[4/4, 5:53 PM] Fatima saleh: *💘💖AKAN SO💖💘* ********************** ⬇ ************************** ********** Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ         01 *18/02/2017* Coffee dinta take hadawa hankalinta a kwance tana kallon NTA don tana son shirin da MTN suke yi na tabo rayuwar mutane. Yarinyar data fi burgeta "Yusra fari" ta karbe show din da fadin. "Yau muna samu wata wasika ne datai matukar bamu mamaki ta kuma taba zuciyarmu. Bamu taba cin karo da abin mamaki ba irin wannan" Hankalinta ta sofi ta mayar kan t.v din tana cakuda coffee dinta da cokali. Aka soma karanta wasikar kamar haka: *NEMAN MOH DA GAGGAWA* *Kai babana ne!!!* Bansan abubuwa da yawa ba akanka.Nadai san sunanka Fu.ad. Kuma kai dan wasan kwallon kafa ne saidai bansan ko wanne club ba. Sannan da jimawa kana shaawar wasannin mota na stunts. Mutane suna kiran ka Moh. An gayamun bakasan dani ba. Ancemun zan fahimta wata rana. Ni nawa mai sauki ne. Wannan shine : shekarata goma sha biyu. Mutuwa zan. Nasan mamata ba zata taba jin dadi ba. Inaso inganka kamun in mutu. Wata rana zata gane. Har yanzun tana sonka sosai. Moh idan ka karanta wannan dan Allah ka dawo. Ba ma saika zama babana ba. Ba saikace kana so na ba ko kabani hakuri. Kawai kazo kaganni. Ina jira amman banida lokaci sosai. *Nana* * Ana gama karanto wasikar mug din coffeen dake hannunta ya subuce ya fadi ya ko tarwatse ko ina na kitchen din. "Nanaaaa..........." Sofi ta kwala mata kira cikin tashin hankali. Ji tayi kafafunta basu da kwarin daukarta. Tsugunnawa tai ta jingina da locker din kitchen din tana maida numfashi. "Ya Allah! Me nana taje tayi ne?" Ta furta a fili. "Mumy......." Ta juya ta sauke idanuwanta cikin na nana data kira sunanta da yanayin tambaya da shakku. Kallon ta take sosai. Jeans ne a jikinta blue sai riga itama blue mai haske. Kanta sanye da hular data lillibe askakken kanta. Duk da ramar da tayi sosai. Bai hana kyawun nan nata fitowa ba. Hawayen dake cike da idanuwan ta ya zubo. Lokaci daya sofi taji zuciyarta ta karye. Hannu ta mika ma nana alamar taje. A hankali ta karasa ta rike hannunta sannan ta zauna kusa da ita. "Nana zaki bata kayanki. Tashi kigani na zubda coffee a wajen" Kaman bata ji mai tace ba ma ta riko hannunta. "Mumy kiyi hakuri. Kawai ina so ingan shi ne ko sau daya" Sauke ajiyar zuciya sofi tai tana kokarin tarbe hawayen dake zubo mata. Ta ina zata fara ce ma Nana tun wata biyu da haihuwarta tai kokarin nemo Moh amman a banza. Ta gaji ta hakura. Haka ma da yanzun shi ne karshen zatonta akan samun saukin Nana din. Bata san duniyar da yake ba. Bakuma tasan inda zata nemo shi ba. Haka ta yanda zata soma gaya ma nana. "Nana bana son ki daga zatonki akan nemo shi ne. Karkizo ba.a ganshi ba" Hawayenta nana ta goge sannan tai mata wannan murmushin dake siye zuciyar mutane. "Ko ba a ganshi ba. Bazanji kaman banyi kokarin nemo shi ba" Murmushin sofi ta mayar mata hadi da fadin. "Badai naso ki kwallafa rai. Oya tashi daga cikin coffee din nan. Ki wuce ki sake kaya ki kwanta" Babu musu nana ta mike. Matsawa tai sosai kusa da sofi ta manna mata sumba a kunci hadi da fadin. "I love you mumy" Mayar mata da sumbar tayi tace "I love you too princess. Maza ki wuce" Har nana tazo fita daga kitchen din sofi ta kirata da cewar. "Ya akai kika kai gidan t.v?" Wani murmushi tai tace. "Mumy a school ne fa muke maganar da fa.iza shine tacemun muje gidan radio can ake kai cigiyar mutum. Shine na rubuta a takarda da aka tashi bamu tsaya lesson ba mukaje. Suka hanamu shiga ma. Saida inata kuka ne wani mutum yazo ya tambaya nace ina neman babana ne kuma ni mutuwa zanyi. Inaso ingan shi. Shine fa yaje damu har ciki ya biya kudi muka bayar da wasikar. Wallahi mumy bance su sa a t.v ba" Tunda ta fara bayanin sofi kallonta kawai take. Tama rasa me zatace dan haka ta daga mata kai kawai. Kallonta take harta bar kitchen din. Sai lokacin tabar hawayen da take kokarin tarbewa suka zubo. Tana jin muryar fu.ad cikin kanta tamkar yanzun abin ya faru. "I don't do happily ever after. Daga randa kika yarda da soyayyata ya kamata kisan banyi kalar wanda zai dinga zarya da yara da pampers ba. Ban kama da wanda zai asarar lokaci da soyayyar shi akan yara ba. Inada su haneef. Ina da su pha.iza. A duk sanda naji marmarin ganin yara zanje gidansu inga nasu" Mikewa sofi tayi ta dauki wayarta ta kira Ansar kamun tunani ya haye mata bugu daya ya daga. "Sofi lafiya dai ko?" Shine tambayar farko da ansar yai mata da wata damuwa a muryarshi. "Nana tana lafiya. Tana dakinta......" Ta amsa shi. Jin yanda ya sauke numfashi yasata murmushi. Ansar kenan badon ita ta haifi nana ba saita rantse yafita sonta. Jin yayi shiru ta ce. "Ansar nana ta ballo aiki" Cike da damuwa yace. "Me tayi?" Cikin nutsuwa ta soma bashi labari iya abinda tasani. "Good. Ni banma san yanda akai wannan tunanin bai zo mun ba" Ansar din ya fadi. "Ni fa banajin za.a ganshi ansar. Bana son nana ta saka ranta akan abinda ba zai taba yiwuwa ba. Nafiso ta samu duk wani farin ciki dazan iya bata kamun ta........." Katse ta ansar yai da fadin. "No sofi. Please No karki karasa. Za.a ganshi and he is going to be a match" Dafe kai tayi dan ya soma mata ciwo da yanayin tunanin data cika shi dashi. "Zamuyi magana anjima dai" Ta fadi muryarta a gajiye. Sallama sukai da ansar din ta fita daga kitchen din zuwa bedroom dinta. *** Tana shigowa office ringing din wayarta yai mata maraba. Kamun ta karasa inda wayar take harta yanke. Ta dauka ta duba. Missed calls har biyar. Ta bude ta lumshe idanuwanta ganin Jabir ne. A ranta tana fatan Allah dai ya sa lafiya. Tana shirin kira kenan. Ya sake kiranta ta dauka da fadin "Honey J....." Kaman yanda take kiranshi. Muryarshi dauke da yanayi na bacin rai yace. "Sai yanzun kika ga damar daukar wayar kenan?" Glass din dake manne a fuskarta ta cire ta ajiye kan table sannan tace "wallahi wayar nabari a office munata fama da marassa lafiya" Tanajin yanda yake jan numfashi ta cikin wayar. Tasan halin shi sarai. Ranshi a bace yake. "Idan kina da lokacin mu kizo gida. Ikram bata da lafiya. Akamun waya naje na daukota a school" Cikin damuwa tace "Ya Salam aida ka kawomun ita nan asibitin mana honey J kasan....." Katse ta jabir yai da fadin "Idan ba zaki dawo ba Jana ki fadamun kawai. Insan yanda zan da yarinyata" Shiru tai hakan yasa jabir kashe wayarshi. Ta sauke wayar daga kunnenta hadi da maida numfashi. Saida ta kira Dr.Farida ta fada mata zata je gida akwai wani abu daya taso ko da an nemeta sannan ta dauki duk abinda take bukata ta fita. * Da sallama ta shiga. Ba kowa a falon dan haka ta taka zuwa dakin baccin su. Nan ma da sallamarta ta shiga. Bataga kowa ba. Jakarta ta ajiye. Ta cire lab suit din dake jikinta ta rataye sannan ta fita zuwa bangaren yara. Saida ta tura kofar sannan tai sallama. Yana zaune gefen gadon ikram yana danna wayarshi. "Honey J......" Hannu ya daga mata tare da fadin. "Shhhhh......." A hankali. Shirun tai ta karasa inda yake. Ikram tana kwance da alama bacci take. Tashi jabir yai ya nufi hanyar kofa ya bude ya wuce. Jana ta sauke wani wahaltaccen numfashi. Sam sam bata son rikici. Ciwon kai yake saka mata. Ta kuma kula yau jabir rikice ne fal a cikin shi. Taba jikin ikram tayi taji shi zafi rau. Musamman kanta. Ta kula da wata leda da take gefe. Ta dauka ta duba.Magunguna ne da katin asibiti. Da alama jabir asibiti yakai ikram. Gyara mata lulluba tai sannan ta fita daga dakin ta samu jabir a dakinsu a tsaye. Karasawa tai inda yake. Ta dora hannunta akan kafadarshi tana kallon idanuwanshi da suke cike da rigima. "Da kinyi zamanki ma. Na rigada nakaita asibiti" Hannunta tasa ta shafi fuskarshi. Yana wani kauda idanuwanshi daga cikin nata. "Sai da nai handing over ne fa na taho. Ya jikin nata?" Hannuwanta ya cire cak daga jikin shi ya wuce ya zauna. Bata dai gaji ba. Dole ta lallaba shi. Dan haka ta bishi kan gadon ta zauna gefe. Hannunta ta dora kan cikinshi. "Kaci abinci?" Ta bukata. Muryarshi a dake yace. "Karki samu damuwa. Indai patients dinki sun samu yanda suke so. Meye matsalarki damu?" Da gaske yau jabir rikici yake ji. Tashi tai ta shiga toilet dan ta watsa ruwa. Inya gama fushin sunyi magana. Jabir gyara kwanciyarshi yai kan gadon. Jana ta gama kaishi bango tana daukar rigimar nan karama ce. Tazo tana wani lallabashi da soyayyarta din nan zata wargaza mishi plan. *** *EUROPE* 20/02/2017 Kwance yake abinshi yanayin yammacin ya saukar mishi da kasala. Yau bayajin zuwa ko ina. Sunyi da Logan zasu fita sai dai bayajin zai iya zuwa ko ina. Wayarshi yaji tana ruri ya dauko ta gefenshi ya daga. Logan ne. "Hello logan. I am sorry......." Kamun ya karasa Logan ya katse shi da fadin. "You are not in the mood huh?" Dafe kai yayi. Yanajin logan ya kashe wayar. Ya ajiyeta gefe. A tsahon shekarun nan Logan ne kadai abokin da ya rage mishi. Yana da abokai amman a gaisane kawai sama sama. Saboda babu wanda zai iya jure halayyar shi. Shi da kanshi da ya samu dama daya guje ma halayyarshi. A da can ma mutum biyu da ko da wasa bazai bar tunaninshi yakai gare su bane suke jure ma halayyarshi. Wayarshi ta sake daukar kara. Dauka yai ya duba. Mamaki bayyane a fuskarshi. Number din Nigeria ne. Yasan ba mamanshi bama daya daga cikin yan gidansu bane tunda yana da number dinsu. Banda mamanshi ba da kowa yake magana ba. Yanda basa kiranshi haka shima baya kiransu. Shekaru goma sha daya da dori yake rayuwarshi lafiya kalau. Batare da kulawar daya daga cikinsu ba. Yana kallo har tai ringing ta tsinke. Ta sake daukar wani rurin. Dagawa yai da alamar takura a muryarshi yace. "Hello..." Shiru akai na dan wani lokaci kamun ace. "Fu.ad............" Wata irin dokawa zuciyarshi tai da saida ya tashi zaune.  Shekaru goma sha daya. Muryarshi na nan daram. Kuma zai ganeta a duk inda ya jita. Lokaci daya komai ya soma mishi yawo a idanuwanshi kamar a lokacin yake faruwa. * *12/02/2006* "It is my life saboda me kowa zai kasa fahimtata" Fu.ad yake fadi cikin hargowa. Girgiza kai lukman yakeyi cikin ganin wauta da rashin hankalin abinda fu.ad din ya aikata. "Wallahi duk yanda kake fadar rashin son haihuwa ban taba kawo wa yai kamari haka ba fu.ad. Ban kuma taba zaton cewa a zamanmu zaka yanke hukunci irin haka ba tare daka shawarce ni ba" saima kaji abinda na sake yi zakai mamaki tunda rayuwa tace bata wani ba. Fadar fu.ad din cikin ranshi a fili kuma yace. "Na saki sofi!!!" Lukman baisan sanda ya dauke fu.ad da wani irin mari ba. Fuskarshi dauke da wani yanayi daya girmi tsana da kyamata yace "Fu.ad anya baka haukace ba? Ko dai makiya sun maka asiri? Na dauka akan auren sofi kawai Allah ya gama jarabtarka. Na dauka ka gama girbar mugayen halayenka" Wata irin dariyar takaici fu.ad yai hadi da fadin. "Zan bar muku kasar gabaki daya. I have set her free. Ta auri wanda zai iya bata yara. Kaima bankwana nazo inyi maka" * *20/02/2017* "Fu.ad........." Kiran da lukman yai masa da alamar yana son tabbatarwa ko shi din ne ya dawo dashi hayyacinsa. Ji yai makoshin shi ya bushe kaman wanda yai kwanaki bai sha ruwa ba. Dakyar ya tattaro wani yawu ya hadiye sannan yace. "Lukman......." Wani numfashi lukman ya ja da saida fu.ad yaji shi ta cikin wayar kamun yace. "Ka tattara ko me kakeyi ka ajiye shi. Ka biyo first jirgin daka samu available zuwa gida" Shekaru sha daya wannan ne maganar farko da lukman zai gaya masa. Cikin rashin fahimta yace. "Meke faruwa lukman? Bangane ba" "Wallahi zakai kuskuren dayafi na barin sofi inhar baka dawo ba" Bai jira amsar shi ba ya kashe wayar. Cikin tashin hankali fu.ad ya sake dialing amman a kashe kaman ba yanzun suka gama magana ba. [4/4, 5:53 PM] Fatima saleh: *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ           02 *19/02/2017* Da kanta ta sauke Nana makaranta sannan ta wuce wajen aiki. Ko jakarta bata ajiye ba taji an kwankwasa kofa. "Shigo" Ta furta cikin sanyin murya. Kaman yanda ta zata ansar ne. Murmushin nan nashi yai mata. Duk da yanayin nauyin da zuciyarta take dauke dashi bai hanata mayar mishi da murmushin ba. Zama tayi kan kujerar office din. Shima ya samu wata kujerar ya zauna. "Ina kwana..." Ta gaishe dashi ya amsa da "Lafiya kalau sofi. Kin tashi lafiya? Ya nana?" Ta langabar dakai gefe daya tace "Alhamdulillah. Kawai dai bana son ganin dokin dake cikin idanuwanta ne. And yau zanga doctor dinta kan test din da akai last week" Jinjina kai ansar yai cikin alamar fahimtar halin da sofi din take ciki. "In shaa Allah za.a ganshi" Wani murmushin takaici tayi. "Ansar idan anganshi bazai donating bafa? Baima son da zamanta ba. Bama na zaton ko da yaji zai dawo tunda baya son yara and........" "please......" Ansar ya katse ta yana ci gaba da fadin. "Babu wanda zaiga Nana bai so ta ba. To hell with him not wanting children. Zai donating indai da zuciya a kirjin shi" Shiru sofi tai. Dan kuwa ita take da tabbacin zuciyar dake manne kirjin Fu.ad. Kaman yanda a duk kallon da nana zatai mata. Cikin idanuwanta take kara ganin zuciyar fu.ad Mikewa Ansar yai yace. "Ina office dina if you need me" Kai kawai ta iya daga mishi saboda wani abu daya dunqule mata a makoshi. Tana kallon shi ya fice daga office din yaja mata kofar. Kanta ta dora kan table din tana maida numfashi. **** Hankalinta nakan rigar da take kallo sam bataji shigowar shi dakin ba. "Me kike yi haka?" Maganar nawaf ta dawo da ita daga tunanin da take. Cikin sauri tai kokarin kauda rigar gefe. "Ba....babu komai" Ta amsa a daburce. Rigar dake gefenta yazo dauka ta rigashi tana rike rigar sosai a jikinta. Hannu yakai ya riko rigar. "Har yanzun baki daina tunanin shi ba ko?" Ya tambaya rai a bace. Rigar ya fisge daga jikinta ya mike daga kan gadon yana nufar hanyar waje. Da sauri ta karasa inda yake ta riko masa hannu tana fadin. "Nawaf wallahi ba haka bane ba. Dan Allah kabani rigar" Hankade ta yai ta fadi. Duk da zafin da taji bai hanata tasowa ta sake riko shi tana magiya ba. Kamata yai yai mata wani irin riko kaman zai karyata. "Duk ranar da na sake ganin wani abu nashi a kusa da gidan nan zan baki mamaki wallahi" Hawaye cike fal idanuwanta saboda azabar rikon dayai mata. Muryarta na rawa take fadin. "Kayi hakuri. Dan Allah kayi hakuri. Amman kaban rigar zan ajiye bazan sake fito da ita ba" Sakinta yai yana girgiza kai. Baisan meke damun nuriyya ba. Bata san yanda yake ji idan ya kalleta yai tunanin wannan banzan farhan din yana yawo a kanta ba. Duk bai isheta ba sai ta dinga dauko abubuwanshi tana tusawa gaba tana kallo. Wucewa yai har yakai kofa. Ta matso ta sake rike mishi kafa. Tana magiya ya bata rigar. Dagota yai daga jikin kafarshi yai mata wani irin mari da saida taga walkiya. Kamun ta gama wartsakewa ya sake dauketa da wani marin. Wannan karin saida ta fadi. A fusace yace. "Ina farhan yake lokacin da na hana ai miki fyade? Ina farhan yake lokacin dana dauko ki daga cikin kunci da kangin rayuwa? Da abinda zaki sakamun kenan nuriyya?" Kuka take sosai. Tasan ya taimaketa. Ba kuma tace bata gode ba. Sai dai babu wanda zai iya rabata da tunanin farhan. Ko kaddara data rabasu da kanta tabar mata farhan a zuciyarta da tunaninta. Duk da ikirarin nawaf. Tana kallonshi ya jefar da rigar ya fita daga dakin. Kukan da take bai hanata rarrafawa ta dauko rigar ba. Fuskarta ta rufe da rigar tana wani irin kuka da zaka san bashi da alaka da marin da nawaf yai mata. **** *01/01/2010* "Zan dawo Nuri. Daga lokacin dana tsaya da kafafuna. Mutuwa ce kawai zata hanani dawowa wajenki" Kuka take sosai. Ta dago da jajayen idanuwanta ta kalle shi. "Yaya Farhan ya rayuwa zata zame mun babu kai? Ta ina zan fara?" Wani irin daci yake ji har kasan zuciyarshi. Bai taba zaton akwai yiwuwar ka tsani mahaifinka ba. Amman ya tabbata da za.a bashi wani zabi zaice a dauke mahaifinshi ne. Ya daina ganinshi ya huta. Daurewa yai dan shi kanshi yana gab da soma kukan. "Na biya miki kudin makaranta gaba daya. Ga wannan....." Ya zaro ATM daga aljihunshi da wasu takardu ya miko mata. "Ki boye su. Duk sanda kike da bukatar kudi. Ki cire. Kudin dana zuba miki basu da yawa. Su kadai suka ragemun Nuri" Kasa tsayuwa tai. Durkushewa tai gabanshi tana wani irin kuka daya karya masa zuciya. Shi kanshi baisan ta yanda zai fara cikakken numfashi babu Nuriyya ba. Sai dai dole yabi mahaifinshi subar kasar. Yana bukatar ya karasa karatunshi. Ya tsaya da kafafuwanshi yanda zai dawo ya cire Nuriyya daga wannan kangin. "Yaya farhan bana bukatar wannan. Wallahi kai nake so a kusa dani" Lumshe idanuwanshi yai da suka sake launi saboda tashin hankali sannan ya bude su yana saukewa akan Nuriyya. Tsugunnawa yai. Yana son ya riko ko da hannuwanta ne ya nuna mata cewar bashi da wani zabi. Yana tuna exact maganar da babanshi ya fada mishi jiya da dare. "Ko kabar yar gidan karuwar nan kabi ni mu tafi. Ko kuma ka zauna da ita anan ka manta cewar kana da wani mahaifi. Amman wallahi zan janye duk wani taimako na akanka. Saboda bazai yiwu kana zubda mun kima da daraja a idan duniya ba" Yasan babanshi sarai. Ya kuma san zaiyi fiye da abinda ya fadama. Kuma yana da tabbacin zai ci gaba da saka masa ido yaga ko ya yanke alaka da nuriyya. Cikin sanyin murya yace. "Nuri banda wani zabi. Zai tafi da khadee ne....." Cikin sauri nuriyya ta goge hawayen fuskarta. Taya ma zata fara son kai har haka. * *19/02/2017* Turo kofar da taji ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta fada. Cikin bala.in sauri ta boye rigar. Nawaf ne. Tanajin shi ya tako ya karaso har inda take zaune shima ya zauna. Kallonshi take taga ko yasha wani abu. Idanuwanshi na nan da kalarsu. Bataga alamun yasha komai ba. Yanda tayi da jikinta ya taba mishi zuciya. Tsoronshi take. Ya dafe kai yana jan iska ta bakinshi. Hannuwanshi yakai ya kamota. Taki kallon fuskarshi. Sosai ya matso da ita jikinshi. Yana ganin sahun hannuwanshi kwance kan fuskarta. Abinka da farar fata. Wani tsanar kanshi yaji. Laifin nuriyya ne tasan shi sarai. Tasan idan ranshi ya baci baya iya controlling din kome yake yi. Kwantar da ita yai kan kirjinshi. Tana ta sauke ajiyar zuciya. Taji kuka tagaji. Yasa hannuwa ya shafi kumatunta duk biyun. "Ki yafemun please......" Ya fada cikin kunnenta. Shiru tai mishi. Dan tsoron yin magana take ji. Lokutta da dama tsoron shi take. Tanaji ya matse ta a jikinshi. "Please nuriyya. I love you. Ai kinsan haka ko? Kinsan ina sonki sosai" Kai kawai ta daga mishi. Tanajin shi ya sauke ajiyar zuciya. Ya mike tare da ita a jikinshi. Toilet yakaita ya wanke mata fuska da kanshi. Yasa towel ya goge mata inda ruwa ya bata. Ya kamo hannunta ya fito da ita. Kan gadon ya kwantar da ita. Da ido kawai take binshi. Ganin yana shirin hawowa gadon yasata fadin. "Takalmi nawaf. Please......." Murmushi ya kwace masa. Ba mantawa yai da takalmi a kafarshi ba. Bai damu daya cire bane kawai. Inba nuriyya ba wa ya isa ya saka shi canza dabi.unsa. Takalmin ya cire yabar socks din. Yahau gadon ya kwanta bayanta ya rikota jikinshi. Bata damu ba dan tasan bai taba takura mata dan biyan bukatarshi ba. Lokutta da dama bata gane kanshi. Jikinta ya kwanta. Har kanshi a bayanta yake. Ya wani nanike mata kaman karamun yaro. A haka barci ya dauke shi. Yanajin son nuriyya har cikin fatar shi. **** *19/02/2017* Mikewa tai da shirin fita daga office din zuwa asibiti ganin karfe sha daya tayi. Don sunyi da Doc.jana zata shiga amsar result din wajen sha biyu. Gara ta fita da wuri. Wayarta taji ta soma ringing. A zatonta ma doc.jana din ce ta kirata. Tasa hannu ta lalubo wayar daga cikin jaka. Zuciyarta taji ta wani doka da karfin gaske. Bango ta dafa ta nemi waje ta zauna. Number din principal din makarantar su Nana ne. Addu.ar duk da tazo bakinta ita takeyi. Ta daga hadi da sallama tana jiran jin abinda tafi tsoro. Ko jikin nana ne ya tashi. A daddafe suka gaisa cikin harshen turanci. "Akwai wasu yan jarida da suka zo tun misalin awa daya daya wuce. Sunki tafiya suna son magana ne da Nana. So nasan zaki so ki sani." Lumshe idanuwanta tayi ta sauke wani numfashin. Dan wannan mai sauki ne. "Karku barsu su je ko da kusa da itane. Gani nan zanzo school din yanzun" Tana kashe wayar ta kira Ansar dan tasan ba zata iya wannan aikin ita kadai ba. Last warning na Doc.jana shine kar a dora ma nana wani stress komin kankantar shi. A halin yanzun yan jaridar can ba karamun stress bane a wajenta. [4/4, 5:53 PM] Fatima saleh: *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ         03 *19/02/2017* Farar suit dinta ta dora saman kayan jikinta sannan ta sanya qaramar hijab itama fara.   Tayi matuqar kyau. Ta dauki qatuwar jakarta sannan ta manna glass fari mai ratsin zaiba.            "Honey J zamu fita tare ne?" Ta buqata. Tun jiya yake sha mata kamshi. Tayi lallashin duniya. Yauma sanda ta tashi tagama hada komai. Tabar Atika ta karasa shirya mata umar dan yasir ya iya komai da kanshi. Bai jirata ba yai breakfast dinshi. Gaisuwarta ma dakyar ya amsa. Idanuwansa da suke dagula mata lissafi ya kafa mata. A daburce tace "alright bara na wuce kawai may be........." Katseta yai da fadin "Jana wato rayuwar wasu tafi maki muhimmanci akan tamu right?" Ta lumshe idanuwanta ta budesu sannan tace "Na dauka mun gama maganar nan fa"    Saukowa yai daga kan gadon yazo inda take ya tsaya suka fuskanci juna. Idanuwansa ta kalla sosai yauma rikici yake ji ita kam ba zata biye masa ba. Juyawa tai da niyyar tafiya ya janyo hannunta hadi da fadin "Jana kina da hankali kuwa?" Zuciyarta ke wani irin dokawa duk da hakan ba baqon abu bane in har jikinsu zai hadu ita dashi.       "Ikram ce kwance a daki" Ya furta a dake. Saida ta hadiye miyau dan bakinta ya bushe sannan tace masa "Nayi mata komai da take buqata bacci ma take and Honey J ikram ba qaramar yarinya bace dan qaramin zazzabi duk ka wani damu" Kallon da yake mata yasata yin shiru. Har wani huci yake,muryarsa daqyar take fita yace "Karamin zazzabi? Jana kin daina damuwa damu ko? Aikinki yafi maki muhimmaci? Good!" Kamin tace wani abu ya fice ya doko qofar da qarfi. Wasu siraran hawaye suka zubo mata. Ta cire glass dinta ta sa hannu ta goge su. Ji take zuciyarta duk bata mata dadi. Tasan yanzun haka patients nacan sunata jiranta. Fitowa tai zuwa falo. Ta samu Jabir zaune kan kujera. Tazo wucewa ta kalle shi ya watsa mata wani kallo. Har takai qofa taji ikram tace mata "Mami yauma fita zakiyi?" "Ya Allah" ta furta cikin ranta ta bude baki zatai magana jabir yace "ikram dakin koma kin kwanta ni zan zauna tare dake." "Thank you pa" Ikram ta fadi tana wucewa. Jana ta kalli jabir da ya dauke fuska yana ta dacin rai. Addu.a tai sannan ta fita daga cikin gidan zuwa inda motarta take. * Kafa yasa ya ture table din dakin yana fadin. "Damn it" Wayarshi ta soma vibrating cikin aljihu. Ya dauko ya duba. Ayna ce. Ya daga hadi da fadin "Hello" Cikin sanyin muryarta dayake burge shi tace "Assalamu alaikum" A hankali ya amsa sallamar. Dabi.ar aina ce bata amsa hello. Tafi gane kai mata sallama. "Zanji ya jikin ikram ne. Naga baka shigo office ba" Murmushi ya kwace masa. Zai iya karantar kunyar da take ji daga muryarta. "Taji sauki. Aiki yama jana yawa a office shine nace zan dan zauna da ikram din" Ya amsa cike da jin dadin kulawar data nuna. "Allah ya bata lafiya. Sai anjima" Batama jira amsarshi ba ta yanke wayar. Ya cire wayar daga kunnenshi yana zuba mata idanuwa. Yasani. Kallon jana kawai na saukar mishi da kwanciyar hankali. Babu karya a soyayyarta da take zuciyarshi. Abinda yafi rikita mishi kai shine yanda yake jin matsayin ayna a zuciyarshi. Gani yake kaman yinin da jana take wajen aiki. Shi ya bada gap din shigar wata zuciyarshi. Shi kanshi yasan a satin nan. Dalilin fada kawai yake nema da jana. Dan hakan ne kawai zaiji kaman baici amanarta ba daya bari son wata ya shigar mishi zuciya. Kwanciya yai ya lumshe idanuwanshi. **** Kwance yake kan kujera. Kanshi na kan cinyar zainab da yake ta danne danne jikin wayarshi. "Zee saikin cinyemun chargy ko?" Lukman ya fadi yana mika hannu zai karbo wayarshi. Hannunshi zainab ta ture tace. "Dagamun cinya nima. Sai in baka wayarka" Gyara kwanciyarshi ma yai. Ta ture masa kai cikin sigar wasa. "Maza karyamun cinya." Dariya yai. "Nikam kin budemun data. Sakonni nata shigowa ko" Dariya zainab tai. Neman rigima ne kawai yasata daukar mishi waya. Whatsapp dinshi ta shiga. "Bara na dinga karanto maka sakonnin saika fadi reply din da kake so in rubuta" Zaro idanuwa yai yace "Idan kuma babyna tamun sako fa?  Saikinga sirrinmu" Murmushi zainab tayi. Tanajin dadin yanda akwai yarda da fahimta mai karfi tsakaninta da mijinta. Shekarunsu na biyar kenan da aure. Da yaransu guda daya ga na biyu nan a cikinta. Amman kullum soyayyarsu da yarda karuwa take. Sam bata da shamaki da wayarshi. Tasan lukman ko da wata tace tana sonshi saiya fada mata. Tun tana kishi harta hakura. Don tasan inya tashi kara aurenshi bata isa ta hana ba. Kuma ba boye mata zai ba. Wani sako ne yaja hankalinta. Da wani yanayi a muryarta tace. "Dee fu.ad ba abokinku bane?" Jin sunan fu.ad a bakinta ya sashi mikewa babu shiri. Wayar ya karbe daga hannunta yana fadin. "Fu.ad???" Da mamaki karara a muryarshi. Hamza ne ya turo masa wata wasika ta wata yarinya. Daga kasa yace. "Lukman anya wannan ba yar Moh bace?" Kanshi yaji ya wani bala.in sarawa. Zainab ta taba hannunshi a tsorace ganin yanda fuskarshi take dauke da tashin hankali. "Dee?  Lafiya kuwa?  Meke faruwa?" Iya saninta fu.ad wani bangare ne na rayuwar lukman da baya so a fada. Ta rasa gane alaqarsu. Tasan cewar abokinshi ne da dadewa. Hakanma wani hotonsu ne data gani ta tambaya. Koda ta bukaci ko fu.ad din na ina yanzu cayai mata tabar maganar. Saboda bai taba boye mata komai ba sai fu.ad yasata girmama rokonshi. Banda yau bata sake maganar ba kaman yanda shima bai kara ba. Lukman wani juyi yaji kanshi nayi. Babu yanda za.ai ace fu.ad nada yarinya. Ta ina?  Ta yaya?  Wacece ita. Ya dauka sofi tabar garin da jimawa saboda ya gwada nemanta bai ganta ba. Zainab ya riko jikinshi ya rungumeta sosai. Rike shi tai itama. Sumbatar gefen wuyanshi tai. Ta janye jikinta dashi tana hada bakinta da nashi da wani salo na kokarin mantar dashi koma menene. A hankali take aika mishi sakonni saida taga yadan nutsu tukunna tace. "Dee meke faruwane wai?" Numfashi ya sauke. A nutse yace. "Zan fada miki. Right now zanje inyi wani abu tukunna" Tare suka mike ta rakashi har bakin kofa. Saida ta sake tallabo fuskarshi ta sumbace shi sannan tace. "Allah ya dawomun dakai lafiya. Ka kula sosai dee" Kai ya daga mata. Ya tsugunna ya sumbaci cikinta sannan yace. "In shaa Allah. Ki kulamin da kanku. Zan kiraki" * Address din makarantarsu nana ya sake dubawa da hamza ya aiko mishi dashi. Makarantar crescent bata mishi wuyar ganowa ba. Kasancewar bata shiga lungu ba. Kai tsaye office din principal ya wuce. Suka gaisa sannan ta tambaye shi ko ta ya zata iya taimaka mishi. "Wata yarinya nake nema. Nana bansan ko da wanne suna take amfani ba dai. But anan makarantar take" Kallonshi principal din take. Yanayin nutsuwarshi da kamala shi yasa ta cewa. "Eh nan makarantar take. Amman gaskiya kayi hakuri. Saboda mamanta ta mana kashedin cewar karmu bar dan jarida ko daya yai magana da ita" Sauke numfashi lukman yai zuciyar shi na wani dokawa. "Badan jarida bane ni. Abokin babanta ne. Kuma ba sainai magana da ita ba. Ko daga nesa ne ki taimakamun in ganta" Saida ta dauki mintina tana tauna maganar tukunna ta mike tace ya biyota zuwa cikin makarantar. Kafafuwanshi har rawa suke. Baima san kalar addu.ar da yake yi ba. Bai kuma san yanayin da yake ji ba. Ta window din ajin suka tsaya. Tace masa kaganta can a front sit. Kaman nana tasan ita suke son gani dai-dai dagowar fuskarta tana dariya akan wani abu da kawarta tace. Kafafuwanshi kasa daukar shi sukai. Bangon wajen ya dafa ya tsugunna yana karanto. "Inalillahi wa ina ilaihi raji.un" Babu adadi. Idanuwanta. Idanuwanta sak irin na fu.ad ne. Yanayin dariyarta. Yarshi ce. Fu.ad yana da yarinya. Ko ina na jikinshi kyarma yake. Wayarshi ya dauko. Lambobin fu.ad da a duk tsayin shekarun nan ko saving dinsu baiba dan kar tsautsayi yasa ya gwada kira ya shiga sakawa. Dan zaune suke daram cikin kanshi. Ta london ya fara gwadawa bata zuwa. Ta europe ya saka. Bugu daya ta shiga........! **** *19/02/2017* Aikam tasan ba karamun taimako Allah yai mata ba data taho da ansar. Yan jarida ne cike bakin kofar makarantarsu nana. Dakyar ya ture su suka shiga ciki. Ba karamar godiya taima principal din ba da bata ko bari nana tasan da zuwansu ba. Bata kuma nemi wani karin bayani ba. Tadai bama sofi tabbacin cewar indai babu yardarta ba zata ma bar kowa yaga nana ba. Fitowa sukai. Cikin yan jaridun harda Yusra fari. Tana zaune a gefe hakan yasa sofi cema ansar ya bata mintina biyu. Sallama taimata. Cikin fara.arta din nan dake burge sofi ta amsa suka gaisa. Ta fada mata itace mahaifiyar nana. Sosai Yusra taji dadi. Dan a yanzun babu labarin dayaja hankalin mutane da social media gabaki daya irin na Nana. Kowa so yake yaga yarinyar. "Da zaki taimaka mana ko da mintina biyar ne. Muyi magana da ita kila zai taimaka wajen gano babanta. Abin ya kara jan hankalin mutane jin cewar baban nana dan wasan kwallon kafa ne" Cewar yusra. Wani murmushin takaici sofi tai sannan ta amsa da. "Hakan ne yasa bana son nana tai magana daku. Kema dan kina burgeni yasa nai miki magana" Cike da tausayawa yusra tace. "Nagode sosai. Ba lallai ki yarda da cewar akwai mutane da dama da kaunar yarki ne yasa su son ganinta ba. Bawai son jin labarinta ba" Jakarta yusra ta bude ta dauko katinta tace. "Please ki kirani idan kin canza shawara. Nagode sosai." Karba sofi tai sukai sallama ta koma wajen ansar. Shi ya sauke ta asibiti dan da motarshi ma suka fito. * Tunda doctor jana ta soma bayaninta babu inda baya rawa a jikin sofi. Tama kasa tambayarta wani abu. Ansar ne ma dake zaune yai karfin halin cewa. "Options nawa muke dashi doc?" A nutse doc jana tace. "Option dayane kawai ansar. Shine transplant idan an samu match" Cikin rawar murya sofi tace. "Idan ba.a samu match bafa?" Shiru doc.Jana tai. Cikin aikinta babu abinda tafi tsana banda wannan bangaren. Kallon mutane a kullum lokacin da zaka fada musu mutuwar wani nasu. Ko lokacin da zaka tarwatsa musu burinsu da magana daya. Cikin wani karfin hali sofi ta sake cewa. "Wata nawa muke dashi da ita in ba.a samu match ba?" Muryar jana can kasa tace. "Rayuwa a hannun Allah take safiyya. Zan iya cewa kasa da wata shidda. Idan Allah yai karfin ikonshi shekara daya" Mikewa sofi tai. Gaba daya kanta taji wani abu yai shiru. Bata jin duk kiran da ansar yake mata. Tafiya kawai take badon tana gane inda take saka kafafuwanta ba harta fita daga asibitin. Ita kanta ba zatace ga yanda akai ta gane motar ansar ba. Ta bude ne kawai ta shiga ta zauna. Gida ansar ya sauke ta. Saida ya tabbatar ta bude ta shiga tukunna ya koma office da wani nauyi a zuciyarshi. [4/4, 5:53 PM] Fatima saleh: *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ            04 *20/02/2017* Wani irin ciwo kanta yake mata da take da tabbacin yana da alaka da kukan datayi. Sai yau ta tabbatar rashin sanin ranar mutuwarka ba karamar Rahma bace. Ba ranar mutuwar nana aka gaya mata ba amman ji take kaman anyi yakin duniya na farko da zuciyarta. Ko ina na ciwuka ne da take da tabbacin ko da sun warke tabonsu zai kasance da radadi har karshen rayuwarta. Tana nan falo kwance Nana ta dawo daga makaranta. Ita take dauko ta. Text din da ansar yai mata cewar ta huta zai je dauko nana dinne ya sa tai zamanta. Wani gajeran murmushi ta dora saman fuskarta ta mike zaune tana amsa sallamar Nana. Tana kallonta ta cire takalminta sannan ta karaso inda sofi din take zaune. "Mumy kinga uncle tunde wai a test din maths ne naci 9.5 cikin 10. Kuma ni nasan na cinye duka 10 din" Cewar nana da take cire hijab dinta da jaka tana ajiyewa gefe. Wannan karon murmushin da sofi tayi ba iya fuskarta ya tsaya ba. Har a zuciyarta. Kallon nana take a ranta tana lissafa tsahon watannin da suke dashi. A fili kuma tace "Banda abinki nana. Ai kinci da yawa" Cikin idanuwa ta kalli sofi da yasa zuciyarta wani kai kawo a kirjinta. Da wani yanayi a muryarta tace. "Mumy meke damunki?" Murmushinta ta fadada dan tasan nana. Yanda yarinyar ke karantarta har mamaki yake bata. Maimakon ta amsa mata tambayarta sai catai. "Tashi ki sake uniform" Babu musu ta mike. Harta tafi ta dawo. "Me anty jana tace?" Kaman yanda take kiran likitar tata da a shekaru biyu da fara rashin lafiyarta sukai wani irin shakuwa. Wani abu sofi taji yazo ya tsaya mata a makoshi. Ta ina zata fara fadama yarta da bata karasa shekaru goma sha daya ba cewar babu tabbacin samun sauki a ciwonta? Wani kasalallen murmushi nana tai dayake fassara damuwa. Loosing hope. Koma me murmushin yake dauke dashi ya taba zuciyar sofi dan bata san sanda hawaye suke zubo mata ba. Karasawa nana tai ta zauna kusa da ita. Riketa sofi tai tana wani kuka marar sauti. Hawaye nana ta shiga goge mata tana fadin. "Mumy ki daina kuka. Ni banajin tsoro. Kawai ina so inga M ne" Sake riketa tai. Tunda ta fara wayau take kiran sunan shi da M kawai. Sofi tayi tayi. Tace intai kokarin claiming wani dangantaka tsakaninsu dashi zai ki dawowa. Hakan kawai na sake tsaya ma Nana a rai. Saboda tasan laifinta wajen taimakon rashin babanta a kusa da ita. Dan haka bata sake kokarin hanata kiranshi duk yanda take so ba. Dakyar ta samu tadan nutsu. Tasa hannu tana goge fuskarta. "Mumy please karki ce a.a bazan iya ba. Inason magana da yan jaridar da suke bakin school kullum" Kai kawai sofi ta iya daga mata alamar ta yarda. Dan magana ta makale mata. Rungumeta nana tai da wani murmushi a fuskarta hadi da fadin. "I love you so much mumy" Shirun dai shi sofi tai har nana ta tashi daga jikinta ta ruga zuwa dakinta. Kafafuwanta ta dora kan kujera ta hade kanta da gwiwa ta sake sakin wani irin kuka. Nana ce kadai hope dinta. Kwarin gwiwarta. Dalilinta na farin ciki. Nana ce kadai adalci data samu a rayuwarta. Ga kaddara da ba zata kautu ba na shirin rabasu. **** 21/02/2017 A kalar tukin da yake yi Allah ne kadai yakai shi kofar gidan yayanshi lafiya. Dan shi kanshi nawaf zai iya rantsewa ko hanya baya gani. Wani irin duhu yake ji cikin kanshi. Zabi daya yake dashi banda gidan yayanshi. Shine club. Saidai duhun da yake ji bai fi karfin alkawarin dayai ma Nuri ba. Yaga alama itace sanadin shiryuwarshi kuma ita zata sake sanadin komawarshi ruwa. Matakin nutsuwarshi har yanzun kokawa suke ta gaske da na rashin nutsuwar. Fitowa yai ko motar bai rufe ba  da gudu gudu ya karasa shiga gidan yana kiran. "Yaya........!" Jidderh da take kitchen tana girki taji kiran bana lafiya bane ta fito a tsorace. Kallo daya tai ma nawaf da yake tsaye hannu daya kan kugu dayan kuma cikin sumar shi. Ta karanci damuwa karara dan haka bata kula shi ba tahau sama da hanzari. Ko sallama batai ba ta tura dakin ibrahim da yake zaune yana ayyuka da laptop dinshi. "Dear ga nawaf ya...... " Bata karasa ba ya mike da hanzari. Yasan abinda zai kawo nawaf gidan shi da wannan lokacin ba karami bane. Hanyar waje ya nufa Jidderh zata bi bayanshi yai mata alama da hannu data dakata. Batai musu ba. Dan in zata fadi gaskiya yanayin nawaf kawai tsoro yake bata. * Yana ganin saukowar t.j bai jiraba ya karasa inda yake. "Yaya nuri. Nuri tana so ta kashe ni. Yaya bazan iya bafa" Ganin yanda ko ina na jikin nawaf yake kyarma yasa t.j kamashi yaja shi zuwa tsakiyar falon. Kan kujera ya zaunar dashi kaman wani karamun yaro. Ya koma da gudu kitchen ya dibo ruwa ya fito. Nawaf ya mikawa hadi da fadin. "Calm down. Sha ruwa sai muyi magana" Cike da kulawa. Babu musu nawaf ya karbi ruwan ya shanye yana maida numfashi cikin kokarin son samun nutsuwa daga halin da yake ciki. "Yaya hira fa muke. Ina bata labarin Mexico. Nine a gabanta. Amman farhan yazo mata a rai tana gayamun yana son garin...... " Dafe kai t.j yai. Dole yai magana da Nuri yake tunani. Ya nutsar da hankalinshi kan nawaf da cewa. "Calm down for goodness sake nawaf. She is yours. Taka kai kadai. Dan ta tuna farhan ba wani abu bane da zaka daga hankalinka and......... " Bai jira ya karasa ba ya mike da hanzari ya nufi hanyar waje. Binshi t.j yai ya riko yana fadin. "Ina kuma zakaje???" Lumshe idanuwanshi yai ya bude su sannan yace. "Na fada maka matsalata kana nunamun ba komai bane. I beat her up yaya! " Sakin shi t.j yai da wani shocked expression a fuskarshi yake girgiza kai. "No nawaf. Karka fadamun ka daki Nuri" Zafin da zuciyar nawaf yake yi yaji ya karu. Shi kanshi yasan baya kyautawa. A ranar daya fara dukan nuri mari ne kawai. Daga daya zuwa biyu. Wani abu yake ji cikin kanshi da baya iya controlling. Yau ya dake ta sosai. Da bata ruga ta kulle daki ba. Zai mata wanda yafi wannan. Muryarshi na rawa yace. "Yaya please help me. Bazan iya rasa nuri ba. Wallahi bazan iya rasata ba yaya" Hannunshi t.j yaja yana fadin. "Zo ka huta sai muje gidan tare" **** Tunda ta koma aiki taje ta duba ikram a dakinta taganta zaune ma tana karatun Qur.ani. Ja mata dakin tai. Fushi suke mata daga ita har babanta. Da lafiya ma ikram bamai yawan magana bace. Shi kanshi jabir din share shi tai. Dan sam bata son rikicin. Nana ce tsaye a ranta da tunanikan rayuwa da dama. Tana yin sallar isha.i ko takan abinci bata bi ba. Tadai fita ne ta kammala yaranta tasa sunyi addu.a itama tai musu. Tana dawowa dakinsu ta saka rigar bacci ta kwanta abinta. Tanajin jabir ya hauro kan gadon. Rikota yai jikinshi ta sauke wani numfashi. Juyowa tai ta fuskance shi. Idanuwanshi kawai ta kalla taga gajiyar dake cikinsu. Wata gajeriyar sumba ya manna mata hadi da fadin. "Nayi kewarki" Murmushi tai mishi "Nima haka. Nayi kewarka sosai na kiraka dazun baka dauka ba" Ya wani langabar dakai "Ke da kika dawo aiki baki bi takaina ba" Kara matsawa tai jikinshi sosai. Bata da amsar tambayarshi dan haka tai shiru. Rungumeta yai sosai. Cikin kunnenta yace. "Jana kibar aikin nan. Please ki barshi" "Honey j baka da matsala da aikina a duk shekarun na.  Me ya canza a cikin wata daya? Menene nake maka da da bana maka yanzun?" Saida ya sumbace ta sosai sannan yace. "Mubar maganar nan for now. Bana son yin fadan" Daga mishi kai tai hadi da fadin. "I love you" "I love you more" Ya fadi ya lalubi switch din dakin ya kashe kamun ya janyota su soma raya darensu cikin kauna da son juna. [4/4, 5:53 PM] Fatima saleh: *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ          05 *21/02/2017* Harya gama bubbuga kofarshi ya tafi bata bude ba. Kuka kawai takeyi. Saida tai mai isarta sannan ta tashi ta shiga toilet. Ruwan dumi ta hada ta shiga ciki ta dan jikinta ko ina ciwo yake. Yanda nawaf ya janyota daga kan kujera ya jefar kasa. Ba karamar buguwa tai ba. Zata iya rantsewa wani lokaci nawaf bashi da hankali. Zaman lafiyarsu na wata biyu ne a shekaru daya da rabi da aurensu. Inhar sunan farhan ya gifta cikin gidan sai an samu matsala. Ta rasa kalar soyayyar nan ta nawaf. Tasan da gaske yana sonta sosai. Inkuma ya daketa yana duk abinda yasan zai faranta mata. Nawaf ya mata halacci. Ba zata manta abin daya fara mata ranar farko ba. **** Ta dawo daga makaranta da yammaci likis. Tafiya kawai take amman da tana da wani waje da zata je da bata koma inda ya zame mata dole ta kira gida ba. Ta jima sosai tsaye a wajen katon flat house din da yake da bala.in jan hankali daga waje. Gidan da zaka iya rantsewa mutanen arziqi ke rayuwa a ciki. Ajiyar zuciya nuri tayi sannan ta kwankwasa kofar mai gadi ya bude mata. Ta gaishe dashi a ladafce tsohon ya amsa cike da tausayinta a muryarshi da yanayin shi. Tun kamun ta karasa cikin falon take jin shewa da hayaniyar maza da mata. Duk da hakan ba bakon abu bane a wajenta bai hanata jin sabuwar tsanarshi a ranta ba. Bata damu datai sallama ba kai tsaye ta karasa falon. Addu.a kawai take ta wuce zuwa dakinta lafiya. Bataki ace babu wanda zai kula da shigarta ba. Kanta a kasa. Muryar Alh.baushe taji yace "Nuriyya kin taso daga makarantar" Bata ko nuna alamun tajishi ba. Zuciyarta sai dokawa take. Ta tsani mutumin nan da za.a bata damar kisa shine na farko dazai fado mata a rai. Jin takunshi yasata kara sauri dan wucewa dakinta. Caraf ya rike mata hannu da duk karfinshi. "Ke ina miki magana zaki wuce ni. Ko uwarki bata isa ta wulakantani ba balle ke banza" Idanuwan nuriyya cike da hawaye take kokarin kwace hannunta. Amman kara janta zuwa jikinshi yake. Kokawa ta gaske suka shiga yi. Dayake Alh.baushe ba karamin bane. Irin manyan mutanen nan ne ya riga yafi karfin nuriyya ta ko ina. Allah ne ya bata sa.a ta gartsa masa cizo a kirji daya gigita shi. Da gudu ta nufi hanyar waje tana ihun da tasan bata da mataimaki sai Allah. Sanin halin gidan da abinda ke faruwa yasa baba maigadi bude ma nuriyya kofa cikin hanzari dan shine kadai taimakon dazai iya yi mata. Wani matashin saurayi ta hango tsaye jikin wata farar mota. Bandashi ko kare babu a unguwar. Juyawa tai ta hango Alh.baushe ya fito da gudu ta karasa wajen saurayin tana wani irin kuka. "Ke lafiyarki kuwa???" Ya tambayeta. Cikin kuka tace. "Ka taimakamun wallahi zai lalatamun rayuwa" Da mamaki a idanuwanshi yace. "Bangane ba" Kamun tai masa bayani Alh.baushe ya karaso inda suke yanata huci kaman mayunwacin zakin da ya kwana bai ci ba. Ko kallon saurayin dake tsaye baiyi ba yakai hannu zai cafko nuriyya data boye bayan saurayin. Batare da tunanin komai ba saurayin ya wanke Alh.baushe da wani irin mari. Hakan yaba nuriyya damar sake labewa bayan saurayin. A dake yace. "Wallahi ka soma taba ta zan baka mamaki" Da alamun kallon da alh.baushe yake ma saurayin yaga babu alamar wasa a bayanin shi kuma yanzun yake ji da kuruciya. Gashi in yaja maganar akai daidai to ni wani yazo wuce wa za.a iya samun matsala. Kallon da yake fassara zaki dawo gidan yai ma Nuri sannan ya juya. Hankalin shi saurayin ya maida kan Nuri dake wani irin kuka cike da tambayoyi da yawa yace. "Meye hadinki da wannan mutumin?" Ta kasa amsa shi wani irin kuka take da yaji yana ci mishi rai. Hannunta ya kama ya bude motar shi ya sakata. Zagayawa yai ya zauna. Ya dauko ruwa dake gefe ya mika mata hadi da fadin. "Ungo ki sha" Batai musu ba ta karba ta sha sosai. Ta bude motar ta wanke fuskarta tana ta sauke ajiyar zuciya. A sanyaye yace mata. "Sunana nawaf" "Nuriyya" Ta amsa shi muryarta a dakushe. * Sallama taji data dawo da ita daga tunanin da takeyi. Kamun ta amsa an sake yin wata. Da sauri ta tsane jikinta ta fito daga ban dakin. Doguwar riga ta zura ta dauki karamun hijab tasa da sauri ta fito tana amsa sallamar. A kunyace tace. "Yaya sannu da zuwa. Wallahi ina wankane shisa kaji shiru. Ina kwana" Kallon ta t.j yake sosai. Wani jini ne ya taru gefen fuskarta harya soma baqi baqi. Ya girgiza kanshi cike da takaici. Waje ya samu ya zauna kawai. Nuriyya ta zauna nesa dashi tana fadin. "Ina anty jidderh?" Numfashi t.j ya sauke yace. "Tana lafiya nuriyya. Ya kike?" "Alhamdulillah" Ta amsa tana dorawa da. "Sai dai nawaf din ya fita" Kallonta t.j yai sosai a nutse yace. "Gidana yaje nuriyya. Me yasa baki taba ko da kirana kin fadamun nawaf na dukan ki ba?" Kanta ta sunkuyar kasa. Taya zata fara kai karar nawaf? Tace me? Gani yai bata da alamar amsa shi hakan yasa shi ci gaba fadin. "Nuriyya yanda yaimun bayani kaman farhan ke yawan kawo matsala tsakanin ku. Kinga dai yanda nawaf yake. Kece abu na farko a rayuwarshi data raba shi da addiction din da mu munyi iya bakin kokarinmu mun kasa. Nuriyya nawaf yana sonki. A kalar nasa haukan. Dan Allah kiyi kokari sunan farhan ya daina fitowa daga bakinki a gabanshi kinji ko?" Muryarta can kasa tace. "In shaa Allah yaya. Mungode sosai. Allah ya kara girma" Mikewa t.j yai yana fadin. "Bakomai nuriyya. Inya sake dukanki ko ki kirani ki fadamun ko jidderh. Ko kizo gidana kinji ko?" Kai nuriyya ta daga masa. Yai mata sallama ya fice. Ta sake lafewa cikin kujera. Ko dan karamcin da yan uwan nawaf suka nuna mata kadai ya isa ta shanye duk wani abu. Ballantana son dashi kanshi nawaf din yake mata. **** *20/02/2017* *EUROPE* Number din lukman ya sake dialing a karo na babu adadi. Daga zuciyarshi har brain dinshi abu daya suke gaya masa. Dan haka bai musu gardama ba. Kasancewar suna hutu ya kara saukaka mishi abin. Kayanshi yake hadawa amman hankalinshi ba kan abin yake ba. Ko menene yasa lukman kiranshi ba karami bane ba. A karo na farko a rayuwarshi dazaiyi abinda wani ya umarce shi dashi. Bai taba ba yaune zai zama tarihi. Passport dinshi ya dauka da duk wasu kana nan abu da yasan zai amfani dasu. Cab ya dauka zuwa airport. Ba abokai gare shi daya damu da susan matsalar shi ba. Logan kawai yaima text cewan zai je gida wani abu ya taso. Shima yana ganin ya shiga ya kashe wayar gabaki daya. Shi kanshi bashida amsar tambayoyin daya san Logan din zai masa. Ba karamar sa.a yaiba da ya samu jirgin dazai tashi cikin awa biyu. Dan haka ya samu waje ya zauna. Shi kanshi bazaice ga kalar tunanin da yake ba. Saboda babu wani wadataccen nutsuwa a tare dashi. Shekaru goma sha daya. Yanda rayuwar take tafiya kawai ma ya isa ya baka mamaki. **** *21/02/2017* *NIGERIA* Har jirginsu ya tsaya fu.ad ji yake kaman a mafarki. Wai da gaske ya shigo jirgin zuwa nigeria. Da gaske kafafuwanshine a kasarshi. Kasar da bai taba zaton zai sake waiwayarta ba. Yana sakkowa daga kafar jirgin rayuwarshi na gifta masa cikin idanuwanshi. Tsayawa yai yana kallon airport din. Ya lumshe idanuwanshi yana shakar iskar kasarshi. Yanajin yanda dumin zafin ranar ke busa shi. A hankali kaman wanda aka kunnama film farkon rayuwarshi ya dawo mishi.............!!! [4/4, 5:56 PM] Fatima saleh: *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ               06 Fu.ad arabi shine yaro na hudu cikin yaya bakwai da Alh.salman arabi da haj.aisha suka mallaka. Alh. Salman da dan asalin garin kano ne kauyen bichi. Sai haj.aisha ita barumiya ce yar asalin garin katsina. Anas shine dansu na farko yana aiki da NNPC da matarshi da yaranshi biyu. Fatima da nurse ce itama da aurenta da yara guda biyu. Haneef da yake shekararshi ta karshe a makaranta. Fu.ad, pha.iza da tagama secondary school dinta. Hassana da hussain yan biyunsu da suke aji hudu kuma sune karshen haihuwa. Alh. Salman basuda yawa gidansu duka su ukune shine babba sai yan biyunsu duk maza. Babansu shahararren dan kasuwane kamun Allah yai masa Rasuwa. Shi kadai ya gado babansu. Wato harkar kasuwanci. Kuma Allah yai masa albarka. Dan yana da gidaje da filayen da shi kanshi inba takardubaka dauko ba bazai ce ga yawansu ba. Dai-dai gwargwado daga alh har haj sun iya bakin kokarinsu wajen ganin sun ba yaransu tarbiyya da ilimi na bokon da addini. Fu.ad ya fita daban da sauran yan gidansu. Tun tasowarshi bashida aiki sai buga wasan kwallon kafa. Yasha kin zuwa makaranta akan wasan ball. Tun suna duka da fada har suka gaji suka soma bashi goyon baya. Tun yana aji hudu secondary ya soma jagorantar garin kano fita kwallo garuruwa. Nasarorinshi sun soma daga shekaru kasa da sha takwasa. Sanda ya shiga aji shidda secondary lokacin ya samu daukaka zuwa kasar Europe. Dole su Alh.salman suka kyale fu.ad ya tafi. Dakyar ya dawo ya zana jarabawar waec kadai. Can ya nemi gurbin karatu. Classes dinshi ma online yake yinsu saboda rashin lokaci. Yakan dawo gida daya samu lokaci. Ya kasance da girman kai da tsanar talakawa wanda haj.aisha da alh.salman ke dangantawa da kudin da yake dasu a shekaru ashirin da biyu. Don su duk arziqinsu mutanene masu saukin kai da girmama dan adam. Labarin zai fara ranar da fu.ad ya cika shekaru Ashirin da biyu a duniya. **** *22/12/2005* "Kasan na kusa tafiya wallahi" Cewar lukman da alamun kosawa a muryarshi. Dariya fu.ad yai da ko gezau maganar lukman din bata shige shi ba. A nutse yake daura takalmin shi. Wani tsaki lukman yaja. "Wanne irin iskanci ne wannan? Ka tara mutane wajen minti talatin ka tsaya yanga. Banza kawai" Bai daice komai ba. Banda lukman din babu wanda ya isa ya tsaya saman kanshi yana mishi wannan maganganun. Lukman abokinshi ne tun suna yara dan makotane. Abokantakarsu ta kara karfafa zumunci tsakanin iyayensu. Ko yanzun da fu.ad ba cika zama yai ba. Bashida wani abokin daya wuce lukman. Bama mai jure zaman kwana biyu da halayyarshi. Dagowa yai ya sauke idanuwanshi da suke ruwan kasa masu wani irin haske kan lukman. "If you will stop nagging for a minute zakaga nagama shiryawa" Harara lukman ya watsa mishi. Ya bude kofar ya fita fu.ad yabi bayanshi. Har sunkai kofa ya tuna yabar wayoyinshi. Da gudu ya juya dan ya dauko dai dai tahowar atika mai aikinsu da sam bata kula da fu.ad din ba. Karo sukai har saida ta fadi. Jikinta na rawa ta mike tana bashi hakuri. Wani irin mari ya dauke ta dashi. "Daqiqiyar ina ce ke?" Lukman ya karaso da sauri ya ture shi. "Atika jeki please" Idanuwan yarinyar cike da hawaye ta wuce da hanzari. Wanu kallo lukman yai masa. "Tir da halinka wallahi. Kaifa ka tureta still ta baka ha....... " Katse shi fu.ad yai da fadin. "Karka sake batamun mood ranar birthday dina. Ka rike wa.azinka banaso. Muje kawai na fasa daukan wayan" Girgiza kai kawai lukman yai suka fita. Ganin Benz din da suka tunkara yasa lukman yima fu.ad kallon baka da hankali. Dafe kirji yai. "Na shiga uku ni lukman. Dan ubanka da wannan motar zakai stunt?  Rashin sanin darajar kudi ko?" Fu.ad ya kwashe da dariya. "chill mana. Birthday ina ne fa. Da ita dai zamu fita. Hamza nacan da motar da zan amfani da ita. Banaso momma tai fadane" Lukman ya bude baki yakai sau uku yana rufewa. Dan ya tabbatar motar dazai ragargaza tafi miliyan biyar. Mota ya bude ya shiga da fatan shiriya wa fu.ad a ranshi. * Suna karasawa wajen fu.ad ya fito aka rudewa da sowa da ihu. "Moh!  Moh!! Moh namu!!!" Kaman yanda suke kiranshi. Wani murmushi ya kwace masa. Sabon girman kai na kara ratsa shi. Ko minti goma basuyi ba. Lukman na gefe yana kallon yanda fu.ad din keta gaisawa da jama.a cikin yangarshi. Wayarshi ta dau ihu. Ya fito da ita ya matsa nesa saboda hayaniya dan yaga pha.iza ce. Dauka yai da sallamarshi. "Yaya lukman in kuna tare da Yaya fu.ad kuzo yanzun Hajiya babba ce ta rasu yanzun Abba yayo waya" Salati lukman yahau yi. Jikinshi yai sanyi sosai. Ya kasa ma amsa pha.iza harta kashe wayarta. Hajiya babba kakarsu fu.ad ce sukanje bichi gaishe da ita da yan gidansu fu.ad. Tsohuwar akwai kirki da karamci. Lokaci yayi. Yakai mintina biyar a wajen yana tuno haj.babba da kirkinta. Jiki ba kwari ya karasa wajen da fu.ad yake da suke shirin fara wasan su da mota yace mishi yazo. "Koma meye ya jira ni in gama abinda zanyi" Fu.ad din ya amsa rabin hankalinshi kan lukman. "Haj babba ce fa Allah yai mata rasuwa shine momma tace muje yanzun" Fito da idanuwa waje fu.ad yai hadi da fadin. "Holy crap. Dammit. Bad timing hajiya. Why yanzun?" Lukman kaman ya kwada mishi mari. Halayyar fu.ad saikace kara lalacewa take ma duk rana. Wato bama mutuwar bace ta shige shi. Yana kallo ya wuce yai magana da hamza sannan ya dawo. Suna mota yana fadin. "Tsohuwar nan tamun tsiya wallahi. Ran birthday dina" Lukman da yake ta ma hajiya babba addu.a ya juya ya kalli fu.ad kamun ya maida hankalinshi kan tuqin da yake hadi da fadin. "Shekaru nawa amman kana surprising dina wasu lokuttan wallahi. Kakarka ce fa. Ita ta haifi abba. Haba fu.ad mutuwa tai ita. Kai tunanin banzan party dinka kake?  Addu.a ma baka san kayi ta ba?  Kaima zaka mutu" Tabe baki yai alamar bai shige shi ba yai rolling idanuwanshi yace. "Whatever. Allah ya jikanta. Bakada aiki sai wa.azi saikace dan gidan limamai" Lukman bai kara kulashi ba har suka kai gida. Dan yasan zasu iya yin rikici inya biye masa. **** Da lukman din suka tafi bichin. Waya kadai yaiwa mamanshi ya fada mata rasuwar. Itama tace zasu biyo su a baya. Fu.ad ne ke tuqin wannan karin. Lukman na gefe. Sai yayar fu.ad din anty fatima da wata cousin dinsu anti maryam. Kukan da suke ya soma kular da fu.ad. Dan shi baiga abin kuka ba. Shekarar hajiya nawa a duniya.  Aita sha miya a ganinsa. Basu tsagaita da yan koke kokensu ba saida suka dauki hanya sosai. Banda lukman dayaima fu.ad magana daya rage gudu su anti fatima ko kula ma basuyi ba. Bai kuma rage gudun ba. Har suka shiga garin bichi duk lungun da suke bi fu.ad bai rage gudu ba. Ba kuma ya horn inzai shiga kwana. Ido lukman ya saka masa. Suna karya wata kwana wani babban mutum magidanci da itace akanshi. Rashin horn din da fu.ad baiyi ba yasa bai kula da shigowarsu ba sai a kurarrwn lokaci. Da hanzari yai kokarin kaucewa. Itacen kanshi na watsewa kan motar su fu.ad din da ko ina. Wani mugun birki fu.ad ya taka daya razana su anti fati. Motar ya bude a fusace ya takasa wajen mutumin daya fadin kasa. Ya tashi yana kakkabe jikinshi. Dai dai fitowar su anti fati daga mota ji kake wani. Tas! Fu.ad ya dauke mutumin da a haife ya haifi irin fu.ad din uku da mari. "Baka ganin motane?  Wanne irin jahilci ne wannan?" Daga anti fatima har su lukman suka karaso wajen da salati. Marin fu.ad anty fatima tai tana salati da girgiza kai da danyen aikin da fu.ad yayi. Mutumin ta kalla da yake rike da kunci yana kallon fu.ad da mamaki a fuskarshi. Hannu fu.ad ya daga lukman ya rike shi a tsawace yace. "Haba mana fu.ad ya isa haka. Wanne irin masifa ne wannan" "lukman daka kyale shi ya rama marin. Dan wallahi ba wata rashin kunya dazai nunamun kuma" Kallonsu fu.ad yai a kyamace ya wuce ya koma mota yana huci. Har kasa anty fatima ta tsugunna tana ba mutumin hakuri. Su duka suka hada baki har da lukman. Mutumin ya jinjina kai. "Bakomai yata. Kuje kawai Allah ya shirya" Mota ta koma ta dauko kudi a jakarta ta dawo inda mutumin ke tattara itacen shi. "Baba ga wannan" Ya dago ya kalleta. Ya girgiza kai yace. "Nagode 'ya ta amman bazan karba ba" Wasu hawayen takaici suka zubo ma anty fatima. Ta goge su ta tsugunna murya na rawa tace. "Badan abinda kanina yai maka ba baba. Kyautatawa ce dan girman Allah ka karba" Ya jima yana kallonta kamun yasa hannu ya karba yace. "Nagode" Ta juya ta shiga mota. [4/4, 5:56 PM] Fatima saleh: *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ                  07 "Fu.ad yaushe ka kara lalacewa haka? Wancan mutumin bai isa ya haifeka ba har zaka iya daga hannu ka mareshi?" Anty fatima ke fadi rai a bace. Wani numfashi yaja da alamun relief. Yace "Thank God bashi ya haifeni ba. And karki sake dagamun hannu ba yaro bane ni" Wani abu ya tokare mata wuya. Anty maryam tace. "Fu.ad rashin kunya ko?" Juyowa yai daga inda yake zaune ya watsa mata wani kallo hadi da fadin. "Mind your own fucking business" Fu.ad ke rashin kunyar amman lukman dake zaune shi yake jin kunya. Gabaki daya ji yake daman motar su pha.iza ya shiga da baiga wannan bacin ran ba. "Ka wuce muje fu.ad. And do us a favour kayi shiru muji da abu daya" Lukman ya fadi ya juya ya kalli anty fatima dake sharar hawaye. Anty maryam kuma tayi tsuru tsuru a gefe yace. "Dan Allah anty kuyi hakuri. Abar maganar nan. Muji da abu daya" Kai kawai anty fatima ta daga. Fu.ad ya wani fizgi motar duk yana gwara su da jikin motar. "Maza kashe mu to" Lukman yace rai bace. Ko kula shi baiyi ba. Kawai tafarfasa yake a ciki. Kaman shi anty fatima zata daga hannu ta mara akan wani tsohon daqiqin talaka. Ya tabbata da basu hada jini ba saiya rama marinshi. Kuma sai yasa an kulle masa ita. Suna karasawa ya samu waje yai parking. Mutane ne cike unguwar kaman zata fashe. Anata alwala kasancewar yamma tayi sosai. Dan a hanzarta akaita makwancinta. "Ku nemi wani ride din home" Fu.ad ya fadi bai jira amsarsu ba ya fice ya doka murfin motar da karfi har wasu dake gefe suka juyo suka kalle shi. "What?!!!" Ya bukata a tsawace. Suka sadda kansu kasa. Yace yan sa idon banza kawai a ranshi. Fitowa su anty maryam sukai sunata kuka. Dan yanzun mutuwar ke kara shigarsu da wani sabon yanayi. Basu bi takan fu.ad ba suka wuce abinsu. Lukman yazo ya raba zai wuce shima fu.ad yace. "Ina kuma zakaje? Aika tsayani ko?" Cikin idanuwa lukman ya kalle shi. "After abinda kai wallahi kunya nakeji ace tare muke" Yana gama magana ya wuce abinshi. Wani mutum yai ma sallama suka gaisa ya karbi butar hannunshi da fu.ad ke jin ai ko wajen zai hade bazai iya wanke ko takalmi da ruwan ciki ba. Ballantana har azo ga jikinshi. Allah kadai yasan daga inda butar ta fito da kuma kalar germs din dake jiki. Motarshi ya bude ya dauko robar faro daya sabuwa. Ya rufe motar. Wajen ya karema kallo dan baiga inda zai tsaya yai alwala ba. Da alamar tsantsar takura a fuskarshi ya hango wani dutse. Ya karasa wajen ya zauna ya kwance takalmin kafarshi. Alwala yai sannan ya mayar da komai ya daure takalmin. Haneef ya hango ya karasa wajen shi. Wani kallo haneef yai masa daga samanshi zuwa kasa. "Ka cire wannan glass din" Haneef yace yana dauko mukullin motarshi daga aljihu. Ya mika masa. "Car dina yana bayan can. Kaje ka dauko takalmi ka cire na kafarka" Kabar mukullin motar yai daga hannun haneef muryashi can kasa yace. "Bana so ana fadamun abinda zanyi. And menene matsalar takalmina?" Wucewa haneef yai ya kyale shi. Gaba daya gidansu haneef ne baya jurar rashin kunyar fu.ad. Bashi bane babba amman har su anty fatima suna ganin girmanshi. Saboda yanada hankali. Magana ma sai dole yake yinta. Baya shiga harkar kowa. Kuma sunfi shakuwa da fu.ad. Ko a yarinta in fu.ad ya janyo rigimar data fi karfinshi haneef din yake shigar masa dole. Shi da kanshi yakan rasa ta ina haneef yake bullowa sanda yake bukatarshi. Wucewa yai ya dauko takalman haneef din yan zire. Ya saka da alkawarin suna dawowa jana.iza zai sake su. Dan sun bala.in bata mishi shiga. Badon haneef bane bama bazai sake ba. * Suna dawowa yaje ya sake takalmanshi. Bai nemi lukman ba. Shima yai zuciyar kowa yai harkar shi. Haneef ya lalubo dakyar saboda taron mutane. Ya mika mishi mukulli yana fadin. "Saikun taho" Da mamaki haneef yace. "Meaning?" "Gida zan tafi. Yunwa nake ji like sosai fa" Jinjina kai haneef yai. "Wai yaushe zakai hankali? Will you go and remove that shoe ka dawo a zauna dakai. Kama ga abba?  Ka mishi gaisuwa?" Kaman fu.ad zaisa ihu yake kallon haneef. "Abba gaisuwan me zan mishi? Bana zo ba anyi jana.iza and dare yana yi fa" Wani murmushin takaici haneef yai. Muryarshi da alamun gajiya yace "Anan zamu kwana har sai anyi sadakar ukku" Wani pale fuskar fu.ad tai. Ya kwana uku a ina?  Wannan garin da tun daya mallaki hankalinshi zai iya kirga zuwansa. Ya bude baki ya tabbatar ma haneef da cewan ya samu matsala inhar yana tunanin zai kwana daya ma ba uku ba a wannan kauyen. Kaman daga sama sukaji muryar abba yace. "Yawwa fu.ad ka kira lukman kuzo zan aike ku" Juyawa yai da fara.a a fuskarshi yace. "Abbah..." Fu.ad ya fadi da farin cikin ganin mahaifin nashi. Dan tunda yazo yau sati daya kenan bai saka shi a ido ba. Da sassafe ya tafi wajen training kamun ya dawo kuma ya fita. "Fu.ad lemuka zaku siyo da ruwa. Sai nama kadai samu mamanku ko ka kirata a waya saita lissafa maka" ATM baba yake kokarin daukowa a aljihu fu.ad yace. "No abba. Zan siyo kome ake bukata. Kabarshi kawai" "Allah yai maka albarka. Ya kara daukaka kaji" Ya amsa da amin. Abbah ya maida hankalinshi kan haneef. "To kai muje ko da za.ai wani abun" Lukman ya kira harta yanke bai dauka ba yai mishi text. "Idiot. Abbah ne ya aikemu to mu hadu mota" Momma ya kira ta fada mishi abubuwan da suke bukata. * Har suka gama siyayyarsu tas lukman bai kula shi ba. Suka koma gida dan su dauko kayan sakewa. Gaba daya fu.ad ji yake an takura ma rayuwarshi. A ina zai kwanta ma?  Me zaici a ina zai wanka? Cake ya kwasa leda biyu ciccike ya dibi cincin da yoghurt da yawa. Zaka rantse sati biyu zaiyi. Yawan training din da yake yi yana burning mishi energy da wuri. Yasan abinda ya diba ya masa kadan. Balle ba wani abincin kirki bane. Ko kaya kala takwas ya diba dan baya iya wuni da kaya daya a jikinshi. A mota ya samu lukman zaune. Lokacin anata kiran sallar isha.i. "Ko muyi sallah mu sauke nauyi?" Fu.ad ya bukata. Kallon shi lukman yai ya fito daga mota sannan yace. "Da ace yanda kake kyautata sallah haka halayyarka take da kaji dadi" Dariya abin yaba fu.ad sosai. "Halina is just fine dan rainin hankali. Ka gama fushin kenan" Yamutsa fuska lukman yai. "You disgust me. Ewww" Da gudu fu.ad ya bishi ya ruga yana dariya. * Waje suke zaune har wajen tara da wani abu na dare. Haneef na kallon yanda fu.ad ke sosa hannuwa alaman sauro ya ishe shi. Dariya yai kasa kasa. Tabararren banza ya fadi a ranshi. Gani yai abun yai yawa dan shi kanshi sauron ya dame shi. Balle kuma fu.ad da kwata kwata bai saba shiga irin wannan wajajen ba. Kallon shi yai shida lukman yace. "Ku tashi muje in kaiku inda zamu kwana ko?" Ba musu suka tashi. Gidan wani dan uwan baban sukaje bayan gidan hajiya babba. Saboda cikin gidan hajiya babba mata ne kawai. Kasancewar daga ita sai yan aikinta da take da rai. Sai wasu yayan dangi da take rikewa. Gidan ba wani babba bane can. "Tafdi" Fu.ad ya fada ganin gidan da suka tunkara. Wani saurayi da zai kai tsaran haneef da sai lokacin fu.ad ya kula dashi. Ya karasa ya bude wani shago jikin gidan da kyauren langa langa. Hannun haneef yaja gefe. Kaman zai kuka. "Kasan bazan iya kwana anan ba ko?" Ya karasa yana nuna shagon da hannu. Hannun haneef ya kama ya sauke kasa yace. "Last i check baka da wani option. Inkuma zakaje kace ma abbah ba zaka kwana bane saika dawo" Kasa ya kara yi da muryar da yakanyi amfani da ita ya samu abinda yake so wajen haneef din da suna yara. "In tafi gida. Da sassafe in dawo" Kallon baka da hankali haneef yai masa. "Please..... " Yanda haneef ya zaro ido zai tabbatar maka da fu.ad fadin please din nan da fu.ad yai abune mai bala.in wahala a wajen shi. Numfashi ya sauke. "Ka hakura fu.ad dare yayi wallahi. Gobe in Allah ya kaimu saika koma gida" Yanda yai da fuska yaba haneef tausayi. Dan yasan bai saba ba sam. Kama hannunshi yai kaman yaro. Yaja shi zuwa cikin shagon. Ko ina share yake tsaf. Da leda a shimfide sai katifa an lailayeta da zanin gado. Kusurwar dakin jakunkuna ne da wasu kaya a rataye jikin kusa. Sai takalmansu can gefen wni bango kan siminti wajen da alamu ledar dakin bata kai ba. Haneef ya karasa ya cire takalminshi ya ajiye inda yaga masu shagon na ajiye nasu. Ya koma kan katifar kusa da lukman ya zauna. Fu.ad suka kalla tsaye kofar dakin. Idanuwan nan nashi kalar na turawa sun wani yi haske. Suka bushe da dariya. Baice musu komai ba dan ya kusa kuka. Ya fara takawa da takalmin bai ko kula haneef dake mishi magana ba. Wani farin hanky ya dauko daga aljihunshi kato ya shimfida kan zanin gadon dake jikin katifar sannan ya zauna kaman wanda zai hau k'aya. "Kai da zakai birkida kan katifar. Meye na saka hanky kuma. Ko kan leda zaka kwana?" Cewar lukman da ya sake bushewa da wata irin dariya. "Fuck you and damn your mouth" Fu.ad ya fadi yana kai mishi duka. "Manners fu.ad. Kamata yai ace momma na wanke maka bakinka da sabulu" Haneef da yake dariya shima ya fadi. Pillow din dake gefe fu.ad ya dauka ya jefa masa a fuska ya kauce pillow din ya samu lukman. Dauka yai ya rama suka soma hauka cikin dakin haneef ya musu ihu. "Dan kaniyarku mutuwa akai mana fa. Kuma ba a gida kuke ba. Ku nutsu please" Dakyar haneef ya samu fu.ad ya cire takalminshi yabar socks. Ga katifa daya su uku. Ga sauro. Tashi fu.ad yai ya hada kanshi da gwiwa kawai yana jira gari ya waye. [4/4, 5:56 PM] Fatima saleh:    *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ          08 Lukman ne ya zo gyara kwanciya yaga mutum a zaune. Idanuwanshi ya ware sosai. Ya lalubo wayarshi ya haska. "Fu.ad?" Ya kira muryarshi cike da bacci. Dagowa fu.ad yai ya kalle shi da idanuwanshi cike da bacci. "Ka kwanta mana" Ya yatsine fuska. "Bazan iya bacci anan ba lukman. Ga zafi ga sauro. Wajen kuma ya matse da yawa. Just go back to sleep i will manage" Girgiza kai yai alamar eh. Haneef dake bacci gefensu ya motsa saboda yanajin maganganu sama sama. "lafiya?" Ya tambaya yana kare idanuwanshi daga hasken fitilar wayar lukman. "Fu.ad ne wai bazai iya bacci ba" Cewar lukman. Wani guntun tsaki haneef yaja. Matsalolin fu.ad yawane dasu. Pillow kawai ya ja ya sauka daga katifar zuwa kasa. Lukman ma pillow ya dauka ya sauka kasa kan leda. "Ku dawo bacci ne bazan iya ba. Zafi ga sauro" Fu.ad ya fadi irritated. "Ka kwanta malam" Inji haneef. Girgiza kai yai. Yasan taurin kan fu.ad kaman yunwar cikinshi. "Lukman tashi mu koma. Dan ubanka karka kwanta" Baccinsu suka koma suka kyale shi. Shikam daya fara baccin ma farkawa yake. Ga kanshi na wani irin ciwo. Kan kunnenshi aka kira sallar asuba. Ya tashi su haneef. Abu dayane matsala. Bandakin dazai shiga. Haneef suka bari dakin suka fita zuwa motar fu.ad din cewarshi zai dauko ruwan dazai alwala. Suna hanyane yace. "Damn. Wallahi nabar brush dina. Ban dauko komai ba" "Karka damu. Sanin halinka yasa na dauko extra" Numfashi fu.ad ya sauke. Sukaje suka dauko. Suka koma. A bakin shagon sukai brush dinsu. "haneef fitsari fa nake ji" "zo ga bakina. Kayi a ciki" Lukman ya bushe da dariya. Wani mugun kallo fu.ad ya watsa mishi kamun yace. "wallahi da gaske. Lokacin sallah na wucewa" Cikin shagon haneef yakoma ya kira khalid mai shagon. Ya tambaye shi ko da akwai bandaki kusa sannan ya fito. "Saika taso" Ba musu ya tashi ga mamakinshi cikin shagon suka koma. Haneef ya bude wani kofa da duk zatonsu wadda zata kaika cikin gida ce. Ban dakine dan matsakaici. Shafe da siminti. A bushe yake tsaf. Bokitin karfe a gefe sai kwandon soso. Sai masai irin namu na gargajiya da murfi a rufe. Wani baya fu.ad yai yana bata fuska kaman zaiyi amai. "Karka cemun anan zanyi fitsari" Takaici ya hana haneef magana. Fita yai yabar masa shagon. Ya fito ya samu lukman yace. "Seriously kana kokari. Ya kake baka fasa bakin fu.ad ne?" Dariya lukman yai ya girgiza kai. Suna nan fu.ad din ya fito fuskarshi a yamutse. "Allah ya kiyaye in ban kwashi infection ba. Ina komawa gida zance asibiti a mun check ups" Fu.ad ya fadi yana samun wani dutse ya zauna zaiyi alwala. "Asibitin murtala ka kwasa ba infection ba" Haneef yace yana masa kallon ka kure rainin hankali. Wannan karon harshi fu.ad din saida ya dara. Tare sukaje asuba suka dawo. Fu.ad nason yadanyi gudu ko ya yake. Nan fa shi dole saiya cire dogon wandon shi yabar gajere da singlet. Ba yanda haneef baiba tunda baizo da kayan gudu ba. Ko yaje dana jikinshi ko ya hakura yaqi. "Idan baka kwashi infection a bandakin nan ba. Zaka makalo a jikinka ne" Lukman ya fadi. Ai ba shiri ya dauki kayanshi ya maida yace ma lukman suje. Tare suka fita gudun. Sun sami wajen awa daya. Dan gari ya fara wayewa. Mike hanya kawai sukai. Dan ma lukman na dan taba kwallo lokaci lokaci. Duk da haka s yana ce ma fu.ad yadan rage gudu. Fu.ad yaji takalminshi yadan kwance. Dan haka ya tsaya ya gyara. Lukman yake ma dariya dayai ma nisa. Tsayawa yai yana jiranshi. Kaman daga sama yaji saukar wani ruwa mai danqo danqo tun daga wuyanshi har bayanshi. Wani numfashi yaja na mamaki. Lokaci daya wani bacin rai ya maye gurbin mamaki. "What the hell!!!......" A fusace ya juya ya sauke idonshi kan yarinyar dake tsaye kofar gida da wata tukunya da bayanta ya gaji da yin baqi. Yanayin fuskarshi kawai ta kalla tace. "Na shiga uku ni safiyya. Wallahi banganka ba" Ta fadi tana zaro idanuwanta. Baisan me ya kamata ya fara yi ba. Gaba daya gefenshi a jike yake. Ruwan koma menene har cikin sumarshi da yake bala.in ji da ita. Har gefen fuskarshi. Da tashin hankali lukman ya karaso yana rike baki. "Fu.ad......" Ya kira da alamomi da dama. Ban hakuri. Tsoro da jimamin abinda zai auku tun kamun faruwarshi. Takawa fu.ad ya soma yi zuwa inda yarinyar take. Numfashi yake ja yana fitarwa. Yana kokarin calming kanshi. Idanuwanshi harsun kara hasken nan da sukanyi idan ranshi yakai karshe wajen baci. Lukman ya riko masa hannu yana fadin. "Please fu.ad......." Kwace hannunshi yayi. Ganin datai ya tunkaro ta har yana gab da ita yasa ta tura masa tukunyar. Da sauri ya rike tukunyar da ta rigada ta gama lalata masa gaban riga. Cikin gida ta kwasa da gudu. * "Innaaaaaa!" Take kira da tashin hankali. Sanin cewar safiyya bamai kwaramniya bace ba. Yasa inna fitowa da sauri dan taga ko lafiya. Bayanta safiyya ta labe tana sharar hawaye. "Ke wai lafiyarki. Meya koro ki?" Inna ke tambaya tana kokarin janyo safiyya daga bayanta. * Ganin fu.ad rike da tukunya a hannu yana danna kai gidan mutane yasa lukman riko shi. "Fu.ad gidan matan aure ne fa. Dan Allah kayi hakuri kazo mu tafi" Juyowa yai da tukunyar a hannu. "wallahi ko ka sakeni ko in kafta maka tukunyar nan. Like hell inyi hakuri" Ganin ran fu.ad ya gama bi yasa lukman sakinshi. Yasan ba.a tempting maganar shi. Tsaf zai kafta masa wannan bakar tukunyar. * Inna nata kokarin banbaro safiyya daga bayanta amman ina. A banza sake makalewa take tana share hawaye. Tafiya inna taji data sata kallon shigowar fu.ad rike da tukunya da hannuwa duka biyu. Ga rigarshi da take fara kal ta gama tashi daga aiki. Jikinshi daga gefe rabi a jike. Dafe kirji inna tai. "Na shiga uku ni lami. Safiyya badai ruwan dan waken bane kikai masa wanka dashi???" Tukunyar fu.ad ya ajiye a kasa. Yana kare ma gidan kallo. Gidan kasane na asali ma kuwa. ko shafe babu a kasan gidan. Kaurayen langa langa. Duk da tsaf yake babu shara. Akwai komatsai cikin gidan. "Dan Allah dana kayi hakuri" Inna ta fadi a raunane. Dan kallo daya zakaima fu.ad kagane hutu da kudin dake tattare dashi. Ga wata isa da gadara dake fita daga jikinshi kaman hayaqi. Daga ma inna hannu yai. "Karki sake hada sunanki da nawa a waje daya. And bake kikaimun laifi ba. Yarki ce da take labe bayanki. Hakurin daga bakinta nake son ya fito" Kallon shi inna take baki a sake. A ranta tace safiyya ta janyo musu bala.i. Wannan tsageran kuma ko daga ina ya fito oho. Da alama dai bako ne a garin dan ko kala kalarshi bata taba gani ba. Safiyya ta fisgo. "Bashi hakuri...." Hawayenta safiyya ta share. Ta sauke idanuwanta cikin na fu.ad. Ta kasa magana saboda tunda take sau daya ta taba ganin mai irin idanuwanshi. Shima aikenta siyan ruwan sanyi akai da azumi gidan malam.mudi ta samu suna kallo. Aka nuno wani bature har tana mamakin kallar idanuwan. Kallon da take masa yasa shi yaji wani iri. Lokaci daya yaji abinda bai taba ji ba a zuciyarshi. Wani squeezing yaji tayi har numfashin shi na son tsayawa. Idanuwanshi ya lumshe dan wani abu dake fizgarshi cikin nata. Dai dai shigowar lukman dayaga shirun yai yawa kar ace wani danyen aikin lukman yayi. Dan yasan kadan da aikin shi. Inna lukman yace ma. "Ina kwana" A mutunce ta amsa ta dora da. "Yaro dan Allah kuyi hakuri. Wallahi safiyya bamai kwaramniya bace na tabbatar da kuskure ne" Hannun fu.ad da yake tsaye kamar an dasa shi lukman yai. Tunda har Allah ya tsare baiyi wani rashin mutuncin ba. Fu.ad kam duk wani rashin mutuncin dayai niyya yanajin shi yana narkewa. Saidai koma menene ba.a masa laifi a tafi a banza. Fisge hannunshi yai yace. "Sai tabani hakuri. Wallahi sai taban hakuri" Da sauri safiyya ta sauke idanuwanta daga cikin nashi jin maganar dayayi. Wani yanayi take ji. Kaman zazzabi ya kamata. Muryarta a sarke ta tsugunna gaban fu.ad tace. "Ka...ka kayi hakuri dan Allah" Sanda ya shigo gidan yai niyya ta ja ma kowa. Duk sai an kulle yan gidan. Saiyai rashin mutuncin da basu taba tunani ba. A karo na farko a rayuwarshi dayaji ya kasa abinda yai niyya ya kuma rasa dalili. Hannu yasa yadan daki goshin shi. Yana son koma menene ya same shi ya warke. Dan ji yai tsugunnawar da safiyya tai mishi baya so. Har lukman ya zaro wayarshi daga aljihu zai kira haneef. Fu.ad ya kalle shi yace "Muje please" Ba musu lukman ya dauki hanyar waje. Dan gaji yake idan ya tsaya fu.ad zai iya sake shawara. Suna fita ya mike hanyar da suka biyo da gudu ba tare da ya waigo yaga ko lukman na biye dashi ba. Wata hamdala lukman yake jerowa dan har ya gama hango su ana rikici a police station. Shi kanshi mamakin abinda ya faru yake. Sai kuma ya tuna yanda fu.ad yake rike da tukunya. Mai zaiyi inba dariya. Hanya ya mika yana sassarfa yana shan dariya. * Babu ko sallama haneef yaji an turo kofar shagon. Kallo daya yaima yanayin fu.ad ya mike da hanzari yana fadin. "Ya Rabb. Fu.ad me ya same ka haka?" Cikin wani sanyin murya ya tsinci kanshi da fadin. "safiyya ce ta watsamun ruwan dan wake" "Ruwan dan wake? Safiyya?" Haneef ya tambaya yana son ya gane ma.anar maganar fu.ad. Sake kallonshi yake daga sama zuwa kasa. "Gaban rigarka kuma fa?" Ya tambaya yana kallonshi sosai. "Tukunyar dan waken ce ta mikomun" Abin yai yawa. Wata irin dariya haneef ya kwashe da ita harda hawaye. Sai da ya samu waje kan katifa ya zauna ya dafe ciki yana dariya. Lukman ne ya shigo da sallama. Kallon fu.ad da yake tsaye yai cuku cuku yake. Ya maida kallonshi ga haneef da ya kasa controlling dariyar da yake. Gefe ya zauna ya tusa tashi. Da sun fara dainawa suka sake kallon fu.ad sai su kwashe da wata dariyar. Tsaye yake yana kallon su. Abin ma ya wuce na takaici. Murmushi kawai yai ya juya musu baya yana kwance takalmin shi. Dakyar fu.ad ya iya controlling kanshi yace. "Wanne police station yan gidansu suke?" Yana mikewa dan yasan dole yaje solving rigima. Girgiza masa kai lukman yai yace. "Ba abinda ya faru fa......." A nutse ya gaya masa duk yanda sukai. Da tsananin mamaki ya kalli fu.ad da yake tsaye daga shi sai boxers yasa rigar daya cire yana goge gashin kanshi yace. "Who are you and ina ka kaimun kanina?" Rigar dake hannunshi ya jefa ma haneef daya cabe ta yana dariya. "But guess what. I am proud of you. Like sosai little one. Yau kaine da hakuri?" Murmushin da ba ko yaushe yake yi ba yaima haneef saboda wani rawa zuciyarshi take yi har yanzun. "In kun gama dariyar wanka nake sonyi. And lukman ka dauko mun kaya a mota" Lukman da yanayin maganar fu.ad bai dame shi ba ya daga kai kawai alamar yaji. Dan inda sabo ya saba da yanda yake magana cikin gadara. "Yan gidan nan suna da karamci. Ga ruwa nan ansa an jawo mana. Kai amfani da bokiti daya kabar ma lukman daya" Haneef yai masa bayani. Wani kwalo idanuwa yai waje. Ya taka a hankali ya tura bandakin yaga ruwa a bokiti. Tunda yake a rayuwarshi banda dazun da asuba baima taba shiga irin wannan bandakin ba. Baima san yazai fara wanka da ruwa a bokiti ba. Juyowa yai ya kalli haneef. "Dame zanyi wankan?" Daure fuska haneef yayi yace. "Wannan ruwan na bokiti. Ka watsa kawai tunda bamu dauko sponge dinmu ba. Yau zanje gida nima in dauko kaya sai in taho dashi" Girgiza kai fu.ad yake alamar ai shifa bai yarda ba. "Ni momma nake son magana da" Ya fadi yana kallon haneef da lukman a lokaci daya kaman wani yaron da akaima laifi yake neman mamanshi ya gaya mata. Ganin sun banza sun kyale shi yasa shi shiga bandakin yana doko yar kofar langalangar kaman zai karya musu ita. Hada idanuwa sukai shida lukman suka sake bushewa da dariya. [4/4, 5:56 PM] Fatima saleh: *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ              09 "A mikomun towel dina" Fu.ad ya fadi yana daga cikin toilet din. "waya hanaka shiga dashi?" Lukman ya fadi. Haneef kam tabe baki kawai yai. "Wallahi zan fito haka" Da sauri lukman ya dauki towel din ya kwankwasa ban dakin. Ya mika masa. Yanayin dariyar da yake. Yasan halin fu.ad babu kunya a idanunshi tsaf zai fito in basu mika mishi towel din ba. Yana fitowa lukman ya shiga. Jakarshi ya dauka. Banda comb da man gashi bai dauko komai ba. Sai kayan sawa da takalma. "bani manka indan shafa ma hannuwana" Vaseline haneef ya mika mishi. Dan shima bai dauko mai ba yace. "Ga dai na masu dakin" Ai da sauri ya janye jikinshi kaman ya miko masa miciji. Ajiye robar haneef yayi yaci gaba da latsa wayarshi. Kaya ya dauka ya sake ya gyara gashin shi da yake ta daukar ido. Kallon shi haneef yai yaga crazy jeans din dake jikinshi. Yaga duk a gwiwar zuwa kwauri. Har jikin cinya yaga ne. Sai riga fara data bala.in kamashi shi ba wani jikin kirki ba. Yasan inya masa magana ma fitsara zai sha ranshi ya baci a banza dan haka yai masa fatan shiriya kawai a ranshi. Dai dai sallamar khalid. Haneef ya amsa da fara.a a fuskarshi. "Ina kwananku" Khalid ya fadi yana ajiye kwanan shan daya shigo dashi a hannu. "Khalid ka tashi lafiya? Ya hidima kuma?" Haneef ke tambaya yana mikewa daga kwanciyar da yai. Khalid ya amsa shi da. "Alhamdulillah" Yana ficewa da sauri. Ya sake dawowa da leda a hannunshi. Kamshin kosai ya cika dakin. Fu.ad dake tsaye ya wani yamutsa fuska. Dan kamshin koma menene aka shigo dashi yana shirin saka shi amai. "Ga abin kari" Haneef yai masa godiya ya sauko ya bude ledar kosan. Gasu manya manya ya dauki daya ya gutsura. Rabon shi da kosai tun wani azumi da atika tayi musu shi. Hada idanuwa sukai da fu.ad dake masa kallon 'Me kake yi haka?' Share shi yai ya ci gaba dacin kosan shi suna dan hira da khalid din dake kallon fu.ad lokaci lokaci. Kayan daya cire ya daga a kyamace yace. "Ina za.a yadda wannan?" Idanuwan khalid ya zaro yana kallon kayan da fu.ad ke kira da a zubda. "Me ya same su?" Ya tambaya sanin fu.ad bazai kula khalid ba balle har ya amsa mishi tambayar dayai yasa haneef saurin cewa. "Yadan fita wata ta watso ruwa ya same shi" "Ayya bara sai na wanke masa su" Cewar khalid. Rolling idanuwanshi fu.ad yai. Ko ance ma wannan dan kauyen zai iya saka kayan da aka tsoma a bokiti yasa kazamun hannun shi ya wanke. "Germs" Ya fadi kasa kasa. Dan bai shirya dogon surutun haneef ba. Zai magana lukman ya fito daga wanka. "Naji kamshin kosai" Ya fadi yana dariya. Wani mugun kallo fu.ad yai masa da ko kula dashi baiba ya zauna gefen haneef sukaci tare. "Ka kawo kayan sai in wanke maka" Kallon khalid lukman yai. Mutanen karkara akwai karamci da sanin darajar mutane. A shekaru zai girmi fu.ad amman yana offering ya wanke masa kaya. Ba ruwansu da girman kai. Da haneef da lukman suka zuba masa ido yanda yake tsaye yana yamutsa fuska. Yason kallon da suke masa. Kaman wanda aka shaqe. Can kasa kasa yace. "Ba abinda zan da kayan ne. A zubar" Tashi khalid yai ya karba yana fadin. "Kai nikam ina so" Ya dawo ya zauna. Wani kallo fu.ad yake mishi. Ya rasa meke damun talakawan nan. Harka iya kasa kayan da wani yai using. Girgiza kai kawai yai. Ya dauko jakarshi. Ya duba. Kudin daya dibo basu shige dubu goma ba dan inba amfani zai da kudi ba ba yake dasu ba. "Wayake da cash a jikinshi? Like 20k or more" Ya tambaya yana kallonsu. Lukman ya mike ya dauko wallet dinshi. Dubu takwas ne. Ya girgiza ma fu.ad kai. "Haneef?" Ya kira da alamar tambaya a muryarshi. "Aikin me nake dazan yawo da 20k?" Haneef ya bashi amsa yana komawa kan katifa. Girgiza kai fu.ad yai yana tuna haneef bai fara aiki ba. Kuma baya karbar kudi a hannunshi sam. Koya tura masa maida mai yake. Garama mota itama sai da ya nuna masa mugun bacin rai tukunna ya karba. "ko 5k tam kamun mu shiga gari. Lukman ban na hannunka." Mika mishi sukai haneef ya bashi 5k din. Ya kirga dubu ashirin. Khalid dai kanshi kasa yana sauraransu. Lukman ya mikama yace. "Give him ion wan him wearin' mi used' Dariya lukman yai ya karbi kudin yace ma khalid. "Gashi fu.ad ya baka ka siya kaya" Ya karbi kudin da mamaki a fuskarshi. Allah kenan rabonka baya wuceka. Godiya ya fara ma fu.ad dako kallon shi baiba ya karasa daura takalmanshi ya dauki key din mota ya fice. Da khalid baiji yai hausa ba zai iya rantsewa yanda fu.ad ya basar dashi bai gane me yake cewa bane. A sanyaye yace ma haneef. "Inata godiya ko baiji ba" Wata kunya ta rufe haneef yace masa. "Kayi hakuri. Bai cika son godiya ba shisa kaga yai shiru" Jinjina kai khaleed yai kawai bai ce komai ba. ** Cake dinshi ya zauna a mota yaci ya sha fresh milk da sun wani dauki dumi. Ac ya kunna. Ya zame kujerar ya kwanta. Kanshi wani ciwo yake ya kuma san baccin dabai samu bane. Dama yasani cikin mota ya kwana. Ya fiye mishi alkhairi da sauro da zafin shagon nan. Wata kewar dakin shi na gida yaji. Ajiyar zuciya yai. Ya sake gyara kwanciyarshi kan kujerar motar ya lumshe idanuwanshi. Bacci mai karfi ya dauke shi da wani nauyi a zuciyarshi daya kasa fahimta. * Safiyya ce tsaye da kayan jikinta na dazun. Wata kokakkiyar atamfa. Fuskarta duk dige digen kwalli na alamar kwalliyar kauyen dake fuskarta. Bata cika haske ba sosai. Bata da tsaho. Banda idanuwanta da suke manya tubarkalla babu wani kyau a fuskarta. Hancinta kaman daga baya akan dan dora mata shi. Ba zaka kirata mummuna kai tsaye ba. Saboda jikinta nada kyau sosai. Tana da kira da dirin da mata da yawa zasu yi hassada da. "Fu.ad..........." Ta kira shi. Mamaki yake dan baisan ya akai tasan sunan shi ba. Baima san me yake tsaye a wajen yana kallonta ba. Yamutsa fuska yai saboda yanayin yanda ta kirashin baya so. Bayason yanda zuciyarshi ta wani matse. Hade fuska yai. Baya son wata alaqa tsakaninsu. Shi ba mata yake kulawa ba. Mazan ma ba kula su yake ba. Ball ce masoyiyarshi. Ita ya runguma. Amanarshi na tare da ita. Ba kuma ya tunanin zai iya hada sonta dana mace shisa basa gabansa. Beside a shekaru ashirin da biyu wanne shiririta zai kaishi soyayya. Dan haka ya zo wucewa ta gabanta. Ta riko mishi riga. "Nima wulakancin zakai mun?" Ta bukata. A fusace ya juya ya sauke idanuwanshi cikin nata. Lokaci daya kankarun dake cikin idanuwanta suka soma kashe duk wata wuta dake cikin nashi. Dukkanin ginin dake kare da zuciyarshi suka soma girgiza. Foundation dinsu na barazanar rugujewa. * A firgice ya bude ido yana jan wani irin numfashi. Ac din motar bai hanashi zufa ba. Zaune ya tashi dirshan. Ya dafe kanshi cikin hannuwanshi. Yana maida numfashi da sauri sauri. Glass din motar ya sauke. Dan iskar dake ciki ta masa kadan. Ruwa ya dauko ya bude motar. Ya kurkure bakinshi ya wanke fuskarshi sannan yasha. Ya koma cikin motar ya hada kanshi da sitiyari yana jin yanda numfashin shi ya samu dai-dai ta. Wannan wanne irin mafarkine. Safiyyar da maganganunta ne kawai mafarki. Amman yanayin da yake ji a cikin mafarkin. Shi yake ji a yanzun. Rawar da zuciyarshi takeyi saima abinda yai gaba. Wanne irin bala.i ne wannan? Yake tambayar kanshi. Baiga hadinsa da yar qauye kucaka ba. Yar gidan talakawa da zata kutso masa kai cikin mafarki. Wani tsaki yaja. Yana mikewa yaji muryar lukman kaman daga sama. "Dan banza ashe kana nan. Anata kiran wayarka kaqi ka dauka" Wayarshi a silent take. Shiru yai ma lukman din ya zagaya ya bude motar ya shigo. Baima kula tare suke da haneef ba saida yaji an bude gidan baya an shiga. "Lukman karbi tukin nan please" Bayajin yan gardamar dan haka ya bude motar ya fita. Lukman ya koma inda ya tashi. Baya ya bude ya shiga. Haneef yace "Me ye haka din?" A kasalance yace. "Em noh' in the mood" Fita haneef yai ya koma gaba. Fu.ad yai luf dashi cikin kujera. Yanajin lukman na maimaita yanayin turancin shi. Ya rasa me yasa indai zai turanci sai lukman ya maimaita yana mai dariya wai ya zama masu jar fuskar nan. Yanayin dayake ji bana rigima bane.  Suka dauki hanya. Wayarshi lukman ya jona yasa kida yana dannawa wakokin suna wucewa. Wata waka ta shigo ta justin biebier (Purpose) harya danna ya canza dan yasan yanda fu.ad ya tsani slow wakoki. Wai sai kace marassa rai. Da hanzari fu.ad yace masa. "Bar ta please. Mayar mana" Mayarwa yai yana kallonshi ta cikin mudubi. Ya fahimci baison surutun yau. Yakuma san akwai abinda yake damunshi. Yasan da kanshi zai fada mishi dan haka yabar wakar kawai. Fu.ad kam wakar na shigar shi ya kuma rasa dalili. Bason slow music yake ba. Saidai kawai yaji wakar tayi dai dai da yanayin da bai san ta inda ya fito ba. Wani mai machine ne ya shigo musu kaman daga sama. Badan a hankali lukman ke tuqinba da munin abin zaifi yanda ya faru. Parking yai suka fito su duka. Fu.ad ya rike baki yana kallon gefen gabar motarshi ya tashi aiki. Benz dinshi da yana da wanda suka fita kudi amman yake mugun ji da. Fuskar shi horrified yake fadin. "Oh no.....oh my God" Yana girgiza kai. Baima kula dasu haneef dake magana da yaron ba. Juyawa yai rai a bace ya ture lukman ya cakumi wuyan yaron. Mutane harsun fara haduwa. Tsayi kawai fu.ad zai nuna mishi. Amman ya fishi girma wani wawan mari ya kwada ma saurayin yana kara mishi wani. Haneef da lukman suka rike shi suna fadin. "Fu.ad control yourself please ya bada hakuri fa. Machine dinshi ne ba brake" Cikin hargowa fu.ad ya ture su yana fadin. "Ciyawa ce a kanshi? Da akace yahau machine ba brake? Kana tunanin ko gidaje da gonakin danginsu za.a siyar zasu biya kudin motata ne?" Cike da takaici yaron yace. "Allah ya baka hakuri" Kallon shi fu.ad yai yanajin kaman ya rufe shi da duka yace. "Aikin talaka kenan. Bada hakuri. Tunda ka gama mun barna dole kabani hakuri. Daqiqin banza" Harya juya yana sake kallon motar shi. Matashin saurayin yace. "Arziqi dai ba hauka bane ba. Allah daya baka muma talakawan zai iya bamu" Tunda ya bude bakinshi haneef da lukman suka karanci kuskuren hakan. A hankali fu.ad ya juya muryarshi can kasa kaman mai magana da kanshi yace. "Me kace?" Haneef ne ya dafa kafadarshi yace. "Forget it fu.ad muje please" Ture hannun haneef yai ya karasa daf da saurayin. Muryarshi very controlled da abinda yake ji yace. "No ya maimaita abinda yace" Shiru saurayin yai. Cikin jama.an wajen fu.ad yace ma. "akwai police station a kusa?" Hakuri suka shiga bashi yace wallahi sai ya maimaita maganar daya fada. Sai yasa an kulle shi. Bai gama balbalin ba. Ashe tun farkon rikicin wani yaga abin zai wuce gona da iri yai saurin karasawa police station din dake nan kusa kusa ya kai report. Nan suka rankaya zuwa police station din. Haneef da lukman na kokarin shawo kan fu.ad din dako saurararsu yaqi yi. Filing report yai yace yana son a biyashi barnar da akai masa jikin mota. Dan yasan basu da kudin biyan shin. Wulakanta yaron yake so ayi. Saboda babu wanda ya isa ya gaya masa magana ko ya fishi kudi basuyi shari.a ba ballantana wannan kazamin talakan. Dukan shi yan sanda suka shiga yi zaka rantse da Allah kayan wani ya sata. Wani abu sai kasata nigeria. Gefe haneef yaja fu.ad. "Wai meke damunka ne? Wallahi kasa su kyale shi ko na kira abbah na fada mishi" Lukman na gefe dan yagaji. Fu.ad ba saurarsu zai ba. Wani dattijo ne ya shigo police station din a rikice. Yan sandan suka kira fu.ad ya karasa inda suke. Kallon dattijon yake akwai inda ya taba ganin shi. Lokaci daya abin yai clicking masa. Shine tsohon da anty fatima ta mare shi saboda. Wannan kazamin tsohon. Shima kallon fu.ad din yake. Yagane shi sarai. Ya rausayar dakai gefe kawai. Nan yan sanda suke kara ma zancen fu.ad gishiri. Ya bude baki zai magana haneef yace. "Fu.ad na taba rokon alfarma a wajenka?" Yai shiru kawai. Haneef ya ci gaba. "Fine ban taba rokon wani abu a wajenka ba. Indai har ina da wata daraja a wajenka. In jini daya ne yake a jikinmu zakai dropping case din nan yanzun" Shiru yai kaman baiji abinda haneef din yace ba. Harma ya dauko waya zai kira abba yaji fu.ad yace. "Fine. Ina son babanshi yaban hakuri" Ya fadi yana kafe idanuwanshi kan dattijon. Haneef yai masa kallon kana cikin hankalinka kuwa. "Allah ya baka hukuri ya huci zuciyarka da kuskuren da yarona yai maka" Cewar dattijon muryarshi na rawa. Haneef fita yai daga police station din lukman na rufa mishi baya. Saboda kunya yake ji. Yaji ya muzanta da abinda fu.ad yayi. Shikam wani murmushi ya kwace masa. Sauran kudin aljihun shi ya zaro yaba yan sandan sannan ya fita wajen su haneef. Su duka babu wanda yace masa uffan har suka tsallaka wajen motarsu suka shiga lukman ya tuqa su zuwa gida. [4/4, 5:56 PM] Fatima saleh: *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ           10 Baima yi kokarin kula su lukman ba. Kaman yanda basu ce masa uffan ba haka shima. Har suka kai gida. Lukman yace ma haneef zaije gida ya kira shi in zasu koma. "Haneef kaban number din mai gyara ma abbah mota" Ko inda yake haneef bai kalla ba ya wuce ya shiga cikin gida. Wani abu fu.ad yaji ya tokare masa wuya. Already bayajin dadin komai. Ga yunwa dake damunshi dan cake din dayaci harya kone. Cikin gida ya shiga. Atika na hango shi ta rakube jikin bango. Kaf yan aikin gidan ya kula dole ke sawa suna haduwa dashi. Wucewa yai dakinshi yai wanka sosai. Sanda ya fito jinshi yake wani fresh. Crazy jeans din dai ya sake maidawa blue. Da farar riga data matse shi. Ya feshe jikinshi da collection din turarukan shi. Dakin haneef ya nufa. Bai damu da yai knocking ba ya shiga. Yana tsaye yana balle links din rigarshi. Jikinshi sanye da wani yadi ruwan toka. Ya matukar karbarshi. "Zan fita. Ba nisa zanba abinci zan siyo in dawo" Ko kallonshi haneef baiba. Zaka rantse ba dashi yake magana bama. Matsalolin fu.ad yawa gare shi. Yasan gulmace shi bayacin abincin yan aiki. Kara son tabara shi mumy ke shiga kitchen ko su pha.iza a dafa mishi. Yau ba sa nan yasan hotel zashi ya kaso dubunnai kan abinci gashi a gida. A kufule fu.ad yace "What is with the attitude? Tun dazun nake maka magana ka share ni" Kallon shi haneef yai cikin idanuwa sannan yace. "Me kake so ince maka? Abinda kake so ba shi kakeyi ba? Meye na neman ra.ayina kuma?" Kallon shi fu.ad yai na wani lokaci kamun yace "Kace in dropping case din kuma nayi. Me kake so inyi again?" Wani numfashi haneef yaja. Karasawa yai inda fu.ad yake tsaye ya sa idanuwanshi cikin na fu.ad. "So nake kasan darajar mutane fu.ad. Kaima wata rana uba zaka zama. Zaka so a girmama ka" Wani murmushin takaici fu.ad yai "Bana girmamaka?  Bana girmama su abbah? And ban taba hango ni da yara ba. Bana son damuwa" Girgiza kai haneef yai. Rashin hankalin fu.ad yawa gare shi. "Just get out of my room!" Lokaci daya yaji bacin ran da yake ta yawo a kasan zuciyarshi ya samu wajen zama. "Haneef! Ni kake kora daga dakinka?" Wucewa yai yaci gaba da hidimar shi. Waje fu.ad ya samu kan daya daga cikin kujerun dakin ya zauna. Wasa yake da zoben azurfar dake hannunshi. Har haneef ya gama shiryawa yana wajen a zaune. "Ba yunwa kace kana ji ba?" Haneef ya tambaya. Shiru yai shima. Bai damu da yunwarshi ba ai. Yafi damuwa da yan kauyen nan da bai ga abinda sukai mishi ba zai dora masa laifi. Ajiyar zuciya haneef ya sauke. Matsala daya da ake samu kenan. Son fu.ad yana hana shi nuna masa kuskurensa. Dama duka yan gidan. Kan hannun kujerar ya zauna muryarshi a sanyaye yace. "Ka tashi kaje ka siyo abincin. In kuma ba zaka koma ba mu tafi da lukman" Dago fuska yai. Ya wani tabare murya. "Ka damu da yunwar danake jine. Zaka kama mun fada kan yan kauyen nan" Murmushi haneef yai. "Sorry okay. Tashi ka wuce. Kai zamanka kawai zamu koma" Da sauri yace. "No zan biku nima" Kawai yaji yana son komawa kauyen. Bakuma yason amsa ma kanshi dalili. Mikewa yai ya kalli haneef yace. "We good?" Daga masa kai yai tare da fadin. "Yeah we are good" Murmushin shi da yakan jima baiba yai ma haneef sannan yace "Barin je in settling da lukman" "Kaje ka sa abu a cikinka tukunna" Girgiza kai yai yana bude kofar yace. "He is more important" * Yana shiga gidansu lukman kanshi tsaye ya wuce dakin su lukman din. Yana zaune yana cin indomie da soyayyen kwai. Ko sallama bai mishi ba yace. "Waya dafa?" Dagowa lukman yai ya kalle shi. "Shine sallamar ka kenan?  To ban sani ba" Dariya kawai fu.ad yai. "Don't be a jerk. 'Mma hungry" Saida yai kaman bazai amsa shi ba sannan yace "Ummie nasa ta dafamun" Bai cire takalmin kafarshi ba ya karasa ya zauna gefen gadon lukman. Sanin halin shi yasa lukman ya mika mishi plate din duka. Bai musu ba ya karba. Saida ya cinye duka sannan ya sha orange juice din dake cikin glass cup da lukman ya zuba bai taba ba. "I am still hungry" Ya fadi yana yamutsa fuska. Mikewa yai yana fadin. "We good?" Kai kawai ya daga mishi. Yasan pointless ne kokarin saka fu.ad a hanya. Yana kallon shi harya fice daga dakin. * Wannan karon fu.ad bai manta komai ba. Zaka rantse wata tafiyar sati biyu zaiyi kayan daya dauka. Harda toiletries gaba daya. Yaje ya zuba cikin Range Rover dinshi ya kira lukman a waya yace musu sun shirya. Haneef da lukman suka zauna gaba. Wannan karin haneef ke tuqin. * Suna shiga mamansu ya kira a waya shi yana missing dinta. "Fu.ad anan ka kwana?" Ta tambaya cike da mamaki. Da fara.a a muryarshi yace. "Eh momma muna tare harda lukman fa. Haneef yace sai jibi zamu tafi gida har daku" Dan jim tayi da alama tana tauna maganar fu.ad kamin tace. "Please banda rigima. Ka zauna tare da haneef throughout kana jina" Saida ya tabbatar mata zai kiyaye sannan sukai sallama. A mota yake zaune yana cin burger. Su haneef na wajen zaman makokin. Bama su gayyace. Shi ba. Wayar shi tahau ihu. Pha.iza ce ya daga yana fadin. "Sis... " "Bro namu mu kadai. Kaga white rice suke dafawa cikin gidan nan...." Kamun ta karasa maganar yace "Ki fito ki duba zakiga baqar Range dina. Ina ciki" Bai jira amsarta ba ya kashe wayarshi. Yana nan zaune pha.iza ta fito. Leda daya ya bata. Ta juya abinta. Kulle motar yai ya fito batare daya san inda zashi ba. Headphones dinshi ya kunna wakar Drake-child's play. Ya ci gaba da tafiya zuciyarshi na masa jagora. Dan bama ya kula da inda yake saka kafarshi. Gaba daya tunaninshi yana wani waje da baisan ko ina bane. Kanshi a kasa. Hannuwanshi na cikin aljihun hoodie din daya dora da zasu fito bawai don kare sanyi ba. Dan gayu kawai. Sai ganinshi yai tsaye kofar gidansu safiyya. Ya rasa yanda akai yazo wajen da kuma abinda yake yi. Kallon kofar gidan yake. Zuciyarshi na masa wani iri. Juyawa yai da niyyar tafiya. Kaman daga sama yaji muryar safiyya tace. "Usman kace lami ta jirani. Yanzun zan fito" Bai san lokacin daya juya ba. Itace a tsaye. Banbancin ta da mafarkin shi hijab da take sanye jikinta. Kwalliyar fuskarta na nan. Muryar iri dayace. "WTF......." Ya fadin jin yanda zuciyarshi ta wani squeezing. Kallonta yake kaman bashida wani muhimmin abu dazaiyi bayan hakan. * Safiyya ta rigada tasan lami na iya kin jiranta. Jin datai a jikinta cewar ana kallonta yasa ta juyowa inda fu.ad yake tsaye kaman an dasa shi. Idanuwanta ta sauke cikin nashin nan da sukai mata tsaye a rai. Ta kasa manta komai nashi. Zuciyarta taji tana ta dokawa. Ta hadiye wani abu dataji ya tsaya mata a makoshi. Mai shanu ta hango yanata faman yima fu.ad ihun ya kauce daga kan hanya amman da dukkan alamu baima san yana yi ba. "Kauce daga hanya zai wuce! " Ta fadi da karfi. Fu.ad ya wani yamutsa fuska da dukkan alamu bai fahimta dash take magana ko da wani ba. Hannu yaji saman kafadarshi an ture shi gefe a fusace ana fadin. "Kurma ne kai kome? Anata magana wa zaka kawoma tsagerancin ku na zamani" Kafadarshi ya kalla. Sawun hannun mutumin ya fito da daudar da baisan ko ta mecece ba jikon farar hoodie dinshi. Headphones dinshi ya cire daga kunnuwa ya taka wajen mutumin daya tabbata ya girmi anty fatima. "Wawan ina ne kai zaka dauki kazamin hannunka ka dora akan kafadata?" Da bala.in mamaki mutumin yake kallon fu.ad. "Yaro rashin kunya zakaimun?  Dan gidan uban waye kai da bakasan........ " Fu.ad bai bari ya karasa ba ya dauke shi da mari. Babu kazamun da zai zagi abbah. Saffiyya batasan sanda ta karaso wajen ba da sauri. Hannu ta daga ta wanke ma fu.ad fuska da yatsunta biyar. Kallon shi take tana gefen mutumin daya mara. "Safiyya?" Mutumin ya kira da alamun tambaya a muryarshi. Tata muryar na rawa tace. "Kawu kabarni. Akan me shine da laifi baiga girman kaba zai daga hannu ya mareka?" * Fu.ad hannu yasa ya taba kuncin shi. Ya sake shafawa ya dawo da hannunshi ya kalla. Sannan ya sake kallon safiyya dake tsaye gefen mutumin dayaji ta kira da kawu. Kwakwalwarshi ta kasa tauna abinda ya faru. Zuciyarshi ta kasa yarda da cewa abubuwa biyu ne suka faru dashi. Wani kazamin talaka mai dauke da dauda ya zagi abbah. Wata kucakar yar kauye ta daga hannuwanta a mare shi. "Marina kikai?" Yake tambayar kanshi fiye da yanda yake tambayar safiyya. So yake wani ya tabbatar mishi da gaske abin ya faru. Can nesa yake jin muryar safiyya dake cike da rauni na fadin. "Eh marinka nai" Kalar ashar din dayai zaisa ko bamaguje yake wajen kunya ta lullube shi. Lokaci daya idanuwanshi suka rine saboda bacin rai. Dagowa yai ya sauke idanuwanshi cikin na safiyya. * Idanuwanshi take kallo. Lokaci daya duk wani abinda ke motsi a jikinta yake fahimtar kuskuren data aikata. Bata san lokacin data matsa bayan kawunta ba. Har lokacin idanuwanta na cikin nashi. Girgiza masa kai take. So take da wannan alamar kawai ya karanci yanda take dana sanin abinda ta aikata. Shi kanshi kawunta kallon fu.ad yake. Da dukkan alamu yaro ne mai karancin shekaru. Saidai a yanzun akwai wani abu tattare da yanayin shi dashi kanshi ya tsorata. Akwai wata isa da tsayuwarshi da fuskarshi kawai ta nuna su. * Takawa yake a hankali kaman mai tafiya kan bawon kwai. Yana kallon yanda jikin safiyya ke kyarma. Ta rike rigar kawunta kaman zata koma cikin shi. Hannu kawunta ya dago yana shirin tare fu.ad. Muryarshi a dake can kasa yace. "Kuskure na uku da zaka aikata shine barin hannunka ya karaso ya taba ko da rigata ne" Da alamu kawu ya karanci gaskiya a maganar fu.ad dan haka ya maida hannunshi inda ya kamata ya tsaya. Karasawa yai daf da safiyya da ta kasa sauke idanuwanta daga cikin nashi. Kome yake ji akanta. Kome yake tunanin akwai a cikin idanuwanta. Abinda ta aikata ya girme shi. Ko wanda yake so yakan nuna masa kuskurensa inhar ya mishi ballantana ita da basu hada komai ba. Aa a ganinshi na biyu kenan da ita akwai abinda suka hada dabai fahimta ba bakuma ya son fahimta. "You gonna' regret this. Bake kadai ba. Gabaki daya danginku.......!" Thanks to *Dimples* for liking fu.ad so damn much. (Wink) [4/4, 5:56 PM] Fatima saleh: *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ                11 Hannu tasa ta goge hawayen da suka zubo mata. "Safiyya da baki mare shi ba" Wani guntun murmushi tai da baikai zuciyarta ba. Tana jin yanda komai ya kwance mata. Tun dazun ta kasa manta shi. Data rufe idanuwanta shi yake mata yawo. Ta kuma rasa dalili. Bata taba zaton zata sake ganin shi ba. Saboda bai mata kama da yan garin ba. Dakyar ta iya samun yar nutsuwar da tace. "Babu wanda zai daga hannu ya mare ka a gaba kawu" Girgiza kai yayi yace. "Yanayin shi dan masu shine. Ina gudun abinda zaije ya dawo bakiga yanda ya tafi a zuciye ba" Ita kanta ta tsorata sosai da yanayin dataga ya tafi dashi. Tana jin maganar shi dayai mata kamun ya tafi "Fu.ad. Sunana fu.ad dan ina son kisan sunan mai fuskar da kika taba. Kisan sunan wanda kika taro ma dangin ki rikici dashi" Wasu hawayen suka sake zubo mata. Ta sa gefen hijab dinta ta goge su. "Bara in shiga gida kawu." Ya jinjina kai sannan yace. "Allah yai miki albarka. Nagode safiyya. Allah ya jishe mu alkhairi" Ta amsa da amin tana shiga gida. Yanayinta inna ta kalla tace "Lafiya safiyya?" Abinda ya faru ta zayyano mata. Inna tasa salati. "Ni maryama meke faruwa damu ne haka. Yau dan uwanki ya sha dakyar hannun yan sanda ke kuma kina son janyo mana wani rikicin?" Murya can kasa kasa tace "Inna kawu fa ya mara. Kuma shine bashida gaskiya. Ina wajen tsaye komai ya........ " Harara inna ta watsa mata tana katse da fadin "Rufemun baki. Shine me? Kema da nake gani da hakuri kin fada daukar halin dan uwanki ko?" Wasu hawaye taji suna bi mata fuska "Kiyi hakuri inna. Bazai sake faruwa ba in shaa Allah" Safiyya ta fadi tana mikewa. Inna ta kalle ta tace "Allah shi kyauta. Ina kuma zaki?" Rausayar dakai tai. Muryarta a sanyaye tace. "Makaranta wai ko addu.ar tashi in samu" "Ai saidai ki hakura yau tunda yamma tayi sosai. Ki zauna ki tayani karasa tuwon nan kawai" Hijabinta ta cire ta amsa inna da to. Tana shiga daki ta ajiye ta fito suka shiga hidimarsu tare. **** Yana karasawa wajen motarshi ya bude ya shiga ciki. AC ya kure ya dora kanshi kan abin tuqi. Numfashi yake mayarwa. Yarinyar nan tayi babban kuskure. Bazai saurari bangaren zuciyar shi dake kokarin tausar shi ba. Bazai saurare shi ba saboda tsakanin safiyar yau da yammacinta wani abu ya samu matsala a ciki. Wani abu ya kwance a cikin zuciyarshi da baisan yanda zai ya gyara ba. Kamun koma meye yaci galaba a kanshi ya zaro wayarshi. Hamza ya kira. Kamun lukman da haneef da zuciyarshi su hanashi ya kira hamza. Ringing din farko ya dauka hadi da fadin. "Moh.... " Bai bata lokaci yace "Ina bichi hamza. Inason kome kake kai dropping. I will pay you. Mota uku nake so ta yan sanda. You call me inkun karaso. Ion' care how much it will cost and be fast" Bai jira amsar dazai bashi ba ya kashe wayar. Sauke kujerar yai sosai ya kwantar da bayanshi yana lumshe idanuwanshi. Marin yana dawo mishi kaman lokacin akai komai. * *One hour later* Zaune suke wajen zaman makokin suna ta hira abinsu. "Nikam ka karasa kallon The 100 kuwa?" Girgiza kai haneef yai yace. "Ni zaman makoki nake fa." Dariya lukman yai. "Zaman makokin wa?" Ya tambaya. Haneef na dariya yace "Finn mana" Dariya sukai su duka kamun lukman yace "Koni fa naji haushin mutuwar finn. Wannan banzar clark din haushi take ban wallahi. Nafison Octavia" Tabe baki haneef yai hadi da fadin. "Octavia broke my heart. Ina son shegiyar taje ta zabi Lincoln" Wata dariyar suka sake yi tare. Haneef ya fara jin jiniya kaman ta yan sanda. Ya juya ya kalli lukman shima da alamu yaji. "Ina fu.ad?" Haneef ya tambaya yana kallon lukman. Mikewa yai daga kishingidar dayai yana dauko wayarshi. "Damn it. Chargy na ya dauke. Goddammit lukman call him yanzun nan" Lukman jikinshi har kyarma yake. Ya lalubo wayarshi yai dialing number din fu.ad. Wayarshi a kashe take. Sake trying yai. Still a kashe. Ya kalli haneef ya girgiza masa kai. Mikewa haneef yai. Da gudu gudu ya dauki takalmin shi. Lukman nabin bayanshi. Pha.iza suka ci karo da ita ta fito daga cikin gida. Kallo daya tai musu tace "Lafiya kuwa?" Girgiza mata kai haneef yai yace. "Lafiya kalau. Ki ajiye wayarki kusa dake dai" Lukman pha.iza ta kalla tace "Yaya lukman me ya faru?" Shiru yai baice komai ba. Zuciyarshi dokawa kawai take. Haneef ne yace mata "May be fu.ad ne. We are not sure yet. Zamuje mu duba mugani" Dafe kai pha.iza tai. Bata kawoma ranta wani abu bane ya samu fu.ad. Yana fadar haka ta soma addu.a Allah yasa ba wani bane ya haye masa. Tasan yana yawan shiga rikici. Wasu su sani wasu kuma haneef da lukman su boye musu. "Zan biku please" Haneef ya soma girgiza mata kai lukman yace. "Ta biyo mu please. Inhar abinda nake tsoro ne ya faru. We need all the help we can get" Tare da pha.iza suka tafi. Saida suka fara duba fu.ad ko zasu ga motarshi wayam wajen yake. Motar haneef suka dauka suka mike hanya. Batare da sun san ina  zasu fara neman fu.ad din ba. **** Ruwan take ja amman zuciyarta bata mata dadi. Ga wani irin yanayi tana ji kaman wani abu zai faru dasu. Kaman daga sama taji muryar babansu yana. "Safiyyaaaa" Da hanzari ta karasa janyo gugar daga rijiya. Ko juye ruwa. Batai ba ta ajiye ta tana nufar hanyar soro data jiwo muryarshi. Iccen dake kanshi ta kama mishi suka sauke tana fadin. "Sannu da zuwa baba. Ruwa nake ja shisa ban jika ba" Murmushi yai mata yana fadin. "Baki je makarantar bane yau?" Gabanta taji ya yanke ya fadi. Ta bude baki zata amsa shi. Jiniyar yan sandan da suke ji nesa nesa ta matso kusa. "Oh Allah dai yasa lafiya. Tun dana taho nakejin kukan nan kaman motar asibiti kaman ta yan sanda" Safiyya ta amsa da. "Amin dai baba. Nima naji. Allah yasa ba gobara bace" "Allah sarki. Amin kuwa. Kauda itacen nan gefe mana. Ko ki dora su saman na jiyan can dana kawo" Iccen ta tsugunna ta fara shirin dauka kamun suji kukan kaman cikin gidansu ake yin shi. Fasa daukar iccen tayi ta dago kai ta kalli baba dake tsaye fuskar shi dauke da mamaki. "Bari in......... " Bai karasa ba yar sanda mace ta shigo ko sallama babu. Bata ko bi takan baba da safiyya dake rafka salati ba. "Ku shigo" Yar sandar ta fadi. Wasu guda hudu ne suka shigo maza. Cikin rawar murya baba yace "Subahanallahi. Lafiya kuwa?  Meke faruwa..... " Alamun sungane me yake nufi basu nuna bama ballanta na suyi yunkurin amsa shi. Cacumar shi sukai kaman barawo suna janshi yana turjewa sukai waje dashi. Safiyya data ruga cikin gida yar sandar na bin bayanta ke kiran. "Inna mun shiga uku. Innaaa yan sanda sun tafi da baba" Da gudu inna ta fito daga daki tana gyara daurin zani. Hannunta dana safiyya yar sandar ta kama ta a jansu suna kuka har kofar gida. Lokacin unguwar harta cika kaman zata fashe. Mutane tsaye cirko cirko suna kallon ikon Allah. Wasu kuma na tambayar me Malam audu zai aikata haka har yan sanda mota uku. Dan kowa yasan halayyar shi. Mutum ne mai fara.a ba.a taba ganin yai rigima da kowa ba. Safiyya dake wani irin kuka tana kokarin kwace hannunta daga rikon da yar sandar tai mata. "Me mukayi muku? Me......... " Cik maganarta ta tsaya mata a wuya ganin fu.ad jingine da mota. Kayan dazunne a jikinshi. Saidai fuskarshi sanye take da wani baqin gilashi na rashin mutunci. Wani karfi taji yazo mata. Ta ture yar sandar. Da gudu tana kokarin karasawa inda fu.ad ke tsaye wasu yan sanda suka sha gabanta. Cikin isa da iko yace. "Allow her wasu cikin ku su tafi da wancen mutumin gidan kawunta ku tattaromun kansu gaba daya. Bance kubar ko jariri ba" Suna bata hanya ta karasa. Tsugunnawa tai gabanshi. Kuka take kaman zata shide. "Dan Allah..... Dan..... Dan girman Allah ka sake su. Ni... Ni nai maka laifi. Ni zaka hukunta" Wani rawa yaji zuciyarshi nayi. Glass din idonshi ya sauke. Ya kafa idanuwanshi kan safiyya dake durqushe gabanshi tana kuka. Gaskiya ta fada. Rikicin shi tsakanin ita da shine da kuma kawun ta. Sai dai yanda yakejin wani yanayi na saukar masa da kasala ya tabbatar masa ita bazai iya hukuntata ba. Bakuma zai yafe hannun data daga mishi ba. Ba halin shi bane a taka shi a bashi hakuri ya hakura. Ba halin shi bane a roke shi ya amsa. Yana da tabbacin abu dayane.  