********************** ? ************************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************? ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ? ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ? ************************** AUREN FANSA 01 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _AUREN FANSA_!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM! Wannan shafin tukuci ne gareku members na pure moment...! FATY AXLAND SUHANA JANNART, AUNTY KHADY, HUSNAH, DEEJA WAZIRI, ZEE YABOUR, UMMUHANEEF, MOMYN SULTAN, UMMYN YUSRAH, ZARAH SURBAJO, MOMYN KHADIJA, UMMA YAHYA MUSA (SISIN MAMA), BIEBIE DEE, NANA FA'AD, FAtY MANSUR (XARAH), FATY KHALID NA SHUKA, SHAFA ABDUL, SUMYNBASH, SALMA ALI WADA, ROOKY KAZ, AISHA ALI GARKUWA, UMMI HAMBALI, UMMEE GARKUWA, RUFAIDA YUSUF, HAFSAT MUSA, SADNAF, FHARIEEDAT, RAFEE'AT, SAMRAH, BIBA WADATA, SEEMALUV, NEERATU LUV, AYSHA HANWA, AYSHA GANA, UMMU SAFWAN, DELU CHOGAL, MRS FAWWAZ (YESMEN TAFEESU), RAFI'AT DIKKO, MAMAN IHISAN.❤️💖🌹 🌹01 🌹 Sautin kuka ne ke tashi a cikin d'akin, daga jin mai yin kukan har cikin ranta takeyin shi, wanda zan iya cewa koma dai menene, ta dad'e a haka, don kuwa idanunta sunyi jajir sannan fuskarta ma tayi ja saboda farar mace dama idan tayi kuka fuskarta ta kanyi ja. A hankali aka turo k'ofar d'akin aka shigo, daga bakin k'ofa yaja ya tsaya yana k'are ma matar tasa kallo a lokaci guda kuma yana girgiza kansa cike da takaici. Sai da yaja numfashi ya had'iye 6acin ransa sannan ya soma takowa a hankali har yazo daidai bakin gadon da matar tasa ke kwance tana kukan fitar rai. A hankali ya dafa ta had'e da kiran sunanta cikin wata irin sigar rarrashi. "Hajiya Bilki." Bata d'ago ba amma ta dakatar da kukan da takeyi hakan ya nuna cewa taji kiran mijin nata. A hankali ya soma magana. "Haba Hajiya Bilki, dama ace bazaki iya d'aukar kaddara ba? Har ki zauna kina kuka saboda Allah ya jarabe mu? Haba Bilki! Kin bani mamaki wallahi." Shi d'inma k'arfin hali kawai yakeyi amma zuciyarsa ta raunana! Tashi tayi zaune gami da share hawayen fuskarta tana fuskantar mijin nata da har yanzu yake tsaye bai zauna ba. Sannan itama ta soma magana cikin 6acin rai. "Don Allah Alhaji ka barni, na gaji da wa'azain nikam gaskiya hak'uri na ya k'are haba! Ta yaya za'ayi ace mun shekara akalla sha biyu da aure amma duk shekara sai nayi 6ari? Meyake faruwa ne? Ka duba fa ka gani kaf danginka bak'ina suke gani gaba d'aya sun tsane ni sun sa min ido! Abin ya fi d'aga min hankali sai jiya da muka je sunan gidan Hajiya Karima bakaga yadda ake nuna ni ba! Gaba d'aya na zame musu tamkar wata mujiya haba!" Ta k'arashe tana cigaba da kuka. Alhaji ya runtse idonsa yana mai jin rad'ad'i a cikin zuciyarsa, tabbas yasan haka maganar take sai dai kuma yasan basufi k'arfin Allah ya jarabe su da rashin haihuwa ba, shi ya d'auki hakan a matsayin kaddara. Don haka sai ya nutsu ya fara magana. "Hajiya Bilki a kullum bazan gaji da fad'a miki ba Allah ubangijinmu mai baiwa ne sannan mai hikima ne, kar ki manta ke d'in baiwarsa ce sannan duk yadda yaga dama yayi dake haka zaiyi dake, Allah yayi miki baiwa da yawa ba dole sai kin samu haihuwa zakiji dad'in rayuwarki ba, ki gode masa da ya baki kyau, arzik'i ya wadata ki da lafiya, sannan uwa uba ya barki da ranki, har akwai abinda yafi wannan jin dad'i a rayuwa?" Gwauron numfashi ya saki tare da zama a kusa da ita yana kallon cikin k'wayar idonta sannan ya cigaba da magana. "Haihuwa ta Allah ce, idan yaga dama zai baki idan kuwa bai ga dama ba duk dabararki bazai baki ba, duk yanayin da kika tsinci kanki kamata yayi, ki d'aga hannunki sama ki gode masa sannan ki rok'e sa gafara da rahama. Wad'annan maganganun nasha fad'a miki su ba tun yau ba amma naga kamar ta iske suke bi. Wallahi ki nutsu kar garin garajenki kije kiyi sa6o, kina jina?" Ta d'aga kanta a hankali yayin da ta sa yatsanta ta share hawayenta. Yayi murmushi irin nasu na manya yace. "Bilki duk ba wannan kizo ki bani abinci yunwa nakeji." Ta6e baki tayi tace "Kayi hak'uri na manta ban girka ba." Yayi murmushi yace "Bilki kenan ya za'ayi mijinki ya fita aiki tun safe amma ya dawo gidansa abincin ci ya gagare shi?" Tace "Haba Alhaji! Yau sati na d'aya fa dayin 6ari ya kamata ka barni na huta mana." Inda sabo ya saba da halin Bilki amma da yake Allah ya zuba masa hak'uri sai kawai yayi murmushi yace "Haka ne Allah ya baki lafiya." "Amin" kawai tace yayinda ta koma ta kwanta gami da bashi baya. Tashi yayi ya fice daga d'akin yana mai jinjina hali irin na Bilki. D'akinsa ya fad'a kai tsaye yayi wanka yana fitowa ya zumbula jallabiya fara ya fito ya nufi kitchen, fura da nono ya had'a mai yawa ya dawo parlor ya zauna had'e da kunna T.V yana kallon tashar Aljazeera. Sai da ya gama shan furar tas sannan ya koma ya kwanta tare da lumshe idanu a lokaci guda kuma ya fad'a kogin tunani a haka har bacci ya sace sa. Awarsa biyu daidai ya farka ya duba agogon da ke mak'ale a bangon hannunsa, k'arfe 4:19pm, zumbur ya mik'e yaje yayi alwala yayi sallah, bayan ya kammala kansa tsaye ya wuce d'akin Bilki tana kwance kan gado tana latsa waya, kiranta yayi a hankali. "Bilki." Tana taunar chewing gum sai da yayi k'ara k'as sannan ta d'ago ta kalleshi tace "Na'am." Ajiyar zuciya ya sauke ya fara magana fusakarsa ba annuri ko kad'an. "Yanzu kina ganin bacci ya kwashe ni amma har lokacin sallah ya wuce ki kasa tashi na inyi sallah?" Tace "Kayi hak'uri na manta ne." Girgiza kansa yayi yace "Allah ya kyauta, zan fita daga can zan wuce na gaida Goggo (mahaifiyarsa) sai na dawo." Ko kallonsa batayi ba tace "To sai ka dawo, daga nan ka siyo man nama mana." Fita yayi daga d'akin yaje ya sake yin wanka ya shirya cikin farin yadi kalar kunun kanwa marar nauyi ya fice daga gidan. Sai da akayi sallar magriba sannan ya wuce gidan Goggo dake cikin Layout a garin Katsina, yana shiga ya fad'a d'akinta kamar yadda ya saba bayan sun gaisa tasa aka kawo masa tuwon masara miyar kuka da man shanu ya ci ya k'oshi ya kora da fura. Nan suka d'an ta6a fira kamar kullum sannan ta soko masa zancen da kullum baya son shi. "Ya maganar aure Hamza?" Yayi dum ya kasa cewa uffan, tabbas shima yana son k'ara auren sai dai kuma yana gudun tashin hankalin Bilki, don haka bai ce komai ba kansa dai na k'asa. AUREN FANSA 02 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 Dedicated to Ummi Aisha and Zeebee💘 🌹02 🌹 "Daman nasan bazaka amsa ni ba Hamza, kuma ni har ga Allah bazan maka dole ba. Sai dai kana buk'atar kaje kayi tunani sosai akan maganar, idan kana da ra'ayin aure to zaka iya yi, idan kuma bakada shi babu damuwa." Shiru yayi yana nazari, yana son faranta ma mahaifiyarsa rai sannan bayason tashin hankalin Bilki, don haka sai ya k'ak'alo murmushin dole yace. "Goggo zan je inyi shawara da Bilki kome kenan zan zo na sanar dake." Murmushi tayi tace "Allah ya nuna mana." Yace "Amin." Bai bar gidan ba sai wurin tara ta wuce na dare, gida ya wuce kai tsaye. Yana shiga ya wuce d'akinsa yayi wanka ya sanya kayan bacci ya fito parlor. Bilki na zaune tana latsa waya tana kallon wani American series, jin alamun shigowa yasa ta kalleshi lokaci guda kuma tace "Har ka dawo?" Yace "Na dawo." A lokacin da yake zama kan kujera yana gyara zaman glass d'in idonsa. Matsowa tayi kusa dashi tare da kwantawa bisa k'irjinsa. Dukansu kowa yayi shiru kafin Bilki ta katse shirun nasu "Hamza, wai ya maganar mu ne?" Yace "Wace magana kenan?" Ta zum6uro baki tace "Ba dai har ka manta ba?" Yayi shiru tabbas yasan maganarta bata wuce tana son kud'i. Tayi murmushi tana mai kashe murya had'e da shagwa6a tace "Kace zaka bani kud'i naje Dubai mana saro kaya." Shiru yayi gami da sauke nannauyan numfashi yace "Bilki kenan, ay mun gama wannan maganar tun rannan kuma nace zan baki, sai dai ba dole sai kinje ba yanzu ay inace sautu ake badawa kuma bama haka ba, ina k'awarki da ke yawan zuwa basai ki bata ba ta kawo maki." Ba haka taso amma ya zama dole ta lalla6a shi don haka sai tace "Duk d'aya ay kuma bakomai sai na bata d'in nawa zaka bani?" Yace "Zan baki dubu 100 ki fara da ita daga baya sai na k'ara maki." Da sauri ta tashi zaune "Dubu d'ari kuma? Ni gaskiya ta mani kad'an." A fusace ya tashi tsaye yace "Toh idan har bakiso gaba d'aya a barshi mana, ya zan baki ki raina? Gskiya ki chanza halinki." Daga haka ya tashi ya shigewarsa d'aki yayi kwanciyarsa maganar auren da basuyi ba kenan don ya fusata. Washe gari ta kama Monday, kamar kullum ya tashi ya shirya kasancewar aikin banki yake yasa tun asuba idan ya tashi baya komawa bacci. K'arfe bakwai daidai ya kimtsa ya fito daman baya jiran breakfast don Bilki bayi takeyi ba, a hanzarce yake komai tashinta yayi daga bacci ya ce mata zai tafi aiki, juyi d'aya tayi tashi tace masa "Toh" sannan ta ja bargo ta rufe har kanta. Girgiza kansa yayi ya shiga motarsa ya harba titi. Wani shop ya tsaya ya sayi bread da yoghurt sai lemo sai kuma kayan tea da biscuit don na office d'insa sun k'are, daman ya kan aje saboda ko yaji yunwa sai yaci kawai. A haka ya isa office d'insa ya soma aikinsa kamar kullum. Haka ya wuni yana juya maganar Goggo a ransa yanata sak'e sak'e, haka dai yake sukuku dashi har lokacin sallah sannan ya tashi ya fice tare da sauran abokanan aikinsa musulmai. Kamar kullum yau ma sai kusan k'arfe 6 ya diro gida, gajiya kam ya gaji ba kad'an ba ga yunwa data addabe shi ga uwa uba ana zafi agarin. Yana shiga gida ya ci karo da Bilki a bakin k'ofa taci ado tayi kwalliya na fitar hankali ga gidan sai k'amshi ke tashi. Taro sa tayi bakin k'ofa tana mai aika masa da sak'koni ta ko wane fanni, a hankali ya ture ta yace "Kinga Bilki na gaji bari naje na fara watsa ruwa kafin lokacin sallah yayi." Murmushi tayi ta sake sa sannan ta koma parlor ta zauna tana binsa ta kallo har ya shige d'akinsa. Sai da ya kimtsa ya fito sannan ya wuce kitchen don neman abinda zaici. Tana kallonsa ya fito da cup d'in tea da biscuit a hannunsa ya zauna kan dinning yaci. Sai da ya kammala tazo ta zauna a kusa dashi tana yatsina baki tana wani yanga da kwarkwasa. Can kuma tace "Alhaji." Bai kalle ta ba yace "Na'am." Tace "Alhaji daman k'awata zatayi bikin k'anwarta shine nake so ka bani kud'i na bata guddumawa ta..." Da sauri yace "Haba Bilki daga dawowata zaki tare ni da zancen wasu kud'i ay sai ki bari na huta dai ko?" Murmushi tayi tace "Haba Alhaji duk bai kai ga tashin hankali ba ka huta sai muyi magana." Bai k'ara magana ba illa tashi da yayi ya fita don yaga lokacin sallar magriba ta gabato. *** "Mummy!" Yaro d'an kimanin shekara goma ya rugo da gudu, Maman tasa na zaune kan wata irin makekiyar kujera tana duba magazine da glass d'in karatu a idanunta. A hankali ta d'aga ido ta kalli yaron da ke ta gudu kafin kuma ya haye bisa cinyar ta yana mai hugging d'inta. Itama hugging d'insa tayi tana kallonsa cike da so tace. "Lafiya ka shigo da gudu haka FARUK?" Yaron da ta kira da Faruk yana mai tsananin murmushi kafin ya rufe baki wani babban mutum dogo fari ya shigo yana sanye da kayan hausawa harda babbar riga, sai da yazo daidai bakin k'ofar da zata sadasa da parlon yaja ya tsaya yana murmushi, sannan kuma yace. "Ay Faruk ya d'auko grade mai kyau, sannan ya lashe baki gaba d'aya wato overall as always." Dukansu suka d'aga ido suka kalli mutumin dake tsaye ya hard'e hannayensa biyu yana murmushi. Matar da aka kira da Mummy ta rungume Faruk sosai a jikinta tace "That's my boy, haka nake so Allah ya k'ara maka basira, toh saura na Islamiyya, idan har kayi k'ok'ari shima akwai kyautar dana tanadar maka ta mussaman." Cike da jin dad'i Faruk yace "Allah Mummy?" Tace "Kayi ka gani I promise." Mutumin dake tsaye ya tako ya shigo parlon, kusa da kujerar dasu Faruk ke zaune ma'ana doguwar kujera, sai da ya cire babbar rigarsa sannan ya zauna yana shafa kan Faruk yace. "My boy aje a cire uniform ayi wanka ko sai kazo muci abinci." Faruk yace "Ok Daddy." Sannan ya tashi da gudu ya shige d'akinsa. Matar da ke zaune kusa dashi mai suna Reemah wadda na k'are ma kallo kyakkyawar gaske ce fara mai yalwar gashi don kuwa har gaban goshinta ya fito. Bana tantama ta had'a iri da larabawa. Kamo hannun mutumin tayi mai suna Adam tace "Muje ka watsa ruwa kaci abinci ko?" Murmushi yayi yana jin son matarsa na k'ara fizgarsa sannan yace "Muje sahibata." Murmushi tayi sannan suka mik'e a tare suka nufi kan bene inda hannunsu na mak'ale da na juna... AUREN FANSA 03 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 Dedicated to my darling Maman Ihsan (SAFNA) much love darl💕💘❣️ 🌹03 🌹 *** Daddare sai da Bilki ta k'ara tada masa da maganar wasu kud'in inda a ranar sai da ya yi 6ata mata rai fiye da tunaninta sannan ya nuna mata ta cika son kud'i, duk dai abubuwan da ya dad'e dasu a ransa shekara da shekaru sai da ya amayar mata dashi, sum sum ta tashi ta koma cikin d'aki tsabar borin kunya. Jingina yayi da kujerar parlon tare da lumshe idanu don ya samu nutsuwa sai dai bai kai ga yin hakan ba wayarsa ta fara ruri, kallon screen d'in wayar yayi yaga sunan da ya bayyana wato My sister, murmushi ya saki na tsananin farin ciki a lokaci guda kuma damuwarsa ta 6ace 6at, d'auka yayi gami da yin sallama, d'ayan 6angaren aka amsa sannan tace. "Ya Hamza! Da fatan an wuni lafiya?" Sai da yayi murmushi sannan yace "Lafiya lau Amina ya gida?" "Alhamdulillah, ya Anty Bilki?" "Tana nan lafiya ya zafi kuma?" "Lafiya lau ya Hamza, da fatan komai lafiya?" Yace "Alhamdulillah ya jiki kuma?" Ta d'an yi murmushi kad'an sannan tace "Alhamdulillah gashi nan muna ta fama." Dariya yayi yace "To Allah ya raba lafiya." Tace "Amin." Sannan ta kuma cewa "Ya Hamza akan maganar mu dai ce yasa na kira ka, kaga yanzu cikina ya shiga watan haihuwa kuma nasha fad'a maka idan na haifi babyn nan na baka shi ka rik'a..." "Amina! Insha Allah ke zaki rik'a babynki sai dai ki dinga kawo min shi hutu." Tayi murmushi mai bayyana hak'ora sannan tace "Ya Hamza na kenan, yaya na na kaina, nidai kayi min alk'awarin rik'a abinda zan haifa koda bayan raina ne, shine kad'ai burina a halin yanzu." Haka kawai sai yaji gabansa ya fad'i cikin firgici yace "Kinga Amina, nasha fad'a maki mutuwa lokaci ne kuma insha Allah zaki ga abinda zaki haifa har ma ki shayar da shi ki daina fad'in maganganu haka ba dad'in ji." Tayi dariya "Ya Hamza mutuwa fa na kan kowa sanin gaibu sai Allah nidai alk'awari na zaka rik'e min kaji?" Nannauyan numfashi ya saki sannan ya d'ora "Naji shikenan are you happy now?" "Yeey! Allah ya bar mana kai ya Hamza, nagode!" Dariya yakeyi sosai itama tana taya sa, sanann ya kawar da wancan zancen ta hanyar jefo mata tambaya "Ya kingama rubuta list d'in abubuwan da kike buk'ata?" Tace "Eh na gama ya Hamza yana hannun Goggo na bata." Yace "Ok zan kar6a insha Allah sai na ga abinda za'a siya." Tace "Toh ya Hamza Allah ya k'ara bud'i." Sai da suka d'an ta6a fira kad'an sannan sukayi sallama ko wane yana mai farin cikin ganawa da d'an uwanshi. Amina k'anwar Hamza ce uwa d'aya uba d'aya, bayan nan kuma su kad'ai ne Goggo ta haifa bayan Amina sai haihuwar ta tsaya, tunda ta haifi Hamza sai bayan shekara kusan bakwai sannan ta haifi Amina, kasancewar su biyu ne kacal yasa suka shak'u da juna sosai Hamza na son Amina kuma yanaji da ita, kullum suna mak'ale da juna tun suna yara har kawo yanzu da aure ya rarraba su kuma, amma kusan kullum sai sunyi waya. Amina tasha ci ma Bilki mutunci akan halayanta da take nuna ma Hamza saboda bazata iya jure ganin d'an uwanta cikin bak'in ciki da k'unci ba. Mijinta ya rasu tun tana da ciki wata biyar Allah ya amshi ransa, ga bashi da uwa bashida uba haka ma shi kad'ai ne mahaifiayarsa ta haifa, bayan rasuwar tasa ta zauna nan gidanta da ke cikin garin Katsina a G.R.A. Wannan kenan! *** BAYAN 'YAN KWANAKI Yau weekend ne Hamza baya zuwa aiki don haka yana gida yana hutawa, bayan ya gama waya da Amina kamar kullum Bilki ta shigo cikin shirin fita unguwa ta sha ado sosai tana ta zuba k'amshi. A hankali yake binta da kallo kafin kuma ya sauke su kan shigar da tayi. Sanye take da wata silky doguwar riga mai dogon hannu kalar brown an mata aikin duwatsu ba laifi rigar ta kamata sai ta yafa gyalen kayan. Haka ma takalminta mai tsini ne kalar kayanta da jaka kalar kayan. Har tazo ta zauna bai bar kallonta ba cike da mamaki, Bilki tace. "Hamza zan fita." Ya kalleta da mamaki yace "Ina zakije?" Ta had'e rai "Gidan Hajiya Laila." Shima ya had'e rai "Ba inda zakije." Ta mik'e zumbur! "Me kace?" Yayi banza da ita, ta rik'e k'ugu tana sassarfa masifa "Hamza! Gaskiya ka takura min haka kawai! Kuma ay dah ba haka kake ba wannan k'anwarta taka duk ta zuge ka." Tashi yayi a fusace yana nuna ta da yatsa "Kar ki k'ara saka Amina a cikin zancen mu saboda babu ruwanta, kina ji na?" "Ahayye nanaye, an ta6o masa rabin rai, to an fad'a Amina ce ke zuge ka kayi abinda zakayi." Bai san lokacin da ya d'auke ta da mari ba yace "Kisani ni mijinki ne, kuma nafi k'arfin ki wulak'anta ni, sannan wallahi kika k'ara fad'in magana makamancin wannan a bakin aurenki!" Ta zaro idanu waje "Iyye! Kan mage ya waye, lallai Hamza yanzu kayi baki, amma tunda ka mare ni don na fad'i gaskiya shikenan kaje Allah zai saka min." Yace "Nidai na fad'a miki ki iya bakinki, kuma fita bazakiyi ba ay inace dai sai na bada izini ko? To mugani idan kin isa!" Har ya tafi ya dawo yace yana mata mugun kallo. "Magana ta k'arshe ina so ki sani aure zan k'ara na gaji da zama da mace irinki wadda batasan inda duniyar ta dosa ba, na aure ki don ina tsananin sonki amma kisani dole zan k'ara aure." A fusace ta cakumo masa wuyan riga kamar kura taga nama. "Aure Hamza! Baka isa kayi min kishiya ba, ni kad'ai ce babu k'ari!" Yayi dariya gami da cire mata hannu daga rik'on da tayi masa sannan yace "Kin isa ne ki hana? Ay baki isa ba aure kamar anyi ne an gama." Yana gama fad'in haka yayi shigewarsa d'aki ko kallonta baiyi ba. Yana jin ihuta tana fad'in "Wallahi babu wacce ta isa ta shigo min gida ta zauna lafiya, wallahi koma wacece sai na kashe ta!!!" AUREN FANSA 04 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 Dedicated to my Zarah Surbajo and Sadnaf💘❤️💘 🌹04 🌹 Zuciyarsa har wani zafi take masa, kwanciya yayi kan gadonsa yana mai maida numfashi sama sama, meyasa Bilki bazata ta6a chanza halayenta ba? Yasani tun kafin suyi aure yake fama da iri iren halayenta na nuni da maita akan kud'i, sam bata gajiya da tambayarsa kud'i, ko lokacin auren su Goggo taso ta hana don sam tarbiyyar Bilki bata yi mata ba, batada kamun kai ga shegen yawo, sai dai a lokacin yadda yake tsananin sonta baijin zai iya hak'ura da ita, a haka yayi ta lalla6a Goggo har ta amince akayi auren. Gashi sam bai iya mata fad'a idan tayi masa laifi sannan bai iya hanata kud'i idan ta tambayesa ya rasa dalilin da yasa haka. So da yawa idan ta tambayesa sai yaji kamar kar ya bata amma sam sai ya kasa haka yayi ta rayuwa da ita tana cutarsa ba tare da ya ankara ba. Gashi da anyi abu ta iya kukan k'arya kuma nan da nan sai zuciyarsa ta karaya yaji yana tausayinta, a haka ta gano lagonsa abu kad'an zata sa masa kuka. Ajiyar zuciya ya saki tare da gyara kwanciya yanzu yasan mafita d'aya ce ya k'ara aure k'ila hakan zai sa ya gane banbancin zama da Bilkin, wata k'ila ma wadda zai aura batada halayen Bilki ya yarda ya amince zai k'ara auren, tashi yayi da niyyar shiryawa yaje ya sanar da Goggo ya shirya ko yau za'a iya d'aura masu aure, wayarsa ta fara ruri. Goggo ya gani a saman screen d'in wayar haka kawai gabansa sai da ya fad'i. A sanyaye ya d'auka gami da yin sallama, da sauri Goggo tace "Hamza kana ina yanzu?" Yace "Inagida Goggo, lafiya dai ko?" Tace "Babu lafiya Hamza, maza maza ka taho asibiti k'anwarka na nan na nak'uda, kuma ta kafe tak'i shiga d'akin haihuwar wai sai ka zo, kuma ga haihuwar tazo kar ta haihu a gaban d'aki Hamza, kayi sauri don Allah." A rud'e yace "Gani nan yanzu wace asibiti ce?" Tace "Alheri clinic kayi sauri." "To." Kawai yace ya fito da gudu daga d'akin, takalmansa ma daban daban yasa tsabar rud'u ga gabansa sai fad'uwa yakeyi. Haka dai ya daure ya figi mota ya fice da sauri, duk da asibitin batada nisa daga gidansa amma gani yake bazai isa da sauri ba. Cikin k'ank'anin lokaci Hamza ya iso Alheri clinic da gudu ya shiga ciki yana tambayar suna ina. Koda yaje hanashi shiga akayi sai da ya kira Goggo yace gashi nan sun hana shi shigowa. Da k'yar ta rok'esu suka barshi ya shigo. Yana shiga ya iske Amina sai faman nak'uda takeyi mai zafi tana kiran sunan Hamza tana kuka. Da sauri ya isa gareta tana ganinsa ta k'ara sautin kuka tana fad'in "Ya Hamza na gode da kazo, wata magana zan fad'a maka." Jikinsa yayi sanyi yace "Koma meye ay sai ki bari ki haihu tukunna..." "Ya Hamza bazaka gane ba bazan iya bari sai na haihu ba, amma don Allah ka tsaya ka saurareni!" Ta fad'a cikin muryar tsawa, tashi yayi ya fara safa da marwa idanunsa sun kad'a sunyi ja, yasan tatsunniyar gizo bata wuce ta k'ok'i, tabbas yasan maganar da ta saba fad'a masa yau ma ita d'in ce zata fad'a masa. Don haka sai yace "Ko meye zaki fad'a na riga na sani, don haka ki tashi a shiga dake d'akin kar ki haihu a nan." Duk'awa tayi tare da fasa wata irin giggitaciyar k'ara wadda bama Hamza ba har Goggo da malaman asibitin sai da suka rud'e, fad'i take "Bazan shiga ciki ba ya Hamza sai kayi min alk'awari na k'arshe." Da sauri ya kalleta "Haba Amina! Meyasa kin faye kafiya ne? Ba mun gama maganar nan tun tuni ba? Meyasa kike tado zancen kuma, ki bari ki haihu zamuyi magana." Girgiza kanta tayi tana hawaye "Kayya ya Hamza, don Allah kayi min alk'awarin kawai." Goggo ce ta sa baki tace "Hamza kasan zafin haihuwa, kawai kayi mata alk'awarin a shiga da ita." Da k'yar ya iya bud'e bakinsa yace "Na maki alk'awari Amina, Allah ya sauke ki lafiya." Duk da zafin nak'udar da Amina keyi ba hanata yin mumushi ba, sannan tace "Nagode ya Hamza nagode!" Juya mata baya yayi don bazai iya jure ganin Amina cikin wannan halin ba, a haka aka shiga da Amina rik'e da hannun Goggo wadda aka samu aka raba su da k'yar." Goggo kuka takeyi sosai ji take kamar Amina bazata fito ba idan ta shiga. Hamza ya zo ya dinga rarrashinta har ya samu tayi shiru. Minti kusan talatin ana abu d'aya Amina ta kasa haihuwa, har an fara shawarar ayi mata CS don da k'yar idan zata iya haihuwa da kanta. Har sun fara shawarar a sanar da 'yan uwanta Allah cikin ikonshi ta haihu. Su Hamza suna jin kukan jariri suka fara murna suna hamdala. Jim kad'an wata sister ta fito da jariri tana zuwa su Goggo suka yo kanta, Goggo ce ta fara cewa "Alhamdulillah! Ta haihu lafiya." Hamza kuwa hannu yasa ya kar6i babyn yana kallo kafin kuma ya kalli nurse d'in yana murmushi sosai. Nurse d'in ce tace "Ta haifi mace." "Alhamdulillah!!" Shine kawai abinda suke cewa. Kafin kuma Goggo tace "Ina ita Aminar? Ba'a gama kimtsa ta ba mu shiga?" Nurse d'in ce tace "Sai dai kuyi hak'uri..." "Me kike nufi da kalamanki?" Cewar Hamza a d'an rud'e, Goggo ma ta rud'e tace "Bamu gane abinda kike cewa ba." Nurse d'in tace "Abinda nake nufi shine kuyi hak'uri Allah ya amshi kayanshi, ma'ana Amina ta koma ga mahaliccinmu." Saura kad'an Hamza ya saki d'iyar sai da nurse d'in tayi saurin amsar ta, Goggo kuwa in banda salati ba abinda takeyi kafufuwanta kasa d'aukarta sukayi ta zauna da sauri. Hamza zaman k'asa yayi dirshen yana salati kafin kuma ya fashe da kuka kamar k'aramin yaro. "Daman Amina tafiya zakiyi da gaske? Tasha fad'a min mutuwa zatayi na kasa yarda." Haka yayi ta sambatu kamar zautacce a yayinda Goggo ke kuka rungume da babyn. Sai da aka fiddo da gawar Amina lullu6e cikin farin zanin gado bisa gado mai taya a lokacin kuma suka gasgata ta mutu d'in. Wurin ya kuma rud'ewa inda Hamza ya rugo ya rugume gadon yana magana da gawar Amina. Goggo na tsaye tana kuka tana tausayin Hamza, da k'yar aka 6am6are shi daga jikin gadon aka sanya ta cikin doguwar ambulance. Hamza na tuk'i yana kuka har baya ganin gabanshi, ga kukan baby dake k'ara rud'a shi. Can gidan Goggo dake cikin G.R.A suka nufa. Suna isa aka shiga da gawar a cikin gida. Bayan anyi ma Amina wanka an mata sutura sai kuma aka d'auketa za'a kaita makwancinta na k'arshe, gidanta na gaskiya! Hamza na ji na gani ya saka Amina cikin kabarinta, Masha Allah Amina tayi mutane don kuwa har tutse akeyi wurin sakata a makwancinta. Bayan an gama kuma suka juyo gida inda su Hamza suka cigaba da kar6ar gaisuwa. Itama Bilki kullum sai tazo amma bata ta6a dafo komai ba a matsayin abincin sadaka ba hasali ma sai tayi kwalliyarta take zuwa bata nuna wata damuwa ba. A haka aka yi sadakar uku ana zaman makoki, inda Hamza ya dangana yana amsar gaisuwar kowa saidai fa baya magana sai dai yayi shiru ya k'ura ma wuri d'aya ido kamar yana tunani. Ko kuma idan akayi masa gaisuwa sai ya dad'e yana kallon mutum kafin kuma ya amsa gaisuwar. Shikenan Amina ta tafi, mutuwa mai yankar k'auna mai raba tsakani, saidai Allah baya barin wani don wani yaji dad'i. Allah kasa mu dace, Allah kayi mana kyakkyawan k'arshe Amin thumma Amin. AUREN FANSA 05 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 Dedicated to mairo😜 aka Maryam Gafai I heart you sis❤️ and my sisi Ammin SS 😘😘😘 🌹05 🌹 BAYAN KWANA BIYU Ranar suna yarinya taci sunan mamanta marigayiya Amina, daman bawani taron sunan da akayi wane taro ma ana zaman makoki? Amina duk da tana jaririya Allah ya zuba mata hak'uri ga bata kuka sosai sai dai idan taji yunwa ko wani abin na damunta. Kammaninta sak na mahaifiyarta ta d'ebo hartta gashinta irin nata ne lub lub, hasken ne kawai bata d'ebo ba sa6anin marigayiya da take fara tas kamar yayanta Hamza amma Amina babyn ita ba fara bace tas, sai dai tana da kyau duk da batada hasken ana ganin kyawunta. Idan ta bud'e ido ta kalli mutum zaka gansu manya ne farare tas! Baya 'yan kwanaki a lokacin Amina ta kwana 20 cif a duniya Goggo ta kira Hamza da Bilki gidanta akan cewa tana son magana dasu. Bayan sun iso suka gaisa Goggo ta d'auko Amina dake kwance kan gado tana bacci, ta mik'a ma Hamza ita tana murmushi tace "Hamza kamar yadda kasani marigayiya ta baka amanar rik'on Amina kuma ka d'auki alk'awarin haka, don haka yau na damk'a maka Amina a matsayin d'iyarka halak malak, da fatan zaka rik'e ta bisa amana." Sai kuma ta juyo ta kalli Bilki tace "Bilkisu ga amanar Amina nan ki rik'e ta amana saboda kar ki manta marainiya ce gaba da baya idan har kika ci zalinta Allah zai mata sakayya." Hamza yace "Insha Allah Goggo kar ki damu ina k'auanar Amina kamar 'yar dana haifa haka nake jinta a raina. Insha Allah zamu rik'e ta amana, Allah ya taya mu rik'o." Goggo tace "Amin, daga cikin dukiyar da mahaifinta ya bar mata a ciki ake siya mata su pampers da su madara, sai kayan sawa da sauran abinda ba'a rasa ba, amma ba kasafai nake amfanin da kud'in ba sai idan ba kud'i hannuna, amma tunda yanzu zata dawo hannunku da zama sheyasa zan damk'a maka kud'inta a hannunka ka adana mata ko ka juya mata su duk yadda kaga ya dace." Jiki a sanyaye Hamza yace "Insha Allah Goggo." Daga haka Goggo ta tashi ta had'o kayan Amina tas sannan ta kira mai gadinta ya saka cikin mota. Sai da suka ci abincin rana sannan suka koma gida, inda ko a mota Bilki ce ta rik'e Amina sannan ga mamakin Hamza bata nuna komai ba har rungume ta tayi tana fad'a ma Hamza d'iyar ta shiga ranta sosai. Ba k'aramin sanyaya mishi zuciya hakan yayi ba, duk wata fargaba dake ransa ta kau yadda yaga Bilki na tarairayar Amina kamar 'yar cikinta. Bayan sun koma gida da daddare Bilki ta had'a ruwan zafi tayi ma Amina wanka tas sannan ta shirya ta cikin kayan baccinta wato overall pink wadda tayi mata kyau, gashin babyn ya wani yi irin pam d'innan sannan duk da haka a nannad'e yake gwanin kyau. Bayan ta gama ta had'a mata madararta ta bata tasha ta k'oshi, sannan ta rirrigata ta tayi bacci, duk akan idon Hamza wanda yake mata kallon mamaki, abinda baiyi zato ba yau gashi Bilki nayi. Bayan ta rirriga Amina tayi bacci zuwa tayi kusa da Hamza tana rok'on gafarar abubuwan da ta masa, bai gasgata ba sai da ya ga Bilki na kuka sosai tana rok'onsa, take ya yarda ta yi nadama don haka sai ya yafe mata suka shirya. Haka cikin dare da Amina tayi kuka Bilki zata tashi ta bata madara har ta koma bacci, gashi sam bata kukan dare yunwa kad'ai ke tashinta da kuma an bata madara zata koma shikenan kuma sai asuba. Da safe ma haka tayi mata wanka tas ta bata madararta, koda wasa Hamza bai yi tunanin za'a samu wata matsala ba daga wurin Bilkin ba. Don haka sai ya saki jikinsa ya manta da maganar k'arin aure. Duk sadda Hamza ke gida to Amina na hannunsa yana mata wasa, yana ce mata "Meenah!" Ya bata madara, ya chanza mata pampers, ya mata tsarki, sannan ya rirriga ta har sai tayi bacci. A haka har sunan ya bita don Hamza Meenah yake ce mata idan yana mata wasa. Watan Meenah biyar amma ta zama wata irin k'atuwa tayi nauyi sosai, da k'yar ake d'aga ta, ga bata wasa da abinci komai ci takeyi, sai dad'a kyau takeyi kullum. Hamza na matuk'ar nuna mata kulawa kullum yana manne da ita especially weekends ranar da ba aiki, baya zuwa ko ina zai zauna gida yana kula da Meenah. Sannan komai yana siya mata daidai gwargwado bai ta6a nuna gazawarsa ba, tsaye yake kai da fata wajen ganin Meenah ta taso cikin ingatacciyar rayuwa. Watan Meenah bakwai daidai Bilki ta samu ciki, Allah cikin ikonshi cikin baya bata wahala, murna had'e da godiya ga Allah suka yi ba adadi. Zo kuga zakwad'i da rawar kai wurin Bilki. Tun cikin bai tasa ba ta fara siyayyar kaya kamar hauka a 6oye, tasan Hamza zai bata kud'i idan lokacin yayi amma tsabar son abin duniya yasa bata iya hak'uri. Ko kuma ta d'auka idan ya aje da yake bai ta6a tunanin tana masa sata ba sheyasa bai farga ba, sai dai idan yaga kamar kud'in ba daidai suke ba yayi ta tunanin yadda akayi ya kashe su. *** Faruk ne kwance bisa gadonsa na alfarma yayi ruf da ciki yana game cikin system d'insa. Sai yanzu na k'are ma d'akin nasa kallo, color d'in d'akin dark da light blue ne, hartta gadonsa blue ne da bed-sheet d'in da ke shimfid'e a sama. Carpet d'in da ke shimfid'e a d'akin blue ne. Gefe guda kuma study table ne shima blue, sai cikin wata k'atuwar box kayan wasansa ne wanda mafi yawa nafi hango jirgin wasa kala kala, hartta kan gadonsa jirgin wasa ne yakai biyar gefensa, d'aya kuma a hannunsa, a raina nace to shi kuma son jirgi yake? Mummy ce tsaye bakin k'ofa tana kallonsa kafin kuma ta k'araso tare da zama a kusa dashi ta dafa shi. Juyowa yayi yana kallonta kafin yace. "Mummy na." Murmushi tayi tana shafa gashin kansa sannan tace "Faruk ya naga kana game? Ba nace kazo ka koyi hardarka ba, ba gobe zaka bayar ba a islamiyya?" Murmushi yayi yace "Nayi Mummy." Tace "Anya Faruk?" Yace "Allah yanzu na gama." Tace "Ok zo muje muyi dinner Daddy da Anisah (auta 'yar shekara uku) suna jiranmu." "Ok." Yace a yayinda ya d'auki jirginsa ya bi bayan Mummy.... MSB💖 AUREN FANSA 06 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 🌹06 🌹 Kan dinning suka nufa inda Daddy da Anisah ke zaune suna labari harda dariya, zama sukayi itada Faruk da Daddy ke musu fira a yayinda Mummy ta zuba ma kowa abincinsa. Wurin kuma yayi tsit sai k'arar spoon ake ji. Anisah ce ta katse shirun ta hanyar jefo ma Daddy tambaya. "Daddy idan na girma me zan zama?" Daddy dake shirin kai loma a bakinsa ya dakata yana kallon Anisah kafin kuma yace "Anisah kenan, duk abinda kike so shi zaki zama ay." Anisah tayi dariya "Ni banason na zama komai nafiso na shiga aljanna." Kowa a wurin sai da ya maida hankalinsa gareta kafin kuma Mummy tace "Insha Allah zamu shiga aljanna kinji ko?" Mummy tace "Abban Faruk ya batun baka manager d'in ko sun fasa?" Daddy yayi murmushi "Ba fasawa sukayi ba Reemah, sai sun duba cancanta kafin su bada, idan na dace a bani manager zasu bani, idan kuma wani ya dace a ba za'a bashi." Tayi murmushi "Haka ne kuma, nidai fatana Allah ya baka sa'a a dukkan lamuranka" Yaji dad'in addu'ar matarsa ba kad'an ba, abinda ke k'ara masa sonta kenan kullum cikin yi masa addu'a takeyi yana murmushi yace "Amin ya Allah Reemah." "Ka fidda ranar da zamu tafi Disney world d'in kuwa?" Reemah tace bayan ta had'iye abincin dake bakinta. Daddy ya sha cup d'in Apple juice kafin yace "Eh zuwa upper week dai insha Allah lokacin su Faruk sun gama exams a islamiyya." "Yeeyy! Mummy Disney world zamuje da gaske?" Mummy tayi murmushi tace "Eh Mamana ko bazaki ba?" Anisah ta zum6ura baki "O'o ni zanje." Faruk yace "Kalle ta to baza'a dake ba." Anisha ta sa kuka "Daddy wai baza'a je dani ba?" Daddy yayi murmushi "Ya isa yace bazaki ba, ay kece head d'in tafiyar gaba d'aya zamu iya barinsa amma ke bazamu iya barinki ba." Gwalo ta ma Faruk tana share hawayenta. Faruk yasa dariya. Anisah tasa kuka. "Mummy kinga Ya Faruk na min dariya ko?" Mummy ta harari Faruk "Zaka fara ko Baba na? Meyasa kakeson ganin kukan k'anwarka ne?" Yayi dariya "Aww dariya ma kakeyi Faruk? Bazaka bata hak'uri ba?'' Ya buga k'afa. "Wannan 'yar yarinyar zan ba hak'uri? Tab bazan bada ba." Daddy yace "Just say sorry Faruk, you know she won't stop crying unless you apologize." Mummy tace "Oya Faruk now!" "Ok sorry!" Take ta bar kukan inda kuma ta cigaba da cin abincinta kafin kuma ta kalli Daddy "Daddy zansha ice cream." Mummy tace "Me nace miki akan zak'i?" Anisah ta turo baki "O'o ni zansha." Mummy zata k'ara magana Daddy ya d'aga mata hannu "Ba ruwanki Reemah, zan siya mata ice cream." Anisah tashi tayi da gudu ta wuce parlor tana tsallen dad'i. Daddy yayi dariya Mummy na taya shi tace "Anisah kenan, badai rigima ba." Daddy yayi dariya "Lokacinta ne, kema kinyi naki ay." Mummy tace "Daddy Faruk fa na wurin." Yayi dariya "To sai me? Sai na fad'i abubuwan da kikayi ay" Da sauri ta tashi tana fad'in "Haba Daddy!" Yayi dariya "Kina tantama ne? Bari kiga..." Kafin ya k'arasa tayi sama da sauri tana dariya. Daddy ya tashi ya bi bayanta "Guduwa kikayi Reemah!" Faruk tsayawa kallonsu yayi yana dariya cikin ransa yace "Allah ka k'ara had'a kanmu what a lovely family!" *** Meenah na zaune kan carpet tana wasa da abin wasanta haka kawai kuma sai tasa kuka, Bilki dake zaune saman kujera tana shan rake tana kallon wani movie da take so kukan Meenah ya cika mata kunne. Tsawa ta daka mata "Ke da Allah kiyi mana shiru yarinya sai shegen kuka haba!" Abinka ga yaro wannan tsawa da aka daka mata ita ta firgita ta yasa ta k'ara fashewa da wani irin kuka. Haushi ya cika Bilki yasa ta tashi tayi shigewarta d'aki ta bar Meenah nan na ta faman kuka kamar zata shid'e. Meenah tayi kuka baiwar Allah har ta gaji. Nan ta kwanta k'asa tayi ta ajiyar zuciya har baccin wahala ya kwashe ta a nan. Bilki na kwance a d'aki ta jiyo k'arar shigowar motar Alhaji. Da sauri ta fito tazo ta d'auki Meenah dake a k'asa ta rungume ta tare da zama kan kujera tana rirriga ta. Haka Hamza ya shigo ya same ta, da murmushi a saman fuskarsa ya k'araso. Yana zama Bilki ta kalle shi "Sannu da zuwa Alhaji." Yana murmushi yace "Yauwa sannu da aiki Bilki, Meenah bacci akeyi?" Tayi murmushi "Eh wallahi yanzu ta gama rigima sai na rirrriga ta tayi bacci." Yayi murmushi "Meenah kenan, ay batada rigima ma k'ila dai baccin takeji daman." Tayi yak'e "Sosai ma ay Meenah baiwar Allah ce batada rigima." Yace "Hakane Allah ya raya mana ita." Tace "Amin." Yace "Bari naje na watsa ruwa na gaji." Tace "Ok sai ka fito." Tana