********************** ⬇ ************************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** DAME AKE ADO part 23. BOOK 4*1 Ma'u kam tana durkushe kankame da kujera saigyada kai take tana nishi, shikuma Ahmad yama rasa mai yakamata yayimata cikin ikon ubangiji tazabga wani irin nishi cikeda kabbara saiga yarinya tafado facal! Ihun yarinyar ne ya ankarar da Ahmad yazura hannu yajanye yarinyar gefe ahankali donyaga kamar zata zauneta saiga mahaifa tafito itama gaba daya ma'u takwantarda kanta ajikin kujera tana maida numfashi Ahmad yarasa maizaiyi saboda ihun yarinyar keyi gamahaifa ajikinta yakalli ma'u yace ma'u mezanyimata ne? Tadan kalli yariyar nima bansaniba yaya kakirawo babar A'ilo dasauri yafice yanufi gidansu babar A'ilo yatarar kofar gidan akulle danhaka yafara bugawa baijima dafara bugawaba suka bude mahaifin A'ilo ne yafito yanatambayar wanene? Yanabudewa yayi arba da Ahmad hankalinsa atashe nan take Ahmad masa bayani yajuya gida yasanarda babar A'ilo suka fito dahanzari suka garzayo gidan Allah yasa baijima dayin siyayyar haihuwaba harda reza acikin kayan kafin karfe dayan dare babbar A'ilo ta kammala komai tagyara maijego da jaririya da kuma dakin Ahmad kam shiya wanke dukkan kayan dasuka baci cikin ransa yanajin son ma'u da tausayinta nakuma shigarsa cikin daren su Umma sukaji lbr donhaka danhaka ana idarda sallar asubah Umma ta iso gidan tun gari baiyi sha ba tatarar da diyarta fes! Ranta yayi tas! Shikuwa Ahmad kwana yayi idonsa akan diyarsa komai dake jikinsa shine ajikin wannan yarinyar ya rungumeta kamar zaimaidata ciki yayita yimata addu'a duk wadda tazo bakinsa Duk wani duba anyiwa ma'u batasami matsalar komaiba sukansu likitici Sunyi mamaki domin ganin ma'u tanada karanci shekaru amman dai sunsan kowace mace da irinjikinta musamman itada tahaihu durkushe daga karshe dai sunbata magunguna itada diyarta suka wuce gida matan yayyenta dasu yayyen nata dukkansu suna jiran dawowarsu Ahmad saibasu labarin kammanin diyar yake yi anata dariya kowa yakagu sudawo din sanda suka iso gidan yacika da murna da hayaniya akadinga shigowa barka hayaniyar ce tasanya lami da diyanta suka gano wani abu yana faruwa agidan Amina tadawo ranta abace takasayin koda magana lami tadubeta tace malam kigaya mana abinda yafaru mana kishigo sum sum saikace tinkuya tome zangayamikine wai waccan banzarce tahaihu.....lami tatashi agigice cikin firgici tace badai ma'u ba? Itamana sunckawa mutane gida da ihu banza kawai!!! Lami takoma tazauna tana huci kamar zatafaahe da kuka Raliya kam takasa cewa komai sai kallonsu kawai take itakadai tasan metaki cikin ranta lami tsinuwa da baki babu wanda batayiwa diyar da aka haifaba ma'u kam taga karamci daga gurin yan uwanta da mijinta don duk yankudin hannunsa da wanda yake tarawa akan diyar nan yakarar dasu itama hajiya amina tadauki soyayya tadora akan diyar nan kullum saitazo ganinta saitake tunamata da Ahmad lokacin dayana jariri Rashin shigowar lami dadiyanta barka yadaurewa Umma kai kwarai dagaske amman tadanne abin acikin ranta gurin yiwa diya huduba saida akasamu sa insa domin shi Ahmad sunan Umma yakeso asamata itakuma Umma tadage sunan mahaifiyarsa za asanya domin ita akwai sunayenta dayawa Auwalu yasaka sani yasaka itakuwa ma'u babu maisunanta dakyar ya amince da hakan akasanyawa diyar sunan Asma'u saiyakejin kamar mahaifiyarsa tadawomasa son diyar yarika shigarsa Ranar suna anyi suna maikayatrwa namasu rufin asiri anci ansha dai misali wannan abu yakoma konawa lami rai Raliya kam har kuka tayi takunshe cikin daki takasa kolekowa waje datuni itace zatahaifi wannan diyar ta halak tayiwa kanta tabbas tashiga cikin tsananin tada sani wacce hausawa sukecewa keyace Adaren ranar suna ciwo yakumeta cikin daki tuntana abin itadaya hartafara kiran mahaifiyarta lami tashigo dakin sukaci gaba amman shiru babu haihuwa sai azaba tun lami naganin abin wasa ne hartafara tsorata shikam malam jibril tunda yafuskanci abinda kefaruwa yashige dakinsa yarufo kofa da lami taga bahaza taje tabuga masa tanakuka yavude kofar ransa abace yaya akayi lfy dai ko? Cikin kuka tace Raliya zata mutu jibril kataimaka mini yagalla mata harara Rayuwar raliya da mutuwarta duk dayane agurina lami don gwara ma tamutu kona huta da abin gori yajuya yashige dakinsa avinsa yaja kofa lami tafashe dakuka gami dajuyawa dakin da gudu savoda jiyo kuwar diyar tata datakeyi sukacigaba da fama amman har tsakiyar dare shiru shikansa jibril saida yakaraya yaleka dakin halin dayaga diyar tasa yadaga masa hankali kwarai dagaske yagigice yanafadin yayazasuyi? Lami tana kuka tace asibiti za'akaita kawai yadan waro ido agigice asibiti gashi banida ko kwandala kuma shi asibiti saida kudi kinsani DAME AKE ADO part 24. Book 4*2 Kaje wurin yayanka mana agidime yanufin gidan yajima yana buga kofa can jimawa malam sulaiman ya iso yana tambayar waye? Jibril yace nine malam sulaiman yabude masa kofa cikeda mamaki dalilin zuwansa cikin dare agidime jibril yayi masa bayanin abinda kefaruwa malam sulaiman yace to aisamun mota cikin wannan daren shine aiki amma bari yashiga yayiwa Umma magana ko akwai dazata iya yi akai? Sanda malam sulaiman yasanarda Umma abinda kefaruwa tayi tsalle tadire tace babu inda zani nima diyata tahaihu yauhar kwana bakwai amman daga lami har yayanta babu wanda yaleko danhka itama babu inda zata tunyana mata fadan har saida yafara yimata magiya dakawo mata hadisai wadanda suka sanyayarmata da guiwa tanufi gidansu lami tana zuwa taga halin da Raliya take ciki tasan lallai tajigata takwanta shabe shabe ga kanda yana yunkurowa yana komawa yakasa nishi lami saikuka takeyi itada Amina Umma takalli lami tace kunada koko? Dasauri lami tace akwai tafice tadauko Umma ta amsa tayi addu'a tatofamata aciki sannan tace adagamata Raliya zaune suka kama Raliya dakyar suka durkusarda ita Umma tace tadafa kujera tatokare kafafuwanta akasa takafamata wannan kunun cikin katon kwanon sha tadinga sha harsaida tashanye shi tas! Cikin ikon Allah saiga karfi yazowa Raliya tafara wani irin nishi da karfi Umma tariketa saiga diya tafado cikin ikon Allah kuma harda mahaifa baki daya lami tafashe murna Umma tadallamata harara keda zaki godewa Allah saikuma saikuma kikama guda? Saiki kawo reza lami tazura da gudu tafara nemo reza da zare Umma ta amsa tayanke ta kulle cibiyar bayan ta yanke Raliya tayi zaune takasa ko motsawa saboda abu biyu keyawo aranta murna darabuwa da abinda kecikinta dakuma abinkunyar dazaifara bibiyarta harkarshen Rayuwarta malam jibril natsaye jikin kofar dakin dadamuwa akan fuskarsa yanajiyo sautin kukan jaririya yazame yazauna yanasallami da damuwa Shikenan shege yatabbata agidansa diyarsa ce tahaifamasa shege yashiga Ukku!!! Umma dai tanagama abinda zatayi takalli lami datayi wuki wuki tace to lami ga Raliya tasauka tasami irin abinda kikajima kinagorantawa Ahmad akai sainace Allah yaraya Ameen lami tabude baki dabakinciki amman batada abincewa dazaiyi daidai da irin maganar Umma tafada mata hartafice daga dakin lami takalli raliya dake zaune kamar tashaketa don bakin ciki takalli diyar wacce kekuka wutsil wutsil da kafafuwa saitayi tsaki tajuya tafice daga dakin dasauri Raliya tabi yarinyar dakallo tamika hannu tadauketa ta kuramata ido fatanta baiwuce tagano dawa diyar kekamaba wanda zatace shine ubanta domin maneman nata nada yawa amman iyakacin kallonda tayiwa yarinyar takasa gano dawa yariyar tayi kama hawaye yakama fitowa daga idanunta soyayyar yarinyar tanashigarta ahankali meyasanya batazauna gidan Ahmad tahaifi wannan yarinyarba kobayan hakanne tabar gidansa Datahuta dagori daduk abinda zaibiyo bayan rayuwar wannan yarinyar data haifa yanzu dakyar lami ta iyadaura ruwan dumi domin takaiwa Raliya tayi wanka basu sami kwanciyaba saiwurin karfe 4 nadare sannan suka kwanta kiran sallar farko Raliya tamike tsam tadauko jakar kayanta tafara zubawa dukkan abinda tasan natane daman sugama yin waya da Ruky tuncikin dare sungama shirya abinda zasuyi bayan takammala shityawa ta juya ta kalli jaririyar dake bacci hawaye yazubomata taji kamar kada tagudu tabar diyarta amman bazata iyacigaba daharka yanda takesoba matukar tanatare da wannan jaririya tagoge idonta dasauri tadauki jakarta tafice har gari yawaye rana tafito lami bata leka dakin da Raliya takeba can yarinya tafara kuka daga cikin daki daga lami har amina babu wanda yakula dakukan datakeyi domin suna tunanin mahaifiyarta nakusa da ita shikam daman malam jibril tunda yafita baidawo gidaba musa kuma tunda akayi rikicin nan baidawo gidaba saiyatare can wani dakin abokinsa dan baisan abinda zaifaru dashiba idan sukaci karo da lami kukan ya ishesu lami tamike afusace tanufi dakin tana fadin Raliya wai uban me kike yine kikabar yarinyar nan tana kuka haka? Tadaga labulen dakin afusace saidai ga mamakinta saitaga dakin wayam babu kowa saijaririya dake tsala kuka tashiga dakin dasauri tafara bincike Raliya! Raliya!! Raliya!!! Amman taji shiru babu ita babu alamunta tafito dasauri takalli Amina cikin ihu kedubaman bandaki ko Raliya tashiga Amina tamike dasauri domin taga mahaifiyar tata arude take tace lami batanan lami tadafe kirji agidime tana fadin nashiga ukku kardai ace yarinyarnan tagudu tabarman diyar nan? Ihun jaririyar yacikamata kunne takoma dakin dasauri tadaukota tarungume tana jijjiga dafadin kemaza dubamana gidan nan sosai harcan gidanu deeje kigani intana can Amina tajuya tanufi hanyar fita lami tacigaba da jijjiga jaririyar hankalinta atashe kamar tazabga ihu taji sanyi aranta Abukamar wasa karamar magana tazama babba! Domin duk inda aketunanin za'asamu Raliya anduba babu ita babu alamunta dole lami tanaji DAME AKE ADO 4**2 tun ina boye halin da nake ciki har iyayena suka fuskanta don na rame na fita daga hayyacina bani da kwanciyar hankali sam ga danbanzan duka danake sha ahannun salim, iyayensa kuma kamar kurame domin sun toshe kunnuwansu daga duk wani kuka na game da dansu, sai asannan nagano salim dan iyayene marasa tarbiyya. shekararmu biyar ina cikin wuya da tashin hankali danmu daya, kwatsam! wata rana salim ya dawo gida abuge daga yin magana ya rufeni da duka har da karaya ahannu wannan shine ya kawo karshen aurenmu domin na gaji da azaba iyayena ke tausaya....... Tayi shiru tana maida numfashi idonta ya cika da kwalla ta cigaba, shekaru uku da mutuwar aurena nakasa samun wanda ya dace dani da burikana, Ahmad ka tuno ummi da soyayyarta cikin ranka? Gaban Ahmad ya fadi ummi ta dawo dashi ruwa tsumdum! amma ya dake yace ummi ko kin manta kina magana da Ahmad SHEGE ne dan gidan asma,u mahaukaciya ne? Nine dai yadda kika sanni ba,a sauyani ba bakuma a siyomin uba a kasuwa ba, me zakiyi da shege ummi? Hankalinta ya tashi ta mike daga inda take kishingide ta kankame wayar tana fadin wallahi bazan ga laifinka ba akan dukkan abinda zaka fada ba, amma ka sani ko mahaifana sunyi da sun sanin rabamu, don sun gano wani mara iyayen ma yafi mai uwa da uba daraja da hali na gari. kayi hakuri Ahmad ka manta da dukkan abinda ya wuce ko bakayi magana ba Allah ya saka maka cikin ruwan sanyi Yayi shiru baice mata komai ba yana maida numfashi har sanda muryarta ta kara sauya masa tunani da fadin ka yafemin Ahmad! Yanda ta furta maganar ya sanyaya dukkan gabbansa baisan sanda