Za.a taba kowa banda ita. Zai tabbatar da marin shi ya fita a jikin duk wani wanda ta damu dashi. Wani numfashi ya sauke yana cije leben shi na kasa. Kallonshi ya maida kan yan sandan da tuni sun tura inna bayan mota. Baba kuma an tafi dashi aje a dauko su kawu. Da ido ya kira yar sandar data riko inna. "Bana son ganinta. Don't touch her. Ki hadata waje daya da mahaifiyarta" Babu musu ta cacumi safiyya. Rike masa kafa tai tana rushewa da kuka. "Na shiga uku ni safiyya. Dan Allah ka rufa mana asiri. Ka kyalemun su inna. Ni kome zakai mun kayi mun. Ni nai maka laifi basu ba" Tsugunnawa yai yasa hannu ya banbare yan yatsun safiyya yana fadin "Let go of me........." Tureta yai yar sandar ta cumimiye mata hijab ta jata tana ihu. Wani irin abu yaji kirjinshi nayi. Kai yake girgizawa saboda baya son me yake ji. Sam baya son abinda yake kokarin faruwa.......! [4/4, 5:56 PM] Fatima saleh: *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ           12 "Wani ya sake trying mun number din fu.ad please" Haneef ya fadi muryarshi a gajiye. Sunkai mintina wajen talatin suna neman wayar fu.ad a kashe. Lukman na shirin sake dialing kira ya shigo. "Hamza ne..... " Yace yana dagawa da fadin. "Hello ina jinka hamza" Wani numfashi hamza ya sauke sannan yace. "Please karka fadama fu.ad. promise me sunana bazai fito ba cikin maganar nan" A kagauce lukman yace. "Wallahi bazai taba jin daga bakinka maganar ta fito ba. Trust me nasan fu.ad bazan so saka cikin rikici dashi ba" Sai da ya dan tauna maganar jim sannan ya nisa yace. "Ya sani na dauko masa yan sanda har mota uku. To be frank bansan abinda zai dasu kenan ba. Yasa an tattara wata yarinya da family nata sunkai su sha biyu. Yanzun haka muna dawanau. Mun kusan shiga cikin gari. Please kuzo abin is getting out of hand. Akwai yara kanana" Haneef lukman ya kalla. Jikinshi ko ina bari yake yi. "Wallahi fu.ad ne haneef........" Abinda hamza ya fada masa ya maimaita musu. Daga haneef har pha.iza salati suke. "Wallahi bansan inda fu.ad ya kwaso wannan halayyar tashi ba. Babban yaya nada zafi amman ba irin wannan ba" Cewar haneef da yake jin kaman ya juya ya koma wajen zaman makokin shi. Ya gaji da halin fu.ad da rigingimun shi. Shisa har baya so yace zaizo. In yana can kasar waje hankalinsu kwance yake. Daga pha.iza har lukman sun kasa cewa komai. Mumyn su kawai taima text cewan tana tare dasu haneef zasu je gida su dawo. * Suna zuwa police station din ya tabbatar an tura su cell an kulle gaba dayan su. Aka dauki statement din shi cewar yana filing charges akan assault. Ya shiga motarshi ya tafi gida abin shi. Alwala ya dauro ya fito ya tafi masallaci yai sallar magrib. Sannan ya dawo. Baibi takan wayarshi ba. Yana sane ya kashe ta dan baya son su haneef su dame shi. Mota yakoma ya dauko sauran burger dinshi da pizza ya dawo babban falo ya kunna t.v yana kallon aljazeera sport. Kallo daya zakai masa kagane idanuwanshi ne kawai akan t.v din. Sam hankalin shi na wani waje daban. A lokutta da dama inyai rashin mutunci irin wannan yana bashi wani satisfaction na daban. Yanajin cewar ya isa. Yanajin cewar an masa ya rama. Sannan bacin ran yakan guje daga zuciyarshi. Dakyar ya karasa tura burger din ya bi da fresh milk saboda yasan jikin shi na bukatar abinci. Yana saurin burning calories. Amman yau bayajin yunwar sam. Ga zuciyarshi ta mishi wani iri. Jikin kujerar ya koma ya kwanta sosai. Ya lumshe idanuwansh. Ba abinda ke masa yawo sai fuskar safiyya da kalar kukan da take yi. Baisan dalilin dazaisa hakan ya dame shi ba. Kukan ya tsaya masa a rai. Yanayin da yake ji bakon abune a wajen shi. * Bayan da haneef bai ba da yan sanda su saki su safiyya amman suka ki sauraron shi. Sun kuma tabbatar masa inba fu.ad bane ya janye case din da kanshi ko bail ba zasu bayar ba. Kallon su safiyya yake da suke rakube cikin cell din mata sunata kuka. Dayan cell din kuma mazane ciki matasa guda biyu duk zasu kai sa.anin haneef din. Sai magidanta. Haneef ya gane dayan magidancin shine wanda sukai karo da danshi a safiyar ranar. Ranshi bace yace ma lukman. "Muje gida kawai. Nasan fu.ad nacan" Jiki a sanyaye lukman ya bishi suka samu pha.iza zaune cikin mota inda suka barta. * Suna parking motar haneef ya bude ya fita. Ko rufe murfin motar baiba saboda ranshi a bace yake. Ko sallama baiba ya shiga gidan.  A falo yaga fu.ad zaune jikin kujera ya rufe idanuwanshi. Wani irin kallo yake masa mai cike da fassarori daban daban. In akwai abinda ya tsana a duniya bai wuce wulakanta dan adam ba. "Fu.ad......." Ya kira muryarshi can kasa. Sai lokacin ya dago ya sauke idanuwanshi da sukai wani duhu kan fuskar haneef. "Yanzun zaka kira kasa a sake su. Bana bukatar jin me ya hadaku. I want them out of that hell hole" Kallon haneef kawai yake. Ya dauke idanuwanshi zuwa kan su pha.iza da lukman da suka shigo dakin da sallama. Lukman ya karasa inda yake ya zauna. Muryarshi a sanyaye yace. "Fu.ad bansan meke damunka ba. Me yake......... " Katse shi yai da fadin. "Cut it please" Mikewa tsaye yai ya kalli haneef da har wani huci yake. A hankali ya karasa dab dashi. Cikin fuska ya kalle shi yace "Ka fita daga maganar nan. Babu ruwanka" "Wallahi wannan karin abbah zan fada ma. Wannan mugayen halayen naka nagaji da boye su. Dan kana da kudi sai ya zama menene? Abbah bashi da kudi?  Wa kaga ya taba wulakantawa?" A tsawace fu.ad yace "Saboda me zata sa hannu ta mareni?  Wallahi sai marina ya fita a jikin gaba daya yan gidansu" Pha.iza dake gefe tace "What? Mari?  Waya mareka bro?" Hankalinshi ya maida kan pha.iza yace "Wata kucakar yar kauye. Ta daga kazamun hannunta ta mareni" Rai a bace pha.iza tace "Ashe ma sune da laifi. Waye uban ta da zata daga hannu ta mareka" Kallon haneef yai dake fassara 'kaga ita ta gane karatun. Saura kai' Muryar haneef can kasa yace "Bana son jin me ya hadaku. Kawai ina son ka sa a sake su ne" Kai yake girgiza masa alamar abinda bazai yiwu bane kamun yace. "Yanda ta mareni saina wulakan ta su sai......... " Mari haneef ya dauke shi dashi. Daya sa iskar dake dakin kanta ta tsaya. Hannu yakai kan kumatun shi cike da mamaki. Pha.iza ta rike baki. Lukman kanshi bai taba zaton haneef zai iya marin fu.ad ba. Cikin bacin rai yace "Kai harka isa ka wulakanta wani? Me kake dashi?  Nawa ne a account dinka?  Yaushe su abbah suka gama daukar dawainiyarka? Fu.ad kai hankali da duniya wallahi" Idanuwanshi cike da wasu hawaye daya ki bari su zubo. Hannun shi har lokacin yana kan kuncin shi. Tun yarinta yafi shakuwa da haneef fiye da kowa. Duk wata rashin kunya. Duk wata fitsara dazaiyi haneef na shanye wa. Babban hukuncin dazai masa shine yaki kula shi. Ko fada ba ko yaushe haneef yake iya mish ba. Haneef ya sha hada kudin break dinshi na makaranta ya bar ma fu.ad saboda yai mita nashi sun mishi kadan. Yau haneef din nan ne ya mare shi saboda wasu talakawa. Ba akan wani abu ba akan yan kauye. Wani daci yake ji a zuciyar shi. Tunda yake duniya bai san ciwon wani abu ba irin na yanzun. Baima taba zaton akwai randa zaiji son zubda hawaye kan bacin rai irin na yanzun ba. Baice komai ba yasa hannu ya zaro wayarshi daga aljihu. Ya kunna ta. Number din inspector din dayai saving dazun yai dialing. Ringing daya ya dauka. "Nai dropping charges din gabaki daya. A sake su" Baima jira amsar dazai bashi ba ya kashe wayar shi. Kusa da haneef dake tsaye yana kallon shi ya karasa. Saida yasa idanuwanshi cikin nashi yace. "Bakai karya ba. Ina alfahari da abinda na tara. Saboda kafi kowa sanin bakar wahalar dana sha kamun inje inda nake a yanzun. Kafi kowa sanin clubs da adadin wasannin danai playing. Kana tare dani a duk zaman asibitin danai in na samu ciwuka. Kana tare dani lokacin da na fara wasa da kano pillars. Kana tare dani lokacin da mack ya fahimci zan iya zama wani abu. Kana tare dani a duk wata wahala tawa. Yau kaine ka daga hannu ka mare ni akan wasu banzaye. Yau kaine hannunka ya taba fuska ta saboda anci zarafina nai kokarin ramawa" Wani numfashi fu.ad ya dauka kamun ya juya da gudu yahau benen zuwa dakin shi. Suna jin karar datso kofar dayai kaman maison karyata. Lukman ya tashi ya bishi. Wani irin kallo pha.iza take ma haneef dake nuna rashin jin dadin abinda yayi. Muryarshi can kasa yace mata "What is with the look?" Kallon shi tai cikin fuska "Wata ta mare shi kabarshi yaji da abu daya. Ba saika kara mishi ba. Na yarda yana da halaye marassa kyau. But he is our brother. Na dauka yan uwa suna goyon bayan yan uwansu ne..... " Hannu haneef ya daga mata alamar tai masa shiru. Saida ta kalle shi na tsayin mintina biyu sannan ta wuce abinta. Kujera ya samu ya zauna ya dafe kanshi da hannuwa biyu dan baisan me ya kamata yayi ba. **** "Kukan nan ya isa haka safiyya" Inna ke fadi ta dora da "Kije ki kwanta kinji. Komai yazo karshe ai" Cikin kuka safiyya tace "Duk ni naja muku inna duk....... " Baba ne ya katse ta da fadin "Bakiyi laifi ba safiyya. Nama ga hakurin yunusa dabai masa komai ba. Ko da yake duniya ce tafi bagaruwa jima" Tashi safiyya tai ta koma dakin su ta shimfida tabarmarta da zannuwa tasa pillow dinta ta kwanta. Wani abu ya tsaya mata a wuya. A bangare daban tana jin tsanar fu.ad. Wani bangare kuma dauke da yanayin da bata san fassarar shi ba. *Washegari* Jikinta babu karfi tagama ayyukan gidan tsaf. Taja ruwa tai wanka. Haka tasha tsuran ruwan koko saboda sam bata jin dadin komai. Jikinta saikace wadda zazzabi ke shirin kamawa. Usman ne ya shigo ya kalle ta yace "Yaya Ado na kira. Yana waje" Ji tai yanayin da take ji ya karu. Kallonta ta kaida kan inna da ta kafeta da idanuwa. Tasan fassarar kallon ta sauke numfashi tace ma usman "Kace gani nan zuwa" Hijab dinta ta dauka. Fuskarta a dakune ta fita. Dakyar ta iya mishi sallama. Yana ganinta ya wani wangale baki. "Amarya ta nan da wata uku in shaa Allah" Ado ya fadi yana kara fadada murmushin shi. Abinda ke tsaye wuyanta taji ya kara girma. Tasan ko sauran kwanaki nawa aurensu ba saiya tuna mata da bakin shi ba. Har yanzun tana jimamin yanda zata zauna da ado a matsayin miji baya bata son shi ko kadan. Ko fara.a take taganshi sai taji ranta ya baci. Babu yanda zatayi ne kawai. Dakyar tace masa. "Lafiya dai ko?" Ya girgiza kai yace "Lafiya kalau. Baba ne yake fadamun ashe wani tsautsayi ya fada gida kuma. Shine nace bari kamun in wuce gona in biyo in muku jaje" "Allah sarki. Aikam mungode sosai. Bara in shiga in fada ma inna sai ka shigo ku gaisa ko?" Safiyya tace tana koma cikin gida ba tare data jira amsar shi ba. Bata jima ba ta fito tace masa ya shigo. Cikin fara.a da mutunci suka gaisa da inna yai musu jaje. Dazai tafi ya kawo dubu daya yaba inna wanda dakyar ma ta karba. **** Safiyya itace yarinya ta biyu cikin yaya uku kacal da malam audu da zainabu suka mallaka a duniya. Kasancewar duk yaran da suka haifa har hudu basa shige kwana arba.in a duniya Allah ke karbar abinsa. Sai akan saminu da shine babba a yanzun. Sai safiyya sai usman. Da malam audu har zainabu yan nan asalin garin bichi ne.  Mutanene masu karamci da gudun rikici. Talakawa ne sosai sai dai Allah ya azurta su da wadatar zuci. Duk yan uwan malam audu sun dan fishi dan abin hannu. Dan shi gonar shi daya yar karama. Ita yake noma yake rufa ma kanshi asiri. Sai dai bai taba damuwa da halin rashi da yake fama dashi ba. Haka rayuwarsu take tafiya. Saminu kuwa. Yunusa kanin malam audu ya samu yan kudi ya siya mishi babur na hannu. Yake acaba dashi. Hakan ba karamin rage ma malam audu wahalhalu yai ba. Domin yanzun haka saminu shi ya biyama kanshi kudin jarabawar aji shidda sakandire. Kuma yake daukar dawainiyar karatun usman. Duk da saka mata a makarantar boko ba damuwar zuri.ar su malam audu yai ba. Hakan bai saka shi kin saka safiyya a makaranta ba. Lokacin da tazo aji uku tai jarabawa bataci ba. Hakan ba karamun damunta yaiba dan har ranta tana da kwadayin karatu. Lokacin Ado dan mai unguwar su ya fara zuwa wajenta. Kasancewar ya fito daga gida na mutunci gashi yaro mai hankali da girmama mutane. Ya fara ginin shi. Manyan shi na zuwa da maganar neman auren safiyya malam audu ya amince. Ba a wani saka abin da nisa ba. Wata hudu kacal aka saka. Abinda ba su sani ba shine biyayya ce kawai ta saka safiyya amsa su lokacin da malam audu yazo da maganar da kuma karin bata kula kowa sai ado din. Amman ko kadan batajin sonshi a ranta. Duk da bashi da makusa. [4/4, 5:58 PM] Fatima saleh: *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ          13 Yanajin lukman na kwankwasawa harya gaji ya tafi. Baya son magana da kowa. Subar shi ya sha iska abin shi. Ai komai yayi su ba dai dai bane ba. Komai yai rashin mutunci ne. A dakin shi yai sallar isha.i. Yaje ya watsa ruwa sannan ya dawo yai kwanciyarshi. Yanajin wayarshi na ringing. Ya duba yaga haneef ne. Rejecting yayi. Ya sake kira ya kara kashewa. Text yaji ya shigo ya bude haneef ne. "Stop acting like a kid and pick the call" Share shi yai. Inya gaji ya hakura. Aikam daya sake kira har hudu bai dauka ba wani text din yai masa yace sun koma bichi. Yana karantawa ya kashe wayarshi gaba dayama. Gara su tafi abinsu subar mishi gidan. A haka bacci ya dauke shi. Wannan karon ma safiyya ta kutso masa kai cikin mafarki. Zaune take gaban wata bishiya tana ta kuka. Shikuma yana tsaye a gefe yana kallonta. Tana dagowa ta kalle shi da fuskarta a kumbure idanuwanta cike da hawaye. Ya farka da sauri. Wani numfarfashi yake fitarwa. A ranshi yana tunanin wannan yarinyar ko dai mayya ce. In ba haka ba shi mafarki ma ko yana yinshi to daya farka baya rikewa. Amman karo na biyu kenan da mafarkinta ya hana mishi bacci. Wanka ya shiga ya sake yi saboda wani iri duk yake jin shi. Daya dawo ya kwanta koya ya rufe idanuwanshi safiyya yake gani. Dakyar ya samu bacci ya dauke shi. *Bayan kwana biyu* Zaune yake dakin shi yana kallo. Gabanshi ledojin snacks ne dayake ci tuli guda da kuma wanda ya cinye. Lukman ya turo kofar ya shiga hadi dayin sallama. Amsa mishi yai. "Wai badai baka shirya ba. Karfe tara ne fa addu.ar nan" "Allah ya jikanta. Na dauka na fada maka babu inda zanje?" Fu.ad ya amsa shi hankalinshi nakan ball din dayake kallo. Girgiza kai kawai lukman yai yace "Sadakar ukkun hajiya babbar ne ba zaka ba fu.ad? Ka kyauta kenan?" Sai lokacin ya juyo ya kalli lukman. "Nake jin ance addu.a duk daga inda kayita zuwa take?  Nace Allah ya jikanta ko akwai inda aka wajabtamun zuwa ne?" "Allah yaye maka" Lukman ya fadi yana juyawa. "Amin. Ka jamun kofar Mr. i know what is right" Bai ko juyo ya bi takan fu.ad ba. Kofar yabari a bude kuma yasan da gangan yayi dan haka ya tashi ya kulle kofar shi. Lumshe idanuwa fu.ad yai yana sauke wani dogon numfashi da baisan yana rike dashi ba. Kirga daya zuwa goma yakeyi cikin kanshi yana son ya dai daita bugun da zuciyarshi keyi. A kwanakin nan biyu a daddafe yayi su. Ga rashin wadataccen bacci. Ga iya kokarin shi da yake na ganin ya karyata dalilin da yasa yake son zuwa bichi. Hakan yasa shi ganin yayi duk wani kokarin shi nakin zuwa wajen addu.ar yau. Tunda dare haneef ya kira shi. Baima daga ba duk da ya huce fushin marin dayai masa. Yana jin share shinne kawai. Yanzun da lukman ya shigo ya kira bichi ba karamun kara mishi son zuwa yake ba. Cake din dake hannun shi daya ci rabi ya ajiye saboda ji yai bazai iya karasa cinyewa ba. Ya maida kafafuwanshi kan kujera ya kwanta cikinta sosai yanajin wata kasala ta rufe shi. Lumshe idanuwanshi yai duk da ba baccin yake ji ba. Wayarshi yaji ta soma ihu. Yai niyyar share ta ya dai dauko ya duba. Da sauri ya daga yana fadin "Hello momma" "Fu.ad lafiya dai ko?  Haneef yace mun ba zaka zo wajen addu.a ba.  Yanata kiranka ma kaqi dauka" Kasa yai da murya sosai yace "Kaina ciwo momma. Bana jin zan iya handling hayaniyar shisa" "Ayya ka sha magani. Ka kwanta. Muma anjima da yamma zamu taho gaba daya ai. Allah ya kara sauki" Ya amsa da "Amin momma. Allah ya dawo daku lafiya" Ta amsa shi ta kashe wayar. Baya son ana mishi maganar zuwa bichi ko kadan. *5:30pm* Yau bayajin zai iya zuwa ball. Dama lukman na nan sai su fita tare. Babban falo ya fito. Jin cikin shi yake wayam kaman ba dazun ya gama loda mishi burger da milkshake ba. Sallamar su pha.iza yaji. Ganin harda abba yasa shi karasawa da fara.ar shi. "Abbah sannunku da dawowa" Da fara.a suka amsa mishi. Haneef yace "ya ciwon kan?" Hankalin shi ya maida kan yan biyu da suke rikici kan waya ya share haneef yace musu "Ku bakwa gajiya da rigima ne" Idanuwan hassana cike da hawaye tace "Hussain ya fasamun screen din waya" Kallon fu.ad yai yace "Nafa bata hakuri. Kuma har tawa wayar na bata nace muyi musaya. Tace bata so wai tawa duk ta gurje" Dariya fu.ad yai. Yasan hassana tana da rikici sosai. Su momma kam wucewa sukai abinsu suka bar su nan. Wayar hassana fu.ad ya karba yaga dan tsagewar datai bama wata bace can. Shi ya siya musu samsung din wancan zuwan dayai. "Yanzun ya kike so ayi?" Fu.ad ya tambaya. A shagwabe tace "A sakemun screen din. Kuma nasan zaiyi tsada sosai" Wayar ya mika mata yace "Kuje da hussain to. Kikai a gyara in zaku karbo sai in baki kudin ko?" Wani murmushi tai mishi kaman ba ita ke shirin yin kuka yanzun nan ba. "Thank you bro" Ta fadi. Murmushi kawai yai ya wuce abinshi. * Da dare su duka suka hadu kan dining table sunata cin abinci. Kaman koda yaushe hassana da hussain rigima suke tayi. Hakan baya nufin babu jituwa tsakaninsu. Sai kayi kokarin taba daya zaka ga yanda suke kaunar junansu. Pha.iza hankalinta nakan fu.ad tunda suka dawo taganshi wani iri dai. Da yanzun ya damu kowa da tsokana. Ko yana tambaya wanne abinci ne momma ta dafa da kanta wanne yan aiki suka jagwalgwala. Saida ta hadiye abincinta sannan tace mishi. "Bro meke damunka?" Kafada yadan daga mata sannan yace "Me kika gani?" "You are strangely quiet" Kai kawai ya langabar gefe bai amsata ba. Momma tace "Da gaskiyar pha.iza meke damunka?" Yamutsa fuska yai hadi da fadin "Kawai banajin dadin jikina ne" "Ka tashi in rakaka asibiti" Cewar haneef daya ture plate din abincin shi da alamun shirin mikewa. "Pha.iza mikomun robar ruwan can" Fu.ad ya fadi kaman ba dashi haneef ke magana ba. Abbah ke kallon su yana murmushi yace "Fu.ad bakajin haneef na magana ne" Sake daquna fuska fu.ad yai yace "Naji shi abbah. Ba saina je asibiti ba" Mikewa fu.ad yai yace musu "Nikam saida safenku. Zan kwana a gidansu lukman ne" Su duka suka amsa shi momma ta dora da "Ka gaishe da hajiyar su lukman din" Ya amsa da "In shaa Allah" Yana wucewa. Ba abinda ya dauka dan har kayan sawa yana dasu dakin lukman. * "Kasan babu abinda na tsana sai a tusani a gaba ana dariya" Fu.ad ya fadi yanajin kaman ya kwada ma lukman mari. Dariya yake har da rike ciki dakyar ya iya cewa "Mayu fa kace fu.ad" Juya idanuwanshi yai yace "To inba mayu bane suka kamani. Ni banajin dadin jikina and bazan iya cewa ga exact abinda ke damuna ba" Abin dariya yake bama lukman. Wai mayu. "Kai ba mai ciki ba balle ince mood swing ka....." Bai karasa ba saboda pillow din da fu.ad ya jefa mishi akai yana dariya shima. Babban dalilin dayasa yace gidansu lukman zai kwana kenan. Yasan zaiji shi light ko yaya yake. Beside baya son magana da haneef. Saboda yana da wani abu a tattare dashi da yake sa kaji kana son gaya mishi dukka abinda ke damunka. Yasan inya tambaye shi zai iya fada mishi. Lukman kam zai iya fadar wani shirmen suyi dariyarsu. Lukman ya rigashi yin bacci. Har tsoron rufe idanuwanshi yakeyi kar yaga safiyya. Amman kaman abin baki. Bacci na dauke shi abinda yake gudu ya faru....! **** "Da yawan lokutta kaddara kan hada abubuwan da hankali baya dauka" Murmushi tai tace "Kaman yanda kaddara ta hada ni dakai" Kai ya daga mata cikin yarda da abinda tace kamun ya sauke idanuwan nan nashi da kalarsu ke bata mamaki cikin nata. Bata san lokacin da tace "Idanuwanka nabani mamaki" Murmushi yai mata da taganshi har cikin idanuwan shin nan kamun yace "Yanda kika shiga nan yana bani mamaki" Ya dafa kirjinshi dai dai inda zuciyarshi take. * Bude idanuwanta tai. Muficin dake gefenta ta dauka ta tashi zaune tana fifita. Amman a banza. Wata irin zufa take da bata da alaka da yanayin zafin da akeyi. Tagaji da wannan abin. Jan kafafuwanta tai. Ta hada kai da gwiwa wasu hawaye masu dumi na zubo mata. Wannan wanne irin abune. Sati daya kenan. Da duk numfashin da zata ja ta fitar da tunanin shi a ciki. Ta ma rasa me take ji game dashi. Saboda wani irin yanayi ne take ji kala kala. Ko lomar abinci zata kai yana nan cikin kanta. Dashi take komai a manne. Bata da ikon bacci mai lafiya ba tare dashi a cikin mafarkinta ba. Gashi wani irin mafarki take yi da duk inta farka sai taji shi kaman gaske. Kalaman da suke ma juna a mafarkin yafi komai daga mata hankali. Kamata yai ace ko mafarkin shin zatayi ace rashin mutunci yake mata. Yanda taga fuskarshi haka take ganinta a mafarki. Ko jiya da dare saida tai kuka saboda bata san abinda ya dace tayi ba. Saurayin da tasan ba zata sake ganin shi ba. Akan me zai manne mata har haka. Saida tai mai isarta sannan taja jiki ta koma ta kwanta. Addu.o.i tai sosai. Bacci mai nutsuwa ya dauke ta batare da mafarkin komai ba. * Jikinta babu wani karfi ta samu tagama sharar gidan. Saida tai wanke wanke sannan taja ruwa taje tai wanka. Shafa man take yi amman hankalinta na wani wajen daban. Ji tai an tabata da sauri ta dago. "Safiyya meke damunki ne kwana biyun nan? Sai aita magana bakyaji?" Inna ke fadi da alamun damuwa. Cikin sanyin murya safiyya tace "Yi hakuri inna. Banjiki bane shisa" "Nasan bakiji ni ba ai. Ina tambaya ne ko lafiyarki?" Saida ta langabar dakai sannan ta amsa da "Bakomai" Da alamu inna bata yarda bakomai ba. Tadai kyale ta ne kawai. Da hanzari ta karasa shafa man. Ta tashi ta dauko wata doguwar riga ta atamfa ta saka. Kasancewar ranar alhamis ne babu makaranta. Yasa safiyya ta koma kan tabarma tai kwanciyarta. Tunda abincin rana ba lokacin zata dora ba. Addu.a take sosai ta fatan yanda tasan ba zata sake ganin fu.ad ba Allah yasa ya fita daga tunaninta har abada......! [4/4, 6:00 PM] Fatima saleh: *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ          14 Agogon shi yake daurawa. A cikin kanshi babu komai sai son barin kasar gaba daya. Son yabar komai inda ya kamata ya zauna daga farko. Amman abinda yake so a zuciyarshi da kanshi ya sha banban. A yan kwanakin nan mafarkan da yake sun yawaita. Har idanuwanshi sun fada saboda bashi da wata wadatacciyar nutsuwa. Komai baya masa dadi. Baya son zama shi kadai. Danma lukman na hutu sai abin yai masa sauki. Gudun haneef yake dan baya son gaya mishi asalin abinda ke damun shi. Ta ina ma zai fara ce masa shi fu.ad yau tunanin mace ya saka shi a gaba. Tunanin macen ma kucaka yar kauye. Abin da dan nauyin fada. Tunda shi baisan me yasa ma yake jin abinda yake ji din ba. Jiyai an turo kofar hadi da sallama. Ya lumshe idanuwanshi ya bude su. Haneef ne ya nemi waje gefen gadon shi ya zauna. Kallon shi yake sosai daya soma damun shi saboda yasan zai karanci damuwa a fuskarshi. Yace "Nasan ba fushi kake mun ba. Avoiding dina kake nakuma rasa dalili. Meke damunka?" Takalmin shi ya wuce ya dauka. Ya dawo ya zauna ya na saka socks. Ciki ciki yace "Ba abinda ke damuna. Kabarni in shirya a nutse" Idanuwa kawai haneef ya zuba mishi. Yanata kallon shi harya karasa shiryawa. Wata yar jaka ya dauka. Hannun shi ya sa cikin gashin shi hadi da fadin. "Fuck this...... " "Language fu.ad.....language please" Haneef ya fadi yana murmushi. Kai kawai fu.ad ya jinjina ya kalle shi yace "Kawai wani abune yake damuna. Banajin zan iya magana akai yanzun. Just drop it" Gira haneef ya daga masa. Yana kallon yanda yake kokawa da kalmar dazai fada. Dakyar ya iya cewa "Please. Just drop it" Mikewa haneef yai yana yar dariya hadi da fadin. "Since you asked so nicely. Muje sai mu biya mu dauki lukman mu rakaka" Bai ce komai ba ya bude kofar ya fita. Cije lebe yai ya rufe idanuwanshi ya bude su da yake fassara baya son abinda ke shirin faruwa. Gaba dayan su suna falo tsaitsaye abbah ne kawai baya nan. A tabare yace "Momma mana. Me yaran nan sukeyi" Dariya sukai gaba daya. Sunsan baya son bankwana. In da za.a barshi zai sulale kowa bai sani ba. Pha.iza tace "Dame kaga ya maka kama?" Hassan ya amsa da "Bro dinmu zamu raka airport" Momma ya kalla idanuwanshi cike da rokonta tace musu suyi zamansu. Dariya kawai tayi tace "Allah ya tsare ya bada sa.a. A duk inda kake addini da tarbiyarka suzo farko fu.ad. Karka zubda su domin rudin duniya......." Fu.ad ya katse da fadin "Banda abokan banza. Banda dauko al.adar da ba tamu ba.....banda banda banda ...momma na haddace duka" Haneef ya tallabe mishi kai. Ya dafe yana fadin. "ouchh that hurt" Dariya sukai gaba daya. Dole ya yarda su pha.iza suka bisu. Lukman suka kira ya fito suka dauke shi shima. Har aiport suka raka shi. Su hussaina na jero mishi tsarabun da suke so ya siyo musu. Ya amsa musu da saiya kira mama yaji suna kokari a islamiyya da boko sannan. **** *Bayan wata biyu* EUROPE. Babu abinda ke taimaka masa sai bacci. Da hannu biyu yake tallabar mafarkan ta yanzun. Da kanshi yake fatan dare yayi ya kwanta bacci. In da babu su baisan yanda zaiyi ba. Komai ya jagule mishi a watannin nan. Komai yakeyi kaman wanda akai ma chargy akai masa loading din abinda ya kamata yayi. Abinci ma timing yai yasa a wayarshi. Da yaga reminder zai tura ma cikinshi komai ya samu badon bakin shi nagane dadin abin ba. Shi ba abokai yake yi ba. Saidai team mates kawai. Maganar data wuce wadda ta danganci abinda yake tarasu bata hadasu. Sai ya wuni baice ma kowa komai ba. Fuskar nan a dakune. Bamai shiga harkarshi kaman yanda baya shiga ta kowa. Da niyyar sai yai wata shidda zai je gida kwana biyu yazo. Amman sam yaga ya kasa. A daddafe yai wata biyun nan. Ticket dinshi dake kan gado ajiye yake kallo. Yana son da duk wani sauran karfi dayake dashi yai fada da son zuwa gida da yake yi. Da duk numfashi da yake shaka yana jin yanda komai ke ruguje masa. Yana so yaganta. In bai ganta ba zai iya karasa gigicewa. Yana da wasa cikin sati uku masu zuwa da zai iya zama silar ci gaban shi. Bazai iya yinshi cikin kwanciyar hankali da nutsuwar da yake so ba inhar baije yaganta ba. Tunda ya tashi damuwa labarinta kawai yakeji. Sai yanzun ne ta iso inda yake. Tunda ya tashi kunci nisantarshi yakeyi amman yanzun ya samu wajen zama tare dashi. Tun girmanshi ya ke dauka an damka mishi ikon tsara rayuwarshi yanda yake so. Yanda ya zanata shine zaikai shekara ashirin da takwas. Zai samu yarinya mai zurfin karatu wadda zata dace da tsarin rayuwarshi ya so. Zai aurenshi babu wata damuwa. Zasuyi rayuwarsu daga shi sai matarshi. Zai rayuwarshi da abu biyune.  Zuciyarshi zata kaunaci abu biyune kawai. Daga ball sai matarshi. Bashi da wajen ajiye wata damuwa. Baisan ya akai kaddara tai masa wannan kamun ba. Bai fahimci asalin abinda yake ji ba sai jiya da yamma daya zauna yana kallon wani film "Heartbeat" tukunna. Abinda ke faruwa dashi shine yake faruwa da guy din ciki. Sun kira abinda yakeji da *So* . Sai dai bai taba dauka cewar *Akan so* zaiji ya rasa farin cikin shi ba. *Akan so* zai kasa walwala.  *Akan so* zai ji ya kasa sakewa yai ball daya taso da ita a zuciya tun yarinta. Wani numfashi yaja ya sauke hadi da mikewa. Yagama tsaida magana. Gobe zaibi jirgin karfe 8. Dan haka ya fita ya ga kozai samu abinda zai saima su pha.iza. **** "Dan Allah ku samamun lafiya lami.  Mutum bashi da ikon yai shiru saikun dame shi da bakar tambaya" Safiyya ta karasa maganar tana zabga wani tsaki. Su lami kam kallon juna suke. Saboda sun rasa kan safiyya a watannin nan. Ta canza gabaki daya. Abu kadan zakai mata sai tahau ka da fada. Sam ba halinta bane. Safiyya nada fara.a da hakuri. Su zasu iya cewa abinda duk ya bata mata rai ba kadan bane. Amman yanzun kullum cikin kunci take. Babu fara.ar nan. Ga wata rama datai. Takan ga kuskure a duk wata magana da zasuyi mata. Wani hawaye suka zubo ma safiyya ta sa hannu ta goge su. Cikin tashin hankali lami tace "Subahanallah. Safiyya kiyi hakuri wallahi ba nufinmu mu bata miki rai har haka ba. Muna tambaya ne kawai dan mun damu" Jummai ta dafata tace "Abinda lami ta fada gaskiya ne. Bamu saba ganinki haka ba shisa muke tambaya" Wasu hawayen taji sun sake zubo mata. Ita kanta halayyarta ta dameta. Sai dai bata da yanda zatayi. Cikin sanyin murya yace "Karku damu. Ba ku kuka batamun rai ba. Abinda ke damuna bashi da alaqa da tambayarku" Fuskokinsu suka nuna alamar jin dadin basu suka bata mata rai ba. Suna gudun tambayarta ko menene. A haka malamin hadith dinsu ya shigo. Anata karatu safiyya hankalinta na wani waje daban. In zaka yankata bata san me suke fada ba. Wannan abinda daya sameta ya isheta. Bata da damar wani kwakkwaran motsi sai taji shi manne da ita. Wani irin mannewa yai mata da zata iya rantsewa tana jin dankonta har a fatar jikinta. Da dare mafarkinshi. Da rana tunanin maganganun shi. A zuciya fatan sake ganin shi tunda na son fitar dashi yaki faruwa. A kwanakin nan abin ya kara tabarbare mata. Ado ne a tsaye a gabanta. Amman fuskar fu.ad take gani cikin tashi. Magana zai mata muryarshi take ji. Tun inna na tambayarta meke damunta. Harta gaji ta hakura. Wani lokacin in tana kwance shiru takanji inna ta shigo ta taba jikinta taji ko bata da lafiya ne. Ta kasa dainawa. Tana son ta tsaida komai kodan mahaifiyarta data damu da ganinta haka. Bata san taya zakai fada da abinda yafi karfinka ba. Abinda ko dan yatsa ba zaka iya daga masa ba ballantana kai tunanin yaki dashi. Tabarma Allah komai. Shi ya dora mata koma menene kuma shi yake da ikon yaye mata shi. **** Hassan na zaune shida hussaina suna kallon wrestling a New World cinema sunata gaddamar da suka saba. Hassan yace "Yarinya kiyi hakuri kawai. Bafa yanda john cena zaiyi da yan shield" Hararar shi tai tace "Ai dan suna da yawane shisa. Inba tsoro ba ayi da dai daya mana" Amsa zai bata suka ji sallama. Da gudu suka tashi suka suka rukunkume fu.ad saboda basu zace shi ba. Da gudu hussaina ta ruga ta na kiran momma data zo ga bro ya dawo. Hassan kuwa yana tsaye yana kallon shi sosai. Saboda tunda ya tashi bai taba ganin fuskar fu.ad da gashi ba. Banda kanshi baya tara gashi ko ina.  Amman yau fuskarshi cike take da gashi. Da alama rabon dayai aski tun sanda zai tafi. Dan ko gashin kanshi haka yake. Ya kara yawa sosai ga babu ko gyaran fuska. Sai yaga duk ya canza masa. Da sauri momma ta fito. Cikin farin ciki tace "Fu.ad zuwa babu sanarwa haka" Da murmushi yace "Nima fa bansan zanzo ba.  Wai na samu kwana hudu ne shine nace barin zo inyi su a gida" Kallon shi take itama. Da damuwa a fuskarta tace "Aikam gara dakazo. Duk ka canza. Fu.ad ji fuskarka. Wai meke damunkane haka?" Yaji dadin pha.iza data fito tana fadin. "Wooo bro. Kaine haka kwatsam" "Nagaji fa. Bara indan watsa ruwa" Ya fadi.  Hassan ya karbi akwatin shi ya hau masa dashi sama. Ba bata lokaci shima yabi bayanshi. Saida yai kira lukman a waya bai daga ba.  Yai tunanin ko yana da lectures din asabar. Text yai mishi sannan ya shiga wanka. Yana fitowa ko mai bai shafa ba. Yasa wani 3 quarter loose da hoodie. Kwanciya yai kan gadon yana jin wata nutsuwa da baisan ta inda take fitowa ba. Kiran lukman ya shigo ya daga wayar yana fadin. "Dan Allah kazo muyi magana" Lukman ya amsa shi da. "Kazo school ka daukeni. Motata na wajen gyara" Bai musu ba ya katse wayar ya na sauka falo. Momma ce tace masa "Kazo kaci abinci" Yana tafiya yace "Sai anjima tukunna. Barin zo momma. Ba dadewa zan ba" "Allah ya tsare" Ya amsa da amin yana ficewa. * "Me ke damunka?" Shine kalmar farko da lukman ya furta masa yana kallon shi. "Safiyya" Ya amsa mishi yana jingina da mota. Shiru lukman yai yana dakuna fuska. Da alama yana tunanin ya taba jin sunan nan. Amman ya kasa tuna ko a ina. Don haka yace "Wacece safiyya?" Wani kallo fuad ke masa dake tambayar yana nufin bai gane ta ba. Hakan ya fahimta ya sa shi cewa "Ni yazan ingane ta?" Ba yanda zaiyi ne shisa zai fadama lukman. Amman harya fara hango kalar iskancin dazai masa. Muryarshi can kasan makoshi yace "Safiyya ta bichi....." Kwalo idanuwa lukman yai kaman wanda aka gayama an sace motar dayakai gyara. "Safiyya daka kulle ma iyaye?" Kai fu.ad ya daga masa. Shiru lukman yai kmun yace. "Allahu Akbar. Allahu Akbar. Umn Allahu Akbar" Da mamaki fu.ad yace "kabbarar me kake kuma" Jinjina kai lukman yai yace "Ina mika yabona ga Ubangijin dake da iko da dukannin halitta. Ubangijin daya dasa maka zuciyarka yake kuma iko da ita" "Hmm.... " Kawai fu.ad ya fadi yana kauda kai gefe. Dan ya san gaskiya ne kalaman da lukman yai. A yan kwanakin nan yagane shi ba komai bane. "Ni bansan yazanyi ba" Kallon shi lukman yake. Dan har lokacin mamaki yake. Rayuwa kenan. Bawai dan yafi karfin safiyya ba. Shi ba mai cika baki bane ba. Amman fu.ad da safiyya. Wani hadi ne da kwakwalwarshi ba zata ko iya dauka ba. "Wallahi abin nan yamun girma fu.ad na rasa ta ina zan fara ko kuma me zan fada" "Ni kawai ina so inganta ne. Shi ne kawai abinda ya dawo dani. Ko ban mata magana ba lukman" Sauke ajiyar zuciya lukman yai yace "Muje ka aske wannan fuskar. Kadan nutsu tukunna muyi magana" Girgiza kai fu.ad yai "Ba aski nake bukata ba. Nutsuwa ta zata samu idan naganta ne kawai" Wani abu lukman yake ji da bazai fassaru ba. Gabaki daya lamarin duniya ya kara tsorata shi. Kalli yanda lokaci daya fu.ad ya birkice. Wato mutum yaji tsoron Allah duk inda yake. Ka gode masa in yana tallaba maka. Zaka gane kai din bakomai bane lokacin da Allah ya saukar maka da kaddarar da zata birkita maka lissafi cikin kankanin lokaci. "In kana so kaganta. Saika aske wannan gashin fu.ad" Baya son yawan surutu dajan magana dan haka ya zagaya ya bude mota ya shiga yana barma lukman wajen zaman driver. Har sukaje shagon mai aski ba suce komai ba. Kowa da abinda yake sakawa a zuciyarshi. Aski akai mishi. Har yadan nutsu. Sai dai askin saiya fito da ramar dayai sosai. Daman shi ba wata kibar kirki ba. Farinne kawai sai dogon hanci. Suna mota ne yaga lukman ya dauki hanyar gida "Ya haka kuma lukman?" Kallonshi yadanyi ya maida hankalinshi kan tuqin da yake yi. "Ai dai kabari inci abinci. In watsa ruwa muyi sallar azahar ko" Hade fuska fu.ad yai. "Ni da mun tafi yanzun.  Ni bama najin yunwa" Shiru lukman yai mishi. Yabarshi yaji da abinda ke damunshi ma. Yaga alamun fu.ad din so yake ya rage damuwar dake ranshi ta hanyar jan shi da rikici. Dole ya hakura suka je gidansu lukman. Yai wanka ya fito. Ba yanda baiyi dashi ba suci abinci yace baya ci. Jiran shi dai yai yagama ci. Tare sukai alwala suka fita masallaci. Suna dawowa sallar azahar lukman ya tukasu zuwa bichi. Da duk kusancin su da bichi da yawaitar karin bugun zuciyarshi. Lukman kanshi da yake gefe sai yanzun yake ganin tsantsar wautar da sukayi. Yana ganin lokacin da fu.ad zaisan menene rayuwa yayi. Lokacin dazai girbi abinda ya shuka. Sai wani tausayin shi ya kamashi. Saboda yasan ko basu raba wannan abin tare ba. Zai samu nashi kason. Fu.ad kam ya rasa inda tunaninsa ya kamata ya tsaya. Ya rasa me ya kamata yaji. Ya dauka farin cikin shi zai dawo daga lokacin da suka dauki hanya. Amman sai yaji banbancin haka. Saima dayagan su cikin garin bichi. Yaga motar tayi corner zuwa layinsu safiyya. Yaga da gaske shine a cikin garin bichi. Shine yazo yaga safiyya. Lokaci daya wata fargaba da tsoro suka cika mishi zuciya......! [4/4, 6:00 PM] Fatima saleh: *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ          15 *Just wanna say a big thanks to SOFTIE for all the prayers and for being #1 fan of Akan So. May Allah be with you sweetheart and the other fans. Love you all.* "Lukman magana nake maka fa" Fu.ad ya fadi ranshi a bace. Waje lukman ya samu yai parking. Ya maida hankalinshi kan fu.ad. "Anan kake nufin zamu tsaya. Ko da kafafunmu zamu karasa wai........ " Shiru yai ganin yanayin fuskar fu.ad din. Tsoro ne a bayyane. Dan sai lokacin nauyin yanayin daya hadasu da safiyya yake danne shi. "Mu koma. I can't, what am i going to say to her" Fu.ad yake fadi a rikice. Yana running hannun shi kan fuskarshi saboda wata zufa da yake ji a jikinshi. Dafa mishi kafada lukman yayi. "Hey. Ka manta ba saika mata magana ba. Kawai ko ganinta kayi. Kabari mu karasa wajen gidansu mu tsaya ko zata fito" Tunda ya fara maganar fu.ad ke girgiza kai alamar bai yarda ba. Gaba daya ya wani birkice. Abin har tsoro ya soma bama lukman. Shikam indai haka so yake ya fara gudun ya kama shi. Kalli yanda gaba daya fu.ad ya wani fita hayyacin shi. Ya kasa samun nutsuwa. Shikam fu.ad jiyai iskar dake cikin motar ta mishi kadan. Da sauri ya bude murfin motar ya fita. Jingina bayanshi yai da motar. A hankali ya zame ya tsugunna yana wani maida numfashi da sauri sauri. Sama sama yake jin lukman na fadin. "Fu.ad? Fu.ad wai lafiyarka kuwa" Dakyar ya daga mishi kai. Ganin yaki tashi yasa lukman kallon shi sosai yace "Ka taso to ka dawo cikin motar" Dago kai yai. "Iskar dake ciki nake jin tamun kadan" "Okay sai mu sauke glass ko abar murfin a bude" Mikewa fu.ad yai yace. "No ka jirani. Barin dan taka in dawo" Da alamun rashin yarda lukman yace. "Anya kam. Kabari dai mu tafi tare" Wani guntun murmushi yai yace "Karka damu banajin a yanayin da nake ciki zan iya wani tashin hankali. Kawai zan ganta ne in dawo" Kai kawai lukman ya daga mishi. Ya kama hanya ya mike. Tun kamun kafafuwanshi su karasa zuciyarshi ke hango gidansu safiyya. * Tsaf ta gama shirinta. Ta dauki jakarta ta duba duk abinda take bukata yana ciki. Kasancewar yau asabar tun karfe biyu sun shiga islamiyya. Allah ya mata tsoron bulala. Shisa dakyar ta tsaya taci abinci. Shima dan inna nata fada ne. Fitowa tai tace "Inna saina dawo" "Allah ya tsare. A dai kula safiyya" Ta amsa da "In shaa Allah" Ta fice. Tana ta sauri. Kawai jitai gabanta na faduwa bata kuma san dalili ba. Ita dai sauri take ta karasa islamiyya ta samu asiya ta biya mata karatun da akai na sira ranar laraba. Tana can tana tunani bataji komai ba. Sam bata kula da mutum ba saida suka zo gab. "Ya Rabbi...." Ta fadi tana kaucewa da hanzari dan sun kusan cin karo. Kaman ance ya dago. Wani irin tsalle zuciyarshi tai kamun yaji ta dai daita a mazauninta. Amman ta wani matse saida ya fitar da wani numfashi. Kwanaki sittin da takwas. Amman jinsu yake kaman watanni sittin da takwas. Ita kanta safiyya kallo daya zakai mata kaga tsantsar razanar dake fuskarta. Hannu tasa ta shafa fuskarta. Dan ta kasa tabbatar da gaskiyar dake gabanta. Gani take kaman mafarkin daren ne ya biyota da ranar nan. Wani rauni ya ziyarci zuciyarta. Lokaci daya ta rasa kome take ji. Ko me ya kamata taji. Kallonta kawai yakeyi. Idanuwanta ta sauke cikin nashin nan da kalar su ke bata mamaki. Idanuwan da ta kasa mantasu. Idanuwan da suke farautarta duk dare tun da ta gansu. "Sofi..... " Ya kira da wani yanayin da zuciyarta kadai ta fahimta. Inalillahi ta shiga jerowa a zuciyarta. Ba wanda ya taba kiranta da sunan daya kirata. Idanuwanta ta sauke daga cikin nashi ta kafe su a kasa. Ji take kaman kasa ta bude ta hadiyeta. Ga kafafunta ta kasa ko da daga su. Ji take ma kaman sun daina aiki. Dan ta kasa motsa su. So yake ta dago ta ci gaba da kallon shi. Zai iya rantsewa yanajin dawowar abinda ya rasa da duk numfashin da yake saukarwa. "Sofi.... " Ya sake kiran sunanta. Kaman da kanshi kadai yake magana. Saboda sanyin muryar dayai amfani dashi wajen kiran sunan nata. Aman taji shi. Ba kiranshi kadai taji ba. Har kusancin shi da ita. Taki dagowa ne saboda tana ta neman inda ta adana tsanarshi ta rasa. Fatan da taje ya tabbata yau. Kuma fata take wani abu da zai kauda shi yazo. Saboda yanayin da take ji ya girmi wanda take zaton tanaji a baya. Jitake zuciyarta kaman ruwa ce ba tsoka ba. Tanajin yanda take narkewa tana mata yawo a wajaje da ba zasu fadu ba. Dakyar taji ta iya cira kafarta. Ta motsa dayar kafar dan ta tabbatar basu daina aiki ba. Gani yai tana shirin rabashi ta wuce. Yaji zuciyarshi ta wani yawata tana son binta. Da hanzari ya tare hanya. "Karki tafi. Kimun magana inji" Ji take kaman ta toshe kunnuwanta ta daina jin muryarshi. Wani irin tasiri take mata naban mamaki. Wucewa ta sake zuwa zatayi ya tare hanya. Dakyar cikin muryar da ita kanta bata gane ba saboda rauninta tace "Ka matsa dan Allah" Ajiyar zuciyar daya sauke yasa ta dagowa cikin hanzari. Suna hada ido tai saurin sauke nata saboda abinda kw cikin idanuwanshi suna neman jan zuciyarta inda bai kamata ba. "Keep talking. Kice koma menene" Kanta a kasa tace "Me kake yi anan?  Duk abinda kaimun bai isheka ba saika biyo ni?" Lumshe idanuwanshi yai. Ya sake bude su. "Banda kalaman dazan dora abinda ya faru akai. Karki dauka da zabi na nazo nan. Inda wani zai hangomun yanayin nan bazan taba yarda ba" Idanuwanta cike taf da hawaye tace "Ka kyaleni. Dan Allah kabarni kawai" Yanayin yanda muryarta ke rawa ya taba shi. Da sauri yana daga hannuwa yace "Zan kyaleki. Ina so muyi magana ne kawai. Kiban number din wayarki" Bata son hawayen da suka cika mata ido su zubo. Bata son ta nuna wani rauni a gabanshi fiye dana yanzun. Ita ina taga waya. Koma tana da ita akan me zata dauki number dinta ta bashi. Taga alama in ba amsa ta bashi ba bazai kyale ta ba. "Ni bani da waya. Ka tafi kawai dan Allah" Hannuwanshi ya hada duka biyun waje daya alamar rokonta sannan yace. "Zan tafi. I promise." Aljihunshi ya laluba. Ya dauko nokia dinshi. Sim din ciki ba amfani yake dashi ba. Pha.iza ta siya mai double. Ta bashi daya. Sai ma yazo Nigeria ne yake bude wayar. Kuma dayar wayarshi ma akwai etisalat. Mika mata nokia din yai yace. "Zan kiraki a wannan wayar sai muyi magana" Idanuwanta ta sauke kan fuskarshi. A tsorace take girgiza masa kai. "Aa. Ni ka kyale ni kawai" Kanshi yaji ya soma ciwo nan take. Shikam bai san yanda zai ba. Ya dauka zuciyarshi zata gamsu da ganinta kawai. Yanzun kam yaji yana son jin muryarta. Kuma taki karbar wayar. "Zan dawo gobe to" Ji take kaman ta rusa ihu. Me yasa bazai gane bane. Bata so ya dawo gobe. Ba taso ya dawo jibi. Bata ma so ya sake dawowa kwata kwata. "Karka dawo......" Kallon dayake mata ya makalar da sauran kalaman. Muryarshi a dake gashi ya kafeta da idanuwan nan yace "In kika karbi wayar mukai magana inba haka ba bansan yanda za.ai in kasa dawowa ba" Ganin tai shiru yasa shi cewa. "Ki kalleni sosai. Da ina da wani zabi ba zaki ganni anan ba" Itama da tana da wani zabi da ba zata ko tsaya inda inuwarshi take ba. Ballantana ma ta saurare shi. Amman rashin zabin ne yabarta da tsayuwa take jin abinda yake fadi. Bayan duk abinda yai musu. So yake tace wani abu. Shi kanshi zuciyarshi ke magana. "Sofi..... Ki karba" Kai take girgiza mishi. Ganin hankalinshi nakan ta karbi wayar ne yasa ta yin saurin raba shi ta wuce. Rufe idonshi yai ya bude su yana fadin. "Damn it..... " Binta yai. Ganin sun jera suna tafiya. Ta kuma tabbatar dasun kara gaba mutane na zaune majalissa. Bayan hakan kowa zai iya zuwa wucewa yagansu. A koma ace an ganta ta jero da wani. Tsayawa tai. Hawayen da take ta tarbewa suka zubo mata. Hannu tasa zata goge su. Baisan yanda akai hannunshi yai kokarin kaiwa fuskarta ba. Sai ganin ta kauce da sauri yayi. "Kar hannunka ya sake kokarin kawowa kusa dani" Safiyya ta fadi tana share hawayenta. Jin yanda ranta ya baci yasa shi saurin cewa "Kiyi hakuri..... " Kalmomin ya sake maimaitawa a zuciyarshi. Yanda suka fitona saukake ya bashi mamaki. Zai iya kirga mutanen daya taba ba hakuri a rayuwarshi. Amman yau gashi ta fito a saukake kan laifin da baiyi bama. Ture wannan yai gefe. Yana cikin kananun abubuwan da basu bane a gabanshi. Kallonta yake. Wasu hawayen suka sake zubo mata. Wani kunci yaji ya lullube shi. Baya son kukan nan. Bai taba zaton kukan wani zai dame shi ba sai yau. Ba damunshi kadai yai ba. Tokare mishi zuciya yai. "Ki daina. Ki bari. Banason ganin kukan nan..... " Sai taji ma kaman dayai magana sake bude ma hawaysn hanya yai. Wasu nabin wasu haka suke zubo mata. Dakyar cikin kuka tace "Nace ka tafi. Sai wani yaganni tsaye dakai?  Me kake so inyi?" Ja yake da baya. Dan yanayin zai iya jure komai banda kukanta. Da baya baya yake tafiya. Yace mata "Na tafi. Na tafi sofi. Banda zabi ne...... " Tana kallo ya juya da gudu ya tafi. Sai taji tana son ya juyo ko da sau dayane ta sake ganin fuskarshi. Ko hakan zai zama na karshe a rayuwarta. Wani irin abu takeji da ta kasa samo masa kalma. Waje ta samu jikin bango ta karasa. Hijab dinta tasa ta goge fuskarta. Tasan ba zata iya zuwa islamiyya ba. Juyawa tai ta koma gida. Da sallama ta shiga muryarta a dakushe tana kokarin boye kome take ji saita shiga daki. "Safiyya?  Lafiya dai ko?" Kanta a kasa tace "Inna kaina ke ciwo sosai. Shine na dawo gida" Cike da kulawa inna tace "Subahanallahi. Sannu. Kije ki kwanta. Ko usman inya shigo yaje ya siyo miki magani" Bata amsa inna ba ta shige daki. Jakarta kawai ta ajiye ta kwanta. Dunkule jikinta tai waje daya. Ko hijab bata cire ba. Wani irin kuka marar sauti ya kwace mata. Ji take yanda kukan ke fitowa daga zuciyarta kaman fu.ad ne zai fita. Amman ina. Yau ya sake dasa mata abubuwan da tasan ba zasu gogu ba. Kuka tai har bacci ya dauketa. * Yana karasawa ya bude mota ya shiga. Yaja murfin ya rufe. Kanshi ya hada da gaban motar yana jin wani irin yanayi. "Fu.ad menene?  Lafiyarka kuwa?" Lukman yake tambaya cike da kulawa. Batare daya dago ba yace masa "Muje gida" "Bangane muje gida ba. Me ya faru wai?  Kaganta ne?" Dagowa yai a kufule. "Do me a favour. Shut the fuck up" Dariya lukman yai. "Easy sharukhan. Karka kawomun cizo. Daga tambaya. In masifa kake ji ka sauke ta wa zuciyarka ba lukman ba. I am just trying to help" Kauda kai kawai fu.ad yai gefe. Baice komai ba. Kilan inyai banza ya kyale shi yagane cewar bayason magana ne gaba daya. Aikam hakan akayi. Wakama lukman din ya saka. Da gangan yasa duk wakokin dayasan fu.ad na cewa baya so. Ya kula baima san yanayi ba. Tunda ya jingina kanshi da kujera ya kalli gefe bai juyo ba. * Ko parking bai bari lukman yayi ba ya bude murfin motar ya fita. Da gudu ya shiga gida yahaura sama zuwa dakinshi. Maida kofar yai ya kulle. Sannan ya zare takalmin dake kafar shi. Nan inda yake tsaye ya cire kaya. Daga shi sai boxers ya shiga toilet. Ruwa masu sanyi ya sakarma kanshi. Yanajin yanda sanyin ruwan baya kaiwa inda yafi bukata. Lumshe idanuwanshi yai. Zuciyarshi na wani irin abu. Fuskar safiyya na masa yawo cikin idanuwanshi. Kunnuwanshi najin muryarta. Komai ya sake cakude mishi. Bai san iya minti nan daya dauka a bandakin ba. Sanda ya fito ya sake kaya. Kwanciya yai dan ji yake kaman wanda akai ma dukan tsiya. Wani ciwo ko ina na jikinshi yake yi da bashi da alaka da gajiya. Kwankwasa kofar yaji anayi. Yai niyyar sharewa. Jin muryar haneef ya sa shi tashi dakyar ya je ya bude kofar. Komawa yai ya zauna kan gadon. Haneef ya karasa ya zauna kusa dashi. "Fu.ad?" Muryarshi can kasa yace "Haneef bansan yazanyi ba ni. Taki karbar wayar muyi magana. Kuma tace in tafi bata so in dawo. Bazan iya ba..... " Yana maganar yana watsa hannuwanshi alamun komai ya kwance masa. Ganin haneef din ya nutsu yana saurarenshi ya sashi sauke numfashi kamun ya nuna kanshi da hannun shi yace "Kalle ni. Kaman wanda ya zautu. Em' clueless....." Gyara zama haneef yai hadi da fadin. "Kamun magana yanda zangane fu.ad. Menene?  Wacece?" A hankali yace "Sofi..... Safiyya. Yarinyar nan ta bichi....." Hannu haneef ya daga mishi yana girgiza kai. "Don't. Please fu.ad karka cemun son ta kakeyi. Karka fara......" "Too late. Abinda nakeji yafi so" Fu.ad ya fadi yana dafe kanshi cikin hannuwa. Haneef kam ya rasa abinda zaice. Kawai abu dayane yake a bayyane. Ko shine a matsayin iyayen safiyya. Ko zata mutu ba zai bata yaron daya wulakanta su ba. Sau wajen hudu yana bude baki zai magana. Amman ya rasa me zaice. "Hmm... " Fu.ad yace yana kauda kai. Dayake nuna cewa ya fahimci haneef kanshi na hango rikicin dake tattare da hanyar da kaddara ta dora shi. A nutse yace. "Munje dazun nida lukman. Kuma gobe ma zan koma saboda ina bukatar sake ganinta" Sai lokacin haneef yace "Karka yi fu.ad. karka sake zuwa ka kara complicating ma kanka abubuwa. It will not work and you know why" Cikin idanuwa ya kalli fu.ad. "Issue dina da ita ne ba da family dinta ba" Kallon baka da hankali haneef yake mishi. "Waye zai baka yarinyar? Kaga fu.ad ka hada kayanka gobe ka koma. Zaifi ma kowa kwanciyar hankali" Fito da idanuwa yai. "Kana nufin in barta?" Kai haneef ya daga masa. "I can't. Bazan iya ba haneef. Ka tafi kabarni kawai...... Just go!" Sanin halin fu.ad yasa haneef tashi ya fita. A yanayin dayake bazai saurari wani abu ba. Inya dan nutsu sunyi magana. Yana fita fu.ad ya kwantar da fuskarshi cikin pillow yanajin gaba daya duniyar ta masa wani irin kunci.........! [4/4, 6:00 PM] Fatima saleh: *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ 17 *A ton of thanks to my big sister from another mother BABYN UF for being #1teamFu.ad. LVYONG* "Inalillahi wa ina ilahi raji.un....." Momma ta fadi bayan haneef ya gama gaya mata kome yake faruwa. "Yanzun duka fu.ad din nawa yake?  Hankalin kirki bashi da shi haneef" Jinjina kai yai ya gyara zama yace. "Nasani momma. Amman ki kalli fa abinda yake yi. Wallahi zai iya samun matsala. Nikam dai a taimaka aje aji" "Hmm bayan tozarcin dayai musu kana zaton zasu saurare mu ne?  Kafi kowa sanin halin abbahnku. Da wahala yaje" Shiru haneef yadanyi kamun yace "In yaga yanda fu.ad ke shirin zaucewa zaije. Nasan bashida wani hankalin kirki. Amman wallahi yana sonta. Kema kinga alama ai" "Kai. Oh Allah na" Momma ta fadi tana sauke numfashi. Wannan wacce irin kaddara ce. Ita tunda take inba a film ko a littafi ba. Bata taba ganin irin wannan abu ba. Bama tasan ta yanda zata fara tunkarar abbah da wannan maganar ba. "Barin je sallah" Cewar haneef yana mikewa. Kai kawai momma ta iya daga masa. * Da yammacin ranar abbah ya dawo daga abuja. Sai da yaci abinci yai wanka ya huta sannan momma ke fada masa fu.ad bashi da lafiya. Dayake zamansu babu boye boye a ciki. Zata iya tunkarar mijinta da kowacce irin damuwa. A nutse ta fada mishi komai da yake faruwa. Shima salatin yake yana mamakin lokacin da fu.ad ya zama haka. "To nikam yazanyi maman fatima. Allah ne yake hora shi" Dayake uwa daban ce a tausa she tace "Alhaji nasani. Amman sai a duba halin da yake ciki. Ko neman auren yarinyar sai a je masa" Girgiza kai yayi. "Bayan abinda kika ce ya musu. Kina tunanin ko fu.ad ya isa aure zasu bashi yarsu ne?  Ku rabu dashi kawai. In yagaji zai hakura" "Allah ya kyauta." Ta fadi tana mikewa ta fice daga dakin. Da alama ranta ya sosu da maganganu shi. * Haneef da lukman ne zaune dakin fu.ad. kallon shi kawai suke. Dan lukman ma da ba.ayi a gabanshi ba a tsorace yake. Gani suke da sunyi magana zai kara shiga matsala. Tunda ya tashi dai baice musu komai ba. Suna kallo ya sauko daga kan gado yai hanyar kofa. Suka hada ido basu ce masa komai ba. Kasa ya sauka ya nufi bangaren su momma. Karo yaci da ita ta fito dakin abbah. "Momma kin masa magana?" Ya tambaya. Ta kalli yanda ya wani fada ya kara haske. "Na masa magana ka kwantar da hankalinka. Zasu je gobe in shaa Allah" Wani murmushi yaji ya kwace masa yana sosa kai ya wuce abinshi. Momma wayarta ta dauko ta kira yaya babba. Dayake dare yayi ta waya tai masa baya nin komai. Tace masa kome yake yazo da safe su kara tattaunawa. * A gidan lukman ya kwana. Baccin shi ya sha hankali kwance. Fu.ad ma ya samu bacci da nutsuwa ta wani bangaren tunda momma tace masa za.a je ai maganar auren shi da safiyya. Haka ya kwana mafarkinta. * Babu yanda yaya babba baiba ya fahimtar da mama cewar fu.ad din ma duka nawa yake. Amman ina tsakanin da da uwa sai Allah. Catai ma umarni ne ta bashi bawai neman shawararshi take ba. Haka dole ya shirya suka dauki hanyar bichi shi da haneef. * Fu.ad ya kasa zaune ya kasa tsaye sai kai kawo yake. Ya kagu yaga sun dawo yaji ya ake ciki. Gashi jibi zai koma. Lukman ya kalle shi yace "ka soma sakani jiri. Ka zauna waje daya dan Allah" Dariya yai da tunda yazo lukman baiganta ba. "Ina ruwanka dani. Wai su haneef sun awa daya da tafiya ko?" "Ko minti goma basuyi ba" Zaro idanu yai. "Ni bana son karya. Kasan ko lukman. Allah ina son ta sosai" Dariya lukman yai. Tun jiya yake fada musu yana son safiyya kaman wani cikinsu yace karya yake yi. * Lokacin da suka isa bichi. Suka aika ai musu sallama da babansu safiyya. Akace yaje gona. Jin da inna tai sun aiko cewa daga nesa suke kuma magana ce mai muhimmanci ta aika usman ya kira shi. Cikin soron gidan aka shimfida musu tabarma suka zauna. Harda ruwa aka kawo musu. Yanda babansu safiyya ya karbe su a mutunce zaka rantse dama can ya sansu. A nutse babban yaya yai masa bayanin cewar kaninsu yaga yarshi yana so. Cikin taushin murya yace. "Allah sarki. Gaskiya mungode kwarai da gaske. Saboda wanda ya nuna ma naka so har abada ya wuce wulakanci. Sai dai kudin sadakinta yakai wata biyu a hannunmu. Yanzun haka bai shige sati hudu ya rage a daura mata aure ba. Kuma gashi bata da wata kanwa ballantana" Wani abu haneef yaji ya kulle a cikin shi. Murya a sake yace "Yanzun baba babu yanda za.ai a dan duba mana. Wallahi yana sonta matuka" Murmushi yai. "Dan nan ka taba ganin inda akai nema cikin nema?  Dama ace ba.a amsa su bane. Mungode matuka" Baki haneef ya bude zai sake magana yaya babba ya katse shi da fadin. "Mungode muma. Ga wannan. Allah yasa hakan shi yafi alkhairi" Sam baban su safiyya yaki karbar kudin da yaya babba ya bashi. Dakyar daban baki ya samu ya karba. Suka tashi suka tafi. * Tabar mar ya shiga da ita gida. A tsakar gida ya ke nuna ma inna kudin yana labarta mata abinda ya faru. Safiyya dake daki tana jiyo su. Tanajin baba ya kira sunan fu.ad zuciyarta ta wani doka. Hade kai tai da gwiwa. Bata san kuma me zatayi ba. Kukane tayi shi harta godema Allah. Wato saida ya turo neman aurenta gidansu. Taya zata samu ta manta dashi inhar a duk rana yana aikata abinda zai sake zaunar mata dashi. Kwanciya tai tanajin daman ace duk wannan abubuwan sun farune a wani yanayi na daban. Saurin kulle shafin dake son hango mata rayuwarsu da fu.ad tayi. Ta shiga na daban. **** Daman a tsaye yake. Tunda yaya babba ya fara ma momma bayani yake matsawa. Kwata kwata babu wanda ya kula da fitar fu.ad. Haneef ne yace "Ba fu.ad nan yake tsaye ba" Sai lokacin kowa ya kula da baya nan. Kallon kallo suke. Da gudu haneef ya haura sama ya tura dakin shi. Baya ciki. Sakkowa yai ya fita. Motarshi bata wajen. Baba mai gadi ya tambaya yace ya fita. Dawowa yai yace musu. "Mota ya dauka" "Fara kiran lukman kaji ko tare suka fita" Wayarshi ya dauko ya kira lukman ya tambaye shi. "Ina gida wallahi. Baikuma cemun zai fita ba. Ya Salam" Kashe wayar haneef yai ya girgiza ma momma kai. Cikin tashin hankali tace "Oh Allah. Wannan wanne irin abu ne" Haneef ya dauki mukullin motarshi yabiya ya dauki lukman batare daya san inda zasu je nemo shin ba. Wayarshi yake ta kira sai ringing take yaki dauka. * Hankalinshi baya tare dashi harya karasa bichi. Yanajin wayarshi na ihu bashida lokacinta. So yake yaje ya ga safiyya ya fada mata bafa zata auri wani ba. Inma ba zata aure shi bane yaji. Inma bata sonshi ne duk zai dauka. Badai zai dauki ta auri wanin ba. Parking yai nesa da gidansu ya fito. Kofar gidansu ya karasa ya aika yaro a kira mishi ita. * Tana kwance abinta. Dan batajin zata iya zuwa islamiyya ranar. Yaro ya shigo wai ana sallama da ita. Bata kawo komai a ranta ba. Zatonta Ado ne. Dan yace mata ta duba lambar takalminta ta fada mishi ya manta. Ta dauka shine ya dawo. Hijabinta ta dauka ta zira takalmanta ta fita. Wani bugawa zuciyarta tayi ganin fu.ad. Gefe gefenta ta kalla ko wani ya taho. Ko ina na jikinta bari yake. Muryarta na rawa tace masa. "Ka tafi kar wani yaganka. Dan Allah ka taimaka ka tafi" Kallonta yake yana wani saukar da numfashi. "In bakya sona na yarda. Inba zaki aureni ba na yarda. Amman sofi karki auri wani. Karki auri wani dan Allah" Ba shi take sauraro ba. Hanya take kallo kar a ganta tsaye dashi. Kai kawai ta daga mishi.. "Najika. Ka tafi" Karamar wayar rannan ya zaro ya mika mata. "Ki karba zamuyi magana" Kai take girgiza masa alamar a.a. "Wallahi inbaki karba ba anan zan zauna. Babu inda zanje" Rufe idonta tai ta bude su. Wannan wanne irine shi cikin mutane. Ta san zai yi abinda ya fada. Jikinta na bari tasa hannu ta karbi wayar. Batare da tasan me zatai da ita ba. "ka tafi to" Kallonta yai sosai. Wayarshi babba ya zaro daga aljihu. Baima tsaya duba yawan kiran da akai masa ba. Safiyya na kallonshi idanuwa bude. Gabaki daya a tsorace take. Batasan me zai ba ya dago wayar idanuwanshi nakan wayar. Hotuna yake daukarta. Yasan zai bukace su kodan kwanciyar hankalinshi. Baya son tsoron dake cikin idanuwanta sam. Ji yake kaman ya dauketa ya kareta daga dukkan abubuwan dake bayyana wannan firgicin cikin idanuwanta. Wayar ya damtse a hannunshi ya sauke idanuwanshi cikin nata. "Ba wannan bane karshe sofi. Zan dawo. Zan hada duniyarmu waje daya. Ban damu da rashin dacewarsu ba......." Bude baki tai ya daga mata hannu. "In har ba zaki fadi abin da zai sama mun sauki ba kiyi shiru. Akwai muryarki cike da kaina da maganganun da suke mun ciwo. Ba saikin kara musu abokan zama ba" Ta nutsu tana kallon fuskarshi. Yanda yake magana. Muryarshi da kominshi. Tana kallonshi ne saboda yanda zuciyarta ke mata bata son manta shi. Tana son ta dauki hotunan shi da zata adana a zuciyarta. Yanda take kallonshi yake kallo. Dige digen bakin dake fuskarta yake jin kaman yasa hannu ya gogesu. So yake yaganta babu su. Yaga fuskarta ita din babu kari ko ragin komai. Da duk wani abu mai motsi a jikinshi yake jin ciwon tafiyar dazai yabarta. Ya rasa ko menene ke fada mishi zata zama tashi. Yanayi ne ko murya ya kasa fahimta. Dakyar safiyya ta iya ce masa "Ka tafi" Kai ya daga mata ya soma tafiya da baya a hankali. "Idan na kira ki dauka" Itama kai take daga mishi idanuwanta kafe akanshi. Takunshi a kasa yake yi amman nauyin shi a zuciyarta take ji. Tana kallonshi harya juya. Yasa hannuwanshi cikin aljihu ya tafi. Jingina tai da bangon wajen. Wasu hawaye masu dumi suka zubo mata. Tasa hannu ta goge su tana hadiye kukan ta. Wayar ta kalla. Batasan ya zatai da ita ba. Danma yar karama ce sosai. Zata iya taita boyonta a jikinta dan bata da abinda zata fada in inna tagani. Cikin gida ta koma. Taji dadin yanda inna bata ko dubeta ba. Tana ta tankaden garin tuwo. Daki ta shiga. Ta boye wayar cikin zaninta. Ta hada kai da gwiwa tana sauke wani irin numfashi. **** Murfin motar ya bude dai dai karasowar motar haneef. Parking sukai. Haneef ya fara fitowa. A fusace yake takowa inda fu.ad yake. "Babu hankali a jikinka ne? Inma tahowa zakai ba zaka iya gaya ma mutane ba? Haba fu.ad?" Tunda ya fara fadan idanuwa kawai fu.ad yake binshi dasu. Dan bayajin yana da karfin amsa shi. Daya tabbatar ya gama mota kawai ya shiga. Ya rufe ya soma kokarin juyawa. Haneef din wucewa kawai yai ya koma motarsu. Lukman daman bai kai ga fitowa ba ma. Dan baisan me zaice ma fu.ad ba. Damuwarshi daya ko wani abu ya same shi a hanya. Bin bayanshi kawai haneef yai da motar. Amman dayake wani irin gudu yake. Fintinkau yai musu. "Dana sani na fito na karbi tukin can" Cewar lukman da alamun damuwa a muryarshi. "Allah ya kyauta. Daman ya lafiyar kura....." Shiru kawai lukman yayi. *** Duk ranar babu wanda yai ma magana. Kome zakace mishi da idanuwa kawai zai bika. Fuskar nan babu annuri sam. Garama momma data tambaye shi ko lafiya yake ya amsa mata da babu abinda ke damun shi. Sundai ki subar shi ya zauna shi kadai. Dole ya kwanta falo har aka dawo sallar isha.i. Matsa masan da momma tayi da karin bayason ko bakinshi ya bude yai magana yasa ya tura ma cikinshi doya da kwai. * Lukman ya zo gidan wajen tara. Sannan suka yi dakin fu.ad din tare. Kwanciyarshi yai yana karatu domin yanada test washegari. Fu.ad kam number din wayar daya ba safiyya ya duba yai dialing. Zuciyarshi na wani dokawa. **** Karin tauhid din da akai musu take zauna tana dubawa tunda tai sallar isha.i. Wani zuuu taji cikin kugunta dai dai inda ta boye wayar da fu.ad ya bata. Da alaman tsarguwa a fuskarta ta dago ta sauke dubanta kan inna. Hira suje tayi ita da baba da alama ma basu san meke faruwa ba. Wani numfashi ta sauke ta mike. "Inna sai da safenku. Allah ya bamu alkhairinsa. Usman da yaya sai da safe" Su usman suka amsata da amin dayi mata fatan tashi lafiya. Inna ce tace "Baki ci abinci bafa safiyya. Haka zakije ki kwanta?" Girgiza kai tayi. "Ai da yammaci naci abinci inna. Kin manta. Banajin yunwa yanzun" "To Allah ya tashemu lafiya. Adai yi addu.a" Ta amsa da "In shaa Allah" Wayar bata daina zuu din da takeyi ba. Daki ta shiga. Ta saki labulen. Can karshe ta koma. Ta dauko wayar. Kallonta takeyi. Irin wayar yayanta ce. Sai dai sabunta ta banbanta su. Zuu din da take ta sake dauka. Cikin kanta take tunanin yanda ya nuna mata ko da zai tafi gona ko wajen express din shi yabar wayar. Green ta danna ta kara a kunnenta zuciyarta na wani yawo wajajen da bai kamata taje ba. Zata iya rantsewa har cikin kunnuwanta tanajin yanda zuciyarta ke dokawa. * Karo na hudu kenan daya sake dialing number din. Hannuwanshi har zufa suke da baisan daga inda ta fito ba. Ji yai an daga. Ya sauke wani numfashi dayake rike dashi. "Sofi........." * Lumshe idanuwanta tai. Tana jin kaman yana gabanta. Bata san me yasa yake ce mata sofi din nan ba. Badai zatai ma kanta karya ba. Sunan na mata wani irin abu da ta kasa fahimta. Muryarta can kasa tace "Sai da safe" * Kai ya daga kaman tana ganinshi kamun yace "Thank you. Thanks for picking. Zan sake kira amman ba da wannan number din ba. Kiyi bacci mai dadi. Cike da mafarkina" * Bata amsa shi ba ta sauke wayar daga kunnenta. Jikinta ko ina bari yake. A hankali ta tashi tazo wajen kofa. Labulen dakin ta daga ta leka taga ko su inna sun jiyota. Suna nan zaune inda tabarsu. Komawa tai. Ta gyara shimfidarta ta kwanta. Cikin kanta take sake dawo da maganganun fu.ad. Bama saiya wahalar da kanshi na cewar tai mafarkin shi ba. Tasan abune da yake a ajiye. **** Yana nan kwance har lukman ya fice dan yana da test karfe takwas na safiyar ranar. Dan haka yaima fu.ad sallama. Yasan sanda zai dawo ya koma. Lukman na fita yai wanka ya fito ya shirya tsaf. Son jin muryar safiyya na damunshi. Waya ya dauka har ya kai kan number dinta ya fasa baya son taji kaman ya takurata. Zai iya lallaba zuciyarshi nadan wani lokacin. Instead hotunanta na wayarshi ya bude. Murmushi ya kwace masa. Hannu yasa ya shafi screen din dai dai fuskarta. Hakan kawai ya saukar masa da nishadi. Jakarshi yar ta system ya dauka. Ya rigada ya zuba komai da yake bukata a ciki. Harya sauka kasa da murmushi a fuskarshi. Haneef ya fara karo dashi. "Wannan murmushin fa?" Kawai sai yaji wata yar kunya tadan kama shi. "Ina kwana.... " Ya fadi maimakon amsa tambayar da haneef yai masa. Zaro idanuwa haneef yai. Gaisuwar da fu.ad yai masa bakon abune a wajen shi. Banda su momma baya gaida kowa. Ko yazo ya same su zaune maganarshi bata wuce 'Hey guys'  ko ya kalle ka ya daga maka kai. Momma ce ta fito kamun ya samu daman tsokanar fu.ad din. Kallon shi tai tace "Badai tafiya ba?" Dan sosa kai yai. "Wlh kam. Ina kwana" "Lafiya kalau..... Amman dai ka tsaya ka karya ko? Kana lafiya dai?" Murmushi ya kara fadadawa. "Lafiya kalau momma. Banajin yunwa. Zan grabbing ko burger ne. Abbah fa?" Kai ta jinjina tace "Yana dakinshi" "Bara inje mu gaisa muyi sallama to..... " Bai jira amsarsu ba ya wuce. Suna nan tsaye ya fito sukai sallama da momma. Pha.iza na bacci. Su hassan kuwa sun tafi makaranta. Dan haka haneef ya tafi ya raka shi. "I mean are you okay?  About...." Katse haneef yai da fadin. "Absolutely..... Ion' wanna talk bouh' it" Bai sake masa maganar ba harya suka kai airport. Sallama sukai da cewar sai sunyi waya, haneef din ya juya da mota......! [4/4, 6:00 PM] Fatima saleh: *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ 18 *For those asking. Ina da blog but honestly bana iya managing nashi for now. You can get my stories on wattpad: LubnaSufyan. Thank you for all the support and prayers. Do include a sister Aysher abdullahi in your prayers. May her soul rest in peace. Amin* Tun daga soron gidan su take jin hayaniyar mutane. Da mamaki tai sallama. Har kasa ta tsugunna ta gaishe dasu, suka amsa. Mikewa tai ta kasan ido take kallon akwati nan da tasan na lefenta ne. Wani abu ne tsaye a wuyanta da ta kada hadiyewa. Daki ta wuce. Ko hijab bata cire ba. Bata taba sanin rashin son da take ma Ado yakai haka a zuciyarta ba. Ta dauka zata iya hakura tai biyayya wa iyayenta ta zauna da ado. Amman yau tunanin hakan kawai yasa numfashinta na wani daukewa. Wayar dake makale kugunta ta ciro. Ta sa hannu ta shafi screen din wayar. Wasu daga cikin maganganun fuad na dawo mata. Yakan kirata sau biyune kawai a rana. Da dare sai kuma da sassafe. Daga sun gaisa bata iya cewa komai Saidai tai shiru tana jin yanda yake gaya mata zai dawo. Kuma zai samar musu hanyar yin rayuwa waje daya. Sakonni kam saiya turo sunfi goma sha a rana. Haka zata bude taita kallonsu. Fin rabinsu baganewa take ba saboda da turanci yake turowa. Kalmomin da take tsinta na turanci ba zasu shige goma ba. Inya hada da hausane kawai zata karanta. Badai ta reply saboda bata iya ba. Inhar tace ga dalilin dayasa take daga wayar fu.ad to tayi karya. Abu dayane take da tabbaci akai. In har ya kira saita daga. Ko tana cikin su inna ne zata shiga bandaki ta amsa wayar. Wasu hawaye ne kebin fuskarta tana goge su. Ita kam bata son Ado ko kadan. * Tana nan zaune shiru taji alamun mutane na tafiya. Kamun wani lokaci gidan yayi shiru. Tana jiyo muryar usman da inna suna magana kan lefen cewar ba karamun kokari ado yayi ba. Akwatina ne hudu. Duk da atamfafin kanana ne sosai. Bakowa ke wannan saar ba a kauyen. Ita kam bata wani damu da kaya ba. Addu.a take Allah ya bata karfin zuciyar daurewa ayi auren nan ko dan iyayenta. * Kaman kullum a kwanakin nan bakwai. Sallama taima su inna ta shige dakinta ta kwanta. Kiran fu.ad take jira. Yau shiru bai kirata ba. Ba zatace ga adadin lokacin data dauka tana jira ba.  Sai taji wani irin yanayi mai wahalar fassarawa. Wani daci mai bambanci dana dazun. Juye juye kawai take baccin yaki bata hadin kai. Ta jima sosai a haka kamun wani wahalallen bacci ya dauketa mai cike da mafarkai. * Tun kamun asuba tai wata irin farkawa da batasan ta mecece ba. Wayar ta zaro ta duba. Ta zuba mata idanuwa kaman fu.ad zai fito ta ciki. Kwancia tai shiru. Kan kunnenta akai kiran sallar Asuba. Alwala tayo tai sallah. Tana idarwa ta kwashe shimfidarta ta gyara dakin. Aikace aikacen daya kamata tayi na safe ta gama tsaf. Sannan ta koma daki ta zauna tana jiran kiran fuad dabai shigo ba. Yinin ranar ji take kaman bata da lafiya. Kaman akwai wani bangare nata dabai cika ba. Saita samu kanta da yima fu.ad addua a duk inda yake ya kasance cikin lafiya. Ga kwanakin bikinta sun mata tsaye cikin kanta. Duka duka yau saura sati biyu cif. Dan tun jiya da dare takejin baba nacewa ba zata sake fita ko ina ba. Ko da islamiya ce ma. **** Matakin rashin kwanciyar hankalinshi ya kara hawa tsakanin jiya zuwa yau da safe. Ya rasa inda ya yadda wayarshi. Tsakanin wajen training da restaurant din daya tsaya yaci abinci zuwa gida. * Wata wayar ya fita ya siya. Ya bada tsohuwar number dinshi aka rufe akai masa wata. Ko gida bai bari ya karasa ba ya saka number din safiyya yai dialing. A kashe wayar take. Yasan ko karfe nawa ne lokacin a nigeria. Saidai baisan dalilin dayasa wayarta take a kashe ba. Kanshi yaji ya soma ciwo na babu dalili. Babban takaicin shi dayane. Hotunan safiyya dayake dasu suna cikin waccen wayar daya yarda. Gashi yai rashin dubarar saka su a system. Gida ya koma ya rage kayan jikinshi ya kwanta muryarta na masa yawo cikin kai tana rage mishi damuwar dayake ciki. **** Usman take jira yazo ya karbo mata battery dinta data aika shi yakai chargy. Daya daga cikin dalilan dayasa take kaunar yaron. Gashi da karancin shekaru amman yana da sirri sosai. Farkon data bashi yakai mata battery dinta ya tambayeta na wanene. Tace masa nata ne. Abu daya daya bukata shine inna tasan tana da waya. Ta girgiza masa kai. Bai sake cewa komai ba ya karba yakai mata. Daga lokacin zai kaimata ya amso mata. Inhar ya sameta da inna baya bata sai su kadai. Haka yauma yana shigowa ta bashi ashirin yaje ya karbo mata. Dan kudaden makarantarta tara su take. Ita bamai yawan ciye ciyw bace ba. Battery din ta saka a wayar. Wani sanyi taji da taga sakonnin shi sunata shigowa.  Tasan yana lafiya. * Lokacin daya saba kiranta ya kirata yauma. Gaisawa sukai tai shiru. Tanajin yace "Sofi kinga ban kira ba ko?  Na yarda wayata ne shisa" A sanyaye ta amsa da "Allah ya mayar da alkhairi" "Amin. Barin barki kiyi bacci ko?  Bana so kiyi ciwon kai" Wani murmushi ya kwace mata. Lokaci daya ya dauke data tuna wannan wayar da suke bata da wani amfani. Asalima karin matsaloline a wajenta. Ya kamata ace tayi duk wani abu da zai nisantata da fu.ad dan da kusanci da yawan tsanar ado a zuciyarta. "Dan Allah karka sake kirana. Ina maka fatan alkhairi a rayuwarka" Da alamun tashin hankali taji yace "Sofi tsaya..me kike nufi?  Saboda me bazan kiraki ba?  Baki san muryarki kadai ce abinda ke rike mun sauran hankalina ba. Please karkimun haka...... " Katse shi tai da fadin. "An kawo lefe na yau. Sauran sati biyu daurin aurena. Meye amfanin kiran nan da kakemun? Ka daina daj Allah. Wallahi kana sake rikitamun tunani ne" Shiru yadanyi kamun yace "Ba zaki auri kowa ba sofi. Zan dawo kamun lokacin. Ni da ke are meant to be. Babu abinda zai shiga tsakani kina jina ko? Kar bakinki ya sake furtamun cewar na daina kiranki. Saida safe" Kamun tace wani abu ya kashe wayar. Batai kokarin goge hawayen da suke zubo mata ba. Dan sun dade da kwacewa daga ikonta. Zuba suke duk sanda suka so fitowa. Duk idan yace ita da shi din nan sai taji wani abu ya yawata mata a zuciya. Tasan babu wani abu wai shi ita da shi. **** Yau sauran kwana uku kacal a daura mata aure da ado. Saidai babu komai a zuciyarta daya wuce kin auren da fu.ad. Tun jiya yake kiranta bata dagawa. Saboda bata son yanda kalamanshi suke mata tasiri. Ya turo sakonni sunfi talatin tsakanin jiya da yau. Duk da inya kira sai tayi da gaske take kin dagawa. Gaba daya ta wani yi zuru zuru. Tun inna na tambaya harta gaji ta kyaleta. Hidima kawai suke abinsu. Dan ranar ma mutanene cike da gidansu anata hidima za.aje ayi jere. Su lami da jummai suka kwance mata kai. Ta wanke tas. Jummai tai mata kitso. Kawai binsu take. Duk yanda sukace mata. Saboda bata da karfin ko yawan magana ma. Su kansu basu dame ta da yawan tambaya ba. * Tanajin wayarta na zuu ta sake gyara kwanciya tana wani hade jikinta. Zuciyarta na dokawa da karfin gaske. Yanda jikinta ke mata har tsoro abin yake bata. Nan da kwana uku ko bata so dole ta cillar da wayar nan. Ta saba da rashin shi tun yanzun. Tana ta kokarin karyata cewar ta kwallafa ranta akan shi. Jitai wayar tai shiru nadan wani lokaci kamun taji ta sake daukar view vibrating. Saidai wannan karon na alamar text ya shigo ne. Wayar ta ciro ta bude. Gajeran sako ne kamar haka. 'Ki na so inyi menene? Na miki wani abu ne?' Lumshe idanuwanta tai. Hawayen dake son zubowa take kokarin umarta da su koma. Wani sakon ya sake shigowa. 'Yanzun zan taho gida. Kiyi bacci mai dadi' Wayar ta mayar tana sauke wani numfashi. Baccine ya dauketa cike da mafarkai masu hargitsi. * Rashin nasarar wasansu bashi bai dame shi kamar kin daga wayarshi da sofi tayi ba. Har wani daci daci yake ji. Babu abinda ya tsaya siya. Haka ya dauki jakar system dinshi sai waya da abinda yake bukata yai airport. * NIGERIA. Basu ji wani mamakin ganin fu.ad ba dan suna saka ranshi cikin satin daman. Daga pha.iza sai momma a gidan. Dan haka suna gama gaisawa yahau sama. Dakinshi a gyare tsaf. Wanka yai ya shirya kanshi cikin jeans baki da riga simple ja. Gashi ya taje ya fesa turaruka yasa takalma suma jaijaye ya fito. Lukman ya kira wayarshi taqi shiga. Gidansu ya wuce kanshi tsaye. Hajiyar su lukman take fada mishi yana makaranta. Bayajin zai iya jiran lukman din dan har wani ihu ihu zuciyarshi take masa. Daga shi har ita hakurinsu bashida yawa akan safiyya. Balle baiji muryarta ba. Dan haka gida ya koma. Mukullin mota ya karba wajen momma yace mata zai fita amman bawai jimawa zai ba dan yamma ta fara yi. Addu.a kawai tai masa ya fice. * Tuqi yake. Yanajin zuciyarshi na bugawa har cikin tafin hannunshi saboda wani maiko da suke yi da zufa. Ac din motar ya duba yaga ko bai kunna ba. A kunne take zufar dayake yi ya daban ce. Komai da yake ji karuwa yai daya ganshi zai sha corner din da zata kaishi gidansu safiyya. Inda ya saba tsayawa ya tsaya. Badan komai ba saidan baya son jama safiyya matsala. Baya sonta cikin damuwa dabamai hanashi parking kofar gidansu. Wayarshi ya dauko yai dialing Number dinta. * Zaune suke a daki. Su jummai nata faman hira. Wayarta taji tana vibrating. Ta lumshe idanuwanta kawai. Tanajin yanda wayar ke wani zuu. Addu.ar duk da tazo bakinta takeyi. Can wayar tai shiru kamun ta kara daukar vibrating . Danne zuciyarta dake mata ihun ta dauki wayar take tayi. Sake daukar vibrating tayi a karo na babu adadi. Can tai shiru sai taji alamar sako ya shiga. Hannu tasa ta lalubo wayar ta gyara zama yanda ita kadai zata iya ganin wayar. Sakon daya turo ta bude. 'Ina wajen gidanku. Ki zo' Kamun sakonshi ya karasa isa inda ya kamata a cikin kanta wani ya sake shigowa. 'Wallahi zan karaso idan baki fito ba. Believe me ba zaki so hakan ba' Wata zufa taji ta lullubeta. Jikinta ya dauki bari. Tasan ba karya yake ba. Karasowa zai gidansu. Ita yanzun batasan yanda zatayi ba. Wayar ta ci gaba da zuu alamar kiranshi ya shigo. Tasan wannan karin bata da zabi. Daga wayar tai ta kara a kunne hadi da mishi sallama daya dawo da hankalin su jummai kanta suna mata kallon mamaki. "Me nai miki?" Lumshe idanuwanta tai tanajin yanda zuciyarta ke wani numfashi data kwana biyu batai ba. Har wata iska ta daban taji tana shaka. "Sofi....ina tsaye tun dazun" Maganarshi ta dawo da ita hankalinta. Cikin sanyin murya tace "Kayi hakuri. Bazan iya fitowa ba akwai mutane sosai. Karka sake dawowa. Na fada maka nan da kwana uku aurena kuma.......... " Katse ta yai muryarshi can kasa dauke da wani irin yanayi da taji ko ina na jikinta yace "Ion' give a damn da mutanen dake nan sofi. Abu biyu na sani. Ba a daura miki aure ba. Sannan ina son ganinki. Idan baki fito ba ni zanzo kofar gidanku ko na shigo har ciki...... " A tsorace safiyya tace "Fu.ad........" Karo na farko da ta dora sunanshi kan harshenta. A zuciyarta take fadarshi ko da yaushe. Wani abu taji na daban. Tanajin sauke numfashin da yai hadi da fadin. "Sofi..... Ki fito please. Idan na kara mintina biyar banganki ba zan karaso" Kashe wayar tai kamun ta amsa. Idanuwanta ta sauke kan su jummai da fuskokinsu ke dauke da tambayoyi kala kala. "Dan Allah ku taimakamun in fita daga gidan nan. Na yan mintuna banaso kowa ya kula da na fita" Safiyya tace musu murya na rawa. Jummai ta kalleta sosai. "Saboda me? Me zakiyi a waje? Dawa kike waya kuma?" Mikewa safiyya tayi tace. "Dan Alla ku taimakamun. Wallahi zan muku bayanin duk abinda yake faruwa" Sai lokacin lami tace "Ni nasan da akwai wata a kasa. Me zai hana ki fada mana yanzun?" Jummai ta gyada kai alamar yarda da abinda lami tace. Kallonsu tai idanuwanta cike da hawaye. "Banda lokaci sosai. Ku taimakamun dan Allah Wallahi zan fada muku.... " Yanda ta karasa maganar da wasu hawaye da suka zubo mata ya karya musu zuciya. Mikewa sukai su duka suna tunani. Kamun lami ta basu dabara. * Ya kasa tsayawa waje daya. Sai kai kawo yake. Har zuciyarshi yake nufin maganganun daya gayama safiyya. Inhar bata fito ba zuwa zai. Kome zai faru ya faru bai dame shi ba. Inhar zai ga fuskarta it will be worth kome zai fuskanta. Hanya yake kallo. Su uku ya hango. Tafiyarta kawai ya gane. Wani lallausan murmushi ya kubce masa. Ajiyar zuciya ya sauke yana takawa ya suka hade akan hanya. Idanuwanshi kafe suke kan safiyya. Sam baya ganin su jummai da suka zuba masa idanuwa. Kallonta yake yana cike guraren da sukai kewarta a kwanakin nan. Kanta a kasa tace "Tunda kaganni ka tafi dan Allah. Wannan ya zama karo na karshe da zaka dawo. Wallahi zaka iya sakani cikin matsala. Bana son fushin iyayena akanka" Kallonta yake sosai. Muryarshi da alamar lallashi yace. "Hey.... Bana nufin na ja miki matsala sofi. Ki fahimceni. Kawai dai ba zaki auri wani bane ba. Nikuma inyi yaya kenan? In sa kaina ina? Kinsan me nake ki kuwa?" Jajayen idanuwanta ta dago ta sauke su cikin nashi. Bata da kalaman da zatai amfani dasu. Kila zai iya karantar halin da take ciki ta idanuwanta. Zai iya ganin yakin da take gabzawa da zuciyarta akanshi. ** Shi da abokinshi hashimu ne suke tafiya cike da nishadi suke hirarsu. Kamun hashimu yace. "Ado wata nake hangowa kaman safiyyarka tsaye da wani ko?" Girgiza kai ado yake da alamun rashin yarda yace. "Haba dai. Safiyya fa kace." Da hannu hashimu ya nuna masa su. Wani abu yaji ya tsaya masa a wuya. Safiyya ce kuwa tsaye da wani saurayi. Da sauri yake takawa ya karasa wajensu hashimu nabin bayanshi. ** Tsaye suke suna kallon kallo. Kaman daga sama su jummai sukaga ado da har wani huci yake. "Safiyya me kike a waje? Waye wannan kuma?" Wani abu taji ya kulle a cikinta. Shikenan abinda take gudu ne ya faru. Dole su inna su sani. Asirinta ya tonu. Cike da matsanancin tsoro ta kalli ado. A daburce ta soma cewa. "umm.... Wallahi..... Ado..... " Fu.ad dake tsaye kallon safiyya yake yanda ta rikice gabaki daya kamun ya maida kallonshi kan ado. "Waye kai kuma din?" Ya tambaya yana masa wani kallon wulakanci. Shima adon kallon da yake mayar masa kenan. "Me kake tsaye da matata?" Ya tambaya. Wata dariyar takaici fu.ad yake. Me ma sofi zatai da wannan dan kauyen. Kazamin yake tambayar kanshi. A fili kuma yace. "Ka kama hanya kawai. And kar bakinka ya sake kiranta da matarka" Ya karasa yana nuna safiyya dake tsaye kamar an dasata. Su jummai kansu baki bude suke kallon ikon Allah. Cikin bacin rai ado yace. "Lallai ma. Kaji mun wani karfin hali. Kai asuwa to?  Malam tunda mutuncinka kabar wajen nan wallahi. Bansan ya akai take tsaye dakai ba. Ba kuma zai sake faruwa ba dan matata....... " Bai karasa ba ji kake wani tas!  Fu.ad ya kwada masa mari. Ai kam ado ba tsaya jira ba ya kaima fu.ad din naushi a fuska. Ramawa yai. Hashimu yai kokarin shiga tsakaninsu amman sai fu.ad ma ya sauke masa naushin dayake kokarin kaima ado. Ko da wasa ba zaka hada girman jiki da karfin fu.ad dana ado shi kadai bama ballantana da hashimu. Kamun kace wani abu hashimu yai sama da fu.ad ya tiqa da kasa. Wata kara safiyya ta saki. Shi aka doka da kasa amman ciwon har cikin zuciyarta taji shi. Dafe fuska tai da hannuwa biyu. Kota ko ina ado da hashimu suke turmusa fu.ad kaman wanda akaima wahayi. Ganin mutane sun fara taruwa yasa jummai da lami jan safiyya tana turjewa tana wani irin kuka. Janta suke tana kokarin komawa kaman zata shigar ma fu.ad da yanzun ya daina ma rama dukan da suke masa. Duk sun fasa masa baki da gefen fuska. Ga shi sun turbuda shi cikin kasa yai futu futu. Sannan mutane suka fara kula aka taru kansu. Dakyar aka janye ado daga kan fu.ad yana fadin. "Kai din banza zaka zo har kauyenmu kai mana fitsara. Wallahi ka sake dawowa sai dai waninka. Safiyya matata ce kana jina!!!" Wasu ne suka kama fu.ad suka daga shi yana maida numfash. Ciwon dayake ji daban ne dana jikin shi. Idanuwanshi da guda daya harya soma rufewa da alamar kumbura yake duddubawa baiga safiyya ba. A firgice yake fadin. "Sofi......... No.....Sofi......." Wani mutum ne ya kama shi saboda yanda yaga kaman jini na kokarin dibarshi. Duba shi yai yaga ya fasa bayan kai. Jini kuma bai bar zuba ba har lokacin. A rikice yace. "Subahanallah. Dan Allah ku kamashi aje ko chemist ne jini yake zubdawa....... " Ture shi fu.ad yai muryarshi harta soma canzawa. Hannu yasa ya dafe gefen kanshi yana fadin. "sofi...... Ta tafi...... " Wani ya dafa yana tafiya yana hade hanya. Mutane suka kamashi. Kanshi ya saki yana ture su. Baya son taimakon kowa. Momma yake so. Gida yake son zuwa. Wannan fadan bana shi bane shi kadai. Dole mutane suka sake shi saboda yanda yake ture su yana fadin. "Fuck off!" Wajen motarshi yana nufa. Kanshi ya sake dafewa yana jin wani luu. Da babu motar daya kai hannu jiki daya fadi. Wani datijjo mai ruwan kamala ya dubi mutanen dake tsaye yace. "Malam garba ka taimaka ma yaron nan mana. Ko gidansu ya fada a tukashi. Kana ganin yanda jini ke dibarsa" Dayake malam garba direba ne. Yana jan motoci. Daga shi har datijjon mutanen arziqi ne matuka da ake girmamawa dagani da mutunci a unguwar. Babu musu ya karasa wajen fu.ad. "Kai kam samari kabari a taimaka maka mana" Dakyar fu.ad yace "Ni gida zanje. Kaina...... " "Sannu kaji. Ka fadamun inda kake sai inje in sauke ka. Ni direba ne" A yanda yake jinshi kaman ba a duniya yake ba. Yasan bazai iya tuqi ba. Haka ya gayama malam garba inda zai kaishi. Shi ya karbi mukullin motar. Ya bude ya kama fu.ad ya saka shi a ciki. Sannan ya kalli dattijon dayai magana yace. "Sai inga wani yazo mu tafi tare. Dan gudun matsala" Kallon kallo suke an rasa wanda zai bishi dan tunda sukaga motar fu.ad din kowa ya sha jinin jikinshi. Datijjon nan ya taka zuwa inda motar take yace "Muje..... " * Sun nisa sosai. Sama sama fu.ad kejin ringing din wayarshi. Hannu yasa cikin aljihunshi ya zaro wayar da screen dinta ya farfashe. Kanshi na wani irin juya mishi. Dakyar ma wayar ta dannu ya amsa ya kara a kunne. "Ina ka shiga haka. Inata kira not reachable" Dakyar ya iya ce ma haneef. "Ka so dai dai dawanau. Please ka taho....... " Cikin alamun razana haneef yace. "Fu.ad are you okay?" Da bala.in dauriya ya amsa shi da. "kazo mana. Ka taho..... " Yanajin haneef na magana amman bazai iya amsa shi ba Kanshima wani ciwo yake da duk karar data shiga kunnen shi. Dattijon dake baya tare dashi ya mika ma wayar da fuska yake rokonshi daya taimaka ya karba. Karba yai ya kara a kunne hadi da sallama. A razane haneef yace. "Waye kai?  Me ya same shi ne wai? Kuna ina?" A nutse ya fara ma haneef bayani da cewa. "Ka kwantar da hankalinka. Mu taimakon shi mukai. Fada sukayi ne yadan samu raunuka. Kaman yanda yace kazo zamu tsaya dai dai dawanau" Jin anyi shiru yasa shi mikama fu.ad wayar da yake jingine jikin kujera. * "Lafiya wai?" Momma ke tambayar haneef da duk ya rikice. "Momma fu.ad.....zan miki bayani...... " Da gudu ya fita daga falon tana kwala masa kira. A harabar gidan yaci karo da lukman. "Muje please...... " Kawai yace suka bude mota. A hanya yake fada mishi iya abinda ya sani. * Dai dai dawanau suka hango Range Rover din fu.ad tsaye. Parking yai suka fita shi da lukman. Wani dattijo suka hango tsaye jikin motar. A kagauce yace "Yana ina?....... " Lukman kam baibi takansu ba. Motar ya bude. Hannunshi yakai ya dafe kai. Kwata kwata kamannin fu.ad din sun sauya. Ga wani numfashi yana ja dakyar. Rasa ina zai kama a jikinshi yai. Dan jinin dayake gani baisan daga inda yake fitowa ba. Haneef ya zagayo ya ture lukman. "Ya Rabb......... " Ya fadi yana zira jikinshi cikin motar ya kamo hannuwan fu.ad ya tallaboshi ya fito dashi. "Fu.ad......." Yake kira amman da alamu ma baisan abinda yake yi ba. Daga shi yai cak a kafada ya nufi mota da gudu. Lukman ne ya tsaya. Ya zaro kudi a aljihunshi ya kamo hannun dattijon nan ya damka mishi hadi da fadin. "Mungode sosai baba" Zagayawa yai inda malam garba yake ya karbi mukullin motar dake hannunshi ya ja motar yana bin bayan haneef. * Aminu kano suka nufa dashi. Suna karasawa sukai parking. Haneef ya bude bayan motar. Lukman ya karaso suka tallabo fu.ad. "Fu.ad....." Haneef ya sake kira yana taba kumatunshi. Dakyar ya bude idanuwanshi kamun ya sake lumshe su ya wani langabe a jikin haneef din. Kasa sukai a tare saboda wani nauyi dabai tsammani da fu.ad din yayi. Lukman ya dafa a rikice yana fadin. "Call for help........ " Da sauri lukman ya tashi ya na karasawa cikin asibitin da gudu. Girgiza shi haneef yake yana fadin. "Wake up fu.ad.....su waye sukai maka haka?" Wasu nurses ne suka fito da wheel chair. Kama fu.ad suka saka shi ciki. Da sauri suka gungura shi. Wata nurse ke cema haneef. "Ba zamu taba shi ba saida yan sanda gaskiya....... " Kai kawai haneef ke jijjiga mata. Lukman ne mai karfin halin dauko waya ya kira su momma yake fada musu. Su taho da yan sanda. Wani numfashi haneef yaja hadi da fadin. "Am going to fucking end ko waye ya taba fu.ad............!" [4/4, 6:00 PM] Fatima saleh: 💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ 19 "Ya isa haka mana safiyya. Sai kinja ma kanki wani ciwon. Tunda kika ga har dare yayi haka da wahala ado yazo ya fadama su baba" Jummai tace tana dan bubbuga bayan safiyya dake kwance jikinta tana wani irin kuka tun barin su wajen. Lami tabe baki tayi. "Ni inama mamakin kine wallahi. Duk abinda yai muku amman kice kin damu dashi?" Idanuwanta ta dago cike da hawaye tace ma lami. "Tun da ance miki zuciyata tasan wannan ko?  Na gaya miki ne dan nai alkawari bawai dan ki auna mun abinda yake faruwa dani ba. Nafiki sanin rashin dacewarshi" "Ki rabu da lami kema safiyya. Allah dai ya kawo karshen abin. Bara mu tashi mu tafi gida. Sai kuma gobe in Allah ya kaimu" Fadin jummai tana janye safiyya daga jikinta. Har suka sa kai suka fita daga dakin ta kasa ko magana. Kukanta ta ci gaba dayi ko zataji sauki. Duk yanda fu.ad ya rama dukan dasu ado sukai masa bai mata ba. Su biyu suka tarar mishi. Koya ta rufe idanuwanta sai taga hoton abin. Girman jiki da shekaru ta tabbata su ado sunfi fu.ad. Wata tsanarshi ta kara cika mata zuciya. Wani irin abu take ji a zuciyarta. Fata take fu.ad din ya kirata taji lafiyarshi. Abinda zai biyo baya bashi ke damunta ba. Lafiyar fu.ad a yanzun tafi mata komai. **** "Haneef kaci wani abu mana" Girgiza kai yai. Ranshi yana baci. Amman bai taba kai matakin na yau ba. Dan har wani duhu duhu yake gani cikin idanuwanshi. Wani abu yake so yakaima duka koma menene yadan rage abinda ke boiling a zuciyarshi. Daga shi sai lukman zaune a dakin da aka kwantar da fu.ad. Bayan tabbatarma da su haneef cewar zai tashi. Yadai samu concussion saboda buguwar dayai akai. Amman komai lafiya kalau. Yana bukatar hutu ne. "Allah lukman ko su waye sai sun gane kurensu.... " Wani numfashi lukman ya sauke. "Fu.ad din dai ya tashi muji ya akai" A kufule haneef yace "I don't care ko shine bashi da gaskiya. Abu daya nasani. They are going to pay for this" Shiru lukman yayi. Dan ko shi tun tasowarsu a yarinta bai taba ganin ran haneef ya baci haka ba. Asali ma shine yake kokarin basu hakuri in wani abin ya taso. * Nan suka kwana tare da haneef. Tunda safe lukman ya tafi saboda yana da lectures. Har wanka nan haneef yayi. Da su pha.iza zasu zo suka taho masa da kaya. Har suka gama zamansu suka tafi fu.ad bai farka ba. Haneef na zaune yana karatu da wayarshi yaji kaman an motsa. Wayar ya ajiye ya matsa sosai kusa da fu.ad. Motsawa ya sake yi. Ya dafe kanshi yana fadin. "Owwhh....... " "Fu.ad?........" Idanuwanshi ya bude a hankali. Ya samu yan mintina yana tunani kamun komai daya faru ya dawo mishi. Abu dayane ke masa yawo cikin kai. Mikewa yai da saurinshi. Haneef ya kama shi dam yana fadin. "Kabi a hankali. Baka ganin ruwa ne a jikinka" Muryarshi a dakushe yace. "Tun yaushe nake nan?" Da mamaki a fuskar haneef ya amsa shi da. "Tun jiya" Dafe kai yayi. Bashida lokaci mai yawa. Gobe ne daurin auren safiyya. Ganin da gaske saukowa yake sonyi daga kan gadon yasa haneef fadin. "Ka nutsu mana. Ina zakaje ne haka?" Yana dafe kanshi dake juyawa. Yace "I need to go haneef. Ba zaka gane bane. I have to........." Tunanin haneef ko buguwar da fu.ad yayi akaine take son bashi matsala. Mikewa yai yana fadin. "Koma ina ne zakaje. Ka jirani anan. I will be right back." Kamun ya amsa shi ya fice daga dakin da sauri yana barin fu.ad zaune. Karin ruwan da ke jikinshi ya cire. Kalle kalle yake cikin dakin. Yako hango mukullin motar haneef. Dauka yayi. Yanajin kanshi na wani sarawa kaman zai balle ya fadi. Takalmanshi dke ajiye a gefe ya dauka. Dakyar ya saka su. Ya lallaba ya fice daga dakin yana nufar hanyar da zata fitar dashi daga asibitin. * Haneef kam fita yai danya kira doc ya fada mishi fu.ad ya farka. Yaci karo da wani abokin shi da tun da suka gama secondary school rabon dasu hadu. Aka tsaya ana gaisawa. Yake tambayarshi kowa ya kawo. "Brother dina ne. Nama fito ne in kira doc. Kaifa" Abokin ya amsa shi da. "Matar brother dina akaima aiki. Ka fadamun number din dakin da kuke. In na fito sai in shigo duba shi" Fada mishi haneef yai. Sukai exchanging numbers sannan ya wuce yai magana da wani likita. * Dakin yagani wayam. Ya girgiza kai. Zaton shi fu.ad na bandaki. Dan hauka kuma ya cire ruwan. Zama yai kan kujera yana jiran ya fito. Har likitan daya kira ya shigo amman fu.ad shiru. Da kanshi ya tashi yaje yai knocking kofar bandakin hadi da kiran sunanshi. Nan ma shiru kakeji. Turawa yai. "Ya Allahu......." Ya fadi daya ga fu.ad din baya ciki. Dawowa yai dakin ya sake dubawa ko dai idanuwanshi sun samu damuwa. Mukullin motar daya ajiye kan drawer ya kai idanshi kai baya wajen. Aiko takan likitan dake tsaye haneef baibi ba ya bude dakin yana fita da gudu. Inda yai parking mota ya karasa baiga motar ba. Tsaye yai dan ya rasa me ma ya kamata yayi. **** Inna ce zaune kusa da safiyya da tun jiya wani irin zazzabi mai zafi ya saukar mata. Ga ciwon kai. Abinma karuwa yai da taji fu.ad bai kirata ba ballantana sakon shi. Dafata inna tayi. "Safiyya ko dai muje asibiti" Girgiza kai tayi. Idanuwanta na cika da hawaye. Yanzun ta kara tabbatarwa ba zata iya zama da ado ba. Ji take in ta aure shi mutuwa zatai ko da kuwa ba zata sami fu.ad ba. Muryarta na rawa da sauri dan karta kasa tace. "Inna dan Allah a fasa auren nan...... " A razane inna ta dafe kirji. "Subahanallahi. Safiyya?  Meya shigeki haka?  Kinsan me kike fada kuwa?" Hawayen da suke idanuwanta suka gangaro. Kai ta daga ma inna alamar tana sane sannan ta ce. "Inna dan Allah....." Rufe mata baki inna tai. Dan jikinta har kyarma yake kar wani ma yaji me safiyya ke fadi. "Zafin zazzabine kawai safiyya. Kiyi shiru karma wani yajiki. Bari inga ko usman ya kawo maganin" Mikewa inna tai ta fice daga dakin. Tabar safiyya ita kadai. Hijab din dake jikinta taja ta rufe kanta tana ci gaba da wani kuka marar sauti dayake fitowa daga zuciyarta. Ba magani take bukata ba. A warware maganar aurenta da ado shi ne kwanciyar hankalinta. Ga fu.ad shiru har yau din nan babu kiranshi babu sakon shi. Addu.o.in duk da suka zo mata ta shiga jerowa tana fatan Allah daya dora mata wannan abin ya kawo mata mafita. **** Wani irin gudu yake da motar.   Koda yaganshi kan titin gidan su safiyya bai tsaya ba. Inda ya saba tsayawa yaja motar ya tsaya. Aljihunshi ya laluba. Ya sauke wata ajiyar zuciya hadi da godema Allah jin wayarshi na ciki. Kunnata yai yaga ta sake mutuwa alamar babu chargy a jiki. Cikin motar yasa chargy yai zaune yana jingina kanshi da sitiyari. Wani irin dokawa zuciyarshi take kamar zata fito daga kirjinshi. Hanya daya ce ta rage masa akan safiyya. Hanyar dayake tsoron safiyya ba zata taba amincewa tabi tare dashi ba. In kuwa har bata bi ba baisan me zai iya faruwa dashi ba. Wayar ya duba yaga ta dan hau. Hannunshi har rawa yake ya dubo lambarta yai dialing. Bai taba jin tashin hankali irin na yau ba tunda yazo duniya. Cikin shi ya wani kulle. * Wayarta taji tana vibrating. Da sauri ta mike daga kwanciyar da take ta dauko ta. Dannawa tai ta kara a kunne tanajin wanni sanyi na ratsa ta. Har zazzabin da takeji ya soma sauki. "Kana lafiya?  Ba abinda ya same ka ko?" Safiyya ta tambaya muryarta na rawa saboda wasu sabbin hawaye dataji sun zubo mata. Shima tashi muryar na rawa yace. "Ina inda kika sameni jiya. Ki fito please. Ki fito tukunna insan ko zan sami lafiya ko bazan samu ba" Kamun tace wani abu ya kashe wayar. Zuciyarta kawai tabiyewa ta mike. Fitowa tai daga dakin. Mutanene cike da gidansu anata hidima. Buta ta dauka dake can gefe kaman zata shiga bandaki. Ta tsaya jim taga ko wani na kula da ita. Hidimarsu suke tasha. A hankali gabanta na wani irin faduwa ta wuce da sauri ya nufi soro. Jin kafafuwanta take kaman na roba tsabar tashin hankali da zullumin kar wani yaganta da take ciki. Hijabinta ta jawo ta sama tana sake rufe fuskarta dan kar wani yagane ta. Unguwar shiru kaman babu mutane. Mamakin kafafuwanta takeyi. Har sarkewa suke su kadai kaman wanda babu kashi a ciki. Motar data gani duk sa bata taba ganin kalarta ba yasa tasan fu.ad ne a ciki. Ta karasa tana dube dube ko wani na ganinta. * Yana zaune sai zufa yake kaman babu Ac a motar. Wani irin yanayi yake ciki mai wuyar fassarawa. Idanuwanshi nakan hanya yana kallon ta inda zata bullo ya hangota. Wani dan karamun relief yaji. Bude murfin motar yayi yace mata. "Shigo Sofi..... " Idanuwan nan nata dake hargitsa masa tunani cike da tsoro ta sauke masa hadi da girgiza kai. "Dan Allah ki shigo muyi magana. Ko kina so wani yaganki?" Da alama maganarshi tai tasiri dan shiga motar tayi da saurinta. Hannu yakai ta rakube jikinta. Gyarawa yai ya rufe motar. Yana kallon yanda ta matse jikin kujera kaman zata shige ciki dan kar hannunshi ya taba jikinta. Gyara zama yayi. "Ni bansan ta inda zan fara ba" Ya fadi yana murza zoben dake yatsanshi kaman zai bashi idea ne. Safiyya kam gabanta ke wani irin faduwa. Dan sauran hankalinta na son tai amfani dashi wajen tunani amman zuciyarta ta fi karfin shi yau. Ita ke da mulkin a hannu. Ganin fu.ad. fuskar shi da take a kumbure. Sanin sanadinta ne hakan ya faru dashi. Jin muryarshi. Komai saiya karasa kwacewa daga hannun ta. Yau zuciyarta ce da mulkin. Saidai tana tsoron hukuncin da zata iya yanke mata. A tsorace da abinda zai iya biyowa fu.ad yace. "Naso ace iyayenki sun bani aurenki lokacin da akazo nemar mun sofi...... Bamu da lokaci. Gobe war haka na rasa ki......" Muryarshi ta wani makale saboda abinda yake ji a zuciyar shi. Lumshe idanuwanta tayi. Tunanin maganarshi na mata yawo. Gobe warhaka ta zama mallakin ado. Girgiza kai take. Ba zata taba iya zama da ado ba. Wautar amincewa aurensa take gani karara. Wani kuka ya kwace mata. Ganin hakan ya sake dagama fu.ad hankali. Jin kukan yake yana wani ci masa rai. "Sofi..... Please. Hanya daya muke da ita. Kizo mu gudu! Kibini muje a daura mana aure a wani waje........ " Da sauri take masa wani kallo dake fadin tabbas bashida hankali. Hakan ya karanta yasa shi karawa da. "Karki mun haka sofi...... Wallahi zan iya mutuwa. Zuciyata zata iya tsayawa in kika auri wani....... " Kuka take sosai. Zuciyarta nason amincewa abinda fu.ad din yazo dashi. Bayan haka ma ai aure yace zasuyi ba wani abin ba. Cikin kuka tace. "Inna fa?  Ga baba ma. Ince musu me?  *Akan So*nka nabarsu?" Abinda ko da wasa wani yace zaiyi a shekarunshi abin ba karamar dariya zai bashi ba wato kuka. Hawaye ne yake jinsu cike da idanuwanshi yau. Shi fu.ad zai kuka wa wata mace. Cikin rawar murya yace. "Ki kalleni mana ni.  *Akan so* yau ni fu.ad zan iya yin komai sofi. *Akan so*nki komai ya warwaremun. Inna da baba zasu gane. Bawai mun tafi kenan ba. Zamu dawo muyi musu bayani" Ganin yanda kalamanshi ke shirin yi mata tasiri yasata bude motar ta fita. Da sauri ya bude yana rufa mata baya. Tsugunnawa yai kasa. Gwiwa biyu yana fadin. "Sofi.... Karkimun haka. Dan Allah karki auri wani" Kallonshi take. Bata damu da duk wanda ma zai wuce ba. Hawaye tagani yana zubo masa. Yana kallonta da idanuwansa da take karantar rokon da zuciyarshi take mata ta cikinsu. Zuciyarta a dake tace. "Ka jirani. Ka jirani anan. Inhar da gaske kana sona zaka jirani. Zanyi wani abu guda daya. Inhar baiyi dai dai ba zan dawo....... " Kamun yace komai ta juya ta koma. Idanuwa ya bita dasu yana kallonta. Mikewa yai ya koma kusa da motarshi yana jin kaman a tashi rayuwar komai ya kare. Zamewa yai jikin motar yana zama a kasa. Cikin dattin dake wajen. Ko damuwa bai ba. Kanshi ya hada da gwiwarshi wasu hawaye dabai san ta inda suke fitowa ba suna zubar mishi. Tari yaji ya soma zuciyarshi na wani irin zafi. Kamar iskar dake cikinta na fita. * Da wani irin karfin gwiwar da batasan daga inda yazo ba. Ta shiga gida. Inna ta hango. Ta karasa wajenta. Hannunta ta kamo tajata zuwa daki. Ita kanta innar mamaki ya hanata magana. Haka tabi safiyya baki a sake. Sakin hannun inna tai ta tsugunna kasa ta rike kafafuwanta. Idanuwanta sun wani bushe. "Inna dan Allah kar a auramun ado. Wallahi bana sonshi. Wallahi zan iya mutuwa idan na auri ado" Salati inna ta saka. Tana kara wani kan wani. Ko dai asiri akaima safiyya ne haka. Wannan wanne irin abune. "oh ni. Safiyya wai me ya shiga kanki haka?  Gobe fa daurin aurenku. Sannan zakice bakya son shi? Aikin ke bakinki yake wata bakwai da suka wuce?" Girgiza kai safiyya take. Inna ta gane mana. Ta fahimci amsarta ita zata yanke mata decision din da take son dauka. Da faduwar gaba da inna keta fama dashi tun jiya tace. "Kinga kiyi shiru. Wallahi inhar babanku yaji maganar nan ranki da nawa inyai dubu saiya baci. Kinfi kowa sanin baya magana biyu. Ko da gawarki za akai gidan ado saikin aure shi. Kar kuma na sake jin wannan sakarcin dan karma wani yaji baki ya kamaki" Kan safiyya a kasa tace. "Ki gafarceni inna. Kice ma baba ma ya gafarceni" Kamata inna tai tana janyewa daga jikin kafarta. A tausashe tace. "Bakomai safiyya. Kita addu.a kinji ko?  Kinga mutane na jirana. Nasan su lami zasu zo babu jimawa" Batace komai ba har inna ta fito. Kar wadda take cikin trance haka take jinta. Mikewa tai. Harta fice babu wanda ya kula da ita. Wani abu can cikin ranta da batasan ko menene ba yanata mata wasu maganganu da bata ganewa. Bakuma ta fasa tafiya tana nufar inda motar fu.ad take ba. * Baisan iya lokacin daya dauka nan zaune ba. Kawai dai yasan komai ya kare masa. Da tafiyar safiyya ta tafi da duk wani farin ciki nashi. Ya rasa meke ja masa tarin nan dake sarke shi. Numfashin shi ne yake fita dakyar dakyar. Kaman daga sama yaji tace "Muje....... " Sam baiji zuwanta ba sai muryarta. Dago kanshi yai. Yana ci gaba da tarin dake tsayar masa da iska. Dakyar ya iya cewa. "Sofi kece ko dai nine nake hallucinating?" Tsaye tai bata ce masa komai ba. Ita kanta ji take kamar ba ita ba. Kamar wani abunne yai taking control din jikinta yake aiwatar da komai. Mikewa yai. Ya bude mata mota yana kallo ta shiga. Tsaye yai na yan mintina yana kallonta. Gani yake kamar zata bace. Kamar komai dake faruwa mafarkine kawai dazai iya farkawa ko da yaushe. Tuqi yake yanayi yana kallon safiyya ko zata bace. Tana nan zaune. Banda fitar numfashinta dayake ji. Zaka iya rantsewa bata motsi. Safiyya kam har lokacin wani shiru take ji cikin kanta. Wani abu ke shirin faruwa da ita. Tana ji a jikinta. Wani abune mai girma data kasa tsayar da aukuwarsa. Gaba daya kamar wadda ta rasa hankalinta take ji. **** Momma ya fadama duk abinda ya faru. Da yanda ya dauko taxi zuwa gida. Salati take. "Anya ba asiri akaima fu.ad ba?  Ko dai aljana ce ya hadu da ita? Wannan wanne iri bala.i ne?" Haneef dake zaune ya karbi ruwan da pha.iza ta miko masa. "Wallahi ni abinma tsoro yake bani kuma. Banma san me zan ba?" Pha.iza ce tace "Mubi shi ko can din ya nufa" Kai haneef ya daga mata yana fadin. "Bara inji ko lukman ya dawo gida. Bazai ji dadi mu tafi babu shi ba" Momma dake tsaye ta rasa abinda zatayi tace "Bara nima in kira abbanku in sanar dashi. Ya kamata a dauki mataki ba sai yaje ya kashe kanshi ba" Wuce wa tai zuwa dakinta inda tabaro wayarta. Tabar haneef din da pha.iza ana dan yan biyu suna makaranta. **** Baisan inda zaiyi dasu ba. Baisan wa zai kira ya daura musu aure ba. Baisan me zaiba. Bayason ya kira lukman ko haneef. Yasan babu wanda zai goyi da bayanshi. Saboda babu wanda yake gane abinda yake ciki. Ko yake ji. Hamza ya kira suna shiga cikin kano ya fada masa inda zai zo ya same su. * Cikin mota yabar safiyya. Ya fita sukai magana da hamza ya fada masa abinda yake so da kuma yanda yake a shirye daya biya koma nawane. Yasan malamin da da dubu goma zai daurama fu.ad aure. Saidai shi kanshi yana ganin rashin hankalin fu.ad din. Duka duka nawa yake dazai jajibo ma kanshi aure. Jin yai shiru yasa fu.ad fadin. "In baka sani ba ka fadamun in nemi wani" "Sorry. Dadina dakai gajen hakuri" Bayanin komai hamza yai mishi. Wajen hamza ya ranci kudi dan bai fito da atm dinshi ba suka tafi. Har lokacin safiyya kaman ba a hayyacinta take bata san meke damunta ba. **** Momma, haneef, lukman, pha.iza, yan biyu, abbah su duka suna zaune a falo jugum. Har bichi su haneef sunje basu ga fu.ad ba. An kira duk wasu abokai da ake tunanin ko yana tare dasu amman shiru. Sam basu san inda yai ba. An kira wayar shi a kashe. Gaba daya hankalin su a tashe yake. Dan hussaina ma kuka take tayi tunda wuka dawo makaranta aka fada musu. Abbah na shirin tashi sukai report police station sukaji sallamar fu.ad. Mikewa sukai su dukansu. Momma na hamdala da Allah ya dawo mata da danta lafiya. "Ina kaje haka fu.ad?" Haneef ya tambaya. Kan fu.ad din a kasa har lokacin yana kuma tsaye bakin kofa ya kasa karasowa. "Ina kaje ka daga ma mutane hankali?" Abbah ne da wannan tambayar. Jin muryar abbah yasa fu.ad dagowa ya dai kasa hada ido da kowa. Muryarshi a sanyaye yace. "Aure nayi.........!!!" * Safiyya kam taba cikin mota a zaune. Tunda aka dauro mata aure da fu.ad takejin bata da lafiya. Hannuwanta take kallo kaman zasu bata amsar abinda take ji. Kaisu tai zuwa fuskarta. Tana son idan ma mafarkin data saba yi ne gara ta farka haka nan kamun komai ya damule mata. Yama za ai ace tayi aure. Batare da sanin baba ko inna ba. Taya ma za.ace ta auri fu.ad din da duk soyyar datai dashi kaso 98% cikin 100%  a mafarki ne. Wata irin dariya ta kwashe da ita. Yau kuma inda haukan mafarkinta ya dauko ta ya kawota kenan. Lallai son fu.ad wata irin kaddara ce mai ban mamaki a kanta. * "What!!!??? " Lukman da haneef da pha.iza suka fada lokaci daya. Abba kam ya dakuna fuska yana jin maganar fu.ad daga sama. Momma ta karasa kusa dashi ta kama kafadar shi ta girgiza tana so ya dawo cikin hankalin shi. Hannunta ya ture a hankali yana kallonsu daya bayan daya. "Da gaske nake aure nayi. Aure aka dauramun. Sofi na aura" Fu.ad ya fadi da wani yanayi a muryarshi. Momma ta juya tana kallon su abbah dan su kawo mata dauki. Tabbas fu.ad ya samu matsala. Kama hannunshi tayi tana son ta jashi ta zaunar amman kaman an dasa shi. "Muje ka zauna a kawo maka ruwa" Momma ta fadi da sigar lallashi. Girgiza mata kai yayi. "Sofi na cikin mota. Me yasa kuke mun wannan kallon?  Da hankali na. Aure mukayi" Fu.ad ya fada yana dubar fuskokinsu. Abba ya kasa cewa komai. Yanzun yake ganin abinda matarshi take fada masa. Lukman ne ya nufi hanyar waje. Dan ganin abinda fu.ad din yake fada ko gaskiyane. Da gudu ya dawo ya kalle su yace. "Da gaske yake tana mota" Haneef ne da pha.iza suke rige rigen fita waje dan gano gaskiyar abinda lukman yake fada. Ko shima abinda yake samun fu.ad din ya hada harda shi. Ganin ta sukai zaune. A tsorace pha.iza ta koma bayan haneef. Ko aljana ce. Karasawa yai ya bude motar ya kalli safiyya da take a firgice. "Fito" Yace mata. Babu musu ta fito tana kallon shi da kuma gidan ma gabaki daya. Kafartata matsar. Tana binta da kallo kaman tana son tabbatar da ko ba kasa bace take takawa. Bata san meke damunta ba. Meke faruwa da itane haka. Sukuma wa.annan su wanene. Pha.iza ke kare ma safiyya kallo. Allah kenan. Mai kaddara yanda yaso. Wannan ce ta rikita bros dinta haka kuwa? Gaskiya inba aljana bace ba to mayyace. Dan ita bataga abinda ke jikin safiyya dazai ja hankalin fu.ad din ba. Komawa tai tana nufar cikin gida. Haneef da safiyya dake taka kasa kaman tana tsoron zata tsagene ta fada da ita. Ko sallama basu yi ba suka shiga ciki. Suna karasa cikin falon sosai. Kallon su take daya baya daya. Sannan ta maida dubanta kan fu.ad dake gefenta. Zuciyarta taji tana wani rawa. Wani abu ya kulle a cikinta. Kallonshi tai cikin tashin hankali tace "Mafarki nake ko da gaske ne?" Shima kallonta yake yana jin wani iri. "Da gaske ne sofi. Aure mukayi" Inalillahi wa ina ilahi raji.un take furtawa cikin zuciyarta. Ba mafarkin komai take ba da gaske ya faru. Da gaske ne tabar komai ta zo ta auri fu.ad. Ta baro inna da baba. Ta watsar da duk wata tarbiya da suka gina mata shekaru goma sha takwas. Wani jiri taji ya kwasheta. Kamun wani ya lura meke faruwa takai kasa...........! *#TeamAS* [4/4, 6:00 PM] Fatima saleh: *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ *Thank you for all the love and support. I feel you guys oceans and galaxies. To team FU.AD* Fu.ad ne yai kanta. Zama yai ya kamata yana jijjigawa. "Sofi. No please. Sofi ki tashi....." Gabaki daya ya wani gigice. Momma ce kawai ta karasa kusa dashi. Tana janyo sofi jikinta tace "Pha.iza miko mun ruwa gashi can.... " Jiki babu kwari pha.iza ta mikoma ta ruwan. Zubawa tadanyi a hannunta ta murza sannan ta shafa ma sofi a fuska har sau biyu. Fu.ad kam ya tattara gabaki daya hankalin shi ya mayar kanta. Wani dogon numfashi taja ta bude idanuwanta a firgice. Janye jikinta tai daga na momma ta matsa ta hade sa bangon. Wani irin kuka ta saki. Karasawa fu.ad yai kusa da ita yakai hannunshi. Yanda ta janye jikinta da hanzari kaman wadda taga miciji yasa shi fasa tabata. Muryarshi can kasa yace. "Hey look at me. Sofi nine. Muna tare fa. Komai zaiyi dai-dai" Kaman daga sama sukaji muryar abba yace "Ko wani zaimun bayanin abinda ke faruwa a wajen nan? Naka sa ganewa" Fu.ad ya dauke idanuwanshi daga kan sofi ya sauke su kan momma yana rokonta data fahimce shi. Saidai ita tama rasa me take ji a lokacin. Mamaki? Bacin rai ko me? Gaba daya kanta ya wani daure. Haneef dake tsaye yace. "Kai muke jira fu.ad" Kallon haneef yai hadi da fadin. "Wacce kalmace baka gane ba cikin maganata ta dazun?" Girgiza kai kawai haneef yai. Rashin kunyar ta dawo kenan. Da magana cikin gatsali da isa. "Wacce maganar banza ce kakeyi haka fu.ad. Me ka fada da zamu gane?" Abbah ne ke fadar hakan rai a bace. Tausasa murya fu.ad yai. "Ya zanyi ne abba? Daukota nai mukaje aka daura mana aure" Karasawa inda yake abbah yai ya dauke shi da wani mari da yasa har iskar dakin ta daina watayawa na wani lokaci. "Sake maimaitawa muji!" Hannunshi rike da kunci yace. "Abbah aure mukai. Wallahi ba karya nake ba" Wani marin ya sake dauke shi dashi. Daya sa safiyya dake gefe kara rike jikinta tana kallon abba. Nadama da kuskuren abinda sukai din na mata yawo a duk jikinta. Balle da taga abbah ya juyo da hankalinshi kanta. Ta sake takurewa da bango kaman zata shige ciki. A fusace abba yace mata. "Idan shi bashida hankali ina kika kai naki?  