ganin shigewarsa ta kalli Meenah taja dogon tsaki, sannan taje ta kwantar da ita a d'akin Meenah d'in kan gado. Bayan Alhaji ya gama wanka suna zaune kan dinning suna cin abinci ya kalli Bilki yace "Bilki a gaskiya ba abinda zance miki sai dai nace Allah ya saka da alkhairi akan aikin ladar da kikeyi. Allah ya baki lada." Ta kalli Alhaji tace "Haba Alhaji meye na godiya ay yi wa kaine, kuma ma Meenah kamar d'iyar dana haifa haka na d'auke ta. Idan har kana min godiya sai naji kamar baka d'auke ta a matsayin 'yar cikina ba." Yayi murmushin jin dad'i "Wallahi ko kusa ba haka bane, kawai dai na yaba da k'ok'arinki." Tayi dariya "Allah sarki. Uhm uhm Alhaji dama madararta da pampers sun k'are shine nace ya kamata a bad a siyo mata wasu." Yace "Wannan ba damuwa zan baki isashen kud'i ki siyo mata wanda zai dad'e, naga kamar tafison madarar ma akan abinci." Tace "Hakane." Bayan sun gama ya d'auko kud'i har dubu goma ya bata. Amsa tayi tace "Shikenan zanje na siyo mata. Yace "Toh ko ki bari idan na fita na siyo mata mana." Da sauri tace "Kai haba kai ina kake da lokaci? Ni da nake gida kullum ka bari zan siyo mata." Yayi murmushi "Toh shikenan." *** Watan haihuwar Bilki ya kama. Kullum sai ta tambaye shi kud'in siyayya bai ta6a hana ta ba saboda har ga Allah ya d'auka Bilki ta shiryu. Wata rana nak'uda ta kama Bilki gadan gadan, Hamza ya kaita asibiti, suna zuwa ba'a jima ba ta haifi 'ya mace. Kyakkyawa fara tas mai k'oshin lafiya. Haka aka cigaba da zaman barka inda komai Hamza yayi mata daidai gwargwado komai yana tafiya daidai. Ranar suna yarinya taci sunan kakarta ta wurin Hamza wato Fatima. Haka aka gama taron suna aka watse lafiya kowa ya koma gidansa.... AUREN FANSA 08 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 Another page for my Ummi Aisha thanks for all the support and care one love dear💖Allah ya k'ara basira Amin🌹 🌹08 🌹 Laila ce ta cigaba da magana. "Ko dai har yanzu baki fahimta ba ne?" Ajiyar zuciya Bilki tayi, sannan tace "A gaskiya Laila ban iyawa, kisa fa kika ce? Don ina son dukiya sai akace na kashe su, gaskiya mu chanza shawara dai." Laila tayi kwafa. "To sai akace mu zamu bisu mu aikata k'udirinmu? Ko kusa ba haka nake nufi ba, abinda nake nufi a nan shine..." Nan naga ta rad'a mata wata magana daga k'arshe dukkansu suka kwashe da dariya. Bilki tana dariya tace "Shegiyar gari, lallai Laila sai dai a barki amma ke shu'uma ce wallahi." Hajiya Laila ta k'yalk'yale da dariya sosai sannan tace "Kema haka." Bilki ta tashi tana gyara zaman d'ankwalinta tana kallon Laila tace "Kamar naji kuman Zarah bari na dubo ta." Laila tace "Yi sauri kuwa nima naji." Jim kad'an sai ga Bilki ta shigo da Zarah a hannunta da alama yanzu Zaran ta tashi daga bacci, tana zuwa Laila ta mik'a hannu ta fara mata wasa, can sai ga Meenah ta fito da alama bacci ta tashi don kuwa kanta buzu buzu yake, saboda yanayin gashinta mai cika kuma ga tsawo sheyasa ko ya ta kwanta sai yayi buzu buzu. Zuwa tayi kusa da Bilki tana murza idanu. Su kuwa sai faman ta6e baki sukeyi. Meenah tace "Maama wunwa." Laila ta ta6e baki tace "Uban me tace?" Bilki tace "Ohon mata, ke tafi can ki bamu wuri." Abinka ga yaro da ba ganewa tayi ba, sai ma ta matso kusa da Bilki ta jingina da ita. Da sauri Bilkin ta hankad'e ta gefe ta fad'i k'asa tim! "Wannan yarinya anyi mayya! Mts." Cewar Laila had'e da jan tsaki. Bilki ta jawo hannunta da k'arfi, Meenah ta fashe da kuka. Kitchen suka nufa ta had'a mata tea a cup tana tsaki sannan ta dire mata k'asa. "Oya zauna kisha yarinya bata aje komai ba sai ci? Haba!" Nan ta zauna ta shanye tas sannan ta fito daga kitchen d'in. Tana gama fad'an haka ta fice taje ta had'o ma Zarah cereal ta koma parlor, Laila ke bata har ta kammala sannan aka bata ruwa. A tare suka girka abincin rana inda Laila tayi ma Zarah wanka, sannan suka dafa fried rice da papered chicken sai had'ad'en salad. Wuraren uku da kwata Laila tayi sallama da Bilki ta tafi gida. Sai wurin biyar saura sannan Bilki tayi ma Meenah wanka ta bata abincin rana. Kamar kullum bayan Alhaji ya dawo gida yayi wanka yaci abinci, suka zauna palor suna 'yar fira kafin a kira sallar magrib. Kasancewar Meenah batasan dawowar Baban nata ba, tana can d'aki tana wasa. Sai data fito, aiko tana ganin shi ta rugo da d'an gudunta ta zo kusa da shi tana fad'in "Dada!" Cike da jin dad'i Alhaji yace "D'iyar Dada ashe ana ciki, zo nan." Tana zuwa ya d'auke ta ya zaunar kan cinyarsa yana mata surutu tana dariya. Can kuma sai tace "Dada kaga Maama ta bije ni d'azu." Ya ware idanu "Me kikayi wa Maama ta bige ki?" Tayi shiru tana kallonsa can tace "Bakomai." Bilki ta taso tana dariya tace "Kai yaro ma dai daban ne, d'azu ne fa na shiga wanka nazo na iske ta tana zubar da madara, shine fa nace mata kar ta k'ara. Alhaji yayi dariya "Ah ah Meenah a daina 6arna ba kyau kinji ko? Idan Maama tace a daina a daina kinji?" Ta gyad'a kai. Sai kuma yace "Bilki ya naga Meenah ta rame ne ko bata son cin abinci?" Tayi dariya tace "Ay Alhaji inda kasan yadda nake da fama da yarinyar nan akan taci abinci ko? Sai kayi mamaki sam batason ci na rasa dalili." Yace "To kuma ya baki sanar dani ba? Muka sani ko wani abin ke damunta? Kinsan yaro tunda ba fad'a zatayi ba." Tace "To k'ila dai." Ya juyo da dubansa ga Meenah "Haba Meenan Dada, meyasa baki cin abinci?" Nan ma shiru. Yayi murmushi "Zaki sha ice cream?" Nan take da washe baki tana murna. Shima yaji dad'i yace "Yauwa to bari idan na fita yanzu kafin na dawo gida zan siyo maki harda biscuit ma." Saukar da ita yayi daga cinyarsa yace "Bilki bari na wuce masallaci lokacin sallah yayi sai na dawo." Tace "A dawo lafiya." Sai da ya fita ta bishi da harara dashi da Meenah dake tsaye a tsorace gaban Bilki. Tana huci tace "Gaskiya abinnan ya fara isa ta, sai wani nan nan yake da yarinyar nan amma naga ba ruwanshi ma da Zarah, lallai Alhaji ka haifi d'iya a cikinka amma ka nuna son d'iyar wata? To da sake mts." Daga nan ta shige d'aki, Meenah na tsaye tana zare idanu. Haka kuwa akayi Alhaji da zai dawo sai da ya tsaya ya siya ma Meenah ice cream da biscuit sai ya k'aro mata kayan lashe lashe na yara. Zarah kuwa wani d'an abin wasa ne na yara ya siya mata tunda yasan bata isa shan wad'annan kayan ba. Yana dawowa Meenah ta tare shi tana murna, ya bata ice cream d'inta nan ta zauna ta shanye tas sannan ya bata biscuit d'inta ta tafi d'aki. Abin wasan yara ya bama Zarah dake hannunsa yana mata wasa. Ita kuwa sai dariya takeyi. Bilki na zaune kusa dasu tana wasa da Zarah. Can Alhaji yace "Ina Meenah tayi ne?" Tayi tsaki a ranta tace "Yanzu ta tafi d'aki ay ta ga k'wad'ayi kuma tunda bazata ci abinci ba." Tashi yayi yana fad'in "Ina zuwa." Ta6e baki tayi tana mai jin haushin Meenah. Yana shiga d'aki ya ishe Meenah kwance k'asa da biscuit a hannunta bacci ya kwashe ta. Murmushi yayi ya d'auko ta ya d'ora ta kan gado, ya gyara mata kwanciya sannan ya kashe fitilar ya fito. Koda ya fito Bilki bata nuna komai ba, Zarah ta k'ar6a tayi d'aki da ita don yi mata wanka. BAYAN KWANA BIYU Bilki ta fito wanka da safe kiran Laila ya shigo, tana d'auka Laila tafara magana "Kash Hajiya Bilki yanzu naji labarin iyalen Alhaji Adam sun koma Abuja gaba d'aya." Da sauri Bilki tace "Haba dai? To yanzu ya kenan?" "Bansani ba nima, plan d'inmu ya rushe don gidansa na Abuja akwai tsaro sosai, ko ina sojoji ne a gidan." Bilki tace "Gaskiya akwai had'ari mu ce zamuyi wani motsi yanzu. Amma ki bari tukunna a sake shawara." "To shikenan." Laila tace tare da katse kiran. Nan tayi ta sak'a da warwara ta rasa mafita. *** Haka rayuwar ta cigaba da gudana har akayi shekara d'aya amma har yau sun rasa wata mafita. A lokacin kuma Meenah ta shekara biyu harda rabi Alhaji ya fara shirye shiryen saka ta makaranta da kuma islamiyya. Don ya fuskanci zata iya da wuri don a yadda ya fahimce ta, ta iya saurin d'aukar abu da kuma maganarta ta fito ga surutu ba abinda bata fad'i. Sheyasa ma yanzu Bilki ta rage takura mata don muddin Alhaji ya dawo zata kwashe komai ta fad'a masa. Tana gudun kar tun baya tunanin komai har ya fara zarginta... AUREN FANSA 09 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 🌹09 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Haka kuwa akayi washe gari da safe Hamza da Bilki suka fita don saka Meenah a makaranta. Gobarau Academy itace makarantar da suka nufa, da zuwansu da komai basu wuce minti talatin ba aka kammala komai aka saka ta Pre nursery, duba da shekarunta kuma a k'a'idar makarantar idan yaro bai kai shekara 3 ba to baza'a saka shi nursery ba daman. Daman 'yan pre nursery ba'a saka musu uniform. A ranar aka barta makaranta kuma ko kuka batayi ba da su Hamza zasu tafi don ta samu abin wasa sai dad'i takeji. K'arfe 12 suke tashi don haka dole Bilki ke d'auko ta don Hamza na wurin aiki lokacin, ba yadda ta iya haka nan take hak'ura tana d'auko ta d'in. Haka rayuwar ta cigaba da gudana cikin hukunci da hikimar ubangiji, Meenah har ta shiga nursery. Meenah Allah ya bata k'walwa komai aka koya mata ta iya sai dai idan ba'a koya mata ba, kuma idan ta dawo gida ta dinga yi kenan ko gajiya batayi. Ba'a saka Zarah makaranta ba sai da Meenah ta shiga nursery 2 a lokacin ita kuma Zarah tana da shekara 3 a duniya yayinda Meenah keda hud'u. Ranar wata juma'a akayi ma su Meenah hutu suna zuwa gida Meenah ta fara neman babanta don nuna mai report card nata, sai dai rashin sa'a yayi tafiya zuwa Lagos a safiyar ranar, tayi ta kuka tana kiran ita Baba. Bilki tana tsaki ta ansa report card nata dana Zarah tana dubawa, abin takaici a wurinta wai Meenah na d'aya tayi ita kuwa Zarah na ashirin tayi cikin su ashirin da shidda. Bilki kamar tayi kuka don takaici. Wato Meenah dai tafi d'iyarta k'ok'ari kenan? "Gaskiya da sake!" Ta kalli Meenah tace mata "Ke! Zo nan!" Meenah tayi tsaye idanunta k'wal hawaye a duniya tana tsoron Bilki, fizgo ta tayi da k'arfi. "Ke dan ubanki sai da kika yi na d'aya wannan karon ma? Kin manta bugun da nayi maki last term kenan? Salon kija babanta ya dawo ya zane Zarah ko? Ke ga mai k'ok'ari ko? Shegiya mai kama da mage! Wuce ki bani wuri!" Da gudu Meenah tayi d'aki tana kuka sosai, jawo Zarah tayi ta rungume tace. "Don Allah d'iyar Baba ki dage kifi waccan yarinyar k'ok'ari kinji?" Zarah ta gyad'a kai. Da rana ta zuba ma Zarah abinci ta shiga wanka, Meenah na zuwa Zarah tace. "Zo muci." Ba musu ta zauna suka fara cin abincin tare. Ba'a jima ba Bilki ta fito wanka tana lek'owa taga Meenah nacin abin da d'iyarta abinda ta tsana! Da tsawa tace "Ke!" A firgice Meenah ta tashi tana kyarma, Bilki ta k'ara daka mata tsawa. "Bana hana ki cin abinci tare da Zarah ba? Shegiya wuce ki tafi d'aki." Tayi d'aki da gudu a tsorace. Zarah ta aje cokalin hannunta tace "Bazan ci ba nima sai da Meenah." Daman Bilki tasan abinda zatace kenan, tsaki taja tace "To sai dai kar kici wallahi amma bazakici tare da Meenah ba, kinji na fad'a miki!" Aikuwa aje cokalin tayi tana fushi sosai ta bar parlon. Tsaki Bilki ta k'ara yi tana k'ara jin haushin Meenah... *** Sauri yakeyi ya dawo gida don nuna ma iyayensa result nasa na shedar kammala jss3 nasa. Driver na yin parking ya fito da gudu yana murna shigarsa keda wuya ya taradda abinda ya d'aga masa hankali, ya kuma gigita shi a lokaci guda, take zuciyarsa ta fara bugawa da sauri a yayinda k'walwarsa ta tsaya cak! ta bar aiki lokaci d'aya!!! Iyayensa ne kwance jina jina, a yayinda wasu mutane kusan su bakwai ke tsaye cikin bak'ak'en kaya hartta fuskokinsu an rufe da black mask! Tsaye yayi ya kasa tantance a wace duniyar yake, take kuma ya fashe da kuka yana fad'in. "Su waye ku? Mey...asa ku...ka kashe min iyaye?" Direwa yayi k'asa yana kuka yana jijjiga iyayen nasa a yayinda yake kiran Anisah! Mutumin yayi dariya yace. "Ka bar kuka yaro, sun tafi inda ba'a dawowa kaima kuma yanzu zaka bisu!" Yakece da dariya sannan ya saita bindigar daodai saitin k'irjinsa ya harba. A gigice ya farka duk da Ac d'in da ke aiki amma hakan bai hana sa yin sharkaf da zufa ba. Ta6a jikinsa ya soma yi amma baiga jini ba, ajiyar zuciya ya sauke ya shiga yin addu'a don ba k'aramin tsoro yaji ba. "Wane wane irin mafarki ne haka..... ?" Ya fad'a yana mai k'ara tunawa da mafarkin da yayi. Zumbur! Kuma ya mik'e ya fice da gudu don duba lafiyar iyayensa don gani yake kamar da gaske ne....! AUREN FANSA 10 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 🌹10 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com "Mummy...! Mu.." A firgice suka farka daga bacci, da mamaki suka ce "Waye?" Kasancewar d'akin gauraye yake da duhu fitila a kashe take, Daddy ya kai hannunsa ya kunna bedside lamp yana kallon Faruk dake tsaye, da sauri Faruk ya rungume mahaifiyar tasa yace. "Alhamdulillah! Ashe duk lafiyarku lau, wallahi naji tsoro." Mummy tayi murmushi don tasan ya k'ara yin mafarki. Tace "Faruk nasha fad'a maka mafarki ba gaskiya bane ka daina d'aga hankalinka akan mafarki, nasha fad'a maka bakaji." Faruk yace "Nasani Mummy amma meyasa a duk lokacin da nayi mummunan mafarki sai naji gabana ya fad'i, sannan na kasa samun nutsuwa, gani nake kamar wani abu na shirin faruwa da mu!" Daddy yace "Haba Faruk! Ka zamo mai tawwakali mana, an fad'a maka mafarki ba gaskiya bane haba! Tashi kaje ka kwanta." Sum sum ya tashi ya fice, Daddy ya kalli Reemah yace. "Wai shin kuwa yaron nan na addu'a a duk lokacin da zai kwanta bacci?" Reemah tace "Yana yi, kullum sai na je na tabbatar da sai sunyi addu'a kafin su kwanta su duka." Daddy ya numfasa yace "To Allah ya kyauta amma sai ya k'ara dagewa da addu'a sosai." Reemah tace "Insha Allah." *** BAYAN WATA D'AYA Zaune yake yana karatu wayarsa ta fara k'ara, ganin sunan Daddynsa yasa yayi saurin d'agawa. "Hello kaine Faruk?" Yace "Eh nine lafiya ina mai wayar nan?" "Sai dai kayi hak'uri mai wayar nan ya rasu dashi da matarsa!" "What? Innalillahi wa'inna ilahir raj'un!" "Ya Faruk!" A firgice ya farka ganin Anisha tsaye gabansa tana kakkarwa, yasa yace "Ke lafiya menene?" Ta fashe da kuka. "Mummy! Ya Faruk Daddy da Mummy babu." Yace "Kamar ya? Ina suke?" Tace "Wasu mutane na nan sun zagaye Mummy da Daddy..." Kafin ta k'arasa ya mik'e da gudu ya fita." Zuwansa keda wuya ya taradda abinda ya d'aga masa hankali lokaci guda kuma ya gigice ya shiga rud'ani! Murza idanunsa ya fara yi don yayi tunanin wannna karon ma mafarki yakeyi, la6ewa ya shiga yi a bakin k'ofa yana sauraren mutanen da ke tsaye. Kusan su hud'u majiya k'arfi. "Hello Hajiya Laila Sunusi! Aikin da kika samu fa an kammala abu biyu ya rage. Na farko bamuga yaransu guda biyu da kika lissafa mana ba! Na biyu takardun gidannan da sauran mahimman takardun da kika ce a baki." "Yes Ma! Ok Ma! Insha Allah na miki alk'awarin cika miki dukkan aikin da kika samu da ke da aminiyarki ya sunan ta ma? Haha yes Bilkisu Ringim! Ok..." Kamo hannun Anisah yayi yana kuka d'akinsa ya fad'a ya kwashi wasu takardu nasa dashi dana Anisah na makarantarsa da abubuwan da yake buk'ata ya jefa jikka suka fito da sauri sukayi hanyar fita. Anisah na kuka shima yana kuka suka fito gate, gaba d'aya masu gadinsu basu nan, security sunfi goma amma yanzu bai ga kowa ba. Adaidaita ya samu suka wuce wata police station, yana zuwa ya fad'a masa dukkan abinda ya gani ya kuma ji sannan yace suzo su ceci iyayensa kafin su mutu. Ba 6ata lokaci suka nufo gidan sai dai da zuwansu abin mamaki ba komai gidan asali ma gidan a rufe yake da kwad'o sai dai gawar iyayensa, nan akayi examining d'insu aka tabbatar da basuda rai, take Faruk ya rasa a wace duniyar yake, kansa yayi dip, hawaye kuwa kamar an bud'e pampo. Sambatu kawai yakeyi yana fad'in. "Daman nasha yin mafarki an kashe mana iyaye! Nace abin kamar zai faru amma ba wanda ya kula ni..." Duk police d'in da yayi yunk'urin tab'asa da niyyar rarrashi turesu yakeyi suna fad'uwa k'asa, gaba d'aya kamar ya zauce. Yama k'i nutsuwa asan ina danginsa suke a sanar masu de abinda ya faru. Gaba d'aya gidan ba mota ko d'aya, motocin mahaifinsa sunfi kala takwas amma yanzu ko d'aya babu. Nan kuma kan Faruk ya fara juyawa kafin ya ankara ya fad'i k'asa tim! AUREN FANSA 11 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 🌹11 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com A hankali ya bud'e idanunsa bakinsa d'auke da salati, sai kuma ya fara kiran "Mummy! Daddy! Wai da gaske ne an kashe su? Ina Anisah? Wallahi duk wanda ya kashe min iyaye sai na rama masu koma waye..." "Alhamdulillah kunga ya farka ma ashe! Sannu ya jikin?" Kallon likitan yakeyi kafin kuma ya fashe da kuka sosai. Da k'yar aka rarrashe shi, sannan likitan ya zauna kusa da gadon da yake kwance tare da dafa sa. "Faruk, hak'uri zakayi iyayenka sun riga sun rasu, kukanka bazai ta6a maido su ba, yanzu addu'arka ita kad'ai suke buk'ata, kayi hak'uri kaganni nan na maka alk'awari k'wato maka 'yancika a gurin azzaluman da suka aikata maka wannan mummunan aikin, kar ka d'aga hankalinka kaji ko?" Ya share hawayensa "Nasani doctor, iyayena basa buk'atar kukana amma kuma ya zama dole nayi kuka, ba wanda zai gane abinda nakeji a zuciyata abin yana min ciwo, zuciyata tana min zafi, iyayena sune komai na, banida kowa a garinnan sai su, don haka dole nayi kuka saboda na rasa komai na rayuwa, na rasa iyayena, sannan na rasa gidanmu da dukiyar mahaifina..." Kuka yaci k'arfinsa. Doctor ya numfasa "Faruk kaganni sunana Dictor Ishaq Aliyu, ni d'an garinnan ne, daga yau na maka alk'awarin taimaka maka har sai ka samu ingantacciyar rayuwa da kai da k'anwarka, inada mata d'aya da yara hud'u, maza na guda biyu sai mata biyu, kar ka damu bazakayi maraici ba Indai kana tare dani don haka ka bar kuka ka share hawayenka." Faruk ya kalleshi da mamaki yace "Da gaske doctor? Zaka taimaka min duk da baka san koni waye ba?" Likitan ya gyad'a kai "Zan taimaka maka kuma zan taya ki fighting battle d'innan har sai kayi nasara, yanzu kaga kwananka hud'a a nan asibitin, kana buk'atar muje gida ka huta." Faruk yace "Nagode doctor! Nagode Allah ya saka da alkhairi! Ya k'ara budi." Likitan yayi murmushin jin dad'i yace "Amin Faruk mu tafi ko?" Yace "Eh, amma ina Anisah?" Likita yayi murmushi. "Gata can office d'ina tana bacci muje mu d'auke ta sai mu wuce." Ba'a d'auki lokaci ba suka iso gidan Doctor Ishaq, gida ne tangameme na gani na fad'a da ke Maitama, lallai shima doctor Ishaq mahashuk'in mai kud'i ne. Shi ya jagorance su har cikin gidan, suna shiga wata mata dattijuwa ta fito da murmushi a saman fuskanta. "Sannu da zuwa Alhaji." Ta fad'a tana k'ok'arin amsar jakarsa dake rataye a kafad'arsa. "Yauwa sannu da gida Malama Rukayya." Tayi murmushi. "Ahh bak'i mukayi kenan, sannunku da zuwa ku shigo mana." Suka shiga suka zazzauna kan kujera. Alhaji ya fara magana, ga yara nan, ki shiga dasu ciki suyi wanka ki basu abinci akwai maganar da zamuyi da ke bayan nan." Tace "To Alhaji." Ta tashi sannan su Faruk suka bi bayanta. Wani d'aki suka nufa daga gani na yaranta ne mazan, tace ma Faruk ya shiga yayi wanka, sannan ta fiddo masa kayan da zai saka. Hannun Anisah taja, ta mata wanka ta saka mata kaya masu kyau. Kan dinning taja su ta zuba masu abinci suka ci sosai sannan suka wuce parlor inda Alhajin ke zaune da alama abinci ya gama ci. Bayan sun zauna Alhajin ya fara magana. "Ina su Yazeed?" Tace "Suna can waje suna buga ball." Yace "Jeki kirawo man su gaba d'ayansu." Da girmamawa ta amsa ta fice. Can sai gata yaran na biye da ita a baya. "Dada welcome." Suka fad'a gaba d'aya. Yace "Thanks, ku zauna." Duk suka zauna, nan kuma suka hau kallon su Faruk. Alhaji ya numfasa ya fara magana. "Hajiya kinga wad'annan yaran guda biyu?" Tace "Eh nagansu." Yace "Yauwa, wannan shine Faruk sai ga k'anwarsa nan Anisah, shine yaron da nake kula dashi a asibiti bayan rasuwar iyayensa." Tace "Allah sarki sune yaran kenan? Allah ya jik'ansu da rahama." Yace "Amin, so nake mu cigaba da rik'esu a matsayin iyayensu, na farko kinga marayu ne gasu yara k'anana, na biyu duk wanda ya taimaki wani Allah zai taimake shi. Yara ne kuma marayu, basuda kowa sai Allah, shine na ga dacewa in d'auko su in rik'e don samun lada, ko ya kika ce?" Ta numfasa. "Haka ne Alhaji, wallahi wannan ba wani abu bane, insha Allah zan rik'e su a matsayin uwa a garesu, Allah ya bamu ikon rik'e amana." Yace "Amin, Faruk wad'annan k'annenka ne gasu nan, kaga wannan shine babba mai suna Yazeed, shekarsa sha biyar sai mai bi masa Hauwa'u ana kiranta Jidda shekararta Sha hud'u, sai k'aninta Nabeel shi yakeda da sha biyu sai auta gata nan Yusra ita keda shidda, don haka kuna jina wannan 'yan uwanku ne ban yarda wani ya nuna musu wariya ba a cikinku, kuna jina?" Suka ce "To Dada." Alhaji yayi murmushi "Faruk ga kannenka nan sai kuje kuyi wasa ko?" Faruk yayi murmushi inda gaba d'aya suka mik'e suka fice. Alhaji ya ce "Allah ya bamu ikon rik'e su amana, ya tona asirin azzaulumai." Tace "Amin ya Allah Alhaji, yaran sun bani tausayi wallahi, Allah ya bi musu hakk'insu." Yace "Amin amin, anjima zanje inyi magana da manyan lauyoyin da na sani, asan me za'ayi a kai." Tace "Hakan yayi daidai, yanzu makarantarsu fa?" Yace "Makarantarsu ba matsala bace na d'auki nauyin karatunsu, yanzu ayi k'ok'ari a saka su makarantarsu Yazeed." Tace "Haka yayi daidai, Allah ya k'ara bud'i." Yace "Amin Amin, bari inje in d'an kwanta kafin anjima zan koma asibiti." Tare suka mik'e ya fice tabi bayansa. (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 🌹12 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com *** Washe gari aka saka su makaranta. Yanzu abubuwan sun ma Faruk sauk'i tunda yanzu gidan da suke basuda matsala, daidai gwargwado suna samun kulawa sosai, sai dai har yau hoton gawar iyayensa ya kasa 6ace masa kai, ko rufe ido yayi sai ya gansu ya kuma ga mutanen da suka kashe su, sannan sunayen da aka ambata har yanzu ya kasa mantawa hasali ma ya samu diary nasa ya rubuta sunanayen nasu. Ya samu shak'uwa mai k'arfi tsakaninsa da su Yazeed komai a tare sukeyi su uku abin sha'awa sun had'e kansu. Duk inda kaga d'aya to zakaga d'ayan. Haka ma Anisah da Yusra sun zama k'awaye, ita Jidda ta girmesu don haka sai dai sama sama suke shiri, daga gaisuwa sai kuma cin abinci ke had'a su. Duk da k'arancin shekarun Anisah ta fuskanci Jidda nada wuyar sha'ani sannan miskila ce ta k'arshe, sai dai akwai kuma kirki halayen nata dai gasu nan a baibai, mutum ce mai wuyar fassara, sheyasa ta lura yaran gidan basu shiga harkarta, don haka itama sai tayi baya baya kad'an. Har yau Anisah ta kasa gane iyayensu sun mutu har abada bazasu dawo ba, don kusan kullum sai ta tambaya. Meyasa suka dawo nan da zama, ina Daddy da Mummy? Yaushe zasu dawo? Haka take tasa Faruk gaba da ire iren wad'annan tambayoyin har idan ya rasa amsa sai tasa masa kuka, dole sai dai yace sunyi tafiya mai nisa kuma zasu dad'e basu dawo ba. To tun wata rana da abin ya fara isarsa ya daka mata tsawa yace tayi hak'uri Mummy da Daddy basu dawowa, da farko ta tsorata amma da Faruk ya zauna yayi mata bayani sai kuma ta fahima, ya kuma d'ora da cewa ta dinga yi musu addu'a kullum, aikuwa tun daga ranar bata k'ara tambayarsu ba haka ma da ta motsa sai tayi musu addu'a. *** BAYAN WANI LOKACI... Zaune suke kan dinning suna breakfast gaba d'ayansu, Dada ne ya aje cokalin hannunsa ya soma magana. "Wai ina Faruk ne?" Hajiya Rukayya da suke kira da Mama tace "Inaga yana ciki kamar wanka ya fito." Sanye yake cikin bak'in wando wulik pencil trowser sai ya d'ora ash shirt marar hannu, tun daga k'afafuwansa ya isa ka gane cewa kyakkyawan mutum ne, don kuwa k'afar tasa fara ce tas kalar larabawa har wani gashi gashi ake gani a tsakankanin yatsanshi na k'afa. Haka nayi ta d'aga kaina har na sauke su kan fuskarsa... tabbas duk inda ake neman namiji toh a nemi wannan mutumin, gashin kansa irin mai cikar nan ne mai yawa sannan nannad'e yake kamar na jarirai. 'Ya Faruk Dada na jiranka fa za'a ci abinci." Kai! Wannan Anisah ce ta k'ara girma haka? Lallai idan na tsaya muku bayani bazaku gane ba, kamarta d'aya da Faruk gashinta mai kama dana larabawa an tufke shi daga can tsakiya amma duk da haka sai da ya zubo bayanta, kyakyawa ce itama. Sanye take cikin light pink dress 'yar kanti. Murmushi yayi mai bayyana hak'ora yace. "Ina zuwa." Da sauri ta fice, turare ya feshe a jikinsa sannan ya zura takalmansa ya fice. Yana zuwa ya gaida Mama da Dada ya samu wuri ya zauna kusa da su Nabeel. Nan aka soma cin abinci. Dada ne ya dakata ya soma magana. "Faruk kamar kullum bazan gaji da ce maka kayi hak'uri ba, wallahi har yanzu kan aiki ake ganin an kamo wad'anda suka kashe iyayenku..." Faruk yayi murmushi yace "Haba Dada wallahi babu damuwa, komai lokaci ne, insha Allah Allah zai bayyana mana su." Dada yayi murmushi, sheyasa yake son Faruk yaro ne mai kaifin tunani, da kuma nutsuwa da hangen nesa. Don haka sai yace "Haka ne, amma insha Allah za'a cigaba da aiki Allah yasa a dace." Suka amsa da "Amin." Dada ya cigaba. "Kunga yanzu kuna dab da gama makaranta, to kamar yadda nayi alk'awari mazan zan tura su Saudia don neman ilimi, to zan had'a da kai Faruk kowa ya za6i abinda zaije ya karanta. Abinda yasa kuka ga na za6i wannan k'asar saboda nayi k'wak'waran bincike ana tsaro sosai da yaran mutane, to kuma yaro ko yaso koya k'i dole ya kama kansa. Amma kamar kullum bazan gaji da jawo hankalinku ba, don Allah ku nutsu ku tsare mutuncinku, kar kuga bana kallonku to ku tuna Allah (S.W.A) yana kallonku, wallahi kuji tsoronsa abinda kuka je nema shi zakuyi, kunaji ko? Allah yayi muku albarka sai ku dage ku fito da grade mai kyau." Suka ce "Amin Dada, insha Allah zamu kiyaye." A haka suka cigaba da karyawa. *** "Mami don Allah ki barni zan sa da kaina." Hajiya Bilki tayi tsaki "Ke da Allah wuce can, ki bari na sa miki." Ta zum6uro baki. "Assalamu Alaikum..." Bilki ta d'ago tana k'are mata kallo. "Wa'alaikumusalam." Daga sama har k'asa na k'are mata kallo, Meenah ce ta girma haka? Tayi tsawo ta k'ara kyau, wannan ita ake kira black beauty, ga gashin kanta duk d'ankwalin da ke kanta hakan bai hana shi fitowa ba... "Mami na gama wanke kayan." Bilki ta ta6e baki. "Kin gyara min kitchen?" Tace "Eh na gyara." "Kinyi shara da wanke wanke?" Meenah tace "Eh nayi..." "Kin wanke toilets?" "Eh na wanke naki..." "Na d'akin Zarah fa? Shifa wa zai wanke?" Ta d'an bata rai. "Mami home work kawai zanyi sai na wanke, an bamu home work har biyar gashi ko d'aya ban ta6a ba." Ta doka mata harara, "Sannu 'yar boko, toh bari kiji bazakiyi ba sai kin gama min aikina tsab a gidannan sannan zaki yi wani home work." Tayi narai narai da fararen idanunta wadda suke kamar an d'iga madara a ciki. "Ke! Bansan iskanci ya ina miki magana kin tsaya kina wani kallon mutane zaki wuce ko sai na mauje ki!" A zahirin gaskiya bawani assignment d'in da zatayi, don ta riga tayi shi da asuba, daman gudun aiki yayi mata yawa sheyasa data gama sallah take home work ko karatu, kawai ta gaji ne tun safe take aiki bata huta ba, daga wannan sai wannan ko kalaci batayi ba... "Mami zan taya ta." Bilki ta 6ata rai "Kiyi ki gani yadda zanyi da ke a gidannan, maza kije kuma kar tayi nata home work d'in sai ta gama maki naki!" Sum sum Zarah ta fice zuciyarta cike da tausayin Meenah... AUREN FANSA 13 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 🌹13 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Duk'e take tana faman wanke toilet Zarah ta lek'o, cikin muryar rad'a rad'a tace. "Meenah bari na taya ki." Meenah ta d'ago tana duban Zarah tace "A'a ki rufa man asiri Zarah, yanzu da Mami tazo zata dake ni." Zarah tayi murmushi "Ay dana ji ta taho zan bari..." "Nidai gaskiya ina tsoro ki bari kawai..." Da sauri Bilki ta shigo d'akin, tana zuwa ta jawo Meenah. "Ke maza kije kiyi wanka ga babanku nan dawowa, bar wankin toilet d'in zan k'arasa..." Halin maman tasu na basu mamaki, sun rasa meyasa da babansu ya kusa dawowa sai ta hana Meenah yin ko wane aiki. Sum sum Meenah ta fice daga d'akin. "Mami meyasa kike sa Meenah aiki ni baki sani? Kuma meyasa idan Baba ya kusa dawowa kike kora Meenah tayi wanka ko taci abinci?" Bilki ta daka mata tsawa "Ke! Kar ki k'ara min ko wace irin tamaya a nan kina jina? Kema fita ki bani wuri." Sum sum ta fita tana jinjina hali irin na uwarta. Ba'a jima ba ya shigo gidan a gajiye, Bilki ta tasa yaran gaba suna kallo ya shigo da ledoji a hannunsa, da sauri Zarah da Meenah suka mik'e suka kar6a kayan hannunsa. Bayan ya zauna yana murmushi yace "Kaza ce da ice cream na siyo maku kuje kuci." Da murna suka shige ciki. Bilki tana murmushi tace "Yaran nan na shan gata Alhaji, kana tunanin baiyi yawa ba kuwa?" Alhaji yayi murmushi yace "Bilki kenan, ay ba wani abu nake musu na gatanci ba, bana sangarta su, haka ma bana 6ata su da kud'i ko wani abin duniya, abinci ne nake basu wanda kuma yin hakan ba laifi bane." Tayi murmushi "Bakayi laifi ba kam nima dama wasa nake maka." Sai kuma yayi ajiyar zuciya "Kinsan abinda ke damuna?" Tace "Sai ka fad'a." Yace "Mutuwar Alhaji Adam, su waye marassa imanin da suka bishi har gidanshi suka kashe shi dashi da matarsa?" Bilki ta had'iye miyau da k'yar tace "Nima abinda yake damuna kenan kullum Alhaji, nasan mahassada ne kawai." Ya numfasa "Wai me duniyar nan keso ta zama ne? Mutane akan kud'i ba abinda bazasuyi ba?" "Uhm...uhm Alhaji bari na kawo maka ruwa kasha." Bai kawo komai a ransa ba yace "To." Aikuwa da daddare Meenah bata samu abincin dare ba, wai ay taci kaza ta k'oshi bataga dalilin da yasa za'a bata abinci ba. Da safe Baban na fita aiki ta jibga mata uban wankinta dana Zarah, duk da suna da mai wanki amma tsabar mugun hali irin na Bilki sai da ta jibga mata wankin daya fi k'arfinta. Tana gama bata wankin ta shigo daidai bakin k'ofa taci karo da Zarah tana fad'in. "Mami idan Baba ya dawo sai na fad'a masa abinda kike ma Meenah idan baya nan..." Finciko ta taji anyi, tayi d'aki da ita tana zuwa ta shiga tsula mata bulala, sai data zane ta tas sannan tace "Wannan kad'an nayi miki akan bayan kin fad'a masa, sai jikinki ya gaya musu, zaki fad'a ko kuwa?" Da sauri ta girgiza kanta tana kuka. Haka dai kwanaki sukayi ta tafiya cike da wahala a gurin Meenah, sam batada lokacin kanta sai aikin gida, bata samun lokacin karatu sai can cikin dare, sheyasa gata nan wata 'yar ficit sai tsawo amma ba kumari, Zarah kuwa wata 'yar duma duma ga ta fara sol fatar jikinta irin ta 'yan hutun nan ce da basu san wahala ba, ita kuwa Meenah batada k'iba sai tsawo. *** A haka rayuwar tayi ta mirginawa, har Meenah ta kai SS3 a yayinda Zarah ke SS2, yaran sun girma sun zama 'yan mata, daka gansu tare sai ka k'ara kallonsu don kuwa ko a makaranta tare sukeyin komai, shiga aji kawai ke raba su. Halayen nasu ne kawai ya banbanta, ita Meenah tana da wani calm attitude, tanada nutsuwa komai nata a hankali takeyinsa, ko maganarta wani a hankali takeyi, ba kamar Zarah da take abu kazar kazar ba, ita tsaye take kamar ba mace ba, she's too lousy dai tana da hayaniya.... Sannan uwa uba Meenah ba irin girkin da bata iya ba, da kuma ko wane irin aiki yi take irin su shara wanke wanke, wanki da sauransu, kuma bata gajiya da gyara wuri koda za'a shekara ana 6ata shi, Meenah bata damu da abin duniya ko wayar da take rik'ewa batada komai na social media a ciki, ita dai kawai tayi waya idan ta kama shikenan, amma Zarah akwai son harkar social media, ga yin hoto kamar hauka, to a wannan fannin ne halayensu suka banbanta, ga son jiki bata iya ta6uka komai na aikin gidan saboda haka ta taso ba'a sata tayi, sheyasa ko gyaran d'akin bata iya ba, sai Meenah tazo ta gyara mata... AUREN FANSA 14 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 Dedicated to Susu, thank you for everything!