baba, Na'im yace "inda kafi auki kenan wallahi, Allah ya raba lafiya, yace "ameen", Ahmad yace saura kai sai ka yi da gaske, yace kaga mallam sai anjima wanka zanyi, ya katse wayar ya wuce bathroom abinsa...... Nasrin ta gama wanka ta fito tayi shafa, ta shafe jikinta da humra mai d'aukan hankali, ta duba kayanta ta rasa wadda zata sa, sai can ta hango bum short red, ta d'auko da riga mai one hand iya cibiya ya tsaya, colour ta white tasa ta feshe jikinta da turare, ta dauki 'yan kunne red and white tasa, tayi kwalliya sossai tasa red lipstick, ta dauko white hula tsakiyar sa a bud'e tasa, tasa red ribbon a tsakiyar, ta sa mouth freshner mai 'kamshin kankana, ta juya ta fito, fitiwanta yayi dai dai da fitowanshi, yasa three quarter wando da shirt shima white, suna had'a ido ya d'auke wuta, da kyar ya had'iye miyau, ta matso da sauri ta d'aga wayanta tana cewa "zo muyi salfie" daman yau zaka bud'e min wasapp nima in fara, ko ya kagani?,.... Ya hankd'eta, yace "you are very stupid" kina haukane, ni tsaranki ne wai, 'yar talaka, 'yar aiki dake,zaki rinka had'a jikin ki dani,toh bari kiji idan ma sona kikeyi ni bana sonki, kuma karki ta'ba tunanin zan so ki idan ma mafarki kikeyi, "you better wake up", dan bazan ta'ba sanki ba.... Tayi murmushi tace "Na'im or white man" sunanka?, let me tell you the fact, bantaba sonka ba, yanda kake ganin an maka dole, nima haka aka min dole, amma ni ina da tarbiya kuma duk wani umarni iyayenah ina 'kokarin bi, domin su suka haifeni, sune gatanah, duk abinda zanyi bazan ta'ba biyansu ba, and let me tell you one thing, da talaka da mai kud'i Allah ne ya hallice su ba mutum ba, kuma shi ya ga dama yayi mai kud'i yayi talaka, Dan haka ni kud'inku basu a gabana, "to hell with you and your fucking money"..... Good sight d'ina kawai ka sani baka san bad sight d'ina, "from now hence forth" zaka san waye Nasrin, bani da kyau in aka kaini bango wallahi, ta harare shi ta juya ta koma d'aki jikinsa yayi sanyi sossai, yayi shiru ya girgiza kanshi kawai ya wuce dining, yaci ya 'koshi ya tashi ya tafi garden...... Nasrin kuwa tunda ta shiga d'aki ta ke kuka, inda ma to gode ma Allah duk masu cewa suna Sonta, 'bata ta'ba amincewa ba, da yanxun wula'kancin da Na'im zai rinka mata sai yafi mata ciwo.... Zata daina shiga harkan Na'im kwata kwata, zata roki Na'ima ta roka mommy a maida ta makaranta kawai, 'kila hankalinta zaifi kwanciya, ta bud'e fridge ta dauko five alive da icing cake 'kanana da aka zuba a ciki, taci ta 'koshi ta rufe kofarta ta kwanta....... *EDITED BY* 🍒 NUSNIM ( *TWIN SIS)*🍒 📝 *DEDICATED TO*📝 Nafee Anker, Mm Shakur, Munay, Mamu, Afra and Rash Kardam Love you all😘 [1/25, 7:57 AM] ‪+234 706 774 5996‬: 👫 *HA'DI DAGA ALLAH*👫 *WRITTEN BY* KHADIJAH AL'EEMAN *56 - 57* ********** ✍🏻bata farka ba sai after sallah magrib, ta watsa ruwa tayi sallah, ta gyara d'akinta, ta fito ta gyara ko ina, ta lura kamar baya nan, ta shiga 'bangaren sa, ta gyara ko ina tasa turare, ta turare gidan, ko ina 'kamshi yake yi...... Taka abinci aka dining ta gyara mai zama amma bata ci ba, ta shiga kitchen ta dafa Indomie ta ci, ta wanke komai, ta gama ta koma d'aki, tayi sallah esha'e, ta sa night gown wandda dashi da babu duk d'aya suke, ta hau gado ta kwanta abinta...... Wuraren nine ya shigo gidan, ko ina tsab tsab, ya wuce dining area, ya bud'e abincin yaga bata ci ba, ya zauna yaci, ya tashi ya wuce sama,ya le'ka fallo bata nan har zai wuce d'akinsa, sai kuma ya fasa ya juyo, ya murd'a kofanta ya Shiga,'can ya hangota a kwance, tayi d'add'aya a gado, ya 'kare mata kallo ya bud'e fridge ya d'auko five alive me shegen sanyi, ya bud'e yana murmushin mugunta, ya watsa mata ta tashi a firgice, taje ta 'kan 'kameshi tana maida numfashi........ Ya tureta ta 'kara 'kan 'kan'kameshi, tana cewa "baby" sanyi nakeji wallahi, ya sa 'karfi ya hankad'eta yace ban hanaki ta'ba ni ba?, bance ki daina ta'ba min jiki ba, duk randa kika 'kara ta'bani "I will make sure I deal the hell out of you, stupid", ta kalleshi 'kasa'kasa tace "heart" to ba kai bane ka watsa min ruwa ina bacci cike da mafarkai kala kala, wai ni da kai muna ta wasa da ruwa,...... Ya watsa mata harara yace "uban wa kika banmawa wancan abinci da zaici?," tace kai fa kace abincin gidan ubanka ne, don haka nima naci na gidan ubana, dan haka ka had'a duka kaci bazan ciba,ya watsa mata harara, yaja gashinta da 'karfi suka fita tana ihu, wallahi "sweet love" akwai zafi, ka sake min gashina please, sai da ya jata har wurin dining d'in yaja kujera taki zama, ya zaunar da ita, ya jawo flasks d'in ya zubo mata tuwon shinkafa da miyan agusi, ya zuba apple juice a cup, ya ce ohya bismillah, ta kalleshi tayi murmushi a ranta tace "bakasan Nasrin bane inada bala'in wayau, karka ga ko university banyi ba, wallahi nafi mai dagiri iya shu'umanci"..... Ke Nasrin ba dake nakeyi bane wai, ta juyo da sauri tace d'azun na bige hannu ko dagawa bana iya wa, to tayaya zan iya cin abinci?, yayi tsaki yace kisa bakinki akan plate d'in ki rinka ci, tace sai kace dabba, wallahi bazan sa ba, yace toh ai keda dabban banbancin Ku kad'an ne, ta d'augo kai da sauri tana kallonsa tace "Na'im ni kake kira da dabba, nan da nan hawaye ya sauko mata kan kumatu, tace mai na maka da zaka rinka kirana da dabba, kace min wawiya, banza, 'yar talaka amma ban ta'ba nuna maka ya dameni ba, Na'im da mahaifina nada rai ko sanina ma bazaka ta'bayi a rayuwa ba, amma saboda mutuwa tamana yankan 'kauna, kuma Allah ya ba mu 'yan uwan baba marasa zuciya, shine dalilin dana fara aiki a 'kar'kashin Ku, kake cin zarrafina yadda kake so....... Iyayenka suka nuna suna son aure na da kai, mahaifiyata ta'ki yadda, amma saboda hujojin da ta kawo mata yasa ta amince, ta min magana a matsayinta na Uwa da ta d'auki cikina na tsawon wata Tara, ta haifeni lokacin da take nakuda tamkar zata mutu, ta raineni, cina, shanah, ta min komai a rayuwa, na yarda na mata biyayya, na amince da aurenka Wanda nasan ba abinda zai tsinana min sai ba'kin ciki da taikaici, saboda ban ta'ba sonka ba, amma saboda in faranta mata rai na yarda na amince da auren Wanda ya tsaneni saboda ni talaka ce, bani da gata, na yi auren 'kaddara, wallahi Na'im da banyi ma Ummanah a'kawarin zama dakai lafiya ba, da na nuna maka bad sights d'in Nasrin,...... Ta mike ta fara tafiya tana kaiwa dai dai wurin steps tace "Na'im rashin biyayya ga iyaye ba komai zai haifar maka ba, sai d'a mara ido, baza ka ta'ba gamawa da duniya lafiya ba", ta juya tayi hayewar ta sama....... Na'im kanshi yaji ya fara sara mai sossai, ya rike yana fad'in " ~Innalillahi wa'ina illaihi raji'un~, a cikin 'kan'kanin lokaci komai ya tsaya masa cak...... *EDITED BY* 🍒 NUSNIM ( *TWIN SIS*)🍒 📝 *DEDICATED TO*📝 Nafee Anker, Mm Shakur, Munay, Mamu, Afra and Rash Kardam Love you all😘 [1/25, 7:57 AM] ‪+234 706 774 5996‬: 👫 *HA'DI DAGA ALLAH*👫 *WRITTEN BY* KHADIJAH AL'EEMAN *58 - 60* *********** ✍🏻Na'im tunda ya shiga d'aki ya kwanta, yake ta tuna nin maganganun Nasrin, abinda take fad'a masa fa gaskiya ne, shi wallahi besan ya akayi ya zama haka ba, shi dai kawai bai ga macen da zai zauna da ita bane har yanxun, "huh" abin na da munsa....... Yau satin Nasrin biyu a gidan Na'im, amma in banda fad'a ba abinda sukeyi, kullum da rigiman da zasuyi, sai dai abinda ta lura dashi, shine ya rage zaginta da yakeyi, amma fa mugunta kala kala yake mata...... Nasrin na zaune a Fallon 'kasa taji anyi nocking, ta tashi ta bud'e, wa zata gani inba Na'ima da Ahmad ba, ta rugume Na'ima tana murna, suka shigo ciki, Ahmad yace Ina maigidan?, Nasrin tace "yana ciki yana bacci a taso shine?, yace gaskiya da zaifi ina son ganinsa, tayi murmushi tace ina zuwa, ta shiga d'akinsa ta ja bargon da ya lullube ta wurga mai, firgigit ya tashi yana salati, tace mallam sai ka tashi munyi ba'ki, ta juya zata fita, kawai taji an kama mata kunne, tayi 'kara sossai har 'kasa saida sukaji, yace haka aka koya miki tashin mutum a bacci ne wai, mai yasa kika rainani ne?, zatayi magana kenan Na'ima ta bud'e kofar ta shigo, ta fara salati tana fad'in wai kai Yayanah yaushe zaka canja halinka ne, har yanxun kuna nan a haka lallai kam, taja hannun Nasrin tace muje d'akinki, Yayanah, Ahmad na fallon 'kasa yana jiranka, suka fice, ya rufa musu baya,..... Sun shiga d'aki, Na'ima tace "haba Aunty Nasrin, meyasa kike biye mai kuna irin wanan abun, baki san yarda zakiyi kija hankalin Namiji bane?, tace "wallahi Na'ima nayi nayi har na gaji", tace "kash" ai ba'a gajiya, makaman ya'ki zaki nemo masu karamci da aminci, bari kiji kinsan yarda ake tarairayan new baby idan an Haifa?, toh haka zaki maida Yayanah, wallahi Aunty Nasrin "you can do it, karki bani kunya mana...... Nasrin tace "hmmm" naji ni bama wannan ba ina so ki ro'ki mommy ina son in koma makaranta, Na'ima tayi murmushi zaki koma school but da sharad'i, tace menene sharad'in?, tayi murmushi tace "sai kin canja min Yayanah, if you do that I promise you zaki koma any type of school of your choice", but now sai kinyi abinda ya dace,...... Tayi shiru idanuwanta sun kawo ruwa, Na'ima tace zaki iya Aunty Nasrin "promise me zaki canja Yayanah" and also you will love him with your heart and soul"?, tayi murmushi tace "In shaa Allah" zanyi 'ko'kari inga na shawo kan wanan matsalar, thank for your care, I really appreciate your efforts", nagode sossai..... A nan ta 'kara mata wasu tips da zata bi domin shawo kansa, tace ina zuwa bari in d'auko bag d'ina nazo miki da wani tsaraba, ta fita bata dad'e ba ta dawo da jakanta, ta ciro humra tace "kinga wannan a gashi zaki rinka shafawa, ta 'kara ciro wani ta mika mata, wannan a jiki zaki rinka shafawa duk wani lungu da sa'ko na jikin ki, ta kara ciro wani kwalban turare tace wannan a jinkin kaya zaki rinka shafashi, sanan kwalliya ba kama hannun yaro duk wani shiga da zai rinka tasar mai da hankali ki rin'ka yi, and kuma nasan gobe zaki fara girki, a nan 'bangaren ba sai na miki bayaniba ke expert ce a nan wurin..... Sanan gobe Yaya Na'im zai fara aiki, karki dinga barin mijinki da yunwa, kiji koh, Dan Allah Aunty Nasrin karki bani kunya, kiyi komai "for the sake of your marriage and also for the sake of our family",...... Tace "Karkiji komai zan baki mamaki ba d'an 'karami ba, daga yau ba sai gobe ba, ko dan son da kuke nuna min, zan faranta muku ni kuma da yardar Allah...... Na'ima tace mungode sossai, Allah ya bar 'kauna, school kuma "In shaa Allah" zaki koma....... *EDITED BY* 🍒 NUSNIM ( *TWIN SIS*)🍒 📝 *DEDICATED TO*📝 Nafee Anker, Mm Shakur, Munay, Mamu, Afra and Rash Kardam Love you all😘 [1/25, 7:57 AM] ‪+234 706 774 5996‬: 👫 *HA'DI DAGA ALLAH*👫 *WRITTEN BY* KHADIJAH AL'EEMAN *66 - 70* ********** ✍🏻Gaba d'aya ya daburce, 'kamshin ya tada mai da hankali, 'karfin hali kawai yakeyi, ya gama sa mata kayan, ta kama hannunsa suka fita, shi dai binta kawai yakeyi tamkar raqumi da akala,...... Suna sauka Ahmad ya fara dariya, yana cewa Romeo and Juliet, irrin wanan soyayya haka, har ankawo abinci babyn mu nata kuka mu dai munci namu ko Nurrul Hayatee?, Na'ima tace wallahi kuwa baby, sun wani shige ciki, kamar su kad'ai ne a gidan...... Nasrin tayi murmushi suka gaisa da Ahmad, tace habebee muje muci abinci, ni wallahi yunwa nakeji, kuma kaima nasan kanajin yunwa, muje koh, ya bita kamar wani 'karamin yaro, ta juyo ta kalli Na'ima suka ma juna murmushi,..... Suka zauna nan ma Nasrin tace ai ita dole a kan 'kafanshi zata zauna, yace ba ga kujera nan ba kija ki zauna mana, ta 'bata rai tace "wallahi indai bazan zauna a kan 'kafanka ba bazanci ba....... Shi kuma yaji yana bukatar taci abincin, sai ya kama hannunta ya zaunar da ita kan 'kafarsa, ya zuba abincin ya fara bata a baki, tana 'koshi ta amsa spoon d'in ta fara bashi, Na'ima ta ta'ba Ahmd ta nuna mai su, ya saki baki yana kallonsu,.... Yace "baby yaushe suka fara wannan shirin haka?, tayi murmushi tace "ai ni dear dad'i naji wallahi, ta canja Yayanah, yanxun zai koma tamkar kowa, wallahi mommy sai taso Aunty Nasrin fiye da tunaninka, yayi murmushi yace "Allah ya 'kara had'a Kansu", tace "Ameen"....... Sai da Nasrin ta tabbatar ya kwoshi sanan ta kyaleshi haka, ta kwashe kayan ta kai kitchen, ta dawo ta samesu sunata hira, ta zauna kusa dashi, tace Aljananah yaushe zamuje gida gaida mommy?, yayi murmushi yace next week "In shaa Allah", tace toh Ubangiji Allah ya kaimu, dukansu suka amsa "Ameen"..... Ahmad yace toh masoya mu zamu tafi, mun gaisheku, Na'im yace "toh mungode", Ahmad yace Kasan mata da son gulma, zo muje waje abokina, Ku samemu a waje, suka fita abinsu...... Na'ima ta juya ta kalli Nasrin tace "wallahi har naji dad'i, ina ta sa miki Albarka, kinga yadda gaba d'aya hankalinsa ya koma kanki beda wani katabus, toh wallahi ki 'kara makaman ya'ki, kin dai ji abubuwan da na fad'a miki koh, ta d'aga kai, "In shaa Allah", I will try my best, tace toh shikenan muje,..... A 'bangaren su Na'im kuwa Ahmad cewa yayi abokina wai meke faruwane?, irrin wannan soyayyar haka, Gaskiya kun birgeni, abokina kar kayi wasa wallahi, Allah ya 'kara dankon soyayya,...... Ahmad ya amsa da ameen, amma kasan menene?, yace sai ka fad'a, nan ya kwashe labarin komai ya fad'a masa,Ahmad yace kasan Allah wallahi