Kinsan darajar sa Allah yai miki kuwa? Kinsan halin da kika bar iyayenki ciki kika bi namiji aka daura muku aure? Ya Rabb. Wannan wanne irin hauka ne kukayi? Kina da tabbacin zai darajaki? Zai zauna dake har abada? Zai soki fiye da yanda iyayenki suke sonki? Wanne tabbaci kike dashi na bazai gujeki ba?......" Da sauri fu.ad ya katse abbah da fadin. "Wallahi zan rike ta abba. Bazan wula....... " Momma abba ya kalla yace "Idan yaron nan bai fitarmun daga gida ba zan ji masa ciwo. Ku fita dashi bana son ganin shi" Momma ta mike tana girgizama abba kai. Karasowa tai inda yake a tausashe tace. "Dan Allah alhaji ka kwantar da hankalinka abi a tsanake......" Safiyya kam wani irin kuka take mai sauti. Abba ya kalle ta yace. "Kukan me zakiyi?  Namiji ne gaki gashi nan" Har wani daci yake ji. Zuciyarshi na masa wani irin radadi. Ganin safiyya yake kamar pha.iza. Ji yake kaman ya batar da fu.ad ya daina ganinsa. Yaushe fu.ad din yai hankali?  Harda zai rabo yar mutane daga gidansu bada sanin iyayenta ba. Sam baya son ganin fu.ad. Muryarshi na rawa ya ke kallon su haneef. "Ya fita bana son ganin shi." Fu.ad dake zaune ya mike. Dan baiga zaman da yake ba. Akan me abba bazai fahimce shi ba. Laifin shi daya bai gaya musu zaiyi aure ba. Yau abbah ya daga hannu ya mare shi har sau biyu. Ya dauka shi kadai ya isa hukuncin laifinshi a wajensu. Abbah bai yarda dashi ba yana ganin zai ci amanar sofi ne. Kuma ma aiba cayai ya rabata da iyayenta ba. Zai kaita suyi musu bayani basu da wani zabi. Safiyya ya kalla. Kukanta na kara mishi zafin dayake ji kanshi nayi. Dan tun dazun yake jin har wani jiri jiri ke dibarsa. "Taso mu tafi" Yace mata. Ware idanuwa tai cike da hawaye. Tana rokon Allah yasa komai ya juye ya zama mafarki. Mikewa tai da sauri. Kila in suka fita daga gidan nan hankalinta ya dawo jikinta. Kowa kaman an dasa shi a wajen. Lukman mamaki ya hana shi tunanin komai. Kallon su kawai yake. Haka yan biyu ma. Sunfi maida hankalinsu kan safiyya. Kayan dake jikinta. Komai nata suna mamakin wannan abu. "Ina kake nufin zaku tafi?" Cewar momma da a yanzun take jin kaman ta rufe su da duka dan takaici. Bata san banbancin halayyar fu.ad din da sauran yayanta na da yawa ba sai yau.  Kanshi a kasa yace "Idan abbah ya huce saimu dawo." Numfashi momma ke fitarwa tana jan wani a hankali. Dan gab take da loosing dan sauran control dinta. Wanda take da bukatarshi dan ta kwantar ma da abbah hankali. Kallon abban tai dake tsaye dafe da goshi tace "Muje muyi magana dan Allah...... " Bai musa mata ba ya wuce. Ta juya ta kalli fu.ad "Ka tsaya inda kake. Wallahi zakaga bacin ran da baka taba zato ba na fito na samu baka nan" Kai kawai ya daga mata. Ta bi bayan abbah. Sai lokacin haneef yace "Why?" Ya bude baki zai amsa haneef lukman yace "Haka ake zaman tare?  Yanke hukunci babu shawara da kowa?" Toshe kunnuwa fu.ad yai yana wani rintsa ido. Ya saki hannuwanshi yana fadin. "Ya isa!  Ku kyaleni please. Akan me kowa zai dinga digamun ayar tambaya ne wai?" Kallon shi safiyya keyi wasu hawayen na sake wanke mata fuska. Duk da ba hayaniya yake ba yanayin yanda yake maganar ya mata wani iri. Oh Allah na take fadi a ranta tana tambayar kanta. Me tayi haka?  Wacce wauta tabari zuciyarta ta aikata mata. * "Dan Allah alhaji karkai haka. Wallahi harda rashin hankali yake damun fu.ad. Dan Allah kazo muje dani dakai. Dasu gaba ki daya mu sami iyayen yarinyar nan" A gajiye abbah yace. "Da wanne ido zan kalle su? In pha.iza ce a matsayin waccan yarinyar bansan me zan ba wallahi......." Ita kanta tasan abinda fu.ad yai babbane. Su dukansu ya taba mutuncin su. Duk da ta kula maganar bata ma gama zama dai dai da abbah ba. Tunda bai fara hango maganganun mutane in maganar ta fita ba. A tausashe tace "Hakan na dora shisa nace muje. Nasan duk inda hankalinsu yai dubu a tashe yake wallahi...." Jinjina kai abbah yai. Saboda yarinyar kawai. "Dauko mayafinki mu tafi. Amman fu.ad yabar falon nan kamun in fita" Da hanzari momma ta wuce ta dauko hijab dinta. Ta fita falo wajen su fu.ad. "Haneef. Lukman ku tafi a mota daya kai da su fu.ad din. Gamu nan zamu biyo bayanku yanzun." Wani dan sanyi fu.ad yaji. Yana godema Allah. Gara ma suje ayi komai yau a kare. Tunda dai sofi ta zama tashi bashida matsala da kome zai biyo baya. * Motar shiru banda kuka da ajiyar zuciyar da safiyya ke faman yi. Ta wani hade jikinta da kujerar. Ta sa kanta cikin hijab tana kuka. Kallonta kawai yakeyi. Zai barta tai kukanta iya yau. Zai bata iya yau kawai tai abinda take so. Duk yanda kukan yake damunshi. Daga yau ba zatai kukan nan ita kadai ba. Bama yajin zai barta tai komai ita kadai. Wannan shine tabbacin da ya dinga bama kanshi da mafarkai da yawa. A hanyarsu ta zuwa bichi yake tsara yanda zasuyi rayuwarsu shida sofi. Daga ita sai shi. Zai nuna mata yanda zai yi komai *Akan so*nta. **** Inna ce tsaye tana kallon kofa tana sharar kwalla. So take taga ta ina baba zai bullo. Yama za.ace an nemi safiyya an rasa?  Ina zataje haka?  Kuma wani abin takaicin shine ko wanda yaga giccinta babu cikin gidan. Maganganun safiyya ke ta dawoma inna. Addua ta shiga yi kar abinda take zato ya zama gaskiya. Ko wani yaima safiyya asiri. Dan tun yaushe take kula kaman bata cikin hayyacinta. Yin komai take kamar wadda aka sakama battery. Shisa ta matsa da tambayarta ko lafiya sai tace bakomai. Duk gidan anyi jugum jugum ana jimamin wannan ikon Allah. Tun suna fama da inna ta zauna har suka hakura suka kyaleta. Ita ina taga zama batasan halin da yarta take ciki ba. Ganin shigowar baba yasa inna tarbarsa da hanzari tana. "Anganta?" Girgiza mata kai yayi. Ta rushe da wani kuka tana kiran Allah daya kawo musu dauki. Shi kanshi baba kallo daya zakai masa ka gane tashin hankalin da yake ciki. Yasan yanzun kam ya kamata yaje ya sanar gidansu ado. Kasa cema inna komai yayi. Yasa kai yana ficewa. * Dai dai kofar gidansu safiyya sukai parking. Gaba dayansu suka fito. Safiyya taji wani sabon tashin hankali. Jikinta ya dauki bari. Batasan da wanne kafa ma zata shiga gida ba. Fu.ad hankalinsa nakanta. Ganin yanda ta sake rikicewa ta a neman shidewa yasa shi kallonta cikin idanuwa. "Breath in....... " Yace mata ganin kaman ta manta yanda ake jan iska. Kula yai bama ta gane me yake nufi ba. "Sofi. Kinga ki kwantar da hankalinki. Kiyi numfashi. Kija iska..... " Can sama take jin muryar fu.ad. Sai da yai mata magana sannan ta tuna numfashinta ne take rike dashi. Shisa take jin duniyar tayi tsaye. Haka ya dinga mata sai da yaga numfashinta ya dai daita tukunna. Hankalinshi ya maida kan abba da yake tsaye shida momma kofar gidansu safiyya. Suna yanke shawarar momma ta shiga. * Yana fitowa yaga mutane tsaye kofar gidanshi da motoci guda biyu. Gabanshi ya sake faduwa. A mutunce suka gaisa da abba. Ya dora da fadin. "Mai gidan nan muke nema" A dadare baba yace. "Nine Allah dai yasa lafiya" Dan sam baima kula da safiyya dake can gefe tana boyewa bayan fu.ad data hango shi. "Alhamdulillah dai. Magana zamuyi" Sauke numfashi baba yai. "To amman dai ina sauri ne. Saboda hankalina ba a kwance yake ba....." Da hanzari abba yace. "Nasan yanda alaka ne da yar wajenka ko?" Cike da mamaki baba ke kallonshi. Abba ya dora da fadin. "Maganar data kawo mu kenan" Juyawa yai. Yaima haneef nuni dasu karaso. Shikam baba ya tsayane yana kallon ikon Allah. Su haneef dake tahowa yake kallo. Safiyya na bayansu dan haka baima hangota ba. Su ukkun dai ya gane su. Musamman fu.ad dayasan fuskarshi ba zata mantu a wajenshi ba. Yaron nan ne daya mare shi. Wanda sukai rikici da iro. Yaron nan marar tarbiya da akanshi ya soma sanin menene tsanar mutum. Haneef kuwa sai yanzun ya tuna shi. Tun randa suka zo neman auren safiyya yake masa kallon sani. Mamaki ya sake cika baba. Ko wani sabon neman auren safiyyar suka zo?  Yake tambayar kanshi. Mamakin shi ya karu da suka karaso yaga safiyya bayansu kaman wadda aka koro. Gabako daya ta wani firgice. Wani abu yaji na neman tsayawa cikin kanshi. Saboda baya so yai connecting abinda yake son yai tunani. Bazai taba ma yiwuwa ba. Momma ya kalla. "Ku shiga ciki da ita ko" Hannun safiyya momma ta kamo. Ta jata suka rakube baba dake binsu da ido suka wuce ciki. Da sallama mama ta shiga gidan da yake cike da mutane ga mamakinta. Da gudu inna ta karaso ta rungume safiyya tana sakin wani irin kuka tare da yima Allah godiya. Yan gidan ma hamdala kowa yake. Wasu kuma na tofa albarkacin bakinsu. Sakin safiyya inna tadanyi yana kallonta dan ta tabbatar da ita dince. Itama kuka take sosai. Innar ma haka tana fadin "On Allah mungode maka" Hankalinta ta maida kan momma dake tsaye kawai. Tana tunanin ta inda zata fara gaya ma inna maganar data kawo su. * A nutse abbah ke ma baba bayanin abinda ya kawosu. Da kuma iya abinda ya sani. Ai yana karasa fadin cewar an daura musu aure da fu.ad kaman yama baba wata allura ne. Da hanzarin gaske yai cikin gida..........! * Inna ta kalli momma dake tsaye. Ta bude baki zatai magana baba ya shigo a fusace. Safiyya dake rike hannun inna ya kama ya wurgar gefe daya tana dakin wani irin ihu. Gaba daya gidan mamaki suke. Safiyya ya kalla yana fadin. "Wallahi na yafeki safiyya. Ko ke kadai nake da ita yau na hakura da ke ballantana ina da wasu........!" Da rarrafe safiyya ta taso taba rike kafafun baba tana wani irin kuka mai taba zuciya. "Baba......!" Tureta yai. Inna dake gefe ta kamata tana kallon baba. Riketa safiyya tai tana wani irin kuka kaman ranta zai fita. "Ki sake ta kawai. Kinsan me yarinyar nan tai mana kuwa? Kinsan guduwa tai da wani suka daura aure? Safiyya wai. Safiyya fa" Baba ke fadi yana jin kaman ya hadiye zuciya ya mutu ya huta da fuskantar wannan abin kunyar. Ture safiyya inna tai daga jikinta tana jero inalillahi......... Tare da wasu cikin yan gidan. Sulalewa inna tai ta fadi. Da sauri safiyya da wasu sukai kanta. Safiyya na riketa tana ihun. "Inna....inna ki tashi. Dan Allah ku yafemun........" Janye safiyya baba yayi daga kan inna. Tana kwacewa yana ihun kuka. Ya jefar da ita gefe. "Ai baki damu da halin da zaki sakamu ba kika biye san zuciyarki. Ki kyaleta. Ki kyakemu kibi wanda kika zaba akanmu" Tare da momma aka yayyafa ma inna ruwa ta farfado. Tana kallon safiyya ta rushe da kuka. "Safiyya wanne abin kunya kika ja mana? Gobe daurin aurenki. Inama kika san yaran da kika bi? Waye shi?" Ta kasa magana sai kuka da takeyi. Baba ne ya amsa ta da fadin. "Yaron da ya daga hannu ya mare ni ne. Yaron daya sa aka kullemu gabaki dayan mu. Shine ta zaba akanmu" Girgiza kai inna take tana kallonsu. Tana so su karyata maganar da baba ya fadi. Ture mutanen dake kusa da ita tayi ta karasa inda safiyya take ta kamata ta jijjiga. "Ki ce mun hakan bai faru ba safiyya. Kice mun baki gudu kin auri wani ba. Dan Allah kice mun baki auri yaron daya wulakanta mu ba" Kuka kawai safiyya keyi. Saida inna ta sake girgiza ta sannan dakyar tace "Nayi inna..... Wallahi nayi babban kuskuren rayuwata. *Akan so*........" Bata rufe baki ba inna ta ture. Tsaye ta mike tana zubda wasu hawayen takaici. "Ki fitar mana daga gida. Wallahi ni bazan miki baki ba. Zan barki da bacin ran da kika saka mu kawai....... " Mikewa tai tana nufar inna. Da sauri taja baya. "Zan miki baki in kika karaso inda nake wallahi. Kije gurin wanda kika zaba. Na hakura dake. Malam ka fitar mun da ita....." Momma ta karasa wajen inna ta kamata tana fadin. "Dan Allah da Annabinsa ki tsaya abi abin nan a hankali. Nasan tayi kuskure. Karku dora laifin nan akanta kawai. Harda danmu. Mu zauna a gyara kuskuren nan" Girgiza kai baba yakeyi. "Kije da ita. Zuwan da kukayi ya tabbatarmun da danku bai biyo halayyarku ba. Kaman yanda tamu tasa kafa tai fatali da duk wani mutuncin mu. Da duk wata kauna da muka taba nuna mata" Safiyya ya kamo dake tsaye yamika ma momma yana fadin. "Nabar muku ita kyauta. Wallahi na yafe muku ita. Kaman yanda mahaifiyarta ta fada. Ba zamuyi mata baki ba. Sai dai zan tsine mata duk ranar da ta zomun gida" Kamo safiyya momma tai tana jin wasu hawayen tausayama yarinyar na zubo mata. Wannan wanne irin bala.ine fu.ad ya jama yar mutane. Kankame momma safiyya tai tana wani irin kuka numfashinta har sama sama yake yi. Hakuri momma ke kokarin basu amman kaman ma tunzura su take kara yi. Dole haka taja safiyya tana tirjewa suka fita. Dan taga alamar sam ba zasu ji wata maganar fahimta ba. * Wani irin kallo abbah kema fu.ad dayake cike da fassarori kala kala. Balle dayaga momma ta fito rike da safiyya dake wani irin kuka. Itama hawaye take ta kalli abba tace. "Gobe daurin aurenta......... Fu.ad......" Kasa karasawa tai saboda kukan da yaci karfinta. Wannan wanne irin abune. Girgiza kai abba yake yana fadin. "Inalillahi wa ina ilaihi raji.un" Me fu.ad yai haka. Me wannan yaran sukai haka. Kallon shi ya mayar kan fu.ad da yake tsaye can gefe. Sannan ya kalli momma. "Ki saketa ta tafi wajen shi. Bana son ganin shi a gidana. Kar su zomun gidana......." Fuskarta ta goge tana sake rike safiyya. "Ina kake so suje? Dan Allah kabari muje gida. Karka yanke hukunci cikin fushi" Cikin idanuwa ya kalleta sannan yace. "Inhar naga fu.ad cikin gidan nan zan iya yanke kowanne hukunci cikin bacin rai. Su tafi gidana na hotoro..." Bata son yi masa musu. Da kanta ta kama safiyya taje ya bude mota ta sakata. Ta dawo ta kalli haneef. "Ka sauke su gidan abbanku na hotoro. Idan na lallabe shi....." Fu.ad dake gefe ya katse ta da fadin. "Kibar shi kawai momma. Ina da wajen da zamu zauna" Cike da wani takaici ta kalli fu.ad. "Bacin ran da muke ciki bai isheka ba ko?" Wani daci yake ji ga kanshi na ciwo. "shisa nace ina da wajen da zamu zauna. Abbah baya son ganina. Saboda me zan zauna masa gida?" Wucewa kawai momma tayi batace komai ba. Batason ya kara bata mata rai. Addu.ar shiriya take ma fu.ad din. Haneef ma wucewa yai dan ya tabbata in ya tsaya zasu kwashi yan kallo ne da fu.ad din. Lukman ya kalle shi. "Really?" Lumshe idanuwanshi yai ya bude su yana saukewa kan lukman. "Banda kai ma please. Abin zai mun yawa" "Banda kana da concussion babu abinda zai hanani punching dinka" Wani gajeran murmushi kawai yai daya tsaya iya fuskarshi ya wuce ya bude motar ya zauna kusa da safiyya dake kwance luf jikin kujera. Yasan lukman sarai. Ya masa fushi amman zasu shirya. Kaman yanda yasan zasu shirya dasu abba. Komai na bukatar lokaci. * Kofar gidan haneef yai parking. Budewa yai ya fita yace ma safiyya ta fito. Babu musu ta fito saboda jinta take wani sama sama. Ga wani zazzabi daya saukar mata. Koya ta rufe idanuwanta sai taga yanda baba ya banbareta daga jikinshi ya cillar. Yanda inna ta tureta take fadin bata son sake ganinta Wani irin radadi take ji. Ga kirjinta na mugun zafi. Zagayawa yai yace ma haneef. "Motata please. Credit cards na and......." Wani mugun kallo haneef yai masa. Baice komai ba ya fisgi motar yana yin reverse. Sauke numfashi yayi. Zai kira lukman. Yasan bazai qi kawo masa ba. Beside ba zama zai gidan nan ba. Baya son komai na abba sai ya huce. Hannun safiyya ya kama. Yanajin yanda take kiciniyar kwacewa yaja ya tsaya. Cikin idanuwanta da har sun kankace saboda kuka ya kalla yace. "Ki kalle ni sofi. Zan dai dai ta komai. Ban miki alkawari zuwa yaushe ba. Amman na miki alkawari komai zai wuce. Ni da ke ne cikin wannan abin. *Akan so*n da mukewa juna ne komai yake faruwa. Ke kadai nake da yanzun. Ni kadai kike da. In baki tayabi ba taya kike so mu gyara komai?" Yanayin sanyin muryarshi taji yana mata wani tasiri na daban. Ta gasgata kalamansa. Ta karbi alkwarinsa. Hawaye suka zubo mata. Kai ta daga masa. Yasa hannu ya goge mata hawayen dake fuskarta. Wani sanyi yaji ya ratsa shi na daban. Kama hannunta yai zuwa cikin gidan. Wajen mai kula da gidan ya karbi keys. Ba wani girma gare shi ba. 3 bedroom flat ne. Budewa yai. Ya tsaya bakin kofar yana addu.a. Kallo safiyya tabishi dashi. Saida ya gama sannan yaja hannunta suka shiga ciki. A falo ya zaunar da ita da kanshi ya shiga kitchen ya dauko cup. Fridge din dake kitchen din ya bude. Bakomai ciki. Numfashi ya sauke yana fadin. "Great.....!" Fanfon kitchen din ya bude ya dibo ruwa ya kawo mata. Ta girgiza masa kai. Bata son shan komai. Lukman ya kira. Wajen sau biyar yaki picking. Text yai ya roke shi daya kawo masa motarshi da wasu abubuwa. Text din na shiga da yan mintina ya sake kiran lukman. Picking yai da fadin. "Karka dame ni. Nake jin abinda ka ga dama kake yi?  Tam nima sai naga dama" Sauke numfashi yai. "Lukman please. Gidan bakomai fa. Badan ni ba. Ko dan sofi....." "Naji....." Ya amsa yana katse wayar. Murmushi yai ya maida kallonsa kan sofi da taja jiki ta kwanta kan kujerar. Zazzabi take ji sosai a jikinta. Kula yai jikinta kaman yana rawa. Da sauri ya karasa inda take. "Sofi..... Menene?" Dakyar ta iya ce masa. "Kaina ciwo... " Hannunshi yasa a fuskarta yaji wani zafi. Ya dauka dazun daya rike hannunta zafin dayaji wani abinne daban. "Damn...." *#TeamAS* [4/4, 6:00 PM] Fatima saleh: *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ 22 *Do include a bro in your du.a. Mustapha may His soul rest in peace. Waya sani ni ko ku wani zai bukaci hakan anjima ko gobe. Allah ya saukaka mana tamu tafiyar. Amin* Safiyya ya kalla yace. "Barin ga haneef a waje" Kai ta daga masa. Ya fice da sauri. Tun daga nesa daya hango haneef jingine jikin mota. Jikinshi sanye da manyan kaya ya daga hannuwanshi alamar surrender. Yana karasawa ya wani yi rau rau da idanuwa hadi da fadin. "Dan Allah kace ba fada zakaimun ba. Wallahi iya ba jiya ma nayi sub din wata biyu" Haneef bai san lokacin da dariya ta kubce masa ba. Fu.ad ya wani dafe kirji dai dai inda zufiyarshi take yana sauke numfashi. "Hankalina ya kwanta. Ina wuni" Daure fuska haneef yai. A ranshi yana fadin. Dole ka gaishe dani tunda baka da gaskiya. Idanuwa kawai ya zuba mishi. Abinda yasan baya so. Gara kai masa masifa a wuce wajen. Cike da kosawa yace. "Alright kamun fadan...." Shirun dai ya sake masa. "Please..... " Hakan yasa haneef fadin. "Bansan me zance maka ba fu.ad. Kome na fada ta gefen kunnenka zai wuce" Da sauri yace. "Zai tsaya ciki. Da gaske nake amman karkamun fushi. In babu kai bazan iya fuskantar su abbah ba" Yanayin daya karasa maganar da wani sanyi yadan taba haneef din. Kallon shi yai da kyau. "Bakajin magana. Abinda kai ba karami bane ba. Bance bazai yafu ba. Auren da aka gina ta hanyar da ya dace ma yana zuwa da matsala fu.ad. Ballantana naku da babu amincewar iyaye ballantana albarkarsu. Kasan rayuwarta ta gama canzawa kenan?" Cikin ido ya kalli haneef yace. "Nasani. Ina sonta sosai. Bani da wani zabi ne shisa" Sai da haneef ya sake gyara tsayuwa tukunna yace. "Na yarda baka da zabi. Amman kana da son kanka da yawa. I really hope zaka so ta rabin yanda kake son kanka" Dariya fu.ad yai. "Em' noh' dah' selfish fa. We good?" Girgiza kai haneef yai. "Not even close" Mota fu.ad yaga yana niyar shiga ya riko masa riga da sauri. "Fu.ad meye haka kaman yaro. Sakemun riga karka dakuna mun...." Haneef ke fadi yana kiciniyar kwace fu.ad dayake rike dashi dam. "Allah sai kace we good sannan" Ikon Allah haneef ya ware ido yana kallo. "Wai kai bakasan ka girma ba? Kana da aure fa yanzun. Haka zakai yara kai kanka yarinta bata gama sakinka ba" Rigar haneef ya saki ya wani dakuna fuska yana fadin. "Banda wajen yara a zuciyata. Naku kawai sun isheni....." Girgiza kai kawai haneef yai yana bude murfin motar. Sake riko shi fu.ad yai. "Please mana. I need mi' bro" Sauke ajiyar zuciya haneef yai. Shi kanshi yasan bazai iya wani fushin kirki da fu.ad ba. "We are good. Tana sonka fu.ad karkai mata butulci please" Murmushi yai sosai sannan ya daga hannunshi alamar salute yace. "Yes sir" Dariya haneef yai ya shiga motar. Ta window din fu.ad ya tsaya yana fadin. "Na siya gida fa. 3 bedroom ne. Barin dauko maka takardun ka ajiye mun a wajenka. Please ina son siyan furnitures da za.a saka anjima. Inzo muje tare" Girgiza kasa kai haneef yai. "Nope. Allah ya sanya alkhairi. Ka dai kara addu.a sosai daukomun takardun sauri nake" Da sauri ya je ya bude motarshi ya dauko takardun ya kawo ma haneef. Wani langabe fuska yai. "Inzo muje?" "Ku tafi da lukman mana" Haneef din ya fadi yana tada motarshi. "Fushi yakemun" Kallonshi haneef yai ya daga gira alamar 'matsalarku ce'. Sannan ya maida hankalin shi kan motar yana janta. "Thank you" Fu.ad ya fadi yana kallonshi harya fice. Wani sanyi yaji. "Saura lukman. Sannan su abbah" Ya fadi yana komawa cikin gida. Inda yabar safiyya ya sameta. Ya karasa kan kujerar da take zaune ya zauna daf da ita. Yana kallon yanda jikinta yai wani iri alamar tana son matsawa. Basarwa yai dole ma ta saba dashi. "Fita zan sakeyi. Saikin mun hakuri kadan. Komai zai dai-dai ta in shaa Allah" Ba fitarshi bace ta dameta. Yanda take jin hucin fitar numfashinta dab da ita. Zuciyarta a kwance take yana zama ta soma tsalle tsalle. Manyan idanuwanta ta sauke masa kan fuska. Kasa daurewa yai. Hannu yasa ya taba kuncinta. Tadan janye fuskarta. Hakan yasa shi sauke hannunshi. "Bara in tafi sofi" Mikewa yai. Tabishi da idanuwa. Abinda ke cikin idanta ya fisgeshi. Komawa yai ya tallabi fuskarta da hannuwanshi duka biyun. Pecking dinta yai a goshi. Sannan ya mike ya fice. Hannuwa tasa ta taba inda nashi hannun yabari. Ta lumshe idanuwanta tanajin yanda har lokacin dumin hannunshi baibar wajen ba. * Kai tsaye gidansu lukman ya wuce. Yako yi sa.a yana dakin shi a zaune yana cin abinci. Da sallama ya shiga ya karasa. Amsa shi ya sauke idanuwanshi kan takalman da ya shigo dasu. "Takalmi fu.ad...." Inda yake tsaye ya tsaya. Nan ya cire takalmin yabarsu tsakiyar dakin ya karasa. Zama yayi. Lukman ya ci gaba da cin abincin shi yana danna waya kamar ma fu.ad din baya dakin. Wayar ya karba ya sakata a key ya ajiye gefe. Kallon lukman yai sosai. "Kayi hakuri. I know em' a shitty friend. Hell ion' even deserve aboki kaman ka. But ina bukatar abokina. Dan Allah kayi hakuri" Cokalin ya ajiye cikin plate dinshi ya dago ya maida hankinshi kan fu.ad daya wani yi rau rau da idanuwa yace. "Kasan dai zaka iya tarata da kowanne irin magana. Bance ko yaushe kake abinda ya kamata ba. Ban kuma damu da ka saurari shawarwarina duk sanda na baka su. Imagine fu.ad zaka yanke hukunci irin wannan ba zaka fadamun ba" Hannuwanshi ya hade alamar neman afuwa tare da cewa. "Na riga da nayi. Kayi hakuri" Murmushi lukman yai. Fu.ad yace. "Menene na murmushi cikin maganata" Daga gira lukman yai duk biyun hadi da fadin. "Dan dawo baya kadan. Kaman hakuri naji kanata bani" Dariya fu.ad yai yana daukar pillow din kujerar dayake kai ya jefa ma lukman. "Shut up" Dariya sukai gabaki daya. Kamun cikin serious voice lukman yace masa. "Safiyya ta maka abinda bakowacce mace zata iya ba. Ko da nine a matsayinta bayan abubuwan da suka faru sai dai sonka ya kasheni wallahi. Dan Allah ka riketa" Dafe kai fu.ad yai. "Seriously. Me yasa kuke fadamun abu dayane wai. Ina sonta. Kun kasa ganewa and zan rike ta in shaa Allah" Daquna fuska lukman yai. "Naji sarkin soyayya. Shahid kapoor. Ba saika gartsamun cizo ba daga fadar gaskiya" Dariya kawai fu.ad yayi. Yasan indai lukman da haneef na tare dashi zai winning kowa a hankali. Hira suka shiga yi. Fu.ad din na bashi labarin yanda komai ya faru da maganar gidan da ya siya. Nan ya jira lukman din bayan yagama cin abinci. Yaje yai wanka ya fito sannan. Saida suka biya ta wani shagon saida wayoyi. Ya basu wayarshi ya dauki wata karamar HTC da kudin. Inba dole ba yafi son ya siya wayarshi acan. Lukman ya tayashi zabar wa safiyya wata Tecno mai kyau. Sannan suka wuce wajen furnitures. Pictures aka dinga dauko musu fu.ad na fadin basuyi mishi ba. Shi sam baya son kayan katako. Wasu ya zaba. Na black silver. Lukman ne yai magana dasu suka gama cinikin komai. Tare da wanda motocin kayan suka tafi har gidan. Da yake in kana bukata su zasu hada maka komai su jera. Haka aka jera musu komai. Lokacin magrib tayi. Daga shi har lukman a gajiye suke. Sun dawo sallar magrib ne fu.ad ya kalli lukman a gajiye yace. "Wai daman haka hada gida yake da wahala?" "Ni kaina ban san da wahala haka ba. Kuma har yanzun akwai abubuwan da babu fa" Dan yamutsa fuska fu.ad yayi. "Babu tv..... " Girgiza kai lukman yai. "Ba wannan bane kadai. Akwai abubuwan da babu" Sauke numfashi fu.ad yayi. "Zan kira pha.iza hopefully ita batai fushi ba. Sai tazo tagani ko?" Jinjina kai lukman yayi alamar yarda da abinda fu.ad din ya fadi. Kulle gidan sukayi. Sai da ya sauke lukman gida. Ya sake biyawa ya hado musu takeaway sannan ya nufi gida. * Tayi kallo harta gaji. Tunani kala kala a ranta. Da taga tunanin su inna da ko ya suke ciki na neman haye mata yasa ta ture su gefe. Dan wata irin kewar inna ke damunta. Lumshe idanuwanta tayi tana tunanin fu.ad. Yanda take mafarkinshi da yanda take ji akanshi. In yana gabanta tafi jin hakan sosai. Goshinta ta sake tabawa kaman zata dangwalo peck din dayai mata dazun a jiki. Taga ya dade sosai dai. Take addu.ar Allah yasa lafiya. Ta tashi ta leka kofa yafi a kirga mussaman yanzun da dare yayi. Sallar isha.i taje tayi. Ta sake watsa ruwa duk da sanyin shi dankam ko gida takan dafa wasu lokuttan. Tai alkawarin in fu.ad ya dawo zata tambaye shi dankam ruwan akwai sanyi da kuma bokiti tagaji da wahalar nan. Wata riga ta saka doguwa fara. Ta daura dankwalin akanta. Tana bukatar inner wears. Suma tafi bukata fiye da kayan sakawa. Tunanin fadama fu.ad kawai sai da wata kunya mai karfin gaske ta kamata. Ta dawo falo ta zauna kenan taji sallamar shi. Wani murmushi ya kwace mata. Ta amsa ta mike ta karasa inda yake tana karba ledojin daya shigo dasu. "Sannu da zuwa. Ka dade sosai.... " Kallonta yake. Rigar ta wani mata kyau. Da murmushi ya amsa da. "Sorry nasani. Munata siye siye ne fa da lukman.  Saura kadan in shaa Allah. Babu dai zazzabin ko?" Kai ta daga mishi. Dan garau take jinta. Banda damuwar dake danne kasan ranta. Karasawa sukai ya zauna kan kujera. Kasa ta ajiye kayan data karba hannun fu.ad ta nemi wata kujerar ta zauna. "Sofi kaina ciwo yakemun fa" Cike da kulawa tace. "Sannu. Daka je ka kwanta kadan huta. Ko in dauko maka magani?" Girgiza mata kai yayi hadi da fadin. "Stress ne kawai. Bari inyi wanka inzo muci abinci. Ko kina jin yunwa?" Tanajin yunwa sai dai kawai ta tsinci kanta dason ta jira fu.ad din ya fito. A hankali tace "Kaje ka fito" Wucewa yazo yi ta gabanta hakan yasa tace. "Umm kaji...." Juyowa yai da duk hankalinshi akanta. "Ya dai sofi? Menene?" Yanda ya zuba mata idanuwa da dukkan nutsuwar shi ya sata jin wani iri. Kanta ta sadda kasa. "Ba wani abu bane babba fa" Waje ya samu ya zauna gefenta. "Komun kankantar shi. Ina jinki" Idanuwanta ta sauke kan fuskarshi tana kin yadda idanuwanta su hadu da nashi sannan a hankali muryarta can kasa tace. "Ruwan wanka. Sanyi gare shi sosai kuma babu bokiti sai dai inta tarowa da hannu" Ware idanuwa yai da mamaki yace. "Bokiti kuma sofi? Ruwan ina kike wanka dashi?" "Ruwan daka kunna mun nai alwala" Baya so ya yarda da maganarta sai ya tabbatar. Mikewa yai yana fadin. "Ta so ki nunamun" Babu musu tabi shi har zuwa toilet din. Fanfon dake wajen alwala ta danna kaman yanda yai sannan ta kalle shi tace "Kaganshi. Ruwan sanyi sosai" Baisan lokacin da dariya ta kubce masa ba. Dariya yake sosai har da dafe ciki. Kallon shi take da murmushi a fuskarta. A kunyace tace. "Nayi kauyanci ko?" Girgiza mata kai yake ya kasa daina dariya har lokacin. She is just too much ya fada cikin kanshi a fili kuma yace. "Sofi......" Kasa magana yai saboda wata dariyar dayaji ta sake kubce masa. Dakyar ya samu ya nutsar da kanshi sannan yace mata. "Zo ki gani" Nuna mata yanda zata hada ruwa bathtub din yayi. Da inda zata cire ruwan ya tafi. Sau uku ya nuna mata tana kallo. Tun a karo na farko ma ta rike komai dan wahala dai kayi abu a gabanta. Tsayawa yai tayi yagani. Da murmushi a fuskarshi yace "Good girl" Murmushi ta mayar mishi a kunyace. "Barin yo wankan ko?" Kai ta daga mishi. Tare suka fice yai dayan bedroom din ita kuma tai zamanta a falo. Kawai dariyarshi take ji cikin kunnuwanta da yake sata murmushin data kasa fahimtar daga inda yake fitowa. Tana nan ya fito. Sanye da three quarter loose mai wasu igiyoyi daga kasan milk sai riga fara data kama shi. Idanuwanshi take kallo. Har yanzun mamaki suke bata. Ta maida dubanta kan gashin shi. Yanayin askin shi na kara bata mamaki tun jiya. Ya wani aske gefe da gefe da bayan kan. A tsakiyar kan nan gashin yake yayi wani coil. Tsaye yai yana kallon yanda idanuwanta ke yawo a fuskarshi zuwa kanshi. Hakan na mishi dadi. Kula tai da yaga tana kallon shi. Ta sadda kanta kasa a kunyace. Yai murmushi. Ya karasa ya zauna kan kafet. Daga jiya zuwa yau cin abinci akan kafet na mishi dadi. Yanzun din ma shinkafar taci. Dan ta dazun ma ta mata dadi ta sha ruwa ta koma saman kujera tana kallon yanda fu.ad ke cin abincin shi. Yana gamawa ya bude ledar wayarsu ya dauko tashi ya bude. Ya ciro charger din da wayar daman tun acan shi ya saka sim dinshi a ciki. Dan saida ma aka kunnata yai tura abubuwan shi yai wiping dayar kamun ya basu. Ta safiyya ya dauko. Ya bude ya saka mata sim din daya siyo mata da memory card sannan yasa battery din ya mika mata. "Ga wayarki" Ware idanuwa tai da mamaki. Ta sa hannu biyu ta karba tana jujjuya wayar. Daga ganin kyanta tasan tana da tsada sosai. "Nikam wannan wayar ai tayi tsada" Dariya yai. Ta dora da fadin. "Gashi ban iya ba...." "Karki damu zan koya miki. Kawo asa a charge kamun mu tashi kwanciya ya cika" Bashi tai. Yasaka da tashi da tata din ya koma kan kujera ya zauna suna kallon arewa24 tare. Shi kadai yake kallon wata drama data burgeshi ta dadin kowa. Ita kam safiyya tai shiru. Ba kallon take ba tunanin rayuwa take. Oh da yanzun tana gidan ado. Ta wani bangaren wani sanyi taji. Dan bata son ado ko kadan. Ko kamun kaddara ta hadata da fu.ad dinma bata son shi. Tsanar shi ta karu ne bayan haduwarta da fu.ad. Inda wani yace mata rayuwarta zata juye haka ba zata taba yarda ba. Kalli kudin fu.ad. Ita kanta tasan ko da wasa bata dace dashi ba. Sam bataji yana mata magana ba. Lumshe idanuwanshi yai. Baya son tunanin nan da take yi. Inda take zaune ya koma. Bataki karasowarshi ba sai fuskarta data ji ya tallaba cikin hannayenshi. Da sauri tasa nata hannuwan kan nashi tana rikewa dam. Hannuwanta yabi da kallo yana jin su har cikin ranshi. Idanuwanshi ya maida cikin nata. Fuskarshi babu walwala yace mata. "Bana son tunanin nan sofi. Bana so ko kadan" Wani rauni taji na daban. Hawayen dake cikin idanuwanta suka zubo. Cikin rawar murya tace. "Kayi hakuri. Zan bari. Ina kewar su inna ne kawai......." "Shhhhhh......" Ya fadi yana goge mata fuska da hannayenshi. Amman kaman kofar fitowar wasu hawayen yake bude mata. Gani yai bazai mishi ba. Rikota mata hannuwa yai ya matso da ita gab dashi. Rungumota yai jikinshi yana lallashi. Kuka tai sosai. Sai da yaji tayi luf sannan a hankali yace. "Komai zaiyi dai dai. Komai zai gyaru in shaa Allah" Kai ta daga masa a hankali take kokarin zamewa daga jikinshi dan nata jikin duk ya mutu. Sakinta yai ya mike ya duba wayoyinsu. Duk sun cika. Cirewa yai ya karasa wajen safiyya ya kama hannunta yaja ta sukayi bedroom din tare. Sai da tahau ya ja mata blanket din tukunna ya zagaya ya zauna kaman jiya. Wayarta ya kunna yace mata. "Matso kigani" Duk da tana jinta wani iri bai hanata yin abinda yace ba. Bayan duk wannan nan da nan din dayake da ita gudun zama kusa dashi shine karshen abinda zatai. Ko ba komai ba haram bane tasan da hakan. Kawai ji take jikinta ba daukar wani dumi ga zuciyarta ba dokawa sosai. Shima matsawa tai sosai kusa da ita. A hankali yake nuna mata yanda zatai da wayar. Inda zata danna tai kira da sauran abubuwa. Mika mata yayi. A hankali take tabawa kaman wadda hannunta zai makale a ciki. Mamaki wayar take bata. Data taba sai taga komai ya wuce. Muryarta dauke da excitement tace masa. "Ana daukar hoto?" "Sosai ma. Kawo ki gani" Mika masa wayar tai. Hannunta ya rike wayar na ciki. Yasa dayan hannunshi yakai camera din ya kunna flasher ya danna. "Kai..... " Ta fadi cike da mamakin ganin yanda ya dauki hoton dakin. Yanayinta na bashi dariya. Sakar mata hannu yai yana kallonta. Mikewa yai zaune kafafuwanta mike kan gadon. Daukar hoton ta sake yi taga yayi. Tai wata dariya. Saita fu.ad tai da camera din ta dauka. Hasken kawai yagani. Ya zaro Idanuwa ta Sakina  daukar shi. Dariya yake yakai Hannu yana karewa. "Sofi daina daukata duk fuskata tayi maiko kina mun hoto......" Tana dariya ta sake daukar wani. Hannuwanta ya riko duka yana janyota ta fada kan cikinshi. Dariyar da take yi ta dauke lokaci daya. Wani numfashi taja daya sa shi fadin. "Fuck me...." Cikin kanshi. Idanuwanshi ya kafa mata. Gabaki daya jikinta ya mutu. A hankali muryarta kamar wadda aka shaqe tace. "Yi hakuri na daina" Saida yai gyaran murya dan jinta take ta makale. Shi kanshi abinda yake ji na neman kwacewa daga control dinshi. "Tsayawa zakiyi in rama" Ganin ya sake mata hannu yasa ta mike daga jikinshi tana maida numfashi ko zuciyarta zata dan rage gudun da takeyi. Hasken wayarshi taji cikin Idanuwanta yana daukarta hoto. Dariya tayi ya Sake daukar wani. Pillow ta janyo tana karewa a dole bata so yana daukarta. Ci gaba yai da dauka yana jinshi wani so light. Gajiya tai ta cire pillow din ta kwanta. Sannan ya sauke wayar yana duba hotunan daya dauketa. Juyowa yai ya nuna mata yaga bacci ya dauketa. Dariya yai. Ya zare wayar dake hannunta ya ajiye gefe. Kanta ya daga ya gyara mata kwanciya. Ya kara ja mata blanket din sannan yakai hannunshi ya kashe musu wutar dakin. Addu.a yai musu su dukansu sannan ya kwanta da wani kwanciyar hankali na daban a zuciyarshi. Hannunta ya laluba ta cikin blanket din ya rike dam. Lumshe idanuwanshi yai a hankali ya ce. "I love you sofi...........!" Kamun wani bacci mai nauyi ya dauke shi. *#TeamAS* [4/4, 6:00 PM] Fatima saleh:   *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ              23 Ya riga safiyya tashi. Sai da yai wanka yai alwala ya fita mota ya dauko kayan da zai sake. Baya son ya ajiye su cikin gidan sam. Dan in son samun shi ne kar su wuce yau ba su koma gidansu ba. Komawa bedroom din yayi. Yanda safiyya ke baccin ta hankali kwance yasa yaji kaman kar ya tashe ta. Gefenta ya zauna ya zuba mata idanuwa. Baya son hannunshi yakai jikinta saboda alwalar dayake da ita. Gefen gadon yadan bubbuga. Ta bude idanuwanta cike da bacci ta sauke su akanshi. "sofi sallah" Ya fadi da murmushi yana mikewa daga kan gadon. Saida ta gama addu.ar tashi daga bacci sannan ta mike zaune. Tana kallon fu.ad ya fice daga dakin. Dafe kai tadanyi. Duk da yau zuciyarta a shirye take da tashi tare da fu.ad bai hanata jin wani iri ba. Ga kewar su inna. Mikewa tai ta shiga bandaki. Saida ta fara yin brush da fu.ad ya ajiye mata sannan tai alwala. Sallah ta gabatar. Addu.a sosai tayi bayan ta idar na Allah ya bama su inna zuciyar yafe mata ya kuma basu zama mai inganci da fu.ad. Dan shi kadai yasan me yake shimfide kan titin kaddarar daya dora su. Tana nan zaune kan kafet fu.ad ya dawo daga masallaci. "Ina kwana" Ta gaishe dashi. Cikin fuska ya kalleta. "Kin tashi lafiya?" "Alhamdulillah. Kaifa?" Dariya yadanyi. "Kina kusa dani. Komai dai dai sofi" Kunya taji ta sadda kanta kasa. Fu.ad din ya dora da fadin. "Yau ba wanka da ruwan sanyi ko?" Dariya tai. "Yanzun ma zanyi wankan ai" Kallonta yai yana wani ware idanuwa. 'Yana da kyau' zuciyarta ta fadi. Sake dakuna fuska yai alamar bai gane abinda ke sata murmushi ba. Hakan ta karanta yasata mikewa. Kamun tai wani abu maganar zuci ta kubce mata. "Kana da kyau" Hannu tasa ta rufe baki. Dariya ta bashi sosai. Da gudu ta nufi bandaki ta rufo yana fadin. "Sofi dawo nan......zaki fito ki maimaita mun in sake ji" Dariyarta ya jiyo daga bandakin. Fita yai daga dakin saboda baya son abinda tunanin tana wanka yake mishi. Yau akwai abubuwa da yawa da yake sonyi. Ga ball yana son zuwa amman yasan bashida wani lokaci. Dole zai hakura zuwa gobe in komai yai settle. Yana nan kwance bacci ya dauke shi. * Wata doguwar rigar ta sake mayarwa. So take ta wanke kayayyakinta amman ta rasa sabulun wanki. Wankan ma da wani abune cikin roba da batasan ko meye ba. Sai kamshi ga kumfa yana dashi. Fita falo tayi ta duba fu.ad bata ganshi ba. Daya daga cikin bedroom din ta tura. Don tana bukatar sabulun wanki. Ganinshi tai kwance yana bacci. Har zata fice taja masa kofar idanuwanta suka hango kayan kan wani table. Karasawa tai cikin dakin. Kayanshi ne duk daya cire daga zuwansu zuwa yau. Dauko su tayi ta ja masa kofar a hankali. Bandakin bedroom din ta koma. Dabara ta fado mata. Tunda dai babu bokiti. Ruwa ta tara a bathtub din ta zuba shower gel din ciki ta kada yai kumfa. Kayan fu.ad ta soma wankewa. Duk rigunan ma fararene. Harda singlet dinshi da boxers. Saida ta wankesu ta dauraye. Sannan ta wanke jeans din da three quarter daban ta dauraye suma. Nata ta wanke da tazo dasu da hijab dinta sannan ta wanke dogayen rigunan datai amfani dasu. Karfen data gani cikin bandakin ta shiga yarfe kayan tana shanyawa akai. * Ya jima da tashi. Wata kasala dai yake ji yasa shi kin sakkowa daga kan gadon. Wayarshi ya lalubo ya duba agogo. Takwas da rabi. Mikewa yai safiyya na manne a zuciyarshi. Baisan sanda bacci ya dauke shi ba. Daga dan hutawa kamun gari yadan waye ya fita ya siyo musu abin da zasuyi breakfast da. A hankali kaman wanda bayaso ya sakko daga kan gadon. Haka ya tako zuwa falo bao ganta ba. Bedroom din da yasan tana can ya nufa. Da sallama ya tura kofar ya shiga. Tana cikin bandaki tsaye tana yarfe hijab dinta. Da mamaki yace "Sofi? Me kike yi haka?" Da sauri ta juyo. Ta lumshe idanuwanta ta bude su akanshi. Tsoro yadan bata saboda bata ji shigowarshi ba. A sanyaye tace. "Allah yasa dai banyi barna ba. Babu sabulun wanki da wannan ruwan nayi" Girgiza kai fu.ad yai yana sauke numfashi sannan yace. "Banna bama karama ba" Rau rau tayi da idanuwa. Shisa da kaman tabari ya tashi daga bacci. Dan dai tana zaune ba wani aikinyi. Amman tasan wannan ruwan da tsada da ganinshi. Murya na rawa tace "Kayi hakuri dan Allah. Wallahi babu sabulu shisa. Bansan da tsada ba amman......." Katse ta yai da fadin. "Damn the shower gel. Bannar da kikamun kinsa hannunki a ruwa. Kina so kiyi mura ne sofi?  Duka yaushe zazzabi ya sake ki? Kinzo kina wani wanki" Ajiyar zuciya ta sauke. Ta dauka barna tayi. "Ba abinda zaimun. Wankin ma ba yawa" Karasawa yai sosai bandakin. Zaro idanuwa yayi ganin harda kayanshi. "Haba mana sofi. Harda kayana fa. Za azo a wanke ai" Shiru tayi dan batasan me zata ce masa ba. Ita a wajenta wannan ba wani aiki bane. Ko dauda kayan basu dashi. Yanda fu.ad din yakeyi saikace ta wanke kaya kala talatin ba kwarori ba. Hijab dinta ta karasa shanyawa. Karasawa yai gefen gado ya zauna yana wani bata fuska. Baiji dadin ganin tayi wanki ba sam. Kawai jiyai bayason tayi kowanne aiki. Yafison komai ayi mata. Ta zauna ta huta karta wahala. Fitowa tai daga bandakin. Muryarshi can kasa yace. "Bana son ki kara yin wanki sofi. Bana so" A sanyaye tace. "Na daina. Kayi hakuri" Kai ya daga mata kawai ya mike yana fadin. "Bara in siyo mana abinda zamuci" "Allah ya tsare hanya" Ta ce. Ya amsa da amin yana ficewa. Gyara zama tayi ta sauke numfashi. Kawai yanda yanayinshi yayi bataji dadi ba. Duk kokarin da yake akanta. Karshen abinda zatayi shine ta bata mishi rai. * Take away ne yayo musu na kwai da dankalin turawa sai yoghurt. A bedroom sukai zamansu suka ci. Sannan yace mata zai fita ya karasa siyayyar komai. Saida suka je falo ya kunna mata kallo sannan yai pecking dinta a goshi ya fice. Ganin maigadi ya bude masa gate ya tuna mishi da cewar yana bukatar maigadi shima. Da kuma yar aiki. Kasa yai da glass din motar yai masa nuni da hannu da alamar yazo. Da sauri ya karaso. Cike da ladabi duk da a haife ya haifi fu.ad din yake masa magana. "Bawani abu bane. Ina son maigadi ne a gidana. Da kuma yar aiki haka. Zuwa gobe ko jibi ma in an samu saikamun magana" Da fara.a maigadin yace. "In shaa Allah za.a samo" Fu.ad bai amsashi ba ya ja glass din motarshi sama ya fice.  Yana hanya ne ya kira pha.iza. Ringing daya ta daga da fadin. "Bro. Ina kwana. Ko dayake ma fushi nake. Hussaina kawai kake nema" Murmushi yayi. "Haba sisto. Kina raina. Thank you da bakiyi fushi ba." Yanajin dariyarta kamun tace. "oh no. Ni banyi fushi ba. Abinda kai super cool bro. Allah kaman a mumbai. So romantic irin......" Katse ta yai yana dariya hadi da fadin. "Gidanku pha.iza...." Dariya take sosai. Muryarshi ya dai daita sannan yace. "In momma zata barki. Ki shirya yanzun please. Flash me zaki rakani yin abu ne" Bata ko tsaya jiranshi taji meye zata taya shi dinba tace. "Be right back" Ta katse wayar. Ko minti biyar ba aiba tsakani ta mishi text da. "Done bro. Call me daka zo kawai" * Kofar gida ya tsaya da motar duk yanda yake so ya shiga su gaisa da momma kuwa. Nan ya kira pha.iza ta fito. Bude motar pha.iza tayi ta shiga hadi da fadin. "Morning bro" Da yar fara.a a fuskarshi ya amsa da. "Pha.iza. Ya momma?" Kallonshi tai tana rufe murfin motar sannan tace. "Tana nan lafiya. Me yasa ba zaka shiga ku gaisa ba?" Girgiza kai yayi yana tayar da motar. "Um um fa. Ba yauba" "amman....." Daga mata hannu yai da ya sata yin shiru. Yaja motar kawai suka nufi gidan daya siya. Dole shi ya sauke yaje ya sa key ya bude gate din sannan ya koma ya shigo da motar. Suka fito shida pha.iza. Ya bude musu suka shiga cikin gidan sannan ya kalleta yace. "Kinga gidana pha.iza. Meye babu? Me ya rage insa. Tun jiya muke tunani da lukman mun rasa" Dariya pha.iza tayi. Tana karema gidan kallo. Ba wani babba bane ba amman yayi kyau. Furnitures din sun mata kyau sosai. "pha.iza ba dariya ba. Ki fadamun" Dariyar ya kara bata kamun tace. "Really bro? Yanzun ku baku ga babu labulaye bane ko daya?" Ware idanuwa yai kamun yai yar dariya yace. "Yeah. Kai wallahi sam fa. Munata tunani. Haba shisa komai yake mun wani iri" Tare suka zagaya da pha.iza tana rubuta duk abinda yake bukata a gidan a wayarta. Musamman kayan amfani na kitchen. saida suka biya bank ya ciri kudi tukunna suka wuce kasuwa. Shi kanshi mamakin kudin daya kashe yayi. Pha.iza ma catai mishi dan furnitures din ma na karfe ne. Dana katako ne sunfi tsada sosai. Duk wani abu da suke bukata suka siyo. Har bayan mota shake yake da kaya. Lokacin da suka dawo gidan suka zauna suna hutawa. Wayarshi ya dauko ya kira safiyya da ringing daya ta dauka da sallama ya amsa yana dorawa da. "Nabarki ke kadai ko?" "Ba komai fa. Inata kallo ne" Ta amsa. Zai rantse yaji murmushin kunyar nan da take cikin muryarta. "Yanzun zan taho in shaa Allah. Ki hada kayanki na nan waje daya. Dana zo zamu taho" Ta amsa shi da. "Bari in tashi to. Allah ya dawo dakai lafiya" Ya amsa da amin yana sauke wayar. Pha.iza ke kallonshi tana wani murmushi. Dariya yai hadi da fadin. "Go away....." Dariya ta kamayi tace. "So cute. Muje tare please kaga bamu gaisa ba" Kai ya daga mata. Tare suka mike suka fita ya kulle gidan. A mota ne take ce masa. "Bro kayan abinci kadai ya rage maka" Daquna fuska yadanyi hadi da fadin. "Zan siyo pha.iza. Itama bansan meye na mata take bukata ba. May be in baki kudi sai kuje tare. Na siyo mata dogayen riguna dai. Bata fadamun me take bukata ba kuma" Jinjina kai pha.iza tai alamar yarda da abinda fu.ad din ya fadi. * Kayan data wanke ta dauko. Nata da na fu.ad din ta linke su tsaf. Ta saka cikin ledojin da sukayo siyayya. Sai kayan wankansu duka a wata leda. Ta koma dayan dakin ta dauko jakar fu.ad ta hada masa kayanshi a ciki. Ta tattara waje daya. Ta koma ta zauna tana jiran dawowarshi. Har mamaki take wai kwana biyu ne kacal ya wuce rabon data saka inna a idanuwanta. Wani nauyi taji kirjinta yayi da tunaninsu. Dakyar ta samu ta yakice tunanin gefe saboda bata son fu.ad ya dawo yaganta cikin damuwa. Sallamar shi taji. Ta amsa tana dorawa da. "Sannu da zuwa...." Karasawa yai falon sai lokacin ta kula da pha.iza data shigo da sallama itama. A sanyaye safiyya ta amsa hadi da cema pha.iza. "Ina wuni...." Dan bude idanuwa pha.iza tai tana kallon safiyya. Tace. "anty aini zan gaishe dake. Ina wuni. Ya gida?" A kunyace safiyya ta amsa da. "Lafiya kalau." Wani dan shiru ya biyo baya. Zama pha.iza tai kan kujerar dake gefe. Ta kasan ido take kallon safiyya. Ta kasa ganin ta inda ta dace da fu.ad dan banda idanuwanta bata ga abu me kyau a jikinta ba. Hancinta dai ba wani dogo ba. Dan pha.iza ma gani tai doguwar rigar dake jikinta daban. Safiyyar ma daban. Ga fuskarta wani tas. Safiyya kam duk jinta take wani iri. Haka kawai bata son kallon da take jin pha.iza na mata. Sai take jin ta duk tabi ta tsargu. Fu.ad dake zaune jikin kujera yana dan hutawa saboda ranar da suka sha da pha.iza ya dago kai ya sauke kan pha.iza. Lokaci daya ranshi ya baci. Ganin kallon rashin amincewa da safiyya dake kan fuskarta. Idanuwa suka hada yai narrowing mata nashi. Ware nata tai tana son gaya masa yanda safiyya batai mata ba sam sam. Baya son yin wata magana gaban safiyya dan haka ya mike tsaye yace. "Ku tashi mu tafi pha.iza. Kinsan fa akwai sauran aiki" Mikewa pha.iza tai da fadin. "Gida zani bro. Kun karasa aikinku ai na muku kokari ma" Safiyya a sanyaye ta mike ta dauki hijab dinta dake gefe ta saka. Pha.iza tabi kokakken hijabin da kallo kawai. Rayuwa kenan. Datai duba da yanda fu.ad ko abincin da atika ta girka bayaci sai abin duk ya sake daure mata kai. Nesa ba kusa ba atika daya ke wulakantawa tafi safiyya komai. Har kyau ta fita. Gashi yanzun yanda suka jata ajiki wayewa ta fara shigarta. Pha.iza ta fara yin gaba tana kallon hararar da fu.ad yabi ta da ita. Ta dakuna fuska tana son gaya mishi ai gaskiya ta fadi bataga inda suka dace da safiyya ba. Kayayyakinsu ya tayata dauka suka nufi bakin kofa. Takalaman data saka yabi da kallo. Silifas ne duk sun koke. Tana bukatar takalmi zai fada ma pha.iza. Motar ya bude ya sassaka kayansu ciki. Ya zagaya ya bude gaba yace ma safiyya ta shiga. Babu musu ta shiga ya maida kofar ya kulle ya karasa wajen pha.iza dake tsaye. Idanuwanshi cike da masifa yace mata. "what is wid' dah' look da kike mata? Bana so pha.iza" Sauke numfashi pha.iza tayi. "Ni na isa inja ne da abinda Allah ya kaddara? Dan batai mun ba bro baya nufin ina rike da wani abu kan aurenku" Bude idanuwa yai. A kufule yace. "Rashin kunya zakimun pha.iza?" Kai ta grigiza masa. "Ni na isa bro. Yi hakuri. Barin wuce gida zan hau napep" Dafe kai yadanyi sannan yace. "Muje in dropping dinki sai mu wuce" Ta bude baki zatai magana yace. "Bana son wata gaddama. Ranki zai baci" Wucewa tai ta bude bayan motar ta shiga. Shima ya zagaya ya shiga. Daya karasa gate saida suka sake magana da maigadi sannan ya wuce. Suna hanya ya kalli safiyya da tai shiru cikin kujera ta hade hannayenta tana wasa dasu. "Yunwa ko?" A kunyace tadan daga mishi kai. Dan tun dankalin safe sai ruwa da shima robar na jiya taje bandaki ta bude fanfo ta tarba ta sha. Ya lumshe idanuwanshi ya bude su kan titin dake gabanshi. Yace mata. "Bari in sauke pha.iza tukunna sai mu biya mu siya abinda zamuje" Kai kawai ta daga masa. Pha.iza dake zaune a baya tana jinsu. Text taima momma ta fada mata duk abinda sukai da fu.ad din. Reply momma tai mata. Sannan tace ma fu.ad. "Bro momma tace ku shiga" Sitiyarin motar yadan doka hadi da fadin. "What dah' fuck pha.iza. Me kikayi? Ni bana son wani fada yanzun fa" pha.iza ta amsa shi da fadin. "Abbah fa baya nan. Yau da sassafe ya tafi abuja" Bai sake cewa komai ba har suka karasa gidan. Shiga yai da motar ciki sukai parking. Da kanshi ya zagayo ya bude ma safiyya. Pha.iza kam harta wuce ciki abinta. Kallonshi safiyya tai a tsorace. Tsayawa yai yasha gabanta. Cikin idanuwa ya kalleta. "Ki yarda dani. Babu abinda zai faru kina jina ko?" Kai ta daga mishi. Ya ce. "Good..." Sannan ya wuce gaba tana binshi a baya har cikin gidan. Tare sukai sallama. Hussaina dake zaune falon ta tashi da gudu ta karasa inda yake ta riko hannunshi fuskar nan cike da fara.a. "Inata missing dinka. Yanzun fa nake ce ma momma nikam zanje inda ka koma tunda kaqi zuwa" Dariya yai sosai. "Nima nai missing dinki ai. Thank you for dah' text lil sis" Ta amsa da. "You welcome....." Tana sakin hannunshi ta karasa wajen safiyya tana riko nata hannun. "Anty. Sannu da zuwa. Amman kwana zakuyi ko?" Fu.ad safiyya ta kalla. Ya daga mata kai dake nuna cewar kar taji komai zata iya magana da hussaina ba wata damuwa. Da fara.a a fuskarta tace. "Umm........" Kaman tana tunani. Hussainata shagwabe fuska. "Bro bazai bari ba ko? Ni nasani" Cikin falon ya karasa inda momma ke zaune. Takalman kafarshi ya cire ya ajiye gefe sannan yaje gab da ita. Tsugunnawa yai wajen kafafuwanta. Ya rike kunnuwanshi kaman wani dan karamun yaro. "momma nayi laifi babba. Dan Allah a yafemun......" Ajiyar zuciya ta sauke. Ta kalli fu.ad. Allah sarki tsakanin da da mahaifiya sai Allah. Tun a shekaranjiya yana ranta. Ko abinci kirki bata sakama cikinta ba tunanin halin da dan nata yake ciki. Sai da haneef yaje ya dawo ne ma jiya ya fada mata yana nan lafiya tukunna tadanji hankalinta ya kwanta. Dan shi kanshi fu.ad din har yanzun bukatar kulawa yake ballantana ace ya kula da kanshi ya kuma kula da safiyya. Zatai magana safiyya suka karaso da hussaina. Har kasa safiyya ta durkusa gefen haneef. Zuciyarta na wani dokawa ta gaishe da momma. Da fara.a tace. "Lafiya kalau. Kuna lafiya dai ko?" "Alhamdulillah" Safiyya ta amsa a darare. Momma ta maida hankalinta kan hussaina. "Kuje da ita dining. Ki hada mata abinci da komai taci" Hannunta hussaina ta kama ta ja. Suna barin fu.ad a nan. "Momma nima yunwa fa" Ya fadi. Ta dan harare shi. Yar dariya yai dan ya rigada yasan ta yafe mishi. Da wahala yake laifi a idanuwan momma. A nutse tace masa. "Fu.ad kayi kuskure babba. Bakai nake jiba. Yarinyar can nakeji saboda yanda iyayenta sukai fushi sosai. Na tabbata zasu jima basu sauko ba. Kuma ko nice iya abinda zanyi kenan. Dan Allah ka rike yar nan. Duk macen da zatai maka abinda tai to ba karamin so take maka ba. Duk idan kuna da wata matsala ina nan. Sannan ka kira abbanka ko bazai daga ba. Shima nasan a hankali zai huce" Shiru yai yanajin nasihar da take ma tana wani shigar shi. Da sanyin murya yace. "In shaa Allah momma bazan baki kunya ba. Allah ya kara girma" Murmushi tayi. "Amin fu.ad. Allah yai maka albarka" Da murna ya amsa da amin yana mikewa tace masa. "Pha.iza tace mun ka siya gida ko?" Da sauri yace. "Eh mumy takardun suna wajen haneef ma. Sauran kayan ne muka siyo da pha.iza yau. Kayan abinci ne kawai ya rage yanzun" Jinjina kai tayi. "Shike nan. Allah ya sanya alkhairi. Yanzun sai insa a dibar muku kayan abincin a store. Abinda babu saiku siya ko?" Shisa soyayyar momma bai hadata da komai ba a zuciyarshi. Badai ta fada amman yasan kaunar da take masa tafi ta kowa a gidan. Godiya yai mata sannan ya wuce dining inda safiyya ke zaune hussaina nata cika ta da surutu. Sai juya cokalin take cikin abinci yasan kunya ce ta hanata ci. Hussaina ya kalla. "em starving fa hadamun komai. Kuma kin cikata da surutu hussaina ya zatayi taci abincin?" Dariya hussaina tayi tace. "Hira muke yi ne........" Ta mike tana zubama fu.ad abinci. Hada idanuwa sukai da safiyya. Sai lokacin ta danji wata yar nutsuwa ganin fu.ad din. "Ki ci abincin kar yai sanyi" Ci ta soma yi a hankali. Dambun shinkafa ne yaji kayan hadi da miyar ganye. Sosai taci abincin dan ya mata dadi ba kadan ba. Fu.ad plate biyu yaci yasha lemo. Sannan ya mike yace ma safiyya ta tashi su tafi. Ta mike a falo suka sami momma. Ta kalle su tace. "Fu.ad pha.iza zata zo. Sai suje wajen mai mana dinki akwai wasu atamfofi suna nan. Sai a dinka mata" Sosai fu.ad yaji dadi dan kamar ta shiga zuciyarshi. "You are dah' best momma." Murmushi kawai tai masa sukai mata sallama. Safiyya tai mata godiya cike da ladabi. Momma ta amsa. "Ku gaida gida. Dan Allah a kula kunji ko" Fu.ad ne ya amsa dan safiyya kunya take ji sosai har suka fita. [4/4, 6:00 PM] Fatima saleh:  *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ      24 *To MRS.DOUCHE aka dimples* "Mama na da karamci sosai" Safiyya tace masa muryarta da wani sanyi. Wani murmushi yayi. Yana so a yabi momma. "Momma bata da matsala sofi. Ni nasan zata soki daman" Langabar dakai tayi kawai. Tana tunanin randa nata iyayen zasu so fu.ad. Ita kanta a yanzun bata san matsayin nata son a wajen su ba ballantana tayi tunanin zasu so fu.ad. Hannunshi taji kan nata. Ya riko hadi da dumtsewa. Bata san yanda yake gane tana bukatar hakan ba. Idanuwanshi nakan tuki yace mata. "Muna cikin wannan tare. Ni da ke. Komai zaiyi daidai" Nashi hannun ta sake dumtsewa tana jin laushin hannun da wani dumi dake ratsa ko ina nata. A hankali ya zame hannunta daga cikin nashi ya ci gaba da tukin da yake yi. * Gidan take ta kallo. Bai kai na hotoro girma ba. Daga wajen kawai zata iya gane hakan. Amman ya fishi kyau. Fu.ad ya karasa yaje ya bude sannan ya dawo ya bude bayan motar yana fito da kayan abincin da momma ta jibgo musu. Kwalin taliya safiyya ta dauka. Fu.ad ya wani fito da idanuwa. "Sofi ajiye da nauyi" Dariya tayi tace mishi. "Zan iya dauka ai" Kallonta yake harta shiga dashi cikin gidan. Tsayawa tai tana jiran fu.ad ya shigo taga inda zasu kai kayan. Kitchen ya nufa tabi bayanshi. Haka tare suka dinga dibar kayan suna kaiwa. Saida suka gama tsaf sannan ya bude lockers din kitchen din suka jera komai. Haka kayan kitchen din da suka siyo da pha.iza suka jera inda suke sonsu. Kallon safiyya yai. Da hijab din jikinta take ta aiki. Ko zafi bata ji. Bai dai mata magana ba. Wayarshi ya dauko cikin aljihu ya duba. Hudu daura minti biyar. Yadan ware idanuwanshi yana fadin. "Muje muyi sallah sofi. Lokaci yayi" Bata ce komai ba suka wuce tare har bedroom din. Shi ya fara shiga ya fito sannan ta shiga itama tayo alwala. Fitowa tai ta same shi cikin dakin. "Ba zakaje masallaci ba?" Ta bukata. Ya girgiza mata kai tafe da fadin. "Lokaci na tafiya. Gashi ban ma san inda zan gano masallacin ba" Kai tadan daga alamar ta fahimta. Kan kafet din dakin yaja musu sallar la.asar. Bayan sun idar suna zaune shiru. Can ya nisa yace "Gobe in Allah ya kaimu zamu je makaranta" Cikin idanuwanta ya fara ganin murmushin kamun ya bayyana a fuskarta. Wani irin squeezing yaji zuciyarshi tayi da rabon dayaji shi tun farkon ganin shi da ita. "Allah ya kaimu goben" "Amin sofi" Shiru suka sakeyi. Dan kalamanta nemarsu take ta rasa inya zuba mata idanuwan nan nashi. "Kinsan yunwa nakeji. Cikina kaman banci komai ba" Dariya safiyya tayi. Tana mamakin inda fu.ad ke kai abinci. Hakan ya karanta a fuskarta ya sake cewa. "Ki shirya girki da yawa sofi. Ina cin abinci sosai sosai" Murmushi tayi ba zatai masa karya ba dan haka tace. "Gashi ban iya abinci masu yawa ba.  Banma iya duk kalar wanda naga kaci ba" Jinjina kai yayi hadi da fadin. "Sai ki koya. Akwai makarantu na koyan girki. Sai in kaiki" Kallon shi tadanyi. Yana son saukaka mata komai. Wani sonshi ya cika mata zuciya. "Nagode sosai" Girgiza mata kai yayi. "Ni da za.a dafama ai nine da godiya" Tunawa tai tana son ya koya mata yanda ake tura sako a wayarta. Mikewa tai ta wuce falo yana binta da idanuwa. Wayar ta dauko ta dawo ta zauna inda ta tashi. "Ina so fa ince ka koyamun tura sako na manta" Da fara.a a fuskarshi yace. "Dawo nan to" Yana nuna mata gefenshi. Matsawa tai ta zauna inda ya nuna mata. Tana jin har kamshin turarukanshi cikin hancinta. Wani numfashi ta ja ta fitar dashi. Kallonta yai sosai. Muryarshi na sauka kasa sosai yace. "Ya dai?" Kai ta girgiza masa. Wayar ya karba daga hannunta ya shiga nuna mata yanda zatayi. Sannan ya mika mata yace tayi. Yanda take duba keypads din kamun ta danna ya sa shi bushewa da dariya. "Sofi........." Dariya yake sosai. "Awa nawa zakiyi kamun kiyi layi biyu" Itama dariyar tayi. Ta mika masa wayar. "Jeramun ABCD din su koma dai-dai" Dariya ya sakeyi. Ganin fuskarta da gaske take ya jera mata su koma dai dai. "Haka suke ai sofi" Girgiza masa kai tai tana sake duba keypads din wayar sannan ta kalle shi tana wani dakuna fuska. "Ba daidai suke ba. Duba kagani" Kara matsawa tai sosai kusa dashi ba tare data kula bama. "Kaga A anan ko. To kallininda B take fa. Nace maka nawa ba dai dai suke ba" Dariya yake. "Sofi please. Sai cikina yayi ciwo?" Dariya tadanyi. Ita kam bata gane wannan malatsai ba. Karbar wayar yayi daga hannunta. "Haka suke na kowanne waya sunan su qwerty......." Jinjina kai tayi. Bata dai ga dalilin dazai sa a jirkita abu ba ga yanda yake. Hannu ta mika tana karbar wayarta daga hannunshi. Ya rike hannunta. Tsayawa tai tana kallonshi. Wayar ya karba ya ajiye gefe ya kamo dayan hannunta ya saka nashi yana ware tafin hannunta. Dogayen yatsunta sun masa kyau sosai. Hannu daya ya kama da nashi duk biyun yana kallon kunshin ta. Bai taba sanun yana son kunshi ba saida yaganshina hannunta. Gaba daya jikinta yayi wani dumi. Idanuwanta nakan nashi hannayen. Zoben dake jikin hannunshi na haggu take kallo. Fuskarta ya kalla kamun yabi inda idanuwanta suke kafe. "Haneef ya saimun....." Maganar dayai ta sa safiyya dago da kai ta kalle shi. "Zoben da kike kallo. Shi yaban gift dana cika shekara sha takwas" Kallon zoben ta sakeyi kamun a hankali ta furta. "Yana da kyau sosai" Zoben ya sake kallo yasa dayan dan yatsan shi yana murza shi. "Ban taba cirewa ba tunda na saka" Ta kula akwai kauna mai girman gaske tsakanin shi da haneef da lukman. Duk da ya fada mata basu hada jini da lukman ba. Zata iya ganin baya banbanta su da haneef. Kusan waje suke a zuciyarshi. Cikinshi yaji yayi kara alamar yunwar dayake ji. Hannunta ya ja zuwa cikinshi yana dakuna fuska. Dariya tayi jikinta da wani nauyi na daban. Sakin hannunta yayi yana mikewa. "Tashi mu siyo abinda zamuci. Mun huta kingani" "Daka barni kaje ka dawo" Tunda ta bude baki yake girgiza kai. "Tashi. Ina zan barki babu mai gadi babu komai. Tashi mana" Mikewa tayi dole suka fita tare ya kulle gidan. Bama suyi nisa ba yaga wani karamun bakery ya tsaya sukai siyayyarsu anan suka koma gida. Suna shiga yaji kaman kiran sallar magrib. Saurarawa yayi ledojin ya mikama safiyya yana fita harabar gidan da sauri. Kiran sallah ne aikuwa. Ciki ya koma yayo alwala ya fito falo ya sameta a zaune. "Taso ki kulle kofar. Karki bude in bakiji muryata ba" Kai ta daga masa da murmushi a fuskarta. Yanda yake mata bayanin zaka rantse yar shekara takwas ce ko kasa da haka zai bari cikin gidan. Itama alwala taje tayi. Falo ta dawo tai sallar anan dan kar fu.ad ya dawo yaita kwankwasa wa bataji ba. Nan tai zamanta tana danne danne waya. Ta shiga nan ta fito. Gani tai ya dade sosai bai dawo ba. Ganin karfe takwas harda kwata ya sata tashi tai sallar isha.i tana idarwa taji kwankwasa kofa. Da sauri taje ta bude. Fuskarshi a hade yace. "Haka nace fa in bakiji muryata ba karki bude" Dariya tadanyi. "Ai nasan babu wanda zai kwankwasa sai kai shisa" Sake bata fuska yayi hadi da fadin. "Still. Ki tambaya waye kamun ki bude" Ta amsa da "In shaa Allah. Kazo kaci abincin tun dazun kake kiran yunwa" Karasawa yai. Ta dauko ledojin ta ajiye su a gabanshi. Bude musu yai. Shawarma ya fara ci. "Kici sofi" Kai ta girgiza masa tana daukar burger. Abinda zata iya ci tun daga idanuwanta zata iya gane shi bama saita wahalar da harshenta ba. Dibowa yai da cokali. "Sai kin tasting fa. Ina kallon ki shekaranjiya ma...." Janye fuska tayi tana girgiza masa kai. "Bazan iya ci bane" "In baki dandana ba ya za.ayi ki gane ko da dadi ko babu" Hannunshi ta kama ta karbi cokalin. Dakyar ta hadiye tana wani yamutsa fuska daya bashi dariya. Sosai ya ci komai ya sha exotic. Yai hamdala ya na komawa kan kujera. Dakyar ta cinye burger din hannunta. Ruwa ta dauka ta bude tasha. Fita fu.ad yayi yai addu.a yasa ma gate dib mukulli. Sannan ya dawo cikin gidan ma yai addu.a ko ina tana kallonshi sannan ya sa mukulli ya kulle ya zaro shi ya karaso ya ajiye kan kujera. "Taso muje muyi wanka mu kwanta. Nagaji ko banyi bacci ba so nake inji ni a kwance" Binshi tai har bedroom din. Saida ya bude jakarshi ya dauki wata T-shirt marar nauyi da gajeran wando sannan ya shiga wanka. Bai wani dade ba ya fito sanye da kayan daya dauka. Kallo daya safiyya tai masa bata kara na biyu ba. Wata kunya ta lillibeta ga wani dokawa da zuciyarta ke mata. Wucewa tayi ta shiga wanka itama.  Ta fito yana zaune kan gado ya kalleta. "Rigar nan tayi girma. Ya zaki iya bacci a ciki. Ki dauko wani marar nauyi" Ita kanta tana jinjina kwanciya cikin rigar. Jakarta ta bude ta dauko atamfarta data zo da ita. Fu.ad ya lumshe idanuwanshi ya bude su. Tana bukatar abubuwa da yawa. Saukowa yayi. Ya bude jakarshi ya dauko mata wata riga loose ya mika mata. Karba tayi ta koma bandakin ta daura zaninta. Ta saka rigar da ya bata. Tsahonne kawai yazo mata jar wajen cinya. Amman rigar tadan kamata. Kunya sosai ta keji tun kamun ma ta firo daga bandakin. Dadi taji data fito hankalinshi nakan wayarshi. Da sauri ta samu waje kan gadon ta dayan gefen tahau. Shikam fu.ad text yaima pha.iza na list din abubuwan da zata kara cikin wanda safiyya ke bukata. Kafafuwanshi ya hawo da kan gadon. Wani shagwabe fuska yai kaman zai kuka. Dazun da suka siya zannuwan gado shaf ya manta da blanket. Safiyya ya kalla fuskarshi a shagwabe. "Babu abin lillibewa. Ko muje gida mu dauko" Kallonshi tai sosai. "Dare yayi fa" Sake shagwabe fuska yayi hadi da fadin. "Bana iya bacci inba lillibe kafafuwana ba" Sauke numfashi safiyya tayi. Mutane kala kala. "A kware zanin gadon mana. Saika lillibe dashi" Kai ya girgiza. "Inba shimfida ma haka bazan iya bacci akan gadon ba" Lumshe idanuwa safiyya tayi ta bude su kan fuskarshi da ya bi ya shagwabe cike da rikici. Saukowa tai daga kan gadon. "Bara in kwaro zanin gadon wani dakin in akwai" Kallo ya bita dashi harta fice. Yana tunanin gaskiya hada gida yafi komai wahala. Dawowa tai da zanin gado a hannunta ta mika masa. Ya karba yana yatsine fuska. "Wannan fa na shimfida ne sofi. Abin lillibewa nake so bashi ba" Kallon shi take. Rigimarshi na da yawa sosai. Yanzun take ganinta. "Kayi hakuri da wannan din iya yau kawai. Kawo kagani in linka maka ya kara kauri" Mika mata yayi. Ta karba ta gyara zanin gadon ta linka shi gida biyu. Inba rigima ma da kaurinshi sosai. Mika masa tayi. Maimakon ya karba saiya ja jiki ya kwanta yana fadin. "Ke kikace zaiyi. Saiki rufamun" Dariya ma ya bata. Lilliba mishi tai taja masa har zuwa ciki sannan ta zagaya ta kwanta gefe. Addu.a tayi ta tofa. Tana gyara kwanciya. Juyowa yai fuskarshi na kallon tata. Duk da da yar tazara a tsakaninsu. "Shine ni bakimun addu.ar ba sofi" Dariya ta sake yi. "Naga kayi kaima ai" Wani shagwabe fuska yayi. "Ni dai kimun. Kuma kin matsa can karshen gado saikin fada. Ki matso kaman zan cijeki" Shiru tai masa. Inda take dinma duk jikinta a sane yake da kusancin shi balle ta matsa. Kadan tadan kara jan jiki. Addu.a tayi tadan tofa mishi iskar. Son jinta yake kusa dashi kaman yay me. Ganin bata da niyyar matsowa ya sashi matsawa sosai gab da ita yana share yanda ta wabi rintse idanuwa. Peck mai taushi ya manna mata a goshi hadi da fadin. "Saida safe" Bata bude idanuwanta ba. Zuciyarta wani irin dokawa take. Tanaji ya kamo hannunta ya rike cikin nashi. A haka bacci ya dauke su su dukansu. * Tana idar da sallar asuba ta shiga bandaki tai wanka. Tunawa tai fu.ad yace karta kara wanki. Dan haka ta cire kayan jikinta ta linke su ta dauko wata doguwar riga light purple ta saka. Ta koma kan gado tai zamanta. Bata damu da jimawar fu.ad ba dan ya gaya mata zai motsa jiki koda taga ya dade bai dawo ba. Kiranshi taji a wayarta. Bata dauka ba dan yace daya zo zai kirata. Tashi tai ta fita ta bude masa gidan. Duk ya hada zufa. Yana wani maida numfashi yake kallonta ta masa kyau. Kanta daure da dankwalin rigar. Yana son ganin fuskartan nan fayau haka. "Sannu" Ta ce masa. Kai kawai ya iya daga mata yana wucewa ciki.  Kan kujera ya zauna yana kokarin daidaita numfashin shi saboda gudun dayai. Hannunshi yakai ya bayan kanshi ya taba. Runtse idanuwanshi yai yana cire hannunshi. Ciwon na mishi zafi har yanzun. Sai lokacin ma ya tuna da wasu su ado da abinda ya faru. Murmushi kawai yayi dan yagama rama abinda sukai mishi tunda ga safiyyar nan zaune a gabanshi. Saida bugun zuciyarshi ya koma dai dai tukunna ya mike ya tafi bedroom. Wanka yayi ya sakko kaya ya fito. Kallonshi safiyya take. Wandon jikinshi yaga ce a jiki kusan daga gwiwarshi har kwauri. Blue ne mai haske sai riga ja a jikinshi. Yayi kyau matuka waje ya samu ya zauna. Tunda ya tashi cikinshi yake ji wayam ga gudun dayai ya kara kona calories. Wata yunwa ke cinshi. So yake bakwai da rabi tayi su fita gabaki daya. Baima san makarantar daya kamata yakaita ba. Da yai tunanin yakaita FAAN inda su hussaina suke. Sai kuma ya fasa. Tunani yazo masa. Yakai ta crescent kawai inda pha.iza ta gama. Ya yarda da makarantar tana da kyau sosai. "Sofi dauko hijab dinki mu tafi. Sai mu ci wani abu a hanya ko?" Tashi tayi ta nufi daki. Cikinta a wani kulle. Tunanin komawa makaranta na mata dadi ta wani fannin kuma yana bata tsoro. Bata san ya zata tsinci kanta a makaranta ba. Gashi ko turanci bata ji. Sai dai ita bamai girman kai bace ta wannan fannin. Tunda ta dauko hijab dinta take ma kanta alkawarin zata tsaya sosai ta maida hankali kan karatunta. * A hanya yai musu takeaway na dankalin turawa da kwai da fresh milk. Ya samu waje yai parking suka ci. Sannan suka wuce. Tun daga gate din makarantar taji ta karaya. Duk kwarin gwiwar data fito dashi ya kara wargajewa da suka shiga cikin makarantar. Ga wani irin girma tana dashi. Kayan makarantar kansu abin kallo ne. Sai dalibai ko ina suna kai kawo. Daka gansu kasan yayan masu hannu da shuni ne. Tsaf dasu. Bata san lokacin da ta kama hannun fu.ad ta dumtse gam cikin nata ba. Yasan a tsorace take. Hannunta ya rike sosai cikin nashi suka wuce office din principal din. Saida suka samu wajen zama sannan ya saki hannun safiyya yana maida hankalinshi kan principal din. Safiyya na zaune tana ta zare idanuwa. Kanta a kasa tana jin yanda fu.ad din suke magana cikin harshen turanci. Bayanin komai yai masa. Da matakin data tsaya a karatu da kuma cewar bata jin turanci gashi bata da takardu ko daya sai dai ya siya mata na nan. Shawara principal din ta bashi cewar safiyya ta fara dafa jss1 fur fu.ad yace baisan wannan ba. Baya so ko kadan matarshi taji kaman an rainata. Kudi shi zai biya. Daga ss1 yake so ta fara. A samu malamar da zai biya ta dinga zuwa gida tana koya mata. Extra lesson komai da ake bukata dan a taimaka mata. Amman ba za.a nuna an raina karatunta ba. Shawara ce taba fu.ad yaki ji. Makaranta ce ta kudi. Kuma sune suke magana. Nan take akai masa lissafin komai daga kan kudin makaranta zuwa na uniform zuwa litattafai. Nan ya biya komai. Da sunce saiya je bank. Ya bada dubu daya yace su aiki wani yakai. Uniform aka duba kala biyu aka ba safiyya. Tasa wata malama ta rakata inda zata cire na jikinta ta gwada wa.annan. Kallo daya zakai mata kasan a tsorace take. Saida ta kalli idanuwan fu.ad yadan daga mata kai da cewar babu matsala sannan tabi matar. Kaman an aunata haka uniform din ya zauna mata. Ta sakko hijab din ta fito. Da kayan data cire a leda malamar ta sakko mata. Kallonta yake da murmushi a fuskarshi tayi kyau sosai. Yace a kara mata kala biyu uniform din. Ca sukai yabar safiyya sai karfe hudu ya dawo ya dauketa. Inyaso zasuyi magana kan wadda zata dinga zuwa gida tana koya mata. Gabansu ya kama hannun safiyya ya jata gefe. Kallonta yai sosai. "Nasan zaki iya sofi. Karki ji tsoron komai kina jina ko? Ga dubu daya kici wani abu. Ina wayarki" Mika masa tayi. Ya karba ya kashe yasa a aljihu ya bata dubun. "Anjima zanzo in dauke ki. Kiyi karatu sosai kinji" Kai kawai ta daga mishi tanajin kamar karya tafi yabarta. Hannu yasa yadan cupping fuskarta yace mata. "I love you" Murmushi tai ta sadda kanta kasa a kunyace kamin ta wuce ta koma inda malamar ke jiranta. Kara kallonta yai sannan ya fice daga office din. * Yana mota ya kira lukman yace masa yana school su hadu acan. Buk ya wuce saida ma yadan jira lukman din ya fito lecture karfe goma. Mota ya bude ya shiga. Kallon fu.ad din yake ya masa wani haske. "Ya naga kayi wani fresh?" Lukman ya tambaya. Dariya fu.ad yayi. "Bana son iskanci lukman. Sofi nakai makaranta shine na biyo ta nan" Wani murmushi murmushi ne fuskar lukman. "Did you?....." Naushi fu.ad yakai masa a kafada fuskarshi nayin wani ja. Girgiza kai fu.ad yake yi. "Inalillahi lukman. Kai bakinka bashi da tsarki. Idan nayi ne ma fada maka zan......" Dariya sosai lukman yai ganin yanda fuskar fu.ad din ke kara yin ja. "Ashe akwai abinda kake jima kunya?" Dariya shima yakeyi. "You are gross lukman" Tashin motar yayi yana juyata. Lukman dake dariya yace. "Kai ina da lectures fa karfe sha dayan nan" Ai kamar ma fu.ad baiji shi ba ya ci gaba da jan motar. "Da gaske nake maka" "You are skipping tunda ba test bane. Yawo zamu" Dariya kawai lukman yayi. Fu.ad rikici. *#TeamAS* [4/4, 6:00 PM] Fatima saleh: *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ      25 Karfe uku da rabi a crescent tai mishi. Sai da ya fara shiga sukai magana da matar da zata dinga zuwa gida tana koya ma safiyya karatu. Ba wata babba bace ba can. Yoruba ce sai dai taji hausa kaman ba gobe. Duka ba zata shige shekaru ashirin da hudu ba. Magana sukai ta fahimta. Fu.ad yai mata kwatancen gidansu. Kusan unguwarsu daya ma. Layi uku ne tsakaninsu. Suna gamawa ya fita waje ya tsaya jikin motarshi yana jiran safiyya ta fito. Sai ware idanuwa yake yaga ta inda zata bullo. Hango ta yai rungume da litattafai. Wani murmushi ya kwace masa. Hango shi tai itama lokaci daya yaga murmushi ya bayyana a fuskarta. Jinshi yake wani iri. Kamar da duk takun da take ta karaso wajenshi har iskar wajen canzawa takeyi. Kaman ya ruga ya rungumeta. Tana karasowa tai masa kyautar wani murmushi daya taba mishi zuciya. "Ina wuni" "Sofi yan makaranta. Sannu da kokari" Ya amsa. Dariya tayi. Ya bude motar ta shiga. Ya zagaya shima ya shiga yaja motar. "Ya makarantar? Badai wata matsala ko?" Girgiza masa kai tayi. "Dukkansu suna da kirki sosai. Wasu ma sun karbi litattafaina zasu tayani rubutun da aka wuce ni" Yaji dadin hakan. Yanda suka karbar masa safiyya. "Babu wanda yai miki wulakanci dai ko? Daga daliban zuwa malamai" Kai ta girgiza masa. Dan ita kanta ta yi mamakin yanda sukai mata karamci. Da sun fara mata turanci. A kunyace tace musu bata ji. Mamaki kawai taga sunyi maimakon raini. Da alama dukkansu yan manyan gida ne. Dan haka ta amsa fu.ad da. "Haka ma sukace zasu taimakamun. Gaskiya suna da karamci" Jinjina kai yayi. Dan Allah ne kadai zai rabashi da duk wanda ya nemi ya raina masa safiyya ko ya wulakantata. Suna isa gida tai mamakin ganin an bude musu gate. Kallon fu.ad tai yagane tambayarta tun kamun ta bude baki. "Dazun yazo. An samo mana mai aiki ma" Tadan ji dadi. Ko ba komai taji motsin mutum banda su cikin gidan. Tayata daukar litattafan yayi yana fadin. "Anjima sai muje a siyo jakar makaranta" Tare suka shiga ciki. Tun daga bakin kofa ya cire takalmin da socks din daya siya mata a makarantar. Kauda su tayi waje daya. Sannan ta shiga ciki. Fu.ad yabi bayanta. Kan kujera ya ajiye litattafan nata. Zuciyarta taji ta wani doka da su inna suka fado mata. Tana tuna yanda baba yaso ta ci gaba da makaranta data nuna tana so sai dai bashida karfin. Zata so ace sun ganta a yanzun. Sunga yanda take makaranta data tabbatar tana da tsada sosai. Tasan zasu ji dadi suga ta samu ci gaba a rayuwa. Ita tana nan bata san halin da suke ciki ba. Bata san wasu hawaye sun zubo mata ba saboda wani nauyi da zuciyarta tayi. Yaga tunani take. Hawayen dayaga ni a fuskarta yasa shi tashi da sauri ya koma kan kujerar da take. Hannuwanshi yasa ya tallabo kafadunta. Jinshi da duminshi ya sa taji ta karasa karaya. Cikin kuka tace masa. "Ka kalleni. Cikin kwana hudu rayuwata ta sauya. Bansan halin da iyayena suke ciki ba.......bansan..... Kawai......" Riketa yai gam. Kukanta na taba mishi zuciya. Ji yake yana wani ci masa rai. "Shhhhh" Luf tai a jikinshi tana sauke ajiyar zuciya. Riketa yayi yasa hannunshi daya yana goge mata fuska. "Laifi na ne sofi. Ki dora shi a kaina. Ni na shiga rayuwarki na hargitsa komai. Kila da banganki sanda naganki ba da ban jefa ki cikin halin nan ba. Da....." Da sauri tasa hannu tasa hannu ta rufe masa baki tana girgiza masa kai idanuwanta cike da hawaye. Karantar maganganunshi take tana jin wani irin yanayi. Muryarta kaman ba tata ba tace. "Da baka ganni a sanda kaganni ba daya na nufin ban sanka ba......." Lumshe idanuwanshi yayi yana sake riketa gam. Dan duk kalaman dayai zuciyarshi karyatawa take. Sumbatar goshinta yai yana jin kaman ya mayar da ita cikin cikinshi dan kar wata kaddara tazo ta ko da gifta ta tsakaninsu ne balle kuma azo maganar ta rabasu. Hannu yakai kan cikinta ya dafa. "Me kika sakamun a cikinki?" Dariya ta danyi tana dora hannunta kan nashi saboda wasu abubuwa da taji suna mata yawo a cikin da tasan suna da alaka da hannunshi. Mamakin yanda take jin kaman shekara hudu sukai ba kwana hudu ba. Wani irin sabo take jin sunyi da fu.ad da ta tabbata ba aikinta bane na zuciyarta ne. Yanda ya samu karbuwa a yanzun take jin numfashi daidaitacce ma da wahala ta iya yinshi in baya kusa mamaki yake bata. Bata san sanda ta dumtse hannunshi gam ba. Hakan yasa shi saurin ce mata. "Sofi menene?" Cikin idanuwanshi take kallo. Kalarsu take karema kallo yau. Ruwan kasar nan masu wani ratsin haske haske. Wani abu ke fisgarta daya sa take son manta yanda ake numfashi. Shima kallon nata idanuwan yake. Yana karantar rokon sa ke cikinsu. "Ina nan sofi. Muna tare. Ba nace miki ni da ke ba" Kai ta daga mishi. Tana sauke idanuwanta zuwa kan fuskarshi. "Me kika ci?" Fuskarta takai hannu tana gogewa hadi da fadin. "Bansan sunan shi ba. A makaranta dai muka siya da su khadija" Dariya yayi. "Kice har kinyi kawaye ma" Itama dariyar tayi. Tana saka hannu a aljihun wandonta. Dari shiddan daya rage ta dauko masa. "Ga canjin. Na kashe sosai dai. Bansan da tsada ba" Ware idanuwa yai yana dariyar mamaki. Dari hudu ta taba ciki. Ganin ya tsaya kallonta ya sata jin duk babu dadi. Tasan ta kashe masa kudi sosai kuma har ranta bata san abinda suka siya da tsada ba da bata fara ba. Muryarshi taji yana fadin. "Sofi Allah ya shiryamun ke" Dariya ya bata sosai sosai. "Amin. Nima ana mikomun canji sai da gabana ya fadi" Wannan karon shi yai dariya. "Kinga ke din nan ko. Daga yanzun in na baki kudin makaranta. Duka ne na baki. In kin kashe fine. In baki kashe ba ki rike canjin" Rike baki tayi. Bata san wacce kalar godiya zatai masa ba. Sai dai addu.a. "Allah ya baka aljanna" Da sauri ya amsa da "Amin. Tare dake muyi zamanmu" Mikewa yai yana riko hannunta. "Kin batamun fuskarki da hawaye. Tashi muje a wanke" Wata yar kunya taji ta rufe ta. Tai masa murmushin nan da yake masa wani abu a zuciya da bashi da kalaman dora shi akai. Binshi tai ya rakata har bedroom din ta wanke fuskarta. Tayi la.asar tun a makaranta. Kallonshi tayi. "Barin watsa ruwa. An bamu aikin gida ban iya ba saika dubamun" Wani daga mata girarshi yai duk biyun yana ciza lebe. Sannan ya fice daga bandakin yana barin zuciyarta da wakar yanda kyanshi yake. * Falo ya koma ya zauna abinshi. Ji yai ana kwankwasa kofa. Ya tashi yaje ya bude. Pha.iza ce an ci uban gayu. Sallama tai masa hadi da fadin. "Ina wuni" Wucewa tai cikin falon. Batama jira amsar shi ba. Ya maida kofar ya kulle. Ya dawo ya zauna. Sai lokacin ya kula da ledar dake hannunta. "Momma tace in kawo muku abinci. Sai kuma muje wajen tela da matarka" Yanda muryarta tayi a kalmar matarka ya mishi wani iri. "Sunanta safiyya. Thank you da kika gane matata ce. In ba zaki tayani sonta ba. Kibar abin a ranki" Sauke ajiyar zuciya pha.iza tayi a sanyaye tace. "Kayi hakuri. Kawai zuciyata ta kasa nutsuwa da ita ne. I have this hunch..... " Katse ta yai da fadin. "Spare me mana. Na dauka kin girmi wannan pha.iza" Dan daga kafada tayi. "Fine. Allah ya baku zama na lafiya" Murmushi yayi. Ya amsa da. "Amin" Yafi so dukansu su tayashi son sofi. Kaman taji ambatonta dayai a zuciya ta fito daga daki. Jikinta sanye da doguwar riga ta dauro dankwalin. Dan tsayawa tai ganin pha.iza. Fuskar pha.iza ba yabo ba fallasa tace. "Ina wuni" A kunyace safiyya tadan karaso ta zauna gefen fu.ad hadi da fadin. "Ina wuni. Ya su mama" "Suna lafiya. Tana gaishe ku. Inajin bama sai munje dake ba. Inada tape kawai sai in auna ki" Hakan ma yafi ma safiyya dadi. Tape din pha.iza ta dauko da yar takarda da biro. Ta auna safiyya ta rubuta. Tana gamawa ta kalle su tace. "Ni kam dai na wuce. Sai anjimanku" A hankali safiyya tace. "Sai anjima. Mungode" Yanda ta yamutsa fuska sai tai mata yanayi da fu.ad sosai sosai. Irin abu daya hancinsu yake yi. "Bro kaji ta. Wai kungode" Dariya fu.ad yayi ya dora da. "Pha.iza ki kawo mata sauran kayan da mukai magana fa" Dan dukan goshinta tayi. "Kaganni ko. Suna mota fa. Barin dauko" Fita tai daga dakin. Batafi minti biyar ba ta dawo da ledoji har hudu ta ajiye musu tsakiyar falon tana juyawa da fadin. "Na wuce....." Daukar ledojin fu.ad yayi ya mika ma safiyya. Ta bude su. Daya kayan baccine sai under wears. Da sauri ta rufe dan tunanin fu.ad yagansu kawai yasata jin kunya. Dayan kuma takalma ne. Ta dauko guda daya ta gwada. Kaman pha.iza ta auna kafarta sun zauna cif. "Sun miki kyau" Fu.ad ya fadi yana kallon yar kafarta da ta burge shi. Kallon shi tayi sosai. "Nagode. Nagode sosai....." "Shhhhhh" Ya fadi yana mata murmushi. Shi ya tayata suka dauki kayan zuwa bedroom din daya soma kira nata. Ya bude wardrobe ya zuba mata kayan ciki. Sannan suka dawo falo. Assignment din english din datai masa magana ta dauko. Yai mamaki sosai ganin rubunta. Ko da yake ba wai a karatu bane abun. Iya rubutu baiwa ce. Ko shi baida handwriting me kyau haka. Wannan sai su haneef. Kaman ya sace lokacin da suke makaranta. Bayani yake mata yaga dai ba iya yi zatai ba. Dole komai sai a hankali. Rubuta mata answers din ya fara yi. Yayi layi biyu yaji tace. "Kai kai kai" Shi kanshi rubutunshi ya kalla ya kalli nata. Saiya kwashe da dariya. Ya manta when last yai rubutu inba a system ba. Dakuna fuska tayi. Alamar rubutun bai mata ba. Idanuwanshi yasa cikin nata yana mata wani cute eyes. "Allah saina rubuta." Dariya tayi. "Kamun a wata takarda sai in kwafa" Dauke littafin yai yana make kafada. "Naqi. A ciki nake sonyi" "In yaga rubutun ba iri daya bafa? Saika jamun bulala" Zaro idanuwa yai fuskarshi nayi wani serious lokaci daya. "Na fada musu matar aure ce ke. Zamu hau bene mu fado da duk wanda ya tabamun jikinki" Dariya kawai tayi. "Nikam kabani littafina" Daga hannunshi yai sama da littafin yana girgiza mata kai. "Nasani ai. Rubutuna bashida kyau ko? A haka zan miki. In ance na waye kice na mijinki ne" Dariya take sosai. Hakan na mishi dadi. Mikewa tai kan gwiwoyinta tana kokarin kai hannu ta kamo nashi dake rike da littafin. "Kaga kana dakuna mun ko?" Dariya yake mata. Sosai ta mika hannunta ta kamo nashi ya janye. Jikinshi ta fada. Binta yaida kallo. Itama kallonshi take sosai. A hankali ya sauke hannunshi idanuwanshi na cikin nata. Har wata iska yake ji shuuu mai wani irin nutsuwa. A hankali yake rankwafowa yana kai fuskarshi dai dai tata. Kusan numfashi daya suke shaka ita dashi. Kara matsawa yake sosai yana jin yanda numfashinta ke fita da sauri. Kwankwasa kofar akai. Ya lumshe idanuwanshi. Da sauri safiyya ta tashi daga jikinshi tana wani maida numfashi. "Fuck....." Ya fadi da alamar kowaye ya bata musu yanayi. Mikewa yai da irritation a muryarshi yana fadin. "Waye?" "Ni ce" Aka fadi. Bai gane muryar ba. Dan haka ya karasa kawai ya bude kofar. Wata mata ce mai matsakaicin shekaru. Kare ma shigarta kallo yake. "Lafiya?" Ya bukata muryarshi a dakile. Cikin taushin murya tace. "Indo ce. Malam isa ya turoni" So yake ya tuna waye ma malam isa? Ganin kamar bai gane ba yasa sata fadin. "Wadda zatai muku aiki ce" Sake tamke fuska fu.ad yai yana fadin. "Oh. Shigo" Matsa mata yai. Ta rabashi ta wuce. Da fara.a safiyya ta tarbeta. "Ina wuni" Ta gaishe da ita. Wani dakuna fuska taga fu.ad yayi. A kiyasce matar zatai shekara talatin. Kasa ta zauna. Safiyya tace mata. "ki hau sama mana" Dan murmushi tayi. "Nan ma yayi" Shiru suka danyi kamun fu.ad yace mata. "Bawani aiki bane mai yawa. Nasan ya baki kudin aikinki na wata biyu. Shara ce. Sai duk aikin dai da take so. Zaki iya dafa abincin da zakuci da maigadi. Yanda kika ga zaifi miki. In kwana zaki dinga yi. Akwai BQ in kuma gida zaki dinga komawa dai" Kallon fu.ad safiyya take. Yanda ya hade fuska kaman bai taba dariya ba. Yanayin muryarshi kaman ranar farko data fara ganinshi. Sai bataji dadin yanda yaima matar nan magana babu wani tausasawa ba. "Ba kusa nake ba. Cikin dawanau nake da zama. Zan dinga kwana anan din. Sai dai zan koma duk ranar juma.a in dawo ran asabar in Allah ya yarda" Wani kallo fu.ad yai mata. Yace "Wazai aikin gidan na ranar juma.a din kenan?" Sake saukar da murya tayi. "Saina gama tukunna. Ran asabar din in shaa Allah da wuri zan dawo" Ganin yana girgiza kai yasa safiyya fadin. "Allah ya kaimu. Babu komai ai. Koni sai inyi" Mikewa fu.ad yayi. Ya dauki mukullan dake gefenshi ya zari wasu ciki ya ajiye kan table din tsakiyar dakin yana fadin. "Ga mukullan inda zaki dinga kwana. Yana nan baya dakin zagaya" Baiko tsaya dubanta ba ya karasa inda safiyya take ya kama hannunta ya mikar da ita yana janta zuwa bedroom din. Suna shiga ya tura kofar ya saki hannunta yana mayar da nashi kan kugunshi. "Idan ina magana da masu aikin nan ki daina saka baki. Kudi na biyata bawai kyauta nace tazo ba. Saboda me zakiyi mata aikinta?" Yanayin shi ma tsoro yabata. Ya wani tamke fuska. A darare tace. "Kayi hakuri" Lumshe idanuwanshi yai yasa hannu yana murza goshi. Kamota yayi ya rungume a jikinshi. Bayason tsoronshi daya gani cikin idanuwanta. Kaman yanda bayason kowa ya raina mishi ita. **** *Bayan sati biyu* Komai na tafiyar musu da ci gaba. Da wata irin shakuwa mai karfi da take kara shiga tsakaninsu. Dan safiyya ji take bata da sauran kowa a wannan sabuwar duniyar da bata san gabas dinta ba sai fu.ad. Cikin satin farko kwana uku ta jera kullum ta dawo daga makaranta sai tayi kuka. Amman yanzun ta hakura. A duk rana da kewar su inna take tashi da ita kuma take kwana. Saidai a hankali take sabawa da ita. Ranar makaranta karfe biyar anty laurat ke zuwa gida ta koyama safiyya karatu. A sati biyun nan sun fara sabawa da ita sosai. Safiyya ta fara sakewa da ita. Haka ma mama indo kamar yanda take kiranta. Tare suke share sharensu in fu.ad baya nan. Mama indo ta dafa musu abinci. Ita ta ke koyama safiyya amfani da kayan kitchen din. Dan tayi aiki gidajen masu kudi bayan rasuwar mijinta yabarta da yara har shidda da suke hannunta. Fu.ad bayaci. Wai kazanta saidai ya siyo musu abincina waje. Itama safiyyar in yana gida bata isa taci ba. Tana gudun fadan shi. Bata kuma son ace gata yana fita waje siye abinci. Ta masa magana yakaita inda zata koyi kalaluwan girkin da yake so yace aikin zai mata yaea ba yanzun ba tukunna. A makaranta kuwa suna gaisawa da duk yan ajin. Haka mazan suna ganin girmanta da aka ce musu tana da aure. Zasu gaisa a mutunce. A natan kuwa khadija da aisha ne suka zama kaman kawayenta. Suna kokarin koya mata karatun turanci da kuma gane yaren. **** Zaune yake dakin lukman. Kallo daya zakai ma fuskarshi kasan yana cikin bacin rai. "Ka share kawai. Zai sakko with time" Cewar lukman. Sake bata rai fu.ad yai hadi da fadin. "Haba lukman? Nan da yaushe. Kullum fa saina kira abbah a waya baya dagawa. Na dauka inya ganni ido da ido yau zai hakura. Amman ina gaishe dashi ko kallo na baiyi ba" Jinjina kai lukman yai. "To ita kuma safiyya tace me? Kai kullum saika ga momma da su pha.iza." Tauna maganar lukman yai. Ya nisa yace. "hakane with time. Itama in shaa Allah zan shirya ta da nata family din tunda ni ne silar bata su" "Ko kaifa. Ashe ka fara hankali" Dariya fu.ad yayi kamun yace. "Jibi fa zan tafi. Ni banma san ta inda zan gaya ma sofi ba" Fito da idanuwa lukman yayi. "Wai bata sani jibi zaka tafi ba?" Sauke numfashi fu.ad yayi. "bama tasan zan tafi dinba at all. Maganar bata taba hadamu ba" Kallon shi lukman yake. "Aikam baka kyauta ba. Yanzun tafiyar zatai mata wani iri" Langabe kai fu.ad yayi. "Aiba ita kadai ba" Harararshi lukman yayi. "Dilla kauce daga nan. Abin ma haushi" Dariya fu.ad yayi ya tabare fuska hadi da fadin. "Em gonna miss her" Rike hanci lukman yayi. "You are disgusting fu.ad" Dariya sukai gaba dayansu kamin fu.ad ya mike. "Barin koma wajen matata. Zama dakin gwauro yana mun somehow" Pillow lukman ya dauka ya jefa mishi. Ya kauce ya fice daga dakin yana dariya. ** Tunda ya koma gida ya samu safiyya da anty laurat zaune a falo sun baje litattafai. Sannu da zuwan anty laurat ma datai mishi dakai ya amsa ya shige cikin bedroom. Kallon safiyya tayi. "Ki je ko yana bukatar wani abu" A iya sanin halin fu.ad da tayi yasa ta girgiza kai. "Idan yana son wani abun zai kirani" Ta amsa tana karasa rubuta abinda takeyi. Kallonta anty laurat tayi. "Look at you. Oya tashi kije. Ko baya bukatar wani abin ki masa sannu da zuwa properly" A kunyace ta mike ta nufi bedroom din. Yana zaune gefen gado yana danna waya safiyya ta shiga da sallama. Wani numfashi ya sauke. Atamfar dakw jikinta ta karbeta. Ga dinki ya zauna mata cif. Wani sonta yake ji yana yawata masa. Hannunshi ya mika mata data karasa. Karasawa tai tasa hannunta cikin nashi tana zama. A tabare yace "Ki sallame ta sofi. Ina bukatar ki a kusa dani" Murmushin nan ya samu mai cike da kunya. Bata ce komai ba ta mike ta fita falo. Murmushi tai tayi batasan ta yanda zata ce ma anty laurat ta tafi ba tunda yau weekend ne. In tazo karfe hudun nan sai magrib. Suna da sauran mintina talatin kamun lokacin tafiyarta yayi. Kallonta anty laurat tayi hadi da yin dan murmushi. "Sai Allah ya kaimu gobe. Ki duba abinda mukai yau" A kunyace tace. "Allah ya kaimu. Nagode sosai" Har bakin kofa ta rakata ta kulle gidan sannan ta koma. Yana zaune inda tabarshi. Agogon wayarshi ya duba. Ya mike tsaye ya taka zuwa inda take. Hannuwan shi yasa kan kafadunta ya jata zuwa jikinshi. Rungumeta yai yana dan rocking dinsu. Sunkai mintina biyar a haka. Baisan yanda zai fara gaya mata zai koma Europe ba. Sai yai sati shidda inya koma kamun ya samu yazo yai kwana biyu. Da ace waje daya zai zauna inya je ba abinda zai hana yaki tafiya da ita. Dakyar ya iya janye jikinshi daga nata hadi da fadin. "Bara inyi alwala...." Kai kawai ta iya daga mishi. Ta karasa gefen gadon ta zauna. Alwala yayi ya fito. Ya tafi masallaci. Tasan ba dawowa zaiyi ba sai yayi isha.i. Dan haka ta shiga bandaki tayo alwalar itama ta fito tai sallah. * Sanda ya dawo masallaci. Mama indo ta shigo tai musu saida safe. Ya kulle nasu side din. Suka ci abincin daya siyo. Dakinshi ya wuce can yai wanka. Itama tayi. Rigar bacci ta saka ta daura dankwali. Taji dadin yanda pha.iza ta samo mata wadatacciya. Duk da haka har yanzun kunya take ji fu.ad na kallonta ciki. * Suna kwance taji ya karasa hade sauran wajen dake tsakaninsu. Sannan yaja blanket din ya gyara musu rufa. Hannu daya ya dora kan fuskarta yana kare mata kallo cikin wutar dakin da bata da hasken kirki. "Sofi bansan ta ina zan fara ba" Murmushi tai mishi. A sanyaye saboda yanda kallon dake mata da kusancinsu ke kashe mata jiki tace. "Ka fara ko ta ina" Numfashi ya sauke. "Kin tuna nace miki ball nake ko?" Ta daga mishi kai alamar ta tuna. Dan bata manta komai da yake fada nata game dashi ba. "Tam kwanakin nan da kikaga nayi. Wani dan hutu ne na samu. Yanzun kuma zan koma" Hannunta ta dora kan nashi dake fuskarta. Dan bataga abin kasa bayani a maganarshi ba. Tunda ya fara ta karanci damuwa a muryarshi. "Allah yasa a koma lafiya ya kuma bada sa.a" Yasan bata gane ba. "Amin....." Ya rasa ta yanda zai gaya mata. Shi kanshi harya soma kewarta tun kamun ya tafin. Muryarshi can kasa yace. "Ba anan kasar ba. Tafiya zan jibi. Sai nan da sati shidda zan dawo......." Mikewa zaune tayi ba shiri. Lokaci daya idanuwanta suka ciko da hawaye. Shima zaune ya mike yana fadin. "Haba sofi. Zamuyi waya kullum zan kiraki. Kuma......." Kuka tasa. Kuka sosai hawaye wani nabin wani. Tafiya zai yabarta har sati shidda. Kamo ta yai yana lallashi cikin kuka tace. "Wa zai kaini makaranta?" Kaman hakan kawai ya isa dalilin dazai sa ya fasa tafiya. "Zan samo driver. Kuma zanma laurat magana kullum ta biyo ta nan a kaiku tare. A dauko ku tare" Kukan ta ci gaba dayi taba girgiza masa kai alamar bata yarda ba. Sake riketa yai jikinshi yana jin yanda ta wani kankame shi. "Bana so ka tafi" Lumshe idanuwanshi yai. Shi kanshi da hawayen zasu zubo daya danji saukin abinda yake ji. Kamo fuskarta yai. Daya bayan daya ya sumbaci idanuwanta. Da duk fuskarta. Hannu yasa ya goge mata hawayen. Kallonta yake sosai. Kamun ya hada bakinshi da nata. Yanajin yanda ta rike jikinta kamun ta sake a hankali. Saboda shine rana ta farko da bakinshi ya hadu da nata. Ya rasa yanda zai mata ne kawai. Sai da ya tabbatar bata da wani karfin kara mishi damuwa tukunna. Janta yai kan kirjinshi ya kwantar da ita. A hankali cikin muryar da kunnenta ne kadai ke ji yake kwantar mata da hankali da kalamai masu taushi. A haka yai musu addu.a yana lallabata har bacci ya dauke su. *#TeamAS* [4/4, 6:00 PM] Fatima saleh: *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ      26 *I don't know what is more sad. That i am in love with a fictional character or that i am in love with a fictional character who is the creation of my own imagination......* Hannunta take kokarin kwacewa daga cikin na fu.ad amman gam ya riketa. Fuskarta cike da kunya tace mishi. "Mama indo fa na kitchen" Daga mata gira yai dake nuna cewar sai me?  Shi bai damu ba. Dayan hannunta tasa ta cire nashi daga nata. Wani shagwabe fuska yayi. "Gobe warhaka saikin nemi hannuwana kin rasa sofi" Da sauri ta kamo hannuwanshi duka biyun ta rike. Har ranta take jin tafiyar nan. Idanuwanta da suka ciko da hawaye ta sauke masa. Da sauri yace. "Yi hakuri. Na daina" "Ina sane da tafiyar nan. Ba saika tunamun ba...." Hannunshi ya zame daga nata ya kama kunnuwanshi duka biyun. "Afuwan. Na daina amman kar hawayen nan ya zubo. Bana son ganinsu" Murmushin karfin hali tai masa. Ta dai kasa cewa komai. Dan tanayin magana kuka zatai. Dab da ita sosai ya karasa. Ya tallabi fuskarta cikin hannuwanshi yana kallon cikin idanuwanta. "Ki kira laurat. Ba lesson yau" Ware idanuwanta tayi cikin nashi tana son ce mishi bata yarda ba. Goshin shi ya hada da nata. Kusan lips dinshi kan nata suke. Wani miyau da bata san da shi ba cikin bakinta ta hadiye. Yana ganin yanda idanuwanta ke yawata wa kan fuskarshi. Hucin numfashinta na karuwa kan fuskarshi. Kan labbanta yai magana da fadin. "Yau ba lesson. Lokacina ne duk yau. Kinji?" Kai ta daga masa gwiwarta nayin sanyi. Wata sumba mai taushi ya manna mata a lips sannan ya saki fuskarta. Wannan karin shi yake maida numfashi yana kokarin maida yanayin dake son kwace masa ciki. "Bara inyo alwala inje la.asar. ki shirya kamun in dawo mu fita" "Nima barin yi sallar. Ina zamuje?" Yatsun shi yai running kan fuskarta. Yana bin inda duk suka taba da kallo kamun yai kasa da idanuwanshi kan labbanta ya tsayar dasu nan. "Sirri ne." Idanshi ya mayar cikin nata ya dora da. "You are gonna be dah' death of me sofi" Fuskarta tadan daquna tana maimaita kalamanshi cikin kanta tana so ta gane ma.anarsu. Wucewa yayi yabarta nan tsaye. Numfashi ta sauke wani sonshi na shigarta. Karasawa tai ta dauki wayarta kan kujera ta kira laurat. Bayani tai mata cewar zasu fita da fu.ad insun dawo da wuri zata kirata. Bedroom ta shiga. Sai da ta watso ruwa tukunna tai alwala ta fito tayi sallar la.asar. Mai ta shafa. Ta murza hoda. Kallon fuskarta take a mudubi. Yanda tai wani haske tai bulbul. Kaman ba ita ba. Mikewa tai kamun tunani ya haye mata. Ta dauko wata doguwar riga ta atamfa ta saka. Dinki ya zauna mata. Simple ta daura dankwalinta ta ta dauko mayafi kalar kayan ta ajiye. Sanda mamansu fu.ad ta aiko mata da kayayyakin kusan kowanne da mayafinshi da takalmi da jaka. Kayan kadai tai amfani dasu. Tunda babu inda take zuwa. Koda take jajen mai kitso wa laurat catai ta kwance ta wanke zatai mata. Haka kuwa akai. Banda makaranta. Ta kwana biyu bata je ko ina ba. Sallamar fu.ad taji yana turo kofar. Ta amsa hadi da fadin. "Sannu da dawowa" Kallonta yake yi. A hankali ya taka zuwa inda take tsaye. Tun daga kafafuwanta ya soma yawo da idanuwanshi har fuskarta. Wani numfashi yake ja yana fitarwa ta bakinshi. "Kinyi kyau. Kinyi kyau sosai" Murmushi tai mishi. Ta dauki mayafinta tana fadin. "Muje ko?" Fito da idanuwa yai yana wani tura baki gaba. "Um um. Kinga kyan da kikai? Nima saina sake kaya" Yanda yakanyi mata tai mishi. Tasa hannuwa ta tallabi fuskarshi tana daga kafafuwa saboda ya mata tsayi. Dariya ya dinga yi mata. Hannunshi ya dora kan kugunta ya dan yi sama da ita. Har mamakin yanda yake dagata takeyi. Ko numfashi bai mayar ba. Saikace dagata din wani abune mai sauki. "uhum sofi....." Yace yana kallonta. Makalo masa wuya tai ta na boye kanta cikin kafadarshi saboda kunyar da ta kamata. Cikin kunne ta rada mishi. "Kayi kyau sosai. Ko baka sake kaya ba" Dariya yai yana sake gyarata a jikinshi. Muryarshi can kasa yace "Indai kince na miki a haka. Zaka iya fita dani. Fine muje" Kaji shi fa. Wai in zata iya fita dashi ma yake fadi. "Kai baka ji kunyar jerawa da yar karkara ba.......wayyoo" Ta karasa saboda cizon dayai mata gefen kafada. Sauketa yayi. Fuskarshi babu alamar wasa yace "Waya fada miki bazan yi rigima da duk wanda ya rainamun ke ba? Ko da kuwa ke dince da kanki" Kanta ta sadda kasa hadi da fadin. "Na daina..." Hannu yasa ya dago mata da haba. "Kar in sake ji. Ke matar fu.ad ce. Kin wuce raini a ko ina" Kai ta daga mishi. Fuskarshi yakai ya sumbace ta sannan yace. "Good. Muje" Mayafinta ta dauko tana maimaita yanda ya fadi 'good' cikin kanta. Saboda taji kalmar tafi a kirga a makaranta. Amman yanayin yanda ya lankwasa ta ya mata dadi. Maimaitawa take tayi. Bakinta dake motsi ya ke kallo. Da mamaki yace "Magana kike" Da sauri ta girgiza masa kai tana yafa mayafinta. "Sofi.....?" Ya kirata yana jan sunan. Murmushi tai a kunyace sannan tace. "Kalmar daka fada nake maimaitawa saboda tamun dadi" Dariya yai kawai a ranshi yake fadin yama za.ai da duk lokuttan da suke wucewa son sofi bazai karu a zuciyarshi ba. "She is fucking amazing" **** Suna mota ya kira wayar anty fatima ya fada mata gasu nan hanyar gidanta. Shi kanshi ya manta rabonshinda gidan. Zaima iya kirga zuwanshi gidan anty fatima. Kome zai siyo saida ya bama momma a aika mata dashi. Saida sukai parking cikin gidan suka fito sannan safiyya tace mishi. "Tsoro nake ji" Dariya yai mata. "Karki damu. Anty fatima bata da matsala" Shiru tai tabi bayanshi. Da sallama suka shiga gidan. Aikam safiyya taga bata da matsala dan da fara.a ta tarbesu. Taja safiyya suka zauna. Fu.ad ta kalla tace "Ina nan ai kule dakai wallahi. Tunda momma ta fadamun shisa kaga ban kira ba" Dariya fu.ad yayi. Hakuri take so ya bata bai kawo mata safiyya sun gaida ba. Ta kuma san saidai tagaji da mitarta dan ba samu zatayi ba. Gaisawa sukai sosai da safiyya danma tanajin kunya. Ko lemo da soyayyen nama da meat pie din data kawo musu kasa ci tai. Mikewa fu.ad yayi yaba fadin. "Anty wucewa zamuyi" Bude baki tai sannan tace. "Kai fu.ad kasa Allah a ranka. Tun yanzun?" Dariya ma ta bashi. "Ba kun gaisa ba?" Mikewa anty fatima tayi. Da ido ta nuna mishi alamar tana son magana dashi in private. Dakuna fuska yayi. Bai dai musa mata ba yabi bayanta zuwa wani dan corridor. Ba wani bata lokaci anty fatima tace. "Bazan judging kome ya faru daku ba fu.ad saboda nasan kaddara kowa da tashi. Allah kuma ya rigada ya rubuta taku tun kamun a haife ku" Wani juya idanuwa fu.ad yai hadi da fadin. "Sai nai kewar islamiya...." Hararshi tayi dan tasan rainin wayau ne yasa shi fadar haka. Ganin tai shiru tana kallonshi ya sa shi fadin. "Ina ji. Just cut it short" "Hmm. Kawai ka rike ta amana. Dan Allah karkai mata butulci" Hade hannyenshi yai waje daya kawai. Sannan ya juya ya wuce. Ya gaji da jin kalaman nan da kowa ke fada mishi. Safiyya ya samu zaune inda suka barta yace mata. "Taso mu tafi" Mikewa tai. Anty fatima ta karaso tana fadin. "Ku dan jira inzo" Lumshe idanuwa fu.ad yai alamar jiran da zasuyi an takura shi. Bata fi mintina sha biyar ba ta fito da leda a hannunta ta mikama safiyya hadi da fadin. "Bansan zaku zo ba" Hannu biyu tasa ta karba tai mata godiya sannan suka tafi. Suna shiga mota fu.ad yace "Anty fatima tafi sonki dani. Bata taba bani komai ba" Dariya ya bata. "Ai mu biyu taba" Turo baki yai yace. "Oh-OH  banji tace dani ba" Ya tashi motar suna fita daga gidan. A hanya tace "Nagode." Da mamaki yace "Godiyar me fa?" "Yanda kake kokarin yan uwanka su karbeni" Shiru yai dan baisan me zaice mata ba. Tsayawa sukai yai musu take away sannan suka wuce gida. * Yau a gida yaja musu sallar isha.i bayan sunci abinci sannan yace mata sannan ya kulle musu kofarsu ya dawo ya kama hannunta sukai bedroom. Cayai mata ta watso ruwa. Zai wuce dakinshi ya watsa ruwa dan so yake su gama tare su kwanta. Haka kuwa akai. Bata jima da fitowa ba ya shigo dakin. Kamshin turarukanshi na wani kashe mata jiki. Kwanciya yai kan gadon ya kamota ya dago ya kwantar kan jikinshi ya lumshe idanuwanshi. "Kewarki nake ji sosai sofi. Tun kamun in tafi nake jinta har raina" Itama lumshe idanuwanta tayi tana sake kankame shi. A hankali zuciyarta ke hada mata kalaman yanayin da take ji kamun tace. "Lokaci zai tsayamun in baka kusa. Komai zai canza. Bana tunanin zan gane hanya ni kadai a duniyarka baka tare dani" Wani nauyi kirjin shi yai mishi. Yana jin yanda zuciyarta ke dokawa a jikinshi. "Duniyata da taki iri dayace yanzun sofi. Bana tunanin nisa zai canza haka. Bakyajin yanda bugun zuciyata ke tafiya dai dai da naki?" Nutsuwa tai tana kokarin jin abinda take cewa. Hannunshi ta kamo ta dumtse. "Bance nisa zai canza yanda bugun zuciyar mu yake ba. Sai dai zai canza yanayin komai a tare dani" Jan numfashi yai. Inta ci gaba da magana haka bazai iya tafiya yabarta ba. "Ki fadi sunana sofi. Sau daya na taba jinshi a labbanki. Ban manta yanayin shi ba. Ina son kari ne. Inason tattara duk wani yanayi in tafi dashi ko zai rage mun kewarki" Hawayen da take rikewa suka zubo. A hankali ta sumbaci wuyanshi saboda dai dai nan kanta ya tsaya. Baisan lokacin da dan sauran control dinshi ya kwace ba. Sosai yake nuna mata yanda sonta ya gama zauna mishi. Yanda zai kewarta. Jikinta ya shiga bari saboda bakuwa ce sosai a wannan salon soyayyar nashi. Riketa yai. Cikin kunnuwanta yake gaya mata kalaman da sirri ne a tsakaninsu. Haka ya riketa a jikinshi yana saukar mata da nutsuwa. Duk yanda yake ji bai danne rashin son tsorata ta ba. Yafi son yabi komai a hankali. Kaman yanda zuciyarshi ke fada mishi. Bai samu lokaci a soyayyarta ba. Lokaci daya tai masa illa. Shisa yai alkawarin bama nuna mata ita dukkan lokacin sa take bukata. **** "Sofi da kin shirya nakai ki makaranta" Girgiza masa kai tayi. "Na hakura da zuwa yau. Ina son ganin tafiyarka" Kyaleya yai. Tunda suka tashi yake fama da ita ta shirya yakaita makaranta takiya. Ita a dole sai taga tafiyarshi ba zata makaranta ba. Tare sukai breakfast. Ya shiga ya sake yin wanka. Lukman ya kira a waya. Dan driver din da aka samo musu sunyi sai gobe zai fara zuwa. Saboda haka shi zai sauke shi airport. Tana zaune tana kallonshi yana ta kaikawo. Harya gama shirin shi tsaf. Kukan da take ta daurewa tun dazun ya kwace mata. Lumshe idanuwanshi yayi. Sannan ya karasa wajenta ya rikota. Muryarshi dauke da wani yanayi yace. "Nace bana son kukan nan. Kullum fa zamuyi waya.  Ko so kike in tafi zuciyata da hoton fuskarki jike da hawaye?" Girgiza mishi kai tayi. Hannu yasa yana goge mata fuska. Dakyar ta iya samu hawayen suka tsaya. "Nace miki kome kike so ki kirani ko?  Zansa lukman ya kawo miki. Kudi na nan inda na nuna miki. Dan Allah banda yawan damuwa" Muryarta a dakushe saboda kukan da tai tace masa. "Duk na rike fa" Dariya yadanyi. Wayarshi yaji tana ringing. Yasan lukman ne dakyar ya samu ya janyeta daga jikinshi yana daukar yar jakar shi. Mikewa tai ta rike hannunshi tana bude wani sabon shafin kuka. Hugging dinta yayi. Gaba daya kalamanshi sun kare. Shi kanshi bukatar lallashin yake. Sun jima a haka yana rike da ita tana kuka. Wayarshi data sake daukar ihu ya sa shi dago safiyya daga jikinshi. Fuskarta ya rike. Sumba yake manna mata ko ta ina a fuskarta batare daya damu da hawayen dake jike a jiki ba. Yau martani take mayar mishi saboda yanda take jin kaman ta bishi. Dakyar ta iya raka shi bakin kofa. Kissing dinta ya sake yi. "I love you. I more than alot love you sofi" Saboda yana tunanin abinda yake ji a zufiyarta yai kadan a dora shi kan kalma uku kacal. "I love you fu.ad" Wabi kumburi yaji zuciyarshi tayi ta cika mishi kirji saboda wani sonta daya karu a lokacin. "Ki kulamin da kanki sosai" Kai ta daga mishi bata son kuka ya sake kwace mata. Tsaye tai harya fice. Da sauri ta koma wajen window ta bude tana kallon shi. Hawaye nabi mata fuska. Har duniyar shi ta zame mata bakuwa ko nisa baiba tsaye tai a wajen har ya shiga motar suka fice. Jikin window din ta hade kanta tana wani irin kuka. Bama taji zuwan mama indo ba sai da ta dafa ta. Juyawa tayi. Wani sabon kukan na zuwa mata. Kamata mama indo tayi ta kaita daki tana lallashinta. Wayarta taji ta dauki ihu. Ta lalubo taga shine ya kira. Mikewa tai zaune tana goge fuska kamun ta dauki wayar. Hakan yasa mama indo bar mata dakin. Murya a dakushe tai masa sallama. Tanajin yanda ya sauke ajiyar zuciya kamun yace "Sofi kuka kika sake yi ko?" Duk yanda take ji bai hanata murmushi ba. "Tun dazunne....." "Hmm yan zun lukman ya sauke ni airport. Saida na biya naima momma sallama tukunna" A sanyaye tace "Aikam ka kyauta. Gidan yayi shiru baka nan" Ya amsa da "Kinga da kinje makaranta zai rage miki kewa" Girgiza kai tayi kaman yana ganinta. "Ganinka anan kusa dani ne kawai zai ragemun kewarka" Hira sukai na dan wani lokaci kamun yai mata sallama da alkawarin zai kira daya isa. Sosai tai mishi addu.ar da bata samu ta mishi ba dazun. Da kewar shi takai makaranta. Duk da sunyi waya da safiyar amman jinta take kamar marar lafiya. Dan dakyar ta iya bacci jiya. Sai da taci kuka ta more. Da safe ma data bude ido taga baya nan sai da tai wani. Anty laurat office tayi abinta. Safiya kuma ta shiga aji kasancewar talata ne ba assembly suke ba. Da fara.a wasu daga ciki mazan ajin suka gaisa da safiyya. Ta karasa ta zauna wajen zamanta. Sosai khadija da aisha sukaji dadin ganinta. "Anty safiyya Allah dai yasa lafiya. Munyi jaje jiya mungaji. Ga wani rashin dabara bamu taba tunanin karbar number dinki ba" Cewar khadija. Aisha ta karba mata da. "Wallahi kuwa. Allah dai yasa lafiya" Safiyya taji dadin karamcinsu. Sai take jin sun rage mata kewar su jummai. Duk da girman jikinsu zaizo daya da su khadija. Dan Aisha na tafita tsayi tasan ta girme su. Antyn nan tun tana hanasu harta hakura. "Maigida na ne ya koma wajen aiki. Kuma bana dan jin dadi" Dariya aisha tayi. "Umm su anty an samo mana baby" Wata kunya ta kama safiyya. Da sauri ta girgiza musu kai. "Nikam dai ba wani baby" Khadija tace "Mukam munji dadi ko aisha?  