❤️ 🌹14 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Bakajin komai a d'akin sai k'yalk'yatar dariya, da k'yar suka dakata, Laila ce ta soma magana. "Shegiyar gari, wato kina nan kina facaka cikin dukiya, kina nan kina taka matsayin da kika d'ad'e kina burin takawa, kina nan kina hawa kud'i ki taka kud'i ki yadda kikeso a cikinsu, lallai shawara d'aukar d'aki yau gashi mun da'auka tayi mana amfani!" Suka sake sa dariya, Bilki tace "A da na bijirewa shawararki, kuma da farko na tsorata amma yanzu abin sai wanda ya gani." Suka sake sa dariya gami da tafa hannu. Laila ta kuma cewa tana dariya "Yayi daidai kin birgeni! Yanzu keda talauci sai dai ko a lahira..." Bilki tace "Kada Allah ya had'ani da shi koda a lahirar ne ma. Yanzu tsoro na kada wata rana a gano mu ya zamuyi kenan?" Laila tace "Daman ay ke bugun Abuja ce, daman ke kalarki bata k'auye bace ba..." Bilki tayi dariya "To kin dai gani, rabona da k'auye har na manta, tunda muka dawo Abuja idan kin ganni k'auye sai dole..." "Assalamu Alaikum..." Ta shigo d'auke da tray d'in lemo da glass cups guda biyu sai plate d'in cincin da dambun nama. Ta ajiye tray d'in sannan ta gaishe su, sai da suka watsa mata harara sannan suka ce "Lafiya." Bilki tace "Kin d'ora abincin rana?" Tace "A'a yanzu zan d'ora." Bilki tace "Aikin me kike da tun d'azu baki d'ora ba har kusan k'arfe sha biyu?" Tace "Wanke wanke ya taru da yawa shine na..." "Yi min shiru a nan!" Ta daka mata tsawa. "Duka duka wanke wanken guda nawa ne da har zaki ce yayi yawa? Sai anyi magana ki dinga rissina kai kamar wata yarinyar kirki, zaki wuce ki d'ora ko sai na san me zan miki!" "Uhm... me za'a dafa?" Tayi tsaki "Ki dafa mana fried rice da peppered chicken, sai ki had'a coleslaw, akwai kaji a freezer ki d'auki guda biyu kiyi amfani dashi. Sai kinsan halin babanku yafison tuwo, kiyi masa tuwo miyar busassar ku6ewa." Da k'yar tace "To." Ta fice idanunta cike da hawaye! "Anya bataji mu ba d'azu?" Cewar Laila cike da damuwa. "Ko taji me za'ayi? Ah babu ay." Sukayi dariya Laila tace "Haka ne fa." Tana kitchen tana yanka kaji Zarah ta shigo tana sanye da wando jeans sky blue sai light pink shirt marar hannu. "Meenah zo ki ga..." Da mamaki take kallonta tana d'aga mata fuska don taga idan idanunta ba k'arya suke nuna mata ba. "Meenah kukan me kike? Hala Mami ce? Me tayi miki?" Ta k'ak'alo murmushin dole tace "Babu komai, wani abu ya fad'a min ido ne." Zarah tayi murmushi "Uhm baki iya k'arya ba Meenah, ni nasan wani abu Mami tayi miki." Meenah tace "Bakomai amma don Allah Zarah zan miki tambaya inaso ki fad'i man gaskiyar abinda kika sani." Zarah tace "Ina jinki." Meenah tace "Don Allah a iya zamanki a gidannan kin ta6a ji koda a wurin wani ne cewar tsintso ni akayi?" Zarah ta k'yalk'yale da dariya harda duk'ewa, Meenah ta kalleta galala cike da mamaki tace "Meye haka wai Zarah? Ya ina tambayarki kin tsaya kina min dariya?" Har yanzu dariya takeyi, da k'yar ta tsagaita tana duban Meenah tace "Anya baki buk'atar ganin likita Meenah? Kanki d'aya kuwa?" Meenah ta k'ule tace "Shikenan sai kije kiyi ta dariyar, gani kike kamar wasa nakeyi ko?" Zarah tace "Daman ay wasan kikeyi, ta yaya ma zaki fara irin wannan tunanin?" Meenah tayi murmushi mai ciwo tace "Dole nayi tunanin haka Zarah, na rasa meyasa Mami bata sona..." Da sauri Zarah ta rufe mata baki "Kar kice haka, ay indai zaki kula halinta ne haka, koni tana min." Meenah tace "Eh amma ba kamar yadda take min ba, dole ne na fara tunanin duk yadda akayi ko tsinto ni akayi ba'a san asali na ba, ko kuma ni 'yar rik'o ce." Zarah ta 6ata rai "To yayi miki kyau, ki cigaba da fad'in haka ni kuma daga yau na daina miki magana a gidannan." Meenah ta juyo da sauri "Haba dai?" Zarah tace "Ki cigaba ki gani." Da sauri Meenah tace "La na bari, ya za'ayi na bari mu 6ata?" Zarah tayi murmushi "Yawwa sweet sis bara na taya ki aikin don ayi sauri, kuma idan kika hanani yi sai na daina miki magana a gidannan." Ta fad'a cike da shagwa6a, Meenah tasa dariya ta kwaikwaiye ta "To bazakiyi ba wuce ki tafi ki kwanta." Zarah tace "Nak'i" Haka suka k'arasa aikin suna zolayar juna, wasu abubuwan sai da Meenah ta dinga koya mata, kuma ba laifi tana fahimta. *** "Wai bazakuyi sauri ku fito ba Jidda? Kodai a tura driver ya d'auko su ne?" Da sauri Anisah ta fito cikin shigar atamfa d'inkin doguwar riga kalar blue and purple sa ta d'ora purple mayafi. "A'a Mama mu zamu d'auko su, nifa na gama shiri su ya Jidda ne tun d'azu basu gama ba." Mama tayi dariya. "Au kin k'agu kiga yayan naki hala? Wannan irin zakwad'i haka?" Anisah dariya, daidai nan sauran 'yan matan suka fito sun sha ado sunyi kyau inda dukansu suke cikin shiga iri d'aya. Yusra tayi dariya "Kai Mama duk kin k'osa a dauko miki yaranki ne haka?" Mama tayi dariya "Ke ni ba kakarki bace, ku wuce ku tafi haka nan." Da sauri suka tafi suna dariya... Jidda ta dubi agogon dake mak'ale a hannunta, k'arfe sha biyu harda rabi ta wuce. "La Ibrahim kayi sauri sun kusa sauka." Ibrahim yayi murmushi "To ranki ya dad'e." Tunda suka dira a airport hankalinsu ya kwanta ganin har yanzu basu sauka ba, amma daga inda suke suna hango jirgin yana niyyar sauka k'asa. Duk sukayi ajiyar zuciya. A hankali jama'a suka fara fitowa daga jirgin, haka ma duk wanda ya hango d'an uwansa sai ya ruga ya taro sa. Tsaye suke kusa da kujerar zama wato (waiting chair) idonsu k'yam saitin k'ofar jira kawai suke suga ta inda zasu 6ullo. AUREN FANSA 15 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 🌹15 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Ba'a fi minti biyar ba suka kunno kai, ko wanensu yana tura trolley nasa, tunda suka fito Jidda ke kallonsa ya za'ayi ta mance da wannan fuskar? Ya chanza gaba d'aya ya zama wani babba, k'irar jikinsa kansa abin kallo ce irin giant d'innan, abinka ga fari sai ya k'ara murjewa ya zama bature sak! Ta kalleshi yana murmushi. "Sannu da zuwa yaya!" Anisah ta ruga tare da mak'alk'ale shi, a yayinda Yusra ke mak'ale da nata ya'yyen, sai a lokacin Jidda ta dawo duniyar tunani. Da k'yar ta daidai nutsuwarta tace "Sannunku da zuwa!" Ko alama bai gane ta ba. "Yauwa sannu... Jidda ko?" "Wow haka muryarsa take?" Ta fad'a tana k'ara kallonsa cike da mamaki. Tace "Eh nice yaya." "Wow duk kun girma..." Suka taya su jan kayan nasu har bakin mota. Tafiya suke amma idonta na kansa. Abu d'aya take maimaitawa a zuci... "What kind of change is this?" Haka aka loda kattunan jakunansu a boot. Koda suka shiga mota shi ya zauna gaba, daga baya babu abinda Jidda keyi sai aikin kallonsa. "Ya Faruk? Ya Faruk? Ya Faruk?" Wannan abu shi take ta fad'i a ranta. Ta d'an k'ara kallonsa ta baya, gashin kansa kad'ai abin kallo ne, ya k'ara kyau akan wanda yake dashi da, sai shinning yake kamar taurari a sama... "Anya bayada iri da larabawa?" "Wa kenan?" Ta kai dubanta tana kallon Najeeb daya tsareta da kallon tuhuma, tace "Uhm uhm bangane ba." Nabeel yace "Rabu da ita tun d'azu na lura da yadda ta chanza." Tace "Na chanza kamar ya?" Najeeb yasa dariya. "Kamar yadda kika fahimta." Daga nan ba wanda ya tanka har suka iso gida. Mama harda d'an gudunta tana fad'in "Welcome home." Suka shiga parlor Najeeb ya kalli matan yace "Ku kai mana kayanmu d'aki." Sannan ya maida kallonsa da Mama. "Bari mu d'an watsa ruwa muyi sallah." Mama tayi murmushi "Eh hakane lokacin sallar azahar yayi ya kamata ayi sallah sai aci abinci, sannunku da hanya." Nabeel yace "Yauwa Mama, ina Dada?" Tace "Yana Ireland yau satinsa d'aya da tafiya, amma insha Allah ya kusa dawowa." Najeeb yace "Ok... hakane munyi waya yake fad'a min batun tafiyar tasa Allah ya dawo dashi lafiya." Aka amsa da "Amin" Daga haka kowa yayi hanyar d'akinsa. Faruk d'akinsa ya burgeshi yadda yayi tsab sai k'amshi da sanyin ac ke ratsa dukkanin illahirin jikinsa, bai tsaya wata wata ba ya fad'a toilet. Yana gamawa ya saka k'aramar riga da dogon wando. A dinning aka hallara kowa yayi serving kansa jollof d'in shinkafa, da pepper soup, sai kaza gasassa sai salad. Sun fara cin abincin ne Mama tace. "Alhamdulillah, Allah na gode maka daka nuna man wannan ranar, ranar da 'ya'yana suka kammala karatunsu lafiya, fatana Allah ya albarkaci karatunku, Allah ubangiji ya baku sa'a." Gaba d'aya sukace "Amin amin." Ta cigaba "Yanzu dai ga Likita Najeeb, ga Detective Faruk, ga kuma Banker Nabeel, kai masha Allah! Allah yayi albarka." Suka ce "Amin Mama mun gode Allah ya saka da alkhairi." Tace "Amin, yanzu dai ya kamata kuyi settling kowane ya nemi mata yayi aure, shine kad'ai abinda ya rage." Duk kansu k'asa basu ce komai ba, itama Mama murmushi tayi a haka suka cigaba da cin abinsu. *** Bayan Wata D'aya...! Zaune yake kan kujerar office d'insa yana faman dube dube a computer d'insa, aka shigo da sallama, a hankali ya d'aga ido ya kalli k'ofa yayi murmushi. "Ah Usman! Shigo mana ya zaka tsaya a bakin k'ofa?" Ya k'araso yana gaishe shi "Ina wuni sir?" "Lafiya lau zauna magana zamuyi." Bayan ya zauna, Faruk ya soma magana. "Wani aiki zan saka, don Allah ina so duk abinda nake nema ka yi k'ok'ari wajen ganin ka samo min duk wani abu zan buk'ata." Usman yace "Insha Allah, ay ba yau ka fara sani aiki ba, kuma duk lokacin da kake sani abu ina k'ok'ari waje ganin na gano maka koma me kake nema." Faruk yace "Haka ne, to yau ma ina tafe da wani aikin mai matuk'ar mahimmanci a wurina." Ya fad'a yana fiddo wani abu a cikin drawer d'in table d'insa. "Karanta kaga." Da ladabi ya kar6a ya soma karantawa. Bayan ya gama yace "Yalla6ai amma suna ne kawai nake gani." Faruk yayi wani d'an guntun murmushi yana juya kujerar da yake zaune akai. Sai da ya d'auki tsawon mintina biyu zuwa uku sannan ya soma magana. "Eh sunaye ne na mutum biyu, bincike nake buk'ata akansu." "Toh yalla6ai." "Yawwa, i want every bit of information regarding them. Ina buk'atar komai idan nace komai i mean everything. Wane gari suke? Wace unguwa? Sunada 'ya'ya? Guda nawa ne? Suna da miji? Meye sunansa? Wane aiki yake? Ina da ina suka fi zuwa? Wace makaranta yaransu suke? Don't left out anything, including their photos." Usman ya gyara zamansa yana fuskantarsa. "Angama amma yalla6ai meyasa kake neman information d'innan haka? Sannan ta ina zan samo hotunan su?" Faruk ya mik'e tsaye tare da dawowa gaban Usman gami da zama saman table a kusa da shi yace "Usman bana son shishigi, aiki na saka shi zakayi min, kawai kaje ka kawo min abinda na saka please banda wasa, sannan hotunansu wannan kai zaka nemo." Usman yace "Hakane insha Allah zanyi k'ok'ari." "Yauwa kana iya tafiya." Daga haka ya fice, inda Faruk yayi murmushi yace. "This is my first step towards my goal, waiting for the next step." Yayi murmushi yana kad'a kai. AUREN FANSA 16 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 🌹16 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com *** Tsaye take a gaban wardrobe tana gyara zaman skirt d'inta, duk da kayan dake jikinta sun mata kad'an hakan bai hana ta yin kyau ba, ji tayi an rungume ta ta baya, tasan baya wuce aikin Zarah. "Auch! Haba mana Zarah so kike ki k'arasa ni ne?" Zarah tasa dariya, tace "To sarkin fad'a, yanzu dai maida wuk'ar albishir nazo miki dashi." Meenah ta juyo da murmushi saman fuskarta tace "Ina jinki." Zarah tace "Fari ko ja?" Meenah tace "Fari k'al ma kuwa." "Baba yace nayi WAEC d'ina yanzu idan naci mu tafi university tare!" Zarah tace cike da murna. Meenah farin ciki ta rasa ina zata sa ranta, dama ta dad'e tana addu'ar su tafi university tare da Zarah, sai dai tasan Baba ne ya hana yace bazatayi ba sai ta kai SS3, amma yanzu ko ya akayi ya yarda? Meenah tace "Amma ya akayi ya yarda?" Zarah tace "Wallahi ikon Allah, kuma fa ba tambayar sa nayi ba, shi da kansa ya kirani yace na shirya yin exam tare da ke." Meenah cike da murna tace "Lallai ikon Allah, Allah yasa kici." Zarah ta rungume Meenah tana murna tace "Amin sisi." "Kai meye kun cika ma mutane kunne da hayaniya?" Cewar Bilki daga bakin k'ofar d'akin tana tsaye, fuskarta ba yabo ba fallasa. Sukayi tsit, ta kuma daka musu tsawa "Ba da ku nake ba?" Zarah tace "Da... dama, Baba ne yace za... zan iya tafiya university tare da Meenah..." Take ta washe baki kamar ba ita ba, tace "Allah d'iyar Baba? Yaushe ya yarda?" Tace "D'azu kafin ya tafi wurin aiki." Bilki tace "Alhamdulillah, yayi daidai Allah ya bada sa'a sai ki dage, tun kafin ace bakida k'ok'ari, ko kuma ace wasu sun fiki." Ta k'arasa tana ma Meenah wani irin mugun kallo. Duk sun san abinda take nufi kuma hakan ya sosa ransu. "Ke! Meenah zo ki matsa man k'afa ta." "Mami zan taya ta." Wani kallo ta watso mata na irin kika k'ara magana sai na kakkarya ki sannan ta fice. Meenah ta dafa ta tana fad'in. "Don Allah Zarah daga yau ki daina cewa zaki taya ni idan tasa ni aiki, wallahi fad'a kike ja man duk sadda kika fad'i haka." "Uhm." Kawai Zarah tace, daga haka Meenah ta juya da sauri zuwa sashen Mami. Da sallama ta shiga, zaune take kan wata kujerar hutawa ta baje k'afafuwanta ma'ana ta mik'ar dasu saman kujerar, tana faman danne danne a wayarta k'irar iPhone 7plus, tana zuwa ta durk'usa har k'asa tace "Gani Mami." Sai data samu tsarabar harara sannan tace "Meya tsaida ki tun d'azu nake zaman jiranki?" Bata ce komai ba kanta na k'asa dai. "Sai anyi magana kiyi sum sum da kai kamar mutuniyar arzik'i..." "Kiyi hak'uri Mami, wallahi ban tsaya yin komai ba nan na taho." Tayi tsaki gami da mik'o mata k'afa. "Ni matsa man k'afata, kuma saura kiyi mani mugunta irin na rannan wllh sai na yi maganinki, don yau sai dai a kaiki asibiti don sai nayi miki lis!" A hankali take matsa mata cikin lalla6awa, sai kuma ta sakar mata k'wanya a kai. "Ke bakida hankali ne? Ya zaki dinga mani abu kamar susar k'adangare?" Sai ta hau yi da d'an k'arfi, nan ma ta kai mata wanda yafi na d'azu zafi. "Yau ga muguwa! Zaki 6alla min k'afa ne?" Ta rasa yadda zatayi, mistake kad'an sai taji k'wanya mai shegen zafi a kanta. Da daddare tana kwance ita dai abin duniya yabi ya dame ta, zuwa yanzu ta yarda ta amince ba Mami ta haife ta ba, ta yarda Baba ne babanta amma sam ta kasa yarda Mami ce ta haifeta. To ina mahaiyarta? Ta rasu ne ko tana raye? Ko kishiyar Mami ce? Kullum ire-iren wad'annan tambayoyin sune suke mata yawo a cikin kai, kuma har yanzu ta rasa amsa. Daga k'arshe ta yarda ta amice mahaifiyarta ta rasu kuma kishiyar Mami ce kawai. Wasu zafafan k'walla suka zubo mata, ita kam batasan dad'in uwa ba, bata san ya ake ji ba idan mutum na tare da mahaifiyarsa. Sama sama tayi bacci gudun makara saboda ga aikin gida ga kuma shirin makaranta. Da asuba ta mik'e bayan ta gabatar da sallar asuba tayi wanka, ta yi aikin gidan kamar kullum, ta had'a kalaci, d'aki ta wuce ta sanya uniform d'inta da basu samu guga ba, bayan ta gama shirinta tsab ta fito don ta karya, tana bud'e kular abinci sai ta ganta wayam! Nan ta hau dube dube amma kaf ba komai a ciki. Mami ce ta sauko cikin kayan bacci da d'aurin gaba tana zuwa tabi Meenah da mugun kallo, ta wuce kitchen. A ranar haka nan ta hak'ura da kalacin daman sun makara, sauk'inta ma Baba ya basu kud'in makaranta da batasan ya zatayi ba. *** BAYAN KWANA BIYU Da sallama ya shigo office d'in, yana zaune yana fama da aiki kamar kullum, d'ago da fuskarsa yayi yace "Shigo mana Usman." Sai da ya kammala abinda yakeyi sannan ya maida dubansa ga Usman dake zaune d'auke da wata babbar brown envelope. "Yalla6ai daman akan aikin da kasani ne, to Alhamdulillah na kammala maka komai shine na kawo maka ka gani." Da sauri ya d'ago yana duban Usman yace "Da gaske ka kawo duk abinda nake buk'ata?" Usman yana murmushi sosai yace "K'warai kuwa gasu." Ya sa hannu ya zazzaro wasu hotuna guda biyar ya dire a gabansa, sannan ya fiddo wani dogon paper mai rubuce rubuce a samanta.... AUREN FANSA 17 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 Dedicated to Kiddies friends 4ever, thanks for the support you are special to me! Love you guys❤️ 🌹17 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com D'aya bayan d'aya yake duba hotunan dake baje a gabansa, sai daya d'auki lokaci kad'an yana analyzing ko wanensu duk Usman yana kallonsa. Sai da ya gama sannan ya d'ago yana kallon Usman yace. "Nagode, sai kayi min bayaninsu." Usman ya gyara zama yace "Yalla6ai ka duba wannan takardar na rubuta komai amma duk da haka zan maka bayani da baki. "Da farko hotunan nan sai da nayi k'wak'waran bincike akansu kafin nazo nan." Hoto d'aya ya d'auko ya mik'a masa. "Wannan sunansa Alhaji Hamza Umar, haifaffan d'an garin Katsina ne kafin ayi masa transfer zuwa nan Abuja. Wannan kuma matarsa ce Hajiya Bilkisu, yaransu biyu kacal duka mata. Babbar itace Amina wadda suke kira da Meenah ga hotonta nan, sai k'aramar wadda babu wani tazara a tsakaninsu mai suna Fatima Zarah. Duk wad'annan hotunan sai da nayi bincike na gano account name d'in d'iyarsa mai suna Zarah duk a nan na kwaso hotunansu, ita Meenah a nata account d'in babu hoto ko k'wara d'aya, hartta handle d'insu yana nan a rubuce a jikin takardar. Sai ita d'ayar mai suna Hajiya Layla ita tana Kaduna da zama da mijinta mai suna Alhaji Sambo, sai d'iyarta k'wara d'aya mai suna Yasmeen." Gwauron numfashi Faruk ya sauke a lokaci guda kuma ya d'auko hotunan yaran nasu da akayi masa nuni dasu yana ta kallonsu yana juya hotunan. Aje hotunan kuma yayi yana kallon Usman tare da d'ora hannayensa saman table d'in yace. "Good job, so anything else?" Usman ya cigaba "Yes, makaranta d'aya suke zuwa mai suna Turkish, ita babbar tana k'ok'arin kammala karatun nata ne while ita k'aramar wato Zarah tana SS2 a yanzu. Duk weekend suna zuwa Katsina wurin mahaifiyar Hamzan mai suna Hajiya Fatima. Idan suka je kamar misali ranar Juma'a zasu dawo ranar Lahadi, amma yanzu bincike ya nuna mani cewar sunyi akalla sati biyu basuje ba, sakamakon jarabawa da d'iyar Alhaji Hamza take shirin zanawa ta fita daga secondary. Alhaji Hamza yakan d'auki yaranshi su fita yawon shak'awatawa duk ranar Alhamis da daddare." Ajiyar zuciyar ya sauke yana kallon Usman ya kuma cewa "Anything else? "Yawwa, ka tambaya ina da ina suke zuwa, to a zahirin gaskiya yaran Alhaji Hamza basa fita yawo, daga makaranta sai islamiyya, amma daga nan basu cika zuwa ko ina ba. Amma kayi hak'uri a 6angaren Hajiya Layla sai na k'ara bincike don bansamu wani information sosai ba, na dai gano cewar tana yawan fita Dubai saro kaya." Faruk yace "Nagode, ka manta ka sanar dani aikin da sukeyi fa." Usman yace "Sorry sir, Alhaji Hamza ma'aikacin banki ne, amma matarsa bata aiki tana harkar kasuwanci, wanda naji ance tana da gidajen mai, shaguna, mall, tana da k'aton shagon saida saide, da sauransu. Haka zalika Alhaji Sambo shi d'an kasuwa ne kuma yana aikin gwamnati." Ya saki ajiyar zuciya yace "Nagode da taimakon da kayi min duk da akan aikinka ne amma ni ka taimake ni ba kad'an ba, so nagode Allah saka da alkhairi." Usman yayi dariya "Haba yalla6ai menene na godiya? Ni keda godiya ay." Faruk yace "Bakomai Usman zaka iya tafiya." Daga haka ya amsa da "To." Sannan yayi masa sallama ya fita. Yana fita ya saki murmushin da shi kad'ai yasan mana'arsa. Murd'a k'ofar akayi aka shigo, Najeeb ne, da murmushi Faruk yace "Ka shigo mana." Bayan ya zauna ne Najeeb ya soma magana "Ka bani mamaki Faruk, ban ta6a tunanin haka daga gareka ba..." Gaban Faruk yayi mummunan fad'uwa, yace "Me akayi?" Najeeb yace "Yanzu daman abinda kake shiryawa kenan baka sanar dani ba? Inda banji me kuke cewa ba da bazaka ta6a fad'a min ba ko?" Faruk yace "Ko kad'an ba haka bane, naso ace sai na gama duk abinda ya kamata sai na sanar maka..." Najeeb yace "To tunda yanzu naji sai ka fad'a min komai." Faruk yayi dariya yace "Akan dai maganar nan ce ta kwanakin baya." Najeeb yace "Maganar iyayenka ko?" Faruk yace "Eh ita, so wani d'an bincike nasa aka yo mani akan mutanen kuma an kawo." Ya k'arasa yana mik'a masa hotunan. Najeeb ya duba bayan ya gama yace. "Ok to menene next move naka?" Faruk yayi murmushin nasa da ya saba yi masu ma'ana daban daban yace "Zan sanar da kai komai, yanzu muje muyi sallah mu dawo." Najeeb yace "Ok muje." A tare suka mik'e suka fice daga office d'in. *** Yana shiga d'akin nasa ya jiyo k'amshin turaren wuta mai dad'i, ga sanyin ac gaurewa da d'akin. Yasan baya wuce aikin Jidda, don ya lura tunda suka dawo take faman d'wainiya dashi, bakin gado ya zauna ya shiga cire takalminsa da safa, bai kai ga gamawa ba ta shigo d'akin nasa, hannunta d'auke da tray d'in ruwa da lemon kwali 5alive, a d'an k'aramin table ta ajiye ta d'ago tana kallonsa cike da kunya, tace "Sannu da zuwa yaya." Yace "Yawwa sannu da aiki." Tace "Yawwa, kana buk'atar wani abu?" Ya d'an karkato gami da kallonta yace "A'a nagode." Daga haka ta fice daga d'akin a yayinda shi kuma ya fad'a toilet don watsa ruwa. AUREN FANSA 18 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 🌹18 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com *** Kwanci tashi babu wuya wurin Allah har su Meenah sun gama zana exams d'in k'arshe. Ranar da suka gama Baba yayi musu kyauta mai tsoka sannan ya musu alk'awarin tafiya Katsina hutu. Murna a wurin Meenah ba'a magana, daman tafison can saboda can tafi sakewa tayi abinda takeso, babu mai takura mata. Haushi Bilki kamar zata fashe, daman duk sadda zasu je Katsina hutu sai hankalin Bilki ya tashi a cewar ta mai mata ayyukan gidan bata nan. Akan dole takeyi har sai sun dawo. A tsarin hutun sati biyu zasuyi inji Baba, don haka tun ranar Meenah ta fara shirin tafiya. Ta wanke kayanta ta goge. Ranar da zasu tafi tunda asuba ta tashi, bayan tayi wanka ta d'auko cikin sabbin kayanta na wata sallah ta saka, blue atamfa d'inkin riga da skirt, tayi kyau sosai. A lokacin data sakko k'asa ta iske Baba da Zarah suna karyawa, yana ganinta yace. "Maza zo kici abinci mu kama hanya." Da saurinta kuwa ta taho tana murmushi. Bayan sun kammala, Hassan mai gadinsu ya shigo ya fara fitar musu da kayansu yana sakawa boot. Bilki ce ta sauko tana yak'e, tace "Badai tafiyar bace?" Baba yayi dariya yace "Itace yanzu zamu kama hanya ma." Ta had'iye 6acin ranta tace "Wai tun yanzu Alhaji?" Sai da yayi murmushi yace "To idan bamu tafi yanzu ba sai yaushe zamu tafi? Katsina fa ba nan ba." Tace "Hakane kam, to Allah ya tsare ya kaiku lafiya." Yayi murmushin jin dad'i yace "Amin." Bayan gama ban kwana, Alhaji ya d'auki hanya zuwa Katsinan Dikko. Sai can yamma suka isa, da gudu su Meenah sukayi ciki suna zuwa suka haye 'yar tsohuwar dake zaune tana hutawa a parlor. "Kai kai zaku 6alla ni ne?" Sai kuma tayi murmushin jin dad'i "Ahh Aminatu da Fatsima ne? Saukar yaushe?" Meenah tace "Yanzun nan muka iso, ina wuni Goggo?" Tace "Lafiya lau, ina Baban naku." Meenah tace "Yana waje yanzu zai shigo." Bata rufe baki ba ya shigo. "Lale maraba da Hamza." Yayi dariya tare da zama k'asa yana kai gaisuwa zuwa ga mahaifiyar tasa. "Mun same ku lafiya? Tace "Alhamdulillahi, ya aiki?" Yace "Alhamdulillah, ya k'arfin jiki?" Tace "Sai godiyar Allah." Yace "Allah k'ara lafiya, daman yaran suka kammala makaranta shine na kawo suyi maki sati biyu, naga sun kwana biyu basu zo ba, ni kuma gobe in Allah ya yarda zan juya." Tace "Kai masha Allah! Allah ya bada sa'a." Suka amsa da "Amin." BAYAN KWANA BIYAR. Kamar kullum bayan Meenah ta sanya kayan baccinta riga da wando kalar dark pink, tana shirin kwanciya Zarah dake kwance tana latse latse a wayarta ta ajiyewa wayar gami da kiran sunanta. "Meenah..." Ta kalle ta gami da yin murmushi tace "Na'am Zarah." Jingina Zarah tayi jikin bangon gadon da take kwance tace "Meenah wai meyasa kika k'i sauraron wannan mutumin? Nafa lura kamar sonki yake da gaske." Take annurin fuskarta ya 6ace 6at! Ta d'aure fuska tamau gami da gyara zamanta kusa da Zarah. "Wane mutumi kenan?" A iya sanin Zarah babu wanda ke takura mata kamar wani wanda ke yawon matsa mata wai ya had'u da ita a Instagram! "Haba mana Meenah, kinfa san wa nake nufi." "Ay ni bai furta man cewar yana sona ba..." Ta fad'a gami da jawo wani novel na turanci mai suna Behind the clouds ta soma bud'ewa tana k'ok'arin karantawa. Zarah tayi ajiyar zuciya tace "Bafa kyau wulak'anci, ki daure ko yaya ne ki sauarare shi." Meenah ta ajiye littafin tana mai kallon Zarah tace "Zarah duk duniya banida aminiya sama da ke, ke kanki kinsan cewa soyayya bata cikin ra'ayina a yanzu, ban iya bama bansan ya take ba, ban kuma san ta ina zan fara ba, nifa tun farko sheyasa nace miki kar ki bud'e min irin wad'annan abubuwan kika k'i ji Zarah, yanzu ga irin ta nan, daman abinda nake gudu kenan." Zarah ta kalle ta da mamaki tace "Me kike gudu?" Meenah tace "Samarin zamani mana, 'yan k'arya mayaudara, ina tsoron ayi min wasa da feelings d'ina, sheyasa ma kikaga ina tsoron yin soyayya..." "Ay ba duka aka taru aka zama d'aya ba, idan kikayi sa'a sai kiga kin samu mai sonki da gaske..." "Zarah da kinyi hak'uri kin k'yale ni bazan iya yin soyayya yanzu ba..." Ta fad'a tana k'ok'arin cigaba da karatunta ranta idan yayi dubu to ya 6ace. "Bazan tilasta miki ba, amma ina rok'onki ki bashi chance idan kikaga alamar mayaudari ne basai ki rabu dashi ba? Menene a ciki? Ni wallahi haka nan kawai yake bani tausayi kullum cikin damuwa yake da ke, ina laifin me sonka? Koda bai furta miki kalmar so yanzu ba, to na tabbata zai furta maki nan bada jimawa ba! Haba Meenah bansanki da wulak'anci ba..." Ta d'aga mata hannu "Ya isa Zarah, naji na amince zan bashi chance, shikenan?" Zarah tayi murmushi "Shikenan, kiyi karatunki sai da safe." Tayi murmushi "Allah ya kaimu lafiya." Gajiya tayi da karatun ta d'auko wayarta gami da duba lokaci. K'arfe 12:53am, ajiye littafin tayi tana k'ok'arin kwanciya message ya shigo ta wayarta. Tasan bai wuce d'an k'wak'war nan, ta fad'a a cikin ranta gami da sakin d'an guntun tsaki. Dubawa tayi. "Hello." "Hey." "No answer?" "How are you dear?" "Hmm." "Are you sleeping?" "Please talk to me mana." Da k'yar tace "Hi." Yana kwance yana latse latse a laptop nasa message nata ya shigo, ya ware manyan idanunsa cike da mamaki, murmushi yayi ya rubuta mata. "Thank God! Naji dad'i da kika man reply, i thought na maki wani laifi ne?" "A'a bakomai..." "So ya kike? Kin dai hanani number ki ko?" "Hmm." "Bakomai kina min rowan jin muryarki mai dad'i ko?" "A'ah..." "To ki bani mana, idan ba rowa ba." Yau yaci albarkin Zarah, don haka sai kawai ta tura masa number d'in. Minti biyu tsakani... Kwance take lamo, zuciyarta na mata sak'e sak'e. Bata ankara ba wayarta ta fara ruri, bak'uwar number ta gani. Da k'yar tasa hannu ta d'auka.... AUREN FANSA 19 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 🌹19 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Tun kafin ta kai ga d'auka haka kawai ta tsinci kanta da fad'uwar gaba, ta kira sunan Allah don neman nutsuwa cikin zuciyarta. Cikin ikon Rabbi kuwa ta samu nutsuwa sai dai kafin ta d'auka tuni wayar ta katse. Ajiyar zuciya tayi, sai dai tana katsewa wani kiran na shigowa. "AssalamuAlaiki yake ma'abociyar kyau, kwarjini da kuma nutsuwa." Abinka da rashin sabon waya da maza, tuni ta rasa nutsuwarta, da k'yar ta amsa masa "Wa'alakumsalam." "Yau dai na taki sa'a tunda har aka d'auki wayata sannan aka d'aga lokacki d'aya, lallai ni mai babban sa'a ne. Ko ba haka ba 'yan mata?" Ta k'ara kiran sunan Allah a karo na biyu, saboda rashin sabo da kuma muryar mutumin da bata san ko waye ba, sai dai me? Jin muryar takeyi kamar ana busa sarewa, bata ta6a jin murya mai dad'i ba irin ta wannan mutumin ba... "Ya kikayi shiru Princess?" Gabanta ya yanke ya fad'i, wai wannan mutumin kamar aljani? Da yayi mata magana sai gabanta ya fad'i. "Nidai muryar nan taki ko dai zan biya ne don na lura tana tsada..." "Ina wuni?" Yayi murmushi, har tana jiyo sautin yana bugun dodon kunnenta, sannan a take tsikar jikinsa ta tashi tayi wani yarr! "Kina lafiya?" "Lafiya lau." "To masha Allah, zan d'an baki dan gajeren labarina, bana so ki zo kina ce min bakisan ko da wa kike waya ba... ko ba haka ba?" Tace "Uhm." Yace "Yauwa, da farko sunana Faruk Adam, shekarata 26 kacal a duniya, iyayena sun rasu gaba d'aya tun ina k'arami, yanzu daga ni sai k'anwata muka rage, ina zaune gidan wani uncle d'ina a garin Abuja. Mahafiyata shuwa ce while babana fulani ne. Yanzu dai na kammala karatuna ina aiki. To kinji kad'an daga cikin tarihin rayuwata, ko zan iya jin naki?" Tace "uhm, Allah ya jik'ansu." Yace "Amin, ina jinki fa." Da k'yar ta iya tattaro nutsuwarta wuri d'aya ta soma magana mai cike da nutsuwa. "Sunana Amina Hamza, mahaifina d'an garin Katsina ne amma yanzu aiki ya kai shi Abuja, na kammala karatuna na fita daga secondary ina jiran admission zan tafi university. Mu biyu ne kad'ai a gidanmu daga ni sai k'anwata mai suna Fatima." Yayi murmushi "Allah sarki Allah ya taimaka, to baki fad'a min shekarunki ba?" Tace "16." Yace "Wow, lallai ashe dai da sauranki yarinya." Tayi murmushi mai cike da kunya. Haka suka 6ata wannan daren Faruk na janta da fira, tun tana d'ari d'ari har ta d'an saki jikinta tana bashi amsa, idan akayi labarin dariya suyi dariya, daga k'arshe ganin har uku na dare ya sashi yayi mata sallama akan zai kirata da safe. Koda ta kwanta kasa bacci tayi, muryarsa kawai takeji cikin dodon kunnenta kamar yanzu yake mata magana. Daman bata sallah sheyasa ma bata tashi da asuba ba. Bacci takeyi har kusan goma da rabi na safe. Juyi d'aya tayi akan gado tayi tozali da wayarta kamar had'in baki sai kuma ta fara ruri. Ganin number d'in jiya ya sata sakin murmushi ba shiri. A kasalance ta d'auka gami da yin sallama. "Good morning! Rise and shine, raina ya bani yanzun nan kika farka daga bacci, ko da yake laifi nane dana hana ki bacci da wuri tun jiya ko? To ayi min afuwa. Bazan sake ba." Cikin ranta tace "Wannan sai kace aku ko gajiya baiyi da magana?" "Ina kwana?" Yayi murmushi "Lafiya lau da fatan princess d'in tawa ta tashi lafiya?" Ta langa6ar da kanta gami da lumshe idanu tace. "Alhamdulillah, thanks." Yace "Yauwa, to yanzu abinda ya kamata kije kiyi wanka sai kici abinci." "To." Kawai tace gami da yi masa sallama ta kashe wayar. Ganin Zarah tsaye bakin k'ofa ya sa gaban Meenah ya yanke ya fad'i. Zarah ta k'araso tana dariya "Love in the air, yanzu don Allah bakiji dad'i ba? Amma ace mutum ya takura ma kansa da rayuwar kad'aici haba!" Murmushi tayi ta sauka daga kan gadon tace "Bari nayi wanka." Tana jin Zarah na d'aga murya tana fad'in "Wai don dai kar ayi maganar zaki wani shige wanka." Murmushi kawai tayi. Wunin ranar zungur a d'aki tayi shi, har dare bata fito ba, ba abinda ke tashinta daga gado sai shiga toilet. Washe gari kuma haka ta tashi sukuku. Zarah ta rasa gane kan yayar tata. Haka dai komai ya cigaba da gudana a tsakanin Meenah ta Faruk, wuni sukeyi mak'ale a waya, zuciyarta ta aminta da shi lokaci guda, ta yarda ta amince shi d'in takeso. Tun da ya turo mata hotunan sa taji yayi mata, lokaci guda ya sace zuciyarta ya kuma tafi da imaninta gaba d'aya, har ta soma cewa cikin ranta "Anya ba surk'ullensu na fulani yayi mani ba?" Wata rana da daddare yana ta kiranta ya sanar mata gobe zaizo wurinta, daman sunyi zaizo Katsina, idan yazo zai shigo su gaisa. A lokacin da yake ta kiranta tana bacci kuma wayar a silent take. Washe gari da safe sai ta iske message d'insa ya turo mata. "Just to say good night! With you in my mind... ?" Sai tayi murmushi ta tura "In both the soul and mind...." A lokacin da ta tura masa sak'on bai gani ba saboda yana cikin jirgi don tahowa Katsina! AUREN FANSA 20 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 Dedicated to each and every reader, you always support me, and i am grateful for that! Thanks alot!❤️ 🌹20 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Awa biyu tsakani ya diro cikin garin katsina, yana isa airport ya ciro wayarsa ya buga ma Meenah waya ya sanar da ita isowar tasa. Zarah bata gama shan mamaki ba sai da Meenah ta shiga kitchen don girka masa lafiyayyen abinci mai rai da lafiya. Coconut rice da miyar kaji, gefe kuma Russian salad ne, sai drinks kala kala. Banda su snacks da aka tanada. Goggo da k'amshi ya cika mata hanci ta fito daga d'aki ta lek'o tana fad'in. "Kai lafiya me kuke dafawa?" Zarah tayi dariya tace "Ay Goggo surukinki ne zaizo, shine fa su Meenah ake ta shiri haka." Meenah ta sunkuyar da kanta tana murmushi, Goggo tayi dariya tace "Ahh lallai kice munada babban bak'o, ay gara dai yayi yazo ko zamu huta hakan nan." Bata gama komai ba sai da k'arfe bakwai harda rabi. Kasacewar yace mata da anyi sallar isha'i zaizo. Tana gama wannan aikin ta shiga wanka ta fito ta shirya cikin wani lace ruwan zuma (coffee brown) da light pink a jikinshi, d'inkin riga da skirt. Da taimakon Zarah ta d'aure d'ankwalin kayan irin na zamin da ake kira mai steps. Ga d'ankunne an sa kalar kayan. Tana gama fesa turare wayarta ta hau ruri da alama Faruk ya iso. A karo na farko taji ta gigice, kasancewar a yau zata ta6a fuskantar wani d'a namiji a rayuwarta da idanun soyayya. Bayan ta d'auka ya sanar da ita isowar tasa cewar yana bakin k'ofa. Ba yadda batayi da Zarah ba akan ta shigo dashi tak'i, harda zolayarta wai ay ba saurayinta bane ita. Hakan yasa ta d'auki waya ta tura masa da message akan yasa a shigo da shi bakin k'ofa (main entrance). Tana bud'e mishi k'ofa suka bi juna da kallo mai kwantar da zuciya, kafin kuma dukkansu su saki murmushi mai d'auke da wani 6oyayyen sirri. Mamaki takeyi akan yadda yafi kyau a fili akan a hoto... Ta kauce ta bashi hanya ya shigo, yanan sanye da shadda marar nauyi kalar sky blue sun kama jikinshi, idonshi mak'ale cikin farin glass wanda ya k'ara fito da cikar kamalarshi na cikakken namiji, wanda boko ya zauna masa sannan kud'i ma suka zauna masa had'e da hutu, ga kuma uwa uba kyau, ba abinda ke tashi a wurin kamar k'amshin turarensa mai sanyaya zuciya. Meenah fa tayi nisa a kallonsa yayi murmushi ya soma karkad'a mata key d'in motarsa, taji kunya sosai ta wuce ciki kanta k'asa, yabi bayanta. Suka zauna kan kujeru parlon Goggo, da k'yar ta ce "Ya hanya? Ya kuma gajiya?" Yayi k'awataccen murmushin dake fizge zuciya yace "Alhamdulillah, ya gida ya hutu?" Tayi murmushi still bata d'ago kanta ba tace "Komai alhmdulillah, yasu Anisah?" Yace "Suna can lafiya lau, ina Goggo da Zarah?" Kafin tayi magana Zarah ta fito da k'aton tray mai d'auke da lemo kala kala da cups d'in glass guda biyu. Sai data dire bisa center table d'in dake parlor sannan ta zauna suka gaisa a mutunce, yace "Ga Zarah nan kenan? Itace sweet sister d'inki. Sannu Zarah ya kike? I've heard so much about you, gaskiya sister nan taki tana ji take." Zarah tayi dariya "Haka ne, nima ina ji da ita ay." Tana gama fad'an haka ta mik'e tsaye ta fice. Ba'a juma ba kuma ta dawo d'auke da wani tray d'in mai d'auke da kuloli guda biyu, plate biyu sai kuma bowl na snacks da salad. Bayan ta dire sum sum ta fice saboda yadda taga sun kasa 6oye soyayyar da ke zuciyoyinsu a gabanta. Ta lek'o don zuwa kitchen had'o tea, daman ita Zarah al'adarta ce duk dare sai tasha ruwan lipton (green tea) kafin ta kwanta, nan ta hango su suna cin abinci a plate d'aya, sai kuma sukayi mata kyau, kuma sun mugun dacewa da juna, abinda Faruk zai nuna ma Meenah shine haske fata don shi fari ne nesa ba kusa ba, Meenah kuwa bak'a ce (chocolate color). Suna cin abincin suna kallon juna, fatar bakinsu kuwa kad'an take motsi daga lokaci zuwa lokaci. Ta koma d'aki tana mamaki sai kace ba Meenah ba, gaba d'aya ta fad'a tarkon so. Kafin ya tafi ya d'auko kyauta gift d'in turare da agogo ya bata, amma sam tak'i kar6a, sai da yayi da gaske har yana neman yin fushi sannan ta kar6a tana godiya sosai. Soyayya tsakanin Meenah da Faruk kullum abin dad'a gaba yake cike da salo na ban mamaki, basu iya yini d'aya basuyi waya ba, haka ma kullum yana kan hanyar zuwa wurinta. Tabbas zuwa yanzu soyayyar da Meenah ke ma Faruk bata misaltuwa, abin mamaki Faruk ya iya tafiyar da soyayya yadda ya kamata ya kuma son hanyoyi daban daban na yadda zai jawo hankalinta gare shi, ga yaci sa'a wannan shine karo na farko data fara sanin yadda ake soyayya, sheyasa a halin yanzu duk wanda zata so zata soshi ne da dukkan zuciya da kuma ruhinta. Faruk ya riga da ya saye zuciyarta farat d'aya, ko irin kalaman da yake furta mata kad'ai ya isa ya saye zuciyar Meenah, don haka sheysa bai sha wahalar yiwa zuciyar Meenah kamun kazar kuku ba! Batada wani tunani sai na Faruk, batada wani ra'ayi sai nasa, sannan batada wani buri sai na mallakarsa a matsayin mijinta na abokin rayuwa na har k'arshen rayuwarta ba. AUREN FANSA 21 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 🌹21 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Bayan kwana biyu da safe sai ga Baba ya diro garin wai da niyyar d'aukar su Meenah, hanakalin Meenah ya tashi don tasan da k'yar idan Mami zata barta tayi soyayya ba, tasan dai Baba baida matsala, amma Mami take ji. Aikuwa tana sanar da Faruk cewar gobe zasu koma Abuja yace shima zai tattara ya koma daman ya gama abinda ya kawo shi, sai ya koma zai cigaba da kawo mata ziyara. Washe gari kuwa suka tattaro suka dawo gida. Duk da hankalinta a tashe yake hakan baisa taji ko d'ar a zuciyarta game da son da takeyi wa Faruk Adam ba. A ganinta shi d'in yasan menene so, yasan darajar abinda yakeson, ya kuma iya tafiyar da shi ta hanyoyi daban daban, ya iya tarairaiyar mace da bata kulawa yadda ya kamata. Sheyasa son da take masa shi yake k'ara bata k'warin gwiwar fuskantar Mami. Suna dawowa kuwa kusan kullum sai yazo, har dai ya zama d'an gida, yadda taga Baba ya amshi Faruk hannu bibbiyu ya sanya dole taja bakinta tayi tsit, kuma kullum yazo Zarah ke raka Meenah fira, hakan yasa ita kanta Mamin ta rasa gane wurin wa yake zuwa, amma tana fatan wurin Zarah yake zuwa, don a yadda take gani mutum ne mai kud'i sosai. * K'arfe takwas na dare kamar kullum Faruk ya isa gidansu Meenah, kasancewar ya zama d'an gida tsakanin Baba da Mami. Bayan sun gaisa da Baba, a lokacin Baba yana da niyyar fita, haka ma Mami tana sama tana fama da lissafin kud'in kasuwancinta. Yana nan zaune yana jiran Meenah. Aikuwa sai gata ta fito tayi kyau kamar kullum cikin material mai taushi silver da ratsin bak'i a jikinshi, d'inkin doguwar riga, d'inkin bai kama jikinta ba. Tun daga nesa suke sakarma da junansu murmushi mai sanyi. Ta zauna a kujerar dake fuskantarsa, centre table ne mai bak'in glass a tsakiya wanda aka d'aura kayan marmari cikin tray kala kala a cikinsa, irinsu Apple, grapes, banana, orange, pear da sauransu. Zamewa yayi ya zauna k'asa gami da rausayar da kai yace. "Barka da hutu!". Dariya ya bata sosai saboda yadda yayi maganar, tace "Alhamdulillah, muna ta sha kam." Yayi shiru zuwa wani lokaci sannan yace. "Zuwa yaushe kike ganin za'a aurar da ke?" Ita dariya ma ya bata tace "Aure ay lokaci ne... sai lokaci yayi sannan." Ya langa6ar da kai yace "Haka ne, amma ni ko yanzu aka bani ke zan kar6a hannu bibbiyu, zan nuna maki k'auna ta ban mamaki, sai dai bansani ba ko ke zaki so ni kamar yadda nake son ki... sannan ina so idan Allah ya kaimu zan sanar da iyayenki cewar aurenki zanyi..." Ta lumshe idanu cikin wata sabuwar k'auna dake k'ara mamayarta, ta kuma k'ara lallu6e mata zuciyarta, tace "Kar kayi tantama a kaina ya Faruk, soyayyarmu had'in Allah ce, i respect you and your values.. Faruk d'in da nake so bana ganin kowa sai shi, bana jin k'aunar kowa sai shi... haka ma banida buri a yanzu sama da mallakarka a matsayin mijin aurena na har abada..." Sai bayan ta furta hakan kuma kunya ta kamata had'e da mamaki, yadda ta zauna tayi ta zuba kamar pampo, amma daga baya sai take ganin kamar su6utar baki tayi. Sai tayi saurin cewa "Nidai fatana ka rik'e soyayya ta, kada kaci amanata, ka yarda dani, idan kayi min wannan to ni kuma nayi maka alk'awarin baka dukkan kulawa." Sai ya rasa abin cewa kuma, murmushi tayi ta sauko k'asa ta shiga yanka masa kayan marmarin yana sha. *** Bilki ta soma tsarguwa da yawan zuwan Faruk cikin gidansu, da yawan ke6ewa da sukeyi shida Meenah akan Zarah suna fira. Ga wata sabuwar al'ada da Meenah ta 6ullo da ita na yawan kwalliya wadda ta gama lura don Faruk take yinta. Ta gigice ta shiga damuwa sosai, neman k'arin bayani takeyi tasan Zarah bazata ta6a fad'a mata ba saboda an ta6o 'yar uwarta haka bata ganin aibunta, su koda wani abin ne ba'ajin ta cikinsu kashewa sukeyi su rufe babu mai ji. Ko fad'a sukayi baya wuce yini d'aya idan kuwa sun dad'e to kwana d'aya ne sun shirya sun kuma manta komai. Don haka taga babu mafita illa ta tunkari Meenah tayi mata bayanin abinda take zargi. K'arfe tara na dare ta raka Faruk ya tafi, tana dawowa ta taradda Mami tsaye gefen gadonta ta hard'e hanyayyenta wuri d'aya tana huci. "Mami....?" Ta dube ta sosai daga sama har k'asa tace "Amina....!" Bata amsa ba illa ta dube ta a yadda take kiranta cikin wata irin murya. Sai kawai ta jeho mata tambaya "Meke tsakaninki da Faruk?" Ta sunkuyar da kanta k'asa, batayi magana ba, sai da Bilkin ta daka mata uwar tsawa mai gigita k'wala. "Bada ke nake magana ba?!" Cikin sark'ewar murya tace "Da...ma yace yana...so...na tun muna Katsina, kuma daman gobe ne Faruk d'in yake niyyar sanar daku muna son junanmu... mun yanke shawarar yin au..." Ji kake tassa!!! Mami ta d'auke ta da wani irin wawan marin da har sai data ga giftawar wuta, ta nemi ji da ganinta ta rasa! AUREN FANSA 22 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 Dedicated to Mrs Fawwaz, Sadnaf, Momyn Sultan, my sakwara, Maman Khady, Jannatuwa, Faridat Musa, Rufaida Yusuf. One luv guys❤️😍 🌹22 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Bilki ta soma magana cikin fushi. "Kin bani mamaki Meenah, yanzu har yaushe idonki ya bud'e da kike neman k'wace ma 'yar uwarki saurayi? Ke ko kunya bakiji ace 'yar uwarki tana son wani kema kina sonsa? Fatima fa k'anwarki ce Amina, ay na d'auka ke mai d'auka ce ki sadaukar mata da wani idan ta kama, amma wai ke! Kece mai k'wacewa Meenah."