karkayi wasa da damanka, kawai ka yarda kana sonta, menene a ciki,... Na'im yayi murmushi, yace amma baka ganin ba zata rama abinda nayi mata ba kuwa?, Ahmad yayi murmushi yace "Nasrin nada hankali, tana da tarbiya ba abinda zata maka, ka yarda dani", yace toh shikenan za gwada, yauwa ko kaifa,....... A dai dai nan suka 'karaso wurin su, suka musu sallama suka shiga mota suka kama hanya..... *EDITED BY* 🍒 *NUSNIM ( *TWIN SIS*)🍒 📝 *DEDICATED TO*📝 Nafee Anker, Mm Shakur, Munay, Mamu, Afra and Rash Kardam Love you all😘 [1/25, 7:57 AM] ‪+234 706 774 5996‬: 👫 *HA'DI DAGA ALLAH*👫 *WRITTEN BY* KHADIJAH AL'EEMAN *61 - 65* *********** ✍🏻A lokacin Na'im ya shigo d'akin, yace toh ai sai a fito a d'aura mana girki koh, Nasrin tace "toh ba yanxun zamu fito ba kai wallahi heart ka cika son kwad'ayi, kai dai kace kayi missing d'in abincinah kawai", duk cikin shagwaba take kallonsa, ya tsaya shi kuma ya saki baki yana kallonta, sai kawai yaji tana burgeshi......... Na'ima tayi gyaran murya tace toh ai yau daga gidan mommy za'a kawo koh, sai gobe zata fara girkin, su Yaya manya an'kwosa a fara cin girkin amarya, toh ai naga ka saba cin abincin ba yau ka fara ba koh, yayi murmushi yace "hmmm, baza Ku gane bane, Nasrin ta tashi da sauri taje ta kwanta a kan kafad'ansa tana bubbuga 'kafa dan Allah Aljannah nah ka d'an kaini bathroom mana inyi wanna, 'kafafuwana ciwo suke min yau wallahi, ya kasa ce mata komai, sai kallonta yakeyi, tace toh ka tsugunna in hau mana, "yace Nasrin kina da nauyi bazan iyaba", tace ni wallahi toh ka d'aukeni sai ka kaini, in yaso sai ka fito, ya kasa ce mata komai kawai ya sunkuceta yayi hanyar bathroom d'in, aikuwa ta juyo ta kalli Na'ima tana murmushi, Na'ima ta d'aga mata babban yatsanta alaman jinjina, a lokacin kuma suka shiga bathroom d'in...... Yana ajiyeta ya juya zai tafi tayi saurin kamo mai hannu tana cewa "White man plss kayi min wankan duk jikina ciwo yakeyi", ya juyo da niyan mata masifa, sai kawai yaga tana mishi wanni kallon da bema san yadda zai fassara shi ba, duk jikin shi ya riga da ya mutu, ta 'ka'kalo murmushi yace "kinga muna da ba'ki a gidan nan, kar suga mun dad'e", tace toh shikenan sai na fito...... Bata jira mai zaice ba ta tu'be kayanta ta jefa a washing mashine,ta d'auko towel, da sauri ya juya ya fita, a lokacin kuma Na'ima ta fita, ya zauna ya dafe kai, yana tuna nin meke damunsa neh, yana jin wani abu ga me da Nasrin amma besan ko menene shi ba, ko dai ya fara son tah neh be sanibah, toh in dai hakane gaskiya akwai matsala,....... Yayi tsaki ya nah 'karyata abinda zuciyarsa ke fad'a masa, anya da gaskene kuwa, bai ankara ba kawai yaji har ta bud'e kofar bathroom d'in ya mi'ke da Saudi zai fita, tayi saurin shan gabansa, tace haba Hubbynah, ka jirani mana in gama shiryawa ko gaida Ahmad banyi ba fa,..... Be ce mata komai ba ya koma ya zauna, taje gaban dressing mirror d'in ta shafa mai, ta d'an dan gwala human da Na'ima ta bata na jiki ta shafa, ta shafa na gashin shima, ta gama kenan ta juyo zata je ta d'auko kayan da zata sa, taga yana Satan kallonta, tana kawowa daidai inda yake tayi saurin sakin towel d'in ta fad'a kanshi, tace "aush" tayi kamar ta yi tun tun'be, yayi saurin ri'kota yana cewa me ya faru, ta ri'ke 'kafa tana cewa na bige 'kafa ne, duk a cikin shagwa'ba takeyinsa,..... Yace "sorry kinji, tashi kisa kaya, tace bazan iyaba ka d'auko min insa please, yayi kamar bazaijeba, sai kuma ya tashi ya d'auko mata jallabiya black da veil white,.... Tace saura bra da pant, yayi shiru yana tunanin ya zeyi ya d'auko, ta 'kara shagwa'be fuska tana kuka, yayi saurin cewa a ina suke ta nuna sight drawer, ya bud'e gasunan birjik a ciki, sai da ya 'kare musu kallo ya d'auko mai iri d'aya (pant da bra d'in) white and black colour ya kawo mata,....... Tace toh kasa min mana, ya zaro ido yace "ni zansa miki?, ta gyad'a kai, yace "toh ai ban iyaba, tace zaka koya ai, ta nuna mai yadda akeyi da hannu, yasa yana wani runtse ido, ita kanta kunya takeji amma ya zatayi, dole ta ajiye kunya gefe, ta gyara mijinta....... Yana sa mata tunda turaren humra nan ya biggi hancinsa duk ya fara da bircewa....... *EDITED BY* 🍒NUSNIM ( *TWIN SIS*)🍒 📝 *DEDICATED TO*📝 Nafee Anker, Mm Shakur, Munay, Mamu, Afra and Rash Kardam Love you all😘 [1/25, 7:58 AM] ‪+234 706 774 5996‬: 👫 *HA'DI DAGA ALLAH*👫 *WRITTEN BY* KHADIJAH AL'EEMAN *71 - 75* *********** ✍🏻Suna tafiya, Nasrin ta kamo hannun Na'im tace Aljanah nah muje ciki koh, ya bita suka shiga ciki,suka zauna a fallon 'kasa, sai kuma Nasrin tayi zunbur ta tashi, yace "Ina zakije?, tayi murmushi tace ina zuwa yanxun zan dawo, yayi murmushi yace ki sameni a Fallon sama ina jiranki, ta gyad'a kai ta wuce........ Ya tashi, ya haura sama shima, ya shiga bathroom dan ya watsa ruwa, ya gama watsa ruwan ya fito ya shafa mai yasa riga "short sleep white da three quarter wando white", ya fesa turaren white men, ya dawo fallon ya zauna yana jiranta......... A 'bangaren Nasrin kuwa, ta cire wannan kayan da ya sa mata, ta d'auko wata riga iya kirjinta kawai ta ke rufewa, ko cibiya bata kai ba, ta dauko wando skin tied iya cinya tasa, ta shafe ko ina da wa'inan turarukan, sanan ta d'auko turaren down hill ta fesa a jikinta, ta raba gashinta gida biyu rabi ta kama da ribbon pink kallan skin tied d'in, kasanshi tasa pin na kama gashi colour sa blue, colour d'in rigan kenan, d'ayan kuma gefen ta 'kara taje shi ta barshi a baje, ta d'auko d'an kunne d'an 'karami pink colour tasa, sanan ta d'auko wani hill d'in takalmi blue colour tasa shi, gashi simple make-up tayi, abin ba acewa komai, tayi kyau sossai, ta kalli kanta a madubi sai kuma ta fara jin kunya, sai kuma ta tuna da maganan Na'ima, nan da nan taji wani 'karfi yazo mata, ta kama hanya ta fita........ Na'im na zaune ya d'an kishin gid'a ya rufe ido don bacci be isheshi ba, ya ji ana hura mai fuska, a hankali ya bud'e ido, ya 'kara rufewa ya bud'e, ya tashi zaune ya 'kare ma Nasrin kallo, yace "tsarki ya tabbata ga mahallincin wannan sura", ya had'iye miyau da kyar....... Be san sanda ya jawo Nasrin ba, ta fad'a jikinsa, ya kai bakinsa kan nata wani irrin laushi yaji, ga wani 'kamshi dake fitowa daga bakinta,...... Saida ya tsose bakinta sossai, da kyar Nasrin ta kwace kanta zata gudu, ya 'kara fisgota ta fad'a kan jikinsa, yanata wani shinshinata, duk ya birkice,da kyar ya saita kansa,....... Yana kallonta, ita kuma ta dukar da kai sai ya d'agota suka koma kan carpet, yace "Nasrin", sunan har kwakwalwar kanta taji shi, don be ta'ba kiranta dashi ba, yayi masifar dad'i a bakinsa, ta amsa a hankali........ Yace ban san da wani ido zan kalleki ba, bansan da bakin da zan ro'ke kibah, dan girman Allah kiyi hakuri ki yafe min duk abubuwan da nayi miki a baya, wallahi bansan me yasa nakeda wannan halin bah, but zama dake da kuma wa'azin da kike min, tare da taimakon Na'ima yasa na fahimci ya rayuwa yake, don girman Allah ki yafe min....... Wallahi ina sonki tamkar raina, ina son muyi zama dake na aminci da karamci tare da mutunta junah, Nasrin zuciya baza ta ta'ba samun natsuwa da kwanciyan hankali ba, matsawar bakice kin yafe min ba, kuma ina so ki furta kina sona kamar yadda nake sanki, inajin ki har cikin raina, ina kuma alfahari dake a matsayinki na matata...... "Nasrin" kuka yaci 'karfinsa, ya kasa magana...... Ta d'ago kanta tana kallonsa ita ma tana hawaye, ta goge mai hawayen fuskarsa tana jijjigashi, tamkar karamin yaro tace "nagode ma Allah daya nuna min wanan ranan, na dad'e ina jiran wanan lokacin sai gashi Allah ya nuna min yau"........ Naji dad'i sossai da Allah ya fahimtar da kai gaskiya, yadda rayuwa take, na yafe maka mijinah domin ni ba jahila bace bare ince bazan yafe maka ba, domin ko Allah muna masa laifi ya yafe mana, toh in haka ne, ni wacece da za'amin abu ince bazan yafe bah...... Assalima yanxun Kaine keda aljannah tah, idan na bika tayi min kyau in ban bika ba kuwa, na gama ta'bewa duniya da Lahira, toh dan me bazan yafe maka bah,....... Wallahi na yafe duniya da Lahira, kuma zan maka biyayya dai dai gwar gwadon iya wata, sai dai kaima ina rokonka don girman Allah ka canja d'abi'unka, kaso talakawa ka taimaka musu, iyayenka ka rinka yi musu biyayya, tsakaninka da kowa ya zama sai dai Sallama kawai, toh rayuwa zatayi kyau kuma kaima zakaji dadi, sannan zanyi alfahari da kai a matsayin miji please........ Yayi saurin sa ma ta hannu a baki alamar tayi shiru, yace "In shaa Allah, zaki sameni mai yin duk wani abu da zai faranta ran kowa, kuma yanxun zan amsa sunana na "white man", domin komai nawa zai zama fari harda zuciyatah...... *EDITED BY* 🍒 NUSNIM ( *TWIN SIS*)🍒 📝 *DEDICATED TO*📝 Nafee Anker, Mm Shakur, munay, Mamu, Afra and Rash kardam Love you all😘 [1/25, 7:58 AM] ‪+234 706 774 5996‬: 👫 *HA'DI DAGA ALLAH*👫 *WRITTEN BY* KHADIJAH AL'EEMAN *76 - 80* *********** ✍🏻Nasrin tayi murmushi, tace "Alhamdulillah", yau ina mai matuk'ar farin ciki, Allah ya amsa adu'o'i nah, gashi Mommy da Daddy ba 'karamin dad'i zasu ji bah,......... Yayi murmushi yace gobe nake so muje gidan, amma su Shureim ba sa nan, tace ina suka je?, yace "sunje gidan Dady Tofiq dukan su" kai gidan bazai min dad'i ba, amma tunda Mommy na nan ba matsa, yayi murmushi yayi 'yar gidan mommy,........ Dare nayi tayi wankanta kamar yadda ta saba, tasha white Night gown d'inta ta kwanta, ba ta dad'e da kwanciyya ba ya shigo d'akin, ya yaye blanket d'in, yace mata "waya gaya miki yanxun ke kad'ai zaki rinka bacci?, ai yanxun mu biyu zamu rinka bacci........ Ta shagwa'be mai fuska tace toh ai ni na fara jin bacci, yayi murmushi yace "mallama tashi zakiyi mu tafi 'bangarenah", ta rufe ido kamar tana bacci, aikuwa bata ankara ba taji ya d'auketa chak, be direta a ko ina ba sai saman gado, ya hau shima, yasa kansa a 'kirjinta nan da nan wannan turaren humra ya daki hancinsa, ya sauke nufashi da sauri, yace "Mine" ina da tambaya, tace "yi tambayarka ina jinka", yace dan Allah menene sirrin wannan turaren, tunda nake ban ta'ba jin turare mai 'kamshin dad'in wannan ba wallahi,...... Tayi murmushi kai dear, turare ne kawai ba wani abu ba, sai yayi murmushi yace tashi muyi sallah, tace "toh ai ni nayi sallah" yace raka'a biyu zamuyi mu gode ma Allah, taji gabanta ya fad'i, don ita wallahi ba abinda take tsoro irrin wannan Daren........ Yace mata tashi mana, ni gashi har nayi ke kina zaune, ta tashi tayo alwala, ta fito, tayi hanyar 'kofa, yayi saurin shan gabanta, yace ina zakije?, tayi murmushi tace hijabi zan d'auko, yace koma in d'auko miki, ta koma ta zauna, ya juya ya fita yana murmushi, a ranshi yace "yarinya duk ki gama wani jin tsoronki"...... Ya kawo mata hijabin, tasa, suka tada sallah, sun idar, yayi mata tambayoyi kamar yadda addinin musulunci ya tanadar, ta kuma bashi amsa yadda ta dace, tana mamakin addini irrin na white man, nan ya kama kanta yayi mata adu'a, daga nan suka mike yaja hannun ta suka koma saman gado.......... Daga nan labari ya fara canjawa, naso inga ko me zai faru, ashe Anee Luv na biye dani tana kallona, daga nan ta jawoni waje tace toh ya isa haka sai a barsu su sha amarcin su, dole ne sai kin d'auko komai ne?,.......... Nace toh Anee Luv da safe na koma, masu karatu nima zan ajiye littafina da abin rubutu, zanje in huta sai gari ya waye da safe na dawo,........ Sai Ince Nasrin da Na'im asuba ta gari....... *EDITED BY* 🍒 NUSNIM ( *TWIN SIS*)🍒 📝 *DEDICATED TO*📝 Nafee Anker, Mm Shakur, Munay, Mamu, Afra and Rash Kardam Love you all😘 [1/25, 7:58 AM] ‪+234 706 774 5996‬: 👫 *HA'DI DAGA ALLAH*👫 *WRITTEN BY* KHADIJAH AL'EEMAN *82 - 85* *********** ✍🏻washe gari na koma a hankali na tura 'kofar falon nashiga, "Na'im na hango zaune da Nasrin a kan cinyarsa yanata lalla'bata yana bata chips a baki, "nace toh fa, wai ni me ya faru ne?, gashi sai wani shagwa'ba takeyi mai, nace oh ni "AL'EEMAN, bari dai in haura sama in le'ka 'bangaren Na'im 'kila akwai abinda ke faruwa......... Ina shiga na hango a canja zanin gado, nace shikenan Nasrin an zama cikakkiyar mace, toh bari in lalla'ba in koma 'kasan nan in cigaba da d'auko rahoto, dan nasan masu karatu an'kosa a ji cigaban rayuwar wa'in nan ma'aurata,...... "Nasrin sai shagwa'ba ake zubawa, Na'im yayi yayi ta tashi ta taka amma ina ta'ki, yace a haka ne kikeson muje gidan Mommy?, ai da sauri ta tashi kamar ba ita ba, Na'im ya rin'ka mamaki, yace ya naga tafiyar har ta koma daidai?, tayi murmushi wallahi heart na warke ka tashi muje gidan su Mommy ka ji, yayi murmushi yace "yau baza ajeba sai gobe, ta shagwabe fuska kamar zatayi kuka, tace haba mana dan Allah ka taimaka min please....... Yace toh naji za'aje, muje mu shirya amma da sharad'i in har kin yarda zamuje, tace "menene sharad'in?, yace idan munje bazaki kyaleni ki tafi wurin mommy bah, har muje mu dawo muna tare kusa da juna, tace "naji na yarda" yayi murmushi yace ohyah muje mu shirya, suka haura sama, zata wuce d'akinta yace ina zakije?, ta ce zanje in shirya mana yace toh muje tare za muyi wanka, ta 'bata rai wallahi in muje wankan nan jagulani za kai tayi har sai time ya wuce, yayi murmushi ya koma ya sakko 'kasa ya zauna yace an fasa zuwa, tace haba manah, toh na yarda, yace "that is my girl", ohya let's go, suka je aikuwa haka akayi saida ya gama jagulata kafin sukayi wanka suka fito, da kyar ya barta taje 'bangarenta dan ta shirya........ Sun shirya sun fito, shi yasa shadda white tasha aiki golden colour ga hula ma golden colour, ita kuma tasa doguwan riga golden colour kwalliyan rigan kuma white, tasa white veil ta yane kanta kamar wata 'yar larabawa, wace "wow what a perfect match", kinga yadda kika yi kyau kuwa kodai my fasa neh, tace haba mana dan Allah nasa raifah, yace toh naji muje...... Sun kama hanya cikin nishad'i da begen juna tare da kallamai masu dad'i har suka kai gidan yayi horn maigadi ya bud'e masa yana cewa barka da zuwa ranka ya dad'e ya tsaya yace "barka dai Mallam Lado mun sameku lafiya yace lafiya lau, suka gaisa da Nasrin, Na'im ya d'auko kud'in da baisan nawa ba ya mik'a mai, maigadi nata godiya tare da farin cikin canjawan Na'im, suka wuce suka shiga ciki, yayi parking suka fito a lokacin Mommy na ba Ado driver sak'o, tana ganinsu ta fara murmushi cike da mamakin ganinsu, Na'im ya mik'a ma Ado driver hannu suka gaisa ya zaro kud'i a aljihunsa ya mik'a mai, ya amsa cike da farin ciki yayi godiya ya wuce........ Mommy ta ruk'o Nasrin tana farin ciki suka kama hanyar shiga ciki, sun sami Daddy a zaune yace manyan bak'i ne yau a gidan namu?, sukayi murmushi dukansu, Nasrin ta gaida shi cike da kunya ya amsa da fara'ar sa, Na'im ma ya gaida shi Daddy ya bashi hannu sukayi musabaha, Daddy yace yanxun nake shirin fita zanje meeting a Misbahul Islam, Na'im yace Allah ya tsare, Nasrin ma tace a dawo lafiya ya amsa tare da sa musu Albarka, mommy kuma ta raka shi, .......... Ta dawo ta kira Nafeesa da ta kawo musu abin motsa baki, ta kawo musu sun gaisa ita ma Na'im yayi mata kyautar kud'i, haka ma'aikatan nan suka rinka zuwa suna gaisawa Na'im na amsawa cikin farin ciki tare da yi musu kyauta, Mommy taji dad'i sissai ta kuma 'kara jin son Nasrin a ranta, ta kuma fahimci yanxun akwai soyayya mai k'arfi a tsakanin su, motsi kad'an Nasrin tayi hankalinsa na kanta........ Suna fira saiga Lukman ya shigo suka gaisa da Mommy Na'im yace muje garden dama ina nemanka suka kama hanya suka fita...... Mommy ta kalli Nasrin tace kinyi k'ok'ari sossai Allah ya biyaki da gidan Aljannah, farin cikin da kika samu ubangiji Allah yasa ki dawwama a cikin farin ciki har 'karshen rayuwarki, Nasrin ta amsa da Ameen Mommy, Nafeesa ce tazo tambayar abinda za'a dafa da rana, Nasrin tace "gaskiya tunda nazo yau ni zanyi girkin, Mommy tace a'a ki huta dai daga zuwa sai shiga kitchen, Nasrin tace dan Allah Mommy ki bari inyi dan Allah, tace "toh shikenan naji ki dafa duk abinda ya dace", tayi murmushi tace Nafeesa muje kitchen d'in ta tashi da k'yar ta nufi kitchen d'in, Mommy ta lura da tafiyar da takeyi tayi murmushi bata ce komai ba...... A 'bangaren Na'im da Lukman kuwa sun sami wuri sun zauna, Na'im ke bama Lukman shawaran yayi aure domin Aure da dad'i wallahi, Lukman mamaki ne ya cikashi wai yau shi Na'im ke bama shawaran yayi Aure, lallai a gaida Nasrin tayi k'ok'ari sossai....... *EDITED BY* 🍒 NUSNIM ( *TWIN SIS*)🍒 📝 *DEDICATED TO*📝 Nafee Anker, Mm Shakur, Munay, Mamu, Afra and Rash Kardam [1/25, 7:58 AM] ‪+234 706 774 5996‬: 👫 *HA'DI DAGA ALLAH*👫 *WRITTEN BY* KHADIJAH AL'EEMAN *86 - 90* *********** ✍🏻"Lukman ya juya ya kalla Na'im yace abokinah yaushe ka canja haka?, gaskiya Nasrin 'yar baiwa ce, kuma Auren ku *HA'DI DAGA ALLAH* ne, gaskiya na jinjina mata ban ta'ba tunani White Man zaka canja haka ba, ya d'aga hannu sama yace ya Allah ka bani mata mai irrin halin Nasrin, Na'im ya amsa "Ameen", suka juya suka koma cikin gida...... Nasrin na kitchen tana had'a white rice da miyar cabbage da yaji hanta, a gefe kuma ta had'a juice d'in kwakwa da dabino da yaji pick milk, gidan ya d'auki 'kamshi mai dad'in gaske,ga gefe kuma ta na had'a pepper soup d'in koda domin 'yan gidan na sonshi sossai...... "Su Na'im ne suka shigo, yake cewa mommy ina matanah?, Mommy ta fara tafa hannu tana salati, Na'im ba kunya kake tambayata ina matarka toh tana kitchen tana girki, yayi sauri juyowa ya kalleta Mommy she is sick fa amma kika tura ta kitchen haba Mommy..... "Ta kalleshi da sauri meke damunta Na'im?, nan fa ya fara Sosa kai besan wani 'karya zai mata ba, can kuma yace kanta ke ciwo mommy, tace shine tace min zatayi girkin na batta, ta kwalla mata kira ta fito da sauri, tace Nasrin kanki na ciwo shine kika shiga kitchen?, Nasrin tace mommy waya gaya miki kaina na ciwo?, Ta nuna Na'im tace shi ya gaya min, ta juya ta kalleshi sai ya kashe mata ido d'aya, tayi murmushi tace mommy kan ai ya daina ciwo, tace toh Allah ya 'kara lafiya duk suka amsa da Ameen..... Suka ji ana cewa irrin wannan 'kamshi haka, suna juyawa sukaga Labiba, Safiyya, sai Shurem, da Sauri suka karasa wurin Nasrin suna dariya, Labiba da Safiyya suka rungumeta suna cewa we really missed you Aunty Nasrin, Shurem kuma yace I missed ur food, your stories in fact everything, tayi murmushi tace Allah sarki toh ai yau gani nazo kuma sai dare zamu koma suka fara murna........ Na'im ne yayi gyaran murya yace lallai ma yaran nan ba Wanda yazo ya min magana, suka juyo suna cewa sorry bros wallahi munyi missing d'in alot da ka d'auke mana Aunty Nasrin, yayi murmushi yace toh ga ta nan yau sai dare ai, suka duga murna,..... "Itakoh mommy cewa tayi toh ai yau kuma baza Ku barta ta huta ba wallahi, shiko Lukman idonsa kyar a kan Labiba yarinyar na burgeshi sossai, Niko nace anya ba sonta yakeyi ba kuwa?, hmmm muje zuwa idan tayi 'kamshi AL'EEMAN zata jine..... "Safiyya kuwa cewa tayi Yaya Na'im nan da two weaks send forth d'in mu hope kaida Aunty Nasrin zaku je?, yayi murmushi yace ai dolen mu muje, za muje ki kwantar da hankalinki, Allah ya kaimu tace Ameen ya Allah nagode...... "A lokacin Dady ya shigo dai dai kuma a na kiran sallah, dukansu mazan suka d'inguma zuwa masalaci yayinda matan suka shige ciki dan yin nasu sallahn........ Sun dawo an hallara a dining Labiba tayi serving d'in kowa, sunci sun sha, Suna ta yaba girkin, Lukman yayi musu sallama ya tafi, suna gidan har dare, missalin 'karfe takwas suka shirya zasu koma, mommy ta 'kara ma Nasrin kayan gyaran jiki da turaruka shi kuma daddy ya 'bata kyautar kud'i wanda nima kaina bansan yawansu ba da kyar ta amsa, suka 'kara yi musu nasiha tare da fatan Alkhairi,.... Suka kama hanya cike da kewar gidan, yayinda su Labiba kamar suyi kuka dan suna matuk'ar son Nabila....... *EDITED BY* 🍒 NUSNIM ( *TWIN SIS*)🍒 📝 *DEDICATED TO*📝 Nafee Anker, Mm Shakur, Munay, Mamu, Afra and Rash Kardam Love you all😘 [1/25, 7:58 AM] ‪+234 706 774 5996‬: 👫 *HA'DI DAGA ALLAH*👫 *WRITTEN BY* KHADIJAH AL'EEMAN *ASSALAMU ALAIKUM* Dukan godiya ta tabbata ga Allah mai kowa mai komai domin shike rayawa kuma shike kashewa toh mungodewa Allah, *Sanan kuma ina mika godiyata gareku a bisa rashin da nayi, da kuma rashin lafiya danayi, naga sakon adu'oin Ku, wasu sun kirani, wasu ta wasapp wasu kuma message sukayi min, nagode sossai ubangiji Allah ya saka da alkhairi, Allah ya bar zumunci*...... 'Yar uwata kuma da na rasa ina rik'on Allahu subhanahu wata'ala da ya gafarta mata yasa aljannah ce makomarta da sauran d'inbin al'umar da suka rasu, idan tamu tazo Allah yasa mucika da kyau da imani... Allahuma Ameen😭👏 *91 - 95* *********** ✍"sun isa gida a kajiye suka haura sama sukayi wanka, sannan suka dawo fallo sukayi fira daga nan ya sunkuceta yayi bedroom da ita, ni AL'EEMAN nace musu asuba ta gari dan naga Na'im sai hararata yakeyi harda rufo 'kofa..... "Yau ta kama za'aje send forth d'in Safiyya suna ta shiri sai yaga Nasrin nata kwaso kaya tana sawa a boat, yace "wai wannan kayan na menene?," tayi murmushi toh ina ruwanka idan muje kagani, suka kama hanya, a hanya suka had'u da Na'ima da Ahmad dama sun biya sun d'auko Nabila, Lukman da Shureim, dan yanxun akwai soyayya mai k'arfi a tsakanin Nabila da Lukman, har Na'im na musu tsiya yana cewa duk sun kwashe mai k'anne sunga yara kyawawa" suke cewa ba komai ai mommy ta Haifa bashi bah..... Sunkai makaranta lafiya Safiyya nata murnan ganin su, tace Yaya Na'im mommy da Daddy fah", yayi murmushi yace toh 'yar gidan Mommy ba gamuba mommy ma yau sai ta huta, Nasrin ta jata zo muje kiga wani abu, ta Ciro kayan boat d'in suka bud'e, wani had'add'en Memo ne, ga biro,sticker's, key Holder's, handkerchiefs ne komai da pic d'in Safiyya a jiki, courtesy kuma ansa ALHAJI HARIS SAIF'S FAMILY..... Na'im ya rinka mamaki yaushe akayi duka wa'in nan bai sani ba, lallai Nasrin a gaisheta, yaji ya k'ara sonta fiye da da, Nasrin ta zama jigo na rayuwarsa, yana kuma alfahari da ita sossai, aka gama suka dawo gida, Nabila da Shureim suka ba Mommy labarin kayan da Nasrin ta kaima Safiyya, taji dad'i sossai ta kuma sa mata Albarka..... "A Haka rayuwa keta tafiya, Nasrin taje gidansu taga anyi gyara ta ban mamaki, data tambaya Ummantah tace ai Na'im ne ya gyara, gashi duk sati sai ya kawo musu kayan abinci, ga k'anenta kowa na zuwa makaranta, farin ciki tayi sossai, domin ba abinda takeso irrin 'yan'uwanta da mahaifiyarta, da suka dawo gida kamar ta goyashi, sai yaji wani sanyi a ranshi ko ba komai tayi murna da abinda yayi mata har ta nuna farin cikinta akai..... Yau sun tashi Nasrin na fushi da Na'im saboda yak'i kaita gidan Na'ima, tana ta gungunai yau fa watan ta kusan shida yak'i kaita gidan ta, Na'ima tayi complain har ta gaji tasa musu ido, suna cikin rigiman ne Ahmad ya kirashi Na'ima ta haihu ta Haifa twins duka Maza, ya fad'a ma Nasrin ai sai ta hau yin rawa a gafansa, tsayawa yayi ya k'are mata kallo, sai kuma taji kunya ta rufe fuskanta, yayi dariya kinsan Allah sai kin min rawa yau idan ba haka ba kuma ba inda zamuje, tayi murmushi tace wallahi zan maka menene a ciki "aikuwa ta fara karkad'a mai jiki har saida ya had'iye miyau, yace to ya isa haka, d'auko mayafinki mu tafi, sunje sunga babies, Nasrin nata jin dad'i..... Kullum sai taje gidan danma Na'im ya hana da kwana zata rinka yi, anti suna yara sunci sunan Na'im da Nasrin dan Ahmad yace dole ayi musu takwara irrin wannan soyayya da suke sha, Na'im akwatuna yayi a inda Nasrin ta taka rawar gani wurin abubuwan da za'a raba na suna, anci ansha ankuma tashi lafiya sai muce Allah ya rays twins....... Yau ya kama ranar jum'a Nasrin na zaune tana tunanin ta fara ganin canjin yanayi a tare da Na'im, toh wai meke damunsa ne?, me kuma yake faruwa?,......... *EDITED BY* 🍒 NUSNIM ( *TWIN SIS*)🍒 📝 *DEDICATED TO*📝 Nafee Anker, Mm Shakur, Munayshat, Mamu, Afra and Rash Kardam Love you all 😘 [1/25, 7:58 AM] ‪+234 706 774 5996‬: 👫 *HA'DI DAGA ALLAH*👫 *WRITTEN BY* KHAFIJAH AL'EEMAN *101 - 105* ************* ✍"Yace toh Hidaya itace yarinyar da ta samu sangarta daga mahaifiyarta, Hidaya 'yar macece, wato idan nace 'yar mace wadda mace ta raineta macen ma 'yar duniya, mahaifin Hidaya ya rasu tun tana da shekara uku a duniya, wasu ma na zargin cewar mahaifiyarta ita ta kashe mahaifinta..... A lokacin da mahifinta ya rasu ba'a dad'e ba mahaifiyarta ta bara bushasha da kud'in gadonsu, bata ganin kowa da mahimmanci, duk abinda ta ga dama takeyi sai dai abu d'aya ta tsaya tasa Hidaya a makarantar boko, har tayi degree d'inta ta kuma samu aiki a kamfanin mahaifinku....... "Ya dafa mata kafad'a yace my dear meyasa kika min wannan tambayan, kinsan Hidaya ne ko kuma wani abin tayi miki?, tace ko d'aya Abban Amir, kasan me ya faru ne?, nan ta kwashe komai ta fad'a masa, yace duk yadda akayi bata barshi haka ba wlh, akwai abinda ta mishi sai antashi da gaske amma yanxun ki kwanatar ma da Nasrin hankali daga nan sai asan abinyi Allah ya kyauta ta amsa da Ameen, muje kaci abinci...... A 'bangaren Nasrin kuwa ta gama gyara ko ina tasa turaren wuta amma me sai daji kwatakwata bata son k'anshinsa, hakanan ta kashe tasaka room freshener ta shiga tayi wanka ta gama komai tayi kwaliyya sai dai adu'arta d'aya Allah yasa ya dawo da farin ciki dan yanxun kamar me aljanu yake, watarana yayi fara'a wata rana ya dawo kamar Wanda aka kashe ma wani, tana tunanin sai gashi ya shigo, ya tafi da Sauri yarungumeta yana cewa I missed my wife, da fatan kina lafiya, ta amsa da lafiya lau Habibi ka dawo lafiya?, yace lafiya lau, muje inyi wanka, suka haura sama amma Nasrin tana tuna nin hali irin na Na'im........ "Yau ta kama asabar ba aiki, Na'im ya shirya yace zanje gida indawo kinsan anfara shirye shiryen bikin Safiyya koh!, tayi murmushi Hubby zan bika dan Allah, yayi murmushi sorry bbynah gobe zamuje kinji, and karki damu sai dare zamu dawo goben In shaa Allah I promise you, tayi mirmishi Allah ya tsare ya kuma kare min kai tayi mai peck a kumatu yayi mirmushi I love you bbynah, tace I love you to my hubby, tana d'aga mai hannu har ya fita a gate d'in..... Ya kai gida lafiya ya samu mommy da Daddy a fallo ya zauna suka gaisa ya sunkuyar da kai yana son yayi magana amma yana tsoro, Daddy ne ya lura da hakkan yace my Son meke faruwa ne akwai matsala ne?, ya d'aga kai, toh muna jinka go on, Daddy Au... Sai kuma yayi shiru, Daddy yace kwantar da hankalinka tell me what is it?, Daddy dama Aure nake son in k'ara!, suka d'ago kai da sauri suka kalleshi..... Mommy ne ta fara magana cikin fad'a kana da hankali kuwa, yaushe kayi Aure ko shekara d'aya fa ba'ayiba, tsaya ma tukunna Nasrin d'in na maka wani abune ko kuma bata kula da kai yadda ya kamata ne?, ko kuma akwai halin da takeyi ne Mara kyau da baka so?, ina maka magana kayi shiru, ka amsani Na'im..... Ya dukar da kai yayi shiru, sai daddy ne yace Na'im meke faruwa ne? wacece kuma wadda zaka Aura?.... *EDITED BY* 🍒 Nusnim ( *TWIN SIS*)🍒 📝 *DEDICATED TO*📝 Nafee Anker, Mm Shakur, Munayshat, Mamu, Afra and Rash Kardam Love you all😘 [1/25, 7:58 AM] ‪+234 706 774 5996‬: 👫 *HA'DI DAGA ALLAH*👫 *WRITTEN BY* KHADIJAH AL'EEMAN *106 - 110* ************* ✍ "Daddy sunanta Hidaya kuma a under company ka take aiki, sannan suna zaune a kinkinau ita da mahaifiyarta, mahaifinta ya rasu tun tana 'yar k'ara ma...... "Wlh Na'im baka isa ba yaushe yaushe kayi aure cewar mommy, har zaka d'auko min wani Aure, shin menene Nasrin d'in tayi maka ko ta maka laifine?, ya girgiza kai toh fad'a min menene dalilin k'ara aure a wannan lokacin?,.... "Mommy dan Allah ki barni in k'ara auren nan domin Allah (S.W.A) na cewa _ki auri mataye bibbiyu, ko uku uku, ko hud'u hud'u, sai yace amma me inhar zakuyi adalci a tsakanin su_ kinga kenan Mommy Allah be hanani k'ara aure ba, domin zan iya zan kuma kwatanta adalci a tsakanin su, sannan Momm yau wata nawa kenan Nasrin ko 'barin wata bata ta'ba yi ba?, ai mommy kema kyaso kiga jikokinki ta 'bangarenah! "Gaban mommy neh ya fad'i har Na'im ne zai fara maganan haihuwa toh idan kuma rashin haihuwa daga wurin shine fah?, amma kuma abinda ya fad'a na cewar Allah ya bashi izinin ya k'ara aure har mata uku yanxun ba k'arya yayi bah! duk a zuciyar ta take fad'in haka..... Ganin tayi shiru Daddy ya fara magana, Na'im kaje idan nayi shawara da d'an uwanah zan kiraka, Daddy dan Allah ina son a had'a da bikin Safiyya ne please Daddy",..... Ba komai Na'im tashi kaje Allah ya za'ba mana abinda yafi alkhairi, Ameen! Ya tashi ya kama hanya ya tafi abinsa..... Mommy ta juyo ta kalli Daddy tace nidai har ga Allah wannan aure be kwanta min a raiba, haba Mokmy yara kiyi mishi adu'a kuma kiyi mai fatan alkhairi, toh Allah ya za'ba abinda yafi alkhairi yace Ameen, ta mike bari inje in duba abinda akeyi a kitchen ta fita....... "Washe gari Na'ima tazo gida dan tsara yadda bikin k'anwan nata zai kasance amma tana zuwa sai mommy ke fad'a mata abinda ke faruwa, sannan ta shaida mata cewar Daddynsu ya kira Alhaji Tofiq ya gaya masa kuma ya bada shawaran a barshi yayi tunda yace zai iya! Na'ima hankalinta ya tashi ta fad'a ma Mommy labarin Hidaya da Ahmad ya fad'a mata, Mommy tace subhanallah yanzun toh ya za muyi ne! Karki damu zansa a mishi saukan al'qurani bayan bikin sannan kuma zamu tsananta adu'a, shima zanyi iya bak'in k'ok'arina inga ya rik'e azkar, sannan ita kuma Nasrin dama na siya mata form kin sani, nan da two weeks zasuje screening ita ba ma sai tayi wani Exams ba tunda Allah ya taimaka tana da JAMB, toh Admission ya fito kuma immediately zasu fara karatu kinga komai zaizo da sauk'i,..... Na'ima tayi ajiyar zuciya shikenan Mommy Allah yasa haka shi yafi Alkhairi amma gaskiya Aunty Nasrin zata shiga wani hali wlh, ba komai Allah shi zai shige mana gaba cewar mommy! Ameen.... "Nasrin da taji Na'im zai k'ara aure har ta d'aga hankalinta amma mommy da Na'ima sun kwanatar mata da hankali, tayi adu'a Allah yasa haka shi yafi alkhairi,..... "Haka rayuwa keta tafiya taje tayi screening d'in kuma Alhamdulillah ta wuce har sun fara lectures sun bata pure chemistry, gashi kuma abinka ga mai kwakwalwa tana fahimtar komai, tana zaune yauma kamar kullum wata tazo ta mika mata hannu tace Assalamu Allaikum, ta amsa mata cike da murmushi a fuskarta, sunana Zainab Abdullahi ina zaune a da mijinah a hayin banki amma gidan iyayenah na unguwar kanawa, kullum ina ganinki kuma course d'in mu d'aya dake please "can we be friends" in har ba damuwa tace "why not" ni sunana Nasrin k'asim muna zaune a isa kaita dake malali dat is gidan aurenah kenan! Amma gidan mu na Unguwar rimi.... "Zainab tayi murmushi Ma shaa Allah, Nasrin ta kalla agogo tace Zainab lokacin Sallah yayi muje muyi kafin time d'in lecture yayi, suka mik'e suka tafi tun daga ranan shakuwa mai k'arfi ya shiga tsakanin su.... "Alhaji Tofiq da Alhaji Haris Saif sunje sun sami 'yan uwan mahaifin Hidaya kuma a basu amma tun a lokacin Alhaji Haris Saif ya fahimci cewa akwai matsala amma ya zeyi tunda Na'im ya kafe dole sai anyi auren nan, yana hango akwai wani abu dake faruwa kamar yadda Mommy ta ke cewa koma menene Allah ya sa mudace..... An tsaida rana lokaci d'aya da Safiyya, Tsakanin Nasrin da Na'im kuwa ba abinda ya canja yau yazo da farin ciki gobe kuma ya juya kamar bashi ba! Ita dai tasa ma sarautan Allah ido kuma bata ta'ba fad'a ma kowa ba in banda sanda ta fad'a ma Na'ima, kuma koda Ummanta taji labari ta kirata ta mata nasiha sossai akan ta zama mai hakuri tabi mijinta shiyasa ita kuma take shanye duk wani abu da zai rinka mata.... "Makaranta kuwa tana maida hankali sossai a tsakaninta da zainab sai mutuntawa da girmamawa kuma suna karatu sossai dan burinsu baifi ace sun fito da first class ba..... Sai ince Allah ya taimaka ya kuma bada sa'a.... *EDITED BY* 🍒 NUSNIM ( *TWIN SIS*)🍒 📝 *DEDICATED TO*📝 Nafee Anker, Mm Shakur, Munayshat, Mamu, Agra and Rash Kardam Love you all😘 [1/25, 7:58 AM] ‪+234 706 774 5996‬: 👫 *HA'DI DAGA ALLAH*👫 *WRITTEN BY* KHADIJAH AL'EEMAN *96 - 100* *********** ✍"Nasrin na nan a zaune har Na'im ya shigo ta tashi ta amsa brief case a hannun sa tayi mai sannu da zuwa ya amsa ba yabo ba fallasa, suka haura sama yana Shiga ya fada toilet ya watsa ruwa, kafin ya fito ta ciro mai kayan da zaisa, ya fito ta d'auko mai zata shafa mai kamar yadda ta saba amma me sai ya dakatar da ita, ya shafa ya juya ya d'auko wasu kayan yasa ya ce muje yunwa nakeji....... "Sun isa dining ya zauna ta fara zuzzuba mai abinci, sai cewa yayi cikin tsawa nace miki yunwa nakeji amma sai aiki kikeyi a hankali, ta d'aga kai ta kalleshi tace haba "hubby" yanxun duk saurin da nakeyi baka gani ba?, dan Allah waya 'bata maka rai? Ka shigo sai fushi kakeyi ni heart a 'yan kwanakin nan bansan meke damunka ba gaba d'aya ka canja na rasa gane kanka a 'yan kwana biyun nan...... Yace wai ke meyasa baki da hankali ne?, kisa min abinci kin tsaya kina min maganan banza, toh bud'e kunnenki da kyau kiji Aure zan k'ara very soon, abinci kuma na fasa ci, barin gidan zanyi inje inda za'abani ba tare da min wasu surutun banza ba, yaja tsaki ya tashi ya fita abinsa..... "Nasrin kuwa abin mamaki ya bata toh ita bata san abinda tayi masa ba, gashi har yana ik'irarin zai k'ara aure, ita bata san abinda tayi masa ba, kuma a iya zamanta dashi bata ta'ba mai wani abu ba, kullum burinta shine taga ta kyautata mishi, kuma ba wai halinsa nada bane ya dawo dashi, tunda da halinsa ne nada bazaice zai k'ara Aure ba, duk da dai ance "mai hali bai fasa halinsa, koma dai menene Allah ya kyauta...... "Haka suke zaune yau ak'alla sun kai wata biyu kenan, wata rana zai zo da fara'a kamar bashi ba wata rana kuma akasin haka, yana abu kamar mai ta'bin hankali, tun bai damunta har yazo ya fara damunta, gashi tana son zuwa gida ya hanata zuwa, tana zaune a fallonta ta rasa abinyi can kuma ta d'aga waya ta kira Na'ima suka gaisa ta tambayi lafiyan twins, Na'ima tace Aunty Nasrin kamar akwai abinda ke damunki, muryanki yayi wani irri, mai ke faruwa ne?,..... "Nasrin ta kwashe komai dake faruwa ta fad'a mata, Na'ima tace me yasa tuntuni baki sanar dani ba, tayi murmushin k'arfin hali tace da nayi tunanin wani laifi nayi masa k'ilan zan iya shawo kan abin, amma me sai naga abin natayin gaba, shiyasa na yanke hukuncin in kiraki sannan nayi nayi naje gida ke nama fita ko nan da can wlh ya hanani, tace karki damu ina zuwa, ta katse call d'in..... "Na'ima ta kira shi tace haba yayanah two dayz ka shareni kwata kwata ka daina ji dani, sannan ga Amir da Amira suma sunata missing d'inka and u refuise to come why, ko min maka wani laifin ne?, ...... Yayi maurmushi ko d'aya my sister abubuwa ne suka min yawa a office, tace toh yayanah Allah ya bada Sa'a, ya amsa da Ameen, tace ya gida ina Aunty Nasrin?, itama kwana biyu Shiru kakeji, yace kedai bari ni yanxun ma wlh haushi take bani sannan kuma ni yanxun Aure ma nake son yi wlh, gaban Na'ima ne ya fad'i tace Yayanah Aure kuma?, Aunty Nasrin d'in yaushe yaushe ka Aure tah?, yau fa Aurenku 8 months fa kwata kwata, me ye dalilin son k'ara Aurenka?, Aunty Nasrin d'in toh me takeyi maka, bata kulaka ne?, ko kuma bata yimaka abinda kake so ne da zaka k'ara Aure?...... "Na'im yayi ajiyar zuciya yace babu ko d'aya nidai haushi take bani kawai, kuma har yanxun bata da ciki, ni kuma haihuwa nakeson yi a yanxun, toh shikenan Yayanah naji, wacece Auntyn nawa?, yayi murmushi ko keh fa, sunanta Hidaya, kuma tare muke aiki a office amma ni ina gaba da itane, tace toh shikenan Allah yasa alkhairi a cikinsa, yace Ameen nagode sai nazo ganin yaranah, sukayi sallama ta ajiye wayan amma tana tunanin ta ina zata 'bullo ma wannan al'amarin abin ne akwai rikitarwa wlh.... "Tana wannan tunanin taji andafata ta juyo da Saudi, Ahmad ne takagani, yace haba dear, meke faruwane tun dazun nake sallama amma baki amsa ba, menene fad'a min,.... "Tace Habibi kai dai bari wani al'amari ne ke faruwa wlh me wuyan fassaruwa, na rasa ta inda zan fara, yazo ya zauna yace menene fad'a min, kafin na fad'a maka bari in tambayeka, Habibi kasan wata wai a office d'insu Yaya Na'im mai suna Hidaya?,.... Ya d'ago da sauri ya kalleta yace dear me ya had'aki da Hidaya?, a ina kika Santa?, kinsan kuwa wacece "Hidaya"?, ta girgiza kai tace bansaniba amma dan Allah ka fad'a min wacece ita...... Yace toh Hidaya itace......... *EDITED BY* 🍒 NUSNIM ( *TWIN SIS*)🍒 📝 *DEDCATED TO*📝 Nafee Anker,Mm Shakur, Munayshat, Mamu, Afra and Rash Kardam Love you all😘 [1/25, 7:58 AM] ‪+234 706 774 5996‬: 👫 *HA'DI DAGA ALLAH*👫 *WRITTEN BY* KHAFIJAH AL'EEMAN *111 - 115* ************* ✍"yau ta kama juma'a kuma yaune d'inbin Al'ummah suka shaida d'aura Auren *LUKMAN MUHAMMAD* da amaryarsa *SAFIYYA HARIS SAIF* da kuma *NA'IM HARIS SAIF* da amaryarsa *HIDAYA HASHIM* an daura lafiya sai dai mommy ta hana yin ko wani event ta dalilin aure Na'im da bata so, Na'ima tayi tayi mommy ta bari ko dinner ce ayi amma fir tak'i yadda, shiko Lukman cewa yayi ana kai mai amaryarsa zai had'a dinner shi da abokanan sa....... "A 'bangaren Nasrin kuwa ba Wanda ta gayyata sai 'yan uwanta da suka zo, 'yan uwan mahaifinta kuwa tasha habaici a wurin su wai ta kasa rike mijinta gashi nan zai mata kishiya, sai dai tayi murmushi kawai abinta, ...... "Mommy ta kira Na'ima tace mata yanxun xa'a kawo amarya kuma daga nan za'a wuce da ita malali a 'bangaren Na'im zata zauna kafin ya kammala d'aya gininsa na Kinshasha, ki shirya kije ki taya Nasrin aiki Ku gyara ko ina ki tabbatar tayi kwalliya ba wata matsala, tunda kinga an riga an tafi da Safiyya ba wanni aiki.... Toh mommy yanxun kuwa In shaa Allah, ta tashi ta shirya ta bar ma Mommy twins ta tafi, taje ta samu sun Riga sunyi komai har abincin da zasu tari 'yan kai amarya, Na'ima tace Aunty Nasrin ya kamata a kunna turaren wuta, tayi murmushi wlh Na'ima bansan meyasa ba kwata kwata bana son k'anshin turaren wuta sai dai asa na tsinke da kuma room freshener, Na'ima ta tsaya kallonta tana nazarinta sossai, idan baku manta ba Na'ima likitar mata ce, taja hannun ta suka Shiga d'aki, Aunty Nasrin yaushe rabon da kiga period d'inki, yau wata biyu kenan wani abune?.... Na'ima tayi hamdala Aunty Nasrin kina da ciki naga alamomi da yawa a tare dake na mai ciki, murna Nasrin keyi sossai, Na'ima tace kinsan me za'ayi bana son kowa yasan da cikin nan ina son ki 'boye ma kowa amma banda Mommy zan gaya mata da kaina..... Nasrin ta yi shiru toh saboda me, ina ce abin farin ciki ne da ya kamata ko kowa bejiba Na'im ya Sani, Na'ima murmushi tayi toh ai ni ba Wanda ma nafi so kar yaji irin Yaya Na'im, toh me yasa bakyaso yaji? cewar Nasrin, Na'ima tace saboda wani dalilin da daga ni sai Mommy muka Sani, kiyi hakuri Dan Allah kada kowa yaji, In shaa Allah na miki na miki alk'awarin ba Wanda zaiji cewar Nasrin tana d'an goge guntun hawayenta...... A 'bangaren Mommy kuwa ankai mata amarya ta amsheta ba yabo ba tafallasa ta d'an mata nasiha daga nan suka wuce malali..... Sunje Nasrin da Na'ima sun amshe su hannu bibbiyu sunci sun sha daga nan aka watse aka bar amarya da k'awayenta, Hidaya ta tashi tana juyi ta dubi k'awayenta tace ya kuka gani Hidaya matan Na'im, suka sa shewa tace yanxun saura abu d'aya ya rage min ko dai in fitar da waccan Mayyan ko kuma in hana ta sukuni a gidan nan, suka kara sa shewa.... "Kunsan wani abu kuwa bata haihuwa juya ce niko a nan ba Wanda be san na ta'ba zubar da ciki ba kunga kuwa ni nasan ina haihuwa, suka k'ara shewa harda tafawa, tace dan haka Na'im sai Hidaya, Hidaya sai Na'im, zama daram dam ko ya kuka ce suka fara dariya suna cewa sossai ma kuwa, ..... Abinda basu sani ba shine Nasrin zata shiga 'bangaren zata ce musu idan suna da bukatar wani abu suyi magana sai dai me ta gama jin komai da suke fad'i salati kawai takeyi tana me furta _Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un_ shine kawai abinda take cewa,..... Yanxun ne ta gane dalilin da yasa Na'ima tace kar ta fad'a ma kowa, amma ta d'au ma kanta alkawarin zata bita duk yadda take so kuma zata dage da adu'oi , ai tasan mai hakuri baya ta'ba ta'bewa ta juya ta koma abinta...... Ango ya shigo da abokanan sa sunyi adu'an alkhairi sun kwashe kawayenta sun maida su gida, dama ita Nasrin kowa ya tafi ta 'bangarenta...... Ya kura su dukansu ya musu nasiha yace idan da mai magana yayi Nasrin tace bata da abin cewa, Hidaya kuwa ta ce nidai a bi ahankali a zauna dani lafiya, idan ba haka ba za'a ga ba dai dai ba, kuma ni ba zan zauna inyi ma kowa girki ba kowa yayi nashi sannan kuma ba za'a rinka shiga sabga nah ba idan ba haka ba wlh za'a ga ba daidai ba na gama magana..... Maganan ta ya bala'in k'ona ma Na'im rai, amma besan meyasa baya iya yi mata magana ba, ya rasa meke damunsa, Nasrin kuwa tashi tayi tace Ango da Amarya asuba ta gari, bata jira cewar su ba ta haye sama abinta...... *EDITED BY* 🍒NUSNIM ( *TWIN SIS*)🍒 📝 *DEDICATED TO*📝 Nafee Anker, Mm Shakur, Munayshat, Mamu, Afra and Rash Kardam Love you all😘 [1/25, 7:58 AM] ‪+234 706 774 5996‬: 👫 *HA'DI DAGA ALLAH*👫 *WRITTEN BY* KHADIJAH AL'EEMAN Godiya ta tabbata ga Allah (S.W.A),ina mika godiya gareku masoyana kan adu'oin ku akan rashin lafiyan Mahaifiyata ina alfahari da ku, Allah ya bar zumunci, nagode sossai wa'inda basu da lafiya Dana gida Dana asibiti Allah ya basu lafiya, Ameen👏........ Wa'inda suka rigamu gidan gaskiya tunda ga zamanin annabi Adam har zuwa yanxun Allah ya jik'ansu ya yafe musu, mu kuma idan tamu tazo Allah yasa mu cika da kyau da imani, Allahumma Ameen..👏 *116 - 120* ************* ✍ "Ango ya kwana d'akin Amarya, sai dai duk magungu nan da Hidaya tayi anfani dashi bashi ya hana Na'im gane cewar ita ba budurwa bace, amma abin takaicin shine ya kasa yi mata magana, sai dai abin na k'asan ranshi...... Nasrin kuwa da ta tashi ta gyara ko ina ta had'a break fast ta cika cikinta, ta koma 'bangarenta ta rufo kofa, da suka Na'im yace "Hidaya yunwa nake ji please ki had'a mana break fast tsaya tayi ta na kalonsa galala, tace wlh bazan yiba daga zuwa ko amarcin ban gama ci ba amma zaka wani ce min in shiga kitchen?, mtsw ta ja tsaki, sai dai tashi yayi ya shiga kitchen d'in da kanshi ba dan yaso ba, saboda dama Mommy bason Auren nan takeyi ba, yasan bazata ta'ba kawo musu abinci ba...... Biyo shi kitchen d'in tayi, Swt hrt why not ka kira Nasrin ko ita zata iya, bana son ka wahala, yayi shiru sai kuma yace ina zuwa ya haura sama sai tabi bayansa, yaje ya samu k'ofan a rufe ya knocking tace waye ne?, ya amsa ta, ta bud'e k'ofan ta gansu a tsaye tace "lafiya?, Lafiya lau dan Allah break fast nake son ki had'a mana, saboda me yasa zan had'a muku break fast kai da kanka kace ka yarda kowa yayi girkin ta, yanxun kuma kana cewa inyi maka break fast?,...... Murmushi yayi kiyi hakuri please ki had'a mana, kinsan amarci muke ci ba mu gama ba ai be kamata in shiga kitchen yanxun ba cewar Hidaya, Nasrin ta kalleta galala tayi wani shu'umin murmushi bakomai "Mine, me kake so kaci?, komai kika min inaso zanci, toh shikenan ba matsala, ta kai mai light kiss a saman lips, ta juya ta wuce ta bar Hidaya da bak'in ciki..... Ta dafa ruwan zafi da ruwan citta da kanun fari, ta dafa white doya ta zuba a food warmer, ta nik'a kayan miya ta soya ta kad'a k'wai ta d'aura egg source da yaji curry da albasa sai k'amshi yake yi, ta na cikin juyawa Hidaya ta shigo tace "kiyi sauri yunwa nakeji" ta d'ago kanta tana kalonta lallai Hidaya wlh ba dan mijina ba ke baki isa in kalleki ba, amma ni nasan darajar Aure kuma ina son mijinah tsakani da Allah, sanan kuma ina Neman ladan da Annabina Muhammad (S.A.W), yake kwad'aitar damu akan aure, ta juye a cikin small bowl ta d'auka zata fita ta juyo tace kinsan ni nayi ilimin Addini kuma nasan darajar Aure ta juya ta fita abinta...... "Hidaya ta fito ta fara masifa tana zage zage wai tace mata bata da ilimi ita jahila ce, Na'im yazo yana cewa wai me kukeyi ne haka?, dan Allah bana son hayaniya, kuzo Ku zauna muyi break fast please yana Jan kujeran dining ya zauna,Nasrin tace ni na riga da na yi nawa ta juya ta haura sama abinta...... Sun zauna suna cin abinci, Hidaya tace "ni wlh abincin nan ba dad'i kwata kwata ci kawai nakeyi, ya d'aga kanshi ya kalleta, "ke" wacece bata iya abincin ba toh har makaranta koyan abinci tayi, sannan kuma ni idan ba abincinta naci ba bana jin dad'i, ya mike ya tura kujeran dining d'in ya juya yace inkin gama ina sama,...... Ta bishi da kallo, tabbas boka beyi k'arya ba daya ce shiga tsakanin su ba abu bane me sauki, sannan koda anshiga ba lallai bane ki rink'a samun yadda kike so ko da yaushe domin su *Had'i daga Allah* ne.... Yanxun ita tuna ninta d'aya ne tason Nasrin ta bar gidan nan, yadda zata ji dad'in juya Na'im yadda taga dama, toh ta ya ya zata samu biyan buk'ata dan ta lura Nasrin ma ba kanwan lasa bace.... Amma tayi ma kanta alk'awarin sai ta yi duk wata kissa da kisisina, da Neman kwararen boka da zai taimaka mata ta raba Auren Na'im da Nasri.... Ko zata samu wannan daman ko baza ta samu ba oho, Ku cigaba da saurarona, nice dai *AL'EEMAN* *EDITED BY* 🍒 NUSNIM ( *TWIN SIS*)🍒 📝 *DEDICATED TO*📝 Nafee Anker, Mm Shakur, Munayshat, Mamu, Afra and Rash Kardam Love you all😘 . [1/25, 7:58 AM] ‪+234 706 774 5996‬: 👫 *HA'DI DAGA ALLAH*👫 *WRITTEN BY* KHADIJAH AL'EEMAN *121 - 125* ************* ✍"Haka rayuwa taci gaba, Hidaya na nan na kulle kullenta na ganin ta kora Nasrin amma abin ya gagara duk wurin bokan da zata je sai ya fad'a mata cewan "*Nasrin ta rik'e ibadah sossai, ga yawan azkhar da takeyi, ko me za'a mata bazai ta'ba kamata ba, ta rasa ta inda zata 'bullo ma abin gashi k'awarta dake bata shawara bata k'asar tabi wani Alhaji Dubai sai next week zata dawo..... "A 'bangaren Na'ima kuwa ta samu mommy ta shaida mata cewan Nasrin fa nada ciki, tayi murna da farin ciki sossai, Na'ima kuwa cewa tayi Mommy me zai hana ki d'auko tah ki dawo da ita wurinki dan ni banyarda da Hidaya nan ba, haka neh Na'ima ni kaina abin na damuna dan yarinyar bata kwanta min a rai ba, amma kinsan me za'ayi? Ta girgiza kai, zan bari sai anyi kwana biyu zan shirya inje inga meke faruwa a gidan, sannan kuma zan kirata inja mata kunne akan ta kulla sossai da cikin kuma kar ta sanar ma kowa sai ya fito kowa zai gane ma idon sa, tace toh shikenan Mommy Allah yasa mu dace, Ameen..... "Yau two weeks ya cika dai dai, Hidaya kuwa murna ya cika ta domin Haulat na kan hanyan dawowa..... Ita ko Nasrin daga school sai d'aki, ta shiga ta rufe abinta tayi karatu idan ta gaji ta kira 'yan gidan su suyita hira a waya,ba abinda ke fitowa da ita sai girki, tsayawa takeyi a wurin sai ta gama ta juye a food warmer ta haura sama dashi...... Sannan koda Na'im ya sameta da maganan cewa Hidaya zata siya kwanakinta, cewa tayi ta barshi kawai ta tashi taje ta samu Hidaya a d'aki tace _kwantar da hankalinki amarya, kinsan ke baki saba jin dad'i da d'umi irin wandda kikaji a 'yan kwanakin nan ba, sannan kuma na fahimci cewan kin fini buk'ata da kuma kwad'ayi tare da sha'awa, lastly but not the list ina shaida miki ni Nasrin Uwar Gida a gidan Na'im na bar miki miji har sai randa zakiji ya isheki sai ki dawo min dashi, maganganun Nasrin sun ta'ba Hidaya sossai zuciyarta taji tana zafi_..... _ta d'aga hannu zata mareta Nasrin ta rik'e hannun tace wa zaki mara ni lallai kam, marinah shine babban kuskuren da zaki tafka a rayuwarki, menene laifina dan na baki abinda kike buk'ata ai godiya ya kamata ki min bawai ki min sakayya da mari ba, ta sauke hannunta ta juya ta kai dai dai saitin k'ofa ta juyo tace_ " _Amarya asha Amarci lafiya_ ta fice abinta...... Ta koma d'aki tana zaune Na'im ya shigo, me yasa zaki ce kin bama Hidaya kwanakin duk da take buk'ata? Ta dago kai ta kalleshi tayi murmushi to ai ta fini buk'ata, naga naima takeyi da kud'inta ma amma kuma sai na mata adalci taje har sai ka isheta, nice na bada wannan izinin, zai yi magana kenan ta hango Hidaya na zuwa tayi sauri ta mik'e tasa bakinta akan nasa, tuni salon labarin ya canja...... Hidaya kuwa tsabar bak'in ciki ya hanata tayi magana da gudu ta juya ta nufin 'bangarenta tana kuka, ta d'aga waya ta kira k'awarta, Hello k'awata wlh ba lafiya a gidan nan kiyi Maza Maza ki zo, toh shikenan ina jira ta kashe wayan tana kaiwa tana komowa..... Nasrin kuwa data lura cewan ta tafi da sauri ta zare jikinta ta matsa gefe, ta had'a rai, ya juya yana kallonta yasa gwiwowinsa a k'asa yana rokonta dan Allah kar ta bari ya kwana a wurin Hidaya wlh haushi take bashi amma sai ya kasa magana, tayi shiru tana nazarin maganan sai ya bata tausayi, ta d'aga shi ta kama mai hannu suka Shiga bedroom ta rufo k'ofar..... Hidaya kuwa Haulat ta iso, suka shige d'akinta a nan Hidaya ta bata labarin komai, toh ke k'awata zama kikayi kika zuba musu ido kina kallo koko mene cewar Haulat, toh bari in baki shawara na farko dai ki tada musu da hankali, na biyu kuma wa'inan kujerun naki sunyi tsufa ba wai cewa zakiyi ya canja ba a'a inkika ce ya canja zai canja muku gaba d'aya, kananzir zaki samu ki watsa musu ki babbake shegu kinga ko a nan kin cusa mata bak'in ciki za'a canja miki kujeru amma ita banda ita sannan kuma jibi idan Allah ya kaimu zan kaiki wurin bok'a kurukus a bayan Layin mu yake aikinsa kamar yankan wuka.... Alla k'awata cewar Hidaya suka tafa, toh kinga Haulat yanxun ya za'ayi kinsannk da buk'ata gashi kuma yana wajenta, abinda za'ayi shine kizo muje tare da Alhaji Mai Gidan Daulah nake, muje ki yakici iya abinda zaki iya na barmiki shi na yau dai d'aya tak..... Allah k'awata suka k'ara tafawa tashi muje wlh a matse nake , suka kama hanya suka fita........ *EDITED BY* 🍒 NUSNIM ( *TWIN SIS*)🍒 *DEDICATED TO* Nafee Anker, Mm Shakur, Munayshat, Mamu, Afra and Rash Kardam Love you all😘 [1/25, 7:58 AM] ‪+234 706 774 5996‬: 👫 *HA'DI DAGA ALLAH*👫 *WRITTEN BY* KHADIJAH AL'EEMAN *126 - 130* ************* ✍Nasrin da Na'im ana can ana soyewa, Naarin koh abin ya mata dad'i ko ba komai ta kuntata ma Hudaya, tunda suka shiga basu fito ba, sai da gari ya fara haske tukunna sannan Nasrin ta fito to had'a musu break fast ta koma ta kulle k'ofa...... "A 'bangaren Hidaya kuwa bata dawo ba sai wajajen d'aya, a lokacin Nasrin ta fito har ta musu lunch ta koma, saboda saida suka biya wurin boka tukunna, ya bata magani tasa mai a abinci amma yace musu karta bari yayi bissimillah..... "Ba wannan bane ya dameta, abinda ya tsaya mata arai shine sanda tace ya bata maganin da zata kora Nasrin a gidan, cewa yayi bazata koriba saboda ta rik'e Ibadah, sai dai a gwada zubar da cikin da ke jikinta, gaban Hidaya ne ya fad'i, yaushe Nasrin ta samu ciki bata sani ba, lallai tayi sake ba d'an kad'an ba........ Ta juya ta kalleshi boka yanxun ya za'ayi? Ya mik'o mata wani bak'in igiya yace wannan ki warware shi a k'ofar d'akinta ta tsalaka magana ta k'are cikin zai zube...... Sai kuma ina son inja miki kunne karki sake ki ma Mijinki maganar cikin nan idan ba haka ba zai lalace, Ku tashi Ku tafi Ku bani wuri,ta ajiye mai makudan kud'i suka kama hanya suka tafi..... Tunda Hidaya ta dawo take jiran fitowan su basu fito ba ta rasa ya zatayi, maganan Haulat ne ke dawo mata, da sauri ta d'auko kalanzir d'in data siyo ta 'boye ta yayyafa a jikin kujerun ta k'yasta a shanan a jikin kujerun nan da nan suka kama, sai dai me, ta tsorata sossai da ganin yadda yake ci....... Da gudu tayi hanyar k'ofan Nasrin ta fara bubbugawa tana ihu "wuta wuta", Na'im ne ya fara jin abinda take cewa, ya fad'a ma Nasrin da gudu suka fito aikuwa wuta ya kama sossai, ya d'aga waya da sauri ya kira fire Bridget ya basu address........ Mai gadi kuma ya bud'e ma Lukman da Ahmad get kenan suka hango hayak'i ai da gudu suka fito ko gama parking basuyi ba, mai gadi na lafiya? Ya hango hayak'i shima da gudu yabi bayansu...... Sun shiga kitchen direct suka nufa suka had'a ruwa da omo, suka dinga watsawa, Allah ya taimaka kujeru uku kawai suka kama, kuma wutan ya mutu, ajiyan zuciya sukayi dukansu a daidai lokacin motan fire Bridget d'in ta shigo, Ahmad ne ya tashi ya je ya samesu dan Na'im ya kasa ko motsawa a wurin, Ahmad ya samesu ya basu hakuri tare da gaya musu yadda abin yake, sunce Allah ya tsare ya kuma k'ara kiyaye gaba sannan suka wuce...... Ya dawo ya samesu ya fad'i musu yadda akayi sai dai me Na'im yaga stain a sauran kujerun da basu k'one ba, saboda kujerun leather set ne, ya matsa zai ta'ba bai kai ga ta'bawa ba ya fara ji, ya kai hancinsa yana sunsuna d'agowan da zeyi ya kalli 'bangaren Hidaya wadda jikinta keta rawa itama shi take kallo, ya nuna ta da yatsa yace "ya akayi kalanzir yazo gidan nan? Sannan kuma ya akayi yazo kan kujerun nan dan nasan gidan nan ba'a anfani da kalanzir? Hidaya tayi shiru tana kallonsa, idonsa ya kad'a yayi ja, Lukman ne ya dafa mai kafad'a yace "pls be a man" ka kwantar da hankalinka k'ila ita ma bata sani ba, Ku zauna dukan ku kubi a hankali har a gane abinda ke faruwa..... "Na'im yace wlh munafuka ce wannan yarinyar, ba kowa a gidan nan daga ni sai ita sai Nasrin, wa zai shigo har nan ya kuma rasa abinda zaisa sai kalanzir? Idan wanine toh wlh sai dai yayi anfani da fetur kuma dika gidan nan za'a zuba shi...... Sannan na tabbata Baba maigadi bazai ta'ba barin wani ya shigo ba tare da izininah ba, sannan sanin kanku ne ba ta inda wani zai shigo gidan nan ba tare da naganshi ba kun fini sannin wannan ko ta yaya ne ba sai na muku bayaniba Ahmad da Lukman....... Ya k'ara juyawa wurin Hidaya zaki fad'a min ko bazaki fad'a min ba sai na tattakaki a nan yanxun nan? Ta juya ta nuna Nasrin ita ta zuba, Nasrin da sauri ta d'ago kanta ta kalleta, kuma kowa dake wurin da mamaki a fuskansa, Ahmad ya katse shirun yace Hidaya, ya za'ayi kice Nasrin ta k'ona kujerun nan, duk cikin mu ba Wanda zai yadda da magananki saboda mufi kowa sanin halin Nasrin, mun zauna da ita ba shekara d'aya ba, ba zaman yanxun bane tsakanin mu da Nasrin tun a lokacin bata nuna mana irin wannan halin ba sai yanxun ina Impossible Hidaya ki sake tuna ni dai...... Itace mana dama tun randa aka kawoni cikin gidan nan take ik'irarin sai taga bayanah gashi kuma ta fara, Na'im ne ya daka mata tsawa k'arya kike munafuka wlh bazata ta'ba akaita abinda kike cewa tayi ba, amma tunda na lallabaki ki gaya min kink'i, ki tafi gidanku karki dawo har sai kin fad'a min yadda akayi.... *EDITED BY* 🍒 NUSNIM ( *TWIN SI*)🍒 *DEDICATED TO* Nafee Anker, Mm Shakur, Munayshat, Mamu, Afra and Rash Kardam Love you all😘 [1/25, 7:58 AM] ‪+234 706 774 5996‬: 👫 *HA'DI DAGA ALLAH*👫 *WRITTEN BY* KHADIJAH AL'EEMAN *136 - 140* ************* ✍Na'im ya rik'e kanshi ya dad'e a haka sannan ya saki kan nasa, Hidaya tayi shu'umin murmushi daga nan ta fara sarrafa shi yadda takeso, ta lura sossai maganin yayi tasiri a kansa, nan da nan ta kira Haulat ta fad'a mata suka dinga ihu a waya..... Tunda ga ranan Nasrin taga canji a wurin Na'im, baya kwana a wurinta bata ganin shi, idan ma ta ganshi ko kallo bata isheshi ba, abin na bala'in damunta, a makaranta tana zaune a k'asan wata bishiya tana abinda ta saba wato tunani, taji andafata, ta d'ago kai tana kallon ko waye, Zainab ta gani a tsaye tana murmushi, ta nemi wuri itama ta zauna..... Tace wai Nasrin kwana biyun nan meke damunki? A class idan muna lectures hankalinki baya wurin, kullum kina cikin tunani, duk kin rame kinyi bak'i wai meke damunki ne? Kinsan dai ba'a son mai ciki na tunani koh? Tayi shiru ba komai Zainab kawai yanayin karatu ne, kinsan dole in damu na k'osa wlh mu gama gashi yanxun 200 level muke, abin da k'osawa wlh.... Zainab ta ce haba Nasrin karki maidani k'aramar yarinya mana wlh karatu baya baki wahala kuma baya saki damuwa, kawai ba kyason fad'a min abin da ke damunki ne, kuma wlh ni ba haka na d'aukeki ba nayi tunanin zamu iya fad'a ma juna matsalar mu, mukuma maganceta ta hanyar bama juna shawara mai kyau, tunda ke ba haka kika d'aukeni ba shikenan, Allah ya yaye miki damuwarki, ta mik'e zan koma class sai kin shigo..... Ta ruko hannunta da Sauri k'awata ki saurareni da kyau kiji wlh ba haka nake nufi ba, ni dai ina son inga ina kare mutuncin Aurenah ne, saboda komai a Aure yana buk'atar sirri, amma ba wai ina 'boye miki saboda wani abu bane, kiyi hakuri dan Allah.... Tayi murmushi Nasrin wlh kina da gaskiya Aure idan ba sirri ba Aure bane, gaskiya kin birgeni kuma na k'ara sonki a matsayinki na k'awata, sai dai wani hanzari ba guduba akwai lokacin da dole sai kin bud'e wannan sirrin amma fa ba kowa zaki fad'a mawa ba, saboda k'awa da kike ganinta sai ta kaiki ta baro dole sai kinyi taka tsantsan, dan haka ba kowani magana zaki kwashe ki fad'a ma kowace k'awa ba, dan haka yanxun mai ya faru ki fad'a min na miki alk'awari zan rik'e miki sirrinki In shaa Allah, kuma zan baki shawaran da baza ta cutar dake ba..... "Nasrin tayi a jiyan zuciya ta kwashe labarin tun daga aurenta da Na'im har zuwa yanxun da suke zaune, Zainab "tace dank'ari! yanxun k'awata kina nufin baisan ma kina da ciki ba? Watan cikinki shida da sati biyu har kin fara zuwa awo amma be sani ba? Amma in tambayeki ita mahaifiyarsa fa? Nasrin tace muna waya da ita sossai ban ta'ba nuna mata wani abu na faruwa ba, kuma koda zan fara zuwa awo, tare da Na'ima mukaje asibitin, garkuwa mukaje kinsan a nan take aiki...... Zainab tace dank'ari a gaisheki Nasrin wlh kinyi k'ok'ari ba kowacce mace bace zatayi abinda kikayi ba, na jinjina miki tunda ko mahaifiyar da ta haifeki baki fad'a mata ba lallai a gaisheki...... Amma wani hanzari ba gudu ba, be kamata ki zauna ki zuba ido kina kallonta bah! Nasrin ta kalleta da sauri kina nufin nima inbi 'yan subbu kenan kai Zainab bazan iyaba wlh, ta dafa ta ba abinda nake nufi ba kenan, ina nufin ki tashi tsaye ki soma adu'a, saukan Al'qurani, yawan yin azkhar kome kikeyi, ki rinka yawan sa ma gidan ki karatun al-qur'ani hakan zai rage wasu masifu da bala'in cikin gidan nan, sannan duk wani asiri da ikon Allah zai karye ba kuma ke kadai zakyi ba, dole sai kin had'a da iyayensa ya kamata ki fad'a musu Susan halin da ake ciki, suma su tashi tsaye domin tasu ma sai yafi kar'buwa tunda su iyaye neh a gareshi, nima zantayaki In shaa Allah zakiga anfanin haka, sannan ki k'ara sama zuciyarki salama ki cire komai a ranki ki kama Allah, zakiga anfanin haka.... Tace nagode sossai k'awata zanyi abinda kikace, wlh kawata ina alfahari dake a matsayin k'awa harnaji damuwar da nake tare da ita ta wuce tunda na samu mafita, ba komai k'awata, k'awancen gaskiya kenan idan kaga d'an uwanka zai fad'a wani hali kayi k'ok'arin cirosa, tashi mu tafi kinji, suka tashi suka kama hanyar class domin lokacin lecture ya kusa...... *EDITED BY* 🍒 NUSNIM ( *TWIN SIS*)🍒 *DEDICATED TO* Nafee Anker, Mm Shakur, Munayshat, Mamu and Rash Kardam Love you all😘 [1/25, 7:58 AM] ‪+234 706 774 5996‬: 👫 *HA'DI DAGA ALLAH*👫 *WRITTEN BY* KHADIJAH AL'EEMAN *131 - 135* ************ ✍tsugunawa tayi tana rok'onsa dan girman Allah kayi hakuri, wlh sharrin shaid'an ne ka rufamin asiri dan girman Allah, kallon banza yayi mata ya juya zai bar wurin Lukman yace kayi hakuri tunda ta fad'i gaskiya, juyowa yayi toh me yasa zata yi haka anmata wani abun ne, ko kawai dan taga 'baccin raina zata aikata haka, Ahmad yayi murmushi kasan halin mata suna da kishi sai hakuri, kishi Ahmad wani irin kishi ne haka mara kangado da har zatayi yinkurin sa wuta a gida? "Nasrin ne ta matsa kusa dashi ta rik'e hannu shi haba " _Namijin zaki, haba tauraronah, haba abin alfaharinah, mijin da kowacce mace take da burin Aure a rayuwarta_ ina hakurinka yake ni nasan kana da hakuri karka zama mara yafiya a rayuwa mana, ka zama mai yafiya a koda yaushe, dan Allah kayi hakuri ka yafe mata laifine ta riga tayi kuma ta baka hakuri, ka saurareta mana ka hakura please...... Ya juyo yana kallon Nasrin naji na hakura amma bazan canja mata kujeru ba haka zata zauna, Nasrin ta girgiza kai a'a canja kujeru ya zama dole amarya ce fa, haka za'a dinga zuwa a naganin k'onanin kujeru? Bazai yuwu ba kayi hakuri ka canja mata, naji zan canja, amma yanxun koh, tunda ga friends d'inka kuje yanxun ku siyo, yayi murmushi toh naji Uwar gida sarautar mata, Allah yayi miki albarka, Ku muje sai mundawo, toh Allah ya tsare cewar Nasrin, ita koh Hidaya binsu tayi da harara, ta juya ta kalli Nasrin tayi tsaki ta wuce, murmushi tayi ta koma 'bangarenta abinta..... Sunje sun suyo kujerun blue black da flowers a jiki golden colour, inda ya siyo su suka kawo a mota suka shiga dashi suka sa, a ka fita da wa'incan......... Da ta fito ta gani sai cewa tayi ya za'ayi a siyo mata kujeran dubu d'ari aiko na Fallon Nasrin dubu d'ari biyu da hamsin ne , ina laifin ya siyo mata na dubu d'ari biyar, sai kuma ta rufe baki kar ya jita, ba godi balle Nagode, shi halin Hidaya na bashi mamaki wlh, shiyasa yake bala'in son Nasrin, ta iya magana gata da biyayya, bata son taga ranshi a 'bace, shi be masan yadda akayi ya Aurota ba kuma da yayi yinkurin sakinta sai ya kasa ya rasa dalili ...... "Yau Hidaya ta amsa girki, haka ta saci hanya taje wurin boka, maganin da ya bata be mata aiki ba, na farkon ne kawai da akayi kafin ta shiga gidan ya kamashi, ya bata wani wai ta zuba mai a abinci amma karta bari yayi bismillah, ya k'ara bata wani turare ta fesa a jikinta da daddare,amma da sharad'i, shi turaren nan duk randa Nasrin ta Haihu ya ga baby ta zata haukace, ta tsorata da jin haka, tace toh aka she jaririn tun a ciki, yayi wani irin k'ara yace Maman a tsaye take tana adu'a sossai, kuma k'anwanshi da mahaifiyarsa suma a tsaye suke Dan haka bazai iya ba ta tashi ta tafi, ta zube mai kud'i ta bar wajen..... Ta dawo tayi girkinta tsab tuwon semonvita da miyan kubewa d'anya tayi, ta barbad'e miyan ta juya sossai, ta shirya komai, a lokacin Nasrin ta fito tana bala'in jin yunwa ta Shiga kitchen domin dafa Macaroni dan shi take jin cin...... Sun fito sun zauna akan dining, tace ni bazanciba yau kwata kwata bakina ba dad'i wlh, yace toh zubamin ni yunwa nakeji, ta zuba mai zai kai baki kenan yayi bismillah sai ta dakatar dashi,yace menene sai tace ba komai,haka suka dinga yi har sau biyar, tsaki yayi ya ajiye abinci ya tashi, tana kiranshi ko sauraronta beyiba ya wuce kitchen, dama k'amshin abincin Nasrin ya cika mai hanci...... Ya sameta ta gama ta zuba wani a plate wani kuma a food warmer, tana wanke tukunyan, sai cewa yayi dan Allah a sammin ko kad'an ne yunwa nakeji, ta juyo ta kalleshi ai yau ba'a d'akina kake ba, ba Amarya tayi girki ba? Ni dai idan zaki bani ki bani, tace idan bazan bada ba fa? "Shikenan, toh bazan bada ba, ta d'aure fuska, aikuwa ya d'auki plate d'in da gudu ya fice ko kafin ta kai ga fita kitchen d'in har ya hau sama, tana kiranshi tana rik'on shi ko ya juyo, ta juya zata koma kitchen d'in taji anja tsaki sai a lokacin ta lura da Hidaya a wajen, murmushi tayi ta ce Amarsu sannu da hutawa, ta shige kitchen abinta, Hidaya kamar ta had'iye zuciya ta mutu..... Da daddare ta shafa turaren nan a jiki lokacin kuma Na'im ya shigo, yana kallonta yaji kanshi ya fara sarawa.... *EDITED BY* 🍒 NUSNIM ( *TWIN SIS*)🍒 *DEDICATED TO* Nafee Anker, Mm Shakur, Munayshat, Mamu and Rash Kardam Love you all😘 [1/25, 7:58 AM] ‪+234 706 774 5996‬: 👫 *HA'DI DAGA ALLAH*👫 *WRITTEN BY* KHADIJAH AL'EEMAN *141 - 145* ************* ✍Nasrin tun sanda Zainab ta bata shawara ta d'auka azkhar takeyi ba kama hannun yaro,sai dai ta kasa fad'a ma mommy halin da ake ciki,Na'ima ma inta tambayeta ya zamansu sai tace komai normal, in tace zatazo sai tace tana school ko ta zo bazata sameta ba.... 'Yauma kamar kullum tana zaune ta gama komai tasa karatun al'qur'ani tanaji, bata lura ba kawai taji ankashe,ta d'aga kanta da sauri Hidaya ta gani a tsaye da Haulat, sai hararanta sukeyi bata ce musu komai ba tsayawa tayi tana kallonsu taga ikon Allah.... Hidaya tace toh 'yar matsiyata anzo ansamu wuri an zauna har ana wani cikama mutane kunnuwa ba dama mutum ya d'an zauna a cikin gidan mijin shi sai an dameshi mtsw, toh ai ke kikayi sake har kika bar gadangare yake sha miki ruwa a tulu, wlh da nice da tuni nayi waje da 'yar iska, kawai tazo tana takura miki kinzuba mata ido kina kallo, horo ya kamata ki rinka bata mai tsanani wlh da kanta zata tattara inata inata tabar miki gida, ki zauna daga ke sai mijinki cewar Haulat...... Hidaya ta dafa ta tace kinsan talaka be iya samun wuri ba k'awata, tazo tayi bake bake amma gaskiyarki ne wlh nice nayi sake, ta juya ta kalla Nasrin tace sai a tattara a koma gidan tsohuwa a cigaba da tallan d'anwake kamar yarda aka saba, Nasrin dake zaune da murmushi a fuskanta ta juya tana waige waige, Hidaya tace cikin ihu ba dake nakeyi ba, ta juyo ta kalleta, dawa kikeyi ne? Haushi ya kamata "dake nakeyi dan iyayenki, Nasrin ta d'aure fuska ba dariya a fuskarta, ta mik'e tsaye tana kallonta sama da k'asa, ta nuna ta da yatsa tace "idan kinayi dani kiyi dani amma karki sake kisa iyayenah a ciki dan sunfi kowa daraja a gurina, wlh kika k'ara anbato iyayenah a maganarki sai na zubar miki da hakoran gaban bakinki, dan ni nasan darajar iyayenah da kuma na gaba dani...... Haulat tace "lallai yarinyar nan har kina da bakin fad'a ma mutane wannan maganar ke 'yar gidan uban wage? Kafin ta k'arasa taji kyakkyawan mari a fuska, Nasrin ni kika Mara an mareki idan kina da abinda zakiyi kiyi in gani, kuma karki k'ara sa mun baki dan ba dake nakeyi ba da matar gida nakeyi..... Hidaya tace lallai Nasrin wuyanki yayi kauri ya isa yanka har kin isa ki maran mu k'awatah? Wacece ke a gidan nan? Murmushi tayi nice nan matar Na'im wadda ya Aura ta sanadiyan k'addara, kuma yake sona tamkar ransa, ina so kusan wani abu, banta'ba bin boka ko mallam ba dan Na'im ya Aureni bah, iyaye sune sanadiyar Aurenah tsakanina da shi kuma yake alfahari da Aurenah kamar yadda nima banta'ba dana Sanin Aurensa ba, yanxun ne ma na fara son Auren Na'im wlh, ba kuma Wanda ya isa ya rabani dashi ko mutum ko aljan sai dai Allah domin Aurenah dashi *Had'i daga Allah* ne........ Hidaya ta daga hannu zata mareta ta rik'e hannu ta wanketa da Marika guda biyu masu rai da lafiya, ta tafi kamar zata fad'i Haulat ta rik'o ta da Sauri, ni kika mara? Wlh sai kinyi dana Sanin marina! Auren nan sai ya zama bala'i a wurinki, sai kinyi nadaman Auren Na'im.... Ku fitan min a d'aki idan ba haka ba wlh sai na illataku, banzaye 'yan iska wa'inda basusan darajar Aure ba, and for your own Information idan na k'ara ganin k'azamen k'afafuwanku a 'bangarena wlh sai na nuns muku wacece Nasrin, dan naga har yanxun bakusan niba, ku fitan min a d'aki shaid'anu kawai, da sauri suka fita, tayi tsaki ta koma ta zauna ta cigaba da jin karatunta.... Haulat ce da jaka a hannunta ta ke cewa k'awata wlh sai kinyi da gaske dan kishiyan nan taki watarana sai ta miki shegen duka, kisan abinda kikeyi wlh kinga yanxun kinsa ta daina kulata kuma kome kikace yayi zaiyi amma ni abinda ke ban haushi wai karkice ya saketa, kuma duk dalilin d'aya ne Auren su *Had'i daga Allah* ne, shine fa kawai dalilin, Hidaya tayi a jiyar zuciya tace dan Allah ki nemomin mafita mana, Haulat tace kawo kunenki kiji ta rad'a mata wani abu a kunne sukayi dariya suka tafa......... *EDITED BY* 🍒NUSNIM ( *TWIN SIS*)🍒 *DEDICATED TO* Nafee Anker, Mm Shakur, Munayshat, Mamu and Rash Kardam Love you all😘 [1/25, 7:58 AM] ‪+234 706 774 5996‬: 👫 *HA'DI DAGA ALLAH*👫 *WRITTEN BY* KHADIJAH AL'EEMAN *146 - 150* ************* ✍"Bayan Haulat ta tafi Hidaya ta zauna tana tunani a kan maganan da Haulat ta fad'a mata, tana nufin _Insa ma Nasrin maganin zubar da ciki a abincita_ toh tayaya hakan zai faru bata barin kitchen d'in sai ta gama dafa abincinta! Menene mafita zatayi anfani da Na'im ta samu abinda take so...... "A 'bangaren gidan su Na'im kuma mommy ne da Daddy a zaune suke tattaunawa, sai ga Na'ima ta shigo da twins d'inta suka ruga da gudu suka haye kan cinyan Daddy suna cewa oyoyo Grandpa cikin gwarancin maganan su, Mommy ne taja wo musu k'afa Ku saukan min karku 'balla min miji suna ta dariya, Mommy ta juya ta kalli Na'ima, wai in tambageki kuna waya da d'an uwan naki kuwa? Tace a'a rabona dashi tun randa muka rinka lallashin Shureim da yace bazai je India karatu ba, dan ko ranan dana kirashi ince mai yazo mu kaishi Airport Hidaya ce ta d'auka wai ya fita ya bar wayan, toh haryanxun ko na kira baya d'auka kuma be kirani ba! Na kira Nasrin nace mata zanzo cemin tayi tana school Na'im kuma na office, daman ni bama shiri da Hidaya shiyasa ma banje ba! Daddy yayi ajiyar zuciya ni kaina ankawo min karar cewa baya zuwa office kullum kuma ko yazo baicika magana ba, Hidaya ke zuwa tayi komai na office d'in ta tafi, kuma ko na kirashi baya shiga, Mommy tace ba lafiya ba gaskiya, daman Daddyn yara sai da na fad'a maka kwata kwata hankalina bai kwanta da Auren nan ba! Ga yarinya da ciki kunsan tana wata bakwai yanxun, Allah kad'ai yasan wani hali take ciki a wannan gidan, kuma ko ankira antambaya sai tace komai lafiya, ni wlh banyarda da zaman su ba! Zanje ingani da idona, dan Allah ka mun uzuri inje in duba! Toh shikenan Ku shirya keda Na'ima sai kuje Allah ya kyauta, suka amsa suka tashi.... "Hidaya ne zaune take cema Na'im (da duk yayi bak'i ya rame kamar bashiba) ina son ka kira Nasrin ka mata magana ta taimaka ta koya min yadda ake kunun gyad'a tunda kana so sai in rink'a maka, ga ce toh kirata ta tashi ta fita tayi hanyar kitchen dan dama tasan yanxun tana kitchen, ta shiga da sallama Aunty Nasrin ina wuni ta juyo tana kallonta da alaman tambaya a fuskarta amma sai ta watsar ta amsa lafiya lau, kije Na'im ne ke kiranki, yana ina yana 'bangarena, ta ce toh! Tana fita a kitchen d'in Hidaya da Sauri ta kwance gefen zaninta, ta ciro kullin maganin ta bud'e had'add'en jalouf d'in taliyan Hausa ne da yaji d'anyen kifi,sai da ta had'iye miyau amma da ta tuna abinda ya kawota tayi sauri ta zuba, ta gama ta rufe, ta kulle sauran maganin ta maida gefen zaninta.... Juyo Wanda zatayi Nasrin ne a tsaye ta hard'e hannayeta tana kallonta, jikinta ne ya fara rawa, tayi murmushi Hidaya kenan ta fincikota ta rink'a janta har saida suka kai fallo, sannan ta saketa lallai Hidaya angaya miki kowa jahili ne kamarki, duk wayanki wlh ni Nasrin na fiki, ke ga munafuka tunda kin assirce Na'im ya kama shi nima bari ki nuna min naki hatsabibanci koh? To bari kiji ni Allah na rik'e ba tsafi da tsubace tsubace ba, karkiga na bakki da Na'im kinata abinda kika ga dama bawai tsoron ki nakeji ba, ba kuma bani da mafita bane na barki da mallaminah ne yadda zaiji dad'in damkeki idan ya tashi wato Allahu (S.W.A), karkiyi tunanin kina cutar damu ne wlh kanki kike cuta bari in gaya miki kiji duk wayyan da kikayi da Mahaifiyarki da kike gaya mata shawaran da Haulat ta baki toh duk a kunnenah, najiki sarai, kinsan shi Allah ba azalimin bawansa bane, duk abinda zaki min wlh na rik'e Allah da mazonsa..... "Hidaya ce ta harareta toh me zaki iyayi, Na'im ya riga ya zama nawa ba Wanda ya isa ya rabani dashi, sai ni nan sukaji ana fad'a, Mommy ce ke fad'in haka ga Na'ima a bayanta, ta wanke Hidaya da lafiyayyen mari, dama sai da na fad'a ma Na'im bana son Auren nan Amma naga ya dage sai yayi, ni nasan baki barshi haka ba wlh, sannan kuma yanxun jikan nawa da za'a haifo min daga tsatsa mai kyau zaki kashe min? Lallai Hidaya kin tabbatar min da ke mahaukaciyya ce, ta juya ta kalli Nasrin wadda idan ba ka lura da kyau ba bazaka gane tana da ciki ba, dan cikinta 'boyayyene, ina Na'im ta ce yana sama mommy, ta haura saman da sauri, ta shiga ko ina kazanta kamar ba mutum ke zama ba gashi yayi bak'i ya rame, yana zaune a k'asa, mommy ta dafa shi yana d'ago kai ya kalli mommy, tace Na'im me ke damunka ne ka koma haka, da kyar ya bud'e baki yana cewa nima bansani ba! ya fara kuka ya k'ank'ame mommy, itama sai hawaye, ta goge mai hawayen, tace ina ka ajiye kadarorinka da suke nan gidan yace yana hannun Hidaya... Da sauri mommy ta shiga bedroom d'in tana dubawa, can kamar ance mata ta duba k'asan gado ta gansu a jakarsu ta d'auko ta fito, ta rik'e mai hannu suka sauko tace ma Nasrin d'auko duk wani Abu da zaki buk'ata ki rufe 'bangarenki kizo mu tafi, Na'ima rakata Ku sameni a waje, Hidaya na gefe duk tayi wani irin ta zazzaro idanuwa, suka d'auko suka bi gefenta suka wuce tana ganin sun fita ta d'auko mayafinta ta shige mota ta kira Haulat su had'u a kan titin Sultan road yanxun nan ta kashe wayar..... Sun had'u ta gaya mata komai da ya faru sai cewa tayi Nasrin d'in nan ta zama mana ciwon ido wlh, zama be ganmu ba muje mu sami boka muyi mai bayanin komai daya faru, suka kama hanyar wurin bokan su... *EDITED BY* 🍒NUSNIM ( *TWIN SIS*)🍒 *DEDICATED TO* Nafee Anker, Mm Shakur, Munayshat, Mamu and Rash Kardam Love you all😘 [1/25, 7:58 AM] ‪+234 706 774 5996‬: 👫 *HA'DI DAGA ALLAH*👫 *WRITTEN BY* KHADIJA AL'EEMAN *156 - 160* ************* ✍"K'arfe hud'u na yamma kenan amma haryanxun mallam shiru be dawo ba, Alhaji Tofiq adu'a kawai yakeyi Allah yasa ba wani abu bane ya faru domin ko number shi ya kira baya shiga, gashi jikin Nasrin yayi tsanani sossai, na dai Na'im ne Alhamdulillah yana jin sauki..... "A 'bangaren Hidaya kuwa tun bayan dawowan su daga wurin boka tsula tsiyarta kawai takeyi, ta kawo waccan namijin ta kawo wannan, amma sai dai ta farayin wani mugun mafarki, sai taga ana binta za'a kasheta, ko kuma a dinga ja mata kunne ta je ta cire abinda ta birne Wanda ta sanadiyar shine Na'im ya aureta dan a duniya ba wadda ya tsana ada irrinta amma tunda taje nijar wurin wani bokanta ya bata wannan abin ta birne shikenan...... Yauma tana zaune abin duniya ya dameta saboda ko a zaune take sai taji ana k'ara ja mata kunne, amma na yau yafi don har ta'bata taji anayi, sai tsorata tah akeyi! Ba Arziki ta tashi ta d'auko mayafi ta kama hanya ta fita, ko mata baza ta iya tuk'awa ba mai a daidaita ta samu ta hau, tayi mai kwatancen wurin, sai fad'a sukeyi da shi, dan ta dameshi da yayi sauri, shi kuma gani yakeyi India baso takeyi ya tashi sama ba to iya gudu kam yanayin shi, da ya gaji da ihunta ya sauketa yace mata kuma tunda sunyi rabi sai ta bada kud'in rabin idan ba haka ba wlh zai tara mata jama'a, ta dinga masifa tana cewa da gatanta da ta hau wannan shegen adaidaitan zai wulak'antata, suna cikin haka sai ga k'awarta mai suna Rashida .m. Zarma ta kalleta wanake gani kamar Hidaya? Nice Rashida Ya kwana biyu? Lafiya lau, ya naga kunata sa'insa da mai adaidaita lafiya? Wlh cewa nayi ya kaini wani waje shine ya ajiyeni a nan kuma sai na biyashi ko ya tara min jama'a, Rashida tayi murmushi kinga irin rayuwar da nake jiye miki koh! "Hidaya ina baki shawara ta gari bakya d'auka ina gamawa sai Haulat ta hure miki kunne ke kuma a bi yarima a sha kid'a, shed'an yayi zigi sai ki bita duk inda tayi, wlh Hidaya alhakin Na'im da Nasrin ne ya fara kamaki tun a duniya ma kenan, kina da gata da komai amma mai adaidaita ya rinka Neman tozartaki yana ci miki mutunci wlh idan baki daina abubuwan da kikeyi ba kin koma ga Allah kinje kin rok'esu yafiya sun yafe miki ba wlh a duniya baki ga komai ba, yanxun kika fara fuskantar matsalili wlh, ni shawara na baki kafin babbar k'awarki tazo ta hure miki kunne, tace "nagode sissai Rashida zanyi anfani da shawaranki In shaa Allah, Allah yasa Hidaya tace ameen, toh yanxun ki bashi kud'insa kizo muje mu rage miki hanya nida babynah neh! Tayi murmushi karki damu zan hau wani adaidatan nagode da kulawarki, toh shikenan sai anjima, ta wuce ita kuma ta biyashi ta hau wani mai adaidata d'in...... *6:45 pm* Exactly time a agogon Nigeria, kuma adaidai lokacin ne mallam yayi sallama a fallon Alhaji Haris Saif, kowa sai farin ciki a fuskarsa aka tareshi cikin mutunci da jin dad'i, a lokacin kuma ake kiran sallah yace Ku tashi mu gabatar da Sallah tukunna daga nan sai muyi abinda yadace muyi, suka mik'e gaba d'ayansu sukayi alwala akayi sallah..... Bayan sunci abinci sun natsu mallam ke basu labarin wahalar da yasha a hanya, Yace "Alhaji wannan matsafin ba k'aramin matsafi bane, bina ya rink'ayi yana son ya kashe da Allah ya taimakeni inayin azkhar sossai daya ga ba sarki sai Allah ya gaji sai ya tafi ya barni, Alhaji Tofiq yace "Allah ya k'ara tsarewa ya kuma kiyaye dukansu suka amsa da ameen, ya d'auko magani ya basu yace a rink'a yi mata hayak'i ana samata a ruwan wanka da ikon Allah zata warke ko me akayi mata ya umurcesu da su fito da ita ..... Bayan anfito da ita, ya bud'e maganin da ya d'ebo ya had'a da garin habbatus sauda, yace akawo mishi garwashi ya zuba nan da nan ta fara gurnani shi kanshi Na'im dayake kwance a kan kujera wani irin atishawa yakeyi ma Wuyan fassaruwa, sai aljani da ke jikin Nasrin ya fara magana _cewan Hidaya ce tasa aka turosu domin su lalata cikin da ke jikinta su kuma kasheta amma sai akayi rashin sa'a sun shiga jikinta amma tana yin aZkhar sossai wannan yasa suka kasa aiwatar da komai a kanta amma yanxun zasu fita ayi hakuri, ta fara wani bak'in amai, daga nan ta fad'i k'asa, mallam yace bacci ne ya d'auketa da ta tashi komai zai yi dai dai, Na'im ma bacci yayi awon gaba dashi, mallam yayi hamdala yana mai k'ara jadda da musu cewan da zaran sun tashi komai zai daidaita..... Nice dai taku *AL'EEMAN*📚📚✏ *EDITED BY* 🍒NUSNIM ( *TWIN SIS*)🍒 *DEDICATED TO* Nafee Anker, Mm Shakur, Munayshat, Mamu and Rash Kardam Love you all😘 [1/25, 7:58 AM] ‪+234 706 774 5996‬: 👫 *HA'DI DAGA ALLAH*👫 *WRITTEN BY* KHADIJAH AL'EEMAN *151 - 155* ************* ✍Sun kai gida Daddy daya ga Na'im saida yayi kuka, ya kira Alhaji Tofiq ya fad'a masa, sai gashi yazo da wani malami, yana kallonshi yace wannan aikin tsafi ne dan yafi k'arfin sihiri...... Ya d'auko ruwan zamzam da ya karata ayatul shifa'a, ya bashi ya sha ya d'auko wani magani da aka had'a dasu "man zaitun, habbatus sauda" da sauransu da yasha adu'oi ya bada yace a rinka bashi da safe cokali d'aya da yamma cokali d'aya ya bada garin habbatus sauda yace a rinka mai hayaki dashi, ya k'ara musu wani magunguna dana wanka, man shafawa da turare, kuma a dinga sa mai karatun alqur'ani mai girma yana ji, In shaa Allah komai nene a jikinsa zai barshi da ikon Allah, aka ce nawa za'a bashi? Alhaji kenan ai d'anka d'ana ne, ba sai abani wani abuba, ba komai Allah ya bashi lafiya, Alhaji Tofiq yayi sallama dasu akan zai dawo zuwa gobe domin yaga yadda jikin nasa yake..... "A 'bangaren su Hidaya kuwa sunje wurin bokan ya basu layu su sami wani dutse su daga su saka, amma su tabbatar bawanda zaiga dutsen harma ya d'aga shi, sannan bayan tafiyarsu zai tura ma Nasrin bak'ak'en aljanu su zasu lalata cikin, suka ajiye masa kud'i suna murna suka kama hanyarsu ta komawa...... "Nasrin ne zaune ta gama ba Na'im magani ta tashi ta shiga bathroom kawai sai taga abu ya gitta ta gefenta bata San ko menene ba, wani tsoro taji da bata ta'ba jin irin shi ba, ta kwalla k'ara ta fad'i, mommy ne ta shigo d'akin domin kawo ma Nasrin d'an wake dan tace shi takejin ci, ta ji k'ara a bathroom da gudu tayi wurin tana shiga ta ganta a kwance numfashi da kyar yake fita, salati ta fara ta fito da sauri ta kwalla ma Na'ima kira da gudu ta shiga d'akin ta ja hannunta suka kamo Nasrin d'in suka kwantar da ita a kusa da Na'im da keta faman baccinsa, Na'ima ta shiga dubata komai normal cikin ba abinda ya sameshi, sai dai abinda ya basu tsoro kamanin Nasrin ya canja, sannan ba abinda takeyi sai kuka ko magana bata iyayi, kukan ma baya fita kwata kwata....... Mommy ne ta shiga d'akin Daddy a kid'ime ta sanar dashi halin da ake ciki, da sauri ya tashi ya bita d'akin ba k'ara min d'aga mai hankali yayi ba ganin Nasrin a halin da take ciki, mommy tace ya kamata ka