yace nayafe miki ummi Wani irin dadi ya cikata tace nagode Ahmad ina fatan zamu dora daga inda muka baro asoyayyarmu? Yayi wani tari da bai shiryaba yace "Nan fa daya! Ai ma,u ce kadai matata ta duniya insha Allahu Farin cikinka ya gushe lokaci guda, cikin damuwa tace kayiwa ma,u alkawari ko rantsuwar bazaka mata kishiya ba kenan Ahmad? Ya kada kai, ko daya ban taba yi mata wannan alkawarin ba amma na sanyawa raina hakan, iyayen da suka rikeni suka maidani mutum kamar kowa suka raineni sanda bansan kaina ba suka bani aure sanda na rasashi yaushe zan iya hada son diyarsu da na wasu matan? Bazan iya ba! koda ace ma,u tana azabtar dani bazan iya hadata da kowacce mace ba, balle ina cikin mazan da ke cikin sa,ar aure da iyali a duniya, don haka bana bukatar kari sai dai nayi miki addu,a ummi Allah ya baki wani mijin daya fi mijinki na farko alkhairi dani kaina......... Sai ta fashe masa da kuka tana fadin don Allah kada kayimin haka Ahmad kada kace zaka rama dukkan abinda na aikata maka, ni mace ce bazan iya dauka ba. Jin kalamanta zai iya karya masa zuciya, bayan kuma yasan ko kukan jini zatayi bazai taba iya yi mata abinda take bukata ba don da ma,unsa tayi kuka gara kowacce mace a duniya tayi kukan jini in ancire mamansa, dan haka da sauri yace kiyi hkr ummi sai anjima! ya kashe wayar. Ya koma jikin kujera ya kwanta tausayin ummi da sautin kukanta suna turereniyar shiga zuciyarsa har baisan sanda aka turo kofa aka shigo ba, sai da aka daki tebur dinsa sannan ya daga kai da sauri kamar wanda ya farka daga barci. Nana ce tsaye ta rike kugu tana kallonsa. Ya wayance Sorry hajiya na tafi wani dan tunani ne. Ka tafi babban tunani dai, wannan tunanin naka baiyi kama dana komai ba bayan na soyayya, ko ka tuna da tsohuwar budurwarka ne? Yayi yake me ya sanya tayi saurin ganoshi? Amma sai ya dake yace waya gaya miki haka? Mubar wannan chapter mu koma ta aikin daya shigo dake. Taja kujera ta zauna ta dora kafa daya kan daya tace. Yau ba aiki na shigo yi ba hira ce ta kawoni, sai kuma nayi katari da samun babban labari akan fuskarka. Don Allah ka gayamini ka taba soyayya Ahmad? Tambayar tazo masa a bazata cikin mamaki yace maiyasa kikayi min wannan tambayar? Ta gyara zama domin nagano da gaske akwai kalmar soyayya a doron kasa, idan na rantse maka bazan kaffara ba ban taba soyayya ba, bantaba jinta cikin jikina ba a baya dukkan rayuwata na karar da ita ne haka bantaba surkata da soyayya ba, bantaba son wani ba, hakan ne ma yasa iyayena da dangina suke zaton ina da mutanen boye (aljanu) musamman da wasu malaman da suka sha fada musu wai bakin aljani ne ya aureni, sunce sai anyi da gaske zai barni nayi aure, su fa sun yarda da hakan shi ya sanya suke lallabani da banka min magunguna a tsawon shekaru ashirin da wani abun da haihuwata babu wanda ya taba matsa mini nayi aure, don ance musu da sun fada ko sun matsamin zasu iya rasani daga lokacin don aljanin wai zai gudu dani. Tayi shiru tana kallon Ahmad dake kallonta da mamakin jin abinda take fada, tayi ajiyar zuciya ta cigaba da magana. Ahmad babu abinda iyayena ke bukata yanzu a rayuwarsu bayan ganin aurena, amman suna tsoron fadamin haka, nasan dukkan abinda aka gaya musu na kuma san karya ne, amma na bisu ahaka don ni a karan kaina bana bukatar auren, ban ma taba jin naga wani mutum ina sonshi ba sai cikin shekarar nan DAME AKE ADO.... 4**6 ya kwanta tausayin ummi da sautin kukanta suna turereniyar shiga zuciyarsa har baisan sanda aka turo kofa aka shigo ba, sai da aka daki tebur dinsa sannan ya daga kai da sauri kamar wanda ya farka daga barci. Nana ce tsaye ta rike kugu tana kallonsa. Ya wayance Sorry hajiya na tafi wani dan tunani ne. Ka tafi babban tunani dai, wannan tunanin naka baiyi kama dana komai ba bayan na soyayya, ko ka tuna da tsohuwar budurwarka ne? Yayi yake me ya sanya tayi saurin ganoshi? Amma sai ya dake yace waya gaya miki haka? Mubar wannan chapter mu koma ta aikin daya shigo dake. Taja kujera ta zauna ta dora kafa daya kan daya tace. Yau ba aiki na shigo yi ba hira ce ta kawoni, sai kuma nayi katari da samun babban labari akan fuskarka. Don Allah ka gayamini ka taba soyayya Ahmad? Tambayar tazo masa a bazata cikin mamaki yace maiyasa kikayi min wannan tambayar? Ta gyara zama domin nagano da gaske akwai kalmar soyayya a doron kasa, idan na rantse maka bazan kaffara ba ban taba soyayya ba, bantaba jinta cikin jikina ba a baya dukkan rayuwata na karar da ita ne haka bantaba surkata da soyayya ba, bantaba son wani ba, hakan ne ma yasa iyayena da dangina suke zaton ina da mutanen boye (aljanu) musamman da wasu malaman da suka sha fada musu wai bakin aljani ne ya aureni, sunce sai anyi da gaske zai barni nayi aure, su fa sun yarda da hakan shi ya sanya suke lallabani da banka min magunguna a tsawon shekaru ashirin da wani abun da haihuwata babu wanda ya taba matsa mini nayi aure, don ance musu da sun fada ko sun matsamin zasu iya rasani daga lokacin don aljanin wai zai gudu dani. Tayi shiru tana kallon Ahmad dake kallonta da mamakin jin abinda take fada, tayi ajiyar zuciya ta cigaba da magana. Ahmad babu abinda iyayena ke bukata yanzu a rayuwarsu bayan ganin aurena, amman suna tsoron fadamin haka, nasan dukkan abinda aka gaya musu na kuma san karya ne, amma na bisu ahaka don ni a karan kaina bana bukatar auren, ban ma taba jin naga wani mutum ina sonshi ba sai cikin shekarar nan shine ya dawomini da rayuwata irin ta sauran mutane wadanda ke dandanar kalma da aman soyayya. Gaban Ahmad ya kama bugawa ganin irin kallon da take masa amman sai ta basar ta kauda idonta daya ciko da kwalla tace ka manta da wannan bani labarin tsohuwar budurwarka ko ita ce matarka ne? Yayi murmushi yana kallonta ta kauda kanta gefe. Yace ke da baki san amo da dandanon soyayya ba yaya kika gane ina cikin soyayya, ko kuma na tuno da tsohuwar budurwata ta da? Tayi murmushi kuma fa hakane kanada gaskiya. Amma ina zaton na gano hakan ne cikin littattafan soyayya na turawa da nake karantawa ko kuma ayawon kallon fina finansu. Koma dai meye sai ka bani labarin nan yau. Yayi dariya lallai da gaske kin shiga cikin soyayya amman babu abinda zan gaya miki bayan nace miki ummi ce tsohuwar budurwata ta bugomin waya bayan ni kuma na ma,u ne ita daya. Gabanta ya fadi yanayinta ya sauya zuwa damuwa da kyar ta iya daurewa tace wacece ma,un? Ya jingina da kujera yana murmushi tamkar ta masa albishir da gidan aljanna. Yace ma,u ita ce matata, mai sona mai darajani fiye da yanda yakamata ta mini, ban hadata da kowa cikin raina da al,amuran rayuwata ba. Cikin gaggawa da rashin sanin abinda ta fada tace Har ni ma? Shirun da yayi yana kallonta ne yasa ta gano ta fadi wani abun daya jima aranta tana nuku nuku dashi. Sai ta dauke kanta daga kallonsa da sauri ta kalli gefe gabanta na faduwa dakin yayi shiru sai karar A.C da ta bugawar zuciyoyinsu. Ahmad kam addu,a yake cikin ransa Allah ya sanya abinda ta fada bashi take nufin fada ba, amma sai ya jiyo sautin muryarta ya cigaba da fadin. Maza da dama sun soni masu kudi da masu mulki da sarauta, amman bantaba kallon kowa da mutunci ba tunda bansan meye so ba, sai kwatsam watarana naci karo da wani tsageran matashi a gidan mai wanda ya tsaya cikin raina har ya karya tarihin zuciyata, tun ina yaudarar kaina da zuciyata karya takeyi bazan taba son mutum irin haka ba har daga karshe na yarda na sallama ina sonka Ahmad. Ta waigo ta kalleshi yayi mutuwar zaune. Ta cigaba da magana idonta na zubda hawaye Nasan ka jima da gano ina sonka domin na gwada maka abubuwa da dama irin na masoya amman kana basarwa nasan badon komai bane sai don ma,unka! Sai dai ina fatan zanci albarkacin ma,un ka sammin kadan daga cikin son da kakeyi mata Like· Report·Jun 14 Nusaybarh Mustapha Ibraheem 123. Tana kaiwa nan ta mike tsam da sauri ta nufi kofar fita Ahmad yana zaune kamar an dasashi ya kasa motsawa daga inda yake yana jin kamar bashi bane ba. Ya bi nana da kallo wacce ta kama kofa zata bude har saida ta bude sannan ta kuma yin magana ba tare data waigo ba. Ahmad ka sanya aranka ba karamin abu ne zai sanya mace kamata mai cika da daraja da kyau da arziki ta fuskanci namiji kamarka ta sanar dashi tana sonshi ba. Tana fadin hakan ta fice. Ahmad ya doki tebur ya dafe kansa dake juya masa yana fadin Ya subahanallah! Lallai lokacin barina cikin wannan So naga kuna korafi dayawa, bari na wakilci@maitama nakarasa muku. DAME AKE ADO....4**8 Haka ranar ya koma gida sukuku ba walwala har sai da ma,u ta fahimci yana cikin wani hali, bata matsa masa da tambaya ba don ya sanar da ita tuntuni akwai matsala a ofis dinsu, don haka addu,a kawai takeyiwa mijin nata. Duk yadda taso faranta masa ta sanyashi cikin farin ciki ta kasayi dole ta barshi shi daya cikin daki don ta kula abinda yafi bukata kenan. Nana kam da kyar takai kanta gida domin kanta wani irin ciwo yake yi da juyawa. Tana yin parking ta nufi gidan da gaggawa, amma bata kai ga ainihin sashinta ba ta yanke jiki ta fadi kasa. A dai dai lokacin hajiya batula mahaifiyarta ta fito daga sashinta ta hangota. Hajiya batula ta fasa kara ta nufeta da gudu tana salati, ta kamata ta dagota sai taga idonta ya juye alamar ta suma. Ta fasa ihu tana kwallawa masu aikin gidan kira. Da gudu suka iso kowa a rude jin kiran da hajiya batulun ke musu, ganin halin da nana ke ciki ya kara daga musu hankali suma. Hajiya batulu cikin kuka take cewa kubani ruwa na yayyafa mata, daga daga cikin matan ta kwasa da gudu sakwanni kadan ta dawo dauke da ruwan robar swan mai sanyi.. Hajiya batulu ta karba saboda tsabar gigicewa ma kurzawa nana shi tayi ajikinta gaba daya. Nana tayi wata doguwar ajiyar zuciya ta bude idonta a hankali. Hajiya batula tayi doguwar hamdala sannan ta kalli yan aikin tana cewa ku taimaka mini ku kamata mu kwantar da ita akan kujera. Suka ciccibi nana aka kwantar da ita ta dauko wayoyinta ta fara neman layin wayar mijinta wanda yake abuja. Bugu daya ya dauka, cikin tashin hankali hajiya batulu tace masa Alhaji nana bata da lafiya, yanzu ta fadi har da suma. Alhaji nura kwangila ya gigice yace, suma kuma me ya sameta? Ta kalli nana dake kwance akan kujera tana kallonta tace bansani ba, dama cikin kwanakin nan na kula bata jin dadi, amma danayi mata magana sai tace babu komai..........Kinga bar bayanin nan haka zanyiwa likita waya yanzu yazo ni kuma zan hayo jirgi na taho yanzu, ki kula da ita kafin nazo. Ya kashe wayar da damuwa a take a lokacin yayi waya a tanadar masa ticket mai zuwa kano. Like· Report·Jun 14 Nusaybarh Mustapha Ibraheem 127. Hajiya batula ta isa ga nana ta zauna ta dora kanta bisa cinyarta tana shafa kanta. Sannu nana, meke damunki? Nana ta rintse ido hawaye ya zubo mata , batason tunawa amma bazata taba mantawa ba domin soyayyar Ahmad ta zame mata masifa, bazata iya rayuwa ba Ahmad ba. Ganin tana hawaye ya kara tayar da hankalin mahaifiyarta ta tace shikenan ya isa daina kukan. Mintuna goma baya sai ga likita ya iso gidan masu hidima sukayi masa jagora har cikin gidan da yake kowa ya sanshi a gidan. Hajiya batula na ganinsa ta mike da sauri tana fadin yauwa karaso doctor ka dubamin ita. Likitan ya isa da sauri ya sauke jakarsa da yake rataye da ita ya fara fiddo kayan awo kala kala. Cikin yan mintuna kadan ya kammala auna nana yayi mata