! Ta share hawayenta cikin tsantsan mamakin Mamin tasu, muryarta na rawa ta soma magana. "Mami Faruk bai ta6a cewa yana son Zarah ba, ni yake so tun asali, ko ita Fatiman ba sonsa take ba, ni bansan ina kika ji cewar saurayin Fatima ne ba, idan ma kina tunanin cewar saurayin Fatima ne to ki daina tun wuri." Sai kuma ta juya mata baya gami da had'e hannayenta wuri d'aya tace "A baya kinsha k'wace min kyauta a makaranta, amma gaskiya yanzu bazan yarda a k'wace min Faruk ba, hak'uri zakiyi ki sa mana albarka!" Sai kawai Bilki tasa salati, yau tana fad'a Meenah na fad'a. "Lallai wuyanki yayi k'wari ya isa yanka, akan nace kin k'wace wa 'yar uwarki saurayi kike neman ki fad'a min magana Meenah." Ta fad'a tana nuna kanta. "Bafa saurayi na bane Mami." Duk suka d'aga ido tana tsaye bakin k'ofa idanunta sun kad'a daga fari zuwa ja! A hankali ta k'araso cikin d'akin tana share hawaye tace "Akan me zaki mare ta akan maganar da bakida tabbas a kanta? Mami! Ki sani Meenah 'yar uwata ce ta jini, ta yaya kike tunanin zata k'wace min saurayi? To bari kiji abinda baki sani ba, Faruk saurayin Meenah ne bani ba, ko don kinga ina zuwa muna fira dashi kikayi tunanin saurayina ne?" Tayi murmushi tace "To ba haka bane, ni kawai mun saba ne sheyasa kikaga ina fita amma lokuta da dama ay tare da Meenah muke zuwa, duk randa kika ga naje ni kad'ai to Meenah ta tura ni akan in je kafin tazo." Ta kalli Meenah dake hawaye wani na bin wani, tasa hannu ta share mata tace "Daina kuka 'yar uwata, kiyi hak'uri da abinda Mami tayi miki, sannan kisa a ranki Faruk naki ne ke kad'ai kinji?" Suka rungume juna suna kuka. Haushi ya kashe Bilku kafin kuma sum sum ta fice daga d'akin cike da kunya! A wannan daren Bilki batayi bacci ba, yadda taga rana haka taga dare. Washe gari Meenah taga fushin Bilki fiye da yadda ta saba gani, da Zarah take sabgoginta, itama sai ta kama kanta a d'aki tak'i fitowa tana karance-karancenta. Sai dai zuciyarta cike take da tsoron Mamin, data tuna marin da tasha jiya sai gabanta ya fad'i. * K'arfe goma na safe Faruk yazo, Bilki na zaune parlor tana chanza channel, tun daga jin sallamarsa tabi ta d'aure fuska yadda bata ta6a yi masa ba. Yana zuwa ya zube k'asa yana gaishe ta, sai kawai ta kafa masa ido bata amsa ba, k'arshe ma sai ta mik'e ta haye bene zuwa d'akinta ba tare da tace komai ba. Meenah na daga bak'in k'ofar kitchen tana ganin komai, ita kunya ma ta kamata ta kuma kasa k'arasowa ciki. Sai da ta d'auki akalla minti biyu sannan tayi ta maza ta shigo parlon kanta a k'asa. Dukkansu sunyi shiru aka rasa mai fara yin magana a cikinsu. Da k'yar Faruk ya daure yayi murmushi cikin basarwa yace "Munyi ma Mami laifi ko?" Ta d'an d'ago suka had'a ido, ta lumshe idanu tace. "Tun jiya take haka, mun rasa gane mata." Yayi shiru cikin tunani, can kuma yace "K'ila bata amince dani ba..." Tayi saurin cewa "Bakomai zata huce ne." Baba ne ya ke saukowa daga mattakalar bene Bilkin na biye da shi tana rik'e da briefcase d'insa, ya hango shi a parlor zaune, da sauri ya mik'e cikin girmamawa yabi bayansa don yaga kamar parlonsa ya nufa daga can 6angarensa. Baba nakan kujera Faruk na gefensa daga k'asa. Bayan sun gaisa kamar kullum cikin mutunci da girmama juna, can Baba yace "Umar Faruk." Ya d'ago da fararen idanunsa ya dube shi yace "Na'am Baba." "Meke tsakaninka da Amina?" Faruk ya rud'e ya shiga inda inda saboda yadda yaga Baban ya masa kwarjini, take kuma ya sadda kansa k'asa. AUREN FANSA 23 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 🌹23 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Baba yayi murmushi yana dubansa yace. "Faruk ka saki jikinka dani mana, ka d'auke ni a matsayin mahaifinka, ka bani amsar tambayar da nayi maka." Ya daure yace "Da...dama Baba, dama... dama... ina so mu lokaci ne, sannan na gabatar maka da kaina a cikin manaiman auren Meenah, duk da dai tace min batada wanda ta tsada, to amma... amma mun daidaita kanmu." Baba yayi murmushi gami da lumshe idanu na 'yan mintina, sannan ya bud'e su a hankali kan Faruk. "Haka ne, Meenah batada wanda ta tsaida, hasali ma kai ne mutum na farko da ta ta6a yin soyayya da shi, sai dai wani hanzari ba gudu ba, kafin na amince maka da auren Meenah, ina so kayi min alk'awarin rik'e ta bisa amana da gaskiya, kar ka ci amanarta kar ka yaudare ta, shine kawai abinda nake buk'ata daga gare ka. Duk da nasan dai mahaifinka mutumin kirki ne kuma ina da tabbacin tarbiyarsa gareku, kuma ina masa addu'a Allah ya jik'ansu da gafara." Yace "Amin Baba, indai wannan ne kar kayi haufi a kaina insha Allah babu matsala." Baba yayi murmushin jin dad'i yace "Alhamdulillah, amma kuma ina so ka bari in tuntu6i yarinyar tukunna inji ta bakinta, nafiso na tabbatar sai a sanar da kai don ka turo magabatan naka." Faruk yayi murmushi. Yace "To Baba babu damuwa insha Allah." Baba yayi murmushi gami da mik'ewa tsaye. Yace "Kana iya tafiya Allah yayi muku albarka. Ya amsa da "Amin." Baba ya yi gaba, Faruk yabi bayansa yana jinjina al'amarin. *** Abu k'arami na neman zama babba, tun tana ganin abin kamar wasa ta fara ganinshi babba. Cikin k'ank'anin lokaci Jidda ta fahimci Faruk soyayya yake, kuma wacce yake so d'in ta kame masa zuciya farat d'aya, duk wani observation nata akan Faruk ta gama gane komai, tausayin kanta ya kama ta. Anisah ce ta shigo d'akin tana tsaye a bakin k'ofa ta k'ura ma Jidda idanu, hannunta d'aya d'auke da cup d'in tea d'ayan kuma yana rik'e da wayarta k'irar Samsung galaxy S6, a hankali ta k'araso ciki tana murmushi. Zama tayi kan gadon da Jiddar ke zaune a kai ta dafa ta. "Yaya Jidda..." Firgit! Ta dawo daga duniyar tunani tana kallon Anisah, sai kawai ta k'ak'alo murmushin dole. Anisah tayi murmushi. Meyake damunki?" Tayi tsai kamar mai tunani kafin tace "Babu komai." Anisah ta girgiza kanta. "Sam ban yarda ba yaya Jidda, na dad'e da ganin chanzawarki, gaba d'aya kin bi kin sussuce kin zama wata iri? Har Mama ta soma tambayarmu abinda akayi miki,a gaskiya yaya Jidda koma meyake damunki ki fito fili ki fad'a mana, k'ila da akwai taimakon da zamuyi miki..." Har yanzu bata d'ago ba kanta na k'asa dai tana kallon wayarta. Yusra ce ta lek'o tace "Anisah ya Najeeb na kira, kuma yace kiyi sauri kiran nada mahimmanci." Sai a sannan Jidda ta d'ago tana dariya tace. "Kice dai za'a je a soye, wai yanzu Anisah har ta girma ta iya soyayya ko?" Anisah ta sunkuyar da kanta k'asa tana murmushi kafin kuma ta fice da gudu ganin zasu sakata gaba da zolaya. Yana zaune a garden bisa kujera yana sanye da jar riga da ash wando (jeans). Kayan sun haska fatarsa da take kalar fatarsa chocolate mai haske, ta k'araso tana murmushi, tun daga nesa yake kallonta har ta iso inda yake. Yayi nisa a kallonta har bai san lokacin data zauna ba, sai data kira sunansa yayi firgit ya dawo duniyar tunani. "Ya Najeeb." Yayi sassanyar murmushi yace. "Anisah kina lafiya?" Tace "Lafiya lau, ya naganka nan kai kad'ai?" Yace "Ke nake jira ki taya ni fira, ko baza'a ta ya ni ba?" Tace "Uhm, daman Yusra tace kana nema na, sheyasa na fito." Yayi murmushi yace "Hakane, ni nace ta kira ki, daman inji batun karatunku ina kukayi applying?" Tace "Nayi applying first choice d'ina a Base nida Yusra, sai second choice mukasa Turkish Nile. Sai last mukasa BUK." Yace "Ok yayi Allah ya taimaka." Tace "Amin." Yace "To ya batun maganarmu ina aka tsaya? Har yanzu fa baki bani amsa na ba, kullum dana miki maganar baki bani gamsashiyar amsa, amma yau ba inda zaki sai kin fad'a min." Cike da kunya tace "Wace magana ya Najeeb?" Yace "Kin fini sani." Ta sunkuyar da kanta tana kallon k'asa, yace "Ke nake saurare fa." Tace "Ya Najeeb, wai yanzu kake nufi za'ayi auren?" Yayi dariya "Eh mana idan har kin amince me ake jira? Bakiji me Baba yace ba? Yace mu dukkanmu zai had'a ya aura damu, yace mazan su fad'i matan da suke so, matan kuma su gabatar masa da wanda suke so, yace so yake yayi gaba d'aya ya huta. Kinga ni da ke sai ayi 'yar gida tuwo na maina. Ko ba haka ba?" Tayi shiru bugun zuciyarta ya k'aru, tabbas tana son Najeeb kuma shima d'in yana sonta sosai. Tace "To ya Najeeb Allah ya tabbatar mana da alkhairi." Yaji dad'in kalamantanta sosai yace "To Amin ya Rabbi, daman haka nake so naji daga bakinki." Tayi murmushi. Sai da suka kammala firar tasu ne kafin kuma su tashi su shige ciki. MSB💖 AUREN FANSA 24 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 🌹24 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Baba na zaune a parlonshi ya kira Bilki yace ta turo masa Meenah. Tana d'akin Zarah a bakin gado tayi tagumi, Zarah kuma na jera kayanta cikin wardrobe da aka kawo daga wurin wanki da guga da safe. Bilki ta shigo d'akin, da sauri Meenah ta d'ago fararen idanunta ta kalle ta, kallo d'aya zakayi mata ka tabbatar da tana cikin damuwa mai tsanani, take Bilki ta 6alla mata harara tace "Taso muje." Ta mik'e a sanyaye tabi bayan Bilkin har parlon Baba, jikinta yayi matuk'ar yin sanyi. Baba na duba newspaper da idanunsa mak'ale cikin farin gilashi a lokacin da suka shigo. Ya ajiye takardun gefe ya kuma cire gilashin yabi Meenah da kallo a lokacin da take zama kan carpet, sai ya saki murmushi yace "Aminatu jiya wannan yaron Faruk yake sanar dani cewar yana sonki, kuma yana so in bashi izini don ya turo da magabatansa, k'warai na yaba da hankalin yaron da kuma nutsuwarsa, amma kinsan bazanyi saurin yanke hukunci kai tsaye ba, ina so inji ta bakinki tukunna. Shin Amina kin amince Faruk ya turo da iyayensa ayi magana, ko kuma baki amince ba?" Farin ciki marar misaltuwa taji ya lullu6e ta har ta gaza 6oye hakan, take kuma ta sadda kanta k'asa fuskarta d'auke da k'ayataccen murmushi. Ta kai dubanta ga Bilki taga yadda ta had'e rai tayi murtuk. "Amina." Ta d'ago ta kalli Baban tace "Na'am Baba." Yace "Ke nake sauraro, shin kin amince Faruk ya turo magabatansa ko baki amince ba?" Da k'yar ta bud'e baki saboda matsananciyar kunyar da takeji tace "Haka ne Baba, kuma na amince." Yayi murmushin jin dad'i yace. "Alhamdulillah, idan yazo kice ya turo magabatansa, Allah yayi muku albarka." Kanta na k'asa tace "Amin Baba." Yace "Tashi ki tafi." Tashi tayi ta fita. Tana fita Bilki tace "Alhaji!" Ya dube ta yaga tayi kicin kicin da fuska yace "Lafiya dai Bilkisu?" Dama kamar jira take tace "Haba Alhaji don me zaka biye wa yarinya daga tace tana son mutum sai ka d'auke ta ka bashi, sannan baka ganin yarinyar nan k'aramar yarinya ce duka duka nawa take da zakayi mata aure yanzu? Ko university fa bata shiga ba, gaskiya ni ban amince ba sam." Sai ya kalle ta yayi murmushi yace "A lokuta da dama ku mata kuna bani mamaki, kina k'in auren Meenah ne saboda k'aramar yarinya ce? To ni banga k'ank'anta a tattare da ita ba, shekaru goma sha bakwai gareta idan baki manta ba wata mai zuwa shekararta goma sha takwas, a hakan ne kike ganin yarinya ce?" Tayi shiru tana ciccin magani. Ya cigaba "Babu wani abu da iyaye zasuyi alfahari dashi face suga sun aurar da 'ya'yansu, shine kad'ai kwanciyar hankalinsu saboda idan zaki auna karatu baifi aure ba, haka zalika zata iya cigaba da karatunta d'akin mijinta. Saboda haka nake gargad'inki da kiyi gaggawar kawar da wannan gur6ataccen tunaninki ki koma hanya madaidaiciya." Jiki a sanyaye tace "Kayi hak'uri Alhaji, a had'o shayin ne ko sai anjima?" Yace "Bari sai anjima." A ranar duk wanda ya kalli Meenah yasan tana cikin matanancin farin ciki. Cike da farin ciki ta lalubo wayarta ta kira Faruk, bugu biyu ya d'auka. "My baby." Ya fad'a yana murmushi. Tayi murmushin jin dad'i. Tace "My soul." Sunan ta dake kiransa kenan. "Albishirinka!" Yace "Goro." "Fari ko ja?" Yayi dariya "In banda abinki ya ina ganin farin goro zan d'auki ja? Ay farin zan d'auka." Tayi murmushi "Haka ne, to Baba ya baka izini ka turo iyayenka my soul." Yace "Wow alhamdulillah! Gaskya nayi farin ciki insha Allah zan sanar da Dada, i love you so much my baby Allah ya nuna mana ranar auren mu lafiya." Tayi murmushin jin dad'i tace "Amin my soul love you too, bari naje Mami tana kirana sai anjima." Yace "Awwn kamar kar ki tafi, amma zan kiraki anjima, take care." Sukayi sallama ta kashe wayan, yana cire wayan a kunnensa ya hango Najeeb tsaye a bakin k'ofa yana kallonsa. Ya hau susan kai yace "Najeeb me kakeyi a nan? Ka k'araso ciki mana." Najeeb yayi ajiyar zuciya ya k'araso ciki ya zauna gefen Faruk kan gado tare da dafa sa. Yace "Faruk a gaskiya banga dalilin da zaisa ka yaudari yarinya ba alhalin ba itace tayi maka laifi ba." Faruk yayi murmushi yana kallon Najeeb yace "Don na yaudare ta shine me? Wannan shine first step da zan d'auka shine auren d'iyarsu!" Najeeb yace "Faruk da zaka ji shawarata da ka k'yale yarinyar nan akwai hanyoyi da dama da zaka d'auki Fansa ba dole sai ta wannan hanyar ba, she's too innocent wallahi dana ganta ta bani tausayi." Nan take Faruk ya fara huci, bak'in ciki had'e da 6acin rai suka taru suka masa dirar mak'iya! Ya mik'e a lokacin ne kuma idanunsa suka sauya kala daga fari zuwa ja tsabar 6acin rai, shi kanshi Najeeb ya tsorata da ganin yanayinsa. Faruk ya soma magana cikin 6acin rai. "Najeeb! Kar ka manta alk'awarin da na d'auka a baya, na k'watar mana 'yancinmu, auren Meenah shine abu na farko da zanyi, don gudanar da duk wani bincike na da zanyi. Idan har ban auri d'iyarsu ba ta yaya zan cimma burina na gano musabbabin yadda aka kashe mana iyaye? Dole sai na kusance su, sun yarda dani sun kuma amince dani, ta haka kad'ai zan sa ido sosai akansu. Bayan haka! Sai nasa sun raina kansu, sai sunyi dana sanin abinda suka aikata, ita kanta Meenah lokacin kad'an nake jira dana aure ta zan kuma wulak'anta ta, dole idan nayi haka abin zaiyi wa iyayenta zafi, to wannan kad'an ne daga cikin abubuwan dana tanada!" Najeeb ya mik'e tsaye da sauri zuwa inda Faruk ke tsaye. "Dan girman Allah ka sauke k'udurinka na wulak'anta d'iyarsu, bata ji ba bata gani ba, haba ya laifin iyayenta zai shafe ta?" "Ya shafe ta! Kai harta karensu ko magensu laifin ya shafe su, na tsane su, na tsane su! Na tsane su! Wallahi duk sadda na kalli Meenah ko wani nata sai na ji kamar yanzu nake kallon gawar iyayena kwance cikin jini." Ya runtse idanunsa gam gami da dunk'ule hannu, take jijjiyoyin kansa suka mik'e tar! "Ka barni na cigaba da abinda na sa gaba, abinda kawai nake buk'ata daga gareka shine fatan alkhairi, amma idan ba wannan ba to bana buk'atar shawararka." Ya fad'a cike da 6acin rai "Haba Faruk! Meyayi zafi haka? Kayi hak'uri don Allah ka kwantar da hankalinka, mubi komai a sannu, insha Allah zaka cimma burinka." Take yayi murmushi. Rungume Najeeb yayi yana fad'in. "Yawwa ko kaifa, haka ya kamata ka fad'a." Najeeb ya k'ak'alo murmushi kurum. * Da daddare bayan Dada yaci abinci sai ya aika a kira masa Faruk, bayan ya shigo parlon Dada yana kallon tashar BBC, rage volume yayi yana kallon Faruk sadda yake zama kan carpet, bayan ya gaishe shi kamar kullum Dada ya soma magana. "Faruk dalilin da yasa na kiraka shine, naji labarin daga wurin Hajiya cewar ka samu matar da kake so haka ne?" Yace "Haka ne Dada." Dada yace "To alhamdulillahi, daman abinda nake jira kenan Allah yasa albarka 'yar gidan waye?" Faruk yace "Sunan mahaifinta Alhaji Hamza, 'yan garin Katsina ne amma nan garin yake aiki baban nata." Dada yace "To yayi kyau, da fatan kayi k'wak'waran bincike kafin ka fara soyayya da ita?" Yace "Eh Dada, mahaifinta ma'aikacin banki ne, shine manager na First bank yanzu haka, kuma mutumin kirki ne, to yama ce na fad'a maka na tura magabatana a yi magana." Dada yace "To alhamdulillah, indai wannan ne babu matsala kar ka damu zamu je insha Allah, ni na d'auki nauyin komai kai da k'anwarka, zan shirya nida Alhaji Musa da Alhaji Sufyan (k'aninsa da yayansa) sai muje insha Allah. Jeka kira min Nabeel da Najeeb." Yace "To Dada." Ya mik'e ya fita, ba'a juma ba suka shigo tare gaba d'aya, bayan sun zauna Dada ya fara magana. "Kamar yadda nayi muku alk'awarin gina muku gidaje, to an kammala, ga ma makullen nan, kai Nabeel bazan baka ba sai ka samo wacce zaka aura, amma da Faruk da Najeeb su tunda suna da wad'anda suke so, sheyasa zan damk'a masu takardun gidajen da kuma mukallen. Sai kuma anyi maku order d'in motoci guda uku, zasu iso nan da sati d'aya insha Allah. Sai abu na k'arshe maganar lefenku Hajara (k'anwarsa) na damk'a mata ragamar yin lefe na kowanenku, abinda zakuyi list sai ku rubuta duk abinda kuke buk'ata, Allah yasa alkhairi yasa ayi damu." Suka amsa da "Amin." Sannan kuma suka shiga jero masa godiya marar adadi tare da fatan alkhairi. Sai yanzu Faruk ke tunanin anya zai iya cin amanar Meenah kuwa? Ko don albarkacin Dada wannan kaya da ya masa haka? Sai dai ya k'udiri a ransa ya zama dole ya d'auki Fansa kota wani hali ne! Jikinsa yayi matuk'ar sanyi a yayinda dayake fita daga parlon. AUREN FANSA 25 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 Dedicated to Miss Hafsy and Aisha Ali Garkuwa❤️ 🌹25 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Da gudu ta fad'a jikin Mama tana kuka sosai, Mama dake had'a kayan wankinta a cikin kwando ta dakata tana kallonta cike da mamaki, sannan kuma tace "Jidda lafiyarki haka zaki shigo kina kuka? Wani abin ne ya faru?" Ta k'ara fashewa da wani kukan har tana shasheka. Hankalin Mama ya tashi matuk'a har ta fara tunanin ko batada lafiya ne ma. "Wai bazakiyi magana ba, ni sa'ar ki ce ina miki magana kin min shiru?" Cikin kuka tace "Mama ki taimake ni! Mama idan na rasa shi kamar na rasa raina ne, bazan iya rayuwa bashi ba Mama ki taimake ni Mama!" Taci gaba da kukanta. Da mamaki Mama tace "Waye kuma idan kika rasa shi zaki rasa ranki? Ke bakida hankali ne? Akan namiji ki zauna kina wannan kukan, ni kin ma bani haushi. Wai waye ana miki magana kin ma mutane shiru?" "Ya Faruk ne Ma..." Ture ta Mama tayi daga jikinta tana kallonta galala sannan tace "Wa kika ce? Wane Faruk d'in?" Cikin kuka tace "Na nan gidan, naji ance aure zaiyi, ni na yarda ya had'a mu ya auremu tare da wadda yake so..." Buge mata baki Mama tayi hakan yayi sanadiyar katsewar maganar tata, ta dafa wurin tana cigaba da kuka. "Lallai yarinyar nan ashe bakida mutunci? Kawai sai a shiga hak'kin yaro babu dalili? Shi baice yana sonki ba haka kawai sai a takura masa, to wallahi ahir d'inki! Kar na kuma jin magana makamanciyar wannan a nan gidan, tun wuri ki fitar da Faruk daga ranki kinji na gaya miki, ashe bakida wayau bansani ba? Tashi ni ki bani wuri." Da gudu ta fice tana kuka, tsakanin d'a da mahaifi kuma sai Allah, take tausayin Jidda ya kamata don haka sai tabi bayanta. Rarrashinta ta shiga yi da nasiha, har ta samu tayi shiru, nan dai tayi ta kwantar mata da hankali cikin hikima da dabara. *** Ranar Juma'a magabatan Faruk suka gabatar da komai na auren d'annasu. Duk wata dukiya da ake buk'ata ta aure da kuma al'ada sun gabatar tare da sadakinsu. Bayan kammala komai aka saka bikin wata d'aya saboda Baba ya buk'aci hakan, don yace yafi so ta fara karatu a d'akin mijinta. Bayan Sati biyu da hakan kuma suka kawo lefe saitin akwati/jaka takwas da kit. Akwatinan sunyi kyau kalar purple. Yanzu bikin ya rage saura sati biyu kenan. To daga nan kuma aka cigaba da shirye shiryen biki, tun daga kan su dilka, gyaran gashi Baba ne yasa aka d'auko ta daga maiduguri mai suna Salima. Matar ta k'ware a gyaren jiki da gyaran amarya. Kwanan ta d'aya amma Meenah ta fara murjewa, ko wucewa tayi sai k'amshin jikinta ya bugo mutum. Kayan d'aki kuwa Baba daga dubai yasa akayi mata order, gado set biyu masu matuk'ar tsada da kyau, sai set d'in kujeru suma biyu, kayan dining da kitchen ma duka a can akayi order komai da komai. Don Baba a shirye yake don nuna ma Meenah gata. Hartta katin d'aurin aure daga dubai d'in aka bugo su, sheyasa ya fita daban ko kallon shi kayi kasan ya had'u! Tun ana saura sati d'aya bikin Baba ya tafi Katsina ya d'auko Goggo. Nan itama aka fara hidimar biki da ita. A 6angaren ango shima shiri sukeyi sosai, don su mutum hud'u ake ma biki, da Faruk da Najeeb da Yusra, sai Anisah, Nabeel da Jidda suka rage kasancewar basu fiddo wad'anda suke so ba. Don haka gidan ya kacame da hidima ba kad'an ba. Events d'in da Meenah zatayi kamu ne kawai tasa sai yinin biki, sai d'aurin aure sai walima sai kai amarya sai ango zasuyi dinner shikenan. Tun ana saura sati d'aya aka fara jere a unguwar Aso Villa, manyan gidaje ne jere guda uku amma kowa da katangarsa haka ma kowa da gate d'insa, babban gida ne ba laifi don yana da wadatar fili, gidan dai yaji shuka banda carpet grass dake shimfid'e a k'asa, ginin zamani mai d'auke da parlor biyu, d'akuna uku, kitchen da dinning. Gidan yayi sai dai fatan Allah basu zaman lafiya! Ranar laraba ta kama ranar da ake ma Meenah k'unshi, nan fa aka zauna daga can garden aka shiga yaryara mata k'unshi. Sai wata kuma daban tana ma 'yan matan amarya da sauransu. Ranar alhamis ranar da ake kamu k'arfe hud'u za'a fara a gama k'arfe shidda. Amarya tayi shiri cikin ja da silver bridal gown wanda ya amshe ta ya kuma yi mata kyau! A yayinda da Zarah suke sanye cikin ashobi pink da black. Bayan an gama shiri aka rufe mata fuska suka tafi wurin kamu. Nan kuma aka shiga gabatar da kamun yadda ya kamata, tun a wurin kuma Nabeel yake ma Zarah wani irin kallon da har sai da ta tsargu, shikam tunda ya ganta yaji ta masa. Anyi taro lafiya, ansha hotuna. K'arfe shidda daidai aka kammala aka watse. Bilki anata fama da jama'a, 'yan uwa, mak'ota, abokan arzik'i, 'yan cin arzik'i, da kuma k'awayenta don haka ko tana cikin 6acin rai ma bazaka gane ba. Hidima tasha kanta, gidanta a cike yake taf ba matsaka tsinke. Hartta dai Hajiya Laila da d'iyarta sunzo tun ana saura kwana biyu bikin. Nabeel dai ya kasa hak'uri ya sanar da Najeeb yana son k'anwar Meenah, aiko yaji dad'in haka. Don haka ya sanar da Faruk, Faruk ya sanar da Meenah ita kuma Meenah ta tuntu6i 'yar uwarta taji ta bakinta. Batayi saurin amincewa ba sai daga baya, take kuwa suka kar6i number juna yanzu har sun fara gaisawa ta waya! Ranar juma'a cikin garin Abuja dubban mutane suka shaida auren FARUK ADAM DA AMINATU HAMZA, NAJEEB DA ANISAH, YUSRA DA SADIQ. Daga nan angwaye suka zarce walima a guest house d'in Dada dake can Asokoro. Washe gari akayi wunin biki, tun safe jikin Meenah ya fara yin sanyi kuma, ko abinci tak'i ci, jinta take kamar wata marar lafiya. Gashi Bilki bata damu ba bare kuma ta tilasta mata taci. Zarah keta lalla6a ta har dai ta samu tasha ruwan tea. Haka aka cigaba da gudanar da wunin biki cike da kwanciyar hankali. K'arfe takwas na dare motocin d'aukar amarya suka iso. Tun a sannan Meenah ta fara kuka, tun tana ganin zata rabu da 'yar uwarta sai kuma hankalinta ya tashi sosai. Take suka rungume juna suna ta kuka mai ban tausayi. Da k'yar wata daga dangin Faruk ta janyota, bayan an kaita parlon Baba take kuma ta fara sabon kuka, shi kansa Baban idanunsa sunyi ja, su Goggo da Bilkin duk suna zaune a wurin, nan aka shiga mata nasiha mai ratsa jini da jijiyoyi, kuka kawai take, suka sassaka mata albarka da fatan zaman lafiya, sannan aka jawo ta wajen mota ana ta rangad'a mata gud'a. A kan hanyarsu ta zuwa hankalin Meenah yayi matuk'ar tashi, tunda zataje inda bata sani ba, bata ta6a rayuwa a ciki ba, zuwa cikin rukunin sabuwar rayuwa mai cike da garari, dad'i ko akasin haka.... AUREN FANSA 26 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 🌹26 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Bayan an kawo amarya masu ganin gida suka gama gani tare da fatan alkhairi, sai kuma suka soma tafiya, nan kuma aka bar 'yan matan amarya wad'anda zasu kwana saboda gobe walima. Haka kuwa akayi washe gari aka gudanar da walima, aka k'are lafiya, bayan an gama aka maido amare gidanjensu, nan kuma su Zarah suka taya ta zama har dare haka sukayi jugum babu mai cewa uffan. K'arfe takwas, tara, goma har da rabi shiru babu ango babu alamarshi. Ganin sha d'aya saura yasa Zarah cewa. Gaskiya nikam na gaji da zaman jiran ango Meenah." D'aya daga cikin cousins d'in su Meenah mai suna Khadija tace "Abinda za'ayi ko idan sunzo ki kar6a mana kud'inmu zan dawo gobe in amsa har ma da sauran kazar da kuka rage ta amarci." Wannan karon Zarah bata tanka ba don takaicin rashin zuwan ango akan lokaci, haka sukayi ta mata bankwana suka bar gidan. Tayi shiru tana tunanin abinda ya hana shi zuwa har wannan lokacin, tayi tagumi. Har kusan sha biyu saura shiru, ta gaji ta yaye lullu6in tayi zaune ta zurfafa cikin tunanin babu ango babu alamarshi. Gyangyad'i ta fara yi tun tana yi sama sama har ta kusa 6ingirewa k'asa. A tunaninta idan ta farka zata ganshi kan gadonta sai dai wayam ta ganta ita kad'ai. Ta mik'e ta sauya kayan bacci ta duba agogo k'arfe 1:36am. Ta koma kan gadon ta kwanta cike da fargaba, sai kuma ta mik'e tana tunanin ko lafiyarsa k'alau don abin ya fara bata tsoro. Wayarta ta d'auko ta kirasa amma abin mamaki wayarsa a kashe! Ta dafe k'irji tare da d'ora kanta bisa pillow tayi lamo. Can bacci 6arawo ya sace ta, a tunaninta zata farka ta ganshi ya dawo amma abin mamaki babu alamarshi. Ta duba agogo 4:50am, a sanyaye ta shiga toilet ta d'auro alwala tayi sallah. Sai da gari ya d'an fara haske ta fito don ta duba ina angonnata kuma taji dalilin da ya hanashi zuwa da daddare. Bata san kan gidan ba haka tayi ta shiga tana fita amma ba alamun mutum a gidan. Ta cika da tsoro haka ta koma d'akinta tana tunanin ko ba'a gidan ya kwana ba? Wanka ta shiga ta fito ta shirya cikin ash material doguwar riga ta d'aura d'ankwalin kayan ta hau gado ta kwanta tare da lumshe idanu tana k'ok'arin tunanin meya faru da angonta haka har ya hana shi zuwa gareta duk da kuwa yana zakwad'in zuwan wannan rana. K'arfe sha d'aya aka soma bubbuga gidan, ta mik'e ta fito har bakin k'ofa tare bud'ewa. "Ina kwana?" Ta fad'a gami da kawar da fuskarta gefe. "Lafiya lau, Bismillah." Bata tanka ba kawai tabi ta gefenta ta wuce tana k'ok'arin had'iye kishinta. Parlor suka zauna sannan tace "Sunana Jidda, ni k'anwar Faruk ce abinci ne aka bada a kawo muku daga gida." Ta fad'a tana matsar mata da kwandon gabanta. Meenah tayi murmushi "Allah sarki, mungode Allah saka da alkhairi." Tayi yak'e tace "Babu komai, ina yayan ko bai tashi ba?" Ta hau inda inda. "Eh... a'a ya tashi ya shiga wanka." Jidda ta sunkuyar da kanta k'asa tace "Allah sarki ni zan wuce ki gaishe shi idan ya fito." Meenah tayi murmushi tace "Zaiji insha Allah a gaida Mama." "Zataji." Ta fice. Bud'e kular ta soma yi, soyayyar doya ce da k'wai da pepper soup sai k'osai da kunu. Kasa cin abincin tayi don rashin zuwan Faruk gareta ya mata zafi duk da kuwa har yanzu batasan dalilin rashin zuwan nasa ba. Bata buk'atar komai a halin yanzu sai son ganin Faruk da kuma son jin dalilin da ya hana shi zuwa. Ganin tunanin bazai mata ba yasa ta jawo kular abincin ta soma ci, kasa ci ma tayi sai kawai ta zuba kunun tasha ta koma kan gado. Wayarta ta d'auko ta k'ara kiransa wannan karon a kunne taji ta amma har ta tsinke ba'a d'auka ba. k'walla suka cika mata ido, lallai al'amarin mai girma ne. Sai da tayi kwana biyu a na ukkun ne taji alamar shigowar mota, da sauri ta lek'a shi d'inne yana sanye da suit kalar toka da wando kalar tokar shima. K'in fitowa tayi don tana tsananin fushi da shi. Tana zaune taji alamun bud'e k'ofa, da alama d'akinsa ya shiga. Sai da ya d'auki akalla minti talatin sannan taji alamun fitowa, da sauri ta kwanta gami da rufe idonta kamar mai bacci. Bud'e k'ofar d'akin yayi yana tsaye yana k'are mata kallo, daurewa yayi ya tako har bakin gadon gami da zama kusa da ita. "My baby..." Ko motsi batayi ba bare yasa ran zata amsa. Kamo hannuwanta yayi yana murza su a hankali cikin salo na k'warewa, bugun k'irjinta ya k'aru. "Haba my baby shirunki yana iya haifar min da matsala babba idan baki amsa ni ba, kinji my baby please ki tashi kiji abinda zan fad'a miki." Tsananin son da take masa shi ya hana ta yi masa musu, tashi zaune tayi fuskarta kuwa kamar an mata albishir da gidan wuta. "Nasan ban kyauta miki ba, amma kiyi hak'uri babban dalili ne yasa kika ga ban zo ba a ranar da aka kawo ki..." Ta kalle shi idanunta cike da kwalla tace "Wane dalili ne ya hana ka zuwa? Wane dalili ne ya hanaka zuwa gareni duk da kuwa yadda kake zakwad'in zuwan wannan rana! Wane dalili ne yasa ka mance dani har kak'i d'aukar wayata a lokacin da nake nemanka? Wane dalili ne yasa a daren da aka kawo ni ka mance dani ka maida ni dani da bola duk d'aya suke a wurinka? Wane dalili ne ya hanaka kwana a gidanka ranar dana fara takowa a gidanka? Wane dalili ne...?" Toshe mata baki yayi da hannunsa yana girgiza mata kai, take hawayen da take rik'ewa suka yi nasarar saukowa, sannan ta bishi da kallo na ina jiran amsa. "Don Allah ya isa haka my baby, wallahi ba laifina bane, Dada ne bashida lafiya dole tasa muka tafi wurinsa..." Ta girgiza kanta. "Dada bashida lafiya meyasa da jidda tazo rannan da safe ta kasa sanar dani hakan, har tambayarka tayi ko kana ciki? Ta yaya mahaifinta bashi da lafiya ta kasa sani?" Take ya hau inda inda. "Eh ay ko ita kanta bata sani ba saboda bata gidan, amma banyi tsammani zaki zarge ni da yin k'arya ba Meenah." Ya k'arasa yana k'ak'alo hawaye. Hankalinta ya tashi tace "Ko kusa ba haka bane, na yarda da kai my soul, amma ka gane duk abinda ya shafe ka nima ya shafe ni, daka sanar dani ko addu'a dana yi masa, Allah ya bashi lafiya." Yayi murmushi "Yawwa my baby ko kefa? To yi murmushi mana." Ya fad'a cike da shagwa6a, hakan ya bata dariya sosai. Kamo ta yayi yana fad'in. "Zo muje na siyo maki abin dad'i." Tayi murmushi suka fice. *** Da misalin k'arfe 8:35pm yayi sallama, Dada na aiki a laptop nasa ya dakata gami da amsa sallamar sannan yayi murmushi. "Ahh Faruk kaine tafe? Shigo mana." Faruk ya shigo bayan ya zauna yace "Dada an wuni lafiya?" Yace "Lafiya lau ya iyalin naka da fatan tana lafiya?" Yace "Lafiya lau Dada daman wurinka nazo." Ya dube shi kafin ya cire gilashin dake idonsa na karatu yace "To gani lafiya dai?" Faruk ya sunkuyar da kai tukunna yace. "Dada daman so nake na nemi izini wurinka zan k'ara aure." A razane Dada ya dube shi gami da gyara zama yace "Aure fa kace Faruk? Aurenku da ko sati ba'ayi ba sai kace zaka k'ara aure? Kaima kasan hakan bazai yiwu ba. Tukunna ma wacece zaka aura?" Ya sukuyar da kai "Dada daman Jidda ce..." "Ban lamunta ba! Idan ma mafarki kakeyi to ka farka!" Mama ta fad'a tana tsaye a bakin k'ofa daga ganinta kasan tana cikin 6acin rai. MSB💖 ********************** ? ************************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************? ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ? ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ? ************************** AUREN FANSA 27 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 Hip!!!hip!!!hipp!!! Hurray!!!!!!! Wishing u long life in Islam and prosperity Faridat Allah k'aro shekaru masu albarka ya kuma k'ara basira da hazak'a Amin💃🏻💃🏻💃🏻😍😍 🌹27🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Gaba d'aya suka dube ta sadda take k'arasowa cikin parlon tare da zama gefen Dada sannan ta d'ora. "A gaskiya Alhaji banga amfanin aurensa ba duka duka yaushe akayi aurennan da zai bijiro mana da zancen wani auren kuma? Haba me kake so duniya tace mana? Ko sati d'aya fa bakuyi ba da aure haba Faruk ka bani mamaki, me tayi maka? Me ta tsare maka? Yarinya salihar baiwar Allah zaka ce zakayi ma kishiya daga yin aure yanzu? To a gaskiya ban lamunta ba Alhaji, ya sake lala." Dada bai ce uffan ba yana dai ta kallon Mama tana zuba har sai data gama sannan ya numfasa yace "Wai da kike ta wad'annan maganganun kece zaki zauna masa dasu ne? Bashi yace yaji ya gani ba? Ba wanda ya masa dole ay, kuma ni bazan iya hanasa yin aure ba, amma abinda nakeso ka sani Faruk shine kasan shi aure ba abin wasa bane, sannan kuma kaji tsoron Allah idan har kayi aurennan tofa dole sai kayi adalci a tsakaninsu, idan kuwa bazakayi adalci ba gaskiya ban yarda ka sake aure ba kuma bada yawu na ba, sannan magana ta k'arshe sai na tuntu6i ita Jiddar naji ta bakinta tukunna..." "Ay Alhaji kar ma ka 6ata lokacin ka saboda Jidda ta dad'e da ciwon son Faruk a cikin ranta, don ma ina kwa6ar ta ay da tuni ta sanar maka tana sonsa, sai dai Alhaji dole fa sai mun tashi tsaye kasan halin Jidda bata jin magana ina gudun kar taje tasa d'iyar mutane a gaba kaga babu dad'i hakan." Dada yace "Haka ne, Faruk a gaskiya sai ka tsawatar ma Jidda sosai saboda duk wani abin tashin hankali ta guje shi, idan kuwa bazata iya kiyaya ba to a fasa auren. Hajiya kira min Jidda tazo ina nemanta." "To Alhaji." Bayan fitar Mama Dada yace "Ina fatan ka sanar da ita Aminar batun k'ara aurenka? Kuma ta yarda ta amince da hakan?" Yayi shiru, Dada ya ce "Alamu sun nuna min cewa baka sanar da ita ba Faruk, to a gaskiya idan kaga ka auri Jidda sai da amincewar Amina, don haka kaje ka nemi shawarar matarka." To kawai ya iya cewa ya mik'e, a daidai bakin k'ofa sukayi kaci6us dasu Jidda zasu shigo, bai tanka mata ba yasa kai ya fice, bayan sun shigo Dada ya soma magana. "Jidda Faruk ne ya zo mana da wani zance wai yana son auren ki..." Bai k'arasa ba ta mik'e cike da murna tace "Dada? Da gaske kakeyi ko wasa? Da gaske Faruk zai aure ni? Mama da gaske kukeyi don Allah?" "Ke meye haka wai!"