kira Tofiq su dawo shi da mallam, da sauri ya koma d'akin shi ya d'auko waya, ya kirashi ya sanar mai..... Ba'a d'au lokaci mai tsawo ba sai gasu sun iso, aka fito mashi da ita, yana kallonta ya ganne meke damunta, ya fara mata Rukiyya amma shiru, ya dinga yi ya kai awa d'aya yana abi d'aya amma shiru kakeji, ya ce Alhaji bak'ak'en aljanu ne masu taurin kai, akwai wani magani da sai naje wani k'auye na nemoshi idan na kawo za'a had'a da garin habbatus sauda ayi mata hayak'i dashi da ikon Allah zasuyi magana zakuma musan Wanda ya aikata mata wannan aikin, kwana goma zanyi kafin nadawo, ga wanan idan kuka bud'e zaku gansu kala biyu ne a ciki da fari da kuma brown, farin zaku shak'a mata a hanci, brown d'in kuma a samata shi a ruwa a bata tasha, In shaa Allah ba abinda zasu mata har indawo sai dai suna nan a jikinta, sukayi godiya yayi sallama dasu Alhaji ya kawo kud'i ya bashi yayi Guziri, yayi godiya ya amsa ya kuma yi sallama da Alhaji Tofiq cewan daga nan garin zai tafi Neman maganin, yayi masa godiya sukayi musabaha ya juya ya tafi abinsa.... "Hidaya ce ita da Haulat a bayan gari sun ga wani dutse a wurin, shi kuma wani mutum ya hangosu sai ya la'be yana lekensu har suka gama suka wuce.... Yana ganin sun wuce ya fito, ya je wurin dutsen toh matanan me sukeyi ne a nan, sai da ya duba ba kowa sanan ya d'aga yaga layu ne kusan guda biyar a wurin, shi tsoro ma yaji yasa hannu ya d'auka ya bud'e su d'aya ansa "Na'im da Hidaya sai mutuwa! Na biyun ansa "Na'im da 'yan uwanshi har abada! Na ukun koh "Na'im da Nasrin rabuwa ta har abada! Na hud'in ansa "sai yadda Hidaya tayi da Na'im" na biyar d'in kuwa "duk inda Na'im yake zai baro ya dawo wurin Hidaya sai kuma wasu rubutu da bai san ko menene ba!..... Saurayin nan ya girgiza kai yana mai adu'a a cikin ransa, duniya gaskiya ta lalace, ya tafi dashi har k'ofar gidansu ya d'auko ashana ya k'onasu, wannan kenan....... "Yau kwanan mallam biyar da tafiya Nasrin sai dai abu mai ruwa ake riketa abata da kyar take sha, bata magana kwata kwata sai kuka, Na'im kuwa Alhamdulillah ya fara samin sauk'i amma har yanxun bai cika magana ba, baya kuma maganan Nasrin ko ya ganta sai dai yayi ta kallonta baya cewa komai.... Yau ne ake sa ran mallam zai dawo, kowa a family yana gidan, 'yan uwan Nasrin ma duk sunzo sun gaishesu sun tausaya mata kwarai da gaske, Mahaifiyarta kuwa da k'anenta kuka kawai sukeyi.... Ohh ni AL'EEMAN ko maganin zaiyi kuwa🤔 makaranta sai kusa Nasrin da Na'im a cikin adu'oinku... Nice dai *AL'EEMAN* *EDITED BY* 🍒 NUSNIM ( *TWIN*)🍒 *DEDICATED TO* Nafee Anker, Mm Shakur, Munayshat, Mamu and Rash Kardam Love you all😘 [1/25, 7:58 AM] ‪+234 706 774 5996‬: 👫 *HA'DI DAGA ALLAH*👫 *WRITTEN BY* KHADIJAH AL'EEMAN *161 - 165* ************* *d'inbin masoyanah ina godiya a bissa yadda kuke kirana kuna nuna damuwarki akan littafi. Had'i daga Allah ina sonki har cikin raina* ✍"Hidaya taje ta cire abinda ta burne daga nan ta kama hanya zuwa gidan Surukanta tana tafiya tana kuka kamar mahaukaciya, kukanta ne ya tashi Nasrin da Na'im, sugunnawa tayi tana rokonsu akan abubuwan da ta musu, Na'im kasa cewa komai yayi domin komai daya faru ganin yakeyi kamar a mafarki.... "Mommy ce ta bashi labarin abubuwan da suka faru, rik'e kai yayi ya rasa mai zaice, ya d'ago idanuwan shi da sukayi ja kamar garwashi ya nuna Hidaya da yatsa yace bazance miki komai ba amma kije duniya ce ta isa kowa riga da wando, ya dukar da kai yana hawaye abubuwan da tayi mai suke k'ara dawo masa babu abinda yafi mai ciwo kamar yadda ya rinka share Nasrin, da ta bashi da Nasrin yana ganin zai iya yafemata amma tunda ta rabashi da Nasrin a lokacin da take da bukatar kulawanshi gaskiya bazai iya yafe mata ta cutar da ita ba d'ankaramin cutarwa ba, mik'ewa yayi yace Hidaya bazan ta'ba yafe mikiba wlh na tsaneki, kije kuma na sakeki saki Uku..... Da sauri ta d'aga kai ta kalleshi ta bishi ta kama kafafuwanshi dan girman Allah kayi hakuri wlh sharrin shaid'an ne da kuma k'awa dake zugani, dan Allah ka yafemi, tureta yayi ya haye sama abinshi..... Juyawa tayi ta kalli Mommy da Daddy ta na rok'onsu, Daddy kasa cewa komai yayi sai kallo da yake binta dashi, ita koh mommy cewa tayi dama ni saida nayi zargin wani Abu, haka kawai Na'im bazai zo da maganar Aure ba, Ashe kece kika k'ulla mugun abu, da kika shigo gidan ma maimakon ki zauna lafiya ki barshi da matar shi kuyi zaman lafiya a'a wannan ma bai isheki ba harda yink'urin kisa, gaskiya kiyi wawta amma kuma kanki kika cuta ba kowa ba Allah ya shiryeki ya kuma yafe miki..... Ta juya wurin Nasrin wadda in banda kuka ba abinda takeyi, ta tsugunna tana rokonta ta yafe mata ta kuma tayata rokon Na'im da ya yafe mata, murmushi tayi hawaye na zuba a fuskarta tace indai nice na yafemiki sai ki rok'i Allah shima ya yafemiki, maganar Na'im kuma kisa a ranki ya yafe miki dan zan mai magana kuma nasan zai saurareni, dan haka kije ba komai, Allah ya yafe mana gaba d'aya, ta mik'e tana fad'in nagode Allah yasaka da alkhairi ta juya tana kuka ta fita..... Nasrin ta mik'e ta haura sama zuwa 'bangaren Na'im na da, ta sameshi a tsaye sai kuka yakeyi tasa hannunta ta zagaye shi ta kwantar da kanta a kafad'ar shi, wani irin shock yaji, tace haba Namijin gaske, bansan ka da rik'o ba karka manta Manzon Allah (S.A.W) ya hanne mu da rik'o ya kuma umurce mu da mu zama masu yafiya, ina son kayi hakuri ka yafemata bagashi ya zama tarihi yanxun ba, a koda yaushe *Ina tare dakai*(littafin Miemie bee), kuma mun zama *jini d'aya*( na Aneelurv), kaga ba Wanda ya isa ya rabu sai Allah ni dakai *Had'i daga Allah* ne, Dan haka kayi hakuri ka yafe mata, muma muna ma Allah laifi ya kuma yafe mana, ya juyo ya rungumeta sossai na yafe mata Dearnah amma kisani ta cutar dani ba d'an kad'an ba, Allah kad'ai zai iya yimun sakayya tsakanina da ita amma tunda kince in yafe mata na yafe mata komai ya wuce..... Yauwa nagode sossai Allah ya k'ara tsaremu daga Sharrin aljani da mutune, ya amsa da Ameen..... "A 'bangaren Hidaya kuwa tana fita wani mai mota ya yanko da gudu ya kwasheta ta fad'i, daya juya yaga ba kowa ya gudu abinsa, sai wani bawan Allah ne yazo zai wuce ya ganta a kwance a wurin ta rik'e k'afa sai kuka takeyi ya karfi wayarta ya kira mahaifiyarta ya gaya mata zai kaita asibitin dutse taje ta sameta a can, ya d'auketa ya kaita, mahaifiyarta taje ta sameta, likita kuma ya gaya musu saidai a yanke k'afar, tayi kuka kamar zata mutu ta kuma yi data Sani ba d'an kad'an ba, Rayuwa kenan..... Kuyi hakuri yau sai ahankali sai kujira next typing Wanda may be shine last episode...... Nice dai *AL'EEMAN*📚 *EDITED BY* 🍒NUSNIM ( *TWIN SIS*)🍒 *DEDICATED TO* Nafee Anker, Mm Shakur, Munayshat, Mamu and Rash Kardam Love you all [1/25, 7:58 AM] ‪+234 706 774 5996‬: 👫 *HA'DI DAGA ALLAH*👫 *WRITTEN BY* KHADIJAH AL'EEMAN *165 - 170* ************** ✍"Hidaya ta shiga matsanancin rayuwa, ga kud'in suna dashi amma ba k'afa, mai aiki aka samo take mata komai, tunda abin ya faru Haulat batazo ta dubata ba, data kirata ma cewa tayi bata garin, alhalin tana nan, ita kanta Haulat d'in tana cikin mawuyacin hali domin ta fara rashin lafiya data je asibiti aka gano tana da HIV Aids, tayi itama nadama da dana sani ba d'an kad'an ba...... "Na'im da Nasrin kuwa sun koma gidan su, babin soyayya sabuwa suka bud'e, data ce wash ko mai yakeyi zai bari ya maida hankalinsa a kanta, gashi yanxun wani shagwa'ba takeyi ya rasa a ina ta koyon wannan shagwa'ban domin gaba d'aya rikita shi take (ni AL'EEMAN nace aikin Zainab ce, duk ita ke koya mata wani kussa da kisisinah), gashi ta k'ara cika ta zama babbar mace..... "Yau cikin Nasrin Nine months, three weaks, suna kwance kamar yadda suka saba, tana mak'ale a jikinsa, ta fara jin bayanta na sarawa, amma ta cigaba da daurewa, can kuma sai mara ya d'auka tun tana iya daurewa har ta fara hawaye, gashi Na'im na bacci bata son ta tasheshi, a hankali ta ja jikinta ta sauka daga gaddon amma kuma sai dai ta turkushe a wurin, kafin kice me har paya ta fashe amma still tak'i tashin Na'im, sai ta fara nishi da k'arfi aikuwa cikin hukuncin Allah baby ya fad'o, sai kuma ta k'ara wani nishi sai ga wani babyn ya k'ara fad'owa,kamar ance sun had'a baki suka fara kuka a tare..... Na'im kamar a cikin mafarki ya fara jin kukan jarirai, bud'e idon da zeyi yaji da gaske ne fa kuma a d'akin yakeji ya sauka ya kunna haske kawai suka had'a Ido da Nasrin da duk ta had'a zufan wahala, ga kuma babies har buyu a gabanta, mamakine da al'ajabi suka cika shi, ya matso ya dafata yana mata sannu, cikin dashashiyar murya tace ya kira mata Na'ima tazo ta yanke cibin tunda harta mahaifa ta fad'o, da Sauri ya duba agogo k'arfe hud'u da rabi, ha daga waya ha kira Ahmad, Ahmad na ganin shine da Sauri ya d'aga ya ce lafiya? Ya gaya mai halin da ake ciki, ya kalla Ni'ima dake kwance a kirjinsa ya tadata da sauri ya fad'a mata, da sauri suka mik'e suka sa kaya ta lek'a ta tashi ido tace idan su Amir sun tashi ki kula dasu zamuje mu dawo, cikin sauri suka fita a gidan...... "Sun isa Na'ima da sauri ta shiga d'akin ta yanke cibin, ta tambayi Nasrin wanda ta fara haihuwa ta nuna mata, ta duba taga mace ne, ta duba d'ayan itama macece, gasu adentical twins ne, da kyar ta gane cewan babban ta d'anfi fad'in fuska akan k'aramar, nan da nan ta had'a ruwa ta gasa Nasrin da kyau da towel sukayi anfani, sannan ta fito tama yaran ta gyara ko ina, ta bud'e gidan da turare..... "Alhamdulillah Nasrin ta sauka lafiya kuma kowa yayi murna ba ma kamar uban gayyar wato Na'im jinshi yake kamar ya had'iye maman da yaran.... Ranan suna Yara sunci sunan Mommy da Umman Nasrin, ana kiransu da Hanam da Hanan, suna ne da aka narka kud'in gaske, kaya kuwa ba'a maga suko su Amir da Amira dad'i sukeji sunyi k'anne, bayan suna da kwana d'aya Mommy tazo zata d'auka Nasrin a nan fa aka shiga daru da Na'im, shi wlh a bar mai matarshi, mommy tace bai isa ba wlh sai ta tafi da ita, yanaji yana gani aka tafi da ita shima ya had'a kayanshi yabi bayansu, yaje 'bangaren shi dake gidan mommy tace kayi ka gama..... *BAYAN SHEKARA BIYAR* "Abubuwa sun faru da yawa ciki harda kammala karatun Nasrin, Nabeela ma ta haifa baby girl ansa mata suna Fatima ana kiranta da ikram, k'annenta ma sun dage sunyi karatu sossai yanxun Haka ma maganar auren biyu daga cikinsu akeyi, "yan uwan babanta yanxun ji da ita sukeyi tamkar kwai, Mommy ma yanxun Shureim kad'ai ya rage mata ta aurar, su Nasrin yanxun hankali ya kwanta gashi kud'i na shigowa ta ko ina, Na'im yayi kiba abinshi yayi kyau, gashi yana Samun kulawa sossai a wurin Nasrin, jinsu sukeyi kamar zasu cinye junan su...... "Nasrin ne a zaune tana duba wani file da zatayi submitting gobe da safe, sai ga wani yaro d'an shekara biyu yana gudu yazo bayanta yana cewa mommy kinga Hanan koh! Ga Hanan a tsaye tana haki, ta kalleta tace meya faru me yayi miki? Toh mommy bashi bane chocolate d'in da Daddy ya siyo mana jiya ni ban cinye nawa ba ya d'auke ya cinye min, toh kiyi hakuri ba k'anin ki bane zan siya miki wani kinji koh! Ta gyad'a kai, sai ga Hanam ta fito tana cewa nima hardani koh mommy? Tace kwarai ma kuwa harda ke suka fara tsalle suna murna, sai ga Na'im ya shigo rige rige sukeyi daga su har Maman su, dariya yakeyi saida ya rungume Nasrin kafin ya fara d'aga yaran d'aya bayan d'aya suna dariya,.... Yace toh kuzo muyi selfie ya ciro wayansa nima na matso ta gefe na shiga Ashe Nasrin ta ganni ta galla min harara tace mallama sai ki kama hanya ki wuce leken asirin ya ishe mu haka nan, na juya jiki a salu'be na fita a gidan, ina jinta har tana saka key dan kar inkoma....... Toh nima anan zan tsaya da abin rubutuna sai kun sake jina acikin sabon littafina mai suna *MA'AURATAH* ********************** ⬇ ************************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** Godiya ta tabbata ga Alla (S.W.A) mai kowa mai komai Wanda shine ya hallici sammai da k'asai da abubuwan da ke cikinsa, shine ya bani baseerar da kuma ikon rubuta wannan littafi, ya Allah ka k'are mu da lafiya wa'inda basu da lafiya Allah ka k'aresu da lafiya,ka jik'an wa'inda suka rasu muma idan tamu tazo Allah yasa mu cika da kyau da imani Allahumameen👏 *GODIYA TA MUSAMMAN A GAREKU* 📝 Excellent writers 📝 Pharty novels 📝 Aneelurv Novels 📝 Nafee Anker novels 📝 Faxy fashion novels 📝 Matan kwarai group 📝 All dostis of Nusfulhayat 📝Daga marubuta group 📝 Stylish Housa novel 📝 Home of Hausa novels 📝 Eshart tsafe novel 📝 Taskar 'ya'ya mata Kai dama Wanda ban anbata ba Dan wlh kuna da yawa, da badan Ku ba da ban kai matsayin da nake a yanxun ba Dukan ku *AL'EEMAN* na sonku *KUNFI KOWA SON WANNAN NOVEL 'DIN* 🍉 Deejah's kitchen group🍉 *AL'EEMAN* na alfahari daku Ina missing d'inku masoyanah na gaskiya 👉 Fatima Ahmad magayaki 👉Aisha Sani d'anladi 👉Zainab Aliyu buratai 👉 Maryam Umar d'an Fulani (Allah ya jik'anki) 👉 Bar'atu Rabi'u sulaiman 👉 Baraka Lawal garba Kai wlh kuna da yawa Allah ya bar k'auna Ban manta dake ba aminiyar kwarai *ANEELURV* *Wannan littafin sadaukarwa ne a gareku* Nafee Anker, Mm Shakur, Munayshrt, Mamu, Afra sai kuma Rash kardam *Khadijah* na sonki *EDITTED BY* 🍒NUSNIM (TWIN SIS)🍒 Sannu da kokari Allah ya bar zumunci Taku a koda yaushe *KHADIJAH AL'EEMAN*📚