wasu yan tambayoyi ta bashi amsa, daga karshe yace da hajiya batula dole sai sunje can asibitinshi anyi mata wasu gwaje gwajen. Hankalin hajiya batula ya kara tashi sosai ta dubi likita tace likita gaya min meke damun diyata? Cikin kwantar da murya likitan yace kwantar da hankalinki hajiya ba wani abu bane ba, ina dai so nasami sakamakon da nake bukata ne. Babu musu ta fara shiryawa aka dunguma zuwa asibiti. DAME AKE ADO 4**9 daga karshe yace da hajiya batula dole sai sunje can asibitinshi anyi mata wasu gwaje gwajen. Hankalin hajiya batula ya kara tashi sosai ta dubi likita tace likita gaya min meke damun diyata? Cikin kwantar da murya likitan yace kwantar da hankalinki hajiya ba wani abu bane ba, ina dai so nasami sakamakon da nake bukata ne. Babu musu ta fara shiryawa aka dunguma zuwa asibiti, Acikin mota tayiwa Alhaji nura kwangila bayanin sun wuce asibiti, alokacin shi kuma yana cikin airport hankalinsa ya kara tashi kwarai da gaske amma ya dake. Dukkan gwaje gwajen daya kamata anyiwa nana, sai dai sakamakon ya dan girgiza likitan don haka yaja bakinsa yayi shiru don bai kamata ya sanar da mace wannan labarin ba. Ana kiran sallahr isha,i alh nura kwangila ya iso garin, kai tsaye asibitin dr musa ya wuce har dakin da nana take ciki lokacin anyi mata wata allurar barci idonta yana rufe, hajiya kuma tanayin sallah. Alh nura ya isa gadon da nana ke kwance ya tsaya yana kallonta sai kuma ya fara lalubar wayar Dr. musa daya tabbatar masa yana cikin asibitin sai ya fita ya nufi ofis dinsa. Yana shiga Dr. musa ya mike cikin girmamawa yana gaisheshi amma bai kula da wannan ba cewa kawai yakeyi Dr meke damun diyata me ya faru da ita? Dr. musa ya jinjina kai yace kwantar da hankalinka alh zauna na maka bayani. Alh nura kwangila kamar bazai zauna ba amman dai ya hakura ya zauna yana kallon likitan. Dr. musa ya zauna ya dakko masa envelop a rufe kamar guda uku ya fara dubawa yana kallon alhaji nura wanda ya kagu yaji abinda zaice. Dr. musa ya fara bayani. Da farko na fara yiwa nana gwajin jini ne na tadda jininta ya hau........... Nanar me zai sanya jininta hawa kuma? Alh nura kwangila ya tambaya a gigice. Dr. musa yace wannan shine abinda ke bani mamaki. Sannan yanayin bugun zuciyarta ya sauya yana dudu fiye da yanda ka,idarsa take wannan dalilin ya sanya nace mu taho asibiti don ayi mata sauran gwaje gwajen, ga mamaki na sai naga zuciyarta ta dan sami matsala don ta buga fiye da yanda ya kamata ta buga musamman lokacin da ta fadi, Allah ya taimaka anyi gaggawar kawota asibiti da wani mummunan abu ya faru da ita. Hankalin alh nura kwangila ya kuma tashi yace. Abin mamaki meye zai sanya zuciyar diyata bugawa har akusa rasa rayuwarta? Kwantar da hankalinka alh, wannan ba wata matsala bace insha Allahu komai zai zama dai dai zata dawo dai dai musamman idan anyi gaggawar gano abinda ke damunta an kuma magance mata shi da wuri. Alh nura kwangila ya gyada kai yana fadin, na gode Dr. bari naje wajen mahaifiyarta. Ya tsare hajiya batula da tambayoyi, abinda ta fada masa yana can kafin yazo shi ta kara fada masa yanzu ma, dole dai su bari diyar tasu ta sami lafiya. Washe gari tunda safe Ahmad ya sami labarin abinda ya faru, hankalinsa yayi matukar tashi, don haka da wuri ya wuce asibitin ya tadda mutane anyi dandazo kama daga kan yan fadanci zuwa dangin hajiya batula dana alhajin, amma ba,a barin kowa ya shiga sai dai ko su gaisa da mahaifan nata ka juya ka tafi. Shima Ahmad din sun gaisa sai dai bai samu ganin hajiya batula ba tana ciki da yake dakin irin na masu kudine har da wani katon falo. Nana tana barci kamar cikin mafarki ta dinga jin muryar Ahmad. Nana tana bacci kamar cikin mafarki ta dinga jin muryar Ahmad lokacin da yake sallama da alh nura kwangila. Da sauri ta bude idonta ta kalli mahaifiyar ta da ke zaune a kusa da ita tayi tagumi cikin sanyin murya tace mummy ba Ahmad ne yazo ba? Hajiya batula tace bansani ba ko kinason ganinsa ne? ta gyada kai alamar eh da sauri hajiya batula ta mike ta nufi falon. Alh nura ya kalleta da sauri ganin ta fito arude yace yaya dai lafiya hajiya? Cikin karewa mutanen wajen kallo tace nana ce tace taji kamar muryar Ahmad wai. Ba wai bane shine yanzun nan ya fita bari na kirashi idon tana son ganinsa ne. Ya dauko wayarshi ya fara neman layin Ahmad bugu daya ya daga har ya tayar da motarsa, amma yace masa ya dawo maza maza nana nason ganinsa. Gaban Ahmad ya fadi yaji kamar kada ya koma din, amma bazai iya kin zuwa ba, don haka dole ya fita daga motar ya nufi dakin gabansa na faduwa yana ta addu,a a cikin ransa. Kai tsaye Alh nura ya shige dashi cikin dakin da nana ke kwance , mutanen dake zaune agurin suka dinga mamakin irin matsayin da Ahmad yake dashi a gurin Alh nura kwangila din daya samu shiga gurin nana. Nana ta kurawa kofar dakin ido dai dai lokacin da Ahmad ya shigo sukayi ido hudu, tayi doguwar ajiyar zuciya murmushi ya bayyana akan fuskarta. Ahmad ya matsa kusa da gadon nata ya tsaya da damuwa akan fuskarshi yace sannu hajiya nana, yaya jikin? Tayi murmushi da sauki nagode da kazo dubani ka kula da komai kafin na koma. Azahiri kowa zai zaci tana magana ne ko taso ganinshi don kamfani da gaske sai dai kasan zuciyarta tayi hakane don ta ganshi kawai. Alhaji nura kwangila da hajiya batula suka kalli juna da mamakin abinda tace. DAME AKE ADO....4**10 Ahmad yayi tsaye kamar bazai tafi ba sai da ya dan jima sannan ya musu sallama ya wuce idonsa ya ciko da kwalla saboda ganin irin halin da nana ta shiga, idonta yayi jawur hawaye ne kawai ke zuba daga cikinsa. Ko da ya isa ofis kasa komai yayi sai tunanin halin da nana ke ciki da ace zai iya taimakonta da yayi, amman bazai iya bari rayuwar nana ta lalace ba dole zai san abin yi. Kwanaki hudu tana cikin asibitin amma babu sauki sai abinda ke karuwa, musamman hawan jininta gashi anyi anyi ta fadi abinda ke damunta ta ki sai kuka. Shi kansa Ahmad tun zuwansa na farko ya kasa kara komawa, don bai son ganin nana cikin halin da ya san bazai iya taimakonta ba. Bayan kwana uku Abangaren nana dai hankalin iyayenta atashe yake kullum yau kam Alhaji nura kwangila ya tabbatarwa kansa da sai yasan abinda ke haddasawa diyarsa wannan halin da take ciki, don suna jin kukan da take kusan kwana tanayi indai ba,ayi mata allurar barci ba. Tana zaune atsakiyar gado tana shan ice-cream ya taso daga inda yake ya dawo kusa da ita ya zauna agefen hadadden gadon dake kama dana gidan wani hamshakin sarki don ya sha gyara. Cikin sanyin murya Alh nura ya kirawo sunanta ta dago kai ta kalleshi gabanta yana faduwa ta amsa. Ya sake kwantar da murya yace nana ki taimakeni ki sanar dani gaskiyar abinda ke damun ranki? Nana ki tuna bani da kowacce diya a duniya sai ke, ke kadai Allah ya bani dan uwana guda daya ne yana kwance cikin jinya ke kadai nake kallo adangina kuma yata, idan kika bari na rasaki bazan yafe miki ba, don babu makawa nima karshen rayuwata yazo...... Yayi dan shiru yana kare mata kallo sannan ya cigaba Nana ki taimaka ki sanar dani abinda ke damunki, ina da kudin da zan siyo miki dukkan abinda kike bukata awannan duniyar, idan kuma ya fi karfin siya zan tayaki da addu,a Allah ya baki shi ko kuma ya sanya sanyi da salama azuciyarki ki fadamin abinda ke damunki nana.. Nana ta sunkuyar da kanta kasa hawaye na zubowa daga idonta tace. Daddy idan na gaya muku abinda ke damun zuciyata zakuji haushina da abin watakila hakan ma ya sanya ku daina tausayamin. Injiwa yagamiki? Dukkan abin da zai sanya ki cuta irin wannan ya wuce mu d'aukeshi k'arami. Ki gaya min Nana ko kin manta nine Daddy d'inki da kike gayawa dukkan damuwarki?" Ta d'ago kai ta kalleshi kamar ba za ta fad'a ba, sai ta ce, "Daddy tun randa na yiwa Ahmad wulak'anci a Gidan mai na fara kamuwa da sonsa, nayi zoto wasa ne ko zan rabu da son a hankali, amma sai abin ya cigaba da hauhawa, cikin raina har ta kai na zamto bani da buri bayan ganinsa kullum, don haka kullum sai naje Gidan Man su, daga baya nayi hanyar da ya sami aiki kusa dani, wannan ya sanya na sami sanyi cikin raina, ban ta6a zaton idan na bayyanawa Ahmad buk'atata zai juya mini baya ba, sai dai na gano halin Ahmad bai sanya akan komai don na gwada masa dukkan abin da zai sanya ya gane ina k'aunarsa amma ya kauda kansa, daga k'arshe da naga sonsa yana neman hallakani ya sanya na sanar da shi amma sai ya gaya mini bai sona bai kuma ta6a sona ba....." Ta fashe da kuka maganar ta kasa ciga da fitowa. Hajiya batula da Alhaji nura kwangila suka bita da kallo da tausayawa basu taba zaton abinda ke damun yarsu kenan ba. Wato hakan na nuna musu ta warke daga cutar dake damunta tun tana da kuruciyarta, wacce suka kashe makuden kudade gurin ganin sun samar mata lafiya. Alhaji nura kwangila ya riko hannunta ya dora kanta akan kafadarsa yace. kwantar da hankalinki diyata nasan illar da soyayya ke yiwa zuciyar dan adam dan ta taba illata rayuwata amma indai akan Ahmad ne kukan ki ya kare da damuwa zan samar miki shi da ikon Allah. Ya mike da sauri yanzu zanje gareshi insha Allahu damuwarki sun kare. Idon nana na zubar da hawaye tana kallon baban nata daya nufi kofa kai tsaye zai fita cikin sanyin murya tace. Daddy don Allah idan yaki yarda kada kace zaka koreshi daga aiki, ganinshi kadai abin jin dadi ne agurina kada ayi masa dole akan sai ya soni. Alhaji nura kwangila yayi shiru bai juyo ba amma tabbas maganar diyar tashi ta shigeshi tausayinta ya kara kamashi ashe akwai wani abu da diyarsa zata iya rasawa awannan duniyar yana raye? Lallai iko yana gurin ubangiji ya kada kansa ya fice. Hajiya batula ta matsa kusa da nana don rarrashinta. Ahmad yana zaune a ofis wayarsa ta fara kira ya dago da sauri ya na kallon screen din wayar lambar Alhaji nura kwangila ya gani gabansa ya fadi amma dai dole ya daga, yana shirin gaida Alh nura sai ya katseshi da cewa kana ofis ne Ahmad? Da hanzari Ahmad yace ina nan Alh. Alhaji nura kwangila, ok to ganinan zuwa. Gaba daya hankalin Ahmad ya gama tashi ji yake kamar ya gudu kada Alhajin ya sameshi amma babu halin yin hakan dole ya zauna ya jira zuwanshi. Lokacin da Alh nura kwangila ya turo kofa ya shigo Ahmad ji yayi kamar akan kirjinsa aka mako kofar saboda wani bugu da yaji kijinsa nayi. Da sauri Ahmad ya mike tsaye yana wa. DAME AKE ADO...4**11 Gaba daya hankalin Ahmad ya gama tashi ji yake kamar ya gudu kada Alhajin ya sameshi amma babu halin yin hakan dole ya zauna ya jira zuwanshi. Lokacin da Alh nura kwangila ya turo kofa ya shigo Ahmad ji yayi kamar akan kirjinsa aka mako kofar saboda wani bugu da yaji kijinsa nayi. Da sauri Ahmad ya mike tsaye yana wa Alhaji sannu da zuwa. Alhaji Nura ya dubeshi yana murmushin yak'e yace, Zauna Ahmad inason yin magana dakai ne, kuma magana ce mai mutuk'ar muhimmanci a garemu. Ahmad ya koma ya zauna cikin sanuyin jiki, gabansa na dukan d'ari- d'ari. Alhaji Nura ya janyo Kujera dake fuskantar wandda Ahmad ke kai azaune shima ya zauna ya tsare Ahmad da ido yana fad'in, Ba sai naji komai daga bakinka ba na san Nana ba ta yin k'arya, ko yaudara, abinda na ke fata daga gareka kawai shi ne ka amince Ahmad, bani da Kud'i ko ikon da zaniya siyan soyayya, domin da zan iya da tuntuni na siyuwa wani soyayyar Nana na aurar daita. Tunda Nana ta taso ta k'i jinin kula Saurayi har zuwa girmanta, hakan ya