? Dada ya daka mata tsawa, zama tayi tana ta murna a yayinda Dada ya cigaba "Kinga Jidda ki nutsu ki saurare ni da kunnen basira, kamar yadda na fad'a miki Faruk yazo man da zancen aurenki, amma inaso kisani kiji tsoron Allah Jidda, kar ki cutar da d'iyar mutane kinsan dai Allah na kallonki, sannan duk wani abin da zakiyi da bai kamata ba na samu labari to ki sani k'arshen zamanki gidan Faruk yazo kenan, don haka ki kama kanki. Hajiya kisa ido akanta sosai, tashi ki tafi." Da gudu ta fice tana zuwa d'akinta ta fad'a kan gado cike da murna, har ma ta fara imagining wai gata can har sunyi aure da Faruk... *** Da sallama ya shigo parlon tana zaune kan kujera tana kallo, tana ganinshi ta mik'e tana murmushi sosai ta k'arasa wurinsa tace "Sannu da dawowa my soul." Ta fad'a tana amsar ledojin da ke hannunsa. Ya kalle ta tana sanye da army green Indian sari d'inkin riga da wando, kayan sun matuk'ar amsarta, fuskarta babu wata kwalliya don Meenah ba ma'abociyar yin kwalliya bace bata ma iya ba, hakan yasa kullum fuskanta take fresh gwanin kyau, d'ankwalin kayan kuwa yana d'aure akanta d'aurin ya zauna daram a kanta. Haka kawai kuma sai ta basa tausayi, ganin mummunna labarin da zai fad'a mata, yana tunanin yadda ma zata d'auki maganar. "My soul inata magana kayi shiru." Ya susa kai yana k'ak'alo murmushi yace "Ohh sorry baby, banji ba me kika ce?" Tace "Nace muje na saka maka ruwan wanka kayi sai kaci abinci." Yace "Ok ok bismillah muje." Tana gaba yana biye da ita, duk wani motsi nasa akan idonsa haka kazalika k'amshin turarenta duk ya cika masa hanci hakan ya haifar masa da kasala, jikinsa ya mutu. Suna shiga d'akinsa yau a karo na farko data ta6a shiga, simple d'aki ne mai d'auke da black gado duka furnitures d'in dake d'akin black ne, hartta wasu 'yan kujerun hutawa guda biyu da table tsakiyarsu suma black ne, carpet black, sai paintin d'akin ne kawai yake fari k'al hakan ya haskaka d'akin. K'amshi gami da sanyin ac kuwa sun had'u sun mata sallama. Kan gado ya zauna a yayinda da ta shige toilet nasa ta had'a masa ruwan wanka ta fito. Tana fitowa tace "My soul ga ruwan can na had'a maka, idan ka fito ina parlor." To kawai ya iya cewa shi duk jikinshi a mace yake ya rasa dalili. Bayan ya fito ya kimtsa cikin kayan baccinsa kalar dark blue, ya fesa turare mai sanyin dad'i ya fito. Tana zaune a parlor tana jiranshi, yana zuwa ta mik'e tana murmushi tace "Har ka fito my soul? Ga abinci nan na girka maka." Yayi yak'e yace "Thanks my baby." Tare suka zauna ta shiga zuba masa tuwon shinkafa miyar ku6ewa d'anya da k'ashin rago a ciki sai man shanu, bayan ta zuba masa da tsiyaya masa lemon kwakwar da tayi masa a glass cup, sai taja kujera tana fuskantarsa, a natse ya fara cin abincin sai dai gaba d'aya hankalinsa ba'a kwance yake ba. Ya kalle ta yaga hankalinta a kwance tana kallonsa, ya k'ak'alo murmushi yace "Baby bangane ba ke bazakici abincin bane?" Tayi murmushi tace "Zanci amma ina so sai kaci ka k'oshi tukunna." Ya kalleta cike da mamaki yace "Sam ban yarda ba, idan bakici ba nima bazan ci ba." Da sauri tace "Haba dai? To zanci." A tare suka ci abincin bayan sun kammala ta gyara wurin. Tana kitchen tana d'auraye plates ya kirata. Ta fito tana zuwa yace. "Baby zauna ina son magana da ke." Tace "to." Ta zauna. Ya had'iye wani miyau mai d'aci tukunna ya fara magana. "Meenah kinsan dai ina sonki ko?" Da mamaki tace "Sosai ma my soul, nasan kana sona amma lafiya?" Yace "Kuma kinsan dai ina k'aunar ki ko?" Tayi murmushi "Nasani." Yace "Yawwa, kinsan kaddara mai kyau da marar kyau ko?" Tayi dariya mai cike da mamaki tace "Nasani mana." Yace "Kinsan kuma dai kowa da tasa kaddarar Meenah, maganar da zan fad'a maki tana da nauyi, amma ina so badan ni ba don Allah da kuma soyayyar da kike min ki fahimce ni." Jiki a sanyaye tace "Don Allah my soul ka fad'a min ko meye, sai kwana kwana kakeyi." Yayi shiru cikin nazari, can yace "Hakane zan fad'a maki amma ina so kiyi min alk'awari guda d'aya." Tace "Na me?" Yace "Bazaki d'aga hankalinki ba sannan bazakiga laifi na ba." Gabanta yayi mummunan fad'uwa, tace "Don Allah ka fad'a min my soul ka barni a duhu don Allah." Tashi yayi tsaye yana mai juya baya don ya kasa ma had'a idanu da ita. Da k'yar ya iya tattaro kalamunsa wuri d'aya, yace "Auren zan k'ara Meenah..." A gigice take kallonsa, kanta yayi wani dum! Nuna sa takeyi da hannu tana fad'in "Anya naji da kyau, sake maimaita mini." Yace "Kiyi hak'uri haka d'in dai nace, aure zan k'ara." "Innalillahi wa inna ilahir raj'iun." Take kuma gumi ya dinga sassarfo mata ta ko ina, kafin kuma taji wani irin kuka ya taho mata cikin tashin hankalin ta fasa ihu sai dai yaji abu ya fad'i k'asa tim! AUREN FANSA 28 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 Wannan page d'in nakune members na MARZAH HAUSA NOVELS, nagode da k'aunar da kuke nuna min, Allah ya bar zumunci amin❤️ 🌹28 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Da sauri ya juya abin mamaki wai Meenah ce kwance kamar ba rai, a gigice yayi kanta ya shiga jijjiga ta, abin mamaki ko alamar motsi babu a tattare da ita. Tunda yake a rayuwarsa bayan mutuwar iyayensa bai ta6a tsintar kansa cikin matsanancin tashin hankalin irin wannan ba, ya rud'e ya shiga tashin hankali mai wuyar fassara. Da gudu kuma yayi dinning ya d'auko robar ruwan sanyi ya shiga bud'ewa har wani kyarma yakeyi. Yayyafa mata ya dinga yi amma ba alamar zata farka, hakan yasa ya juye mata shi gaba d'aya a fuska, aikuwa take ta saki ajiyar zuciya sannan ta bud'e idanunta wanda suka kad'a sukayi ja kamar garwashi, tarr take kallonsa kamar sabuwar halitta, shi d'in ma ita yake kallo babu ko k'yaftawa, a hankali ya sure ta in banda sannu babu abinda ke fita a bakinsa. D'akinsa ya wuce ya shimfid'ar da ita kan gado sannan ya nemi wuri ya zauna gefen ta har yanzu ita yake kallo. "Sannu Meenah... ya kike ji yanzu?" Kauda fuskarta tayi daga kallon da take masa zuwa d'ayan 6angaren sannan kuma hawaye suka shiga kwarara daga idanunta masu zafin gaske. "Meenah..." Ko motsi batayi ba bare yasa ran zata amsa. Hannunta ya kamo duka biyun yana murzawa, runtse idanunta tayi a take kuma wasu hawayen sukayi nasarar saukowa, tana cikin mawuyacin hali mai wuyar fassara, ita kad'ai tasan me takeji a halin yanzu. "Tabbas nasan dole kiji ba dad'i, nasan kin fara tunanin bana sonki ko? Sheyasa nace zan k'ara aure ko Meenah? Ina so ki fahimce ni Meenah har yanzu ina sonki kuma ina k'aunarki babu abinda ya chanza, auren da kika ga zanyi yana d'aya daga cikin kaddara ta, ina so a matsayinki na musulma ki d'auki kaddara Meenah, kawo wata mace cikin gidannan bazai chanza son da nake maki ba, nidai fatana ki yarda kuma ki amince don bazan iya k'ara aureba ba tare da kin amince ba." Fuskarta ya shafa ya cigaba "Wallahi ko yanzu kika ce kar nayi aurennan na fasa kenan ko da kuwa yanzu za'a d'aura shi, kuma ko wacece zata shigo cikin gidannan zan zamo mijin da zai kare miki martaba da kuma mutunci, har abada bazan wulak'anta ki ba, nidai fatana inji ta bakinki a halin yanzu Meenah..." Wani gumi ya ziyarce ta, wato dai da gaske kishiya zai mata kenan? Ita kam batada sa'a a rayuwa, ta taso tun tana k'arama tana d'and'ana bak'in ciki a koda yaushe ba kwanciyar hankali, tana tunanin auren da zatayi hutu ne a gareta ashe tayi kuskure. Sai dai kuma dole zatayi hak'uri tunda haka Allah ya kaddara mata ita kam. Ta yunk'ura ta tashi zaune tana mai share hawaye duk da kuwa wani na bin wani amma dole ta share, kanta kuwa kamar ana sara mata guduma haka takeji. Cikin wata irin muryar data dishe tace "Haba my soul, meyasa sai ka nemi izini a wurina sannan ka k'ara aure? Ka manta Allah ya halasta maka daga mace d'aya zuwa hud'u? Bana cikin irin matan da idanunsu ke rufewa da kishi har su fad'a halaka, Allah ya halasta maka aure ni wacece da zan hana? Ay ban isa ba ma." Tayi murmushi mai ciwo ta cigaba. "Ba k'arin aurenka ya fi d'aga min hankali ba, kasan me ya tada man hankali?" Yace "A'ah." Tayi murmushi "Wai ace aurenmu da ko sati ba'ayi ba amma ace zakayi aure, sannan kuma ina tsoron ka daina sona ne sheyasa ko kuma ka gaji dani." Yace "Haba my baby, kima daina irin wannan tunanin har yanzu ina sonki, kuma insha Allah zan cigaba har in mutu." Tayi murmushi "Na yarda da kai my soul, kuma ina alfahari da kai a matsayin mijina, a koda yaushe ina gode ma Allah da ya bani mai sona mai kuma k'aunata, idan aurennan alkhairi ne Allah ya tabbatar, idan ba alkhairi bane ba Allah ya za6a maka mafi alkhairi." Gabansa yayi mummunan fad'uwa, ya lumshe idanunsa kafin ya bud'e, ya kalle ta cike da sha'awa! Tunda yake a rayuwarsa bai ta6a cin karo da mace makamanciyar wannan ba. Matsowa yayi dab da ita yace "A gaskiya kafin a samu mace irinki a wannan zamanin sai an tona Meenah. Nima ina so ki sani ina sonki ina k'aunarki sannan ina alfahari da ke a matsayin matata." Duk da tana cikin wani hali hakan bai hanata yin murmushi ba, ta yunk'ura zata tashi jiri ya kwashe ta, da sauri Faruk ya taro ta sai kuma ta fad'a jikinsa haka ya rungume ta kamar wata jaririya. Wani shock ya kama ko wanensu, sannan kuma suka dubi juna cikin ido. Sun kai minti kusan d'aya a haka kafin Meenah ta fara kauda tata fuskar tana k'ok'arin tashi daga jikinshi. Duk ya dabarbarce, kwanciya tayi sakamakon wani bacci da taji yana neman kwasar ta. Duka duka batafi second goma ba bacci yayi awon gaba da ita. Jikin Faruk yayi matuk'ar sanyi, sannan kuma take ya fara tsintar kansa cikin wani irin yanayin da bai ta6a tsintar kansa a ciki ba. Wani abu yaji yana bin dukkanin illahirin jikinsa tun daga kansa har zuwa tafin k'afarsa, take tsikar jikinsa ta tashi tayi wani yarr! "Hasbunallahu wani'imal wakil." Shine abinda yake fad'i, sannan ya mik'e jiki a sanyaye ya fad'a toilet, a gaban sink ya tsaya tare da bud'e pampo ya shiga wanke fuskarsa, bayan ya gama sai ya tsaya yana kallon kansa kuma ta mirror, ba abinda idanunsa ke gani kamar fuskar Meenah, wani gurin tana murmushi wani gurin kuma dariya, tsintar kansa yayi yana mai murmushin shima. Da sauri kuma ya girgiza kansa ya fice daga toilet d'in yana ta faman maimaita "No." Kwanciya yayi gefenta tare da rufe idanu yana jin wani bak'on al'amarin da bai ta6a ji ba a tsawon rayuwarsa ba.... Sassanyar iskar asuba mai k'unshe da ni'ima tare da tarin albarka shi ya daki fuskar Meenah kasaancewar tagogin d'akin a bud'e suke. Hakan yasa taja dogon numfashi tare da motsawa, tayi tsawon minti biyu a haka kafin a hankali ta fara k'ok'arin tashi zaune. A natse ta juya tana maida kallonta kan Faruk da baisan inda duniyar take ba. Tuni abinda ya faru jiya ya fara dawo mata, nan ta yunk'ura cikin k'arfin hali ta mik'e duk da batajin k'arfin jikinta, kasancewar tana fashin sallah sai ta taka a hankali zuwa jikin window. Hadari ta gani sosai, iskar damina had'e da yayyafi ya daki fuskarta, hakan ba k'aramin dad'i yayi mata ba, tayi ta shak'ar iskan gami da ware hannayenta don ya ratsa ta sosai, take taji ta samu k'arfin jikinta fiye da dah. Ruwan saman ne ya sauko mai k'arfi, ta mik'a hannayenta duka ta tari ruwan. K'arar ruwan saman ne ya farkar da Faruk, idanunsa k'yam a kanta, sai yau ya ta6a ganinta ba d'ankwali, gashin kanta ya zubo har bayanta hakan ya faru ne saboda cirewar ribbon d'inta jiya da daddare. Kanta a nannad'e yake kamar na jarirai gashj bak'i wuik! Yayi zumbur ya mik'e tare da duba time ganin lokacin sallar asuba yasa ya mik'e da sauri ya nufi toilet. Har ya gama sallarsa a d'aki Meenah batasan yanayi ba. Tana can tsaye tana kallon ruwa na sauka k'asa, abin burgeta yake tun tana k'arama, ita dai rayuwarta tana son ruwan sama yanzu haka ji take kamar ta shiga ciki tayi wanka. A hakan ya cigaba da kallonta wanda baison yana yi ba. "Ina kwana." Ta fad'a gami da zama gefen gado. Yayi murmushi "An tashi lafiya? Ya k'arfin jiki?" Tace "Alhamdulillah." Har yanzu kallonta yake ganin ba wani yanayi na damuwa a tattare da ita dangane da maganar jiya ba. "Lokacin dana suma jiya kasan me ya kamata kayi min amma ka kasa sai rud'ewa, ashe dai kana sona haka?" Take gabansa ya fad'i, ya rasa dalili da ta ambaci yana sonta sai ya tsinci kansa da fad'uwar gaba? Yana jiyo dariyarta har cikin kansa. "Yanzu dai ina so ka fad'a min kai da ka ganni cikin wani irin yanayi ka rasa abinyi saboda kana tunanin ko mutuwa nayi? Ashe kana tsoron rasa ni?" Ta k'arasa maganar tana dariya. Yayi dum, sannan ya mik'e ya zauna gefenta tare da rik'o hannunta yace. "Ay dole na tsorata tunda ina ganin zan rasa masoyiyata ta hak'ik'a." A zahirin gaskiya baisan ya furta wad'annan kalaman ba... Don haka sai yayi saurin tashi tsaye yana fad'in "Bari nayi wanka yau zan fita office da wuri." Da mamaki ta kalleshi "Yanzu fa k'arfe shidda." Yace "Eh wurin bakwai nakeson barin gidannan." Tace "Ok bari na had'a maka breakfast kafin ka fito." Da sauri ya tsaida ta "A'a kar ki wahalar da kanki tunda bakyajin dad'i." Tayi dariya "Haba ba wani wahala bari yanzu zan gama." Bata jira amsar sa ba ta fice da sauri. Ya dad'e tsaye a wurin kafin yayi saurin shigewa toilet. MSB💖 AUREN FANSA 29 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 Dedicated to Anty Zee and AishatFareeda❤️ nagode da k'auna😍 🌹29 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Bayan ya gama shirinsa yayi breakfast sai ya fara k'ok'arin fita, ba yadda Meenah batayi dashi ba akan ya hak'ura a gama ruwannan yak'iya yace aikin da zaiyi yana da mahimmanci sosai. Haka nan ya d'auki umbrella ya fice cikin ruwannan. Bayan ya fita kuma ta hau aikin gida kamar kullum, ta kimtsa ko ina ta turara gidan da tuararen wuta ta bi da freshener ta fesa ko ina. Tayi kalacinta bayan ta gama tayi wanka ta shirya cikin wani simple lace kalar sararin samaniya (sky blue) da pink. Tana shirin d'aura d'ankwali wayarta ta fara ringing, ganin Zarah yasa tayi murmushi ta kara a kunne. "Assalamu Alaikum..." Zarah tayi murmushi "Wa'alaikumusalam, ya kike?" Meenah tace "Uhm bansani ba bayan kin manta dani ma." Zarah ta d'anyi dariya tace "Haba sis, ni na isa ne? Gani nayi bai kamata na takura miki ba nasan kina can kina cin amarci yadda ya kamata, ba kya buk'atar takura..." "To aku sarkin magana ya isa haka, ya garin ya su Mami?" Tace "Suna nan lafiya, daman kiranki nayi naji idan kina gida zan biyo, daga school nake ance admission ya fito shine naje na dubo mana..." Cike da murna Meenah tace "Haba don Allah? Munci?" Zarah tayi dariya tace "Oho sai nazo dai, amma ina fatan ango baya gida don wallahi idan yana nan zan wuce gida kawai." "Haba mana Zarah wallahi baya nan kizo ina kewarki da yawa." Zarah tayi murmushi "Nima haka sai nazo." Da haka sukayi sallama. Minti sha biyar tsakani Zarah ta iso, rungume juna sukayi suna murna, Meenah ba k'aramin dad'in ganin Zarah tayi ba. Can ta shiga kawo mata kayan motsa baki su lemo da cake, su dambun nama da sauransu. Meenah tayi murmushi tace "La Zarah kinga yadda kika jik'e kuwa? Meyasa kika fito cikin ruwa? Ki shiga d'akina ki cire wad'annan kayan ki saka nawa." Tace "Tab kayanki sun mani kad'an ay." Meenah tace "Inji waye? Akwai wanda sukayi min yawa ay." Zarah tace "To." Tunda Zarah tazo take bin Meenah da kallo, har dai Meenar ta tsargu a lokacin da take tsiyaya mata lemo a cikin glass cup, bayan ta gama ta koma ta zauna tana kallon Zarah tace "Wai lafiya kike min wannan irin kallon haka?" Zarah ta zuba mata idanu, kafin kuma ta saki ajiyar zuciya tace "Meenah gani nayi kin rame sosai, akwai abinda ke damunki ne?" Meenah tayi murmushin da bai kai zuci ba tace "Babu komai me kika gani?" Zarah tace "Haba Meenah, tsawon shekarun da muka d'auka tare da ke nasanki, nasan idan kina cikin matsala ko akasin haka, kuma a matsayina na k'anwarki bai kamata ki 6oye min abinda ke ranki ba Meenah." Meenah taja ajiyar zuciya tace "Hakane, bawai na 6oye miki abinda ke raina bane, kawai abinda zan fad'a ne nasan zai rud'a ki had'e da mamaki marar misaltuwa." Da mamaki Zarah tace "Niko zanso inji menene wannan da zai rud'a ni haka zai kuma bani mamaki." Meenah tace "Uhm bari kedai, to ki nutsu kar ki rud'e dan Allah Zarah, to ba komai bane ba illa wai Faruk zai k'ara aure..." Lemon da ta kai bakinta shi yayi sanadiyyar k'warewar da tayi hakan yasa ta dinga tari, da k'yar Meenah ta dinga bata ruwa har tarin ya tsaya tana ta faman yi mata sannu. Sai da ta nutsu Zarah tace "Wai wane Faruk d'in tukunna Meenah?" Meenah ta d'anyi dariya tace "Akwai wani Faruk da kika sani bayan mijina ne? Shi dai nake nufi Faruk da na aura a matsayin mijina to shine zai k'ara aure." Salati Zarah ta shiga yi cikin tashin hankali sannan tace "Faruk dai your soul Meenah? Wai aura fa kika ce? To kuma shine kika zauna kamar baki damu ba?" Meenah tayi murmushi "To ya kikeso inyi? Kashe kaina zanyi ne? Abinda Allah ya kaddara waya isa ya hana? Nidai na rungumi kaddara kuma ina fatan wadda zai aura mutuniyar kirki ce, sannan ina fatan bada tashin hankali zata shigo min ba, amma nidai idan mijina na sona banida matsala." Zarah nata kallonta tana magana cike da mamaki, sai data gama Zarah tace "Lallai an gaishe ki Meenah, kinyi k'ok'ari sosai, ba kowace mace bace zatayi abinda kikayi ba, ni gaskiya inda nice bazan yarda ba, sai anyi tashin hankali ba kad'an ba, tab kishiya fa lallai!" Meenah tayi dariya. "To Allah ya kyauta dai, kedai kiyi ta addu'a Allah ya baki miji na gari shine kawai. Wai shin ina Nabeel kuna ta shan soyayya ko? Kuma yana zuwa zance ko kuwa?" Zarah tayi dariya "Han! Kin cika ni da tambaya wane zan fara amsawa?" Suka d'ara su duka, Meenah tace "Duka zaki amsa mana." Zarah tayi murmushi mai bayyan hak'ora tace "To Nabeel yana nan lafiya lau, yana ta zuwa wurina and kuma Baba yace ya turo iyayensa." Cike da murna Meenah tace "Masha Allah! Allah ya tabbatar da alkhairi Zarah." Tace "Amin... yauwa Meenah ina za'a samu mai aiki?" Meenah tace "Mai aiki kuma? Me za'ayi da ita?" Zarah tace "Mami mana, ta matsa ita 'yar aiki takeso, wai gwara ta samo don idan nayi aure nima babu kowa gidan." Meenah tace "To kin ta6a ganin na samo masu aiki ne? Amma zan tambayi Faruk ko yasan inda ake samu." Zarah tace "Yauwa nagode, batun result naga sunayenmu sun baki Business admin ni kuma Biology." Cike da murna Meenah tace "Alhamdulillah, kin anso admission letter?" Zarah tace "No sunce sai next week, so zamuje sai muyi registration." Nan sukayi ta murna marar misaltuwa. Kafin Zarah ta tafi sai da ta taya Meenah tayi abincin rana, shinkafa da miya sukayi da salad. Bayan sun kammala Zarah ta fara shirin tafiya. Nan sukayi bankwana akan Meenah zatazo gida ta gaida su Baba, Zarah kuma ta tuna mata batun mai aiki. *** Tarin takardu ne da laptop a gabansa ya tasa gaba yana kallo, amma a zahiri hankalinsa baya wurin idonsa ne kawai ke kan takardun, tunanin Meenah yasa shi a gaba ya hana shi sak'at har ma ya rasa inda zai sa kansa. B'angare d'aya na zuciyarsa yana tunani akan yadda zai cimma burinsa, d'ayan 6angaren kuwa, Meenah ce tayi masa tsaye a rai duk yadda yaso yakice ta daga ransa abin yaci tura. Sai ma dad'a gaba abin yakeyi. K'wank'wasa k'ofar akayi, ya bada izini aka shigo, matashiyar budurwa 'yar kimanin shekaru ashirin da biyar (25) a duniya, suna kiranta da young detective, saboda sabuwar shiga ce sannan gata yarinya. "Sir wai kana nema na ko?" Yace "Yes ina nemanki, bismillah." Tace "Ok sir." Bayan ta zauna ne yace "Wani taimako zakiyi min Hajir, amma kafin nan bari na baki labarin komai tukunna." Nan ya shiga bata labari tun daga farko har k'arshe sannan yace "To yanzu kinji inda nakeson focusing, ina so kije kiyi tunani nima zanyi tunanin hanyar da zamu dinga samun information daga gidan, da naso muyi magana sosai but gaskiya na gaji kuma bana d'an jin dad'in jikina, so zan tafi." Ya duba tima k'arfe 3:47pm. Yace "La'asar ta kusa, zan je masallaci idan na tashi daga nan, sai na wuce gida, zuwa gobe idan nazo zamuyi magana." Tace "Insha Allah." Yace "Ya batun case d'innan da akayi assigning d'inki kin gama shi kuwa?" Tace "Na gama amma case d'in ya bamu wahala sosai, sai dai cikin ikon Allah munyi succeeding." Yace "Haka ake so ay, nima akwai cases masu bani wahala amma da mutum ya sa confidence a ransa da kuma jajircewa akan aikin sai kiga komai ya tafi yadda ake so." Tace "Haka ne." Ya mik'e ya soma tattara komatsansa cikin briefcase yace "Hajir zaki iya tafiya, sai goben insha Allah." Tace "To sir Allah ya kaimu." Yace "Amin." Daga haka ta fice a yayinda ya kammala kimtsa kayansa sannan ya fice daga office d'in.... AUREN FANSA 30 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) 🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹 🌹30🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Mairo Gafai Allah ya baki lafiya yasa anyi a sa'a 😍 Daga d'an nesa yakejin kamar ana k'wala masa kira, hakan ya dakatar dashi daga bud'e motarsa da yakeyi. Hango Najeeb yayi yana k'arasowa cikin d'an gudu gudu, tun daga nesa yake hango sa kamar yana cikin damuwa. Sai da ya k'araso dab da shi sannan Najeeb yace "Wai tafiya zakayi da wuri haka? Wurinka nazo fa." Faruk yace "To, kuma gashi har na rufe office zan wuce gida, amma idan maganar batada tsawo mu shiga daga ciki." Najeeb yace "No batada wani tsawo sosai, no need ma mu shiga daga ciki muna iya tsayawa a nan." Faruk yace "Ok kafin nan ya gida ya k'anwata da fatan ana kula min da ita sosai?" Najeeb yace "Haba mana kai kason yadda nakeson Anisah ay, dole ma na kula da ita. Yawwa wata magana nake ji daga gida cewar zaka k'ara aure, shin gaskiya ne ko ba gaskiya bane ba?" Faruk yace "Wannan magana gaskiya ne, haka take." Najeeb yace "Amma ka bani mamaki Faruk, ta yaya zaka k'ara aure yanzu? Daga yin aurenku, baka bari nan gaba kad'an idan ma zaka k'ara sai ka k'ara. Haba Faruk..." Faruk yayi murmushi yace "Najeeb kenan, gani nayi fa ba haramun bane k'ara aurennan, sannan ba wata bare bace zan aura 'yar gida ce." Najeeb yace "Nasani mana, amma baka ganin Jidda bata dace da kai ba?" Faruk sai ya kama dariya yace "Ta yaya?" Najeeb yace "Haba Faruk, yarinyar nan kasani sarai batajin magana, kullum cikin yawo take, gata ta tara k'awaye a gida, baka ganin yadda su Dada ke fama da ita? Kai baka tunanin ta zame maka matsala a gidanka da kai da iyalinka nan gaba? Kuna zaman lafiya kaje ka jajibo ma kanka masifa har gida...?" "Wa'iyazubillahi! Haba Najeeb ka daina kira min masifa a gida, insha Allah babu abinda zai faru sai alkhairi. Kuma da kake batun Jidda bataji zan gyara ta, kai kanka zakayi mamaki." Najeeb ya kad'a kafad'a alamun oho yace "Well it's your choice not mine, don't say I didn't warn you to." Faruk yace "Yawwa kuma nagode da shawara, zamu iya tafiya?" Najeeb yace "Of course, ni zan tafi sai anjima a gaida gida." *** A gajiye ya shigo gidan, tana zaune kan kujera ta zaman mutum uku, hannunta rik'e da remote tana chanza channel d'in da take muradin kallo. Tunda ya shigo yake binta da ido, a tsawon rayuwarsa bai ta6a ganin Meenah cikin irin wannan ado haka ba. Wani dark blue leshi ne a jikinta mai yarfin golding, ga wasu duwatsu dake rauraya daga gaban rigar, d'inkin an mata wanda ake cema da peplum sai skirt da ya kamata, d'aurin d'ankwalin kuwa kamar don ita akayi shi, tana sanye da 'yan kunne da sark'a kalar kayanta, yadda kasan wata matar shugaban k'asa ko wani gwamna saboda yanayin shigarta ya nuna hakan. K'amshin gidan ya had'u ya gauraye dana sanyin ac, hakan ba k'aramin dad'i yayi masa ba. Bata ankara ba sai ganin mutum tayi tsaye a gabanta, murmushi ta sakar masa mai saurin fizge zuciya a yayinda ya mayar mata ba 6ata lokaci, sannan kuma ta tashi a hankali ta k'araso inda yake tana mai tafiya cike da nutsuwa. Shi dai yana tsaye yana binta da idanu, ta amshi briefcase d'insa tare da kama hannunsa tace "My soul lafiya ka dawo da wuri haka?" Ya dube ta cikin kulawa yace "Wallahi kuwa na gaji ne, sannan yau bawani aiki sosai." Tace "Ok muje kayi wanka ko abinci zaka fara ci?" Ya girgiza kansa alamun a'a yace "Bari inyi wankan dai zai fi, sai inci abincin daga baya." Hannunsa take ja yana biye da ita har d'akinsa sannan ta shiga ta had'a masa ruwan wanka kamar kullum, bayan ta fito ta taimaka masa ya rage kayan jikinsa, sannan ta fice ta bashi wuri ya kimtsa. Bayan sun gama cin abinci ne suna zaune a parlor suna hutawa Meenah ta soma magana. "My soul don Allah na tambaye ka?" Ya gyara zamansa yana fuskantarta yace "Eh Allah yasa nasani." Tayi murmushi tace "Daman... nace ina kake ganin za'a samu 'yar aiki?" Yace " 'Yar aiki kuma? Me za'ayi da ita?" Tace "Mami daman keso, ni bansan inda ake samu ba shine nace bari na tambaye ka." Hajir ta fad'o masa a rai, take kuma ya fara murmushi ganin wata dama ta samu da zaiyi amfani da ita kuma bazai bari ta wuce shi ba. Sai yayi saurin cewa. "Haba indan wannan ne kar ki damu, Mama na da masu aiki, so samowa bazaiyi wahala ba, zan mata magana." Cike da jin dad'i tace "Kai nagode sosai my soul." Ya d'an tsunkuli gefen kumatunta yace "Anything for my baby." **** Washe gari a office yasa aka kira masa Hajir, tana zuwa yace ta zauna, bayan ta zauna ya soma magana. "Kamar yadda nayi miki bayani jiya zamuyi magana, to shine yanzu zan miki bayani. Da farko wani aiki zakiyi min, sannan don Allah ina buka'atar had'in kanki Hajir." Hajir tayi dariya "Insha Allah sir." Yaji dad'i yace "Da farko ina so ki chanza identity d'inki gaba d'aya." Cikin rashin fahimta tace "Bangane ba?" Yayi ajiyar zuciya yace "Ma'ana ina so ki tashi daga Hajir, 'yar gayu, mai ilimi, mai kud'i ki koma Atika bak'auya, marar ilimi, marar kud'i sannan kuma 'yar k'auye sannan Atika 'yar aiki, amma kar ki damu aikin naki bazai dad'e ba, sannan zansa a linka miki albashinki fiye da yadda ake baki." Da mamaki tace "Naji bayaninka, amma zan iya sanin dalili?" Yace "Yawwa, dalili kuwa shine, information nake buk'ata daga wurinki dangane da labarin dana baki jiya, dangane da mutuwar iyaye na. Abinda nake so dake zakije a matsayin 'yar aiki. So aikinki yana buk'atar hak'uri, dauriya, jajircewa, da fatan kin fahimta?" Tace "Na fahimta sir, kuma insha Allah baza'a samu matsala ba. Na farko taimako zanyi, duk da ban ta6a cin karo da aiki irin haka ba, amma na maka alk'awarin zaka same ni mai cika alk'awari. Sannan insha Allah zaka same ni mai hak'uri da kuma dauriya." Yaji dad'i sosai ya cigaba "Alhamdulillah, da farko zan d'an baki wasu kud'i kije kasuwa ki siyo 'yan atamfofi ki kai ayi miki d'inkin 'yan k'auye, sai ayi ta wanke su har su k'ok'e, daman ba masu tsada bane hakan bazaiyi wahala ba. Na biyu idan kin zama ready sai ki sanar dani sai nasa a kaiki inda zaki fara aikin. Na uku duk wani abu da kikaji ya zamanto kin rubuta shi inda hali ma ki mani vnote, ko kiyi duka biyun. Sannan zan siya miki k'aramar waya marar tsada ki saka sabon sim card yadda bawanda ya sanki da layin don kar a samu matsala. Aikinnan Hajir yana buk'atar lura da sa ido, ko wane motsi nata akanki, duk abinda kikaji ki rubuta ki kuma yi recording. Da munsamu muka had'a duk wani information da zamu buk'ata shikenan, sai na fad'a miki yadda za'ayi. Kar kiyi wani abu da zata gane ke ba 'yar k'auye bace, kar ki kuskura ki nuna kin iya turanci, kuma ki mata biyayya duk abinda ta saki kiyi. Shine kawai abinda nake buk'ata a wurinki." Ta saki ajiyar zuciya tace "Tabbas bazan baka kunya ba sir, insha Allah na maka alk'awarin taimaka maka wurin gano abinda kakeson ganowa, yanzu dana tashi daga nan zan wuce kasuwa sai na siyo abubuwan da nake buk'ata, ka bani nan da kwana biyu, zan zo sai ka kaini wurin aikin." Yayi murmushi mai bayyana hak'ora yace "Kai naji dad'i sosai wallahi, Allah ya bada sa'a, zan rik'a turo maki da kati lokaci zuwa lokaci, duk sadda kike buk'atar wani abu sai ki kirani. Ki tafi da babbar wayarki saboda recording d'in sai ya zamana kin 6oye ta yadda baza'a gane ta ba. Sai ki rik'a fiddo k'aramar kina amfani da ita. To make it more successful zaki iya rik'ayin wayar k'arya kamar kina kiran iyayenki kuna gaisawa a can k'auye." Tace "Babu matsala insha Allah." Yace "Yawwa." Nan ya fiddo cheque ya rubuta mata kud'i masu tsoka sannan yayi mata godiya ta tafi. AUREN FANSA 31 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* *_We don't just entertain we touch the heart of readers_* PML 🌹31 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Komai tsab tuni ta kammala, ita da gida sun d'auki haske da k'amshi. Ta dafa masa Chinese rice with vegetable soup, sai salad. Bayan ta gama sai ta fad'a wanka ta kammala ta fito, yau ranar farko data bud'e 6angaren English wears, ta fiddo wani shegen tight wando kalar ash gashi marar tsawo da riga dark pink mai k'aramin hannu. Ta dad'e tana shawarar ta saka su, daga k'arshe dai tayi shahada ta sa duk da tana jin kunya amma dole ta yakice ta wuri d'aya. Bayan ta saka kayan sai ta taje kanta da mayuka masu k'amshi tayi parking d'inshi da pink ribbon daga can tsakiya sai jelar ta sauko bisa gdon bayanta. Tabi da turaruka masu dad'i. Ta gama shiryawa da kusan minti goma idanunta na kan k'ofa har ta gaji da kallo, ta jawo laptop nata da Baba ya siya mata itada Zarah ta soma daddannawa, bata ankara ba sai taji charab an kamo ta. Ta mik'e zumbur cike da tsoro, sai data juyo suka kalli juna yayi murmushi. "Ashe kinada tsoro haka baby?" Ta zum6uro baki abinda ke birgesa tace "A'a ba tsoro naji ba." Yace "Tsoro kika ji mana, bayan na gani da ido na." Tayi dariya tace "Sannu da zuwa." Yace "Yauwa." K'irr! K'arar door bell ta shiga dodon kunnensu, ya dube ta yace "Koma ciki Bala direba ne zai shigo da kaya." Tayi ciki bata k'ara fitowa ba, ta wuce ta had'a masa ruwan wanka, da kanshi ya lek'o yace fito muyi fira. Tayi dariya tace "Kai dai ka shigo ka watsa ruwa kaji dad'i." Yace "Angama baby." Da taimakonta ta zare masa komai, ya shiga toilet, ta fiddo masa singlet da gajeren wando. Yana fitowa kuma yace "Zo ki shafa man mai." Da mamaki kuma ya dubi kansa wanda baisan ya furta hakan ba. Ta sunkuyar da kanta k'asa tace "Uhm bari naje na gyara dinning." Da sauri ta fice inda shi kuma ya cigaba da kallon k'ofar data bi, ajiyar zuciya ya saki ya shirya tsab ya fito. Suna tsakar cin abinci wayarsa ta fara ringing, ganin Jidda yasa gabansa ya fad'i, cikin sanyin jiki ya d'auka sannan ya dubi Meenah data tsare shi da idanu. Yace "He...llo." "Hello ya Faruk a gaskiya fushi nake da kai." Yayi yak'e yace "Menayi?" Tace "Har yanzu ko kazo wurina ko? Daman nasan baka sona." Yace "Ba haka bane zanzo..." "To yaushe?" Ya kalli Meenah har yanzu shi d'in take kallo. Sai ya mik'e sum sum ya shiga kitchen. Zuciyarta ta sosu, ko ba'a fad'a mata ba tasan da mace yake waya. Macen ma wadda zai aura, bata ankara ba hawaye suka zubo mata, jin alamun tafiya yasa tayi saurin goge hawayenta cikin dakewa ta k'ak'alo murmushi tana dubansa a lokacin da yake zama kan kujera. Ya d'an murmusa yana kauda fuska cike da kunya. Sai da suka gama cin abincin ne ya mik'e yana aduba agogon hannunsa. K'arfe 8:44pm. Kallon Meenah yayi yace "Zan fita bazan jima ba zan dawo." Tace "Yanzu? Ina zakaje?" Yayi yak'e yace "Ahh karki damu bawani dad'ewa zanyi ba." Da sauri ya koma ciki ya sake shiri cikin light brown yadi mai matuk'ar taushi, har hular kansa kalar kayan, yayi kyau sosai. Kiss yayi mata a kumatu yace "Sai na dawo baby." Haka tana ji tana gani ya fita, sai k'amshinsa da ya bar mata a hanci, wanda ta tabbatar wurin budurwa zaije. Kuka ya k'wace mata ta yi d'akinta da gudu ta fad'a kan gado. Zuciyarta na tafasa kamar ruwan zafi. *** Tsaye take a gaban madubi ta ci ado na k'in k'ari kai kace zataje tarbar matar gwamna, sanye take da wani french lace kalar ja da adon silver a jikinshi. Wardrobe nata ta bud'e, ta fiddo wani kwalli da turare da wata laya da k'awarta Luby ta bata. "Wallahi idan kikayi amfani da kayannan Jidda kin gama da Faruk, sai yadda kikayi dashi, sannan ba abinda zai sa a gaba sai ganin ya mallake ki a matsayin mata, don haka ki tabbatar kinyi amfani dasu a daren da zai zo. Sannan wannan kuma a abinci zaki barbad'a masa ko lemo da zarar yasha yazo hannu!" Wannan shine maganar da Luby ta fad'a mata a lokacin da tazo ta kawo mata kayayyakin. kwallin ta shafa ta fesa turaren, sai wata laya da akace ta rik'e a hannunta gam kar ta saki har sai ya tafi. Bayan ta kimtsa wayarta ta fara ringing, ganin mai kiran yasa ta saki murmushin mugunta sannan ta d'auka cikin kashe murya tace "Hello my dear." Yace "Gani nan parlon Dada, da mun gama gaisawa zan iso main parlor ki jira ni a can." Tace "Angama honey." Kashe wayar yayi ba tare da ya k'ara magana ba. Dada ne yake shigowa, bayan ya k'araso ya zauna nan suka gaisa. Dada yace "Ya gida ya iyali?" Yace "Alhamdulillah." Dada yace "Tunda nace ka nemi yardar matarka baka k'ara zuwa ba ko?" Yace "A'a Dada wallahi aiki ne yasa ni a gaba, nayi magana da ita ay ta yarda ta amince." Dada yayi murmushi "To kaga ka sauke nauyi, Allah ya tabbatar da alheri." Yace "Amin Dada, yanzu ma wurin Jiddar nazo mu fahimci juna." Yace "Madallah, babu matsala." Daga haka ya mik'e ya fice. A sadda Jidda ta fito Faruk na zaune kan kujerar zaman mutum biyu yana latsa waya, tun kafin ta k'arasa ya k'ura mata ido har ta iso yana kallonta. Ta dube shi sosai ta zauna kusa da kujerarsa don ya shak'i k'amshin sosai tace Sannu da zuwa." A kasalance ya amsa a take yaji wutar sonta na ruruwa a ransa kamar ana kunna ashana. Ta dube shi sai taga ya tsare ta da idanu tace "Yaya Faruk ina wuni ya gida?" Ya kad'a kai tare da lumshe idanu, ji yake kamar ya kamota ya rungume, ita kam sai matsar layar takeyi tare da wani kad'a jiki tana wani fari da ido. Ya sake dubanta sai yaga tayi wani kyau ji yake kamar ba wacce tafita kyau... Ta katse masa tunani da cewa "Bari na kawo maka abin motsa baki." Yace "A'a da kin barshi ma bana jin yunwa." Tayi wani fari da ido tace "Ayi haka? Ay ko ruwa kasha kaida ba bak'o ba?" Sai wani kashe murya takeyi. Yayi murmushi yace "To kawo min ruwan dai ya isa, amma kar ki dad'e don ban gaji da kallonki ba." Tace "To yanzu zan dawo." Ta mik'e cike fa yauk'i da yanga ta tafi, shi kuwa sai binta yake da ido har ta shige kitchen. Ya lumshe idanu kafin ya bud'e jira kawai yake yaga ta fito ko zaiji sanyi a ransa.... MSB💖 AUREN FANSA 32 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) PURE MOMENT OF LIFE WRITERS *_We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_* P.M.L Alhamdulillah duk wani masoyina da ya damu dani nagode sosai Allah ya saka da alkhairi! Naga sak'konnin gaisuwarku na kuma gode da kulawa Allah ya bar zumunci ameen. 