Zamu sha suna wallahi. Har anko sai munyi" Gani tai da gaske suke yi. Da sauri tace. "Kai ni bama mu taba....." Shiru tai saurin yi. Ta kasa karasawa. Lokaci daya kunya da tuna girman rike sirrin aure da suka tabayi a islamiyya ya zo mata. Su khajida da sun gama gane inda ta dosa kallonta suke kaman maganar datai itace mafi girma da ban mamaki da suka ji duk shekarar. Da wani yanayi khadija tace. "Tafdi. Anty kina so wata ta kwace miki miji ko?" Wani rass safiyya taji gabanta ya fadi. Ita sam bata taba wannan tunanin ba. Aisha ta jinjina kai. "Sosai ma kuwa. Gashi so hot" Duka khadija takai mata. Tai saurin cewa. "Ke bakya karantawa a litattafan hausa?" "Wallahi kuwa. Ji cikin NI DA DIYATA na anty ayna yanda yasmeena ta kwace ma deela miji" Cewar khadija. Kaman safiyya zatai kuka take kallonsu. Muryarta a sanyaye tace. "Ni ban taba karantawa ba. Ina ake samu...." Da mamaki khadija tace. "Baki na da waya ba?" Ta daga musu kai. "Kin zo da ita?" Girgiza kai tai wannan karin ma. Dan maganar a kwace mata fu.ad. Hango fu.ad nama wata murmushi ma balke magana kawai yasa kirjinta na wani zafi. Akwai ma abubuwa da yawa da take son koya. Bata iya kalar abincin shi ko daya ba. A rauna ne tace musu. "Ina son in iya kalar abubuwan da yake ci ma. Ban iya dafa ko daya ba" Dafata khadija tayi. Hadi da fadin. "Karki damu zamu koya miki. Gobe in Allah ya kaimu kizo da wayarki da kudi a siya kati. Zamu bude miki whatsapp mu koya miki amfani dashi. Zaki karu sosai wallahi. In shaa Allah weekend din nan zanzo gidansu aisha saiki bamu address dinki muzo gidanki mu yini duk mu koya miki wasu girki" Kallonsu take ta rasa bakin da zatai musu godiya ma. "Allah ya biyaku da kalar karamcin da kuke nunamun" Dariya ta basu suka amsa da amin. **** Haka rayuwa ta ci gaba da tafiyarma safiyya. Da duk rana kewar fu.ad na karuwa a zuciyarta. Sai dai a hankali su khadija ke wayar mata dakai. Kaman yanda sukai alkawari haka suka zo gidanta suka yini ranar. Sosai take karuwa dasu. Littafi ta samu suke rubuta mata girgike girke ga groups na girki da suka sakata. Duk da bata iya cewa komai saboda yanda typing ke mata wahala da qwerty din nan. Tana budewa tabi tana karantawa kuma tana karuwa. Ga litattafan hausa da take samu. Suna ma rage mata kewa da daddare. Taita shan karatu. Mama indo na taimakawa wajen kara koya mata wasu girkin. Haka in taga wani a waya ta cire kunya ta nuna ma anty laurat. Yanzun lesson din awa daya suke sauran awa dayar a kitchen suke yinta tana koya mata girki. * Kwanci tashi har satin dawowar fu.ad yayi. Safiyya ta kagu ya dawo ta tarbe shi da sababbin abubuwan data koya sabo dashi. Pha.iza tazo dubata yafi a kirga. Haka lukman duk da baya shigowa sai dai ya tsaya a harabar gidan tasa hijab ta fita su gaisa. Indai zaizo saiya kawo mata abubuwa. Wani lokacin harda kaji ko biscuit da chocolates kala kala. Wannan kenan. [4/4, 6:00 PM] Fatima saleh: *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ    27 Kallon kanta take a mudubi. Wannan ne kaya na biyar data saka tana cirewa. Yanzun riga da skirt ne na atamfa brown. Ya karbeta sosai. Ba wata kwalliya a fuskarta banda jagirar datai. A sati dayan nan da khadija ta koya mata jagira ta zama kwararriya. Kaman ba ita ba. Ga hannunta ya sha kunshi. Har gida su khadija suka kawo mai kunshi jiya tai nata jan lalle da baki. A hannuwa da kafa. Murmushi take ita kadai. Ba karamar kewar fu.ad take ba. Ji take yaki sauri ya karaso. Sai kamshin turaruka take. Musamman humrar da anty fatima ta bata. Inta shafa saita wuni da ita a jiki. Falo ta fita ta sake duba dining. Komai a shirye yake. Mama indo ta tayata gamawa tun dazun ta koma nata bangaren. Window ta leqa ko zata ga ta inda zai bullo. Ta gaji da tsayuwa a wajen ta koma bedroom. Sam ta kasa zama waje daya. Sai yawo take cikin gida. Dakin shi ta shiga da ta feshe da turaruka. Ta zauna kan gadon. Ta lumshe idanuwanta ta bude su. Ta kagu yazo yaga yanda duniyar shi ta canza ta. "Sofi........." Muryarshi taji da sauri t bude idanuwanta. Baya cikin dakin. Zuciyarta na son fita daga kirjinta tabi inda taji kiranshi da yanda take doka mata. "Sofi........." Ta sake ji. Bata san sanda kafafunta sukai hanyar fita dakin ba. Tsakiyar falo taganshi tsaye hannunshi rike da akwati. Sai jaka rataye a hannunshi. Tun daga takalmin kafarshi ja ta soma kallo zuwa crazy jeans din dake jikinshi blue. Sai hoodie din da yake sanye ita fara da ja. Sannan ta tsaya kan fuskarshi. Hannuwanshi ya bude mata yana tarbarta da wani murmushi daya sa zuciyarta ci gaba da kokarin fita daga kirjinta ta same shi. Kafafuwanta har sarkewa suke kamun ta karasa inda yake. Taimaka mata yai ta hanyar kamo hannayenta. Su ya fara kaiwa bakinshi yana kissing babu kakkautawa. Ji yake kaman ya hadiyeta ya ciccike ramukan missing dinta dayai sannan ya fito da ita ya kare mata kallo. Lumshe idanuwa tai tana jin dumin hannayenta cikin nashi. Labbanshi kan hannuwanta. Sai taji kaman wani abu ya dan matsa cikin zuciyarta da batasan ba dai dai yake ba sai yanzun. Dagowa yai ya kalli fuskarta. Wani abu ya fadi can kasan makoshi da ta kasa gane wanne yare ne. Kamun ya jata jikinshi yai hugging. Tana jin yanda ya sauke wata ajiyar zuciya. Hannuwanta tasa a bayanshi tana kankame shi. Cikin kunnenshi take fadin. "Sannu da zuwa. Nayi kewarka sosai" Kissin gefen fuskarta yayi kamun yace "Ba sosai ba tunda kina iya dorawa akan kalamai" Murmushi tayi. So take ta sake kallon fuskarshi amman zuciyarta na mata ihu saboda tunanin rabata da jikin fu.ad data keyi. A hankali ya kamota yana dawo da ita zuwa ga dubanshi. Idanuwanshi ke yawo kan fuskarta. Sai kace ba sofin shi daya tafi ya bari ba. Ta kara wani kyau. Sai yaga kaman yankan idanuwanta sun kara girma da wani haske. Sumba ya manna mata a kowanne ido. Muryarshi can kasa yace. "Kinyi kyau sosai" Itama tashi fuskar take kallo. Akwai abinda ya canza mata. Gashin kanshi take kallo. Haba tasan ya canza ko yaya ne. Maimakon askin data saba ganin shi dashi wannan karon suma ce cike da kan ko ina. Irin old school din nan. Hannunshi ta kamo taba fadin. "Muje kayi wanka" Jakar dake rataye a hannunshi ya sauke tsakiyar falon. Ya dago da hannunta. Dayan ya kamo yana kallon su. "Banson ina son kunshi ba saida na fara ganin hannuwanki dashi" Murmushin nan da yake bala.in so tayina kunyace. Juya idanuwanshi yayi. Sofi na karasa kashe mishi zuciya ba kadan ba. Ta gefe ya zagaya hannunshi ya tsayar dashi kan kugunta suka yi dakinshi a haka. Yana turawa wani kamshi mai sanyi ya daki hancinshi. Kallonta yadanyi. Yai murmushi kawai saboda bai da abinda zaice. Gefen gadonshi ta zauna ya dauki towel ya shiga wanka. Tuna abinda ta karanta tayi. Da sauri ta mike ta bude wardrobe dinshi. Rasa kayan da zata dauko mishi tayi. Irin wandon jikinshi tagani baki. Ta dauko masa sai wata porlo fara kal ta ajiye masa kan gado. Turaruka ta dauko ta feshe kayan dasu sannan ta samu waje ta zauna. Har yanzun zuciyarta ta kasa tsayawa waje daya. Tana nan zaune ya fito daure sa towel da singlet. Lokaci daya bugun zuciyarta ya karu. Ga wata kunya data lillibeta. Daurewa tayi ta dauki cream din data ajiye a gefe ta karasa inda yake kanta a kasa. Dora shi tai kan tafin hannunta ta mika mishi kanta na kasa. Murmushi yake tunda ta taso saboda banda kafafuwanshi babu inda idanuwanta ke iya kaiwa. Hannunta da man ya hada ya rike ya jata jikinshi. Yai wani kasa da murya kamun yace. "Ba tayani zakiyi ba?" Hakan ne niyyarta amman sai taji kunya duk ta rufeta. Kai ta daga mishi. Man ya saka cikin hannunta ya jata. Sam taki kallonshi. Kan gado ya zauna. Ta ajiye man a kasa ta na tsugunnawa. Man ta dangwala tana murza shi cikin hannunta. Kanta a kasa yake amman tanajin idanuwan fu.ad kafe a kanta da suke sata jin wani iri. Kafarshinta kama kaman yaro ta murza mishi man tun daga kwaurinshi zuwa kasa. Sake dangwalowa tayi ta dan daga kafarshi tana hada tafin hannunta da tafin kafarshi ya wani motsa yatsun kafar. Sake kokarin murzawa tai ya janye kafar yana dariya. Baya so komai ya taba mishi tafin kafa. Wajen is ticklish. Kula tayi tai dayar kafar taba janyo ta. Hannun tasa da sauri jikin tafin kafarshi tana wasa da ita. Ba shiri ya mike yana dariya hadi da murza kafafun jikin kafet. Kaman yana son goge abinda tabari. Dan har lokacin yana jin hannuwanta jiki. Gaba daya tsikar jikinshi tai wani irin tashi. Dariya sosai safiyya take yi. Ta dauka ita kadai ke jin wannan abin. Shi a kafa ne. Ita wuyanta ne bata so a taba sam. "Ka zauna a karasa" Dakuna fuska yai yana daga mata kafada daya. "Bana so....." Kallonta yake da murmushi a fuskarshi. Dariya take mishi sosai sosai. Towel din dake kugunshi yasa hannu ya cire. Wani ihu ta saki tana rufe idanuwanta. Dariya ya kama yi sosai harda rike ciki. "O. M. G sofi da boxers dina fa....." Mikewa tai da gudu tabar dakin. Har yasa kaya dariya yake. Man ya karasa shafawa a hannuwanshi kawai sannan ya fita. Tana zaune falo tana raba idanuwa. Yana kallonta ya sake kwashewa da dariya. Tai kasa da kanta tana murmushi. Mikewa tayi tana nufar dining. Yabi ta ya zauna cikinshi har wata kara yake. Muryarshi babu wasa yace mata. "Sofi wayai girki?" Tun kamun ma ta bude warmers din. Kallon fuskarshi tayi. "Ni na dafa maka" Kai ya dan daga kawai. Yunwa ke cin shi tun shigowarshi. Ganin safiyya dine ma yasa ya share. Tana budewa wani kamshi ya doki hancin shi. Plate ta dauka ta zuba mishi farar shinkafar data dafa da ruwan kwakwa. Sannan ta samu dan wajen zuba miya ta zuba masa miyar data sha ganye da naman kaji. Ta saka cokali a ciki ta tura gabanshina nutse. Wani dan kwanon ta dauka ta zuba dambun naman da tayi a ciki ta ajiye masa a gefe. Sannan ta dauki cups guda biyu daya ta zuba masa ruwa daya ta zuba masa exotic. Tunda ya tafi suna nan shaqe da fridge. Ba damunta sukayi ba. Ba sha take yi ba. Komawa tayi ta zauna ta zuba mishi idanuwan. A sanyaye tace. "Ban san me kafi so ba. Bansan ko kana cin wannan ba" Cokalin yasa ya dibi miyar ya zuba a gefe yadan cakuda. Ci yayi yadanyi jim. Gabanta faduwa yake yi kar ko abincin bai mishi ba. Dagowa yai ya sakar mata wabi murmushi mai taushi hadi da fadin. "Yamun dadi sofi. Kin iya girki haka bakya mun?" Yar dariya tayi tace. "Da baka nan na koya. Anty laurat da su khadija suke koyamun" Sosai yake cin abincin. Takuma ji dadin ganin yana cin abinda ta girka da hannuwanta. Kallonshi take. Yanayin yanda yake cin abinci na burgeta tun randa ta fara gani. Zaka rantse yanayin dan cin abinci kawai aka halitta mishi shi. A nutse yake yi fuskarshi na nuna yanda abincin ke mishi dadi. Dagowa yai ya kalleta. "Ke ba zakici ba?" Ya bukata. Kai ta girgiza mishi. Nutsuwa tayi tana kallonshi. Tsaf ya cinye plate din data zuba mishi ya na fadin. "Sofi karamun......" Kara mishin tayi. Baima cinye ba yasha lemon kadan ya shanye ruwan yana hamdala. Kallonta yai. "Thank you" Ta rasa me yasa turancin shi ke mata daban. A kunyace tace. "Don't mention" Ware idanuwanshi yai a kanta. Tasa hannu tana rufe fuska hadi da yin dariya. "Bude fuskarki sofi. Naji dadi fa. Come on bude fuskarki ki kalle ni" A hankali ta sauke hannunta. Ta kalle shi. Yanayin dake fuskarshi na kara mata kwarin gwiwar yi masa magana da iya turancin datai kokarin ji. "You look good" Dariya yai cike da jin dadi. Mikewa yai ya zagaya inda take ya dan tsugunna ya sumbace ta. "I fucking love you sofi" Dan dakuna fuska tayi hadi da fadin. "Meye fucking?" Dan sosa kai yayi maimakon amsa tambayarta sai cayai. "Taso kiga....." Yana kama hannunta zuwa falon. Zama sukai tare ya janyo akwatin ya bude. Wani dan box ya fiddo. Zobe ne me kyau sosai silver. Ya zaro shi daga dan gidanshi. "Banma san ko zai zauna a yatsunki ba...." Hannunta ya kamo cikin nashi yasa zoben a yatsanta na biyu yadanyi yawa. Na tsakiyar ya saka. Cif ya zauna. Kallon zoben da takeyi. Da F a tsakiya. Wani box din ya dauko ya bude ya mika mata. Iri dayane saidai na shi S ne a jiki. Kaman yanda yai mata tai mishi. Ta kama hannunshi ta saka zoben. Saidai na shi yatsa na biyu ya zauna. "Nagode....." Hannunta ya kamo ya sumbaci inda zoben take. Itama mayar mishi da abinda yai mata tayi. Dariya yayi ya fito da wasu takalma pink da sukai mishi kyau ya mika mata. Itama kyau sukai mata sosai ma. Mikewa tayi tana ture kunyar dake addabarta gefe ta manna mishi sumba a kunci sannan ta koma ta zauna. Ya kasa daina murmushi. Cikin kanshi yake godema duk wanda ya canza sofin shi haka. Mayar da akwatin yai ya rufe san sauran kayan dake ciki na su pha.iza ne. Kallon safiyya yai. "Ina son zuwa gida amman ban gaji da ganinki ba wallahi" Dariya tai mishi. "Kaje nasan suma sunyi kewarka. Ina nan me zan dafa maka?" Hannu yakai ya tallabi fuskarta. Sannan yace "Akwai sauran abincin dana ci dazun?" Ta daga mishi kai. Ya lumshe idanuwa kamun ya bude su akanta. "Zan taho da fruits. Shi zan sake ci" Da mamaki take kallonshi tasan da yawan mutane basa son sake maimaita kalar abinci a rana daya. Tace "Shi kaci yanzun fa. Ka fada wallahi indai na iya zan dafa maka" Mikewa yai yana murmushi. "Banda matsala da cin kalar abinci daya kullum indai zai mun maganin yunwa balle kuma inya mun dadi" Fu.ad bazai gaji da bata mamaki ba. Har kofa ta rakashi. Ya sumbace ta sannan ta tafi. Kwanonin daya bata ta dauke daga wajen tai kitchen dasu. Bata wani jira mama indo ba tunda ba yawane dasu ba ta wanke. **** Yana shiga gida husssaina ta fara ganinshi da gudu ta karaso ta rike shi. "Inata kiranka baya zuwa ashe ka dawo ne. Kaga nace anty pha.iza takai ni gidanka ta kiya" Dakuna fuska fu.ad yayi. "Pha.iza bata kyauta ba. Kibarni da ita. Ni zanzo dakaina in dauke ki muje" Rike da hannun hussaina data karbi akwatin daya shigo dashi ta na tayashi ja suka shiga cikin gida. Gaisawa sukai da momma take tambayar safiyya. "Momma ina haneef?" Da fara.a tace. "Yana wajen aiki" Zaro idanuwa fu.ad yayi. Sau nawa sukai waya da haneef bai fada mishi ya fara aiki ba. Muryarshi a sanyaye yace. "Bai fadamun ba" Kallon wanna matsalarku ce momma tai mishi. Dan bai shafeta ba. "Nayi kewar abbah sosai" A tausashe momma tace mishi. "Yana dakin shi. Shima jiya ya dawo" Bai ko bari ta rufe baki ba ya mike. Tana kiranshi ko juyowa baiba ya wuce da saurin shi. Kwankwasa kofar dakin yayi. Muryar abba ta amsa shi da. "Shigo......." Sallama yayi ya tura kofar. Hade rai abbah yai da yaga fu.ad ne. Karasawa fu.ad yayi ya tsugunna gaban abbah. Idanuwanshi ya sauke cikin na abbah. "Wallahi na gane laifina abbah. Ya zanga albarka in kana fushi dani? Abbah baka daga wayata. Baka son ganina. Laifin danai bazai yafu bane?" Ganin abbah yai shiru yasa shi riko hannunshi da nashi duka biyun. Cikin ido yake kallonshi yana so yaga nadamar kuskuren daya aikata cikin idanuwanshi. "Abbah ka yafemun dan Allah. Bazan sake ba. Kamun kowanne hukunci banda nisantata" Gaba daya yanayinshi ya karyarma da abbah zuciya. A sanyaye yace. "Allah yai maka albarka" Da sauri fu.ad ya amsa da. "Amin abbah nagode. Nagode Allah ya kara girma" Hira suka danyi da abbah sannan ya mishi sallama ya fito. Momma ya kalla da fara.a a fuskarshi. "Ni da abbah mun shirya" Numfashi momma ta sauke. Taji dadi sosai. Dan har tsoron yin maganar fu.ad take a gaban abban. Wucewa yai da fadin. "Momma na tafi. Ina so inga lukman sannan in wuce gida" Ta amsa da "To shike nan. A kula da Allah" "In shaa Allah" Fu.ad ya fadi yana ficewa. * Ya jima sosai wajen lukman suna hira. Har yamma likis kamun ya mike da fadin. "Bara in wuce kar magrib tayi" Lukman yace. "Ya kamata kuwa. Kabarta ita kadai" Wayarshi ya zaro yana danne danne. Kamun ya kalli lukman yace. "Sofi tana fadamun kana zuwa duba ta. Bana son in fada ta cikin waya......." Kallon shi lukman yayi yana katse shi da. "Wallahi karka fara. Karka sona fu.ad" Wayarshi taji text ya shigo. Ya dauko ta kan gado. A kufule ya kalli fu.ad. "Meye hakan?" Dan ganin kudi ne ya tura mishi a account. "Biyana zakai kome?" Da sauri yake girgiza kai. "Bazan taba iya biyanka karamcinka ba lukman. An biyani kudina ne na wannan watan. Nayi laifi dan na bama dan uwana?" Sauke numfashi lukman yayi. Fu.ad din ya dora da. "In baka karba zanji kaman ban isa in maka kyauta ba" "Ba haka bane fu.ad abin ne yana yawa" Girgiza kai fu.ad yayi. "Zami bata duk randa ka sake cemun ba maka abu yayi yawa lukman. Kaman kana zagin abokantakarmu ne. Zakaimun fin haka in kaine a matsayina" Jim lukman yadanyi kamun yace "Hakane. Nagode....." Dakuna fuska fu.ad yayi. "Emotional freak....." Dariya sukai su duka sannan sukai sallama fu.ad din ya fice. Haneef ya kira bugu daya ya dauka da yin sallama. Amsa shi fu.ad yayi ya dora da. "Nazo baka nan" "Yanzun na shigo gida. Ruwa kawai na watsa momma ke fadamun" "To bari in karaso gidan yanzun nima na fito gidan su lukman" Amsa shi haneef yai da fadin. "Alright...." Sannan ya kashe wayar. * "Ashe ka fara zuwa aiki baka fadamun ba" Da mamaki haneef yace. "Seriously?" Yana kallon fu.ad cikin fuska. Langabe kai yayi. "Eh mana. Ko addu.a ai zan maka dai" Tabe baki haneef yayi sannan yace. "Yaushe rabon daka fadamun zakai abu?  Bari nai inka dawo kaji" Sake langabe fuska fu.ad yayi. "Na dauka we are good fa. Maganar ta wuce" "Nace bata wuce bane?" Sosai fu.ad ta kalle shi. "Please. Bazan sake bafa. Kaga abbah ma ya daina mun fushi. Wallahi naji daban da momma ta fadamun." Sauke numfashi haneef yai yana kallon fu.ad. "Shikenan. Muje muyi sallah naji an kira" Tare suka wuce masallaci suna taba hira. Ana idar da sallah fu.ad yace gida zaije dan ya bar sofi tun dazun. **** Wata mika fu.ad yayi kan gadon hadi da yamutsa fuska yana kallon safiyya dake kwance gefenshi. "Gajiya ko?" Ta tambaye shi cike da kulawa. Hade sauran space din daya rage tayi tsakaninsu. Yana dora hannunshi kan nata. Kanshi ya mayar kan pillow dinta yana hade goshinsu. Wani tabare mata fuskarshi yayi. "Sosai fa. Jikina duka ciwo" Hannu tasa ta dangwale mishi hanci ya rike hannun yana sumbatarshi. Lokaci daya ya shiga nuna mata yanda yai kewarta. Mamaki da sonta ne ya shige shi jin yanda ta saki jiki dashi take tarbar duk wata soyayyar shi da yake son nuna mata. Kaman wanda aka dokama guduma akai yai tsaye cik. Fuskarshi safiyya ta taba dan jin yai tsaye kaman wanda ya sandare. Muryarshi can kasan makoshi yace mata. "I love you" Yana gyara mata kwanciya a jikinshi. Bata amsa shi ba. Shiru kawai tayi yanajin har bacci ya dauke ta. Dafe goshin shi yai. Sam bai zaci zata sake dashi haka ba. Ba a shirye yake ba. Baya son kuskure daya ya ja masa dana sani. Yai hakurin kusan watanni biyu da dori. Kwana daya bazai canza komai ba. Sosai yai bincike kan tsarin iyali komawarshi. Saidai gaba daya wanda ya danganci bangaren mata akwai complications da side effects da yawa. Bazai taba iya risking din sofi ba. Duk da akwai yiwuwar taki samun matsalar da ake samu. Amman bazai iya daukar wannan ba. In kuma aka samu matsalar bazai taba yafe ma kanshi ba. Zai amfani da protection a yanzun kamun ya samu yanda yake so yai maganin matsalar gabaki daya. Dakyar ya samu wani wahalallen bacci yai gaba dashi. ** Sallar asuba ya dawo ya dawo ya sake kayan jikinshi ya fita jogging. Yana dawowa ya samu safiyya a kitchen. Ta baya ya rungumeta. Hannuwanshi ta kama tanajin yanda zuciyarshi ke dokawa da sauri da sauri da fitar numfa shin shi. "Sofi baki shirya ba?" Ya fadi yana wani maida numfashi. Kwan da take soyawa ta saki hannunshi yana rungume da ita ta baya ta juya. Sannan tace. "Shirin me?" "Makaranta...." Ya amsa cikin kunnenta. Murmushi tayi tana kokarin janye jikinta daga rikon dayai mata. Sake makata yai yana fadin. "Um um fa....." Sauke frying fan din tayi daga kan wuta ta ajiye gefe tana rike hannayenshi sannan ta juya suka fuskanci juna. "Ka kyaleni in karasa aikina" Cikin idanuwa yake kallonta. "Bakwai saura sofi. Zaki makara" Murmushi tai mishi. "babu inda zani." Ware idanuwa yai. "Saboda me?" "Saboda kana gida. Saboda kwana yau kadai nake da ita tare dakai. Sai kuma bayan wata nawa kace?" Yanda ta karasa maganar ya sashi langabe mata fuska. "Haba mana sofi kina magana kaman laifina ne" Ajiyar zuciya ta sauke. "Kwana biyune sunyi kadan" Saida ya sumbace ta sannan ya hada goshin shi da nata. "Nasani sofi. Bake kadai ba" Sumbatar shi tai a goshi. "Kaje kai wanka inyi aikina" Wani shagwabe fuska yayi. "Ni an koreni" Dariya tayi kawai. Ta juya ta ci gaba da aikinta. Ta baya ya hada kumatunta dana shi sannan ya wuce. Ta lumshe idanuwanta soyayyarshi na shigarta. Har ranta kwana biyu ya mata kadan. * Wajen goma na suna zaune a falo ta dauki wayarta. Game din BASE da khadija ta tura mata ta nutsu tanayi. Wayar taji fu.ad ya fisge ta kalle shi fuskarta a shagwabe. "Kaban wayata" "Me kike yi" Hannu takai ta karbe wayarta kamun tace. "Wani game ne mai dadi khadija ta tura min" Komawa yai kan kujerar da take. Mai guda daya ce dan haka ya dagata ya zauna sannan ya zaunar da ita kan cinyarshi. Game din suka dinga yi tare. Ya kai hannu zai danna ta ture hannunshi. "Bafa nan bane. Saika sa an kamani......" Dangwala wa yai ta mintsine shi. "ouuchh sofi da zafi fa....." Wayarshi tahau ringing. Safiyya ta mika hannu ta dauko mishi. Lukman ne. Tana game dinta ya gama wayarshi. Matse ta yai jikinshi sannan yace. "Fita zanyi" Hade rai tayi. "Haba mana. Dan Allah kace ma lukman yabarmun kai yau" Dariya tabashi. Wayar ya mika mata. "Kira shi ki fada mishi" Murmushi tayi a kunyace tana tashi daga jikinshi. Mikewa yai shima yai cupping fuskarta. "I love you......" "I love you too" Ta amsa shi. Sannan ya fice. Hijab dinta ta dauko ta zagaya ta kira mama indo dan ta tayata ko gyara cefane ne dan girkin yai mata sauri. * "Wai me zakayi a chemist?" Lukman ya tambaya cike da rashin fahimta. Narrowing idanuwan shi fu.ad yayi yana fadin. "Ba kyau yawan bincike" Lukman da hankalin shi ke kan tukin da yake yadan juyo ya kalli fu.ad din kamun ya ci gaba da abinda yake. "Allah ko?" Shiru yai ya kyale shi. Bakin wani babban chemist lukman yai parking. Ya kalli fu.ad yace. "Kai sauri......." Bai dai kula shi ba ya fice daga motar. Yakai minti sha biyar sannan ya dawo. Sosai lukman ke nazarin shi ya zauna kanshi a kasa yana wasa da zoben hannunshi. "Fu.ad?..." Ya kira cike da alamar tambaya. Dago fuskar shi da tai wani ja yai ya kalli lukman sannan ya maida hankalinshi kan zoben shi. "Ba damuwar ka bane. Just drop it......" Kallonshi lukman ya ci gaba dayi. "Me ka siyo?" Ya bukata. Dago idanuwa fu.ad yai ya kalle shi cikin ido. "Banda kai please. Ni da kudina mai chemist da mutanen dake ciki sun bi ni da kallon dake screaming dan iska. Saboda me mutane ba zasu bar abinda bai shafesu bane?" Rike baki lukman yai yana wani jan numfashi. Cike da tashin hankali yace. "Tell me ba abinda nake tunani bane fu.ad......" Katse shi yai da fadin. "I don't want kids. Fucking shut up....." "Fu.ad?" A kufule yace. "Fucking stay out of this lukman" Shima a kufule yace. "Fine......." Ya fisgi motar. Lumshe idanuwa fu.ad yayi. Baisan sanda yan nigeria zasu canza ba. Shiga abinda babu ruwansu...........!" *#TeamAS* [4/4, 6:00 PM] Fatima saleh: *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ               28 *Thank you for all your support and comments. Daga yanzun akan kowacce chapter zan saka sakkoni ukku da sunayen wanda suka turo mun su. Meye naku ra.ayin AKAN SO?* Tana yin sallar la.asar ta koma falo ta zauna tana kallo. Tun da suka ci abinci fu.ad ya sake fita. Anan ya sameta da ledoji a hannu da safiyya tasan kayan ciye ciye ne a ciki. Tun tana mamakin kalar cin abincin fu.ad harta daina. Kasa ya zauna yana ajiye komai. Robobin ice cream ya fiddo guda hudu ya ajiye. Ya kalli safiyya da idanuwanta ke kanshi. "Sakko mu sha" Batai mishi musu ba ta sakko. Ta dauko roba daya ta bude. Harya soma koya mata yan ciye ciyen nan. Bata ko shanye rabi ba ta ajiye. Dan yanzun tana iya fara tari. Sam basa shiri da sanyi. "Kinyi me kenan?" Fu.ad ya bukata yana ajiye robar daya shanye ya dauki wata ya bude. "Na koshi. Saika yi mura ko?" Ware idanuwanshi yai akanta. Yana ci gaba da shan ice cream dinshi. Hankalinshi ya maida kan film din da take kallo na hausa zuri.a. "Wai duk yaran ta ne wannan ukkun?" Ya tambayi safiyya ta amsa shi da. "Eh mana. Abin sha.awa ko" Yamutsa fuska yai hadi da fadin. "OH-OH ..." Da mamaki take kallonshi. "Basu burgeka ba kenan" Girgiza mata kai yayi. "Ko kadan...." Dariya ya bata. "Inka haifi naka zasu burgeka" Ware idanuwanshi yai akanta yana fadin. "Wa?  A duniyarmu babu yara sofi. Daga ni sai ke" Dariya ya bata. Fu.ad akwai zolaya ta fadi a ranta bata ce mishi komai ba har akai magrib. Sannan ya fice masallaci. Kwashe robobin ice cream din daya shanye guda uku tayi. Sauran nata kuma ta bude fridge ta saka in mama indo ta shigo ta bata. Kamun ta wuce dakinta. * A kwance ta fito daga wanka ta same shi kan gadon yana danne danne da wayarta. Zama tayi gefenshi. Ya dago ya kalle ta. Sosai yakai kanshi jikinta yana shakar kamshinta. "Wanne irin turaruka ne wannan?" Dariya tadanyi. "Bansan sunan su ba. Anty fatima ta hadomun randa mukaje gidan tan nan" Sake shaka yai yana wani sauke numfashi. Sun mishi dadi sosai. "Nima a shafamun" Hannunta ta goga a fuskarshi. "Gashi nan" Rike hannun yai. "Wayau ko sofi?" Boye kanta tai a jikinshi. Sumbatarta yai sannan ya jata sosai suka koma tsakiyar gadon. Wata irin soyayyarshi yake nuna mata mai tsayawa a zuciya. Dakyar yakai hannu jikin switch din ya kashe musu kwan..........." * "I love you so so much sofi. Nagode...." Yake fadi yana sumbatar kanta. Ya wani riketa kamar za.a kwace mishi ita. Tun dazun ya fadi mata i love you din nan yafi a kirga. Ta kasa cewa komai saboda sanshi da kunyarshi da suka hadar mata. "Tashi muyi wanka sofi" Wani makalewa tai a jikinshi. Ko ina ciwo yake mata. Kai ta girgiza mishi. Yar dariya yayi ya mike daga kan gadon. Wanka ya shiga yayi. Yana fitowa ya goge jikinshi ya hau kan gadon. Dago ta yayi. Sam taki hada idanuwa dashi. Cik ya dauketa yana nufar toilet da ita. "Zan iya zuwa da kaina........" Cikin fuska ya kalleta. "Kin tabbata?" Kai ta daga mishi. Bai sauketa ba sai daya kaita cikin bandakin sannan ya janyo mata kofar a hankaki. Wardrobe ya bude ya dauko mata wata rigar baccin. A hankali ya tura bandakin ya mika mata. Sanda ta fito bakin kofar bandakin ta same shi a tsaye. Hannunta ya kama suka hau gadon tare. Riketa yai jikinshi. Wata sumba mai taushi ya manna mata. Hannu tasa tana ture shi. "Yi hakuri....." Ya fadi yana sauke numfashi. "Bacci nake ji......" Ta karasa muryarta can kasa. Gyara musu blanket yai yai musu addu.a. Cikin sanyin murya yaji ta sake rike shi tace. "Tun daga ranar daka shigo rayuwata komai ya dai daita..." Da murmushi a fuskarshi ya ce. "Bansan akwai abinda na rasa ba a tawa rayuwar saida na mallake ki..." Sumbatarta yai a goshi yana jin numfashinta ya canza alamar bacci ya dauketa kamun shima wani ni.imtaccen bacci yai gaba da shi. * Sama sama yake jin kiran asuba. Dakyar ya iya tashi ya shiga bandaki yai alwala. Bai tashi sofi ba dan yasan shiya hana mata baccin kirki jiya. Ya fita masallaci. Yai mamaki daya dawo ya sameta zaune kan kafet. Karasawa yai ya zauna gefe. A kunyace tace mishi. "Ina kwana...." Dan rankwafa kanshi yai yana kallon fuskarta da taki dagowa. "Sofi ki kalle ni mana" Hannu ma tasa ta rufe fuskarta tana dariya. Janta yai jikinshi. "Nagaji da kunyar nan fa. Taso kiga in kara rage ta......." Ture shi tai tana dariya. "Kin tashi lafiya? Ba inda ke miki ciwo ko?" Kai ta daga mishi alamar babu. Tana mikewa. "Ina zaki?" "Zan shiga kitchen in hada maka abinda zaka karya kamun ka tafi" Riko mata hannu yayi. "Sai sha goma zan fita. Barshi sofi mudan kwanta. Anjima in na shirya zan siyo mana wani abu" Hamma tayi kamun tace. "Allah ya kaimu" Kallonta yake sosai. Yana sake gode ma Allah daya bashi ita. "Bacci ko?" Ya bukata. Daga mishi kai tayi alamar eh. Mikewa yai ya kama hijab dinta ya cire ya ajiye gefe daya yana fadin. "Kuma hakuri zaimun saboda na fishi bukatarki" Murmushi tayi tana sadda kanta kasa. Hannunshi ya dora saman kafadunta yana mata wani irin kallo. "Say mi' name sofi. Ina son ji akan lips dinki" Murmushin dai ta sake yi. Hade space din dake tsakaninsu yayi. Cikin kunne yake gaya mata kalaman da sirri ne tsakaninsu. Kanta ta boye cikin kirjinshi tana dariya kamun ya soma aika mata sakon da yasa daga shi har ita tsayuwar ta gagare su. Dan haka ya jata kan gadon.....! * Takalminshi yake daurawa sofi da comb dinshi a hannu yanajin yanda take yamutsa mishi sumar kanshi da comb din. A dole taje mishi take tana kokarin kwantar da ita baya. Karasa daura takalmin yai ya riko hannayenta duk yana sauke idanuwanshi cikin nata. "Kwana biyu sun mun kadan....." Ta fadi can kasan makoshi. Ya lumshe idanuwa. Tun kamun su hada gado ma kewarta na azabtar dashi ballantana yanzun. Yasan sai ya fita shiga damuwa. Mikewa yai ya zaro wayarshi daga aljihu. Kumatunshi ya hada da nata ya daga camera din yana daukarsu hoto. Wani kuma ya rungumota ta baya. Sannan ya mayar da ita aljihu. Yai cupping fuskarta. "Tafiyar lokaci ne kawai abinda ke rike ni inhar nabar nan. Saboda nasan da duk mintin dazai wuce da kusantar kwanakin da suka ragemun in sake ganinki" Hannunta ta dora kan nashi tana kokarin tarbe hawayen fuskarta. "Banda kallon turawa wanda suka fini kyau....." Dariya ta bashi ba kadan ba. Yana dariya yace. "Sofi idanuwana kadai zasu kalle su. Na miki alkawari zuciyata na tare dake komin nisa" Har ranta ta yarda da maganarshi. Tanajin tsakanin jiya da dare da yau da safe soyayyar daya nuna mata babu shakku a cikinta. Hannunta ya kama ya dora kan kirjinshi dai dai inda zuciyarshi take. "Karfin  dokawarta zamanki ne a ciki" Batasan lokacin data cire hannunta ba ta sumbaci inda yabari. Cikin idanuwa ta kalle shi. "Ina sonka. Ina sonka sosai" Hugging dinta yai yana jin wani irin emotion da baisan ta yanda zai fara fassara shi ba. Kofa ta raka shi. "Allah ya tsaremun kai a duk inda kake. Allah ya bada sa.a ya dawomun dakai lafiya......" Ta karasa maganar muryarta na rawa. Girgiza mata kai yake. Baya son hawayen dayake gani cikin idanuwanta. Sumbatarta ya sake yi sosai yana kokarin shanye duk wata damuwa da take ciki. "Sai munyi waya" Kai ta daga mishi tana kallo harya fice yai wajen mota inda driver ke jiranshi. Ajiyar zuciya ta sauke tasa hannu ta goge hawayen da suka zubo mata. Sannan ta koma cikin daki ta kwanta. Kiran fu.ad kawai ta tsaya jira su sake yin sallama kamun wani bacci mai nauyi ya dauke ta cike da mafarkin fu.ad. **** In tai duba yanda kwanaki suke wucewa suna zama satika. Yanda satika ke wucewa zuwa watanni abin har mamaki yake bata. Wai yanzun har sunyi watanni bakwai suna cikin na takwas da fu.ad. Kusancin su na bata mamaki sosai. Dan ji take yi kamar sunyi shekaru ne ba watanni ba. Banda kewar su inna da take manne zuciyarta tana tunasar da ita abinda suka rasa na cikar farin cikinsu. Zata iya rantsewa babu matar data kaita sa.ar miji. Danma lokaci na musu kadan. Duk da hakan baya hana fu.ad nuna mata doyayarshi. A watannin nan duk bayan sati takwas yake zuwa yai kwana biyu. A dawowarshi ta biyune ya bude mata account. Da kanshi suka je ya koya mata yanda zata cire kudi ta ATM wanda bai mata wuya ba saboda ci gaba sosai data samu a bangaren karatu. Su khadija ke bata shawarar ta tafi account class dan abu biyu zaka dauka daman a aji hudu. Safiyya art ne da account nata combination din kuma sunga tafi gane calculations. ** Wannan dawowar ya karanci akwai damuwa tattare da safiyya. Kyaleta yai saida ya nutsu ya huta sannan. A hankali yace mata. "Sofi meke damunki?" Kallonshi tayi a sanyaye ta girgiza kai alamar babu komai. Tashi yai daga kujerar da yake a koma ya tsugunna gabanta ya kalle ta sosai. "Wa kike dashi dazai ji damuwarki fiye dani?" Wasu hawaye masu dumi suka zubo mata. Ware idanuwa fu.ad yai. "Subahanallah sofi dan Allah menene?  Ko na miki wani abu ne?" Kai ta girgiza mishi alamar a.a. ya koma gefenta ya zauna ya riko hannunta. "To menene?" Kallonshi tai wasu hawayen na sake zubo mata. "Ina kewar su inna sosai. Kuma kwana biyun nan ina yawan mafarkinsu. Kawai ina son sanin halin da suke ciki ne......" Ta karasa tana kwantar da kanta a jikinshi. Kamata yai yana jin wani iri a zuciyarshi. Kamata yai ya mikar da ita tsaye. "Muje ki shirya mu tafi" Da sauri tace "Ina?....." Ba wani alamar razana yace "Wajen su inna. Abinda ya kamata inyi ne tuntuni. Rashin son ganinki cikin damuwa ya hana" A tsorace take girgiza mishi kai. Riketa yai a jikinshi. Kuka take tana tuno yanda su inna suka koreta. "Sofi please. Bana son kukan nan ko kadan. In bamuje ba ba zaki daina ba" Kankame shi tai tana girgiza kai. "Tsoro nake ji" Kissing dinta yai a goshi yana kamata zuwa bedroom. "Ina tare dake. Ni da ke zamu iya yin komai a tare. Zamuje in su inna sun karbemu fine. In basu karbemu ba zamu dawo. Zamu sake komawa wani lokaci. Zamuyi ta komawa har sai sun karbe mu" Da maganar shi ta samu dan kwarin gwiwa ta shiga bandaki ta wanke fuskarta. Ta fito ta dauki mayafinta tasa takalmi suka fita. * Wani irin dokawa zuciyarta take saboda tsoron da take ji. Tun fu.ad na kokarin janta da hira harya hakura. Sai dai lokaci lokaci zai kai hannu yadan taba nata yana son nuna mata yana tare da ita a duk abinda zai faru. Zuciyarta ci gaba tai da dokawa fiye dana da ganin anyo kwanar layinsu. Komai take ji yana kwance mata. Harya karasa kofar gidansu yai parking. A tsorace ta kalle shi idanuwanta cike da hawaye. Hannu yakai ya rike nata. Cikin sanyin murya yace. "Be strong sofi. In shaa Allah komai zai zo da sauki" Hawayen da suka zubo mata ta goge. Tana kallo ya fita daga motar ya rufo. Zagayowa yayi ya bude mata. Ganin taki fitowa ne yasa ya kamo hannunta ya fito da ita. Gabanta faduwa take. Ji take kaman ta ruga ta koma mota. Idan su inna suka sake korarta fa? Suka sake mata abinda yafi na farko. Wani bangare na zuciyarta kuma yake fada mata bakomai ai. Ko dai sun sake korarta tagansu. Taga suna nan lafiya. Hankalinta saiya dan kwanta. Tare suka taka har kofar gidansu. Kafafuwanta sun mata wani irin nauyi. Bude baki safiyya tai zatai masa magana dai dai fitowar wata yarinya daga gidan da zata kai shekaru sha biyar. Da mamaki safiyya ke kallonta dan zata rantse bata taba ganinta ba kaman yanda ita ma take kallon safiyyar. Wani miyau ta hadiye sannan tace ma yarinyar. "Sannunki...." Ta amsa da. "Ina wuni" A tsorace safiyya ta kali fu.ad sannan ta maida dubanta zuwa ga yarinyar. "Su inna suna ciki?" Da mamaki yarinyar tace. "Innarmu kike nufi?" Safiyya ta girgiza mata kai. "Aa masu gidan" Cikin rashin fahimta yarinyar tace "Mune masu gidan ai" Da sauri safiyya ta tureta ta shige cikin gidan bata damu da yanda fu.ad ke kwala mata kira ba. Wata mata ta samu tana jan ruwa. A tsorace ta saki gugar ya koma ciki ganin safiyya babu ko sallama. "Ina inna?" Ta tambaya tana karema gidan kallo. Cike da tsoro matar tace. "Wacece ke? Daga ina haka babu ko sallama wacce innar?" Girgiza kai safiyya take. Zuciyarta na barazanar barin kirjinta. Kallon matar tayi idanuwanta cike da hawaye tace. "Dan Allah masu gidan nake nema" Sai lokacin matar ta gane inda ta dosa. "Allah sarki. Mu muka siyi gida. Watansu biyu kenan da tashi" Wani abu safiyya ke ji yana mata yawo cikin kunnuwa. Da gudu ta fito ta samu fu.ad dayake kai kawo a kofar gidan. Da sauri ya kamata ganin tana shirin shidewa. Fuskarta yake dan bubbugawa. "Sofi menene?" Dakyar numfashinta na wani sama sama tace. "Sun tashi. Basa gidan...... Wallahi basa nan" Ware idanuwa fu.ad yai. Kamun yadan saita kanshi sanin tana bukatar shi. "Aa sofi. Ki kwantar da hankalinki. Babu inda suka je. Ki jirani anan bari in tambayo mutanen can" Kai kawai ta daga mishi tana kallonshi ya tsallaka inda majalissar take. Yana magana dasu. Wani irin dokawa zuciyarta takeyi. Yana tahowa ta kasa jira ya karaso ta taka suka hade. Fuskarshi kawai ta kalla zarginta ya tabbata. Tsuggunewa tai a wajen tana sakin wani irin kuka. Rikota yai dakyar. Ya jata ya bude motar ya rufe saboda mutane sun soma kallonsu sannan ya zagaya ya shiga shima. Saida ya ja motar suka fita daga unguwar gabaki daya suka hau titi tukunna yai parking ya nutsa hankalinshi kan safiyya dake zaune ta hade jiki tana wani irin kuka. Dafe kai yayi. Tuqa motar yai saboda yamma ta soma yi likis. Yanzun a kira magrib. Insun je gida ya san yanda zaiyi da ita. * Da zazzabi ta kwana ruf a jikinta. Dayai maganar suje asibiti ma kuka ta sake saka mishi dole ya hakura ya kyaleta. Da safe ma shiya tayata har wanka tayi fuskar nan ta kumbura. Shima yai wanka tunda ranar zai tafi. Saida ya gama shiryawa tsaf tukunna ya dawo inda take kwance. "Kina so inyi menene?  In tafi inbarki da wannan damuwar?" Shiru tayi tana kallonshi. Saboda bazai taba fahimtar abinda take ji ba. Ya ci gaba da fadin. "Na gaya miki ba jimawa zan ba. Idan na dade sosai sati hudu. Kuma ina da kwanaki da yawa. Na miki alkawari zan nemo su sofi. Duk inda suka je ni zan nemo su. Ko baki yarda dani bane?" Da sauri ta dago ta kalle shi. Ta kasa magana. Kawai so take ya mantar da ita ciwon da take ji a zuciyarta ko na awa dayane. "Please......" Kawai ta furta tana barin idanuwanta na nuna mishi bukatarta. Lokaci ya kalla. Awa daya da rabi yake da ita kamun jirginsu ya tashi. Hannunshi ta kamo tana mishi wanni kallo daya batar mishi da tunanin da yake yi.......!" * Tun yana wanka yake jinjina kuskuren dayai. Son safiyya ya rufe mishi ido. Ko da yake babu yanda za.ai ace rabo ya gifta a dai dai lokacin nan. Beside yadai kusa maganin matsalar gabaki daya. A gurguje ya shirya. Kissing safiyya kawai yayi yana fadin. "Sai munyi waya. I love you......" Sannan ya fice daga dakin da sauri. Ajiyar zuciya ta sauke tana lumse idanuwanta........ ! *#TeamAS* [4/4, 6:01 PM] Fatima saleh:   *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ     29 *Kuyi hakuri. Saboda chapter din tayi tsaho bazan samu saka sakonninku ba. Kuci gaba da turomun ra.ayoyinku AKAN SO. Zamu hadu a chapter na gaba in shaa Allah. Nagode* "Ni dai ba surutu ba. Yunwa nake ji kazo ka dauke ni please" Dariya lukman yayi ta cikin wayar sannan ya amsa da. "Ni nace kazo babu sanarwa. But seriously ban sa ranka yau ba. Duka satinka uku ko?" Daquna fuska fu.ad yai hadi da fadin. "Oww lukman. Surutun nan in kazo munyi. Ka taho nidai" Dan jim lukman yayi kamun yace. "Ba wani dan ladabi" "Please.." Fu.ad ya fadi yana kashe wayar da alkawarin shake lukman in ya karaso. So yake yaga fuskar sofin shi saboda sam bata sa ranshi ba. Daya kirata jiya harda kukanta saboda yace bazai dade ba yana kuma gaya mata saiya kara kwana goma. Murmushi yake tayi shi kadai. Yana hango soyayyar da zai nuna mata yau din nan. Ji yake kaman yai tsuntsuwa ya karasa gida. Motar lukman ya hango. Ya mike bashida kayan komai sai jakar system dinshi.  Hannunshi cikin aljihun 3-quarter dinshi ya taka zuwa inda lukman yai parking. Ya bude motar yana fadin. "Allah yai maka yanda kamun lukman" Dariya yai yaja motar. "Ya hanya?" Lukman ya bukata. Hararshi fu.ad yai ya sake yin dariya. "Da na taimaka nazo? Bacci nake wallahi ka wani tashe ni" Wannan karin fu.ad din ne yai dariya. "Haneef na kira nace yazo ya daukeni. Zagina ma yai" "Madallah. Nima kawai saboda safiyya. Da sai dai ka shiga taxi" Hira suke jefi jefi da lukman har suka karasa. Bai shiga da motar ba iya kacin shi kofar gidan fu.ad din. "Zan shigo anjima in shaa Allah.  Ka gaishemun da hajiya please" Tabe baki lukman yai. "In ka shigo kaje da kanka" Ficewa fu.ad yai daga motar yana fadin. "Zanzo dinne ai. Sai anjima" "Ka gaida safiyya....." Wucewa fu.ad din yai. Lukman ya juya da motar. * Zaune take kan kafet tana yanke farce. Kwankwasa kofa taji anyi. Bata kawo ma ranta komai ba tace. "Shigo....." Zatonta ma anty laurat ce. Tunda suna hutu yanzun. Wani lokacin indai ta fito takan biyo su gaisa da safiyyar. Dago kai tayi dataji an turo kofar. Wani ihun murna ta saki ta tashi da gudu ta karasa ta rukunkume shi. Dariya yake shima hugging dinta yai sosai. Sun jima a haka sannan ya sake ta yana sumbatarta. "I miss you sosai sofi" Ta kasa daina fara.ar da take yi. Hannu tasa tana jan kumatunshi. "Shine kace mun sai nan da kwana goma ko" Rike hannunta yai yana fadin. "Wayyo sofi. Yi hakuri ina son surprising dinki ne fa" Jakarshi tasa hannu ta cire daga bayan shi tana kama hannunshi. Kan kujera ta ajiye jakar a hankali dan tasan system dinshi ce a ciki. Zama yai yana kwance igiyar takalminshi. Ya ajiye su gefe ya sauke mata idanuwanshi dake cike da gajiya. "Yunwa sofi" Hannunta rike sa kugu ta harare shi a zolayen ce. Hadi da fadin. "Bansan da zuwanka ba ai. Banda abinci" Ware idanuwanshi yai akanta. Ya yamutsa fuska. "Da gaske?" Kai ta daga mishi alamar eh. Kai ya dafe dan inyace har saiya fita ya siyo abinci yunwar nan ta gama wahalar dashi. Coffee ne kawai a cikinshi. Shima dan baccin daya ji yana jine ya sha. Baici komai ba. Ganin yanda yai da fuska yasata kwashe wa da dariya. Kitchen ta wuce ta samu plate ta zubo mishi taliyar datai jalof da dankalin turawa. Duka ta juyo mishi dan tasan da wahala ma ta ishe shi. Tana gamawa ta zuba ma maigadi da mama indo nasu ta juye tata a warmer. Bama taci ba ashe rabonshi ce. Da cokali ta taho mishi da cup. Ta soma ajiye abincin kan table taja shi zuwa inda yake. Sannan ta wuce ta zubo mishi lemo a cup din ta hado da robar ruwa. Tana fadin. "Bari ko dankali in kara soya maka...." Da sauri yace. "Dawo please. Wannan zaiyi rikeni na wani lokaci. Zauna kawai inganki" Murmushi tayi. Ta samu waje ya zauna tana kallonshi yana cin abincin cike da yanayin nan da yake burgeta. Hira suke danyi kadan kadan harya gama. Rakashi tai ya shiga wanka ta zauna ta jirashi ya fito. Ita ta tayashi shiryawa ya gama tsaf sannan yai kissing dinta. "Bara inje gida sofi. Inma dauko mana wata motar nagaji da wannan" Murmushi tai mishi. "A dawo lafiya. Ka gaishe dasu" Tare suka fita falo ya dauki jakar system dinshi ya fice. Kitchen ta shiga ta dora indomie. **** Su hussaina na islamiyya. Bai samu kowa gidan ba sai momma da haneef. Take fada mishi babban yaya ma yai accident amman da sauki tunda babu karaya sai ciwuka. Sama yahau ya samu haneef suka gaisa. "Muje gidan babban yaya mana in duba shi" Gyara kwanciya haneef yai. "Sa.ankane ni da zamu jera muna zuwa unguwa tare" Dariya fu.ad yayi. "Dan Allah" "Ka kyaleni fu.ad bacci zanyi" Daga nan saman fu.ad ya wage baki yana kiran. "Mommaaa!!!  Kice haneeef ya rakani!!!" Mikewa haneef yai yana toshe Kunnuwa fu.ad ya kama dariya. "Wallahi ranka zai mugun baci. Kaje ku tafi da kukman mana" Juya idanuwanshi fu.ad yayi. "Hajiya ta aiki lukman. Ka tashi muje tare" Yasan halin fu.ad sarai bazai barshi ya huta ba inba tashi yai ba. Dole ya mike suka fito tare. Motar fu.ad din suka shiga. Haneef ya dauke jakar system dinshi dake ajiye a inda zai zauna. Saida ya zauna ya dora jakar kan cinyarshi. Fu.ad yaja motar suka tafi. * Basu wani dade gidan babban yaya ba. Dan yama fita sai matarshi kawai suka gaisa da. Fu.ad din yace a gaishe masa dashi zasu dawo ko zuwa gobe ne in Allah ya kaimu. Sun fito suna hanya ne fu.ad a dole saiya tsaya ya siyi shawarma. Biris yai da tsegumin da haneef yake mishi. Yai parking din motar ya fice. Siyowa yai ya dawo suka wuce gida zai ajiye haneef din. Fu.ad ya fara fitowa daga motar. Haneef ya bude motar shima yana fitowa jakar dake hannunshi yakai zai ajiye zip din ya bude. Da sauri ya tare system din da takardun da suke kokarin zubowa yana fadin. "Ya Rabb......." Komai yake kokarin gyarawa yanda yake wasu takardun asibiti suka ja hankalinshi. Zaro su yai ya rufe motar yana dubawa. Fu.ad ya zagayo bangaren haneef din. Das yaji gabanshi ya wani fadi ganin takardun da suke hannun haneef. Har ranshi yai niyyar gaya mishi amman ba yanzun ba. Sam ba ta haka yaso haneef yagani ba. A hankali yace. "Haneef....." Hannu kawai haneef ya daga mishi fuskarshi kafe kan takardun dake hannunshi. Lumshe idanuwa fu.ad yayi. Baya son damuwa da wani ciwon kai. Fuska haneef ya dago ya kallo fu.ad da wani irin yanayi da yasa zuciyar fu.ad dokawa. Kallon shi haneef yake yana so yaga ina kaninshi yake. Kaninshi daya san bazai taba wannan abin bai shawar ce shi ba. Kaninshi da bazaiyi wannan rashin hankalin ba. Wannan ba fu.ad din saya sani bane. Wani fu.ad ne a tsaye a gabanshi da baisan daga inda ya fito ba. A tsorace fu.ad yace. "Haneef nine...." Saboda ya karanci kallon da haneef din ke mishi. Takardun ya sake kallo ya dago ya kalli fu.ad. Girgiza kai fu.ad yake ganin katangar da ke ginuwa tsakanin shi da haneef din lokaci daya. Tunda yake a rayuwarshi bai taba jin yayi kuskure har cikin ranshi ba kamar yanzun. Kuskuren daya shiga tsakanin shi da dan uwanshi. Cikin gida haneef yai da takardun a hannu. Da gudu fu.ad ya bishi yana fadin. "Haneef. Ka saurareni dan Allah....." "Mommaaaaaa!" Haneef ke kiranta. Hannunshi fu.ad ya riko ya fisge yana ture fu.ad din. "Don't. Just don't....." Fuskar haneef daya kalla yasa shi tsayawa kawai yana dafe kai. "Damn.....!" Momma ce ta fito daga daki da sauri kallo daya tai ma yanayinsu tace ma haneef. "Lafiya? Me ya faru?" Dai dai lokacin da abbah yai sallama. Momma ta amsa mishi. Ganin su cirko cirko yasa shi cewa. "Me ke faruwa ne?" Kallon haneef momma tai. Shikuma ya kalli fu.ad idanuwanshi da wani irin distant look a ciki. Har yanzun ya kasa yarda da abinda yake gani. Takardun ya sake dubawa dan ya tabbatar da gaske ne abinda yake gani fu.ad ya aikata. "Fu.ad wai lafiyarku kuwa? Kuna ji anata magana kunyi shiru" Cewar momma a tsawace. Idanuwa fu.ad ya sauke a kanta. Shi baima niyyar gaya musu ba. Daga lukman sai haneef. Sake kallon haneef yai da idanuwanshi yake rokonshi da abin ya tsaya tsakaninsu. Kai ya girgiza mishi ya maida hankalinshi kan momma. Sannan ya dubi abbah. Pha.iza ce ta fito daga kitchen itama tai tsaye tana kokarin fahimtar abinda ke faruwa. Cikin wata irin murya da wani yanayi a fuskarshi haneef yace. "Momma fu.ad. Fu.ad bashi da hankali ko kadan.........." Kanshi ya nuna da duk hannayenshi ya ci gaba da fadin. "Ni banda wata daraja a idanuwan fu.ad ban isa ya fadamun ba kamun yai wannan haukan" Ya karasa yana mikama momma takardun data karba bakina sake. Lumshe idanuwa fu.ad yai hadi da fadin. "Haneef......" Hannu ya daga mishi alamar baya son ji. Sannan ya juya ya sauke idanuwanshi kan fuskar fu.ad. "Bana son ji. Bana son jin duk wani abu dazai fito daga bakinka........" Takardun momma ke dubawa hannunta har rawa yake. Idanuwanta sun tsaya kan kalma daya *VASECTOMY*. Cikin kanta take duddubawa inda ta adana bokonta take son fahimtar kalmar. Kai take girgizawa. Abbah dake tsaye ya karaso ya karbi takardun daga hannunta yana fadin. "Wai menene?" Dubawa ya shiga yi. Jingina da bango fu.ad yayi yana jin kaman ace yana da wani sihiri da zai iya bacewa bat. Su neme shi su rasa da su tirke shi kan abinda yake tunanin bai shafe su ba. Rayuwarshi ce ba tasu ba. Wani irin kallo momma take ma fu.ad muryarta na rawa tace. "Kace mun kokarin yi kake baka aikata ba......" Abbah ma idanuwa ya zuba mishi. Yana jiran yaji amsar dazai bayar dan ji yake zuciyarshi har wani daci daci take yi saboda takaici. Duk wata kaddara mai muni da zata auka mishi daga fannin fu.ad take tasowa. Yau shi ya haifi yaron da baya son haihuwa. Daya bayan daya fu.ad ke kallon fuskokinsu. Cikin sanyin murya yace. "Na riga nayi momma. Shi ya mayar dani wannan karin. Inajin cikin ku abbah ne kawai baisan bana son yara ba. Na sha fada ba sau daya ba. Kuma a gabanku. Ban dauka dan nayi wannan zai zama wani babban abu ba..." Wannan karin momma ce ta karasa inda fu.ad yake ta dauke shi da mari. Rike kunci yai yana kallonta cike da mamaki. Abinda bata taba mishi ba tun daga yarinta sai yau. A kufule tace. "Fu.ad ka fita idona wallahi. Har yaushe kai hankalin da zaka yanke irin wannan hukuncin" Pha.iza kuwa tana ta ware idanuwa jin fu.ad yace. "Banga wani abu a vasectomy ba momma. Rayuwata ce wannan saboda me zaku kasa fahimta....." Da mamaki da wani yanayi momma ke kallon fu.ad. Daga hannu tayi zata sake marin shi abbah yai sauri ya rike hannunta da fadin. "Ki rabu dashi kawai. Ba zamu zauna shi kadai yana bata mana rai ba. Alhamdulillah tunda bashi kadai muka haifa ba. Kai da ba a haihuwa za a haifoka ne. Duka shekarunka nawa da har zaka yanke hukuncin baka son zuri.a?" In ran fu.ad yai dubu ya baci. Ya rasa meye abin daga hankalin cikin wanna abin. Jikinshi ne. Rayuwarshi ce idan basu bashi goyon baya ba sai su zuba mishi ido. Kanshi a kasa yace. "Abbah bani da wajen su ne a rayuwata. Yanzun nake kokarin building career ta. Dame zanji? Me......" Hannu abbah ya daga mishi yana jin kaman ya shake shi ya huta kawai. Muryarshi a dake yace. "Duk wani abu daka sani naka ne a gidan nan ka kwashe. Aje ai building din career lafiya. Kar kafarka ta kara shigomun cikin gida?" Gabaki dayansu ware idanuwa sukai akan abbah. Momma kanta kallonshi take yi tana ganin tsaurin hukuncin daya yanke. Su hussaina ne suka shigo da sallama an rasa me bakin amsa musu. Abbah suka fara rikewa da murna kamun hussaina taga fu.ad. Da gudunta ta karasa inda yake ta riko mishi hannu. Duk da abinda yake ji bai hana shi yi mata wani guntun murmushi ba kamun ya maida dubanshi zuwa abbah daya ce. "Kaji abinda nace. Kabarmun gida fu.ad kabarmin gida karka sake shigomun ballanta na inganka raina ya baci" Momma ta kalli abbah kamun tai magana yace. "Zabi biyu kike dashi. Ko ni ko danki. Nagaji da halinshi. Ban haifi yaron da zai samun hawan jini ba. Tunda ban saka ma nawa iyayen ba." Yana rufe baki ya juya ya nufi sashin shi.  Wasu hawaye suka zuboma momma ta kalli fu.ad tace. "Kaga abinda rashin hankalinka ya janyo ko" Hussaina da bata fahimci meke faruwa ba ganin momma na kuka yasa ta kama ita. Pha.iza ma kukan take. Wani numfashi fu.ad yaja yana jin gaba ki daya duniyar ta mishi zafi. Zuciyarshi yaji ta wani bushe. Saboda me abbah zai mishi haka. Akan ya zabi ya tsara rayuwarshi ba tare da ra.ayin kowa ba. Hussaina dake rike da hannunshi ya kalla. Yasa hannu ya cire nata ya nufi sashinsu. Kowa kallo yabi shi dashi harya bacema ganinsu. Dakin shi ya shiga. Jaka ya dauka ya bude wardrobe dinshi. Kayane kawai a ciki. Gani yai babu abinda zai dauka ciki. Karema dakin kallo yake. Wani pink din hanky ya hango kan gadon shi. Hussaina ta bashi shi. Bazai manta ba har yana ce mata na mata ne tace ta rubuta sunanshi a jiki da hannunta har cakewa tai da allura zaice baya so. Hannu yasa ya dauki hanky din yana jin kaman ya ciro zuciyarshi ya ajiyeta gefe daya yadan huta. Dakin yake kare ma kallo. Yana ma kanshi da zuciyarshi alkawarin kin sake tako gidan ma ballantana dakin. Bazai saka ma abbah hawan jini ba kaman yanda yace. Lumshe idanuwanshi yai tamkar wanda yake son dibar duk wani memory daya taba spending cikin dakin ya adana su dan karsu bace mishi. Jakar ya ajiye kan gadon saboda babu abinda zai zuba ciki. Wardrobe dinshi ya sake budewa ya dauki wata riga da momma ta taba siyo mishi. Bai taba sakawa ba saboda ta mishi girma sosai. Ya ajiyene saboda yasan yanda ta siyo mishi rigar cike da kaunarta a wajenshi. Kafarshi da wani irin nauyi ya ke takawa ya fito daga dakin. A hankali ya janyo kofar karar rufeta na rufewa da wani kyaure a zuciyarshi da baisan inda ya samo shi ba. Dakyar kafafunshi suka kai falon. Suna tsaye inda yabarsu. Pha.iza ya fara samu. Tana tsaye tana kuka. Kallonta yake. Muryarshi a dakushe da dacin abinda yake ji yace. "Be safe. I will always love you" Rike mishi hannu tayi tana wani irin kuka saboda ta kasa ma magana. A hankali ya zame hannunshi daga nata ta durkushe a wajen tana wani irin kuka. Kome fu.ad ya aikata. Bataga dalilin dazai sa a kore shi daga gidan ba. Abbah ba kanshi kadai ya kamata ya duba ba har dasu. Wajen momma ya karasa ya zuba mata idanuwa. So yake ya kalleta sosai dan zai musu nisan da bainsan randa zai sake ganin fuskarta ba. Cikin kuka tace. "Karkayi fu.ad karka sake wani kuskuren. Kaje gida zan shawo kanshi......" Kaiya girgiza mata yana jin wani abu game da abbah daya kasa fahimtar ko menene. Zuciyarshi yaji ta kara bushewa. "Momma ki yafemun. Zamana zai iya samar miki da matsala......" Kasa karasawa yai saboda wani abu daya tsaya mishi a wuya. Wuce ta yai ya karasa inda haneef yake. Baya kaunar abinda yake gani cikin idanuwan haneef sam. Baya son yanda yake kallonshi. Karantar hugging dinshi da fu.ad ke shirin yi yasa haneef dan matsawa baya. Ware idanuwa fu.ad yayi da mamaki. Cikin wata irin murya haneef yace. "Inhar ka tafi karka dawo. Inka tafi ka tabbatar da ka barmu kenan. Ka tabbata shine kuskure na biyu mafi girma da za ka aikata........" Wani abu daya tsaya mishi a wuya yake kokarin hadiyewa amman yaki wucewa sam. Shima haneef din ya tsane shi kenan. Kallon shi yai sosai baice komai ba ya nufi hanyar waje. Da gudu hussaina ta bishi ta rike masa riga tana kuka. "Ina zaka tafi wai?  Momma kuce ya tsaya" Lumshe idanuwanshi yai. Ya juyo ya tallabi fuskarta dake jiqe da hawaye. Rankwafawa yai ya sumbaci goshin ta. "Duk nisan dazan kina zuciyata hussaina....." Hassan ya kalla. Ya girgiza mishi kai hadi da fadin. "Karka tafi. Kome kayi muna bukatar ka. Wazai je yaga ko zan iya zama dan ball nima? Wa zai rabani fada da hussaina?" Miyau fu.ad ya kara hadiya. Dakyar ya iya cewa. "Ga haneef nan. Ga pha.iza gasu babban yaya" Girgiza mishi kai hussaina take. "Babu wanda zai somu kaman ka. Dan Allah karka tafi" Banbare hussaina yake kokarin yi daga jikinshi. Pha.iza ta karaso inda suke idanuwanta a bushe. Hussaina ta kama ta janye tace. "Tunda ya zabi yabarmu ki kyale shi mana. Sai mu fasa rayuwa dan baya nan?" A hankali yace. "Pha.iza...." Ware idanuwanta tai akanshi. Irin kallon da haneef yake masa yake gani cikin idanuwanta. Wani numfashi yaja kamun tace. "Ka tafi abinka. Kaunarka ba zata kashe mu ba" Jan hussaina tayi da take wani irin kuka tana kokarin kwacewa. Momma ya kalla ta kauda kai gefe. Itama ya karanci zabin dasu haneef suka bashi take bashi batare data furta ba. Wucewa yai da duk takun da yake zuwa fita daga gidan yana jin yanda yake barin wani bangare na zuciyarshi. Dakyar yakai mota. Ya bude ya shiga Wani dishi dishi yake gani.......! * Ta rasa me yasa gabanta yake ta faduwa tun dazun. Wayarta ta dauko ta kira fu.ad har sau uku bai dauka ba. Mikewa tai taje wajen window ta tsaya saboda haka kawai taji hankalinta ya kasa kwanciya. Tana nan tsaye taga motarshi ta karaso. Wata ajiyar zuciya ta sauke saboda yanda taji hankalinta ya kwanta. Tana ganin ya fito daga mota ta karasa ta bude kofar. Dai dai shigowarshi. Bai ko sallama ba yajata jikinshi yai hugging dinta. Wani sauki sauki yake ji a zuciyarshi. Hugging dinshi tai itama tana karantar akwai abinda ke faruwa. A hankali ta zame jikinta ta daga kai tana kallon fuskarshi. Wani irin haske taga idanuwanshi sunyi. Gabaki daya ya canza kaman ba fu.ad din data saba gani ba. A tsorace takai hannu ta taba kuncin shi. "Menene?" Ta tambaya da wani yanayi a muryarta. Hannunta ya rike ya sauke numfashi kamun yace. "Abbah ya koreni sofi. Baya son in sake shigar mishi gida" Ware idanuwa tai ta rike baki hadi da fadin. "Inalillahi wa ina ilaihi raji.un. Me kayi mishi? Ko akan aurenmu ne? Baka ce ya hakura ba...." Ganin yanda ta rikice yasa shi rikota jikinshi. Kuka take wanda baya so saboda tana kara rikita mishi lissafi. Tana kirjinshi kwance luf tace. "Me kayi?" A hankali yace mata. "Vasectomy....." Da rashin fahimta tace. "Menene shi din?" Dan bata san ma.anar abin ba bakuma taga alakarshi da korarshi da abbah yai ba. Muryarshi can kasa taji yace. "Kwayayen haihuwata na kashe gabaki daya." Kamar wadda akaima allurar rashin kuzari take dagowa daga jikinshi. Yana jin yanda take zamewa daga jikinshi. Wani irin ihu zuciyarshi keyi. Kallon safiyya yake harta bar jikinshi ta sauke idanuwanta cikin nashi da wani yanayi. Kunnuwanta ke amsa maganar da yayi. Takai mintina biyu tana tauna nauyinta. A hankali maganar ke yawata zuciyarta. Tana gayama duk wani waje daya yarda da fu.ad cewar karyane. Son shi da yake mata na karyane inhar baya son hada jini da ita. Inna!  Baba!  Yaya!  Usman!  Zuciyarta ke jero mata a hankali.  Duk danginta duk wata rayuwa tata. Yanda ta fito daga gida tabi fu.ad take gani cikin idanuwanta.  Yanda tabar komai ta biyo soyayyarshi ta karya take hangowa. Komai karyane. Duniyarshi tashi ce shi kadai. Karya yake dayace ta shigo ciki. A bakin kofa ya ajiyeta saboda babu wani waje a zuciyarshi da duniyar shi sai son kanshi. Cikin muryar da bata gane tata bace idanuwanta cikin nashi tace. "Saika baro gidan? Kabar kowa?" Cikin rashin fahimtar tambayar ta yace. "Me zan zauna inyi sofi? Bani na zabi in tafi ba?  Abbah ya koreni saboda na zabi tsara rayuwata ba tare da shawararsu ba" Sai yanzun tagani. Sai yanzun taga fu.ad sosai. Sai yanzun taga babu komai a tare dashi sai son kanshi. Shi yasa ya aureta. Shi yasa ya yanke musu hukunci kaman shi kadai yake da haqqi akan hakan. Kallon safiyya yake. Yanda take matsawa baya. Rikota yakai hannu yayi ta ture shi da wani irin karfi. "Ashe baka sona?!!!....." Wata guduma yaji ta doka cikin kanshi. "Ashe karya ne duk kalamanka?" Wanna karin zuciyarshi ce yaji ta rabe gida biyu. Dakyar ya iya cewa. "Sofi....." Cikin tsawa tana wani dafe kai tace "Bana son ji fu.ad!!! Waya baka ikon yanke mana wannan hukuncin? Ka taba tunanin inkai baka son yara ni ina so? Ashe duk karyane. Duk karyane komai?" Sauran lemar dake cikin zuciyarshi yaji ta karasa bushewa tsaf. Dariyar takaici yai yace. "*Akan so*nki nai wanna abin. Saboda bana so ke kiyina jikinki ki cutu. Ki rasa inda zaki dora darajar sona sai kan karya sofi?" Girgiza kai take wasu hawaye na bin fuskarta. "Karka gayamun me kai *Akan so* ni safiyya ya kamata in bada wannan labarin fu.ad. Nabar komai *Akan so* ashe karya ne baka son hada jini dani" Kai ya dafe a tsawace yace. "Enough safiyya!" Saida ta razana. Ji yake kamar kanshi Zaiyi bindiga. Wai dame zaiji ne. Kallonta yake kaman bai taba ganinta ba. Kamun yace "I don't do happily ever after. Daga randa kika yarda da soyayyata ya kamata kisan banyi kalar wanda zai dinga zarya da yara da pampers ba. Ban kama da wanda zai asarar lokaci da soyayyar shi akan yara ba. Inada su haneef. Ina da su pha.iza. A duk sanda naji marmarin ganin yara zanje gidansu inga nasu" Karasawa tai inda yake ta cakumi wuyan rigarshi. Tana wani kukan dana sani. "bansan baka da soyayyar bawa kowa ba sai kanka da banyi kuskuren yarda da karyarka ba. Ka cuceni fu.ad. ka rabani da kowa. Ka sa zuciyata ta yarda dukkan alkawurranka" Hannunta ya kama yana jin yanda zuciyarshi ke tarwatsewa. Bai taba zaton safiyya zatai mishi haka ba. Cikin idanawa ya kalleta yace. "Baki san me kike fada ba sofi. Zamuyi magana in kin nutsu" Wucewa yazo yi ya fita daga gidan dan yadan sha iska ta riko shi gam. Wata irin tsanar shi da bata san cewar akwai irinta ba a duniya na ziyartarta. "Bana son ganinka wallahi. Bana son sake ganinka" Kafafuwanshi yaji suna wani irin rawa. Rike hannayenta yai muryarshi na rawa yace. "Sofi....." Kai take girgiza mishi tana wani irin kuka. "Nasan ba zaka taba iya bani soyayyarka ba saboda ban taba ganin mai son kai irinka ba. Ba kuma zaka iya bani yaran dazan sami soyayarsu ba? Na rabu da iyayen da suke sona na biyoka bayan baka da abinda zaka bani" Kallonta yake. Kallonta yake sosai yana auna maganganunta yana ganin tsantsar sonkan dayai mata. Hannu yasa yai cupping fuskarta dam. Kwacewa take so tayi saidai bata da karfin hakan. "Ina sonki sofi. Wallah ina sonki" Kallonshi take hawaye ba sake bin fuskarta. "Kabani yara. In har kana sona da gaske ba karya kake ba" Numfa shin shi dake kokarin kwacewa yake kokarin kamawa. Zai iya bata yara ne ta hanya daya. Kallota yake yana girgiza kai. Sai lokacin wasu hawaye suka zubo mishi. Sosai yake girgiza mata kai. "Kabani yara in kana sona fu.ad......." Lumshe idanuwanshi yai wasu hawayen suka sake zubowa yana jin dirarsu tare da dukkan zuciyarshi. A maimakonta wani irin abu na maye gurbin data bari. Dakyar ya iya fito da kalaman da suke shirin kashe shi har lahira. "Na sake ki saki daya sofi......." Kwacewa tai daga hannunshi tana yin kasa. Saboda yanda kafafuwanta suka kasa daukarta. Baya son sake kallonta karya kasa tafiya. Karya kasa bata abinda ta nema saboda yana da son kanshi kamar yanda ta fada. Wani irin gunjin ihunta ya daki kuncin shi. "I hate you fu.ad. Bana fatan sake ganinka a rayuwta." Wani numfashi yaja ya na takawa zuwa waje "Mayaudari......!" Takawa ya sake yi  "Na tsaneka fu.ad nayi dana sanin kaddarar da duk tasa na fara ganin fuskarka a rayuwata....." Kofa ya bude batare daya juya ba. Ko kalamanta basu kashe shi ba sun kashe abinda yai saura ba zuciyarshi. Motarshi ya bude ya dauki jakar system dinshi. Komai da yake bukata yana ciki. Fita yai daga gate din gidan ya miki hanya yana jin shi kaman bashi ba. Ya fita titi baima kula da motar lukman ba sai da yai parking ya fito ya biyoshi ya dafa shi. Juyowa yai. Gaba daya a firgice yake. Lukman yace. "Yanzun haneef ya kirani. Fu.ad me kayi?" Murza kanshi yai kamun ya kalli lukman sosai. "It is my life saboda me kowa zai kasa fahimtata" Fu.ad yake fadi cikin hargowa. Girgiza kai lukman yakeyi cikin ganin wauta da rashin hankalin abinda fu.ad din ya aikata. "Wallahi duk yanda kake fadar rashin son haihuwa ban taba kawo wa yai kamari haka ba fu.ad. Ban kuma taba zaton cewa a zamanmu zaka yanke hukunci irin haka ba tare daka shawarce ni ba" saima kaji abinda na sake yi zakai mamaki tunda rayuwa tace bata wani ba. Fadar fu.ad din cikin ranshi a fili kuma yace. "Na saki sofi!!!" Lukman baisan sanda ya dauke fu.ad da wani irin mari ba. Fuskarshi dauke da wani yanayi daya girmi tsana da kyamata yace "Fu.ad anya baka haukace ba? Ko dai makiya sun maka asiri? Na dauka akan auren sofi kawai Allah ya gama jarabtarka. Na dauka ka gama girbar mugayen halayenka" Wata irin dariyar takaici fu.ad yai hadi da fadin. "Zan bar muku kasar gabaki daya. I have set her free. Ta auri wanda zai iya bata yara. Kaima bankwana nazo inyi maka" Kallonshi lukman yake. Ya zo ya rabashi yana wucewa. Murya a dake yace. "We are done fu.ad. Banga me ya rage ba. Be safe" Kallonshi kawai fu.ad yayi ya wuce abinshi. Yana ganin motar lukman din tazo ta wuce shi fuuu. Wata irin dariya fu.ad ya kwashe da ita yana jin cewar ya samu matsala. Dariya yake sosai kamar mahaukaci..............!!!" * *21/02/2017* Yanzun ma dariyar ya kwashe da ita sabo da baiga haukan da ya sake tako da kafarshi nigeria ba bayan shekaru sha daya............! *#TeamAS* *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ         30 ((Oh my!! This love story is a different one! So unique👌🏻 in its own way... I must confess Sis Lubnerh you're indeed a genius when it comes to writing about any aspect of life!😍 Labarin Fu'ad da Sofi ya samu matsuguni a zuciya ta.There love its surreal! So pure in its own way but full of flaws which are yet to emerge. Bijirewa umarnin iyaye ba karamin laifi ba ne, dole sai ka ga consequences din shi nan gaba,ko da kuwa kuna son juna ne tamkar Ku hadiye juna,sai Allah ya jarrabce Ku for going against their wish... Ina tsoron ganin ranar da Sofi zata farka ta ga Fu'ad din ta ya nisance ta..Ina tsoron ranar da komai da suka dade su na ginawa ya ruguje........Allah Sarki Sofi...I wish this wouldn't happen amma dole a nuna miki kuskuren ki...... Loobnerh you gonna take it easy on Sofi plzzzzzzz... #NowTeamSofi😔))  *Thank you ummie jafar* Tun jiya ya kasa samun wani wadattaccen bacci. Haka ya daure yaje aiki. Yana tasowa ya wuce gida. Wanka kadai yayi. Abincin ma dan zee ta tusa shi gaba babu inda zai fita babu komai a cikinshi yasa shi danci kadan. Wani irin abu yakeji cikin zuciyarshi daya jima da manta yanda yake. Tunani da mamakin yiwuwar samun ya a wajen fu.ad kawai yake yi. Tunani yake zuwansu nawa da shi da haneef gidan fu.ad. A kulle sai maigadi. Karshe ma cayai musu an siyarma da wasu gidan. Har bichi sukaje asalin gidansu safiyya akace musu sun tashi. Baisan ko haneef ba. Amman shi ya sake gwadawa bai samu safiyya ba sannan ya hakura. Wayarshi ya dauko ya kira haneef yaji ko yana gida. Dan bayason ya karasa kuma ya samu baya nan. Kanshi tsaye ya wuce rijiyar zagi inda gidan haneef yake. * "Wai lukman sai kace wani bako" Cewar haneef bayan sun gaisa da lukman din. Murmushi lukman yadanyi hadi da fadin. "Ba jimawa zanyi bane shisa. Ya su ummie?" Jingina da mota sannan ya amsa shi da. "Suna nan lafiya. Ina junior da zainab?" "Yana islamiyya daga nan zan biya in dauke shi." Wayarshi lukman yasa hannu a aljihu ya dauko ya budo sakon da hamza ya turo mishi kamun ya mikama haneef. Karba yai ya karanta saqon. Cike da rashin fahimta dakin yarda da abinda idanuwanshi suke ganar mishi ya dago ya kalli lukman. Wani murmushin takaici lukman yai hadi da fadin. "Yar fu.ad ce haneef....." Girgiza kai haneef yake cikin rashin yarda. "Bazai yiwu ba lukman. Kawai dai wata ce daban. Ta ina?" "Wallahi yar shi ce. Naganta da idanuwana. Idanuwanshi. Fuskarshi komai haneef........" Sau uku haneef na bude bakinshi yana mayarwa ya rufe. Ya rasa meya kamata yaji. "Na kira shi jiya. Na fada mishi ya dawo kamun ya sake wani kuskuren. Bamu kadai zai rasa ba wannan karin. Inajin ba tada lafiya yarinyar. Tana bukatar shi" Wayar haneef ya mika ma lukman yana jin wani abu ya tsaya mishi a wuya. "Da baka bata lokacinka ba. Ba dawowa zaiba lukman. Kanshi kadai yasani. Bana tunanin zai dawo saboda wannan yarinyar" Jinjina mishi kai lukman yai. Dan yafi kowa sanin halin fu.ad. Ga shi baima fada mishi dalilin daya sa yace ya dawo ba. Saikace baisan yanda fu.ad yake da umarni ba. Sauke numfashi yai yace. "Safiyya na garin nan haneef" Wani abune ya fadoma haneef. Kar dai ace safiyya bata bar gidan nan ba. Kawai tasa ace bata nan ne. Kallon lukman yai yace. "Kasan me. Jeka dauko junior daga islamiyya. Zan dubo safiyya i will call you ko me ake ciki. Zan manta yanda na tsani fu.ad a yanzun saboda indai wannan yarinyar yarshi ce tana bukatar family dinta" Dariya lukman yai ya girgiza kai kawai ya bude motarshi ya tafi. Tsanar fu.ad itace abu na karshe da yasan zuciyarsu ba zata iya ba. Haneef dinma mota ya shiga ya fice. Text yaima ummie ya fada mata ya fita dan bazai iya komawa ciki ba. Koya ya rufe idanuwanshi a hanya fuskar fu.ad yake gani. Yanayin shi. Komai na kanin nashi. Sauke ajiyar zuciya yai. Yana marhabin da duk memories din da suke dawo mishi. Yaushe rabon daya barsu haka.......! **** Zaune suke suna cin abinci a tsakiyar falon suna kallon Harry Potter a mbc 2. "Nace miki wannan ne na karshen fa mumy. Inda suke canza kala suyi kaman harry...." Saida ta hadiye abincinta sannan tace. "To ni banganshi bama....." Jinjina kai Nana tayi abincin da take ci na mata wani iri a baki. A hankali ta ajiye cokalin cikin plate din da suke sharing ita da sofi. Abincin bakinta take taunawa tana kokarin hadiye shi a hankali a hankali. Amai taji yana neman taho mata. Da gudu ta mike ta nufar bedroom dinta. Sofi ta ajiye cokalin ta bita tana fadin. "Nana....." Toilet ta sameta tana kwara amai kaman zata fito da yan cikinta. Dafa bayanta tai harta gama aman tsaf tana mata sannu. Zuba mata ruwa tayi ta wanke bakinta da fuskarta. Ta taimaka mata ta cire kayan jikinta. Saboda galabaitar datai sofi tai mata wanka. Ta nadota da towel ta kamota suka fito. Wata doguwar riga marar nauyi ta dauko mata ta bata ta saka. Kallonta sofi takeyi. Yanda idanuwanta suka shiga ciki. A satin nan ta kara ramewa. Sai hasken fatar. A sanyaye tace. "Muje asibiti nana" Ware idanuwanta tai akan fuskar sofi da saida taji gabanta ya fadi. Ko a zuciyarta bata son kiran sunan shi saboda ciwon da take ji. "Ba sai munje ba. Nikam kwanciya kawai zan in huta" Sam bata son takura mata. Taba jikinta tayi taji babu zazzabi. Hankalinta yadan kwanta kadan. Kwanciya nana tai. Sofi ta gyara mata blanket sannan ta zauna gefen gadon tana sauke numfashi. Jitai kaman ana kwankwasa kofa. Tadan kara saurarawa. Kwankwasawa ne. Da mamaki a fuskarta ta mike. Waye zaizo a wannan lokacin. Tasan dai idan Ansar ne kiranta zaiyi a waya kamun yazo. Mikewa tayi tace ma nana. "Barin ga waye yake buga kofa....." Bata jira amsar nana ba ta fice daga dakin tana fadin. "Ana zuwa....." Karasawa tai wajen kofar batare da tunanin komai ba ta bude. Wani irin tsalle zuciyarta tayi tana shirin fitowa daga kirjinta. Batasan lokacin da kafarta taja da baya ba. Da mamaki karara a fuskar haneef na ganinta. Itace kuwa. Safiyya ce. Lokaci daya ya hango ta tana yar karamarta wannan kuma ta zama babbar mace. Banbancin waccen safiyyar da wannan a bayyane yake. Waccan akwia yarinta. Tsoro da kauyanci a tattare da ita. Wannan safiyyar babu alamar yarinta ko kadan a tattare da ita. Wannan safiyyar ta mishi kwarjini saboda tayi kama da wadda wani abu bazai razana ba. Safiyyar nan babu kauyanci a tare da ita. Sosai take kallonshi tana girgiza kai. Shekaru goma sha daya ta boye musu. Sai yau ne za.ace kwatsam sun ganota. Muryarshi a sarqe yace. "Why safiyya? Saboda me kikai mana haka?" Bataji taruwar hawayen ba. Zubar su kawai taji. Muryarta na rawa tace. "Kaimun adalci haneef. Bayan abinda kaninka yaimun wanda ya taba ganinshi ma bana son alaka dashi........." Lumshe idanuwa haneef yayi yana jin nauyin tambayar da yayi mata. Kawai ya kasa jurewa ne. Saboda yana jin kaman da hannunshi a abinda fu.ad din ya aikata dan haka yaso ya nemo safiyya ya taimaka mata ko zai rage yawan laifukanshi. Bude baki yai zai magana ta makale. Idanuwanshi suka kafe kan yarinyar dake tahowa. Bin inda yake kallo saffiya tai taga nana da take kallon haneef itama. Sannan ta maida kallonta kan sofi tana karasawa kusa da ita. Riketa a jikinta sofi tayi tana kallon haneef da dakyar ya iya janye idanuwanshi daga kan nana. Saboda duk wani shakku kan maganar da lukman ya fada mishi ya gama gogewa da ganin nana da yayi. Wata kewar fu.ad ta ziyarce shi. A hankali nana tace. "Mumy?" Tana son tambayarta waye haneef din dan bata taba ganinshi ba. Kallonta safiyya tayi tadan daga mata kai. Alamar babu damuwa zata iya karasawa wajen haneef tai mishi magana. A hankali ta taka zuwa inda haneef yake saboda batajin karfin jikinta. Idanuwanta ta sauke kan fuskarshi hadi da fadin. "Ina wuni....." Ya kasa magana. Ya kasa cewa komai da irin abinda yakeji. Tsugunnawa yai dan tsahonshi yazo daya da nana. Hannuwa yasa yai cupping fuskarta yana son ganin da gaske ne ko mafarki yake. Idanuwanshi ke yawo a fuskar nana. Kamun ya kalli safiyya dakyar yace. "Ya sunanta?" Fuskarta ta goge kamun a sanyaye tace. "Safiyya. Muna kiranta Nana" Jinjina kai haneef yayi yana jin yanda lokaci daya son yarinyar ya shigar mishi rai. Mikewa yayi ya kalli safiyya. Ta fahimci yana son magana da itane. Hannun nana ta kamo tana fadin. "Kije ki kwanta ki huta nana. Zanzo yanzun" Haneef ta kalla tai masa murmushi hadi da fadin. "Sai anjima....." "Ya Rabb...." Haneef ya fadi yana binta da kallo harta shige ciki. Kamar ta daya da fu.ad. Komai nata. "Ka shigo" Safiyya ta bukata a hankaki tana wucewa cikin falon. Bakin kofa haneef ya ajiye takalminshi sannan ya bita.....! **** Necktie dinshi ya warware ya jefar dashi gefe. Ya cillar da suit din dake hannunshi kan gado. Gidan yayi wani shiru yasan duka yaran suna islamiyya. Jana kuma tana wajen aiki. Waje ya samu gefen gadon ya zauna yana dafe kai. Kwata kwata jinshi yake ba dai dai ba. Baisan haka ayna takai a zuciyarshi ba sai yau. Sau shidda yana zuwa office dinsu suce mishi bata zo ba. Tun dazun yake kokawa da zuciyarshi kan kiranta a waya. Dawowar dayai ya samu gidan ba kowa ya kara mishi damuwa. Waya ya dauko ya lalubo number dinta ya kira. Ringing biyu tayi ta daga hadi da mishi sallama cikin sanyin muryar nan tata dake saukar mishi da kasala hadi da gaishe dashi. "Lafiya kalau. Yau dai lafiya ko? Bakizo wajen aiki ba" Ya bukata. Ta amsa shi da fadin. "Mama ce bata jin dadi. Ga gidan sai mu kadai da muka dawo asibiti shine na zauna kar inbarta ita kadai" Lumshe idanuwa jabir yayi yanajin wata nutsuwa. Har hankalinshi yadan kwanta. "Allah sarki. Ya jikin nata yanzun?" "Da sauki sosai. Nagode da kulawa" Murmushi yaji yadan kwace mishi. "Allah ya bata lafiya. Kimun text na address din inzo in dubata" A hankali tace. "Da kabarshi kar dawainiyar tai yawa" "Haba bakomai. Ki turomun yanzun fa" Ta amsa da. "In shaa Allah. Nagode" Ya kashe wayar yana mikewa. Jinshi yake wani iri. Harya ajiye wayar ya dauka. Jana ya kira harta gama ringing bata dauka ba. Jefar da wayar yayi kan gado. Ya shiga wanka. * Wata shadda ya saka ruwan kasa mai cizawa. Ya dora hula da bata kai shaddar haske ba da takalmi ya daura agogonshi. A shekaru talatin da takwas jabir nada wani kwarjini naban mamaki. Mutum ne shi mai son rike girmanshi da bawa kowa hakkin shi. Baki ne. Sai dai yana da kyau dai dai nashi da tsayi matsakaici. Sajen dake fuskarshi ya kara mishi wani kwarjini na daban. Kasancewar shi da na farko a gidansu ya riga ya saba da dawainiyar kannenshi guda biyu da duk mazane tun bayan rasuwar mahaifinsu. Kusan komai shi yake musu musamman da mamansu ta rasu. Shine uwa da ubansu duka. Ya auri murjanatu tana level 2 tana karantar medicine. Haka rayuwarsu ta ci gaba da tafiya da ci gaba mai inganci. Duk da ba zaa kira jabir mai kudi ba yanda rufin asiri daidai gwargwado. Wannan kenan. * Saida ya tsaya ya siyi kayan marmari leda biyu mai layi layi sannan ya wuce unguwar court road inda ayna tai mishi text. Gidansu bai mishi wahalar ganewa ba. Yana zuwa ya kirata a waya ta fito. Sanye take da atamfa a bazai iya fadar skirt bane ko zani saboda hijab din da take sanye da ita doguwace har ta kai kwaurinta. Murmushin nan ta tarbe shi dashi da har saida kumatunta ya lotsa duka biyun. Komai na ayna burge shi yake matuka. Gaisawa sukai ya sake tambayarta jikin mama. Tace su shiga ciki ya dubata. Haka kuwa akayi ya dauki kayan marmarin daya siyo. Mamansu ayna ta karbe shi da karamci abin har mamaki ya bashi. Daga ita har ayna godiya sukai ta mishi kaman ya kai musu wani abu mai girma. Sannan ayna ta rakoshi har wajen motarshi. "Nagode sosai yallabai. Allah ya saka da alkhairi." Murmushi jabir yayi. "Yallabai din nan yaki fita bakinki ko ayna?" Murmushin nan dai tayi dayaji shi har zuciyarshi. Yasan lokaci yayi daya kamata ya fadama ayna yana sonta. Kuma da aure. Saidai yana auna nauyi da ma.anar hakan a rayuwarsu shi da jana. Farko gani yake kamar yawan nisantar shi da jana take yine yasa son ayna ya shiga zuciyarshi. A yau kam ya gane koya yaso ya karyata zuciyarshi son ayna ya samu waje daram. Kuma dole ya sanar da wuri kar a samu matsala. Harya bude baki zai furta mata saikuma ya ce "Shikenan. Ni zan wuce Allah ya kara sauki. Zaki samu shigowa gobe in Allah ya kaimu ne?" Kai ta daga mishi hadi da fadin. "Eh in shaa Allah. Ai ta warware ma. Ka gaishe dasu ikram da madam. Nagode" Ya amsa da. "Zasu ji. Sai munyi waya" Ya shiga motar ya tayar ya tafi. A hanya ya yanke hukunci fara sanar da jana kamun ya gayama ayna. Bazai iya ci gaba da jan rigima da ita ba kan aikinta tunda yasan karya yake ma kanshi cewar aikinta ne yasa shi son ayna. **** A daddafe nuriyya ta gama girki. Ta jera komai a dining table din sannan ta koma kitchen ta wanke kayan duk da ta bata. Tana maida komai wajenshi ne taji takun tafiya a bayanta. A tsorace ta juya. Ta sauke idanuwanta kan kyakkyawar fuskar nawaf. Murmushi yai mata da shakku a idanuwanshi. Dan matsawa tai baya kadan. Tana tsoron kowanne kallar nawaf ne ya shigo tunda ba tantancewa take ba. A hankali ya taka inda take. Ya dora hannayenshi akan kafadarta. Goshin shi ya hada da nata. Kamar zaiyi kuka yace. "Ki yafemun nuri. Bazan sake ba. Dan Allah ki yafemun" Hannunta ta dora kan nashi dake kafadarta ta rike sosai. "Ina sonka nawaf. Kaima kasan ina sonka sau nawa zakaimun alkawarin ba zaka sake ba? Sau......" Dan yatsan shi ya dora kan labbanta yana fadin. "Shhhhhh. Kinfi kowa sanin matsalata. Kinsan bana iya controlling temper dina. Musamman *Akan so*nki. Bana son jin sunan farhan a labbanki ko kadan" Kauda kai tai gefe bata son yaga hawayen dake taruwa a idanuwanta. Ta rasa me yasa yakasa gane girman farhan a rayuwarta. Fuskarta ya kama ya juyo da ita yana sauke idanuwanshi cikin nata. So yake yaga ko tunanin farhan din banzar nan take yi. Ya rasa me yake dashi da shi nawaf bashi da. Me yai mata dashi bai mata ba? Makaranta ce. Sai me kuma?  Yana ina lokacin daya sha kwatarta a hannun mazan dake son lalata mata rayuwa? Farhan bashi bane ya fito da ita daga gidan karuwan nan. Shi ne. Ya rasa me zaisa ta dinga fifita farhan daya tafi yabarta akan shi. Yanayin idanuwanshi nuri ta kalla. Tasan abu kadan zai iya birkita mishi sauran tunanin dayake dashi. Kuskure kalilan yake jira Light kiss ta manna mishi a labbanshi sannan tace. "Kayi hakuri nima. Bazan sake ba. Muje muci abinci" Ta karasa maganar tana kokarin wucewa. Hannunta ya riqo ya janyota tana komawa. Kallon fuskarta yake. A hankali yasa hannu ya shafi inda jini ya kwanta. Da sauri ta rike hannunshi tana janye fuskarta. "Da zafi ko?" Ya tambaya. A hankali ta daga mishi kai. Jiyai ya tsani kanshi gabaki daya. Rungumeta yai a jikinta cikin kunnenta yake fadin. "I am so so sorry Nuri. Dan Allah ki yafemun" Matse shi tai sosai. Zaman gidanshi ya fiye mata inda ta fito. Ko banza tasan babu mai cutar da ita sai shi. "Na yafe maka. Muje muci abinci" Sakinta yai. Ya kama hannunta suka wuce dining din tare. **** Taxi ya tara yace yakaishi wani hotel me kyau. Har lokacin mamaki yake ba kadan ba. Ya rasa tsatsayin dayasa yai abinda lukman yace.  Meye yake dashi ma a nigeria da ya dawo ma? Momma kadai ke son shi. Ita kadai ce ta neme shi bayan watanni shidda da tafiyarshi. Harsu haneef babu wanda ya taba nemanshi yaji yana da rai koya mutu. Duk yanda yake kaunarsu suka watsar dashi. Suka ki fahimtarshi ko kadan. Saboda sun cika son kansu. Haka ya biya kudin kwana biyu a hotel din ya wuce room dinshi. Wanka ya fara yi. Yai sallar azahar da baiyi ba ya mayar da la.asar dan yaga ukku harda rabi. Ordering abinci yayi. Dakyar ma ya iyaci dan jiyai taste din na mishi wani iri saboda ya jima rabonshi dajin shi. Sannan ya fito. Yana tunanin meya kamata yayi daga farko. Da kafarshi ya taka yana kallon yanda garin kano yabi ya canza gabaki daya. Wani waje yagani da ake siyar da simcard ya karasa ya siya dan bashida sim din Nigeria. Ya rigada ya karya shi tuntuni. Ya siya kati. Sannan ya saka. Number din da lukman ya kirashi da ita jiya ya sake trying. A kunne take wannan karin. Ya lumshe idanuwa yana jin ringing din wayar. Sake jin muryar lukman ya sa shi jin wani daci daci a zuciyarshi. Dana sanin bin abinda lukman ya bukata bayan duk sun guje shi. "Hello....." Lukman ya sake fadi a karo na biyu kamun fu.ad ya hadiye wani abu daya tsaya mishi a wuya yace. "Bansan meya sani yin abinda kace ba. Ban kuma san dalilinka na nemana bayan duk shekarun nan ba. Buh' koma meye gani a nigeria...." Da sauri lukman yace. "Fu.ad? Da gaske kazo?  Alhamdulillah" "Hmm...." Kawai fu.ad ya fadi yana sauraren lukman din kamun yaji ya dora da fadin. "Kaje gidanka. Koma menene dalilin zaka gani" Yamutsa fuska fu.ad yayi. "Wanne gidana kuma?" "Wanne gida kake da?" A kufule yace. "Lukman bana son rainin hankali kasani. Kawai kamin bayani yanda zan fahimta" Shiru lukman yai. Fu.ad ya duba wayar yaga tana reading. Dan zatonshi ma ko network ya katse kiran. "Kana jina fa lukman" Cikin sanyin murya yace "Wai ka gama masifar. Dan nafara dana sanin kiranka danai" Dafe goshi fu.ad yai yana jin alamar ciwon kai ya fara mishi sallama. "Dayake ma ban roki ka kirani ba. Duk tsahon shekarun nan saina fasa rayuwata da babu kiranku a ciki?" Wani numfashi yani lukman ya sauke. Kamun yace. "Allah yasa abinda zaka samu ya canza rayuwarka gabaki daya. Kaje gidanku kaida safiyya......!" Kashe wayar lukman yayi. Gabaki daya fu.ad yaji jikinshi yayi wani sanyi. Jin sunanta a bakin lukman. Gidansu shida safiyya. Sofinshi tana gidansu.......! *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ         31 *Godiya mai yawa ga duk wanda ya bata koda second daya ne ya kalli littafina. To the fans of Akan so. Kusani ana tare. I love you guys* Fu.ad na nan yanda yake. Bazai taba canza halinshi ba. Ya dauka a shekarun nan ya karanci kuskuren shi. Saima abinda ya karu. Son kanshi yana nan. Shekaru goma sha daya babu abinda ta canza fu.ad dashi. Zee ce ta fito da cikinta daya turo. Murmushi yai mata a kasalance. Ta mayar masa da martani. "Ki bimun yarinya a hankali zee" Dariya tayi. "waya ce maka yarinya ce?" Ta karasa ta dafa cinyar lukman din kamun ta zauna gefen shi. Kanta ta kwantar kan kafadarshi. "Inaji a jikina ne kawai. Kinsan zuciyata bata mun karya" Daga mishi gira tai hadi da fadin. "Ko?" Sarai yasan me hakan ke nufi. Kan junior har kayan mata yaita kwasowa shi a dole jikinshi ya bashi mace za.a haifo sai gashi ta haifo namiji. "Wannan karin fa da gaske nake" Dariya kawai tayi. Tambayar da take son yi mishi na ci mata zuciya. Kamun tasan fu.ad nada wani muhimmanci a rayuwarshi ta dauka haka kawai yasama junior sunan dan yana burge shi. Sai daga baya ta gane sunan fu.ad din ya mayarma junior. Kuma tun yana jariri baya kiranshi da fu.ad din. Shi ya fara ce masa junior kamun kowa ma ya dauka. Inba makaranta ba babu mai kiranshi da fu.ad. Tana son jin labarin shi da fu.ad ko yaya ne. Dan duk abinda ke da muhimmanci a rayuwarshi ta sani. Ya boye mata fu.ad ta rasa dalilinshi. "Ina son tambayarka ne fa. Amman ina tsoron bata maka rai" Kallonta yadanyi hadi da fadin. "Kiyi tambayarki babu damuwa" Sai da ta nisa sannan tace. "Nasan ka roqeni kar na zurfafa tambaya. Kawai ina son sanin duk wani abu dake da muhimmanci ne a rayuwarka. Waye fu.ad a wajenka?" Wata ajiyar zuciya lukman yayi. Wayar da sukai da fu.ad din yan mintinan da suka wuce na kara yi mishi wani iri. Jin yai shiru yasa zee cewa. "Kayi hakuri. Bansan ranka zai baci ba wallahi. In shaa Allah bazan sake tambayar komai a kanshi ba" Kanshi ya jingina da nata dake kafadarshi cikin sanyin murya yace. "Yau zaki san komai game dani da fu.ad zee......... ****  Kai kawo yake tayi cikin dakin tunda ya dawo aiki. Kira uku yaima nuri wayarta a kashe. Ita da tace mishi ba dadewa zatayi ba. Duk da yasan inda taje bai hana ranshi baci ba. Wani abu yake ji na mishi yawo cikin kai. Yakan tsinci kanshi cikin wannan halin inhar Nuri tai mishi nisa. Waje ya samu ya zauna yana running hannuwanshi cikin kai. Kallo daya zakai ma yanayin nawaf kasan yana da matsala ba karama ba. Jin jirin mota yasa shi mikewa ya karasa jikin window din. Nuri ce gaban mota da wani wanda yake tunanin ya taba ganinshi amman ya rasa ko a ina. Murmushin da yaga Nuri tamai yasa shi jin wani abu ya soki zuciyarshi. Yana kallo ta bude motar ta fito ta fadi ma matashin wani abu dabaisan ko meye ba. Amman yaji yana son cire mishi hakoran can dayake ta bude ma Nuri. Kanshi zafi yake. Yana kallo yaja motar yai baya da ita. Nuri kuma ta yo hanyar shigowa gidan. Da sallama ta turo kofar. Ganin nawaf tsaya yasata sakin mishi wani murmushi. Fuskarshi a hade yake kallonta. "Waye wancen Nuri?" Batare da tunanin komai ba tace mishi. "Mijin amal ne. Dazan kiraka kazo ka daukeni yace bara ya saukeni ma. Sannu da gida kaga na dade ko?......." A tsawace yace. "Shine kike bude mishi hakora? Dan yana mijin amal sai akace ya kawoki gida? Cike da mamaki Nuri ke kallonshi. "Nawaf? Karka cemun kishinka har da mijin amal" Baisan lokacin daya dauketa da mari ba. Wani ihu ta saka tana matsawa da baya rike da fuskarta. "Babu namijin daya ke da hurumin zama mota daya dake bandani. I don't care ko wanene shi" Wasu hawaye taji sun zubo mata. Wai meke damun nawaf ne? Ta dauka shaye shaye ne kadai matsalarshi kuma ya daina. Zata iya rantsewa abinda yake yanzun marar hankali ne kawai zai yishi. Muryarta na rawa tace mishi. "Kayi hakuri. Bazan sake ba" Lumshe idanuwa yai. Dana sanin marin dayai mata na ziyartar shi. Karasawa yai ya kamata ya rungume tsam a jikinshi. "Bana son ganinki da kowa. Baki da kowa sai ni Nuri. Baki da inda zakije sai nan........" Sake matse shi tai. Tasani. Basaiya tuna mata ba. Tasan bata da kowa sai shi. Bata da inda zataje sai gidanshi. Bata da inda yafi nan din. Shine bargonta. Shine makangin da take dashi tsakaninta da zama da matar data fi tsana fiye da komai a duniya. Matar da zata iya bada ranta in za.a canza kaddarar data zo da ita a matsayin yarta. Gara ko wacce wahala da koma ma rayuwa da ita. Zata iya jure duk wani duka na nawaf indai hakan na nufin rashin komawa rayuwar da ta riga da taima bankwana........! **** "Dady........." khadee ta fadi tana rugawa da gudu ta rike kafafuwan haneef. Lumshe idanuwanshi yayi yanajin wani sauqi sauqi a zuciyarshi. Tsugunnawa yai ya tallabi fuskar yar tashi yana kallonta. Ji yake kamar ya bude kirjinshi ya sakata ciki ya boyeta kar wani abu ya samar mishi ita. Yau ganin Nana dajin matsalarta ba karamin daga mishi hankali yai ba. Tunanin wani abu ya rabashi da khadee kawai yasa yana jin numfashin shi na wani tsaitsayawa. Riketa yai a jikinshi yana matseta gam. Fu.ad yayi kuskure. Duk da haushin yanda yabarsu da yake ji bai hana shi hango mishi kuskuren daya aikata ba. Bai hanashi tausaya ma halin dazai shiga da wannan jarabtar da Allah ya dora masa ba. A haka ummie ta shigo ta same su tana rike da Alhaji dayake da sunan mahaifinsu haneef din wato Muhammad. Daukar khadee yai ya karasa inda take tsaye ya hadasu su duka ya rungume yana godema Allah da ni.imar dayai masa ta kyautar iyali masu cikakkiyar lafiya. Cikin kunnenshi ummie ke cewa. "Lafiya?" Dan bata taba ganinshi haka ba. Sumbatar goshinta yai. Sannan ya sumbaci Alhaji dake ta babbaka dariya abinshi. Ya sumbaci khadee ma yana kara rike su jikinshi sosai. "Ina kaunarku da yawa ummie. Ina sonku. Allah ya kara muku lafiya" A hankali ta amsa da. "Amin...." Tana kara rike shi dan ko bai fada mata ba tasan akwai abinda ke damunshi. Saidai yana da zurfin ciki. Ko ita bako yaushe take jin damuwarshi ba. Saidai yanayin kaunarshi dabanne a wajen su. * Ko da dare fur haneef yace dasu khadee zasu kwana karta kai mishi yara ko ina. Batai musu ba ta kwantar dasu tsakiyarsu. Hannu yasa kansu khadee kaman wani zau kwace su. Kallonshi take da mamakin shi yau. "Habeebi ba zaka fadamun damuwarka ba ko?" Cikin sanyin murya yace. "Kawai ina bukatar yarana a kusa dani ne ummie. Ko nayi laifi?" Hannu takai ta shafi sumar kanshi da murmushi hadi da fadin. "Bakai komai ba. In ba zaka iya fadamun damuwarka ba karkai kokarin nunamun babu ita. Saboda zan iya karantarka a duk yanayi habeebi" Murmushin ya mayar mata yana sauke numfashi. "zan fada miki. Kimun hakurin zuwa safiya. Yanzun ina bukatar jinkune a kusa dani kawai" Kai ta jinjina mishi. "Allah ya kaimu goben lafiya." Ya amsa da. "Amin. I love you" Murmushi tai mishi yanda baya gajiya da fada mata yana sonta na mata dadi kamun tai musu addu.a gabaki daya. Hannunta riqe cikin nashi yaransu a tsakiyarsu bacci ya dauke su cike da kaunar juna. **** Tunda ta dawo aiki gaba daya batajin dadi. Nana itace marar lafiya ta farko data bari ta shiga zuciyarta har haka. Har ranta fata take a samu match Allah ya taimaka a ceci rayuwar yarinyar. Bata samu jabir a gida ba sai yaran kawai sun dawo daga makaranta. Yasir da Umar sunata assignment dinsu. Ikram na kwance cikin kujera tana danne danne da tablet dinta. Umar kadai yai mata oyoyo. Ta rike shi jikinta. Tayi kewar yaran nata sosai. Yasir ma sannu da zuwa yai mata ta amsa tana zama. Sai lokacin ikram ta dago. "Sannu da zuwa" Kallonta tai. Fuskar nan a murtuke. Miskilanci da rikici tsaf na jabir babu wanda ikram ta bari. "Yawwa ya jikinki?" "am okay" Ta amsa a taqaice tana mikewa. Falon tabar musu. Jana ta girgiza kai kawai. Yau ko jabir dinma yazo da rikicin shi bata da karfin jurewa. Nan tabar su yasir din ta wuce dakinsu. Wanka tadanyi dan gaba daya a gajiye take tayo alwalar magrib. Tana nan zaune inda tai sallah jabir ya shigo da sallama. Ta amsa tana mishi sannu da zuwa. Gefen gado ya zauna yana kallonta. Baisan ta inda zai fara ba. Har zuciyarshi abinda yake ji akan jana bai canza ba. Inma bazai karya ba sonta karuwa yake a zuciyarshi. Kaman yanda son ayna yake daban. Kowanne wajen shi daban. Dafe kanshi yai cikin hannayenshi. Kallonshi jana tayi. Mikewa tai ta cire hijab dinta ta karasa gefenshi ta zauna. Kafadarshi ta dafa. Hakan yasa shi dagowa ya sauke idanuwanshi kan fuskarta. "Menene? Gajiya?" Ta jero mishi tambayoyin lokaci daya. Kai ya girgiza mata. Hannuwa tasa ta tallabi fuskarshi tai kissing kumatunshi gefe da gefe. "To menene? Bana son ganinka cikin damuwa kasani ko?" Hannuwanta ya kama ya sauke daga fuskarshi. Bashi yake bukatar lallashi ba itace. Yanda yake kallonta yasata sanin akwai matsala. A sanyaye tace. "Honey J kodai kan aikina ne?" Hannunta ya riko. "Idan nace eh zai canza ra.ayinki?" Ya tambaya. Kai ta girgiza mishi dan ba zatayi karya ba. Babu abinda zai canza ra.ayinta kan aikinta. Tana son mijinta sosai. Kaman yanda yake bangare na rayuwarta hakama aikinta. A nutse yace. "Good. Kaman yanda na daina ma kaina karyan cewar rashin samun kulawarki ne yasani jin abinda nake ji..........." Zuciyarta taji tana dokawa a tsorace. Hannunta ya riko a hankali ya dora kan kirjinshi dai dai inda zuciyarshi take sannan cikin idanuwa ya kalleta yace. "Kar ki dauka abinda zan fada yanzun ya canza wajen zamanki anan. Karki dauka sonki zai taba girgiza a zuciyata. Kar abinda zan fada yai sanadin taba zaman lafiyarmu" A tsorace tace. "Honey J.........." Da sauri ya katse ta da fadin. "Ki barni in karasa please. Ina sonki. Ina sonki sosai babu abinda zai canza haka. Kinmun halaccin da babu macen da zata taba yimun shi Jana. Bazan manta ba kuma. Banda iko da zuciyata daban bari tai miki abinda tai miki ba. Ina son wata jana..........!!!" Wani shiru taji cikin kanta kaman wani ya doka mata guduma a ciki. Lokaci daya taji wani irin kishi da bata taba tunanin tana dashi ba. Da sauri ta soma jero duk wata addu.a da tazo mata. Sama sama taji jabir ya sake rike hannunta gam cikin nashi yace. "Ban fada mata ba. Nace zan fara fada miki tukunna..." Yanda yai maganar cikin rashin makama yasata sake jin wani abu a zuciyarta. Saikace fara fada mata yana son wata bayan ita zai rage mata kishin shi. Hawayen dake son zubo mata take kokarin controlling. A hankali ta kalle shi. Saida ta hadiye miyau yafi sau biyar kamun ta iya cewa. "Wacece? A ina take? Yaushe ka fara sonta?" Kallon fuskarta yake. Ya kasa karantar komai akai. Ya kasa ganin ko ranta ya baci ko bai baci ba. "Ayna.u mardiyya sunanta. Wajen aikin mu daya. Bansan ko tun yaushe ba jana. Farko na dauka ko dan bakya zama sosai yasani son wata. Shisa naso kibar aiki ko zan daina ji ban........." Riko hannunshi tai. Ta sumbata a hankali daya sashi yin shiru. Muryarta na rawa tace mishi. "Ya isa honey J. Zuciyarka badon ni kadai akayi ta ba. Baka da laifi a cikin son wata. Ka fada mata. Allah ya tabbatar mana da alkhairi. Zan roqeka yanzun ko da bazan iya ba nan gaba. Bazan iya hanaka aure ba. Bazan iya hanaka abinda Allah ya halatta ba. Ina rokonka karka wulakanta ni dan kayi wata....." Bude baki yai zai magana. Tasa hannunta kan labbanshi tana girgiza mishi kai kamun ta ci gaba da cewa. "Karka mun alkawari. Bana son alkawari ko daya. Saboda bana son ka dora zuciyata kan abinda zaka zo ka kasa inji kaman kaci amanata. Allah ya baka ikon yin adalci. I need to be alone please......" Hannuwanta ya rike ya matse gam yana jinjina ma kokarinta. Wata kima da girmanta na sake cika mishi zuciya. Daga abokai yasha jin labarin tashin hankali da hauka da matansu keyi in suka zo da maganar kishiya. Yanda jana tai mishi ba karamin daraja ya kara mata ba. Duk da barinta ita kadai a yanzun shine karshen abinda yake sonyi bai hana shi mikewa ba. Wani light kiss ya manna mata a labbanta data kasa mayar mishi da martani. Fita yai daga dakin. Tana jin yaja mata kofar ta ja jikinta kan gadon ta dunqule ta saki wani irin kuka marar sauti. Wani radadi take ji cikin zuciyarta da wanda ya taba shiga cikin irin halin data shigane kawai zai fahimta. Wanda yasan ya raba soyayyar miji take. Ya tunanin zama da wata yake. Ya raba farin cikin jabir yake. Kuka take sosai. Ji take kaman taita kurma ihu. A iya zamansu da jabir bata taba hango raba soyayyarshi ba. Ko da wasa bata taba hango kalar wannan ranar ba. Tasan shi na mace ne har hudu. Sai dai hakan bai rage mata jin abinda take ji ba. Dan dazun ji take kaman ta shaqe shi dayake gaya mata yana son wata. Ganin datai shedan na shirin saka mata hannu a zuciya yasata mikewa dakyar ta shiga bandaki tayo alwala. Sallar isha.i ta idar. Wani sabon kukan ta tisa. A hankali takai hannu ta dauko Qur.an din dake ajiye kan drawer din gado. Ta bude. Tana karantawa tana kuka har wata nutsuwa ta fara saukar mata. A hankali take jin zafin da zuciyarta keyi na hucewa. Sosai tai addu.o.i sannan taja jiki ta koma kan gadon ta kwanta. Ko yaran kasa fita tayi tai musu saida safe kaman yanda ta saba indai tana gida. Tana nan kwance sai juye juye take taji jabir ya shigo. Kwan dakin ya kashe. Tana jinshi ya hawo kan gadon. Rikota yai ta bata cikin kunnenta ya shiga rada mata kalaman da sirrinsu ne. A hankali take jin wani sonshi na kara shigarta. Cikin sanyin murya tace. "Ya kamata ikram ta sani" Saida ya sumbaci gefen fuskarta sannan yace. "Zan fada mata da kaina. Ba yanzun ba. Sai ayna ta karbe ni....." Da sauri ta juyo ta cije mishi labba. Janye fuskarshi yai yasa hannu yana shafa wajen. Muryarta a dakushe tace. "Karka sake kiramin sunanta cikin dakin baccinmu. Balle kuma kan gadona. Jikinka hade da nawa honey j. Suna ne kawai ya kamaci labbanka" Dariya yai sosai yana hade goshin shi da nata. Tai kokarin tureshi ya riketa gam. "Gabana harya fadi. Na dauka kin daina sona shi ya hana miki kishina" Mintsinar mishi hannu tayi. Ya birkitata yana riketa sosai. A hankali ya shiga nuna mata yanda kowacece ta shigo rayuwarshi soyayyarta bata da fargaba. Da salonshi ya shiga tabbatar mata da har abada akwai inda takai a zuciyarshi da ya girmi hangen ayna.........! **** Tun cikin taxi abinda ke manne a kirjinshi madadin zuciya ya ke wani numfasawa har suka karasa. Bakin gidan mai taxi din ya sauke shi. Ya dauko kudinshi yabashi dan saida ya biya wafa dashi yai canzin kudin dake jikinshi. Hotel ma credit card ya biyasu dashi. Lumshe idanuwanshi yayi ya na jan wata iska data shiga har cikin kirjinshi. "Sofi......." Ya furta a hankali. Karo na farko a shekaru sha daya da bakinshi ya bude da sunanta. Sai dai in ya gifta mishi a tunaninshi. Wani irin zafi yaji a kirjinshi. Yakai hannu wajen ya bude idanuwanshi yana wani yamutsa fuska. Da wani irin nauyin kafa ya taka ya karasa kofar gidan. Kallon gidan yake. Yana tuna ranar farko daya fara zuwa gidan shi da haneef. Sake yamutsa fuska yayi. Haneef din daya watsar dashi. Haneef daya yanke alaqa dashi kaman yanda abbah yayi kawai saboda ya nemi tsara rayuwarshi babu shawararsu. Ji yai ranshi ya wani baci. Baisan wanne hauka yasa ya biyewa lukman ba. Yazo nigeria. Yanzun kuma ya taho nan. Hannu ya daga zai kwankwasa kofar gate din. "Na tsane ka.......!" Yaji muryar sofi cikin kanshi. Kwankwasa kofar yayi yana sake jin maganarta radam cikin kanshi kaman tana gabanshi. "Bana son ganinka wallahi. Bana son sake ganinka" Lumshe idanuwanshi yayi. Kirjinshi zafi yake masa sosai sosai. Wani numfashi yake fitarwa da sauri da sauri ko zai ji saukin abinda yake ji. Bude kofar da maigadin yayi ne ya dan taimaka mishi. Ware idanuwanshi yai kan fuskar maigadin. Kallon fu.ad yake. Ganin kamannin da sukai sosai da nana ya sashi bude mishi kofar hadi da fadin. "Alhaji sannu da zuwa." Ko kallonshi fu.ad baiba ya shiga cikin gida. Wani abu yaji ya kulle a kasan cikin shi. Yai kuskure babba. Son famo ciwukanshi ne su dawo danyu suna zubda jini yasa shi biyewa lukman. Sai dai ya rigada yazo. Babu komawa baya kuma. Dakyar kafafuwanshi suke motsi suna taka mishi. Komai na rayuwarshi a gidan ke ta masa yawo cikin kai. Dakyar ya karasa kofar gidan. Tsayawa yai ya rufe idanuwanshi yana kokawa da abinda yai saura a zuciyarshi. kwankwasawa yai. Yana jin koma meye a kirjinshi na dokawa da karfin gaske. * Dakyar ta iya mikewa daga kan kujerar ta nufi kofa. Tun tafiyar haneef tasha kukanta ta more. Sai take jin jikinta duk babu karfi. Bata tambayi ko waye ba. Kawai bude kofar tayi. Cik zuciyarta ta tsaya. Idanuwanta suka kafe a kanshi. Ya kara girma. Jikinshi sanye da normal jeans blue. Sai tshirt ja data kama shi. Banda girma sosai daya kara. Sai sajen dake kwance a fuskarshi da gashinshi daya rage ma yawa. Tsaye zuciyarta tayi. Tana shirin manta yanda ake shakar numfashi. Idanuwanshi yawo suke a fuskarta. Baiga ta canza da komai ba. A hankali yake jin abinda ke kirjinshi na budewa. Yai tunanin bashida sauran zuciya ashe a boye take cikin abinda yake tunanin ya maye gurbinta a kirjinshi. A hankali take budewa. Sofinshi ce. Ta kara kyau fiye da yanda yabarta. Muryarshi dauke da wani irin yanayi yace. "Sofi........" Sai lokacin taji zuciyarta ta numfasa cike da wani abu daya girmi tsanarshi. Kallonshi take tana kokawa da iskar data ke son shaqa saboda yanda ta dauki mintina wajen biyu bata shaqeta ba. Kofar data ke rike da ita taja tana son kulleta yasa hannu ya rike kofar yana kallonta. "Kofar gidan nawa zaki kulle a fuskata sofi?" Wani abu taji ya tokare mata wuya. Ji tai kaman ta kwada mishi mari. Nana ce kawai dalilin daya sa ba zata kira maigadi ya dauke shi ya fitar mata dashi ba. "Daga randa ka sa kafarka kabar gidan nan kai loosing right din ka na kiranshi naka" Wani murmushin takaici fu.ad yayi. Ashe shi yai shekara goma sha daya yana kokawa da murmushi duk sanda tunaninta ya fado mishi. Tana nan ta kara kyau abinta. Baya ranta. Tsanarshin data fadi da gaske ne tana jinta. Cike da takaici yace. "Ko sofi?" Bata son sunan nan yanzun. Bata son yanda sunan yake kaiwa zuciyarta yana wani matse mata ita. "Karka sake kirana da wannan sunan. Sunana safiyya" Kallonta yake da mamaki. Sofi ta koyi rashin kunya. Sosai shi take kallo cikin ido tana fadama magana babu tausasawa. Ware idanuwanshi yai a kan fuskarta. "Kin canza sosai" Kallonshi kawai tayi. Tana ganin yanda yake nan da halinshi data kasa kallo acan baya. Ji take daman baizo ba. Saboda bata son yanda Nana ta saka shi a ranta. Tasan kuma ba sonta zaiyi ba. Babu son kowa a zuciyarshi sai nakanshi. Basu da waje a zuciyarshi. Daga ita har yarta. Bude baki tai zatai mishi magana ta hango Ansar ya taho. Batasan lokacin da murmushi ya kwace mata ba. Wani dan guntun murmushi fu.ad yaji ya bayyana a fuskarshi. Yaushe rabon dayaji shi haka har ranshi. Ta wani kara kyau. Yana son murmushin nan a fuskarta. Ganin hankalinta na wani waje yasa fu.ad juyawa. Wani abu yaji ya tokare mishi wuya. Waye wannan datake ma murmushi haka. Kallon kallo suke da Ansar da fu.ad din. Hannu Ansar ya mikama fu.ad dakyar ya karba sukai musabaha. Kanshi tsaye ansar ya wuce zuwa cikin falon. Safiyya tace mishi. "Yanzun nake shirin kiranka. Najika shiru" Da biyu take maganar. So take fu.ad yagane bashida wani muhimmanci a rayuwarta yanzun. Kuma yaji hakan. In a shekarun nan yana tunanin yayi dana sanin tafiya. Abinda yakeji yanzun ya linka nada. Wani ne zaune a falonsu shida sofi. Da ido Ansar ke kallon safiyya yana tambayarta. Duk da kamanin daya gani kawai ya tabbatar masa da wannan ne fu.ad din. Yanayin shi kawai yasan zai aikata abinda safiyya ta bashi labari. Saboda akwai wani attitude tattare da fu.ad dako wanda bai sanshi ba zai karanta a kallo daya. Sake kallon safiyya yai. Duk yanajin wani irin awkwardness ya baibaye dakin. Ita tana tsaye. Shi a zaune a falo. Fu.ad din kuma yana bakin kofa a tsaye ya kafe su da idanuwa. Kai tadan girgiza mishi alamar yanzun fu.ad din yazo. Ansar ya bude baki zai magana maigadi ya rugo da gudu. "Hajiya ga wasu mutane nan su da yawa bakin kofa. Wai sai sun shigo suna son ganin Nana" Hada ido safiyya da ansar sukai. Kamun Ansar ya mike ya bi maigadin zuwa kofa. Karasawa tai ta dauki mayafinta dake kan kujera. Tazo ta raba fu.ad dayake tsaye kaman an dasa shi ta wuce tabi su Ansar. Yan jarida ne cike da kofar gidansu. Ta lumshe idanuwanta tana tunanin yanda akai suka gano gidansu. Ansar ta kalla da idanuwanta da suke rokonshi da yasan yanda zaiyi da yan jaridar nan. Bata son su ganta a yanzun. Duk da ta ma Nana alkawari. Ba haka ta shirya fu.ad yaji labarin Nana ba. Tazo ma babu matsala batai tunanin zai karbeta ba. Ballantana yanzun kuma. Kaman yaji zancen shi take a zuciyarta ya karaso inda take. Saijin muryarshi tayi yace mata. "Me yake faruwa? Me wannan suke yi anan?" Lumshe idanuwanta tayi ta bude su hadi da fadin. "Ba matsalarka bace ba" Kamun yagama mamaki ta juya tayi cikin gida. Binta yayi da sauri yana fadin. "sofi........" Ko tsayawa batai ba balle yaima tunanin zata juyo. Yana ina shekaru sha daya da suka wuce. Sai yanzun zai tambayeta meke faruwa. Bai tsaya ya tambayi mezai faru da ita ba kamun ya tafi. Ya manta tabar komai *Akan so* bana kowa ba nashi. Badon Nana da zata iya komai *Akan so*nta ba bai isheta ko kallo ba ballanta har musayar magana. Baida wannan darajar a idanuwanta ko kadan. Kofa ta tura ta shiga. Tana kokarin tarbe hawayen dake son zubo mata. Ta riga ta ma kanta alkawari tagama kuka akan fu.ad ba tun yanzun ba. Tana shiga cikin gidan Nana na fitowa daga dakinta. Da alamun bacci a fuskarta tana murza ido. Ganinta kawai yasa zuciyar sofi wani yawatawa da kaunar yar tata. Zata iya komai saboda ita. Koda kuwa daina numfashi ne indai zatai hakan da sanin cewar rayuwar Nana zata ci gaba. A shirye take. Cikin abubuwan da zata iyayi harda jure ganin fu.ad da jin muryarshi duk da yanda suke yi mata kaman zuciyarta zata tarwatse saboda ciwo. Kama Nana tayi tana kokarin janyeta ta mayar da ita daki. Bata son taga fu.ad saiya fara sanin da zamanta tukunna. "Sofi......." Taji ya kira. Wani yarr taji duk jikinta. Tsaye tai cak. Sannnan a hankali kaman mai ciwon wuya ta juya. Nana dake jikinta ta fito ta tsaya tana kallon fu.ad. shi da yake tsaye idanuwanshi kafe kan safiyya sam bai kula da Nana ba. Safiyya ta mayar da dubanta kan Nana tana ganin yanda ta ware idanuwanta tana kallon fu.ad. Inda yaga fuskar ta tabi da kallo ya sauke kanshi. Yako yi Nasarar sauke idanuwanshi cikin na Nana. Lokaci daya yaji komai ya tsaya mishi. Kallonta yake da wani irin yanayi. Kallonta yake saboda yana tunanin bai taba ganin halittar datai mishi kyau ba kamarta. Kallonta yake yana jin yanda komai na jikinshi ke narkewa da kaunarta. Kallonta yake yana jinta kaman wani bangare na rayuwarshi. Kamun yaji zuciyarshi ta yamutse. Idanuwanta. Akwai wani abu tattare da idanuwanta da yake son gane komeye. Kaman wanda aka daka da karfe akai abin yazo mishi. Irin idanuwansu daya sak. Hancinsu da bakinsu iri dayane. Ba saiya tsaya wahala ba. Wannan yarinyar tamkar an ciro shi ne an ajiye a jikinta. Jiyai ko ina na jikinshi na kyarma. Wani murmushin takaici sofi tai hadi da fadin. "Fu.ad ga Nana fa........." Ya kasa janye idanuwanshi daga kan Nana duk da yaji abinda safiyya tace. Baya son dai kona second daya ya daina kallon fuskar yarinyar. Nana safiyya ta kalla tace. "Ga M." A tsorace Nana ke kallonshi. Tana ganin kaman datai wani abu ba dai dai ba bacewa zaiyi. Tunda tai wayau take jin kaunarshi cike da zuciyarta. Tunda tai wayon sanin menene mahaifi take jin son ganin shi koda sau dayane a rayuwarta. Wani murmushi ya kwace mata duk da hawayen da suka zubo mata. "Kaine babana..........." Bangon dake wajen fu.ad ya dafa saboda yanda yaji kafafunshi na rawa da maganar data fito daga bakin Nana. "No way........!" Ya furta yana girgiza kai. . *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ               32 *Seriously ina feeling kaunarku. #AnaTare* Yana sauke khadee makaranta ya wuce gidansu. Tun daga yarinta shi fu.ad yake bari da goge daudar barnar da yayi. Ba bakon abu bane wannan. Saidai rabon da maganar fu.ad ta gifta cikin gidansu ma an dauki shekaru. Momma na kokarin yi musu tun yana gidan. Sai suyi shiru su dukansu. In abinci akeci bamai kara magana har a gama. Sai tabari. To yanzun dinma shi fu.ad ya bari da zuwa yiwa momma bayanin safiyya na nan. Bata bar garin ba kaman yanda suke dauka. Tana nan daram kuma harda yarinya. Yar fu.ad. * Da sallama ya shiga gidan. Dai dai fitowar Hassan daga shi sai 3 quarter da singlet. Da fara.a ya amsa sallamar hadi da fadin. "Yaya haneef ina kwana" "Antashi lafiya? Babu aikine yau?" Hassan yadan sosa kai. "Akwai fa. Yanzun naketa shiri. Yasu anty ummie da khadee?" Kallonshi haneef yayi sosai. "Khadee ai tayi fushi. Tanata tambayarka" Dariya hassan yayi. "In shaa Allah zanje in daukota tai mana weekend." "Allah yasa. Momma ta tashi ne?" Dan yamutsa fuska yai kamun ya amsa da. "Tun asuba da muka gaisa. Bansan ko ta koma bacci ba. Ka kira wayarta mana" Kai haneef ya daga masa yana lalubo wayarshi daga aljihu. Wucewa hassan yayi abinshi. Waje ya samu ya zauna ya kira momma a waya yace mata yana babban falo. Ko mintina biyu ba aiba ta fito. "Ina kwana" Haneef din ya gaishe da ita a ladabce. Saida ta karaso inda yake sannan ta amsa shi da. "Lafiya dai ko haneef?" Dago kai yai hadi da fadin. "Lafiya kalau....." Shiru yadanyi yana tunanin ta inda zai fara mata maganar kamun cikin sanyin murya yace. "Akan fu.ad ne........." Wani irin dokawa zuciyar momma tayi. Saboda yau kwana uku kenan bata samun wayar fu.ad din. Kuma bai kirata ba kaman yanda yakanyi. Tanata tunanin ko lafiya. Babu dai wanda zata tunkara da maganar ne shisa tabarma ranta abin. Jin sunanshi a bakin haneef yau ba karamun tayar mata da hankali yai ba. A kagauce tace. "Eh meya faru?" Ganin yanda ta tsorata yasa haneef girgiza kai da saurin fadin. "Jiya ne lukman yazomun da wata wasiqa da take ta yawo a labarai da yanar gizo gabaki daya. Akan wata yarinya Nana da take neman babanta. Cewar yana tunanin yarinyar yar fu.ad ce........" Ware idanuwa momma tayi akan haneef cike da rudanin jin maganar da yake yi kamun ya ci gaba da fadin. "Nayi kokwanto sosai ko da ya fadamun yaje makarantarsu yarinyar yaganta. Shine nai tunanin ko safiyya na garin nan. Shine jiya da yamma bayan mun rabu da lukman din naje tsohon gidansu da fu.ad din. Momma tana nan. Ta boye mana ne saboda bata son alaka da duk wani wanda ya hada jini da fu.ad bayan abinda ya faru. Nakuma ga yarinyar. Nana din. Yar fu.ad ce babu ko musu a ciki........" Cike da tashin hankali momma ke kallon haneef. Dakyar ta samu kanta da fadin. "Ta yaya? Nakejin fu.ad ga abinda yayi. Bazai taba samun yara ba?" Rausayar dakai gefe haneef yayi. Dan shi kanshi baisan yanda akai ba. Koma dai ya akai yarinyar fu.ad na nan. Sauke numfashi yayi. Momma ta gyara zama sosai. "Wallahi na rasa ta cewa ma. Yanzun ita safiyyar ta kyauta mana kenan? Babu neman da bamuyi mata ba......." Da sauri haneef yace. "Banga laifinta ba Momma. Tasan ko gabaki dayanmu irin halin fu.ad ne damu? Bama wannan ba. Duk mai sauki ne yanzun. Ita yarinyar......." Katse shi tai da fadin. "In dai yar fu.ad ce kaman yanda kace tana bukatar dangin babanta. Tana kuma bukatar babanta. Oh Allah!" A sanyaye yace. "Tana bukatar babanta ne fiye damu. Inhar zai sauke son kanshi ya dawo. Saboda bata da lafiya. Bata da wani lokaci mai tsaho......." Da wani sabon tashin hankali momma ke kallonshi. Yar murnar da zuciyarta ta fara yi tana birbishewa. "Tana da cancer. Fu.ad ne karshen hope dinsu akan rayuwar yarinyar...." "Inalillahi wa ina ilaihi raji.un. Wai meke faruwa ne a rayuwar fu.ad? Wannan yaro Allah kadai yasan abinda ya boye