jagoranci tunaninmu da kuma fad'hn wasu Malamai cewar wai aljani bak'i ne ya aureta, yanzu kuma sai gashi allah ya kawo mana maganin abin rana d'aya, nana ta furta da bakinta cewa tana sonka Ahmad. Ahmad kayi duba da kyau ga wannan lamari, nana yarinya ce mai kyau da tsari kamar nana ace ta tunkari namiji tace masa tana sonshi ka san ba k'aramin abu bane, Kamar nana ace ta tunkari namiji tace tana sonshi ba karamin abu bane, ka taimakeni Ahmad ka auri nana don Allah. Ahmad kansa yana kasa tunda alh nura kwangila ya fara magana, da ace akwai mutumin da zai iya yiwa wani abu ko da ranshi bai so ba to bai wuce Alh nura ba, amma bazai iya yiwa ma,un shi kishiya ba dan yiwa ma,u kishiya kamar yiwa ummansa ne, mutanen da suka raineshi suka bashi mace yaya zai iya yi musu haka? Bashi da amsar da zai iya baiwa Alh nura kwangila dan haka ya dukar da kansa kawai. Alh nura kwangila ya zuba masa ido da mamaki sannan yace. Ahmad ko akwai wani abu da nana take wanda ranka bai bukata ko kuma tana da wata illah ne gaya mini don banyi zaton wani namiji zaiki diyata ba a wannan lokacin. Ahmad ya girgiza kai yana fadin, ko daya babu wani abinki dana gano a wajen nana amman..........Sai kuma yayi shiru ya sara ma mai zaice. Lallai Ahmad ka nunamin kai namijin duniya ne, hakan kuma ya sanya na kara yarda nana tayi zabi, don nayi imanin wani zai so nana ko don arzikinta ko kyanta ko dan nasabarta amma ko daya bai burgeka ba daga cikin wadannan abubuwan. Ahmad ya kada kai tunda nake ban taba sanya kwadayin abun kowa araina ba na wadata da abinda nake samu, amma kayi hakuri Alhaji ina cikin halin da ba zan iya aurar wata ba. Alhaji nura kwangila ya sake kallon Ahmad da tsananin mamakin karfin halinsa amma hakan kara birgeshi yake da kuma nuna masa shine mijin daya dace da diyarsa nana.Cikin kwantar da murya yanzu Alh nura kwangila ya cigaba da magana. Yanzu kam alfarma nake nema ka dubi halin da nana take ciki, bani da kowacce diya sai ita kadai zan iya rasata saboda sonka ka ceci rai Ahmad, ka ceci rayuwarta daga cikin bakin cikin dake damunta. Jikin Ahmad yayi sanyi lallai yakamata yayi wani abun akai, amma kuka bazai iyayin abun kai tsaye ba don haka yace da Alh nura Alhaji ka bani dan wani lokaci zan yi shawara tukunna. Ran Alhaji nura yayi dan sanyi , ko ba komai ya samu magana mai dadi amma cikin ransa mamaki da tu,ajjibi ne ke cikashi yau kuma haka Allah ya kaddara masa kamar shi ya buge da rokon wani akan wani abu da bai da iko akansa, bayan da shi kullum ake roko. Wannan kadan kenan daga ikon Allah. Alhaji nura kwangila ya girgiza kai ya mike yana fadin. Hakan ma yayi, amma bazan baka dogon lokaci ba gobe kamar wannan lokacin zan dawo dan jin shawarar daka yanke nagode. Alh nura ya juya ya fice, Ahmad ya bishi da kallo da fargaba da tsoron abinda zai biyo baya. Yau kam ransa asake ya isa gida, halin daya ga ma,un ya kara sanya ransa yin dadi, ita da yayansa suna cikin kyakkyawar shiga gwanin sha,awa. Ma,u ta mike ta taroshi da jin dadin yadda ta ganshi cikin farin ciki, ya mannata akirjinsa yana sumbatarta suna dariya, tayi masa duk abinda ta saba yi masa suka wuce daki. Yau suna cikin farin ciki gurin cin abinci take bashi labarin zuwan amina gidan dayake tayi aure shekaru hudu da suka wuce, Allah ya hadata da wani dan kasuwa akantin kwari da yayi mata karyar shi mai kudi ne yana da katon gida da mota. Akayi aure sai gashi ta kare a daki falle biyu a gidan, hakanan ta tarar zaman da zatayi ita da kishiya ne da kuma tarin yaya guda shida tayi kuka da bakin ciki amma ba ta da zabi bayan zaman auren. Malam sulaiman shi yayi komai na auren nata tare aka hada da musa wanda yanzu yake zaune a gidan Ahmad daya bashi aro saboda yawon haya ya ishesu, kuma tunda taje gidan mijin Allah ya jarrabeta da haihuwa ga babu don kuwa karya yayi irin mutanen nan ne yan kayi nayi masu tsayawa abakin hanya, DAME AKE ADO 4**12 mutanen nan ne yan kayi nayi masu tsayawa abakin hanya, wadanda suke tsayawa idan mutum zaiyi siyayya su nuna masa shago wataran ma sai aje a wuni ba,a samo komai ba, ga iyayenta suma babu ta ko,ina su abarsu suji da hidimar diyar dake gabansu wacce suke kiranta da yar raliya saboda ba,ayi mata radin suna ba balle ragon suna ko wani abu. wannan kadai ya zamewa lami ishara. Sai da yakai loma bakinsa sannan ya kalleta yace ina jinki ma,u, yaya tazo nan gidan kuma ita da tace har abada babu ita babu mu? Ma,u tayi murmushi tace bari kaidai yaya yunwa da bala,i ne suka isheta taje can gidansu babu shine tayo nan tana zubar da hawaye da fadin na taimaka mata bayan ni babu mai bata cikin dangi tasan tayi abubuwa marasa kyau ita da mahaifiyarta garemu amma hannunka bai rubewa ka yanke ka yar don kwanansu biyu babu abinci sauran yan hayar gidan dama basa shiri sam da ita kishiyar sun hade mata kai don haka dole tayo nan. Kai bakaji zance ba sai kace ta sami tabin hankali. Kai talauci baiyi ba sam aduniya haka na harhada mata kayan abinci harda na sawa dana yara ta dinga kuka tana godiya. Duniya kenan. Ahmad ya gyada kai, kadan ma suka gani, duk wanda bazai iya kallon ikon Allah yayi shiru ba sai ya tofa tashi ko yayi kazafi akai ai yana tare da jin haushi da bakin ciki indai awannan duniyar ne. Suna ta cin abinci yana tunanin ta inda ya kamata ya bullo mata da abinda ke ransa can ya daure yace wai ya ya naji shiru ne anyi watanni da yaye malam fa? Ta dafe kirji Don Allah yaya kada kaja mini ina zaman zamana Allah ne yace na huta ka barni kawai. Yayi yake hakane idan kin gaji basai na kawo miki kanwa tayi ba. Ta kalleshi da sauri da mamakin abinda yace amma ta kasa furta komai sai kada kai da yake kawai. Ganin haka ya sanya yace ma,u yanzu ace ga wata mace tana shirin rasa rayuwarta saboda ni da kaunata har ta dinga shiga cikin mawuyacin hali na jinya zaki iya yarda na aureta? Gabanta ya kuma faduwa duk da tasan wasa yakeyi tace watakila na iya watakila kuma bazan iya ba. Dadi ya cikashi jin ta dan sakko har tana murmushi yace. Wani abu ne ke faruwa mai ban mamaki ma,u wai kamar ni Alhaji nura kwangila ke roko har da durkusawa kamar zai yi kuka, ko da yake yana da gaskiya. Akan me yake rokonka kuma? ta fadi da fargabar jin abinda zai fada. Ya kalleta ganin har lokacin babu wani tashin hankali ko bacin rai akan fuskarta ya sanya ya cigaba da magana. Bazan boye miki komai ba ma,u nana ta nuna tana sona naki bata fuska har ta gaji da nuni ta sanar dani da bakinta. Ma,u tayi mutuwar zaune akan kujera sai taji kamar ya faskara mata gatari ne akan tsakiyar kanta ta kasa motsawa. Ganin bata ce komai bane yasa Ahmad ya cigaba da magana. Ban boye mata ba na fada mata gaskiya ban sonta, hasalima bazan iya hada matata da kowacce mace ba, bazan iya mata kishiya ba, ranar da bacin rai tabar ofis dina ashe wau faduwa tayi a gida bayan anyi bincike aka gano tana dauke da ciwon zuciya daya kamata cikin dan lokaci. Bayan mahaifanta sun gano dalilin faruwar hakan suka tsirani da magiya kamar zai mini kuka akan na auri diyarsa na rasa mai zance masa tunda na fada masa gaskiya bana son diyarshi amma ya tsaya yimin magiya daga karshe nace ya bari nayi shawara da iyalina tukunna. Har ya kammala bayaninsa ma,u tana jinsa kamar cikin gajimare yake mata ihu cikin kunnuwanta. Ta daina fahimtar komai, bugun zuciyarta ya sauya abinda ta jima tana zargi ya tabbata kenan ta kuma tabbatar karya Ahmad ya shirya mata yanzu don ya sami auren nana don haka sai tayi murmushi cikin ranta tace zaka iya rubuta littattafan hikaya lallai amma a fili cewa tayi. Amman bai kamata ka bar nana ta rasa rayuwarta ba bayan dumbin alkhairan data aikata maka. Tana gama fadin hakan ta mike ya bita da kallo baki bude ya gaza gano inda zancen nata ya dosa shin da gaske takeyi ko kuwa gatse ta masa yakamata yaji cikakken bayani daga gareta. Taku uku ma,u tayi ana hudun juwa ta debeta ta fadi kasa tim! Ahmad ya tashi da gudu a gigice ya nufeta yana kurma salati, ya tallafota yana jijjigata gami da kiran sunanta amma ma,u ta suma. Ya mike da sauri ya samo ruwa ya tallafota ya zuba mata afuskarta ta bude idonta da sauri tana ganinta a rike ajikinshi ta fashe da kuma ta fara kokarin kwacewa daga jikinshi amma ta kasa domin jikinta ya mutu lubus! Cikin kuka take fadin me ya sanya baka barni na mutu ba Ahmad? Mamaki ya kamashi har ya kasa boyewa ya waro ido yau shi ma,u ke kira da Ahmad kai tsaye abinda bata taba fadi ba tsawon rayuwarta. A fili yace Ahmad fa kikace ma,u? Ta yunkura ta mike da kyar tana kuka tace. Na fada me kuma ya rage tsakanina da kai tunda ka zama mayaudari azzalumi, ni zaka yaudara? ni zaka cuta? Bayan ka tauyemin rayuwa kaje kuma yanzu zaka auro yar masu kudi da ilimi banson kara ganin fuskar macuci irinka. Juwa ta kara dibanta tayi tagal tagal zata fadi ya mika hannunsa zai tareta yana fadin ki yi hakuri ki zauna ma,u ki bari nutsuwarki ta dawo tukunna. DAME AKE ADO 4**14 Mahaifinmu ya fara gano amfanin ilimi. Mahaifinmu ya rasu lokacin Yayana Abdullahi yana da mata biyu ya zama cikakken d'an kasuwa, Yayana Alahaji Abdullahi ya sami nasibi akan harkar kasuwancinsa da ya gada gurin Mahaifinmu da yake ya d'an sami ilimi k'alilan na zamani, kuma yana da nasibi akan Kasuwancin. Yayana shi ne ya d'auki dukkan nauyin rayuwata, naji dad'i fiye da lokacin da Mahaifiou yana, sai na kasance matsayin d'ansa kuma k'aninsa. Uwargidanshi ta kasa zama saboda rashin haihuwawarsi da kuma fitinar matarshi ta biyu HAJIYA LAMI wacce ta kasance Mace mai fad'an tsiya da iko, Hatta ni kaina ina samun matsala da ita, fitar Uwargidan ya sanya Hajiya Lami ta k'ara mik'e kafa tana yin duk abinda ta ga dama tsawon shekaru. Da yake Alhaji Abdullahi bai da fad'a balle fishi, shi ya sanya ta rami abinda take so. Sannan Mahaifiyarmu ma mace ce mai kau da kai, a haka har shekaru suka ja. lokacin da na kammala karatun sakandire yayana abdulahi ya fara neman auren ASMA'U, wacce ta kasance 'yar d'au uwan mahaifinmu, wato da kakanta da namu bokan wasa ne. Dangi sun yi murna da hakan, don kwata-kwata baza a iya cewa ga auren da aka yi na ZUMUNCI a cikin wannan Iyali namu. Sai dai Hajiya Lami ta tayar da hankalinta ta kuma yi dukkan abinda zata iya ganin hana auren, amma sai da Allah Ya k'addara akayi auren. Bayan anyi auren anan ma tsugune bata k'are ba duk da ba gidansu d'aya c, a wannan lokacin Yayana ya biya minh kud'i na fita k'asarwaje karatu, * amman ina jin labarin gida. Hajiya Lami ta d'an sassauta bala'inta ganin shekaru sun ja har kusan biyar Asama'u bata sami haihuwa c, sai take ganin kowa zai zauna haka me. Shekarar da ma dawo daga karatu ma had'a Degree da Master's a shekarar komai ya faru, kasancewar Yayana Abdullahi ya gina k'aton Kamfani a Kano wanda shi ne ya zama na sarrafa Mai da Kayan Abinci. Kuma Allah Ya sanya Nasiai akai. Hakan ya sanya ya d'auko Asma'u ya ajiyeta anan ita kuma Hajiya Lami tana can garin mu na Yan Liman cikin Jigawa. Allah Ya sanya nasibi da albarka akan wannan dukiya ta Yayana a garin Kano, sa6an kuma Allah Ya k'ara saukar masa da rahamar samun cikinka Ahmad. Babu wanda ya san Mahaifiyarka Asma'u tana daciki har yayi wata uku a jikinta saida ciwo ya dameta na kaita Asbiti daga nan aka tabbatar da ciki ne da ita na tsawon wata uku! Yayana yayi farin ciki da jin wannan labari, har ya kasa 