😘 Haka masu kirana da turo man sak'ko don jin lafiyata kuma nagode sosai Allah ya bar zumunci.😘😍 Wannan page d'in naku ne members na AUREN FANSA FANS, thank you so much for everything!😍🌹 🌹32 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Duka duka batafi minti ashirin ba ta dawo hannunta d'auke da tray mai d'auke da lemo a cikin glass cup da aka riga aka zuba, gefe kuma kwalin lemon 5alive ne. Tafe take tana faman smiling tana kashe ido, tafiyar ta kuwa kamar tana tsoron taka k'asa, fuskarta cike da fara'a da nishad'i kallo d'aya zakayi mata ka tabbatar da hakan. Da isowarta sai ta rissuna a hankali ta ajiye tire d'in, sannan ta dawo ta zauna a kusa dashi tace "Ya Faruk ga ruwa kasha." Kallonta yake bako kyaftawa zuciyarsa tana ayyana masa abubuwa da dama game da ita. A hankali ta mik'o masa lemo tace "Bismillah." Bai iya mata musu yakeji koda kuwa yaso hakan, don haka sai ya kar6a ya fara kur6a kad'an kad'an, kuma a hakan suna ta6a fira. "Kamar yadda na fad'a ma Dada cewar nazo mu daidaita kanmu to kema haka zan sanar da ke, don haka me zakice game da hakan? Duk da kuwa na dad'e da sanin sirrin da ke ranki shiru kawai nayi, amma duk da haka ina so naji ta bakinki, kin shirya aure na ko kuwa?" A cikin ranta mamaki take yadda tashi d'aya ta sato zuciyarsa a tafin hannunta! Lallai indai kuwa hakane komai zaizo mata da sauk'i tunda har ya kamu da wuri haka. A fili kuwa murmushi tayi tace "To yadda za'ayi ka samu Dada da maganar don maganar tana hannun manya, amma tambayar amsar ka itace, eh na yarda kuma na shirya aurenka ya Faruk." Yayi murmushi "Kina so na kenan?" Ta gyad'a kai cike da farin ciki, yayi murmushi yace "To ba matsala ay, kuma gaskiya bana son aja lokaci mai tsawo, in zan samu ne ma nan da sati biyu yayi min, amma da yake zanyi gyaran inda zaki zauna ana iya sashi nan da wata d'aya." Tace "To duk yadda kace ni yayi min." Da zai tafi ya fiddo kud'i masu tsoka ya bata, yace "Kya sa kati da wannan, sai munyi waya." Ta kar6a tace "Nagode." Sukayi bankwana ta shige d'aki, tana zuwa ta kira Luby, ta kwashe labarin komai ta fad'a mata, ta sanar mata ya bata kud'i masu tsoka. Luby tayi shewa "Duniya sabuwa, kinga a nan kenan kin harbi tsuntsu d'aya da igiya biyu." Jidda tayi dariya tace "A gaskiya nagode Luby bansan ya zanyi ba idan baki ba, kin taimaka min sosai." Luby ta k'yalk'yale da dariya tace "Somin ta6i ne ay, ya Faruk sai ya raina kansa, sai ya dawo kamar zai maki sujjada" Jidda taji dad'i tace "Nagode 'yar uwa sai munyi magana gobe." Sukayi sallama ta kwanta rigingine tana tunanin ranar da zata mallaki Faruk a matsayin mijinta. Koda ya koma gida bai iske Meenah a parlor ba, kuma sai yaji bai wani damu ba, d'akinsa ya wuce kansa tsaye yayi wanka ya kimtsa cikin kayan bacci ya hau gado ya kwanta, sam ya kasa bacci sai tunanin Jidda da ya addabe shi, wayarsa ya d'auko ya kira ta amma har ta tsinke ba'a d'auka ba, ya sake kira a karo na biyu nan ma sai da ta kusa tsinkewa ta d'auka. "Hello ya Faruk..." Ya lumshe idanu kafin ya bud'e, sannan yaja ajiyar zuciya yace "Kar dai har kinyi bacci na tashe ki?" Tayi murmushi "Eh na fara sama sama dai, da fatan ka koma gida lafiya?" Yace "Lafiya lau, gani nan ma har nayi shirin bacci." Ta mik'e da sauri daga kwance da take tace "La ya Faruk kuma shine ka kira ni? Idan amaryarka ta farka taga kana waya dani fa?" Yayi murmushi "Kar ki damu bazata farka ba, besides tama san da maganarmu so kar ki damu." Tayi wani shu'umin murmushi tace "To shikenan ya Faruk sai da safe." Ya 6ata rai "Kar dai har mun gama firar?" Tace "Eh." Yace "Gashi ban gaji da jin muryarki ba." Tayi dariya "La ya Faruk, nima haka, amma bacci nakeji yanzu. Yace "To shikenan sai da safe." Tace "Allah ya kaimu love you." K'itt! Ta kashe bata jira ya bata amsa ba. Ya sagale wayar a kunnensa ya kasa cirewa. Haka ya kwanta da tunaninta har garin Allah ya waye. Kallo d'aya zakayi mata ka tabbatar da tana cikin matsananciyar damuwa, banda idanunta da suka rikid'e suka koma ja alamar rashin bacci da kuma kukan da tayi a daren jiya. Sanye take da wani navy-blue atamfa d'inkin riga da skirt sai wani yalolon gyale data gyala a saman kanta. Kwata kwata yau batada kumari haka take jinta wani iri tunda ta tashi batada walwala. Tsaye take a kitchen tana faman had'a masa kalaci mai rai da lafiya. Sai da ta kammala komai ta jera saman dinning sai ta koma ta kimtsa kitchen d'in. Tana tsakar yi ne taji alamun tafiya, hakan ya dakatar da ita gami da fitowa daga kitchen d'in. Sanye yake da uniform d'in aikinsa wato komai in black tun daga sama har k'asa, ta k'ara dubansa a karo na biyu gami da yin murmushi. Maimakon ya maida mata murtani sai ya fara k'ok'arin gyara zaman belt d'in wandonsa. Hakan ba k'aramin k'ona ranta yayi ba gami da bata mamaki tsantsa. Ta daure tare da had'iye 6acin ranta ta k'araso inda yake tsaye tace "Ina kwana?" Bai motsa ba ya amsa "Lafiya." Ta dai daure tace "Naga kana shirin fita baka karya ba." Sai a sannan ya d'ago yana dubanta amma fuskarsa babu annuri ko kad'an kamar wanda aka aiko ma da sak'on mutuwa. Yace "Azumi nakeyi." Tace "To... wane iri naga yau ba Monday ba kuma ba Thursday ba?" Ya k'ule da tambayarta sai ya kalle ta kad'an yace "Dole sai wannan ranakun Allah ya halasta azumi? Mutum yana iya yi ko yaushe don samun lada." Ta k'ak'alo murmushi tace "Haka ne kam, Allah ya bada lada." Yace "Amin, ni zan wuce sai dare zan dawo yau." Tace "To a ina zaka sha ruwa?" Yace "Zan siya abinci, don yau aikin da ke gabana da yawa da k'yar zan samu dawowa wannan lokacin yau." Tace "To." Har yayi hanyar waje sai kuma ya dakata tare da karkatowa kad'an yace "Gobe za'a fara gyaran gida, za'a k'ara fasa d'aki da parlor da kitchen daga can baya." Bata tanka ba don ta gane inda maganar ta dosa, shi kuwa gogan daga haka kawai sai yasa kai ya fice don shi ko ganinta bai son yi yau, Jidda kawai yake tunani. Yana fita ta fashe da kuka mai tsanani don ko maganar auren da ya tarkato bata d'aga mata hankali irin yau da taga yadda ya chanza mata. *** Yana office yana shirin fita don an kirasa wai akwai wani kisa da akayi a wani gida, zasu je bincike. Yana tsakar tattara mahimman abubuwan da zai buk'ata aka shigo da sallama. Ya amsa tare da bada izinin shigowa, sai dai a yadda ya tsaya yana kallonta cike da mamakin sauyawar da tayi kamar ba Hajir ba, gaba d'aya ta zama bak'auya sak! Sanye take da wani tsanwar atamfa ta k'ok'e sosai, d'inkin k'auyawa riga da skirt, sai d'ankwalin daban, fuskarta harda d'ige d'igen kwalliya. Hakan ba k'aramin dariya ta basa ba. Sai da yayi mai isarsa sannan ya dakata yana kallonta yana tafa hannu. "Bravo! Lallai kinyi k'okari Hajir, aww na manta Atika ashe. Aikinki yayi kyau, are you ready?" Tace "Yes sir." Yace "Good, d'auko kayanki inada wani aikin da zamuje muyi yanzu, amma ina iya kaiki gidana da zarar na dawo sai mu kaiki gidan da zaki zauna." Tace "Haka ma yayi sir." Kayanta ta d'auko dake cikin ghana most go tabi bayansa. Da sallama suka shiga, tana zaune a parlor tana karatun wani novel, ganin Faruk ya shigo yasa ta dakata gami da amsa sallamar tasa. Tare suka shigo da Hajir, bayan sun zauna Faruk ya soma magana. "Meenah wannan 'yar aikin da kika ce a samo miki ce, sunanta Atika, yanzu ina sauri zan koma aiki, so zan barta nan sai na dawo sai mu kaita ko?" Taji dad'i sosai suka gaisa da Hajir a mutunce sannan tace masa. "Ay naji kace yau zakayi dare a wurin aiki, why not ka bari na kaita da kaina ko ya ka gani?" Ya mak'e kafad'a alamun oho yace "Hakane tunda kin iya mota ki d'auki d'aya daga cikin nawa sai ki kaita, ni zan koma." Ta masa a dawo lafiya ya fice. Meenah ta kalli Hajir tace "Don Allah ki tashi daga k'asa ki koma kan kujera." Hajir ta koma kan kujera tana ta faman murmushi. Meenah tayi murmushi tace "Ko kefa, bari na k'arasa abincin rana kici sai na kaiki ko?" Hajir tace "To nagode." Meenah tayi murmushi ta mik'e ta shiga kitchen. BELLO ‹ › Home View web version Monday, 7 August 2017 Maryam Saidu at 08:23 AUREN FANSA 33 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) PURE MOMENT OF LIFE WRITERS _We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_ P.M.L Kuyi sorry Fans muna fama da matsalar rashin wuta🤗 🌹33 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Bayan ta kammala abincin suka ci sai ta zarce zuwa gida don kai ta, Bilki bata zargi komai ba sai ma murnar samun mai taya ta aiki dama Zarah keyi to zata fara zuwa makaranta ga bikinta da za'a sanya. Nan aka gabatar mata da ayyukan da zata rik'a yi tun daga su shara, wanki, wanke-wanke, girki da sauransu. Kafin ta tafi sai da shiga wurin Baba da ke zaune parlor yana kallon news, ganin Meenah ta shigo ya sanya yayi murmushi, ya bita da kallon k'urilla a lokacin da take zama kan carpet. "Baba ina wuni?" Ya gyara zamansa yana kallonta yace "Lafiya lau Amina, ya gida ya kuma mai gidan naki?" Tace "Duk lafiya lau Baba yana wurin aiki." Yace "Madallah, naji zancen zai k'ara aure hakane?" Ta had'iye miyau mai d'aci tace "Hakane Baba." Yace "Kinsan komai muk'addari ne daga Allah Amina, kar ki d'aga hankalinki ki jure, ki zamo mace mai hak'uri da biyayya kinji? Allah ya za6a maku mafi alkhairi, ya bada zaman lafiya." Tace "Amin Baba nagode, daman zan wuce gida yanzu." Yace "To ki gaida mijin naki, da fatan baki buk'atar wani abu?" Tace "A'a Baba." Yace "Kuma zaku tafi jami'ah, ku kula sosai, karatu kukaje yi shi zakuyi Allah ya taimaka." Tace "Insha Allah Baba, amin." Sukayi sallama ta tafi gida. K'arfe goma saura ya shigo gidan, tana zaune tana karatun alk'ur'ani, daga bakin k'ofa yaja ya tsaya yana sauraron muryarta tana karanta suratul Mujadala, yayi tsaye shi bai shigo ba haka ma shi bai fita ba, take kuma ya tsinci kansa cikin nutsuwa don karatun yana masa dad'i. Sai data kai aya sannan ya shigo, ganinshi ya sanya tayi saurin mik'ewa ta isa garesa gami da amsar brief case d'insa, tayi murmushin da bai kai zuci ba tace "Sannu da zuwa." "Yawwa." Kawai yace ya wuce zuwa ciki, ranta ya sosu ta dai daure ta bishi ciki a lokacin data shiga taji alamun watsa ruwa. Sai kawai ta fito ta zauna parlor tana kallo abinta. Shiru bai fito ba har kusan sha d'aya ta wuce, ga ita kuma tana kunyar binshi d'aki yanzu kada ya fassara ta, sai kawai ta mik'e ta tattara abincin tasa fridge ta wuce d'akinta. Gaba d'aya ta kasa bacci sai uban tunani, ko a mafarki akace mata Faruk zai mata haka bazata yarda ba. Ganin hakan bashi ne mafita ba ya zama tilas ta kai kukanta ga Allah don shine zai share mata, toilet ta fad'a ta d'auro alwalla ta fara sallah tana kai kukanta ga Allah. Tana wurin har akayi sallar asuba, hakan yasa tana gama sallah kanta ya fara yi mata barazanar ciwo, ta lalla6a ta kwanta ba'a d'au lokaci ba bacci yayi awon gaba da ita. Cikin baccin ne taji kamar ana ta 6arar da abubuwa, a gigice ta farka tana salati, duba lokaci tayi k'arfe 11:41am lallai tasha bacci. Hijabinta ta d'auko ta sauko daga gadon, tana lek'owa taga mutane maza suna ta aiki a gidan, gabanta ya yanke ya fad'i, maganar Faruk ta dawo mata a cikin kanta. "Gobe za'a fara gyaran gida, za'a k'ara fasa d'aki da parlor da kitchen daga can baya." Dafe kanta tayi da ke juya mata sannan ta fara bin bango ji take kamar zuciyarta zata fad'o k'asa. Note ta gani a bisa drawer d'inta hannunta na kyarma ta d'auko ta warware ta ta soma karantawa... "Na tafi office, kamar jiya yau ma azumi nakeyi kar ki wahalar da kanki yin wani girki sai dare zan dawo, idan masu aikin nan sun gama da na yau ki shiga d'akina ki d'auko 5k ki basu zan kirasu na masu bayani." Wani k'ululun bak'in ciki ne ya tokare mata mak'oshi, ta daure tayi ta maza ta maida note d'in ta ajiye a inda ta d'auka, ta rasa dalilinsa na shan ruwa a waje, at least ko bai dawo da wuri ba ay ya kamata ya ci abincin data girka masa komai dare, amma ta lura kamar baya son cin abincin ne gaba d'aya a nan. Da k'yar ta sha ruwan tea ta koma d'aki ta kwanta, k'arar aikin gidan ne ya ishe ta shi yasanya ta kasa baccin kirki. Allah ya taimake ta Zarah tazo zasuje makaranta registration, tayi ta murna ta kirasa don shaida masa amma bai d'aga ba sai kawai ta aika masa da sak'o. Cikin sa'a kuwa suka kammala komai suka dawo gida, Zarah tsabar haushin gyaran inda kishiyar yayarta zata zauna yasa ko gidan bata iya shiga, daga waje sukayi bankwana ta tafi gida. Yanda ya umarce ta hakan tayi don kuwa k'arfe shiddan yamma suka gama, ta shiga ta d'auko masu kud'in ta basu suka tafi. Haka kullum sai sun zo da safe su gama k'arfe shidda, da yake ana sakin kud'i sai gashi ginin har ya mik'a sosai. A zamantakewar auren Meenah kuwa babu abinda ya chanza gaba d'aya Faruk ya chanza mata kamar bashi ba, bai damu da ita ba bare cinta, shanta da kuma lafiyarta. Abincinta ma baya ci ko tayi masa, tun yana bata excuse har ya fara fitowa 6aro 6aro yana ce mata bazai ci ba. Ga abu kad'an fad'a da masifa, nan da nan sai ya hau fad'a ba dalili. Nan kuwa yana can ya tare wurin Jidda, wani lokacin can yake da anyi sallar isha'i har goman dare. Kuma komai ta bashi ci yakeyi, gaba d'aya ya sussuce ya rikice. Hakan yasa aka sanya bikin sati uku masu zuwa, don ya kusa kammala aikin gidansa saura kad'an ya rage, haka aka tattara aka sanya bikin aka had'a dana su Zarah da Nabeel. Shi kuma ya cigaba da had'a lefe da kuma akwati biyu na kayan fad'ar kishiya da zai kai ma Meenah. AUREN FANSA 34 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) PURE MOMENT OF LIFE WRITERS _We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_ P.M.L 🌹34 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Meenah kuwa duk wani abu bazata fasa yi masa ba, har girki sai tayi koda kuwa bazaici ba, ga tana k'ok'ari wajen ganin ta kai zuciyarta nesa don gudun fitina, sauk'inta ma yanzu shiryen- shiryen bikin Zarah ya fara kankama hakan yasa ta rage yawan shiga damuwa, don kuwa tana gida kuma bata cika dawowa ba sai yamma. Karo na farko da ta fara shiga gidan Aneesha tunda sukayi aure, bayan ta shirya cikin green d'in material d'inkin doguwar riga sai ta gyala gyale marar kauri sosai. Da sallama da shiga gidan, Aneesah na kitchen tana fama da girki taji sallama ta lek'o, murmushi tayi tace "Bismillah shigo." Bayan ta zauna Aneesah ta shiga kawo mata lemo da kayan motsa baki, yau duk kunya ta kama Aneesah ganin itace k'arama kuma ko sau d'aya bata shiga gidan ba. Meenah tayi murmushi tace "Baki gane ni ba ko?" Aneesah tace "Nagane ki mana, matar ya Faruk ce nasanki." Meenah tace "Allah sarki ya gida?" Tace "Lafiya lau." Shiru ya biyo ba, na 'yan mintina sai suka kafa ma tv ido ana wani film. Meenah ta katse shirun ta hanyar mik'a mata kati "Daman Iv na kawo maki na bikin sister d'ina." Aneesah tayi murmushi tace "Allah sarki, Allah yasa alkhairi yasa munada rabon gani." Tace "Amin ni zan koma." Aneesah tace "Haba tun yanzu? Na d'auka sai kin ci abinci tukunna." Meenah tace "Kai haba, bamuda nisa ta yaya zan cinye ma amarya girkin angonta?" Aneesah tayi murmushi cike da kunya tace "Kai a'a wallahi ba haka bane." Meenah tayi dariya tace "Kedai wasa nake miki, idan na dawo next time zanci insha Allah." Aneesah tace "To ina zuwa." Ta mik'e ta shiga ciki, can ta dawo hannunta d'auke da leda tana murmushi tace "To ga wannan." Meenah tace "La harda wahala haka?" Aneesah tace "Ba wata wahala wallahi." Meenah tace "To nagode ni zan tafi." Aneesah tace "Nima zan shigo, ay kina WhatsApp ko?" Tace "Eh inayi." Aneesah tace "Zamu rik'a gaisawa insha Allah, nagode sosai wallahi." Meenahtace "Babu komai wallahi." Sukayi bankwana ta tafi, tunda Meenah ta tafi Aneesah ke raya kyawunta da kirkinta, sai taji haushin kanta da meyasa bata ta6a shiga sun gaisa ba, amma ta k'udiri a ranta zasu fara zumunci daga yau. **** Meenah sun soma lectures, yanzu damuwarta ta ragu sosai, kuma tayi sa'a yana bata mota idan zata tafi. Ranar litinin da daddare sai ga Faruk ya shigo da akwatina guda biyu, tunda Meenah ta ganshi tasan na menene, don haka bata nuna damuwarta ba ko kad'an, sai ma fatan alkhairi da tayi masa. Hakan ba k'aramin mamaki ta basa ba, kuma sai ta bashi tausayi, nan ta bubbud'e akwatina ta gani bayan ta gama ta tashi ta shiga ciki. Ya dad'e zaune ranar farko da ya ji auren ya fita a ranshi kuma. Mik'ewa yayi cikin sanyin jiki ya bita ciki, tana kwance a d'aki tayi ruf da ciki idanunta a lumshe, hakan ya k'ara bayyanar da zara zaran eye lashes nata. Ya dad'e tsaye yana kallonta kafin ya tako a hankali yatsaya yana k'are mata kallo. Sanye take da 'yar k'aramar vest pink color sai tasa pink dogon wando, harta ribbon d'in kanta pink ne, daga gani ba bacci take ba amma kuma tak'i bud'e idanunta. "Meenah..." Ta bud'e idanunta a hankali ta sauke bisa fuskarsa da yake kallonta kafin ta amsa da "Na'am." Sai kuma ya rasa abin cewa, ya sosa kai yace "Dama zuwa nayi naji ko kina lafiya." A ranta tace "Sabon salo sai kace damuwa yayi da ni bare kuma lafiyata." A fili kuwa cewa tayi "Lafiya lau." Shi yadda take sharesa d'innan yaji ba dad'i, yayi missing kula da shi da takeyi, amma yanzu ko kallonsa bata son yi, magana ma da k'yar take amsa masa. Da yanzu ta tambeyesa ko yana buk'atar wani abu, amma yanzu ta daina. "Ko kana buk'atar wani abu ne?" Yayi sauri yace "A'a, sai da safe." Tace "Allah ya kaimu." Ta rufe idanunta alamun bacci, ya dad'e tsaye yana kallonta kafin ya fita daga d'akin a sanyaye. Yana shiga d'akinsa ya iske miss calls ba iyaka daga Jidda, kiranta yayi bugu d'aya ta d'auka. "Haba my dear ina ka shiga inata kiranka?" Yace "Sorry na shiga wanka ne." Yace "Ok daman kud'in da zan siya anko ne na 'yan mata baka bada ba..." Yace "Kud'in anko kuma?" Tace "Eh da kud'in k'unshi." Yace "To fah har nawa?" Tace "Gaba d'aya dubu 500 ne!" Yace "What? Dubu 500? Gaskiyar magana ko banida su, bazan iya baki dubu 500 ba." Tace "Haba mana my dear, wai nan fa na maka sauk'i." Yace "Dubu 100 zan baki, idan baki so good and fine." Tace "Wai wannan fad'an na menene daga tambayarka kud'i?" Yace "Jiya jiya kika tambayeni dubu 200 na baki, shekaranjiya dubi 50, yanzu kuma dubu 500, to banida su." "Don Allah kayi hak'uri ka bani, daga yau bazan k'ara tambayarka wasu kud'in ba." A fusace yace "Ke kar ki raina min hankali fa! Na riga nace bazan baki ba, don haka sai da safe." K'it ya kashe wayar, cike da jin haushinta, gaba d'aya haushinta yakeji. Yau ko baccin kirki ya kasa, haka yasa ya mik'e ya lek'a d'akin Meenah tana kwance tana bacci peacefully, ta masa kyau sosai, sai dai dole ya koma d'akinsa ya kwanta amma ina ya kasa bacci, sai gabansa dake ta fad'uwa ya rasa dalili. Washe gari sai ga 'yan jere, nan sukayi ta hidimarsu ita kuma Meenah ko fitowa ma batayi ba, tana d'aki tana jinsu suna ta aikin jerensu, har dare suna nan basu gama ba, har washe gari sai da suka dawo da safe suka k'arasa wanda basu idasa ba. Itama Meenah jeren Zarah suka tafi the next day, hakan ba k'aramin dad'i yayi mata ba. Biki nata matsowa yau saura kwana biyu a d'aura aure.... AUREN FANSA 35 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) PURE MOMENT OF LIFE WRITERS _We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_ P.M.L 🌹35 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Washe gari aka kai lefen Zarah akwati bakwai da kit, yayinda aka kai ma Jidda akwati takwas da kit. An fara gudanar da shagalin biki a wadace, sai dai matsalar Jidda d'aya da ta masa maganar kud'i sai sunyi fad'a, sannan idan har suna tare yana nuna mata so da k'auna marar iyaka amma da zarar sun rabu shikenan ko kiranta baiyi sai dai ita ta kirasa. Hankalinta ya fara tashi haka kuma ta soma tunanin ko maganin ya fara dena aiki ne? Ranar da akeyin event d'in Jidda anyi kwalliya ta gogaggun 'yan matan nan, ta had'u har ta gaji duk da ba wani kyau gareta na azo a gani ba. 'Yan matanta kansu da ka kallesu kaga gagaggun 'yan mata masu ji da kansu, Luby best friend d'in amarya ita nata ashobin ya banbanta da na sauran ya kuma fi tsada da kyau. Suma kuwa su Zarah na can suna shan tasu hidimar, da yake bazasuyi abubuwa da yawa ba, kuma bikin nasu yafi tsari da kyau. K'arfe biyar da rabi Faruk ya iso ya kira wayar Jidda, can sai ga ta fito itada k'awayenta su da yawa kamar wata tawaga. Bayan sun iso aka fara gabatar da events cike da kwanciyar hankalin, Luby ita ta fara bud'e wurin da rawa yadda kasan ba kowa wurin haka take tik'ar rawa ba ko kunya. An gayyato amarya da ango don taka rawa, shi kam ango kunya ta hana shi rawa sosai ba, ita kuwa amarya bako kunya sai wani rausaya takeyi kamar ba amarya ba. Faruk sai yanzu yake k'ara gane halin Jidda, bai ta6a tunanin haka take ba. Sai yanzu ya fara tunanin aurensu shida Meenah komai cikin tsari haka akayi shi. K'arfe sha d'aya aka tashi taron, ya ajiye Jidda gida shima ya nufi nasa gidan. Washe gari ya tashi yana ta hidimar d'aurin aure. K'arfe biyu daidai dubban mutane suka shaida auren Jidda da Faruk sai Zarah da Khaleel. Dad'i Meenah takeji Zarah kusa da su za'a kawo ta, bayan an gama aka zarce 'yar walima da Faruk ya had'a masu. **** Tana zaune kan gado taji ana maganar an d'aura aure, haba kanta ya k'ara girma ji take kamar a mafarki, mutumin da take ganin shine class d'inta yau ta malleke shi a matsayin miji, wani murmushi tayi tare da lumshe idanu, Luby ta daka mata duka a baya tace "Banza keda wa kike murmushi ke kad'ai?" Ta dube ta tace "Ina tunani gami da yin mamaki wai yau nice na zama matar ya Faruk ya zama mallakina fa kenan?" Luby tace "Ke ni ba wannan ba, kinsan mutumin nan yana da mata, kuma kinsan yadda yake k'aunar ta kawai suddabarunki ne yake aiki, baki gudun maganin ya bar aiki mu shiga uku mu lalace? Ke nifa na fara ji miki tsoro kar ya wulak'anta ki, sannan yasan babu, baki gudun labari yasha banbam?" Ras ras! Gabanta ya yanke ya fad'i tace "Haka ne fa, ko da yake ay kin min tanadi mai kyau kar kiji komai." Luby tace "Keni sheyasa nake son auren yaro wanda baisan dawon garin ba, amma masu mata ay sun san komai." Haka aka cigaba da shagalin biki, jikin Jidda yayi mugun sanyi saboda gudun abinda zaije ya dawo tsakaninta da angonta. K'arfe tara da rabi motoci suka soma layi a k'ofar gidan su amarya, bayan fad'a da nasihohi daga Mama da Dada har Faruk sai da yasha fad'a sosai da nasiha. Uwar gida kan gida Meenah tana zaune a d'akinta ta ci ado tsayawa fad'ar kwalliyarta ma 6ata baki ne. Gud'a ta matan da suka rako amarya itace ta fara yo sallama, Meenah ta danne kishinta sosai ta k'ak'alo murmushin dole, amarya tana rik'e a hannun wata mata. Kansu tsaye d'akin amarya suka nufa, 'yan kawo amarya, k'ofa ce kawai zatayi linking d'inka zuwa d'ayan 6angaren na sashen Jidda. Masu kawo amarya suka shiga zagaye gidan don kashe kwarkwartar ido. Suka gama kallon komai sukayi niyyar tafiya gida. Washe gari akayi walima k'arfe biyar na yamma Hajiya Lami ta rik'o hannun Jidda ta nufi parlon Meenah, sukayi sallama Meenah ta amsa. Hajiya Lami ta ce "To ga amarya nan don Allah ku had'a kanku ku zauna lafiya, yanzu an bar haukan kishin nan zaman lafiya shi kowa ke buk'ata. Tayi murmushi "To Allah ya taya mu rik'o." Suka tashi suka maida amarya d'akinta bayan iyayen sun kama gabansu, d'akin ya rage daga amarya sai 'yan matanta wad'anda ke zaman jiran ango. Luby tace "Kar fa kiganta kamar mutuniyar kirki ki raga mata, idan tace miki kul ki ce mata cas cas! Kinji na fad'a miki." Nan sukayi ta zuga ta har akayi isha'i. K'arfe takwas, tara, goma, shiru ba ango ba alamunshi, har dai sha d'aya ta wuce Luby tace "Nidai zan tafi gida na gaji da jiran ango." Haka suka tarkata suka tafi, Sai dai ta dinga binsu da ido don batada bakin magana da kuma tana son jin dalilin rashin zuwan ango duk da tanadin da tayi masa, haushi kamar zai kashe ta. "Kar dai yana wurin waccan tsinanniyar?" Gabanta ya fad'i, ta hau sak'e sak'e, tayi ta kiransa yana rejecting, daga k'arshe ya tura mata sak'o kamar haka: "Kiyi hak'uri ki bar kirana yau bazan shigo wurinki ba." Ta rud'e ta gigice gashi maganin idan aka wuce yau shikenan ya kare! Ta hau salati tana cigaba da kiransa amma ina sai ma ta kira taji ta a kashe. Safa da marwa takeyi daga k'ofa zuwa gado, tana tunainin mafita a gareta, don akwai had'ari muddin ango baizo gareta ba a daren yau ba! AUREN FANSA 36 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) PURE MOMENT OF LIFE WRITERS _We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_ P.M.L 🌹35 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Washe gari aka kai lefen Zarah akwati bakwai da kit, yayinda aka kai ma Jidda akwati takwas da kit. An fara gudanar da shagalin biki a wadace, sai dai matsalar Jidda d'aya da ta masa maganar kud'i sai sunyi fad'a, sannan idan har suna tare yana nuna mata so da k'auna marar iyaka amma da zarar sun rabu shikenan ko kiranta baiyi sai dai ita ta kirasa. Hankalinta ya fara tashi haka kuma ta soma tunanin ko maganin ya fara dena aiki ne? Ranar da akeyin event d'in Jidda anyi kwalliya ta gogaggun 'yan matan nan, ta had'u har ta gaji duk da ba wani kyau gareta na azo a gani ba. 'Yan matanta kansu da ka kallesu kaga gagaggun 'yan mata masu ji da kansu, Luby best friend d'in amarya ita nata ashobin ya banbanta da na sauran ya kuma fi tsada da kyau. Suma kuwa su Zarah na can suna shan tasu hidimar, da yake bazasuyi abubuwa da yawa ba, kuma bikin nasu yafi tsari da kyau. K'arfe biyar da rabi Faruk ya iso ya kira wayar Jidda, can sai ga ta fito itada k'awayenta su da yawa kamar wata tawaga. Bayan sun iso aka fara gabatar da events cike da kwanciyar hankalin, Luby ita ta fara bud'e wurin da rawa yadda kasan ba kowa wurin haka take tik'ar rawa ba ko kunya. An gayyato amarya da ango don taka rawa, shi kam ango kunya ta hana shi rawa sosai ba, ita kuwa amarya bako kunya sai wani rausaya takeyi kamar ba amarya ba. Faruk sai yanzu yake k'ara gane halin Jidda, bai ta6a tunanin haka take ba. Sai yanzu ya fara tunanin aurensu shida Meenah komai cikin tsari haka akayi shi. K'arfe sha d'aya aka tashi taron, ya ajiye Jidda gida shima ya nufi nasa gidan. Washe gari ya tashi yana ta hidimar d'aurin aure. K'arfe biyu daidai dubban mutane suka shaida auren Jidda da Faruk sai Zarah da Khaleel. Dad'i Meenah takeji Zarah kusa da su za'a kawo ta, bayan an gama aka zarce 'yar walima da Faruk ya had'a masu. **** Tana zaune kan gado taji ana maganar an d'aura aure, haba kanta ya k'ara girma ji take kamar a mafarki, mutumin da take ganin shine class d'inta yau ta malleke shi a matsayin miji, wani murmushi tayi tare da lumshe idanu, Luby ta daka mata duka a baya tace "Banza keda wa kike murmushi ke kad'ai?" Ta dube ta tace "Ina tunani gami da yin mamaki wai yau nice na zama matar ya Faruk ya zama mallakina fa kenan?" Luby tace "Ke ni ba wannan ba, kinsan mutumin nan yana da mata, kuma kinsan yadda yake k'aunar ta kawai suddabarunki ne yake aiki, baki gudun maganin ya bar aiki mu shiga uku mu lalace? Ke nifa na fara ji miki tsoro kar ya wulak'anta ki, sannan yasan babu, baki gudun labari yasha banbam?" Ras ras! Gabanta ya yanke ya fad'i tace "Haka ne fa, ko da yake ay kin min tanadi mai kyau kar kiji komai." Luby tace "Keni sheyasa nake son auren yaro wanda baisan dawon garin ba, amma masu mata ay sun san komai." Haka aka cigaba da shagalin biki, jikin Jidda yayi mugun sanyi saboda gudun abinda zaije ya dawo tsakaninta da angonta. K'arfe tara da rabi motoci suka soma layi a k'ofar gidan su amarya, bayan fad'a da nasihohi daga Mama da Dada har Faruk sai da yasha fad'a sosai da nasiha. Uwar gida kan gida Meenah tana zaune a d'akinta ta ci ado tsayawa fad'ar kwalliyarta ma 6ata baki ne. Gud'a ta matan da suka rako amarya itace ta fara yo sallama, Meenah ta danne kishinta sosai ta k'ak'alo murmushin dole, amarya tana rik'e a hannun wata mata. Kansu tsaye d'akin amarya suka nufa, 'yan kawo amarya, k'ofa ce kawai zatayi linking d'inka zuwa d'ayan 6angaren na sashen Jidda. Masu kawo amarya suka shiga zagaye gidan don kashe kwarkwartar ido. Suka gama kallon komai sukayi niyyar tafiya gida. Washe gari akayi walima k'arfe biyar na yamma Hajiya Lami ta rik'o hannun Jidda ta nufi parlon Meenah, sukayi sallama Meenah ta amsa. Hajiya Lami ta ce "To ga amarya nan don Allah ku had'a kanku ku zauna lafiya, yanzu an bar haukan kishin nan zaman lafiya shi kowa ke buk'ata. Tayi murmushi "To Allah ya taya mu rik'o." Suka tashi suka maida amarya d'akinta bayan iyayen sun kama gabansu, d'akin ya rage daga amarya sai 'yan matanta wad'anda ke zaman jiran ango. Luby tace "Kar fa kiganta kamar mutuniyar kirki ki raga mata, idan tace miki kul ki ce mata cas cas! Kinji na fad'a miki." Nan sukayi ta zuga ta har akayi isha'i. K'arfe takwas, tara, goma, shiru ba ango ba alamunshi, har dai sha d'aya ta wuce Luby tace "Nidai zan tafi gida na gaji da jiran ango." Haka suka tarkata suka tafi, Sai dai ta dinga binsu da ido don batada bakin magana da kuma tana son jin dalilin rashin zuwan ango duk da tanadin da tayi masa, haushi kamar zai kashe ta. "Kar dai yana wurin waccan tsinanniyar?" Gabanta ya fad'i, ta hau sak'e sak'e, tayi ta kiransa yana rejecting, daga k'arshe ya tura mata sak'o kamar haka: "Kiyi hak'uri ki bar kirana yau bazan shigo wurinki ba." Ta rud'e ta gigice gashi maganin idan aka wuce yau shikenan ya kare! Ta hau salati tana cigaba da kiransa amma ina sai ma ta kira taji ta a kashe. Safa da marwa takeyi daga k'ofa zuwa gado, tana tunainin mafita a gareta, don akwai had'ari muddin ango baizo gareta ba a daren yau ba! Maryam Saidu at 06:16 AUREN FANSA 37 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) PURE MOMENT OF LIFE WRITERS _We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_ P.M.L 🌹37 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com A zuciye ta shige ko gabanta bata gani sosai, tana shiga suka d'ago suka dube ta sai sukayi ido hud'u da Faruk, wani tsananta ya sake dira a zuciyansa ga wani zafi yana ji a k'irjinsa, yanzu a yadda yakeji baya jin son wata 'ya mace a duniya in ba Meenah ba, ya kalli inda Jiddar ke tsaye da rik'ak'en k'ugu tana kad'a jiki kamar wata mazari. Wayancewa yayi ya jefo mata tambayar rainin hankali "Jidda ya gida?" Ta yamutsa fuska gami da yin fari da ido tace "Lafiya." Yayi murmushi kad'an yace "Kina son wani abu ne? As you can see I am busy here." Tambayar ta bata haushi sosai ta kuma 6ata mata rai ainun, ta dube shi tace "Inada buk'atarka ko ka manta matsayinka gareni?" Yace "A'a ina sane, kije zanzo muyi maganar." Ta cika tayi fam tace "Babu inda zanje, wai shin ya Faruk wane irin aure mukayi? Na k'iyayya ko na soyayya?" Yace "Bafa haka bane, nace ki dai je zanzo, idan kuma kina da buk'atar wani abu ki fad'a min." Tayi shiru tana tunani, ta dubi Meenah da ke tsaye kamar abin bai dame ta ba, sai tayi mamakinta sosai, ta d'auka Meenah macece mai sauk'in kai har ma tayi tunanin zatasa baki a cikin maganar ko don ta taimaka mata, to me hakan ke nufi? Kawai sai Jidda ta fita da gudu daga d'akin tana dana sanin zuwan da tayi da kuma zubar da class d'inta da take da shi a gaban kishiya da kuma mijin da bai damu da ita ba. Sai dai ta k'udiri gana ma Meenah wuta, har sai ta gane matsayinta a gidan, a shirye take don ganin hakan ta faru kuma sai ta fi kowa farin cikin ganin hawayenta! Washe gari da safe Meenah na kitchen tana had'a kalacin safe Jidda na la6e tana jiran ta gama don ta san abinda ta shirya mata! Sai da Meenah ta kammala abincinta soyen dankali ne da sauce d'in k'wai, ta zuba ma Faruk nasa a plate da na kowa sai ta koma d'akinsa don sanar masa ya fito ya ci abinci. Tana ganin ta shige sai ta fito cikin sand'a ta bud'e abincin Faruk ta zazzaga ma sauce d'in uban yaji sannan ta zazzaga ma dankalin gishiri mai yawa. Tafiya taji ya sanya ta koma d'akinta a guje tana dariyar mugunta don yau zatayi kallon fad'an da Faruk zaiyi ma Meenah. Sai murna takeyi. Meenah ta shigo d'akinta ta kalle ta tace "Ki fito kici abinci ko." Tayi 'yar dariya tace "Yanzu kuwa." Da d'an tsalle tsalle ta fito daga d'akin sannan kuma ta nutsu tabi bayan Meenah. Kowa ya nutsu kan dinning zasu fara cin abinci, Faruk ne zai fara cin abinci har ya fara d'ebo dankalin kawai kwatsam Meenah ta lura da d'igen d'igen yaji a gefen plate d'insa sannan ga abincin ya chanza kala ya zama jawur, take ta fara tunanin yadda akayi hakan ta faru, sai ta kai dubanta ga Jidda yanayinta kad'ai ya isa ya tabbatar ba wanda ya aikatan hakan sai ita. Cikin dabara ta kwa6ar da lemon da ke cikin cup a gaban faruk, hakan ya dakatar da shi daga cin abincin da zaiyi wanda saura k'iris ya kai bakinsa. "Subhanalillah garin yaya hakan ta faru?" Meenah ta mik'e da sauri tana cewa "Kayi hak'uri wallahi ban lura ba, bari na goge." Cikin dabara ta janye abincin Faruk ta matsar kusa da abincin Jidda ta shiga kitchen ta d'auko tsumma ta soma gogewa, ta faki idon Jidda ta sauya abincin dana Faruk sai ta tura na Jidda a gaban Faruk da sauri. Bayan ta gama ta dawo ta zauna tace "Sorry please, kaci abincin mana." Yace "Ay da kin bari sai da aka gama kika goge." Tace "Hakan yayi ay kaga yanzu sai aci abincin cikin kwanciyar hankali." Ya d'ebi abincin ya kai bakinsa, Jidda nata kallonsa tana dariyar mugunta sai dai me? Bata ga komai ba sa6anin abinda tayi tsammani, ta shiga rud'ani, ta kalli plate d'inta sai taga na Faruk ne aka chanza mata, ta kai dubanta ga Meenah taga tana mata kallon irin ya kika ga nayi k'ok'ari ko? Meenah ta k'ura mata ido tana murmushi, Faruk ya d'ago ya dubi Jidda yace "Ya naga bakya cin abincin ne? Kici mana yayi dad'i." Meenah tayi murmushin mugunta tace "Eh kici abinci Jidda, yayi dad'i sosai." Ta fad'i haka har yanzu bata bar murmushin ba, ba yadda ta iya haka ta d'ebo ta kai spoon a bakinta, take taji wani irin yaji da gishiri ya had'an mata, ta dinga taunawa da k'yar tana hawaye tana gogewa don kar a gane. Faruk ya kammala cin abincinsa ya mik'e yana fad'in "Zan tafi aiki, sai na dawo." Meenah tayi murmushi tace "Sai ka dawo, amma bari na gyara maka zaman rigarka." Yayi murmushi yace "To." Ta gyara masa sannan ta fita raka sa bakin mota, suna fita Jidda tayi toilet da gudu tana faman tari da kakarin amai, sai da ta d'auki lokaci mai tsawo tana wanke bakinta sannan ta fito tana faman goge bakinta da har yanzu bai bar mata yaji ba. Kaci6us tayi da Meenah a bakin k'ofa ta hard'e hannayenta duka biyun tana murmushi. Ganinta yasa ta d'an dafa ta tace "Meyafaru?" Jidda ta kwa6e mata hannu cike da masifa tace "Muguwa! Azzaluma kawai." Dariya ta su6uce mata tace "Muguntar me nayi? Sannan kuma zalunci me nayi?" Jidda ta dalla mata harara sannan tace "Wallahi kin bani mamaki Meenah, nayi tunanin ke macece mai sauk'in kai ashe ba haka bane? Ashe haka kike?" Meenah ta dawo tana fuskantarta ido cikin ido da hannayenta a hard'e sannan tace "K'warai ina da sauk'in kai idan aka bini ta sauk'in kai, sannan kuma ina da wuyar sha'ani idan aka bini bata lalama ba, Jidda kar kiyi tunanin kina ganina kamar bansan abinda nakeyi ba, to da hankalina sannan kallonki nake tar! Nasan ke wacece sannan nasan wane irin zama ya kawo ki, a dah nayi niyyar muyi zaman lafiya dake, amma tunda na gano sirrinki da kuma k'udirinki na son rabani da Faruk na sake taku. Wallahi baki isa ba, kinyi kad'an kice zaki rabani da Faruk, nasani