kan kaddarar shi" Sauke numfashi haneef yayi. "Wallahi dakyar nai bacci jiya. Idan kika ga yarinyar..... Kika ga safiyya din........" Kasa karasawa yai saboda yanda zuciyarshi ke karyewa da tunanin yanayin damuwar dake cike idanuwan safiyya. Da kuma yanda tunda yake a rayuwarshi bai taba ganin yarinya mai dauriyar Nana ba. Kalar kaunar daya gani tsakaninta da safiyya bai taba ganin irinta ba. Cikin wata nisantacciyar murya momma tace. "Yau zan magana da abbanku. Zan maganar da yai shekaru sha daya yana kaucema dashi. Zan kiraka anjima koya mukai dashi. Ka tashi ka tafi aiki" Mikewa yai. Dan so yake yadan fita ko iska yasha yaji saukin abinda ke zuciyarshi. "Sai na dawo" "Allah ya bada sa.a....." Har yakai kofa ta kira sunanshi ya juya. "Ka kira kaninka" Runtsa mata idanuwa kawai yayi ya bude su ya juya ya fice. **** Kwance yake kan kujera tana zaune kasa dai dai kanshi suna kallon wani film a tablet din nawaf din 'wrong turn'. A tsorace take saboda horror film ne. A hankali nawaf ya lallaba hannu ya ja mata kunne. Kara ta saki tana neman yar mishi da tablet. Dariya yake sosai. "Nur tsoranki yayi yawa wallahi." Hararshi tayi a wasance. Hannunshi ya dora kan kafadarta yana dariya. Rikota yai yana doro kanshi gefen nata. "Ina sonki sosai. Ki rike wannan ko da wata rana bana nan. Ki yafemun......" Da sauri ta gyara zamanta ta fuskance shi. Kanta ta dora a jikin kujerar gaf da fuskarshi. "Wacce irin magana kake yi haka?" Lumshe idanuwanshi yayi. "Kawai inajin wani irin ne Nur. Inajin kaman bazan jima ba......" Da sauri tasa hannu ta rufe bakinshi dan har idanuwanta sun kawo hawaye taf. Babu inda zashi yabarta. Zata iya tuna lokacin data fara sanin wani abu dadin rayuwa. ********************** ⬇ ************************** ********** Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** Bazata manta ranar farko data fara haduwa da farhan ba. Ranar da yunwa ta isheta. Tun safe take jin yunwa amman Anty kaman yanda take kiran mahaifiyarta ta hanata abinci. Asalima catai sai taje unguwa da wani mutum da bata san shi ba tukunna. Itakuma tace ba zata je ba. Akwai wani lokaci da anty tace tabi wani unguwa. Sukaje tun cikin motarshi ya dinga tabata. Taita zunduma ihu. Dole a hanya ya sauketa. Hakan yasha faruwa. Tun anty na jibgarta kaman jaka harta hakura ta kyaleta. Reza gareta koyaushe a jikinta bata rabo da ita. Ko kusa. Tunda ta illata mutum hudu suke shakkar tabata ko yaya. To yanzun saidai anty ta hanata abinci. Cewarta ba zata zauna tana ci da ita a banza bata morarta da komai ba. Ga makaranta tana son komawa tun da sukai jarabawar gama primary kawayenta duk sun ci gaba anty tace ba zata biya mata ba tunda ta rainata. Tsaye take kofar gida tanata kuka. Shikuma yazo wucewa yake tambayarta komenene. Yanayin shi lokaci daya taji ta yarda dashi. Kukan da take kaman ranta zai fita yasa shi riketa jikinshi yana lallashinta. A tsayin shekarunta tara a duniya farhan ne mutum na farko daya taba nuna mata irin wannan kulawar. Ranar farko ta juye masa matsalarta tas. Tun a ranar ya tambayeta ko tasan inda ake siyar da abinci a unguwar ta daga mishi kai. Dubi uku ya bata yace ta boye ta dinga siyen abinci. Haka kuwa akai yai tafiyarshi. Ba afi sati biyu ba batasan ya akaiba ya sake dawowa. A haka rayuwar ta ci gaba da tafiyar musu. Har wata irin shakuwa ta shiga tsakaninsu da farhan din. Randa ya kamata ya mayar da ita makaranta anty ta fito zatai masa karnukanci suka dibi yan kallo. Farhan yace zai kwaso mata yan sanda ya tona mata asiri. Dolenta ta kyale shi. Haka farhan ya zamarma Nuri wani haske cikin duhun dake rayuwarta. Bata taba sanin akwai wata rayuwa mai nutsuwa ba sai da ta hadu da farhan. * Hannun nawaf ta kamo ta dumtse cikin nata. "Bana son kana mun irin wannan maganar sam. Bana so" Mikewa zaune yai. Sumbatarta yai a goshi ya mike. "zafi nake ji barin dan watsa ruwa....." Binshi tai da kallo saboda akwai Ac a dakin ga fanka amman yace zafi yake ji. Sauke numfashi tayi harya shige bedroom din yabarta nan falon zaune. Sallama taji. Da fara.a ta amsa. Makociyarsu ce Maimunatu. Tace ta shigo ta zauna sai dai a tsorace take. Saboda tasan yanda nawaf ya tsani maimunatu. Saboda wata rana daya kamata tana fadama Nur din cewar ya akai ta auri nawaf. Ai ta san yan gidansu tun tuni. Mahaukaci ne dan shaye shaye. Kaca kaca yai mata ya koreta. Yanzun ma batasan wanne tsautsayi ya shigo da ita ba. Suna gama gaisawa sun zauna jim. Kawai nawaf ya fito. Maimunatu ya kalla dake zaune yana jin wannan duhun dake rufe mishi kai ya bayyana. Karasowa yai yaja hannun Nur yai bedroom da ita. Dan bazai manta warning din dayai mata kan maimunatu ba. Wani irin mari ya dauke ta dashi. "Jakar ina ce ke? Bance miki bana son kara ganin waccen matar a gidana ba???" Azabar marin da takeji baikai ta zuciyarta ba. Ga wani tsoro daya rufe ta. "Dan girman Allah nawaf kayi hakuri wallahi..........." Wani marin ya sake wanketa dashi da sai da taga wani haske ya gilma mata. Kunnenta yadan daina jin iska sosai. Wani mugun kallo ya watsa mata yace. "Just two minute na baki ki fita ki sallameta ki dawo ina jiranki......." Da gudu Nuri ta fice daga dakin. Tsayawa tadanyi ta goge fuskarta sannan ta karasa. A dake tace ma maimunatu. "Ki tafi dan Allah. Ki tafi karki jamun matsala......." Bata jira amsarta ba ta juya abinta. Inda ta bar nawaf ta same shi a tsaye. Idanuwan nan sun sake launi. Gefe takai kallonta. Wani gwangwani ne a ajiye sannan ta dawo da hankalinta kan nawaf a tsorace tace. "Nawaf me kasha?" Wani shakar iska yayi. "Bana son yawan tambaya. Ki kyaleni! Kaina ciwo yake mun!" Ya fada a tsawace yana wani daddafe kanshi. Ja da baya Nuri tayi dan tasan ba cikin hankalinshi yake ba. Allah kadai yasan abinda ya hadama cikinshi. Ficewa tai daga dakin kamun ya illatata.......! **** Girgiza kai yake ya kasa dauke idanuwanshi daga kan Nana. Ta ya ya samu ya'? Ta ina? Neme neme ya shiga yi cikin akwati nan da suke binne a kanshi. Possibilities yake nema na cewar Nana yarshi ce. Wata dariyar takaici safiyya tayi tana kallonshi. Tasan dole yai mamaki. "Ka dauka zaka iya tsarama kanka rayuwa ne? Saboda kai kake da iko da ita ko?" Bai damu da yanayin muryarta ba. Da tambayar da take masa da gayya. Ba ita bace a gabanshi. Yarinyar nan ita zuciyarshi keta dauka hotuna tana adanawa wajaje daban. A hankali yana sassarfa ya taka har inda nana ke tsaye da manyan idanuwanta irin nashi tana kallonshi cike da wani irin abu cikinsu. Kaman tana tsoron karasawo inda yake karya bace. Zai iya karantar shekarun datai tana jiran irin wannan ranar cikin idanuwanta. Kallonta yake. Baisan lokacin daya tsugunna kan gwiwoyinshi ba. Hannunshi na rawa ya dagashi ya taba kuncin Nana yaji ko ta gaske ce. Yaji ba rayuwa bace ke son yin wasa dashi kaman yanda ta saba. Ba wani rubutun kaddarar bane da yake tunanin kan dutse yake sai daga karshe gogewar shi ta zama tamkar akan ruwa. Ba wani farantin cike da farin ciki bane kaddara keson miko mishi saiya saka hannuwa biyu ya karba ta fisge hadi da mishi gwalo ba. Dumi yaji a hannunshi. Sosai ya dago dayan ya tallabi fuskar Nana. Yan hannuwanta ta sa akan nashi tana tabawa. Muryarshi a dishe can kasan makoshi yace mata. "Em real....." Saboda yanda yaga tana tsoron taba shi. Yan yatsunshi ta kama cikin nata ta dumtse. Wata irin ajiyar zuciya ta saki. Kamun ta saki yatsun nashi ta kai hannunta kan fuskarshi ta tallaba kaman yanda nashi yake a fuskarta. Rankwafawa tai ta hada goshinta da nashi tana kallonshi cikin idanuwa. Fu.ad zai iya rantsewa bai taba sanin wata nutsuwa kamar wannan ba. Zai iya rantsewa an halicci zuciyarshi ne kawai dan ta buga tazo dashi wannan lokacin ya tsinci kanshi da kaunar wannan yarinyar. Zai iya rantsewa babu farin cikin dayakai na ka dora idanuwanka kan halittar data fita daga jikinka. Safiyya dake tsaye gefe ta rike baki. Wasu hawaye ne suka zubo mata. Abinda take gudu kenan. Shine yake faruwa a gaban idanuwanta. Tana ganin yanda daga kallo daya fu.ad ya sace zuciyar Nana kaman yanda yaima tata. Tana tsoron abinda ya faru da ita ya faru da Nana. Domin iya wahalar duniya a shekarunta tagansu. Bata son ta hada da ciwon zuciyar rashin kaunar fu.ad. Dan tafi kowa shaida yanda radadi da rashinta suke. Tafi kowa sanin zafin abin. Ta kuma fi kowa sanin bashida zuciyar kaunar kowa banda kanshi. Nana kuwa tasha tunanin me yasa za.ace itace zata mutu bayan ga tsofaffi nan. Da duk wani hankali nata tayi tunani ta kasa gane kalar zabe na mutuwa. Tsoronta daya. Kar ta dauketa bata saka M a idonta ba koda sau dayane. Bata san dalilinshi na barin rayuwar mumynta ba. Bakuma ta damu ba. Abu dayane a zuciyarta a yanzun. Kaunar M wadda ta linka ta da da ganinshi. Sai take jin duk abinda ta rasa ta samu yanzun. Cikon kaunar da bata samu ba. Batasan lokacin da wata dariyar farin ciki ta kwace mata ba. Fu.ad jiyai zuciyarshi ta bude tana maraba dajin sautin dariyar Nana. Baisan dalilin dariyarta ba amman ta saka shi farin ciki marar misaltuwa. Shima baisan lokacin da dariya ta subuce masa ba. Sosai dariya suke su duka biyun kaman wanda suke cikin wani irin farin ciki. Girgiza kai safiyya take saboda batasan me fu.ad yake nufi da wannan abin da yake yi ba. Zata iya komai akan Nana ciki harda kareta daga fu.ad in har zai zama barazana ga farin cikin yarinyar. Duk da yanda zuciyarta ke mata wasi wasi da kokwanto da yawa bai hana yanayin su fu.ad saka zuciyarta wani matsewa ba. Cikin kanta take fadin. "Dan Allah karkimun haka. Karki budemun kofar da na dade da rufewa" A hankali sautin dariyarsu yake ragewa. Su ci gaba da kallon juna. Hannu nana tasa ta kara tallabar fuskarshi har lokacin goshinta na hade da nashi. Muryarta ta saukar dai dai kunnenshi. "Na dauka bazan taba ganinka ba" Wata irin iska yaji tana fita daga zuciyarshi. Kamun wani irin daci ya ziyarce ta. Janye goshin shi yai daga na nana ya maida kallonshi kan safiyya dake tsaye ta zuba musu idanuwa. Sannan ya sake kallon Nana. Lokaci daya ya tuno randa rabon Nana ya gifta. Randa zai tafi da suka hada gado da safiyya babu kariya. Wani irin duhu duhu yake ji na lillibe mishi zuciya da bacin rai. Shekaru goma sha daya ta boye mishi wannan abin. Yasan bata san ganinshi. Ta tsane shi. Nana ya ke kallo sosai. Amman ta boye mishi Nana abune da bazai iya yafe mata ba. Kula yai Nana na yamutsa fuska kamar wadda take cikin wani mawuyacin yanayi. Kallon fuskarta yake yana manta damuwar komai banda abinda ke sata yamutsa fuska haka. "Are you okay?" Ya bukata cikin taushin muryar da bai taba amfani dashi ga kowa ba sai ita. Wani irin numfashi take shaqa da sauri sauri kamun jini ya fara biyo hancinta idanuwanta su fara wani kakkafewa. Jiyai zuciyarshi na shirin tsayawa. Riketa yai dam a rikice ya kalli safiyya data karaso inda suke tsaye da gudu tana karbar nana daga hannunshi. Data riga da ta suma tun kamun karasowar safiyya. Girgizata safiyya take tana kiran. "Nana........" Hannunta fu.ad ya riko yana kallon safiyya a rikice yanajin zuciyarshi na wani irin dokawa. "Meya sameta?" Shiru tai ta kyale shi tana dube dube. A tsawace yace. "Damn it sofi magana nake miki. What the fuck is wrong with my daughter?" Kallonshi take tana jin yanda yake kure managing hakurinta. Akan Nana zaice zai mata ihu? Ashe ma me yake damun yarshi. A kufule tana kara jan Nana jikinta tace. "Da gaske kake? Ka ji me kake fadi kuwa? Yar' kafa kace fu.ad? Anya baka sha wani abu ba?" Dai dai shigowar Ansar. Ganinsu tsugunne yasa shi karasowa da sauri. Basu kula dashi ba suna watsama juna wani irin kallo dake nuna mintina kadan suka rage su farma juna. Bai ko bi takansu ba ya janye Nana daga jikin safiyya yana sabarta akan kafadarta. "Me kika tsaya yi haka safiyya. For goodness sake kin manta warning din Dr.Jana ne. Mtswwww.........." Da gudu Ansar ya fice da Nana. Safiyya ta dauki mayafinta zata bi bayanshi taji an riko mata riga an fizgota. Kallon shi tai a fusace. "Bana son neman rigima. Kabarni ya'ta tana bukatata......." Mikewa tsaye yai hannuwanshi kan kugu ya na kallon safiyya cikin fuska. Har wani huci yake saboda bacin rai. "Shekaru goma sha daya. Komin tsanar da kikaimun zaki iya fadamun ina da yarinya?" Bata da lokacin yin wannan rigimar. Tana juyawa ya sake shan gabanta. "Meke damunta da wancan mai katon kan ya sani ni ban sani ba?" Hade hannyenta tai waje daya muryarta na rawa. Idanuwanta cike da hawaye tace. "Please and please ba yanzun ba......" Da gudu ta fice daga dakin yabi bayanta. Ansar ya riga yai tafiyarshi. Bude motarta tayi ta shiga. Fu.ad ya bude gefe ya shiga. Bata da lokacin tsayawa masifar shi dan tasan ita yake ji. Dukan sitiyarin motar tayi ta bude ta fice da gudu ta koma cikin gida tana dauko mukullin motar. Ta dawo ta tasheta taja ta fita daga gidan. Can kasan makoshi batare daya kalleta ba yace. "A karo na ukku zan sake tambayarki meke damun yarinyata? And bana son yanda wancan ya dauketa kaman yanda iko akanta" Hankalinta nakan titi tace. "Mintinanka nawa da bayyana cikin rayuwarmu da har kake tunanin kana da wani muhimmanci a ciki? Ko kaga alamar na damu da abinda yai maka da wanda bai maka ba?" A fusace ya kalleta. Gaba daya ta canza. "sofi kar kice zakimun rashin kunya. Bance mun gama maganar nan ba......" Shiru tai ta kyale shi. Batai parking ko ina ba sai bakin asibitin. Bata jira fu.ad ba ta fice abinta. Binta yai shima. Ansar suka samu a waiting area yana tsaye yana ta kai kawo. Yace ma sofi. "Dr.Jana ta tafi gida. But Dr.james ke dubata. Basu cemun komai ba tukunna" Kallon su fu.ad yake. Yanda Ansar keyi zaka rantse shine baban Nana. Wani irin karyewa yaji zuciyarshi nayi. Shi ya kamata ace yana abinda yake ba wannan mai katon kan ba. Duk laifin safiyya ne. Ya dauka kara tabbatar da ta tsane shi zai masa ciwo sosai. Sai yaji baiji ciwon shi kaman yanda yake jin ciwon maye gurbinshi da wannan yayi ba. Safiyya ta cuce shi data boye mishi Nana. A hankali ya taka inda suke tsaye suna magana ita da Ansar. Tsakiyarsu ya shiga ya fuskanci Ansar. "Excuse me. In ba zata iya fada maka ba ni zan fada maka. Mungode sosai da karamcinka da kawo Nana asibiti. Family time yanzun. Ko zaka dan bamu waje" Kallon shi Ansar yake. Daga yanda yaji labarinshi baiyi mamakin maganganunshi ba. Badon shi yake tsaye anan ba. Ba kuma dan safiyya ba. Kaunar dayake ma Nana Allah ne kadai yasani domin shi ya halitta mishi ita. Murmushi yaima fu.ad yadan dafa kafardarshi sannan ya kalli safiyya yace. "Barin siyo wannan allurar in dawo...." Kasa cewa dashi komai tayi harya wuce. Wani kallo ta watsa ma fu.ad hadi da fadin. "Fadanka dani ce babu ruwan Ansar a ciki" Tabe baki yayi. Dr. james jana ta hango da sauri ta karasa wajenshi. Fu.ad na binta. Kallon safiyya yayi yace. "Na ba dad dinta ya kawo wata allura. She is stable yanzun. Zamu riketa anan gaskiya" Da sauri fu.ad yace. "He is noh' her dad. I am...." Da mamaki Dr. James ke kallon fu.ad. Kamun yace wani abu safiyya ta harare shi tace ma doctor din. "Karka damu dashi. Zan iya shiga in ganta?" Kai ya daga mata yace. "Eh amman banda hayaniya" "Nagode sosai....." wuce yai yana fadin. "Call me in an kawo allurar" Dakin da aka saba ajiye Nana safiyya ta nufa. Juyowa tayi taga fu.ad na biye da ita. Tsayawa tai ta lumshe idanuwanta ta ware su akanshi. "Bata bukatar kowa a kusa da ita sai family dinta......." Hannu fu.ad ya daga mata dan in taci gaba da magana zai iya kwada mata mari. Zagin da take masa ya ishe shi haka. "Wallahi a shirye nake da in birkita asibitin nan da duk wanda yake son gayamun bazan iya ganin ya'ta ba. Kaman yanda nake a shirye mu hau sama mu fado ni dake akan boyemun ita da kikayi....... Ki wuce muje kamun inyi abinda zamuyi dana sani sofi." Wani miyau ta hadiye. Tasan zai iya yin fiye da abinda ya fada. A hankali ta tura dakin. Nana na kwance kan gado jikinta jone da Na.urori. Da alamun bacci take. Yanzun da idanuwanta suke a rufe ramar datai ta sake fitowa sosai. Tsaye fu.ad yayi bakin kofar yana kallonta. Kaman ba ita bace ta gama dariya mintinan da suka wuce. Wani irin abu zuciyarshi take mishi. Baya sonta akan gadon nan. Baya son ganinta ko kadan. Yafison ganinta kaman yanda yaganta dazun. Kaman mai ciwon kafafu haka yake takawa harya karasa bakin gadonta. Zuciyarshi na rawa sosai. Tsugunnawa yai. Ya kama dan yatsanta guda daya a hankali saboda karin ruwan dake jikin hannun. Idanuwanshi dauke da wani yanayi mai nauyi ya kalli safiyya. Abinda tagani a fuskarshi bata taba ganin kalarshi ba a iya lokacin data sanshi. "Please sofi........." Lumshe idanuwanta tayi tana kokarin mayar da kukan da ke shirin kwace mata. Tun dazun take daure yanda ganinshi ya karya mata zuciya. "Leukemia take dashi........" Girgiza kai fu.ad yake yana so tace masa bata gaya mishi yarshi na dauke da cancer ba. Bata gaya mishi ya makara ba. "Akwai chemo sofi..........." Hawayen da take tarbewa ne suka zubo. Tasa hannu ta goge su kamun cikin raunin murya tace. "Sau uku ana mata chemo therapy. Ta rokeni saboda ba zata iya daukar wani ba......" Ta karsa maganar wasu hawayen na sake zubo mata. Mikewa yai ya fice daga dakin bai damu daya rufe kofar ba. Tafiya kawai yake batare daya san inda yake saka kafarshi ba. Baya ganin komai a gabanshi sai ciwon dake shirin rabashi da yarinyar dako cikakkiyar awa daya baiyi ba da saninta. Mutanen dake wucewa sai dai su su kauce masa dan baya ganinsu. Ansar ne yaganshi. Kafadarshi ya dafa yana fadin. "Lafiya?........" Baiko kalle shiba ya cire hannunshi daga kafadarshi ya wuce. Baya bukatar kowa. Baya bukatar kowa sai momma. Baya son gayama kowa damuwarshi sai lukman. Baya son kowa ya gaya mishi yayi kuskure sai haneef. Baya son kowa ya lallashe shi sai momma.............!!! *#TeamAS*        *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ       33 *Shout out to mutanen nan biyar. Dimples remember how much i don't like you. Ummie jay #IfYouKnowYouKnow. Miemiebee i want to be like you when am matured. Biebie Isa #AnaTare. Anty sis Nagode da dukkan karamci* Wani sama sama yake jinshi. Karar motocin dake wucewa can yake jinsu nesa. Saboda abu dayane kwakwalwarshi ke iya processing a yanzun. 'Yar' shi na da cancer'. Can sama sama yake jin kamar muryar sofi na kiranshi. Bai ko bi takanta ba saboda bata gabanshi a yanzun. Komai na rayuwarshi a gefenshi yake a ajiye. Nana ce kawai ya rike gam tun daya sauke idanuwanshi akanta. Da gudu safiyya ta karasa bata damu da mutanen dake wurwucewa ba. Tasha gabanshi. Kallonta yake ya daquna fuska alamar bai fahimci me take yi ba. "Badan na damu ba. Nana ta farka tana tambayarka........" Jin sunan nana yasa shi ware idanuwanshi akanta sosai. A tsorace yace. "No bazan iya ba. Bazan iya facing dinta ba.........." Kallonshi safiyya take yanda yake girgiza kai yana daga hannuwa. Lokaci daya taga girman da fu.ad yayi a jikine kawai da fuska. Har yanzun zuciyarshi akwai yarinta fal a cikinta. Sosai ta kalle shi. "Shisa nace karta sake ta saka a zuciya dan bakata da wajenta....." Wani abu yaji tun daga yatsan kafarshi ya taso mishi har cikin kirji. Safiyya na son kule shi ya kula. Baice mata komai ba ya juya ya na komawa hanyar asibitin. Dan karamin murmushi tayi tabi bayanshi. Har suka shiga cikin asibitin. Yana zuwa bakin kofar dakin da Nana take ya rike handle din yai tsaye. Gabanshi faduwa yake sosai. Nan safiyya ta karaso ta same shi. Kallonta yai kaman zaiyi kuka. "Em' scared sofi......." Sauke ajiyar zuciya tayi. Tana jin yanda duk inda ta cika da tsanarshi a zuciyarta ya fara gogewa. Sauke idanuwanta tayi. Ta karasa ta raba gefenshi ta tura kofar ta shiga tabarshi anan tsaye. Kaman mai ciwon wuya yadan zira kai ya leqa. Nana na zaune kan gadon suna hira da Ansar dake gefenta. "Mai katon kan nan bai tafi ba kenan......" Ya fadi kasa kasa. Shiga yai a ciki. Sai lokacin nana ta ganshi. Wani murmushi da tai mishi baisan lokacin daya mayar mata da martani ba. Karasawa yai har inda Ansar yake zaune kan kujera. Hannuwa yasa bayan kujerar yaja ta baya ji kake wani qiiiiiiiiii. Dariya ce ta kusan kubce ma safiyya ganin yanda Ansar ke ware idanuwa. Da alama ya tsorata sosai dajin yanda fu.ad yaja shi. Yarinta nacin fu.ad har yanzun. Bata kuma san ranar dazai girma ba. Ko kallon su fu.ad baiba ya zauna gefen gadon Nana. Hannu yasa yai cupping fuskarta yana kallon ta da murmushi a fuskarshi. "Na dauka ka tafi. Mum tace mun kana nan. Na kasa yarda ne kawai. Kayi hakuri bani da lafiya ranar daka zo...." Da sauri ya girgiza mata kai hadi da fadin. "Shhhhh Nana. Wani abu na miki ciwo? Em' here now. Komai zaiyi dai dai. Ni da ke zamu yaqi ko menene kina jina ko?" Wani irin tsalle zuciyar safiyya tayi jin kalmar nan ta 'ni da ke'. Mikewa tai da sauri ta karaso inda fu.ad yake. Cikin idanuwa ta kalle shi. "Ina son magana dakai" Ta buqata. Wani yatsina fuska yayi. "Ina jinki." Hanyar waje ta nuna masa da dan yatsanta idanuwanta cike da masifa. Kallon Nana yayi yace. "Yanzun zan dawo......." Ya karasa yana mikewa hadi da watsama Ansar kallon karka soma matsowa kusa da ita. Sannan suka fice shida safiyya. Tana jan kofar a hasale tace mishi. "Karka sake yi mata alkawurranka da babu komai a cikinsu sai karya. Zan iya yin komai akan yarinyata. Koda hakan na nufin nisantata dakai" Kallon da yake mata zai tsorata duk wani wanda baisan shi ba. Kamun yace. "Kinji me kike fada kuwa? Nisantata dani ai kin riga da kin gama. Bazan yafe miki ba inhar wani abu ya sameta. Akan me zaki boyemun ita?" Kallon shi take da mamaki. Har yana da bakin tambayarta dalili kenan. "I don't do happily ever after. Daga randa kika yarda da soyayyata ya kamata kisan banyi kalar wanda zai dinga zarya da yara da pampers ba.......! Ka tuna ko saina karasa maka?" Ta fadi tana jin wasu hawaye na son zubo mata. Dafe kai yayi. "Damn it sofi. Zaki rikeni akan maganar danai shekaru goma sha daya? Me kike dauka? em' noh' gonna accept her. Sofi me kika sha ne?" Kallon fuskarta yake. Yanzun kan wannan maganar da yayine zaisa ta boye masa yarinyarshi. Ji yake in baibar ganinta ba komai zai iya faruwa. Tambaya daya ce a ranshi yanzun. Dayaji zai bar mata wajen nan. Zai bar kallonta yana jin yanda zuciyarshi keyi kaman ta kama da wuta. "Akwai hope?" A hankali ta daga mishi kai. Bai jira komai ba ya juya ya shiga dakin. Yana shiga Ansar ya mike domin ana kiran magrib. A wajen ya samu safiyya yace mata zai wuce gida. Tai mishi godiya sosai sannan ta shiga ta samu fu.ad zaune gefe yana magana da Nana tana ta kyalkyalar dariya. "Bara inyo sallah in dawo" Mikewa yai saida ya watsa ma safiyya hararar data zabi tai biris da ita sannan ya fice. Ajiyar zuciya ta sauke. Cikin sanyin murya Nana tace. "Kome ya shiga tsakaninku yana da kirki sosai mumy" Shiru tayi ta kyale Nana dan wasu maganganun intana yi hankalinta ya girmi shekarunta. Itama alwala tayo ta dawo ta shimfida dankwalinta ta tashi sallah dan basu dauko komai ba garin sauri. * Tunda ya idar da sallah gabaki daya addu.ar shi ta yau babu kowa a cikinta banda Nana. Allah yake roqo daya hukunta duk laifikanshi ta wata hanyar yabawa Nana lafiya. Yana nan akai sallar isha.i sannan ya bar masallacin ya koma asibitin. Nana tana bacci. Baiko kalli safiyya ba balle tai tunanin zaice mata wani abu. A hankali tace. "Dan Allah ka duba mun ita inje gida in dawo........" Batare da ya kalleta ba ya amsa da. "Ba saikin tambaya ba" Bata ce komai ba ta wuce ta tafi. Hannun nana ya sa cikin Nashi ya hada kanshi da gadon zuciyarshi na mishi wani irin nauyi. Tun randa ya cika shakaru ashirin da biyu a duniya kamar wata takarda ce yasa hannu akai. A duk lokacin dayai tunanin ya samu farin ciki sai wani abu ya gifta mishi. Yana nan zaune har safiyya ta dawo. Ko sallamar datai bai amsa ba. Kanshi na hade da gadon Nana. Dan zatonta ma bacci yake. Abinci ta zuba tadan ci. A hankali taga ya dago. Wani plate din ta samu daban ta zuba mishi hadi da fadin. "Ka sakko kaci abinci" Sai lokacin ya kalleta. Kai ya girgiza mata. Tunanin saka ma cikinshi wani abu a halin dayake ciki ma neman saka shi amai yake. Kaman wadda tai mishi dole ya kara daquna fuska ya girgiza kai. "Naji ka da farko ai" Ta fadi tana maida abincin cikin warmer. Matsalarshi ce ko yaci ko karya ci bawai don ta damu bane ta bashi. "Daka tafi dare yana yi........" Kallon dake fassara kin samu tabin hankali yaima safiyya ya kauda kai gefe. Bashida lokacin asara akanta yanzun. "Kana jina fa" Runtsa idanuwa yai alamar ta takura shi sosai sosai kamun yace. "Karki sake batamun rai sofi. Bazai mana kyau ba wannan karin. Badon ke nake zaune anan ba. Saboda yarinya tane" Shiru tai ta kyale shi kawai. Ya mayar dakanshi jikin gadon ya kwantar hannun Nana na rike da nashi. Bata san koyai bacci ba ko baiyi ba. Shimfida ta gyara ta kwanta da mayafinta. A karo na farko da bacci ya dauketa in har suna asibiti da Nana. Dan zuciyarta a nutse take ta wani fanni daya bata mamaki. **** Saida tagama hada musu breakfast sannan. Ta dafa ma umar indomie ta soya mishi kwai ta sa mishi a warmer dinshi ta hada komai a basket ta ajiye mishi. Wucewa tai ta shiga wanka tabar atika ta shirya mata umar din. Sanda ta fito jabir na zaune yana danne danne da wayarshi. Bata bi takanshi ba ta cigaba da shirinta. Gaisuwa ce sunyita tun dazun. Saida ta gama shiri tsaf sannan ta karasa inda yake zaune. Fuskarshi ta rike cikin hannuwanta ta sumbace shi a gefen fuska hadi da fadin. "Ka kula da kanka please." A sanyaye yace mata. "kema haka. Ina sonki ki rike wannan" Murmushi tayi tana wucewa. Saida takai kofa sannan tace. "Allah ya bada sa.a ya tabbar da alkhairi........" Kasa jiran amsar jabir tayi tai saurin fita taja kofar. Bakin kofar ta tsaya hawaye suna siraro mata. Hannu tasa ta goge su tana karanto du addu.ar data zo mata. Sannan tasa glass dinta ta fice. **** Kitso akai mata bayan an wanke kan. Bata son wani kana nan kitso duk da wadatar gashi da Allah yai mata. Guda sha biyu akayi mai kyau sosai. Ta rasa meke damun nawaf. Yanda ya birkice jiya bata taba ganin hakan ba. Duk abinda yake bai taba zaginta ba. Amman yana yin bacci jiyan ma ya tashi shikenan. Kaman mai aljanu haka ya tashi garas. Sauke ajiyar zuciya tayi. Ta bude purse dinta ta biya kudin wankin kai da kitson da akai mata ta fito. Gicci tagani taji zuciyarta ta wani irin dokawa. Tsayawa tai ta rufe idanuwa tana karanto addu.o.i sannan ta bude su taci gaba da tafiya. Wannan bashi bane karo na farko da take tunanin taga farhan ba. Sai kuma tazo taga tunaninta ne ke wasa da ita. "Nuriyya......!" Wannan karin ba da wasa zuciyarta take ba wajen dokawa. Yau abin yayi yawa. Ci gaba tai da tafiya. "Nuriyya........." Taji an sake kira a karo na farko. Da sauri ta juya tako sauke idanuwanta kan kyakkyawar fuskar farhan. Girgiza kai take cike da rashin yarda. Babu ta yanda za.ayi ace farhan ne a gabanta. Yanda yaga tana kallonshi ya tabbatar mishi da cewar bata yarda shi bane ba. Ta kara girma sosai. "Nuriyya......" Da hawaye a idanuwanta ta dafe haba da hannayenta biyu tana kallonshi. Muryarta na rawa tace. "Yaya farhan......" Sauke ajiyar zuciya yayi. Yana gayama zuciyarshi da auren wani akan Nuriyya. Lokaci daya ya fara jero neman gafarar Ubangiji. Sauke murya yai yace. "Kina lafiya? Baki da matsalar komai dai ko?" Hawayen da take tarbewa ne suka zubo mata. "Yaya farhan yaushe ka dawo? Yaushe ka dawo ni bansani ba?" Da wani yanayi a zuciyarshi mai nauyi da yake kokarin dannewa yace. "Watana bakwai da dawowa. Ancemun kinyi aure shisa ban nemeki ba. Baki da matsala dai ko?" Ya karasa tambayar da damuwa sosai a muryarshi nason jin ko tana lafiya. Kai ta ke daga masa. Alamar eh. Lokaci daya taga ya sauke ajiyar zuciya kamar wanda aka sauke ma wani nauyi mai girma. "Ki zauna cikin farin ciki. Shine kawai burina. Bai kamata mu tsaya anan ba. Naganki ne bazan iya jure kin miki magana ba......." Ta kasa cewa komai banda hawayen da take wani nabin wani. Ganin farhan ya mata dadi. Don tana yawan tunanin ko yana raye ko akasin hakan. Murmushi tai mishi tasa hannu tana goge fuskarta. Kaman ance idonshi yakai kan gefen fuskarta da har lokacin hannayen nawaf na kwance rudu rudu a wajen. Ga wani jini dayake kwance a saman goshinta. Cike da tashin hankalin farhan yace. "Dukanki yai nuri?" Cikin hanzari ta girgiza kai. Karshen abinda zata so shine nawaf yama ji taga farhan. Idanuwa a kankance farhan yace. "Ki fadamun idan yana dukanki. Karkiji tsoron komai" Kai ta sake girgiza masa idanuwanta cike da hawaye. Dubawa yake gefe gefe ya hango wani kanti. "Ki jirani anan. Ina zuwa......" Da gudu ya karasa wajen shagon ya siyo biro da littafi. Ya yagi takarda ya rubuta mata number din wayarshi sannan ya dawo. Mika mata yayi ta karba. Ya kalleta sosai cikin fuska yace. "Ban damu dako dan waye ba. Ko waye shi. In ya tabaki ki kirani." Kai ta daga mishi. Dakyar ya iya juya ba tare da ya sake ce mata komai ba saboda inhar zai tsaya ya kara ganin wannan kwanciyar jinin a fuskarta za.a iya samun matsala. * Ganin ya dawo da wuri yasa shi son suprising nuriyya yaje ya daukota a saloon. Ya hangota tsaye da wani da baisan kowaye ba. Wani irin duhun kishi ya lillibeshi. Nuriyya tashi ce shi kadai bata kowa ba. Yana cikin mota yaga wancen ya wuce. Ita kuma ta karasa bakin titi ta tare napep ta shiga. Jan motar yai da gudun gaske ya wuce.............! **** Shiryawa take maganganun Abbah na mata yawo. "Kina son saka yaron nan a ranki. In muna ranshi aida ya waiwaye mu. Kinsan bazan hanaki ba idan kina son zuwa kije. Allah shi kyauta" Sauke numfashi tayi. Ta saka hijab dinta. Haneef ta kira a waya ringing din farko ya daga hadi dayin sallama. Ta amsa mishi ta dora da. "Haneef ka sake fadamun address din gidan fu.ad yanzun zan tafi......" "Banida wani aiki sosai momma. Ki jirani sai inzo in kaiki" Ta amsa da. "To shikenan Allah ya kawoka" Ta kashe wayar bayan ya amsa ta da amin. Ta zauna tana jiranshi. **** Lukman na zuwa office ya kira hamza a waya. Dan haneef ya fada mishi duk me ya faru. "Hello...." Hamza ya fadi ta dayan bangaren. "Hamza ya gidan da iyali duka?" "Alhamdulillah ya naka?" "Duk suna lafiya. Daman abin nan ne daka turomun. Ban samu na kira ba sai yau......" Da hanzari hamza yace. "Wallahi abin yana raina. Ina son ka tabbatar mun ne tukunna" Dan gyara zama lukman yayi kamun yace. "Yar shi ce da gaske hamza. Yanzun haka maganar da muke yana gari" Yanajin numfashin da hamza yaja kamun yace. "Akwai damuwa. Ni ta yanda zan fadama hussaina ne matsalar. Nafison taji daga wajena" Yar dariya lukman yayi. Rigimar hussaina da fu.ad banbancin su kadanne. "Kunfi kusa. Daman abinda zan fada maka kenan" Sake sauke numfashi hamza yayi. "Ba damuwa. Nagode......." Wayar ya ajiye. Shi kanshi inba ganin yarinyar nan yayi ba hankalinshi ba wani kwanciya zaiyi ba. Wasu yan ayyuka ya karasa da suke gabanshi sannan ya tashi yaje yai report cewar bayajin dadi zai tafi gida. Haneef ya kira yake fada masa shima yanzun ya dauko momma gidan zasuje. Suka tsayar da magana cewar su hadu acan din. **** Tunda safe yana yin sallar asuba ya dawo baice ma safiyya komai ba ya dauki mukullin motarta dayake ajiye a gefe ya fice. Hotel din ya koma yai wanka ya sake kaya. Ko awa daya baiyi ba yagama komai ya fito. Rasa me zai siyawa Nana yayi. Hakan yasa shi siyo mata gasasshiyar kaza da fresh milk da alkawarin zai tambayeta mai ta fiso. Hakan kawai ya wani tokare masa a wuya. Yarshi baisan me tafi so ba. Kawai dan safiyya ta boye mishi ita duk shekarun nan. Haka ya koma asibitin da sake sake da yawa a zuciyarshi. Doc din Nana ya samu tazo. Tace musu zata duba wasu marassa lafiyan. Zatai magana dasu nan da awa daya. Safiyya tai mata godiya ta fice. Idanuwa fu.ad ya sauke a kan safiyya hadi da fadin. "Bata tashi ba har yanzun?" Kai ta daga mishi ta amsa tambayarshi da. "Alluran da akai mata ne. Zata tashi dasun sake ta" Waje ya samu ya ajiye ledojin dake hannunshi. Ya zauna kan kujera ya zubama Nana idanuwa. Safiyya bata san lokacin da ta tsinci kanta da cemishi. "Ka karya?" Kai ya girgiza mata alamar a.a kamun yace. "Bana jin yunwa ko kadan" Lumshe idanuwanta tayi ta ware su akan fuskarshi da take kan Nana kaman kallon da yake mata ne zaisa ta bude ido tace. "In har kana son kula da ita kana bukatar lafiyarka. Kaci wani abu saboda ita" Kai ya girgiza mata. Kanshi ciwo yake mishi. Baya son cin komai. Bata bi ta kanshi ba. Haka ta zuciyarta dake son ja mata matsala. Tea ta hada mishi mai kauri. Ta mike tsam taje ta ajiye a gabanshi. Takoma ta zauna. Binta yai da kallo sannan ya maida hankalinshi kan cup din tea din. Ya dauka ya soma kurba a hankali. Dakin shiru kamun wayar sofi ta dauki ringing. Yana kallonta ta daga hadi da yin sallama. "Wallahi bama gida. Muna asibitin imzad......" Shiru yaji tayi kamun ta sake cewa. "Eh shi...." "To ba damuwa. Allah ya kawo ku" Ta sauke wayar. Ta kalli fu.ad daya zuba mata idanuwa. Duk da bai tambaya ba tasan bayani yake jira tai mishi. "Momma da su hanif ne. Suna hanya" Lumshe idanuwa fu.ad yai yana ajiye cup din tea din gefe hadi da fadin. "Fuck........" Kallonshi sosai safiyya tayi tana jin wani sabon mamaki na kamata. "Fu.ad......." Ta kira a hankali. Kallonta yai yana daga girarshi duka biyun. "Karka cemun suma........" Kasa karasa tambayar tayima dan batasan ta ina zata fara ba. Ya fahimci so take taji in har su momma ya bari duk shekarun nan. Cike da takaici yace. "Me kike tsammani? Bakwa son ganina ku dukanku" Dafe kai tayi tana salati a ranta. Tun zuwan haneef ta karanci hakan tadai ki yarda ne kawai da zarginta sai yanzun. To meye na damuwa tunda ma kowa nashi yabari. Har yan uwanshi dan ita yabarta ba tare da juyowa ba sai me. Bata jin komai game dashi sai kudin da yake turowa account dinta lokaci lokaci. Wanda tunda ta samu aiki bata kara tabawa ba sai da Nana ta soma rashin lafiya. * Ta wani fannin fu.ad yaji dadi sosai. Saboda tun jiya su yake bukata. Shi bai saba kalar wannan tashin hankalin ba. Daurewa kawai yake yi yana dannewa a zuciyarshi. Karin abin jiya sofi tace mishi akwai hope. Suna nan zaune doc jana ta leko tace su bita office. Ganin safiyya ta wuce ya sa shi mikewa hadi da fadin. "Ita kadai zamu bari?" Ya karasa maganar yana kallon Nana. Doc jana tai murmushi tace mishi. "Karka damu. Ba zata farka dan yanzun ba." Shikam duk da haka bayason barin wajen Nana kona minti biyar. A haka yabisu har office din doc jana. Suna zama ya kalleta yace. "Bana son all nasihar nan da dogon zance. Kawai ki fadamun abinda ake bukatar yi. Koma menene" Kallon safiyya tayi tadan daga mata kai alamar babu damuwa kawai tai mishi magana. Cikin nutsuwa take mishi bayani da kuma stage din da cutar Nana takai. Ji yake har wani zafi zafi jikinshi yakeyi mishi. Bayason bayanin nan. Muryarshi can kasa ya katse doctor jana da fadin. "Do mi' a favour. Muje wajen maganar solution....." Sauke ajiyar zuciya doc jana tai sannan tace. "Hemotopoietic stem cell transplantation (HSCT) sai dai yana da hadarin gaske ga wanda zai donating din. Sannan a stage din......." Hannu ya daga mata hadi da fadin. "Kawai ayi komenene. Kome kuke son cirewa a jikina. Kawai ta warke shine bukatata" Kallonshi safiyya keyi zuciyarta na wani irin yawatawa. Komai na kwance mata. Bata taba zaton fu.ad zai damu bama dahar zai baro duk inda ya tafi yazo. Da yazo bata taba zaton zai kalli nana ba ballantana tayi tunanin zai bada hadin kai. Muryar doc jana ta katse ta da fadin. "Zamuje dakai yanzun. Za.ai running wasu tests mugani ko zaka zama match" Bawani bata lokaci fu.ad yabi doc jana suka bar safiyya nan da mamaki matuka a fuskarta da zuciyarta duka. Tana sake jin yanayin nan na jiya dake goge mata tsanarshi a wasu bangarori data adana na zuciyarta. Mikewa tai ta fito daga office din kenan wayarta ta kama ringing. Tana dubawa taga haneef ne. Fita tai waje batare da tayi picking ba dan tasan sun isone shisa suke kiranta. A waje tagansu su uku. Momma da haneef da lukman. Da fara.a a fuskarta ta karasa inda suke ta gaishe dasu. Momma ta amsa ta da. "safiyya daman kina nan?" Shiru safiyya tayi tana sadda kanta kasa. Sai yanzun take ganin rashin kyautarwa abinda tayi. Koba komai momma ta nuna mata kauna da karamci. Amman a lokacin bata son ganin su ne. Gaba daya laifin fu.ad ya shafesu. Tuna hakan kawai taji tsanar shi na sake dawo mata. Dafata momma tayi tace. "Abinda ya wuce ya wuce. Muje inga jikata" Babu musu tai gaba suna binta a baya har dakin da Nana take. Momma ta zauna zuru tana kallon Nana da yanda kamaninsu suka baci da fu.ad. Ta rasa me zatace. Addu.a tai mata ta mike ta kalli haneef tace. "Haneef ka mayar dani gida. Mun dawo anjima........" Ta karasa muryarta na rawa. Dan ganin Nana ya karya mata zuciya sosai. Ga kewar dan nata data addabeta. Lukman ne yace. "Ina fu.ad din?" Sannan yazo ma momma data tambaya. Suka zuba mata idanuwa su duka ukkun. "Yana wajen......." Bata karasa ba ya turo kofar da sallama. Idanuwanshi suka tsaya kan momma da itama ta zuba mishi ido. Wata irin kewarta da muryarta kawai da yakeji lokaci lokaci bata cike mishi ta taso. Wani irin abu yakeji da baida kalmomin dazai dora shi akai. A hankali kafarshi ke takawa har ya karasa inda take. Hannuwanta ya kama ya dumtse cikin nashi. Ya kasa magana saboda yanda yakejin wani abu na shake mishi wuya. "Fu.ad." Momma ta furta a hankali tana jin yanda wasu hawaye ke taruwa a idanuwanta. Ya kara girma ya zama babban mutum. Hannunta yakai bakinshi ya sumbata har lokacin ya kasa magana. Saidai idanuwanshi dake fada mata yanda yai kewarta. Yanda rashinta yafi tabashi fiye dana komai. Idanuwanshi suka bar fuskarta zuwa cikin dakin. Haneef yagani tsaye ya jingina da bangon dakin yana kallonshi. Wani irin dokawa zuciyar fu.ad takeyi. Hannuwan momma ya saki ya taka kafafuwanshi kaman anyisu da dutse saboda nauyin da sukai masa. Gaban haneef ya karasa. Duk yanda yake gayama kanshi baiyi kewar dan uwanshi ba ya karyatu a yanzun. Kauda kai haneef yai gefe. Fu.ad din ya matsa inda ya mayar da fuskarshi. Ya sake kaudata gefe alamar baya son ganinshi. "Haneef........" Ya fadi kaman zaiyi kuka. Sai lokacin ya ware idanuwanshi kan fu.ad din. Yana neman duk wani haushin shi da yake ji yana rasawa. Hannuwanshi yakai ya kama kunnuwanshi yanda yakanyi insuna yara sosai yama haneef din laifi. Ganin yai kasa yana shirin tsugunnawa yasa haneef saurin dagoshi. Da sauri fu.ad ya kalle shi. "Please........" Ya fadi da take tattare da wata irin kauna da ban hakuri da yakeji har ranshi. Hugging dinshi haneef yai suna sake ajiyar zuciya. Lukman kallonsu yake. Yanzun ya tabbatar ko dan uwanshi da suka hada jini iya kaunar daza mishi kenan. Ba kadan yai kewar abokantakarsu da kaunarsu ba. Karasowa yai kusa da lukman da wannan murmushin yana daga mishi gira duka biyun. Wani irin naushi lukman yakai mishi ya tare da hannu. Yarfe hannunshi ya shigayi yana dakuna fuska. "Wannan na rashin bawa kowa zabi ne....." Haneef ne ya fara dariya kamun fu.ad din sannan lukman. Ba karamar kewarshi sukeyi ba. Muryarshi na rawa yace. "Kuncika son kanku. Shine ko sau daya baku taba kirana ba" Wannan karon har haneef ne ya taho da niyar kawoma fu.ad din naushi ya ruga ya boye bayan momma. Girgiza kai tayi tace. "Ku kyalemun yaro mana" Zama sukai su dukansu. Sai yanzun yakejin shi wani iri. Kaman an rage mishi wani irin nauyi a zuciyarshi. Fada musu yake Nana zataji sauki dan doc tace mishi jibi zasu dawo su karbi result din. Safiyya dai na gefe tana ta kallonsu. Karo na farko tun da nana ta fara rashin lafiya da bataji ta ita kadai ba. Hamdala takeyi a zuciyarta. Muryar Nana sukaji tace. "Mumy....." Gabaki dayansu suka tashi suka zagayeta. Daya bayan daya take kallonsu. Haneef taima murmushin nan nata. "Nasanka" Dariya haneef yayi. Ya ja mata hanci a hankali. "Inye ashe kina gane mutane haka. Kinsan sunana?" Kai ta dan girgiza. "Uncle haneef." Ya kalli lukman dake gefe yace. "Wannan kuma uncle lukman" Wani gagging sound fu.ad yai dayasa haneef harararshi. Taya za.ace fu.ad nada yarinya baya shi kanshi yarinta na cikinshi. Kallon haneef momma tayi tace. "Kanku kawai kuka sani ko?" Dariya sukayi. Nana na kallon momma tace. "Granny......." Fu.ad yai dariya hadi da fadin. "Momma an tsufa. Kinga tagane ki babu wani introduction" Safiyya bata san lokacin da hawaye suka zubo mata ba. Tayi kuskure sosai data boye musu Nana. Jibi yanda suke nuna mata kauna kaman su karbe mata ciwon dake jikinta. Son kanta ne yasata boye musu ita. Ca sukai zasu tafi da alkawarin zasu dawo da yamma in ba.a sallame su ba. In an sallamesu zasu zo gida. Iya kofa fu.ad ya rakasu dan yanda Nana ta farka bayajin zai iya matsawa ko ina. Safiyya ce ta tafi ta rakasu. Fu.ad ya koma gefen Nana ya zauna yana ce mata: "Sannu. Banson mai kike so ba ina son siyo miki dazun dana fita" Dariya Nana tayi dayaji har sautinta har zuciyarshi. "Ni komai inaci fa. Kaban labari" Yadanyi shiru kaman yana tunani kamun yace. "Wanne iri?" Yanda ta daquna fuska yaji zuciyarshi har wani tsalle tsalle take. "She is so damn cute" Ya fadi a zuciyarshi kamun Nana tace. "Kowanne iri. About you and mum" Ware idanuwa yai sannan yai kasa da muryarshi yace. "Amman sirrine fa" Dariyar ta sake yi. Ta mika mishi karamin yatsanta hadi da fadin. "bazan fadi mata ba i promise" Dariya sukai su duka sukaji safiyya ta turo kofar. Su dukansu suka ware idanuwansu akan ta iri daya. Hade fuska tayi. "Gulmata kuke ko?" Kallon juna sukai sannan suka girgiza kai. Wani irin sama taji numfashinta yayi. Komai nasu iri dayane. Karasawa tayi ta zauna daga dayan gefen gadon. Ta sumbaci goshin nana. Dariya nana tayi kadan dan tasan so take taji ko da zazzabi a jikinta. "Zakici wani abu?" Kai Nana ta daga mata alamar eh. Ta dora da fadin. "Nagaji sosai. Ina anty jana mu tafi gida" Kai safiyya ta girgiza mata tana hade rai. Fu.ad ya kalleta yace. "wacece anty jana?" A dake safiyya ta amsa shi da. "doc dinta" Mikewa fu.ad yayi haryakai kofa safiyya tace. "ina zaka?" Kallonta yai da yake fassara da gaske tambayata kike. Kamun yace. "Bakiji me Nana tace bane? Gida take son zuwa" Da mamaki safiyya tace. "sai kuma akace abinda take so shi za.yi mata. In lokaci yayi zasu sallameta ai. Rigima ce kawai" Tabe baki yai alamar wannan bai dameshi ba. "Gida take son zuwa. Bandamu ba koda hakan na nufin a kwashi duk abinda ke cikin asibitin zuwa gida." Bai jira me zatace ba ya fice abinshi. Nana tai mata wani murmushi har hakoranta suka fito hadi da fadin. "I love him......." Harararta safiyya tayi. *#TeamAS* *#AnaTare* *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ              34 *#AnaTare* *Nagode da fatan alkhairinku a gareni. Ina jin dadin comments dinku da yanda kuke nuna kaunarku ga littafina* Da sallama ya tura kofar yana shiga dakin gefen gadon Nana ya zauna. Idanuwan nan nata ta ware kan fuskarshi. Yai mata murmushi hadi da fadin. "Ruwan nan kawai zai kare mu tafi gida" Safiyya dake gefe taja numfashi tare da cewa. "Me kaje kayi?" Cikin fuska ya kalleta. Ya wani yi narai narai da idanuwa. "Nikam me zanyi?  Rokonta nai kawai" Tabe baki safiyya tayi dan tasan roko yana karshen littafin fu.ad da ba kowane yake gani ba. Da fara.a Nana tace. "Thank you M" Da confusion yake kallonta. "M?" Ya maimata da alamar tambaya. Puppy eyes Nana tai tana fadin. "Oh-oh......" Daga mata gira fu.ad yai yana dan daquna fuska alamar ita yake jira tai masa bayani. Kallon safiyya tayi tadan daga mata kafada dake nufin ita ta fara saita karashe. Sauke numfashi Nana tayi. Cikin sanyi murya tace. "Mumy ta fadamun kana stunts da. And ana kiranka da Moh. Ina tsoron kar in claiming wani dangantaka tsakanin mu kaqi dawowa. Shine nake kiranka M. M koda yaushe" Wani abu yaji yai squeezing a kirjinshi. Safiyya ya zuba ma idanuwa yana tunanin meye abinda ta gaya ma Nana dazai saka ta wannan tunanin. Tambayar shi take karanta cikin idanuwanshi batare daya furta ba. Hade fuska tayi dan bata son meyake so da ita ba. Bayan ya watsar da ita tsahon shekarun nan. Tun dawowarshi safiyya ke bata mishi rai. Kaman duk tsahon shekarun nan data ja mishi nisanta da ita bai ishe shi ba. Saita kara da saka ma yarshi wannan tunanin. Baisan lokacin dayace. "Shekararta nawa?" Yana jin wani zafi a kirjinshi. Batare da fahimtar dalilin tambayarshi ba safiyya tace. "Eleven...." Lumshe idanuwanshi fu.ad yayi yana dafe goshin shi dayake jin wasu abubuwa na mishi yawo. Shekaru sha daya na rayuwar Nana ya rasa. Mikewa yai. Yana son fita yadan sha iska kamun ya fadi wata maganar da baya so Nana taji. Jiyai an riko hannun shi. Juyowa yai ya kalli Nana da idanuwanta suke cike da hawaye. Girgiza mishi kai tayi. "I am sorry na kiraka M. Bansan wanne suna kake so ba. Please karka tafi" Wani irin rauni zuciyarshi tayi. Numfashi yake fitarwa da sauri sauri saboda yanda yake jin gara ace asibitin nan ne ya baje da hawayen dake cikin idanuwan Nana. Da sauri ya samu waje gefenta ya zauna. Hannuwanshi yasa ya tallabi fuskarta. Muryarshi a dakushe yace. "Babu inda zani Princess. Ina nan tare dake........." "Ummmm" Safiyya ta fadi alamar bata kama zancen ba. Yana jinta hakan kuma ya mishi ciwo ba kadan ba. Zai sauke mata in basa gaban Nana. Zai iya daukar duk rashin kunyarta data koya yanzun. Banda gaban Nana. Karshen abinda zaiso shine tasa ma yarshi yi mishi wani kallo na daban. Mikewa safiyya tayi ta fice ta na dan doko kofar da karfi. Yabita da kallo kamun ya mayar da kallonshi kan Nana datai murmushi tace. "Karka damu. Na yarda dakai" Ware idanuwa yayi. Kamun yai yar dariya. She is smart. Ya fadi cikin zuciyarshi. Kamun yace wani abu Nana tace. "Zaka zauna damu?" Dariya yayi. "Kina son mumynki ta yankani ko?" Dariya take sosai. Inda rayuwa zata tsaya a haka zai iya cewa farin cikin data miko mishi mai dorewa ne. * Dr. Jana na hango safiyya ta karasa wajenta hadi da fadin. "Naso mu rike Nana sai zuwa gobe. Bazan iya masifar babanta ba" Sauke ajiyar zuciya safiyya tayi. "Dan Allah kiyi hakuri......." Murmushi Doc jana tayi mata hadi da fadin. "Karki damu. Ko zazzabi kikaji jikinta ku dawo. Abin na spreading da sauri fiye da yanda muke zato" Wasu hawaye suka ciko idanuwan safiyya. Addu.a take Allah yasa fu.ad yazo dai dai da abinda ake bukata. Dafa mata kafada doc jana tayi sannan ta wuce. Mayafinta ta janyo tana goge idanuwanta. Sannan ta wuce ta koma. Zaune ta same su fu.ad yana ba Nana labari. Kallonsu take. Ta kasa nutsuwa dashi. Tana tsoron kar tarihi ya maimaita kanshi. Wata zuciyar tace koma menene yaxo ai. Kuma yana nan yana son taimakon Nana. Zatai focusing akan wannan kawai. Zata danne son shake shin da ke taso mata. Zatai kokarin boye abinda ya faru tsakaninsu inda yake duk shekarun nan. Gyara zama tayi tana kallonsu. Da yanda sukai kama ba yar kadan ba. Ko mintina goma ba.ayi ba ruwan dake jikin Nana ya karasa karewa. Tasowa safiyya tayi ta kashe. A tsorace fu.ad ya kalleta. "Me kikeyi?  No kirawo doc suzo su cire mata" Kallon da gaske kake? Safiyya tai mishi kamun ta koma kan abinda take kokarin yi. Mikewa yai a dake yake fadin. "Da gaske nake. Ba aikinki bane ba zaki tabamun yarinya ba...." Wata dariyar takaici tadan kwace mata. Karfin hali take kallo kiri kiri. Yana son nuna mata yafita damuwa da Nana ne. Riko hannunshi Nana tayi hadi da fadin. "It's ok. Tana ciremun wani lokaci" Girgiza ma Nana kai yayi idanuwanshi na kafe kan safiyya hadi da fadin. "Lokacin bana nan ne......" Bude baki tayi zata amsa shi. Doc jana ta shigo dakin. Hankalinshi fu.ad ya mayar kan ta da cewar. "Wanne doka ya baku damar barin wanda ba doc ko nurse ba taba marar lafiya?" Safiyya ta kalla. Dan batama gane kan tambayarshi ba. "Ignore him. Yana jin dadin magana shi kadai wasu lokuttan" "WTF sofi." Idanuwanta ta ware mishi dake nuna a shirye take ta biye mishi su kwashi yan kallo gaban Nana. Mayar da maganar da yake shirin yi yayi. Doc Jana ta wuce ta zare ma Nana ruwan. Ta cire abin daga hannunta tasa auduga tana danne wajen kamun ta sakarma Nana. Da sauri fu.ad ya kamo hannun yana saka audugar ya danne mata. "Sannu." Murmushi Nana tayi. Tana kallon yanda yake dakuna fuska kaman abin a hannunshi yake. Hakan kuwa yakeji har ranshi. Doc jana tace. "Please ko ciwon kai take ji ku dawo da ita." Kai suka jinjina mata su duka biyun ta kalli Nana tace. "Allah ya kara sauki" Da murmushina fuskarta ta amsa da. "Amin anty jana. Meke damunki?" Da mamaki sosai Doc Jana ta kalli Nana. Sosai take jin mamakin tambayarta. Hakan yasa Nana fadin. "Ko yaushe kina mun hira har ki gama dubani. Banda yau da safe da yanzun kuma. Kina kawomun milkshake ko zuwa mukai ban kwana ba. So kawai wani abu na damunki" Lumshe idanuwa doc jana tayi. Tana bude su kan safiyya. Allah ya bata yarinya mai tattare da baiwa kala kala. Safiyya tace. "Nana....." Hannu doc jana ta daga mata alamar babu komai. Tsakaninsu ne. Hankalinta akan Nana tace. "Yeah wani abu na damuna. Karki damu i will be ok. Sorry ban kawo miki milkshake din ba. Kina bina ok?" Murmushi tai har hakoranta suka fito. "Alright nagode anty jana. Kiyi addu.a komai mai wucewa ne tunda kina da lafiya" Wannan karin fu.ad ne ya ware idanuwanshi kan safiyya da tambayar haka Nana take so smart ko kuma shi kadai ne ya kula. Kai tadan rausayar gefe da nufin. Haka nake fama. Murmushi yai dayakai har zuciyarshi. Mouthing ma safiyya yai. "She is my daughter" Dake nuna dole ta zama smart. Wato ta biyoshi. Dariya safiyya tai data janyo hankalin nana da doc jana kanta. Ta dan hade fuska. Mikewa doc jana tayo batace musu komai ba ya fice. Rankwafawa fu.ad yai ya kama Nana yana dorata kan kafadarshi. Dariya ta kamayi tana fadin. "Ka sauke ni zan iya tafiya da kaina fa......" Girgiza mata kai yayi. Yana kara yara mata zama a kafadarshi. "Princess basa tafiya da kafarsu" Dariya take sosai. Safiyya yake kallo tana tattara kayyakinsu cikin wata jaka. Karasawa yai yana kokarin daukar jakar. Ta janye hadi da watsa mishi wani kallo. "Bana so" Dan daga kafada yai alamar matsalarta ce. Ya wuce ya hude kofar ya fita da nana dake ta mishi surutunta. Sauke ajiyar zuciya safiyya tayi. Lokaci daya ya shigo rayuwar Nana ya sace zuciyarta. Yanda yan uwanshi sukai mishi dazun bai bata mamaki ba. Son shi baya bari aga laifinshi. Wannan a jininshi yake. Daukar jakar tayi da mukullin motarta daya ajiye gefen gadon nana tabi bayansu. Tsaye ta same fu.ad nana nakan kafadarshi. Bude musu motar tayi. Baya ya bude ya saka Nana shima ya shiga. Kallonshi tayi. Ya wani kauda ido. Ita zata tuqa. Inda yake zaune nan Nana zata zauna. In tsarin bai mata ba ta dawo baya su koma gaba. Ta karance shi tsaf dan haka ta zagaya ta bude motar ta shiga ta tayar tana daukar titi. **** Tana shiga cikin gidan taga motar nawaf. Lumshe idanuwanta tayi tana sauke ajiyar zuciya. Tsayawa tayi na wajen mintina biyar tana kokarin mayar da fuskarta dai-dai. Ganin farhan ba karamun shock yazo mata dashi ba. Ta kuma san nawaf kaman yunwar cikinta. Yana karantar komai a fuskarta. A hankali ta taka zuwa cikin gidan ta tura kofar da sallama. Yana jingine da bango a tsaye. Ya dago idanuwan nan ya sauke su akanta. Yanayin su tagani tai tsaye taki karasawa ciki. Takowa nawaf yayi yazo daf da ita yana fitar da numfashi da sauri da sauri. Muryarshiba dakushe yace. "Waye kuke tsaye dashi a bakin saloon?" Wani irin dumm taji cikin kunnuwanta kamin zuciyarta ta dauki duka. Tambayarshi ta girgiza ta. Abinda ta tsaya tana kokarin boyewa ne. A tsawace ya ce. "Tambayarki nake nuri" Ja tai da baya kadan. Ya damqo hannunta kaman zai karyata. Kokarin kwace hannunta takeyi ta kasa. Jijjigata yayi yana fadin. "Dawa kike magana Nuri? Waye shi?" Cikin kuka tace. "Ka sakemun hannu....." Mari ya dauketa dashi yana kara jijjigata. "Ki fadamun waye kike tsaye dashi?" Batasan lokacin da wani karfi yazo mata ba. Ture shi tai gefe tana sakin wani irin kuka. "Farhan ne!!! Saika kyaleni yanzun ko?" Ta karasa maganar tana goge fuskarta. Wani irin abu zuciyarshi takeyi. Duhun nan ya cika mishi kai. Janyota yai ya hadata da bangon dakin. Yaci gaba da dukanta kunnuwanshi basa jin ihun da Nuri keyi. Maigadin gidan yaji ihun yai yawa daga inda yake ya shigo yaga ko lafiya. Salati ya saka yana kokarin janye nawaf. Amman kaman ma sake tunzura shi yake. Tun Nuri na ihu harta daina saboda ta yi laushi ba kadan ba. Dakyar maigadi ya janye nawaf daya fice daga gidan dan in yana ganin Nuri baisan abinda zai iya faruwa ba. Girgiza kai kawai maigadi yayi daya ga Nuri ta motsa ya fice. Dan shigowar dayai ma ba huruminshi bane. Jiyai abin sai addu.a. Da bala.in karfin hali tana hawaye taja jiki ta janyo jakarta dake gefe. Kuka take sosai. Ta tabbatar nan gaba nawaf kasheta zaiyi. Tana jure komai ne saboda bata da inda zata juya ma. Mamanta ce. Ita kuma data koma gidan karuwai gara ta mutu a gidan nawaf. Ganin farhan. Ganin farhan yasa taji tana da zabi. Rayuwa a gidan nawaf da yake tunanin zai jigeta a duk sanda yai niyya saboda ya mata alfarma ta aurenta. Yanzun take ganin komai a saman farar takarda. Bakin rubutun kaddarar auren nawaf daro daro. Yanzun ta sake tabbatar da yan uwan nawaf sunsan dan uwansu mai lafiyane ba zasu taba bari ya auri yar gidan karuwa da ba asan asalinta ba irinta. Koda kuwa liman ne rataye saman kanta saboda kamun kai. Hakan da karin bata da inda zata yasa take shanye duk dukan nawaf. Yai mata alfarma mai girma. Amman itama ta mishi. Tana tare dashi a duk cutar shaye shayen dake damunshi. Tana tare dashi a duk wannan stage din. Ita ta bashi kwarin gwiwa ta zame mishi mudubi a lokacin da bashida inda zai duba fuskarshi. Ita ta zame mishi titin daya hau yagane hanya lokacin daya bace. Itace silar shi zuwa rehab.  Har aka shawo matsalar shi ta shaye shaye sannan sukai aure. Sannan yan uwanshi suka kauda kai daga mugun gidan da ta fito domin sunsan in babu ita zai iya komawa inda babu wanda zai iya taro shi. Dafa kasa tai da niyyar tashi wani irin ihun azaba ta saki jin wani zogi datai yana har cikin ranta. Hannunta ta rike da dayan tana juyi saboda azaba. Kuka take sosai. Dayan hannun mai lafiyar ta dafa dashi ta mike zaune hawaye na zubo mata. Ko ina na jikinta ciwo yake. Mayafinta dake gefe ta janyo ta goge bakinta inda ya fashe sannan ta mayar gefen fuskarta tana flinching saboda zogin da wajen yake. Jakar ta janyo ta fito da wayarta. Number din da farhan ya bata tun a napep ta haddaceta ta yaga takardar. Hannunta na rawa take shigar da number din ta kira ta kara a kunne tana wani irin kuka.......! **** Hamma yaga Nana nayi. Yace mata. "Bacci ko?" Ta daga mishi kai. Janta yai ya kwantar da kanta a cinyarshi yana jin wata irin kaunarta na shigarshi. Can kasan zuciyarshi wani abu na daban yana tafasa. Abinda ya kamata ace yana yi ne shekaru sha daya. Sai yau ya samu dama kawai saboda safiyya ta zabi ta boye mishi ita. * Sanda suka karasa gida Nana har tayi bacci. A hankali fu.ad ya daukota daga motar. Safiyya ta karasa ta bude musu gidan. Kan kujera ya kwantar da Nana. Harya mike da sauri yace ma safiyya. "Ba zata fado ba?" Bata kalle shi ba ta amsa da. "Damuwata ce wannan" A kufule fu.ad yake kallonta. "Me kike nufi?" "Duk abinda ka fassara" Motsi yaga Nana tayi. Da sauri yakai hannu ya dan tallabeta. "Damn it sofi. Karta fado fa" Sauke numfashi tayi. Ya soma isarta kuma. "Kana ina shekara goma sha daya. Sai yaune zaka damu da fadowarta? Kana ina ka tallabeta lokacin data fado duniya? So please baka da wajenta a rayuwarka. Baka da lokacin asara a sonta. Karka dame ni" Tafasa zuciyarshi take yi. "Karki fara. Karki fara dora lefin akaina. Bana nan saboda baki neme ni ba. Bana nan saboda kin zabi ki boyemun ita......." Dakatar dashi tayi tana jin yanda yake taso mata da bacin ran data jima tana binnewa. Cikin idanuwan ta kalle shi. "Ba kama ka nai na turaka waje ba. Kafafuwanka ka dauka ka fice. Me kake tunani?  Duk abinda nai *Akan so*nka bai isheka ba? Ko a lokacin inada sauran abinda ya rage in baka? Na baka zuciyata fu.ad. Nabar duniyata na shigo taka. Nabar kowa nawa sabo dakai......" Tana jin wasu hawaye masu dumi na zubo mata. Kallonta yake yana jin zuciyarshi na auna nauyin maganganunta. Wani murmushi yai da baikai zuciyarshi ba. "Sofi ba sai kin jefomun abinda kikai akaina a fuska ba. Ina sane dashi. Saboda me ni ba zaki duba abinda nai akanki ba?  Ba zaki duba girman abinda nai miki ba?" Bata son ganin shi sam. Saboda yanda take tunanin dazun tsanarshi na gogewa daga zuciyarta shirme ne. Tana nan daram. "Ka fitarmun daga gida please. Dan Allah ka tafi" Nana ya kalla. Sannan ya sake kallon safiyya. Bai sake ce mata komai ba ya fice daga dakin. Son kai. Son kan sofi yayi yawa. Da wannan tunanin a zuciyarshi har yakai titi ya tari taxi zuwa hotel din daya sauka. **** Kwance yake kan kujera cikin falon gidan nashi. Kallon ko ina na dakin yake da irin kayan kawa na duniya dake ciki. Wanda sam basuda amfani a wajenshi. Kirjinshi zafi yake mishi sosai. Tunda ya dawo numfashi yake yana tafiyar da komai yanda ya kamata ayi bawai dan yana jin dadin shi ba. Dadin me zakaji na duniya in babu kowa daya rage maka wanda ka damu dashi? Nuriyya ce last hope dinshi na jin dadin rayuwa. Ita kadai take ragemishi dayake jinta kamar family. Komai ya tarwatse mishi dayaji tayi aure. Yai yunkurin nemanta ya fasa saboda yana gudun kar ganinshi ya ja mata matsala. Yasan ba kowane zai iya auren Nuriyya ba duba da inda ta fito. Wanda duk ya aureta dole yana sonta. Soboda yasan *Akan so*nta dole yai rikici da yan uwanshi akan asalinta. Wannan dalilan su ya rike. Su suke tare shi daga neman nuriyya sai yau. Daya ganta inda bai taba zato ba. Ya kasa jurewa saida yai mata magana. Saidai ga mamakinshi duk abinda ya hanashi nemota karya ne. Ba haka abin yake ba. Daga yanayinta kawai yasan meke faruwa a rayuwarta. Saboda ba bakon abu bane a tashi rayuwar. Cikinshi ya taso tun wayanshi har ya zuwa yanzun. Ya kuma jima da sanin matan da suke cikin irin halin da nuriyya take ba karamar matsala bane. Baka da yanda zakai ka taimaka musu inhar basu suka baka dama ba.  Yagani akan mahaifiyarshi har rasuwa ta risketa. Wayarshi datai ringing ba karamun taimaka mishi tai ba don harya soma saka wuka yana tona ciwukanshi. Wayar ya dauka da take ajiye kusa da kanshi. Bakuwar number ce. Dagawa yai hadi da fadin. "Hello?" Murya a sarqe yaji ance. "Yaya farhan....." Da sauri ya mike daga kwanciyar da yake yana tattara dukkan hankalin shi kan wayar. Yasa hannu biyu ya riketa. "Nuri. Nuriyya kina lafiya?" Yana jin yanda kuka ke sarqeta ta cikin wayar dayake kona mishi rai. "Nuri kimun magana. Dukanki yai ko?" Dakyar ta iya cewa. "Eh" Wani abu dayaji ya taso mishi tun daga dan yatsan kafarshi yai tsaye a kirjinshi yana tafasa. In aka bashi bindiga maza masu dukan matansu zai fara harbewa. Saboda babu zalincin dayakai wannan. Har wani huci yake. Muryarshi a dake yace. "Calm down nuri. Bake kadai bace. I am here. Fadamun address din gidan" Dakyar ta iya karanto mishi. Mikewa ya da wayar a kunnenshi ya dauki mukullin mota. Ko gidan bai ja ba. Ya karasa wajen motarshi yana fadin.. "Zanzo yanzun kinajina. Ki kulle dakinki. Karki bude mishi sai kinji na kiraki" Bata amsa ba ta kashe wayar. Ya shiga mota yai baya da ita. Maigadi ya bude mishi ya fice daga gidan yana addu.a ya samu sanyi ko ya yake a zuciyarshi kamun ya karasa. **** Yana zuwa alwala kawai yayi. Anan yai sallar azahar. Dan kamun ya fito ya nemi masallaci lokacin sallar yaja sosai. Tunawa yai ya kamata yasa ma cikinshi wani abu duk da bakinshi baya so. Ordering fried rice yayi da farfesu. Dakyar ya iya cin rabi. Ya kira room services suka fita da kayan. Wanka ya sake yi ya fito ya kwanta. Idanuwanshi ya rufe babu komai a cikinsu banda Nana. Dariyarta. Murmushinta zai iya rantsewa sautin muryarta har cikin zuciyarshi yake jinta. Bacci ya dauke shi cike da mafarkin Nana. * Sanda ya tashi har anyi Asr. Dan haka sallah yayi. Yana zaune a inda yai sallah wayarshi ta hau ringing. Dagawa yayi yaga num din lukman. Ya amsa da fadin. "Hello......" "Kuna asibitin ne har yanzun?" A sanyaye yace. "Aa an sallame su. Suna gida. Ni ina hotel din dana sauka" Tambaya lukman yai ko a ina ne. Ya fada mishi yace ya jira shi gashi nan zuwa. Ko mintina talatin ba aiba ya sake kiran fu.ad cewar yana wajen hotel din. Wayarshi ya dauka da mukullan dakin ya fito. * A mota ya samu lukman zaune. Ya bude ya shiga. Shiru sukai su duka kowa ya rasa me zaice ma kowa kamin fu.ad yace. "This is awkward" Dariya lukman yayi. "Bansan ta inda zan fara ba" Murmushi fu.ad yayi hadi da fadin. "Banda abin fada. Daga lokacin dana tafi babu komai a rayuwata banda ball. So banda abin fadi" Nisawa lukman yayi. "Ina da zainab. Da junior da wani yana hanya mace ko namiji" Da mamaki fu.ad ya kalle shi. "Kana da mata da yaro lukman?" Kai ya daga mishi. Wani nauyi zuciyarshi tayi. Baisan ta inda zqi fara kamo abubuwan daya saki ba. "Ina jin nauyin ince ka kaini in gansu lukman" Shi kanshi wani iri yake ji. Sun rasa abubuwa da yawa a tsakaninsu. Da wani yanayi a muryarshi yace. "Kiran da zakayi shegen taurin kai ya hanaka" Dariya fu.ad yayi. "Irin wanda ya hanaka kirana ko?" "Shut up" Lukman ya fadi yana tayar da motar. Fu.ad baice komai ba har suka nufi hanyar dayake tunanin gidan lukman ne. Yanda rayuwa ta tafi da sauri haka yake mamaki. Bashida komai da yake kallo balle yaga gudunta.........! *#TeamAS* *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ              35 *Haka Allah yake ikon shi. Lokaci daya sai ya aiko maka da mutanen da zakaji kaman ka sansu tun farkon halittarka. You are not only a friend but a sister. I don't have to mention her name. ALLAH YA SADAKI DA DUKKAN ALKHAIRI SIS YAF* *Saqon addu.o.inku ya sameni. Nagode. Tabbas #AnaTare* Kuka take sosai. Can kasan ranta wani abu na fada mata babban kuskure tayi na kiran farhan. Idan kuma haukan nawaf ya hada dashi fa? Ba zata taba yafe ma kanta ba in wani abu ya same shi ta sanadinta. Daga wani bangaren kuma yana gaya mata kome nawaf yai mata bai kamata ace tabarshi ba. Yana tare da ita lokacin da take da bukatar taimako itama. Kamun ta karasa tunanin wayarta ta katse ta. Tana dubawa taga number din farhan ne gabanta ya fadi. Salati ta shiga jerowa hadi da mikewa dakyar. Wata azaba ta ratsata har tsakiyar kanta saboda zafin da taji a hannunta. Tallabe shi tai sabbin hawaye na zubo mata. Dakyar ta iya daukar mayafinta ta dan yafashi. Ta riqe wayarta hadi da hannunta da take jinshi ba daidai ba. Tai waje. Kallo maigadi yabita dashi. Tana fita kofar gida taga motar farhan yana ciki a zaune. Karasawa tayi ya miqo hannu ya bude mata murfin. Tana shiga farhan ya kalli fuskarta yace. "Ya Ilahi. Nuri......." Yama rasa me zaice. Kowaye nuri ta aura zai iya cewa rashin tausayinsu in baizo daya da babanshi ba kadan ya hana. Inba rashin imani da dabbanci ba. Baiga abinda zaisa ka ware karfi kana ma mace wannan dukan ba. Duk ya fasa mata fuska. Yanda ta runtsa idanuwa ta sake dafa hannu yasa shi saurin kai idanshi wajen. A tsorace yace. "Nuri saki hannun nan mugani" Batai musu ba ta saki hannu. Wani zogi da radadi yasa idanuwanta suka kawo hawaye. Girgiza kai farhan yayi. Ji yake kaman a bashi bindiga a ajiye mishi nawaf yaita harbi sai yaga babu sauran rai a jikinshi. Ya karyata. Hanunta a karye yake. Wani daci yake ji a ranshi. Zuciyarshi na hango mishi mamanshi a kwance jini na binta. Yana hango abubuwa da dama na rayuwar shi. Tayar da motar yayi suka nufi amini kano. Bai tsaya bata lokaci ba ya nemi wani abokinshi dake aiki a wajen. Dan yasan yanayin Nuri ba zasu kula su ba babu yan' sanda. Shiya tsaya musu aka karbi Nuri farhan ya samu waje ya zauna da wani irin nauyi a zuciyarshi. Abu dayane yake gani. Ko garin kano zata hade sai ya raba Nuri da wannan azzalumin. Koda zai mutu yana kokari kuwa. Daga kan mamanshi yai rantsuwa sai inda karfin shi ya kare akan masu irin wannan halin. * Bai san inda yake ba. Tunda ya dauki mota kawai tuqi yake. Harya samu waje yai parking. Kanshi ya hade da sitiyarin motar. Zuciyarshi kuna take kaman ana zuba mata garwashi. Da ace yana da tabin hankali sai aima haukan daya sauke kan Nuri uzuri. Runtse idanuwanshi yayi yana hango yanda ya taka mata fuska. Wani irin ihu ya saki daya fito daga maqoshin shi. Kanshi ya daga ya doka kan sitiyarin motar. Yana maraba da zogin daya ziyarce shi. Kuka yake saboda komai ya masa zafi. Gabaki daya duniyar ta hade mishi. Halin dayabar Nuri yake tunawa. Tayar da motar yayi yaja ta da karfin gaske yana hawan titi. Gida ya wuce kanshi tsaye. Yana parking ko kashe motar bai tsaya yi ba ya wuce cikin gida da gudu. Jini ne a falon kan tiles din. Bango ya dafa yana jin yanda kafafuwanshi ke son kasa daukar shi. Baisan ya mata wannan dukan ba. Baisan inda hankalinshi yake ba. "Nuri!!!....." Ya kira da wata irin murya. Da bin bango idanuwanshi kafe kan jinin dake kwance kasa kaman wanda zai taso ya kama shi yake tafiya. Kamun ya juya ya shiga dakin su. Bata ciki. Da karfi ya shiga kwala mata kira. Babu inda bai duba ba na gidan amman bata nan Da gudu ya fito ya tambayi maigadi ko yaga Nuri yace mishi ta fice. Dafe kai yayi da hannayenshi biyu. Shikenan ya rasata. Motarshi ya shiga. Ya jata. Yanda ya figi motar har maigadi saida ya tsorata. Yana hanya ya lalubo wayarshi ya kira yayanshi. Bugu daya ya daga. Yana wani irin kokawa da numfashin shi yake fadin. "Yaya nuri. Nuriyya ta tafi........" Magana yayan nashi yake amman bayajin komai cikin kunnuwanshi da kanshi sai kalma daya. Sakin wayar yayi yana jin wani luuu. Kamun ya saki motar gabaki daya ya dafe kanshi dake wani juya mishi. Hakan yasa motar ta kwace daga hannunshi ji kake wani quuuuuuuu. Sama nawaf yaji motar tayi. Yana jinta ta dawo kasa dashi. Tana jujjuyawa kamun ya daina jin sautin komai cikin kunnuwanshi. Wani abu yaji yana bin fuskarshi kamun wani irin duhu mai tsanani ya lillibe komai na duniyarshi...........! **** Suna parking din motar hassan na fitowa daga gidan dauke da junior saman wuyanshi suna hira. Kallon shi fu.ad yake yi. Lokaci daya ya hango hassan din daya bari. Ya kalli wannan saurayin dake tahowa. Baxai iya fassara abinda yake ji a zuciyarshi ba saboda baisan komenene ba. Idanuwa ya dago ya fara sauke su kan lukman da yace mishi. "Hassan ana ganinka daman" Sam bai kula da fu.ad ba. Yar dariya yai ya amsa da. "Ina wuni. Wallahi aiki babu lokaci sosai. Yanzun ma naje gidan yaya haneef nace bara na biyo........" Kasa karasa maganar yai ganin fu.ad. A hankali duk fara.ar dake fuskarshi ta soma dakushewa har ya zamana babu ita ko kadan. Junior ya sakko daga kan wuyanshi zuwa kasa. Da gudu ya ruga wajen lukman ya rike hannunshi. A dakile hassan ya dauke idanuwanshi daga kan fu.ad ya mayar kan lukman. "Zan wuce. Sai anjima....." "Hassan......." Fu.ad ya kira. Banza yai ya kyale shi. Yana karasawa inda machine dinshi yake ajiye ya hau. Kallon lukman fu.ad yayi. Yadan ware mishi idanuwa dake fassara babu ruwana. Da hanzari fu.ad ya karasa inda hassan yake yana kokarin tayar da machine dinshi. Hannu yasa kan handle din machine din ya riqe dam. Gefe hassan ya kalla dan baya son sake ganin fuskar fu.ad dinma kwata kwata. Zagayawa fu.ad yayi muryarshi a sauke yace. "Hassan" Batare da nuna alamar sanayya ba yace. "Sannun ka fa" Yaji yanayin muryarshi sarai. Ya share da fadin. "Hassan please mana. Ka daina mun magana kaman yau ka fara ganina" Sai lokacin ya ware idanuwanshi kan fuskar fu.ad din. Ranshi a bace yace. "Nasanka ne?" Dan runtsa idanuwa fu.ad yayi ya budesu. "Harshenka bazai canza matsayina a wajenka ba" Kallon mamaki hassan ke mishi kamun yace. "Wanne matsayi kenan?" Ya wani kankance idanuwa. Fu.ad ya amsa shi da. "Yayanka" Wata irin dariya hassan yai. Kamun lokaci daya ya hade rai. Ya hanga mishi lukman dake tsaye rike da junior. "Kaga wancen shine yayana. Yaya haneef. Babban yaya. Banda su banda wani yaya. Oh na manta da wanda ya yarda mu kaman bamu taba hada alaqa dashi ba. Now if you will excuse me inada abin da zanyi....." Kokarin jan machine din yake fu.ad ya riqe dam. "Saboda me yasa baka kirani ba? Ko da yake ba wannan ba. Kawai zanji ya kake" Cikin idanuwa ya kalli fu.ad. Da gaske yake tambayar dayai. Yaga alama inya tsaya biyewa fu.ad ranshi kara baci zaiyi. Shekaru goma sha daya sai yanzunne zai dawo yace zai zama yayanshi. Gaba daya cikin yan gidansu burin hassan bai wuce inya girma ya zama irin fu.ad ba. Shine role model dinshi. Daga randa yasa kafa ya wargaza duk wata alaqa dake tsakaninsu ya hada da burin hassan din ciki. Machine din ya tayar yaja shi baya. Batare daya sake kallon fu.ad din ba yaja. Har ya kusa gate ya tsaye. Juyowa yai yaga fu.ad din tsaye yana kallonshi. Da alamar roqo a fuskar shi hassan din yace. "Do me a favour. Karka je inda hussaina take. Bata bukatarka. Mu duka bama bukatarka. Bana son ka sake hurting dinta. Akwai wanda suka damu da ita da yawa" Bai jira amsar shi ba yaja machine din ya fice. Hannuwan shi yasa ya rufe fuskarshi yana sauke numfashi. Yana tsanar yanda zuciyarshi ke fada mishi bai duba halin da kowa zai shiga ba yai abinda yayi. Lukman yaji ya dafa shi. Hakan yasa ya bude fuskarshi ya sauke idanuwanshi da har sunyi ja saboda bacin rai. "Bana son maganar please......" Dan daga mishi kafada kawai lukman yayi. Ya daina saka matasalar fu.ad a rai. "Ga junior...." Kallon yaron fu.ad yayi ya shafa kanshi hadi da yi mishi murmushin da baisan ta inda ya fito bama a yanayin da yake ji. Lukman yace ma junior. "Ga uncle fu.ad...." Dariya junior yai yace ma fu.ad. "Nima dayan sunana fu.ad ne" Da sauri fu.ad ya dago ya ware ma lukman idanuwa. Murmushi yai yadan daga mishi kai. Alamar yes sunan junior kenan. Wani irin abu yaji a zuciyarshi. Bayan duk abinda ya faru. Da wani irin yanayi a muryar fu.ad din yace. "Ion' deserve duk wannan" Dan yatsa lukman yakai kan labbanshi yana nunama fu.ad din yai shiru kawai hadi da fadin. "Zumuncinmu naiwa" Kasa magana yayi. Kawai yaja junior jikinshi ne ya riqe tsam yana rasa abinda zaice ko abinda ya kamata yayi. "Muje ciki ku gaisa da zainab" Kai fu.ad ya girgiza mishi. Bazai iya ganinta ba yanzun. Bazai iya tuna abinda ya kamata ace yaima lukman bai mishi ba. "Zan tafi lukman. Zamu gaisa wani lokaci. Ka kula dasu duka" Kai lukman ya daga mishi. Gabaki daya yanayin fu.ad din ya bashi tausayi. "Muje in sauke ka to" Lukman ya fadi yana kokarin zaro mukullanshi daga aljihu fu.ad yace. "Karka damu. Zan taka har saina danji dai dai" Magana lukman zai ya katse shi da. "Please" Sauke numfashi lukman yayi. Yama rasa me zaice. Fu.ad din ya shafa kan junior hadi da fadin. "Boy me kake so?" Da sauri junior yace. "Machine irin na uncle hassan" Yar dariya fu.ad yayi. "Umm sai ka girma kaman uncle hassan then. Amman yanzun zan siyo maka wanda bai kaishi ba" Cike da jin dadi junior yace. "Yeee ina so. Dady uncle zai siyamun machine" Murmushi lukman yayi. Ya rasa me zaice har lokacin. Fu.ad ya kalle shi yace. "Zamuyi waya...." Ya wuce yana fita daga gidan. **** Lafiya kalau suka ci abincin dare gabaki daya da yaran kaman babu wata matsala. Jabir na nazarin yanayin jana. Zai iya karantar damuwar da take ta son boyewa. Kishin da take son dannewa nashi. Yau tare dashi suka raka yaran suka kwanta banda ikram. Dan ji take ita ta girma. Suna kulloma yaran daki ya rike hannun jana. Sumbatar hannun yai. Tai mishi wani murmushi a kasalance tana zame hannunta. Dakinsu ta wuce yabi bayanta. Tana zaune kan gado jabir ya samu waje dab da ita ya zauna shima. Wani irin dokawa zuciyarshi take. Yanda komai yake tafiya da sauri na bashi mamaki. Kaman yanda karbarshi da ayna tayi. Duk da batayi hakan ba saida ta fara tambayarshi ko matarshi tasani. Ya amsa ta da cewar saida ya fara fada mata. Da saqon janar a wajenta. Sosai ayna taji dadi domin ta fada mishi bata son namijin da bashida adalci ko kadan. Sauke numfashi yai. "Jana....." Yaja sunanta. Idanuwanta ta sauke mishi. Sai ya sake jin kwarjininta ya cika shi. A sanyaye yace. "Ayna ta amince dani. Bana son aja lokaci tunda ni ba yaro bane dazan tsaya wannan abubuwan. In anjima wata uku" Wani irin numfashi jana taja tanajin yanda zuciyarta take tafasa. Wannan karin ta kasa jure hawayen da take ji. Suka zubo mata a hankali. Jikinshi jabir ya jata. Tana wani irin kuka marar sauki. Sumbatar kanta yai da duk wani waje inda bakinshi zai iya kaiwa yana dan bubbugata sigar lallashi. "Jana bazan taba wulaqantaki ba in shaa Allah. Wallahi ina sonki. Ina sonki sosai. Badan bana sonki zan kara aure ba. Bansan dalili ba nima......" Jin yanda duk ya rikice yasata dagowa ta hada bakinta da nashi nadan wani lokaci. Sannan ta kalli fuskarshi. Hannunshi ta riqo ta dumtse cikin nata. "Nasani honey J. Ina sonka nima. Bazan iya hana zuciyata kishinka bane. Allah ya sanya alkhairi. Ina ma ayna godiya da karbar mijina da tayi. Allah ya bani ikon tayaka sonta. Allah ya tabbatar da alkhairi ya kaimu wata ukkun" Lumshe idanuwa yai. Yana ma Allah godiya daya bashi mata kalar jana. Haqiqa ita din alherice a rayuwarshi. Riketa yai tsam a jikishi yana kwantar dasu. Yanajin yanda take kuka a hankali har ranshi. Sun jima sosai a haka. Kamun ta zame daga jikinshi. Toilet ta shiga ta dauro alwala. Yana kwance yana kallonta ta shimfida kafet ta fara nafila. Tun yana kallonta har bacci ya dauke shi. Sosai jana take roqon Allah harda kukanta daya bata karfin zuciya ya bata juriya na danne kishin da take ji. Taima jabir dinma addu.a ta fatan Allah ya tabbatar mishi da alkhairi. Kishin shi bai sata baqin ciki da auren shi ba sam. Akan kafet din tai bacci. Da wata irin nutsuwa taban mamaki.....! Haqiqa rashin tabewa na tare da duk wanda ya riqi addu.a da kai kukanshi wajen Allah. **** "Hello....... Hello nawaf wai baka jina ne?" Ibrahim ke fadi kamun ya kula kiran ya katse. Ajiyar zuciya ya sauke ya mike daga kwanciyar da yake. Jallabiyar jikinshi ya cire yana sake kaya yana kwalama Jidderh dake kitchen kira. Da saurinta ta karaso "Afuwan dear. Ban jika bane....." Ganin yana sa kaya yasata fadin. "Ina zaka?" Saida ya balle maballan shaddar shi sannan ya amsa ta da. "Nawaf ne wallahi. Bansan me yai ba. Yace nuriyya tabar gidan. Kinsan shi dai zai iya yin wani haukan. Ya kira baya jina. Kuma sai kira nake taqi shiga. Zanje in duba......." Bai karasa ba wayarshi dake kan gadon ta hau ringing. Ya dauka yana fadin. "Inaga ma shine....." Dubawa yai yadan daquna fuska ganin sabuwar number ce. Ajiyewa yai ya karasa saka links din rigarshi. Jidderh tace. "Bakai picking ba....." "Baquwar number ce" Ya fadi a taqaice lokacin da wayarshi ta sake daukar ringing. "Bansan sau nawa zance maka ka dinga daga baquwar number ba. Emergency ake gudu wallahi. Ko wata lalurar ta daban" Dan daquna fuska ya sake yi alamar ya takura. Kamun wayar ta yanke. Dauka yai yana kallonta da fadin. "Saina dawo" Ta bude baki zatai magana ringing din wayar ya sake katse ta. Ta kalli ibrahim da yake fassara. Kaga me nake ce maka ko. Wayar ya daga ya kara a kunne hadi da fadin. "Hello....." Daga dayan bangaren aka ce. "Please ko waye yazo titin dake zoo road ta wajen masallaci. An samu mummunan hatsari ne kuma wannan shine number na karshe a wayar mai hadarin. Babu rai a jikinshi. Kazo da hanzari" Subuce wa wayar tai daga hannun ibrahim. Wani irin jiri yaji na dibarsa Baisan sanda yai kasa ba. Yana dafa gadon. Da sauri jidderh ta riqo shi a rikice take fadin. "Menene? Dan Allah kaimun magana....." Yana wani irin jan numfashi ya amsa ta da. "Jidderh nawaf.....nawaf..... " Girgiza shi take tana fadin. "Menene?  Me nawaf din yayi?" Wata zufa yake ji tana fito mishi tako ina na jikinshi. "Nawaf......yai accident...." Wani irin kuka jidderh ta saki tana riqe baki. Waje ta samu ta zauna itama ko ina na jikinta na kyarma. Mikewa ibrahim yayi. Ya dauke wayarshi yana fita daga dakin da gudu. Babansu ya fara kira yana bude mota yana shiga.......! **** Tunda ta tashi daga bacci taganta wani shuru shuru bata ce komai ba. "Nana? Lafiya?" Daqyar ta iya ce mata. "Cikina ciwo mumy..... Ciwo sosai" A rikice sofi ta mike. Ta kama nana ta sabe ta a kafadarta. Mayafinta ma a kafada ta dorashi ta dauki mukullan motarta ta fita. Saida ta kwantar da Nana bayan motarta sannan tazo ta bude gaban ta shiga. Maigadi ta fadama kowa yazo yace suna asibiti. * A hanya yai sallah. Ya samu taxi zuwa gidan safiyya da wani irin nauyi a zuciyarshi. Sam baiji dadin abinda hassan yai mishi ba. Mai taxi din na ajiye shi ya bashi kudinshi ya karasa ya kwankwasa. Maigadi ya ce mishi suna asibiti. Allah yaso mai taxi din bai tafi ba. Dan haka ya koma ya shiga yana fadin mishi sunan asibitin. * Kasancewar ta kira doc jana ta rigada tabar asibitin yasata wucewa emergency da nana. Suna zaune suna dan jira aka shigo da wani yai hadari da gudu. Idanuwa Nana ta kafe a kanshi. Tana kallon fuskarshi. Duk da jinin dake jiki da yanayin yanda suke wuce dashi bai hanata gane shi ba. Ganin yanda jikinta ke kyarma ne yasa safiyya kamata tana kokarin boyeta jikinta dan ko ita nata jikin bari yake. Tureta Nana tayi tana binsu da kallo har suka bace ma ganinta. Sakkowa tai daga inda take zaune. Safiyya ta kamata. Kuka take. Kuka take sosai tana fadin. "Mumy shine. Wallahi shine......" Kamata safiyya tayi tana kokarin lallashinta amman a banza. Tasan zata iya samun matsala. Shocked na komai ko excitement in yai yawa yana iya bata matsala. Dai dai shigowar fu.ad wajen. Yanata hange hange ya hango su. Da gudu ya karasa. Ganin kukan da Nana keyi yasa shi jin wani abu ya soki zuciyarshi. Da hawaye cike idanuwan safiyya tace. "I need to calm her........" Tsugunnawa fu.ad yai. Ya tallabi fuskar Nana cikin hannunshi yana kokarin hada idanuwanshi da nata. "Shhhhhhhh. Nana kalle ni" Kuka take sosai. Har numfashinta na wani sama sama. Sai lokacin ta sauke idanuwanta cikin na fu.ad muryarta na sarqewa tace. "Shi ya taimakeni na ganoka. Shi ya biyamun kudi...... Shine ya biya aka sa wasiqa ta..... Mutuwa zaiyi ko?" A rikice fu.ad ya kalli sofi. Dan zancen Nana babu wanda ya fahimta. Dafe kai safiyya tayi zatai magana Nana ta ci gaba da jan wani irin numfashi. Zaka rantse asthma attack ne ya kamata. Jikinshi fu.ad ya riqota yana kwalama duk wani wanda zai saurare shi kira. Da gudu kuwa wasu nurses sukayo kansu. Kokarin karbar Nana suke a hannun fu.ad yaqi basu ita. Ji yake kaman zai miqa musu zuciyarshi. Saida safiyya tace. "Fu.ad ka basu ita. Taimaka mata zasuyi...." Sannan ya sakar musu Nana yana binsu da gudu. Dai dai dakin sukai kokarin dakatar dashi. "She is mi' daughter. Babu hankali a jikin duk wani wanda yake tunanin zai hanani shiga....." Ganin da gaske fu.ad din shirin bangaje nurse din yake. Likitan dake ciki yace tabarshi ya shigo. Tsaye yai yana dafe da haba yana kallonsu. Wata allura sukaima Nana. Har lokacin bata daina kokawa da numfashin taba. Kamun tai wani laqwas. Wani tsalle zuciyar fu.ad tai kaman zata baro kirjinshi. Yaune rana ta farko a rayuwarshi da yasan meye asalin tsoro. Da gudu ya karasa kan gadon da take yana ture likitan dake kokarin sakama Nana ruwa. Tsugunnawa yayi. Yasa hannu ya taba fuskarta. Muryarshi a dakushe yace. "Me kukai mata?" Dafashi likitan yayi. "Relax. Allurar bacci mukai mata. Tana bukatar hutu sosai" Yana nan tsugunne suka gama mata duk wani taimako da take bukata a lokacin. Likitan yace fu.ad ya fito daga dakin dan tadan huta. Ya ki. Barinshi sukai. Hannun nana da bashida komai ya kama ya sumbata. Ya kamashi ya dora kan fuskarshi yana rufe idanuwanshi. Tunanin abubuwan daya rasa na rayuwarta ne ke wani irin ci mishi zuciya. Dazai iya daya karbar mata wannan ciwon. Dan a yanzun ji yake tafi mishi muhimmanci akan komai na rayuwarshi........! *#TeamAs* *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ           36 *Dukkan mai rai mamaci ne! Allah ka kawo mana sauqi cikin tamu tafiyar. Page din nan ya tabani fiye da tunaninku* Yana so ya bude idanuwanshi ya kasa. So yake ya kwace daga inda tunanin shi keson janshi. Ya kwammace ya ziyarci ko ina banda nan. Banda ranar farko da ya karbi abinda ya rusa mishi rayuwa. Saidai ya zamana bashida karfin komai. Bashida karfin fisgewa daga riqon da koma menene yai mishi. A hankali ya bayar dakai. Ya daina kokarin kokawar da yakeyi. Ya bari koma menene ya dauke shi yaja shi inda yake son kaishi. **** *Nawaf in ss3* "Nawaf ka cika tsoro wallahi. Wannan yafi komai daka taba trying bada kalan charge din da ake buqata" Girgiza kai nawaf yayi yana kallon awwal hadi da fadin. "Nifa Codien din nan ma ina so inbari ne. Na kasa kar a gane a gida" Dariya sosai awwal da haroon suke mishi. Kamun haroon yace. "Kaban dariya maza. Saikace wani karamin yaro. In zaka ja kaya kaja kaya kawai" Ajiyar zuciya nawaf ya sauke. Yana tsoron karban kwayoyin dake hannun awwal dan baisan kalar karfinsu ba. Codien dinma dan ya zamana kowa a ajinsu yana sha. Kullum kallon karamin yaro suke mishi. Shine abinda ya fara jan hankalinshi. Shekara daya kenan ya kasa dainawa. Sam baya jin dadi inhar bai sha ba. Dafa kafadarshi awwal yayi. Yana mika masa kwayoyin dake hannun shi. "Ka karba. Ba zakai dana sani ba. Duka kwana nawa ya rage mana mu karasa jarabawar mu?  Wannan ne lokacin holewa" Dariya haroon yayi. "Kaman kasan yau akwai clubbing ba" Karban kwayar nawaf yayi. Yasa a aljihu ya wuce yabarsu nan. Dan yaga lokacin sallah yayi. Ba damuwa sukai da suyita ba. Shikam in akwai abinda ya tsana bai wuce wasa da sallah ba. Ko da lokacin sallah baiba shi bazai zauna ya saurari shirmensu kan mata ba. Har addu.a yakanyi. Allah ya kare mishi zuciyarshi daga zina. Shan codien wani abune daban. Amman zina na daya daga cikin manyan laifukan da baya so ya hada shi da Ubangijinsa. * Wannan rana itace ta farko da nawaf ya fara shan kwaya. Abin bai tsaya iya nan ba. Kamun su gama makaranta saida ya zamana har cocaine suna sha. Alh. Haladu shine mahaifin nawal. Dan kasuwane da yaranshi hudu duk maza da suka haifa da matarshi haj. Asiya. Kabir, khamis, Ibraheem sai autansu nawaf. Tarbiya dai dai misali sun yi kokarin baiwa yaran nasu. Nawaf ne kawai kaddara ya rubuta musu. Ibrahim shiya fara gane nawaf din na shaye shaye. Kuma shiya sanar da mahaifiyarsu. Lokacin yagama jarabawarshi ta waec da neco. Babu iya kokarin da basuyi ba na ganin sun rabashi dasu haroon. Amman ina. Hakan yasa su yanke hukuncin su turashi karatu England. Haka kuwa akai. Saidai wannan ya zamana babban kuskuren su. Dan abin harya so ya taba mishi kwakwalwa. Lokaci da dama zai dinga abubuwa kaman marar hankali. Maimakon ya zama silar shiriyar nawaf kaman yanda suke tunani saiya qara zama sanadin lalacewarshi. Dakyar ya kammala karatun shi ya dawo gida nigeria. Rayuwa taci gaba da tafiyar musu. Saboda Alh. Haladu yasan mutane da dama. Yasa nawaf samun aiki a wani company da suke atamfofi. Yana zuwa aiki. Ga biyayya kaman me. Saidai shaye shayen kawai. Duk da dawowarshi nigeria yasa sun sake jonewa dasu haroon bai sauke mishi aqidarshi ta kin son kusantar zina ba. Har lokacin daya hadu da Nuriyya. Ita ta soma dauke hankalinshi daga shaye shaye. Kamun daga bisani wata irin soyayyarta ta shige shi. Tasan matsalarshi. Hakan baisata kyamatarshi ba. Domin shi yana da asali koda kuwa a cikin rijiyar giya yake kwana ya wuce gori. Nuriyya ta soma zama silar shiriyar nawaf. A hankali har iyayenshi suka san da ita. Da gudu suka karbeta. Babu kyamata babu komai. **** "Nawaf........" Yanajin muryar Ibrahim yana kiranshi sama sama. Bama tashi kadai ba. Ta mutane da yawa. Muryarsu yake ji cikin kunnuwanshi amman nuriyya yake gani a zuciyarshi. "Nuri...." Ya fadi. Ibrahim dake bakin gadon ganin bakin nawaf yai motsi yasa shi kara matsawa da sauri yana kasa kunne. Su mama kam banda kuka babu abinda sukeyi. Dan harsun rigada sun hakura da nawaf. Yakai awa biyu da kawowa asibiti kamun a samu zuciyarshi ta ci gaba da bugawa. "Nuri...." Ya sake fada wannan karin da dan karfi. Khamis dake tsaye ibrahim yaima nuni da su kira likita. Da saurin shi yaje ya taho dashi. Zuwa yai ya sake duba nawaf. Suna tsaye cirko cirko. Bai bude idonshi ba. Banda Nuri da bakinshi ke kira babu inda ke motsi a jikinshi. Doc din ne yake tambayarsu ko wacece Nuri. Ibrahim ya amsa shi da cewar matarshi ce. "Ku kirata. Ku kirata da sauri......" Cewar likitan yana ma nawaf din wata allura kamun ya fita. Su dukansu ibrahim suka zuba ma idanuwa. Tashi yai jiki a sanyaye ya fice daga dakin yana ja musu kofar. Wayarshi ya dauko ya lalubo number din nuri yai dialing........! **** Yana zaune ya zuba ma sarautar Allah ido doc da nurse din suka fito. Doc din ya dafa farhan yace ya biyo shi. Babu musu ya tashi ya bishi har office din. Sosai yake kallon farhan. "Nasan wannan ba hurumina bane. Saboda Allah me matarka zatai maka kai mata wannan dukan?" Wani daci farhan yaji cikin zuciyarshi. Cike da qunan rai yace. "Hakane kam. Ya take?" Baison kallon da likitan yake masa. Duk da yana son fada mishi bashi bane ba. Gara Allah ya dauko rayuwarsa daya gwada masa rabar dazai daga hannu akan mace. Kaman yanda ya fada. Ba huruminshi bane ba. Yan rubuce rubuce yayi a takarda sannan ya mikama farhan din hadi da fadin. "Ka siyo wannan magungunan yanzun. Inka shiga dubata taci wani abu sannan a bata" Karba yai ya mike hadi da fadin. "Nagode" Bai kula shi ba. Shima bai damu ba ya fice. Kai tsaye pharmacy ya wuce ya siyi magungunan da aka bashi sannan ya koma zuwa dakin da aka kwantar da Nuri. Duk da gadaje uku ne cikin dakin. Ba kowa sai ita kadai. Da dori a hannunta daya karye. Kallo daya farhan yai mata ya sauke idanuwanshi. Baya son sake kallonta saboda ji yake yana son shakare nawaf. A hankali ya karasa inda take yaja kujera ya zauna. "Sannu" Idanuwanta ta dago dakyar saboda nauyin da take jin sun mata. Cike suke da hawayen dasu basu zubo ba. Su basu koma ba. Cikin sanyin murya tace. "Inajin kaman wani abu ya faru dani daban sani ba" Kallonta yai. A tausashe yace. "Banda wannan akwai wani abu dazai faru dake?" Daga kafadu tai alamar itama bata sani ba. Takai hannunta mai lafiya tana goge hawayen da suka tarar mata cikin idanuwa. "Koma menene yana da girma. Saboda ina jin shi har raina" Sauke numfashi farhan yai. Baisan amsar daya kamata ya bata ba. Saboda haka yace. "Me zakici? Ance kici wani abu sannan kisha magani" Ita kam batajin tana son cin wani abu. Banda jin da take wani abu ya faru da ita. Ga nawaf ya mata tsaye a zuciya. Ta so nawaf. Tana son nawaf. Saidai tana jin tsoronshi sosai. Bayan abinda ya faru yau. Bai barta da wani zabi ba. Wayarta dake hannun farhan ta soma ringing. Kallon juna suke. Ya zaro wayar daga aljihunshi ya mika mata. Gani tai yaya ibrahim ne. Gabanta ya yanke ya fadi. Allah kadai yasan abinda zai faru yanzun kuma. Tasan wajen shi nawaf yaje. Wani irin tsoro ya cika mata zuciya. Idan nawaf yaji tabiyo farhan bata san me zai faru ba. Hawayen da suka zubo mata tasa bayan hannu ta goge. Wayar ta yanke. Kamun ta sake daukar wani ringing din. Kallon ta farhan yake. Shi bai isa ya tayata yanke hukunci ba. Duk kuwa yanda yake so. Sakata tai a silent. Tana jujjuya wayar a hanunta kanta a kasa tace. "Shekarar mu daya da wani abu da aure. Babu wanda yamun dole. Ina son shi saboda ya taimake ni kaman yanda kaimun. A kasan duk wannan dukan nawaf na da halayya me kyau. Yana da zuciyar da kowacce mace zata so......" Shiru tadanyi. Dan batama san dalilin dayasa take wannan maganganun ba. Kawai tana jin ya kamata taima farhan don bayani ne. Ta so shi shima. Son shi dabanne dana nawaf. Tana son ya fahimci tana son mijinta har yanzun. Tsoron shine yake son girmar son. Wasu hawayen suka sake zubo mata dataga kiran yaya ibrahim na sake shigowa kamun tace. "Yana da matsala. Yana shaye shayen manyan kwayoyi kamun aurenmu. Yabari na wani lokaci kamun satika biyu da suka wuce. Ban tabbatar ba amman naga alamu ne kawai. Yana bukatar taimako. Yana bukatata nikuma......nikuma kaganni anan" Murya a dake farhan yace. "Kalle ni nan Nuri. Ba ina son yanke hukunci bane. Ko in nuna nafi karfin kaddara ko makamancin hakan. Komenene dalilinshi. Ko menene naki. Babu amfanin zama da namijin da yake miki wannan dukan. Shi ya baki rayuwa?" A hankali ta girgiza mishi kai. "Saboda me zaki mika mishi ita yai yanda yaga dama? Saboda kina jin cewa ya miki taimako?" Sai lokacin ta dago kai ta kalli farhan. "Ina zanje? Gidan magajiyar karuwai da abin dariya itace mahaifiyata?" Dafe kai farhan yayi cikin hannuwanshi yana girgiza kai. Baisan ta inda zai fara mata bayani ba. Sai yanzun datai wannan maganar abin ya fado mishi. Ta ina zai fara gaya mata lokacin dayaje aka fada mishi tayi aure bashi bane kawai labarin daya samu? Wayarta ta sake kallo. Message ne ya shigo. Hannunta na rawa ta cire wayar daga key. Ta bude message din. "Nasan abinda zaisa ki tafi ba karami bane Nuri. Bansan me zance ba. Ko ta ina zan fara. Dan Allah kizo......." Bata karasa karantawa ba farhan yace mata. "Ba ita ta haifeki ba Nuri. Baki da alaka ta jini da ita ko kadan......" Cikin kunnuwanta take jin maganar na mata wani irin yawo. Tana son fahimtar abinda maganganunshinke nufi. Idanuwanta kafe kan screen din wayar. "Accident da nawaf" Tagani cikin sentence daya da suma ta kasa fahimtarsu. Sosai ta bude idanuwanta kan screen din wayar. Kalma ukku kacal take ganewa. Sunan asibitin. Nawaf da kuma hadari. Kamun wani abu ya yamutsa cikin cikinta. Jiri take ji yana dibarta daga zaune. Dakin na wani irin juyawa. Hannu takai ta na dafe kanta hadi da rintsa idanuwa. A razane farhan yace. "Nuri!!!" Sama sama take jinta. Wani irin yanayi ne da wanda ya san tashin hankali kadai zai iya fahimtarshi. Yanayi ne da ba kowa ne zai gane ba. Kafafuwanta ta sakko daga kan gadon. Tadanyi jim tana jin garin yadan saitu sannan ta diro tana mikewa. Kalle kalle take. Ta hango mayafinta. Tana kallon bakin farhan na motsi saidai kunnuwanta basa jin me yake fadi. Nawaf kawai. Wajen nawaf take son zuwa. Takalmanta ta janyo ta saka a kafarta. Ihun magana farhan ke mata amman yaga alama bata ganewa. Cikin wata irin murya tace. "Ka kaini wajen nawaf. Yaya farhan ka kaini wajenshi......" Ya kasa gane me take nufi ko meye sanadin faruwar wannan abin. Ko maganar daya fada mata ce? Gani tai kaman baya ganewa. Wayarta ta dauko dake kan gado ta mika mishi ya karanta text din. Ware idanuwa yai. Ba tare da tunanin komai ba yace mata. "Muje......" **** Zame jikinshi yai a hankali zuwa kasa. Ya zauna batare da damuwa da cewar kan tile bane ba. Ya dafe kanshi da dukkan hannuwanshi biyu. Addu.ar duk da tazo bakinshi yake karantawa ko zai samu sauqin abinda yake ji. Bai taba sanin haka ake jin mutuwa ba sai da yai tunanin babu numfashi a tattare da nawaf. Bai taba sanin haka daci da radadin rabuwa da wanda ka shaqu dashi kake kauna yake ba sai yau yadan dana kadan daga ciki. Sai dai da daukrwar wancen yanayin da mayewar gurbin shi da wani sabo. Fargaba da tashin hankali. Tunanin zai iya rasa kaninshi kowanne lokaci. Fatanshi Nuriyya ta bude text din dya tura mishi. Ko da nawaf rasuwa yai bazai ji baiyi wani kokarin komai ba. Rawa yaji zuciyarshi nayi. Wayarshi yaji tana ringing. Ya daga ganin nuriyya ce yasa shi saurin dagawa da sauri. Sai dai ba muryarta yaji ba. Wata murya yaji daban an mishi sallama. Ya amsa gabanshi na wata irin faduwa. Roqon Allah yake karya hada musu abu biyu lokaci daya. Can yaji an dora da "Muna cikin asibitin. Daga farko. Kuna ina?" Dakyar ya iya cewa. "Barin zo" * Daga nesa yake hango wata kaman nuriyya. Inka dauke raunukan dake fuskarta da kuma hannunta dayake a karye. Tsaye take da wani matashi da inbai girmi nawaf ba zasu zo shekaru daya. Da sauri ya karasa inda suke. Kallon nuriyya yake. Kar dai ace nawaf ne yai mata wannan dukan. Girgiza kai ibrahim yake yana rike baki. Idanuwa nuriyya ta ware a kanshi. Idanuwanta a bushe suke. Babu alamar komai a ciki. Bai taba ganin idanuwa haka ba sai yau. Muryarta a dake tace. "Yana ina?" Ko sallamar farhan ibrahim bai tsaya amsawa ba balle ya karbi hannun daya miko masa ya juya. Bawai dan wani abu ba. Sam bai kula bane. Suka bishi a baya. * Bata jin komai. Kaman an rufe mata duk wata kofa da kafa ta jin wani tashin hankali tun dazun. Komai ya tsaya mata cik. Har lokacin data tura kofar dakin da nawaf yake. Bata hango shi daga inda take tsaye saboda su mama da suke zagaye dashi. Kafafuwanta da wani irin nauyi ta karasa cikin dakin. Suna jin takun tafiyarta suka juyo. Ganinta yasa suka matsa daga jikin gadon. Tana sauke idanuwanta kan nawaf zuciyarta tai wata irin dokawa da take ji har cikin kanta. Kallonshi take. Kanshi nade yake da bandage. Gefen fuskarshi ma haka. Inhar baka sanshi ba ba zaka gane shi ba. Inda ba shida bandage din dinkine yakai hudu. Da duk takun da take da karin karfin bugun zuciyarta. Gaba daya jikinshi na.urorine harda abin abinci ta hancinshi. Gani tai tafiyar daga inda take zuwa gadonshi ta mata wani irin tsaho. Kaman so ake ta kare mishi kallo. Taga yanda ya koma kamin nan ta karasa inda yake. Hakan kuwa take. Kafafuwanshi duka biyun a nade suke da irin abinda hannunta ke ciki. Bata taba sanin zaka iya jin tarwatsewar zuciyarka ba sai a wannan lokacin. Bata taba sanin haka tashin hankali yake ba sai a yanzun nan. Bata taba gane rayuwa ba abakin komai take ba saida ta karasa bakin gadon da nawaf yake kwance. Hannunta na rawa sosai tai kokarin kaishi kan fuskar nawaf. Saidai ta rasa inda zata ajiye shi. Ko ina ciwuka ne. Kafafuwanta taji suna wata irin rawa. Ta dafa gadon dakyar tana zama. Bakinta ta bude saidai kalma ko daya ta kasa fitowa. Banda wani irin ihu da take jinshi cikin zuciyarta da kanta amman sautin shi yaki fita. Hannunta ta sauke kan kirjin shi. Kai take girgizawa. Fata take ta farka daga wannan mafarkin da takeyi. Su koma gida abinsu da nawaf dinta. Koda kuwa markadata zai dingayi karewr duka inhar zata ga fuskarshi babu wannan abin. Yanayin Nuriyya da nawaf din ya sake karya zuciyar duk wani wanda ke cikin dakin. Su kansu mazan daurewa kawai suke. Can Allah ya taimaketa muryarta ta dan dawo. "Nawaf......" Ta fadi. Baiko motsa ba ballanta na tai tunanin yajita ko zai bude ido. "Nawaf......!" Ta sake kira wannan karin da karfi. * Ji yai kaman muryar nuriyya. So yake ya bude idanuwanshi amman sun masa wani irin nauyi. Yana ji da wata irin murya ta sake fadin. "Nawaf ka tashi......!" Kokarin bude idanuwanshi yake yi daga duhun dake riqe dasu. Nuriyya ce. So yake ya tashi ya bata hakuri. So yake ta yafe mishi. Yana jin yafiyarta ce kawai zata yaye wannan duhun. Da wani irin karfin hali ya samu ya soma motsa idanuwanshi. Ji yake komai ya mishi nauyi. Kamun a hankali ya bude idanuwanshi. Ya dade sosai kamun ya fara ganin alin haske haske. "Nawaf......" Ta sake fadi. Baya son yanayin da yakeji cikin muryarta. Raunin da yakeji fiye dana kowanne lokaci ne. Sake kiran sunanshi tai. Sai lokacin ya fara ganinta dishi dishi. Yanaji daga can gefe wani kaman yaya khamis na fadin. "Call the doc" Saidai baya ganinsu. Nuriyya dinma dishi dishi yake ganinta. Kanshi yakeji kaman ana doka mishi wasu irin karafa ciki. Ya rasa a ina ma yake jin ciwon a jikinshi. Har cikin tsokarshi ciwo yake ji mai tsanani. A hankalo fuskar nuriyya ke washe mishi. Dakyar muryarshi can kasa yace. "Nuri...." **** Bude idanuwanta tayi ta sauke su kan fu.ad dake zaune yana rike da hannunta. Wani murmushi yai mata dayau ta kasa mayar mishi. Kamun ta kalli gefenta. Sofi ce zaune.  Sake maida kallonta tai kan fu.ad. "M....." Ta kira shi a hankali. Hannunta ya sake dumtsewa cikin nashi yana jin yanda zuciyarshi ke bukatar suna mabanbancin wanda take kiranshi dashi. Sumbatar hannun yayi hadi da fadin. "Princess. Sannu" "Ku kaini wajen shi" Wani numfashi fu.ad yaja saboda safiyya ta mishi bayanin komai tun dazun. Harta gama fada mishi baice komai ba. Saboda baya son zuciyarshi ta fara tauna dukkan maganganun. Komai zai iya faruwa. Nana tafi bukatarshi. Komai da nashi lokacin. Ba Nana kadai ke son ganin wannan bawan Allah  ba. Har shima yana son ganinshi. Yana son mishi godiya akan karamcin dayai ma Nana. Yana son mishi godiya duk da tayi kadan akan abinda shi yai mishi. Baida wani abin da zai iya bayarwa banda wannan. "Zaki ganshi. Yanzun ki huta sosai. Kici abinci kisha magani sannan" Kai ta girgiza mishi tana dakuna fuska. "Yanzun nake son ganinshi" Sauke numfashi fu.ad yai yana kallon sofi data kawo mishi dauki. Kauda kanta tayi gefe. Tasan halin Nana. Ba ta cika nacewa kan abu ba. Saidai duk lokacin da tayi haka din. Lankwasata abune mai wahala. Kawai sai dai ai mata abinda take so shine kwanciyar hankalin kowa. Hannunta ya sake dumtsewa cikin taushin murya yace. "Baki yarda dani ba? Nace miki zamu je. Kici abinci kisha magani tukunna........" Kwace hannunta Nana tayi. Ta kauda kai gefe idanuwanta na cikowa da hawaye. Ba zasu gane ba. Ta jima tana son sake ganin shi tai mishi godiya. Ko sunanshi bata sani ba. Ranar ta dauka zasu fito su same shi a waje. Sanda suka fito baya nan. Tun ranar duk fitar da zata yi tana duba fuskarshi a fuskokin mutane da dama. Dawowar fu.ad yasa ta sake son ganinshi. Saidai taba mishi addu.a. Tana mishi addu.ar samun wadatacciyar lafiya a rayuwarshi. Dan a wajenta tana jin banda mumynta da babanta babu abinda yafi mata lafiya muhimmanci. Yanzun data ganshi. Cikin jini. Tana so ta ga halin da yake ciki. Hawayen dake idanuwanta suka zubo. "Ba zaku kaini inganshi ba sai na mutu ko shi ya mutu tukunna ba......" Da sauri fu.ad yakai hannu ya rufe mata baki. Fuskarshi babu walwala ko kadan yace. "Shhhhhhhh zamuje. Zamuje Nana ki daina wannan maganar. Ya girmi shekarunki" Hannunshi ta kama dayaje bakinta ta sauke shi. Mayarwa yai yana goge mata hawayen dake fuskarta. Kamun ya mike. Safiyya na kallonshi ya fice daga dakin sannan ta taso daga inda take ta zauna kan kujerar daya tashi. "Kinsan ba....." Da sauri Nana tace "Mumy please. Ina son ganinshi. Kuma ina son magana da yan jaridar nan." Da mamaki safiyya take kallonta. Ta dauka ta manta da maganar tunda fu.ad din ya dawo. Duk da bawai hakura sukai su da son magana da Nana din ba. "I thought M ya dawo. Shikenan" Girgiza kai Nana tayi. "Ina son magana dasu har yanzun. You promise mumy" Jan numfashi safiyya tayi ta fitar kamun tace. "Zan kira su. Damun bar asibiti in shaa Allah" Sai lokacin tai murmushi. "I love you mumy" Dariya safiyya tayi takai hannu taba dan jan hancin Nana din. "Sarkin rigima. I love you more" Girgiza kai tayi bata yarda ba. Zatai magana fu.ad ya turo dakin da sallama. Suka amsa mishi. "Nagano dakin da yake. Saidai family kawai ake bari ganinshi" Da sauri Nana tace. "Kuje dani. Zasu barni" Girgiza kai fu.ad yayi. Baya son sake ganin hawaye a fuskarta. Kai ya sake zurawa waje ya hango likitan da sukai magana dashi ya taho. Hanya ya bashi ya shiga cikin dakin. Ya cire ma Nana karin ruwan dake jikinta yana barin abin a jiki dan in sun dawo a mayar mata. Da idanuwa fu.ad yai mishi godiyar fahimtarshi da yayi. Tahowa yai inda Nana ke kokarin sakkowa daga kan gado yana son kamata. Hannunshi ta dafa ta kalle shi tace. "Zan iya fa" Tana saukowa. Takalmanta ta saka. Ta dauki yar hijab dinta ta saka a kanta. Sai yaga tayi wani irin kyau kaman ya saceta. Daukarta yaxo yi ta matsa baya. Da murmushi tace. "Um um. Zan iya" Girgiza mata kai fu.ad yai yana kawo hannuwa zai dauketa. Ta rike su duka biyun. Idanuwanta take yawatawa cikin fuskarshi kamin ta furta. "Ina son yin komai da kaina yanzun da zan iya. Zakuyimun amman da dan saura" Runtsa Idanuwanshi yai yana jin nauyin da zuciyarshi tai a kirjinshi. Yama kasa cewa komai sai hannunta kawai daya kama cikin nashi. Kallon safiyya yake da wani irin yanayi da shi kanshi ya kasa fassarawa. Kamun yaja Nana a hankali suna takawa zuwa kofa. Binsu safiyya tayi tana jin wani irin abu na daban. Ta kasa fassara kallon da fu.ad yai mata. Sai dai ta kwammace hararar data kan samu lokaci lokaci a wajenshi da wannan kallon mai cike da fassarori da yanayoyi kala kala. * Kaman yanda fu.ad din ya fada. Family ne kawai zasu iya ganin nawaf. Fu.ad nata fama amman sunqi saurarenshi. Nana ta ja mishi hannu. Nuna mishi tai daya dagata. Dan basa hangota saboda counter din data boye su. Dagata yai. Likitocin dake wajen ta kalla idanuwanta cike da hawaye. "Please please ku barni inganshi. Bazan yi wani hayaniya ba. I promise. Yamun taimako a rayuwata. Shi ya tayani gano babana. Ina so in ganshi please please" Kallon Nana suke su dukansu. Daya daga cikin likitocin ya gane Nana. Murmushi yai. Koma bai ganeta ba bazai iya hanata ba. Cayai su jira yaje yai magana da wani cikin family din nawaf din. Yakai mintina goma kamin ya dawo yace zasu iya wucewa. Sosai sukai mishi godiya. Wannan karin fu.ad bai sauke Nana ba. Shibya dauketa har suka karasa dakin da aka fada musu. **** Sam allurarar baccin da sukai ma nawaf taqi kama shi. Wani irin kuka nuriyya keyi mai taba zuciya. Tana kallon murmushin da nawaf keson mata cikin idanuwanshi. "Ki yafemun Nuri. Ki yafemun duk abinda nai miki" Hannunshi ta sake damtsewa gam. Bata son wannan kalaman da yake ta maimaita mata tun dazun. "Ki fada kin yafemun inji da kunnuwana" Dakyar cikin kuka tace "Na yafe maka nawaf. Ka yafemun nima" Dakyar yadan gyara kanshi da alama hakan ba karamin wahala yai mishi ba. "Nagode nuriyya. Ina sonki. Zuciyata ke kadai take so. Kece ta farko a cikinta kuma ke zaki zama ta karshe. Ina farhan?" Tambayarshi ta mata wani iri. Dago ido tayi ta sauke su kan farhan dake gefe. Yaji tambayar da nawaf din yayi. Dan haka yadan karasa. Sai lokacin family din nawaf suka gane wanene shi din. Dan bama tashi suke ba. "Ka kula da ita. Ka sota fiye da yanda na sota. Karka bar hawaye ya zuba a idanuwanta kaman yanda nayi. Karka daga hannunka akanta kaman yanda nai. Ka zama farin cikin ta tunda na kasa. Ka kula da Nuri farhan" Duk wani haushin nawaf da yakeji ya nema ya rasa. Dan yanzun ya tabbatar da nawaf da babanshi mutanene ne mabanbanta. Duk abinda ya faru daya masa fahimta ya fahimci nawaf na son nuriyya. Son da yake tunanin ko shi bazai iya mata ba. Sai yanzun ya fahimci taimakon da nuriyya ke fadin nawaf na buqata. Muryarshi a dakushe yace "Kai zaka kula da nuriyya. Kai zaka zama farin cikinta. Saboda duk muna tare dakai. Zamu taimaka maka" Baice komai ba. Saboda yanda yake jin a jikinshi sun gama taimaka mishi. Idanuwanshi yakai kan mamanshi da babanshi da suke tsaye sun zuba mishi idanuwa. Kallon da yake musu yasa ya suka karasa inda yake da sauri. Farhan ya matsa musu ya na komawa gefe. Cikin sanyin murya yace. "Ku yafemun. Na saka ku bacin rai da yawa a rayuwata. Ku tayani roqon Allah ya yafemun......" Kuka sosai mama takeyi. Yana jin kukansu har cikin zuciyarshi. "Ina su yaya khamis" Dukkansu suka karaso inda yake. Suma yafiyarsu ya nema. Ibrahim ne karshe. Shakuwarsu dabance ko a cikin yan uwanshi. Kallonshi ibrahim yake da wani irin yanayi. "Karka fara nawaf. Muna tare. Babu inda zaka je. Inka tafi dawa zan kula?" Da karfin hali yai masa murmushi saboda ciwukan dake fuskarsh. "Zaka kula mun da su mama. Zaka kulamun da duk wanda na damu dasu. Zaka kulamun da kanka. Yaya nagaji sosai." Dafa shi ibrahim yai. Ya mike yana fita daga dakin. Dai dai zuwan wani likita dake tambayarshi wasu abubuwa da bai fahimta ba. Yadai amsa shi da to ne kawai. Yana nan tsaye ya hango wasu su biyu suna karasowa inda yake tare da wata yarinya kyakkyawa a sabe a kafadar namijin. Karasowa sukai wajen shi sukai mishi sallama ya amsa musu. Fu.ad yace. "Nan ne dakin da nawaf yake?" Kallonsu yake dan baigane su ba sam. Zai iya rantsewa bai taba ganin su ba. Hakan fu.ad ya fahimta yace "Muma bamu sanshi ba. Kaga wadda ta sanshi nan. Yamana karamcin da bazai mantu ba. Shisa muke son ganinshi inba damuwa" Yanda nana ke kokarin ya sauketa ne yasa shi sakkota a hankali. Karasawa tai ta kama hannun ibrahim. "Dan Allah kabarni inganshi. Zan mishi godiya ne kawai" Dan dafe kai ibrahim yayi. Inhar sunce nawaf ya musu karamci waye shi zai hana su ganshi. Da kanshi ya kama hannun Nana zuwa dakin. Su fu.ad na biye dasu. Kallo daya safiyya tai mishi tai baya idanuwanta na kawo hawaye. Bata da juriya irin wannan dan haka ta dakata. Koshi fu.ad daga gefe ya tsaya. Kallon family din nawaf yake. Yanda suke a hargitse yana jin zuciyarshi na cika da wani irin tsoro. A hankali Nana take takawa har inda nawaf yake kwance da wata a gefenshi tana wani irin kuka. Su dukansu kallon nana suke. Dai dai fuskarshi ta tsaya tana kallon shi. "Ya jikinka?" Ta tambaya. Sosai nawaf yake kallonta yana son gane inda ya taba ganinta. Ga zuciyarshi na wani irin zafi. Yana jin yanda yake kokawa da numfashin shi. "Da sauqi" Ya fadi a hankali. "Naga babana." Tace mishi. Sai lokacin ya tunata. Oh rayuwa kenan. Cike da taushin murya yace mata. " Naji dadi. Ya jikinki" Dan daga kafada tai alamar yana nan kamun tace. "Zan maka godiya ne. Da banga babana ba badan kai ba. Ba haka naso in ganka ba. Na kasa ganewa ni fa. Na rasa me yasa mutuwa ta zabeni. Kuma kaganka yanzun." Murmushi nawaf yai mata kamun yace. "Lokaci da dama mutuwa tana da rudani. Sai dai hutu ce ga mumini. Ina son in huta. Ina son in samu nutsuwa" Jinjina kai Nana tayi kaman ta gane me yake nufi. Fuad yadan dafa kanta. Ya kallo nawaf. "Mungode sosai nawaf. Allah ya baka lafiya" Sai yake jin wata nutsuwa ta daban. Ko ba komai sanadin shi wannan yar yarinyar ta gane babanta. Da idanuwa ya amsa saboda ya gaji sosai. Sosai nana ta matsa kusa da kunnen shi yanda bamai iya ji tace. "Kana jin tsoro?" Shima da rada takai kunnenta yace mata. "Sosai. Amman ganinki yasa na daina" Wani murmushi tayi kamun ta sake ce mishi cikin kunnenshi. "Nagode. Allah ya baka aljanna. Sai mu zama abokai acan" Lumshe idanuwanshi yai yana jin kaunar Nana har ranshi. Kama hannunta fu.ad yayi. Tace. "Zan dawo....." Baice mata komai ba. Har sunkai kofa yace "Ya sunanki?" Juyowa tai da murmushin nan sannan tace "Nana safiyya" Kai yai kokarin daga mata wani irin tari ya sarqe shi. Da gudu Nana tai niyyar karasawa ganin yanda jini ke fitowa daga bakinshi fu.ad ya dauketa. Kwantar da ita yai a kirjinshi tana wani irin ihun kuka ya fita da ita daga dakin da gudu. Gaba daya family din nawaf suna kanshi. Sun rikice sosai kowa kwala mishi kira yake. Nuriyya tana rike dashi da hannunta tana jijjigashi. "Nawaf ina zaka tafi kabarni?" Sosai take kuka. Shi kanshi farhan wasu hawaye yaji sun cika mishi idanuwa. Mama kuka take kaman zata shide. Yaya khamis ya kasa koda motsawa daga inda yake. Babane yaga yanda numfashin nawaf ke sama ya soma karanto mishi kalmar shahada da karfi. Aikam kaman nawaf ya na saurarenshi. Yana karanto mishi muryarshi na rawa. Nawaf din na maimaitawa daya bayan daya. Dagaji harshen shi harya karye. Kuka suke sosai. Ibrahim na rike da hannunshi daya yana kallon yanda numfashin shi ke sarqewa. Muryarshi bata fita sosai. Kamun komai ya tsaya.......! Fita baba tai daga dakin. Yaya khamis ne ya karaso yasa hannu ya rufe mishi idanuwanshi yana zubda hawaye. Kallonshi nuriyya take yi. Tana jinta kaman ba a duniya take ba. Ibrahim mikewa yai yana ja da baya. Ya kasa yarda nawaf yabarsu. Ya kasa yarda da abinda yake gani. Mama na mikewa ta yanke jiki ta fadi. Da gudu sukai kanta. Nuriyya kuwa ta  zuba ma nawaf idanuwa. Tana kallon murmushin dake kan fuskarshi. Hannu tasa a hankali ta taba jikinshi. Sanyi taji yayi karara. Girgiza kai take yi. Sake taba shi tayi kamin a hankali ta jijjigashi. Gani tai yaqi motsi. Gabaki daya yanayinshi ba iri daya bane da nata. Mikewa tayi tana girgiza kai. Wata irin gigitacciyar qara ta saki tana faduwa kasa......! *#TeamNawaf* *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ            37 *PLEASE inajin dukkan comments dinku nakuma gode. Abu daya zance sa readers na AKAN SO. Gaba dayanshi zai zama da happy ending. Sai dai ina tafiya da reality as much as i can. So please amin hakuri in gama cikin kwanciyar hankali. ILYA* *Naga addu.o.inku daga kan masu mun text da masu kirana a waya. Allah ya saka da alkhairi. Alhamdulillah na samu sauqi sosai. Hopefully zaku dinga jina lokaci lokaci. #AnaTare* Kallon fu.ad take sai kai kawo yake da Nana akan kafadar shi yana ta bubbuga bayanta a hankali. Tunda suka dawo daga ganin nawaf yake lallashinta har tai bacci. "Ka kwantar da......." "Shhhhhhh" Fu.ad ya katse ta yana daquna fuska. Shirun tayi ta zuba masa idanuwa kawai. Da alama baya ji da ganin kowa banda Nana a yanzun. A hankali take jin wani abu a zuciyarta yana dokawa a hankali. 