6oye murnarshi ya sanar da Dangi na can yan Liman. Cikin k'ank'anin lokaci labari ya fasu har ya isa kunnen hajiya lami. Like· Report·Jun 21 Nusaybarh Mustapha Ibraheem Tayi mutuk'ar bak'in ciki da jin wannan labarin, ta kuma k'uduri aniyar ganin bayan cikin nan. Kwatsam! Watarana ina 'Dakina kasancewar ina Kano Gidan Asma'u, lokacin Yaya yana can Yan Liman daga ni sai ita a Gida. Cikin dare daga 'Dakina na dinga jiyo ihu da hargowarta, abin ya bani mamaki don na san ita ba ma'abociyar rigima ba ce ba, don haka na fita da gudu, sai na taddata cikin Falonta tana ihu tana wurgi da duk wani abu dake cikin 'Daki. Na nufeta da sauri da mamaki ina tambayar abin da ya faru, amma sai na kula sam bata cikin hayyacinta na fara k'ok'arin rik'eta amma abin ya faskara, don watsi tayi dani gefe, na kuma mik'ewa da sauri na rake k'ok'arin rik'eta, a wannan karon ma ta k'ara watsar dani. Da abin ya faskara sai ma fice gurin masu Gadin Gidan suma suka kawo mini d'auki muka turata cikin d'akin Baccinta muka kulleta aciki. Nayi ta buga Wayar Gidan Yaya Abdukahi Land line amman ba a d'auka ba. Haka muka kwana cikin damuwa da tashin hankali, sai da gari ya waye sannan hajiya Lami ta d'aga kiran Like· Report·Jun 21 Nusaybarh Mustapha Ibraheem Ta sanar dani yayan baya nan, da yake wancan lokacin babu wayar hannu, haka na hau mota na nufi garin 'yan liman na sanarwa da Iyayenmu da Yayana. Muka d'ungumo gaba d'aya cikin tashin hankali da tsananin damuwa muka dawo Kano. kai tsaye aka wuce da ita Gidan masu TABIN HANKALI, DAME AKE ADO 4**15 da aka samu na game da warkewarta kullum sai dai a kulleta a cikin 'Daki sai da kyar ake samu ta d'an daina buge'bugen da take sai Rawa da Wak'a. Ga kuma Ciki a jikinta. Daga k'arshe dai Likitocin Asibitin suka bamu shawara akan gsky mu gwad na Aljanu don abin nata yayi kama da sanmu, amman sun ce zasu yi mata Allurar bacci yanda zamu ji dad'in tafiya da ita Gida. Hakan ko akayi, bayan anyi mata Allurar baccin muka sanyata a bayan Mota muka d'auki hanyar 'Yan Liman, muna tad nine ke vk'a Motar Yayana yana baya kusa da Asma'u ya d'ora kan Asma'u akn Cinyarsa. Muna tafe muna hira har bacci ya d'auke Yayana ya jingina da kuera ya fara bacci sosai. Kwatsam! muna tsaka da tafiya sai naji an shak'o wuyana an rik'e k'am. na fara k'ok'arin k'watar kaina na saki kan mota ina salati da kiran yaya don na gano Asma'u ce ta shak'o min wuya. yaya ya tshi a gigice yaga abinda ke faruwa ya fara k'ok'arin 6an6areta daga wuyana amma abin ya faskara, motar ta k'ara gudu tana yawo akan titi, muna ta ihu da salati har hatsarin ya afku. bamu farka ba sai a gadon Asbiti, ni kam bayan buguwa babu abinda ya sameni, shi kam yayana ya sami karaya da buuwa a baya, sai dai bayan ya farka Matarshi da cikin jikinta ya fara tambaya, sai dai mummunan labari ya riskemu cewar mu kad'ai aka gani zube a gefen titi motarmu ta kama da wuta. Wannan ya sanya jikin yaya k'ara rikicewa don ance matarshi ta mutu da kuma cikinsa wanda ya sanya rai da shi. Tun daga wannan lokacin har yau ba a kuma samun lafiyar yaya ba, shi da kanshi ya ce a maidashi Saudiyya don yafi jin dad'in Likitocin can da kuma zama acan. Hakan ya sanya aka sai masa gida mahaifiyarmu ma ta koma can gurishi da zama. Bayan Allah ya toni asirin Hajiya Lami ta hanyar zuwan wani d'an uwanta Gidan suna hira naji ashe ita ce ta shiryawa Asma'u wannan ciwo da Bokanta. Nayi kuka saboda jin irin mugun tuggun da Hajiya Lami ta shiryawa Asma'u, na sanar da Yaya abin da ya faru aka had'a meeting na gaggawa na Iyalinmu da Hajiya Lami na fara fad'in dukkan abinda naji tana fad'a, nan da nan hankalinta ya tashi ta fashe da kuka tana fad'in Tsautsauyi ne ya kaita ga aikata hakan. Yayana yana kuka ya ce za saki Hajiya Lami saki uku!! Ta sanya hannu aka tana ihu da rak'on ayi hak'uri ba zata k'ara ba, wannan ma wai tsautsayi ne da sharrin Shaid'an! babu wanda ya kulata don ta illata rayuwar yayana, ba zai k'ara samun macen da zata aureshi ba tunda ya zama mara lafiya. wannan shi ne dalilin rabuwar yayana da Hajiya Lami wacce yanzu take cikin mugun hali na ciwon hauka ga rashin gata.... Alhaji Nura Kwangila ya goge hawayen dake zubo masa yana dariya lokaci guda. Naji dad'i, na godewa Allah daya k'ddara Asma'u bata rasu ba saida ta haihu. Ina zaton ganinka Ahmad zai iya sanya Yayana ya sami sauk'i daga ciwo da azabar da yake ciki tsaawon shekaru, Don ya kasa mantawa da Matarshi Asma'u, Mace tagari, mai KARAMCI. Saboda kyautayi da gatan da ta nuna mini ya sanya da na haifi d'iyata na mai da sunanta akanta, watoNANA ASMA'U! Wani irin dad'i da farin ciki ya mamaye Ahmad, har ma ya rasa abin da zai farta, sai yak'e kawai yake, k'aunar Nana ta fara shga ransa! Ganin abin ya ke kamar a cikin Mafarkim da ya saba idan ya kwanta bacci. Wai yau shi ne ya san asalinsa da dalilin haukan Mahaifiyasa? Ashe Mahaifiyarsa bata aikata wani abu na sa6on Ubangiji ba? Malam Sulaiman yayi doguwar Kabbara da godiya ga Allah cikin tsananin farin ciki da murna. Umm kam bakinta yak'i rufuwa ashe zata ga wannan ranar a rayuwarta? Kowa jinsa yake wani iri daban, kallo d'aya za ka yiwa kowa kaga mamaki da farin ciki k'arara akan fuskarsa.. Atake anan aka yiwa Hajiya Amina waya ta iso Gidan. Itama tayi mamaki da farin cikin jin Ahmad d'an gidan manya ne! Aka dinga murnaHatta Malam Jibril sai da ya shigo da yaji hayaniya tayi yawa, don duk Mazan Gidan sai da aka kirawosu a Waya suka zo. Mamaki da tu'ajabi ya kamshi saboda ganin Alhaji Nura Kwagila a cikin Gidan a zaune a tsakiyarsu Malam Sulaiman suna tattaunawa, don duk wanda ya kwana ya hantse a garin nan ya san Alhaji nura Kwangila! Yau kuma musu dukiya babu iyaka ne suka zo Gidansu?" Ya ayyna hakan a cikin ransa Sai kuma yaji wai k'anin Baban Ahmad ne, iko sai Allah. Da kyar Alhaji Nura ya iya barin Gidan, amma da rok'om gobe za a bashi dama ya tafi da Ahmad can garinsu na 'Yan Leman sannan zai yi masa Visa shi da Iyalinsa su tafi Saudiyya gurin Mahaifinsa da Kakanrsa. Wannan dare mai muhimmanci ne ga Ahmad da duk wani mai k'aunarsa. Bayan sun koma Gida ya k'ank'ame Ma'u yana kukan dad'i da farin ciki. Ma'u ashe ina da rabon ganin Dangina da Mahaifata? DAME AKE ADO 4**16 Ma'u yana kukan dad'i da farin ciki. Ma'u ashe ina da rabon ganin Dangina da Mahaifana har da Kakata? Ashe ina da rabon yin farin ciki da alfarin yanda kowanne d'a keyi da iyayensa da danginsa? Ma'u me yafi wannan dad'i a gareni? Me zan yi na godiya ga Allah? Tabbas ni d'an gatan Ubangiji ne, bai ta6a tozarta rayuwata ba bai ta6a wulak'antani ba. me zan cewa Allah? Yana magana yana kuka, amman daga gani kukan farin ciki nd. Itama Ma'u kukan take yi na taya Mijinta murna da kuma rarrashinsa. Tace masa, Sallah zamu kwana muna yi da yin godiya ga Allah da Ya k'addara mana ganin wannan lokaci. Wannan shi ne kad'ai hanyar da zamu nunawa Allha farin cikinmu. Ya kad'a kai yana fad'in "Haka ne, tashi mu fara. idan su Lami kuwa, wuk'i-wuk'i Lami tayi jin aslin Ahmad tana zare ido. Lallai taga d'umbin darasi a rayuwarta. Malam Jibril yace mata, Shi ya sanya kullum nake gaya miki babu kyau wulak'anta d'an Adam. Yau dai ga iyayen Ahmad da kike yiwa gori kullum shi SHGE ne? Danginsa dangi ne masu asali da arziki. Ke yanzu ina dangin jikarki d'iyar Raliya suke? Kinga hakan ya tabbatar miki kece mai SHEGE ba shi ba. Sai kawai Lami ta fashe da kuka tana fad'in, Lallai nayi kuskure da ba zai gyaru ba, me ya sanya na biyewa zuciyata har na aikata wannan abun? Kaicona!!!" Malam Jibril yace, Lami ai baki daima kuka ba tunda har yanzu baki san halin da d'iyarki Raliya take ciki ba. 'Diyar Raliya ta iso ta zauna akan cinyar Lami tana fad'in Ke Lami me akayi miki kike kuka?" Lami ta kalli Yarinyar da tausayin halin da ta janyowa rayuwarta, da yanzu itace zata kasance cikin wannan Daular. AGidan Alhaji Nura kam d'an k'arimin falm aka yi, domin yanda ya shiga da farin ciki yana k'wallawa Matarshi da d'iyarshi kira ya basu mamaki, don ba halinsa bane ba. Suka fito da tsananin mamaki suna tambayar abinda da ya faru. Hajiya Batula tace, Duk yanda akayi an taida lokacin auren nan da Ahmad. Dad'i yacika Nana Alhaji Nura Kwangila ya kad'a kai, "Wannan abum yafi auren Nana da Ahmad, fara cikine akan farin ciki, ku zauna na gaya muku abin da ya faru. Ba musu suka zauna. Alhaji Nura Kwangila ya kallesu yana murshi yace, Ashe Ahmad d'ana ne, d'an d'an uwana ne! Shi ya sanya ni da d'iyata Allah Ya jarrabemu da tsananin sonsa da k'aunarsa!!" Hajiya Butla ta cika da mamaki, domin ta san duk abinda ya faru ga Yayan Mijinta, duk da lokacim ko taunanin aurenta ma ba'a yi ba, amma ta yaya hakan zata kasance? Nan Alhaji Nura Kwangila ya kwashe labarin duk abinda ya faru ya sanar dasu Nana ta dake tsalle ta rungume Mahaifyarta wucce ke yin dariya tana fad'i, Sakarya kina manta ba ki da laya ne? Sanan ta kalli Mijinta da farin ciki. Bam ta6a jin irin wannan labarin ba ko cikin Littattafan Hikaya ko kuma cikin fina-finai da ake yi ba. Wato a sam da ake tunanin Asm'u ta mutu, ashe ita tana can cikin mawuyacin hali, sai da Allah Ya cika lamarin sa na haihuwar Ahmad sannan ta cika? Lallai wad'annan mutane da suka rik'eshi sun cancanci yabo. Ya ce, Lallai kam. Shi ya sanya ya kasa had'a d'iyarsu da kowacce Mace a duniya, domin sun bashi aure ne sanda kowa na duniya suka k'i bashi d'iyoyinsu. Tsarki da iko sun tabbata ga Allah Mahalinccin kowa da komai, mai yin yanda yaso, kuma a lokacin da ya so! Nana tafi kowa farin ciki, wato bayan Ahmad zai zama mijinta kuma zai kasance d'an uwanta na jini, koma ya kasance. Suma dai a haka kowa ya kwana da abin da yake sakawa a cikin ransa, amman duk Umman Ahmad tafi kowa farin ciki, don d'anta ya fita daga sunan SHEGE daga masu yi masa kallon hakan. Washe gari da sasafe Alhaji Nura Kwangila da Iyalinsa suka nufi Gidan Malam Sulaiman. Lokacin Ahmad bai k'aso ba shi da Iyalinsa sai da aka kirasu a waya sannan suka taho. Alhaji Nura ya tahu da manyan motoci don tafiyar harda su Umma da Hajiya, Su Ahmad suka iso aka fara gaggaisawa. Ma'u da Nana aka had'a ido kowacce gabanta ya fad'i da ganin 'yaruwarta. Shi kam Ahmad dakewa yayi yakasa kallon inda Nana take duk da yana jinta a jikinsa amatsayin 'yar uwarsa a yanzu, amma yana jin kunyar Ma'u don ba zata zaci haka ba. Nana ce da kanta taisa inda suke ta kalleshi tana murmushi da fad'in, "Yayana wannan ce Antina Ma'u? Ya kalli Ma'u yana murmushi wacce tad'an saki ranta yace, "Eh ita ce, kin ganta nan Maman Yarana. Nana tayi yak'e tana fad'in, Antina ina kwana? Ma'u ta d'an saki jiki suka gaisa, amma zuciyarta na bugawa. Ashe Nanan ma bata wuce tsarrarta ba, tayi zaton wata k'atuwar Macce iri KISN BOKON nan. Nana kam ji tayi ta d'an tsorata don ta kula Ahmad yana balain son matarshi Ma'u daji da ita, kuma babu wani abu da zata nuwa Ma'un, don babu wanda zai ta6a yin zato Ma'un tayi auren fari balle ace har ta haifi 'ya'ya. Da aka tashi shiga Mota sai tace ita Motar Ahmad zata shiga, yaran suka koma motar Alhji Nura wanda shi ya buk'aci hakan da kansa,. DAME AKE ADO 4**17 don kallonsu faranta masa rai yake yi, don yana ganin suna fara yawa ke nan cikin iyalinsu, don duk yanzu sai tsffi da dangi na nesa can. Ma'u bata so hakan ba, amman bau yanda za tayi iya, sai dai kishinta ya gaza 6oyuwa