ta yadda kika k'waci soyayyarsa ta k'arfi da kuma ta magani, anma kisani duk abinda aka d'ora shi ba bisa tirba ta gaskiya ba to labari ne." Jidda ta daka mata tsawa "Ke Meenah! Yafa isheki haka, shiru shiru fa ba tsoro bane gudun magana ne, kar ki nemi ki fad'a min magana yadda kikeso fa." Meenah tace "Ni ba fad'a zanyi da ke ba, amma kisani zan fad'a zan kuma k'ara fad'a ke baki isa ki rabani da Faruk ba, saboda yana yi min true love ne babu boka babu malami, soyayyarmu had'in Allah ce, kuma banga ta yadda zaki raba abinda Allah ya had'a ba, duk naji conversation d'inku keda k'awarki sannan a shirye nake nayi fighting back don ganin baki rabani da Faruk ba." Jidda tace "Haka kika ce?" Meenah tace "Haka nace." Jidda tace "Shikenan mu zuba, niko bama Faruk ba har gidannan sai na raba ki dashi, ta yadda idan kika fita har abada bazaki dawo ba." Meenah tace "In kin dama ki rabani da duniyar nan gaba d'aya bama gidan ba, sannan kisani babu abinda kika isa kiyi min sai abinda Allah yayi min, sannan ina so ki sani k'arya fure take bata 'ya'ya!" Jidda tace "Zaki gani." Meenah tace "Zanga alkhairi." Daga haka ta sa kai ta fice zuwa d'akinta, inda ta bar Jidda tsaye kamar gunki in banda cizon yatsa babu abinda takeyi, gaba d'aya idanunta sun sauya daga fari zuwa ja, cikin sanyin jiki ta koma d'akinta tana mai mamakin Meenah da kuma maganganun data fad'a mata a yau. BELLO ‹ › Home View web version Saturday, 26 August 2017 Maryam Saidu at 06:17 AUREN FANSA 38 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) PURE MOMENT OF LIFE WRITERS _We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_ P.M.L 🌹38 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Daddare bayan sallar maghrib Faruk ya kirawo su a babban parlor yana son magana dasu. Bayan sun iso ya fara magana kamar haka. "Abinda yasa na tara ku a nan shine, na farko ina so ku sani shi aure ba abin wasa bane, sannan ban k'ara aurennan da wata manufa ba sai alkhairi, kamar yadda kuka sani ana yi wa ko mace kwana biyu ko uku, don haka na ware kwanaki biyu zan rik'a yi wa ko wacenku, ranar girkinki ya zagayo zaki kar6i girki, saboda Meenah ba baiwa bace da zata rik'ayi maki girki sai dai kici. Sannan banison raba abinci, idan girkin d'aya ne to zata dafa ma duka gidan abinci, da fatan kun fahimta?" Meenah tace "Mun fahimta." Yace "Yauwa daman shine maganar." Jidda ta k'ule meye na ci mata mutunci a gaban Meenah? *** Da safe Faruk na d'aki yana shirinsa zai fita aiki Jidda ta shigo sai faman zum6uren baki takeyi, ya kalle ta ya kawar da kansa tare da cigaba da abinda yakeyi, ta matso kusa dashi tace "Ya Faruk ina son magana da kai." Ba tare da ya kalleta ba yace "Ina jinki." Kai tsaye tace "Mota nakeso ka siya min." Ya dakata daga abinda yakeyi ya juyo yana kallonta cike da mamaki yace "Mota fa kika ce? Anya kina da hankali kuwa?" Tace "Da hankalina ai itama d'ayar matar taka tana hawa mota, ni bana hawa, don haka ance kayi adalci a tsakaninmu nima sai ka bani mota." Yayi ajiyar zuciya yana fad'in "Jidda, Jidda, a gaskiya rigimarki ta fara isata, idan kina maganar mota dana bawa Meenah ina kikaga tana zuwa inba makaranta ba? Ke kuwa ba zuwa makaranta kike ba saboda bakici Jamb ba koba haka ba? Don haka tunda bakya zuwa makaranta ni ba motar da zan baki, da dai kina zuwa ne wannan is understandable sai na d'auki d'aya daga cikin motocina na baki kema kina zuwa makaranta, don haka kar na k'ara jin wannna maganar a bakinki ma." Ta juyo cike da masifa tace "Ni gaskiya baka kyauta min ba, kawai don nace ka bani mota sai ka min gori? Ni gaskiya ka bani mota tam." Yace "Bazan bada ba zo ki k'wata, ko ita Meenah ba rok'a na tayi ba ni naga dacewar hakan na bata, don haka kema idan naga ya dace na baki zan baki." Ta fara jijjiga jiki tana masifa "Kawai don nace a bani mota shine mene? Naga dai motocinnan kana da su to meye don ka bani d'aya?" Yayi tsaki yace "Ke kinga tashi ki fita ki bani wuri, mota kuma zo ki k'wata sai muga ta tsiya, sakaryar banza wadda batasan ciwon kanta ba, kullum ke kenan rigima daga kice wannan sai kice wannan? Haka kikaga 'yar uwarki nayi ne? Haba!" Tashi tayi ta fita tana wannan cika tana batsewa ita a dole an 6ata mata rai, shi kuma Faruk tsaki kawai yakeyi har ya kammala shirinsa. Haka ta koma d'akinta zuciyarta na rad'ad'i ta dubi agogo k'arfe bakwai da minti hud'u 7:04am, Faruk mamaki yake bata kafin suyi aure kamar zai maida ta cikinsa, amma sunayin aure komai ya chanza mata, gashi bata son sanar da Luby halin da take ciki gudun kar ta mata dariya sheyasa ma ta bar abin a ranta. BAYAN KWANA BIYU Bayan kwana biyu kuma ta samu Faruk ya lafa mata tunda har yana kwana d'akinta kuma yana kulata, don haka sai ta fara jijji da kanta a gaban Meenah, wai ita nan ta fara samo kansa. Meenah ta kira Faruk a waya ta tambayesa zataje gida kuma ya barta, don haka ta shirya tsab direba zai aje ta, don yau ma Zarah zataje gida itama, ta fito parlor nan ta iske Jidda nata faman shan kankana duk ta 6ata wurin, Jidda badai k'azanta ba. Jidda ta d'ago ta dube ta a shek'e ta ta6e baki sannan tace "Fita zakiyi ne?" Meenah tace "Gida zanje." Jidda ta bushe da dariya sannan ta dubi Meenah tace "Haba Malama ke dai fad'i gaskiya, ashe duk k'aryar banza ce kikace kissa tafi magani, tunda gashi zaki fita neman maganin kema? Sai dai kin makaro don kinga yanzu Faruk ya k'ara dawowa hannuna kuma, kuma kisani na riga nayi miki nisa sannan a sannu zan tantance miki da magani da kissa wane yafi tasiri, kuma yanzu kika soma ganin chanji don nayi alk'awarin sai kin bar gidannan kika k'aryata ni, to muje dai zuwa, don haka kema kinbi sahu ay sai mu goga ni da ke." Meenah tayi murmushin da ya k'ara bayyanar da kyawunta tace "Ko shakka babu ni na fad'a miki kissa tafi magani tasiri kuma zaki gani, babu boka babu Malami, nayi alk'awarin nuna miki tasirin da kissa take da shi, ki fara k'irga daga yanzu na baki kwana bakwai kima fara lissafi tun daga yanzu, sannan banga ta yadda kina k'azanta zaki iya zama da miji lafiya ba ko wannan kad'ai ya isheki, ni na tafi sai na dawo." Tasa kai ta bar gidan, Jidda ta sake bushewa da dariya tana wani huro chewing-gum d'in da ke bakinta tayi k'wai tace "Da sannu dai zan ci ubanki sai kin gwammace kid'a da karatu." **** Gaba d'aya Meenah ta dage da addu'a ba dare ba rana, sannan ga extra kula tana masa da kuma kaucewa duk wata hanya da zata sa su samu sa6ani, lalla6a sa takeyi kamar k'wai, shiyasa ma take ganin chanji sosai. Yau da rana abinda yake so tayi masa wato waina da miya, ta masa zo6o mai dad'i da kunun aya tayi masa tasani sarai yafison abubuwan gargajiya akan tarkacennan. Yana cikin cin abincin ne Jidda ta shigo ta wani kashe d'ankwalin ture kaga tsiya tana taunar chewing- gum, da sauri ta janye plate d'in tana ma Jidda wani irin kallo. Tace "Baby ban yarda da abincinnan ba, ka daina ci kazo na had'a maka wani." Meenah ta mik'e tace "Sai dai ki jira zuwan ranarki." Faruk yace "Kinga Jidda don Allah ki wuce ki bamu wuri banason tashin hankali." Cike da mamaki ta kalle shi tana kad'e kai tace "A gaskiya bazakaci abinnan ba, saboda sam ban aminta dashi ba." AUREN FANSA 39 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) PURE MOMENT OF LIFE WRITERS _We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_ P.M.L 🌹39 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Meenah ta dube shi tace "My soul bai isheka ba abincin ko?" Ya gyad'a mata kai, ta mik'o masa hannu ya sa nasa cikin nata tace "Zo muje na had'a maka wanda yafi wannan, babu mamaki k'ila tana son cin wannan ne." Baiyi gardama ba yabi bayanta suka nufi sashenta, tana tsaye da plate a hannunta suka fice, galala take kallonsu har suka fice, babu shakka Meenah ta yi gaba a halin yanzu ta barta baya, dole ne ma ta d'auki mataki akan haka. Ta fito daga sashen cin abinci (dinning) ta nufi sashenta. Zaune take abin duniya ya ishe ta, ta sak'a wannan ta warware, daga k'arshe ta mik'e ta fito daga d'akin tana cizon hannu. Shiru babu motsin kowa, da alama suna cikin d'akin Faruk, haushi ya turnik'e ta kamar zata fashe. *** Dawowarsa kenan daga gidan, rashin ganin Meenah bata tarosa ba ya tabbatar tana makaranta don tace masa yau zatayi test har biyu. Yana shigowa yaci karo da Jidda daga bakin k'ofa sai faman washe baki takeyi. "Sannu." Tace dashi tana taunar chewing-gum, yayi tsaki yace "Yauwa." Ya sa kai zuwa d'akinsa yana Allah wadaran da mace marar tarbiyya. Yana zaune bakin gado yana cire safarsa ta shigo sai wani cika take tana batsewa. Zama tayi gefensa tace "Ya Faruk magana nazo muyi." Yace "Yanzu Jidda daga dawowata sai ki tare ni da wata magana kuma, ay kya bari in huta dai ko." Tace "Nidai ka bari na fad'a maka." Ya dakata yace "Ina jinki." Tace "Ay dai kace kai baka tauye hakkin iyalanka ko?" Yace "Haka ne." Tace "Yauwa, to tunda baka tauye hakkin iyalanka so nake ka barni na tafi Dubai, na karanta Fashion and Design." Ya karkato yana dubanta yace "Da igiyar wa?" Tace "Da igayarka mana." Yace "Kinga Malama banson zancen banza, ta yaya kina matar aure kawai don rashin hankali sai ki tafi wata uwa duniya da sunan karatu, ke bari ma kiji ni ba irin mazan nan bane da mata ke juya su yadda suka ga dama ba, don haka wallahi sai na sa6a maki kika k'ara yi min zance makamancin wannan." Cike da shagwa6e tace "Haba don Allah ya Faruk, wai ni meyasa kake min haka ne? Saboda Allah ita Meenah ay ka barta tana karatu sai ni zaka hana ni." Yace "Ita Meenah ba kina ganin cikin garinnan take ba? Yau ga zancen banza zancen wofi, ke nafa gaji da rigimarki haba! Mutum kullum da abinda zaice daga wannan sai wannan to wallahi na gaji." Kawai ya tashi ya bar mata d'akin. Ita kuwa sai tasa kuka tana ta magana ita kad'ai. **** Ranar wata Juma'a Luby tazo gidan, nan suka baje suna fira. Jidda ta dubi Luby tace "Luby gaskiyar magana nayi dana sanin wannan aure, banida tantama alhakin Meenah ne ke bibiyata, ke tunda nazo gidannan ban ta6a tsintar farin ciki ba daidai da rana d'aya ba, nikam na gaji wallahi auren ma ya fita raina, mutumin nan sai shegen kulle baya bani abinda nakeso, ga abin takaici wai Meenah yanzu tayi min in mata batada tsoro ko kad'an, ke wallahi aurennan na gama shi sai ya sake ni." Zumbur Luby ta mik'e tana salati tace "Yanzu Jidda abubuwa nata faruwa shine bansani ba? Baki iya fad'a min? Sai da abubuwa suka jagule miki suka fi k'arfinki shine zaki sanar da ni yanzu ko?" Jidda tace "Kiyi hak'uri Luby wallahi na d'auka zan shawo kan abin ne." Luby tace "Aiko sai mun d'auki fansar abinda tayi miki, bata isa ba, wacece ita? Ke kin bani kunya kinfa girme ta, amma kin zauna tana juya ki." Jidda tace "A'a Luby ke kinsani sarai mu da magani mukayi aiki, ita fa? Ay ba d'aya bane ba ma." Luby tace "Shikenan, amma kar kiyi saurin karaya, aure kuma yanzu kika soma shi, yo mekenan idan kika tafi tun yanzu, ay ko baki warci wani abu ba ni kya wabto mani, kuma ke ina son da kike masa? Ko dama k'aryar banza ce?" Jidda tace "Luby don bakisan irin wahalar da nake sha ba, babu fa yadda muka iya saboda matarsa tayi mana zarra." Luby tace "Wallahi k'arya takeyi! Kedai ba kina amfani da kwallin da turaren ba?" Jidda tace "Wallahi ina yi, kedai Luby munzo inda aka kere mu." Luby tace "Yanzu akwai wani abu a wurinki?" Jidda ta girgiza kai "Babu komai sai tarin wahala da takaici." Luby tace "To zan san matakin da zan d'auka, zan dawo anjima ko gobe." Washe gari da sassafe ta dawo, ta d'auki Jidda amma sai da suka shirga ma Faruk k'arya sannan ya barsu da k'yar, shima akan kar su dad'e. Suna tafe a mota Luby tace "Kar ki damu k'awata, zan kai ki inda za'a share miki hawaye." Jidda tace "Ina kenan?" Luby tace "Me kike ci na baka na zuba, kedai ki tsaya ki gani." Luby ta koro ma Barmuje bayani, yayi 'yan tsubbace tsubbacensa zuwa can yace da Luby "An 6ata aiki ay, saboda tun farko sai dana fad'a miki kar ya wuce daren farko baiyi tarayya da ita ba, amma ina bakuji ba, sannan kuma sai da ya fara yin tarayya da uwar gidanki akanki, don haka aikinki bazai ta6a yin tasiri ba! A yanzu komai ya wargaje saboda uwar gidanki tana da rik'o da addini sosai, a gaskiya kafin wani abu ya kamata da wuya. Ina tunanin kawar da ita ne kawai zai baki damar mallakar mijinki don haka sai kisan abinyi." Suka kalli juna itada Luby tace "To yanzu meye abinyi?" Barmuje yace "Akwai maganin da zan baki, zaki zuba mata a wani abun sha, kamar koko, fura da sauransu, wannan abin da kike gani guba ce data sha ita da duniyar nan sai dai a lahira." Luby tace "Akwai wata hoda da ka bani jiya, inaga kamar zata fi yi mata amfani." Yace "Tabbas! Zaifi sauk'i sai dai zan k'ara gargad'inki da kada ki kuskura ki shak'i hodar nan don idan kika shak'a.... hahaha to kema zaki bak'unci lahira, idan kuma baki mutu ba... haha! To zaki wahala a nan duniyar sai kin zamo abin tausayi." Luby tace "Zata kiyaye ma." Da haka suka baro dajin da Barmuje yake, suka dawo gida. Luby tace "Yanzu dai ga maganin nan, kuma kinji gargad'in Barmuje wallahi kibi a sannu." Jidda tace "Haba kar ki damu komai zai tafi yadda akeso." Luby tace "In ta mutu ki sanar dani, zan had'a mana grand party." Jidda tace "Ay dole ne ma wannan." Suka k'yalk'yale da dariya gami da tafawa. Daga haka sukayi bankwana Luby tayi gida cike da murna. **** Meenah na kwance a d'aki tana baccin rana inda Jidda ta lalla6o da hodar a hannunta, Jidda ta huro mata hodar tayo baya da sauri, sai dai mey? Memako Meenah taji wani abu sai ma ita Jiddar ta kurma uban ihu sakamakon jikinta dake mata rad'ad'i. Meenah ta farka tana salati sannan ta fito da sauri ganin meke faruwa. Jidda ce a tsakar parlor tana kurma ihu tana soshe soshe, Meenah tayo kanta tana tambayar lafiya? Ture ta Jidda tayi, sannan tayi d'akinta da gudu ta fad'a toilet tayi wanka da ruwa masu sanyi sosai. Sai dai babu wani sauk'i data samu. Ta kasa zaune ta kasa tsaye, kuka kawai takeyi, ga sam ta hana Meenah ta ta6a ta, sai surutai takeyi marassa kan gado. Hijabinta ta saka ta fito parlor a lokacin Meenah na sallah d'akinta, aiko da sauri ta fito ta tafi gidansu. Mama na d'aki tana sallah ta shigo tana kuka, sai tirje tirje takeyi, bayan Mama ta sallame ta juyo tace "Ke lafiya..." Bata k'arasa magana ba Mama taja baya cike da tsoron ganin fuskar Jidda kamar ba tata ba, Mama ta fito da gudu tana salati tana fad'in "Wacece ke?" Jidda na biye da ita tana dariya tana cewa "Ni ce, nice naje wurin boka nida Luby muka anso magani zamu kashe Meenah." Mama tasa salati tana fad'in "Jidda. Meya kaiki? Mekika zama? Innalillahi wa inna ilahir raj'iun! Jidda." Jidda tasa dariya, sai ta susa kai, ta susa jiki tana zum6uro baki tace "Wai laifina ne? Kaji man Mama, nifa kawai d'ora ni akayi akan turbar nabi kuma." Ana haka Dada ya dawo, shima cike mamaki yake tambayar lafiya. Mama ta kwashe komai ta fad'a masa abinda Jidda ke cewa. Dada yace "Da alama fa kamar hauka takeyi ko?" Mama tace "Nima shi nagani." Suka sa salati, Dada yace "Duniya budurwar wawa Jidda, Allah ya shiryeki, Hajiya kamo ta ki kai ta d'aki ki rufe kafin mu san abinyi." Tace "To." Ta kamo Jidda, tana tirjewa da k'yar suke tafiya, Jidda taci kwalar Mama tana dariya tace "Ina zaki kaini? Iye?" Mama tace "Muje d'aki ki kwanta." Jidda tasa dariya, can kuma tasa kuka, can tasa dariya, sai kuma tasa kuka, ta jawo hancin Mama ta matse tace "Daman haka boka yake? Laifin duk na Luby ne saboda ita ta kaini tun farko, saboda ban ta6a zuwa ba ay ko?" Mama tana kuka tace "Eh muje." Mama ta sha wahala don da k'yar ta kai ta d'aki ta rufe, sai dai taji ana bubbuga k'ofar ana ihu, can taji dariya, can taji surutai, can kuma taji ana cewa "Boka, boka, Barmuje sunansa." Mama tayi tsaye tana kuka, tace "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, Jidda kinga halin da kika jefa kanki ko? Kinzo kiyi wa wata asiri ya dawo kanki, duniya ina zaki damu? Ka haifi d'a amma baka haifi halinsa ba. Allah ka shirya shine kawai abinda zan ce miki Jidda, Allah kuma ya yaye miki." Dada ya kira Faruk ya sanar masa yazo yana nemansa yanzu yanzu. Ba'a d'auki lokaci ba ya iso, Baba ya kwashe komai ya fad'a masa, Baba ya d'ora da cewa "Ina so idan ta warke ka sallame ta, baka buk'atar cigaba da zama da ita, tunda har kamar Jidda tasan tayi kisa ay kaga zama da irinsu ba amfani. Faruk yace "Allah ya kyauta, Allah kuma ya bata lafiya." Baba yace "Amin." Faruk yace "Bari na dubo ta, daga nan sai na nemi asibitin da za'a kaita." Baba yace "To kabi a hankali, don jikin ba dad'i." A hankali ya tura k'ofar d'akin tana zaune dirshen a k'asa tana kwa6a sabulu da toothpaste cikin wata roba, ya kalle ta duk ta shafa ma kanta, ya zauna a bakin gado yana kallonta cike da tausayi, wannan wace irin rayuwa ce? Wai Jidda tasan taje wurin boka? Ya kalli Dada dake tsaye a bakin k'ofa sannan ya maida dubansa ga Jidda da ke shafa sabulun a jikinta. Ya gama kallonta yayi mata adduo'i sannan ya tashi ya fita. Ba'a d'auki lokaci mai tsawo ba ya je ya nemo asibitin da za'a kaita, daga nan aka kwasheta da da k'yar daga gidan. Faruk ya sanar ma sauran 'yan uwanta suma sunyi jimami sosai, daga k'arshe sukayi mata fatan shiriya da samun lafiya. *** AUREN FANSA 40 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) PURE MOMENT OF LIFE WRITERS _We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_ P.M.L 🌹40🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com Ya shigo gidan a lokacin da ya tarar da Meenah a bakin k'ofa, tana sanye da brown and cream atamfa d'inkin riga skirt, tayi kyau sosai, da sauri ta taro sa ya k'ura mata idanu yace "My baby ya akayi ne?" Yaushe rabon da taji sunan nan a bakinsa har ma ta manta, tayi murmushi tace "Jidda ce tun d'azu banganta ba, ko da saninka ta fita?" Ya kwashe labarin komai ya fad'a mata, tace "Ikon Allah kenan, amma Jidda bata yi wa kanta adalci ba, amma sai inga duk bai kai na saki ba my soul." Ya kamo ta suka dawo parlor suka zauna yana kallonta sosai yace "Rabuwa da Jidda shine mafi alkhairi a garemu my baby, saboda a gaskiya bazan iya cigaba da zama da ita a matsayin matata ba, besides ba'a son raina na aure ta ba." Ta dube shi cike da mamaki tace "Bangane ba my soul." Yace "Wato akwai wata rana na fito zan tafi aiki sai naji Jidda na magana da mahaifiyarta tana ce mata ita ba wanda takeso sai ni, a nan naji Mama na ta rarrashinta akan tayi hak'uri tunda ni ba sonta nakeyi ba, tun daga wannan lokacin sai na karaya nake ganin kamar ban kyauta ba, abin yana ta damuna sosai, a ganina abinda kawai zanyi na faranta ransu shine na bijiro da maganar auren Jidda, a tunanina sun mani komai a rayuwa bai kamata d'iyarsu tana sona nak'i ta ba." Meenah ta kamo hannunsa tana murmushi tace "A gaskiya kayi tunani mai kyau kuma ka kyauta, sai dai daman tun farko kayi min bayani da sai nafi fahimtarka my soul." Yace "Naso yin hakan my baby, amma a lokacin sai na rasa dalilin da yasa na kasa fad'a miki gaskiya, kuma wallahi bansan yadda akayi ba sai dai naji ance wai matata ce, abin zai baki mamaki is like bansan abinda nakeyi ba, kuma a lokacin Jidda tayi amfani da magani wajen jawo hankalina gareta, nidai kawai idan ta warke zan sallame ta, taje can ta nemi wani daidai da ita." Tace "Bazan iya saka yin abinda baka so ba, duk abinda kaga yafi dacewa kayi ni kuma zan baka goyon baya d'ari bisa d'ari my soul." Ya kamota ya rungume a k'irjinsa gami da lumshe idanu yace "Sheyasa nake sonki my baby." Tace "Nima haka, yanzu muje kayi wanka kaci abinci ko, na dafa maka abinda kafi so." Cike da jin dad'i yace "Allah my baby?" Tace "Wallahi kuwa." Yace "Shikenan muje, don yau ma kece zakiyi min wanka da kanki." Ta tashi tana fari da ido tace "Muje." Ta wuce yabi bayanta. **** Yana zaune a office d'insa aiki yasha gabansa wayarsa ta fara ringing, ganin Hajir ya sanya ya dakata ya d'auka. "Hello Hajir." Tace "Hello Sir ina wuni?" Yace "Lafiya lau, ya dai?" Tace "Aikinka na kammala komai Sir, yanzu ya za'ayi?" Cike da jin dad'i yace "Da gaske kin had'a komai da komai?" Tace "Yes Sir komai ya kammala." Yace "Wow Weldon Hajir, a gaskiya nayi matuk'ar farin cikin jin haka, yanzu abinda za'ayi, ki shirya zuwa gobe zan shigo gidan, dana kiraki sai ki fita daga shigar Atika ki koma Inspector Hajir d'inki. Sauran bayanin zan kiraki. Yanzu wani d'an bincike nakeyi akan wad'anda suka turo domin kashe iyayena, nama kammala don har na tura a kamo yaran, don muna buk'atarsu." Tace "Yayi haka sir, sai Allah ya kaimu goben." Yace "Amin, thank you." Daga haka sukayi sallama, Faruk yayi murmushin jin dad'i sosai. **** Kiran farko na sallar asuba a kunnensa akayi, domin ba bacci yake ba, saboda tsabar farin cikin kalar matar da Allah ya bashi, shi kwata kwata bai k'ara tabbatarwa ba sai yau, tambayar kansa yakeyi anya kuwa akwai wanda ya kai shi sa'a? Ya lalubi bed side lamp sannan ya dube ta tana bacci, numfashinta yana fita a natse. Kyakkyawar fuskarta nata annuri, yayi ta kallonta baya ko kyaftawa har sai da idanunsa suka kawo ruwa sannan ya dawo hankalinsa, ya sunkuyo a hankali ya manna mata light kiss a goshinta, ya numfasa, Allah kad'ai yasan tarin son da yake mata. Da k'yar ya lalla6a ya sauka daga gadon ya shiga toilet yayi wanka ya fito da alwalarsa, ya shimfid'a sallaya yayi nafilfili har alfijir ya fito, sannan ya nufi masallaci. Yanda ya barta haka ya dawo ya same ta, yayi tsaye a gaban gadon rungume da hannayensa yana kallonta. "Wai lallai baby an gaji." Ya zauna gefenta ya tallabo kanta sannan yace "Meenah... Meenah..." Ta bud'e ido a hankali tabi shi da kallo har idon ya washe gaba d'aya. Yace "Ki tashi kiyi sallah, ko gajiyar ce ta hana ki tashi?" Ta runtse ido tana k'ok'arin tashi, yayi murmushi kawai ya d'aga ta cak sai toilet, ya tarba ruwa masu d'umi ya saka ta ciki, ita kuwa idonta har yanzu a lumshe yake, yana tsaye yace "Haba ragguwa sai kace first time dai." Tayi murmushi kurum, daga haka ya fita ya bata wuri don ta kimtsa. Tsawon minti 20 tafito, ya matso yana dariya. "Ragguwa kawai ni tuni naje masallaci na dawo." Ta wuce shi tayi shirin sallarta tana jin wani irin nishad'i marar misaltuwa. Kwanciyarsa yayi, ta gama sallarta tayi adduo'inta gami da mik'a godiyarta ga Allah da ya karkato mata da hankalin mijinta gareta tana fatan su dauwwama haka har k'arshen rayuwarsu. Sai kuma ta tuna Jidda ko a wane hali take yanzu? Ta dad'e tana mata addu'ar samu sauk'i, tana gamawa sai kawai ta maida kanta bisa sallayar tana lazumi. Ya d'ago yana dubanta yace "Ya zaki kwanta a nan?" Tace "Haka nan." Yace "To kodai?" Ta k'udundune fuskarta da hijabi ta k'yale shi, cicci6o kanta yayi ya d'ora bisa jikinsa yace "Tashi mu koma kan gado." Tayi shiru tana kallon kyakkyawar fuskarsa, yace "Allah yayi miki albarka my baby." Taji dad'i sosai ta amsa da "Amin my soul." Ya cigaba da fad'a mata dad'd'an kalamai masu rikita lissafi, ganin haka yasa na tashi na baro d'akin, sai dai fatan Allah ya kawo k'azantar d'aki.. AUREN FANSA 41 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) PURE MOMENT OF LIFE WRITERS _We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_ P.M.L 🌹41 🌹 http://MaryamSBello.blogspot.com A hankali ta bud'e idonta juyi d'aya tayi ta hango shi bakin wardrobe da alama wanka ya fito yana shirin fita, duba agogo tayi k'arfe 8:30am, zumbur ta mik'e tana mamakin abinda ya haddasa masa makara yau, zaune ta mik'e tana kallonsa yana k'ok'arin d'aura agogo a hannunsa, ta sauko daga gadon ta kamo hannunsa tana cigaba da sa masa. "Yau ka makara my soul." Jin yayi shiru ya sanya ta d'ago tana dubansa da mamaki, damuwa ta gani k'arara bayyane a fuskarsa wanda idanuwansa ma sun nuna hakan. "Meyake damunka my soul?" Yace "Babu komai, kije kiyi wanka yau tare zamu fita, sannan ki sanar da Zarah ta tamabayi mijinta ya bata izini zamu fita tare da ita." Tayi shiru tana tunani can kuma tace "Lafiya?" Yace "Koma me kenan zaki gani nan da lokaci kad'an, kedai kawai ki kirata ki sanar da ita." Tace "To." Sannan ta wuce tana tunanin dalilinsa nace mata haka. Tayi wanka ta sanya bak'ar after dress, tea kawai suka sha inda a waje sukayi kaci6us da Zarah inda take shaida musu da mijinta zasu tafi yace zai kaita, haka ma Anisah tazo a daidai sadda zasu shiga mota, itama ta shaida musu mijinta zai kaita, nan kuma kowa ya fara shirin tafiya. A mota babu wanda yayi magana ko wane da tunanin da yakeyi, ta kai dubanta ga Faruk da alama ya zurfafa cikin tunanin, ta ta6o sa tace "My soul wai meke faruwa haka ne? Sannan duk ina zamuje da su Anisah?" Ya karkato kad'an ya kalle ta sannan ya maida kansa ga titi yace "Ki gafarce ni my baby." Tace "Akan me fa?" Yace "Kawai ki yafe min akan abinda zai faru yau." Cikin rashin fahimta tace "Me zai faru yau?" Bai kai ga bata amsa ba wayarsa tayi ringing, ya d'auka yace "Hello Usman." Usman yace "Muna hanya ka turo mana address d'in." Yace "Muma muna hanya, zan turo maka sai mun had'u d'in." Ya kashe kiran ya tura masa address d'in. Meenah da zuciyarta fal damuwa tace "Kaji my soul, wai meke faruwa?" Yace "Kiyi hak'uri zaki ga koma menene." Ganin ya d'auki hanyar unguwarsu ya sanya tace "Daman gida zamu shine kak'i sanar dani?" Ya d'anyi murmushin k'arfin hali a zuciyarsa yace "Nasan yau zanyi breaking heart d'inki my baby, amma abinda zanyi ya zama dole in ba haka ba hankali na bazai ta6a kwanciya ba." Ya kalle ta yaga ta zurfafa cikin tuanani, yayi ajiyar zuciya a lokacin da ya karya kwanar layinsu Meenah. Ganin motoci a k'ofar gidansu ya sanya ta d'an razana kad'an gami da zaro idanu waje, ya kalleta ya kawar da fuskarsa gefe, yasan kota masa tambaya baisan abinda zai ce mata ba. Yayi parking ya fito daga mota, yana d'an kalle kalle, ganin ba motar Usman ya sanya yasan bai iso ba, amma motoci hud'u sun iso na abokanan aikinsa, su Zarah duk sun iso inda take ta tambayar abinda ke faruwa. Amsa d'aya take samu wato, "Nima bansani ba." Su Najeeb ne kad'ai suka san abinda ke faruwa saboda ya sanar musu daman. Ya d'auki waya ya kira Hajir ya sanar mata yana k'ofar gida. Tace she's ready tun d'azu. Nan suka cigaba da tsara plan d'in nasu. Ita dai Meenah bata k'ara magana ba illa dai gabanta da ya tsananta bugu. A 6angaren Bilki kuwa tunda ta tashi da safe k'awarta ta iso akan yau zasu walimar bikin d'iyar wani sanata da za'ayi a cikin garin Abuja, Baba kuwa yana d'akinsa yana wanka zai fita, shiryawa tayi cikin wani dank'areren leshi mai matuk'ar tsada sai k'yalli takeyi, wayoyin da ke hannunta sun kai kala uku kuma manyan wayoyi masu tsadar gaske, ta fito parlor sai zuba k'amshi take kamar shagon saida turare, kaci6us tayi da Hajir sanye cikin bak'ar after dress tayi tsaye a bakin k'ofa idanunta manne cikin bak'in glass wato no respect. Suka ja suka tsaya Bilki ta kalle ta daga sama har k'asa tace "Ke Atika meye haka? Ina aikin dana saki zaki zo kiyi wa mutane tsaye a ka haka! Matsalar d'an k'auye kenan ka wayar da shi sai daga baya ya nuna yafika wayewa. Mts." Laila tace "Gaskiya kam da alama don wannan yarinyar 'yar rainin hankali ce, ke Malama ki bamu wuri zamu wuce." Hajir ta kalle su da chewing-gum a bakinta sai hannunta dake hard'e tace "Wacece Atika don Allah?" Bilki tace "Ahh! Kiji min neman magana fa, yo wacece Atika 'yar aiki in ba ke ba? Kaji min yarinya zata nemi ta maida ni k'aramar yarinya." Laila tace "Gaskiya wannan ta samu wuri da yawa. Da nice ke da tuni na sallame ta don bazan iya ba, zan iya farfasa mata jiki." Bilki tace "Eh gaskiya ne, ke Atika! Ki wuce kije ki d'ora girkin rana kafin mu dawo." Hajir ta kallesu a wulak'ance tace "I'm sorry to say Hajiya, amma bazanyi ba, sai dai idan kece zaki je ki d'ora." Suka fara salallami suna tafa hannu, Laila tace "Wai bazaki gaura mata mari ba, ni wallahi sheyasa kikaga bani d'aukar 'yan aiki saboda bansan wadda zan kwaso ba, ya za'ayi ki zauna kina fad'a tana fad'a? Ki d'auki mummunan mataki akanta mana." Bilki tace "Lallai kin k'oshi da sadda aka kawo ki kamar zakiyi min sujjuda amma yanzu kin k'oshi kin mik'e k'afa ko? Lallai sannu Atika, to wallahi kizo ki kwashi kayanta ki bar min gida munafuka kawai." Hajir tayi murmushin mugunta tace "Daman yau zan bar miki gida Hajiya kar ki damu." Bilki tayi tsaye ta rasa ma me zatace sai tafa hannu kawai takeyi. Minti goma tsakani Faruk ya doka sallama, Bilki ta washe baki tace "Ah kinga surukinmu ne yazo, sannu da zuwa Faruk." Ya shigo yana k'are ma gidan kallo, yana d'aga kwalar rigarsa yace "Ki gyara kalamanki Hajiya ba Faruk zakice ba, Inspector Faruk Adam Ishaq zaki ce." Suka kalli juna itada Laila, Laila ta rad'a ma Bilki a kunne "Adam Ishaq fa yace, me hakan ke nufi kenan?" Hajir tayi murmushi ta cire after dress d'inta ta dawo kusa da Faruk tace "Sunana Inspector Hajir ba Atika ba." Bilki tace "Ke kamar ya keba Atika bace, to wacece ke?" Meenah da Zarah da Anisah suka shigo ganin Ikon Allah a daidai nan Baba ya sauko yana gyara hular kansa ganin mutane da hayaniya ya sanya yaja tsaya yana tambayar lafiya? MSB💖 BELLO ‹ › Home View web version Friday, 8 September 2017 Maryam Saidu at 14:37 AUREN FANSA 42 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) PURE MOMENT OF LIFE WRITERS _We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_ P.M.L Ina yi ma d'aukacin musulmai barka da sallah, da fatan munyi sallah lafiya? Allah ubangiji ya maimaita mana Amin thumma Amin! ❤️ Wannan page d'in nakune Faty Ladan, Hauwee Bash, Asma'u Ammani, Hafsat Kabeer, Farida Bature, Feedn, Machika, and Aisha Basheer dama sauran wad'anda ban ambata ba, nagode da k'aunar book d'innan da kukeyi.😘 Fatan alkhairi ga Auren Fansa Fans😍Allah ya bar zumunci.❤️ 🌹42 🌹 Cikin girmamawa Faruk ya isa inda Baba ke tsaye ya gaishe shi ya amsa masa yace "Meyake faruwa ne haka a nan?" Faruk yayi murmushi yace "Yanzu zaka fahimci komai Baba." Faruk ya koma inda Hajir ke tsaye yace "Hajir ina so ki bani wayar nan dana baki zan duba wani abu." Hand bag d'inta ta bud'e ta fiddo ta mik'a masa, ya maida dubansa ga Bilki yace "Ina so ki nutsu ki kalla." Tace "Bangane abinda ke faruwa a nan ba, don Allah ayi mana bayani mana." Faruk yace "Abinda nake k'ok'arin yi kenan ay." Wayarsa ya zaro daga aljihu ya kira bugu d'aya aka d'auka yace "Usman bud'e motata ka d'auko min system d'ina tana nan daga bayan seat, sai wasu wayoyi amma ba'a jiki suke ba suna nan a gefe sai ka d'auko mun su duka." Bansan me Usman yace ba naji dai Faruk yace "A'a motar a bud'e na barta kawai ka bud'e, yanzu yanzu muna jira don Allah." Baba yace "Wai lafiya haka Faruk? Har yanzu ban fahimci inda ka sa gaba ba." Faruk yace yana k'ok'arin maida wayarsa aljihu "Yanzu zaka fahimta Baba." Bilki kuwa kamar ruwa ya cita haka kurum gabanta ya tsananta bugu, don har wata kyarma take duk da batsan abinda ke faruwa ba. Usman ne yayi sallama hannunsa d'auke da laptop da wayoyi, Faruk ya kar6a inda ya aje ta a saman center table d'in dake ajiye a parlor d'in, yayi ta had'e had'ensa ya jona nan ya had'a can, cikin minti kad'an wani video ya bayyana a saman screen d'in laptop nasa. Ya juya ta setin da kowa ke tsaye ya danna play. Hoton farko video Bilki inda take waya da Laila a gameda makircin da suka had'a, maganar yadda take kwasar dukiya da shawarwarin da Laila ke bata akan yadda zata dage wajen cigaba da juya dukiyar. Next scene kuwa hoton Laila ne da Bilki suna zaune cikin d'aki suna maganar yadda suka kashe Hajiya Reema da Alhaji Adam, take Bilki ta fara zufa itada Laila, wannan abu ya basu mamaki ya akayi aka d'aukesu hoto haka? "Waye ya d'auki wannan videon?" Ta fad'a jikinta na kyarma, Baba kuwa kallonta kawai yana salati, inda Zarah da Meenah ke tsaye suna kuka suna mamaki. Scene na gaba kuwa yana d'auke da video d'in Laila da Bilki inda Laila ke narrating yadda akayi kisan da kuma shawarar su cigaba da 6oye sirrinnan, har Bilki ke nuna mata tsoronta kar wata rana asirinsu ya tonu. Laila tana nuna mata asirinsu a rufe yake babu mai ji. "Wallahi bani na kashe su ba, wallahi Laila ce ta kawo wannan shawarar." Bilki ta fad'a tana kyarma, Laila tace "Dana baki shawarar wa yace ki d'auka don haka kina da laifi kema." Bilki tace "Nidai wallahi kin cuce ni Allah ya isa wallahi." Laila ta buga tsoki tace "Aikin banza, yo Allah ya isarki me zatayi min?" Faruk ya cigaba da displaying duk wani abu da aka d'auka na Bilki da Laila, tare da voice notes, Baba da zufa ta jik'e shi jagab, ya kalli Meenah da Zarah yaga yadda suke kuka, sannan ya juya ga Bilki da take borin kunya suna chachar baki itada Laila suna ta k'ara bankad'e asirinsu da kansu. "Tun farko ina zaman zamana kika kawo wannan shawarar kika ce mu kashe su..." "Dana kawo shawarar nace dole kibi ne? Kema a lokacin kina jin haushin Alhaji Adam, akan ya samu kujarar da kikeso mijinki ya mallaka ko nayi k'arya?" Bilki tace "K'arya kike munafuka algunguma, abin naki harda sharri kuma? To wallahi..." Maganarta ta katse ne sakamakon wani zafafan mari da Baba ya d'auke ta dashi, har sai data ga gilmawan wuta sannan ta nemi ji da ganinta ta rasa na wuchin gadin. Dafe kuncinka tayi cike da azaba kafin kuma ta ankara ya k'ara d'auke ta da wani wanda yafi na farko zafi, kyarma ta fara yi inda hawaye ke ambaliya a saman fuskarta, ya d'aga hannu zai k'ara wanke ta da wani marin cikin azama Meenah ta rik'e masa hannu gam gam tana kuka, tace "Kar ka k'ara mata wani Baba, ka rabu da ita don Allah." Baba ya fara k'ok'arin k'wace hannunsa yana nuna Bilki yace "Ashe ke mutuniyar banza ce bansani ba? Shashasha marar mutunci! Ashe ke muguwa ce? Makira! Anya kinada imani kuwa? Kin bani mamaki ban ta6a zaton haka daga gareki ba..." Sai ta fara borin kunya tana fad'in "Yo har abin kunya ya wuce daga gareka? Kai fa kana zaune da mutum ka kasa gaya mata iyayenta na asali tsabar rufa rufa!" Baba yace "Ki min shiru a nan, anya kina da hankali kuwa?" Tace "Ras nake, yo tunda aka tona min asiri na wa zan iya rufewa kuma? Ai wallahi sai na fasa k'wan! Ke Amina! Kalleni nan Alhaji bashi ya haife ki ba! Haka nima ba nice na haife ki ba! Kije ki tambaye shi inda iyayenki suke." Gaban Meenah yayi mummunar fad'uwa, dafe k'irjinta tayi a yayinda hawaye suke kwarara a fuskarta, Baba take kallo tace "Ni 'yar tsintuwa ce ko?" Faruk kuwa tsaye yayi cike da mamaki a yayinda k'walwarsa ta tsaya cak da aiki.... AUREN FANSA 43 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) PURE MOMENT OF LIFE WRITERS _We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_ P.M.L Dedicated to First Lady 😍 PML You are the best Allah ya bar mu tare👌🏼😉😌 🌹43🌹 Cikin wani irin yanayi yace "What?" Bilki kuwa k'ara d'aga murya takeyi tana fad'in "Ke Amina ba mu muka haife ki ba." Laila tana ta d'an zunguranta akan ta bari ina bata ma saurareta ba. Baba ya sunkuyar da kansa yana mai tsananin jin haushin Bilki, ko kusa bai so Meenah tasan matsayin ta ba, a ganinsa hakan zai iya haifar mata da damuwa sosai, da yawan tunani, duk da yasan sanin matsayintan ba wani abin bane don kuwa cikakiyyar 'yar sunnah ce, hakan yasa ya tattaro nutsuwarsa yana kallon Meenah data tsareshi da ido kamar yau ta fara ganinshi, yace "Kar ki damu zan sanar da ke komai, Faruk kammala aikinka sai mu tattauna." Da k'yar Faruk ya tattara nutsuwarsa amma gaba d'aya hankalinsa naga Meenah da kuma son jin in da gaske ne zancen Bilki. Police guda biyu ke tsaye a waje Faruk ya kirasu suka shigo, da hannu kawai ya basu order wanda su kad'ai suka san me yake nufi, sara masa sukayi sukace "Yes sir..." Fita sukayi ba'a jima ba sai gasu sun dawo da matasan maza majiya k'arfi su kusan biyar masu k'iran 'yan daba, ko su Zarah sai da suka tsorata da ganinsu, sai wani huran hanci sukeyi suna zare idanun kamar kura taga nama. Take jikin Laila ya fara 6ari don kaf d'insu ta ganesu, haka zalika ita kanta Bilki sai ta fara salati tana bada hak'uri da neman gafara. Faruk yace "Wad'annan sune wad'anda kukayi assigning suka aikata kisan da hannunsu, suka kashe min iyayena..." Take tsikar jikinsa ta tashi idanunsa suka kawo ruwa, ya kai dubansa ga Anisah yaga tana kuka itama, duk sai ta basa tausayi a ransa yace "Ke kenan da bakida wayau a lokacin bare kuma ni." Bilki tace "Ni dai bansansu ba. Billahi bansan ko su waye ba." Baba ya daka mata tsawa "Yi mana shiru a nan! Ko so kike sai na sa an harbe ki ne da bindiga? Ga laifi an kamaki dumu dumu amma kina k'aryatawa?" D'aya daga cikin 'yan daban suka ce "Tabbas nine wanda Hajiya Laila ta kira take sanar dani irin aikin da za'ayi musu, sannan sukayi min alk'awarin mak'udan kud'i idan na aikata abinda suka sani, ita kuma Hajiya Bilki ita bani umarnin kisan tace idan ban aikata ba to tabbas ni zatasa a kasheni, haka sukayi min ko wanensu zai bani dubu d'ari biyar biyar idan aikin ya kammala. Don haka na samu abokanan aikina na sanar musu yadda zamuyi aikin. Ko bayan faruwan haka sai da suka mallaka min gida da mota wai a cewarsu farin cikin abinda nayi musu ne." 