'Ina sonki sofi' kalamanshi suka fado mata. Kowa ya turo kofar ya taimaka mata ba kadan ba. Murmushi ta dora kan fuskarta ganin Ansar ne. Shima murmushin ya mayar mata. Fu.ad dake tsaye yana kallon su yadan runtsa idanuwanshi yana jin kaman ya shaqare Ansar din nan. Ya ringimo katon kanshi yazo. Karasawa yai ya mikama fu.ad hannu. Ya karba yana kauda kai gefe. Murmushi ansar yayi. Fu.ad din nan na bashi dariya ba kadan ba. "Ya jikin nana?" "Da sauqi. Mungode" Ya amsa dakyar. Karasawa yai yaja kujera ya zauna suna gaisawa da safiyya. Wani irin abu yaji ya tsaya mishi a wuya. "Zan wuce safiyya. Idan Nana ta tashi ki kirani a waya mu gaisa" Kasa kasa fu.ad yace. "Kaman kasan bama bukatarka" Harara safiyya ta watsa mishi. Ya dan bude mata idanuwa dake fassara 'Gaskiya na fada'.  Murmushi Ansar yayi ya mike ya ajiye ledar dake hannunshi. Mikewa safiyya tayi. "Ina zaki je?" Fu.ad ya bukata yana tsare ta da idanuwa. Wucewa tai tabi bayan ansar. Safiyya ta raina shi yanzun shine tunanin da yake yi. Karasawa yai a hankali ya kwantar da Nana yana gyara mata kwanciya yaji an kwankwasa kofar. "Yes....." Ya furta batare daya juya ba. Sallama akai aka turo kofar. Duk dadewar dayai baiji muryarba bai hana shi ganeta ba. Da sauri ya juya dan ya tabbatar da abinda kunnuwanshi suka ji. Aikam hamza ne. Shima tsaye yai rike da kofar yana kallon fu.ad din. A hankali ya saki handle din kofar da yake rike dashi ya na shigowa cikin dakin sosai. "Hamza....." Fu.ad ya fadi cikin sigar gaisuwa. Da dan guntun murmushi hamza ya amsa da fadin. "Moh...." Sosai ya karaso cikin dakin. Sai lokacin yaga da mutum a bayan hamza.  Daga kasan kafafuwanta ua fara yawatawa da idanuwanshi. A hankali har yakai kan fuskarta inda ya tsayar dasu cak. Tsaye take tana wasa da hannayenta. Idanuwanta na yawo ko ina na dakin banda kan fu.ad. Wani abu yaji zuciyarshi tayi. Ga bakinshi ya wani bushe. Dakyar ya hadiyi miyau ya furta. "Hussaina. Little sis" Hannuwanshi yasa ya goge fuskarshi da yake jin kaman zufa a jiki. Mikewa yai daga kan gadon ya karasa inda take tsaye. "Hussaina........" Bata kalle shi ba. Asalima rabashi tai ta wuce inda hamza yake tsaye ta tsaya kusa dashi sosai. Hannuwanta ta saki. Takai daya ta kama na hamza ta dumtse gam. Idanuwanta na kasa. Kallonta sosai fu.ad yayi. Inda take tsaye. Sannan ya maida hankalinshi kan hannunta. Hannun hussaina cikin na hamza a dumtse. Lokaci daya ya fahimci me hakan yake nufi. Sai sannan ya lura da yanayin hussaina. Cikine a jikinta harya turo. Hussaina tayi aure. Lumshe idanuwanshi yai. Yakai hannu yana murza goshin shi da yake jin wani abu na yawatawa. Safiyya ce ta turo dakin da sallama ta shigo. Tagansu tsaye cirko cirko. Kallon hussaina take. Sai lokacin ta gane ta. "Hussaina?" Dagowa tai ta sauke idanuwanta kan safiyya. "Anty na" Da sauri fu.ad ya kalleta. Baisan yanda yai kewar muryarta ba sai yanzun. Baisan kewarta dayai tayi girma haka ba sai yanzun daya ganta. Wani abu yake ji a dukkan jikinshi. Gaisawa safiyya tai da hamza sannan suka gaisa da hussaina. Taja musu kujeru suka zauna. "Ya jikinta?" Hussaina ta bukata. Safiyya ta amsa ta da. "Da sauqi. Bacci take" Kai hussaina tadan daga mata hadi da dorawa da. "Daman munzo dubata ne. Zamu dawo gobe in shaa Allah" "Allah ya kaimu goben. Mungode sosai" Da sauri hussaina ta katse ta da fadin. "Saboda ita nazo. Badan kowa ba" Kallonta safiyya tayi ta rasa me zatace. Mikewa tai hamza ma haka. Gani yai sun nufi kofa. Da sauri ya karasa inda suke. "Hussaina.....!" Bude kofar tayi ta fice. Hamza ma haka. Da sauri fu.ad yabi bayansu. Gudu hussaina take tana nufar hanyar da zata fiddata daga asibitin. Tsayawa hamza yai yana tare fu.ad. Hannunshi dake kan kafadarshi fu.ad yabi da kallo. Yana jin wani irin daci a zuciyarshi. "Me hakan ke nufi hamza?" Da wani yanayi a muryarshi hamza yace. "Please ka kyaleta kawai. Ba lafiya gareta ba sosai....." Ture hannun hamza fu.ad yai yana mishi wani irin kallo. "Ka sake bani dalilin binta kenan" Dafe kai hamza yai kamun yace. "Look. Ba wai ina so in hanaka bane. Kanwarka ce. Amman inada hurumin dazan damu da lafiyarta" Kaman daga sama fu.ad yace. "Kana sonta?" Kallon wannan wacce irin tambaya ce hamza yaima fu.ad. "Kawai ka amsa ni. Kana sonta?" Wani dan murmushi hamza yai. "Baka ga shaida a jikinta ba" Duka fu.ad yakai mishi ya kauce yana dariya. "That is disgusting hamza. Kanwata ce" Dafa shi hamza yadanyi. "Karka damu. Ina son hussaina. Ina sonta sosai wallahi. Please zata sauko. Right now space take bukata kabata" Sauke murya fu.ad yai sosai. "Badamuwa. Just...... Just take care of her" Kai ya daga mishi. Yana kallo ya juya yakoma. Hanya ya nufa yana ficewa daga asibitin. Cikin mota ya samu hussaina a zaune ta hada kanta da jikin motar tana wani irin kuka. Saida ya shiga motar ya kullo sannan ya matsa ya rikota. Hannunshi ta rike cikin nata ta na dora fuskarta akai. Kuka take sosai da sosai. "Shhhhh baby please. Kukan ya isa...." Cikin shesshekar kuka tace. "Duk....duk shekarun da nake son mishi magana.... Yanzun ban kula shi ba..... I.....i miss him sosai...." Hannunshi ya zame daga nata. Ya tallabi fuskarta. Cikin idanuwa ya kalleta. "Shima yai kewarki." Girgiza kai hussaina tayi. "Daya neme mu. Saboda me bai neme mu ba duk lokacin nan?" Bashida amsar tambayarta. Don haka yasa hannunshi yana goge mata fuskarta. "Saikin haifo mana baby rigimamme ko" Murmushi tayi. Yadan kissing gefen fuskarta. "Ko kefa. Komai zaiyi dai dai kinjini ko? Bana son kukan nan" Gyara zamanta tayi tana kara goge fuskarta. "I love you" "I love you more" Ya fadi yana kunna motar..... **** Kwance take jikin mamansu nawaf. Tun jiya bayan ankai nawaf makwancin shi ta nemi hawaye ta rasa. Sai dai zuciyarta da take ji kaman anbi takanta da mota. Ga wani irin zafi da take ji tana mata. Bawai bata yarda da cewar nawaf ya rasu ba. Tadai kasa yarda data rasa shi har abada. Ta kasa yarda da cewar ya tafi bata gama fada mishi duk irin son da take mishi ba. Bata gama fada mishi duk yanda take godiya da kalar taimakon dayai mata ba. Tunda yasanta burin shi yaga ya tsameta daga rayuwar da take ciki. Amman ita ta kasa janye shi daga tashi. Kirjinta tafasa kawai yake kaman an zuba mishi garwashi.  Maganar mutane sama sama take jinta. Gaba daya duniyar ta mata wani irin empty. Ji take ba tada kowa daya rage mata a cikinta. Duk da farhan da zuciyarta ke sane da zamanshi bai hanata jin bata da kowa ba. Tana jin mazaunin nawaf daya bari a zuciyarta can wani gefe da take da yaqinin har tata mutuwar ta same ta babu abinda zai cike shi. **** "Tun dazun inata maka magana baka ce komai ba?" Ajiyar zuciya ya sauke. "Banda abinda zan fada indai kan fu.ad ne saboda na jima da cire shi daga zuciyata ballantana ya dame ni" Dafe kai momma tayi. Wani lokacin sai taga da gangan ake cewa fu.ad din na da taurin kai. "Ni dai zanje in sake dubo yar yarinyar nan." "A dawo lafiya. Allah ya bata lafiya" A sanyaye ta amsa da. "Amin thumma amin" **** Baije ko ina ba sai hotel din daya sauka shima wanka yai ya sako kaya ya dawo. Safiyya taje ta dawo. Yana zaune kusa da Nana da tunda ta farka bata ce mishi komai ba tayo shiru. Ya rasa me zai fara ce mata. Duk sai yake jin shi ya wani daburce. "Ya rasu ko?" Ta tambaya. Da sauri fu.ad ya riko hannunta yana girgiza mata kai. "Kibar wannan maganar Nana. Mumynki taje ta dawo. Zata taho da abinda zamuci. Ko kina son wani abin daban?" Kai ta girgiza mishi tai shiru kawai. Tun jiya yaqi barin zuciyarshi tazo mishi da zancen nawaf saboda ba karamun tsorata shi hakan yake ba. Da dare baiyi bacci ba sam. Ya rasa me ya hana shi bacci sai yanzun ya tuna result din test din da akai mishine zasu karba yau. Zuciyarshi yaji wasu abubuwa na tsinkewa a ciki suna barin mazaunin su. Matsawa yai wajen fuskar Nana ya sumbaci goshinta. Wani kasalallen murmushi ta sakar mishi. "Mumy ta koya maka ko?" Murmushin ya mayar mata. Yadan daga kafada alamar baima fahimci me take nufi ba. "In mumy tana son jin ko jikina da fever bata son tambaya haka take yi fa. Bata san nagane ba" Dariya fu.ad yayi. "I love you......" Da sauri ya ware idanuwanshi akanta. Yana jin yanda zuciyarshi ke ta tsalle tsalle cikin kirjinshi. Baisan wanne abin arziqi ya aikata ba a rayuwarshi daya cancan ci wannan kalaman da Nana ta fada mishi. Wasu irin akwatina ya bude ya rufe su ciki dan bazai so ya batar dasu ba. Kallon shi nana tayi ta ci gaba da fadin. "Ina kaunarka kaman yanda nake kaunar mumy tun kamun in sanka" Sake sumbatar ta yai a goshi yana riko hannunta. Baisan kalaman da zai amfani dasu ba dan ya gaya mata kalar yanda yake jin kaunarta daga randa ya dora idanuwanshi a kanta. Hannun ya kamo ya dora kan kirjinshi. Wasu emotions ne yake ji ta ko ina suna danne shi. Muryarshi nadan rawa yace. "Kaunar da nake miki ta girmi abinda kenan ciki" Dariyar nan dayake jin sautinta yafi na komai daya taba ji cikin kunnuwanshi tayi. Kasa tai da murya tace. "Ta fi ta mumy?" Ware idanuwanshi fu.ad yadan sake yi akanta. Itama nata a ware suke cikin nashi kamun su bushe da dariya a tare. Haka safiyya ta turo kofar ta same su. Tun daga bakin kofar take jin sautin dariyarsu. Suna kallonta suka sake wata sabuwar dariyar. Da mamaki take kallon su. Girgiza kai kawai tayi ta karasa gefe ta ajiye kayayyakin dake hannunta. "Nana tashi muje in miki wanka" Daquna fuska tayi. Tana turo baki. "Na iya fa" Kallonta safiyya take. "Muje in tayaki to" Daka kallo fuskarta kasan bata so. Kawai dai ta sakko ne daga kan gadon. Saida ta sumbaci fu.ad a kumatu sannan. Kallon shi tayi sosai. "Kaje gidansu please. Nima zan mishi addu.a" Kai fu.ad ya daga mata hadi da fadin. "I promise" "Thank you" Ta fadi. Tana wucewa toilet din. * Ita kanta safiyya tunda taga doc jana tazo ta dudduba Nana bata ce musu komai ba ta bita taji maganar result din tace mata sai karfe hudu haka ta dawo ta zauna gabanta na wata irin faduwa. A haka fu.ad ya fita yai sallar azahar ya karbi key din motarta ya fita ya siyo musu take away da lemuka ya dawo. Amman daga shi har safiyya sun dan taba ne kawai saboda Nana ta musu magana. Bawai dan suna jin dadin abincin ba. "Mumy baki kiramun su ba fa har yanzun?" Sauke numfashi safiyya tayi. Ta dauko wayarta da jakarta. Lalubo dan katin da yusra fari ta bata tayi. Ta duba number dinta a jiki. Text tai mata sannan ta dago ta kalli nana. "Na masu magana yanzun" Daga nan kan gadon inda take tai kissing tafin hannunta ta hura ma safiyya hadi da fadin. "You are the best mum ever" Dariya tadanyi. Fu.ad dake gefe ya tabare fuska. "Princess mumynki kawai kika sani ko?" Dariya Nana tayi. Ya sa hannu ya dan taba kuncin shi. Babu musu ta matsa kan gadon ta sumbaci kuncin shi. Yace. "Ko kefa" Wayarshi dake gefe ta dauka. Bai hanata ba. Ta mika mishi saboda akwai key a jiki. Kallonta yai yadan kalli safiyya sannan ya ware mata idanuwa. Hannu tasa ta rufe bakinta tana danne dariyar da take ji. Sannan ta saka 'Safiyya' a jikin wayar sai dai ga mamakinta wrong password. Kallon fu.ad tayi ta daquna fuska alamar baiba. Yadan daga mata kafada yana murmushi dake nuna ta sake guessing dai. Dan daga idanuwa tayi tana tunani. Can tace. "Yes......" A fili. Dariya yai. Safiyya ta kalle su. Su biyun nan bata gane yanda suke magana. Saidai ko taji sunyi dariya. 'Sofi' ta rubuta sannan tai masa 👌 sign da hannu alamar ya bude. Images takai. Hotunan ta ta fara gani duk tana bacci. Ta dago ta kalle shi. Bai ce mata komai ba ta ci gaba da swiping gaba tana kallon hotunan dake ciki. Yawanci duk shida abokanshi ne da kayan ball. Gaba daya hotunan babu wanda yai fara.a a cikinsu. Fita tai ta shiga wata folder din daban amman key ne a jiki. Sake kallon fu.ad tai da tambaya a cikin idanuwanta. Ta juya mishi wayar yaga folder din. Wani numfashi yaja sannan yadan yi gefe da kanshi cewar ta sake saka sunan dazun. Ware mishi idanuwa tai yasan so take ta fadi kalar son da yake ma sofi. Ya girgiza mata kai yana dakuna fuska. Dariya ta kamayi ta bude folder din. Hotunan sune shida safiyya a ciki lodi guda. Tasa hannu ta shafi screen din tana kallon yanda suke dariya a tare. Haka taci gaba da wucewa sa duk hoton da zata gani da qarin karfin alkawarin da take daukarwa kanta na saita zama silar komawarsu koda shine karshen abinda zatayi. Saida ta kai karshe sannan ta koma ta bude video record ta soma daukar fu.ad dake zaune yana kallonta. "Me kike?" Ya tambaya. Dariya ta kamayi. Ta juya wayar saitin safiyya data ce mata. "Nana ki bari fa" Sauke wayar tayi tai saving video din. Mikewa fu.ad yayi yana miqa da jikinshi yace ma nana. "Karfe nawa" Duba wayar tayi. "Karfe uku da minti arba.in" Da sauri ya fita baima san lokaci yaja ba haka. * Yana dawowa daga masallaci yana hango motar lukman. Dan haka suna gaisawa suka shiga ciki tare. Da fara.a Nana tace. "Uncle lukman...." Gefen gadon ya zauna ya shafa kanta. Sai da suka gaisa da safiyya sannan ya maida hankalinshi kan Nana da fadin. "Ya jikinki" Dan daga mishi kafa tayi dayaga ta masa yanayi sosai da fu.ad. Bata san ana ce mata ya jiki saboda bata son ganin yanda idanuwan mutane ke canzawa in zasu mata tambayar. "Ina uncle haneef?" Lukman ya amsa da. "Nasan zai zo" Yana rufe baki suna jin turo kofa da sallama. Mikewa lukman yai yana fadin. "Momma sannu da zuwa" Su dukansu gaishe da ita sukai. Fu.ad ya janyo mata kujera ta zauna suna hira da Nana. Doc jana ta shigo suka gaggaisa ta sake duba Nana tace ma safiyya. "Zaku iya tafiya gida ma. Inda wata matsala dai ku dawo" "In shaa Allah. Mungode sosai" Yar ledar data shigo da ita ta mika ma nana da ta karba tai hugging dinta hadi da fadin. "Thank you anty jana" Da murmushi ta amsa da. "Don't mention sweetheart." Hankalinta ta mayar kan safiyya tace. "Zan ganku yanzun kamun ku tafi" Wani irin dokawa fu.ad yaji zuciyarshi tayi kaman zata fito daga kirjinshi. Binta safiyya tayi. Fu.ad ya kalli lukman sannan ya fita shima. Juyowa safiyya tai idanuwanta cike taf da hawaye ta hade hannayenta duka biyun cikin sigar roqo. Muryarta a sauke tace. "Ina bukatar yin wannan nikadai. Please......" Saida yaja numfashi ya fitar dashi sannan yace. "Ki daina irin wannan maganar sofi. Bana so wallahi" Kai ta daga mishi. "Na daina. Ba zaka gane ba. Ina son fara ganin result din ni kadai....." Juyawa tai tana goge hawayen da suka zubo mata. Binta zaiyi yaji an rike mishi hannu. Juyawa yai lukman ya sake shi yana fadin. "Ka kyaleta. A karo na farko a rayuwarka kaji rokon da akai maka mana" Jingina fu.ad yai da bangon wajen baice komai ba. Yaga yarshi ce yana da right din dazaiga result din baisan me yasa safiyya zata dage ita kadai zata gani ba. * Sanda ta shiga office din doc jana na zaune da takardun a babban envelop. Waje ta samu ta zauna jikinta babu karfi ko kadan. Ita kanta bata bude result din ba tunda ta karbo shi daga lab. Dan har ranta tana kaunar Nana. A shekarun nan biyu yarinyar ta wani shiga ranta. Gabanta na faduwa ta bude envelop din ta zaro takardun da na Nana dana fu.ad din. Kallonta safiyya take idanuwanta cike da buri. Runtsa idanuwa doc jana tayi. Lokaci daya wata irin zufa ta karyo mata. Kallon safiyya tayi. Da kallo dayan datai mata komai ya tarwatse. Da wannan kallon taji dalilin rayuwarta ya kare. Da wannan kallon datai mata taji ta karasa rasa komai na duniya. Cikin wata irin murya da bata gane tata bace tace. "Wata nawa nake da?" Bude baki doc jana tayi safiyya ta daga mata hannu hadi da sake maimaita tambayarta. Sauke numfashi doc jana tayi tana jin idanuwanta na cika da hawaye. "Da yanayin yanda komai ke spreading kasa da wata hudu" Mikewa safiyya tayi. Tana jin yanda kafafuwanta ke takawa sai dai komai take ji kaman ba nata bane ba. A haka ta fice daga office din bata ko kula da cewar bata ja mata kofar ba. * Tsaye suke nesa da office din kadan shida lukman yana jin yanda yake fada mishi komai zaiyi dai dai in shaa Allah. Baice uffan ba. Shi kadai yasan halin da zuciyarshi take ciki. Ganin safiyya ta fito ya sa daga shi har lukman suka karasa inda take. "Sofi......." Juyowa tai ta kalle shi kamun ta ci gaba da tafiya. Zuciyarshi yaji ta ci gaba da dokawa. Ita kanta bata san inda zata ba. Wani waje take son zuwa inda ba kowa. Inda babu wanda ke ciki sai ita da halin da take ji. Da sauri fu.ad ya bita. Tare hanyar yayi. Yana mata wani kallo cike da bincike. Idanuwanta ta dago ta sauke cikin nashi tana son yaga yanda zuciyarta ke ciwo. Girgiza mata kai yake yi. "No sofi. Dan Allah karki fadamun. Please na roqe ki banda sauran zuciyar da zata dauki wani rashin" Kafafuwanta taji sun kasa daukarta. Durqushewa tai a wajen tasa fuskarta cikin hannunta tana sakin wani irin kuka marar sauti. Matsawa yake da baya. Ya kasa gane meke shirin faruwa dashi. Babu abinda yake gani cikin idanuwanshi yana gilma mishi banda fuskar Nana. Lukman ya dafashi a tsorace yace. "Fu.ad ya akai?" Ture hannunshi yai yana ci gaba da ja da baya a hankali kamun ya juya da gudu ya nufi hanyar office din doc jana bai damu da yanda lukman ke kwalla mishi kira ba. Tura kofar taji bana wasa bane. Da sauri ta dago kai ta sauke idanuwanta kan fuskar fu.ad. "Yes ko No?" Ji take da da yanda zatayi da tayi. Sai dai babu. Ko da anyi transplant dinma ba wai warkewa zatai ba. Lokaci ne ake sa ran zata kara samu. Muryarta can kasa tace mishi. "No" Lumshe idanuwanshi yai. Yana jin yanda zuciyarshi ke rugujewa kala daban dana lokacin barin shi nigeria. Juyawa yai hannuwanshi cikin aljihun wandon shi. Yana jin yanda girman kalmar da jana ta fada ke samun waje cikin jikinshi. A hankali komai ke tafiya kamun yakai inda zai zauna daram. Iskar asibitin ta mishi kadan. Lukman yaga yasha gabanshi. "Fu.ad..... " Kallon lukman yai. Kallon shi yake da roqo cike da idanuwanshi kaman hakan zai sa lukman ya taimaka ya karbi kadan daga cikin nauyin da zuciyarshi tai mishi. "Fu.ad kaimun magana please. Safiyya ma taki cemun komai. Wai menene?" Yana jin yanda iskar tai mishi kadan. Dan numfashin shi harya soma samun matsala. Yana fitar dashi da sauri sauri yace. "Lukman my little girl. Yarinyata...... Yarinyata lukman....." Yanda yake watsa hannaye yana jan numfashi yasa lukman kama shi yaja shi gefe yana jingina shi da bangon wajen. "Calm down. Me yake faruwa?" Numfashin shi yaqi kaiwa inda yakamata har yanzun. Yana jin yanda komai yake amsa wa cikin kanshi. "Mutuwa zatayi lukman......." Ware idanuwa lukman yayi yana jin yanda tashi zuciyar ke karyewa. Kallon fu.ad yake da ko ina na jikinshi kyarma yake. Haneef ya hango yana tahowa. A hankali ya karaso inda suke. Kallo daya yai musu yasan ba lafiya ba. "Lukman?" Ya tambaya a dan tsorace. Cike da wani irin yanayi lukman yace. "Nana....." "Inalillahi wa ina ilaihi raji.un......" Haneef ya fadi yana kallon fu.ad dan in shi yana jin zuciyarshi na mishi wannan zafin baisan yanda ta fu.ad take ba a yanzun. Hannu yakai a hankali ya dafa kafadar fu.ad din sai lokacin ya dago. Hawaye ne suka biyo fuskarshi. Abinda rabon da haneef yagani tun suna kanana. Zame jikin shi fu.ad yayi ya hada kanshi da gwiwa. Kuka yake kaman karamin yaro. Nana mutuwa zatayi. Shine abinda yake ta masa yawo. Dafa shi lukman zaiyi haneef ya rike shi yana girgiza masa kai. Wannan ba abu bane da kowa zai iya taimaka mishi. Dole subar shi. Shi da kanshi zai accepting abinda ke faruwa. Fu.ad kam bai taba jin duniya ta mishi kunci ba sai yau. Yar shi da ko damar saninta bai samu ba. Kuma wannan ba laifin kowa bane saina safiyya. Sofi ta boye mishi ita gashi yanzun mutuwa zatai. Mikewa yai yasa hannu ya goge fuskar shi yana shaqar iska mai nauyi kamin ya fitar da ita. Daga haneef har lukman kallo suka bishi dashi. Hanya ya nufa da lukman kadai yasan safiyya ce a wajen. Dan haka yabi bayansh. Hakama haneef. Tana nan zaune inda suka barta tana wani irin kuka. Karasawa fu.ad yai dab da ita. Ta dago da jajayen idanuwanta da fuskarta data kumbura ta kalle shi. Wani irin abune cikin idanuwanshi. Muryarshi a dakushe yace. "Saboda ke bazan san abubuwa da yawa ba akan Nana. Saboda ke na rasa shekaru goma sha daya na rayuwa tare da ita. Bake ya kamata kiyi kuka ba sofi. Saboda ko da ace yau babu Nana kina da shekaru goma sha daya a cikin kanki da zaki dinga dubawa kina samun sauqi. Banida komai!!! Banida abinda zan duba nata banda watanni!!! Wallahi bansan yanda akai zuciyata tai kuskuren sonki ba!!!" "Fu.ad...." Haneef ya kira shi dan yasan yanayin da yake ji zai iya saka shi fadar abubuwan da zai zo yana nadama daga baya. Mikewa safiyya tayi taba kallonshi cike da tsanar da take ji tashi da rashin adalcin da rayuwa take mata ta ko wanne fanni. Batare data kalli haneef ba tace. "Kabarshi!  Kabarshi ya fadi duk abinda yake so ya fada. Kabarshi ya fadin son ranshi dan baisan kowa ba sai kanshi. Kana da bakin da zaka doramun laifi fu.ad?" Ji yake kaman ya makareta. Taya zata iya tsayawa gabanshi tana masa wannan kallon kaman shine da laifi. "Kai ka tafi. Ban kama ka na turaka waje ba!  Kai ka zabi kabarni. Saboda me zaka ga laifina?" Sosai yake kallonta. "Saboda me zaki kasa ganin a kowanne zabi danayi kece a cikinshi? Kina son yara nikuma bazan iya baki ba. Sai nayi laifi dan na barki ki auri wanda zai iya baki abinda na kasa?" Girgiza kai safiyya take tana jin wasu hawayen na zubo mata. Kama shi haneef yai yana fadin. "Wannan bazai baku mafita ba fu.ad......." Kwacewa yai yana kallon shi da fadin. "Ni nai mata laifi inma laifi ne haneef saboda me zata hukunta mu harda Nana? Saboda me zata hanamun rayuwa da yata?" Ya karasa maganar da wani sanyin murya daya karyama daga haneef har lukman zuciya. Muryarta can kasa safiyya tace. "Na nemeka. Na nemeka daga lokacin dana gane ina da cikin Nana. Na nemeka fu.ad gaba daya numbers dinka a kashe" Kallonta yake yana tuna yanda ya kashe wayoyinshi gabaki daya na tsayin watanni. Kamun cikin daga murya da kukq safiyya tace. "Ya kake so inyi?! Meye banyi *Akan so*nka ba? Saboda me zaka dauka kai kadai ne zaka rasa Nana? Ko ka dauka ka fini sonta?" Kallon lukman yai. "Kaji ta ko? Kaji ta ko lukman. Zan dauki yarinyata. Zan kaita ko wacce kasa ta duniya. Zan kashe komai dana mallaka dan ta samu lafiya" Wata dariya safiyya tayi da bata san daga inda ta fito ba. "Welcome to reality fu.ad muhammad arabi. Inda tarin dukiya bazai maka amfanin komai ba! Zunubanmu ne muke girba ta wannan hanyar. Wallahi fushin iyayene muke gani" Kuka take sosai. Kalamanta sun girgiza shi. In haka rasa da yake me su abbah suka ji da ya tafi? In haka soyayyar yara take wacce iri su momma ke masa dayake dauka a arha? Tabbas safiyya ta fadi gaskia. Gaskia sofi ta fada. Barin iyayenshi ne ke bibiyarshi. Fushin abbane yake bibiyarshi. Kallonta yai da wani irin nauyi. "Zamu gyara komai. Babu wanda zai iya saving Nana. Allah daya dora mata ne kawai zai iya. Sofi zamu gyara komai. Zamu ba kowa hakuri. Inna da baba. Su abbah. Zamu fara ganin dai dai in suka yafe mana" Hawayen dake zubo mata tasa mayafinta tana gogewa. Da wani sabon kwarin gwiwa ta kalli fu.ad. "Komai zai gyaru in suka yafe mana. Munyi kuskure na daukar zamu iya tsara rayuwarmu da kanmu" Jinjina kai fu.ad yayi. A karo na farko yana ganin laifukanshi a shimfide. Haqiqa babu mai iko sai Allah. Babu wanda ke tsara komai sai Shi......! *#TeamAs* *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ           38 *Ina godiya da fatan alkhairi kaman ko da yaushe. Ba sai na ce komai bama kunsan #AnaTare* Juyawa fu.ad yai safiyya ta dakatar da shi da fadin. "Please ka dauki mukullin motata kuje gida da Nana. Bazan iya ganinta ba yanzun......" Ta karasa maganar muryarta na rawa. Kai ya daga mata alamar yaji ya dan kalli haneef da yake masa wani kallo dake kara karya mishi da zuciya. Sannan ya wuce. Shi kadai yasan yanda yake jin zuciyarshi. Yakai mintina biyar tsaye riqe da handle din kofar yana maida numfashi. Addu.a yake Allah ya bashi karfin gwiwar fuskantar nana batare da zuciyarshi ta sake karyewa ba. A hankali ya tura kofar yana jin sallamar da yake sonyi tsaye a ranshi taqi fitowa. Idanuwanshi ya sauke kan momma. Muryarshi a dakushe yace. "Gida zamu tafi. An sallameta" Da fara.a momma tace. "Alhamdulillah. Aikam nima bara na tashi......" Kai yadan daga mata. Nazarin shi take kwata kwata a birkice yake hankalinshi kaman baya jikinshi. "Fu.ad?" Ta kira cike da alamun tambaya. Kallonta yai sosai yana roqonta da idanuwanshi da karta tambaye shi komai. A hankali ya girgiza mata kai. Shiru tayi tana mikewa tace ma nana. "To yar tsohuwa nikam zan wuce sai nazo duba ki ko?" Dariya Nana tayi da sautinta yasa fu.ad jin zuciyarshi ta wani matse kaman zata fashe. Baya son tuna karancin lokacin dayake dashi najin wannan sautin. "Ni zan zo ai. Mumy zata kawo ni in kwana gidanki" Murmushi momma tai mata. "Allah ya kawo ku lafiya. Ya kara sauqi" Ta amsa da. "Amin. Allah ya tsare hanya" Momma na tafiya ta amsa ta da. "Amin thumma amin" Raba fu.ad tayi ta wuce batare data ce mishi komai ba. Yaji dadin hakan dan baya jin zai iya wata magana a yanda yake jin shi. Kayan su ya fara tattarawa dan baya son ko kallon inda Nana take. Saukowa tai daga kan gadon tazo inda fu.ad ya saka warmers dinsu a babbar leda ta kamo hannunshi tana ja. Sai da ya ja wani numfashi ya sauke shi batare daya kalle ta ba yace. "Princess ina jinki...." Sake jan hannun shi tayi. Bata son yanda yake kin kallonta din nan sam. Tasan me hakan yake nufi. In tun yanzun zasu fara mata irin hakan nan gaba bata san me zai faru ba. A hankali ya juyo ya sauke idanuwanshi da suka sake launi kan fuskarta. "Ina mumy?" Ta tambaya tanajin komai baya mata dadi. Bata son ganinsu cikin damuwa ko kadan. Da da yanda zatai ta cire musu da tayi. Dakyar yace mata. "Sunyi gaba dasu lukman ni dake zamu tafi" "Hmmm" Nana ta fadi ta saki hannunshi taje tana saka takalminta da hijab. Sannan ta dawo ta kama hannunshi suka fita tare. Saida ya bude bayan motar ya zuba kayayyakin ciki sannan ya bude ma nana ta shiga ya zagaya shima ya shiga. * "What is wrong?" Nana ta tambaye shi kaman daga sama. Dan kallonta yai sannan ya maida hankalinshi kan tuqi da fadin. "Bakomai me kika gani?" Sake lafewa tai cikin kujerar motar tace. "Kayi shiru tun dazun" Shi kanshi bai kula da cewar tunda ya soma tuqin baice komai ba. Yanajin yanda hannuwanshi ke wata zufa duk da AC din motar a kunne yake. "Bako....." Da sauri ta katse shi da cewar. "Please kar kamun karya. Na tsani aimun karya" Sauke numfashi yai. "Tsana is not a nice word princess" Sauke murya tayi tace "Kayi hakuri" Kai yadan daga. "Yau dinne babu dadi shine kawai" Ba karya ya fadi ba. Gaba daya ranar bata mishi dadi. Tun kamun a fada mishi wannan mummunan labarin. Hankalinta ta mayar kan titi sosai tana kallo hanya. Da wani irin yanayi mai nauyi da bai taba ji a murya yarinya mai shekarunta ba tace. "You are not a match ko?" Motar yaji tana kokarin kwace mishi. Kamun ya samu yadan dai daitata yana rage gudun da yake. Wani irin yawo zuciyarshi take yi cikin kirjinshi. Wani abu daya tsaya mishi a wuya ya hadiye. Zufa yake ji ta wajaje da dama tana fito mishi. Baya son mafa karya ko kadan. Saidai baisan ta inda zai fara gaya mata gaskiya ba. Tsoro ne cike fal a zuciyarshi. Koda Nana zata sani baiso daga shi sai ita ba. Tafi sabawa da sofi. Zata so kasancewa da ita a wannan lokacin bashi ba. Duk da fadar hakan a kanshi kawai ba karamin ciwo abin yake mishi ba. "Princess......." Ga mamakinshi gyara zama tai ta zuba mishi idanuwan nan nata iri daya da nashi. "Ya mumy take? Ya ta dauki hakan? Bata ji dadi ba ko?" Nana ta jero mishi tambayoyin lokaci daya. Damtse steering wheel din yayi kaman zai karya shi. Tagane. Tasan bai matching ba. Muryarshi a sarqe ya amsa ta da. "Pretty bad" Shiru yai dan baisan kalaman dazai dora yanayin safiyya akai ba. Dashi kanshi. Dan har yanzun jiyake gabaki daya duniyar shi tayi wata irin girgiza da komawarta dai dai abune mai wahala. Ko yanzun da yake tuqi kokawa yake da zuciyarshi da duk wani abu nashi ya yarda cewar babu abinda zai iya yi ma Nana. Shiru tai na lokaci mai tsayi. Tukin yake amman ji yake kamar garin zasu bari. Kwata kwata yaki masa sauri. Yama manta da ya rage gudun motar sosai. Ta gefen idanuwanshi yaga ta cire hijab dinta. Yadan kalleta ya maida hankalinshi kan tuqi yana jin wani irin yanayi da bashida kalaman misaltawa. Hular dake kanta da tunda ya ganta irin sune a kan ko yaushe bata taba cirewa ba tasa hannu ta fitar. Kanta ta shafa da babu gashi ko kwara daya. Ya sake juyowa ya kalleta. Ji yake kaman wani abu na matse mishi zuciya. Kirjinshi zafi yake sosai. "In fada maka wani abu ba zaka fada ma kowa ba? Kayi alkawari" Kai ya daga mata ya kasa magana. Wannan wacce irin rayuwa ce. Shekararta sha daya. Kamata yai ace tana can tana wasanta tana tunanin wanne Disney movie ne yafi wani kyau. Wanne riga yafi burgeta. Bawai zaune anan ba da kanta babu gashi ko kadan. Ji yake zai iya bayar da komai dan ta samu hakan ciki harda tashi rayuwar. "Ina tsoron in mutu" Jiyai wani abu ya tsane a fuskarshi. Dayake da tabbacin duka jinin dake jikinta ne ya koma wani waje. Kamun lokaci daya wani abu mai yaji ya mamaye mishi idanuwa. Hannunta ya kamo da nashi guda daya ya dumtse gam dayan nakan steering motar. Yasan shi ba mai yawan kuka bane. Amman wannan yarinyar ta zaune kusa dashi ta taba mishi zuciya. Yarinyar shi. Jininshi. Yarinya kwal daya da kaddara ta miko mishi kuma yanzun zata sake karbewa. Wasu hawaye ne yana jin taruwar su da ke da wani irin ciwo. Yana jin yan kananan fingers dinta sun matse mishi hannu gam kamun tace. "Kar kai kuka. Please. Kawai ina son in samu wanda zan fada ma ne. Bazan iya fada ma mumy ba. Tana cikin damuwa mai yawa bana so in kara mata.....nasan daka zo ta kara sama ranta zan ji sauqi kuma........" Shiru tai. Saida yadan yi gyaran murya ya hadiye wani yawu yana maida hawayen dake son zubo mishi kamun yace. "Kuma me?" Sauke ajiyar zuciya tayi. "Kawai ina so in fada ma wani inajin tsoro ne ba tare da yace mun komai zaiyi dai dai ba" Kai yadan daga mata cikin fahimtar abinda take fada din. Shi kanshi a tsorace yake saboda me zai kasa fahimtar nata tsoron. Sauke murya tai tace. "Kawai ina son kowa ya zama dai dai ne" Da sauri ya fadin abinda yasan karya ne. "Zamu zama dai dai. Kina iya fadamun kome kike so Nana......zamu zama dai dai.... Duk da....." Saida yaja numfashi a jere yafi sau uku yana fitarwa kamun ya iya karasawa cikin rawar murya. "Duk da hakan baya na nufin ba zamuyi kewar ki duk rana ba" Ya juyo yadan kalleta yana jin yanda zuciyarshi ta rabe gidaje da dama. Murmushin da tai mishi sam bai rage masa radadin dake kirjin shi ba. Da gudi in aka bashi zabi zai karbi cancer dinta. Ya riga da yayi rayuwa. Wannan lokacin daya kamata ace tayi tata ne. Saidai zuwa yanzun idan akwai abinda rayuwa ta koya mishi shine bai da iko da tsari na rayuwarshi. Alkalamin kaddara ya rigada ya dade da rubuta mishi tashi. Da wannan tunanin ya karya corner har suka karasa gida. Maigadi ya bude musu. Suna parking din motar safiyya na fitowa tai tsaye bakin kofar shiga gidan. Kama murfin motar nana tayi tana sauke wani irin numfashi me nauyi hadi da fadin. "Daren yau mai tsayine......." **** Kwance take tana juya text din da jabir yai mata tun da yammaci kan maganar ayna. Rayuwa take dubawa. Ta lumshe idanuwanta. Tasan yana wajen ayna zance ya fada mata. Sai dai maimakon ta hango shi babu komai cikin kanta sai fuskar Nana. Babu abinda take tunawa sai yanayin tashin hankalin da iyayenta suke ciki. Sai take ganin rayuwa babu wanda tazo ma da adalci irinta. Babu wanda ke da kwanciyar hankali irin nata tunda har tana da nutsuwar da zata zauna tana kishi. Godiya ta shiga jeroma Ubangiji da kalar ni.imar dayai mata. Bata san iya lokacin data dauka a haka ba. Sam bataji shigowar jabir ba saida ya hawo kan gadon inda take ya sumbaci kuncinta. "Honey j" Ta furta a sanyaye tana bude idanuwanta kan fuskarshi. Murmushi tai mishi. Ya mayar mata. "Naji kana kamshi. Ko ayna ta feso maka turaren angonci tun yanzun" Tana kallon yanda sonta ke yawo cikin idanuwanshi. Mamakinta jabir yake sosai. Yana kuma jin tsoro can kasan zuciyarshi kar sai anyi auren ta birkice masa. Sauke murya yai. "Jana. Are you okay kuwa?" Saida ta mintsinar mishi kunci sannan tace. "Me yasa kake tambaya?" Gyara zamanshi yayi kan gadon sosai ya kwanta rigingine kaman yanda take. Kanshi yaja ya hada da nata sannan ya soma magana cikin sanyin murya. "Na kasa yarda cewar bakya bani matsala dan zan kara aure. Ina jin kaman kina boye komai ne a kasan ranki. Ina jin kaman zaki iya birkicemun in anyi auren nan" Kanta ta juyo ta sa idanuwanta cikin nashi. Takai hannu ta kamo nashi hannun sosai take kallonshi. "Honey j yau na sake ganin abinda ya kara karyamun zuciya. Yau naga abinda rayuwa take tattare dashi mai muni da kunci. Ko kamun ingani kishi na dawainiya dani. Kuma har yanzun bai daina ba. Sai dai banida dalilin damuwa inhar ina ganin wannan soyayyar cikin idanuwanka. Fatana daya kar wani abu ya canza ta" Sauke numfashi yai. "Ina sonki sosai jana. Nagode da kalar kaunar da kika nunamun. Allah yasa kece matata har a aljanna" Sosai taji dadin addu.arshi. Itama tata takeyi musu. Allah ya basu zama na fahimta ya bashi zuciyar yi musu adalci. Hannunta ta dora kan cikinshi sannan tace. "Kaci abinci?" Hannunshi ya dora kan nata. "Ina zanci abinci naki yana jirana?" Dariya tayi tana mikewa. Ta sauka daga kan gadon. Ta zagayo.  Saida ta rankwafa sannan ta sumbaci gefen fuskarshi. Hannu yasa ya kama kanta ya sumbace ta a labba sannan yai mata rada a cikin kunnenta. Dariya tai sosai tana girgiza kai. "Ka tashi nikam muje muci abinci" "Duk abinda uwargida take so" Ya fadi da murmushi. Girgiza kai kawai tai ta wuce da wata kaunar shi mai nauyi a zuciyarta.......! **** Ya rasa abinda yake masa dadi a zuciyarshi. Sam tunda ya koma gida ummie ma da tazo tana tambaya cayai mata ba komai. Karantar datai baya son surutun yasa taba shi waje. Ya kuma ji dadin hakan ba kadan ba. Wayarshi ya dauko ya nemo number din pha.iza ya kira. Ringing din farko ta daga hadi da yi mishi sallama ya amsa mata ta dora da fadin. "Kowa lafiya dai ko yaya haneef?" "Hmm pha.iza ya mukai dake?" Ya bukata yana tuna maganar dayai mata tun jiya. Dan saida ya fara kiran abdulkadir mijinta ya roke shi daya barta tazo asibitin yau kamun ma yai mata magana. Shiru ta danyi kamun ta ciki ciki ta amsa shi da. "Kayi hakuri yaya haneef. In shaa Allah zan samu lokaci inzo. Kawai zuciyata ce ta kasa hakura wallahi" Dafe kai haneef yai. Yau yaga rayuwa ba komai bace ba. Yar yarinya ma kenan da bata da wani zunubi mai yawa Allah ya dora mata wannan ina gasu. "pha.iza kijini. Gabaki daya rayuwar nan bata da tsaho. Mu dukanmu munyi kuskure da muka zabi mu share fu.ad kaman yanda yai mana. Daya mutu fa? Ban fada miki yarshi bata da lafiya ba? Yar karama ce. In kika ganta zaki sota sai dai cancer take fama da. Allah baiyi rayuwarta zatai tsayi ba. Fu.ad na bukatar soyayyarmu ne ba fushin mu ba pha.iza. Dan Allah ku yafe mishi yaji da abu daya" Yana jin yanda ta amsa da "In shaa Allah" Dakyar sannan ta kashe wayar yasan kuka take. Sauke wayar yai yana tunanin yanda rayuwa zata iya birkice maka cikin kankanin lokaci. **** Tunda Ansar yazo suke zaune su duka hudun a falon an rasa wanda zai fara magana. Nufin safiyya su dukansu in Nana tana ganin su zasu iya comforting din ta. Amman abin ya gagara. Rashin iyayenta zafin shi dabanne a zuciyarta. Bata san asalin ciwon da zuciya zata iya ji ba sai yanzun. Tasan babu wanda zai fahimce ta sai wadda tasan dadin haihuwa. Sai wadda tasan me rayuwa da d'a yake. Dan daka raina har tsayin shekara goma sha daya. Ki jariri ne ka rasa hakan nada ciwo sosai balle wanda irin wannan shakuwar ta shiga tsakaninku. Mikewa daga kan kujera nana tai inda take zaune kusa da fu.ad. Yana kallonta ta taka har ta karasa inda sofi ke zaune kan kafet tayi shiru. Zama Nana tayi ta na matsawa sosai kusa da safiyya. Hannuwanta ta bude ta rungume ta. Sosai ta matse sofi a jikinta. Wani irin kuka marar sauti ne ya kwace ma sofi. Ita ya kamata tai ma Nana wannan bawai ita ta lallashe ta ba. Tissue din dake hannun ansar yasa yana goge idanuwanshi da yake jin sun kawo hawaye. Bazai manta shekaru hudu Kenan da kaddara ta hadashi da safiyya. Taje neman aiki a company din da yake aiki. Tun daga ranar ta shiga zuciyarshi. Hakan bai karu ba sai lokacin dayaga Nana. Itace sanadin shakuwar su da safiyya har yaji labarinta. Nana ta hadasu. Bazai manta yarinyar ba da lafiyarta. Yarinyar da duk wanda zai ganta sau daya zai jima bai mantata ba. Bazai manta shekaru biyu da sanin su dayai ba Nana ta fara wannan rashin lafiyar. Yana tare dasu a duk lokacin nan. Duk da bai aure da wuri ba. Kuma matarshi har yanzun Allah bai azurta su da samun haihuwa ba tun bayan barin datai bai hana shi jin nana kamar yarshi ba. Yana kaunar yarinyar har ranshi. Kuma ko shi yasa rai da samun lafiyarta. Sai yau din nan da safiyya ta fada mishi. Sosai abin ya tabashi. Yanzun kam ganin yanda suke manne da juna da safiyya ya kara karyar mishi da zuciya sosai. Fu.ad kallon su yake. Yana kokarin tarbe nashi hawayen. Zai zama strong for Nana. Ta roqi hakan daga wajen shi. Bai gaba ganin yarinya mai karancin shekaru irinta ba tunda yake. Duk dai bawai yaga yara da yawa bane. Yana jin ita din ta dabance ba kuma dan tana jininshi ba. Ansar yake kallo yanda gabaki daya ya birkice. Sai yanzun yaga tsantsar kaunar da yake ma Nana. Kuma zuciyarshi ba zata taba manta wannan ba. A hankali nana ta janye jikinta daga na safiyya. Tasa hannu tana goge mata fuska. Kamun ta mike. Wajen Ansar ta nufa da yake kan kujera a zaune. A tsayen da take ta bude hannuwanta shima tai hugging dinshi. "I love you. I love you so much uncle Ansar" Take fadi cikin Kunnuwanshi. Kai kawai yake dagawa yana riketa a jikinshi a hankali. Saboda yanajin kalar ramar datayi ta cikin rigarta. Ji yake daya matse ta sosai zai iya karyata. Dagota yai ya sumbaci goshinta da kuncinta kamun ya sake riketa a jikinshi. Magana tai mishi cikin kunne yanda shi kadai zaiji. "Can you do me a favour?" Muryarshi a dakushe shima cikin rada yace. "Ko menene ki fada nana" Sai da ta sauke ajiyar zuciya yana ji kamun tace. "banida lokaci mai yawa. Ina son maida auren su mumy. Kana son mumy kaima ko? Nasan ba zaka ji dadi ba" Yar dariya ansar yayi. Tabbas Nana ta koyar dashi abubuwa da yawa. Ciki har da karfin hali. A hankali ya amsa ta da. "Umm Nana bazan iya da dadynkin nan ba. Na bar mishi" Dariya tai cikin kunnenshi daya sa shi dariya shima. Tun daga sanda yasan safiyya ya karanci wajen mutum daya take dashi a zuciyarta. Koda yana sonta dole zai hakura. Kaunar dayake mata yana jinta kamar yar uwarshi ne. Nana ta katse mishi tunaninshi da fadin. "You are the best uncle Ansar. I love you" Lumshe idanuwanshi yai. Rashinta zai bar wani waje mai girma a zuciyarshi. "I love you more princess din mumynta" Fu.ad kam ji yake daman shi aka runguma haka. Kota ina bukatar lallashi yake. So yake wani ya lallashe shi har sai ya fitar da dukkan ciwon nan da yake cikin zuciyarshi. Sai yanzun ya fahimci abin da Nana tace da ta fadi mishi tana tsoron mutuwa. Ba tsoro take ji wa kanta ba. Tana tsoron abinda mutuwarta zatayiwa wanda take kauna. Zai iya rantsewa Nana ta dabance. Komai nata. Maganganunta da hankalinta ya girmi shekarunta nesa ba kusa ba. Tana tsoron abinda mutuwarta zataiwa mamanta. She is the strongest girl daya taba gani a rayuwarshi. Yana kallo tana takowa zuwa inda take. Saidai yasan ko zuciyar da take da kwari irin tata tana bukatar tallabi. Kokarin saka kanshi yake a matsayinta ya kasa gane me zaiji ace yau yasan a hankali a hankali komai nashi na lalacewa. A lokaci daya kuma yana jin ya kamata ya zama strong saboda halin da zai saka wanda yake kauna a ciki amman ya kasa fahimta. Harta karaso kusa dashi kirjinshi kaman an kunna mishi wuta saboda zafin da yake masa. Goshinta ta hada dana shi tana tallabar fuskarshi da hannuwanta. Yasan kwarin gwiwa take son samu daga wajen shi. Duk yanda yake jin kaman numfashin shi zai tsaya bai hana shi yin alkawarin zai zamar mata abinda take bukata ba. Bashida wani abu dazai bata. Yana jin hucin numfashinta da take fitarwa akan fuskarshi ya ki yarda su hada idanuwa saboda baya son taga raunin da take dashi. "Nagaji sosai. Bacci nakeji" Ta fadi muryarta na wani irin sauka kasa sosai. Bashi bane a matsayinta amman a gajiye yake. Saida yasa hannuwanshi ya dorata kan kafadarshi sannan ya mike da ita. Dakin dayakaita rannan ya nufa. Bai ajiyeta ko ina ba sai kan gadon a hankali. Ya gyara mata kwanciya. Ya zauna gefen gadon. Idanuwanta ta lumshe ta dora hannunta kan cinyarshi hadi da fadin. "Dady!!!" Saida kalmar ta amsa yafi a kirga cikin kunnuwanshi sannan ta samu wajen zama a zuciyarshi. Wani irin abu yake ji da bazai fadu ba. Sai maimaita kalmar yake yi. Cikin kanshi yana jin tana zama wajaje da yawa. Baisan yana bukatar jin ta kira shi haka ba sai yanzun. Da sauri yasa hannu yana goge hawayen da yake jin kaman su fito mishi dan baya son ta bude ido tagani. Jin yai shiru yasa ta fadin. "Zan iya kiranka dady?" Da sauri yace. "zan fi kowa sa.a in kika kirani haka princess" Murmushi tai hadi dayin hamma. Tai shiru yana kallon yanda numfashinta ya canza alamar bacci ya dauketa. Gyara mata hannunta yayi. Ya mike ya zuba mata idanuwa na wani lokaci. Baya son fita daga dakin yana son ya kalleta sosai. Yaita kallonta kamun tabarshi. Saidai a yanzun yana bukatar yadan jinyaci ciwukan dake kirjinshi ko dana yan awanni ne. A hankali ya fice daga dakin yana ja mata kofar. Baisan yana rike da wani numfashi ba sai yanzun ya sauke shi. Inda yabarsu safiyya nan ya same su. Kanshi a kasa ya nufi kofa sannan yace musu. "Tayi bacci" Bai jira amsar da zasu bashi ba ya fice daga dakin........! *#TeamAs* *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ                39 *Mutane da yawa na fadin sunyi sa.a a rayuwarsu. Nagane hakan lokacin da rayuwa taimun kyautar kanwar da Allah baisa mahaifiya zata bani ba* *ZAPHIRA ke kyauta ce a gareni daga Allah. Ina miki fatan alkhairi a komai na rayuwarki. Ba saina fadi yanda nake kaunarki ba. Kema kinsani* *Sorry saboda rashin jina kwaba biyu. Ina busy ne sosai bana samun damar typing sosai. Godiya da kaunarku. ILYA* *#AnaTare* Sosai ya riko zee jikinshi. "Nagode sweetheart. Ban taba zaton zaki fahimce ni ba" Hawayen daya taru a idanuwanta taji ya zubo. Tasa hannu ta goge su. Muryarta can kasa tace. "Haba dee. Da zuciya a kirjina fa. Waye zaiki fahimtarka" Har cikin ranshi lukman yake jinta. Baisan wanne kalar so zainab ke masa ba. Zai iya cewa yafi kowa dace da mata irinta. **** Zaune yake ya hada kanshi da gwiwa. Bazai ce ga iya abinda yake damun shi ba. Komai ciwo yake mishi. Tun daga zuciyarshi. Kanshi da koma ina na jikinshi. Yanajin kaman mota tabi takanshi sai dai babu wani ciwo a jikinshi daga waje. Daga ciki yake jin ciwon. Mikewa yayi. Zaman nan bazai mishi ba. Zaman nan bashi Nana take bukata ba. Tana bukatar yayi setting komai. Ya roki yafiyar zunubansa datake biya. Dan haka ya mike ya ja iska ya fitar da ita ta bakinshi hadi da ficewa ya kulle dakin yasa key din a aljihun shi. * Tun da taxi ta ajiye shi bakin kofar gidansu abinda yai saura daga zuciyarshi yake wani irin dokawa. Ga wata zufa har cikin tafin hannun shi. Koda maigadi ya bude masa yake tambayarshi wa yake nema. Kallonshi kawai yai. Ya rasa me zaice. Yau shi ake tambaya wayake nema cikin gidansu. Kalle kalle yake kaman yaune rana ta farko daya taba shigowa gidan. Komai na nan yanda yasan shi. Wata irin ajiyar zuciya ya sauke yabar maigadin nan tsaye yana binshi da kallo. Da Alama ya mishi kama da yan gidan shisa ya kyale shi. Da wani nauyi kafafuwanshi ke takawa har suka kaishi cikin gidan. Kaman a lokacin ranar daya bar gidan ya faru haka abin ke masa yawo cikin idanuwa. Komai na dakin shine banda furnitures. Zai iya rantsewa yana kallon su wani lokaci can baya su duka zaune suna hira. Wata irin kewar hakan ta saukar mishi. Cikin muryar dabai gane tashi bace yai sallama. Jin shiru ya sake sashi daga murya da sake yin sallamar. **** Tunda ta dawo gida ta kasa daina zubda kwalla. Nana ta tsaya mata a rai ba kadan ba. Dakyar ta iya samu ta watsa ruwa. Haka abbah ya dawo ya sameta. Shima ruwan ya watsa yaci abinci suka zauna falonsu yana kallon tashar Nat geo. Yana kallon abubuwan al.ajabi. Remote control din dake hannunshi ya ajiye gefe ya fuskanci momma datai nisa cikin tunani. Saida yai magana sau uku bata ji ba ya tabata. "Meke damunki?" Cikin sanyin murya tace. "Baka son jin wannan matsalar nasani" Da mamaki ya ce. "Wanne irin magana ne wannan. Abinda yake damunki ai yana damuna ne" Sauke ajiyar zuciya momma tayi. Cikin nutsuwa ta fada mishi duk abinda yake faruwa. Lumshe idanuwanshi yai yana jin wani irin abu na mishi yawo a zuciya. Tun ran da fu.ad yasa kafa yabar gidan abin yake manne da zuciyar shi. Bai ya nunawa ne kawai bawai dan baya damun shi ba. Bacin rai yasa shi yai furucin dayai ba wani abu ba. Bai taba dauka fu.ad zai tafi yaki waiwayarsu ba. Ya dauka abune na karamun lokaci. Zai gane yayi laifi yazo ya roqi gafararsu komai ya wuce. Ya kasa ko da furta ma momma cewar yana kewar dan nashi kaman yanda take yi. Yana son sake ganin shi ko sau dayane domin mutuwa ba sallama take ba. Bacin rai duk shi ya hana. Yanzun da take fada mishi maganar Nana har ranshi yake jin dacin abin. Yasan bakinshi ne ke dawainiya da fu.ad. Fushin daya dauka ne. Hakika fushin iyaye babbar musifa ce ga yayansu. "Baka ce komai ba" Momma ta fadi muryarta na rawa. Ya kasa kallonta. Idanuwanshi a kasa yace. "Ina fu.ad din yanzun?" Girgiza mishi kai tayi. "Haneef yace ya sauka a hotel ne. Ban san kowanne ba" Bude baki abbah yayi zai sake magana suka ji sallama. Saurarawa suka yi. Sallamar suka sake ji wannan karin da dan karfi. * Fitowa su momma sukayi tare ita da Abbah dan su dukansu sunji kaman muryar fu.ad din. In da ya dauka zuciyarshi dokawa take ba komai bane akan yanda yake jinta yanzun. Zai iya cewa su momma dake tsaye suna ganin hakan ta cikin rigarshi. Hannu yakai wajen ya danna yana kokarin saita zuxiyarshi daga dokawar da take yi. Bakin shi na rawa idanuwanshi kafe kan abbah yace. "A.... Abbah....." Kallon shi abbah yake. Ya girma sosai kaman ba fu.ad din shin nan ba. Dan shi daya fi so fiye da kowanne cikin yayanshi ko da baya nunawa. Yana kallon fu.ad din na takowa zuwa inda yake. Ya kasa cewa komai. Kallon shi yake yana tuna tsahon shekarun da suka wuce bai neme su ba. Baisan yanda akai kafafuwanshi ke kaishi wajen abbah ba. Zai iya cewa tsantsar kaunar shi da yake yine a zuciyarshi ke janshi. Saboda a shekarun nan yaki barin zuciyarshi ta fada mishi yanda yai kewar abbah. Yana amfani da fushin da yake yi dashi ne yana danne komai. Inda Abba yake ya karasa. Hannuwan abbah ya fara kamawa ya sumbata duka biyun. Wani irin abu yake ji yana masa yawo. Baisan lokacin da kafafuwanshi suka kasa daukar shi ba. Tsugunnawa yai yana sakin hannun abbah. Da duk hannayenshi ya rike kafafuwan abbah. Duk abinda yake daurewa tun dazun ne yake dawo mishi. Ciwon da yake ji. Dacin da yake ji. Rashin adalcin da rayuwa ke mishi ta kowanne fanni. Baisan lokacin da hawaye suka fara zubar mishi ba. Kan gwiwoyin shi ya koma ya sake rike kafafuwan abbah dam yana wani irin kuka marar sauti. Gabaki daya jikinshi rawa yake. Ko ina na jikinshi bari yake. So yake yace abbah ya yafe mishi kalma ko daya taqi fitowa daga bakinshi. So yake ya fada ma abbah yau yaga wautar daya aikata. So yake ya fada mishi yau yagane amfanin neman shawara. Yagane irin kaunar da suke mishi. Ya gane ba takura mishi suke yi ba. Ya gane irin wannan ranar suke guje mishi. Yana jin abbah ya tsugunno yana riko shi da nufin ya dago shi daga jikinshi. Girgiza mishi kai yake. Hawayen harda wanda yaki bari ya zubar lokacin daya tafi yau sun samu hanya. Dole sai abbah ya tsugunna hannuwan fu.ad ya riko muryarshi dauke da yanayi na tausayawa da kaunar dan nashi yace. "Fu.ad kai controlling kanka. Saika ce mace. Da karfin hali aka san namiji" Girgiza kai fu.ad yai. Yana kamo hannuwan abbah yasa fuskar shi a cikin su. Yau lallashi yake bukata. Mahaifin shi yake bukata. Cikin kuka muryarshi na wani irin sarqewa yake fadin. "Abbah nagane soyayyarku mai girma ce a gareni. Wallahi nagane duk wata soyayya kasa take data iyaye. Abbah ka yafemun. Ka yafemun ko zan samu inga dai daina rayuwata......." Hawaye yaci gaba da zubdawa yana damtse hannayen abbah kaman karamin yaro. Momma dake tsaye itama ta kasa tarbe nata hawayen. Kallonta fu.ad yai da fuskar shi da harta kumbura. "Ku yafemun. Dan Allah ku yafemun....." Muryar abbah na rawa yace. "Na yafe maka fu.ad. Na yafe maka duniya da lahira" Wani irin sanyi yake ji yana ratsa shi na daban. Momma ya kalla. Kai kawai take iya daga mishi alamar itama ta yafe mishi. Ta dade da yafe mishi. Kallon abbah yai sosai. Idanuwanshi na sake cika da da wasu hawayen. "Abbah mutuwa zatai. Nana zata mutu. Abbah ku taimakamun ita kadai nake da a duniya. Nayi wautar da in ta tafi bazan sake sanin meye dadin da ya kalleka cike da kauna a idanuwanshi ba. Bazan sake sanin.......abbah" Kasa karasawa yai yanda yakejin numfashin shi har wani sama sama yake yi. Dakyar abbah ya kamashi yaja shi kan kujera ya zaunar dashi. Nasiha ya shiga yi mishi da nuna mishi girman yadda da kaddara a musulunce. Jikin fu.ad ya kara yin sanyi. Momma ta kawo mishi ruwa ya sha. Suna nan zaune aka kira magrib. Bangaren abbah fu.ad din yabi shi sukai alwala suka fita masallaci tare. * Tare suka ci abinci a plate daya. Sai dai duk wani motsi da fu.ad zai saiya sake kallon abbah yace. "Abbah ka yafemun" Saida ya gaji yace mishi. "Fu.ad komai ya wuce. Anan zaka kwana yau. Gobe kaje ka kwaso kayanka ka dawo gida...." Kai ya jinjina ma abbah alamar yaji. Wata irin girmamawa ta daban yake jin yana musu. Wata irin kauna daya san ko rabin wadda suke mishi bata kai ba. Wanda ya haihu yasan meye dane kawai zai iya sanin girman kauna har haka. Har sukaje sallar isha.i da abbah suka dawo. Dakin shi tun nada momma ta bashi mukullin ya wuce. Yai mamakin ganin dakin fes. Komai na nan babu abinda aka canza. Wani irin abu yaji na daban na masa yawo. Duk wanda ya dauki soyayyar iyaye abin wasa hakika yana daya daga cikin marassa rabo. Kwanciya yai yanajin sanannen yanayin dake cikin dakin na nutsar dashi. Yau zai huta. Yau zaiyi jinyar ciwukanshi. Zai tattara duk wani strength daya san Nana na bukata daga wajen shi. **** Tunda ta tashi ta zabi kayan Nana data san tafi so. Wata doguwar riga ce ta atamfa purple. Ta dauko mata takalmanta da hijab purple. Dan sunyi da yusra zata zo karfe goma na safiyar ranar dan suyi magana da Nana. Kitchen take tana soya kwai nana ta shigo. Sanye take da riga da wanda kanta da hula. Duk ramar datai bai hana safiyya ganin tayi mata wani irin kyau daya taba mata zuciya ba. Kujera ta janyo ta hau sama. Safiyya ta lumshe idanuwa. "Nana na hanaki tsayuwa kan kujerar nan. Sai kin fado ko?" Dariya tai tana leqa frying pan din da safiyyar ke soya kwai hadi da fadin. "Na tsaya da kyau bazan fado ba. Mumy in tambayeki?" Saida ta juya wainar kwan dake ciki sannan ta amsa da. "Uhum ina jinki" Shiru tadanyi na wani lokaci. "Kinyi alkawari ba zakiyi kuka ba in na tambaya?" Wani miyau safiyya ta hadiye dan tun kamun ma ta tambaya din taji hawaye na taruwa a idanuwanta. Muryarta a sarqe tace. "Ina jinki" "Menene soyayya? Ya ake ji in ana soyayya?" Cike da mamaki safiyya tace. "Me yasa kike tambaya?" "Oh oh mumy. Karki yi kuka please idan na fada miki" Jinjina mata kai tayi. Idanuwa nana ta ware kan fuskarta hadi da fadin. "Saboda nasan bazan girman da zansan ya akeji ba shisa nake so ki fadamun" Abun dake tsaye wuyanta take ta so ta hadiye ta kasa. Dan gyaran murya tai tana kifta idanuwanta cikin son maida hawayen dake son zubo mata. Kettle ta dauko ta dora musu ruwan zafi sannan ta fuskanci Nana tace. "Soyayya wani abune mai girma Nana. Babu kalaman da zaka dora girmanta akai. Wani irin yanayi ne na daban" A nutse Nana ke kallonta tana son fahimtar me take fada. Kamun taci gaba da cewa. "Lokacin da kake son wani zakaji zuciyarka ta cika. Bata gane komai sai wannan yanayin. Zakaji kaman daman can an halitta maka zuciyarka ne domin mutum dayan nan" Tunawa take. Tana tuna yanda taji son fu.ad. Yanayin soyayyar shi a zuciyarta. Komai dawo mata yake da wani irin bazata. "Haka kikaji da dady?" Nana ta tambaya muryarta da murmushi. Hararta safiyya tayi. Shagwabe fuska nana tayi. "Mumy please. Waye zai fadamun in bake ba?" Yar dariya safiyya tayi. Karya itace karshen abinda zata so taima Nana a wannan lokacin. Dan haka ta zabi ta gaya mata gaskiya. "Ya girmi hakan da dad dinki" Cike da jin dadi Nana tace. "Har yanzun?" Wannan tambaya ce da bata son amsa ma kanta ita. Bata son ta fara wannan tunanin ko da wasa. Da wani rauni ta kalli Nana hakan yasata fadin. "I'm sorry" Murmushi tayi. "Daukar mana wannan kikai mana falo gani nan zuwa" Ba musu Nana ta dauki plate din dankali da na wainar kwan ta wuce. Sauke numfashin da take rike dashi tayi. * Suna gama breakfast din Nana tace zataje ta kara yin wanka. Itama safiyyar wankan taje tayi. Tana fitowa yusra ta kirata suka gaisa. Tace mata zata iya tahowa a shirye suke. Atamfa ta saka daviva ruwan hoda ta matukar amsar jikinta. Duk da babu wata kwalliya a fuskarta. Tana zuwa falo ta zauna Nana ta fito sanye da doguwar rigar daya fito mata da ita da er hijab. Kallonta safiyya take. Harda jan baki pink a lebenta. Dan murmushi tayi. "Bana so inyi kama da marassa lafiya. Bana son mutane su kalle ni da irin abinda nake gani cikin idanuwanku bayan basu sanni ba" Sauke idanuwanta tai daga kallon da take ma Nana a sanyaye tace "Wanne irin kallo ne muke miki Nana?" Karasowa tai kusa da safiyya ta zauna. "Tausayi. Sona duka a tare. Inkun mun bana jin kaman banida lafiya. Amman in anty jana tamun banajin dadi. Bana son ganin shi a idon kowa sai naku" Sauke ajiyar zuciya safiyya tayi tai shiru saboda bata san me zata ce ba. Wasu maganganun idan Nana tayi sai su saka rasa naka kalaman. **** Da motar abbah yaje hotel din ya dauko komai nashi yai Check out ya dawo. A gida yai wanka sukai breakfast gabaki daya. Wata irin kewar Nana yake ji. So yake kawai yaje ya ganta. Shiya fara mikewa daga kan dining din hadi da fadin. "Momma aramun motarki" Kamun ta amsa Abbah yace. "Ka dauki mota daya cikin nawa kawai" Saida ya kalli abbah sosai sannan yace. "Nagode abbah. Allah ya kara girma" "Amin. Kaje daki mukullan suna nan gefen gadona" Kai yadan daga alamar to. Haryazo wucewa abbah yace. "Fu.ad......" Dawowa yai ya zauna. Yana bama abbah dukkan hankalin shi. "Ka kawomun ita anjima inganta" Cike da kaunar abbah cikin idanuwanshi yace. "In shaa Allah" Sannan ya mike. 406 ya dauka dan shi yanzun duk wani kyale kyalen duniya ya fice mishi a rai. Daya shiga ciki yaja motar wani murmushi ya kwace mishi. Rayuwa ba komai bace ba. Wai yau shine kwata kwata bai damu da mota ba. Ta zame mishi wani abu dazai hau ya biya bukatarshi. Bai kuma damu ba. Abin ya bashi mamaki. Cike da tunani barkatai yahau titi. **** Kwankwasa kofa sukaji suna zaune suna hira ita da Nana. Ware idanuwa Nana tai kan safiyya. "Turo" Safiyya ta fadi. Dan ta dauka yusra ce. Fu.ad ne ga mamakinta. Kallon shi take. Sanye yake da jeans blue. Sai wata hoodie fara kal. Hular na kanshi. Yaja hannun hoodie din zuwa gwiwar hannun shi. Yai wani irin kyau. Sallama yai. Ta amsa a sanyaye saboda hakan take jin jikinta ya mata wani irin sanyi. Da gudu Nana ta tashi taje ta rukunkume fu.ad tana fadin. "Dady. Inata missing dinka" Dagota yai jikinshi. Ya sumbaci kuncinta duka biyun sannan yace. "Princess ta sha kyau yau. Inata missing dinki nima" Wayarshi ya lalubo cikin aljihunshi da dayan hannun. Dayan na rike da Nana dake faman murmushi bakinta yaki rufuwa. Camera din ya bude ya daga ya dauke su. Sake rike shi nana tayi yana ta daukarsu. Sumbatarta yai a kunci yana daukar su a haka. Hannunshi mai wayar yasa yana nuna mata alamar tai kissing dinshi a kumatu. "Dady zan shafa maka lipstick" Daquna fuska yai dake nuna bai damu ba hadi da juya mata idanuwanshi. Dariya tayi. Ta zagaya hannayenta duka biyun a wuyanshi sannan ta sumbaci kumatunshi ya dauke su wajen kala goma. Sannan ya kalli safiyya. Saurin kauda kai tayi. Dan ta fahimta sarai. Babu abinda zai ja mata daukar hoto dashi. Nana ya kalla yana wani matse lips waje daya. "Mumy please kizo muyi" Ta fadi. Ware mata idanuwa safiyya tayi alamar bata so. Nana tace. "Dady zaka dauki pic da mumy" "Banda matsala princess. Duk abinda kike so" Fu.ad ya fadi yana karasa maganar da kallon safiyya. Harara ta watsa mishi wato itace take da matsala. Mikewa tai. Sai lokacin ya samu damar kallonta sosai. Numfashin shi yaji yana masa wasa wajen fita da komawa. Ta canza in all the good ways. Kyanta ya fito fiye da da. Kallon da yake mata yasa ta tuna babu mayafi a jikinta. Kallon shi tai taga idanuwan nana basa kanta. Yanda iya shi kadai zai gani ya fahimta tace "Bana son kallo" Daga mata gira yai duka biyun. Ta taka ta karasa inda yake. Duk da bayanshi ta tsaya bai hana kamshin da take ya cika mishi hanci ba. Mamaki yake sosai saboda collection din smart din daya daina amfani dasu ne saboda suna tuna mishi ita. Shine a jikinta. Sake baza hanci yai kamshin na tuna masa abubuwa da yawa. Dakyar ya iya daga camera din ya dauke su kala biyu duka safiyya na bayanshi ta wani hade fuska. Zai dauki na ukkun aka kwankwasa kofar. Tasan wannan karin yusra ce. Da kanta taje ta bude kofar. Aikam yusra ce sanye da doguwar riga fara. Tai rolling farin mayafi. Hannunta dauke da wata jaka. Da fara.a suka gaisa da safiyya ta shigo ciki. Gaishe da fu.ad tayi ya amsa a dakile.  Saida ta zauna sannan tai ma Nana murmushi hadi da fadin. "Nana" Murmushin Nana ta mayar mata. "Ina kwana" Ta fadi yusra ta amsa. Yarinyar ta mata kyau. Basai an fada mata ba tasan mutumin dake rike da ita shine babanta. Dan ga kamanni nan. "Gata tazo Nana" Fu.ad Nana ta kalla. "Dady sauke ni" Kallonta yai yace. "Wacece?" "Yar jarida" Lokaci daya idanuwanshi sukai wani irin haske. Sake rike nana yai gam. Baya son yarshi a TV balle duniya ta kalle masa yarinya. Baya son labarinshi a kunnuwan kowa. Baya son duniya ta kalle shi da matsayin uban daya kasa yima yar shi komai. Saida yaji Nana nason sauka da kanta sannan ya ajiyeta. Yusra ya kalla. "Bana son ki dauki komai nata....." Ya maida hankalinshi kan safiyya "Ina son magana dake" A dake tace. "Seriously fu.ad? Kabari mugama tukunna" Kara bata mishi rai take "Ki taso ku muyi a gabanta" Mikewa tai. Kitchen ya nufa tsabar masifa ce fal a cikinshi. Abin yaso ya bata dariya. Suna karasawa tace. "Saika cemun yunwa kakeji drama king" Dariya tayi saboda yanda yake mata kallon rashin fahimta. Lokaci daya yaji ya sake kulewa. Ya ma zama wani game wajenta. "kitchen ka kawo mu. Me kake tunanin zan dauka?" Sai lokacin ya kulla. Yadan dakuna fuska dan ya kasa ganin abin dariya cikin lamarin. "Bana son yarinyata a TV. Bana son kowa ya kalleta da kalar me zai fada. Saboda me ma zaki kirasu?" Hannunta ta dora kan kugu tana kallon ikon Allah. "Na dauka tun a asibiti na fada maka tana son magana dasu. Kace bakomai" Kallonta yake dake fassara ashe baki da hankali? "Na dauka kingane dan a gabanta ne. Bakiga idanuwana ba?" Yar dariya tai cike da takaici. "Ka fada mata da kanka" "Bana son ince kar tayi abinda take so" Ya fadi. Bata san randa fu.ad zai bar son kanshi ba. Bata ga rana ba. Shi bashida zuciyar dazai ce ma Nana aa sai ita kenan. Kaman daga sama suka ji ance. "Dady" Da sauri suka kalli Nana a tare. Idanuwanta kan fu.ad a kafe tace. "Na hakura tunda baka so" Tsugunnawa yai. Ya sa hannu ya tallabi fuskar Nana cikin hannuwanshi. "Princess bana son maganganun mutane ne. Bana son ki zama abin kallo da magana. Bana son kowa ya miki kallon something weak and fragile. You are my daughter Nana. Zuciyata ba zata iya dauka ba" Tallaban hannuwanshi dake fuskarta tayi da nata. Murmushi tai mishi. "Ba saika mun bayani ba. Bansan me yasa nake son magana da ita ba. Na hakura tunda baka so" Sunbatar goshinta yayi. "Thank you princess" Dariya tai mishi. "Kubarni in fada mata da kaina" Kamun suce wani abu da gudu ta fice daga kitchen din. Suka kalli juna shida safiyya suna sauke numfashi a tare. * Zama tai gefen yusra. "Anty bazan yi ba. Dady baya so. Na hakura. Amman ki tambayeni ko me kike so zan amsa miki indai ba zaki saka a TV ba" Murmushi yusra tayi mata. Duk yanda take son tasa labarin yarinyar nan baikai yanda ta fahimci babanta ba. Ko itace ba zata so yarta a TV ba sam. Hira suka danyi kadan da yusra. Tana tambayarta ya akai taga babanta duk ta amsa ta. Rokon Nana tayi sukai hoto tare. Sannan ta mike ta kalli su fu.ad dake bayansu. "Nagode sosai. Allah ya bata lafiya" Suka amsa da amin. Har kofa safiyya ta rakata sannan ta dawo. Fu.ad baice mata komai ba. Wajen Nana yaje ya zauna. "Zan je unguwa. Idan na dawo zamuje tare dake okay?" Kai ta daga hadi da fadin. "A dawo lafiya. Love you" Wani kumburi zuciyarshi tayi. Saida yai hugging Nana yanajin kaman ya mayar da ita cikinshi kar wani abu ya sameta sannan ya ce. "Love you more" Dariyar nan da yake so tai mishi cikin kunnuwanshi sannan ya saketa. Mikewa yai ya sauke idanuwanshi kan safiyya. Wani irin kallo yake ma safiyya data kasa fahimtarshi. Muryarshi ya saukar sosai. Idanuwanshi na cikin nata yace. "Zan dai dai ta komai. Zan cika miki wannan alkawarin" Lumshe idanuwanta tayi. Tana jin yanda yake fama mata tsofin ciwukanta. Hular rigarshi ya cire daga kanshi ya kalli Nana yai mata murmushi sannan ya nufi hanyar kofa. * Yana fita daga gidan lukman na kiranshi a waya. Dagawa yai hadi da fadin. "Lukman....." "Fu.ad ya ne? Ya nana?" Saida yai jim ya amsa da. "Okay i guess" Yanajin yanda lukman ya sauke numfashi kamun yace. "Kana gidan ne?" Girgiza kai yai kaman yana ganin shi. "Ina hanyar bichi. Bankai da fita daga cikin gari ba tukunna dai. Em' gonna make it right. Duk abinda na bata" "About time fu.ad. Daka fadamun da munje tare" Murmushi yai. Har ranshi yaji dadin maganar lukman din sai dai wannan abune da zaiyi shi kadai. Baya son kowa ya tayashi. Yagaji da yanda tun yarinta lukman da haneef ke share hanyar daya bata. Wannan karin zaiyi komai. Laifin shine shi kadai kuma shi kadai zai gyara. "Nagode lukman. Nagode fiye da yanda zan iya fada. Kuskure na ne. Ina son gyarawa da kaina." "Hmm. Be safe. Just be safe fu.ad" Yar dariya yai. "Yeah whatever. Ka shafamun kan junior......" Sai yanzun ya tuna. Yadan daki steering motar hadi da fadin. "Em such a bad uncle. Nama junior alkawari lukman ko ka tunamun" Dariya kawai lukman yai ya kashe wayar. Ajiyeta yai gefe ya mayar da hankalin shi sosai kan tukin da yake yi. Daya dawo anjima zai cika alkawarin nan. **** Tura dakin ikram yai da sallama. Tana kwance kan gadon ta tana karatun Qur.an. Saida takai ayar sannan ta amsa shi. Qur.an din hannunta ta rufe ta ajiye gefe a hankali. Da dan murmushi tace. "Pa?" Dan tasan ta musu saida safe tun kamun isha.i. Bakuma al.adarshi bane shigowa dakinta babu wani dalili. Gefen gadon ya zauna. Yana rasa ta inda zai fara. "Lafiya dai ko? Ina mumy?" Ganin yanda duk ta rikice yasa shi saurin cewa. "Komai lafiya ikram. Kawai ina son magana dake ne" Gyara zama tayi kan gadon. "Alright. Ina ji" Saida ya sauke numfashi sannan yace. "Zan kara aure ikram. An sa rana yau. Nan da wata biyu" Shiru tayi tana kara tauna maganar shi na tsayin mintina biyar kamun tace. "Why?" Tana tsare shi da idanuwa. Dan daga kafadar shi yai. "Just......" "Kana son mumy?" Kai ya daga mata. Dan tana jin tsoro. Taga yanda kishiyar maman kawarta jawahir take basu wahala. In tana bata labari takan gode ma Allah da babansu bai kara mata ba. Sosai ta kalle shi. Tsoro cike fal da idanuwanta. Hannunta ya kamo. Yana son ya fara zame ma yayanshi aboki da zasu iya magana ba tare da shakka ba. "Kinsan zaki iya fadamun komai ko? I am your dad. Your best friend ikram" Kai ta jinjina. "Kawai ina jin tsoro. I love mum sosai. Kaima haka. What if ta kwace mana kai" Da wani irin yanayi yace. "Babu wanda zai kwace muku ni in shaa Allah. Babu abinda zai canza. You will be there for me dake da mum inki dasu umar. Ba zaku bari kowa ya kwace ni ba.?" Fuskarta babu wasa tace. "Sosai ma. Promise komai bazai canza ba?" Saida yai jim sannan yace. "In shaa Allah. Kumin addu.a Allah ya tabbar mun da alkhairi. Shi nake bukata" Sai lokacin tai mishi murmushi. Yasan da wuya ta sake cewa wani abu. Ikram bamai yawan magana bace ba. Har yakai kofa tace. "Pa....." Ya juyo ya kalleta. "Thank you" Murmushi jabir yayi. Ya jinjina mata kai kawai ya fita yana ja mata kofar. Numfashi ya sauke yana juya idanuwanshi. "So awkward...." Ya fadi kasa kasa. Ya na takawa zuwa dakin su. Jana ya samu inda yabarta tana dudduba wasu takardu. Idanuwanshi taji suna mata yawo ta dago ta kalle shi sai raba idanuwa yake. Dariya ya bata. "Ya dai?" Dan rausayar dakai yayi. "Kin banni da ikram ni kadai ko?" Dariya ta sake yi. "Baga shi harka gama ba. Nace maka ba wani wahala" Karasawa yai ya zauna kusa da ita. Takardun dake hannunta ya karba ya ajiye gefe daya. "Lokaci na ne yanzun. A taimakamun a ajiye office work din nan jana" Shagwabe fuska tayi. "Nabar ma ayna ai" Ware idanuwa yai. "Tun yanzun?" Dan murmushi tai cike da kishi. Har daci take ji a wuyanta. Ya karance ta tsafa dan haka ya matsa daf da ita sosai. "Naki ne ni jana. Kinsan wannan ko?" Daga mishi kai ta iya yi. Duk soyayyar nan a kwanaki sittin da wata zata dinga rabata. Addu.ar ta ci gaba dayi a zuciyarta. Saida taji wata nutsuwa ta saukar mata sannan ta fara nuna ma jabir kalar soyayyar da take mishi......! **** Kanshi tsaye gidan su safiyya ya wuce da wani irin yanayi na nasara da yake saka shi murmushi shi kadai. Da sallama ya shiga. Nana na zaune tana kallon cartoon network. Ta ruga tqna mishi sannu da zuwa. Safiyya ta fito daga daki. "Sannu da dawowa" Ta fadi. Kai yadan daga mata. Yana kallonta hadi dayin murmushi. Komai nasu ya kusan gyaruwa. Zai bata mamaki bada jimawa ba. "Zamu fita da Nana" Ya fadi. Kai ta daga mishi. Da gudu nana ta ruga daki ta dauko hijab dinta da takalmi ta dawo. Safiyya tace. "Nana ko goodbye?" Da sauri tana dariya ta karasa wajen safiyya ta rungumeta. Sakinta tai ta juya tana fadin. "Sai mun dawo" "Allah ya tsare hanya" Safiyya ta fadi. Fu.ad ya kamq hannun nana cikin nashi suka fita. Wata ajiyar zuciya ta sauke gidan na mata wani irin shiru. * Yana tuqi ne nana tace. "Dady in rokeka?" Kai ya daga mata. Dan bayajin akwai abinda zata nema indai zai iya dazai kasa yi mata. "Ka auri mumy. Dan Allah ku koma aurenku!" Wani shiru yaji cikin kanshi. Zuciyarshi na tsayuwar wucin gadi kamun ta ci gaba da aiki. "Please. Tana bukatarka in bana nan. Kana bukatarta in bana nan. Tana sonka sosai. Dan Allah karka ce No" Zufa ke keto mishi ta ko ina. Nana na tambayarshi abu mai girma. Tana tambayarshi abinda bayajin zai iya. Bashida abinda zai ba safiyya. Bashi da farin cikin da take bukata. Parking yai gefe yana maida numfashi. "Nana...." Ya kira sunanta yana rasa me zai ce. Ta ina zai fara fada mata sakin safiyya dayai yanci ne ya bata. Farin cikin daba zai iya bata vane ya barta ta samu da wani. Idanuwan nana cike da hawaye tace. "Ka daina sonta ko?" Da sauri ya girgiza kanshi. Son da yake ma safiyya bazai taba misaltuwa ba. Sonta yasa yabarta. *Akan so*n da yake mata ya zabi ya barta inhar zata samu farin cikin da shi bazai iya bata ba. Hawayen da suka zubo mata tasa hannu ta goge. Tana son tagansu sun koma. Tana son hakan fiye da yanda take son lafiyarta. "Please dady. Bana so inbar mumy ita kadai. Bana so...... Bata da kowa......" Kuka Nana take yi. Jinshi yake har cikin tsokarshi. Kamo Nana yayi yana tallabar fuskarta yana goge mata hawayenta da sauri. Dan shi kanshi da zai samu wanda zaima kuka yi zaiyi. "Ina sonta Nana..... I love your mum. Ita kadai zan so har abada....." Cikin kuka nana tace. "To ka aureta" Cikin rasa yanda zai ce ma Nana yasa shi fadin. "Banda abinda zan bata. Banda komai dazan bata" Rike hannuwanshi Nana tayi. "In tana sonka a haka fa? Zaka aure ta?" Kai ya daga ma Nana. Son da yake ma safiyya mai girma ne. Yasan bata son shi ta tsane shi yanzun. Ta kuma kara tunda bashida abinda zai bata. Yaji dadi saboda zai bata mamaki zuwa gobe da safe in shaa Allah. Zai bata abinda yasan tana so. Abinda yai mata sanadin salwantarshi. "Zan ma mumy magana. Kaji" Kai ya daga mata. Ya goge mata fuska hadi da fadin. "Bana son kukanki. In kuma na sake gani zan fasa" Da sauri tasa hannu ta sake goge fuskarta. "Na daina. Kayi hakuri bazan sake ba" Murmushi yai. "Good girl..... Zauna sosai to" Gyara zamanta tai ya tayar da motar suna tafiya..........! *#TeamAS*   *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ         40 *"Turomun number dinta inba mamanta mamaki"* 😂😂😂 *Wannan maganar make my day.* *Ayna.u mardiyya (dimples) Allah yabarki da masu kaunarki. Ba saina fadi matsayinki a wajena ba. #ICDWAWFEY* *Biebie Isa Allah yabar zumunci. You know #AnaTare* *To the readers ina godiya da yanda kuke biye dani. Da hakuri da rashin update akan lokaci. ILYA😍* Kwance yake shi kadai a daki. Ya kira number din nuriyya a kashe. Yau kwana uku kenan da rasuwar nawaf. Bai samu yai magana da ita ba. Yana son yaji yanda take. Shi kanshi dayaga Nawaf na mintina rasuwar ta bala.in tsaya mishi a rai. Lumshe idanuwanshi yai. Kaman hoton film rayuwarsu ta wani lokaci ta fado mishi. *Years Back* Kitson da ake mata tace a barshi haka, zata zo gobe da Safe a k'arasa mata. Mai kitso tace "Maman Farhan da kin bari an gama, saura Kadan a gama." Tace "Aa, yanzu maigidana ya shaida min yana kan hanyar gida, kar yazo gida ya iske ba na nan, zan dai dawo gobe" Da sauri ta saka Mayafinta ta fito daga saloon din ta ja Motarta ta nufi gidanta da ke k'asan layi. **     Zaune yake kan Motarshi,  Fuskar shi ba annuri d'aure kamar Lion da ya kwana hudu be ci Abinci ba, tana shiga Gidan Gabanta ya yanke ya fadi ganin shi. K'irkiro Murmushi tayi ta k'arasa gunshi, "Welcome Dear you are home Already" mugun kallon da ya jefeta dashi ne ya sa hanjin cikinta kururuwa. "Daga gidan Uban wa Kike?" Dankwalin kanta ta zame, Baki na rawa tace "daga gidan kitso nake, kuma ai na maka text" Gashin kanta ya damk'a, Ta sandara ihu Zafi ya sa ta kiran sunanshi, "Muhammad Don Allah kayi hakuri, you are hurting me" Be saurareta ba ya jata har Parlo inda ya yasar da ita a k'asa kamar Gabage. Kuka takeyi sosai, ga Zafin kitson ga kuma na jan Gashi, Belt ya shiga Zarowa, ta san dawan Garin, tayi sauri tashi zata gudu ya sa k'afa ya tande ta, ta fadi k'asa, wani ihu ta saka. Muhammad be ji tausayin ta ba haka ya shiga lafta mata wannan belt din kamar Allah ya aiko shi sai da ya gaji don kanshi kafin ya barta. **** Straight Islamiyyar su Farhana ya nufa, ya ci ko sa'a sun tashi, dama abunda baya so ya zo yayi ta jira, da gudu ta k'araso gunshi tana fadin "YaYa Farhan, ina ta jiranka" Murmushi yayi yace "Sorry muje Gida" * Tana jin dawowar su tayi saurin tashi don shiga dakinta, bata kai ga shiga dakin ba taji Farhana a jikinta. "Mummy, me ya sameki?" Rasa abun da zata ce mata tayi, ta fara kame kame. Daga nesa Farhan ya k'are mata kallo, fuskarta duk bruises ya matso kusa da ita  a nutse yace da k'anwarshi; "Farhana je ki cire Uniform dinki" Ba gardama ta dauki jakkarta tayi daki. "Mummy, Daddy ya sake dukkan ki ko?" Ta shiga girgiza kai ta rasa ansar da zata bashi, a fusace yace "For how long zaki cigaba da enduring dukkan da yake miki?" Jiki a sanyaye tace "Kayi hakuri, zai bari" A fusace yace: "Till when zai daina dukkanki? Sai kin aurar damu? Mummy shekaru na Sha takwas, tun ina Shekara 4 nake ganin yana Abusing dinki, Allah kadai yasan tsawon lokacin da kikayi cikin wannan halin, Mummy put an end to this please. Ki kai shi K'ara, befi k'arfin Hukuma ba, akwai Agency na Women Rights and Child Abuse, he's been Abusing us all for quiet a Long time, Mummy i hate seeing you like this" Murmushin takaicin tayi tace "Farhan i cannot, Ni ba kowa bace face Marainiyar Allah, banda kowa, banda wanda zai tsaya mun, Kai da k'anwarka ne Farinciki na, i can endure all this for you, so everything is going to be fine" Takaici ya hana Farhan magana, ya saba jin wannan maganar daga gun Mahaifiyarsa, haushi ya sa shi fita daga Parlorn. **** Wayarshi datai ringing ta katse mishi tunanin da yakeyi. Ya dauko ya duba. Dan guntun tsaki yaja ganin bakowa bane yan mtn ne saikace zasu bashi wata tsiyar. Mikewa yai da wani nauyi a zuciyarshi ganin lokacin sallah yayi. Yana son yin wani abu wa matan dake cikin rayuwar domestic abuse saidai baisan ta inda zai fara ba. Da wannan tunanin a zuciyarshi ya fita masallaci. **** Yana rike da hannu nana da sallama suka shiga babban falon a tare. Momma ta amsa su. Kwace hannunta Nana tayi daga cikin na fu.ad ta ruga da gudu tana fadin. "Granny...." Da fara.a momma ta riko Nana jikinta. Fu.ad kam yarinyar dake zaune kasa tana wasa yake kallo. Ta mishi kyau ba kadan ba. Karasawa yai yasa hannu ya dauketa ya kwantar da ita kan kafadarshi. Ya hada fuskarshi da ta yarinyar yana rocking dinsu a hankali. Yanda tai luf yake jin abin har cikin zuciyarshi. Lumshe idanuwanshi yayi yana jin kamshin yar yarinyar da baisan na menene ba. Powder ce ko turare. Muryarshi can kasa yace. "Momma babyn wacece?" Kallon shi take yanda ya lumshe ido yana jijjigasu shida babyn. Ta kalli nana dake jikinta. Gaba daya sai tausayinshi ya cika mata zuciya. Da sanyin murya tace. "Arfat. Yar pha.iza ce" Bude idanuwanshi yai yana ware su kan momma. Zuciyarshi tai wata irin dokawa. Sauko yarinyar yai daga kafadarshi data soma bacci. Hakan yasata fara kuka. Kallonta yake sosai.  Yar fara ga wasu kumatu. Jijjigata yake taki yin shiru. Ya bude baki zai magana. Pha.iza ta fito daga hanyar daya san ta kitchen ce hannunta dauke da feeder tana daure murfin. Tsayawa tai cak. Idanuwanta kan fu.ad. Shima kallonta yake. Wani miyau ya hadiya. Zaka rantse arfat tasan akwai wani abu dake faruwa daya fi kukan da take muhimmanci. Shiru tayi. Kallonta yake. Kaman ba pha.izar daya sani ba. Tayi girma sosai. Bude baki yai. "Pha.iza....." Baima san maganar bata fito ba. Ita dake tsaye daga nesa zata iya karantar sunanta akan labban shi duk da bai fito ba. Shekaru sha daya. Ya sa kafa ya fice yabarsu batare daya juyo ba. Wani abu ya tsaya mata a wuya. Mikewa momma tayi ta kama hannun Nana. "Zo muje....." Ba musu Nana ta mike tana rike da hannun momma. Dan sam bata kuka da pha.iza ba suka nufi sashin momma a tare. A hankali pha.iza take takowa tana jin yanda idanuwanta ke cika da hawayen dataqi bari su zubo. Karasowa inda yake tayi. Hannu ta mika zata karbi Arfat. Ga mamakinsu yarinyar kara makale fu.ad tayi. Dariya yai yana bude idanuwanshi. Kallon arfat pha.iza tayi ta daquna fuska. "Baki san uncle dinki bai damu damu ba kike makale shi ko?" Wani abu yaji a kirjinshi da maganarta. "Pha.iza......" Ya fadi da wani irin yanayi. Cikin idanuwa ta kalle shi. "Shekara sha daya. Ko ka dauka weeks ne?" Ya rasa me zaice mata. Arfat ta karbe daga hannunshi data soma kuka. Ta samu waje kan kujera ta zauna tana lallashinta. Gabanta ya tsugunna yana wani dafe kai. "Pha.iza please......" Sai lokacin hawayen da take rikewa suka zubo. Muryarta dauke da dacin da take ji tace. "Da sai wani cikin mu ya rasu zaka dawo? Baka taba tunanin ka waiwaye mu ba ko sau daya. Why? Laifin da mukai maka yai girma har haka? Da bro lukman bai kiraka ba ba zaka taba dawowa ba ko? Ka manta kana da yan uwa? Ko baka sonmu baka tunanin mu muna sonka? Bro ko......." Hannunta ya kama da sauri yana katse mata abinda tai niyyar fadi. Idanuwanshi ya sauke cikin nata. Yana so taga nadamar dake cikinsu. Yana so taga yanda girman kaunarsu yake a zuciyarshi kamun yace. "Ni mai kuskure ne pha.iza banda abinda zan fada. Ki yarda dani da ina da iko dana koma shekaru sha daya na gyara komai. Ina biyan kuskuren dana aikata da zuciyata pha.iza............ki yafemun" Hannunta tasa tana goge fuskarta. Ta riga ta yafe masa. Duk da za.a dauki lokaci kamun ta daina jin dacin laifin shi. Jin tayi shiru ya sashi fadin. "Ki yafemun. Bance ki manta ba......." Katse shi tai da fadin. "Na yafe maka bro. Ka yafemun nima. Dana kiraka. Dukkanmu muna da laifi. Yan uwantaka abune mai girma. Zumunci abune dabai kamata bacin rai yai sanadin yankewarshi ba. Daya daga cikinmu ya kamata ya ajiye bacin rai ya nemi daya. Duk bamuyi ba. Yanzun sai mu duba gaba....." Kai yake jinjina mata alamar duk yaji abinda taje dan yaji din. Baya son ko tunanin abindq zaisa ya nisance su yanzun. Komawa yai kan kujera gefen pha.iza ya zauna. Arfat take kallo. "She is so cute......" Mika mishi ita tayi. Ya karbeta. Hannuwanta tasa tana sake goge fuskarta. Da dan murmushi tace. "Sauran will love to meet you" Dariya fu.ad yayi. "Su nawa?" "Su hudu...." Ware idanuwa yayi sukai dariya gabaki daya. "Akwai kabir da muke kira (Amir)  yana da sunan in-law dina. Sai Yassar da yasir. Ridwan sai arfat gata nan" Da mamaki fu.ad ke kallonta. "Kina da twins?" Ta daga mishi kai. Lokaci daya fuskarshi ta canza. Muryarshi can kasa yace "Nayi missing abubuwa da yawa......" Yanda yai maganar ya taba mata zuciya ba kadan ba. Cikin taushin murya tace. "Make sure bakai missing wani abu ba nan gaba okay?" "Damn right....." Dariya sukai gabaki daya. Lokacin da suka ji sallama. Su duka suka daga kansu zuwa hanyar shigowa falon. Hassan ne. Yana ganin fu.ad yai baya zai koma. Da sauri fu.ad ya mikama pha.iza arfat yana binshi da gudu. "Hassan......." Bai tsaya ba. Asalima kara sauri yai batare daya juyo ba. Yana jin takun fu.ad din ya karaso inda yake. Hannu yasa kan kafadarshi yana juyo dashi. Fuskar hassan babu annuri yace. "Sannunka" Yana sake juyawa. Lumshe idanuwa fu.ad yayi. Ya sake juyo da hassan. A kufule yace. "Hit me! Yell at me in kana so. Buh' for goodness sake ka daina mun kaman baka taba sani na ba" Ture shi hassan yayi da hannuwa duka biyun hadi da fadin. "Da gaske baka so? Baka son inayin kaman ban sanka ba? Kasa kafa kabarmu? Ko ance ba zuciya a kirjinmu kaman kaine? Saboda me zaka dawo kasan ba zama zakai ba. Ka tuna mana yanda muke kaunarka ka sake tafiya ko me?" Har wani huci hassan yake. Komai na rayuwarshi. Tun tasowarshi duk wani burinshi bai wuce na ya zama kaman fu.ad ba. Shi kadai yasan abinda tafiyar fu.ad tai mishi. Tai musu gabaki daya. Sosai fu.ad ya kalle shi. "Babu inda zani hassan. Ba inda zan sake zuwa. Kaima ka yafemun mana ko zan ji sauqi a rayuwata" Wani kallo hassan yake mishi cike da rashin yarda kamun ya juya. Hannunshi fu.ad ya riko. "Hassan....." Juyowa yai ya na zame hannunshi daga na fu.ad murya a gajiye yace. "Ka kyaleni. Please kabarni kawai....." Girgiza kai fu.ad yake. Yaga abinda kyaliya tai mishi a baya baya fatan tarihi ya sake maimaita kanshi. "Ba zaka iya yafemun ba hassan? Zan fahimceka in ba zaka iya ba? Ka fadamun cikin idanuwa sai in sani. Ka fadamun ba zaka iya sake bani daman zama yayanka ba." Girgiza mishi kai hassan yake fuskarshi dauke da wani yanayi mai wahalar fassarawa. Murya a sarqe yace. "Kullun har shekara biyu nida hussaina sai mun zauna. Munyi tunanin laifin me mukai maka mu. Saboda me baka neme mu ba? Laifin abba ne ya shafemu ko me? Mun kiraka daga farko bama samu. Muka gaji muka daina. Hirarkanma muka bari kaman yanda kaima ka watsar damu. Kayi hakuri idan bana son ganinka yanzun. Bance bazan yafe maka ba. Amman zaidan dauki lokaci" Hade hannayenshi hassan yayi waje daya yana dorawa da. "Please kadan barni tukunna" Kai fu.ad ya daga mishi badan yaso ba. Badan baiji ciwon maganganun hassan ba. Saidan a kwana biyun nan ya fahimci menene asalin rayuwa. Ya soma koyan dora bukatar wasu akan tashi. Cikin sanyin murya yace "Bakomai hassan. Na fahimta koda banso hakan ba. Sai dai ina son kaga Nana. Inada duk lokacin da nake bukata. Bata dashi....." Da mamaki hassan ke kallonshi. Dan sam yaki zama ai mishi maganar fu.ad din. Momma ta fara yabar mata wajen saita kyale shi. "Wacece Nana?" Dan murmushin nasara fu.ad yai hadi da fadin. "Muje cikin gida kaganta......." Ba musu hassan din ya bishi suka koma cikin gida. Tsaye yai bai zauna ba. Fu.ad ya nufi bangaren momma ya taho da Nana. "Ina su amir?" Ya tambayi pha.iza. "Suna gida. Zasu zo muku hutu in sun gama exams ai" A sanyaye yace. "Allah ya kaimu" Dago kan dazai ya sauke idanuwanshi kan Nana. Kallonta yake sosai kamun ya maida kallonshi zuwa kan fu.ad. Kamanninsu yake gani qarara. Yana tunanin inbai manta ba ance fu.ad bazai iya haihuwa bane ko me? Sanadin hakan ne ma har yabar gida. Kallon Nana fu.ad yayi yace mata. "Ga uncle hassan" Kallonshi Nana take. Ta kallo fu.ad tana ware idanuwa a hankali tace. "Kuna kama dady" Murmushi fu.ad yayi. "He is ma' lil bro" A hankali ta taka ta karasa wajen hassan. Pha.iza ma kallonta take dan sai yanzun taganta. Labarinta kawai taji wajen su hanif. Kama hannun Nana hassan yai data miko mishi. "Ina wuni...." Shafa kanta yai yana rasa me zaice mata. Gabaki daya abubuwan sun masa yawa cikin kai. Dakyar ya iya ce mata. "Nana. Zanzo mu gaisa sosai okay?" Kai ta daga mishi.  Yadan mata murmushi ya saki hannunta yana ficewa daga dakin. Wajen pha.iza Nana ta koma ta gaishe da ita tana tallaban kumatun arfat. "Ina son kanwa nima. Amman banda ita. Duka yan class dinmu suna da fa" Kallon fu.ad pha.iza tayi yadan daga mata kafada. Indai Nana ce yanzun ta fara jin maganar da bata da amsarta a bakinta. Momma ce ta fito daga daki. Fu.ad ya kalli agogon hannunshi ya kalli momma hadi da fadin. "Yamma nayi momma.  Zamu tafi" "Dady......." Nana ta kirashi cike da alamun bata so a tafin. Dakuna mata fuska yayi ta make mishi kafada itama tana daquna tata fuskar alamar bata gaji bafa. "Ba zaka bari abbanku ya dawo ba. Yana son su gaisa da Nana" "Zan dawo da ita gobe in Allah ya kaimu. Zata wunin muku anan ma" Jinjina kai momma tayi. "Allah ya kaimu. Yar tsohuwa me An dafa miki" Dariya Nana tayi tace ma pha.iza. "Anty dan Allah ba granny bace tsohuwa? Kinji wai nice tsohuwa" Dariya pha.iza tayi. "Ki kyale granny taga kinfita kyau ne" Kallon momma Nana tayi tana jijjiga kai alamar kingani nafiki kyau. Dariya ta basu gabaki daya kamun fu.ad yace. "Taso mu tafi" Sumbatar arfat tayi a goshi kamun ta mike da fadin. "Anty zaku zo gobe?" Girgiza mata kai pha.iza tayi. Langabe fuska Nana tayi. "A kawo babyn nan to. Ya sunanta?" "Arfat sunanta. Ai dole ma in kawo miki ita. Kanwarki ce. Kinga in en class dinku sunce suna da kanwa kema kice kannenki da yawa. Su biyar ne" Rike baki nana tayi cike da jin dadi. "Suma za.a kawo su?" Pha.iza ta amsata da. "Eh suma zasu so suga anty Nana" Karasawa tai wajen pha.iza tai hugging dinta. Cikin kunne tace mata. "Nagode anty" Ta sake pha.iza dake cike da mamakin Nana. Bata taba ganin yarinya cike da kauna irinta ba. Zata iya rantsewa yarinyar ta dabance a cikin halittu. Jibi yanda ta manne mata a zuciya daga ganinta. Lumshe idanuwanta tayi data tuna abinda ke tattare da Nana. Tana kallonta harta karasa wajen momma tai hugging dinta hadi da fadin. "Sai gobe. Zanzo da camera dina muyi video" Ta saki momma ta ruga wajen fu.ad dake tsaye tasa hannunta cikin nashi. Ya kalli momma da tace musu. "Ka gaishe da safiyya" Ya jinjina kai. "Zataji. Pha.iza sai munyi waya" Kai ta daga mishi. Yaja hannun Nana datake waige tana daga ma arfat hannu suka fice. * Baby dream ya biya da Nana ya shiga kwasar mata kayayyaki daga na sawa zuwa takalma. Kamo hannunshi Nana tayi ya juyo ya kalleta yana mayar da hankalinshi kan wasu takalma da sukai mishi kyau. Sake janyo hannunshi tayi. "Dady....." Dauko takalman yai ya miko mata hadi da fadin. "Na.am. Sa wannan kigani zai miki" Karba tayi ta mayar inda ya dauko su. Ya dakuna mata fuska. Ta ware mishi idanuwanta. "Ya isa haka. Mu tafi gida......" Girgiza kai yayi. "Sai mun kara....." Yana tunanin yanda ya rasa shekaru goma sha daya na siya mata abubuwa. Yasan bazai iya biyansu ba amman yana so ya kamanta. Sosai Nana ta shagwabe mishi fuska. "Nagaji dady. Nagaji sosai" Hannu yasa ya riko fuskarta. Yana feeling goshinta da wuyanta ko da zazzabi. Sauke numfashi yai dayaji babu. Babu shiri yajata da kwandon da suka zuba kaya zuwa wajen biyan kudi. Tunawa yai da alkawarin dayai ma junior yace ma Nana ta jira shi anan karta je ko ina. Ya koma ciki bangaren kayan wasan yara ya dauko ma junior machine ya dawo. Credit card dinshi ya bayar dan bashida cash a hannunshi suka cire kudinsu aka daukar musu zuwa bayan mota. Kiran sallar magrib yaji ya lumshe idanuwan shi. Bude motar yai Nana ta shiga. Yadan tsugunna yace mata. "Idan nabarki naje nai sallah ba komai?" Kai ta daga mishi taba lafewa jikin kujerar. Dazun da take cema fu.ad tagaji dan yabar siyayyar da yake yine. Da gaske gajiyar take ji yanzun. Ko ina na jikinta ciwo yake. Ganin yana tsaye har lokacin yasa tace. "Really. Kaje ka dawo. I will be okay" Sumbatar goshinta yai. Ya rufe murfin motar ya wuce masallaci. Acan ya samu buta yai alwala. * Sanda ya dawo ya zagaya ya bude motar Nana tayi bacci. Fasa zama yai ya zagayo bangarenta ya dauketa. Bayan motar ya mayar da ita ya kwantar sannan ya dawo ya shiga ya kunna motar. A hankali yake tuqin dan baya so ya shiga wani rami dazai tsalle ya tashe ta. * A kafada ya sabi Nana tana ta bacci. Ya kwankwasa. Safiyya tazo ta bude mishi jikinta sanye da shadda light blue dinkin doguwar riga daya karbi jikinta sosai. Sauke ajiyar zuciya yai. A dan daburce tace mishi. "Sannu. Bacci tayi" Kai ya iya daga mata a yanayin da yake jinshi. Nana tazo karba ya girgiza mata kai. "Saikin yarda mun yarinya" Rabata yazo yi. Ta matsa mishi ya wuce tana bin bayanshi. "Duka Nana din nawa take da bazan iya daukarta ba" "Oh-Oh yaushe kikai kwarin daukar Nana din? Ke kanki kina bukatar daukar" Kallonshi take da mamaki. Fu.ad ya rainata. Ya wuce ya kwantar da Nana kan gadon ya cire mata takalma ya gyara mata kwancia. Zuwa yai ya wuce safiyya ya fice daga gidan. Da kanshi ya shiga kwaso ledojin siyayyar da sukai yana shigowa dasu cikin falon. Saida ya gama tas. Sannan yace ma safiyya. "Ki shirya Nana gobe wajen karfe goma zankaita wajen su momma. Kema ki shirya zamuje wani waje" Yar dariya tai dake nuna wasa kake ko? Ganin fuskarshi tayi ko murmushi babu. Hakan yasata fadin. "Wai da gaske kake?" "Yep" Ya fadin yana jan P din. Hade fuska tayi. "Ina da abinyi. Beside banga me zaisa na bika wani waje ba. Nana din dai zan fahimta saboda momma. Kazo ka dauketa" Idanuwa ya tsareta dasu dayasa ta fara jin duk ta takura a dake yace. "Ki shirya karfe goma" Bai jira amsarta ba ya juya. "Fu.ad bafa inda zanje" Ko saurarenta baiba ya fice daga dakin. Ta juya idanuwanta. Taga alama yana jin dadin ganin ranta ya baci. Kayayyakin daya ajiye ya zo ta shiga dubawa. Kayan sawa ne da takalma lodi guda. Tana mayar dasu kaman daga sama taji Nana na fadin. "Mumy....." Juyawa tai takalli Nana dake murza idanuwanta da hannu. "Ina dady?" A sanyaye tace. "Ya tafi ba dadewa" Dafa kafadar safiyya tayi ta zagayo tana zama. "Bacci nakeji" Ta fadi. Murmushi safiyya tayi. "Baccin kike ai kika tashi Nana" Muryarta cike da baccin da takeji tace. "Banyi sallar magrib bafa. Kuma ga isha.i" Dan shiru safiyya tayi. "Tam tashi maza. Kiyi sallah saikizo ki ci abinci kisha magunguna ki kwanta" "Naci dambun nama wajen granny. Banajin yunwa" Jinjina mata kai safiyya tayi tana maida hankalinta kan kayan dake baje falon. "Sunyi yawa ko?" Nana ta tambaya a sanyaye. Shiru safiyya tayi bata san amsar da zata bata ba. Ta dora da fadin. "Wasu ma bazan saba. Na kasa fada mishi ne saboda naga yanata so ya saimun. Wai zamu koma a kara. Mumy ko zaki fada mishi sun isa?" Hannu safiyya takai tadan ja mata hanci saboda yanda take jin idanuwanta na cika da hawaye da gaskiyar maganganun Nana din. "Oya tashi muje tare. Nima banyi sallar isha.i ba" Mikewa Nana tayi. "I love you mum" Murmushi safiyya tai mata. Suka shiga bedroom din tare. * Ja musu bargo safiyya tai tai musu addu.a cikin sanyin murya Nana tace. "Mumy in roke ki wani abu" "Kome princess ke so" Cewar safiyya. Sauke numfashi Nana tayi. "Bana so in bata miki rai. Kimun alkawari zaki duba magana ta. Ba zaki ji haushina ba" Da mamaki safiyya tace. "Nana ki fadamun. Komenene zan duba in shaa Allah" Juyawa Nana tayi ta fuskanci safiyya sosai. "Ki auri dady. I mean ki sake auren shi please......" Wata irin dokawa zuciyar safiyya take yi. Ga kanta da ya sara. Bata taba tunanin wannan rokon daga wajen Nana ba. Ta sake aurar fu.ad? "Na fada mishi. Yace bashi da abinda zai baki. Nana  bangane ba amman yana sonki sosai mumy. Please indai zaki aure shi yace zai aureki......" Katse ta safiyya tai da fadin. "Nana!  Kinma fu.ad magana?" A tsorace Nana ta daga mata kai. Tana sake ware idanuwanta kan safiyyar. "Kiyi hakuri mumy. Please karkiyi fushi. Kawai bana so in tafi inbarki ke kadai. In da dady zai kula dake. Bana so in barki ke kadai. Bana so......" Kamota safiyya tai jikinta ta rungume gam. Cikin kunnenta take fadin "Shhhhhhh......waye yace zaki barni?" Kuka nana take jikinta har rawa yake. Sai kokarin maida numfashi take. "Please mumy zaki aure shi?" Ba zata iya fadin abinda take ji ba. Abinda tambayar Nana take mata. Yanda zuciyarta ke mata wani irin ciwo. Dakyar ta iya fadin. "Kiyi bacci Nana. I love you..." "Mumy please" Cikin son Nana tai shiru safiyya tace. "Okay. Okay naji zan duba okay?" Dariya Nana tayi ta sumbaci kumatun safiyyar kamun ta zame jikinta ta kwanta sosai. Bata jima ba bacci ya dauketa. Safiyya kam juye juye kawai take. Ta rasa kalar tunanin daya kamata tayi......! **** Yana shiga gida ya ajiye mota baima karasa ciki ba ya juya ya fice dan yanajin ana kiran sallar isha.i. Yana kan hanyar dawowa daga masallaci ne yaji wayarshi tai kara alamar text ya shigo. Ya bude: "Kurna babban layi. Layin birji gida mai number 85" Murmushi ya kwace mishi. Fita yai daga text din yasa wayar a key ya mayar aljihunshi. Hamdala yake ma Ubangiji da ya bashi wannan Nasarar har yakai gida. Ya taka kafarshi zuwa cikin falo yaji ance. "Kaji...." Juyowa yai. Hassan ne a tsaye duk ya daburce. "Hassan lafiya dai ko" Hannunshi yasa cikin sumar kanshi ya yamutsa. Kamun ya dauko wayarshi dake cikin aljihu. Fu.ad na tsaye yana kallonshi. Dan yatsa hassan ya daga mishi alamar minti daya. Dan daga mishi kafada fu.ad yayi. Yana kallonshi yana latsa wayar ya kara a kunne nadan wani lokaci kamun yace. "Hussaina gashi nan........." Wayar ya mika ma fu.ad yai tsaye. Karba yai ya kara a kunne hadi da fadin. "Hello....." Cikin sauri yaji muryar hussaina na fadin. "Me yasa ka tafi bro. Nayi kewarka sosai. Kayi hakuri ban maka magana ba a asibiti. Ina fushi ne kawai shisa. Amman zanzo. Zamu zo nida hamza yace zai kawoni" Yar dariya fu.ad yai hadi da fadin. "Lil sis...... Breathe... Yanzun nan" Yana jin dariyarta kamun tai shiru tana maida numfashi. Har ranshi yake jin kaunar hussaina. Banda su abbah yafi kewarta akan kowa. Kaunarta dabance a wajenshi. Cikin serious magana yace. "Ki yafemun kanwata. Nayi kewarki da yawa. Na muku laifi babba. Ki yafemun dan Allah ki........." Katse shi hussaina tayi da fadin. "Na yafe maka bro. Tuni fa. Kawai ina danyin fushi ne daman....." Wani numfashi mai nauyi fu.ad ya sauke yanajin kaman an sauke mishi katon lodi dake kanshi. "Ki kula da kanki sosai kinji." "In shaa Allah kaima haka." Katse wayar tayi. Ya mika ma hassan da wani irin yanayi cikin idanuwanshi. Tsaf hassan ya karanci rokon da fu.ad ke mishi. Ya kara damke fuska ya karbi wayarshi. Yana kallon yanda fu.ad ya wani langabe fuska ya na juyawa. "Bro......" Hassan ya fadi. Da sauri fu.ad ya juyo fuskarshi na tambayar hassan ko da gaske ya kira shi da bro. Kaman yana son amsa tambayar dake fuskar fu.ad yace. "Bro...." Rike fuska fu.ad yai da Hannuwanshi duk biyun cike da jin dadi. "Nagode hassan. Nagode sosai" Dariya hassan yai hadi da fadin. "We are good tun dazun. Kawai nabarka ne kadan kara sweating kadan" Ya karasa maganar yana kashe ma fu.ad ido. Duka fu.ad yakai mishi ya kauce yana dariya. Girgiza kai fu.ad yai ya shige cikin gida. * Saida suka ci abinci dasu abbah ya shiga dakinshi ya watsa ruwa ya fito. Ji yake gabaki daya ya gaji. Ya dan kwanta. Da yana son zuwa yakai ma junior machine dinshi bayajin zai iya. Bacci kawai yake so yayi. Wayarshi ya dauko ya kira lukman suka gaisa. "Da gidanka zanzo yanzun fa" Lukman ya amsa shi da fadin. "Yawwa ina jira" "Na fasa ai. Jikina ciwo fa. Zan kawo ma junior machine dinshi ne daman. Ko zaka zo ka karbar mishi?" "Waye? Tab! Bamai fito dani da daren nan" Dariya fu.ad yayi. "Sai ni ne zan fito ko? Hmm. Ka shafamun kan junior. Ka gaishe da madam" "zasu ji in shaa Allah...." Lukman ya amsa kamun suyi sallama ya kashe wayar. Gyara kwancia fu.ad yai. Addu.a yai ya lumshe idanuwanshi. Saidai ga mamakinshi. Babu abinda ke mishi yawo banda fuskar safiyya. Hakan ba bakon abu bane. Saidai tun randa ya sauke idanuwanshi kan Nana bashida tunanin komai sai nata. Yauma yana tunanin safiyya data addabe shi nada alaqa da rokon da Nana tai mishi. A haka bacci ya dauke shi........! *#TeamAS* *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ www.Loobnerh.blogspot.com Wattpad: LubnaSufyan             41 *Hakika babbar kyauta da zaka samu a duniya itace ta 'Ya'ya. Idan har ina jin yanda nake ji a zuciyata idan na dauki yaran wasu. Zan so sanin me ake ji randa zan rungumi nawa yaran. Allah ya azurta duk wani mai bukatar haihuwa da Yara masu albarka* *Soyayyar iyaye wata baiwace da wanda Allah ya azurta da ita ne kawai zai fahimta. Allah ka sakama iyayen mu da mafififin alkhairi* *TO ALL MUMS and DADS. Thank you for loving us duk da ba zamu taba muku rabinta ba* *#AnaTare* Three piece suit yasaka Baki da fari. Bai sha wahalar dora ta saman ba dan baya son takura ko kadan. Yanzun ma dan inda zashi baya son a mishi kallon karamin yaro kuma bashida wasu manyan kaya ko daya. Dacan ma ba sakawa yake ba. Ballantana yaushe rabonshi da nigeria. Turaruka ya feshe jikinshi dasu sannan ya fito. A falo ya samu su momma suna karyawa. Ya gaishe dasu a ladabce sannan ya zauna. Wata irin yunwa yake ji. Sosai yaci dankali da kwan da momma ta zuba mishi ya hada da tea sannan ya mike yana fadin. "Momma barin je in kawo Nana din. Amman ina so in biya ta gidan lukman dan karya fita aiki kamun in wuce in dauko ta" "A dawo lafiya. Ka gaishe da lukman din. Nace kwana biyu bai kawomun junior ba" Murmushi fu.ad yai hadi da daga mata kai. Ya maida hankalinshi kan abbah. "Abbah bakaimun addu.a ba" Murmushi abbah ya mayar mishi. "Allah ya tsare ya sanya albarka" "Amin. Hassan bai tashi bane?" Fu.ad ya bukata. Momma ta amsa shi da. "Ai ya tsufa wajen aiki. Yana rigan kowa tashi" Wucewa fu.ad yai yana fadin. "Alright. Saina dawo" **** "Mumy dan Allah in kwana?" Dan jim safiyya tayi tana jinjina maganar Nana din. Bawai bata so ta kwana bane. Tasan kewa zata dame ta. Amman tana bukatar sanin dangin babanta. Suma su santa. Ko ba komai sun nuna mata kauna lokaci daya. "Sai dai zaki tafi da magungunanki. Ki bama momma su duka" Da sauri Nana tace. "I promise zan sha duka. Nagode mumy" Murmushi kawai safiyya tayi mata. Ta dauko mata kayan da zata saka da kuma wasu kala biyu sai na bacci sa takalma guda biyu. "Mumy kibani cikin wanda dady ya siyo mun jiya." Dan dafe kai safiyya tayi. Ta manta da kayan shaf. Mikewa tai taje ta dauko mata su. Ta zazzage wa.ancan daga leda ta saka mata sababbin. Purple hijab din data dauko mata zata mayar. Ta rike da fadin. "Zan sa wannan" Sakar mata safiyya tayi. Ta barta anan tana daukar wani riga da pencil trouser cikin wanda fu.ad ya siyo mata. Tasan Nana bata son a tayata shiryawa inba bata da lafiya sosai ba. Dan haka ta shiga wanka tabarta anan tana shiryawa abinta. **** Fu.ad bai samu junior a gida ba. Kasancewar juma.a ce ya tafi makaranta. Yau dai saida lukman yaja shi har cikin gidan suka gaisa da zainab. Yanayin karamcin zainab ya burge fu.ad. Suna gama gaisawa tai mishi godiyar machine din daya saima junior ta bar musu wajen. Lukman yace mishi. "Allah ya bar zumunci" Dakuna fuska fu.ad yai yana harar lukman. "Bana son iskanci lukman." Dariya yai. "Daga na maka godiya" Juya idanuwanshi yai. Sarai yasan lukman din neman magana ne. Dan haka ya share. Numfashi ya sauke yace. "Naga no iyayen sofi lukman. Ga address din nan ma" "Ma shaa Allah. Kai amman naji dadi sosai wallahi. Allah kenan. Gaskiya naji dadi. Ka fada mata ne?" Girgiza ma lukman kai yayi. "Nace ta shirya dai zamuje wani waje amman ban fada mata ba. Nafi son in surprising dinta" Dan daga kafada lukman yai. "Daka fada mata dai" Sake girgiza kai fu.ad yai. "Ni ba wannan ba kasan me?" "Saika fada...." Kaf yanda sukai da Nana fu.ad ya fada ma lukman ya dora da cewa. "Bazai zama adalci wa sofi ba lukman. Banda abinda zan bata. Nabarta shekarun nan dan ta samu farin ciki. In.... In har akace babu Nana zai zama kaman zamu raba zunubaina ne da ita bayan batai komai ba......" Dafa kafadarshi lukman yayi. "Idan ka duba rayuwar fu.ad ba komai bane a cikinta sai tarin wahala. Jin dadin dake cikinta kalilan ne. Nasan tabbas bazai zamana adalci wa safiyya ba. Rashin yara ba karamin abu bane ko ga matar da batasan dadin su ba ballantana. Amman na yarda da Nana. Ba fata nake ba. In babu ita kana bukatar safiyya. Haka duk yanda safiyya zata nuna akwai soyayyarka a tattare da ita. Tana bukatarka...... Inhar zata aureka ina bayan Nana" Dafe kai fu.ad yayi. Zai iya jure rashin safiyya inhar zatai farin ciki. "Banda abinda zan bata......" Katse shi lukman yayi. "Bance kana dashi ba. Amman akwak soyayyarka ko? Zaka cemun baka sonta ne?" Daga girarshi yai sama duka biyun hadi da fadin. "Ina jin haushinta. Ta boyemun Nana" "Really? Da gaske kana jin haushinta ta boye maka Nana?" Lukman ya tambaya cike da jin haushin rashin adalcin dake cikin maganganun fu.ad din. Cikin dacin rai yace. "Sosai ma. Bata da right din da zata boye mun ita. Bata dashi......" Gyara zama lukman yai. Yasa hannu yadan daki goshin fu.ad din. Daya ture hannun lukman yana fadin. "Meye haka?" Wani murmushin takaici lukman yayi. "Ina so inga ni ko kana bacci ne in tasheka?" Daga mishi gira fu.ad yai cike da alamun cewar bai fahimci me ya kawo wannan cikin maganar da yayi ba. "Me kake so safiyya tayi fu.ad? Kasa kafa ka tafi? Ta je filin jirgi ta sa musu kuka su kaita kasar daka ke? Bayan bata sani ba?......" Magana fu.ad zai lukman ya katse shi. "Ka bari ingama please. A halin daka barta dan sauran hankalin dake jikinta kake so shima ta mika maka? Ka taba tunanin bari ka dawo saboda bata da kowa a garin kano sai kai? Ka taba tsayawa kace me zatayi taci abinci? Ka taba tunanin ita kadai zata ringa kwana a karancin shekarunta? Ko ka manta *Akan so* tabar komai da kowa nata? Fu.ad ka manta kaine komai nata kamin ka yanke hukuncin sakinta lokacin data fi bukatarka? Rannan a asibiti bata fada maka tai kokarin nemoka lokacin data gane tana da ciki ba? Allah kadai yasan rudanin da ta shiga da dimauta na renon cikin Nana ita kadai batare da mataimaki ba. Ina tare da zainab daga randa ta samu cikin junior har haihuwarshi. Wallahi saida na kara ganin darajar hajiya ba kadan ba. Dan Allah inhar zakaga laifin safiyya ka daina furta shi a gabana. Saboda raina baci yake sosai. Kana tunamin abubuwan dana zabi na manta" Maganganun lukman yawo suke masa cikin kai suna sanyaya mishi duk wata gaba dake jikinshi. Lokaci daya wani irin laifi mai girma yake mishi mayafi. Cikin son kauda yanayin yace. "Nasa ana turo mata kudi. Ana turo mata kaso biyu cikin duk wani abu dazan samu" Girgiza kai lukman yai yana fadin. "Hmm. Babu abinda zaima laifinka adalci fu.ad. Kudi bakomai bane in har babu kulawa" Lumshe idanuwa fu.ad yayi. Lokacin dayake jin komai ya kusan dai daita sai kuma komai ya dawo mishi baya. Ajiyar zuciya ya sauke. Ya mike tsaye yana saka hannayenshi duka biyun ya goge fuskarshi dayake jin alamar zufa. "Zan gyara komai" Mikewa lukman yayi. "Karka ce zaka dora sabon gini kan foundation din daka bari. Ya riga da ya lalace fu.ad. Ka sake komai daga farko. Ka tabbata kayi shi da kwari" A sanyaye ya amsa da. "In shaa Allah. Nagode lukman. Nagode da komai" Jinjina mishi kai yai sukai sallama. Da wani irin nauyin jiki fu.ad ya bude mota ya shiga. **** Handle din kofar ya kama ya murda. A hankali ya tura hadi dayin sallama. Bai rufe bakin shi ba yaji Nana a jikinshi ta makale shi. Baisan lokacin da murmushi ya kwace mishi ba. Duk yanayin da yake ji bai hana wani farin cikin ganin Nana dabaisan daga inda ya fito ba ziyartarshi. Tsugunnawa yai dan tsayinsu yazo dai dai yace mata. "Princess tayi kyau" Dariya tai a kunyace hadi da fadin. "Kayi kyau sosai kaima. Ina kwana" "Kin tashi lafiya? Yanzun dana shigo ne kika shafamun kyanki" Dariya Nana ta sake yi. "Ni ina lafiya. Kai mana pictures....." Kamun ya amsa tace. "Kai!  Na manta. Barin dauko camera dina....." Ya bude baki ta bar jikinshi tana rugawa da gudu. "Oh. Nana!  Kibi a hankali" Ai bata ma jishi ba ta shige daki da gudu. Ita take gudun shi zuciyarshi ke dokawa karta fadi. Safiyya ta fito sanye da atamfa. Dinkin simple ne sai dai ya karbeta sosai. Fuskarta babu yabo ba fallasa tace mishi. "Ina kwana" Idanuwanshi kafe kanta. Zuciyarshi na karanta mishi kyawun datai ya amsa da fadin. "Kin tashi lafiya? Su momma na gaishe dake" "Alhamdulillah. Ina amsawa. Nagode. Kace ina gaishe dasu nima" Zai amsa Nana ta fito da gudu da camera din a hannunta. Gaban fu.ad ta tsaya tana danne danne a jiki. Kamun ga daga 📷 din saitin shi tana fadin. "Dady me kafi so?" Dariya yai. Ya kalli safiyya yana bude mata idanuwa yana son tambayarta me zai ce? Tabe baki tayi. Tana sake damqe fuska. Ganin da Nana tayi ya kalli safiyya yasa ta tabare fuska tana turo baki tace. "Dady na dauka kafi sona" Sai lokacin ya dawo da hankalin shi kan Nana yana mata kallon 'Me kika ce?' Sake turo baki tayi. "Haka nace me kafi so. Ka kalli mumy" Safiyya dake tsaye tace. "Nana.....!" Dariya tayi ta juya camera din saitin safiyya. "Ke me kika fi so?" Fu.ad safiyya ta kalla? Daya amsa tambayar Nana da hankalinta na kanshi. "Mumy!  Kema?" Da sauri safiyya ta ce. "Ke princess. Nafi sonki" Shagwabe fuska Nana tayi. "Dady kika fara kallo kema. Zanje wajen granny nasan ita tafi sona" Dariya fu.ad yayi ya kamo Nana jikinshi. "Inji waye. Ina son princess fiye da kowa." Murmushi Nana tayi taba daga camera din saitinsu ita da fu.ad hadi sa fadin. "Hello. Ga M. Shine dady na. Dady say Hi" Dariya fu.ad yake sosai. Yanda take ma camera din magana kaman wata mutum. "Nana camera ne fa" Dire kafafuwa nana tayi. "Dady be nice. Ina son camera din nan sosai fa." Dariya fu.ad ya sake yi. Nana ta dakuna mishi fuska sannan ya soma kokarin controlling dariyar. Yanda kome Nana tayi yake sashi dariya har mamaki yake bashi. Da dariyar a muryarshi yace. "Hi camera" Yana daga hannu. Gaba daya yanda ya biyewa Nana suka zama wasu yan yara yaba safiyya dariya. Da sauri ya daga idanuwa ya kalleta. Murmushi yake. Yana tuna yanda yake son dariyarta.  