akan Nana, duk da Ahmad yana nunawa ita ce fa Matarsg ta gaskiya abar sonsa. Shi ne mai tuka Motar Ma'un nakusa da shi, Nana tana baya sai suka yi kamar basu san da ita ba suka dinga hirarsu sai jefi-jefi Ahmad ke d'an tsomata yace, "Ko Kanwata? Sai tayi murmushin yak'e kawai, har sai da tayi dana sanin shiga Motarsu a yanzu ta kuma gano waye Ahmad da kuma yanda ya d'auki Ma'u cikin ransa ba ta da had'in da kowacce Mace, don haka Addu'a kawai ta rink'ayi akan Allah Ya kaisu lafiya zuciyarta bata buga ba. Wannan abin da yayi shine ya sanyayawa Ma'u ranta, ta tabbatar Mijinta bai son Nana kwata-kwata, kuma dukkan abinda yake gaya mata gaskiya ne. Lokacin da dangi suka ji waye Ahmad sun yi ta murna da mamaki, musamman Gidan kakanninsu don har yanzu matan nasa sua man cikin gidan gadonsu, Alhaji Nura Kwangila shi ke musu komai tunda Allah bai basu haihuwa ba, aka yi ta yawo da Ahmad ana nunashi da sanya masa albarka, sai da suka kwana biyu a garin sannan suka koma Gida. Cikin wannan kwanakin kuma Nana ta gano lallai Ahmad da Ma'u sun yi nisa, amman bata karaya ba tana nan akan bakanta don tasan idan ta zamo Matarsa dole ya sota kuma yayi adalci tsakaninsu. Duk wani mutum dake Kamfanin saida yayi mamakin jin wai Ahmad d'an Gidan Alhaji Abdullahi yayan Alhaji Nura Kwangila ne, randa suka suka shiga ofis Alhaji Nura ya mai da masa muk'amin D.G. hannunsa, Nana kuma ta koma kan Kujerarsa, don yace shi ya fi dacewa da Kujerar, sannan ya fara nemar musu Visa da Passport, musamman Ahmad da Iyalinsa, ya kuma bayar da izinin gina wani k'aton Gidansa daya fara yace a ci gaba da aiki. Babban Gidane sosai. Sannan aka sauyawa Ahmad Mota mallakinsa ta kansa tare da bashi kwautar Kud'i masu yawa yafara gyara gidanshi da iyalinsa kamar yanda Alhaji Nura ya ce. A dukiya irin ta Mahaifnka ya kamata ace ka sauya. Shi Ahmad rasa me zai yi da Kud'in ma yayi, sai kawai ya dinga yiwa Iyayensa da 'yan uwansa da Ma'u abin alkhairi da su, har Ma'un ta dinga fad'a akan irin kashe Kud'in da yake mai yawa haka. Ahmad yace bai yi yawa ba don bai ci ko rabin Kud'in da Baffansa ya tura masa cikin Rkawun d'insa ba. Rayuwa ta sauya. Daman dare d'aya Allah kan yi Buture! Sun sami tafiya Saudiyya gaba d'ayansu Nana da Ma'u da Ahmad da Yaran da Alhaji Nura. Idan akwai wani abu da ke burge Ma'u ga Nana bai wuce yanda take son 'yayanta daji dasu ba, tunda suk had'u da Yaran ta share iyayen, bayan gaisuwa bata k'ar bi takansu ba, don ta kula suna gab da haddasa mata dawowar ciwonta, suka dinga hirarsu da yara. Alhaji Nura kwangila na kallosu da dariya, ba ya ganin laifin Ahmad, ganin son da yake nunuwa Ma'u, don Iyayenta da ita kanta Yarinyar sunyi masa halaccin da bai kamata yajuya musu baya lokaci guda ba. Sannan akwai SOYAYYA DA SHAK'UWA mai k'arfi a tsakaninsu kuma. Sunisa Gidan Alhaji Abdullahi wanda yake babban gaske tun daga waje, sun isa Gidan suka tadda Hajiya Ruma a Falonta tana kallo, Tsohuwa mai Ran karfe! Jin dad'i da kwanciyar hankali sun bayyana a jikinta, duk da fatarta da jikinta ya nuna tsufanta. Tayi matuk'ar mamaki da ganinsu, zuwan babu zato. Bayan an gaisa ta janyo yaran gurinta cike da sha'awa. Alhaji nura Kwangila yace, "Hajiya da da hali hutune ya kamacemu, amman abum da ke tafe damu ba zai barmu mu huta ba idan bamu fad'a ba. Ina Yaya Abdullah yake? Tace, Tun safe masu hidama suka tafi Harami da shi...." Tana cikin mamaganar sai ga shi nan an shigo da shi cikin wani Keken Guragu irin na masu hali mai amfani da wutar Lantarki, da kansa kuma yake tafiya. Farin ciki ya cika fuskarsa da ganin Alhaji Nura Kwangila da nana, shi kuwa Ahmad zabura yayi ya mik'e da sauri yana kallon Mahaifinsa. Tabbasa babu makawa wannan Mahaifinsa ne! sai yanzu ya gano da waye yayi kama, don yana kalloo hoton Maiaifiyarsa ya kasa gano kamarsu, ashe da shi yayi kama. Shi kansa Alhaji Abdullahi yaran ya fara yiwa magana suje gurinshi, Suka tafi da gudunsu suna dariya da mamakin kekensa. Sai da bka nutsu sannan aka fara gaisawa, sannan Alhaji Nura ya kalli Yayansa ya ce, Yaya dawa wannan Matashin yayi kama?" Alhaji Abdullahi ya kalli Ahmad sai sauri wanda bai maida hankalinsa akansa ba tunda ya shigo. Ya k'ura masa ido, rai idonshi ya ciko da k'wallah yace, Da ace NANA ASM'U ta haihu da zan ce d'anta ne wannan, domin babu abinda ya raba kamanninsa da nawa sanda ina cikin k'uruciyata! Duk inda wannan yaron ya fito jininmu ne, jinin Buba Wali wanda muka had'a Kaka na had'u da shi, don iyalan Gidansa ne ke kama dani. Hajiya tace Wannan haka yake. Ahmad yayi ajiyar zuciya da jin dad'i. Lallai ya k'ara sakankan cewa Mahaifinsa. Alahaji Nura ya mik'e yana musmushi ya ciro Hoton Asma'u wanda take mace ya nufi Alhaji Abdullahi da shi ya nuna masa ya ce, Yaya ka shaida wannan wace ce? Alhaji Abdullahi ya kar6i Hoton DAME AKE ADO 4**18 Alhaji Nura ya mik'e yana musmushi ya ciro Hoton Asma'u wanda take mace ya nufi Alhaji Abdullahi da shi ya nuna masa ya ce, Yaya ka shaida wannan wace ce? Alhaji Abdullahi ya kar6i Hoton ya k'ura masa ido, sai ya hau Salati yana fad'in, Subhanallahi! Wannan ai Asmu'u ce Nana Ma'una ce! Hajiya Ruma ta mik'e da gaggawa ta amshi hoton, sai ta koma ta zauna tana salati tare da fa'in, Nura ina ka samo Hoton Gawar Asm'u, Yarinyar da aka ce mana ta rasu cikin Mota ta k'one k'urmus! ko Tokarta ba asamu ba?" Alhaji Nura yayi murmushi yana kallonsu ganin duk sun gigice sannan ya fara basu labarin abinda ya faru da Asma'u da d'an da ta haifa har zuwa yau. Yana kaiwa k'arshe Alhaji Abdullahi ya kalli Ahmad ya ce, Wlh wannan shi ne d'ana! kai jinina ne!! Zo nan na rungumeka naji dad'i don Allah!!!" Ahmad ya mik'e da sauri yaisa ga Mahaifinsa ya d'ora kansa bisa cinyarsa yafashe da kuka yana goge kan kamar wani k'aramin yaro. Alhaji Abdullahi ya shafa kansa yana hawaye shima. Ahmad ke fad'in, ashe inada Iyaye masu daraja haka na dinga shan gori da hantara sboda rashinsu? Ashe nid'an gatane gaba da baya? Amma na godewa Allah da Ya sanya Iyayena dana rayu a gurinsu basu tagayyara rayuwata ba! Na godewa Allah da ya had'ani daku sanda nake tsananin buk'atarku. Maganganunsa sai da suka dinga sanya kowa kuka. Alhaji Abdullahi yace, Ka daina kuka Ahmad, wallahi ban ta6a jin dad'i da jin jinin jikina yana tafiya dai-dai kamar na yau ba. 'Dana ina jin kamar zan iya mik'ewa tsaye yanzu, kamani na gani zan tashi, domin naji kamar na warke babu rauran wani ciwo a Jikina! Ahmad ya mik'e da sauri ya kama Mahaifin sa, sai ya mik'e tsaye da k'yar! Amm ya kasa tsayuwa sai ya kwanta jikin d'an nasa yana fad'in, ashe zuciyata ce ta mik'e ba gangar jikina ba, Nayi zaton na tashi daga yau. Alhaji Nura ya isa kusa da shi ya kamoshi zai zaunar da shi, sai Ahmad yace, "Barshi Kawu zan iya. Wannan kama da ya gayawa Alhaji Nura Kwangila ya sanya shi jin wani irin dad'i da nishad'i. Yace, "Lallai yaya yanda zuciyata ta warke insha Allahu k'afafuwanka ma zasu warke da yarda Allah. Hajiya Ruma da Ma'u sun kasa koda mutsi sai hawaye. Ita kuwa Nana kallon Ahmad kawai take yi da jin dad'i. Dukkan sakwan sonshi na k'ara shiga ranta. An jima ana hira Sallah ce kwai ke tashinsu, sai da dare yayi sannan kowa ya nemi Makwancinsa. Alh Abdullahi yana jin kamar ya lashe Ahmad da Iyalans. Hajiya Ruma kuwa ta rik'e Ma'u katamau a jikinta suna jin kamar su cinyeta saboda kasancewarta Mata mai son d'ansu, don Ahmad ya basu labarin irin son da Umman Ma'u da Iyalin Gidanta ke masa. Sai dare kowa ya nemi makwancinsa. Cikin gidan nan kowa ya koma sashinsa da yake babban Gida, Ahmad ba zai iya rabuwa da Ma'unsa ba, don haka sashi d'aya suka d'auka, amman yaran runa gurin Hajiya Ruma, amman yini suke yi gurin Alhaji Abdullahi. Su kansu Likitoci sun yarda Alhaji Abdullahi ya sami lfya, daman sun san ba ainahin Ciwonshi ya hanashi tafiya ba sai bak'in ciki da CIWON ZUCIYA ne wacce ta warke yanzu garas! Babu sauran rauni a tattare da ita. Kafin sati guda sai ga shi ya fara k'ok'arin mik'ewa tsaye. Ahmad ya maida rayuwarshi gaba d'aya ga Mahaifinsa yana taimakmsa, shi ke yi masa komai, wanda hakan kullum ke k'ara faranta masa ranshi yana sanyashi nishad'i da sa samun suk'i, Ga Ma'u kuwa, tun bata sakin jiki da Nana har ta hak'ura ta sakar mata. saboda yanda take k'aunar 'ya'yanta da janta a jikinta, da taga kuma kowa ya gane tana kishin mijinta ne, bayan ko babu komai k'anwar Ahmad ce wacce ta dalilinta Mijinta ya gano dansa. Kuma taga babu wani aibu na soyayyar da Ahmad ke yiwa Nana, ko ita keyi masa, hakan ya sanya ta ga babu amfanin cigaba da shariyar. Nanan ce ta dinga janta zuwa Harami suna Addu'a da Salloli. Cikin zuciyar Nana Addu'a take yi akan Allah ya sassauto zuciyar Ma'u ta bata aron Mijinta ko da sau d'aya ne cikin sheka. Ita kuma Ma'un godiya take yiwa Allah bisa rahamar da yayi musu. Wai yau ita ce a gaban 'Dakin Allah mai girma, ne yafi wannan dad'i? Satin su uku suka fara shirin komawa Nigeria, amma Alhaji Abdullahi da Hajiya Ruma suka dage suma sun gama zaman Saudiyya tunad mai jinyar ya sami sauki yanxu har yana tafiya da sanduna biyu irin na masu kud'in larabawa, don haka tare suka tattara suka dawo Nigeria. Dayake Alhaji Abdullahi yana da Gidanshii bai sauka a can ba, sai ya sauka a Gidan d'an uwanshi aka bada umarnin a gyara mashi nasa. Cikin kwanaki biyu aka sauya komai na Gidan, xa koma sabo dal! hatta Fenti suka koma shi da Mahaifiyarsu da masu Aikinsu wad'anda daman dasu suka tafi can K'asa mai Tsarki (Saudiyya). Lokacin da aka had'u da su Malam Sulaiman da Alhaji Abdullahi kuka kawai Alhaji Abdullahi ya fashe da shi, don ya rasa bakin da zai yi godiya gasu Malam Sulaiman, k'arshe yace dole zasu bar wannan Gidan nasu cikin sati guda su koma wani sabo cikin rukunin Gidajen da ya gina. DAME AKE ADO.. 4**20 Sai tace babu komai kawai, don ko me zai yi mata ba zai wanke kansa ba a wajenta. shi da kanshi ya gano rashin kyautawar da yake yiwa Nana. Bai ta6a zuwa Gidansu da sunan zuwa Zance ba duk kuwa da halaccin da Mahaifinta yayi masa ya kamata yayi musu d'an wani abu da zasu ji dad'i. Don haka xau daga ofis yace da Ma'u ya wuce Gidan Babansa ne, amman sai ya wuce can. Yatarar da Hajiya batula da Alhaji Nura suna ta hira, yawanci akan Bikim ne wanda ya rage saura sati uku. Sun yi farin ciki da ganinsa ya ya zauna suka gaisa suka d'an ta6a hira cikin 'yar kunya ya ce, "Kawu wai ina Budurwar K'auyen man tayi ne ban gamta ba?" Alhaji nura Kwangila ya kalli Hajiya Batula da farin ciki fal fuskarsa yace, Tana can shashinta ko tana kallo ko bacci Ahmad ya mik'e tsaye yace, bari naje na tsokanota. Ya nufi sashin nata kai tsaye, Dad'i ya cika su Alhji Nura, wannan shi ne karo na farko da Ahmad ya ta6a numa wani abu ma kulawa akam 'yarsu Nana. Alhaji Nura ya dubi Hajiya Batula ya ce, "Kin gani ko na gaya miki? Watarana za a wayi gari Ahmad yana son Nana Ai jini guda ba k'arya bane ba. Hajiya Batula tayi dariya da jin dad'i ta ce, Lallai na yarda da fad'inka Alhaji. Nana tana Bam'Dakinta tana Wanka Ahmad ya shigo yana k'walla mata kira. 