'Yan sandan suka matso kusa da su Hajiya Laila sukace "You're under arrest for the murder of Hajiya Reemah and Alhaji Adam, you have the right to remain silent, because anything you said will be used against you in a court of law." "Don Allah ka gafarce ni, ku yafe min abinda nayi." Ta matso kusa da Meenah tace "Ki yafe min irin cin zalin da nayi miki a baya, nasan kin sha wahala a wurina ki yafe min." Baba yace "Kamar yaya?" Zarah ta matso tana share hawaye tace "Baba, tunda na taso nake ganin yadda Meenah ke fuskantar wulak'anci, mugunta da kuma zalunci a wurin Mami, bugun yau daban na gobe daban, ga sata aiki kamar jaka, abinci kuwa data gama wannan sai a sata wani, wanke wanke, wanki, wankin toilets, shara, goge goge, duk Meenah ce keyi. Sannan bata cin abinci sai ka kusa dawowa, haka zata wuni da yunwa ga uban aiki, da ka kusa dawowa zata korata tayi wanka taci abinci yadda bazaka gane ba. Ko nayi yunk'ura fad'a maka sai Mami ta hana, ko tace zata zane ni muddin na sanar da kai..." Baba yace "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! Bilki ashe yadda na d'auke ki ke ba haka kika d'auke ni ba? Tun farko dana san haka kike da ban d'auki amanar maraininiyar Allah na baki ba, amma kisani akwai ranar hisabi kuma Allah sai ya mata sakayya..." "Na tuba Alhaji, ka yafe min..." "Bilki kije na sake ki saki d'aya..." Kowa sai da ya zabura jin sakin da Baba ya yiwa Bilki, sannan ya bita da nasiha da fatan zata gane kuskurenta, haka aka saka musu ankwa itada Laila aka jasu suna tirjewa da maganganu suka fice. Faruk gaba d'aya jikinsa yayi sanyin abinda yaji, wai Meenah marainiya ce? "Me nayi? Na d'auki alhakin baiwar Allah." Ya fad'i a cikin ransa. Duk da daurewarsa sai da k'walla suka zubo masa, ya share sannan ya bi bayansu Bilki inda Anisah ma tabi bayansa, suka bar gidan. Suna fita Meenah ta kifa kanta a hannun kujera tayi ta kuka kamar ranta zai fita, Zarah na ta aikin rarrashinta inda itama kukan takeyi, Baba yaja su suka shiga cikin d'aki yana ta faman rarrashinsu. ***** Daddare kowa ya nutsu a parlor amma daka kalli kowa kasan ba a cikin nutsuwa suke ba. Baba ya maida dubansa ga Meenah yace "Dalilin da yasa ban ta6a fad'a miki ba shine, na farko baniso kiyi kukan maraici, na biyu baniso ki shiga damuwar rashin iyaye, don kinsan yawan damuwa ga yaro ba abu bane mai kyau, amma ina mai baki hak'urin 6oye miki da nayi duk da nasan you have the right kisani." Nan ya kwashe labarin komai ya fad'a mata, su waye iyayenta da kuma yadda akayi ta dawo hannunsu da zama. Sannan ya d'ora da cewa "Duk da nasan banyi niyyar fad'a miki ba amma wallahi ji nake kamar an sauke min wani nauyi da ke bisa kaina, Meenah bana fad'a miki maganar nan ba don ki shiga damuwa ba, a'a na fad'a miki ne bisa tirsasawa da akayi min, sai dai ina rok'onki da kada ki d'ora damuwa a ranki don Allah, sannan ki cigaba da yiwa iyayenka addu'ar samu rahama daga Allah, inda suka tafi muma zamu iske su wata rana." Ya fad'a da guntun k'walla a idanunsa. Meenah ta share hawayenta tace "Wallahi Baba ban ta6a sanin cewar bakai ka haifeni ba saboda babu alama, duk wani gata ka min shi, sai dai nace Allah ya saka da alkhairi, amma kasani har yanzu bazan daina ganinka a matsayin mahaifina ba saboda kaima mahaifina ne saboda yaya kake ga mahaifiyata don haka duk d'aya ne, kuma insha Allah na maka alk'awarin cire damuwa a raina." Yace "Alhamdulillah, ke kuma Fatima kema kar ki shiga damuwar ganin mahafiyarki da aka kama, ki cigaba da yi mata addu'a." Tace "Insha Allah Baba." Faruk da ke zaune jikinsa sanyi k'alau yace "Baba inada magana idan an bani dama." Baba yace "Bismillah mana." Faruk ya sunkuyar da kansa saboda nauyin maganar amma kuma dole ne ya fad'i, don ya samu su yafe masa. Yace "Baba, ka gafarce ni, nayi kuskure babba." Sai kuma yayi shiru, Baba yace "Kuskure kuma Faruku? Na me?" Ya kalli Meenah yaga shi d'in take kallo, sannan ya maida kansa k'asa yana wasa da zoben azurfar da ke hannunsa yace "Wallahi Baba da zan auri Meenah ba sonta nakeyi ba... daman don na d'auki fansar abinda akayi wa iyayena ne sheyasa na aureta..." Ras! Ras! Gaban Meenah ya yanke ya fad'i, ya d'ago ya kalleta yaga idanunta sun kad'a sunyi jawur! Tana masa kallon mamaki had'e da tsana... "Meenah nasan nayi kuskure a nan amma wallahi..." Da gudu tayi ciki tana kuka mai sauti...! Zarah ta bi bayanta da gudun itama tana k'wala mata kira... AUREN FANSA 44 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) PURE MOMENT OF LIFE WRITERS _We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_ P.M.L http://MaryamSBello.blogspot.com 🌹44🌹 A bakin gado Zarah tayi arba da ita ta kifa kanta tana kuka kamar wacce aka aiko ma da labarin mutuwa, a hankali ta k'arasa gami da zama gefenta ta d'an dafata sannan ta kira sunanta cikin sigar rarrashi. "Meenah..." A hankali ta d'ago da jajayen idanunta tana kallon Zarah a yayinda hawayenta suka cigaba da zuba ba k'akk'autawa, Zarah ta sa hannunta ta share mata hawayen tace "Haba Meenah, meye haka? Meye abin kuka a nan? So kike sai wani ciwon yaje ya kama ki a banza? Don Allah kiyi shiru ku fahimci juna keda mijinki." Meenah tayi murmushin da ya fi kuka ciwo tace "Zarah, a halin yanzu ba zaki gane halin da nake ciki ba saboda bake bace aka yaudara ni ce aka yaudara, ke kina can zaune lafiya da mijinki kina sonsa yana sonki, ni kuwa fa? Ashe wanda nake matuk'ar so kamar raina ashe yaudara ta yakeyi? Mutumin da zan iya sadaukar wa rayuwata domin farin cikinsa, mutumin da nake da burin samun zuri'ah ta gari da shi, mutumin da nake kallo a matsayin masoyina na hak'k'ika ashe shi ba haka yake kallona ba, ya cuce ni! Ya cuci rayuwata, yayi min wasa da feelings ba kad'an ba, wallahi Zarah namiji mugu ne, namiji bashida tabbas! Allah wadaran namiji!" Zarah tace "Haba Meenah! Ki saurari kanki ki daidaita tunaninki, yes na yarda Faruk bai kyauta miki ba, kuma baiyi amfani da hanyar da ya dace ya d'auki fansa ba, amma tunda yayi admitting a gabana dake da Baba kinsan yayi namijin k'ok'ari, ina so ki sani ba ko wane mutum bane zai iya haka ba, ya kamata ko nan kiyi respecting decision d'insa, kuma ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba ya na matuk'ar sonki a yanzu, kuma ya gane kuskurensa." Ta mik'e tsaye tana huci "Sonsa na banza, bana so ya rik'e kayansa, kuma nidai na gama zama da mayaudarin mutum kamar Faruk, bazan koma gidansa ba!" Zarah ta mik'e tana kallonta galala kafin tace "Are you kidding me? In ma wasa kike ki daina tun wuri, Meenah kamar yadda na fad'a miki da farko zan kuma maimaitawa, Faruk yana sonki ko ki yarda ko kar ki yarda, koda can baya sonki to yanzu Allah ya d'ora masa. Don haka kiyi tunani." Baba ne ya aiko kiransu, suka mik'e jiki a sanyaye suka fice, a parlor suka iske Faruk kallo d'aya zakayi masa ka tabbar da hankalinsa a tashe yake, tunda suka shigo ya kafa mata ido ita kuwa ko kallon inda yake batayi ba, suka samu wuri suka zauna k'asa, Baba ya fara magana. "Da farko dai ina so nayi muku nasiha akan zaman duniya, gaba d'ayanku nan musulmai ne, kuma shi musulmi a duk inda yake ana so ya zamto mai hak'uri da kuma juriya da kuma imani, tabbas Faruk baka kyauta ba a wani 6angaren, amma kuma ina so ke Aminatu kiyi hak'uri na tabbata yanzu Faruku yana sonki bada wasa ba, kuma tunda ya fito fili ya fad'a miki bai kamata kuma ki juya masa baya ba. Don haka ina so kiyi hak'uri ki d'auki k'addara, kuma komai na duniya mai wucewa ne, ki rik'e mijinki kiyi masa biyayya don shine gatanki duniya da lahira." Meenah tace "Nagode Baba, amma ni gaskiya bazan koma gidansa ba, ya sauwak'e mini kawai." Ba Faruk kad'ai ba hartta Baba sai da ya razana da jin kalaman Meenah, Faruk sunkuyar da kansa kawai yayi yana jin tashin hankalin da bai ta6a ji ba. Baba yana kallon Meenah yace "Aminatu, kalamanki basuyi min dad'i ba, don banyi zaton kamar ki mai ilimi da aiki da shi zai furtawa mijinki haka ba, amma ina so ki sani saboda gaba duk wani 6acin rai in zaizo miki to kisan irin kalaman da zaki furta. Mijinki dai mijinki ne. Sannan zancen ya sake ki ma bai taso ba, idan ma ya taso sai kiyi tunani wa kuma zaki aura? Maza majoritin mu halinmu a rufe yake, kafin kuma ki gane halin sai kin zauna da mutum. Aminatu duk rintsi kiyi hak'uri ki zaunawa aurenki, kedai ki cigaba da add'ua, duk wani hargirsi idan ya taso a tsakaninku kok'ari zakiyi wajen ganin kun zauna kun warware matsalarku." Ya gyara zamansa ya d'an yo gaba daga jinginar da yayi, yayi ajiyar zuciya ya cigaba "Kin bani kunya Meenah, ban ta6a tsammanin haka daga gareki ba, ni kome Faruk yayi na yafe masa, don haka kiyi k'ok'ari ki yafe masa kema. Ki tashi ki fara shirin komawa d'akinki, Allah yayi maku albarka ya kwa6e muku duk wata fitina." Ya kai dubansa ga Faruk yace "Allah ya jik'an iyayenka ya gafarta masu, ga matarka nan sai a kiyaye gaba, ka kula da ita da kuma kanka, kasan dai matsayinta yanzu, don haka ka rik'e ta amana Allah yayi maku albarka." Yace "Amin Baba, na gane kuskure na kuma insha Allah hakan bazata sake faruwa ba, nagode sosai insha Allah zan kula da Meenah, zan kuma rik'e ta bisa amana da gaskiya." Cike da farin ciki Baba yace "Amin, zan shiga daga ciki na d'an kwanta." Sukayi sallama ya fice. Zarah ita da mijinta su sukayi mata rakiya har gidanta da misalin k'arfe biyar da rabi na yamma, suna nan har akayi sallar isha'i bayan sunci abinci suka fara shirin tafiya, Zarah ta k'ara yi mata fad'a sannan ta bita da nasiha, sukayi sallama dasu suka shige gida suma. Bayan ta shigo ta maida k'ofar ta rufe, yana nan tsaye bakin k'ofa yana faman murmushi, ta kauda fuskarta tace "Ya dai?" Yace "Bacci nakeji my baby, amma inaso na fara yin wanka kuma ke nakeso kiyi min da kanki, kinsan na gaji da yawa rabona da bacci mai dad'i har na manta." Ta so ce masa bazatayi ba amma tuno da nasihar Baba ya sanya bata musa ba ta bishi da "To." Ta kunna masa ruwan zafi da taimakonta ya watsa, ta taimaka masa ya shafa cream mai k'amshi shi kuwa duk wani motsinta akan idonsa yake. Ta kammala ta tafi tayi wanka ta fito sanye da kayan baccinta masu kyau da kuma firgita tunani, sai zuba k'amshi take ya cije lips d'insa na k'asa yace "My baby, kullum k'ara chanza min kikeyi, yanzun ma sai naga kinfi ko yaushe yin kyau." Duk da taji dad'in kalaman nasa haka bai hanata turbune fuska ba tana cigaba da linke kayansa da ya cire yanzu. Yayi murmushi ya mik'e ya jawo ta ta fad'o bisa k'irjinsa yana kallonta cike da so da k'auna marar misaltuwa, ita kuwa k'ok'arin k'wace kanta ta shiga yi wanda ta kasa saboda irin rik'on da yayi mata.... AUREN FANSA 45 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) PURE MOMENT OF LIFE WRITERS _We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_ P.M.L # *WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM # *IG PML WRITERS # *https://www.facebook.com/PML_-Writers- FANS-459256761123035 # *http://maryamsbello.blogspot.com _wannan sune safikan mu da zakuna ziyarta dan neman nvl d'in mu. Fatan mu Allah ya baku ikon zuwa Ameen_❣️ 🌹45 🌹 Ya d'an yi tsai yana dubanta, ta kawar da fuskarta gefe, yace "My baby, ki tausaya min ki kula ni, idan har kika za6i ki guje ni to wallahi rayuwata tana cikin matsala, nayi laifi tabbas kuma na gane kuskure na har ma na bada hak'uri, to meyasa bazaki yafe min ba? Allah ma muna masa laifi ya yafe mana bare mu mutane? Wallahi ina k'aunar ki, da zaki bani dama da na nuna maki hakan Meenah..." Shirun dai ta kuma yi, yace "To in bazaki yi magana ba, kiyi hak'uri ki saki ranki, kin hak'ura?" Ya shafi fuskarta yana mai juyo da ita, take tayi k'asa da k'wayar idonta. "Kinji ni baby? Ki tuna matsayina a gareki, na baki hak'uri kiji tausayina don Allah Meenah. Da me zanji? Kina fushi dani kink'i hak'ura, ke kad'ai fa guda nakeda a halin yanzu, ina zansa kaina Meenah? Please please! Tuba nake, na tuba bazan k'ara ba, kar6i wannan takardar ki gani abin farin cikin da ya same mu." Ya zura mata takardun cikin hannunta, ta kalla shek'ek'e ba tare da ta karanta ba ta mik'a masa yace "Yanzu har kin duba baby?" Ta gyad'a masa kai, yace "To me kika gani?" Tace "Oho!" Kalmar data ambata a ciki kenan ashe ta fito fili, yayi murmushi yace "Daman wannan takardar k'arin ilimi ne aka tura ni na tsawon shekara biyu wanda zanyi shi a k'asar ingila, shine nake neman shawararki saboda karatunki." Har ranta taji dad'in alherin da ya same shi wanda ta tabbata yaga hakan a fuskarta Sai kawai ta ce masa "Na taya ka murna, sai dai duk yadda ka tsara yayi min." Yayi murmushi yace "Alhamdulillah naji dad'i, sai dai inaga kamar zamanki a nan don ki k'arasa karatun naki yafi, amma zan rink'a waiwayanki, bawai natafi har sai na kammal ba ne, a'a zan rink'a ziyartarki, donma in banda ina son kiyi karatun da k'afata k'afarki, yanzun ma idan kinfson mu tafi taren sai mu ajiye shi gaba kya yi shi." Ba tare da ta kalleshi ba tace "Babu damuwa, kaje zan zauna." Yayi murmushi yace Ay da yake yanzu level 3 zaki shiga kinga dana dawo kin kammala insha Allah, kinga dana dawo sai mu baje soyayyarmu yadda ya kamata." Tace "Allah ya taimaka." Haka yayi ta lalla6a ta kamar k'wai, sai wani riritata yakeyi yana yi mata kalamai masu tausasa zuciya har ya samu ta d'an sauko daga dokin data hau har ma tana d'an kula sa. Washe gari ne yayi shirin aikinsa, bayan ya kimtsa ta raka shi bakin motarshi yace mata yau da wuri zai dawo yaci abincin rana ta masa amala da miyan ku6ewa d'anya, ta bishi da "To." Da fatan dawowa lafiya. Yana tafiya ta tashi tayi wanka ta kimtsa gidan sannan ta hau mota tare da kud'in da ya bata ta nufi kasuwa, ta siyo garin amala da k'ashin rago da ku6ewa, tana dawowa ta fad'a kitchen ta fara kacaniyar dafa abinci, k'arfe d'aya da rabi daidai ta gama 1:30 pm, tana gamawa ta fad'a wanka ta fito ta shirya cikin wata atamfa dark blue d'inkin riga da skirt d'inkin ya zauna dabas a jikinta. Amma shiru ba alamunshi har wajen uku, ta d'auko wayarta ta shiga neman layinsa nan ma bai d'auka ba. "Oh God!" Ta fad'a tare da jefar da wayar ta mik'e bisa doguwar kujera, sama sama bacci ya ringa fisgarta tana k'in yi don bata son baccin yazo. Can wayarta ta fara ruri ta mik'e zumbur ta d'auka yace "Baby zan aiko a d'aukar min abincin nan don meeting zamu shiga yanzun nan, idan nace sai na dawo kafin na koma zan makara." Tace "Sai ka turo bakomai." Ta mik'e ta had'a shi cikin basket, ta kira d'an almajirinta Yusha'u tace "Koda bacci zai d'auke ni idan wani yazo ka d'auko basket bisa dinning ka mik'a masa." Yace "To Anty." Ta koma tayi kwanciyarta. Itace bata tashi ba sai k'arfe hud'u har da 'yan mintina, tashinta yayi daidai da k'wank'wasa k'ofa, ta mik'e zaune daga kwanciyar tana gyara d'aurin d'ankwalinta, sannan ta mik'e tayi tattaki izuwa bakin k'ofa gami da bud'ewa. Wata budurwa ce sai dai ko ba'a fad'a mata ba tasan yarinyar tana cikin matsala babba. Ta bata izinin shigowa, ta koma kitchen ta had'o mata kayan lashe lashe da tand'e tand'e, ta koma ta zauna suka soma gaisawa a mutunce, Meenah tace "Baiwar Allah sai dai ban gane ki ba, sannan meya faru da ke haka naga jikinki duk ciwo haka?" Maimakon budurwar tayi magana sai kawai ta durk'usa har k'asa tare da fashewa da wani irin kuka mai tsanani. Meenah ta razana tana tambayar lafiya? Da k'yar budurwar ta tsagaita daga kukan da takeyi sannan ta fara magana cikin sanyin jiki. "Mu talakawa ne tu6us, wanda har cin yau yakan gagare mu, Allah yayi ma mahafina rasuwa da jimawa, sai mahaifiyata, mahaifiyata ita take fafutukar nema mana abinci da kuma kud'in makaranta, ba irin aikin da batayi ba, haka muka cigaba da rayuwa mahaifiyata itace komai na, sai dai a kwana a tashi na had'u da hatsabiban k'awaye wanda suke hure min kunne har na biye musu na kai kaina a halaka!" Ta share hawayenta ta cigaba. "Nazo na fara fita lokacin dana ga dama na dawo lokacin dana ga gama, tun mahaifiyata na fad'an tana duka na har ta gaji ta bini da addu'a, gashi bana jin maganarta, nabi na raina ta ban d'auke ta a bakin komai ba, tasha yi min kuka akan abubuwan da nake mata amma ni ko a jikina, na had'u da samari 'yan k'arya suna min wayau suna kaini hotel su bani kud'i, daga nan idanuna suka ida bud'ewa gaba d'aya, bana ji bana gani, sutura kuwa sai wadda na cire duk akan idon mahaifiyata, har ta kai ta kowa mahaifiyata bata iya fita unguwa, data fita za'a fara nuna ta ana gulmarta. Kwatsam wata rana sai na had'u da Jidda..." Thursday, 14 September 2017 Maryam Saidu at 23:38 AUREN FANSA 46 ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) PURE MOMENT OF LIFE WRITERS _We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_ P.M.L # WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM # IG PML WRITERS # https://www.facebook.com/PML_-Writers- FANS-459256761123035 # http://maryamsbello.blogspot.com _wannan sune safikan mu da zakuna ziyarta dan neman nvl d'in mu. Fatan mu Allah ya baku ikon zuwa Ameen_ 🌹46🌹 Da mamaki Meenah tace "Jidda kuma? Meye mahad'inki da ita?" Budurwar tace "Nasan zakiyi mamakin idan na sanar da ke ni ba kowa bace face Lubabatu wacce aka fi sanin da Luby..." Meenah ta mik'e tsaye a razane tace "Luby? Kece haka?" Luby da kanta ke k'asa tace "Eh nice! Nice Luby aminiyar Jidda, ki zauna Zan k'arasa bayani na." Ta k'i zama still tana kallonta da mamaki, Luby ta sake d'agowa tace "Ki zauna don Allah ba don ni ba." A hankali ta koma ta zauna tace "Ina jinki." Luby ta cigaba "Kamar yadda na fad'a miki a baya cewar na had'u da Jidda a wurin bikin wata 'yar makarantar mu da akayi, duk da ba ajinmu d'aya da Jidda ba amma a ranar muka k'ulle muka zama best friends. Nice sanadin lalalacewar Jidda, ni na d'ora ta bisa gur6attaciyar hanyar ita kuma ta bi, a tare muka cigaba da harkar mu ta bin maza da sauransu. Nidai yanzu ba komai ya kawo ni ba illa nazo neman gafararki, ba don ni ba don Allah ki yafe min, nayi kuskure amma yanzu na gane kuskure na, ki gafarce ni..." Meenah tace "No kar ki damu ni banida rik'o, kuma na yafe maku, Allah ya tsare gaba, sai dai garin yaya kika ji wannan ciwon haka a hannu?" Ta kai dubanta ga hannun dake nad'e da bandage gaba d'aya tace "Wannan a ranar muka samu sa'insa da mahafiyata akan ina so na fita da misalin k'arfe takwas na dare, a lokacin mahaifiyata ta tashi tace ita sam bazan fita ba, niko na dage akan sai na fita sai dai ayi wacce za'ayi, na fad'a mata maganganun sannan nayo hanyar waje, sai dai daidai bakin k'ofa mahaifiyata ta tako da sassarfa tana fad'in, Lubabatu idan kika sa k'afa kika fita ban yafe maki ba, daga haka kawai ta juya ta koma gida, ni kuma kawai naja tsuka na fice abina ba tare da na damu ba. A ranar hotel muka kwana bayan mun gama abinda mukeyi muka zarce club, muna can har asuba, sai da gari ya fara haske sannan muka fito don komawa gida. Sai dai me? Muna kan hanya nida saurayin nan nawa muna jin kid'a muna rawa a mota ba tare da mun ankare ba muka yi had'ari, shi saurayin nawa take ya cika ni kuwa asibiti aka wuce dani rai a hannun Allah, sai dana kwana bakwai ban farfad'o ba, bayan na farfad'o naji likita na cewa sai an yanke min hannu, nayi kuka nayi kuka, nayi bak'in ciki, nayi nadama ba kad'an ba. A ranar nayi Allah wadarai da son abin duniya gami da bijire wa iyaye, nidai cewa nayi ban yarda ba, daga nan akayi wa hannuwa na hotuna (Scan) kusan kala uku, gashi banida kowa dole ni likitan yake tunkara da maganar. Yace min k'ashin hannun ya lalace da yawa, ya ratattake k'ashin, wato sai an yanke su, ido waje na zaro nace "Duka hannuwa na?" Yace "Eh to, zai iya yiwuwa dukansu amma gaskiya hannu d'aya yafi samun dameji wanda idan aka d'auki lokaci zai iya ru6ewa, zamuyi iya k'ok'arinmu muyi miki 'yan dabaru a shi d'ayan hannun, idan Allah ya taimaka sai ya zauna. Sannan abu na biyu wurin yin 'yan bincikenmu mun gano kina d'auke da wannan cutar wato cutar H.I.V AIDS." Luby ta d'an dakata saboda kukan da yaci k'arfinta, haka itama Meenah sai da tayi hawayen, Luby ta cigaba. "Wani abu naji ya sokeni a k'irji kamar an sara mani mashi, kuka nakeyi tamkar raina zai fita, gaba d'aya duniyar da abinda ke cikinta sun fitan min a rai, likita ya zayyano min kud'in aiki wato gaba d'aya miliyan biyu harda rabi, kaina ya d'auki chaji sosai, nace su sallameni na tafi na samo kud'in aikin sai na dawo. Suka sallame ni nayi gidanmu, na tarar da mahaifiyata tana ganina ta razana tana tambayar meyasame ni, na koro mata bayani, tayi ta min fad'a tace ita ba ruwanta dani don haka na tafi na nemo kud'in da kaina daman na saba neman kud'i, ta koro ni na fito ina kuka. Babu wadda ta fad'o min rai kamar Jidda, nasan ko bata bani kud'i ba zata taimakeni da shawara, sheyasa na taho nan." Meenah ta kalli Luby kallo na k'urilla sannan itama ta koro mata nata bayanin. "A gaskiya Luby idan har kud'in aiki kike nema sai dai kije ki nemi taimako kamar su gidan radio, wurin manyan k'asa, sannan Jidda da kika zo nema bazaki same ta ba, saboda Jidda dai ta haukace." A razane tace "Ta haukace kuma?" Meenah tace "Eh ta haukace, a ranar da kuka je wurin boka amso maganin da zaku sa min ta saka min ya koma mata, tun daga wannan ranar ta fara hauka tana tona muku asiri, yanzun ma zancen da nake miki ana can ana hadaniyar fidda ta can k'asar waje neman magani. Luby wato ita daman duniya haka take, duk yadda ka d'auke ta haka zata zo maka, tabbas kin tafka babban kuskure a rayuwarki, waya ce miki iyaye abin wasa ne? Musamman uwa, kin wulak'anta uwarki ya za'ayi kiga daidai a rayuwarki? Kin bi boka ya za'ayi kiga daidai a rayuwarki? Kinyi zina ya za'ayi kiga daidai a rayuwarki? Shekara da shekaru kina shayar da mahaifiyarki gubar 6acin rai, ke ba yarinya ba ak'alla zaki kai shekaru ashirin da shidda yanzu a yadda nake kallonki, yaci ace yanzu kina gidan mijinki kina bautar Allah amma kin tsaya shashanci, shekarunki sun kai ace kinyi hankali ki gane halin da duniya ke ciki, abinda yafi miki kije ki rungumi mahaifiyarki ki nemi gafara, ki mata biyyaya sannan ki gyara rayuwarki tun kafin ki koma ga mahaliccinmu. Ina so ki maida komai kamar tafiyar ruwa ki kuma tari gaba, ki yarda da kaddara mai kyau ko marar kyau, wallahi Allah gafurur Raheem ne, kuma insha Allah nima zan taimaka miki da wani abin, cikin gadon mahaifina zan baki wani abu sai ki k'ara cikin kud'in aikin da za'ayi miki." Ta bud'e baki cike da mamaki sai kuma hawaye suka fara wanke mata fuska. "Meenah, nagode! Nagode Allah ya saka da alkhairi, Allah ya k'ara bud'i, Allah ya jik'an iyaye yayi mana gafara, bani da bakin da zan gode maki, na bibiyeki da sharri ke kuma kin saka min da alkhairi, haka rayuwa take daman ko wannan ya ishemu ishara." Meenah tayi murmushi "Kar ki damu, bakomai wallahi ai yiwa kai ne, wannan ba wani abu bane." Tana kallo Meenah ta mik'e ta shiga d'aki, ba'a jima ba ta dawo hannunta d'auke da paper, ta zauna tana mik'a mata. "Gashi." Tasa hannunta mai d'an lafiyar ta kar6a tana kuka, Meenah tace "Yanzu shiga ta na kira Faruk, na masa bayani shine yace na k'ara miki shima ya bayar." Luby ta duba tace "Har dubu d'ari uku? Kai nagode Allah ya k'ara bud'i." Meenah tace "Wannan ba abu bane ba babu damuwa, Allah ya k'ara tsare mana imaninmu, ya tsare mu daga fad'awa halaka, Allah ka shirye mu ya ganar da mu." Luby tace "Amin ya Rabbi." Luby bata tafi ba sai da Meenah ta bata abincin rana tana mai k'ara mata fad'an ta nemi yafiyar mahaifiyarta, a haka ta bar gidan tana mai jinjina al'amarin. BAYAN SATI BIYU **** Ranar wata talata, tana zaune taji horn d'in motarsa, ta mik'e cike da mamakin ganin ya dawo da wuri, ta lalla6o ta fito don tun jiya bata jin dad'i. Ta k'arasa wajensa sai fara'a yakeyi yana mata murmushi itama tana tayasa duk da batasan dalilin farin cikin nasa ba. Ta kar6o jakarsa suka jero har parlor ta dire jakar ta d'auko masa ruwan sanyi a fridge ta tsiyaya masa ta bashi. Bayan ta zauna tace "Lafiya ka dawo da wuri yau?" Ya kuma dubanta yace "Lafiya lau, tafiyar nan ce ta taso wai jibi jibin nan zamu tafi, kin tuna maganar da mukayi a baya ko?" Tace "Eh na tuna." Yace "To itace yau abin ya ida tabbata." Tace "Masha Allah, yanzu jibi zaka tafi?" Yace "Insha Allah." Tace "Zaku dad'e kenan?" Yace "Da shekara biyu zamuyi amma yanzu insha Allah bazai wuce shekara d'aya ba mun juyo, kuma in mun dawo zamu iya samun chanjin aiki da kuma k'arin girma. Yanzu ma so nake naje na shaida masu Dada maganar kuma ke nakeso ki raka ni." Ta d'an yamutsa fuska tace "To amma fa ni bana ma jin dad'i." Ya zaro idanu yana k'are mata kallo, yace "Kodai abin arzik'in ne ya samu?" Tace "Me kenan?" Yaja hancinta yace "Kinfini sani, amma banga ta zama ba tashi zakiyi mu tafi asibiti a auna ki don a tabbatar." Kafin ma tayi magana ya zura mata hijabinta pink color tare da jawo hannunta suka nufi mota. Ba k'aramar murna Faruk yayi ba da yaji daga bakin likita cewar ciki ne da ita har na kusan wata biyu, tun da suka shiga mota yake washe hak'ora kamar gonar auduga. ‹ › Home View web version Thursday, 14 September 2017 Maryam Saidu at 23:39 AUREN FANSA 47/END ✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨ ⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐ 🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹 🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹 ✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨ ⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐ ✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨ ⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 AUREN FANSA!!! 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹Na🌹 🌹MARYAM S BELLO🌹 (MSB) PURE MOMENT OF LIFE WRITERS _We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_ P.M.L # WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM # IG PML WRITERS # https://www.facebook.com/PML_-Writers- FANS-459256761123035 # http://maryamsbello.blogspot.com _wannan sune safikan mu da zakuna ziyarta dan neman nvl d'in mu. Fatan mu Allah ya baku ikon zuwa Ameen_ 🌹47 🌹🔚 A ranar sukaje wajen Dada, ya dad'e yana sa masa albarka tare da fatan dacewa, sannan ya ce lallai lallai sai ya bashi takardar Jidda don data warke ya mik'a mata, yasan dole zata koyi hankali. Haka Faruk ya rubuta ya mik'a ma Dada, haka ma Mama tayi masa fatan dacewa da sanya albarka. Daga nan suka wuce gidansu Meenah ya shaida ma Baba, Baba ya bishi da doguwar addu'a ya sanya masa albarka. Sai dai tun ana gobe zai tafi hankalinsa ya tashi bai ta6a tunanin daidai da kwana d'aya zaiyi nesa da Meenah ba gashi har za'a shafe watanni bai ganta ba, yana shigowa d'aki a lokacin tana kwance kan gado ya zauna gefenta yace "A gaskiya Meenah bazan iya tafiya na barki ba, kawai kiyi hak'uri ki shirya mu tafi tare." Ta juyo tana dubansa tace "Nidai jeka ka barni, ina nan gida Nigeria bazan iya binka ba a yadda nake jina d'innan." Ya tur6une fuska ya shiga zayyano mata matsalar da zai shiga idan bata bishi ba, har da cewa tayi differing semester d'in mana idan suka dawo sai ta gyara. Da k'yar ta lalla6a sa yayi hak'uri ya barta, amma idanunshi sun kad'a sunyi ja, haka itama ta wuni tana kuka har bacci yayi awon gaba da ita. A daren ranar Meenah taga tarairaiya kamar wata k'wai, ya dad'e yana shayar da ita zuma kafin kuma suyi bacci mai dad'i. Washe gari ya fara shirin tafiya, kafin ya tafi sai da ya nemo mata wata mata dattijuwa da zata zauna da ita har ya dawo, haka suna ji suna gani sukayi bankwana har airport ta kaishi, sai data ga tashin jirginsu sannan ta dawo zuciyarta na k'una ta rasa meke mata dad'i. Haka ta kwana tunaninsa har ciwon kai ya sauko mata wanda kafin safe zazza6i mai zafi ya rufe ta, sai da tayi ta shan magaunguna sannan ta samu taji sauk'i. Shi kuwa gogan naka yana sauka masaukinsa dama ya siya sabon sim, yana sawa ya kirata, bugu biyu ta d'auka. "Hello." "Baby ya nake jin muryarki can k'asa ko jikin ne?" Ta lumshe idanu tace "Eh to zazza6i ne yake d'an damuna amma da sauk'i." Ya rude ya shiga mata tambayoyi. "Kinsha magani? Yanzu meke miki ciwo? Ya kike ji yanzu?" Tayi murmushi "Wallahi yanzu kam bana jin komai sai kasala, so ya hanya? Ya kuma gajiya?" Yace "Alhamdulillah, gani nan na sauka masaukina yanzu zanyi wanka sai na kwanta na huta." Tace "Ai gara kayi bacci kam, sannu." Yace "Yauwa baby, kema sannu." Sun dad'e suna fira kafin suyi sallama, kowane yana jin kewar d'an uwansa. Meenah ta cigaba da karatunta cikin kwanciyar hankali, kullum cikin missing Faruk takeyi sai dai kullum suna mak'ale a waya suna fira basa gajiya da junansu. Sun cigaba da zumuncinsu itada Zarah kusan kullum suna ziyartar juna, haka ma Anisah wacce ke fama da tsohon ciki itama tana k'ok'ari wajen ganin tana zumunci dasu Meenah. **** BAYAN WATA BAKWAI Meenah na zaune a parlor tana cin guava kamar a mafarki taji horn, ta yunk'ura da k'yar ta lek'a ta window ganin motar haya ya sanya ta fara mamakin ko waye? Bata gama mamaki ba sai data ga ana fiffido da akwatina daga boot, gabanta ya fad'i batayi tsammanin ganinsa yanzu ba, yayi wani kyau yayi k'iba sai k'yallin hutu yakeyi. Ga k'asumbar nan tasha gyara sai walk'iya takeyi. Ta lalla6a ta fito bakin k'ofa daidai nan ya k'araso yana murmushi, take ya ware hannuwansa duka biyun alamun ta iso gareshi. Ta dafe cikinta daya turo gaba tare da sunkuyar da kanta k'asa, yayi murmushi tare da takowa daf da ita sannan ya rungume abarsa tsam tsam kamar za'a k'wace masa ita don ma tulelen cikinta ya hana shi ya rik'e ta sosai. Ya sumbace ta a goshi yana dubanta yace "Wow! Baby cikinnan fa yayi miki kyau sosai." Ya k'arasa yana kashe mata ido d'aya, tayi murmushi, ta zum6uro baki cikin shagwa6a tace "Shine zaka taho ban sani ba?" Yayi dariya "I'm sorry baby, just wanted to surprise you daman." Hannunta ya rik'o suka k'arasa ciki, ta taimaka masa ya rage kayan jikinsa yana ta zolayarta wai yanzu ta zama k'atuwa ko tafiya da k'yar takeyi, ita dai sai dariya takeyi. Bayan ya huta kuma ya shiga bubbud'e akwatina yana fiddo mata tsarabarta, kaya ne mak'il akwati guda na kayan baby wanda babu abinda babu a ciki, kaya masu kyau da tsada, sai akwati guda nata wanda ya k'unshi leshi, atamfa da su kayan bacci da kayan kwalliya da sauransu, tayi murna tayi ta masa godiya ba adadi. A ranar dukkansu sunyi kwanan farin ciki da kuma kewar juna. Washe gari sai ga Jidda itama ta warke ras, tazo neman gafara kuma duk sun yafe mata, tace ta samu mijin aure, sun taya ta murna da fatan alkhairi inda har Faruk yayi mata alk'awarin bata tasa gudumuwar. A kwana a tashi ba wuya wurin Allah yau Allah ya sauki Meenah da misalin k'arfe biyu na dare, Faruk yana tare da ita har ta haifi santalelen d'anta k'ato mai k'oshin lafiya, bayan an gyare shi tas aka mik'a ma Faruk shi sai kallonsa yakeyi cike da sha'awa, ya sumbati kumatun Meenah yace "Wane suna zamu sa masa?" Tayi murmushi tace "Duk sunan da kaga ya dace dashi ka sa masa." Yayi masa hud'uba da sunan mahaifinsa wato Adam amma za'a ringa kiransa da Khalifa. Ranar suna anyi taron suna lafiya kuma ya k'ayatar mai jego tayi fes da ita tana sanye cikin wani golden lace sai k'yalli takeyi kamar wata amarya. Mai jego da d'anta sun cigaba da samu kulawa sosai a wurin Faruk, ga yalwatar arzik'i musamman da akayi masa k'arin girma kud'i sun zauna masa sosai, hakan yasa Meenah ta bashi shawarar ya gina masallaci ya kuma ringa bada tallafi a gidan marayu, ba k'aramin dad'i shawarar nan tayi masa ba, yayi tasa mata albarka yana jin dad'i. A haka har sukayi arba'in inda ta cigaba da karatunta a lokacin ne kuma ita Zarah ta haifi d'iyarta mace sun sha suna babyn taci sunan mahaifiyar Nabeel wato Sadiya, za'a ringa ce mata Nasreen. A yanzu su Meenah har sun kammala karatunsu suna jiran result. **** Zaune take tana shayar da Khalifah Faruk ya fito daga d'aki da alama bacci ya tashi, yana zuwa ya rank'wafo yana sumbatar kanta, yace "Zo muje na baki wani abu." Ta mak'ale kafad'a alamun a'a tace "Nak'i wayon, nasan dalilin da yasa ka kirani." Yayi murmushi yace "A'a fa result d'inki zan nuna miki." Da sauri ta aje Khalifah ta mik'e tsaye tana murmushi tace "Da gaske? Mu je nagani." Ya wuce tabi bayansa suna shiga yasa ma k'ofar key yana dariya k'asa k'asa, tace "La daman wayau zakayi min ko? Ni gaskiya ka bud'e min na fita." Yace "Nak'i, ga key d'in zoki k'wata." Ta nufo sa ta fara k'ok'arin k'wace key d'in aikuwa ya damk'e ta yace "Wana kama?" Ta fara kukan shagwa6a tana fad'in. "Wayyo my soul, mun bar Khalifah shi kada'ai a parlor fa kar yayi kuka." Yace "To tsaya mu nema masa k'anwa sai ki tafi." Tace "Nidai a'a." Yace "Aiko baki isa ba." Ya fara k'ok'arin zage mata zip da k'yar tayi nasarar k'wace kanta tana ta faman dariya sosai sannan ta d'auki pillow ta jefe shi da shi har yanzu bata bar dariya ba. Nufo ta yayi ya chafke ta yace "Zan baki punishment, kina jifan mijinki." Kafin tayi magana ya had'a bakinsa na nata.... ALHAMDULILLAH!!! Alhamdulillah da Allah ya nuna min farkon book d'innan da k'arshensa lafiya! Darasin dake ciki Allah ya bamu ikon d'auka, kuskuren da ke ciki Allah ya ka yafe mana. Godiya ta musamman ga dukkanin masoya na da wanda na sani da wanda bansani ba kusani a duk inda kuke ina k'aunarku. Fatan alkhairi ga duk wani mai karanta novel d'ina, Allah ya bar zumunci Amin. Daga k'arshe ina mai bak'in 😭😭cikin sanar da masoya na cewar zan dakatar da rubuta 😭😭😭novel zuwa wani lokaci bisa wasu dalilai wanda basai na fad'e su ba da fatan masoya na zasuyi min uzuri zasu kuma fahimce ni, nagode da k'aunar da kuke nuna mun nima kusani ina k'aunar ku a duk inda kuke.😘 ********************** ? ************************** ************* Ai Hausa Novels **************** *************************? ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ? ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ? **************************