Yanda idanuwanta ke cika da wani abu da bazai iya dora ma kalamai ba. Camera din Nana ta mayar saitin safiyya tana fadin. "Mumy na dariya" Girgiza kai safiyya tayi. Tasan video Nana ke daukar su. "Ban iya shiririta ba Nana. Wuce ki dauko kayanki ku tafi" Sai lokacin Nana ta juyo cike da jin dadi tace ma fu.ad. "Mumy tace in kwana wajen granny" Shima yaji dadi. Nana ta wuce zata dauko kayanta. Da idanuwa yake nuna ma safiyya godiyarshi can gefen zuciyarshi girman laifin shi da lukman ya nuna mishi na nan manne. "Kin shirya? In mun sauke Nana kuka gaisa da momma sai mu wuce ko?" Sauke numfashi safiyya tayi "Na dauka tun jiya nace maka ba zanje ba" Mikewa tsaye fu.ad yayi. Ya tabbata ya sauke idanuwanshi cikin nata kamun yace. "Ki yarda dani. In baida muhimmanci bazan tambaye ki ba" "Kaman yarda dakai a baya yamun wani amfani" Ta fadi muryarta cike da takaici. Yaji zafin maganar data yaba mishi har ranshi. Sai dai wannan ba lokaci bane dazai tsaya yana mata bayani tunda yasan kome ta fada shi ya janyo. "Sofi please....." Wani murmushi tai da hakoranta kawai ta bude mishi. Kamun ta hade fuska. "Ka iya wannan ka tsaya kana bani umarni kaman yarka" Shirun dai yai. Dan bashida bakin magana yau.  Yana kallon hararar data watsa mishi kamun ta wuce cikin bedroom din. Sauke ajiyar zuciya yai. Bata san ina fu.ad yake so suje ba. Sai dai ta rasa me yasa gabanta yake ta faduwa tunda safe. Bata kuma san dalilin daya sa take son ta bishi ba. Koma ina ne koma menene zata iya tarar napep ta dawo in bai mata ba. Mayafinta ta dauka ta yafa. Ta kamo hannun Nana suka fito. Murmushi ya kwace ma fu.ad saboda yanda sukai mishi kyau kaman ya sace su. Wayar shi ya dauko ya bude camera yana karasa inda suke ya tsaya gefen Nana. "Me zakayi?" Safiyya ta tambaya. Bai kulata ba ya daga camera din yana musu hotuna kala biyu sannan ya kama hannun Nana suka fice. Ta girgiza kai kawai. Karfin halin shi na bata mamaki. Sam bata so ta tuno bukatar Nana akanshi. Yanda ta kwana da abin a ranta kawai ya isheta ba saita tsokano shi da safiyar nan ba. Saida ta kulle gidan sannan ta same su a mota. Nana ta shiga gaba ita da fu.ad. safiyya kam bayan motar ta bude ta zauna. Tana jero addu.o.i a zuciyarta saboda bata san dalilin bugun zuciyarta ba. ** Ba karamin dadin ganinsu momma taji ba. Suka gaisa da safiyya. Su zauna fu.ad yace. "Momma sauri muke. Akwai inda zamuje ki mana addu.a" "Aika bari dai tadan huta ko?" Girgiza kai yayi. "Yau juma.a fa. Gashi har sha daya ta kusa. In muka dawo sai mu biyo" Jinjina kai momma tayi. "A dai kula dan Allah. Sai kun dawo. Allah ya bada sa.a" A sanyaye safiyya tace. "Amin. Mungode momma" Dan tsugunnawa fu.ad yai ya sumbaci Nana a kumatu. "Banda rashin ji okay?" Kai ta daga mishi tana murmushi. "Love you kai da mumy" Murmushi safiyya tayi sannan suka juya ita da fu.ad din suka fice. Bayan motar ta bude ta shiga tana wani daure fuska. "Ba magana zan miki ba. Ni bana son neman rigima ko kadan" Cewar fu.ad daya shiga motar yana jan murfin. Taji shi sarai. Ta zabi tai shiru ne kawai saboda jin su ita kadai dashi cikin motar ya isheta. Yanda zuciyarta ke son kwacewa da gudu ta kaita ziyara lokutta da yawa ya isheta yaki da. Basai ta tsaya kula fu.ad ba. Ta mudubi ya kalleta. Yanda ta lafe jikin kujerar motar tana lumshe idanuwa. Addu.a yai ta neman sa.a kamun ya murza key din motar. **** Ga mamakin safiyya bakin wani gida sukai parking. Fu.ad ne ya fito ya barta cikin motar. Tana kallonshi yana daga kai yana kallon number din gidan. Tsaye yai yana yan waige waige kamun yaga wata yarinya tazo wucewa. "Ke!  Zo dan Allah" Kallon fu.ad yarinyar tadanyi a tsorace ta tsaya. Shi ya matsa inda take yace mata. "Anan unguwar kike?" Kai ta daga mishi. Yadan ja numfashi ya fitar hadi da fadin. "Ko kinsan sunan mai gidan nan?" Da mamaki bayyane a fuskar yarinyar ta amsa shi da fadin. "Malam audu." Wani tsalle zuciyar fu.ad tayi "Matarshi fa?" "Ni bansan sunanta ba. Kowa Inna yake ce mata" Ganin ta soma gajiya da tambayoyinshi yasa shi fadin. "Nagode sosai. Dan Allah ki dan shiga kice musu sunyi baqi" Ba musu yarinyar ta shiga. Bata fi mintina uku ba ta fito tace. "Ance ka shiga" Godiya yai mata. Ta jinjina mishi kai kawao ta wuce abinta. Ji yai jikinshi yai wani iri. Dakyar ya karasa yace ma safiyya. "Fito muje" Yanayin shi data ga ya sauya lokaci daya yasa ta mayar da musun da take son mishi ta bude motar ta fita. Matsawa yai yasa hannu ya zare key din motar shi ya kulle ta yasa a aljihu sannan ya kama hanya suka nufi gidan. Tunda suka taka cikin soron gidan zuciyarta ta tsananta dokawar da take har fu.ad yai sallama yana danna kai. * "Ai da kin bari na leqa naga ko su waye" Jinjina kai inna tayi dake zaune kan darduma. Shikuma yana saman kujera. "Bazai shige yaron nan ya yake da suna ba. Abokin wannan dan da yace zai kawo matarshi ta gaishe damu yau" "Au. Nama manta fa" Sallama suka ji. "wa alaikumussalam. Ku shigo" Inna ta fadi. Tana janyo hijab dinta dake ajiye gefe ta saka. * Wani irin dokawa zuciyar safiyya tayi. Muryar data amsa sallamar. Shekaru sha biyu bazai sa ta manta taba. Sai dai gasgata cewar ba kunnenta bane yake mata gizo abu ne mai wahala. Kafafuwanta taji suna mata rawa. Ga wani irin tsoro da ya cika mata zuciya. Fu.ad ya soma sakai cikin gidan yana sake yin sallama. Sosai Inna ke kallon shi tana son tuna inda ta san fuskarshi. Baba dake zaune ya dafa kujera ya mike saboda yanayin rauni na manyantaka daya kama shi. Duk da sajen dake kwance fuskar fu.ad bai hana shi gane shi ba. Babu yanda za.ai ya manta fuskar dayake kwana da ita a zuciyarshi ya tashi da ita ba. Fuskar datai sanadiyar salwantar yarshi. Baki baba ya bude yana kallon fu.ad ya daga hannu yana nuna shi sai dai kalma ko daya ta ki fitowa daga bakin shi. Duk da zuciyarshi cike take da tambaya guda daya. "Ina 'Ya ta?" Sai dai ya kasa furtawa saboda yanda yake jin wani jiri na dibar shi. Kallon su fu.ad yake yana jero godiya wajen Ubangiji daya tabbatar mishi da wannan nasarar. Matsawa yai gefe ya kasa karasawa cikin gida. Sai lokacin safiyya ta samu damar shigowa dan fu.ad ya tare hanya. A hankali idanuwanta suka sauka kan Inna dake zaune. Sannan ta maida dubanta wajen baba dayake tsaye idanuwan shi cike da rashin yarda cewa ita ce. Wani abu take ji. Yana mata yawo tun daga dan yatsan kafarta har zuwa tsakiyar kanta. Lokaci daya jikinta ya dauki kyarma. Kafafuwanta take so ta matsar su karasa da ita wajen su Inna da take hangowa ko sau daya ne ta nemi gafararsu kamun su bace mata. Kamun ta farka daga mafarkin nan da takeyi su sake subuce mata. Amman ta kasa. Ta kasa saboda yanda babu karfi ko kadan cikin kafafuwanta. Tana kallo baba yana takowa. Duk da tsufan dayai bai hanata ganin shi ba. Bai hanata gane shi ba. Tana jin raunin da take gani cikin tafiyarshi har zuciyarta. Gani take yafi awa daya bai karaso ba. Gani take wata kaddara zata iya giftawa kamun ya karaso gareta saboda ita ta kasa kaiwa inda yake. Numfashinta take kokawa dashi wajen fita saboda tashin hankalin da take ciki. Gab da ita baba ya karaso ya kura mata idanuwa. Rike numfashi safiyya tayi tana tsoron kar ta sake shi baba ya bace. Karta saki numfashin da taja ta farka daga mafarkin da take. Tana jin yanda kirjinta ke zafi da neman iska. Kanta ke wani irin juyawa saboda karancin iska amman taqi sakin wadda take rike da ita ballantana ta shaki sabuwa. Zata iya jure kowace azaba a yanzun in har hakan na nufin ba zata kokawa azabar rashin su inna ba. Cikin rawar murya baba ya juya ya kalli inna yace. "Taso kigani. Safiyya ce. Safiyya ce ta dawo......!" Da sauri inna ta taso har tana sassarfa. Gefen baba ta tsaya. Dan ta ki tasowa ne kar tazo taga ita kadai ce safiyya kema gizo kaman yanda take mata lokutta da dama. Hannu tasa ta taba kuncin safiyya tana son jin ko da gaske ita dince. Jin hannun inna a kuncinta ya sa safiyya sakin numfashin da take rike dashi. Muryarta na wani sama sama ta rike hannu inna gam tana fadin. "Innaaaaa!" Idanuwanta ta mayar kan baba dake tsaye. Dayan hannunta takai ta kamo nashi tana dumtse wa sosai cikin nata zuciyarta na wani irin dokawa. "Babaa!" Tana jin yanda zuciyarta ke rage gudu alamar zata iya samun matsala ko da yaushe. Tana jin yanda dan karfin halin da take dashi saboda Nana yana rugujewa. Tana jin yanda ko ina na jikinta ke budewa da bukatar iyayenta data dinga dinkewa a tsahon shekarun nan saboda Nana na bukatarta. Wani irin jiri na dibarta take fadin. "Ku yafemun inna...... Baba ka yafemun. Dan Allah........ku yafemun....." Tana jin yanda duniyar ke juya mata. Kafun kafafuwanta su karasa mutuwa. Da neman yafiyar su inna a bakinta tai kasa. Tana wani irin fitar da numfashi kamun komai ya tsaya......! Su duka ukkun kanta sukai. Inna na tallabe da ita a jikinta tana jijjigata. "Safiyya ki tashi. Wallahi mun riga mun yafe miki da dadewa. Dan Allah ki tashi......" Hannunta baba ya kama. "Safiyya tashi kinji. Mun yafe miki ai tun tuni. Kinji innarki ma tace ta yafe miki. Ki tashi tunda Allah ya hada fuskokinmu da rayuwarmu" Fu.ad ya rasa me ya kamata yayi. Buta ya hango da gudu ya karasa karshen gidan ya dauko butar. Ruwan ya zuba a hannunshi ya yayyyafa ma safiyya dake jikin inna. A hankali take motsawa kamun ta soma bude idanuwanta. Sama sama take jin muryar Inna na fadin. "Safiyya...... Safiyya ki tashi kiga mun yafe miki...." Ware idanuwanta tayi jin muryar inna. Ta ko sauke su kan fuskar inna. Da sauri ta mike daga jikinta. Hannuwanta tasa ta tallabi fuskar inna. Tana so tagani da gaske ba mafarki take ba su inna ne a gabanta. Sannan ta maida dubanta wajen baba dake zaune kan siminti batare daya damu ba. Yanda take ji a zufiyarta ba zai taba faduwa ba. Allah kadai yasan yanda take jin rashin su domin shi ya rubuta mata kaddarar rabuwa dasu. Kanta ta kifa jikin inna tana sakin wani irin kuka mai tsuma zuciya. Inna ma kuka take sosai ta dora kanta a bayan safiyyar. Kuka suke sosai daya sa fu.ad dayake a tsaye jin wani abu na mishi yawo cikin idanuwa. Su duka sun dandana rashin iyaye sunji yanda yake. Gara shi akan safiyya. Bazai taba misalta yanda take ji ba a yanzun sai dai ya kwatanta. Kuka take sosai. Batare da sun kula ba fu.ad ya fice ya basu waje. Dagowa safiyya tayi ta kama hannun inna jikinta na wani irin bari hawaye na wanke mata fuska. "Inna da gaske kune? Ba mafarki nake ba inna?" Kai inna ta iya daga mata. Wani irin kuka take da take jin fitowarshi na mata ciwo a zuciyarta da idanuwanta. Baba ta kalla muryarta na rawa. "Baba dan Allah ka yafemun. Wallahi na muku laifi mai girma nasani. Na kunyata ku a idan duniya. Na jefar da soyayyar da kukaimun akan wadda ta ziyar ceni daga baya. Baba nayi wauta mai girma" Kwallar data taru a idanuwanshi yasa riga ya goge. Cikin rauni yace. "Safiyya kinyi laifi kam. Sai dai kaddara bata wuce kan kowa. Bacin raine ya hanamu fahimtar kaddararki ce tazo a haka. Mun jima da yafe miki duk da baki sake waiwayarmu ba" Kallonsu take cikin tashin hankali take fadin. "Naje baba. Wallahi naje aka ce mun kun tashi.......ba wanda yasan inda kuka komaaa" Ta karasa maganar wani irin kuka na kwace mata. Sosai inna ta rike safiyya jikinta. "Surutun mutane yasa muka tashi. Maganganun su yasa muka baro bichi" Kuka safiyya take yanzun kam kaman zata shide. Sanadinta sun jure kunci mai girma. *Akan so* ta ja ma iyayenta muzanci da tozarta mafi girma. "Inna rayuwata ba zata taba yin dai dai ba idan baku yafemun ba" Riketa inna tayi ganin yanda jikinta ke kyarma tana fadin. "Mun yafe miki safiyya. Mun yafe miki duniya da lahira. Kasancewarki tare damu yanzun shine abu mafi girma daya faru damu a shekarun nan" Baba ya dauka da cewa. "Laifinki baisa mun daina kaunarki ba safiyya" Kai kawai ta iya daga ma baba saboda tasan yanda girman wannan kaunar tasu take. Tasan yanda ciwonta yake. A haka inna ta kama safiyya tajata suka shiga daki. Baba da kanshi ya je ya dauko cup yazo ya fasa ruwa ya zuba ya mika ma safiyya. Hannuwa biyu tasa ta karba ta shanye tas tana jinjina kalar kaunar dake tsakanin da da mahaifanshi.......! *#TeamAS* *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ www.Loobnerh.blogspot.com Wattpad: LubnaSufyan               42 *Tabbas duk wata daukaka bata zuwa ma bawa babu jarabawa a cikinta.* *Da yawan kusancinka da Mahaliccinka da yawan kaddarar dq zaka fuskanta. Allah ya bamu hakurin zama da juna. Allah ya bamu juriya da kauda kai daga zagin da muke sha a kullum* *Habibtee Allah ya kara daukaka. Allah ya kara hakurin zama da mutane. Ki kauda kai. Ki toshe kunnenki.* *#AnaTare* Hannun Inna safiyya ta kara kamawa ta rike cikin nata. Dan gani take kaman zata bace kowanne lokaci. Dayan hannun ta kamo mayafinta tana goge hawayen da suke zubo mata. Muryarta a dishe saboda kukan da takeyi tace. "Inna kun yafemun da gaske?" Kwalla Inna ta share tana daga ma safiyya kai. Ta mayar da kallonta zuwa wajen baba dake zaune yana kallonta ciki  da wani yanayi. "Baba...." Girgiza mata kai yayi alamar tayi shiru. "Mun yafe miki safiyya. Duniya da lahira. Kema ki yafe mana bacin rai ne yasa muka ko....." Da sauri safiyya tace. "Baba kabari. Bakuyimun komai ba. Wallahi bakumin komai ba...." Kasa karasa maganar tayi saboda wani abu daya tsaya mata a wuya. Kokarin hadiye shi tayi ta kasa. Muryarta kasa kasa tace. "Ina yaya?" Wani murmushi Inna tayi da safiyya taji tana son ace itace sanadin bayyanarshi. Murmushi ne dake cike da alfahari. Irin murmushin da kowanne da zaiyi farin ciki ace shine sanadin bayyanarshi a fuskar mahaifanshi kamun tace mata. "Yana nan lafiya safiyya. Yana aiki a gidan radio. Da matarshi da ya'ya biyu" Murmushi safiyya tayi kamun lokaci daya wani abu na daban ya maye gurbinshi. Har ranta take jin shekarun data rasa tare dasu da bazasu taba dawowa ba. "Zanso ingansu" Ta fadi a sanyaye komai na dawo mata. "Zaizo ya kawo su anjima da yamma" Baba ya fadi da kalar murmushin dake fuskar inna. Hade hannayenta safiyya tayi tana son taga sun kalleta da irin alfaharin nan. "Kinbar mijinki a waje. Ba zakice ya shigo ba" Inna ta fadi. Kallonta safiyya tai da sauri hawaye na sake taruwa cikin idanuwanta. Girgiza ma inna kai take wani kukan na kwace mata. Ranar da fu.ad yabarta na dawo mata kaman lokacin abin ya faru. **** Kofa take kallo tana son ta gasgata da gaske fu.ad yasa kafa ya fice bayan furta mata kalmar data wargaza duniyar da suka gina. Kalmar dake barazanar tsayar mata da bugun zuciyarta. Mikewa tai hannuwanta na rawa take kallonsu. Kamun ta mayar da kallonta zuwa ko ina na dakin. Da sauri ta karasa wajen kofa ta kama handle din ta bude jikinta na rawa. Kallon hanyar waje tayo taga ko alamar fu.ad bata gani ba. Ya tafin da gaske. Zame jikinta tayi wajen kofar tana zama. Wani irin kuka ta saki daya fito tun daga zuciyarta da take jin tana tarwatsewa. Sautin kukanta ne ya shigo da mama indo data zo wucewa taji ta. Ganinta durqushe tana wani irin kuka yasa mama indo karasowa inda take da sauri. "Subahanallahi. Safiyya lafiya?" Kamata mama indo tayi. Safiyya ta makale jikinta tana wani irin kuka mai taba zuciya. "Safiyya menene? Ko wani ya rasu?" Ta kasa magana jikinta bari kawai yake da karfin kukan da take. Da wani ya rasu zaifi mata sauki saboda wannan abune da ka riga da ka san zai faru. Abinda fu.ad yai mata ko da wasa bata taba hango shi ba. Dago kai tayi muryarta na rawa tace. "Ya sakeni............ya tafi. Komai ya..... Komai ya kare......bani da kowa" Fadar datai ya sake tabbatar da abinda yake faruwa. Da gaske bata da kowa. Babu su inna. Fu.ad kadai ya rage mata shima ya tafi abinshi. Numfashinta taji yana wani irin daukewa saboda tashin hankali. Bata da kowa. Bata da inda zataje a wannan duniyar da batasan kanta ba. Tanajin yanda mama indo ke girgiza ta. Saidai sam ta kasa dai daita numfashinta dake daukewa. Wani irin duhu taji ya mamaye kanta kamun daga bisani duhun ya zo har cikin idanuwanta.......! **** "Safiyya!!!" Inna ta fadi tana girgizata da katse mata tunaninta. "Safiyyaa....!" Da sauri tana ware idanuwanta kan Inna tace. "Na.am" "Lafiyarki kuwa?" Ta girgiza kai. Ita kadai tasan abinda zuciyarta ke mata. Nauyin da take ji a cikin. Wasu zafafan hawaye na sake biyo fuskarta tace ma Inna. "Alhaki bai barmu mun samu farin ciki ba. Rashin albarkar iyaye a auren mu ya sa baiyi nisa ba. Ya sakeni shekaru sha daya da suka wuce" Daga inna har baba wani shocked Expression ne dauke a fuskarsu. Safiyya tai wani murmushi cike da takaici. "Karkuyi mamaki inna. Babu dan dazai ga dai dai babu albarkar iyaye a rayuwarshi......." Cikin nutsuwa take basu labarin yanda komai ya faru. Take basu labarin nana. Yanda inna ta rikota jikinta cike da kauna da tausayawa ba karamin taba zuciyar safiyya yayi ba. Cikin kuka take fadin. "Nana din ma ba mai tsahon kwana bace ba inna" Baba ne ya jinjina kai yace. "Hakika rayuwa wani abu ce mai cike da darussa kala kala. Dabara daya ce mai rai zaiyi. Shine kokarin gyara lahirarshi" Cike da yadda da abinda baba yace inna ta karbe da fadin. "Babu komai da yake da tabbas a zaman duniya. Dawamammen farin ciki na tare da wanda ya cika da imani" Sake kwanciya safiyya tayi jikin inna. Dumi da kaunar mahaifiyarta na saukar mata da wata nutsuwa ya daban. Kamun baba yace. "Da kun maida aurenku safiyya. Kaddarar data hadaku mai girma ce. Allah ne kadai yabar ma kanshi sanin abinda ke tattare da rayuwarku" Mikewa zaune safiyya tayi zuciyarta cike da nauyin maganganun da baba yayi. Ba auren fu.ad bane matsalarta. Ba rashin haihuwarshi bane damuwarta. Dan daga randa ta san tana da cikin Nana ta fahimci haihuwa kyauta ce ta Allah. In ya rubuta maka samu baka isa ka canza hakan ba ko min kinka kuwa. Da nisantaccen yanayi a muryarta tace. "Baba bana son sake rasaku. Na dandana hakan yafi komai ciwo da daci. Tunanin rasa Nana baikai tashin hankalin tunanin kin sake ganinku ba" Sauke numfashi baba yayi. "Ba zaki rasamu ba safiyya. Mutuwa ce kawai zata rabamu in shaa Allah. Muma munji rashinki wallahi" Ta rasa daga inda sabbin hawaye ke sake zubo mata. Muryarta na rawa tace. "Bazan sake abinda babu albarkarku a ciki ba. Komenene" Jinjina kai baba yayi. Ya mike da fadin. "Ina zuwa" ** Zaune yake cikin mota ya lumshe idanuwanshi. Baisan iya lokacin daya dauka ba a haka. Babu tunanin komai a ranshi banda na safiyya da nana. Su kadai yake gani cikin zuciyarshi da idanuwanshi. Hadata da iyayenta shine abu na farko dayake alfahari da bata shi. Ko ba komai ya dawo mata da wani bangare na rayuwarta dayai silar salwantar dashi. Ya samu nutsuwa daya kasa samu na tsayin lokaci. Bazai taba manta abinda yagani cikin idanuwanta da kan fuskarta ba lokacin datai tozali dasu inna. Kaman yanda bazai manta yanayin dayaji ba lokacin daya rike hannuwan abbah bayan lokaci mai tsayi. Kauna kenan. Wannan itace kaunar dake tsakanin mahaifa da yayensu. Kaunar da Allah ne ya dasata shi kadai yasan girma da nauyinta. Abinda yake ji akan Nana babu kalaman da zai amfani dasu wajen fassarawa. Yasan zafin kaunar iyaye. Yasan darajarsu bazai taba bari su sake kubce masa ba. Ji yai an kwankwasa glass din murfin motar. A nutse ya dago daga jinginar dayai da kujera. Ganin baba ne yasa shi bude wa ya fito da sauri. Zuciyarshi na wani irin dokawa dan ya dauka wani abune ya samu safiyya yace. "Baba lafiya dai ko?" Murmushi baba yayi yace mishi. "Ba abinda ya sameta" Wata kunyace ta lullube fu.ad ya sadda kanshi kasa ganin baba ya karanci manufar tambayarshi. "Muje ciki sai muyi magana a nutse" Ba musu fu.ad ya rufe motar yabi bayan baba har cikin gidan. Daki suka nufa. Kan safiyya dake lafe jikin inna fu.ad ya sauke idanuwanshi. Nutsuwar dake kan fuskarta ya saukar mishi da wani nishadi na daban. Waje ya samu kasa ya zauna duk da kujerun dake cikin dakin. Wata kunyace ta kamashi dayake tuna girman laifukan daya aikata musu. Baisan ta inda zai fara ba. Kanshi a kasa yace. "Wallahi bansan ta inda zan fara ba. Ni mai laifi ne a gareku inna. Inajin nauyin rokar yafiyarku saboda laifina mai girma ne" Shiru fu.ad yai kanshi a kasa yanajin yanda laifukanshi ke danne shi. Baba yace. "Allah ma ana mishi laifi ya yafe ballantana dan adam. Mu suwaye da zamu rike ka da abinda kai nadama akai? Abinda ya faru ya rigada ya faru. Bai kamata muna duba baya ba. Mukam mun yafe duniya da lahira. Allah ya yafe mana gabaki daya" Inna ce ta amsa da amin. Dan fu.ad ya kasa magana. Yana jinjina ma karamcin su baba ne. A nutse baba yace. "Safiyya ta fada mana komai. Kaman yanda na fada mata san sake fada maka. Ina tunanin kaddarar data hadaku tana da girma. Dakun yafi juna kun maida aurenku kodan yarinyar dake tsakaninku. Ku kula da ita a tare zaifi" Da sauri fu.ad ya dago ya kalli safiyya. Sosai yake duba idanuwanta yaga ko zaiga tsanar shi ko kin yarda da maganar baba. Ya kasa karantar komai. A tsorace yace. "Baba bansan me zance ba. Bana son sake yima kowa laifi......" Ya karasa maganar yana ware idanuwanshi kan baba. Murmushi yayi. "Babu damuwa. Kuyi shawara a tsakaninku. Karku dauki lokaci. Rayuwar bamai tsayi bace ba. Yar'ku na bukatarku" Cikin sanyin murya fu.ad yace. "Banda shawara nikam. Ina son yin komai dai dai ne. Ina son gyara komai saboda ban samu nayi daga farko ba. Zan magana da abbah yau in shaa Allah" Kai safiyya ta sadda kasa hawaye ba zubo mata. Oh rayuwa kenan. Albarka inna da baba suka saka musu hakan ya musu dadi sosai. Shiru yadan gifta na wani lokaci cikin dakin. Kowa da abinda yake sakawa cikin zuciyarshi. Fu.ad hamdala yake ta jerowa. Yasan bai cancanta a sake bashi auren safiyya ba. Saboda bashida abinda zai bata. Saidai bazai iya hana zuciyarshi son sake aurenta ba. Ya sake tabbatar da sonta da yake yana nan daram. Babu inda yaje. Muryarshi ya sauke kasa sosai yace. "Baba zan tafi. Zan kirata in fada mata idan munyi magana dasu abbah" "Allah ya bada iko ya tabbatar mana da alkhairi" Fuad yana mikewa ya amsa da. "Amin baba. Inna nagode sosai. Allah ya kara girma" Safiyya ya kalla. Yana jin nauyin yai mata magana gabansu inna yasa kai ya fice daga dakin. Inna tace ma safiyya. "Kije ko zakuyi magana" Dakyar ta iya mikewa jikinta ya mata wani irin nauyi. Yanajin takunta ya juyo da sauri. Tsayawa yai harta karaso inda yake bakin kofar da zata fitar dashi soron gidan. Ta rasa ta inda zata fara mishi magana. Kome zatace. Abubuwan da take ji suna da yawa yau. Ganin tayi shiru yasa shi fadin. "Tunda Nana na gida. Saiki kwana wajen su inna kema ko?" Taji dadi sosai. Dan ko bai fada ba batai niyyar binshi su koma ba. Saidai yaune rana ta farko data rabu da nana. Da zata kwana a wani waje ba tare da yartata ba. Ba zatai ma kanta karya ba. Har kewar nana ta fara damunta. Ga tsoron kar aki kula da ita yanda ya kamata. Gani take kaman wani abin zai faru. Idanuwanta cike da tsoro tace ma fu.ad. "Kar a bata madara da yawa. Na bata magungunanta duka da zatai amfani dasu. Karka barta taje wajen ruwa. Ko tasha abu mai sanyi sosai. Ka taba jikinta duk minti sha biyar kaji ko da zazzabi. Daka ga tayi shiru ka tambayeta. Bata son fada in wani abu na mata ciwo. Karta kwana ita kadai and kuma dakaga matsala dai ka kirani please......." Murmushi fu.ad yayi. Wani burge shi take yanda duk ta daburce sai lissafo mishi ka.idoji take. Ganin kallon da yake mata yasa tadanyi murmushi itama. "Ka kula da ita sosai dan Allah" "Karki damu. Babu abinda zai same ta in shaa Allah. How bouh' in kira kuyi magana lokaci lokaci" Taji dadi sosai. Ta daga mishi kai alamar hakan ya mata. Harta juya yace. "Sofi....." Juyowa tayi ta zuba mishi ido. A raunane yace mata. "Banda abinda zan baki sofi. Kinsani ko?" Batace komai ba. Shiru tayi tana son fahimtar maganarshi. Ya dora da fadin. "zan fahimta idan bakya son sake aurena. Wallahi zan fahimta duk da zuciyata ba zata so ba" Gaba daya ya karasa kashe mata jiki. Ita yanzun burinta yagama cika. Ta ga su inna ta samu yafiyarsu. Shi kanshi haushin da yake bata ta neme shi ta rasa. Duk da ba zata iya tsayar da abinda take ji a kanshi ba. "In har baba ya hango kaddararmu mai girma ce banida bakin musu." Da sauri yace. "Farin ciki nake so ki samu. Ko da ba tare dani bane ba" Sauke numfashi tayi. "Na same shi a yau fu.ad. Nagode da cikamun alkawarin nan" Wani kasalallen murmushi yai mata. "Hmm sofi. Alkawarin daya daukeni shekaru" Kallonshi tayi. "Bance ga ranar dazan cika miki alkawarin nan ba. Amman komin dadewa zan gyara komai. Wannan shine kalamanka a gareni. Ko harka manta?" Wannan karin murmushin dayai har cikin zuciyarshi yakai. "Ban manta ba. Ban manta komai ba" Jinjina mishi kai tayi. Ta juya tanajin shi ya furta. "Nagode. Nagode sosai sofi" Bata juyo ba. Da murmushi a fuskarshi ya fice daga gidan. * Daki safiyya ta koma ta zauna gefen inna. Sai yanzun abinda ke manne a ranta ya fado mata. "Inna ina usman?" Ta bukata. Kaninta mai sonta. Usman da lokutta da dama in nana tayi wani abin takan tuna mata dashi. Hada ido taga inna da baba sunyi kamun suyi shiru kowa na sadda kanshi kasa. Wani irin bugawa taji zuciyarta tayi. Lokaci daya tsoron da ta kasa fadar kalarshi ya rufeta har tsikar jikinta ta tashi. Muryarta a sarke tace "Innaa" Kauda kai gefe inna tayi. Safiyya ta mayar dashi kan baba. "Baba ina kanina? Ina usman? Dan Allah ku fadamin" Cikin wani yanayi baba yace. "Ya rasu safiyya. Shekara hudu kenan. Ciwon ciki na yini daya...." Kanta ke juya mata. Girgiza kai take yi tana jin zufar dake keto mata tako ina. Inna ta kama hannunta. "Sai hakuri safiyya. Allah baiyi zaku sake hada fuska a duniya ba. Yafi kowa jajenki. Babu inda bai nemeki ba" Wani irin kuka ya kwace ma safiyya marar sauti. Zuciyarta take ji kaman ta ciro ta ajiye gefe tadan samu sa.ida saboda zafin da take mata. Usman ya rasu. Rufe idanuwanta take tanajin yanda suke mata wani yaji yaji amman hawaye ko daya yaki fitowa. Tana tuna shi. Tana tuna komai nashi. Yanayin maganarshi. Rikota inna tayi jikinta amman sam safiyya taki. Matsawa tayi ta hade kanta da gwiwa so take karsu lallasheta. Subarta taji mutuwar usman. Taji rashin kaninta da bata samu ta mishi sallama ba. Kaninta dazaiji ta manta dashi saboda ko sau daya bata taba aika mishi da sakon addu.a ba tunda bata san ya rasu ba. Mutuwa na da daci. Dacinta bazai fahimtu ga wanda baisan yanda take ba. Wanda bai taba rasa wani makusancin shi ba. Allah sarki usman yaron kirki. Yaro nai cike da kauna da fahimtar kowa.....! **** Bai kokarin hana zuciyarshi tsalle tsallen da take ba. Yana cikin mota ya kira lukman. Bugu daya ya daga. "Bazawari" Baisan lokacin daya kwashe da dariya ba. Ya manta rabon dayai kalarta haka. Wai bazawari. Lukman din ma dariya yake. "Ni yanzun na girma na kusan aurar da junior. So banida lokacin ka dankaji" Cewar fu.ad din yana dariya. Shima lukman din dariya yake. "Amman lukman baka da mutunci wallahi. Wai bazawari....." Yana dariya shima yace "Gaskiya ce baka so nasani. Yane? Yasu nana" Komai daya faru ya juyema lukman daya sauke ajiyar zuciya ya na fadin. "Na yarda kam fu.ad. Kaddararku da safiyya babu mai fahimtarta idan ka duba" "Hmm. Hakane kam. Yanzun zan tsaya masallaci inyi sallar juma.a in kana free mu hadu gidan yaya babba mana. Banje bafa tunda na dawo" Lukman ya amsa da. "Babu damuwa to. Nima yanzun wanka kawai zan infi to sallar. Zan dai kiraka idan na fito" "Alright. Godiya" Fu.ad ya amsa yana kashe wayar . ** Yana fitowa daga masallacin sarki kanshi tsaye kundila ya wuce gidan babban yaya. Ya kira lukman shima yace mishi yana hanya yama kusa kaiwa. Bakin kofar gidan ya sami lukman maigadi ya bude musu suka shiga sukai parking motocinsu. Sunci sa.a babban yaya na gida. Sosai anty sa.a matarshi tai mamakin ganinsu. Musamman fu.ad dan gara lukman wani lokaci sukan zo da haneef. Bayan sun gaisa ta shiga ciki ta kira musu babban yaya. Yana fitowa ya ware idanuwanshi da mamaki. Duk da momma ta fada mishi fu.ad din ya dawo bai hanashi mamaki ba. Waje ya samu ya zauna. Suka gaisa da su fu.ad. "Daman nace zanzo in gaishe dakai ne" Fu.ad ya fadi yana murmushi. Babban yaya ya harare shi. "Aikam kai baka da kirki ko kadan fu.ad" Dan sosa kai fu.ad yayi a kunyace. "Ayi hakuri babban yaya. Bazai sake faruwa ba in shaa Allah" "Allah ya kara shirya mana kai. Dan kam bakajin magana fu.ad. Ya jikin nana din?" A sanyaye yace. "Da sauqi tana gidan momma ma" Jinjina kai babban yaya yayi. "Momma ta fadamun komai. Ina jirankane daman. Muma mun hada jini da ita ai. Saboda me ba za.a auna mu ba? Ko dan bamu da mutunci a idonka har yanzun?" Da sauri fu.ad yace. "Haba mana. Wallahi sam ba haka bane ba. Ko daya wannan tunanin bai zomun ba. Saboda abune mai girma da hadarin gaske.  Dan Allah karkace haka. Nagane kuskurena" Kallon shi babban yaya yayi sosai. Lukman dake zaune yace "Ai hakuri babban yaya." Jinjina kai yayi. "Bakomai. Komai ya wuce. Zan magana da kowa tun daga kan su hassan inason kowa yaje a auna shi ranar monday" Fu.ad shiru yayi. Ya rasa abinda zaice. Ya rasa kalar kaunar yan uwanshi a gare shi. Jiki a sanyaye ya mike. Dan tsaf zuciyarshi zata iya karyewa. Wani irin yanayi yakeji dayake bukatar ya zauna shi kadai ya jinyace shi. "Nagode" Bai jira amsarshi ba da sauri ya fice daga falon. Lukman ya kalli babban yaya yace. "Abubuwan ne sun mishi yawa. Yana ganin kaman bai cancanci dukkan karamcin da ake mishi ba" "Menene amfanin yan uwantaka idan babu taimako a tsakani? Zumunci abune mai girman gaske lukman. Bamu hada jini dakai ba. Iya abinda zan ma fu.ad shi zan maka. Zakumin laifi. Zanyi fushi daku. Zaku gane kuskurenku zan kuma yafe muku. Wanna shine zama na hakika. Wannan itace kauna ta gaskiya" Maganganun babban yaya sun shigi lukman ba kadan ba. Ya kara darajta girma na zumunci. Godiya ya sake yima babban yaya kamun suyi sallama. Sanda ya fito babu motar fu.ad. Tashi ya shiga yai gida abinshi. Yasan zai neme shi in yana bukatarshi. **** Ya dade cikin mota bayan yai parking bai fito ba. Ya hade kanshi da gaban motar kawai yanq jinjina kalar kaunar da babban yaya ya nuna mishi yau. Haka ya kamata ace yan uwantaka ta kasance. Haka ya kamata ace an girmama zumunci. Idan ya tuna ranar daya sa kafa yai watsi da wanna kaunar yakanji ciwo marar misaltuwa. Yakanyi dana sani dashi kadai zai fahimce shi. Bude motar yayi ya fito saboda yanda yake jin iskar dake ciki ta mishi kadan. Yana kaiwa kofa haneef na fitowa. Da fara.a yace "Yanzun nake shirin kiranka. Momma tace mun kunje wani waje da safiyya" Jajayen idanuwanshi fu.ad ya sauke kan haneef daya sashi saurin karasowa ya na dafa kafadar fu.ad din. "Lafiya? Fu.ad meya sameka?" Dafe kai fu.ad yadanyi. Ga abinda ya same shi nan. Muryarshi a dakushe yace. "Ion' deserve dukkanku. Dukkan kaunarku ban....." Katse shi haneef yai da fadin. "Daga ina wanna shirmen yake fitowa? Kar in sake ji fu.ad. Inba so kake ranka ya baci ba" Kama hannuwan haneef din yayi yana tsugunnawa kan gwiwoyinshi. Bai damu da yanda haneef din ke fadin. "Fu.ad ka tashi. Wai meye haka?" Hawayen dayake rikewa ne suka zubo mishi. Hawayen farin ciki ne da samun yan uwa irin su. Murya na sarkewa fu.ad ke fadin. "Hada jini daku alfahari ne a wajena haneef. Kaunarku mai girmace a gareni" Rike da hannayen fu.ad cikin nashi haneef ya kama shi yana dago shi. Saida ya saki hannunshi daya sannan ya zaro hanky daga aljihunshi ya mika ma fu.ad. "Saboda Allah ka shiga cikin gida kagani. Su khadee duk suna nan. In kana hawaye haka ai anyi abin kunya. Bakasan ka girma bane yanzun?" Langabe kai fu.ad yayi yasa hanky din yana goge fuskarshi. Dakuna fuska yayi. "Na girma ai. Na kusan aurar da ya'ya" Sosai haneef ke dariya. Shekaru kam sun ja. Amman akwai bangare na fu.ad dayasan da wahala ya girma. Yanzun haka yanda ya dakuna fuska cike yake da yarinta. Halittace ta fu.ad wannan. Yana bukatar dukkan kulawarsu duk girman dazaiyi. "Nikam ina da wajen zuwa. Sai munyi waya ok?" Kai fu.ad ya daga mishi yana fadin. "Hanky dinka" Girgiza mishi kai yayi. "Ewww waye zai karba? Nabar maka" Ware idanuwa fu.ad yai kamun ya kwashe da dariya. "That is gross haneef" Dariya kawai yayi ya wuce. Shima hanky din ya kalla. Saidai bazai iya cillar dashi ba. Da murmushi a fuskarshi ya shiga gida. Kaman yanda haneef ya fada gidan a cike yake da yara da suka saka murmushin shi ya kara fadada. Karasawa yai wajen su. Yana ganin su yassar yagane su. Kamarsu daya sak da pha.iza. Gaishe dashi sukayi. Nana na zaune ita da wata yarinya mai kyau da yake son gane ko yar wacece. Nana ta kalle shi tana murmushi. Dayar yarinyar dabaisan sunanta ba tace. "Kaine uncle fu.ad?" Dariya yayi ya daga mata kai. "Zo mu gaisa mana" Ba musu ta taso tazo wajenshi. Ya tallabi kumatunta duk kaunarsu ta cika mishi zuciya. Bai taba sanin haka kaunar yara take ba sai randa ya dora idanuwanshi kan Nana. Kaman ta bude mishi wani wajene da baisan dashi ba. Yanzun duk inda yaga yara sai murmushi ya kwace mishi. Biye su yai suna ta shiririta har momma ta fito. "Fu.ad yaushe ka dawo?" Kallonta yayi a gajiye. "Ban dade ba momma. Sannu da hidima. Wallahi yunwa nake ji sosai" Momma ta daga mishi kai. Mikewa yayi ya karasa inda nana take zaune tayi wani shiru. "Lafiya dai ko nana?" Murmushi tayi ta daga mishi kai. "Na sha magani ne. So yana sani bacci kuma shisa. Ina mumy?" Dan dakuna fuska yayi. "Zan baki labari anjima" Da ido ta nuna mishi ta fahimta. Ya wuce inda momma tabi yabarsu nan. Yana cin abinci yake ba momma labarin komai. Taji dadi. Tuni take son mishi magana kan auren su da safiyya din sai dai bata son kara mishi tension. Ya dora da fadin. "Naje gidan babban yaya ma" Kai ta daga ta amsa shi da. "Eh ya kirani kuna fita yake fadamun yanda kukayi. Yakamata kaje gidan antynku ma" Saida ya hadiye abincin dake bakinshi sannan yace. "Aikam wallahi. In shaa Allah anjima. Dana gama cin abinci wanka zan indan huta sannan" Mikewa momma tayi da cewar. "Allah ya kaimu. Bara inje. Nasan yanzun abbanku zaizo sai in mishi magana aji yanda za.ayi" "Ba damuwa momma. Allah ya kara girma ya tabbatar mana da alhairi" Ta amsa da amin tana wucewa. Sosai yaci abincin sanna ya tashi ya nufi dakinshi........! *#TeamAS* *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ www.Loobnerh.blogspot.com Wattpad: LubnaSufyan                    43 *#AnaTare* *Babu abinda yakai dan uwa dadi. Babu abinda yakai zumunci muhimmanci. Saboda me zamu cika zuciyarmu da kiyayya bayan zamu iya cika ta da kauna?* *Saboda me zamu riki junanmu bayan zamu iya bayyana laifin junanmu mu yafi juna komai ya koma dai dai?* *Saboda me zamu zabi jin haushin junanmu bayan zamu iya bata lokacin mu kan bayyana murmushi a fuskokin juna?* *Na yarda da kauna. Na yarda kauna abu ce mai girma. Na yarda na zabi farin ciki sama da akasin shi. Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa. Amin thumma amin* "Fu.ad idanuwanka kenan?" Dan sosa kai yayi yana murmushi. Anty fatima ta sauke numfashi hadi da fadin. "Ka kyauta" Sai lokacin tun zamanshi falon ya dago idanuwanshi ya sauke su kan anty fatima da duk wata nadama dake cikinsu. Saukowa yai daga kan kujerar dayake zaune ya saka gwiwoyinshi kan kafet din dakin ya hade hannayenshi waje daya. Muryarshi a dakushe yace. "Nayi laifi anty. A yafemun dan Allah. Kaunarku a gareni tafimun komai muhimmanci a yanzun. Bazan taba iya dawo da shekarun nan ba. Amman zan iya gyara na gaba. Ki yafemun" Kallon shi take. Tabbas fu.ad ya musu laifi su dukansu. Tana kallonshi yasa hannu a aljihunshi ya ciro wani abu. Kallonta yai yana mika mata hannunshi dake dumtse kamun daga baya ya bude shi. Agogo ne na hannu. A ko ina taganshi zata gane shi. Idanuwanshi ya saka cikin nata. Da wani irin yanayi a muryarshi yace. "I want mi' sister back. Ina son sister dina data koyamun yanda zangane wannan agogon na hannuna. Ina son sister na da muke shiga kitchen hada salad tare. Ina son sister na da take tare dani lokacin da nake sneaking zuwa ball. Anty fatima please......" Ya karasa maganar yana sauke muryarshi kasa idanuwanshi cike da hawayen dayake rike dasu. Komai na dawo mishi kaman lokacin ya faru. * Kitchen suke da anty fatima tana yanka kwan da ta dafa zata hada musu salad. Yana tsaye gefe tace mishi. "Fu.ad karfe nawa. Ga agogona nan kusa dakai" Daukar agogon yai. Ya tsura mishi idanuwa. Babu lamba ko daya a jiki. Dakunq fuska yai yadan daga girarshi hadi da fadin. "Yazan ingane? Babu number ko daya a jiki" Dariya anty fatima tayi hadi da fadin. "Karka cemun baka iya reading wannan agogon ba fu.ad" Cije lebenshi na kasa yai yana ware mata idanuwanshi. A kunyace yace. "karki fadama haneef. Zaita tsokana" Fuskarta babu alamar wasa tace mishi. "Bazai ji ba. Zan koya maka" Murmushi yai. "Really?" Kai ta daga mishi. "You are the best sis kinsani ko?" Dariya kawai anty fatima tayi hadi da fadin. "Gashi na matane dana bar maka" Da sauri yace. "Ban damu ba. Ina so sai insa a aljihuna" Kallon fuskarshi tayi. Da gaske yake son agogon yake in tabar mishi. "You can have it. Karka zo wajena in wani ya tsokane ka da agogon mata" "Zan fasa bakin duk wanda yamun dariya saboda ke kika bani" **** Hawayen dayake idanuwan anty fatima suka zubo. Hannu tasa ta karbi agogon tana juya shi. Bata taba zaton fu.ad nada shi ba har lokacin. Bata sake ganinshi dashi ba bata kuma tambaya ba. Hannu tasa ta goge idanuwanta muryarta na rawa tace. "Kana dashi har yanzun daman?" Kallonta yayi da murmushi yace. "Ina mantawa na daura a hannuna. Saina dauko na duba naga ya dainayi nake Tunawa" Dariya tadanyi. "Fu.ad......." Katse ta yai da fadin. "Please. Please i want her back" "Ka tashi fu.ad. Komai ya wuce. Your sister is here and always will be" Murmushi yai cike dajin dadi ya mike ya zauna kan kujerar. "Har yanzun watermelon eyes ne dake anty fatima" Dakuwa tai mishi ya kwashe da dariya. Yana jinshi wani light. Mikewa yai yana fadin. "Bani agogo na nikam in wuce. Yamma nayi sosai" Mika mishi tayi hadi da fadin. "Saura mu sake nemanka mu rasa" Dariya kawai yayi yana wucewa. "Nikam sai munyi waya" "Ka gaishemun dasu momma" Ya amsata sannan ya fice. **** A hanya yai sallar magrib sannan ya koma gida ya samu hassan zai maida su khadee gida saboda washe gari duk yaran suna da islamiya. Kiran hassan yayi ya zaro credit card dinshi yaba hassan hadi da fadin. "Ka biya dasu ka siya musu ko chocolate. Ice cream. Kome dai suke so" Karba hassan yai. Harya juya fu.ad yace mishi. "Ka siya duk abinda kake so" Girgiza kai hassan yai. "Ina aiki bro. Ka manta" Dariya fu.ad yayi. "Ka girma ko?" Dan daga mishi kafada hassan yayi sannan ya wuce abinshi. Falon ya karasa ya samu Nana na kwance kan kujera tayi pillow da cinyar momma tana bacci. Ya samu waje ya zauna yana sauke ajiyar numfashi. Gaba daya jinshi yake a gajiye. Ba irin gajiya ta ciwon jiki ba. Jinshi yake emotionally drained. Kallon momma yayi tai mishi murmushi. "Mungama magana da abbanku. Da yace kuje yauma. Nace abari zuwa gobe tukunna da safe in Allah ya kaimu. Saika kira safiyya ka fada mata ko" Jinjina kai yayi. "Allah ya kaimu. Bara inje sallar isha.i in dawo" Ya karasa maganar yana mikewa. "Allah ya karba mana" Ya amsa da amin yana ficewa. ** Yana dawowa daga sallar isha.i abinci yaci ya wuce dakinshi ya watsa ruwa sannan ya sake kaya yasa wata T-shirt marar nauyi da three quarter loose. Kasa ya sauko zuwa falo. Yana shirin kiran momma yaji ya Nana sai gata ta fito jikinta sanye da rigar bacci pink sai hular dake kanta ma pink. Wani irin dokawa zuciyarshi take yi da kaunarta. Murmushi tayi mishi ta karasa inda yake ta kama hannunshi. Kujera suka samu suka zauna. Nana ta kalle shi tana ware idanuwanta kan fuskarshi. Tun kamun ta furta ya karanci tambayarta cikin idanuwanta. Dan haka ya hutar da ita ta hanyar amsa ta da fadin. "Ni da mumynki. Zamu koma da aurenmu gobe in Allah ya......." Bai karasa maganarshi ba yaji ihun murnar Nana ta fada jikinshi ta zagaya hannuwanta kan bayanshi ta kankame shi. Yanajin dariyar da takeyi. Shima dariya yayi. Farin cikinta na kara mishi wanda yake ji. Dakyar ya samu ya banbare ta daga rikon datai mishi. Ta make kafadarta tana sake komawa ta kankame shi. Kyaleta yai saidata gama murnar da kanta sannan ta dago daga jikinshi ta gyara zamanta kan kujerar. Kanshi ta tallabo da hannuwanta duka biyun ta hada goshinsu tare. Ji take yagama mata komai na duniya. "Nagode dady. I love you so much. Nagode sosai" Cikin idanuwa yake kallon yarta shi yana jin kaunarta har cikin jininshi. Yanajin kaunarta ta yanda bazai iya fassarawa ba. Wannan son is priceless. Kalar kaunar dabance da wadda yake ji akan safiyya. "Ina mumy yanzun?" Muryashi can kasa yace mata. "Tare da mumyn ta da dadynta" Sake ware mishi idanuwa nana tayi. Tana sauke murya tace. "Suna nan?. Sauran grannies na suna nan? Mumy ba ita kadai bace yanzun?" Kanshi dake jikin nata yadan daga. Yana kallon yanda ta lumshe idanuwa wata nutsuwa na sauka kan fuskarta. Idanuwanta a lumshe har lokacin goshinta na hade da nashi tace "Na taba tambayarsu. Mumy taita kuka ban sake ba. Me ya faru dasu?" Raba goshin su yayi ya tallabi fuskar Nana cikin hannuwanshi. Wani irin nauyi yake ji cikin zuciyarshi. Amman yafison wannan gaskiyar ta fito daga bakinshi. Yafiso ya fadama Nana da kanshi. Saidai wanne irin bayani zakaimq yarinya yar shekara sha daya. Cikin sanyin murya tace. "Ba saika fadamun ba in baka so. Naji dadi da mumy take tare dasu. Shi kadai ya isheni" Wani abu ne yai masa tsaye a wuya. 'She is so fucking matured' ya fadi a ranshi a fili kuma yace mata. "No zan fada miki. Bansan ta ina zan fara ba" Daga mishi gira tayi dake nuna itama batasan ta inda ya kamata ya fara ba. Ya sauke ajiyar zuciya. "Ina da shekaru ashirin da biyu Nana. So young and stupid. Nayi wani kuskure da bai kamata inyi ba. Bazan iya fada miki kuskuren ba. Amman abune marar kyau sosai. Hakan ya bata komai. Ni da mumynki da kowa namu" Kai ta jinjina mishi alamar ta fahimta. Bata son ganin yanda idanuwanshi suke. Kaman abinda yake fada yana mishi tsananin wahala da ciwo. Hannunshi dake fuskarta ta ture tana kama shi cikin nata ta dumtse. Muryarta a tausa she tace. "Bana son ji dady" "Why?" Ya bukata yana tsare ta da idanuwana. "It is hurting you. Nikuma bana so" Hugging dinta yayi. Yanayin na karya mishi zuciya. Wannan yarinyar daban take a cikin mutane. Bai taba ganin irinta ba. Muryarta cike da kaunarshi tace. "Ka gyara komai ko dady? Komai ya wuce yanzun?" Muryarshi a dakushe da yanayin da yake ji yace mata. "Yeah. Komai ya wuce thanks to you" Dariya tayi tana dagowa daga jikinshi. "Kira mumy in mata good night" Ba musu ya dauko wayarshi ya duba. Tinawa yayi bashida number din safiyya ma. Yai wiki wiki da idanuwa yanajin wata yar kunya ta kamashi. Sosai nana take dariya. Ya dakuna mata fuska. "Ka fada inji dady" Kai hannu yayi yaja mata hanci ta ture hannunshi tana dariya sosai. Karanto mishi number din safiyya tayi. Ya kira bugu daya ta dauka da sallama. Nana ya mikama. Ta karba suka gaisa. "Mumy bani su mu gaisa please please please" Dariya safiyya tayi daga dayan bangaren tace. "Sun kwanta nana. Kema ki kwanta kice dadynki ya kawoki gobe sai ki gansu ok" Turo baki nana tayi ta kalli fu.ad daya daga mata gira da tambayar lafiya? "Wai sunyi bacci gobe ka kaini" Tace ma fu.ad ya daga mata kai. Safiyya dake dayan bangaren tace. "Kikace me nana?" "Nida dady ne" Bata jira amsar safiyya ba ta mikama fu.ad wayar. A dan daburce yace. "Hello" Shiru tadanyi da alama itama ta tarasa abinda zatace mishi. Kamun tace. "Komai lafiya dai ko?" "Lafiya kalau. Tana lafiya" Shiru suka sake yi kamun tace. "Saida safe kenan?" Dasauri yace. "No. Zamuzo dasu abbah gobe" "Allah ya kaimu. Ka kula da ita" Yadan daga kai kaman tana ganinshi ya mikama nana. "Good night mum. Take care. Love you" "Love you too princess" Ta fadi tana kashe wayar. Kallon fu.ad nana tayi. "That is awkward" Ware idanuwa yai yana mamakin yanda Nana taji turanci haka. Sai kuma yai tunanin jss1 akace mishi take kuma da alama makarantarsu nada kyau sosai. Kuma gaskia ta fada. Wayarsu da safiyya is kinda awkward. Dariya yayi. Hamma nana ta fara ta kalle shi. "Na gudu wajen granny dady bacci nake ji" Kai ya daga mata. "Sleep well. Banda snoring" Ta wani dakuna fuska kaman ya fadi kazanta. "Ewww dadyyyyy!" Dariya sosai fu.ad yake. Nana ta soma dire kafafuwa. "Ni bana snoring. Ka tambayi mumy" Dariya yake. Saida yaga yanda nana ta dakuna fuska ya samu ya tsayar da dariyarshi. "Go and sleep" "Bana snoring" Ta fadi tana dora hannuwanta kan kugunta. Dariya fu.ad yayi. "Bakya snoring. Na yarda" Murmushi tayi ta matsa kusa dashi ta sumbaci kumatunshi. "Good night dady. Love you" "Love you more" Wucewa tayi. Yanajin tana fadin. "Nooooo i love you moreee" Yai dariya kawai yana sake shigewa kan kujerar. Dakyar ya iya mikewa ya tafi dakinshi. Yana addu.a bacci mai nauyi ya dauke shi cike da mafarkin sofinshi. **** Tana zaune gaban mudubi tana shafa powder a fuskarta. Hannuwanshi ta fara ji kan kafadarta sannan ta sauke idanuwanta cikin nashi ta mudubin dake gabanta. Murmushi yai yana sumbatar gefen fuskarta. Lumshe idanuwa yayi. "Ina son kamshin turarukan nan naki jana. Bana gajiya dajin su" Dariya tayi ta dora hannuwanta kan nashi hadi da ture su. "Nikam kabarni in shirya" Dakuna fuska jabir yayi. "Ke yanzun saiki barni gidan nan shiru? Yara duk sun tafi islamiyya" Dankunnenta take kokarin sakawa ya karbe daga hannunta yana makala mata ta amsa shi da. "In banje ba yau banda lokaci sosai. Rabona da gidan hajiya anfi sati hudu fa honey j" Langabe fuska yai yana daukar dayan dan kunnenta ya saka mata hadi da jan kunnen. Dukan hannunshi tayi tana fadin. "Wayyo. Da zafi fa" Daga mata gira yayi. "Nikam banajin zama ni kadai" Juyowa tayi ta fuskance shi. Idanuwan shi cike suke da rikici. Yau kwana uku kenan da fada mishi zataje gidan hajiya yanzun kuma zai rigime mata. "Kai dan zaman majalissar da maza suke bakayi balle ince ka fita" Hannu yasa ya mintsinan mata kumatu yana matsewa. Ta ture shi tana shafa wajen. "Kinsan babu abinda na tsana banda zaman majalissa. Me suke banda gulma da kallon matan mutane" Ta shagwabe fuska. Hannunta nakan kumatunta inda ya mintsina. "Shine saika mintsine ni" Ya daga mata kai. "Kisan yanda zakiyi dani. Muje in kaiki gidan hajiyar ma ko? Sai mu gaisa" Girgiza kai take yi. "No. I mean in caps. Wallahi nagode. Ni sai bayan azahar zan dawo idan naje" Tasan halinshi da wuya yabari suyi minti sha biyar. "Honey j. Kaga ka kyaleni in shirya" Hannuwanshi ya hade kan kirjinshi ya zuba mata idanuwanshi masu rikita mata lissafi. Da sauri tace. "Kaje wajen ayna" Dan batason yanda fadar hakan kawai yake saka zuciyarta wani irin tafasa. Ya karance ta tsaf. Karasawa yai inda take yasa hannuwanshi ya tallabi fuskarta. Cikin idanuwa ya kalleta kamin ya manna mata sumba mai taushi. "Saikin dawo. Babu inda zanje. Zan kwanta inyi bacci" "I mean it honey J. Ka....." Kallon dayai mata yasa ta rufe bakinta ya jinjina kai. "You are doing enough. Nasan me kike dannewa *Akan so* na jana. Basaikin kara da abinda zai cutarmin dake ba. Bana so kinajina. Karki kure hakurinki" Kai ga daga mishi a sanyaye tace. "Thank you" Da hannuwanshi dake fuskarta yake nuna mata yanda muhimmancinta yake a wajenshi. "Ki kulamin da kanki" Ta daga mishi kai tana sa hannunta ta cire nashi dake fuskarta saboda yanda yanayin kallon da yake mata da komai da take karanta cikin idanuwanshi suke saukar mata da kasala. Cikin kanta take kirga satikan da suka rage musu. A kasan zuciyarta tana addu.a kar komai ya canza musu. Kar soyayyarsu ta girgiza. Da wannan tunanin a ranta ta karasa shiryawa. Saida ta karasa inda yake zaune kan gado ta sumbace shi sannan ta fice. **** Zaune take kasa. Ta dora kanta kan cinyar hajiyarsu dake zaune kasa. Kuka take mai cin rai. Gabaki daya abinda take dannewa ne a zuciyarta a kwanakin nan take ture shi gefe ya bude mata daganin hajiyarsu. Hannu hajiya ta dora kan jana da tana shigowa falon ta karaso ta zauna gabanta ta dora kanta a cinyarta tana wani irin kuka. Da jabir baizo har gida ya fada mata ba. Da yanayin kukan janar ya daga mata hankali. Batai kokarin hanata ba. Kawai ta dora hannunta a kanta ne. Cikin son nuna ma yar tata tana tare da ita a koda yaushe. Dago fuska jana tayi da harta kumbura ta kama hannuwan hajiya tana wani gogasu kan fuskarta. Cikin kuka take fadin. "Bana bakin ciki da auren da jabir zaiyi hajiya duk da na kasa hana zuciyata zafin kishin shi. Babu wanda zan gayama inajin tsoron auren na saike. Babu wanda zan nunama rauni na ya fahimta hajiya. What if tazo ta tarwatsa mana komai?" Cikin idanuwa hajiya ta kalli jana murya a tausa she tace. "Na fahimci tsoranki murjanatu. Na fahimta wallahi. Nakuma jinjija ma kokarinki. Ina alfahari da karfin halin da kika nuna. Koni bance zan iya irinshi ba. Ki godema Allah wannan baiwace daba kowacce mace yaima ba. Naji dadi da yanda bakiyima kaddara gardama ba duk da kina tsoranta. Abu biyu zuwa ukku zan fada miki" Kai jana ta daga tana sauraren hajiya kaman gabaki daya duniya bata da wani aiki da ya wuce hakan. Har ranta tanajin yanda ruwan da take ciki yakawo har bakinta. Bata da abin kamawa ta fito daga cikin shi daya wuce shawarwarin mahaifiyarta. Hajiya taci gaba da fadin. "Karki yarda zafin kishi ya canza kaunar da tausayin dake tsakaninki da mijinki. Karki bari addu.a ta kubce miki a kowanne hali da kika tsinci kanki. Ki zauna da ita da zuciya daya. Ko zata cuceki Allah zai zamana yana tare dake saboda babu mugun abu a zuciyarki. Ko koma gidanki batare da tsoron nan a zuciyarki ba murjanatu. Kaddararki ta jima da bushewa. Tsoro ko rashin hakan bazai canzata ba. Hanyoyi na Ubangiji suna da girma. Kiyi addu.ar alkhairi. Ki mika ma Marubucin kaddararki komai naki. Zai nuna miki hanya idan kin rasa ta" Wata irin nutsuwata daban jana take ji a cikin zuciyarta. Hannu tasa ta goge fuskarta. Ta sake kwantar da kanta kan cinyar hajiya. Muryarta a dishe saboda kukan da tayi tace. "Madallah da mahaifiya irinki hajiya. Madallah da mahaifiyar datake kama hannuna a koda yaushe zuwa hanyar gaskiya. Ina kaunarki hajiya. Allah yabarmin ke" Dariya hajiya tayi. "Ke dai kice Allah ya hadani da mahaifinku a aljanna. Ita nafi bukata" Murmushi jana tayi tana ma mahaifinta addu.ar samun Rahma a zuciyarta. Kamun ta sauke numfashi. **** **** Da safe wajen karfe goma duk sun gama shiryawa daga shi har abbah. Lukman da haneef ma sunzo gidan. Nana da camera a hannunta su haneef sun biye mata sai shiririta suke. Kar lukman yaji labari. Fu.ad ya kalle su ya girgiza kai. Gaba daya nana ta mayar dasu yan yara. Har ya juya ya maida hankalinshi wajen abba ya sake juyowa da sauri. Kallonsu yake sai yake tunanin shima kenan haka yake zama yaro in yana tare da ita kenan? Ya bude baki zai magana yaya babba ya shigo. Su duka gaishe dashi sukai shikuma ya gaishe da abbah da momma. Fu.ad ya kalla. Jeans ne blue a jikinshi da riga fara sal da ita. Ya girgiza kai hadi da fadin. "Kai haka zamuje gidan surukai dakai da kananan kaya?" Sosa kai fu.ad yai yana ware idanuwa hadi da fadin. "Banda ko daya ne" Haneef babban yaya ya kalla. "Kayanka ba zasuyi ma fu.ad ba?" Girgiza kai haneef yayi. Dan fu.ad ya fishi tsayi yanzun kam. Na lukman kuma daga tsayin har girman ya mishi kadan. Sauke ajiyar zuciya babban yaya yayi. "Allah ya rufa asiri to" Abbah da momma kam dariya suke musu. A hankali nana ta mike ta taka har inda babban yaya yake. Kallonshi take. Sai lokacin ya kula da ita. "Ina kwana baba babban yaya" Tace mishi dan haka taji suna kiranshi babban yaya. Lukman ya fara kwashewa da dariya kamun si haneef su dauka. Har babban yaya saida ya murmusa. Kallonsu nana take cikin rashin fahimtar me suke ma dariya. Kamo hannunta babban yaya yayi. "Rabu dasu nana. Kina lafiya?" "Lafiya kalau nagode" Ware idanuwa yai da dan mamakin wayan yarinyar. Kamun ya kalli su haneef yace "Muje ko?" Ba musu suka mike. Lukman ne ya kama hannun Nana suka fice. Momma na musu Allah ya bada sa.a. Mota daya suka shiga da babban yaya da abbah. Su kuma su haneef suka shiga mota daya. Fu.ad ke tuqin dan shi yasan gidan. * Kofar gida suka tsaya fu.ad ya sake kiran safiyya yace musu suna kofar gida.  Ko mintina biyar ba ai ba tsakani ta kira tace su shiga. Kwace hannunta nana tayi daga na lukman ta ruga da gudu cikin gidan lukman yace. "Au nana dan munzo ko? Zaki fito ki same ni" Bata juyo ba dariya kawai tayi. Suka shiga ciki su dukansu. A falon da suka shiga jiya aka tare su. Ware idanuwa fu.ad yake ko zaiga safiyya amman babu alamar ko Nana ma balle yai tunanin zai ga safiyya. Inna ma suna gaisawa dasu abbah ta  kawo musu lemuka da ruwa da fice daga dakin. Su dukansu ruwan kawai suka sha. Babban yayane kawai ya fasa lemon exotic guda daya ya sha. A nutse suke magana tsakanin abbah da baba. Fu.ad kam bayajin me suke fada kwata kwata saboda hankalinshi ba akansu yake ba. Zuciyarshi bata tare dasu. Tana wajen safiyya a yanzun. Mamakin yanda rayuwa ta canza musu lokaci daya yake. Canji tai musu me kyau. Kaddararsu ta sauya su daga duhun data jefa su zuwa haske mai ban mamaki. Lukman ya zungure shi. Da sauri ya dago kai ya kalle shi. Ware mishi idanuwa yai alamar ya dawo da hankalinshin kan maganar da ake yi dan ya kula baya tare dasu. Yanajin su abbah suka tsayar da magana cewa ranar za.a daura aure karfe hudu. Saboda a samu damar sanarma mutane. Babu ma yanda basuyi da baba ba akan ya karbi sadakin ya rike yace aa kawun safiyya ne zai amsa sai an kira shi tukunna. Mikewa sukayi akai sallama gabaki daya. Su abbah suka fara ficewa. Fu.ad ya kalli haneef daya zare mishi idanuwa alamar ya wuce su tafi. "Bara in kira safiyya ta turo nana" Tura shi haneef yayi. Kasa kasa yake fadin. "Ba wata Nana. Kabarta anjima inmun dawo mun tafi da ita" Hakoranshi fu.ad ya bude haneef gabaki daya saikace mai tallar abin goge hakori hadi da fadin. "To ko nima in zauna anjima in kunzo saiku tafi dani" "Fu.ad!" Lukman ya fadi. Daga kafada fu.ad yai yana ware idanuwa yace ma lukman. "What? Meye dan kun barni?" Swatting dinshi haneef yai a bayan kai ya tsugunne yana fadin. "Ouchhhh me nai ne wai ku?" "Wuce mu tafi" Haneef ya fadi yana hade fuska. Turo baki fu.ad yai kaman yaron da aka kwace ma sweet. Ya wuce yana fadin. "I so don't like ku biyun nan" Dariya sukai suna tusa shi gaba haneef na fadin. "We so don't care!" *#TeamAS* *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ www.Loobnerh.blogspot.com Wattpad: LubnaSufyan             44 *I know you guys will want to kill me after reading this chappy. But karku manta i promise. A HAPPY ENDING* *Ina godiya da kaunarku. ILYA* *#AnaTare* Wayarshi ke ringing. Yadan ja karamin tsaki saboda sam bayajin magana koma wacce iri ce. Hannunshi yasa ya tallabi goshin shi. Wayar ta sake daukar ringing. Daukota yayi da niyyar kashewa gabaki daya. Ganin sunan dake jiki yasa har hannunshi ke rawa wajen picking. Wani irin dokawa zuciyarshi take. Dakyar ya nemo muryarshi ya iya fadin. "Nuriyya" Shiru tadanyi. Yasan tana jinshi dan haka ya sake cewa. "Are you okay?" Maimakon ta amsa tambayarshi sai catayi. "Mafarki nake ko da gaske ne kacemun ba anty bace mahaifiyata?" Yasan yanayin da take ciki. Baya son kara mata damuwa. "Please muyi wannan maganar idan kin kara nutsuwa kin....." Katse shi tayi da fadin. "Ka fadamun kawai. Ina son sani ne" Muryarshi a dakushe yace. "Ba ita bace mahaifiyarki nuriyya. Ta tsince ki ne ta rike ki" Yanajin kukan daya kwace mata. Tabashi take ta ko ina na jikinshi batare datai amfani da hannayenta ba. Kukan ta na shiga har kasan zuciyarshi yana yawo. "Nuri..." "Karka sake kirana da Nuri please.....Na... Haka yake cemun..." Ta karasa maganar muryarta na rawa da alamun kukan da take yi. Gaba daya bayajin dadi. Ya bude baki zai magana ta kashe wayar. A hankali ya ciro wayar daga kunnenshi ya bita da kallo. Ajiyewa yayi yana sauke numfashi. **** Kan gado ta saki wayar ta kwanta. Kuka take mai taba zuciya. Abu dayane yake mata yawo akai. Ada tasha dauka cewar anty ce mahaifiyarta. Yafi a kirga tana tambayarta waye mahaifinta tana shan jibga harta hakura ta daina. Duk tsahon lokacin nan tana ma kanta kallon wadda aka samu ta hanyar banza. Ta dade da making peace dinta da wannan bangaren. Ada tasan wacece mahaifiyarta. Yanzun komai ya canza mata. Bata san wacece ita ba. Batasan ina aka samo ta ba. Har yanzun tabon samu ta hanyar banza bai bace mata ba. Shin yarda ta akai? Ko me ya faru da ita. Wani tsoro ne yake shigarta. Jan kafafuwanta tayi ta hade jikinta sosai kan gadon. Nawaf din da take kallo take tunanin tana da wani a fadin duniya shima baya nan. Ya tafi inda bazai taba dawowa ba sai dai ita taje ta same shi. Bata da inda zata kama. Bata da inda zataje. Ba zata ce ga makomarta ba idan tagama takaba. Tasan darajar hakan take ci a gidansu nawaf. Fadar sunanshi kawai wani ciwo take ji marar misaltuwa. Wanda baisan yanda dacin mutuwa yake ba bazai fahimci halin da take ciki ba. Text taji ya shigo wayarta. Hannu takai ta dago da wayar ta duba. Farhan ne dan haka ta bude. 'Idan kina bukatar wani abu. Ina nan. Kirana kawai zakiyi. Please ki kula da kanki' Ajiye wayar tayi ta lumshe idanuwanta tana rasa exact abinda take ji. **** Zuciyarshi wani irin dokawa take tun da su abbah suka tafi ya kasa samun nutsuwa. Ji yake kaman kaddara zata sake kwace mishi safiyya. Ji yake kamar ba za.a daura auren nan ba. Ya kasa zama. Sai kai kawo yake yi cikin dakinshi. Kama handle din kofar yai zai fito wayarshi ta kama ringing. Zarota yai daga cikin aljihunshi. Ganin lukman ne ya kara ma zuciyarshi gudu da dukan da take yi. A sanyaye ya daga hadi da fadin. "Lukman...." "An daura fu.ad. An mayar da aurenku da safiyya" Lumshe idanuwa fu.ad yayi ya jingina jikinshi da kofar dakin yana jero ma Ubangiji godiya. Muryar lukman ta katse shi da fadin. "Fu.ad....." "Ina jinka lukman" Wani numfashi lukman yaja kamun yace. "Ka kula da ita. Zai wahala inta kubce maka ta sake dawowa. Ba kowa bane yake sa.a irin taka a rayuwarshi" A sanyaye ya amsa da. "In shaa Allah. Nagode lukman" "Allah ya sanya alkhairi" Lukman ya fadi yana kashe wayar kamun fu.ad din ya amsa. Baisan me yasa yaki zuwa ba. Babu yanda babban yaya baiba yace kanshi ciwo yake. Abbah yace a kyale shi aiba dole saiyaje ba. Takawa yai ya karasa kan gadonshi ya zauna. Safiyya yaima text da kalma daya. 'NAGODE' Batai mishi reply ba. Baikuma saka ran daya ba. Dan haka bai damu ba. Nan ya zamanshi yanajin dawowar su abbah bai fita ba. Yana son kasancewa shi kadai dinne na wani lokaci. Koda na iya ranar ne. Bai fito ba saida ya dauro alwalar sallar magrib tukunna. **** Tunda baba ya dawo ya fada mata an sake daura auransu da fu.ad ya fice da Nana take kwance daki tana kukan da bata san dalilinshi ba. Inda ance rayuwa zata sake maidata matsayin data dade da goge shafinshina zuciyarta ba zata yarda ba. Tana jin sallamar inna ta shigo dakin. Da sauri ta mike tana goge fuskarta hadi da amsa sallamar a sanyaye. Gefen gadon inna ta zauna da wata leda a hannunta. Ta dora ledar kan gadon ta budeta. Atamfofine guda biyu a ciki. Takalma sai abin hannu da sarka. Da hawaye cike taf idanuwan inna muryarta na rawa tace ma safiyya. "Bayan usman ya kammala aji shidda jarabawarshi batai kyau ba. Akace saiya gyara wata shekarar. Sai ya bukaci zai dinga zuwa aikin kafinta da ya soma yi tun dawowarmu makaranta tasa dole ya ajiye. Cikin kudin dayakan samu yana mana siyayya dasu. Kama daga kaya zuwa abubuwan ciye ciye......" Shiru inna tayi tana goge hawayen da suka zubo mata. Tun da inna ta kira usman wasu sabbin hawaye ke zubo ma safiyya. Nata zaman makokin ne take yanzun. Ciwon mutuwar usman sabone a wajenta. Su inna suna da shekara ukku su ririta nasu ciwon. Itakam yau kwana daya kenan da samuwar nata. Turama safiyya kayan inna tayi. "Ko da muka hakura da nemanki. Usman yafi kowa sa ran dawowarki. Shi ya siyo kayan nan yaban in ajiye. Da daidai ya siyo yana sa ran zaki dawo ko yaushe karya zamana kin dawo bai siya miki komai ba. Yakance kuna hirar sana.a tare yakan fada miki bashida sha.awar karatu......." Kasa karasawa inna tayi dan haka ta mike kawai ta fice daga dakin. Kayan safiyya tasa hannu akai. Kaman taba kayan datayi ya bude mata hotunan usman a zuciyarta. Fuskarshi take kallo. Murmushin shi take gani. So take ta tuna yanda sautin dariyarshi yake. Yanda muryarshi take cikin kanta ta kasa. Wani irin tsoro taji ya shigeta. Sosai take jin tsoron har cikin tsokar jikinta. Lokaci ya kwace mata wannan bangaren na usman. "Ya Allah...." Ta fadi wasu irin hawaye masu dumi na zubo mata. Da gaske ta manta yanda sautin muryar usman yake. Atamfafin ta janyo jikinta hannuwanta na rawa. Fuskarta ta hada da kayan tana kuka marar sauti tana fadin. "Allah ya kai haske kabarinka usman. Ban samu bankwana dakai ba balle in roki gafararka...." Sosai take kuka tana rike kayan a jikinta. A haka yayanta ya shigo ya sameta. Bataji sallamarshi ba saboda gabaki daya duniyar a birkice take jinta a lokacin. Saida taji ya zauna gefen gadon sannan ta dago fuskarta dake jikin kayan da usman ya siya mata ta sauke su kan yaya. Sama sama taji numfashinta nayi. Jiya taita sa ranshi ya kira inna yace mata bazai samu zuwa ba. "Yayaa......." Ta kirashi cikin yanayin ciwon da zuciyarta takeyi. Da sauri ta sakko daga kan gadon ta zauna kasa. Hannuwanshi ta kama. "Yaya ka yafemun. Yaya babu usman yau. Usman ya tafi ya barmu...." "Shhhhhhh safiyya ya isa. Ya isa haka" Ai kaman ma ya sake bude mata wani sabon shafin kukan. Tana rike da hannuwanshi. "Dan Allah safiyya kiyi shiru. Soyayyarmu usman yake bukata ta hanyar addu.a" Dago jajayen idanuwanta tayi. "Ba zaka gane me nake ji ba yaya. Kai ka mishi sallama....." Kallonta yake. Shi kuwa zai gane me take ji fiye da ita. Dan uwa daya ta san ciwon rashin shi. "Karki fara safiyya. Karki sake ki yankema abinda baki sani ba hukunci. Ba zaki taba sanin me ake jiba lokacin daka mutuwa ta dauke maka dan uwanka guda daya. Kaddara ta watsa yar uwarka duniyar da baka sani ba. Karki yankema abinda baki sani ba hukunci" Fuskarshi take kallo. Hannuwanshi ta saki tasa hannu ta goge tata fuskar. "Ka yafemun yaya. Naji rashin ku fiye da zatonka. Wallahi na horu da rashinku. Ciki harda bacewar muryar usman daga gareni. Na rasa abubuwa da yawa......" Wayarshi taga ya dauko. Yana daddanawa. Mika mata yayi ta karba hannunta na rawa. Videos ne. Da sauri ta danna play. Idanuwanta lokaci daya suka sake cikowa da hawaye. Usman ne yana dariya. Da alama shi yake daukar kanshi video din yana fadin. "Bansan me yasa nake ji a jikina bazan sake ganinta ba. Koma menene Allah ya fini sanin shi." Murmushi yayi cike da wani yanayi dayasa safiyya mikama yaya wayar tana hade kanta da gwiwa. Muryar yaya a dishe yace mata. "A wayarshi na dauka bayan ya rasu. Date din jiki ya nuna yai recording kwana biyu kamun rasuwarshi. Dake a zuciyarshi ya rasu safiyya. Usman na kaunarki fiye da yanda kike zato. Mu duka munyi rashin shi. Addu.armu yake bukata a yanzun" Ai bata jin nasihar yaya. Yabarta kawai tai kukanta. Yabarta taji mutuwar usman saboda shi ya rigada yaji tashi. Tana jin ya mike bata dago da kanta ba. "Naji dadi da na sake ganinki kamun mutuwa ta gifta mana. Allah ya sanya alkhairi" Bata amsa shi ba. Tanajin ya fice daga dakin ta koma kan gadon ta ci gaba da kukanta. Saida tadaina jin hawaye ba fita sannan. Tana kwance tana tunanin yanda rayuwa da duka duniyar ma ba komai bace text din fu.ad ya shigo. Dubawa tayi ta ajiye wayar. Tana rasa abinda ya kamata taji. **** Har ya tashi da safe bazaice ga abinda yake damunshi ba. Kawai yanajin wani irin yanayi ne daya kasa fassarawa. Koda anty fati tazo gidan gaisawa sukayi. Ita da momma suka shirya suka tafi gidansu safiyya su taho da ita. Haneef zai kira yaje suyi magana sai gashi ya shigo gida. Kallo daya yaima fu.ad ya karanci yanayin fuskarshi. Saida ya zauna sannan yace mishi. "Me ke faruwa?" Gyara zama fu.ad yai ya fuskanci haneef sosai. "Em' quitting?" Cike da rashin fahimta haneef yake kallonshi. "Me kenan? Bangane ba" Jan nunfashi fu.ad yayi ya sauke shi a hankali. "Football. Zan quitting......" Katse shi haneef yai da fadin. "No. No fu.ad ba zakayi abinda zaka zo kai dana sani ba" Murmushi fu.ad yayi. Muryarshi kasa kasa yace. "Bazan dana sani ba haneef. Ko ban dawo ba na kusan ajiyewa. Ko da bankai inda nake da buri ba. Nayi. Nakuma ji dadinta. Yanzun kunfi mun komai muhimmanci. Ina son kasancewa tare daku. Na rasa shekaru sha daya. Bana son rasa kwanaki ba a kusa daku ba. Contract din danai signing ya kare. Sabone zan signing karshen watan nan.  Em' done.  Zanje in kare komai in dawo" Sosai haneef yake kallonshi da alamun maganganun fu.ad din basu zauna mishi daidai ba. "Are you sure?" Ya bukata. Kai fu.ad ya daga mishi yana murmushi. Haneef ya lumshe idanuwanshi ya bude su. "Allah ya tabbatar da alkhairi to" "Amin ina khadee?" Murmushi ya kwace ma haneef dajin sunan yar tashi. "Tana islamiyya" Hira suke kamun hassan ya shigo. Da murmushi a fuskarshi ya gaishe dasu ya nemi waje ya zauna. Yanayin zaman ya sake karfafa niyyar fu.ad. Yanda yake ji a zuciyarshi bai taba jin hakan akan ball ba. Yan uwanshi sunfi mishi komai muhimmanci. **** "Daka shigo ciki" Cewar ayna bayan sun gaisa da jabir. Girgiza mata kai yayi. "Wucewa zan na biyo mu gaisa. Ba jimawa zan ba" Murmushi tayi a kunyace. "Ina su ikram da anty?" Murmushin ya mayar mata. "Duk suna lafiya. Jana tana gaishe dake" Dagowa tayi tadan ware mishi idanuwanta da alamun mamaki. Ya daga mata girarshi duka biyun hadi da fadin. "Kina mamakine? In batace ba bazan fada miki ba" "Kawai dai.... Bansan ma me zance ba" Murmushi jabir ya sake yi. "Jana mutuniyar kirki ce ayna. Ina sonta fiye da yanda zan iya fada miki. Zan aure kine saboda ina sonki badan na rasa komai a wajenta ba. Banda haufin zata girmamaki duk da ta girmeki. Bance ki tayani son jana ba. Saidai ina son ki tayani girmamata saboda tana da muhimmanci a rayuwata" Sauke ajiyar zuciya ayna tayi. Wani son jabir da kimarshi na kara shigarta. Cikin fuska ta kalle shi. "Kaima mutumin kirki ne jabir. Daga lokacin da maza suke neman aure saikaji suna kushe matansu na gida dan su burge yan matan da zasu aura din. Da ace ka bude bakinka da mummunar kalma akan anty kimarka zata ragu a idanuwana. Bansan ko kaddararka ba akan mata biyu ta tsaya ba. Saboda zanji a raina yanda kake fada akan anty haka zaka fada akaina. Allah yabani ikon tayaka bata girma gwargwadon iyawata. Bazan maka alkawarin komai ba saboda bana so ka daga zatonka fiye da yanda zan iya" Yar dariya jabir yayi. Hankalin ayna da yanayinta shi ne abinda ya fara so tattare da ita kamun ya kula da kyawunta. Ba fara bace kamar jabarshi.  Bakace kuma bata da dogon hanci kaman na jana saidai idanuwanta na burge shi sosai. Intai murmushi yanda dimples dinta ke fitowa yana mishi kyau. Komai nata ya sha banban dana jana. Yana son su su duka biyun. "Nagode ayna. Nagode da karamcinki. Zan wuce sai munyi waya ko?" Kai ta daga mishi tana murmushi. "Ka kula da kanka. Ka gaishe dasu ikram" "Zasu ji in shaa Allah. Ki kulamun da kanki" Ya fadi yana bude murfin motarshi. Addu.a tai mishi dayaji dadinta kamun suyi sallama. * Fita yazo yi daga motar yaga deposit slip a ajiye. Janyo su yai da mamaki dan yasan baije bank ba duk satin nan. Yana niyyar zuwa biyama su ikram kudin makaranta bai samu zuwa ba yabari sai weekend. Dubawa yayi. Ya ware idanuwanshi. Girgiza kai yayi ya fito daga motar yana shiga cikin gidan. A kitchen ya samu jana tana soya doya da kwai. Ya shiga da sallama ta amsa shi. Ta baya ya rungumeta jikinshi. Tai dariya tana ture shi. "Honey J aiki nake" Gam ya riketa jikinshi. Cikin kunnenta yace. "Ban hanaki aikinki ba ai" Hararshi tai duk da baya ganinta. "Please. Ka sakeni in karasa" Dariya yayi. Ya saketa yana matsawa suka jera. Kwanon kwan yaja gabanshi ya shiga zuba mata wata yankakkiyar doyar a ciki. "Ina kaje haka?" Ba tare da tunanin komai ba yace mata. "Wajen saminu naje saina biya muka gaisa da ayna. Tace tana gaishe daku ma" Wani tafasa taji zuciyarta nayi ga wani irin kishi daya turnuqeta. Shiru tayi tana jero addu.o.i cikin kanta. Tanajin idanuwan jabir na yawo a fuskarta. Taki bari su hada idanuwa ta kafe su kan aikin da take. Saida ta tabbatar zata iya magana batare da kishin da take ji ba cikin muryarta kamun tace. "Muna amsawa mungode. Tana lafiya dai ko?" Kai kawai ya daga mata. Saida ta karasa kwashe doyar ta rufe warmer din ta sauke man sannan ya sake janyota jikinshi. Slips din ya zaro daga aljihunshi ya kamo hannunta yasa su a ciki. "Janaaa...." Ya kira da wani irin yanayi. Dubawa tayi. Ta lumshe idanuwanta babu inda bata neme su ba. Sai yanzun ta tuna da motar jabir din ta fita ranar. "Jana hidimar tana yawa" Hannuwanshi ta zame daga jikinya ta juya suka fuskanci juna. Idanuwanta ta sauke cikin nashi. "Meye hidimar a ciki? Biyama yaranmu kudin makaranta? Honey j baka barina in tayaka da komai. Ko mai na zubama motata sai kayi fada. Please ina so in taimaka nima" Hannu yasa ya murza goshin shi. "Bawai taimakawa bane baba so kiyi jana. Bana so ki sangartani ne da yawa. Kar inzo in kasa sauke nauyin da Allah ya doramun. Hakkin kula daku akaina yake" Sumbatarshi tayi a hankali kamun ta janye da fadin. "Nasani. Kuma kanayi ina son yin wani abune nima. Meye amfanin aikin da nake in baka bari ina kashe kudin?" Murmushi yayi. Ya dora hannuwanshi kan kafadarta. "Nagode jana. I love you kinsani ko?" Kai ta daga mishi da murmushi. Har ranta take jin sonshi. "Kamun yara su dawo zo mu siyo ice cream" Ya karasa maganar yana jan hannunta. Riko shi tayi. "Honey j. Ice cream kawai. Promise?" Dan dakuna fuska yayi. Taja iska mai nauyi taba fitar da ita hadi da girgiza kai. Tasan shi sarai. Inhar zata siyi wani abu sai ya kashe mata rabin kudinta. Ba yanda zatai da halin jabir. "Allah ya shiryamun kai" Dariya yayi yana jan hannunta suka fita daga kitchen din tare. **** Ya fara damuwa kuma. Su momma sun kusan awa hudu yanzun. Baisan me yasa suka dade ba. Shi kewar nana ma ta dame shi. Wayarshi ya dauko ya kira safiyya. Ringing din farko ta kashe. Da mamaki yake kallon wayar. Zai sake kira text dinta ya shigo. 'Ina tare da su Momma" Murmushi yayi. Yasan sarai kunyar daga wayarshi take gabansu momma dan haka ya sake kira wannan karin ko ringing din farkon batai ba ta sake kashewa. Text din ta ya sake shigowa. 'Please mana. Reply ya mayar mata. 'Kun taho?' Bata bashi amsa ba ya sake tura wani. 'Zan ta kira har saikin daga sofi.' Reply tai mishi. Yai murmushi. 'Muna hanya' Ajiye wayar yayi ya lumshe idanuwanshi. Tattare da wata nutsuwa da take saukar masa akwai wani irin yanayi daya kasa fahimtar ko na menene. Yanajin kaman wani abu mai girma zai faru dashi. "Allah kai kasan iya abinda zamu iya dauka. Allah ka bamu juriya a duk lokacin da zaka jarabcemu" Ya fadi yana sauke muryarshi kasa kasa. Yana ganin yan aikin gidan nata hidima. Hussaina ce da wannan rigimar. A dole sai sunyi walima iya su kawai. * *Karfe 4:00* Ko ina ka duba na gidan cike yake da farin ciki. Zainab da safiyya zaune sunata hira. Zaka rantse sunyi shekaru tare bawai ranar kawai suka hadu ba. Nana ta karaso wajen safiyya. "Mumy aramun wayarki in kira anty jana" Lokaci daya safiyya ta mayar da hankalinta kan Nana. Hannuwa tasa tana taba fuskarta da wuyanta. Murmushi nana tayi hadi da fadin. "I am ok mumy. Kawai ina son tambayarta abu ne" Sauke ajiyar zuciya safiyya tayi. "Kin tabbata?" Kai Nana ta daga mata kamun ta mika mata wayar. Wucewa Nana tayi da dan saurinta tana barin area din gabaki daya. Kasan kafar benen da zai kaika sama ta shiga ta zauna. Number din doc jana ta nemo ta kira ta kara a kunnenta. Zuciyarta dokawa take yi. Taso ace tana kusa da dadynta zatai kiran nan saboda tana jin wani kwarin gwiwa idan tana tare dashi. Sai dai wannan abune da take bukatar yinshi ita kadai. Hukunci ne akan rayuwarta data ke son yankewa ita kadai batare da kowa ba. "Assalamu alaikum. Maman Nana" Aka fadi daga dayan bangaren. "Wa alaikumussalam. Anty nice ba mumy ba" Da mamaki a muryar jana tace. "Nana lafiya dai ko? Ba jikin bane ba?" Girgiza kai nana tayi kaman tana ganinta kamun muryarta a sanyaye tace. "Ina so in tambayeki ne kawai" "Ina jinki nana" Numfashi nana taja tana son zuciyarta ta rage dukan da take kamun tace "Nasan dady is not a match. Naji suna maganar zuwa gobe a auna kowa agani. Ina so in tambayeki. In an samu match. Zan warke ne gabaki daya?" Shiru jana tayi na dan mintina kamun tace. "Ki kaima mumynki wayar Nana muyi magana da ita" Girgiza kai nana take. "Aa please. Ki fadamun kawai ina son sani ne. Baki san yanda nake ji ba amman kinsan me yake damuna fiye da mumy Ina so in sani ne. Zan fahimta idan ba zaki gayamun ba" Da wani irin rauni a muryar jana tace. "Aa. Zakiji sauki sosai ne" "Amman zan ci gaba da rashin lafiya irin wannan?" Tana jin yanda jana ke fitar da numfashi alamar a wahalce take amsa tambayoyin nan. Itama a wahalcen take saurarenta. "Bako da yaushe ba" Daga kai nana tayi alamar ta fahimta "Thank you anty jana. You are the best doc" "Hmm" Kawai ta iya fadi kamun nana ta kashe wayar. Lumshe idanuwanta tayi kamun ta tashi ta fice daga falon zuwa harabar gidan. Hango su fu.ad tayi suna zazzaune su dukansu suna hira. Babban yayane kawai baya wajen. Ko takalmi babu a kafarta ta ruga da gudu. Kaman ance fu.ad ya dago idanuwa ya kuwa sauke su kan nana. Ita take gudun shi zuciyarshi ke dokawa karta fadi. Da alama ganin yanda gaba daya hankalin fu.ad ya bar kansu yasa gaba dayansu suka maida kallonsu inda na fu.ad din yake. Tana karasowa jikin fu.ad ta fada ta kankame shi. Riketa yai yaba shushing dinta da alamar lallashi duk da baisan abinda ya sameta ba ji yake har zuciyarshi. Ko ina na jikinta kyarma yake. Yanajin yanda hawayenta ke jika mishi riga. Ya sake riketa yana rocking dinsu hadi da lumshe idanuwanshi. "It is ok princess. Ina tare dake. Fadamun menene?" Su haneef kallonsu suke. Gaba daya yanayin su yasa jikin kowa a wajen yayi sanyi. Dago Nana fu.ad yayi daga jikinshi yana sa hannuwa ya tallabi fuskarta. Cikin idanuwa ya kalleta yana son taga yanda yake jin zai iya bata komai in yana da halin hakan. "Talk to me. Menene?" Muryarta na rawa tace. "Bana so kuje dady. Bana so kuje asibiti gobe. Bana son transplant din" Wani irin dokawa zuciyar fu.ad tayi wannan karin shi jikinshi ke kyarma. Girgiza mata kai yake "No..... No nana. Ba zaki barmu ba kina jina. Za.a samu match in shaa Allah" Hannunta tasa ta ture nashi daga fuskarta. Kallonshi take da wani irin yanayi dake nuna cewar bazai fahimta ba. Bazai taba fahimtarta ba. Baya son kallon da take mishi. Baya son ganin irin wannan kallon a fuskar yarinya kamarta. Hannu yakai zai kamo nata ta ture shi tana matsawa. "Bana so dady. Da gaske nake karku je bana so" Gabaki daya ta birkita mishi duniyar cikin yan mintina. "Nana calm down muyi magana." Da ihu tace. "Nooooo!" Haneef ya kalla da yanayin neman taimako. Girgiza mishi kai yayi dan baisan me zai ba. Ya maida kallonshi kan lukman. Baima wani tsaya ba dan yasan lukman yafi shi rauni. Kasa Nana take kallo kaman zata iya samun wata mafita daga yin hakan. Muryarta can kasa tace. "I am sorry dady. Kai kadai zaka fadama mumy karta daga burinta kaman yanda take fadamun. Bazanyi ba. Bana so kowa yaje" Fu.ad ji yake kaman zuciyarshi tabar kirjinshi yadan huta na wani lokaci. Ya bude baki zai magana Nana ta matsa kusa dashi. Kamo hannunshi tayi. "Dady ko anyi ba warkewa zanyi ba. Zai karama kwanakin mutuwata nisa ne. Zai karamun wahala fiye da wannan. Ba zaku gane me nake ji ba dady. Komai ciwo yakemun........" Zafi yakeji a wajaje na jikinshi da bazai iya fada ba. Hannunta takai tana zame hijab din jikinta. "Kalli dady. Gashina bazai kara fitowa ba. Kowa na zuwa school ni bana zuwa yanzun. Na daina jin taste din wasu abincin a bakina. Dady please bana son zama sick duka rayuwata. I want to die. I want all of it to stop in huta. Dady komai ciwo yakemun dan Allah kar kumin abin nan. Kubarni in huta dady" Ta karasa maganar hawaye na zubo mata. Mikewa lukman yayi yana barin wajen saboda yanda yake jin hawaye na shirin zubo mishi. Hassan ma barin wajen yayi. Janta jikinshi fu.ad yayi yana rungumeta. Haneef kam dafe kanshi yai cikin hannayenshi yaba fitar da numfashi da matukar wahala. Cak fu.ad ya daga nana jikinshi ya mike tsaye har ranshi yanajin shekarun daya rasa tare da ita. Da wani irin yanayi ya nufi cikin gidan. Ko sallama baiba ya shiga falon. Ya wuce su pha.iza dake tsaye suna magana ita da anty fati. Baya ganin kowa sai safiyya. Ita yake hangowa zaune. Ita kadai idanuwanshi ke gani. Zuwa yanzun hankalin kowa ya koma kanshi. Yana karasawa inda safiyya take ya sauke mata Nana kan cinyarta. Dan dafe kanshi da hannu daya yayi yana sauke shi cike da frustration. Kallon safiyya yake. Muryarshi a dakushe yace. "Ki kalleta sofi. Bata son transplant ko da an samu match. Ta hakura da rayuwa saboda ta mata wahala." Ware idanuwa safiyya tana rungume Nana jikinta hadi da sumbatarta. Ji yake kaman kanshi zai tarwatse. Ta samu wannan na shekaru sha daya. "Kina da wannan na shekara sha daya sofi. Bani da komai dazan rike and fuck it!  She is dying!" Kuka safiyya take. Ita fu.ad yake dorama laifin shekarun daya rasa tare da nana. "Kai ka tafi. Kuma na nemo ka ban sameka ba......" Ta fadi hawaye na sake zubo mata. Anty fatima ce ta karaso ta daga fu.ad a kafada ya ture hannunta. "Ba wani. Na rasa yarinyata saboda ke! Na rasa ganinta da lafiyarta. Na rasa kaita makaranta. Na rasa best moments tare da ita" Goge fuska safiyya tayi tai murmushin takaici hadi da fadin. "Tabbas duk ka rasa wannan. Tare dashi ka rasa ganinta lokacin da batada lafiya. Ka rasa ganin lokacin da she was so sick bata ko iya tashi daga gadon ta. Ka rasa ganin lokacin da gashinta ke kakkabewa daga kanta. Ka rasa ganin lokacin da take tisa uniform dinta na islamiyya dana boko tana kallonsu saboda ita ba zata iya zuwa ba. Ka godema Allah daya sa baka ga duk wannan lokuttan ba fu.ad saboda su kadai sun ishi zuciyarka ciwo har karshen rayuwarka" Tana karasa magana tasa fuskarta cikin hannunta tana fashewa da wani irin kuka. Zainab ma dake kusa da ita kukan take ballin anty fatima sarkin kuka. Saukowa daga jikin safiyya nana tayi. Ta zo dai dai wajen fu.ad ta tsaya. Muryarta can kasa tace. "Stop it dady. Ka daina ba laifinta bane ba. Ba laifinta bane da nake da cancer. Baka ga nima na rasa duk abin nan da dady na ba? Da lafiyata? Karka sake mata fada bana so. Tamun komai" Bude bakinshi fu.ad yayi yana fitar da iska saboda ta mishi wahalar fita ta hanci. Yanayin da yake ji babu wanda zai fahimta. Yanajin gabaki daya babu wanda yakaishi son kai da rashin adalci. In akwai wanda zaiji ba a kyauta mishi ba Nana ce. Ita ce da ciwon a jikinta. Yasa matan daya fi so bayan momma kuka hankalinshi ya kwanta. Bude baki yai zaiyi magana nana ta juya wajen safiyya tace. "Gaskiya dady ya fadi mumy. Zaki iya fiye da kokarin da kikai wajen nemo shi" Kai safiyya ta daga mata. Itama tasan da hakan data kira shi bata same shi ba zata iya zuwa gidansu a nemo shi bawai ta hakura ba. Saboda Nana din badan ita ba. Takowanne fanni Nana akaima rashin adalci. Takawa Nana tayi ta karasa inda momma ke tsaye tana zubda kwalla. Kamo hannunta tayi. "Ki kaini in kwanta bacci nakeji" Goge fuskarta momma tayi ta kama hannun nana suka wuce bangarenta. A hankali fu.ad ya taka zuwa inda safiyya take zaune. Tsugunnawa yayi. Hakan yasa zainab dafa kujerar ta mike dakyar saboda cikinta ya shiga wata na bakwai kenan. Hawayen dake fuskarta ta goge. Da kai ta nunama su anty binta dasu bar musu falon. Su dukansu bangaren momma suka wuce suna barin fu.ad da sofi. Kamo hannuwanta fu.ad yayi. Wani irin abu taji har tsakiyar kanta. Shekaru sha biyu rabonta da fu.ad sai yanzun da ya tabata tasan babu abinda ya canza. Dago fuska yai ya kalleta kamun hawaye su zubo mishi. Baisan me zaice mata ba. Kalamai duk sun tsaya mishi. Ta karance shi tsaf. Su dukansu suna cikin yanayi marar misaltuwa. Hannunta ta zame daga nashi ta na tallabar fuskarshi. Hawayen take goge mishi tana girgiza kanta duk data kasa tsayar da nata. Matsawa ya karayi ya dora kanshi kan cinyarta hawaye na sake zubo mishi. "Ki yafemun safiyya. Bana nufin dukkan abinda na fada dan Allah ki yafemun" Kanta ta dora kan nashi dake cinyarta. "Na yafe maka fu.ad. Ka yafemun daban trying sosai ba" Sake makalewa yai a jikinta yanajin yanda yai rashinta sosai. Kuka suke tare na shekarun da suka rasa. Na yanda kaddara ke gara su..........! *#TeamAS* *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ www.Loobnerh.blogspot.com Wattpad: LubnaSufyan          45 *Please ku kara hakuri dani. 5 more chapters to go in shaa Allah. Ina godiya da kaunarku* *Hussaina ubandiya kaunarki a gareni ba zata fadu ba. Ban kuma da bakin dazan miki godiya. ILYTDMAB* *Mum bilki Allah ya shirya miki zuri.a Allah ya baki abinda kike nema duniya da lahira* *TASKAR NOVELS this page is for you guys. #AnaTare* Fu.ad yakai su gida da kanshi. Nana ma bacci take dan haka ya sabeta a kafada yakaita har dakin sofi ya kwantar da ita. Yana fitowa ya samu sofi tsaye bakin kofar. Idanuwanshi yake yawatawa kan fuskarta ba tare da yasan abinda yake son gani akai ba. Kallon nata na nutsar dashi ta fanno ni da yake kasa fahimta. Da duk wani abu dake jikinshi yake son sake jin duminta ko na minti biyu ne. Baya son takura ta. Yarda da aurenshi datai bayan tasan bashida abinda zai bata kadai ya ishe shi. Beside zuciyarshi ciwo take kaman me. Lumshe idanuwanshi yai yana fitar da wani numfashi mai nauyi kamun yace mata. "Zanyi tafiya gobe in shaa Allah. Zan dawo may be zuwa next week ko kamun...... " Yana bude bakinshi ya fara magana taji zuciyarta na wani irin dokawa cile da tsoro. Zai sake tafiya zai sake barinsu. Yanzun kam sam zuciyarta ba zata iya daukar wani rashin nashi ba. Katse shi tai da fadin. "Karka tafi......." Idanuwanta ta sauke cikin nashi ta tabbata yaga tsoro da shakkun da ke cikinsu. Kasa hakuri yai da sauri ya taka ya hade space din dake tsakaninsu. Hannu yasa ya tallabi fuskarta yana jin jikinshi ya dauki wani irin dumi. Sosai ya kalleta. "Zan kare komai ne sofi. Zan dawo gabaki daya. Ki yarda dani karshen abinda zuciyata zatayi shine nisanta dake" Hawayen da ke rike cikin idanuwanta suka zubo. Muryarta a sarke tace mishi. "Usman ya rasu......" Kallonta yake da mamaki yana juya maganarta cikin kanshi yana tunanin inda ya taba jin sunan da alakar sunan da ita. Lokaci daya ya tuna. Ware idanuwanshi yai kamun yace. "Allahu Akbar. Sofi. O. M. G. Sofiiii" Ya rasa me ya kamata yace mata. Langabe kanta dake cikin hannuwanshi tai gefe cikin wani irin sanyin murya tace. "Nagode....." Ji yake kaman ya dauke mata ciwon daya san take ji. Ciwon da har yanzun baisan asalin dacin shi ba sai dai ya kamanta. Rikota yai jikinshi yana hugging din. Tsam tai a jikinshi tanajin sanannen yanayin da ke tattare da hakan datayi tunanin ya bace mata. Hannuwanta ta zagaya tana sake rike shi. Kadan kadan take ji yana hura mata wajajen dake mata zafi batare da wata iska na fita daga bakinshi ba. Sunkai mintina biyar a haka. Kamun tadan zame jikinta ta dago tana ware idanuwanta a kanshi "Ka kwana tare damu yau" A tausa she yake kallonta. "You don't have to........ Bana son takura ku sofi. Zamu iya bin komai a hankali" Girgiza mishi kai tayi "Nana zata so hakan. Indai zaka kwana batare daka zaci wani abu da ya wuce hakan ba banda matsala" Kai ya daga mata. Ya fahimci komai. "Zanje gida sai in dawo. Ki kula dake da Nana" Kai ta daga mishi kawai tana jinta daban ta wajaje da dama. Yanayin ba bako bane a wajenta amman ya mata wani iri. Sai daya sumbaci kumatunta yanajin son yin fiye da hakan ya danne sannan ya juya ya nufi kofar yana ficewa. Sauke numfashi safiyya tayi ta wuce cikin daki inda Nana take. * A gida yaci abinci da sallar isha. Yai sallama da kowa dan bayajin zai biya da safe sannan ya wuce daga can zai tafi. Komai da yake bukata ya dauka yasa a mota ya wuce gidansu safiyya. Yana shiga nana ta rugo da gudu ta rike mishi kafafuwa. Dago ta yai zuwa jikinshi. "Princess bakiyi bacci ba" Girgiza mishi kai tayi tana dakuna fuska. "Mumy tacemun zaka kwana anan. Shine nake ta jiranka" Murmushi yayi yana cire takalman kafarshi kamun ya karasa da ita tsakiyar falon. Idanuwanshi ya sauke kan safiyya da take sanye da doguwar riga ta farar shadda. Ta mishi kyau ba kadan ba. "Sannu da gida" Yace mata yana zama gefe gare da nana daya zaunar kan cinyarshi. "Yasu momma?" Safiyya ta bukata. "Suna lafiya suna gaisheki" Kamun ta amsa shi Nana tace "Dady zaka tafi gobe?" Ya jinjina kai alamar eh. Yana dorawa da fadin. "Da wahala inyi sati daya. Idan na dawo shikenan bazan sake komawa ba" Dariya nana tayi alamar taji dadin hakan kamun kuma ta dakuna fuska. "Zanyi missing dinka kuma" Shima dan dakuna fuska yayi. Badan yana tunanin safiyya ba da ya fasa tafiya gobe yai booking musu waje ya tafi da Nana. "Ko zaku rakani?" Nana ya tambaya amman idanuwanshi nakan safiyya. Murmushi kawai tayi. "Nikam bana son jirgi fa. Bazani ba dady" Ware idanuwa fu.ad yai dake tambayar da safiyya ko da gaske Nana take. Kai tadan daga mishi. Dariya yayi. "Da gaske? Me yasa?" Dan daga mishi kai tayi. "Kawai tunanin hawa ina ciki can sama. Owww a daina maganar jirgi please" Dan ja mata hanci yayi yana dariya. "An daina princess" Hira suke a hankali tana jikinshi safiyya kam kallonsu take shi kadai ya isheta nishadi. Har nana tayi bacci a jikinshi dan magungunan data sha ma sun isa daukarta. Safiyya ya kalla. Sannan ya mike da Nana. Bayanshi tabi. Ya kwantar da nana kan gado. Yana gyara mata kwanciya ta juya ta rike mishi hannu gam. Kokarin zamewa yake amman yanayin rikon da tai mishi in ya motsa ta sosai zata iya tashi. Zama yai kan gadon yana jan kafafuwanshi a hankali ya kwanta gefenta. Safiyya ya kalla. "Bana so in tashe ta" Kai ta daga mishi. Ta zagaya dayan gefen Nana ta zauna tana jingina bayanta da gadon ta lumshe idanuwa. Badan fu.ad din ba da sun manta da sunyi bacci. Dan Nana ta koya mata bacci da wuri sai dai ko in sun zauna kallo ne. Kwanciya ta gyara idanuwanta a rufe tana fadin. "Bacci nake ji fa" Dariya ta bashi. "Ina ne dakina?" Ya tambaya shiru yaji ya sake fadin. "Sofi" "Umm" "Ina zan kwanta" Da alamar bacci da takura a muryarta tace. "A kwance kake fa. Ni ka barni bacci nake ji" Murmushi yai. "Good night to" "Oww ka daina magana" Dariya yayi. Yanajin ta sauke ajiyar zuciya tana kara gyara kwanciya. Hannunta daya ta dora kan Nana da alamun ta saba da hakan. Nana najin hannun safiyya kanta ta saki na fu.ad ta juya kwanciya tana kara matsawa jikin safiyya din. Kallonsu yai yana jin daban. Kaunarsu mai girma ce. Bond din dake tsakanin su bazai taba kamo shi ba. Matsawa yai kusa da Nana ya zagaya da hannunshi ya riko su ita da safiyya yana sauke wani numfashi. Addu.a yai musu su dukansu ya tofa musu kamun ya lumshe idanuwanshi cike da kaunarsu. **** *BAYAN SATI DAYA* Kallonta yake. Tana sanye da material blue mai haske da mayafi dark blue hakama takalman kafarta. A hankali ta tako zuwa inda yake ta hura mishi iska cikin idanuwanshi. Ya dago hannunshi kaman maison kare iskar yana dariya. "Kaman baka taba ganina ba?" Ta fadi tana dariya. "Anya jana zamu fita kuwa? Kinyi kyau bana so kowa ya kalle ki" Daga mishi gira tai da fadin. "Eyen? Nikam ka wuce mu tafi" Bata fuska yai yana kallonta. Da gaske har ranshi yana kishin wani yaganta haka. Janyota yai jikinshi tana ture shi ya hada bakinsu. Sun dauki lokaci a haka kamun ya sake ta yana maida numfashi. "Honey j mana. Ka gogemun jan baki" Murmushi yayi. "Bana son kowa ya kalleki dashi a bakinki. In nace ki goge batamun lokaci zakiyi" "Shine zaka shanye?" "Yafimun sauki ai. Muje" Batai musu ba tasa hannunta cikin nashi suka fice tare. Shiya bude mata mota ta shiga sannan ya zagaya. Suna hanya ne yace mata. "Kayan lefe fa zamu siyo" Shiru tadanyi kamun cikin sanyin murya tace mishi. "Ina zamuje?" "Ban sani ba fa. Shisa na taho dake" "Mu shiga kantin kwari kawai. Akwai inda nake siyayyar kaya sai mu duba idan sun maka" Dan jim yayi sannan yace. "Hakan ma yayi" * Aikam hakan sukayi. Sosai jana ta ture kishin da take ji gefe ta taya jabir suka zabi kyayyaki daga kan atamfofi zuwa lesses zuwa shaddoji dai dai karfin shi. Shagwabe mata yai yagaji zasu dawo su karasa wani lokacin. Dan haka suka juyo suka dawo gida. Wanka ya shiga. Jana kam tayo alwala tai sallar la.asar sannan. Yana fitowa itama wankan ta shiga. Yana kwance kan gado sanda ta fito. Ta kalle shi ya wani tabare fuska. "Nagaji fa" "Tabara kawai kakeji. Ba yawo mukai ba waje daya ne muka tsaya" "Nikam sauran ke zaki karasa please" Girgiza mishi kai tayi "Zan dai rakaka in kana so" Baice komai ba. Baya son kure hakurin da take yi. Hakanma ya gode. Hannuwanshi ya bude. "Zo muyi magana" Ba musu ta karasa ta zauna gefen gadon. Kama hannunta yai ya kwantar da ita. Gidan yayi shiru kasancewar yaran suna gidan hajiya weekend. Juyawa yai suka fuskanci juna. Ya kama hannunta ya sumbata kamun yace. "Please i need you to be honest with me. Ki fadamun ra.ayinki kan wannan. Ni na baki zabi" Kai ta daga mishi dake nuna zatayi yanda yace kamun ya dora da fadin. "Yawwa. Kinga bangarena ba amfani nake dashi ba. Kusan komai anan nakeyi. In bakida matsala ayna zata zauna anan. If kina da matsala da hakan zata zauna a gidana na dakata" Shiru tayi tana nazarin maganarshi kamun tace. "Zan amsaka. Me kake so a ranka kai?" Ganin alamar gardama zai mata yasa ta fadin. "Please ka amsani. Ina son sani ne" Sauke ajiyar zuciya yai. "Zanso ganinku waje daya. Rabakun ba matsala bane a wajena. Bana son takura ki ne kawai" Matsawa tai tana dora kanta a kirjinshi. Taji dadin wannan karamcin dayai mata har ranta. Bakowanne namiji bane yake baka zabi irin wanda jabir ya bata. Sosai take juya maganarshi a ranta. Bata son ta kasa cika rokon dayai mata nata fada mishi gaskiya. "Bakomai bane inta zauna anan din. Roko daya nake maka. Addu.a daya nake maka honey j. Allah ya baka ikon yi mana adalci" Lumshe idanuwa yai ya bude su akanta cike da yanda yake jin sonta. "Amin Ya Allah. Nagode jana. Allah yai miki albarka" Yatsanta ta saka ta rufe bakinshi. "Amin. Ka manta babu godiya a tsakaninmu?" Hannun ya kama yana cizon yatsan a hankali. Kwacewa tai tana yarfe yatsu. "Haba mana. Da zafi fa" Daga mata gira yai kawai dake nuna yasan da zafin ai. Naushin kafadarshi tadanyi a hankali. Kamun muryarta da fuskarta babu alamar wasa tace. "Idan kana da hali muje gobe in raka ka karasa siyayyar nan" Girgiza kai yayi. "Me yasa? A bari zuwa next week nikam nagaji. Ko kije ke kadai" Jan numfashi tayi ta fitar "Saboda ina so kagama komai yabar gidan nan. Ina son jin zuciyata free kadan. Bansan ko kagane me nake nufi ba. Inajin kishinka sosai. Bazan iya dauka inajin maganar auren nan ba kullum. Nasan yana nan. Believe me nasani kuma bana jayayya dashi. Saidai bana so ana mikomun shi gaban idona kullum" Saurin dumtse hannuwanta yayi cikin nashi da fadin. "Dan Allah kiyi hakuri. Ban sani ba wallahi. Zamuje gobe mu karasa in shaa Allah" Yar dariya tai ganin yanda duk ya nuna baiji dadi ba da tunanin kaman yana hurting feelings dinta. Sumba mai taushi ta manna mishi. "Nagode da fahimta" Janta yai jikinshi. "Yanzun nan kika ce ba bu godiya ko. Zo nan to" Dariya take tana ture shi. Kamun ya kashe mata jiki da wata irin soyayyarshi mai wahalar mantawa. **** Sallah ta idar. Wani irin kadaici ke damunta wanda ta kasa fahimtar daga inda yake fitowa. Lumshe idanuwanta tayi tana tuna fuskar nawaf da murmushin shi. Cikin kunnuwanta take jin muryarshi yanda yake fadin. "Ina sonki Nur" Murmushi tayi ta bude idanuwanta kamun lokaci daya gaskiyar ba zai taba dawowa ba ta sake zauna mata. "Allah ya haskaka kabarinka nawaf. Ka tafi kabarni da kewarka mai yawa" Ta fadi a sanyaye dan zuwa yanzun lokutta irin hakan neman hawaye take ta rasa. Saita wuni ita kadai a daki abinta. Inba mumyn nawaf din tazo tace mata ta fito suci abinci ba. Ko dacan ita bamai yawan magana bace ba. Balle kuma yanzun. Jinta take duniyar ita kadai kaman bata da kowa. Bata da wanda zata duba ta kira shi da nata. Sai yanzun taji hawayen na taruwa. Gara da tana da anty. Duk da dacin gaskiyar hakan in ta juya duniya zata ce ga jininta komin bakinshi. Amman yanzun bata san daga ina ta fito ba. Yaya ansar yace anty tsintarta tayi. A ina? Ta yaya? Shine bata tsaya tambaya ba dan tasan shima da wuya idan ya sani. Ya akai ta bata? Su waye asalin iyayenta. Su waye danginta? Suna da rai? Basu da shi duk bata sani ba. Wani abu ne take jin ya kulle a cikinta. Sai yau data dan nutsu tasan tashin hankalin rasa nawaf daban dana sanin bata da asali. Batada wani da zata duba ta kira nata. Wannan tashin hankalin daban yake. Ta tuno yanda yan uwan nawaf suke zagaye dashi cike da kauna kaman su yi karo karo na ranakunsu na duniya su kara mishi. Yanda suke kuka na rashin shi. Yanda a kullum daga kanta har su mamanshi suke wuni yimishi addu.a. Hawayen da suka taru idonta suka zubo da wani dumi. Wazai nuna mata wannan kaunar? Wa zai mata irin addu.ar nan idan ta mutu. Da ace suna da yaro ne ita da nawaf ko ba komai in dangin nawaf suka kalli yaron in bata zasu iya tunata suyi mata addu.a. Kira taji ya shigo wayarta. Ta dauko wayar dake kan gado tana zama. Yaya ansar tagani rubuce a jiki. Tadan murmushin takaici. Kaman wani zai kirata banda shi din. Ta fadi cikin ranta. Daga kiran tayi ta kara a kunnenta. Yai mata sallama data amsa da wani yanayi. "Nuriyya menene? Kukan ne baki daina ba har yanzun ko? Sau nawa zan fada miki addu.arki yake so?" Ai kaman maganganunshi sun bude mata sabon shafi ne. Cikin kuka tace. "Bashi bane yaya farhan. Kawai ina tunani ne" Tana jin yanda yaja numfashi hadi da fadin. "Tunanin me? Saikin sama kanki ciwo ko?" Ta girgiza kai kaman yana ganinta. "Banida kowa a duniya dazan kira nawa yaya farhan. Dana gama takaba bansan menene mako mata ba. Bansan ina zani ba daga nan. Bansan wacece ni ba. Bansan asalina ba ban......" "Shhhhhh please nuriyya. Bana son wannan tunanin da kike. Ki daina fadin haka. Kina da inda zakije. Kina da ni. Kina jina kina dani. Ba zaki taba rasa inda zakiyi ba in ina nan. Ina so zamuyi magana amman da sauran lokaci saikin gama takaba kina jina. Bana son irin tunanin nan" Cikin sanyin murya har lokacin hawayen basu daina zubo mata ba tace. "Na daina. Yaya farhan dan Allah ka tayani duba wacece ni. Ka tayani dubawa ko zan samu dangina. Ko nima zanga wani nawa" "Ki bari nuriyya. Zan tayaki. Zan dubo miko na miki wannan alkawarin please ki daina damuwa har haka kinji" Kai ta daga tasa hannu tana goge fuskarta. "Na daina in shaa Allah" "Uhum. Ko ke fa. Zan fita yanzun. In kina son wani abu ki kirani" "A dawo lafiya" Ya amsata yana kashe wayar. Ajiyeta tayi gefe ta zame ta kwanta tana lumshe idanuwanta cike da tunani kala daban daban. **** Yau kwananshi biyu da dawowa. Duka kwana biyun wajen su safiyya ya yisu. Kusan komai nashi na gidan. Hakan ba karamin dadi yake mishi ba. Sun gama magana da abbah kan zuwa karshen satin daya kara samun nutsuwa zasu fara tafiya dashi dan yaga yanda harkar kasuwanci yake. Tunda ya dawo safiyya ta koma aiki abinta sai tabar mishi Nana. Haka zai wuni biyema shiriritarta. Ko suyita yawo abinsu. Yanzun hakan ma ice cream suka fita suka sha. Fu.ad din ya siyi kaji gasassu suka biya da Nana yagaishe dasu Inna. Sun kuwa ji dadin ziyarar duk da ba dadewa sukai ba. Da gida zasu koma nana tace aje wajen momma. * Suna shiga gidan yaga momma da anty fatima da alama anty fatima fita zatayi. Gaisawa sukai da fu.ad din. "Mun zo ke kuma har zaki tafi" Dan dakuna fuska tayi tace. "Asibiti ma zan wuce fu.ad" Ware idanuwa yai. "Ya Rabb. Waye ba lafiya?" "Hamza ne yayo waya sun kai hussaina tana nakuda yanzun can zan tafi" Jiyai zuciyarshi na dokawa. Momma ya kalla. "Is she okay?" Dariya tadanyi duk da damuwar dake fuskarta. Anty fatima ce tadan daki goshinta. "Fu.ad Allah ya shirya mana kai. Ance maka tana nakuda kana tambaya if she is okay. Kasan she is not. Allah dai ya sauke ta lafiya. Momma bara in tafi karya zama ba yan uwanta tare da ita. Ki kira pha.iza inata kira taqi shiga tunda na fito" "To shikenan. Allah ya sauke ta lafiya" Cewar momma. Anty fatima ta amsa da amin. "Ko inzo muje tare?" Fu.ad ya bukata. Kamun anty fatima ta amsa momma tace. "Ba abinda zakai mata. Ko ita da wuya subarta ta shiga balle kai namiji. Kai mata addu.a kawai daga nan" Shiru yai yana dakuna fuska har anty fatima ta fice. Yana kallon momma da nana suka wuce abinsu. Babban falo ya zauna shiru yana tunani. Anan hassan ya shigo babu ko sallama. "Bro ina momma?" Kallonshi fu.ad yayi. "Lafiyarka kuwa?" Hannu yasa cikin gashin kanshi ya yamutsa kamun yace. "Inata kiran hussaina number dinta a kashe. Na mijinta kuma baya zuwa. I know she is not okay. Inaji a jikina ne kawai" Murmushi fu.ad yai. Jini daban ne. Bond din dake tsakanin hassan da hussaina yasa yana ji a jikinshi in tana cikin matsala. "Calm down. Tana asibiti zata haihu ne" Sauke numfashi hassan yayi. "Wanne asibiti?" Fu.ad ya amsa shi da. "Ban sani ba wallahi. Yanzun anty fatima ta tafi kuma. Buh' momma tace maza basa zuwa. Ba zasu barka ka shiga ka ganta ba" Wayarshi yake dannawa da alama anty fatima zai kira hadi da fadin. "I don't care zan tsaya a waje. Ina son zuwa....." Wucewa yai yana ficewa daga dakin. "Hassannnn" Fu.ad ya kira. Aiko juyowa baiba ya wuce abinshi. Fu.ad yaja numfashi yana girgiza kai. Shi kanshi ya damu. Musamman daya san mata har mutuwa suke wajen haihuwa. Akwai team mate dinshi da matarshi ta mutu wajen haihuwa. Wani tsoro yake ji har ranshi. Ya dauko wayarshi da shirin kiran anty fatima saiga momma ta fito tana fadin. "Hussaina ta haihu. Namiji" Sauke wani numfashi fu.ad yayi da baisan yana rike dashi ba. "Alhamdulillah. Momma tana lafiya dai ko? Ita da babyn?" Kai momma ta daga mishi tana murmushi. Kamun nana data fito ta rike mata hannu da fadin. "Granny muje muga baby din. Ina son babies fa" Dariya momma tayi. "Ke da kaninki. Zakuje ku ganshi ni kam ba yau ba" Shagwabe fuska Nana tayi. Ta kalli fu.ad. "Dady please" Murmushi yai. "Zamuje harda mumynki anjima" Dariya tayi hadi da fadin. "Muka dai banda tsofi ko dady" Ware mata idanuwa yai kamun momma takai hannu taja mata kunnuwa. "Wayyooo" Nana ta fadi tana rugawa wajen fu.ad. Dariya kawai yayi. "Je ki dauko hijab dinki nasan mumynki ta dawo daga aiki. Sai muje muga babyn ko?" Da gudu ta tashi ta nufi bangaren momma ta dauko hijab dinta. Sallama sukai mata suka wuce abinsu. * Indomie da dafaffen kwai suka samu safiyya na zaune tana ci. Zama sukai gefe. Nana tace "Mumy har ice cream muka je muka sha." Harararsu tayi saboda bakinta a cike yake da abinci. Saida ta hadiye ta nuna su da fork din dake hannunta. "Ku biyun nan baku da kirki" Dafe kirji sukayi a tare suna ware mata idanuwansu masu kala daya. "Yes baku da kirki. Kunsan bazan ci abinci ba baku ragemun ba ko?" Langabe fuska Nana tayi. Fu.ad yai saurin cewa. "Nace Nana ta ajiye miki fa. Tace mu cinye kina cina office" Kallonshi Nana tayi harda gasping. "Dady......" Ware mata idanuwa fu.ad yai dake fassara ko ba ayi hakan ba? Kallonta ta mayar kan safiyya da ido take rokonta ta fahimta. Dariya safiyya tayi. "Nasan princess ba zata ci bata tunani ba" Dakuna fuska fu.ad yayi. "Me kike nufi?" Daga mishi kafada tayi alamar duk abinda ya dauka hakan take nufi. "Mumy wajen baby zamuje. Babyn anty hussaina" Sosai fara.a ta bayyana kan fuskar safiyya. "Hussaina ta haihu ne?" Ta tambayi fu.ad ya daga mata kai. "Ke mukazo mu tafi muga baby din a tare suna asibiti ma" "Kai Alhamdulillah. Na koshi ma bara inyi wanka sai mu tafi" Nana ta sakko kasa ta dauki plate din tana komawa kan kujera dashi. "Dawo ki ajiyemun abuna in na dawo zan cinye. Ku da kukaci delicious" Dariya nana tayi tana dibo wa da fork din. "Dadi bude bakinka muci" Ture hannunta yayi. "Um um ke na koshi fa" "Please.... Pretty please" Ta fadi tana mishi wani puppy eyes da ya kasa ce ma aa. Bude baki yai ta saka mishi. Bakinshi a cike yake fadin. "Nana nakoshi wallahi kici" Cokali daya tasa a bakinta ta dakuna fuska tana hadiye shi batare data tauna ba ta ajiye plate din saboda yanda taste dinshi yai mata wani iri a baki. "Kici mana" Cikin sanyin murya tace. "Ba yunwa nakeji ba daman" Kai ya daga mata ba tare da tunanin komai ba. Haka suka zauna suka jira safiyya ta fito suka kama hanya. Suna hanya ne ya kira anty fatima tace musu suna aminu kano. Safiyya tace ma fu.ad. "Munje hannunmu na dukan cinya" Dariya ta bashi. "Tunanin da nake kenan fa. Ko mu biya baby dream mu siya abu" Kai ta daga mishi. Haka kuwa sukai baby dream suka fara biyawa suka siya kayan babies masu yawan gaske. Ba yanda baiba su hada kayan safiyya tace aa. Kowa ya siya da nashi kudin yakai. Itama ai kanwarta ce. Har pha.iza can suka sameta. Fu.ad ko ta kansu baibi ba idanuwanshi kan hussaina da take ta murmushi. Ya karasa ya zauna gefenta. "Hey lil sis. Sannu" Dariya tayi tana kasa da kanta a kunyace. Babyn na hannun anty fatima ta taso tana miko ma fu.ad shi. Kallonshi yake a hannun anty fatima. Ya mishi kyau sosai. Sai bacci yake. Yatsan shi yasa yadan taba fuskar shi. "He is so so cute..." Ya fadi da wani nisantaccen yanayi a muryarshi. "Ka karbe shi mana" Anty fatima ta fadi. Ya girgiza mata kai alamar aa. Ganin shi yake dan kararrami. Mika mishi shi tayi. Ya ware idanuwa yana bude hannayenshi ya karbe shi. Nana ta taso daga wajen pha.iza tana  kokarin hango shi. Zama fu.ad yayi suna kallon yaron tare. Safiyya ta taso ta karaso wajensu. Mika mata shi fu.ad yayi yana tashi daga wajen ta zauna. Rocking dinshi take a hankali. Tana murmushi. Fu.ad ya kalleta ya kalli Nana sai yaji wani abu tun daga yatsan kafarshi ya taso yazo dai dai zuciyarshi yayi tsaye. Da sauri ya fice daga dakin yana doko kofar da dan karfi. Kallon safiyya su anty fatima sukayi sannan suka kalli kofar. Tashi tayi ta bama anty fatima babyn ta fita tabi fu.ad. Yana tsaye bakin kofa hannayenshi cikin aljihun wandonshi. "Me hakan yake nufi?" Safiyya ta bukata. Ya juyo ya zuba mata idanuwanshi. "Baki gani ba kenan? Sofi bazan iya baki wancen farin cikin ba. You loook so so........." Kasa karasawa yayi saboda dacin dayake ji har zuciyarshi. Sauke numfashi tayi. "Ka daina tunanin nan please. Na samu nana koda bamai tsahon kwana bace a duniya naji me akeji. Na wuce gorin haihuwa har abada. Nasan soyayyar ya'ya wannan kawai kyauta ce mai girma" Yanayin yanda ta karasa maganar ya mishi wani iri. Karasawa yai batare da damuwa da cewa a asibiti suke ba yai hugging dinta. "I am so sorry sofi. Ni ya kamata ace ina biyan zunubin kuskuren danayi bawai mu raba tare ba" Sake matse shi tayi. "Ni da kai. Ko ka manta ne. Ka dinga hango me mukayi *Akan so* zamu jure wannan in shaa Allah. Allah yasan damu" Kissing gefen fuskarta yayi. "I love you" "Nasani....." Kawai ta amsa shi da. Hakan take amsawa duk idan ya fadi i love you din nan tun bayan maida auren su. Tana jin sonshi. Sake furta mishi zai dauki lokaci. Da alama ya fuskanci hakan. **** Shagali sosai akayi bayan sunan hussaina. Lokacin fu.ad ya fara gane kan kasuwancin su. Duk da abbah bai fara fita kasa she dashi shigo da kaya ba. Saidai yabarshi nan shagunan su na cikin kantin kwari. Haka rayuwa tafi gaba da tafiyar musu cike da kauna da zumunci mai ban mamaki har bayan *Wata biyu*............!!! *#TeamAS* *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ www.Loobnerh.blogspot.com Wattpad: LubnaSufyan          46 *A rayuwa bakomai da kake so bane kake samu. Ba komai da katsara bane yake zame maka alkhairi* *Bakomai da kake ki bane sharri akanka. Lokutta da dama zaka samu jarabta fiye da zatonka. Karka dauki hakan kaman cewar kai kadaine* *Ka dauka cewa kusancinka da Ubangiji mai girmane shisa ya dora maka ita* *Ummu sudais. Mjay. Amalus. Hasken annuri. Safiyya galadanchi. Billy galadanchi. Samrah. Hashal anani. Idan mace NAGODE tayi kadan sosai. Kawai #AnaTare* *TASKAR LUBIEE MAITAFSIR. Wannan page din nakune* Kanta a kasa tun zamanta wajen. Idan tace batajin zuciyarta kaman zata fado saboda kuna karya take. Inda wani fraction na zuciyarta na tunanin auren jabir zai fasu yau ga tabbatarshi nan a gaban idanuwanta. "Fatan zaku bani hadin kai wajen ganin mun zauna lafiya cikin amana da aminci da juna?" Cewar jabir da idanuwanshi ke yawo akan su duka biyun. Nisawa jana tayi sai lokacin ta dago da kanta ta kuwa sauke idanuwanta cikin na jabir. Tana karantar farin cikin dake cikinsu da yau ba ita bace sanadin bayyanar shi. Dan murmushi tai mishi ya mayar mata nan take kamun ta maida dubanta ga ayna da kanta yake lillibe tanata wasa da hannayenta. Sauke numfashi jana tayi saboda yanda wani kishi na ban mamaki yake dibarta. Ganin ga kugun ayna gana jabir. Muryarta a sanyaye tace. "Bazan maka alkawarin komai ba honey J. Fatana Allah ya bamu hakurin zama da juna ya tabbatar mana da alkhairin dake cikin aurenkun" "Amin" Jabir ya amsa yana tabbatar da ya nuna mata godiyarshi a kan fuskarshi. Murmushin dai ta sake mishi tana dorawa da fadin. "Amarya ga amanar mijina. Allah ya bashi ikon yi mana adalci" Shiru ayna tayi amman har ranta tana jinjina kokari irin na jana. Batajin zata iya wannan kartin halin. Mikewa jana tayi tana fadin. "Ango nikam zan barku saida safe ko? Na baku sati hudu aci amarci lafiya" Ware mata idanuwa jabir yai daya sa ta juya tana nufar hanyar fita daga bangaren ayna din. Muryarshi can kasa yace ma ayna. "Bara in rakata in dawo" Kai kawai ta daga mishi. Sosai ta sake ganin kokarin jana yanda taji wani kishi ya turnuke ta dajin maganar raka jana kawai. Tana fita daga bangaren ta dafa kujerar dake falo tanajin duk jikinta ko ina bari yake yi. Wasu siraran hawaye suka zubo mata. Hannu tasa ta goge su a fili take furta. "Allah kabani juriya. Allah ka bani hakuri. Allah kai ka dora mana kishin nan Allah kabani mai sauki......" Ta baya taji jabir ya rungumeta. Ta lumshe idanuwanta tana sauke numfashi hadi sa shakar kamshin turarukan dake jikinshi. Kamshin na mata bakunta a hancinta saboda bata saba jinshi a jikinshi ba sam. Komai na mata wani iri. Sumba ya manna mata gefen kuncinta cikin kunnenta yace. "Jana sati hudu. Yayi yawa. In ke ba zakiyi kewata ba ni zanyi taki. Saboda me zaki mana haka" Hawayenta take kokarin mayarwa. Tasa hannu tana cire nashi dake kugunta. Kaman ta tunzura shi daya sake matse ta dam. "Please you are making this hard honey j. Ka bar yarinya ita kadai kaje abinka sai da safe" Juyo da ita yai suka fuskanci juna ya dora hannunshi daya kan kafadarta yasa dayan yana dago da habarta idanuwanshi cikin nata. "Ina sonki. Ina sonki sosai ki rike wannan" Kai ta daga mishi. Ta manna mishi sumba yar karama a kumatunshi hadi da hugging dinshi. Har ranta takejin wata irin kewarshi taban mamaki. A hankali ta zame jikinta hadi da fadin. "Saida safe." Bata jira amsarshi ba ta juya ta tafi. Dafe kai yayi ta wani bangare daban yana jin zuciyarshi tayi nauyi kamun ya juya ya koma bangaren ayna. * Tana karasawa dakinta kan gado ta fada ta saki wani irin kuka zuciyarta nayi kaman zata fashe. Lumshe idanuwanta tayi abinda zuciyarta ke hango mata yasata mikewa babu shiri. Bandaki ta shiga ta dauro alwala. Salloli ta fara jerowa na farko in za.a yankata bata san me take ba saboda wani irin duhun kishi da take ji. Wani irin kunci marar misaltuwa. Haka ta ci gaba tanayi hawaye na zubo mata har wata nutsuwa ta soma shigarta. Yanzun kam a nutse take sallolinta da bata san iya lokacin data dauka tanayi ba. Tana idarwa ta zauna kan daddumar tana sauke ajiyar zuciya. A hankali taji an turo kofar. Da mamaki ta dago kai tana kallon kofar. Kai ikram ta zuro tana lekowa. Ido biyu sukai da jana. Hakan yasata dan tsayawa ganin janar na kallonta. "Kawai zan dubaki ne mumy" Ikram ta fadi. Wani abu na daban jana taji a zuciyarta. Da hannu tai mata alama ta shigo. Karasowa tai cikin dakin ta zauna gaf da jana. Hannunta ta kama. Dan dazun ta leqo ta sameta kife kan gado tana kuka. "Are you okay?" Kai jana ta daga mata. Muryarta a dakushe tace. "Bakiyi bacci ba?" Kai ikram ta girgiza mata. "Na leko naga kina kuka. Na kasa bacci ne. Dady yana wajenta ko?" Ganin jana tai shiru yasa ikram tabe baki "Na tsane ta wall....." Bata karasa ba jana ta dille mata labba dayasa ta saurin kai hannu tana kallon maman nata cike da mamaki. "Kar in sake jin wannan maganganun a bakinki. Kina jina? Me tai miki? Bakisan Pa dinki na sonta ba? Zakiyi respecting dinta ki koyi sonta kema kinajina? Babu inda zataje she is here to stay you deal with it" Turo baki ikram tayi dan tana taya mamanta kishi har ranta. Tana kuma mamakin ke yasa mumynta zata ce ta so matar nan datai turo musu kai cikin rayuwa. Kallonta jana takeyi. Ga kanta na wani irin ciwo ga ikram zata kara mata wani ciwon kan kuma. Bata son yarinyar ta taso da tsanar kishiya tun tana yar mitsitsiyarta. Beside ita ba kalar matar da take son turama yaranta akidar tayata kishi bace ba. Tarbiyarsu da kasancewarsu masu nagarta yafiye mata komai muhimmanci. Kamo ikram din tayi daba musubta kwanta kan cinyarta tana hade jikinta. Cikin taushin murya jana tace. "She is not our enemy ikram. Ba a tsanar mutum babu dalili. Ba abu bane me kyau. Ki bata chance kiga halinta. Zaki iya mun wannan kokarin? Ki mata kirki?" Kai ikram ta daga ma jana. "Promise?" Kai ta sake dagawa. Jana tadanyi murmushi. "Tashi kije ki kwanta. Dare yayi sosai" Mikewa ikram tayi ta kalli jana tana shagwabe fuska. "Mumy zan kwana anan please" Nisawa jana tayi. Ta kalli gadon. Ba dakinta bane ita kadai kusan gaba daya rabi da kwatar rayuwarsu da jabir anan sukayita. "Muje in kwana a dakinki" Ware idanuwanta ikram tayi sannan tai murmushi. Mikewa ikram tayi ta kamo hannun jana suka mike tare. Dakin ikram din suka nufa. Ita ta gyara ma jana wajen ta kwanta sannan tahau gadon ta kwanta taja kashe musu kwan dakin ta na sake matsawa jikin janar tana sauke numfashi. Addu.a jana tayi musu. Tana jin ikram din tana sake numfashi alamar bacci ya dauketa. Hannun ikram din ta kama cikin nata ta dumtse wata nutsuwa na saukar mata. Addu.o.i ta shiga jerowa duk kalar da suka zo kanta. Kamun bacci ya dauketa..........! **** "Wai menene dadin wanna shirin da kika like wa?" Fu.ad ya tambayi safiyya da gaba daya ta mayar da hankalinta kan My Tv series suna maimaita shirin Bade ache lagte hai. Batare data juyo ba tace mishi. "Ba zaka gane ba" Remote din dake kusa dashi ya dauka ya danna yana canza channel din. Juyowa tayi. "Ohhhh please ka mayarmun" Turo mata lips dinshi yai. "Wanna shirin yafini muhimmanci" Kaman zata fashe da kuka tace mishi. "Bai fika ba. Now please ka mayarmun ana wuce wa fa" Remote din ya mika mata yana dakuna fuska. Mikewa yai daga kwanciyar da yake hadi da fadin. "Barin duba Nana" Kai ta daga mishi. Tasan bacci take. Da wahala magungunan data sha su saketa da yanzun. Jikinta ya soma zafi kwana biyun nan. Ya dafa hannayenshi kenan zai mike Nana ta fito daga dakin tana dakuna fuska. Kallonta yake ta kara ramewa fiye da sanda yazo. Wani abu ya soki zuciyarshi. Murmushi yai mata data kasa mayar mishi saboda yanda take ta kokawa da numfashinta. Dakyar ta iya cewa. "Mumy....." Da sauri safiyya ta juya ta kalleta. Wani irin jiri ke dibar Nana din ta soma ganinsu bibbiyu saboda yanda numfashinta yaki kaiwa. Kanta yayi wani irin zafi kamun taji gabaki daya duniyar tana juya mata. Fu.ad ya soma mikewa da gudu ya karasa wajenta yasa hannu yana tallabeta saboda karta fadi. Girgiza ta yake amman ko motsi batayi. A rikice yake cema safiyya. "Sofi please kiyi wani abu. Bata numfashi....... Wallahi bata numfashi" Wani yawu safiyya ta hadiya. Ba wanna bane na farko a wajenta shisa take da yar nutsuwa fiye data fu.ad din. Daki ta shiga ta dauko hijab dinta da mukullin mota. "Dauko ta mu tafi asibiti" Girgiza mata kai fu.ad ya shiga yi yana sake rike nana gam a jikinshi. "Taki tashi sofi" Dafa kafadarshi tayi cikin taushin murya tace. "Zata tashi. Sai munje asibiti. Please fu.ad ka taso" Mikewa yai yana sabar nana a kafadar shi suka fice tare. Bayan motar ya bude ya shiga yana kwantar da ita a jikinshi. Wayarshi ya dauko bayan safiyya ta tashi motar suna ficewa daga gidan. Momma ya kira ta daga da yi mishi sallama. Ko amsawa baiba yace mata. "Momma nana..... Muna hanyar asibiti yanzun" Bai jira amsarta ba ya kashe wayar. Yana sake jijjiga nana ko zata bude idanuwanta. Zuciyarshi ciwo take kaman ya cire ya ajiye. * Ta window din yake tsaye yana kallon yanda wajen likitoci hudu suke kan Nana an saka mata oxygen mask ya juyo ya kalli safiyya da take zaune ta hade kanta da gwiwa. Kusa da ita ya koma ya zauna ya dafa kafadarta. Dagowa tayi ta kalle shi. Muryarta da yanayi na damuwa tace. "Zan kira su inna ne. Ina so su ganta before you know........ May be" Hannunshi ya zagaya yana kwanto da ita jikinshi. Kansu ya hada yana fadin. "No sofi......ki daina cewa haka. This is not it. Wata nawa akace? Ba shidda ba yanzun fa ake wata na hudu. Muna da sauran time" Ita yake fadawa amman dakaji yanayin yanda yake maganar kasan cewa yana kokarin convincing din kanshi ne fiye da safiyya din. Batace mishi komai ba sai sake makalewa datai a jikinshi. Tanajin kukan da zuciyarta takeyi amman hawaye ko daya sunki zubo mata. Suna nan zaune momma ta zo. Tashi fu.ad yayi ya karasa wajenta yana kallonta so yake tace mishi komai zaiyi dai dai. Ta fada mishi nana zata samu sauki Ta fada mishi komai baizo karshe ba. Kai momma ta girgiza mishi. Hakan yasa shi dafe goshi. Raba momma yayi yana ficewa daga wajen gabaki daya. Kusa da safiyya ta karasa ta zauna. A hankali safiyya tace mata "Ina wuni" Dafa ta momma tayi saboda bata san me zata ce mata ba. Nana jikarta ce idan har tana jin wanna fargabar bata san su kuma me suke ji ba. "Fu.ad......" Safiyya ta fadi tanajin hawayen da suka ki fitowa tun dazun suna zubowa. "Kinsan halin shi safiyya. Yana son zama shi kadai a yanzun. Inba haneef ko lukman ba bazai saurari kowa ba" Wayarta safiyya ta cire daga key tai ma haneef text. "Muna asibiti da Nana." Ko minti biyu ba aiba tsakani ya dawo mata da amsa. "On my way" * Zaune yake bakin kofar asibitin saboda yanda yaji iskar ciki ta mishi kadan. Baya son tunanin komai banda na lafiyar nana. Ko kadan bai kula da motar haneef ba. Saboda hankalinshi na wata duniya ta daban. Tun shigowarshi asibitin ya hango fu.ad din zaune. Har yai parking ya fito. Hannayenshi ya hade waje daya hadi da murzasu lokaci daya kuma yaja iska yana fitarwa ta bakinshi. Sannan ya taka ya karasa wajen fu.ad din ya dafa shi. Da sauri ya dago. Ganin haneef din ya bashi mamaki nadan lokaci. "Haneef" Ya fadi cikin alamar gaisuwa. Zama gefenshi haneef yai hadi da fadin. "Me kakeyi a waje?" "Iskar cikin ce nakejin tamun kadan na fito nan" Ya amsa shi. Dafa shi haneef yayi. "Ba yaro bane kai fu.ad. Ya kamata ka  koyi tarbar matsalolinka. Gudunsu bazai canza komai ba" Tauna maganganun haneef din yake yanajin gaskiyarsu na zaunawa tare dashi. "I...i.... Ni bansan me ya kamata inyi bane ba" Wani irin helplessness yake ji da tunda yake a rayuwarshi bai taba jin kalar shi ba. Mai yakai kana sane cewar da duk mintinan dake wucewa rayuwar yarka yake tafiya dashi tashin hankali? Jinjina mishi kai haneef yai. Ko bai fahimci kalar abinda fu.ad yake ji ba yana kamantawa. Kuma yana tausaya mishi. "Ka tashi muje. Kana bukatar spending duk wani lokaci tare da ita. Zata so haka" Mikewa fu.ad yayi yanajin zuciyarshi na wani irin dokawa. Hannunshi yasa cikin na haneef kaman karamin yaro. Kyale shi haneef din yayi. Yasan yana bukatar kwarin gwiwane in rike hannunshi yana samar mishi da hakan saboda me zai hana shi? Lokacin da suka karasa ciki basu ga su momma a waiting area din ba dan haka suka shiga cikin dakin. Suna zaune gefen Nana kaman yanda suka zuba mata idanuwa zai sa ta samu sauki. Haneef gaisawa sukai da momma da safiyya yana musu yamai jiki kamun ya samu waje ya zauna. Zagayawa fu.ad yayi ya koma saitin kan Nana. Hannu yasa ya shafi goshinta da alama bata ma san duniyar da take ba. Dan rankwafawa yai ya sumbaci goshinta yana sauke murya. "Allah ya baki lafiya princess. I love you so much. Kinsani ai ko?" Dafe fuska safiyya tayi cikin hannayenta. Momma da haneef suka hada idanuwa suna rasa kome ya kamata suyi. * Zuwa yamma gabaki daya dakin ya cika. Tun daga kan anty fatima duk sunzo. Har zainab dan da lukman yace ta zauna saboda cikin satin ake sa mata ran haihuwa kuka ta kamayi. Dole ya taho da ita. Doc ne ya shigo sake duba Nana yagansu cikin dakin. Ware idanuwa yayi hadi da fadin. "Gaskiya ku fita. Ana so ta samu hutu wadatacce ne. Ba.a son hayaniya ko kadan" Kallonshi lukman yayi yace. "Kamun ka turo dakin nan kasa ran zaka ganmu fiye da mu goma a ciki?" Girgiza mishi kai doc din yayi. "Kaji magana ko daya na fita daga dakin?" Ya sake girgiza mishi kai. Rai a bace lukman yace. "Do your damn job ka barmu muji da abinda yake damun mu." Fu.ad dake gefenshi ya rike hannunshi. Idan zai kirga wannan ne karo na biyar daya taba ganin ran lukman a bace "Lukman please. Kabarshi yai aikinshi. In yana ganin zamu takurata sai mu fita" Cikin idanuwa lukman ya kalle shi yace. "Ku fita ban hanaku ba. Ina nan nikam" Kallon doc din fu.ad yayi. Shi yanzun kam bayajin wani karfi ko na sisi balle har energy din rikici. Hakan doc din ya kula dashi. Yanajin idanuwansu gabaki daya akanshi. Dan haka yabarsu tunda da gaskiyar lukman ba surutu suke ba. Wanda suke tsaye suna tsaye. Wanda suke zaune suna zaune abinsu. Baiga matsala tare da kasancewarsu a dakin ba. Kalar kaunarsu ga nana har mamaki ta bashi. Dubata yayi yaga komai na tafiya yanda suke tsammani sannan yace. "Ko motsi tayi kumin magana" Kai kawai fu.ad ya daga mishi. Safiyya ce mai karfin halin yi mishi godiya kamun ya fice daga dakin. * A asibitin sukai sallar magrib da isha.i ganin babu wani canzi yasa momma ta tusa kowa tace ya tafi gida. Tunda sunga Nana din. Addu.a tafi bukata daga wajensu ba wannan zaman ba. Kan dole suka tattafi. Daga safiyya sai fu.ad aka bari a asibitin. Kallon shi safiyya tai yana zaune ya tusa Nana gaba yana jira yaga ko motsi tayi. Tace mishi. "Kaci wani abu" Girgiza mata kai yayi saboda bayajin zai iya saka ma cikin shi wani abu. Da sauri ya dago kai yace ma safiyya. "Bamu fadama Ansar ba" Dafe kai tayi itama tanajin rashin kyautawar hakan. Text tayi mishi ta fada mishi tana bashi hakuri. Shi kanshi fu.ad din yasan Ansar nada hakkin sani koba komai yai dawainiya mai girma da Nana kuma bazai manta ba. Bayan haka yasan ita kanta Nana ba zata yafe musu ba in taji basu fada mishi ba. Aikam kasa hakura yayi. A daren saida yazo yaga nana duk da bai jima ba ya koma. Ansar na tafiya safiyya ta sauka kasa dan kafafuwanta sun gaji. "Ka sauko kaci abinci" Kai ya girgiza mata. Ko magana baya sonyi. Gajiya tayi ta hakura ta kyale shi. Saida ta kira su inna kaman yanda ta saba tai musu saida safe take fada musu suna asibiti ma sannan ta kwanta. Damuwar dake zuciyarta bai hana barawon bacci sace ta ba cike da mafarkai barkatai. Hannunshi fu.ad yasa cikin Na nana ya dumtse yanda koya dayan kuma yana kan cikinta ya dora kanshi jikin gadon yanda data motsa zaiji. Anan bacci ya dauke shi......! **** A dakin ikram tai sallar asuba sannan ta tashi ikram din itama ta shiga toilet tayo alwala. Tun jiya sun san duk da monday ce ba zasu je school ba saboda gajiyar hidimar biki. Fita jana tayi daga dakin ta tashi sauran yaran suyi sallah suma in yaso sai su koma baccin su. Ta tashi atika ma. Sannan tai dakinta. Tana shiga dakinta wanka tayi ta fito ta zira ma jikinta wata doguwar riga ta atamfa dinkin simple ta daura dankwalinta sannan ta nufi kitchen. Dankali ta fara ferewa tana so ta taya atika dan kar aikin yai mata yawa. Ta dora kenan ta dafa shi atika ta shigo kitchen din. Tare suka kama aikin. Zuwa bakwai da kusan rabi sun gama komai. Sauri sauri jana ta kara watsa ruwa ta fito tana shirin tafiya aiki. Dan ta makara sosai yau. Tana karasawa ta lalubo wayarta taima jabir text ta fada mishi ta wuce office. Ga mamakinta text dinshi har hudu tagani. Biyu jiya da darene yake mata godiya daya kuma saida safe. Biyun da safen na ne yake tambaya yata kwana ya yara. Dayan yanzunne ba jimawa ya turo mata shi. "Please reply" Murmushi tayi. Har ranta taji dadin kalar kulawar daya nuna mata. "Afuwan honey J. Yanzun na dauki wayar. Duka mun kwana lafiya. Fatan kaima. Zan wuce office ne yanzun saina dawo. Love you" Ta tura. Har zata saka wayar cikin jaka wata zuciya daban da mai kishin data hanata tambayarshi ya kwana ayna take ce mata bata kyauta ba. Ko badan ayna din ba jabir zaiji dadi.  Kamun ta kasa tai saurin tura mishi wani sakon. "Ya amarya ta kwana?" Ta dauko glass dinta kenan tana fesa turaruka masu saukin kamshi dan ita kadai kejin abinta inba gab da ita mutum yazo ba sosai. Ta kama handle din kofar zata bude taji an turo. Hakan yasa ta danyin baya. Jabir ne. Idanuwanta take yawatawa kanshi. Sanye yake da jallabiya. Ya mata kyau murmushin dayai mata yasa taji wani irin kishi ya rufeta. Musamman da ta tuna bata san adadin kalarshi da ayna ta samu ba a daren jiya Saurin rintse idanuwanta tayi tana korar shaidan dazai hada mata fitina da sanyin safiyar nan. "Ina kwana" Ta fadin kanta a kasa. Hannunshi taji yasa jikin habarta ya dago da ita. "Jana kinsan bana so in anamun magana aki kallon fuskata ko?" Murmushin karfin hali tayi "Afuwan. Ya kuka tashi?" "Alhamdulillah. Harkin gama shiryawa?" Kai ta daga mishi tana fadin. "Eh kam. Ga breakfast dinku can a kitchen sai kaima atika magana ta shirya muku komai in kun tashi. Zata iya hada muku lunch. Yara suna bacci yau bq zasuje school ba" Kai ya daga mata. "Mungode sosai jana. Sai munyi waya ko?" Kamun ta amsa shi ya manna mata peck a labbanta ya juya. Sauke numfashi tayi ta fice hadi dayin addu.a. * Tana shiga asibitin tai sign in ake fada mata Nana tana nan. Saida taji zuciyarta ta doka. Yau din nan tai niyyar kiran safiyya taji ya jikinta. Saidai itama abubuwa sun mata yawa akai. Yanayin yarinyar kawai yana sa taji kaman bata da matsala a tata rayuwar ko kadan. Jakarta kawai ta ajiye office ta dauki abubuwan da take bukata ta dauki file din Nana da aka ajiye mata kan table dinta ta nufi dakin........! **** Kaman yanda rayuwa ke tafiyarma su fu.ad haka ma take a wajen nuriyya. Washe garin data fita takaba kaman yanda farhan yai alkawari yaje sukai magana. Tayi kuka sosai dayai mata maganar aure sai take ganin kaman hakan cin amana ne wajen nawaf. Kaman yayi kusa. Saidai shi kanshi farhan yai mamakin yanda family din nawaf sukai tsaye akan abin. Yanda tare da taimakonsu suke nuna ma nuriyya auren da zatayi ba komai bane a wajensu. Ba zasu dauka taci amanar nawaf ba ko kuma hakan yayi kusa ganin watanni ko biyar ba a cika ba da rasuwarshi. Sun fahimci tana bukatar kulawa kuma su bazasu iya bata ita ba. Gabaki daya abinda nawaf ya mallaka tun kwana bakwai da rasuwar shi da akace za.a raba yan uwanshi suka yafe ma nuriyya. Dan haka su suka shige gaba aka daura auren farhan da nuriyya.  Ba ta da wasu da zata kira yan uwanta balle ace za.ayi wani shagali. Bangaren farhan kuwa yasan yana da yan uwa bawai bashida su ba. Sai dai zumuncin dake tsakanin su ya dade dayin nisa. Baima bi takansu ba tunda family din nawaf sun musu wakilci su duka biyun. Shi kanshi yaji wani iri dayaga daga shi sai ita a mota lokacin daya zo daukarta. Har suka kai gidanshi tana wani irin kuka da yake ji har zuciyarshi. Suna shiga gidan ya kama hannuwanta yana kokarin riketa jikinshi. Kuka take sosai tana ture shi. "Yaya farhan bazan iya ba wallahi. Dan Allah kayi hakuri" Ganin yanda ta rikice yasa shi rikota gam. Karfi yasa ya riketa jikinshi gam yana kokarin nutsar da ita. "Ba abinda zan miki nuriyya. Wallahi ba abinda zan miki. Ki nutsu zan zame miki duk abinda kike bukata a yanzun har lokacin da zaki so fiye da hakan. I promise kome kike so in zama" Ya sauke ajiyar zuciya jin tayi luf da ita a jikinshi tana kuka a hankali. Da gaske yake mata zai zama duk abinda take so. Son da yake mata mai girma ne. Yasan tana bukatar lokaci mai yawa. Ya aureta ne da wuri haka saboda yana son tasan koda bata da kowa a duniya tana dashi. Yana son kula da ita irin kulawar da bata taba samu ba a rayuwarta. Tana jikinshi ya jata har zuwa kan kujera ya sa hannunshi ya goge mata fuskarta. "Kiyi shiru kar kanki yai ciwo please nuriyya" Kai ta daga mishi tana kokarin hadiye kukanta. Ya mike ya shiga kitchen dinshi ya dauko mata fresh milk ya ajiye sannan ya fice ya dauko naman daya siya tun dazun. Dakyar ya samu nuriyya tadan ci. Ya tambayeta ko tayi sallah. Ta daga mishi kai. Mikewa yai ya kama hannunta. Dakinshi yakaita ya tabbata ta kwanta bata bukatar komai sannan yai mata saida safe ya fice. Sake shigewa cikin bargo nuriyya tayi tana ajiyar zuciya. A karo na farkona rayuwarta ta samu wata nutsuwa da bata taba sanin akwaita ba.......! **** Kwanansu hudu a asibiti. Cikin kwanakin nan babu wanda baizo yaga nana ba. Daga kan abokan arziqi har yan uwa. Cikin kwana hudun nan tun tana bude idanuwanta tai magana har takai ga sai dai in taji muryarsu ta bude idanuwanta dakyar ta mayar dasu ta lumshe. Daga fu.ad har safiyya ba kuka suke ba amman kallo daya zakai musu kaga ramar da sukayi saboda tashin hankali. Yauma kaman kullum wajen nana suka kwana sai dai me. Tun jiya rabon data bude idanuwanta. Fu.ad yai maganar duniya amman shiru kake ji. Hannunta ya murza yaga bata motsa shi ba. Mikewa yai ya taba goshinta. Ya sake kama hannunta ya murza. "Dammit nana wake up please....." Tasowa safiyya tayi su duka suke kokari amman nana taqi ko motsi. Da gudu safiyya ta fita dan ta kira jana......! #*TeamAS* *#AnaTare* *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ www.Loobnerh.blogspot.com Wattpad: LubnaSufyan             47 *Tabbas babu wani abu da yake da tabbas a cikin duniya. Babu komai cikinta sai tarin dauda da rashin kwanciyar hankali* *Ba zaka gane hakan ba sai lokacin da kaddararka ta jarabta ya juyo kanka* *Gabaki dayan littafin nan yana tabani fiye da yanda yake taba ku. Saboda kaso 60% cikin 100% ba fiction bane gaskiya ce* *Yana tabani ta yanda babu wanda zai fahimta. Ta wani fannin yana fifitamun ciwuka da raunikan dana samu a tsahon rayuwata* *Ciwukan da basu gama ciwo ba. Ciwukan da nasan in har ina duniya ban gama samun kalarsu ko fiye dasu ba* *Godiya ta tabbata ga Allah a kowanne hali* *zainab Askira. Rukayya Abdulkadir. Mardiyya isyaku and Nasiba. Amina mashasha. Yasmeen Tafeesu. Ummie khaleel. Fatima Aliyu(childhood friend). Sha.afatu saleh. Da wanda ma ban lissafo ba kusan AnaTare. Like AnaTare sosai sosai* Doc jana na shigowa dakin na.u.ororin dake manne jikin Nana ta shiga dubawa. Kallonta fu.ad yake cike da tashin hankali. Da gudu yaga ta fita basu fi mintina biyar ba suka dawo su hudu. Kama hannun safiyya yayi tana tirjewa tana ce mishi. "Ka sakeni. Kabarni babu inda zan tafi....." Gam ya riketa jikinshi tana wani irin kuka. Tashi zuciyar ta bushe. Wani iri yake jinta yanda babu kalaman da zai bayyana ta dashi. Bakin kofar dakin da Nana take ciki suka tsaya har lokacin safiyya dake kuka tana jikinshi. Habarshi ya dora saman kanta ya lumshe idanuwanshi yana fadin. "Allah kabamu juriya. Allah duk yanda kai damu dai dai ne...." Baisan iya lokacin da suka dauka a haka ba sai da yaji bude kofar. Da sauri safiyya ta zame daga jikinshi tana kallon doc jana. Ta gabansu sauran likitocin suka fito suka wuce. Safiyya bata jira komai ba ta wuce cikin dakin. Shikam fu.ad tsayawa yayi ya zuba mata idanuwa. Nata idanuwan taji sun cika taf da hawaye. Daga kan Nana tai alkawarin ba zata sake karbar wani cancer patient ba. Zuciyarta ba zata iya dauka ba. Muryarshi a dakushe yace. "How many days?" Saida takai mintina biyu tana kokarin controlling emotions dinta sannan tace mishi. "A few hours max......" Tana rufe bakinta ta juya da gudu tana barin wajen saboda bata son fu.ad yaga hawayen dake zubar mata. Bata son yaga yanda take ji ita da bata hada jini da nana ba kenan. Bangon wajen yasa hannu ya laluba jikinshi na bari. Kalmomi hudu ta fada amman shi a wajenshi gabaki daya farin cikin su ta tarwatsa. Cikin kunnuwanshi yake jin amsa kuwwar da kalmominta suke mishi. Yasan yana cikin shock saidai baisan yanda zai ya fita ba. Wata dariya ce yaji ta kubce masa da baisan ta inda ta fito ba. Wayarshi ya dauko ya kira haneef ya daga da fadin. "Fu.ad ya Nana din?" Cikin muryar da bai gane ko tashi bace yace. "Kuzo ku mata bankwana haneef. Awanni kadan take dashi" Yanajin yanda haneef yaja numfashi ta cikin wayar ya sauketa daga kunnenshi bai damu daya kashe ba ya sata a aljihunshi. Handle din dakin ya kama zuciyarshi na wani irin yawo da zai iya rantsawa yanajin bugun da take har cikin kunnuwanshi. Turawa yai a hankali. Safiyya na rike da hannun Nana tana tsugunne kasan gadon tana wani irin kuka da yaji ya tsaya mishi a wuya. Gefen gadon ya zauna ta dayan bangaren yana kama hannun nana daya ya rike shima. Jiyai kaman tayi motsi hakan yasa shi fadin. "Princess......" "Daadyyy......" Ta fada. Da sauri safiyya ta dago ta na zama kan kujera. Hannunta daya tasa tana goge hawayenta. "Nana kina jina" Idanuwanta a rufe take. "Mumy ya aljanna take?" Ta tambaya muryarta na rawa tana wata irin kokawa da numfashinta. Kuka ya hana safiyya magana. Fu.ad ya hadiye wani miyau yace. "Princess babu wanda yasan exact yanda take. Waje ne mai cike da ni.imomi fiye da zaton dan adam. Wajene da yake da farin ciki. Kwanciyar hankali da natsuwa ta har abada" Murmushin da Nana tayi har cikin ranshi yaji shi. "Babu rashin lafiya?" Kai fu.ad ya girgiza duk da bata ganin shi. "Babu ko kishin ruwa Nana. Babu komai banda farin ciki.........!" Yana kallon yanda kirjinta ke dagawa dakyar saboda yanda take kokawa da shigar iska abin na mishi wani iri. "Duk ciwon nan zai tafi?" Wannan karin kasa amsata yayi. Saboda wani abu ya rike kalamanshi. Bakinshi ya bushe tas. Muryar safiyya na rawa wasu sabbin hawayen na zubo mata tace. "Zai tafi Nana. Babu kunci ko kadan a cikinta. Wajene da mai laifi da marassa laifi ke da burin shiga" Murmushin Nana ya sake fadada. Hannayensu dake rike a cikin nata da dan sauran karfin da take ji ta dumtse. "This is not a good bye. Wannan na nufin sai kun taho. Yana nufin ina jiranku a aljanna......" Lumshe idanuwanshi fu.ad yayi. Safiyya ta kife kanta jikin gadon in tana zaton taji mutuwar usman abinda take jina yanxun ya linka wancen fiye da zatonta. Wani irin daci ne har cikin naman jikinta. Wani ciwo ne marar misaltuwa. "Ya Allah......" Nana ta fadi kamun fu.ad yaji ta saki hannunshi. Bude idanuwanshi yayi lokaci daya da dagowar safiyya. Jikinta na bari da wata irin fargaba marar misaltuwa take kallon nana. Kaman tana bacci da murmushi a fuskarta. "Nana...." Ta kira a hankali muryarta dauke da fargabar da take ji. Idanuwanta cike taf da hawaye ta dago ta kalli fu.ad da tashi zuciyar ke son fitowa daga kirjinshi. Sam basu ji turo kofar haneef da lukman ba ballantana sallamarsu. Idanuwansu na kafe da juna. Kamun safiyya ta sake maida hankalinta kan Nana. Wani irin abu fu.ad ya hadiye daya tsaya mishi a wuyanshi. Haneef na kallon nana yakai hannunshi ya dafe kanshi. Lukman ya kalla ya girgiza mishi kai yana son gaya mishi ba abinda suke zato bane ba. Bashi bane sam. Karasawa lukman yai ya dafa fu.ad. Ya juyo ya kalle shi ya sake maida hankalinshi kan Nana daga shi har safiyya tsoron tabata suke ji. "Nanaaaa" Safiyya ta sake kira muryarta na karyewa. Lukman yakai hannu ya tabata kafarta. Dumtse kafar yai cikin hannunshi. Yaji tayi sanyi. Da sauri ya saki kafar nana yana goge hannunshi sosai jikin kayan jikinshi yana son cire yanayin dayake ji manne jiki har lokacin. "Barin kira doc" Haneef ya fadi a tsorace yana fita daga dakin. Ko mintina biyar baiyi ba ya dawo da wani doc. Aune aunen shi ya shiga yi. Kamun yadan runtsa idanuwa ya dafa kafadar lukman dake tsaye sannan ya girgiza ma haneef kai. Yana ficewa daga dakin. Mikewa tsaye safiyya take tana ja da baya tana girgiza kanta. "Dan Allah ku cemun lafiyarta kalau. Dan Allah kucemun wani abu bai sami Nana ta ba.......! Kar kucemun tabarni. Kar kucemun wannan shine bankwana.......! Wallahi ban shirya ba. Ban shirya ba....." Hannu fu.ad yakai a tsorace ya dora kan kirjin Nana dai dai zuciyarta. Wani irin shiru yaji. Ya dago idanuwanshi ya kalli lukman. Hawaye yaga sun zubo daga idanuwan lukman din. Cike da wani yanayi yace ma lukman. "Ta rasu ko?" Juya baya lukman yayi. Haneef ne ya karaso yana dafa fu.ad din. Ture hannunshi yayi still dayan nakan kirjin Nana. "Em okay. Kawai ku fadamun. Ina so wani ya tabbatar mun ne. Ta rasu?" Dakyar haneef yace. "Ta rasu fu.ad" Hannunshi ya dauke daga kirjinta ya mike daga kujerar dayake zaune ya koma gefen gadon ya zauna. Hannunta dayake karara ya kamo ya sumbata. Sannan ya tsugunna ya sumbaci goshinta yanajin wani yanayi da bai taba ji a jikinta ba. Batare daya dago ba yace. "Allah yasa mutuwa hutu ce a gareki Nana. Allah yai miki Rahma. Allah ya sadaki da fiye da abinda kike zaton Aljannarki ta kunsa" Yana karasawa ya mike tsaya. Wajen safiyya dake girgiza mishi kai ya nufa. Hannuwanta ya kama yana kallonta. "Safiyya zo ki mata addu.a" Wasu hawaye masu ciwo da dumi suka zubo mata. "Ku duba sosai. Dan Allah ka duba. Bata rasu ba" Kamata yai ya rungume tsam a jikinshi yana rocking dinsu. Yasan shirun nan da yakeji cikin kanshi da zuciyarshi ba na lafiya bane. Yasan dole ne koma ina ya adana ciwon daya kamata ace yana ji zai dawo mishi. Zai dawo mishi batare da shiri ba. Wani yawu ya hadiya. A hankali yake ce ma safiyya. "Dukkan mai rai mamaci ne sofi. Bakiji me Nana tace ba? Wannan ba bankwana bane ba. Kizo ki mata addu.a" Kai take daga mishi tana jin zuciyarta na wani irin tsaitsayawa da ciwon da take ji. "Inalillahi wa ina ilaihi raji.un....." Fu.ad ya fadi cikin kunnenta. Ai kaman ya tuna mata abinda ya kamata tayi ta shiga jero wa jikinta na wani irin bari. Wani kwarin gwiwa taji ta samu wanda batama san daga inda ya fito ba. Tare da fu.ad suka taka wajen da Nana take kwance. Kallonshi tai ya daga mata kai alamar zata iya. "Ki mata addu.a tana jinki sofi. Taji yanda kike kaunarta" Muryarta na rawa tace. "Allah ya sadaki da Rahmarshi Nana. Allah ya baki hutun da kike ta nema. Zamuyi kewarki. Allah ya haskaka kabarinki kamun ki karasa mishi....." Yanda ta karasa maganar yasa fu.ad kamota yana janyeta daga wajen nana. "Bangama ba fu.ad banga mata bankwana ba" Kanta yakama ya kwantar a kirjinshi yana janta a hankali yana fadin. "Zaki kara wani in munje gida" Da kanshi ya fita da ita ya bude mota ya sakata a baya ya kullo sannan da gudu ya dawo. Lukman na jingine da bango idanuwanshi kafe kan Nana da take kwance kan gado. Fuskarshi ta wani irin kumbura. Fu.ad ya sauke numfashi. "Lukman taho ku tafi gida da safiyya" Girgiza mishi kai lukman yayi yana kasa magana. Kama hannunshi fu.ad yayi kaman karamin yaro har lokacin idanuwanshi na kafe kan Nana. Yana sake ganin yanda duniya ba komai bace ba. Yar yarinya kenan da bata da wasu tarin zunubai. Ballantana kai babba da gulmar wasu ma kadai ta isheka tashin hankali. Bude mishi gaban motar fu.ad yayi ya shiga ya mika mishi mukullin motar. "Can you drive?" Ya tambaya. Kai lukman ya daga mishi. Ya sauke numfashi yana kallon safiyya data hade kanta da gwiwa a bayan motar. "ka kaita wajen momma gamu nan zuwa" Sake komawa fu.ad yayi yana mamakin kanshi. Ya kamata ace yanajin wani abu amman kawai dai ya rasa ko me yake ji. Inda yabar haneef nan ya same shi. Baibi takanshi ba ya shiga tattara kayayyakinsu yana zubawa cikin jakar da suka fito. Saida ga gama tas sannan ya mikama haneef daya karba yana kallon fu.ad din da mamaki. "Fu.ad?" Ya kira cike da shakku yana son tabbatar da ko yana lafiya. Saida ya dauki takalman nana dake ajiye a kasa ya hada su waje daya sannan ya amsa da. "Na.am.......sa takalman Nana a ciki kar abarsu" Jinjina kai haneef yayi ya karbi takalman yasan akwai matsala tare da fu.ad din. Yana kuma tsoron sanda mutuwar zata gama zauna mishi. Karasawa kan gadon da Nana take fu.ad yayi ya dagota a hankali kaman tana bacci ya sabeta a kafadarshi. Ya kalli haneef hadi da fadin. "Muje ko" Ba musu haneef ya kama hanya jikinshi a sanyaye. Suna fita daga dakin suna cin karo da doc jana. Kallo daya tai musu tayi baya. Fu.ad yace mata. "Doc......!" Dawowa baya tayi. Kallonta yai. "Ki mata bankwana. Kina da muhimmanci a wajenta" Sai da ta lumshe idanuwa sannan tace. "Allah ya jikanta ya baku hakurin rashin ta" "Amin mungode. Sai wata rana" Ya fadi suna wucewa. Mamakin shi haneef yake. Akwai babbar matsala. * Kofar gida haneef yai parking saboda mutane har sun fara taruwa kofar gidan. Ya zagayo ya bude ma fu.ad bayan motar. Ya fito sannan ya tallabo Nana ya sake sabeta a kafadarshi. Haneef kadai ya tsaya gaisawa da mutane suna mishi gaisuwa. Cikin gida fu.ad ya wuce. Saboda baya son yanda kowa ke kallonshi din nan. Lokaci daya maganar nana ta fado mishi. Haka suke kallonta cike da wannan yanayin a idanuwansu kenan? Sake tallabeta yai jikinta yana rasa menene yai mishi daban cikin hakan. Yana sallama yasa kafarshi cikin gidan anty fatima na sakin wani irin kuka. Momma ma fuskarta harta kumbura. Tasowa tayi ta karbi nana daga hannun fu.ad din tana nazarin fuskarshi. "Fu.ad...." "Em okay momma. Kuyi mata wanka bara mu siyo abinda ya kamata. "Hassan ya tafi" Momma ta fadi tana goge fuskarta da dayan hannunta.  Kai fu.ad ya daga mata. "Abbah fa?" "Yana waje. Bai jima da fita ba" Kai ya sake daga mata ya juya. Yana shirin fita inna na shigowa tana goge fuska. Kaucewa yai gefe dan yaga yanda tana ganinshi wasu hawaye suka sake zubo mata. Da sauri yabar dakin. * Su haneef ya samu suna alwala. Kofar gidan ya cika makil da mutane. Shima alwala yayi yace ma haneef. "Ina lukman?" A sanyaye haneef yace. "Yaje ya taho da zainab" Kai ya daga mishi kawai yana mikewa. Ansar ya hango ya nufo su. Tsayawa yai ya karaso ya mika ma haneef hannu sannan fu.ad din. Muryarshi na rawa yace. "Yanzun naje asibiti ake fadamun. Na kira safiyya ta sai wata ta daga taban address din nan. Ya Allah. Oh Nana......" Kasa karasawa ansar yayi sai fuskarshi daya sa cikin hannayenshi yana wani irin jan iska. Mutuwar nana yake ji har cikin zuciyarshi. Dafa shi yaji anyi ya bude fuskar ya sauke idanuwanshi kan fu.ad. "Sai hakuri. Kai mata addu.a shi tafi bukata" Kai kawai ansar ya daga ma fu.ad din. Sai kuma ya sake kallonshi sosai wannan karin. Girgiza kai yake kamun ya maida dubanshi kan haneef. Abbah fu.ad ya hango yabarsu haneef nan tsaye. Ansar yace ma haneef. "Is he okay?" Dan daga kafada haneef yayi hadi da girgiza kai. "Allah dai ya rufa asiri" "Amin. Oh Allah" Cewar Ansar yana samun waje ya tsugunna dan rasuwar na tabashi ba kadan. *30 minutes later* Su hudu suka shigo cikin gidan. Dashi da lukman,haneef sai babban yaya dan su dauko gawar nana. Ai nan tashin hankalin yake. Suna nufo inda take kwance an hadata. Safiyya ta taso da gudu ta rike nana jikinta. "Dan Allah ku tsaya. Ku tsaya ban gama ganinta ba" Momma dake wani irin kuka ta taso ta kama safiyya. "Kiyi hakuri safiyya. Kiyi hakuri" "Momma dan Allah kice su kara tsayawa. Kar su tafi da ita....." Riketa momma tayi a jikinta. Kamun anty fatima ta taso ta tayata. Fu.ad da kanshi yasa hannu ga dago Nana yana jin shiru cikin kanshi da ko ina na jikinshi. Sosai gidan ya sake rikicewa banda. "Inalillahi wa ina ilaihi raji.un....." Babu abinda suke fadi. Haneef ya runtsa idanuwanshi yana bude su. Yana jin dadin yanda basu saki Allah ba. Yana kuma da tabbacin zai saukaka musu dacin rashin Nana. Hakika sabo ake yiwa kuka. Safiyya ba kallon sun nufi kofa da nana ta rarrafa dan ta kasa tashi. Ta karasa wajen inna tana boye kanta cikin cinyar inna hadi da sakin wani kuka da takejin fitowarshi daga wani waje na zuciyarta da bata san yana nan bama. Shikenan ita da Nana har abada.....! Inna ta riketa itama kukan take saboda yanda mutuwar nana ta sake fama mata ciwon mutuwar usman. Tasan me yarta take ji. Tasan halin da take ciki. Abu daya inna take da yaqini akai. Allah daya dora musu yasan dasu. Inhar suka rike shi zai basu mafita.......! **** Dakyar ta iya kai kanta gida. Dan lokacin tashi baiba ma tace gida zataje bata da lafiya. Ko sallama batai ba ta zauna falon ta na ajiye komai anan. Dafe kanta tai cikin hannayenta. Tun mutuwar mahaifinta rabon da ai mata wata mutuwa data tabata. Sai yau rasuwar nana ta girgizata sosai. Hawaye ke zubo mata. Wani nabin wani. Bata ji fitowar ayna ba sai maganarta taji. "Anty? Yaushe kika dawo? Sannu" Dagowa tayi wasu hawaye na sake zubo mata data sa hannu ta goge su. Ware idanuwa ayna tayi ta karasa inda jana take ta zauna. Kusan sati daya kenan da zuwanta gidan nan. Banda gaisuwa babu abinda yake hada su da jana din. Hakama yaranta zasu gaishe da ayna din kullum. Ko bata fito ba sanda zasuje school zasuyi sallama bangarenta su gaishe da ita sannan su wuce. Kuma hakan ya mata dadi yanda jana tasa suke bata girma. "Anty lafiya dai ko? Ko wani ya rasu?" Kai jana ta daga mata. Ba zata ce ta tsani ayna ba. More like tana kishi da ita ko tace tana kishin jabir da soyayyarshi. Cikin sanyin murya tace. "Wata yar yarinyace. Nana sunanta patient dina ce kusan shekaru uku. Mun saba sosai yau ta rasu" Dafa ta ayna tayi tana jin duk babu dadi. Ita mutuwar yara na mata wani iri. Jikinta sanyi yake. "Allah sarki. Allah ya jikanta ya ba iyayenta hakurin rashi" "Amin ayna nagode" Kayan da jana ta cillar tsakar dakin ayna ta tattara mata waje daya hadi ta kauda mata gefe tana wucewa. Dawowa tayi da ruwa da cup. Ta bude ta zuba ta mikama janar. Ta karba tasha. Sosai taji dadin karamcin da ayna tai mata. "Nagode ayna" "Bakomai anty. Kiyi hakuri ki mata addu.a sai tasan kin damu da ita sosai. Ko kije kidan watsa ruwa ko zaki samu natsuwa" Mikewa jana tayi ta kalli ayna tace. "Nagode fa. Bara in shiga daga ciki" Kai ayna ta daga mata hadi da murmushi. Jakarta ta dauka ta wuce ciki. Ayna ta bita da kallo. Tana fatan wannan zaman lafiyar da suke ya da jana da ganin girman juna ya dore. Yanda bata shiga harkarta bata damu da harkarta ba kawai yana burgeta. Bata son tashin hankali sam. Ta kuma kula jana bata da matsala. Sai yanzun taga dalilin dayasa kullum sai jabir ya yabi halayyarta. Tai ma kanta alkawari zata sa ido ta karanci jana tsaf ko itama zata dinga samun koda rabin yabon da jabir yake mata ne. **** Tun daga hanyar dawowa daga makabarta lukman ke kallon yanda fu.ad ke ta duba hannayenshi kaman yana son ya tabbatar da su na nan ne ko yana mamakin ganinsu a jikinshi. Haneef ya tabo ya nuna mishi fu.ad din daketa jujjuya hannunshi sauri sukayi suka karasa wajenshi suka jera tare. Lukman ya kira sunanshi a hankali. Baiko juyo ba balle suyi zaton yaji. Kawai tafiya yake yana kallon hannuwa shi daya dago su. Haneef ya kai nashi hannun ya kama daya na fu.ad. Sai lokacin ya dago ya kalli haneef idanuwanshi cike da wani irin ciwo da yake ji a kirjinshi. "She is gone haneef. Da hannuwana na kamata na sata a kabarinta. Da hannuwana na dibi kasa na taya aka zuba mata. Haneef wannan shine soyayyar ko? Da kaina na dinga duba ko an manta ba a rufe wani waje da kyau ba. Iya kaunar dazan nuna mata kenan ko?" Lumshe idanuwa haneef yayi. "Ya Allah...." "Itama haka tace kamun Allah ya dauki abinshi......." Fu.ad ya fadi yana juyawa ya kalli lukman. "Daman aronta aka bamu ko lukman? Kaga Allah ya dauki abinshi tunda yafi mu sonta" Hannunshi dayan lukman ya rike yana matsewa dam. Dayai magana hawayen dayake ji zubo mishi zasuyi. Fu.ad na bukatar dukkan strength din dazai samu daga gare su. Haneef addu.a yake su karasa gida lafiya kar fu.ad ya samu break down a hanya. Hankalinshi bai kwanta ba sai da yagansu kofar gidansu. Sai da yaga sun shiga harabar gidan tukunna. Fu.ad dake tsaye idanuwanshi kafe a kasa ya kalla ya sauke numfashi. Saida ya dafa kafadarshi sannan yace. "Fu.ad kayi hakuri. Dukkanmu babu mai tabbacin bazai bi Nana yanzun nan ba. Ita mutuwa ba sallama take ba. Ba kuma jira take ka shirya ba. Idan bata zo kanka ba kasa a ranka a kullum kaine ko wani makusancinka ko wani wanda baka sani ba. Bazan ce nasan ciwon da kake ji ba. Amman kayi hakuri dan Allah" Girgiza kai fu.ad yake. "Haneef ta rasu. Shikenan ko?" Har ranshi ciwo yake ji marar misaltuwa. Ganin fu.ad din cikin yanayin da yake yanzun. Amman yasan gara yanzun da dazun. Dazun sam ba cikin hankalinshi yake komai ba. "Ta rasu fu.ad da gaske ta rasu. Allah ya baku juriya" Hannunshi yasa ya ture na haneef. Yanajin kiran shi da suke shi da lukman bai ko juyo ba balle ya kalle su. Lukman ne zai bishi haneef ya rike mishi hannu. "Kabarshi yaji ta lokaci daya ya huta" Kai lukman ya daga ma haneef yana karasawa cikin rumfunan da aka kafa a harabar gidan ya zauna ya hade kanshi da gwiwa. * Cikin gidan ya shiga bai damu da yawan matan dake ciki ba. Asalima baya ganinsu abu dayane ke yawo cikin idanuwanshi. Yanda suka binne Nana. Hotone daya san ya zauna zuciyarshi na har abada. Hanyar dakinshi ya nufa. Kafarshi ta taka benen farko yaji an rike hannunshi. Juyowa yai ya sauke idanuwanshi kan fuskar momma. "She is gone momma. Ta rasu" Ya fadi yana wani irin fitar da numfashi. Momma ba zata iya ganin shi hakan ba. Sakin hannunshi tayi ta juya. Ba mutuwar nana take tsoro ba daman. Wannan tana kan kowa. Abinda mutuwarta zata haifar shi take gudu. Safiyya ta kalla da ke zaune can gefe. Suna hada ido momma ta juya ta kalli fu.ad sannan ta sake kallon safiyya tana son nuna mata suna bukatar juna. Shikam fu.ad da gudu ya karasa hawa benen. Kawai so yake ya karasa dakinshi. Jikinshi na rawa ya murza handle din yako ci sa.a babu key ajiki dakin ya bude. Kafafuwanshi suka kasa daukarshi a tsakiyar dakin. Durkushewa yayi yana dafe kanshi cikin hannayenshi. Jikinshi ko ina bari yake yi. Da sauri sauri yake fadin. "Allah na karbi jarabawarka da hannu bibbiyu. Allah ka kawomun dauki. Allah ka kawomun dauki......" Jiyai an dafashi. Hakan yasa ya dago da kanshi daga cikin hannayenshi sannan ya juyo safiyya ce fuskarta a kumbure. Wasu hawaye suka zubo mata. Kama hannayenta yai yana gogasu kan fuskarshi. "Sofi ta rasu. Nana tabarmu har abada" Kai take daga mishi tana wani irin kuka. Ta kwantar da kanta a cinyarshi. Nashi kan ya dora a bayanta yana jin hawayen shi na zubowa. Kuka suke sosai. Kukan rashin yarsu. Kukan tausayin kansu domin ita da tata tai kyau ba ita bace abin tausayi. Su da tabari cikin duniyar da babu tabbas sune abin tausayi..........! *#TeamAS* *#AnaTare* *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ www.Loobnerh.blogspot.com Wattpad: LubnaSufyan                 48 *A ko da yaushe a rayuwa idan kace zaka dinga duba baya. To da wahalar gaske gaban tai maka dai dai* *Bazai rageka da komai ba dan ka yafe. Ba ace ka manta ba. Wannan abune mai wahala. Baiwa ce da bakowa Allah yaiwa ba* *Sai dai ka sani ana ci gaba da zama da juna ne bawai dan an manta bacin ran daya faru ba. Ana zama ne saboda an YAFE* *Allah ya nuna mana RAMADAN lafiya. Amin thumma amin* *Ba saina ce nagode da comments dinku da prayers ba saboda ai #AnaTare. Like sosai sosai* *TWO MORE pages In shaa Allah* Yana shigowa gidan da sallama yaga baiga nuriyya ba. Ciki ya shiga ya duba bedroom dinta. Dan yasan bata cika zama falo ba. Tafi gane tai kwance a bedroom din in bashi ya dawo yazo ya fito da ita ba. Zuciyarshi yaji tana dokawa babu dalili. A rikice ya fito yana fadin. "Nuriyyaaaa" Da saurinta ta fito daga cikin. Idanuwanta ta sauke cikin nashi. Wata ajiyar zuciya ya sauke yana tura hannunshi daya cikin sumar kanshi. Da mamakin ganin tsoron da har lokacin bai barshi ba yasata fadin. "Yaya farhan. Lafiya dai ko?" Kai ya daga mata yana dora murmushi a fuskarshi. "Ina kitchen ne banji shigowarka ba" Ta fadi a sanyaye hadi da dorawa da. "Ka daina tunanin zaka nemeni ka rasa yaya farhan. You are the only family da nake da. Please banajin dadi" Kunyarta yaji ta rufe shi. Har ranshi yana tsoron ya nemeta ya rasa. A yanzun shima bashida wani family bayan ita. "Na daina. I am sorry" Kai ta daga mishi alamar komai ya wuce. "Nace ki daina damuwa da dafa abinci. Zamu iya fita waje muci" Dan murmushi tayi mishi tana jin wani quna a zuciyarta. Nawaf ya koya mata kyamar abincin waje komin tsaftar restaurant ko hotel kuwa. "Ba wani aiki bane. Tunda babu yawa" Kai ya daga mata ya zagaya ya zauna kan kujerar. "Zo mu zauna" "Barin sauke girki sai inzo" Ta fadi tana juyawa. Bata fi mintina goma ba ta fito. Waje ya samu gefenshi ta zauna. Kallonta yai sosai. Muryarshi da fuskarshi tana nuna mata muhimmancin maganar da yake son fada. "Naje gidan anty ne yau. Naje inji ko tana da wani abu da ya rage na lokacin data tsince ki. So ba a samu komai ba sai School back dinki. Na karbo amman ban bude ba. Banma san yanda zakiyi handling abin ba na bari in fara fada miki" Kan nuriyya a kasa tana jin hawayen da suka taru a idanuwanta suna zuba. Zuciyarta dokawa take. "Nuriyya....." Ya kira a hankali. Tun a hanya yake tababar fada mata. Yadan samu a satin nan ta fara warwarewa har tana dan hira dashi. Zai jagula komai akan maganar da babu tabbas a cikinta. Babu ma wani hope ko za.a samu wani clue cikin jakar. Hannunta takai ta kamo na farhan ta dumtse. Karo na biyu da jikinsu ya hadu tun zuwanta gidan. Kaman yanda yai mata alkawarin zama duk abinda take son shi ya zame mata har saita shirya canzuwar hakan. Bai karya ba. Beside inya kula bata son magana bata waje yake. "Ina tsoron a bude jakar da kace ka karbo a samu babu komai a ciki. Ina tsoron ko bazan taba ganin dangina ba. Idan ina dasu kenan. Bansan me ya kamata inyi ba" Dayan hannunshi yasa ya hade nata cikin nashi duka biyun. Cikin idanuwa yake kallonta. Sannan yace. "Rashin budewa a duba zai sa ki zama cikin tambaya a ko da yaushe. Budewar bazai cutar dake ba nuriyya.  Kilanma ki tuna wani abu. Allah kadai yasan me ya boye miki a bayyanar gaskiyar nan. Inkuma kina so magana da anty ne directly sai muje" Da sauri ta girgiza mishi kai. Wani irin tsoro na shigarta. In akwai abinda tafi tsana bai wuce ta sake dora fuskarta kan azzalumar mata kaman anty ba. Ko a mafarki bata fatan Allah ya sake hadasu ballantana kuma idanuwa biyu. "Bana son sake ganinta yaya farhan. Na tsaneta wallahi" "I understand...." Da rauni a muryarta tace. "Zamu bude jakar tare. In babu kai bazan iya ba" Kasa controlling emotions dinshi yayi. Ya kara matsawa ya sumbace ta a kunci sannan ya saki hannunta ya mike yana ficewa daga falon. Hannu tasa ta goge fuskarta. Zuciyarta na wani irin dokawa. Tana jin ya shigo da sauri ta daga kai ta kalle shi. Kamun ta maida kallon kan yar jakar dake hannunshi. Kurar da jakar tayi ya hana asalin kalarta ta fito. Kaman ash colour. Kara sowa yayi ya zauna. Sannan ya mika mata jakar ta karba tana jujjuyata. Da duk wani abu na jikinta take son taji wani connection tsakaninta da jakar ko ta tuna wani abu ko ya yake amman ta kasa. Muryarta na rawa tace. "Na kasa tuna komai yaya farhan" Dafa hannunta yayi. Ya na karbar jakar ya ajiye kan kujera. "May be shekarunki ba masu yawa bane da zaki rike wani abu. Ki bude" Kai ga daga mishi. Zuciyarta na wani irin dokawa. Ji take kaman inta bude jakar zata iya ganin wani abu dazai tuna mata asalinta. Ta wani fannin kuma tanajin tsoron yanda ta daga burinta har haka. Jin farhan ya sake dafa hannunta ya sata jan wani numfashi sannan ta sa hannu kan zip din jakar ta bude. Bugun zuciyarta na karuwa. Hannu tasa ta daga jakar hadi da zazzageta kan kujerar. Tasa hannu tana taba kayyakin da suka zubo daga ciki kaman zasu bata amsar data kasa samu. Books ne a ciki gabaki daya na yan Nursery 1. Farhan ne yasa hannu ya dauki guda daya daga ciki. Yaga inda anty taga asalin sunan Nuriyya kenan. Gashi nan da manyan baki a rubuce. 'Nuriyya habeeb danori'. Habeeb danori farhan yake maimaitawa cikin kanshi yana tunanin inda ya taba jin sunan. Sosai yake dubawa. Dan ware idanuwa yai ya kalli nuriyya da idanuwanta ke kafe kan littatafan da take ta shafawa. Ya bude baki sai ya fasa. Gidan mai ne yagani wajen bachirawa. Sai dai zai iya yiwa habeeb danori da yawa cikin garin kano. Baya son ya daga mata burinta sai ya tabbatar tukunna. Duk da yana da wani irin feeling mai karfi kan hakan. Bazai daga mata buri yazo ya tarwatsa shi ba. Yana kallonta ta dauki littafi daya tana sa hannu tana shafa wajen da sunan yake. "Asalin sunana Nuriyya. Anty tagani. Taga sunana ta kasa kaini inda dangina zasu nemeni. Saboda me? Meye ribarta na tsintata ta kasa kaini inda za a ganni? Amfanin me nai mata?" Shiru farhan yayi saboda baisan me ya kamata yai mata ba. Matsawa yayi ya kama Hannuwanta. Kwacewa tayi. "Saboda me? Ina da family kaima kagani. Kaga shaida yaya farhan me yasa zata tarwatsa mun rayuwa? Duk shekarun na ina tunanin ko kalar mahaifina bazan taba sani ba. Ina tunanin mahaifiyata karuwa ce. Kasan tashin hankalin dake cikin hakan?" "Nuriyya please calm down....." Farhan ya fadi. Cikin hargowa tace. "No yaya farhan. Ba zaka taba ganewa ba saboda kayi normal rayuwa ba irin tawa ba" Kallonta yake maganganun data fada suna masa wani irin zafi. Muryarshi can kasa yace. "Nuriyya. Ki bar maganar nan. Zan nemo miki su in shaa Allah" Hawayen da suke zuba idanuwanta tasa hannu ta goge. "Idan kuma ba sa nan fa? Ba zaka taba ganewa ba" A tsawace yace. "Yes bazan gane ba nuriyya. Na dauka kinsan kadan daga cikin rayuwata. Kinsan waye babana. Bance yafi anty ba. Ban kuma ce kalar su daya ba. Ki kalle ni sosai. Na miki kama da wanda yai rayuwa normal?" Shiru tayi tana kallonshi yanda ya birkice lokaci daya. "Ko kin taba tambayata ina kanwata da nake baki labari? No baki tambaya ba. Ni kuma ban fada miki ba saboda what is there to tell? Ince nuriyya kinsan me ya faru da farhana kuwa? Ina kallo babana ya sha giya ya bugu yace saita bishi sun fita unguwa. Ina tsaye saboda tace tana son zuwa gudunma tashin hankalin shi nabarta. Bayan komai na jikina na mun ihun kuskuren hakan. Ina kallo yaja mota suka bar cikin gida ban tsayar dasu ba. Yeah naga kuskurena awa biyu tsakani da aka jeramun gawarsu a gabana. Sai dai kinsan me? I deserve the pain na mutuwar farhana saboda ni ne sila. Him? That Monster? I wish baiyi mutuwa mai sauki ba......" Inalillahi wa ina ilaihi raji.un kawai nuriyya ke fadi cikin zuciyarta. Sai yanzun taji dalilin da duk murmushin da farhan zai akwai wani irin sadness a karkashi shi. Hannu tasa ta dafa mishi cinya. Amman kaman ma baya jinta. "Yaya farhan....." Ta fadi hawaye na zubo mata ganin yanda jikinshi ke kyarma. Yanda komai nashi ya canza. Yanayin ciwon abinda yake ji bayyane a fuskarshi. Juyowa yai ya kalleta sosai. "I don't know exactly yanda kike ji. But bake kadai kike hurting ba. Bake kadai bace nuriyya" Mikewa tai ta matsa ta zauna kan cinyarshi. Kamun yagama mamaki tayi hugging dinshi sosai. Kuka take. Shikam ya kasa. Yanajin kalar raunukan da yake dasu zafinsu da ciwonsu ya girmi hawaye. Riketa yai a jikinshi yana jin yanda yanayin ke fifita mishi inda yake masa zafi. Sumba ya manna mata a gefen fuska. "Ki daina kuka. In shaa Allah zan nemo miki family dinki. Za.a gansu" Kai take dagawa tana sake kankame shi. Cikin kunnenshi tace. "Kaima ka gano naka please. Ka gano mana family dinmu" Shiru yayi yana juya maganarta. "No naki dai nuriyya. Mum na bata da kowa. Shikuma....... Yeah sunyi gefe lokacin da yake abusing dinmu. Saboda yana da kudi babu wanda zai iya mishi magana" Sake rike shi tayi. "Nasani. Ka yafe musu dukkanmu muna kuskure a rayuwarmu" Lumshe idanuwa farhan yayi. "Mu bar maganar for now please" Dagowa tai daga jikinshi. Ta kalli fuskarshi sosai. "For now" Ya daga mata kai da yake nuna alkawarin zasu sake maganar amman ba yau din ba. Komawa tai jikinshi ta kwanta luf. Ya riketa yana lumshe idanuwanshi. Rayuwa makaranta.....! "Na dauka sai da yamma zamu tafi" Safiyya ta fadi a sanyaye tana kallon fu.ad. Girgiza mata kai yayi. "Mu koma gida kawai. Zama anan bazai sake komai ba." Kai ta daga mishi ta na dauke idanuwanta daga fuskarshi. Tana jin ciwon yanda zata koma gidan su da yake cike da memories din nana. Yau kwana hudu kenan da rasuwar. Su dukansu kallo daya zakai musu ka fahimci yanda rayuwa ta koya musu darasi da dama. Musamman safiyya da fu.ad da sukai wata irin rama. Ya karanci me take gudu tsaf. Ya share ne saboda yasan gudu wa feelings dinsu bazai canza komai ba. Da yawan gudun da suke da yawan yanda zai musu zafi idan ya kamo su. Ya riga da ya fada ma momma zasu koma gida tun dazun. Itama da taga kaman yayi sauri dayai mata bayani saita fahimta. "Bara to in dauko mayafina sai in sallama da momma" Kai kawai fu.ad ya iya daga mata. Baiko zauna ba dan yasan ba dadewa zatai ba. Shi kanshi zuciyarshi cike take da tsoron kalar ciwon da zaiji in suka karasa gidan. Kewar Nana har cikin tsokarshi yake jinta. A zuciyarshi wani irin fili ne tabari da babu wanda zai iya maye shi. Wajenta ne ita kadai. Lumshe idanuwanshi yai hannuwanshi cikin aljihu. Murmushinta ya tuna da yanda take bude idanuwanta idan taganshi. Baisan sanda murmushi ya kwace mishi ba. Cikin zuciyarshi yake fadin. "Allah ya haskaka kabarinki nana. Kin barmu da kewa ko? Nagode da tare da kewarki akwai moments irin wa.annan" Tabashi yaji anyi. Da sauri ya bude idanuwanshi ya sauke su cikin na safiyya. Lokaci daya murmushin dake fuskarshi ya bace. "Murmushin me kake?" Hannunta ya kama suka nufi hanyar fita. Cikin sanyin murya yace. "Bakomai kawai na tuna yanda Nana take nata ne bansan sanda ya bayyana ba" Ga mamakin su duka biyun dariya safiyya tayi. A karo na farko tun rasuwar nana. "Kasan akwai lokacin da ina fever. Naji nana shiru inata kira ashe tana kitchen. Kasan me take?" Da murmushi a fuskarshi ya girgiza mata kai. Dariya ta sake yi lokacin sun karasa bakin motar. Tsaye fu.ad yai yana kallonta yana son ta karasa bashi labari. Cikin fuska take kallonshi. "Kwai ta soyamun ta hado tea. She was 7 lokacin. Karka ga fuska ta sanda ta shigo dakin. Ranar na fara jin tsoro a rayuwata. Ina tunanin data kone fa? Ko ta zubo ma kanta ruwan zafi. Abinda tayi ya tabani sosai na kasa mata fada. Karka ga fuskata lokacin da nai tasting wainar kwan. Goodness. It was awful" Wanna karin fu.ad ne yai mamakin daga inda dariyarshi ta fito. Daga shi har ita dariya suke. Kamun wasu hawaye masu zafi su zubo ma safiyya. "I miss her. Every second da bata nan ina jinshi a ko ina nawa wallahi" Rikota yai jikinshi yana matse ta dam. Shi kanshi yanajin irin ciwon da take ji. "Sofi kina da memories irin wannan ke. Banda su da yawa. Dan Allah ki dinga sharing mun nima in samu? Zamu saba da kewarta a hankali. Komai zaiyi mana sauki" Dagowa tai daga jikinshi tana goge fuskarta. "Zan sharing maka duka. Duk wani babban abu da karami dazan iya tunawa" Kai ya daga da murmushi a fuskarta. Itama kasa boye nata murmushin tayi. Tace mishi. "As much as tunanin nana zai mana ciwo. Farin cikin dake tattare dashi mai girma ne" "Ta tafi tabarmu da kewarta ne. Shisa zaiyi ciwo. Amman kuma tabar mana abubuwan farin ciki da yawa. Ina jina da sa.a sosai dana santa a rayuwata" "Nima haka...... Muje gida dai" Kai fu.ad ya daga yana sauke numfashi hadi da bude ma safiyya motar. Shiga tayi ya rufe sannan ya zagaya ya shiga shima. * Suna hanya sun kusa kai gida ma wayarshi ta hau ihu. Saida ya rage gudun da yake sannan ya lalubota daga aljihunshi. Dubawa yai yaga lukman ne. Ya daga ya kara a kunnenshi. Kamun yace wani abu lukman yace. "Fu.ad please ka gayama hajiya muna nan Aminu kano. Zainab ke labour. Inata kiran wayarta baya zuwa" Ware idanuwa fu.ad yayi. "Wallahi nima na fito. Bara na kira momma sai taje su taho" Kaman lukman zaiyi kuka yace. "Please kai sauri. Ni kadaine a wajenta" Katse wayar yayi. Fu.ad ya mikama safiyya wayar. "Lukman ne. Kira momma kice su taho ita da hajiya. Zainab ke nakuda kuma ba kowa wajenta" Da sauri safiyya ta lalubo number din momma. Allah ya taimaka ringing daya momma ga dauka. Fada mata tayi. Sannan ta ce ma lukman. "Da munje asibitin ma ai" "Are you sure?" Kai ta daga mishi tana masa kallon dake fassara tambayata ma kake. Lukman da zainab ake magana ba wasu ba. * Sun riga su momma zuwa asibitin. Lukman suka samu kallo daya zakai masa kasan yana cikin tashin hankali. "Ya zainab din?" Safiyya ta tambaya. Kai ya girgiza mata alamar bai sani ba. Kallon wajen fu.ad yake yana mamakin ganin lukman din ne kawai. "Ina family dinta. Ka kira mamanta?" Kallonshi lukman yayi. A sanyaye yace. "Bata san babanta ba. Da cikinta ya rasu. Wajen haihuwarta mamanta ta rasu. Ita kadai ce wajensu" Kai fu.ad ya girgiza. Yana jin wani abu daya tsaya mishi a wuya. Har safiyya kasa cewa komai sukai. Lukman ya yatsina fuska. "Basu damu da ita ba. Lokacin da naje neman aurenta yi sukai kaman sun gaji da ita. Kaman daman jira suke su samu maraba da ita" "Hmm duniya kenan. Rayuwar duka guda nawa ce" Fu.ad ya fada yanajin wani tausayin zainab din ya cika zuciyarshi. Safiyya ta bude baki zatayi magana su momma suka karaso. Kaman zuwansu wajen ya taho da sa.a. kamun ma suce wani abu. Nurse ta fito tana tambayar wanda suka kawo zainab. Su dukansu suka nufe ta suna tambayar yaya. Murmushi tayi. "Ta sauka lafiya. Ta samu baby girl. Suna cikin koshin lafiya. Zaku iya ganinta nan da mintina sha biyar in an shiga da ita dakin hutu" Su duka hamdala suke. Cikin yanayin murnarsu fu.ad ya matsa ya kamo hannun safiyya ya rike. Dumtsewa nashi tayi tasan tambayarta yake ko she is okay. Shisa ta amsa shi itama. Duk da halin rashi da take ciki bai hanata taya su zainab farin ciki ba. Haihuwa kyautar Allah. Momma ta bude jaka ta zaro kudi taba nurse din hadi da yi mata godiya. Nan suka tsaya suna jira a fito da zainab din dan su shiga su ganta. Aikam ana zuwa aka fada musu zasu iya shiga su ganta. Suka dunguma su dukansu. Tana kwance babyn na gefenta. Momma ta fara daukar babyn ta mika ma lukman ya karba. Hamdala yai daya saukar da matarshi lafiya kamun ya kai kunnen babyn saitin bakinshi. Kiran sallah yai mata cikin kunnen kamun da addu.o.i sannan ya matsa wajen fu.ad mika mishi ita yai. "Kai mata huduba" Ware idanuwanshi fu.ad yayi cike da alamar tambaya. "Ko wanne suna yai maka" Lukman ya fadi kasa kasa. "Ya sunan maman zainab?" Fu.ad ya fadi yana karbar yarinyar da yakejinta yar kararrama a hannunshi. Kallonta yake so cute. Yanajin wani abu a xuciyarshi daya kasa bama suna. "Aisha" Kai fu.ad ya daga ma lukman saboda bazai iya magana ba a yanayin da yakeji. Addu.o.i sosai yaima yarinyar ya mika ma lukman ita. Yanajin yanda yai kewar dan nauyinta a hannunshi a iya mintinan datai wajen shi. Hajiya lukman ya mika ma yarinyar. Ta karbeta itama tai mata addu.a sannan tabawa safiyya. Idanuwanta cike da tausayawa. Karbarta safiyya tayi ta kura mata idanuwa kamun tace. "Zainab kamarku daya lukman ka bata mun daughter da guntun hanci" Dariya sukayi. Suna jinjina ma karfin halin safiyya din. Da idanuwa lukman ya ke rokon hajiya da su dan bashi waje da zainab. Tasan dalilin hakan ta dafa momma kamun ta mike. Ta fahimci so take subar dakin. Dan haka babu wani bata lokaci ita da momma suka fice. Fitarsu ta fahimtar dasu safiyya. Ta mike hadi da bama zainab babyn. "Allah ya raya ya sanya mata albarka" Kasa dakai zainab tayi. Tana jin kunyar safiyya din. Dan murmushi tayi ta kalli fu.ad suka fice daga dakin suma. Karasawa gefen gadon lukman yayi. A tsorace yake kallon zainab. Hannu yakai ya taba fuskarta. "Sannu zee na. Allah ya miki albarka. Allah yasa kece matata har a aljanna" Cike dajin dadin addu.arshi ta dafa hannunshi dake kan fuskarta "Amin. Zan yi alfahari dee. Samun miji irinka sai an tona. Bazan taba manta karamcin da kaimun ba. Kaime komai nawa kai....." Saurin janye hannunshi yai daga fuskarta yana rufe mata baki. "Shhhhh. Bana so. Banaso kina fadar haka. Abinda nai miki in kyauta ce kinbani linkinta da junior. Idan bashi ne kin ribamun riba mai girma. Ina sonki zee. Zan fahimta in kin fasa niyyarmu. Wallahi bazan taba kallonki da abin ba. Saboda cikin ba a jikina ya zauna wata tara ba. Bani nai miki naqudarshi ba. Bana so kiyi abinda zakiyi nadamarshi dan farin cikina ba....." Wannan karin ita ta rufe mishi baki. "Ko da nake nakuda da niyyarmu daram a zuciyata dee" Sauke numfashi yayi ya mike. Sumbatar ta yayi yana nuna mata godiyarshi. Yana daukar mata alkawarin kin manta wannan karamcin. * Leqo da kanshi yayi wajen dakin yace. "Momma ku shigo. Fu.ad......" Su momma wucewa sukayi. Ganin su fu.ad sun tsaya yasa shi fitowa daga dakin gabaki daya. "Ku shigo mana" "Zamu dawo lukman. Gida zamu tafi yanzun" Girgiza kai yayi alamar bai yarda ba. "Nidai ku shigo. Safiyya kema biyema fu.ad zakiyi ko?" Kallon fu.ad safiyya tayi da idanuwa take rokonshi dasu koma din. Gani yake kaman ba zata iya handling emotions din ba shisa yake cewa su tafi gida. Kai yadan daga mata. Ta saki hannunshi dake cikin nata. Suka shiga dakin a tare lukman na gabansu. Tsaye sukai daga dan nesa su duka wannan karin sun rasa me ya kamata suyi. Hada idanuwa safiyya tayi da zainab. Zainab din tai mata wani murmushi data kasa fahimtarshi. Kasa mayarwa tayi dan yanda take jinta. Suna kallo lukman ya je wajen zainab tasa hannu ta miko mishi babyn. A hankali ya tako inda su fu.ad suke ya tsaya da babyn a hannunshi. Juyawa yai ya kalli hajiya. Yaga alfaharin dake cike da idanuwanta. Farin cikin dake kan fuskarta dazai jima tunosu kawai na saukar mishi da nishadi. Dan daga mishi kai tayi dake nuna me yake jira? Yayi kawai. Juyawa yayi ya sauke idanuwanshi cikin na fu.ad. Fuskarshi dauke da wani yanayi yace. "Lukman ni me zan da yara? Idan ina bukatarsu ga naka nan zaka haifa. Ga  haneef ga su pha.iza zan gansu" Sosai yake kallon idanuwan fu.ad din saida yaga alamar ya tuna exact maganganunshi shekarun da suka wuce. Yaga dana sani da nadama dake cikin idanuwanshi. Sannan yace. "Yes rabin maganarka babu karya a ciki fu.ad. kana da mu. Kuma yanzun kana bukatar ya'ya. Saidai daya kawai zamu iya haifa maka......" Lukman ya karasa maganar yana mika mishi babyn. Kallon safiyya fu.ad yayi sannan ya kalli lukman ya kalli babyn. Muryarshi na rawa yace. "Me kake nufi?" Dan ya kasa fahimta. Duk da kunnuwanshi sunji maganganun lukman. Zuciyarshi taki yarda ta karbe su. "Kaji ni ai. Baby muka haifo maka ni da zainab...." Hannu fu.ad yakai kan kirjinshi yana dafe inda zuciyarshi ke wani irin tsalle kamar zata fado. Momma ya kalla ita kanta mamaki ne karara a fuskarta. Ta kalli hajia idanuwanta cike da tambaya da hawaye. Tana so taji ko da saninta lukman zaiyi wannan abin. Kai hajiya ta daga mata hadi da fadin. "Wacece ni in shiga tsakanin yan uwa?" Hawayen da suka zubo ma momma ta goge tana fadin. "Na rasa abinda zan fada" "Ki sanya musu albarka" Kai momma ta daga ma hajiya tana kallon su fu.ad wanda dakyar ya iya cewa. "Lukman please. Ka daina mun irin wasan nan" Kallon baka da hankali ko? Lukman yai mishi kamun ya sake mika mishi babyn. "Ka karbeta fu.ad....." Jikinshi ko ina bari yake. Idanuwanshi cike taf da hawaye ya mika hannu ya karbi babyn. Safiyya ya kalla. Ta matso kusa dashi tana sa hannuwanta jikin nashi suna rike babyn tare. Ta kasa tsaida hawayenta. Sun kuma kasa daina kallon babyn. Dakyar fu.ad ya dago da kanshi yace ma lukman. "Wallahi zamu riketa da kyau. Zamu kula muku da ita" Zainab data dafa gadon ta mike zaune tace. "Mu asuwa? Zaku kula da yar'ku dai." Kallon ta sukayi sannan suka kalli lukman. Suna son jin ko gaskiya ne abinda ta fada. Daga mishi kai lukman yayi. "Ba riko muka baku ba fu.ad. Aisha fu.ad Arabi. Mu muka haifeta. Amman yar'ka ce fu.ad. Allah ne shaidarmu akan wannan. Zamu amsa sunan masu haihuwarta ne kawai." Hawayen da suke idanuwan fu.ad suka zubo. Bai kokarin gogesu ba saboda yanajin yanda wasu ke sake fitowa. Kuka suke sosai shida safiyya suna rike da yarinyar har lokacin. Shi kanshi lukman kukan su yasa hawayen zubo mishi. Harsu hajiya ma da zainab din. Hannu lukman yasa ya goge fuskarshi. "Enough please." Girgiza kai fu.ad yake. Saboda ya kasa tsaida su. Bai taba tunanin wannan karamcin daga wajen lukman ba. Bai taba tunaninshi daga wajen haneef bama balle lukman. Allah kenan. Ya karbi nana cikin Hikimar shi kuma ya basu wata kyautar. Kyautar dako a mafarki basu taba zaton ta ba. Mikama safiyya babyn fu.ad yai duka yasa hannu yana goge hawayen dake bin fuskarshi. "Lukman........" "Shhhh inhar zumuncin mu yakai inda na dauke shi zakai shiru ba zaka ce komai ba" Shiru fu.ad yai yana runtse idanuwanshi. Takawa yai ya karasa wajen zainab. Tsugunnawa tai kan gwiwoyinshi. Hannuwanshi na rike da gefen gadon. Kasa ce mata komai yayi. Ya kife kanshi jikin gadon kawai hawaye na ci gaba da zubi mishi. Me zaka ce ma wanda ya dauki farin ciki ya baka? Babu wasu kalamai. Muryar zainab na rawa tace. "Nagode da karamcin dakaimun. Nagode daka sakama yarka sunan mahaifiyata. Allah ya raya muku ita" Dago kai yayi ya kalli momma yace. "Momma kinji itace takemun godiya wai. Really? Wai nine nai mata karamci. Momma da wanne baki zan musu godiya? Wallahi ban cancanci wannan karamcin daga wajensu ba sam" Hajiya ce tai mishi dakuwa. "Gidanku fu.ad da irin maganganun nan. Kar in sake ji. Ka tashi ku wuce gida ma. Mu ma da zainab ta warware gidan zamu tafi" Mikewa fu.ad yayi. Ya karasa inda lukman yake tsaye. Hugging dinshi yai. Lukman ya ture shi yana dan tari. "Maza ragargazamun kashi kar inci naman suna da kyau" Dariya fu.ad yayi yana girgiza kai. Safiyya ya kalla datake takowa ta karaso wajensu. Lukman ta kalla. "Allah ya karramaka linkin yanda kai mana. Allah ya baka aljanna" "Amin safiyya. Allah ya jikan Nana" Kai ta daga mishi hawaye na zubo mata. Karasawa tayi ta zauna gefen zainab. Hannunta daya rike da babyn dayan kuma ta saka shi cikin na zainab. "Mahaifiya tace kadai zatai mun irin abinda kikaimun. Allah yabarki da mijinki yasa zamanku har a aljanna. Zamu kula da ita na miki alkawari" Murmushi zainab tai mata. "Kome zaisa lukman farin ciki. Amin Allah ya jikan Nana ya raya muku baby" Kai safiyya ta daga tana jin hawayen na sake zubo mata kamun tace "Ki shayar da ita. Kar a dauki alhakinta. In yaso sai mu karba in....." Katse ta zainab tayi. "Banda enough milk. Ko junior madara yasha. Karki damu" Lumshe idanuwa safiyya tayi tana sauke ajiyar zuciya. Kai kawai ta daga ma zainab ta mike. Fu.ad ta kalla. Basu da sauran abinda zasu fada. Wannan karin sun manta da su momma dake wajen. Hannunta safiyya tasa cikin nashi suka juya suka fice. Zainab ta kalle su tana sauke numfashi. Tana jin kewar yarta har ranta. Sai dai tana da yaqinin zasu kula da ita fiye da su ma kila. Kallon lukman tayi. Kalar yanda ya kalleta ya wanke mata duk wani shakku daga zuciya. * Basu bar asibitin ba saida suka nemo  doc din yara ya basu shawarwarin dazai basu tukunna. Suna mota safiyya rungume da babyn. Lokaci lokaci fu.ad na juyowa ya kalle su. Sun kasa cewa komai har yanzun. Kamun fu.ad ya kori shirun da fadin. "Muje mu siya ma Mimi kaya tukunna" Kallonshi safiyya tayi. "Mimi?" Kai ya daga mata hadi da fadin. "Sunan maman zainab ne. So zamu boye ko daman. Kuma nana tace inda tana da kanwa zata dinga kiranta mimi" Murmushi safiyya tayi. "Nana ga kanwa kin samu. Saidai Allah baiyi zaki ganta ba" Jin rawar da muryar safiyya take yasa fu.ad fadin. "Mimi kinji mumynki ko? Big sis dinki ba zata taba ganinki ba. Amman ke zaki ganta. Ina da pictures da labarai da yawa" Murmushi safiyya ta sake yi. Tana jin su inna kawai take son tai magana dasu ta fada musu sauyin daya shigo rayuwarta. Ta nuna musu kyautar Allah yawane da ita. Inya jarabceka badan ya manta dakai bane. Saidan Yafi kowa sonka ne. * Aikam biyawa sukayi. Siyayya kawai fu.ad yake kaman baisan wahalar neman kudi ba. "Ya isa haka" Cewar safiyya. Girgiza mata kai yayi yana dakuna fuska. "Bafa a baby zata zauna ba. Inta kara girma zamu dawo. Kaga wanna zasu zama waste. Abarsu haka" Jim yadanyi kamun ya jinjina mata kai cikin yarda da abinda tace din. Zuwa sukayi suka biya kudin kayan aka diba aka zuba musu. Boot ya cika dam. Kaya har bayan motar. Suka shiga sannan safiyya tace. "Mimi akwai hakuri. Har yanzun batai kuka ba. Bacci take tayi ma. Da naso muje gidansu inna mu nuna musu ita. Mu dai je gida in hada mata madara tukunna. Inmun huta sai muje ko" Kai ya daga yace mata. "Ke kika riketa dazun. Yanzun ni zan riketa kiyi driving" Kafada ta makale alamar bata yarda ba. "Inji waye? Kai zakai driving" Shagwabe fuska fu.ad yayi. "Please......" Bude motar tayi ta fita tana zagayawa ta bude shi. Fitowa yayi ta bashi Mimi sannan ta shiga wajen daya fito shikuma ya zagaya. A hankali ya shiga yana rufe kofar hadi da kallon mimi da take ta baccinta kamun safiyya ta tayar da motar su tafi. * Fitowa tai da madara a hannunta ta samu fu.ad a tsaye inda tabarshi tun shigowarsu. Hankalinshi kwance yake zuba ma mimi labari. Dan murmushi tayi. Yanayin da take ji bazai barta ta fada mishi mimi bata jin me yake fada ba. Karbarta tayi ya shiga bedroom din yayo alwalar sallar la.asar ya fito ya wuce masallaci. Jin gidan take yi shiru. Tasan da gaske Nana ta rasu. Tai accepting hakan. Amman wani bangare na zuciyarta gani yake kaman Nana zata fito daga dakine tana tambayarta inda ta samo baby. Lumshe idanuwanta tayi tana maida hawayen da take ji.  Addu.a sosai taima Nana. Mimi nagama shan madarar ta sake komawa bacci. Taso ta sake mata wankane. Saita hakura tabarta ta huta. Dan gadonta da suka siyo ta dauka  sannan ta wuce bedroom din. Saida ta saka ta a ciki ta lillibeta sannan ta shiga bandaki ta dauro alwala ta fito tai sallar la.asar. * Tana kwance kan gadon abinta hannunta daya kan gadon mimi ta dora shi. Sosai tunanin rayuwa take da abinda ke cikinta. Taji an hawo gadon an riketa ta baya. Sauke numfashi tayi. "Banji shigowarka ba" Sumbatar ta yai a kai ta baya sannan ya amsa da. "Bana son tunanin nan please" Shiru tayi. Tunani kam dole ne sai a hankali tukunna. Jin yanda ya riketa yasa ta dora hannunta kan nashi tana shirin zame jikinta. "Sofi. I miss us. Please....." Shirun da tayi ya bashi amsar da yake bukata. Cikin mintina ya fara nuna mata kalar kewarta da yayi shekarun nan. Yake nuna mata yanda soyayyarta take tare dashi duk nisan da sukayi.....! ** Bai iya fita magrib masallaci ba. A gida yaja musu shida safiyya da wata kalar kaunarta ke masa yawo.  Ga wata nutsuwa. Tare suka shiga toilet din da abin wankan da suka siyoma mimi. Safiyya tai mamakin ko uhm mimi batayi ba. Tace ma fu.ad "Kasan Nana kukan wanka take?" Ware idanuwa yayi sannan ya kwace da dariya. "Nana da kukan wankan. Baki fadamun ba ai dana tsokane ta" Murmushi safiyya tayi. Jin yai shiru yasa ta dagowa ta kalle shi. Ruwan tadan diba ta watsa mishi a fuska. Da sauri ya kawo hannunshi ya kare yana fadin. "Sofi mana....." Ware mishi idanuwa tadanyi kamun ta maida hankalinta kan mimi da take sakawa a towel. "Kai kace banda yawan tunanin" Kallonta yai yace. "Ina jin kewarta sosai...." "Nasani nima haka. Allah ya bamu mimi. Duk da samunta bazai hana mana kewar nana ba. Zai bamu sabon farin ciki." Kai ya jinjina mata. "Me zamu ci? Wani abu simple dai" I ta batama jin cin komai saidai tasan in taki shima haka zai kwana tun breakfast din da momma ta takura su suka ci da safe. "Ka zauna da mimi karmu barta ita kadai. Sai in dafa mana indomie" Karbar mimi din yayi yana kallon yanda tayi kyau cikin fararen kayan sanyin da aka saka mata. Wani irin kaunarta ke shigarshi a hankali. "Mi daughter" Ya fadi a hankali kaman yana son sake tabbatarwa tashi din ce. Babu mai kwace mishi wannan kyautar. * Indomie din sukaci. Sukai sallar isha.i. Ya zauna da mimi safiyya ta watsa ruwa sannan ta fito shima ya shiga. Tana kwance kan gadon ya hau ya kwanta gefenta yana nazarin fuskarta. "Gadon inajin shi very empty babu Nana." Baice komai ba ya sauka daga kan gadon. Mimi ya dauko daga nata gadon a hankali. Har mamakin ina ya iya daukar jariri yake. Towel dinta ya mika ma safiyya yana nuna mata ta shimfida. Batai musu ba ta shimfida. Ya kwantar da mimi tsakiyarsu sannan ya kwanta. Murmushi yadan mata. "Better?" Kallon mimi tayi ta lumshe idanuwa tana ma Allah godiya kamun ta bude su kan fu.ad. "Much better" Sake gyara kwanciya yayi yana kallon fuskarta yace. "Ya kikayi all the years da bana nan?" Girgiza mishi kai tayi. "Bana son tuna baya. Ina son kallon gaba ne kawai" Shagwabe fuska yayi. "Ina son ji ne" Kai ta daga a hankali ta fara mishi bayani da fadin. "Ba wani abu much fa. Sati biyu bayan nagama kukan nagama zuba idanuwa baka dawo ba. Nakoma school. Ina amfani da kudin dake cikin gidan inayin komai da nake bukata kamun su kare. Cikin Nana bamai wahala bane. Dan bana wani amai ko wani abu. Ina cin abinci sosai sosai dai. Anty Laurat ta fara cemun ina da ciki. Kamun in noticing Changes din da kaina. Saina fara dibar kudin dake bank. Muna zuwa da ita mu dauko. Tun ina mamakin yanda suka ki karewa har nazo nasan kaine kake turowa. Really bana son tuna duk wannan. Kawai i was so happy bayan haihuwar Nana and sad da baka nan. Sad da bansan ko inkana nan zaka so ta ba. So koma yanai rayuwa ba abin dubawa bace a yanzun. Kasan abu daya koda kai nisa. Ko yanda bana son in fada. Da kulawarka na rayu. Da kulawarka muka rayu duk shekarun nan ni da Nana. If bakai tunanin turo mun kudade ba........" Sauke numfashi tayi tana kasa karasawa. Muryarta a sarke tace. "Please mubar maganar nan. Baya ta zauna a baya. Mu duba gaba kawai" Hannunta ya kamo ya dumtse yanajin wani abu ya tsaya mishi a wuyanshi. "Kisani wallahi dazan iya. Da inada iko dana koma baya na canza komai" Dan murmushi tayi. "I know. I.... I love you" Ta fadi. Ware idanuwanshi yai da hakan yai mata yanayi da nana sosai. "Thank you." Ta daga mishi kai hadi da hamma. Dariya yai. Itama haka kamun suyi addu.a su kwanta. A karo na farko tun rasuwar nana da suka samu bacci.........! **** "Ina zamuje baka fadamun ba har yanzun yaya farhan" Kallonta yadanyi sannan ya maida hankalinshi kan tuqin da yake da murmushi a fuskarshi. "Home. Your home" Da rashin fahimta tace. "Bangane ba" "Zaki gane nuriyya....." Girgiza kai kawai tayi ta gyara kwanciya cikin kujerar. Ga mamakinta corner suka shiga. Bata sake mamaki ba saida taga sun nufi wani katon gida an bude musu. Kallon farhan take har yai parking. Sannan ya juyo ya kalleta. Fuskarshi da wani farin ciki yace mata. "Kin shirya ganin family dinki" Hannu takai tana rufe bakinta cike da mamaki. Idanuwanta na kawo hawaye. "Da gaske yaya farhan" Ya daga mata kai. "Da gaske nuriyya. Family dinki na jiranki" Ko ina jikinta rawa yake. Ta kasa cewa komai saboda gani take data sake bude baki zuciyarta fitowa zatao saboda dokawar da take. Tana kallo har farhan ya fita ya zagayo ya bude mata. Hannunta ya kamo ya fito da ita. Dakyar kafafuwanta ke daukarta. Dam ta rike hannun farhan dake cikin nata. Ta kasa yarda. Gani take da tai wani wrong motsi wannan mafarkin bacewa zaiyi. Kamata yai suka hau steps ukku dazai kaika kofar gidan sannan suka tura kofar. Farhan ya shiga da sallama. Muryoyi taji fiye da biyu sun amsa farhan. Idanuwanta cike suke taf da hawaye ba sosai take ganinsu ba. Blinking tayi tana fito da hawayen da suka tarar mata. Sannan ta ware idanuwanta tsakiyar falon. Kan wata mata idanuwanta suka fara sauka. Ta kuma kasa janye su saboda yanda take jin zuciyarta na wani irin abu. Wata irin kaunar matar na shigarta data kasa fahimta. Kaman daman can an halicci zuciyarta ne kawai dan ta kaunace ta. A hankali take takawa zuwa inda matar take tsaye idanuwanta itama kafe kan nuriyya da batasan tana karasawa ba. Tsakiyar falon suka hade da matar. Hannunta takai da yake rawa tana taba fuskar nuriyya. "Nuriyya....." Ta fadi. Hannunta dake fuskarta nuriyya ta kama ta dumtse tana jin wani yanayi da bata tabajin shi ba a rayuwarta. Batasan lokacin data rungume matar ba. Kuka suke a tare. Ko ba a fada mata ba zuciyarta tasan wannan mahaifiyarta ce. Sosai suke kuka kamun wani babban mutum dake tsaye yace. "Hajiya aikin saketa muma muganta ko" Sakinta hajiya karima tayi. Tana goge fuska kawai bata taba sa ran zata sake ganin yartata ba. Duk da kullum da tunanin halin da take ciki take kwana take wuni. Takowa yai. Hannuwanshi yasa ya tallabi fuskar nuriyya. Yana kallon yar tashi da suka cire rai da sake ganinta sai yau da farhan ya same shi yake mishi tambayoyi. Hawaye yaji sun zubo mishi kamun yai hugging nurriya suna ma Allah godiya. Sun dauki mintina a hakan kamun ya dago nuriyya yana goge mata fuska. Hannunta ya kama ya shiga janta wajen yayyanta maza har biyar. Sai kannenta su biyu maza. Ita kadaice ya mace da Allah ya basu. Yinin ranar cikin yan uwanta tayi shi. Dan farhan tafiyarshi yayi. Saidai bata yarda ta kwana ba. Duk yanda take so da yanda yan uwanta suka so. Ba zata iya barin farhan shi kadai ba bayan wannan halaccin dayai mata. Tai alkawarin shima saita sa ya nemi nashi yan uwan dan yaji abinda take ji itama. Wannan farin cikin wajen shi da ban ne. Girman kaunar yan uwantaka bata taba haduwa da wata. Allah ne ya hada jini daya waje guda. Shi kadai Yasan hikimar haka. Zumunci abune mai girman gaske.......! *#TeamAS* *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ www.Loobnerh.blogspot.com Wattpad: LubnaSufyan                49 *Abubuwa da yawa suna faruwa damu a rayuwa. Na bakin ciki. Na farin ciki. Sai dai a cikin kowannensu idan muka duba akwai darasi* *Zumunci na da girma. Wasu lokutan zumuncin dake tsakaninka da wanda baka hada jini dashi ba yana kaiwa mataki babba* *In zaka yarda karka yarda da yawa. Karka daga burinka akan komai. Ka yarda da Allah. Ka muka burikanka a wajen Allah. Sauran zasu zo da sauki* *Allah ya nuna mana Ramadan lafiya* *Farida Aminu.(A duk lokacin dazan kwanta da dare inda zan iya ganin yanda taurari suka tsaru muryark nakeji anty farida. "Baby ki kalli yanda Allah Yai ma sama ado da taurari masu kyau. Hikimomi na Ubangiji yawa ne dasu.)* *She was so sick. Ban taba ganin kalarki ba. Nakan tunaki da hawaye. Saidai girman murmushin saninki yakan rinjayi hawayen* *Auwal Aliyu.(Nai kuka. Nai kuka uncle auwal. Sai da baka nan nagane muhimmanci zumunci. Mutuwarka tazomun da darasi na fahimtar gaggawa cikin ziyara a duk lokacin dana samu dama* *Dalilai da yawa basu sa nasanka ba. Hakan bai hanani kewarka ta yanayin da bazai fadu ba. I wish and wish......* *Adam Abdullahi Gambo. (You raised me. Kana nan lokacin dana fara tafiya. Lokacin dana bude bakina. Lokacin dana dora tukunya danyin girkina na farko. A tare dakai nasan menene rayuwa. A tare dakai nasan menene hakuri. A taka rayuwar na samu shafukan nawa)* *Ba kakana bane kawai kai. Babana ne. Mamana ne. Yayata. Yayana. Abokina. Abokiyata. Alhamdulillah dana sanka a rayuwata* *Ummiee (Har yau idan wani ya kira LUBA da muryarki sunan yake karasowa kunnuwana)* *Me zance? Me zan fada akanki ummie? Ina kalaman suke? Ina kaunarki yayi kadan wallahi. Nayi kewarki bai isa ba* *Uncle sulaiman (Kewarka na damuna idan na duba abubuwa da dama. Ya Allah. Ban taba ganin fuskarka da wani abu daya wuce fara.a ba.)* *Allah ya jikanku. Allah ya sadaku da Rahmarshi. Allah ya haskaka kabarinku. Allah ya hadamu a aljanna in gaya muku kalar kaunar ku da nake daban samu na fada muku ba* *Wannan ba bankwana bane. Wannan yana nufin sai na taho* *SA.ADATU HABEEB (May Allah ease your pain and suffering. May Allah make your departure an easy one)* *I..... I feel your pain? Scratch that. I will never know what you are going through. It just hurt a lot (Allah kaine abin godiya a kowanne hali) *#AnaTare* *Saura epilogue in shaa Allah* *BAYAN SHEKARA DAYA* Wani irin zama su jana suke mai natsuwa. Duk da wata doguwar hira bata hadata da ayna. Yara dai tunda ita tama fita zama dasu. Wani lokaci ma ko tana gidan ayna ke kula dasu. Hakan bai dameta ba. Tadai saka idanuwa ne saboda taga ko yanayin tarbiyar da ta dora yaranta akai ya sake. Ga mamakinta sai dai ya karu. Kananan abubuwan da bata tsayawa ta kula ko ma tace bata da lokacin kula dashi ayna na tsaya mata akan hakan. Yau ma kaman kullum ta gama shirinta tsaf da yake dakinta jabir yake kuma yama rigata shiryawa tare zasu fita. "Jana sai mun latti ko?" Ya tambaya yana sake duba agogon dake hannunshi. Da murmushi a fuskarta tace. "Ka tafi inka gaji da jira" "Zaki hau napep kenan?" Ya bukata yana tabbatar da idanuwanshi sun sauka cikin nata kamun yai tambayar. Yana kallon yanda take wani matse labba yasan tsokana ce fal cikinta. "Kadai hau napep honey j" Dafe kirji yayi. "Yes. Ka manta motata ce? Inkuma ayna zata ara maka tata ne to kaje ka amso" Rausayar dakai yai gefe "Allah ya horemun in sake siyan wata motar yanda in dayar ta samu matsala ba sai an mun goriba" Dariya jana tayi sosai. "Amin. Ko in ara maka? Ka siya inka samu ka biyani" Karasawa yayi inda take ya zagaya hannuwanshi zai rungumeta ta mike da sauri. "Nagama shiryawa" Girgiza mata kai yake alamar bai yarda ba. "Zo nan kiga in tayaki" Pillow ta dauka kan gadon ta jefa mishi tana daukar jakarta. Ya rike yana dariya. Tare suka fita. Jana ta tsaya a falon ya wuce bangaren ayna ya fada mata sun wuce. Bata daukarma kanta gulmar yima ayna sallama ba dan zata tafi work. Tana danne abubuwa da yawa. Saidai bata takura kanta ba. Shi dai da yake wajibi akanshi yayi. Sai dai ayna ta burgeta yanda kullum ko da jabir na dakinta saita zo da kanta sun sallama da janar. Fitowa yayi ya ce ma jana. "Bata da lafiya. Zazzabi ne ruf jikinta" "Subahanallah......" Jana ta karasa tana ture jabir din ta wuce dakin ayna din. Karo na farko sa kafafuwanta suka taba taka bedroom din ayna a shekara daya datai a gidan. Koma tace bangarenta gabaki daya. Sai dai insun hadu a babban falo sannan. Sosai ta dudduba  ayna. Sannan ta taimaka mata ta tashi daga kan gadon. Take fadama jabir sai sunje asibiti dole. Bai musa ba ya bata mukullin motarta ya dauki na ayna din. * Abinda jana take zato ne. Ta lumshe idanuwanta tana danne wani kishi da take jin ya taso mata. Wayarta ta dauko ta kira jabir. Ringing din farko ya daga. "Albishirinka amman saika bani goro" Tana jin murmushin da yake cikin muryarshi. "Saikin zabi kalar goron da kike so. I promise" Yar dariya tayi. "Ayna nada shigar ciki sati hudu" Tana jin yanda yaja numfashi hadi da fitar dashi kamun addu.o.i su biyo baya. Sosai ta rintse idanuwanta. Hakan dayai ba bakon abu bane saboda itama yayi duk cikin yaransu. Ta rasa ko menene na jin kishi a ciki. "Thank you jana. I love you. Ki zabi goronki" Saida tadan yi jim tana son danne abinda take ji kamun tace. "Sai nayi tunani tukunna. Barin fada musu ina da patient mu koma gida. Babu dadi in kaita in barta ita kadai" "You don't have to do this jana. Atika na nan ai" Girgiza kai tayi. "Badon kai nayi ba. Ko ni. Nayi saboda karamcin da ke tsakanin su da yarana." Shiru jabir yadanyi kamun yai mata sallama. * Kaman yanda ta fada hakan tayi kuwa. Har daki ta raka ayna ta tambayeta ko tana bukatar wani abun tace mata aa. Sosai tai mata godiya. Murmushi kawai tayi ta fada mata tana dakinta indai tana bukatar wani abu ko flashing tai mata sannan ta fice. Gyara kwanciya ayna tayi. Jana mutuniyar arziqi ce. Bakowa ne zai dace da kishiya irinta ba. **** Zaune suke tana yanke ma farhan farce. Sukaji sallama da sauri ta saki kafarshi ta mike tana amsawa. A fadace yace. "Nuriyya ki daina saurin mikewa haka. Saikin jika baby na ciwo ne ke kam?" Dariya tayi tana mamakin farhan. Cikin da bai wuce sati uku ba ko motsin kirki bata da ikon yi sai yayi fada. Sosai fara.arta ta karu ganin anty maimuna. "Anty maimuna. Sannu da zuwa" Nuriyya ta fadi. "Ki kara so mana" Da fara.a a fuskar anty maimuna ta karaso dakin. Farhan ya kalleta yana murmushi. "Anty maimuna. Ina wuni" Saida ta samu waje ta zauna sannan tace mishi. "Lafiya kalau farhan. Ya mai jiki?" Ya amsa da "Ta warware sosai anty. Muna cewa mu samu lokaci mu shigo mu gaishe daku" Zuwan nuriyya ya katse musu hirar. Lemo da cup ta ajiye ma anty maimuna a kasa. Ta na samun waje gefe ta zauna. "Aikam dakin bar drink din nan. Daga gida nan nayo fa. Ya jiki?" Murmushi nuriyya tai a kunyace. "Naji sauki" "Allah ya kara sauki ya raba lafiya" Farhan dake zaune kan kujera ya amsa da. "Amin thumma amin" Zungurinshi nuriyya tayi tana mamakin rashin kunya irin ta farhan. Anty maimuna kanwar babanshi ce uwa daya uba daya. Mikewa anty maimuna tayi. "Bara kuga inzo in wuce. Nan har gidan hajja zanje" "Anty wannan irin zuwa da wuri haka?" Cewar farhan. Nuriyya ta karbe da fadin. "Wallahi kuwa. Daga zuwa sai tafiya" Dariya anty maimuna tayi. "Daman jikinki nazo dubawa. Zumunci ai yanzun aka fara in banda abinku. Duk ana tare" Har kofa suka rakata suna shigowa nuriyya tasa kafadarta ta ture shi. "Kai ko? Harda cewa amin. Kasa inata jin kunya" Dariya sosai farhan yayi. "Jimun ke please. An mana addu.a me kyau bazan amsa ba?" Turo baki tayi tana dakuna mishi fuska. Hannuwanta ya kamo yana janta jikinshi. "Me nace kan turo bakin nan a gabana?" Kanta ta boye a kirjinshi tana dariya. Rungumeta yai tsam a jikinshi yana jin duminta. Yana godema Allah daya tsara mishi rayuwarshi da ita a cikinta. Yana kuma sake gode Ma Allah da yasa ya bi shawarar nuriyya ya nemi dangin babanshi. Laifin babanshi mai girma ne a gare shi. Waya sani wata rana ya iya yafe mishi. Ba zaka taba fadar me zai faru dakai ba a rayuwarka. Sosai ya sake matse nuriyya a jikinshi. Kasa kasa tace mishi. "Idan mace muka haifa sunan ta farhana in shaa Allah" Murmushi yayi. "Idan namiji ne sunanshi nawaf" Dago wa tai daga jikinshi hawaye ba taruwa a idanuwanta. Wasu irin emotions na mata yawo. "Da gaske? You will name him that?" Kai ya daga mata yana sa hannu ya tallabi fuskarta. "Da gaske sunanshi nawaf. Indai muka haifi namiji ko ba wannan cikin ba" Sumbatarshi tai tana nuna mishi godiyarta. Kamun ta kwantar da kanta a kirjinshi. "I love you. Thank you" "I love you more. Allah ya jikan nawaf" Ta amsa da. "Amin. Allah ya jikanmu muma. Munfi nawaf bukatar wannnan addu.ar saboda karshen shi yayi kyau. Namune abin tsoro" "Shhhhhhhhh. Zaki kashemun jiki" Farhan ya fadi. Dan maganganunta sun tsorata shi lokaci daya. Kuma sun shige shi. Dariya nuriyya tayi. "Idan jikinmu yana sanyi lokaci lokaci kilan yasamu shiryama mutuwarmu kamun ta same mu" Sauke numfashi yai. Yai shiru yana jin duminta da kamshinta. Lokaci daya kuma maganganunta na zauna mishi. **** Blocks din robar dake gabanta take shiryawa kaman katanga. Mimi dake zaune saitasa hannu tarwatsa tana wata dariya dake saka safiyya dariyar itama. Sunkai rabin awa zaune suna wannan shiriritar. Intai dariya saitai wani gwaranci da ita kadai take son fada. A shekara daya mimi yarinya ce mai cikakkiyar lafiya. Gashi bata da rikici sam. Indai tayi kuka to bata da lafiya. Indai da kayan wasa to bata da matsala. Tun ranar sunan mimi safiyya tai resigning. Tagaji da aiki. Tunda fu.ad na tsare mata duk abinda take so. Tana son bama Mimi dukkan kulawar da take bukata. Sallama safiyya taji. Sake baki tayi tana kallon fu.ad daya turo kofar ya shigo. Ware mata idanuwa yayi. "Ki amsa sallamata ba kina mun wannan kallon ba" "Seriously ka gudo daga kasuwa ne ko?" Dakuna fuska yayi. "Ni ban gudo ba. Kuma akwai su lawal a shagon. Missing ya'ta nake na zo in ganta" Karaso wa yai falon hadi da fadin. "Hey sweetheart. Dad is home" Tanajin muryarshi ta ci gaba da doka hannuwanta tana tarwatsa blocks din tana dariya. Kallon safiyya yayi dake fassara kingani itama tayi kewata. Girgiza kai safiyya tayi da murmushi a fuskarta. Fu.ad sai abarshi. Haka yake yi daga kasuwa zai gudo gida yaga mimi sannan ya koma. Wani lokacin ma daukarta yake yi. Sai safiyya taita fada tukunna. Wasu ranakun saidai tagaji tabarshi. Hannu yasa ya dauki mimi yana hada goshinshi da nata. Yarinyar ta saba wasan da yake mata. Ita ta soma girgiza kanta jikin nashi suna dariya tare. "Mimi is so cute. She is so cutee" Dariyarsu tabama safiyya dariya sosai. "In zubo maka abinci ko?" Ta bukata. Ya girgiza kai. "Restaurant naje naci delicious" Mikewa safiyya tayi tana kallon shi. "Res....  Me? Aidaka kirani kace kar insa abinci dakai. Zaka je kaci wanda yafi shi dadi" A kasalance ya kalleta. "Nikam banajin yin ringima sofi. Yunwa naji and restaurant din yana kusa damu. Mukaje muka ci abinci. Ba saiki barshi da dare muci ba?" Sosai take kallonshi. "Da daren ma kaje restaurant. Akwai wani a kusa damu" Ta fadi ta na matsawa hadi da karbe mimi daga hannunshi ta juya da yarta a hannu tana barin falon. Dariya fu.ad yake sosai. Yana so yaga safiyya na fadan nan. Kyau take kara mishi kaman ya mayar da ita cikin shi. Saida yai mai isarshi sannan ya tashi ya bita bedroom din. Tana zaune kan gado da mimi a tsakiyar gadon. Sarai taji shigowarshi. Taqi juyowa. Tsayawa yai wajen katon hoton nana daya ke cike da bangon dakin ya kalleta. Yana jin wata irin kewarta taban mamaki. Hannu yasa ya shafi kumatunta a jikin hoton. Sannan yadan daga kafadarshi. "Mumynki fushi take mun. Harda kwace Mimi daga hannu na bayan tasan saboda ita kawai na baro da kasuwa" Shiru yai. Zai iya rantsewa yaji sautin dariyar nan ta nana dake saka shi farin ciki na daban. "Yeah mumynki akwai rigima sosai" Juyowa safiya tayi. "Dadynki akwai son kai sosai. Ya fada miki kome yaimun. Abinci fa a restaurant bayan yasan ni kaina bana iya ci saiya dawo" Kallon hoton fu.ad yayi ya daga girarshi da ke fassara mumynki bata karantata kaman yanda kikeyi. Yasan da tana nan tunda ya bude baki zata gane wasa yake. Sannan ya juya ya taka har inda gake. Gefen gadon ya zauna. Ya dauko mimi ya dorata kan cinyarshi sannan ya kalli safiyya da take wani basar dashi. "Ki kalle ni sofi" Kauda kai tayi gefe. "Please........ Sofiii" Ya fadi yana jan sunanta yanda yasan ba zata iya mishi gardama ba. Juyowa tayi ta sauke idanuwanta cikin nashi. "Goodness. Kina kyau da fada" Naushin shi tai a kafada. Ya wani dakuna fuska yana fadin. "Ouchhh yi hakuri sofi" Hannuwanta tasa ta matse mishi kumatu tana fadin. "Kasan in akwai abinda na tsana baifi kaci abinci a wani waje ba" Ture hannunta yai yana gyara ma mimi zama kan cinyarshi. "Ki kyaleni nikam. Yunwa nakeji cikina sai ihu yake tun dazun" Dariya tayi tana mikewa. Wani irin jiri ya dibeta ta tafi luu. Da zafin nama fu.ad ya fisgota yana zaunar da ita kan gadon. Kanta ta dafe da hannuwa biyu tanajin yanda dakin ke wulwula mata. A rikice fu.ad ke fadin. "Subahanallah. Sofi menene? Lafiyarki kuwa?" Gaba daya hankalinshi ya tashi. Saida tadanji jirin ya fara tsaya sannan tace mishi. "bakomai fa. Kawai ina jin jiriri ne wasu lokuttan" Muryarshi babu alamun wasa a ciki yace. "Tun yaushe?" "Wajen sati biyu. Amman bai fara damuna ba sai kwana biyun nan" A kufule yace. "Sati biyu sai yanzun nake ji? Damn it sofi in wani abu ya same ki fa?" Ganin yanda ya birkice yasata dafa hannunshi. "Really ba wani babban abu bane ba. Kawai jiri ne. Babu inda kemun ciwo banda shi" Ture hannunta yayi. "Tashi mu tafi asibiti" "Ba wani......." Kallon dayai mata yasa ta katse maganar. "Kaci abinci sai muje" Muryarshi a dake ya mike da mimi a hannunshi. "Bana jin yunwa" Mikewa tayi tana dafa shi da fadin. "Kayi hakuri" Kallonta yai taga yanayin dake cikin idanuwanshi. "Har yau inajin cewa kaman da nazo da wuri nana zata kasance tare damu. Nasani ba tunani me kyau bane ba. Amman na kasa dainawa. What if wani abu ya sameki? Dan Allah karki sakemun irin wannan. Da ciwo sosai" Jikinta a sanyaye tace. "Bazan sake ba. Please kayi hakuri" Dan dafe kai yayi. "Ya wuce. Dauko mayafinki muje mu dawo" "Dakaci abincin sannan" "Abinci can wait. Saimun dawo" Tasan halinshi.  Tsayawa gaddama babu amfanin dazai dan haka ta wuce ta dauki hijab dinta ta saka. Suka fita. **** Kallon jana suke su dukansu. Kallonta suke kaman kaho ne ya fito mata tsakiyar kai da maganar data gaya musu. Kallon da suke mata ya bata dariya sosai. "Wai menene kuke kallona haka? Nace matarka nada ciki na wata daya da sati biyu. In baku gane turancin ba" Safiyya kallon fu.ad take zuciyarta na wani irin dokawa. Shima kallonta yake lokaci daya maganganun doctor din daya jagoranci yi mishi surgery na vasectomy suka dawo mishi. Cikin harshen turanci yake fada ma fu.ad din cewar. "Ko da bayan shekaru ko watanni matarka ta samu ciki karka zargeta. Ka dauka jikinka ya warkar da kanshi. Yana faruwa ga wasu mutanen." Hannu fu.ad yakai yana tsane gumin daya tsattsafo mishi. Zufa yake ta ko ina. Ta bakinshi yake jan iska saboda ya daina jin shigarta na wani lokaci. Mimi ya sake gyara ma zama kan jikinshi. Su dukansu sun kasa magana. Hawaye ke zubo ma safiyya wasu nabin wani. Tunani take wanne kyakkyawan aiki ta yi da Allah ya bata wannan kyautar. Shi ka shi fu.ad tunanin da yake kenan. "Oh Allah. Ina bayin da suka sake ka suka kama waninka? Hakika suna cikin bata mai muni" Ya karasa maganar yana jin wasu hawaye masu dumi sun zubo mishi. Hannunshi safiyya ta kamo da nata duka biyun. Ya dago dasu ya sumbace su saboda mimi dake hannunshi. Ya kasa tsaida hawayenshi. Allah Ya dube shi da Rahma ya mishi kyauta daya yanke rai da samunta. Hakika indai kana da rai. Baka fidda rabo. Saidai Rabonka yai jinki. Inda Allah ya rubuta maka shi to saika samu. Mimi kaman tasan farin cikin da suke. Ta kyalkyale da dariya. Kallonta sukai a tare suna murmushi though hawayen da suke zubdawa. Doc jana kuwa gyara zama tai tana kallon su tana koyan darussa masu dama daga rayuwarsu. Da murmushi a fuskarta. Kallon cikin safiyya fu.ad yayi ya kalli mimi. Ita kuma kallonshi take. Lokaci daya abinda su duka biyun suke tunani ya bayyana a fuskarsu. Hannu safiyya takai da sauri ta karbi mimi tana rungumeta. Hawaye na sake zubo mata. "No please. Ba zasuyi mana haka ba" Yanda tai maganar yagane so take ya tabbatar mata. Sadda kanshi kasa yai da wannan sabon farin cikin daya same shi fargaba na rabuwa kusa dashi. Mikewa yayi ya mika mata hannunshi tasa nata ciki suka juya. Jana murmushi ta sake yi dan ganin sun tafi wata duniya ta daban. Sanda suka samu natsuwa sun nemeta. **** Daga bedroom ya fito zee na zaune a falo kan kafet da plantain chips a gabanta tana ci tana danne danne da wayar lukman din. Kusa da ita ya tako ya zauna. Hannu yakai zai dibi chips din ta janye. Dakuna fuska yayi. "Bani wayata nima. Wai meye ma amfanin wayarki? Kullum sai kin cinye mun charge" Dariya tai tana janye wayar gefe. "Taka tafi dadin amfani" Kallonta yai yana daga mata gira. Dan wayarta tafi tashi tsada da komai. "Muyi musanya to" Makale kafada tayi. "Ni dai ka kyaleni ina karatuna" Kwanciya yayi yai filo da cinyarta ta ture kanshi. Ya sake komawa. "Dee ka dagani. Duk ka mokalemun ci nya." Dariya ta bashi sosai. "Dan kan nawa guda nawa yake? Nafijin dadin kwanciya anan dinne kawai" Cikinta ya kalla. "Nifa na kagu inga ajiyata ta nuna" Murmushi zee tayi. "Kwanan shi nawa dazai fito? Dan ba a jikinka yake girma bako?" Gyara kwanciyarshi yayi. "Da kinga yanda ake laulayin ciki kuwa." "Allah ko? Me zakayi?" Juya kwanciyar yai yana kallon fuskarta. "Ai ko wanka sai kinmun. In na zauna waje daya sai dai ki daukeni ki mayar wani waje in nagaji. Ke abinci ma inba a baki ba kuka zansa. Rikici kala kala" Jinjina kai zee take da wani murmushi a fuskarta. Mikewa lukman yai daga kan cinyarta yana kallonta muryarshi babu wasa yace. "Wallahi wasa nake miki." "Aifa. Ashe ni wahala nake sha. Ga yanda ya kamata ace ina yi......." Katse mata magana yai da fadin. "Aa wallahi. Yanda kike yin nan ma ya isheni" Girgiza kai tayi. Zatai magana kenan sukaji sallamar su fu.ad. Da fara.a suka tarbesu. Zee ta kawo musu ruwa da lemo. Bama su sha ba. Mimi na hannun fu.ad tana bacci. Yanayin sanyin jikinsu lukman ya kalla. Yasan akwai damuwa a tattare dasu. "Lafiya dai ko?" Ya tambaya cike da kulawa. Takardar dake hannun safiyya fu.ad ya karba ya mikama lukman. Cike da rashin fahimta ya karbi takardar ya duba. Ta asibiti ce. Sunan safiyya ne rubuce a jiki. Wani irin dokawa zuciyarshi tai ya soma dubawa babu wata nutsuwar kirki a jikinshi. Idanuwa ya ware. Yana sake daga takardar yana dubawa. Mamaki karara a fuskarshi. Fu.ad ya kalla da ya zuba mishi idanuwa da wani irin yanayi. Sakkowa fu.ad yai daga kan kujerar gwiwoyinshi a kasa gaban lukman. Safiyya ma sakkowa tayi hawayenta har sun soma zuba. Kan fu.ad na kasa yace. "Daga asibiti nan muka zo. Bamu je ko ina ba. We have to know. We need to know ko hakan zaisa ku karbeta......" Da rashin fahimta zainab take kallon su duka ukkun. Dan taga alama ita kadaice bata fahimci meke faruwa ba. Takardar dake hannun lukman ta karba ta na dubawa. "Please don't take her away. Please lukman wallahi......" Kasa karasawa fu.ad yayi saboda yanda wani abu ya tsaya mishi a wuya. Ga kirjinshi na wani irin zafi. Kallon Mimi yake dake baccinta a jikinshi. Hannunta daya rike gam da rigarshi. Wani zafi yake ji a kirjinshi kaman wuta. Tunanin rabashi da yarinyar nan kawai ji yake zuciyarshi na neman bugawa. Wasu hawaye masu zafi suka zubo mishi. Safiyya dake gefen fu.ad taja hijab dinta ta goge idanuwanta muryata na sarqewa tace. "Zamu..... Zamu hakura da babyn jikina.....dan Allah kubar mana ita" Kallon zainab lukman yayi. Muryarshi dauke da wani emotions da ya kasa tsayarwa akan komai yace mata. "Kingan su ko zee?" Ita har sun sakata hawaye ma. Tasa hannu ta goge su. Har ranta tana musu murnar kyautar nan da Allah yai musu. Kuma zuciyarta na mata wani irin yawo kan kaunar da take karanta suna ma Mimi. Kaunar da ta dauka jininka ne kawai zakai ma. Ko tsakanin fu.ad da lukman ta fahimci akwai yiwuwar bare yai maka kaunar da dan uwanka ne zai maka. "Allah saina fada ma abbah abinda kaimun. Taya ma wannan banzan tunanin zai zo maka? Safiyya kema ya shafa miki yarinta ko? Allah zaku sani idan na fadaku da abbah" Dago kai fu.ad yayi ya kalle shi. Yasa hannu ya goge fuskarshi. Muryarshi a dakushe yace. "You are not a fucking kid lukman" Hararshi lukman yayi. "Kasan fu.ad ai ko? To ka kalle shi zaka san na girma sosai. Marar hankali kawai. Wallahi da ba gaban yarka bane saina kwada maka mari ko zaka dawo hankalinka" Zainab ta fara dariya. Kamun safiyya ta dauka. Fu.ad kanshi murmushi yake. Lukman kam ya kasa ganin abin dariya har yanzun. "Kubarmun gida please. Ku tafi kamun ku kara batamun rai" "Sorry......." Fu.ad ya fadi. Sake dakuna fuska lukman yayi. "Please...." Kallonshi lukman yai ya ware idanuwa. "Dan sake cewa please muji?" Dariya fu.ad yayi. "Fucking grow up" Dariya sukayi a tare. Kamun in a serious murya fu.ad yace. "Nagode. Kamun abinda ko haneef baimun shi ba lukman. Kaunarka a gareni mai girma ce. Taya zan iya biyanka?" Dafa kafadarshi lukman yayi. "Ka kasance dan uwana har karshen rayuwata. Ka kasance cikin farin ciki gwargwadon iyawar ka. We are even" Wasu hawayen fu.ad yaji sun cika mishi idanuwa. Baisan me ya same shi da kuka ba kwanakin nan. Sai dai kawai yaji suna fitowa. "Hakika hanyoyin Ubangiji Masu Girma ne. A kanku na yarda ko asibiti ka hadiye in Allah yai niyyar baka kyauta baka isa ka kauce mata ba. Akanku na yarda da cewa a dukkan hakuri akwai riba. A dukkan tsanani akwai sauki saidai jinkiri zai iya samuwa. Allah ya dawwamar muku da farin ciki" Cewar zainab da takejin wata nutsuwa ta daban. Ko da family dinta basu damu da ita ba. Ga wasu da bata hada jini dasu ba tana jinsu har cikin jininta. A kasalance safiyya tace. "Hmm zainab. Amin. Amman Allah ya bamu zuciyar karbar jarabawarshi shine addu.ar da muka fi bukata. Da yawan farin ciki da yawan jarabta. Wannan shine asalin Kusancin mu da mahaliccinmu" Kai suka jinjina cike da jin maganganunta. Ganin yanda jikin kowa yai sanyi yasa lukman cewa. "Kunsan da nana taga fuskokin ku me zata ce? Nayi laifi ko? Uncle ya naga kowa is looking so serious?" Yanayin muryarshi da tuna Nana yasa su dariya su dukansu. Nana ta musu nisa amman memories din data bar musu nasa su farin ciki. Har bakin mota su lukman suka rakasu. **** Saida suka biya gidansu inna. Babu wata kunya fu.ad ya fadama su inna kyautar da Allah yai musu. Addu.a sukai musu gabaki daya kamun su wuce gidansu fu.ad. Yana parking din motarshi suka fito suna cin karo da haneef. Gaisawa yayi da su yana tambayar ya mimi. Mika mishi ita safiyya tayi yaga bacci take yace tabarta karsu motsata ta tashi. Wuce wa cikin gida safiyya tayi abinta. Tabarsu nan. Hugging din haneef fu.ad yayi cike da farin ciki. Harya sake shi da mamaki a fuskar haneef. Kamun fu.ad yace. "Allah heal me haneef. Sofi ciki gareta" Ware idanuwa haneef yayi kamun jikinshi yai sanyi. "Allahu Akbar. Allah kenan fu.ad. oh.  Alhamdulillah" Sosai haneef yai murna da mamaki da kuma jinjina lamari na kaddara. Kamun suyi sallama fu.ad ya shiga cikin gidan. Safiyya ya samu da momma a zaune. Sallama yai ko jira momma ta amsa baiba ya karasa tsakiyar falon ya zauna kasa. Kafafuwanta ya kama da hannayenshi yana dora kanshi a cinyarta. Wai saida yazo gabanta girman abinda ya samu ya sake lillibe shi. Hawaye ke zubo mishi. Ya rasa bakin dazai fada ma momma wannan labarin. "Fu.ad lafiya? Subahanallah. Safiyya me ya faru?" Sadda kanta kasa tayi. Kukan da fu.ad keyi nasa hawayenta sake zuba. Jin yanda momma ta daga hankalinta yasa shi cikin kuka fadin. "Momma sofi ciki take da. Zan sake haihuwa. Momma addu.arku a kanmu da albarkarku tayi tasiri." Hamdala momma take. Addu.arta kullum bai wuce Allah ya basu rabo ba. "Fu.ad ai abin farin ciki ne bana kuka ba" Dagowa yai gana goge fuskarshi. "Kukan farin cikine momma." Murmushi tai musu. Basu jima gidan ba suka wuce.....! **** Tsakiyar dakin suka tsaya. Mimi na hannun safiyya. Mayafinta ta cire ta ajiye. Tana kallon Mimi sannan ta kalli fu.ad. "Allah ya jikan Nana. Zata so ganin wannan ranar" Karasowa fu.ad yayi kusa da ita yana hade sauran space din dake tsakaninsu. Yasa hannu ya dago da habarta. "Tana inda yafiye mata nan sau dubu. Saimu cika aikin daza mu sameta" "Allahumma amin" Safiyya ta fadi da murmushi. Rikota yai ita da mimi jikinshi yana kissing goshinta. "Alhamdulillah da rayuwarmu ta baya ta koya mana darussa da dama. Alhamdulillah da rayuwar da muka samu yanxun. Alhamdulillah da duk tsarin da Allah yai mana nan gaba" Rikoshi tai da dayan hannunta tana jin wata kaunarshi ta daban tana ratsa ta. "Ina sonka sosai. Kaddarar data hadamu ta koya mana darussa da dama. Alhamdulillah" Murmushi yayi. "Ta kara mana imani. Alhamdulillah. Ina sonki sosai" Ya fadi yana lumshe idanuwanshi. Wata nutsuwa na ratsa shi. Tabbas duk wanda ya Rike Allah ya yarda da Kaddara mai kyau ko marar kyau yana tare da Nasara. *#TeamAS* *💘💖AKAN SO💖💘* ~Written by~ :Luβπα Sufyαπ www.Loobnerh.blogspot.com Wattpad: LubnaSufyan           50 *EPILOGUE* *Tabbas zan kewar characters din dake cikin AS gabaki dayansu. Sai dai ina jin dadin yanda suka taba rayuwata ta fanni da dama. Da kuma yanda suka taba rayuwar readers din* *Abu uku daga Luβπα Sufyαπ zuwa ga dubban mutanen dake nuna mata kauna* *1. Rayuwa makaranta ce mai fadin gaske. Zata hadaka da mutane kala kala. Zata tabaka ta inda baka zato. Ta wani fannin farin ciki. Ta wani fannin akasin hakan. Ka riqe ALLAH a komai* *2. Kaddara. Banda kalaman da zan amfani dasu wajen kokarin fassarata. Saboda haka zance duk kalar daka tsinci kanka a ciki. Abu biyune mafita. Ka karbeta sanin kana daga cikin masu kusanci da Ubangiji. Mummuna ko mai kyau. Ka riqe ALLAH a komai* *3.Zumunci da hakuri. Abubuwane da suke gogayya da juna a lokacin da rayuwa ta tabaka ta rukuni da dama. Karka duba kalar kaunar yan uwanka a gareka. Ba wannan bane mai muhimmanci. Ka duba girman kaunarka a garesu. Ka riqe ALLAH a komai. Zai kasance dakai a komai* *Nagode. AnaTare. Like sosai AnaTare. Like seriously AnaTare. Irin totally AnaTare* "I feel ridiculous cikin kayan nan wallahi" Dakuna fuska safiyya tayi tana balle mishi maballin rigar. Ta kalle shi sosai. Kalar shaddar ruwan kasa ne mai haske sai yai shige da idanuwanshi. "Kaga yanda kai kyau" Damqe fuska yai yana jin gabaki daya manyan kayan sun takuranshi. Duk ya shake. "Nikam dakin barni nasa riga da wando abuna" Daure fuska safiyya tayi. "Ka kalli luku da mimi sun girma. Ko affa (Mai sunan baban safiyya) ya girma. Yaushe zaka fara saka manyan kaya. Oya muje" Fuska a daqune da alamar takura ya fita falon. Mimi ce a zaune da litattafan islamiya baje a kasa tana assignment. Jin tafiya yasa ta dago. Sauke idanuwanta tai kan fu.ad lokaci daya ta yamutsa fuska. Kallonta safiyya tayi. Gaba daya expressions din nan irin na fu.ad ne. Duk ya koya mata. "Menene wannan kasa dady?" Ta tambaya fuska a yatsine. Hararta safiyya tayi. Fu.ad ya kalli safiyya dake fassara 'Bana gaya miki ba'. "Kaya sunan su. Manyan kaya" Safiyya ta amsa ma mimi. "You look different" Mimi ta fadi tana maida kanta wajen assignment din da take. Karasawa fu.ad yayi bai damu da zaman dayai a kasa zai squeezing mishi kyanshi ba. "Daban in a good or bad way?" Ya bukata. Dagowa mimi tayi tadan murmushi ta rausayar da kanta gefe alamar tana tunani. Dakuna mata fuska fu.ad yayi. Hakan ya bata dariya. "Kana sakawa ko yaushe. In a good way" Murmushi yayi. "Kome queen take so" Ware idanuwa safiyya tayi. "Tunda yar ka tace kayi kyau ka yarda. Ni da na fada ai baka dauka ba" Kallonta Mimi tayi da smug face. "Yafi sona ko dady?" Tsare shi da idanuwa safiyya tayi. Yadan ware mata idanuwa. Mikewa yai daga kusa da mimi ya taka inda take. Idanuwanshi ya sauke cikin nata. Godiyarshi da kaunarta yake nuna mata. Yake son tabbatar mata. A shekaru goman nan rayuwa ta musu wani irin sauyi naban mamaki. Allah ya musu kyauta yara har biyu bayan mimi dukkansu maza. Yanayin kallon da yake mata ya kashe mata jiki. "Ina sonki sosai" Ya fadi kasa kasa. Dakuna mishi fuska tayi alamar Mimi na falon. Dan juyawa yayi yaga bama ta su Mimi take ba. Rankwafawa yai. Tai saurin matsawa. Da sauri ta juya tai bedroom dinsu. Yabi bayanta. Yana shiga tasa hannuwanta jikin wuyanshi. "Kai ko" Tarin wasa ya fara. A dole ta shaqe shi. Sauke hannayenta tai tana dariya. "Ka bata mun yarinya. Duk irin abinka ta dauka" Cute face yai mata. "Like daughter like dady" Murmushi safiyya tayi. Tana kai hannu tare da ja mishi hanci. "Allah ya rayamun ku" "Amin. Tare dake ma" Ya fadi yana janyota jikinshi. Sumba ya manna mata mai taushi a lips. "Alhamdulillah da kyautar iyalai irinku" Ta amsa da. "Alhamdulillah da kaddara irin tamu" Lumshe idanuwanshi yayi. Yana hugging dinta jikinshi. "Ina tunanin me Nana zata ce ne da zata ganni da wannan kayan" Dariya safiyya tayi. Cikin kwaikwayon muryar Nana tace. "Dady me mumy ta baka kasa haka?" Sosai yake dariya da dukkan zuciyarshi. Yanajin dadin yanda har yau memories din Nana na saka su farin ciki irin wannan. Ta wani fannin yana jinjina ma rayuwa. Yana kara ganin yanda take tamkar makaranta. Kowa da yanda zai fahimci tashi.............!!! Nikuma anan nake muku sallama. Da fatan alkhairi a rayuwa gabaki daya. ********************** ⬇ ************************** ********** Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** *ALHAMDULILLAH* *Aliyu tsagem. Fahad. Ayna.u mardiyya. Ummie jafar. Yusra abdu fari. Biebie Isa. ALLAH YA SADAKU DA ALKHAIRI A DUK INDA KUKE* *Whatsapp* Daukacin wa.annan groups din - Taskar novels. - Taskar Lubabatu maitafsir -Taskira -Ummie jafar novels -Billy galadanchi novels -Da sauran da ba zasu lissafu ba. *Ina godiya da karamcinku. Ina muku fatan alkhairi a duk inda kuke* *WATTPAD* *Bazan taba iya lissafo gabaki daya sunayenku ba. Ku sani. Wallahi dukkan comments dinku yana da muhimmanci gaske a wajena. Dukkan kwarin gwiwarku yana da tasiri a rayuwata data rubutuna gabaki daya. Kaunata a gareku mai girma ce* *Architect ishaq (Bifham) fatana a gareka guda dayane. (Ka zama cikin nutsuwa da kwanciyar hankali) *YAYA. (Kana nan a bakin ciki da farin ciki. Kana nan sanda na rasa hope akan komai. Kana nan a ko ina. Ina fatan Allah ya kasance dakai a ko ina na rayuwarka) *Allah ya hadamu a aljanna* *Ina neman gafarar duk wanda na batama. Na yafe ma kowa. Laifin dayaimun a bisa sani ko rashin sani. Allah ya yafe mana gabaki dayanmu. Amin amin* *AnaTare* *ALLAH YA NUNA MANA RAMADAN LAFIYA* (Amin thumma amin)