'Ke budurwar K'auye kina ina ne? Sam bata jiyorhi ba har ya shigo uwar 'Dakinta. Dai-dai lokacin ta fito daga Ban'Daki suka yi ido hud'u da juna, gaba d'aya jikin Nana a waje yake, don d'an Tawul d'in da ta d'aura bai kai ko rabiin cinyarta ba, ga kanta da wuyanta a bud'e, duk wanda ya san siffar kyau da tsarin mutane ba zai tsaya mamakin halittar nana ba wanda Ahmad bai ta6a kula da ita ba sai yau. Ko don hankalinsa bai ta6a kawa kanta bane oho! dukkaninsu suka yi saranda kowanne na k'ame. Ita kunya ce, Shi kuma wani abu yaji ya daki zuciyarshi wanda babu makawa yasan sha'awa da sontane yake ratsashi. Lallai ya yarda Ubangiji gwanin hikimane daya halittawa Maza auren Mace sama da d'aya, don zuciyarsa zata iya son Mace fiya da d'aya, da yaso ya cuci kansa. Canin yanda ya k'ura mata ido ya sanya tayi gyaran murya, sai alokacin ya farga, kunya ta kamashi, ya juya da sauri yace, "Ina jiranki a Falo idan kin gama shiryawa. Wani irin dad'i ya shigeta. Lallai ta yarda Mahak'urci. Mawadaci ne watarana. Bata ta6a ganin irin wannan kallon daga idon Ahmad ba sai yau. Lallai ta yarda a yanzu Ahmd d'in ya fara somta kamar yadda itama take tsananin sonsa da k'aunarsa. Tayi tsalle ta fad'a kan Gado tana ihun da murna, tare da yiwa Allah godiya da Ya nuna mata wannan lokaci. Ta ma rasa wacce irin kwalliya zatayi, ta jima tana za6e har ta k'are akan wata doguwar riga mai kama jikinta ta atamfa mai had'i da Yadi da ake kawosu daga Dubai masu d'an duwatsu. Rigar na dacewa daita k'warai da gaske, kuma tayi masifar yimata kyau Ta fesa turarruka masu k'amshi ta nufo Falon data tabbatar Ahmad yana ciki yana jiranta tana rangwad'a. Kamshin Turaren da yaji mai sanyi da dad'in shi yasa shi yin saurin d'ago kai yana murmushi. Koda ya kalleta sai ya sake yin murmushin ya ce, "Ee, lallai Budurwar kauye, ashe kin iya kwalliya? ta turo baki gaba tana fad'in, "Gaskiya Yaya Ahmad ba naso ka daina ce mini budurwar Kauye. Cikin shagwa6a take maganar. Yayi dariya da jin dad'i ya ce, "Shi ke nan na daina, zo man ki zauna ki bani labarn k'uruciyarki naji. Ta fashe da dariya ta zauna suka kama hira. Bai farga ba sai da kiran Ma'u ya shigo Wayarsa, ya dubi Agogon bango dake kafe a falon ya ga k'arfe goma na dare har ta gota, ya mik'e da sauri yana fad'in, Ya Salam! Ma'u ta gaji da jirana har tayi kirana Bari na wuce. Nana ta had'e rai da takaici, a yau tana murna ta d'an fara samoshi amma Ma'u ta 6ata mata bajat! Bai kula da halin da Nana ta shiga ba sai ya nufi Kofar fita daga Falon. A lokacin su Alhaji Nura Kwangila sun bar Falon da ya samesu d'azu hakan yasa Ahmad ya sake tabbatarwa lallai hirar tasu da Nana tayi nisa. Koda ya isa Gida Ma'un bata gano komai ba, domi haka ya rink'a bata labarin Yaranta da ba babanshi da Kakarshi da irin Diramar da suke yi tana ta dariya. Tunda daga wannan ranar kullum dare sai yace zai je gurin Babansa ya wuce gurin Nana, amma yana fara biyawa ya gaisa da Baban nasa yaga yaransa sannan ya wuce gurin Nana. A hankali SABO DA SHAK'UWA ya fara shiga tsakaninsu, amman ko da wasa bai ta6a yarda Ma'u ta gano ba. Ita kanta Nana ta gano Ahmad yana balain kaffa-kaffa da duk wani abu da ya shafi Ma'unsa, shi ya sanya ma bata had'a kanta da ita kwata-kwata. Rana cta k'arya sai dai uwar d'iya taji kunya! inji masu iya magana, domin lokacin auren Nana da Ahmad yayi, Alhaji Nura ne yayi komai, sai dai yayi adalci, don duk wani abu da aka sanyawa Nana a cikin Kayan Lefe an sanyawa Ma'u shi, sai k'alilan ne suka ban-banta, don haka kamar sabo Lefe aka sanyawa Ma'u a matsayi kayan fad'ar Kishiya. DAME AKE ADO 4**20 Biki ne irin na masu kud'i da gata, abin dake bawa Ma'u bak'in ciki shi ne, ta rasa wanda zai tayata bak'in ciki, don Gidajen 'yan uwanta dake cikin Kwatas d'in nan kowa hidimar Bikin ce a gabanshi, haka Gidan su, haka Gidan Alhaji Nura Kwangila, haka Gidan su Hajiya Ruma, idan akwai mai tausaya mata da nuna mata damuwa bai wuce Hajiya ba sai kuma Ahmad da bai nuna damuwarshi ko zumud'in auren a gabanta sam har ta kanji kamar dole aka yi masa a ranta. Hankalin Ma'u bai tashi ba sai da aka zo d'aura aure taga irin d'umbin jama'ar da aka tara sannan da irin kud'in da yaye ke kashewa da saboda bikin. Sai da aka zo jeren Nana hankalinta ya gama tashi don bata ta6a ganin kaya irin na Nana ba ko cikhn Fim, don Hajiya Batula da kanta ta dinga nuna irin abinda za a yiwa d'iyarta a k'asar Dubai, duk da tana ganin matuk'ar kyau da tsarin gidan sai da ta ranna kanta da taga irin kayan da ake shigowa da su gidan da irin hidimar da ake yi kamar ba a son kud'in. Shi kanshi Ahmad irin shigar da yak'e yi sai take ganin kamar yanzu yafi k'arfinta, don wasu dakakkun Shaddoji ya yaduka Alhaji Nura Kwangila ya d'anko masa a Dubai, kuma a can Gidan yake shiryawa sai dai ya shigo mata. Ran da aka d'aura aure farin cikinsa ya kasa 6oyuwa dom ganin Mahaifinsa ya taka K'afarsa babu Sanda yana hawayen farin ciki, sannan Danginsu daga can 'yan Liman sun zo, yaga duk wannan taron don shi ake yi, don haka ya gaza 6oye farin cikinsa sam! Wannan shi ne abin da ya k'ara tayar da hamkalin Ma'u don ranar Ahmad bai kula ta kanta ba, tunda ya fice tun safe sai kwanciyar bacci ta dawo da shi Gidan. Can Gidan Baban nasa ya zauna ana ta hira da wasa da dariya da 'yan uwansa. San da ya dawo ya tarar da gidan cike da mutane, don haka kai tsaye 'Dakinsa ya wuce ya watsa ruwa ya fito yana shirin kiran Ma'u sai kuma ya kama Waya da Nana data kirashi. Anan ya shantake har bacci ya d'aukeshi bai nemi Ma'u ba. Yana tashi da safe ma da shirn fita yafito, kasancewar Abokinshi Jabir yashir yamasa'Yar walima suda Abokansu da suka yi Karatu, san da ya riga 'Dakin Ma'u don yin magana da ita aka ce tana Wanka, shi kuma ba zai iya tsayawa jiranta ba, saboda an dameshi da kiran a Waya, don haka ya juya ya fice. Wannan abin ya k'arawa Ma'u tsoro a ranta har take ganin tata ta k'are guqin Ahmad, ba shi da sauran lokacinta, kuma yanzu bata k'ara ganinshi a Gidan ko jin Wayarshi ba har dare sai 'yan kawo Amarya suka fara jerin gwano da Motoci, tun tana iya ganin adadin motocin da suke ta zuwa har ta kai ga gaza yin hakan, harabar Gidan k'ato ne zai iya cin motoci k'anana hamsin, kuma 6angare Nana da Ma'u daban, akwai 'yar tazara mai nisa ma. Asalin Gidan Alhaji Nura Kwangila ne da ya 6ata shekaru yana ginawa ya bai wa Ahmad da zummar shi zai k'ara gina wani Gidan nasa. Gud'ar kawo Amarya da ake yi kamar cikin ran Ma'u ake yinta, gashi lokacin babu kowa a Gidan, duk jiya aka zo mata, daga ita sai musu Aiki sai ta fashe da kuka ta had'a kai da bango tana kuka. Gabaki d'aya Gidan yayi mata zafi da kunci, Babu abinda take so illah ta fita ta barshi ko yata huta. Tana nan har 'yan kawo Amarya suka watse. Can wajen k'arfe goma da 'yan mintuna Ahmad ya iso Gidan. Kai tsaye 'Dakin Ma'u ya nufa, ya sha mamakin ganin bai ga komai akan fuskarta ba na 6acin rai, don ita kad'ai ta san abin da ta k'udurce a cikin ranta. Ya d'an zolayeta tana murmushi ya buk'aci suje sashin Amarya tace ba dai yau ba sai gobe. Ya ajiye mata kasonta da ya shigo da shi yayi mata sai da safe ya nufi sashin Nana cikin d'okin da yakasa 6oyuwa akan fuskarshi don yau kusan tare ya yini da nana, Kwalliya ta dinga yi ta tsumashi k'warai da gaske, wannan abin ya yiwa Ma'u ciwo k'wari da gake, yana fita ta k'ara fashewa da kuka. Wai yau Ahmad d'inta ne ke nuna zumud'in akan wata mace ba ia? ta dinga kuka, kusan haka ta kwan da damuwa. Shi kam Ahmad yana shiga 'Dakin Amaryarsa ya d'an zolayeta tak'i sakin jiki sai ya sureta cak suka yi ban'aki yin alwala idnta a rufe da kunya. A gsky a matse yake da Nana don tun randa ya ganta kusan tsirara sha'awarta ta gama nuna a cikin ranshi, don haka suna idar da Sallar ya fara nuna mata buk'atarshi da yake itama ta jima da jiran wannan lokaci bata yi wani nok'e- nok'e ba ta bayar da kanta. Abin da ya bashi mamaki bai wuce ganin bai sha wata wahala kamar yadda ya sha akan Ma'u ba, nan da nan yaji ya gamsu. Bayan ba haka yake so ba, yayi kykkyawan shirin da zai yi yanda yaso, sai dai bai samu ba yanayin shekarun Mace 'yar shekar 16 17 da mai shekara 23 da 24 akwai bambanci, don ita 'yar 17 komai nata k'ank'ani yake bai saki ba, sa6anin na wacce ta d'an yi shekaru 20. Sannan kuma a daren ya fuskanci Nana tana da tsawon buk'ata, sai yayi mamakin dalilin da sanya ba tayi aure da wuri ba. Ko da yake da alamunta bata ta6a yin mu'amala da wani na. DAME AKE ADO 4**21 Ko da yake da alamunta bata ta6a yin mu'amala da wani namiji ba don ta d'an wahala, amman sai yaji daren farkonshi da Ma'u yafi wannan nesa ba kusa ba, amman ya bar abin a cikin ranshi. Ita kuma Nana wannan shi ne dare mafi alkhairi a rayuwarta. Sai a yau ta gano ashe tana k'warar kanta da rayuwarta, jikinta yana bukatar wani abu da take tauye masa lallai Ahmad ya kai ta gurin da baa ta6a zuwa ba, bata ma ta6a Mafarkin zuwa ba. Da safe duk da Ma'u tana ranshi gajiya da kasala bai barsu sun fito da wuri ba rai wajen karfe goma sha daya na safe. Lokacin sun shirya ya ce da Nana tazo su shiga gurin Ma'u su gaisa suka jera suka nufi shashin nata. Masu aiki suna ta hidimarsu, suka shiga suka dinga gaishesu, sai wata Yaya abu ta fito daga Kicin da sauri ta mik'awa Ahmad wata takarda tace inji Hajiya tace a baka. Da mamaki yace "Wacce Hajiya ke nan? Ciki ldabi tace, 'Hajiya Ma'u mana...." Tana ina yanzu, tana cikin 'Dakin ne?" Tace, "Eh ta fita tun wajen Asuba....." Ya katseta da fargaci "Ma'un! ina ta tafi? "Wallahi ban sani ba nima Alhaji. Damuwa da tashin hankali suka bayyana akan fuskarsa, sai ya ce Babu damuwa jeki kawai. Ya kalli Nana dake kallonsa da fargaba sannan ya maida hankalinsa ga wasikar ya bud'e. Ga abinda ta k'unsa, Mijina Ahmad. Nayi iyakacin kokari na danne zuciyata na zauna da kai, amman na kasa don na gano a yanzu kayi mini nisa, ka girmi rayuwata, wancan Ahmad din Mijina da muke dai-dai shi ne Talakan nan mai kula dani, da cina da sha na, mai kula da yanda na kwana da yanda na tashi, ba kai ba babban mutum! A yanzu rayuwarka tafi dacewa da d'iyar masu Kud'i da arzik'i irinka ba wadda kake taimako ba, mai ilimin degree da Master's da wayewa. Rayuwarka ta girmi ta Ma'u yanzu, don haka naga yafi dacewa na matsa na baku guri, na san ba zaka iya sakina ba saboda kunya da tunanin kad duniya ta zageka, don haka na hutar da kai na tafi inda ba zaka k'ara ganina ba, ba zakaji kunyar iyayena ka sakeni ba, amma ina son wata rana ka furta sakina ko cikin ranka ne, don kada nayi ta yawo da aurenka. Ga kuma amanar 'ya'ya nan, wata k'ila zan gansu watarana. A lokacin daza ka ci karo da wannan wasik'ar tawa tuni nayi nisa daga inda kake! ina yima ka fatan alkairi kai da Matarka! -ASAM'U MATARKA A BAYA Wani irin abu yabi ta jininshi ya wuce zur! Kamar wutar nepa taja shi, ya waro ido da fad'in, "Wht? Me kika aikata haka Ma'u, yaya kike tsammanin zan rayu babu ke?" Nana ta kalleshi ganin kamar yana shirin zarewa ne tace, Yaya Ahmad lfy, me ya faru?" Cikin kid'ima tace, "Ma'u ta gudu! Tabbas cikin satin nan na wofintar da rayuwarta, ban damu da damuwarta ba, hakan ya sanya ta yi zaton na daina sonta ne! Yaya zan yi, na shga ukuna, wallahi idan babu Ma'u ba zan rayu ba, bari naje na gayawa Abba da Umma....." Sai ya juya ya nufi hanyar fita daga Falon, nana tayi hanzarin ruk'oshi da sauri tace, "Haba yaya Ahmad, wannan matsala ce tsakaninka da Matarka, ka san ko ina Ma'u zataje ba zata yi nisa da kai ba, 6acin rai ne ya sanyata tafiya, idan ka gayawa iyayenta kamar ka tona muku asiri ne, zaka iya janyowa su yi fishi da ita" Maganganun Nana suka shgeshi yace, Haka ne, Yanzu me ya kamata nayi? Don Allah gaya mini Nana, kaina ya kulle, ina tsananin son Matata!" Ta ciza baki tace, Kaje kowanne Gida da kasan zataje Bada sunan cigiya ba da sunan kaje gaishesu ne, ta haka zaka gano inda ta shiga..." Yace, "Yauwa haka za ayi Bari na dawo. Yafice da sauri a rud'e, ta bishi da kallo idonta ya cika da k'wallah. Lallai Ma'u tayi nisa a zuciyar Mijinta, idan kuma tace sai tayi gasa da ita zata iya zamantowa a cikin takaici, abu d'aya ne zai janyo sonta ya zama d'aya dana Ma'u ko ma ya fishi shi ne Asiri, wanda bata ta6a sha'awar yin sa ba, don wad'anda taji labrin sun yi ma bai amfana musu da komai ba. Ta goge hawayen dake zubo mata ta nufi sashinta. GA AHMAD kuwa, dukkan inda ya san zai samu Ma'u sai da yaje har yamma tayi masa ya gaji lik'is ba tare da ya gano inda take ba, ya fara sarewa da tunanin ko ya sanar da iyayensa, don duk Wayoyinta Ma'u a kulle suke. TUN DA MA'U ta isa garin zaria gidan k'awarta Maryam wacce tayi aure kusan shekaru uku da suka wuce ta auri wani Soja take kuka da k'yar Maryam ta rarrasheta ta sanar da ita abinda da ya faru ta had'a da rok'onta akan ta rufa mata asiri ta barta kada ta gayawa kowa tana gurinta har zuwa sanda zata san inda zata tafi don ba zata ta6a komawa gidansu ba ko gurin damginta ba har abada! Maryam tayi matuk'ar mamakin jin labarin da Ma'u ta bata, amman sam bata ga laifin Ahmad a cikin wannan labari ba, ko don ita ma tana da Kishiyar ne? ita ce Amarya. Da Ma'u ta san irin halin da Kishiyarta ta shiga san da zai aureta da ta ce Ahmad d'an Aljannah ne, don haka ta fara baiwa Ma'u hak'uri da bata labari kala-kala na Mazajen da zasu yi aure, DAME AKE ADO 4**22 duk da jikin Ma'u yayi sanyi amman tace ma ta ita dai ta kyaleta. Daga k'arrhe ta d'ora da ce mata. "Yanzu haka mijin nata yana gidan Uwargidan zai mata kwana biyu ba zata k'ara ganinsa ba sai bayan kwana biyu koda cuta zata kasheta ita da d'anta kuwa, ga rashin wadatasu da yake yi, aikinta shi ne gatanta (Da yake tayi Karatu mai zarfi har digiri) amman tana lalla6a aurenta domin ta jima bata sami yin saba. Duk da maganganun Maryam sun shigi Ma'u amman kishi ya rufe mata ido tace ta kyaleta, Sai ta rok'eta ko Massage ne ta yiwa 'yan Gidansu ta sanar da su inda take don hankalinsu ya kwanta, sai Ma'u tace ashe tana fatan Ahmad ya dawo mata ma ke nan? Haka suka dinga tata6uza har dare yayi. Sai dai wani abu da yake bai wa Maryam shi ne, tsawon yinin wannan Rana Ma'u tana kallon huton Ahmad Mijinta a cikin wayarta da ta sanya sabon layi, abin sai ya bai wa Maryam dariya. Wajen k'afe gama na dare aka fara buga K'ofar gidan da yake Gida ne irin na k'ananan masu rufin Asiri, babu Maigadi. Da sauri Maryam ta d'auki Wayarta tace, "a k'araso? yauwa gani nan zuwa. Ta nufi Kofa, sam Ma'u bata kawo komai a ranta ba. Tana kwance akan Kujera ta rintse idonta har suka turo K'ofa suka shigo. K'amshin Turaren da taji ne ya sanyata bud'e ido da sauri, Turaren Ahmad daya ne, tun yana talakansa har zuwa yanzu da yayi kudi, don haka ko cikin Bacci ba zai 6ace mata ba. Yana tsaye jikin Kofa idonshi yayi jajir! kamar Gauta, duk yayi bak'i yarame, yini daya tal! Bak'in ciki ya cika Ma'u, ta kalli Maryam da tsananin takaici da harara. Maryam tace, Kiyi hak'uri Ma'u, idan har na bar Mijinki da iyayenki cikin damuwa bayan na san halin da kike ciki ban yi musu adalci ba, ban kuma cika masoyiyarki ta gsky ba. Ma'u ta mik'e a fusace ta nufi K'ofar fita, amman Ahmad ya cafkota ya matseta tsam a jikinsa, ta dinga fisge-fisge da k'ok'arin k'wacewa amma ta kasa, sai ta fash da kuka tana fad'in, Me ya sanya ka biyoni, nace bana son aurenka, kaje ka zauna da 'yar uwarka. jininka, ka barni na tafi dom Allah Yaya! Ka tafi Yaya!!" Tana magana tana kukka, amman tana rik'e gam a jikinsa ya ki sakinta. Sai da tayi mai isarta tayi shiru tana shesshek'ar kuka, Maryam tana tsaye tana kallon ikon Allah, soyayyar Ma'u da Ahmad na burgeta. Cikin sanyin murya Ahmad ya fara magana, Wallahi Ma'u da Maryam bta sanar dani kina gidanta ba da babu abnda zai hana zuciyata bugawa, tun daga lokacin dana gano baki tare dani ban huta ba, ban sha ruwa ko mukurwa goda ba, ban ci abici ko loma daya ba, Na gode kwarai da gaske, Allah Ya bar zumunci. Ya dauko Bandir d'in Kudi da bai san adadinsu ba ya bata ta amsa da zumud'i tana godiya, don daman wata yayi nisa bata da kud'i, kuma komai nata ya kare. Har gaban Mota Maryam ta rakasu, sai da taga tafiyarsu sannan ta juya ta nufi gida. Bayan ta kulle gidan a ranta tana cike da sha'awar soyayyar Ma'u da Mijinta Ahmad su dai kam basu yi sa'ar aure ba sam! A can hotel d'in Ahmad ya dinga lalla6a Ma'u da k'yar ta yarda zata yi wanka tace amman ba zatayi tare da shi ba, dole ya kyaleta. Tana daga Ban'Dakin taji kira ya shigo Wayarshi, don bai jima da kunna Wayar ba, sai ta jiyoshi yana "Eh na ganta...!!" Ban san sanda zamu dawo ba gaskiya....Sai da safe...!!" Daga yanda yayi maganar ta san da Nana yake, sai taji tausayin Nanan ya kamata tana bin Namiji yana mata yanga. Shi kuma haushin Nana yake ji yanzu don yana ganin kamar itace ta janyo masa duk wannan matsalar ma. A6angaren nana har sai da tayi hawayen takaici. Duk da Ahmad yaso samun wani abun a wajen Ma'unsa amma sai yaga ta had'e rai ta kwanta a Falo ma, dole ya k'yaleta. Washe gari da safe suka wuce Kano. Nana taji dad'in ganinsu taji dad'i, tay murna, ya had'u guri d'aya yayi musu nasiha da rok'on arzik'insu su zauna lafya. A gurin ne Ma'u tace ta bai wa Nana kwananta na Wata guda, Ahmad bai ji dad'in haka ba, amman babu yanda ya iya tunda lalla6ata yake yi. Ita kuwa Nana dad'i ne ya kamata har farin ciki ya bayyana akan fuskarta. Cikin wannan Watan Ahmad ya shiga tsananin damuwa da tashin hankali, ya yin da Nana ta more Amarcinta yanda taso. Mijinta ya d'ebe mata dukkan damuwa da kewa. ita kuwa Ma'un da wannan damar tayi amfani gurin neman NAFISA LILI 'YAR NIJAR ta harhad'a mata Magunguna na gyaran jiki, wato MAI DA TSOHUWA YARINY! Ta dinga Sha da Tsarki dana Turare. Cikin wannan lokacin ita kanta ta san ta sauya, don haka Ahmad idan ya ganta kamar ya cinyeta, Don akwai sanda ya gaza hak'uri ya matseta a d'aki suka dinga rikici tace wallah ta d'auki alk'awarin bazata ci amanar nana ba sai dai suje gabanta ya gaya mata shi ne yace sai ta karya, abinda ta san ba zai iya ba. Haka dole ya hak'ura ya kyaleta don ba yai iya yin Raping d'in Matarsa ba, don yana matse k'warai da gaske, dole ga nana ya kai bukatarsa. DAME AKE ADO 4**23 Dole ga nana ya kai buk'atarsa. Wannan ya yiwa Nana dad'i, wannan abu da ma'un tayi mata ya sanya take girmamata k'warai da gaske, sannan ta rik'eta kamar 'yar uwa, za a gaisa ayi wasa da dariya dai-dai gwargwado. Ammam ranar da Ahmad zai koma 'Dakin Ma'u Nana ta raina kanta ganin yanda yake ta zumud'i da rawar k'afa har taji Kishi ya rufeta a ranta tace sai kace ba gurin tsohuwa zai je ba. Tun daga iri rigar baccin da Ma'u ta sanya ta tsokanoshi ya dinga binta da kallo tana wani kwarkwasa da yanga har dai ya gaji ya janyota yana fad'in, "Yarinya wallah baki isa haukatani ba. Ta fashe da dariya don ta gano ya shiga tarkonta.Ranar kam saida ta raina kanta don a daren nan saida ya fanshe watanshi guda, musamman da yaji ta kamar ba Ma'unshi ba ta koma masa wata 'yar Budurwa kamar daren Amarcinsu. Wannan daren kam sun k'arar da shi gurin nunuwa juna yanda suka yi rashin juna. AHMAD ya gama gano yanayin Matansa, don haka yaci Maganin zama da kowacce dai-dai halinta. Ita dai Nana tana da tsananin buk'ata, don haka kafin girkinta ya fita sai ta isheshi, ita kuma Ma'u shi ne yake da tsananin buk'atarta saboda gyara da kuma yanayin halintarta, don haka har Nana ta ganoshi dole ran Girkin Ma'u d'okin yake yi da zumud'i, ita kanta Ma'u ta gano hakan, sai dai yana iyakacin k'ok'arinsa gurin ganin ya kamanta gsky da adalci a tsakaninsu, sai dai bai isa ya 6oye soyayyar ma'u ba, duk da itama Nana yana bata wani matsayi na ita ce jininsa, 'yar uwarsa da yake sun fahimci juna sai suka zauna lfya. Cikin shekarar ne duk Allah Ya albarkacesu da smun juna biyu, tsakaninsu wata guda ne kacal, Nana ce tafara haihuwar k'aton Namiji yaci sunan ABDULLAHI (Mujahid), Yaron da yaga soyaya da gata gurin dangin 'Yam Leman. Sai kuma Mau da ta kara haifo Mace. Itama ta sami gata, Ahmad dai shi ne mutumin da ya karya alk'adarin canfin danginsu na haihuwar d'a d'ya ko biyu, sai gashi da biyar cur! wannan ya sanya iyayensa jin dad'i. Adalci da Ahmad yayi a Gidansa da ya kwantarwa da Ma'u hankali shi ne hana Nana yin aiki ya ce shi ya dace ya nemo, duk da Nana ta damu da farko, rigima har gurin Babanta, amman da bata sami goyon baya gurin Iyayenta ba dole ta hak'ura, don Babanta yace ita kanta Mahaifiyarta digiri biyu gareta, kuma saboda k'warewarta a makaranta suka had'u suka yi aure, amman bata aiki saboda su Family d'insu suna da tsananin kishi, wanda tayi a baya ma Allah Ya amfana. Hakan ne ya sanyayar mata da guiwa, Ahmad ne yayi k'ok'arin k'ulla auren Mahaifinsa da Hajiya Amina don Mijinta shekaru biyu ke nan da rasuwarshi. Hakan ya yiwa kowa dadi Musamman kakarshi data damu yayi aure. Ita dai nana tun daga haihuwa 1 shiru babu k'ari da yake itama jinin iyalin ne suke ta6ata. GAME DA UMMI kam a yanzu ta yarda Ahmad yafi karfinta da ta gano matsayinshi dole ta samarwa kanta lafya, amman Iyayenta sun yi da sun sani da takaici, musaman da Mahaifin nata ya gano mahaifin Ahmad tsohon Ubangidansa ne, shi ke bashi kaya kafin kaninsa ya cigaba da bashi. wata rana kafin tayi aure ta hadu da Ahmad a Super Market ta gaya masa shi kadai take so amman ta hakura da shi zata auri wani ta bashi tausauyi kwarai da gaske, sai dai ya san bai isa ya karawa Ma'u kishiya ba, sai ya amshi lambar Accunt dinta ya tura mata kudi masu yawa wanda dasu ne tayi komai na auremta. WATA RANA sunje Gidansu da yamma ana ta hira sai suka jiyo kuka a harabar gidan, suka fito da sauri dasu Umma dasu Ma'un da Yaya Auwal da sauransu da yake duk ranar Lahadi da yamma annan ake hake had'uwa ayi ta hira. Lami suka gani dawata k'armasashiyar Mata kamar Fatalwa, Matar ta fadi Lami na kokarin tashinta tana kuka, ta lalla6a ta tasheta ta rungume a jikinta tana takawa da kyar! har ta isa kusa dasu ana tsaye cirko-cirko. Mal. Sulaiman ne yace, Lami wace ce kuma wannan? Cikin kuka Lami tace, "Yaya Raliya ce! Kusan Wata hud'u ke nan da aka kawota da cuta mai karya garkuwar jiki (H.I.V) dukkan abinda nake da shi ya k'are gurin Magani, kullun Mahaifinta idan zai zo gurinka sai nace ya gaya maka sai yace a'a shi ba zai fad'a maka ba, shi ne ni kuma da naga kamar zata mutu ne na kwasota tafiya bata iya yi don ku taimaka mata. Yaya Auwal yace, Raliya ce wannan Lami Subuhanallah!" Kowa ya tsorata da ganin yanda Raliya ta koma Yaya Auwal yace a kaita Asibitinshi zai yi mata komai kyauta, shi kuma Ahmad ya basu Kud'i mai yawa yace kuma duk k'arshen Wata ta dinga zuwa gurin Ma'u tana amsar Kud'i. Raliya da Lami suka fashe da kuka. Umma tace "Ato, duniya ke nan, tafi duk yanda ka d'auketa, sakayya ce take zuwar muku. Suka lalli juna da mamaki. TAMMAT BIHAMDILLAH!. ********************** ⬇ ************************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ **************************